[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur ....... 1 Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Wanan novel din kirkirarren labari ne. "au Khaleel ne shine kawani tsaya a bakin kofa bazaka shigo ba" murmushi dake kara fito da kyanshi yayi ya shigo dakin da gudu yaron dake jikin matar yatashi yayo kanshi da muryan shi irin ta yara yace "Uncle Khaleel" tsalle yayi hakan yasa kakkyawan matashin dake sanye da Shadda sky blue wacce akamai dinkin 3quater daya kara amsan cikakken jikin shi yadau yaron ya shilla shi sama yace "my boy" sanan ya sakko dashi ya zauna akan kujeran dake falon yana sunnar dakai ahankali yace "ina yini Mama" tashi matar da akalla zatakai 45 tayi tareda daukan plate din data gama bama auta abinci aciki tai murmushi tace "Khaleel manya bazadai mubar yar kunyan nan bako, ai shikenan bari naturo ma ita" ya kalli Auta wanda tuni ya maida jikin Khaleel din filin wasa tace "Oya Auta kadai san ba wajen ka Khaleel yazo bako, tashi mutafi ciki" noke kai yayi yaron yace "oh'oh" tabe baki tayi ta wuce sama abinta. Khaleel ya kalli yaron saida yafara jujjuyawa ya tabbatar daba kowa adakin sanan ya kalli yaron ahankali yace "My Boy where is Anty Aisha?" sauka yaron yay daga jikinshi yafara tafiya sanan yace "cana dacinta cana cifan citso" shigowan wasu yara kyawawa guda uku mata biyu sai namiji daya yasa yay shiru da sauri suka yo wajen Khaleel atare suka gaidashi "Ya Khaleel welcome" murmushi yamusu yaja kumatun wacce tafisu girma yace "Hello my fatty Fatima" sanan yaja kumatun dayar wacce ita kebi mata yace "Hello my skinny Maryamu" sanan yaja kumatun dayan namijin yace "Hello my Hafiz Ibrahim how was the madrasa today?" kasan cewa islamiyan su 3 narana ake zuwa ataso su 8 nadare achan suke sallar la'asar, magrib, da issha'i atare yaran sukace "Fine Uncle Khaleel" suna mugun son Khaleel Shima haka yake sonsu, Chocolate din daya kawomusu ya basu nan sukamai godiya cike da murna suka tafi sama dan nunama mummy. Yaye labulen dakin Mum tayi hakan yasa ta juyo da sauri, wata faran budurwa ce dabazata wuce 22 ba, doguwa ce sosai amma batada kiba, zaune take akasan dakin su tana tsifan gashi. Haba Mama tarike tace "eyye yau iskanci naki ne yatashi ko meye kin bar bawan Allah shikadai har yanzu a falo" dan turo baki tayi a shagwabe batare datace komiba, kwafa Mama tayi tace "yo ai shikenan bari nacemai yatafi abunshi" da sauri ta mike tsaye tace "uhmm damafa umm" Mama ta juyo tace "dama me?" shiru tayi tana wasa da yatsar ta dan murmushi Mama tayi tace "will u get out of this room my friend" dogon hijabin ta dake kan gado taja tafita daga dakin tsayawa tayi anan corridor tasa hijabin sanan ta wuce, kada kai Mama tayi tace "andai kusa nan da 4 weeks ne mumuku auren kowama ya huta fitinan nun yara" ta shiga dakin Ibrahim rike da hannu auta dan jimai haddan dazai bayar gobe. Tunda take sakkowa daga stairs yake kallon ta harta karasa sakkowa ko kallon inda yake ba tayi ba ta wuce kitchen abinta fridge ta bude ta ciro zobon data hadamai da yamman nan mai sanyi wanda yaji cucumber da water melon, ta daura jug din akan tray sanan tasa karamin glass cup akan tray din tadau tray din tafito ahankali take tafiya kaman batason taka kasa wanda dama haka tafiyan nata yake karasowa gaban shi tayi da sauri ya mike ya karbi tray din hannu nata wanda dama haka dabi'an shi yake, tunda tasan shi bata taba kawomai abu ta ijiye da kanta ba dan da sauri yake tashi ya karba. Ganin ya karba yasa ta dauko table ta ijiye agaban shi ahankali hannu tasa ta karbi tray din, hannu shima yasa ya sake karban tray yayi yana kallon kakkywar fuskarta wanda kwayar idonta yake kasa dan taki yarda su hada ido, cikin wata irin murya wanda ita kadai yakema muryan nan aduniya yace "My Eesha" kin amsawa tayi saima sakinmai tray din datayi. ahankali yadan tsugunna ya ijiye tray din still yana kallon fuskar ta tashi tayi fuuu zatabar wajen hakan yasa ya rike gefen hijabin ta chak ta tsaya batare data juyoba hakan yasa ya sauke ajiyan zuciya tareda yin taku biyu yazo gaban ta, sakin Hijabin yayi yay folding hanunshi a kirjinshi yana kallon fuskarta dahar lokacin taki kallon shi, cikin wani irin tattausan murya irin na lallashin mai fushi kuma karamin yaro yace "My Eesha" kin dago kanta tayi saima yatsun ta datake ta wasa dashi, kallon upstairs yayi ganin babu kowa a saman yasa yakara matsowa dab da ita ahankali yace "My Eesha please look at me" saida tai kusan 10 seconds sanan tadago idanunta dake kyalli sabida yanda hawaye ya cika su tam, hakan bakaramin tadamai da hankali yayi ba Kara tausasa murya yayi yace "am sorry" ajiyan zuciya ya sauke kaman shima zaiyi kukan sabida yanda hankalin shi yatashi "My Eesha nabar wayana a office ne nadan fita waje just to come back na tarar da Zainab tai picking call dinki, wlh trust me I don't have anything to do with her please am sorry Saheeba" hawayen ne suka shiga gangarowa sosai lumshe idonshi yayi ahankali kafin ya budesu ya kalleta sosai idanunshi sukai jaa cikin wata irin karamin murya yace "please ki share hawayen ki okay" ahankali tasa bayan hanunta ta goge hawayen tas, ajiyan zuciya ya sauke sanan yace "kin yafemin my Eesha?" gyadamai tayi hakan yasa yay murmushi sosai yace "to adan kalleni mana" ahankali ta dago manyan idanunta ta kallai tareda sakin mai murmushi daya lobar da dimple dinta ciki sosai wani sanyi yaji har karkashin zuciyan shi ita tafara yin gaba sanan yabita a baya tsugunnawa tayi ta tsiyaya mai zobon a cup sanan ta koma ta zauna akan kujeran dake facing nashi daukan cup din zobon yayi yakai bakin shi yasha wani irin sanyi da zobon yayi ga dadi mai sanyaya rai lumshe ido yayi ya kwankwade duka yasake karawa ya shanye yasake karawa hakan yasa ta ware ido cike da mamaki, daga mata gira yayi yace "my Eesha bazan iya forming ba gaskiya is too sweet" kyalkyacewa tayi da dariya Jin horn din mota yasa ta tashi da sauri yana kallon agogo karfe goma harda minti biyar cikeda rashin Jin dadi yace "oooohh wai su Abba harsun gama hiran dawuri haka ne" dariya tamai tareda mai gwalo ta tashi da saurin tayi kitchen hakan yasa yaciro car key din shi daga aljihu yarike a hannu daidai lokacin tafito da baban goran Eva dake cike da zobo tasamai a ledda binta yake da kallo harta karaso gaban shi ta ijiye akan table sanan ta dago batare data kalleshi ba tace "good night" dadan gudun ta tayi sama saida takai karshen stairs sanan ta juyo ganin ita yake kallo har lokacin yasa ta wara ido tace "go" make mata kafada yayi hakan yasa tasake murmushi tace "go" kara make kafada yayi yaki tafiya bude baki tayi zatai magana daidai lokacin anbude kofa ta arce da gudu ta shige dakin su. Daukan ledan goran zobon shi yayi ya sunnar dakai yana dan sosa keya kaman mara gaskiya yace "welcome Abba" kallon shi mutumin yayi from head to toe sanan ya girgiza kai yay gaba abunshi hakan yasa kaman wanda aka hankada yay hanyar kofa "Khaleel" yaji muryan Abba hakan yasa adan firgice ya juyo yace "naam Abba" Hawa stairs Abba yafara yi sanan yace "tell ur Dad sun chanza time din meeting din daga 9 zuwa 11 :30" ahankali yace "to Abba sanan ya bude kofa yafita, motar shi ya shiga gate man ya bude mai yafita daga gidan. Gidaje uku ne duka tsakanin su yay horn aka budemai gate, parking yayi ya shiga ciki babu kowa a parlor hakan yasa ya wuce sama, direct dakin Mum ya wuce bata ciki hakan yasa ya kwanta kan gado ya lumshe ido fuskar Eesha ke mishi yana, bude kofa da akayi yasa yadan bude ido kadan yace "Ammi" batare data kalleshi ba ta zauna agaban madubi tana share ruwan dake fuskarta, ahankali yasake cewa Ammi juyowa tayi ta harareshi tace "look Khaleel please kabarni nai bacci nariga nasa Ilham ta kaima abincin ka daki, ka girma amma wlh kafi kaninka fitina" dan yatsine fuska yayi yace "Ammi I don't want food I want another thing" ajiye cream din da Ammi ta dauko tayi ta juyo fully tana facing dinshi sai a lokacin ta lura da damuwan dake kan fuskar shi hakan yasa tace "mekake so to?" dan murmushi yayi sanan ya sosa kai kaman mara gaskiya yace "Ammi kinsan u are d best, u always brings me first, my one and only sweet Mama" murmushi Ammi tayi tace "Khaleel bangane wanan sweet mouth dinnaka ba just tell me wat do u want" kara sosa kai yayi tareda noke murya yace "please Ammi kima Dad magana Yama Abba magana please, Ammi nidai gaskiya arage tsawon bikin nan tunda dai next week zata gama exam basai ayi bikin upper week ba" yakara she maganan yana kallon fuskar Ammi data kafeshi da ido baki sake. Ahankali yasake cewa "Ammi naaaaa" ahankali yaga Ammi takai hannu tana kokarin ciro slippers din kafanta hakan yasa yay jumping daga gadon da gudu yay waje yakucan cin karo da Dad da sauri ya matsa yace "sorry Dad" ya bar wajen da sauri ya shiga dakin shi yana haki. Visit mamanshakur.wordpress.com for all my write-up [6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 2... Shiga dakin Dad yayi yabi Ammi da kallon tambaya murmushi kawai tayi tadau man shafawan ta tsayaya a hannu tace "wlh Alhaji dan nan naka baida kunya cewa yayi wai nacema tunda Aisha zata gama exam next week wai please ayi bikin upper week he is tired of waiting" murmushi Abba yayi tareda daukan news paper shi dake kan gado yace "Zan sami baban Aisha da maganar gobe" da sauri Ammi ta kalleshi tace "what?" bude jaridan Dad yayi yace "I said zan sami Baban Aisha da maganar" da sauri Ammi tace "haba Alhaji kuwai maza maisa tunanin ku daban ne, mu bangaren mu mata bamu gamaba fa ina aka gama shirya yarinya eyeh" tabe baki Alhaji yayi yace "ke yanzu baki gaji da ganin katon matashi a gidan nan ba, abin dadi ne ma yaran sun kosa suyi auren gwara mumusu kafin shaidan ya shigo lamarin" yatsine fuska tadanyi tace "ai shikenan". Saida yay shafa'i da wuturi sanan ya kwanta a kan makeken royal bed dake dakin shi, wayarshi ya jawo tareda kashe bedside lamp din dailing number dayay saving da heartbeat yayi saida wayar yakausa katsewa sanan ta dauka batare datace komiba, shiru shima yayi hakan yasa ta lumshe idonta shima lumshe idonshi yayi sanan yace "my one and only Eesha" cikin siririyar muryarta tace "kana gida?" murya Chan kasa yace "yes dear, tell me how are was your day?" ahankali tace "my day was bad" da sauri yace "why? Maisa my Eesha?" shiru tadanyi nayan sakanni kafin chan kamar wacce zatai kuka tace "I don't wanna talk about it" lumshe ido yayi in so much pain yace "maisa baki yarda daniba, there's nothing going on between me and her, my Eesha I love you don't you get it? Zuciyata taki ce kadai, I don't think wanan zuciyar nawa zata taba son wata mace aduniyan nan sama dake, my Eesha trust me please or kinason nafara miki kuka ne?" da sauri ta girgiza mai kai kaman yana wurin murmushi yadanyi sanan yace" don't worry bayan bikin mu zan lallasheki da kyau okay" make kafada tayi tareda cewa "oh'oh" dan murmushi yayi mai kara yana kara jin wani irin zafin sonta na ruruwa a rashin, ahankali yace "wani paper kukeda shi gobe?" cikin sanyin muryanta tace "GNS221" "hope you read very well?" ahankali tace "eh" "wat time is the exam" murya chan kasa tace "afternoon paper ne 2 to 4" ahankali yace "okay" shiru sukadan yi na kusan 5 min ahankali yace "My Eesha" murya chan kasa tace "uh" kara kwantar da murya yayi yace "ina sonki dayawa, I love you so much my Eesha" murmushi tayi tasa hannu ta rufe fuskarta dashi murmushi yasakeyi yace "bazaki cemin you love me ba" turomai baki tayi tace "su Faty fa na nan" ware ido yayi yace "nizakima wayau yaran da tuntuni sunyi bacci" murguda mai baki tayi tai shiru kara kwantar da murya yayi yace "haba babyn khaleel yakuri to fadamin kodan kadanne that you love me please my Eesha" shiru tadanyi hakan yasa ya lumshe ido yana jira ahankali da dan karamin muryanta tace "I love you Ya Khaleel" dip ta kashe wayan wani irin dadi ne ya lullube shi da sauri yasake dailing number amma bata dauka ba yasan dama bazata daukaba text ya tura mata "good night my Eesha, I love you" yay sending sai bayan ta karanta message din sanan ta rungume wayan tareda yin addu'an bacci. Shirye yake da uniform dinshi na navy bakaramin kyau dan farin rigan yasake haska bakin fatar shi, dining ya karaso ya gaida Dad da Ammi dasuke cin abincin su wayar shi ya ijiye da car key akan dining yay sama dakin kanenshi ya bude ganin suna gaban mirror Ilham nama ihsan makeup yasa yawani ja dogon tsaki yace "wlh if I count 3 baku tafi dining ba yau saida kuje school da kafa, one two" da gudu suka tashi suka dau jakunkunan su ta gefenshi suka fito ajiye cup din tea Ammi tayi tace "da kyau haba Yara sai sufi awa uku ana shafe shafen banza" zama sukayi daidai lokacin ya karaso dining Shima ya zauna ihsan tai serving nasu, Abba ne yafara gamawa yaciro 5k yabama Ihsan yace "gashi nan kuyi amfani dashi a school" ya kalli Mum nina tafi, godiya sukayi sukamai da addu'an Allah kiyaye. Shiya fara mikewa hakan yasa Ilham ta langabar dakai tana kallon Ammi, Ammi tace "Son kadan jirasu su gama nasu break din mana" hararan su yayi yace "Mum sunsan zasuyi break suka tsaya fentin fuskan su, my friend will u get up ko na tafi abina" hakanan suna kunkuni suka tashi sukama Ammi sallama. A bakin gate din Baze university yay parking kaman zasuyi kuka suka ce "Yaya Khaleel dan Allah ka shiga damu daga nan zuwa lecture hall danisa wlh" wani yar dariyar mugunta yayi bayan ya kalli kafafuwan su yace "gashi anci uban hill fa" yakara fashewa da dariya Ilham sarkin kuka harta fara matsar kwalla Ihsan tace "kai Yaya Khaleel bazamu kara batama lokaci ba" saida yagama daddana wayar shi sanan ya kunna motar ya shiga dasu sabida sundan bashi tausayi abakin lecture theater ya ajiye su tareda basu 5k sanan ya wuce aiki dan yay latti. Tun daga nesa ya hangota tana sanye cikin sky blue hijab mai hula fuskarta fayau ba makeup, lips dinta sunyi jaa sosai hakama hancin ta, ahankali take tafiya tanadan yatsine fuskarta fitowa yay daga motar ya jingina da motar tareda rungume hannayen shi a kirji bata lura dashi ba hakan yasa ta cigaba da tafiya, dan yatsine fuska tasakeyi tareda cire Jakarta data rataye a kafadar ta bude tissue ta ciro tasa akan hancin ta ta rike sabida atishawa takeji ahankali yafara tafiya harya karasa inda take a tsaye muryan shi kawai taji akanta "My Eesha meke damunki" dago idanunta tayi ta kalleshi yana sanye da uniform alamun daga office yake idanunshi boye cikin black shade wani sassanyar murmushi ta sakin mai, hannu ya mika mata ya karbi jakan hanunta har lokacin yana kallon fuskarta yace "baki da lafiya ne?" yatsine fuska tasake yi tace "am fine just mura nake yi" ganin yanda yan school din ke ta kallonsu wanda apparently shi suke kallo yasa ta gimtse fuska tace "mutafi" bude mata front seat yayi ta zauna sanan ya koma mazaunin driver ya zauna ya tada motar suka fita daga school din ganin yanda taketa atishawa yasa yay parking agaban wani pharmacy, maganin mura yasiyo mata da bottle water sai kuma cold farm fresh yogurt, bude side dinta yayi ya tsaya ahankali ya bude kwalin maganin ya ballo guda biyu yabata tareda bude marfin goran ruwa ya mika mata yatsine fuska tayi kaman zatai kuka murya chan kasa yace "please my Eesha for my sake" hakan yasa tasha da kyar kaman zatai amai da sauri ya karbi goran ruwan sanan ya bude mata yogurt din yabata yace "take this sabida karki amai" karba tayi ya maida kofan ya rufe mata sanan ya koma mazaunin driver ya tada motar, batawani sha dayawa ba ta rufe ta ijiye, ahankali yace "are you okay?" gyada mai kai tayi kafin ta lumshe ido within one minute bacci yay gaba da ita, murmushi yayi dan yasan tana tashi cikin dare tayi karatu ahankali yake tuki haryakai anguwan su, abakin gate dinsu yay parking ya juya yana kallon ta yanda take baccin ta hankali kwance hancin ta yay ja sosai abunku da farar fata, hakama lips dinta wani irin sonta yaji nakara shigan shi ahankali yakira sunan ta "My Eesha, My Eesha" bude ido tayi kadan kafin tabude su duka magungunan da yogurt din ya dauka yasa acikin Jakarta yabata, ahankali tasa hannu ta karba yace "ko muje hospital ne?" da sauri ta girgiza kai ahankali tace "am fine idan naje gida zansha ginger tea I will be fine" dudda baiso ba hakanan yace "okay on ur phone to, I will call you later" gyada mai kai tayi ahankali ta bude kofa ta juya zata fita da sauri yace "My Eesha" juyo dakai tayi ta kalleshi murmushi yamata yace "I love you" murguda mai baki tayi tafita da sauri, dan murmushi yayi tareda girgiza kai saida ta bude gate dinsu ta shiga sanan ya kuna motar yay reverse office dinsu ya wuce dan excuse ya dauka yafita dama. Zaune yake akan kujera yana rubuta report da laptop dinshi knocking akayi hakan yasa yabada izinin shigowa wata kakkyawar baby ce ta shigo office din wacce akallla zatai 26 tana sanye da daoguwar riga ta yafa gyalenta idanunta a cikin black shade kallo daya yamata ya dauke kanshi akanta yacigaba da abinda yakeyi, ahankali taja kujeran gaban table din ta zauna tareda ajiya handbag dinta akan table ta cire dark shade din ta ijiye kan table idanunta har sundan kumbura sunyi ja alamun taci kuka sosai take kallonshi bataki suyi ta zama ahakaba har karshen rayuwan su at least yarage mata wahalan da take ciki. Kusan 20mins yayi kafin yagama report din yatura head quarter dinsu na Lagos sanan ya kashe laptop din batare daya kalleta ba yace "what brings you here Zainab?" da kyar ta iya tattaro courage din dayadan rage mata ahankali tace "nazo nabaka hakuri I know I shouldn't have picked d call, please forgive me khaleel" takarashe maganan tareda ciro tissue daga jakanta tana goge hawayen daya zubo mata sosai ta bashi tausayi shiya rasa mesa Zainab ke sonshi haryau bai tabajin koda digon sonta aranshi ba. Ahankali yasauke ajiyan zuciya yace "am sorry too Zeenat I shouldn't have acted d way I did jiyan, Zeenat you are too good and Charming soul, banason kiyi wasting precious time dinki akaina, u know dis, duka duka bikina baifi two weeks ba, am sorry to say but my heart belongs to Aisha kadai, please move on and kimanta dani kinji Zee" sosai hawaye ke bulbulo mata ita kadai tasan yanda takeji ahankali ta mike tsaye tadau jakanta da shade dinta tafita daga office din da gudu. Lumshe ido yayi tareda fuzar da iska ba karamin tausayi tabashi ba sosai yamata addua Allah yahada ta damai sonta haka, ganin 5 tayi yafara shirye shiryen tafiya gida [6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 3... Around 9 yakirata ringing uku ta dauka cike da damuwa yace "my Eesha ya muran?" cikin wata irin siririyar murya tace "Alhamdulillah yadena" da sauri yace "are u sure kodai you are just scared ne Kisha maganin daren ki" dan dariya tayi tace "am serious fa, yaragu sosai nasha ma ginger tea dazu Mama tamini" dan ajiyar zuciya ya sauke yace "okay" shiru suka danyi ahankali yace "My Eesha inaso nadan fita" shiru tadanyi kafin tace "ina zakaje?" "just wanna hang out with some friends, colleague dina na birthday yau" kaman mara lafiya tace "okay" kara sassauta muryanshi yayi yace "what? Menene saheeba" girgizamai kai tayi tace "babu komi kawai zanyi kewanka ne" murmushi yayi yace "don't worry khaleel naki ne my Eesha and I promise dazaran nadawo I will call u is dat okay?" gyada mai kai tayi tace "uhm" "okay I love you bye" ajiye wayar tayi ta tashi tafita jin Mama na kiranta dakin Mama ta shiga ta zauna akan gado tace "Maman mu gani" spoon Mama tacire acikin cup din dake hanunta tace "gashi shanye" karban cup din tayi tana yatmuse baki ita wlh tagaji da wayan nan abun da Mama kebata daga mai bauri, sai mai gishiri da mai daci, gashi ba halin zubarwa agaban ta kesata tasha, ajiye cup din tayi tadau ruwan dake gaban mirror tasha da sauri tana yatsine fuska tace "haaaa Mama daci wlh" hararan ta Mama tayi tace "gulmamma ashe keda Khaleelu so kuke ayi auren dazaran kin gama exam ran Friday nan ko, oh ni ya'su wanan wasu irin yaran zamani ne" Mama tarike baki, zaro ido tayi waje dan bama tagane inda zancen Mama din tadosa ba tace "ni Maman mu" Mama dataji kaman ta make ta tace "eh kefa, to ai bukatun ku yabiya Abban ki yace dazaran kingama final exam dinki dis Friday upper Saturday bikin ki, Kinga yau saura kwana 9 kenan happy?" arude ta dafa kirji tareda zubewa nan kasa afalon tafara rantse rantse cikin kuka "wlh Maa nidai abari sai nan da 4 weeks din, Mama I don't know wanna leave you please" yanda tadage tana kuka yasa Mama sakin salati da tafi da hannu tace "da jiya kuka gama shirya abunku bakisan zakiyi kuka ba, keda naso immediately bayan kin gama exam natura ki Sudan amiki gyaran jikin 3 weeks shine kukai hadahaden kuko, ai bari Khaleelu yazo Shima jiranshi nakeyi marasa kunyan yara kawai" sosai tafashe da kuka hakan yasa Mama tafita daga dakin tace "inkin gama kije ki dafama auta indomie" nan tabarta sosai taci kukan ta sanan tabar dakin tareda yin kwafa. koda yadawo yakira yakira taki dauka yasan bata bacci saisunyi waya da kyar ya iya yay bacci batare dayaji muryan taba, da safe ma haka yakira taki dauka karshen ta ma kashe wayar tayi. 11 a makaran tar su tamai yay parking yana jiran tafito daga exam hall sabida 12 zasu gama, 11: 45 tafito tana sanye da milk color Hijab har kasa da bakin flat shoe karasowa yay gabanta ya karbi handbag dinta as usual bata hanashi saidai taki bari suhada ido hakan yasa yagane tana fushi dashi, bude mata gaba yayi saida ta zauna ya rufe sanan yakoma ta dayan bangaren Shima ya zauna yay facing dinta yace "are u happy now kin hanani bacci jiya sanan kuma kin hanani zama nai aiki" wasa tacigaba dayi da yatsun ta batare data kalleshi ba hakan yasa yace "My Eesha menayi talk to me I can't take dis punishment" shiru tasake mai hakan yasa yace "please" kwallan daya zubo mata ta share da sauri tace "mesa kasa aka maida bikin upper Saturday" takarashe maganan tareda rera mai wani sabon kuka ahankali, dan murmushi yayi tareda shafa kanshi yace "to everyday u keep driving me crazy nakosa ki zama tawa" yakarashe maganan yana dan dariya ciki ciki hakan yasa tasake harzuka takara narkemai da kuka kama bakin shi yayi yay shiru yadan daure fuska ya dafa kanshi tsayar da kukan tayi ta kalleshi cikin shagwaba tace "what?" kaman zaiyi kuka yace "bakomi yaune na gane cewa am just wasting my time amma baki taba sona ba my Eesha, I feel like hanging my self nahuta, no I feel like na shiga beach ruwa yatafi dani, no I feel like namaida kaina kifi kawai asoyani aisaiki huta ko" yakarashe maganar tareda kifa kanshi a sitiyari mota dan inyacigaba da kallon ta dariya zaiyi sabida yanda yaga tashin hankali karara akan fuskarta, ta tsani ta ganshi cikin damuwa hankalin ta tashi take. Dawata irin calm voice tace "am sorry" girgiza kai yayi batare daya kalleta ba yace "No my Eesha u are not, kawai ki barni naji dakai na" kaman mara gaskiya tace " kayakuri to na yarda" murmushi yayi ya dago kanshi ya kalleta tareda kara narke mata yace "a'a abarshi in four weeks time din kinsan bazan iya jure kina fushi dani ba, I can manage myself tunda baki damu daniba" da kyar ta shawo kanshi sanan suka shirya yay parking agaban gidansu ya kashe motar dago da kanta tai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta sakinmai murmushi tace "infadama wani secret?" da sauri yace "yes my Eesha" bakin hijabin ta tarike tana dan murmushi hakan yasa yace "ha'an tell me nakosa" shiru tadanyi tana dan waswasi kafin tace "kasan mesa at first I was angry danaji an matso da bikin kusa?" "No" kaman zatai kuka tace "naga wani agogo" tadanyi shiru tare da juyar da kanta ta kalli window motar tace "dama tara kudin dinkin danake yi nakeyi har kudin yacika in saima, ranar bikin mu agogon nakeso kasa, but kaga yanzu bangama tara kudinba kuma kasa anmatso da bikin kusa" jin yay shiru baice komiba yasa ta juyo da kanta ta kalleshi tsantsar sonta tagani kwance akan fuskar shi hakan yasa tamai murmushi wani irin gauron ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe ido danji yake kaman yajawota ya rungume iska yaji anhuramai a fuska hakan yasa ya bude ido ya saukesu akan kakkyawar fuskarta cikin tsantsar kauna dawata irin calm voice yace "incika miki kudin kisaimin my Eesha?" girgiza mai kai tayi tace "I want to use my hard earned money, da gumina nakeso nasai ma dashi inda bahaka ba danai amfani da kudin da Abba da Ammi keban tuntuni, nasan zan sami dinki I will be able to complete the money" hannunta yakai zai kama da sauri ta janye tana hararanshi ahankali tareda murguda mai baki ta bude kofar motar tafita ta bude gate ta shiga gida. Hannu shi ya daura kan kirjinshi dake bugawa very fast ahankali yace "Ya Allah kabani Eesha" kunna motar yayi yabar anguwan. Bude ido yayi afirgice ya kalli agogo zaro ido yayi yace "wat those girls will kill me today" agurguje yafada bayi yay wanka yafito ya shirya cikin farin shadda gizna dayay mugun karban shi yadau turare ya feshe kanshi dashi sanan yadau waya da car keys dinshi yafita daga dakin da sauri dakin mum ya shiga yace "morning Ammi" ajiye littafin Azkar din dake hannunta tayi ta kalleshi tace "ango in the next seven days antashi lafiya" murmushi yayi kaman baijiba yadau mug din tea daya gani akan stool din dake gaban Ammi ya kwankwande sanan ya ijiye mug din yace "Ammi ina su Ihsan" tabe baki tayi tace "nizaka tambaya kasan kunyi alkawarin yau asabar karfe tara zaka kaisu shine yanzu ake ganinka ai sunce sunfasa zuwa hanyar kofa yayi zai fita Ammi tace" Son" juyowa yay yace "Na'am Ammi" mayar da kanta tayi kan littafin hannunta kafin tace "anjima yan uwan babanku da babar ka zasuzo yau za'akai akwatin" takarashe maganan tareda dago kanta tana kallon fuskar shi wani kunyar Ammi yaji yakamashi hakan yasa yafita dakin da sauri ya shiga dakin su Ihsan. Dariya Ammi tai kawai ta kada kai babu wanda yasan halin dan nata kaman ita. [6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 4&5... Dankakaren falon gidan su acike yake dam da yan uwa dan yau Alhaji Ismail wan baban Khaleel wanda suke kira da Abba ya iso daga Yola tareda yaranshi da matayen shi biyu, Hajiya Amina wacce itace babba yaranta uku Mustapha babban danta da yanzu yay aure matar shi bata haihuwa, sai Yusuf shine na biyu shine saan Khaleel tare suka taso sun shaku sosai, sai autar su Fa'iza wacce ke SS3 a boarding school. Amaryan Abban Kuma Mujiba yarta daya wacce takeda shekara daya aduniya, gabaki daya falon ya kachame da hira idan ka gansu gwanin ban Sha'awa. Yusuf ne ya kalli Khaleel dake danna waya yana shan tea yace "kai tashi muje mu amso dinkin mu, and su Shareef na jiran mufa a barrack dinku" yatsine fuska yayi sanan ya maida wayar aljihu ya harare shi yace "muje" tashi sukayi Yusuf yace "Abba zamudan fita" da sauri Ihsan tace "Ya Yusuf ku dawo dawuri fa, 4:30 daidai ne walimar babu afircan time" ta kalli Fa'iza da Ilham tace "ku tashi muje gidan su Aisha ma, nasan amma fara lallen tanata min flashing" Car key Khaleel ya dauka suka fita dukan su tare. Karfe 4 aka fara tafiya da kawayen amarya wajen event din ganin su Eesha basu fitoba yasa Mama ta shiga dakin nasu, su Ihsan ne da wata kawar Eesha wacce suke aji daya anan University Abuja. Kasa magana Mama tayi ganin yanda Eesha tai mugun kyau abunka da wacce bata saba kwalliya ba, murmushi su Ihsan sukayi, Ilham tace "Mama tai kyau ko, Fa'iza ce tamata makeup dinan" murmushi kawai Mama tayi tajuya tabar musu dakin, ahankali Aisha ta dago kanta ta kalli fuskar ta a madubi murmushi tayi sabida taga tama kanta kyau, Khadija ce ta dagata tace "tashi muje, yau idan Khaleel ya ganki na tabbata hmmm" dariya sukayi bakaramin kunya taji ba ta turesu tafita daga dakin da gudu, binta sukayi nan suka shiga motar da aka barmusu driver ya jasu zuwa wajen venue walimar. Wa'azi aka musu mai ratsa jiki, mai sanyaya rai mai kara Imani, sosai kowa yay hawaye, barinma amaryar, bayan angama aka rarraba kyaututtuka akai ciye ciye sanan aka fara kawo motocin komar dasu gida. Gaban wata babar jeep Khadija ta kaita kirar Brabus, bude marfin motar tayi ahankali ta shiga sanan ta mayar da kofan ta rufe juyawa tayi da sauri ta wuce ta shiga wata motar daban. Kin dago kanta tayi dudda taji yanda kamshin turaren shi ya bude motar, cikin wani irin calm voice taji yacema driver mutafi. sundan jima suna tafiya kafin ahankali ta dago kanta ta kallai karaf suka hada idanu hakan yasa ta juyar da kanta da sauri tana murmushi. Parking motar taji anyi anbude gaban motar anfita matsowa yay kusa da ita kadan dawani irin murya chan ciki yace "wife" duk yanda taso karta kallai hakan ya gagara samin kanta tayi da juyowa ta sauke mai kyawawan idanunta akanshi, ganin kallon dayake mata yay yawa yasa ta huramai iska a fuskar murmushi yayi, ahankali tace "Mesa kake kallona haka?" takarashe maganan tana turamai baki, murmushi yasakin mata kafin yakara matsowa kusa da ita, da sauri tai yunkurin matasawa hannunta yarike yana wani irin kallon fuskar ta, jikinta ne yafara rawa ta bude baki zatai magana, dayan hanunshi ya daura akan lips dinta yana girgiza mata kai da idanunshi dasuka xhanza launi kaman basuba, ahankali yadaura goshin shi akan nata lumshe ido yayi jin yanda take numfarfashi, dawani irin murya yace "ina sonki sosai my Eesha" Ahankali ya dago da kanshi hannu yasa yay cupping fuskar ta sauke idanunshi yay akan lips dinta dake shining sabida Jan bakin dasuka ji wani irin abu ke fizgar shi ahankali yakai bakin shi zai daura da sauri ta kawad da kanta kirjinta na mugun bugawa dan tunda take dashi baitaba mata hakaba, wani irin hawaye ne ya zubo mata tai sauri ta share sanan tadan kalli fuskar shi wanda ita yake kallo da idanunshi dasuka kankance kofa ta bude da sauri tafita ta bude gate ta shiga gidan su. Yafi minti uku a zaune kafin ya bude kofar ahankali yafito front sit yakoma ya kunna motar yaja yabar wajen. Gaishe da kawayen Mama tayi dake falon a kunyace ta wuce sama, su Khadija da Ihsan ne ke gwada kayan ankon su da aka kawo musu, zama tayi a gefen gado tana yatsine fuska tace "wash Allah wlh nagaji" dariya duka yan matan sukayi Khadija ce tace "ai dole sannu kinji" yanda tai maganan yasa Ilham ta kwashe da dariya tace "ai Yaya Khaleel shegen naci shi bazaima bari gobe tayiba yawani..." hararan ta Eesha tayi tace "yan sa ido Yaya Khaleel dina baida naci duk cikin sone" kama baki dukan su sukayi suna kallonta cike da mamaki, Ihsan ne tace "iyye kike karemai muma Allah bamu mai sonmu" dariya tayi tareda cire doguwan rigan jikinta ta yarage saura shimi da dogon sket, ta ninke ta ijiye akan gado, murmushi tayi ganin fuskar Khaleel namata gizo, hannu tasa ta cire dan kunnen kunnenta ta ijiye agaban mirror sanan ta juyo ta kallesu ganin duk ita suke kallo yasa tasake murmushi tace "bazaku gane yanda nakeson yayan nan naku bane, inama Ya Khaleel son da ina ganin ko bayan namutu banjin son zai mutu ba, Ya Khaleel namijin tal da har yau banga irinshi ba, mutum ne mai tausayi, kirki ga amana da addini, nasan yanada matsalan zuciya da yawan fushi but alkairan shi sun mamaye wanan, sabida Ya Khaleel ne Auta ke raye da yanzu ya mutu, kuntuna randa gidan mu yakama da wuta duk anfito damu but Auta na ciki, Ya Khaleel was d one daya koma duddu uban wutan nan yaje ya dauko Auta, saida ya kone a hannu garin hakan, haryau tabon na jikin shi" share dan guntun hawayen daya zubo mata tayi ta mikama Ilham da Ihsan hannu tace "Yaya Khaleel dina is my everything bazan taba son wani sama dashi ba" murmushi tayi ta sake su ta wuce bayi danyin wanka. Banjin daga Khaleel har Eesha wani daga cikin su yay wani bacci mai kyauba, Eesha su Ihsan da Khadija ne suka tasata agaba wai takosa, shiko Khaleel abangaren shi Yusuf da friends dinshi ne suka tasashi gaba wai yakosa yaki bacci dariya yay yaki musu magana. Misalin 9:30 nasafe na ranan bikin mutane sun cika gidan makil, Aisha ce zaune akan gadon dakin ta tasa wata atampa English wax da aka mata stone work yay kyau sosai, wayarta ta dauka tai dailing number Khadija ringing daya ta dauka, tace "Eesha am coming back yanzu na siyo agogon, gama ninan nafito daga Dunes Abuja taxi nake nema nahau" murmushi Eesha tayi daya mugun kara mata kyau tace "nagode Tawas, kiyi sauri please inaso nabashi yasa kafin lokacin daurin auren ne" katse wayar tai tana murmushi tun jiya bai kirata ba tasan hala fushi yakeyi, murmushi tayi tadau wayar Flashing tama su Ihsan dan sun tafi gidan su dauko kayan makeup din Faiza sunki dawowa. Wuraren goma da rabi Khadija ta dawo da sauri Eesha ta karbi ledan da akwatin agogon ke ciki, ciro agogon tayi ta bude daga box din wow tace, agogo ne mai kyau Rolex wanda tasaimai da kudin ta 75,000 naira, gashin golden color rufewa tayi ta dau wayarta dailing number Khaleel tayi saida takusa katsewa sanan ya amsa. Murmushi tayi kafin yay magana tace "am sorry Yaya Khaleel" Ahankali ya lumshe ido danji yayi wani sanyi ya ratsa zuciyar shi, dawani irin murya tace "kana ina kana gida ne?" dan murmushi yayi sanan yace "a'a muna bakin layi shagon dinki Ibrahim tela, kayan dazamu sa gabaki daya fashion designer damuka bama dinki yamana wandunan sunyi tsawo sosai shine muka kawoma Ibrahim yarage mana, Mesa kike nemana Kuna bukatan wani abune, nazo?" girgiza kai tayi tace "a'a kabarshi bari nina zo, I want to give you something, something special" da sauri yace "kina amarya kifito akalle min ke lallai to naki, bari am coming" dan dariya tayi sanan tace "ni to ai kofar gidanmu da mutane banaso su ganmu tare ne saisa, Kuma su daddy ne da friends dinshi, saisa nakeson nazo am coming" katse wayar tayi tadau dogon hijabin ta har katsa tasa, Khadija dake shiryawa tacema "Ina zuwa, insu Ihsan sunzo afara miki makeup din, bari nakaima Khaleel wristwatch din" tafita daga dakin a tsakar gida taci karo dasu Mama da yayyin ta, kallonta daga sama har kasa Mama tayi tace "ina zaki haka" Kaman zatai kuka tace "Mama abu zanbama Khaleel a waje plzz" Mama zatai magana Yarta dasuke Kira da inna asabe tace "tafi kinji Eesha" ta kalli Mama tace "kibarta mana daga yauma gidan mijinta zata koma tabarmiki gida, tunda yana kiranta aisaitaje" da sauri tafice tana dariya dan tasan Mama da hanata zatayi, hango su Baba tayi a barander waje hakan yasa taja gaban hijabin ta dan karsu ganeta tazo ta wuce tafita sadaf sadaf daga gate din, da sauri take tafiya hartakai bakin titi, yana tsaye a shagon ya hangota zata tsallako kasan cewa kofar glass ne a shagon, murmushi yayi yacema Yusuf "am coming my queen wanna see me" hararan shi Yusuf yayi shikuma yajuya yafita daga shagon, tana hango shi ta sakin mai murmushi, murmushi yamata sanan ya mata alamu da hannu ta tsaya bari shi ya tsallako, murmushi tasake yi ta make kafada sanan ta kalli titi ganin babu wani abun hawa yasa ta shiga titi ta tsallake first lane, hakan yasa shi ya tsaya yafasa tsallakowa yana mata tattausan murmushi. Kaman ance ya waiga nan yaga wani trailer daya dauko yashi yataho dawani irin mugun gudu tsaki yayi yace "Wayan nan reckless drivers dinan ko" alamu yakara yima Eesha da hannu ta tsaya, gyadamai kai tayi Dan trailer kawai take jira yawuce ta tsallake titin nabiyu, kara taji hakan yasa ta kalli trailer da sauri tayan gaban ne yafashe hakan yasa motar fara kwana, ganin motar yayo dakalin tsakiyar titin datake tsaye zai fadi akai yasa tai ihu "subhanallah Wayyo Allah" tai baya da sauri ta fada titin bayan ta, kararrarraaa naji wani irin kara dayasa gabana bugawa. [6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 6&7... Dawani irin mugun gudu ya tsallako titin bai damu da babban trailer dayama fadi ba, tsayawa yayi a akan dakalin tsakiyan titin ganin motoci kusan uku su bubbuge juna, waigawa yayi sanan yasake waigawa again dan baiga Eesha ba, ahankali yace "kodai taji tsoro ne ta koma gida?" hanunshi yaji anrike da sauri ya daga kai Yusuf yagani ya rikemai hannu gam, gasu Ibrahim tela da abokanayen shi yan wajen aiki da suka daura hannu aka suna kallon titin ganin yanda mutane harsun cika wajen suna ku matsa aciro ta tana numfashi, wani irin fuzge hanunshi yayi daga Yusuf ya shiga titin, mutane kawai yake turewa kaman zararre yana kutsawa cikin crowd din, Yusuf da abokanansu ne suka bishi da sauri ture mutanen yayi duka harsaida yakai dadai saitin wata bakar jeep, kasa yabi da kallo kaman zararre ganin jini nabin wajen, da sauri ya tsugunna ya leka kasan motar, hango Eesha yayi hakan yasa ya tashi da sauri kaman zararre yace "ku matsar da motar da sauri masu motocin suka shiga, ahankali aka mammatsar da motocin, tsugunna nawa yayi ya jawota ya daura kanta akan kirjinshi yana kallon fuskarta yama kasa magana, murmushi tamai jini nafito wa daga bakinta, kokarin yimai magana take amma takasa da sauri Yusuf ya tsugunna ya dafa kafadar Khaleel ahankali yace "Aisha kice La'ilaha illallah Muhammadur rasulullah" bakinta ne ke rawa haka Yusuf ya dinga maimaita mata harta karba, da kyar ta daga dayan hannunta da ledan agogon ta ke ciki ta daura akan hanun Khaleel, sanan hanunta yay lagwal. "Abba Abba" kanin Eesha ne Ibrahim yazo da gudu da farin shaddan anko dinshi ajiki, Abba dake tare da abokanan aikin shi yace "lafiya Ibrahim" yana haki yace "Abba anyi hatsari sosai akan titi wlh" subhanallah Abba yafadi shida abokanan shine suka tashi dan zuwa dubawa, Karo sukaci da Babban Khaleel da wanshi suma zasu dubawa hakan yasa dukan su suka dunguma zuwa titin. Salati gabaki dayan crowd din wajen suka dauka, kowa ya kasa motsi barinma mutumin daya bigeta wanda yake arne yaci suit jikin shi yay mugun sanyi, ahankali Yusuf yakai hannu ya rufemata idanu, Khaleel ya kalla dayaga kallonta yake kaman zai cinyeta yace "Khaleel Khaleel" ko kallon shi Khaleel baiyiba har lokacin yana tsugunne da ita akirjinshi. Tashi tsaye yayi idanunshi sun xhanza launi, hango su Abba yayi kana ganinsu kaga tashin hankali karara akan fuskokin su, ahankali suka tako zuwa wajen tsugunnawa baban Eesha yayi ya kalleta shiru yayi yana addu'a sanan ya kalli Khaleel yace "Khaleel" ko dago kai Khaleel baiyi ba har lokacin fuskar ta yake kallo yay shiru da sauri Ibrahim tela ya koma shago ya dauko wata katuwar tabarman shi dayake yanka dinki akai, karaso wa yayi yamika ma Baban Khaleel ya karba, zuwa wajen yayi ya warware, ahankali baban Eesha ya mika hannu zai karbe ta wani irin ihu yayi yasake riketa yace "karku tabamin matata, bacci take" dariya yayi ya kalli fuskar ta yace "My Eesha sleep kinji idan kin tashi saimutafi, kitashi kafin karfe daya fa dan lokacin zaa daura mana aure" Ahankali baban Khaleel yake furta "innillahi wa innailaihi raji'un" ahankali yace "Son saketa zamu kaita gida amata sutura" ko kallon mahaifin nashi baiyi ba, hakama Baffan shi Abba babu wanda ya kalla cikin su, Yusuf ne da abokanansu su kusan takwas suka rirrike shi da kyar aka dauketa akai gida da ita, Khaleel kam ahaka abokan shi da Yusuf suka rirrike shi yana maganganu dako gane meyake fadi basayi suka taho kofar gidan su Eeshan dashi. Ance kowani rai mamaci ne, mutuwa bata baka notice, once lokaci yayi you just have to go, mu kusanci Allah mu nisanci zunubai, muyawaita istigifari bamusan kozamuga gobe ba. Babu wanda ya yarda Eesha bata, Mama gani take ya'ta da yanzun nan tazo tacemin zata fita dama ajali ke kiranta?? Khadija kam kasa magana tayi kuka kawai take, su Ihsan dasu Faiza da kanin Eesha bansan wama ke lallasan wani ba, Maman Khaleel da Umma da Mujiba ma duk zuwa gidan su Eesha sukayi. Ko alwala ma yima Khaleel akayi sosai yafita hayyacin shi hanunshi damke da ledan da Eesha tabashi yana wasu irin surutai, haka aka mata Salla aka kaita, aka dawo shikenan fa duniyan. Yauce Rana uku da rasuwan Eesha, babu wanda zaiga Khaleel dabazai yi kuka ba, koka zo gaisuwa bakai niyyar kuka ba shiza kagani kai kuka, ko abinci yakici, ruwama saidai abashi wanda ya shiga ya shiga sauran su zube akasa dan baya zukan ruwan da kanshi, ko wanka yakiyi balle ma wani abun, bayama kowa magana saidai yay ta maganganu shi kadai, addu'a ake mai bana wasaba amma har lokacin ba chanji, Maman Eesha duk idan ta kallai saitai mai kuka, Ammin shi kam baa cewa komai. Misalin 1:25 na dare kowa na dakin shi, karan fashe fashen abubuwa ne yasa kowa ya mike daga kan gado dan dama bawani baccin kirki kowa keyiba, afrigice Yusuf ya farka gefen shi ya duba ganin babu Khaleel dake kusa dashi yasa yay jumping daga kan gado yafito daga dakin, cin Karo yayi da Abban shi da Umma, Abban shi zaiyi magana saiga Daddy da Ammi sun fito, su Ihsan ma haka atare suka dunguma suka sauka kasa kitchen sukayi dan nan sukejin karan. Shiga sukayi da sauri Khaleel suka gani dauke da tabarya a hannu yana faffasa koma me hanunshi yakai yana ihu yana magana "ba Kaine bakin jeep dinba Kaine my Eesha ke karkashin ka, ku ku 5 ne" tawarwatsa kwanuka kawai yakeyi, ko kallon su Abba dake kiranshi baiyiba, Yusuf ne ya fizge tabaryan ya ijiye hakan yasa ya ture Yusuf, da sauri Ammi ta juya ta koma falo danji tayi wani mugun kuka yazo mata, Ihsan ma fita tayi da sauri jikin Ammi tafada sai kuka da kyar Umma ta lallashe su, wani irin murmushi Mujiba tayi mai wuyar fassara kafin ta dawo falon ta zauna. Baban Eesha Abba yakira dan babban likita ne shi, within 2min ya iso, da kyar su hudun suka iya kama Khaleel dubashi baban Eesha yayi kafin yamai alluran bacci, nan bacci yay gaba dashi akan dogon kujera. Ajiyar zuciya Abban Eesha yayi kafin ya kalli Abba yace "I think Khaleel yay developing mental issues". [6/8, 5:37 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 8&9... "But gobe in Allah ya kaimu da safe sai mu kaishi clinic dinmu a dubashi" kowa kasa magana yay afalon da kyar Abba yace "mungode" Sallama yamusu yatafi zuciyar shi cike da tausayin Khaleel, Aisha bata amma Khaleel kai Allah gamu gareka, girgiza kai yayi yatafi kawai. Gabaki dayan su a falon suka kwana dan sosai Khaleel ke surutai cikin bacci. Around 8 baban Aisha yazo shirye cikin suit bakake da kyar Yusuf suka fito dashi suka sashi amota sanan aka tafi asibitin wani babban likita daya kware a bangaren mental Baban Eesha ya kaisu wajen shi, nan yazo gaban Khaleel ya tsaya ya dudduba shi sanan ya Kalli Daddy dayay shiru yana kallon ikon Allah yace "Ya sunan shi?" Abba ne ya iya yay magana yace "Muhammad Khaleel" rubuta wa Dr yay a file din daya shigo dashi ya maida duban shi ga Khaleel daketa motsi da bakin shi, "Khaleel" Dr yakira sunan shi, shiru kaman ma bada shi akeba, Yusuf ne ya matso wajen ahankali yace "Dr tun randa abin yafaru bai kara mana magana ba, is as if baima sanmu ba" rubuce rubuce Dr yayi, ya dauko wani abu kaman bindiga ya daura akanshi nakusa 1min sanan ya cire, rubuce rubuce yayi sanan yamika musu prescription sheet yace "asiyo mai wanan magungunan" Ahankali Abba yace "meke damunshi?" murmushi Dr yayi yace "post traumatic stress disorder, but zai dinga zuwa therapy bayan kwana bibbiyu, and zan sashi a medication, bayan 2 weeks inhar babu improvement sai musan abin yi" godiya sukamai sanan Yusuf yatafi siyo maganin suka tafi gida. Yau kimanin 2 weeks kenan gidan nan babu wanda bai rame ba sabida Khaleel, babu wanda yake yadda dashi baya wanka, baya ma kowa magana abinci ma ko Ammi tasamai abaki wanda yaga damane zai hadiye sauran akasa, har yanzu Baffa da Family shi basu komaba dan bazai taba iya tafiya yabar kaninshi da wanan wahalar ba yasan yanda kaninshi keson Khaleel, bashi kadai ba duka familyn ma akwai wanda bayason Khaleel ne. 10 a office din Dr yamusu ajiyar zuciya Dr ya sauke kafin ya Kalli Abba yace "Sir Khaleel yaki responding to treatment, inda acema ya yarda yay magana ne ko awajen therapy dinshi ne it would have been a great difference dakomi yazo mana da sauri" "to to Dr yaza ayi yanzu?" cewar Abba "Alhaji yanzu is time for the second treatment abinda nakeso daku shine ku cire, kokuma ku fitar dashi daga environment din incident dinan, inma da hali yabar Abuja for now, ai zaku iya daukar mai excuse a wajen aiki na medical leave ni zanmai recommending, duk wani abu dazai dinga tunama kwakwalwan shi Aishan ku nisan tashi daga abin, kana ganinshi ahaka kome daya dangan ci Aisha yasani so ku nisan tashi daga memory and ku dinga cheering dinshi up now more than ever he needs love da pampering kome yakeso kumai koma menene shizai sa yay healing fast" godiya sosai suka mai sanan suka tafi. Koda suka kai gida kwantar da Khaleel sukayi a dakin shi Yusuf ya zauna dashi, Ammi dasu Umma Abba ya kalla yace "kubiyo ni" falo suka fita suka zazzauna Abba ne ya Kalli Daddyn Khaleel yace "inason na wuce da Khaleel yola kaman yanda Dr yabamu shawar anisan tashi daga nan koya kagani achan saimuga Yaya zaiyi healing idan babu improvement saimu fita dashi waje koya kagani" gyada kai Daddy yayi ahankali yace "to Yaya nima nafison hakan, ke Amina saiki hadamai kayan shi ko" gyada kai Ammi tayi da sauri, Ihsan da hawaye ya cika mata ido tace "Abba nima zan biku" Ammi ne ta kalleta tace "exam dazaku fara next week fa? Don't worry duk lokacin dakukai hutu saikuje ku dubashi" murmushi Umma tayi tace "addu'an ku Khaleel yafi bukata yanzu bawani abuba, Alhaji tun jiya Gwaggo ke kirana tana tambayana yaushe zamu dawo bansan mezan cemata ba" "banason na tada mata da hankali ne, idan mukoma ma fadi mata meya faru" wani irin murmushi Mujiba tayi tana kallon fuskar Daddy Khaleel tana kada kafa. Washe gari jirgin Rana sukabi suka koma yola, haka gidan ya dawoma Ammi da kanen Khaleel wani iri, ba karamin wani iri Ammi takeji ba da kyar ta lallaba kanta ganin zazzabi nason kama su Ilham. Yau kusan watan shi daya kenan a yola, yana zaune a dakin Goggon wacce ta hadamai fura take bashi abaki, yana sanye da farin t-shirt wacce ba karamin dambe suka sha da Yusuf ba kafin yabari asamai, ahankali Goggo ta ijiye kofin furan, tadau handky ta share mai bakin shi da rigar jikin shi dan gabaki daya fura zubewa yake wanda ya shiga bakin shi ne yake lashewa, Abba dake tsaye akansu ta kalla tace "Sama'ila ni ni wlh jikan nan nawa tausayi yake bani, ace yaro yafita daga hayyacin shi baima sanmuba yanzu" kecewa tayi da kuka sosai ta kwance bakin zani tana share fuska zama Abba yayi yace "to Mama idan kina kuka haka mumuce mene, namayi magana da baban shi dazunan, jibi zamu fitar fashi waje saudiyya zamu, akwai wani likita dana sani a wajen yace mukawoshi in sha Allah zai sami lpy har magana zai fara" da sauri Goggo tace "dagaske Sama'ila" gyada mata kai Abba yayi tace "Alhamdulillah" shafa kan Khaleel din tayi tace "Allah nagode ma, dazaran ya warke zan nemo yarinya yar kirki mai hankali da natsuwa na auramai hakan zaisa ya wartsake" tashi Abba yayi yace "bari nadan fita" "adawo lahiya" part din Mujiba yatafi a uwar daki ya sameta tana kan gado tana watsapp baiko kalleta ba ya bude wardrobe babban rigar shi ya dauka yasa sanan yace "kihada min kaya jibi zamu fita da Khaleel waje" adan zabure ta kalli Abban tace "Alhaji maisa zaka wani kashe kudin ka Yaron nan yariga ya haukace bazai taba warke wabafa" wani irin kallo dayamata yasa tadanyi murmushi ta kwantar da murya tace "bahaka nake nufi ba, ni gani nayi tayaya treatment din zaiyi progressing bayan baya cewa uffan balle asan meke mai ciwo daka bari yafara magana tukun, duk kawani damu saikace Yusuf ne baida lpy" wani irin kallo ya watsa mata ya nunata da yatsa cikin fushi yace "ki kiyaye ni Mujiba, ki kiyayeni fa, and Yusuf da Khaleel basu da bambanci awurina duk yayana ne, baki isa kiraba kan family naba kinajina ko" fita yay daga dakin ranshi abace, sosai abin ya konama Mujiba rai, ai wlh yanda naso kaninka yakini, dasonshi nake wahala da dawainiya, bankara ganin farin ciki ba, haka danshi ma zai wahala bazai taba samin farin ciki ba arayuwar nan ba, ko Allah ma nabaya na, ai saisa ya kashe yarinyar batare danai komiba, warke wa dai bazaiyi ba bi'iznillahi, koma ya warke farin ciki yakare mai arayuwa. Tsaki tayi ta wurgar da wayar ta tashi ta shiga bayi. Saudiyya. Ba karamin cigaba aka samu a treatment din Khaleel ba, dan yanzu dazaran yaji kiran salla zai tashi yay alwala yayi, magana ne idan anmai saiyaga dama zai amsa, gabaki daya ya chanza ya dawo shiru shiru kaman ba Khaleel mai rahan nan ba, idan Ammi tabashi abinci zaici kadan ya ijiye mata, idan yagaji ya kwanta ya daura kanshi akan cinyar ta ya lumshe ido, sosai aka dage damai addu'a dudda haka sunji dadin yasoma samin cigaban nan. Dr yahana amai maganan Eesha ko kadan. Ganin cigaba sosai yasa Dr ya sallame su suka dawo Nigeria Ammi da Daddy suka wuce Abuja, Baffa da Yusuf suka wuto dashi nan yola. [6/8, 5:37 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 10... Da sallama ya shigo dakin Goggo, ganinshi dayayi kwance akan katuwar dogon kujera ear piece akunenshi ya lumshe ido yana sanye da white t-shirt sai dogon black jeans yasa yakarasa shigowa dakin, hannu Yusuf yasa ya cire earpiece din daga kunenshi ya jawo hanunshi ya zaunar dashi bude idonshi yayi ahankali yadaura akan Yusuf yay shiru as usual batare dayace komi ba yana kallon shi da idanunshi masu kama da madara, hanunshi Yusuf yaja yana kokarin tadashi tsaye yace "zomuje karakani jor let's go out" kaman marason yin magana yace "am not going" fitowa daga uwar daka Goggo tayi hanunta rike da goro tace "waye yanzu yatada min da Babana" baki tarike tana hararan Yusuf tace "shine kadatashi Yusufa? Yaro na hutawa abinshi dan bakin ciki" wajen Goggo yaje yace "goggo tayani mai magana please kicemai ya rakani mufita" zama kusadashi Goggo tayi tace "Babana katashi mana kabi dan uwanka kufita, yau kusan wata shidafa kenan baka taba fitaba banda masallaci, jibi kanka kaki aski iye, aya aya tashi kabishi kafin kadawo zan dafama dambu dakaina kaji Dan'nan" ahankali shima Yusuf yace "please Bro for my sake" shiru yadan yi sanan yay musu murmushi yace "okay" sabida murna Yusuf saida ya rungume Goggo suka tafa, tashi sukayi Goggo tarakasu har wajen mota tana musu adawo lafiya kafin sufita tadawo cikin gida. Dukan glass din window Mujiba tayi zuciyar ta nazafi wani irin ihu tayi ta cire dankwalin kanta tayar "no.. No ooo" kaman mahaukaciya taje wajen fridge ta bude goran ruwa ta dauko ta bude tasha sanan ta ijiye, jin har lokacin zuciyanta bai dena zafiba yasa tace "nooooo nooo yaushe har yawarke daga haukan?? Yaushe, dahar zai fara fita" wani irin ajiyar zuciya ta sauke tace "I have to do something bazan taba bari ka warke daga haukan dakake ba, banason nataba ganin koda digin farin ciki a fuskan iyayenka khaleel, inaso mahaifinka ya daddana azabar dayasani na shiga" goran ruwan takara dauka tasha ruwa sanan ta ijiye tace "Khaleel nadau alkawari bazaka taba samu farin ciki da haske arayuwan kaba har abada, yanda mutuwar Aisha yasa kasami ciwon hauka kashiga kunci da bakin ciki ahaka rayuwar ka zata kare harka koma ga ubangijin ka wanan alkawari nane ni Mujiba agareka" tawani fashe da kuka kafin ta kwallama mai aikinta kira dagudu tazo wani irin tsawa tamata tace "zoki gyaramin kumbana". Saida suka shiga hanya sanan Yusuf ya kalleshi ganin yay shiru yana kallon motocin dake tafiya akan titin yasa yace "kasan inda zamu kuwa" girgizamai kai yayi, murmushin jin dadi Yusuf yayi at least yau yana amsamai yace "anguwar tsamiya, Abba yaturani nakai ma Malam Isya wanan kudin" yanunamai wani katon envelope dake tsakakanin su sanan yace "Malam Isya yanada kirki shike kulan ma Abba da gonakin shi saisa duk idan Abba yay zakka yake bashi" shiru yayi yana sauraron shi hakan yasa Yusuf yace "gaskiya yau zakayi aski gashin nan naka yataru dayawa ga sajenka yay bususu, idan zamu koma saimuyi branching barbing saloon ko" shiru yayi baice komiba haka Yusuf yay ta janshi da hira sabida Ya Mustapha yace adena barinshi alone adinga yawan mai hira, Kuma Alhamdulillah ga so much improvement yanzu yau dakanshi yaje dakin Goggo at least yana amsa magana, jiyama shiya koyama Fa'iza assignment dinta, gashi yau ya yarda yabiyoshi sunfita. Lumshe ido yasake yi ya maida hankalin shi sosai Kan tukin dayake yi yana tunanin zuci yace "Ya Allah ka warkar da bawan nan naka gabaki daya, ya Allah kadawomai da farin ciki rayuwar shi, ya Allah kasanya mai danganar rashin Aisha kabashi wacce tafita, itakuma Allah ka jikan ta" haka yayta tunanin zuci harsukakai kai kofar gidan Malam Isya. Parking yayi yafito yadawo ta bangarenshi ya budemai kofan yace "zomu shiga ciki" yatsine fuska yayi "am not going" murmushin jin dadi Yusuf yakara yi ganin yanda yay dogon magana yau yace "okay I will be right back bazan dadeba". Barin wajen yayi shikuma yadan kwantar da kujeran yay relaxing bayan shi tareda lumshe ido. Dadan sauri take tafiya wanda yay kama da ahankali, goyone abayan ta wanda yarinyar data goya ke kuka sosai kaman ansatota adaburce Yarinyar tace "yakuri Miemie gawani shago chan muje nasai miki ruwa" ahankali takara sauri harta wuce motarsu Yusuf, Dumm yaji kirjinshi yawani irin mugun bugawa, hannu ya daura akan kirjin tareda kara lumshe idanunshi. Karasawa tayi shagon abirkice tacema mai shagon "Malam a bani ruwa guda daya" kwanto Miemie tayi daga bayanta tariketa a hannu sanan ta ciro naira hamsin daga jakanta tabama mai shagon takarbi pure water tasa abaki ta bude, sama yarinyar tayi abaki da sauri yarinyar tafara zukan ruwan hakan yasa budurwan tasaki wani murmushin kwanciyan hankalin tace "dats my gurl dama kishi kikeji shine kikemin ihu kaman nasa to kiko, ke wlh Miemie kin iya jarababben ihu" ganin yarinyar na neman shanye ruwan yasa ta fizge daga bakinta tace "cikin ki zai fashe, is okay Miemie" wani irin ihu yarinyar tayi da saida ya amsa ko ina a anguwan dan ihu tayi kaman an yankata, ahankali ya bude ido yana waige waige jin ihu dan kokadan yanzu bayason hayaniya, idanunshi ne suka kai kan yar karaman yarinya dake kan shoulder wata data bashi baya tana jijjiga yarinyar.. "Miemie I promise bazan kara fita dakeba, saidai nabarki agida, sai mutum zai fita kiyita binshi kina kuka kaman zaki mutu inmun fito kiyita min kuka" Mai shagon ne yay dariya yace "hajiya ai haka yara suke ungo chanjin ki" ahankali ta juyo sabida batason ta tada Miemie dataji tafara gyangyadi akafadanta chanjin takarba daga hanun mai shagon sanan ta juyo... Goge idanunshi yayi dan yakara tabbatar da abinda yagani lips din shine suka fara rawa "My.. My... My.. My Eee.. My Eesha". [6/9, 3:34 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 11... Bude marfin mota yayi yafita ko kulle kofan baiyiba yawuce wajen shagon da sauri kaman zai fadi yakarasa wajen daidai tagama goya Miemie abayanta, dan jakanta ta dauka daga kan table din wajen ta rataya akafada sanan ta juyo, mutum tagani agaban ta ya tsaya chak yay folding hannu akirji yanawani irin kallonta, wani irin mugun tsoro yabata daga juyawa tadau jaka saiga mutum abayanta kaman aljani ta ina yafito. Addu'a tafara azuciyar ta kafin tayi gefenshi sadaf sadaf zata wuce yace "My Eesha" ta gefenshi take kokarin rabawa ta wuce kai tsaye yakara tare ta yana sake kallon fuskar ta yace "My Eesha?" ahankali yarinyar ta kalli gefenta da bayanta dan kara tantance dawa yake magana "Eesha yimin magana, talk to me mesa kika gudu kikabarni eh" matsawa baya tafara yi dan yanzu tafara tabbatar da aljanine wanan dan jibi uban gashin kanshi wanda yafi na Miemie yawa, gabaki daya jikintane yafara bari takoma baya ganin kaman zai sata ajikin shine, hanunta ya kama ya rike gam adan rude, cike da murna, da murmushi yace "My Eesha am soo happy" yakara kamo dayan hanun nata ya rike arude yace "wlh is real, kece fa my Eesha maisa kika tafi kika barni for more than a year eh" da karfi ta fizge hannayenta bakinta har rawa yake tace "stop touching me, kai waye kaganni kawai kafara tabani" share kwallan daya gangaro mata tayi tace "niba Eesha bane" tajuya da sauri zata bar wajen dan idan takara minti biyu da mutumin nan wlh zata iyayin fitsari ajiki, hanunta ya kama ya fizgota saida ta bugu dashi yana mata wani irin kallo yace "is you, karya kike, kece, Aisha nane ke" ya nuna fuskar ta, kokarin fizge kanta take ganin yaki sakinta yana kallon ta kaman zai cinyeta yasa tafara waige waige, mai shagon nan takira da muryan kuka tace "Mallam dan Allah zoka rabani da bawon Allahn nan, wlh, wlh niban sanshi ba, dan Allah kataimake ni" takarashe maganan tana sheshekan kuka, fitowa mai shagon yayi ya kalli Khaleel da hankalinshi nakan yarinyar daya rike gam yace "Yallabai lpy dan Allah maike faruwa ne" kaman zai hadiye ta da kallo yasake rirrike shoulder dinta yana kallon fuskarta ko kyaftawa ba yayi batare dayama bi takan mai shagon ba yace "My Eesha plz come with me, zomuje gida, su Ammi sunyi kewanki sosai, please karki sake barina kinji" yakarashe maganan gwanin ban tausayi, ahankali taji fitsari na gangara yanabin cinyarta tunda take bata taba tsorata da firgita irin nayau ba sosai kuka keson ya subuce mata,, ahankali ta kalli fuskar mai shagon tace "wayyo Allah na, Mallam na shiga uku wlh ni bansan Shiba, dan Allah karabani dashi, na shiga uku... " "stop saying bakisanni ba it hurts" wani irin tsawa ya daka mata ya daura hanunshi daya akan kirjinshi jin wani irin zafi, hakan yasa ta fashe da kuka tsabagen firgita yasa ta mika hannu tana kokarin kamo rigar Mallam mai shago daya tsaya yana kallon ikon Allah, mutum daizai rirrikeka haka tabbas yasankane to ita ya akayi take cewa bata sanshi ba. Bayason ya shiga case din dan daga ganin motar Yaron yasan dan masu kudine shagon nan nashi dashi yake ciyar da Mata yen shi da yayan shi, ganin anzo siyan abu yasa yakoma cikin shago, sosai tafashe da kuka tace "Mallam dan Allah kadawo karka banni dashi" "My Eesha" yakira sunanta, ahankali yace "muje gida" hanunta yakama yanaja ihu tafarayi da karfi ta tace "Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ka sakeni, Wayyo Allah nabani" ganin yakai ta gaban wani mota yana shirin budewa yasa tai dabara ta take kafarshi hakan yasa yasaki da sauri sabida hill din yamai zafi akafa sosai, da gudu ta arce hakan yasa yabita da gudu shima yace "no my Eesha don't leave me again, dan Allah come back" sosai take gudu ga Miemie abayanta tana kuka, yana binta. [6/9, 8:14 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 12... Da kyar ta tseremai ta labe awani lungu tana haki sosai da tari, tunda take batajin ta tabayin irin gudun nan datayi yauba, dafe kirjinta tayi dan jitayi kaman zai fito sabida yanda yake bugawa, jin kaman motsi yasa tafice daga lungun da sauri ta bullo wani anguwa dat is very quiet mai kyau, da dan gudu gudu takara sa gaban wani katoton gida dakeda brown gate, bude gate din tayi ta shiga ciki da sauri, katoton gidane dakeda flowers a tsakar gidan sai motoci kusan biyar a compound din, ahankali take tafiya dan ta bala'in gaji kaman zata fadi sai zufa take kofa ta bude ta shiga babban sitting room din da aka rabashi bangare biyu bangare daya ansanya kujera Kiran royal brown sai dayan Kuma asha ga wani makeken tv bango daketa aiki shi kadai danba kowa adakin, maida kofar tayi tarufe sanan tadaura kanta akan kofar tareda da lumshe ido ta dafe kirjinta tana sauke ajiyar zuciya, wata matace mai aikin su da akalla zatai 30 tafito daga kitchen dauke da katon food flask tazo dining ta ajiye zata juyane ta hango ta tsaye a jikin kofa, dan murmushi tayi ta karaso cikin falon cike da fara'a tace "a'a su Anty Islam har an dawo ne" ahankali ta bude ido murmushi ta kakalo ware ido Matar tayi tana kallonta ganin yanda idanuwan ta sukai ja tace "Islam badai ahaka zaki koyi rainon bako yanzu Miemie ne tasa kika galabaita haka harda kuka" hannu takai dan ta kwanto kyakyawar baby da tunda ta ganta take tsalle a baya dan ta dauketa, kwanto ta Islam tayi ta mika mata murmushi matar tayi tace "oyoyo an babyn mamanta, iyye andawo daga anguwa ne da Anty Islam" dariya yarinyar takeyi sosai kaman ba ita ke shegen kukan nan ba, zanin goyon Islam ta mika mata sanan tawuce wajen stairs hawa tayi ta tafi sama, dogon corridor ne da dakuna kusan shida a wurin, wani kofa ta bude ta shiga dakine dake dauke da gadon yan boarding house saidai shi wanan na katako ne da akamai fenti pink, bunk biyu ne kadai adakin sai center carpet shima pink, da study inda uban littatafai kekai, gaban wardrobe taje ta tsaya tana kallon mirron dake jikin kofan wardrobe din ahankali takai hannu ta warware rolling din gyalen dake kanta dogon gashinta ne ya warware ya zubo har kirjinta dan tsaki tayi ta ciro ribon din daya hade da gyalen ta kama gashin, doguwar rigan jikinta tacire tabar shimi da sket ajikinta kan gado taje ta kwanta tareda sauke ajiyar zuciya dan har yanzu kirjinta bugawa yake. Harwajen motansu Mallam isya ya rako Yusuf yana karamai godiya ganin marfin mota abude yasa Yusuf ya bude bangaren shi da sauri ganin ba Khaleel aciki yasa ya fara waige waige adan arude, Malam Isya ne yace "lpy Yusuf" arude yace "nabar Khaleel a mota bangan shibane" ganin yanda ya rude yasa yace "karka damu bari mudan tambaya" samarin dake gaban shagon Adamu yatambaya dan Allah kunga wani matashi bako nane" da sauri Yusuf yace "yanada gashi sosai akai" da sauri mai shago yace "to kodai wanan wanda ya rike yar mutanen ne yace yasanta? Dan naga gashi rututu akanshi" da sauri Yusuf yace "shine a ina ka ganshi?" "anan gaban shago na ya rike wata yarinya datasai ma wata yar baby ruwa yanace mata Eesha wai sutafi gida" ahankali Yusuf yace "Eesha kace?" "eh haka naji yanata kiranta nidai" "to yanzu ina suke" "Naga tagudu yabita chan sukayi" Ya nunamai hanyar dasuka bi da gudu Yusuf yabi hanyar da aka nunamai hankalinshi atashe. Akarshen layin Yusuf yaganshi ya zauna akan wani dakali ya rike kanshi, karasawa wajen Yusuf yayi ya daura hanunshi akan kafadar shi, dago kai yay ya kalli Yusuf da idanunshi dasukai jajir, zama Yusuf yay kusa dashi ahankali yace "Khaleel wat is d matter?" murmushi yay mai ciwo yace "yau naga wata da ta tunamin da Eesha, for a second I tot she was my Eesha, yanda Eesha ke tafiya haka yarinyar ke tafiya" shiru yadanyi kafin yafuzar da iska yace "I think am loosing my mind" hanunshi Yusuf yarike gam ya girgizamai kai Yace "Khaleel Eesha tariga ta rasu bazata taba dawowa ba, and inhar son dakake mata is real kamata yayi kadawo normal kai kaman yanda kake da, kazaci inda Aisha na nan she will be happy da yanda kadawo ne? Bakama mutane magana, bakacin abinci kullum kana daki Ammin ka kullum saita kira Umma kusan 5 times tana tambayan jikin ka, duk ka rikita gabaki dayan family mu is that fair do you think Aisha zatai murna dajin labarin nan?" shiru yayi kawai yana kallon Yusuf, tashi Yusuf yayi daga dakalin yace" mutafi "ahankali ya sauko daga dakalin waigawa yasake yi kafin yajuya sutafi. "Islam, Islam" ahankali ta bude ido, wata yar budurwa ce wacce suke kai daya da Islam tana sanye da doguwar rigar atampa ja take tashin ta, yatsine fuska tayi cikin muryan bacci tace "uhnnn wat Farida" yaye bargon data lulube dashi Farida tayi tace "kitashi" juyawa tayi ta kife cikin muryan bacci tace "leave me aloneeee" tsaki Farida tayi tahau up bonk dinta ta kwanta abinta, tsaki tasakeyi tace "Islam" shiru tamata bata amsaba, hakan yasa tai kwafa tace "okay o dama Anty Hindu ne tazo kinsan ta very well" zabura tayi ta tashi ta zauna ware manyan idanunta tayi, leko dakai Farida tayi daga sama ganin ta tashi ta zauna yasa tai dariya, juyo dakai tayi ta kalli Farida hannu tasa ta dafe goshinta tace "Faree please da gaske tazo?" gyada mata kai Farida tayi, da sauri ta tashi gaban wardrobe taje zaro wani abayan ta baki tadaura akan dan singlet din dake jikinta ta wuce tafita daga dakin. [6/11, 9:19 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 13... Juyowa kakkyawar matar tayi tace "Islam yaushe kika tashi Farida tacemin kanki na ciwo sannu ko, kinsha magani?" Gyada mata kai tayi sanan takara matsowa kusa da Mum tai wani kini kini da fuska kaman zatai kuka da murya chan kasa dan tasan Allah yama Anty Hindu baiwar kunne tace "Mum wai mesa tazone, yanzu dukzata damu mutane da masifa" murmushi kawai Mum tayi ta girgiza kai tana arranging abincin a babban tray mai kyau tace "yayar mahaifin nakine kike cewa haka akanta ko yaran zamani, matsamin kiga na wuce jekiyi salla" fita Mum tayi ta barta a kitchen din, fitowa tayi takoma sama tana shiga daki Farida ta fashe da dariya tace "our Baba sister don land again" tsaki Islam tayi tana balle boturan abayan datasa Farida tace "wlh ko yau datazo jinayi kaman inyi kuka shikenan yanzu mun shiga uku" abayan Islam ta wurga akan gado tai hanyar bathroom Farida tace "Islam wai dan Allah mesa Anty Hindu batason muna kiranta dawani suna kaman irin su Mama, Inna ko Goggo tunda dai yayar daddyn muce amma saidai muce Anty Hindu" hararan ta Islam tayi tace "go and ask her" tabude bathroom tashiga batare data karabin takan taba, daga murya Farida tayi tace "okay nikikema iskanci ko next time bazan rufamiki asiri ba wlh" daga bayi tadaga murya tace "eh karkiyi din" dariya Farida tayi dan tasan abinda zatayi. wanka tayi tareda dauro alwala tazo tai sallan magrib sanan ta kalli Farida dake daddana waya tace "Daddy is back zomuje muyi dinner" sakkowa Farida tayi suka sauka kasa, afalo aka zazzauna yara mazane manya guda uku biyu manya sai karami da bazai wuce 5 years ba akan cinyar Daddy duk ana zaune anacin abinci, gaishe da Daddy sukayi ya amsa musu sanan suka zauna kusa da Mumy, rice ta zuba a plate da pepper soup na goat meat, spoon tasa a abincin tanata wasa dashi takasaci tunanin abinda yafaru yau kawai take, tunda ta sakko Daddy ke lura da ita, dan gyara murya yayi yace "Islam" da sauri ta dago kai ta kalli Dad ahankali tace "Na'am Daddy" "meke damunki?" murmushi tayi da sauri ta girgiza kai tace "bakomi Daddy kaina ke ciwo har yanzu" Yayan ta Abdallah dake gefenta mai kimanin 25 years ne ya kalleta yace "kinsha magani?" gyadamai kai tayi, murmushi yamata yace "eat to ko kadanne" rice din tadebo takai baki tafaraci. A massallaci suka fara tsayawa sukai magrib sanan suka wuto gida. Part dinsu suka wuce, direct bayi ya shiga yay wanka yafito sanye da bathrobe white ajikinshi ganin Yusuf baya dakin hakan yasa ya zauna akan kujera lumshe ido yay nayan sakkanni da sauri ya bude tareda fuzar da iska tashi yayi yaje gaban wardope ya canza zuwa milk color jallabiya, tsayawa yayi agaban madubi yadau turare a fesa, wayar shi yagani dake jikin madubi hakanan yaji yanaso yakira Ammin shi, daukar wayar yayi yakoma kan kujera ya zauna yay dailing number Ammi ba karamin mamaki Ammi tayiba dataga kiranshi na shigowa ba, ringing biyu ta dauka cike da murna tace "Son" har cikin ranshi yaji wani irin natsuwa, ahankali yace "Ammina I missed you" share hawayen daya zuboma Ammi tayi da sauri azuciyar tako godiya takema Allah, Allah na godema daka amsa addu'a ta, ya Allah kadawo mai da farin ciki da walwalan shi back, ka bashi mace tagari wacce zata maye gurbin Aisha. "Ammina are you there" da sauri yace "yes Son, ya kake hope kanacin abinci sosai ko" Ahankali yace "eh" murmushi sosai tayi tace "are you okay" shiru yayi baice komiba cikin wani irin muryan lallashin yaro tace "how about tomorrow kayi your two fevorite thing, read your Quran, and kaje ka buga kwallo ko kaje stadium ka kalli kallo anyone dakayi is okay" murmushi mai kara yay tunawa da dafa Ammin ce ke masifa duk idan yaje kwallo, murmushi yasake yi yace "okay Ammi bari naje nai salla" katse wayar yayi yatashi yafita dan zuwa massallaci. Washegari da safe yadade yana karatun AL qur'ani da muryar shi mai dadi, sai wajen 9 yarufe ya ijiye haka nan yaji kaman ancire mai wani nauyi dake damunshi arai, yajuya ya kalli Yusuf dake bacci abinshi, bathroom ya shiga yay wanka yafito ya shirya cikin brown shirt, short sleeve ne hanun rigar ya kama muscle dinshi hakan yakara bayana girman muscles din, dogon black jeans yasa dayamai kyau sosai ya dauko turaren shi ya fesa, ya zira takalmin shi Prada, agogon da Eesha ta bashi ya dauka daga gaban mirror, shafa agogon yayi yay shiru yana kallonshi, ahankali ya daura ahannun shi sanan yadau car key dinshi da waya yay hanyar fita daga dakin, da Goggo yacikaro tana dauke da tray hakan yasa ya karba tace "ina zaka haka?" komawa dakin yay da tray din tana biye dashi abaya yace "inaso nai aski ne" washe hakora tayi danba karamin dadi tajiba tace "toai saikayi break ko, kaga dakaina fa a hadama, ina Yusufa" muryan Yusuf sukaji daga bedroom cikin bacci yace "tsohuwar nan kidena batama mutum suna, niba Yusufa aka yanka rago aka samin ba" hanyar bedroom din Goggo tayi tace "uwar kace tsohuwa, katambayi Sama'ilan koni saida na yanka maka rago da aka haifeka" da sauri Yusuf yaja bargo ya rufe kanshi jin ta shigo bedroom din, duddu Goggo ta zubamai Abaya tace "dan kan uba" ihu sosai Yusuf yayi abin yabama Khaleel dariya, cup din shayin ya ijiye yadau one slice bread ya shafa cheese spread dake dakinsu yaci, da tissue ya share baki yay murmushi jin Goggo da Yusuf nata daru yadau wallet dinshi yasa a aljihun bayan wandon shi yafita daga dakin. Wani babban barbing saloon yaje aka mai aski da gyaran fuska ba karamin kyau yayiba sanan yabiya kudin yabar shagon, ganin he is running out of fuel gashi baida enough cash atare dashi yasa yay parking agaban wani ATM ganin akwai 2 people infront of him yasa ya tsaya ya jingina da motar shi yana kallon titi, ihu yaji hakan yasa ya juya da sauri, wata yarinya yagani ta fashe da kuka tana nuna wani guy dake gudu ga jakar ta a hanunshi tana cewa barawo ya kwacemin jakana. [6/11, 9:19 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 14... Tashi tayi tazo gabanshi da sauri, hawayen dake zubo mata ta share cikin muryan kuka tace "please help, ya kwance min jakana, credentials dina and everything are inside" baice mata komiba ya koma cikin mota ya kunna motar yabi guy din daketa gudu yana kokarin shiga wani layi gaban shi yasha da mota ya fito da sauri Guy din yajuya zai kara guduwa, taku biyu yay ya riko guy din ranshi abace da daga hannu zai wanka mai mari da sauri yaron yabashi jakar yace "dan Allah mallam kayakuri wlh yunwa yasa nai hakan, kayakuri dan darajan Allah" shiru yayi dan yaron yabashi tausayi duka duka bazai wuce 22 ba, anatse yace "idan kanajin yunwa kamata yayi kaje kafita ka nemi aiki kasamu kaci abinci stealing daukar abun wasu ba kyau, hakki zai bika" wallet dinshi yaciro daga aljihun bayan wando ragowan cash din dayake dashi yaciro yabashi sanan yabashi card din Abba yace "kaje address din company nan zansa abaka aiki kaji" tsugunnawa yayi yaron yanamai godiya murmushi yamai yace "tashi katafi don't worry" daidai lokacin ta iso wajen dan tun dazu take tsaye tana kallon abinda yafaru. Tafiya yaron yayi shikuma Khaleel ya mika mata jakar tareda bude mota ya shiga, yana kokarin tada motar ne tace "thank you so much, am grateful, ammm by the way am Farida Maikano and you?" dago kanshi yayi ya kalleta sai alokacin ma ya lura da fuskarta black beauty ce yarinyar tana sanye da doguwar riga na lace orange dakeda rantsin baki, ta yana black gyale akanta, murmushi tasake mai tace "u really help me wlh credentials dina duka suna ciki nagode ko" murmushi yadan mata batare dayace komiba ya kunna motar zai tafi da sauri takara matsowa jikin motar kaman zatai kuka tace "baka fadamin name dinka ba and u are going is dat fair?" murmushi yasake mata ganin yanda takeda surutu sai ta tunamai da Ihsan ahankali yace "just call me MK" kaman mai tunanin tace "MK, MK Mk?" tasake kallonshi alamu tambaya ahankali yace "zaki iya kirana Muhammad" murmushi tamai tace "wow MK nafiso, Muhammad na tsofaffi ne" murmushi yasake yi dan dukta cikashi da surutu yace "bye" girgiza kai tayi tace "please dan tsaya kaji dan Allah" Jakarta ta bude taciro wani memo ta rubuta number ta da sauri ta yagi paper ta mikamai tace "please please ka kirani this is my number kaji, dan Allah" ajiye mai tayi ajikinshi ganin yaki miko hanunshi sanan tamai bye, tafiya yayi haka tabi motar da kallo baki abude saida motar yabace sanan tace "gosh he's so handsome, jibi muscles dinshi bumbum, awwwn my superman" Ta wani lumshe ido. [6/12, 1:16 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 15 &16 ATM gallery din yakoma yaciro cash sanan yawuce gida. Wuraren 4 suka shigo gidan, dawani irin gudu Farida taje ta fada jikin Mum tace "oyoyo Mummy na mundawo" murmushi Mum tayi tace "wanan murnan na lafiya ne" ta kalli Islam dake kokarin bude bottle water tasha dan kishi takeji tace "Ya school din Islam hope kunbama Olayinka credentials dinku danace" gyada mata kai Islam tayi sanan takafa goran abaki, tashi daga jikin Mum Farida tayi tace "Mum yunwa nakeji sosai" tai hanyar kitchen taji andaka mata tsawa "my friend will you leave there! wuce sama kije kafara wanka ki canza kayan jikin ki kafin kinemi abinci, yara duk anbi anbata su" takarashe maganan tana huhhura hanci tana kallon Mum dako daga kai batayi ba, saima marking scripts din dake gabanta da takeyi, turo baki Farida tayi ta juyo tai stairs hakama Islam tabi bayan ta sum sum sukazo suka wuce ta sukai dakinsu. Dakinsu suka shiga duk ransu abace, suka zauna akan gado, murmushi Farida tayi tafada jikin Islam tace "no Anty Hindun nan bazan bari tai running mood dina yauba am so so happy" baki a sake Islam ke kallonta irin lafiyan ki lau, dariya tayi sosai sanan tasa hannu ta Fizgo Islam suka fada kan gadon a kwance tace "Islam yau I met my superman, wlh Islam yanada mugun kirki, kinsan nasauka daga mota a bakin ATM ba ke Bala ya wuce dake school ba, shine fa bayan naciro kudi wani barawo ya fizge jakana ya gudu, haba saiga giant huge gallant superman dina ya kwatomin jakan, and ko, baima barawon komiba saima kyauta dayamai ya bashi card wai yazo address din zai bashi aiki" ajiyar zuciya ta sauke tace "Sis kingan shi wlh kyakkyawane sosai, black arab, gashida kirki, he is so cute" ba karamin mamaki abin yabama Islam ba tace "Auwal dinki fa Faree?" tsaki taja tace "please karki karamin maganan shi nidai" murmushi tasake yi sanan ta bude ido ta kalli Islam daketa kallonta cike da mamaki tace "gist me jor dazu ina hall Fahad yakirani wai yanaso yazo gida kin hanashi, mesa kika hanashi yazo yaga Dad?" kaman zatai kuka ta tashi tana zage zip din sket din dake jikinta na material tace "kinga Anty Hindu tazo banason anything dazaisa tasani agaba wlh banason masifar ta" da sauri Farida tace "to shikenan saiki hanashi zuwa?" turo baki tayi batace komiba ta zame sket din ta ninke, tashi Farida tayi tace "shikenan karki gayamin gaskiya zurfin ciki saiya miki illa wataran" tai hanyar bayi da sauri ta rike hanunta hawayen datake kokarin boyewa ne yadan zubo da sauri ta share cike da damuwa Farida tace "talk to me Islam" ahankali ta zauna abakin gado tissue ta dauko ta share fuskar ta sanan tace "yasami wani job offer ne a Dubai kuma in two months time akace yay resuming yafara aiki, shine yake damuna yanaso yazo gida ya gaida su Dad, shiwai so yake muyi aure yatafi dani chan, so yake ai auren nan da 2 months, and because nace karyazo shine yaketa fushi jiya ko kirana baiyiba text kawai yamin jiya wai yatafi Abuja yin some papers zai dawo ran monday" "and all this while baki fadamin ba kikai shiru tun jiya nake lura dake kaman abu nadamin ki nadaiyi shiru, wai mesa kike hakane why are you my sister idan nima zaki dingamin zurfin cikine" girgiza kai tayi ahankali tace "am sorry Faree bansan tayaya zan fara fadan miki bane" hugging dinta Farida tayi ta shafa kanta tace "stop crying" share fuskan tayi sanan ta saketa ahankali tace "tun muna SS3 kuke soyayya da Fahad, baki taba bari yazo gidaba kibarshi yazo yaga Dad koma mezai faru ya faru" girgiza kai tayi tace "yanzu fa muka fara University sai kawai nai maganan aure, Anty Hindu da Dad zasuce dama aure nakeso maisa nabari ya kashe min kudi a school, am scared" tureta Farida tayi tace "banza kekika sani sabida tsoro zakije kiyi asaran love dinki, bari naje I will tell mum" tai hanyar kofa da sauri Islam tarike mata hannu tace "dan Allah karki fadama Mum, we will sort it out ran monday idan ya dawo, zance yafara aikin tukunna nan gaba sai muyi auren" sosai ta mugun bama Farida tausayi hakan yasa tace "okay shikenan amma karki bari abin yaja muku matsala" gyada mata kai tayi tadanyi murmushi sanan ta wuce bathroom da gudu jin Anty Hindu ta kwalla musu kira. Tun jiya da daddare duk ringing din da wayar ta zaiyi da gudu take dubawa taga ko bakuwar number ne amma duk wayanda tasani ne, babu sallan dazatayi da bazatai addu'a Allah yasa ya kirata ba, ko bayi zata shiga wayar na hanunta dan Karya kira yaga baa dagaba. Koyau da safe data tashi saida tai mafarkin shi hakan yasa tana bude ido ta duba wayarta bataga any miss call ba tsaki taja duk ranta adagule. Batai niyyar zuwa Saturday lecture da aka samusu ba amma sabida yanda duk taji batajin dadin komi ne yasa ta tashi tai wanka ta shirya cikin wani brown Abaya da aka bishi da stones ba karamin kyau yamata ba gyale ta yana akai Islam dake nannade cikin bargo tace "ina zaki?" turare ta fesa sanan tadau jaka ta kalli Islam tace "inada Saturday lecture ne, bye baby girl" ahankali Islam tace "bye" tafita tayi dakin Mum ta shiga tamata sallama sanan tafito Bala driver ne ya dauketa suka fita, jakar ta tabude tasake ciro wayar ganin har yanzu babu miss call yasa ta ijiye wayar akan cinyar ta ta dafe kai dan bakaramin daci taji zuciyar ta namata ba, sun kusa kaiwa school ta tuna bata dauko calculator ba sabida bakin ciki gashi calculation course zasuyi hakan yasa tacema Bala "malam Bala please danyi parking agaban super market dinan bari nasiyo abu" gaban wani babban super market Bala yay parking purse dinta da waya kawai ta riko tafito ta shiga ciki, bangaren littatafai taje nan taga calculator ta dauka, wajajen su ice-cream tayi tadanyi tsaki maybe zata dan rage zafi da ice-cream din, fridge din tabude ta ciro ice-cream ta juyo zata tafi wajen biya kaman ance ta daga kai ta hango Khaleel tareda Yusuf sunci sky blue shadda gizna da aka musu dinki half jumper ga wata hula kube sun kafa akai sai kace zasuje biki suna kwasan su snacks da littafi dan zasuje ma Fa'iza visit a boarding school ne. Wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar ta ajiye abubuwan tayi a kanta din accounter tace "am coming" da sauri tai wajen su da murmushi akan fuskarta tace "Hi MK" Yusuf ne yafara juyowa saikuma Khaleel daya dago kai ya kalleta yana kokarin tuna fuskar, kamar zatai kuka ta kalli Khaleel tace "shine baka is kirani bako MK" sai alokacin ya tunata, dan murmushi yay yace "how you?" har cikin ranta takejin muryar shi da yanda yay maganan tace "fine" Yusuf ta kalla sanan ta kalli Khaleel din tace "dan uwanka neko" gyada mata kai yayi Yusuf ta kalla tace "ina yini" cikeda fara'a yace "Lpy Lau sis, yasu Mum nd Dad" purse din hanunta taketa wasa da igiyan sanan tace "suna lpy" dan kallon Khaleel dake kokarin dauko gwangwanin Milo tayi tace "shine baka kirani bako MK" ajiye milon yay a cart sanan yace "sorry battery na was flat jiya ne saisa" murmushi tamai har cikin zuciya sanan tace "okay" Yusuf ne yace "how about nabaki number shi dan ya iya mantuwa kina ganinshi haka, incase ya manta baikirakiba sai kimai flashing ko" kama rigar Yusuf yayi tabaya yanda bazatai ganiba hanunshi Yusuf ya bige ya shiga karanto mata number tana saving sanan ta kallesu tace "okay kayana nachan bye" ta daga musu hannu cike da fara'a, bye suka mata sanan tawuce tatafi, turashi Yusuf yayi yace "at least be a gentle man kabiya mata kudin abinda tasiya" zaiyi magana Yusuf yakara tureshi hakan yasa yajuya yatafi badan son ranshi ba, murmushi Yusuf yay ya dunkule hannu ya saki a iska yace "yess". ATM card taciro tana shirin biya da POS ya mika nashi, ahankali ta kalli gefenta ganin shine yasa wani dadi ya lullubeta, samata akai a leda aka bata ta karba sanan ta juyo cike da dan kunya tace "thank you, am going to school karnai latti, bye" hannu yadaga mata yana mata calm murmushi dake melting heart tai hanyar fita security ya bude mata kofan. [6/12, 1:16 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 17... Hararan shi Yusuf yayi daya dawo yace "shine ko abani labari, who is she?" dan yatsine fuska yayi yace "a girl I met yesterday" da sauri Yusuf yace "and??" tsayawa da tafiya Khaleel yayi ya kalleshi yace "and wat, nace jiya muka hadu I just helped her out ne da wani guy ya kwace jakarta shikenan" murmushi Yusuf yay suka cigaba da tafiya chan yace "she is nice" ahankali yace "yea ga shegen surutu ba" dariya Yusuf yayi batare daya kara cewa komiba sukaje suka biya kudin kayan sanan suka wuce school dinsu Faiza. Tsabagen farin cikin daya mamaye zuciyar ta batamasan me aketayi a class ba dan murmushi kawai take tana kara kallon special number Khaleel datai saving da my superman. Haka tai wasting 4 hours lecture dinan tunanin Khaleel barinma yanda yawani zo ya mika ATM card yabiya kudin nanne yafi tsumata. Koda daddare Islam bacci tayi ta barta ido biyu sabida jira take Khaleel ya kirata ganin har 11 bai kirata ba yasa ta dialing number shi har tagama ringing bai dauka ba, sake kira tayi nanma bai daukaba wani iri taji sosai ahankali ta ijiye wayar taja bargo ta kwanta ta rufe ido da kyar bacci ya dauketa. "Goggo jikan ki yay kawa fa" ajiye maficin datake fifita musu wani dan kasko data daura ruwan shayi akai anan tsakiyar falon ta tayi tace "kai da gaske Yusufa" kallon Khaleel dayay kaman bejishi ba yayi yace "gashi nan ki tambaye shi, wlh Goggo yarinyar badai hankali ba, ai in sha Allah watarana zan kawo miki ita ki ganta" sosai Goggo taji dadi, batace komiba ta sauke shayin daketa uban kamshi ta zuzzuba musu a cup, dauka yayi yay sipping kadan sanan ya ijiye saida yadanyi sanyi sanan ya dauka ya shanye ya goge baki ya tashi ya Kalli Yusuf yace "zanje Gym" kafin Goggo takirashi yafita daga dakin da sauri dan bayason surutun su, part dinsu ya wuce ya shirya cikin kayan gym, wata gym singlet ne dake kama jiki mai ruwan toka tadan budemai kirji sosai yasaka, sai dogon wandon shimin, yasa sport shoe na Nike, yadau wani dan madaidaicin towel ya daura akafada yadau car key da wayar shi, da sport bottle dake cike da warm water na glucose and lime yafita. "ke Farida, Farida, wai bataji nane" tana zaune a dining itada Islam suna hira taji Anty Hindu na kwala mata kiran nan kaman ana yaki, da sauri ta tashi tana amsawa, sama tayi tai sallama tabude dakin Anty Hindu dake zaune da Dad suna magana, kudi Anty Hindu ta mika mata tace "ki kira bala ya kaiki inda nake siyo fruit a kasuwa yasan wajen kisiyo, babu fruits agidannan yau" karban kudin tayi tajuya tafita daga dakin, dayake tariga tai wanka tunda sassafe yasa Hijab dinta kawai ta dauko da wayarta ta sakko, dining tazo tasami Islam na taya Mum yanka kubewa ta kalli Mum tace "Mumy Anty Hindu ta aikeni kasuwa plz Islam tarakani" Mum ta kalli Islam tace "zaki?" gyada kai tayi "tashi kutafi to, amma kuyi sauri" da gudu Islam tai sama Hijab ta dauko milk daya kai mata gwuiwa tadaura akan atampa dayake jikinta tabita suka fita waje bala ya dauke su suka tafi. Suna zaune a motar takara dailing number Khaleel saida wayar ta kusa katsewa ya dauka, ajiyar zuciya ta sauke mai kara har saida Islam ta kalleta, dawani irin calm voice tace "good morning Mk" ahankali yace "ya kk" murmushi tayi daya bayyana fararen hakoran ta tace "Alhamdulillah" "gud" yafada tareda yin shiru itama shiru tayi, hayaniyar dataji ata bangaren shi ne yasa tace "ina kake haka da ake hayaniya sosai?" wlh kawai dan bayason wulakanci ne saisa amma dis girl is really disturbing him, kaman bazaiyi magana ba chan dai yace "gym" da sauri tace "wani gym?" shiru yayi hakan yasa ta kalli wayar ganin yana kan line har yanzu yasa ta mayar kunne tace "hello are you there" batare daya amsa ba yace "infinity gym, bye gat to go now" Ya katse wayar. Bala ta kalla tace "dan Allah Bala dan kaini infinity gym" da sauri Islam ta kalleta tace "ba kasuwa aka aikemu ba" yarfe hannu sama tayi tace "dalla forget kasuwa, I wanna see my superman face tukun" tabe baki Islam tayi ta juya ta cigaba da kallon hanya, agaban wani babban building da aka rubuta infinity gym ajiki bala yay parking. Hannu Islam ta daura akan kirjinta sabida yanda taji yana bugawa. [6/13, 8:48 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 18... Bude motar Farida tayi ta zagayo ta bangaren Islam ta bude kofar tace "zomuje ku gaisa da superman dina" girgiza kai Islam tayi tace "sabida Anty Hindu ta hadamu ta mana rashin mutunci ko, nidai ban kudin Bala ya kaini na siyo" wani dadi ne ya kama Farida takama kumatun Islam taja sanan tamata peck tace "luv u Islam dina, idan kun siyo ko, kubiyo ku daukeni saimu koma tare" karban kudin Islam tayi tareda mata murmushi taja kofan motar ta rufe sanan ta kalli Farida yanda take washe baki yasa tace "at least adan rufe bakin ko ta superman" murguda baki tayi sanan tajuya security dake bakin wajen ya budemata ta shiga tana waige waige, babban wajene da sanyin ac ya cika ko ina, bangare daya gym ne sai dayan bangaren da ake saida any type of fruit salad da smoothies and fresh veggies da coffee. Waige waige tadinga dan wajen da dan mutane ga wani calm music dake tashi kadan kadan, hangoshi tayi akan treadmill machine yana gudu, karasawa wajen tayi ta zaga ta gabanshi ta tsaya ahankali tace "good morning Mk" saida yadanji tsoro daya ganta agaban shi kaman anjehota daga sama, wanan wace irin yarinya ne, murmushi kawai yamata batare dayace komiba yacigaba da gudu abinshi, wasa takama yi da bakin hijabin ta fuskar ta yay wani iri, yanda take wasa da bakin hijabin saiya tunamai da Eesha, ahankali yasa hannu ya kashe machine din sanan yadau towel dake kan kafadar shi ya share zufan dayayi sanan ya sakko yadan wuce ta ya dauko dumbell yadawo ya zauna akan kujera, kujeran dake kusa dashi ya nuna mata yace "sit" murmushi tamai ta zauna shikuma yacigaba da daga dumbell din da hannu, baki tasaki a bude ganin yanda jijiyoyin muscles dinshi ke tashi. Ajiye dumbbell din yayi akasa ganin yanda ta kafeshi da ido kaman zata hadiye shi yay folding hanunshi a kirji yana kallonta wani irin kunya taji hakan yasa ta kawad da kanta tace "dama nazo na gaishe kane kawai, naji kace you are here and I know dis place very well" murmushi kawai yamata batare dayace komiba yadau bottle dinshi yabude yana shan ruwan tace "Mk wai mesa bakason min magana ne?" cire bottle din yayi daga bakin shi da sauri ya kalleta, murmushi tasake yi tace "kagani bakason yima mutum magana, tell me about your sef to, kaman family, career and everything about you, I wanna know u more" wani waiter ne yazo wucewa yakira shi yazo sanan ya kalleta yace "me kikeso aka wo miki" wani irin dadi ne ya lullubeta tawani langabe kai kaman baby tace "anything of your choice" maida duban shi ga waiter yayi yace "bring one avocado smoothie and one strawberry smoothie" juyawa waiter yayi yatafi ganin yana daddana wayarshi kirar IPhone Xmas yasa tai wani iri kaman zatai kuka tace "Mk" dago kai yay ya kalleta tace "tunda you don't wanna go first ni I will tell you about my self" ajiye wayar yay daidai lokacin waiter yakawo musu smoothies din a wasu cups masu kyau da straw aciki, daukan na strawberry yayi yabata shikuma yadau na avocado, wani irin murmushi tayi tace "yamasan fevorite dina" kaiwa bakinshi yayi ya zuko kadan sanan ya kalleta ganin shi take kallo yasa yace "am listening" wani dadi ne yakamata tana mugun son yanda bakinshi keyi idan yana magana, ajiye smoothie tayi akan tray sanan tace "my family name is maikano, Babana dan asalin Fulanin nan yola ne, yanada one sister yayar shice amma, mai suna Anty Hindu, Anty Hindu Allah yay mata baiwar masifa, abinda ma yarabata da mijinta kenan bata taba haihuwa ba. So daddy na nada two wives but tafarkon yanzu she is late, tarasu lokacin I think I was either 13 ko14 years old, yara biyu ta haifan ma baban mu Yaya Abdallah wanda yanzu yagama mechanical engineering yayi applying short service na soja, yama samu yanzu haka yana can kaduna suna training, sai yarta tabiyu mai suna Islam wacce muke age mate" murmushi tasake mai ganin yay paying attention yana jinta tace "amma fa na girmi Islam dinfa ni kaga an haifeni March itakuma December but the same year kagani ai na rigata shan iskan duniya ko?" gyada mata kai yayi, tace "mum dina itace second wife we are three, yayana Ibrahim yanzu yana hostel a zaria dan ABU yakeyi, saini saikuma my 5 year old brother mai suna Sameer yana basic 1 yanzu, so My mum ita tai training dinmu dukan mu ta lura damu sabida Mumyn Islam was always sick sikla ce, thank god Islam da yaya Abdallah ba sicla bane suba, anata fita da ita abroad ana mata magani" shiru tadanyi ahankali yace "sorry Allah jikanta" murmushi tamai tace "Ameen, so tareda Islam muka taso tundaga nursery ajinmu daya saiyanzu damuka shiga University ne nake Mass com ita kuma tana Home economics, kasan difference dinmu? Ni am free minded, am very free and friendly, Islam is friendly oo idan tasaba dakai but tanada zurfin ciki, she is my only friend and sister and am her only friend and sister, I love her so much and she loves me so much, my mum yar yola ce itama fulani, tana aiki lecturer ce anan AUN, tana koyar da yan food and nutrition, Mumyn Islam kuma yar Sudan ce daga chan dadyn mu ya aurota. So this is my story tell me yours" murmushi yamata daidai lokacin wayarta yay ringing, ganin Islam ne yasa tai picking "okay tace" fuskarta ya nuna alamun rashin jin dadi ahankali tace "I have to go su Islam na waje sunzu daukana, bye but next time is your turn u will have to tell me about yourself and your family too" murmushi yamata yace "okay" harta fara tafiya ta dawo da sauri tawani langabe mai kai tace "bazama karakani ba?" wayarshi ya dauka ya ijiye cup din smoothie dake hanunshi yace "okay" ita ke gaba yana biye da ita abaya. [6/13, 8:48 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 19 & 20 Harsuka kai wajen kofa security ya bude musu sosai yaji kirjin shi yabuga hakan yasa ya tsaya tareda shafa wuyanshi, waigowa tayi ta kallai tace "why did you stop bazaka zo ku gaisa da Islam ba?" murmushi yamata ya girgiza kai yace "nah, next time ma gaisa bye" bye tamai yajuya yatafi, ahankali tajuya tafita cike da farin ciki ta bude mota ta shiga Bala yaja sukabar wajen. Cikin gida suka shiga Bala kuma yabiyo su da fruits, da Miemie taci karo a falo tanata wasa da toys din Sameer da gudu Islam ta dauketa ta shillarata sama tana mata wasa, Farida Kuma ta wuce sama dan kaima Anty Hindu sakkon ta. Daukar Miemie tayi ta wuce kitchen Mum da Maman Miemie ne suna yanka nama gaidasu tayi tareda cire hijab ta ijiye akan kofa ta kalli Mum tace "mum ni zanyi" tashi Mum tayi tace "sarkin son aiki bari to na wanke hannu saina tafi da Miemie" hannu ta wanke a tap sanan tadau Miemie suka fita, naman tarike ma Maman Miemie suka dinga yankawa har suka gama, ta tayata suka gama hadadden girki tare, fried rice sukayi da pepper meat sai fruit juice dasuka hada suka jera a dining sanan Islam ta wuce sama dayin wanka. Wuraren 9 Farida ta tashi afirgice ta kalli agogo a rude tace "na shiga uku Islam shine baki tashe niba dan kinga yau bakuda lectures ko" bude ido Islam tayi cikin bacci tace "sorry nima bacci ne ya kwasheni bayan nagama azkar" daka mata duka Farida tayi abaya ta shige bayi da gudu, ihu Islam tayi tareda buga kafa ta rike bayanta tace "wlh kinci bashi saina rama" leko dakai Farida tayi ta kalleta tamata gwalo tace "kindai san baki da karfi ko I will break ur borns, ragagagga" pillow Islam ta dauka ta jefa mata hakan yasa ta fashe da dariya ta koma cikin bayin da sauri ta rufe kofa Islam ta daga murya tace "Allah sama kiyi latti muguwa kawai" dan bayanta har yanzu zafi yake mata Farida badai zafin hannu ba. (name ur friend dake da zafin hannu, hahah nidai Humi ne wlh😂). Agurguje tai wanka tafito ta tsaya agaban mirror tana shiryawa tana hango fuskar Islam yanda take turo baki, ajiye hodan hanunta tayi tawani zo ta rungume Islam tace "haba tawas sorry to daga wasa, wayyo nasan da zafi ko muga bayan" kokarin tabamata baya take hakan ya mugun bata dariya, dariya dukan su biyu sukahauyi, Islam ne tafara dakatawa tace "wai bazakisa kayaba sai kinyi latti" da gudu ta tashi taje gaban wardrobe ta dauko simple material tasa tadau gyale ta tsaya gaban madubi tana rolling tace "yau Fahad zaizo ko?" gyada kai tayi tace "eh yama dawo jiya wai, yace muhadu a quiks cafe bayan sallan la'asar" pin ta dauka ta kama gyalen sanan ta rataya bag tace "kici gayu sosai fa idan zaki, haka akema maza su haukace akanka, idan superman dina ya ganni har kasa magana yake sabida kyan dayake ga inamai wlh" tai wani fari da ido, kama baki Islam tayi tace "you with this ur superman Faree, wlh kinyi nisa" tace "Islam saima kin ganshi wlh black Arab ko inhar kinsansu he is just like one of them, anyways ki lallaba Fahad fa, idan kuma yaki yarda call me zanzo na same ku awurin na sasan taku u know am good at dat natafi kimin addu'a dan wlh tunanin superman yahanani yin karatu bansan komiba Allah" tabude kofa tafita, girgiza kai Islam tayi tace "Allah shiryeki, gud luck anyway". Tun kafin la'asar tazo ta shiga wanka ta dauro alwala tafito, jin ana kiran sallan la'asar yasa ta shimfida dadduma tai salla. Bayan ta idar ne ta zauna agaban mirror ta tsantsara kwalliyar ta very light hoda ta shafa tasaka kwalli daya kara bayyana hasken idanunta, sanan ta gyara giranta da brush haka nan taji tanajin sa jan baki, red janbaki ta dauko tasa hakan yakara fito da kyan fuskarta leben yakara kankancewa kaman na jaririya, body splash da body spray ta dauko ta fesa sanan taje gaban wardrobe ta tsaya tana tunanin kayan dazata saka wani black lace dinta dake dauke da small small design din red flowers ta dauko doguwar riga akama dinkin A-Shape, sanya kayan tayi ba karamin kyau yamata ba yafito da shape dinta sosai, gaban madubi ta koma tadau brush tai brushing dogon gashinta dashi sanan takama da ribon ta nannade ta cusa a tsakiyar ribon din, jan plain gyale ta dauko mara stone ta yafa tadau flat takalmin ta channel mai igiya ta baya shima red ba karamin kyau baki da ja dressing din yamata ba, phone dinta kawai ta dauka da dan karamin coin purse dinta tarike, humuran da xoxo ta hadamata ta tsiyaya ta shafa kadan a hanunta dan badai kamshi ba sanan tawuce tafita daga dakin, sanin Anty Hindu ne kadai agidan yasa tai sallama tabude kofa ta shiga dakinta, dan tsugunnawa tayi kadan tace "sannu da hutawa Anty Hindu" kallonta tayi daga sama har kasa tana hura hancin nan nata as usual tace "ina zaki ba kince anyi canceling lecture ku nayau ba?" gyada mata kai tayi tace "eh, dama zandan je gidan su yar ajinmu na karbo handout dina ne" saida Anty Hindu tagama nazarin ta sanan tanuna mata kan drawer tace "dauko car key dina na aiki Bala, kidaiyi tuki ahankali" murmushi tayi harda juya kai tace "thank you Anty Hindu" key ta dauko tafita daga dakin cike da murna. Gaban wata Toyota camry taje ta shiga kunnawa tayi taja motar cike da kwarewa mai gadi ya bude mata gate tafita abinta, 20 min yakaita quiks cafe parking tayi tafito tana takunnta daidai ta shiga, wani waiter ne yazo yace "are you Miss Islam Maikano?" gyadamai kai tayi yace "Mr Fahad yamuku reserving table please come with me" binshi tayi ya kaita wani hadadde table dake zagaye da kujeru biyu, zama tayi yace "meza akawo miki Hajiya?" girgiza mai kai tayi tace "don't worry inyazo" juyawa yayi yatafi, wayarta ta dauka tai dailing number Fahad bai daukaba harya katse, text dinshi ne ya shigo ta bude da sauri "princess am sorry please give me 20-30min Abba ne baida lpy muna hospital but yanzu nan zan fito nazo" reply tamai "Allah bashi lpy, take your time". Kunna data tayi ta shiga watsapp tana duba messages wanda yawanci na groups ne, ganin Khaleesat tai posting Noorul Huda yasa ta gyara zama tana karanatawa ba karamin dadi novel din kemata ba harta gama karanatawa baizo ba, agogo ta kalla taga biyar da rabi saura minti biyu, number shi tafito dashi zatai dailing message dinshi ya shigo tai maza ta bude "am sorry my luv bazan iya zuwaba, jikin Abba yay tsanani an kwantar damuma. Luv u" reply tamai "Allah yaba Abba lpy, please take care of him, Luv u 2" ta senda mai sanan tadau car key da purse tafito ta shiga mota tabar Cafe din, tadanyi tafiya mai nisa kafin ta shiga wani uban traffic dan tsaki tayi tasa hannu ta kunna radio. Hakanan yau yaji yanason yabuga kwallo hakan yasa ya shirya cikin jersey ya sanya takalmin kwallo yadau key mota yafita, yadanyi tafiya mai nisa dan stadium yakeson yaje yahadu da traffic dukan kujeran motar yay sabida haushi dan bayason afara bugawa bashi, kashe motar yayi ya bude yafito dan yaga maiya kawo traffic haka gashi ko moving motoci basayi, wata mota yagani babba tafadi gashi ankawo wata babbar mota dake daga mota ana kokarin cireta daga hanya sabida motoci su samu su wuce hakan yasa yadawo mota ya zauna, wani mai saida ayaba ne yazo ta bangaren glass din haggu yace "mallam ga ayaba sun nuna sosai gasu da shegen dadi" alamu yamai da hannu cewa bayaso hakan yasa mai ayaban ya wuce tareda barin jikin window hango Islam yayi tadaura waya a kunne tana magana, da sauri ya goge idanunshi sanan yasake kallon wajen, sosai yaji heart dinshi na racing kaman zai fita gani yayi ta ijiye wayar ta kunna motar ta tafi, wani wawan horn ya danna ma motar gabanshi ganin anfara tafiya, dawani irin mugun gudu yabi bayan motar Islam ganin tamai dan nisa, haka yadinga binta abaya hartakai layinsu, horn tayi agaban gate dinsu kusan sau uku gateman bai budeba hakan yasa tai parking ta bude kofa tafito daidai shima yay parking yafito daga motar shi, batama lura da motanba tadan duka ta mika hannu tadauko purse dinta dake kan sit ta maida kofar motar ta rufe ta juyo kadan yarage bata fada jikinshiba sabida yanda ya tsaya akusakusa da ita, atsorace ta jingina da motar tana kallon fuskar shi, wani irin kallonta yake kaman zai cinyeta, idanunshi data kalla yasa ta tuna fuskarshi a rude tace "innalillahi, wayyo Allahna, you again!" atsorace ta bangaje shi ta ruga da gudu ta bude gate din gidansu ta shiga, da gudu shima ya bude gate din yabita ciki. [6/13, 10:55 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 21 & 22 Kafin takai tsakiyar compound ya cimmata yasha gabanta, chak ta tsaya tana waige waige duk ta rude dan kar wani ya gansu barinma Anty Hindu, arude tahada hanunta biyu 🙏🏿 tace "dan Allah karabu dani, waikai ajjani ni" sosai idanunshi suka xhanza kala ga heart dinshi dake wani irin mugun racing yana duka fat fat fat, gabaki daya yanda take magana yasa yaji kanshi yafara juyawa, ahankali yakai hanunshi daya yadafe kan, da wata irin murya ya kalleta yace "are you my Eesha" girgiza mai kai tayi arude yace "then who are you? Mesa idan na ganki bana iya hakura?" sake girgiza mai kai tana waige waige tace "wlh ni ba wacce kake nema bane, plz go karka sani a wahala" cire hanunshi yayi daga kai yay folding hanun a kirji yana wani irin kallonta, sosai jikinta ke rawa tace "na shiga uku, mallam inkana ma Allah katafi karabu dani" ganin ko gezau baiyi ba har lokacin kuma ita yake kallo kaman wani sabon maye yasa tace "kaji dan Allah katafi bani bace wacce kake nema ba, wlh in aka ganni dakai anan yau na shiga uku" takarashe maganan tana yarfe hannu idanunta sun cicciko da hawaye, ajiyar zuciya ya sauke da muryarshi datai mugun rauni yace "please don't cry kinji" yay maganan kaman zaiyi kuka ahankali yace "naji zantafi but on one condition" ware ido tayi tana kallon shi, ajiyar zuciya yadan sauke sanan yace "gobe by 4 zanjiraki a bakin layin nan, magana nakeso muyi, inhar bakizo ba zan biyoki har gida" gyadamai kai tayi tana waige waige tace "eh na yarda, naji please katafi Abbana yakusa dawowa" kallon fuskar ta yay nayan sakkanni kaman mai nazarin wani abu ahankali ya tako zuwa gabanta da sauri ta matsa baya, kallon kwayar idonta yayi da sauri ta kawad dakai ganin ya cikamata ido, ahankali yace "please karki kara fita ahaka" yay maganan yana nuna gyalen data yafa, kaman mai rada yace "I don't like it" yanzu dai tayarda mutumin nan baida lpy me ruwan shi da gyalen ta, "bye" taga ya daga mata hannu, yana fadin haka yawuce ta gefen ta yafita daga gidan yana tafiyan nan kaman Boss. Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke ta dafa kirji, tafi minti 5 tsaye a inda take da kyar ta iya daga kafa tafara tafiya ta bude kofar falo ta shiga, hamdala tayi dataga babu kowa sadaf sadaf take tafiya harta kai dakinsu ta bude kofa ahankali dan bataso Anty Hindu ma taji tadawo. Gab da magrib Farida tashigo gidan a gajiye, Islam tace "Ya lectures yau, sannu yan mass com kunajin jiki" yatsine fuska tayi tace "ni wlh duk am not happy yau lectures yasani yau banga my superman ba" tabe baki Islam tayi tareda kwanciya ta lumshe ido dan har yanzu bata dawo daidai ba, wai wayeshi ne? tsaki tayi ta tashi ahankali tai bathroom dan dauro alwala. Atare da Farida yau duk suka tafi school dan itama tanada lectures yau. Wuraren 3 tagama lectures dinta Farida ta kira tace mata ta wuce ita bata gamaba hakan yasa tafara tafiya har tafito bakin gate, Keke napep takeson ta tare tahau. "Assalamu Alaikum my Princess" daukar mai muryan yasa ta juyo murmushi kwance akan fuskarta, wani dogon guy ne mai farar fata, yanada jiki ga saje daya yawaita a fuskar shi, ya sanya wani lallausan yadi brown sai kamshi yake, baki ta bude zatai magana ya girgiza mata kai yana hararan ta dawasa yace "karma kifaramin wanan dadin bakin naki, shall we" Ya nuna mata motar shi, murmushi kawai tayi ya bude mata gaba ta zauna sanan ya zaga ta dayan bangaren ya shiga ya zauna hakan yasa yace "Ya jikin Abba?" wani irin kallo yamata sanan yace "Alhamdulillah yaji sauki" shiru sukadan yi tana wasa da yatsa shikuma yana kallon dogayen yatsun ga fararen dogayen kumbunanta dake mugun birgeshi, jingina yay da kujera anatse ya kira sunan ta "Islam" dago kai tayi ta kallai ganin ita yake kallo yasa ta mayar da nata idanun kasa ajiyar zuciya ya sauke yace "mesa kika zabi azabtar da zuciyata sabida kinsan kece ke mulkata? Islam!" Yasake Kiran sunan ta dawani irin yanayi yace "nagaji inaso nai aure, niba yaro bane, banyi kokari ba tun kina secondary school fa muna tare, please my princess ki yarda naje nasami su Dad ayi finalizing everything kinji" ahankali tace "school dina fa" gyara zama yay ya fuskanceta yace "kina tunanin bazaki cigaba da school bane bayan kinsan yanda nakeson karatu eh princess" girgiza mai kai tayi yace "muna komawa chan zan nema miki University mai kyau kifara yi kinji My Islam" murmushi tamai sanan tace "tom amma please kabari nafara ma Mum maganar kaji" murmushi yamata yace "to naji rabin raina" yawani daga mata Gira, ahankali tace "Ya jikin Abba yaji sauki sosai?" "Alhamdulillah an sallamemu inama ajiye su agida nataho na ganki, I missed my princess so much" rufe fuskarta tayi da hannu sabida yanda yabata kunya, kunna motar yayi yana murmushi yafara tafiya fira sukeyi jefi jefi gwanin ban sha'awa yana shiga kwanar layinsu yay parking dan dama anan yasaba fakin bata bari yakai ta har kofar gidan su, tafito, daga mai hannu tayi shima haka yana wani murmushi jiyayi inama gidan su zasu haka saida yaga ta bude gate ta shiga sanan yatada motar yabar anguwan su. Maman Miemie da Anty Hindu tasamu a falo gaidasu tayi tawuce sama danyi wanka gashi ana Kiran sallan la'asar hakan yasa ta shiga bayi, muryan Farida dataji itama ta dawo yasa tai sauri tagama wankan ta dauro alwala tafito da saurin ta dan tabama Farida labarin yanda sukai da Fahad akan gadonta taga Farida ta kwanta tana bacci ko kaya bata cireba, murmushi kawai tayi ta girgiza kai tace "lazy gurl" gaban wardrobe taje dan pink rigar ta data kaimata har gwuiwa tasaka sanan tadau zani ta daura tasaka hijab tahau kan dadduma tai sallan la'asar. Koda ta idar sauka kasa tayi dan debo abinci, jellof rice ta debo da fried plantain tadawo sama ta zauna tanaci, ture kwanon gefe tayi ta daura kanta akan gado tana duba watsapp messages dinta. Sama da awa daya da rabi kenan yana bakin anguwan su dan ko la'asar ma anan masallacin bakin titin yayi, yana sanye cikin wani farin yadi mai kyau ya daura hula akai, agogon dake hanunshi wanda Eesha ta bashi ya kalla 5:25, kunna motar yayi yay kwana ya shigo anguwan nasu yay parking a kofar gidan su shiru yayi yakasa fitowa, toshi yanzu wama zaice yazo nema baima san sunan ta ba, yafi minti uku a zaune ganin zuciyarshi takasa hakura yasa ya fito ya rufe motar. Mai gadi dake zaune kan benci a kofar gidanne yataso da sauri dan yagane shi mutumin daya gani jiya da Islam ne lokacin daya fito daga kewaye, washe baki yayi yace "yallabai barka dazuwa, wajen hajiya kazone?" shiru yadanyi dan baigane wace Hajiya yake nufiba, zaiyi magana mai gadi yace "koba Kaine wanda nagani tareda hajiya jiya kasa kayan kwallo?" murmushi yamai yace "eh nine" mai gadi yace "to biyoni dan Alhaji yacemin na dinga kai baki cikin gida bayason yaran shi na tsayawa a waje" bai jira amsar Khaleel ba yabude gate ya shiga Khaleel yabi bayanshi har suka kai wajen kofar shiga dakin mai gadin ya juyo yace "bari nagaya musu" bude kofa yay ya shiga ciki Anty Hindu da Maman Miemie ne suke dan hira ya gaidasu yace "hajiya dama wanine yake neman hajiya Islam, gashi nan ma" zama Anty Hindu ta gyara tace "okay shigo dashi" fita mai gadin yay yace "ance kashigo" sosai yaji kirjinshi nabugawa ahankali yabude kofar ya shiga mataye biyu yagani Babbar daya gani wacce daga gani kasan tama girmi Ammin shi yadan duka kadan yace "ina yini Hajiya" murmushi Anty Hindu tayi tace "Lpy Lau" ta kalli Maman Miemie dake zaune gefenta tace "jeki kirata" ta kalli Khaleel dake tsaye har lokacin kanshi akasa dan wani irin kunya yaji yakamashi tanuna mai kujera tace "bismillah zauna mana" ahankali ya zauna itakuma ta bude newspapers dake kan table din gabanta ta cigaba da karanatawa. Bude kofar dakin tayi Islam dake gyangyadi ta shigo ta tabata tareda kiranta tace "Islam Islam" Farida cikin bacci tace "maman Miemie kuna damuna plzz" maganar Farida ne yatada Islam Maman Miemie tace "Anty Hindu na kiranki tana palo" da sauri ta mike tsaye, da dan gown dinan iya guiwa da gashin ta datai parking yana lilo tafito daga dakin, dayake daga sama Anty Hindu kadai zaka iya hangowa danshi yana kan kujeran dake ta ciki sakkowa tayi ta shigo falon kai tsaye tazo gaban Anty Hindu ahankali tace "gani Anty" rufe jaridar Anty Hindu tayi tace "banike neman kiba game neman kinan" ta nuna mata Khaleel da tunda ta shigo idanunshi ke kanta, juyowa tayi ganinshi yasa numfashin ta ya tsaya chak zazzaro idanu tayi tana kallon shi unbelievably, wawwaigawa tayi hijabin Maman Miemie data gani akan stool din dake kusa da Anty Hindu ta dauka da sauri ta saka dan juyawa tayi ta kalli fuskar Anty Hindu ganin ita take kallo yasa ta daburce cikin inda inda tace "uhnn dama dama" ta nunama Anty Hindu shi da hanunta tace "uhn, dama brother yar ajinmu ce, ta turoshi ne yakawo min note ko" ta kallai ware ido yay ya kalleta zaiyi magana tai sauri tace "yauwa ina note din data baka ka kawomin din?" kasa magana yayi dan baima san mezece fa, kara kallon Anty Hindu tayi ganin ita take kallo har yanzu yasa tace "ahhh yana mota? Muje na amsa saika tafi ko" tai hanyar fita daga dakin ahankali ya tashi ya kalli Anty Hindu yace "sai anjima Hajiya" murmushi tamai tace "daga zuwa ka tsaya kasha drinks mana" da sauri Islam tace "yana azumi ko, yau Monday" ta kalleshi gyada kai yayi yana dan murmushi, murmushi itama Anty Hindu tamai tace "to shikenan mun gode agaida su Mum" bude kofa Islam tayi tafito yabiyo ta abaya yana wani irin murmushi. [6/16, 8:26 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 23 & 24 Saida takai bakin gate sanan ta juyo ta kallai cikeda masifa tace "wai wat is ur problem with me ne eh? Dan Allah ka rabu dani" "I can't" yafada tareda folding hanunshi a kirji yana kallonta, kwafa tayi tace "okay shikenan duk randa nama kara saka ka a idona sainai reporting dinka to police station" dan murmushi yayi dan baiso tadena magana ba, ta gefenshi tazo zata wuce yariko bakin hijab dinta da sauri ta dawo tana waige waige ko akwai wani a tsakar gidan ta kalleshi tace "na shiga uku wanan wai kai dan Allah wani irin mutum ne, wlh wlh kaga na rantse sau biyu niba nice wacce kake nemaba, Allah zan hadaka da Abba nafa this is not norm...al" hanunshi dayasa akan bakinshi yamata alamun tai shiru yasa takasa karasa maganan da kyau kirjinta nawani irin mugun bugawa gashi yaki sakin bakin hijab din nata balle ta gudu, ahankali yadan zo kusa da ita kadan, sosai taji kirjinta ya cigaba dawani irin mugun racing gashi takasa magana kaman yay mata magic dawani irin murya yace "will you marry me plz?" jin maganan tai daga sama da sauri ta kalleshi danta tabbatar shiya fada inko dai shiya fada to mutumin nan baida lpy, dawani irin murya yace "plzzzzz" wani karfi taji yazo mata ta fizge hijabin ta tana wani irin hararan shi da manyan idanunta, batare datace komiba tazo zata wuce ajiyar zuciya yadan sauke yace "at least kifada min sunan ki to kafin kitafi" juyowa tai ta kalleshi taja tsaki ta wuce fuuuuu, yafi minti uku a wajen da kyar yadaga kafan shi ya bude gate yafita kanshi nawani irin ciwo, shi kadai yasan me yakeji. Ahankali ta bude kofa ganin Anty Hindu bata falo yasa da gudu tai sama ta shiga dakinsu, Farida tagani zaune tanacin abinci tace "waye yazo wajen ki Fahad ne?" tsaki tadanyi tacire hijabin Maman Miemie ta ijiye tace "wani unwanted guest ne" tai tsaki tawuce bathroom dan tadan wanke fuska jin har yanzu kirjinta na bugawa. Yau dasafe takeda lectures while Farida Kuma sai 11, da wuri ta shirya cikin atampa ta daura Maroon hijab akai dayay mata kyau Bala ya dauketa a mota aka bude musu gate suka fito, hada ido sukayi da Khaleel dake sanye cikin sport wears kafarshi cikin Nike sport shoes yana jogging agaban gidan su, gadan towel dinshi akafada yana goge zufa idan yayi, wani heart melting murmushi ya sakar mata daya fito dayar wushiryar shi, ya daga mata hannu alamun Hi, sanan ya cigaba da jogging abinshi kaman da gaske, dauke kai tayi daga kallonshi ta turo baki tacema "Bala mutafi" samun kanta tayi da kallonshi ta mirror mota taga ya daga mata hannu da sauri ta dauke kai. Around 3 tadawo kaman jiya Fahad ne ya sauke ta abakin layinsu ta dandaro da kafa, a kusa da gidan su ta ganshi tsaye ya rike wani katoton balloon da aka hura an rubuta I love you ajiki murmushi kwance akan fuskar shi yana kallonta, dauke kai da sauri tayi ta cigaba da tafiya. Biyota yay da sauri yasha gabanta wani dan Kati mai kyau pink yaciro daga aljihun shi ya bude an rubuta "please tell me your name" . Fizge katin tayi tayar ta kalleshi masifa tai niyyar mai amma saitakasa ahankali tace "please leave me alone" da sauri ta wuce shi ta shiga gida tabarshi nan tsaye. Wuraren Magrib Farida tashigo gidan dakinsu ta shigo ta zauna akan gado batare datacema Islam dake rubutu komi ba, kallo Islam tabita dashi sanan tace "Faree wah happen a school why are you like this?" hawaye ne yazubo sharr daga idonta, ajiye biron dake hannunta tayi tadawo kusa da Faridan ta dafata tace "meya faru me aka miki" fadawa tayi jikin Farida tafashe da kuka da kyar tai shiru duk hankalin Islam yatashi tace "baki da lpy ne?" girgiza mata kai tayi sanan tace "tun jiya bayan mun rabu nake kiran my superman yaki dauka, wlh har Gym dinan saida naje yau amma bayanan ban ganshi ba, nakasa komi ko lectures ma babu wanda nagane, I don't know why he is not picking my calls" tafashe dawani kukan, ba karamin tausayinta Islam tajiba hannu tasa ta share mata hawayen tace "stop crying hala baya kusa da wayan ne kokuma ansace mai wayan, please stop crying in sha Allah zai kiraki kokuma kuhadu" gyada mata kai Farida tayi, murmushi Islam tayi tace "oya cire kayanki bari naje nakawo miki abinci ta superman". Washegari zazzabi ne yarufe Farida hakan yasa Anty Hindu tace ta zauna kartaje school yau Abba Kuma yakira Dr. Bala ne ya dauketa a mota ana wangale gate ta ganshi yana jogging yauma, baki ta tabe ta dauke kai abinta suka wuce shi dudda haka saida ya daga mata hannu. Da yamma ma data dawo haka ta ganshi zaune shida mai gadi suna hira murmushi yamata yace "welcome" dauke kai tayi da sauri dan duk inta kalleshi heart dinta bugawa yakeyi ta shige cikin gida da sauri. Ba karamin murna yay ba da Ammi ta turo mishi su Ilham da Ihsan suzu suyi hutu, ga Fa'iza ma sun suma mid term break hakan yasa gidan yacika da hayaniyan su. Zaune suka dukan su a katoton falon Goggo wanan Karan ma harda Umma duk sai hira ake shi kadai ne ke kwance ya lumshe ido kawai yana jinsu. Yusuf ne yace "why not mu dan hada get together gobe Saturday da yamma" ihu Ihsan tayi harda tsalle tace "Ya Yusuf wlh is gonna be fun to a ina zamuyi?" shiru yadanyi yana tunani sanan yace "anan falon Goggo but zamuyi decorating, and zaku iya inviting anyone, kawai games zamu buga sai Kuma drinks and have fun shikenan" ya dakama Khaleel duka yace "Ya kagani" batare daya bude ido ba yace "yea" finciko hanunshi yayi yace "bawai Yea ba ATM dinka zaka basu suje kasuwa su siyo abubuwan decorating dakin tsohuwar nan" hararan shi yayi yace "kai maiya sami ATM dinka" dariya Yusuf yayi yace "ai am d organizer ni zanyi handling inviting guest, kai a cash aspect din kawai anan muke bakatan ka, dan ban wayar kama" mikamai wayar yayi ya amsa yace "mezakai dashi?" tashi Yusuf yayi saida yakai bakin kofa sanan yace "I want to invite your Farida" yafita da gudu, da sauri Khaleel yatashi ya bishi yana kiran shi Yusuf Yusuf. Part dinsu Yusuf ya shiga kafin Khaleel yazo ya kulle yana jinshi yana kiran shi amma yay bedroom ya rufe kofa, zama yay akan gado ya bude wayar dan dama babu key, duba contact dinshi yayi yaga babu wani suna Farida, wajen kira yaduba nan yaga wani number daketa kirashi baya dauka hakanan yaji ajikin shi wanan ne number yay dailing ringing daya ta dauka da sauri tace "Mk" dan dariya Yusuf yayi yace "ba MK bane Yusuf neto" ahankali tace "ina Mk inata kiranshi baya dauka" yace "eh baida lpy ne saisa yasani na kiranki ma, dama munada family get together ne yace he will be happy idan you come" wani murmushi tayi tace "dagaske?" "why not ai yanzu u are part of the family, anyways karna cikaki da surutu gobe ne 4pm sharp, zan miki forwarding address din" da sauri ya kashe wayar jin Khaleel kaman zai cire kofar da bugu ya tura mata address din gidan su sanan ya ijiye wayar yazo ya bude kofan ya ruga da gudu yana kiran Goggo. *JARABTA* Maman Abd Shakur 25 & 26 Gayu Farida taci sosai kaman zataje gasar Islam Kam tanata dariya dan tasan wajen superman dinta zata Bala ne ya kaita har kofar gidan tacemai 5:30 yadawo ya dauketa yace mata to sanan yatafi. Wayar Khaleel dake hannu Yusuf ne tai kara dan tun safe ya dauke wayar ya boye a wurin shi dan yasan Khaleel zai iya yaki daukar wayar idan tazo, tashi yayi yaje wajen Khaleel yace "Bros tana waje fa jeka shigo da ita" wani kallo yamai danji yake kaman ya bindige shi, ganin baida niyyar magana yace "tariga tazo wulakanci ba kyau please ka shigo da ita naji na yarda koma me zakamin inta tafi Kamin please" wani kallo yamai sanan yajuya yafita daga dakin Goggo ahankali, juyowa Yusuf yayi suka kashe da kanin nasu dukan su suna rawan murna Fa'iza tace "wlh nakosa naganta" kara gyaggyara decorations din flowers din dakin sukayi sanan suka zazzauna akan baban lallausan carpet din dasuka shimfida akan tiles. Gate ya bude yafito tunda yake takowa take kallonshi tafiyar shi kadai gusar mata da tunani yake kayan turawa ne ajikin shi white shirt ne yadan bude boturin saman sai dogon jeans blue daya saka, wani irin murmushi takemai tace "barka da yamma Mk" dan murmushi yamata yace "shall we" yana gaba tana biye dashi abaya cike da kunya har part din Goggo, wani ihu da tafi su Yusuf dasu Ilham suka dingayi hakan yasa Farida ta labe abayan Khaleel tana kukkule fuska dan ba karamin kunya tajiba, wani irin kallo yakema Yusuf dako ajikin shi saima wani dadi dayake ji, Ihsan ne taje bayan Khaleel din ta kalli Farida dake rurrufe fuska cike da kunya, tabata hannu tace "am Ihsan his sister nice to meet you" hanunta Ihsan ta rike ganin taki bude fuska, tajata takaita wajen su sunata ihu sunajin dadi, da gudu Fa'iza ta kunna music suka hau tika rawa, Yusuf yazo gaban Khaleel dake kallonshi yana wani irin kwaso mai shoki harda gwalo, Farida kuma dasu Faiza sun sata a tsakiyar su sunata rawa abinsu. Gabaki dayan su dadi sukeji Khaleel yay budurwa, sosai sukasha rawa abinsu shi waje ma yasamu ya zauna yana kallon su, Farida sai satar kallonshi take, sunyi kusan 15 minutes suna rawa sanna Yusuf ya rage karan music din Ilham ta tashi ta kwaso drinks da chicken kebab din dasuka hada. Juice kawai Farida ta iya sha sabida yanda suke nan nan da ita duk tadinga jin kunya bayan sun gama ne Yusuf yace "okay once again atafa ma our special guest Farida... Daaaa" yawani kara gunna, suka wani kwashe da tafi, sanan yace "oya time for our game" yan matan suka mimmike suna yeee. Akan carpet suka zazzauna sukai circle Yusuf yakamo hanun Khaleel batare daya kalli fuskar shi ba ya zaunar dashi, sanan ya dauko wani bowl dake dauke da papers da akai folding ya daura ma kowa one one paper ajiki harda Farida sanan ya ijiye bowl din ya zauna kusa da Khaleel yay folding leg kaman yanda kowa yayi yace "papers din nan each of them contain a question da dole saika amsa mana ka fadi gaskiya so starting from me bari na duba Naga wats my question" budewa yayi sanan ya karanta "who is your best friend?" murmushi yay yanuna Khaleel yace "dis dude shine best friend dina" Fa'iza ta bude nata tace "what do you hate most" dan dariya tayi tace "wanke wanke wlh" daka mata duka Yusuf yayi yace "lazy girl" Ilham ne tabude nata tace "izifi nawa kika haddace?" gwalo Ihsan tamata dauke kai tayi tace "ashirin, suratul Ankabut zuwa Nas" Ihsan ta karanto nata "meke saki kuka?" shiru tadanyi tace "ciwo, idan ina ciwo" sai Farida ahankali ta bude nata ta karanto "who do you love?" shiru tayi Yusuf yace "answer now is ur turn" ahankali ta kalli fuskar Khaleel da sauri ya kawad da kai murya chan kasa tace "him" wani murmushi dukan su sukayi Ihsan ne tace "him, waye him?" juyo dakai tai ta kalli Ihsan a kunyace tai murmushi taki magana, Yusuf ne yace "barta tamayi kokari ai, ya kalli Khaleel ya daga mai gira yace" Mk is ur turn" ajiyar zuciya Khaleel ya sauke ya bude takardar shiru yay ganin tambayar, Fa'iza tace "karanto muji question dinka Yaya" ahankali yace "wakake so?" shiru yadanyi kafin ahankali yace "My Eesha" sosai maganar ta daki Farida, hawaye ke kokarin zubo mata da kyar tai controlling dinsu tadanyi murmushin yake daidai kiran Bala na shigo wayanta dan biyar da rabi ya wuce har da kusan minti goma, tashi tsaye tayi ahankali tace "natafi anzo daukana" "dawuri haka ai bamu gamaba" cewar Ilham murmushi tamusu tace "zan dawo wataran" hanunta Ihsan ta kama tace "muje ki gaisa da Umman mu da Goggo mu fita daga dakin tayi tana dan waigen fuskar Khaleel, sosai Umma taji dadi barin ma Goggo sai addu'a take mata saida suka fito Ihsan tace "sis Eeshan dayake magana fa ta rasu, saisa dakika shigo rayuwar shi yanzu muke murna sosai in sha Allah dake za'ayi" batasan Sanda ta sauke ajiyar zuciya ba, ta share kwallan daya zubo mata murmushi Ihsan tamata sanan tarike mata hannu tarakota har waje, Khaleel ta gani da Yusuf jikin motar Bala suna jira su fito, dan murmushi Khaleel yamata yace "thanks for coming" murmushi tamai back yadaga mata hannu ta shiga mota suka wuce. Yau Monday bata da lectures amma sabida Farida data kirata tamanta da presentation dinta dake cikin file akan table Kuma yau zasuyi yasa ta tashi ta shirya tana tsaki. Sauka falo tayi tadau presentation din akan table tafito Bala ne ya dauketa suka fito daidai yay parking motar shi a kusa da gidan su batama lura dashi ba suka wuce, ajiyar zuciya ya sauke sanan ya kunna motar ya bisu har AUN. Parking Bala yayi a parking lot tafito hanunta rike da file dakuma waya data kara a kunne, kasa dauke kanshi yay daga kanta bata lura dashiba sabida glass din motar shi tinted ce. Maida wayar tai cikin jaka tadan jingina da wata mota tasa kumbanta abaki tanaci dan taga yadanyi tsayi, Farida data hango tadan taho da gudu gudu, yasa ta karasa wajenta file din tabata ta karba ta bude tagani murmushi tayi sanan ta mikama Islam hannu suka tafa tace "bari nai sauri an fara amma ba'akai group dinmu ba" tana fadin haka tama Islam bye ta wuce ta tafi dadan sauri dawowa motar Islam tayi ta shiga Bala ya kunna sukabar wajen. ba karamin mamaki yayiba dayaganta da Farida, wayar shi yaciro da sauri neman number ta yafara dan baitaba kiranta ba, da kyar yagane number yay dailing, Farida data kusan class dinsu tanajin ringing ta duba wayarta ganin superman ne wani farin ciki ya rufeta da sauri tai picking, "Hello Mk" ahankali yace "how you" murmushi tayi tareda yin wani fari ta cigaba da tafiya tace "fine, yasu Ihsan" shiru yadanyi kafin yace "inaso nadan tambaye ki wani abu" baki tawani washe tace "ok" yace "ina parking lot din school dinku.." "school dinmu?" ta katse shi yace "yeah, naganki da wata, I think kaman tabaki wani folder ne, who is she?" "Farida Maikano" taji ana kiranta is time for her presentation kenan da sauri tace "Mk I will call you later, zanyi presentation ne bye". *JARABTA* Maman Abd Shakur 27... Sai yamma ranan tabar school tana komawa gida taci abinci bacci yay awon gaba da ita, Islam bata tasheta sabida tasan bata salla. Atare yau suka fito Bala ya dauke su waige waige tadinga yi awaje ganin yauma bata ganshi ba tabe baki tayi tace "hala yagaji ya hakura ne" ahaka suka kai makaranta kowacce tai department dinta. Misalin 11 Mum na zaune adakin ta wayar wata baban kawarta senior lecturer ce itama ta kirata dauka mum tayi tace "Hajiya hope baki shiga school bayau?" "ahh'ah ban shiga ba yau banda lectures" matar tace "kin ganni nan ma fitowa ta kenan driving ma nake wlh wani good student of mine yazo yake cemin nabar school din now, wai student zasuyi protesting sabida party dasukaci SUG wai cuwa cuwa sukayi, an kinsan yaran nan Allah kadai yasan mesuka shirya" arude mum ta mike tsaye tace "Hajiya sadiya yata na makaranta" katse wayar tayi tadau car key dinta dake kan carbod tadau hijabi tafita arude, taja mota dawani irin gudu tafita, number Farida tai dailing cikin sa'a ya shiga tana dauka tace "kina ina?" murmushi tai tace "gani nan mum nama fito daga massallaci ne zan koma class" da sauri mum tace "Kifito yanzun nan kizo baki gate, right now" yanda Mum tai magana yasa tace "Mum lpy?" tsawa Mum ta dakamata "nace kifito bakin gate yanzun nan am coming right now" juyawa Farida tai da sauri tadinga tafiya harta kai bakin gate tafita, tsayawa tayi abakin titi daidai lokacin Mum ta iso, wining glass down mum tayi tace "get in" bude kofa Farida tayi ta shiga tana kallon fuskar Mum, kunna motar mum tayi sukabar wajen ta kalli Mum tace "Mum lpy mesa kika kirani lectures gareni fa" batare data kalleta ba Mum tace "riot students zasuyi i just got d information yanzun nan saisa nazo daukar ki dakaina" da sauri Farida tace "Mum Islam fa? Turn d car muje mu daukota tana lecture theater department dinsu sunajiran lecturer" tabe baki Mum tayi ta cigaba da tuki abinta, "Mumm" Farida ta kirata dawani irin murya, ahankali tace "she always considered her mum" mum ta harareta tace "and nikuma yata mace dayane which is u, Kuma kimin shiru anan wlh kona wanke miki fuska da mari" wani hawaye mai zafine ya zuboma Farida tace "Mum I tot kinason Islam, inhar bazaki koma mu daukota ba to ki saukeni nakoma koma menene yasamemu tare" wani mugun kallo mum tamata tace "waya cemiki bana sonta?? Kawai dai danka danka ne" sosai Farida taji kuka yazo mata da kyar ta hana kanta yi wayarta ta ciro daga jaka Mum tace "wlh inkika kirata saina bata miki rai, ita yarinya ce once anfara riot din she will find her way out so karki sake ki kirata, I know wat am doing" sosai taji tanajin haushin uwartata ahankali tace "ni dama ba kirama zanyi ba, watsapp zan shiga" wani irin kukan zuci ta dingayi tayaya yanzu zata taimaki Islam? Mk ne yafado mata rai, text yes text zatamai, da sauri ta shiga massage tafara typing "Mk zaka iya tuna fuskar wacce kace kaganmu jiya tare? If yes please help me get her out of the school now, riot students zasuyi, please nasan wat am asking is a bit much but you are my superman, taimakon mutane is ur periorty, tana theater din Home economics department, thank you" ta turamai. Yana kwance akan gado yana danna wayar sakon ya shigo mistakenly hanunshi ya danna sakon ya bude dan baiyi niyyar budewa ba. "subhanallah" yafada bayan yagama karanta text din da sauri yadau car key yafita daga dakin. Zaune take achan sama, last roll din sit din lecture theater, bata sami gaba ba sabida taje massallaci tai salla bata shigo ajin dawuri ba, sai hayaniya ake chaaa ana jiran malamin, Class chairman dinsu daya fita siyo kati dan yakira lecturer awaya ne yaleko ta window yana numfarfashi sama sama yay ihu yace "everybody run yaki sukeyi, wlh teargas zasu wurgo yanzun nan" dudda yan ajin basu gane kan zancen shi ba amma numfarfarshin da akaga yanayi yasa aka tattashi tsaye ana gudu, tashi tsaye Islam tayi tana Kalle kalle, ta window sukaga wasu students dasuka fenfenta fuskokin su dan kar aganesu sun wurgo teargas ta window yafado ajin, fuuufuufuu yafara wani irin popping yana fitowa yana hayaki, ihu yan ajin suka fara, ture ture ake kawai kowa na neman takanshi ga waje yan protests din na dambe da securities, hijabin ta tasa ta taushe hancin ta dan batama gani da kyau sosai tana sakkowa daga matattakalan tsakiyar ajin, tari tafara yi sosai idanunta na juyawa, bangajeta akayi hakan yasa tai gefe zata fadi wasu students dasuma sun haukace suna neman hanyar fita sabida tarin dasuke suka kara bigeta luu taji hannunta yay kasa tai dayan bangaren, hakan ya bayyanar da hancin ta ta shaka, ga idanunta dake wani azaban yaji ga hayaniya ga tarirrika Kala Kala, ga ihun mata daban daban, tsugunnawa tayi anan tsakiyar stairs tafashe da kuka zuciyar ta kaman zai fito sabida tsoro da fargaba, gawani irin tari datake yi tace "wayyo Allah Mamana" wayansu student da basa ganine sukazo wucewa tuntube sukayi da ita hakan yasa dukansu kusan su bakwai suka fada kanta duka kowa na tari. Ba lallai nai typing gobeba sabida yau nakuma da mugun yawa lol😜 [6/16, 8:30 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 28 & 29 Da kyar ya iya gane department dinsu dan duk student din daya gani zai tambaya gudu yake, a parking lot din department dinsu yay parking yafito yana waige waige, few people kawai yadan gani suna gudu dan duk an watse, saikuma wanda yagani sunyi fenta jikin su suna dambe da securities wasu kuma na faffasa windunan aji wasu na kona taya gadai sunan. Da dan gudu gudu yake tafiya yana zagaye wajen da kyar yagano theater din, hayakin dayaga yana fitowa ta windunan yasa yakarasa wajen da gudu, hanunshi yasa ya taushe hancin shi ya shiga baya gani hakan yasa yaciro wayar shi daga aljihu ya kunna yana haskawa some student ya gani sun faffadi ta gaban ajin harda maza suna tari, tadasu yafara yi yana kamasu yana fitar dasu waje, tsayawa yay awaje yana dan fifita idonshi sabida wani irin azaban yaji dayake mai na teargas, bude boturan shirt din jikinshi yay yacire rigar ya kulle hancin shi dashi, haka yadinga fififto da students dayaga sun zuzzube yana hashaska fuskokin su amma bai gantaba, saida yagama fito dasu sanan yafara hawa stairs din yana hashaskawa ga idanunshi dake mai zugi, wasu group din student yagani again anan tsakiyar stairs din wasu akan wasu daddaga suna tari duk sun kasa tashi, daddaga su yay yana kaisu waje, mai Hijabin daya gani a karkarshin su ta kife yasa yaji kirjin shi ya buga dim! ahankali yadan juyo da ita, ganin fuskar Islam jini nabin goshinta idanunta a kulle yasa jikinshi yafara rawa, jakarta data rataya ta wuya yay maza ya cire mata yarike jakan a hannu sanan ya dauketa ya fara sakkowa daga matattakalan, wani kusa kujera ne yaji yawani kece shi acinya saida wandon shi ya yage, bai damuba tafiya kawai ya cigaba dayi yana sakkowa, fitowa yay daga ajin yana kallon fuskar ta, tunawa yay da randa Eesha ta rasu, jijjigata yayi arude yace "dan Allah karki barni, please stay with me" harda gudu yahada yay inda yay parking da ita, bude bayan motar yayi ya kwantar da ita ya rufe, rigar shi daya rufe hanci dashi ya cire ya yar ya bude gaba ya shiga ya zauna tareda ajiye jakarta a kusa dashi, ya kunna motar yabar school din dawani irin mugun gudu, wani hospital yagani akan hanya Salama Clinic da gudu ya shiga yay parking daidai lokacin yaji wayarta dake cikin jaka na ruri bude jakar yayi ya dauko wayar, yasaka a aljihun shi batare dayama kalli screen dinba yafito, bude baya yayi ya dauko ta chak idanunshi sunyi jajir ya shiga cikin hospital din da ita, nurses din dake reception ne suka tashi ganin yanda jini kebin fuskarta, wani gado suka turamai ya kwantar da ita, daya daga jikin su ta ruga da gudu kiran Dr, daya Kuma ta cire mata hijabin jikinta ta mikamai ahankali ya karba yana kallon fuskarta, Dr ne yafito ya karbi handglove yasa yafara kokarin tsayar da bleeding din forehead din yadan waigo yace "maiya faru?" tari yadanyi sanan yace "school dinsu ke zanga zanga shine akasa teargas" Dr yace "okay tana bukatan madaran ruwa kaima haka" sanna sukai cikin wani daki da ita da sauri yabisu Dr ya nunamai kujera yace "calm down sit and relax, zamuyi aikin mune, kaje ka kawo mana madaran" yajuya ya shiga dakin ya rufo kofa, ahankali yakoma ya zauna akan kujera hijabin ta dake hanunshi ya daura akan fuskan shi jin hawaye na neman zubomai, ringing yakara ji wayarta nayi ahankali yacire hijabin daga fuskarta yaciro wayar ya kalli screen din "Abba" yagani, kasa picking yayi harta katse, sake kira Abba yayi hakan yasa yay picking yakai kunne, "Ummi dafatan komi a school lpy, hankalina yaki kwanciya sai tunanin ki nake?" shiru yayi baice komiba, Abba yasake cewa "are u there Ummi?" da kyar ya tattaro courage yace "Abba muna asibiti?" yacigaba da tari adan rude Abba yace "Asibiti? Wani Asibiti? Ina Ummi? Wake magana?" da kyar dan muryan shi ta dinshi makogwaran shi har yaji yakemai yace "salama clinic, riot akayi a school, tadan sami injury, muna asibiti" "innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ganinan zuwa" kashe wayar Abba yayi, kasa hakura yay yatashi yaje gaban kofan yadan leka glass din, oxygen yaga an mata fixing, sanan Dr na dressing ciwukan data samu a goshi da gwuwowinta da hannu, komawa yay ya zauna idanunshi sunyi jajir ya dafe kanshi dayaji yana wani irin mugun sarawa. Wani list wata nurse takawo mai tace "ga abubuwan da ake bukata, kaje ka siyo a pharmacy" ahankali ya karba yafita yaje pharmacy ya siyo harda madaran ya kawo ya bata yasake zama dan kanshi bala'in ciwo yake, ringing wayar Islam tayi hakan yasa ya amsa, Abba yace "ina reception din asibitin a ina kuke?" Daidai Abba ya bude kofa ya shigo reception din sanye da manyan kaya, tashi yadanyi tsaye dan baijin zaima iya tafiya ba sabida yanda kanshi ke sarawa, Abba nagani shi yagane shi ganin wayar Islam a hanunshi yakara so inda yake yana kallon kafar shi ganin yanda kafan ke jini yace "subhanallahi basu duba ka bane jibi yanda kafar ka ke jini, nurse" ya kwalama nurse kira, wata nurse data fito daga dakin da aka shigar da Islam ta karaso inda yake tace "thank God kakawota da wuri mun samu mun tsayar da bleeding din she is out of danger, bacci take yanzu sabida duk wanda yasha teargas need sleep sabida system dinshi yay relax" murmushi yama nurse din dan sama sama yake gane mema take cewa sabida yanda yaji kanshi ke juyawa, ahankali yaji jiri na dibar shi yay baya zai fadi da sauri Abba ya rikeshi yace "subhanallahi" turo gado nurse din tayi Abba ya kwantar dashi tace "ai namaga mugun kokarin shi yasha uban teargas dinan har ya iya tuki ma yakawo ta ba abinda ya samai, and I told him yasha madara fa" shigar dashi wani daki sukayi dan bashi kulawa, fitowa Dr yayi yace "Kaine mahaifin ta?" Abba yace "eh, zaka iya zuwa ka ganta she is fine amma bacci take" shiga dakin Abba yayi ya zauna akanta kumatun ta ya shafa tareda sauke ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah, banason wani abu yataba samin ki Ummi ke kadai nake gani dakike tunamin da mahaifiyar ki" wayar shi ce tai ringing da sauri ya dauka ganin Anty Hindu ce yace "Yaya ina asibiti fa, Salama clinic Islam ce duk taji ciwo wai students ne ke riot a makaran tarsu, shine wani bawan Allah yakawota shima gashinan ba lpy". "Maman Ibrahim Islam na asibiti fito fito mutafi" arude Mum da Farida data fashe da kuka suka fito daga daki, Mum tace "meya faru?" Anty Hindu tace "baban su yake cemin wai zanga zanga ake a makarantar su, Islam duktaji ciwo mutafi" Hijab Farida ta dauko zata bisu Mum tamata tsawa tace "yanzun nan Sameer zai dawo daga school dawa zai zauna idan yazo? Wuce ki zauna my friend" fashewa ta karayi dawani irin kuka Anty Hindu tace "yi shiru jeki zauna ai zamu dawo, saike kije yanzu dai kar Sameer yadawo ba kowa gidan" fita sukayi sukabarta. Abba ne ya shigo dasu sukaje dakin Islam sosai jikin Mum yay sanyi bata taba zatan abinda tayi zaiyi resulting to this ba. Tashi Abba yayi yace "bari naje naduba bawan Allah daya taimaketa" Anty Hindu tace "muje nima nagode mishi daga nan" Mum suka bari tareda Islam dake bacci suka fita daga dakin, dakin da aka kwantar da Khaleel Abba ya bude ya shiga, bacci yake, Anty Hindu ne ta kallai sanan ta kalli Abba tace "kaga shine yaron danake fadama ranan nan". Sake kallon fuskar shi Abba yayi daidai lokacin wayar Khaleel dake gefenshi akan bed yay ringing dauka Abba yayi yaga an rubuta Abba ajiki, Anty Hindu tace "waye?" "baban shine?" Anty Hindu tace "to kadauka mana ka fadamai dansu na asibiti yakamata su sani" fita Abba yayi dan yadau wayar. Bayan yagama wayar ya wuce ya biya kudin komi both ba Khaleel da Islam sanan yadawo ciki, Abba ne yasake kira hakan yasa yafita dan shigo dasu, ba karamin mamaki yayiba dayaga dan Aminin kasuwancin shine, musabaha sukayi tareda kara jajanta lamarin sanan suka shiga ciki. Tareda Abba da Yusuf Babban Islam suka shigo dakin da sauri Yusuf ya karasa kusa dashi ya zauna Abba yay ajiyar zuciya yace "Allah sawake, ya yartaka dafatan dai babu wata matsala babba" Abban Islam yace "a'a Alhamdulillah bacci ma take, kampanin nanko sun kiraka? abubuwa sunsa na manta ban kirakaba" kafin yay magana Anty Hindu tace "kunsan junane" murmushi dukansu sukayi Abban Islam yace "amini nane muna kasuwanci tare" gyada kai tayi tace "masha Allah" Abba yace "muje ko mudubata" tashi dukan su sukayi harda Yusuf suka shiga dakin da aka kwantar da Islam, ba karamin mamaki Yusuf yay ba dayaga yanda Islam ke kama da Eesha ko wanan ce wacce Khaleel yataba cewa yagani? Ajiyar zuciya yadan sauke yace "bambamcin su kawai shine wanan tafi Eesha jiki kadan" . Gaisawa da Mum Abba yay yamata ya jiki sanan suka baro dakin. *JARABTA* Maman Abd Shakur 30... Da magrib yatashi yana karema dakin kallo Yusuf daya gani akan kujeran dakin yana kallonshi, yace "wat happen?" dan murmushi Yusuf yamai yace "kasha uban teargas ne ka sume ma mutane" tashi yay ya zauna yana dan yatsine fuska sabida yanda ciwon kafarshi kemai zafi, Yusuf ya nunamai wata white t-shirt daya fita ya siyomai yace "ga riga kasa ka dauro alwala see dadduma kazo kai sallan asri da magrib mutafi gida dan an riga an sallamemu" rigar ya saka sanan ya shiga bayin dakin ya dauro alwala yazo yay salla. Bayan ya idar yana kan dadduma wayar Islam dake kan gadon tai kara hannu ya mika ya dauko "My Heart beat" wani irin bugawa kirjinshi yayi dayaga sunan, duk yanda yaso ya hakura yakasa saida yay picking call yasa a kunne daga dayan bangaren Fahad yace "princess inata miki text baki replying, I miss you yau ba muyi wayaba" wani abune yaji ya tokare mai zuciya, "Hello my princess are u there luv?" "mallam karka kara kiran layin nan, an riga an mata miji am her husband to be, so be very careful" yafada cikin fushi ya katse wayar, tashi yay ya linke daddumar yabama Yusuf dake kallonshi baki bude yadau wayar shi batare daya kalli Yusuf ba yace "muje" fita sukayi sanan ya juyo ya Kalli Yusuf ahankali yace "am coming" zama Yusuf yay akan kujerun dake reception din shikuma yay hanyar dakin da Islam take, ahankali ya bude kofar, dayar gajeren sallama dan bama tajishi ba tana zaune kan gado da doguwar riga ajikinta na atampa kanta da bakar hula da aka dan matsar dashi baya sabida bandejin goshin, ta mikar da kafafunta taja doguwar rigar zuwa saman gwuiwowinta tana hura ciwon dataji dake mata zafi. Ahankali yake daga kafa haryakai bakin gadon ya tsaya yay folding hanunshi a kirji cikin sanyin murya yace "is it paining you?" gyada kai tayi tana yarfe hannu tana hurawa batare data dago kaiba dan gabaki dayan hankalin ta nakan ciwon, dago kai tayi da sauri ta kalleshi da katon bandejin dake goshinta da sauri ta saukar da rigarta ta rufe kafafun ta, dan murmushi yayi sanan ya zauna abakin gadon yana fuskan ta hararan shi tayi tace "waikai duk inda nake sekazo, tracker kake amfani dashi ne? Wlh ko kafita daga dakin nan kona kirama Abbana nahadaka dashi komame zai faru ya faru" murmushi yasake yi sanan yace "how are you feeling now?" dauke kai tayi ta turo baki, sosai yake kallonta sake juyo dakai tayi ta kalleshi tace "wai bazaka fitaba sai su Abbana sunzo, okay bari na kirasu" bude baki tayi zatai ihu yadaura hannu akan lips dinshi alamun tai shiru, kasa magana tayi kaman wacce yama magic saima dauke kai datayi daga kallon dayake mata jitake kaman ta makeshi, hanunshi yasa a aljihun wandon shi yaciro wayarta ya mika mata juyowa tayi tana ganin wayarta ta karba da sauri akuma dan rude tace "a ina kasamo wayata?" baice komiba yatashi tsaye yana kallonta yace "waye My heartbeat" da sauri ta kallai sanan ta harareshi tareda murguda mai baki tace "meruwan ka and kafita daga nan" kallon cikin idonta yayi yace "well I told him karya sake kiranki because am ur husband to be" kwalalo ido tai ta kalleshi da so much pain a idanunta tace "Fahad din nawa ka fadanma haka?" gyada mata kai yayi yace "yes" azuciye ta juya tana waige waige pillow dake bayanta ta raruma ta jefamai da duka karfin ta ya chafe yana murmushi har saida hakoranshi suka bayyana daidai lokacin Anty Hindu da Abba suka shigo, Abba yace "Ummi Khaleel din kike bugama pillo mutumin daya taimakeki dabadan shiba da Allah kadai yasan mezai sameki" da sauri ta kalli fuskarshi, dan murmushi yamata sanan ya tako yadan duka ya ijiye filon abayanta ahankali yace "I will come and check you tomorrow, I love you" yay maganar ta yanda ita kadai zata iyaji ya juyo ya Kalli Abba da Anty Hindu yace "Abba saida safen ku" addu'a sosai da godiya Abba da Anty Hindu sukamai sanan ya juya zai fita daga dakin dan waigowa yay ya kalleta daidai lokacin itama tadan dago kai suka hada ido hannu yadaga mata alamun bye, kawad dakai tai da sauri murmushi kwance kan fuskarta. [6/17, 6:38 PM] Maman Jedda: Novels *JARABTA* Maman Abd Shakur 32 & 33 Kaman mai rada yace "I love you so much, zuciya ta bazata iya jure rashin kiba, nasan baki sanni ba but please give me a chance, ina sonki sosai" dan hawaye taji ya gangaro mata, girgiza mata kai yayi ahankali yace "will u marry me please" dan lumshe ido tayi tareda dagamai kai maganar Anty Hindu dataji tawaje ya mai do da ita hankalin ta da sauri ta tashi ta zauna ta kawad dakai kirjinta na bugawa sosai tashi tsaye yayi shima yana kallon fuskarta, bude kofa Anty Hindu tayi ta shigo ita da Dr, dubata Dr yayi sanan yace "Hajiya babu wata matsala, nan da yan kwana biyu yan ciwukan nan zasu warke zaku iya tafiya" Anty Hindu tace "to nagode Dr, bari nakira Bala yazo ya dauke mu" da sauri Khaleel yace "basaikin kirashi ba nina kaiku Hajiya" yay maganar yana kallon fuskar Islam da har yanzu taki kallonshi, "to shikenan, ke tashi mutafi" ahankali ta mike tsaye tadau Hijabin ta tasaka shiya fara fita sai ita da Anty Hindu dasuka fito suna biye dashi abaya kofar baya ya bude musu suka shiga sanan yarufe sanan yakoma gaba yabude motar ya shiga ya kunna yafara driving har suka fita daga hospital din, ta mirror gaban mota yaketa kallonta amma taki dago kai saima wasa da yatsun ta da taketayi, har cikin compound ya shiga dasu suka fiffito da sauri tai cikin gida dan bataso su sake hada ido, Anty Hindu ce tamai godiya cike da fara'a da addu'a sanan ya kunna mota yafita daga gidan. Afalo taga Farida ta zauna taci uban tagumi tsakanin jiya da yau duk tai zuru zuru tana ganin ta ta taso da gudu ta rungumeta tsam tsam sakinta tayi ta kalli fuskarta tace "sannu Islam ya jikin?" dariya ma tabama Islam hakan yasa tai dan dariya tace "ke dalla am fine ciwo fa kawai naji, Ina Mum?" jiki a sake tace "tana daki" tace "bari naje na gaishe ta" sama tayi saida ta gaida Mum tamata ya jiki sanan ta wuce dakinsu bayi ta shiga tai wanka da ruwa mai dumi sanan ta fito, light kaya tasa tazo ta kwanta akan gado dan bacci takeso tayi ta lumshe ido, fuskar Khaleel tagani yana mata murmushi da sauri ta bude ido tajuya dayan gefen tasake lumshe ido tuna sanda ta daura fuskar ta akan hanunshi tayi, bude ido tayi da sauri ta tashi ta zauna tareda jan uban tsaki dan mugun haushin kanta takeji tayaya ma tai hakan wat was wrong with her, waya ta dauka tasake dailing number Fahad bai dauka ba, message ne ya shigo wayar ta bude bakuwar number ce hakan yasa ta bude "I love you so much. Khaleel" wirgi tai da Wayan akan gado tareda yin tsaki "mutum sai shegen naci anaci" Misalin 9 na dare Yusuf ya shigo part dinsu ya sameshi yana zaune yana daddana waya gefenshi kuma tea ne daketa kamshin su citta, zama Yusuf yay kusa dashi yadau tea ya kurbe hakan yasa ya kalleshi batare dayace komiba, murmushi Yusuf yayi yay gyatsa sanan yace "idan ma masifa zakamin naji amma kafara zuwa Abba na kiranka" filon dake kan kujeran yadau ka ya naka mishi akai sanan yabar dakin. Sallama yayi ya shiga dakin Abban, shi kadai ne sanye da farar jallabiya idanunshi acikin medicated glass yana karanta littafin addu'oi samin waje yay ya zauna akasa. Saida Abba yagama sanan yarufe ya ijiye gefe ya kalleshi yace "Son" "Na'am Abba" Abba ya gyara murya yace "ahh dama magana nakeso nai dakai kan yar abokina, nafison naji daga gareka ne dan mahaifinta yacemin yayarshi tace kun dan dade da sanin juna dan har gidan su kajema" shiru yadanyi yana nazarin fuskar Khaleel din sanan yace "kana sonta ne?" sosai yaji kunyar maganan Abba hakan yasa yadanyi murmushi yana sosa keya, dan dariya Abba yayi yace "a'a to to to, wanan murmushi haka Khaleel ta eh ce ko" dan gyada kai yayi kanshi akasa Abba yace "to masha Allah dama nariga nai magana da mahaifinka ran sati zaizo sai muje nema maka auran ta, banason awani nisanta bikin sabida dazaran anyi auren kukadan yimana kwana biyu anan saika koma bakin aikin ka ko" gyada ma Abba kai yayi Abba yay murmushi yace "saura dan uwanka yanzun nan nagama dashi nabashi wata daya idan Bai fito da mataba nizan nema mai" dariya Khaleel yayi wanan karan, Abba yace "tashi katafi Allah muku albarka". Sheshekan kuka datake ji yasa ta farka cikin tsakiyar daren nan, ahankali ta mika hannu ta kunna wutar dakin hakan yasa baccin idonta ya washe sosai, wawwaigawa tayi bataga kowa akasa ba hakan yasa ta sakko daga gadon, Farida tagani ke kuka a kwance da sauri tahau matattakalan bonk din tahau kan gadon ta dago ta, ta zaunar da ita takai hannu arude ta taba wuyan ta tace "baki da lafiya ne?" girgiza kai Farida tayi tana goggoge hawayen dake zubowa kaman an bude famfo, komawa tayi zata kwanta Islam tariko hanunta tace "talk to me please, problem shared is problem solved" fadawa tayi jikin Islam tafashe dawani irin kuka harda shesheka hakan yakara ruda Islam ta kankameta tace "Faree konaje na taso Mum ne?" girgiza kai Farida tayi ahankali tace "wlh Islam ina mugun sonshi, son da bazan iya kwatanta miki ba, amma kwata kwata bama ya daukan wayana yanzu, baya kulani na rasa yanda zanyi da kaina" kama fuskarta Islam tayi tace "listen listen kidena kuka kinata wahala shi baimasan kinayi ba, ki manta dashi jor, kanme zakizo kina wahala, ki manta dashi" girgiza kai tayi tace "bazan iyaba, I tried but nakasa I love my superman so much Islam bazaki gane bane" shiru Islam tayi cike da tausayin ta ahankali tace "to kinfada mai kina sonshi?" girgiza kai tai alamun a'a, tace "to duk randa kika sake ganinshi kinfada mai am sure zaisoki back" murmushi tadanyi ahankali tace "thank you Islam" kwantar da ita Islam tayi sanan ta kwanta agefen ta sukaja bargo suka kashe wutan dakin. Gabaki dayan su suka hadu suna aiki a kitchen sabida Abba yace zaiyi baki sha daya zasuzo, Farida ta rame har Abba saida ya tambaye ta meke damunta tace bakomi Wuraren goma suka gama aka zuzzuba abincin a hadaddun kuloli, sanan kowa yawuce daki danyin wanka. Suna shiga daki Farida ta kulle kofar su hadda sa sakata sanan ta kalli Islam dake kokarin cire kaya tace "kinsan me mommy tacemin?" girgiza kai Islam tayi tace "cewa tayi wai aurenki fa za'a zo nema yau" sosai taji kirjinta yabuga dum! Farida tace "kinsan dama baki bani labarin yanda kuka karasa da Fahad ba dama kin yarda yaturo ne?" arude ta girgiza kai tace "cemai fa nayi sainayi magana da Mummy, baifadamin zai turo ba and kona kirashi baya picking fa rabona damagana dashi tun Ina hospital" dariya Farida tayi harda kama ciki tace "yamin daidai, gwarama daya turo kinadai ji Abba yace mungama school dinan zai xhanza mana wanine, to mezaki zauna kiyi har next year, wlh nima dazaran na sasanta da superman dina aure zamuyi abunmu na cigaba da school din a dakina" tsaki Islam tayi ta ijiye wayar tace "kinga yaki picking ko" gwalo Farida tayi tace "ke dalla chan ki kyaleshi idan aka samuku rana yau ai automatic soyayya ce zata wani kara kulluwa" harara ta wurgamata tasake dariya tareda yin wurin kofa tace "kinga bari naje na debo mana abincin mu a flask dan dazaran iyaye sunzo bamu sake sauka kasa ina zasuga Amarya kafin aure" takalmi ta dauka ta jefamata da sauri tafita daga dakin tana dariyan shakiyanci rabon datai dariya haka harta manta. Wuraren sha daya da rabi suka iso Babban Khaleel da Baban Eesha sai Kuma Abba da wasu abokana yen shi biyu duk sunci manyan kaya, da kanshi baban Islam yamusu iso nan suka zazzauna afalo ana gaishe gaishe kafin Mum da Anty Hindu da Maman Miemie suka fito aka gaggaisa sanan aka gabatar musu da abinci sukaci suka sha sanan aka fara magana. Basu boyema Baban Islam komi akan Khaleel ba ba karamin tausayin shi yajiba, nan ya yarda ya amince yabasu Islam yace ai tun randa Anty Hindu tafada mai yatura a kamai binciken halin shi Alhamdulillah duk yan anguwa sunce mutumin kirki ne ga zuwa massallaci. Aka fara maganan sa rana wata biyu yace amma Abba ya roki alfarma abarshi wata daya sabida suna son Yaron yakoma bakin aiki ya dade rabonshi da aiki nan baban Islam ya yarda, Baban Eesha ne yafita ya shigo ga jakunkunan gorori mai gadi ya tayashi dauka da su sweet nan aka ijiye dubu dari kudin nagani Ina so Anty Hindu tawani saki guda. Bayan anyi finalizing everything aka rufe taron da addu'a sanan suka wuce massallaci danyin sallan azahar dagangan suna dawowa suka tafi murmushi akan fuskar kowa. *JARABTA* Maman Abd Shakur 34 & 35 Aika Mum yayi takirasu zama sukayi su biyun afalon Abba yay gyaran murya yace "burin kowani uban ne yaga yarshi ta sami miji dan mutunci yaro mai hankali da addini da hikima, to Alhamdulillahi Ummi nariga namiki miji wanda kika sanshi sosai Muhammad Khaleel" ba karamin bugawa kirjinta yayi ba har saida ta dago kai ta kalleshi ya cigaba yace "mun riga mun gama magana da iyayen shi, an saka rana sati hudu, bayan biki zankudan yi kwana biyu anan yola sanan ku wuce Abuja sabida ya koma aiki, idan kinada any abu dakike so ki fadama Mummy ku sai asiyo miki" Ya gyara zama ya kalli Farida akunyace ta labe abayan Islam tace "Abba nima kwanan nan zan fito da nawa" murmushi kawai Abba yayi yace "Faridan Abba kenan to Masha Allah, Allah nuna mana ku tashi kutafi" atare suka fito daga dakin Farida ta kalleta tadan zaro ido tace "ke waye kuma Muhammad Khaleel nazaci Fahad ne ya turo?" kasa magana tayi sabida wasu hawayen bakin ciki da suka zubomata da gudu ta bude kofar dakinsu ta shiga ta zauna akan gado, Farida ta zauna akusa da ita tace "waye Muhammad Khaleel din?" kwallan daya dan zubomata ta share tace "wani ne fa datunda muka hadu duk inda naje saiya bini kaman maye, yace yana sona ni banason shifa Fahad dina nakeso" Farida tace "to mesa baki fadama Abba baki sonshi ba?" turo baki tayi ahankali tace "kasawa nayi wlh kaman antushe min baki" murmushi kawai Farida tayi tace "lemme not waste my saliver akanki dan ga sonshi nan kuri aidonki, nidai duk randa yazo I will love to meet him o" tashi tayi fuuuu ta dau wayarta ta shiga bayi ta rufe tai dailing number shi harya gama ringing bai dagaba saida ya katse ya kirata back cikeda tsiwa tace "nace ina sonka ne dazaka tura gidanmu?" murmushi yayi sanan yay magana ahankali yace "ai basai kince kina sonaba wife, gangar jikin ki, rohin ki, murmushin ki, kwayar idanunki sun riga suncemin suna sona so mezan jira? Yau dayake fada kikeji shine harda kirana bayan idan nakira ki u don't pick" rasa abinyi tayi hakan yasa ta fashe mai da kuka dan dariya yayi kafin ya sassauta murya yace "please don't cry, how about gobe nazo na lallasheki da kaina" tsayar da kukan tayi tace "Allah inkazo gidanmu saina cirema kafafu" wanan Karan dariya yayi sosai, shiru tadanyi tana sauraron yanda sautin dariyar nashi ke fita kaman Karya dena, dan shiru yayi kaman yasan meke zuciyar ta yace "you like how I laugh, na cigaba?" da sauri ta kashe wayar tana dan murmushi bude kofar tayi tafito daga bayin Farida ta harareta tace "kai Islam keko, kina so kina iskanci hegiya pretender" dauke kai Islam tayi kaman bataji taba tazo zata zauna akan gado filo Farida ta naka mata hakan yasa ta fada gado tana dariya ita kanta mamakin kanta take to Mesa tama kasa fushi. Wuraren biyar na yamma yazo yana sanye da shadda mai ruwan toka sai kamshi yake, Anty Hindu tasa aka shigo dashi saida suka gaisa sanan tabar falon sama taje tasami Farida da Islam zaune tace "ke tashi ki xhanza kayan jikin nan naki Khaleel yazo" ganin Anty Hindu ta tsaya masu akai yasa ta tashi shiryawa tayi cikin simple brown material da akai mata doguwar riga ta daura milk color hijab din gida daya tsaya mata acinya tadan shafa hoda tasa lipgloss tadan fesa turaren Posess sanan ta kalli Farida tace "zomuje ki ganshi fa" girgiza kai tayi tace "ke haka akeyi jeku fara gaisawa tukun anjima zanzo" fita Islam tai daga dakin. Shigowa falon tayi batare data kalleshi ba ta wuce kujeran 2 sitter dake kusa da kujeran daya zauna ta zauna tana gyaggyara hijabin jikinta. Ahankali yataso yazo ya zauna akan kujeran datake ya fuskanceta yana kallon fuskar ta batare dayace komiba, dan dago kai tayi ta kallai, hararan shi tayi sanan ta turo baki tace "katashi kabarmana gidan mu" make mata kafada yayi hakan yasa ta dauke kai da sauri dan wani iri taji, ahankali kaman mai rada yace "I miss you ummina" dan dago kai tayi suka hada ido hakan yasa tasake dauke kai, tagumi yay ya cigaba da kallon ta kaman yau yafara ganin ta, batare data juyoba tace "stop looking at me" girgiza kai yayi yace "I can't" juyowa tayi tace "kabar mana gidanmu kuma" girgiza kai yasake yi yace "I can't" juyowa tayi cike da masifa tace "ninace ina sonka ne dazaka tura aje wurin Abban mu" Ahankali yace "but I love u" yay maganar murmushi kwance kan fuskarshi, ahankali yace "Are you angry with me?" hararan shi tayi ganin yamaida ita wawiya, hannu yasa a aljihun rigar shi yaciro chocolate bude chocolate din yayi yadan matso kusa da ita ya Kalli fuskar ta yace "kinsan ance chocolate na mantar da mutum fushin dayake yi ko" yay maganar yana kallon kwayar idonta... Ahankali Farida ke sakkowa daga stairs sanye da hijab harta shigo falon, numfashin ta taji yana neman barin kirjinta ganin Superman dinta da Islam suna wani irin kallon juna... Cikinsu babu wanda ya lura da Farida, kallonshi Islam tayi sanan ta kalli chocolate din daya bude yana miko mata make kafada tayi tace "I don't want" dan matsowa yay kadan ya sassauta murya kaman me lallaba yaro yace "plzzzzzzz" yanda yaja plz din haka tajishi har cikin ranta ahankali ta mika hannu zata karba girgiza kai yayi batare dayay magana ba ya nuna mata bakinta da yatsa yace "haaa" wai mutumin nan magic yake minne dudda yanda taso tahana kanta kasawa tayi ahankali ta bude bakinta kadan, murmushi yayi yakai chocolate din bakinta yana kallon fuskarta Islam! Farida takira sunanta dawani irin murya da tunda suke bata tabajinta dashi ba, adan rude ta juyo dan yanda Farida takira sunanta saida ta firgita shima ita ya kalla, gyara zama yay sanan yace "Hi how u?" dan wlh yamanta sunan ta, da kyar ta iya kakalo murmushi tace "fine" murmushi yamata sanan yace "don't tell me u two are sisters" Ya kalli Islam sanan ya kalleta ya nuna Islam yace "itace dama Islam din dakike ta bani labari" gyada mai kai tayi tana kokarin danne hawayen dake barazanar zubomata, yay murmushi yana wani irin kallon Islam kaman ya cinye ta yace "I see" dan murmushi tamai sanan tace "bye" tajuya tafara tafara hawa stairs, tashi Islam tayi zata bita dawani irin murya yace "ina zaki My Ummi, we are not done yet baki karbi Chocolate dinba" wani irin hawaye ne mai zafi ya zuboma Farida da sauri sauri tai tawuce dakinsu jin yanda Superman kema Islam muryar dabata sanshi da ita ba, dama yanama magana haka?. Zama Islam tai ahankali ta kallai dauke kai tayi sanan tace "dama ka San Farida ne?" gyada kai yayi yace "yea I helped her once haka dawani thief ya kwace mata jaka and daga nan I think mun sake haduwa twice ko I think, ashema sisters neku, Kinga ko Allah ma wants me to marry u tunda har yasa nasan yar uwarki" tashi tayi tsaye tace "bye" da sauri shima ya tashi yace "but I don't wanna go now" hawaye ne yacika idonta tadan kalleshi sanan ta dauke kai, ahankali yace "okay I will go, Plz don't cry" dan matsowa yayi ya tsaya a gabanta ya mika mata chocolate din yay murmushi yace "u have to eat it before i go" bakinta yakai hakan yasa ta kawad dakai, tsayawa yay yana nazarin fuskarta kaman something is wrong ahankali yace "Are you okay?" murmushi tayi tadan bude baki hakan yasa yay wani murmushi daya bayyana fararen teeth dinshi yasaka mata chocolate din abaki ta gutsiri kadan sanan ya cire yana murmushi, dadan sauri tabar wajen murmushi yayi saida yaga tai sama sanan yafita daga dakin tareda kai sauran chocolate din bakinshi. Ahankali ta bude dakinsu jikinta yay mugun sanyi ganin Farida tsaye a tsakar dakin idanunta sunyi jajir alamun taci kuka, ahankali ta maida kofar ta rufe ta shigo dakin tace "Faree wlh ban.." hannu Farida ta daga mata tace "banason naji komi daga gareki" nuna kanta tayi in so much pain tace "nizaki yaudara? Ni Islam ur own blood, ur only sister, daga nace yaje ya taimaka miki ranan a school shikenan har kin nunama su Abba shi aka samuku rana ko" share hawayen daya zubo mata tayi tace "no wonder ko waya zakiyi dashi bakiyi agabana, ko dazuma bayi kika gudu sabida karnaji mekuke cewa, duk idan nai maganar shi saidai kiyita cemin na manta dashi, na shareshi, my God u fooled me Islam" sosai Islam ke kuka tana girgiza kai tace "bahaka bane wlh" ta matso kusa da ita zata tabata wani tsawa Farida ta daka mata tace " don't touch me you cheat! Mara Imani, mai bakin hali, trusting and liking u sune biggest mistake din danayi arayuwata wlh, mai bakin hali kawai kamar uwarta" tsayar da kukan datake tayi ta kalleta tace "Faree dan Allah karki kara zagin min mama kinga tariga tamutu ba kyau" nunata Farida tai da yatsa tace "an zagadin, ance uwarki kika biyo da wanan bakin halin" mari Islam ta kaimata abaki hakan yasa Farida ta taba bakinta jini tagani hakan yasa wani zuciya ya dauketa da haushin kwace mata superman datayi ta chakume Islam, da sauri Islam data mugun tsorata dan ganin idanun Farida ta rike hanun Farida inda ta chakumeta tace "yakuri dan Allah bada gangan na mareki ba" buga Islam tayi da bango, Islam tai wani wahalallen kara, duk iya karfin ta takasa ture Farida, kara Fizgo Islam tayi daga bangon tawani nakata akasa kan center carpet din tsakiyar dakin ta finciko gashin Islam tanaja, azaban da Islam taji yasa ta dana mata cizo a hannu da sauri Farida tasaki gashin nata tana duba hanunta, azabure Islam tamike zata gudu waje Farida ta tadiyota da kafa jikake dimm tafadi tai kara, Farida da zuciya tariga ta debeta ga shaidan daketa zugata tai kan Islam tahau ruwan cikinta tana kima kaman ta sami kayan wanki, da kyar Islam ta iya kai hannu tana kokarin kama gaban rigar ta. [6/18, 10:30 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 40 & 41 Wani mugun kallo ya watsama Faridan batare daya damu da maganan mutanen wajen ba ya juya zai tafi, kafarshi Islam ta rike gam gam tareda daura fuskarta akan gwuiwar shi tafashe da mugun kuku harda shesheka tace "bakace kana sona ba, inhar kanasona son gaskiya, so sabida Allah to ka yarda ka auri Farida, dan girman Allah do it for me" fincike kafarshi yayi yakara juyawa zai tafi da sauri tabishi da gwuiwa ta kama kafarshi again gam sanan ta dago kai ta kallai suka hada ido, ahankali ta saki kafarshi tahada hannayenta tace "inhar kanasona da gaske, ka aure ta karta kashe kanta, yar uwata ce bazan taba yafema kaina ba idan wani abu yasa metaba, dan darajan Allah am begging you" yanda take kuka tana rokanshi yasa ya tsugunna ya dagota sama kallon cikin idonta yay yace "stop crying" ahankali ta tsayar da kukan tana kallon fuskarshi yace "abinda kikeso kenan na auri Farida?" Ya tambayeta "jama'a zataci shinkafar fa" da sauri Islam ta juya ganin Farida na kokarin kai shinkafar bakinta ta daga hannu tace "stop, stop Faree ya yarda, zai aureki" kallon ta Farida tayi sanan ta kalli Khaleel din tana goge hawaye, Islam ta kallai tace "please tell her ka yarda" yadade yana kallon fuskar Islam din kafin ahankali ya juyo ya kalli Faridan da kyar ya iya cewa "yea na yarda I will marry u" murmushi Islam tayi tana goge hawayen dataji ya zubo mata, Farida takara goge hawayen dasuka ki dena zuba tace "and kayarda dazaran na sakko zamuje gida direct ku fadama Abba kun yarda" yadade yana kallon fuskar ta sanan yace "yea, now come down" yasa hannu ya danne mata ladder, murmushi Farida tayi ta kabar da shinkafar rice din dake hanunnata tafara sakkowa saida ta sakko kasa ta fada jikinshi ta rungumeshi tana kuka sosai tace "I love you so much Mk, wlh Ina mugun sonka, Allah ya jarabceni da sonka, I love you my superman" ihu mutanen wajen sukeyi suna tafi da sauri Islam ta sanya hijabin ta tarufe fuskarta jin kuka yazo mata sosai, da sauri ta juya zatabar wajen karaf taji anrike hanunta hakan yasa ta dago da rinannun idanunta taga Khaleel ne wanda Farida ta shige jikinshi tana kuka yana kallon kwayar idonta, fizge hanunta tayi da gudu tabar wajen tai bakin titi Keke napep ta tare ta shiga ciki tacemai suje sosai take kuka mai Keke na tambayan ta lpy. Cireta daga jikinshi yayi batare daya kalli fuskarta ba yace "mutafi" yana gaba tana biye dashi suka karasa har wajen motar ya shiga itama ta bude gaba ta shiga sai murmushi take tana kallon fuskarshi kaman yau tafara ganinshi, kunna motar yayi sukabar wajen, a kofar gida suka ganta zaune akan bencin mai gadi, parking yayi suka fito ta kalli Farida tace "dama kunake jira mutafi wurin Abban" da sauri ta bude gate ta shiga batare data kalleshi shiba Farida ta kallai tace "muje my superman" Atare suka shiga cikin gidan direct falon Abba sukayi suka shiga da sallama, yana zaune tareda Mum dake tayashi arranging some business papers. Daga Abba har Mum din binsu sukai da kallo ganin yanayin idanun yaran nasu. Gaban Abba Islam taje ta tsugunna ahankali tace "Abba dan Allah kahada Farida da Khaleel aure bada niba please Abba, don't ask me why amma dan Allah kahada su aure ni banaso" tunda take maganan Khaleel yay folding hanunshi akirji yana kallonta idanunshi sunyi jaa, with so much confusion Abba ya kalleta sanan ya kalli Farida da Khaleel dake tsaye sanan yadawo da kallonshi ga Islam yace "wai meke faruwa ne Ummi, wanan wace irin magana ne kikazomin dashi haka, meke faruwa?" gyara zama Mum tayi tace "Alaji zan fadama" dan shiru tayi tana kallon fuskar Islam sanan ta kalli Alhajin tace "ni dama ban fadamaka bane sabida banason kaga kaman na tsangwami Islam ne, ka tuna fadan da ita da Farida sukayi kwanakin baya, to ashewai Islam ce bayan Farida tagama bata labarin soyayyar ta da Khaleel shine Islam taje ta kwacema Farida dake son Khaleel sosai Khaleel" shiru Abba yayi yana nazarin maganar Mum sanan ya kalli Islam yace "haka abin yake Ummi?" ahankali ta gyada kai ganin yanda Abba ke kallonta yasa tace "am sorry Abba" batare daya kalleta ba yakira Farida, ahankali Farida tazo gabanshi ta tsugunna Abba yace "haka zancen yake?" gyada kai tayi sanan tace "Abba inason Khaleel sosai shine ta kwacemin shi" tafashe da kuka tareda daura kanta akan cinyar Abba, shiru Abba yayi sanan ya kalli Islam ahankali yace "kinason Khaleel ko baki sonshi, tell me the truth?" ahankali ta juya ta kalli Khaleel da ita yake kallo sanan ta kalli Mum data jeho mata wani uban hararan, kallon Abba tayi sanan ta girgiza kai tana kokarin hadiye kukan dake zuwan mata tace "a'a bana sonshi" da sauri Abba yace "dama kinyi hakane dan ki bakan tama yar uwarki rai ko?" da sauri ta girgiza kai, dago kai Abba yayi ya nunama Khaleel kujera, kasa zama yay akujeran ya zauna akasa, ahankali Abba yace "Wakake so cikin su wazaka aura? Banason tauyema kowa hakkin sa, yaran zamanin nan kuncika matsala wlh, ka fadamin gaskiya Khaleel wakake so acikin su wazaka aura?" kallon Islam yayi hadamai hannu tayi sanan ta girgixamai kai tana hawaye da sauri ya dauke kai, ya kalli Farida dake kallonshi kirjinta na bugawa idanunta sun cicciko da hawaye ahankali yace" "Farida" murmushi Abba yayi yace "shikenan Allah Sanya albarka, Allah muku albarka dukan ku saikaje ka sanar da iyayenka" Ahankali yatashi yafita daga dakin, sauka yayi yafita daga gidan ya shiga mota ya daki sit din motar yafi sau dari, wani bakin ciki mara misultuwa yaji yanaji da kyar ya iya tuka kanshi yakai gida. Abba ya kalli Islam yace "mesa kika aikata irin abin nan Islam?" Mum tace "Alaji bawanan ma kadai ba da Farida tamata magana shine fa takifa mata mari ranan harda fasamata baki, haba haka ake abu a duniya, daga yar uwarki tabaki labarin saurayin ta saikibi takasa kije ki kwace mata shi, kasan shi namiji wawane hala saisa lokacin ya biyemata ya yarda har aka turo, yanzu dai alhaji tunda komi yay daidai basaika hukuntata ba nariga na yafemata, faridama ta yafe mata shikenan magana ta wuce a cigaba da shagulgulan biki zamu aurar da ya" Ahankali Abba ya sauke ajiyan zuciya yace "hakane kutashi kutafi" fita sukayi daga dakin Farida ta bangajeta ta shige dakin Mum binta tai da kallo kafin ta wuce dakinsu a daddafe ta fada gado taci kukanta tai bacci. Manya manyan hajiyoyi masu gyaran jiki Mum ta daukoma Farida nan fa aka fara gyara amarya ciki da waje idan kunga Farida en tai mugun kyau bakin fatarta har kara walkiya take, ko tak baya hadata da Islam idan Islam zata wuni tana mata magana bazata kulata ba hakan yasa kullum Islam na daki, Maman Miemie nema idan tazo aiki takan dan kawomata Miemie ta dauketa suyita wasa, Khaleel bai kara zuwaba, Farida bata damuba tunda wani zubin yanadan picking call dinta suyi magana daya biyu ya katse. Yau saura sati daya biki yaune aka kawo akwatin Farida saitin goma sha biyar, su Umma da Mujiba datai kini kini da rai dawasu kawayen sune suka kawo inda Mum da kawayenta lecturers suka tarbesu akaci akasha, akasha guda, dazasu tafi aka basu tukuici. Da daddaren ranan Anty Hindu tadawo daga dubai da kayayyakin daki data siyo anata murna Koda Islam tazo gaishe ta kallonta tayi daga sama har kasa tace "ke ciwo kikayine haka wanan rama" murmushi tayi tace "eh amma naji sauki" tsaraba Anty Hindu tabata sanan ta wuce dakinsu ta kwanta. Washegari da safe Abba yafita da wurin kasancewar yanada aiki, Mum ce ta turo akwatinan Farida ta shigo dasu dakin Anty Hindu one by one tace "ga akwatin Farida nan Anty?" kallonta Anty Hindu tayi cike da mamaki tace " Farida Kuma wace Faridan?" kama haba Mum tayi tace "au Abban su bai fadamiki ba, ai Anty Kwai ne yafashe gaskiya ta futa, ashe fadan nan da yaran nan sukayi kan Khaleel ne, wai Islam kwacema Farida Khaleel fa tayi, shine da kanshi Khaleel din yay tattaki yazo yafadi ma Abba shifa Farida yakeso ba Islam ba" tunda take maganar Anty Hindu ke kallonta tace "Khaleel din yace hakan" "eh" murmushi Mum tayi tace "ga akwatin ki duba kisa mana albarka" tabe baki Anty Hindu tayi tace "nayafe fitanmun dasu daga daki" tabe baki mum tayi tafita dasu tana kunkuni tace "yar bakin ciki kawai" sosai Anty Hindu taji ranta ya baci da zancen, wanan wani irin abune. Family Khaleel kodaya fadan musu abinda ke kasa basu wani damuba kasancewa sunsan Faridan dama. Yau thursday da kyar Yusuf ya tirsasa Khaleel yatashi suje gidan su kaima Farida kudin fati, da wasu yan abubuwa, da kyar yatashi ya shirya dan wlh bayason yamaje gidan balle yamaga Islam shiryawa yay cikin shadda Light brown shadda daya mugun amsan shi ba karamin kyau kayan sukamai ba sai uban kamshi yake, fara tsayawa sukayi sukai isha'i sanan suka tafi. Farida taci uban lalle dan gobene walima tasanya wata atampa da tasha uban stones, kallon Sameer dake kusa da ita tayi ganin kiran Khaleel ya shigo wayarta tace "jeka cemusu su shigo falo Ina zuwa" fita yay da gudu, ta zauna agaban mirro tana shafa hoda. Ahankali take sakkowa daga stairs sanye da doguwar riga na atampa jada baki ta daura gyale black akai, so take taje kitchen ta dafa Indomie kamshin turaren dataji yasa ta daga kai hada ido sukayi daidai suna shigowa falon hanunshi rike da Sameer tsayawa yay chak yana kallonta hakan yasa Yusuf ya Kalli inda yake kallo, da sauri takarasa sakkowa ta shiga kitchen, jingina tai da fridge ta dafe kirjinta jin wani abu ya tsayamata awuya, tayi kusa 20 sec ahaka sanan ta shiga store ta dauko Indomie guda daya da egg daya tafito, kamshin turaren shi taji da sauri ta daga kai ta kallai suka hada ido ganin ya kulle kofar kitchen din yasa ta ijiye kwan da Indomie akan fridge tajuya da sauri ta bude kofar dazai satada da backyard tafita, babu haske sosai a backyard din dan kwan fitilar wajen ya mutu hasken wata ne kawai ke haska wajen, tafiya ta soma yi da sauri zata zaga, hanunta taji ankama da sauri ta juyo fizgota yayi da karfi fuskarshi a daure yasata abango yana wani irin kallon fuskar ta, ahankali yake matsowa har ya matso kusa da ita sosai wanda gab din tsakanin su baifi tsawon yatsa ba dan tanajin saukar numfashin shi, sosai kirjinta ke bugawa hakan yasa ta kawad da kanta gefe, ahankali yakai hannu ya kama habarta ya juyo da kanta kin kallonshi tayi ta saukar da idanunta kasa, hanunshi daya ya daura a bangon wajen dayan kuma na habar ta murya chan kasa yace "look at me, kin kasa kallonane sabida kinsan u are forcing me to do dis?" sosai kirjinta ke bugawa, lumshe ido yayi sanan ya budesu akanta ahankali yace "bakyacin abinci ko, look at your neck" yasa hannu yana shafa kashin wuyarta buge hanunshi tayi hanun nata ya kama da sauri yadan matse hakan yasa tai yar kara tana yatsine fuska yace "it hurt ko?" gyadamai kai tayi, dan murmushi yayi yace "zuciya hurt more than this sau dubu dabara sabida abinda kika sata tayi" yakarashe maganan tareda sakin hanunta yana nuna mata zuciyar shi da yatsa, dan shiru yayi yana kallon fuskar ta dan har yanzu taki yarda suhada ido, hannu yakai yarike habarta yadaga kanta kaman mai rada yace "kinfiso na auri yar uwarki ina dawainiya da sonki araina ko" shiru tamai, kasa daurewa yayi ahankali yahada goshin su yana kallon idonta, hakan yasa itama ta dago idanunta dasuka cika da hawaye ta kallai bakinshi taga yay motsi yace "I love you Islam" fashewa tai da kuka sosai, hannu yakai ya share hawayen dake zubowa batare daya cire forehead dinshi daga nata ba, ahankali ya saukar da yatsar tashi akan lips dinta, shafa su yayi yana kallon idonta, hannunta tasa ta bigemai hannu, lumshe ido yayi ya maida fuskar shi ta gefen kunnenta ta, goga mata sajen shi akumatun ta yayi wani yarrr tajj yabi kowani gashin fatarta sabida yanda gashin sajen suka tattaba fatar, kokarin tureshi tafara yi hakan yasa ya cigaba da gangaro da sajen nashi har wajen lips dinta, ahankali ya juyo da kanshi daidai ta wajen hakan yasa lips dinshi yahadu da nata. Wlh kun daman saisa namuku typing. Gaskiya Naga Farida tafi fans, lol. I love guys. [6/22, 7:53 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 47 & 48 Yakamo hanunta yarike gam yana yar dariya, turo baki tace "kasaken" make mata kafada yayi yaja hanunta har gaban wardrobe, wani madaidaicin black hijab yaciro ya warware yasaka mata sanan yarike mata hannu ya kalleta yace "banason ana kallon mu goody bag dina muje naraka ki" akunyace ta dauke kai, tare suka fita daga dakin suna zuwa dining tafara kokarin kwace hanunta sabida mutanen datagani su kusan five ga manyan kuloli kusan 5 dasuka ajiye a tsakar falon, kin sakinta yay ahaka suka shigo falon, kasa daina kallonta su Ihsan sukayi, tana tsaye agefenshi tadan kallesu tace "ina kwanan ku" manyan matan guda biyune suka amsa da lpy lau, harara ya watsama su Ihsan yace "ku baku iya gaisuwa bane" atare suka taso sukazo inda take tsaye Ihsan ta mika mata hannu tace "ni sunana Ihsan his sister, welcome to our family" ahankali tai murmushi ta bata hannu, Ilham ma tace "sunana Ilham welcome to the family" murmushi tamata tace "thank you" Fa'iza ma tace "nice Fa'iza welcome and u are very very cute wlh" murmushi tai tace "thank you" hanunta Ihsan tarike tace "ga masu lalle nan mum tace amiki idan angama za'a kaiki chan family house ne, muje afara yimiki sai muyi dishing abinci kiyi breakfast ko" gyada musu kai tayi sukaja hanunta hakan yasa yasaketa, dan juyowa tai ta kallai tai raurau da ido, girgiza mata kai yayi alamun no, ya kalli Ihsan yace "ku kullan min da ita kuma, ko kuda karku bari ya tabata, bari naje" hanun yadaga mata alamun bye kunya taji yakamata ta dauke kai da sauri su Ihsan sunata mata dariya. Harara ya balla musu sanan ya juya yafita daga dakin yana kallon fuskar ta. Lalle aka fara zizara mata, daya nayin na hannuwa dayar kuma na kafafu, Ihsan ta debo abinci tana bata abaki, Ilham kuma da Fa'iza sun kwanta akasa suna bata labarin Khaleel suna tafawa suna ihu, bakaramin tunamata da Farida sukayi ba, sosai taji tana kewan yar uwan nata da kyar ta iya tahana kanta yin kukan. In less than awa daya lallen ya bushe da aka mata sabida sanyin ac dakuma fanka dasuka kunna, wankewa akayi ba karamin kyau lallen amaryan yamata ba, sanan aka wanke mata gashi akai using handryer aka busar dakan sanan aka fara yaryada mata kitso yan mini mini. Sai Wuraren azahar suka gama sanan suka tafi yarage daga ita saisu Ihsan sosai tasaki jiki dasu sabida yanda suketa janta jiki kaman sun santa, sata tai wanka sukayi suka shiryata cikin wani ubansu lapaya, Fancy glamour suka dauko ta chanchara mata makeup din amare idan kun ganta bazakuce itabane, sanan suka kira Umma cewa sun gama, Umma tace "to, yanzu za'a zo ataho da ita". Anty Hindu ne dawasu mata duk sunci gayu sukazo gidan, rungume Anty Hindu Islam tayi zatai kuka ta girgiza mata kai, sanan ta lullubeta mata fuska aka dauketa suna wakoki aka tafi da ita gida fuskarta a rufe, ta lapayan ta take hango yanda gidan ya cika da mutane sai taga gidan su kaman ba biki akeyi ba, wani babban falo taga an shiga da ita an zaunar da ita akan kujera Anty Hindu ta zauna a gefenta tana gaggaisawa da mutane anata guda, wata matace dataga suna kama da Khaleel taci gayu sosai tazo gaban su, Anty Hindu tace "ga maman mijinki nan" yaye lullubin fuskarta Ammi tayi, ahankali tasa hannu ta daga habarta kasa dago ido tayi sabida kunya hawaye taji ya gangaro, murmushi Ammi tayi tace "masha Allah daughter" sababbin kudi taciro ajaka yan 500 tadinga mata manni ana guda har saida kudin yakare sanan takoma ta zauna, haka ma Umma tazo ta wanketa da liki, duk wanda yazo Anty Hindu tana fadamata waye, sosai aka dinga ihu ana guda sanan aka tafi da ita bangaren Goggo, Goggo Kam harda rawa sabida murna tai manni tai manni har saida duka kudinta ya kare, wata malama tagani ta tashi tai musu wa'azi da addu'a sanan Goggo tace "to kowa yatafi abarmata amaryan ta tahuta" haka duk aka watse ya rage Anty Hindu da Ammi da Umma, tashi sukayi suka shiga uwar daka Goggo sunata magana, muryan Goggo taji tana cewa gaskiya anan zata zauna. Fitowa sukayi Ammi tazo ta dafata tace "kinajin yunwa insa akawo miki abinci daughter?" akunyace ta girgiza kai, murmushi Ammi tai ta kalli Anty Hindu tace "daughter na badai kunya ba" dariya Anty Hindu tayi daga nan duk suka fita suka basu wuri, sosai Anty Hindu tamata wa'azi da fada akan tabi mijinta, sanan tacemata Khaleel yamata sabon akwati set daban daban har 6, Abban ta duk yahada an wuce mata dasu gidanta na Abuja. Sai bayan sallan Isha Anty Hindu ta tafi ba karamin kuka tasha ba hakanan ta hakura tai shiru gyangyadi tafara yi akan kujeran Goggo sabida yanda tagaji gakuma kukan datayi hakan yasa Goggo tace "tashi ki shiga ciki ki kwanta abinki ki huta kinji, sannu yarnan yan iskan yaran nan duk sun wahalar dake" murmushi tai dan hakanan taji Goggo ta shiga ranta gatadai tsohuwa amma akwaita da tsafta, "au bazaki tasoba" Goggo tai maganar tana kokarin tashi daga kan tabarmar data shimfida a tsakar dakin, kamo hanunta tayi tace "muje ki kwanta bakisan bacci nada amfani ga lafiyar dan Adam ba" kofar uwar dakanta ta bude da gadon ke agyare tsaf tace "jeki kwanta abinki zanga dan kan uban dazaizo yafita dake, jekiyi baccin ki saida safe kinji yar albarka" gyada kai tayi sanan tace "saida safe Goggo" kwanciya tayi akan gadon da aka gyara tsaf dakin sai kamshin turaren wuta yake within 2 min bacci yay gaba da ita, Goggo dake kishingide akan tabarma taji ana kokarin bude kofar ta tashi tayi ta zauna da kyau tana wawware ido, Khaleel ne ya shigo sanye da doguwar jallabiya sai kamshi yake yawani daure fuska yace "ina matata? Daga barinta tazo gidan naku shikenan kuma bakusan ku komar da ita inda kuka daukotaba?" ko kallonshi Goggo bataiba taja filo abinta takara kwanciya sanan tace "jeka tambayi uwarka, bata fadama daga yanzu anan gida zata zama ba, to saikun koma Abuja ne zata tare a gidanka" karaso wa ciki yay yace "nida matar tawa lallai nema" yazo zai wuce yay bedroom Goggo ta mike tsaye da sauri tasha gabanshi ta rike kugu hakan yasa yaci birki yana kallonta cike da bacin rai, dariya tayi tarike haba tace "mara kunyar banza, fitarmin daga daki tunda bakai ka ginamin ba wlh kona hadaka da ubanka" ganin Goggo ta daure babu alamun wasa tawani rike kugu yasa yajuya yafita daga dakin rai abace, Goggo tarakashi da dariya sanan ta maida kofa ta rufe harda saka Sakata tace "fitinannun yara" kwanciya tayi abinta rai fes tace "dan kanuba to yarinya sai tasha gyara sanan za'abaka, idanma nabari ka kara sata a ido ba sunana Lami ba" lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya. Direct part din Ammi yawuce duk ranshi a dagule Yusuf yagani zaune afalo yana jiran Ihsan tagama dafamai Indomie dayace tadafamai, yana ganinshi ya gimtse dariyar datazomai, ko kallonshi baiyi ba ya shiga bedroom din Ammi wata kawarta ya tarar tana magana da ita hakan yasa yaje kusa da ita ya zauna, sallamar matan tayi sanan ta juyo ta kalleshi tace "Ya akayi Son?" da kyar ya iya cewa "Ammi wai kekika cema Goggo karta bari Islam tabini anan zata dinga kwana" Ammi taso tai dariya da kyar ta saita kanta sanan ta kallai tace "eh nafiso kawai ran Sunday idan duk mun tafi Abujan basai ta tare wajenkaba, yanzu ga duka family anan mezataje tai ita kadai achan gidan kadaici zai isheta mana" zaiyi magana tace "ka bacemin daga nan I have alot of things to do" tashi yay yafita daga dakin duk ranshi acinkushe ta gefen ido yaga Yusuf ya ijiye Indomie hanunshi yanamai dariya ciki ciki haka yay kaman bai ganshi ba yana zuwa dai dai inda yake yadau plate din Indomie yace "wlh bazaka ci shiba" Yusuf ya kwalama Ammi kira yace "Ammi kinga wai akaina zai huce takaicin shi" da sauri Khaleel yafita yay part dinsu ya kulle kofa ya ijiye Indomie anan kan kujera yawuce bedroom yafada kan gado kasa bacci yayi sai juye juye yake daga baya yatashi ya shiga bayi kawai ya dauro alwala yazo ya kabbarta salla. Bari muleka Faridan mu. Idan kunga Farida saikun tausayamata ta rame sosai, da kyar Mum kesata taci abinci, bata da aiki sai daukar waya taita dailing number superman da baya shiga ko kadan, Abba kullum wa'azi yake mata da fada, Mum dai duniya yay mata zafi hakan yasa wani zubin idan Farida tafara kuka itama jonata takeyi suyi tayi tare, ba irin Allah ya isan da basuma Islam ba sabida bakin ciki. Hakanan yau Wednesday taji tanajin fita kotadan ga rana, doguwar riga baka tasaka ta yana gyalen ko hoda bata shafaba tafito daga gidan danko Mum bata fadimawa ba, keke napep ta tare tace "yakaita Infinity gym" ta shiga ciki yaja har wajen yana ijiyeta ta ciro kudi ta bashi, sucurity ya bude mata ta shiga ciki, wani kukane yazo mata ganin treadmill din data taba ganin superman dinta akai, da kyar ta hadiye hawayen ta karasa wajen eatry din, order strawberry smoothie tayi ana kawomata ta karba tareda bada kudin tanata kallon smoothie din tana tuna ranan da superman dinta yasaimata yabata ahankali tace "menama Islam haka datamin irin wanan abu? Mesa nakasa cire sonshi araina why, please God inaso na manta dashi please" share da kwallan daya zubomata tayi tadau smoothie zatakai baki da sauri ta ijiye ta kife kanta akan table din tana wani irin kuka mai cinrai, "hey is everything okay" dago kai tayi suka hada ido da Yusuf dake sanye cikin sport wears hanunshi rike da cold bottle water, share ido tayi ta juya da sauri ta duba ko suna tareda superman dinta ne taga shikadai ne, juyoda kai tayi ta harari Yusuf tace "wat are you doing here?" kujera Yusuf yaja ya zauna yana kallon fuskarta yace "nothing banmasan kebace" tashi tsaye tayi tajuya zata bar wajen dan wani irin haushin Yusuf takeji da sauri yabita juyowa tai cike da masifa tace "kadena bina harda kai aka hadu aka yaudaran, Islam Islam" takira sunanta saikuma tajuya tafita daga wajen da sauri jin wani kukan ke zuwan mata suna fita Yusuf yasha gabanta yace "hear me out, kidena blaming sister ki wlh batada laifi, Allah kuwa trust me" bakin gyalen ta tasa akan fuskar ta tafashe dawani kukan, jitake kaman zuciyata zai fashe, ba karamin tausayin ta Yusuf yaji tabashi ba ya tsaya kawai yana kallonta da kyar tai shiru ta kalli Yusuf da rinannu idonta tace "koma menene at least for d sake of ni yar uwartace, tasan yanda nake sonshi saitaki auren shiko" ta dago kai ta kalli Yusuf tace "kataba son wata?" girgiza mata kai yayi alamun a'a hakan yasa tadanyi murmushi tace "bazaka taba iya gane wat am going through ba, Islam" tasake kiran sunan Islam tana wani irin dafa kirjinta da sauri tajuya tabar wajen akan bakin titi ta tare napep ta shiga tana goggoge ido da bakin gyale. Sosai Yusuf yaji jikinshi yay sanyi wanan wani irin sone, yanda take haukan son Khaleel dinan shikuma haka yake haukan son Islam, oh Allah kayaye ma wanan baiwar naka wanan son maso wanin, ahankali ya juya ya shiga ciki. Islam dai sai gyaran jiki ake mata in and out, Goggo yanzu kulle kofa take idan baka kwankwasa ka fadi sunanka ba bazata taba budewa ba duk dan kar Khaleel ya ganta take wanan. Dayake yau asabar yasa anata shirye shirye kowa na hada kayanshi dan gobe zasu tafi, Wuraren 11 Khaleel yafito daga part dinsu yana sanye da jeans black da blue t-shirt mai gajeren hannu, fuskar nan tashi adaure har wata yar raman dole yayi sabida rashin ganin Islam, dakin Ammi yayi yasameta zaune kusa da Dad datake hadama tea gaishe su yayi suka amsa, Dady ne yace "mekake so son" kallon fuskar Ammi yayi hakan yasa ta dauke kai ahankali yace "dama Dady inaso Ammi tasa Islam muje ta tayani hada kayan mune nachan gidan tunda gobe zamu tafi" Dady ya Kalli Ammi yace "kiramai matarshi tazo sutafi ta tayashi mana" Mum zatai magana Daddy yace "ki kirata nace banson jin komi" murmushi Khaleel yayi hakan yasa Ammi ta watsamai harara sanan ta wuce tafita tai dakin Goggo saida tai magana sanan Goggo tabude ta shigo Islam dake sanye da riga da sket nawani soft material mint green dake zaune rike da wayar Ihsan tana karanta wani novel tace "dauko Hijab dinki kizo Islam" ajiye wayar tayi tadau hijab Goggo tace "ina zata?" "Kiranta Alaji yake" black hijab tadaura akan kayan tabi bayan Ammi har falo, tunda ta shigo yake kallonta ganin yanda fatarta har wani kyalli take takara haske, dudda tasaka hijabi bai hanashi ganin yanda tawani kara cikowa ba tai fresh like honey wine, gaida Abba tayi cikeda girmamawa tana kallon Khaleel ta gefen ido dudda tadanyi kewanshi amma taki Koda kallonshi balle ta gaidashi, Abba ya nuna mata Khaleel yace "kuje kuhado kayanku na dayan gidan dan gobe da safe zamu tafi" ahankali tace "to daddy" fita Khaleel yayi batare daya kalleta ba hakan yasa tabi bayanshi kirjinta nadan bugawa, mota ya shiga hakan yasa ta bude gaban motar ta shiga ta zauna tarufe, kunna motar yayi suka fita daga gidan su aranta tace "nan da nanne bazai iya zuwa da kafaba, lazy fellow" horn yay mai gadinsu yabude yay parking yafito ya shiga ciki saida tai kusan 2min a motan sanan tafito jiki duk asake, ahankali ta bude kofar ta shiga falon, da kyar ta iya daga kafa takai tsakiyar falon ta tsaya ganin bata ganshi ba, tabaya taji anrungumeta hakan yasa saida tai yar kara sabida tsoro, tsamtsam ya rungumeta yakawo kanshi ta wurin kunnenta yace "I miss you" juyo da ita yay yakai hanunshi yay cupping fuskarta ya kalli cikin idonta yace "did you miss me" dan murmushi tai sabida yanda yay maganan ta dauke kai, zama yay ya daurata akan cinya yana kallon fuskarta yace "waye lazy fellow?" adan rude ta kallai ta dafe kirji, ganin yanda yake kallonta yasa ta tashi da guda tana dariya tai hanyar bedroom tace "bafa dakai nakeba" harta zauna akan gado taji yabude dakin da gudu ta tashi zata shiga bayi ya rikota tabaya tareda cire hijabin jikinta ya matseta yana kallon idonta yace "Wana kama?". [6/22, 7:53 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 49 & 50 Dan dariya taji yazo mata, kawad dakai tayi sanan tace "sorry" ahankali, kamo hanunta yay ya zauna akan gado ya daurata akan jikinshi yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "did you miss me?" daura kanta tayi akan hanunta akunyace tace "uhm" bakinta tarufe da sauri dan wlh batasan lokacin da maganan yafito ba, hade kansu yay wuri daya ya hade hannayenshi biyu ta bayanta yana dan jijjigata akan kafarshi, murya chan kasa yace "banjiki da kyau ba" dan dago kai tayi ta kalleshi suka hada ido batare data cire idonta daga kanshi ba ta sanya hanunta ta baya ta bige hanunshi ta tashi da gudu ta tsaya abakin kofa sanan ta juyo ta kallai ta gyadamai kai kaman yanda yara suke sanan tace "yea I miss yhu" bude kofa tai tafita da gudu tai kwanciyan ta afalo akan dogon kujera tareda daura filon kan kujeran akan fuskarta. Alamun tahowar mutum dataji yasa tadan zame filon kadan daga kan fuskarta ta kalleshi maida filon tayi da sauri ganin sun hada ido kirjinta na bugawa sosai, zama yay ya dauki kafafun ta ya daura akan cinyarshi yana mata waiwayi akafa, motsi ta dingayi tareda kara rike filon ta danne fuskarta aciki, jin bakinshi datayi akan babbar yatsar kafarta yasa taji wani yarr batasan lokacin data saki filon yafadi akasa ba, kasa daure yanda yake sarrafa yatsun nata yake ta mirgina ta kifa tareda daga kafafun nata sama hakan yasa sket dinta yay kasa kafafun suka bayyana ta lumshe ido tana cuccusa fuskar ta acikin kujera, ahankali ya kamo kafafun ya kwantar sanan ya kwanto ta bayanta yakai bakinshi saitin kunen yakira sunanta "Islaaam" yanda yaja sunan yasa takasa daurewa saida tabude idanunta dasuka kankance ta kallai, tashi yay ya zauna ya sanya hannu ya dagota itama ta zauna tana lumlumshe ido, hanunta yakama yarike gam ahankali yace "ina sonki dayawa Islam please don't ever leave me, I love you sama da yanda kike tunani, u know something" kai ta girgiza mai tareda kwantar da kanta kan kafadar shi, kanshi ya daura akan goshin ta yasanya hannayen shi yay cuddling nata very tight sanan yadan sauke ajiyar zuciya yace "are you fine?" gyada mai kai tayi, ahankali yasake sauke ajiyar zuciya yace "nai mafarkin kine jiya saisa nasa Abba yace kiboyini nan, I just wanted to know idan kina lpy" lumshe ido tayi akan kafadar nashi tana kara shakan kamshin dayakeyi datake mugun so cikin siririyar muryarta tace "mafarkin mekayi?" murmushi yay tareda kissing forehead dinta yace "it doesn't matter now, all I want you to know is I love you very much Islam" da sauri ta maida kanta kirjinshi tareda lumshe ido sabida yanda yakesa takejin kunya, ahankali yaciro kanta daga kirjinshi yana wani irin kallon fuskarta bude ido tayi kadan ta kallai da sauri ta kankame idon ganin ita yakema wani irin kallo, saukar bakinshi dataji akan lips dinta bazato ba tsammani yasa ta bude ido da sauri tana kokarin kwace bakin matseta yay ajikinshi yana mata wani irin zazzafan kiss, hanunshi taji abayanta yana shashafawa batare daya raba bakin nasuba zip din rigarta taji yaja kasa kokarin tashi tai daga jikinshi hakan yabashi damar cire rigar da kyau ya ijiye gefe, kankame idonta tayi sosai cike da kunya ganin yanda yake kallonta, ahankali yasaki bakinta da idanunshi dasuka soma ja yana kallon yanda take kakkare kirjin da hanunta, hanunta yakama yanadan murmushi yana wani irin kallonta ganin yanda taki bude ido, jin hanunshi akan bra dinta yasa tadanyi ihu ta shige jikinshi sosai jikinta na rawa ta fashe da kuka tace "please sto... " bai bari takarasa maganar ba yasake hade bakinsu wuri daya ya kwantar dasu akan kujeran ya shiga wasa da ita da zafi zafi gashi yaki bata daman yin magana hawaye kadai take iya zubarwa, bude kofa akayi aka shigo dakin kai tsaye hakan yasa ya dago kai tareda maida Islam bayanshi itama bude ido tai atsorace jin anshigo dakin tai lamo abayan shi duka hannayenta nakan kirjinshi dan rungumoshi tai tabayan, daure fuska yay tamau yace "mekika zoyi anan?" yana maganan ne tareda daukar rigar Islam dake kan kujeran yana bata da sauri ta karba ta saka, kasa cire ido tai akanshi ganin cikakken kirjinshi gawasu six packs dasukai layi gwanin ban sha'awa, jijiyoyi sun fiffito a muscle dinshi "mekekazo yi agidan mu nace?" Ya daka mata tsawa hakan yasa Islam tadan leko da kanta daga bayanshi bayan tagama saka rigar bakinta har rawa yake tace "Faa.. Faree" wani irin kuka ne da kishi yakawo ma Farida wuya da kyar ta iya kakalo murmushi tace "am sorry nazo gidan ku bada izinin kuba, dama damaa" takasa karashe maganan sabida wani irin kuka dataji yazo mata, da sauri Islam ta sakko daga kan kujeran zataje wajenta riketa yayi yasa hannun shi abayanta ya zuge mata zip din rigar, hakan yasa Farida taji wani sabon kuka yazo mata da kyar ta share idonta tace "dama nazo na roki gafarar kune akan duk abinda nayimuku, zan tafi Umara gobe, anjima zan tafi Abujama, so I just tot nazo sabida mu shirya, shine nace Bala yakawo ni tunda yace yasan gidan yataba kawo Anty Hindu" takarashe maganan tana kuka dan takasa daurewa yanda tagansu yasa taji kirjinta namata zafi, fizge jikinta Islam tayi daga nashi taje da gudu ta rungume Faridan hakan yasa ta fashe da kuka sosai tace "Islam am sorry, please kiyafe min abubuwan dana miki kinji kema naji Anty Hindu tana cewa gobe zaku tafi ko please forgive me" girgiza mata kai tayi tace "am sorry too Faree, please kiyafe min" girgiza kai Farida tayi tace "bakimin komiba, please kiyakuri da duk abinda nayi" tai maganan tana kallon Khaleel, rigarshi dake kan kujera yadauka ya saka sanan yazo wajen kamo Islam yay ya share mata hawayen datake ya girgiza mata kai yace "is okay, stop crying Baby" ture hanunshi tadanyi ganin yanda Farida ke kallonsu ahankali yace "bari nadan baku wuri to" yadan matso da bakinshi wurin kunnenta yace "zanje gida, but idan nadawo zamu cigaba daga inda muka tsaya" dan tureshi tayi tana kallon fuskar Farida murmushi yay ya saketa sanan ya kalli Farida ahankali yace "make your self at home bari naje gidanmu bye" tunda yake maganan takasa dauke idonta akanshi, fita yay yana kallon fuskar Islam ya rufo musu kofa. Rungumeta Islam tasakeyi sanan taja hannunta suka zauna akan kujera tana kallon fuskarta tace "Faree da gaske kin yafemin dan Allah?" dan murmushi Farida tayi tace "how about nadafa miki wanan sweet Indomie dana ke miki agida kici kawai dan ki yadda komi yawuce awurina" cike da murna Islam tace "to tashi muje mu dafa" ta mike tsaye harda jan hanun Farida tashi Farida tayi tace "ki zauna abinki, nizan dafa miki gawayata nan ki karanta Soyayyar mu yau Fati Teejay tai posting" da sauri ta karbi wayar sabida tana mugun son littatafan faty, Farida ta kalleta tace "inane kitchen din? " nunamata tayi da hannu tareda kwanciya dan ta karanta novel din, Farida tajuya ta shiga kitchen din, Indomie biyu ta ciro da Kwai tafara dafawa, komawa tayi ta kulle kofar kitchen din sanan tadawo gaban gas din ahankali ta bude jakarta ta ciro sniper tabare ledan tabude sanan ta zuba acikin ruwan Indomie, tai maza tai grating attarugu da yawa da albasa ta zuba aruwan sabida ya kashe warin sniper, saida tagama dafa Indomie dayay mugun kyau a indo ga egg agefe ta bare sanan taje gaban fridge ta dauko sabon exotic dayay sanyi sosai ta bude ragowan sniper ta zuba aciki ta jijjiga sosai sanan tahada komi a tray tadau fork da glass cup tasaka sanan wurgar da goran sniper a bin dake kitchen din, tadawo tadau tray tabude kofa tafito falon, table taja ta ijiye mata tace "tashi tashi kici" ta mika hannu ta karbi wayarta takoma ta zauna wurin ringing tone ta shiga ta danna hakan yasa wayar tai kara ta mike da sauri ta kalli Islam da ita take kallo tace "Abba nakirana bari natafi zaikaini airport ne saisa yake kirana nadawo" Islam tadan tabe fuska tace "to Indomie mufa bazaki tsaya muciba" hararan ta tayi tana murmushi tace "sabida nai missing flight dina ko" tashi Islam tayi tsaye da sauri Farida ta maida ita ta zauna tace "dalla kekuma sai Indomie yahuce, I cook it with luv so kici da kyau bye" murmushi Islam tayi tace "Allah kiyaye hanya, I love you Faree bye" fita Farida tai daga dakin tana daga mata hannu. Komawa Islam tayi ta kwanta ta lumshe ido danji tayi hankalin ta ya kwanta yanda Farida tadena fushi da ita, jin kamshin indomie ya ishi hancin ta yasa ta tashi ta zauna fork ta dauka ta debo ahankali takai bakinta dan yatsine fuska tayi tana tunawa tace "kaman wari warin kalanzir" hadiye wa tayi dan ba karamin dadi Indomie yayi ba, ahankali ta sake debo na biyu takai bakinta hadiye wa tayi tana yatsine fuska tace "kodai akwai kalanzir agidan nanne" exotic din ta dauka ta jijjiga sanan tabude ta zuba a glass cup takai bakin ta tana sha, cire cup din tayi tana jujjuyawa tana shinshina jikin cup din, kodai hancin tane kejin warin kalanzir dinan tasake tambayan kanta, sanyin da exotic din yayi yasa takarashe kwankwadewa ta ijiye cup din, sanan ta tashi taje gaban TV tai plugging ta kunna, remote ta dauka tasaka zee world sanan tadawo ta zauna akan kujera takara daukan fork tadebo Indomie zatakai bakine taji cikinta yadanyi wani irin kara tareda tsukewa kadan, dan zabura tayi tareda yamutse fuska but tagama period mekuma cikinta ke haka, batare data kawo komi ba takara kai Indomie bakin ta ta hadiye da kyar, tashi tayi tana shahshafa cikinta sabida yanda taji kaman hanjinta na vibrating. [6/23, 1:42 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 43 & 44 Parking Abba yay yafuto yazagayo ta inda take ya budemata kofa, tama kasa tashi tana mamaki mekuma sukeyi anan ga Khaleel, inane ma nan, hannu Abba ya mikomata yace "sakko" ahankali ta sakko da kafarta dake sanye cikin flat shoe dinta black, maida kofar Abba yay yarufe sanan yafara tafiya tana biye dashi abaya dan dukar dakai kadan Khaleel yayi yace "sannu da zuwa Abba" murmushi Abba yamai ya shiga gaba Abba da Islam na biye dashi abaya ya bude musu kofa suka shiga wani babban falo dayasha kujeru ash color ansa labulaye masu kyau baki da ash, dakin sai kamshi yake ga sanyin ac dayakara karama dakin dadi, ga babban tv bango dake aiki saidai babu kara, zama Abba yay akan kujera har lokacin yana rike da hanunta ya zaunar da ita a gefenshi, karasa shigowa Khaleel yayi yaje zai zauna akasa Abba ya nunamai dayan gefenshi ahankali yazo ya zauna yanadan satan kallon fuskar Islam wacce kanta ke kasa. Gyara murya Abba yayi sanan yafara da addu'oi ya kalli Islam yasa hannu yaciro bandir din yan dubu daidai a aljihunshi ya ijiye akan jikinta yace "Ummi ga sadakin kinan, dazu aka daura aurenki da Khaleel" da sauri ta dago kai ta kalli Abba jikinta har bari yake murmushi Abba yamata yace "nariga nasan komi, yanzu dai abinda nakeso dake shine kibi mijinki sau da kafa karki manta aljannarki na karkashin kafarshi, Koda wasa karki batama mijinki rai ki kasance mace mai addini, ibada hakuri da jarumta dakuma tsafta, har mahaifiyarki ta koma ga Allah bazan iya tuna randa ta taba batamin raiba" murmushi yadanyi sanan ya mike tsaye, ahankali Khaleel ya mike, hannu Abba yasa ya dagota sanan yarike hannunta ya kamo na Khaleel yasaka hanunta aciki ya Kalli Khaleel yace "ga amanar yata nan nabaka Muhammad ka kular min da ita, Allah ya baku zaman lpy Allah ya albarkaci auren, Abban ka yacemin ran Sunday zaku wuce Abujan ko" Ahankali yace "eh Abba sati daya kawai zamuyi anan" murmushi Abba yay yace "to shikenan ubangiji Allah ya kiyaye yakuma baku zaman lpy ka kular min da amanata na yarda da tarbiyanka Khaleel" murmushi yay yace "in sha Allah Abba" "to masha Allah nabarku lpy" yajuya zai tafi sai alokacin taji wani mugun kuka yazo mata fizge hanunta tayi daga hannu Khaleel da gudu taje ta rungume Abba tabaya tana kuka sosai tace "Abba dan Allah karka tafi kabarni, dan Allah" dan juyowa Abba yayi danba karamin karyarmai da zuciya tayi ba, ahankali ya dagota ya sharemata fuskar tareda sumbatar goshin ta ya girgiza mata kai yace "ai auren kenan Ummi, kiyakuri kinji dole natafi ki zauna da mijinki, haka iyayenmu duk aka musu, take care daughter" alamu Abba yamai da hannu ya riketa hakan yasa ya rikota Abba yajuya yatafi, sosai tafashe da kuka harda majina tureshi tayi ta zube a wajen tana kuka. Farida takira Khaleel yayi sau goma baya dauka, daga bayama saitaga bata iya kiranshi dan kaman ma yay adding dinta a black list, mutanen dazasu kai Amarya sun gaji da jira suka fara watsewa dai dai yarage daga Mumy sai wasu kawayen ta guda biyu da ita Faridan dake sanye da lapaya ajiki duk tai sukusuku gabanta sai faduwa take idanun nan sun fiffito waje. Shigowan Abba yasa Mum da Farida suka mike batare daya kallesu ba yace "kusame ni afalo na" yay gaba suna biye dashi abaya, zama yay a babban kujeran shi ya nuna musu waje, kofa Anty Hindu ta bude ta shigo dakin cike da murmushi ta kalli Abba tace "harka kaita kadawo?" gyada mata kai yayi tareda cire hular dake kanshi ya ijiye a saman kan kujera Mum ce tace "Alaji naga kana cire hulane, kiran mutanen nan fa yakamata kayi azo atafi da amarya wanan wani irin abune, ko sai gobe zasuzo ne" wani irin kallo Abba yamata sanan yace "ai anriga ankai amarya tun dazu" batare daya sake kallon Mum da fuskarta ya nuna alamun tambaya ba yacema Farida "zonan" tashi tayi jikinta a sanyaye taje gaban Abba ta zauna, ahankali yasa hannu a aljihun shi yaciro ticket din makka dakuma car key yabama Farida yana murmushi yace "kinga wayan nan duk nakine mota sabuwa, ga ticket din makka wanda ranan lahadi mai zuwa jirginku zai daga ko Faridan babanta" murmushi tama Abba tace "nagode Abba" gyara zama Abba yayi yace "Farida yanda nake sonki haka nakeson Ummi, saisa nake kokarin yin adalci atsakaninku, kinsan hadarin auran mijin dabaya sonka kuwa? Ai yaro kodan gidan kirki ne inhar baya sonka gwara ka hakura dan duk yanda zuciyar shi take dole saiya cutar dakai dan zuciyar nan dakike gani bata da Kashi Farida, ko yayyinki maza Abdallah da Ibrahim wlh bazan taba bari su auri wacce basaso ba sabida nasan zasu cutar da itane" ajiyar zuciya ya sauke sanan ya dafa kanta kaman yanda ake lallashin yaro yace "Farida nariga nasan komi, Khaleel bake yakeso ba Islam yakeso saisa nahada auren shi da ita bawai da wani abu ba, saidan shine abu mafi alkairi agareki, amma yanzu ga ticket dinki idan kinje Umarah kiyi addu'a in sha Allah mijinki na nan zuwa, and Koda banma hadasu aure bayau one way or d other saiya aureta dan Matar mutum kabarin sa, kiyakuri kinji karki bari komi ya tsaya miki arai, aure lokaci ne, wani rashin alherine kinji" gyadama Abba kai tayi tana hawaye, Mummy da duk ranta ya dagule yanzu mezatace ma kawayen ta ta kalli Abba tace "gaskiya Alhaji anzuba sonkai awajen nan, kirikiri shikenan kanuna kafison Islam, yarinya tama Farida kwacen saurayi Kuma ka auramata ha..." tsawa Anty Hindu tamata tace "kwace saurayin gidan ubanwa eh? To bari kiji jiya yaron nan saida na aika aka kiramin shi bayan kun watse kun tafi walimar ku, har cikin falon nan na Abba ya shigo saida nasa shi yafadiman gaskiya, ni tun bayau ba nasan Islam yakeso, Islam yafara haduwa da a garin nan, sanan maganar so baitaba hadashi da Farida ba daga taimako ta likemai, ai har labarin haukan datayi nacin shinkafar bera saida nasamu" takalli Farida dawani mugun ido tace "ba shinkafar beraba ko taliyar bera ce kije kisiyo kici dan uwaki kezaki mutu kafira kinji ko walakiri ya narkeki ehe mara hankali kawai" da gudu Farida ta tashi tafita daga dakin tana kuka, tsaki mum taja tamike tabi bayan yarta, Anty Hindu ta kalli Abba tace "tana dawowa daga Umarah kanemi Yaron kirki mumata aure kafin tajawo mana abin kunya tunda dai zuciyar uwarta ta dauko" ta wuce tafita daga dakin tana masifa, Abba ya girgiza kai wanan yayar tashi hmmm ba'a cewa komi. Ahankali ya tsugunna agabanta yadaura hannayen shi akan gwuiwarta ta turemai hannu cike da masifa, murmushi yamata yace "stop crying to kinji" make kafada tayi ta cigaba da kukan ta, murmushi yamata yace "okay" tashi tsaye yayi ya cire babbar rigar shi ya zauna agabanta ya lankwashe kafa yay tagumi yana kallon yanda take kukan, hararan shi tayi sanan ta janyo hular hijabin ta tacigaba da kukan, dan dariya yayi ya sanya hannayen shi biyu ya maida hijabin baya hakan ya bayyana fuskar ta, turo baki tayi ta daga hannu kaman yanda yaro yake idan zai daki mutum tana kuka, murmushi yayi ya sanya hannayen shi ya rike kunenshi tareda langabar dakai ahankali yace "am sorry plzzzzzzz" kawad da kanta tayi tacigaba da gunjin kukan ta, ahankali yadawo ta inda fuskarta yake murya chan kasa yace "please stop crying ya isa haka, zomuje kiyi wanka let's have dinner" yay maganan yana rikemata hannu, fizge hanunta tayi tace "bazan yiba" murmushi yasake yi ganin masifa takeji yau, matsowa yasake yi kusa da ita yakai bakinshi saitin kunnenta ahankali yace "oh are u shy? Okay bari ni naje nafara yi" kin kallonshi tayi saima goge goge hawayen datake yi, ahankali ya mike tsaye yawuce ya shiga wani yar corridor dazai sadashi da bedroom din, tashi tayi tsaye da kyar jin yanda cikinta ke ciwo waige waige ta dinga yi kozata ga wani abu dazata iya rubutu dashi, akan dining table ta hango wani leda dataga an rubuta thanks for coming ajiki, dama ya taho dashi ne danyabama mai gadi, budewa tayi taga memo da byro da goran bottle water da duk anrubuta sunanta da nashi ajiki, memo ta dauka da byro dan tsaki tayi dan wlh Allah yagani bayanda zatayi yine bude marfin byro tayi sanan ta rubuta "please I, I, please I need pad" sosai taji wani irin kunya nakamata ajiye byro tayi akan dining din sanan ta dawo cikin falon, ajiye memo tayi kusa da wayarshi tabar page din datai rubutun abude yanda dazaran yazo zai gani, ta koma kan kujeran ta kwanta tana tunanin gida da Farida. Alamun tafiyar shi dataji yasa ta lumshe ido da sauri yana sanye da farin jallabiya sai kamshi yake, shigowa falon yay yana kallon fuskarta ganin memo kusa da wayarshi yasa yakarasa wajen dan yasan babu komi akan kujeran daya shiga ciki, daukan memo yayi ya duba, dago kai yay ya kalleta yana murmushi, daukan key din motar shi yayi dake kan center table da wallet dinshi yasa a aljihun ahankali yazo gaban kujeran datake ya tsugunna ba karamin bugawa kirjinta yayi ba jin ya daura hanunshi akan nata data daura akan cikinta yana shafa fatar hanun nata, dayar hanunshi kuma a saman kan hijabin ta ahankali yace "am coming bari naje nasiyo miki" dan dukowa yayi yamata peck a kumatu ya mike tsaye yana kallon yanda jikinta ke rawa murmushi yayi yafita daga dakin. Abunku da GRA gabaki daya shagunan duksun kulle tsaki yayi yadau wayarshi sako yaturama Ihsan kanwarshi sanan yay kwana yadawo, agaban gidansu yay parking dayake tsakanin gidan da inda akakai Islam baifi gida uku bane tsakani, yana zaune a car Ihsan ta bude gate tafito sanye da Hijab hanunta rike da Leda tana kallon fuskar Khaleel tana murmushi, daure fuska yayi ya mikamata hannu tasaka mai tana dan dariya ciki ciki tace "ka gaisheta Ya Khaleel" harara ya zuba mata yace "nidan aiken kine" eh din tace taruga da gudu tashiga cikin gida murmushi yay ya kunna mota yabar wajen yay horn agaban gidansu mai gadi ya budemai yay parking motar yafito, bude kofa yay dayar sallama tana kwance inda yabarta idanunta a lumshe takowa yay inda ya barta ya ijiye ledan a gefe ahankali yakai hanunshi waist dinta hakan yasa ta firgita ta bude ido da sauri tareda ture hanunshi, murmushi yamata yasaketa sanan yadau ledan yabata ahankali ta karba tareda kawad dakai, hanunta ya kama yace "to tashi kije ciki kiyi wankan" uhn tace tareda turemai hannu folding hannayen yay a kirji ya tsaya yana kallonta ganin gabaki daya duk a tsorace take yasa yay hanyar kitchen yace "am going to the kitchen, jekiyi wankan ki" saida taga ya shiga kitchen din sanan ta wuce hanyar dataga yabi dazu, daki dayane tak a corridor hakan yasa ta bude dakin ta shiga babban gadone royal yaci hadadden zanin gado, sai wardrobe din bango sai yar center carpet a tsakiyar dakin kofar bathroom din tagani yabari abude ta wuce ta shiga tarufe. Takai kusan 10min atsaye tana tunane tunane wai yanzu shikenan haka dama ake aure, shikenan ta auri wanda Farida ke mugun so bayan tai rantsuwa bazata taba auren shiba yanzu ya hukuncin rantsuwarta?. Jiki asanyaye tacire hijabi da doguwar rigar ta ijiye a gefe sanan tafara wanka, sai bayan tagama wankan tarasa yanda zatayi gashi ko kaya daya bata dashi kuma doguwar rigan yadan yi staining balle tamaida, hijabin ta dauka tasaka sanan tadan bude kofa kadan ta leka dakin hada ido sukayi daidai yana ijiye tray din abinci akan drawer dan murmushi yay ya dauke kai ganin she's so uncomfortable, batare daya kalleta ba yace "am coming" ajiye tray din yayi yakoma gaban wardrobe ya bude wani dan madaidai cin akwati ya dauko ya kawomata nan gaban bayi ya ijiye batare daya kalleta ba ganin ya zauna abakin gado ya juya mata baya yana daddana waya yasa ta tsugunna ta bude akwatin wani doguwan rigan bacci ta dauko mai dan mutunci da undies sanan tadan dago kai ta kallai ganin baya kallonta yasa ta koma bayi da gudu ta shirya tass, rashin sabulu wanki yahanata wanke doguwar rigan, folding tayi tafito daga bayin sanye da hijabi ta tsugunna tasa rigan acikin akwatin sanan ta rufe ta daga akwatin tsaye, ahankali take tafiya tazo zata wuceshi ta fita da sauri dan wani irin tsoro taji tanaji yanda daga ita sai shi agidan nan, hanunta ya riko ya janyota ya daurata akan kafarshi da sauri ta mike tsaye jikinta har rawa yake, tashi shima yay tsaye yasa hannu ya yaye hijabin ta yacire ya wurga kan gadon da sauri tasa hannu tana kakkare gaban rigan kanta akasa duk jikinta na rawa, ahankali taji yakamo hanun yasaka hanunshi cikin nata ya zaunar da ita abakin gadon ya dauko tray din abincin ya zauna kusa da ita dan har jikin su na gogan juna, lafiyayyen fried rice ne da kaji sai cold exotic drink da bottle water ga magani data gani agefe, baice mata komiba ya debo rice din a spoon yakai bakinta girgiza kai tayi jikinta har baribari yakeyi tace "zan zanci dakaina" hannunta ta mika zata karbi spoon din ganin yanda hanunta ke rawa yasa ya ijiye spoon din ahankali ya daura hanun nashi akan nata yakai dayan hanun kumatunta yakira sunanta ahankali "Islaam, Hey relax is me" bata kalleshi ba, spoon din yasake dauka yadebo rice din yakai bakinta very calm yace "please" Ahankali ta bude bakinta kadan yasa mata taci da kyar ta iya tai 5 spoon sanan tace "am okay" bayason yatakura ta hakan yasa yadau maganin dake tray ya ballo kwara biyu yabata yana murmushi yace "for d stomach" Ya nuna cikin ta kawad dakai tayi ta karba yadau ruwa ya bata tasha tana yatsine fuska, tashi tayi tai hanyar kofa zata fita batare daya kalleta ba yace "kizo ki kwanta anan idan nagama cin abinci nixan kwana a falon" dan kallon fuskarshi tayi ganin baya kallonta kokarin debo rice yake hakan yasa ta dawo ciki ahankali tahau gadon nesa dashi sosai ta kwanta tareda jan bargo ta rufe jikinta duka kanta kawai tabari awaje. Yaci iya cinshi shima yaji ya koshi yatashi tsaye rike da plate din kallonta yayi yanda ta takure waje daya ta juyamai baya murmushi yayi ya bude kofa yafita kitchen ya wuce ya ijiye tray din yafito falo yay locking kofa sanan ya kashe TV ya kashe wuta sanan yay hanyar bedroom din, bude kofa yay ya shigo hakan yasa takara kudundunewa, kashe wutar dakin yay sanan yawuce bayi yay kusan 10min sanan ya bude kofa yafito duk tana jinshi, agaban wardrobe ya tsaya ya cire jallabiyar jikinshi yamaida a hanger sanan ya ijiye, zagayowa yay ta inda take kwance ta bakibakin gadon ya tsugunna batare dayace komiba, azabure ta tashi zaune tana kokkomawa baya tana sheshekan kuka, hayowa yay kan gadon ya zauna agabanta tareda kunna hasken wayarshi ya haskata, kare fuskar tayi da hannu tana kara matasawa baya tana kuka ahankali, kafafun ta yakama yaza yana murmushi hakan yasa tai zuit ta kwanto flat, hayowa kanta yay batare daya hade jikinsu ba kulle idanunta tayi gam tana kuka sosai, ahankali yace "shiiiii" gum tayi ko tari bata karaba, hanunshi yakai tabayan wuyarta yadan dagota kadan yasa hanun ya zare ribbon din data kama gashin ta dashi ya yar akan gadon hakan yasa gashin ya barbazu akan filo ya tsaya yana kallon yanda ta kamkame idonta kirjinta na bugawa fat fat, wayarshi ya dauka ya kashe flash light din sanan ya kwanta a gefenta, hanunshi yakai yadaura akan cikinta hakan yasa takara zabura zata mike ya riketa tareda janyota tafado kan jikinshi. [6/23, 1:42 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 45 & 46 Yunkurawa tayi ta tashi yasa hannu ya kwato da kanta kan kirjinshi yana shafa bayanta ahankali yace "sleep" gabaki daya atakure take sabida yanda yawani riketa hakan yasa ta lumshe ido kirjinta na bugawa fat fat fat tafi hour daya takasa bacci sabida yanda yake shafa bayannata sai mutsu mutsu take daga bayane baccin dole yasace ta, hakan yasa tai relaxing gabaki daya ajikinshi tana ajiyar zuciya ahankali. Jinyanda jikinta yasaki yasa yagane tai bacci, ahankali gudun kada ta tashi yamika hanunshi ya kunna bedside lamp yana kallon fuskarta yaune rana ta farko daya tabamata kallon kurinla haka, gani yake kaman Eeshan shi yake kallo, dan lumshe ido yay ahankali yace "Allah ya gafarta miki my Eesha" ahankali ya bude ido tareda sa hannu asaman gashin ta yana shafawa jin gashin taushi gashi warawara, d'ayar hanunshi ya mika ya kashe bedside lamp din sanan ya mayar da hanun yanata shafa kanta ahaka wani bacci mai mugun dadi da natsuwa yay gaba dashi. Wuraren 3 nadare ta farka sabida fitsarin datake ji, jinta datayi akan mutum yasa ta tuna inda take, kokarin cire hanunshi daga bayanta take takasa gashi dakin duhu batagani ko kadan ahankali taji yace "mekike so" bata ganin idonshi da kyar cikin muryan bacci tace "hanunka" hannu ya mika ya kunna bedside lamp din da sauri ta dauke kai ganin yanda idanunshi suka kara kyau sundan kankance sabida baccin dasukayi, ahankali yasaketa hakan yasa ta sauka daga jikinshi da sauri sanan ta zauna daga bakin gadon tana waige waige neman hijabin ta dan bataso ta tashi agabanshi ahaka ganin bataga hijabin ba gashi fitsari takeji sosai yasa tadan juyo ta kalli fuskarshi a lumshe taga idanunshi hakan yasa ta mike tsaye harda dan gudun ta tashiga bathroom din jin kaman fitsarin zai zubo, bata wani dade ba tafito tsayawa tayi tadan kallai ganin har lokacin idanunshi a lumshe yasa tafara tafiya ahankali tadan kwanta ta baki bakin gadon taja bargo ta rufa murmushi yay ahankali. Hartadan fara gyangyadi taji yamata peck a kumatu ya tashi ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito, jallabiya yasaka ya shimfida dadduma yafara salla tun tana kallonshi har bacci yay gaba da ita. Kamshin turaren dataji yacika mata hanci ne yatada ita daga baccin datake, ahankali take bude ido harta gama budesu Khaleel tazani zaune kusa da ita yaci uban shadda dark brown har kyalli take, ya gyara gashin kanshi da sajen shi sunata shining ya zauna yana kallon fuskar ta, tashi zaune tayi tadan dauke kai ahankali tace "ina kwana" murmushi yamata tareda kamo hanunta ya mikar da ita tsaye jitayi ya rungumeta hakan yasa ta tsorata batare daya saketa ba yace "morning Baby ya darenki" yay maganan tareda sakinta, kauda kai tayi, murmushi yasakeyi mata da sauri tabar wajen wajen akwatin daya bata jiya taje budewa tayi ta ciro wata atampa vilisco dataga an dinka yanama cikin leda da duk wani abu dazata bukata sanan tadan juyo kaman mara gaskiya ta kallai hada ido sukayi hakan yasa ta dauke kai ta tashi ta shiga bayi da sauri ta rufo kofar harda saka key dan bata yarda dashiba wanan kallo kaman wanda yaci maita. Saida tagama wankan sanan ta shirya ta shafa mai tasaka kayan da aka mata dinkin riga da sket, ba karamin haushi rigan yabata ba dan V neck akama dinkin saidai kayan sun mugun amsanta, black da pink ne kalar atampar hakan yakara fito da hasken fatar ta, rashin comb yasa ta tattare gashin nata tai pakin dinshi ahaka sanan ta daura dan kwalin dan simple daurin tayi, gaban mirror bayin taje ta tsaya tana kallon kanta wani haushi ne yazomata ganin yanda gaban rigan yasa kana hango saman kirjinta dan rigan yakamata chas ajiki, tsaki tayi ta tuge daurin dan kwalin kanta ta warware sanan tadan yafa aka yarufe mata har wuya sanan tafito, ganin baya dakin yasa ta bude box din ta maida kayan data cire ta feshe jikinta da turaren data gani sanan tarufe akwatin tana kokarin daga akwatin taji yay sallama ya shigo, ciki ciki ta amsa batare data kallai ba ta daga akwatin ta juyo fadawa jikinshi tayi dan kwata kwata batasan yana bayanta ba, kokarin fita daga jikinshi tayi da sauri, yadaura hannayen shi a waist dinta yana kallon idonta mayar da kanta kasa tayi takai hanunta ta daura akan nashi tana kokarin cirewa daga waist dinta, kama hanunnata yay yarike hakan yasa ta fizge hanun da karfi ta tureshi ta juya zata tafi, fizgota yay ya zauna akan gado ya daurata akan cinyar shi kokarin mikewa take amma yariketa gam, dayan hanunshi yasa ya yaye lullubin datayi da dan kwalin ya ijiye agefe yana kallonta kawad dakai tayi gefe ta daure fuska, ahankali taji yakai hannu yana shafa wuyanta wani irin yarr taji tanaji ga heart dinta na racing, ture hanunshi tayi hakan yasa ya rike hanunta gam sanan ya mayar da danyan hanun nashi yana shafa wuyan nata wani iri taji tanaji hakan yasa tafara jujjuyar da kanta kaman wata kadangare, da kyar ta iya ta fizge hanunta ta tashi dagudu zatabar dakin ajikin kofa ya ritsata hakan yasa ya daura hannayen shi biyu a jikin kofar yasata a tsakiya yana mata wani irin kallo, hannu tasa tafara kakkare kirjinta tai crossing hannayen ta daurasu akafada ta yanda bazaiga komiba idanunta suka cicciko da hawaye, cire hanunshi daya yay daga jikin kofar ya daura akan hanunta yarike yacire hannun daga kafadan yana kallon fuskarta, ahankali ta shiga reramai kuka tana mutsitsike ido, hannu shi yasa ta bayanta jikinsu ya hadu tadan komar da kanta baya still tana mutsitsike idanun dake fitar da kwalla, hanun nata yakamo yacire daga ido yadan hura mata iska a ido sanan yace "meke damunki" kokarin cire hanunshi take daga bayanta ya girgizamata kai tareda hada forehead dinshi da nata, hancin shi ya goga akan nata yadan kalli kwayar idonta sanan yace "talk" kokarin kawad dakai take yaki bata daman yin hakan, da kyar tace "kama Farida alkawarin aure, jiya ta shirya she was so happy she invited all her friends shine ka aureni bayan I already told u bazan aureka ba, ashe wayau kamana, Allah kadai yasan wani hali Farida ke ciki yanzu, why did you do dis?" takarashe maganan tareda da fashemai da kuka, tunda take maganan yake kallonta baki ya bude zaiyi magana sukaji muryan wasu mata na buga kofa ta waje, handky yaciro daga aljihu ya share mata hawayen sanan ya kamo hanunta ya zaunar da ita akan gado yace "am coming". Falo yafita yabude kofa su Ihsan yagani da wasu manyan mata guda uku, Ihsan tai murmushi tace "Umma tace nakawo su, za'a mata lalle ne da gyaran kai, kuma wai kaje" cike da rashin jin dadi ya kalli matan yace "ku shigo" komawa yay ciki yasame ta azaune hanunta ya kama ta tada ita tsaye yace "wurinki akazo, zomuje" make kafada tayi hakan yasa yay folding hanunshi a kirji yana mata wani irin kallo da sauri tajuya zata fita daga dakin yakamo hanunta. [6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 47 & 48 Yakamo hanunta yarike gam yana yar dariya, turo baki tace "kasaken" make mata kafada yayi yaja hanunta har gaban wardrobe, wani madaidaicin black hijab yaciro ya warware yasaka mata sanan yarike mata hannu ya kalleta yace "banason ana kallon mu goody bag dina muje naraka ki" akunyace ta dauke kai, tare suka fita daga dakin suna zuwa dining tafara kokarin kwace hanunta sabida mutanen datagani su kusan five ga manyan kuloli kusan 5 dasuka ajiye a tsakar falon, kin sakinta yay ahaka suka shigo falon, kasa daina kallonta su Ihsan sukayi, tana tsaye agefenshi tadan kallesu tace "ina kwanan ku" manyan matan guda biyune suka amsa da lpy lau, harara ya watsama su Ihsan yace "ku baku iya gaisuwa bane" atare suka taso sukazo inda take tsaye Ihsan ta mika mata hannu tace "ni sunana Ihsan his sister, welcome to our family" ahankali tai murmushi ta bata hannu, Ilham ma tace "sunana Ilham welcome to the family" murmushi tamata tace "thank you" Fa'iza ma tace "nice Fa'iza welcome and u are very very cute wlh" murmushi tai tace "thank you" hanunta Ihsan tarike tace "ga masu lalle nan mum tace amiki idan angama za'a kaiki chan family house ne, muje afara yimiki sai muyi dishing abinci kiyi breakfast ko" gyada musu kai tayi sukaja hanunta hakan yasa yasaketa, dan juyowa tai ta kallai tai raurau da ido, girgiza mata kai yayi alamun no, ya kalli Ihsan yace "ku kullan min da ita kuma, ko kuda karku bari ya tabata, bari naje" hanun yadaga mata alamun bye kunya taji yakamata ta dauke kai da sauri su Ihsan sunata mata dariya. Harara ya balla musu sanan ya juya yafita daga dakin yana kallon fuskar ta. Lalle aka fara zizara mata, daya nayin na hannuwa dayar kuma na kafafu, Ihsan ta debo abinci tana bata abaki, Ilham kuma da Fa'iza sun kwanta akasa suna bata labarin Khaleel suna tafawa suna ihu, bakaramin tunamata da Farida sukayi ba, sosai taji tana kewan yar uwan nata da kyar ta iya tahana kanta yin kukan. In less than awa daya lallen ya bushe da aka mata sabida sanyin ac dakuma fanka dasuka kunna, wankewa akayi ba karamin kyau lallen amaryan yamata ba, sanan aka wanke mata gashi akai using handryer aka busar dakan sanan aka fara yaryada mata kitso yan mini mini. Sai Wuraren azahar suka gama sanan suka tafi yarage daga ita saisu Ihsan sosai tasaki jiki dasu sabida yanda suketa janta jiki kaman sun santa, sata tai wanka sukayi suka shiryata cikin wani ubansu lapaya, Fancy glamour suka dauko ta chanchara mata makeup din amare idan kun ganta bazakuce itabane, sanan suka kira Umma cewa sun gama, Umma tace "to, yanzu za'a zo ataho da ita". Anty Hindu ne dawasu mata duk sunci gayu sukazo gidan, rungume Anty Hindu Islam tayi zatai kuka ta girgiza mata kai, sanan ta lullubeta mata fuska aka dauketa suna wakoki aka tafi da ita gida fuskarta a rufe, ta lapayan ta take hango yanda gidan ya cika da mutane sai taga gidan su kaman ba biki akeyi ba, wani babban falo taga an shiga da ita an zaunar da ita akan kujera Anty Hindu ta zauna a gefenta tana gaggaisawa da mutane anata guda, wata matace dataga suna kama da Khaleel taci gayu sosai tazo gaban su, Anty Hindu tace "ga maman mijinki nan" yaye lullubin fuskarta Ammi tayi, ahankali tasa hannu ta daga habarta kasa dago ido tayi sabida kunya hawaye taji ya gangaro, murmushi Ammi tayi tace "masha Allah daughter" sababbin kudi taciro ajaka yan 500 tadinga mata manni ana guda har saida kudin yakare sanan takoma ta zauna, haka ma Umma tazo ta wanketa da liki, duk wanda yazo Anty Hindu tana fadamata waye, sosai aka dinga ihu ana guda sanan aka tafi da ita bangaren Goggo, Goggo Kam harda rawa sabida murna tai manni tai manni har saida duka kudinta ya kare, wata malama tagani ta tashi tai musu wa'azi da addu'a sanan Goggo tace "to kowa yatafi abarmata amaryan ta tahuta" haka duk aka watse ya rage Anty Hindu da Ammi da Umma, tashi sukayi suka shiga uwar daka Goggo sunata magana, muryan Goggo taji tana cewa gaskiya anan zata zauna. Fitowa sukayi Ammi tazo ta dafata tace "kinajin yunwa insa akawo miki abinci daughter?" akunyace ta girgiza kai, murmushi Ammi tai ta kalli Anty Hindu tace "daughter na badai kunya ba" dariya Anty Hindu tayi daga nan duk suka fita suka basu wuri, sosai Anty Hindu tamata wa'azi da fada akan tabi mijinta, sanan tacemata Khaleel yamata sabon akwati set daban daban har 6, Abban ta duk yahada an wuce mata dasu gidanta na Abuja. Sai bayan sallan Isha Anty Hindu ta tafi ba karamin kuka tasha ba hakanan ta hakura tai shiru gyangyadi tafara yi akan kujeran Goggo sabida yanda tagaji gakuma kukan datayi hakan yasa Goggo tace "tashi ki shiga ciki ki kwanta abinki ki huta kinji, sannu yarnan yan iskan yaran nan duk sun wahalar dake" murmushi tai dan hakanan taji Goggo ta shiga ranta gatadai tsohuwa amma akwaita da tsafta, "au bazaki tasoba" Goggo tai maganar tana kokarin tashi daga kan tabarmar data shimfida a tsakar dakin, kamo hanunta tayi tace "muje ki kwanta bakisan bacci nada amfani ga lafiyar dan Adam ba" kofar uwar dakanta ta bude da gadon ke agyare tsaf tace "jeki kwanta abinki zanga dan kan uban dazaizo yafita dake, jekiyi baccin ki saida safe kinji yar albarka" gyada kai tayi sanan tace "saida safe Goggo" kwanciya tayi akan gadon da aka gyara tsaf dakin sai kamshin turaren wuta yake within 2 min bacci yay gaba da ita, Goggo dake kishingide akan tabarma taji ana kokarin bude kofar ta tashi tayi ta zauna da kyau tana wawware ido, Khaleel ne ya shigo sanye da doguwar jallabiya sai kamshi yake yawani daure fuska yace "ina matata? Daga barinta tazo gidan naku shikenan kuma bakusan ku komar da ita inda kuka daukotaba?" ko kallonshi Goggo bataiba taja filo abinta takara kwanciya sanan tace "jeka tambayi uwarka, bata fadama daga yanzu anan gida zata zama ba, to saikun koma Abuja ne zata tare a gidanka" karaso wa ciki yay yace "nida matar tawa lallai nema" yazo zai wuce yay bedroom Goggo ta mike tsaye da sauri tasha gabanshi ta rike kugu hakan yasa yaci birki yana kallonta cike da bacin rai, dariya tayi tarike haba tace "mara kunyar banza, fitarmin daga daki tunda bakai ka ginamin ba wlh kona hadaka da ubanka" ganin Goggo ta daure babu alamun wasa tawani rike kugu yasa yajuya yafita daga dakin rai abace, Goggo tarakashi da dariya sanan ta maida kofa ta rufe harda saka Sakata tace "fitinannun yara" kwanciya tayi abinta rai fes tace "dan kanuba to yarinya sai tasha gyara sanan za'abaka, idanma nabari ka kara sata a ido ba sunana Lami ba" lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya. Direct part din Ammi yawuce duk ranshi a dagule Yusuf yagani zaune afalo yana jiran Ihsan tagama dafamai Indomie dayace tadafamai, yana ganinshi ya gimtse dariyar datazomai, ko kallonshi baiyi ba ya shiga bedroom din Ammi wata kawarta ya tarar tana magana da ita hakan yasa yaje kusa da ita ya zauna, sallamar matan tayi sanan ta juyo ta kalleshi tace "Ya akayi Son?" da kyar ya iya cewa "Ammi wai kekika cema Goggo karta bari Islam tabini anan zata dinga kwana" Ammi taso tai dariya da kyar ta saita kanta sanan ta kallai tace "eh nafiso kawai ran Sunday idan duk mun tafi Abujan basai ta tare wajenkaba, yanzu ga duka family anan mezataje tai ita kadai achan gidan kadaici zai isheta mana" zaiyi magana tace "ka bacemin daga nan I have alot of things to do" tashi yay yafita daga dakin duk ranshi acinkushe ta gefen ido yaga Yusuf ya ijiye Indomie hanunshi yanamai dariya ciki ciki haka yay kaman bai ganshi ba yana zuwa dai dai inda yake yadau plate din Indomie yace "wlh bazaka ci shiba" Yusuf ya kwalama Ammi kira yace "Ammi kinga wai akaina zai huce takaicin shi" da sauri Khaleel yafita yay part dinsu ya kulle kofa ya ijiye Indomie anan kan kujera yawuce bedroom yafada kan gado kasa bacci yayi sai juye juye yake daga baya yatashi ya shiga bayi kawai ya dauro alwala yazo ya kabbarta salla. Bari muleka Faridan mu. Idan kunga Farida saikun tausayamata ta rame sosai, da kyar Mum kesata taci abinci, bata da aiki sai daukar waya taita dailing number superman da baya shiga ko kadan, Abba kullum wa'azi yake mata da fada, Mum dai duniya yay mata zafi hakan yasa wani zubin idan Farida tafara kuka itama jonata takeyi suyi tayi tare, ba irin Allah ya isan da basuma Islam ba sabida bakin ciki. Hakanan yau Wednesday taji tanajin fita kotadan ga rana, doguwar riga baka tasaka ta yana gyalen ko hoda bata shafaba tafito daga gidan danko Mum bata fadimawa ba, keke napep ta tare tace "yakaita Infinity gym" ta shiga ciki yaja har wajen yana ijiyeta ta ciro kudi ta bashi, sucurity ya bude mata ta shiga ciki, wani kukane yazo mata ganin treadmill din data taba ganin superman dinta akai, da kyar ta hadiye hawayen ta karasa wajen eatry din, order strawberry smoothie tayi ana kawomata ta karba tareda bada kudin tanata kallon smoothie din tana tuna ranan da superman dinta yasaimata yabata ahankali tace "menama Islam haka datamin irin wanan abu? Mesa nakasa cire sonshi araina why, please God inaso na manta dashi please" share da kwallan daya zubomata tayi tadau smoothie zatakai baki da sauri ta ijiye ta kife kanta akan table din tana wani irin kuka mai cinrai, "hey is everything okay" dago kai tayi suka hada ido da Yusuf dake sanye cikin sport wears hanunshi rike da cold bottle water, share ido tayi ta juya da sauri ta duba ko suna tareda superman dinta ne taga shikadai ne, juyoda kai tayi ta harari Yusuf tace "wat are you doing here?" kujera Yusuf yaja ya zauna yana kallon fuskarta yace "nothing banmasan kebace" tashi tsaye tayi tajuya zata bar wajen dan wani irin haushin Yusuf takeji da sauri yabita juyowa tai cike da masifa tace "kadena bina harda kai aka hadu aka yaudaran, Islam Islam" takira sunanta saikuma tajuya tafita daga wajen da sauri jin wani kukan ke zuwan mata suna fita Yusuf yasha gabanta yace "hear me out, kidena blaming sister ki wlh batada laifi, Allah kuwa trust me" bakin gyalen ta tasa akan fuskar ta tafashe dawani kukan, jitake kaman zuciyata zai fashe, ba karamin tausayin ta Yusuf yaji tabashi ba ya tsaya kawai yana kallonta da kyar tai shiru ta kalli Yusuf da rinannu idonta tace "koma menene at least for d sake of ni yar uwartace, tasan yanda nake sonshi saitaki auren shiko" ta dago kai ta kalli Yusuf tace "kataba son wata?" girgiza mata kai yayi alamun a'a hakan yasa tadanyi murmushi tace "bazaka taba iya gane wat am going through ba, Islam" tasake kiran sunan Islam tana wani irin dafa kirjinta da sauri tajuya tabar wajen akan bakin titi ta tare napep ta shiga tana goggoge ido da bakin gyale. Sosai Yusuf yaji jikinshi yay sanyi wanan wani irin sone, yanda take haukan son Khaleel dinan shikuma haka yake haukan son Islam, oh Allah kayaye ma wanan baiwar naka wanan son maso wanin, ahankali ya juya ya shiga ciki. Islam dai sai gyaran jiki ake mata in and out, Goggo yanzu kulle kofa take idan baka kwankwasa ka fadi sunanka ba bazata taba budewa ba duk dan kar Khaleel ya ganta take wanan. Dayake yau asabar yasa anata shirye shirye kowa na hada kayanshi dan gobe zasu tafi, Wuraren 11 Khaleel yafito daga part dinsu yana sanye da jeans black da blue t-shirt mai gajeren hannu, fuskar nan tashi adaure har wata yar raman dole yayi sabida rashin ganin Islam, dakin Ammi yayi yasameta zaune kusa da Dad datake hadama tea gaishe su yayi suka amsa, Dady ne yace "mekake so son" kallon fuskar Ammi yayi hakan yasa ta dauke kai ahankali yace "dama Dady inaso Ammi tasa Islam muje ta tayani hada kayan mune nachan gidan tunda gobe zamu tafi" Dady ya Kalli Ammi yace "kiramai matarshi tazo sutafi ta tayashi mana" Mum zatai magana Daddy yace "ki kirata nace banson jin komi" murmushi Khaleel yayi hakan yasa Ammi ta watsamai harara sanan ta wuce tafita tai dakin Goggo saida tai magana sanan Goggo tabude ta shigo Islam dake sanye da riga da sket nawani soft material mint green dake zaune rike da wayar Ihsan tana karanta wani novel tace "dauko Hijab dinki kizo Islam" ajiye wayar tayi tadau hijab Goggo tace "ina zata?" "Kiranta Alaji yake" black hijab tadaura akan kayan tabi bayan Ammi har falo, tunda ta shigo yake kallonta ganin yanda fatarta har wani kyalli take takara haske, dudda tasaka hijabi bai hanashi ganin yanda tawani kara cikowa ba tai fresh like honey wine, gaida Abba tayi cikeda girmamawa tana kallon Khaleel ta gefen ido dudda tadanyi kewanshi amma taki Koda kallonshi balle ta gaidashi, Abba ya nuna mata Khaleel yace "kuje kuhado kayanku na dayan gidan dan gobe da safe zamu tafi" ahankali tace "to daddy" fita Khaleel yayi batare daya kalleta ba hakan yasa tabi bayanshi kirjinta nadan bugawa, mota ya shiga hakan yasa ta bude gaban motar ta shiga ta zauna tarufe, kunna motar yayi suka fita daga gidan su aranta tace "nan da nanne bazai iya zuwa da kafaba, lazy fellow" horn yay mai gadinsu yabude yay parking yafito ya shiga ciki saida tai kusan 2min a motan sanan tafito jiki duk asake, ahankali ta bude kofar ta shiga falon, da kyar ta iya daga kafa takai tsakiyar falon ta tsaya ganin bata ganshi ba, tabaya taji anrungumeta hakan yasa saida tai yar kara sabida tsoro, tsamtsam ya rungumeta yakawo kanshi ta wurin kunnenta yace "I miss you" juyo da ita yay yakai hanunshi yay cupping fuskarta ya kalli cikin idonta yace "did you miss me" dan murmushi tai sabida yanda yay maganan ta dauke kai, zama yay ya daurata akan cinya yana kallon fuskarta yace "waye lazy fellow?" adan rude ta kallai ta dafe kirji, ganin yanda yake kallonta yasa ta tashi da guda tana dariya tai hanyar bedroom tace "bafa dakai nakeba" harta zauna akan gado taji yabude dakin da gudu ta tashi zata shiga bayi ya rikota tabaya tareda cire hijabin jikinta ya matseta yana kallon idonta yace "Wana kama?". [6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 49 & 50 Dan dariya taji yazo mata, kawad dakai tayi sanan tace "sorry" ahankali, kamo hanunta yay ya zauna akan gado ya daurata akan jikinshi yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "did you miss me?" daura kanta tayi akan hanunta akunyace tace "uhm" bakinta tarufe da sauri dan wlh batasan lokacin da maganan yafito ba, hade kansu yay wuri daya ya hade hannayenshi biyu ta bayanta yana dan jijjigata akan kafarshi, murya chan kasa yace "banjiki da kyau ba" dan dago kai tayi ta kalleshi suka hada ido batare data cire idonta daga kanshi ba ta sanya hanunta ta baya ta bige hanunshi ta tashi da gudu ta tsaya abakin kofa sanan ta juyo ta kallai ta gyadamai kai kaman yanda yara suke sanan tace "yea I miss yhu" bude kofa tai tafita da gudu tai kwanciyan ta afalo akan dogon kujera tareda daura filon kan kujeran akan fuskarta. Alamun tahowar mutum dataji yasa tadan zame filon kadan daga kan fuskarta ta kalleshi maida filon tayi da sauri ganin sun hada ido kirjinta na bugawa sosai, zama yay ya dauki kafafun ta ya daura akan cinyarshi yana mata waiwayi akafa, motsi ta dingayi tareda kara rike filon ta danne fuskarta aciki, jin bakinshi datayi akan babbar yatsar kafarta yasa taji wani yarr batasan lokacin data saki filon yafadi akasa ba, kasa daure yanda yake sarrafa yatsun nata yake ta mirgina ta kifa tareda daga kafafun nata sama hakan yasa sket dinta yay kasa kafafun suka bayyana ta lumshe ido tana cuccusa fuskar ta acikin kujera, ahankali ya kamo kafafun ya kwantar sanan ya kwanto ta bayanta yakai bakinshi saitin kunen yakira sunanta "Islaaam" yanda yaja sunan yasa takasa daurewa saida tabude idanunta dasuka kankance ta kallai, tashi yay ya zauna ya sanya hannu ya dagota itama ta zauna tana lumlumshe ido, hanunta yakama yarike gam ahankali yace "ina sonki dayawa Islam please don't ever leave me, I love you sama da yanda kike tunani, u know something" kai ta girgiza mai tareda kwantar da kanta kan kafadar shi, kanshi ya daura akan goshin ta yasanya hannayen shi yay cuddling nata very tight sanan yadan sauke ajiyar zuciya yace "are you fine?" gyada mai kai tayi, ahankali yasake sauke ajiyar zuciya yace "nai mafarkin kine jiya saisa nasa Abba yace kiboyini nan, I just wanted to know idan kina lpy" lumshe ido tayi akan kafadar nashi tana kara shakan kamshin dayakeyi datake mugun so cikin siririyar muryarta tace "mafarkin mekayi?" murmushi yay tareda kissing forehead dinta yace "it doesn't matter now, all I want you to know is I love you very much Islam" da sauri ta maida kanta kirjinshi tareda lumshe ido sabida yanda yakesa takejin kunya, ahankali yaciro kanta daga kirjinshi yana wani irin kallon fuskarta bude ido tayi kadan ta kallai da sauri ta kankame idon ganin ita yakema wani irin kallo, saukar bakinshi dataji akan lips dinta bazato ba tsammani yasa ta bude ido da sauri tana kokarin kwace bakin matseta yay ajikinshi yana mata wani irin zazzafan kiss, hanunshi taji abayanta yana shashafawa batare daya raba bakin nasuba zip din rigarta taji yaja kasa kokarin tashi tai daga jikinshi hakan yabashi damar cire rigar da kyau ya ijiye gefe, kankame idonta tayi sosai cike da kunya ganin yanda yake kallonta, ahankali yasaki bakinta da idanunshi dasuka soma ja yana kallon yanda take kakkare kirjin da hanunta, hanunta yakama yanadan murmushi yana wani irin kallonta ganin yanda taki bude ido, jin hanunshi akan bra dinta yasa tadanyi ihu ta shige jikinshi sosai jikinta na rawa ta fashe da kuka tace "please sto... " bai bari takarasa maganar ba yasake hade bakinsu wuri daya ya kwantar dasu akan kujeran ya shiga wasa da ita da zafi zafi gashi yaki bata daman yin magana hawaye kadai take iya zubarwa, bude kofa akayi aka shigo dakin kai tsaye hakan yasa ya dago kai tareda maida Islam bayanshi itama bude ido tai atsorace jin anshigo dakin tai lamo abayan shi duka hannayenta nakan kirjinshi dan rungumoshi tai tabayan, daure fuska yay tamau yace "mekika zoyi anan?" yana maganan ne tareda daukar rigar Islam dake kan kujeran yana bata da sauri ta karba ta saka, kasa cire ido tai akanshi ganin cikakken kirjinshi gawasu six packs dasukai layi gwanin ban sha'awa, jijiyoyi sun fiffito a muscle dinshi "mekekazo yi agidan mu nace?" Ya daka mata tsawa hakan yasa Islam tadan leko da kanta daga bayanshi bayan tagama saka rigar bakinta har rawa yake tace "Faa.. Faree" wani irin kuka ne da kishi yakawo ma Farida wuya da kyar ta iya kakalo murmushi tace "am sorry nazo gidan ku bada izinin kuba, dama damaa" takasa karashe maganan sabida wani irin kuka dataji yazo mata, da sauri Islam ta sakko daga kan kujeran zataje wajenta riketa yayi yasa hannun shi abayanta ya zuge mata zip din rigar, hakan yasa Farida taji wani sabon kuka yazo mata da kyar ta share idonta tace "dama nazo na roki gafarar kune akan duk abinda nayimuku, zan tafi Umara gobe, anjima zan tafi Abujama, so I just tot nazo sabida mu shirya, shine nace Bala yakawo ni tunda yace yasan gidan yataba kawo Anty Hindu" takarashe maganan tana kuka dan takasa daurewa yanda tagansu yasa taji kirjinta namata zafi, fizge jikinta Islam tayi daga nashi taje da gudu ta rungume Faridan hakan yasa ta fashe da kuka sosai tace "Islam am sorry, please kiyafe min abubuwan dana miki kinji kema naji Anty Hindu tana cewa gobe zaku tafi ko please forgive me" girgiza mata kai tayi tace "am sorry too Faree, please kiyafe min" girgiza kai Farida tayi tace "bakimin komiba, please kiyakuri da duk abinda nayi" tai maganan tana kallon Khaleel, rigarshi dake kan kujera yadauka ya saka sanan yazo wajen kamo Islam yay ya share mata hawayen datake ya girgiza mata kai yace "is okay, stop crying Baby" ture hanunshi tadanyi ganin yanda Farida ke kallonsu ahankali yace "bari nadan baku wuri to" yadan matso da bakinshi wurin kunnenta yace "zanje gida, but idan nadawo zamu cigaba daga inda muka tsaya" dan tureshi tayi tana kallon fuskar Farida murmushi yay ya saketa sanan ya kalli Farida ahankali yace "make your self at home bari naje gidanmu bye" tunda yake maganan takasa dauke idonta akanshi, fita yay yana kallon fuskar Islam ya rufo musu kofa. Rungumeta Islam tasakeyi sanan taja hannunta suka zauna akan kujera tana kallon fuskarta tace "Faree da gaske kin yafemin dan Allah?" dan murmushi Farida tayi tace "how about nadafa miki wanan sweet Indomie dana ke miki agida kici kawai dan ki yadda komi yawuce awurina" cike da murna Islam tace "to tashi muje mu dafa" ta mike tsaye harda jan hanun Farida tashi Farida tayi tace "ki zauna abinki, nizan dafa miki gawayata nan ki karanta Soyayyar mu yau Fati Teejay tai posting" da sauri ta karbi wayar sabida tana mugun son littatafan faty, Farida ta kalleta tace "inane kitchen din? " nunamata tayi da hannu tareda kwanciya dan ta karanta novel din, Farida tajuya ta shiga kitchen din, Indomie biyu ta ciro da Kwai tafara dafawa, komawa tayi ta kulle kofar kitchen din sanan tadawo gaban gas din ahankali ta bude jakarta ta ciro sniper tabare ledan tabude sanan ta zuba acikin ruwan Indomie, tai maza tai grating attarugu da yawa da albasa ta zuba aruwan sabida ya kashe warin sniper, saida tagama dafa Indomie dayay mugun kyau a indo ga egg agefe ta bare sanan taje gaban fridge ta dauko sabon exotic dayay sanyi sosai ta bude ragowan sniper ta zuba aciki ta jijjiga sosai sanan tahada komi a tray tadau fork da glass cup tasaka sanan wurgar da goran sniper a bin dake kitchen din, tadawo tadau tray tabude kofa tafito falon, table taja ta ijiye mata tace "tashi tashi kici" ta mika hannu ta karbi wayarta takoma ta zauna wurin ringing tone ta shiga ta danna hakan yasa wayar tai kara ta mike da sauri ta kalli Islam da ita take kallo tace "Abba nakirana bari natafi zaikaini airport ne saisa yake kirana nadawo" Islam tadan tabe fuska tace "to Indomie mufa bazaki tsaya muciba" hararan ta tayi tana murmushi tace "sabida nai missing flight dina ko" tashi Islam tayi tsaye da sauri Farida ta maida ita ta zauna tace "dalla kekuma sai Indomie yahuce, I cook it with luv so kici da kyau bye" murmushi Islam tayi tace "Allah kiyaye hanya, I love you Faree bye" fita Farida tai daga dakin tana daga mata hannu. Komawa Islam tayi ta kwanta ta lumshe ido danji tayi hankalin ta ya kwanta yanda Farida tadena fushi da ita, jin kamshin indomie ya ishi hancin ta yasa ta tashi ta zauna fork ta dauka ta debo ahankali takai bakinta dan yatsine fuska tayi tana tunawa tace "kaman wari warin kalanzir" hadiye wa tayi dan ba karamin dadi Indomie yayi ba, ahankali ta sake debo na biyu takai bakinta hadiye wa tayi tana yatsine fuska tace "kodai akwai kalanzir agidan nanne" exotic din ta dauka ta jijjiga sanan tabude ta zuba a glass cup takai bakin ta tana sha, cire cup din tayi tana jujjuyawa tana shinshina jikin cup din, kodai hancin tane kejin warin kalanzir dinan tasake tambayan kanta, sanyin da exotic din yayi yasa takarashe kwankwadewa ta ijiye cup din, sanan ta tashi taje gaban TV tai plugging ta kunna, remote ta dauka tasaka zee world sanan tadawo ta zauna akan kujera takara daukan fork tadebo Indomie zatakai bakine taji cikinta yadanyi wani irin kara tareda tsukewa kadan, dan zabura tayi tareda yamutse fuska but tagama period mekuma cikinta ke haka, batare data kawo komi ba takara kai Indomie bakin ta ta hadiye da kyar, tashi tayi tana shahshafa cikinta sabida yanda taji kaman hanjinta na vibrating. [6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 51 & 52 Da kyar ta iya ta zauna akasa ta daura kanta akan kujera tana wani irin numfarfashi da baki tana cije baki tana jujjuya kafa sabida yanda taji kaman ana jajjage acikin nata, wasa wasa abu sai gaba yakeyi wani irin barje dataji cikin nata nayi yasa tawani irin buga kai akasa tana mukurkusu ahankali tace "wayyo Allah na, cikina na shiga uku" kokarin kamo kujera take ta tashi tsaye hala cikin yadena, da kyar ta iya janyo filo daga kan kujeran ta tusa akarkashin cikin nata ta, ji tayi kaman takara azaban datake jine, nukurkushewa ta dinga yi a wurin tana jujjuya kai tana dukan kasa da awahale tace "Ya Khaleel" tafara kokarin jan jiki dantai wajen kofa amma takasa ta kife kanta anan kasa tana dukan tiles din wajen da hannu, kofa taji anbude an shigo tsabagen azaban datake ji tama kasa dago kai ahankali ya tsugunna yana shafa kitson kanta daya mugun mai kyau yace "mekike yi akasa haka" yakarashe maganan yana murmushi wani karfi ne taji yadan zomata da kyar ta tashi tsaye tahau kan jikinshi ta yaye rigarta sama tana wani irin lankwashewa tanuna mai cikin ta dan tamakasa magana, adan rude ya kalli cikin ganin yanda yake wani motsi up and down da kyar tace "cikina Ya..." kasa karasa maganan tayi tawani shige jikinshi tana bangarewa, fashewa tayi da kuka sosai ta kankameshi tana wani irin mika, adan rude ya wawwaigawa baiga kowaba da sauri yaciro fuskarta daga jikinshi yace "ina Farida?" kasa magana tayi saima wani kanannade shi data sakeyi tana wani irin lankwashewa kaman macijiya tana kuka, hanunshi ya daura akan cikin wani irin motsi da kara yaji ba karamin faduwa gabanshi yayiba ciro kanta yayi daga jikin nashi ya kwantar da ita anan kasa ahankali da idanunshi dasukai jajir yace "am coming" tashi yay yay bedroom yana kwallama Farida kira "Farida Farida" har bayi saida ya bude bata, hakan yasa yafito ya shiga kitchen da sauri nanma bata harzai fito saiya hango farin leda dakuma farin marfi akasa kusa da bin, hakanan yaji zuciyar shi bata kwantaba shiga kitchen din yayi yana kallon ko'ina dan wari warin magani yakeji, digon wani abu daya gani akan fridge kaman mai yasa yasaka yatsa ya dangwala yakai hanci ya shinshina warin magani yaji kaman kalanzir da sauri yakoma wurin bola inda yaga farin marfi akasa ya daga yakai hanci same wari yaji tashi yayi yana kalle kalle bolan ya leka ganin Goran sniper a kwance cikin bolan yasa yaciro yana kallon goran dan yasan babu irin goran nan agidan, harda dan gudunshi yakoma falon plate din Indomie daya gani yaje yadaga yanama abincin wani irin kallo, shinshina abincin yayi da sauri ya ijiye yadau juice din ya tsiyaya a cup abu kaman maimai dayagani a kwance kan saman juice din cikin cup din yasa ya dafa kirjinshi jin yanda ya buga da karfi yace "innalillahi wa innailaihi raji'un" harda dan gudunshi yazo inda take kwance tana wani irin numfarfashi tana kuka yace "waya baki abincin chan shikikaci?" kasa magana tayi saima wani irin kukkule ido datake yi tana bubbuga kanta akasa danji take kaman ana tsitsinke hanjin cikinta, kama fuskarta yayi yay tapping kumatun ta da karfi yace "wayabaki abincin chan" kara fashewa tai da kuka tana nunamai cikinta da kyar ta iya cewa "Fa.. Far" wani irin ihu tayi ta buga kanta akasa sabida yanda cikinta yay wani irin kara dahar shi saida yaji da gudu yay gaban tv danhar yana huge kafa da center table, key mota yadauka ya dauke ta yafita tsakar gida da gudu yana kwalama gateman kira "budemin gate" kwantar da ita yay abayan mota yarufe da gudu ya shiga gaba yatada suka fita agidan, yanda take juyejuye sabida azaba har saida tafado kasa daga kan kujeran juyowa yay da idanunshi dasukai jajir yakira sunan ta "Islam, Islam" kasa amsawa tayi saima bubbuga kai datake yi a jikin kujeran. Allah ne kawai ya kaisu asibitin lafiya dan yana tuki yana kallon bayane yanda take nukurkusu akasa. Idan kaga Khaleel zaka zaci ya haukace ne sabida yanda yake ihu a asibitin, da gudu aka karbeta Dr yace "maiya sameta" da kyar ya iya cewa "I think sniper aka bata" ganin yanda tawani bankare zata Fado daga kan gadon da aka daurata yasa ya riketa yace "Islam Islam am here babu abinda zai sameki kinji" cikin wani daki akai da ita ya bisu amma akace yafita. Har sunkai layinsu itada me napep din daya dauketa sai kuma taji jikinta yay wani irin mugun sanyi yanzu sabida namiji zata iya kashe Islam? Wata zuciyar tacemata amma ai idan ta mutu zai aureki, dafe kanta tayi tana girgizawa da sauri tace "no no, I can't do dis, Islam jini tace " da sauri ta kalli driver tace "malam komar dani GRA dan Allah kayi sauri" juyawa sukayi addu'a kawai take ido arufe Allah yasa bataciba jikinta har wani bari yake, har suka kai sauka tayi tacemai yajirata da gudun ta ta shiga gida mai gadi namata magana amma Kota kanshi batabi ba, a bakin kofa ta tsaya ganin plate din Indomie andan ci kadan sanan ga dan kwalin material dinta akasa maganan mai gadi taji tabayan ta yace "Hajiya basanan yanzun nan alaji yafita da ita kaman hajiyar ba lpy ne" wani irin bugawa kirjinta yayi tai wani irin suman tsaye, da kyar ta iya cemai to ganinan fitowa, wani luuu tayi zata fadi da kyar ta iya dafa bango tana kwalalo idanu tareda dafe kirjinta kaman wata mahaukaciya tafara lalubar jakarta watsar da komi tayi na jakan kasa ta ciro wayarta hanunta har wani barbar yake number Abba tai dailing ringing daya Abba ya daga kafin yay magana tace "Abba, Abba, Abba na kasheta, Abba nakashe yar uwata, wlh wlh bansan meyakai ni bata sniper ba, Abba na shiga uku shairin shaidan ne" maganganu kawai take zaroma Abba kaman zarrara hakan yasa Abba hankalin shi yatashi kodai Farida ta zarene ahankali yace "Farida mekike fadine haka wakika kashe?" "Islam, Abba kanwata, yar uwata jinina nakashe yau, Abba..." katse wayar Abba yay jin yanda take xazzaro maganganu kaman mara lpy number Khaleel dayaji kotaje gidan sune dan yasan batasan gidan bama, yay dailing number saida ya kusa katsewa yay picking ahankali yace "Abba" tashi tsaye Abba yay daga kan kujera dan yanda yaji muryan Khaleel yasa kirjinshi yawani irin mugun bugawa "Khaleel meke faruwa yanzun nan Farida takirani" da kyar Khaleel ya iya cewa "muna general hospital Abb..."wayarce tafadi kasa ta tarwatse sabida yanda jikinshi ke wani irin rawa, ganin ankara gunguro Islam daga dakin datake, wani irin abu kaman babban straw abakinta wata nurse kuma ta rike jakan ruwa da ake dura mata ta bakinta dan yay washing cikinta sunyi ICU da ita, da gudu yabisu amma har an shige da ita anrufe kofar bubbuga kofar yake kaman zai fasa yana kiranta, ahankali ya sulale ya cusa kanshi acikin kafafu tareda sanya hannu akan wuyarshi yafi 15mins ahaka a wurin, bayanshi yaji andafa hakan yasa ya dago jajayen idonshi Abba yagani da Anty Hindu dakuma Mum kana ganinsu kaga tashin hankali karara akan fuskokin su. Farida tafi minti 10 tsaye a wurin sanan ta daddafe bango tafito tana ganin jiri ta shiga napep din tareda cemai muje, tafiya kawai suke dan gabaki dayanta bata hankalin ta da kyar tace "kaini asibiti" "wani asibiti hajiya" Ahankali tace "kowanne" tafiya suka dingayi yay parking agaban general hospital yace "kije wanan sunfi kwararrun likitoci Allah sawake" duka kudin purse dinta taciro tabashi kaman wata tababba take tafiya har taje reception tana waige waige Allah sa nan suke, hijabin Anty Hindu ta hango ta cikin emergency ward hakan yasa ta daga kafa da kyar ta shiga ward din, tsayawa tayi daga ta wurin kofa tafashe da kuka sosai tana kallon su yanda suka tsattsaya gaban ICU. Dago kai Khaleel yayi karap suka hada ido da ita, mikewa tsaye yayi kaman namijin zaki yana kallonta hakan yasa Abba suka jujjuya suna kallon inda yake kallo, hannu ya daura akan belt dinshi na jikin wando yana kwancewa batare daya dena kallonta ba, wani irin Fizgo belt din yayi azuciye koni bantaba ganin Khaleel ahakaba wanan zuciya hmmm! Ko kallon fuskar su Abba da mutanen dake ward din baiyiba yay inda take tsaye yana tafiya kaman wani mayunwacin zaki jikake fui fui fui dukan Farida yake da belt Kota ina... Ahankali Islam ta rike hanun Dr yake daddane cikinta tana amayar da ruwan dasuka duramata ta baki, wani irin hawaye ne ya gangaro daga gefen idanunta da kyar ta iya magana tace "please stop abinan dakekemin yamafi min azaba kan komi, please I want to see my husband" yanda tai maganan yasa jikin Dr yay sanyi sosai, wani irin tari tayi hakan yasa ruwa yakara fitowa daga bakinta tace "please I want to see him" ahankali Dr yajuya yafita daga dakin hango Khaleel dayayi yana chasa Farida ga mutane duk antaru ana kallo su Abba dai na tsaye danko yunkurin kwatota basuyiba Mum ce ke kuka sosai, da gudu Dr yay wurin yana "subhanallahi" rike belt din yayi yana kallon yanda Farida ke kuka kaman zata mutu, dawani irin ido Khaleel da kallai, girgiza mai kai Dr yayi tareda janshi yace "kayakuri, Matar ka nason ganinka" bin bayan Dr yayi aka budemai dakin ya shiga kadan tabude idonta tana kallonshi da sauri yay kanta yana shafa kanta hawayen daya gangaromai ya share yama forehead dinta kiss yama kasa magana hanunshi yaji tarike gam hakan yasa ya dago kai yana kallon fuskarta, twisting jikinta tayi tareda fito da ruwa sosai daga bakinta tashi yayi zaije yakira Dr yaji takara kamkame hanunshi da sauri ya kalleta, dan murmushi tamai sanan ta bude bakinta da hakoran ta dasuka dan hade tafara magana, da sauri yakai kunen shi saitin bakinta yaji tace "Yaya Khaleel inaso Kamin alkawari" tadanyi shiru tana numfashi sama sama tace "inasonka sosai, I love you so much Muhammad Khaleel" daura fuskarshi yay akanta ahankali ya lumshe ido wani irin zazzafan hawaye ne suka zubo daga idonshi suka sauka agoshin n ta da kyar yace "and I love you more than anything Islam, please stop talking, kidena magana kinji u will be fine lemme go and call d Dr" yajuya zai tafi hanunshi takara kankamewa tana kallonshi da idanunta dasuka kankance tafara magana, kai kunenshi yayi saitin bakinta ahankali yaji tace "Kamin alkawari, promise me zaka auri Farida idan namutu, Farida na sonka so na gaskiya, promise me" Ahankali ya dago kanshi dudda bata da lafiya bai hana ya mata wani irin mugun kalloba ya fizge hanunshi daga nata yana goge wasu hawayen bakin ciki dasuka zubo, da kyar ta iya daga hannu ta mikamai idanunta na fitar da hawaye ta gefe, ahankali ya tako zuwa gabanta yarike hanun gam zatai magana yadaura yatsan shi akan lips dinta ya girgiza mata kai idanunshi sunyi jajir, idanunta yaga sunsoma jujjuyawa wani irin nishi tayi tafara wani irin nannade kanta tana bankarewa sabida yanda cikin nata yafara wani iri kaman ana kakkatse duk wani hanji naciki, ihu Khaleel yay yace "Doctor". [6/23, 11:35 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 53... Ihu yake yana kiran Dr tareda danna alarm din gefen bed nakiran Doctors, hakan yasa Abba yana ganin Doctors din sunzo zasu wuce dawayan su nurses suna gudu yabisu hankali atashe suka shiga dakin... Wani irin mugun rawa da jijjiga jikinta keyi tana kallon sama idanunta na kakkafewa tawani irin bankarewa dan kumfa kumfa na fitowa daga gefen bakinta ta rike zanin gadon gam, riketa gam Khaleel yayi yana wani irin ihu "Islam-Islam stay with me" yanda yaga jikinta ko ina narawa tana wani irin mimmikewa yasa yafara "innalillahi wa innalillahi raji'un, innalillahi wa innalillahi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati" harda gudu Doctors da nurses din suka karaso wajen gadon da sauri wani babban Dr dan tsoho nema ya kalli wata Nurse yace "kunna Defibrillator, her heart is over racing" handglove ya dauka daga gefen gadon yasa da sauri yadau paddles din defibrillator ya rike yay robbing dinsu together sanan yadaura akan kirjin Islam dake kakkarwa yay ihu yace "clear" kaman electric shock wani irin bangarewa Islam tayi sanan takara komawa kan gadon bam, cirewa yay yana kallon machine din yana reading abunda yake nunawa sanan yakara putting dinsu together ya daura akan chest dinta yay shouting "clear" kara bangakarewa tayi tayo sama sanan takoma kan gadon idanunta na kukkulewa wani irin kara machine din yafara "diiiiiii , din, din, din, din" ahankali Khaleel yafara komawa da baya da baya yana kallon fuskarta yana dafa bango, sama sama yakejin Dr yana "cewa one more time we can't loose her" dumm yaji kunenshi yayi sanan ya dauke, ganinshi yay duhu, yay baki, chan sama sama kaman daga nesa yaji machine din yay kara sosai sanan kuma shiru, sama sama yaji likitocin suna "we are loosing her.. Time of de... " dip yaji kunenshi ya dauke yadena jin komai idanunshi suka rufe ruf. Good morning lovelies 😍 [6/23, 11:35 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 54... Ahankali yake bude idanunshi dasuka mai mugun nauyi ga kanshi dake mugun sarawa, da kyar ya iya bude idanun duka ya sauke su akan wani Dr dayaga ya rikemai hannu yana shafa tafin hanunshi yana bubbugawa, sama sama yakejin doctor nacemai "can u here me, I need you to tell me your name" kadan kadan idanunshi ke kukkulewa ganin gabaki dayan dakin na juyamai in a circle, kara bubbuga tafin hanun nashi Dr yayi yana rubbing tsakiyar yana kallon fuskar shi da kyar yasake bude idon yadan kallai kadan yace "can you hear me? Me sunanka?" da kyar ya iya bude bakinshi sabida wani irin nauyi dayamai sosai yace "Islaaam, I want to see her" yana maganan yana kukkule ido har suka rufu tass, murmushi Dr yayi ya juyo ya kalli su Ammi harda Goggo dasuka tsattsaya kowannen su hankali tashe yay murmushi yace "Alhamdulillah ya farka, anytime from now zai farfado full.. " "Islam" da Khaleel yakira yasa dukansu harda Dr sukai kanshi wanan karan yabude idon duka saidai kanshi dayaji yana mugun ciwo, Ammi ne tai maza ta rike hanunshi tana share hawayen dataji yazo mata, ahankali ya kalleta yace "Ammi ina Islam?" shafa goshin shi Ammi tayi tana girgiza mai kai tace "kafara hutawa tukunna Son, kasan yau kwanan ka Uku unconscious ko" ta kalli Dr dake checking pulse dinshi tace "Dr yayake yanzu?" murmushi Dr yay yace "Alhamdulillah he's pulse is stable, blood pressure din kuma yadawo normal, ku taimaka mai yay wanka da lukewarm water it will really help him" kokarin tashi yake amma yakasa sabida yanda kanshi yaji kaman zai fadi ahankali ya kalli Abban shi da Umma da Yusuf da Goggo dake wajen dakuma Anty Hindu da idanunta sukai jajir sabida tausayi hanunshi ya daga da kyar yay pointing Anty Hindu ahankali yace "ina Islam dina?" bude kofar dakin akayi hakan yasa dukansu sukabi kofar da aka bude da kallo wheelchair din asibiti yafara gani, dan dago kanshi kadan yayi da taimakon Mum yana kara kallon kofar, Abban Islam yagani ya gunguro Islam dake zaune akan wheelchair ta duke kai sosai dan bata iya dagowa complete sabida cikinta, lips dinta sun kumbura sosai sunyi jajajir bakinta nata dilallar da miyau, kasa dauke kanshi yay daga kanta har Abba yakawota jikin gadon dayake ya tsaya, kokarin tashi yake Yusuf yayo kanshi zai taimakamai ya tashi dagamai hannu, alamun yabari, rike kanshi yay ya sakko daga kan gadon da kyar kaman zai fadi, da kyar ya iya ya tsugunna agabanta ya mika hannayen shi ya daura akan fuskarta ya dago kanta yana wani irin kallonta idanunta alumshe, ahankali dawata irin murya mai taba zuciya yace "Islam" shiru tayi batare data bude idonta ba batare datace mai komiba, ahankali Abba yace "Muhammad Khaleel Ummi tasamu nakasu guda biyu, na farko dai tana fama da wanan uncontrollable zuban miyau wato drooling, nabiyu kuma tunda ta farfado ko uppan batace ba, Dr yace yana tsammani Sniper yamata dameji a wuya ne amma basuyi concluding ba, sanan bata iya mikewa tsaye sabida intestine dinta wai basu warkeba tukun, and kaga bakinta yanda yakoma" Abba yadanyi shiru sanan ahankali yace "banason na daurama dawainiya aka, after all yar uwarta ce ta maida ita haka, to Khaleel idan baka sonta, idan bazaka iya zama da itaba wlh bazan taba ganin munin kaba, bazan ji haushi ba, zaka iya sauwake mata" tunda Abba yake maganan yakasa dauke ido daga kanshi gawasu jijiyo yi dasuka fiffito a forehead dinshi, da kyar ya iya janye idanunshi daga kan Abba sanan ya kalli Islam dahar lokacin taki bude idonta, ahankali yasake matasawa kusa da ita yadade yana kallon fuskarta da bakinta dake dulalar da miyau ya daura kanshi akan cinyar ta ya fashe da kuka sosai, Yusuf ne yafara fita daga dakin jin idanunshi sun kawo ruwa, hakama sauran iyayen da Dr suka fita daga dakin yarage daga shi sai ita, yafi 5min yana kuka sanan ya dago kanshi ya share idanunshi da kyar dan muryanshi ma ta dishe yace "Wife" ahankali ta bude ido ta sauke su akan nashi, ganin yanda yake kallonta yasa ta daga hanunta ta rufe fuskar ta tana wani irin kuka mara sauti dan kunyan fuskarta take sosai, hannu yasa yakamo hanun ya saukar dasu yana girgiza mata kai, hanunta ya daura akan kirjinshi daidai wajen zuciyar shi ya goge kwallar data zubomai yace "kinga wanan zuciyar, only beat for u" ahankali yace "koma yakike, koma yakika koma, koma menene you will always be my Islam, my one and only wife, wacce nakeso wholeheartedly" sosai yaga take kuka ahankali ya kai hannu ya share mata hawayen dake zubowa yace "am sorry, am sorry Islam is all my fault" hannu tasa ta kara kare lebenta tana kawad dakai dan ba karamin kunya takeji ba idan yana kallonta, wani hawayen yasake gogewa ya juyo da fuskar nata tareda saukar da hanun nata yana girgiza mata kai ganin yanda take kuka mai cin rai, ahankali yakai bakinshi ya daura akan katon lips dinta dake fitar da miyau. Guys yau weekend am a little busy ne so manage this I love you all. [6/25, 2:17 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 57 & 58 Batare daya dago kaiba yace "Islaaam" kadan ta kallai dan wahalan bude idanunta duka takeji sosai, murmushi yay ya matso da kujeran saitin fuskarta yasa hannu yana shafa kitson kanta ahankali ya sumbaci forehead dinta sanan ya shafa wurin yana kallon fuskarta murya chan ciki yace "I have to go yanzu 7 ake koran mutane but da sassafe zanzo gobe" shiru yay yana kallon fuskar ta ganin kaman tai bacci danta lumshe ido, addu'an bacci ya tofa mata sanan ya matsar da kujeran baya yatashi, yadade a tsaye kafin ya juya da zumin tafiya hanunshi yaji takama da sauri ya juyo ya kalleta, girgiza mai kai yaga tanayi da dan idanunta data bude kadan ga wasu hawaye dasuke gangarowa ta gefen idon, da sauri ya kwanto da kanshi daidai saitin fuskar ta yasa hannu ya share hawayen ahankali yace "u don't want me to go" daga kai tayi wanan karan tana kuka sosai, "okay nafasa tafiya" yafada tareda zama ya riko hanun nata data rike shi dashi yana shafawa kadan kadan, dayan hanun Kuma yana share mata hawayen datakeyi sanan ya ijiye hanun agefen filon yana shafa gaban goshin ta, ahankali tasanya fuskarta cikin hanun tareda sauke ijiyan zuciya sanan ta lumshe ido within 3min bacci yay gaba da ita, numfashin ta dayaji yana sauka ahankali ahanunshi yasa yagane tai bacci, ahaka wata nurse ta shigo dakin cikin harshen turenci tacemai lokacin tafiya yayi yatashi yatafi itace mai kula da ita, kallon fuskarta yayi kafin ahankali ya zare hanunshi ya mike tsaye tareda sanya hannayen acikin aljihu ya tsaya yana kallonta kara komawa yayi ya tofeta da addu'a sanan ya juya yafita daga dakin yana leken fuskarta. A reception yasami Ihsan sanan suka fito daga asibitin taxi yatare musu suka shiga, tafiyan kusan 20min sukayi sanan sukai parking agaban wani dan madaidaicin gida, kofar ya bude ya shiga Ihsan na biye dashi Yaron dazu suka tarar yanata mopping kasan dakin murmushi yamai yace "weldone Raymond" zama akan daya daga cikin kujerun yay yana kara karema gidan kallo, babban falone da akamai penti off white irin dakunan turawan nan saita bangare daya kuma kitchen ne wanda komi yake a gyare, sai dan corridor da dakuna biyu ne awajen kowanensu da bayi aciki, saida Raymond yagama yamusu sallama yatafi shikuma yatashi ya shiga daya daga cikin dakunan hakan yasa Ihsan ta tashi itama ta shiga dayan dakin dan yin wanka tai salla saita fito tadan sama musu abinci. Zaune yake shida Anty Hindu suna magana akai sallama jin muryan su Abban Khaleel yasa yatashi tsaye yana murmushi tareda basu izinin shigowa ganinsu tareda Farida idanunta sunyi zuru zuru yasa ya daure fuska ya nuna mata kofa "fitan min daga gida, fita nace" fashewa tai da kuka ta tsugunna jikinta har wani barbar yake tace "Abba dan Allah kayakuri kayafe min" Su Abban Khaleel ne suka saka baki suna tausasa shi da kyar ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Anty Hindu gyadamai kai tayi hakan yasa ya kalleta ya gyara murya yace "shikenan na hakura amma inada sharadi daya kifito da miji nan da sati biyu kokuma nahada ki daduk wanda naga dama namuku aure" sosai take kuka tana share ido, Anty Hindu sai wanke ta da harara take tace "tayaya ma Farida har kikasan da sniper kika bama yar uwarki, Farida bamu baki irin tarbiyan nanbafa, maisa kika bama yar uwarki guba?" shiru tayi tana matso kwalla Anty Hindu tace "badake nake magana ba" da sauri ta share hawaye da kyar tace "ranan da Bala ya kaini gidan tun kafin yay parking akofar gidan mukaga wata mata a tsaye baka tanada dan jiki, yana parking nafito zan bude gate na shiga sai kawai naga takira sunana Farida, nace mata Na'am, na tambayeta ya akayi kikasan sunana, murmushi tamin tace ai taganni randa nazo gidansu get-together, shine tacemin wai yanzu na yarda kanwata ta aure wanda nakeso bazan yi komiba niba mace bace, shiru nayi bance mata komiba, shine tacemin Ina sonshi? Ahankali nace eh, tace amma ai nasan idan kanwata ta mutu zai aureni nace mata eh, shine tabude jaka tabani sniper tace gashinan nasan yanda zanyi nabata idan tamutu ai shikenan zan auri wanda nakeso" shiru tadanyi tana goge hawaye kowa na falon na kallonta ahankali tace "wlh Abba banyi niyyan bata ba, nidai kawai na karba ne dan kaman tamin asiri tana bani na karba nasa ajaka na shiga cikin gidan, to Ina ganin fuskar Khaleel dinne shine shine wlh bansan meya shigeniba shine na a.. " takasa karashe maganan tana kuka sosai da kyar tai shiru Abban Yusuf ne yace "matar tafadi miki sunanta?" girgiza kai tayi tace "a'a tadaice taganni randa nazo get together, ni bansan taba" shiru kowa yay na falon Kafin Abban Khaleel yay dan murmushi yace "komi yawuce Allah ya yafemana gabaki dayan mu, tashi kitafi abinki" Ahankali ta tashi tafita daga dakin dakin Mum ta shiga ta rungume Mum tana kuka, tureta Mum tayi ta harare ta tace "Farida kinsan kai, haba Farida a ina kika koyo wanan mugun halin, tausayi kawai kikabani saisa na rokesu ayafe miki amma da wlh bazan yiba, haba wanan bakin hali har ina" shiru Mum tayi jin tasake rungume ta tana kuka kaman zata mutu hakan yasa tashiga bubbuga bayanta tana bata hakuri tace "bakomi zakaso ka sameshi ba Farida, Allah ya jarabce ki dason bawan Allah nan amma hakanan zaki dau dangana danba mijinki bane" tai maganan tana share mata hawayen dake zuba. Daga Abban Yusuf harna Khaleel jiki asanyaye suka dawo gida kowanne su na zargin mutum dayane amma kasancewa babu proof yasa kawai suka share suka dawo gida. Da sallama ya shiga part dinta, dakinshi direct yay niyyar wucewa ganin bai ganta a palour ba, daidai ta kofar dakin ta dake rufe yazo wucewa dariyar dayaji tanayi yasa ya mika hannu zai bude handle din tsayawa yay chak batare daya bude kofan ba jin tai dariya tace "ai ingaya miki shinai niyyan kashewa amma na rasa ta yanda zan shiga gidan, kinsan ba shiri nake dashiba idanma na shiga nace mene, saiko ga kanwar matan, kinsan ko lokacin datazo gidanmu nazaci itace yakeso ashe ba itabane kanwartane yakeso, dan naji lokacin dasu Ihsan suke labarin yanda yar ke sonshi kazakaza kaza, shine Ina ganin yar nai instigating dinta sosai, na bata abin nace tabama kanwar tasha kinga ai idan tamutu zai aureta" dariya tasake yi sosai sanan tace "wawiyar ta yarda not knowing fully dat kaina nake taimaka nasan dai yanda yakeson mai kama da Eeeshan nan tunda bansami daman kashe shi ba idan na kasheta kinga ai za'a koma gidan jiya" wani dogon uban tsaki taja tace "ke bata mutu bafa, amma dai rai a hannun Allah dan mutum mutumin ce yanzu, batada amfani" Ahankali yaji tace "hmmmm bazaki gane bane takano, wlh Allah ya jarabce ni dason kaninshi ne tun randa yazo dashi tadi wajena, na fadinma kanin amma shi yama tsaneni haka na auri wanshi Ina dawainiyar sonshi kirikiri sabida ni yadena zuwa yola yanzu ma badadan bikin danshi ba da bazai zoba Kuma wlh bakigani ba ko kallo ban isheshiba saisa nace zan dandanamai azabar rayuwa, zanso yasan yakake ji idan karasa abinda kake mugun so, Kuma Kinga yanda yakeson yaronne shikadai ne namijin shi, ai kinga idan na kashe Yaron koya karashe rayuwan nashi a haukace sabida mutuwar mai kama da Eeshan ainaci riban abinda mahifin shi yamin, yanzu ma idan bata mutuba zansan abinyi" dan dariya tayi tace "to shikenan ki gaidamin dashi idan yafita ki kirani, takano tawa kenan" tai wani uban shewa. Shirun dayaji yasa ya bude kofa ya shiga dakin adan firgice ta kallai tanadan murmushi tace "harkun dawone Alaji?" yafi minti biyu yana kallonta sanan yace "na sakeki saki biyu, ba wanan kadai ba zanje nai filling complain akanki a police station ba Khaleel kadai ba koma waye awanan family wani abu yasake sama keza'azo akama, kije keda Allah" yana fadin haka ya rufomata kofar bam yabuga yawuce, da gudu tabiyoshi har tsakar gida tana bashi hakuri amma ko sauraronta baiyiba saima sake juyowa dayayi yace "kifara tattara yinaki yinaka kibar min gida, karki sake kitafin min da ya" yana gama fadin haka ya shiga mota yabar gidan, ahanya ya kira Abban Khaleel yace "maisa baka taba fadamin halin Mujiba ba, abinda tama" dariya yadanyi sanan yace "Yaya nazaci yarinta ne" murmushi Abba yayi yace "kazo kasaman a office muyi magana". [6/25, 2:17 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 59 & 60 🇬🇧 Taxi yatare ya shiga motar suka fara tafiya wani shago ya hango da ake saida teddies masu kyau cema mai taxi din yayi ya tsaya ya shiga shagon wani jan teddy yasai mata mai kyau da taushi yabiya kudin yadawo mota ya shiga ya zauna yana kallon teddy din yanda yarike flower. Ahankali yatura kofar ya shiga dakin bata kangadon ma hakan yasa ya ijiye teddy akan gado, maganar nurse dayaji tana cewa gently raise your head yasa yaja kujera ya zauna yana kallon kofar bayin, wajen 3 min da zaman shi sanan nurse din tabude kofa ta gunguro ta akeke an chanza mata rigar asibiti zuwa pink amma desame design ne fuskar ta dadan ruwa ga nurse din rike da karamin farin towel a hanunta saida takawo ta bakin gadon sanan nurse din ta gaida Khaleel daya kasa cire idonshi akan Islam dan gani yay bakin yadan sabe jan dayayi ya ragu sosai, tsugunnawa nurse din tayi zata share mata ruwan fuska da towel din hanunta ya tashi tsaye yana tattare hanun doguwar rigar dayasa yace "may i" yay maganar tareda mika ma nurse din hannu murmushi tai tace "sure" tabashi towel din tsugunnawa yayi yana kallon fuskar ta yakai towel din kan fuskar yana share mata ruwan ahankali, lumshe ido tayi tadan saukar da ajiyar zuciya wuyarta ya share sanan ya dauketa ahankali daga kan kujeran sabida karya fama mata ciwo ya mike tsaye yana kallon fuskarta, ahankali tadan bude ido takallai kara gyara kanta tayi akan kirjinshi tasake sauke ajiyar zuciya, kwantar da ita yay akan gado ya rankwafo yamata runfa batare daya dagoba yace "good morning wife" hanunshi dayaji ta rike yasa yadan dago ya kalli hanun, murmushi yamata sanan ya zauna yakai hanunshi kan filon ya budemata yana kallonta, ahankali tasake matso da fuskarta tadaura kan hanun sanan ta lumshe ido tareda sakin ajiyan zuciya takara kankame dayan hanunshi data rike within 1min bacci yay gaba da ita, batare datamaga teddy ba. Murmushi Nurse din dake tsaye tana kallonsu tayi cikin turenci tace "her mind is at ease anytime u are around, inhar tana ganinka haka kullum zaiyi helping recovery nata" murmushi yamata batare daya dena kallon fuskarta ba hakan yasa nurse taje ta bude wardrobe din dakin ta ciro wani ruwa dake cikin farin gora ta ijiye akan table din gefen gadon tace "wanan ruwan zata sha dazaran ta tashi, bari naje inta tashi ka danna mana alerm" tana fadin haka tajuya tafita daga dakin, yadade yana kallonta kafin ya daura kanshi agefen gadon shima bacci yay gaba dashi dan jiya kasa bacci yayi sabida tunanin ta. Yau kwana su sha bakwai a asibitin, sosai condition din Islam ke improving dan bakin tass ya warke babu kumburin babu zubar yawu tana iya hadeye magani yanzu, cikin ne yanzu ake kai, kullum Khaleel na tareda ita abinda ke dagashi daga dakin salla ne kokuma idan zaije siyo magani a pharmacy hospital, shima idan zaije to Ihsan na wurin, Ihsan taita karanta mata novel tana murmushi kadan kadan, idan kaga yaci abinci to coffee ne yadan sha, baya iyacin wani abinci ko Ihsan ta girka saidai yay wasa da abincin kawai yatashi yabarshi, jiyake kaman ciwon yadawo jikinshi. Zaune suke adakin itada Ihsan dake karanta mata wani novel tana kwance kan gado suka bude kofa suka shigo hakan yasa ta dago kai ta kallai shida Dr Om ne suna dan magana, murmushi Dr yay ya kalleta suna karasowa jikin gadon yace "how's my patient doing" dan murmushi tamai tana kokarin gyara kanta akan filo, ya makala mata wani abu kaman camera karama a hannu sanan yace "Gud, I need you to do something for me, inaso kitashi ki tsaya naga" karamin tablet din hanunshi ya daddana sanan ya kalli Khaleel yace "dago min kanta" ahankali Khaleel ya dago kanta ya zaunar da ita, kafarta Om yanunamai hakan yasa ya sauko da kafarta kasa yana kallon fuskar ta, kallonta Dr yayi yace "now try and stand on your feet" dan dafa bango tayi Khaleel ya tsaya kusa da ita dan karta fadi ya sakin mata murmushi tare da nunama ta thumb dinshi alamun good, ahankali take daddafa bango harta dan tsaya amma aduke tana dan ciccije lebe sabida zafin datake ji, dadi Dr Om yaji yace "gud now try and raise ur head, stand straight, inaso naga inda yarage dabai warke bane acikin" fuzar da iska tayi tareda karasa mikewa ahankali ahankali Khaleel yace "sorry wife" Dr Kuma na duba tab din hanunshi, kasa daurewa tayi jin zafin yay yawa tacire hanunta daga bango tai luuu zata fadi Khaleel yatare ta da sauri hakan yasa ta fado kanshi wani irin shocking yaji tunda ga yatsar shi har brain dinshi sabida yanda hanunshi yakama kirjinta mistakenly, itama wani iri yarr taji duka karfin ta tasa tadan juyar da jikinta ta yanda abin ya sauka daga hanunshi ta lumshe ido tana sauke numfashi, yafi 3minute ahaka sanan ya kwantar da ita ahankali yaja bargo ya lullubamata yana kallon idonta dasuke alumshe, maganar Om ce yadawo dashi daidai yace "Khaleel zokaga" zuwa yay ya kalli tab din yace "kaga wanan mucus dinne keda inflammation dazaran ya sabe shikenan zata iya tana mikewa tana komi saimuyi focusing kuma a dawo da maganarta" rungume shi Khaleel yayi cikeda murna yace "Alhamdulillah, Dr am grateful" fita Om yay daga dakin yanata dariya. Cikin sati daya cikin ya warke fess, takan tashi tai tafiya ahankali ta shiga bayi da kanta tai alwala tai salla, kuma takanci abincin dan har tuwo ranan nan Ihsan tamata Kuma taci sosai danyamata dadi, Khaleel ko babu wanda ya kaishi murna harda yima nurses kyauta. Zaune suke adakin yana bata tea abaki kiran Om daya gani yasa ya dauka ahankali yace "okay" sanan ya katse wayar Ihsan yamika mug din tea yace "zoki bata am coming Om nason ganina" fuskar Islam ya kalla dake kallonshi da idanunta masu kama danamai jin bacci yace "am coming wife" fita yay yawuce office din Om shiga yay ya zauna, Om ya bashi wayansu hotuna yace "kaga wanan hoton damukama wuyan tane, babu any damage a vocal dinta so Ina suspecting infection ne awuyan dake hanata magana, yanzu abinda zanyi shine zan bata magunguna sanan zan sallameku inyaso every every week zaka dinga kawota chech up tunda for now ai babu wata matsala saita maganan ko" kasa boye murnanshi Khaleel yayi hakan yasa Dr yafara rubutu akan paper asibiti yace "ko aje ai amarce hmm" yagama rubuce rubucen ya mikamai yace "your discharge letter, I will be expecting you guys next week Thursday" ahankali ya karba yana murmushi sanan ya mikamai hannu sukai musabaha tareda kara godemai sanan yafita daga dakin, dakinsu ya shiga Ihsan dake zaune agefen gado tana nunama Islam wani hoto yazo ya daga yana jujjuya ta yana murmushi dariya tayi tace "Ya Khaleel menene wai?" murmushi yamata yace "an sallamemu" yay maganar yana kallon fuskar Islam ahankali yaga taja bargo ta rufe fuskarta tana murmushi dan wlh tagaji da asibitin sosai itama. Ihsan ya kalla yace "tashi kitayata shiryawa bari naje nakira taxi" fita yay daga dakin yana Satan kallonta, shiryawa tayi cikin dogon black skirt din kanti na jean tasa shimi fari tadaura sweater akai pink dan garin da sanyi sanan Ihsan tamata rolling black gyale sanan tasamata flat slippers, tahade yan littatafai da kayansu dasu tea dake dakin ajakan trolley ta kulle ta daga, shigowa dakin yay yana kallonta tana zaune akan gado kanta akasa hanunta rike da teddy daya saimata kallon Ihsan yayi yace "fita da jakan taxi din na waje" jan jakan tayi tafita shikuma ya karasa cikin dakin har gaban gadon ahankali ya daura hannayen shi akan nata ya dagata tsaye ya karbi teddy ya ijiye akan gado kasa daga kai tayi ta kalleshi, jinta tayi kawai ajikinshi ya rungumeta tsamtsam tareda kissing gefen wuyanta. [6/25, 2:22 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 55 & 56 Ya sakin mata light kiss gudun karya ji mata ciwo sanan ya dago kai ya kalleta murmushi kwance akan fuskarshi, jiyay duk wani ciwon kan da yakeji yabace, sake kai hannu yayi ya share hawayen daya gangaro mata tareda girgiza mata kai yace "am here for you now, koma inane I don't care saina kaiki koda bangon duniya ne inhar zaki sami lpy, zakiji sauki in sha Allah, stop crying..." dan kwankwasa kofa akayi Anty Hindu ta shigo takaraso inda suke ta kalli Khaleel sanan tace "Dr nason ganin ta, za'a wanke mata bakinne, kaga yanzu ma yadan warke tadan iya hadiye tea mai sanyi yau, amma tunjiya babu abinda take iyaci da bakin danyay jajir kaman kuna, bari nakaita" da sauri yatashi yakoma bayan keken yace "zankai ta Hajiya" dan hararan shi Anty Hindu tayi tace "banason gardama Muhammad, ba gamunan ba duka, salla yakamata kayi tukun yanzu sai asan abinyi, oya shiga bayi ka dauro alwala saika wuce massallaci, idan ka Ida aisai kazo kasamemu a dakin nata" tana fadin haka ta gungurata suka fita daga dakin, zama yay akan gado ya dafe kanshi tareda fuzar da iska shikadai yasan yanda yakeji, wayarshi ya dauko dake gefen gado yay dailing wani number yafi minti biyar yana magana aharshen turenci sanan ya katse wayar ya shafa kanshi yana fuzar da iska, ahankali yatashi ya shiga bayin dakin ya dauro alwala sanan yafito yafita daga dakin baiga su Abba awajen ba hakan yasa yawuce massallacin dake cikin asibitin. Saida ya gama salolin dasuka hau kanshi sanan yafito daga masallacin yana tafiya ahankali dan yay nisa acikin tunani, mutum yagani yasha gabanshi ya tsugunna hakan yasa yadan tsaya yana kallonta ba karamin ramewa tayiba tai duhu sosai idanunta duksun fada ciki, fashewa tai da kuka sosai ta hade hannayen ta tace "dan girman Allah kayafe min, wlh shirin shaidan ne saida nayi sanan hankali na yadawo, am very sorry Mk, dan Allah na tuba kayafemin" tunda take maganan yake kallonta harta gama kara daure fuska yayi kaman baitaba murmushi ba ya matsa zai wuce takara tasowa tasha gaban shi tace "dan Allah, kaga Abba yakoreni daga gida idan kaima baka yafemin ba dame zanji, am very sorry, dan Allah inaso naga Islam na roketa gafarta please" hannu takai zata kama kafanshi hakan yasa yace "wlh if your hand should touch my leg, wlh saina ballasu tass, just stay away from me, kinason ki ganta sabida kibata another poison dinne?" cizon leben shi yayi cikin fushi ya nunata yace "stay away from me dan zan iya.." shiru yay yawuce dan koda minti daya yakara awajen zai iya mata abinda shikanshi bazaisoba, fashewa tayi sosai da kuka ta tsugunna awajen har wani irin ajiyar zuciya take saukewa sabida wahala, gashi ba halin ta shiga sabida Abba yamata mugun warning akan yin hakan. Dakinta yay daidai lokacin Dr na fitowa hakan yasa yabi Dr office dinshi, zama yay ya nunamai waje ya zauna, kafin ma Dr yafara magana yace "Dr Inaso a sallamemu sabida gobe nakeson nafita da ita, UK 🇬🇧 zan kaita" murmushi Dr yayi yace "dama advice din danake so nabaku kenan, nan Nigeria 🇳🇬 bamuda kayan aiki inda bahakaba aida zamu iya komi, bari nabaka sallaman amma kadan bari anjima kadan saika tafi da ita dan ansamata ruwa sa karfi da kuzari dawasu allurai, kasan she is very weak sabida rashin abinci aciki" rubuce rubuce yay yabashi yace "ga Bill dinku nan kaje account kabiya" karba yay yatashi yafita daga dakin, account yawuce direct da POS yabiya, yaciro ATM card dinshi yabasu nan yabiya kudin komi sanan ya karbi ATM card dinshi ya maida wallet yabar wajen. Ahankali ya bude dakin ya shiga kowa na dakin Ammi na kan gado ta daura kanta akan cinyarta ta mikar mata da hannun da akasa ruwan tana shafamata kai ahankali dan bacci take, ajiyar zuciya yadan sauke ganin tana bacci sanan ya kalli iyayen nasu anatse yace "Abba zan fita da ita waje, gobe nakeso mutafi, and inaso Ihsan tarakamu, nariga nai magana da Omprakash babban Dr ne tun ina school achan na sanshi yace nazo da ita" Ya kalli Ihsan dake zaune tai zuru zuru yace "ke taso muje gida muhada kaya dagangan am going to the airport nai booking first flight to UK gobe" Ahankali Abban Islam yace "inada contacts din ambulance flight, medical transport gwara su, sabida incase of zazzabi ko wani abu suna tareda nurses da doctors dat will attend to the patient acikin jirgin, abokina ne pilot dinsu to inaga shizai fi koya kuka gani" Abban Yusuf yace "hakan yamafi kyau Alaji kamusu magana saimuyi handling komi" Ya kalli Khaleel yace "ku kutafi gida to kuhada kaya da duk wani abu dazaku bukata inyaso matan saisu zauna da ita" shida Yusuf ne suka fita Ihsan tabisu abaya. Fita Abba yay daga dakin dan kiran abokin nashi kan maganan ambulance flight din hakan yasa Mum ta fuskanci su Abba ahankali cike da girmamawa tace "Alaji dan Allah kitayani rokon shi ya yay hakuri ya yafema Farida tadawo gida, bata dawani uba daya wuce shi, ina zataje yau kwana uku kenan daga yau ta kwana agidan wanan kawa gobe agidan waccan, nasan tai babban kuskure wanan abun datama yar uwarta amma tai nadama wlh sai neman gafara take, kaga yahanata tama shigo dakin nan balle tanemi gafarrar yar uwartata, dan Allah kuyakuri kuyafe mata Alhaji, yarinta da rashin hankali sukasa ta aikata wanan mummunar abin" takarashe maganan tana matse kwalla, ajiyar zuciya Abban Khaleel ya sauke yace "in sha Allah zamu mai magana, gaskiya hukuncin yay tsauri, ai hannunka baya rubewa ka yanke kayar korarta daga gida zai iya jefata cikin wani halakar, tunda dai tai nadama ta yarda tai kukkure ai shikenan komi ya wuce, ita kuma Allah yabata lafiya" yay maganar yana kallon fuskar Islam dake bacci abinta akan cinyar Ammi. Fita sukayi daga dakin hakan yasa Anty Hindu ta zubama Mum wani irin mugun harara, dauke kai Mum tayi tana goge ido. Washegari wuraren 10 suka shigo airport din, bangaren private jet terminals suka tafi, sukai parking mota suka fiffito, yana sanye cikin kananan kaya Jean da t-shirt fara, yafito da Islam dake wheelchair Anty Hindu ta shiryata cikin light kayan kanti pink skirt da riga, an samata hula, tsugunnawa yay agaban ta yamata peck a kumatu tareda share mata wuya da soft towel sabida yanda miyau yabata mata jiki yay murmushi yace "you will be fine kinji wife" tashi tsaye yay ganin su Abba da kowa sun fiffito, Yusuf kuma ya gunguro akwatinan guda biyu, tafiya duk suka fara shikuma yana turata har suka kai gaban jirgin da sauri nurses din cikin jirgin suka sauko daukar ta sukayi awani gado suka shiga da ita ciki Ihsan ta rungume Ammi tana daga musu hannu ta shiga, murmushi Abban Islam yay yace "Allah maka Albarka Muhammad, kaje Allah ya kiyaye hanya Allah kaiku lpy" ahankali yace "Ameen" Ya rungume Ammin shi sosai fuskar shi ta shafa sanan tace "take care of my two daughters kanajina ko" gyada mata kai yayi sanan ya daddaga musu hannu yajuya ya shiga cikin jirgin sukuma su Abba sukabar filin jirgin, ahankali jirgin ke tafiya harya daga. Kan kujeran dake kusa da ita ya zauna hanunta yarike yakai kirjinshi ya rungume yana kallon fuskarta, dayar hanun kuma yana shahshafa goshin ta dashi, kadan kadan take bude ido tana kallonshi har bacci yay gaba da ita. Karfe 6 na yamma suka sauka jirginsu ya sauka a UK saukowa sukayi aka shigar dasu motar ambulance din datazo daukan su aka tafi dasu asibitin, har lokacin hanunta na sakale cikin nashi yana kallon fuskarta dan bacci takeyi har yanzu, suna kaiwa hospital din doctors suka karbeta akai ciki da ita sanan suka zauna, wayarshi ya ciro ya chanza line zuwa old Sim dinshi na UK yana chanza wa ya kunna wayar yay dailing wani number bayan sunyi magana ya kashe ko 10min ba'ayi ba wani bature dan yaro dabazai wuce 20 ba yazo jakunkunan su ya amsa sanan yacemai ta harshe turenci yakaimai gida sanan ya bashi kudi yaron yatafi, Ihsan ta kallai tace "Ya waye shi" murmushi yamata yace "wani yarone tun Ina school na sanshi, errand boy ne, yanada kirki" tashi yayi yace "lemme get something for you" restaurant yaje coffee kadai ya siyoma kanshi ita kuma yasaimata snacks sanan yadawo yabata ya zauna, Dr Omprakash ne yafito yakirashi hakan yasa ya bishi office, murmushi Om yamai ya mikamai hannu suka kashe sanan ya nunamai kujera yace "ka zauna" zama yayi sanan Om yace "I have good news" dan murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya ya gyara zama Om yace "zata warke, yanzu dai for now step by step zamu dinga daukan treatment dinta, target dinmu na farko bakinne which for sure zata warke, we will be able to stop d drooling and kumburin komi zai dawo daidai sabida tasamu ta dinga shan maganin dazai warkar da intestine nata tasamu tana mikewa, den daganan ne zamu fara duba abinda ke hanata magana inma any damage ne za'ayi surgery komi ya dawo daidai in sha Allah" ajiyar zuciya ya sauke tareda mikamai hannu yace "thank you so much Dr" murmushi yayi yace "zaka iya zuwa ka ganta kasan 7 ake koran visitors and kasan hospital dinan ba'a bari kowa ya kwana da patient, so jeka ganta kafin 7 tayi" murmushi yay yatashi yafita daga dakin. Ahankali ya bude dakin datake ciki, wata nurse yagani tana saka mata safa akafa an chanza mata kaya zuwa kayan asibitin gaishe dashi nurse din tayi sanan tafita, karasowa jikin gadon yayi yaja kujera ya zauna ya daura kanshi akan cinyarta yana kallon fuskar ta. [6/26, 4:58 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 61 & 62 Yafi minti biyu ahaka sanan ya saketa ahankali yana kallon fuskar ta dan taki yarda su hada ido, murmushin gefen baki yayi sanan yadau teddy yarike tareda rikemata hannu daya yace "let's go" ahankali ahankali take tafiya yana binta ahaka har suka fita daga dakin hasken wuta bau data gani awajen yasa ta daga dayar hanunta taka kokarin kare fuskarta dan tadade rabonta da haske, sai kakkauda kai take, daukarta kawai taji yayi hakan yasa ta kalleshi afirgice, gira daya ya dagamata hakan yasa tadanyi murmushi tamaida kanta ta kwantar akan kirjinshi, ahaka ya dinga tafiya yana kallon fuskar ta harya fito da ita sanan yasata acikin mota Ihsan nata musu dariya sanan ya koma ciki asibitin ya karbo magungunan yafito ya shiga gaban motar mai motar ya tada suka tafi, sai kallonta yake ta madubin kanta ta daura akan shoulder Ihsan dake nunama ta wani game datake bugawa, ajiyar zuciya yadan sauke sanan ya maida kanshi yana kallon hanya. Agaban gidan su mai taxi yay parking Ihsan ta fito tabude mata kofa ahankali ta fito ta tsaya satan kallonshi karaf suka hada ido yana kokarin bama mai taxi kudi da sauri tadan dauke kai kaman bashi take kalloba, akwatin su Ihsan taciro daga bayan mota shikuma ya karaso wajen zai dauketa ta girgiza mai kai kaman zatai kuka, hannunta ya rike yasa key yabude kofar suka shiga ciki, ko ina agyare tsaf tsaf sai kamshin room freshener dakin keyi, dakinshi ya bude ya shigar da ita Ihsan kuma tawuce dakinta. Akan makeken gadon dake dakin dayaci zanin gado fari da bargo fari ya zaunar da ita sanan ya kunna na'urar dake sanya daki dumi sabida sanyin garin, bayi ya wuce ya shiga ya dauro alwala jin ana kiran sallan magrib dan anguwan akwai massallaci, fitowa yayi daga bayin yana kokarin warware hanun rigar jikinshi daya nannade sabida alwala dayay ya kalleta yace "bari naje massallaci, kema tashi kije kidauro alwala ki salla" fita yay dadan saurin jin antada, a kitchen yaga Ihsan na kokarin dafa abinci hanyar fita daga dakin yay yace "kibar girkin nan zan taho da takeaway" kashe gas din Ihsan tayi ta wuce dakinta dayin salla dama wlh tagaji. Da sallama ya turo kofar dakin ya shigo yana kallonta ganin ko motsawa batayi daga inda yabarta ba, maida kofar yay yarufe yakaraso cikin dakin yazo kusa da ita stool din gaban mirror yajawo ya ijiye agabanta yazauna akai, hanunshi yakai yafara warware vail din kanta anatse yace "kinyi sallan?" girgiza mai kai tayi, karasa warware gyalen yayi ya ciro ya ijiye akan gadon yasa hannu yadaga habarta hakan yasa ta kallai murya chan kasa yace "kingaji ko?" gyadamai kai tayi akasalance dan batada karfi ko kadan, kafarta ya dauko ya daura kan cinyarshi yace "sorry, dazaran kinci abinci zaki sami karfi" takalmin ya cire ya ijiye akasa sanan ya dauko dayar kafar ya daura akan cinyarshi ya cire takalmin yana kallonta, ahankali ya ijiye kafar akasa sanan ya mike tsaye ya dauketa tadan tsorata dan bata zaci ita zai dauka ba hakan yasa kirjinta yabuga tana zazzaro idanun tana kallonshi atsorace, murmushi yamata sanan yajuya yay hanyar bayi da ita batare daya dena kallonta ba itama haka, Karan bude kofa dataji ne yasa ta janye idanunta daga nashi tai maza ta juya bayi taga ya shiga da ita, akan wani irin kujeran datagani abayin kaman bishiya ya zaunar da ita sanan yahada ruwa a bathtub maidan zafi sabida sanyin da akeyi sanan yadau goran sabulu ya tsayaya a ruwan ya rufe ya maida ya ijiye, wani irin kamshi ne ya gauraye duka bayin tashi yayi yadawo inda take zaune ya mikar da ita tsaye hannu yadaura akan sweater jikinta yana kallon fuskar ta yace "zokiyi wanka zakiji dadin jikinki" kokarin cire mata sweater yake hakan yasa ta daura hanunta akan nashi tana girgiza mai kai kaman zatai kuka, mayar da hanunta kasa yayi sanan ya karasa cire mata sweater ya wurga kan laundry basket da sauri ta tsugunna ta rungume kanta duka jikinta na rawa sabida shimi kadai ce ajikin nata, ahankali shima ya tsugunna ya shafa kitson kanta daya soma tsufa yace "bakiso kiyi wankan nekuma?" da sauri ta dagamai kai, dan murmushi yasake yi yace "okay tashi am going" juyawa yayi yafara tafiya hakan yasa ta mike tsaye tana goge yar kwallan daya zubo daga kai tayi suka hada ido da sauri ta tsugunna tana kakkare gaban rigar ta, dariya yay yajuya yafita I daga bayin, dadduma ya shinfida mata sanan ya bude wardrobe wani light half gown iya cinya haka yaciro mata mai spaghetti hand jane rigar tanada tauchi sosai dan cotton ce, yadauko mata hijabi da plain zani dan ta daura tai salla ya ijiye mata sanan ya kalli agogo ganin takwas da kwata yasa yafita daga dakin dan zuwa massallaci. Tafi minti sha biyar a ruwan zafin dan ba karamin dadi yamata ba rabon datai wanka me kyau haka ai tama manta, saida tagama sanan tafito ahankali tana dan daddafa bango towel din data gani fari sai kamshi yake ta dauka ta dauro tadan bude kofa kadan ganin baya dakin yasa tafito, ahankali tadan tsugunna tadau rigar data gani akan dudduma tasaka ba karamin kyau rigar yamata ba bayi takoma ta ijiye towel din sanan tafito ta daura zanin tasaka hijabi tai salla magrib da Isha tadan dade zaune sanan ta tashi ta cire hijabin da zanin ta ijiye gaban madubi taje ta zauna dan mai takeso ta shafa jin jikinta yawani bushe kayau, mai ta dauka ta tsiyaya ahannu ta shafa a fuska, hannun rigar tadan saukar sabida tashafa man akafada daukar man tayi ta tsiyaya ahannu tafara shafawa akafadan hannun dataji akan nata yasa ta dago kai da sauri danko kadan bataji shigowan shi dakin ba, dawowa ta gabanta yayi tareda ijiye hannayen nata yana kallon fuskar ta, saukar da nata kasa tayi sabida wani irin kunya dataji tanaji gashi yawani cika mata ido, daukar man yayi batare dayace mata komi ba yakai kan kafadar nata ya tsiyaya kadan sanan ya ijiye, slowly yakai hanunshi ya daura akan kafadar da sauri ta kulle runtse idanunta gam sabida yanda sanyin hanunshi yamata wani irin shocking ajiki, gently yake massaging man all over shoulder har zuwa cikin bayanta hakan yasa tadan matso gaba tareda dan juyar dakai sabida yanda takeji, fito da hanun yayi daga bayan yasake daukar man ya shafa mata a hannayen ta, kafarta ya dauka ya daura akan kafarshi yadan ja rigar zuwa sama kadan jin shiru baifara shafaman ba yasa tadan bude ido ta kallai hada ido sukayi hakan yasa ta mayar da nata ta rufe tareda daura hanunta akan rigarta ta rike sosa, man ya dauko ya tsiyaya akan cinyar yasa hannu ya shafa mata man harya gama ya mayar ya dauko dayan ma yay haka sanan ya ijiye, numfashin shi dataji gab da fuskarta yasa tasake bude ido kadan takallai da sauri ta mayar ta rufe ganinshi gab da ita yanamata wani irin kallo kirjinta sai bugawa yake sosai, saukar bakinshi dataji akan nata yasa tai baya luuuu zata fadi da sauri ya riketa tareda sakin bakin ya dangwali dogon hancin ta yace "fear fear, muje kici abinci kisha magani" ahankali tabude ido ta kallai makemai kafada tayi sanan ta juyar dakai tamai pointing hijabin ta dake kan dadduma alamun yabata, yiyayi kaman bai gane metake nufi ba ya mikar da ita tsaye da sauri ta labe abayan shi tana tattabe baki kaman zatai kuka ta rike rigar shi gam tana turashi da dayar hannun, dariya yayi yafara tafiya tana rike dashi abayan shi haryakai jikin gado, tray daya ajiye na abinci dayayo musu ya daga batare daya juyoba yace "to zauna kici abincin, ni am going outside ma basai kinsa hijabin ba" fitowa tayi daga bayanshi ta zauna tana kallon fuskarshi tray ya ijiye kusa da ita batare daya kalleta ba sanan ya dauko maganin dazata sha ya ballo mata ya mikamata karba tayi sanan tadau ruwan goran dake kan tray din tana kokarin budewa kasawa tayi sabida batada karfi ko kadan hakan yasa ta mikamai batare daya kalletaba ya karba ya budemata sanan ya mikamata shan maganin tayi hakan yasa yajuya yafita daga dakin, dakin Ihsan ya shiga ya tarar tana bacci ga takeaway dataci tabarshi awajen girgiza kai yayi kawai ya kwashe sanan ya kashe mata wuta yarufo mlata kofar. Yadade yana magana da Ammi saida yagama ya kwanta akan kujeran yana kallon news a CNN wurare 11 yatashi ya kashe tv tareda rufe kofa sanan yawuce ciki, dakinsu ya shiga akan gado ya ganta kwance hakan yasa yawuce bayi yay wanka yaduro alwala yafito jallabiya ya saka yadawo gaban mirror ya feshe jikinshi da turare karan turaren ne yatada ita daga baccin datafara kadan ta bude ido ta kallai dadduma dataga ya shimfida yahau kai yasa ta sake lumshe ido tareda gyara kwanciya abinta tacigaba da bacci. "hey" taji yana shafamata fuska ahankali ta bude idonta dasuke cike da bacci saidai bata iya ganinshi sabida duhun daya cika dakin, hanunshi taji akan cikinta yana shafawa cikin wata irin murya dabata saba jinshi daitaba yace "ina kemiki ciwon aciki koya dena duka?" dagamai kai tayi, ahankali taji yajawota jikinshi bedside lamp ya kunna amma saiya mayar da wutan zuwa dim sanan yajuyo dakai ya kalleta ganin tanason ta kwace kanta yace "kin tuna ranan dakika ce Ya Khaleel I love you" murmushi tayi sabida yanda yay maganar was funny, kara jawota jikinshi yayi yahade kanshi da nata yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "kin tuna?" dan murmushi tayi ta janye kanta daga nashi taja bargo ta rufe fuskarta, bargon ya fizge hakan yasa tai yunkuri zata juya da sauri yarikota hakan yasa ta kallai shima ita yake kallo sunkai kusan 3min ahaka ita tafara janye nata idon daga kanshi ta juyamai baya taja bargon tarufa dashi harkai sabida idonshi namata wani iri, shima bargon yaja ya rufa dashi harkai birkitota yay tajuyo tana facing dinshi yanda taga idanunshi sun chanza launi ne yasa ta maza zata juya rikota yayi tareda matso da kanshi saitin fuskarta ahankali yay whispering "I love you Islam, bari nadan baki wani labari" kawai saukar bakinshi taji akan nata tun tana zaton irin dai normal light light kiss din daya saba matane sai taji nayau daban ne, wani irin kissing dinta yake kaman yasami abinci hakan yasa tafara kokarin kwace kanta but rashin karfin dake tattare da ita bai barta ba, sosai ya shiga mata wasu irin wasanni dake birkita ta hakan yasa jikinta yafara rawa, hanunshi acikin rigar ta yasa tafara kokarin tashi dan matseta yay kadan ahankali yace "labari zan baki wife relax". [6/27, 7:33 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 63 & 64 Wani irin hot romance yake mata kaman wani mayunwaci, sosai take kuka kaman zata shide hawaye ko kaman anbude pampo hakan yasa ya saketa tareda tashi ya zauna abakin gadon yafi minti biyar ahaka sanan yatashi ya shiga bathroom, da sauri tadau rigarta daya yar akasa ta saka tasakko daga gadon hartana neman faduwa tafita daga dakin da sauri, dakin Ihsan ta shiga ta kunna wuta kan gadon tahau ta kwanta agefen Ihsan dake bacci taja bargo ta lulluba kirjinta nabugawa sosai kaman zai fito. Yadan dade a bathroom din daga baya yafito daure da dan towel a kwankwaso hanunshi Kuma rike da karami yana goge fuskarshi daga kai yay ya kalli gadon ganin batanan yasa yafita daga dakin falo yafara zuwa ganin bata wurin yawuce dakin Ihsan hangota dayay kan gado kusa da Ihsan tawani lullube da bargo har lokacin jikinta bai dena rawaba yasa yadan saki karamin murmushi maida kofar yay yarufe musu yakoma dakinshi. Ihsan ce tafara tashi ganin Islam kusada ita yasa abin yabata mamaki tashi tai ta shiga bayi ta fito daure da alwala sanna ta tashi Islam din tace "jekiyi alwala" Ahankali ta tashi daga kan gadon ta shiga bayi Ihsan kuma takabbarta salla, bayan ta idar tai azkar sannan tafita danta daura musu breakfast afalo suka hadu da Khaleel sanye da jallabiya yadan dafe kanshi da sauri tace "Ya Khaleel bakada lpy ne" dan yatsine fuska yayi sanan yace "just headache" "ayya sorry, Ya Khaleel inaso natafi fa ance munada test a school next tommorow" zama yay akan kujera tareda jinginar da kanshi yace "maisa yanzu kike fadamin to" komawa tayi cikin kitchen din tabude drawer tace "nima jiya da daddare wata course mate dina take fadamin damuke chatting" dan girgiza kanshi yayi jin yanda ciwon ke damun shi yace "okay bari naduba in akwai flight yau da daddare ko gobe saina miki booking" tashi yay daga kan kujeran ya shiga ciki kofar dakinsu ya bude ganinta akan dadduma yasa ya shiga dakinsu laptop ya dauko yafara searching flight to Nigeria luckily yasami wanda zai tashi yau by 10 nadare dan babu gobe shiya mata booking sanan ya ijiye laptop din akan kujeran yatashi yahau kan gado yaja bargo yadan rufe kafanshi so yake yay bacci sabida yanda kanshi ke kwankwasa cikin kankanin lokaci bacci yay gaba dashi. Sanye da hijabin Ihsan tafito ahankali tabude kofar ta shiga dakin nasu ta mayar ta rufe kadan kadan take tafiya ganin bacci yakeyi, wajen wardrobe taje ta bude kayanta tagani agefe agoge hakan yasa taciro wani doguwar rigar atampa dasauran abubuwan dazata bukata ta rufe sip din sanan ta juyo ahankali tadan daga kai ta kalleshi yanda yake saukar da numfashi ahankali yasa takafe shi da ido anya tataba kallon Khaleel haka kuwa, Jan kafa tayi tadan matso jikin gadon kayanta data rike ta ijiye agefe tasa hannu taja bargon tadan lullube shi da kyau sanan tadau kayan tajuya tafita daga dakin adakin Ihsan ta shirya sanan tafito tasameta afalo atare suka karasa girkin. Wuraren daya yatashi shima dan kiran sallan dayaji ne daurewa yay yamike ya shiga bayi wanka yasake yi sanan ya dauro alwala yafito ya shirya cikin dogon jean da sweater yawuce massallaci Koda yadawo Ihsan kadai yasamu afalo kallonshi tayi tace "har yanzu kan bai denaba kasha maganin kuwa Ya Khaleel wlh bakason shan magani? Bari nakawo ma abinci saikasha maganin ko" zama yay akan kujera yace "namiki booking flight to Nigeria 10 nadare zaku tashi" murmushin dadi tayi sanna tawuce takawo mai breakfast dinshi kadan ya iya ci yature abincin yatashi daki yakara komawa ya kwanta batare dayasha paracetamol ba. Kofa tabude ta shigo dakin ta tsaya atabakin kofa tana kallonshi dan taji lokacin da Ihsan kecemai yasha maganin, mayad da kofar tayi tarufe tazo kusa da gadon tadan rankwafo tana dan leken fuskarshi ganin ya lullube da bargo hada idon sukayi hakan yasa ta juyar dakai da sauri batare databar wajen ba ta tsaya tana wasa da yatsu, ajiyar zuciya yadan sauke yafito da hanunshi ya kamo nata zafin dataji yasa ta hayo gadon tana kallon fuskarshi murmushi yadan mata yace "kinyi kyau wife" Ya daura hanun nata akan kirjinshi yadan lumshe ido, dayar hanunta tadaura akanshi hakan yasa yadan bude ido yanda take kallonshi ne yasa ya janyota jikinshi ya kwantar da ita agefenshi ahankali yace "just headache I will be fine idan nai bacci tareda ke a kusa dani" murmushi yamata yadan rungumota jikinshi hakan yasa tai lamo tanajin yanda numfashin shi ke fita tun tana saurara har bacci itama yay gaba da ita. Wuraren biyar da rabi Ihsan tazo ta kwankwasa musu kofan jinsu shiru gashi har anyi sallan la'asar shiya fara bude ido cikin bacci yace "come in" maganar shi ya farkar da ita hakan yasa tabude ido ta kallai suka hada ido, bude kofar da Ihsan tayi ta shigo yasa taji wani kunya yakamata tafara kokarin ya saketa dan ta tashi amma yaki, murmushi Ihsan tayi tace "Ya Khaleel shida saura fa niduk nakosa muje airport din saisa nazo natasheku" tabe baki yay yace "saima nahanaki tafiyar" dariya tai sanan tajuya tafita daga dakin ya juyo da kanshi ya kalleta yanda taketa mutsu mutsun ya saketa ta sauka, ahankali yace "muje kitayani yin wankan to, kinga yanzu am feeling much better dama dankin gudu jiyane kikasa ciwon kan dole ya kamani" dan murmushi tayi tareda boye fuskarta abayan hanunshi, dauke hanun yayi yadaura a bayanta hakan ya bayyanar da fuskarta yace "wai mesa kin cika kunya ne?" make mai kafada tayi hakan yasa yadan jawota kadan ya daura kanta akan kirjinshi yana shafa bayanta yace "inda ace Eesha na raye da hala ace ku yan biyune" dan dagokai tayi ta kallai hancinta ya lakata yace "zanbaki labarin ta wataran yanzu tashi muje muyi salla" tashi yayi yadago ta ya sauko da ita daga kan gado da sauri ta fizge hanunta ta shiga bayin ta rufo kofar ta dauro alwala ta fito tana nonnoke kai murmushi yay kawai ya shiga bayin shima. Saida sukayi magrib sanan suka tafi airport din bayan sun biyata wani super market yasa tai shopping abinda takeso, koda zata tafi dan jirginsu yafara boarding ba karamin kuka Islam tayiba ta rungume Ihsan dan sosai taji tana sonta, daga musu hannu tayi ta tafi hakan yasa tafada jikin Khaleel tana kuka mara sauti da kyar ya lallasheta tai shiru sanan suka fito daga airport din suka taho gida. Alwala duk sukayi shiya jasu Isha sanan yadan fita dan yayo musu take away. Koda yadawo bai sameta a dakinsu ba murmushi kawai yayi yawuce dakin Ihsan tana ganinshi ta tashi zaune dukta rude dan bata manta daren jiyaba, take away dayayo mata yabata sanan yafita daga dakin, budewa tayi taci shinkafar iya cinta sanan ta mayar ta rufe tasha ruwa tashiga bayi ta sake yin brush tafito ta kwanta abinta. Adaddafe yay nafila sabida wani sabon zazzabi da ciwon kai dayaji ya rufeshi. Yunkurin amai dataji kaman amafarki yasa ta bude ido, hannu tadan mikar ta kunna wutar dakin tana kallon ko'ina takai dubanta ga agogom dake manne abangon dakin karfe uku da minti goma. kakarin aman data sakeji yasa ta mike tsaye da sauri kirjinta na bugawa tabude kofa tafita daga dakin, kanta ta daura akan kofar dakinshi adan rude tabude kofar ta shiga cikin dakin jin daga nan takejin karan, daidai lokacin ya bude kofar bathroom shima yafito adan duke ko tsakar dakin bai iya karasowa ba kawai taga ya zube akasa kaman ma ya suma ne, da gudu ta shigo dakin ta tsugunna a inda yake takai hannu arude ta taba goshin shi duka idanunshi alumshe suke ga jikinshi zafi sosai, arude tashiga jijjiga shi tana kuka, ganin ko motsi bayayi yasa ta tashi da gudu ta dauko wayarshi dake kan gadon budewa tayi hanunta na rawa number Dr Om ta Nemo a contact tai dailing number ringing biyu ya dauka "Hello Khaleel" bude baki tayi tana kokarin yin magana amma magana taki fitowa, wuyanta tashafa tana runtse idanu da karfi tana kokarin magana amma Ina takasa, sosai take kuka tana nuna Khaleel da dayan hanunta, daga ta dayan bangaren Om yace "Hello Khaleel kanajina kuwa, hello" iya karfinta take bude baki tana kokarin fitar da magana amma takasa saima wani irin zafi dataji makogwaranta nayi "Hello are you there, I guess d network is bad" katse wayar yayi hakan yasa ta jefar da wayar akan gado tana kuka jikinta har rawa yake dawowa inda yake tayi ta tsugunna tasa hannayen ta a kirjinshi tana jijjigashi sosai tana girgiza mai kai, tashi tayi da gudu ta shiga bayi ta debo ruwa a kofi tazo ta tsugunna ta yayyafamai amma ko motsi baiyiba, wani irin kuka tasake fashewa dashi tasa hannunta tana shafa wuyarta tana bude baki wani irin runtse idanu tayi sabida azaba tana nishi sosai "Ya'a'a'" tafada da wata irin murya, ahankali taga yadan bude ido dasuka kankance sukai jaa ya kalleta da sauri ta daura kanta akan kirjinshi jikinta har rawa yake sabida yanda take kuka, tashi tayi daga kirjin nashi ta taimaka mai ya zauna yajingina da bango yana kallonta da idanunshi dasuka xhanza launi, da dan gudu tafita daga dakin kitchen taje ta kunna ruwa a heater kettle nan da nan ya tafasa ta zuba a mug, tea ta hadamai mai kauri sosai ta dawo dakin ta ijiye agaban shi wajen drawer taje ta bude ledan magungunan ta tabude tana cicciro magungunan kwalin tana dubawa tana yarwa, paracetamol datagani ta dauko tadawo inda yake ta tsugunna tabaro guda biyu tasaka mai abaki yatsine fuska yay da sauri takai tea bakinshi hakan yasa yadan sha ya hadiye maganin, ahaka ta dinga bashi har yasha kusan Rabin kofin yadan mata murmushi kadan yace "am okay" sosai yaga tafashe da kuka tahau kan jikinshi ta shafa fuskarshi tareda mai alamun sorry da hannu, lumshe mata ido yay yabude hakan yasa ta rungume shi tsam tsam tareda sake fashewa da kuka, sunfi minti uku ahaka motsin dataji yanayi yasa ta ciro kanta daga kirjinshi ta kallai baki taga yana cijewa da sauri ta tashi daga jikinshi tareda kamamai hannu ta tadashi gado tasa yahau itakuma ta koma tadau mug din dayasha tea dashi tafita daga dakin takai kitchen sanan ta dawo dakin ta rufe kofar bayin daya bari abude, ahankali yake binta da kallo dayar pingilar rigar baccin dake jikinta. Kashe wutar dakin tayi sanan tadawo kan gadon itama tahau ta shige jikinshi sosai ta rungumoshi tasa hanunta tanata shafamai bata irin yanda akema yaro da baida lafiya dan hanun kuma tana goge hawayen dasuka kasa dena zuba dan wani iri taji tanaji mutumin dayake ta kula da ita ashe baida lpy kasa dena kukan tayi sai share hawayen take da bayan hannu hanunshi taji akan samar fuskarta ya share mata hawayen sanan ya rungumeta tareda matseta ba takawo komiba dan tazaci ciwon ne kesashi haka, ahankali yakai hanunshi bayan rigarta yadaura akan igiyar da ake kulle bayan rigan dashi ya warware. [6/29, 11:47 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 65 & 66 Bakinshi yakai saitin kunenta da kyar yace "Islaam I wanna make u mine" yana fadin haka yahade bakinshi da nata wani irin hot kiss yake bata yasa hannu yacire yar rigar yayar ya shiga wasanni da kowani sassa da bangare na jikinta kukan datake yi yasa yafara lashe hawayen yahade bakinshi da nata, tun tana mutsu mutsu harta gaji ta cigaba da karban zazzafan sakonnin dayake bata addu'oin dayafara karantowa yasa tafara kokarin tureshi da karfi da kyar hartana wani irin runtse ido da cijewa tace "ya'aaa Khal" takasa karashe kiran sunan nashi sabida yanda take shafa wuyanta dataji yana mata zafi, ahankali ya daga kai da idanunshi dasuka kankance cike da mamaki yace "maimaita abinda kikace?" har wani irin runtse ido take tace "ya'aa'a Khaleel" wani irin farin ciki yaji ya lullube shi duddu maganan na breaking yace "maimaita kuma inji wife" sake dagewa tai tace "ya'aaa Khal.. Khaleel" wani irin rungumeta yay cikeda farin ciki yace "Alhamdulillah" murmushi tamai tana kokarin kwance kanta dan ba karamin faduwa kirjinta keyiba kara jawota jikinshi yayi yana mata wani irin kallo yace "ko ki natsu kokuma nai abinda nai niyyar yi" da sauri ta kwantar da kan nata akan kirjinshi tareda lumshe ido jikinta na rawa haka ya dinga shafa bayanta har yaji takara nauyi numfashin ta na fita ahankali. Kasa bacci yay sabida farin ciki ahankali ya kwantar da ita akan gadon yana shafa kanta yay kusan minti biyu yana kallonta sanan yatashi ya sauka daga gadon, kanshi yadan dafe ya lumshe ido sanan ya bude tareda cije baki yawuce ya shiga bayi. Yakai kusan minti ashirin abayin sanan yafito daure da towel yana kallon innocent face dinta akan gado, gaban wardrobe yaje yasaka singlet da jallabiya fara sanan yadawo ya shimfida dadduma rakatanil fajiri yayi sanan yataso yadawo kan gadon kumatun ta yaja dadan karfi hakan yasa ta yatsine fuska kaman zatai kuka ta turomai baki batare data bude idoba dan kunyan shi takeji sosai, dan dariya yayi yaja hancinta yace "tashi kije kiyi wanka kiyi salla zan tafi massallaci ne koso kike namiki dakaina?" da sauri ta girgiza mai kai batare data bude idoba ta nunamai kofa sanan ta turashi tana turo baki dariya yayi yatashi yafita daga dakin. Bayan ya idar da salla yay azkar sanan yafito daga masallacin number Om yay dailing Om dake office dinshi a hospital ya dauka yace "Hello Khaleel ka kirani dazu banajin mekake cewa" da sauri Khaleel yace "bar wanan maganan I have good news, yautai magana but is not dat clear haka amma takira sunana harsau biyu" "wow, dama I was expecting dis new dats very great" "nakawo ta anjima kaduba ta?" "kabari gobe kuzo dan dasafen nan zan koma gida yau a hospital na kwana" murmushi yayi yace "okay thank you Om, regards to the family" katse wayar ya kalli sararin sama yanda garin yay blue blue asuba gawani sanyi dake ratsa shi ahankali yace "Alhamdulillah" wani irin farin ciki yake da fara maganan Islam, murmushi yayi yawuce gida. Da sallama ya shiga gidan dan gari haryadan yi haske, da sallama ya shiga dakin nasu agyare yaga gadon kaman ba akai suka kwana ba hakan ba karamin dadi yamai ba, karan ruwan dayaji abayi yasa yagane tana ciki gaban wardrobe yaje ya cire jallabiyar yay hanging dinta akan hanger yanadan yatsine fuska jin kanshi nadan sarawa kadan kadan, kamshin sabulu dayaji yasa ya maida kofar wardrobe din ya rufe yakalli kofar bayin tsaye take agaban kofar bathroom din tana wani jajjan dan farin towel din daya tsayamata a iya cinya, turo baki tayi ganin yanda yake kallonta ta koma tabayan kofar ta leko da kanta tanadan hararan shi, zama yay akan gado yana kokarin cire singlet din jikinshi kaman bashi yagama kallonta ba yace "aiko saidai ki kwana abayin nan Madam" yarfe hannu tayi kaman zatai kuka yana kallonta ta wutsiyar ido yay dan murmushi abinshi, ahankali tafito daga dakin tana sanda dan so take ta dauko hijabin ta datai salla ta ninke ta daura akan stool din gaban mirror, da sauri tai grabbing hijab din tana kokarin warwarewa tasa ya fizge hijabin ya ijiye yana mata dariya yace "wlh baki isaba" turomai baki tayi ya nuna kanshi yace "ni kikema haka" daga kai tayi alamun eh, yatsar shi yasaka abaki yadan ciza sanan yafito dashi yace "okay u ask for it" daukanta yay chak ya jefata akan gado da sauri ta yunkuro zata tashi ya hayo gadon raurau tai da fuska ahankali tace "sor'ry" yanda tai motsi da bakin ya tsaya yana kallo ga lips din sunyi pinkish dasu, yabi wuyarta da bakin kitson ta dake diddiga da ruwa da kallo, yanda taga idanunshi sun soma chanza launine yasa ta mike tsaye da sauri zata tashi fizgo towel din yayi hakan yasa towel din faduwa akasa wani irin ihu tafasa da ya kusa kashemai dodon kunne ta shige jikinshi ta kanannade shi tareda sa tafukan hanunta tana rufemai fuska tana kuka sosai, shi dariya ma tabashi, hannunshi yakai yacire nata daga kan fuskarshi hakan yasa tasake mayarwa tana wani irin bobboyewa ajikinshi, hanun nata yakamo yahada yarike yana kallon fuskarta wani irin rawa jikinta yafara, ahankali ya sanya hanunshi yashafa saman kan idanunta hakan yasa ta lumshe ido jikinta na rawa ya kwantar da ita akan gado tareda daura kanta kan tattausan filon dake wajen, hanunta tamika tana kokarin taja bargon tarufe jikinta taji ya rike hanun ya ijiye agefe, anatse ya rankwafo da kanshi daidai saitin fuskarta dawani irin murya mai ratsa kofofin zuciya yace "open ur eyes" girgiza mai kai tayi jikinta narawa, ahankali ya saukar da lips dinshi asaman goshin ta ya sumbaci goshin saida taji wani irin hakan yasa tai yunkurin juyar da fuskarta amma baibata damar hakan ba saima gangaro wa dayayi danshin lips dinshi nabin tundaga goshin ta har zuwa kan hancinta yakara sakin mata wani kiss din, dadan dade a wajen yana sauraron yanda numfashi ke fita ta hancin ta sanan yasake gangaro wa yadaura lips dinshi akan nata wani dan nishi tasaki "ahhh" sabida yanda taji, sosai yake kissing lips dinta hanunshi akan cikinta yana shashafawa yana gangarowa sama mutsu mutsu tafara yi jin yana neman kamo kirjinta, hakan yasa ya danneta, sosai ya shiga wani iri zazzafan wasanni da ita dake neman shidar da ita, saida ya tabbatar ya karar da dan kuzari da karfin fada da mutsu mutsu datake dashi sanan yafara karanto addu'o'i ya maida Islam tashi. [6/29, 11:47 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 67 & 68 🇳🇬 Da sallama Farida ta shigo falon Abba ta zauna tareda dukar da kai kasa, Jaridar dake hanunshi ya ijiye agefe ya dago kai yana karemata kallo idan kaga yanda ta rame kaman mai wani ciwo, tai wani irin yaushi, wani irin tausayin tane ya shigi Abba amma hakan bai hanashi daure fuska ba ya kalleta tareda gyara murya yace "ina jinki" dago kai tayi ta kalli Abban ahankali tace "Abba dan girman Allah ka karamin lokaci wlh banda kowa har yanzu ne Abba, dan Allah" takarashe maganan kaman zatai kuka hakan yasa Abba ya kasa dauke idonshi daga kanta da hannu yamata alamun tazo hakan yasa taje gabanshi ta zauna duktai wani iri da ita ya kafeta da ido, hanunta har rawa yake ta daura akan kafarshi tawani irin fashe da kuka tace "Abba wlh na tuba na mugun yin nadaman abinda nama Islam, babu randa zanyi salla da bazan nema mata addu'a samin lpy ba, Abba dan Allah kadena fushin nan dani dan Allah kayakuri kayafemin ka kiramin Islam na rokesu suma" ta kife kanta akafarshi tana kuka hanun Abba dataji akanta yasa ta dago fuskarta ta kalleshi, share mata hawayen yayi dadan murmushi akan fuskarshi yace "nadade da yafe miki Farida komi yawuce" murmushi sosai tayi ta goge kwallar tace "nagode Abba" kanta Abba yasake shafawa yace "inaso kifadi mini gaskiya meke damunki maisa kika rame haka Farida, kar wani ciwon yazo ya kamaki, meke cinki araine" wani sabon kukanne yazo mata dukda yanda taso ta danne kasawa tayi tafashe da kuka sosai da kyar tai shiru Abba yace "inajin ki" wasu zafafan kwalla ta goge ahankali tace "Khaleel, Abba narasa ya zanyi nakasa cire sonshi azuciyana, nina rasa wanan wani irin sone, narasa yanda zanyi da raina, Abba please help me wlh zuciyata har wani zafi take kamar garwashi" sosai Abba yaji tabashi tausayi ya gyara zama yace "inaso kiyi azumi koda uku ne sanan kullum zan dinga tadaki da daddare kidinga kiyamul laili ki roki Allah yabaki ikon cin wanan jarabawan, haka Allah yake abinshi yakan jarabce ka da komi yaga yaya zakayi, so kidage kici wanan jarabawan karki biyema zuciyar ki ta kaiki ga halaka, kikoma ga Allah sai kiga Allah yassare miki matsala dake damunki, bari nabaki labarin Khaleel dinan kiji sabida kingane cewa auren nan nashi da Islam Allah ne kawai yahada, robone atsakanin su saisama har yazo garin nan suka hadu har sukai aure" nan ya gyara zama yabama Farida labarin Khaleel tiryan tiryan yanda su Abba suka bashi, ba karamin mamaki Farida taiba, bakin da Abba yay yasa tafito daga dakin jikinta duk asake. Da kyar ya iya controlling kanshi yabarta ganin yanda take numfashi kaman zata shide dama bawani lafiyan kirki gareta ba yakoma gefenta ya kwanta yana kallon fuskarta da hawaye kebi ta gefen ido tana wani irin saukar da ijiyan zuciya, da kyar ya iya daga hannu ya lalubo hanunta yakama yarike gam yadan runtse ido danbai masan mezaice mataba, hanun yajawo yadaura akan bakinshi yadan sakin mata light kiss akai sanan ya mayar ya ijiye, sakkowa daga kan gadon yayi hakan yasa ta kara runtse idanunta, dan murmushi yayi yawuce bayi yahada mata ruwa mai zafi sosai yafito hanunta yarike zai tado da ita yace "zomuje kiyi wanka Baby" fizge hanun tayi cikin kuka tamake mai kafada batare data kallai ba tace "uhm 'uhh" dan rankwafo wa yay yace "u will feel better" kara makemai kafadar tayi tana kuka abinta, hannu yakai zai tabata ta tureshi tana turo baki ta tashi zaune da kyar tana rurrufe jikinta da bargon tana kukan banza batare data kallai ba, ahankali ta saukar da kafafunta kasa tai jimm, jikin gadon ta dafa ta mike tsaye da kyar tana faman kakkare jikinta da uban bargon dataja, dan murmushi yayi yay folding hanunshi yana kallonta, wani irin kuka take rerawa mai kama da waka takara kamo bargon tana tattarewa sabida yanda yabazu akasa sanan tafara kokarin daga kafanta dan tai tafiya wani azaba dataji yasa tasake kara karfin kukan ta ta kankame bargon da hannu daya dayan hanun kuma tana yarfewa, tashi yay yazo gabanta yanadan murmushi yakai hannu zai riketa ta bugemai hannun tana kuka takuma ki yarda su hada ido, kara kai hanun yayi zai tabata takuma bige hannun hakan yasa yay folding hanun akirjin yana mata wani irin kallo yace "okay dannama kyaleki kikemin tsiwa angaya miki nakoshi ne" kaman daga sama yaji tafado jikinshi tawani kamkame shi tana kukan da nidai nakira na banza 😂 sakin hanun yayi ya rungumota da kyau yana patting bayanta yakai kanshi saitin kunenta dawata irin murya yace "is okay am sorry kinji, da zafi ko?" gyada mai kai tayi tana kara gyara kwanciyar kanta akan kirjinshi, dan murmushi yayi yace "sorry to, muje kiyi wanka kici abinci u will be fine kinga sha biyu tayi" cirota yayi daga kirjinshi tareda manna mata light kiss a lips sanan yawani dauketa kaman jaririya sukai bayi. [7/1, 2:02 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 69 & 70 Da taimakon shi tai wanka ta tsarkake kanta sanan yanado ta a bathrobe yafito da ita sai wani murmushi yake ya zaunar da ita abakin gado, yar doguwar riga maidan kauri yaciro mata sabida sanyi sanan yakawo mata mai ya shafa mata yadau rigar zaisa mata ta fizge tana turo baki murmushi kawai yayi yajuya yafita daga dakin, kitchen ya shiga yadauko egg yasoya mata dan abinda kadai ya iya kenan aduka girki sanan yahada mata tea yadau bread dukya jera akan tray din yakoma dakin, shi yadinga bata tanaci harsaida ta sanye tea sanan ta kauda kai, magungunan ta ya dauko mata da paracetamol yabata tasha sanan ya zauna gefenta ya rike mata hannu gam yana kallonta dan dago kai tayi kadan ta kallai zata kawad dakai yasa hannu yajuyota yana murmushi yace "thank you Islam" kunya sosai yabata hakan yasa ta boye kanta ajikinshi kwantar da ita yayi yace "bari naje nai wanka nima" yawuce bayi hakan yasa ta gyara kwanciya ta lumshe ido tana tunanin su Abba da Farida ahaka bacci yay gaba da ita. Ranan gabaki daya haka yawuni yana kulla da ita duk idan zatai wanka saiyasa takara shiga ruwan zafi. Washegari bata wani tashi da zazzabi ba shiya taimaka mata ta shirya cikin doguwar riga baka tai gayu kaman irin larabawan nan sai kallonta yake kaman zai hadiyeta hakan yasa ya jawota jikinshi ya rungumeta sosai sanna ya rike mata hannu suka fita daga gidan bayan ya kulle gidan hospital suka tafi inda Dr Om ya dubata he was so happy da yanda tai maganan yace musu ai tariga da ta warke zama su iya tafiya basai sun kara dawowa ba unless akwai any complication. Khaleel ya kasa daina murmushi nan yama Om godiya suka fito wani hadadden saloon ya kaita yana rike da hanunta suka shiga da sauri turawan suka tarbesu suna musu sannu da zuwa zama yayi akan wani kujera sanan yace "a kwance mata kitso a gyara mata gashin kar amata wani kitso" zaunar da ita sukayi akan kujeran gaban madubi suna kwance kitson duk idan zata dago kai ta kalli mirror sai sun hada ido hakan yasa ta murguda mai baki ya nuna kanshi ta madubin irin ni? Takara murguda mai tareda gyada kai murmushi yayi ya mata kwafa tamai fari da ido baki yadan bude yana kallonta kafin ya dauke kai ya jawo Jaridar dake nan tsakiyar dakin kan center table ya bude zai karanta yakara dago kai ya kalli fuskarta ta madubi gwalo tamai hakan yasa yay maza ya maida kanshi kan Jaridar yana murmushi kasa kasa. Kusan 3 hours ya dauke su gama tsifan da wanke gashi da gyara shi danhar stretching gashin saida akai mata gashin yakara tsawo saiwani kyalli yake sanan suka juyomai da ita sukace "sir yamaka haka kokuma akara wani abu?" dagokai yayi tareda rufe jaridar hanun nashi yana kallonta yanda gashin ya bazu a bayanta dan basuyi mata pakin ba, ba karamin kyau tamai ba ya kalli baturiyar yace "is fine amma kimin parking gashin sanan kima bakin gashin coils, nafison hakan" dariya baturiyar tayi sosai ta kalli Islam tace "wanan mijin naki yama fiki sanin abinda zai miki kyau" yanda yafada hakan ko tayi aiko ba karamin kyau hakan yamataba sanan Matar tasake juyo da ita tace "Ya yanzu?" dago kai yayi ya kalleta tawani turomai baki wayar hanunshi ya maida aljihun gaban riga sanan yama Matar alamun perfect 👌 da hannu, tashi Islam tayi daga kan kujeran ahankali dan duk ta gaji da zaman adan hankali tai tafiya jin zafi zafi akasan har zuwa inda yake yana kokarin bude wallet dinshi ahankali yace "muje gida saiki shiga ruwan zafi zai dena miki zafin gabaki daya" gyadamai kai tayi yaciro kudi dayawa yabama Matar aiko ba karamin dadi tajiba tace "musu come back soon" suka fito mota suka shiga ta daura kanta akan kafadar shi sabida yanda tagaji gyara mata kwanciyar yayi gabaki daya ajikinshi nan nan da nan bacci yay gaba da ita, sai Wuraren 6:50 suka kai gida sabida yanda dan holdup yakamasu ahanya. Ahankali yay tapping fuskarta hakan yasa tabude ido ta kallai kofa yabude mata tafita sanan shima yafito ya sallami mai motar yabude musu kofa suka shiga gidan, zata wuce daki ya kamo hanunta ya matseta ajikin bango yana mata wani irin kallo "wakike ma gwalo and all sort of things dazu?" dan turo baki tayi kafin tasaki bakin da sauri tace "sorry" girgiza kai yayi yace "inaa naki saina.. " bakinta yakama ya shiga kissing dinta kaman zai cinye bakin jin tsayuwa na neman gagararta tafara kokarin silalewa kasa ya rikota ya zaunar akan kujera batare daya saki bakinba kiran sallan da aka kirane yasa ya saketa yana kallonta da idanunshi dasuka dan chanza launi yace "jekiyi wanka kiyi salla bari natafi massallaci" tashi yayi yawuce yafita tadade zaune daga baya ta tashi duk jikinta yay tsami ga zafi zafi datake ji, bayi ta shiga tahada ruwa mai zafi sosai tashiga sanan tai wanka tafito tai salla. Bayan sallan Isha ya shigo gidan da takeaway yatasa ta agaba taci abincin da kyar ya dauko magani yabata tasha, wayarshi ce tai ringing ya dauka ya kalleta tareda nuna mata wayar yace "Abba ne and is video call" da sauri ta dawo kusa dashi, ganin dan shimi ne ajikinta yasa ya nuna mata hijabi tasaka sanan yay picking call din Abba ne da duka yayin ta Ya Abdallah Ibrahim harda Sameer auta bakaramin dadi taji data gansu ba tanata murna suma sai murnan fara maganan ta suke sunamata ya karfin jiki tace "Alhamdulillah taji sauki, Abba yamusu addu'a sosai suka amsa da Ameen ahankali tace "Abba ina Faree?" janye fuskar shi Khaleel yay daga wayar yana mata wani irin kallo, bama ta lura dashi ba sabida yanda take kallon wayar Abba "yace gatanan itama dukta damu zatai magana dake" Bama Farida dake gefe wayar yayi hakan ya bayyanar da fuskar Farida, hannu Islam tasa abaki jin kuka yazo mata ganin yanda Farida ta chanza ahankali tace "Faree wat happen to you like this? Innalillahi bakida lpy ne?" murmushi Farida tayi with so much regret yar uwarta data damu da ita hakane ta cutar sabida namiji da kyar ta iya girgiza kai sabida kukan dayazo mata ahankali tace "Islam dan girman Allah kiyafe mini na cutar dake sosai, wlh wlh dis time dagaske nake natuba Islam natuba, dan Allah kiyafe min bazan sake abinda nayiba" takarashe maganan tana kuka sosai itama Islam din kuka tafashe dashi ta sauko daga kan gadon ta zauna akasa tana kuka da kyar tace "Faree nima am sorry, wlh bakimin komi ba, I understand your actions, nadade dayafe miki u are my only sister ke kadai gareni I can do anything for you, tell me bakida lpy ne meya sameki kika rame haka?" girgiza mata kai Farida tayi tareda goge kwallan dake zuba tace "bakomi kawai zafi zuciyata kemin ne koda yaushe amma ko ciwon kai banayi" sosai Islam ta fashe da kuka tace "sorry Faree" kasa daure yanda take kuka yayi hakan yasa ya sakko kasan yazo kusa da ita ya zauna tareda daura hanunshi akan kanta ya kwanto dakan nata kirjinshi yana bubbuga bayanta kokarin tureshi takeyi sabida yanda Farida ke kallonsu amma shiko fuskar wayar baima kalla ba danko fuskarta bayason gani, tarin dasuka ji Farida nayi sosai yasa tajuya ta kalli wayar sosai Farida ke wani irin tari Islam tace "sorry are you ok, kisha ruwa" dan murmushi tayi tana kokarin hadiye tarin takai hannu bakinta jini tagani da sauri Islam da kaman idanunta zasu shiga wayar tace "Faree blood, tarin jini kike?" hannu taga Farida ta daura akan kirjinta tana wani irin tari tana kallon fuskar Khaleel dahar lokacin baima kalli screen dinba hasalima lumshe ido yayi tareda jingina da gado yakai hanunshi cikin hijabinta yana wasa da jelar gashin ta, sosai Farida ke tari jini nabin bakinta takama zuciyar ta da hannu daya tana kallonshi har lokacin, Islam tace "Faridaa, Abba" ta kwalama su Abba datake jin hayaniyan su kira, da sauri su Abba da Ya Abdallah suka zo wajen daidai ta lumshe ido ahankali tace "M.. K" banbare wayar Abba yayi daga hanunta ya kalli Islam yace "bari mu kaita asibiti, Allah kara sauki Islam" katse wayar yayi Islam tafashe da kuka sosai sai a lokacin yabude idonshi ya kalleta bakaramin cin ranshi kukan nata yakeba yacire mata hijabi ya ijiye hanunshi yakai saman kan idonta yana share hawayen datake yi yajawota zai rungume cikin kuka ta turemai hannun tace "bakaji yar uwata bata da lafiya bane" dan bude ido yayi ya kalleta da kyau sanan yace "to ai naji Abba yace zaikaita hospital ko" kara fashewa tayi da kuka ta tashi taje gaban wardrobe tana ciro kayanta tace "ni wlh nigeria zamu koma yanzu nan Farida batada lpy I need to be with her" "babu inda zamu" yafada cikin kakkausar murya yana kokarin cire rigar jikinshi da sauri tadawo gabanshi ta kalleshi tace "sabida ba kanwar kabace ko?" wani irin kallo yamata sanan yace "yes" kan gado yahau yaja bargo abinshi tareda lumshe ido bakaramin ciwo maganan yamata ba tsugunnawa tayi ta dinga kuka akasan wajen takai kusan minti biyar sanan ta tashi bargon daya rufa dashi ta yayemai ta jefar hakan yasa yabude ido ya kalleta, daure fuska tayi ta tsayar da kukan datake tace "wlh bazakayi baccin ba bayan kaine sanadin ciwon nan datakeyi, is all ur fault, Kaine kasamata wanan ciwon am sure ciwon zuciya ne yakamata, tunda nahadu dakai matsaloli keta faruwa dani, tunda nahadu dakai farin cikina yaragu, karabani da my only sister, is because of you yar uwata takusa kasheni, ta tsaneni, taso kashe kanta sabida kai, ni bana sonka Farida ke sonka, ka sakeni dan Allah ka aureta karta mutu da ciwon zuciya, are you dat wicked dabaza sota Koda sau daya bane? Karka kashemin yar uwa, kasaken... " kasa karashe maganan tayi sabida wani irin mugun mari daya dauketa dashi. [7/1, 2:02 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 71 & 72 Dafe kuncinta tayi tana shafawa, jikinta har wani irin barbar yake sabida yanda taga fuskar shi bata taba ganinshi hakaba, nuna ta yay da yatsa cike da bacin rai, dawa ta irin kakausar murya yace "ni kike gayama magana haka akan wacce ta kusan kaiki lahira? Ni kike ma rashin kunya?" kasa magana tayi saima jada baya da tafara yi tana kuka sabida yanda taga idonshi ba karamin tsoron shi taji ya shige ta ba, wani irin kallo yamata abubuwan data fadin mai yana yawo akanshi juyawa yay yafita daga dakin tareda bugo kofar sabida tsabagen yanda ranshi yabaci. Zubewa tayi a wurin tafashe da kuka sosai tafi hour daya tana kuka daga baya bacci yay gaba da ita anan kasan. Dakin Ihsan ya shiga ya zauna tareda dafa kanshi yafi minti biyar ahaka dan rashin yay bala'in baci da kyar ya mike tsaye tareda fuzar da iska yawuce ya shiga bayi ya dauro alwala yadawo dakin yasaka jallabiyar shi daya dauko ya kabbarta salla. Ahankali take bude idonta ganin gari yay haske yasa ta mike tsaye da dan sauri, cije baki tadanyi sabida zafin dataji ta bude kofar bayi ta shiga brush tafara yi sanan ta gasa kanta tai wanka ta dauro alwala tadan lumshe ido sabida yanda taji kanta namata ciwo, towel ta daura tabude bayin tafito hada ido sukayi yana sanye da jersey ya zauna abakin gado yana daure igiyan sport shoe din kafarshi, kallo daya yamata ya dauke kai tareda cigaba da abinda yakeyi kasa karasowa cikin dakin tayi ta tsaya a wurin tana wasa da yatsun ta wani irin shakkar shi taji tanayi karan fesa turare dataji yasa tadaga kai tadan kalleshi yana tsaye gaban mirror yana fesa turare ahankali tace "ina kwana" ijiye turaren yayi bayan yagama fesawa yajuya zai fita daga dakin batare daya kalleta ba yace "kintashi lpy" baijira mezata ceba yabude kofa yafita daga dakin, kofan tabi da kallo yanda yabuga kofar har cikin ranta saida taji ta runtse ido, wani irin kuka ne taji yazo mata tafara kukan da kyar ta shiru tawuce wardrobe taciro wata simple doguwar riga ta saka tadau hijabi tasa tai salla, ta dade zaune tana azkar daga baya tamike ta cire hijabi ta ijiye jin tanajin yunwa sosai. Dakin tafara gyarawa tass tafashe ko ina da turaren daki sanan ta shiga dakin Ihsan din nanma ta gyreshi tass sanan tawuce falo ta gyara dudda babu wani datti ta shiga kitchen din, shiru tayi tana kallon ko ina wani irin kuka ne taji yazo mata, Indomie da tagani kawai ta iya dauka da kwai daya ta dafa ta juye adan karamin plate tadau fork tawuce dakinsu tadan ci dan jitayi batada wani karfin cin abincin, magungunan ta dake gaban mirror tagani wani kuka takara ji yazo mata inda yana nan dashi zai bata da kyar ta mike tsaye ta dauko su tasha tahada da paracetamol duk tasha tafito da kwanon tazo ta ijiye ta kwanta akan doguwar kujera tana kallon TV ahaka bacci yay gaba ita. Wuraren 2 ya shigo gidan na rana ya dade tsaye afalo yana kallonta karfin yawuce ciki yayo wanka ya fito daure da towel ya zauna akan kujera yaja laptop dinshi booking flight yamusu dazai tashi gobe dan shima jitayi duk ya gaji da garin gwara ya koma Abuja kawai yafara aikin shi, karfe 11 nadare jirgin nasu zai tashi gobe mayar da laptop din yayi yarufe ya dauko mai ya shafa sanan yadau kayan dazaisa yafita daga dakin yakoma dakin Ihsan yay kwanciyar shi. Karan dataji yasa ta bude ido ahankali tana karema falon kallo, a kitchen ta ganshi tsaye yana kokarin daukan heater kettle yana sanye da farar singlet dayar 3 quarter kafarshi cikin slippers, tashi tayi daga kujeran tazo wajen kitchen din yanajin ta amma yaki kallonta hanunta yaji ta daura kan nashi cikin sanyin murya tana kokarin karban kettle din tace "kawo nasama, mekake so nama?" batare daya kalli fuskarta ba yasa dayar hanunshi yacire hanunta dake kan nashi ya bude tap yatara kettle din yana diban ruwan, saida ya dibi daidai wanda yakeso sanan ya kashe tap din yarufe kettle din yajona shi da igiyar shi, dan juyowa yay ya kalleta yace "i can manage" ta gefenta yazo zai wuce tariko hanunshi da sauri muryan ta har rawa yake tace "am sorry, dan Allah kayakuri idan kaji haushin abinda nace jiya ne, babu yanda zanyi ne Farida yar uwata ce, my only sister kaji" takarashe tana wani rera sabon kukan dan juyowa yay ya kalleta hakan yasa tadan tsagaita kukan datake yi, hanunshi ya fizge daga nata yakara mata wani kallo sanan yace "nasani i know she's ur only sister" ya maimaita mata maganar da tamai na karshe yawuce wurin kettle din ganin yana tafasa ya kashe ya dauko mug zai juye ruwan aciki da sauri ta tsayar da kukan datake yi tazo wurin tace "kawo natayaka" daukar kettle din yayi ya tsiya ya ruwan aciki batare daya kalleta ba yace "zan iya da kaina" ajiye kettle din yayi ya dauko nescafe ya zuba aruwan da honey sanan yadau spoon yafita daga kitchen din yawuce falo ya barta anan, yana gamasha anan falo yabar cup din ya shiga ciki ya chanzo kaya zuwa Jean da t-shirt daya daura jacket akai yazo yafita daga gidan, wani irin abu taji ya tsaya mata arai hawaye kawai taji yana fita ta dinga goge wa ranan hartai bacci bata ganshi ba, da safe ma data tashi bata ganshi ba tadai ga note a gefenta kan gado daya rubutu ta hada kaya yau zasu tafi wani dadi ne taji ya lullube ta zataje taga Farida, bayan sallan Isha ya shigo gidan afalo ya sameta zaune da doguwar riga ja ajikinta ga akwatin su babba data hada kaya ta fito dashi falo, baiko kalleta ba ya shigo yaja jakar yafita da ita waje sanan ya dawo duk tana tsaye, tashi jakar yafito dashi batare daya kalleta a yace "muje" bayanshi tabi jikinta duk asalube suka fito ya kulle gidan yabama Raymond dake waje key da wasu kudi Yaron yarakasu har wajen mota suka shiga yana daga musu hannu suka wuce airport. Bayan sunyi checking in suka zazzauna suna jiran afara boarding, goma dayan kai aka fara boarding suka shiga jirgin nan jirgin ya tashi jarida yake ta karanatawa abinshi chan yaji kanta akan kafadar shi Jaridar yarufe yadan kalli fuskarta bacci yaga tanayi hakan yasa yadan gyara mata kwanciya tareda sauke ajiyar zuciya shima ya lumshe ido. Karfe tara da minti arba'in jirgin su ya sauka a airpot din Abuja, ahankali take bude ido harta bude su duka hada ido sukayi hakan yasa ya dauke kai da sauri, daga kanta tayi daga kafadar shi tana zare ido, fara fita akayi daga jirgin hakan yasa yatashi itama ta tashi sauka sukayi wata mota tazo ta dauke su ta ijiye su a gaban luggage claim nan suka jira akwatinan su suna zuwa ya kwasan musu ya gungura tana bishi abaya suka fita daga arrival din wani driver sune da Ammi ta turo musu yazo ya karbi akwatinan daga hanun shi yana gaidasu cikin fara'a, Khaleel ne ya amsa suka shiga motar sukabar airport din. A wuse gaban wani babban gida driver yay horn aka bude musu suka shiga ahankali tafito daga motar mai gadi yazo ya cicciro akwatinan daga bot shikuma driver yakoma cikin mota yamusu sallama yabar gidan, kofa ya bude ya shiga haka yasa tabi bayanshi duk agajiye wani hadadden duplex ne, falon anmai fentin brown da milk, furniture din cikima kalan su kenan, upstairs dataga yayi yasa tabi bayanshi dadan sauri wani falon tasake gani a upstairs din sanan ga dakuna uku, wani daki taga ya shiga kasa binshi tayi tabude dayar dakin akwatin ta da tagani adakin yasa ta gane nanne natama, karasa shiga dakin tayi tana karema dakin kallo anma dakin fentin baby pink ga akwatin ta da aka jera asaman wardrobe kaya tacire ta shiga bayi tai wanka Koda tafito abinci tagani lafiyayyen white rice da stew ga farfesu agefe duk anjera mata a tray, salla tafara yi sanan tazo ta zauna taci iya cinta ta ijiye sauran akan drawer gefen gado ta kwanta sabida ta mugun gaji within 2min bacci yay gaba da ita. Koda tatashi da asuba tai salla tai karatun al Qur'ani sake komawa bacci tayi sai wuraren 7: 30 ta farka bayi ta shiga tadan kuskura bakinta tafito tasaka hijabi, ahankali tabude kofa tafito daidai shima yafito sanye da uniform dinshi na navy bakaramin kyau yayiba, dauke kai yayi da sauri daga kallonta, harda dan saurin ta takarasa gaban shi ahankali tace "good morning" batare daya kalleta ba yace "morning" juyawa yay zaibar wajen ta bishi da saurin ta ahankali tace "uhmm dan Allah kadan kiramin Abba inaso inyi magana da Farida ne" batare daya kalleta ba ya cigaba da sauka daga kan stairs din sanan yace "bazan kiraba" da kyar ahankali tace "to yaushe zamuje yolan?" baiko kalli fuskarta ba yace "babu inda zaki" wani irin kuka ne taji yazo mata, fita daga gidan yayi da sauri, ta dade tsaye a wurin tana hawaye sanan takoma dakint. Saida taji yunwa na neman mata illa sanan ta sauko kasa tana neman kitchen sallama dataji yasa ta amsa wata ma tace da zatai 29 haka tanadan murmushin ta tashigo tace "sunana kande nice mai tayaki aiki mai gidan ne ya turo ni, ai tunda akazo akai jere nike zuwa kullum Ina gyara gidan, yau da safe ya kirani yacemini kun dawo nazo natayaki aiki" dan murmushi tai ta gaishe da Matar, tare suka shiga kitchen suka dafa abinci mai rai da lafiya sai kallon yar torch light phone din matar take ahankali tace "indan ari wayar ki?" da sauri Kande tace "eh gatanan" ta dauka ta mika mata karban wayar tayi tafita daga dakin taje parlor ta zauna number Abba tasaka tai dailing ringing biyu Abba ya daga da sallama da sauri tace "Abba Ummi ce" murmushi Abba yayi yace "Ummi dazuko nake tambayan mijin ki ke yake sanar dani yana wajen aiki toya kuke ya karfin jikin naki" ahankali tace "Alhamdulillah Abba ya Farida" ajiyar zuciya ya sauke yace "ga Farida nan sai addu'a batama San wanda ke kanta ba" wani kuka ne taji yazo mata hakan yasa ta taushe bakinta "amma muna ta addu'a in sha Allah zata sami lpy so karki damu kanki ki kula da kanki kinji kinsan kema baki dade da samin lpy ba, Allah muku albarka duka" kasa amsawa tayi ta katse wayar tafashe da kuka sosai, kande tafito daga kitchen din da gudu tana lpy, kasa amsawa Islam tayi saima kukan datake yi da kyar tai shiru ganin yanda Kande dukta damu ta mika mata wayarta dadan murmushi tace "Ya tace batada lpy" Kande tace "to ai addu'a zaki mata ba kukaba Allah bata lpy" ahankali tace "Ameen nagode" share idonta tayi tace "dan Allah tayani diban abinci kibama su mai gadin, kema ki diba" murmushin dadi kande tayi sanan tace "to" diba tayi ta kaima su mai gadi Sanna itama tazo tadiba a yar kula tamata sallama ta tafi. Har dare haka ta wuni tana kuka, bayan tai sallan Isha tashiga bayi tai wanka tafito daure da towel, yunwar dataji tana addabar cikin ta yasa tafito daga dakin ta sauko kasa, kitchen ta shiga ta bude warmer ta dibi dan rice a bowl karami tadau spoon tafito daga kitchen din tareda kulle kofar, karan anbude kofar sitting room yasa ta daga kai hada ido sukayi yana sanye da uniform da sauri ya dauke kai yazo yafara hawa stairs da sauri ta ijiye abincin akan dining tabishi sama harya bude dakinshi ya shiga itama tabude dakin ta shiga wani kamshi ya bugi hancinta, dakin tsaf tsaf komi fari, ko kallonta baiyiba saima kokarin bude boturan rigar shi dayake yi, ahankali tace "Ya Khaleel dan Allah yaushe zamuje duba Faridan?" ko kallonta baiyiba saima karasa cire rigarshi yayi ya ijiye agefe ya tsugunna yana kokarin kwance igiyar takalmin kafarshi, duka ya kwance ya ijiye agefe yatashi tsaye yana kokarin cire dogon wandon uniform din jikinshi, tadan matso kusa dashi jikinta nadan rawa tana gyara towel din jikinta adan tsorace tace "eh yaushe zamuje" bai kalleta ba saima zame wandon dayayi yace "babu inda zaki" sosai tafashe mai da kuka hakan yasa yabude bayi ya shiga abinshi kuka take sosai tasa hannu tanata murza idanu tace "dazu dana kira Abba yacemin batasan wake kanta ba, Farida is suffering, tun ina yarinya mu biyu Mummy ta raine mu tare, Farida ita ke tare min fada a school, ita ke bani snacks din break, itake rikemin hannu, she is my best friend, so kake karaba mu yanzu?" tacigaba da kuka sosai kaman yanda yara suke suna kuka suna magana, da kyar tai shiru tana sauke ajiyar zuciya tace "tun ranan da ka karbo mata jakanta Farida take sonka, Farida loved u so much, Allah ne ya jarabce ta da wanan son and ni take fadama komi, yanzu she is seriously sick bazaka sakeni ka aure ta ba, wlh idan wani abu yasa meta bazan taba iya yafema kaina ba" takara fashewa da kuka harda shesheka, cikin kukan tace "kaki kiramin su nai magana da ita, sanan kuma bazaka barni naje naduba taba rabamu kake so kayiko hmmm" tacigaba da rera kukan sabida yanda abun ke mata ciwo, ya dade tsaye abakin kofar bayin daure da towel yana kallonta sabida ta juyama kofar baya, wani irin cije lips dinshi yayi sanan ya fuzar da iska sabida yanda ranshi ya mugun baci, rufo kofar bayin yayi da karfi har saida tai kara hakan yasa ta juyo a firgice ta kallai, ganin idonshi yasa ta tuna marin da tasha ranan da sauri tai hanyar kofa zata bar dakin ya fizgo hanunta ihu mara kara tayi, jijjigata yay rai abace yace "bazaki yolan ba, and saki kikeso ko baza'a sakekin ba, barima kiga" towel din jikinta ya fizgo ya yar arude tafara kokarin tsugunnawa tace "na shiga uku dan Allah ka yakuri Ya Khaleel, wlh bazan karaba" jefata yayi kan gado. [7/2, 9:28 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 73 & 74 Bakaramin wahala Khaleel yabata ba dan wlh ta gurzu, tun tana iya rokonshi daya ya hakuri har takasa magana sai ajiyar zuciyar wahala take tana kuka, wuraren 3 ya saketa tafashe da kuka kasa kasa tana saukar da numfashi juyowa yay ya kalleta fuskar nan adaure yace "get out" da sauri ta dira daga gadon dan wani irin mugun tsoron shi taji tanaji anan kasa ta tsugunna tadau towel dinta ta daura tana goge hawayen dake zuba, sanan tafita daga dakin tanadan dingishi ta shiga dakinta bayi ta wuce direct. Runtse idonshi yayi da karfi sabida yanda kukan ta ke taba rashin shiya rasa wanan wace irin jarabta ce, da kyar yatashi ya shiga bayi yadan dade sanan yafito ya tsane ruwan jikinshi da towel yasaka jallabiya yahau kan dadduma yafara salla. Da aka tada salla asuba ne yafito yawuce massallaci saida gari yay haske yadawo yawuce dakinshi ya shirya cikin shirin zuwa aiki yafito kofar dakinta yabude da sauri ta tashi zaune kan gado jikinta har wani bari yake sabida yanda taji wani irin tsoron shi daya shigeta bakinta har rawa yake tace "in ina kwana" bai amsa taba saima harara daya jefeta dashi yace "ki tashi ki shirya ina jiranki amota" barin wurin yayi so yake ya kaita gidan su ko tadan walwala, yasan idan ya barta a gida haka zata wuni tana kukane. Yakai kusan 15 minute amota ta glass ya hango ta tafito sanye da riga da zani na brown and yellow atampa tasaka brown hijab da takalmi da brown jaka fuskarta dadan hoda da kwalli sosai tamai kyau tana tafiya ahankali, bude kofar gaban tayi ta shiga ta zauna hakan yasa yaja motar batare daya cemata kala ba har gidan su, parking yayi ababban compound dinsu yafito hakan yasa tafito tana biye dashi har suka shiga gidan da sallama su, Ihsan dake falo dan dama yariga yakira Ammi yace suna zuwa suka taso da gudu suka wuce shi suka rungumeta suna ihu Ammi da Abba dake sakkowa dan rakoshi tayi zai tafi aiki tace "karku karyamin daughter bafa hankali cikakke gareku ba Ilham" sakin ta sukayi suna dan turo baki, murmushi tayi tazo gaban su Ammi kanta akasa dan bakaramin kunyan su takejiba tace "ina kwana Abba, Mummy ina kwana" dagota Ammi tayi tace "daughter ya jiki" Abba yace "kun iso lpy" murmushi tayi tace "Alhamdulillah" Ilham ne tazo tace "muje dakin mu Amaryan Bros" dan murmushi tayi suka riketa Ammi tace "kujata ahankali mana" shidai yana zaune a dining yadau apple yanaci yabisu da kallo dan ajiyar zuciya ya sauke ganin murmushi akan fuskarta, tareda Abba suka fita yacema Ammi zai biyo ya dauketa idan yataso daga aiki. Abinci Ammi tahada mata sanan takira Ilham ta sakko ta dauka ta kai mata sai nannan suke da ita sai wajen karfe sha daya sanan suka shirya badan sunso ba suka tafi school shima sabida test din dasuke dashi ne. Ita kadai suka bari adakin hakan yasa tai shiru tana tuna jiya wani zazzafan hawaye ne taji sun fara zubo mata, kofar dataji anbude da sallama yasa ta share hawayen da sauri amma Ammi tariga tagani tashi tayi ta zauna akan gadon Ammi kuma ta shigo ta zauna a gefenta tana kallon idonta tace "lpy daughter kike kuka menene?" girgiza kai tayi tareda kakalo murmushi tace "bakomi Ammi" hanunta Ammi ta rike tace "menene karki boyemin komi, ni mahaifiyar kuce un menene daughter fadamin wani abin yamiki?" girgiza kai tayi da sauri tana kokarin tsayar da wasu hawayen dake shirin zubowa ahankali tace "Farida ne batada lpy Mummy" da sauri Ammi tace "subhanallah tun yaushe?" "tun muna chan" cike da tausayi Ammi tace "oh Allah meke damunta?" fashewa tayi da kuka hakan yasa Mum ta shafa bayanta tace "bansani ba amma tanata tarin jini Abba yace bama tasan wanda ke kanta ba" "shine baisan ya kaiki tun jiya kuje dubiya ba, zaizo ya sameni ne, in sha Allah gobe goben nan zansa shi ya kaiki kuje ku dubo ta, dena kuka kinji tashi muje dakina kin zauna ke kadai awanan dattin dakin nasu" dan murmushi tayi dan ba tawani ga dattin da Ammi ke fadaba banda kayan sawan su dasuka tara akan gadon, tashi tayi suka fita daga dakin tareda Ammi sosai tasaki jiki da Ammi ganin yanda taketa janta jiki tabata wasu magunguna tasha sanan tahada mata wasu aleda dazata tafi dasu ta dinga sha da yogurt, Ammi ta kunna mata kallo wai dukdan tasaki jiki. Bayan sallan magrib ya shigo gidan afalo yasameta dasu Ihsan suna bata wani labarin novel sai dariya take dan bama ta lura dashi ba, hada ido sukayi da sauri ta hadiye dariyar ta janye idonta daga nashi ganin yanda yake kallonta, daure fuska yayi dukan su suka gadaishi bai amsa suba yawuce dining dan yunwa yakeji sosai, warmer yabude yadebo potato porridge dayaji nama ya zuba a plate yasa spoon, Ihsan tace "Ya Khaleel Ammi na kiranka" daukan plate din yayi yawuce sama dashi, da sallama ya shiga dakinta ya zauna akan gadonta yanacin abincin, kallonshi tayi ta daure fuska tace "mesa bakakai Islam ta gaishe da yar uwarta ba" plate din abinci ya ijiye agefe baice komiba hakan yasa Ammi ta sassauta murya tace "haba son koma me Farida tayi yariga yawuce ai, so kake karaba su danka auri wanan, karka manta fa tare suka taso koma me yar uwarta tamata bazata taba dena sonta ba eh son, kai yanzu idan aka cema Ihsan ko ilham basu da lpy basuma san inda kansu yakeba yazaka ji eh?" shiru yayi hakan yasa Ammi tai murmushi tace "don't be selfish, inaso gobe kubi jirgin safe kutafi yola" ahankali yace "Ammi aikina fa" "nadai goben, gobe ai Friday basai kudawo ran sunday ba, haba Son" dan murmushi yayi yace "shikenan naji" abincin shi ya dauka ya cigaba daci ya cinye, fridge dinta dake nan daki ta bude ta daukomai ruwa agora tabashi ya karba yasha sanan ya sauka kasa wanan karan basa falon massallaci yawuce yaje yayo Isha sanan yadawo tareda Abba suka shigo, afalo suka sami Ammi suka zauna sunata hira sai wuraren goma sanan Abba yacemai oya yatashi yadau matarshi sutafi, Ammi ta tashi tawuce sama, dakinta takira Islam din tabata abubuwa dayawa aleda sanan tamata addu'a suka fito har wajen mota suka rakata, Abba dakanshi yabude mata gaban motar ta zauna yarufe duk suka daga musu hannu jitayi kaman karta tafi sukabar gidan, amota shiru dukansu sukayi har suka kai gida tabude mota zata fita batare daya kalleta ba yace "ki shirya gobe da safe zamu yola" yafita daga motar batare dayajira cewarta ba bayanshi tabi ta shiga dakinta wanka kawai tayi ta kwanta. Wuraren 8 suka tafi airport din bata wani dau kayaba banda hadadden lace din dake jikinta orange da black shikuma shadda ce ajikinshi fara gizna sai uban kamshi yake, karfe goma da arba'in jirginsu ya sauka a yola driver su daya kira yazo ya dauke su dayake Abba yafadi mai a general hospital suke nan direct yasa driver ya kaisu, parking yayi suka fiffito gabanta sai faduwa yake yanda taga ko kallonta bayayi wani super market ya shiga yayo sayayya dabatasan nameba sanan yadawo yana gaba tana biye dashi abaya har cikin asibitin cardio ward taga sun nufa daki na uku taga yay salama ya shiga tabi bayanshi, Mummy ce kadai adakin da Farida take kwance oxygen manne a hancin ta tana bacci, Mum tabisu da kallo Khaleel yace "ina kwana Mum yamai jiki" daidai nan Islam ta karaso gabanta ahankali tace "ina kwana Mummy yamai jiki" ko kallonta Mum batayi ba saima kallon Khaleel tayi tace "sannu da zuwa Muhammad, Alhamdulillah gatanan dai jiki da sauki" dudda abin ya daki ranshi yanda bata amsa gaisuwan Islam ba sai bai nuna komiba yawuce inda Farida take yaja kujera ya zauna a saitin fuskarta yana kallon fuskar ta tareda ijiye ledar hanunshi agefen ta yay shiru, kasa karasowa wurin gadon tayi sabida yanda Mum ke hararan ta, tashi Mum tayi ta kalli Khaleel tace "ina zuwa Khaleel zanje naduba ko testes dinta are ready nakaima likitan ta" ahankali yace "to mumy saikin dawo" fita daga dakin tayi tareda wanke Islam dawani irin mugun harara, daidai lokacin Farida tafara mutsu mutsu da ido zata tashi da kyar ta iya bude baki tace "Mk, Mummy ku kiramin Mk" kara jan kujeran yayi ya matso kusa da gadon sosai ya rankwafo da kanshi saitin fuskar ta ahankali yace "Farida na" wani irin dukan zuciyar ta sunan yayi hakan yasa ta dago kai ta kalleshi da sauri, ta wutsiyar ido yake kallon fuskarta hakan yasa yasake cewa "Farida na bude idonki gani nan nazo" ganin tana kokarin bude ido yasa yajuyo fuskar nan kaman bai taba murmushi ba yace "dan bamu wuri" kaman wacce kwai yafashe mawa aciki ta juya tafita daga dakin, bude ido Farida tayi dasukai jajir, dishi dishi take gani amma bai hanata ganshi ba kokarin cire oxygen din take daga hancin ta yataya ta cire wa, ahankali tace "Kaine ko idonane kemin gizo" dan murmushi yayi dan ta mugun bashi tausayi yace "nine" wani irin fashewa tai da kuka tana tari da kyar ta iya cewa "kayafe min dan Allah kadaina fushi dani, nariga na hakura nabar ma Islam kai, banason na mutu kana fushi dani please" takarashe maganan tana tari, hanunshi yay folding a kirji tareda daure fuska yana kallonta yace "fine naji zan hakura zan yafe miki only idan kin yarda zaki warke, forget everything and move on, and I promise zan kula dake like a sister, deal?" gyada mai kai tayi da sauri tana murmushi tace "deal" dan murmushi yamata shima yace "gud" ta wutsiyar ido ya hango Islam na leko su ta window kaman wata munafuka dan kasa hakura tayi ga zuciyar ta sai wani iri take mata, dan murmushin gefen baki yayi ganin ta ya kalli Farida yace "zakici abinci?" da sauri ta gyada mai kai, tashi yayi ya koma ta bayan gado ya dago da gadon ta yanda kanta zaiyi sama kaman ta zauna sanan ya koma, ledan daya shigo dashi ya bude ya dauko pringles ya budemata ya mika mata ta karba ya dauko bottle water ya budemata shima ta karba tasha tanata kallonshi, ahankali ta tsulalle ta tsugunna wajen window tanajin wani irin kuka kuka, zafi zafi, fushi fushi, daci dacin dabatasan ko nameba taji tanaji, gawani irin abu daya tokare mata zuciya, kallon Farida yayi dakeci ahankali tanata kallonshi tana sauke ajiyar zuciya yace "bari naje gida zan dawo anjima" gyada mai kai tayi yafita daga dakin. Fitowan shi data gani yasa ta mike da sauri tabi bayanshi ko kallonta baiyi ba saida yakai wajen motar su sanan ya juyo ya kalleta, shi itama take kallo da idanunta dasuka dan chanza kala zatai magana ya tari numfashin ta yace "basai kinbani ba kiyi zaman ki agidan ku zan aiko miki da takardar ki sabida afara shirye shiryen aurena da Farida" yabude mota ya shiga batare daya jira mezatace ba suka bar hospital din, jingina tayi dawata motar dake wurin jin zata fadi kafin ta tsugunna tana wani irin numfarfashi kaman mai asma, wani irin kukane taji yazo mata wuya ba shiri tafara rera shi. [7/2, 9:28 AM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 75 & 76 Tadade tsugunne a wurin tana raira kuka kafin ta mike tsaye da kyar ta share fuskarta da kyau tabar wajen tana tafiya kaman zata fadi sabida rashin karfi, ahankali ta tura kofar dakin da sallama ta shiga Mummy ce kadai zaune tana waya kaman ma da Abbane sai kuma Farida dake rungume da gwangwanin pringles din dayabata tana bacci, karasa shigowa dakin tayi ta maida kofar ta rufe, katse wayar Mumy tayi ta kalleta tace "me kuma kikeyi anan bakibi mijin naki bane?" girgiza kai tayi ta karaso gaban Mumy ta tsugunna ta daura hanunta akan cinyarta ahankali tace "Mummy dan Allah kidena fushi dani kiyakuri kinji" wani irin murmushi mai ciwo Mum tayi ta ture hanunta daga jikinta tace "Islam kenan inda kin kirani da sunana ai dayama fi dan kin dade da nunamin cewa nibani na haifeki ba, hakurin me kika bani iye? Mekika mini?" share kwallan daya zubomata tayi da bayan hanun muryar ta har rawa take tace "Mumy wlh bani bane kawai naga Abba yakaini gidanshi ne, ni bansan ya akayi ba dan Allah mumy am sorry" "are you?" Mum ta tambaye ta tana mata wani irin kallo, gyada mata kai tayi, dan shiru Mum tayi sanan tace "ai ga Faridan nan kinsa mata ciwon zuciya inta mutu ai duk a dadin ki saikiyita rayuwan ki da Khaleel tunda miji yafi miki yar uwa, Islam ni kikama abunan, ni Islam" ta nuna kanta da yatsa, "ni dana raineki uwarki nafama da sikila, oh duniya kenan, yata ke wahala haka sabida ke Islam" girgiza kai tayi tafashe da kuka sosai, tsawa mum ta daka mata tace "wuce, fita daga dakin nan, karki kara shigowa, nidai ba Mummy ki bace daga yanzu, ki nisanta kanki daga yata tariga ta hakura da mijin ki, kuyita shagalin ku, itama Allah zai bata wanda yafishi, yinan" ta nuna mata kofa, kasa fita tayi saima wani sabon kukan datake tana shashare fuska da hijabi, hakan yasa mum ta nunata da yatsa tace "wlh idan kika tadar min ya daga bacci bazan barki ba zan mugun sabamiki, ki wuce ki fita kafin na kaimiki hannu munafuka, nafada miki nidai ban tsaneki ba, bakimin komiba, kuma bazan taba cutar dakeba dan nima banason acutar min da ya, amma kawai dai bani bake ne, kuma ki rabu dani da yata, dama baban kune yahada mu to acigaba a hakan, wuce kawai kifita" sum sum sum tawuce tafita daga dakin ta zauna anan kujerun da aka jera a gaban record inda patient ke jiran folder tana kuka tana shashare fuska. Haka ta zauna awurin o har azahar tawuce tafita taje massallaci tai alwala tai salla ta dawo takara zama a wajen saiduk taji tagaji gawani irin yunwa datake ji, bini bini mum na fitowa saidai ta watsa mata harara takoma ciki, gashi babu wani dan gidan su dayazo balle tadanji dadi, itane azaune awurin har la'asar, duwawun ta har zafi yake sabida zaman kujera, ta tashi ta wuce massallaci tai salla, kwanciya tayi awurin har dan gajeren bacci yay gaba da ita wuraren biyar ta tashi tafito ta wanko fuska tadawo cikin hospital din ta zauna a wurin tanata kallon dakin jin hanayina, ganin Mum tafito ta wuce ta kara zuba mata harara yasa ta mike tsaye tana waigen Mum ganin tai nisa yasa tayi dakin, Khaleel tagani wanan Karan ya chanza kaya zuwa Jean da riga ya zauna akan kujera yana kokarin bude takeaway daya yoma Farida da idonta biyu sai kallonshi yake, dan karasa shigowa dakin tayi tana satan kallanshi, Farida ne ta kalleta dayar muryar ta dabata fita da kyau tace "tun dazu natashi inata tambayan ki ina kikaje?" murmushi ta kakalo tazo kan gadon ta zauna ta wurin kafar Farida tace "ina mosque ne nai salla sai bacci ya kawasheni" tai maganan tana satan kallonshi, dan murmushi yayi ya kalli Farida yace "Mac and cheese ne nakawo zakici ko? Lemme feed u" gyadamai kai tayi tana soft murmushi, fork yasa aciki zai debo yabata da sauri ta tashi ta karbi take away daga hanunshi bakinta har rawa yake tace "un zan.. Zan.. Ni zan bata" ita kanta batasan yaushe tai hakan ba, dago kai yayi ya zuba mata ido itama shi take kallo da kyar ta janye idonta daga nashi jin kwalla yataru ta juya ta kalli Farida dake kallon su tace "is being long bari nizanyi feeding dinki" debo wa tayi takai bakin Faree ahankali ta bude ta karba tana murmushi, shima murmushi yay aranshi sanan yaciro wayarshi daga aljihu yana dannawa bini bini yana satan kallonta. Saida ta cinye sanan ta ijiye take away a gefenshi tana kallon fuskarshi amma yaki kallonta komawa gefen Farida tayi ta zauna tana Satan kallonshi ganin wayarshi yake ta daddanawa abinshi, dan gyara kwanciya Farida tayi tace "what are u doing Mk" dago kai yay ya kalleta ya sakin mata murmushi yace "kinaso kigani?" gyadamai kai tayi, ya matso da kujeran dayake kai jikin gadon ya nuna mata wayar hakan yasa tadan matso da kanta tana kallon wayar game din ball yake bugawa hakan yasa tadanyi kara ashagwabe tace "nito ai ban iya wanan game dinba kamin bayani" dan gyara zama yay ya saci kallonta yanda take kallonsu kaman idanunta zasu fado kasa yace "kinga wanan shine goal keeper, ga defender, ga midfielders sune yan tsakiyan nan, ga referee shine mu hura wusur, sukuma linesman dinan suke assisting referee, ga strikers suke gaba" janye fuskarta tayi daga wayar ta kalli fuskarshi tace "haka kasan kan kwallo Mk" batare daya kalleta ba yay murmushi yace "best sport dina kenan" ahankali ta mike daga kan gadon zata fita hakan yasa Farida ta kalleta tace "ina zaki kizo mijin ki ya koyamana yanda ake kwallon tare" dan lumshe ido tayi dan sosai takeson danne hawayen dake zuwan mata sanan ta budesu tajuyo tace "namanta da abu a massallaci ne am coming" da sauri ta juya tafita, dan murmushin gefen baki yayi ya kalli Farida yace "ya karfin jikin?" murmushi tayi tace "Alhamdulillah na warware" tashi yayi yace "zan tafi saikuma gobe" da sauri tace "to kajira Islam din tazo saiku tafi" murmushi yay yace "baki da lpy, ai nace ta zauna ta kula dake idan kin warke sainazo na dauketa mu koma gida" sosai abin yamata dadi tace "thank u so much Mk bye" bye yamata yafita daga dakin yana waige waige yana nemanta, fita yayi yanata Kalle Kalle kozai ganta hango ta yayi karkashin wata bishiya ta zauna tanata share kwalla, kasa daurewa yayi ya karasa wurin kamshin turaren shi kadai taji ta dago kai tana kallon fuskarshi daure fuska yayi yace "lpy kike kuka ko bakida lpy ne?" girgiza kai tayi hakan yasa ya tabe baki yace "dama nazo nabaki takardar kine, dan rikemin" yay maganar yana mikama ta byro ya kai dayar hannu aljihu kaman zai ciro wani abu ba karamin racing heart dinta yake ba da kyar har wani irin runtse ido take tace "ta.. Takardar mene?" tsayawa yay da tura hannu aljihu yace "bakince na sakeki ba na auri Farida, am coming jirani anan kaman nabarta takardar a mota" , mikamata byro yayi yace "rikemin wanan bari na dauko takardar saina rubuta miki" bai jira mezatace ba yajuya yay hanyar mota, batasan mesaba amma wani irin kunci da bakin ciki da tsoro taji ya diran mata arai, yar da byron tayi a wajen ta juya da sauri harda dan gudu tai hanyar massallaci ta shiga bangaren mata harda jan kofan tana rufewa ta zauna kirjinta na bugawa sai zazzaro ido take. Koda yadawo bai ganta a wurin ba bakaramin dariya yayiba harda rike ciki komawa mota yayi ya shiga ya tada yabar hospital din. Sai bayan magrib ta koma ward din dakin ta shiga lokacin Abba da Anty Hindu da Mummy duk suna wajen gaishe su tayi, Anty Hindu tace tabi Abba su tafi gida ta huta tunda mijinta yace anan zata kwana gobe da safe tazo, Abba tabi da Mumy dan Anty Hindu ke kwana da safe kuma mumy tazo ta wuni. Wuraren 9 na safe ta sakko shirye cikin doguwar rigan atampan ta na gida tadauko hijabi ta rike da Mumy taci karo tafito daga kitchen rike da kula a shirye zata tafi, wani mugun kallo ta wurga mata tace "ina zaki, karna naji kince asibiti, ba nace ki nisan cemu, nida ita bama bukatar ki Islam kirabu damu, wlh inhar na ganki a asibitin nan kome namiki kekikasiya da kudin ki" wucewa Mum tayi tafita daga dakin ranta abace ahankali ta sulale ta zauna akasan wurin tafashe dawani irin mugun kuka batasan ma meke mata dadi ba tarasa inda zata sa kanta, takai kusan minti 30 tana kuka gashi ba kowa a gidan sai ita, tashi tayi ta zauna akan kujera tai tagumi daga baya kuma ta kwanta tana ijiyar zuciya, sake tashi tayi dan tarasa meke mata dadi hijabin tasaka tafita waje ta zauna kan bencin me gadi tana kallon mutane daidai dake wucewa alayin nasu idanun nan nata sunyi fayau sun kumbura, wani dan yaro da bazai wuce 2 years ba tagani yafito daga wani gida dake facing nasu ya shiga hanya yana wasa da bindigar ruwan hanunshi ga mota na zuwa da sauri ta mike tsaye da gudu taje ta dauke yaron daga kan titin tanamai murmushi har motar ta wuce, yaron mai kyau dashi gashi dan lukuti tace "mesa kafito kai kadai waje", daidai lokacin wata yar mata haka dabazata wuce 25 ba tafito sanye da dogon hijab. [7/2, 2:18 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 77 & 78 Ta karaso inda suke tsaye tace "laaa nan kayo Sadiq daga shigana wanka fa" murmushi Islam tayi ta mika mata yaron, karban shi tayi tace "nagode, nanne gidanku bansan kowa a anguwan ba, jiya jiyan nan mukazo daga Abuja biki gidan baban shi, gidan yacika ne saisa mukazo nan gidanmu, Ya sunan ki?" gyada mata kai Islam tayi ta nunama ta gidansu tace "ga gidan mu nan" matar tace "ba shakka" juyawa Islam tayi ahankali tace "bye" komawa kan bencin tayi ta zauna hakan yasa Matar tabita da kallo kasa tafiya tayi saikuma tadawo inda Islam take, hakan yasa tadaga kai ta kalleta murmushi Matar tamata tace "Sunana Husna Maman Sadiq mekike yi ke kadai awaje?" jitayi kaman ta fama mata ciwo hakan yasa kwalla yataru a idonta, kawad dakai tayi da sauri tace "bakowa ne agidan mu saisa" "ayya to zomuje gidana muyi hira nima ai sai anjima bayan sallan la'asar baban shi zaizo ya daukeni muje dinner, zomuje" maida Sadiq tayi hanun haggun ta, tasa hannun dama takamo hannun Islam kaman tasanta, tashi Islam tayi ta bita badan tasoba suka shiga gidan gidane dan daidau mai kyau dashi ko ina sai kamshi yakeyi zaunar da ita kan kujera tayi sanan tacire hijabi ta ijiye nan kan kujera ta wuce kitchen ta kawo mata drink mai sanyi da snacks ta ijiye mata a gabanta sanan ta zauna kusa da ita ganin tanata kallon Sadiq dake wasa da kayan wasanshi anan tsakiyar falon tace "baki fadamin sunan kiba kawas" juyoda kai tayi ta kalleta ahankali tace "Islam" baki tarike tace "waiwaiwai Islam no wonder kike da shagwaba ai duk masu sunanku haka suke inada kanwa ma haka sunanta Islam" murmushi kawai tayi tace "ni bana shagwaba" "shine dan amfita an bakki ke kadai kike ta kuka ga idanun kinan sunyi jajir" da sauri Islam ta kalleta, dan murmushi tayi tace "bahaka bane kawai" shiru tayi tasa bayan hannu ta goge idanunta, ita kadai tasan yanda takeji bakaramin zafi kirjinta yake mataba, da hijabin ta lullube fuska jin wani irin kuka yazo mata sosai take kukan mara sauti tana wani irin sauke ajiyar zuciya, hanun Husna taji akan hijabin ta janye daga fuskarta hakan yasa tadago rinannun idanun ta kalleta da sauri ta tashi zatabar dakin Husna ta rikota "ina zaki?" Ahankali tace "gida zani" girgiza kai Husna tayi tace "zoki zauna babu inda zaki saikin fadamin meke damunki, zonan mai sunan kanwata" zaunar da ita Husna tai akan kujera sanan taja center table ta zauna agabanta tareda mikamata ruwa ta karba tasha kadan ta ijiye, dafata Husna tayi tace "mecece matsalar Islam? Wanan kuka haka bana lafiya bane? Bansan kiba amma wlh daga ganinki jinai kaman naga yar kanwata, kifadi mini matsalar kona taimaka miki da shawarwari dakuma addu'a" hartagama maganan bata dena kallon Husna ba girgiza kai tayi tace "bakomi kawai kawai" takasa magana "zurfin ciki na halaka mutane fa, yana sakaka cikin matsaloli dabaka taba zatan zaka shigaba, idan bazaki fadimini ba bazan takura kiba dan nasan yau kawai mukasan juna baki saba daniba, amma dai kidena saka damuwa aranki karya jamiki wata matsalar kinji mai sunan kanwata" gyada mata kai tayi tana tunanin maganganunta zurfin ciki da rashin fadama Farida labarin Khaleel tun lokacin data hadu dashi shi yajawo musu wanan matsalar fa, da sauri ta kalli Husna ahankali tace "zan fadamiki please bayan nagama fada miki ki gayamin me kuskurena" murmushi Husna tamata tace "ok inajinki to" shiru tadanyi kafin tace "Ya Khaleel ne matsala ta" saikuma tai shiru kaman tana tunanin wani abu Husna tace "waye Ya Khaleel" dan ijiyar zuciya ta sauke sanan tace "mijina" shiru tasake yi sanan tadago kai tasake kallon fuskar Husna hakanan taji zuciyar ta ta natsu da ita ahankali ta shiga bata labarin tun ranan farko tada fara haduwa da Khaleel filla filla har zuwa yau da safe abinda yafaru tagama labarin duka tana matsar kwalla kafin ta kalli Husna datai tagumi tana kallonta, tagumi Husna tacire tareda sauke ajiyar zuciya tace "wlh Islam kin tafka uban rashin hankali, ai gwara ya sakekin tunda ke banza ce mara wayau" da sauri ta daga kai ta kalleta kirjinta na bugawa, hararan ta Husna tayi tace "eh mana bake mai yar uwa ba kinacema mijinki mai sonki ya sakeki akanta ai shikenan ya sakekin, wai inama yan uwan mummyki sukene da suka barki babu abinda kika iya na zamantakewa da daraja miji" kwalla ta share tace "Abbana humanitarian ne, yana zuwa gari gari yana bada taimako yana taimakon mutane, to lokacin dayaje Sudan wani gidan marayu anan yaga Umma na tana fama da sikla shine fa yaji yana sonta dayake shi AA ne saiya auro ta yataho da ita nigeria, Ummana batada yan uwa, Mummy kawai na san yan uwanta" sosai Husna taji tabata tausayi hakan yasa ta sassauta murya tace "Islam abinda kikama Khaleel wlh bai daceba ki rokeshi ya yafemiki tun kafin lokaci ya kure miki ke yanzu dayake nuna ya damu da Farida yakike ji?" Ahankali ta shiga rera kuka tunawa da yanda ya dinga koyama Farida kwallo jiya datayi da kyar ta tsayar da kukan ta kalli Husna da rinannun idanun nan tace "abun cizona yake sosai azuciya" dan dariya Husna tayi tace "bari namiki ta hausanki idan kika gansu tare abin na cizan miki zuciya shine kuma zakice baki sonshi, nan gabama zuciyar taki yagewa ma zatayi gabaki daya in kika cigaba da ganinsu tare, ko kinfiso kiyita ganinsu tare ne yana bata kulawa?" girgiza kai tayi "yariga ya aureki babu aure tskaninshi da Farida, kinriga kin tafka babbar kukure, kin kira mijin ki wicked sanan ki cemai shine yasaki aduk matsalolin nan dakike ciki Islam, mutumin daya zauna dake lokacin dakike ba mutum ba yasoki ahaka yabar aikinshi yana jinyanki, zamanin nan a ina ake samin namiji haka, keme yar uwa ko, to wlh tun wuri ki bashi hakuri kafin ki rasashi gabaki daya ko so kike ya sakeki kikoma ma Fahad ne?" Girgiza kai tayi tace "ni banmasan inda Fahad yake yanzu ba shiya koranmin shi, kuma Mum ta karbi wayana hala yanata kirana baya samuna" saikuma tafashe da kuka da kyar tai shiru ta kalleta tace "Maman Sadiq wlh zuciyata zafi takemin" "aike kikaja ma kanki zaki bata auran ki akan wayanda basu damu dakeba, keme yan uwa gashin kin dameshi ya kawoki yabarki dasu kinata shan wulakanci anma hanaki zuwa asibitin" ahankali tace "Yaya zan bashi hakuri yariga yace nai zamana agidan mu zai aiko min da takardar" murmushi Husna tayi tace "Khaleel na sonki bazai taba sakin kiba, kece dai yanzu zaki lallabo shi ki shawo mana kanshi, akwai hanyoyi daban daban da ake lallaba miji abashi hakuri yanzu dai tunda kina gidan kune kuma anhanaki zuwa asibitin balle ku hadu duk randa yazo zakici gayu sosai kije ki dane jikinshi ki rungumo kayanki kina mammatse shi da kukan kissa ki cemai kin tuba ya yakuri" nan Husna ta shiga bata shawarwari da dabaru na gidan aure da yanda zata shawo kanshi sai wuraren 1 takoma gida salla tayi tafito jin Abba ya dawo tareda Anty Hindu gaishe su tayi Abba yace "maisa baki biyo Mummy kinje asibitin ba?" "kaina ke ciwo Abba" Anty Hindu tace "kindai sha maganin ko?" gyadamai kai tayi, Abba yay murmushi yace "ai muna ma tareda mijin naki a asibiti yakecemana zaidan barki anan anturashi wani assignment a Lagos zaidan yi kwana biyu dafatan dai kinamai addu'a sosai ko?" gyada kai tai ahankali dan bazata iya magana ba ayanda kirjinta ke bugawa Abba yay murmushi yace" masha Allah haka akeso akodayau she mace takasance mai yawan yima mijinta addu'a da fatan alheri, jeki huta idan ciwon kan baidena ba kizo kifadamin saina kira likita yadubaki" gyada musu kai tasake yi sanan takoma daki bakaramin kuka taciba ranan yanzu shikenan sakin nata zaiyi shine yakema su Abba kwana kwana, bahalin taje gidan Maman Sadiq dan sunriga sundawo. Abangaren Khaleel ko kadan baiji dadiba dayazo hospital din baigantaba yana zaune ne kuma sako yazo daga wajen aiki ana neman su a headquarter dinsu na Lagos zasuyi wani assignment shine ya fadima Abba zaidan barta anan dan gobe zai tafi Lagos din idan yadawo saiyazo ya dauketa Abba yamai fatan alheri washe gari yabi jirgin safe zuwa lagos cike da kewanta. Wasa wasa yau sati biyu kenan rabonta da Khaleel, duktabi tai wani irin ga Mummy tabi ta tsangwameta wani zubin ma idan su Abba ko Anty Hindu nanan ne take dan sarara mata, jiya aka sallamo Farida amma dakinta takaita, tsakanin Farida da ita kuwa yanzu bakaman da bane suna magana bawai basayi ba amma dai bakaman daba, Farida bata tsaneta ba kawai dai tanajan jiki da itane dan duk idan ta dade tare da ita tuna da takeyi saitaji tanajin haushi, tariga tama Mk alkawari zataji sauki and forget d past, sabida son datake mai abinda take kokarin yi kenan yadawo daga lagos yaga ta warke rass takoma Faridan da, Son datake ma Khaleel wani irin sone da tanajin har abada harta mutu bazata denaba, saisa takedan nisanta kanta da Islam sabida batason tana ganinta zuciyar ta tafara kulla mata wasu abubuwa dazaisa Mk ya tsaneta again, komawane zata aura nan gaba batajin zata daina son Mk ba superman dinta. Idan har Abba ko Anty Hindu basa gidan to tana daki dan batason tama hadu da Mummy, Abba yakan cemata Khaleel yakira shi, Farida ma takan cemata yakirata taita wani jin dadi hakan bakaramin ciwo yake mataba dan baitaba kiranta ba Koda ta wayar Abba bane dagaske kenan rabuwan da ita zaiyi, daki take shiga wani zubin taci kuka abinta ta godema Allah, dan Maman Sadiq sun riga sun koma Abuja amma tanada number ta takan kirata da wayar Maman Miemie idan tazo aiki suci hira, sanan kafin su koma tabata wasu magun guna da kullum take sha dan koyau ma tasha da yogurt adaki abinta, hakadai tacigaba da maneji wani irin mugun kewan Khaleel take da nadamar abubuwan data fadimai dan tariga ta gane duk duniyar nan banda Abban ta shine mutum nabiyu dake sonta so na gaskiya. Kwanaki sunja lokaci nata tafiya yau kimanin wata daya da kwanaki biyar kenan rabonta da Khaleel, yaukam zazzabin data tashi dashi ne yasa Anty Hindu da kanta ta fadanma Abba nan aka kira Dr, bayan ya dubata yace "maleria ne" magani yarubuta mata Abba yasiyo Anty Hindu tasa tasha, Mum dai zamanta tai afalo tana marking script ko agefen kwalanta, Farida kuma ta debomata abinci dan sosai tabata tausayi takawo mata. (har yanzu fa wanan son dake tsakanin su nanan kawai dai Son Khaleel ne matsalan two sisters dinan) Wuraren 6 ta tashi na yamma tadanji dadin jikinta, hakan yasa ta shiga bayi tai wanka da ruwan dumi tafito dan pink gown dinta na gida tasa dake tsayama ta a gwuiwa tasaka dogon hijabin ta dake sharan kasa tai sallan la'asar jin anfara kiran magrib yasa tayi sanan tayi azkar din yamma tacire hijabin ta linke ta ijiye ta kwanta akan gado tana maida numfashi, gabaki daya duk tayi wani irin laushi ga jikinta har yanzu da sauran dumi, lumshe ido tayi har bacci yadan soma tafiya da ita sama sama taji ihun Farida daga kasa "oyoyo MK, oyoyoo" da sauri ta tashi ta zauna, kasa hakura tayi tadan mike tsaye tareda saka silifas tabude kofa kadan maganganu taji kasa kasa kaman muryan su Abba, komawa tayi ta zauna abakin gado gabanta na faduwa sosai, bude kofa akayi hakan yasa ta daga kai Farida ne tashigo dakin da gudu jikinta har wani rawa yake tana murmushi tace "Mk yadawo Islam kinga yanda yay kyau kuwa, laa banma bashi ruwa ba" da sauri tajuya tafita daga dakin, harara Islam tabi bayanta dashi jin wani irin kishi ya turnike ta saikace mijinta ne yazo taja tsaki, tashi tayi afusace taje gaban wardrobe dinsu wani ubansu soft material taciro blue da akabishi da zanen flowers gold, zama tayi agaban madubi ta chanchara uban kwalliyan da ita kanta batasan ta iyaba tasaka red janbaki tadan shafa lip gloss akai hakan yasa lips din na wani irin maiko maiko yana kyalli kaman sabon candy da aka gamayi, tashi tayi tabuga uban dauri sanan ta dauko turaren khumar da Husna ta bata na matan aure ta shafe jikinta dashi dakin yadau kamshi sanan tadan kalli kanta amadubi dudda tarame amma baihana kayan karbanta ba tareda fito da kyanta da dirin ta dan sun dan kamata sosai, takalmi tazira sanan tabude kofan tafito tana wani irin kamshi akan bene ta tsaya hango Farida datayi ta zauna akan kujeran dake kusa danashi tanata mai hira, ta wutsiyar ido ya hangota har wani irin ajiyar zuciya ya sauke sabida yanda yay kewan ta yawani juya mata baya yabiye ma Farida suna hira harda dariya, wani irin abune taji ya tokare mata zuciya kasa daurewa tayi takarasa sakkowa daga benen da sauri ta tsaya tana kallonsu, ganin duk sunmaki lura da ita babu wanda yace mata Kala yasa taji zuciyar ta na tafarafasa ai wlh yau saita nunama Faree nan Khaleel mijinta ne ehe, da saurin ta harda wani dan gudu gudun ta taje kaman daga sama tawani fada jikinshi ta kankameshi tana kukan shagwaba ahankali tace "Ya Khaleel nai kewan ka sosai" wlh ya tabbatar da inda yay alwala babu abinda zai hana alwalan karyewa wanan irin runguma haka damafa adaddafe yay wanan wata dayan a Lagos, wani irin kara shigewa jikinshi takeyi tana hahhade kirjinsu tare, kasa daurewa yayi ya sanya hannayen shi duka biyu yay cuddling nata tareda sakin wani irin sassanyar ajiyar zuciya, tashi Farida tayi tabar falon tanajin wani iri iri hakan yasa Islam takara bin bayanta da harara tana tura baki taredayin lamo ajikinshi tana shakan kamshin turaren dayake yi. [7/2, 2:19 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 79... Ganin Farida tabar falon tai sama yasa yaciro ta daga kirjinshi murya chan kasa yace "me haka nazo nabaki takardar ki kin wani shishigemini jiki, is over, today we are going our separate ways abinda kikeso kenan ai, bakiga nida Farida munyi making perfect coup.." daura hanunta tayi a bakinshi tareda kara matsowa cikin jikinshi tana girgiza mai kai tana turamai baki a shagwabance, "Hasbunallahu wa ni'imal wakil yarinyar nan naneman kasheshi ne wai" Ahankali ta zame hanun daga kan bakinshi ta kwantar da kanta a kirjinshi kaman wata baby tareda sakalo hannayenta ta bayanshi tana wani irin sheshekan kuka mai taba ran miji tace "dan Allah karke sakeni, wlh natuba bazan karaba, am really sorry, dan Allah karka rabu dani i cannot live without you, u are my endocrine" idan ba kana kusa dasu bane bazaka tabajin abinda suke cewaba, da kyar ya tattaro dan karfin daya rage mai dan tagama kashemai jiki ya ture ta yace "am wicked fa kin manta ne, tunda na shigo rayuwar ki matsaloli kawai naketa jamiki" hannunta takai takama kunnuwanta biyu, bilhakki take mai kuka tana girgiza mai kai tace "nai kuskure babba dana kalli fuskar mijina, mai gidana, mai sona abin alfahari na nagaya mishi wayan nan munanan kalaman, dan Allah ka gafarceni, inda inada karfin maida lokacin baya dana tariyo wanan lokacin na goge maganar danayi da eraser, Ya Khaleel i love you please karka rabu dani, ka hukuntani amman dont live me my endocrine" ahankali ya mika hannu yacire hanunta daga kunen nata data rike ya daga habarta yana kallon kwayar idonta dawata irin murya ya kashe mata ido daya yace "dole kam inhukun taki dawan nan bakin mai tsiwa, amma agado ake hukuncin" a kunyace ta fisge fuskarta ta fada kirjinshi tana murmushi kasa kasa, bakinshi yakai saitin kunenta yace "kinman ta ina gidan sirikai nane ko kike ta mammaneni haka, sokike na saki layi ko" girgiza kai tayi tareda sakinshi tana murmushi ahankali, hanunshi yasa ya shafo janbakin kan lips dinta yakai yatsar bakinshi yana lasa yana wani irin kallonta yace "jeki dauko abubuwan ki mutafi gidan mu" [7/3, 10:24 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur 80... Tashi tayi ahankali ta mike tsaye tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi, shima ita yake ma wani irin kallo da kyar ta iya janye nata idon tai stairs tana murmushi kasa kasa, haka yabita da kallo harya dena hangota, shi kadai yasan yanda yakeji akan matar nan nashi. Kofar dakinsu ta tura ahankali ta bude babu kowa aciki, dan ajiyar zuciya ta sauke ta shigo yan tarkacen ta tahada a jakarta ta sanya hijabi tafito, dakin Mummy tai sallama ta shiga Farida ta gani tai filo da cinyar Mummy idanunta sunyi jajir dasu, maida kofar tayi tarufe takaraso ciki ta tsugunna agaban Mummy tana wasa da zip din jakarta ahankali tace "zamu tafi Mum" harara Mumy tabita dashi kafin ta tabe baki tace "Allah yayi, to agaida gida" ahankali ta mike tsaye ta juya zata fita tana satan kallon Farida dataga ta lumshe ido, harta daura hanunta akan handle zata mudra taji Farida tace "Islam wait" waigowa Islam tai ahankali, sakkowa Farida tayi daga kan gadon, zuwa gaban Islam tayi ta rungumeta tsamtsam hakan yasa Islam ma ta rungumeta back tareda sauke ajiyar zuciya, wani irin zazzafan hawaye Farida taji yazubo mata da sauri tasa hannu ta share tana daga idanunta sama kokarin hana kanta kukan datake ji, bakinta takai kunen Islam dawata irin murya chan kasa tace "please take care of Mk, dan Allah ki kula dashi Islam, Allah baku zaman lpy" sakin Islam tayi takoma kan gadon ta kifa kanta akan filo tana sheshekan kuka sosai, wani irin hararan bakin ciki Mum tabita dashi kafin taja dogon tsaki ta kalli Islam din dako kwakkwaran motsi takasa kaman wacce tai mutuwar tsaye tace "bazaki fita daga dakin nan ba ku tattara kubar gidan nan kosai kun dawo mata da ciwon datake" wasu irin zazzafan hawaye ne suka zubomata kafin ta juya da sauri tabar dakin, falon Abba tayi bayan ta tsaya ta goge fuskarta tass, suna tare da Anty Hindu kafin ma tai magana Abba yace "zaku wuce kenan?" gyadamai kai tayi, Anty Hindu ta riko hannunta tace "Alhaji ka sauka gamunan zuwa" fita yay daga dakin Anty Hindu kuma taja hannunta zuwa dakinta, wasu magani dake robobi daban daban tadauko mata tace "kin gansu nan yau dinan naje airport na karbo su kawata daga Cameroon nasa ta turamin sabida nabaki, wlh idan baki shaba sainazo har gidanki na bugi kudina dakika sa nai asara" tagama maganan tana kokarin bude wani gora wani magani tace "shanye wanan agabana" karba tayi tasha tana yatsine fuska sabida dadi dadi da ne dashi, murmushi Anty Hindu tayi ta karbi goran daga hanunta tace "gud girl kinga kafin kukai yafara aiki ajikinki, tashi muje ki kula da mijinki da kyau, kimai biyayya, karki sake kisa zancen Farida aranki duk wanan hauka datake dazaran tasami miji, tasami mai sonta zata mata dama waye Khaleel ne, kizama mai hakuri da juriya, mara korafi kuma, kindaiga abinda yawan korafi da masifa yajamin sakoni akayi" dan murmushi tayi batare data bari ta ganta ba, karban jakanta tayi ta sakamata magungunan aciki sanan ta riko hanunta suka sauko falo inda Khaleel da Abba keta magana anatse, har mota suka rakasu suna musu addu'a suka tafi sanan suka koma cikin gida, dakin Mum Abba yabude ganin Farida dayayi akan gado tana gunjin kuka batare datamaji shigowan shiba yasa yajuya kawai yafita yana girgiza kai lamarin Farida sai du'ai shifai yasan ba randa zaiyi salla dabazai rokan mata Allah yakawo sauki cikin lamarin nan nataba, tareda nemamata miji nagari, yasan Allah maji rokon bayinsane watarana sai labari. Agaban wani massallaci yay parking ganin antada sallan Isha'i ya kalleta yawani kashe mata ido yace "bari nai salla babyn Khaleel" dauke kai tayi da sauri hakan yasa ya zagayo ta wajen window ta yawani kanne mata ido rufe fuskarta tayi da hannu tana murmushi yajuya da sauri ya shiga matsalin yay wajan yin alwala. Jingina da kujera tayi ta lumshe ido dan Ac daya barmata a kunne na ratsa jikinta sai taji tana wani irin jin bacci bacci, bude kofar motar bayan da akayi yasa ta bude ido tadan waigo, shine abu taga ya dauka dabata ga kome ba yamayarda kofar ya rufe ya dawo gaban ya bude ya zauna sanan ya jiye mata wani dan kwali da akai rapping dinshi da jan rapping shit anmaida shi kaman fulawa akan cinya, wani irin sassanyar murmushi tayi ta sanya hannu ta dauka tana kallon abin ahankali yace "open it tsaraban kine" gyada mai kai tayi ta ijiye akan cinyarta ta warware flower saman ta warware rapping shit din, kwalin sabuwar wayar Samsung tagani na latest model dinsu, wani irin ihu tayi ta matso ta rungume shi hakan bakaramin mai dadi yay ba, yay murmushi yana shafa bayanta, ahankali ta sakeshi tama wayar kiss ta kalleshi ganin ita yake kallo tace "thank you, Allah ya saka da alkairi ya kara bude ya karemin kai" sosai yaji dadin addu'an harsaida ya washe hakora ya kunna motar suka cigaba da tafiya, bude kwalin tayi taciro wayar ta kunna sai jujjuyata take, aranta tace "finally zan koma watsapp nama Maman Shakur magana tasani awanan hadadden group dinan nata" wani irin dadi taji hakan yasa ta kalli fuskarshi ganin tukinshi yake hankalin shi nakan hanya yasa tai murmushi tana kallon sajen shi yanda yake ta kyalli. Ahaka har sukazo GRA kofar gidan su Abba taga zasu wuce da sauri tace "baza muje mu gaida su Abba da Ya Yusuf ba?" dan juyowa yay yamata wani irin kallo dayasa ta dauke kai da sauri yace "gobe mazo" daidai nan yay horn mai gadi yabude gate shiga yayi yay parking ya bude motar yafito, ahankali itama tabude tafito hannunta yakama yanadan waigawa baya, ganin mai gadi harya rufe gate ya koma dakinshi yasa yawani dauketa afirgice ta kallai dan ba karamin tsorata tayiba, kanne mata ido yayi yasa hannu ya bude kofar dakinsu ya shiga da ita ciki, da jikinta yasa ya maida kofar yarufe tareda manne ta ajikin kofar yana mata wani irin mahaukacin kiss batasan lokacin data saki jakar dake hannuntaba yafadi kasa, jikinta har wani rawa yake dan har yanzu bata sababa, sake daukar ta yayi batare daya raba bakinsu ba yay hanyar bedroom da ita, akan table din dining ya daurata shiya tsaya a tsaye yana kissing dinta, sakin bakinta yayi ya cire hijabin jikinta tareda tumbuke daurin dan kwalin ya yar anan kan kujerun dining yana wani irin kallon idonta kasa kallonshi tayi ta kawad da kanta kirjinta na wani irin mugun bugawa ga lips dinta dake wani irin zagi dan tass ya shanye janbakin nan, hanunshi taji akan habarta ya juyo da fuskarta tareda sa hannu ya ware kafafunta ya shiga tsakakaninsu ya matso dab da ita sosai hartana jin saukar numfashin shi da yanda kirjinshi ke bugawa fast fast, kara matsota yayi hakan yasa akunyace ta boye fuskarta a kirjinshi sanan tasa duka hannayen ta ta tattaro rigar soft yadin jikinshi ta kakkare fuskar ta dashi ta nannade kafafunta a bayanshi gam hakan yakarasa ya mannu da ita kaman zasu koma one, wani arin ijiyar zuciya mai kara yasaki da saida yasa ta dago kai ta kalleshi dan ita kunya ce tasa ta nannade kafar tata a bayanshi, da wata irin murya kasa kasa yace "zaki kasheni Islam, ahhh" kankameta yayi tareda saka hannu ya cire ribbon din dake kan gashin ta ya barbazar da gashin yana wani irin kallon fuskarta, bakinshi yakai saitin idanunta hakan yasa ta lumshe su da sauri kirjinta na fat fat, wani irin kiss mai kara yama saman idonta nata hakan yasa taji wani irin yirrr dahar saidai taji kanta nawani irin motsi, daukar ta taji yakara yi yay bedroom d ita yawani wurgata agado tai kara wash Allahna, murmushi yayi yayo kanta yahade bakinsu ganin yana kokarin zuge zip din rigarta yasa ta fizge bakinta da kyar ahankali tace "banyi salla ba" sakinta yay ahankali jiki asake hakan yasa ta tashi da sauri tafada bayi kafin yakara kamata, wanka tayo tafito daure da towel tana wani mammatse baki tana kallonshi tana dauke kai kaman yarinya, lamo yayi akan gado tareda janyo filo ya rungume yakasa dauke idonshi daga kanta, batada kaya agidan hakan yasa yar rigar singlet din maza tashi fara datagani ta dauko ta wuce bathroom ganin yanda yake kallonta, saka wa tayi amma takasa fitowa ganin rigar ko cinyarta bata kaiba, ga hammatar duk abude ana hango abubuwa, dan tsaki tayi ta daura towel akirji tafito taki yarda su hadda ido tabude kofa tai falo jakarta ta dauka taciro zani tadau hijab a dining ta dawo dakin bata sameshi akan gado ba hakan yasa ta kabbarta salla. Yana fitowa shima wankan yayo da alwala yasaka jallabiya ya zauna abakin gado yana jiranta tana idarwa yajasu nafila raka'a biyu tare. Sosai yamusu addu'a bayan ya idar ya kalleta tareda daukan car key yace "mexaki ci babu abinshi agidan nan" jingina tayi da jikin gado tace "banajin yunwa naci abinci agida" tai maganan tana wani lumlumshe ido, ajiye car key yayi dan shima akoshe yake ya cire jallabiyar yadawo inda take zaune akasan dagashi saidan boxer na Louis Vuitton ya zauna agefenta, kin kallonshi tayi, ahankali ya jawota jikinshi hakan yasa tai lamo tana shakan kamshin da fatarshi keyi, ya sanya ta kan kafafun shi kanta akan hanunshi kaman yanda ake daukar yara ya kalli fuskar murya chan kasa yace "meke damunki ur body is warm?" bude ido tayi kadan tareda turomai baki tace "bakaine ba kasa naketa ciwo ba" dan murmushi yayi ya lashi bakin data turamai yace "ai mun shirya ko hukuncin kine kawai yarage wanda yanzu zaki karbeshi" shigewa jikinshi tayi tawani kankameshi tana dariya tace "uhn'un to ai nace kiyakuri" hanunshi yasaka tacikin hijabin ya kwance kullin zanin ya warware tareda cire zanin ya ijiye agefe, kara shigewa jikinshi tayi ta fashe da kukan shagwaba tana kokarin rufe cinyoyin nata da hijabin dake jikinta, dagota daga jikinshi yayi yasa hannu ya cire hijabin da karfi, ihu tayi mara sauti tawani fashe da kuka takara komawa jikinshi har saida tasa ya buge da gado ta daga hannayenta sama tana kokarin rufemai ido dan karyagan ta dawannan gantalallen shimin, murmushi yayi batare daya hanata ba aiko tana ida rufemai idanun da hannayen nata ya shammaceta ya tura duka hannayenshi ta hammata shimin dayake wide open yakamo.. Uhm. [7/5, 4:47 PM] Maman Jedda: *JARABTA* Maman Abd Shakur Karshe!!! Kara tasaki maidan karfi tareda cire hannayen ta daga fuskarshi arude ta kallai yawani irin lumshe ido da budesu yana kallonta batare daya dena abinda yakeyi ba, fashemai tayi kuka tana kokarin kwace kanta tana turamai baki tace "wash Ya Khaleel dazafi fa" matso da fuskarshi yay saitin nata yace "barito nabude na kalli inda ke zafi a wurin" ganin yana kokarin kwaye shimin duka yasa tabuga kara tana kuka sosai ga kunya dukya addabeta, hakan yasa yasaketa tareda daukarta kaman wata yar yarinya ya kashe musu wutar dakin ya kwantar da ita kan gado, sosai nakejin kukanta hakan yasa nabaro musu dakin tareda kullo musu kofa. Ko hanunta bata iya dagawa da kyau sabida wahala, sallama adaddafe da taimakon shi tayi, ya kwanta agefenta sai dariya yakemata hakan yace "hukuncin ki kenan" aiko ta dinga rusamai kukan shagwaba hakadai ya dinga aikin lallashi har wuraren bayan sallan la'asar ganin taji sauki yasa ya shirya ta sukaje gidansu Abba nan aka zauna aka dinga hira har saida sukaci abincin dare sanan Abba yace sutashi sutafi gidansu. Suna shiga gidan tafara kukan shagwaba dan batason yakara bata wuya irin najiya, aiko share ta yayi yawuce daki ganin taki zuwa yasa yazo ya dauketa kaman baby yasa taje tai wanka, bayan tafito da kanshi ya shiryata yadawo da ita kan gadon ya zauna tareda sanya kanta akan kirjinshi yana shafawa ahankali ya shiga bata labarin Eesha, dayazo wurin mutuwarta da abubuwan daya sameshi bayan ta rasu yasa ta dinga kuka dan bakaramin tausayi yabataba tai taima Eesha addu'a sosai sanan ta cigaba da hawaye, da kyar yasamu ya lallabata tai bacci yana girgiza ta akirjinshi. Washegari da sassafe Yusuf yakaisu airport sukabi jirgi suka tafi Abuja sabida yanada aiki da safen agida ya ijiyeta sanan yawuce office, da yamma yadawo yasami gidan tsaf sai kamshin turaren wuta yake dadi hakan yamai yasameta a dakinta yace "shirya mufita" da sauri ta tashi tana murna ta shirya tai kyau da ita, hanunta yakama yarike suka fita compound mota yabude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga anguwan su taga sunje tanata murna tazaci gidansu zashi saitaga yay parking agaban wani gida dake kusa da nasu yafito yabude mata suka shiga compound din tare, sallama yayi abakin kofa Mum ta amsa tace "muryan Khaleel nakeji, ga ango ga ango, Auta jeka cemai ya shigo" tashi Auta yay da gudu yazo yabude kofa turus ya tsaya yana nuna Islam yace "Anty aita" yajuya da sauri yakoma wajen Mum yace "Mumy Anty aita tadawo daga tafiyan da kikace tayi" ahankali ta daga kai ta kalli Khaleel da jikinshi yay sanyi sosai dan murmushi yamata yace "nanne gidansu Eesha, mu shiga" hanunta yarike suka shiga ciki sai yanzu Mum tagane mai Auta ke nufi, tsayawa turus tayi tana kallon Islam ko kwakkwaran motsi takasa, hanunta Khaleel yasaki yamata alamu taje dadan saurin ta Islam taje tafada jikin Mum tawani fashe da kuka dan wani irin mugun tausayi da son matan taji tanaji, kanen Eesha su Ibrahim da Faty da Auta yaje yakira duk tsayawa sukayi suna kallon Mum da Islam yanda Islam ta kankameta tana kuka, da kyar Mum ta tattaro karfinta taciro ta daga jikinta hannu tasa ta sharemata hawayen datake itama ta share nata murmushi tayi ta kama hanunta ta zaunar da ita akan kujera ta kalli faty tace "kuje ku kawo musu abun sha" tajuyo ta kalli Islam tace "ya sunanki baiwar Allah kina mugun kama da marigayiya Aisha badadan nasan tariga tarasu ba da sainace kece wlh" kwalla Islam takara sharewa ahankali tace "Allah jikanta da rahama Mumy" dukan su sukace amin, Khaleel yay murmushi yace "Mum sunanta Islam, lokacin dana fara ganinta a yola haka nadinga binta nima" murmushi Mum tayi tana kara kallon Islam din hatta yanayin sanyinta irin na Eesha ne ahankali tace "ikon Allah kenan gaskiyar kakan mu tana yawan cewa mutum bibbiyu bibbiyu ake hallittar su aduniya, Allah sa mucika da imani" haka suka zauna dasu Mum da kanin Eesha dasuka zagaye Islam sunata mata labarai wani irin son yaran taji tanaji hakanan sai taji kaman kanninta najini ne, bayana sallan isha ma tareda Abba suka dawo shima yay mamakin ganin Islam, basu bar gidanba saida mum ta cikasu da alkairai gidansu suka biya sanan suka wuce gida. Bayan wata hudu Rayuwa sai tafiya take yayinda bikin Yusuf yau saura sati daya dawata yar abokin Abban su aka hadashi yana ganin yarinyar kuma yaji ta kwanta mai. Farida kuma hakanan ta yardar ma wani guy daya nace mata badan tadaina son superman dinta ba, nan Abba ya binciko halin yaron yarone nagari barrister ne hakan yasa Abba yace yaturo akasa biki wata biyu. Akai akai Mum ke turo kanin Eesha suzo sumata wuni, hakan bakaramin dadi yake mata ba, tana mugun son yaran dan suna da hankali ga ilimin addini. Ranan Friday da yamma suka sauka ayola kasancewa gobe ne daurin auren Yusuf, adaddafe tai sallan isha sabida yanda zazzabi duk yabi yarufe ta hakan yasa Khaleel yadamu da kyar taci abinci yabata paracetamol tasha yace inhar zazzabin bai kwanta ba asibiti xasu gobe nan bacci yay gaba da ita ya gyaramata kwanciya, koda safiya da karfinta ta tashi ta shirya da sauri cikin ankon su na family miji wani blue atampa ba karamin kyau yamata ba yafito da hasken fatanta sosai, gashi tai bulbul da ita, sai kallonta yake ganin yanda ta cicciko, shiryawa shima yayi cikin fara shaddan ankon dasukayi da angon yadauko hijabi yasaka mata sanan yakama hanunta suka fito har gidansu sassan goggo ya kaita ya kalli Goggo yace "kuma kar asamin mata aiki dan batajin dadi" harara goggo ta watsamai tace "nikake ma fi'ili munafiki mtswwe" taja tsaki tareda rike hanun Islam tajata zuwa uwar dakanta, murmushi yayi yajuya yafita ganin Yusuf na kiranshi, gidan yacika makil da mutane itadai tana taredasu Ihsan a bangaren goggo zuciyar ta sai tashi yake sabida yanda kamshi turare kala kala na mutane ke shiga hancin ta, yatsine fuska tayi ta kwanta akan gado tana juye juye Ihsan tace "lpy ki Islam" bata iya amsata ba sabida wani irin amai dayazo mata da gudu tai bayi ta dinga kwararawa hankalin su Ihsan dukya tashi, haka ta dinga amai tun suna zatan maybe batasan mutane ne ko hayaniya hardai Fa'iza da gudu taje ta kira su Mumy da Goggo dake waje wajen baki, Koda suka iso tana kwance kan gado kaman numfashin ta zai dauke Ihsan na fifitata, Ammi ne ta dagota zaune ta taba kanta tace "meke miki ciwo daughter" kasa magana tayi ta fashe musu da kuka tana wani irin mikewa tana yunkurin amai amma babu abinda ke fita sabida dukta amaayar da abin cikinta ga jikinta zafi, arikice goggo tace "na shiga uku, uban mekuka bata taci?" yanda goggo tai maganan yasa su Ihsan duk suka rude mu bamu bata komiba, Umma ta kalli Fa'iza tace "daukomin car key mu kaita asibiti tunda duk mazan suna wajen daurin aure" da kyar ta iya tashi da taimakon Ammi suka riketa suka sakata amota akai asibiti da ita, gado aka bata akamata allurai a drip na tsayar da amai, gwajin farko ya nuna ciki gareta na kimanin wata daya aiko zokaga murna wurin su Ammi da Umma dan subiyu kawai suka kawota sukabar Goggo dasu Ihsan agida, nan dai Dr yace "bari inta tashi zasu iya tafiya, zai rubuta mata wasu magunguna" arude Khaleel ya shigo asibitin daga wurin daurin aure danhar Ihsan takira ta fesamai, ganin su Umma namai wani irin kallo yasa ya dauke kai yawani shamur ya kalli Dr dake mikamai hannu yace "kaine mijin wacce suka kawo" Khaleel ya gyadamai kai yana waige waige dan neman ta yake "congratulations Matar ka nada juna biyu" juyowa Khaleel yayi ya kalli Dr baisan lokacin daya daga Dr samaba abunku damai karfi yana wani jujjuya shi, dakin dayaga Ammi ta shiga tana tabe baki ya ijiye Dr yace "am coming" da sauri yabi bayan Ammi ya shiga bacci yaga tanayi ga drip ansamata wani irin dadine ya lullube shi ya dinga godema Allah ranan dai Khaleel yay kyauta dayawa, Yusuf sai iskanci yakemai yana "ka godemin ranan bikina ne kasami gud news dinan" , harara ya ballamai yace "anjima dai zamu kaika kaima ka wurga kwallon cikin ragan ka ai" , baki Yusuf yarike yana kallon shi yace "ikon Allah damafa ance idan namiji yay aure fitsararre yake zama" tabe baki yayi yace "kaga tafiyata" yawuce abinshi, dan fita nemo mata goriba anyi anyi da ita mezataci tace zuciyarta tashi take wai goriba takeso 😂 Ba karamin kulawa Khaleel yake bataba itama dudda cikin nabata wahala bai hanata zakewa wurin bama mijin nata kulawa ba da nunamai tsantsan so, haka bayan wata biyu suka dawo bikin Farida sosai sukamata alkairai takuma musu godiya, Mum dai ko kala batace ma, koda zaakai Farida bai bari tajeba sabida batada wani cikakken lpy bayan kwana biyu suka dawo Abuja. Farida ta rungumi mijinta dudda har yanzu son Mk na nan daram aranta amma tariga ta rungumi kaddara ta nunama zuciyar ta ba komi kakeso kasamu ba, saidai fa! Son superman dinta wani irin sone da Allah yasa ya shigeta lokaci daya dan haka shi kadai zai iya zare mata son nan lokacin daya. Abba duk ran Friday yake kiran duk yaran nashi yaji lafiyar su tareda musu addu'a. Tsakanin Mum da Islam kuwa babu abinda ya chanza dama ance ba kowa bane zaisoka a duniyar nanba, takan kirata awaya ta gaisheta dudda sama sama take amsata, Anty Hindu kuwa har Abuja takan zo ta duba Islam din. Bayan shekara biyar. Wani yaro sak baban shi danhar bakin fatar mahaifin nashi yayo baiyi farin Islam ba ya zauna akan dining table ga white rice da egg agabanshi babu stew sai kuka yake a shgwaban ce, Islam data kara kyau tawani kara cika da kiba tai tagumi tana kallonshi danji take kaman ta bugai rigiman Imam yay yawa wlh, yaro shekara hudu amma har yanzu sai shegen kukan banza, kofar da aka bude yasa yaron yay jumping yaje ya rungume Khaleel dake sanye da uniform da gudu yakara fashewa da kuka, ciro shi daga jikinshi Khaleel yayi yace "waya tabamin yaron baba" turobaki yayi yace "Dady Mumy tabani rice ni tuwon grandma nakeson ci" yawani fashe da kuka harda buga kafa, Khaleel ya tashi tsaye ya dauke shi tareda saba wa akafada yace "muje kaji Dady boy gidan grandma din" da gudu Islam taikan kujera zata dau hijabi ya harareta yace "wai ban hanaki gudu ba kin zaci ke kadaine" turo baki tayi tareda shafa dan cikin dake jikinta na 3month, rike baki Khaleel yayi yace "au kin koyama Imam turo baki shima wanan na cikin zaki koyamai ne" dariya tayi tadau hijabin tasaka tazo kusa dashi tace "dan Allah nima zani tuwon Ammi nakejin ci" make mata kafada yayi hakan yasa ta lakaci hancin shi tace "haba my big baby, kaga kaine big imam kuma small baby" dariya Khaleel yayi yace "yeee my daddy is a big baby" dukansu sukahau dariya, rungume Khaleel tayi ta kalli fuskar Khaleel sanan ta kalli Imam tace "ur Daddy is not just my big baby" ahankali ta saukar da kanta a kirjinshi ta sauke ajiyar zuciya tace "your Daddy is MY EVERYTHING" da hannu daya Khaleel ya rungumeta yace "and u are MY ROCK Islam, ina mugun alfahari dake" ihu Imam yayi yace "Dady me too hug me" saukar dashi Khaleel yayi suna dariya suka sakashi atsakiyan su sanan Khaleel ya rungume dukansu yace "Allah yahada mu haka a aljanna" atare harda Imam sukace "Ameen". END!!! Yan uwa anan nakawo karshen wanan kirkirarren littafin mai suna *Jarabta* na tsara littafin nanne sabida cewa da akayi nayi mugun kama da wata Amina wacce ta rasu, Allah ya gafarta mata, Allah ya yafemin kura kuren danayi aciki. Albishirin ku! Sabon littafina mai suna *SANGARTATTCE* na nan tafe, in ki/kanason karanta wanan littafin dazan fara mai kayatar da zuciya zaka tura naira dari biyu 200 zuwa wanan account number 3107021073 First BANK AISHA MUHAMMAD Saiku turamin evidence na kun biya a number watsapp dita kaman haka 07012181461 saina sanyaku a group danjin wanan labarin mai kayatar da zukata. Saina jiku masoyan littatafan maman Shakur. Littatafai na Anatu Siddiqa Matar soja Ameesha Rayuwar Humairah Dole kisoni Tawa ce Khaleesat Nisful hayat Kabilar mu Kaine sirrina Umar Faruqh Madinah Jarabta Zaku iya samun su a blog dina kaman haka mamanshakur.wordpress.com Sanan zaku iya following dina a wattpad "mamanshakur" banriga nagama saka littafaina awurin ba, amma ina kanyin hakan ne. I love you guys, ranan Lahadi da izinin Allah zan fara kawo muku labarin *Sangartattce* 07012181461 zaku iya watsapp dina dan magana, gyara kokuma wani abin daban. One luv❤