[12/30/2021, 8:13 PM] Ayshercool: .🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA Page 1 PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * Anda no WITA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA jinjina ta musamman ga Swt Sisyna (Nanatou) Allah ya bar ƙauna. Me gayya me aiki shugaba a bar koyi Safna Aliyu Jawabi. Sa'adatu Abdullahi Madubi (My red) Anty Asmy Jafar Mummyna Nafisa Ummu ɗahira Da dukkan membobin ƙungiyar perfect writer's association Godiya ta musamman ga, iyayena ƙawayena 'yan uwa da abokan arziki, tare da masoyana a duk inda kuke a faɗin duniya. Alhamdilillah, ina miƙa Godiya ta ga Ubangiji maɗaukakin sarki, yadda na fara a sa'a Allah yasa in gama a sa'a. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in Domin gyara, sharhi ko shawara 07063065680              _ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, GASHI YA DIRA DA ZAFINSA, GAJEREN LABARINE ME TARIN ILIMANTARWA DA NISHAƊANTARWA KAFIN ZUWAN LITTAFIN RUƊUN ƘURUCIYA, COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE BUƘATA, BAZAN DINGA POSTING KULLUM BA, SANNAN BABU LALLAI IK DINGA DOGON PAGE, SANNAN DAN ALLAH BANDA BIYONI PC ANA DAGA FARKO, ZANYI IYA ƘOƘARINA INYI SHARING GROUPS, KUMA KU DINGA TAYANI SHARE PLEASE, COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE BUƘATA, GA WANDA BASU KARANTA LITTAFIN AƘIDATA BA, KARKU BARI A BAKU LABARI, KUZO IN BAKU PART1 KYAUTA KU SAI 2&3 AKAN FARASHI ME SAUƘI, TAKU HAR KULLUM AYSHERCOOL_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Da misalin ƙarfe goma na dare, Gari yayi shiru, wasu daga cikin al'umma sun adana kawunansu a cikin gidajensu, domin hutawa rayukansu hidindimun da akayi da Rana. Sedai a ɓangare guda kuma sautin kiɗane ke tashi a wani ƙaton ɗakin taro, mutane nata shiga da fita kamar Rana, se kaiwa ake ana komowa da Abinci da abin sha kala kala, da gani base ka tambaya ba kasan bikine ake na masu hannu da shuni, duba da haɗuwa da tsaruwar ɗakin taron, da kuma kalar mutanen dake zarya a gurin, da uwa uba danƙara danƙaran motocin dake fake a harabar gurin taron. Ango da amarya na kan high table suna kallon wanda suka halarci bikin nasu, Yayin da ƙawayen amarya da abokan ango, dangi 'yan uwa da abikan arziki keta cashewa a filin rawa, anata bajinta gurin zuba musu kuɗi, dj se ƙara zigasu yake suna ɓarin kuɗi yayin da matan keta cashewa. MC ne ya fara magana ta speaker yace "Masha Allah, gaskiya na yadda wannan bikine na masu arziki, madalla ƙawayen amarya da abokan ango ina godiya da wannan bajinta da ku ka nuna, da kuma kara da ku ka yiwa Amarya da ango, sedai ana tsaka da wannan shagali na samu sanarwar, isowar wasu hamshaƙan jiga jigan baƙi da suka amsa gayyata domin tayamu nishaɗi a wannan biki na 'ya'yan gata, wannan baƙin ba kowanne bane face DJ Sultan, tare da 'yan tawagarsa na rawa, ciki hadda wannan tauraruwar taku, wadda ludayinta ke kan dawo, tauraruwarta ke haskawa a cikin manyan yara da suka yadda da kansu wajen iya cashewa, wato gimbiya Amira, nasani ga dukkan wanda suka saba zuwa guraren taron biki, birthday da makamantan su, da duk wanda yasan dj Sultan da tawagarsu nasan sun san wannan gimbiya, kai ga wanda bema santa ba yau ze santa, zatazo ta baje mana baiwarta ta nishaɗantar damu, ina fatan kuma zaku nuna mana farincikinku ta hanyar nuna bajintarku, DJ idan ka shirya, Sultan da jama'arka muna buƙatar ganinku akan stage" Wata waƙa aka saka me sanyi, wasu mazane suka dinga fitowa, suna sanye da baƙaƙen wanduna da fararen riguna, bayanta an rubuta Dj Sultan, sekuma sunayen su a ƙasa, su huɗu haka suka zo suka jeru a tsakiyar filin, suka sunkuyar da kai, kamar masu jiran umarnin wani, sumarsu duk ta sha dying, kowanne da kalar askinsa, wanine ya kuma shigowa filin shima, sanye da shiga irin tasu, ga uwar suma akansa se ƙyalli take ya tsaya a cikinsu suka zama su Biyar. Mutane sun zuba ido  suna jiran ganin gimbiya Amira, kowa ya zuba ido wasu tyni sun zaro wayoyi zasu ɗauka, amma aka shafe wasu mintuna bata bayyana ba, se jan rai da ake yi, har wasu suka fara ƙosawa. lokaci ɗaya aka canza waƙa, aka saka wani kiɗa me sauti da ɗaukar hankali, Ta wata ƙofa ta fito, sanye da crazy jeans, da baƙar riga, ta ɗaure kanta da siririn ɗan kwali ta zubo kitson gashin doki da tayihar ɗuwawunta, ƙafarta sanye cikin wani uban takalmi kamar na sojoji, tana da matsakaicin tsayi, idanunta kamar na Japanese, tana da dogon hanci, sedai ba fara ce tas ba, tana da shape ɗin jiki me kyau, dan kayan sun zauna a jikinta sun kamata tsam tsam a jikinta, kana ganin duk wani shape na jikinta, kallo ɗaya zaka yi mata kaga yarinya ce ɗanya, dan dudu ba zatafi shekaru sha shida zuwa sha bakwai ba, amma tana da jiki me kyau da ɗaukar hankali. Yanayin tafiyar da take, yana tafiya daidai da sautin kiɗan dake tashi, shewa mutanen hall ɗin suka shiga yi, suna tafa mata dan yadda take tafiyar cike da ɗaukar hankali da burgewa, tsakiyar mazan nan taje ta tsaya, tana tsayuwa suka ɗago kansu daga sunkuyarwar da sukayi. Wani irin kiɗa aka saki, aikuwa suka fara rawa a tare, sedai yadda Amiran take rawa kamar ba jikin ɗan Adam ba, Kamar me jikin roba, tafi mazan nan iya sarrafa jikinta cikin ƙwarewa da jan hankali, duk inda ta karya jikinta kota lanƙwasa haka mazan nan keyi, duk wani tsalle da juyi haka itama ke yinsa, attach ɗin kanta na bajewa. Nan da nan hall ya ɗau shewa, masu video nayi Masu hotuna nayi, nan aka shiga ɓarin kuɗi akan Amira. Sunyi rawa kala kala Babu alamar Amira ta gaji da rawar nan, suka nishaɗantar da mutane sosai, agogon hannunta ta kalla, ta silale daga kan stage ɗin, se nemanta akayi aka rasa. "Mungode mungode, DJ Sultan da tawagarsa, jinjinar ban girma ga Gimbiya Amira, munagodiya da wannan gudunmawar da aka bamu, Muna fatan Allah ya maida gimbiyarmu gida lafiya" Amira kuwa zuwa tayi ta canza shiga, ta saka doguwar riga akan kayanta, kamar ba ita tayi wannan uwar rawar ba. Zagayawa tayi inda dj suke zaune, tace  "Sultan, yau mun samu kuɗi sosai, bani 10k zan hau Mota, senaji alert" Sultan ya kalleta Yace "ke Amira, har 10k?" "Eh ko ba zaka bayar bane?" Sultan yace "A'a, ni na isa ince bazan bayar ba? Ni a wa?" "Dalla ka hanzarta ka bani, zan tafi gida inje mu fafata, kuma fitar yau tayi kyau, dan mun samu kuɗi wallahi maga ba dai dai ba zanyi dirar mikiya a Chamber inyi rashin mutunci" Sultan yai murmushi yace "ki huta gimbiya, bame miki ba daidai ba ai girmanki ne, in bake babu mu" ya ƙarasa maganar Tare Da ƙirgo kuɗi ya bata. Yayin da aka cigaba da shagalin biki, ita kuma ta silale tai waje abunta, agogon hannunta ta kalla, sha biyu saura na dare, kuma gurin bikin ma basu da niyyar tashi yanzu. Cikin hanzari ta fita titi, duk babu masu abun hawa, se  ɗaiɗaiku, ji take tamkar ta rufe ido ta ganta a gida, dan ta san yau da drama. Wata uwar ƙatuwar motace ta alfarma tayi parking a gabanta, aka sauke glass ɗin motar. Wani Babban mutum ne a ciki, wanda a ƙalla ze kai shekaru hamsin da biyar, ya kalli Amira Yace "Baby ina zuwane muje in sauke ki?" Ƙare masa kallo tayi, ta ɗauke kanta. "Haba Me kyau, be kamata kiyi ta tsayuwa a gurin nan ga dare ba, ina zakiyi". "Hausawa zanje" ta bashi amsa. "Ok shigo in saukeki Mana" Ba tunanin komai, Amira ta buɗe gaban motar ta shige abunta, wani sanyi da ƙamshin turaren jikinsa sun gauraye cikin motar. Ya fara jan motar a hankali, ya kalleta Yace "Gimbiya Amira, kinci sunan naki gimbiya fa, gaskiya kin nishaɗantar damu sosai, na daɗe banga 'yar baiwa ba kamarki" Ɗauke kai tayi kamar bata san meyake cewa ba, ya ɗan kalleta Yace "magana fa nake Gimbiya" Maimakonsa ta bashi amsa, se tace "Idan kaje zoo road zan sayi abu" "Meye abun?" "In munje ka gani" ta bashi amsa Yaita surutunsa amma taƙi Magana, suna zuwa gurin masu gasa kaji tace "yawwa ɗanyi parking, zan sai kaza" Yace "haba Amira, aiba girmanki bane, bari inje in siyo miki" Bata kuma cewa komai ba, ya fita daga motar, ya ɗan jima sannan ya dawo motar, hannunsa ɗauke da manyan ledoji, ɗaya na kaza ɗaya kuma na abun sha, ya miƙa Mata. Tasa hannu ta karɓe tace tagode. Tai tayi masa kwatance har sukazo bakin wani layi, ta kalleshi tace "Nagode fa a nan zan sauka" "Ahh haba dai, mu ƙarasa inga gidannaki mana" Ta kalleshi tace "gidana kuma? Kaga a nan zan sauka zan ƙarasa" "Amma Yakamata muyi exchanging number, sannan ai Yakamata muyi sallama" Amira tace "Yallaɓai wace sallama kuma?" Ya wani matso daf da ita yana ƙasa da murya Yace "haba Gimbiya, wannan ai ƙwalele ne, duk yadda kikaje kikayi wannan karairayar kice zamu rabu ba sallama haba Baby" Yai maganar yana ƙoƙarin naniƙar Ameera, hannu tasa zata buɗe motar amma taji a rufe, ta juyo a fusace tace "malam ka buɗemin in fita, bana son iskanci fa" "Wane irin bakya son iskanci, nifa bana son wani kame kame, meye na wani damuwa ko ɓoye ɓoye, bayan kin nuna wace ke, kinyi talla na biyo kuma kiƙi siyarwa, kinga in dai kuɗine baki da Matsala, zan kashe miki ko nawa ne" Zaro ido tayi tace "dagaske?". Da sauri ya jinjina kai Yace  "ƙwarai dagakse mana" Kamar abun arziki ta zira hannu a rigarta, ba zato ba tsammani ta zaro wata 'yar ƙaramar wuƙa, se ƙyalli take ta kalleshi tace "Wallahi, idan har baka buɗemin motar nan na fita ba, sena yanka wannan ubsn tumbin naka da wuƙar nan, kuma in toshe duk wata hanya da za'a gane nina yi". Zaro ido yayi Yace 'ke kina mace kike yawo da wuƙa haka, har kike iƙrarin zaki kasheni?" "Saboda irinka nake yawo da ita ai, dan naje nayi talla se akace maka kowane jaki nake sayarwa, ko ana ciniki ta dole ne, na kasa ka taya, nace bazan siyar ba, base ka ƙyaleni ba, ni harƙallata ba kowa nake siyarwa ba seme rabo ina fatan ka gane?". Yadda Amira ke maganar cikin ɓacin rai da zazzaro ido, suka tabbatar da zata iya aikata Abinda tace, cikin hanzari ya cire lock ɗin, ta buɗe motar da sauri, ta ɗauki ledar kazarta ta shige wani layi me duhun gaske. Tana shiga ta cire takalmanta, ta riƙe a hannu ta kasa da gudu tai cikin layin, a bakin ƙofar wani gida tai birki, ta dinga sauke numfashi, seda ta dawo hayyacinta sannan ta shiga gidan cikin sanɗa. Babu kowa a makeken tsakar gidan, dan haka ta ajiye takalmanta ta shiga cikin wani ɗaki ta ajiye jakarta da ledar hannunta ta fito tsakar gidan. Hanyar banɗaki ta nufa, cikin sanɗa amma taji ance  "daga ina kike dan ubanki?". Cak ta tsaya ta juyo a hankali, wani matashine a tsaye yana huci, da zazzare ido. "Nace daga ina kike?" Matashin Ya maimaita tambayar cikin tsawa. "Daga neman na kaina" ta bashi amsa kai tsaye. "Ni kike gayawa neman na kanki kika tafi? Kin tafi yawon karuwancinki shine se yanzu zaki shigo mana gida, kina ta zubar mana da mutunci a idon duniya, to bari kiji in gayamiki daga yau se yau idan kika kuma tafiya yawon iskancinki kikayi dare, to karki shigo mana gida, ko kuma ki tarkata kayan ki ki shiga duniyar gaba ɗaya ki bar mana gida, zefi miki kwanciyar hankali" "Ai wallahi tallahi babu ɗan matar daya isa ya koreni daga gidan nan, dan gidan ubanane, kuma karuwanci sana'ane, wani idan ya kasa nasa kasuwancin ba'a siya, nikuwa Alhamdilillah, idan na kasa har wawa ake, kuma wallahi yanzu na Fara" A harzuƙe yace "ni kike gayawa haka?" "An gaya maka ɗin, haifata kayi da bazan gaya maka ba?" Cikin zafin nama ya kai mata mari, ta goce da sauri, ta ware muryarta a wannan daren ta shiga kurma ihu, ga gari yayi shiru saboda dare amma ta dinga kurma uban ihu. Wani dattijo ne ya zare sakatar wani ɗaki ya fito Yace "idan kanawa ma'aikin Allah Usman ka ƙyale yarinyar nan, karta tara mana jama'a ni wallahi lamarinta tsoro yake bani yanzu" Usman yace "wallahi Baba dan taga ana ƙyaleta ne, duk ta zubarwa da mutane mutunci maimakon tayi iskancin nata a ɓoye amma seta nuna duniya ta sani, shegiya karya" Amira tace  "wallahi niba karya bace, kuma wallahi ka kuma yunƙurin dukana sena maka illa, ko in sa a zanemin kai wallahi, dan yanzu ba da bace" Usman Yace "kana gani ko Baba?" "Ƙyaleta duniya ce, wanda bezo bama jiransa take, rabu da ita abokin yi take nema" Haka suka koma ɗakunansu suka ƙyale Amira. Ta shiga banɗaki ta fito, taga yadda kowa ya rufe ɗaki yana bacci, ta nufi inda ake girki, ta bubbuɗe kwanuka, amma ba'a bar Mata Abinci ba. Ta kalli kwanukan, ta sake kallon yadda kowa ya rufe ƙofa yana bacci, tace 'wallahi tunda aka ƙi ajiye min abinci se kowa ya tashi" Ta ɗakko ƙaton murfin tukunya ta fito tsakar gida, ta saita ƙofar ɗaki ɗaya ta jefi ƙofar da ƙarfi da murfin babbar tukunya, nan take ya bada wani razanannen sauti, wanda ya sanya wanda suke ɗakin kurma ihu, kafin su gama ihun ta sake jefa wani murfin, nan da nan ta tashi da yawa daga ilahirin mazauna gidan, ba iya na cikin gidan ba harda maƙota, suka tashi a firgice. "Amira, baki da hankali? Wane irin dabbanci ne wannan? Meye haka kika yi?" "Ba dole inyi rashin mutunci ba, dan wulaƙanci ace baza'a ajiyemin Abinci ba, sedai ayita sani aiki kamar jaka a gidan nan, wallahi idan ba'ayi wasa ba sena tada balli, a raba gidan nan a bani gadon ubana a ciki, idan yaso in dinga ci da kaina, tunda an maida ni mara galihu a gidan nan" Wata matace ta ɗora hannu a ka tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wane irin bala'i ne? Wace irin annobace wannan? Shikenan bamu da kwanciyar hankali a gidan nan, saboda wannan sheɗaniyar yarinyar?". Usman Yace "ka gani ko Baba, daka bari ɗazu na jiƙa mata jikinta da duka, da duk haka bata faru ba" Baba yace  "duka kuma na nawa? Wane irin dukane ba'a mata ba, wannan yarinyar bata da rabon shiriya, kamar jaka haka take, wallahi ina ga gurin 'yan Hisba zan kaita bazan iya ba taf" "Kokuma ka tattara ka maida ita gurin wan uwarta ba, tunda yafi mu arziki" Amira tace  "ba gidan uban da zanje in zauna, nan ne gidan su Ubana wallahi ba inda zani, in kun gadama ku Kaini prison, ku zaku tonawa kanku asiri ba ruwan Amira". Abun takaici ta shige ɗakinsu ta rufo ƙofa, harda saka sakata, ta barsu a tsakar gida suna cigaba da masifarsu suka ɗai, ɗaya daga cikin wanda suke kwance a ɗakin ta kalleta tace  "dan Allah karki shigo muma ki tayar mana da hankali, ki buɗe mana ƙofa zafi mukeji" Amira tace "bazan buɗe ba, wallahi idan baki wasa ba, zamu zauna ba bacci yau se Asuba" "Allah ya baki haƙuri" Ɗayar kuwa da take cikin bargo tsaki tayi tace  "wallahi Allah ya isa hanamu baccin da kika yi" "Asiya kika yiwa Allah ya isa bani ba" A fusace ta yaye bargon ta tashi zaune tace "karki kuskura ki sake zagarmin uwa" "To uwatace da bazan zageta ba, an zageta Asiya kikayiwa Allah ya isa, Allah ya ban haƙuri da ake zagin tawa uwar" Zata kuma magana ɗayar tace  "dan girman Allah Sadiya ki ƙyaleta, abokin yi take nema, ƙyaleta da halinta" Sadiya tayi ƙwafa tace  "matsiyaciya kawai" Amira tace  "nice ma Usman, ba sana'a se zaman banza da sa ido da kurin dukan mace" Haka suka ƙyale Amira, dan yanzu kusan ƙarfe biyu da rabi na dare ne, idan suka biyeta baza suyi bacci ba. Ta gyara zamanta, ta ɗakko ledar kazarta ta shiga ci tana korawa da sassanyar madara, suna jin ƙamshi da yadda take tauna ƙashi, amma ba wanda ta bawa. Seda ta kammala, tayi gyatsa sannan ta nemi gurin kwanciya, Allah ya isa kam ta sha ta a gurin mutan gidan harda maƙwabta. Da Asubar fari ta tashi, ta gabatar da sallar Asuba, ta koma cikin bargo tai kwanciyarta. Bayan gari yayi haske mutanen gidan suka dinga fitowa ɗaya bayan ɗaya, kasancewar gidan family house ne, me ɗauke da mutane da dama a ciki, ɓangare ɓangare ne a gidan, amma duk 'yan uwane. Sashin su Amira suka dinga haɗuwa, suna maida yadda akayi na hanasu bacci da Amira tayi daren jiya, fitinar Amira ta fara addabawa mutan gidan nesa ba kusa ba. Suna cikin tattaunawarne wani babban mutum yai sallama shida wannan dattijon na jiya da daddare wato Baba, suna ganinsa suka ce "Yawwa, barka da zuwa dama kai muke jira Baffa" Sadiya tace "Ai wallahi Baba gara da kaje ka taho da Baffan, tunda shi tana jin tsoronsa, haka kurum duk mutuncinmu ya zube a idon mutane saboda Amira, ta addabi kowa bata jin maganar Kowa, ai gara da kazo daren jiya ko rintsawa bamuyi ba, saboda tijararta" Wanda aka kira da Baffa yace "ku barni da ita, ina makirar take?" "Tana ɗaki tana bacci" cewar mahaifiyarsu Sadiya. Baffa yace  "tasomin ita dan ubanta, yau zata yabawa aya zaƙinta" Sadiya ta tafi ɗakinsu da rawar jiki, "Ke Amira ki tashi ana kiranki" Tai maganar tana dukan katifar Amira, maimakon ta tashi sema taja tsaki, ta sake shigewa bargonta. "Ke Amira kirankifa ake yi" "Ke dalla malama ƙyaleni, in kinga na amsa wani kira tona Allah ne, babu 'yar ƙatuwa ko ƙaton dazesa in fita tsakar gida Yanzu" Sadiya tace "jar uba, Baffa salahun ne ɗan ƙatuwa"? Zumbur Amira ta tashi zaune, kafin tayi magana Baffa Salahu ya shiga bubbuga ƙofar ɗakin yana cewa  "zaki fitone kizo kiran da nake miki ko sena shigo?" Cikin zumɓura baki Amira ta sakko daga kan katifarta, ta ɗau wayarta ta saka a aljihu, ta ɗau kuɗaɗen ta suma ta saka a aljihun wandon dake jikinta  ta fito, maimakon ta nemi hijjabi ta suturta jikinta, amma ta fito a haka, gajeren wando ne a jikinta, da wata matsatsiyar vest, ta baje kalbar attach dake kanta. Baffa Salahu yace "Ke baki da hankali baki da ɗa'a ko? Shine kika fito a haka saboda baki da Kunya?" "To waini ya zanyi? Idan na tsaya saka hijjabi masifa zakayi min, yanzuma kuma ban tsira ba". Baffa yace "nine nake masifar ko? Amira ba kiwa kanki adalci ba wannan mumunnar rayuwar da kika ɗauka, kina 'ya mace da iliminki da komai amma kika zaɓi yawon ta zubar, duk danginmu bamu taɓa samun wanda yai abunda kika aikata ba, abun kunya kamar wanda kike ba'a taɓa samu ba wallahi". Amira tace "Baffa wane irin abun kunya kuma? Nifa ban taɓa cikin shege ba" "Ni kike gayawa baki taɓa cikin shege ba? To je kiyo cikin shegen karki fasa dan ubanki, idan akace a rayuwa 'yar Habiba zata yi karuwanci, za'a ƙaryata hakan amma segashi kina zubar mana da kima da martaba a idon duniya, daga uwarki har ubanki babu mutumin banza kaiconki Amira, kaico". Wani irin abune ya tokarewa Amira a zuciyarta, taji kamar ta fasa ihu, amma tai shiru ta sunkuyar da kai, Baffa nayi Baba nayi, su Yaya Usman ma suka saka baki, aka dinga mata faɗa da tashin hankali a ka, gashi Amira ta tsani faɗa a rayuwarta. Seda suka yi me isarsu, Baffa yace  "duk ranar data kuma fita gantali tayi dare, ko Usman ko Zailani a cikin mazan gidan nan, a samu wani yai mata dukan tsiya, sannan duk randa ra kuma yiwa wani rashin kunyar ko iyashege azo a gayamin, se naci mutuncinki Ja'ira mara kamun kai, kuma daga yau ko ƙofar gida kar a sake bari ta fita, wuce kije ki tattare wannan kwanukan ki wanke, ki ɗora abincin safe, dan matan gidan nan ba bayinki bane suda yaransu, a wanke a ɗora a dafa a baki kici, kuma ki cika musu ciki da iskanci ba" Amira ta kalli uban wanke wanken dake zube a gurin, da uwar tukunyar da ake ɗorawa a gidan dan girka Abinci, ta kalli furfurar dake kai da gemun Baffa Salahu, tabbas ba dan wannan furfurar ba da seta yanka masa rashin mutunci. Amma lokaci ɗaya ta sauya kamar ba ita ba, cikin ladabi tace  "zanyi insha Allah, zan wanke kwanukan sannan zan dama kunun karyawar, Allah ya baku haƙuri" Kamar gaske ta nufi inda murhu yake, masu zagi na cigaba da zaginta, suna faɗar albarkacin bakinsu, taje ta iza wuta ta miƙe tai hanyar banɗaki, tana zuwa ta suri hijjabi a jikin katanga, tai waje da gudu.... Ayshercool 07063065680 [1/2, 11:06 AM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥                 WUTA A MASAƘA                                         Page 2 PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * Anda no WITA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in                          Page2 Amira na jin yadda aka biyo ta ana ƙwala mata kira, amma ta arta da gudu tayi waje, a ƙofar gida ta ƙarasa saka hijjabin data ɗakko akan katanga, tai titi a guje, ta hango wani me napep ta ɗaga masa hannu, ya tsaya ta shige tai gaba abunta. Baffa ya tasaya yayi saroro, yace  "haka yarinyar nan ta zama? Inyi mata magana amma ta zari hijjabi ta gudu" Baba yace  "kaɗan ma ka gani, ba abinda ka gani kai kana gefe, mutanen dake cikin gidan nan mu zamu ƙarar da iya shegen da yarinyar nan take yi, iskanci da rashin mutunci iri iri, haka take aikatawa" Ya jinjina kai yace  "lallai lamarin yarinyar nan ya gawurta, idan ta dawo gidan nan, ɗaureta za'ayi a mata shegen duka, duk inda taje zata dawo ai, koma a sakata a mari kowa ya huta" Nan suka cigaba da kwashewa Amira Albarka, Amira kam taiwa me napep kwatancen inda ze kaita. Ana zuwa inda zata sauka, ta sauka ta bashi kuɗinsa, ta shiga wani layi. Allah ya temaketa, da kuɗinta da wayarta suna cikin aljihun Wannan wandon nata. Ƙofar wani ƙaramin gida taje, ta ƙwanƙwasa ƙofa, ta buga ya kai sau uku sannan aka zare sakata aka buɗe, namijine ya buɗe wanda aƙalla ze kai shekaru talatin da biyu, ya kalleta yai murmushi yace  "Anty Amira ashe kece, sannu da zuwa" Yai maganar yana bata hanya, tace "Yawwa, tana nan kuwa?" Yace "Gaskiya taje kai Khalil Asibiti baya jin daɗi, Khairat kuma na makaranta" Abunda ya faɗa ɗin be hana ta sa kai ta shiga cikin gidan ba, kai tsaye ta wuce falo ta samu guri ta zauna, sannan tace "Abban Khalil meya samu ɗana, da har aka kaishi Asibiti?" Abban Khalil yace "wallahi zazzaɓi yake yi, bari inje in dawo yanzun nan" Amira tace "to shikenan" Yasa kai ya fita, ta kunna kallo ta miƙe akan kujera abunta, ya kai mintunta goma sha biyar sannan ya dawo, daya dawo ɗinma yai sallama ta amsa kitchen ya wuce. Amira tana ta chatting ɗinta, aka jima segashi ya shigo da faranti ɗauke da kayan tea, harda soyayyan ƙwai yace  "tunda naga kin mana dirar safiyar nan, nasan baki karya ba kuma mu mun cinye namu" Amira ta kalleshi tace 'dana san wahala zakamin haka da tabbas bazan bari kayi ba" "Wannan ɗinne wahala? Tashi ki karya malama kafin in fushi Yanzun nan" Amira tai murmushi tace  "Allah ya baka haƙuri, Nagode". Ya fita ya bar mata falon, ta zauna ta karya, ta fito da kwanukan tsakar gida ta tarar yana ta harhaɗa kwanuka ze wanke. "Abban Khalil, me zakayi haka? Ka bari idan ta dawo tayi mana" Yai murmushi yace "ahh haba dai, ya za'ai ta tafi kai yaro Asibiti ban rakata ba, in bar mata aikin gida bayan ban san lokacin da zata dawo ba, ai gara in rage Mata" Amira tace "kaga ɗan aljanna, ka barshi zan mata aikin kafin ta dawo". Yace "A'a, ke ai baƙuwa ce" "Kaji ka wai baƙuwa, Allah ka bari zanyi ka tafi kasuwarka" Da ƙyar ya yadda ya tafi, ta tarar har wake ya dafa saura shinkafa, ya bar kuɗin siyan salak, ta jinjinawa haƙuri da tausayi irin na Abban Khalil. Se sha biyun rana Sannan matar gidan ta dawo, tai sallama Amira ta amsa, ta shiga falon ta tarar da Amira. "Ke kuma saukar yaushe?" Amira tace "tun safe nazo, ba kya nan se Abbansu Khalil, kin tafi kin barshi da aikin gida saboda rashin tsoron Allah" "Ke dalla yimin shiru, ba ɗansa na tafi kaiwa Asibiti ba?" "To kuma se akace ki bar masa aikin gidan?" "To dakeni uwata, kona sa shi, ko ban sashiba in dai Abban Khairat ne se yayi, ba ruwansa" Amira tace "Allah Sarki, Anty Fa'iza kinyi dacen miji wallahi, ana cewa da anyi aure wata ɗaya biyu ake dena wannan soyayyar da kulawa, amma ke gashi haihuwar ki biyu, shekaru shida da aurenku, amma haryanzu sonki yake kamar lokacin da yake neman aurenki" Fa'iza tace "bari kawai Amira, shiyasa tun a wancan lokacin na dage seshi, su Baffa suka sani gaba da zagi da cin mutunci dan nace bazan auri Alhaji Yahaya ba, kin san ɓarin kuɗi ya dinga musu, kowa ya juyamin baya a gidan nan, Inna ma ƙiri ƙiri ta dinga zagina da cin mutumci wai na mannewa matsiyaci na liƙe ni se Bashir nake so, Wallahi da Alhaji Yahaya na aura baze dinga tarairayata haka ba" Amira tace "bari Anty Fa'iza sha'anin gidanmu se Allah kawai, amma munyi rayuwar wahala, kamar ba'a gidan aka haifi iyayenmu ba, ni kaina yau da Sassafe akaje aka taho da Baffa zasu min tijara, yazo yana wassafamin wasu ƙa'idojinsa na banza, ni kuwa na zari hijjabi na arto nan, se sun sake ganina a gidan ai, sun taru a kaina suna ta cin zarafina suna zagina, danma Allah ya temake ni Inna bata nan, tsohuwar nan kallonta kawai nake, idan naje da abun duniya na kaimata, ta karɓe tana dariya, idan wulaƙancinta ya ciyota kuma ta kama cemin karuwa, ni kuwa nace ta dena cin abina" Fa'iza tace  "Amira maganar Allah da ma'aiki, abubuwan da kike aikatawa basu dace ba, kuma kema kin sani Amma.... Amira ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu tace  "ba shawararki nake nema ba ko wa'azi, indai zan samu namiji me kirki nagari kamar Bashir wallahi zanyi aure in dena abunda nakeyi, muma ajiye wannan maganar aside Please karki ɓatamin rai, sakkomin yarona naga ya tashi, kin bar yaro duka ya rame" Fa'iza ta girgiza kai, ta sakko Khalil ta miƙawa Amira, Amira ta karɓeshi ta rungumeshi a jikinta, tana shafa kansa tana "Sannu kaji My Boy, mamanka ta barmin kai duk ka rame" Fa'iza tace 'tunda gaki kinzo ai shikenan, ki kula dashi" Amira tace "tabbas zakiga yadda zan kula da Yarona, naga sha biyu da rabi, ban kayanki in saka muje mu ɗakkko Khairat daga makaranta, dan daga ni se kayan baccina na fito" Fa'iza ta bawa Amira kaya ta canza, ta ɗau Khalil ta goyashi suka fita. ************************ Sannu a hankali yake tuƙa motar, kamar yana jin tsoron hanyar, yanayi yana kallon agogon hannunsa, lokaci lokaci yakan lumshe idanunsa, tare da buɗesu yana  ɗan kalle kalle. Sannu a hankali ya ƙaraso ƙofar wani ƙaton gida, sau biyu kawai yai hone ya ɗan tsaya, buɗe gate ɗin akayi ya shiga cikin gidan da motar tasa, ya ɗan ɗau lokaci a cikin motar sannan ya fito daga cikin motar. Megadi yana tsaye a jikin motar, yana jiran fitowarsa, koda ya fito ridinawa dattijon yayi yana faɗin 'barka da dawowa ranka ya daɗe" "Yawwa barka, mutan gidan suna ciki ne?" Megadin yace "Eu yallaɓai, Suna nan" Yace "Good, buɗe bayan mota akwai trolley ɗina, ka kaimin ɗaki" "To yallaɓai" Sanye yake da wandon sojoji, sekuma baƙar shirt me gajeren hannu, dogone na gaske me siffar ƙaƙƙarfa, kallo ɗaya zaka masa ka san bashi da fara'a sosai, dan ransa a haɗe yake babu annuri, wani irin taku yake kamar wani boss, ya nufi ƙofar da zata sada shi da cikin gidan. Yana tura ƙofar falon, sanyin AC da ƙamshin turaren wuta ya bugi hancinsa, ya ɗan lumshe idonsa sannan ya shiga falon da Sallama. Ba kowa a falon, ya nemi Guri yai zamansa, ya kwanta akan doguwar kujera ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, dan ko takalmin be cire ba. Ya kai mintuna shabiyu sannan aka buɗe wata ƙofa a cikin falon, wata babbar mace ce ta fito daga ƙofar hannunta ɗauke da ƙaramin robar youghurt. Tana ganinsa a kwace tai turus, tace "kai dan ƙaniyarka saukar yaushe? Maimakon ka kirani a waya kawai se in ganka?" Murmushi yayi ya tashi zaune yace  "Hajiya Ammi, maimakon amin sannu da zuwa amma an tareni da ƙorafi, dama cewa nayi let me suprise you, Amma tunda bakya so bari in koma" Tai dariya tace 'eh tashi ka koma ɗin, dan tunda ka tafi 'ya'yana suka sake, dodonsu baya nan" "Aikuwa gani na dawo, kowa ya kintsa zamansa" Ammi tai dariya ta samu Guri ta zauna, tace  "sannu da zuwa ya hanya?" "Alhamdilillah Ammi". "Ya fama da bindinga ya fargaba?" Yai dariya yace 'haba Ammi, fargaba se mata, mu idan muka fita aiki ai mun san a ɗayan biyu muke, ko mu kashe ko a kashe mu, dan haka Bama fargabar komai, ina Boss ne?" Ammi tace  "yau kuma Uban naka ne Boss? Yanzun nan ya fita Allah yayi bazaku haɗu ba, mhmm Kodayake ma ban sani ba ko shi yasan yau zaka zo, dan naga kafi sonshi a kaina, jeka kayi wanka ka canza kaya, kafin nan na kammala Abinci kazo kaci" Yace "to Ammi, ina mutan gidan ne?" "Yaufa ranar aikice, duk suna makaranta ai" Yace "ok" Daga nan ya fito daga falon yabi kan wata baranda, dan zuwa ɗakinsa. yana shiga  ya ƙarewa ɗakin kallo, duk da baya cikin ɗakin amma ɗakin fes dashi, komai tsaf tsaf da alama ana shigowa a gyara dukda baya nan, beyi mamakin hakan ba tunda dama tsafta ɗabi'ar Amminsu ce, be taɓa tafiya ya dawo ya tarar da ɗakinsa da datti ba. ya ciro wayoyinsa ya ajiye ya cire kayan jikinsa, ya ɗauki towel ya ɗaura da nufin ya shiga wanka, amma wayarsa ta fara ringing. Ringing tone ɗin wayar ne ya sanar da shi me kiran wayar, dan haka yai murmushi ya dawo ya ɗauki wayar yasa a kunnensa sedai beyi Magana yai shiru. Muryar mace ce tace "Hello, Hello, My own kana jina kuwa?" "Ina jinki Babyna, ya akayi ne?" "Wai zaka dawo yau ɗin kuwa?" Tai maganar a kasalance. "Shagwaɓaɓɓiya kawai, ban taho yau ba, bazan samu dawowa yau ba, sedai zuwa jibi in Allah ya kaimu zan dawo" "Haba dan Allah, wai yanzu ma ba zaka dawo ba? Haba My ni gaskiya.. "Ke gaskiya me? Jibin ma ba tabbas na zan dawo" "Wallahi ji nake Kamar inyi kuka, wallahi bakaji yadda nake so in ganka ba, wata huɗu fa bamu haɗu ba, zanyi kuka, ni duk raina ya ɓaci duk na damu in ganka" "Dallacan shagwaɓaɓɓiya kawai, na shigo gari anjima zanzo insha Allah" "Wayyo Allah daɗi, dan Allah ka taho yanzu kaji my love?" "Gaskiya sena huta, yanzun nan fa na dawo, Gashi Ammi zatamin girki" "To naji, amma kaci na Ammi kaɗan, idan kazo kaci nawa kaji My Own" Yai murmushi ya shafi sumar kansa yace  "As you wish my Ihsan, yadda kike so haka za'ayi, amma amin izini inzo anjima, in ɗan samu hutu, saboda na sha hanya" Ihsan tace  "Shikenan My Own, ka huta sosai kaji, ina nan ina jiranka kazo inta kallonka, bari in ƙyaleka ka huta" Yace "Ba dan wanka zan shiga ba da mun cigaba da wayar, in cigaba da jin muryar nan taki me saukar min da nutsuwa" "Nima sauraron muryarka yana samun nutsuwar zuciya my, ka kasance cikin farin ciki semun haɗun" "Jinake Kamar kizo ki tayani wankan nan, Allah dai ya kaimu lokacin bikinmu, ya nunamin Ranar da zaki zama mallakina Ihsan" Katse kiran tayi, dan idan ta ƙyaleshi ze fara sakin layine, shima a ɓangarensa yayine dan ya tsokaneta, dan yasan take zata kashe wayar, dan Ihsan akwai Kunya. ********************* Amira tana gidan Fa'iza har yamma, dan bata da niyyar tafiya, Fa'iza taji daɗin zuwan Amiran, suna zaune sunata uwar hirarsu suna dariya, wayar Amira ta fara ringing, sunan Sultan ne ya fito akan screen ɗin wayarta. Ɗaga wayar tayi tace "Ya ake cikine?" Fa'iza tace "maimakon kiyi Sallama?" Harararta Amira tayi tace "Ina jinka" Sultan yace "Ke maimakon ki kirani, kiji ya ake ciki, ko kuma kizo ayi lissafi amma koki nemeni a waya?" Amira tace "nasan kuɗina bazasu ciwu bane, idanma anci se an fitar dasu" Sultan yace "waya isa cin kuɗin gimbiya? Ai anyi kyakkyawan samu jiyan nan, wallahi kina wuta Amira kina bada kala fa, mun samu kuɗi sosai jiyan nan, sake turomin account Number ɗinki, zan turomiki kuɗi sannan akwai wani zazzafan News" "Wait, nawa ma zaka turamin ne inji?" "Dubu ɗari da hamsin ne". Amira tace "meya cinye hamsin ɗin su zama ɗari biyu"? "Haba Amira, wallahi naki yafi na kowa yawa, kin san bazan cuceki ba, saboda in bake ba DJ Sultan, wallahi ban cuceki ba, su muti duk dubu talatin suka samu" "Shikenan naji, turomij haƙƙina" "To ai bakiji sauran zancen ba, wani Alhaji ya bada iPhone a baki, yace kin burgeshi sosai, akwai bikinsa da za'ayi a Abuja, yana gayyatarmu kuma wallahi zamu samu kuɗi sosai Amira, dan bikin ɓrayin gwamnati ne basa jin kuɗi Sam" Amira tace "kai Sultan Abuja kuma? Gaskiya Iskancin nawa be kai nan ba, a yadda ake sace mutane inje a saceni bame karɓoni, idan na tafi Abuja kuma ai se a koreni daga gidan gaba ɗaya" "Haba Amira, kina abu kamar baki waye ba, satin da za'a fara bikin zamu tafi kuma idan ta jirgi kikace jirgi za'a biya mana, za'a kama mana Hotel ɗakinki daban, idan sun koreki daga gidan seki sai naki, dan nasan Idan Alhazan nan suka ganki zasu saki bakin aljihu" Amira tai ajiyar zuciya tace "senayi shawara tukuna, Yanzu dai fara turomin wannan kuɗin". "To yanzu zan turomiki insha Allah, amma dan Allah ki yanke shawarar da wuri, saura sati biyu bikin" "Kai dan Allah karka isheni mana, nace zanyi Shawara" "Shikenan ai girmanki ne Gimbiya, ina saurarenki" Tunda Amira ta fara wayar nan Fa'iza take binta da kallo harta gama, tana ajiye wayar Fa'iza tace  "Amira yanzu seki tafi Abuja yawon rawa? Wakike dashi a Abujan? Kinga Amira ki kiyayi kanki" "Anty Fa'iza, ko naje Abuja ko banje ba sunana Ƙaruwar, babu abunda ze canza sema gyaramin kasuwancina, dan can ne zan haɗu da manyan attajirai in samu kuɗi sosai" "Amira, wataran fa ke uwace, meyasa baza kiyiwa kanki faɗa ba, ki dena wannan abun da kike? Ɓatawa kanki suna kike sake yi fa, kuma labarin abunda kika aikata har 'ya'yanki, ki samu ki nutsu ki nemi miji kiyi aurenki" "Anty Fa'iza aikin gama ya gama fa, abu kan yafaru ake maganinsa base yafarau ba, na riga nayi nisa karki tsammaci zan ji kiranki" "Amira, haryanzu baki makara ba, ni kaina bana jin daɗin abunda kike fa, gaba ɗaya... Amira bata bari Fa'iza ta ƙarasa ba taja tsaki, ta miƙe tace "na fuskanci dan nazo gidanki ne kike nema ki takuramin, gara in tafi in barmiki gidan" Fa'iza ta riƙeta tace "haba Amira, ya za'ai ince bana son zamanki a gidana" Fizge hannunta tayi, tai waje sedai tana fita tsakar gida, Sega babur ɗin Bashir mijin Fa'iza ya dawo, yana shigowa ya kalli fuskar Amira yaga ranta a ɓace, yace "Anty Amira, lafiya kuwa?" "Lafiya lau" ta bashi amsa a ciki. Yace"A'a ba lafiya ba, naga ranki a ɓace, ko Ummu Khairat ce ta miki wani abun?" "Eh itace". Yace "Subhanallah, metayi miki?". "Dan nazo gidanta shine zata dinga min faɗa, shine nace tafiyata zanyi" "A'a baza'ayi haka ba ai, Ummu Khairat kina inane?" Fa'iza na jinsu amma tayi banza dasu, Bashir yace "muje falon mu same ta" Suka shiga cikin falon, suka tarar da ita a zaune tana jinsu, ya kalleta yace "Maman Khairat, meyasa zaki dinga yiwa Anty Amira faɗa? Laifin metayi ne?" "Ta gaya maka kome tayi mana" Yace "A'a, ni base naji ba, amma dan Allah tunda bata so a dena mata faɗa, haba tana Maman Khalil ki dinga mata faɗa a gaban 'ya'yanta, Anty Amira ƙyale wannan Yayar taki, yi zamanki Ranar da kikeso seki tafi" Amira tace "shiyasa nafi sonka a kanta ai, kai bakamin faɗa se ita, ni dama Alhaji Yahayan ta aura, ni kuma na aureka kowama ya huta" Fa'iza tace "Amira ki aureshi mana, ga ɗaki nan a tsakar gida kizo mu zauna" Bashir kawai yai murmushi, dan rigimar Amira bata ƙarewa sam. Amira tace  "ni bani yarana, tare dasu zamu kwana" Tasa hannu ta ɗauki Khalil, ta kama hannun Khairat zuwa ɗaya ɗakin. Bayan fitarsu, Bashir ya kalli Fa'iza yace "Ummu Khairat, ki dinga haƙuri da Amira, sannan kin dinga mata Addu'a, yawan faɗan da kike mata bazesa ta dena abunda take ba" Fa'iza tai ajiyar zuciya, amma takasa cewa komai, amma harga Allah rayuwar da Amira take tana damunta sosai. Yana tsaye a jikin motarsa, ya ciro wayarsa ya ɗan daddana sannan yasa a kunnensa. "My heart gani na ƙaraso" "Alhamdilillah, shigo ciki ka jirani a guest room gani nan" "A'a, ni sedai kizo ki tafi dani, saboda ina samu damar fanshe kallonki da banba sosai tsawon lokaci" Murmushi tayi tace "yadda kake so haka za'ayi angon Ihsan" Shima murnushi yayi ya katse kiran, yana nan a tsaye sega Ihsan ta fito, jikinta sanye da doguwar rigar Abaya, tana da kyau sosai Dan haka bata damu da kwalliya ba sam, sedai tayi kyau matuƙa a cikin kayan. Tun daga nesa take masa murmushi, Yayin da shi kuma ya kafeta da idanunsa, wanda seda hakan ya ɗan sata jin nauyinsa, tana zuwa inda yake tsaye ta ɗago manyan idanunta ta kalleshi tace "Soja marmari daga nesa" "Au kema haka zakice My Ihsan?" "Ba kirarin da ake muku kenan ba? Amma aini a kodayaushe marmarin ganinka nake, bakaga yadda na rame ba saboda rashinkaba kusa dani, watanni huɗu fa My love, gaskiya na sha wuyar rashin ganinka, Gashi ba ko yaushe muke waya ba" Tai maganar kamar zatayi kuka saboda tsabar shagwaɓa, ya ɗanyi murmushi yace "cigaba mana, meyasa kikayi shiru? Ni wannan rigimar taki burgeni take yi wallahi" "Hakama zakace ko?" "Ta ya zance idan ba hakan ba my beb? Ok let's go inside se inyi rarrashi" Tai masa jagora zuwa falon mahaifiyarta don su gaisa, mahaifiyar Ihsan na ganinsu tare da faɗaɗa murmushinta tace "Sannu da zuwa babban ɗa, ashe ka dawo ɗin kuwa?" Yai murmushi ya zauna akan kujera yace "na dawo, ɗazun nan" Tace "Masha Allah, ya aikin naku ya hanya"? "Alhamdilillah" "Masha Allah, Allah ya ƙara tsarewa, amma kai ƙibarka kayi Imran, kamar ba wanda yaje aiki ba" Yai murmushi yace "ƙibar wahala ce Mummy" Ta dings masa dariya tana dama ana ƙibar wahala? Bayan sun gama gaisawane suka, tafi guest room inda suke zama suyi zance idan yazo. "My own, Amma zaka daɗe kafin ka koma ko?" Imran yace "gaskiya ba wani daɗewa zanyi ba, befi inyi sati uku ba zan koma daga nan kuma se bikinmu zan dawo" "Wayyo Allah na, anya idan akayi bikin za'a barmin kai kuwa My own? Ina kewarka sosai ƙishirwar ganinka na addabar ruhina idan kayi nesa dani" "Ihsan, gani nake Tamkar nafiki azabtuwa, bazan iya kwatanta miki halin da nake shiga ba, saboda nesan da muka yi da juna, amma inaga akwai yiwuwar idan anyi bikinmu mu tafi can tare" Ihsan tace "kasan wani Abu love?" "A'a sekin faɗa" "Nifa saura sati biyu in tafi Abuja, zamuje bikin wani ɗan uwan su Mummy, kuma ina kyautata zaton kafin in dawo zaka koma" Kalar tausayi Imran yayi yace 'yanzu tafiya biki zakiyi ki barni?" "Jinake kamar in fasa tafiya fa, ina son inta kallonka, in fanshe tsawon lokacin da ban ganka ba, ga kuma Islamiyya ma bana son inyi missing sam, amma idan banje ba, Mummy za tayimin gorin rashin zumunci ne" Imran yace "karki damu, kije bikinki My love, babban Abinda ke sake burgeni dake shine riƙo da Addininki, yanzu dai ina abunda kika ajiye min?" "Bari in kawo maka" Ta shiga cikin gida, tazo ta gabatarwa da Imran Abinci da abun sha, aikuwa yaci sosai sunayi suna hira cike da shauƙi da ƙaunar juna. Seda ya kammala ta kwashe kwanukan, suka cigaba da hira kamar karsu rabu, tana ta masa shagwaɓa, jiyake inama ace gobene ɗaurin aurensu, ya shammaceta ya riƙo hannayenta biyu cikin nasa, take ta rikice tace "Dan Allah kabari, bana so kasan ba kyaufa Love, dan Allah ka dena taɓani" Idonya harya canza, saboda yadda take a tsorace, ya zuba mata idanunsa da suka sake hanata sukuni, ya sumbaci hannayenta yace  "Allah ya mallakamin ke cikin Aminci Ihsan, ina sonki sosai" Tai ajiyar zuciya tace "naji, amma dan Allah ka bari, kar wani abu na saɓon Allah ya shiga neman aurenmu, kar Auren yaƙi albarka" Murmushi yayi ya sakar mata hannu yace  "Allah ya ƙara hasken makaranta malamata" "A'a ɗaliba dai" tai maganar a ɗan sanyaye tana sunkuyar da kai. Imran yai mata Sallama ya tafi, cike da shauƙi da soyayyar Ihsan. Da Imran ya tafi seda ya tsaya a masallaci yai sallar magariba, sannan ya ɗau motarsa ya tafi gida. Yana zuwa ya tarar da ƙannensa duk a falo suna hira, sunata jiran dawowarsa, yana yin sallama suka amsa cike da fara'a da shauƙin ganin ɗan uwansu, suka shiga jera masa sannu da zuwa. Cike da basarwa yake amsa musu, ya ƙarasa kusa da mahaifinsa ya durƙusa yace "Abba ina wuni" Abba yai murmushi yace "wato shine daga dawowarka, maimakon ma ka bari inzo in ganka, baka tsaya ba kai ficewarka ko? Ko dai gurin sirikartawa aka tafi ne?" Kunyace ta kama Imran, ya sunkuyar da kansa, yana sosa ƙeya. Mummy tace "dan wulaƙanci yaran nan nata jiran ka dawo, sunata ɗokin ganinka, Amma suna maka sannu da zuwa kana amsa musu da ƙyar" Imran yace "Kai Mummy, nafa amsa musu" Abba yace "ƙyale wannan Mummyn taka, ya aikin ya kuma hanya?" "Lafiya ƙalau Daddy, aiki kam an shashi Alhamdilillah" "Masha Allah, to barka da zuwa". Nan suka cigaba da hirarsu, cike da ƙaunar juna, da kuma kewar junansu gaba ɗaya. ************************** Kwanan Amira Biyar a gidan Yaya Fa'iza, a zaton Fa'iza an san Amira tana gidanta. Amira na jin daɗin zama a gidan Fa'iza, dan ba takura sam, musamman yadda Bashir yake lallaɓata, Bashir bame kuɗi bane, se wadatar da zuci da son kyautatawa iyalinsa, Amira ta ƙudiri anyiar zata koma gida, amma seta tabattar da ta sake ɓata musu rai tukuna. ya kasance za'ayi bikin wata classmate ɗinsu Fa'iza, tare sukaje ƙunshi da kitso, Amira duk ta biya kuɗin, tace seta bi Fa'iza gidan biki. Fa'iza ba yadda ta iya da Amira haka suka shirya suka tafi gurin bikin nan tare, suna nan a zaune a gurin taron, Amira ta kushe kwalliyar wannan ta kushe ta waccan, tayiwa wasu ba'a se dariya takewa mutane, se iya shegenta take son ranta, daga tace kalli acucin waccan kamar kwano ko kalli ɗinkin waccan kamar balbela, se tace kalli fuskar waccan kamar tayi gobara, seda Fa'iza taji dama bata zo gurin bikin ba, saboda wulaƙancin Amira, can Fa'iza hankalinta ya ɗauke ta nata gaisawa da ƙawayenta, ana cafkewa ana hirar yaushe gamo. Amira ta silale ta tafi gurin me DJ ta sameshi tace "Dj naga ba a wani liƙi a gurin nan, ka samun waƙa nasan in dai na taka nayi rawa, dole za'a zuba kuɗi saboda ga abokan ango nan sun fara zuwa, kuma naga wannan 'yan matan duk basu iya rawa ba, se wani tsalle suke suna lanƙwashewa kamar wasu kwaɗi" Ya buɗe baki yace  "Allah dagaske? To bari mu gwada wace waƙar zan saka miki?" Amira tace "Aiba kyauta zan maka ba, biyana zakayi" Dj yace "baki da matsala" Kawai Fa'iza na ɗaga kanta ta hango mituniyarta ta a tsakiyar filin rawa, cashewa kawai take ba kunya ba komai, Fa'iza ta dafe kai, nan da nan wanda suka santa suka fara kiran sunanta, Gimbiya Amira a kori 'yan gala. Fa'iza ta rasa abunda yake mata daɗi dan takaici. seda kowa ya dare ya bawa Amira filin rawar nan, aikuwa kamar yadda ta faɗa abokan ango sun zuba mata kuɗi sosai. Isowar ango da Amaryane, yasa ta tsahirta aka basu fili Domin su shigo, ta zaga gurin DJ ta karɓi 'yan canjinta tai waje, duk da yadda wasu suka biyota wai suna sonta, babu wanda ta saurara, ta tari me Napep tace  ya kaita gidansu, dan tasan idan ta koma gidan Anty Fa'iza zasu haura, dan ranta ya gama ɓaci sosai. (Nikam nace ta manta cakwakiyar da ta baro a gidan, kwana biyar bata nan🙄) Ayshercool 07063065680 [1/3, 5:22 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥                 WUTA A MASAƘA                                         PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in     ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                               Page3 Tana zuwa unguwar su ta sauka, ta biya me napep kuɗi, ta shige gida kanta tsaye, seda ta shiga ma ta fara tunanin tijarar da zata sha yau, kwana biyar bata gida, dakewa tayi kanta tsaye ta shige, da sallama ta shiga abunta lokacin ana ta kiraye Kirayen sallar magariba, ta tarar ba kowa a tsakar gidan se Babarsu Sadiya tana iza wutar girki. Ta ɗago ta kalli Amira tace 'ke daga ina? Kwana biyar Amira Babu wanda yasan inda kike? Yanzu kinwa kanki adalci kenan?" Tsaki Amira tayi ta shige ɗakinsu, ta tarar da Sadiya da Amina suna salla, ta ajiye mayafinta taje tayo alwala ta tada salla, bayan ta idar tana lazimi tana jin yadda su Sadiya keyi da ita. Amina tace  "hmm lalacewa ta ƙaru, likkafa ta cigaba, su O'o yanzu har kwana ake a waje" Sadiya tace "kwanaki dai, yau kwananta nawa bata gidan nan, ni azo a gayawa Baba gaskiya a raba mana ɗaki da ita, baze yuwu ba, kar muje mu kwashi cuta wallahi" Banza Amira tayi musu, ta ƙarasa laziminta, tana tunanin abunda zata fuskanta idan Baba ya dawo. Tana cikin wannan tunanin ne akayi Sallama da Sadiya, saurayinta yazo ta tashi ta fita. Baba ne yai Sallama ya shigo shida Usman, sun dawo daga masallaci, suna shigowa Maman su Sadiya ta fara kora bayani. "Baba, se yau Allah yayi wannan mara albarkar ta dawo, kwana biyar cif bata gidan nan, Babu wanda yasan inda take kwata kwata, kaga alamu sun bayyana ƙarara tafi ƙarfin kowa yanzu, Babu alamar nadama a tare da ita balle asa ran tuba" Baba yace "ni nama rasa abun faɗa akan wannan yarinyar wallahi, har kunyar shiga cikin mutane nake, saboda abunda take aikatawa" Wata matar ce ta fito daga wani ɗaki tace  "Ai Malam dole a san abunyi, tun bata kwaso mana abun kunya ba, ko ta kwaso wata cutar taje ta gama mana a gida ba" Maman Sadiya tace "kokuma ta hana yaranmu auruwa ba, tunda gidansu ɗaya kar ace duk halinsu ɗaya" Saboda tsabar ƙarfin hali irin na Amira, bata nuna tasan da ita suke bama, ta fito abunta zata wuce gurin da ake girki. Tsawa Usman yai mata yace "Ke! Gidan ubanwa kika tafi tsawon wannan lokacin?" "Gidan Uban mutum" ta bashi amsa Amira ta bashi amsar cikin natsuwa. "Ni kike zagi?' yai maganar yana nunata da yatsa. "Kai ka ɗaine Mutum a gurin nan? Bana son kalen jaraba fa tom, ban kula kowa ba dan haka a sauraramin" Baba ne ya kawo wuya, yace  "ke wace irin yarinya ce mara albarka haka? Ke yanzu bakiji kunyar haɗa ido damu ba ma? Kin tafi gantali babu wanda yasan inda kike? Kwana biyar Amira ba wanda yasan inda kike?" "Wai Baba sekai ta min iƙrarin abun Kunya, haryanzu fa ba cikin shege ba ɗan dakan kuka ba ƙanjamau, ba wanda na ajiye balle aji daɗin nunawa, amma kun isheni, nifa wannan abun da kukemin ne yasa na bar gidan nan naje na sarara na dawo" Usman ya kai mata duka, yace  "Amina, maza jeki ki rufe min ƙofar gidan nan, yau sena tattaka wannan ƙaramar mara mutuncin, yadda in akace gobe ta kuma fita bazata fita ba" Be rufe baki ba, Amira ta dafe ƙeya tai waje, aikuwa Usman ya biyo ta, bata zame ko ina ba se inda Sadiya ke zance ita da saurayinta, tana ihu tana "na shiga uku, zasu kasheni, dan Allah yayanmu kasa baki" Ta tattake daddumar da suke kai, taje bayan saurayin ta tsaya tana cigaba da ihu, miƙewa saurayin Sadiya yayi yana faɗin lafiya kuwa? Usman ya ƙaraso yana "Wallahi yau zaki gane kurenki, tunda ke rashin mutunci shi kika saka a gaba, zaki yabawa aya zaƙinta" Cikin marairaicewa da karairaya, Amira ta cewa Saurayin Sadiya "Yaya dan Allah kasa baki, dukana zeyi dan Allah ka hanashi" Baba ne ya ƙaraso inda suke shima, wanda hakan yai daidai da shigowar Zailani, Zailani yana dubawa yaga Amira yaga su Usman a tsaye cirko cirko kamar zakaru. Yace "Wannan almirar uwar gantalin ta dawo kenan, shine daga zuwanta zata fara ɗagawa mutane hankali, tun daga waje ake jin ihunta, gidan ubanwa kika tafi?" Saurayin Sadiya yace "dan Allah kuyi haƙuri, macece kubita a hankali karku daketa, zaku iyayi mata illa kuyi haƙuri dan Allah" Usman yace "baka san halin wannan sheɗaniyar bane, shiyasa kake kareta" Sadiya kam gaba ɗaya takaici ya cikata, ta rasa mema zatayi ta huce, kawai tana zaune tana tsinkar furen soyayya, wannan mahaukaciyar ta watsa komai, kuma ta zubar Mata da mutunci a gaban saurayin. Amira kuwa kan saurayin ta kalla, ya sha uwar zanna bukar ɗinsa, kawai a ranata taga kansa ma ɗan dakon kara, ga dogon wuya kamar raƙumin dawa, ga yadin jikinsa duk ya tashi saboda tsufa, ji tayi kamar ta ƙyaƙyace da dariya, amma ta haɗiye dariyarta, saboda tasan a jazabar da take. Yace "koma me tayi ina nema mata afuwa dan Allah, ayi haƙuri a ƙyaleta" Suna can suna maganarsu tai cikin gidan, da sauri ta shige ɗakinsu ta banko ƙofar ta saka sakata. Suka koma cikin gida, suna tunanin meye mafita akan Amira, dan lamarin nata sam ba sauƙi kullum ƙara taɓarɓarwa lamarunta sukeyi. Amina taje zata shiga ɗakinsu, amma ta tarara Amira ta garƙame ƙofa da sakata, tai bugun duniya amma Amira taƙi buɗewa, tun tana bugawa harta koma magiya amma Amira tayi burus da ita. Zailani ne yace "wai bakyaji ne? Bazaki buɗe ƙofar ba?" Amira daga ciki tace "bazan buɗe ba, yau ni kaɗai zan kwana a ɗakin nan, kowacce ta tafi ɗakin uwarta ta kwana" Amina tace "Ai naga ba ubankine ya gina gidan ba, danme zaki kulle ƙofa wane irin wulaƙancine wannan, dalla malama ki buɗe mana ƙofa" "Bazan buɗe ba, kuma wallahi aka cigaba da takuramin a gidan nan, sena gangamo abunda duk zesa a haɗamu a kullemu" Zailani yace 'anya wannan yarinyar ƙwaƙwalwarta bata fara samun matsala ba kuwa?" Maman Amina tace "zunzurutun iya shege ne, ba wani taɓin ƙwaƙwalwa" Amina kam tasan tunda Amira ta furta baza su kwana a ɗakin ba tasan bazasu kwanan ba, ba yadda ba'ayi ba Amira tace bazata buɗe ba. Can Amina ta gama zancenta, ta dawo gida tana masifa  "Wallahi idan Amira ta kuma shiga sabgata, sedai ayi mutuwar kasako, koni ko ita wallahi, wanne wane irin rashin mutunci ne? Tazo har kan sallayar da nake zance tana kurma ihu, ta nemi ta tattake mana ƙafafuwa, sauran ƙiris ta take masa cinya, gaba ɗaya ta zubarmin da mutunci yau, ji nayi kamar ƙasa ta tsage in shige wallahi" Amira ta leƙo ta window tace "to maƙaryaciya, ɗuwawunsa na kusa takewa ba cinya, wani abu a tsomale kamar an jiƙa tsimma, zakizo ki ishi mutane yan yen yen, Wallahi in dai baza'a dena min cin kashi a gidan nan ba, kunya yanzu kuka fara jinta" Sadiya tace "to dan ubanki ke ina naki tsomalallen? Waye yake zuwa gurinki banda 'yan iska irinki?" "To ai da sauƙi, tunda dai ana zuwa ɗin, ina zaune zaki sha mamakin wanda ze Auri Amira, ƙasaitaccen mutum dan ni me tsadace" "A gidan ubanwa wani me tsada ze kwasheki? Kara da kiyashi, ya kwashi cuta?" Bata kulata ba, ta  jefowa Amina wayarta ta window tace "ke kuma ga wayarki nan, wannan matsiyacin saurayin naki Na'ibi yake ko liman ya ishi mutane da kira, be iya komai ba bashi da ko sisi se kiran wayar tsiya, ƙazami me yawo da silifas" Maman Sadiya ce da suke cewa Ummma tace "dan Allah ku ƙyaleta, idan ba hakaba a banza ranku ze cigaba da ɓaci, bazata canza hali ba" Sadiya tace "malama ni buɗe ƙofa zan canza kaya" Amina tace "tun wuri ki nemi nayi, dan tace bazata buɗe ƙofar nan ba" "Saboda me bazata buɗe ba" Tace "kowa sedai ta kwana a ɗakin uwarta, yau ita kaɗai zata kwana a ɗakin" "Saboda ɗakin na ubanta ne? Wallahi seta buɗe" Sadiya taje ta shiga jijjiga ƙofar, tana wani irin mahaukacin bugu, da gudu Baba ya fito daga ɗaki yace  "Au Halima, kema biye mata zakiyi kuyi? Shikenan maza biye mata ku taru ku haukatani, koku ɗoramin wani ciwon daze ajali na" Amira tace "ko ciwo be kamaka ba zaka mutu, dama gashi ka tsufa, ai da ka ƙyaleta, wallahi naso ta jijjige ƙofar ɗakin nan yau, dama ga damuna ta kusa, nikuma in jijjige tagar kowama ya huta, in damuna tazo kowa yaji jiki" Suna ji suna gani haka suka yiwa Amira Allah ya isa, suka tafi ɗayan ɗakin cikin ƙanensu, wanda harda masu fitsarin kwance a cikin yaran, haka suka shiga suka kwanta, dan Amira bazata taɓa buɗe ƙofar ba kome zasu yi, dan idan ta furta zatayi abu se tayi, sedai ai mata duk abunda aka ga dama. Sadiya tai ƙwafa tace "ai dai bazata dawwama a ɗakin ba, wallahi gobe in Allah ya kaimu sena mata dukan tsiya kona samu in huce, yau bala'in nata kusan a kaina ya sauka, gara mu daku a kece raini dan uwatta" Amina tace "kedai bari, wallahi ina da abubuwan yi da yawa a ɗakin nan, amma saboda hatsabibanci tai mana wannan iskancin, wallahi karki saurara mata ki mata shegen duka, zan tayaki , dan ni kaina yau na gama ƙulewa, tafa fasamin waya jefomin ɗin da tayi" "Kema seki fasa mata baki ki huce, naga gidan nan kamar tsoronta akeji, zamu koya mata hankali" Ɗakunan iyayensu duk da ƙannensu, ga kakarsu bata nan balle su kwana a ɗakinta, haka suka kwanta cikin yara, shimfiɗar banda zarnin fitsari ba abun take, ƙarshe a ƙasa suka kwana, Sadiya nata tsinewa Amira tana mata Allah ya isa. Da Asubar fari, Kafin kowa ya tashi, Amira ta tashi, taje tai alwala ta ɗau sallaya tai waje, ta bar gidan, ta koma soron kusa da ƙofar gida ta shimfiɗa tai zamanta, seda aka kira sallar Asuba taji alamar mutanen gidan sun fara tashi, ta zare sakata tai waje abunta da daddumarta kame me zuwa tuhajjud. Lunguna ta dinga bi tai nisa da gidan, ta samu guri tai sallar Asuba, sannan ta cigaba da bin lunguna ta tafiya hankalinta a kwance, tai tafiya me nisan gaske sannan ta samu masu Napep suka fara fitowa, ta tsare wani ta kwatanta inda ze kaita. Gidan Anty Fa'iza ne, safiya ce sosai lokacin da taje, ta ƙwanƙwasa ƙofa Ta ɗan daɗe tana ƙwanƙwasawa kafin a buɗe. "Anty Amira kece?" Cewar Bashir daya buɗe ƙofar. "Eh nice Abban Khairat" Ya bata hanya ta shige, Fa'iza dale tsakar gida ta kalli Amira ƙafafunta duk sunyi ƙura, ga sallayarta a hannu "Lafiya kuwa Amira?" "Lafiya lau" ta bata amsa *Amma na ganki da sassafen nan"? "To ba dole ki ganni da sassafen nan ba, ana shirin yadda za'a naɗamin duka yau a gidanmu, shiyasa tun Asuba na gudo, dan bazasu dakeni ba kamsr jaka" Bashir yace  "Shiyasa tuntuni nace ki dawo gidan nan mu zauna, ki bar musu can ɗin amma kika ƙi, banda abunsu meyasa zasu ce zasu dakeki?" "Abban Khairat, baka san ita me ta aikata ba, wani lokacin harda halinta itama, ban gayamaka abunda tayimin jiya ba a gurin biki da mukaje ba, daga inda ta gama tiƙar rawarta daga nan ta gudu gida, ban sake ganinta ba se yanzu da taje ta kunno wata wutar a gidan" Zumɓura baki Amira tayi, ta shige ɗaya ɗakin tai kwanciyarta. Fa'iza zatayi magana, Bashir ya girgiza mata kai, tare da yi mata alamar tayi shiru, tayi haƙuri. Ya jata zuwa ɗakinsu. Gidansu Amira kuwa se gani sukayi ƙofar ɗakinsu Amira a buɗe ta kama gabanta, Baba yace "wannan yarinyar yaushe ta bar gidan nan?" Umma tace 'waya san mata?" "Kenan cikin dare ta fice, kokuwa ya akayi?" "To waye ya sani?" Suka cigaba da salallami, da jinjina rashin jin Amira. Baba yace  "ni mamakina ko ina ta tafi, a wannan cikin daren oho?" Umma tace 'ina kuwa zata banda yawon iskancinta data saba?" Haka Baba ya fita Masallaci yana tunanin ta ina ze ɓullowa lamarin nan. Amira kam bata farka ba se shaɗaya na rana, hankali kwance ta sha baccinta, ta farka taje ta haɗa Abincinta ta karya, ba tare da ta gayawa Fa'iza laifin da tayi za'a zanetan ba a gida. Sadiya tana wankin kayanta tace  "Allah ya temaki wannan jakar bata kwana a gida ba, wallahi da ta kwana a gida da yau na saɓa mata kamanni" Amina tace "ina zata kwana a gidan, tunda tasan abunda ta aikata, ta kwana a waje wajen iskancinta" Sadiya tace "aikuwa da, dan masifa tsakar gida ta bar gidan nan saboda wulaƙanci" Wata dattijuwace tai Sallama hannunta ɗauke da kaya, suka amsa gaba ɗaya suna "Yadikko sannu da zuwa, Yau Allah yayi an dawo kenan"? Tace "eh fa, na sha ƙauye sati Uku kenan" Suka karɓi kayan hannunta, ta ciro kuba a jakarta ta buɗe ɗakinta, Umma ce ta fito daga ɗakinta tana "Sannu da zuwa Yadikko, ya hanya?" "Alhamdilillah duk suna a gaisheku" "Muna amsawa, amma da sassafe kika taho? Naga kin ƙarado da wuri?". Yadikko tace "ai ana idar da sallar Asubahi, gari ya fara haske nace a kaini tasha in hau Mota, ina magajine d ban ganshi ba?" Sadiya tace "Baba yanzun nan ya fita, amma ze dawo" Nan suka shiga hira tana basu labarin hanya, Babane yai Sallama suka amsa gaba ɗaya yana ganin ƙofar ɗakin Yadikko a buɗe ya ƙarasa ɗakin yana "Yadikko, ashe kin dawo?" "Eh magaji na dawo" Ya shiga ɗakin yana "Sannu da zuwa, ya kika barosu?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, waini ina wannan Amira ne? Ban ganta ba tunda na dawo, na saba ana shigowa gidan nan da hayaniyarta ake fara cin karo, amma naji shiru tazo ta sharemin ɗakik nan dan yayi ƙura" Umma tace "taɓɗijan wace Amiran? Ai Yadikko se fatan Allah ya shirya, dan jiya kwananta biyar bata gidan nan ba wanda yasan inda take" Zare ido Yadikko tayi tace "ban gane kwana biyar ba, ina ta tafi?" Baba yace "gantalinta na banza ne, abun ya ƙaru fiye da kima, dan na kira Baffa yazo ya mata faɗa ta shura takalmanta, ta gudu se data kwan biyar bata nan, se jiya ta dawo jiyanma, daga dawowarta ta shiga neman magana, tsakar dare ta buɗe ƙofa ta bar gidan nan, ba wanda yasan inda take, a gaskiya ni Yadikko na gaji da halin wannan yarinyar, an daka an daka amma ba canji, an zaga anyi barazanar amma kullum sake lalacewa take, yanzu har kunyar fiya nake cikin mutane, saboda nunani ake" Umma tace "bama wannan ba, kar muje ta kwaso mana cuta ta gama mana ita a gidan nan" Yadkko tace  "lallai, Amadu ya mutu ya bar mana jaraba, kace iskancin nata gaba yake ƙarayi, to baze yuwu ba, tun kan ta ƙarsa fanɗarewa ta ɗakko mana abun magana gara asan abunyi" Umma tace "to Yadikko meye abunyin da za'ayi?" "Ni nasan abunyin, ke Sadiya koke ko Amina, ingo wayar nan lalubomin lambar wan uwarta, shima yasan abunyi tun wuri, in yakama ya ɗauketa shi ya riƙeta, ai yafimu arziki" Amina ta karɓi wayar tace  "da wani suna akayi saving lambar?" Yadikko "inaga kamar Ali ne, Alin Kaduna haka zakiga sunan" Baba yace  "Nikam Gwaggo kinga wannan tunanin sam be zomin ba" "Aini gashi yazomin, tun wuri yazo asan yadda za'ayi da ita kowa ya huta" Aka lalubo lambar aka miƙamata. ******************** Kamar a mafarki yaji wayarsa tana ringing, ya buɗe idanunsa ya janyo wayar, seda yayi murmushi sannan ya ɗaga ya kara a kunnensa, amma yai shiru yana sauke numfashi. Cikin muryarta me daɗin sauraro a kunnuwan Imran kamar me raɗa tace  "My Own" "Mmmm" ya amsa ba tare da ya kuma cewa komai ba. "My own" ta kuma maimaitawa. "My heart" ya amsa. "Yawwa, dama so nake naji ka amsa, bacci kake ne?" "Bacci nake Baby, wayarki ce ta tasheni" "My own ɗan hutu, bacci da ranar nan, ina fatan kayi salla?" "Chance na samu, dole inyi bacci idan na koma bakin aiki bana samun hutu sosai, shiyasa nakeyi yanzu kan in koma" "Hakane, Amma ya sallar kayi kuwa, kasan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace salla ginshiƙin Addini ce, wanda ya tsaida ita ya tsaida Addini, wanda ya barta ya bar Addini" Imran yace  "Allahu Akbar, Sayyadata shiyasa nake matuƙar ƙaunarki, nayi salla My Ihsan kwanciyata kenan, bacci ya ɗaukeni kika kirani" Ihsan tayi ajiyar zuciya tace "bari in ƙyaleka, kwanta kayi baccinka kaji abun sona" "No, aini jin muryar nan taki ta isheni, ta fiyemin baccin nan da zanyi, ni ji nake da ma kina kusa dani, ki min tausa, jikina ciwo ya ke" "Mhmm I hope kaci Abinci?" "Ba kya son zancen kenan? My Ihsan Allah dai ya nuna min ranarvda zaki zama tawa, inyi maganin wannan kunyar taki" Tace "bafa ka bani amsa ba, kaci Abinci?" "Wallahi Ihsan banci ba" Cikin shagwaɓa tace  "wato wahalar mim da kanka kake, se ulcer ta kama ka? To nayi fushi" Ransa a ɗan ɓace ya murɗa ƙofar ɗakim dake cikin falon ya fito, tana zaune tana rubuce rubuce ta ɗago kanta ta kalleshi tace "Abba lafiya kuwa?" Ɗan girgiza kai yayi yace "lafiya amma ba lau ba, aika Minal ta kiramin yayanta yanzun nan" "Amma lafiya kuwa Abba? Meke faruwa ne?" "Saka a kiramin shi dai" Minal ta tashi ta tafi ɗakin Imran, taje ta tarar da shi a kwance a akan gadonsa yana waya, yana kallon Minal, Amma be kulata ba ya cigaba da wayarsa "Babyna karki fushi dani mana, baccine ya hanani cin Abinci, haba my" yai maganar cikin shagwaɓa kamar ƙaramin yaro. Minal mamakine ya kamata, yadda yake waya Amma su idan yana musu magana kamar wani dodo, se da ya kammala wayarsa, sannan yace  "ke meye haka kikazo ki ka sani a gaba kina kallona?" "Dama Abba ne yace yana son ganinka, yanzun nan a falo" Imran yace 'naji jeki ki bani guri" Minal ta juya ta na mamakin yayan nata. Minal na shiga falon ba daɗewa, sega Imran ya shiga da sallama ya samu Guri ya zauna, kusa da Abba a kan carfet yace "Abba gani" Abba ya kalleshi yace "Imran kasan meyasa na kira ka?" "A'a Abba" "Ina zaune a ɗaki, aka kirani a waya akace min wai ƙanwarka rashin ji take yi" Mummy cikin Rashin fahimta tace "wai wace ƙanwar tasa?" "Yarinyar nan Amira, ɗazu kakarta ta kirani, wai rashin ji take musu, se ta bar gida tafi sati bata gida, abun ya ɗagamin hankali matuƙa, da kaina naso inje gobe in Allah ya kaimu, amma ina da tafiya ta gaggawa gobe in Allah ya kaimu, ina son ka wakilceni kaje ka jiyomin meke faruwa ne?" Mummy tace  "Abba, wai ina yarinyar nan tana hannun dangin uban ta? Ai sune a haƙƙu su kula da ita, amma wani labarin za'aje a jiyo maka kuma?" "Yarinyar nan nima 'yata ce, dole hankalina ya tashi, gaba ɗaya na shiga damuwa, Amira 'yata ce gatse gatse kakarta ta gayamin wai yanzu karuwanci take, kuma harta bar gida tayi kwanaki ba a san inda take ba" Imran ya ɗago da sauri ya kalli Abbansa yace  "Wai Abba wannan'yar yarinyar ce take karuwanci? Wannan yarinyar 'yar mitsitsiya?" "To Gashi nan dai, haka akace min, wai duk ta gagaresu bata jin maganar Kowa, yawonta takeyi" Imran ya jinjina kai yace  "Shikenan Abba, zanje goben in Allah Ya kaimu, inga meke faruwa" Abba yace "yawwa Imran, Allah yayi maka albarka" Me kuke tunanin ze faru, idan Imran yaje gidansu Amira, za'a magamce matsalar ko kuma zata masa halin. (Idan ba'a comment akwai gaɓar da zanje in ajiye in dena rubutawa tabbas🙄🙄🙄 kokuma me so sedai yabi watpad) Domin gyara, Sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 [1/4, 9:26 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                 4 Imran ya miƙe ya koma ɗakinsa yana sake tunanin Amira, duk da anyi shekaru rabon daya ganta, amma yasan ba babba bace ba yarinya ce ƙarama, amma ace wai harta san ta fara yawon banza, ta bar gida taje tayi kwanaki a wani guri, lallai zamanin nan ya zama se Addu'a kawai. Amira ta na kwance akan doguwar kujera tana game a wayarta, Sultan ya kirata a waya. Seda ta ɗanyi tsaki sannan ta ɗaga tace "kiran me kake min haka?" Yace "na turo miki kuɗinki, Amma kinƙi zuwa ki karɓi wayarki, kuma satin nan muna da aiki fa, akwai bukukuwa hadda dinner" "Tom naji, se kuma me?" "Ko zaki zo ki bada training ne? Ina son a baje basira sosai, ga wanda ya baki wayar nan yana ta min tuni, yana nanata min zuwa Abujan nan gurin bikinsa fa" "Kai ka rabu dani da wannan Abujan" "Amira meyasa?" "Ina tsoron inje wani abu ya sameni a hanya fa" "Insha Allah babu abunda ze sameki Amira, dan Allah ki yadda muje, zamu samo kuɗi sosai fa" "Gaskiya zuwan nan nawa Abuja ƙila wa ƙala ne, babu tabbas sedai insha Allah gobe in Allah ya kaimu zan shigo, zan bada training" Sultan yace "Dan Allah Amira kiyi tunanin, ina jiranki". Tace "abunda na yanke zakaji, karka damu" Sukayi Sallama ta ajiye wayar, Fa'iza ta kalleta tace "Amira, wai har yanzu baki bar maganar zuwa Abujan nan ba? So kike ki ƙarawa kanki abun faɗa ko?" Amira tace "An daɗe ba'a faɗa ba, ko naje ko banje ba baza'a fasa faɗa ba, dan haka ni be dameni ba" "Amira ba yanzu nake jiye miki ba, gaba akeji musamman idan Allah ya baki miji, ko bayan kin haihu a dinga faɗin abunda kikayi" "To waini kinji nace miki zani ne, bafa zuwa zanyi ba" "Gaskiya ce  dai, ko ba kyaso dole in gaya miki ita" Amira ta miƙe tace "Ni tafiya ma zanyi" "Allah ya kiyaye hanya" Fa'iza ta bata amsa Khairat tace "Anty Amira dan Allah ki zauna karki tafi" Amira tace "Sorry daughter na, ai zan dawo insha Allah, ina son nima naje gidanmu ne, amma ina dawowa" "To ki dawo da wuri" "To Shikenan, Insha Allah zan dawo da wuri, ki gaishemin da Abbanku" Fa'iza bata kulasu ba, Amira ta fice ta kama hanyar gidansu. Da sallama ta shiga Kamar yadda ta saba, sedai duk da akwai mutane a tsakar gidan babu wanda ya amsa mata, itama bata damu ba ta wuce ɗakinsu, ta cire hijjabin jikinta ta fito tsakar gida, da niyyar yin alwala sakamakon kiraye kirayen sallar magariba da akeyi, Yadikko ce ta fito daga banɗaki, tana ganin Amira tace  "Ke Daga ina haka?" Amira tace "ni yakamata in tambayeki saukar yaushe?" "Ban sani ba, ina tambayar ki kina tambaya ta" "Daga waje mana, naje wani gurine" Amira ta bata amsa. "Wato ke abun naki cigaba yayi, har ki bar gida sati guda ba wanda yasan inda kike ko? Wallahi Amira iskanci ba abunyi bane" "Yadikko, tun a baya Yakamata a gayamin haka, ba a yanzu ba da nai nisa, Iskanci yana kaimin yana min rana, dan haka bame zuwa rana tsaka yace in dena in hanu" Yadikko tace "Hakama zaki ce? Baki da ta ido ko Amira? Kike faɗin Iskanci ya miki rana" "To da dare yaimin, ai rana yayi min, ina zaune waze dinga bani kuɗi, Iskanci ma sana'a ne na kasa na samu, dan haka yamin rana". Tana gama maganar taja butarta tai banɗaki, bayan tayi alwala taje ta tada salla. Amina tace "aikin banza, dama dena wannan sallar kikayi, dan ba karɓuwa take ba, kije ki gama bin maza a waje kiyi saɓo san ranki, dan munafunci kuma kizo ki tada salla ƙaryar banza kawai" Amira tai mata shiru, ta cigaba da sallarta, ta idar tayi adddu'ointa ta koma gefe ta kama wayarta, ba tare da ta sake tankawa kowa ba. Shikam Imran gaba ɗaya abun duniya ya tsaye masa, daya tuna Wai Amira ke karuwanci, meta sani a sha'anin rayuwa, yaushe ta san ciwon kanta da har zata kai jikinta ga maza, a biyata kuɗi har ta fita tayi sati bata gida dan abun takaici. Yana cikin tunanin ne Ihsan ta kira shi, yasa hannu ya ɗaga wayar, ya saka a kunnensa tare da yin Sallama. Ta amsa masa sannan tace "My kana Lafiya?" "Lafiya ƙalau my heart, ya kike ya mutan gidan?" "Lafiya ƙalau, But it seems like something is wrong with you?". "No, Babu wata damuwa dama zanje kano n gobe in Allah ya kaimu" "My me zakayi a kano kuma?" "Eh Abba ne ya aikeni, zanje ganin wata cousin sister ɗina ne" A sanyaye Ihsan tace "cousin sister kuma My? Na zaci cousins ɗinka duk mazane? Baka taɓa gayamin kana da cousin ba mace ba" Imran yace "ta ɓangaren Abba ina da cousin mace, mazan da kika sani duk na ɓangaren Ammi ne" "Amma ba zaka daɗe ba ko?". "Ihsan, yarinya ce fa ƙarama, Abba ne yace inje in duba masa ita, kuma dan yana da inda zashi ne goben in Allah ya kaimu,  da da kansa zeje ya ganta, ki kwanatar da hankalinki Yarinya ce ƙarama sosai, dan nasan kishi ne yake damunki" Ihsan tai nannauyar ajiyar zuciya tace "My own, tabbas kishine ke damuna, ina sonka sosai shiyasa nake kishinka, Allah karya kawo lokacin da zan buɗe ido in ganka da wata, bazan iya jurewa ba My" Ta ƙarasa maganar a raunane, kamar za tayi kuka. "Ihsan meye abun ɗaga hankali kuma? Imran naki ne ke kaɗai, kin san halina bana kule kule, musamman idan kikayi duba da yadda soyayyarmu ta fara, kuma na gayamiki yarinyar ƙanwata ce, yarinyace sosai, wata matsala ce ta taso Abba yace inje in duba masa ita, amma ni nafi ƙarfin shekaru biyar rabona da ita" "Shikenan my Own, i trust you, na yadda da dukkanin maganganun ka, amma yaushe zaka dawo?". "Da wuri zanje in dawo, yaushe zanje in kwana a garin mutane, da wuri zanje in dawo Insha Allah" "Allah ya kaika lafiya, ya dawomin da kai lafiya my own, Amma zakazo muyi sallama ko?" "Ai da sassafe zan tafi Ihsan, bana zo muku gida da sassafe ba" "Ni dai kazo dan Allah My" "Ƙarfe bakwai fa zanzo" "Eh dan Allah kazo ni dai" "Shikenan, Insha Allah zanzo kan in tafi ɗin" "Allah ya kawomin kai lafiya, ya tsaremin kai, ya yafe maka kura kuranka, Allah ya sada ka da dukkanin Alkhairin duniya dana ƙiyama" "Ameen ya Allah abar ƙaunata, shiyasa nake matuƙar ƙaunarki nake alfahari dake, Allah yayi miki albarka matar Imran" "Ameen my love, i love You" "Love You too babyna" ya ƙarasa maganar tare da yi mata kiss ta waya. Ihsan ta sauke wayar a hankali ta ɗorata a kan ƙirjinta, ta lumshe idonta tana jin yadda ƙaunar Imran ke ratsa lungu da saƙo na zuciyarta, ta lumshe idanunta tare da tunani kala kala, ji take tamkar ta janyo lokacin auren nan, saura befi watanni biyu ba ya rage, amma tana jin tamkar saura shekaru biyu ne, dan gani take kamar ba zasu zo ba. "Ihsan! Ihsan! Ta ji muryar Mummynta, "Na'am  Mummy gani nan" "Na kiraki ya kai sau biyar, amma baki amsa ba" Ihsan ta tashi zaune tace "yi haƙuri Mummy, waya nake ne banji ba" "Sarkin waya, ke ko gajiya bakyayi, Allah dai ya kaimu ayi bikin nan kowama ya huta" Ihsan tai murmushi ba tare da tace komai ba. Mummy ta zauna a kusa da Ihsan tace "Ina fatan kin sha maganin nan?" Ɗan tura baki Ihsan tayi tace "mhmm ni gaski Mummy.... "Ke gaskiya me?" "Maganin ne ba daɗi, kuma fa ɓatan ciki yake" Mummy tace "to dama ana shan magani ne dan daɗi? Haka zakije gidan Auren ba gyara?" Tura baki Ihsan tayi tace  "Mummy ai ina sha" "Inma ba kya sha kyaji dashi, Hajiya Ramatu tana Dubai, ta turomin samfiran lesussuka, tace ki zaɓi wanda za'a kawo miki na dinner" Ihsan tace "Mummy ni duk wanda aka kawo shikenan" "A'a zan turomiki ta what's app ki zaɓa, bazan zaɓa miki ba kice beyi ba' "Shikenan Mummy, in kin turomin Zan zaɓa din" ******************** Amina na tsaka da baccinta, tan enjoying baccin sosai kasancewar dare yayi sosai, tana cikin abun rufarta, tana ta kwasar bacci. Ji tayi kamar an jefata a kogi, sakamakon jin ta tsundum a cikin ruwa me tsananin sanyi, cikin razani da tashin hankali tai firgigit ta tashi tana kurma ihu. Amira ta gani a tsaye a kanta da bokiti. "Me nayi miki zaki jiƙani da ruwa haka? Wane irin wulaƙancine haka?" Amira tace 'na miki hakane dan in tasheki in ja miki kunne, ɗazu da magariba ina salla ina jin kina wai ina gama yawon iskancina, sannan inzo ina salla, naso na baki amsa a ɗazun, sedai nace bari in bari se cikin dare daga ni seke in baki amsa, shiyasa na tasheki, idan ubanki Baba Lawan, shike karɓar salla idan nayi, dan Allah ki tashi Yanzu ki wanke ƙafa, kije ki ƙwanƙwasa masa ƙofa kice masa, daga yau idan na kuma salla karya karɓa, shine zaki tabbatar min da kin isa. Idan kuma bashi yake karɓa ba, daga yau kika kuma shiga sabgata, duk abunda na miki ke kika siya, ki fita hanyata tun wuri, idan ba haka ba wallahi duk wanda ya taɓani sena ɓata masa rai" "Amma Amira yakamata ki zubamin wannan uban ruwan a daren nan ina bacci?" "Ni ba ruwana daya kamata kobe kamata ba, ke kin duba yakamatan ne kika gayamin abunda kika gayamin ɗazu, daga yanzu seki dinga yiwa bakinki linzami akan Amira" Amina ta kalli yadda ruwa har gudu yake a tsakar ɗakin, ta jiƙe katifar nan sharkaf da ruwa, Sadiya ce tayi juyi ta jita camɓal a ruwa, a razane ta miƙe zaune ta zaci fitsarin kwance tayi, taga fitila a kunne, ga Amina a zaune Amira tsaye a kansu, taga ruwa yana gudu a tsakar ɗakin. "Lafiya meye haka?" Amina cikin tsananin takaici tace  "Jiƙamu tayi da ruwa" Sadiya tace "akan me?" Amina ta rasa amsar da zata sake bawa Sadiya. Sadiya tace "yanzu meye ribar abunda kikayi mana? Kawai ki tayar mana da hankali ki hanamu bacci" "Idan har bazaku dena shiga sabgata ba, nima bazan fasa ɗaga muku hankali ba" Ta juya ta fita da bokitin, haka suka tashi suka fita da katifar waje, tana ɗigar da ruwa. Amira ta samu guri tai zamanta akan bokiti, a tsakar gida kamar aljana, tana jiran su gama gyara ɗakin taje ta kwanta. Baƙin ciki ya ishi Sadiya, suka gama gyara ɗakin, suka tsane ruwan duk da ya jiƙa ɗakin, Sadiya ta ciko bokiti da ruwa itama ta wankewa Amira jikinta da ruwa nan a tsohon daren nan. Amira ta gigice saboda yadda taji zubar ruwan sanyin ba zato ba tsammani, ta miƙe a gigice, tana ɗigar da ruwa ta kalli Sadiya ta kalli jikinta, ta jiya ta kandamo ruwa ta dinga antaywa a cikin ɗakinsu. Nan da nan rigima ta kacame a wannan uban daren, faɗa da bokitai, da ɓarnar ruwa, Zailani ne ya fara shigowa cikin gidan, ya tarar dasu suna ta faɗa, suna neman suyiwa Amira taron dangi, amma se buga musu bokiti take sun kasa taɓata, ga shi sunyi kaca kaca da ruwa a gidan. Tuni su Yadikko ma suka fito tsakar gida, suka tarar da wannan aika aika a cikin wannan uban daren. Yadikko tace "masifar yarinyar nan ta isheni, nagaji wallahi wace irin yarinyace ke haka mara hankali?" Kowa Amira yake bawa laifi, banza tayi musu ta shiga ta canza kaya, ta wuce ɗakin Yadikko. "Ke dan ubanki fitomin daga ɗaki, ba zaki je nima ki ɗagamin hankali ba, fito ƙaramar sheɗaniya, masifarki bata tashi se cikin dare kowa na bacci" Baba yace "Yadikko dan Allah ki ƙyaleta, wannan yarinyar se an dangana da malaman ruƙiya, dan wannan aikin tabbas akwai hannun sheɗanu a ciki" A taƙaice dai yauma ba wanda yayi baccin kirki a gidan, saboda halin Amira na rashin kirki. Gari na wayewa ta canza kayanta ta fice, ta bar gidan gaba ɗaya. Da safe Imran ya tashi ya shirya tsaf, cikin ƙana nan kaya, ya tafi falon Ammi, ya durƙusa ya gaisheta ta amsa masa sama sama Sannan tace "har zaka tafin ne?" "Eh Ammi, zanje ina son in dawo da wuri ne" 'shikenan, kome ze faru ban yadda a haɗa kai da kai a kawomin wannan yarinyar gidan nan ace in riƙe ba, taje can dangin ubanta su riƙeta, aisu Yakamata su riƙeta ba wani ba, dan haka ka kula" "To Ammi insha Allah, ki cewa Abba na tafi idan ya tashi" "Shikenan, Allah ya kiyaye hanya" "Ameen, Ammi Nagode" Ya tashi ya fita, a ƙofar gidan su Ihsan yai parking, ya kirata a waya da sauri ta ɗaga wayar tace "my own ka tashi?" "Gani a ƙofar gidanku, leƙo muyi sallama zan wuce kano" Ihsan tace "da wuri haka? To gani nan zuwa" Yana nan tsaye sega Ihsan ta fito, ta sanya zumbulelen hijjabi tun daga sama har ƙasa, ta ƙaraso inda yake tsaye tace "good morning" "Morning Beb, how are you?" "Fine Alhamdilillah, kayi kyau sosai" Yai murmushi yace "Nagode sosai, kim damu inzo muyi sallama kafin in tafi, shine na biyo gani nazo, ina fatan shikenan" 'hmm kusan shikenan, But am so much jealous, bana son kaje wata ta kallarmin kai, wannan kyan da kayi kamar ka zauna inta kallonka nikaɗai" Yai murmushi yace "Ihsan kishinki yayi yawa a kaina" "Kenan yin hakan laifine?" "Ni na isa ince laifine, nasan ƙaunace tasa kike kishina, amma ki sha kuruminki, ni nakine har abada Ihsan, kuma na gayamiki yarinya ce ƙarama ba babba ba, ki kwantar da hankalinki kinji my wife" "Shikenan na kwantar, tunda naji tabbaci daga bakinka Mijina, Allah ya tsaremin kai ya kiyaye hanya, ga wannan ka dinga taɓawa a hanya" Ta ƙarasa maganar tana miƙo masa leda, yasa hannu ya karɓa ya kalleta yace "Nagode sosai My Wife, take a very good care of yourself kinji Babyna" "Insha Allah, sannan da naso muyi Maganar kayan da zamu saka na dinner, Amma kaje kawai mayi magana ta chat" "Shikenan, bari inje sena dawo" "Allah ya tsaremin kai habibina" "Ameen" Ya shiga motar ya kunna, tana ɗaga masa hannu, yaja motar ya tafi, seda ya bar harabar gurin Sannan ta juya ta koma gida. Amira kam da sassafiyar nan, restaurant ta tafi taje taci Abincin ta ta ƙoshi, wajen ƙarfe goma na Safiya, ta tafi office ɗin su Sultan. Suna ganinta suka fara shewa, suna mata barka da zuwa, cikin sakin fuska ta amsa musu, ta ƙarasa ciki Sultan ya saki fuskarsa yace "Sannu da zuwa gimbiya" "Yawwa Sannu, nazo ka bani wayata da kace an bani" Sultan yace "Gimbiya ikon Allah, ke tunda muka rabu a gurin bikin nan baki sake zuwa office ba se Yau" "Kai dai bari kawai, ɗakkon wayar in gani" Ya tashi yasa mukulli ya buɗe wata drower, ya ɗakko wayar a kwali ya miƙa mata. Tasa hannu ta karɓa, ta buɗeta tace "Wow, yanzu Sultan wannan tawace?" "Ƙwarai kuwa taki ce, wanda ya baki itane kuma ya gayyacemu bikinsa, kin san kuwa idan mukaje bikin nan abunda zamu samo da yawa" Ɗan shiru tayi tace "gaskiya zuwana Abujan nan babu tabbas, kamar yadda na gaya maka, sedai idan na canza shawara zakaji" "Dan Allah Amira kiyi wani abu da gaggawa, wallahi zamu samo kuɗi sosai, kuma tamkar sake tallata kanmu ne, tunda manyan mutane ne zasu je gurin bikin" "Kai ƙyaleni, se yadda ta yuwu kawai, Yanzu haka ina da gurin zuwa ne" Sultan yace "haba dai, bayan munyi dake yau akwai training, satin nan fa muna da biki" "Ka basu training ɗin bakomai fa, akwai inda nake gaggawar zuwane, kasan ni dai baka da Matsala dani" "Amma Amira" Ai bata jira ba taja jakarta tai waje, dan karma ya lallaɓata yace seta tsaya. Gurin Saloon taje, aka gyara mata kai, akayi mata kitson attachment ƙanana,  se azahar Sannan ta bar gurin, taje ta kuma siyan Abinci, ta cika cikinta sannan ta wuce gida. Imran kuwa tuni ya sauka a garin kanon dabo, seda ya sake kiran Abba a waya yayi masa kwatancen gidansu Amira, sun masa kyakkyawar karɓa, sedai ya tarar Amira bata nan, nan suka saka Imran a gaba, suka dinga gaya masa abunda akayi da wanda ba'ayi ba akan Amira, sedai Sadiya se wasu abubuwa take dan ta ɗau hankalin Imran, amma yaƙi kallonta. Baba yace "gantali iri iri ba wanda yarinyar nan bata yi, ga tara maza banda raye raye, da tashin hankali da take janyo mana a unguwar nan, banda idan iskancinta ya tashi ta hana mutanen gidan nan bacci da takeyi" Imran yai shiru, gaba ɗaya abun ya ɗaure masa kai, yace "yanzu ina Amiran take?" Yadikko tace  "ai tunda tai tijararta ta cikin dare, tun duku duku tasa ƙafa ta bar gidan nan, ba wanda tayi wa sallama" Imran yace "Amma ya kai aka bari har abun nata yai nisa haka ba'a sanarwa Abba ba? Kuma naga ga manyan maza samari a gidan nan, suma ta gagresu kenan?" Baba yace "mun zaci abun nata zamu iya shawo kansa da wuri, amma abu ya gagara, duka, zagi kurari ko faɗa baya tasiri a kanta, ko jinjirar jaka na ta ganta akan taurin kai da rashin ji" Sadiya tace "wallahi Yaya baka san halinta ba, jiya bakaga yadda ta jiƙamu da ruwa ba cikin dare, ta hanamu Bacci wulaƙanci kala kala ba wanda bata mana, zagi dagamu har iyayenmu bamu tsira ba" Imran yai shiru yace "ku bani lambar wayarta" Amina tace "ai babu wanda yake da lambar wayarta a gidan nan, si bamu kai ta bamu lambarta ba" Abun ya ɗaurewa Imran kai sosai, abun nasu kuma harda sakaci, Amma ya za'ati ace yarinya ɗaya tal ta gagaresu?ya sha mamakin abunda aka gaya masa akan Amiran. Yana nan zaune Baffa Salahu ma ya shigo, shima yana tarar Da Imran ya zauna yana sake kora masa abubuwan da Amiran takeyi. Kamar daga sama sukaji Sallamar Amira, Amina dake tsakar gida ta amsa tana dariyar mugunta, Amira ko a jikinta, tana ta tauna cingam. Yadikko tace "kaji ta can ta dawo, tun farar Safiya da ta fita se yanzu Allah yayi mata dawowa" Imran yace akira masa ita, Sadiya ta tashi jiki na ɓari ta fito tsakar gida tace "Ke Amira kizo ana kiranki" Amira tace "wace ke ɗin taki? Karki sake ki kuma kirana da ke, kin san bana son raini" "To ai cewa akayi in kiraki" "Kuma wanda yace ki karani yace kice min ke? Waye yake kiran nawa?" "Kije ɗakin Yadikko ki gani" Ta kalli ƙofar ɗakin taga takalma, ta kalli Sadiya tace "wannan uban takalman fa? Me aka ƙulla in shiga a cinyeni, wai tukuna ma wannan ƙaton takalmin me kyan nan na waye? Dan nasan gidan nan babu me arzikin wannan takalmin" Sadiya tace "Yaya Imran ne fa yazo" "Waye kuma Yaya Imran? Ke dalla ke kika sanshi, bazani ba" Ta shige ɗakinsu abunta, Imran yana jinsu duk yadda suka yi da Sadiya, ya fito daga ɗakin Yadikko ya kalli Sadiya yace "tana ina?" Sadiya ta nuna masa ɗakinsu, yasa kai ya shiga, yana shiga ya tarar da Amira a tsaye sanye da doguwar rigar material, wadda ta kama jikinta sosai, kamar idan tayi kyakkyawan numfashi rigar zata buɗe, ga attachment ta saki har ɗuwawunta, yayi matuƙar mamakin ganin yadda Amiran ta girma haka, tai tsawo tayi fresh kamar ba ita ba, fuskarta ba kwalliya amma tsaf da ita se tauna cingam take. Ɗagowa tayi tai tozali da Imran, take gabanta ya faɗi, dan ita ta manta dashi gaba daya a rayuwarta, tsayawa yayi suna kallon kallo da shi. "Zauna magana zamuyi" Imaran yai maganar yana kallonta. Ta samu Guri ta zauna ta harare harare, ya kalleta yace "daga ina kike?" Ta sunkunyar da kanta tace "daga sana'a" "Wace irin sana'a?" Amira tace "ta neman kuɗi" "Ai sunan sana'ar nake son ji" "Sana'a nake da jikina, ina neman kuɗi" ta bashi amsa. Mamakine ya cika Imran, ba kunya ba tsoro ta bashi wannan amsar. "Ke bakiji kunyar abunda kika faɗa ba?" Zumɓura baki tayi tace "ai ba sata nayi ba, da zanji Kunyar faɗa" "Meye dalilinki na fita a haka? Da wannan shigar" "Nifa gaskiya ka dameni da tambayoyi, na gaya maka a saye na rufa, amma se wani sake tambayata kake, to karuwanci nake kamar yadda kake sonji, ko aka gaya maka kafin in dawo" Wani ranƙwashi da Imran ya sakar mata a tsakiyar kanta ne yasa ta kurma ihu a gigice. Imran yace "Ke bakiji kunya ba kike cewa karuwanci kike? Banza mara kamun kai, harkije waje ki dinga kwana saboda baki san darajar kanki ba kamar Saniya?" "Ya za'ayi in san darajar kaina, bayan tun tasowata ba'a nunamin ni me daraja bace" tai maganar tana kuka, saboda seda fitsari ya cika mata mararata saboda azabar zafin ranƙwashin da yayi Mata. "Wace irin magana kikeyi haka? Baki san Akuyace take bada jikinta ga kowane banza ba, ke Akuyace ko karya da kike tallar jikinki, dan maza du biyoki su biya buƙatar su su baki kuɗi, kamar motar haya" Amira taji zafin maganganun sa amma tace  "Ai nima ba kowa nake bawa jikin nawa ba, dan haka niba Akuya bace, ka iya bakinka karka sake kirana da Akuya, karuwancina me lasisi nakeyi, kuma baka da bakin magana akan abunda nakeyi" Tana rufe baki zuciya ta tinziro Imran Yasa ƙafa yai Ball da Amira, abunka da soja duk girmanta, seda ta gara har kanta ya bugu da ƙafar keke, Amira ta sake fashewa da kuka tana "karka kuma dukana, bani da me kula dani dan me bazan fita inda zan samu ba, idan ka kuma dukana Allah ze sakamin, ka ɗau hakkina karka kuma dukana" Imran ya cigaba da mammake Amira, tana kuka tana kwakwazo, amma bakinta yaƙi mutuwa, yasa hannu ya riƙe kunnenta, azaba tasa jikinta ya hau rawa, ta haɗa gumi ga hawaye, kamar kunnenta ze cire. Hannunsa riƙe da kunnenta yace "meyasa kike abunda kike aikatawa?" "Kuɗi nake so" ta bashi amsa tana kuka. "Dan kina son kuɗi seki dinga karuwanci, bazaki sana'a ba?" "Ni bazan iya ba kuɗin kawai nakeso, fame kula dani kuma bame bani" "Dole ne ki riƙe kuɗin? Meyasa bazaki kira Abba ki gaya masa ya dinga tura miki kuɗin ba?" "Ni bana roƙo" "Amma kin iya yawon banza ko, yawon befi roƙon abun kunya ba?" Dukda a cikin azabar da take, amma be hanata cewa "wallahi yawon da nake ya fiye min, in roƙi wani abu ko a gurin waye, ka sakarmin kunne na malam karka illatamin kunne" Imran ya sakar mata kunne ya miƙe tsaye, ya zare belt ɗin wandonsa, beyi niyyar dukanta ba, amma yaga abun nata bana ƙare bane ya rufe ƙofa, da niyyar yai mata dukan tsiya, Amma Amira ta fashe da kuka ta shiga magiya. "Dan girman Allah kayi haƙuri, karka dakeni bazan ƙara ba, wallahi yanzu ma inaga ka karyani dukana da kayi da wannan ƙafar taka, dan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama kayi haƙuri, wallahi na dena bazan kuma ba" Da ƙyar muryarta take fita, saboda kuka, fuskarta tai jawur. Imran yace "Ƙarya kikeyi bazaki dena ba, naga alamar kina da taurin kai" "Wallahi bani da taurin kai, kaina me laushi ne,bazan sake ba ninace maka bazan kuma ba, Allah na dena" "Rufemin baki, ko in saki tsallen kwaɗo a tsakar gida yanzun nan" Amira tai gum da bakinta, se hawaye kawai dake cigaba da zuba. "Idan aka kuma kiran Abba, akace gashi kinyi wani abu, in miki me?" "Wallahi kazo duk abunda kamin nina janyowa kaina, bazan kuma ba daga yau insha Allah" Ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗakko kuɗi ya watsa mata, yace "in dai kuɗine gasu nan, idan sun ƙare kiyi waya a baki wasu, idan na kuma samun labarin kinyi wani abu makamancin wannan, wallahi nazo zakiga abunda zan miki, Enugu zan kaiki aikin soja, in kaiki barrack su azabtar dake tunda baki da kai, wawiya shashasha kawai" Amira ta sunkunyar da kanta, jikinta nata zugi, yayi ya gama ya buɗe ƙofar ya fita. Yana fita Amira tabi bayansa da harara, jikinta se zugi yake mata, saboda yadda ya dinga balla da ita, ga ranƙwashi da murɗe kunne. Imran yaje sukayi magana da su Baffa, ya dawo ƙofar ɗakin ya tarar da ita tana nan zaune tana kuka, yace "am going for now, lokaci lokaci zan dinga zuwa, kuma na bada lambar wayata, da kinyi wani abu amin waya a gayamin, wallahi kika bari ska kirani akace kinyi ba dai dai ba, zakiga yadda zanyi dake" Amira bata cemasa komai ba, harya gama sababinsa ya juya ya yai sallama da mutan gidan yace ko waje kar a sake barin ta fita, idan aka hanata abu ko tayi gaddama a kira shi, suka tabattar masa za'ayi yadda yace , daga nan ya  tafi. Amira tai watsi da kuɗin daya bata zuciyarta na ƙuna, ga baƙaƙen maganganu da yayi mata, ga kuma wahala ta sha, da ƙyar ta ja jikinta ta ɗakko wayarta, ta kira Sultan. Ringing biyu ya ɗaga yace Allah ya temaki Gimbiya. "Ka gayawa mutumin nan, ina nan zuwa garin Abuja, zanje gurin bikin nan!!! In ba'a comment zan dena posting gaskiya Share Please Follow me on watpad@ Ayshercool7724 Or what's app 07063065680 . [1/6, 5:20 PM] Ayshercool: . 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                  5_6 Sultan da ƙarfi yace "wow, that's my Queen, Gaskiya kin gama birgeni Amira, zan gaya masa nasan zeyi farinciki da jin haka sosai" Amira ta share hawaye tace "Ka gaya masa kawai, kaga idan ma be biya kuɗin jirgin ba ni zan biya, zan tafi ku sameni a can" "A'a me yayi zafi? Tare ma zamu tafi ai, amma naji muryarki wani iri kamar kina kuka, lafiya kuwa?" Ɗan gajeren tsaki tayi tace "manta kawai, ni dai na gaya maka ne kawai, tafiyar nan dani za'ayi ta insha Allah" Tana gama maganar ta katse kiran, ta shafa kunnenta dake ta zugi, da jikinta da keta mata raɗaɗi tai ƙwafa tace "wallahi tunda akamin haka an taɓo masifa, sena ɓatawa kowa rai kuma sema tabattarwa wannan sakaran be isa ba, nize wulaƙanta ga duka ga miyagun maganganu, dani kuke zancen" Tai maganar tana goge hawayen dake bin fuskarta, Amina ta shigo ɗakin ta kalli yadda Amira tai zaman dirshen tana kuka, ga kuɗin da aka bata tayi watsi dasu, fuskarta tayi jawur. Amina ta kwashe da dariya tace "yau Allah ya dubemu ya karɓi Allah ya isarmu, Allah ya kawo mana maganinki, ni dama ya ɓallaki kowa ya huta" Sadiya ta biyo bayan Amina tana faɗin "kedai bari, ai gara da aka mana maganin banza, ashe iskancinta na ƙaryane sega shi tana ihu tana ayi haƙuri, ballagaza kawai" Amira tai shiru ta cigaba da kukanta, gaba ɗaya taji ta tsani komai ma, ya zubar mata da mutunci a gaban mutane, bebi ba'asin komai ba yaci zalinta yai gaba, take taji haushi da tsanar Imran sun mamayeta gaba ɗaya. Ranar wuni sukayi bakinsu shiru, saboda uwar hayaniyar ta sha wuya, zuwa yamma zazzaɓi ya rufeta saboda kukan da tayi, da kuma ciwon da jikinta yakeyi ga ciwon kai, haka ta shiga bargo tana rawar sanyi, sedai dulk da haka saƙawa take tana ware abunda zatayi ta huce abunda akayi mata, amma Zuwa Abuja kam sedai idan ta mutu, amma muddin tana raye se taje. Imran kuwa har ya shiga garin Kaduna, yana tunanin Amira da abunda take aikatawa, abun ya ɗaure masa kai gaba ɗaya yarinyar nan ta fitsare, wai harta kalli tsabar idonsa ta gaya masa wai karuwanci takeyi da jikinta dan ta samu kuɗi. Ya daki sitiyarin motarsa da ƙarfi yace "wace irin rayuwa ce wannan? Yarinyar da Yakamata ace tana makaranta, amma itace ke yawon ta zubar ba kunya ba tsoro ƙaramar yarinya kamar wannan ta ɓata image ɗinta, ga fitsara da rashin ta ido, take yaji wani mugun haushinta da ƙyamarta sun kamashi. A haka ya ƙarasa gida da tunani kala kala, seda yai sallar magariba sannan ya shiga gida. A falo ya tarar da Ammi, ya nemi guri ya zauna, Ammi tace "Imran ya hanya? Na kiraka bata shiga fa, har hankalina ya fara tashi" "Alhamdilillah, inaga rashin network ne, tun ɗazu na dawo na tsaya nayi salla ne kum.... Be ƙarasa ba wayarsa ta fara ringing, ya ɗakko wayar yaga sunan Abbana a kai, ya saita nutsuwarsa sannan ya ɗaga wayar "Salamu Alaikum Abba Barka da yamma" Abba yace 'yawwa Imran, yaya ka dawone?" "Eh Abba na dawo, Yanzu na shigo gidan ma" "To Alhamdilillah, yaya ka barosu ya ake ciki ne?" Imran yace "to Abba, maganar ce dai Babu daɗi, dan yarinyar nan ta riga ta kangare kusanma zan iya cewa tafi ƙarfinsu, kuma da bakinta ta amsamin tana yawon banza, wai kuɗi take so babu me bata, ba kaga shigar da ta dawo da ita a jikinta ba, abun dai se Addu'a kawai" Abba yace 'innalilallahi wa inna ilaihi raji'un, garin yaya suka bari yarinyar nan ta lalace hakane? Kuma naga kamar da ba haka take ba?" "To Abba, abun nata ne dai se Addu'a kawai, amma ta zama muguwar fitsararriya, na bata kuɗi kafin in taho nace idan tana buƙatar wasu, ta kira ka a waya a tura mata, amma akwai buƙatar kaje da kanka, ko makaranta ce a nema mata, dan bani da tabbacin ma ko makarantar secondary ta gama, idan Kuma wani abun ne yakama ayi mata, se a duba a gani" Abba yai ajiyar zuciya me ɗauke da damuwarsa yace "Shikenan Imran, idan na dawo ma ƙarasa tattaunawa, amma banji daɗin labarin nan ba, amma Nagode sosai, zan san abunyi Insha Allah" "To Abba, Allah ya dawo da kai lafiya" "Ameen Son" Ya katse wayar, tuni Ammi ta yamutsa fuskarta tace "ko meye ze ɗaga hankalin sa kuma, bafa shiya lalata yarinyar nan ba, laifin dangin ubanta ne bana wani ba, ai suke da alhakin riƙeta ba shi ba, kuma wallahi ka kuskura kasa ya kawomin wannan yarinyar gidan nan se ranka ya ɓaci, baza'a lalata min tawa 'yar da na daɗe ina gina tarbiyyar ta ba" "Ammi ai bance ya kawota gidan nan ba, Amma Abba yakamata yayi wani abu akan yarinyar nan" "Kai dalla rufemin baki, Gobe in Allah ya kaimu kaje Hana boutique, nayi Magana dame gurin, ka karɓo wasu riguna, da za'a saka a lefenka" "To Ammi Nagode sosai, Allah ya ƙara Arziki" Ya miƙe jiki a sanyaye ya tafi masallaci dan gabatar da sallar isha'i. Bayan ya dawo ya tarara an kai masa Abincinsa ɗakinsa, ya zauna yaci sannan ya ɗakko wayarsa, ya kira Ihsan. "Hello masoyi" "Na'am, abar ƙaunata kina lafiya?" "Alhamdilillah, ya hanya?" "Nayi fushi, bayan baki kirani ba" Ihsan ta marairaice murya tace "haba My Own, tunda kaje kano mukayi waya, daga baya idan na kira bata shiga, na kira meenal tace min baka dawo ba, ɗazu naji Mummy suna waya da Ammi tace ka dawo, kuma lokacin salla ne, shiyasa ban kiraka ba, saboda nasan wataƙila kana salla ne" Imran yai murmushi yace "to shikenan masoyiya ta, kin wuni lafiya?" "Lafiya ƙalau, sedai kewarka da ta dameni my own" "Nima nayi missing ɗinki tawan, naso in biyo in zo in ganki, Amma nagaji sosai, kuma ina cikin damuwa ne" Ihsan tai ajiyar zuciya tace"naji alamin damuwa a muryarka, sedai ban matsaka bane saboda wataƙila abin ba hurumina bane, kar in shiga hurumin da ba nawa ba" Imran yace "hakane Ihsan, amma abun ya dameni sosai yadda bazan iya ɓoye miki ba" "Mene ne wannan yake damun gwarzon mazaje, da har yake nema ya hanamun shi sukuni?" "Ihsan, gurin wannan'yar uwar tawa da Abba ya aikeni, Ihsan abun da na tarar ya ɗagamin hankali sosai" Ihsan tace "subhanallah wani abun ne ya sameta?" "A'a lafiyar ta ƙalau, sedai ta ɗauki layin daze ruguza rayuwar ta, koma ince ya ruguza rayuwar ta gaba ɗaya" Ihsan tace "haryanzu ban fahimceka ba My" "Yarinyar nan ta ɗauki hanyar banza, tana bin maza saboda kuɗi, kuma bata jin kunya ko shakkar ta faɗi abunda take, Abun takaicin yarinyace ƙarama da befi ace tana makaranta ba" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, amma ya akayi ta lalace ina iyayenta" "Iyayenta sun rasu, a hannun dangin babanta take" Ihsan tace "so Sad, Amma addu'a yakama ayi mata, Ubangiji Allah ya shiryeta yasa ta dena, irin wannan tunda kaga tana haka, wataƙila tunda ta fara ba'a ɗau matakin daya dace bane" "Hakane nima nayi tunanin haka, amma abun ya dameni" Ihsan tace "ka dena damuwa, addu'ar ka tafi damuwar, bana son abunda ze dameka, ka rame kan lokacin bikinmu" Imran yai murmushi yace "kina ɗokin lokacin nan kuwa My Ihsan" "Eh mana" "Anya kuwa? Gaskiya ban yadda ba na fiki damuwa sosai, kamar in janyo lokacin nan haka nakeji" "Hmmm My Own kenan, ka kwanta ka huta kaji, nasan ka gaji sosai" "Idan na kwanta bazan iya baccin ba yanzu" "Meyasa?" "Tunaninki zan tayi, da mafarkin gashi munyi Aure" Tai murmushi tace "kwanta in maka addu'oin kwanciya bacci" Ba musu ya kwanta ya lumshe idonsa yace "na kwanta my wife" Cikin muryarta me daɗi ta shiga karantowa  Imran addu'oin kwanciya bacci, Imran yai shiru yana saurarenta wata irin nutsuwa tana saukar masa, a haka bacci ya kwashe shi. Amira kuwa kwana tayi da zazzaɓin nan, da ƙyar tayi sallar Asuba ta koma kwanta, tana jin yunwa sosai, rabonta da Abinci tun jiya da rana, ga ulcer ha duka da ɓacin rai, abun ya haɗu yai mata yawa, cikinta ya ƙulle yana mata ciwo, tai ta juyi a ɗakinsu, amma Babu wanda ya damu da ita, murna ma suke Gidan yayi tsit, saboda Anyi maganin Amira. Can ta fita tsakar gida da gudu, ta shiga sheƙa amai, ga ba komai a cikinta, ta dinga kakari ba abunda yake fita se yawu, idonta yai jawur ta riƙe cikinta saboda yadda yake yamutsawa. Tafa hannu Yadikko ta shiga yi tana 'la'ilaha illalahu, Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, jama'ar gidan ku fito ku fito me nake gani haka? Dama tunda na dawo Nake ganin wasu alamu a tare da yarinyar nan, shikenan ta faru ta ƙare, anyiwa me zani ɗaya sata, ta ƙunso abun" Aikuwa nan aka dinga fitowa, aka kewaye Amira dake ta fama amai ya fito, amma ba komai a cikinta, ta gama amanta ta zauna a guri ɗaya tana hutawa. Sadiya tace "shikenan dai abun Kunya ya tabbata a gidan nan, cikin shege dai gashi an yayimo shi saura kuma cuta" Umma tace "taɓ, mutuncin gidan nan kuma ya ɓare, yanzu za ai ta gantali damu a bakin duniya, wace irin masifa ce wannan" Amira ta tashi ta ɗebo ruwa ta kuskure bakinta, ta koma ɗaki tai kwanciyarta, kamar bada ita ake wannan surutan ba. Nan suka saka sabon faifai akan Amira, wasu suna a kira Imran a waya, wasu suna a bari a tabattar tukuna. Har magariba Amira bata sa komai a cikinta ba, dan haka ta kasa ko miƙewa tsaye, ta dinga juyi tana kuka tana wayyo Allah cikina, zan mutu. Baba yace "ina ga fa yarinyar nan ɓari zatayi, ta san tana da cikin ne ta sha wani abu dan ya zube" Yadikko tace "ko kuma dukan data sha jiya ne yasa cikin fita, ba yadda ba zata faru ba" Usman ne yai Sallama, suka amsa masa gaba ɗaya, ya gansu cirko cirko a tsaye yace "lafiya? Meke faruwa ne?" Yadikko tace "meke faruwa kuwa? Ai kasan baze wuce matsalar wannan yarinyar ba Amira, ciki take ta kwaso mana" Sakin ledar hannunsa yayi yace "ciki kamar yaya?" "Kamar yadda aka gaya maka mana, baka ji ne?" Cewar Umma. "Amma ya akayi kuka san ciki ne?" Yadikko tace "yo tell m safe take amai, meye inba ciki ba? Ciki ta ƙunso ta sha wani abun ta zubar dashi kuma yaƙi fita tana ta wahala" Usman ya nufi ɗakinsu Amira da sauri, ya ɗaga labule ya ganta a kwance tana juyi, tana wayyo Allah cikina. Ya shiga ɗakin ya durƙusa yace "Amira, menene meya sameki?" Cikinta ta nuna masa, amma ta kasa magana, se jujjuya kanta da takeyi. Usman yace "yakamata a kaita Asibiti, koma menene a can zamu ji" Sadiya tace "uban waye ze wani kaita Asibiti? Ta mutu ma waya damu, tunda bata ji kunyar kwaso abun kunya ba, ai se a barta ta sha wahalarta ita kaɗai" Usman yace "Baba, kasan halin mutanen gidan nan, duk da halin Amira idan ba a kaita Asibiti ba ta mutu a haka, se an ƙulla maka wani sharrin, gara ma a kaita Asibiti, kuma duka mugun halin Amira, da yadda take ɓatawa mutane rai, bazan manta yadda ta dinga min wahala ba, lokacin dana karye a hannu, yarinyar nan tana da tausayi, kuma koba komai tana da alaƙa da mu" Baba yai ajiyar zuciya yace "shikenan, a kaita ba dan halinta ba" Usman ya samo Napep, aka sakata a ciki aka kaita Asibiti. Suna zuwa aka karɓeta, aka gayawa likita abunda yake damunta, ya rubuta mata tasa tasai, akayi result ya nuna typhoid ce da malaria ke damunta, sekuma ulcer. Yadikko tace "likita yarinyar nan fa cikine da ita, taje ta sha wani abun dan ya zube take ta shan wahala haka" Likita yace "ba matar aure bace?" "Ba wani Aure budurwa ce' inji Yadikko. Likita yace "to ai har test ɗin ciki akayi mata, ba ta da komai kuma tace shekarnjiya ta gama al'ada, amma duk da haka mun mata test bata da juna biyu" Yadikko tace "a'a kun dai haɗa baki, amma ba yadda za'ai ace ba ciki bane" Usman yace "to ai Allah ne ya rufa mana Asiri Yadikko, koke so kike ace cikin ne Asirinmu ya tonu a gari?" Amira kamar ta fasa ihu, jin yadda Yadikko ta kafe akan lallai se an tabattar da cikine da ita, aka yiwa Amira ƙarin ruwa da Allurai, ta samu sauƙi aka sallameta. Tunda ta koma gida ba wanda yasake jin kanta, ta dena shiga sabgar kowa take rayuwarta ita kaɗai, a zatonsu duk ta kintsune saboda barazanar Imran. Sedai haryanzu bata yadda da a sata aiki tayi ba, ko wani ya nemi ya rainata ba. Bayan kwana uku ta warke, sedai rashin ƙarfin jiki, tana zaune a ɗakinsu su Amina suna karyawa, Yadikko ta shigo da waya a hannunta ta kalli Amira tace "karɓi nan Imrana ze miki magana" Wata uwar harara Amira taiwa Yadikko, ta ɗauke kanta daga kallon Yadikko. "Bazaki karɓa ba ina miki magana?" Amira ta zumɓura baki, sannan ta karɓi wayar. "Wayarce bazaki karɓa kenan? Ana miki magana kikayi banza" Shiru ta kumayi ba tace komai ba. "Ba kyaji na ne?" "Ina jinka" Amira ta faɗa a daƙile. "Amsawa ce baza kiyi ba kenan?" Amira tace "nifa bani da lafiya, kuma ni ka takuramin" "Eh rashin lafiyar taki aka gayamin, You Are pregnant, and you take abortion pills, are you really ok?" Ya ƙarasa Maganar a fusace Amira ta kalli Yadikko, tasan itace zata gaya masa, wani malolon baƙin ciki ya tokare mata ƙirji. Cikin tsawa Imran yace "ba kyaji na ne? Uban waye yai miki ciki har kika je kikayi ƙoƙarin zubarwa?" Amira tai shiru ba tace komai ba. "Ba magana nake miki ba? Definitely zan shigo kano a satin nan insha Allah, Enugu zan kaiki makarantar kangararru su horaki ta nda baki da mutunci, kuma ki gayamin waye ya miki ciki?" "Kaga dan Allah ka dena min tsawa, idan kaga dama ka kaini bangon duniya makarantar sheɗanu bata kangararru ba, ina ruwanka da lalacewa ta? Meye naka a ciki? Meye alaƙata da kai dan ina ɗaga maka ƙafa ba tsoronka nakeji ba, inka ga dama ka yo fiffike kazo yanzu" Ta ƙarasa maganar hawaye na zuba a idonta, tai wurgi da wayar Yadikko tsakar gida, aikuwa wayar ta tarwatse a gurin, ta miƙe tsaye ta kalli Yadikko tace  "abunda kikemin ya isheni, ya isa haka, na gaji, nayi ƙoƙarin yi miki biyayya iya yina, Amma ke kullum burinki, kiga kin tozartani, se zaƙewa kike akan lallai senayi abun kunya, Yadikko da kakata fa kikayi kishi ba da uwata ba, me nayi miki? Me nai miki Haka a rayuwa kike burin kiga masifa ta sameni, Insha Allah abinda kike min fata sedai ki ganshi a kan su Amina ba a kaina ba" "Ke Amira, Yadikko kike gayawa haka?" Cewar Zailani "Na faɗa ɗin, a gabanta likita ya faɗi abunda ke damuna, Amma ta dage cikine dani harta kira wan uwata a waya ta gaya musu, to cikin ne dani nayi cikin kuma kome na ke aikatawa a rayuwa da sa hannunki da zuriyarki, kuma wallahi rashin ji yanzu na fara mu zuba mu gani, koni ko ke!" Amira ta juya ta ɗau jakarta, da wayarta ta fito zata fita, Zailani ya biyota yana ƙoƙarin hana ta tafiya, amma tace wallahi ya taɓata seta masa illa, ta sa kai ta fice tana cigaba da zubar da hawaye. Da taji garin ya mata zafi bata da gurin zuwa, sama da gurin Yaya Fa'iza Dan haka yanzu ma gidanta ta wuce, tana zuwa ta tatar da Bashir na wanke babur ɗinsa, yana ganinta ya fara murmushi yana "Anty Amira Sannu da zuwa" Sedai ganin da yayi idonta na zubds hawaye ne ya ɗaga masa hankali, kai tsaye ta wuce falon Fa'iza, tana zuwa ta zauna ta cigaba da kuka. Fa'iza tace "Anty Amira, meyasameki haka? Meke faruwa?" Bashir yace "Amira lafiya kuwa?" Kasa magana tayi ta cigaba da kuka, can ta ɗago tace  "Fa'iza Yadikko, in Yadikko wallahi idan ba tayi wasa ba, sena karya matar nan wallahi" Bashir yace "Subhanallah, me tayi miki" "Yaya Bashir na gaji, am tired, ban san me matar nan take so dani ba, ta kira wan mahaifiyata tace musu ina yawon banza, ya turo ɗansa yai min rashin mutunci shekaranjiya, hadda duka, na kama rashin lafiya munje Asibiti, a gabanta likita yace malaria da ulcer le damuna, Amma ta kuma kiransu a waya tace wai ciki ne dani, nayi abortion nake ta sha wahala, meye haka takemin? Me nayi mata dan tayi kishi da kakata seta ɗoramin karan tsana? Bata fatan abun Alkhairi ya kusanceni se ita da zuriyarta, wallahi zan shiga duniya in bar mata gidan" Bashir yace "Subhanallah, ki dena faɗar haka, shiyasa nace ki dawo Gidan nan mu zauna, ki baro can ɗin kawai, su dena ɓata miki rai, Allah ba ze hana yadda za'ayi ba" Amira tace "ni ba zan dawo gidanku in zauna ba, saboda Allah be ɗora maka ɗawainiya ta ba, wanda Allah ya ɗorawan tunda sunƙi yi Shikenan" Fa'iza tace "Amira, ire iren wannan abubuwan nake jiye miki yasa nake miki faɗan ki dena abunda kike, dole ko kinyi abu ko baki ba ace kinyi, Saboda halinki da ɗabi'un da kikeyi" Amira tai shiru, zuciyarta na cigaba da tafasa, da zafi akan abunda ake mata, shikam Bashir haƙuri yaita bata yana rarrashinta. Message ne ya shigo wayar Amira, ta ɗakko wayar ta duba, Sultan ne ya turo mata saƙo "Ina ta kiran wayarki, Amma baki ɗaga ba, komai ya zama ready, jibi in Allah ya kaimu zamu tafi" Kashe wayar tayi ta mayar aljihun wandonta, ba tare da tace komai ba, Bashir yace "Ummu Khairat, sama mata abunda zata ci, naji tace bata da lafiya" Fa'iza ta zuba mata Abinci ta bata. Imran kuwa lamarin Amira ya dena bashi mamaki, yadda ta gaya masa baƙaƙen maganganu ma ya ɗaure masa kai sosai, hankalinsa ya tashi jin Wai har ciki tai yunƙurin zubarwa, yaita bin lambar Yadikko amma bata shiga, dan tunda Amira tai jifa da wayar komai na wayar seda yayi ɗai ɗai. Yaji kamar ya kira  Abba a waya ya sanar masa, amma yasan hankalin Abba ze tashi ne, kuma yana da hawan jini, kuma ma dai wannan ba labarin faɗa bane, dan haka ya yanke shawarar ze kuma komawa Kano, dan yaga me ze iyayi akan lamarin, ya bar maganar a ransa ko Ammi be gayawa ba. Wajen ƙarfe tara na dare Amira tace ita gida zata koma, Fa'iza tai tai da ita ta kwana a gidanta tace ba zata kwana ba, Bashir yace ze mayar da ita gida, nan ma tace bata yadda ba. Ta kama hanyar komawa gida ita kaɗai, data koma gidanma ba wanda ta kula kuma babu wanda ya kulata, ta shiga ɗakinsu, ta nemi guri ta zauna ta shiga haɗa abubuwan da zata buƙata a wata travelling bag. Ta gama haɗawa tsaf, sannan ta nemi gurin kwanciya, cikin dare Sultan ya kirata a waya yace mata yana ƙofar gidansu, ta tashi ta ɗau jakar nan data haɗa, taje ta zare sakata ta buɗe ƙofar, ta bawa Sultan jakar, ya karɓa ya tafi da ita, ita kuma ta koma ɗakinsu. Imran yana ta shirin yaga ta yadda za'ayi ya koma Kano, aka kira shi daga gurin aiki akace lallai yaje ana san ganinsa, Babu yadda zeyi ya kaucewa wannan kiran, haka ya haɗa kayansa, yaje yai Sallama da Ammi, ya biya ta gidansu Ihsan dan yayi mata Sallama. Tunda Ihsan taji komawa zeyi taji kamar ta ɗora hannu a ka tayi kuka, tace "Yanzu my Own komawa zakayi?" Imaran yace "to Ihsan ya zanyi? Dole in koma kar in fuskanci hukunci" Tai ajiyar zuciya tace "to yanzu se yaushe kuma?" "Nan da sati biyu insha Allah" ya bata amsa cikin damuwa. "Ya salam, lokacin bikinmu yazo daf  fa kenan" "Eh Ihsan, ya zanyi idan ba hakan ba, But am sorry kiyi haƙuri kinji? Ba laifina bane, nima ba haka naso ba" "Shikenan My, da har nace da Mummy na fasa zuwa Abujan nan, amma gara in tafi dama saboda kai na fasa" "Ba haka naso ba my, Amma ba yadda na iya, kinga kan lokacin bikinmu yazo, ina dawowa se biki mu tare kawai" Ɗan murmushi tayi tana sunkunyar da Kai, sukayi Sallama ya tafi. "Ali 'yata! 'yata Ali! Aliyu 'yata Kar ka bari 'yata ɗaya dana bari ta lalace, dan Allah Ali kayi wani abu a kai, kar 'yata ta lalace kaima 'yarka ce, dan Allah Ali ba dan ni ba 'yata 'yata 'yata Aliyu!!! Share Please Follow me on watpad@Ayshercool7724 What's app@07063065680 [1/7, 7:03 PM] Ayshercool: .🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. *Innalillahi wa innalillahi raji'un, ina me amfani da wannan dama, wajan miƙa ta'aziyya ga ɗaukacin al'umar musulmi akan rashin da mukayi na Shehin _malami, Dr. Ahmad banba B.U.K ina fatan Ubangiji Allah yayi masa rahama yasa ya huta, in tamu tazo yasa mu cika da imani*_ Afuwan banyi Editing ba                                                               6_7 A gigice Abba ya farka daga baccin da yake cikin tashin hankali, mafarki yake da mahaifiyar Amira, ta riƙe rigarsa tana kuka akan ya temaka kar 'yarta ta lalace. Ya dafe kansa yai shiru yana tunani, can ya miƙe yaje ya ɗakko wayarsa, ya nemo lambar Imran ya kirashi, sedai wayar taƙi shiga sam. Ya duba lambar Ammi ya kirata, a ɗan firgice ta farka daga baccin, jin wayarta tana vibrating, ta duba screen ɗin wayar ta kalli agogo, dare yayi sosai ta ɗaga wayar tace "Hello, Abba lafiya kake kira a wannan daren haka?" Abba yai ajiyar zuciya yace "ina Imran yake?" Cikin Rashin fahimta tace  "Imran kuma? Me Imran ze maka a wannan daren?" "Ya kike tambayata ne? Yana nan ko baya nan?" "Ai Imran tun safe ya koma Maiduguri, an masa kiran gaggawa" "Yasalam" "Amma Abba lafiya, nifa ka tayarmin da hankali" Abba yace "Bari kawai, mafarki nayi da Zahra'u" "Wace ce kuma Zahra'u?" Abba  yace "'yar uwata mana, nai mafarki da ita tana kuka, tana in kula mata da 'yarta karta lalace, na tsorata ƙwarai ina ga tunda Imran baya nan, ni zan dawo gari zanje inga meya kamata inyi akan yarinyar nan" Ji tayi kamar ta zagi Abba dan takaici, a hasale tace "yanzun Dan Allah akam wannan abun ka nemi ka tayarmin da hankali, a wannan uban daren ina bacci? Mafarki ne fa kayi ba gaske ba, kawai ka ɗagamin hankali ka hanani bacci" "Kinga ba kowane mafarki ne kawai ba, wannan mafarkin da nayi ba kawai bane, an nusar dani kuskure na ne ta mafarki, wanda yakamata in gyara tabbas" "To yanzu me kake nufi?" "Duk yadda ake ciki gobe in Allah ya kaimu zan dawo, zuwa jibi insha Allah zanje inga yarinyar nan da kaina, something is not wrong, seda Safe kawai" Ya kashe wayarsa ya ajiye, ƙirjinsa na cigaba da bugawa da sauri da sauri, Ammi kuwa tsaki tayi, ta jefa wayar bayanta, tace  "Aikin banza, kawai ze ɗagamin hankali akan wata banzar yarinya, sekace nina saka ta yawon banzan" Tai tsaki ta juya ta cigaba da baccinta, tana takaicin Yadda Abba ya tashe ta ya ɗaga mata hankali a wannan Uban daren. Ana idar da salar Asuba, Amira ta ƙarasa tattare duk abunda take buƙata tai waje, su Sadiya na kallonta amma ba wanda ya iya ce mata wsni abu, dan yadda tske cika tans batsewar nan, duk wanda ya tanka mata zata iya sauke masa rashin mutunci. Haka ta fita zuwa Office ɗinsu na rawa, ta tarar dasu Sultan sun shirya tsaf, ana jiran mutum biyu, seda suka karya wajen ƙarfe goma sannan suka tafi airport. Sultan yana kula da yadda Amiran bata walwala sam, yaso yai mata magana amma ya fasa, saboda wani lokacin halin Amira se a hankali, tana da sauƙin kai, amma bata fiye son a shiga lamuranta ba. Se ƙarfe biyu Sannan suka ɗaga, Amira na Jin yadda jirgin ya tashi, maimakon hakan ya sanya Amira cikin farinciki kasancewar karonta na farko kenan da ta hau jirgi, sema wani baƙinciki da ya addabi zuciyarta data rasa na menene, kawai ta jingina ta lumshe idonta, hawaye na zuba daga idonta. "Gimbiya Amira yau an hau jirgi, ba saban ba, za'a ƙaro wulaƙancine" Sultan yai maganar yana murmushi, sedai ganin Amiran na hawaye yasa jikinsa yin sanyi. Cikin damuwa yace "Amira lafiya kuwa? Kukan me kike haka?" Girgiza masa kai tayi alamar bakomai. "Amma Bakomai kike kuka haka? Karki sa hankalin mutane ya dawo kanki fa" Ta goge hawayen ta tace "karka damu, bakomai" Haka Sultan ya ƙyaleta, amma Amira ta kasa tsaida hawayen dake bin fuskarta. ***************************** "Amma Alhaji Ali baka ganin tafiyatka a yau zata iya kawo matsala, kana cikin kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa, kuma kusan kaike jagorantar kwamitin nan, be kamata ka bar garin nan yau ba" "Dole in bar garin nan yau ɗin nan, ina da damuwa ne, kano nake son zuwa gobe in Allah ya kaimu" "Amma wace irin damuwa ce da bazaka iya haƙuri a gama ganawar ba sannan ka tafi?" "Hashim, bazaka gane ba sam, nasan abunda zan gayawa Excellency, Amma ƙarfe uku zanbi jirgi in koma" Hashim yace "shikenan, Allah ya kyauta koma menene" Alhaji Ali ya amsa da "Ameen" Yadikko ta fito tsakar gida tana cewa "ina wannan yarinyar take ne, ta kassaramin waya wayata taƙi tashi, ta fito ta bada kuɗi a kaimin ita gurin gyara" Amina tace  "wai wace yarinyar kike nufi?" "Amira Mana" Amina tace "to bayan idar da sallar Asuba ta fita" "Ta fita taje ina?" Sadiya tace "wa take gayawa inda zata? Gantalinta ta fita, yau hadda jaka ta haɗa ta tafi" Yadikko tace "jaka gidan ubanwa taje? To ko ina taje ina nan zatazo ta sameni, wallahi seta biyani wayata" Yadikko ta cigaba da sababinta, tana se Amira ta biyata wayarta data fasa mata. Alhaji Ali daga airport be tsaya ko ina ba, se gidansa sedai sam Ammi bata wani nuna murna da dawowarsa ba kamar yadda take a baya ba idan yaje wani guri ya dawo ba, dan ya fara bata haushi akan yawan zancen Amira da yake kwanan nan. Tunda ta masa sannu da zuwa, ta bashi Abinci bata bashi chance, ko fuskar da zasu tattauna maganar Amira ba. Minal ce ta shigo falonsa tana faɗin "Abba, ya kuma ka dawo gida yau, base jibi in Allah ya kaimu zaka dawo ba?" Abba yace "na dawone saboda batun 'yar uwarku" Minal tace "wace 'yar uwa tamu? Anty Khadija?" "A'a, 'yar uwaku dake Kano, Amira" Ammi tace  "Dan Allah ka dena haɗamin yara da wannan yarinyar, ni yarana nutsatstsune" "Koma dai menene, ni 'yata ce kuma dole in damu akanta" Ammi tace  "eh kai ta zamewa dole ba yarana ba, ka dena haɗata dasu" Abba yai shiru yana tunani, sam Ammi bata masa kara a kan 'ysn uwansa, Magana in dai bana 'yan uwanta ba, sam bata son taga yana morawa wani nasa komai, be kuma  cewa komai ba ya tashi ya shiga bedroom ɗinsa, ji yake kamar ya tafi Kano a lokacin, sedai Yamma ta riga tayi, ba damar yin hakan lokaci ya ƙure sosai. Amira kuwa tuni suka sauka a babban birnin tarayya, Sultan yai musu jagora zuwa Hotel ɗin da aka kama musu, Amira ɗakinta ita kaɗaice, Babban ɗakine sosai dan yafi nasu Sultan girma da kyau, hatta Abincin da zasu ci ayi bikin a gsma, seda aka biya musu, Sedai gaba ɗaya Amira a damuwa take, kawai dai gata nan ne dai, ji take kamar ko rawar ma bazata iya ba ranar bikin Washegari da wuri Alhaji Ali ya shirya ya tafi Kano, be tsaya ko ina a ba se ƙofar gidan kakanin Amira, da shida jami'an tsaron dake masa Rakiya, a wasu rantsatsun motoci na Alfarma, wanda seda aka mutane suka fara tunanin waye wannan ya kawo musu ziyara haka layinsu. Yai Sallama ya shiga gidan, a ƙofar ɓangarensu Yadikko ya tsaya yana Sallama, Baba ne da kansa ya fito dayake daf yake daya fita, yayi mamakin ganin Abba, dan rabonsa da gidan nan a ƙalla ya shekara shida, tun kafin a masa muƙami a gwamnatin tarayya. Baba ya washe baki yace "Alhaji Ali kaine ke tafe da kanka haka? Masha Allah yau mun karɓi babban baƙo Bismillah shigo" Alhaji Ali ya shiga yana faɗin "Ayi haƙuri munyo sammako haka ba sanarwa" Baba yace "haba dai bakomai, sha ɗaya na Safe ai ba sammako bane, sannu da zuwa Yallaɓai" Kana kallon Alhaji Ali zaka san shine mahaifin Imran, saboda suna kama sosai. Aka masa iso har ɗakin Baba, nan Yadikko ta shiga rawar kai tana washe baki tana  "Sannu da zuwa, Sannu da zuwa Alhaji Ali, ya hanya sannunka da zuwa Sannu Sannu, kai Zailani zokaje ka siyo masa ruwan roba, manya basa shan irin ruwan da muke sha" Abba yace  "A'a bakomai, na taho da ruwana a mota, nagode sosai" Suka shiga gaisawa da yaushe gamo, can Abba yace "nifa banga 'yata ba, nazo ne in gani inda yuwuwar in tafi da ita, saboda labarai marasa daɗi da naji a game da ita, sam abun be min daɗi ba, na turo Imran yazo shima, sedai feedback ɗin dana samu daga gareshi sam banji daɗinsa ba, abun ya tsayemin shiyasa na ajiye ayyukana na taho kawai" Baba yace "to Amira dai iya ƙoƙari munyi a kanta, ɓangaren kulawa da ita, cinta shanta suturarata da kuma makaranta, munyi iya ƙoƙarin mu bata tarbiyya nagartacciya kamar wadda muke bawa duk wani ɗa dake gidan nan, Amma Amira taƙi, hankalinta na kan wani abu daban" Yadikko ta ɗora da cewa  'Sam Amira bata jin magana, ga fitsara da rashin Kunya, taurin kai ga neman magana, ga rashin ta ido da gantali na tsiya a cikinta, ranar da yaron wajen ka yazo nan ma, ba kaga yadda suka fafata ba, seda ta masa rashin Kunya ya bubbigeta, bayan tafiyarsa a garin yawonta ta kwaso juna biyu, ta sha magani ta zubar ya dinga wahalar da Ita, seda muka kaita Asibiti, idan ta bar gidan nan se tayi kwanaki fiye da goma Babu wanda yasan inda take, samari kuwa babu kalar wanda basa zuwa gurinta, lamarin nata dai ba arziki a cikinsa sam" Alhaji Ali ya dafe kansa cikin damuwa yace  "yanzu ina Amiran take ne?" "Eh to, yaron gurinka ya kira waya aka gaya masa ga abunda tayi, yace ze kaita makarantar kangararru, tun jiya da farar Safiya ta bar gidan nan ba wanda yasan ina ta tafi" Abba yai shiru na wasu 'yan daƙiƙu, yana tunani gami da nazari akan yadda ze ɓullowa lamarin, can yace  "Shikenan, yanzu dai duk yadda ake ciki dan Allah idan ta fawo, a kirani a waya a sanarmin, zanga abunda zanyi idan ta kama mu koma can Kaduna da ita shikenan, semu tafi ta koma can a nema mata makaranta" Baba yace "ai ta gama sakandare bana" Abba yace "eh high institution nake nufi" Yadikko tace  "amma bazamu so ka ɗauke mana ita ba, dukda rashin jinta bazamu so ka rabamu da ita ba, muma muna ƙaunarta" Abba yace "sedai yadda ta yuwun kawai" Ya miƙe da nufin ya tafi, Yadikko tace "to Yallaɓai sedai Amiran ta lalata min sabuwar wayata, idan ta dawo ban san dame zan kiraka in sanar maka ba" Abba yace "ai wannan ba Abun damuwa baane" Yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko kuɗi ya ajiye mata yace "gashi nan, ki sai wata wayar sauran kici goro" Ta amshe tana washe baki tana dariya, suka fito tsakar gida, Su Sadiya suna gaisheshi, suma duk yabi ya basu kuɗi. Yadikko ta kuma karkacewa tace  "ai Yallaɓai wannan sune 'yan uwan nata, ba wadda ba tayi saukar alƙur'ani a cikin su ba, wallahi nutsatstsune gasu nan, baka ga yadda ake yaba tarbiyyar su a unguwa ba" Abba yace "Masha Allah, Allah ya ƙara tsare mana su gaba ɗaya" Yadikko ta sosa kai tace  "Ai naga shima yaron gurin naka ya girma sosai, masha Allah gashi nutsatstse ne" Abba yace "Au Imran, ai shi yanzu haka sojane" Yadikko tace "Soja marmari daga nesa, masha Allah, to Yallaɓai meze hana a ƙara ƙulla alaƙa da danƙon zumunci, a yaran nan yazo ya nemi ɗaya daga cikinsu ko Sadiya ko Amina?" Abba yai mutm yace  "Allah sarki, ai Imran ya kusa Aure, befi sati biyu ya rage bikinsa ba, za'a aiko muku da katin gayyatar ku har gida" Seda Yadikko ta canza fuska, amma ta maze tace  "Ahhh Alhamdilillah, kace mun kusa zuwa Kaduna garin gwamna, to Allah ya kaimu lokacin lafiya" Haka suka raka Abba har gaban motacinsu, ya shiga sukayi Sallama ya tafi, Yadikko ta koma gida tana mita, "yo ni tunda an kusa auren ɗansa base ko shi ya auri wata daga yaran nan ba, muma mu dangwali arziki amma shikenan daga ƙwauri se gwiwa, har yana batun ya ɗauke wannan watsatsiyar wato taje ta huta, mu mu zauna a wahala, daga nan ma a rufa ta samu wani hamshaƙin ya aureta, to wallahi baze yuwu ba, baze yuwu ta bar gidan nan ba, gara mucigaba da zama, taita gurza Rashin mutumcin, mu zauna a wahalar tare. Umma tace "Yadikko naso mutumin nan ya amsa ɗansa ya auri ɗaya daga yaran nan, ai da mun rage zafi da sun fita zakka, duk 'yan matan gidan nan ba wadda ta taɓa auren wani me ɗan abun hannu, duk se talakawa" Yadikko tace  "waccan makirar Fa'iza, ba yadda ba'ayi da ita ba ta auri Alhaji Yahaya amma taƙi fafur, da ko ba komai ko umarar nan naje, da an rage wasu wahal halun, shiyasa nakeson ko Sadiya ko Amina wata ta samu me ɗan maiƙo" Umma tace "to Ubangiji Allah yasa a samu ɗin" "Bari kawai, ai idan suka kawo katin bikin nan, dole ne mu tafi gaba ɗaya harsu ɗin, idan yaso ko a cikin manyan mutanen fa zasuje a samu su samo miji nagari, ba wannan samarin da suke binsu ba, basu ajiye komai ba basu bawa wani ajiya ba, banda ƙaddara aisu Sadiya kalar manyane" Nan kansu ya dinga kumbura, Sadiya ta fara raya abubuwa a ranta, fan harga Allah Imran yayi mata musamman zuwan nan da yayi, ya burgeta sosai. Amira na kwance a ɗakinta na Hotel, tayi shiru tana tunani, taji ana knocking, tashi tayi taje ta buɗe ƙofar, Sultan ne tare da wani mutum, bata ce komai ba ta saki ƙofar suka shigo, a nan falo suka zauna, ita ma ta nemi guri ta zauna a wata kujerar. Mutumin ya kalleta yace  "gimbiyarmu, fatan kinzo lafiya?" "Ƙalau" ta bashi amsa a taƙaice. Ya ɗan gyara zama yace  "A gaskiya naji daɗin amsawa da kikayi, har kika baro Kano kika taho Abuja halartar taron bikina, naji daɗi sosai nayi farinciki" Se yanzu Amira ta gane ashe shine wanda ya gayyacesu bikin, oho ita bata san waye bama, ita dai babban abunda yasa ta ƙarfafa ta taho garin Abuja shine tazo a huta, ta rage baƙin cikin dake damun ta a zuciya. Ta dubi mutumin tai murmushi tace "Naga saƙonka an bani waya, harna fara amfani da ita, nagode sosai kuma insha Allah zamuyi iya ƙoƙarin mu mu nishaɗantar a gurin nan, Allah ya sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya" Yace "Ameen ya Allah gimbiyarmu, ko zaki iya bani lambar wayarki?" Amira ta girgiza kai tace "No need, duk abunda kake buƙata ka gayawa Sultan ya gayamin" Ya jinjina kai yace  "Shikenan yadda kike so haka za'ayi, sedai zan gayamiki garin Abuja garine na samun kuɗi sosai, performance ɗinki ze janyo miki mutane sosai, dan haka ki dage ki ƙara shiri" Amira tai murmushi tace "bana buƙatar wani shiri, wanda nazo dashi ya isheni". "I like your confidence dear, Akwai manyan mawaƙa daga kudancin Nigeria suma zasu halarci taron bikin, amma gaba ɗaya nafi farinciki da zuwanki akan kowa gurin nan, nasan ba zaki bani kunya ba" Amira tace "Allah yasa" "Kamar yaya Allah yasa?" Sultan yace "Ai zuwanta garin Abuja bashi ne ba, kayi addu'a taje gurin taron, dan wannan gimbiyar, gimbiyarce ta gaske, komai nata ganin dama ne" Mutumin yace  "Ahh tofa kace aiki be ƙare ba, dan Allah gimbiyarmu ki halarci bikin nan Please, kece gishirin bikin nan Please" Murmushi tayi seda haƙoranta suka Bayyana, tace  "idan har ina raye kasa a ranka naje taron bikinka, dan bana karya alƙawari" Ba laifi sun sha hira sosai, Sannan mutumin nan ya tafi. Abba kuwa shiru shiru, ya dinga sauraren kira yaji ance Amira ta dawo, amma shiru gashi haryanzu yana yawan mafarki da Ƙanwarsa, akan ya kula da 'yarta karta lalace, abun se damunsa yake ya rasa inda zesa ransa, gashi ta kasa ta tsare akan lallai ita baza'a kawo mata Amira gidanta ta zauna ba, shi dai Abba bece komai ba ya cigaba da yiwa iyayen Amira addu'a, da fatan duk inda take Allah ya karkato hankalinta ta koma gida, dan yana nadama akan rashin tallafar rayuwar Amira, dukda a yadda ya gani dangin mahaifinta sunyi ƙoƙarinsu akan taribiyyarta amma ta lalace, ƙila suna takurawa ne gurin tarbiyyar shiyasa ta kangare musu. Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, hall ya kai hall, ƙaton hall ne wanda yaji kayan ado sosai, ba ƙarya ma halarta taron 'yan hutu ne, ankon dake jikin 'yan matan dana iyaye ze tabattar maka da masu kuɗi ne, gashi da yawansu farare ne tas kamar basa shiga rana. Tuni manyan mawaƙa suka fara baje kolin baiwar murya da Allah subhanahu wata'ala yai musu, Ango da amarya tuni suka iso, tun a hanya yake kiran waya yaji idan su Amira sunje, amma aka sanar masa basuje ba. Ango da Amarya na zuwa gurin taron, hall ya ƙara yamutsewa, da ɗaukar hotuna da shagulgula kala kala. Da mota akaje aka ɗakko su Amira, harabar gurin kawai abun kalloce, Amira ta tsaya tana ƙarewa harabar gurin kallo, doguwar rigar abayace a jikin Amira, ta yafa mayafin a kanta, sannan ta saka face mask ba a iya gane fuskarta, suka sakko daga motar, har zasu shiga gurin wayar Amira ta fara ringing, tace su shiga zata biyo bayan su. Ta ɗaga wayar ta saka a kunnenta "Hello Amira, ina kika shiga ne, naje gida yau ance bakya nan, gashi Abban  Kaduna yanata kiran waya yana tambayar kin dawo?" Amira tace  "meye nasa na inda na tafi? Meye damuwarsa bayan ɗansa daya tura shine kuma ya wanke ƙafa yaje da kansa?" "Amira Yanzu dai kina ina ne? Nazo gida ance kwananki huɗu bakya nan, ina zuwa akace an san ina da lambar ki, in kira inji kina ina?" Amira tace "somewhere in the world" "Wane Irin somewhere in the world? Amira kina ina?" "Anty Fa'iza kin dameni fa, ina ruwan wani da inda na tafi naje in huta ne" "Malama ɗan matsa kinzo kin cikewa mutane hanya" wata siririyar murya ce tai maganar, Amira ta ɗago ta kalleta daga sama har ƙasa, ta ɗauke kanta ta cigaba da wayarta. "Malama Magana fa nake miki" Budurwar ta sake maimaitawa, Amma Amira tai burus da ita. Yunƙurin sake yiwa Amira magana tayi, amma Amira cikin tsawa tace "ke dalla karki isheni, jiki a bushe ke ba ƙiba ba, amma kin isheni wai na cike hanya, in bazaki wuce ta nan ba shikenan" Ta kalli Amira tace  "ke ɗan saurara mana, wama ya gayyaceki gurin nan har kike nema ki gayamin Magana ne iyee?" Amira cigaba da wayarta tayi, dan yadda ranta yake a ɓace ɗin nan zata iya buga wannan shashashar da ƙasa. "Amira keda wa kike magana ne?" "Anty Fa'iza, dan Allah kiyi haƙuri, sanin inda nake bashi da amfani, idan kin sani ma ranki ne ze ɓaci, se anjima kawai" Ta kashe wayar ta shiga hall ɗin, ashe tunda su Sultan sukazo ake mata kirari, ake koɗata Sultan na hangota ya ƙarasa inda take yace  "Amira ki hanzarta mu ake jira tun ɗazu fa" Bata tanka masa ba, taje ta cire abayar jikinta, seda aka kashe fitala na wasu 'yan lokuta sannan aka kunno fitilar. Amira ta bayyana akan stage, kamar kullum idan zatayi rawa, a tsuke take a cikin riga da wando, Attached ɗin nan har ƙugunta, nan fa aka saki kiɗa Amira ta shiga baje kolin rawa, ita da tawagar Sultan, gurin ya ɗau sowa da ihu, nan aka dinga bajakolin kuɗi akan Amira, sam bata jin jikinta, rawata kawai takeyi. Tunda tai tozali da Amira gabanta yai Wata irin mummunar faɗuwa, saboda tsananin kamanin da take da Imran, nan ƙirjinta ya shiga dukan uku uku, wannan yarinyar tana da alaƙa da Imran ne kokuwa dai kawai kamanni ne? Tasan dai Minal sam bata kama da Imran, amma wannan kamanin nasu sun ɓaci sosai. Nan ta shiga tunanin wacece wannan take rawa haka? Meye alaƙarta da Imran. Aka bawa su Amira hutun taƙaitaccen lokaci, kafin a sake kiransu kan stage kowa se jinjina mata yakeyi, na iya ƙwarewarta a rawa. Aka sanar da isowar wani shahararren mawakin kudancin Nigeria, wanda sunansa ya zaga ciki da wajen Nigeria harma da wasu sassa na duniya, shima aka dinga tafi ana masa sowa. Amira tai shiru tana tunanin irin kuɗin da aka liƙa musu, yanzu akwai irin wannan mahaukatan kuɗin, amma idan ba da dalili makamancin wannan ba, baka isa ka cisu ba, an gwammace a zubar dasu a gurin taro dan a faɗa ace anyi, ire irenta masu rangwamen gata, sedai in zasu sauka daga hanyar da ta dace shine zasu samu irin wannan kuɗaɗen. Tana cikin tunanin ne taji an dafata ta baya, ta juya taga yarinyar ɗazuce da suka haɗu a bakin ƙofa, sedai bata gane Amira ba saboda ɗazu Amiran ta saka mask. "Sannu da ƙoƙari 'yar uwa gaskiya kin burgeni sosai" Amira tace "Nagode" "Amma dan Allah ko zan iya tambayar ki wani abu?" Amira tace "No ba shi nazo yi ba" Tai gaba ta bar Ihsan a gurin a tsaye. Aka kira wannan shahararren mawakin ya hau kan stage, ya karɓi mic ya fara zuba waƙa shima, mawaƙin na daga cikin manyan mawaƙan da Amira ke sauraren waƙoƙin sa, from no where Amira ta fara bin salon waƙar tasa tana rawa, aikuwa abun ya ƙayatar dan rawar ta hau sosai da waƙar da yake yi. Ba ƙaramin burgeshi Amira tayi ba, ƙarshe dai tare sukayi performance ɗin shi da Amira, shi yana bake basirarsa ta waƙa Amira na baje tata a fannin rawa. Biki yayi biki, Amira ta samu kuɗi sosai da sosai, mawaƙin nan yazo ne yayi mintuna talatin ya tafi, amma se gashi ya zarce lokacin daze bar gurin. Ya karɓi mic yaiwa Ango da amarya fatan zaman lafiya, sannan ya yabawa Amira irin baiwar da take dashi, haryake cewa be kamata ta ɓoye baiwar da Allah yai mata ba (🙄🙄🙄 masu ziga mutane suna tamɓele, duka wata baiwa idan ba ta addini ba shirme ce) Ya ƙara da cewa zata iya zama wani abu da wannan rawar da ta iya haka, ya jinjina mata ya yabawa ƙoƙarinta da yadda ta burgeshi sosai. A take ya nemi yaga Amira a kan stage, Amira ta basar ta fito kan stage ta tsaya, mawaƙin yai alama da a miƙo masa wani abu, aka miƙo masa abu a ƙaramin kwali. Yana buɗe kwalin ya fito da mukullin mota, ya miƙwa Amira seda ta tsaya tana kallonsa ya sake miƙa mata, murmushi tayi sannan ta miƙa hannu ta karɓa, ya miƙa mata hannu su gaisa, amma ta girgiza masa kai tace  "I am Muslim" Nan ma aka cigaba da cecekuce, da taya Amira murnar kyautar mota data samu a gurin, banda kuɗin liƙi, dan son bajinta haka wasu masu kuɗin suka cigaba da bata kyaututtuka. (Ina jin takaicin irin wannan kyauta da ake bawa makaɗa da mawaƙa, bayan tarin malaman da muke dasu, da masu ilimin addini, Yanzu anfi bawa mawaƙa da 'yan film mahimmanci fiye da manyan malamnmu) Mawaƙin nan yasa aka kira masa Amira, suka sake gaisawa yace "a gaskiya nayi mamaki da kikace ke mususlma ce, dama akwai wani video na waƙata da zanyi shooting next week, yarinyar da zan saka tana min wasa da hankali, idan bazaki damu ba ina son inyi featuring ɗinki a waƙar, hakan zesa duniya ta sanki sosai" Amira ta ɗanyi shiru sannan tace  "A ina za'ayi shooting ɗin?" Yace "eh to, zamuyi wani a nan Abuja wani kuma a Lagos, amma ina son zamu fara cover na waƙar, zamuyi hotuna tare za'a saka" "Shikenan, na yadda za'ayi hotu nan, amma fitowa a waƙar se nayi nazari" Yai murmushi yace "zamu iya zama abokai"? Amira ta girgiza masa kai alamar A'a, ta wuce ta barshi a gurin, nan aka finga hotuna da Amira, da ƙyar ta zame suka bar gurin. Abba ba yadda ya iya haka ya koma Abuja, yana sauraren ta ina za'ace masa Amira ta dawo. Yana zaune a Office yana aiki, amma yana ta zancen zuci, buɗe ƙofar Office ɗin akayi tare da sallama, ya ɗago ya amsa. Alhaji Hashim ne yace  "Alhaji Ali, kasan meke faruwa kuwa?" "A'a seka faɗa" "Wallahi hoton wata yarinya ne yake yawo a social media, me matuƙar kama da kai, wani mawaƙi yasaka hotunanta wai ze saka ta a sabuwar waƙa, se haɗa hotonka ake da nata wai anya ba 'yarka bace?" Alhaji Ali yace "Ni kuma?" "Ƙwarai kuwa kamar ku ɗaya sosai, kuna kama, sedai kana ganin yarinyar kaga fitsararriya" Alhaji Ali yace "ni kuwa wacece haka?" Alhaji Hashim ya ɗakko wayarsa ya daddana ya miƙawa Alhaji Ali. Yasa hannu ya  karɓa yana dubawa cikin tashin hankali yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un" Share Please Masu Comments ina godiya sosai da sosai, ina jin daɗin Comments ɗin yana bani ƙwarin gwiwa sosai. Domin gyara, Sharhi ko shawara 07063065680 [1/8, 9:33 PM] Ayshercool:    🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. Afuwan banyi Editing ba                                                               9_10 Abba ya nanata innalillahi wa innalillahi raji'un ya kai sau goma, Alhaji Hashim yace  "Aliyu ya dai? Koka santa ne?" "Hashi akwai damuwa fa" "Damuwar me?" "A game da wannan yarinyar, ba wai wai bane, 'ya ce a gurina, 'yar ƙanwatace data mutu ta bari, gaskiya bazan ɓoye maka ba nafi shekaru biyar rabona da ita, tana hannun dangin mahaifin ta, kawai se a tsukin  kwanakin nan akamin waya akace, tana rashin ji na tura Imran yake ya gano min meke faruwa, yaje ya mata faɗa da jan kunne, ranar da nace maka zan koma gida kano zan tafi, ai gurinta naje ina zuwa suka cemin kwananta kusan huɗu bata gida bsu san inda take ba, na bar saƙon da zarar ta dawo a kirani a waya a sanarmin, kawai se gashi kazo min da wannan hoton, kuma wallahi kwanakin nan kusan kullum senayi mafarki da mahaifiyar ta tana min magiya a kan kar in bar 'yarta ta lalace, nayi Nadamar rashin bawa yarinyar nan mahimmanci, kuma abunda ya janyo haka naga dangin babanta na matuƙar ƙoƙari akanta" Alhaji Hashim yace "aikuwa da matsala, dan abokan adawa zasu iya amfani da wannan damar gurin yamaɗiɗi da kai a bakin duniya, musamman za'abi diddigi a gano alaƙarka ds ita, da kuma yadda ka gaza kulawa da ita, harta zama haka, dan wannan yarinyar tana kama da kai fiye da yadda take kama da 'ya'yanka" "Hashim yanzu meye abunyi dan Allah?" "Abunyi dai kam dole a nemo shi da gaggawa, yanzu duk yadda za'ayi a tabattar an samo inda yarinyar nan take, dan ance jiya akayi hotunan a gurin wani biki a Abuja, kuma shi mawaƙin ya bata kyautar mota" Alhaji Ali yace  "A Abuja akayi bikin?" "Eh a can ne, a gurin akayi hotunan" "To yanzu a ina zan gano yarinyar nan ni kuwa, bana son inyi wani kyakkyawan motsi daze sa 'yan Adawa su farga da halin da ake ciki" Alhaji Hashim yace "kabi komai a sannu, zamu shawo kan matsalar Insha Allah, zan sa a duba min nan Abujan, za'a ganta insha Allah" "To Allah yasa" Ɓangaren Amira kuwa, sunyi hotuna da mawaƙin nan, sedai sunyi hotunan ne tana sanye da atamfa da kuma jallabiya, sunyi kyau sosai, sedai wanda akayi agurim party ne take sanye da riga da wando. Sultan yana ta sake zigata akan ta amince da maganar mawaƙin nan, a fara haskota a cikin raye raye, zatayi kuɗi da kuma suna a duniya, ita dai bata amsawa Sultan ba, ƙarshe ma cewa tayi ya bata guri zata kwanta dare yayi. Kamar yadda ta buƙata, bayan fitar Sultan, ta shiga tai wanka ta saka kayan baccinta, ta hau gado ta kwanta, Amma gaba ɗaya kewar gida ta dameta sosai, dukda gidan nasu ba wata tsiyar suke tsinana mata ba, amma tana son komawa gida gaba ɗaya garin ya isheta. Ji tayi ana knocking ɗin ƙofarta, ta duba agogo ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare, tayi zaton Sultan ne dan haka ta miƙe ta zira hijjabi, ta tafi buɗe ƙofar, tana zuwa bakin ƙofar tace  "waye?" Daga waje taji muryar namiji yace "buɗe ki gani" Ba fargabar komai ta buɗe ƙofar, Ango ne da kansa a wannan daren, ta kalleshi tace "lafiya na ganka a nan a wannan daren?" "Haba ki bari in shigo mana Magana zamuyi" Ta bashi hanya ya shiga, yana ƙoƙarin shiga bedroom ta tsayar dashi tace "karka shigarmin bedroom, meya kawoka a wannan daren?" "Haba Amira meye na wani kar ins higa bedroom, anyway harkar arziki ce ta kawoni" "Ina jinka" ta amsa tana ƙare masa kallo. "Kinga jiya a gurin nan ba ƙaramin kasuwa kikayi ba, manyan mutane nata naman contact dake, ciki hadda manyan masu muƙami a ƙasar nan, wanda zaki samu kuɗi fiye da wanda kika samu jiya a gurin bikin nan" Amira tace "ina jinka" 'to shine mazo muyi yarjejeniya" "Tame fa?" "Zan haɗaki da manyan mutane a garin nan, amma sekin yadda dani tukuna?" "Yadda kamar yaya kenan?" "Waike seki ta wani abu kamar ba 'yar hannu ba, kawai ki amince dani ehh kin gane karatun dai" Amira tai murmushi tace "wannan ai me sauƙi ne, muddin zaka haɗani da Manyan mutane, kuma gashi za'a kai maka amarya gobe in Allah ya kaimu Amma ka taho gurina, Nagode ƙwarai dama ina neman me tayani kwana, damuwa ta isheni" Yai murmushi yace "Allah my mirat?" Yai maganar yana matsowa kusa da ita da ƙoƙarin taɓa ta, Amira tace  "Yanzu ace duk yadda amaryarka ta sha gyara, wani ya kai mata farmaki kamar yadda kake shirin yi yanzu ya zakayi?" Yace  "ahh haba dai, ai babu me yasa n wannan gangancin, duk wanda yaima zan iya hallaka shi" "Amira ce banza kenan ko?" "Ahh no, Amma aike kin saba yi shiyasa nima nazo, kuma ai hanyar Alkhairi zan miki" Amira tace "ƙwarai kuwa nina saba yi kam, dan san'ata ce anyway, shiga ka watsa ruwa kafin nan na shirya" Ba tunanin komai ya shiga murna, ya tuɓe daga shi se gajeren wando ya buɗe toilet ya shiga, yana shiga ta maida key ta waje ta rufe shi a cikin banɗakin Ta tattara kayanta tsaf a Akwatinta, tana jin yadda yake jijjiga ƙofar ze fito amma yaji a rife, ta haɗa kayanta tsaf, ta kwashe agogonsa takalamansa, hula wayoyi da mukullin motarsa da komai na aljihunsa, na kuɗi da ATM cards ɗinsa ta bar ɗakin ta kulleshi ta waje a ɗakin, tai ficewarta. Ta fice daga Hotel ɗin, ta dinga tafiya ba tare da tasan inda zata ba, seda tayi nisan gaske da Hotel ɗin sosai sannan ta tsaya, ta cire sim cards ɗin wayoyinsa ta kakkarya ta zubar, ta kira wayar Sultan, tai sa'a kuwa ya ɗaga yana ɗaga wa tace  "Sultan, duk abunda kuke ku bar Hotel ɗin nan, Asubar fari ku hawo motar da aka bani ku bar garin nan, dan ni bana Hotel ɗin yanzu haka" Cikin mamaki Sultan yace "Amma saboda me? Meke faruwa?" "Akwai matsala ne, idan kuma kuka zauna za'azo a kamaku a banza ba ruwana" Tana gama maganar ta kashe wayarta, tayi searching a wayarta, inda wasu Hotels ɗin suke, ta samu abun hawa ta tafi wani Hotel ɗin can nesa da gari sosai, taje ta kama ɗaki ta kwana a ciki. Ɓangaren Ihsan kuwa duk yadda taso samun Imran a waya abu ya gagara, tun ranar da taga Amira hankalinta yaƙi kwanciya sam. Yanzu ma gwada layinsa take amma baya shiga, ta koma what's app ta masa Magana. Kamar mintuna biyar dayi masa magana taga ya amsa. Ta sake tura masa saƙo kamar haka "Ina ta trying layinka amma baya shiga, baka kirani ba kuma' "Am sorry, muna cikin daji ne, amma muna hanyar fitowa zamu kwana, gobe insha Allah da safe zamu fito dajin ne ba network sam" "Shikenan, ina fatan kana lafiya ƙalau" "Lafiyata ƙalau, jibi in Allah ya kaimu zan dawo gida, zan ɗau hutu na Aure da zanyi" "Kai amma nayi farinciki my own, Allah ya kawomin kai lafiya" Imran yace "Ameen, kin koma gida daga gurin bikin ne?" "A'a, ranar laraba zamu koma, dama ina ta son tambayarka wani abu, wallahi wata nagani a gurin bikin nan, me matuƙar kama da kai, hankalina ya tashi sosai dana ganta" "Ni kuma? Wacece wannan haka? Kuma meyasa hankalinki ya tashi?" "Kawai ji nayi ba tayimin ba, bana ƙaunarta sam, wata fitsararriya da ita kuma ni ban taɓa ganinta a Family ɗinku ba, sedai kamar da kuke ta ɓaci" Imaran yace "ikon Allah se kallo, nikam ban san wata me kama dani ba, da zata Abuja gurin biki" "Ka zata wasa nake ko? Bari in turo maka hotonta ka gani" Nan Ihsan ta tura masa hotunan Amira, da videos harda wanda tayi da wannan mawaƙin. Imran ya jiya hotunan nan, babu ko tantama Amira ce, hotunan ta ne ba wata ba, take yaji ransa ya ɓaci sosai zuciyarsa har tafasa take, gantalin nata harya kai ta tafi Abuja? "Ya naji kayi shiri bakayi reply ba?" Imran yace "gaskiya ban santa ba, kawai dai ikon Allah ne nima naga muna kama sosai, amma gaskiya ban santa ba" Ihsan tace  "har hankalina ya ɗan kwanta, dan nayi zaton wannan cousin ɗin taka ce da kace min tana Kano" Gaban Imran ya faɗi, amma yace "meyasa kikayi zaton itace?" "Naga kuna kama sosai ne, kuma kace min tana yawo bata jin Magana shiyasa" Imaran yace "hakane, amma ai na gayamiki ita waccan yarinya ce, bsta kai wannan ba" "To ai itama wannan ɗin ba wata babba bace, dan dai tana da jiki ne" Imran yace "naga alamar rigima kawai kike ji, ki kwanta seda Safe Allah ya tashemu lafiya, sena dawo" Ya rufe datar sa, yai shiru yana sake nazarin hotunan Amira, ga video da aka bata kyautar mota, ga na rawa da tayi a gurin, yai ajiyar zuciya, gaba ɗaya ransa ya gama ɓaci yama rasa abunyi kwata kwata. Da Asubar fari Amira ta bar Hotel ɗin nan, ta kakkarya ATM ɗinsa ta watsar, ta tafi tasha taje ta hau Mota, gaba ɗaya fargabar kar a saceta a hanya ta kau a zuciyarta, babban burinta kawai ta bar garin Abuja. Ƙarfe takwas na safe tuni sun kamo hanyar Kano, suna tafe tana Addu'a Allah ya kaita gida lafiya. Sultan ma tunda Amira tai masa gargaɗi, ana sallar Asuba suka hau motarta da aka bata suka bar Hotel ɗin da suka kwana, suma suka kamo hanyar Kano, Suna tunanin wace cakwakiya Amira ta haɗa haka, wadda ta sakasu barin gari ba shiri. Shikuwa Ango yana banɗaki a rufe, ya jijjiga ƙofa ya buga ƙofar amma ba wanda yaji, saboda ta kulleshi Sannan ta kulle ɗakin, tun yana bugawa da ƙarfi harya haƙura ya nemi guri ya zauna a banɗakin nan ya kwana har gari ya waye, yana nan zaune yana tunanin yadda zeyi ya bar gurin nan, tare da zargin kansa yadda ya faɗa tarkon Amira da wuri haka, yayi mamakin Yadda Amira ta yaudare shi haka, babban abunda ya dame shi shine yadda yasan ana can ana jiransa gurin tafiya ɗaurin Aurensa. Gurin ɗaurin Aure kuwa ana ta neman Ango, an nemeshi sama da ƙasa an rasa, an kira layinsa ba adadi amma taƙi shiga, ga lokaci yana neman ƙurewa ba wanda yasan inda ya tafi sam. Amira kuwa kafin sha biyun rana tuni ta isa garin Kano, tana shiga Kano tayi kyauta da kayan Ango Hassan a danja, ta bawa mabaratan danja kayan, hatta kuɗinsa da ta kwashe a hanya tai kyautar su (sadaka da kayan Sata 🙄😲) Ko gida bata je ba ta wuce gidan Anty Fa'iza, Anty Fa'iza ta kalleta tace "sannu" Amira bata amsa ba ta ajiye kayanta, ta kamfaci ruwa ta shiga banɗaki, zuwa tayi ta watsa ruwa tai wanka, ta shiga Kitchen ɗin Anty Fa'iza ta zuba Abinci taci, seda ta ƙoshi ta samu guri tai kwanciyarta, bata kula Anty Fa'iza ba ita m bata kulata ba. Se bayan azahar Sannan ta tashi, tai salla, Kiran Sultan ne ya shigo wayarta, ta ɗaga tace "ya ake ciki ne?" Sultan yace "muna Kano tun ɗazu, amma meyasa kikace mu dawo haka ba shiri?" Amira tace "ba ruwanka, tunda ka dawo lafiya shikenan, na zaci za'a kamaku a hanya ma, saboda ba'aiwa motar license ba, yanzu dai so nake ka samo me siye, a saida motar nan a bani kuɗi na" "Amma meyasa zaki siyar?" "Saboda ba tare aka bamu ba, ka saida mota ka aikomin da kuɗina, sannan ka haɗomin da kuɗina na gurinka" "Shikenan, yadda kike so, za'a duba me siyan" "Yawwa" Amira ta katse kiran. "Yanzu Amira seda kika je Abujan nan ko? Duk kafafen sada zumunta babu abunda yake yawo banda hotunan ki, Amira shifa rashin ji bashi da rana, Sannan kuma bashi da riba, yanzu hotunan ki se yawo suke gaki ga Arne, ga kyautar mota, ke bakya gudun bakin mutane Amira? Bazaki riƙe maraicinki ki tsuguna in da Allah ya ajiyeki ba ko Amira?" Ko ɗaga kai Amira ba tayi ba, balle ta tankawa Fa'iza tai mata banza, kamar ba da ita take ba. Fa'iza ta kira Usman a waya ta gaya masa ga Amira ta dawo tana gidan ta, suna gama wayar, Usman yaje ya gayawa Yadikko. Baba yace  "bari a kira kawunta a gayamasa, gata ta dawo" Yadikko tace  "kul, kar wanda ya sake ya kirashi ya gaya masa, idan fa kuka gaya masa yazo, to ɗauketa zeyi ya tafi da ita, idan kuma ya tafi da ita shikenan, nikuma sonake wannan ɗan nasa ko shi su dinga zuwa, saboda a samu su Auri wata daga cikin yaran nan" Umma tace "to yanzu Yadikko baza'a ce musu gata ta dawo ba?" Yadikko tace  "baza'a faɗa ba, ai gara ta ƙara baƙin jini a idonsu, yadda bazasu ɗauketa su haɗa da 'ya'yan su ba" Haka kuwa akayi, babu wanda ya kira su Abba yace ai Amira ta dawo, sedai tuni hotunan ta sun zaga ko ina, ta zama topic of discussion, ko ina zancenta kawai akeyi, labari ya cika inguwarsu hadda batun motar da aka bata. Ango Hassan kuwa an bada cigiyarsa har gurin 'yan sanda, ana zaton ko sace shi akayi. Ma'aiktan Hotel sukaje da safe gyara ɗakin Amira, Amma suka tarar a rufe, sun zaci ta fitane, suka tafi, da yamma ma ɗakin a rufe har dare, aka ɗakko mukullin ɗakin aka buɗe sedai ba kowa a cikin ɗakin. Jin an buɗe ɗakin yasa Hassan a dinga jijjiga ƙofar banɗakin yana ihu, wanda zeyi sharara ya fita da gudu, yaje ya tattaro ma'aikatan Hotel ɗin, akazo aka buɗe sega Hassan a cikin banɗaki, daga shi se gajeren wando, jikinsa se tsuma yake saboda wahala. Nan aka shiga kallon kallo, dan gaba ɗaya labarin ɓatansa ya fara zaga gari, gashi ba wanda be san anyi bikin ba, kasancewarsa shahararrene, amma abun mamaki se gashi a Hotel, ya kwana a banɗaki. Haka aka samo masa kaya ya saka, yana ƙudurce irin wulaƙancin da zewa Amira idan ya haɗu da ita, shikenan mutuncinsa ya zube a idon duniya. Abba kam komai ya ƙwace masa, ya rasa mene mafita akan wannan lamarin, yana son yasa a duba masa Garin Abuja a nemo Amira, Amma yana tsoron a gane suna da alaƙa da ita, ko ta fuskanci ana nemanta ta gudu. Imran kuwa tuni ya sauka a Kaduna, ya sauka cike da takaicin yadda Amira ke nema ta zubar musu da mutunci, dan shima yaga yadda hotunanta dana Mahaifinsa ke yawo, ana tambayar anya ba 'yarsa bace. Koda Imran ya koma gida ya lura da damuwar dake kwance a fuskar mahaifinsa, sedai be masa maganar Amira a gaban Ammi ba, dan kar tayi faɗa, dan tun da ya dawo take masifa akan Amira, Abba dai be tanka mata ba, se tunanin mafita da yakeyi. A masallaci Imran ya samu Abba suka taho tare, Imran yace  "Abba naga kana cikin damuwa, meke faruwa ne?" Abba yace "Imran maganar Amira ce, wai yanzu har arnan nan na kudu mawaƙa take hotuna dasu, gashi ana haɗa hotuna na da nata, ana tambaya anya ba 'yata bace? Idan abu ya fito zanji kunya na gaza kula da yarinyar nan harta zama haka" Imran yace "wai dama Abba kai ma ka gani?" "Eh Imran na gani, an nuna min tunda na gani na kasa samun nutsuwa, har Kano naje bata gidansu, nace in ta dawo a kirani, kawai naci karo da hotunanta a gurin biki a Abuja, bikin ɗan Professor Latif" Gaban Imran ya faɗi, ta tabbata Ihsan da Amira ta haɗu kenan? Ya dake yace  "to yanzu Abba meye abunyi kenan? Yakamata a samu mafita da gaggawa" Abba yace "munyi maganar da Alhaji Hashim, yace in saurareshi kuma naji haryanzu bece komai ba" "Abba ba zamu tsaya jira ba, yakama yarinyar nan duk inda take a nemo ta" Abba yace "A'a, bana son garaje Imran, mubi komai a hankali ka bari zuwa Gobe in Allah ya kaimu inyi magana da Alhaji Hashim, nasan yasa a duba ta a Abuja ne" Imran yace 'to shikenan Abba, bari muji me zece ɗin, amma ina tsoron taje ta kuma janyo mana wani abun tereren" "Karka damu, insha Allah ba zata kuma wani abun ba, muyi mata Addu'a Allah ya shirya ta" Ai shi Imran ba shiriyar Amira ce ta dameshi ba, yadda ze hukunta ta kawai yake tunani, suna zamansu lafiya zata janyo musu abun faɗa a duniya. Koda suka shiga gida, Imran ɗakinsa ya wuce Abba kuma ya shiga cikin gidan. A falo ya tarar da Ammi da Minal, suna hira Ammi na kallonsa ta share shi, Minal ce tace "Abba sannu da zuwa" Yace "Yawwa Minal sannunki" Tace "Abba me invitation ya kawo fa, an kai maka ɗakinka, saura zanje in karɓo gobe in Allah ya kaimu zamu karɓo namu, zamu kaiwa Anty Ihsan" Abba yai murmushi yace "Masha Allah, to Allah ya kaimu goben Lafiya" Daga nan ya wuce ɗakinsa, Minal tace  "Ammi wai meyasa baki kula Abba ba?" "Ke ƙyaleni da maganar uban nan naku, yana nema ya jajubo mana Matsala" "Ammi matsalar me kuma?" "Wannan yarinyar ce ta tsaye masa a rai, take gagara shine nima zezo ya ɗagamin hankali, naga yana take taken yaje ya ɗakkota ya dawo da ita gidan nan, shiyasa na ja da baya na zuba masa ido, in ga iya gudun ruwansa karma yaga fuskar daze kawo min wannan yarinyar gidan nan" Minal tace "taɓɗijan, Ammi cewa fa ake karuwanci take, kinga hotunan ta kuwa a media"? "Ai shiyasa na zuba masa ido inga iya abunda zeyi" Minal tace  "Wallahi Ammi karki yadda akwo miki karuwa wallahi" "Barni da shi kawai, ai ya dena ganin walwalata har sena ga matakin daze ɗauka a kan lamarin" Imran se tunani yake akan meye mafita akan lamarin Amira, kar maganar ta cigaba da bazuwa a ɓata siyasar mahaifinsa, kuma kimarsa ta zube duniya ta zage shi. Wayarsa ce ta fara ringing, yana jin ringing ɗin yasan Ihsan ce. "Hello Masoyi" Imran yace  "Na'am masoyiya" "Ka wuni lafiya?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya kike?" "Lafiya ƙalau masoyi, ya naji muryarka wani iri ba lafiya ne? Ɗazu ma da mukayi waya muryarka wani iri, still yanzuma haka" "Bakomai Baby, don't mind ba abunda ke damuna" "Baby ya shirin bikinmu? Ɗazu munyi waya da Meenal, tace an kawo katin ɗaurin Aure ko?" "Eh Ihsan an kawo, za'a kawo miki naki, ina jiran a kawo na party ne in haɗa in kawo miki" "Yanzu ba zaka zi gobe in Allah ya kaimu ba"? "Baby kiyi haƙuri, ina ta shirin bikinmu ne" "My own, naga a gajiye kake bari in barka se Allah ya kaimu gobe, ka kwanta ka huta kaji nawan" "To cwt heart, have a nice dreams Baby" yai mata kiss ta waya. Ihsan ta lumshe ido tace "I love You my Imran". "Love you too baby, am missing you Baby, zan shigo gobe in Allah ya kaimu in ganki" "Wow nice to hear that My Own, wallahi naji daɗi sosai, Allah ya kaimu kazo kaga yadda na fara canzawa saboda gyaran da nake" "Allah Babyna, Allah ya kaimu goben, inzo in gani" "Ameen have a nice dreams Honey" ta ƙarasa maganar tana Sukayi Sallama ya kashe wayar yana murmushi, sedai Amira na faɗo masa ya haɗe rai gaba ɗaya takaici ya mamaye shi. Koda Ammi ta shiga ɗakin Abba, kwanciyar ta tayi bata kula shi ba, Abba ya dudduba invitation na ɗaurin Aure da aka kawo, ya fara tunanin yadda za'a fara rabon invitation ga manyan mutane, wayarsa ce ta fara ringing ya ɗaga "Assalamu alaikum Alhaji Hashim" "Wa'alaikum salam, Alhaji Ali yarinyar nan fa ta bar garin Abuja, na sa Anyi bincike a ɓoye, bata Abuja, nace kuma can gidan nasu ba'a ce maka ta dawo ba?" Abba yace  "Gaskiya basu kirani ba" "To yanzu dole mu nemi abunyi da wuri, ka shirya gobe in Allah ya kaimu ka shirya muje Kanon muje mu san yadda za'ayi a neme ta a Kanon, kuma ina son inga yarinyar nan dan a gano meye bakin zaren" Abba yai ajiyar zuciya yace  "Shikenan, Allah ya kaimu goben, zamu haɗu insha Allah se muje muga yadda za'ayi" Alhaji Hashim yace "to Allah ya bada goben". Ammi tana jinsu tai juyi taja tsaki, ta gyara kwanciyarta. Abba ya kalleta ya ɗauke kai, shima yaja Guri ya kwanta. Seda Safe Abba ya sanar da Imran, zasu kuma tafiya Kano, Imran be musawa Abba ba, ya shirya suka biya ta Gidan Alhaji Hashim, suka ɗauke shi suka kama hanyar Kano. Suna cikin tafiya Ihsan ta kira Imran a waya, yana ɗagawa tace  "My Own ka tahone? Ka ganni nan na maka kwalliya, na maka girki ka taho da wuri Please" Imran yace  "Amm, amm very Sorry Ihsan, Na tafi raka Abba Kano ne" "Kano kuma?" "Eh Kano Ihsan, zamuje gurin wannan cousin ɗin tawa dana gayamiki" "Again, Amma Imran me kuma zaka kuma zuwa yi gurinta? Me zakayi mata hakane? Nikam kodai akwai abunda kake ɓoyemin ne?" "Calm down mana, ba abun ɗaga hankali bane, ki kwantar da hankalinki kina jina?" 'kaga ƙyaleni dan Allah, nida tun farko baka cemin zaka zo ba da duk ban sa rai ba" Kawai ta kashe wayarta, Alhaji Hashim da Abba hankalinsu na wani gurin, basu san me Imran yake a waya ba, da yake na gaba a kusa da direba, su kuma suna baya. Imran ya ajiye wayar ya dafe goshi, baya son ɓatawa Ihsan rai, kuma da alama tana kishi ne sosai, gaba ɗaya haushin Amira ya ƙara kamashi, duk a dalilinta komai nasa na kwaɓewa, kamata yayi yanzu yana can ya fara rabon IV, amma yana nan yana gantalin inda za'a gano ta. A ɗakin Yadikko aka sauke su, Su Amina se kaiwa suke suna komowa, a tsakar gidan nan saboda su Imran, Amma gaba ɗaya abunda ya kawosu shine a gabansu, wato yadda za'a ga Amira. "Alhaji Ali, batun wannan yarinyar fa se Addu'a kawai, dan haryanzu babu wanda zece ga inda take, sedai a koma gefe a cigaba da Addu'a" Alhaji Hashim yace "to yanzu ina da ina take zuwa, kamar ƙawaye ko 'yan uwa haka, dan gaskiya akwai buƙatar a gano inda take a nan kusa, saboda idan hotunanta suka cigaba da yawo, kuma ta cigaba da fitina akwai matsala, na farko siyasar Alhaji Ali zata taɓu, kuma ita kanta yarinyar yakamata a temaki rayuwarta" Yadikko tace "to yanzu waya san inda a tafi? Kufa kuka zo da labarin a Abuja tai wannan hotunan, har da kyautar mota ta samu, mufa gaba ɗaya ta gagaremu tafi ƙarfinmu, bata ganin kowa da gashi, dan da tana ganin mutuncinmu da bata tsallake ta bar gidan nan ba tare da ta sanar da inda zata ba, zubar da ciki tayi ko warkewa ba tayi ba tasa ƙafa ta kuma tafiya" Dukda Imran a ƙule yake da Amira, amma yaji hasuhin yadda Yadikko ke ƙara tonawa Amira Asiri  a gaban Alhaji Hashim. "Amm yanzu ba batun wannan ake ba, ina da ina take zuwa, suwaye ƙawayenta"? "Ai ita ta san inda suke haɗuwa da ƙawayen nata, dan duk irinta ne ita tasan inda take zuwa ta haɗu dasu, dan babu iyayen arzikin da zasu bar yaransu suyi mu'amala da ita tunda ga rayuwar data zaɓa, yanzu haka bance tana garin nan ba tana can inda ta tafi gantalin nata data saba, dan da..... "Assalamu alaikum" Amira tai sallama. Domin gyara Sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 . [1/10, 2:59 PM] Ayshercool:                         🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. Afuwan banyi Editing ba                                        11_12 Amsa mata Sallamar sukayi, ta shigo ɗauke da jakarta ta matafiya, Imran na jin muryarta ya miƙe ze fito, Alhaji Hashim ya riƙe shi yace "Imran, kabi komai a hankali" Imran ya jinjina kai ya fito, Abba cewa Yake "Imran yi a hankali, banda fushi nan naka" Imran Yana fitowa sukayi ido huɗu da Amira, seda cikinta ya juya amma tai banza kamar bata ganshi ba, tana ƙoƙarin shiga ɗakinsu. "Ke daga ina kike?!" Yai mata wata razananiyar tsawa, seda ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, amma tai banza da shi, ta fasa shiga ɗakin ta ajiye jakarta a tsakar gida, ta samu guri ta zauna tana tauna cingam ɗin bakinta, tana jiran Imran yai mata duk abinda yaga dama. Alhaji Hashim ne suka fito tare da Abba, Amira ta ɗaga kai ta kallesu, sedai kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, saboda yadda take jin haushin Abba daga shi har iyalansa, haushinsu take ji. Alhaji Hashim yayiwa Imran alama da ido sannan ya kalli Amira yace  "Masha Allah, ashe wannan ce 'yar tawa da kake bani labari, tubarkallah gata me kyau kamarka ɗaya da ita, a bamu tabarma mu zauna daga nan mu gaisa da ita" Yai maganar yana nazarin Amira, kasancewar sa masani a fannin kimiyar sanin halayen ɗan Adam. Kana ganin shigar jikinta zakaga fitinaniya, bata kuma kallonsu ba ta ɗauke kanta tana wasa da yatsun hannunta, Imran kam kamar ya ɓarar da ita haka yake ji. Aka miƙo tabarma Abba ya shimfiɗa suka zauna, ita kuma Amira na kan turmi, ganin sun zauna ita kuma tana sama, yasa ta miƙe zata bar gurin. Alhaji Hashim yace "ina kuma zakije?" "Ɗakinmu mana" ta bashi amsa kai tsaye, shi dai Abba yakasa cewa komai se binsu da ido. Alhaji Hashim yace "haba Amira muda muka zo ganinki se kuma ki tafi ki barmu?" Amira tace "Niba gurina kuka zo ba, kunzo gurin mutanen gidan nan ne, dan a gaya muku halina kuma an zauna an gaya muku komai, kuma in zuwane ai a baya Yakamata azo a ganni ba a yanzu ba" Tai maganar ƙwalla na taruwa a idonta. A hasale Imran yace 'Ke ana miki magana zaki yiwa mutane rashin Kunya?" "Karka ƙara yimin tsawa na gaya maka, akan me ina ruwanka dani? Tunda kazo ban kulaka ba meye nayimin tsawa" Amira tai maganar cikin tsiwa. Imran ya harzuƙa, amma Alhaji Hashim ya girgiza masa kai yace  "Yaya Imran gaskiya ka dena yi mata tsawa, kai baka san lallaɓa ƙanne akeyi ba, ai nan ba barikin soja bane, zoki zauna mu gaisa mana" Tana zumɓura baki tazo ta zauna a ƙasa akan takalmanta. "Ya kika zauna a ƙasa? Hau kan turmin ki zauna mana" inji Alhaji Hashim. "A'a ai bekamata kuna ƙasa ina sama ba" tai maganar tana share hawayen da take ta ƙoƙarin riƙewa. Shiru Abba yayi yana kallonta daga baya yace  "Amira ina wuni" Shiru tayi ta sunkunyar da Kai, ya kuma maimaitawa amma bata ɗago ba kanta na ƙasa. Alhaji Hashim yace  'Abbanki yana gaisheki baki amsa ba" Shiru ta sake yi ta ƙi ko ɗago kanta, Imran yaji kamar ya tashi yayi ball da ita, ana mata magana ta yiwa mutane banza. Kamar wadda aka yiwa dole ta kalli Abba tace "ina wuni?" Yai murmushi yace "lafiya ƙalau, kin dawo lafiya?" Tace "eh" Yace "masha Allah" Alhaji Hashim yace "naji ance har kyautar mota aka baki, ina motar ne mu shiga a maida mu gida a ciki" yai maganar yana murmushi. Ita dai Amira bata san wannan mutumin ba, amma ya fara isarta da magana, amma ta maze tace "Ai nace a saida motar a bani kuɗina, ni bana son Mota" "Eyya baki bari munzo mun gani ba, shikenan tunda kin siyar, da cewa zanyi Allah ya tsare yasa a kashe lafiya, amma tunda kin siyar ba damuwa, amma meyasa kika siyar ba zaki dinga hawa ba ki ragewa kanki zirga zirga, gashi ance ma zaki fara fitowa a waƙa ko?" "Nifa ba wata waƙa da zanyi, kawai dai munyi hotuna ne, kuma ni nafi buƙatar kuɗin akan motar shiyasa na siyar da ita" Abba yace  "Amma Imran ya gayamin ya baki kuɗi, meyasa baki kirani kince in ƙara miki wasu ba kika tafi Abuja" Imran ya ƙure ta da ido cike da takaicim yadda ake wani lallaɓata, ita kuma tana Magana tana tura baki, aikuwa ta ɗago ido sukayi ido huɗuda Imran ta galla masa harara, Sannan tace  "Ni bana roƙo" "To ai babanki ne, babu laifi dan kin roƙe shi" Yadikko kuwa tuni ta ƙule, dan a zatonta za'ai ƙuli ƙulin Kubura da Amira ne, tana zuwa su dirar mata da zagi da cin mutunci, amma taga saɓanin hakan, Alhaji Hashim se lallaminta yake yi, ko Imran ya yunƙura ze mata wani abun, seya hana shi yi. Amira tun tana ɗaure fuska tana amsa tambayoyin da ƙyar, a hankali seta fara sakin jikinta, musamman da Alhaji Hashim, saboda yadda yake mata magana a nutse cikin rarrashi. A hankali Abban ma da take basarwa ta fara ɗan sakin jikinta dashi, amma da sunyi ido huɗu da goga Imran seta Galla masa harara. A nan take gaya musu  "ai ni da banyi niyyar zuwa Abujan nan ba, dole ce ta sani naje" Abba yace "wace irin dole?" "Kuɗi nake tarawa, wanda zasu isheni in tafi ƙasar waje karatu" Alhaji Hashim ya ɗago ya kalleta yana nazarin amsoshin da Amira take basu, dsga bisani yace  "Masha Allah, ai wannan tunani ne me kyau, Allah ya bada sa'a, yanzu dai mun taho da katin bikin Yayanki, mun bawa mutan gidan nan nasu, kema ga naki musamman aka taho miki dashi, ai zakije ko?" Amira ta kalleshi tace "waye kuma Yayana?" "Imran mana gashi a kusa dake" Ɗan ja da baya tayi nesa dashi tace  "Aikuwa wadda zata aureshi zata kwashi mara Imani, kuma ni ba Yayana bane ba, dan nasan baze ci zalin ƙanwarsa da suke ciki ɗaya ba kamar yadda yayi min ba, hadda ze kainin Enugu Sojoji su koyamin hankali, ni bazan zo ba" Tai maganar tana satar kallon Imran, seda Abba yai murmushi yace "ƙyaleshi, dan ƙaniyarsa an gayamasa kowama irinsa ne, taya za'a kaiki wani Enugu, rabu dashi, yakamata ki halarci taron bikinsa" Amira tace "ni gaskiya bana son zuwa inda za'amin wulaƙanci, ko a dinga gayamin magana, bana mantuwa ko an shekara dubu idan ina raye, in dai aka ci mutuncina bana mantawa, shiyasa bana son zuwa, kuma ni gaskiya wannan kallon da yake min tsoro yake bani, wallahi idan naje gidansu ze iya dukana, dan bashi da tausayi" Ba Abba ba shi kansa Alhaji Hashim seda yayi dariya banda Imran da ya sake shan kunu, Alhaji Hashim yace  "haka yake wannan fuskar shanun ai, ki ƙyaleshi ai ba gurinsa zaki zo ba, kuma ba dan shi zaki ba" "Amira tace Ai da dan tashi ne cewa zanyi Al'yasa a fasa Auren, dan bashi da tausayi, ranar da yazo nan ya dinga ball dani da ƙafarsa, kuma nasan bazewa ƙanwarsa ba" tai maganar tana sake yiwa Imran kallon banza. Abba yace "Allah ya baki haƙuri, ni dai fatana kizo ɗin kinji yarinyar kirki, ni zan aiko da mota ma a ɗakkomin ke" Amira tace  "shikenan, naji zanzo insha Allah" "Kin tabattar zaki zo dai ko?" 'bana saɓa alƙawari" ta bashi amsa. Imran kam ya cika yai fam, gashi an hana shi magana, maimakon su Abba su ɗau mataki, sun biye Mata se lallaɓata suke tana shirme. Haka suka cigaba da hira da Amira, mutan gidan ma gaba ɗaya abun haushi ya basu, sun saka ran za'aiwa Amira rashin mutunci da tijara, amma an wani sata a gaba se rarrashinta ake kamar ƙwai akan Dutse. Suna fita Yadikko tace  "Kai Magaji tashi maza ka bisu, kaji me zasuce karka kuskura ka bari a tafi da yarinyar nan, maza jeka kaji me suke cewa" Aikuwa Baba ya tashi, ya biyo bayansu. Amira ta rakasu har gaban danƙareriyar motarsu, Banda Wadda jami'an tsaro suka rakosu da ita. Abba yace  "zan saimiki kayan anko kema a ɗinka miki, za'a ajiye miki idan kinzo seki saka kema" Tace "Hmm gayyar soɗi kenan fa, zanzo da tsummokaran da Allah ya bani, abun masu kuɗi ina ni ina saka kayan da masu kuɗi zasu saka" Amira akwai abun takaici, ana lallaɓata a shawo kanta, tana sake buɗewa, a fusace Imran ya daka mata tsawa yace "ban gurizan shiga mota, Shashasha kawai" Seda ta ɗan ruɗe saboda ko yaya yai mata tsawa seta razana, Imran yana mata kwarjini sosai, shiyasa daya mata tsawa jikinta yake tsuma. Kallonsa tayi ranta a ɓace, annurin fuskarta ya ɗauke ta juya zata koma gida, Abba ya fara yiwa Imran faɗa, ya taka inda Amira take ya ɗakko kuɗi a Aljihunsa ya bata, Amma taƙi karɓa, sema hawaye data farayi kawai ta shige gida. Jikin Abba gaba ɗaya yayi sanyi, Alhaji Hashim yace "Imran da alama tana shakkarka, amma be kamata ka dinga mata tsawa ba, yarinyar da ake lallaɓawa a gano bakin zaren zaka dinga yiwa tsawa haka? Irin wannan yaran ba kowane lokaci ne tsawa ko kurari ke aiki akansu ba, sema dai ya tunzura su, ita tarbiyya ba ko yaushe take buƙatar tsanani da takura ba, wani lokacin seda rarrashi da jan yaro a jiki, wannan yaro faɗa da zare ido baze mata aiki ba, attention take buƙata da rarrashi, yanzu babban abunda yakamata shine mu samu ta zo Kaduna, kar ace za'abi ta tashin hankali da hayaniya, mu bita a sannu, da tazo shikenan" Abba yace "to idan tazo Kadunan meye abunyi na gaba?" *Zan gaya maka, idan na gama nazari" Suna shirin shiga mota su tafi, Baba ya fito ya samesu yace  "Masha Allah, Alhaji baku tafi ba kenan?" Abba yace "eh, amma yanzu zamu wuce insha Allah" "To amma nace ya batun Amiran, wani mataki zaka ɗauka akan lamarin nata"? Alhaji Hashim yai sauri yace  "karka damu, abunda muke tattaunawa kenan, idan mun tsaida maganar abunda ya dace zamu sanar muku insha Allah, amma dai a cigaba da haƙuri da ita dan Allah, mun san ana haƙuri amma a ƙara, zamu san abunyi a kai insha Allah" "Amma ina fatan dai ba ɗauke mana ita zakuyi ba?" "Haba dai, ya za'ayi ku raini yarinya ace za'a rabaku da ita, za dai a duba ne mugani tunda tana son karatu zamu maida ita makaranta, kuma a sama mata koda wata sana'ar ne" Baba yace  "shikenan, hakan babu laifi, Allah ya maida ku lafiya" Suka amsa da Ameen, suka masa ihsani, sannan suka tafi. Suna cikin tafiya Alhaji Hashim yace "amma wannan tsohuwar ba ita ta haifi baban yarinyar nan ba ko?" Abba yace "Eh, kishiyar kakarta ce" Yace "shiyasa no wonder" Abba yace "meka gani?" "A'a bakomai, ni wallahi yarinyar ma birgeni tayi, wannan ba zatayi wahalar saitawa ba da taimakon Allah da jajircewa, rashin ji ne kawai, amma tana da sauƙin hali, sedai akwai mulki" yai maganar yana murmushi. Abba yace "wani sauƙin hali tana wannan aika aika haka?" "Ai zata shiryu insha Allah" Amira kuwa harta shiga gidan bata kula kowa ba, ta shiga ɗakinsu ta zauna tayi shiru tana saƙawa tana warwarewa, tana tuno  abubuwan da suka wuce, da wanda suke faruwa a yanzu. Jiki a sanyaye, ta tashi taje ta ɗauki buta ta shiga banɗaki, ta fito ta zauna a tsakar gida. Amina ce ma ta taho zata shiga banɗakin, Sadiya tace  "ke Amina, kisa gishiri da omo ki wanke banɗakin nan kafin ki shiga, karki je ki tsuguna ki kwashi cuta, dan yanzu likkafa ta cigaba, har da Arna ake iskancin" Yafikko tace "ƙwarai kuwa, kisa Omo ko wanke banɗakin nan da kyau, Allah ɗai yasan me taje ta yayimo mana, karku tsuguna ku kwashi koren Sanyi" Amira tai shiru, kamar bada ita ake ba. "Yo banda rashin mutunci da Akuyanci, ace biye biyen ya wuce kan musulmai, sekin dan gana da kiristoci masu fitsari a tsaye, basa wankan tsarki, basa tsarkin gasu da biye biyen tsiya, amma suma kije kina binsu, Babu abunda ze hana ki shiga banɗaki a kwashi Sanyi, harda ma abunda yafi Sanyi" Suka dinga cashewa Amira, tana zaune tana jiksu bata ce musu uffan ba, kuma bata tashi daga inda take ba. Su Alhaji Ali kuwa, daga gidansu Amira, seda suka tsaya rabon IV ga Manyan mutanensu dake Kano, sannan suka kama hanyar Kaduna,Se bayan la'asar su Abba suka koma, Imran ya sauka a gida, su Kuma su Abba suka wuce wani gurin. Imran ya shiga gida, kai tsaye cikin gidan ya fara zuwa, ya tarar da Ammi a falo, ya zauna yace "Ammi sannu da gida" Ta ɗago ta kalleshi tace "daga ina kake?" "Tare da Abba muke, munje Kano ne rabon IV" "Ƙarya kakeyi, kunje gurin wannan yarinyar ne ko?" Imran yace "Eh munje gurinta, daga nan kuma mukayi rabon invitation, Amma Ammi meya faru?" "Au tambayata ma kake ko? Za'a haɗa kai da kai a munafurceni, yana son ya ɗakko yarinyar nan ya dawo da ita gidan nan, to baze yuwu ba wallahi, bame ajiyemin Karuwa a gida, ina da 'ya Mace a lalatamin ita a banza, baze yuwu ba" "Ammi bafa cewa yayi zata dawo gidan nan ba, hasali...... "Rufemin baki" tai maganar a hasale. Naga kafi goyon bayan ubanka a kaina, kome zeyi seka dinga rufa masa Asiri, koma dai menene a baya ban karɓeta ba ba zan karɓeta a yanzu ba data zama 'yar gagara" Imran dai yai shiru, bece komai ba, taita mita tana faɗa, harta gaji tayi shiru, Sannan ya tashi ya bar falon. "Kai kai kai kai! Waye ya kashe wutar girkin nan? Umma! Umma! Waye ya kashe wutar girkin nan wai" Umma daga ɗaki tace  "kamar yaya? Ki iza wutar mana,  amma se ƙwalamin kira kike" Sadiya tace "bafa mutuwa wutar tayi ba, jiƙa murhun akayi da ruwa" Umma ta fito da sauri, ta nufi gurin murhun, an jiƙeshi sharkaf da ruwa Babu yadda ma ze kama, ga itacen da yake ajiyema wanda ake girkin dashi an jiƙashi da ruwa. Yadikko ce ta fito da carbi a hannunta tace "wai meke faruwa ne, Abincin haryanzu be gamu ba?" Sadiya tace "wane irin Abinci ya gamu an jiƙe murhu da ruwa" Yadikko tace "innalillahi wa innalillahi raji'un, Yanzu ɗan wakem be dahu ba?" "Ina fa ya dahu, yanzu na gama jefawa fa na shiga inyi salla" "Ina Amira take?" Sadiya tace "waya san mata?" "To wallahi itace da wannan aikin, Babu wanda zeyi wannan Haukan idan ba ita ba, shikenan Abincin nan ya ɓaci dan baze ciwu ba" cewar Umma da ranta ya gama ɓaci. Yadikko tace "yanzu idan an siyo wani icen baze ba?" Sadiya tace 'ta yaya zeyi? Tafa jiƙe murhun gaba ɗaya, ta jiƙe itacen da ruwa, yanzu kafin a siyo wani, a hura wutar ai aiki ne jawur, ɗan wake dai ya riga ya gama ɓaci, se a nemi abunyi" Yadikko tace "wannan yaro ko matsiyaciya, an mutu an barmu da jaraba, da masifa ita duk wani abun da za'a ce mata Allah wadaranta shi takeyi, shegiyar yarinya watsatsiya, ta sani sarai babu wanda yaci ko Abinci rana a gidan nan, ni ji nake kamar an kwashemin hanji saboda yunwa, shine ta mana wannan baƙin zaluncin, Allah wadaran wannan sheɗaniyars yarinyar" Usman yace "to ance a lallaɓa wan uwarta ya ɗauketa kowa ya huta, kimce ba haka ba, baza'a ɗauketa taje ta huta ba, dan haka dole mu haƙura mucigaba da kwasar baƙin ciki da takaici, yanzu dai ɗan wake ya ɓaci, sedai a bawa Awaki, kowa kuma yayi ta kansa" Amira kam bayan tayi wannan aika aika, ficewarta tayi tai nata guri, tasan koba komai ta haɗa musu zafi da takaicinta zasu kwana, duk da abunda tayi musun, besa ta huce daga abunda suka yi mata ba, na zagi da cin mutuncinta da suke ba yau ba gobe ba. Imran kam gaba ɗaya beji daɗin Abunda Ammi tayi ba akan maganar Amira, idan bata yadda Amira ta dawo Gidan nan ba an tsareta an sa mata ido ba, to lalacewa kam Yanzu ta fara, duk da shima baya goyon bayan dawowar Amiran gidan nasu, saboda kar tayi silar lalacewar ƙanwarsa, amma be kamata a ƙyaleya ta cigaba da wulaƙanta ba.   Gefe guda kuma ga tunanin Ihsan, wadda a wayar da sukayi ya lura ranta yayi matuƙar ɓaci, dan ya kirata bata ɗaga ba, yana yin Sallar isha'i, ya canza kaya ya tafi gidansu Ihsan. Ya kirata a waya Amma bata ɗaga ba, ya tura mata saƙo  "Ina gidanku yanzu, ina jiranki" Tana ganin message ɗin kamar ta share, amma taji ba zata iya ba, dan haka ta zira hijjabinta ta fito, yana tsaye a jikin motarsa, ya ƙarasa inda take, ta cigaba da tafiya yana bin bayanta har sitting room ɗin da suke zance. Ta samu guri ta zauna, amma ba tace komai ba, seda ya ɗan ƙura mata ido na wasu lokuta Sannan yace "Mu Ihsan dama zaki iya fushi dani haka? Har in kiraki ki ɗaga wayata? Why" Kasa Magana tayi, sedai ta girgiza masa kai. "Anya kuwa kina sona, har naje Kano na dawo tunanin yadda zan ɓullo miki nakeyi, duk na shiga damuwa, kinƙi ɗaga wayata balle inji muryarki hankalina ya kwanta, baki san muryarki ce cikamakim nutsuwata ba? Gaba ɗaya wunin yau haka na wuni ba daɗi, kin dena sona ko?" Da sauri ta girgiza masa kai, "to meyasa kika ƙi ɗaga wayat? Kina fushi dani ko?" Tai shiri ba tace komai ba. "Kiyi haƙuri kinji Babyna, nima ban san da tafiyar bane, ina Bacci da Safe Abba yazo ya tasheni yace in shirya zan rakashi Kano, na kira wayarki a kashe, shiyasa ban sanar miki ba, ko kinfi son in saɓawa Abba ince ba zanyi abunda yace ba?" Girgiza masa kai tayi tace  "ba haka nake nufi ba, wallahi My haka kurum duk lokacin da kace min zaka Kano se inji gabans yana faɗuwa, bana son zuwa kanon da kake yi, kawai se inji kamar wani abu mara daɗi ze faru, wanda ze zama barazana ga Soyayyata da kai" Imran yai murmushi yace "My Wife, kishi kawai ke damunki fa, yarinyar nan na gayamiki halin da takeyi, ta yaya ina da mace kamarki zan kalli wata, duk wasu qualities da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya lissafa game da mace tagari kina dasu, Ubangijin Allah ya baki, tayay zanyi tunanin kallon wata mace? Kinfi kowa sanin bana kalle kalle, kuma ta yaya zan kalli wadda take yawace yawace, kawai Yarinyar ko bana son ƙanwata ce, kuma mun haɗa jini da ita, kinga ba yadda na iya, Akwai alaƙa me ƙarfi a tsakaninmu, amma ni ba wani abu mummuna daze faru akan Soyayyar mu, nibke nake so kawai, kuma ni bayan ke bazanyi wani Auren ba, kin san bana ra'ayin ajiye mata fiye da ɗaya, ke ɗin kawai kin isheni, Amira ƙanwata ce kawai" Gaban Ihsan ya faɗi tace  "Ameera kuma?" Yace "Eh sunanta kenan" Tunawa tayi da Yarinyar da tayi rawa a Abujan nan, kuma itama sunanta Amira, ga kuma kaminin da suke ita da Imran, anya ba itace wannan Amiram ba?. To amma ai ta nunawa Imran ɗin hoton yarinyar, yace shi be santa ba, bashi da wata alaƙa da ita, kawarda wannan tunanin kawai tayi daga ranta, ta barwa ranta cewar, suna ne kawai yazo ɗaya.   Ta kalleshi tace "to ya kuka dawo ya hanyar?" "Alhamdilillah, mun kai invitation ma, Minal tacemin Mummy taje gidanmu Ɗazu ta taho da naku" "Eh taje ɗazu, akan maganar gurin Dinner ne, kuma anyi settling komai" "To Alhamdilillah, ya biki kuma da kikaje, kinyi kyau sosai a hotunan da kika turomin, seda naji kishibya kamani kar wani ya gani ya ƙyasa" Ihsan tace  "hmm ai daga dinner ɗin nan, akayi mother's event washegari, aka fasa auren nan" Ya kalleta da mamaki yace "kamar Yaya aka fasa Auren?" "Ni dai wahsegarin Dinner, Mummy tace lallai mu dawo gida saboda shirye-shiryen namu bikin, se waya akayiwa Mummy ranar ɗaurin Aure wai ba'a ga Ango ba ya ɓata, ana ta cigiya se bayan kwana biyu aka ganoshi a Hotel, yaje gurin Karuwa ta kulleshi a banɗaki" Imran yace "Subhanallah, banda ganganci ga Matarka za'a kai maka, meya kaishi zuwa gurin Karuwa? Meyasa mutane bamu maida Zina komai bane? Muke rintse ido ga bala'in dake cikinta muke abunda muka ga dama?" "Mhmm kaima dai ka faɗa, yanzu duk zancen ya bazu, dan baka hawa social media ne sosai, da ka gani" Imran yace "Abun ba daɗi gaskiya, Allah ya kyauta" Ta amsa da Ameen. Ya sake kallon Ihsan yace "My kinga yadda fatarki ke sheƙi kuwa? Me kike shafawa hakane se ƙyalli kike fa" Rufe fuskarta tai tana murmushi. "Gaskiya nima a bani kayan gyaran jikin im dinha gyarawa, ko kinfi som a kawo miki ni a haka?" Dariya Ihsan tayi tace  "kaji ka, tome zaka gyara ai a gyare kake already my Own" Nan suka cigaba da hirarsu cike da nutsuwa da farantawa juna rai. ***************** "Alhaji Ali, mafita ɗayace ta rage maka akan yarinyar nan, idan ba haka ba wallafa idan abokan adawa suka ɗagoka, to tabbas se sunyi me yuwuwa sun zubar maka da mutunci a idon duniya, se sun watsa siyasar ka" "To meye abunyi yanzu?" Abba ya faɗa cikin damuwa. "Abunyi ɗayane, kaga a yadda na lura da yarinyar nan, kulawa take buƙata, da wanda ze dinga saurararta, tana da ambition me kyau a ranta, tana son karatu, kuma ni banga alamar wannan gidan nasu ana kula da ita ba gaskiya, ni gaba ɗaya Tsarin mutanen gidan bemin ba, da alama ka banzatar da ita a baya, kuma rashin gata yasa ta zama haka, amma idan ta samu gata da janyowa a jiki, ta samu tsayayyen me kula da ita, insha Allah zata nutsu" "To banƙi ta taka ba Hashim, amma wallahi Jamila ba zata bari yarinyar nan ta zauna a gurina ba, tun tana ƙarama akace in ɗauke ta, Jamila yace bazata riƙe ta ba, kuma na lura haryanzu abun yana ran Amira, kuma a yanzu haka ma, bata shiga sabgata saboda kar ince zan kawo Amira gidan nan ta zauna, gaba ɗaya kaina ya kulle" "Ai Ali ka sakarwa matar nan da yawa, ba gidanka bane ko kuɗi kuka haɗa kuka siya, kana da ikon da zaka kawo wanda kakeso ya zauna, amma tunda ka saba mata a haka ba yadda zakayi, seka samu ka aurar da ita nan kusa, inba haka ba kuma wallahi lalacewar da zatayi nan gaba se tafi ta Yanzu, kana ji tana tara kuɗi take zata tafi ƙasara waje karatu, me kake tunani idan ta tafi? Kuma ko a nan ƙasara ka barta, aka nema mata makaranta idan ba ayi dagaske ba, lalacewa zata cigaba dayi, dan haka kodai ka dawo da ita gidanka ta zauna koka aurar da ita" "Ya salam, Hashim wa zan aurawa Amira? Bana son in aurawa wanda ze mata gori ko ya dinga wulaƙanta ta, wallahi ban san ina ƙaunar yarinyar nan ba se yanzu da aka cemin ta lalace, kuma nasan ina da laifi a lalacewar tata, kuma yanzu kullum se nayi mafarki da mahaifiyar ta, tana min magiya" Alhaji Hashim yace "kaga, Asiri a rufe ka Aurawa Imran, ka haɗa masa biyu ai yana da kuɗin riƙesu, in yaso a ɗaura auren karta tare se tayi Istbra'i, ta zauna ko a gidana ne, bani da matsala da maiɗakina, zata fuskanta, a mata gwaje gwajen da duk yakamata" Alhaji Ali yace "Mata biyu lokaci ɗaya, idan nai haka nawa Imran adalci kuwa?" "Ali baka da wata mafita idan ba wannan ba, Duk wanda zaka aurawa Amira Asirinka baze tonu ba, tana jin tsoron Imran, kuma yin hakan kamar Jihadi ne, tunda Addini be haramta ba, amma idan ba haka ba ban san meye abunyi ba" (😂😂😂 Godiya ga masoya, Comment ɗinku ke bani ƙarfin gwiwa da nishɗi, Wato idan kukayi Comments daya girgizani, bana gajiya da typing, amma idan nai posting naji shiru, da na fara typing nake fara hamma in ajiye) Ayi share saboda Allah. Ayi following ɗina a watpad akan Ayshercool7724 Ina maraba da sharhi gyara ko shawara, banda biyoni ace in bada page kaza 🙄 07073065680 . [1/12, 2:04 PM] Ayshercool:       🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. Afuwan banyi Editing ba                                 KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI                                           13_14 Abba yai shiru yana nazarin maganganun Alhaji Hashim sannan yace  "banƙi maganar ka ba Hashim, amma duk da ni na haifi Imran, idan na tursasa masa ya auri Amira, kamar ban masa adalci ba, da ita yarinyar daze aura da fari ba, kuma ina gudun ya wahalar da ita tunda ba sonta yake ba" "Eh to, da wannan dan wannan, amma ka sani, da kai da kaya mallakar wuyane, zaka iya tursasa shibya kyautata mata, kuma koba komai ka isa dashi, saɓanin ka aurawa bare ita, wanda baka isa dashi ba, ni da ina da ɗa babba wanda ya isa aure, ba abunda ze hana in sa ya auri Amira, hakan Jijadi ne se Allah yai maka Rahama, ya goge maka laifin watsi da zumunci da kayi a sanadin hakan" Alhaji Ali yace "hakane maganarka, amma yadda zan tunkari Imran da wannan maganar nake tunani, da kuma mahaifiyarsa, kasan Yarinyar daze aura ɗin yarinyar ƙawartace, kar inje shiya amince, su kuma su ɗagamin hankali" "Da ita da ɗanta a ƙarƙashinka suke, dan haka ka tunkare shi da maganar kaji me zece, nasan baze baka kunya bama" Alhaji Ali yai ajiyar zuciya yace "shikenan Ubangiji Allah ya wuce mana gaba" "Ameen" Ammi na zaune suna hira da Minal, akan yadda Abba ya fita harkarta shima, gashi bata san meyake shiryawa game da Amira ba, tana ta mita tana wassafawa Minal, wayarta ta fara ringing, Minal ta ɗakko wayar ta miƙa mata. Maman Ilham ce take kiranta, ta karɓi wayar ta ɗaga "Hajiya Jamila, maganar kajin nan nayi magana da me kajin, yace 50 pieces zamu samu kawai a gurinsa" "Maman Ihsan a sake dubawa, mu samu su cika ɗari mana, bana son muyi bikin da za'a tafi damu a baki, sonake ayi biki na kece raini, naji Babansa ma ze sai mana sa, wanda za'a saka a Abinci, wannan kaji na  dinner ne, ina son sake masa magana, amma kwana biyun nan bama jituwa, shiyasa na ƙyaleshi, amma tun yanzu yakamata a sai san a ajiye" Maman Ihsan tace "Subhanallah, lafiya dai ko?" "Barni kawai Laɗifa, Magana ce akan wata Yarinya, 'yar ƙanwarsa, ƙanwar fa ta mutu yace ze ɗakkota in riƙe nace bazan iya ba, shine yanzu ta girma yarinyar ta zama fitinanniya shine yaketa take taken, wai ze kawomin ita gida, gani da yarinya mace, salon ta ɓatamin ita, shiyasa na ɗauke masa wuta inga iya gudun ruwansa" Maman Ihsan tace "gaskiya idan yayi haka be miki adalci ba, ya zaki zauna da ƙatuwar budurwa karuwa a gida, kina mata kallon biri tana miki na Ayaba, gasky idan yai haka be kyauta ba, amma gara ki lallaɓashi ayi auren yaran nan ba Tare da wata matsala ba" "Shikenan, zan san yadda za'ayi, zan tuntuɓeshi ki gaida Ihsan ɗin". "To shikenan zataji, seda Safe" Ihsan data shigo tun ɗazu ta tsaya tana jiran Mummy ta gama waya, ta kalleta tace  "Mummy da Ammi kike waya ko?" "Eh da ita ne har Imran ɗin ya tafi ne?" "Eh ya tafi"  ta samu Guri ta zauna Sannan ta kuma cewa "Mummy, naji kamar tana ce miki wai wannan ƙanwar tasa zata dawo gidansu ne ko?" "Kai Ihsan, yanzu dama kasa kunne kikayi kina jin abunda nake faɗa?" Ihsan ta girgiza kai tace "ba haka bane Mummy, Imran ya bani labarin yarinyar, sedai a duk lokacin da za'ay zancenta se inji gabana yana faɗuwa, sama bana ƙaunar maganarta, gashi Yanzu ana zancen zata dawo gidansu" "To ke meye haɗinki da ita da zaki damu kanki akanta? Inma gidansu zata dawo da zama akanki zata zauna? Ina gidanki daban?" "Mummy, Yarinyar cousin ɗinsa ce kuma kamar yana nuna damuwa akanta fa" tai maganar cike da karaya. Mummy ta riƙo hannunta tace  "haba Autan Mummy, tun kan ki shiga gidan Aure kin fara da karaya haka? Ki kwantar da hankalinki sekin so wata zata raɓi mijinki, kuma yarinyar da take yawon banza ina zatayi kima a idon Imran bayan gaki" tai maganar tana murmushi. Ihsan tace "hakane Mummy, amma kin san mazan yanzu ba'a iya musu fa" "Ke dallcan, don't put that in your mind Baby, ba ruwanki da wata kanki kawai zaki kafa, kuma Imran yana sonki sosai baze yi abunda ze saki damuwa ba" Ihsan tai ajiyar zuciya tace "Shikenan Mummy, na dena damuwa insha Allah" Shikuwa Imran kamar kullum sannu a hankali yake tu(insa harya shigo layinsu, wani matashine tsaye a jikin wata Mota yana danna waya, Imran ya ƙara gudun motar ya tafi yai kan matashin kamar ze bigeshi sannan yai wani wawan birki. Matashin seda ya ja da baya, Imran ya fito daga motar yace "kai yaushe ka dira ba labari?". Matashin yace "ban sani ba, takeni da mota dan ubanka, kayi jinyata a Asibiti, sedai kaci amarcin a nan Asibitin gurin jinyata" Imran ya kwashe da dariya yace "kaifa ₦an iska ne wasu lokutan, to ya? Ya ake ciki ne ka diro ashe?" "Ba dole in diro ba, tunda ka addabeni in dawo gani na dawo, ka bani uwar da zaka bani" Imran yace "wace uwar zan baka kuwa? Kawai dama danka dawone ka tayani hidimar bikina' "Ɗan rainin hankali, nima ina hanya na samo wata zazzafa, kuma insha Allah wuf zan da ita" "Karma dai kayi, ka zauna kaita ruwan ido" "Ai nayi mamakin lokacin da ka fara soyayya, har kake shirin Aure ka barni, dole in zuciya Yaseen, kamarni Khalid ace Imran ya rigani Aure, gaskiya wannan ci bayane a gareni". Imran yai dariya yace "wai yaushe ka shigo ne?" Khalid yace "da magaribar nan ne, nake gidanku Ammi tace min baka nan, shine naje nai Salla sekuma gaka ka dawo" "Fatan ka dawo lafiya, ya hanya?" "Alhamdilillah, mushiga cikin gidan se muci Abinci mucigaba da tattaunawa" Daga nan suka shiga gidansu Khalid. Hajiya Amira kuwa, tunda ta lalata musu ɗan wake tasa ƙafa ta bar gidan nan, ta tafi nata garari a gari da wannan magaribar, sedai duk inda ta wuce wasu na nunata, ana cewa itace wadda aka baiwa mota, wadda zata fito a videon raye raye, ita kam ko a jikinta hakan sam be dameta ba, sabgar gabanta kawai takeyi. Se wajen sha ɗaya saura na dare se gata ta dawo Gidan, kamar kullum yauma da Sallamar ta ta shiga gidan, sedai ba wanda ya amsa mata, saboda a ƙule suke da ita. Ta turo ɗaurin ɗan kwalinta gaban goshi, alamun itama daidai take da kowa, duk wanda ya kawo mata rainin tana daidai da shi ta wuce ɗakinsu, su Amina na zazzaune kamar marayu, sedai sun cika sunyi fam se harare harare sukeyi, ta share su ta ajiye 'yar ƙaramar jakarta da ledar hannunta. Yadikko ta fito daga banɗaki, ta nufo ɗakin su Amira, ta ɗaga labule ta kalli Amira tace "tauraruwa me wutsiya ganinki ba Alkhairi ba" Amira tace "yau kuma kirarin da zakimin kenan? Naji na karɓa kuma nagode sosai" "Yanzu banda rashin imani da tausayi, Abincin da zamuci ki ɓata kika jiƙe murhun da itacen, saboda rashin tsoron Allah, Amira kina son ki gama da duniya lafiya kuwa? Ke kwata kwata bakya neman Albarka kullum cikin kalen jaraba kike" "Yadikko, idan nazo gamawa da duniya lafiya ki hana, idan ke zaki saka in gama da duniyar lafiya ki hana dan Allah, ni kuna so ku gama da duniyar lafiya kuka zauna kuka dinga kwashemin Albarka kuna zagina jiya, duk cikinku aka rasa me cewa Allah ya shiryi Amira, se masu kiramuk watsewa da kwaso cuta, dan nayi hoto da mutum shikenan Iskanci nake dashi? Ƙaddarama hakanne idan su Amina ne haka zaki zauna kina kwashe musu Albarka kokuma Addu'a zakiyi musu?" Amina tace "ke saurara, karki kuksakura ki kuma gwada misalin rayuwar da kike akanmu, muba irinki bane kike can kiyi abunki Amma ki dena misali damu" Yadikko tace "gaya mata dai, ai ba kowane irinki ba, babu yadda za'ayi su Amina suyi abunda kikeyi, ban sani ba ko a can tsatonku ne da irin haka, shine kema kika tsotso a nono aka barmana masif...... "Ya isheki haka Yadikko! Amira ta faɗa cikin tsawa  "wasa yayi wasa Amma banda zungurin uwar miji da taɓarya, karki sake ki zagarmin iyaye, gaba ɗaya ba wanda yake raye sun mutu, iyaye da kakkannina, kuma ke kin san a tsatsonsu Babu wanda yai karuwanci, karki ƙara sako su a ƙazamar maganarki, in ba haka ba zan ɗau mataki, ni ɗin dai da kika saba yiwa kiyi tayi, Amma ban yadda ki taɓa iyayena ba tunda basa raye, ba abunda sukayi miki dan haka baki da hujjar da zaki dinga danganta abunda nake dasu" Yadikko ta hangame baki jin yadda Amira ke tatala mata rashin mutunci, saɗara saɗara. "Yanzu Amira ni kike gayawa wannan maganar haka?" "Na gayamiki ɗin, kika kuma zagin iyayena ko kakata wallahi sena miki rashin mutunci, nagaji wallahi" Yadikko ta fashe da kuka, tana "Innalillahi wa innalillahi raji'un, yau na shiga Uku, 'ya'yana da jikokina babu wanda ya taɓa sani kuka, babu wanda ya taɓa sani magana seke, daga taimako na riƙeki kin zame min bala'i, tir da halinki Amira, Allah ya kwashe miki albarka mara mutunci mara imani, da ikon Allah Se karuwanci ya zama silar jefaki cikin bala'in da bazaki iya fita ba" Jikin Amira ne ya fara tsuma, hawaye na bin fuskarta, ta tabatta da Yadikko ta haifi iyayenta babu yadda za'ai tai mata wannan fatan, kullum burinta taga Amira ta tozarta, tai tayi mata miyagun Addu'oi da jan alkaba'i. Su Sadiya ne suka shiga rarrashin Yadikko, suna bata haƙuri, jin kukan Yadikko yasa su Usaman suka shigo gidan suna tambayar ba'asin kukan Yadikkon. Cikin kukan take cewa "waze sani kuka idan ba wannan makirar Yarinyar ba? Kullum burinta taci mutuncina da tsufana da komai, nasan da kakarta ce ni ba zata mata haka ba, ta kalli tsabar idona ta zageni tsaf taimin wankin babban bargo, ko tsufana bata duba ba, yarinyar nan bata da mutunci, bata san darajar furfira ba sam. Kalaman Yadikko sunyi tsauri kuma sun tsaya a zuciyar Amira, tamkar ta haɗiyi ƙayar kifi me dafin gaske haka take ji a ƙirjinta, Yadikko makirar tsohuwace ta gaske, ta iya shirya kalamai da Magana, ƙarya da ƙarairayi ba wanda bata iya ba, gata da daɗin baki da fuska biyu dan haka babu wuya ta ƙulla maka sharri. Amira ta buɗe akwatinta ta shiga gyara kayan ciki, yayinda Hawaye ke zuba ba ƙaƙƙautawa a cikin idonta, tana jik zafin addu'oin da Yadikko take mata, ba tayi yunƙurin kare kanta akan abunda Yadikko ta faɗa ba, saboda a gurin Amira basu isa ta tsaya tana gaya musu abunda ya faru ba. Sadiya tace "ji munafuka, wai itama kukan take Jahila wadda bata san darajar furfura ba" "Furfura me daraja, ita ta cancanci girmamawa, ba furfurar banza ba me son zuciya" Amira ta bawa Sadiya amsa. "Ke dan uwarki Yadikko ce me furfurar banza? Baki da mutunci Amira?"  Zailani yai maganar yana kallonta. Ko kallon inda yake Amira ba tayi ba, ta cigaba da kukanta, Zailani ya ƙule ya fita tsakar gida ya ɗakko ice, Yadikko cewa take rafkawa shegiya a muƙamiƙinta, tunda bata da mutunci. Yana shiga ɗakin yai kan Amira ya soma sauke mata icen nan, ji tayi kamar kafaɗarta ta cire, take Amira ta ciro ƙaramar wuƙa a rigarta, tana kuka tace "wallahi ka kuma dukana da icen nan, sena yanke ka da wuƙar nan, sena maka kaciya da ita ince fyaɗe zakamin. Da sauri Yadikko tace "ƙyale shegiya Zailani, karta maka halin karuwan, dama ta saba ganin tsiraicin maza, tunda ba abunda ta hango seyi maka kaciya, karta kassaraka dan idan tayi maka kaciya da wuƙa ta kashe ka kuma bata da Asara" "Ni zaki kalla kice zaki yiwa kaciya? 'yar daba kika koma bayan karuwanci?" "Nace ka ƙyaleta kar tayi maka illa a banza" Sukai waje, Amira kuwa ta zauna a gurin ta cigaba da rusa kuka kamar an mata mutuwa, ga zafin dukan data sha, ga zafin irin rayuwar da ake mata, me cike da ƙalubale da cin zarafi. Imran se bayan goma na dare ya ƙarasa gida, dama ya riga yayi dama, yana zuwa wanka kawai yayi ya hau kam gadonsa ya janyo waya, ya kira Ihsan suka cigaba da waya da, kamar zasu cinye juna, kowannen yana nunawa ɗan uwansa irin yadda yake ƙaunar ɗan uwansa. Abba kuwa ya rasa yadda ze tunkari Imran da wannan maganar, saboda gani yake idan yayi haka kamar bewa Imran ɗin adalci ba, da ita kanta yarinyar daze aura ɗin, Amma yayi tunanin yayi tunanin ya rasa ina mafita akan lamarin banda wanda Hashim ya gaya masa, gashi sam shima ya fita sabgar Ammi, dan yasan idan taji maganar nan za'ayi tashin hankali ba kaɗan ba. Amira kuwa yau kusan kwana tayi ba tayi bacci ba, ta sha kuka ta sha kuka, kamar ta shiɗe, ta dinga tunani daban daban, ji take kamar ta gudu ta bar gidan nan, amma idan ta gudu ina zata? Haka taita wannan tunani har Asuba tayi. Gari na fara haske Amira ta kintsa tai ficewarta, ta tafi gidan Anty Fa'iza, can ma da taje bata kula kowa ba, ta samu guri tai kwanciyarta, zuciyarta na mata raɗaɗi akan irin rayuwa da takeyi. Imran ya fara zama busy, saboda hada hadar shirin bikinsa, dan an shiga satin biki, amma Abba yana jin nauyin gayawa Imran matakin daya ɗauka a game da Aurensa da Amira. Abba yana shirin fita, sega kiran Alhaji Hashim, Abba ya ɗaga suka gaisa Sannan yace "Alhji Ali ya ake ciki ne? Ka sanarwa da yaron kuwa?, Zuwa yanzu yakamata ace an tsare yarinyar nan ta fara istubra'i fa" "Hashim na kasa sanar masa, ba dan ina shakkarsa ba, ba kuma dan baze abunda nake so ba, sedai ina tunanin ita kanta mahaifiyarsa yadda zata ɗau maganar" "Aikuwa idan baka faɗa musu yanzu ba, komai ze kacame maka, ko kana nufin se ranar ɗaurin Auren zega an ɗaura masa aure haka ba saninsa, an shiga satin biki, ita kanta yarinyar daze aura ɗin akwai buƙatar ka samu aje a sanar da magabatan yarinyar nan suma su sani" Abba yace "to shikenan, zan san yadda zanyi Insha Allah" Alhaji Hashim yace "to babu laifi, nima zanyiwa Meɗakina Magana, seta zauna a gurinmu, har gwaje gwajen da yakamata se ayi mata" "Nagode sosai Hashim, Allah ya bar zumunci" Abba ya ajiye wayar, ya ɗanyi shiru Sannan ya fito, ɗakin Imran ya nufa, yana zuwa yai knocking, Sannan ya buɗe ya shiga. Imran ya shirya cikin dogayen kaya, da alama fita zeyi, yana ganin Abba yace "Abba da kanka, da ka kirani ai se inzo da kaina" "Ni na kira ango, ai gara inyi tattaki inzo da kaina" Imran yai murmushi cikin jin kunya ya sunkunyar da kai. Abba yace "Imran magana nazo muyi" Imran yace to Abba. Suka zauna Abba na kan kujera, Imran yana zaune akan carfet. "Imran wata alfarma nazo na nema a gurinka, sedai ban san yadda zaka kalli abunba" Imran yace "Abba wannan wace irin alfarma ce haka? Wadda kake tunanin bazan iyayi maka ba? Ba abunda baka mana ba a rayuwa, mezesa in kasa maka wani abu da ka buƙata a gurina?" "Imran bana son kaga dan ni na haifeka zan maka dole ko in cutar da kai, shiyasa na kira abun da alfarma, ba dole zan maka ba, alfarma ce zan nema idan kaga zaka cutu base kayi ba, ba zan maka dole ba" "Abba dan Allah ka dena kiran alfarmar nan, amma me kake so inyi maka haka?" "Imran, munyi magana da Alhaji Hashim ne akan wannan yarinyar Amira, kuma muka cinma matsaya aurar da ita, ko hakan zesa ta nutsu, sedai mun duba babu wanda ze iya riƙeta da mutunci da amana idan ba kai ba, kaine ɗan uwanta zaka iya rufa mata Asirin abinda tayi a baya, saɓanin idan ta auri bare, a taƙaice dai ina son zaka auri Amira ne, ka haɗa ta da Ihsan, amma ba dole zan maka ba, Kamar yadda na gaya maka a fari, amma hakan kamar jihadi ne, da ceto rayuwar yarinyar daga tarwatsewa gaba ɗaya, ban yanke wannan hukuncin dan in cutar da rayuwarka ba, amma me kace?" Wani irin gumi ne ya shiga ratsa Imran, duk da sanyin AC daya cika ɗakin, amma wata irin zufa yake, tabbas ya shiga tsaka me wuya, dan sam ba shi da ra'ayin zama da mata biyu, saboda baya son fitina da damuwa, kuma ga wadda ake so ya aura, fitinanniya lamba ɗaya, wadda a zahiri ma shi ƙyamarta yake yi, amma ance ya aureta ya haɗa da Ihsan, anya kuwa ze iya? Can wata zuciyar tace 'kai har akwai alfarmar da Abbansa ze nema a gurinka ka kasa yi masa?  Bayan haihuwarka da yayi ya sadaukar da lokacinsa, ƙarfinsa dukiyarsa gurin gina taka rayuwar?. "Kayi shiru ba kace komai ba Imran" Cikin sanyin jiki Imran yace "bakomai Abba, yadda kace haka za'ayi" Abba yai murna yace "Alhamdilillah Masha Allah, dama nasan ba zaka bani kunya ba Imran, zanje in samu magabatan Ihsan suma muyi magana dasu, Sannan za'ayiwa Amira daukkan gwaje gwajen da suka kamata, insha Allah nasan ma Babu wata matsala" Imran kam gaba ɗaya kansa ya gama kullewa, a ransa yace ko wani gwaji za'ayi mata ba ruwana, dan bazan iya haɗa jikina da Yarinyar data gama raba jikinta ga maza a titi ba. Bema san me Abba yake cewa ba se jin muryar Abba yai yana "Nagode, Nagode sosai Imran, Ubangiji Allah yayi maka albarka, Allah ya haɗa kanka da iyalinka, ya zaunar daku lafiya, yadda kayi min biyayya Ubangiji Allah yasa yaranka su bika haka, sannan zan canza maka gidan da zaku zauna, seku zauna a gidana na Bamako gaba ɗaya, bana son ka rarraba kan iyalinka, insha Allah baza kayi dana sani ba a rayuwarka na gode sosai my Son" Ya shafa sumar Imran, Sannan ya tashi ya fita cike da farinciki da annashuwa a ransa. Imran kuwa zaman daɓaro yayi yana tunani, da wani idon ze kalli Ihsan, meze fara gayamata, ba abunda ze hana tayi masa kallon mayaudari, kimarsa zata ragu a idonta, taya ze fara zama da wannan Yarinyar, mara ta ido da shegiyar fitina, Amira ta rasa qualities da yawa da ake nema a gurin mace, tabbas daba Abbane ya nemi wannan alfarmar ba, da kowaye ya nema baze yi ba, dan sam Amira ba ta dace da tsarin rayuwarsa ba. Yana nan zaune, Khalid ya shigo ɗakin Imran, cike da mita ya kalli Imran yace "kai ka rainamin hankali gaskiya, kaje ka shanyani ina zaman jiranka, kawai kazo nan kayi zamanka kana tunani haka akeyi?" Imran yai shiru bece komai ba, se tagumi da yayi da hannunsa bibiyu. "Wai ba magana nake maka ba ka shareni? Ka wani yi uban tagumi kamar ance Ihsan ta mutu" Imran ya sauke hannayensa yai ajiyar zuciya, tare da sake dafe kansa. "Wai zaka tashi mu tafi ne kokuwa?" "Kaga a fasa fitar nan kawai" "Saboda me, wai kai meke damunka ne, ka wani nustu kamar marayan muzuru, ka tashi mu tafi malam lokaci yana ƙurewa" "Kaga a fasa fitar nan kawai" Khalid ya kalleshi da mamaki yace "Kamar ya a fasa? Ban gane ba" Imran yace "Khalid ina cikin damuwa ne, bazan iya fitar ba". "Damuwar me, kai da zakayi aure, ai damuwa semu gawauraye" "Khalid mata biyu wai zan aura lokaci ɗaya" "Kamar yaya?" Khalid ya tambaya cike da rashin fahimta. Nan Imran ya warwarewaa Khalid komai. Khalid yace "lallaai kana cikin tsaka me wuya mutumina, amma Allah yasa haka shine mafi Alkhairi, insha Allah zakaga sakamakon biyayya, kayi haƙuri Imran, inaji a jikina zaka samu Alkhairi a sanadin Aurenta" Imran kawai ya tashi ya tafi ɗakinsa yaje ya kwanta, dan yama rasa abunda zeyi gaba ɗaya. Alhaji Hashim kuwa tuni yayiwa matarsa bayani akan Amira, kuma ta bashi tabbacin ita a kawo mata Amira zata riƙe, dan gaba ɗaya yarinyar tausayi ta bata da Alhaji Hashim yayi mata bayani. Kasancewar mahaifin Ihsan ya rasu, Alhaji Ali da waliyan Imran, a ranar sukaje suka samu wan mahaifinta akan mata biyu za'a aurawa Imran a gurin ɗaurin Aure, Ihsan da kuma 'yar uwassa, shima wan mahaifin nata be nuna fushi ko ɓacin ransa ba, sedai yace musu  "komai muƙaddari ne, kuma bawa baya wuce ƙaddararsa, Allah ya basu zaman lafiya ya haɗa kansu, amma kun san halin mata, se Addu'a, dan haka karku sanar musu da zancen, ni zan sanar musu idan lokacin da yakamata yayi, idan aka gaya musu yanzu ba zasu bari ayi bikin lafiya ba" Abba yace"Allah ya wuce mana gaba, mungode sosai da wannan karamcin naka, Allah ya albarkaci yaranmu gaba ɗaya" Imran kam bacci ma gagararsa yayi, yana kallon Ihsan tana kiransa amma ya kasa ɗaga wayar, saboda zatonsa An sanar mata ai ita da Amira ze aura. Amira kam ta dena shiga sabgar mutanen gidan, duk wulaƙancin da sukayi mata, amma suna ta shirye shiryen zasu bikin ɗan uwanta Kaduna, Amira kallonsu kawai takeyi, 'yan gidansu akwai son abun duniya fiye da kima, basa iya ɓoye zalamarsu sam. Amira Ta fito tsakar gida, Sadiya nata wanke wanke, ta baje kwanuka gashi ta zubar da dagwalon ƙanzo da komai, Yadikko tazo wucewa Amira ta kauce ta bata hanya, kawai ta taka ruwan omo, santsi ya kwasheta ta faɗi ƙasa, cikin kwanuka da dagwalon wanke wanke, ta buge ƙeya da tukunyar ƙarfe. Take ta kurma uban ihu, ta dafe kanta wai Amira ta hankaɗeta, ko takanta Amira bata biba, tai gaba abunta. Baba ya fito ya dinga yiwa Amira tijara, yana faɗin ya gaji da wannan tashin hankalin, baza'a kashe masa uwa a banza ba, Amira seta bar musu gida. Ko kallaonsa ba tayi ba, ta ɗauki gyalenta da jakarta ta fice ta bar musu gidan. Da safe Imran yana kwance, yana ta tunani ranar ne za'a fara bikinsa, Amarya za tayi henna day amma baya cikin nutsuwarsa, still Ihsan tana ta kiransa amma yaƙi ɗagawa ƙarshe ma ya kashe wayarsa gaba ɗaya, dan be san meze ce mata ba. TV dake bedroom ɗinsa na tayi ita kaɗai, can aka nuno mawaƙin nan da Amira tayi hotuna dashi a Abuja, wai ze kai ƙarar Amira kotu, sunyi yarjejeniya zata fito a waƙoƙinsa, amma tai tafiyarta bema san inda ta shiga ba, dan haka 'yan sanda suna nemanta, duk inda take. Imran ya tashi zaune, ya dafe kansa yama rasa me Yakamata yayi. Wai wannan itace wadda ake son ya aura, wannan watsatsiyar Yarinyar. Ya ɗakko wayarsa ya kira Baba a waya, Baba ya ɗaga lokacin yana tsaka da banbami akan Amira. Imran yace "Ina Amira take?" "Ai lamarin wannan yarinyar banma san me zance ba, kwana biyun nan masifa kawai take janyo mana, ta saka ƙafa ta fice ta tafi gantalinta, shekaranjiya tayiwa Yadikko zagin cin mutunci, dan an mata magana ta ɗakko wuƙa kamar wata 'yar daba, yau kuma ta hankaɗa Yadikko cikin tukwane ta kusa suma saboda yadda ta bugu a kanta, gaskiya na gaji ba..... Imran da maganganun Baba ke sake kunnashi yace  "kaga ba kira nayi ka wassafamin wannan takicin ba, duk inda take ku nemota, koku turomin lambarta inyi tracking ɗinta, zan shigo Kano anjima, idan ba haka ba ta gangamo wata rigimar, wadda ba iya kanta zata tsaya ba harku zata shafa, dan haka duk inda zaku samo labarta ku nemo ku turomin, zanyi tracking in nemota, tun kafin abun data janyo ya zama out of control" Imran ya katse wayar yai jifa da ita akan gadonsa ya furta "Oh My God, Allah ka dubeni wai wannan ce zata zama matata, wannan yarinyar yasalam, am Sorry My Ihsan, baki cancanci haka daga gareni ba, amma dole inje in ɗakko Yarinyar nan kan 'yan sanda su kamata, abun kunyar zemin yawa, ace matar da Imran ze aura a hannun 'yan sanda, Sunan Abba ze ɓaci nima mutuncina ya zube" Ya ɗau wayarsa ya kira Khalid, Khalid ya ɗaga, Imran yace "Khalid ka shirya zaka rakani Kano yanzu Please!" (Oga Imran za'aje a ɗakko mana amarya 😂😂😂) Share, Share, And share as much as you can please, masu nema daga farko yana nan a watpad a account ɗina Ayshercool 7724 Ayi vote, ai following please Masu san what's app group kuma ga link nan, mata kawai banda maza Please, Sannan akwai dokoki a group ɗin, in kina ɗaya daga groups ɗina karki joining please https://chat.whatsapp.com/EAYHhAEJQPk8uGg2IeCQhX 07063065680. [1/15, 6:38 PM] Ayshercool:           🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥                 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                 KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI                                                            17_18 Imran ya kalleta a fusace yace "nan yai miki kama da gidan karuwai ne?" Murguɗa masa baki tayi ta ɗauke kai. Khalid yace "Amira gidansu Imran ne fa, ki shiga bakomai, baki ga 'yan biki suna shiga suna fita ba" Ta ƙarewa gidan kallo, sannan ta kalli Imran tace "muje" Idan Imran ya biyewa Amira, ze iya yi mata dukan tsiya a gurin nan, kawai ya wuce yai gaba, Amira tabi bayansa. Mata nata tsokanarsa suna ango ka sha ƙanshi. Cikin gidan suka shiga, ya wuce Falo Amira na biye da shi. Minal suna zazzaune a falo da ƙawayenta, da babbar Yayarsu Khadija wadda daga Ita se Imran, ita tayi Aure tuntuni. Khadija ce ta fara ganin Imran da Amira, ta kallesu tai murmushi tace "Imran kai da wa nake ganinka haka kamar Amira?" Amira dai tayi turus, tana kallon Anty Hadiza. Jin ance Amira yasa Minal waigowa, duk yadda ake faɗar rashin jin Amira da yadda ta ganta a hoto, ba ta zaci zata ganta a haka a fili ba, tafi kyau da class Sosai a fili. Imran yace "eh ita ce" Hadiza tace "masha Allah, Nikam yaushe rabon da inga Amira tun tana ƙarama sosai, yanzu waze ce ita ce, ta zama hamshaƙiyar mace" Wata a ƙawayen Minal tace "wannan ba ita ce wani mawaƙi yace zata fito a vidon waƙarsa ba?". Minal ta kwaɓe baki tace "ita ce" "Wow Gaskiya naji daɗi dana ganta, ashe 'yar uwakku ce, wallahi ni burgeni tayi" Cikin isa Imran yace "ke minal, ki bar abun da kike kije ki kaita ɗakinki, ki nuna mata toilet tayi salla, Sannan ki bata babban hijjabi" Amira kuwa kamewa tayi a gefe, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Minal ta zumɓura baki, cikin ƙunƙuni tace  "ɗakina, toilet ɗina, kuma kayana, taɓɗijan Allah ya kiyaye inyi sharing da wata" Cikin muryarsa me razanarwa wasu lokutan yai mata tsawa "dan ubanki me kike cewa? Ni nake miki Magana kike min ƙunƙuni?" A hargitse Minal tace  "A'a Yaya, dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba da kai nake ba" "Kai Sarkin masifa, tun daga ciki ake jiyo hargowarka, lafiya kake wa 'yata shouting haka?" Ammi ce ke maganar lokacin da ta fito daga wani ɗaki. Ba tsammani ta kalli inda Amira take,  sukai ido huɗu da juna, ko za'a naɗe ƙasa a dawo, Amira ba zata manta fuskar Ammi ba, da wasu abubuwa da suka shuɗe shekarun da suka gabata ba. A wulaƙance ta ƙarewa Amira kallo ta kalli Imran tace "lafiya wannan fa?" "Abba ne yace inje in taho da ita yau, a fara biki da ita" "Saboda bikin nata ne, kokuma na ƙanwar uwatta?" Amira ta ɗago ta kalli Ammi, ta maida kanta ta sunkunyar. Anty Hadiza tace "Ammi, Amira ce fa ko baki ganeta bane?" "Ke zam cewa baki ganeta ba, baki da labarin rashin jin da yawon ta zubar ɗin da takeyi, babu inda hotonunata da rashin kunyarta basu shiga ba, kawai se a ɗebo jiki a kawomin ita cikin gida, saboda me to baze yuwu ba, ba a gidan nan ba sedai wani gurin" Hadiza tace "Haba Ammi, koma menene dalili ne ya kawota, kuma na ɗan lokacine, ana gama biki fa zata tafi" Gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kansu, aka dinga bawa Ammi rashin gaskiya da nuna mata illar abunda tayi, jin mutane nata surutu ba yadda ta iya, haka ta ƙyale Amira, saboda gudun surutan mutane. Imran ya kuma kallon Minal yace "bakiji me nace bane?" Miƙewa Minal tayi, Imran ya kalli Amira yace "ki bita kije ta baki masauki, a baki hijjabi ki rife jikinki" Duk da sanyi da jikin Amira yayi, hakan be hanata zumɓura baki ba, dan da ta san gidansu Imran ze kawota, da duk tunballen tsiyar da za'ayi sedai ayi ba zata yadda taje gidansu ba. Minal tai gaba Amira tabi bayanta, suna shiga ɗakin Minal ta juyo ta gallawa Amira harara tace "ga toilet nan ki shiga, kuma ki kula karki sake kimin taɓe taɓen abunda ba shikenan ba, kuma karki min fitsari a ƙasa, kinji na gaya miki" Amira ba tace uffan ba, dan ta san kome akayi mata Imran ne ya janyo da ya kawota gidan, dan da tana gidansu babu me mata wannan rashin mutunci haka. A masallaci Imran ya sake haɗuwa da Khalid, suka wuce gidansu Khalid, a hanya Imran ya bashi labarin irin karɓar da Ammi tayiwa Amira. Khalid yace "ai nasam za'ai haka, ni babbar fargabata ma suzo su san wannan maganar, akwai fa sauran rikici" Imran yace "bari kawai, aini na zubawa sarautar Allah ido kawai, dan ban san abunyi ba" "Ka kwantar da hankalinka, Allah ze baka mafita insha Allah" Seda suka raba dare suna hira, Sannan Imran ya tafi gida, lokacin duk an rurrufe ko ina, kuma be haɗu da Abba ba sam balle ya gayamasa ya ɗakko Amira, dan haka kai tsaye ɗakinsa ya wuce yaje ya kwanta. Amira kam duk a takure take, ba wanda ya kulata balle ya bata Abinci, ga gajiyar hanya data ɗebo, gashi bata san ko ina ba, Minal da ƙawayenta se wulaƙanci sukewa Amira, Minal tana gaya musu ai Amira karuwace, se wannan guda ɗayar ta farko da tace Amira tana burgeta itace bata biye musu ba. Da daddare akazo gurin kwanciya, Minal ta kalli Amira tace  "kinga, me aiki zata shigo yanzu ta kai ki inda zaki kwana, nan ɗakin zamu kwana ne nida ƙawayena, bama son takura ina fatan kin gane?" Amira ba tace komai ba, ga kaya tana son canzawa, bata ɗakko komai nata ba, kawai Imran ya kawota ya ajiye yai tafiyarsa, taji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan takaici. Me aikin ta shigo ɗakin ta kalli minal tace "Anty gani" "Yawwa, dama zaki wanke min banɗakina ne bana son sharing da jagwalgwalo, kin sanni da ƙyama, kuma an shiga banɗakin But before that, ki kaita inda na gayamiki za ta kwana" Me aikin ta kalli Amira tace "taho in rakaki" Ba musu Amira tabi bayan me aikin nan, sedai inda me aikin ta kaita ne ya bata mamaki, abun ya ɗaure mata kai, da faɗi da girman gidan nan, a rasa inda za'a kaita se Kitchen, kitchen ɗinma a cikin store, duk ga kayan Abinci a jibge kamar abun banza, an saka mata tsurara katifa wai ta kwana a gurin. Amira ta ƙarewa gurin kallo, ta ja tsaki ta fice ta koma falo ta bar me aikin a gurin, ta samu guri a gefen kujaerun falon ta zauna. Mutane kowa ya samu gurin kwama amma Banda Amira. Haka ta kwana a falon nan a zaune, ga garin da sanyi ga baƙunta, da Asuba can waje ta fita tai alwala, tana ƙarewa gidan kallo da yadda zata bar gidan nan, ko Imran ya sani kobe sani ba, ta ƙudirce gari na yin haske zata gudu, ta koma Kano. Yadikko kam ta bugu sosai, dan se an rirriƙeta take iya tashi, amma sam bakinta yaƙi mutuwa, banda zagi da kwashewa Amira albarka ba abunda takeyi, wai itace tai silar faɗuwarta ƙasa. Umma da su Sadiya suna ta haɗa kaya, zasuje biki ita kuwa tana kwance, duk jiki yayi tsami. "Wai yanzu niba yadda zakuyi dani, a lallaɓa a tafi dani gurin bikin nan?" Zailani yace "ina za'a kaiki, ki zame musu kaya? Ya zasuyi dake? Jinyarki za suje suyi kokuma bikin zasu? Kawai ki haƙura ki zauna, a yaran gidan Baffa Salahu ko su Habiba ne suzo su dinga tayaki zama, kafin su dawo Amma wallahi kikace zaki bisu ma wahala zaki sha" Haka sukayi ta fama da Yadikko, akan lallai se an tafi da ita gurin biki, seda taga ba sarki se Allah ta haƙura da zuwan. Washegari da Safe suka gama shiri tsaf, suna jiran Fa'iza taje su haɗu a nan gidan su tafi gaba ɗaya. Amira kuwa gari na fara hasake, wajen ƙarfe takwas na Safe tana tunanin idan ta fita ina zatayi, Anty Hadiza ta fito daga ɗakin Ammi tace  "Amira, ya baƙunta?" Amira ta kalleta tace "lafiya ƙalau, ina kwana?" "Lafiya ƙalau Amira, naga kina ɗari ɗari ki saki jikinki fa, nan gidanku ne, ki saki jiki da kowa duk 'yan uwanki ne" "Gidansu a gidan ubanwa? Gidana dai gidan mijina, gidansu yana Kano, kuma 'yan uwan 'yan uwana ne, ta nemi nata 'yan uwan ba nawa ba, mu babu kalarta a 'yan uwana" Amira tai shiru ta sake sunkunyar da kai, zuciyarta na tafasa, Hadiza tace "Ammi why?" "Ke dalla rufemin baki ko in zageki yanzun nan" Suna barin falon Amira ta miƙe daga inda take zaune, dama jakarta na jikinta, ta zira takalmanta tai waje. Mutane nata shiga suna fita, Amma tana zuwa bakin gate, ɗaya daga masu gadin ya taso ya kalleta yace "ina zaki?" "Fita zanyi" Amira ta bashi amsa. "Zuwa ina?" Ya tambayeta. "Kamar yaya? Su sauran wanda suke fitan tambayarsu kake yi?, Kokuma ni ka raina, dan Allah ka bani guri in fita" "Gidan ubanwa zaki idan kika fita?" T muryar Imran taji ba tsammani, waiwayowa tayi da sauri ta ganshi a tsaye, sanye da jallabiya fara. Haɗe rai tayi sosai tace  "Ni gida zan tafi, gidanmu zan koma" "Hmm tunda dama ke kika kawo kanki ko? Kin ɗauka haka nan na kawo ki nan ɗin kina da damar da zaki fitane? Da kin matsa kin fita da se sun harbe ƙafarki da bindiga, sakarya kawai wuce muje ciki ni" Ai kawai Amira ta sa masa kuka, harda hawaye tace "gaskiya ni ba zan koma ba, haka kawai ni ban san kowa ba ka kawoni ka ajiye ni, se wani kallo na ake ana gayamin magana, ni gaskiya gidanmu zan koma, duk da bamu da komai Amma ni ya fiyemin nan" Imran ya ƙare mata kallo sannan yace "waye yake gaya miki maganar? Koda yake koma me akayi miki aike kika janyo, ubanwa yace kiyi abinda za'a gaya miki maganar, wuce muje ba gidan uban da zaki, in kinga kin fita daga gidan nan to ni ko Abba ne wani ya fita dake, amma daga nan har ƙarshen layin nan, kika fita zasu dawo dake, wuce mu koma" "Dan Allah kayi haƙuri, ni wallahi bazan iya zama a gidan nan ba, ka ƙyaleni in koma" Attention ɗin mutane ya fara dawowa kansu, wata mata tace  "Imran yau fa ranar farinciki ce a gareka, banda cin zali dan Allah, nam ba barikin soja bane" Imran kawai yai murmushi, matar na wucewa ya bugawa Amira wata irin tsawa, me matuƙar razanarwa, a gigice ta nufin cikin gidan da sauri, ya riƙo hannunta, yabi ta bayan gidan da ita zuwa sashin Abba. Minal kuwa da akan idonta, Amira ke kuka, Imran ya riƙe hannunta se cewa tayi "Ahha baɗala, kar dai Yaya Imran ake gwadawa karuwancin, aikuwa bari inje in gayawa Ammi" Sashin Abba suka shiga, Amira tana kuka amma tana ƙarewa gurin kallo, dan ita bara taɓa shiga gida me kyan wannan ba a rayuwarta. Abba yana ganinsu yace "oyoyo 'yar gidan Abba" Jin muryar Abban ce yasa ta dawo hayyacinta daga kalle kallen da takeyi. Taje ta samu guri ta zauna, Imran ma ya zauna, Abba yace "ki hau kan kujerar mana"  girgiza kai Amira tayi ta sunkunyar da kanta ƙasa. Abba yace "ai ni be gayamin ɗakko ki ya tafi yi ba, ai da tun daren jiya mun gaisa, se yanzu da safen nan fa ya gayamin" jikin Abba ne ya ɗanyi sanyi, ganin hawaye a idon Amiran. Abba yace "lafiya kuwa Amira? Imran ko kayi mata wani abun ne?" Imran yace "Niba abunda na mata" Amira ta ɗago ta harari Imran, Abba yace "gayamin me yai miki?" "Ni kawai yake ya ɗakkoni, ban shirya ba ban komai ba, ban taho da komai nawa ba, daga ni se kayan jikina,yazo ya ajiyeni ya tafi, tun a hanya nace ina jin yunwa Amma ya ƙyaleni yazo ya ajiyeni ya tafi, kuma banci Abinci ba, kuma ni dan Allah kace ya maida ni gida, ko tasha a kaini in hau mota in koma, ni bana son zama a nan gidan" tai maganar cikin kuka. Abba yace "yi haƙuri ya isa haka, besan baki ci Abinci ba, amma ga nawa cna kije ki zuba kici, za'a kawo miki kayan da zaki amfani dasu, kuma ki kwantar da hankalinki anjima 'yan gidanku zasu zo, ki bari suzo idan aka kammala biki sekuyi tafiyarku gida, kuma abunda yasa ya kawoki nan, kinga akwai rigimar da kika janyo, 'yan Sanda suna nemanki Wannan mawaƙin ya kai ƙararraki, kimga Yakamata muyi settling wannan mtsalar be kamata a ce an kama ki ba, kinga da baki je Abujan nan ba da duka haka bata faru ba" Amira ta share hawayen ta tace  "aini dama bance zan fito a waƙarsa ba, kawai nace masa zanyi tunani ne, kuma ni ƙarya yai min, bikin wannan Hassan ɗin, ɗan gidan ƙaramin ministan man fetur muka je, mun samu saɓani dashi, shine suka haɗa baki" Abba yace "saɓanin me? Kuma meyasa kika je Abuja?" Amira tace  "eh muna harkar bukukuwa, mc da kaɗe kaɗe shine aka gayyacemu can, da mukaje anyi bikin kuma ya biyoni Hotel ɗin da nake muka samu Saɓani". zuciyar Imran kamar ta fashe, saboda maganar Ihsan data faɗo masa  "AN FASA AUREN, SABODA AN KAMASHI A BANƊAKI A HOTEL KARUWA TA RIFE SHI" Wani irin baƙinciki da takaici suka ziyarci zuciyar Imran, Abba yace "shikenan a bar maganar ta wuce, zanyi waya da mahaifin shi Hassan ɗin, Imran miƙo kayan breakfast ɗin nan ka haɗa mata" Imran ya kalli Abba zeyi magana, Amma Abba ya girgiza masa kai. Haka yana ɓacin rai ya haɗawa Amira tea, ga soyayyen dankalin turawa da ƙwai. Amira tace "ni bana cin wannan shayi kawai zan sha" Abba yace "saboda me?" "Ni ƙosai nake so, shi muke ci a gidanmu da Safe" Abba ya kalli Imran daya ɓata fuska yace  "Imran, ko za'a samu me ƙosai a nan kusa?" A ɗan hasale Imran yace "Abba kai ma dai kasan babu wata me ƙosai a unguwar nan, waye ze sai wani ƙosai? Sekace a ƙauye" Abba yace "cin ƙosan ne se a ƙauye?, idan aka ɗan zagaya ai za'a iya samu, ka duba ko zaka samo mata mana" Wani matsiyacin kallo Imran yaiwa Amira, ta ɗauke kanta kamar bata ganshi ba, ya miƙe yana mitar shi a ina ze wani samo ƙosai. Amira tace "ya barshi ma, zanci wannan ɗin". Abba yace "to shikenan, dawo ba se kaje ba" Imran kasa ya jinjina kai ya dawo ya zauna, cike da takaici da ɓacin rai. Amira ta dinga cin Abincinta, Abba yace "ai Munyi waya da 'yan gidanku, suma sun taho suna hanya, yanzu Imran zeje ya karɓo miki kayanki na fitar biki" Amira ba tace komai ba, ta cigaba da cin Abincin ta, yayin da Imran ya ɗaure fuska tam. Ammi ce ta shigo ɗakin Abba, tana zuwa tsakiyar falon tai turus ganin Amira zaune tana cin abincin Abba. "Ke me kike yi a nan gurin nan, har kike cin abinci a wannan kwanon?" Abba yace "Amiran ce baki gane ba, kokuma me?" "In ma na gane ta seme? Me take a nan nake tambaya?" Gaba ɗaya Amira taji Abincin ya fita daga ranta, saboda masifar Ammi. Abba yace "nine nace a kawon ita nan" "Amma inda mutane suke, be isa ta zauna a can ba se an kawota a nan?" Miƙewa Amira tayi tace "na ƙoshi" Abba yace "zauna ki ƙarasa cin Abincin ki" Amira tace "A'a na ƙoshi" Ta juya zata fita, Imran ya tashi yabi bayan ta, yace "ke karki koma cikin gidan nan, biyoni" Tabi bayan Imran, part ɗinsa ya nufa ta bishi a baya, suka shiga falonsa, suna shiga ya mai da ƙofa ya kulle yasa key ya kalleta yace "a nan na yadda ki zauna, karki kuskura kije ko ina daga nan, kinji na gaya miki, kuma wallahi kika min taɓe taɓen abunda ban saki ba, sena ɓata miki rai" Ba tace komai ba ta zauna akan kujera, tana ƙarewa ɗakin kallo. Har yai gaba ya juyo yace "kuma wallahi, idan kika sake kika kuma fito da wani iyayi a gaban Abba, wallahi a gaban nasa zan zaneki, sa'anki ne ni da zaki sa a aikeni siyo miki wani ƙosai, sa'anki ne ni?" Ya tambayeta cikin tsawa. Amira ta girgiza kai, yace "ki sake ki gani, zaki ga yadda zanyi dake, banza kawai". Shiru tayi bata ce masa komai ba, ya wuce bedroom ɗinsa, ya jima a ciki tana ita kuma tana zaune a falon, tayi shiru kamar mayya, be kula ta ba yazo ya fice daga falon, ya kulleta ta waje. Tsaki tayi, ta hau kan kujera 3seater, ta kwanta tai shiru tana tunani, gaba ɗaya ranta a ɓace yake, hankalinta duk yayi gida, burinta kawai ta ganta a gida, dan gaba ɗaya gidan nan da mutanen cikin su ba suyi mata ba, Sannan ta ƙwafe Minal akan abun da tayi mata, abun ya ɓata Mata rai sosai. Ammi kuwa sam Abba ƙim biye mata yayi, taita mitarta harta gaji ta haƙura, daga baya tace  "Nayi waya da  Babar Ihsan, tace min ance mata an canza gidan da za'ayi jeren kayan amarya, zuwa gidanka na Bamako, shine nace meyasa aka canza? Bayan naga gidan Imran ɗinma babban gidane ya ishe su, ya zasuyi da wannan uban gidan su biyu?" Abba yace "Eh akwai dalilin yin hakan" "Meye dalilin?" Ta tambayeshi tana kallonsa. "Zakiji a nan gaba kaɗan" "Nifa na kasa gane kanka tunda bikin nan ya ƙarato, meye bazaka gayamin yanzu ba, ni me zance musu suna nan suna jirana in gayamusu dalili, zau tafi jeren kaya?" "Suma zasu san dililim ba da daɗewa ba, sannan ba wani abun tashin hankali bane"  yana gama maganar ya miƙe ya fita ya barta a falon. Kusan mintuna talatin da fitar Imran, se gashi ya dawo, ya buɗe falon ya ajiye mata leda a gabanta yace  "gashi nan, kayan wanka ne a ciki da tooth brush, ga toilet nan a Falo ki shiga kiyi wanka, idan kin ga dama kiyi abunda ban saki ba, in dawo kiga yadda zanyi dake" Maimakon ta motsa sema lumshe idanunta da tayi, tai masa banza, be sake kulata ba, ya ɗau abunda yake buƙata ya kulle bedroom ɗinsa ya barta a falo, ya kuma kulleta yai tafiyarsa. Gaba ɗaya suka gama shirinsu, Anty Fa'iza bata ƙara so ba, suka kirata a waya tace musu kayanta da nauyi, dan haka su haɗu a tasha gurin hawa mota. Yafikko tace "nikam ban so tafiyar nan babu ni ba, amma duk yadda zakuyi Ke Sadiya da kuma ke Amina, kuyi duk yadda zakuyi, ku janyi hankalin yaron nan kanku, ko shi ko kuma mahaifinsa, mu samu ko wata daga cikinku ne ku aura muma, mu huta, kai Amma Amira ta cuceni da ta ka dani ba damar inje gurin nan, shegiya watsatsiyar Yarinya, mara hankali, ko da yake ta yiwa kanta itama, tunda ta tafi gantalinta ba wanda yasan inda take, ita ma ba taje ba, nima banje ba da kunje ku gaywa Alhaji Ali kar ya ga ba 'azo da ita ba, tana can ta tafi iskancinta, sannan dan Allah duk abinda kuka samo ku ɗan ragomin nima" Haka taita musu zantuka, daga nan suka kama hanya suka tafi tasha, suka haɗu da Fa'iza a can, suka hau Mota. Dasu Umma sukaje gidan su Imran, suma ba wani takansu Ammi tabi ba, amma duk da haka an basu masauki, an kai musu Abinci, Minal se wani gani gani take musu, kamar taga wani abu na daban. Amira wuni tayi a cikin falon Imran, ga yunwa ta isheta, ga waya ba caji ta rasa abunda za tayi taji daɗi kawai ta hau kuka, tayi me isarta sannan ta Share hawayenta. Imran kuwa, suna gurin Bridal shower, shida abokansa dan ya ma manta da wata Amira, shagalinsa kawai yake, sedai lokaci lokaci gabansa ya kan faɗi idan ya tuna mata biyu za'a aura masa, kuma haryanzu daga Ammi har Amaren Babu wanda ya sani. Se bayan isha'i sannan Imran ya dawo gida, shima a gajiye yake sosai, a harabar gidan 'yan mata matan nan na family ɗin su Ammi suka dinga tsokanarsa, wai dama she yana soyayya gashi harzeyi Aure. Amina ce ta hango shi, ta tuni da huɗubar Yadikko, ta tsaya 'yan matan nan suka ragu, sannan ta nufi inda Imran yake, tana zuwa ta zube ƙasa ta gaisheshi. Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa mata yace "she kunzo?" Tace "eh munzo tun ɗazu, sedai ba'azo da Yadikko ba, tunda Amira ta hankaɗeta ta faɗi ƙasa bata iya tashi, kuma ita ma Amiran ba'azo da ita ba, babu wanda yasan inda take, tunda ta fice yawonta ba wanda yasan inda take" Imran yace "Ba yawo ta tafi ba, ni naje na ɗakkota jiya" be kuma cewa komai ba yai gaba abunsa. Ya bar Amina a tsaye tana mamaki, gurinsu Fa'iza ta koma, tace "wai dama Amira tana gidan nan?" Fa'iza tace "eh tana nan, tun da muka zo nake zuba ido inga a ina zan ganta, tun jiya Imran yaje ya ɗauketa suka taho" Sadiya tace "wai shi Imran ɗin da kansa?" Fa'iza tace "eh mana, har gidana yaje nemanta". Gaba ɗaya mamaki ne ya cikasu, Amma sukayi shiru, basu kuma cewa komai ba. Imran yana zuwa ya buɗe falon ya shiga, ya sha Manyan kaya se ƙamshi yake, Amira tana zaune tai tsuru da ita kamar kyanwa, be kulata ba ya wuce ɗakinsa, yaje yai wanka ya canza kaya, ya fito falon yaje ya buɗe fridge ɗinsa, komai yana nan yadda yake, bata taɓa komai ba, ya kalleta babu alamar taci Abinci tun breakfast. Ya ɗakko wani ƙaton cake, da lemo ya Kawo ya ajiyemata a gabanta, yakuma ɗaukar kayansa yai waje ya kulleta a ciki. Khalid na ganin Imran yace "Angon biyu lafiya kuwa? Yau a nan zaka kwana ne?" "Eh waccan yarinyace tai ƙoƙarin guduwa da safe, Allah yasa na nunawa security ita, da tuni ta gudu da safe, shine na kulleta a ɗakina" Khalid yaita dariya yace "Yaseen kafi son Amira akan Ihsan, irin wannan tattali haka?" "Nifa daɗina da kai rashin hankali wasu lokutan, ni na gaya maka ina son wannan yarinyar ne? Kawai ba yadda zanyi ne, nasan idan ta gudu nine a wahala, ni za'a sa in tafi yawon nemanta" Khalid baya son yaja zancen suyi faɗa, dan haka ya ƙyale Imran. A daren Amira ta cire kayan jikinta, ta wankesu a banɗakin falon Imran, da yake akwai liquid soap a ciki, ta saka sabuwar  doguwar rigar jallabiuar daya kawo mata, taƙi yin Bacci saboda kar tana bacci, Imran ya shigo ya shiga toilet ɗin nan yaga kayanta a ciki, dan harda underwears ɗinta ta wanke. Seda kayan nan suka bushe, ta kwashe su daga banɗakin, Sannan hankalinta ya kwanta, ta kwanta akan doguwar kujera bacci ya ɗauke ta. Da safe Imran yazo ya kawo mata Abinci, sedai be kulata ba, ya ajiye mata ya tafi, ya maida ita kamar wata ɗaurarriyar Akuyarsa. Ranar Alhamis yakama za'ayi dinner, kowa nata shiri ana hada hada amma an kulle Amira a ɗaki. Gashi ance mata 'yan gidansu zasu zo, amma Imran ya kulleta, gashi tana tsoron masa rashin kunya ya casa ta, dan ba kowa a gurin daga shi se ita. Imran na shiga cikin gida yana son ya karɓi abu a hannun Ammi, Anty Hadiza tace masa "Imran nikam ina Amira ne? 'yan gidansu suna nemanta amma basu ganta ba tunda suka zo" Imran yace "eh zasu haɗu a gurin dinner, tana ɗakina" "Me takeyi a ɗakinka?" "Jiya guduwa taso tayi, shiyasa na rifeta a ɗakin na koma gidansu Khalid, akwai magana fa, naso in samu lokaci in ganki amma ba time" "Labarta min, meye maganar?" Imran ya ɗan taɓe baki yace "zaki ji very soon, Yanzu dai nemomin Ammi" Da ƙyar aka gano Ammi cikin jama'a, ya karɓi abunda ze karɓa ya fita. Mutane wasu duk sun watse sun tafi gurin make up. Amira tana  kwance tayi shiru, tayi kukan ta gaji, Imran ya buɗe ɗakin ya shiga. Ya kalleta yace "kinyi wanka?" Ba tare da ta kalleshi ba tace nayi "Kuma shine kika zauna haka busu busu baki shafa mai ba?" Sekace ya bata man da zata shafa ɗin, banza tai masa kamar bata ji ba. Ya kuma ajiye mata kaya yace "tashi ki shiga bedroom ɗin nan kisa kayan nan ki ɗauki mai akan mirror ki shafa ki zo ina jiranki yanzun nan" Ta karɓi kayan ta shiga ɗakin nasa, ta rufe ƙofa se tsaki take tana zumɓura baki, ta ƙarewa dressing mirror ɗin kallo, mayuka kamar na Mace. Ta buɗe ɗakin ta kalleshi tace "babu me gurguwa a ɗakin" Ya kalleta yace "wace gurguwar?" "Shine man da nake shafawa, ni bana shafa irin wannan" "Kin wuce ko sena zo nayi ball dake? Me kuturwa kike shafawa bame gurguwa ba" Ta bugo ƙofar da ƙarfi ta koma cikin ɗakin tana tsaki, wani danƙareren less ne, dark blue a cikin ledar, an ɗinka shi riiga da skirt, ko ina aka samu size ɗinta oho? Se takalmi da jakarsa, da mayafi da kayan yari da sarƙa. Amira ta saka kayan nan tsaf a jikinta, fuskarta babu makeup ba komai, ta ɗaura ɗankwalin tai wani irin kyau, ta kalli gadon Imran, tsaf dashi tai zamanta a kai. Tana jin yana masifar ba zata fito ba, Amma tai masa banza, a fusace ya buɗe ƙofar bedroom ɗin, ta ɗago idanunta ta kalleshi, kamar ba ita ba, kayan nan sun mata cif a jikinta. Dama  Abba ne yasa yayi wa  Usman waya, yace ya  bashi lambar Fa'iza yace a taho da size ɗin kayanta da takalmi, shine aka ɗinko mata. Tana zaune akan gadonsa, "bazaki taso ba kenan? Waye yace ma ki haumin gado?" Tashi tai daga kan gadon, tana ɗan tura baki, ya kai idonsa kan turarukansa yaga yadda tai masu aiki, ko ina ƙamshi kawai yake. Kawai ya girgiza kai, dan ya gaji da magana, duk taku ɗaya idan tayi, cike yake da ɗaukar hankali, haka ta taho kamar zata bangaje shi ta fito falon ta tsaya, tana hararsa ta gefen ido. Suka fito harabar gidan, mayafin kayan na riƙe a hannunta, bata yafa ba, ta riƙe jaka da hannu ɗaya, wani soja ta hanga da uniform a tsaye a jikin wata mota, sukaje bakin motar, Imran yacewa Sojan "gata nan ka kula da abunda nace maka" Sojan ya jinjina kai, Amira ta kalli sojan ta kalli Imran, Imran Ya haɗe rai yace "idan ta maka rashin Kunya ko taurin kai, ka harbeta ni na saka ka kawon gawarta!!! Amira tace "Na shiga uku, harbi kuma kamar wata 'yar fashi!!! Share Please (🤣🤣 Me Oga Imran ke shirin yine haka? Da cakwalkwalin cakwakiya fa, Ina jiran jin Comments ɗinku) Please don't come to my inbox, And start telling me from page 1 please. Wanda yake nema daga farkon, ya duba watpad @ Ayshercool 7724 Domin gyara, Sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 [1/17, 12:46 PM] Ayshercool:          🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥                 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                                                     19_20 Imran yace "Eh ka harbeta idan tayi maka rashin mutunci ka harbeta a ƙafafumta" Amira ta tsaya tana kallon Imran, aka buɗe mata ƙofar motar ta shiga, Sojan yaja suka fita, seda Imran yaga fitar motar Sannan ya juya ya nufi gidansu Khalid. Ƙofar wani katafaren gurin gyaran jiki da kwalliya sojan nan yai parking, ya fito ya buɗewa Amira ƙofa, Amira taƙi fitowa ta kalli gurin sannan ta kalli sojan tace "nan kuma ina ne?" "Eh nan ne yace a kawoki, bari in mata Magana" Taɓe baki Amira tayi, ta cigaba da kalle kallenta. Ya koma gefe yai waya, mimtuna kaɗan sega wata farar mata ta leƙo, tai murmushi tace "tana ina?" Sojan yace "gata nan a cikin mota, ki fito ki shiga' Seda Amira taja aji sannan ta fito daga motar ta shiga gurin, matar ta bawa Amira guri ta zauna. Katafaren gurin gyaran jiki ne da guaran kai na mata, gurin ya haɗu sosai. Matar ta nunawa Amira wata kujera a gaban mudubi tace "zoki zauna a nan mu fara kar lokaci ya ƙure" Amira tace "wai me zakiyi min ne?" "Yi haƙuri, ba wani abu zan miki ba, kwalliya ce akace zan miki" "Kwalliya kuma, waye yace kiyi min?" "Kai kekam akwai daru da tambayoyi, daga gidan Alhaji Ali ne" Taɓe baki Amira tayi tace "ki bari inyi salla tukuna, dan idan akayi lokacin salla yayi wanketa zanyi ba ruwana" Me kwalliyar tai murmushi tace 'to ta salla" Haka kuwa akayi seda Amira tayi Salla sannan aka fara kwalliyar, harta samu Guri ta saka cajin wayarta. Se magariba aka gama kwalliyar, sedai Amira ta haɗu tayi kyau sosai, me kwalliyar taita ɗaukarta hotuna, har sukayi musayar lambar waya. Sojan nan na waje ba inda yaje yana jiran Amira, dan ba ƙaramin warning Imran yai masa a kanta ba. Dukda haka seda ta saka ya tsaya, ta cire kuɗi a POS, yana yi yana kaffa kaffa karta tsere. Ihsan ma tana can kai ya ɗau caji, tana gurin kwalliya, tana son ayi a gama kan Imran yazo ɗaukarta, dan baya son jira. Amira kuwa tuni ta isa gurin dinner ɗin, seda ta tsaya a bakin ƙofa ta ƙarewa ko ina kallo sannan ta shiga, tana ta waige waige, can ta hango Anty Fa'iza da su Amina, da gudu ta ƙarasa inda suke ta rungume Fa'iza tana 'oyoyo" Fa'iza tace "kai Amira wannan kwalliyar fa?" 'hmm kedai bari kawai" tai maganar tana janyo Khairat jikinta, tace "Sadiyayye ya hanya" Sadiya ta ɗan kwaɓe fuska tace "Alhamdilillah, ashe ke tuntuni kina nan?" "Wallahi kuwa, har gurin su Sultan yaje ya ɗaukeni na sha tijara, kai mitumin nan bashi da imani, seda na kwana biyu a ɗakinsa, a rufe kamar wata Akuya sedai ya kawomin Abinci ya kulleni yai tafiyarsa, ai naga tasku" Amina da Sadiya suka haɗa ido, suka ɗan jinjina kai a tare, Fa'iza tace "Ai gidana ya fara zuwa nemanki, tun daga Kaduna yake tracking ɗinki, yana zuwa gidana kuma ki bar gidan shine ya biki can gurin Sultan" "Aini nan Alla Alla nake a gama bikin nan in koma gida na gaji da zaman garin nan sam babu daɗi" Suna cikin hirar ne sega Minal da tawagar ƙawayenta sun shigo, ana ta sanar da cewa ango ya kusa isowa shi da Amaryarsa. Minal suka zauna akan kujerun bayan su Amira. Can Amira tace 'nifa na ƙagu inga wace me tsautsayin ce zata auri wannan jarababen mutumin mara tausayi" Ɗagowa Minal tayi ta kalli Amira, amma Amira ta cigaba da maganar ta. "Dan wallahi duk wadda ta kwashi Wannan, ta shiga uku, banjin ko ɗan rarrashin nan ya iya, banda tsawa da hantara be iya komai ba" Fa'iza tace "kai Amira ki bari mana, ɗan uwanki ne, kuma kina cikin 'uan uwansa be kamata ki faɗi haka ba" "Na faɗa aje a gaya masa, dan baki san da yadda ya ɗakkoni daga Kano ba, yadda kika san dabba haka yaimin, yana jana ina kuka ina masa magiya, amma ko a jikinsa sema zagina da yake" Minal da ta fara ƙulewa da maganganun Amira, wanda dama Amiran tana sane takeyi ta ja tsaki tace "Ai dabbar ce ke, dole ai treating ɗinki kamar su" Maimakon Amira ta nuna taji haushi, kota rama seta ɗakko wayarta tace "hey guys let's snap pics" Nan ta shiga yin hotunanta hankali kwance, can tace "Nifa jikina tsuma yake, zanje a sakarmin sauti in cashe" "Dan girman Allah kiyi haƙuri, ki rifa mana Asiri mu koma gida lafiya" Anty Fa'iza tai maganar tana riƙe skirt ɗin Amira. Amira tai murmushi tace "cikani tunda ba ɓarauniya kika kama ba" Aka sanar da isowar Amgo da Amarya, wanda sojojine zasu shigo dasu da bridesmaids. Suna nan zaune aka saki wani kiɗan parrate, sega sojojin nan sun shigo cikin shigarsu ta ɗamara, suna taku daidai da kiɗan dake tashi, abun gwanin burgewa. Haka suka rakasu har kan high table, Ihsan ta sunkunyar da kanta a cikin mayafi, shiyasa Amira bata ganta sosai ba. Seda aka ɗan jima sannan Imran ya ɗagewa Ihsan mayafin kanta, ta sha make up gata fara sol, tayi kyau matuƙa. "Taɓɗijan dama Wannan ce matar daze aura ɗin, ai na taɓa ganin wannan a Abuja, duk iyayin nasa ya ƙare a wannan skelaton ɗin, aba kamar bata cin Abinci, ga wani make up an mata kamar tsohuwa, gaskiya me kwalliyar nan ta cuceta" Minal ta kuma waigowa tana kallon Amira, se cin zarafin Imran take da Ihsan hankalinta kwance, kuma ga wasu daga cikin 'yan uwan Ihsan ɗin a gurin a zaune. "Da kike kushe Ihsan, kin san ko banza ta fiki komai, ita kamilalliya ce ba irinki ba watsatsiya, wadda bata san darajar kamta ba" Maimakon Amira taji haushi se cewa tayi "matan ma dai suna suka tara, yo wannan idan tai kwalliya ta fito gaban miji maimakon ta burgeshi ai tausayi zata bashi, ya zata ko bata da lafiya, ai mace tai juyi aga tana da abun kallo shine take mace, amma wannan se kace tana cin ƙanzo, gaskiya wannan Imran ɗin bashi da wayo be iya zaɓen mace ba, gata wata busu busu da ita kamar zabiya" Amina tace "haba Amira, dan Allah kidena mana, waike duk inda kika je sekin nemi magana, ina ruwanki ne" Anty Fa'iza tace "Ai shine, dan Allah Amira ki bari, Minal kiyi haƙuri please" Minal tace "ita zaki gayawa ta bari, wallahi idan bata dena zagin Anty Ihsan ba, nima bazan bar gaya mata magana ba, ina ruwanta damu, ita ya gani yace yana so, iya har tana da bakin magana, kota kushe wani, ita da take da abun faɗa, karuwar banza ballagaza" Amira bata rama ba, sema bin waƙar dake tashi Yanzu take, sojojin nan sukaje suka canzo kaya, suka cika kan stage suna rawa, se ihu suke suna cashewa, suka janyo Imran daga kan kujera, suna ɗaga shi sama. "Kai gaskiya ma dai wasu sojojin mahaukata ne, kalli abinda sukeyi kamar basu da hankali, bayan rashin imani harda shirme, wai waɗan nan sojoji ne taɓ" "Sojojin ne marasa hankali?" Amira tace "eh sune, kuma hadda Yayanki, su marasa hankali shi mara Imani, na faɗa tashi kije ki gaya masa, tun da nazo ƙyaleki kawai nakeyi, kuma ina ji a zuciyata in ba wani iko na Allah ba se Amira ta bar miki babban tabo, kallonki kawai nake sokuwa da baki kamar jaɓa" Wata ƙawar Minal tace "kinga taso mu bar gurin nan, wannan'yar jaraba ce wallahi, neman abokin yi take nema, Minal ƙyaleta mu farinciki ne ya tara mu ba tsiya ba" Minal tace "kamar kuwa kin san 'yar matsiyatan ce, shiyasa take abu  a haka, ni ba inda zanje, ina nan idan ta faɗi ɗaya in gayamata goma" Tun Anty Fa'iza tana ƙoƙarin shiga tsakani ta rabasu, Amma abu ya gagareta, Minal ta kasa gane Amira tana sane take kunnata tana bala'i, seda ta tabattar ta ɓatawa Minal rai yadda ya kamata sannan ta miƙe ta nufi filin rawa, inda yake ango da Amarya ne kawai a tsakiyar filin, Imran yanawa Ihsan liƙi tana sunkunyar da kanta ƙasa. Tana tunakarar inda suke, Ihsan ta ɗago kanta, aikuwa sukayi ido huɗu da Amira, Amira ta sakar mata murmushi, tunda Amira ta taho hankalin mutane Ya dawo kanta. Takaici ne ya kama Imran ganin yadda ta taho jikinta babu ko mayafi, Amira na ƙarasowa ta fara dariya, se dariyar da take tai mata wani mugun kyau, ta kalli Ihsan tace 'Yayata liƙi nazo yi muku, Allah ya sanya Alkhairi, ya baki ikon haƙuri da juriya akan halin mutumin da kika aura" Nan gaban Ihsan ya shiga harbawa, ta ɗaga kai tana wa Imran kallon tuhuma, gaba ɗaya Imran ya rasa mema zeyi. Amira ta buɗe jakarta ta ɗakko kuɗi, ta fara liƙa musu, tana yi tana murmushi, gaba ɗaya Ihsan tausayi da dariya take bawa Amira, a ƙalla Ihsan zata kai shekaru Ashirin da biyar, amma ƙirjinta kamar 'yar shekara sha huɗu, siririyace sosai sedai fara ce tas ajin farko. Khalid ne ya hau kan stage ɗin yace, "Amira matsa kusa dasu in muku hoto" Amira tace 'to bari a temaka musu, suyi hoto da celebrity" Wani sojane ya ƙaraso shima, yace Amira ta kawo wayarta a ɗaukar mata hotunan, se cewa tay "Allah ya kiyaye ta ajiye hoton Imran a wayarta" Imran ya kalleta kawai ya ɗauke kai, ta tsaya a jikin Imran, yayin da ya tsaya yana kallon Amira, Ihsan kuma tanawa Amira kallon tsana da takaici. Imran ya kalli Amira yace "malama ina mayafin kayan da na haɗa miki dasu?" "Ni ajiye shi" ta bashi amsa "Dama dan ki ajiye na baki?" "Kaga malam karka takuramin mana, haba ka barni in huta nagaji da wannan ƙarfin halin naka" Imran kawai ya bita da kallon mamaki da takaici. Aka dinga hotuna, Khalid seda yasan yadda yayi yaiwa Imran hotuna akan high table harda Amira, saboda itama Amrayar ɓoye ce. Ana gama hotuna ta sakko, an saka waƙar da take so, nam ta fara takawa, cikin salonta na burgewa da jan hankali, sedai bata girgiza jikinta wannan karon, amma rawar ta ta ta bada kala. Nan fa ta fara shan liƙi, Imran ya dafe kansa yana fesar da numfashi, Ihsan kamar zata fashe da kuka tace "Imran wace wannan yarinyar?" "Amira ce" ya bata amsar kai tsaye. "Amma Imran, kai kace min yarinya ce, kuma na nuna maka hotonta kace ba ka santa ba, ashe ita ce Amiran, itace kake zuwa gurinta a Kano? Imran dama zaka iya ɓoyemin wani abu?" Hawaye suka fara bin idon Ihsan. Dan wata muguwar tsana da kishi ne suka baibayeta, ba namijin daze wa Amira kallo ɗaya ya kauda idonsa, mussaman surar jiki da Allah yai mata, amma a haka Imran ya dinga ce mata ai Yarinyace ƙarama, kuma yazo yai mata ƙarya, Amira 'yar galace luma Karuwa, kallo ɗaya zakayiwa idonta kasan fitsararriya ce. Wani irin gumi ya shiga tsatstafowa Ihsan, hawaye wani na bin wani Imran yai ƙasa da murya yace "dan Allah Ihsan kiyi haƙuri, zan miki bayanin komai" "Bana buƙatar bayaninka Imran, ka bani kunya wallahi" tai maganar kanta a ƙasa tana goge hawayw ta cikin mayafinta. Hankalin mutane yana kan Amira, dan haka ba kowa ya lura da abunda ke faruwa ba. MC ne yace "kai Masha Allah, 'yar baiwa muna godiya da wannan gudunmawar ta hanyar nishaɗantar damu da kikayi, ga tsabar farinciki Amarya tana zubar da hawayen farinciki, Amarya Wannan rana ce me girma ya farinciki a gareki, dan haka be kamata aga kina hawaye ba, ango yakamata ka Share mata wannan hawayen mana. Imran kam ji yayi gaba ɗaya taron bikin ya fita daga ransa, yaji dama Amira bata zo gurin taron ba, Abba ne ya matsa Lallai taje, ga abubuwa na shirin kwaɓewa, yana ƙoƙarin ya rarrashi Ihsan amma a hasale tace masa "dan Allah malam ka ƙyaleni" Yana ɗaga kai ya hango Amira a zaune, Matasan sojojin nan zarata, sun kewaye kujerar da take, suna ta mata surutu, wani lokacin tayi murmushi wani lokacin kuma ta bisu da kallo. Wayarsa ya ciro yaiwa Khalid message ya maida ita cikin Aljihunsa, Ƙannen mahaifiyar Ihsan suka je suka kamo hannunta daga kan high table, suka sakata a tsakiyar filin rawa suna jujjuyata suna mata liƙi. Maman Ihsan ce tace "ke Ihsan wannan wane irin sakarci ne haka, sekace wadda za'aiwa Auren dole? Kukan me kikeyi haka?" "Ahh ki ƙyaleta, ze iya yuwuwa kukan farinciki ne, kuma ze iya yuwuwa tana tunanin sabuwar rayuwar da zata shi ne" cewar ƙanwar mahaifin Ihsan. Aka shigo da Imran ma tsakiyar filin, Ammi da su Minal suna masa liƙi. Khalid ya ƙaraso inda Amira take, yace yana son Magana da ita, tana ganin mutuncin Khalid dan haka bata musa masa ba, ta tashi suka koma gefe ya kalleta yace "Imran yace  a maida ke gida yanzu" "Saboda me, naga ba'a tashi ba?" "Eh haka dai yace min" "Gaskiya bazan tafi yanzu ba, kowa yana nan a maida ni gida ni kaɗai, wallahi bazan tafi yanzu ba se an tashi" Khalid ba yadda beyi da Amira ba, amma tace fafur ba zata koma gida yanzu ba. Khalid ya zaga yaje kunnen Imran ya gaya masa yadda sukayi da Amira,  Imran yaiwa Khalid raɗa a kunne, Khalid ya koma inda Amira take, Imran ma ya koma gefe. Imran ya kira wayar Khalid, Khalid kuma ya bawa Amira, Imran yace  "Malama ni nace a maida ke gida yanzun nan, ki bar gurin taron nan" "Wai saboda me? Naga dai bani nace zanzo ba, kasa aka kawoni, kuma  kowa yana nan sekace a maida ni gida, wallahi bazan tafi yanzu ba, sedai in tashi akayi" Imran yace "ni kike gayawa haka?" "Toni me nace, idan kuma baka son in zauna seka zo ka maida ni gida, Amma baza'a maida ni gidan nan inje in zauna kamar mayya ba" Yana ƙoƙarin sake yin Magana, Amma Amira ta katse kiran ta bawa Khalid Wayarsa. Khalid yace "Amira ki dena yiwa Imran haka baze ji daɗi ya baki umarni kiƙi bi ba" "To me nayi masa, kawai ina zaune yace sena koma gida haka akeyi?" "Yi haƙuri, baki san dalilinsa na faɗar hakan ba, kiyi haƙuri a maida ke, nida kaina zan maida ke gidan ma" Amira ta tura baki irin bata so ɗin nan ba, Khalid yace "yi haƙuri Amaryarmu, tashi muje karya miki faɗan nasa idan kuka koma gida" 'Amaryarku kuma? Wuce nan ga amaryarku can bushashshiya kamar karan dawa" Tai maganar tana jujjuya idonta, tuna sakin layin da yai yayi, yai saurin cewa "Ai kyan da kikayi baza'a banbanceki keda Amrayar bane" "To bari in kira su Yaya Fa'iza, se ka maida mu tare" "A'a, akwai motocin da zasu maidasu, keɗin dai ki taso mu tafi" "To ai banci Abinci ba, kuma ina jin yunwa dan azabtar dani yai tayi, sedai ya bani cake, ko abunda bazan ƙoashi ba" Khalid yai dariya yace "an ajiye miki komai naki, yana mota taso muje in kaiki" Haka ta miƙe tai gaba, jikin nan nata bako mayafi suka fita daga hall ɗin, seda suka fita akan idon Imran sannan hankalinsa ya kwanta, amma ya ƙule ƙwarai da Amira yau, dan ji yai tamkar ya maƙureta a gurin nan. Har cikin gida Khalid ya shiga da motar, sannan ya fito ya buɗe mata motar ta fito, ya bata babbar leda cike da duk wani abu da'aka raba a gurin nan, ta karɓa ta kalli Khalid tace "Nagode sosai Allah ya saka da alheri, kana da kirki sosai ba kamar wancan masifaffen ba" Khalid yace "ba ruwana kumfi kusa" "Ba wani kusa, waze raɓi wannan masifaffen, seda Safe" tana gama faɗin haka ta tafi. Khalid yai murmushi, wato gaba ɗaya Amira simple ce, babu babban abunda yake biyar da ita cikin sauƙi irin rarrashi, bata son faɗa dan shi ke sata taurin kai, sedai kuma Imran is very serious Man, be fiye son shirme ba. Khalid ya hau motarsa ya koma gurin bikin, sedai yana zuwa ya tarar Dangin Ihsan sun ɗauketa sun tafi da ita gida, dan ta kasa kwantar da hankalinta kuka kawai take, ga jiri yana ɗibarta, ƙarshe ba Amarya aka ƙarasa dinner, seda Ammi ta tambayi Imran ko dai wani abun yai mata, yace shi be mata komai ba. Haka aka tarkata kowa ya fara kama gabansa, saboda dare yayi ga Amarya ta tafi. Su Sadiya da Amina aka samu banza, Abinci kamar zeyi Magana haka suka dinga lodar Abinci, suka dinga fakar idon mutane, suna kwashe lemuka da kajin da 'yan gayu suka bari, Ummma kuwa dama teburi teburi ta dinga zagawa, Sauran cake ne ko donut ko kaza haka ta dinga tattaresu a leda, shinkafa kuwa duk haɗamarsu seda syka tureta, haka lemuka ma suka sha iya shansu, suka dinga saye sauran. Amira kuwa kayanta na ɗakin Imran, tana son ɗaukar doguwar rigar daya sai mata ta saka, ta canza wannan kayan na jikinta, Amma ɗakin na rufe dan haka ta haƙura. Akwatin Anty Fa'iza ta gani a wani ɗaki, taje ta buɗe sega shi hadda kayanta irin wanda take zuwa ta bari a gidanta tazo mata dasu. Tai murmushi ta ɗauki wata riga da wando na bacci, taje ta watsa ruwa ta sauya kayan jikinta, ta cire wannan leshin daga jikinta, tai alwala tai sallar magariba da isha'i taci Abincin ta, sannan mutane suka fara dawowa gidan daga gurin dinner. Taje ɗakin Ihsan, ta kwantar da wata katifa, ta ɗauki bargo akan gadon Minal ta kwanta, ta ciro wayarta ta hau chatting. Ji tayi hayaniya na ƙaruwa, alamar mutane nata dawowa, yau a shirye tale da duk wani Iskanci na Minal, yau idan ta taɓata ba zata ɗaga mata ƙafa, shiyasa ma tazo ɗakin ta kwanta. Aikuwa babu jimawa sega Minal ta shigo, ta kunna fitilar ɗakin sega Amira tayi lumui a cikin bargo, akan katifa ga wayarta tana chatting. "Kan Uba, ubanwa ya baki izinin shigomin ɗaki harki kwanta" "Ubanki ne" ta bata amsa, sannan ta maida kanta kan wayarta. "Ni kike cewa Ubana?" Amira tai mata banza, bata kulata ba. "To wallahi sekin bar ɗakin nan, ai ba da babanki aka haɗu aka gina ɗakin ba, Karuwar banza data wofi, har zaki zo ki naniƙarmin bargo haka, mara mutunci mara tarbiyya, kece me kushe mutane da raina mutane, bayan kece me abun faɗa* Jin hayaniya yasa Anty Hadiza ta shigo ɗakin tana faɗin "Ke Minal, ke da wa haka? Muryarki kawai ake jiyowa kina masifa, lafiya?" "Ina fa lafiya wannan ƙaramar karuwar tazo ta kwantamin a ɗaki, wallahi seta barmin ɗakina, mar tarbiyya kawai baki ji yadda ta dinga zagin Yaya Imran ba, tana kushe Ihsan, dan tana taƙama da ƙaramin Iskancinta" Amira ta miƙe ta kalli Minal tace "karki ƙara cewa ina taƙama da ƙaramin iskanci, da babban nake taƙama, kuma na zagi Imran ɗin waye yace yamin abunda zan zageshi? Ki kiyayeni wallahi" Amira tai maganar cike da kashedi tana nuna Minal. "Bazan kiyaye ki ɗin ba, kuma kema na zegeki karuwa kawai 'yar gidan karuwai mara tarbiyya" Amira tace "Naji nagode, amma nikaɗaice Karuwar, banda iyayena" Ta koma ta kwata, Anty Hadiza tace "gaskiya banji daɗin abun nan da kukayi ba, kamar ba 'yan uwa ba da giemanku da komai kamar wasu ƙananan yara, Minal karki kuma ce mata karuwa kinjibna gayamiki" "To Anty Hadiza ba karuwar bace? Ai karuwar ce mara amfani, kai kuma wallahi seta barmin ɗakina" Tai kan Amira, ta janye bargon jikin Amira, tana ƙoƙarin fizgo Amira akan katifa, aikuwa Amira ta shaƙoata, take kokowa ta ɓarke a tsakaninsu Anty Hadiza da sauran mutanen dake gurin suka kasa rabasu, aka samu wata taje ta gayawa Ammi, wadda dawowarta kenan, aikuwa a sukwane Ammi tai ɗakin Minal, jin ana can ana tumurmusar autarta. Tana zuwa taga an taru akansu, amma sunƙi rabuwa, da an rabasu Amira ta haƙura se Minal ta kuma dako tsalle Lallai seta rama abunda Amira tai Mata. Shikuwa Imran tunda suka taho da Khalid, baya jik me Khalid yake faɗa, dan hankalinsa baya jikinsa sam, tunani daban daban ya cika masa zuciya, harya rasa wanne zeyi ma. Suna zuwa gida Imran ya fito daga motar, sega Anty Hadiza tace "Yawwa, gara da Allah ya kawoka, wallahi Amira da Minal ke dambe tun ɗazu an kasa rabasu" "Kamar yaya dambe kamar wasu maza"? "Ni dai zo muje, ƙil in suka ganka su bari" Cikin sauri ya shiga cikin gidan, Ammi na ganinsa tace "maza zoka ƙwatarmin 'yata daga hannun wannan azzalumar da kuka haɗa kai da mahaifinka kuka kawomin gida, ta saba dambe da maza a bariki shiyasa take da ƙarfi kamar namiji, nibkarta kashemin 'ya dan idan ra kashe ta bazan yadda ba" Imran wani takaici ya mamaye zuciyarsa, yaje yana ƙoƙarin janye Amira da gaba ɗaya idonta ya rufe, Amma ta gasa masa wani lafiyayen cizo a hannunsa, aikuwa yasa hannu ɗaya ya fizgota a jikin Minal, yai jifa da ita gefe guda. Cikin kuka Minal tace "Na faɗa na kuma, Karuwa 'yar gidan Karuwai, ballagaza mara tarbiyya kawai" "Shut up!" Yaiwa Minal tsawa yace "banzaye sekace karnuka, dambe a gaban jama'a dan abun Kunya, Ke Minal ubanwa yace ki biye mata kin san ba ƙarfinku ɗaya ba, ta fiki girma ita faɗa a cikin ta kamar Karya, tai da maza tayi da mata" "Niba karya bace, karka sake cemin karya, dan ban taɓa faɗa da maza a titi ba, kuma wallahi ta kuma zagina sena maƙure mata wuya, kuma in kana da zuciya ka ƙyaleni in tafi gidanmu a daren nan, dan nan ba gidan ubana bane kamar yadda ake goranta min" 'ni kike gaywa haka?" Yai maganar yana nuna kansa. Cikin kuka tace "eh na faɗa ɗin" Hanyar waje yayi ya ƙyaleta, ta zauna tana kuka, Minal ma kukan take tana cigaba da mita se Amira ta bar mata ɗaki, mutane kuwa kowa da abunda yake tofawa, ai sega Imran ya dawo da wata wayar wuta a hannunsa, ya rufe ɗakin nan, wanda suke ciki suna ciki ya soma zuba musu ita su biyun. Dama gashi a ƙule yake da Amira, yau duk ransa a ɓace yake. Minal na ihu tana bawa Imran haƙuri, tana kiran Amminta tana bashi haƙuri, Amira kuwa Ihu take tana Allah ya saka mata. Hakan kuwa ya fusata shi, ya koma kan Amira ya dinga zuba mata wayar nan a jikinta, ga kayan baccin jikinta Nylon ne, ta ɗora hijjabi a kai. Amma tuni hijjabin yai nasa guri ya bar Amira, "Allah kaga abunda wannan bawan naka yakemin, Allah ka sakamin wallahi na barka da Allah" Kowa na gudun tunkarar Imran ya ƙwaci Amira, saboda duk wanda yazo gurin ze iya haɗawa da shi, Ammi ta window ta dinga kiran sunan Imran tana karya kashe mata 'ya, Amma be saurareta ba. Anty Fa'iza ma da tuni suka dawo, ta dinga masa magiya akan ya ƙyale Amira, dan ta san idan ze kashe Amira ne bakinta baze mutu ba, dan Amira akwai taurin kai, kuma bata son duka sam. Allah ya temaketa ta buɗe ƙofar ɗakin, tai waje da gudu jikinta na tsuma, saboda ta daku ba ƙarya. Abba kuwa daga part ɗinsa ya dinga jiyo hayaniya sama sama, yaji abun yaƙi ƙarewa dan haka ya fito, yana fitowa yaga Amira ta fito da gudu tana kuka, tayi hanyar waje sedai tana zuwa har an rufe gate ɗin dan haka Abba ya samu damar cin mata, ya riƙo hannayenta yana faɗin  "Amira lafiya kuwa? Meyasameki haka?" Kasa magana tayi se kuka da take kamar ranta ze fita, Anty Fa'iza ce ta ƙaraso ta cewa "gaskiya ba zamu kwana a gidan nan ba, tunda munzo anyi biki Allah ya amfana, Imran ze iya illata Amira" Cikin rashin Fahimta Abba yace "meyafaru ne?" "Faɗa ne ya haɗa su da Minal ya dake su, Amma dukan da yai wa Amira ya wuce tunani, tana mace be kamata ya mata wannan dukan ba, kalli jikinta fa" Gwanin ban tausayi, fatarta duk ta tara jini, wani gurin ya farfashe se rawar sanyi take tana kuka. Abba yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imran ɗin ne yai mata haka?" Dukda dukan da Imran ɗin yai mata, sam be huce ba ransa a ɓace yake sosai, yana fitowa harabar gidan yaga Abba a tsaye riƙe da hannun Amira, Mutane duk a tsaye a gurin. Gabansa ne ya faɗi ya ƙarasa gurin, yana zuwa zeyi magana Abba ya dskatar dashi yace "base kace komai ba Imran, nagode gara da ka nuna min irin riƙon da za kai Mata nagode sosai" "Abba ba haka bane, walla... "Shuy up! Meye ba hakan ba, da ka kasheta fa? wane irin duka ne wannan, waye ma yace kasa hannu ka daketa? Ka kyauta ba abunda zance maka se godiya" Abba yace a kawowa Amira Hijjabi, ya tafi da ita sashinsa, aka kawo hijjabi ta saka, amma still jikinta rawa yake, Anty Fa'iza zata bisu yace bakomai base ta bisu ba. Abba da kansa ya ɗakko bargo ya lulluɓeta, ya nemi guri ya zauna yana tunani, Imran ya rasa abunda zeyi gaba ɗaya Aurensa yazo masa a baibai. Ammi ce ta shiga sashin Abba tana faɗa "wallahi Abba ka bani mamaki, ko takan Minal baka bi ba bayan itama ya daketa, se wani abu kake akan Yarinyar nan, zan sake jadadda maka wallahi ba zata zauna min a gida ba, ka basu kuɗin mota gobe su tafi, ta kama min 'ya ta daka kuma shima yazo ya haɗasu ya daka, amma kai ta ita kawai kake baka ta 'yarka. Abba bece mata uffan ba, ya kalli inda Amira take, jikinta na cigaba da rawa se surutai take, yaje inda take kwance ya ɗan ɗaga bargon ya dafa goshinta, jikinta ya ɗau zafi sosai. Ran Abba ya sake ɓaci sosai, ya ɗau wayarsa ya kira Imran, ba'a daɗe ba sega Imran yazo jiki na rawa. Abba yace "kaga sakamako abunda kayi ko?" Imran ya sunkunyar da kai ƙasa. "Gidan Alhaji Hashim zamu tafi Yanzu, ka kaita mota gani nan fitowa" Amira ta tashi tana jiri, tabi bayan Imran, ita dai bata san ma yadda akayi taje mota ba se ganinta tai a Mota, Ammi tana ta masifa tana tambayar meye ba'asin zuwa gidan Alhaji Hashim a daren nan, amma Abba ya shareta ya fice. Suna tafe Abba na yiwa Imran faɗa "Imran idan bazaka iyayimin alfarmar da na nema a gurinka ba, tun wuri ka gayamin in nemi wani yayi min" "A'a Abba zan iya" "Aini na tsorata da lamarinka ne Imran, ka bani mamaki sosai" "Abba dan Allah kayi haƙuri, yarinyace sam bata da kunya, dambe fa sukayi ita da Minal a gaban mutane" "Du da haka, mata lallaɓasu akeyi, karka kuskura ka saba musu da duka mutuncinka ze zube a idonsu, mussaman duk irin wannan na rashin imani, duk randa ka kuskura ka daki wata a cikinsu duk hukuncin da nayi maka kai ka janyo shi" "Insha Allah bazan sake ba" Amarya Ihsan kuwa tunda suka koma gida take Kuka, aka rasa gane kanta sam, wani mugun kishi da haushin Imran suka mamayeta, ga tsanar Amira da take ji a ranta. Yayan Baban Amira ne yazo, yace ai masa magana da Maman Ihsan. "Kaine a tafe da daddare haka? Ina fatan lafiya ƙalau?" Yace "eh lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya hidima?" "Hidima Alhamdilillah, muna ta fama daga gobe in Allah ya kaimu dai an gama kowa ya huta" "Hakane, dama wata maganace ke tafe dani, kin san komai muƙaddari ne daga Allah, dan haka kafin in gayamiki koma meye, ina son kuyi tawakkali daga ke har Ihsan" "Lafiya kuwa? Auren suka fasa kokuwa?" "A'a ba Aure suka fasa ba, kamar yadda suka canza muku gidan da za'ayi jere hakan ya faru ne sakamakon wani hukunci da mahaifinsa shi angon ya yanke, ze aurawa ɗansa mata biyu ne lokaci ɗaya, bayan Ihsan akwai wata da za'a ɗaura Aurenta da Imran gobe in Allah ya kaimu, su biyu kenan !!! Domin Sharhi gyara Ko shawara Ayshercool 07073065680 [1/19, 2:13 PM] Ayshercool:             🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥                 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                     21_22 "Nifa ban fahimci abinda kake nufi ba, kamar yaya mata biyu za'a aura masa?" "Da hausa fa nayi miki bayani, ba da Yarabanci ba, Mijin Ihsan da za'a ɗaura musu Aure gobe in Allah ya kaimu, su biyu za'a aura masa, ita da abokiyar zamanta" A fusace Maman Ihsan tace "aikuwa ba zata saɓu ba sam, ni za'a ciwa mutunci a munafurta, daga ina wannan banzar maganar ta fito? Kuma ba'a gayamin tuntuni ba se ana i gobe za'a ɗaura Aure, dan cin fuska da cin zarafi" "Kinga ki dakata mun dan Allah, gudun irin wannan matsalar da rashin tawwakalin yasa ban sanar muku ba, tun kafin a fara bikin nan, suka zo suka sanarmin ni nace kar su gaya muku, in ba haka ba bazaku bari ayi bikin nan ta daɗin rai ba, kuma nine matsayin uba ga Ihsan, Auren nan bau fashi za'ayi shi gobe insha Allah, kin sani sarai bana Magana biyu, idan kinso kije ki rarrasheta ki kwantar mata da hankali, idan kin so kije ki zigata ki tayar mata da hankali kisa idan taje gidan miji ta kaso Auren, ke zaki zauna da ƙaramar bazawara a gida, idan kuma kina ganin duk wannan dandazon jama'ar da kika tara, zasu watsene a fasa Auren, ke kika jiyo se yadda kuka zaɓa" Yana gama maganar ya tashi ya fice. "Wallahi ba zata saɓu ba wai bindiga a ruwa, dan bala'i Auren fari yarinyar ba zata zauna ta huta taci amarcinta ba, za'a haɗata da wata a auren fari, Lallai Jamila ta munafurceni, dani take zancen". Ta ɗakko wayarta ta kira layin Ammi, sedai Ammi bata ɗaga ba, saboda tana can tana rarrashin Minal, saboda dukan da ta sha, gashi a ƙule take jiran su Abba take su dawo ayi wadda za'ayi akan Amira, Dan duk abunda za'ayi se Amira ta bar gidan nan a gobe. Maman Ilham ta dinga surfa masifa, tace sedai a fasa Auren baza'a ci mata mutunci ba, hankalin mutane'yan biki ya fara dawowa kanta, aka fara ƙoƙarin jin ba'asin abunda ya sata masifa haka a wannan daren, bayan dawowa daga dinner. Yayarta ce taja hannunta suka uwar ɗaki, ta rufe ƙofa tace  "Ke Murja, ki rufawa kanki Asiri kamar yadda Allah ya rufa miki, karki yadda a fasa Auren nan, ki taushi yarinyar nan taje ta tsuguna a ɗakinta tunda Yaron nan yana sonta tana sonshi nasan ba'ayi muku adalci ba, da ba'a gayamuku da wuri ba, amma bari kiji bar ganin Ihsan na da wannan kyan, samun miji irin wanda ta samu yana da wuya a wannan zamanin, dan haka kuyi haƙuri, taje ta zauna sedai kawai ki tashi tsaye ki gyara 'yarki ta riƙe mijinta, ki tabattar ta zama Mowar gida, idan ba haka ba kin san yadda muke cikin 'yan Uba da maƙiya, duk dangin nan namu gashi wasunmu na da kuɗin amma babu yarinyar da ta samu miji kamar na Amira, gashi ɗan shahararren mutum, ga kuɗi da kyau suna dashi, dama Auren nan na Ibsan a wuyan wasu yake, idan kika sa aka fasa Auren nan wallahi a cikin maƙiya za'a samu wanda ze lallaɓa ya bashi tashi 'yar ya haɗa biyun, Mussaman ke da Akuyarki tayi kuka a dangi gara ki rufawa kanki Asiri" "Amma Yaya Atine an min adalci kenan? 'yar guda ɗaya a haɗata da kishiya, kuma a kasa gayamin se ana gobe ɗaurin Aure?". "Kiyi haƙuri, kedai ki samu tayi aure ta tashi daga gaban ki, wallahi aka fasa Auren nan sekin rasa inda zaki sa kanki saboda surutan mutane, gara ayi surutan akan su biyu ya aura, da ai surutan kin hana Auren, da azo daga baya taje suyi miki aika aika, dan ni na tsorata da yadda suke son juna, tunda tazo gidana hutu, na gane ba ƙaramin so take masa ba" Jiki a sanyaye Maman Ilham tace "shikenan Yaya Atine, amma ya zan gayawa Ihsan? Ina jin tausayinta sosai" "Ki ƙyaleta karki gayamata yanzu, naga kamar tana cikin damuwa yanzu haka, kuma zata iya bijirewa tace ta fasa auren, kuma abunda bama so kenan" Haka Yaya Atine taita kwantarwa da Maman Ihsan hankali.. Imran kuwa har suka je gidan Alhaji Hashim, be kuma cewa uffan ba, sam baya nadamar dukan da yaiwa Amira, saboda ƙiriniyarta da rashin jinta yai mata yawa, duk da kusan ƙarfe sha biyu na dare, suna zuwa gidan Alhaji Hashim aka buɗe musu gate, dayake Abba ya sanarwa da megidan zuwansu. A harabar gidan, suka tarar da Alhaji Hashim, ya ƙaraso inda sukayi parking ɗin mota, Abba ya fito suka gaisa ya kalli Abba yace "Ali lafiya dai ko? Meke faruwa ne haka?" "To lafiya amma ba lau ba, Imran ne ya kama Amira ya zaneta wallahi, yanzu gaba ɗaya jikinta ya ɗau zafi, nayi tunanin kaita Asibitin da me ɗakin ka take aiki, se kuma na tuna sunje gurin Dinner ɗazu, kuma ba lallai tana night duty ba, kuma daɗin daɗawa dai, gobe in Allah ya kaimu za'a ɗaura Aure, bana son a samu wata matsala sam" Alhaji Hashim yace "Eh gara daka kawota nan ɗin, dukda dama munyi da kai bayan an ɗaura zata zauna a nan ne. Ya ƙarasa gaban motar ya kalli Imran yace "Imran meyasa ka dakarmin 'ya ne, ka fiye zuciya da saurin fushi, dole ka rage wasu abubuwan da kake yi, tashe ta naga kamar bacci take yi, ka shigo da ita, bari in taso matar gidan" Abba yace "Afuwan fa, zamu takurata" Alhaji Hashim yace "No karka damu, ai ita tana nan tana jiran zuwan Amira dama, bari in mata Magana" Imran ya buɗe ƙofar motar ta baya, ya daddaki Amira yace "Malama ki tashi" A hankali ta motsa, dan baccin wahala ne ya ɗauketa, ga jikinta yayi zafi zauu, ko ina na jikinta Banda raɗaɗi, ba abunda yake mata. A hankali ta fito daga motar, jiri na kwasarta, ta jingina da jikin motar, taji yadda jikinta ke zugi, ta tuna yadda Imran ya dinga jibgarta ɗazu kawai ta fashe da kuka, harda sheshsheƙa. Abba yace "yi haƙuri Amira, zaki iya tafiyar ko a riƙeki?" Ta girgizawa Abba kai, Alhaji Hashim ya fito yace "Bismillah ku shigo" Abba yace "Imran riƙe hannunta karta faɗi" takaici ne ya kama shi ganin yadda Amira ke wani sake lanƙwashewa, tana tangaɗi. Baya son yin musu da Abba, dan haka ya riƙe hannunta, suna tafiya a hankali amma kuka take, Abba yai gaba ya rigasu shiga, Amira ta fuzge hannunta daga nasa, taƙi shiga cikin falon ta tsaya ƙyam a waje tana kuka. "Zaki wuce ki shiga ko sena ɓarar dake a gurin nan?" "Bazan shiga ba ɗin, ba ɓararwa ba yanka ni zakayi, Mugu kawai" Muryarta ta shaƙe saboda kuka, ko fita bata yi sosai amma bakin yaƙi mutuwa. Aikuwa ya shige ya barta a gurin, yana shiga ya tarar har matar Alhaji Hashim ta fito falon, Abba yace 'ina Amiran kuma?" "Tace ba zata shigo ba, tana tsaye a waje" ya basu amsa. Abba ya girgiza kai ya taso ya fito wajen, tana tsaye jikinta nata rawar sanyi se kuka takeyi, Abba yace "Amira ki shigo mana, dubaki za'ayi a baki magani ai" Girgiza kai tayi tace "dan girman Allah a maidani gida, dan Allah kayi haƙuri ku maida ni gida kafin ɗanka ya kasheni,  dan Allah kayi haƙuri ku kaini inda zan hau mota in koma gida" Abba yace "naji amma ki tashi mu shiga a duba lafiyarki, nan gidan Alhaji Hashim ne fa, kin tuna shi" Matar Alhaji Hashim tace "Ohh dama wannan ce 'yar tawa? Ai na ganta ɗazu a gurin biki, kizo mu shiga ciki kinji" Maimakon ta tashi, sema ta zube akan gwiwowinta tana yiwa Abba magiyar ita dai a maida ita gida, sedai kan Abban ya kuma magana, Amiran ta faɗi a gurin sumammiya. Gaba ɗaya sukayi kanta suna kiran Innalillahi wa innalillahi raji'un. Imran ne ya ɗauketa ya shiga da ita falon aka kwantar da ita, ta ɗakko ruwa me sanyi tana shafawa Amira a fuska, ta cirewa Amira hijjabin jikinta, seda Imran ya ɗan tsorata ganin illar da yaiwa Fatar Amira. Duk fatarta tayi taruwar jini, harda wani sashe na fuskarta, akwai almar duka. Hajiya Nafisa matar Alhaji Hashim, wadda suke cewa Anty ta ɗago ta kalli Abba tace "waye yai mata wannan dukan haka?" Abba yace 'gashi nan ɗanki ne Imran" Anty tace "da wani ne ba kai ba Imran, da tabbas sena kai ka Human rights, haba Imran kamar ba wayayye ba? Ya zaka zage ƙwanjinka akan mace kamar haka, kuma ma wadda zaka aura, 'yar uwakka ce fa, ai kamats yayi kowani kaga ze mata haka, ka tsaya mata amma kai da kanka, dan abun kunya, kuma da alama jikinta baya son duka, dan shine ya samata wannan zazzaɓin, amma karku damu zata farfaɗo insha Allah, zanyi amfani da wannan damar ma, a ɗibi jininta a daren nan a kaishi lap, ayi mata duk gwajin daya dace" Abba yace "to shikenan Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi ya bar zumunci" Suna nan zaune a daren, aka sakawa Amira ruwa bacci ya ɗauke ta. Haka nan a daren Abba da Imran suka kuma komawa gida, suna tafe Abba yana ƙara yiwa Imran Nasiha. Ammi kuwa bata ga kiran Maman Ilham ba se bayan sha biyun dare, bata bi kiram ba saboda a ganinta dare yayi, tace bari ta bari seda Safe ta kirata. Imran kam kasa bacci yayi, yana tunanin ya Ihsan zataji idan taji labarin su biyu ze aura, ya tabbata maƙaryaci kuma mayaudari kamar yadda ta faɗa, tun farko yakamata ace ta sani, ba yanzu da lokaci ya ƙure ba, Amira ta ɓata masa komai, ga Yadda ran Abba ya ɓaci saboda dukan da yai mata, wannan yarinyar a sanadinta Komai na tafiya ba yadda ya so ba. Haka ya wayi garin Allah duk da tarin gajiyar da yake ɗauke da ita, amma ya kasa bacci, ranar ɗaurin Aurensa ne, amma sam baya murna da ranar, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake. Da Safe wajen ƙarfe takwas da rabi, aka takurawa Ihsan taci Abinci, haka nan gabanta yake ta faɗuwa, maimakon tayi farinciki da ranar ita ma faɗuwar gaban ce ke damunta. Bayan ta gama cakalar Abinci, ana cewa me kwalliya zata zo ta mata kwalliya, kafin 'yan ɗaurin Aure suzo, Yaya Atine taje ta sameta ta cewa ƙawayenta su ɗan basu guri, aikuwa suka fita suka basu guri. Ta rufe ƙofa ta dawo ta zauna a kusa da Ihsan tace "Ihsan ina son ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurareni, ina son ki ɗau abunda zan gaya miki a matsayin ƙaddara kamar yadda muka ɗauka ni da mahaifiyarki, jiyavda daddare wan Mahaifinki yazo bayan an dawo daga gurin Dinner, ya gaya mana wani abu da ya girgiza mu, amma kamar yadda na taushi mahaifiyarki ta haƙura ta kwantar da hankalinta, kema haka nake so kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, kamar yadda kika sani anjima za'a ɗaura miki Aure da Imran, sedai ku biyu zaku aure shi" Ihsan ta kalli Yaya Atine tace "Kamar yaya kenan?" "Eh, haka wan mahaifinki yazo ya gaya mana jiya daddare, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, amma keda abokiyar zamanki za'a ɗaura Aurenku yau" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyasa Imran zemin haka? Dama abunda yake shiryamin kenan? Duk yadda na bashi yadda amma shi ba haka bane a gurinsa, dama nasan za'ai haka, tuntuni nake ganin take takensa amma soyayya ta rufemin ido, to yaje ya auri duk wadda yake so, amma Aure ni da Imran babu shi, na haƙura na barwa kowa cece na bar mata Imran, na haƙura, bazan Auri Imran ba wallahi na haƙura!!!" Tai maganar cikin kuka me ban tausayi, Yaya Atine tace "Ihsan karki wa kanki biyu babu, wan mahaifinki yace ɗayar Umarnin mahaifinsa ne yasa ze Aureta, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki" "Ni ba wani hankali na da zan kwantar, an cuceni an yaudareni, idan 'yarsu ce ni zasu min haka ne, ba wani Auren biyayya dama can an shirya wulaƙantani ne, ni ba zan zauna da kishiya ba, na haƙura da Imran na fasa Auren" Nan da nan Ihsan ta birkice, ta dinga koke koke tana bori, tace Allah karta ba zata auri Imran ba, jikinta ya riga ya gama bata Amira ce matar da ze Aura su biyu. Rarrashin duniya amma Ihsan fafur taƙi sauraren kowa, se kuka da takeyi kamar zata shiɗe, nan da nan idanunta suka kumbura, ta fita hayyacinta kamar wadda akace za'a kashe. Imran kuwa ya kasa komai, se aikin tunani harya faɗa saboda damuwa da tashin hankali, ga tausayin Ihsan da yake ji, saboda yasan yadda take kishinsa da ƙaunarsa, yasan tabbas an mata ba daidai ba, haka Khalid yazi ya same shi a kwance a ɗakinsa. "Imran meye hakane? Anjima fa ɗaurin Aure amma kana kwance kamar wani ruwa, dan Allah tashi mana" Imran ya tashi zaune yai ajiyar zuciya ya dafe kansa yai shiruu. Khalid ya dafa shi yace "Imran ya dai? Akwa matsala ne?" Imran yai ajiyar zuciya yace "Khalid, wallahi sam bana murna da wannan ranar, ina jin tausayin Ihsan, ina ji a jikina ban mata adalci ba, na cutar da rayuwarta, na ɓoye mata abubuwa yanzu tana min kallon mayaudari maƙaryaci, ban san wace irin karɓa zan samu a gurinta yau ba, gefe guda waccan mahaukaciyar jiya dan rashin nutsuwa suka hau dambe da Minal, a gaban mutane jiya a gidan nan, naje na rabasu amma yarinyar nan taƙi jibharda cizona, zuciya ta ɗebe ni, na mata duka jiya, a daren Abba yasa muka tafi kaita gidan Alhaji Hashim, kusan a sume ta kwana, saboda ko kafin mu bar gidan nan, zazzaɓi ya rufeta tana ta layi, yanzu haka Abba kusan fushi yake dani, ni ji nake dama ban ɗakko maganar Aure ba, komai ya kwaɓemin ya lalace". "No karka faɗi haka, ka kwantar da hankalinka komai ze wuce, tabbas Ihsan abar tausayi ce ta cancanci a tausaya mata, duba da irin son da take maka, amma a zahiri Amira ce abar tausayi, kuma gaskiya dukan ta da kayi baka kyauta ba, dan ba shine mafita ba sam, ni dai ina baka shawara da kaji tsoron Allah Sannan ka kamanta adalci a tsakaninsu duk da nasan Amira ba zaɓinka bace zaɓin Abba ce, amma kayi haƙuri Auren Amira da zakayi tamkar Jihadi ne, ko da baka sonta ka ji tausayinta ka riƙeta tsakani da Allah, ko dan Saboda maraicinta da kuma 'yan uwantakar dake tsakanin ka da ita" Imran yace "ita wannan yarinyar tana tausayin kanta ne ko duba maraicinta, ni ina tsoron zamansu Guri ɗaya da Ihsan ta cutar min da mata a banza" "Itama ai matarka ce, kuma bana jin duk abunta idan Ihsan bata kulata ba ba zatayi mata ba" "Kaga Khalid ƙyaleni, bata wannan nake ba, ni ta Ihsan nakeyi itace a raina" "Ita waccan ɗin daka sumar bata gabanka kenan?" "Wallahi ko tausayinta banji ba, ina dukanta tanamin Allah ya isa, kai Yarinyar nan idan mutum ya biye mata, seya kusa kasheta ma" "To kai waye yace ka dake ta? Baka san irin Amira rarrashi suke buƙata ba" Tsaki Imran yayi ya miƙe ya nufi banɗaki, dan ko zancen Amira baya son ji, a ganinsa a dalilinta ne yake neman rasa farincikinsa. Amira se wajen ƙarfe Bakwai ta farka, ta ƙarewa ɗakin da take ciki kallo, tunanin tayi ta tuna abunda ya faru jiya da daddare dukan da ta sha a hannun Imran, da kuma yadda suka zo wannan gidan, ta tashi zaune a hankali, ɗakin ɗan madaidaici me kyau, ta kalli hannunta taga ruwa a jikinta, ta sunkunyar da kanta tai shiru tana jiran taga ta inda wani ze shigo ta nemi yadda zatai, tayi salla. Turo ƙofar ɗakin akayi, aka shigo da Sallama wata matace ta shigo, ta kalli Amira tace "ashe kin tashi ya jiki?" "Da sauƙi" Amira ta amsa a hankali. Ta ƙarasa shiga cikin ɗakin tace "bari in cire miki ruwan, ki shiga banɗaki kiyi wanka kizo kiyi salla kafin Antyn ta fito" Amira ba tace Komai ba, ta cire mata Ruwan, ta nuna mata banɗaki, ko ina na jikinta yayi tsami se raɗaɗine ke ratsa fatarta. Matar ta bata hijjabi da towel, Amira ta shiga banɗaki, ta haɗa ruwa me ɗumi ta fara zubawa a jikinta, wani irin zafi ya ratsa ta, kawai ta fashe da kuka, ƙarshe da ƙyar tai wankan ta fito. Tana fitowa ta samu an ajiye mata ƙaton Hijjabi da sallaya, ta zira hijjabin nan tayi salla, ta idar ta zauna tayi Azkar. Sedai jikinta ba ƙwari sam, ta miƙe ta nufi gaban mudubin dake ɗakin, ta cire hijjabin jikinta ya zama daga ita se towel, ta soma ƙarewa jikinta kallo fatarta tayi ruɗu ruɗu tayi ja, wani gurin a kumbure ya fashe, kawai ta fashe da kuka, hakan yai daidai da shigowar Anty, tana faɗin "Amira Ashe kin tashi?" Ta tarar da Amira a gaban Mudubi tana kuka, ko ba'a gayamata ba tasan dalilin kukan nata, dan haka ta ƙarasa inda Amira ke tsaye tace "haba Amira ya kuka haka? Kiyi haƙuri nasan Boss be kyauta ba daya dakeki, nima ya bani haushi amma kiyi haƙuri kinji" Tai maganar tana kamo hannun Amira, ta zaunar da ita a bakin gado tace, ga kayanki nan ki saka, yanzu za'a kawo miki abun karin kumallo da magani, ki dena Kuka kinji yarinyar kirki?" Amira ta jinjina mata kai, tana cigaba da Share Hawaye, ta kalli Anty tace "dan Allah ki bugawa Abba waya, kice yace wa Su Anty Fa'iza su taho mu tafi gida, koni kisa a kaini tasha in koma gida, dan bazan ƙara zuwa garin nan ba, wannan ne karo na biyu da nayi dana sanin zuwa garin nan" tai maganar tana sake fashewa da kuka. Anty tace "yi hakuri Amira, insha Allah wannam zuwan naki Kaduna, shine zuwa Mafi Alkhairi kiyi haƙuri". Haka Anty ta zauna taita aikin rarrashin Amira. Abba yana ta shirinsa, sega Ammi ta shiga ɗakinsa ta sha shadda, tayi rasa da ita kamar ba ita ta haifi su Imran ba. "Gani naga ka aika a kirani" Abba yace "eh, dama na aika a kiraki ne dan in sanar dake wata mahimmiyar magana, yakamata tuntuni ki san maganar amma sanin halinku ku mata musamman ke yasa ban gayamiki tuntuni ba" 'meye halin nawa da kake kashedi a kai?" Abba yace "ba wannan ba, kamar yadda a baya naso in riƙe Amira amma kika ƙi yadda shi...... "Abba nifa maganar yarinyar nan ta isheni haka wallahi, naga ƙarewa ka ɗauketa bata kwana a gidan nan ba, yau za'a gama biki ta tarkata tabi 'yan uwanta su koma gida mungode Allah yasaka da Alkhairi, nifa ban riƙe Yarinyar nan a baya ba, a yanzu fa bazam riƙe ba gaskiya" "Inke ba zaki riƙe ba ɗana Imran ze riƙe" 'kamar yaya kenan? Yaron daze Aure yanzu za'a kwashi wannan kwazgwamemiyar Baligar a kai masa gida, gata Karuwa, ina Ihsan zata iya riƙe Wannan yarinyar, da yaya Ihsan ta girmeta? Ba tafi Ihsan girma ba, dan Allah Abba ka dinga faɗar abunda ze yiwu mana, 'yan uwa ta ma ba zasu yadda ba, nima bazan goyi bayan hakan ba" Abba ya kalleta yace "Amira ba a 'yar riƙo zata je gidan Imran ba, a matsayin matarsa zata je ita ma" "Kamar Yaya? Kana nufin Imran ze auri Karuwa ya haɗa da 'yar mutane?" "Ƙwarai kuwa, idan ke ban isa dake ba, na isa da ɗana, dan haka Imran ze Auri Amira" "Amma kaima kasan wannan abun bame yuwuwa bane, wallahi in dai da raina Imran baze Auri wannan fitsararriyar ba, yaje ya auro duk wadda yake so, amma Banda wannan yarinyar". "Aikin gama ya gama Jamila, saboda a gurin ɗaurin Aurensa da Ihsan, za'a ɗaura Auren sa da kuma Amira!. Aikuwa a kiɗime tace  "akan me zaka yanke wannan ɗanyan hukuncin saboda me? Nima fa ina da haƙƙi akan Imran kamar yadda kake da shi, saboda me zaka min haka? Baka gudun lafiyar ɗanka da na 'yar mutane daze aura, kuma ka kasa sanar dani tuntuni se daidai wannan lokacin da awanni suka rage a ɗaura Aurensa, saboda me zaka yimin haka? Akan me? Wallahi baka min adalci ba kuma ba kayiwa 'yar mutane Adalci ba kum.... "Ya isheki haka Jamila, da Imran da Amira duk 'ya'yana ne, kuma na yanke hukuncin da naga ya dace ba wanda ya isa ya canza min, this is my final decision" Wani irin gumi ya dinga karyo mata, fuu ta koma cikin gida ɗakinta ta wuce, tana zuwa ta ɗau wayarta ta kira Maman Ihsan, ta kirata ya kai sau Uku Sannan ta ɗaga a hasale tace "Wai meye kike ta kirana haka? Ni da na kiraki jiya kika ƙi ki ɗaga se yanzu zaki isheni da kira, bayan kin san abunda kuka ƙulla ke da ɗanki, kun shirya wulaƙanta mun 'ya" "Dan Allah Murja kiyi haƙuri, ashe ke kinma san meke faruwa, to ni Wallahi Allah kenan ban sani ba se yanzu, Yanzu da suke shirye shiryen tafiya ɗaurin Aure sannan ya gayamin, saboda yasan idan ya gayamin bazan bari duk yadda zan se na hana, shine be gayamin ba se yanzu, wallahi gaba ɗaya hankalina a tashe yake" Maman Ihsan tai ajiyar zuciya tace "to Ihsan ma yanzu aka gayamata, gaba ɗaya ta birkice tace ita ta fasa Auren, ta haƙura da shi ta barwa waccan ɗin, naji tana cewa wai Yarinyar Karuwa ce" "Eh Karuwa ce wallahi, 'yar ƙanwarsa ce, Yanzu haka jiya da daddare baki ga dukan da Imran ɗin yai mata ba, amma dan Allah ki tasuhi Ihsan ki kwantar mata da hankali, nasan matakin da zan ɗauka akan lamarin, amma dan Allah kuyi haƙuri, ban san da Maganar nan ba se yanzu, ku ƙyaleni dasu, ai Imran ni na tsuguna na haifeshi, ba inda Auren nan zeje nina gayamuku, ki kwantar mata da hankali dan Allah, kuyi haƙuri nasan ba ai muku adalci ba" "Shikenan Allah ya kyauta, ni dai tsorona kar a sawa yarinyata wata cutar daban" "Wayace miki za'a kai ga nan ma? Ki bar komai a hannuna kawai kuyi haƙuri" Suka gama wayar, ta kira Imran, Imran na ganin kiran Ammi gabansa ya faɗi, ƙirjinsa ya finga bugun uku uku, yasa hannu ya ɗaga wayar. "Kana ina ne?" "Ina gidansu Khalid" ya bata amsa "Kana sane da Mahaifinka ze aura maka wannan Karuwar Yarinyar?" Imran yace "wace Karuwar kuma Ammi?" Yai maganar a saɓule. "Wace banda wannan sheɗaniyar 'yar ƙanwar tasa" Imran yace "Na sani Ammi" "What! Dama ka sani amma baka gayamin ba? Kuma ka amince zaka Aureta?" "Ammi ya zanyi? Abba be taɓa roƙata wata alfarma ba se wannan, se ince bazan masa ba? Ni kaina bana son Auren nan ba yadda zanyi Ammi. "Dalla rufemin baki, Shashashan banza, algungumi ni zaka gayawa baka son Auren? Da baka son Auren ai da tuni ka sanarmin, musan matakin da zamu ɗauka, amma ba a tashi gayamin ba se Yau, ya rage awanni a ɗaura maka Aure da Ihsan kawai se inji hadda wannan Yarinyar, ka bani kunya ka bani mamaki Imran, gashi can kasa 'yar mutane a damuwa tana ta haƙura da kai ta fasa Auren, Yarinya me nutsuwa da tarbiyya kayiwa kanka, indai karuwace gaka ga ta nan" Cikin karaya Imran yace "Ammi dan Allah ki saurareni kiji" kashe wayarta tayi ta ƙyaleshi. Ya ajiye wayar ya zauna Ya dafe kansa, ya easa mema zeyi yaji daɗi. Khalid ne ya dinga rarrashinsa, yana kwantar masa da hankali. Tuni sakamakon gwaje_gwajen da akayiwa Amira ya fito, bata ɗauke da Kowace matsala da ka iya kawo tangarɗa ga Aure, kama da gwajin cuta me karya garkuwar jiki wato HIV, ciwon hanta HEPATITIS B, Rukunin jininta BLOOD GROUP, Genotype, Gwajin ciki, PREGNENCY TEST gaba ɗaya lafiyar Amira ƙalau. Ɗaurin Auren da aka saka ƙarfe sha ɗaya, ƙarshe se bayan da aka idar da sallar Azahar aka ɗaura shi, masallaci ya cika maƙil da manyan mutane, waliyyan Ihsan sun ɗanyi jinkirin zuwa ga mutane sun fara ƙosawa, dan haka aka bada sakamakon gwajin Amira aka fara ɗaura Auren Imran da Amira, ana cikin ɗaurawa ne waliyyan Ihsan suka ƙaraso, bayan an gama na Amira aka ɗaura na Ihsan da Imran.     Amma Ihsan tana can gida tana bori akan ita lallai bata son Imran yanzu ta barwa Amira shi, dan ko an ɗaura an kaita seta dawo. Seda "yan ɗaurin Aure suka dawo Sannan mutanen gida suka san mata biyu aka Aurawa Imran, ciki harda Yarinyar da ya zane jiya da daddare. Nan gida ya ɗau cece kuce, su Fa'iza sam basu san meke faruwa ba, ita gaba ɗaya hankalinta yana kan ya Amira ta kwana, ga jakarta da wayoyinta duk a nan ta barsu, ita Fa'izan ce ta ɗauke mata su. Duk yadda abokan Imran sukayi dashi akan suje gidansu Amarya ayi hotunan ɗaurin Aure ƙi yayi, dan be san da wani idon ze kalli Ihsan ba, da suka dawo gida ma, suka yi walimarsu ta angwaye sam baya walwala, kuma ya kasa shiga cikin gidansu, wanda basu san mata biyu ze aura ba se ranar suna ta zolayarsa, suna ya akai ko a gurin Dinner Amarya ɗaya suka gani, se ranar ɗaurin Aure suji Amare biyu ne. Shi dai Imran ba wanda ya tankawa, dan shikaɗai yasan meke damunsa. Gida ya cika da jama'a, ana ta shiga ana fita, ana Allah ya sanya Alkhairi, Abba yasa Anty Hadiza ta nemo masa Fa'iza. Ko da Fa'iza taje Abba ya sanar da ita halin da ake ciki seda ta girgiza, tasan tabbas akwai daru, nan ta shiga tunanin ko ya Amira zata iya zama da Imran, shi zuciya ita taurin kai da rashin kunya, ta wani fannin an temaki rayuwar Amira, amma ta wani ɓangaren akwai ƙalubale. Abba yace "Yanzu ki ɗakko mata kayanta da tazo dasu nan, direba ze kaiki Gidan Alhaji Hashim, ki kai mata kayanta, za'a maida ku Kano, sannan zanzo da kaina har Kano, in yiwa su Yadikko bayani in Basu haƙuri akan hukuncin dana yanke ba tare da saninsu dangin mahaifinta ba" Ita dai Fa'iza ta kasa cewa komai, jiki a sanyaye taje ta tattaro kayan Amira, da nasu kayan Aka haɗasu da direba zuwa gidan Alhaji Hashim. Har suka tafi hanya basu san meyafaru ba, sun ɗauka zasuje su ɗakko Amira ne su tafi gida. Suna ta murna da irin shatara ta Arzikin da aka basu, da wanda suka sato a gidan, sam dukan da akayiwa Amira baya gabansu, sema murna da sukayi suna Allah ya ƙara. Da sukaje gidan Alhaji Hashim kuwa, dama direban sojan nan ne daya kai Amira gurin make up, yace "mutum ɗaya ce zata shiga, dan ita kaɗai aka san da zuwanta ku ku zauna a Mota" Amina tace "ooh ji wani makirin iyayi". A sanyaye Fa'iza ta shiga gidan, a falo ta tarar da Anty suka gaisa tace "dama nice wadda nazo gurin Amira" Anty tai murmushi tace "Sister ɗinta ce ke?" Fa'iza tace "Eh" Aka nuna mata ɗakin da Amira take, Amira na ganin Fa'iza ta miƙe ta fara share hawayenta tace "Yawwa muje, dama tun ɗazu ke nake jira, gara mu bar garin nan kan a kasheni" "Amira ba dake zamu tafi ba, kayanki na kawo miki, keda Garin Kano sedai kije da ziyara" A fusace Amira tace "Kamar Yaya? Me kike nufi?" "Saboda yanzu ke Matar Imran ce, an ɗaura Masa Aure dake da Ihsan!!!" SHARE PLEASE (Nayi dogon page yau, am expecting your Comments. Ko ya Amira zata karɓi Wannan batun Auren? Ku kasance da Alƙalamin Marubuciyarku wato Ayshercool, domin gyara Sharhi ko shawara ku tuntuɓeni akan 07063065680 or Follow me on watpad@ Ayshercool7724) [1/21, 6:08 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. (INA WA INNALILLAHI RAJI'UN, NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE GA YARAN DA AKA SACE AKA MUSU KISAN GILLA A KANO DA KUMA ZARIYA, UBANGIJI ALLAH YAI MUSU RAHAMA YA KAWO MANA TSARO A ƘASAR NAN, ALLAH YA BAWA IYAYENSU HAƘURIN JURE RASHIN SU) *_Masha Allah, gaskiya ina jin daɗin yadda kuke Comment da nuna soyayyar ku ga littafin WUTA A MASAƘA, nagode sosai Ubangiji Allah ya bar ƙauna, ina jin daɗin sharhin da kuke akan labarin_*                             22_23 A fusace Amira ta sake cewa "inji ubanwa? Ke waye ya gaya miki wannan shirmen dan Allah bana son wasan banza, ni mu tafi kawai" Haɗe rai Fa'iza tayi tace "duk wasan da muke dake na taɓa miki irin wannan ne? Ni karɓi wayoyinki da sauran kayanki, suna waje suna jirana zamu tafi" "Can ta matse musu su da wanda suka ɗaurawa Auren ba dai Amira b, kuma wallahi bazan kwana a garin nan ba" Kan Fa'iza tai magana tuni Amira tai waje abunta, Anty dake Falo ta tashi da sauri tace "A'a, Amira ya haka? Ina zakije kuma?" Amira tace "gida zamu koma, an gama biki ga mota can a waje zamu tafi gida" Anty tace "wani gida kuma Amira? Ai babu ke ba komawa gida baki san an ɗaura miki Aure bane? Kiyi haƙuri ki koma ki kwanta kin san baki da lafiya" Aikuwa Amira ta ɗora hannu a ka tace "Na shiga uku ni Amira, wai dama dagaske An ɗauramin Aure da wannan Mugun? Meyasa za'amin haka? Dan anga ni marainiya ce shine za'a Auran wanda ya kusa kasheni? Wato idan ya kasheni ba wanda yake da Asara? Meyasa za'amin Auren dole? Ni wallahi gida zan tafi, gara zaman gidanmu da zama da wannan Mugun mara imani, wallahi ni gida zan koma" Ta rirriƙe Fa'iza tana rusa kuka, tuni hawaye ya wanke mata fuska, Alhaji Hashim ya sakko daga kan benensa, jin kukan Amira da yayi. Yana zuwa ya tarar Amira ta riƙe Fa'iza tana kuka, itama Fa'iza seta saka Kuka ta rungume Amira tace "Amira kiyi haƙuri, ki rungumi ƙaddara kinji, dan Allah karki kuma aikata wani abun daze rusa rayuwarki, ina miki fatan Alkhairi da fatan Imran ya zame miki Mijin marainiya" "Wane mijin marainiya Anty Fa'iza? Kalli jikina fa kalli dukan da yaimin, babu tausayi ba imani, ni wallahi bana sonsa, meyasa za'amin Auren dole dan babana ya mutu, Fa'iza kinfi kowa sanin wahalar dana sha, yanzu na cancanci sake faɗawa wata wahalar? Meyasa kuka bari akamin wannan Auren? Meyasa?" Kasa magana Anty Fa'iza tayi, ita kanta Anty jikinta sanyi yayi dan Amira ta bata tausayi sosai. Alhaji Hashim ya ƙarason inda suke, yace "Amira cikata su tafi kar suyi yamma a hanya" "Dan Allah ku barni in koma gidanmu, wallahi niba matar Aure bace bana son wannan Auren, karku rabani da 'yan uwana alhalin bani da kowa a nan se Allah, wanda kuka saka ya Aureni baya ƙaunar ko ganina, ku dubi maraicina ku rabu dani dan Allah" Alhaji Hashim ya haɗe rai sosai yace "ki cikata su tafi nace" Amira ta saki Mayafin Fa'iza, ta durƙushe a gurin ta sake fashewa da kuka, Anty Fa'iza tanayi tana waigowa harta kai ƙofar falon. "Dan Allah Anty Fa'iza karki tafi ki barni a nan, dan ƙaunarki da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam" Da sauri Fa'iza ta bar falon tai waje tana goge hawaye. Tana zuwa mota su Amina suka shiga rattaɓo mata tambayoyi, 'Ina Amiran? Mutuwa tayi kike wannan kukan haka?" Fa'iza ta goge hawayenta tace "mu kaɗai zamu tafi ba Amira" Sadiya tace "Saboda ne kuma?" "An ɗaura mata Aure" Umma tace "Aure kuma? Kamar yaya kenan?" "Kiran da akayi min ɗazu kenan, mata biyu aka Aurawa Imran, da ita da waccan Yarinyar". Amina tace "ita wa wai?" "Ita Amira mana" ta basu amsa Suka haɗa baki sukace "Innalillahi wa innalillahi raji'un" "Ya naji kuna salati haka?" Amina tace "dan Allah wai dagaske kike koda wasa?" "Y za ai in muku ƙarya, da ƙarya nake meya hana mu tafi tare da ita, ko baku ji ɗazu ana zancen mata biyu aka aura masa ba" Sojan da yake jansu a motar yace "gaskiya ta gaya muku, Oga mata biyu ya aura Amira da Ihsan haka aka sanar a gurin ɗaurin Aure" Umma tace "Amma ya za'ayi a aurar da ita ba tare da izinin dangin ubanta ba?" Fa'iza tace "in dai Aure ya cika sharuɗan da suka dace bisa koyarwar addini, babu wani batun amincewar wani" Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi, dan ba ƙaramin shanmatarsu akayi da wannan lamarin ba. Amira kuwa take jiki ya sake rikicewa, wani zazzafan zazzaɓi ya sake rufeta, aka maida ita ɗakin da take aka cigaba da samata ruwa da allurai. Haka aka ƙarasa wunin bikin nan duk ba daɗi, danshi kansa Angon bashi da cikakkiyar lafiya dan da ciwon kai ya wuni, Ihsan ma na can nata fama da nata darun, tace ba ita ba zaman Gidan Imran, yaje yai harkarsa tai tata, yaje ya zauna da waccan matar tasa, Yayin da Gimbiya Amira ma haka ta wuni cikin yanayin kuka da rashin lafiya. Da magariba 'yan ɗaukar Amarya sukaje, amma Ihsan fafur taƙi fitowa, rarrashin duniya amma tace ba ita ba Imran, ƙarewa taje ta ƙule a gado taƙi tashi. Aka kira Yayan Babanta aka sanar masa, babu jimawa se gashi yazo gidan, har ɗakin da take ya shiga cikin tsawa yace "ke bana son sakarci da iya shege, mu zaki kunyata, wallahi kin bani mamaki Ihsan, ina tarin ilimin naki, na Addini dana zamani, amma ki dinga wannan shashancin haka, tashi kije kiyi wanka kisa kayanki ina falo ina jiranki, da kaina zan kaiki ɗakin miji" Kasancewar Ihsan na tsoronsa sosai, haka ta tashi taje tai wanka tana kuka tana komai, ta sa kaya aka fesheta da turare, Mummy ta dinga cewa "kiyi haƙuri Ihsan, ki kwantar da hankalinki, zamu san abunyi Insha Allah, ki tafi kina Addu'a" Haka aka saka Ihsan a mota, Wan babanta ya tafi kaita ɗakin miji. Gidan Da Abba ta bawa Imran ya haɗu sosai, anyiwa Ihsan kaya na gani na faɗa masu kyau da ƙayatarwa, ɓangaren Amira ne a rufe ba'a sa komai ba a ciki tukuna. Seda Ya raka Ihsan har cikin bedroom ɗinta sannan ya shiga yi nata Nasiha "Ihsan nasan babu matar da takeson kishiya, amma ki tuna ƙarin Aure ga namiji umarnin Ubangiji ne idan har ze Adalci, karki ja da hukuncin Allah, ki zauna da mijinki da zuciya ɗaya, kiyi masa biyayya ki zauna lafiya da abokiyar zamanki, batun waiwani karuwace ko menene ba ruwanki da surutan mutane, seda aka bincika lafiyar ta kafin ya Aureta, kuma ita ba yanzu zaki tare bama, se nan gaba, dan haka kiyi haƙuri, ki zauna lafiya a gidanki Ubangiji Allah ya haɗa kanku ya baku zaman lafiya" Sam Ihsan harya gama surutansa ya gama bata san meyake cewa ba, hankalinta na can wani gurin tana tunane tunane, dan sam maganganun sa basu shigeta ba, bama sta saurareshi ba balle maganganun su shigeta. Imran kuwa kamar mara laka, haka yayi wanka ya sa kaya, ya shiga cikin gidansu, mata na ta rangaɗa masa guɗa ana Soja angon mata biyu. Part ɗin Abba ya tafi ya shiga ya tarar da Abba na kallon labarai, yana ganin Imran ya saki murmushi yace "Ina gwanin wani ga nawa, Angon Amira Angon Ihsan" Imran ya sunkunyar da kai cikin ladabi ya durƙusa a gaban Abba yace "Abba zan tafi, sannan ina amfani da wannan dama gurin godiya ga Ubangiji da ya nunamin wannan rana, da kuma godiya gareku iyayena bisa jajircewarku, da goyon bayanku a gareni har kawo wannan lokaci, Allah yasaka muku da mafificin Alkhairi, nasan bani da abun da zan biyaku da shi face Addu'a, sannan ina neman Afuwarku idan akwai laifi dana aikata ina sane ko cikin rashin sani, ina neman ku yafemin" Seda Abba yaji ƙwalla ta taru a idonsa, dan yana matukar son Imran. "Imran na yafe maka, kuma ka cancanci yabo da jinjinawa, haƙiƙa kamin biyayya kuma ina fatan biyayyar da kayimin yayi sanadiyyar shigarka aljanna, sannan ina me maka wasiyya da ka kula da iyalinka kaji tsoron Allah a gurin yi musu adalci, saboda gaba ɗaya suna da haƙƙi akanka, karka fifita wata akan wata, nasan Ihsan kake so ba Amira ba, amma ina fatan ka dinga ɓoye hakan a gaban Amira, gudun kar taji Babu daɗi, tashi kaje Allah yayi maka albarka" "Ameen Abba nagode" Imran ya miƙe jiki a sanyaye ya nufi cikin gida gurin Ammi, sedai yana tunakarar cikin gidan gabansa na cigaba da faɗuwa. Ya sameta a falo da mutane, tana ganinsa ta haɗe rai sosai, mutane nata masa Addu'a ta fatan Alkhairi wasu na masa nasiha akan Adalci. Ammi tace "shiga bedroom ka jirani" Imran ya tashi ya shiga bedroom ɗin Ammi ya zauna yana jiranta, cam se gata ta shigo ta maida ƙofa ta rufe ta kalleshi tace "Sannu ko" Ya sunkunyar da Kai ƙasa, "Nace Sannu, ka haɗa kai da ubanka kun munafurceni, ya maka Aure sannu ɗan gata" Imran yace "wallahi Ammi biyayya naiwa Abba na Auri Yarinyar nan, ba zan iya ce masa A'a bane, amma wallahi ba laifi na bane". "Dallacan rufemin baki, ni zakaiwa ƙarya? To ka buɗe kunnenka da kyau ka saurareni, Ihsan itace matarka da na aminta da ita, dan haka ba kai ba Amira! Karka kuskura ka yadda wani abu ya shiga tsakaninka da ita, ban da Abun Mahaifinka mezakayi da Yarinyar titi wadda ta gama raba jikinta ga maza daban daban ka auri sauran titi, Mazinaciya! Haka nan Imran yaji kalmar Mazinaciya ta daki ƙirjinsa da ƙarfin gaske, dan seda yai ajiyar zuciya saboda hakan. "Kasan abunda kake ciki tun wuri, a waje ba'a iya controlling ɗinta ba, dan ka Aureta ne zata dena gantalin mussaman kai da ba mazauni ba, da ka bar gari itama ta kama gabanta azo ana haifar yara ana gwamutsa maka wanda suke naka da ba naka ba, karka kuskura ka yadda wani abu ya faru tskaninka da ita, zuwa randa zata gaji ta tattar tayi gaba, bana son yin fito na fito da Mahaifinka akan magnar nan saboda naga yadda ya ɗaukaki Maganar, idan na matsa zamuyi Babu daɗi dashi, naji ana cewa tana gidan Alhaji Hashim, se bayan wani lokaci zata tare, kota tare ba ruwanka da ita kaji abunda na gayamaka?". Imran yace "Naji Ammi, kuma zan kiyaye insha Allah' "Tashi ka ban Guri maza" Imran ya tashi ya fita, maganganun Abba na masa yawo a ka, gana Ammi gefe kuma ga ra'ayin zuciyarsa dan yafi karkata ga maganganun Ammi, dan baya jin ze iyayin wata mu'amala da Amira saboda kallon ƙazanta yake mata. Haka ya fito jikins a sanyaye, suka shiga motoci zuwa gidan Imran, a hanya su Khalifa suka sai kaji da youghurt suka raka Imran da su gidansa. Koda sukaje duk an watse se Ihsan da wasu Cosuin sister's ɗinta guda biyu, nan abokan ango suka dinga zolayarsu, Ihsan dai ta takure ta duƙunƙune a gado, taƙi ko ɗago fuskarta ta kallesu, haka suka gaji suka miƙe zasu tafi. "To Amarya zamuce ko uwargida?" Cewar wani abokin Imran. Khalid yace "Amaryar dai, Uwargidan bata tare ba tukuna, kasan na waccan aka fara ɗaurawa" "What so ever dai, tunda wannan ce ta fara zuwa a gurinmu itace uwargidan, to Ango Allah ya sanya Alkhairi, semun zo rako Amarya kuma" Sukai musu sallama suka tafi, Ihsan a ranta tace "ta tabbata dai Amira aka fara ɗaurawa Aure sannan ita" Bayan Imran ya dawo daga rakasu, ya shigo bedroom ɗin Ihsan, ya daɗe a tsaye yana kallonta, sannan ya ƙarasa ya hau kan gadon ya zauna, ya ɗagota daga duƙunƙunewar da tayi a cikin mayafi. A fusace ta ture hannunsa, taja da baya idanunta sunyi jawur sun kumbura, alamr ta sha kuka bana wasa ba. Jiki a sanyaye Imran yace "Ihsan, nasan kina fushi dani ne, amma haryanzu ko sau ɗaya baki bani dama na miki bayani ba" Cikin dashashshiyar muryarta data sha kuka tace "wani bayani nake buƙata daga gareka, banda wanda na hani a zahiri? Kamin ƙarya ka ɓoyemin abubuwa wannan itace sakamakon Yadda da nai da kai? Kace min yarinya ce ƙarama, kace min babu komai a tsakanin ka da ita, ba yau ba gobe kana hanyar Kano, mekake a Kano sekace min Abba ne ya aikeka, ashe shirin Aurenku ake, har hotonta na nuna maka, na haɗu da ita a Abuja se cemin kai baka santa ba, katsam se Ranar ɗaurin Aure aka gayamin ai mu biyu zaka Aura, Imran duk da kasan yadda nake sonkabda kishinka, amma ka rasa dame zaka sakamin se wannan yimin kishiya da Karuwa, kuma gurin ɗaurin Aure aka fara ɗaura Aurenka da ita sannan nawa, kuma ka ɓoyemin baka gayamin ba, am disappointed on you, kaje kayi rayuwarka inyi tawa, dama 'yar uwaka ce na bar maka ita kaje ku ƙarata" Gaba ɗaya jikin Imran yai sanyi, ya miƙa hannunsa ze rungumota jikinsa ya rarrasheta, amma ta miƙe ta sauka daga kan gadon da sauri, tana kuka hawaye na bin idonta haka ta sakko ta na kallonsa. Imran ya dafe kansa, ya rasa mema Yakamata yayi, Gaba ɗaya kansa ya kulle. Ƙarshema ɗaya ɗakin tai tafiyarta ta kulle ƙofa ta kwanta, dan haushin Imran take ji. Su Fa'iza kuwa daf da magariba suka isa Kano, yana sauke su yai salla ya juya. Yadikko ta fara jin sauƙi, dan tana iya tashi ta lallaɓa ta fito tsakar gida da kanta, tana jin sallamarsu Amina ta hau washe baki "Sannunku da zuwa mutanen Kaduna, marabanku lale, ai nayi zaton se gobe zaku dawo, an gama biki yau, ku huta sannan ku taho" Ganin fuskokinsu tayi duk wani iri, ba karsashi, ba fara'a ba komai kamar wanda suka dawo daga jana'iza. "Wai meye haka naga kuna wani haɗe fuska kuna muzurai? Ko wani abun akayi muku? Ko dai akwai matsala ne" Sadiya tace "Yadikko labarin babu daɗin ji ne, shiyasa kika ganmu haka?" 'to ku gayamin abunda ya faru mana, ni da nake saka ran inga kun dawo min da daddaɗan labarin daze sa in taka rawa, Amma kuce min wai mummunan labari" Amina tace "Yadikko Amira" "Meya sami Amiran? Taje gurin bikin ne? Naga nan ta bar gidan nan ta tafi nata gantali" "Ai ranar data bar gidan nan dan munafurci, Alhaji Ali ya turo ɗansa ya ɗauketa zuwa can gidan sa" Cikin ƙosawa Yadikko tace "se akayi yaya kuma? Ba dai kuna nufin a can zata zauna ba?" Umma tace "bari dai in taƙaita miki Maganar nan, sun Aurar da Amira" Wani Mugun haɗe rai Yadikko tai tace "Kamar yaya? Wace irin maganar banza ce wannan, Ban gane sun Aurar da Amira ba, da izinin wa aka aurar da itan? Ke tsaya ma wa aka Aurawa?" Sadiya tace "ɗansa ya aurawa, kusan dai zan iya cemiki bikin Amira mukaje Garin nan, mu kanmu bamu sani ba, Fa'iza kawai aka gayawa" "Ku dalla bana son shirmen banza da hauka" Umma tace "wallahi dagaske ne, anjima ki kira Fa'iza ki tambayeta, wallahi ya aurawa ɗansa Amira, mata biyu ya aura lokaci ɗaya" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, amma wannan mutumin nan anyi munafuki tsinannen, dama sintirin da yake gidan nan kenan, abunda suke ƙullawa kenan da baƙin hali da mugun abu, shine be aura masa nutsatstiya ba a cikinku se wannan watsatsiyar Yarinyar, ashe shima watsasten ne ban sani ba, Zailani ya shigo ya kiramin shi a waya, inji dalilin daya sa ze aurar da ita ba tare da izinin mu ba" Amina tace "Yadikko koma fa me zakiyi mutumin nan yafi ƙarfinki, kuma an riga an ɗaura ba yadda zamuyi" "In Allah ya yadda Auren nan ba inda zeje, saboda tsiya da baƙar mugunta, Yarinya ta gama gantalin ta da watsewa kuma ta Auri miji kamar Wannan Yaron, shima ɗan banza munafuki yazo yaita zazzare mata ido amma ya koma ya Aureta dan tsiya da baƙin hali, bayan gaku kamanmu nutsatstu" Sadiya tace "Yadikko, ki kwantar da hankalinki, bana tunanin ya Aureta ne dan yana sonta, ana gobe za'a ɗaura Aure, baki ga dukan da yai mata da wayar wuta ba, yanzu haka ma tana can bata da lafiya, in dai da wannan Mugun halin nata ne ba iya zaman Aure zatayi ba, sakota zeyi kwanan nan" Yadikko tace 'ke bari, wannan Yarinyar algunguma ce, se ta baki mamaki kiga ta zauna lumui, bari ayi sallar magariba, a saka kati a waya a kiramin Alhaji Alin inji ba'asin wannan maganar, amma wannan abu sam bame yuwuwa bane" Haka Yadikko ta cigaba da sababi da nuna adawa ƙarara da Auren Amira. Anty Fa'iza kuwa gaba ɗaya damuwa ta hanata sukuni, bayan sallar isha'i Bashir ya dawo, ya tarar da ita a gida ta dawo, yaji daɗin tarar da ita a gida, dan tunda sukai Aure bata taɓa zuwa wani gurin tayi kwana biyu ba, shiyasa duk ya damu gidan yai masa faɗi, ba ita ba yara da Khairat kawai ta tafi, namijin ta barshi a gidansu Bashir. Yana zuwa ya rungumeta yana "sannu da dawowa Ummu Khairat, maimakon kimin waya kice gaku nan in miki girki, kawai sedai in dawo in ganki" Tai murmushi tace "to yanzu ba Gashi nayi girkn ba ni" "To ya hanya ya kuka baro su?". "Lafiya ƙalau, anyi biki lafiya an gama" "Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi, bari in zuba mana Abinci, in munci ki bani labarin gidan bikin". Fa'iza kawai tayi yaƙe, dan bata son daga dawowarsa ta gaya masa matsala, suna cin Abinci yana mata hira yana tsokanarta, sedai ya lura Abincin kansa ba wani ci take ba, kuma bata responding ga maganganun da yake. "Ummu Khairat, meke faruwa ne na ganki kamar a damuwa fa" "Wallahi Abu Khairat damuwa fa akwai ta" "Subhanallah, wace irin damuwa kenan?" "Baka tambayeni ya muka ƙarke ina mutuniyarka ba?" "Wallahi tana raina, ina son in tambayeki ita, nayi zaton kun taho tare ta wuce can gidane" "Hmm Amira tayi Aure" "Kamar ya?" "Kamar yadda na gaya maka" "Bana son wasa fa, wane irin Aure ana zaune ƙalau" "Baka yadda ba kenan?" "Ej gaskiya ban yadda ba, wane irin Auren haka lokaci ɗaya ba manemi ba bincike bakomai, Kodayake nasan tana da manema, amma ba sune a gabant ba" "Wan mahaifiyarta ya bawa ɗansa Aurenta, yau aka ɗaura musu Aure ya Auri mata biyu, yanzu haka Mun baro Amira a can, ta zama matar Imran" Bashir yai shiru sannan yai murmushi yace "ta wani fannin inayiwa Amira murna, tabbas Aure tamkar mutuwane, lokacine dashi idan yazo dole ayishi, Ubangiji Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya" "Abu Khairat akwai matsala fa" "Matsalar me kuma Allah ya rufa mata Aisiri, kina kiran matsala" "Imran baya son Amira sam, jiya da daddare baka ga dukan daya mata da wayar wuta ba, kasan halin Amira da rashin son raini, ƙanwarsa ta tsokaneta suka hau dambe, aikuwa ya haɗasu yana duka, Amira ta masa Allah ya isa, ƙarshe a wani gidan ta kwana harda suma, aka dinga mata ƙarin ruwa, kuma wayewar garin yau aka ɗaura mata Aure dashi, ina tausayin Amira matuƙa ina jiye mata irin zaman da za tayi da Imran ga kuma kishiya, ga babar Imran kanta bata sonta, Amira ta sha wuyar rayuwa, naso ta samu miji nagari me sonta, sedai ta ɗaukarwa kanta wata rayuwa ta daban, wannan Auren an mata shine fa dan a samu ta nustu ba wai dan shi yana sonta ba" Bashir yace "Allah sarki Amira, bata da burin da ya wuce Allah ya bata miji me haƙuri da sonta komai talaucinsa, ki kwantar da hankalinki ita irin tata jarrabawar kenan, da kuma ƙaddarar insha Allah ina fatan da kuma sa ran Auren nan ze zame mata haske da kuma Alkhairi a rayuwart, amma ni kaina ina tausayinta sosai" Suka cigaba da tattaunawa da yiwa Amira fatan Alkhairi. Gidan Oga Imran kuwa, haka kowa ya kwana a ɗaki daban, kowa yana saƙawa da warwarewa a cikin zuciyarsa. Imran ko sallar Asuba be fita ba, a gida yayi sallarsa. Da gari yai haske Ammi ta bawa direba Abinci ya kawo musu, a gate yaje ya karɓo Abincin yace bame shigowa Ihsan bata jin daɗi. Ya karɓi Abincin ya shiga dashi cikin gidan, Ƙofar ɗakin da Ijsam ta kwana yaje ya tura ya shiga da Sallama, tana zaune a guri ɗaya tayi shiru tana zancen zuci, ya sake yin Sallama ta ɗago ta kalleshi amma bata amsa ba, ya ƙaraso ya zauna a gabanta yace "Ihsan ga Abinci Ammi ta aiko dashi, ki tashi muje mu karya" "Na ƙoshi" ta bashi amsa a taƙaice. "Dan Allah Ihsan karki horamin kanki da yunwa, ki tashi muje kiyi breakfast" "Dan Allah ka dena pretending ko nuna kamar ka damu da halin da nake ciki, ka ƙyaleni ka bari zuciya ta ta samu nutsuwa, karka yaudareni kasa in sake Amincewa da kai a karo na biyu" Imran yasan ba'a kyautawa Ihsan ba sam, shiyasa yake ta rarrashinta, amma fafur taƙi sauraronsa haka ya ƙyaleta ya tashi ya bar Mata ɗakin. Amira kam jiki ƙara rikicewa yayi, ga duka ga kuna damuwar an mata Aure ba tare da saninta ba, an Aura mata mutumin da takewa Kallon mugu mara imani, dan haka zazzaɓi ya ƙaru ba abunda take banda aikin Kuka, Anty tayi rarrashin duniya amma sam Amira bata dena kukan nan ba, saboda ita kaɗai tasan abinda take ji a zuciyarta. Ammi ta ɗau gaba da Abba, sam bata shiga sabgar Abba, shima yai watsi da ita, ya cigaba da rayuwarsa, yana zaune yana duba wasu takarfu sega kiran Baba, ya ɗaga wayar suka gaisa. Baba yace "Wani labari mukaji ne, shine muka bugo muji sahihancin labarin daa bakinka" Abba yace "eh nasan labarin baze wuce batun Auren Amira ba, dama ko baku bugo ba ni nai niyyar zan bugo muku waya, sannan in tako ƙafa da ƙafa inzo, da farko dai zan fara da neman Afuwarku da baku haƙuri akan yanke hukunci da nayi ba tare da izinin ku ba a matsayin ku na dangin mahaifinta, nayi hakane badan in muzanta ku ba, sedai nayi hakan ne saboda sanin halin ita Amiran, muddin tasan da Maganar Auren zata iya bijirewa hakan, na duba naga Aurar da Amira ga Imran ita kaɗaice masalaha, wadda zata hanata rashin jin da takeyi, shiyasa na sama mana sauƙi ni da ku, kuma bana buƙatar komai daga gareku, yanzu haka komai da iyaye sukewa 'yarsu nayi mata, na sai komai ina jiran seta kusa tarewa sannan aje a shirya mata ɗakinta, ku kwantar da hankalinku dan Allah" Yadikko tai maza ta fizge wayar tace "Amma fisabilillahi ranka ya daɗe baka kyau mana ba, dan akwai wanda mukayi wa alƙawarin bawa Auren Amira, amma kawai semuji ka aurar da ita, ka maida mu ƙanan nan mutane" Abba yace "Subhanallah, ai ban sani ba, baku taɓa gayamin cewar Amira tana da manemi ba, da kun gayamin tunda fari ai da se a san abunyi tun a lokacin amma yanzu bakin alƙalami ya bushe, kuyi haƙuri ku bawa wancan ɗin haƙuri" "Koma dai meye mutuncinmu ya zube mun zama masu Magana biyu, ƙirƙiri mun yiwa wani alƙawari amma mun gaza cikawa" "Ai nace kuyi haƙuri, ni idan nazo ku haɗani da shi in masa bayani nasan ze Fahimta" "Banji daɗi ba gaskiya, ace yaro kamanme kamar wannan yaron ka aira masa wannan yarinyar, bayan ga mata nutsatstu kamanmu har tayin jikokina nai maka, amma kace zeyi Aure, kawai se naji haɗashi da Amira Yarinyar da kwararo kwararo ba inda bata zuwa bin Maza" Abba yace "Subhanallah, abar maganar nana dan Allah, ya riga ya wuce insha Allah ya zama tarihi, Insha Allah shiriyarta ce tazo a sanadin Auren nan" be jira me zasu kuma cewa ba ya kashe wayarsa. Kwanan Ihsan uku a gidan Imran, amma sam taƙi amincewa Imran yaje inda take balle wani abu yafaru, dan fafur take nuna masa bata ta tasa yanzu. Da daddare bayan sallar isha'i Imran yana falo yana kwance yai shiruu, ya rasa abunda yake masa daɗi, message ɗin Abba ya shigo wayarsa. "Ku buɗen ƙofa, ina ƙofar gidanka" Imran ya tashi da sauri ya tafi gate, yana buɗewa yaga Abba, murmushi Imran yai yace "Abba sannu da zuwa" Abba yace "Yawwa Ango" Imran yai masa jagora har cikin gidansa, a falo Abba ya zauna suka gaisa da Imran. Abba yace "Ina 'yar tawa take?" Imran yace 'bari in kirawo ta" Jiki a sanyaye ya tafi ɗakin Ihsan, tana zaune a gefen gado yai Sallama, daƙyar ta amsa masa a ciki, Imran yace "kizo ga Abba yazo, yana son ganinki a Falo" Ba tace masa komai ba, ta miƙe ta saka hijjabi ta bishi falon, fuskarta ba yabo ba fallasa haka ta gaida Abba. Abba ya amsa cikin kulawa, nan yai tayiwa Ihsan nasiha tare da bata haƙuri akan abunda akayi mata, nayi mata kishiya ranar Aurenta ba tare da saninta ba, yaita mata Nasiha yana rarrashin ta. Daga ƙarshe yace Imran ze rakashi unguwa, ba daɗewa zasuyi ba. Imran ya tashi yabi Abba, ya rufe Ihsan ta waje, ya shiga motar Abba, Suka tafi. Suna tafe a hanya Abba yace "Imran ka sake duba ya jikin Matarka kuwa? Bana jin kota waya ka kira kace ya jikinta? Imran ina sake jan kunneka da kaji tsoron Allah akan riƙon da zakayiwa marainiyar nan, kayi adalci a tsakaninsu, tunda baka san yakamata ba shiyasa nace ni bari inzo in ɗaukeka muje a sake duba jikinta" Imran yai shiru ya cigaba tuƙinsa. Suka isa gidan Alhaji Hashim, sukai parking sannan suka shiga, a falo suka tsaya sukai Sallama akayi musu izinin shiga. Anty na ganin Abba tare da Imran tace "gaskiya munyi fushi, fushi muke daku irin sosai ɗin nan, haka akeyi ai mana laifi amma ba ban haƙuri ba dubiya ko ta waya" Abba yace "tuba muke, Allah ya bada haƙuri" Alhaji Hashim ne ya shigo falon yana faɗin "Ƙyalesu zamu haɗe a Human rights tunda abun hakane" Abba yace "wannan kuma kai da shi, ɗanka ne yai maka laifi bani ba" Suka zauna suka gaggaisa, suka ƙara yiwa Imran Allah ya sanya Alkhairi, Abba yace "ina Amiran ne? Ya jikin nata?" Anty tace "'yar tawace akwai zuciya, ta bi ta damu kanta ba irin rarrashin da bana yi, amma ta damu kanta da koke koke, ga zazzaɓin nan ko sauka bayayi saboda damuwa, ina tsoron ta jawa kanta wani ciwon" Imran a ransa yace 'ni banyi kuka na sa abun a raina ba se ita, se taje taita yi ai" Abba yace "Yasalam, nasan a rina ai, yanzu tna ina?" Anty tace "Imran shiga ka taso ta tana ɗakin kusa da dining" Imran kamar yace baza shi ba, haka ya miƙe ya shiga ɗakin da Amira take, tana zaune akan gadon, ta rame sosai mussaman a fuskarta, ya ƙarasa cikin ɗakin gaban gadon da take, ɗago idonta tayi ta harareshi sama da ƙasa ɗauke kanta, se a lokacin ya lura da raunin dake gefen idonta, da tabon hannayenta da suka fara baƙi, a lokacin ya tabbatar da dukan da yai mata bana wasa bane. "Kizo ana nemanki a Falo" Ko gezau ba tayi ba balle ta motsa. "Ba kyaji ina miki Magana?" Kawai ta shige cikin bargo tai kwanciyar ta, wani takaici ya ƙule Imran, yana mata magana amma ta maida shi wani banza, kawai ya hau kan gadon ya janyota, aikuwa ta ware muryarta tace "Wayyo Allah ciwona! Dalla ni Ka cikani". Cikata yai da sauri yana kallonta da mamaki, Wannan ai salon Ace wani abun yai mata ne. Muryar Anty suka jiyo tana "Imran me kake mata ne? Kar muyi haka da kai fa" Amira kuwa hararasa tayi, ta sakko daga kan gadon ta fito falon, haka nan cike da kunya da takaici ya shima ya biyo bayanta, a ƙasa ta zauna ta sunkunyar da kanta tace "Abba ina wuni" "Lafiya ƙalau Amira, Amira haka zamuyi dake, kalli yadda kika rame fa, meyasa?" Aikuwa kamar ya fama mata inda yake mata ƙaiƙayi ta fashe da kuka tace "Abba ni bana son Auren nan, dan Allah a maida ni gida" Imran ji yayi Kamar yai tsaki, amma ya daure. Abba yace "haba Amira, ba muyi miki Auren nan dan cutar dake ba, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki kinji, Muna so ki samu lafiya da wuri ki Tare a ɗakinki, Insha Allah Imran ze kula dake" Alhaji Hashim ya ciro sadakinta dubu hamsin a aljijunsa, ya miƙawa Imran yace ya bawa Amira. Ya karɓa ya ajiye mata akan cinyarta, Amira ta ɗago idanunta da suke ta zubda ruwa ta gallawa Imran harara, ji take tamkar tai masa Allah ya isa ta huta. Akai tayi musu Nasiha ita da Imran, sedai daga ita harshi ba wanda ya maida kai akan abunda ake gaya masa, kowa da abunda yake saƙawa a ransa, suka gama aka sallami Amira, ta miƙe zata tafi ɗaki Kuɗin jikinta suka zube ƙasa. Alhaji Hashim yace "Zoki tafi da kuɗin mana, naki ne haƙƙinki ne" Amira ta durƙusa ta ɗau kuɗin kawai ta tafi jikin Anty ta ajiye mata kuɗin a jikinta, Anty ta rungume Amira ta cigaba da rarrashin ta, wato Amira sam bata gajiya da kuka. "Anty ni wallahi irin mijin Anty Fa'iza nakeso, wallahi wannan Imran ɗin cin zalina ze dingayi". Alhaji Hashim yace "A'a baze ci zalinki ba, Yayanki ne fa yana sonki ze kula dake sosai, Imran rakata ɗaki taje ta kwanta" Ya rasa meyasa aketa wani sake cuso masa Amira, Anty tace "tashi kije kuyi sallama" Tana tashi tai gaba abunta bata jira Imran ba, Imran yabi bayanta dan ba yadda zeyi. Suna zuwa ɗakin ya ƙarasa da sauri ya cinmata, ya kalleta yace "Ni kike cewa zan ci zalinki a gaban su Abba saboda makirci ko?" "Dukan da kayi min Adalci ne? Ka dinga dukana ka ƙyale ƙanwarka wallahi Allah yana kallonka" "Allah ya isa kike min kenan?" '"ni ban maka Allah ya isa ba" "Ƙarya nake kenan?" Ta girgiza masa kai, ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa yai tsaki ya juya ya fita. Domin Sharhi, gyara Ko shawara Ayshercool 07063065680. [1/23, 4:41 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                         25_26 Imran na fita Amira Tayi tsaki, ta kwanta akan gadonta taja bargo, kwata kwata da ta tuna dukan da Imran yai mata se taji ta tsaneshi bata ƙaunar ganinsa. Imran kuwa a harabar gidan ya tarar dasu Abba, sukayi Sallama dasu Alhaji Hashim suka tafi. Suna dawowa cikin gidan, Anty Nafisa ta tafi ɗakin Amira, tana shiga tai sallama Amira ta amsa, Anty tace Amira tashi zaune Magana zamuyi. Amira ta tashi zaune, Anty ta zauna kusa da Amira tace  "Amira wace irin sallama kukayi da mijinki ne?" Amira tace "mijina kuma?" "Eh mijinki Imran mana" ita Amira mantawa take wai Imran yanzu mijinta ne, idan ma aka faɗa se taji wani banbarakwai. Maimakon ta bata amsa se tayi shiru ta sunkuyar da kai. Anty tace  "Amira, duk da Imran ba sonki yake ya aureki ba kefa zaki nemo soyayyar nan da kanki" Ɗan tura baki Amira tayi a ranta tace "ji wata Magana mara ma'ana, ni zan bishi ya soni lallai" "Ki dena tura baki, kamar yadda na gaya miki ke zaki nemo soyayyar nan da kanki, sannan karki kuskura ki kuma ce masa mugu, ko yana cin zalinki yanzu mijinki ne shi, ki manta da abunda yafaru gaba ɗaya, ki fuskanci rayuwarki, banda gaya masa baƙar magana ko abunda ze tunzurashi, ko kin fiso ya sakeki ki zama ƙaramar bazawara?" Ba Kunya Amira ta ɗaga kai alamar eh, "au kin fiso ki zama bazawara, ya sakeki?" Amira ta kuma jinjina mata kai alamar Eh. "Lallai Yarinta na ɗawainiya dake, amma meyasa kike so ya sake ki?" "Ni wallahi ba irinsa nake so in aura ba, bashi da tausayi" "To ke wane iri kike so?" "Irin mijin Anty Fa'iza nake so" Anty tai murmushi tace "wane iri ne wai wannan mijin na Anty Fa'iza?" Amira ta gyara zama tace  "kinga fa shi mijin Anty Fa'iza yana lallaɓata sosai, gashi da sauƙin kai, yana da matuƙar haƙuri, kuma yana son yai abunda ze burgeta, gashi da fara'a da yawan murmushi, amma ba irin wannan Imran ɗin ba da ko dariya bayayi" Wani ƙasaitaccen murmushi Anty tayi, ta fuskanci Amira 'yar soyayyace tafi son wanda ze dinga lallaɓata yana biyewa taɓararata. Ta kalli Amira tace "Ai baki san wani abu ba, sufa maza tamkar yara suke a gurin mace, duk yadda kika so zaki sarrafa su, amma bata ƙarfin tuwo ba ta hikima da rarrashi, idan kin so seki maida Imran ɗin irin yadda kike so" "Taɓ, wannan sarkin hantarar baze taɓa zama irin Mijin Anty Fa'iza ba, inaga irinsu basu da yawa ma a duniya" "Ke waye ya gayamiki haka, kiyi tayiwa Imran Addu'a, ze zama irin yadda kike so insha Allah kinji yarinyar kirki" Amira ta gyaɗa kai ba dan ta gamsu ba, Anty tace "naga tunda kika ga Imran harkin ɗan sake, anya ba zamu tataraki mu kaiki ba?" Ɗan zaro ido Amira tayi tace "a'a ni kawai na ɗanji ƙwarin jikina ne, ba zuwan sa bane, in dan zuwansa ne bakiga yadda ya janyo ni akan gadon nan ba kamar wata kaza" Dariya Anty tayi tace  "bari in aiko Fadila ta kawo miki ko tea ne ki sha, seki samu ki sha magani" Fadila ƙanwar Alhaji Hashim ce, Aurenta ya mutu ta dawo nan gidan da zama. Amira tace "Aa karki sata aiki, bari inzo in karɓa" "Meyasa zaki ce kar in sata aiki, ƙanwata ce fa" Amira tace "Ai ta girmeni, be kamata ina zaune tayimin abu ba" Anty ta ɗan yi shiru tana nazartar Amira sannan tai murmushi tace "tashi muje Kitchen ɗin tare, ai nafison in ga kina tattakawa jiki yana ƙara ƙwari" Amira ta sakko daga kan gadon tabi Anty, tunda Aka kawo Amira gidan yaune ranar farko da ta ɗan saki jiki da Anty haka, har sukayi doguwar magana, amma da ba ruwanta dasu sam. Imran da ya koma gida har Ihsan tayi bacci, ya wuce ɗaya ɗakin yai wanka, ko ta kan Abinci baya bi, dan sam baya jin daɗin komai a bakinsa, ya bi lafiyar gado ya kwanta, sedai fara baccinsa ke da wuya Amira ta dinga masa gizo a cikin bacci, ya dinga mafarki da ita,farkawa yayi a hankali hankali ya buɗe idonsa, ya ɗakko wayarsa ya ga ƙarfe biyu da rabi na dare. Ya ajiye wayar yai shiru yana tunani, ya daɗe yana jiran ranar daze zama inuwa ɗaya da Ihsan dan nuna mata irin ƙaunar da yake mata, sedai kash ranar tazo masa da ƙalubale, be samu damar cika burinsa ba, Amira tayi kutse a ratuwarsa ta kassara komai, haka ya cigaba da juyi akan gadon nan, yana tunani ta ina ze ɓullowa al'amura, ga Ihsan sam taƙi saurararsa, miƙewa yai zaune a hankali ya sakko daga kan gadon, ya buɗe ƙofa ya nufi ɗakin da Ihsan take. Ya tura ƙofar a hankali, ɗakin ya gauraye da duhu, ya kunna fitilar wayarsa ya hangota kwance tana bacci, a hankali ya taka yaje ya hau kan gadon da take, ya kwanta ya hasakata da fitilar ƙaramar wayarsa zubawa kyakkyawar fuskarta ido, wadda tai fayau saboda kuka da damuwa. A hankali ya matsa inda take, ya janyota jikinsa, kamar a mafarki Ihsan taji Imran a jikinta, a zabure Ihsan ta farka tana neman ta kurma ihu, ta dire daga kan gadon nan da sauri tana zazzare ido. "Ihsan meye hak? Nine fa Imran ne kina nema kimin ihu a daren nan" "Akan me zaka zomin ɗaki ban sani ba, kawai ka fara rungumeni haka akeyi?" "Dama na Aureki ne dan inzo mu dinga kallon juna? Ihsan meyasa haka ne? Ina tarin ilimin addinin dana sanki dashi?" "Idan ba Aurena kayi dan ka kalleni ba, ai naga bani kaɗai ka Aura ba, kaje gurin karuwar da aka aura maka mana, dan Allah Imran ka ƙyaleni ni babu wani sauran abu ko fahimta daya rage tsakanina da kai, ka ƙyaleni inyi jinyar zuciyata akan yaudarar da kaimin" Maganganun Ihsan sun ɓatawa Imran rai matuƙa, ya ƙare mata kallo tsaf, dudu Ihsan idan yai niyya duk Wani abunta baze hana shi abunda yai niyya ba, sedai baya son cutar da ita, ya rasa wace irin zuciya ce da ita haka, yadda sukai soyayya be taɓa tunanin dan wani abu ya gifta na ƙaddara zata masa haka ba. Be ce mata uffan ba, ya ɗauki wayarsa ya fita ya bar mata ɗakin, saboda tsabar takaici a Falo Imran ya kwana, ya rasa abunda yake masa daɗi, ana Aure a samu nutsuwa da kwanciyar hankali, amma shi banda damuwa ba abunda ya fuskanta a Auren. Ƙarfe tara na Safe Ihsan tana can tana baccinta, ya shirya ya fice ba tare da yabi ta kanta ba, be zame ko ina ba se gidan su Khalid. Yaje ya tarar da Khalid yana breakfast, Khalid na ganinsa ya fara murmushi "Angon biyu, Kai angwaye na ƙyalli suyi ƙiba kaikuma naga kamar ramewa kayi, lafiya kuwa?" Imran kawai ya nemi guri ya zauna yai shiruu, yama rasa ta ina ze fara. "Kayi shiru, ko da akwai matsala ne?" "Khalid a satin nan zan koma gurin aiki insha Allah" "Kamar yaya zaka koma gurin aiki? Harka gama hutun angwancin ne?" "Wane hutun angwanci Khalid? Na rasa mema zanyi inji sanyi a raina, gara in nesa da Ihsan, kwata kwata taƙi saurarata, ta sawa kanta damuwa da tashin hankali akan Amira, taƙi saurarata taji wani uzuri daga bakina gaba ɗaya, jiya Abba yasani a gaba wai dol se munje mun duba Amira, itama mukaje ta cazamin Kai, se koke koke take wai an Aura mata Mugu, ni dana san hakane da tunda fari banyi Auren nan ba, gara in nesa dasu in bar musu garin, suje su ƙarata" Khalid ya ɗanyi murmushi yace "Imran kenan, tun yanzu fa kenan, ina ga in Amira ta tare suka zama su biyu, a gaskiya Ihsan ta bani mamaki sosai, ban zaci za tayi maka haka ba, amma ka sake bata chance kayi haƙuri kasan tana da matuƙar kishi sosai, amma ka jinkirat tafiyar nan ko zaku daidaita" "Khalid ba abunda zan jinkirta, Insha Allah bakin aikina zan koma suje su ƙarata, zan nunawa Ihsan ko babu ita zan iya rayuwa saboda na fuskanci kamar lallaɓata da nake ne yasa take nema ta wulaƙanta ni, dama ita waccan bata tata nake ba, da ita da babu duk ɗaya" "Kaga Imran ina rabaka da nuna halin ko in kula ga Amira, karka bari ta gane kana ƙinta, in ba haka ba ba ruwana, karkazo nan gaba Allah ya jarabceka da soyayyar ta" "Soyayyar wa, wannan mara Kunyar banzan fitsararriya, kai kaga abunda ta dingayi jiya, bata da ta ido sam, a gabana take cewa bani da imani, zataga rashin imani kuwa" "Ita wannan da ta san kai me Imani ne kake kyautata mata ai gashi tana baka wahala, itama Amiran dan baka janta a jikine yasa take maka kallon mara Imani, kuma ga yadda kake treating ɗinta babu tausayi, dole tace baka da imani ai" Imran ya miƙe yace "malam niga mota ta nan zan bari a gidanku, zan ƙarasa gida inje ɗakin in huta, bana son Abba yasan nazo" Khalid yace 'Yadda kace Angon biyu" Imran be kula shi ba yai waje, gidansu ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya wuce sashensa yai kwanciyar sa ba tare da kowa yasan yaje gidan ba. Jikin Amira da sauƙi sosai, ta tashi tai wanka ta canza kaya a cikin wanda aka bata, ta fita falo seda ta gama ƙarewa falon kallo, sannan ta nufi inda Kitchen yake, ta tarar da Fadila nata aiki tana ƙoƙarin haɗa abun karin kumallo ita da Me aikin gidan. Amira tace "Anty Fadila ina kwana?" Fadila ta kalli Amira da fara'a tace "Alhamdilillah, 'yar gidan Anty jiki yai sauƙi, ya ƙarfin jiki kuma?" "Alhamdilillah, naji sauƙi sedai ina kewar gida sosai" "Allah sarki, haka Aure yake Amira ki kwantar da hankalinki zaki saba ne" "To wai a nan zan ta zama?" Fadila tace "A'a haba dai, kin matsu ki tare a gidanki ko?" Amira ta zare ido tace "rufamin Asiri, kawai tambayarki dai nayi" "Ba a nan zaki zauna ba, zaki tare a gidanki nan da wani ɗan lokaci insha Allah" Amira ta ɗan taɓe baki tace  "ni dama an ƙyaleni na tafi gida, in yaso daga baya na dawo" "Zama da mune bakya so kenan ko?" Tai saurin girgiza kai tace "A'a wallahi, ina da kaya a gida da nake buƙata" "Karki damu, duk abunda kike buƙata kiyi Magana" Amira bata amsa ba tace  "bari in tayaku aikin" Fadila tace "A'a, kar Anty ta fito tace an samata ke aiki" Amira tai murmushi tace "ba abunda za tace, ta karɓi ferayr dankali a hannun Fadila" Wayarta ce ta fara ringing, wayar da se yau ta kunnata tunda aka kawota gidan, tana son ta kira su Anty Fa'iza amma taga yayi Safiya da yawa ta fasa. Ta ɗaga tace "Hello My blood" "Gimbiya kina lafiya kuwa?" Amira ta murmusa tace "lafiyata ƙalau Sultan, ya kake ya aiki?" "Amira wai da gaske An miki Aure?" "Eh Sultan, an min Aure" "Amira wane irin Aurene haka ba shiri ba labari? Dagaske kuma wannan da yazo ya tafi dake ɗin shiya Aureki?" "Eh Sultan shine, ɗan uwana ne" "Anya Amira an miki adalci kuwa? Wallahi ina tsoron mutumin nan karya dinga cutar dake, sam bashi da tausayi wallahi shaƙar da yaimin lokacin da yazo Office ɗin ji nai kamar na mutu wallahi" Ƙwallace ta taru a idon Amira, Sultan ya damu da ita sosai, ta kalli tabon dukan dake jikinta, ta haɗiye kukan dake shirin ƙwace mata tace  "Karka wani damu, babu wata matsala lafiya zamu zauna dashi insha Allah" "Anya Amira, kina ganin babu Matsala?" "Babu wata matsala malam, Baza'a zaɓamin abunda ze cutar dani ba, ya labari harka tana garawa kokuwa?" Sultan yace "ina wata harka babu ke, nifa tunda ya tafi dake ban sake samun nustuwar zuwa gurin wani sha'ani ba, harga Allah bana baƙinciki da Aurenki Amira, hasali ma ina murna kin samu miji kinyi Aure, sedai naso ace kin samu miji nagari me sonki sosai, bana son ki sake wahala a rayuwarki" "Allah sarki ɗan uwana rabin jikina, bani da wata alaƙa ta jini da kai, sedai ka damu dani sosai Sultan, karkaji komai Zan zauna lafiya da Imran insha Allah" "Shikenan Amira, Ina miki fatan Alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya, Amira banda rashin ji da taurin kai kinji, kiyi haƙuri kiyi masa biyayya, Allah ya baku haƙurin zama da juna" Duk da hawaye ya cika idon Amira, amma ta ƙaƙaro murmusa tace "Nagode sosai Sulty guy, karka damu zan zauna lafiya da mijina insha Allah, take care of yourself kaji" "Rufan Asiri kar mijinki yaji kina faɗin haka, yasa azo a casani se anjima" Amira ta kashe wayar tana murmushi, Fadila tace "Amira wannan kuma waye? Hala saurayinki ne?" "Ba saurayi na bane, kuma ba ɗan uwana bane, kawai Allah ne ya haɗani dashi, abokin kasuwanci na ne, yana jin tausayina ne sosai, ya sha shiga riski saboda ni, bazan manta da Sultan ba" "To Amma dai kiyi a hankali, kar Mijinki yaji kina waya dashi ya zaci wani abune a tsakaninku" Amira tai murmushi tace  "Ya daɗe be zata ba, ai yasan wadda aka aura masa, dan haka meye na zargi ko wani tunani" Fadila tace "Amira, Aure fa ba abun wasa bane ba, rayuwar da kikayi a baya daban, wadda kika shiga daban, karki kuskura ki ɓatawa kanki suna a sameki da wani mummunan aiki da Aurenki, dan Allah ki kiyaye" Amira tai murmushi me cike da ma'anoni daban daban tace  "to insha Allah zan kiyaye" "Yawwa ko ke fa" Ba Anty ba hatta Alhaji Hashim yaji daɗin yadda Amira ta fara sakewa, ba kamar da yadda ta takure kanta ba. Yadikko kuwa baƙin cikin duniya yabi ya ishe ta, wai Amira tayi Aure, duk da yawon ta zubar ɗin da tayi amma ta samu danƙareren miji kamar Imran ta aura, da fari cewa tayi su Baffa Salahu su kai ƙarar Abba, wai akan ya Aurar da Amira, ba da izininsu ba alhalin suke da hakkin Aurar da ita tunda mahaifinta baya raye, dangin uba suke da maganar Aure bana Uwa ba. Usman ne ya ankarar da ita yace "Yadikko, ki rufawa kanki Asiri tun wuri, Allah kaɗai yasan meya tsara tunda akayi Auren nan faka faka haka, kuma idan kika sa suka kai ƙarar me kikeso ayi? Na farko dai Aure ya ɗauru tunda ya cika dukkan sharuɗan da addini yazo dasu, sedai ace anyi ba daidai ba daya aurar da ita, na biyu Kuma kin san dai ba raba Auren nan za'ayi ba, ga uwa uba shi wanda ya aurar da ita ɗin wani ne a sama, baki da kuɗin da zakija dasu, kawai kiyi haƙuri ki koma gefe kiyiwa su Amina Addu'a suma Allah ya basu maza nagari wanda yafi na wanda Amira ta samu" Yadikko tai ajiyar zuciya tace 'ni babban abun takaicin, yadda suka dinga sintiri a gidan nan shida ɗansa, amma aka rasa wanda ze buɗe baki yace mana ga abunda ake shiryawa, da kunturun makirci, suka auri karuwa suka bar na ƙwarai" "To ke meye naki a ciki, suje su ƙarata an rage mana Matsala ma" "Wane rage matsala, ni ba gara ace tana gidan nan a cigaba da matsalar ba, su Sadiya su Auri yaron ba" "To koma dai yane, Yanzu jabbal ƙalam, tunda an riga an Aureta se haƙuri" Haka Yadikko ta kasa ɓoye bƙin cikinta da Auren Amira, Sosai take nuna tana adawa da Auren, yayinda labarin Auren Amira ya cika gari, kiwa ya dinga mamakin irin yadda Amira tai Aure lokaci ɗaya haka, duk da irin tarin fitinarta da rashin jinta. Tafi tafi rayuwa na cigaba da tafiya, Imran sam ya dena shiga sabgar Ihsan, yai watsi da ita ya dena nuna yasan da zamanta a gidan, wataran da sassafe kafin ta tashi ya fice, baze dawo ba se dare, ya ajiyemata duk wani abun buƙata, amma fa ba ruwansa da ita. Ranar wata laraba da Safe, Ihsan ta tashi daga bacci ta fito falo taga takadda akan Centre table na falonta, ta ɗauka ta duba taga Imran ne ya ajiye mata saƙo  "Na koma gurin aiki, in kina buƙatar wani abu na bar kuɗi a wardrobe ɗina" Gaban Ihsan ne ya faɗi, tai shiru tana tunani To yanzu idan gurin Amira ya tafi fa? Take taji wani gumi yana tsatstsafo mata, jiki na rawa taje ta ɗakko wayarta ta kira shi, sedai be ɗaga ba, se a yanzu take tunanin wautar da tayi na share Imran, hakan ze iya bashi damar tafiya gurin Amira. Tana nan tana wannan zulumin taji ana buga gate, ta saka hijjabi taje ta buɗe ƙofar, tana buɗewa taga Ammi ce da Minal suka zo. Murmushi tayi tare da yi musu sannu da zuwa, ta jagorancesu zuwa falonta. "Ammi sannunku da zuwa, da kun kirani na ɗora muku wani abun ai" Ammi tace  "A'a sauri mukeyi, nace mu biyo inzo in dubaku zamu wuce ta wajen gidan nan nace bari in leƙoku, ina Imran ɗin?" "Ammi ai ya koma aiki yau". "Kamar ya ya koma aiki yau? Amma ya akayi be gayamin ba? Hutun nashi ya ƙare ne?" Ihsam tace "kiran gaggawa akayi masa shiyasa ya tafi be miki sallama ba" Ammi tace  "shikenan, na biyo ne dama inga komai lafiya kafin inyi zuwa na musamman, sannan ki kula ki kwantar da hankalinki, waccan Yarinyar da ita da babu duk ɗaya, karma ki a ranki kina da kishiya, ki sake kiyi rayuwarki a gidan mijinki, na yiwa Imran kashedi sosai akan Yarinyar nan, jira nake ta tare inga ta inda zan ɓullowa lamarin in kashe Auren ba tare da mahaifinsa ya zargi wani abuba, karki kuksakura ki bata damar da zata ga kafar da zatai masa shishshsigi, kin san karuwai a waje ma ƙwacen miji suke balle tana matarsa, duk ds na lura shima ba shi da interest akanta, mahaifinsa ne duk ya haɗa wannan kwamacalar, shiya tursasashi ya Aureta, shikuma ya amince ba tare da ya nuna baya so ba, kowane ɗa yafi son uwarsa amma shi kam, yafi son ubansa a kaina" Ihsan ji tayi kamar Ammi tai mata allura, tabbas idan tai wasa hankalin Imran ze iya karkata kan Amira, Dan haka dole tayi wani abu a kai, ashe dagaske dai takura masa akayi ya Auri Amira ba dan yana sonta ba. A gurguje Ammi tayi sallama ds Ihsan suka tafi, tunda suka tafi abun duniya ya ishi Ihsan, ta ɗau waya ta kira Imran kusan 5missed calls anma yaƙi ɗagawa sam. Baƙin da ta dingayi ne suka dinga ɗauke mata hankali, amma wani sashi na zuciyarta na can tunanin mafita, dan bata zaci Imran ze iya watsi da ita haka b, harta kirashi yaƙi ɗagawa ba. Ɓangaren Abba ma hankalinsa ya kwanta, mussaman daya sake zuwa gidan Alhaji Hashim ya tarar da Amira ta saki jikinta, ta dena koke koke da damuwa, yanzu bashi da wata fargaba na za'a kirashi ace masa ga Amira ta aikata wani lafi, dan haka ya samu nutsuwa harya koma bakin aikinsa. Ihsan kam abun duniya ya isheta, kwanan Imran biyar da tafiya amma yaƙi ɗaga wayarta, ta tura masa message ba adadi amma beyi responding ɗin ko guda ɗaya ba. Rana ta shida da Safe ta sake jarraba kiran wayarsa, Babu tsammani taji ta ɗauka, kawai ta sa masa kuka. "In kuka zakimin zan kashe wayata, meyafaru?". "My meyasa zaka tafi ka barni dan Allah?". 'saboda ba kya buƙata ta, babu amfani cigaba da zaman namu shiyasa na bar miki Gidan" "Haba My, kishinka ne yasa nai abunda nayi, But i regret it, Ammi tazo ranar da ka tafi, ta gayamin takura maka akayi ka Aureta, dan Allah kayi haƙuri, wallahi ina sonka mijina". "Ina tantama akan son da kike min Ihsan, tunda kika gaza yimin uzuri ki saurareni" "Dan Allah kayi haƙuri My Own, kishine ya rufemin ido, ina sonka sosai" "To yanzu me kike son ayi?" "Dan Allah ka dawo" "Na riga na dawo bakin aiki, se ƙarshen wata zan dawo" "Dan Allah kayi haƙuri, am missing You am sorry please" Imran yai ajiyar zuciya yace  "Shikenan naji, ki kwantar da hankalinki, zaki biyoni nan ne?" Da sauri tace "Eh zan biyo ka" "To shikenan, zan turomiki kuɗi ki biyo jirgi ki taho" "Alhamdilillah, insha Allah zan taho, amma kamar baka haƙura ba My Own" "Ya wuce mana, karki damu take a very good care" Ihsan taji daɗin ɗaga wayarta da Imran yai, nan da nan ta fara shiri, domin zuwa ta riski masoyinta a Ikko. Anty kuwa tana matuƙar jan Amira a jiki, hakan yasa ta saki jiki da Anty sosai, suna matuƙar mutunta ta da girmamata, ba hantara ba tsangwama ba Komai, Anty tana ta monitoring ɗin Amira da son gano matsalolin Amira, sedai a zaman da sukai Babu wata alama da ta gani da take nuna rashin jin da ake faɗa akan Amira. Tana girmama kowa, sedai kusan kullum setayi zancen dama irin Mijin Anty Fa'iza ta Aura. Yanzuma suna zaune a falo suna kallo, Fadila da Amira suna hira, Anty Fa'iza ta kira Amira  "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" Amira tace  "Malama uwargida dai sarautar Mata, ko kin manta ni aka fara ɗaurawa Aure"? Seda Anty ta kalli Amira tai murmushi, tare da girgiza kai. Fa'iza tace  "mara kunya, Allah ya baki haƙuri, Uwargida Imran, ya kike ya mutan gidan?" "Lafiya  ƙalau, ina 'ya'yana ina ɗan aljanna?" Fa'iza tace "duk suna lafiya, ɗazu ya gama zancenki kan ya fita, yace in kira ki ince yana gaisheki" "Allah sarki Yaya Bashir nawa, kice ina amsawa ya dena nemana ko?" "Haka kurum ya nemeki yai miki me? Ranar da Sultan yazo nemanki ya bani labarin shaƙar da Imran yai masa, haka kurum nima a shaƙen miji" Amira tai dariya tace  "haba dai, ai duk ke kika jamin wannan abun, da tun farko kin Auri Alhaji Yahaya, nikuma na Auri Abu Khairat da ba shikenan ba" Fa'iza tace 'mara mutunci, ai gara da aka miki Auren, na fuskanci da zaki samu dama sekin Auri mijina kin zama kishiya ta" "To tun yaushe ma, ke Allah ne yasa mijinki ne, da mijin wata ne ai da sedai taji wani zancen" "Taɓ kishi da irinki se macen da ta shirya ai, gara dai da kika Auri Imran ɗin shine dai dai dake" "Kyaji dashi dai, anjima zan kiraki ki haɗani da Khairat a waya, inji muryarsu" "Zan haɗaku Insha Allah, dan kusan kullum se sunyi zancenki suce min wai yaushe zakizo, gidanku kuwa sunata sababi wai an Aurar dake basu sani ba" "Mhmm, ni nama rasa me zance, kuma suna raina wallahi, duk cikinsu ba wanda ya kirani ko a waya, ni zan nemesu insha Allah zan kira su in gaishesu" "Shikenan, ds kin kyauta ki gaida mutan gidan". "Zasuji insha Allah"  Amira ta kashe wayar. Anty tace  "Amira wai ya kuke da Fa'izan nan ne?" "Yayata ce, cousin ɗina ce" "Amma kike gayamata  zaki Auri mijinta?" Amira tai murmushi tace  "tasan tsokanarta nake ai" "Anya baza taji ba daɗi ba, koda yake ai kema kinyi Aure yanzu". "Idan ma tana ji sedai tayi haƙuri, dan mijinta yayi a rayuwa, irin wannan mijin haƙurinsu idan baka musu biyayya ba se su kaika wuta, baya fushi sam da wuya, ko faɗa sukayi bata da gaskiya amma dan a zauna lafiya se yaita bata haƙuri, idan nike da mijin Anty Fa'iza, ai binsa zan yi sauda ƙafa, bazan bari ma yai fushi ba, itama ta sha wahalar rayuwa Allah ya musanya mata da mafi Alkhairi" Fadila tace  'to shi Imran ɗin da Allah ya baki, ba zaki bishi sau da ƙafan ba?" Murguɗa baki Amira tayi ta ɗauke kai, alamar ba wannan maganar. Anty tace "A'a shina zata bishi sau da ƙafan mana, ai Amira Yarinyar kirkice, next week insha Allah Ina son muje dake Kasuwa ki zaɓi abunda kike buƙata, amma za'a kirashi ki fara tanbayarsa tukuna" Amira tana jin abunda Anty ta faɗa amma ta basar kamar bata ji ba. Ranar juma'a da yamma, Ihsan ta sauka a garin Lagos, Imran da kansa yaje ɗakkota a airport, tana ganin Imran ta tafi da gudu ta runguneshi, shima rungumetan yayi yana murmushi yace 'i miss You my Ihsan". "Miss you too Hubby" Suka shiga motarsa suka tafi, tun kan ta sauka tuni yasa anyi order Abinci ya ajiye mata. Gidansa a cikin Barrack yake, flat ne madaidaici me kyau sosai, gidan ya burgeta sosai, tai wanka ta canza kaya suka zauna suna cin Abinci, tana sake lallaɓa Imran tana bashi haƙuri, dan ta lura be huce gaba ɗaya ba. Ihsan an haɗu da maza, dan yau Imran ya samu abunda yake so a gurin Ihsan, hakan yasa ta wanke duk laifin da tayi masa, sedai Ba laifi ta ji jiki, gaba ɗaya Imran ya manta sunyi faɗa, suka jone suka shiga sabuwar Rayuwa shida Ihsan, me cike da soyayya da kulawa, gaba ɗaya ya manta da wata Amira a rayuwarsa, se daga baya ma Ammi tasan Ihsan tabi Imran. Amira tai waya da Anty Fa'iza tace "taje gidansu ga kwasar mata kayanta gaba ɗaya, ta haɗa mata dana wajenta ta ajiye mata" Da la'asar Amira ta fito ta samu Anty a Falo tace  "Anty, ina son zani wankin kai, dan Allah kisa a rakani" Anty tace  "Eh gaskiya yakamata kam, dam kuma nayi miki zancen zuwa kasuwa, bari a kira Imran ki nemi izninsa" Haɗe rai Amira tayi tace "Izini kuma?" "Eh mana ba mijinki bane, seda izininsa sannan zaki fita" Amira ta ɗan kumbura fuska, wai mijinta tunda sukazo da daddare shi da Abba, be ƙara bi takanta ba, ko ya kira yaji halin da take ciki ba, se yanzu za'a wani kirashi wai a tambayeshi zata fita, fan tana jin nauyin Anty ne da wallahi ba zata kulashi ba itama. Ganin lambar Anty tasa Imran ya ɗaga wayar, dan seda yaga lambar Antyn ne Amira ta faɗo masa, ya ɗaga da fatan Allah yasa ba wani abun tayi musu ba. Anty tace "Ango wannan shiru haka, ba amo ba labari baka ko waiwayar matar taka" Cikin jin nauyi Imran yace "wallahi Anty Nafisa abubuwa ne suka ɗanmin yawa, harkar aikin namu ne ba sauƙi" "Ka koma bakin aikin kenan?" "Eh na koma tuni" "Ahh to masha Allah, kace Ihsan ɗinma tana nan ka barta?" "A'a Ihsan tana tare dani, da ita na taho muna nan gaba ɗaya" Kasancewar wayar a hansfree take, Amira tana jin maganar da suke, aikuwa nan da nan Amira ta haɗe rai. Rainin hankali, ita am barta a nan bata ga tsuntsu bata ga tarko, ita ba matar Aure ba ita ba sakakkiya ba tana zaune a gidan mutane, dan ita bata ma san zaman me take a gidan ba, Amma ya ɗau matarsa sunyi tafiyarsu, irin zaman da zataje tayi a gidan nasa kenan? Ta tambayi kanta. Anty tace "dama Amira ce tana son taje gyaran kai, kuma ina son taje Kasuwa zamuyi 'yan saye saye, nace bari in kira mu nemi Izini" Imran yace "seta dawo" "A'a bari in baka ita ku gaisa, ta tambayeka da kanta" Anty ta miƙawa Amira wayar, Amira kamar karta karɓi wayar nan, zuciyarta se wani tafasa take kamar ta tsaga ƙirjinta ta fito. Tasa hannu ta karɓi wayar, ta danne fushinta tace "Yayana barka da yammaci ya aiki?" Imran a ransa sabon salon rainin wayo. Ya basar yace "Alhamdilillah" "Dama zanje a gyaramin kai ne, Shine nake neman Izini" "Sekin dawo" Imran ya bata amsa. 'Nagode, ka gaishemin da ƙanwata kuma Yayata, wato Amaryata" Daga nan ta kashe wayar, ta sake haɗe rai ta miƙawa Anty wayarta. Ba ƙaramin mamaki Amira ta bawa Anty ba, ga kishi nan ƙarara a fuskarta, amma ta danne taiwa Imran magana cikin nutsuwa. Anty tace  "Amira kishi haka?" "Anty wane irin kishi kuma? Ni ba kishi nake ba" "To me kikeyi?" "Bakomai" ta faɗa kamar za tayi kuka. Anty ta jinjina kai tace "lallai gidan Imran akwai kallo, Amira kishi ne gashi nan ƙarara a fuskarki, sedai kin birgeni da kika ɓoye kishin naki, baki nuna masa ba" Amira kasa magana tayi, kawai ta tashi ta tafi ɗakinta, danji take kamar an ɗora mata dutse a ƙirjinta, jin Imran na can shi da matarsa, ita kuma an barta a nan. Anty ta jinjina kai tace "taɓɗijan Amirana kishi tun yanzu?" Amira kam tana zuwa ɗakin ta rufe ƙofa ta tsaya tana sauke numfashi, tace  "Lallai ma an rainamin hankali, zaman da zanje inyi a gidan nasa kenan, ita yana sonta ya bata kulawa ni kuma ina kallonsu? Baze yuwu ba, ba zanyi boranci a gidamu, inzo gidan miji ma inyi boranci ba, dani suke zancan da shirina zan tare a gidan Imran, ba zan ɗau kowane kalar cin kashi ba, zan nuna musu WATA KISSAR..... Sai mata!!! (Wanda be karanta littafin wata kissar sai mata ba, an barshi a back 😜😜😜🤪) Gaskiya ba ƙaramin jin daɗin sharhin ku nake ba, shiyasa nake muku dogon page, ina godiya da kulawa masoya 🥰😍😍😍😍🥰 Share Please Follow me on watpad@ Ayshercool7724 Domin gyara, Sharhi ko shawara 07063065680 [1/25, 8:34 PM] Ayshercool:       🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                          27_28 Imran kam seda ya ƙarewa wayar kallo, tare da jinjina kalmar Yayana da Amira ta kirashi da shi, yasan wani sabon iyayin ne yasa ta faɗi haka, wani gajeren tsaki yaja, ya ajiye wayar ya cigaba da aikinsa. Amira kam tunda ta shige ɗakin nan bata sake fitowa ba, ta zauna ta dinga saƙawa tana warwarewa, tana tunanin irin zaman da za tai a gidan Imran, daga Imran har matarsa da danginsa babu me ƙaunarta. Imran kam ya samu nutsuwa sosai, hankalinsa a kwance yake sosai, cin amarcinsu kawai suke da Ihsan. Yana kwance yana kallo, Ihsan ta fito tana yamutsa fuska, ya kalleta yace "My beb, ya dai naga kina ɓata rai?" Ƙarasowa tayi ta kwanta a jikinsa tace  "yau bana jin daɗin jikina gaba ɗaya" Murmushi yai ya shafa dogon gashinta yace  "kodai kodai?" Ihsan tace "kodai me?" "Ko an gamune, kin sama mana Baby?" Gaban Ihsan ne ya faɗi, a ranta tace ji wata Magana, daga yin Auren se maganar ciki. "Ya naji kinyi shiru ne?" "My, daga yin Aurenmu se ciki kuma, ko gama cin amarcin banba se ciki, kasan fa ciki yana bawa mata wahala sosai" "To meye a ciki Ihsan? Ai Arziki ne da yawa suna nan suna nema basu samu ba, ina fatan Allah yasa ciki ne, ko biyu ki haifamin sekiyi planing ki huta" "My D Service ɗina fa?" "Bakomai, Allah baze hana mu yadda zamuyi ba, Allah ya bamu masu albarka" Yai maganar yana kissing goshinta, murmushi kawai tayi ta rungumeshi sosai ta lula duniyar tunani. Amira ta kai kwana biyu kafin ta sake sakin ranta, dan duk batun Imran ta dameta, Anty kuma tana ankare da ita, ta tausaya Amira matuƙa, ta fuskanci Amira nada kishin gaske sedai kuma ta iya siyasa sosai da sosai. Amira tana cin Abincin Safe tana ta cakala, ba wani ci take sosai ba, Anty tace "Amira, anjima ki shirya zamuje kasuwar, idan yaso gyaran kan gobe in Allah ya kaimu se Fadila ta rakaki" Amira tace "to Anty, bari in gama se in fara shiri"  ta kammala cin Abincin, amma maimakon ta tashi seta ɗakko wayarta ta kira layin Yadikko, amma bata tafiya, seta kira ta Usman. Seda ta kusa katsewa sannan ya ɗaga yai Sallama. "Yaya Usaman manyan gari, ko nemana ma ba'ayi ko, wato Allah ya rabaku dani babu me neman inda nake, bakomai rayuwa ce" Usman yace "Ni mamakine ma ya kamani a ina kika samu lambata?" "Ji wata tambayar rainin hankali, dama can ina da ita ai" "Kina da ita amma baki taɓa kirana ba ai, kuma wake da lambarki a gidan nan? Ba wanda yake da lambar ki" "Hmm duk da haka wannan ba uzuri bane, ai da kukaji labarin Aurena haka ba shiri, kwace bari kuji ya wannan marainiyar take ciki, meyakamata ayi mata? Koda yake ai ba sona kuke ba, nice dai duk inda na shiga kuna raina, yanzu ya kake ya gidan?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya amarci ina mijin naki?" "Yana Lagos gurin aiki" "Naji ance ai baki tare ba ko?" "Eh ban tare ba, amma nakusa insha Allah, Ina su Sadiya da Yadikko uwar faɗa" "Kowa lafiya ƙalau" "Kai musu wayar mu gaisa, na kira ta Yadikko bata shiga" 'to bari in kai musu" Ya shiga cikin gidan da wayar a hannunsa, ya tarar da Yadikko na shan koko da ƙosai, ya miƙa mata waya yace "gashi za'ai magana dake" Ta kalleshi tace "waye?" "Karɓi kiji mana" Yadikko ta krɓi waya ta saka a kunnenta. "Hajiya Yadikko me abun mamaki, ba faɗa meya kawo gaba? Har labarin Aurena ya riskeki amma ki gaza nemana, ko kice ya nake ciki? "To in nemeki ince miki me? Ko in miki me?" "Ba abunda zakimin, amma ko yaya ai kyanuna kin damu dani, amma dai shikenan ya kuke yasu Baba da kowa da kowa?" "Ji yadda kike wani tambaya ya suke, irin kin damu dasu ɗin nan, aifa kin damu dadu da baki haɗa kai da wan uwarki anmiki Aure ba izininmu ba" "To ni meye nawa a ciki, yadda baku san da labarin Auren ba nima ban sani ba, sama taka naji wai an ɗauramin Aure da Imran" Yadikko tace "to amma kuma kika zauna? Aida seki ce masa bakya son sa, akanme za'a miki Auren dole, ni kik ban mamaki m, ina bakin nakinda tsiwar taki, da har zaki bari a miki Aure ba saninki kuma ki zauna kiyi shiru?" "To Yadikko idan ban zauna nayi shiru ba me kike son inyi?" "Ai irin haka ski ce masa bakya so, ko kina son Imran ɗin ne? Ina kwanaki har nan gida yazo ya sameki ya dinga tamaula dake a gidan nan, kuma nan akazo aka bania labarin ana gibe ɗaurin Aure ya kamaki ya zane, to da irin wannan zaki zaman Aure, ai irin haka kamata yayi ki gayawa babansa bakya son sa" Amira tai murmushi tace "Yanzu Yadikko, kawai se in dubi tsabar idon Abba ince masa bana son ɗansa, to ai duk isaknacina wasu lokutan nasan abunda yakamata da wanda be kamata ba" "To Yanzu dai zama zakiyi dashi kenan? Ya dinga muzguna miki yana dukanki? Nifa da cewa nayi ko ƙararsa zamuyi, ya Aurar dake ga ɗansa ba izininmu, kuma ɗan nasa ma har dukanki yakeyi dan a ƙwatar miki haƙƙin ki, idan yaso ko raba Auren ne ayi, ki fito ki auri wanda kike so yake sonki" "Taɓɗijan aikuwa da kun kai ƙara da kunji Kunya, dan bazan yadda a kashemin Aure ba, kinga kajin da nake ci kuwa, Allah ya hutar dani ya rabani da Karuwanci da kuke faɗa ya rufan Asiri in tonawa kaina, ai ba dani ba, zamana zan in lumui a gidan, koda ze dinga dukana kuwa, balle ba duka ba zagi tsakanina dashi, lallaɓani ma yakeyi, kin san Karuwa da shiga rai, mussaman yadda na goge a iya duniyanci, nan komai available baki ga da kazar dana karya ba yanzu haka, ga shayi me kauri falo da AC, ga luntsumemen gado, anjima in tashi in saka matsatsun kaya, koma tsirara in taka masa rawar gala a gabansa ya kalleni yana murmushi, yaushe zan yadda amin sagegeduwa, an rabani da bin kwararo da wannan gidan namu gidan tashin hankali, aini Allah ya rufan Asiri, su Sadiya ma ina musu Addu'a Allah ya ɗaga su daga wannan gidan ko dan tijararki"  Amira tai maganar tana wani makirin murmushi. "Yanzu Amira ni kike gayawa, kina rawar gala tsirara a gaban miji?" "Au nayi a gaban wasu banzaye ma balle mijina, meye amfanin ƙirar da Allah yaimin in dai bazan juyasu a inda ya dace ba, gari banza ma naje nayi an min liƙi, balle yanzu da nake me dalili na ibada" Yadikko tace "Amma kuwa idan hakane wannan Imranan munafuki ne, yaita nuna yana jin haushinki, baya ƙaunarki amma ya aureki, harma ya saki jiki dake?" "Au kina mamakine Hajiya Yadikko, Amira ce fa ai bari kawai wani abun baze faɗu a waya ba, kusa lokacin da za kuzo kema kici kajin nan da nake ci, da ina kusa da sena dinga aiko miki ki adana tsufanki, yanz idan nace na gaji da naman kaza, anjima Imran ze aiko da na zabi, aini Alhamdilillah Allah ya 'yanto ni" Wani irin baƙin ciki ne ya tikare zuciyar Yadkko, wato Amira ma jin daɗinta takeyi, taso ace tana can tana wahala amma taji saɓanin haka. "Yadikko ya naji kinyi shirune? Ki gaida Mutan gidan gaba ɗaya, zanje in ɗorawa Mijina sanwar rana" "Amma naji kina da kishiya ko?" "Eh, ina da kishiya mana" "Kuma lafiya kuke zaune da ita?". "Ai ba ruwan wani da wani nida ita, kowa zaman kansa yakeyi, Yadikko se anjima, zanyi girki in gyara jikina, sannan Anty Fa'iza zata zo ta ɗebar min kayana na nan gidan Please, duk abunda aka san nawane kar a taɓamin" Amira ta katse wayar, ta ɗan tsurawa wayar ido, wasu hawaye suka cika idonta, ta rasa meyasa Yadikko bata son ganin duka wani abu na cigaba ya raɓeta, ta fison ta ganta a wahala da tashin hankali, tafi son taga ta wulaƙanta, sama batayi murna da jin abunda Amira ta faɗa ba, so tai taji Amira tace tana cikin wahala. Amira tace "ya Ubangiji Allah, ka jiɓanci lamurana, kaimin ɗauki akan zaman da zanyi a gidan Bawan Allah nan, Allah karka kawo dalilin da zesa maƙiya suga hawaywna ko su ganni a rana, Allah yadda suke ƙina kar bani ikon ƙinsu ko cutar dasu, Allah ka shiryesu ka ganar dasu ka maida su kan tafarkin ka madaidaici" ta ƙarasa addu'ar a hankali cikin karaya. Yadikko kuwa cewa tai "ni ungo wayarka, munafukar yarinya 'yar hau, ni zata kira ta gayawa daɗin Aure, dan ubanta tun kan a haifi uwarta nai Auren nan nima, amma dan fitsara harda gayamin tana zama tsirara a gabansa, yo aikin banza ma, tsirara nawa tayi a gaban ƙarti daban daban, shima shashasha soloɓiyo, namijin hotiho ya rasa wadda ze Aira se Wannan karuwar, dama tana tafiya tuɓi tuɓi da mazaunai ai dole su tsole masa ido ya Aureta, duk wannan hantarar da zagin da yake mata ahse kurin banza ne" Amina tace "ai bazaki san kurin banza bane, se kinga irin shegen dukan da yayi mata daren da za'a ɗaura musu Auren nan, ya farfasa nata jiki da duka, ke bakyace Aurarta ze ba" Sadiya tace "nifa ban yadda da abunda ta faɗa ba, wannan Yarinyar makirace maƙaryaciya, ya za'ai mutum yana sonkabya maka wannan dukan" Amina tace "ke bar maza da gulma, kin san uwarsa fa ba son ta take ba, se iya dukan nata dan yai pretending, amma ai a ɗakinsa ta dinga kwana, kuma takanas yazo har garin nan ya ɗauke ta, ke ƙaddara ma baya sonta, Yarinyar da ta saba bik mazama, ina ga shi, shima barikin zata masa ya manne mata" Yadkko tace "dan abun takaici, kalli koko nake sha babu ko sikri, ƙosan nan kamar a jefi gardi dashi dan tauri, shi kansa yajin ƙosan kafi zabi yasha babu maggin kirki a ciki, amma wai tana can tana cin kaza, kai Allah ya isa, yanzu da kuke Auren yaron nan, ai da ɗaki za'amin a gidan wallahi inje in tare nima in ɗan murmurw" "Yanzu dai ki dena cin zarafin ƙosan nan, ki daure ki cigaba da tura abunki" cewar Aminaa. "Ke barni ni takaici baze bari in ƙarasa cin wannan gardin ƙosan ba, 'yar banza Allah yasa duk lokacin da taci kazar taita zawayi, ya zamana ba ita ba cin kazar gaba ɗaya. Haka Yadikko taita soko burutsunta, taita bayyana hassadarta ƙarara akan Amira, ba tare da kunya ko tsoron Allah akan hakan ba. Amira kuwa wanka taje tayi, ta shiraya a cikin riga da skirt da dogon hijjabi. Ta fito domin su tafi kasuwa, suna tafe a hanya suna hira, Anty tace  "Amira, me kike ganin za'a saimiki da sadakin ki ne?" "Bakomai" ta bata amsa. "Kamar yaya bakomai, ki faɗi me kike so, inya kama ayi ciko a saimiki, Abbanki ne yaimin waya yace a tambayeki" "Nifa Anty kome kuka siya yayi shikenan" "Ke a ranki babu wani abu da kikeso?" "Eh, bana son komai ni dama ki riƙe na bar miki" "Tunda tare zamuyi zaman Auren dake ko? Yarinya gara kici Sadakinki, Addini ne ya halarta miki abunki" Amira bata sake cewa komai ba, ta dinga kallon titi da gurare, tana sake ƙarewa garin kallo har  suka kai wani ƙaton shagon saida kayayyaki. Bayan sun isa ne Anty tace "muje duk abunda kike so ki ɗauka, banda alkunya naga wasu lokutan akwaiki da kawaici, An bada isashen kuɗi ayi miki siyayya" Amira tace "to" Suka shiga, sukayi siyayya sosai, suka taho hanya aka bada kayan Amira ɗinki, da wanda Antyn ta siya suka nufi komawa gida. Misalin ƙarfe tara na dare, Ihsan ta gyara gado ta shiga wanka, ta fito sannan Imran ya shigo ɗakin, ya nemi guri ya kwanta yana kallon Ihsan tana shiryawa. Ta kalleshi tace "ya da kallo hakane?" "Au to kar in kalleki? Idan ban kalleki ba wa zan kalla?" "Babu, gara kaita kallona" Yai murmushi yace "yakamata ki tsahirata wannan shafe shafen, kizo ki kwanta haka" "Ka barni in kinatsa a hankali kayi baccinka ban hanaka ba" "Bazan iya bacci ba kya jikina ba" Wani murmushi ta kuma yi masa sannan tace "to shikenan my D, gani nan" Ta saka night gound ɗint, sannan ta nufo gadon tana masa murmushi, tana ƙarasowa ya janyota kan gadon yana murmushi yace "the beautiful lady my eyes ever saw in the earth" "Kaji ka, duk kyawawan matan da suke garin nan?" "Ihsan kawai idanun Imran ke iya hangowa, Ihsan ce kawai macen da Imran ke iya gani a cikin dubabbanin jinsin da ake kiransu da suna Mata" Kalaman Imran suka dinga Ratsa kwanya da jinin jikin Ihsan, wayarsa ce ta fara ringing, yan ɗago wayar yaga My Dad, seda gabansa ya ɗan faɗi yai fatan Allah yasa lafiya. Ya tattara dukkanin nutsuwarsa yace "Abba yana kira, bari in amsa wayar" Ihsan ta jinjina masa kai, ta gyara kwanciyarta a jkinsa. "Salamau Alaikum, Abba barka da dare" "Yawwa barka, kuna lafiya?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah Abba" "Ya wajen aikin naka, ya Ihsan ɗin kuma?" "Komai lafiya ƙalau Abba, ya aiki" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ai ban san da Ihsan ka tafi ba, munyi Magana da Hajiya Nafisa akan kayan ɗakin Amira, tace akwai buƙatar a bar wancan dana zaɓa a sauya da wani, ya danganta da tsarin ɓangaren Amiran, a samo kayan da zasuyi kyau, kasan sha'anin  mata da tsarabe tsarabe, wayarka bata shiga na kira ema inji ko kana gida yacemin ai baka nan daga kai har Ihsan ɗin, ina son jin yaushe zaku dawone? Za suzo su duba ɓangaren Amiran" "Amm....amm Abba da ni cewa nayi, se Allah ya kaimu ƙarshen next month zamu dawo" "No Amira zata tare before then, kuma ina son ka dawo kan lokacin tariyar, saboda su duba abunda zasu duba kana nan" "To Abba, insha Allah za'ayi yadda kace, amma Abba nace meze hana ita Amiran ta zauna a gidana da zan zauna da farko, kowacce ta zauna gidanta daban?" "A'a, ai nan gidanma yalwatacce ne, ze isheku karka raba kan iyalinka, ni anya makuwa kana kira kaji halin da take ciki kokuma kaji lafaiyarta?" "Eh Abba, muna waya da Anty" "Ba kana waya da Anty ba, da Amira ya kamata kayi waya tunda itace matarka, kaji lafiyarta tunda tana da hakki akanka" "To Abba insha Allah, zan kira" "Idan na tuntuɓa naji baka kira ba zan ɓata maka Imran" "Insha Allah hakan ba zata faru ba, zan dinga kiran" "To shikenan, ka gaisarmin da Ihsan ɗin dan Allah" "To Abba zataji insha Allah" Ihsan kuwa tuni ta bar jikin Imran, jin ana masa maganar Amira, da batun Amira zata tare, ta juya masa baya. Imran ya ajiye wayar ya matsa kusa da ita yace  "My dear meyasa kika juyamin baya?" Banza tai dashi kamar ba taji meyake cewa ba. "Ihsan magana fa nake miki" A ɗan hasale tace  "to me kake so ince maka? dan Allah ni ka ƙyaleni " "Yanzu meye abun fushin kuma Ihsan? Ya kike son inyi, Abba ya haɗamin zafi kema ki haɗamin me kikeso inyi in bijire masa?" Kawai Ihsan ta fara kuka, hadda sheshsheƙa. Rungumeta yayi a jikinsa yace  "is Ok, na gane kiyi haƙuri in dai Amira ce ni ba ruwana da ita, ba dai gida bane tazo ta zauna, nike ce kawai mata ta ke nake so Ihsan, ni tsakanina da Amira ido, dan Allah karki ɗaga hankalinki kinji my wife" Yai maganar yana share mata hawaye. "Imran dan Allah ka riƙe Min amana, wallahi bazan iya jure sharing ɗinka da wata ba, ina matuƙar sonka da kishin ka dan Allah karka ci amanata, ban san ya zanyi ba randa na buɗi ido naga kana zaman Aure da Amira ba" "Kwantar da hankalinki, Ni ke kaɗaice tawa, ke kaɗai zuciyar Imran ke so da ƙauna, Auren Amira Auren biyayyane da bin umarni, ke kuma Auren soyaya mukayi dake" yai maganar yana sake hugging ɗinta a jikinsa. Da haka ya lallaɓa Ihsan, kalamansa sukayi tasiri a zuciyarta, harta haƙura ta biye masa. (🙄🙄🙄) Washegari Amira ta shirya, Fadila zata rakata gurin kitso, Anty tace "Yawwa Amira, Abbanki yamin waya Imran zasu dawo very soon insha Allah, ana so ki faɗi kalar kayan da kike so a samiki, koma muje dake ki nuna wanda kike so, se kuma kayan Kitchen duk Abbanki ya turomin kuɗi ki kirashi ki masa godiya, sannan kuɗin kitsonki ma nayiwa Imran magana, shine yakamata ya biya kuɗin, ya turo dubu biyar, shima ki kirashi ki masa godiya" Tura baki Amira tayi tace "Nifa bani da lambarsa" "Eh ni ina da ita ai, kije ku dawo zan baki" Amira bata kuma cewa komai ba, tai gaba abunta. Sukaje saloon, akai mata kitson attachment ɗinta kamar Yadda ta saba, tai ras da ita sannan suka dawo gida. Taje ta tarar Anty tayi baƙuwa, an kawo mata wasu kaya, bata damu da ta san komeye ba suka gaisa da baƙuwar Amira tai wucewarta. Bayan tafiyar matar Anty ta kira Amira ɗakinta, tace  "baki nunamin kitson ba" Amira ta cire hular kanta, kitsone ƙanana na attachment yayi matuƙar yi mata kyau. Anty tace "masha Allah, kitso yayi kyau sosai, i wish mijinki yazo yaga kitson nan, amma Amira kin san ba kyau kitson ƙari ko? Gashi kema kina da gashi kiyi ƙoƙari ki dena" Amira ba tace Komai ba se sunkuyar da kai da tayi, Anty ta ɗakko wasu manyan robobi se ƙamshi suke ta ajiyewa Amira a gabanta tace  "ga wannan kayan sabulai ne nasa aka haɗo miki, ga na wanka nan dana mayukan shafawa, ga turarukan wanka nan dana shafawa, dan Allah Amira karki wasa, ki kula kiyi amfani dasu yadda yakamata, na kashe kuɗi sosai akan kayan nan, sonake kiyi tsaf dake kafin ki tare in gyaraki Sosai, dama gashi naga kema 'yar gayu ce, kayanki gobe in Allah ya kaimu za'a karɓosu daga gurin tela, ki dage da kayan gyaran jikin nan sosai kinji Amira" "Insha Allah zanyi Anty, nagode Sosai Allah yasaka da Alkhairi" Ta ɗebi kayan nan ta tafi dasu ɗakinta, yanayin robobin kawai sun isa kasan an kashe kuɗi sosai akan kayan nan ba kaɗan ba, daga sabulan mayukan zuwa kayan turaren, Banda kayan mayukan gyaran jiki da suka siyo a kasuwa. Hatta Abincin da Amira take ci seda Anty ta daidaita mata shi, ganye yafi yawa a cikin Abincin da take ci, da kayan fruit mussaman data lura Amira ma'abociyar kayan marmari ce. "Minal, wai kinji babanku ko? Wai next month Yarinyar nan zata tare a gidan Imran wai lallai lallai su dawo" Minal tace "Wai dan Allah dama dagaske Abba yake akan Auren nan?" "Gashi kuwa kina gani, ai tunda aka ɗaura Auren an gama, dole in san abunyi akan lamarin nan" "Nifa Mummy tsorona Allah, tsororna kar taje idan baya nan ta cutar da Anty Ihsan, dan nika ɗai nasan dukan da naci a hannunta, ƙarfi ne da ita kamar gardi, tsaf zataiwa Anty Ihsan dukan tsiya, dan tafi ta girma" "Aikuwa wallahi bazan laminci ta daki 'yar mutane ba, duk ran da ta daketa seta koka inda ta fito kuma yanzunma ina nan akan bakana, sena kashe wannan Auren tun kan Imran ya fara tunanin wani abu a kanta, duk da ya tabattar min da shi babu son yarinyar nan a tare da shi, a yanzu na yadda amma namijine ba tabbas garesu ba, suna dawowa zanyiwa tufkar hanci, zanje gidan nasa da kaina" "Aikam dai gara ki ɗau matakibda wuri Ammi, dan idan kika bari aka cutarwa da Mummy 'yarta zata ga ba'ai mata adalci ba" "Ai bama zan fara bari hakan ta faru ba" Amira ta dage da gyaran jiki kamar yadda Anty ta buƙata a gurinta, nan da nan fatar Amira ta fara sheƙi, dama tana da haske sedai ba fara ce ba, irin chocolate ɗin nan ce, tai ras da ita kai baka ce wani abu na damunta ba, an karɓo mata ɗinkunan ta, ta shiga wannan ta fita wancan tai ƙalau da ita, idan akace maka Amira ce ma baka yadda ba, saboda wata nustuwa da ta ƙara yi, duk inda ta gifta se ƙamshi kawai takeyi. Yanzu ma Amira ce ta fito, ta soka wani uban ɗaurin ɗan kwali a gaban goshinta, dayake megidan ma duk a Abuja suke aiki da Abban Imran, dan haka takan sake tai shigar da take so, da yake Anty ba tada ɗa namiji. Anty tana falo tana yiwa wata mata Nutritional counselling, da illar yawan cin Abinci mai da yaji da mata keyi. Anty Nafisa na matuƙar burge Amira, mussaman yadda patient ɗinta kan biyota har gida, gashi ba hantara ba tsangwama, ta iya tarairayar su da jansu a jiki, tai musu bayanin abubuwan da basu gane ba, gashi ta san kan zaman rayuwar duniya, komai nata sannu a hankali take binsa. Amira taje ta zauna tana sauraren yadda Antyn take bayani, wani abun in Anty ta faɗa se kunya ta kamata, wani kuma tayi dariya. Haka Anty ta gama ta sallami matar sannan ta kalli Amira tace  "Uwargida sarautar Mata, irin wannan kyau haka" Amira tai murmushi tace "Antyna kenan, nikam ina son Aikin Asibiti yana matukar burgeni sosai" "Dagaske kina so Amira?". "Dagaske Anty" "Kai amma naji daɗi sosai, kin san aikin Asibiti yana da mahimmanci musamman ga 'ya mace, bari Abbanki ya dawo zamuyi magana dashi insha Allah, naji daɗin hakan, ɗazu Imran ya kira amma kina bacci, bari a kira shi yanzu" "A'a Anty base kin kirashi ba, idan kin kira ma ban san me zance masa ba" Haɗe rai Anty tayi tace "ƙaniyarki zaki ce masa, nifa bana son shirme Amira, ki kiyayeni fa akan Imran, idan kuma zuba masa ido zakiyi ki zama 'yar kallo in kin tare shikenan ni ba ruwana" Anty ta ƙarasa maganar tana kiran lambar Imran, ta miƙawa Amira wayar, Amira ta karɓa tare da sake tura ɗaurinta gaban goshi ta harɗe ƙafa tana tura baki" "Hello wake magana?" Taji muryar Ihsan ta daki dodon kunnuwanta. Haushi ne ya kama Amira, Amma tace "Amira ke magana, mijinmu yana kusa ne? Ohh Sorry bamu gaisa ba kina lafiya, ya amarci?" Anty ta ɗagawa Amira babban yatsanta alamar jinjina 👍. Tsaki Ihsan tayi tace "ke ƙaramar Karuwa ki kiyayeni ki kiyayi mijina, mijinku keda wa? 'yar alfarma har kika da bakin cewa ina mijinku, mijinku keda wa? Mijin Ihsan dai kuma karki sake kiran wayarsa na gayamiki" Amira a zaune take ga sanyin AC, amma nan da nan ta fara gumi, ta miƙe tsaye, Anty taji abunda Ihsan ta faɗa, dan haka ta shiga girgizawa Amira kai. Ga mamakinta Seji tayi Amira tace "Allah ya huci zuciyarki ƙanwata kuma Yayata, sanin mijin waye tsakanin nida ke wannan lokacine ze banbanece mana, ki bari in tare, dama ba wani abu bane ba, ya kira ɗazu ina bacci ne, shine Anty ta kira shi zan masa godiya, naga saƙo ina godiya Allah ya ƙara Arziki" Da sauri Ihsan tace "Saƙon menene?" "Sirri ne tsakanin mata da miji meye naki na sekinji? Ki miƙamin wannan saƙon kawai shiya san godiyar ta meye" Daga nan ta kashe wayar, tazo ta miƙawa Anty ran nan nata a ɓace. "Anty tace Amira nace miki kishi na damunki kin musa min, shikenan dai na jinjinawa dauriyarki da ɓoye fushi, ki ƙara haƙuri nasan zaki fuskanci ƙalubale a gidansa, amma kiyi haƙuri ki daure, naji maganganun da ta gaya miki, ki rabu da ita ko zata gayamiki karki kulata wataran se labari kinji, amma fa ba ziga ba kin burgeni da amsar da kika bata"  Anty ta ƙarasa maganar tanawa Amira murmushi. Amira kam ɗakinta ta koma, ta garƙame ƙofa, tace "kan uba ni wannan daskararriyar Yarinyar zata cewa Karuwa 'yar alfarma, ashe za'ai ƙaramin yaƙi duk ranar da muka haɗu ido da ido tace min 'yar alfarma, nafi ƙarfin a Aureni dan amin Alfarma, zata ga Karuwa ganin idonta, da na aje karuwancin a gefe, amma naga bazamu daidaita da su ba, se naje gidan nan da karuwancina, zan nuna mata hatsarin da Karuwa ke dashi, na zata kira da 'yar alfarma da Amira kuke zancen" Nan Amira ta cigaba da masifa ita kaɗai a ɗaki, dan ranta yayi matukar ɓaci. Ihsan kuwa zubawa wayar Imran ido tayi, tana jujjuya maganganun Amira, Imran ya fito daga wanka ɗaure da towel yana goge ruwan wankan jikinsa yace  "sweetheart, zoki shafa min mai tunda ma fito daga wankan" Gani yai Ihsan tana binsa da kallon tuhuma, ga wayarsa a hannunta ya kalleta yace "lafiya kuwa?" "Meye haɗinka da Amira har take kiran wayar ka?" Ƙarasowa yayi ya karɓi wayar yace  "kamar yaya, ni bani da lambarta ƙila a wajen Anty Nafisa ta karɓa" "Amma har take gayamin ince maka taga saƙo ta gode, Imran anya ba yaudarata kake ba?" Shiru yai yana kallon Ihsan, shi dai yasan babu wani abu daya haɗa shi da Amira, Anty ce tace ya turo da kuɗi Amira tai gyaran kai, shima dan yana kunyar Anty ne ya tura, amma yanzu Ihsan zata ɗaga masa hankali" Share Ihsan yayi yaje ya fara ƙoƙarin saka riga, dan be san me ze gayawa Ihsan kuma ta yadda dashi ba. "Au banza ma zakayi min?" 'to me zance miki ne? Ban san me zan gayamiki ki yadda dani ba, tunda kin yadda da abunda ta gayamiki shikenan, seki tayi ai" Yana gama maganar yai waje abunsa, Ihsan tabi bayansa da kallo, tana jin kamar zuciyarta ta tsaga ƙirjinta ta fito. Tofa!!! Domin gyara, Sharhi ko shawara http://wa.me/+2347063065680 [1/27, 6:30 PM] Ayshercool:        🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                      29_30 Bayan fitar Imran, Ihsan ta rasa abunda yake mata daɗi, gaba ɗaya ta rasa meke mata daɗi, shigowar Amira rayuwarsu babbar barazana ce ga farin cikinta, gaba ɗaya taji ta tsani Amira wani mugun haushinta take ji. Ɓangaren Amira ma tunani kawai take akan irin zaman da zatayi a gidan Imran, dan ta ƙudirce a ranta ba zata juri wulaƙanci ba ko kaɗan. Ihsan seda ta wuni cir Imran be dawo gida ba, dan se bayan tara n dare sannan ya dawo Gidan, da ya dawo ɗin ma be bi ta kanta ba, ya nemi guri yai kwanciyar sa ya bi lafiyar gado abunsa. Mamaki ya cika Ihsan, ita da akaiwa Laifi amma shine yake fushi, yai watsi da Ita, gani tayi Imran ba shi da niyyar saurararta. Har wayewar gari ya shirya yai ficewar sa gurin aiki, koda wasa bata taɓa kawo akwai abunda ze kawo mata tangarɗa a rayuwar auren da suka tsara yi ita da Imran ba, se gashi katsam Amira ta kutso rayuwarsu. Ihsan gaba daya ta shiga damuwa da tunanin idan Amira ta shigo gidan wani irin zama zasuyi, dan yau da gobe se Allah, Amira ta cika macen da zata wuce a kalla, tai shiru tana tunanin ina mafita. Se magariba sannan Imran ya dawo, kuma ba wannan ne lokacin da ya saba dawowa ba, ta tashi ta karɓi ƙatuwar jakarsa ta sojoji, be kulata ba ya wuce ɗaki abunsa, yai wanka ya fita sallar magariba, be dawo ba se isha'i, bayan ya dawo yace "My a kawo Abinci ne?" "No karki damu naci Abinci" "Haba my D ban cancanci haka daga gareka ba, kana nufin kar inyi kishi akanka kenan? Wani kalar zama zamuyi kuma ranar da ta tare? Akwai yiwuwar ka juyamin baya kenan?" "Ihsan ba haka bane, na rasa ya ki ke son inyi ne, na miki bayani amma kin kasa ganewa, kishi yana rufe miki ido da yawa, kin kasa fahimta ta gaba ɗaya, ni ba wani abu tsakani na da Yarinyar nan, na gaya miki komai da yadda aka yi na Aure ta, amma kin kasa fahimta, ta yaya zata gaya miki magana ki yadda, baki san halin yarinyar nan bane, idan har ki kace zaki biye abun da zata dinga faɗa, to tabbas za mu dinga samun saɓani, ni ba burina bane in dinga ɓata miki rai ba, ina sonki Ihsan meze sa in muzguna miki? Amma kishi yana rufe miki ido da yawa Why Ihsan?" "Kayi haƙuri Please, ba zan sake ba insha Allah" "Yawwa ko ke fa my deari, I miss you fa" Yai maganar yana rungumeta, tare da faɗaɗa murmushinsa, da haka suka shirya suka sake jefa babin Amira a kwandon shara. Amira kam ita kanta ta san fatar jikinta tayi kyau, kamar bata shiga rana, ta ƙara ƙiba hutawa kawai take, kusan kullum tana tare da Fadila, tana koyon girke girken 'yan gayu wanda bata iya ba, sam Amira ba ta da ƙyuya, Akwai gyara bata son ƙazanta kwata kwata. Wasa wasa seda Imran ya shafe watanni biyu shi da Ihsan a Lagos, Abba ya kira zeyi faɗa akan rashin dawowarsa, Anty tace  "ita tace bakomai su bari sa dawo daga baya saboda wasu dalilai" Nan kuwa tayi hakan ne dan tabattar da Amira ta ɗau gyara yadda ya kamata, kuma duk iya nazari da binciken da Anty tayi akan Amira ta kasa tabattar da abinda ake zargin Amira na karuwanci gaske ne ko ƙarya ne, ita dai a barta da shirme wasu lokutan da taurin kai, amma sam ba ta ga wani abun ashsha ko aibu a tare da Amira ba. Tunda Imran yai zancen za su dawo Kaduna Ihsan ta shiga damuwa da faɗuwar gaba, saboda yadda ta tsani Amira ko zancenta ba ta son ayi, se ta ji gaba ɗaya hankalinta ya tashi. Kwanansu Biyu da dawowa Kaduna, amma ba taji anyi zancen tariyar Amira ba, ta cewa Imran tana son Zuwa gida za ta je ta gaida Mummy, da ga nan kuma za ta je ta gaida Ammi, Imran da kan shi ya kaita gidan su, ya shiga su ka gaisa da Mummyn Ihsan, sannan yace ta bari da daddare ze zo ya ɗauke ta suje gidansu ta gaida Ammi. Ihsan tayi murna sosai zuwanta gida ta ga Mummynta, saboda tayi missing ɗinta sosai. "Ihsan kinyi ƙalau abunki, lallai Ikko ta karɓe ki" Ihsan tai murmushi tace "Mummy kenan, ni nifi missing ɗinki akan Komai fa" "Wane missing ɗina, bayn kin bi mijinki Lagos ba labari, se da ki ka je can da kwana biyu sannan na sani" Jiki a sanyaye Ihsan tace "Mummy tafiyar ce ta zo min babu shiri fa" "Kamar ya ya babu shiri, nima nayi mamakin wannan tafiya taki cikin gaggawa" "Mummy zama na da Imran a tsorace na ke, yanzu nake sake gane wasu da ga halayen sa wanda ban sani ba a baya, ban taɓa sanin yana da fushi haka ba, idan nai masa laifi se yayi watsi dani gaba ɗaya ya shiga yin ratuwarsa shi kaɗai" Mummy tace "to ke da ga Aurenku me ze sa harki fara masa abunda za kuyi faɗa?" "Mummy kin manta ba ni kaɗai bace ?" "To se me dan bake kaɗai bace? Meye ruwanki da ita?" "Hmm, Mummy wallahi Karuwa bala'i ce,  Imran ya tabattarmin da ni ka ɗai yake so, amma Yarinyar nan tana nema ta zama bara ga soyaya ta da ma Aurena da Imran" "Ke fito kimin bayani dalla dalla mana, yi min Magana kai tsaye, naga dai bata tare ba haryanzu" "Mummy, ni da Imran bama taɓa samun matsala se idan anyi zancen yarinyar nan, ni ba na iya ɓoye fushi na da kishi, shi kuma da nayi fushi akan ta seyai banza dani wai ya nake son yayi, kuma mahaifinsa ne yake matsawa akan al'amuran ta, shi ba sonta yake ba ba kula ta yake ba, amma idan har mahaifinsa ya cigaba da tura mas ita akwai matsala Mummy" Mummy ta ja ajiyar zuciya tace "kwantar da hankalinki, ai ba a banza na yadda aka kai ki ɗakin nasa duk da wannan cin amanar da akayi mana ba, idan ubans yana tura masa ita, ni kuma zanwa tufkar hanci ta ɓangaren mahaifiyarsa, ki kwanta kiyi baccinki a ɗakin Aurenki, ba zan zuba ido wani Abu mara daɗi ya faru dake saboda wani Babansa ba, ni na san abunyi" Ihsam ta rungume Mummynta tana "Yawwa Mummy na, shiaysa nake sonki Sosai, amma da hankalina duk a tashe yake wallahi" "Ki kwantar da hankalinki, miƙomin wayata, tun yanzu zan mata magana, yadda in kunje can ɗin zata san me za tayi" Cikin murna Ihsan ta miƙa mata wayarta, ta karɓa ta kira Ammi, wayar tana fara ringing Ammi ta ɗaga tai sallama tare da faɗin "Hajiyata manyan ƙasa, ya gida ya business?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya aiki ya Meenal, kwana biyu ba ta zomin ba" "Tana lafiya, harkar school ce ta sako ta  a gaba, nace ba dan ba dan ba ai se a fasa school ɗin nan, duk tabi ta ranar min da ita, dama gata ba jiki ba gaba ɗaya ya zabge saboda harkar makaranta ba ta da lokacin kanta".. "Allah sarki, ai ba'a fasa makaranta ba, se haƙuri, Allah ya bada sa'a ace ina gaisheta" "Za ta ji insh Allah" Mummy tace  "kin sam su Ihsan sun dawo, gata ma ta zo min" "Eh na sani ya gayamin, dan shi ya zo ma jiya, ya cemin anjima insha Allah ze suzo mu gaisa, dan son kai shine ta fara zuwa gurinki ko?" Mummy tai murmushi tace "to wannan kuma i taku keda 'ya'yan naki, sedai ta zo min da batun wai wannan Yarinyar zata tare ko?" "Hmm kedai bari, Yarinyar nan yadda ki ka san a kaina zata tare wallahi, nayi nayi da babansa ya yadda a raba musu gida amma yaƙi, kwata kwata na rasa abunyi wallahi, baban su na da haƙuri sedai akwai taurin kai" "To ni dma ba wani abu baane ba, dama cewa zanyi dan Allah idan sunzo anjima a ƙara ja masa kunne, kar azo ana samun matsala, kin ga dai na farko yarinyar nan tayi yawon ta zubar, kuma Hajiya Nafisa ita ta yiwa yarinyar nan test, zasu iya haɗa baki da ita ace yarinyar nan lafiyarta ƙalau, alhalin baza'a rasa wani abun a tare da ita ba,  a dai ja masa kunne ya kula, kar a samu matsala" "Ki kwantar da hankalinki, na daɗw da yi masa wannan takarar, babu abunda ze faru insha Allah, dan nima ban shirya amsar jika a gurin karuwa ba, kuma shima ya tabattarmin da babu abunda ze faru, na zubawa babansa idone dan in bi komai a hankali, amma zanyi duk me yiwuwa raba auren nan zanyi ba inda zashi" "A' Hajiya Jamila, kar ace mun haɗa kai an kashe masa Aure a zagemu fa" "To base aita zagi ba, aimu mafitar yaranmu kawai kuke nema, karki damu ki kwantar da hankalinki, zan sake jan kunnensa insha Allah" "To shikenan Nagode sosai, se sunzo ɗin". "To shikenan Allah ya kawo su Lafiya" Mummy na katsae kiran, Ihsan tace "haba Mummy, naji ana za'a kashe Aurensa da ita kuma kina cewa kar ace kun kashe Aure?". "Au so kike in nuna ƙarara ga abunda nake so? Ke baki san rayuwar duniya'yar siyasa bace, ai ina sane na faɗi hakan" "To shikenan, ni Allah yasa kar ta tare ma a kashe Auren" "Ameen, nima da na fi son hakan ai" Haka Ihsan suka cigaba da hirarsu da Mummyn ta, suna tsara irin rayuwa da kuma zaman da Ihsan za tayi da Amira ko da ta tare ɗin. Se bayan sallar magariba sannan Imran yaje ya ɗakko Ihsan suka tafi gidansu Mummy ta bata magunguna da sauran abubuwan gyara. suna zuwa gidan su Imran Minal ta rungume Ihsan tana murna tace "Anty Ihsan shine kika fara zuwa gurin Mummy kika wuni se yanzu zaki zo mana ko? Ni na mayi fushi ki koma kawai " Ihsan tai murmushi tace "lallai, ni banyi fushi ba seke, sau ɗaya fa kika zo gidana, shima Ammi ki ka rako, ba dan haka ba ba zan ganki ba" "Kai Anty Ihsan kwanan ki nawa a gidan ku ka tafi lagos, kuma shi Yaya Imran fa yana faɗar baya son a dinga zuwar masa gida idan yai Aure" "Haba My, shikenan mu ba za'a zo inda muke ba" Hararsu Imran yayi yace "cigaba da biye mata tana miki shirme" Ammi ce ta fito daga ɗaki tana faɗin "mutanen Lagos" Ihsan ta zube ƙasa tace  "Ammi ina wuni" "Lafiya ƙalau Ihsan, ya gida ya kika baro Mummyn" "Lafiya ƙalau Ammi" Tace "Masha Allah, Imran ya aikin"? "Aiki Alhamdilillah Ammi, ya gidan" "Gida gamu a cikinsa, Minal kawo musu Abinci su ci a nan ko su tafi da shi, dan da ku mu ka saka sanwa" Imran yace "ai idan ma ba'a sa ka damu ba a ɗora wata, ina Abba ko be dawo ba?" "Yana gurin aiki, se Allah ya kaimu sati me zuwa ze dawo" Nan suka dinga hira, Minal ta kawo musu Abinci, Imran ya zage yana ci amma Kunya ta hana Ihsan cin abincin, duk da kuwa ta saba da gidan sosai, amma haka nan ta dinga jin nauyin cin abincin. Ammi ta shiga ɗaki yin sallar isha'i, Imran ya kalli Minal yace "ba mu guri zan bawa mata ta Abinci" Minal miƙewa tai tana ɓoye dariya a ranta tace "Lallai ka ga masoya" Tana tafiya ya janyo Ihsan jikinsa yace "kin wani ƙi cin abinci, Gara tun wuri ki saki jiki kici Abincin nan, oyo open Your mouth" Haka Ihsan ta lafe a jikinsa yana bata Abinci, tana amshewa, Ammi ce ta fito daga ɗaki Da hanzari Ihsan ta bar jikin Imran cike da kunya, Ammi tai murmushi tace "Ihsan kenan" Imran kam basarwa yayi kamar ba wani abu da ya faru, Ihsan kam kamar ƙasa ta tsage ta shige dan Kunya. Ammi ta zauna sannan tace "Imran naji daɗin yadda na fuskanci kuna zaman lafiya, nasan lallai a wannan dawowar ta ku Mahaifinka ze ce se waccan Yarinyar ta tare, to ina son in sake ma ka jan kunne ne, kar ka sake zuwan Yarinyar nan ya zama barazana ko silar rushewar farincikin da nake gani a Tare da ku, kasan irin zaman da za kuyi, ba kai ba shiga sabgar yarinyar nan, kuma na ga a tsaye take idanunta ba bu alamar mutunci, kar ka kuksakura ka bada ƙofar da za ta saka Ta raina maka mata, tsakanin ka da ita ido, tun da ubanka ya dage ka Aureta ka Aireta ga gida nan taje ta zauna, ni ba zan lamunci in haɗa zuriyata da Karuwa ba, ka kula kuyi hankali da ita. Ke kuma Ihsan, karki kuskura ki biye mata, dan ba cikakken hankali ne da ita ba, zata iya yi miki illa idan kika ce zaki biye mata, ba ruwanki da ita, ki bi mijinki ku zauna lafiya duk yadda zanyi zanyi inga Auren nan beje ko ina ba, goyon bayan ku kawai nake buƙata nan kusa zan mitstsike Auren nan" Da ƙarfi ƙirjin Imran ya buga, kawai se ya saki Amira, da wani idon ze kalli Abba idan ya sake ta? Ammi tace "Naga kayi shiru, ko ka nada Magana ne?" "A'a kawai ina zancen zuci ne, ba damuwa Ammi insha Allah zan kiyaye abunda kika faɗa" "Yawwa Allah yayi muku Albarka, ina ƙara gaya muku baku ba yarinyar nan ko shiga shirginta, kuyi rayuwarku daban tayi tata" Haka Ammi taita jaddada musu, suka tashi tafiya ta kawo kyautuaka ta bawa Ihsan. Ko da suka koma gida Ihsan ta riga Imran yin gaba, Abba ya kira wayar Imran, Imran ya ɗaga suka gaisa da Abba. Abba yace "Imran naji kun koma ko?" "Eh Abba yau kwananmu uku da dawowa" "Yawwa to dama bugowa nayi in roƙi alfarma, dan nasan idan ban nema ba baza'ayi min ba, ina so aje a duba 'uar marainiyata, kaji ko da abunda suke buƙata saboda tariyarta" "To Abba insha Allah, kuma dama nayi niyyar gobe in Allah ya kaimu zanje gidan Antyn insha Allah" "Yawwa yaron Kirki, haka nake son ji, ba danni ba kuma ba dan Amira ko halinta ba, a daure a taimaka a kulamin da marainiyar nan dan Allah Imran, ka ta ya ni wanke laifin da na aikata a baya, ka riƙe Yarinyar nan da mutunci, ka manta da irin nata laifukan ita ma dan Allah" Gaba ɗaya jikin Imran yayi sanyi yace "Insha Allah Abba, zanyi ƙoƙarin kula da ita" "Yawwa Imran Allah yayi maka albarka" "Ameen Abba nagode". Shiru Imran yai yana jujjuya maganganun Ammi da na Abba, ƙarshe dai ya wuce cikin gidan shima. Da safe Amira ta kira Anty Fa'iza video Call, tana nuna mata ɗakin da take rayuwa a gidan Anty, suna ta hira suna dariya, sega Anty tayi sallama, Amira tayi sallama da Fa'iza tace "Anty ina kwana?" "Bazan amsa ba bayan baki fito mun gaisa ba har gashi zan fita aiki" "Yi haƙuri Anty" "To na haƙura, sarkin bada haƙuri, daɗina dake kenan, in ance kinyi laifi ba jayayya se bada haƙuri, ina ga yau mijinki ze zo, nayi magana da Abbanki, sedai ban san lokacin da ze zo ba, sonake ku shiga Kitchen keda Fadila ku yi masa Abinci, in case ze zo ina gurin aiki so nake ki kashe kala ki ɗau wanka dan Allah, ban da tura masa baki banda rashin kunya, kiyi Kwalliya ki shafa turarukan ki, yadda seya kasa tafiya" Aikuwa zumɓura bakin Amira tayi tace "Anty ban da kunya kenan?" "A'a kina da kunya mana, Amma shi kina masa rashin kunya wasu lokutan shiyasa bakwa jituwa, ki tashi ku shiga Kitchen tare kiyi masa abinci" "Taɓ shine ze ci Abincin da na girka, ni da ba sona yake ba, Anty kawa ki bari in yazo a bashi Ruwa da lemo" "Musu zaki dani kenan?" "A'a waceni musu da ke Anty, an gama bari in wanka inje inyi abunda kika ce" "Yawwa Amirana, shiyasa nake sonki ai, akwai biyayya, irin wannan biyayyar indai ita za'ayiwa Imran, ba yadda zeyi yace baya son 'yata, son kowa ƙin wanda ya rasa" "Anya Anty Imran ze soni? Jikina na bani zan sha wahala a gidansa, Ihsan yake so" "A'a Amira, meye na wani karaya, kina mace ta na mace, Imran ɗin me, I beg ki shirya karɓarsa, very soon zaki tare insha Allah, weekend zamuje ganin gidan nan da 2weeks insha Allah zaki tare a ɗakinki" Murmushi kawai Amira tayi tace  "A dawo lafiya Anty" "Yawwa 'yar Anty, Allah yasa" Bayan fitar Anty Amira ta fito, ta karya suka shiga Kitchen tare da Fadila, snacks ne sukayi se fruit salat suka saka a fridge, da ga nan kuka Amira ta ɗora girkin rana. Sedai har Antyn ta dawo Imran be zo ba, Anty tace "Amira Imran ɗin ya zo kuwa?" "A'a Anty be zo ba, ina ga fa baze zo ba tun da la'asar tayi" "No Babansa ne yacemin zezo, insha Allah ze zo, idan kuwa be zo ba a wannan karon to tabbas sena gayawa Babanku" Ita dai Amira ba tace komai ba, ta koma ɗakinta ta ɗakko rani tayi wa Yatsunta ado da jan rani. Ta fito daga ɗakinta zata buɗe ƙofar da zata shigar da ita falon taji muryar Imran, komawa tayi ciki ta sake shafa turaruka, sannan ta fito saye da riga da skirt na Atamfa, ta ɗora ɗankwalin kawai a kanta bata ɗaura ba ta fito, tai pretending kamar ba ta san da zuwansa ba. Anty tace  "'yar halak, ai gata nan ma ina shirin a kiraki, gashi yazo" Waiwaya yayi inda Amira ke tsaye, ya ga tayi wani ƙalau da ita, duk da dare ne amma haka be hanashi ganin kyan da ta ƙarayi ba tayi ƙiba abunta, kayan jikinta tamkar a jikinta aka ɗinka su, sun zauna cif a jikina ta bada wani shape me ɗaukar hankali, tahowa tayi cikin falon fuskarta ba walwala ta kalleshi tace "Sannu da zuwa" Shiru yayi be amsa mata ba, Aikuwa haushi ya kamata ta nemi guri kusada Anty tai zamanta tana kallo. Imran da Anty suka cigaba da hirar lokacin da zataje taga gidan, aje ayiwa Amira jeren kayanta. Anty tace "tashi ki kai masa Abincin ɗakin varrender" Amira ba tace Komai ba ta miƙe ta tafi Kitchen, ta na shiga Kitchen ta fara haɗa tray sega Fadila ta shigo da hoda da turare a hannun ta tace  "malama tsaya ki sake kintsa fuskarki, ni ya ganki fes ya fiye min Wannan Abincin da kika girka masa" "Wai meyasa ku ka damu da shi hakane?" "Wai muka damu da shi, muka damu da ke dai ba shi ba" Ta shafawa Amira powder, ta sake fesheta da turare, dama bakinta akwai jambaki Tun rana da ta saka, aka gyara ɗaurin ɗan kwalin nan, se Amira ta ƙara kyau, kamar wata matar hamshaƙin attajiri. Ta haɗo tray da kayan Abinci ta fito, sedai daga Antyn har Imran ba kowa a falon, Fadila tace "kai masa ɗakin, nasan yana can, banda tsiwa dan Allah" Amira ta kwaɓe baki irin taji ɗin nan amma ba lallai ba, ta shiga ɗakin da Imran yake, yana zaune yana daddana wayarsa, ya ɗago ya kalleta ya basar, ta zo ta ajiye masa tray ɗin akan Centre table, ta janyo table ɗin gabansa, sannan ta zauna a kujerar kusa da tasa. Sun kai mintuna goma, ba wanda ya kula Wani, Can Imran da turarenta ya hana shi sukuni yai ta maza yace  "baki iya gaisuwa ba ko?" "To ba na maka magana ɗazu ka ƙi kulani ba, shiyasa naga kar yanzun ma in gaishe ka kaƙi kulani" tayi maganar a ɗan shagwaɓe. Imran yace "dakyau" "To ai dai ba laifi nayi ba, amma ina wuni" Kamar yadda tai tasammanni shirun yai mata, ya kuma maida hankalinsa kan wayarsa. Ƙasa tayi da murya tace  "ba zaka kulani ba ko?" Nan ma be amsa mata ba. Wayarsa ce ta fara ringing taga an rubuta Lovely. Ko ba'a gaya mata ba tasan Ihsan ce, aikuwa ran Amira ya ɓaci ya ɗaga wayar yasa a kunnensa yace  "Hello My Wife" Kan ya kuma cewa wani abu Amira ta fizge wayar da ga kunnensa tana huci, ta katse kiran. A fusace ya kalleta yace "ke meye haka? Rashin hankalin zaki min kenan?" "Eh rashin hankalin zan maka, ai naga nima matarka ce, ka ɗauketa kun tafi lagos kuyi wata biyu ina nan ko ta kaina baka bi, kuma kun dawo ka zo tun ɗazu nake maka magana amma ka shareni, ita tana kiran wayarka shine ka ɗaga" "Zaki bani wayata ko sena tattaka ki a gurin nan?" Jiki a sanyaye ta bashi wayar, ya kalleta yace  "karki taɓa tunanin haɗa kanki da Ihsan, Ihsan mata tace kuma mace me kima da na aura dan ina sonta, ke kuwa fa umarnin Abba yasa na Aureki dan haka karki kuskura ki sake haɗa kanki da mata ta dan ba sa'arki bace, ba kuma matsayin ku ɗaya a zuciya ta ba" Abunka dame Arhar hawaye, tuni ta lumshe idonta, wasu hawaye masu ɗumi suka biyo kyakykyawar fuskarta, ta ɗago fararen idanunta, tana masa wani irin duba tai murmushi tare da taune gefen leɓenta ta kamo hannun Imran ɗaya cikin nata tace  "Dan Allah da me Ihsan tafi ni?, Me nayi naka kake min Wannan ƙiyayar hakane?duk fitinar fa da ka ga ina yi nima ina da msu sona, ban rasa masoya ba, Amma meyasa kake son yi min wulaƙanci ne?" Zare hannunsa yai daga nata, sakamakon wani abu da yaji ya ziyarci zuciyar sa ba shiri, ya kalleta yace "Ihsan nutsatstiya ce kamila, ke kuma.... "Ni kuma Karuwa ce ballagaza ko?" Tai saurin ƙarasa masa maganar. "Nasan abunda zaka faɗa kenan, amma ita Rahama ta Allah ce, se kaga ya shiryeni ya yafe min" ta ƙarasa maganar tana share hawaye, ta share hawayenta tsaf sannan tace "mijinmu me zan zuba maka a cikin Abincin ka ci" "Bana ci, ki kwashe kayanki" Amira ta watsa masa wani kallo tace "Yadda ka gani, da kaci da karka kaci wannan matsalar ka ce, tunda ba abunda yai saura zan iya tafiya?" "Ni kike gayawa haka?" "Ai ba wani abun nace ba, kawai cewa nai zan iya tafiya?" "Tsaya mu fita tare, bana son tamabayoyin Anty" Amira tai gaba, Imran yana binta a baya, sedai ya ƙurawa bayanta ido, yadda take tafiyar kamar tana sane, ta fito Falo. Anty tace "Ba dai har zaka tafi ba Imran?" "Eh Anty tafiya zanyi" Amira tace  "Anty kinga yaƙi cin Abincin ko, dama seda na gaya miki kika sa na wuni ina faman yi masa girki amma ya ƙi ci" "Haba Imran, tun Safe take aikin karɓarka amma ka ƙi cin Abincin, jeki ɗakko ki kawo masa nan, ba a haka Imran, wata nawa bakwa tare duk da tana matarka ai seka ci, ba'a gwasale mace kaji ko" Lallai Amira ta iya tsiya, yanzu tace kar Allah yasa yaci, amma ta fito ta haɗa shi da Anty. Haka ta ɗakko Abincin ta dawo da shi Falo, seda yaci tukuna saboda yana kunyar Anty sosai. Se kusan tara na dare sannan ya tashi ze tafi, su kai sallama Amira ta tafi raka shi, sedai kan ya ƙarasa inda motar take ta rigashi ƙarasawa, ta jingina a inda zesa mukulli ya buɗe ƙofar ta kalle shi tace  "dan Allah, idan na tare a gidanka ka zama me min adalci, nafi kowa sauƙin kai, sedai ban yadda in cutar da kowa ba nima kar a cuceni, idan har zakayi adalci a tsakaninmu kuma matarka ta kiyayi gayan magana mara daɗi ka sai zaman lafiya a gidanka, nafi kowa farinciki da son zaman lafiya, saɓanin haka kuwa, za'aga ba dai-dai ba, sannan ka gayawa Ihsan da ni take zancen, naji tana cewa anmin alfarma an Aureni, ni wannan be dameni ba, amma zata gane ta bi mijina lagos sunyi wata biyu nikuma an shanyani a nan, zaku biya laifin da ku kaimin" Mamaki ne ma ya kama Imran, Amira sam ba kunya ba ta ido, wai anbi mijinta Lagos, kenan itama kishin za tayi a kansa? "Bani guri zan tafi gida kar in dare a hanya, na bar ta a gida ita kaɗai" Ƙara lafewa tayi a jikin motar tana kallonsa, tace  "ni da ka bari a nan watanni biyu ban ganka ba baka damu ba ko? Ihsan itace mace ko?" Yau Imran yake ganin duniyanci a gurin Amira, matar da ta dinga kuka tana an Aura mata mugu ita seya saketa, amma ita ce take wannan abun" Gani yai wankin hula ze kaishi dare, dan haka ya sa hannu ze janyeta daga jikin motar, dan duk jikinsa ya mutu, ba shi da energy ɗin daze cigaba da mata shouting, dan idan yayi ma ko a jikinta. Sedai wani shocking yaji daya riƙota, wanda hakan yasa shi saurin sakinta yace  "dan Allah ki matsa ki bani Guri zan tafi" Tace "To Mijin Amira"  ta bashi Guri ya shiga motarsa ya fita. Ta gyaɗa kai tace "zaku gane baku da wayo, daga kai har skelaton ɗin matarka" Amira ta koma cikin gida, a Falo Anty tace "Amira Imran ya fasaltamin gidan, base munje ba, na turawa masu shagon kalar kayan da ya dace, gobe in Allah ya kaimu za'aje a karɓo kayan da sauran siyayya, daga nan za'a wuce jere, ranar Friday insha Allah zaki tare!!! "Anty in tare kuma?" "Eh ki tare Amira, hakane yakamata, babu amfani zamanki a nan, saboda abunda ake hasashe ba haka bane, kuma na fuskanci rashin zama guri ɗaya dashi ne yake sake saku wani abun, gara ki tare da wuri" Gaba ɗaya se jikin Amira yayi sanyi, Anty tace "ki kwantar da hankalinki kinji Amira, bakomai Allah ya iya mana ya baku zaman lafiya" Fadila tace "Ameen Anty" "Gobe in Allah ya kaimu, da kaina zan ajiyeki gurin masu gyaran gashi, ki fara shirin tarewa" Imran ma a hanyar tafiya gida tunani ya dinga yi, lallai Amira ma ba baya ba gurin kishi, gata da tsiwa da neman maganar tsiya, ita kuma Ihsan ga rashin haƙuri da saurin hasalar tsiya, ga Anty tace masa Ranar juma'a Amira zata tare, koya zeyi da wannan gwaramar da rikicin?...... Share Please Domin Sharhi, gyara ko shawara 07063065680. [1/29, 1:51 PM] Ayshercool: *_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, INA KUKE MASOYA AYSHERCOOL, MASOYA LITATTAFAN TA, KAMAR SU WATA KISSAR SAI MATA, WUTA A MASAƘA, ABDULJALAL,AƘIDATA, DA DAI SAURAN SU TO GA SANARWA TA MUSSAMAN, INA ME FARINCIKIN YI MUKU ALBISHIR DA FARA SAKIN SABON LITTAFINA NA RUƊIN ƘURUCIYA, LABARI ME TARIN FAƊAKARWA DA ILIMANTARWA GAMI DA NISHAƊANTARWA, KUMA BULALIYA GA IYAYE, RUƊIN ƘURUCIYA ZE TAƁO ABUBUWA DABAN DABAN GAME DA RAYUWAR MATASAN YARA WANDA SUKE KAN ADOLECSEN PERIOD, IRIN HATSARIN DA WANNAN SHEKARUN SUKE DA SHI, DAMA SAURAN ABUBUWA NA ILIMANTARWA DA KUMA NISHAƊANTARWA, ZAKU IYA MORE KARANTA WANNAN LITTAFIN AKAN KUƊI NAIRA ƊARI UKU KACAL, LITTAFIN ZE FARA ZUWAR MUKU BIYAR GA WATAN FEBUARY DA YARDAR ALLAH, ZAKU IYA TURA KUƊINKU TA 0009450228, AISHA ADAM, JA'IZ BANK, KU TURA SHEDAR BIYA TA 07073065680, DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR 07063065680*_ [1/29, 3:47 PM] Ayshercool:      🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                           31_32 Da farko Amira ta shiga fargaba, jin Anty ta ambaci tariyarta a kurkusa, daga baya kuma gara ta tare idan yaso ayi duk wadda za'ayi, wayarta ta ɗakko ta kira Anty Fa'iza, tayi sa'a kuwa ta ɗaga. "Malama lafiya zaki kirani a yanzu, ina tare da mijina?" "Iyee seki gayawa wanda bashi da mijin ai, Anty Fa'iza na wuce wannan yanzu fa" "Ke dalla can, ya akayi ne?" Amira tace "Normal, tun da yana kusa ba shi mu gaisa" Fa'iza ta miƙawa Bashir wayar, ya karɓa tare da faɗin "Assalamu alaikum" "Wa'alaikum salam, Yaya Bashir barka da dare" "Yawwa Amira barka, ya kike ya gidan?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah,  ya yarana ya aiki?" "Alhamdilillah kowa lafiya Amira, fatan dai komai lafiya babu wata matsala?" "Babu wata matsala Yaya Bashir" "To Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya banu zaman lafiya me ɗorewa" "Ameen ya Allah Yaya Bashir, nagode sosai" Ya miƙawa Fa'iza wayar, ta karɓa tace "ina jinki" "Anty Fa'iza ranar juma'a in Allah ya kaimu zan tare fa" "Haba dai" "Wallahi dagaske nake" "Allah sarki, to Ubangiji Allah ya nuna mana yasa ki shiga ɗakin Aure a sa'a Amira" "Ameen Anty Fa'iza, but am scared" "Scared of what kuma?" "Kin san ba sona yake ba, ina tunanin irin zaman da zanyi da su, ga zuciyata da rauni, kin san wasu lokutan bana iya jure wasu abubuwan, mussaman wulaƙanci da tozarci, ni gaba ɗaya na rasa me yake min daɗi ma" "Amira ki kwantar da hankalinki kinji, babu abunda ze faru insha Allah, sedai dole kiyi haƙuri da wasu abubuwan da zaki gani, amma kiyi haƙuri na ɗan lokaci ne Komai ze wuce insha Allah". "To shikenan Allah yasa, zaki zo tariyar ne?" "A' gaskiya, sedai bayan an kaiki zanzo, bani da lafiya ne Amira" "Kice an gamu kenan?" "Aka gamu dame fa?" "A'a Allah ya kaimu nan da watanni mu zo suna" "Ko dai mu muzo suna Kaduna ba" Amira tace "Idan Ihsan ta haihu kenan?" "Idan kin haihu dai, ke ba kya fatan ki haihun ne?" "Mhmm Anty Fa'iza kenan, ni dai zan turomiki kuɗi account ɗinki, da list ɗin abunda nake son kin siyomin, a kai tasha ki sakomin a mota" "Me kike buƙata haka?" "Zan turomiki ta message, kin san bani da lefe, kuma gidan nan sun min iya yinsu, wallahi baki ga kuɗin da suke kashemin ba, zan sako miki dubu ɗari biyu a account kimin siyayyar, idan basu isa ba seki min Magana". Fa'iza tace "dubu ɗari biyu Amira, ina kika samu kuɗi haka?" "Motar da aka bani a Abuja na saka Sultan ya siyar, ya turan kuɗin account ɗina, kuɗin da suke account ɗina sun kusa million Uku wallahi" A tsorace Fa'iza tace "million uku Amira?" "Ƙwarai kuwa, zan turomiki ma da kuɗin kayan sallar yarana" "Lallai, sannu Attajira, Yayan naki ya sai miki bedsheets guda uku da plasma, yace a baki,  kiyi haƙuri ba shi da kuɗi ne, Sultan ma ya kawo wata ƙatuwar MP da Dinner set, se babban frame da agogo yace in zanzo a kawo miki, ince yana miki fatan Alkhairi, dan ya goge lamabarki daga Wayarsa, tun da kinyi Aure, ni kuma na sai miki turaruka da flask na tea, kiyi haƙuri Amira bani da kuɗi wallahi, amma ban so Aurenki yazo min a haka ba, kiyi mana afuwa" Kawai Amira ta fashe da kuka, "Amira ya da kuka kuma?" "Anty Fa'iza, wallahi kukan daɗi nake, ashe haka kuka damu dani? Nagode sosai da kulawarku Allah ya saka da Alkhairi, ki miƙamin saƙon godiya ta ga Yayana, Sultan kuma zan kirashi in masa godiya, nagode Anty Fa'iza" "Bakomai Amira, ai kanmu mu ka yiwa, idan ba muyi miki ba waza muyiwa? Ki dena kuka Ina jiran ki turomin ɗin, zanje in miki siyayyar insha Allah" "To shikenan Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" "Ameen seda safe" Amira kashe wayar, ta ajiye tana murmushin jin daɗi, duk da yadda dangin mahaifinta sukayi watsi da ita, amma a hakan wasu suna ƙoƙarin faranta mata rai. Washegari da rana Anty tana ta shirin zasu fita, su Ajiye Amira a gurin gyaran gashi, se ga Anty Hadiza tazo Yayar su Imran. "Khadija kece a gidan sannu da zuwa" "Yawwa Anty, kice har kun shirya?" "Eh fita zamuyi yanzu" "Allah yayi zan sameku kenan, Abba ne ya kirani a waya yace inzo muje tare, ni kuma ban kiraki a waya ba nasan kina zuwa gurin aiki, nace in bari in bari se Bayan sallar Azahar" Anty tace "Aikuwa Abba ya kyauta da ya turoki muje tare, Bari ki sha lemo ki huta semu tafi" "A'a ni da nazo a mota, ai ba wani hutu mu tafi kawai" Amira ta fito cikin doguwar baƙar riga, ta naɗe kanta da mayafin doguwar rigar, ta riƙo ƙaranar jar jaka, sam bata san da zuwan Anty Hadiza ba, Amira na ganinta tai murmushi ta ƙaraso falon tace  "Anty sannu da zuwa" "Yawwa Amaryarmu, na miki laifi rabonmu dake tun ranar da aka baro gidanmu dake ba wanda ya kuma zuwa, kiyi haƙuri dan Allah" Amira tace  "bakomai Anty, ya gida" "Lafiya ƙalau Amarya, kinyi kyau sosai Amira Masha Allah" Fadila tace 'tana jin kunyarki ne, da haka za tace miki uwargida sarautar Mata dai" Anty Hadiza tace "Ahh hakane fa, ita ce Uwargidan sarautar Mata kam, masha Allah, Ubangiji Allah yasa ki shiga a sa'a" Amira tace Ameen. Anty ta fito suka tafi, a gurin Saloon suka ajiye Amira su kuma suka tafi gurin siyayya. Ba ƙarya sun yiwa Amira siyayya ta gani ta faɗa, kama daga kan furnitures, kayan Kitchen, electronics ba abunda basu sai mata ba, kaya na gari masu matuƙar kyau, ba su cika mata tarkace da yawa ba, sedai an sai mata kaya masu tsada da kyau. Furnitures ɗin Amira light and dark purple, kujerun dining ɗin ta da labulaye duk purple ne, daga nan shagon da sukayi siyayya, Anty Hadiza ta kira Imran a waya, ya ɗaga tare da yin sallama, ta amsa sannan tace "Angon biyu ya kana ina ne?" "Ina gida" "Lallai ɗan hutu, haryanzu ba'a gama cin agwancin ba, gashi zamu kawo maka wata matar" "Wace matar?" "Wace matar kuwa ban da Amira, gamu nan mun gama siyayya zamu shigo jere tare da su Anty Nafisa" "To sekun zo" "Yawwa, ka gaida min da Ihsan ɗin kan mu zo" "To zataji" Imran yana babban falo, ya tashi ya ɗakko mukulli, ya buɗe ƙofar da ɓangaren Amira da babu komai a ciki, se ƙamshin sabon fenti dake tashi, ya koma ƙofar ɓangaren Ihsan, ya tarar da ita a kwance a kan gado tana chatting, ta kalle shi tace 'hey my D, any problem?" Ƙarasowa yayi ya zauna a kan gadon da take yace  "Khadija ce ta kirani a waya Yanzu, wai za su shigo su yiwa Amira jeren kaya" Ras! Gaban Ihsan ya faɗi, take taji duniyar ta mata duhu tana juya mata, tace "wai wace Khadijan?" "Anty Hadiza na, za suzo da matar Alhaji Hashim suyi jeren". Ji tayi ƙirjinta yai mata nauyi, tai shiru tasan tunda akayi jere to tariya ma tazo, ta so ace gaba ɗaya dangin mijinta ma na bayanta, amma alamu sun nuna Khadija ma na bayan Amira kenan, tunda take rawar ƙafar zuwa jere. Imran yace "ya naji kinyi shiru ne?" "To ni me zance, ince wani abu ranka ya ɓaci, shikenan Allah ya kawo su Lafiya" "Yawwa my wife, gara ki dinga ɓoye kishinki, dan Allah karki wani abu da zesa su raina min ke kin ji masoyiyata" Ta jinjinawa Imran kai tana murmushin yaƙe, ƙasan zuciyarta kuwa kamar ta fasa ihu, Imran ya jinjina mata kai, ya sumbaci goshinta ya ta shi ya fita daga gidan. Yana fita ta Ihsan ta fashe da matsanancin kuka me ratsa zuciya, ta dinga kuka tayi me isarta, sannan ta janyo wayarta ta kira Mummynta. Mummy na ɗagawa taji kukan Ihsan, a gigice tace  "Ihsan lafiya kuwa? Kukan ne kike yi haka? Wani abun ne ya faru?" Cikin kuka tace "Mummy, wai yau zasu zo mata jere tarewa za tayi fa Mummy" "Kai amma kin ɗagamin hankali gaskiya, shine kika zauna kina asarar hawayenki  akan aikin banza, me akayi akai wata banzar karuwa da zaki tashi hankalinki kina wannan kukan kamar uwarki ta mutu? Dalla ki share hawayenki karki bari su zo su raina ki, su zi suyita jeren mana a akanki zata zauna? Ki jirayi zuwanta ki san irin zaman da zakiyi da ita shikenan fa, dalla kiyi maza ki wanke fuskarki karsu zo suga alamar kinyi kuka ma, idan ba haka ba kuwa zaki zubarwa da kanki kima" "Mummy kin san wani abun takaici kuwa? Wai harda Anty Hadiza za'azo jeren da wulaƙanci, ni na fuskanci kamar ita murna take da wannan tariyar, in ba haka ba neye na zuwa jeren" "Ke ina ruwanki, ba se taita yi ba, tunda tai uwatta tana bayanki ba shikenan ba, rabu da ita itama za'a san abunyi a kanta zan san yadda za'ayi da ita, ki tashi ki kintsa tunda wuri kinji ko?" "To Mummy" 'yawwa, maza ki share hawayenki" Haka Ihsan ta tashi, ta wanke fuskarta ta kintsa jikinta, cikin wani rantsatsten leshi. Babu jimawa sega su Anty sun ƙaraso gidan, su suna motar gida kayan kuma suna babbar motar kantun da suka je. Tun daga harabar gidan Anty take yaba tsaruwar gidan, suka shiga katafaren ƙaton falon me ɗauke da manyan kujeru da labulaye, ga dining a gefe, da Kitchen da extra ɗaki a falon se Manyan ƙofofi guda biyu, ɗaya ɓangaren Ihsan ɗaya na Amira. Suka dinga kwaɗa sallama, amma shiru babu wanda ya amsa, Anty ta tura ƙofar da alamu suka nuna ba komai a gurin, hakan ya tabbatar Mata da nan ne ɓangaren Amira ne. Da ta shiga nan ma falo ne, da ɗakuna biyu da Kitchen a falo, a cikin Kitchen ɗin da store,  se kuma toilet a kowane ɗaki. Gidan Imran masha Allah yayi kyau sosai, Anty Hadiza ce ta shiga ɓangaren Ihsan ta tarar da ita tana kallon TV. "Iyee Ihsan kina nan dama muke ta sallama kika ƙi amsawa, kina jin motsinmu amma ki kayi shiru, yanzu da sata ma muka shigo shikenan Sedai muyi mu fita?" "To me zance ne?" "A'a ba'a haka, fito ku gaisa da Anty Nafisa ai be kamata muyi sallama kina ji ki sharemu ba" Haka Ihsan ta fito tana cunkusa baki, tana Zuwa ta tarar Da Anty Nafisa da Fadila a babban falo, ta ƙare musu kallo sannan ta yastina fuska tace "sannunku" Anty tace "Yawwa Ihsan, ya kike ya gida?" Ihsan ta ɗan keɓe baki tace "lafiya" Ta nemi guri ta zauna a falon, ta kunna kallo ko ta kansu ba ta sake bi ba. Nan ma'aikatan shagon nan suka shigarwa da su Anty kayan nan, suka taya su jera furnitures ɗin nan, kan wani lokaci tuni shashen Amira ya ɗau kyau, suka jere mata Kitchen ɗin ta, suka gyara komai tsaf. Suna gidan har bayan sallar isha'i, se wajen tara na dare suka kammala komai, Ihsan ko ruwa bata basu ba, haka ta ƙyalesu su kai aikinsu suka gama, suna shirin tafiya ne se ga Imran ya dawo. Cikin girmamawa Imran suka gaisa da su Anty, Ihsan ta fito tana ta wani iyayi da rawar kai ita a lallai ga me miji, Anty tace "Imran shigo kaga ɓangaren Uwargidan naka mana, dan in nace Amarya ba ta so tace ita uwargida ce sarautar Mata" Faɗin haka da Anty tayi, ba ƙaramin baƙantawa Ihsan rai yaiba, Imran ya bisu yaga ɓangaren Amiran, komai yayi normal, Imran yace "gaskiya kaya sunyi kyau masha Allah" Anty Hadiza tace  "Imran babban falon nan ma Kayan furnitures ɗin Na Ihsan ne?" Imran yace "No nata suna ɓangaren ta, ni na saka Wannan". Tace 'nifa ince, ranar da muka zo ai babu furnitures a babban falon, waye ya tayaka zaɓan Kayan nan ne? Sunyi kyau sosai". "Ammi ce ta zaɓe su". Anty tace  "ba wannan ba, ya batun kayan lefen 'yata Imran? Ga tariya za'ayi shima yakamata ka biya kuɗin gyara" "Anty na kashe kuɗi sosai da bikin nan, bani da kuɗi yanzu" "Amma ka iya siyan furnitures ɗin falo ko?" Imran ya ɗan sosa ƙeya yana murmushi, "to gaskiya muna binka bashin kayan lefe, a gida na yi mata siyayya amma wannan daban, kaima zaka mata lefenta" Suka fito falo suna maganar, Imran yace "to Anty, idan Allah ya horemin zanyi Insha Allah" "Yawwa haka nake son ji, yanzu kawo abunda ya sawwaƙa, za tayi kitso da lalle da gyaran jiki na tariya" "Anty bani da kuɗi fa, just recently na biya harajin shaguna na kasuwa, kuma kinga yanzu tsakiyar wata ne ba'ayi salary ba empty nake" "Allah Imran seka kawo abunda ya sawwaka" Imran yana ji yana gani yace wa Anty, kan Amiran ta tare ze turo kuɗin, Ihsan kamar ta rusa ihu, ji take kamar ta maƙurewa Anty wuya yadda take ta cusowa Imran Amira. Daga nan ya raka su har mota suka tafi, suna tafe a hanya suna hirar jeren da sukayi wa Amira, Anty tace "gaskiya Khadija, matar Imran ba ta da ta ido, duk da an san abun da aka mata babu daɗi, amma be kamata tai mana irin wannan karɓar ba sam ban ji daɗin hakan ba" "Mhmm Anty kenan, Allah dai ya kyauta, ni kaina da ta sanni farin sani baki ga yadda tai min ba?" Fadila tace "ai sauƙinta ita ma Amiran ba kanwar lasa ba ce, amma wannan da sokuwar kishiya zata samu, zata ga wulaƙanci" Anty tace "hakane kam, sedai duk da haka zan ja wa Amiran kunne a kanta, kuma Khadija da alama dai Amminku ba ta son Amira da  Auren ta da Imran, dan tun ranar Dinner da muka haɗu aka kawo Amira gida na ba ta sake kira na a waya ba" "Gaskiya ba zan ɓoye miki ba bata so, an taɓa kawo Amira tun tana ƙarama ta riƙeta tace ba zata riƙe ba, duk da ni ba Ammi ce ta riƙeni ba mahaifiyarta ce ta riƙeni, amma Ammi ba ta son dangin Abba suje sam, kuma Yanzu da aka aurawa Imran Amira, ba ayi shawara da ita ba, kuma gashi ana ta cewa Amira karuwace, shine duk dalilin da ya sa ba ta son Auren" Anty tai ajiyar zuciya tace "Ai shikenan, ni Allah ya bani 'ya ina so, iya zama na da ita ban ga wani abu da zesa in tabattar da Amira Karuwa ba ce, ke hatta wayarta na karɓa chats ɗimta da komai, ba abunda ban duba ba, ina doubting ace Yarinyar nan karuwa ce, na dai yadda ba ta ji tana da rawar kai, amma gaskiya ban tabattar da maganar karuwanci ba" Hadiza tace "to Allah ne dai masanin gaibu" Suka cigaba da hira, suka kai Hadiza gida suka sauke ta, sannan suka tafi. Bayan tafiyar su Anty, Ihsan tace  "wai da gaske tura musu kuɗin nan za kayi?" "To idan ban tura musu ba ya kike so inyi?, Ko so kike ta gayawa Abba yazo yana fushi da ni?" "To in hakane nima se ka bani, wannan shine adalci" "Ihsan a gabanki fa na ce bani da kuɗi, bani da kuɗi wallahi, kuɗin kenan zan ɗauka in basu, saboda kar a samu matsala, kuma naga ke lokacin bikinmu ma baki, kiyi haƙuri mana" "Yanzu matsayina ɗaya da ita kenan? Dan ka bani lokacin bikina, shine yanzu ba zaka bani ba,ita ka bata" Shareta Imran yai, yai mata shiru yaƙi kulata. Da su Anty suka koma gida, Amira harta koma tuni, wannan karon ma, kan nan ya sha kitso ko tsaga baka gani, saboda yadda sukai ƙanana sosai, ga yawa an mata ƙari sosai. Washegari Imran ya tura musu dubu hamsin, ya lallaɓa Ihsan ya bata dubu Ashirin dan a zauna lafiya, ba tare da tasan nawa ya turawa su Amira ba. Tuni Amira ta turawa Anty Fa'iza abunda take so ta sai nata da kuɗi, tai mata siyayya ta sako a mota zuwa Kaduna, Amira ta gayawa Anty, aka aika direba ya je ya karɓo mata kayan daga tasha. Amira taji daɗin abubuwan da suka sai mata taita murna tana jin daɗi. Har gida me lalle taje ta zanawa Amraya Amira, Amira tai shar da ita se sheƙi take kamar ba ita ba, ga wani sassanyan ƙamshi dake tashi daga jikinta duk inda ta ratsa, tun ana gobe zata tare jikinta yai sanyi sosai, Alhaji Hashim baya gari, amma ya kira a waya yai mata fatan Alkhairi, tare da yi mata nasihohi masu ratsa jiki kamar 'ya da uba, Amira ba zata taɓa mantawa da kara da mutuncin da Alhaji Hashim da Anty Nafisa sukayi mata ba, ba dangin iya bana Baba, amma sun mata kara da nuna mata soyayya. Ana gobe Amiran zata tare, Anty Nafisa ta kirata ɗakinta, ta zaunar da ita, ta kalle ta tace "Amira, yanzu lokaci yayi da zaki shiga sabuwar Rayuwar Aure, wadda ta sha bamban da irin wadda ki kayi a waje, kin san da yadda akayi Auren nan naki, fatana a gareki shine, kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, duk matar da kika gani a gidan Aure haƙuri take, kuma ita ma haƙuri ake da ita, dole kiyi haƙuri Amira, nasan zaki fuskanci ƙalubale a gidan Imran, amma nasan komai ze wuce nan ba da daɗewa ba insha Allah, in dai hasashen da nake a kanki ya zama gaskiya, komai ze wuce amma sekinyi haƙuri, kishiyarki Ihsan ba sa'arki bace, ta girmeki dan haka banda mata rashin kunya, ko neman Magana, bance ki yadda a wulaƙanta ki ba, amma ban da neman rigima, ki yiwa mijinki biyayya, ki san da irin lafazin da zaki dinga masa Magana, kiyi duk yadda zakiyi ki ja hankalinki kansa, karki ce baya sonki ki zuba musu ido, Flight for your right, you are such a beautiful lady Amira, kuma kina da kirki, duk wannan cika bakin da yake ze dena ne, na yadda da 'yata bana shakkar ta kara da kowace mace a gurin miji, Allah ya bada sa'a ya albarkaci rayuwarki  am gonna Miss you dear" Anty tai maganar tana gogewa Amira hawayen dake zubowa kan fuskarta, Amira ta rungume Anty tana kuka tace "Nagode, Nagode Anty Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi, Ubangiji Allah ya biyaki ladan kula da marainiya, kina cikin sahun mutanen da suka fuskance ni, suka fuskanci abun da na ke so, zama na dake kin kula dani, kamar 'yar da kika haifa, ba kyara ba hantara, ba ki taɓa kallona da laifin da akace ina aikatawa kin ƙyamace ni ba, at least nima naji wani abu na daga daɗi da farinciki da masu iyaye a raye suke ji' Jiki a sanyaye Anty ta shiga sharewa Amira hawaye tace  "Amira karki sani kuka mana, nima marainiya ce, i knows what you go through, i know the feelings, shiyasa ni duk in da ɗa yake nawa ne, saboda nasan da ɗa da dukiya ba'a mugunta a kansu, se in moreki fiye da yadda zan mori 'ya'yan dana haifa, dan haka karki damu, You Are my daughter, tashi muje in rakaki ki kwanta, dan ki tashi gobe in Allah ya kaimu da wuri, dan na ɗan gayyaci mutane, za'azo ayi ƙwarya ƙwaryar walima kan a kaiki" Haka Anty ta raka Amira ɗakinta, har da rufeta da bargo ta kshe mata fitilar ɗakinta tare da rufe mata ƙofa. Amira ta lumshe idonta Hawaye na zubowa tace  "Allah ka jiƙan iyayena, ka sakawa da Anty da gidan Aljanna, ka kareta ka tsare mata zuriyarta ita da mijinta" Washegari da safe 'ya'yan Anty, suka iso gidan suma, Anty ta na da yara mata 'yan biyu, ɗaya lawyer ce ɗaya likita, suna Auren wasu manyan attajirai suma 'yan biyu, Anty ta gayyaci mutane abokan aikinta da maƙota, cewar za tayi walimar tariyar 'yarta. Sun san halin Anty da kwashe kwashen yaran mutane, ta riƙe 'ys'yan 'yan uwa da dama, ba ruwanta ita duk in da ɗa yake nata ne, shiyasa ba wanda ya damu da in da ta samo Amira. Yadda halin Anty yake na kirki haka 'ys'yanta suke, dan su sa kai wa Amira kwalliya ma, suka dinga hotuna, Anty Hadiza ma a gidan ta wuni ita da yaranta, gaba ɗaya jikin Amira a sanyaye yake, da magariba Anty ta sa Amira tai wanka, aka saka mata kaya sannan aka naɗa mata lafaya, fuskarta ba make up amma tayi kyau sosai. Zuwa sallar isha'i, suka tafi raka Amira, tana ta kuka, hadda Anty aka tafi raka Amira, se tashin ƙamshin turare take. Duk da Amira kuka take, amma ta yaba da tsaruwar gidan, mussaman yadda aka kashe mata kuɗi a ɓangaren nata, kayan ta duk 'yan waje ne komai yayi kyau. Akwai wasu da cikin 'yan uwan Ihsan a gidan, sun zo su tayata zama da sa ido, saboda kawo Amira, se wani harare harare suke, suna yada baƙaƙen maganganu, yadda suka zaci Amira ba haka su ka ganta ba, duk da tana cikin lafaya, amma hakan be hana idanunsu ganin kyan diri da Allah ya bata ba. Wanda suka rako Amarya na ta yaba kyan ɗakin Amiran.. Imran ya koma gida, Anty ta fito da Amira babban falo, ga Imran a zaune ga Ihsan, tace "Imran ga Amanar Mahaifinka nan, kamar yadda yake faɗa, ya bani riƙonta na wani ɗan lokaci, gashi na kawo maka ita na damƙa maka, ina me naka Nasiha da kaji tsoron Allah, sannan kayi adalci a tsakanin iyalinka, Ihsan matarka ce, Amira ma haka, dan Allah ka manta da wasu batutuwa da suka faru a baya, ka fuskanci iyalinka ka riƙe su da amana, Ihsan ga Amira nan, ƙanwar bayanki ce kin girmeta, dan haka hankalinku ba ze taɓa zuwa ɗaya ba, dan Allah kiyi haƙuri da ita, ku zauna kamar 'yan uwa ba kishiyoyi ba" Kwaɓe baki Ihsan tayi ta juya ƙeya tare da faɗin taɓ, se da Imran ya kalleta. Wata ƙanwar maman Ihsan tace "A'a fa baiwar Allah, ba wani kamar 'yan uwa ita fa kishiya duk in da take kishiya ce, waye ze wani riƙi kishiya 'yar uwa ta kassara ka, kowa dai tai zaman kanta" Imran yace "ya haka ana musu nasiha ki na zigasu?" Anty ba ta nuna ta damu ba ta ɗora da cewa "Amira, Ihsan yayarki ce, duk da kina da'awar kece Uwargida amma ta girmeki kuma ta rigaki shiga gidan mijinku, dan haka dan Allah ku zauna lafiya ban da rigima, kiyi wa mijinku biyayya ki girmama kishiyar ki, kin ji 'yar Anty?" Amira ta jinjina kai tace "Insha Allah" Anty tace "to Imran, ka na da abun faɗa ne?" "A'a ba ni da wani abun cewa, kin gama komai ai, ni dai fatana su zauna lafiya, mussaman 'yarki dan kin san halinta, ban da ɗaukar magana, kamar yadda ki ka gayamata, Ihsan gaba ta ke da ita, dan haka dole ta girmamata" Aikuwa Amira ta ɗago suka haɗa ido, ta gallawa Imran harara, harda fari da ido da murguɗa baki" Imran ya ɗan girgiza kai, Anty tai musu Addu'oin zaman lafiya, suka maida Amira ɗakinta. Anty tace "zamu tafi, ga miyarki da nai miki, da kayan snacks duk suna Kitchen ɗinki, idan garin Allah ya waye, ki ɗibarwa abokiyar zamanki nata, Allah ya baku zaman lafiya, aita haƙuri Amira, shi Aure ɗan haƙuri" Amira ta jinjina kai tana share hawaye, ita kanta Anty seda tai ƙwalla, saboda a ɗan zamanta da Amira sunyi sabo me ƙarfin gaske, saboda Amira akwai shiga rai sosai. Bayan tafiyarsu dama Amira ba ta tsammaci ganin Imran ba, dan haka ta miƙe taje ta zazzaga part ɗinta komai yai kyau, ta je rufe ƙofar part ɗinta ta leƙo babban falo, ta ga su Imran su ma sun rufe ƙofa, girgiza kai tayi, ta rufe ƙofar ta koma ɗaya da ga bedrooms ɗin ta, wanda aka shiryamata kayanta a ciki, ta canA kaya ta nemi Guri ta kwanta. Ɗaya bedroom ɗin, gadon ƙarfe ne a ciki da mudubi se abun rataye jakun kuna. Sam Amira ta kasa bacci, se tunane tuane da take, ɓangare guda tana murna, wai duk wannan kayan nata ne, ita ma yanzu matar Aure ce, ɓangare ɗaya kuma ta na jin takaicin an kawo ta gidan Aure, amma ko kalli ba ta ishi mijin nata ba, da ƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta. Ɓangaren Imran ma, Yau se da yai zaman rarrashin Ihsan, dan koke koke taita yi masa, yai ta rarrashinta yana kwantar mata da hankali. Kiraye kirayen sallar Asuba ne ya farkar da Amira daga baccin da take, tai sallar Asuba da addu'oin Azkar, ta koma ta sake kwanciya,  wajen ƙarfe tara ta tashi, tai wanka ta shirya cikin riga da skirt, ta fito babban falon, wata magazine Amira ta gani akan Centre table, da gani ta Imran ce dan duk abubuwan sojoji ne a jiki. Tana nan zaune tana kallon magazine ɗin, aka buɗe ƙofar part ɗin Ihsan, Ihsan ce ta fito sanye da rigar bacci iya gwiwarta, kanta babu ko ɗan kwali, ta saki baƙin gashinta da alama ba ta daɗe da tashi ba, tana Ganin Amira a falo ta ja tsaki, Amira tai murmushi tace "Yayata ina kwana?" "Kinga malama, ki riƙe gaisuwarki ina ruwanki da ni ne?". "Haba Ihsan, gaisuwar ma ba wani abu ba"? "Eh gaisuwar, bana son salon bariki kin gane ko? Kiyi rayuwarki in yi tawa" Amira tace "A'a, ni baza ai haka da ni ba, ya za'ai mu zauna gida ɗaya ba gaisawa, any way nace Ya tashi ne?" Ihsan da ke ƙoƙarin nufar dining ta tsaya cak, ta waigo ta kalli Amira tace "karki wannan gangancin, Ina ruwanki da tashin sa ko rashin tashin sa, yarinya ta ki kama kanki tun wuri, ba ki da miji a gidan nan" Kawai Amira tai dariya tace "ƙarfin hali, aron ɗan kunnen sirika, ai shikenan zamu gani" Amira ta sake maida hankali kan magazine ɗin da ke gabanta. Ihsan ta dinga shiga part ɗinta tana fito da kayan Abinci, ta jere akan dining, ta kuma komawa part ɗinta, se gasu sun fito tare da Imran, ya rungumota a jikinsa, suna dariya Amira ko ɗaga kai ba tayi ba balle ta kallesu, duk da yadda taji ƙirjinta na harbawa da sauri. Sukaje har kan dining, Imran ya ja kujera ya zauna, Ihsan tace "kayi breakfast lafiya, bari inje inyi wanka kan ka kammala" Imran yace "Waze bani Abincin in kika tafi?" "Haba My, yanzu zan dawo fa, kai kayi wankan ka, You know i suppose to bath, bazan daɗe ba" Imran yace "shikenan, kiyi sauri amma zan fita" Ihsan tace "Ok Darling" tai maganar tare da kissing ɗin Imran ta juya suka haɗa ido da Amira, ta gallawa Amira harara sannan ta wuce part ɗin ta, Amira tabi Ihsan da kallo, a cikin rigar bacci kamar balbela, Ihsan na shigewa Amira ta miƙe ta nufi dining ɗin. *_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, INA KUKE MASOYA AYSHERCOOL, MASOYA LITATTAFAN TA, KAMAR SU WATA KISSAR SAI MATA, WUTA A MASAƘA, ABDULJALAL,AƘIDATA, DA DAI SAURAN SU TO GA SANARWA TA MUSSAMAN, INA ME FARINCIKIN YI MUKU ALBISHIR DA FARA SAKIN SABON LITTAFINA NA RUƊIN ƘURUCIYA, LABARI ME TARIN FAƊAKARWA DA ILIMANTARWA GAMI DA NISHAƊANTARWA, KUMA BULALIYA GA IYAYE, RUƊIN ƘURUCIYA ZE TAƁO ABUBUWA DABAN DABAN GAME DA RAYUWAR MATASAN YARA WANDA SUKE KAN ADOLECSEN PERIOD, IRIN HATSARIN DA WANNAN SHEKARUN SUKE DA SHI, DAMA SAURAN ABUBUWA NA ILIMANTARWA DA KUMA NISHAƊANTARWA, ZAKU IYA MORE KARANTA WANNAN LITTAFIN AKAN KUƊI NAIRA ƊARI UKU KACAL, LITTAFIN ZE FARA ZUWAR MUKU BIYAR GA WATAN FEBUARY DA YARDAR ALLAH, ZAKU IYA TURA KUƊINKU TA 0009450228, AISHA ADAM, JA'IZ BANK, KU TURA SHEDAR BIYA TA 07073065680, DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR 07063065680*_ [1/31, 2:02 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. *_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, INA KUKE MASOYA AYSHERCOOL, MASOYA LITATTAFAN TA, KAMAR SU WATA KISSAR SAI MATA, WUTA A MASAƘA, ABDULJALAL,AƘIDATA, DA DAI SAURAN SU TO GA SANARWA TA MUSSAMAN, INA ME FARINCIKIN YI MUKU ALBISHIR DA FARA SAKIN SABON LITTAFINA NA RUƊIN ƘURUCIYA, LABARI ME TARIN FAƊAKARWA DA ILIMANTARWA GAMI DA NISHAƊANTARWA, KUMA BULALIYA GA IYAYE, RUƊIN ƘURUCIYA ZE TAƁO ABUBUWA DABAN DABAN GAME DA RAYUWAR MATASAN YARA WANDA SUKE KAN ADOLECSEN PERIOD, IRIN HATSARIN DA WANNAN SHEKARUN SUKE DA SHI, DAMA SAURAN ABUBUWA NA ILIMANTARWA DA KUMA NISHAƊANTARWA, ZAKU IYA MORE KARANTA WANNAN LITTAFIN AKAN KUƊI NAIRA ƊARI UKU KACAL, LITTAFIN ZE FARA ZUWAR MUKU BIYAR GA WATAN FEBUARY DA YARDAR ALLAH, ZAKU IYA TURA KUƊINKU TA 0009450228, AISHA ADAM, JA'IZ BANK, KU TURA SHEDAR BIYA TA 07073065680, DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR 07063065680*_                                33_34 Kan Amira ta ƙarasa Imran ya haɗa tea yana shirin fara cin Abinci, Amira ba fagabar komai ta ƙarasa ta nemi Guri ta zauna a kan kujerara da ke facing ɗin Imran, ta ɗan ƙura masa ido. Ɗagowa yayi ya kalleta, tai murmushi tace "Ina kwana" "Lafiya" ya bata amsa a taƙaice ya fara cin Abincin sa. "Ka kwana lafiya?" "Da ban kwana ba za ki ganni a nan?" "No Allah ya huci zuciyarka" Ta ɗauki spoon dake kan plate, tai Bismillah ita ma ta fara cin dankali da miyar ƙwan da ke gabansa. Ya kalleta yace "meye haka?". Ta ɗan tura baki tace "Yunwa nake ji, tun ɗazu na tashi amma baku fito ba, kuma Kitchen ɗina bakomai se snacks ɗin da nazo da su, kuma ni abu me ɗumi nake so" Tai maganar tare da janyo kofin gaban Imran, ta kai bakinta ta na shan tea ɗin. Saboda gudun rigimar Ihsan, ya sa Imran miƙewa ya barwa Amira kayan breakfast ɗin, ya koma sashin Ihsan. Yaje ya tarar da ita ta shirya ta na ƙoƙarin fitowa, ta kalleshi tace "ya dai My d, are you done?" 'yes dear" "Anya ka ƙoshi kuwa? Ko dai rashina a kusa da kai yasa ba ka ci da yawa ba" Yai murmushi yace "No, na ci sosai na ƙoshi ne" "To shikenan na yadda, amma muje ni ka bani inci". "Ok amma base mun koma falon ba, inda saura a Kitchen ɗakko in baki a nan" "Meyasa?" Ta tambayeshi tana kallonsa. "Saboda tana falon, ni kuma bana son rigima" "Amma meye haka se kace ana tsoronta, shikenan saboda zuwanta se in dena walwala da sakewa a gidana?" "Ihsan, bana son duk wani dalili da ze ɗagamin hankali, ƙarewa Abincin nawa ma ita na barwa take ci, na ƙyaleta bana son abunda ze disturbing peace ɗina, kiyi haƙuri" Kamar Ihsan za tayi kuka tace "Yanzu in dafa maka Abinci dan cin fuska ka bata ta cinye" "No Baby, ni na isa inci fuskarki saboda ita, ina cikin mood na soyayya ne, ba na son ta ɓata mana shiri, ko tai sanadiyyar da zamu samu rashin jituwa, muje Kitchen ɗin in dafa miki wani abun da kaina in baki" Ihsan ba ta son ya hasala, dan shi idan yai rarrashi ɗaya biyu baya na uku, tsaf ze ɓata rai ya fita harkarta, dan haka ta haƙura ta haɗa sauran Abincin suka koma falonta suka ci. Wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi, Suna falon Ihsan suna shan soyaya, aka ƙwanƙwasa ƙofar falon. Imran yace "shigo" Amira ce ta shigo, da kwanukan da tai breakfast ta wanke su tsaf, se wasu manyan plate da ta zuba snacks ta saka poil paper tai wrapping ɗin su. Ihsan na jikin Imran yana wasa da gashin kanta, amma ganin Amira ya sa ta miƙe zaune, tana bankawa Amira uwar harara. Amira kam murmushi ta saki ta ƙaraso inda suke, tace  "Ihsan ga kwanukan ki, na wanke miki nagode Sosai, ta ajiye kwanukan a gaban su, sannan ta ɗau plate ɗaya ta ajiyewa Imran, tace "Captain ga naka, Ihsan kema ga naki" Ihsan tace "Me zanyi da wannan abun? Dalla ɗauke ki fita da shi ko mun ce miki muna jin yunwa ne?" Amira tace "Haba Ihsan, meye na wani Maganar kalar yunwa a nan, ai kyauta ce ba wani abu ba fa" "Eh na faɗa mu ba kalar yunwa bane, ba ma so ɗau abunki ki ƙara gaba, idan ma wani abun ki ka sa a ciki dan ki mallake shi to wallahi kinyi ƙarya, munfi ƙarfinki wallahi, sedai ki kalleshi daga nesa, dan ba kalarki bane" Amira tai murmushi tace  "naji shi mijin namu ba kalar yunwa bane, amma kefa, dan Allah idan ana Maganar yunwa ko makamancin yunwa, ki dena saka baki, dan ba ki da maraba da kalar yunwar" "Amira!" Imran ya kira sunanta da ƙarfi, "Matar tawa kike gayawa haka?" "Bakaji ni me tace min bane, har tana wani Maganar zan zuba wani abu in mallake ka, ai idan har zanbi malamai dan mallakar miji ban kai karuwa ba, mu zuba mu gani ni da ke, na ɗaga miki ƙafa ne saboda be kamata daga zuwana ace mun fara samun saɓani ba, amma am ready for you" Amira ta miƙe ta tafi, Imran ya dafe kai yace "Ihsan why? Na gaya miki duk yadda zaki kija girmanki kar yarinyar nan ta rainaki, amma kin kasa hakan, da ta kawo abu kika san ba kya so se ki karɓa ki bayar, amma abun da kike ze sa ta rainki, ni kuma bana son hakan, kuma ba zan iya haushi ba yau ba gobe ba, saboda gidana ba ba gurin aiki bane, ko filin daga da zan ta ɗaga maƙogwarona ba, shiyasa tun farko nake fargabar zama da mata biyu matsalolinku ba sa ƙarewa" Ya miƙe ze fita saboda ransa ya gama ɓaci, Amma Ihsan ta riƙeshi ta marairaice fuska tace "am sorry dear, ba zan sake ba insha Allah" Da ƙyar ta lallaɓashi ya haƙura, dan Imran akwai zuciya. Amira kam tun da ta koma ɗaki, ranta yake a ɓace, bata sake fitowa ba har magariba, saboda yadda zuciyarta ke ƙuna, tun Abincin safen nan bata sake cin komai ba. Bayan ta idar da sallalr magariba ne, sega kiran Anty ya shigo wayarta, cikin murna ta ɗaga tace "Antyna" "Na'am, Amira na ya kike?" "Lafiya ƙalau Amarya, au uwargida ya kike ya Gidan, ina fatan ba wata matsala?" "Ba matsalar komai Anty, ya Anty Fadila" "Tana lafiya ƙalau, ya mijin naki?" "Yana lafiya, ya fita sallar magariba ma" "To masha Allah, duk ki gaishe su, aita haƙuri kinji Amirana?" "To Antyna, nagode sosai" "Yawwa, seda Safe ki gaishe min da Imran ɗin". "Zeji insha Allah" "Allah yasa wata tara cif in zo in ɗau jikana" Amira cikin jin kunya tace "kai Anty" Ta katse wayar tana murmushi, ta kalli wayar tai shiru, be kamata ta gayawa Anty yadda Imran yaƙi saurararta ba, kawai ta ajiye wayar tana ajiyar zuciya. Tana nan kan dadduna, har akayi sallar isha'i, bayan tayi salla ta idar ta tashi tai wanka, ta shirya a doguwar rigar baccinta ta kwanta, harta fara bacci amma yunwa ta tashe ta, taji cikinta ya ƙulle. Duk kayan soye soyen nan basa kanta, saboda taci tun a gida, maiƙonsu ya isheta. Miƙewa tayi ta fito babban falo, taga Imran a zaune da matarsa suna kallo, a yanayin da ta gansu ba ƙaramin ɓata mata rai yai ba, suna kallo ta buɗe ƙofar ta fito, amma basu fasa abunda suke ba, da sauri ta juya ta koma, aikuwa a falon ta ta zube ta fashe da kuka, taji wani irin baƙinciki ya dinga taso mata, tana ayyana abubuwa daban daban a ranta, a ƙa'ida ita ke da miji, amma ta sharesu ta ƙyalesu, amma shine dan wulaƙanci ganin idonta ma be sa sun bar abunda suke ba. Haka ta ja jikinta ta koma ɗakinta, ga yunwa ga kishi yana cinta, da ƙyar bacci ya ɗauketa. Da safe duk da bata son cin kayan snacks ɗin nan, haka ta tura su a haka ta karya. Ya zamana duk lokacin da Amira zata falo, in dai zata haɗu da Imran da Ihsan, se Ihsan tayi wani abu da ze ɓatawa Amiran rai, dan seta ga Amira seta fara tsirar rungume Imran, tana shagwaɓa. Amira kam setai kamar bata gani ba, sedai ƙasan zuciyarta Kamar ta fasa ihu haka take ji, dan wani lokacin seta koma ɗaki take ɓuya tayi kuka, bata taɓa zaton zafin kishi ya kai haka ba se yanzu da take ɗanɗana" Amira Babu wanda ta gayawa halin da take ciki, a haka a daddafe har tai sati guda, gashi suna waya da Abba, yana ce mata ya kusa zuwa gari zezo ya gansu, amma bata taɓa gayamasa ga abunda ke faruwa ba, ta lura Imran yana matuƙar son Ihsan, dan haka ya kan kaucewa abunda ze ɓata mata rai. A haka a daddafe, Amira tai sati guda a gidan Imran, tana ƙoƙarin kaucewa fitowa lokacin da duk tasan zata haɗu da su Imran a falo. Yauma Amira tana kwance tana baccin safe, kasancewar yau weekends, ta duba agogo ƙarfe sha ɗaya, miƙewa tai ta fito tana tunanin Imran ya fita, dan haka da rigar baccinta a jikinta ta fito, sedai tana fitowa taga Imran yana nan yana falo be fita ba, kallo ma yakeyi shi da Ihsan. Imran ya ɗaga ido ya kalleta daga sama har ƙasa, ya saki ajiyar zuciya ya ɗauke kansa. "Ina kwananku?" Ta gaishesu. Imran ya kalleta ya jinjina kai, yayin da Ihsan ko motsawa ba tayi ba, balle ta kalli inda Amira take ba, seda Amira ta nufi dining, sannan Ihsan taga shigar dake jikin Amiran, ai ba shiri Ihsan ta miƙe zaune, ta kalli Imran amma taga ba Amira yake kallo ba, hankalin sa yana kan TV. Amira taje ta bubbuɗe kwanukan dake kan dining, ta samu sun rage Abincin ta kama ci. "Ke kika ajiyemin da zakije ki taɓa min kaya ba izinina?". Kunnen uwarshegu Amira tai da Ihsan, ta cigaba da cin Abincin ta. Imran ya kalli Ihsan ya girgiza mata kai alamar tai shiru. Imran satar kallon Amira yake ba tare da Ihsan ta sani ba, Amira ta kammala cin Abincin ta, maimakon da ta gama ta koma ɗakinta, se ta tashi ta koma kujerar da ke facing ɗin Imran, ta zauna tana kaɗa ƙafa tana danna wayarta. Imran ya kasa dena kallonta, saboda kusan sashi mafiya yawa na rigar Net ce, gashi ta baje kitson attachment ɗinta, ta haɗe rai kamar ba ita ba. Tana ɗaga ido sukai ido huɗu da Imran, hararasa Amira tai ta kashingiɗa a jikin kujearar ta lumshe idonta. Takaici ne ya kama Imran, ganin ta kama shi yana kallonta har da hararsa, Cike da salon tura takaici, ya fara kissing ɗin Ihsan. Duk yadda Amira ta so ta daure kasawa tai, se ga hawaye na bin fuskar Amira, Ihsan ta bawa Amira baya dan haka bata ganin Amira, Imran ke facing ɗinta Imran yaiwa Amira murmushin mugunta, ganin tana kuka. Nan da nan tai sauri ta goge hawayen, dan kar ma Ihsan ta gani ta rainata, duk taɓarar da suke  a gabanta ta maze, ta cigaba da dannan wayarta, sedai ƙirjinta har wani nauyi yake mata saboda azabar kishi, Imran ya riga ya fara gano Amira ma na da tsananin kishi. Seda suka tashi suka bar falon sannan Amira ta bawa hawayenta damar zubowa sosai, tafi jin haushin Ihsan fiye da yadda take jin na Imran, jiki a sanyaye ta tashi ta tafi ɓangaren ta itama. Amira ta tsiri se suna falo, za tai shigar matsatsun ƙananun kaya ta fito, ta fito musu a Karuwarta da suke faɗa. Da safe Amira ta sanya wani ƙaramin wando da wata 'yar ƙaramar riga,ta fito tana ta gyara babban falo tana goge TV, se ga Ihsan ta fito, ita kanta da tai arba da Amira seda gabanta ya faɗi, ta kalli Amira tace "ke meye haka ne wai?" "A ina kenan?" "Wannan wac irin banzar shiga ce? Malama gidana ba bariki bane bafa, dan me zaki wannan shigar ki fitomin falo bayan kin san lokacin fitar mijina ne yanzu" Amira ta kalleta tace "kema kije kiyi irin shigar mana dan ki hana shi kallona, ki kiyayeni fa na daɗe da fita sabgarku nima ku barni inyi rayuwata" "Ni kike gayawa haka?" "Na gayamiki ɗin, uwata ce ke? Kema in kin cika mace kije ki saka mana ki fito, in kuma ba ki da abun sawa ki nuna Ni da nake da shi seki bari in saka in fito ya kalla, da yaje waje ya kalla fa?" "malama rufemin baki, wallahi ki kiyayeni baki isa ki zo gidana kimin karuwanci ba wallahi, mijina yafi ƙarfin ki" "Waye mijin naki da yafi ƙarfin tarkon Karuwa, ki zuba ido kiyi kallo zaki ga Karuwa ganin idonki wallahi, zan nuna miki abunda karuwa zata iyayi" "Me zaki iyayi, ƙarya kike mijina ya faɗa tarkonki, asararriya wadda ta gama raba jikinta ga maza a titi, a kai mata alfarma akaa Aureta" Amira tace "Kinga bariki tayi riba, na gama gantali nazo na Auri mijin shashasha ba" "Ni kike cewa shashasha?" "Na faɗa, Shashasha me kama da bushshen kifi" "Ke Amira wa kike cewa shashasha?" Muryar Imran ne dake ƙoƙarin fitowa daga ɓangaren Ihsan. Sedai yana ganin Amira yai sororo yana kallon Amira, saboda shigar da tayi, cikin jarumta irin ta Maza ya dake yace "baki da kunya ko, ke ba'a gayamiki magana kiji ko? Kike ce mata Shashasha, ke akwai babbar shashasha ma sama da ke? Ke ba'a kalleki ance miki shashasha ba kece me dogon bakin ce nata Shashasha ko? Kika bari na kuma jin Magana makamanciyar wannan kin gayawa mata ta sena ɓata miki rai" Amira tace "Wallahi ni ba shashasha bace" "Ni kike cewa ke ba Shashasha bace?" "Eh ni ba shashasha bace, kuma wallahi ta kuma cemin Karuwa sena nata rashin mutunci, sena maƙure mata wuya na kakkaryata" Imran yace "An faɗa miki Karuwa, ba Karuwar bace? Ina nan har Abuja kika tafi gantali gurin rawa, ki kai hotuna da ƙaton Arne, yana nema ya sa a kulleki, ko duk ƙarya a kai miki? Ga ranar rashin ji nan, kika kuma ce mata Shashasha sena saɓa miki" Tuni idon Amira ya ciko da ƙwalla, ta kalleshi tace "ni idan ka kirani da Karuwa ba yamin ciwo dan ba Kai ka fara ba, Amma idan matarka ta kuma cemin Karuwa wallahi sena mata rashin mutunci" Tai maganar tana zirara da hawaye daga idonta. "A gabana kike cewa zaki ci mata mutunci?" Amira dai ba dan kar tayi ƙarya ba, se tace ciwon zuciya ya kamata, saboda baƙin cikin da take kwasa. "Eh wallahi ta kuma cemin Karuwa sena mata dukan tsiya wallahi" Aikuwa Imran yai kan Amira, ta ruga da gudu tai part ɗinta, aikuwa ya bita ya cinmata a bedroom ɗinta, kan gado ta haye ta tsaya tana masa magiyar "dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba" "Ba dai baki da kunya ba, zanyi maganinki" Ya maida ƙofa ya rufe "wayyo Allah na shiga uku, dan Allah kayi haƙuri" Nan suka shiga wasan zilliya, Amira ta shammace shi ta baya, ta rungumeshi tana "dan Allah kayi haƙuri karka dakeni" Gaba ɗaya se Imran ya rasa nutsuwarsa, yasa hannu ze cire hannayenta daga jikinsa, amma ta sake maƙaleshi sosai, yai ajiyar zuciya yace  "cikani" "A'a ni dai dan Allah kayi haƙuri" "Ai na haƙura, cikani kawai" "A'a wallahi tsoro nakeji dan Allah karka dakeni" "Ai nace ba zan dake ki ba, ki cikani kar raina ya ɓaci"   Shiru tai kuma taƙi cikashi, ya shammaceta ya rabata da jikinsa ya  fizgota gabansa, tai fiƙi fiƙi da ido, kamar wadda ta aikata rashin gaskiya. Imran yace "Allah ya shiryeki" Maimakon ta amsa seta hau tura baki, tana masa wani kallon ƙasan ido. Seda ya shafe wasu seconds yana kallonata, sannan ya bar part ɗin nata. Ita Ihsan zatonta zuwa yai yayiwa Amira rashin mutunci. Amira ta dena fitowa sosai balle ta shiga sabgarsu, saboda ba ƙaramin baƙin ciki suke ƙunsa mata ba. A Kitchen ɗin falo Amira kan shiga ta samo abun dafawa, dan nata Kitchen ɗin ba Komai a ciki, sedai ya ajiye mata a Kitchen ɗin Falo. Gajiya tai da zaman shiru, ta fito Falo da niyyar ɗaukar abun da zata dafa, sedai ta na fitowa gabanta ya faɗi, dan Ammi ce ta zo ita da Minal, suna falo suna hira da Ihsan Imran ma yana falon suna hira. Jiki a sanyaye Amira ta ƙaraso falon tace "Ammi sannu da zuwa, ai ban san da zuwanku ba" Ammi ta kalleta sama da ƙasa tace "dama nace miki na zo dan ke ne? Ko kuma ce miki a kai gurinki na zo? Gurin matar ɗana na zo, ba ke ba" Amira ta sunkuyar da kai tai shiru. "Ki tashi ki bani guri, ki dena wannan sumi sumi da kan, dan ba zaki yaudareni ba, ba zakimin Karuwanci ba, kuma ki tabattar kayanki suna ƙulle, daga yanzu zuwa ko wani lokaci zan iya murƙushe wannan Auren naki, dan ni gaba ɗaya zuriyarmu Babu Karuwai, gara tun wuri ki fara tattara komatsanki, bamu da buƙatarki ba dan Baban Imran ya matsa ba me zeyi dake? Sauran titi" Amira ta sunkuyar da kai, hawaye na ta bin fuskarta. Ihsan tace "Ammi ki gaya mata ke ko taji, se wani rawar kai take a Lallai seta ƙwace Imran" Minal tace "a hakan? Wallahi Yaya Imran yafi ƙarfin haka" Kawai se Imran yaji ba daɗi maganganun da ake mata, se tsiyayar da hawaye take, amma yai shiru bece komai ba, kar yai wani abu da ze tunzura Ammi. Suka ƙarewa Amira cin mutumci, abun mamaki Amira duk wannan tsiwar ta Amira amma haka ta gaza cewa komai. Ta koma ɓangaren ta jiki a sanyaye, ji take kamar ta kira Anty, ko Fa'iza ta gaya musu halin da take ciki a gidan Imran, amma ta danne tai shiru ba ta gayawa kowa ba. Sedai Ranar tayi kwanan baƙin ciki sosai, zuciyarta a cunkushe bacci ya ƙauracewa idonta, saboda ɓacin rai, ga ƙiyayyar miji da kishiya, gata mahaifiyarsa ita dai gata nan ba wani gatan Kirki. Suna kwance akan gado, Ihsan tana ta zuba taɓararta, Imran yace "My Wife, ina son zan roƙe ki wata alfarma ne" "Ina jinka my own" "Dan Allah ki dena Kiran Amira da Karuwa, kamar yadda ta buƙata duk da nasan ba'a canzawa tuwo suna, bana son yawan kukan da take" Tashi zaune Ihsan tai tace  "Imran me kake nufi? Son ta kake kenan?" "Ko ɗaya, sedai ina tsoron Abba ya gano irin zaman da muke, nasan ba ƙaramin ɓatamin rai ze ba" "Kar ka damu insha Allah ba ze gane ba, a haka harta gaji ta tattara kayanta ta tafi ta bamu guri" Imran murmushi kawai yai be kuma cewa komai ba. Abun mamaki duk san Amira da bacci, amma ya gagareta, tai sallar Asuba, tai addu'oi da karatun Alqur'ani, amma idonta babu bacci, ta koma kan gado ta kwanta ta rintse idonta amma bacci yaƙi zuwa. Gajiya tai da kwanciyar ƙarfe tara da rabi ta fito, ta kama aikace aikace duk dan ta rage damuwa. Ji tayi ana ƙwanƙwasa ƙofar babban falon, taje ta sako hijjabi ta buɗe, Abba ta gani a tsaye hannunsa riƙe da wayarsa. Murmushi Amira tai tace "maraba da babban baƙo" "Yawwa Amira, in shigo?" "Shigo mana Abba" Tai masa iso zuwa falon, tace  "Abba jiya su Ammi suka zo, ya akai baku zo tare ba?" "Ai ni jiya bayan sallar isha'i na sauka, kuma naji Lallai ina son in zo inganku, nace bari inyi sammako dan anjima ma ina da gurin zuwa" "Masha Allah sannu da zuwa, ya su Ammi sukaje gida" 'lafiya ƙalau, ina Imran ɗin da abokiyar zamanki?" "Yana ɓangaren ta, ina ga basu tashi bane" Abba ya kalli idanun Amira da ke kumbure yace  "ina fatan dai lafiya ba wata matsala?" "Ba matsalar komai Abba, se kewar Anty Nafisa da su Anty Fa'iza na" "Lallai kinji daɗin zaman Gidan Hashim, ita ma tana kewarki sosai" "Gaskiya naji daɗin zaman Gidan sosai, ta na da kirki, ta kula dani kamar 'yar da ta haifa" "Ai na samu labarin hakan, nima nyi farinciki sosai" "Abba bari in musu magana, su zo ku gaisa" Amira ta miƙe ta shiga part ɗin Ihsan, ta na ta addu'a, Allah karya sa taga abun da ze sata kuka. Da sallama ta shiga falon, Imran ya amsa tace masa "Ina kwana" "Lafiya ƙalau" "Gaskiya My, kai nata magana ta dena shigomin, akan me se ina buƙatar keɓewa da kai zata dinga faɗomin ɗaki" Ihsan tai maganar tana kwaɓe fuska. Dama Amira a ƙule take da su tace "dalla rufemin baki, kina magana da baki kamar an yaga tsumma, uwar me zanzo gani ko yi a part ɗin naki, daƙiƙiya jahila, in kun ga dama ku zo falo Abba ne ya zo" Ai Imran yana jin haka ya miƙe da sauri, cike da fargabar Allah yasa ba gayawa Abba tai irin zaman da suke ba, ya zari jallabiyarsa da sauri ya zira ya fito. Amira kam komawa gurin Abba tayi suka cigaba da hira, Imran ya fito yana kallon fuskar Abba ko ze gano wani abu a fuskarsa. Se dai Abban na ganinsa yai murmushi yace "Sannu ɗan hutu, ace har yanzu baka tashi ba?" Ɗan sosa ƙeya Imaran yai yace "Abba sannu da zuwa" "Yawwa, ya gidan ya Iyalan naka?" "Duk suna lafiya ƙalau Abba" "Ina ɗaya 'yar tawa ban ganta ba?" Imran yace "yanzu zata fito" Amira ta miƙe ta cigaba da shirin haɗa breakfast. Da ƙyar Ihsan ta danne zuciyarta ta fito, dan haushin Abba take ji sosai yake ƙular da ita. Ta ƙaƙalo murmushin dole, ta fito ta gaisheshi. Abba yana shirin tafiya, Amira tace lallai seya tsaya ya karya, seda Abba ya tsata ya sa albarka, saboda ya riga ya karya a gida, ranar su Imran ma Abincin Amira suka ci saboda idon Abba. Abba ya tashi ze tafi, Amira taje ɗakinta ta ɗakko turare me kyau, ta saka a wata 'yar jaka ta biyo Abba da shi. Ta tarar da Abban da Imran a jikin motarsa, yana masa Nasiha. "Abba ga wannan ka fesa" Abba yai murmushi yace "duk wannan nawa ne?" "Abba ba yawa" "To Nagode, Ubangiji Allah yayi Albarka, ina fatan dai babu wata matsala ko?" Amira ta kalli Imran sannan ta kalli Abba ta girgiza kai. "Amira bana son ɓoye ɓoye, naga kina kallon Imran, idan yana miki wani abun da ba kyajin daɗinsa ko yana muzguna miki ki gayamin" Ƙwalla ce ta taru a idon Amira, amma ta daure tace "ba abunda yakemin Abba" Abba ya kalli Imran a ɗan hasale yace "Anya Imran ba wani abu kake wa Yarinyar nan ba? Nifa ban gamsu da amsar da ta bani ba, Imran kaji tsoron Allah, in kasan cutar min da ita kake gara a nemi mafita da wuri, kar mu sake wani laifin" Inda inda Imran ke neman farayi, Amira tace "Abba ka dena yi masa faɗa, ba abunda yaimin fa, ni kawai haryanzu 'yan gidanmu sunƙi zuwa" "Anya Amira, wannan ne kawai ze sa inga damuwa a fuskarki, ki gayamin gaskiya" "Abba Gaskiya na gayamaka Abba, ba abunda yaimin na rashin daɗi, ina kewar 'yan gidanmu ne kawai" "To shikenan, na yadda da abunda ki ka faɗa, zamuyi waya da su Insha Allah, za'a ga yadda za'ayi" Amira tace "Nagode Abba, a gaida su Ammi da Minal" "Za suji insha Allah" Imran yai mamakin yadda Amira ta rufa masa Aisiri, Abba ya tsare shi ya cigaba da yi masa Nasiha. Amira kam ciki ta koma, ta cire hijjabin jikinta, ta fito a skin tied jeans ɗinta, vest ta tsefe kanta, ta haɗa da attach ɗin tai parking gashinta, ta zo tana tattare kayan da aka ɓata na Abinci, ta zuba ruwa tana mopping falon. Ihsan na fitowa ta kalleta ta ja tsaki, Amira ta rasa dalilin da ya sa Ihsan ba ta son zaman lafiya, ko bata kula ta ba se ta nemi abunda zata takale ta da faɗa, shiru Amira tai Mata ta cigaba da abunda take. "Dama aikin wanke wanken kika je kika fara a gidajen masu kuɗi, dan kinfi da cewa da hakan, dan ƙarshen karuwa ba kyau ne da shi ba" Amira girgiza jikinta tai tace "Ke aka ɗaukeni aiki a gidan masu kuɗi ai akwai gwarama, yadda mijinki ke sakin baki ya kalla suma haka zasu saki baki su kalli kaya, mussaman idan matansu irinki ne, aba a jingine kamar allo, ke ba fasali ba ba shape ba, ai duk namijin da ya auri irinki sedai haƙuri da maleji, dan baki da maraba da maza" Aikuwa Ihsan ta ƙule tace "Eh na naji, amma na fiki kima a idon miji, duk da ni me kamar mazance Karuwa kawai" "Da ubanki na fara, shiya koyamin" Buɗe baki Ihsan tayi, ta fusata ainun, maganar da Amira ta daki ranta, ta rasa abunda za tayi, kawai taje tai ball da Ruwan mopping ɗin Amira, tace "karki ƙara zagarmin Uba, Uba na ya mutu ba sa'anki bane, kuma Ubana ba mazinaci bane" Amira ta kalli yadda tai mopping amma Ihsan ta kwarar mata da ruwa a gurin, Amira tana damuwa da gyaran falon nan, saboda kana shigowa shine a farko kan ka shiga in da kowacce su take, tun da Amira tazo Ihsan ta dena gyara falon, Amira ce keyi, Amma ta zubar mata da ruwa agurin. Amira tace "can ta matse miki, ina sake miki kashedi ne, duk randa haƙurina ya ƙare sena koya miki hankali, kina kuma cemin Karuwa da ubanki na fara yi, idan kin son sa ki dena gayamin, idan baki dena ba kuwa wallahi baki fini baki ba, banda ma nayi sanyi ke kin san wace Amira, ɗaga muku ƙafa kawai nake, Amma wallahi da rigimata seta hanaku sukuni a Gidan nan, shi Ya sani ai, kuma wallahi daga yau na dena shiru, dai dai nake da ku" Imran ya shigo yace "to kaji sarakan faɗa, ke Amira kullum bakya iya zama sekin nemi Magana ko?" Ta kalleshi up and down tace "eh dayake nice Sheɗan ba, dole kace min ina neman faɗa, to bani na fara ba, ga ƙaramar ibilishiyar da ta tsokaneni nan" Ihsan ta fashe da kuka, tace  "Imran zagin mahaifina tayi tace mai mazinaci, Ubana da yake binne ya mutu, me yayi mata zata zagarmin uba, tace masa mazinaci?" Kalmar ta daki Imran yace  "Mazinaci kuma?" Ihsan ta jinjina kai alamar eh. "Amira waike wace irin banza ce? Saboda rashin daraja, da rashin sanin kimar iyaye ki kira uban wata Mazinaci?" Girgiza kai Amira tayi tace "Captain kayi bincike mana, ni me tacemin na gaya mata haka? Kuma ni ban.... "Shut up i know you can do more than that, wulaƙancin naki har kan iyaye, mara Kunya fitsararriya, ke kina da bakin  kiran Mahaifin wata Mazinaci, bayan baya raye, kece Ma.. "Shut up Imran, wallahi karka soma kirana Mazinaciya, na yadda dan ancemin Karuwa matsalarku ce, amma wallahi ka kirani Mazinaciya sekayi mamakin abunda zan aikata, kun fara ƙureni haƙurina ya ƙare, za'ayi irin zaman da kuke so, kuma wallahi idan matarka bata kiyayeni ba sena mata illa wallahi" Ta ƙarasa Maganar tana hawaye, harta juya zata tafi, ta kalli Imran ta kalli bokitin da Ihsan ta zubar mata da ruwan mopping, ta ɗau bokitin ta jefawa Imran shi a ƙirjinsa tana huci, a ƙoƙarin ta na samun sanyi daga raɗaɗin da zuciyarta ke mata. Tofa! Share Please A gaskiya ba zan iya gayamuku farincikin da nake ji da Comments ɗin da kuke ba, ina godiya sosai da sosai, Allah ya bar zumunci, Comment ɗinku na sani nishaɗi. Ga masu san shiga group na RUƊIN ƘURUCIYA, You can subscribe it for ₦300 only. Shima nasa salon daban ne, don't miss it. Ayshercool 07063065680 [2/2, 4:25 PM] Ayshercool:               🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                                                 35_36 Saroro Imran yai yana kallon Amira, da tuni idanunta su kai ja, ta juya ta koma part ɗinta zuciyarta na wani Mugun tafasa. Duk da jifan sa da Amira tayi da bokiti, ko gezau be ba haka bokitin ya daki ƙirjinsa da ƙarfi ya faɗi. Ihsan zuba ido tai ta ga Iya abun da Imran ze, ta ga matakin da ze ɗauka akan Amira, amma taga kawai yai waje ba tare da yace komai ba ko ya ɗau wani mataki ba. Mamaki ne ya cika Ihsan, wai kenan Amira taci bulus? Me Imran yake nufi da ƙyale Amira ba tare da wani hukunci ba? Ta masa wannan fitsarar har da duka amma ya gaza ɗaukar mataki? Amira kam seda tai ƙaramin hauka a ɗaki ita kaɗai, gaba ɗaya ta fita hayyacinta saboda kuka, ta zama kamar wata wadda ta daɗe ta na cuta, idanunta suka kumbura su kai jawur saboda kuka. Haka tai me isar ta ta haƙura, ko Abincin rana kasa ci tayi saboda yadda take jin zuciyarta. Imran kuwa bayan fitarsa Khalid ya kira shi a waya, kamar ya share kiran kar ya ɗaga, seda ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. "Malam wai baka kusa da wayar ne da se da ta kusa katsewa sannan zaka ɗauka, ko duk matan ne suka ɗauke maka hankali?". "Ƙyaleni kawai Khalid, suna neman su maida ni mahaukaci ne kawai". "Mahaukaci kamar Yaya?" "Wai dama haka Auren mata da yawa yake? Kullum cikin faɗa da tashin hankali, yau ni Amira ta jefawa bokiti a ƙirji, ni nama rasa me zanyi, dan idan nace zan dake ta rainani zata yi kawai, kuma zan iyayi mata illa, dan duka zan mata na gaske" Khalid yace "Subhanallah, wai haryanzu Amira ba tai hankali ba kake nufi?" "Ina Wannan yarinyar za tai hankali, kullum cikin faɗa kamar dage, ba afuwa a lamarinta kullum cikin neman rigima". "A'a Imran, haka kurum ba zata nemi rigima ba, me a kai mata ta nemi rigima, ka dinga mata adalci fa" "Kaga dan Allah ƙyaleni, karka ƙara tunzurani, dan tunanin hukuncin da zan mata nake" "Wane hukunci, ai tunda ba ka hukunta ta a lokacin ba kawai ka manta, kayi haƙuri ya wuce kawai". "Saboda rashin mutunci, ta min laifi kuma in ƙyaleta?". "Kai me kai mata tai maka hakan?" Tsaki Imran yai yace "ka ga, kiran me kayi min ne?" "Dama kira nayi inji lafiyar ka, sannan ka kalli News ɗazu da safe kuwa?" "A'a ban kalla ba, ni ban ma gaya maka ba, ɗazu Abba ne fa yazo yana tafiya suka fara rigima, abun da ya bani mamaki ne wuce yadda Yarinyar nana ta rufamin Asiri a gurin Abba ba" "Asirin me ta rufa maka?" "Nifa tun da ta tare, ba abunda ya haɗani da ita, ko ɗakinta ba na zuwa" Khalid yace "tirƙashi amma ba ka da Imani Imran, wallahi ba ka kyautawa kanka ba" "Khalid look, Yarinyar nan da a nutse na Aureta, zan iya haƙuri in zauna da ita har wani abu na auratayya ya haɗani da ita, amma to be sincere, ina jin takaici idan na kalli Yarinyar nan na tuna abubuwan da tayi, kuma ace mata ta ce, raina ɓaci yake" "Imran waye ya gaya maka ana Jihadi cikin sauƙi ne, yanzu an samu ta nustu ta zauna a gidanka ba yawo, ba komai kana ganin rashin kula da ita ɗin nan baze sa ta koma kan laifin da take a baya ba?" "Wai da Aurena tayi gantali?" "Ƙwarai kuwa" Khalid ya bashi amsa. "Wallahi da sena kasheta" "Sannau uban marasa hankali, ai seka kashe ta ɗin, kai baka sauke nauyin da Allah ya ɗora maka ba, saboda wani usless excuse ɗinka ba, za ka wani cika baki, back to business, kace ba ka kalli News yau ba ko?" "Eh ban gani ba, mene yafaru?" "Our heroes are killed in the yesterday operation, more than 30 of them were killed, and some of them were injured" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, may their Souls rest in Jannatul firdausi" "Ameen, abun ba daɗi sosai, so You have to get set, Komai ze iya faruwa" Imran yace 'ai kullum a cikin shiri muke, ko mu kashe ko a kashemu, Allah ya bamu zaman lafiya a ƙasar nan" "Ameen ya Allah, se anjima zanyi wani aiki ka gaida matanka" "Hmm se anjima". Imran ya kashe wayar yana jinamin labarin da Khalid ya ba shi na  kisan da akaiwa sojojin, a fafatwarsu da 'yan ta da ƙayar baya. Imran be koma musu gidan nan ba se da yai sallar isha'i. Daya dawo ƙofar part ɗin Amira a rufe, ya tafi ɓangaren Ihsan, ya tarar da ita a bedroom fuskarta babu walwala sam, dan da ƙyar ta amsa masa sallamar da yai.. Be kulata ba ya shirya ya shiga wankansa, ya fito ya sanya kayan baccinsa, yana ƙoƙarin kwanciya. "Wai yau a ina ka wuni ne?" "Kin aike nine?" "A'a amma gani nai ba haka kake ba" "To ya zanyi, idan ba haka nake ba yanzu na fara, ku kenan kullum cikin faɗa da ɗagmin hankali naras wace me gaskiya wace mara gaskiya, kuma idan Amira na da fitina wasu lokutan kece kike tsokanarta, kuma seda na miki kashedi akan shiga harkarta" "Wane irin shiga harkarta nai, ita wanan se an shiga harkarta take abunda take? Taci mutuncin mahaifina ta buga maka abu amma ka ƙyaleta ba abunda kai mata" "Me kike so in mata, in bita in ta duka, ba kiga ni abunda tamin na rufin Asiri ba yau? Ke da ta gayawa Abba abunda ke faruwa Allah kaɗai yasan abun da zemin, shiyasa na ƙyaleta" "Yanzu dai kana nufin taci bulus kenan ko?" Tsaki Imran yai yaja bargo ya rufe jikinsa ya lumshe idonsa, bin Imran tai da kallo, wani mugun haushinsa ya mamayeta, itama kwanciya tai ta juya masa baya, dan tayi alƙawarin wannan karon ba zata lallaɓashi ba. Washegari ya kama ranar da Ihsan zata fara zuwa gurin da za tai service, mass communication ta karanta, dan haka zata fara aiki a wani gidan Jarida, ko saurarar Imran ba tai ba, tai breakfast tai ficewarta. Imran ma kintsa wa yai ya fita, ba tare da wani da ga cikinsu yaiwa Amira sallama ba. Rashin abunyi ya dami Amira, ta tashi ta sauke kayan wardrobe ɗinta gaba ɗaya ta sake shiryawa, ta sassauke kayan Kitchen ɗinta, suma tayi rearranging ɗinsu, ta fito nan babban falon ma, ta gyara ta kunna turaren wuta, tai girki iya cikinta wajen ƙarfe sha biyu ta kammala komai tai wanka ta fito falo ta zauna. Ta kunna tv tana kallo, jin ƙarar buɗe gate tayi, ba ta motsa ba ta cigaba da kallonta, babu jimawa aka fara knocking ƙofar falon. Tana ji tai Banza taƙi buɗewa, se kuma can ta miƙe ta tafi ta buɗe. Imran ne a tsaye, ya kalleta yace "kina ji ina bugawa amma kika ƙi buɗewa?" "Da can Ni nake buɗe maka? Naga ko ka saka key ka buɗe ko matarka ta buɗe maka" ta juya ta koma falon tana cigaba da mita. Doguwar rigar material ce a jikinta pink me adon baƙi, kanta ba ɗankwali ta koma ta nemi guri ta zauna, Imran yabia bayanta da kallo harta je ra zauna, ba shi da lokacin Amira a yanzu, dan haka be bi takan abunda ta faɗa ba ya wuce. Tana kallonsa ya kai ya kawo, ya shiga Kitchen ɗin falo ya haɗo cornflakes ya zo ya zauna ya na ci, da alama yunwa yake ji, ƙila Matar son ba ta bashi Abinci ba yau, Amira ta faɗa a zuciyarta. Ya kammala ya ajiye kofin a gurin, ya tashi ze tafi. "Gaskiya ku dena cin Abinci kuna barmin a falo, nifa ba baiwarku bace ehe, in ba haka ba wallahi aka kuma cin Abinci aka barmin a Falo sena jefe kwanon waje" Waiwayowa Imran yai ya kalli inda Amira take, ya dawo da baya yazo ya zauna a kujerar da take, ya ƙura mata ido. Seda ƙirjinta ya buga, dan wani Mugun kwarjini yai mata, da harya sa ta ɗan tsorata. "Meyasa kika rainani ne?" "Ni ba raina ka nai ba, naga baka buƙatar haƙurin da nake ne, shiyasa nake son inyi irin zaman da kake so" "Ni kike gayawa haka?" "Aini kullum ko nayi laifi ko ban ba a gurin ka laifi nayi, kuma nice mara Gaskiya, gara duk abun da yazo raina in faɗa maka, in yaso in ka ga dama ka kashe ni ka huta, tun da matarka bata laifi seni, kullum idan abu ya haɗamu se ka goyi bayan ta, gara in gaya maka duk abunda ya zo zuciyata, in yaso ka maidani in da kaje ka ɗakkoni" Imran ya ƙara ƙureta da ido yace "Mata ta bata laifi ai, ko baki san kuna da banbanci ba, ba zan taɓa goyon bayanki ba, saboda ba kya ji sam, kinga illar rashin jin magana kenan, da tun a baya baki saba da fitina da rashin ji ba babu yadda za'ai a dinga baki rashin gaskiya, ina son matata sosai shiyasa na Aureta, ke kuma saboda ki dena rashin ji na Aureki, amma saboda tsabar rashin mutunci, har kike zagarmin Mata, kuma kike min rashin kunya ko? Saboda samun guri harda kuka dan na rungume matata, kin fiye rigimar gangan" "An zageta ɗin, wallahi ta kuma ɓatamin rai sena mata rashin mutunci wallahi, in ba tai wasa ba sena mata illa, kuma ba runguma ba ka maida ita cikin ka ba abunda yaimin zafi" Imran yana mamakin yadda Amira ke Kishi akansa, shi dai yasan ba'a kishin abu se ana sonsa, ya kasa gane inda Amira ta dosa. Imran ya ƙara kallonta yace "Ƙarya kike, Kishi ke damunki, kuma bazan dena rungumeta ince ina sonta ba, kiyi mata illar kiga yadda zanyi dake, duk Matar da tai rashin ji a lokacin 'yan matanci ba ta taɓa daraja a gidan Aurenta, abun da a kaita nuna miki kenan kika kasa ganewa, darajar kamilar mace daban yake da wadda ta kasa tattalin kanta, dan haka karki sake haɗa kanki da Ihsan" Amira ji tayi kamar Imran ya zuba mata garwashi a zuciyarta, nan da nan ta shiga sana'ar ta ta kuka, ta kalli cikin idon Imran, kawai ta fashe da kuka. "Baka da adalci, wallahi se Allah ya sakamin abun da kake min, na barka da Allah" "Ni kike cewa kin barni da Allah dan nace ina son mata ta?" "Na faɗa na faɗa! Mara adalci bayan dukan da kamin ana gobe zaka Aureni, ka ɗau matarka kuka tafi lagos wata biyu, na tare a gidanka kana cigaba da muzgunamin kai da matarka, wallahi se Allah ya sakamin, Allah yana kallonka!" Tai maganar tana kai masa duka ko ta ina a ƙirjinsa, ta haukace masa, riƙe hannunta yai gam, saboda yaji zafin maganganunta, da tace ta barshi da Allah, cikin haɗe rai ya murɗe hannayenta biyu. Wani marayan Kuka Amira ta saki, tare da lumshe idanunta hawaye na Zuba ta gefen idonta. "Wallahi kika kuskura kikamin Allah ya isa, se na nuna miki soja kike Aure ba civilian ba, Shashasha mara hankali" Ya saki Amira ta zube a gurin nan, "Na barka da Allah, Allah ya sakamin, Mugu Azzalumi wanda baya tsoron Allah, Allah ne gatan maraya kuma insha Allah seya nuna maka ka taɓa marainiya" Jin maganar Amira yai ta dira a zuciyarsa, dan gaba ɗaya mantawa yake Amira marainiya ce, be juya ya kalleta ba, ya wuce part ɗin Ihsan. Ko da ya shiga ɗaki shiru yai yana lissafa abubuwa a ransa, yana tausayin Amira, amma ita bata tausayin kanta, bakinta da tsiwarta ke ƙular da shi, ko da zuciyarsa ta karaya a kanta, yana son ya ɗaga mata ƙafa, amma da ya tuna Karuwa ce se yaji a duniya babu wadda ya tsana sama da Ita. A haka Ihsan ta dawo gida ta tarara da Imran, dama daren jiya ba Magana suke ba, ya shareta itama ta share shi, amma dai ta fuskanci kamar wani abu yana damunsa. Ta shiga Kitchen ta fara ƙoƙarin ɗora girki, amma still Imran be kulata ba, sema tsunduma da yai a kogin tunani. Se ƙarfe Uku ta gama girkin, ta sameshi a ɗaki tace "ga Abinci can na kai maka dining" 'na ƙoshi" shine abun da yace mata, ya tashi ya fice. Da ya fito Falo ƙofar sashen Amira ya dinga kalla, juya wa yai ya fice daga gidan gaba ɗaya. Abubuwan da Imran keyi sun fara bawa Ihsan mamaki, alamu sun fara nuna kamar Amira ta fara tasiri akan sa, idan ba haka ba ya za'ai ta masa abunda tai masa kuma ya ƙyaleta be ɗau mataki ba. Wayarta ta ɗakko ta kira Mummynta. Mummy na ɗagawa cike da damuwa Ihsan tace "Mummy akwai matsala fa" "Matsalar me kenan?" "Mummy, gani nake kamar Imran ze saɓa alƙawarin da yaimin, jiya yarinyar nan baki ga abunda tai masa ba amma ya ƙyaleta, kuma ya ɗau fushi dani, na bashi Abinci yaƙi ci, nima watsar da shi zanyi ba zan iya ba, mutum se baƙar zuciya tsiya" "Ni ban gane ba, me tayi masa ne?" "Faɗa mu kai da ita, ya shigarmin ta buga masa bokiti a ƙirjinsa amma ya ƙyaleta, dama jiya babansa ya zo, yana ta ƙara nanata masa wai yayi adalci, ni gaskiya bazan yadda in haɗa miji da wannan jakar ba" "Idan ba zaki yadda ki haɗa miji da ita ba, ai ta ƙwace shi ta barki, ke da wannan zaune a gidanki zaki yi watsi da mijinki, dama abunda take so kenan, to maza kiyi watsi da shi karki janyo shi ki tattala shi, ni na rasa meyasa baki da wayo wasu lokutan, ki manta da lamarinta ki kama mijinki gam karki ba da wata dama daze kalleta" "Mummy, kinga shigar da take tana yawo a gida kuwa?" "Ke ma meya hana kiyi, a banza a waje tabi mazan wasu ina ga wanda aka ɗaura musu Aure? Muna nan muna ƙoƙarin ganik yadda zamuyi, kawai ki cigaba da haɗasu faɗa da ita, kuma ki kame shi sosai ki riƙe shi sosai" "Shikenan Mummy nagode" "Yawwa ki gaishe shi" *To zeji" Ta ajiye wayar tai shiru tana tunani akan maganganun Mummy, yanzu haka za ta cigaba da bin Imran, yana mata wulaƙanci wasu lokutan, dole tayi yadda za tai ta cigaba da haɗa gwaramar da za'a kori Amira, ko a raba musu gida gaba ɗaya,in yaso ta riƙe Imran ta hanashi zuwa inda Amira take, a haka har ta gaji ta kama gaban ta. A mira kuwa tana tsaka da kukan ta sega wayar Yadikko, abun ya bata mamaki ƙwarai, nan da nan ta goge hawayenta ta ɗaga wayar tai sallama. Yadikko tace "wato Amira kin samu duniya kin manta damu" "Haba Yadikko, ya zan manta daku, ni na isa ne, gani nai kamar kum manta dani, Babu wanda ya nemeni, seni na neme ku, shiyasa kawai nima na dena kiran ku a waya" "Hmm ai shikenan, kina nan lafiya kuwa?" "Sumul ma kuwa, baki ga yadda nai ƙiba ba, ƙalau nake" "Ya kishiyarki kuma da mijin naki?" "Lafiyar mu ƙalau Alhamdilillah" "Kuma yanzu Imran ɗin yana sonki?" "Dama ya taɓa ce miki baya sona ne? Yana son abarsa lumui muke zaune" "Hmm ai shikenan, ai yaron nan ya banu mamaki, duk abun da ya dinga miki, kuma se gashibya Aureki kuna zaune" "Eh, haka lamarin Allah yake" Yadikko tace "dama zamu zo ganin ɗakinki ne, zamu zo garin Kaduna" Cikin Amira ya bada ƙuuuu, tace "Aikuwa zamuyi tafiya ni da Captain, sedai in mun dawo" "Yaushe zaku tafin?" "Very soon, sedai in mun dawo" "To shikenan, idan kun dawo ɗin seki sanar mana" "To shikenan Yadikko, kice Usaman ya turon account lambarsa in turo masa kuɗi a sai miki kaza" "Ahh har kuɗi yake dunƙulewa ya baki kenan?" "Ƙwari kuwa, Kuɗaɗe ma ba kuɗi ba, a turomin zan tura kuɗi a sai miki kaza ki more tsufanki" Yadikko tace "to madalla, ai na ɗauka an manta dani gaba ɗaya" "Haba dai ni na isa, a gaida kowa da kowa" Yadikko na katse wayar tace "tsinanniyar Yarinya, Allah ya kawo sanadin da za'a sakoki, makirar banza yana can tana hutawa, ku nemomin Usaman yazo a turo kuɗin, raba arne da makami ai ibada ne" Umma tace "wai dagaske Yadikko zuwa gidan nata zakiyi?" "Ƙwarai kuwa, se naje naga ƙwal iwar daka". "Aikuwa ma biki, muma muje muga tsiyar da take ci take hura hanci tana fafa" Yadikko tace "ai ko bangon duniya zauje su dawo, se naje gidan Amira na gano" Amira kuwa ido ta zubawa wayar, tana tunanin idan su Yadikko suka zo suka ga irin zaman da take shikenan zasu zuba ruwa a ƙasa su sha ne dan murna. "Allah ka kawomin ɗauki dan alfarmar shugaba Sallallahu alaihi Wasallam" Ta miƙe ta gabatar da sallar la'sar, ta zauna tai Addu'oin ta da azkar, sedai still zuciyarta babu daɗi, ta rasa yaushene ita ma zata samu farinciki a rayuwarta. Gaba ɗaya ta gaji da zaman Gidan Imran, ji take kamar a kurku take, ba walwala ba abokin hira, ga wulaƙanci da cin fuska da take fuskanta, gaba ɗaya taji zaman Gidan ya isheta, babban falo ta dawo ta kwanta, ta kunna TV, sedai sam hankalinta ba' kan TV ɗin yake ba. Imran restaurant yaje ya cika cikinsa, sannan ya nufo gida, yana tafe yana tunanin maganganun Amira da tace "ta barshi da Allah" tabbas ya gaza kamanta adalcin da ya dace Ihsan ta fito tana wani yatsine yatsinen fuska, kallo ɗaya Amira tai mata ta ɗauke kai, dan a ciki take da Ihsan, jira take tace mata tak, ta yaga ta. Aikuwa seda Ihsan tai Magana "malama nan fa ba filin gala bane da zaki ƙure mana sautin kiɗa a gida" Gyra kwanciya Amira tayi, ta cigaba da kallon TV, banda neman tashin hankali irin na Ihsan da rashin son a zauna lafiya, Music ɗin ƙasa ƙasa yake tashi, shima a cikin film ne aka sako waƙar, amma ta tsaya tana neman faɗa. Dama Amira ƙiris take jira, ga haushin Imran a ranta ga Ihsan na ƙoƙarin tunzurata. Ihsan kawai ta ɗau remote ta kashe TV, Amira ta miƙe tsaye tace "meyasa zaki kashe min TV" "Saboda nan ba gidan magajiya bane, kuma ba gidan Gala bane, gidan mijina ne" "Ni kuma daga yau zan maida shi gidan galar, na gaya miki karki ƙara shiga sabgata" Amira ta sa hannu ta fizge remote ɗin hannun Ihsan. "Wallahi ba za'a mayar min da gida na gala ba" "Tun da mijinki ya auri 'yar gala, dole ayi gala a gidan nan" Amira ta kunna TV, ta na komawa ta zauna, Ihsan ta kuma kashe TV tace "in kina da zuciya, ki koma in da kika fito gidan karuwai, kiyi a can" Ai Amira yadda ta kawo wuya, idonta har rufewa yake saboda ɓacin rai, tana tashi ta janyo wuyan rigar Ihsan, tai jifa da ita tsakanin kujeru. Wani uban Ihu Ihsan ta saki, ganin bakinta na zub da jini, Imran da ke ƙoƙarin rufe mota a gigice, ya nufo falon hankali a tashe jiyo kururuwar Ihsan. Yana shigowa ya tarar da Ihsan a durƙushe, baki na zubar da jini, Amira na tsaye ta na huci. Imran ya ƙarasa in da Ihsan take da sauri, ya ɗagota bakinta yai jawur yana jini, ga goshin ta ya kumbura. Amira tace "wannan kaɗan kenan kika gani, ki kuma buɗe baki gayamin baƙar Magana wallahi sena tattakaki a gidan, sena watso miki haƙora waje. Imran ya dinga goge mata jinin dake bakinta, ya kalli in da Amira take, idanunta duk sun kumbura, da alama ta daɗe tana kuka ne. Maganganun ta suka kuma dawo masa na tabar shi da Allah, jikinsa ya kuma yin sanyi musamman da ya tuna yadda ya mirɗa hannayenta ɗazu ta dinga zubar da hawaye, girgiza kai kawai yayi yaja hannun Ihsan zuwa sashin ta. Suna zuwa bedroom ɗinta ya saki hannunta ya kalli Ihsan yace "meya haɗaki faɗa da ita har tai miki haka?" "Ai mema ya haɗamu kake tambaya? Ba zaka ɗau mataki ba, kalli bakina da goshina amma ka tsaya kana kallonta, wai me kake nufi ne?" "To me kike so inyi, ya kike son in yi ne? In bita in ta duka Ihsan? Kokuma in ta faman ɗaga murya saboda na Auri mata biyu, kamar a kaina aka fara aure, na miki kashedi na miki jan kunne akan karki dinga shiga sabgar Yarinyar nan Amma kin ƙi ji, ki cigaba da biye mata watarana seta miki lahani" Ya juya ze fice, hawaye shaɓe shaɓe a fuska Ihsan tace "yanzu kana nufin ta daki banza kenan? Banda zagi na da cin mutumci na iyayena da take, yau har da duka amma ba za ka ɗau mataki a kai ba" "Ihsan na gaji da halinki na yawan ƙorafi, ke kullum cikin yi miki laifi ake, an tired na gaji da wannan yawan ƙorafin naki, she's also human being, ba zan ƙare kullum cikin shigar miki faɗa tana rainani ba, in kinga dama ki cigaba da shiga sabgarta ranar da ta karyaki kyayi bayani" Imran ya juya ya fita yana huci, fashewa da kuka Ihsan tayi ta ɗakko wayarta, lambar Ammi ta nemo ta kira. Ammi ta ɗaga wayar tare da yin sallama, kuka Ihsan ta saka hadda sheshsheƙa. "Subhanallah, Ihsan lafiya kuwa?" "Ammi na gaji, na kasa gane inda Imran ya dosa, matarsa ce ta dakeni, baki ga bakina ba kuma ba matakin daya ɗauka, Ammi na fara jin tsoron ko wani abun tayiwa Imran, da ma na ganta tana binne wani abu rannan, Ammi dan Allah kiyi wani abu" "Amiran ce ta dakeki?" "Wallahi Ammi duka na tayi, har da fasan baki" "Kina me kika tsaya ta dakeki, baki samu abu kin rusa mata a ka ba, saboda wulaƙanci, gani nan zuwa gidan naku, shima Imran ɗin ze gauraya dani, gani nan zuwa" Ihsan ta ajiye wayar tace "wallahi ba zaka maida ni 'yar iska ba, da mahaifiyarka zan dinga haɗaka, har seka rabu da wannan banzar" Amira kuwa zamanta tai a falon, ta cigaba da kallon TV, labarai take kallo, taga yadda ake sanar da kisan sojoji a daji, da irin wahalar da suke sha a daji, gaba ɗaya ko motsi ba tayi, ta ƙurawa TV ido, ba zato ba tsammani taji Imran ya janyota daga kan kujerar . Kunnenta ɗaya ya riƙe yace  "ban gayamiki bna son rigima a gidana ba, ko nan yai miki kama da gurin dambe da zaki daketa, dan kinga kinfi ƙarfinta ko? Kin manta dukan da nai miki kenan kina son in sake Miki wani kenan?" Shiru Amira tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa, "idan kika kuma yunƙurin dukanta, ko makamancin haka sena rama mata, kin saba dambe da hauma haumarki a waje to ni ba zakimin a nan ba, na gaya miki" Ya dungurar da ita a gurin, ya miƙe ya juya ze fita, kawai yaji sheshsheƙar kukanta, har yaje bakin ƙofa ya juyo ya ganta zaunia gurin, tana kuka girgiza kai kawai yai ya fice. Seda akayi sallar magariba sannan Amira ta tashi ta koma ɓangarenta. Tana nan kwance takaici yana nuƙurƙusar zuciyarta, Hasbunallahu wani'imal wakil kawai take maimaitawa don samun sassauci a ranta. Ihsan ta gani a kanta ba zato ba tsammani, ɗaga kai tayi ta kalli Ihsan. "Kin zata kin dake ni kim daki bulus ne, ai wallahi gidan nan ko da tsiya se kin barmin gida, kije uwar masu gidan tazo da kanta, dan in tabattar miki da na fiki power a gidan nan" Seda ƙirjin Amira ya buga, jin Ammi ce ta zo gidan, Ihsan ta juya ta fice daga part ɗin. Amira ta miƙe ta sanya hijjabi ta fita falo, ta tarar da Ammi a zaune, Imran na ƙasa a gefe, Ihsan ma haka. Amira tai sallama ta nemi Guri ita ma ta zauna, Ammi ta kalleta a wulaƙance tace "ai na zata ba zaki fito bane hakima" "Ammi sannu da zuwa" "Rufen baki, ba sannu da zuwanki na zo ji ba, wato kin far fafutukar haɗa husuma a tsakaninsu, hadda duka kin fara gwada halin naki na 'yan tasha, ki Aure mata miji sannan ki dake ta banda binne binnen da kike dan ki rabasu ko? Wallahi ba da  ina tunanin wani abu ba, wallahi da A daren nan zan sa ya sakeki ki koma in da kika fito, 'yar marasa mutunci mara tarbiyya kawai, wallahi da wasa kika kuma gangancin dukan Ihsan seya sakeki, kuma yanzunma ba haƙura nayi ba se na kashe Wannan Auren, da ɗana baze zauna da Karuwa ba lalatacciya irinki. Kai kuma, wallahi ko da wasa na sake jin ta daki Ihsan ba ka ɗau mataki ba, ni zan zo in ɗauka kuma sena ci mutuncin ka" "Ammi ya zanyi, kullum cikin tashin hankali suke, Ihsan ta kasa jan girmanta, ta fiye kishin tsiya... "Rufemin baki, ya ba za tayi kishi ba? An Auro Karuwa an ƙaƙabo mata gida? Dole tai Kishi, haka kurum saboda son a sani na Mahaifinka ya ƙaƙabo maka wannan yarinyar, wadda ta gama gantalinta a waje, ta gama bin maza a bariki, ya sa ka Aureta, ai ko ba ta so seta bar Gidan nan, ba zan zuba ido ina kallo a kawomin mugun iri cikin zuriyata ba wallahi" Amira ta ɗaga kai ta kalli Ammi, ta sunkuyar da kai, Imran ransa ya ɓaci da gayawa Ammi da Ihsan tayi, a jejjere A 'yan kwanakin nan baze iya lissafa adadin lokutan da ya ga Amira na kuka ba, shi tsoronsa ma kar wani ciwon ya kamata. Ammi ta wanke Amira da baƙaƙen maganganu da cin mutuncin a gaban kishiya, Amira ta kawo iya wuya, dan zuciyarta raya mata take ta zagi Ammi, in yaso Auren ya mutu da hujja kowama ya huta, amma ta daure zuciyarta taita ambaton Allah. Seda Ammi tayi ta gama, Sannan ta tashi ta tafi, Ihsan ta riga Imran dawowa falon, ta kalli Amira ta kwashe da dariya tace  "a zatonki bariki sekayi Iskanci sannan zaka iyata, wallahi na fiki Rashin mutunci kuma gidane sekin barmin shi da mijina wallahi" Amira ba ta ko ɗaga kai ta kalleta ba, Imran ya shigo ya kalli inda take zaune, ba ta tashi ba, sosai yajiata bashi tausayi, Ammi taci mutuncinta da yawa, amma haka shima ya shareta ya wuce ya barta a gurin. Ihsan ta zaci Imran yana shigowa zasu shirya, sedai taga sam ko kulata beyi ba. "My wai haryanzu fushin kake?" A fusace yace "tambayata ma kike? Idan har Amira zata iya rufamin Asiri ta ɓoye laifina a gurin mahaifina, ke meyasa kikamin haka? Am disappointed on you" "Amma meye dan na gayawa Ammi, na faɗa mata ne dan taiwa tufkar hanci, kar inje ka zagaye ka koma gurinta" Ran Imran ya ɓaci matuƙa, be kuma tanka mata ba ya bar mata ɗakin, ya koma ɗaya ɗakin ya rufe ƙofa. Da Asuba ya fito zashi sallar Asuba, sedai ga mamakinsa ya ga Amira kwance a falon nan inda suka barta, a gurin ta kwana. Seda Imran ya firgita, ya ƙarasa inda take da sauri, sedai yana dubawa yaga  Bacci take, se ajiyar zuciya take. Ya ɗan ƙuramata ido, gaba ɗaya tausayinta ya mamaye zuciyarsa. Tashi yai yaje salla ya dawo, sedai da ya dawo ya tarar ta tashi daga gurin. Wani zazzafan zazzaɓi ne ya rufe Amira, ga ɓacin rai ga damuwa, se rawar sanyi take a ɗaki ita kaɗai. Message ne ya shiga wayar Imran, ana nemansa da gaggawa turasu Zamfara aiki. Nan da nan ya fara shiri, duk da a ƙule yake da Ihsan, yaje ya sameta yace "Ihsan, Anjima zan tafi Zamfara, an turamu aiki" Cikin ko in kula tace "Seka dawo" Abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, duk da sun samu saɓani amma ta kasa nuna a sign of care to him. Amira ji tai sanyi ya dameta saboda zazzaɓin dake jikinta, fitowa tai Kitchen na Falo, dan ta dafa tea ta sha ko zata dena jin sanyi. Imran ta gani sanye a Uniform ɗinsa na Sojoji, hannunsa riƙe da wayarsa ya sata a kunnensa yana Magana. "Wallahi Abba nima cikin dare naga message ɗin, an turamu Zamfara ne kasan last week an kashe sojoji sosai, to ina cikin wanda aka tura, naso in biyo gida in muku sallama, amma an zo ɗaukata zamu tafi ne yanzu" Saroro Amira tai tana kallonsa, dagaske Zamfara ze tafi. Har ze fita Amira ta ƙarasa da sauri in da yake, ta riƙe hannunsa. Waigowa yayi ya kalleta, ya kalli inda ta riƙe hannunsa, ya kalli fuskarta duk cizon sauro fuskar a kumbure. "Wai Zamfara zaka tafi?" "Eh, can zan tafi" ya bata amsa. "Dan Allah kar ka tafi, kashe sojoji ake" Kallon Amira yai, dagaske take maganar, mamaki ne ya cika shi, duk da tarin abun da aka mata, amma tana kiran kar ya tafi, ana kashe mutane. "I was Born to serve my country, ko in dawo a raye ko a kashe ni, just pray for me" Ya kai hannu ya goge hawayen da ke zubowa daga idonta, hakan yasa yaji jikinta da zafi yace "idan na mutu a can forgive me please!" Domin gyara, Sharhi ko Shawara Ayshercool 07063075680 [2/4, 7:37 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                            37_38 Sake fashewa da kuka Amira tayi tace "ni dai ba na son ka tafi" Ɗan shiru yai yana kallonta "meyasa ba kya so na tafi?" "Ana kashe mutane, kuma bana so a kashe ka" Jikin Imran yai sanyi sosai, ya kalli yadda ta riƙe hannunsa, ga idanunta na zubda hawaye. Gyara tsayuwarsa yai, ya ɗago fuskarta, ta na kallonsa, fuskarta duk cizon sauro ga idanunta sunyi jawur" A hankali yace "kin kwana a falo sauro ya cije ki, kinga zazzaɓi ya rufeki, kije ki kwanta zuwa anjima ki kira Anty a waya, a kawo miki magani, zan tafi abokan tafiya ta suna jirana, dan Allah ban da faɗa ko tashin hankali, ni na tafi" Ya zame hannunsa a hankali, ya juya ya fara tafiya, bayansa ta bi da kallo, har ya fita daga falon. Jiki a sanyaye ta koma ta Kitchen, ta leƙa window, ta ga sojoji a harabar gidan jikinsu da Uniform, suka hau mota suka fita. Amira ta zauna a Kitchen ɗin ta haɗa kai da gwiwa tana maimaita 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sun yi nisa a tafiyar, Imran ya kira Anty, tana tsaka da aiki ta ga kiran nasa, amma tai ƙoƙari ta ɗaga wayar "Anty barka da safiya" "Yawwa barka Imran, ya kake ya gida?" "Lafiya ƙalau, ya aiki?" "Aiki Alhamdilillah, mun fito tun ɗazu" "Masha Allah, dama Anty nace dan Allah idan ban takura ki ba, kinga an turani aiki Zamfara ne, kuma na bar Amira ba lafiya, ban san lokacin da zan dawo ba, nace in ba damuwa ko zata zauna a gurinki, kan inga yadda Allah zeyi damu, tunda babu me kula da ita a gidan" Anty tace "Ni da 'yata amma ka dinga cewa in ba zaka takuramin ba, ai gara da ka gayamin inje in ɗakko abata, yanzu Zamafaran aka turaku Imran?" "Wallahi kuwa Anty, kin ganmu a hanya ma" "Subhanallah, to Ubangiji Allah ya tsare mana ku, ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, Amirana kuma Allah yasa rabo muka samu" Imran yace "Rabon me kuma Anty?' "Rabon Baby mana, zan ɗau jika" "Hmmm Anty kenan, ai mana addu'a dawowa lafiya" "Insha Allah zamuyi, Allah ya tsare" "Ameen Anty nagode" Ya katse wayar. Duk da yasan Ammi tana jin haushin sa amma ya kirata a waya, suka gaisa ta amsa masa sama sama, yace "Ammi ina buƙatar addu'rki, ina hanyar Zamfara ne" Ba shiri ta ware murya tace "wace irin Zamfara kuma?" "An turamu aiki ne, na so in biyo muyi Sallama, amma kiran na gaggawa ne, kuma abokan tafiya ta suka zo, shiyasa kawai na taho" Ammi tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, To Imran Allah ya tsare mana ku, ya kiyaye ku, Allah ya dafa muku ya shiga lamarinku, Allah ya dawo mana daku lafiya" tana maganar se hawaye. "Ammina ki kwantar da hankalinki, ba abinda ze faru insha Allah" "Ai hankalina ba ze kwanta ba, se Allah ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare" "Ameen Ammi nagode" Ta ajiye wayar jikinta a sanyaye, Minal ta shigo ɗakin Ammi ta ganta wani iri, tace "Ammi meya sameki naga kamar kinyi kuka?" "Bari kawai, Imran ya tafi Zamfara yanzu mu kai waya da shi" "Zamfara kuma Ammi?" "Eh Wai Zamfara, suna hanya ma" "Mun shiga uku Ammi, kashe sojoji ake sosai a gurin faɗan nan fa" "Hmm, Nifa tuntuni bana son aikin sojan nan, Babanku ya goyi bayansa yaje ya nema masa, mutum yayi masters meye na wani aikin soja maimakon ya nemi aiki, duk wani abun tsiya babanku ke gayyato masa shi, ko taya shi aikatawa" "To Ammi yanzu haka ya tafi ya barsu a gida ɗaya, Anty Ihsan da wannan 'yar damben" Ammi tace "aikuwa, taɓ aikam baze yuwu ba, taje taiwa 'yar mutane lahani a banza" "Wallahi kuwa dan kin san zata aikata" "Aikuwa ta taɓa ta se ta bar gidan nan, bari kawai mayi Magana da Maman Ihsan ɗin ta koma gida kawai, ta bar mata gidan kafin ya dawo" "Aikuwa dai da yafi, ni dama anjima zanje gurin Mummyn". "Shikenan, bari inje gurin babanku inji meze ce, bana son inyi abu ya zo yanamin sababi, na ga kwanan nan tun da ya aurawa Imran Yarinyar nan yabi ya canza, amma canzawarsa ba ze canza ƙudurina akan Auren nan ba" Minal tace "nima dai na gani Ammi, bari inje in fara shiryawa" Anty se la'asar ta tashi daga gurin aiki, kai tsaye gidan Amira ta wuce, dan ta duba jikinta kamar yadda Imran ya buƙata. Da sallama ta shiga falon, amma shiru ba'a amsa ba, ga mamakinta Ihsan na falon a kwance tana kaɗa ƙafa. Anty tace "Barka da gida, ina sallama amma baki amsa ba" Ɗagowa Ihsan tayi ta kalli Anty, ta ɗan yatsina fuska tace "banji bane" "Allah sarki, ya gidan fatan kuna lafiya"? "Lafiya ƙalau" Ihsan ta amsa da mata da ƙyar. Anty tace  "Nace Amira tana nan ne?" "Bani da tabbas, tunda ba'a kaina take zaune ba" Mamaki ne ya cika Anty, tace "to Allah ya baki haƙuri" Ta wuce ɓangaren Amira, ta shiga da Sallama amma shiru ba kowa a falo, kiran sunan Amira tai, amma taji shiru, ta ciro wayarta ta kira Lambar Amira, amma bata ɗaga ba. Kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Amira, tai Sallama sannan ta shiga, A duƙunƙune ta hango Amira akan gado, tana ta rawar sanyi ga sautin kukanta da yake tashi ƙasa ƙasa. Da sauri ta ƙarasa bakin gadon tana kiran sunan Amira, Amira da ƙyar ta iya ɗaga idonta ta kalli Anty. "Amira lafiya meya sameki haka?" Tai maganar tana yaye bargon jikin Amira, Amira dai kasa magana tayi se kuka, Anty tace "yi shiru ya isa kukan, bari in haɗa miki ruwa kiyi wanka, kin ci Abinci ma kuwa?" Amira ta girgiza kai. Anty ta jona ruwa a heater, ta haɗawa Amira ruwa, ta rakata banɗaki, ta dawo ta gyara mata gado ta canza mata bedsheet. Tayi mamakin yadda Amira ke Rashin lafiya har jikinta ya zama haka, kuma bata gaya mata ba, Amira ta rame sosai idanunta . Ta shiga Kitchen ɗin Amira, amma babu kayan Abinci a ciki, ta dawo ɗakin ta tarar Amira ta fito daga wankan. Ta kalli Amira tace "na duba Kitchen ɗinki, Banga komai na Abinci ba, se ɗan abunda ba'a rasa ba" Cikin muryar marasa lafiya tace "suna Kitchen ɗin falo" "Amma Amira ya akai kika bari jikinki yai haka bakije Asibiti ba, kuma baki gayamin ba? Ko dai ciki ne?" Amira ta girgiza mata kai alamar A'a. Anty tace "wani irin A'a, in ba ciki ba to wani rashin lafiya ne ze maida ke haka lokaci ɗaya duk kin rame, kamar bake ba, yanzun me kike son ki ci?" "Bakomai" "Kamar yaya bakomai? Gayamin abunda kike so maza" "Anty bana jin yunwa fa" "Aikuwa dolen ki kici Abinci" Anty ta tashi ta fita falo, Ihsan ta ɗaga kai ta kalleta, ta ɗauke kanta ta cigaba da kallo, tana faman hura hanci. Anty tace "Ashe Amira ba lafiya haka?" "Banda abunki Anty, ni na Aureta da zan san tana da lafiya ko kuma babu?" Anty ta sake tabattar da ba zaman lafiya Amira suke da Ihsan a gidan ba, ba ta kuma kula Ihsan ba ta wuce Kitchen ɗin, tuwon semovita da miyar ganye taiwa Amira, ta zo ta sa Amira a gaba da ƙyar taci Abinci, sannan ta ɗauki sample ɗin Amira na jini, tace zata tafi dashi, a kai lap a binciki meke damunta. Amira ta fashe da kuka tace "Anty dan Allah mu tafi tare" "Mu tafi tare saboda me, bayan ga ɗakinki, kuma ba muyi haka da mijinki ba?" "Anty ni dai dan Allah ki tafi dani" "Amira ina na taɓa jin anyi haka, ai bamu nemi Izini ba" "Anty in kin tafi waze kula dani? Kuma bani da lafiya sosai fa" Anty tai murmushi tace "shagwaɓaɓiyya 'yar gidan Anty, Amira in cikin ne ma haka za'ayi rainon cikin da wannan taɓarar? Bari in kira mijinki a waya, idan yake da network in tambayeshi inji me ze ce" Amira ta jinjina kai, Anty taiwa Imran missed calls sun kai biyar, amma wayar taƙi shiga. Tace "Amira wayar Imran ba ta shiga, yanzu meye abunyi?" Gaban Amira ne ya faɗi, kar dai har sun shiga daji? Wata irin ajiyar zuciya tayi, tare da faɗin Hasbunallahu wani'imal wakil. "Amira na lura akwai damuwa a tare da ke, mu tafi taren kawai, in wayar tasa ta shiga na masa bayani, ko in kira Abbanki in gayamasa" Cike da farinciki Amira ta jinjina kai, Anty ta ɗakko hijjabi ta bawa Amira ta saka, ta ɗaukar mata duk abunda take buƙata, suka fito. Ba kowa a falo, Anty tace muje mu yiwa abokiyar zamanki sallama, kan mu tafi" Amira ta girgiza kai tace "A'a Anty, mu tafi kawai, ki ƙyaleta" "No ba za'ai haka ba, ba ze yuwu mu tafi ba muyi Mata sallama ba" Anty na cikin Maganar se ga Ihsan ta fito, hannunta riƙe da plate ɗin Abinci, kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta. Anty tace "Ihsan, zan tafi da abokiyar Zamanki, bata da lafiya sosai, zan kaita Asibiti, idan da halin dawowa zan dawo da ita, idan babu kuma zan riƙeta se ta warke" "To ni kuma meye nawa a ciki?, Naga bani na Aurota ba kuma ba zamana take ba, ai ba lallai senaji in da zata ba" A ɗan hasale Amira tace "Anty dan Allah ki rabu da ita, taho mu tafi ni jiri nake ji" Ihsan tace "Allah ya raka taki gona, yasa daga nan ba zaki dawo ba" Mamaki ne ya cika Anty sosai, Lallai zargin ta ya tabatta, babu zaman lafiya tsakanin Amira da abokiyar zamanta. Anty ba ta kuma cewa komai ba, suka ƙarasa mota ta saka Amiea a mota suka tafi, suna tafe Amira na ta kuka da ciwon kai da jiri, hakan yasa suka wuce Asibitin da Anty take aiki. A kai mata duk tasa tasan da za'ai mata, amma ba'aga komai ba, babu ciki ba malaria Babu typhoid. Antu ta saka aka gwada BP ɗin Amira, sedai tayi mamakin sakamakon da aka gaya mata, seda ta karɓa ta sake yi da kanta, But still thesame result. Anty ta kalli Amira tace "Amiea, zan tambayeki wani abu, kuma gaskiya nake so ki gayamin, idan kikamin ƙarya, zan ɓata miki rai" Amira tace"to insha Allah ba zan miki ƙarya ba" "Meke damunki haka da yasa jininki ya hau?" "Bakomai" Amira ta bata amsa. "Bance karki min ƙarya ba? A baya an taɓa cewa kina da hawan jini"? Amira ta girgiza kai alamar a'a. "To ne yake damunki da har zaki haɗu da hawan jini a wannan shekarun naki haka? Ki gayamin me kike ciki a gidan Imran?* "Anty bakomai fa, kawai an turashi Zamfara ne, shine na damu kuma ana kashe mutane a can" Anty ta ƙura mata ido tace "ina jinki se kuma me, dan ban yadda wannan ne dalilin da ya sa ki kai wannan ramar ba, lokaci ɗaya haka, ga kuma jininki ya hau ba, da fari na zaci ciki ne, amma tunda ba shi bane, ki gayamin meke damunki" "Anty zan gayamiki, amma kimin alƙawarin idan na gayamiki dan Allah karki gayawa kowa" Anty tace "Naji, ba wanda zan gayawa" Amira ta share hawayen ta tace  "Anty, ni marainiya ce, na tashi ba uwa ba uba, mahaifiyata ita ta fara rasuwa, ina da shekaru huɗu gurin haihuwa, da ta rasu babana be sake Aure ba, babana shikaɗai mamansa ta haifa, abokiyar zaman Yadikko, shima yana matashi mamansa ta rasu ta barshi, dama babansu ne kakana ya fara rasuwa, bayan rasuwar iyayena, Yadikko ce ta riƙeni abokiyar zaman kakata, sedai a zaman da Yadikko tai da kakata, mace ce me bala'in kishi, ta tsani kakata ta azabtar da ita sosai a yadda na samu labari, wannan ƙiyayyar da takewa kakata da iyayena, ita ta shafeni na tashi a wahala, Yadikko ba ta ƙaunata ko ƙaunar cigabana, taso in fi haka lalacewa in tagayyara a rayuwata, katsam akaimin wannan Auren, abun ya tsaya a zuciyarta ita da iyalanta matuƙa, da naso yin bore akan Auren, amma na nutsu nai tunani naga shine rufin Asiri na, duk da zafi da rashin haƙuri irin nawa, amma na danne zuciyata na ƙudiri a niyar zaman Auren, duba da nasihohin da ku kaimin, sedai mahaifiyar mijina ba ta sona, tace in zauna cikin shiri a kowane lokaci zata iya kashe Auren nan, Banda cin mutunci da wulaƙanci da Ihsan takemin, kinga dole inyi haƙuri tunda gidanta ne, ita Miji yake so bani ba, Anty yanzu idan Auren nan ya mutu, haka mariƙiyata take fata, amma ko Auren be mutu ba, ni zan mayarwa Captain abunda ya kashe a Aurena ya sawwaƙe min, tun kan mahaifiyarsa tasa yaimin korara wulaƙanci kamar yadda ta taɓa yimin lokacin da aka kawoni ina ƙarama akace ta riƙeni" Hawaye na zuba Amira take gayawa Anty maganar, jikin Anty yai sanyi ƙwarai, tayi mamakin abunda Ammi tayi, a haka gata wayayyiar mace, amma ya zama na banza, ba tace Komai ba taje ta haɗo wasu allurai ta yiwa Amira, ko mintuna ashirin ba'ayi ba bacci ya kwasheta, Anty ta zauna ta zubawa Amira ido, wani irin tausayin yarinyar yana ratsa zuciyarta. Tafiyar su Amira babu daɗewa se ga Ammi taje gidan, Ihsan ta tashi da fara'arta tana "Ammi sannu da zuwa" "Yawwa Ihsan" "Ammi ba ki gayamin zaki zo ba ina Minal?" "Minal tana gidanku gurin Mummy, ɗazu babansu ya koma gurin aiki, tace min zata ta kwana biyu ba taje ba, mu kai waya ɗazu da Imran ashe kuma zamafara aka tura shi?" Jiki a sanyaye Ihsan tace "wallahi kuwa Ammi, kin ganni nan gaba ɗaya na kasa sukuni, haka na wuni jikina ba daɗi, ina ra masa Addu'a Ubangiji Allah ya dawo dashi lafiya" "Ameen, ni kaina hankalina a tashe yake da wannan tafiyar, sedai ina fatan Ubangiji Allah ya dawo da shi lafiya, amma sam hankalina yaƙi kwanciya ƙarfin hali kawai nakeyi, naji kina kin wuni jikinki ba daɗi Allah yasa jika na kusa na ɗauka" A kunyace Ihsan ta sunkunyar da kai tace "ina cikin damuwar tafiyarsa ne kawai" "Ai shikenan, idan ma ɓoyewa kike dole ze fito a gani, nace ina wannan Yarinyar take ne? Na zo ne inga yadda za'ayi, idan zamanku a tare ze yuwu bayanan, kar inje na saki baki a can ta miki illa" Kwaɓe baki Amira tayi tace "ɗazu uwarta ta titi tazo ta tafi da ita wai bata da lafiya" Ɗan zaro ido Ammi tai tace  "kamar yaya ba ta da lafiya, ba dai wani abune ya faru ba tsakaninsu ba?" "Taɓ, ai Ammi ba wannan zancen, tunda kika zo jiya da daddare take kuka, shine Matar Alhaji Hashim tazo ta tafi da ita wai ba ta da lafiya" "To ai yayai kyau, suje can su ƙarata, sekiyi zamanki ma ki huta, ai na zaci tana nan ne musan abunyi" "A'a sun tafi ɗazu" "To ai hakan ma yafi ai, se mu cigaba da Addu'a, Allah ya tsareshi ya dawo da shi lafiya" "Ameen, insha Allah" Amira kam seda ta kwana ɗaya a Asibiti, Anty ba ta sake yi mata maganar abunda yake damunta ba, aka sassaka mata ruwa da allurai, washegari da Anty ta tashi daga gurin aiki ta tafi da ita gida. Fadila na ganinsu tare ta tarosu, tace "Sannu Amira banje na duba ki ba, ina makaranta Anty tace yau za'a sallame ki" "Bakomai Anty Fadila ai na warkema" "Duk da haka kin rame sosai Amira, amma kin daɗe kina rashin lafiya?" "A'a, ban daɗe ba, kawai dai na rame ne" Anty tace "Fadila kawo mata Abinci" "Aka zubawa Amira Abinci shime da kyar ta ci Abincin nan" Anty tace karta koma ɗaki, tasan idan ta shiga ɗaki kwanciya za tayi, dan haka Fadila ta kaira tayi wanka, ta dawo falo ta zauna. Haka kuwa akayi, tai wanka ta dawo falo ta zauna, Fadila na tai mata hira amma sam hankalin Amira baya kan Fadila, ta ƙurawa TV ido amma ba kallon take ba. Anty ta fito daga ɗakin ta, tace "sannu Amira" "Yawwa Anty" Anty ta zauna kusa da Amira, suka fara hira da Fadila, can Amira tace  "Anty, wai idan sojoji suka tafi daji, a ina suke kwana ne?" Anty tace "Amira kenan, banda abunki ni ba soja ba ya zan in san inda suke kwana? A dajin dai suke kwana" "Anty waye yake basu Abinci kuma?" Anty ta kalli Amira tace "Amira tunanin mijinki kike kenan?" Amira ta girgiza kanta tace "A'a kawai na tambayeki ne" "Hmm Amira kenan" Har sunyi shiru Amira ta kuma cewa "Anty lambar Captain ta na shiga kuwa?" "Amira, Imran yana nan lafiya fa, kin san jininki ya hau amma kina ta sake ɗaga hankalinki, munyi waya da shi jiya ma, ki kwantar da hankalinki kinji Amira" "To Anty" Gaba ɗaya tausayin Amira ya kama Anty, lallai Amira ta damu da Imran matuƙa. Haka Anty taita ƙoƙarin kwatarwa da Amira hankali, kwanan Amira uku a Gidan Anty, Alhaji Hashim ya dawo gida, yai mamakin ganin Amira a gida. Yace "Amira lafiya dai ko, naga kin rame haka?" Amira tace "lafiya ƙalau Daddy, bani da lafiya ne kawai" "Subhanallah, to Ubangiji Allah ya sawwake" "Ameen Daddy" Seda suka shiga ɗaki Daddy ya nutsu yaci Abinci, sannan yace "Naga Amira a gida, tace min dai bata da lafiya, ina fatan hakane" Anty tace "to kusan hakane Daddy, Sau ɗaya Allah ya bani haihuwar yara tagwaye, amma ji nake kamarni na haifi Amira, duk da na riƙe yara da yawa kan Amira, amma ƙaunarta daban ce a raina, saboda ina matuƙar tausayinta fiye da yadda kake zato, nasan maraici nasan zafinsa, abokinka Alhaji Ali ya aurawa ɗansa Amira bisa ga yin katanga ga lalacewar da tayi, amma ka sani ba'a gyra ɓarna da ɓarna, shekaranjiya Imran ya tafi Zamfara, ya kirani akan cewar Matarsa ba lafiya, naje na tarar tayi rama sosai, na zata laulayi ne, sedai bisa ga binciken da nai damuwa ce cunkus a zuciyar yarinyar nan, ta yadda ta kai jininta ya hau fiye da tunani, a abunda ta gayamin, uwarmijinta na barazanar zata kashe mata Aure, bamu haifeta ba amma tayi biyayya ga maganarmu ta rungumi zaman Aurenta, amma mahaifiyar Imran da kishiyarta na muzguna mata, duk da ta ɓoye laifin Imran ba ta gayamin ba, amma nasan tabbas shima akwai tasa gudummawar a abunda ake mata, tana gudun mutuwar Aurenta, saboda inda ta fito suma ba ƙaunarta suke ba, duk da bakomai ya gayamin ba, na lura tana da ɓoye sirrinta, amma banji daɗin abunda Hajiya Jamila takeyi ba, itana fa uwace ta haifa, ni idan abun baze yuwu ba, idan Allah ya dawo da shi, ya rubuta takarda ya saketa, ni ina so zan riƙe kuma insha Allah, duk da abinda suke zargin tayin zata samu miji nagari, mata nawane sukai karuwanci aka Auresu, aka zauna da su suka dena abunda suke, Ihsan 'yar gwal ce ta ba zata zauna da kishiya ba, to idan baya so ya saketa ni zan riƙeta, ba yau na fara riƙe 'ya'yan wasu ba, acikin hamshaƙan mutanen nan zan samo mata miji, wanda ze riƙeta" Bilhaƙƙi Anty take faɗa, dan seda ƙwalla ta taru a idonta, Alhaji Hashim yace "easy Maman Yara, kwantar da hankalinki mana, ai abun duk be kai haka ba, ki kwantar da hankalinki, zanyi magana da Alhaji Alin, abun baze kai ga saki ba" "Gara dai kuyi maganar, tun wuri yasan matakin da ze ɗauka, dan idan hawan jini ya kasheta matarsa ce da matar ɗansa suka kasheta" "Allah ya baki haƙuri maman Amira" Alhaji Hashim yaita bawa Anty haƙuri yana rarrashin ta. Amira kuwa wayar Anty ta ɗauka, ta ɗau lambar Imran, ta koma ɗakinta ta dinga kiran wayarsa, amma a kashe bata shiga, hakan ya ƙara ɗagawa Amira hankali, ba ta taɓa tunanin Ta damu da Imran haka ba, bata iya baccin kirki, haka zata tashi tai nafila cikin dare tana addu'a Allah yasa yana lafiya. Da safe Anty ta aika Fadila akan lallai Amira ta fito falo, ta karya tare dasu, dan in aka kai mata ɗaki baci take ba. Haka Amira ta fito, har ƙasa ta durƙusa ta gaida Daddy ya amsa cikin sakin fuska yace "'yar Antyn ta ya jikin naki?" "Naji sauƙi Daddy" "Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi" "Ameen Daddy, Anty ina kwana?" "Lafiya ƙalau, maza zauna a zuba miki Abinci". "Anty Azumi nake ai" "Azumin me baki da lafiya?" "Azumi nake Allah yasa Imran ya dawo lafiya, ana ta kashe su a daji" Tai maganar hawaye na zubawa daga idonta, Anty ji tai kamar tayiwa Amira kuka, tabbas Amira ta fara son Imran ne. Daddy yace  "banda abunki Amira, ke da baki da lafiya ina ke ina Azumi? Addu'a ma da kike masa ta wadatar, yana nan lafiya insha Allah, zauna kici Abinci" Suka tursasa Amira, tana ci tana goge hawaye, ita kanta bata san ta damu da Imran haka ba, se daya tafi wannan Yaƙin. Bayan ta gama Anty ta bata magani ta sha, ta koma ɗakinta ta ɗau wayarta ta kuma kiransa amma a kashe, message ta rubuta masa kamar haka. "Assalamu alaikum warahmatullah, duk da bani da tabbacin a wani hali kake yanzu, na kira wayarka ba ta shiga, amma ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, Ubangiji Allah ya tsareku, ya baku nasara akan abunda kuka je yi" Ta gama rubuta message ɗin ta ajiye wayar a hankali, tare da lumshe idonta, ta na addu'ar Allah ya dawo da Imran lafiya, duk da baya sonta, amma tana jin kamar yana da mahimmanci a rayuwarta, rashin sa shima ze sake barin wani babban giɓin a rayuwarta. Kamar yadda Alhaji Hashim be yiwa Alhaji Ali maganar nan ba, saboda yasan Alhaji Ali da haƙuri amma yana da zuciya sosai, yasan yadda Alhaji Ali ke murna da Auren Amira da Imran, yana jin hakan kamar wanke laifinsa na baya ne, muddin yaji wani abu na Ammi na ƙoƙarin kashe Auren, tabbas za'ayi ba daɗi, dan haka yai shiru da bakinsa ya ƙuduri se Allah yasa Imran ya dawo lafiya ze zauna da shi. Ihsan kam hankalinta kwance take zuwa service ɗinta, ita kaɗaice a gidan ba kowa, taje inda take so ta dawo sanda ta ga dama, wataran ma ta kwana a gidansu. Seda Imran ya shafe kwana Ashirin da biyar babu wanda yaji daga gareshi, Amira duk ta sukurkuce, ta dami kanta ta gaza nutsuwa sam, se aikin koke koke da take fama da shi. Alhaji Hashim ya gayawa Alhaji Ali, cewar Amira tana gidansa ba lafiya, Alhaji Ali baya gari amma ya kira babbar 'yarsa Hadiza taje ta duba Amira, bayan ita Babu wanda yaje dubata. Ranar da Imran ya kwana Ashirin da takwas, Alhaji Hashim ya shigo ya tarar da Anty a Falo yace  "Maman Yara, Alhaji Ali ze shigo garin nan cikin dare insha Allah, an bada sanarwar gobe in Allah ya kaimu tawagar su Imran zasu dawo, da yawa daga cikin su sun rasa rayukansu, dan haka gobe in Allah ya kaimu zamuje mu gani, yana rayen ne ko kuma ta Allah ta kasance, dan tunda suka tafi sau ɗaya babansa yai waya da shi" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah yasa ba abunda ya sameshi, wayyo Allah na" Gaba ɗaya suka juya inda Amira take, ashe tana Kitchen basu sani ba. Da sauri Anty tai kanta tana faɗin "Amira calm down ba fa mutuwa yai ba" "Anty i give up, dan Allah Daddy ya gayamin in ya mutu' Daddy yace "ba mutuwa yai ba, zuwa zamuyi mu ɗakko shi" "To dan Allah zan biku" "Naji, amma ki kwantar da hankalinki kinji, Allah ya kaimu goben" Da ƙyar suka lallaɓa Amira, ta haƙura. Alhaji Hashim yace "Ina ganin ikon Allah, gaskiya Yarinyar nan ta tashi hankalinta da yawa". Anty tace  "hakane, ni fatana Allah yasa kar ya gane tana masa wannan son, ya dinga wahalar da ita, amma yanzu ka amsa mata da itan zaku tafi?" "To idan ban amsata ba ya zanyi, kina ganin zata sume a gurin" "Allah yasa yaron nan yana nan ƙalau," Ya amsa da "Ameen" Amira tunda ta idar da sallar Asuba take zaune, tana lazumi gari na fara haske tai wanka, ta saka kaya ta fito Falo. Daddy na fitowa tare da Anty suka ganta zaune a Falo, Anty jinjina kai kawai tayi dan mamaki. Daddy yace "to Amira taso mu tafi, sedai ki zama me tawakkali da koma me zamuje mu tarar kinji ko?" Amira ta jinjina kai, ita dai Anty ba ta so aje da Amira ba, saboda ba ta san me zasu tarar ba. Haka ta shiga mota, suka tafi gidan Alhaji Ali suka fara zuwa, suka tarar Ammi tana ta kuka, tace itama da ita zasu tafi. Abba yace "Hashim ya na ganka da Amira, haka kika rame haka?" Alhaji Hashim yace "ba dole ka ganni da ita ba, ta tashi hankalinta da yawa shiyasa nace gara mu tafi tare" Suna nan suna tattaunawa, Ammi ta fito ita da Minal, sedai tana ganin Amira tai turus ta haɗe rai tamau, Amira ta gaisheta amma tai banza da ita. Suka ɗunguma a mota suka tafi, suna tafe kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarsa, Amira ta shiru tana ta addu'a a zuciyarta. Motocin sojojine da yawa a gurin, ga sojoji manya da ƙanana da mutane a gurin, kowa yana duba nasa, ga gawarwaki ana ta firfito dasu. Suka firfito daga Mota, ƙirjin kowa na dukan uku uku, dan basu san me zasu tarar ba. Alhaji Hashim yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Ubangiji Allah ya jiƙan musulmin ciki da suka rasu" Jiki a sanyaye Abba yace "Ameen" Ammi se kuka take ita da Minal, Amira kam zuciyarta harta bushe, hawayen sun dena zuba. Amira ce ta tafi da gudu, ta kutsa cikin sojojin nan, Abba yace "Subhanallah, ina zata kuma? Tana hayyacinta kuwa?" Babu zato yaji an rungumeshi ta baya, be motsa daga inda yake ba, kuma be waigo ba, sun kwashi wasu daƙiƙu a haka, a hankali yasa hannu ya janyota daga bayansa, sake rungumeshi tai tana hawaye tace "Alhamdilillah, You Are alive Captain" Jikinsa gaba ɗaya a sanyaye, ganin Yadda Amiran tai wata uwar rama, Amirama mamakin ramar da yayi take, yai baƙi Uniform ɗin  jikinsa sunci ƙaniyarsu suma, wani gurin duk ya yayyage, kallo ɗaya zakayi masa kasan an fafata a filin daga. Ɗan murmushi yai ya ɗagota daga jikinsa yace "ke da wa kuka zo?" "Da su Abba, da Ammi" "To ki dena kukan mana tunda ban mutu ba" Murmushi tayi amma hawayen suka ƙi tsayawa, yasa hannu ya goge mata hawayen yace "ɗagani, karki ɓata kayanki da datti" "Bakomai zan wanke" Ya riƙo hannunta, suka fito inda su Ammi suke, Abba yai murmushi yace "Alhamdilillah" Ammi da Minal suma suka tafi inda yake suka rungumeshi. Alhaji Hashim yace "Sannu Imran, ka ga yadda ka koma kuwa?" Murmushi kawai Imran yai Yace "to Ya za'ayi, tunda mun riga mun shiga aikin" Alhaji Hashim yace "gaskiya ne, Allah ya ƙara muku ƙwarin gwiwa, se ka samu isasshen hutu kuma" Imran yace "Yallaɓai ai ba hutu, nan da sati biyu insha Allah zan koma Lagos" Abba yace "Lagos kuma?" Imran yace"eh Abba" Ammi tace "nifa gaskiya na gaji da wannan aikin, haba dan Allah kaga yadda ka koma kuwa?" Abba yace "ki gode Allah tunda yana raye" Imran yaita zuba ido amma be ga Ihsan ba, suka hau mota domin komawa gida, Abba yace "gaskiya wannan karon in zaka koma Lagos, ka tafi da Amira, tunda wancan karon da Ihsan ka tafi, wannan tafiyar a tafi da ita!!!... SHARE PLEASE! AMIN AFUWA BAN EDITING BA ABUBUWA SUNYI YAWA (Ina ɗimbin godiya ga Comments ɗin da kukemin, nagode ƙwarai, sedai batun in dinga posting kullum baze yuwu ba, abubuwa sunmin yawa, ga sabon littafina na RUƊIN ƘURUCIYA zan fara, masu tambayar document na WUTA A MASAƘA ban kammala littafin ba, yanzu nake kan rubuta shi, ina godiya da kulawa" Ayshercool 07063065680 [2/6, 7:35 PM] Ayshercool:         🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                                                                      39_40 Shiru Imran yai be ce komai ba, Ammi ma ba tace uffan ba, jira take suje gida ta tabbatar idan da gaske Abba yake Wannan maganar. Gidan Imran suka nufa kai tsaye,aka ajiye Imran da Amira, Amira tace zata bi Alhaji Hashim su koma gida, yace "wani gidan kuma Amira?" "To ai ban gayawa Anty zan zauna ba, kuma bani da lafiya" "Ai ga magnin nan ya dawo, kije ki kula dashi, zamu dawo muyu masa sannu da zuwa ta mussaman". Ammi se hararar Amira take, Amira ta nuna kamar bata ga me Ammin take ba. Suka shiga cikin gidan, ɓangaren Ihsan a rufe na Amira ma haka, Amira ta duba Kitchen ɗin falo, ta ɗakko mukulli, ta buɗe part ɗinta, ta kalli inda Imran ya zauna a kan kujera, tace "Naga Ihsan bata nan, bari in haɗa maka ruwa kai wanka". Jinjina mata kai yayi, ba tare da yace komai ba, taje ta haɗa ruwan ɗumi a banɗakin bedroom ɗinta. Ta fito falo tace "Captain bisimillah na haɗa" Ya miƙe yabi bayan ta, yana cike da mamakin ina Ihsan ta tafi haka? Ba ta san da dawowarsa bane ko kuwa me hakan yake nufi? Duk da ta kwan biyu ba ta gidan, amma komai nata tsaf da shi, Imran ya samu ruwan ɗumi, yai wanka kan ya fito har ta shiga Kitchen, ya zauna a gaban mudubi yana ƙarewa kansa kallo, shi kansa yasan ya rame, saboda anyi gwagwarmaya a dajin nan. Amira ta shigo zata masa magana amma tai turus tana kallonsa, se taga kamar ba shi ba, ya zama wani ƙato sosai. Ya kalleta yace "Ya dai?" "Amm bakomai, da..daama zance ne, in kawo maka Abinci nan in na gama?" "No zan zo nan falon in ci"  ya faɗa a taƙaice. Ya fito Falo, ya buɗe jakarsa ya fito da wando na sojoji da shirt ya saka, Amira ta zo ta ajiye masa kayan Abinci, ta haɗa masa tea, da dafaffiyar doya da miyar ƙwai. Yadda Imran yake zura Abincin nan a tumbinsa, zaka san lallai ba ƙarama wahala yaci ba, Amira se kallonsa take kamar ba ta taɓa ganinsa ba, ita tausayinsa ne ma ya dinga kamata, duk yai duhu. Amira tace "Sannu" Imran ya jinjina mata kai kawai, ya cigaba da zura Abincin sa. Kallon gefen kafaɗarsa tai tace "meya sameka a nan?" "Bullet ne" ya bata amsa. "Harbin ka akayi?" "Eh harbi ne" Ta jinjina kai, can ya ture kayan Abincin yace "ya ƙoshi" Amira ta kwashe kayan Abincin, ta kai Kitchen, taje bedroom ta ɗakko masa bargo da fulo, ta fito tace "ga fulo ka kwanta kafin ta dawo daga gurin aikin" Imran ya karɓa ya kwanta tare da lumshe idonsa. Har ta miƙe zata tafi yace "Amira" Seda tsigar jikinta ta tashi, ta waigo tace "Na'am" "Ya jiki?" "Naji sauƙi ai" Ɗan ƙura mata ido yai, dan sabon salo ta saka uban hijjabi taƙi cirewa, amma duk da haka kana iya gane ta rame sosai, kamar wanda a kaiwa dole yace "Meya sameki ne?" "Bakomai, kawai rashin lafiya ne" ta bashi amsa, Yai ajiyar zuciya be kuma cewa komai ba. Ta koma ɗakinta, tana cigaba da hamdala, kasancewar Imran yana raye. Anty kuwa tana ganin Alhaji Hashim shikaɗai tace  "yaya, ina Amiran lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau, Mun ɗakko Imran, ya dawo lafiya ƙalau" "To ina Amiran"? "Na baro ta a gidan mijinta" Anty tace "Daddy why? Ya za'ai ka bar musu ita?" "To Anty ya kike so ayi?" "Gaskiya ban niyyar ba da Amira Yanzu ba, sena san meye matsayinta a gurin Imran" "A'a matarsa mana" "A'a fa Daddy, nifa ban gane kan wannan abun da kayi ba, nan na zauna na baka labarin irin abunda ke faruwa kuma seka bar masa ita" "Calm down Madam, yarinya ba ta da lafiya, ita ta fara hango mijinta taje ta taro abunta tana murna, ga sirikanta kawai se in taho da ita, haba Antyn Yara" "Gaskiya ni dai banji daɗin abunda kai ba Daddy" "To Allah ya baki haƙuri, amma gara da na barota a can, dan Yarinya na kewar mijinta, ai tsakanin miji da mata se Allah, ki ƙyale sha'anin yaran nan kawai" "A'a dole in dinga saka ido, saboda baza'a mayarmin da 'ya bora ba" "Koma dai menene, kiyi haƙuri" Anty tace "ba wani inyi haƙuri, ka yi min laifi kawai" "Naji kuma ai na bada haƙuri, ai nima 'ya ta ce" yai maganar yana murmushi. Ammi kuwa bayan sun koma gida, ta samu Abba a part ɗinsa, ya kalleta yace "ya dai sarkin ƙorafi?" "Magana nazo muyi" "Maganar me ne?" "Wai dagaske kake da Yarinyar nan ze tafi Lagos?" "Eh dagaske nake" "Amma saboda me?" Abba yace "ban gane saboda me ba, Saboda matarsa ce, wancan lokacin ya tafi da Ihsan, wannan karon ya tafi da Amira" "Amma.... Abba yace "bana son Amma nan dan Allah, na gama Magana wannan karon da ita ze tafi" Ammi ta harzuƙa, amma ta dake tace "naji da ita ze tafi, amma ina son kayi tunani a raba musu gida, dan gaskiya Yarinyar nan ba ta da cikakken tunani, kan Imran yai tafiyar nan ta kama Ihsan ta daketa, harta fitar mata da jini" Abba ya kalleta yace "ban gane ta daketa ta fitar mata da jini ba?" "Ai shine bayanin da nake maka, shiyasa ni tun farko da kai shawara dani ba zaka yanke Wannan hukuncin ba, yana zaman zamansa yana da wadda yake so ka ƙaƙaba masa Auren Wannan yarinyar mara kunya mara ta ido, gaskiya a raba musu gida, kar ta yiwa 'yar mutane lahani" "Kinga saurara, da na yanke hukuncin Auren nan, seda naji ta bakin Imran kan ayi Auren nan, kuma zanje gidan zanji abunda yake faruwa, da kaina inga akwai yiwuwar raba musu gidan, ina son Imran yai zama me adalci a tsakaninsu shiyasa na haɗasu, amma zanje Gidan da kaina" Gabanta ya ɗan faɗi bayan tayi tunanin idan ya samu labarin taje Gidan taci mutuncin Amira fa? Lallai ita ma se nata ran ya ɓaci. Da sauri tace "Amma ai da ba se kaje ba, kawai dai na gaya maka ne kasan hukuncin da ya dace ka ɗauka, kuma ai be kamata a bar Ihsan ita kaɗai ba, tunda lokacin da ya tafi da Ihsan ita Amiran ba ta gidan" "Nifa na gama yanke hukuncin da naga ya dace dan haka ki rabu dani" Yai Maganar tare da miƙewa ya bar mata falon nasa gaba ɗaya ta raka bayansa da uwar harara. Ammi ɗakinta ta koma, ta ciro wayarta ta kira Ihsan, Ihsan na ɗagawa Ammi tace "ke wai kina ina ne?" "Ina nan Ammi, meya faru ne?" "Kina nan a ina, yau mijinki ze dawo, suka tafi da waccan shashashar gurin taro shi, ke ba kya nan, muka biya muka ajesu a gidan su, nan ma ba kya nan, ke wace irin mara wayoce ne haka?" "Au Ammi dama yau ze dawo? Ai ni babu wanda ya gayamin fa, Yanzu yana ina?" "Ke kina zaune harse an gayamiki, ita ya a kai ta sani? To ki hanzarta ki tafi gidan, dan kin bari ta fara tararsa, Allah ya kiyaye dai amma ki hanzarta ki koma ki karɓi mijinki" "To Ammi Insha Allah" Ihsan ta katse wayar tace "Kai, taɓɗijan, Lallai banga ta zama ba, ta shiga harhaɗa jakarta zata koma gida. Sosai bacci ya kwashe Imran, lokaci lokaci Amira ta kan leƙo ta duba taga yana lafiya, sannan ta koma ɗakinta. Ƙarshe ta dawo falon ta zauna, tana karatun littafi a wayarta. Se azahar ya tashi daga baccin, ya cewa Amira zeje masallaci, seda ya fita Sannan maƙotansa suka san ya dawo, a nan suka gaggaisa suka masa Barka da zuwa, tare da yi masa barka da arziki. Ya koma gida ya tarar har Amira ta ajiye masa Abincin Rana, ya nemi Guri ya zauna akan kujera ya lumshe idonsa. Ƙarar buɗe ƙofar Amira ne ya sa shi buɗe ido ya kalli inda take, crazy jeans ta saka, da wata fitinanniyar riga, attachment ɗin nan har ƙugunta, kamar za tayi rawar galar, hannunta riƙe da ƙaton robar popcorn. "Captain ka dawo? Ga Abinci fa" Seda Imran ya ɗan shagala da kallonta, can ya dawo hayyacinsa amma bece Komai ba. Kusa da shi Amira taje ta zauna tace "wai ko wani abun yana damunka ne?" Girgiza mata kai yai alamar a'a. "To sakko kaci Abincin, in dai Ihsan ce ta kusa dawowa tana gurin aiki ne, nasan tunaninta kake" Da sauri Imran ya kalleta, itama ta ƙureshi da ido, babu ko ƙiftawa, zuciyarsa ta shiga bugawa da saurin gaske, a jere ya dinga ajiyar zuciya, ya miƙe ya zauna a ƙasa, ta zuba masa Abinci. Ya miƙe ƙafa yaci abunsa, dan ba ƙarya Amira ta iya girki, sedai yana ci yana satar kallon Amira, duk da ta rame amma kayan sun mata kyau sosai, sun zauna a jikinta. Ta maida hankali tana kallon TV kamar ba ta san yana kallonta ba, seda ya gama yace "Am done, zoki kwashe kwanukan" Maimakon ta amsa, juyowa tai da Wani irin kallo, ta ɗan lunshe idanunta, seda Imran ya ɗan dirirce, cikin rangwaɗa ta zo gabansa ta kwashe kwanukan, ta dawo falon ta zauna, ta kalleshi tace "ko kana buƙatar wani abun ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Suna nan zaune kamar kurame, Anty ta kira Amira a waya, Amira ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Assalamu alaikum, Anty" Anty tace "wa'alaikum salam, shine kika biyewa Daddy ya maida ke gidan Imran ba tare da ɗaukar wani mataki akan abunda ake miki ba ko?" A shagwaɓe Amira tace  "Ba haka bane Anty, shine yace in zauna fa" "To ni ba ruwana tunda kika koma, ba tare da ɗaukar mataki ba, in wani abu ya faru zance Allah ya kyauta ne kawai" "Subhanallah, Anty bafa haka bane, Allah Daddy ne yace sena zauna" "To shikenan naji, naji yacemin dake Imran ze koma Lagos ko?" "Eh nima haka naji yace" "That's very good, zan ganki kafin ku tafi Insha Allah, ko dai inzo ko kuma ke kizo" "To Anty nagode sosai, insha Allah zan zo ma" "To shikenan, hmm Amira kenan, har kin ware daga rashin lafiyar ko saboda kinga mijinki" Gaba ɗaya kunya ta kama Amira, Bata sake cewa komai ba har Anty ta kashe wayar. Ta ƙasan ido yake sake kallon Amira son ransa, gaba ɗaya bata da makusa, tana da ƙira me kyau ga iya gayu, ga shagwaɓa, gata 'yar wanka sedai abunda ɓata masa rai dai ɗaya ne, Amira was prostitute before. Ihsan ce ta buɗe ƙofar falon, ta shigo fa Sallama, ta na shiga ta tarar da Imran a zaune, da gudu ta ƙarasa in da Imran yake ta faɗa jikinsa tana faɗin "oyoyo my heart, you are welcome" Rungumeta shima yai yana murmushi yace "Thank you sweetheart, ina kika tafi haka? Baki je taroni ba, kuma na dawo ba kya nan?" "Am sorry my, naje gurin aiki ne, kuma ba wanda ya gayamin yau zaka dawo, i really miss you my dearest love" Tai maganar ta na sake maƙalƙale Imran, shima maƙaletan yai a jikinsa, yana shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da ke tashi a jikinta. Ɗaga kai tai ta kalli Amira dake zaune, tana ta watsa popcorn ɗinta a baki, ga shigar dake jikinta, ta nuna kamar ita kaɗaice a falon bata san sun wanzu a gurin ba, haka kurum taji a ranta yanzu idan wani abu ya shiga tsakaninsu fa? Take ƙirjin Ihsan ya buga da ƙarfi, amma ta daure tace "let's go in My dear, i really miss you, muje ciki in nuna maka irin yadda nai missing ɗinka My D" Ba kunya se ga Imran ya ware yana murmushi, ya rungume Ihsan suka shiga part ɗinsu, Amira ta bisu da kallo tai wani murmushi me ciwo tace "da ni kuke zancen, ni dai tunda Allah ya dawo da kai lafiya Alhamdilillah" Tana shiga part ɗinta, kiran Fa'iza ya shigo wayarta, rabon da suyi waya da Fa'iza tun tafiyar Imran da Anty ta zo ta tafi da ita. "Anty Fa'iza, yau kin tuna dani ne?" Fa'iza tace "ban sani ba, sena ɗura miki ashar tukuna, kira nawa na miki ba kya ɗagawa, kuma ba zaki biyo ba, ni na fara tunanin ko wani abun ne ya sameki ma, na kira Abban su Imran yace kina lafiya ba kya jin daɗi ne kawai, nace ko kalar naki laulayin kenan na wulaƙanci" "Wai ba damar Mutum yai rashin lafiya, se a fara wani laulayi a'a naƙuda nake" "Bar ganin ba kya kusa dani, kikamin iya shege sena zageki" Amira tace "to Allah ya baki haƙuri, ya kike ya gida ya Yayana?" "Kowa lafiya ƙalau, ya jikin naki?" "Naji sauƙi Alhamdilillah" "Wai meya sameki ne?" "Mhmm, bani da lafiya ne kawai, kuma a ka zi aka turamin miji Zamfara, dole hankalina ya tashi in kasa lafiya ai" Fa'iza tace "ba shakka daɗi miji, sannu Amira wai yaushe kuka daidaita ne haka, har ake Wannan kewar da ɗaga hankali a kansa?" "Kinji Anty Fa'iza da wata Magana, mace da mijinta ai se Allah harki dinga tambaya ta wai yaushe muka shirya, kin manta lokacin da kike min iyayi ke ga me miji, to nina yanzu na hau layin ai" "Ke bana son Iskanci irin naki, nifa Yadikko ta matsa akan lallai se sunzo gidan ki, nifa na rasa ya zan mata, in ma ki sa musu lokaci, kokuma ki gansu ko kin shirya ko baki shirya ba" Amira tace "Akan me zasu zo ko na shirya ko ban shirya ba, hak akeyi? Kice musu bana gari kawai" "Ta yaya, bayan Abba yace musu kina nan, gara ki san abunyi, zuwa za suyi nan kusa" Amira tai ajiyar zuciya tace 'ke ba zaki zo ba?" "Amira bani da lafiya, kuma bani da kuɗin mota ne" "Zan turomiki, kuzo a ranar ku juya a ranar, kuma ki taho min da su Khairat ɗina" "Iyee dan wulaƙanci, aikuwa ba zan zo ba" "Anty Fa'iza ba haka bane, zaman da nake a gidan nan ba ni kaɗai bace, ina da kishiya kuma ba zaman lafiya muke ba, bana son su zo su samu abun faɗa, ko suyi wani abu daze zubarmin da mutunci a gabanta" Anty Fa'iza tace "Eh to kuma hakane, shikenan zan biyo su muzo tare, mu taso da Asuba, nasan takwas zuwa tara munzo, a dawowa ma mu taho da wuri, shikenan, in sun tsaida ranar na miki Magana" "To shikenan, in zaki taho ki taho min da kayan daɗi kin san mara lafiya" "Mijinki be san in da ake sai da kayan daɗin ba ne? Ba zan siyo ba, kina ta wani kwana kwana Allah ya raba lafiya". Murmushi kawai Amira tayi, ta kashe wayar ta kalli cikinta tace "wai wa ya ga Amira da ciki, ko ya zanyi oho min?" Ihsan ta kalli Imran a shagwaɓe tace "my Own naga ka rame sosai" "To ya ba zan rame ba, wata guda a daji, bamu daɗe bama, duk da an karkashe wasu, But Alhamdilillah muma mun samu gagarumar Nasara" "Allah sarki My, ai ban san yau zaka dawo ba, amma gayamin me kake so in dafa maka kaci?" Tai maganr tana shafa gefen fuskarsa. "Ai naci Abinci" ya bata amsa "Kamar yaya kenan?" "Amira ta dafa Abinci ta bani" Jiki a saluɓe ta kalli Imran tace "saboda me zata dafa abinci ta baka kaci?" "Saboda na dawo a galabaice, ke kuma ba kya nan, dole ina buƙatar Abinci" "Amma my meyas baka kirani a waya ba?" "Da wace wayar? Ni wayata ba caji a ciki" "Dan Allah My kar ka sake cin Abincin ta, ni wallahi bana son mu fara faɗa daga dawowar ka, amma gaskiya banji daɗi ba, ina fatan wani abu be faru tsakaninku ba yadda na tarar da ita daga ita se kai a gidan nan da wannan shigar" Imran yace "Look Ihsan, don't add me another stress please, I need to rest, ban shirya fara jin complains ɗinki ba, tunda har yanzu baki yadda da ni ba shikenan" A shagwaɓe tace "no is not like that at all My, na yadda da kai have a rest my Dear" Tai maganar tana shafa fuskarsa. Se zuwa magariba sannan Imran ya watstsake gaba ɗaya, kamar ba shiba sedai ramar nan tana nan da yayi. Bayan ya dawo daga sallar isha'i, Abba ya kira wayarsa suka gaisa, Abba yace "Imran ya jiki ha gajiya?" "Abba komai lafiya ƙalau Alhamdilillah" "Kaje Asibiti kuwa?" "Ai Abba lafiyata ƙalau ba wata matsala" "No, duk da haka yakamata a bincika lafiyarka, ban so daga dawowarka in fara maka surutu akan gidanka ba, amma kayi haƙuri ba yadda na iya ne, nace mahaifiyarka tai min magana akan tana so a raba musu gida, wai Amira ta daki abokiyar zamanta harda ji mata rauni, ya a kai ban san Maganar ba?" Imran yai ajiyar zuciya yace "Abba, misunderstanding ne kawai tsakaninsu, kuma na sasantasu tun kan in tafi, dan haka ba wata matsala Abba" "Yawwa ɗan gidan Abba, haka nake son ji dama, Ubangiji Allah yai muku albarka gaba ɗaya" "Ameen ya Allah Abba, nagode sosai" Ya taka ya ƙarasa gida, dan bejin ze iya zuwa ko ina, yana buƙatar yaje gida ya huta. Duk da yadda Imran yake a gajiye, ga raunuka da suke jikinsa, amma ya ɓoye ga rashin cikakkiyar lafiya, amma ba Wanda ya gayawa, haka ya suka sha soyayyarsu shi da Ihsan, yana mamakin yadda har yanzu Ihsan bata taɓa fashin period ba, yana fatan ubangiji Allah ya dube shi kar ya jarrabe shi da rashin haihuwa, mussaman ga irin aikin da yake yi, duk da ita mutuwa ba ruwanta da aikin da mutum yakeyi, amma kowani lokaci ze iya rasa ransa saboda aikin nan, gashi bashi da wani ɗa, be sani ba ko Allah zesa ya samu nan kusa. Ya shafa kan Ihsan dake kwance a jikinsa yace "My, haryanzu babu wani labari ko, ina son Yara sosai Ihsan" Gaban Ihsan ya faɗi tace "My ka fara ƙosawa ko? Ni kaina ban san meyafaru ba, Amma dan kayi haƙuri ka tayani Addu'a, Ni kaina ina fatan in samu ɗin" "Ba ƙosawa nayi ba, ki kwantar da hankalinki, Allah yana sane damu ze bamu very soon insha Allah" "Allah ya amsa" "Ameen Swtheart" Imran soyayyar su kawai suke sha da Ihsan, sam Amira ta nuna bata damu da zamansu bama, ta dinga ɗauka tamkar ita kaɗai take rayuwarta a gidan. Imran yai kamar ya manta da zaman Amira, amma ƙasan zuciyarsa yana saƙa abubuwa da dama a kanta, yana mamakin kulawa da tausayawa da take nuna masa lokuta da dama, haka nan seya dinga jin tausayinta, mussaman idan ya tuna ranar da take cewa ta barshi da Allah, ita marainiya ce, duk da abun da yake mata hakan be hana daze tafi tai hawaye ba. Kuma be hana ta dinga tura masa messages na fatan Alkhairi ba, be hana da ya dawo ta karɓeshi hannu bibbiyu ba. Ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli agogo yaga dare yayi sosai, Ihsan na ta faman baccinta, ya miƙe a hankali ya ɗau system ɗinsa ya fita falo ya zauna. Amira kam idonta biyu a lokacin, tana falonta Salla, ta idar da Addu'onita, ta cire hijjabin zata koma bedroom, amma jin motsi a babban falo yasa ta ɗan tsorata, ta Ajiye hijjabin ta lallaɓa za taje ta rufe ƙofar falonta, karma in wani abun ne ya shigo mata ɗaki. Sedai tana leƙawa ta hango Captain yana danna System, ajiyar zuciya tayi, ta fito falon, ɗan ɗaga kai yayi ya kalleta, ya mayar ya sunkuya yana aikinsa. A kusa dashi ta zauna, ta kalli System ɗinsa, taga samfuran bindigogi ne kala kala, yake dubawa. Ta ɗan jingina da jikinsa tace "ka bani tsoro fa" Be kalleta ba yace "tsoron me?" "Motsin ka naji, naji tsoro sosai" "Meyasa baki bacci ba har yanzu?" "Baccin ne be zo ba" Ya jinjina kai yace "yakamata ki kwanta, mussaman da baki da lafiya kinyi rama sosai" Amira ta sake kwanciya a jikinsa tace "ai ni dama nafi son in rame ɗin" "Meyasa kike so ki rame?" Tana sane tace "Na fi son in koma kamar Ihsan nima" "No, gara ki zauna yadda kike kinfi kyau" Ɗan ƙura masa ido tai, tai murmushi tace "dagaske ina da kyau Captain?" "Eh kina da kyau mana, tunda kike kama dani, kuma kinga ni kyakykyawa ne" Sosai Amira take dariya, tace "ji yabon kai, ka bari a faɗa mana, ba fa wani kyau ne da kai ba fa" "Ki bari mata ta ta jiki, kina cewa bani da kyau, duk abunki tunda mata ta tace ni me kyaune nasan ina da kyau, kika bari ta jiki faɗa zakuyi, kuma ki ka mata rashin kunya in zaneki" Tsaki Amira tayi tace "dan Allah wai zaman me nake da kai, tunda baka sona, dan Allah ni ka sakeni in Auri wanda yake sona". Kallonta Imran yai yace "so kike Abba yai fushi da ni kenan?" "Ai cewa zan nina ce ka sakeni, dan Allah ka sakeni, wallahi bayan tafiyar ka hawan jini seda ya kamani saboda ɓacin rai" tai maganar tana hawaye "In jinin ya hau Akwai magani ai" Kallon Imran take, sam be damu da damuwarta ba, miƙewa tai ta tafi ya barshi a gurin. Yabi bayanta da kallo har ta shige, seda ya ɗanyi murmushi, daga ƙarshe ya koma ɗaki ya kwanta, amma da yayi juyi se Amira ta faɗo masa rai, Gaba ɗaya tunaninta ya hanashi bacci, Abincinta me daɗi, muryarta ma me daɗin sauraro. Ihsan ta shiryawa Imran breakfast, ta fita gurin aikinta, da yake Imran be tashi daga bacci ba, ta tafi gurin aiki, Ihsan na fita, Amira ta kwashe kayan Abincin Ihsan, ta jera masa nata. Da Imran ya tashi daga bacci, yai wanka ya fito, ya zauna ya kwashi Abincinsa, ba tare da sanin wanda yai girkin ba. Se la'asar Ihsan ta dawo, ta shiga Kitchen da hanzari ta ɗora girki, daf da magariba ta kwaso Abincin ta kawo dining ɗin babban falo, sedai ta tarar da kwanukan Abincinta a ƙasan dining. Mamakine ya kamata, ta bubbuɗe taga yadda ta zuba masa Abinci be taɓa ba, tana tsaye tana tunani sega Imran ya shigo, ya ƙarasa dining ɗin yana faɗin "My kin dawo? Ya aikin?" Ta kalleshi tace "ya a kai nai maka girki ba ka ci ba?" Imran yace "ni ɗin naci mana". Ta buɗe foodflask sega Abinci a ciki, babu alamar an taɓa. Yace "Aini ba wannan flask ɗin na gani da safe ba" "Kaga irinta ko, inyi magana ace na fiye neman Magana, wanne na ajiye idan ba Wannan ba" Amira ta fito daga sashenta, hannunta riƙe da ɗan ƙaramin kwandon shara na Kitchen, Imran yace "Amira, meyasa kika ɗauke Abincin Ihsan kika ajiye naki? Haka akeyi" Amira tace 'Ai ba Ihsan ce kawai matar gida ba, nima matarka ce, akan me sedai ta dafa ta baka ni zaman me nake, to nagaji shiyasa nai mata haka, rashin adalcin da akemin ya fara isata saura ma raba kwana" "Shut up!" Imran ya daka mata tsawa, "ke duk yadda za'a lallaɓaki sekin nemi magana, meyasa ki kai haka? Ko dan kin ban Abinci ranar da na dawo naci, shine ki kai haka? Ke idan baki nemi Magana ba ba kyajin daɗi ko? Waye ya saki? Kuma da ubanwa zaki raba kwanan fitsararriya mara Kunya"? Wata uwar harara Amira ta watsa masa tace  "koma da ubanwaye" "Ni kike gayawa haka?" "Tsakanin wuta da Aljanna wacce mallakinka da zaka sani, wanda zesa inji tsoron gaya maka magana?" Take ta koma masa ainihin Amiran ta, mara jin magana. Cikin zafin nama yai kanta, amma ko gezau balle tai yunƙurin guduwa. Yana zuwa ya murɗe kunnenta ɗaya, seda ta wani uban fitsari ya matsota, "ni kikewa rashin kunya ko? Kinga kwana biyu ina saurara miki ko? Shine kika samu damar yin wannan rashin mutuncin ko?" Riƙe hannunsa da ya riƙe mata kunne tai tana kuka, ya dungurar da ita a gurin, ya nufi inda Ihsan take, ya riƙo hannunta yace "Am sorry my, kiyi haƙuri wallahi ban san yadda a kai haka ta faru ba" Ya ja hannun Ihsan zuwa ɗakinsu, yaje yaita lallaɓata yana tunanin yadda ze gaya mata ze tafi da Amira Lagos. Seda ya tabattar ta haƙura, sannan ya tashi ya fita sallar magariba, ya wuce Amira a falo tana kuka, shi har mamakin yadda Amira ɓarin hawaye kamar ba daga jikinta yake zuba ba yake, ya wuce ta ya tafi masallaci. Ihsan ta fito ta kalli Inda Amira take ta yatsuna fuska tace  "Wallahi in dai zaki cigaba da takara da ni a gidan nan, baƙi ciki Yanzu kika fara kwasa" Amira bata tanka mata ba, tai ta gama ta koma ɗakinta. Imran ya dawo daga salla, ya kuma hango Amira a zaune, yana nan tsaye be shigo ɗakin ba, se aka ɗauke wuta, nan da nan ta miƙe da sauri, tan waige waige tana ƙoƙarin laluben hanya, dan ba laifi Amira akwai tsoro. Jin ta tayi a jikin mutum, ware murya tai za tayi ihu, amma ya haɗe bakinsa da nata, ƙoƙarin ƙwacewa take daga jikin Imran, amma ya riƙeta gam. Seda yai me isarsa sannan ya kai bakinsa kunnenta yace "to fitsararriya, ga rashin kunya ga tsoro, ki shirya kayanki jibi in Allah ya kaimu zamu tafi Lagos tare" "Bazanje ba, ka tafi da Wannan ƙandararriyar" "Ni kike cewa ba zaki ba, ai ƙandararriyar ta fiyemin ke, Abba zaki cewa ba zaki ba, saboda idan na tafi dake ba wani amfani da zakimin, kuma a ƙandaren nake sonta" "Eh kaita son nata, ni cikani in tafi, ka murɗemin kunne ban maka Komai ba" "Cigaba da ɗaga murya, ta zo ta ganki a haka zaki mata bayani ne, hadda saura raba kwana saboda baki da kunya" "To tsoron ta nakeji? Ai ba tsoronta nake ji ba, kuma ina kai ina tunanin Kunya a tare da Karuwa, ni ka ƙyaleni dan Allah" Ɗan saroro yai yana kallonta, duk da a duhu ne tana sauke numfashi a fuskarsa shima yana sauke mata, a hankali ya cikata ya juya ya nufi part ɗin Ihsan. Yana shiga ya zauna, sega wayar Abba nan, ya ɗaga ya gaida Abba, Abba yace "Imran yaushe ne tafiyar ka Lagos ne?" "Abba jibi in Allah ya kaimu ne" "To kasan dai yadda mu kai da kai, wannan karon tafiyar ta Amira ce, dan haka kai mata Magana ta fara shiri, nayi waya da kakarta da zasu zo da weekends, amma na gaya musu zaku tafi lagos, se Allah ya dawo daku tukuna" "To Abba, zan gayamata insha Allah" Ihsan ta kafe Imran da ido ko ƙiftawa ba tayi SHARE PLEASE A ko yaushe ina alfahari da ku, ina jin daɗin sharhin da kuke akan littafin nan, ina matuƙar godiya sosai, masu gyara, sharhi da ƙorafi duk ina godiya, wanda ban samu amsa saƙonninsu ba a dinga min Afuwa, abubuwane da yawa, sannan dan Allah masu bina pc suna in basu daga farko, ko in basu oage kaza, dan Allah ku dinga min uzuri, abubuwa sun min yawa sosai, ku dinga tambaya a groups ko Ku duba a watpad, nasan sone yasa kuke neman littafin, amma dan Allah a dinga min uzuri, sannan ga wanda suka turan kuɗin ruɗin Ƙuriciya kuma, su sakemin magana Please in saka su a group, this week zan fara free pages insha Allah, Nagode" Domin Sharhi, gyra ko shawara 07063065680 [2/8, 7:57 PM] Ayshercool:  🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                 *🌈NIMCY'S LIBRARY🌈* _Readers gareku, masu tambayar old books na NIMCYLUV SARAUTA, tayi shiru ne domin tana bada bunus kafin azumi, to Finally the day is here, tana sai da littafan ta gaba ɗaya akan 3k gaba ɗaya littafan guda 14 ne, to bisa Bunus ɗin da tayi na tsayin sati guda dukkan mai so zai biya 1500 mai makon 3k😍, nasan baku karanta littafan ta na baya ba, da am sure za kuce sunma fi na yanzu daɗi❤️🤨_ So what are waiting for.....??? Go and subscribe your own... Abu Maleek Sirrin mu Uncle ne The new emir Izzar so Sai na aureta😍 Tsintacciya E.t.c guda 13 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 a biya asha karatu Tabbas za kuyi farin ciki littafan babu baya #Love #Romance #Destiny Bonos ya fara 6/2/2022 Share fisabilillahi😍                                                                        41_42 Ya ajiye wayar, ya kalli Ihsan zeyi magana ta ɗaga masa hannu, "Yanzu Imran da ita za ka tafi, ina ji ina gani ka barni a nan? Ka ɗauketa ku tafi, Imran ina alƙawarin da kai min? Nasan ba zaka taɓa cikawa ba". Tai maganar zuciyata na matuƙar tafasa. Imran ya gyara zamansa Sannan yace "Ihsan, wallahi dan ta ni kin san ba zan ɗau yarinyar nan in ce zan tafi da ita ba, da kunnenki kin ji ai, Abba ne ya bada umarnin nan ba wai ra'ayina ne hakan ba, ki fahimceni mana". "Ni ka ƙyaleni, ba abunda zan fahimta, wannan ai cin fuskane taya zaka je ka zauna daga ita se kai a gida, kuma hankalina ya kwanta ba abunda ze faru? Gaskiya ni ban yadda ba" "To me ki ke so ayi? In cewa Abba bazan tafi da ita ba ko kuma yaya?, Da da bani da Aure mutuwa nayi? Ko kuma kwanakin da nayi a daji ba mace wani abu ta sameni, ke kanki da nake so  in ki kamin laifi muna kwana shimfiɗa ɗaya kuma in ƙaurace miki, meyasa kike tunanin wani abu ze haɗani da ita, haryanzu kin kasa yadda dani" Gaba ɗaya maganganun Imran jin su take a matsayin kalaman yaudara da rainin hankali, ta miƙe ta ɗau wayarta, ta tafi ɗayan ɗakin ta rufe ƙofarta. Imran ya shafi sumar kansa, ya kwanta akan gadon, ya fuskanci idan ya biyewa matan nan zasu maida shi mara hankali, kowacce da kalar tata rigimar, ba ƙaramin kwarjini ne da shi ba ko a wajen aiki, amma idan ya dawo gida mata su dinga caza masa kai, ya ɗakko wayarsa ya hau chatting. Yana dubawa ya ga Khalid online, yai masa sallama Khalid ya amsa yace "kai Angon biyu ya? Ka wartsake kenan?" "Tun yaushe, zan dawo aiki ma" Khalid yace "Haba? Yaushe zaka zo?" "Jibi in Allah ya kaimu, zan taho insha Allah" "Masha Allah, wannan karon kai ɗaya zaka taho ne?" "Ina fa, Abba yace sena taho da Amira" Khalid ya tura masa emoji na dariya yace "gaskiya Abba ya kyauta, ka ga an biyata kwanakinta da Ihsan tayi" "Wallahi Khalid mata na da matsala ta gaske wallahi, Ihsan ta ɗau fushi da kumbura baki Abba yace in tafi da Amira, ban taɓa sanin haka Ihsan take ba, ban san da yawa daga halayenta ba se da na Aureta, ta fiye ƙorafi da rashin haƙuri, ina tausaya mata da ɗaga mata ƙafa amma ba ta gani sam" "Ai dama hakane, kai ma nasan ba ta san da yawa daga halayenka ba se yanzu da ku kai Aure, sedai ku cigaba da haƙuri da juna, ka dai rarrasheta kar ka tafi ka barta a damuwa" "Ai na fara gajiya da rarrashin nan, anyway na san dai abunyi" "Aikam ya kamata kasan abunyi tun da wuri" "Shikenan sena shigo Lagos ɗin" "Allah ya kawo ka Angon Amira" Imran yace "za kaga Angon Amira, idan Ihsan ta jika" "Ai ni Amira nakeyi dama" Suka cigaba da hirarsu ta abokai. Ihsan kuwa zuciyarta na tafasa ta kira mahaifiyarta a waya, kusan missed calls uku bata ɗaga ba, ta ajiye wayar tana safa da marwa a ɗakin, tana jin Kamar zuciyarta tai bindiga. Mamanta ce ta biyo kiran da tai nata, da hanzari ta ƙarasa ta ɗauka, ta na ɗagawa tace "Mummy na shiga uku" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, kika shiga uku da me?" "Mummy wai da Amira ze tafi lagos, na rasa me naiwa tsohon nan ya tsaneni, baban Imran sam baya ƙaunata, baya sona da ɗansa, akan mw za'a ɗau Amira a tafi da ita? Me nayi masa haka fisabilillahi, kin san Yarinyar nan karuwa ce, wallahi tsaf zata iya jan hankalinsa" Mummy tace "tsaya, wai waye ya gayamiki da ita ze tafi ne?" "Ammmi yanzu fa yai waya a gabana da Abban, ya sake maimaita masa ashe tun da ya dawo aka tsara in ze tafi Lagos ya tafi da ita, amma be gayamin ba, wallahi Ammi tsoro nakeji, karya tafi da ita kashina ya bushe yaje tai masa wnai abun" "Ke kwantar da hankalinki, ba abunda zefaru nasan abunyi" "Mummy meye abunyin to?" "Ki ɗan sauraramin, zan waiwayeki Insha Allah" "To amma fa Mummy jibi zasu tafi" "Ba abunda zefaru tsakanin su, nina gayamiki" "Amma Mummy, wane tabbaci ki ke da shi akan hakan?" "Ke ina ruwanki ne? Ina da abunyi ni a kai" "To Mummy, Allah yasa abun yayi". Ta kashe wayar a sanyaye, ta gayawa Ijsan hakanne dan kawai hankalinta ya kwanta, amma ba ta da wani abu da zata iyayi a kai, tasan halin Ihsan da damuwa da saka abu a rai. Lambar Ammi ta kira, seda ta kusa katsewa sannan ta ɗauka tace "Afwan bana kusa da wayar ne,barka da dare" Mummy tace "Yawwa barka, ya iyali?" "Alhamdilillah, ya zafin nan?" "Gashi nan Alhamdilillah, nace kin san kuwa Imran jibi in Allah ya kaimu ze tafi Lagos da matarsa?" "Bari kawai, naji wallahi ba yadda ban ba akan in shawo kan mahaifinsa a janye maganar nan, amma abu ya gagara duk ta in da na ɓullo masa seya kange, kwana biyu na kasa gane kansa, amma ku kwantar da hankalinku, Shi Imran ɗin na san yadda zan dashi, tunda nina haifeshi dan Allah karku damu akan Wannan Yarinyar" "To shikenan, dama Ihsan ɗin ce ta kirani a waya hankalinta a tashe, shiyasa nace bari in kiraki, amma tunda kince haka shikenan" "Bakomai, dan Allah ki kwantar mata da hankali, ba wani abu Insha Allah" Mummy tace "shikenan, seda safe, ki gaisarmin da daughter na please" "Za taji insha Allah". Amira kuwa cike da nishaɗi ta koma ɓangaren ta, tana ji a jikinta burinta na daf da cika tunda Imran ya fara sakin layi, ga kuma tafiya za suyi tare. Anty ta fara kira a waya ta sheda mata cewar zasu tafi Lagos jibi tare da Imran, Anty taji daɗin hakan sosai tai murna, Antyn tai ta yiwa Amira Nasiha, sannan ta gargaɗeta da anyi mata wani abu na ba daidai ba wanda ba ta gansu da shi ba ta sanar da ita. Amira tace Anty ta bawa direba Akwati ya kawo mata, ta haɗa da tata dan tata ƙarama ce, wadda zata haɗa kayanta a ciki. Imran haka suka kwana ɗaki daban daban shi da Ihsan, da sassafe Ammi ta kirashi a waya, wai ta na son ganinsa, ko karyawa beba ya tafi gidansu. A bedroom ya iske Ammi, tana karyawa, ya gaisheta ta amsa masa sama sama, yace "Ammi naji kince kina nemana, Allah yasa lafiya?". "Lafiya ƙalau, da ma ba wani abu bane ba, batun tafiyar ka da Yarinyar nan da ubanka ya dagw a kaine na kiraka in maka kashedi, kamara yadda na sha gaya naka da farko, ni ba zan taɓa murna da haɗa zuriya da tsohuwar kilaki ba, dan kowa irin Arziki yake bibiya bana tsiya ba, ina me ja maka kunne da kiranka da babbar murya, ba kai ba Wannan Yarinyar kar inji ko inga abunda ze ɗagawa matarka Ihsan hankali ko ya ɓatamin rai, ina Ganin mutuncin mahaifiyar Ihsan dan haka ba zan taɓa bari ko in goyi bayan a wulaƙanta mata 'ya ba, idan kuka je Lagos ka nemi wani gidan a Barrack ko a waje ka ajiyeta, karka kuskura ku zauna a gida ɗaya tare" Da mamaki ya kalli Ammi yace "Amma Ammai, idan na ajiyeta ita kaɗai wani abun ya sameta Abba ze ɓatamin rai". "'yar yayace ita da swka kula da ita ko kuwa? Kabi umarnina ka zauna lafiya, idan ka kuskura wani abu ya shiga tsakinka da Yarinyar nan zan iya mummunan saɓa maka, bana ƙaunar yarinyar nan so nake yadda tazo gidanka ta fita ba tare da wani abu ya haɗaka da ita ba" Imran ya jinjina kai yace "to naji zan kiyaye insha Allah" Ammi tace "da yafi maka, ka tashi kaje falo ka karya" Tai maganar tana miƙewa tsaye, falo suka fito jikin Imran duk a saluɓe, suna fitowa Abba yana shigowa falon, ya kalli Imran yace "kai lafiya kuwa, kake tafe a safiyar nan?" Imran ya dake yace "lafiya ƙalau Abba, nazo yi muku sallama ne kasan gibe in Allah ya kaimu da la'sar zamu tafi" Abba yace "Au ai na zaci wani abunne ya faru, maimakon ka taho dasu ko ka tabo da ɗaya se ka taho kai kaɗai? Ko da kwaɗayin girkin mamanka ne ya kawo ka?" Imran ya ƙaƙalo murmushi yaiwa Abba yace "A'a Abba" "To shikenan, ina Minal ta kawo mana kayan Abinci nan mu ci gabaɗaya" Aka kawo musu Abincin nana, suka ci tare, suna ci Abba yana sakewa Imaran Nasiha daban daban akan Rayuwa, da kuma riƙe matansa da amana da gaskiya gami da adalci a tsakaninsu... Anty kuwa da kanta ta kaiwa Amira akwatin, ta nunnuna mata abubuwan da sukafi mahimmanci ta tafi dasu. Sannan tace "Amira, you got a very nice to win your husband heart, kin samu cikakkiyar dama daga ke seshi, ba wani shamaki ko damuwa da zata gifata muku, ki tabbatar da kinyi duk me yiwuwa ki janyo hankalin sa kanki, sannan ki duƙufa da addu'a kin san itace gaba akan Komai, ki jajirce ki ƙwatarwa kanki 'yanci a gidan miji, kishiyarki ba ta fiki Komai ba, duk abunda ake nema agurin mace kema Allah ya baki, dan haka ki dage kiyi ƙoƙarin yin duk wani abu da zw janyo hankalin sa kanki kinji ko?" Amira ji tai tamkar Anty ta san halin da take ciki a gidan, duba da yanayin nasihar da take nata, Amira tace "to Anty insha Allah, zanyi abunda kika ce" Anty ta bata wasu zafafan turarraykan, da kayan gyara jiki sannan tai mata fatan Alheri ta tafi" Amira ta raka Anty har bakin motarta, suna tsaye suna magana Ihsan ta dawo, tana zuwa ta gansu a tare da Anty ta ja wani uban tsaki ta wuce, daga Amira har Ihsan ba wanda ya kulata, suka cigaba da maganarsu bayan sun gama, sannan Anty ta hau mota ta tafi. Tafiyar Anty babu daɗewa sega wasu 'yan uwan Ihsan sunzo, cousins ɗinta biyu da ƙawayenta biyu. Ihsan ta saukesu a Babban falo, suka baje suna hira, ta kawo musu Abinci suka zauna nan suna ci ɗaya daga cikin su tace "ke wai ni ina kishiyar taki ne, tun da nake zuwa ban taɓa ganinta ba fa, duk zuwan da mu kai bata nan" Ɗaya tace "to ta ina zata zauna, matar da aka ce miki Karuwa ce, sufa irin wannan ba denawa suke ba, da Auren ma se subi maza" Ihsan ta yatsina fuska tace "ba dai kishiyata ba, dan wannan ba ta kai kishiya a idona ba, Karuwace fa bin maza take, kwararo kwararo aka ɗakkota aka liƙa masa dan a temaka mata, kuma zaman gadi take dan ba ta kai mijina ya saurareta ba wallahi" Wata uwar shewa suka saki gaba ɗaya "Lallai Ihsan ba ki da dama, wato liƙa masa ita a kai, to ai shikenan, ni dai ina son in ganta" Suna cikin hirarsu 'yar halak sega Amira ta fito, hannunta da labulaye zata bada wanki, ta kalli Baƙin Ihsan da su kai tsit saboda fitowarta, tace "baƙi mu kayi ne? Sannun ku da zuwa" Shiru su kai, se ɗaya daga cikin su ce tace "Yawwa sannunki" A fusace Ihsan tace "Nabila ina ruwanki da ita? Meye na amsa mata, gurinta ki ka zo?" "Au ko itace kishiyar taki ne?" "Itace fa" "Kan uba, lallai wannan ai 'yar galace, ba itace kwanaki akace za ta fito a wata rawa ba, video ɗinta ya dinga yawo ba" Ihsan tace  "to itace ta sa aka fasa Auren Uncle Hassan, ta rufeshi a banɗaki" Wucw su Amira tai, taje ta kaiwa me wanki kayan, ta dawo ta kuma wuce su zata shiga parr ɗinta. 'gaskiya wannan annamimiyar Karuwa ce, taɓɗijan wallahi kibi a sannu kar kema tai waje dake, Allah ma ya tsare kar a samiki HIV, tunda tabi musulmi tabi Arna dan tsabara iya Akuyanci" Amira ta juyo ta kallesu tai murmushi tace "Ai Karuwanci ya gama min Komai, nai suna nai kuɗi a dalilinsa ƙarshe kuma Allah ya bani mijin sokuwa na Aura, ai Karuwanci yai riba" ta ƙarasa Maganar tana shigewa ɓangaren ta, nan suka ɗau salati gaba ɗaya, suka dinga ziga Ihsan, suka dinga zigata akan yadda za tai da Amira, ita kuma ta dinga cika baki tana cewa ai mijinsu baya sonta, dan ko ɗakinta baya shiga, ta dinga gayamusu yadda Imran yake wulaƙanta Amira, suna shewa suna ƙara ɗorata a keken ɓera. Yadda Ihsan tai watsi da Imran, shima haka ya shareta, dan ya gaji da aikin rarrashin ta, shima ya shiga haɗa nasa kayan, tun daren ds zasu tafi Ihsan take fargaba take faman koke koke, ta bi ta dami kanta ta ƙi cin Abinci saboda fargaba. Amira ma ta kammala shirinta tsaf, ta haɗa duk wani abunda take buƙata, wajen ƙarfe sha ɗaya na safe, Imran ya shiga ɓangaren Amira, kai tsaye ya tafi bedroom ɗinta, ya tarar da ita daga ita se underwear tana shafa mai, da alama wanka tayi. Ya ɗanyi turus saboda tozali da kyakykyawar surarta, fatarta se wani sheƙi take kamar bata shiga rana, Gashi ta shafa mai se ƙyalli take, gashi ta ciko da ga Wannan ramar da tayi, saurin ɗauke kansa yayi yace "ki zama cikin shiri tun ƙarfe biyu zamu tafi airport, idan kuma kika ɓatamin lokaci ba jiranki zan ba, zan tafiyata ne" Ɗago idanunta tai tana kallonsa tai wani murmushi tace "to My zan shirya da wuri insha Allah" "What? Waye my ɗin naki?" Yai Maganar yana kallonta Ta ɗan kashe murya tace "Gashi nan a tsaye a gabana, namijin duniya sha gwagwarmaya, soja maganin wani sojan, ɗaya kake tamkar da goma, sadauki me abun bajinta, dogo Mijin Amira me hannun kyauta" Imran be san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba, that girl is very Funny at times, duk da abun haushinta yafi yawa, yace "Kin fiye shirme, ni dai ki shirya da wuri" "An gama ranka ya daɗe, na haɗa Akwatina ma" Yace "good sannan ya juya ya fita" Tabi bayansa da kallo tai murmushi haɗi da jinjina kai. Ta shirya cikin riga da skirt na shadfa, ta fito falo, tana ta kaiwa tana komowa tana shiri, ta fita farfajiyar gidan ta tarar da Ihsan tana waya, Ihsan ta watsa mata wani Mugun kallo, Amira tai murmushi tace "Wai ke dama da na gayamiki se zaki san kin tafi da mijina Lagos kinyi wata biyu, ba ki zaci zan rama ba kenan? Ai dama na gayamiki tuntuni gara tun da wuri ki dena wannan harare hararen, he is now my not yours, don't ever under estimate the power of a Woman like me, Karuwancina me license ne, kuma lokaci ne yazo da zan ɗanɗana miki abunda kika min, wallahi Ihsan se kin zubar da hawaye fiye da yadda kika sa na zubar, bana riƙo ina da manta abu, amma kin shiga sahun Mutanen da har in koma ga Allah ba zan manta abunda su kai min ba, ni ba zan cutar da ke kamar yadda kika min ba, Amma daga yanzu ki rubuta ki Ajiye cewar Imran namu ne mu biyu ba ke kaɗai ba, Ihsan iliminki na addini da larabcin da kike ba suyi miki amfani ba, idan har son tsakani da Allah ki kewa Imran, bekamata ki zuba masa ido ya kai kansa ga halaka ba, hakkina kawai ya isa ya nesanta shi rahamar Ubangiji, Amma son zuciya ya katange miki idanunki, kanki kawai kike kallo, Yanzu zan nuna miki match ɗin da kika tari ba ki da 'yan wasa sam, yanzu za'ai playing game ɗin yadda yakamata, zan nuna miki kishi da Karuwa se macen da ta shirya"  ta ƙarasa Maganar tana huci, ta bar Ihsan a gurin baki a buɗe tana kallonta. Amira ta koma ɗaki ta kwaso Akwatinta, ta fito dasu harabar gidan ta ajiye, da duk abubuwan da take buƙata. Ihsan kuwa ɓangaren ta ta koma, ta fashe da kuka hadda sheshsheƙa, ji take kamar ta kunnawa gidan wuta duk su mutu a ciki saboda baƙin ciki, Imran se biyu saura ta shigo gidan, a gurguje ya leƙa ɓangaren Amira, ya tarara ta shirya tsaf, yace "yawwa gara da kika shirya ai, an sa miki kayanki a mota, kaya kawai zan canza mu tafi" "Ya ma za'ai in tsallake maganar Husband ɗina, na shirya tuni" Bece komai ba ya wuce part ɗin Ihsan, aikuwa ya tarar tana ta uban kuka, idonta kamar an zuba mata barkono, sunyi jawur kamar ba ita ba, ya zauna ya dinga bata haƙuri yana kwantar mata da hankali, Wani Mugun haushin Imran take ji, ji take tamkar ta shaƙeshi, dan ita gani tai Kamar yana ɗokin tafiyar, ya miƙe a gurguje ya watsa ruwa, ya canza kaya yace "Ihsan ko bakin mota ba zaki rakani ba?" Girgiza kai tayi tace "A'a kuje kawai" "No taso ki rakani" Haka ya janyo Ihsan suka fito, yana ta cigaba da rarrashin ta yana rungumeta, Amira kuwa ta sha ɗaurin ture kaga tsiya, tayi parking ɗin gashinta. Fuskarra babu kwalliya amma shar da ita tai kyau se ƙamshi take. Amira gani tai Imran ya lalace a gurin Ihsan, se hawaye take yana goge mata yana Magana ƙasa ƙasa. Amira tace "My love kace kar in ɓata maka lokaci, na shirya da wuri amma kai ka tsaya Sallamar ta isa haka" Gaba ɗaya suka tsaya suna kallon Amira, kalmar my love ɗin da Amira faɗa ce ta daki ƙirjin Ihsan, ba shiri ta zame hannunta daga na Imran ta koma cikin gida, Idan Imran yace ze bita yasan faɗa zasuyi babu lallai ma ta saurareshi, ga lokaci yana ƙurewa dan haka kawai ya nufi inda motar take. Ya buɗe gaban motar ta shiga, sojan da ya kai Amira gurin Kwalliya shine Yake jan motar, Imran be cewa Amira uffan ba, itama ba ta tanka masa ba, har sukaje airport. Ƙarfe biyar da mintuna goma suka isa Lagos, se wajen shida saura sannan suka isa gidan Imran da ke barikin soja na Ikoyi. Amira ta san tazo Lagos saboda bambancin al'ada, tunda syka shigo cikin Barack ɗin take ganin mutane kala kala, har suka isa gidan Imran. Da alama akwai kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da abokan aikinsa, dan tun daga gate da suka taho, yake gaisawa da mutane. Gidan ɗan madaidaici ne me kyau, kan Imran yazo yasa aka gyara gidan, amma duk da haka gidan yayi ƙura sosai, ba wani gayara a kai masa na musamman. Imran ya kalleta yace "ki shiga wancan ɗakin akwai toilet kiyi alwala kiyi salla. Ta amsa masa da to. Ya shiga ɗaya ɗakin, yai alwala yayi salla, saboda lokacin salla ya ƙure ba ze samu wanda za suyi jam'i a masallaci ba, ya idar da salla ya fito ya tarar da Amira a zaune a inda ya barta ya kalleta yace 'Ke sallar ma ba zakiyi bane? Nace ki shiga kiyi alwala kiyi salla amma kin zauna" A gajiye take ta ɗan zumɓura baki, kai tsaye  tace "period nake" Ɗan taɓe baki Imran yayi yace 'ai seki tashi ki shiga da kayan, ko a nan zaki ta zama?" "Nifa gani nai gidan duk ƙura, a haka zan saka kayana?" "Zauna in zo in gyara miki" yai maganar cikin gatse. Knocking ƙofar falon a kayi, Imran yaje ya buɗe wata mata ce me ɗan shekaru ta shigo hannunta ɗauke da flask na Abinci, suka gaisa da Imran cikin broken English Matar tace "Oga wannan kuma sister ɗin ka ce?" Imran yace "A'a matata ce itaama" Matar tace "Ka rabu da waccan ne?" "A'a matana biyu ne ai" Matar tace "yayi gata kyakykyawa, ga Abinci na kawo muku, dama megidana ne yace ai muku girki zaka zo" Imran ya karɓa yana murmushi yace "mungode sosai Iya Bola" ya karɓi flask ɗin ya shiga dasu, ya ajiye ya kalli Amira yace "bagidajiya baki iya gaida Mutane ba ko? Kina kallonta tana kallonki amma ki kasa gaisheta" "To ni me zance mata, ni iya turanci nayi? Ni ba wani gane me take faɗa nake ba" "Ai dama ina zaki gane, tunda ki ka ajiye makaranta kika dena zuwa, ki ka kama shirme" Amira tace "ni wallahi ban ajiye makaranta ba, dan nayi Candy kuma Anty tace min ma zan cigaba da makaranta, naga ma dai a makarantar tamu ba irin wannan turancin ake ba" Ta ƙarasa Maganar hadda murguɗa masa baki, gajeren tsaki yayi yace "Nan barrack ne ba inda kika saba haukanki ba, idan kika kuskura ki kayi shirme casaki za suyi kuma ba abunda ya shafeni, ta shi kije Kitchen ki ɗakko plate kizo kici Abinci" Tashi tai tana yatsuna fuska, ta shiga Kitchen ɗin duk yayi ƙura, ta ɗauki plates ta ɗauraye ta fito falon. Ya karɓa ya buɗe flask ɗin Abincin, teba ce da miyar shuwaka, ta sha bushshen kifi da ganda, se ƙamshi take. Imran ya ɗibi nasa ya tura mata sauran, yaje ya wanko hannunsa yazo ya zauna, ita dai se binsa take da ido kamar wata sokuwa, ya fara cin Abincin yaƙi kulata, Yunwa ta isheta dan haka ta  matsa  gabansa ta sa hannu, be kulata ba ya cigaba da cin Abincinsa. Loma ɗaya tayi da ƙyar ta haɗiye, ga tsamin garri, ga miyar ɗan banzan yaji ga ɗacin shuwaka,  ja da baya tayi tana suɗar baki saboda yaji "ni gaskiya ba zan iya cin wannan Abincin ba, ba daɗi ga yaji, ni gaskiya bana cin teba" Imran sake jan plate ɗinsa yayi, ya cigaba da aika tebarsa, Amira ta koma gefe ta zuba masa ido, ya gama ci yaje ya wanke hannunsa, ya fita ya barta. Ta gaji ga yunwa tana ji amma ta tashi ta shiga ɗakin da ya nuna nata, sauran kayan Ihsan ta gani a ɗakin, ta kwaso kayan ta ƙulle ta ajiyesu a gefe ta shiga aikin gyaran gidan nan, tun daga ɗakunan, har zuwa banɗakuna falo da Kitchen, haka ta gyara ko ina yai fes. Se da Imran yai sallar isha'i sannan ya dawo Gidan, ya sissiyo kayan Abinci da kayan amfani, yai makin ganin uban aikin da Amira ta sha, yaje bakin ƙofar ɗakin da take, yai knocking. "Yes come in" Ya ɗaga labule yace "ga kayan Abinci can na kawo, ki tashi ki dafa wani abun ki ci" Tace "to in dafa da kai ne?" "A'a zan ƙarasa wannan tebar" "Zafa ta ɓata maka ciki, ka bari in dafa Abinci da kai" "Nace miki zanci wancan" "Shikenan" ta bashi amsa. Duk wani abu da yakamata Amira tana yiwa Imran, gyaran gida yi masa girki, ruwan wankansa da duk abunda yakamata tana masa, sedai gurin kwanan kowa daban, Kwanakin su Huɗu a Lagos, amma Ihsan bata taɓa kiransa a waya ba ko da wasa, ya zuba ido yaga iya gudun ruwanta amma, ko flashing ba tayi masa ba. Ya ɗau wayarsa da kansa ya kirata amma taƙi ɗagawa, yai mata missed calls sun kai goma amma taƙi ɗaga ko guda ɗaya, haushi ya kamashi ya harzuƙa yai jifa da wayar cike da jin zafin abunda Ihsan tai masa, hakan yai daidai da fitowar Amira da kwanuka. Ta kalli Imran tace "lafiya kuwa?" Banza yai mata ya cigaba da sauke numfashi, ajiye masa Abincin tayi tace "Koma meye Allah ya baka haƙuri" ta ajiye masa Abincinsa ta bar masa falon dan kar koma meye ya huce a kanta. Hankalin Amira ya ɗan kwanta, duk da ba shiga shirginta yake ba amma ta sarara da ɓacin ran da take shiga saboda Ihsan, da yadda yake wulaƙantata saboda Ihsan. Da safe Amira ta na cikin aikace aikacenta Imran ya shiga gurin da yake motsa jiki, ta kammala breakfast ta bishi ɗakin bata taɓa shiga ba se yau, manyan ƙarafa ne a gurin da yake Gymming da su, a ranta tace "taɓɗijan bayan wahalar da ake basu gurin training, har wani Gymming yake saboda tsabar wahala" ta zuba masa ido tana kallonsa, ya ɗago ya kalleta yace ya dai. "Bakomai na gama girki" "Ok ina zuwa" ya bata amsa ya cigaba da abunda yake. "Ka dai ɗaga ƙarfen nan a hankali, kar ƙirjinka yai ciwo" ɗan murmushi yai bece mata komai ba. Wasu lokutan idan Imran ya fita tun safe se dare yake dawowa, kaɗaici yafara damun Amira, taji gaba ɗaya zaman garin ya isheta, ga maƙotanta duk ƙabilu ne taji gaba ɗaya zamab garin ya isheta, ga Imran ba ruwansa da ita. Yau be dawo da wuri ba, dan harta gaji ta kwanta bacci, can ta farka taji motsin Imran a Falo, ta taso ta fito ta sameshi a Falo, yana kallon Ball. Taje ta zauna a kusa da shi tace "Baby ashe ka dawo, bacci ne ya ɗaukeni" Yamutsa fuska yai yace "Baby kuma?" "Eh mana Baby" Hmm kawai yace, yana ƙara volume ɗin TV. "Wai meyasa yau baka dawo da wuri ba?" "Kinfa isheni, ki ƙyaleni da wannan surutan naki" Ɗan rausayar da Kai tayi tace "hmm shikenan, nasan da Ihsan ce ba zakace mata haka ba, ban san dalilin da yasa ka tsaneni haka ba, shikenan good night"ta tashi jiki a sanyaye ta tafi ɗakinta. Kawai se yaji be kyauta ba, yaji tausayinta, tana ta ƙoƙarin yin abunda ze faranta masa amma yana gwasale ta, se yaji ba daɗi. Kashe Kayan kallon yayi, ya tafi makwancinsa, ya zauna ya ɗakko System ya shiga dube dube, sedai ko mintuna goma be ba da shiga ɗakin, Amira tayi Sallama. Ya amsa mata, ta shiga ta zauna amma tai shiru ba tace Komai ba, "ya akayi ne?" "Alfarma nazo nema a gurinka" "Ina jinki" Hawaye ne ya fara bin fuskarta tace "dan Allah ka barni in koma gida, ka kaini inda zan hau ko motace, ban san  in takuraka da yawa, naga kamar biyoka garin nan na takura maka da yawa, kuma dama kace ba wani amfani zan maka ba, dan Allah kayi haƙuri zan koma in yaso se matarka ta biyo ka, kuma dan Allah kan in tafi Imran ka sakeni dan girman Allah, tunda nai Auren nan na buɗe sabon shafin ƙaddara a rayuwata, ban taɓa jin daɗin Auren nan ba, dan Allah ka sakeni" Ƙura mata ido yai yana kallon yadda take kuka, "na miki kama da namijin da ze Auri mace ya saka?" "Ni dai koma mene kawai ka sakeni dan Allah, banga amfanin Auren nan ba, na gaji! Na gaji! Am tired wallahi, duk da nasan ni ba wani zurfi nayi a ilimin addinin ba, amma nayi iyayina gurin yin biyayyar Auren nan, amma zuciya ta ta fara rayamun wani abu daban, baka ƙaunata baka tausayina hankalinka yana kan Ihsan, ka sakeni in samu wanda ze Aureni duk da laifin da nai a baya tunda na dena yanzu" Kashe System ɗin yai, yai kwanciyar sa yaja bargonsa, yaƙi kulata. Aikuwa ta ƙule, ta janye bargon daga jikinsa "Imran wallahi ba zaka maida ni mahaukaciya ba, am so much tired na gaji, dan girman Allah ka sakeni tun da ba ka ƙaunata, ni ka ƙyaleni in samu me sona in Aura" kuka take iya ƙarfinta Imran yace "A hakan zaki samu me son naki ya Aureki? Waze Auri 'yar gala?". "Eh a hakan wani ze Aureni ya zauna dani, ya soni a yadda nake" Cikin son cusa takaici Imran yace "au haba?" Fashewa ta sake yi da kuka, hadda sheshsheƙa, sosai ta bawa Imran tausayi, ya miƙe zaune ya shiga ƙoƙarin sake janyo bargonsa, amma ta riƙe bargon tana kuka. Haɗawa yai da ita da bargon a jikinsa, yace "rufemin baki ki dena min kuka, me nayi miki zaki dinga min kuka a daren nan? Saboda tsabar baƙin kishi da ke damunki zaki ce sena soki, to baza'a sake ki ɗin ba, zama kuma yanzu kika fara" Kuka ta cigaba da yi kamar wata ƙaramar Yarinya. Amira ta fuskanci kunnata kawai Imran yake. Tsaki tayi ta miƙe daga jikinsa, "ni kike wa tsaki?" "Na maka tsakin, mugu mara adalci kawai, wallahi Allah yana kallonka, kuma wallahi sena gayawa Abba duk abunda kake min, na dena rufa maka Asiri, Baka da adalci Imran ina ga baƙin cikin ka ne da na matarka ze kasheni, dannewa kawai nake ina maka biyayya dan cika umarnin Ubangiji, Amma wallahi na gaji" "Ni kike cewa mugu mara adalci?" "Na faɗa na kuma, mugu mara adalci! Mugu! Na faɗa Allah ya sakamin abunda kuke min" Miƙewa zaune yai ya fizgo ta da ƙarfin gaske yace "bari in gwada miki adalcin da kike so ɗin...... 🙄🙄🙄🚶🚶🚶) Ina Ganin sharhinku yana sani nishaɗi godiya nake 🥰🥰🥰😂 masu zagin Ihsan kuma, zan cireku a group ɗina dan a team ɗinta nake 😎😎😎 Gyara Sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 [2/11, 3:25 PM] Ayshercool:   🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                             43_44 Se da Amira ta saki ƙara, sakamakon yadda Imran ya janyo ta da ƙarfi sosai. Ba sani, ba sabo, ba tausayi, ko sassauci Imran ya aikata abunda zuciyarsa ke raya masa akan Amira, ya aikata abunda yake so kansa tsaye, ba tare da wani tausayi ko rangwame ba, sedai kash duk yadda ya zaci abun ba haka yake ba, saboda abunda ya tarar ya girgiza shi ya bashi mamaki matuƙa, he never thought that Amira was virgin. Seda ya dawo hankalinsa yaji wata irin nadama ta saukar masa, dan kusan abunda ya aikata ba shi da maraba da Fyaɗe, sedai kawai dan matarsa ce, ya kalli in da Amira ke kwance kukan nata ma ba ya fita, se sheshsheƙa da ajiyar zuciya kawai da take yi. Hannu bibbiyu ya sa ya dafe kansa, yai shiru yana tunani daban daban a zuciyarsa, kunya da tarin Nadama suka baibaye shi. A hankali ya kuma kallon Amira, jiki a sanyaye yace "Sannu" Bata ko motsa ba balle ta amsa, ta cigaba da kuka. Ya janyo bargo ya lulluɓe ta, ya miƙe jiki a sanyaye ya bar ɗakin. Gaba ɗaya Amira ta kasa banbance a halin da take ciki, a sume take ko a farke ta kasa ganewa. Ɗagota Imran yai daga kwanciyar da take, ya ɗaura mata towel, yana ƙoƙarin ɗaukanta amma ta bige hannunsa ta sakko daga kan gadon. "Ki tsaya in taimaka miki mana, na kai miki ruwa toilet ɗina" Wani banzan kallo tai masa tace "bana so" Ta lallaɓa jikinta, ta shiga ban ɗaki, ta nemi guri ta zauna, tana zubar da hawaye. Imran kuwa sake zama yayai yana tunani, ta yaya Amira zata zama virgin? Dama haka tana faruwa ko kuwa dai dama duk abubuwan da take ba ta aikata Zina?. Nan damuwa ta tarar masa, ya dinga tunani daban daban, yana cikin tunanin ta buɗe ƙofar banɗakin ta fito. Imran ya tashi da sauri ya tafi inda take, yana jera mata sannu, sedai a sannun nasa ko ɗaya ba ta amsa ba. Ta nufi ƙofar fita daga ɗakin. Da sauri yace "ina kuma zaki? Ki zo ki kwanta a nan, in duba first-aid box ɗina, in baki magani" "Bana so, ba zan sha ba ka riƙe abunka Imran, ai ni be kamata ka tausayamin ba, saboda Karuwace ni da aka tirsasa ka Aura dan ka taimaka Mata, Alhamdilillah yau burina ya cika, kaine ɗa namiji na  farko da na fara sani a rayuwata, kuma kaima ka sheda hakan, dan haka daga rana me kamar irin ta yau, kar ka sake kirana da Karuwa, kuma ka sanar da matarka da 'yan uwan ka ni ba Karuwa bace, abunda yake hanani maida martani idan an gayamin Karuwa, shine bani da hujjar kare kaina, Yanzu kuwa na samu wallahi duk wanda ya kuma cemin Karuwa dai dai nake da shi, zan mayarwa mutum daidai da abunda ya gayamin, ni ba Mazinaciya bace, bana aikata zina ban taɓa ba kuma ba zan fara ba, Imran kome na zama A duniya duk lalacewar da nayi a duniya da sa hannunku a ciki kune sila, kasan irin baƙar wahalar da na sha kuwa? Ka san irin raɗaɗi da zafin maraici kuwa,? Maraici na rashin uwa da uba, kuma na tashi a tsakanin maƙiya, mahaifiyarka taƙi karɓata, na tashi ina gararanba a gari wasu lokutan abunda zanci ya gagarrni, bayan tulin aikin da nake kamar jaka, ba wanda ya damu da ina jin yunwa, ƙishirwa ko bani da lafiya, ba wanda ya damu da wani kalar Abinci zanci a ina zan kwanta, saboda na rasa babban jigo abun jigina wato iyaye, ina da ɗan uwan mahaifiya a raye me tarin dukiya, amma na kasa samun gata, kiyayewar Ubangiji ita ta tsareni har na kawo wannan lokaci, amma idonku ya rufe kun gaza ganin naku laifin, kullum se jifana da muguwar kalma me muni, me ɗacin gaske Karuwa, hmmm don't try to pretend that kana jin tausayina yanzu, a baya na fi buƙatar tausaya wa, da ja a jiki amma ban samu ba, se baƙin wulaƙanci da na fuskanta a gidan ka, bakomai Allahn da ya ɗauki iyayena ya na ƙaunata kuma baze bari in taɓe ba" Tai maganar hawaye wani na bin wani, tai ficewarta da ga ɗakin, ta tafi ɗakinta ta faɗa akan katifa ta sake fashewa da kuka. Imran kuwa kasa motsi yai, Lallai an Cutar da Amira da kalma me munin gaske, amma koma da maraici wani abun ita ta janyowa kanta, dan babu yadda Za'ayi mutum yana aikata abunda takeyi ace ba Iskanci take ba, ga raye raye, ga shigar banza da gantali ga tsantsan fitsara da rashin kunya, ba wanda ze yadda ba karuwa ba ce. Haka Imran yaje yai wanka, duk jikin sa a saluɓe, ya gyara gadon ya nemi guri ya kwanta, tunani duk ya cika masa zuciya tare da matsanancin tausayin Amira. Da gari ya waye, da kansa yai gyare-gyaren gidan nan gaba ɗaya, ya dafa tea da yake ba wani iya girki yai ba yavfita ya siyo bredi. Sedai har ƙarfe goma Amira ba ta fito ba, wanda ƙa'idar ta bata wuce ƙarfe takwas duk baccin da za tai, ɗakinta ya nufa ya shiga da sallama, ya hangota kwance akan katifar dake ɗakin a cikin bargo. Ya ƙarasa ya ɗan janye bargon, ya daddaki filon da ta ke kai yace "Amira ki tashi ki karya, rana ta fara yi, idan yaso in kin karya se muje ko Asibiti ne" Ƙare masa kallo tayi tace 'meye naka a ciki, da in karya ko kar in karya? Ina ruwanka dani Karuwa ka ƙyaleni mana" "Naji amma kiyi haƙuri ki tashi, se muje ko Asibitin Barrack ne a duba ki" "Muje Asibiti kace musu me, You rape your wife because you thought she's not virgin? Haka zaka gaya musu? To ni ba haka nake ba, ko da nake karuwa na san daidai, ba zan taɓa fallasa Asirin Aurena ba" Imran yace "Amira rape kuma?" Cikin hawaye tace "akwai maraba da rape da abunda kaimin jiya ne? Babu maraba ai, kuma ka dena wani pretending kana lallaɓani, dan ka samu wani abu daga gareni, seka sakeni daga Garin nan Kano zan koma na gama Aurenka" Haɗe rai yai yace "dan kinga ina lallaɓaki shine zaki dinga gayamin Magana?" Tashi zaune tayi tace "An gaya maka ɗin, na faɗa kaji haushi ka rabu dani" "Naji, amma muje ki karya" "Ba zanci ba" Tai maganar tana Share hawaye, Ƙarshe Imran se tashi yai ya bar mata ɗakin, abun duniya ya ishi Imran, tabbas anwa Amira ba daidai ba, mussaman yadda ya dinga dizgaya da kalamai marasa daɗi. Wunin ranar haka dinga koke koke, kuna taƙi saurarar Imran. Imran yana ɗakinsa ya kira Khalid a waya. "Kai lafiya kake kirana a daren nan? Ya kake ya Lagos?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, Amma fa akwai matsala ina cikin damuwa" "Sarkin matsala, meke faruwa Kuma?" "Khalid, Amira ce, naiwa Yarinyar nan ba daidai ba, Amira ba Karuwa bace, abun ya bani mamaki, how could this be possible, and worse part of it is that, ta dage wai sena saketa ta koma Kano, ni wannan be dameni ba, ina jin kunya akan abunda nai mata" Khalid yace "kaga abunda na dinga gaya naka kenan a baya, amma kai kunnen uwar shegu dani Imran, na gaya maka ka sassauta ƙiyayya akan Yarinyar nan, duk da dama can kan son ta, son zuciya ne ya rufe maka ido, kawai seka haƙura ku rabu tunda haka take so, da ka cigaba da gallaza mata" "Wane irin in saketa kuma? Kaifa ka fiye abun haushi wallahi, wane irin in saketa?" "To in baka saketa ba me zaka mata? Ace ka Auri yarinya over 4_5 month, amma baka taɓa sauke hakkinta na Aure ba, da lafiyar ka da Komai ka tare a gurin mace ɗaya, gaskiya ba kayi adalci ba, kuma wallahi na goyi bayan ka sawwaƙe mata, tunda ba ka da adalci" Tsaki Imran yai ya kashe wayarsa, dan kalaman Khalid sun fara fusata shi. Yai shiruu yana zancen zuci se ga kiran waya, yayi mamakin ganin lambar Ihsan, ya sa hannu ya ɗaga, "My" "Na'am Ihsan" ya kira sunanta. "My ka manta dani baka ta tawa ko?" Tai maganar cikin kuka. Imran yace "Ihsan me zance, ko ya zan dake? Na taho amma kika kasa kirana a waya, ni ban fushi ba na kiraki a waya, amma nai miki miss calls kusan goma, amma ki ka gaza ɗaukar ko guda ɗaya, ya ki ke son inyi?" "Wallahi ina kishinka da kewar ka Imran, na kasa samun nutsuwa ko Abinci ba na iya ci, gani nake komai ze iya faruwa, hankalina yaƙi kwanciya sam" "Ihsan dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki dena ta da hankalinki kar ki saka wani ciwon a kama min ke dan Allah" "Imran ba zan iya ba, zuciyata kamar zata tsaga ƙirjina, dan Allah ka dawo please" "Ihsan ta yaya zan dawo? Aiki fa nake yi a nan ɗin" "Imran zuciyata ta kasa jurewa, dan Allah ka dawo gida" "Ihsan, kin san ba abune daze yuwu ba, in baro aiki na in dawo ba, kuma kin san nam kusa baza'a bani wani pass ɗin ba" "Au haka kace? Shikenan nagode Imran, ka dena sona ka dena damuwa dani, koma meye inje baka damu ba ya sameni, shikenan"  ta katse wayarta. Imran yabi wayar da kallo, be taɓa zaton Ihsan na da wannan halayen ba, na tsananin kishi haka da ƙorafi ba, a waje sam ba ta nuna masa wannan halin ba se yanzu, shikam a yanzu duk sedai kowa ma yai haƙuri dan aikin gama ya gama. Amira kuwa zuwa kwana uku ta samu sauƙi, da ƙwarin jikinta, sedai sam ba ta shiga sabgar Imran, ko girki idan tayi a Kitchen take ajiye masa nasa, ko gaisheshi ta dena yi, harkokinta kawai take, ga fitinanniyar shigar da takeyi ko yana nan ko baya nan, hakan ba ƙaramin hana Imran sukuni yake ba, sam baya jin daɗin yadda take shareshi, take nuna halin ko in kula a gareshi, gefe guda ga wata irin fitana dake damunsa akan Amira, amma yana jin nauyin tunkararta, saboda yasan iya Rashin kyautawa ya aikata mata. Imran ya dawo daga gurin aiki a matuƙar gajiye, ya zauna a falo da shi da takalminsa da jakarsa, ba wanda ya kai ɗaki ya kashingiɗa ya lumshe ido, Amira ta fito daga ɗakinta sanye da mini skirt da kuma vest, hannunta riƙe da cup taje ta zauna. Imran ya buɗe ido yana ƙarewa surar jikinta kallo, ya ɗanyi gyaran murya yace "Sannu da gida" "Yawwa sannu da zuwa" "Ko zan iya samun Abinci?" Yana Kitchen ta bashi amsa. "Dan Allah ki kawomin, na gaji sosai" Da farko shiru tayi kamar ba taji meya yace ba, se kuma ta tashi ta kawo masa, tana gama ajiyewa ta miƙe zata tafi yace "Ki dawo ki zauna mana" "A'a zanyi abu a ɗaki ne" Imran yace "ok shikenan, amma dan Allah ina neman wata alfarma ne" "Ok ina jinka" "Dan Allah ina son zaki rakani wani taro ne, in Allah ya kaimu Ranar Saturday" Kallonsa Amira tayi tace "ba inda zani, wake ado da Karuwa har ya ɗauketa ya shiga da ita taro, wannan ai aikin Ihsan ne matan ƙwarai, ta biyo jirgi ta taho ta raka ka" "Eh ai yanzu ke nake so ki rakanin tunda ba ta nan, kowa zeje da wani nasa, nikuma kinga daga ni seke a nan" "Ni da bani da amfani, me zanje in maka? Ko ka manta kace idan kazo dani ba wani amfani da zan maka, idan ka manta ni ina sane" Tana gama Maganara ta wuce ɗakinta tana cigaba da mita. Imran yai shiruu, Amira ƙanwarsa ce, gari banza ba ta isa gaya masa Wannan maganganun ba, amma da yake yasan shike da laifi ba abunda ze iya yi mata sedai ido. Ba yadda be da Amira ba akan ta rakashi, amma tace ko me zeyi ba zata ba. Haka Imran ya dinga fama da Amira, gefe ga Ihsan da ke kiransa tana sake sauke masa nata shirmen, harya ka ya dena ɗaga wayarta, saboda ɓata masa rai da take yawan yi. Ranar da Imran zeje taron, bayan ya dawo daga sallr magariba ya shirya ya fito, sedai yana fitowa yaga Amira ta sha Kwalliya cikin doguwar riga dark blue, wadda taji aikin stone Sosai, se walwali suke, ya tsaya yana kallonta, tace "muje ko?" "Zaki rakani ne?" Tace "eh" Imran yai murmushi yace "Masha Allah, muje" Suka fito tare, Imran ya rufe gida, suka shiga motarsa suka fita. Tunda Amira ta zo garin nan bata taɓa fita ba ko sau ɗaya se yau, duk da duhu ya fara yi amma hakan be hanata yin kalle kallenta ba, wani Guri suka je Imran yai parking ya fito, amma ita bata fito ba. Imran yace "munzo ai, ki fito" "Ina ne nan?" "In da zan saida ke ne?" Ya bata amsa. Ta fito tare da faɗin "ai ko ka saida ni ba daraja zan ba, Saboda kasan na gama bin kwararo" Imran bece komai ba, ya rufe motarsa yai gaba tana binsaa baya. Wani ƙawataccen ɗakin taro suka shiga, mutane na ta shiga suna fita, wasu da shigar hankali wasu da ta ban haushi, kasancewar gamayyar musulmi ne da wanda ba Musulmi ba. Imran ya kai Amira wani teburi yace "ki zauna a nan ki jirani, zanje in canza kaya" Ƙin zama tayi tace "haka kurum, wallahi ba zaka tafi ka barni b, muje tare" Haka ta bishi har inda ze canza kayan, ta jirashi ya canza ya fito, suka zo suka zauna. Suna zama ba daɗewa aka fara Rabon Abinci da drinks, Amira tace "wai me za'ayi a nan ɗin ne?" "Walima aka shiryawa wanda suka samu ƙarin matsayi, da wanda sukai ƙoƙari agurin yaƙi" Suna maganar aka kawo musu Abinci, da lemuka aka ajiye musu, shinkafa ce fried rice, ta sha kayan lambu ga danƙwaleliyar kaza akan kowanne. Amira tace "gaskiya nifa ci zanyi" "Ai dama dan kici aka baki, nima zanci ai" Amira ta kalli Abincin Imran, ta sa cokali ta ɗauke kazar kan Abincin Imran tace "Wannan kazar dani ta dace, kai ba'a so kayi ƙiba, ni kuma kaga dama can ina da ƙibata" Imran yace "haka akeyi, a baki taki a bani tawa kice se kin cinye da tawa?" "Eh ɗin, duka zan cinye na bar maka shinkafar" "Amira muna da kaji a gida fa, karki ba da mu mana Please" "Abunka da 'yar ƙauye ai sedai kayi haƙuri kawai, kuma ma aini baka saimin kazar amarci ba, amma ka saiwa Ihsan" Imran yace "hmm rigumammiya, ai seki cinye" Yaja shinkafarsa ya fara ci, wasu couples a kusa dasu, duk da basa jin hausa amma su Imran sun burge su, dan ba ƙaramin dariya suia basu b, kai kace wasu masoyane da suka daɗe suna shan soyaya. Wata soja ce tazo wucewa, ta kalli Imran tace "ya na ga kana cin Abinci ba nama, garin yaya" Imran ya nuna mata plate ɗin Amira yana murmushi, matar tayi dariya tace "kace anfi ƙarfinka ne, bari akawo maka wata" Amira tace "ya ƙoshi" Imran yace "ba se kin kawo wata ba, wannan ɗin ta isa"  matar ta wucesu tana musu dariya. "Kin sa ana kallonmu, muna faɗa akan  kaza" "Eh munyi ɗin ina ruwan wani, wai wannan matar me kama da maza itama soja ce, na ganta da wandon sojoji" "Allah yasa taji ki, zaki bayani" Kamar kasan da tana min magana, kawai hangowa nai ta nausheni, dan na ɗauke maka kaza, wai da daga nan se Asibiti emergency, dan wannan hannun nata kamar itace, kamar ba na mace ba, kuma ta na da miji?"  tai maganar tana dariya. Imran kallon Amira yake, she's very Funny and jovial. Yace "tana da miji hadda yara" "Taɓ lallai" Ta sa fork da spoon tana yanko kazar, tana bawa Imran a baki yana karɓe kayarsa. Aka fara kiran wanda za'a karrama, tace "wai kai baza'a baka ba?" 'ai ban dani, masu ƙwazo ake bawa" "Kai, ana nufin kai baka da ƙwazon ne? Da na san baza'a baka ba da bzan zo ba wallahi" Tana cikin mitar aka kira Imran, zumbur ta miƙe tana tafawa Imran, tace "You deserve it dear". Imran yai murmushi ya kama hannunta, suna tafe ana musu hoto yaje ya karɓo ƙaton frame ɗin da aka bashi, da hotonsa da sunansa, da rank ɗinsa na major, kan a bashi seda aka dinga koɗashi, ana faɗar jajircewarsa. Amira kamar ita aka bawa, ta karɓe frame ɗin ta riƙe. Suka dawo in da suke zaune su ka zauna, tace "da ba'a baka ba da tafiyata zanyi" "Kin san hanya ne in kin tafin" "Ai da tare zamu tafi, amma tunda an baka tashi Mu tafi gida" "Ki tsaya a ƙarasa, Yanzu za'a gama" Basu baro gurin nan ba se bayan goma na dare, tun a hanya Amira ke gyangyaɗi. Seda Imran ya tsaya a hanya ya sai gasassun kaji, da youghurt me sanyi, sannan suka tafi gida. Suna zuwa ta bar Imran da kaji, tai ɗakinta da frame ɗin nan, ta na zuwa tai wanka haɗe da alwala ta fito tai salla. Har ta kwanta Imran ya shigo yace "ga kazarki can na biya a dena min gori, kuma naga kin zo kin kwanta ba ki ci ba" "Se da na roƙa za'a saimin, na ƙoshi se gobe in Allah ya kaimu zan ci" Ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita akan katifar, yace "to bani frame ɗina" "Taɓ, ai ba zan bada wannan frame ɗin ba, idan mun koma gida a falo na zan kafe shi" "Kin haƙura zamu koma taren ne?" "A'a, Kano zan tafi, daga nan ba zan tsaya ko ina ba se Kano" Imran yai ƙasa da murya yace "wai ke meyasa abu baya wucewa a gurinki ne? Ba in da zaki koma se ɗakinki" "Nifa ka dena wannan kashemin Muryar, dan nayi Imani da Allah da ka sameni saɓanin budurwa haka zaka cigaba da min wulaƙanci, kuma na da baka so, ai matar so ta isheka, ni temakamin a kai" Shiru Imran yai, be kuma cewa komai ba yana ajiyar zuciya, bi sa kasada ya jarraba Amira ko zata yadda da shi? Bisa ga mamakinsa, ba taurin kai ba gaddama ta ƙyaleshi yai budurinsa, abun ya bashi mamaki sosai, tabbas yasan da Ihsan a matsayin Amira, ba zata taɓa yadda da shi ba. Imran ne ya fara tashi ya shiga yai wanka, da kansa ya haɗa mata ruwa itama, bayan ta fito daga banɗakin ta tarar da shi kwance akan katifar. "Ya naga haka?" Tai maganar tana ɗan haɗe rai. Imran yace "me kika ganin?" "Ka tafi ɗakinka mana kwanciya zanyi" "Ai a nan zan kwana" "Saboda me?" "Saboda nan ɗin ɗakin matata ne" Wani kallon banza Amira taiwa Imran, a ranta tace "lallai wasu mazan halinsu se Allah, ji yadda ya ke wani kwantar da murya wai ɗakin natarsa" Amira tace "matarka dai Ihsan ba Amira ba" "Amiran ma matata ce" "A yanzu ba, amma a baya ai ni ban kai a kalleni a matsayin matar ba" Amira ta dinga masa tsiwa son ranta, amma Imran ya gaza cewa Komai saboda yasan ba shi da gaskiya. Taje ta kwanta tana mitar ita gaskiya ya tashi ya bar mata ɗaki, tunda ya gama abunda ya kawo shi. Imran ya rungumeta sosai sannan yace "Dan Allah Amira abunda ya faru ya wuce Please" "Baze taɓa wucewa ba" "Meyasa, dan Allah kiyi haƙuri ya wuce, ban san yadda akai ma kika yadda da ni ba, har kika nuna farinciki ki akan nasarar da na samu, hakan ya nuna baki da riƙo, dan Allah ki yafemin Komai ya wuce, nasan kina da zuciya me kyau Amira" Amira a ranta tace "Ai nia ba irin sokuwar matarka bace, da zan biyewa abunda yafaru nima in wulaƙantaka ba, in je ka hango wata, da Wannan damar zan mallaki abunda ta gaza riƙewa, in rama cin zarafin da tai min" A fili kuma tace  "Imran ban jina zan taɓa mantawa da mummunar kalmar Karuwa da mutane da yawa suka dinga jifana da Ita, kalma me nauyi da munin gaske, tabbas nasan nayi kuskure da na biyewa son zuciyata na dinga tafka taɓara son raina, ba tare da sauraron maganar kowa ba. Mutane sun gaza yi min adalci ko yaya, babu wanda yasan dalilin da yasa na zama haka, babu wanda yai tunanin me za'ayi dan tallafar rayuwata, da dawo dani kan hanya se zagi cin mutumci da miyagun maganganu da mummunan fata. Haƙiƙa maraici abu ne wuya da ɗaci, kuma Allah yana jarabtar bawansa ba dan baya sonsa ba, wanda duk ya tashi cikin maraici idan har ba mariƙi ka samu nagari ba, haka zaka tashi a rayuwa me wahala da ƙunci. Bayan rasuwar mahaifiyata, na kasance a hannun dangin mahaifina, Yadikko bata ƙaunar kakata, mahaifiyar Abbana, Abbana a hannunta ya ƙarasa tashi, ta asabtar da shi azabtarwa me muni, ta yadda seda ta raba tsakaninsa da mahaifinsa, duk da tsakanin gidan mahaifina da gidan su babanmu ba nisa, amma mahaifiyata ta sha wahala a hannun Yadikko. Duk da ba itace ta haifi Abbana ba, amma Mamana ta mata biyayya sosai, bayan rasuwar mahaifiyata aka kaiwa Yadikko ni, duk abunda za'amin na cutarwa, yana gani baze iya Magana va, saboda yana mata biyayya kamar mahaifiyarsa. Ina da shekaru huɗu zuwa biyar mahaifina yai hatsarin mota ya rasu, bayan an share zaman makoki haka na zauna a gidan Yadikko da ya kasance family House, da yawa duk 'ya'yanta ne a gidan da matansu, da ma Abbana shikaɗai Mamansa ta haifa. Ba wanda ya damu dani a gidan nan, duk da ƙanƙantar shekaruna, hakan baya hana Yadikko da iyalanta azabtar dani, ta hanyar sani aiki me wahala wanda yafi ƙarfina. Banda duka akan ƙanƙanin laifi, duka  wanda shekaruna sunyi ƙanƙanta ai min wannan dukan. Watarana lokacin ina da shekaru takwas a duniya, Abba yazo daga Kaduna duba ni, ya zo ya tarar bani da lafiya, ga Yadikko ta iya siyasa, dan haka ba'a gane azabtar dani take, tai ta nunawa Abba ai tana sona, suna ƙoƙari a kaina. Abba ya fito ze tafi, wani maƙocinmu ya samu Abba yace "idan da hali, tunda ɗan uwan mahaifiyata ne, ya tafi dani ya riƙeni, idan ba haka ba izayar da ake min ze iya sawa in rasa raina ko nakasta ni. Abba yazo Kano, yace lallai tafiya zeyi dani, shi ze riƙeni. Yadikko tace baze yuwu ba, seda suka kai ruwa rana sosai, sannan Yadikko ta bari ya ɗaukeni ya tafi dani. Se dai muna zuwa, Ammi ta ganmu tare, ta haɗe rai tace ya ta ganmu mu biyu?. Yai mata bayani, a take Ammi tace wallahi ba zata riƙeni ba, ɗan riƙo ba ɗan goyo bane, duk abunda zaka masa baza'a gani ba, gar tyn wuri yasan in da ze kaini amma ba gidanta ba, da fari ina ta murna zan baro baƙar wahala da aiken gidanmu, amma karɓar da Ammi tai min yasa na sha jinin jikina, ta dinga faɗa tana ɗaga murya tace a Lallai se na bar gidan. Abba yace tayi haƙuri washegari ze maida ni, haka akayi kwana na ɗaya a  gidanku, ban manta ba akan tiles na kwana, ga sanyi gashi ban saba ba, washegari Abba ya maida ni hannun su Yadikko. Rayuwa ta cigaba da tafiya a haka, kullum jiya i yau, maƙocinmu shine ya sani a makaranta, duk yaran gidan nan suna zuwa amma banda ni, maƙocinmu ya sani a makaranta. Wataran sedai in saci jiki in gudu makaranta, ga rashin Abinci ga rashin kulawa, idan yuwa ta isheni se in daidaici lokacin cin Abinci a maƙota sannan in ci, ta ƙarfi da yaji na koyi kwaɗayi. Idan aka je Guri naga Abinci jikina har tsuma yake a bani in ci saboda yunwa. Kaya sedai in an samu kwance a bani in saka, wai salla tayi a saimin kayan salla ba ruwan kowa dani, kuma ga gidan da mahaifina ya mutu ya bari suka saka 'yan haya a ciki, suna karɓe kuɗin, suka ƙi bari a raba gado, ƙarshe baffa salahu ya tashi Auren 'ya aka saida gidan su kai hidimar biki. Anty Fa'iza itama mamanta ta rasu, 'yar gurin Baffa Salahu ce, itama ta sha wahala sedai ta ta bata kai tawa ba, saboda ita jikar Yadikko ce, itace wataran ta kan kula ta bani kaya ko ta saimin takalmin sawa, saboda tana 'yan sana'oi. Kasancewar gidan Yadikko akwai manyan samari a gidan, suka fara amfani da damar rashin galihuna, suna nema su lalatani, idan naƙi se asan yadda za'ai a ƙullamin sharrin da za'amin dukan tsiya a gidan, dama Abinci ba ban ake ba se an gadama, ya zaman har daga naƙota se a turo wai inje, a sani wanke wanke share share da aike, wataran in nayi a bani Abinci, wataran nayi a bati, ga rainon 'ya'ya, duk wadda ta haihu a sirikan Yadikko rainon yaron nan a kaina yake. Sadiya da Amina sun ɗan girmeni, amma kusan kanmu ɗaya saboda ina da jiki, amma duk wani aiki suna zaune sedai a sani, idan kuwa rigima ta haɗani da su, nice bani da gaskiya se zagi da duka da cin mutunci. Duk motsin da zan, ko inyi laifi ko ƙiriniya irin ta yaro  sedai Yadikko tace "Allah ya watsa ni, insha Allah munyi hannun riga ni da abun arziki, yadda kakata ta mutu a tsiyace nima haka zan mutu, kuma se na barwa zuriyar Hafsatu wato kakata mummunan abun kunya" Tun abun yana damuna har nazo ya dena damuna. Akwai tazarar gaske daga Makarantar mu zuwa gidanmu, amma haka nake kwasa a ƙafa inje in dawo, har talla Yadikko ta kasamin, bayan ga jikokinta, amma duk da haka ina naniƙe da ita, nice wankinta, kitsonta lallenta, gyaran gurin kwancciyarta, aike idan zata aikeni bangon duniya ne ba zan taɓa musawa ba, zanje da ƙafafuwana. Ba ni da ƙyuya ko ƙyashi, ga biyayya ga kowa, duk Alkhairi na ga Yadikko da iyalanta hakan be hanasu cigaba da yi min fatan lalacewa ba, an haka ai kayiwa Fa'iza Aure, bayan an kai ruwa rana taƙi aurar wani me kuɗi da suke so ta aura. Na fara zama budurwa, amma babu kayan gyara, gashi bana son ƙazanta, ina son kayan kwalliya nima in gayara, amma babu me bani, brezia wannan se in Fa'iza ta bani kwancen ta ta, akwai lokacin da wandon da zan saka guda ɗaya ne tak dani, shima duk ya mutu, ba kayan turare ba me saimin audugar da zan amfani da ita lokacin al'ada, gashi na zama budurwa. Allah yai min ƙirar jiki me ɗaukar hankali, hakan yasa maza suka dinga bina, suna son suyi amfani da rashin gata na su ɓatamin rayuwa. Duk da haka akan samu na arziki suzo neman Aurena, amma da an zo tambaya se su Baba su ɓatani a gurin iyayen mutum, suce ni mutuniyar banza ce, a faɗar Yadikko ba zan Aure ga su Amina a zaune ba. Islamiyya da ƙyar na samu nai sakukar Alƙur'ani, saboda kullum cikin korata ake ban biya kudin makaranta ba, ga shi zan kammala sakandire babu kuɗin jarrabawa, nan na shiga tunanin yadda zan na samu kuɗi. Ina da wata 'yar ƙaramar waya, da na kan kaiwa me caji yaimin turi kyauta, a unguwar su Fa'iza, ya turan funa funai, da raye raye. Tamu ta zi ɗaya da shi sosai, ya kan cemin ƙanwarsa, ya bani labarin yana da ƙanwa Amira, amma tana ƙarama sosai ta rasu, wasu lokutan har kyautar kuɗi yake bani, abunka da me buƙata ko a'a bana cewa nake karɓewa. Wataran naje gurin Sultan me caji, akace yana bayan layi gurin wani biki, na bishi can ina zuwa na tarar da shi a can, yana cikin yaran D.J. Ya koma gefe muna magana, nace masa "Yayana, naje ka turan cigaban series ɗin nan ba ka nan, ashe kana nan" Sultan yace "eh ina nan, biki aka gayyacemu, ki bari in kin dawo zan turamiki" Ana haka aka kira Sultan zeyi wata rawa kan zuwan amarya, sedai aka rasa macen da za suyi rawar tare, me DJ ya saka naira dubu goma ga duk yarinyar da tayi wannan rawar. Take na shiga lissafi da tunani, idan na samu dubu goman nan, zan sai phants, brezia, pad da underwear, bani da takalmi me kyau, gashi ko turare bani da shi, sedai in nai wanka in jiƙa gishiri in shafa. Ban gama yanke hukunci ba, na tsinci kaina a wannan Filin rawa, saboda burina in samu wannan kuɗin in biya tarin buƙatun da nake da su, wannan shine ma somin faɗawata harkar raye raye........... Gyra, sharhi, ko shawara Ayshercool 07063065680. [2/13, 7:52 PM] Ayshercool:     🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                               45_46 Amira ta cigaba da cewa "tun daga lokacin da na fara iya hawa kan stage, a gaban dubun dubatar jama'a inyi rawa, kunya ta ƙauracewa idona, mussaman da Ni nake ɗaukar ɗawainiyar kaina, ni nake wa kaina komai, dan haka na dinga ganin nafi ƙarfin kowa, ba wanda ze taka ni in saurara masa. Sultan ya dinga goyon bayana, yana tafiya dani guraren raye raye, sedai ya kan cemin 'Amira ba'a son raina nake zuwa dake gurin rawa ba, ina fatan Ubangiji Allah ya baki miji me sonki, wanda ze riƙeki da amana" Ya yadda yaje dani ko ina, in dai fannin rawa ne ba zan ba shi kunya ba, sedai be yadda wani yaci mutuncina ba, Mutane na zaton mutuniyar banza ce ni, sedai duk wanda ya raɓeni da maganar banza, sena masa ƙaramin hauka, dan tabbas har da ƙaramar wuƙa nake yawo saboda tsaro. Idan aka ɓatamin rai a gidan, gidan Anty Fa'iza nake tafiya, saboda tun tasowa ta ban san wani abu wai shi rarrashi ko ja a jiki ba, amma ba dangin iya ba na Baba, mijinta Bashir yake mutuntani, yake girmamani kamar ƙanwarsa. Shiyasa nake tafiya gidan inyi kwanaki, tunda aka gane ina zuwa raye raye, Yadikko ta laƙaba min kalmar Karuwanci, ni kuma na karɓa na hau kai na zauna, na nuna mata na amince itan ce, saboda ba abunda zanyi wanda zesa ta janye abunda take faɗa a kaina. Wannan shine dalilin da yasa nake rashin ji, nima ba son raina bane rashin gata ne, mata da yawa suna lalacewa ne saboda rashin gata, wata da ta rasa breziar da zata saka gara ta bada jikinta ta sam kuɗi, amma ni bana aikata zina ni ba karuwa bace. Tai maganar tana rushewa da wani irin kula me Ratsa zuciya. Imran yai ajiyar zuciya, ya rungumeta tana dukan bayanta a hankali da sigar rarrashi yace "Am so sorry Amira, tabbas an miki ba daidai ba, an cutar dake sosai mussaman da munanan kalamai, daga gareni amma dan Allah ina neman afuwarki Amira, dan Allah kiyi haƙuri ki yafemin" Ba ta iya cewa Komai ba , se cigaba da kukan ta da tayi, ya rungume ta yana shafa bayanta. Tun daga ranar Imran ya shiga matsananciyar Nadama, yake nan nan da Amira, duk a ƙoƙarin sa na wanke laifinsa, dan tabbas yasan abunda mahaifiyarsa ma tayi ba ta kyauta ba, na nunawa Amira tsana tun tana ƙarama, ba zata taɓa mantawa da abunda tai mata ba, da wanda take mata a yanzu ba. Amira ta nuna kamar ba abun ɓaci rai da Imran ya taɓa yi mata, hakan ba ƙaramin ƙara mata kima yai a idon sa ba, duk da wasu lokutan idan taso tsiya, rashin mutunci take masa, amma baya duba hakan dan shi be zaci ma za ta iya saurarsa ba haka da wuri, saboda yadda ya dinga mata a baya. Tana kula dashi sosai, ba ƙorafi da yawan kawo matsala, sedai in kishin ya motsa ko Ihsan ta kira ta yayyaɓa masa Magana son ranta. Basu ƙara raba gurin kwana ba, daren da yake idan ya fita ya dena, kullum yana manne da Amira (maza manya, ya manta da kashedin Ammi 😂😂😂) Ranar Saturday yana baccin safe, Amira ta tashi duk tayi aikinta, tai wanka tai kwalliya, ta zo ta zauna kusa da shi, ya ɗora hannunsa a ƙirjinsa yana bacci, ta ɗora nata hannun akan nasa, hannunta ya sha jan rani, ta ɗau wayarsa ta ɗauki hotunan hannunsu a haka, ta ajiye masa wayarsa. "Amran ka tashi ka karya mana" tai Maganar tana shafa gefen fuskarsa. Ya buɗe ido a hankali ya kalle ta, yai murmushi yace "You look so cute" Wani irin fari tai masa sannan ta kashe masa ido tace "dama dan ka yaba nai kwalliyar, tun da ka yaba kwalliya ta biya kuɗin sabulu" Murmushi yai ya shafa gashinta yace "Amira Amma wannan gashin ki ne ko?" Ta jinjija masa kai alamar eh. "Ka tashi muje ka karya, bana son ulcer ta kama min kai fa" "Duk yadda kike kula dani ɗin nan, ina ulcer zata ganni, kiss me se in tashi" Tashi tai daga jikinsa tace "naƙi wayon" Wayarsa ce ta fara ringing, Amira ta ɗakko za ta bashi, amma taga my wife a kai, ai kuwa ta haɗe rai tai rejecting ɗin kiran. "Amira ya haka?" "Nifa gaskiya na fara gajiya da halin matar nan, ta barni in sarara Nima, Lokacin da kuka tafi kuka barni ni kirana kake? Ya za tabi ta addabeni wallahi ba zaka ɗaga wayar nan ba" Ta kashe wayar gaba ɗaya, Imran yai ajiyar zuciya yace "muje inci Abincin" Yasan dai rigimace Amira ta janyo masa tashin hankali a gurin Ihsan. Bayan Imran ya karya, har bayan azahar yana gida, se wajen la'asar sanan ya fita, bayan fitarsa ya duba wayarsa, yaga missed calls ɗin Ihsan rututu da na Ammi. A kiɗime ya kira layin Ammi, dan yasan da ƙyar in ba ƙararsa Ihsan ta kaiwa Ammin ba. Aikuwa yana kira ta ɗaga, "Sannu mara mutunci sallamamme" Imran yace "Subhanallah, Ammi meyafaru?" "Dole ka tambayeni meyafaru mana, kira nawa nai maka baka ɗauka ba? Ihsan ta kiraka kai rejecting kaƙi ɗagawa, nima na kira kaƙi amsawa saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci ko? Wato kana tare da Karuwa Imran ka tsallake maganata kenan ko?" "Yasalam, Ammi ba haka bane ba, ina tare da oganane, meeting akayi ba damar in ɗaga waya shine dalilin, amma banda haka ba abunda ze sa in ƙi ɗaga wayarki, ko in bijirewa maganarki" "Hmm ai na zata ka fara biyewa waccan watsatsiyar ne, gaba ɗaya Ihsan ta tashi hankalinta, duk yadda za kai kayi ka dawo gida ka kula da matarka" "Ammi ba za'a bani pass Yanzu ba" "Be dameni ba, ka dawo gida kawai ni ban yadda da zamanka da wannan Yarinya a guri ɗaya ba, kome kake ka baro kazo ka kula da matarka" "Shikenan Ammi, zan va yadda za'ayi, amma ko ta biyo jirgi ta taho nan ɗin?" 'ban yadda ba, ka dawo shine Umarnin da na baka" "Shikenan, zan dawo insha Allah" Ba ta kuma magana ba, ta katse wayar, Imran ya dafe kansa yai shiruu ya rasa abunyi gaba ɗaya, Ihsan ta fara sire masa da abubuwan da take masa sun fara ƙular dashi. Yadda Imran ya fita ba haka ya dawo ba, hakan yasa Amira ta fuskanci Imran ɗin yana cikin damuwa, dan haka tace "Amran" Ya kalleta yace "Nifa na kasa gane ma'anar Amran ɗin nan" Tai murmushi tace "Amira_Imran shine Amran" "Wow, sunan yayi kyau sosai my dear" Ta jinjina kai tace "meke faruwa ne?" "Wai Ihsan ba lafiya, Ammi ta matsa in koma gids, zan karɓi pass mu koma" "Allah ya bata lafiya, wataƙila mun kusa ɗaukar baby ne" Kallonta Imran yai, koma har zuci ta faɗi maganar ba, tayi ƙoƙari ƙwarai gurin ɓoye damuwarta. Watan su Ɗaya da sati biyu cif a Lagos, Amira ta sha kula da taraiya, kamar yadda Imran ya samu kyakkyawar kulawa daga Amiran, gaba ɗaya sunyi ƙiba kai kace yanzu yai Aure. Amira ma tau wani fresh kamar ba ita ba, ta ƙara kyau da nutsuwa sosai. Abun takaici da suka isa gidan Ihsan bata nan, Amira ta wuce sashenta ta shiga gyagygyarawa. Imran yace "Amira bari inje guda gurin Ammi" "Shikenan, kace ina gishesu" Bayan fitar Imran, seda ta gyara ko ina ta ɗora girki, sannan ta kira Anty a waya. Anty ta ɗaga tare da sallama. Amira ta amsa tace "Uwata ta kaina" "Na'am 'yar albarka, ya kike ya Lagos?" "Ai mun dawo Anty". "Ahh haba yaushe kuka dawo?" "Ɗazun nan muka dawo" "Meyasa baki gayamin ba, ai da nasa an muku girki" 'bakomai Anty, ina Yayata, koda yake ita jiya munyi chatting da ita".. "Tana nan ta tafi school, ina fatan dai komai lafiya ko?" "Lafiya ƙalau Anty" "To shikenan, dan Allah ban da rigima, ku zauna lafiya ki kula da mijinki yadda ya kamata" "Insha Allah Anty, Nagode" "Yawwa se anjima" Ta ajiye wayar ta fito, fitowarta ba daɗewa sega Ihsan ta dawo, kamar waa korarriya duk tayi rama tai wani iri. Murmushi Amira tai mata tace 'Sannu da zuwa Ihsan" Kallon banza Ihsan ɗin tai mata taj uban tsaki ta shige. Amira tai murmushi tace "Iska na wahalar da me kayan kara" Imran kuwa yana zuwa gida a Falo ya tarar da Ammi, tana ganinsa annurin fuskarta ya ɗauke gaba ɗaya, ta haɗw rai ya durƙusa ya gaisheta ta amsa da ƙyar tace "ka g damar dawowa kenan?" "A'a Ammi, pass ne ban samu da wuri ba" "Rufemin baki da zancen wani pass, 'yar mutane ta na ta fama da rashin lafiya amma ko a jikinka, kaje kai zamankansabida kaka tare da Karuwa ko? Imran idan ka kuksakura na samu labarin wani abu a tsakanin ka da Yarinyar nan se nayi mummunan ɓata maka rai, wanda baka taɓa zata ba, bna son Yarinyar bana ƙaunarta, kuma ba zata cigaba da zama a cikin zuriyata ba balle a samu iri daga garera ba, sam bazan marba da ɗa daga Karuwa ba" Gumi ne ya shiga tsatstafowa Imran, dan yasan aikin gama ya riga gama, inma cikinne wataƙila Amira ta samu, dan baya nacewa Ihsan ma kamar yadda yakewa Amira, kuma baya jin ze iya sake yadda ya nesanta kasan da ita, mussaman zamansu ɗin nan, da suka samu wata irin shaƙuwa da soyayya a tsakanin su. "Ammi dan Allah kiyi haƙuri, kinga Amira idan lalacewar da tayi da halinta wani abun mun bada gudunmawa, ƙil da kin riƙeta ta samu kulawa ba lallai haka ta sameta ba" "Karuwa tafi uwarka kenan da kake gayamin magana ko? To ban riƙe ɗinba kuma bazan riƙe ba, kaima kuma ba zaka riƙe ba, ina daf da datse wannan Auren dan ba sonshi nake ba" Imran da ya sunkuyar da kai yai shiru, tai ta zazzaga masa masifa, seda tai ta gaji, sannan ya tashi ya tafi ransa a mummunan ɓace. Da ya koma gida ya tarar da parr ɗin Ihsan a buɗe alamar ta dawo, bega Amira a falo ba, dan haka ya shiga paer ɗin Ihsan, ya sameta tana sallar la'asar, ya zauna ya jira ta idar, ta tashi ta naɗe sallayarta, ta ajiye. "Ihsan baki ga na dawo bane?" "Na gani mana me kake so in maka?" Ya jinjina kai yace "ya jikin naki?" "Ai da ka damu da jikina da baka kai wannan lokacin ba ka dawo ba, da ka dawo lokacin da nake jin zuciyata na daf da tarwatsewa, takaici da baƙinciki suka kwantar dani, amma har in kiraka a waya ka dinga rejecting, hakan ya tabattarmin da kaci amanata saboda waccan Karuwar, ka gaza cika alƙawarin da kaimin, in ba haka ba, ya za'ai in kiraka kai rejecting call ɗina, in maka magiya kaƙi dawowa?" "Yanzu Ihsan irin wannan karɓar yakamata ki min? Wata guda da sati guda bama tare, ai idan ma laifin nayi miki kya bari ki min sannu da zuwa hakalina ya kwanta, seki min duk abunda zakimin ko, irin abunda yake haɗani dake kenan, ke ba kya uzuri, ba kya tunanin komai abunda zuciyarki ta raya miki shi kikeyi" "Eh abunda zuciyata ta rayamin shi nakeyin, meyasa kamin alƙawarin da ba zaka iya cikawa ba? Ka dena sona kake na barwa karuwa kai" "Karki kuma ce mata karuwa, bana son tahsin hankali daga dawowata" "Na faɗa, ba karuwar bace, karuwa na faɗa na ƙara" Idan Imran ya cigaba da tsaiwa, zuciya zata iya ingiza shi, yaiwa Ihsan lahani, dan haka ya fito daga part ɗinta, zuciyarsa na tafasa. A falo yai karo da Amira, tana masa Magana amma idonsa ya rufe yai waje da sauri. Hakan ya tabattar mata da Faɗa sukayi da Ihsan, Amira tace 'cigaba da wulaƙantashi, ke da gatanki da mahaifiyarki amma ni da nake marainiya ai dole in rungume shi hannu bibbiyu. Amira ta zauna a falon, tana cin Abinci, Ihsan ta fito kamar wadda aka watso, ta kalli Amira tace "aikin banza jaka ƙazamar bariki" Amira tace "naji nagode" 'jahila daƙiƙiya me bin maza a kwararo, wallahi se nayi maganinki zaki ga abunda zan miki, sena miki abunda ba zaki taɓa mantawa ba, idan ma wani Asirin ki kai masa idonsa ya fara rufewa ki saurari abunda zan miki" "Alhamdilillah da kika fara ɗanɗan abunda kika min a baya, kuma wannan baƙin cikin yanzu kika fara shi, idan kin so zamu zauna lafiya, zamu Zauna lafiya ƙalau dake, amma idan akasin haka kika zaɓa na shirya, ina daidai dake wallahi, karya kawai" "Uwar ki ce karya bani ba" Amira tace "kin biya babarki ladan haihuwa, ita ki kaiwa wannan zagin" Ihsan ta kawao iya wuya tace "Karuwa kawai" "Suna ne, Karuwar Imran ba" Ihsan taga alama kamar kalmar karuwan ta dena ɓatawa Amira rai, ra dena jin haushi sam idam ta gaya mata, taji Tamkar ta zuba ihu ko taji sauƙi a zuciyarta. Imran se wajen ƙarfe tara na dare sannan ya koma gidan, Ihsan ta rufe ƙofar ɗakinta, ya shiga nasa ɗakin dake part ɗinta, ga wata yunwa da take damunsa, ya dawo falo ya zauna ya dafe kansa. Amira idonta biyu dama, ta fito da wata shu'umar riga a jikinta, ta zauna kusa da Imran tace "Babyna kaci Abinci kuwa? Meya ɓata maka raine?" Girgiza kai kawai yayi ba tare da yayi Magana ba. "Dan Allah koma meye kayi haƙuri, in kawo maka Abinci zaka ci?" "No bana jin yunwa" "Haba major, kalli cikinka meka ci tyn da muka dawo? Gaskiya se kaci Abinci bari in kawo maka" Ta tashi ta zubo Abinci ta kawo masa, da kanta ta dinga bashi a baki yana ci, daga ƙarshe kuma ta lallaɓa ta janye shi zuwa part ɗinta. Se da Amira ta tabattar ta mantar dashi wata Ihsan, Suka kwana tare seda Asuba ya bar part ɗinta ya tafi masallaci. Wasa2 kusan sati guda da dawowar su Amira, amma kullum se Ihsan sunyi rigima da Imran, ita kuma Amira na ta sake lallaɓa kayanta. A haka Imran ya bawa Amira dubu ɗari uku na kayan lefe da be mata ba. Suna kan sati na biyu da dawowa, su Yadikko suka zo gidan, da su Amina da Sadiya da Anty Fa'iza, sunyi mamakin yadda suka ga Amiran ta canzan, ta ƙara ƙiba tai shar da ita. Ɗan uwa ɗan uwane, duk lalacewarsa Amira tai murnar ganinsu a gidnta, ta dinga farinciki ta rasa inda zata tsoma ranta dan daɗi. Ihsan na gurin aiki, Imran ma baya nan amma yasan da zuwansu. Yadikko tace "yanzu Amira kece a wannan danƙareren gida haka Amira?" "Wallahi kuwa Yadikko, haka lamarin Ubangiji yake ai, ya kuke ya gida yasu Yaya Usman" Fa'IZA tace "dui suna lafiya, yau Allah ya nufa Yadikko ta zo ɗakin Amira hankali ya kwanta" Su Amina anata yaƙe, amma ƙasan zuciyarsu baƙin ciki ne fal, kamar su fitar da Amira daga gidan, suna can sun tsaa ruwan ido sun kasa fidda miji, saboda babu wani me ɗan abun hannu da yazo. Nan da nan Amira ta shiga gabatar musu da Abinci, da yake tun kan suzo ta ɗora musu girki, ta gabatar musu da Abinci yaji nama, ga lemuka suka ware ciki suna zubawa, ƙasan zukatansu baƙin ciki kamar ya kashe su, sam ba haka Yadikko tai zaton tararwa ba, saboda ta zaci zata tarar da Amira a tagayyare a wahala, amma ta ganta a nutse cikin kwanciyar hankali. Imran ne ya fara dawowa, Amira ta tsareshi tun a falo, tace "Sweet Amran, su Yadikkon sunzo" "Ok muje ciki mu gaisa" Suka jero zuwa falon tare, gwanin sha'awa, ganinsu tare seda Sadiya ta ƙware dan haushi. Imran yace "Ashe mayan baƙin namu sun ƙaraso, Fa'iza ya hanya Sannu Yadikko" Fa"iza tace "Alhamdilillah, mun sha hanya kam" "Ya megidanki kuwa?" "Wallahi yana nan lafiya duk yana gaisheku" Yadikko tace "Sannu Imrna" Yace "Yawwa ya hanya, an saki doguwar tafiya ga jikin girma" "Ai wannan bakomai, ya haƙuri ya fama da halinta"? Imran yace "Alhamdilillah, halinta na kirki ba" "A'a, ai kasan abunne se a hankali dole se ana tambaya, kasan me hali wasu lokutan ba fasa halinsa yake ba, se ana bibiya ana saka ido tukuna, eh ai naga ƙoƙarin ka da na Mahaifinka da yasa ka Aureta, duk da kun san hali irin wannan se ka dinga taka tsantsan kana sa ido, mussaman da akace tafiye tafiye kakeyi, ka dinga saka nata ido sosai da sosai, kasan irin wannan ba denawa suke ta daɗin rai ba, idan yarinya ta saba yawon banza dariƙe kuɗi a hannunta... Fa'iza a fusace tace "haba Yadikko meye hakane wai? Wannan wace irin magana ce?" Duk da Imran yasan Amira ba karuwa bace, Amma abunda Yadikkon tai ya baƙanta mata rai, kuma dan cin fuska a gabanta. Yadikko tace "barni in faɗa, ai da ba tai ba ba za'a faɗa ba, ba yadda ba'ayi akam ta dena harkar bin maza ba... Tuni mutuncin tsohuwar nan ta gama zubewa a idon Imran, mussaman da Amira ta bashi labarin rayuwar da tayi a hannunta, da alama itace karuwar tsohuwa me fuska biyu. Imran ba kunya yace "dan Allah bana son kuma jin wannan maganar, ya riga ya wuce, kuma ni na yarda da Amira ɗari bisa ɗari, saboda nasan ba karuwa bace, ni ne mijinta ni zan tabattar da haka, ana ta cemin Karuwa ce, ni ba haka na tararar ba, dan haka wannan maganar ta wuce, bana son in sake jinta, kar a kuma jifarmin mata da wannan mummunar kalmar dan Allah, in aka ci mutuncin ta mutuncina aka taɓa, nikuma ba zan lamunci cin zarafinta ba" Hawaye ne suka shiga zubowa a idon Amira, hadda ajiyar zuciya, kawai ta rungume Imran tana kuka, Yadikko ta fusƙi da kai, cike da borin Kunya, Imran yaja Amira Zuwa bedroom ɗinta, ya janyota jikinsa yace "meyasa kuma kike kuka? So kike su rainamin ke?" Ta girgiza masa kai "to ki dena kuka, ai Allah sheda nima kuma sheda ne, matata budurwa na samu abata, dan haka ba zan sake lamuntar a zagarmin ita ba, ko aci mutuncinta ba, saboda ina son abata" Rungumeshi Amira tai tace "i love You too Amran" Rarrashin ta ya dinga yi, gashi ita ba wuya ka rarrasheta, ko faɗa sukai da ya ɗan rarrsheta ya mata kalamai shikenan ya wuce a gurinta, saɓanin Ihsan me azababben taurin kan tsiya. Fa'iza tace "gaskiya Yadikko abun da ki kayi baki kyauta ba sam, ya za ai abu ya riga ya wuce ki dinga dawo da shi baya, anyi abun nan inma karuwarce in ma ba ita bace, shi yacw yaji ya gani, meye kuma na dawo da bara bana?" Yadikko tace"Ke rufemin baki, bana son sakarcin banza dana wofi, na faɗa ɗin ki dakeni" Fa'iza tace "ba haka bane Yadikko, amma dai abunda ki kai be dace ba wallahi" Se da Imran ya tabattar da hankalinta ya kwanta, sannan suka fito, ko da suka fito ɗinma, Amira tai pretending kamar ba wani abu da Yadikkon tai mata. Ana haka se ga Ihsan ta dawo gida, ta tarara da gidan da mutane, ga su Yadikko da Fa'iza, bata manta fuskar su ba, ta gansu a gurin Dinner bikinta. Ko kallo basu isheta ba, Fa'iza tace "laa Yadikko ga kishiyar Amira, sannu Ihsan ko?" Kallonsu tai sheƙeƙe tace "ba dai kishiyata ba, dan wannan kucaka ce a gurina sauran titi" Fa'iza tace "toooo ikon Allah" Amina tace "wai da ganin wannan kishiyar Amiran a tsaye take, ita ce dai dai da ita ai" Fa'iza ta tashi tabi Amira kitchen inda take wanke kwanukan da suka ci Abinci tace "Amira yanzu kishiyar ki ta dawo" Jiki a sanyaye tace 'Allah yasa kar Yadikko tai wani abu da zata zubarmin da mutunci a idonta" "Amira ba ksa zaman lafiya da ita ne? Daga na mata Magana ta faɗan baƙar Magana" Amira tai nannauyar ajiyar zuciya tace "ina fa zaman lafiya Anty Fa'iza, kin ganta nan kullum cikin neman tashin hankali take, abun dai se godiyar Allah, ga mahaifiyar Imran ma ta sani a gaba duk na rasa abunyi" Fa'iza ta dafa kafaɗar Amira tace "kiyi haƙuri Amira, taki jarrabawar kenan, daga wannan se wannan amma ina fatan Ubangiji Allah ya kawo miki ɗauki da gaggawa" "Ameen Anty" Imran kuwa jin motsin dawowar Ihsan, yasa ya shiga ɗakinta yace "Ihsan kin gaisa da 'yan uwan Amira a falo kuwa?" "Nice zan gaisa da wannan matsiyatan? Ahalin tarkace da jaraba, Irin karuwai Allah ya kiyaye" "Ihsan da farko na roƙeki akan kiran Amira da Karuwa da kike ki dena kinƙi, to Yanzu zan gargaɗeki na gaji da abubuwan da kike min na gaji, idan kika kuma kiranta da Karuwa ko bata ɗau mataki ba ni zan ɗauka" Kallonsa tai da mamaki tace "me kake nufi?" "Ina nufin karki sake kiranta da Karuwa" yana gama faɗin hakan ya juya ya fice. Nan tai turus, ta ƙara tabattarwa da kanta Amira taiwa Imran Asirine, duk kwanan da Imran yake a ɗakin Amira ba ta taɓa sani ba, ita zaton ta kawai a ɗakinsa a yake kwana. Ya raba musu kwana amma sam bata gane hakan ba, a nata haukan be bari ta gane hakan ba. Su Yadikko seda suka wayi gari a gidan Amira, da safe Imran yai musu Alkhairi me yawa, Haka Amira ma sannan suka tafi rakasu tasha a motar Imran. Ihsan kuwa dama tunda ta wucesu a falo, ba ta sake fitowa ba har suka tafi. A hanyarsu ta dawowa Amira tai shiru kamar tana tunani, Imran yace "gimbiyar meke damunki ne?" "Bakomai, kaina ne kemin ciwo, kwana biyun nan haka nake fama" "Amma baki gayamin ba, ko dai damuwa ce?" "Ba wata damuwa, kawai na rasa meke damuna ne, gashi bana iya cin Abinci" "Amma meyasa baki gayamin ba?" "Ai naga ba wani abun damu bane" "A'a abun damune mana, bari muje Clinic a duba min ke" Wani Clinic suka je, aka duba Amira aka bata magunguna, suka taho gida. Da suka je gida har ɗaki ya kai Amira yace ta kwanta ta huta, saboda likitan da ya duba ta yace akwai buƙatar ta dinga samun isasshen bacci. Washegari lahadi ce, Amira ta tashi gata nan ga ta nan jikinta ba daɗi, ga jiri dake damunta. Minal ta zo gidan ita da wata ƙawarta, Ihsan suka zauna suna hira. Amira taga kwanciyar ba zata kaita ba, dan haka ta tashi ta fito. "Ahh Minal ke ce a gidan namu yau, ya Ammi?" Minal ta kalli Amira tace "Ji wani munafurci, meye haɗinki dani kike wani yau nice a gidan?" "Ohh Sorry, Allah ya baki haƙuri" Ihsan tace "haka take, shegen shishshsigin tsiya, da munafunci ita lallai se an shiga harkarta" "Anty Ihsan waze hulɗa da Karuwa, ba gaira babu dalili yanzu ma banda ƙaddara da Abba ya ƙaƙabo mana ita, waze so haɗa kansa da wannan tsohuwar kilakin?" "Ke Minal me kike cewa!? Suka ji muryar Imran da ke shigowa, jikinsa sanye da farar jallabiya. "Meye haka kuke yi ne, baki da hankali ki ke faɗar wannan maganganun akan matata, kuma 'yar uwakki?" "Wallahi ni ba 'yar uwata bace" "Ni kike gayawa haka?" "To Yaya ba karuwar bace? Ai kowa yasan haka" Ba zato ba tsammani Imran ya kwashe Minal da mari. "Dan ubanki ni zaki dinga gaywa wannan maganar, tashi ki bar min gida" Ai gaba ɗaya buɗe baki sukayi dan mamaki. Nan da nan jikinsa ya hau tsuma, dan sam baya son raini. "Imran, Minal ce fa dan me zaka mareta dan tace mata Karuwa? Ba karuwar bace?" Imran yace "saura kema, Na dena ɗaga miki ƙafa, ya isa abunda kukewa Amira ya isa haka? Amira ba mata ta bace kawai, jinina ce kuma ba karuwa bace na tabattar da Hakan" Amira kuwa tuni ta fara kuka, saboda tasan abunda ze biyo bayan marin da yaiwa Minal, ba ƙaramin tashin hankali bane. Minal kam ɗaukar jakarta tai waje tana kuka. Sedai abun takaicin, da taje gida Ammi ba ta nan. Ta zauna ta dinga rizgar kuka ita kaɗai a gida. Amira kuwa zama tai tana kuka, saboda tashin hankali. Imran yace "Amran ɗina meye kuma na kukan baki da lafiya fa" "Ka mari Minal, kasan Ammi zata zo, zamu fuskanci fushinta" "Amira, na gaji da cigaba da jin ana jifanki da munanan kalamai, nafi kowa sanin ke ba karuwa bace, dan haka zanyi iya yina a dena kiran ki da wannan sunan" Girgiza kai tayi tace "Amran na riga naiwa kaina tabo" "No zan goge tabon nan da kaina insha Allah, my wife is not prostitute" Yai maganar yana goge mata hawaye, seda ta dena kukan sannan ya ƙyaleta. Ihsan kuwa kamar za tayi  hauka, ganin Imran ya mari Minal saboda Amira, kuma gashi itama ya fara mata kashedi. Gaba ɗaya hankalinsa ya koma kan Amira. Abunda ya farun ya hana Amira bacci sam, ga wani zazzaɓi da ya rufeta, gaba ɗaya ta rasa meke mata daɗi, gashi a lissafinta yau ba kwananta bane, balle Imran yazo ya ɗan lallaɓata ta samu tayia bacci. Fitowa tayi babban falo, tai sa'a Imran yana kwance yana kallon ball, aikuwa ta ƙarasa inda yake ta zube a jikinsa. Da sauri yace "subhanallah, Amrina lafiya kuwa, wannan zazzaɓin fa?" Shiru tayi tana juya kanta a ƙirjinsa. "Ko mu tafi Asibiti ne?" "No" "Jikinki yai zafi da yawa, ko in shafa miki ruwa?" Ta jinina masa kai alamae eh. Ta tashi zaune, yaje ya ɗebo ruwa a wata roba, da ƙaramin towel, yazo ya zauna a kusa da ita. Ya zare rigar jikinta, ya shiga jiƙa towel yana shafa mata a jikinta. Ihsan kuwa yau kasa jurewa tayi, duk da haushin Imran da take ji, ta miƙe ta tafi ɗakinsa, amma baya ciki. Da sauri ta nufo falo, tana zuwa tai tozali da baƙin gani a falon. Take ta zunduma uban ihu, wanda yasa Imran saurin sakin Amira suna kallon Ihsan. "Wallahi se na kasheki, ni zaki yiwa haka? Ni zaka ciwa amana, wallahi sena ga bayan ku, nafi ƙarfin aci amanata, wallahi sena miki illa" Tayo kan Amira gadan gadan tana ihu, Imran ya tare ta, yace "wallahi ba zaki taɓata ba, me tai miki? Tunda kin watsar dani kince ba kya sona, ai ba laifi bane dan na koma gurinta, tunda Allah yasa bake kaɗai nake Aure ba" Ranar dai babu wanda yai rintsawar kirki, saboda bala'in Ihsan ga Amira ba lafiya, haka ta dinga masifa a daren nan maƙota naji. Da sassafe Imran ya taya Amira ta shirya ze kaita Asibiti, sedai suna zuwa falo suka tarar da Ammi ga Ihsan da Minal. "Sannunka ɗan banza mara mutunci, yanzu Imran ni zaa kaiwa haka, ka nunamin ban isa ba? Ka fifita karuwa akan matarka da ƙanwarka, ka mararmin Minal, Imran kana tsoron Allah kuwa? Wato kasa ƙafa kai fatali da sharaɗin da na gindaya maka ko?" "A'a Ammi ba fatali nayi da maganarki ba, dan Allah ki tsaya ki saurareni in miki bayani" "Bayanin ubanka zakamin, ka fara bijiremin saboda 'yar iska karuwa.. Kan Ammi ta rufe bakinta, Amira ta fara sheƙa amai a gurin 😲😲😲 Domin gyara, sharhi ko Shawara Ayshercool 07063065680. [2/16, 8:15 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                              47_48 Gaba ɗaya suka mai da hankalin su kan ta, ta yunƙura zata bar falon amma abun yaci ƙarfinta, haka ta tsaya ta yi shi a falon. "La'ila ha ilalla la, Muhammad rasulillah Sallallahu alaihi Wasallama, Imran me nake gani haka? Ba dai ciki ne da Yarinyar nan ba?" Gaba ɗaya Imran ya dirirce yace 'Amm, mm dama, dama fa bata da lafiya Ammi, ba ta jin daɗi jiya har Asibiti muka je aka ce typhoid ne da ulcer ke damunta" "Zan ɗura maka ashar ka kuma nema ka rainamin hankali, uwar typhoid ɗin da uban ulcer, kalli yadda yarinya ta ɗashe, tai haske amma kace min ulcer" "Allah Ammi ba su cemin ta na da ciki ba" "Rufemin baki, ni zaka rainawa hankali, wannan uban aman da tai ne za ka ce wai ma malaria ne, ka kyauta ds tsallake umarnina Imran, amma ka tabattar ka nemwa ɗan da zata haifa wata kakar ba ni ba, dan ba zan karɓi ɗan da ya fito daga tsatson karuwai ba, dan bani da tabbas na ka ne ko ba naka ba" Duk da Amira na fama da kanta, dan a inda ta gama amana, ta kwanta akan kujera, gaba ɗaya jikinta yai sanyi, gaɓoɓin ta na mata ciwo, ga wani irin azababben ciwon kai da jiri da ke damunta. Ihsan kuwa ɓangaren ta tayi da sauri, tana kuka yanzu Dagaske Amira ciki ne da ita, shikenan ta tabbata Imran ya zama nata, dan yadda yake ƙawazucin ta samu ciki ba ta samu b, Amira ta samu ze sake tattare wa ne a gurinta. Nan ta sake jinjinawa ƙarya da rashin alƙawarin maza, yanzu duk daɗin bakin nan da yai ta mata, da alwashinsa akan ba ze kusanci Amira ba, katsam se aka haihu a ragaya, wai Amira da ciki. Ta sake rushewa da kuka hadda sheshsheƙa. Shikuwa Imran cigaba da lallaɓa Ammi yayi da rantse rantse, "Ammi dan Allah karki sheganta abunda take ɗauke da shi, wallahi Ammi Amira ba karuwa bace ba, na rantse miki" "Eh tunda dama taje ta maka surkullen da zatayi dole ka zo gabana kana gayamin haka, kana nufin duk gantalin da ta dinga yi, har wasu garuruwan da'awa ta tafi ko jihadi? Ina ce nan hotunan ta suka dinga yawo tana rawar gala, wace 'yar mutuncin ce za tai abunda tayi?" "Na sani Ammi, amma maraici ne da rashin gata ya sa ta tashi a haka, amma ba karuwa bace" "Wallahi ka kuma cemin ba karuwa bace, zan zabga maka mari, shashasha dama tunda ka saki labule da ita ai dole ka faɗi haka, kar idan ka koma ta hanaka, ka kyautawa ranka, kuma bari in naka kashedi, billahilazi duk ranar da ka kuma dukar min yarinya saboda kilaki seta bar gidanka a ranar, kuma yanzu ma ba ƙyale ku nai ba, ba zan bari a haifi wannan cikin a gidan nan ba, dan ina tantama a kansa, ka bani mamaki ka bani kunya idan har kai ke da alhakin cikin nan Imran, kuma zan maka kashedi da gargaɗi idan harka kusakura ka canzawa Ihsan, ko kai mata wani abu mara daɗi naji labari, wallahi zamu gauraya da kai. Ta juya ta nufi paet  ɗin Ihsan. Da sauri Imran ya nufi in da Amira ke kwance, ke ta zubar da hawayw jiki ba ƙwari. Ya sa hannu ya ɗagata cak ya shiga da ita parr ɗinta, a gurguje ya ɗakko duster ya goge aman, dan kar ma Ammi ta fito ta ganshi yana aikin aman da Amira tayi. "Ihsan dan Allah ki dena wannan kukan, ki zuba ido zan ɗau tsatsuran mataki akansu, wannan cikin baza'a haife shi a gidan nan ba, ban taɓa tsammanin Imran ze kaucewa magana ta ba, yaje ya aikata abunda ya ga dama ba, amma kiyi haƙuri dan Allah" Ihsan dai kasa magana tai, saboda batun cikin nan ya girgiza ta, Ammi ta dinga rarrashin ta, sannan tace "gaskiya Ihsan dole ayi wani abu, idan da yiwuwar aje Asibiti a dubaki, ya za'ai ita harta ɗau ciki ke kuma haryanzu shiru, ko dai wani abun ki ke yi ne?" "Ni ba abunda nake yi" "Amma abun da mamaki gaskiya, gaskiya ki shirya kije Asibiti, dan tunda ita ta samu Imran lafiyarsa ƙalau maybe matsalar daga gare ki ne, kije a bincika" Ihsan ba tace komai ba, dan abun ma haushi ya bata, kwata kwata yaushe akai Auren da za'a fara wannan maganar, ai yadda ba ta samu ciki ba dole Amira ma ta rasa nata. Ammi dai ta gama maganganunta ta tafi, a harabar gidan ta tarar da Imran, yace "Ammi kin fito?" "Bam sani ba, sakarai wanda ya rako maza duniya, har kake rawar kai akan karuwa, ka mari ƙanwarka Saboda ita, kake wulaƙanta matar da take sonka saboda Allah, nutsatstiya kamila duk saboda karuwa ko Imran? Ka kyauta nima ka saurari matakin da zan ɗauka, saboda gaza cika umarnin da na baka" Ya sunkuyar da kai yai shiru, tayi ta gama sannan ta tafi. Tana tafiya Imran ya koma part ɗin Amira da sauri, ya tarar tana nan in da ya kwantar da ita. Da hanzari ya kulle ƙofar part ɗin ya haɗa ruwan zafi, ya cire mata kayan da tai aman a jiki, ya ɗauke ta zuwa banɗaki. Wanka ya taya ta tayi, sannan ya kamo hannunta zuwa bedroom, ya zaunar da ita a bakin gado ya shiga share mata hawayenta yace "Amran, dan Allah ki dena kukan nan haka, insha Allah komai ze wuce, kinga Amm tazo ta ɗagamin hankali, ga rashin lafiyarki ga kuka kina yi, da wanne zanji? Dan Allah ki dena kuka Amira" Ya dinga share mata hawaye, yaje fridge ya ɗakko tuffa, ya zauna ya yayanka mata ya bata, ya samu ta karɓa ta ci sosai. Ya bata wasu kayan ta saka sannan ya rungumota zuwa mota. Ihsan na jin ƙarara motar Imran, ta tashi da sauri ta leƙa, ga hango ya saka Amira a gaban motar sun fita. Kuka ta fashe da shi tace "wallahi da ni kake zancen Imran, za ka gane ba ka da wayo, zaku ga abunda zan muku, daga kai har ita se na ga baya Wannan cikin, Allah ya isa tsakani na da kai Imran!" Tai maganar tana dukan bango, ta zube ta cigaba da kuka a gurin. Imran ya kalli Amira yace "Amran, ko Asibitin su Anty zamu?" Amira tace "A'a" 'saboda me" "Gaskiya kunya nake ji, kar inje cikin ne da gaske" Imran yace "to da da wasa ne? Ai tun da kika ji Ammi ta faɗa cikin ne Amira, ni dai Allah ya tabattar" Ajiyar zuciya tayi, ta tuno da kalaman Ammi, na ba zata karɓi duk wani jika da ga tsatson karuwa ba. Gaba ɗaya jikinta yai sanyi, rai shiruu ba ta kuma cewa komai ba. Wani Asibitin kuɗi sukaje, suka ga likita aka rubutawa Amira teses, Sedai sakamakon ya nuna tana ɗauke da juna biyu na watanni biyu. Imran ya dinga washe baki yana murna, yace "Allah ya raba lafiya ya in ganta mana my Wife" Murmushi tai kawai ta sunkuyar da kai, dan ba wani murna take da cikin ba, mussaman idan ta tuna da kalaman mahaifiyar Imran. Aka basu magunguna, aka ƙara mata ruwa da allurai, sannan suka nufi gida. Da suka koma gidan ma dai, kwanciya Amira ta kuma yi duk da ɗan ji ƙarfin jikinta ba kamar da ba. Imran yace "Amran, Sannu kinji, Allah ya raba ki da cikin nan lafiya, ya nunamin abun da zaki haifa" Tai murmushi cike da damuwa tace "Ameen, Amma" "Amma me?" "Ka na ji Ammi tace ba ta son abun da zan haifa, dan bata yadda ma naka bane" "Shh, ya isa haka, ni da nai ai na san nawa ne, kuma Allah sheda ne,dan haka ki dena damuwa masoyiya, Ammi ma zata gane abunda take miki ba daida bane, amma dan Allah ki yafe mata saboda nasan hakkinki ze kamata" Ta ɗan gyara kwanciyarta tace "Hubby, bani fa kowa se Allah seku, ina son in riƙi Ammi uwa a matsayin matar da ta kawo mijina duniya, kuma matar uba a gurina, wato wan mahaifiyata, dan haka ban taɓa riƙonta da Allah yai mata wani abu saboda abunda take min ba, ina fatan Ubangiji Allah ya sa ta kalleni a matsayin 'ya kuma matar ɗa ne kawai" Imran yai ajiyar zuciya yace "Your heart isa always different Amira, nagode Sosai Ubangiji Allah yai miki tukuici da gidan aljanna" "Nima nagode Sosai, Ubangiji Allah ya tsaremin kai a duk in da kake, yasa ka gama da duniya lafiya" "Ameen sweetheart" yai maganar yana kissing goshinta. Ya miƙe ya fita daga ɗakin, Amira ta lumshe idanunta ta na tunanin maganganun Ammi, anya akwai lokacin da ze zo Ammi ta so ta kuwa? Bata ƙaunar ta ba ta taɓa tunanin wannan ƙiyayyar za ta gushe da ga ran Ammi. Kiran Anty ne ya shigo wayarta, ita ta manta da batun wata wayana dan kusan kwana biyu ba ta ko ta;a wayar ba. Ta miƙa hannunta ta ɗakko wayar, ta saka a kunnenta "hello Anty" "Amira lafiya kuwa, tun ɗazu nake kiran wayarki baki ɗaga ba"? "Am sorry Anty, munje Asibiti ne na bar wayar a gida" "Subhanallah waye ba lafiya haka?" "Anty nice" "Ahh to ko dai abun ne ya samu?" Amira tai shiru cike da jij nauyin Antyn, Anty tace "Masha Allah Alhamdilillah ala kulli halin, Allah kai ne abun godiya, amma meyasa baku zo Asibitin mu ba?" "Eh yace muzo nan, nikuma gaskiya ni na ce kar muzo nan" "To meye a ciki Amira, ai abun farinciki ne, abun jin daɗi ya same mu, Ubangiji Allah ya raba lafiya, irin wannan ai seki gayamin, ko Abinci in dinga aiko miki, dan nasan irin wannan situation ɗin bakomai zaki iya ci ba" Amira tace "hmmm" a ranta tace dama Ammi ce ke wannan farinciki haka, duk da cikinta ba halak ne, amma tana jiyewa abunda zata haifa ƙiyayyar da ze fuskanta daga dangin ubansa. Anty tace "Amira lafiya kuwa, naji kin ce hmmm kuma kinyi shiru?" Kawai Amira ta fara kuka, cikin damuwa Anty tace "Ya salam, Amira menene? Ki gayamin meyafaru?" "Anty bana son in dinga gayamiki abun damuwa, amma har ga Allah bana farinciki da cikin nan" "Kai Amira baki da hankali ne? Wasu an nema ido rufe da kuɗinsu kice ba kya murna da cikin? Kina kallon abokiyar zamanki ban sani ba in ba yanzu ba, Amma Allah be bata ba, ke kuma kin samu zaki ce ba kya murna? Meye hujjarki bayan da Aure kika samu" "Anty, Ammi tazo gidan nan da safe, a gabanta na dinga amai sedai ta nuna ba ta maraba da hakan, kuma tace ita tana doubting idan na Imran ne" ta ƙarasa maganar cikin kuka. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ni wai meke damun Hajiya Jamila ne kamar ba taje makaranta ba? Wane irin abu ne haka take yi kamar ba musulma ba? Idan ita bata maraba da shi mu munayi, kuma ɗanta yasan ai ɗansa ne, dan haka kark kuma sa wanan a ranki, mu mun gode Allah da ya raba baiwar sa ya bamu, Allah ya rabaku lafiya in ba sa so kema kuma va kya so, in kin haifa ni ki bani, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki raini cikin ki ki haihu lafiya, idan kika kuskura jininki ya hau da ciki, zaki iya jijjiga idan kin haihu, dan haka kar inji ko in ga kince ba kya son ciki, ki lallaɓa abunki kiyi Addu'a Allah ya rabaku lafiya kin ji jo?" Amira tace "To Anty Insha Allah" "Yawwa Amira, me kike buƙata in sa Fadila ta girka miki a kawo miki?" "Bana son komai Anty, naci Abinci" "To shikenan, da kinji kina son wani abun ki kirani a waya kinji Amira" "To Anty insha Allah, nagode Sosai" "Yawwa, Allah yayi albarka" Amira ta ajiye wayar. Imran kam ɓangaren Ihsan ya nufa, yaje ya tarar da ita tasha kuka, duk tayi wani iri saboda azabar kishi, tausayinta ne ya kama shi, duk da wasu lokutan halinta ne yake ja mata komai, amma yaje ya zauna a kusa da ita, sedai yana zama ta matsa daga kusa da shi. Hannu ɗaya ya saka ya janyita ta ƙarfin tsiya, tana fizge fizge amma ya riƙeta gam ya zuba mata ido, cikin kwantar da murya yace "haba Ihsan, wallahi kin bani mamaki, yanzu duk da tarin soyayyar da ki ke min amma zaki iya juyamin baya haka? Gaba ɗaya kin watsar dani, ta yaya Hankalina baze karkata wani gurin in nemawa kaina mafita ba?" "Dan Allah ka ni ka ƙyaleni, kaje ka ƙarata ka rabu dani bana son ganinka ma, maci amana kawai, ka min alƙawarin da ka san ba zaka iya cikawa ba, kuma kana nema ka juyamin baya" Imran yace "tabbas nayi dana sanin yi miki alƙawarin da na gaza cikawa, amma ni ko sau ɗaya bani da niyyar juya miki baya, kece ma ki kai watsi dani gaba ɗaya, kuma karki kalli tarayyata da Amira a matsayin cin amanarki, Ihsan na biye miki a baya nayi kuskure, saboda Amira itama matata ce tana da hakki a kaina, ama na take na dinga biye miki dan kar hankalinki ya tashi, amma ni haryanzu ina sonki a raina, matsayin Amira daban a gurina, kema matsayin ki daban a gurina dan Allah ki kwantar da hankalinki mu rayu cikin kwanciyar hankali" "Ba dai dani ba, kaje can dai ka rayu da ita ba da Ihsan ba" Riƙe ta yai ya fara kissing ɗinta a hankali, amma ta dage iya ƙarfinta tana tureshi, Imran ya kalleta yace "Ihsan meke damunki hakane?" Ta tofar da yawun bakinta tace "ban sani ba, Allah ya kiyaye ka haɗa baki da Karuwa sannan ka samin bakinka a nawa Allah ya suttura" Murmushin takaici yayi Yace "she's virgin, ba Karuwa bace, idan ma karuwar ce ta fiki sona duk da yadda ki ke da'awar kina so na, da Amira ce ba zata mik abunda kike min ba, duk da tarin laifukana a gareta ba ta taɓa watsar dani kamar yadda kike ba, satina biyu da dawowa amma kin ƙauracewa shimfiɗa ta gaba ɗaya, na biyoki amma still kin min wulaƙanci, dan me ba zanje in da  za'ai maraba da ni ba? Amira na da wata daraja ta mussaman a idona, saboda halayenta, abunda tai a baya ma kuskure ne, ina fatan Ubangiji Allah ya yafe mata, kiyi wa kanki faɗa Ihsan kishi ba hauka bane, gidan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam mata goma sha ɗaya ne, duk da son da yake wa Nana A'isha radiyallahu anha, abokan zamanta goma ne, balle ke Ihsan, ina ilimin ki da na sanki da shi? Ina tarin karatunki na addini, duk kishi yasa kin ajiye a gefe? Allah ya ganar dake akan lokaci, ki shirya jibi insha Allah zan tafi Lagos, tare zamu tafi" "Ba zani ba, ka ɗau barbaɗaɗiyyar matarka ku tafi tare" "Ai kuwa ko a ƙafa na jata bina za tayi, matar aljanna kenan" Ihsan taji kamar tabi Imran ta shaƙeshi. Yana fita ta kuma rushewa da kuka, ta sa hannu ta ɗauki wayarta tana kuka ta kira Mummy. "Hello Mummy kina ina ne?" "Ina gida lafiya?" "Mummy Ina fa lafiya, Mummy Imran ya yaudareni mugu ne, bayan tafiyar su Lagos kinga ta dawo da ciki, gaba ɗaya wulaƙanci yake min, ya dena saurarata ya dena shiga harkarta na shiga uku Mummy ta ƙwacen mijina" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, dagaske ciki ne da ita?" "Ciki ne da ita Mummy, kuma yau a gaban Ammi ta dinga amai" "To me Jamilar tace?" "Mekuwa tace? Ta yi musu hargowa ta tafi, na abunda yafi damuna shine da tace min wai inje Asibiti a dubani, ɗanta lafiyarsa ƙalau tunda matarsa ta samu ciki, ni shikenan na shiga uku" "Ki kwantar da hankalinki Ihsan, ba ki shiga uku ba" "Wallahi na shiga Mummy, shikenan Bani da wani amfani yanzu, zuwa nan gaba duk da tace ba zata krɓi jika da ga gurin karuwa ba, nan gaba idan ban haihu ba, ko dai ta karɓi 'ya'yan Amira, ko kuma ko ta sa ya ƙaro Aure" "A'a ki kwantar da hankalinki, hakan ma ba zata faru ba insha Allah" "Mummy k ka ce in kwantar da hankali na, how? Ta yaya Hankalina ze kwanta, bayan ni da ke mun san batun kwanciyar hankali babu shi? Shikenan ni na san abunyi, sedai a zauna kowa ma ya rasa" Ta kashe wayarta ta zauna a gurin tana cigaba da kuka. Da daddare Imran yana gurin Ihsan, sedai fafur taƙi sauraron sa, shikuma ya gwada mata ƙarfi, gaba ɗaya Abun duniya ya sake ƙule Ihsan, ya tashi yai tafiyar sa ya barta, nan ta ƙara tabattar da Imran yanzu ba ta gabansa. Ya kints jikinsa ya shiga gurin Amira, ya tarar tana bacci amma jikinta raɗau da zazzaɓi, ya shafa gashin kanta ya sumbaci goshinta sannan ya bar ɗakin. Da safe ma seda ya koma gurin Amira, ya tarar idonta biyu ya dafa tea ya bata, tai wanka yace "ko kina sha'awar wani abun in siyo miki" Tace "A'a bana son komai, idan naci ma amai zanyi" "Sannu Amira" "Yawwa my dear" "Bana jin daɗin rashin cin Abincin nan da kike yi" "To ya za'ayi larura ce ai, kasan me nake sha'awar ci?" "Se kin faɗa" "Ina wannan tebar da aka kawo mana, ranar da muka je Lagos?" "Eh na gane" "To da zan samu ita nake so" Imran yace "bari in fita zan duba gurin masu sai da Abinci, ko zan samu" "No i don't mean you should buy it for me, kawai dai gaya maka nayi" "Da na iya da da kaina zan miki Amira" Amira tai murmushi tace "Never mind" Imran ya gyara zama yace "Amira, zan koma Lagos , amma Ihsan ta ƙi yadda mu tafi tare, kinga dama ba ki da lafiya ko zamu tafi tare?" Girgiza masa kai tayi tace "A'a, ai wannan zuwan da ita ya kamata ka tafi, idan ka tafi dani ba kayi adalci ba". "Amma kin san haryanzu akwai sauran sati uku da ya kamata muyi tare, watanmu biyu da sati ɗaya da ita lokacin da muka tafi Lagos" Amira ta harareshi tace "meya hana a biyani tun a wancan lokacin se Yanzu?" Yai murmushi yace "Allah ya baki haƙuri" "Yawwa Amran, dan Allah nace ina son zuwa Kano, ko sati biyu inyi kan ka dawo" "Wa kika ajiye a Kanon da zaki je?" " 'yan uwana mana" "To ban yadda ba, ko zaki ba Yanzu ba" "But Why?" "To banda Fa'iza gurin wa zaki je? Kuma ko sati biyu ba'ayi da barin su nan ba" "Haba Amran, ko ba komai Yakamata in je, tunda na baro Garin ban kuma zuwa ba fa" "A yanzu dai ban yadda kije ba, sedai ko nan gaba" "Shikenan" "Yawwa tawan, shiyasa nake yinki, duk da tsiwar ki ana iya saki ko a hanaki, keep it up dirling" Duk da taji haushin hanatan da yayi, amma tai masa murmushi. Har satin ya shuɗe Imran be koma gurin aiki ba, saboda yanayin jikin Amira, tana shan wahalar cikin nan sosai, yana matuƙar tausayinta sosai, ga rashin cin Abincin komai taci se tai amai, kankana ko apple suka ɗai ke iya zama idan ta ci. Gefe guda Ihsan abubuwan ta sam ba sauƙi, kullum gaba suke yi, tashin hankalin yau daban na gobe daban, kullum da kalar rikicin da zata ɓallo wanda ze ɗagawa Imran hankali. Imran yana tausayinta ne, amma ya ga abun nata ba na ƙare bane. Amira ta gaji da kwanciya, ta ɗan fito babban falo dan ta huta, taji ƙamshi ya cika gidan, Ihsan tana suyar dankali da ƙwai. Nan da nan jikin Amira ya hau tsuma, yawunta ya tsinke, taji ranta ya biya. Ta tashi ta koma ɗakin ta dan ta dena jin ƙamshin amma abun ya gagara, ta shiga Kitchen ɗinta da niyyar itama ta girka, amma tana haɗo kayan gyara dankalin taji bata so, wanda yake ƙamshin nan kawai take so. Amira ta fito ta nufi part ɗin Ihsan, ta na zuwa ta tarar da Ihsan a Kitchen tana aiki. Tace "Ihsan sannu da aiki" Ihsan ta ɗago ta kalleta tace "uban me kika shigo yi min? Meya kawoki munafuka" "Dan Allah kiyi haƙuri, dan girman Allah ki sanmin dankalin nan, ko kaɗan ne" "Sannu mayya, nace sannu mayya, ai gara ki biyoni ki sake gayamin ki na da ciki, wallahi idan baki bar part ɗina ba, sena ƙona ki da mai, Allah ya sa cikin ya zube uban kowa ma ya huta" "Naji, koma dai menene ni dai dan Allah ki sanmin Ihsan ko kaɗan ne, dan son da kike wa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam" "Wallahi ko ƙiyama zaki tafi, idan baki ci ba se dai ki tafi, dan wallahi ba zan bayar ba matsiyaciya algunguma tsohuwar karuwa" Hawayen takaici ne suka fara zubo mata, ba abunda Ihsan ta gaya nata ne ya ɓata mata rai ba, rashin bata dankali ne ya baƙanta mata rai. Ta fito daga part ɗin hannunta riƙe da plate tana kuka, har Imran ya shigo tana zaune da plate a gaba tana kuka. Imran yace "Amira lafiya meya sameki haka?" "Ihsan ce ta hanani dankali" "Wane dankalin?" "Dankali take soyawa nace ta sanmin ya hanani" "To dena kukan ya isa haka" Ya nufi part ɗin Ihsan, ya tarar ta gama grikinta, har tayi wanka yace "Ihsam meyasa kike hakane?" Ta kalleshi tace "kamar yaya?" "Ihsan meyasa baki da tausayi ne?, Amira kina kallo tana fama da rashin lafiya amma ko sannu ba ki taɓa ce mata ba, bata ko iya cin Abinci, amma duk da irin zaman da kuke tazo tace ki bata abu ki hanata, haba Ihsan" 'ni na mata cikin da zan girki in bata, bazan bayar ba ban niyya ba" "Eh gaskiya ne, ni nai ciki, kuma ni nake nemowa in kawo gidan nan, dan haka baki isa ki hanani iko da abinda yake mallakina ba" Yana gama maganar ya shiga Kitchen da kansa, ya zubawa Amira dankali yai waje. "Imran kar ka bata Abinci na ba kai ka dafa min ba" Ko saurararta be ba, yaje ya samu Amira ya bata, Amira kamar ta goya Imran dan murna, ta dinga cin dabkalin nan tana murmushi. Allah ya temake ta harta gama ba tayi amai ba. Ihsan ta koma ta shiga safa da marwa a ɗakinta, tana tunanin yadda za tai taga Amira ta rabu fa cikin nan, ko ta tsiya kota bala'i. Ihsan fafur tace ba zata bi Imran ba, dan haka ya ƙyaleta, amma ana gobe ze tafi ya kai Amira gidan Anty, shi kuma ya tafi Lagos, lokacin cikintavya cika watanni uku cif. Amira ta ɗanji dama dama komawarta komawar ta gidan Anty, duk da ba ta dena laulayin gaba ɗaya ba but, ta kan samu ta ci Abinci sosai. Duk lokacin da Imran yake gida, yana kiran Amira ya ji ya jikin ta, sukan daɗe suna waya suna hira. Ɓangaren Ihsan ma ya na kiranta, wataran ta ɗag suyi rigima, wataran kuma taƙi ɗagawa gaba ɗaya, duk ta maida hankalinta kan yadda za tai ta raba Amira da cikin nan, kuma ta koreta. Wataran da daddare Anty tace "Amira, sako mayafinki muje gidanku" Amira ta kalli Anty da mamaki tace "wane gidan namu?" "Gidan su mijinki mana" Take gaban Amira ya faɗi, saboda tasan karan batta ta da Ammi ba daɗi. Bata son yiwa Anty musu, dan haka ta  ɗau mayafinta suka fita. Anty tace "Abban ku yana gari ne, ya dawo, kuma ya daɗe baya gari, shiyasa nai girki za mu tsaya a hanya mu sai fruit, muje ki gaishe shi" Hankalin Amira ya ɗan kwanta ta, jin Abba yana gari ta san Ammi ba zata mata komai ba. Tace "Amma naji daɗi, kwana biyu ban ganshi ba" "Ai shiyasa nace muje tare". Da suka je gidan, Anty ta riƙo fulasan kayan Abinci, Amira ta riƙe ledojin kayan marmari, tana gaba Anty na biye da ita. Amira tai knocking ƙofar falon, Minal ce ta zo ta buɗe ƙofar, tana ganin Amira ta haɗe rai tana mata kallon banza. Amira ma haɗe rai tayi, tace 'ban Guri in wuce" Minal za tayi magana kenan, taga she tare suke da Anty, dan haka tai shiru. Suka shiga falon, cikin sa'a kuwa Abba yana falon a zaune yana kallo. Yana ganinsu yai murmushin yace "manyan baƙi ke tafe a daren nan?" "Gamu nan dai, nace bari muzo mu kwashi gaisuwa" "Ahh Lallai kun kyauta, ina mutumin nawa ko baya gari?" Anty tace "Ai Daddy kusan watansa uku be zo ba, Hajiya Jamila ina yuni?" Ammi ta ɗan yatsina fuska sanan ta amsa. Amira ta gaida Abba sannan ta gaida Ammi. Sun daɗe suna hira a gurin, Abba yace "tunda 'ya ta ta kawon Abinci, Minal zoki ɗau naku Abincin nata zanci" Amira tace "Abba ni zanci nakan" Yace "shikenan kinga anyi musaya" Suka yi dariya, Minal ɗakinta ta tafi dan takaici, dan ta tsani Amira akanta Yayanta a mareta kuma ake wulaƙnta Ihsan. Se kusan goma da rabi sannan suka tafi, Abba yaita sawa Amira Albarka yana wa Anty godiya. Bayan tafiyarsu Ammi tace "daka sa ba zaka ci Abincin nan ba be kamata ka sa in girka ba" Abba yace "Jamila, ke kina da kunyar yi min Magana ma? Ace ina nan da raina, amma matar abokina ita ke ɗawainiya da 'yar 'yar uwata wadda take 'ya a gurina, kinji kunya Jamila, kallonki kawai nake, ba irin wahalar da ban miki ba ke da 'yan uwanki, amma ni kin gaza min kara akan'ya guda ɗaya Nagode" Yana gama maganar ya tafi ya barta a gurin. Se da Imran yai wata biyu be dawo ba, cikin Amira harya fara fitowa, tunda ya tafi basu kuma haɗuwa da Ihsan ba. Ranar da yai mata waya ze dawo kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna, nan taje gyaran kai da lalle, tace za ta koma gida saboda dawowar Imran. Ana gobe ze dawo Anty tace "ba zan bari ki tafi ke kaɗai ba, ban san me zasu miki ba, ku tafi da Fadila, idan ya dawo ta taho. Haka Fadila tabi Amira gidan, su kaita shirye shiryen karɓar Imran, sedai tun da tasa ƙafarta a gidan, Ihsan ta fita ba ta sake dawowa ba se Ranar da Imran ɗin ze dawo. Ranar da ze dawo da safe Fadila ta bar gidan, ta koma gidansu. Se wajen huɗu na yamma sannan ya dawo, Amira ta sha kwalliya se zuba ƙamshi take, ta kame a falo. Yana shigowa da ita ya fara tozali, ta ƙara haske ga cikinta ya fara tasawa. Da gudu taje ta rungume shi, shima rungumeta yai yana cewa "I miss You Baby" "Miss you too my dear, ya baby na?" "Shima yayi missing ɗin ka" ta faɗa tana dariya. Dan kar Ihsan tai surutu, ya je part ɗinta, sedai ba wata tarbar kirki ya samu daga gurinta ba, dan bata sauya zani ba. Shi kuwa ya koma ɓangaren Amira, yaci ya sha yai wanka, Amira na ta nan nan da shi. Ko da dare yayi be ko kalli in da Ihsan take ba, yai zamansa a part ɗin Amira. Sun kwanta kenan, ya janyo ta jikinsa yana "I Miss You Lovely dear" "Miss you More" Tai maganar tana rungumeshi, sedai tana rungumeshi ta saki wani razanannen ihu, ta zabura ta tashi daga jikinsa tana ihu. KUYI HAƘURI BANYI EDITING BA NAYI BUSY OVER Ayshercool 07063065680. [2/18, 9:32 PM] Ayshercool:       🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                          49_50 Imran ya kalli Amira a gigice yace "Amira meye haka? Lafiya kuwa, meyafaru?" Cikin kuka tace "wani abu naji a jikinka kamar ƙadangare" "Ƙadangare kuma Amira? Bakomai a jikina fa" "Wallahi ƙadangare ne a jikin ka" Ya tashi ya kunna fitla, ya cire vest ɗin jikinsa, ya juyo mata bayan yace "kin gani bakomai a jikina" Ƙirjin Amira se dukan uku uku yake ta na sake ƙare masa kallo, tabbas bakomai a jikinsa, amma ita kam taji tamkar ƙadangare ne a jikinsa. Da ƙyar ya lallaɓata ta yadda ba komai a jikinsa, ta dawo ta kwanta, a cikin matsananciyar fargaba ta yadda da Imran, dan gani take kamar da ya taɓa ta zata ga ƙadangaren. Imran ya manta da batun ƙadangare, ya sha soyayyar sa, sedai har sukai wanka bacci ya ɗauke shi Amira ba tai bacci ba. Ta dinga juyi tana karanto duk Addu'ar da ta zo bakinta. Can bacci ya ɗauketa, sedai tai mafarki ƙadangaru sun babibaye jikinta, haka ta kuma tashi a razane tana gumi, ƙarshe haka ta kasa bacci, har Asuba tayi. Gaba ɗaya fargabar komawa baccin ma take, dan haka ta zauna akan dadduma ta cigaba da lazimi, gari na yin haske ta fita Kitchen ta ɗora breakfast. Har ta kammala Imran yana baccin sa, seda tai wanka ta shirya tsaf tai kwalliya cikin ƙananan kaya, sannan ta tafi bedroom ɗin da Imran ke kwance, ta kunna turaren wuta. Ta hau gadon da yake kwance, ta ɗan yaye bargon jikinsa, ta hau kansa tace "My cwt Amran, wake up na, babyn ka na jin yunwa fa" Murmushi yai ya sake gyara kwanciyarsa, itama murmushin tayi, ta zira hannunta cikin bargon da niyyar ta rungumoshi, sedai taji ta danƙi ƙadangare. Take ta zunduma ihu, ta dire daga kan gadon da gudu tana kurma uban ihu. A zabure ya miƙe yace "Amira lafiya wai? Meye hakane?" "Wallahi ƙadangare ne a jikin ka" "Wai wane irin ƙadangare ne haka? Bakomai a jikina, ki kwantar da hankalinki" Yai maganar yana ƙoƙarin tunkaro ta, amma ta sake fasa ihu a gigice tace "ba ga ƙadangaren nam yana bin ka ba, kar ka zo in da nake, gashi nan ina kallo yana binka" Wan ƙaton ƙadangare Amira ke gani a jikin Imran, girmansa ya shallake girman ƙadangaren da take gani a zahiri, gashi a duniya Amira ray tsani ƙadangare. Ganin Imran ze tinkaro ta yasa ta jiya ta zura da gudu Falo tana ihu, ihun Amira da Ihsan ta jiyo ysa ta fito da sauri. Garin gudu Amira tai gware bango, ta faɗi a gurin, amma ta miƙe ta kuma sheƙawa a guje. Imran ya biyo ta yana "dan Allah Amira ki tsaya, kar ki jiwa kanki ciwo ko abunda ke cikinki" Ina idonta ya rufe tai waje da gudun gaske, kan ta je gate Imran ya cin mata, ya riƙota gam. Wata gigitacciyar ƙara ta saki, tamkar wadda ake yayyanka wa da wuƙa, ganin Imran yana nema ya ɗorata a kan ƙadangaren da ke jikinsa. Silalewa tayi sumammiya a jikinsa, cikin damuwa ya ɗauke ta zuwa falo, ya shimfiɗe ta. Ya ɗaga kai ya kalli Ihsan da ke binsu da ido yace "Ihsan dan Allah bani ruwa in shafa mata ko zata tashi" Wata uwar harara ta banka masa ace "Allah ya kiyaye, Allah yasa daga haka ma ta mutu, alhakina ne ya kamata koma menene" Ta ja tsaki tai tafiyarta, seda Imran ya buɗe baki dan mamaki, ya tashi ya shimfiɗe Amira, ya tafi fridge ya ɗakko ruwa me sanyi, yazo ya fara shafa mata. Ajiyar zuciya ta ding saukewa, a hankali yace "Amira kina gani na"? Da sauri ta buɗe ido, tana ganin Imran ta miƙe zumbur daga jikinsa, ta fara ja da baya tace "dan girman Allah ka dena zuwa in da nake, kaje ka cire ƙadangaren da ke jikin ka, dan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ka tashi ka bar falon nan, kaje ka cire abun da ke jikin ka" A ɗimauce Imran yace "Amira, jikina ba komai ni bana ganin komai fa" Kuka ta sake fashewa da shi tana ja da baya, tana ƙoƙarin miƙewa ta sake artawa  a na kare. Ya nufo ta da sauri ze sake riƙeta amma ta faɗi a gurin. Yasa hannu ya ɗauke ta, ya maida ita falonta, yaje ya kwantar da Ita. Ya ɗakko wayarsa ya kira Abba, bugu biyu Abba ya ɗaga yace "Soja marmari daga nesa" "Abba akwai matsala" Abba yace "subhanallah, matsalar me?" "Abba Amira, na easay meke damunta, tun jiya take koke koke tana ihu, sam na kasa gane kanta" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Amiran meya sameta?" "Ban sani ba Abba, da naje kusa da ita take fara ihu, na rasa meke damunta" Abba yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya kawo mana ɗauki, gashi ina Kebbi yanzu haka, amma kira antynta a waya ka mata bayani, duk yadda ake ciki ka gayamin" "To Abba Nagode" ya katse wayar ya kira wayar Anty, Anty ta ɗaga da sallama, ko gaisjeta be tsaya yi ba yace "Anty Amira ba lafiya fa" "Subhanallah jikin ne?" "Anty tun jiya take ihu, na kasa gane kanta yanzu haka tana sume ne, sam ba ta son ko in da take inje fa" "Yasalam, gani nam zuwa, kwantar da hankalinka gani nan" Imran ya ajiye wayar yana cigaba da kallon Amira, dake numfashi kaɗan kaɗan. Befi mintuna arba'in ba, sega Anty ta iso a kiɗime, kai tsaye ta nufi ɓangaren Amira, taje ta tarar da ita a kwance kamar gawa, Imran ya zuba mata ido yayi tagumi. Anty tace "Imran, meya sami 'yata?" "Anty nima ban sani ba, gaba ɗaya taƙi tsaywa ma in fuskanci meke damunta, se ihu kawai take' Anty taje ta kama hannun Amira, ta ɗaure ta nemo jijiya tai mata wata allura, Sannan ta sa Imran ya dinga shafa mata ruwa me sanyin gaske. Wata irin ajiyar zuciya tayi, kamar za ta shiɗe Sannan ta koma numfashi normal. A hankali Amira ta buɗe ido,ta kalli Anty tace "Anty yaushe ki ka zo?" "Yanzun nan Amira, mijinki yai min waya ba ki da lafiya, kinga bani da kwanciyar hankali kenan" Amira za tai Magana idinta ya sauka a na Imran, aikuwa ta zabura ta ƙanƙame Anty tana salati. Anty tace "Amira lafiya kuwaa?" "Anty dan Allah ke ki gaya masa ko zeji, ki ce masa yaje ya cire ƙadangarem da ke jikin sa wai shi baya ganinsa" Anty tace "wani irin ƙadamgare kuma? Ai bakomai a jikinsa" "Wallahi akwai, wai Anty kema ba kya ganinsa ne, dan Allah karku ce nika ɗai nake ganinsa, gashi nan a kwance a ƙirjinsa fa" Anty tace "shikenan yi shiru, Kai Imran nima naga ƙadangarwn nan, kaje ka cire shi daga jikinka" Anty tai maganar tana ƙiftawa Imran ido. Imran jiki a sanyaye ya bar falon yana waiwayen Amira. Anty tace  "ya tafi cirewa, ki kwantar da hankalinki ki yi ta Addu'a kinji?" "To Anty ina yi, nace masa yaje cire ƙadangare a jikinsa, amma yaaƙi kuma binsa yake" Anty tace "ai yanzu yaje cirewa, tashi ki karya, naji yace baki ci komai ba" Amty ta zubawa Amira Abinci, ta sata a gaba taci. Imran kam barin Gidan yai gaba ɗaya, har bayan azahar Anty na tare da Amira. Seda ta tabattar Amira ta ɗan sami nutsuwa sannan ta kunna mata karatun Alqur'ani. A hankali bacci yai awon gaba da Amira. Wajen la'asar Imran ya dawo, ya tarar Anty ba ta tafi ba cikin damuwa yace *Anty ya ake ciki? Ya jikin nata?" Anty tace "jiki Alhamdilillah, amma ina tunanin ko ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta ne ta na bata wrong perception, ko dai wani abun daban. Amma ga karatun Alqur'ani nan na saka mata, ka cigaba da kula da ita zuwa Gobe in Allah ya kaimu muga yadda hali zeyi" Imran yace "to Anty, amma ina fatan cikin jikinta be samu matsala ba, saboda faɗuwar da ta dinga yi" "Cikinta yana lafiya ƙalau, da wani abu na fita za ta gayamin, sedai ka kula sosai" Imran yai ajiyar zuciya yace *to Alhamdilillah, insha Allah zan kula nagode sosai Anty' Su kai sallama ta tafi. Ga mamakin Imran har wajen magariba Amira ba ta Tashi ba. Gashi yanzu fargabar zuwa in sa take yake, kar yaje ta sake birkicewa. Haka nan ya daure ya koma gurin Amira, ya ga halin da take ciki. Ya tarar da ita ta na ta bacci, ko motsin kirki ba tayi, ga sautin karatun Alqur'ani na tashi. Seda ya tabbatar lafiyar ta ƙalau, sannan ya koma babban falo. Aka fara kiraye kirayen sallar magariba, yai alwala amma yana gudun ya fita salla, Amira bw san a ya zata farka ba, gashi ita Ihsan ko a jikinta kamar mara imani. Da yai alawara falon ya dawo ya tada sallar magariba. Amira kam kamar wadda aka tasa ta farka, tai miƙa tana faɗin Alhamdilillah. Sedai taji kamar wani abu na bin ƙafarta, ta tashi zaune da sauri ta ga meye, taga ƙanana 'ya'yan ƙadangare. Aikuwa ta diro daga kan gadon nan tana tsalle tana faɗin "Innalillahi wa innalillahi raji'un" A guje Imran ya sallame sallar da ta tayar,yayi part ɗinta da gudu. Yana zuwa su kai karo tana ƙoƙarin fitowa da gudu, ta cire skirt ɗin jikinta ta yar, ta cire rigar jikinta, ta na ƙoƙarin yage vest ɗin ciki. Imran yana ƙoƙarin riƙeta ta kuma tozali da ƙadangaren da take gani a jikinsa, sun ƙari sun zama uku. Nan ma wani uban ihun ta zunduma, ta juya da gudu zata koma, gwanin ban tausayi ga ciki a jikinta, amma sam hakan baya hanata zurawa da gudu dan nemawa kanta mafita. Sosai take ihu kamar ta zare, abunda ba taso ɗin dai Imran ya riƙeta gam yana karanta mata duk Addu'ar da tazo bakinsa. Da farko da yaji jikinta ya saki ya zata baccin ta koma, seda ya lura da kyau ya ga ashe suma tayi. Imran yai shiru yana rungume da ita yace "What happens to you my dear,  meya sameki Amira na? Ubangiji Allah ka kawo mana mafita kai mana ɗauki a lamarin marainiyar nan, Allah ka yaye mata abunda yake damunta. Ya ɗauketa zuwa cikin bedroom kan gadonta, ya kwantar da ita, ya sake kunna mata karatun Alqur'ani, sannan ya kulle ɗakin ya tada salla. Bayan ya idar ma Addu'a yaita mata, na fatan samun lafiya daga kowane irin ciwo ne ma ke damunta. Har wajen sha biyun dare Imran be rintsa ba, yana gadin Amira. Bacci ne ya ɗan sace shi, ba tare da ya sani ba baccin nasa ya fara nisa sosy. Cikin baccin ya kuma jin hargowarta, ya buɗe idonsa a razane, ya ga ta sake cire kayan jikinta tana ƙoƙarin buɗe ƙofar, se jijjiga ƙofar take tana waige waige tana ihu. Imran ya janyo ta, ya rirriƙeta ya dinga karanta mata duk abinda yazo bakinsa, sedai ga mamakinsa da ta fara abun seta fara yunƙurin faɗuwa, dan yau kam ta faɗi be san iyaka ba. Ihsan kuwa tsaki tai, dan sun uzzura mata, Amira ta hanata sakewa da ihun da takeyi. Ta taso ta kulle ƙofar part ɗin ta tace "Ai kaɗan ma kika gani, da haka hauka har abada haka zaki tayin shi, ba ke ba hankali har abada, zaki san kin auri mijina, kina ƙoƙarin mallake shi, kaima da ƙafafuwanka zaka dawo, idan kaga ta haukace ta dena amfana maka Komai" Taja tsaki ta rufe ƙofarta. Imran kuwa yadda yaga rana haka yaga dare, sam ne rintsa ba saboda yadda larurara Amira ke neman shallake tunanin sa. A nan ɗakin nata yai sallar Asuba, ga abun damuwar ita bata hayyacinta gaba ɗaya balle a samu tai sallar. Bayan ya idar da sallar Asuba, tana sume, haka yai mata wanka ya kintsa ta, ya sa ta a mota ya fita. Ƙarfe Bakwai saura se gashi a gidan Anty. Fadila ce ta buɗewa Imran ƙofar falo, ta ganshi da Amira a hannunsa, ta bashi guri ya shiga yaje ya kwantar da ita. Fadila tace "Imran, lafiya kuwa? Meya sameta haka? Jikin ne dai?" Imran yai ajiyar zuciya yace "kuyi haƙuri na zi muku da sassafe, jiya sam ba muyi bacci ba, na kasa gane kan Amira gaba ɗaya" Yai maganar cikin karaya, Fadila tace "Subhanallah, insha Allah zata warware, bari inwa Anty magana" Fadila ta shiga ciki, Imran kuma ya zubawa Amira ido dake shimfiɗe kamar ba rai a jikinta. Anty na fitowa tai salati tace "Imran ba dai jikin ne ba?" Imran kamar ze kuka yace "Anty na tsorata da abun da Amira ta yi, daga tafiyar ki jiya zuwa wayewar gari, kayan jikinta take cirewa tana ihu, wai ƙadangaru ne suke binta, faɗuwa kuwa ta faɗi ba'a dadi se suma, da ta farka se ihu, Allah yasa ba wani abu ne ya sameta a ƙwaƙwalwa ba, Allah ya sa Amira ba taɓun hankali ta samu ba" Abun mamaki sega ƙwalla a idon Imran, Anty tace "haba Imran, ka kwantar da hankalinka ka karɓi ƙaddara a yadda tazo maka, ni nafi tunanin wannan ciwon nata shafar aljanu ne, ina ga gurin masu ruƙiyya zamu" Fadila tace "ko kuma Asiri a kai mata ba" Anty tace "ƙaniyar ki, wane irin Asiri kuma ana zaune ƙalau? Waye ze mata wani Asiri? Duk abunda ya samu bawa yace Allah karya kuskura yace wani ne yai masa, Allah da ya ɗora maka ze yaye maka, idan ma wani ne Allah yana kallo, kul na kuma jin zamcen Asirin nan" Fadila tai ajiyar zuciya kawai, wannan abu in ba Asirin ba, shekaranjiya suna tare da Amira lafiya ƙalau, suna shirin dawowar Imran, katsam kuma se a wayi gari daga dawowarsa ta zama haka? Imran yace "Anty meye abunyi to?" "Abunyi shine kaje gida mu gani, idan ba ta ganinka ko zata da wo hayyacinta sosai, idan kuma ba haka ba dole ma dai se an dangaan da malaman ruƙiya'" "Ai ni Anty bana son ayi abun kauce hanya ne, ko ai shirka" "Haba Imran, kamar banje Islamiyya ba, ai da ayar Allah za'a mata magani, kaje gida bakomai Allah ya yaye mata" Imran yace "Ameen" ya muƙe ze tafi, ya zubawa Amira Ido, daga jiya zuwa yau tayi wata uwar rama, duk tayi wani iri. Ya girgiza kai ya fita jikin sa a sanyaye, saboda ya tsorata da lamarin Amiran. Gidan Anty Hadiza ya nufa, duk da da 'yar tafiya daga gidan Anty zuwa gidan Hadiza, amma haka Imran ya tafi. Yai sa'a mijinta ya fita kai yara makaranta daga nan ze tafi Office. "Imran lafiya na ganka da safiyar nan? Yaushe rabonka da gidana tun da na ganka taka ce ta kawo ka" Imran ya jinjina kai ya zauna cike da damuwa yace "Khadija ina cikin damuwa, bani da mataimaki se Allah, Ammi yakamata in kaiwa damuwata, sedai ba dama kullum sedai cikin zarya nake gidan Alhaji Hashim, Anty ke min komai, na fara jin nauyin baiwar Allah nan ina ganin kamar ina ɗora mata nauyi da yawa, ke kuma ba wani shiga cikin mu kike ba kina gefe, tunda ba a gidanmu kika tashi ba, bana son ma Ammi tasan wani abu, shima faɗa za tayi" "Ni se wata magana kake sama a ƙasa, meyafaru wai?" "Khadija, Kin san dai Ammi ba ta son Amira tana ce mata karuwa" "Eh na sani" "Khadija wallahi Amira ba karuwa bace, ni kaina nayi mamaki gami da nadamar abunda nai mata a baya, Amira ba karuwa bace" Khadija tace "ai ni Anty ce ta fara gayamin, tace a zaman da tai da Amira, da yadda tabi hikimomi daban daban, bata ga wani abu da ya nuna Amiran karuwa bace" Imran yace "duk da tarin wulaƙanci da na dinga mata, ban taɓa bata hakkinta na Aure ba, se tafiyar nan da mukayi Lagos tare, a nan na gane ba karuwa bace, katsam Allah ya bata rabo" Khadija tace "Ahh masha Allah, abun ba labari, kace Mun kusa ɗaukar ɗan Imran" "Khadija ki dena wasa mana, Ammi taje har gida taci mutuncin Amira, tace bata yadda ba ma wai cikin ba nawa bane, ga Ihsan ta haɗa min zafi ta tayar min da hankali, saboda kishi da rashin mutunci, nayi nayi ta bini muje Lagos tare taƙi, nika ɗai na tafi, seda nai wata biyu na dawo, sedai tunda na dawo Amira ma ta birkice, da ta ganni se ta fara ihu tana zabure zabure wai ƙadangare take gani a jikina" "Ƙadangare kuma?" "Eh, wallahi jiya ko bacci ba muyi ba, tai ta cire kayanta tana ihu, Allah yasa ba haukacewa za tai ba" Khadija tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu Ina Amiran take?" "Tana gidan Anty na barta" "Meyasa baka kawota nan ba? Ni matsalata da kai zurfin cikinka yai yawa Imran, ni laifi ne idan ka kawomin ita nan? 'yar uwata ce fa ƙanwata ce, ai ba zamu haɗu mu biyewa Ammi ba" "To aini gaba ɗaya na rasa abunyi ne deeja" "Shikenan, kar ka damu insha Allah zata warke, ka koma gida zanje in duba ta amma ka kwantar da hankalin ka" Taita rarrashin sa, ta sa shi yaci Abinci sannan ya tafi gida. Abun takaicin da yaje gidanma, Ihsan ta wanke ƙafarta ta fice nata guri, dan sam abunda ya samu Amira be dameta ba. Amira kam har Azahar sannan ta farka, ta ganta a gidan Anty, ta kalli Fadila tace "yaushe na zo nan?" "Imran ne ya kawo ki" Ɗan zaro ido Amira Tayi tace "dan girman Allah kar ku bari yazo in da nake, wallahi ƙadangaren jikin sa ze kasheni" Fadila tace "Ai ba ya nan, ya koma Lagos ma gaba ɗaya" Seda Amira ta ji haka sannan hankalinta ya kwanta, Anty ta shigo tasa Amira tai alwala, ta rama sallolin da ake binta, ta ɗau Alqur'ani tana karantawa. Anty tana gefe tana kallonta, Imran ya kira Anty a waya dan jin ya jikinta, Amira na jin muryar Imran a waya, ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta. Abun ya ɗaurewa Anty kai sosai, tabbas maganar Fadila akwai ƙamshin gaskiya a ciki, ze iya yuwuwa sihiri ne a kaiwa Amira, ko muma dai sheɗanu ke damunta. Anty ta kawar da duk wani abu da zesa Ayi ko da zacen Imran gaba ɗaya. Da daddare Anty Hadiza taje duba Amira, sedai tayi mamakin ganin yadda Amiran tai wata uwar rama, duk ta canza kamanni. Anty Hadiza ta jimanta yadda taga jikin Amira, abun ya shallake yadda take tunani sosai. Amira ko zancen Imran ba ta son ji, kowani abu da yake da alaƙa da shi, idan har ba za'ai mata zancen sa ba to zata zauna lafiya ƙalau, amma da anyi zancensa za ta fara zabure zabure kamar za ta hau bori. Anty ta dage da saka karatun Alqur'ani ba dare ba rana, dan Amira yanzu ko san ibadar ba tayi, seta takura mata take salla, ta yi azkar ga ciki na ƙara girma yana fitowa dan ya shiga wata na shida, amma wani lokacin idan abun ya motsa, haka zata ga ƙadangarun nan na binta, ta miƙe tana ihu tana cire kayan jikinta, haka za ta faɗi ƙasa ga ciki a jikinta. Imran ma yai muguwar rama, ko Abincin kirki baya iya ci, kullum cikin yi wa Amira Addu'a yake, akan Allah ya bata lafiya, ko tambayar Anty ze ya jikin Amira sedai ta chat ko message, in ba haka ba da taji da shi ake waya zata rikice. Ihsan kam ko da wasa ba ta taɓa tambayarsa ya me jiki ba, ba abunda yai mata zafi yawonta ma ta sa a gaba, ko ta tambaye shi ko bata tambaya ba ba ya hana ta ficewarta, ko gurin aiki ko gurin ƙawayenta. Imran ya tattarata ya watasar shima, ya koma ɓangaren Amira ya tare gaba ɗaya, idan ya tuna irin Karamci da soyayya da haƙuri da Amira take da shi, da kawaici ya tuna halin da take ciki yanzu gaba ɗaya se jikinsa yai sanyu, ya shiga damuwa. Da safe yana shirin fita, dan yana sa ran washegari ze koma aiki, Ammi ta kirashi a waya tace yaje gida tana son ganinsa. Haka ya shirya ya tafi, sedai kamar kullum yana zuwa ƙorafine da faɗa akan Ihsan. Imran yace "Ammi baki san halin da Amira take ci ba? Ammi Amira na fama da larura gaba ɗaya hankalina ba'a kwance yake ba, na rasa ya zanyi" "To Ihsan ce ta ɗora mata da zaka tattara ta kai watsi da ita? Ko kuwa ba ta da haƙƙi akanka ne? Ba ruwanka da ita ba ruwanka da Abincinta ba ruwanka da komai na ta, haka akeyi, ko ita ta ɗora mata?" Wani irin takaici ya kama Imran, ita Ihsan kwananta nawa da ƙaurace masa, amma ta samu bakin kawo ƙararsa dan wulaƙanci da rashin sanin ciwon kai. "Ammi, yanzu rashin lafiyar Amira ba abun dubawa bace? Haba Ammi Amira fa mutum ce ba dabba ba, yau ko dabbace idan tana cikin halin larura zaka tausaya mata, Ammi yau ko kafiri da yafi kowa saɓon Ubangiji Allah yana son kayansa tun da ya halicce shi, ballanta na Amira da abunda take aikatawa daban abunda ake zargin ta da shi daban, kuma ko hakane abunda ake faɗar tana aikatawa, ta cancanci a tausayawa halin da take ciki Ammi, marainiya ce ki hasaso ace ba ranki ne makamancin halin da Amira ta shiga ya faru da wani daga cikin mu, haba Ammi ke fa uwace" Ya ƙarasa maganar cikin matsananciyar damuwa, ya tashi ya bar mata gidan gaba ɗaya. Gidan sa ya wuce ya tafi cike da damuwa, yana zuwa ya tarar da Ihsan ta naɗe a falo tana kallo tana cin chips. Ya je ya kashe tv ya kalleta a fusace yace "Ihsan ban taɓa tunanin rashin imaninki ya kai haka ba, kina kallon halin da abokiyar zamanki ke ciki amma ko a jikinki" A fusace ta kalleshi tace "to me kake so in muku? Ni na ɗora mata ina ruwana da abinda ya sameta kai ta shafa kai da ita, kuma hakkina ne ya kama ta, dama ƙarshen karuwa kenan, Allah ne ya tashi kamata" Imran ji yai zuciyarsa tana wani irin tafasa, yaji kamar ya shaƙo Ihsan ya kakkaryata kowa ma ya huta. Ya dage ya daidaita nutsuwarsa, kawai ya bar falon. Ta raka shi da harara tace "ai baƙi ciki yanzu ka fara, sema kaga ana ɗaɗɗaure ta, ana kai ta gidan mahaukata tukuna za kayi bayani" Ta tashi taje ta sake kunna television ta cigaba da kallonta. Washegari da asubar fari, ko sallama Imran be wa Ihsan ba ya tafi, ya koma Lagos. Abba ya dawo Kaduna, ko gida beje ba ya tafi gidan Alhaji Hashim, dan duba Amira, Sedai shima yayi mamakin ganin yadda Amiran ta koma. Yaga da gaske sam ba ta son zancen Imran, ga duhu da rama tayi. Suka tatauna da Anty, suka tsaya akan ai ta mata saukar Alqur'ani ba abunda ya gagari Allah. Imran yana gurin aiki amma hankalinsa na Kaduna kan halin da Amira ke ciki, kullum cikin addu'a yake Allah ya yaye mata abun da ke damunta. Kusan watannin Amira biyu a haka, aka samu ta dena guje guje da ƙoƙarin cire kayan jikinta, sedai ba ta Magana, dan seta wuni ba tace uffan ba. Abba ya samu Ammi da faɗa, ya nuna mata matuƙar ɓacin ransa akan rashin nuna damuwa da halin da Amira ke ciki, dan ko duba ta ba ta je ba. Ba shiri Ammi tai shirin zuwa duba Amira, saboda tijarar da ta sha a gurin Abba. Ta fuskanci yadda ran Abba ya ɓaci komai ma ze iya aikatawa, dan haka ta lallaɓa shi, ya kaita gidan Anty da daddare ta duba Amiran. Tun da su Ammi suka shiga falon, ta zubawa Ammi ido, Abinci ne a gabanta tana cakala, Anty na ta takura mata ta ci. Ammi tayi mamakin yadda cikin Amira yai girma sosai. Tunda suka shigo, Amira ta ƙurawa Ammi ido. Abba yace "Amira, ya akayi ne?" Amira ta fashe da kuka tace "Abba ka ganta ko, ta hana Imran ɗina zuwa gurina, ya dena zuwa in da nake, ya dena kulani ya tafi ya barni" tai maganar kamar ƙaramar Yarinya tana kuka. Anty tace "Amira dagaske kina son ganin Imran?" Amira ta jinjina kai tana kuka tace "bayan ya dena zuwa gurina, kuma ina son in ganshi" Abba yace "to ai ke kika ce ba kya son yazo in da kike" "Ni bance ba, ina son in Ganshi" Abba yace "Alhamdilillah, sauƙi ya fara samuwa, Allah ya krɓa mana" Ammi tace "haka dama ta koma?" Anty tace "mhmm, me zamu ce Jamila? Ai naga baki damu da halin da take ciki ba" Ammi za tai Magana aka kira Abba a waya, yana ɗagawa aka sanar da shi, Imran ya faɗi a gurin aiki, an kai shi Asibiti jininsa ya hau, baya gane wanda yake kansa ma!!! Amin afuwa ban editing ba, kuma ina cikin sabgar biki ne, ayi haƙuri. Ayshercool 07063065680 [2/22, 7:21 PM] Ayshercool:     🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                           51_52 Gaban Abba ya faɗi amma ya dake, cike da jarumta yace "ok to shikenan ba damuwa, zan kira insha Allah" Ya ajiye wayar, Amira ta kalli Abba tace "da shi kake waya ko? Ka bani in masa Magana" Abba yace "ba dashi nake magana a waya ba, wayarsa ba ta shiga amma insha Allah zan masa magana yazo da kansa ya ganki" Amira ta jinjina kai tana share hawaye. Sukai musu sallama suka tafi. Gaba ɗaya Amira ta zama ita ba me hankali ba, ita ba mahaukaciya ba, se ana zaune lafiya seta birkice gaba ɗaya ta fara sambatu. Jikin Abba gaba ɗaya a sanyaye yake, suna tafe a hanya Ammi ta kalli Abba tace "lafiya kuwa? Naga duk jikin ka a sanyaye?" Abba yace "lafiya ƙalau, kawai yanayin jikin Amira ne ya ɗagamin hankali gaba ɗaya" "To ai Addu'a za kai mata Allah ya bata lafiya, bawai ka ɗaga hankalinka ba kasan kaima ba cikakkiyar lafiya ce da kai ba" Abba yace "hakane, Allah ya bata lafiya" Haka suka tafi gida, jungun jungun kamar masu zaman makoki. Minal tana falo tana kallo suka shigo, bayan Abba ya wuce ne Minal ta kalli Ammi tace "Ammi, lafiya naga Abba a haka, me kuma ya faru?" "Mhmm ke ni duk yadda nake tunanin lamarin Yarinyar nan abun ya wuce nan, abun nata ma dai gashi nan kamar hauka ne dai ya kamata" "Hauka kuma Ammi?" "Eh hauka mana, banda haka me zesa ta dinga zabure zabure tana ihu, wai ƙadangaru take gani, hadda ƙoƙarin yin tsirara?" "Taɓɗijan kuma fa hakane, Yanzu shikenan ta haukace kenan?" "To waye yasan mata? Amma abun nata ma hadda Iskanci, daga gani na ta hau kuka wai na hana Imran zuwa gurinta, salon ta haɗamin wata kutungwilar" "Kuma dai? Anya ba ƙarya take ba tana sane take wannan abun? In ba haka ba meye dan ta ganki zata fara kuka tace kin hanshi zuwa gurinta" "Oho ita ta sani, inma gaske take inma ƙarya take ita ta shafa" "Ba fa abunda ba zata iyayi ba, kin san tsohuwar karuwa ce, ba duniyanci ko pretending ɗin da ba zata iya ba, gara ma ai hakan Ammi sa rabu salin alin kinga base kin kashe Auren ba, tunda baze zauna da Mahaukaciya ba" "Hakane, dan nima ba zan lamunta ba sam, tunda ta haukace se a raba Aure ga uban ciki tana fama ga hauka" Minal ta ɗan taɓe baki tace "Allah ya kyauta, hadda alhakin Anty Ihsan ma da suke ɗauka" Suka cigaba da hirarrakinsu. Abba kam da ya shiga ɗakinsa zama yai yayi shiru, abubuwa suka cakuɗe masa yama rasa wanne ze kama, wanne ze fara tunanin mafita a kai. Wayarsa ta fara ringing, ya ƙurawa wayar ido, yana tunanin karya ɗauka a kuma sanar masa da wani tashin hankalin. Seda ta kusa tsinkewa sannan ya sa hannu ya ɗauka ya kai kunnensa. "Assalamu alaikum" Ya amsa da "wa'alaikum salam" "Barka da dare, Abba Fa'iza ce yayar Amira" Abba yace "ok Fa'iza kina lafiya? Ya gidan naki ya yaran?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, Abba na kira layin Amira ne baya shiga, 'yan kwanakin nan idan na kirata sedai Antu ta ɗaga ko tace min tana bacci, ko kuma idan ta bawa Amiran sw inji tana Magana wani iri, tace min bata da lafiya, amma 'yan kwanakin nan na kira wayar tata sam ba'a ɗauka, na kira ta Imran shima bata tafiya sam, shine ma bugo a taka inji ko lafiya?" Abba yace "lafiya ƙalau, kin san shi Imran yana fama da wannan aikin nasu, babu isasshen lokaci, wani lokacin kuma ba lallai in da yake da service ba, ita kuma Amira ba ta da lafiya ne amma anata ƙoƙari akanta insha Allah zata warware nan kusa" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Abba meya sameta haka? Ni gaba ɗaya hankalin fa ya kasa kwanciya na rasa abunyi gaba ɗaya,jikina yana bani akwai matsala" "A'a ki kwantar da hankalinki ba wata matsala, tana Gidan Alhaji Hashim kuma matarsa tana iya yinta akanta, kin san tana da juna biyu shine yake bata wahala" Fa'iza ba dan ta yadda ba tace "To shikenan Abba, ai mata sannu dan Allah" "Za taji insha Allah mu kwana lafiya" Tace "Allah yasa" Abba kam ko bacci kasawa yayi, dan rashin sanin takamaiman halin da ɗansa ke ciki, ga Amira itama tana fama da tata larurar. Abba ya tashi yaje ya ɗauro alwala, ya tada salla ya kaiwa Allah kukansa akan iyalan sa. Allah sarki Anty, Tunda Abba ya tafi basu rintsa ba, saboda ta shiga matuƙar damuwa ganin yadda Amira ke neman ta sake rikicewa, ta hanasu bacci da koke koke, ita Imran ɗinta. Sa iya kiran hakan samun cigaba akan lafiyar ta, ko kuma sauyin salon rashin lafiyar ta ta, a baya bata son ko jin sunan Imran ɗin, amma yau ta birkice ita shi take son gani. Da fari da murna Anty ta kira wayar Imran, da niyyar yi masa albishir akan cigaban da aka samu, Amira tana nemansa tana son ganinsa, amma fafur wayar Imran taƙi shiga. Ta kira yafi sau a ƙirga amma bata shiga, Fadila ma ta kira a wayarta ammma sam ba ta shiga, ga Amira nata kuka kamar jaririyar goye. Ƙarshe Anty se allura tai mata sanna n aka samu tai bacci. Washegari Abba ya fara booking ɗin jirgin da ze tafi Lagos, ba tare da ya gayawa Ammi halin da ake ciki ba. Bayan Abba ya dawo Katsam Ihsan ta faɗowa Abba a rai, dan shi wasu lokutan ma mantawa yake da ita. Yace "Nikam ina abokiyar zaman Amira ne Ihsan?" Ammi tace "tana nan lafiya" "Taje ta duba Abokiyar zaman nata kuwa, nifa ko ɗuriyarta ba na ji" Ammi tace "eh taje ta duba ta, kasan tana zuwa service ne, shiyasa bata samun zama" Abba yace "shikenan" Washegari da sassafe ya bi jirgi ya tafi Lagos. A cikin Asibitin bariki aka kwantar da Imran, a can ya tarar da Khalid abokin Imran, da yake shine last wanda sukai waya da Imran, dan haka shi aka fara kira aka sanar masa halin da Imran yake ciki. Abba ya kaɗu da ganin halin da ɗan nasa yake ciki. Yana kwance unconcsoius, se ruwa da yake shiga jikinsa a hankali. Abba yai shiru yana cigaba da tasbihi da fatan lafiya ga 'ya'yansa. Imran yayi rama sosai, se tsawon amma duk jikin babu. Aka rubutawa Abba tasa tasan da ake son aiwa Imran. Abba yace shi Kaduna ze koma da Imran, yana da ƙwararrun likitoci da suke duba shi da iyalansa, idan abun yafi ƙarfinsu za su turasu ƙasashen waje. Khalid yace "to Yanzu Abba haka za'a ɗauke shi mu koma Kaduna?" "Eh Khalid, dole haka zamu koma Kaduna, ni bana son zaman garin nan, nayi mamakin meke damunsa haka har ta kai shi ga shiga wannan halin" Khalid yace "kasan yana cikin damuwar rashin lafiyar matarsa, munyi waya da shi ba daɗewa aka kirani aka cemin ya faɗi" "Allah ya tashi kafaɗinsa" Khalid ya amsa da Ameen. Sukai processing abun da Yakamata suka koma da Imran Kaduna. Kai tsaye aka wuce da Imran Asibiti, aka kuma rubuta masa tasa tasai, duk aka kaishi a kai masa, sedai ya nuna babu Matsala a ƙwaƙwalwarsa partial stroke ne, sedai ana ta ƙoƙarin samu aga jinin sa ya sauka. Ammi hankalinta ya tashi, ganin Abba ya fita tun farar Safiya be gayamata in da za shi ba, gashi har ƙarfe sha ɗaya na dare, be dawo ba kuma baya ɗaga wayarta. Se sha ɗaya da rabi ya dawo, yana shigowa cikin damuwa tace "Abba meyasa zaka ƙi ɗaga wayata, kuma ba ka gayamin in da ka tafi ba, duk Hankalina ya tashi" "Imran ne ba lafiya, naje na ɗakko shi ne daga Lagos, yana nan Kaduna a Asibitin doctor Nura" A gigice tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imran ɗina ba lafiya amma ka kasa gayamin? Meya sameshi haka?" "Kinga ki kwantar da hankalinki, ba wani abun tashin hankali bane, kawai dai damuwa ce ta ɗan masa yawa, amma yana samun kulawa ta mussaman" "A'a gaskiya se naje na ganshi, akan me zaka ɓoyemin kaƙi gayamin?" "A'a ba in da zaki fita, ki bari Allah ya kaimu gobe se kije ki ganshi" "To Yanzu waye ze kwana da shi?" "Khalid yana gurinsa, tare muka taho, shine ze kwana da shi" "Amma wace irin damuwa ce zata dame shi haka har ta kai shi ga shiga wannan halin?" "Ahh halin da matarsa ke ciki mana, idan ke be dameki ba ai dole shi ze dame shi, tunda yana zaune da ita tare suke kwana suke tashi, tana masa biyayya daidai gwargwado ai ta cancanci ya shiga damuwa saboda ita, yanzu da yake naki ɗan ne a kwamce ba lafiya, kalli tashin hankali ƙarara a fuskarki, kalli damuwa amma waccan da yake ba taki ba ce ba, seda nai surutu nai mita sannan ki ka je dubata, ban da tsangwama da takura da barazanar zaki sa a saketa da kike mata, duk ina sane Jamila kallon ki kawai nake yi, bata taɓa zuwa ta sameni ta cemin ga laifin ɗana ba, ko ga abunda kike zuwa kina musu ba, amma labari yana dawowa kunne na, ki ƙaddara Ba kya raye Imran yake kan gado Asibiti a kwance ba me temaka masa alhalin kina da ɗan uwa a raye, amma a barshi ba me kula da shi, kwatankwacin abunda ya faru da Amira kenan, har in koma ga Allah ba zan dena nanata matata da mu kai Aure sama da shekaru talatin da wani abu ta kasa min alfarma ba, duk da tarin Alkhairan da ni nai mata ba" Jikin Ammi ne yai sanyi, tai shiruu tana nazari, Yanzu kenan ace ba ta raye Imran ze iya shiga wani hali makamancin wannan ace bame zuwa kansa balle ya kula mata da shi? To amma ta yaya zata riƙe Yarinyar da ta gama lalacewa, bayan ga ta da ɗiya mace ita ma, idan ta koya mata Mugun hali fa? Haka tai shiru tana cigaba da tunani, ga batun Imran na kwance a gadon Asibiti ga wannan maganganun da Abba yai mata. Washegari tun da safe Ammi ta shirya, tai girki ta sanar da Minal halin da Imran ke ciki, ta kira Hadiza ma ta sanar mata, taita kiran wayar Ihsan amma ba ta shiga dan haka ta ƙyaleta. Abba a gajiye yake sosai, dan haka su Ammi ne suka fara yin gaba, yace ze zo daga baya. Cikin ikon Allah ko da suka je Asibitin suka tarar Imran ya farfaɗo, har Khalid ya kai shi yai alwala, ya Bashi Abinci ya kwanta. Ammi ta ƙarasa gaban gadon Imran da sauri, tace "Imran sannu ya jikin naka" Jinjina kai yayi alamar da sauƙi. "Kai kam Imran me kasa a ranka haka kake neman ka halaka kanka da kanka, da ƙuruciyarka amma ace jininka yai irin wannan hawan har abun ya kai ka ga faɗuwa" Shiru Imran yai ya lumshe ido be ce Komai ba, shika ɗai yasan meyake ji game da Amira, yana cikin tsananin fargaba da tashin hankali akanta, ga tausayinta da yake ji sosai, tun asalinta a wahala ta tashi, ya Aureta nan ma bata sauya zani ba, lokacin da yake ƙoƙarin ya bata farinciki iya iyarwasa kuma ga ƙaddara ta larura ta sameta, ga pressure Ammi da ta Ihsan, amma still a haka Ammi ke tambayar dalilin da yasa ya shiga damuwa. Aka dinga zuwa dubiyar Imran a Asibitin nan, wajen azahar Anty tazo duba Imran dan sam bata san Imran ba lafiya ba. Tunda Ammi taje Imran be Magana ba, sedai Anty na zuwa ya buɗe baki a hankali yace "Anty ya jikin mata ta?" Seda haushi ya kama Ammi, taji kamar ta kwaɗe shi amma ta dake ta basar. Minal kuwa sallama tai musu, ta tafi gida domin ɗora sanwar rana. Anty tace "jikinta da sauƙi Imran, ya naka jikin?" "Alhamdilillah" "Allah ya ƙara afuwa, ai se ɗazun nan Abban naka yake gayamin kana Asibiti, kuma an samu cigaba sosai a rashin lafiyar tata, tana ta tambayar ka" Murmushi Imran yai yace "yanzu tana son ganin nawa kenan?" "Ƙwarai kuwa, dan tana ta faman daru, ita ka tafi ka barta bari in kira maka ita a wayar Fadila" Ammi taxe "A'a Hajiya Nafisa, baya jin daɗi be kamata a sake ɗaga masa hankali ba" Da sauri Imran yace "A'a ni dai Anty kiramin ita" Ammi tace "a hakan kana kwancen zaka iya Magana?" "Eh Ammi, a kirata yau watana biyu rabona da ita, a kiramin ita dan Allah" Anty ta kira layin Fadila tace ta bawa Amira. Amira tana kwance tana wasa da gashin kanta, Fadila ta miƙa mata wayar. Amira ta karɓa ta kara a kunnenta, sedai shiru be ce komai ba, itama ba tace komai ba sukai shiru na wani lokaci, Imran ne ya fara sauke ajiyar zuciya, da fari Amira ba ta san waye akan wayar ba, seda taji yai ajiyar zuciya, tana jin ajiyar zuciyarsa ta fashe da kuka tace "Amran ka tafi ka barni ko" Lumshe idon sa yayi, sega hawaye na gangarowa daga idon Imran a hankali yace "Ai kece kika ce ba kya son ganina" "A'a ni bance ba, ƙadangaren jikinka ne bana son gani, amma ina son in ganka dan Allah ka dawo, mu koma gida dan Allah, na daɗe ban ganka ba" Ajiyar zuciya ya kuma yi, yana murmushi, duk da hawaye na bin gefen idonsa yace  "Nima ina son in ganki, ki bari idan na dawo daga Lagos zan zo har gidan Anty in ɗauke ki mu koma gida" Murmushi tai tace "to idan zaka dawo zan maka girki da kaina, zanje gida in wanke maka kayanka, in gyara ko ina nasan gidanmu yayi datti yanzu" A haka kamar ta fara dawowa hankalin nata, amma wani lokacin se tana cikin magana seta fara sako shirme. Imran yace "to shikenan, ki cigaba da yi mana Addu'a kinji, Sannan ki dena kuka ki dinga cin abinci sosai" "Ai ina cin Abincin, me kake yi Yanzu?" 'bacci nayi na tashi" ya bata amsa "To ka gaishemin da kowa da kowa kaji" "Suwa kenan?" "Nima ban sani ba kowama kawai kace ina gaisheshi" "Allah ya baki lafiya Amran ɗina" Tace "Ameen" Duk yadda Imran yaso dakewa kasawa yayi, ya fashe da kuka a gurin, ta tabbata dai Amira ta na da taɓun hankali, jin kukan nasa yasa Amira itama ƙara sautin nata kukan. Ammi ta fizge wayar tace "meye haka Imran kamar wani shashasha, kalli fa kuka kake yi sekace wani sakarai" Imran be kula Ammi ba, ya ɗora tafukan hannayensa biyu a fuskarsa yana cigaba da kukan. Khalid yace "Ammi, tsakanin mata da miji ai se Allah, tun daga yarintar mu ban taɓa ganin Imran yana kuka haka ba, kin san lamarin ya kai a jinjina tun da kika ga yana kuka, kiyi haƙuri amma" Anty kuwa karɓe wayarta tayi a tanta tace "ai gara da Allah ya nuna miki irin son da ɗanki yake mata, wataƙila kya ɗagawa 'yar mutane ƙafa". Tunda Amira su kai waya da Imran, take murna. Anty na dawowa tace "Anty yau munyi yawa da Imran" Anty tace "haba, ya a kai wayar tasa ta shiga?" "Fadila ce ta kirashi a waya, yace min ze zo, ya kusa dawowa azo ai min kitso" Anty tai murmushin tace "inye ka ga matar mijinta, ai dole azo a nemo me kitso kam" Amira ta dinga murna, baki ya buɗe ai Imran yace ya kusa dawowa. Kwanan Imran uku a Asibiti, cikin ikon Allah ya warware gaba ɗaya, sedai abunda ba'a rasa ba. Se Ranar da aka sallame shi, sannan Ihsan ta san ba shi da lafiya, daga wayarta harta mamanta ba ta shiga. A kiɗime Ihsan ta tafi gidan su Imran, dan hankalinta ya tashi sosai da jin wai har kwanciya yai a Asibiti, Amma abun mamakin sam Imran ya ƙi kulata, yaƙi ko kallon in da take. Ammi ta ja ta ɗaki tace "Ihsan waike wace irin sokuwar mace ce ne haka? Ace mijinki ba lafiya amma wayoyinki sam basa shiga, kina me ki kai sake ya fara san Yarinyar nan haka harda yi mata kuka?" Zare ido tayi tace "kuka kuma Ammi?" "Kuka jiya a gabana sukayi waya, hadda kukan sa saboda ita yake Wannan rashin lafiya, ke kenan kullum ba kya nan wayoyinki a kashe, gaskiya ki canza hali" Ammi tai tayi mata faɗa, bayan sun fito Ihsan tace a maida shi gida tayi jinyarsa yace baya so, ba inda za shi ta barshi a gidansu. Maman Ihsan ma da 'yan uwanta duk sun zo duba Imran, sedai sam yaƙi sauraran Ihsan, ko ƙaunar ganinta ma baya yi kwata kwata. Yana ta magiyar a kai shi yaga Amira, ko a kawota amma Ammi ta share zancen. Alhaji Hashim ya dawo gari, dan ya samu labarin rashin lafiyan Imran da na Amira, Amira ya san da rashin lafiyarta dan yazo ya tarar da ita a gida wancan Zuwan da yayi. Jin da Amira tayi ana Maganar Imran, za'aje gurinsa yasa tace itama se anje da ita. Da Anty za tace a'a, Amma Alhaji Hashim yace "je ki shirya ina nan ina jiranki, tare zamu tafi" Amira cikin murna ta tafi ɗakinta. Anty tace "Daddy, ya zakace a tafi da ita, tana ganinsa zata birkice fa" Yace "to haka zata dawwama ba zata ga mijinta ba, ai se suna haɗuwar za'a gane an samu cigaba ko kuwa? Tunda aka samu take zancensa ma ai kinga an samu cigaba, munyi magana da wani malami akan matsalar ai, na kuma yiwa shi Alhaji Alin Magana, dan haka bakomai muje da itan" Amira ta fito sanye da dogon hijjabi, a haka kamar lafiyarta ƙalau ba abunda ke damunta. Suka shiga bayan mota ita da Fadila, Anty da Alhaji Hashim kuma a gaban motar. Suna zuwa gidansu Imran ta ga kamar wani baƙon guri sukaje daban, ita dai babban burinta shine ta ga Amran ɗin ta. Suka nufi cikin gidan, suna shiga falon suka tarar da Ammi da Minal, ga Ihsan da Anty Hadiza, se Imran da ke cin Abinci. Suna shiga akan Imran ta fara sauke idanunta, kallo ɗaya tai masa ta gane ba shi da lafiya ne, ya ɗago ya kalleta ya miƙe cikin sauri yace "Amira" Kallonsa ta tsaya tana yi, kamar ba ta gane shi ba, sedai ba gane shi ne ba tai ba, a tsorace take kar ta je ta kuma ganin abunda ba ta so. Ba kunyar Komai Imran ya ƙarasa inda take yace "Amira baki gane ni bane?" Ɗan hararsa tayi tace "gani nai ka tsufa" Be bi takan mutanen da ke falon ba ya rungume Amira, yaji yadda cikinta ya tokare shi. Sedai zeyi ya yaji jikinta ya fara rawa, kan yai wani yunƙuri tuni ta suma. Jiki a sanyaye ya zauna da ita a jikinsa, yana hawaye. Ammi da Ihsan ji su kai kamar su rufe shi da duka. Alhaji Hashim ya shigo falon, suka gaisa da Su Ammmi, yaga yadda Amira ke sume a jikin Imran jikinta yana rawa yace "ka kwantar da hankalinka, munyi magana da Abbanka, Akwai makamin da ze zo ya dubata kayi haƙuri, zata warware insha Allah, ina Alhaji Alin yake?" Imran yace "yanzu ze fito insha Allah" Ihsan kuwa tayi mamakin ganin yadda cikin Amira ya girma haka, dan gaba ɗaya zatonta cikin ya zube, gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba jin ance Malami ze zo ya duba Amiran. Abba ya fito suka gaisa da Alhaji Hashim, suka cigaba da tattaunawa akan yana yin larurar Amiran. Aka kunnawa Amira karatun Alqur'ani, suna nan zaune megadi yazo ya sanar da isowar malamin. A kai masa iso ya shigo, aka gaggaisa ya kuma tambayar Imran yadda Amira ta fara Rashin lafiyar. Yasa kowa ya bar gurin, se Imran kawai da Anty se Abba, yasa aka kawo ƙaton bedsheets, aka rufe Amira da shi, Imran yana rungume da ita. Malamin ya bawa Imran tofi a jarka yace ya shafa mata a fuska, ayoyin faƙƙu sihir ne a ciki. Imran ya karɓa ya shafa mata, sannan malamin ya fara karanta Alqur'ani, sedai farawarsa ba wuya Amira ta fara miƙa, ta finga rawar sanyi kamar me jijjiga. Cikin wata irin wahalalliyar murya kamar me gudu Amira tace "dan Allah kayi haƙuri, ka ƙyaleni haka" Malamin yace "meye dalilin ka na shigar wannan baiwar Allah?" "Eh na daɗe a jikinta, na shiga jikinta saboda yanayin shigar da takeyi ne, kuma asali turani a kai jikinta, ni ke sakata raye raye da jin kiɗa, aka kuma bani aiki akan in haukata ta, nace ba zan iya ba saboda ina sonta, shine aka bawa wani jinin baƙaƙen kaji, aka rubuta sunanta da na wani aljani da sunan mijinta, a kai mata Asiri da ƙadangaren, ba danni ba da hauka za tayi sosai" Abba yace  "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Innalillahi wa innalillahi raji'un, wace irin masifa ce wannan?" Malamin yace "ba wani ba dan kai ba, Allah ne kawai ya kiyayeta, be kuma ɗora mata wahala ba, yanzu ina son kaje ka bar jikinta kuma kaje ka tone abunda kukai mata, sannan ina maka nasiha da kaji tsoron Allah, ba abunda tai maka amma ka shiga jikinta kuna cutar da ita, baka tunanin ita ma halittar Allah ce kamar kai?" "Dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba dani aka mata Asiri ba, ni dai kawai ina jikinta ne ina sa ta rashin ji, amma insha Allah yau zan bar jikinta, tunda ka ga nima musulmi ne, kuma ina son gamawa da duniya lafiya" Malamin yace "Naji, ai shiyasa zan maka adalci in ƙyaleka, saboda albarkacin musulunci, kaje abunda kai Allah ze hukunta ka, amma sonake a karya wannan sihirin sannan ka bar jikinta" "Yanzun nan ma kuwa malam, Nagode sosai da adalcin ka" Imran yace "ke tanbaye shi waye yai mata Asiri yake ƙoƙarin haukata min mata?" Malamin ya girgiza kai Yace "ka kuwa san babu halittar da ta kai aljani ƙarya, ze iya yiwa wani sharri, koma waye kawai ka barwa Allah kar kai bincike, Allah ya bata lafiya kawai" Ya cigaba da karantawa Amira Alqur'ani, amma babu wani reaction da ta kuma yi, se bacci da ya ɗauke ta. Ya bada Addu'oin da za'a bawa Amira ta dinga karantawa, da wanda za'a karanta mata a ruwa ta dinga sha, da dokoki da za'a kiyaye dan samun lafiyarta. Abba ya kawo alheri me yawan gaske ya bawa malamin, tare da yi masa godiya. Abba sun daɗe suna jimanta abunda sukaji game da Amiran. Imran kam ɗakin Minal ya kainAmira ya kwantar, ya kasa motsawa ko nan da can, ya zuba mata ido kamar wata sabuwar halitta daban. Ihsan kuwa ta cika ta batse, ganin yadda hankalin kowa ya koma kan Amira, ta kwashi jakarta tai tafiyarta daga gidan. Imran yana nan zaune kusa da Amira, ta motsa a hankali tana, ya zuba mata ido a hankali tayi miƙa tare da yin salati. Imran ya matso kusa da ita yace "My Amran ya jikin?" Ta kalli Imran tai murmushi tace "bacci nayi ne haka me nauyi?" Imran yace "eh kusan haka" "Ina su Antyn ko sun tafi sun barni?" Imran yace "kin san lokacin da kuka zo ne?" Tace "Na sani mana" "Amira baki missing ɗina ba ko?" Ya ɗan faɗa a shagwaɓe. 'ni na isa ince bana kewar ka, tsoro nake ji kar in taɓaka inji wani abun" Janyo ta yai jikinsa yace "ba abun da za kiji ai kin warke" "Wallahi tsoro nake ji" ta faɗa kamar za tai kuka. Nan Imran ya warware mata abunda yaf faru gaba ɗaya. Sosai ta fashe da kuka tana tunanin laifin me tayi wa wani haka, da za'ai mata wannan abun. Imran ya rungumeta yana ƙoƙarin kawar mata da damuwar da ta tsinci kanta a ciki. Ya kalli cikinta yace "Allah sarki yarona ya sha wuya, Allah yasa karki haifeshi da lotsatsen kai, saboda yadda ki ka dinga faɗuwa da cikin nan, Alhamdilillah yana nan be zube ba" Tai murmushi tare da shafa cikin nata. "Imran yaya ta farka ne?" Suka ji muryar Anty na nufo ɗakin, a sukwane Imran ya sakko daga kan gadon, ya gyara yace "eh ta farka" Kallo ɗaya anty tai musu ta maze tace "Alhamdilillah, Amira ya kike jin jikin naki yanzu?" "Alhamdilillah Anty" "Kin warke dai ko yanzu ba ƙadangarun?" Sunkuyar da kai Amira tai tana murmushi. Anty tace "Abba ya tura ai muku saukar Alqur'ani a gida, ki fito jama'a su ganki aji daɗi, kin samu sauƙi". Imran yace "Anty amma zamu iya tafiya gida ai ko?" "A'a seta ƙara murmurewa" A marairaice Imran yace "Anty, ina cikin damuwa sosai, sedai na barwa Allah komai amma dan Allah ki sa baki a bani Amira mu koma gida yau tunda taji sauƙi Please" "Kai amma dai ba haka naso ba gaskiya, naso ka bari muga improvement ɗin da za'a samu, amma ban san dalilinka ba, zanwa Iyayen naka Magana, daga nan kawai ku tafi" Imran yace nagode sosai Anty, Allah ya biya ki da aljanna. Ammi kamar taiwa Imran dukan tsiya haka take ji, saboda wannan rawar kan da yake akan  Amira. Kamar yadda ya buƙata, da magariba ya ɗau Amira suka tafi gida tare, dan ba kunya ya nuna yana buƙatar matarsa a tare da shi. Da suka je gidan ma, nan nan ya cigaba da yi da Amira, tamkar mata ɗaya gareshi, ko da wasan wasa be kalli sashin da Ihsan take ba. Amira ta fuskanci ko zancen Ihsan baya son ji. Bata dame shi ba itama, ta shiga hidima da mijinta, Imran kuma fafur ya hanata aikin komai, shima ya shiga lallaɓata. Duk da shima yana fama da kansa, ita ma warkewar ta kenan, amma tabbas sunyi missing juna Sosai da sosai. Tun Amira na tsoron kar wata matsalar ta sake faruwa, amma taga ba abunda yafaru, tun tana fargaba harta haƙura ta saki jikinta da shi. Imran ya dage akan kula da Amira, da Addu'oin da aka bata da sauransu, da kansa yake kaita Asibiti gurin awon ciki. Se dai tunda Amira ta koma gidan kuma take munanan mafarkai da Yadikko, ta ja bakinta tai shiru ba ta gayawa kowa ba. Tuni ta gyara wayarta, ta shiga waya da su Anty Fa'iza, da sauran abokan arziki, a ƙasa da sati guda tai ras kamar ba ita ta sha wannan wahalar ta watanni ba. Imran na zaune a falo, yana bawa Amira Abinci a baki tana ta zuba taɓararta. Ihsan ta faɗo falon kamar korarriya, Imran ko ɗaga kai be ba balle ya kalleta. Ihsan tace "wallahi Imran Allah ya isa tasakani na da kai, mugu Azzalumi kawai, abunda ka ke min se Allah ya saka min, kuma insha Allah se alhakina ya kuma kama ku, ba iya aljanu se tayi hauka tuburan ta bi bola". Amira tace "da ikon Allah ba zanyi hauka ba Ihsan, kema kuma ba zaki ba" Imran yace "Ihsan ni kike cewa Allah ya isa ko?" "Eh na faɗa, Allah ya isa azzalumi mara adalci" "Ni ban hukunta ki saboda naki halin ba, ni zaki zo kaina ki gayawa wannan miyagun maganganu haka ko? Lallai nayi ganganci na kuma godewa Allah da ya sa ban zamo daga masu butulci ga iyaye ba, Mahaifina ya zaɓa min mata ina hangen tasowar Wuta a Maƙera katsam se ga WUTA A MASAƘA, kallonki kawai nake Ihsan, na miki talala ne, akwai Ranar da dubun ki za ta cika" Be tsaya saurarata ba ya tashi ya bar falon, Amira tabi bayansa da sauri, tana ganin rashin kyautawar abunda Imran yayi. Sedai tana shiga bedroom ɗin taci karo da wayarta tana ringing. Sunan Sisto ne akam wayar, ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta, "Amira Yadikko fa babu lafiya, ita da Amina, an kasa gane kan abunda yake damun su, Yadikko na ta kiran sunanki" "Innalillahi wa innalillahi raji'un" shine abunda Amira ta faɗa ta fashe da kuka. Imran yace "ke lafiyarki kuwa?" "Yadikko ce babu lafiya, gobe in Allah ya kaimu Kano zanje" "Kano kuma, ga tsohon cikin zaki tafi Kano?" "To kana ji Yadikko ba lafiya, idan kuma ta mutu fa ban ganta ba?" Shi mamaki ne ma ya isheshi, yanzu dui da tarin abunda Yadikko tai mata, amma tana kuka saboda Yadikko ba lafiya, sosai ta birkice da koke koke. Imran yace "kwantar da hankalinki, naji da kaina ma zan kaiki, ai kinyi ƙoƙari tunda aka kawo ki Garin nan baki je gida ba" Ko bacci bata iyayi ba, da ƙyar ta iya haƙuri zuwa wayewar gari. Wajen ƙarfe goma, suka nufi hanyar Kano, Imran ya sai kayayyakin da za su je dubiyar da su, suna tafe tana kuka Imran yana kwantar mata da hankali. Se azahar suka isa Kano, suka tarar da mutane sosai a gidan su Amira, da sauri Amira ta shiga gidan, ta shiga ɗakin Yadikko, tana zuwa ta tarar da Yadikko a kwance, duk fuskarta ta kumbura suntum tayi baƙi, duk gashinta ya kaɗe ta zama kamar wata horror. Ga su Baba da Kawu duk a zazzaune suna share hawaye. Amira tace "Yadikko meya sameki haka?" Yadikko ta fashe da kuka tace "Amira dan Allah ki yafemin" Amira tace "Ni ba abunda ki kaimin Yadikko, meke damunki ne?" "Amira tun tasowarki nake cutar da rayuwarki, na kasance me biye biyen malamai, tun lokacin zamana da kakarki, bana ƙsuanarta sam, malamai suka gayamin idan kin girma zaki zama wata, shine hankalina ya ƙi kwanciya, na sa aka haɗaki da aljani, dan ki lalace amma abu ya ƙi yiwuwa, shine na dinga haɗawa da makirci ina ce miki karuwa, Auren nan da ki kai a raina yake, jikokina naso mijinki ya aura ba ke ba, da naje gidanki naga daular ki ke ciki, abun ya sake ƙuleni, shine naje nasa a kai miki Asiri da ƙadangare, gashi yanzu abun ya dawo kaina ni da Amina, tana can an kulleta tana hauka tuburan, dan Allah ki yafemin Amira!!! Domin gyar, sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680. [2/28, 6:24 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. *_Assalamu alaikum warahmatullah, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga ɗaukacin dangi na bisa ga rashi da mukayi na Kakana, ina fatan Ubangiji Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa. Ina miƙa saƙon godiya ta ga wanda suka kirani a waya, da wanda suka turamin saƙonnin ta'aziyya, na gani Nagode sosai Ubangiji Allah ya bar zumunci ya bada lada, Nagode sosai_*                            53-54 Rawa jikin Amira ya fara yi, ta matsa gefe daga kusa da Yadikko tana bin ta da ido kamar ta ga wata aba daban. Baba yace "dan Allah Amira kiyi haƙuri, ki yafewa mahaifiyata, tabbas nasan mun biye mata gurin muzgunawa rayuwarki da tsangwamar ki, wanda haka kakarki ta fuskanta daga gare mu zuwa mahaifinki da ke kanki, amma ban zaci Yadikko zata iya yi miki Aisiri haka ba, amma dan girman Allah ki yafewa Yadikko Amira" Amira kam kasa magana tayi, se fashewa da wani irin kuka na tausayin kanta, Yadikko ta cutar da ita cuta me munin gaske, ba dan Allah ya temake ta ba da yanzu tana can tana hauka. Imran da yake tsaye a bakin ƙofa ya ji komai, ya tako cikin ɗakin ya kalli Yadikko yace "da yawa abun da mu bayi ke mantawa da shi shine, ita duniyar ba matabbata bace ba, ita wadda ki kai kishin da ita yau tana ina? Shi wanda ki kai kishin akansa yana ina? Shi mahaifin Amiran shina da kika azabtar yana ina? Tunaninki ke kiyi gadin Duniyar kenan? Meye a cikin duniyar gaba ɗayanta, meye laifin da Amira tai miki a rayuwa? Ba ita ta tsarawa kanta irin ratuwar da za tai ba, Allah ne ya tsara mata dan me zaki ce se an canza? Ke da Allah dan ƙarshen cutarwa kin mata, tunda kika so haukata ta, kuma ko da Amira ta rasa hankalinta ba zan taɓa yadda in auri jikokokin ki ba, saboda na gane duk abunda kike faɗa akanta sharri ne kawai da makirci Amira ba mutuniyar banza bace, wahala ce ta maida ita haka, kuma insha Allah in har ina numfashi, Amira ba zata tagayyara ba, zan zame mata uwa uba ɗan uwa sannan kuma miji, insha Allah wahalarta ta zo ƙarshe, ba zata sake kukan maraici ba" Yana gama maganar yasa hannu ya ɗago ta tana ta uban kuka, ya janyo hannunta za su fita daga ɗakin. Baffa Salahu ya riƙe ƙafar Imran yace "dan girman Allah Imran kuyi haƙuri,  kasa baki ta yafewa Yadikko" Imran yace "wannan ba hurumi na bane, ruwanta ne ta yafe mata, ruwanta ne ta ƙyaleta, amma da kasan iya wahalar da ta sha tsayin watanni uku zuwa huɗu akan larurar da tayi ta isa Allah ya kamata, banda azabtar da ita da ku kai tun ƙuruciyarta banda yarfe da ƙage da kuka dinga mata, dan kawai marainiya ce, mahaifiyar ta ta auri mahaifinku, ni ba zan tulasta mata ba, tana da damar yin abunda ta ga shine dai-dai" Ya ja hannun Amira suka fito, Sadiya ta taho da sauri gaban su Amira tana kuka tace "Amira dan Allah ki yafemin, kar inje abun da ya samu su Yadikko nima ya sameni, dan Allah ki yafemin Amira" A fusace Amira tasa hannu ta haɗa Sadiya da jikin bango tace "duk irin azabtarwar da kukamin a gidan nan, na yi iya ƙoƙarina akan in danne zuciyata, in maida komai ba komai ba, saboda mun fito tsatso ɗaya da ku, duk ƙyama da wariya da kuka dinga nunamin, amma ban taɓa zaton zaku iya aikatamin abunda ku kai min yanzu ba, bazan yafe muku ba na barku da Allah, Allah ya bi min hakkina" Imran ya janyo Amira, dan yaga a zuciye take matuƙa kar tai masa asarar Babynsa, dan yaga yadda jikinta yake rawa, da yadda ta janyo Sadiya kamar ita kaɗai ce ba cikin a jikinta. Waje yai da ita, ya sakata a mota ya rufe ya zaga ya shiga ya kunna yaja motar. Suna tafe tana kuka, Hannu ɗaya yana tuƙi ɗaya kuma ya rungumota yana rarrashin ta yace "Haƙiƙa rayuwarki darasi ce Amira, gaba ɗaya mutane na miki kallon baibai, a yayin da idan aka duba aka zago laifin na masu aibataki ne, kinyi rayuwa a wahale ba tare da mataimaki ba se Allah, ni kaina ina Nadama akan abubuwan da suka faru a baya, amma Please and please Amira, kiyi haƙuri ina ƙara naman afuwarki a karo na babu adadi, saboda nayi zaton WUTA A MAƘERA katsam sega WUTA A MASAƘA. Amira zuciyarki me kyau ce, kina da haƙuri da yafiya, nasan an cutar dake, amma insha Allah ba zan sake bari ki zubda hawaye akan rashin wani abu ba, insha Allah zan rayu da ke da zuciya ɗaya, zan faranta miki iya gwargwadon iyawata, kiyi haƙuri ki dena kuka" Cikin kuka tace "Imran" "Na'am Amira" "Imran me na yiwa Yadikko? Laifin me nayi mata? Meyasa zata min haka? Imran duk yadda zan kwatanta maka ba zaka gane azabar da sukamin ba, why? Laifin me nayi mata haka?" Tai maganar tana sake rushewa da kuka. Parking Imran yai ya shiga share nata hawayen yace "ba abunda ki kai musu, sedai ki gode Allah ke 'yar gatan Allah ce, ya dubi zuciyar ki ya sa abunda sukai miki be tasiri akanki sosai ba ya mayar musu abunsa kansu, kuma ya ganar da mijinki abunda suke faɗa akanki ƙarya ne, ina sonki Amira son da bazan iya musalta miki ba, kuma har gobe ina jin nauyin ki akan laifin da nai miki, ki kwantar da hankalinki kinji Cwthrt, ki dena kukan nan komai ya wuce, mu koma gida mu buɗe sabon shafin rayuwa me cike da Soyayya da ƙaunar juna" "Thank you my Brother" Tai maganar tana murmushi, cikin son nunawa Imran ta gamsu da maganganun sa. Yace "Never mind Dear, me zamu tsaya mu siya kici ne nasan kin fara jin yunwa yanzu?" "Muje gidan Anty Fa'iza" ta bashi amsa. Imran ya ja mota zuwa hanyar gidan Fa'Iza, duk da haka suna tafe Amira na share hawaye, ya fuskanci zubar da hawayen shine samun sauƙinta, dan haka be cigaba da takura mata ba ya ƙyaleta. Suna zuwa gidan Fa'iza yai parking, ba ta ce masa komai ba ta buɗe motar ta fita, ta shiga gidan. Da sallama ta shiga ta tarar da Bashir yana wankin kayan su, Fa'iza kuma na Kitchen tana girki. Itama Fa'iza na ta cikin ya tsufa, dan yafi na Amira tsufa ma, da ƙyar take tafiya haihuwa ko yau ko gobe. Fa'iza na ganinta tai murmushi, tace "lallai yarinyar nan, zuwa ba sanarwa to koma bana murna da Zuwan" Bashir yace "ba ina da zata koma, duk da ni kunya ma naji, ban taɓa zuwa gidanta ba amma ina maraba da zuwan nata" Yaran Anty Fa'iza kuwa da gudu suk tafi suka rungume Amira, Amira ta rungume su, sedai ta kasa Magana. Fa'iza tace "Khairat ƙyale Amira baki ga halin da take ciki ba, kar ki buge mata kan ɗa" Duk yadda Amira ta so dakewa kasawa ta yi, ta fashe da kuka a gurin. Bashir yace "Subhanallah, Amira Lafiya kuwa? Meyafaru kuma?" Kasa magana Amira tayi, se cigaba da kukan tana daga tsaye. Fa'iza ta kama hannunta suka shiga ɗaki, tace "Amira lafiya kuwa? Ko Imran ɗin ne yai miki wani abun?" Ta girgiza kai tace "tare muke yana waje ma" Bashir yace "Amma kika barshi a waje? Amma ina fatan lafiya dai" "Anty Fa'iza, kin san rashin lafiyar da nayi aka ɓoye miki kusan taɓin hankali na samu, wata na uku ko in da nake ba na son Imran ya zo, wai ashe Yadikko ce tai min Asiri, aka kirani jiya ba ta da lafiya na tayar masa da hankali se da ya kawoni yau, shine take gayamin asiri tai min? Me nayi mata haka?" Amira tai maganar hawaye na zuba daga idonta, Fa'iza tace "Amira ki ɗauka wannan jarrabawar ki ce a haka, shekaranjiya naje gidan, da bakinta nima take gayamin ita tai miki Asiri, wanda ni ban san ma takamaiman rashin lafiyar da ki kai ba, Abba ya ɓoyemin kema da kika warkw baki gayamin ba, ance min kawai laulayi ne kike, na kaɗu matuƙa da jin abunda Yadikko ta gayamin, sedai ban miki zancen bane dan bana son tayar miki da hankali, Ba abunda za muce wa Allah se godiya da Allah yasa abun beyi tasiri akanki sosai ba" Amira tai shiruu tana cigaba da jin yadda zuciyarta ke cigba da bugawa, da zunzurutun mamakin abunda Yadikkon ta aiakata mata. Bashir ne yaiwa Imran iso, ya shigo Gidan, nan suka cigaba da tattaunawa gami da jajantawa juna akan abunda ya samu Amiran. Fa'iza tai musu girki, suka ci Abinci su kai salla, sannan suka kama hanyar komawa Kaduna, sedai suna fitowa daga unguwar su Fa'iza sega Sultan a babur ze wuce. Da sauri Amira tace "Amran tsayar min da Sultan mu gaisa dan Allah" Imran ya sha gaban hanyar da Sultan ze wuce da mota, aikuwa a fusace Sultan yace "malam meye haka? Ko dan kaga kana mota shine zaia min wannan gangancin?" Imran na sauke glass Sultan ya ganshi, gabansa ya faɗi dan be manta shaƙar da Imran ya taɓa masa ba. Imran yai murmushi ya miƙa masa hannu, a tsorace Sultan shima ya miƙa masa hannu, yana son tabbatar da ko dai ba Imran bane gizo yake masa. Imran yace "ƙanwar ka ce tace in tsaya ku gaisa" Yana gama maganar sega Amira ta fito daga motar, Sultan na ganinta ya kafe babur ɗin ya sakko yace "Gimbiya Amira kece?" "Nice Sultan, ka watasar dani gaba ɗaya" Sultan ya sosa kai yace "ke tsoron mijinki nake ji shiyasa, kuma kinga kinyi Aure be dace in dinga bibiyar ki ba" Imran ya fito daga motar yace "ka de na tuna baya, wannan ya wuce ai, kuma Amira ta gayamin dukkanin alaƙar dake tsakanin ku saɓanin ni wadda aka gayamin, kuma nagode Sosai da gudunmawar da ka bata a rayuwa, duk da ta wani fannin gudunmawar ba ta arziki bace, amma duk da haka ka temaketa, Nagode sosai, kuma ba zan yanke zumuncin da ke tsakanin ku ba, insha Allah duk ran da muka zo Kano, zan nemeka ku gaisa" Sultan yace "Alhamdilillah, Allah sarki rayuwa, inaiwa Amira burin Auren mutumin daze kula da ita, saboda wahalar rayuwa da ta sha, da fari banji daɗin Aurenka da ita va, amma yadda na ganta ya tabattar min tana cikin nutsuwa sosai, Allah ya ƙara haɗa kanku ya baku zaman lafiya" Imran yace "Ameen ya Allah, nagode Sosai Sultan" yaiwa Sultan alheri sannan suna tafi. Amira tace "meyasa ka yadda muka gaisa da Sultan, har ka masa alheri ka yadda da cigaban zumuncinmu?" Imran yace "Saboda na baki dukkanin yarda Amira, na san ko bana raye ba zaki zubar da mutuncinki ba, sannan Son da Sultan yake miki gamon jini ne kawai, ba sonki yake dan ya Aureki ba, yana sonki dan tausayin ki ne, kuma tare na ganku, dan haka be kamata in datse zumuncin ba, kuma insha Allah zan cigaba da bibiyarsa in ga ta inda zan temaki rayuwarsa, kamar yadda ya temaki taki da koya miki rashin ji" Murmushi Amira tayi da seda haƙoranta suka bayyana, a lokaci guda kuma hawaye na bin kuncinta. Imran yan cigaba rarrashin Amira, yana sake kwantar mata da hankali da bata tabbacin zeyi iyayin sa, dan ganin ta samu farincikin da bata samu a baya ba. Amira ta nisa tace "Amran, na yadda da duk abunda ka faɗamin, sedai haryanzu ina da sauran damuwa sosai" "Damuwar meye?" Ya tambaye ta. "Har yanzu Ammi ba ta ƙaunata, sannan bana son kaiwa Ihsan irin abunda kaimin nasani babu daɗi, ni idan na yafe maka ita ba lallai ta iya yafe maka ba" Haɗe rai Imran yayi yace "me nayi mata?" "Ka dena shiga sabgarta, ka dena zuwa inda take gaba ɗaya, ranar kwananta ba ka zuwa inda take sedai ka kwana a ɗaya bedroom ɗin nawa, baka cin Abincin ta, wannan abun babu daɗi sam, nasan ciwon hakan dan Allah kayi haƙuri ka koma mata, kar a shiga hakkinta, bana son Allah ya kama ka da laifin rashin adalci" Kallon Amira yai, yana jinjinawa haƙurinta, yai murmushi yace "'yar aljanna kenan, Allah ya barmin ke Amirana, kullum zuciyarki fes kamar Abba haka kike" "Naji kana neman ka maida abun jokes" "Au aljannar ce jokes Amira?" "A'a ba haka nake nufi ba, But atleast ya kamata ka ɗau maganar tawa da mahimmanci" Yace "serious na ɗau maganarki Amira, Ammi zata gane abunda takeyi kuskure ne nan ba da daɗewa ba, sedai kamar yadda kika fuskanci ƙaddara a taki rayuwar, nima Auren Ihsan ne tawa ƙaddarar" Ta kalleshi da mamaki tace "kamar yaya kenan?" Gaba ɗaya annurin fuskar Imran ya ɗauke, damuwa ta maye gurbin fuskar tasa, idanunsa su kai jawur yace "Amira a zamana da Ihsan, na mata dukkanin adalcin da zaka iya yiwa abunda kake so, kina kallo saboda ita na biye mata na kasa sauke  naki hakkin da ke kaina, sedai ina tunanin wuta a maƙera se ga WUTA A MASAƘA!" Amira tace "nifa ka sani a duhu, me kake nufi ne?" "Zaki gane very soon, but let's keep this aside, Bana son Maganar gaba ɗaya" Se bayan la'asar sosai sannan suka isa Kaduna, a part ɗin Amira suka sauka, yai ya jasu jam'i sukai sallar la'sar tare. Amira tace "My me zan ɗora maka ne, nasan kana jin yunwa yanzu" Imran ya kalleta yace "No, ba zaki wahalar min da kanki da Babyna ba, zanje in mana takeaway" Amira ta ɗan yatsina fuska tace "nifa kasan ban fiye san Abincin siyarwa ba". "Ni kuma baza'a wahalar min da mata da ɗana ba" Amira tace "masu mata da ɗa manya" Tai Maganar tana murmushi ta shafa cikin nata tace "Allah ne yayi cikin na da nisan kwana, da tuni babu shi" "Ai ba ƙaramin godiya nake wa Allah ba, ni kaina nasan ikon Allah ne ya riƙe cikin nan, ina fatan Allah ya ƙara inganta mana shi, ya rabaku lafiya" "Ameen my Amran" Haka suka cigaba da hira se daf da magariba sannan ya tashi ya fita salla, daga nan ya samo musu abunda zasu ci. Amira ta tashi gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, ta shiga banɗaki tai alwala ta fito tai sallar magariba. Tana kan daddumar da tai salla tana lazimi, taji ana kurma ihu a falo, da hanzari ta miƙe ta fito falon da sauri. Sedai me tana fitowa ta ci karo da Imran ya shaƙo Minal da hannu ɗaya yai jifa da ita, yana dukan Ihsan kamar jaka. Da saurin gaske Amira tai kansa, tana faɗin "lafiyarka kuwa? Meye haka kake matarka ce fa da ƙanwarka" Ba shi da niyyar saurarar Amira, dan tamaula kawai yake da Ihsan, Amira ta nufe shi ta riƙe shi, amma ya hankaɗeta Allah ya temake ta ta faɗa kan kujera akan hannunta, amma duk da haka seda taji ɗan cikinta ya juya. Seda ya dake su iya yinsa, tun suna ihu har suka kasa gashi Imran ya kulle ƙofar falon. Kawai ya koma gefe ya zauna akan kujera yana zub da hawaye. Amira ba tayi fushi ba ta sake jan jikinta, ta ƙarasa in da yake tace "haba dan Allah, meyasa zaka mus wannan dukan haka? Me sukayi maka? Kuma ka zauna kana kuka why? Ka sani a duhu" Imran kasa Magana yai, ya kuma kallon Ihsan baƙin ciki ya kuma mamaye masa zuciya. Ya sake tashi a fusace ya dinga takata da ƙafarsa. Amira ta firgice Sosai, ta koma part ɗinta, ta ɗau waya ta kira Abba yana ɗagawa tace "Abba dan girman Allah idan kana gari ka zo gudanmu, wallahi Imran ze kisan kai, ya sumar da Ihsan yana nema ya kashe Minal, dan Allah ka zo" Abba gaba ɗaya ya rikice yana ƙoƙarin sake tambayar ta, amma ta kashe wayar, ya miƙe a razane Ammi tace "lafiya kuwa?" "Ina fa lafiya wai Imran yana can ya sumar da Ihsan, ya shaƙe Minal" "To me sukai masa?" "Nima ban sani ba, bari inje gidan inji" Ammi tace "A'a muje dai tare inji ba'asi, in ka barni ai hankalina baze kwanta ba" Nan ta ɗakko hijjabinta suka nufi gidan Imran. Amira na katse kiran ta fito falon da sauri, amma babu alamar sassauci a tare da Imran, dan yanzu Minal yake ta gwarawa a bango. Sake gigicewa Amira tai, ta kira Anty a waya tana kuka, tace "Anty dan girman Allah idan Daddy yana nan ko wani yazo yaiwa Imran Magana, ze kisan kai wallahi" "Amira wace irin kisan kai kuma?" "Wallahi Anty ze kashe su Ihsan na kira Abba haryanzu be zo ba" Gaba ɗaya hankalin Amira ba a kwance yake ba, dan haka ba tai mata wani Bayani sosai ba, hakan yasa itama Antyn ba shiri ta nufi ɗakin Daddy ta taso shi. Gaba ɗaya Imran a gigice yake, zuciyarsa wata irin tafasa take ji yake tamkar ya kashe Ihsan ya huta. Dan Ihsan ko motsin kirki ba ta iyawa, da ƙyar take sauke numfashi, dan tasha duka, Minal kuwa bakinta se fidda jini yake. Imran ya koma gefe ya zauna ya dafe kansa, jikinsa na wata irin tsuma. Amira kam komawa gefe tayi ta zuba masa ido, tare da bin su Minal da ido, tana mamakin laifin da sukai masa haka. Suna nan zaune aka fara buga ƙofar falon, Amira ta kalli ƙofar taga a rufe take, bata san in da ya ajiye mukullin ba. Yana ji ana bugun ƙofar, amma yai banza se da ya gaji da jin bugun, sannan ya tashi jiki a sanyaye yaje buɗe ƙofar falon, Anty ce da Alhaji Hashim, Anty ta shigo tana faɗin "Imran lafiya kuwa? Meke faruwa ne haka?" Imran be ce komai ba ya wuce cikin falon ya zauna. Alhaji Hashim ya kalli inda su Minal ke baje, suna numfarfashi yace "Imran meke faruwa haka a gidanka?" Imran yai shiru be Magana ba, ana cikin haka sega su Abba sun iso gidan. Mamaki ne ya kama Ammi ta nufi inda Minal take da sauri tace "Imran meye haka? Me kai musu me sukai maka haka?" Shiru Imran yai ya zubawa Ammi ido. "Ba Magana nake maka ba? Me kayi haka? Ina fatan ba akan wannan ballagazar Yarinyar kai musu wannan abun ba?" Abba yace "Imran, kai magana mana" Imran ya share Hawaye yace 'bazan Magana ba, se an kira mahaifiyar Ihsan da wan mahaifinta tukuna" Alhaji Hashim yace "meyasa se an kirasu mu bamu isa ba?" Anty tace "bamu san meyasa yace haka ba, a kira su kawai" Haka akayi aka kira Iyayen su Ihsan, sedai lokaci lokaci Imran yana share hawaye. Gaba ɗaya abun ya ɗaure musu kai. Ba jimawa se ga Mummyn Ihsan da wan mahaifinta. Suma abun ya basu mamaki ganin yadda aka hallara haka da yawa a falon. Mummy tace "lafiya kuwa?" Anty tace "muma abunda muke son ji kenan yace se kunzo" Abba ya kalli Imran yace "to muna sauraren ka" Imran ya ƙurawa Ihsan ido sannan yace "ki gaya musu abunda ki kai min" Girgiza kai ta shiga yi tace "Imran dan Allah kayi haƙuri ka rufamin Asiri, karka tona min Asiri" "Ihsan na baki duk wata dama da zan iya, kallonki kawai nake, amma hakan be sa kin fuskanci na san me kike ciki ba, yau an kai point ɗin da ba zan iya jurewa ba, kuma ina tabattar miki daga gurin nan, zaki ƙara gaba ki barmin gida na" A gigice Ihsan ta shiga girgiza kai tace "dan Allah Imran kayi haƙuri, kar kaimin haka" A fusace Imran ya kalli Minal yace "ke  se ki gaya musu abunda ku kai" Girgiza kai Minal tayi tana kuka, amma ta kasa Magana. Abba yace "to kai ka gaya mana, mana muna jinka kuna tai mana wasa da hankali" Imran yace "Abba, lesbian na kama Matata da ƙanwata su nayi red-handed, a gadona na Aure bayan ta ƙauracemin sama da watanni, Abba matata da ƙanwata fa" Tsit kowa yayi, se tashin salati da Sallama da ke tashi a falon. Amira kuwa gani tai be dace ya musu wannan tonon Asirin haka ba, dan tun kan ya sani ta san Abunda Ihsan take, tun lokacin da suka haɗu a Abuja, ta ganta a Hotel ɗin da ta sauka, tare da wata hamshaƙiyar mace dai tai suna a dandalin sada zumunci, kuma wadda ake raɗeraɗin sana'arta kenan. Ammi tace "ƙarya kake Imran, wannan sharri ne ban yadda ba" "Ammi wace riba zan tsinta idan na musu ƙarya? Ga su nan ki tanbaye su mana, Ana zaton WUTA A MAƘERA sega WUTA A MASAƘA, wane irin cin mutuncin ne ba'ayi wa Amira ba ana ce mata Karuwa? Duk da ku Iyaye ne a gurina, amma ranar wanka ba'a ɓoyen cibi, ni na fara sanin Amira mace, ba karuwa bace, yau daga Kano muke gurin duba kakarta, duk rashin lafiyar da Amira tayi ita tai mata Asiri, kuma da bakinta take faɗar Amira ta yafe mata saboda ƙagen da ta dinga mata, Ammi ki tambayesu idan ƙarya nayi musu?" Ammi tace "Minal da gaske ne abunda yayanki yake faɗa?" Minal ta jinjina kai cikin kuka, Ammi ta ɗora hannu a ka ta fashe da kuka tana salati. Anty tace "Alhamdilillah ala kulli halin, tunda Allah ya wanke Amira, kuma ni tun zamanta a gurina na tabattar da ba karuwa bace, wannan shine abun da turawa ke cewa 'Never judge book according to it's cover' sannan Magana ta biyu Imran haƙuri za kayi, ka rufawa matarka da ƙanwarka Asiri, ka cigaba da zama da ita kayi haƙuri" Imran yace "over my dead body, i already write her divorce, bata ne kawai ban ba, ina tunanin in bata ko in yafe mata, Yarinyar nan ba kalar rashin mutunci da cin fuskar da ba tai min ba, a fari na biye mata ita da mahaifiyata na dinga muzgunawa Amira, daga baya komai ya daidaita, ita kuma ta juyan baya da wulaƙanci da cin mutunci, da fari Ihsan was not virgin, seda ga baya na gane, amma na rufa mata Asiri ban nuna mata ba, secondly na ganta da ɗinki a cikinta nace mata meya sameta, tace min an taɓa mata aikin appendicitis ne, ashe ba haka bane, mahaifa aka cire mata, amma ya Aureni a haka ban sani ba, badan mahaifina ya auramin Amira ba haka zan cigaba da zama da ita ban sani ba, likitan da yai mata aikin was a military doctor, mun haɗu a Lagos muna tare da ita, daga baya ya gayamin shine likitan da yai mata tiyatar nan, se kuma yau na kamata red handed da ƙanwata, Ihsan me nayi miki haka?" Nana aka shiga kallon kallo, aka rasa wanda ze fara Magana, da kyar Alhaji Hashim yai jarumta yace "Ihsan muna son ji daga gareki, meye gaskiyar abunda Imran ya faɗa?" Ihsan tana hawaye tace "Imran be ƙarya ba duk abunda ya faɗa hakane, bayan rasuwar mahaifina babu wanda ya damu dani da mahaifiyata, ba wanda yake kula damu, kowa ta kansa yake kawai, ana haka Mummy ta fara bin gidajen Manyan masu kuɗi tana wanke wanke, idan na tashi daga makaranta ina binta gidan aikinta, abunda ake biyanta na albashi be taka kara ya karya ba, baya isarmu buƙatunmu na rayuwa. Katsam megidan yaje mata da wani batu, yace akwai aikin da aka bashi zeyi, amma da ƙaramar Yarinya ake so kamar ni, lokacin ina da shekaru goma sha biyar, yace ze bata kuɗi naira dubu ɗari biyar, ba tunanin komai ta amince, mutumin nan ya tafi dani, ya dinga amfani da ni ta bayana, da sunan yana neman wata biyan buƙatar da bokaye sukace se yayi hakan. Nayi kuka nayi kuka akan hakan, amma dana gayawa mahaifiyata sam bata damu ba, hankalinta yana kan abunda mutumin nan yake bata ne kawai, ya canza min makaranta zuwa ta kuɗi, ya sani a Islamiyya me tsada wadda a nan na sauke Alqur'ani na haddace wani sashi, duk lokacin da ya bushi iska ze nemeni ya danƙara mana kuɗi masu yawan gaske, wasu lokutan har Abuja yake tafiya dani. A haka ana wannan haramtacciyar alaƙar matrsa bata sani ba, ita kuma ta janyo mahaifiyata tana sama mata 'yan aiki ta kaisu gidan ƙawayenta, amma a baɗini less ake dasu, itama matar gidan ta fara bibiyata tana nemana, tana kashemin maƙudan kuɗaɗe, nasan manya manyan matan da take hulɗa da su, ba abunda ban sani ba na sirrinta, gefe guda ga alaƙar dake tsakanina da mijinta, wadda bata sani ba, babu wanda ya isa yace yasan ina wannan harkar saboda a zahiri ina iya yi na inga na tsare mutuncina. Na tarawa mahaifiyata maƙudan kuɗaɗe, ta wannan ƙazamar hanyar, sedai a wannan harkar da nake, na gamu da larura wani ƙari ya fitomin a mahaifa, a yadda ba yadda za'ai da shi sedai a haɗa da mahaifata a cire, haka a kaimin aikin nan cikin sirri ba wanda ya sani. Ranar da na fara ɗora idona akan Imran naji duk duniya ba namijin da nake so sama da shi, nai aniyar tuba daga waccan mummunar rayuwa da nake yi, da taimakon Allah da mahaifiyarsa na samu soyayarsa harya Aureni. Amma a hakan sheɗan ya cigaba da ƙawatamin ƙanwarsa Minal, sedai lokacin da mukaje gidan uwaɗakina da Minal tare, ita ta rigani bayyana nata buƙatar akan Minal, kuma bamu wani sha wahala gurin shawo kan Minal ba. Tun da Imran yai watsi dani ya fara tatara hankalinsa akan Amira, ni kuma kishi yasa na koma ruwa, na cigaba da saƙa a mugun zare na, ba tare da sanin Asiri na ya daɗe da tonuwa ba, amma dan Allah Imran ka yafemin, ku rufamin Asiri. Tsit sukai suka kasa Magana, se Ammi da ta fashe da kuka hadda sheshsheƙa. Imran ya miƙe tsaye ya nufi part ɗin Ihsan, ya dawo da takadda a hannunsa ya jefawa mahaifiyar Ihsan, yace "ki tattar 'yarki ku barmin gida" Ihsan tace "dan Allah Imran kaimin afuwa, ka rufamin Asiri" Ammi tace "wallahi baze miki afuwa ba, muguwa Azzaluma kawai, kun cuceni kun ɓatamin 'ya, kun sa na tsaya ya auri Ihsan, ashe abun naku zalunci ne" Abba yace "Ai shi Allah ba Azzalumin sarki bane, yadda kika takurawa Amira, da tsana da Mugun fata, sega WUTA A MASAƘA, Yarinyar da kika ƙallafa ranki a kai, sega sakamakon ki nan, kisa a ranki wannan alhakin Amira ne, Ubangiji ya nuna miki shi shiriyar 'ya'ya ba a hannun mutum take ba, a hannun Ubangiji take" Ammi tana kuka tace "tabbas maganar ka haka take, Amira dan Allah ki yafemin, nasan na cutar dake, rashin sani ne dan Allah ki yafemin" Amira ta share hawaye tace "ni Ammi ba abunda ki kaimin, komai ya wuce" Alhaji Hashim yace "shiyasa Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace mu faɗi alkairi ko muyi shiru, shiyasa aibata mutum dan yana aikata wani laifi be kamata ka aibata shi ba, seka nemawa al'ummar musulmi shiriya gaba ɗaya, sannan kai ɗan uwan mahaifin Wannan Yarinyar ko kana da ta cewa?" Yace "A'a me kuwa zance, sedai ince Allah ya kyauta, tunda lokacin da suka ƙulla wannan sharrin ban sani ba, Allah ya kyauta kawai zance" Ihsan tana kuka, haka mahaifiyarta ta sa ta a gaba suka bar gidan. Ammi ta tashi zata sake rufe Minal da duka Abba yace "A'a ki ƙyaleta haka, kema magninki ki ɗau yadda ki bawa ƙawa, har in bana gari ki barta taje ta kwana a gidan ta, wake me ƙawa, Allah yasa hakan ya zame miki darasi" Haka suka tafi gida, Anty kuwa riƙe hannun Amira tai tace "Congratulations my dear, Allah ya wanke ki yau" Amira murmushin yaƙe kawai tayi, suka tafi gida. Ranar kusan kwana sukai Amira na rarrashin Imran, dan kuka ya dingayi sosai kamar ƙaramin Yaro, ya rungume Amira yana  "Am sorry my wife, ko yafemin Amira, nayi zaton wuta a maƙera ne, ta shammace ni ta tashi a MASAƘA, ki yafemin Amira" "Amran, mungama wannan maganar ai, ni ba abunda kai min" Ammi tayi kuka sosai da sosai, akan abunda Ihsan ta aikata mata na lalata mata 'ya. Khalid ya taɓa nuna yana son Minal, Ammi ta nuna se tayi karatu me zurfi. A satin Abba yaiwa Khalid magana, akan in dai haryanzu yana sonta suzo ayi Magana. Aikuwa Khalid jiki na tsuma ya sanar da iyayensa aka aika gidansu Minal. Sati guda da zuwan su Amira Kano, Yadikko ta rasu, sedai mutuwar ta girgiza Amira sosai, Imran yace ba inda zata ta'aziyya. Amira tace "nima bance se naje dole ba, amma na yafewa Yadikko duniya da lahira, Allah ya yafe mana gaba ɗaya" Imran ya jinjinawa haƙurin Amira da tausyi, Ammi kuwa sosai take son wanke laifukan ta a gurin Amira, dan haka mussaman take zuwa ta rakata awo, tayi mata girki tai ta bata haƙuri tana neman yafiyar ta. Da Imran ya koma Lagos kuwa, Ammi tace Lallai Amira ta koma gidanta da zama, Anty kuma tace bame ƙwace mata 'ya, da ƙyar a kai sulhu Anty ta ƙyale Amira a gidan Ammi. Sosai Minal ta dinga jin kunyar Amira, Amira kuma ta nuna mata tamkar ba abunda ya taɓa faruwa, kamar bata san Minal ta aikata wani abun ba. Da fari Ammi ta dena shiga sabgar Minal gaba ɗaya, amma Amira ta nuna mata illar yin hakan, Minal ta nemi afuwar Amira, Amma Amira tace ta manta da Wannan zancen, ta ɗauka ba wani abu da ya taɓa faruwa. Watan cikin Amira tara da kwana uku ta fara naƙuda, Ammi ta kaita Asibitin su Anty, aka karɓi haihuwar ta a can, ta haifi kyakykyawar 'yarta mace wadda ta ɗebo kamannin Ammi sosai. Washegarin haihuwar Imran ya dawo Kaduna, yai murna sosai da haihuwar, yaiwa Jaririyar huɗuba da sunan mahaifiyar Amira Fatima zahra. Haihuwar tai daidai da lokacin bikin Minal, dan haka aka haɗa bikin da Sunan. Ihsan kuwa komawa tsohuwar harkarta tayi gaba ɗaya, ta koma gurin wannan mutumin da ya fara ɓata ta, wanda ya kwaso cutar ƙanjamau itama ta samu, ƙarshe tazo kyan da take taƙama da shi ya gushe, saboda larura, kuɗin da suka tara ta wannan mummunar hanyar suka ƙare, ga rashin lafiya ga babu. Imran kam Seda Amira ta sake haihuwa, sannan ya nema mata makaranta, ta samu Admission taje tai karatun midwifery. Suka zauna cikin kwanciyar hankali da ƙaunar juna, ga zuriya da Allah ya albarkace su da ita, kuma suka shirya da uwar mijinta suka zauna lafiya, Minal ma ta Khalid yana sonta, sedai itama Allah ya jarabceta da fitinar ƙannen miji, duk da ga gida ga gida suka zauna, amma suka sata a gaba basa ƙaunarta. Zumuncin su Amira ya ɗore, ita da Fa'iza, Abba ya samawa Bashir aiki a wani babban kamfanin abokinsa a Kano, kasancewar yana da degree yayi karatu. Sultan ma ya bar sana'ar DJ, ya koma makaranta. Amina kuwa harta koma ga Allah, tana hauka tuburan, Sadiya ta samu wani me mata uku ita ta huɗu ta aura, kishiyoyi da 'ya'yan miji suka maida ita tamkar baiwa, sedai duk da abun nan da sukaiwa Amira, baya hanata temaka musu. Jajircewar Imran da gaskiyarsa akan aiki, yasa ya kai har muƙamin General na Sojoji, gefe ga kasuwancin sa yana yi, ga mace ta gari da tarin zuriya. TAMMAT BI HAMDILLAH, DUK DA NACE GAJEREN LABARI N, SE GASHI YA KAIMU IN DA BAN ZATA BA, INA FATAN AN AMFANA DA DARUSSAN DAKE CIKIN LABARIN, KUSKUREN DAKE CIKIN LABARIN KUMA INA FATAN UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA. HAR ILA YAU ƘOFATA A BUƊE TAKE DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA KO TUNTUƁENI KAI TSAYE AYSHERCOOL 07063065680 KAR KU MANTA LITYAFIN RUƊIN ƘURUCIYA SHIMA YAZO DA NASA SALON NA MUSAMMAN, DAN ZAN IYA CEWA NASA SALON YAFI WUTA A MASAƘA MA, KU HAZARTA KUYI SUBSCRIBING AKAN NAIRA 300 KACAL KAR AYI BABU KU. NAGODE ƘWARAI DA ƘAUNAR DA KUKA NUNAMIN AKAN LITTAFIN NAN. KU KASANCE DANI DON CIGABA DA SAMA MUKU DA LITTATAFAI MASU ILIMANTARWA DA FAƊAKARWA. TAKU HAR KULLUM AISHA ADAM (AYSHERCOOL) 0706306568.