[1/18, 7:57 PM] null: *✿ MUNAFUKIN MIJI ✿* Nimcyluv@Arewabooks Page 1 BRIGHT PENS🤙🏼 Free batch Ridayya tana durƙoshe dafe da turtsetsen cikinta, kwalbar fiya-fiya ɗin can waje guda wacce ta gama aunawa cikinta ita. Zufa ce take yanko wa ilahirin jikinta, tun gabɓanta na motsi da rawa har ya zamana ya saki bata da kuzari da ƙarfin qiwwar taimakawa kanta. Idanunta da suke rufe ne hawaye mai zafi ya shiga bin gefensu, wani irin zafi da raɗaɗi take ji a ƙasan zuciyarta wanda sannu a hankali yake mamaye dukkan wata tsoka ta zuciyar, bata taɓa tunanin illar da fiya-fiyar zata yi wa abinda ke cikin cikinta ba, more especially da tun ɗazo ta daina jin motsin halittar ciki. “Ya Allah!” Ta furta a ƙasan maƙoshi daidai lokacin da kumfa ta fara fita daga cikin bakinta, ta ƙara runtse Idanunta, a cikin halin rayuwa ko mutuwa take, amma hakan baya hana mummunan abubuwan data gani a zahiri gilmawa ta cikinsu, abin na zaune daram a zuciyarta wanda ko fiya-fiya ɗin data sha bai kaita zuwa kushewa ba, tabbas abin na iya kaita kabarinta hakan yasa take kokawa da zuciyarta wajan ganin ta daina bugawa da soyayyar mijinta. Ridayya bata san adadin lokacin data ɗauka kwance saman ledar tsakar ɗakinta ba, tana faman jujjuya kanta kafin numfashinta ya tsaya gabaɗaya ta daina jin sautin muryar MEER wacce kullum ta zame mata tamkar busar sarewar Algaita. "Baby kamar ƙarar ƙofa na ji fa?" Ta faɗa da ƙyar cike da tsoro, domin iya adadin zamanta a gidan Ridayya bata taɓa ganinta ko zaune kujera ɗaya da MEER ba, balle ɗaki ɗaya. Zameer ya yi shiru sai kuma ya miƙe a hankali yana gyara zaman gajeren wandonsa ya nufi ƙofar tare da buɗewa, ganin ba kowa a tsakar gidan sai hasken wutar nepa ya sanya ya zura slipper ɗinsa ya nufi ɗakin Ridayya bata cikin parlon sai ya shige uwar ɗaki kai tsaye, yana shiga ya rusketa kwance a ƙasa ta bawa ƙofa baya, ganin kamar bacci take ya sanya Zameer ɗaga kafaɗusa dukka biyun ba tare da damuwar zuwa dubawa yaga mene ya sanya ta kifa cikinta ba, mene ya sanya ta kwanta a ƙasa ba? Meer ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, yana jin fargabar data dirar masa na yayewa da alama motsin da suka ji da ƙarar ƙofar iska ce mai ƙarfi ta kaɗa tunda tsakiyar dare ne. Yana komawa ɗakin ya samu Khairiyya tsaye tana ganinsa ta matsa ta ce "Ita ce ko?" Ya yi shiru yana kallonta ta sake cewa "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Matarka ta ganmu baby" "Keee!!" Meer ya faɗa a taƙaice yana ƙanƙantar da idanunsa a kan Khairiyya kafin ya shafa sumar kansa yana yin ciki, Khairiyya ta langwaɓe ta ce "Baby ina magana kana sharewa? Ina Ridayya take? Ta gan mu tare ko?" Cikin tsawa cike da masifa ya ce "Saurara, ni kam ki saurara mini da ihu saman kai na" Ya ɗan hargitse mata nan take, Khairiyya ta yi shiru domin ta san halin Meer ciki da waje yanzu zai zama kamar Mahaukaci idan ana masa surutu akan shi. "Ka buɗe mini ƙofa na fita" Khairiyya muryarta na ɗan rawa ta faɗi maganar a lokacin na farko da tsoro haɗi da shakkar Ridayya ya saukar mata a zuciya wata matsananciyar kunyar ta, ta dirar mata ainun ba tare data shirya ba. Babu macen da zata jure ganin mijinta wanda ke shirin zama uban abinda zata haifa yana kula wasu ƴan matan, balle kuma har ta ganshi tare da wata mace a cikin gidansu na sunna, a ɗaki ɗaya, kwance gado ɗaya ko ita da kanta idan bata kashe yarinyar ba, to babu abinda zai hanata sanyata jinya wajan ganin ta illata ta. "Baby ka buɗe mini ƙofa" "Shiittt...!" Meer ya ce a kasalance yana ƙara juya mata baya, ya fahimci da gaske Khairiyya bata san tasirin da muryarta keyi a zuciyarsa ba, gashin jikinsa a mimmiƙe gudun bugun zuciyarsa ya ƙaro fiye da kima, bai san meke faruwa da shi ba, ya kuma kasa ganewa, bashi da lokacin zama ya tantance halin da yake, photon Khairiyya ne zane daram a zuciyarsa, surar jikinta ke masa yawo a cikin idanunsa. "Wallahi ba zan iya kwana gidan nan ba, matarka zata kashe ni, zata kashe ni tana mugun son ka" Sai a lokacin ya juya ya kalleta yana mata mitsi mitsi da ƴan iskan idanunsa ya ce "Tana so na, tana son abinda nake so...," Ya ɗan ya yi jim, kafin ya ce "Ki nemi guri ki kwanta, kina takura ni da ganinki a idanuna kina matsawa zuciyata!" Da rashin fahimta Khairiyya ta kalli Meer domin bata gane ainahin abinda kalaman shi suke nufi ba, ta rasa wajan da zata zuba su da zasu auna zancan ta fahimta. Kokawa yake da zuciyarsa da gaske wajan ganin ta daina dokawa da tunanin Khairy, da hana kansa juyawa ya sake ganinta a karo na babu adadi, riƙe kansa ya yi da kyau a zuciyarsa yake faɗin "Ƙarya kike, da gaske ƙarya kike Khairy baki isa na yi tunaninki ba" Tunaninta ke neman jirkita zuciyarsa dukda kasancewar ɗaki ɗaya suke, da ƙyar ya kauda wannan tare da zaro wayarsa ya shiga Internet, ƴan mata ya fara kalla sai dai yana da a ji ba ko wacce yake dannawa like ba, duk yar da ki ka kai da burge Meer. Kamar yadda ya a saba, kafin sallar subhi ya yi alwala tare da gabatar da raka'atul fjr. Tana tsaye gaban daƙin tana kiran sunan Ridayya kafin ta ga ji ta ce "Ikon Allah, duk abinda ya hana Ridayya yin ƴar tsala ba ƙarami bane, Allah ya sa lafiya take" Ta furta tana riƙe plate ɗin hannunta, har ta juya ta ji hankalinta bai kwanta ba, sunan Ridayya daya gilma ta zuciyarta ya sanyata dokawa da ƙarfi. Da sauri ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ta manta Ridayya bata taɓa bari ka shigar mata cikin uwar ɗaka amma ta shure wannan sharaɗin, was the first abinda idanun Zainaba ya gane mata, Ridayya ce yashe a ƙasa bata motsi fatar nan ta jikinta ta ƙara yin baƙiƙƙirin kumfar bakinta har yanzu fita take, a gigice Zainaba ta yar da da plate ɗin siyan ƴar tsalar tana faɗin "Innalillahi, Ridayya mai haƙuri mene ya sameki ƴar nan" Ridayya bata numfashi, gangar jiki baya magana, kunnenta sun jima da dauɗewa. Ganin da gaske Ridayya ta zama gawa ya sanya Zainaba fita da sauri tana faɗin. "Bawan Allah, mijin gidan kana ina, na ce kana ina" Shiru ba amsa! Bata damu ba domin tana da yaƙinin bai san halin da matarsa ke ciki bane, ta nufi ɗakin Zameer kai tsaye tana ɗaga labule ta tsaya ganin mace zaune a tsakiyar katifa daga ita sai short skirt, da riga ba zata huce half-vest ba. "Khary?" Ta faɗa a gigice domin ba wanda bai san cewa Khairiyya ƙanwar Meer ba ce, Khairiyya ta miƙe jiki na rawa da ɓari da ƙyarma, ta kasa cewa komai sai laɓɓanta da suke kokawa da juna Zainaba ta ce "Sannu Khairy" "Don....don....," Khairiyya ta kasa faɗar abinda take son cewa, domin ta ɗauka Zainaba ta fahimci komai, itama Zainaba shiru ta yi, ta yi amfani da tunaninta na mace mai hankali na daidai shekarunta ta gane akwai abinda ke faruwa _something is fishy...!_ Ta gyara tsaiwa ta ce "Sannu na yi miki, sannun ne bakya so Khairiyya?" Ta girgiza kai Idanunta cike da hawaye ta ce "Ridayya ta turo ki yankani ko? Ta gano cewa ni ba ƙanwar mijinta Zameer bace kamar yadda yake faɗa mata kullum? Ta gano bani da haɗi da shi ta ko'ina, ta gano ni bama ƴar asalin garin kano bace balle na zama ƙanwar Meer? Ta gane hakan da gaske ta fahimta!" Zainaba ji ta yi komai na kanta ya tsaya, ƙwaƙwalwarta kamar za ta yi hooking haka take ji, Kallon Khairiyya kawai take kamar zautacciyya kai ka ce ita akaiwa hakan. Khairy ta ce "Yanzu yanzu zan bar gidan wallahi don Allah karku mini komai.....," Zainaba ta girgiza kai ta ce "Bantan Uba kibar ina? Nan gida? To ai ko za ki fita a raye dole sai dana kasa a jikinki, za ki rasa hannu ko ƙafa" Hawayen takaici ta goge ta ce "Ke macace, watarana za ki ji baƙin cikin da kika saka Ridayya, ki yi tunani rayuwar da fasiƙa mazinaciyya a gidan aurenka matsayin ƙanwar mijinka ashe duk ƙarya ne, Allah ba zai barku ba daga ke har mijin nata" Tana faɗin hakan ta jawo ƙofar tare da saka key ta rufe Khairiyya a ciki, da sauri ta juya inda Ridayya take amfani ta yi da wayarta ta shiga ɓangaren kira, last number da aka kira shi ne _RAYUWATA_ Ta yi masa kira biyar ba amsa, daga number sai ta sister Diyya. Ƙara dubawa ta yi taga an saka Yaya Bilal, Zainaba bata tsaya jinkiri wajan dannawa Yaya Bilal kira ba, kamar wanda yake shirye na tsammanin kiran nata tana shiga ya ɗaga ta cikin wayar ya ce "Auta kiran safe haka" Shiru Zainaba ta yi muryar Bilal ta yi zaune daram a zuciyarta, wani dakakken sauti ne dake fita kamar busar Algaita a nutse ba hargowa, jin shiru ya sanya Bilal yin jim da gaske ba Auta ba ce, sam bai ji bugawar da zuciyarsa ke masa ba a duk sanda sukai kusa ko a waya ne, bai ji wannan maganaɗisun dake kwasar shi a kullum yana jirkita duniyarsa ba. Bai ce komai, don baya da zarafin cewa ɗin magana mara dalili bata tsarinsa ko waye ya kira da number Auta dole akwai dalilin kiran, sai dai ya yi imani Zameer ba zai taɓa kiran shi ba. Zainaba ta sauke ajjiyar zuciyar da take riƙe da ita tun ɗazo, kafin ta ce "Your... Your.......," Bilal ya dakatar da ita da cewa "Riƙe ƙinƙinarki, ina take?" Da ƙyar ta ce "Babu tabbacin tana raye ko babu, zahirin abinda Idanuna ke ganin Ridayya ta mutu..." Ƙit! Ta ji an kashe wayar ba tare da anjira ta kammala magana ba, ta daɗe tsaye tana sake kiran number amma ba'a ɗauka, bata san lokacin data shafe tsaye akan Ridayya ba, idanunta akan screen ɗin wayar, kamar daga sama ta ji an banko ƙofar ɗakin, Zainaba ta yi saurin yin baya bata iya gane fuskar wanda ya shigo ba, saboda ba kowa ta sani a familyn Ridayya ba, tana iya cewa this is the first time ta Idanunta yaga wannan halittar. BILAL ya tsaya fuska haɗe ganin inuwar mutum, can kuma ya saka gabaɗaya ƙarfinsa ya kinkimi Ridayya da ita, da cikin jikinta kai tsaye waje ya nufa ya sata a bayan motarsa, har zai shiga sai kuma ya tsaya ba tare daya kalli Zainaba dake tsaye ƙofar gidanta ba ya ce "Mi.. mijin nata?" Ya furta da ƙyar yana saka hannu wajan gyara lins ɗin hannunsa, sai a lokacin Zainaba ta kula da jinin dake kwance a goshinsa ta ce "Ko dana shigo gidan ban tarar da shi ba, ban san yaushe ta kasance a haka ba nima Allah ne ya nufa na zo siyan ƴar tsala a wajanta zan bawa yarinya, jin shiru na shiga ɗakinta na tarar da ita a haka, na yi ƙoƙarin kiran mijinta baya gidan sai wata dana gani a daƙinsa.." hannu Bilal ya ɗaga mata tare da shiga mota da sauri yabar unguwar, Zainaba ta riƙe haɓa ta ce "Ji ƙaddara maganar ma wahala take masa, da shi da Zameer ɗin halinsu ɗaya" Juyawa ta yi ta shiga gidanta a ranta tana jinjinawa haƙuri da irin makauniyyar soyayyar da Ridayya kewa Meer take. Bilal tuki kawai yake ba tare daya san inda yake cilla kan motar ba, yasan akan titi yake ya kuma san asibiti yake son zuwa mafi kusa da shi, maganganun Zainaba ke masa yawo a kunnensa, babu abinda ya tsaya masa irin wai ƴar tsala Ridayya take yi? Me Ridayya ta rasa? A kan soyayyar miji ta wulaƙanta kanta har haka? Ta zama abar surutu a dangi da unguwa! Yana tsaye a reception kansa a ƙasa tun ɗazo da aka shigar da ita Emergency yake kai kawo a wajan daga ƙarshe ya nemi waje ya zauna, inuwar daya gani a kansa ya sanya shi ɗaga idanuwansa akan Mami ya sauke Amma ya sauke ganinsa ya ɗan rage numfashi Amma ta ce "Uban masu gidan ya jikin na Auta? Meke faruwa ne?" Bilal couldn't speak, ya kasa magana ta sake cewa "Na cewa Abdullahi ya biyoni muje shi da Khalifa amma sun ce sun jima da cure hannunsu akan lamarin Ridayya mene ya faru da sassafe? Hajja A'isha taƙi cewa komai" Kafin Bilal ya yi magana Dr ya fito yana share zufa, ganinsa ya sanya Bilal miƙewa Likitan ya ce "Kai ne mijinta?" "Lafiya Dr? Karka ce mana Auta Ridayya ta mutu karka faɗa zaka tarwatsa zuƙata da yawa" Dr ya sake kallon Bilal ya ce "Mijinta ne kai?" Bilal dai kamar an sanya allura tare da ɗinke bakinsa, ya kasa cewa komai banda dokawa a ko wacce daƙiƙa babu abinda zuciyarsa ke yi, sunan Ridayya kaɗai na iya tarwatsa zuciyarsa, jin sunan yake kamar saukar dalma a ƙahon zuciyarsa, ya kasa sabawa da jinsa har yanzu, kalmar mutuwa ita ce ba zai taɓa lamunta ba, ba zai yarda akwai ta idan har akan Ridayya ne. "Shi ne, mijinta ne" Amma ta bawa Dr amsa, Dr ya yarda domin zufar dake goshin Bilal ta gama bayyana masa amsar tambayar shi "Follow me, _Ku biyoni_" Ya juyawa zuwa office ɗin Dr ɗin. "Mai suna mu shiga mana" Ya riƙe numfashi da sauri yana girgiza kai bata jira me zai ce ta kama hannunsa zuwa office ɗin. Dr ya kalli Bilal bayan cike cike a hankali ya ce "Kai ne mijinta da gaske?" Bilal ya sake shiru Likita ya ɗora da "Baka da Imani, baka da tausayi, baka cancanci zama mijinta ba, da gaske kai mugun miji ne" A hargitse Amma ta ce "Saurara! Aibatawar ta mece? Kake ƙoƙarin tsine masa bayan bakai cikinsa ba balle haihuwar shi?" Dr ya ce "Bana da shakka ko tsoro, ya halatta tsinuwa ta tabbata a kan shi, matarka na ɗauke da ciki amma baka taɓa bata ƙwayar magani ba? Sai takura mata ake wajan tarayya? Sexual violence? Gashi abinda ke cikinta ya ruɓe yanzu haka" Cikin tashin hankali Amma ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ɗa ya ruɓe a cikin Ridayya? Bamu da labarin bata taɓa zuwa asibiti ba" Dr ya yi murmushin takaici ya ce "Amma ke uwar miji ce ko Hajiya? Ƙiriƙiri kina ƙoƙarin danne laifin ɗanki? Wallahi da ina da iko maka shi zan a court ni kaɗai nasan halin da yarinyar ke ciki, ga ciwon yunwa daya kamata" Miƙewa Bilal ya yi yana ganin duhu a idanunsa jiri na neman yar da shi, Amma ta ce "Bilal!" Bai tsaya ba ta sake cewa "Bilal karka kuskura naga ƙafar a cikin mota balle kayi gigin yin driving" Sai a lokacin ya juya ya kalleta kafin ya ce "Ki daina mini ihu Amma ki daina na roƙe ƙi" Ficewa ya yi ta kalli Dr ta ce "Yanzu ya ake ciki?" Ya ce "An yi aikin an cire babyn, Allah ne ya yi da rayuwarta a gaba muna jiran tashin ta ne" Miƙewa ta yi ta bi bayan Bilal tana zuwa parking space na harabar asibitin motarsa na ficewa, wayarta ta ɗauka ta kira Junaid yana ɗauka ta ce "Maza duk abinda kake ka baro kasuwa kabi Bilal yana driving hankalinsa a tashe yake kuma" Junaid ya yi jim kafin ya ce "Amma ina zanga Bilal yanzu?" A tsawace ta ce "Da kyau, ya maka kyau ina faɗa kana faɗa Junaid duk abinda ya samu Bilal zaka sha mamaki" Wani mahaukacin driving yake kamar zai bar gari, yana jin yau ko zai dauwama a gidan yari a cikin biyu sai dai a yi ɗaya, ko Zameer ya kashe shi ko kuma shi Bilal ya kashe Zameer har halira, idan ya so hukuma ta kashe shi shima. #Ridha #Meer #Bilal #Junaid #Khairy #MeerRidha #ZamanAure #FreeBook #Nimcyluv #08164069385 Comment da share shi ne zai tabbatar mini da yadda kuka amshi Labarin🥰👏🏻Ina son ku, soyayyaZALLAH💋💖 Not edited👏🏻 [1/18, 7:57 PM] null: *✿ MUNAFUKIN MIJI ✿* Nimcyluv@Arewabook BRIGHT PENS🤙🏼free batch Page 2 Har wani jan hawaye ne ke kwanciya a idanun Bilal, wanda yake ƙara tabbatar da mai kallonsa halin da zuciyarsa ke ciki a bayyane, duk da haɗiye abubuwan daya zama ɗaya daga cikin ɗabi'arsa. Babu abinda yake ɗaga masa hankali irin kalmar sana'ar “Ƴar tsala" da Ridayya take Meta rasa a duniya? Ta zaɓi miji sama da komai. Ƙiitttt! Sautin ƙarar haɗuwar motoci biyun ya bayar, cikin saurin driven ɗaya motar ya riƙe nashi kan motar, da hanzari ya ɗago da nufin sauke bala'in dake cin ransa tun a hanya, wanda ya gani cikin ɗaya motar ya sanya bakinsa tsayawa a hangame sai kuma ya buɗe ya ce. "Bilal" A fili kuma da ƙarfi Junaid ya furta hakan saboda ta'ajjujin ganin Bilal gashi a tsakiyar titi amma tunaninsa da hankalinsa ya rabauta. Junaid ya zuro kansa ta gilashin motar ya ce "Bilal! Bilal!" A gigice Bilal ya dawo tunaninsa yana take motar a fili ya ce "Su.. Subuhanallahi" Ya faɗa da ƙyar, sarai; ya gane mamallakin muryar kawai ya zo masa a bazata ne, baya so, da gaske sam baya son kutse cikin lamarin shi, ya daidaita nutsuwarsa har lau bai kalli Junaid ba. "Bilal ina magana ka manshe ni banza" “Junaid zanci Ubanka, wallahi zanci Ubanka ka sake kiran ko kalmar B balle Bilal ka tsahirta mini" Tun da ya ji Bilal ya yi zagi ya san ba sauƙi, a hankali ya ce "Girman naka ne idan ka yi zagin ma babu laifi, ka sassauta ka yi parking da motar taka mu yi magana" Junaid ware idanunsa akan Bilal. Bilal ya yi shiru, domin danja ke riƙe da shi dama da tuni ya san inda dare ya yi masa "Karka ce mini akan Ridayya kake haka, ban yi zaton haka daka gareka ba, ko da kowa a mafarki ne, Ridayya dai? Uhmm!" Kammala maganar ya yi daidai da bada damar shigewa Bilal ya take giyar motarsa, da sauri Junaid ya mara masa baya, ganin da gaske ba zai daina binsa ba ya sanya Bilal juyawa ya ɗauki hanyar gida kai tsaye. Bilal na zuwa ya fita daga cikin motarsa, daidai nan Junaid ya fito yana faɗin "Don Allah ka saurare ni, Amma ta turo ni, kai ba a iya gane halin da kake ciki balle hukuncin da zaka ɗauka" Bilal ya tsaya yana ware idanunsa akan Junaid, wata kalar dokawa zuciyarsa ke masa baya ƙaunar jin maganar da duk ta shafi Ridayya. A fili ya ce "Junaid ka haife ni ne? Shayar dani ake? To; tun kafin na fasa maka baki ka saurara mini" Ya shige bayan kammala maganar, sashin Baba ƙarami ya nufa, Junaid kuma ya shige sashin su Amma. Tunani fal a ransa na abubuwan da suke faruwa a rayuwar Ridayya. Zameer tun sassafe bayan dawowa daga masallaci ya shirya tsaf cikin yadi mai laushi ya yi kyau sosai, kwarjinin da nutsuwarsa ta bayyana a fili, asalin kyansa wanda yake ƙara narkar da zuciyar Ridayya ya fiddo kansa da kansa, wani sahihin kyau ne da shi wanda sai ka nutsa zaka gani, baya da hayaniya a kame fuskarsa take koda yaushe. Yana ɗaura lins ɗin rigar Khairy ta dube shi sosai sai kuma ta ce "Meer fita zaka yi ne?" Ta furta a kasalance, wanda hakan ya yi tasirin wajan Meer, duk yadda yake kokawa da kansa wajan ganin ya gujewa kallonta haƙarsa bata cimma ruwa ba, zuciyarsa ta sanya ƙata tare da shure gargaɗin na Meer, yana riƙe kansa ba tare da zato gabaɗaya yaga idanunsa kwance akan kyakkawar fuskarta fara tas da ita, irin farin da yake so. "Kina zalunta ta Khary, Karki sa na sake aikata abinda ban shirya ba" Khairy ta juya idanunta, fusga numfashin Meer ya fara a gaggauce, ya juya mata baya. "Idan ka fita dame zan yi breakfast?" A taƙaice ya ce "Ina raguwar Indomie dana kawo miki katan guda?" Ta ce "Saura biyu, ƙwan ma haka" Yana ƙanƙance ido a wannan karan duk nacin zuciyarsa ya yi alƙawarin bazai taɓa juyawa ya kalli Khary ba "Indomie biyu Khairy bai isa ba? Ba isa ba Khairy?" Ta miƙe tsaye, daga ita sai kayan bacci. “Ba zan samwa matarka ba, Meer ina son matarka ta san wacece ni da ma'anar zamana a gidan nan, kai da kanka kasan kaf danginka babu mai suna Khairiyya" Ya girgiza kai a hankali ya ce "Ke da kika san dangin nawa, Ridayya bata sani ba" Ganin yana ƙoƙarin fita ya sa Khairy shan gabansa ta ce "Ka daina saka mini sunan matarka cikin lamarina, na ga ji da kwana zuciyata na dokawa na barazanar da zan iya samu wajan matarka, ka zaɓa kawai" Ya juya ya kalleta "Baki da hankali Khairy, zaɓa kike so na yi? Karki saka na yi abinda zuciyoyi zasu ɓaci" Yana faɗin hakan ya fice daga cikin ɗakin, bayan ya tabbatar Khairiyya ba zata buƙaci komai ba. Sanda ya fito ko ƙofar ɗakin Ridayya bai kalla, ya dai yi mamakin rashin fitowa taskar gida da ba ta yi ba, bai damu da rashin zuwa gaishe ba, haka bai damu sanin abinda ya hanata fitowa ɗin ba, ya yi wajan yana baza ƙamshin turaren shi, kamar kullum. Zameer na fita P.o.s ya ƙarasa, ya cire raguwar kuɗin daya tura a wayar Ridayya, bayan cirar kuɗin wajan mai shayi ya je, ya haɗa masa shayi da biredi da lafiyayyen ƙwai, baya son abincin waje amma bashi da zaɓi, haka ƙaddara ta zaɓa masa. Wayarsa ya ji tana ƙara ganin number Ridayya ya sanya shi sakin siririn tsaki ba tare da wani dalili ba, kira biyar akai masa duk akan idanunsa har ya kammala ya tashi, kai tsaye wajan da suke caca ya nufa maza da yawa kamar shi ke jira. "Zameer wai a haka kake son ka ciwo miliyan biyun? Baka da rabo a caca" Meer ya yi mitsi mitsi da idanu, ba tare da ya ce komai ba, yana kallon an raba ƴan wasa za a fara kartawa. "Gaza ka rabu da shi, yana wasa damu ne sai na ƙarar masa da arziƙin matarsa" AY ya faɗa yana dariya sosai "Idan bai ci miliyan biyun ba, ai ya sake ciwo mata kamar yadda ya yi a baya....," Cikin tsawa Zameer ya ce "Bana so, zan mannawa mutum hauka yanzu ko da wasa kuka sake furta haka" A.y ya ce "An bar maganar yanzu na saka dubu hamsin" Gaza ya ce "Na saka dubu hamsin nima" Zameer ya yi shiru "Kai me ka saka Meer?" "Ɗan kunnen goal" "Goal? Ina ka samu goal?" A.y ya furta da mamaki sosai. Zameer bai tanka ba, burinsa ya yi nasara a wasan ya tashi da dubu wajan ɗari biyu, wasa ya yi wasa aka cinye shi tun kafin su yi magana ya miƙa musu ɗan kunnen goal ɗin ya miƙe tsaye. Yana miƙewa Usman na zuwa da mamaki yake kallon Zameer kafin ya ce "Zameer ya mai jiki kuma?" Meer ya buɗe ido alamar rashin fahimta Usman ya ce "Ashe kuma mai ɗakinka bata ji daɗi ba, hadda suma" Wani gumi Zameer ya ji yana tsastsafowa daga goshinsa da ƙyar ya ce "Ka ce me?" Usman ya ce "Wallahi tallahi nake faɗa maka, na ɗauka daga asibiti kake ashe baka shina ba? Ai wani mutum ne mai mota kyakkawa da shi daka gani mai kuɗi ne shi ne ya ɗauketa, kumfa nata fita daga cikin bakinta, a cewar mai ɗakina" A makake Zameer ke sauraron Usman tare da kallonsa, wani irin jirkitaccen yanayin Meer yana son shigarsa da gaske, idan wanda yake zato ne yaushe ya dawo gari? Bai san irin uzurin daya bawa Usman ba, ya san dai tabbas ya yi magana sai dai baya da tabbacin abinda bakinsa ya furtawa Usman ɗin. Zameer ya yi tsaye ya rasa ta ina zai fara kashe gobarar dake shirin tunkaro shi? Bashi da ishasshen ruwan kashe ta, duk wasu gasusuwan jikinsa sai dai suka amsa yanayin da yake ciki, bashi da matsala da Ridayya, addu'ar shi Allah yasa ba wanda yasan da zaman Khairy a gidan shi. Daga wajan cacar gidansa ya shige lokacin bai samu kowa ba, sai Khairy da Zainaba ta rufeta bayan ya buɗe ƙofa Khairy ta miƙe jikinta na rawa ta ce "Mun shiga uku Zam, meke faruwa ne wai?" Ya haɗe fuska sosai ba walwala, ganin yanayinsa ya sanya Khairy nutsuwa a hankali ta ce "Mene nufinka na ajjiyeni a gidanka ba tare da sanin matarka ba? Ita ƙarya fure take bata ƴa ƴa, ramin ƙarya ƙurarre ne Zam" A zafafe ya ce "Ya isa, ya isheni Khairy, ina tunanin lokacin da zaki koma hotel da zama ya yi" Khairy ta riƙe ƙugu tare da yin shewa tana tafa hannayenta biyu "Like seriously? Ni a hotel? Wallahi yadda na faru zamana a gidanka mutuwa ce kawai zata raba ni da shi, zama daram mai naƙuda taga katifa" Bai furta komai ba, sai kansa dake faman juyawa masa. "Au yaushe akwai ɗaran bare kwanɗi? Tsoran Ridayya kake?" Ya girgiza kai a hankali ya ce "Ni ai ban taɓa ce miki ina tsoran Ridayya ba" Khairy ta ce "Oh! Son ta ka fara kenan? Tausayinta kake?" A karo na farko cikin rayuwar auren su ya ce "Bana nufin haka, ni bance ba kawai nasan ban shirya rabuwa da ita ba" Ya miƙe tsaye yana duba lokaci ya ce "Zan je gidanmu, nasan dole za su duba Ridayya, zan duba daidai lokacin da zasu fito na kira ki ya zamana zuwanki asibitin ya yi daidai da zuwansu ku shigo kamar tare ok" "Kuɗin napep?" Zameer ya dubeta yama rasa me ya sanya take son haukata shi haka kawai, ƙoƙarin shigewa jikinsa take shi kuma yana kokawa da zuciyarsa da abubuwan dake fusgarsa da gaske zuwa gare ta, fuskarsa ta shafa ta ce "Ina buƙatar ka" "Zuwa anjima" Ya furta yana mata dubu ɗayar data rage masa, ɗakin Ridayya ya nufa ya shiga dubawa cikin sa a yaga kuɗin da take ajjiyewa na tanadin haihuwarta, ya ɗauki kuɗin fuskarsa cike da nutsuwa ya duba yaga a dubu talatin da biyar ɗari takwas ne babu, hankali kwance ya fice daga gidan zuwa nasu. Har kwana biyu Bilal bai sake dawowa ko hanyar asibitin ba. Da yamma Amma na zaune idanunta akan Ridayya da bacci ya ɗauketa ta juya ta kalli Mami ta ce "Idan ki kaga Ridayya ta koma gidan mijinta ki ce ni ban haifo ba, koda hakan zai zama ajalinta" Murmushi kawai Mami ta yi bata ce komai ba, cike da baƙin ciki da kuma takaici Amma ta juya ta kalli Zainaba data zo duba Ridayya ta ce "Baiwar Allah karki faɗa mini abinda hankali ba zai iya ɗauka ba, don idan har ya tabbata haka ne sai na ɗaure shi" Zainaba ta gyara zama ta ce "Hajiya ni kaina na girgiza, bani da ƙarfin qiwwar shaida miki yarinyar ba ƴar uwar shi bace, amma ina da yaƙini zaman da suke ba mai kyau bane, tun Ridayya na amarya yarinyar take cikin gidan" Amma ta miƙe tsaye ta shiga safa da marwa, tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskarta. Zainaba gulma na cinta kamar mijinta ta ce "Allah sarki masu siyan ƴar tsala suka dinga bani saƙon gaisuwa wajanta, nina ɗauka ma haihuwa ce amma ganin kumfa na fita ta cikin bakinta ta saka jikina ya yi sanyi" Mami dai kanta na ƙasa tana duba azkar, Amma ta ce "Wacce irin kumfa kamar mai dafarar mutuwa, ita Ridayya ɗin?" Zainaba ta shafa kanta ta ce "Haka fa Hajiya, to dana shiga ɗakinta naga babu komai sai katifa na ɗauka ko sanyi ne ya kamata" A gigice Amma ta juya tare da kallon Zainaba, Mami kuma jin maganar ta yi kamar saukar ruwan sama, jikinta ya yi sanyi kamar wacce akaiwa bugun shekararriyar dawa, ta kasa ɗauke ganinta daga kan Zainaba a hankali ta juya ta kalli Ridayya dake bacci, wata kyakkawar bugawa zuciyar Mami ta yi a karo na farko, duk wani rauni na uwa mahaifiya ya fito, sai yanzu ta lura da baƙin da Ridayya ta sake yi, baƙi na fitar hayyaci ga wani ƙaton ƙashi a wuyanta, babu wata sauran ƙiba a jikinta daka ƙashi sai fata, sai siririn hancinta daya sake fitowa. Naman jikin Amma har rawa yake saboda tashin hankali ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, kina nufin duk yawan kayan ɗakin da muka kai Ridayya dasu babu? Ina suke ina suka tafi ina Ridayya takai su?" Zainaba ta ce "Nidai babu abinda na gani banda katifa ko labulan arziƙi babu" Sai yanzu hankalin Amma ya dawo kan maganar Ƴar tsala kenan Ridayya ke yin ƴar tsala? Waya ta ɗakko tana duba number kiran farko ko gaisuwa bata tsaya amsawa ba ta ce "Bilkisu ki ɗauki mota yanzu ki biya ta gidan Zuhura ku je gidan Ridayya ku duba mini kayan ɗakinta" Bilkisu ta ce "Gidan Ridayya?" "Haka na ce Bilkisu ko ba zaki iya bane?" Kamar Amma na ganinta ta girgiza kai ta ce "Ba zuwa ne ba zan yi ba, wallahi ban shirya ƙunsar takaicin Ridayya da gidanta bane, amma bari na shirya" Amma kashe kiran ta yi daidai nan Dr ya shigo ya ce "Hajiya ina mijin nata? Tunda ya kawota bai dawo ba kwana biyu kenan" Cike da ban haushi ta ce "Ba shi ne mijinta ba, Dr daman cike nake da kai ka saurara mini" Dr ya ce "Hajiya ki same ni a office" Yana faɗa ya fice daga room ɗin rai ɓace. "Dr ka sani gaba da kallo meke faruwa ne?"Dr ya jinjina kai a hankali ta ce "Ki yi haƙuri ke da Bilal, na yi magana cikin ɓacin rai" Amma ta girgiza kai ta ce "ƙara faɗar mini da gaba kake, maganarka bata gabana kai da Bilal na san yana sane da ita, Bilal ba mijin Ridayya bane, mijinta ko ƙafarsa bata shigo asibitin nan ba har yanzu" Dr ya dinga kallon Amma kana ya ce "Kenan yana sane matarsa ta sha fiya-fiya shi ne ya yi sanadiyar suman da ta yi ya ƙarasa taɓa abin cikinta, banda tana da ƙararren kwana da tuni wata maganar ake ba wannan ba, idan takunka bai ƙare a duniya ba daman sai dai kawai sha wahala, amma maganar gaskiya Hajiya Ridayya tana cikin wani hali, dole a kula da ita" Tunda ya fara magana take kallon bakinsa kamar ta fahimta kamar bata gane ba, kalmar fiya-fiya ta tsaya mata a maƙoshi, Ridayya da shan fiya-fiya? Ko kuma Zameer ya bata? Dr ya katse shirun ta hanyar faɗin "Za mu yi mata wankin ciki, violence ya yi yawa a zaman aurenta" Miƙewa Amma ta yi ba zata iya cewa ga sanda ta shigo room ɗin ba, gani kawai ta yi Junaid ya riƙeta yana faɗin "Amma lafiya? Gaggauta faɗa mana abinda ke faruwa" Girgiza kai ta yi idanunta cike da hawaye ko gabanta bata gane ta yi waje, sam bata lura da Zameer ba wanda ya shigo ba jimawa hakan kuma ya yi daidai da farkawar Ridayya. Zameer ya matsa dab da Ridayya yana daidaita nutsuwarsa, a hankali take binsa da kallo kamar mai son gano gaskiyar da yake ɓoye a zuciyarsa? Ta runtse Idanunta lokacin data tuna maganar Mardiyya, ko a mafarki ba zata taɓa yarda Zameer zai ci amanar so da ƙauna, haɗi da yardar da take masa ba. Magana take son yi ta gagara sai wani hawaye mai zafi daya shiga fito mata. Zameer ya kama hannunta duka biyun ya ɗora a saitin zuciyarsa daidai inda take doka masa yana sarƙe numfashi zuciyarsa na tsukewa tare da curewa waje guda, ya rasa inda zai lalubo abinda babu shi ko kaɗan a zuciyarsa wanda zai nunawa Ridayya a hankali ya ce "Karki nisa dani Mai sona" Ta girgiza masa kai da ƙyar ta ce "Idan har na yarda ba zaka ci amanata ba meyasa zan yi nisa da kai?" Meer ya sauke numfashin da yake ta riƙe a nutse ya ce "Zuwana na biyar kenan kina bacci, kin bani tsoro, idan kin barni ke kan ki ba zaki iya rayuwa ba" Wani sanyi da nutsuwa Ridayya ta ji yana sauke a zuciyarsa, ciwon da ƙirjinta ke mata yana yayewa wani irin yardar Zameer ya ƙara ninkuwa fiye da ƙima a ranta. "Ka siyar da ɗan kunnen?" Ya yi shiru ta saka hannunta mai lafiya ta juyo da fuskarsa zuwa gare ta ta ce "Mene?" A taƙaice ya ce "Kunyarki nake Ridha, da kunya na ce miki ɗan kunnen goal ɗin ki ya faɗi" murmushi mai kyau ta yi wanda ke ƙara fiddo ramarta ta ce "Haba dani da kayana duk mallakina ne Rayuwata, daman kai zan bawa kuɗin ka siya mana kayan abinci da iccen wanka sbd haihuwa kuma kaga yadda Allah ya yi" Ya jinjina kai "Kamar kin san ina buƙatar kuɗi" Ta yi saurin buɗe ido ta ce "Me zaka yi da kuɗin?" Ya marairaice fuska yana sumbatar hannunta a hankali yake ɗan sauya yanayi ya ce "Mai sona kike tambayata me zan da kuɗi, sbd kulawa dake matata" Ai Ridayya duk duniya ji ta yi ba macen da tafi ta zarra da samun miji kamar Zameer "Ka duba ɗakina ƙasan filo akwai kuɗi" Da sauri ya fara girgiza mata kai ya ce "Haba idan na ɗauka ke kuma fa Mai sona?" Ta haɗe fuska ta ce "Ka fini buƙata,kuma ina yin dashi da ribar ƴar tsala na kusa ɗauka" Ya yi murmushi ya ce “I love you mai sona” "Kai" Suka ji an furta Gabaɗaya suka juya Bilal ne tsaye bakin ƙofa cikin waganbari da ya yi masa kyau hannunsa zube cikin aljihu, idanunsa akan Zameer ya ce "Zo ka fita" Zameer ya ce "Matsayinka nawa?" "Na wan matarka" Zameer ya miƙe tsaye idanunsa akan Ridayya ya ce "Ridayya kina gani, ƴan uwanki baza su taɓa barina dake ba, kullum cikin jure wulaƙancin su nake saboda kawai ina son ki, sau nawa ina zuwa suna hanani shigowa wajanki?" Zameer ya girgiza kai yana ƙoƙarin ganin ya bayyana rauninsa a fili yadda Ridayya zata gasgata maganar shi ya ce "Cewa sukai ni na ɗora miki fiya-fiya wai don na kashe ki, Ridayya na san lokacin da kika sha fiya-fiya, tun safe na fita ina fafutukar ganin na rufa mana asiri na riƙe ki da kyau amma basa gani, ɓaraho suke son na zama? Ko ɗan fashi da makami? Me ya sa Ridayya me na yi ƴan uwanki?" Ridayya jikinta ya fara rawa, Junaid mamakin munafurcin Zameer ya kashe shi a tsaye kamar wata mace? Bilal ya ce "Ka fita, ka zo ka fice daga room ɗin nan" "Ba zan fita ba, wajan matata na zo" Bilal yana zuwa ya ɗauke Zameer da mari, har ya ɗaga hannu zai rama sai kuma ya fasa ganin yadda Ridayya ta runtse Idanunta. Bilal ya ce "Idan kai baka san darajar rayuwar Ridayya ba kamarwa wanda ya san darajarta" Zameer ya ce "Ok kana nufin na saketa ka aura? Aure zaka kashe mata ashe" Junaid ya san da gayya Zameer yaƙi rama dukan, sbd idanun Ridayya banda hakan sai dai su daki juna. Bilal ya dunƙule hannu ya kaiwa bakin Zameer naushi da ƙarfi ya ce "YES! I do love her, I love her ka saketa idan ka haifo" “Bilal!!" Ridayya ta kira sunan Yaa Bilal, wanda hakan ya yi daidai shigowar su Bilkisu da Zuhura, Amma, Mami da Baba ƙarami, sai Khairy da Mama da Karimatu. Babu wanda bai girgiza da jin sunan Bilal gatsal a bakin Ridayya ba, domin har Baba ƙarami baya iya cewa Bilal sbd darajarsa da suke gani kaf dangin shi ne babba. "RIDAYYA!" Mami ta kira sunanta, ta nufeta zata daketa Baba ƙarami ya ce "Karki fara Fatima, ba kiga mijinta ake duka ba?" Amma ta ce "Babu yadda za a yi Uban masu gida ya daki mijinta ba dalili kasan halinsa ba komai yake damunsa ba, yarinya ta fifita miji akan kowa?" Bilal ji ya yi idanunsa na neman ɗaukewa, baya son yarda Ridayya ce ta furta wannan sunan daga bakin da yake jinsa har rai da mutuwa, wani baƙin ciki ya wanzu a zuciyarsa ƙirjinsa ya yi masa nauyi. Cikin rashin sani ya sake dunƙule hannu ya kaiwa Zameer naushi nan take bakinsa ya fashe, wani irin Miskilin Meer ya yi. A gigice ta fisge ƙarin ruwan, jini ya fara zuba sam bata damu da hakan ba, idanunta cike da wutar son mijinta.. "BILAL!" Ta kira sunan Yaa Bilal ta ce "Mijina kake duka kamar ɓarawo haka? Da gaske mijina kake duka? Daman kai kake hana shi zuwa gidanmu?" Da mamaki gabaɗaya mutanen wajan ke kallon Ridayya Bilal ya ce "RIDAYYA! Sunana kike kira haka...," "Na faɗa BILAL, ba haka ne sunanka ba? Bana ƙaunarka kamar yadda baka ƙaunar mijina, ba zan kai ka ƙara ba, Allah ya isa dukan mijina da ka yi...," Wani mugun mari Junaid ya kai mata ya ce "Banza, akan wannan mijin? Daman ni na sallamaki duk wata damuwarki is never be my headache" Ridayya ta fashe da kuka ta ce "Ko namana zaku yayyenka wallahi ina ƙaunar mijina, ina ƙaunar shi fiye daku" Mami kallon ƴarta take tana jin wani takaici na rufeta yanzu abin tsoro yake bata, anya Ridayya lafiya take? Bata haukace ba, Zuhura murmushin ɓacin rai take wacce irin soyayya ce mai hana ganin laifi yaushe Ridayya zata yarda Meer ba ƙaunarta yake ba? Amma ta kalli kowa idanunta ya sauka akan Khairy sai kuma ta juya ta kalli Bilal da jiri ke neman kada shi ta kalli Ridayya data riƙe hannun Meer a fili ta ce "Komai ya zo ƙarshe In sha Allah a yanzu ba sai anjima ko gobe ba Zameer zai saki Ridayya ba saki ɗaya ba saki uku muke buƙatar ya yi mata yanzu!..... #Ridayya #Meer #RiyyaBilal #Khairy #Amma #Soyyaya #Saki #Dangi #Nimcyluv #08164069385 Free book ne karanta ki yi comment please bani da group👏🏼👏🏼🥰🥰 [1/18, 7:58 PM] null: *MUNAFUKIN MIJI* Nimcyluv@Arewabooks Page 3 BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Ridayya ji ta yi ciwon da zuciyarta ke yi mata ya dawo sabu fil, cikin wani irin rikitaccen tashin hankali daya gama mamaye ilahirin lungu da saƙo na ƙofofin halittar ƙirjinta, wacce take ƙara kissima mata soyayyar Zameer a kullum. "Kada ki nemi kashe ni da rai na Amma, kada ki ce zaki hukata ni ta hanyar da zuciya, gangar jikina ba za su ɗauka ba" Ganin amma taƙi yar da ta kalleta, ya saka Ridayya sakinta tare da juyawa ta kalli Zameer dake tsaye, idanunsa cike da hawayen daya gama ƙirƙirar su a wajan ta ce "Kalamanki kamar fitar dalma haka suke sauka a ƙirjina Amma, rabani da mijina kamar bayyanar ranar mutuwata ce, wallahi duk duniya ba wanda nake so sama da Zameer idan ki ka cire Mami, ina ji a jikina bayan bautar Ubangiji; Allah ya halicce ni domin na rayu da soyayyar Meer, me ya sa kuke ƙoƙarin kashe ni da rai na? Bayan ina numfashi? Kuna kallona na faɗa muku ina son shi mene ribarku idan kun rabani da shi" Ridayya ta ƙare maganar tana jan numfashi a wahale, komai nata ya yi tsayiyuwar sojojin da suke tsaka da fareti. Murmushin baƙin ciki da kuma takaicin halin Ridayya Junaid ya yi, duk yadda ya tursasa zuciyarsa wajan ganin bata ɓaci ba, a kan haukan da Ridayya ke yi musu a cikin asibiti abin yaci tura. "Makauniyyar soyayya ko? Ridayya anya ba ki haukace ba? Kin san kalaman da bakinki suke furtawa Amma? Ko giyar wake kika sha kin yi tsararo ki sauke mana ita a nan, ramin da kika haƙa kin yi kaɗan ki faɗa ciki da mu, sai dai ki kwashi turɓayar data rufe miki ƙofifin zuciyarki ki rufe kan ki da ita wallahi" A hargitse Junaid yake maganar kamar zai kai mata dukan ɓarin makauniyya. Baki Ridha ta buɗe, a ƙoƙarinta na son fayyace musu irin so da ƙaunar da Zameer yake mata, amma sun sanya audiga mai kauri tare da toshe kunnuwansu, tilas baza su saurari kukan nata ba, balle surutanta wanda suke musu kama dana sabon kamo. "Yaa Junaid wall...," Wani mahagon mari aka ɗauke Ridayya da shi, daga bahagon hannun daya jima bai duka ba. Mami ta rasa me zata furta akan Ridayya, da gaske duk wata kalma da zata yi futar mashi daga cikin bakinta ba za ta yi kyau ba, abin ba zai haifar da ɗa mai ido ba, bata so yin mummunan kalamai akan Ridayya, domin yin haka na nufin ƙara lalacewarta, tabbatacce ne kaifin bakin uwa akan yaranta. “Ridayya!!” Ta kasa faɗin abinda ta yi niyya, cikin hanzari kamar tafiyar hadari a saman gajimare ta fice daga cikin room ɗin. Amma ta juya ta kalli Baba ƙarami dake tsaye yana nazarin yanayin da Bilal ke ciki, wanda kalaman Ridayya suka jefa zuciyarsa cike take ɗauke da rufaffen kuma ɓoyayyen sirrin da yaƙi bawa kowa damar fahimta, sai yanzu da a nutse da kuma idanun basira daya saka Baba ƙarami yake wassafowa yana gina shi a tubali ma'ana. "Ridayya ki ƙaddara silar mutuwar aurenki zai saka ki haɗiye zuciya ki mace, wallahi sai Zameer ya sakeki a yanzu...," "Assha! Assha ban so ki ka rantse ba, ina jiye miki kaffara musamman ta azumi" Baba ƙarami ya tari numfashin Amma da hakan. Ta rusuna a ladabce cikin girmamawa ta ce "Ka yi mini haƙuri da afuwa kada ka dakatar da ƙudirana na ceton Ridayya daga duhun rijiyar data zama shekararriya, karka hana ni ina son kawo ƙarshen alaƙar dake tsakanin su biyun" Baba ƙarami ya girgiza kai a hankali kuma ya nemi saman kujera tare da zaunawa akai, ya jima da fahimtar idan aka biyewa mata maimakon a gyara ɗaya sai goma ta ɓaci. Bilal zufar dake yankowa a saman goshinsa yake saka hannu a hankali tare da sharewa, dokawa zuciyarsa take da wani irin sabon sauti da bai taɓa jin irinsa ba a tattare da shi. Ya saba da bugun luguden da take masa a ko wacce da ƙika dake tafiya, ta dalilin tunanin Ridayya, al'amarin da ya gama addabar rayuwarsa ta kowacce siga. Sunanta kaɗai yana sawa halittar gashin dake kwance a saman fatarsa mimmiƙewa, tsigar jikinsa na tashi ƙirjinsa na dokawa da ƙarfin da yake kasa fitar da numfashi. A yanzu ma haka ɗinne Bilal kokawa yake da zuciyarsa wajan ganin bai juya ya kalli Ridayya da yanayin da take ciki ba, baya fatan ace hawaye ne suke fita daga kwarmin idanunta, ba zai jure ba, da gaske ba zai jure yanayin da take ciki ba. Juyawa ya yi da nufin barin ɗakin jinyar dake cikin asibiti jiri na kwasarshi kasancewar yana da kyakkawan jiki a buɗe ya saka hakan bai faru ba. "Babban mutum" Baba ƙarami ya kira Bilal, kiran daya dakatar da shi daga ficewa, yana tsaye inda yake. "Dawo ka zauna" Ya bashi umarni kai tsaye. Bilal gwada taurin kansa ne baya so, surutu da idanun jama'a na ƙarasa kassara masa ƙarfin qwiwarsa. A nutse ya nemi waje can gefe ya tsaya baya jin zaman komai na wajan gundirarsa yake, Junaid ma ya tsaya kusa da Bilal. Baba ƙarami ya kalli Ridayya dake durƙoshe hawaye yaƙi tsaya mata ya ce "Auta dawo kan gandonki kin ji" Ta miƙe da sauri Zameer ya matsa cikin son nunawa kulawa da tsantsar soyayya ya kama hannun Ridayya a bayyane yake cewa. "Sorry AMOIR, ina tare dake ina so da ƙaunarki" Ya faɗa a fili a hankali daidai kunnenta ya ce "Ina son zamanki a gidana, ko babu komai gida da mutum kuma mace Rahama ne" Nutsuwa ya shiga saukarwa Ridha a zuciya ta san idan aka raba auren Zameer ba zai taɓa jurewa ba, ba zai iya zama da ko wacce mace ba bayan ita. Bayan kowa ya zauna, Amma, Mami data shigo, Balkisu da Zuhura sai ƴan'uwan Meer mama da Karimatu da Khairy wacce ke tsaye idanunta akan Bilal. "Bamu da hujjar kashewa yarinya aure babu dalili, babu da zarafin aikata wannan ɗanyen aikin da gaske" Cewar Baba ƙarami. Amma ta buɗe baki zata yi magana ya yi saurin dakatar da ita da faɗin "Ki bani dama na yiwa Ridayya tambayoyi waɗanda amsoshinsu da su zan kafa hujjar raba auren" Ya juya kan Ridayya ya ce. "Auta ki ji tsoron Allah ki faɗa mini gaskiya, idan kin mini ƙarya Ubangiji yana gani ba zai barki ba" Gabaɗaya jikinta ya yi sanyi kamar kazar da ƙwai ya fashewa, ta jinjina kanta alamar “To” Baba ƙarami ya kalli Ridayya da kyau ya ce "Ridayya kina samun abincin da za kici a gidan Zameer? Safe, rana, dare?" Daram! Dam! Zuciyarta ta bada sautin fashewar tayar mota. Rabonta da cin abinci sau uku a rana tun satin amarcinta, ko abinci ta samu tana haƙura ta bawa Zameer ita tasha ruwa, tun tana ciwon ciki har lalurar ya zame mata jiki. Da wanne harshe za ta yi amfani da shi wajan kare kanta? Tasan waye Baba ƙarami mutum ne mai tsayawa akan ra'ayinsa kaifi ɗaya ne shi, gabaɗaya inuwarsa halayyarsa take bi zubin nagartarsu ɗaya da Bilal. "Ridayya!" D sauri ta ce "Na'am Abba" Ya haɗe fuska "Bani da cikakken lokacin jiranki bani amsata" Zameer ya buɗe baki da nufin cewa wani abu Baba ƙarami ya dakatar da shi ya ce "Tsahirta mini tukunna" Ridayya ta share duka gaskiyar data gino akai tsayin shekaru tasan a'a yana nufin mutuwar aurenta da Zameer wanda bata ƙaunar haka, ko ƙasa zata dinga kwaɓawa tana ci don yunwa ta aminta ta rayuwa da shi. "Abba Zameer bai taɓa hanani abinci ba, kullum cikin faɗan bana son abinci yake mini ma, kafin ya ƙare ya ajjiye wani" Ba ita da ta yi ƙaryar ba, hatta shi da kansa Zameer ya jijjiga ya ɗago kai yana kallonta a ransa yake furta. "Munafuka, maƙaryaciyya ko kwanan shinkafa ban taɓa ajjiyewa ba balle buhu, yunwa duk ta cinyeta ta ƙara mata duhun fata kamar kalwa" Baba ƙarami ya aminta, domin bai taɓa ji ko ganin ta zo neman abinci ko ta ce babu ba, bata taɓa cewa a bata kuɗi ba. Ridayya tasan Bilal zai rufa mata asiri, ba zai taɓa ƙaryata kalamanta ba, baya sati bai tura mata kuɗi a cikin account ba. "Ina kayan ɗakinki suke? Mene ya haɗaki da sana'ar ƴar tsala?" Kai tsaye ta ce "Abba gobara mukai kayan suka ƙone da ƙyar na tsira da sauran, ƴar tsala kuma ina sha'awar sana'a shi ne dalili" "Ƙarya kike, ɗakinki bai yi kama da inda akai gobara ba, balle tashin wutar ya cinye furnitures ɗinki" Bilkisu ta ce "Gaskiya kam, tsaf ɗakin yake inda akai gobara daban suke" Ridayya ta ɗago kai ta kalli yayyin nata kafin ta ce "Na siyar, bana buƙatar su ne" Zuhura ta ce "Kin siyar ko mijinki ya siyar Ridayya?" Ƙirjin Ridayya ya fara ɗagawa ta fara gani bibbiyu, hawaye na bin kuncinta ita sam ba taga dalilin da zai saka a dole a sanya bakin almakashi wajan datse halataccen aurenta da masoyinta ba. "Ya isa, tambayar ƙarshe mene ya haɗaki da shan fiya-fiya? Ba kuma shan gangan ba, shane da nufin kashe kai a huta da rayuwar duniya, mene hujja? Duk soyayyar ce?" Ta yi shiru domin ta fara fita daga cikin hayyacinta, hankalin Zameer yana kan Khairy da yaga ta zubawa Bilal Idanu, hankali tashe duk da dauriyar da yake son yi yake binta da kallo, ina dalilin bin Bilal da wannan kallon? Junaid kuma idanunsa akan Zameer yana ganin yadda yake bin Khairy da kallo. "Abba magani na ajjiye a irin kwalbar fiya-fiya ɗin, na gama cin abinci zan sha tsautsayi da ƙaddara ya saka na ɗauki kwalbar fiya-fiya ɗin. Abba don Allah karka tambayi wanne magani ne me ya sa kuka tsane ni saboda ina son mijina? Kai ma tsanata za ka yi?" Zuhura ta yi kan Ridayya zata daka Zameer ya yi saurin shiga tsakiya ya riƙe Ridayya ya ce "Sai dai ki dakeni, me ta yi muku? Saboda kawai na kasance mijinta? Saboda bata son wanda kuke so ai nasan cewa Bilal son ta yake shi ne hujjarku ta raba aurenmu" Zameer ya faɗa cike da munafurci. Baba ƙarami ya ce "Saketa ta zauna likita na zuwa, yau za a yi komai a gama idan har Bilal na son Ridayya tabbas na yi farin ciki, amma son bai masa rana ba, ya riga da YA YI SAKE, idan kuma na tabbatar yana sonta to a yanzu zaka saki Ridayya tunda babu idda a kanta shi kuma a yanzu zan ɗaura masa aure da ita" Wani ihu da kururuwa Ridayya ta yi kamar mahaukaciya ta ce "Wallahi bana son shi, bana ƙaunarsa Allah zan iya kashesa idan kuka yi gigin rabani da Zameer, ko mijina zai dinga yankar naman jikina yana ci na yar da zan zauna da shi har mutuwa, zan yi nisa daku zan manta daku mijina shi kaɗai ya Isheni rayuwa ban damu da kowa da komai ba, ba abinci, ba suttura, ba magani idan ba komai idan ƙasa ce zata zama abincina,ko duka zai dinga lakaɗa mini ba ruwanku zan zauna da Zameer amma ban taɓa ƙaunar Bilal ba" Kamar mahaukaciya haka Ridayya ta zama, ta mance cewa a gaban Baba ƙarami take wanda shi ne mahaifin Bilal, ko mutuwa tana jin kunyar idon mahaifi balle Ɗan'adam. "Yau na tabbatar Ridayya baki da hankali, ke da bakinki kike furta kalmar tsana ga Bilal? Kin mata halaccinsa ko? Banda shi da kuma darajarsa da baki isa kin auri Zameer ba, shi ne ya yi uwa tare da makarɓiyya ya tsaya miki" Bilkisu ce ke maganar wacce ke zaune ta nuna Ridayya da hannu tamkar zata kai mata duka. Cikin ƙarin wani ɓacin ran Bilkisu ta ɗora da faɗin. "Kalar naki halaccin kenan? Irin godiyar da zaki masa kenan? Ba shakka" Muryar Ridayya na rawa ta ce "Ku kashe ni kawai idan hakan zai faranta ranku, don Allah wallahi da a rabani da Zameer gwara ni na kashe kai na" Gabaɗaya kallonta suke da wani irin mamaki, razani da rashin hankali. A karo na biyu Ridayya ta kalli inda Bilal yake, cikin sa a suka haɗa Idanu. Wata tsinkewar gaba ce ta gitta ta zuciyarta, kaifin idanunsa ya sanya ta ji zuciyarta na bugawa, jikinta ya ɗauki ɓari na abubuwan da take ji a duk sanda ta kalli idanun Bilal, dukkan wata halitta dake jikinta sai data amsa yanayin da Ridayya ke ciki, wanda kallon Bilal ya haifar mata. Yana mata wani irin kwarjini ko motsinsa ta ji gabanta faɗuwa yake ba tare da sanin dalilin hakan ba, tsigar jikinta duk sun mimmiƙe suna amsa yanayin maikama da ji da motsin buƙatar abu daga gare shi. Cikin sauri ta ce "Asstagafirullah!" A nutse Bilal ya juya tare da ficewa, sai a lokacin Junaid ya ce "Wace kuma waccan?" Meer ya kasa ɗago kansa kai tsaye ya fahimci Khairy Junaid ke magana wacce ta bi Bilal da kallo da zai shige. "Tare muke" Kai tsaye Meer ya furta hakan ba tsoro, duk basu kawo komai ba, ganin ƴan'uwan Meer ɗin suna wajan sai hakan ya shaida musu Khairy wata ce a familyn nasu. Fita sukai daga cikin room ɗin aka bar Zameer da Ridayya wacce take cikin tsananin ciwo, tun bayan fitarsu yake chatting da ƴan mata. Saƙon Khairy ne ya shigo. "Ka gaggauta fitowa,ina buƙatar ganinka" Ya cilla wayar cikin aljihu tare da miƙewa tsaye. Ridayya ta ce "Ba dai tafiya zaka yi ba?" Ya dubeta ransa na ɓaci ya ce. "To bari na tsaya na goyaki" Ta saki baki, yanzu akan idanunsa kowa na danginta ya saka ƙafa ya fice ya barsu tunda shi ta zaɓa. "Idan ka tafi wa zai kula dani? Kana ganin babu kowa?" Ya saki tsaki cikin ɗaga murya ya ce "Karki takura ni...," Ko me ya tuna sai ya yi shiru a hankali a taushashe ya ce "Mai sona idan na zauna a nan ƴan uwanki zasu ɗauka da gaske zaman banza nake, dole na fita na kawo miki abincin dare da kuɗin siyan magani" Nutsuwa ce ta saukar mata, ta yi imani kafin samun miji irin Zameer abu ne mai wahala ta ce "Na fahimta RAYUWATA, Allah ya kiyaye ka dawo mu kwana tare" Ya mutsa fuska Zameer ya yi yana juyawa Ridayya ta ce "I love you Rayuwata" Ko a kwalar rigarsa haka kalaman nata ya jisu, har ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce "A inama kuɗin suke?" Ta maimaita ya fice abinsa.. Har ƙarfe biyu na dare babu labarin Zameer, Ridayya ta ci kuka sosai ganin tana shirin mutuwa babu wanda ya dawo a gidansu hakan bai dameta ba, addu'a take Allah ya sanya Zameer lafiya yake shirun ya yi yawa. A karo na takwas ta sake kiran number shi cikin sa a aka ɗauka a hankali ta ce. "Rayuwata!" Wani irin tsalle da bugun casar gero cikin turmi haka zuciyarta ta yi, ihu da surutan Zameer ne ya cika kunnenta, da wani irin sauti can ƙasa wanda kai tsaye ba zata iya fahimtar kalar shi ba. "Rayuwata! Meer!". Maimakon ya bata amsa sai saukar wata murya ta ji a kunnenta ana cewa. "Ka yi a hankali, kar a jiyo muryarka, ban saba ba wannan shi ne yi na na farko... #Ridha #Bilal #Meer #Baba ƙarami #Murya #Dare #ZamanAure #Nimcyluv Free book ne a ko'ina ka karanta ka yi comment da share. Wattpad domin ku ake posting, comment ake buƙata da vote. [1/18, 7:59 PM] null: *⁦✿ MUNAFUKIN MIJI⁦ ✿* Nimcyluv@Arewabooks BRIGHT PENS🤙🏼free batch Page 4 *BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🏼 *CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_ Tsari👯🏻‍♀️ Duk page ɗaya 200 Duka littafin kuma 600 Shafi biyar a littafi ɗaya 1000 A littafai uku kuma 3000 Domin ƙarfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙🏼👯🏻‍♀️🫶🫶🏼 Ridayya ta ɗauka kunnenta ne ya sa mu matsala, cikin sauri ta zame wayar daga jikinta tare da saka hannu ta shiga bubbuga kunnen a fili ta ce "Babu mamaki ruwa ne ya shiga ciki, ya toshe ƴar ƙofar ɗaukan sautin har take naɗo mini masifa da bala'i" Ta mayar da wayar a hankali duk da ƙirjinta dake bugawa da muryarta ke rawa bai hana ta tattaro jarumta kamar jinin Iliya ɗan mai-ƙarfi ba ta ce "Rayuwata, ni ce matarka Ridayya ka na ji na?" Ta yi maganar cike da ƙarfafawa kanta qiwwa, da share gurɓataccen zaton da zuciyarta ta yi mata akan Zameer. Shiru babu amsa sai wayar data fara shuuuu!! Kamar kammalawa shirin gidan rediyo ya yin rufewa, da yin ban kwana da masu sauraro. "Asstagafirullah! Allah na tuba ka yafe mini, daman nasan sharrin shaiɗanne kawai yake son kissima mini wani mummunan zato akan Meer" Ta yi shiru; tana sauraran bugun zuciyarta da take mata, kamar luguden gidan biki. Duk yadda idanunta ya su runtsawa da samawa kanta nutsuwa al'amarin ya gagara, bacci ya ƙaurace wa idanunta. "Allah ya gani ina so da ƙaunar mijina, Yaa B ka yi haƙuri ba yin kai na ba ne, bana jin zan iya rayuwa ba tare da Zameer kusa dani ba" Hawaye ya shiga zuba daga kwarmin idanunta, zuciyarta na tsananta bugawa ki manin daƙiƙar gudun lokaci. Da ƙyar bacci ya ɗauketa gab da asuba, ba wani na kirki ta yi ba ta ji ƙarar wayarta alamar shigowar saƙon karta kwana, cikin ganɗoki ta ɗauka zuciyarta na faɗa mata Meer ganin wanda ba ta yi zato ba ya saka ta ƙura wa saƙon Idanu. Alert ɗin kuɗi ne, sai gajeren saƙo daya biyo bayan alert ɗin. Ridayya ta rufe idanunta, da gaske tana buƙatar taimako, daga na kuɗi har na kulawa, tana buƙatar sharing damuwarta da wanda zai fuskance ta, wanda zai kyautata mata zato akan soyayyar Zameer ba wanda zai dinga ganin laifinta ba. Ta zubawa sunan Bilal idanu, wanne irin abu za ta yi masa wanda zai tsane ta? Tsana mai muni ya dinga ganin baƙin ta kamar yar da a yanzu take ganin nasa? Kuɗi ne kimanin dubu hamsin ya tura mata zuwa asusun bakinta, yasan da gaske tana buƙatar su. "Yaa Bilal why? Me ya sa? Bana ƙaunar ka, na tsane ka gwargwadon tsanar da ka yi wa mijina, ba kai ba duk wanda zai wulaƙanta Zameer a duniyar nan ko waye zai i ya wulaƙan ta shi..." Ta yi maganar a fili kuma a raunace, sunan Yaa Bilal data ambata yana mata amsa kuwwa! A cikin kunnenta, bugun zuciyarta na ƙaru wa duk a dalilin jin sunan Bilal ɗin ya fita a bakinta. Har aka gama sallah tana nan a zaune, da ƙyar ta yunƙura zuwa banɗakin dake cikin ɗakin asibitin. Shiru ba kowa sai ita, ga aikin da akai mata, ga gubar fiya-fiya data sha, ga damuwar zuciya wacce take tunanin babu wanda ya haddasa mata irin danginta. Mijinta bai rage ta da komai ba. Nas ce ta buɗe ƙofa hannunta ɗauke da kayan duba mara lafiya, ta tsaya gaban Ridayya tana mata tambayoyi da ƙyar take buɗe baki wajan amsa mata har ta kammala. "Can i ask you dear?" Ridayya ta kalli Nas sai ta jinjina mata kai alamar "Why not?" "Thank you" A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana kallon Ridayya dake matar da shekarunta a haife zata haifi Ridayya a nutsu ta ce. "Tunda nutsatstan magidancin nan ya kawo ki asibiti na fahimta a kwai damuwa a tattare dake, na ji tamkar ƴata Safiya ce a cikin condition ɗin da kike ciki, ƴa ƴa na kowa ne bawa sai mai shi. Zan so ki buɗe zuciyarki ki aminta dani ba zan cutar dake ba, ki faɗa mini mene damuwarki please, i just feel your pain" Kan Ridayya a ƙasa ta kasa cewa komai saboda yar da ba ta jin daɗin al'amarin da yake riskar ta a yanzu. "Ki yar da dani, mene dalilin shan fiya-fiyan da kikai? Ba rashin sani bane yunƙurin kashe kai da kai kikai ɗiyata, na karanci damuwar dake shimfiɗe a fuskarki what's going on? Waye shi? Su kuma su waye? Kyakkawan namijin nan waye?" "Shawara kika zo bani, ko kin shirya faɗa mini mugun abu game da lafiyata? Ko kina son sanar dani mijina na cutata kema" Ridayya ta faɗa tana mai kallon Nas ɗin da raunatacciyar muryarta. Nas ta kama hannun Ridayya ta ce "Ta ya ya zan aibata miki miji ba tare da sanin ya zamanku yake ba? Ai mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo, rumfar kara ragayar mai shi" Ridayya ta jinjina kai a ranta ta samu nutsuwa da nurse ɗin a taushashe ta ce "Wanda ya kawo ni asibitin nan zan iya ce miki ubana ne...," "Uba kuma?" Nas ta dakatar da Ridayya da faɗin haka. Ridayya ta ce "E, Abbiey na ne" Nas Hajjara kallon Ridayya take da mamaki kuma ta kasa fahimtar abinda take faɗa ko dai bata gane wanda take nufi ba ne? "Mamaki ko? Bana ƙarya, ban san yadda ake yinta ba, mutum ɗaya ne ya taɓa sani yin ƙarya a duniya, yanzu kuma na zama shaharriyar maƙaryaciyya" "Ba mamaki bane, abu ne mai kama da almara kin gane wanda nake magana akan shi ƴar nan?" Murmushin takaici Ridayya ta yi da kanta ta san ba ta yi wa Yaa Bilal adalci da halacci ba, ta yi ƙasa da kanta saboda harbar da gefen kanta ya yi a hankali cikin raunatacciyar muryarta ta ce "Uhm" "Wani fari zubin buzaye? Mai girman jiki, wani mara fara'a da rashin son magana sosai, wani mai yawan dafe kai? Wani mai tsayi da kuma faɗi...," Da sauri Nas Hajjara ta ce "Lallai ba shakka shi nake nufi, waye shi a wajanki? Domin na ɗauka shi ne mijinki sanda ya kawo ki asibitin hankalinsa a tashe ko takalmi babu a ƙafar shi, waye wannan ɗin?" "Babana, Abbiey na" "Ikon Allah, bai yi kama da babanki ba, amma mene yake faruwa tsakaninki da shi da kuma sauran?" "Long story, _labari mai tsayi_* Ridayya ta faɗa a taƙaice domin ta fara jin hirar na hawar mata ka, yunwa take ji ga damuwa da ta yi mata ƙatutu a zuciya ki numfashi da ƙyar take haɗiya. "Ƴar nan zan so jin labarinki da yar da akai kika auri wannan mijin naki wanda ke shirin salwantar da rayuwarki" A gigice Ridayya ta ɗago rinannun idanunta da suka gama jirkicewa sai kuma ta saki dariya kamar mai taɓin hankali, ta girgiza kai ta ce "Ko a mugwayen mafarkan da nake yi a kullum, bana fata da gaske bana fata na yi mafarkin rayuwata ta baya, babu komai cikinta babu kowa a wancan rayuwar sai Abbiey ba kowa cikinta, da rayuwar baya data yanzu maja ce, mizaninsu ɗaya, rayuwata a jirkice take a baibai take na shiga uku ni Ridayya....," Kukan da bata samu damar yinsa lokacin da idanunta ya yi mata mummunan gani a ɗakin Zameer shi ne take yinsa a yanzu, shi kansa kuka rahama ne rashin yi tauye zuciya da abinda ke cikinta yake. Bata son tuna komai, amma abun kamar an yi masa wahayi sai gilmawa ta idanunta yake tamkar majigi. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangijn ka tausaya mini ka sa na farka naga bacci nake, wacce irin rayuwa nake ciki ne? Shin daman haka aure yake? Ko wacce mace kalar baƙin cikin da take ɗanɗana kenan ko ni ɗaya ce, daman da ake cewa aure ɗan haƙuri ne hakan shi ne haƙurin?" Sosai Ridayya ke kuka tana buga kanta da ƙarfen gadon jikinta na karkarwa, duk wanda ya ganta dole ya tausaya mata ita kaɗai tasan abinda take haɗiya, damuwar aure na son haukatar da ita shekarunta sun yi kaɗan, ƙwaƙwalwarta ta gaza ɗauka. "Mene laifina don zuciyata ta so wanda take ganin shi daidai da ita? Mene laifina don gangar jikina ta so rayuwa da wanda take ganin shi ne mahaɗin rayuwarta, bangon da zan jinkina na ji daɗi? Me ya sa bangon ke shirin yar dani ƙasa ya ruftu mini aka? Me ya sa na kasa yar da ko gasgata abubuwa da yake mini? Idan ko wanne bawa da ƙaddarar shi tabbas tawa ƙaddarar ta _SO!_ ce, lissafin ƙaddarata _ZAMEER_ ne, Allah kar ka hukunta ni da zunubaina baya na tuba Allah na tuba kar ka hukuntani na yi ladama" Nas Hajjara ta rirriƙe Ridayya da jini ke zuba a saman goshinta ta ce. "Babu ƙarya a lafuzzanki da gaske So jarabta ne kuma ƙaddara ne, da so kawai Ubangiji yaga dama sai ya hukunta bawansa da shi, aure ibada ne, kuma ko wacce mace a duniya haƙuri take a gidan mijinta, duk wacce zata fito ta ce miki zama lafiya ne wani abun ba a ɗauke kai a yi haƙuri ki ce mata na ce ƙarya take, domin ko tsakanin harshe da haƙori ana saɓa wa" Nas ta kwantar da Ridayya wacce ta gama fita hayyacinta ta ce "Wallahi tallahi da na ganki na ɗauka tsohuwa ce, kin wani ranƙwafa idanu ƙwala-ƙwala ga baki da ya yi tsayi ƙashi kamar zan ajjiye jarkar ruwa, babbar matsalar yaran yanzu basa bambance SO da BIRGEWA, ƙuruciya da tashan balaga ne kawai ke ɗibansu da tsinanniyar zumar soyayyar nan ta samarin yanzu da take hurewa yaranmu kunne, yarinya ta na ce akan yaro bayan bata da tabbaci idan son gaskiya take masa" Faɗa sosai Nas Hajjara take yi kamar zata ari baki, burinta a yanzu bai shige ta ji labarin Ridayya ba da yar da akai ta auri Zameer mene alaƙarta da Yaa Bilal wanda ta bawa sunan Abbiey? "Who knows the truth? _Only God knows!_" Ta tambayata ta bawa kanta amsa. _Waye ya san gaskiya? Ubangiji ne kaɗai ya sani_. Kasancewar a file ɗin Ridayya akwai information nata da number wayar Bilal data Zameer. A kusan lokaci guda aka kira su. Zameer na zaune bayan ya kammala karyawa lafiyayyar Indomie ya ci da ta ji kifin gwangwani ya haɗa shayi mai kauri shi da Khairy. Duk a cikin kuɗin da Ridayya ta ce ya ɗauka. Khairy dake kwance kanta a cinyarsa wandon ball ɗinsa na jikinta ba ko riga ta kifa cikinta ta ce "Baby ba kiranka ake ba?" Zameer ya yi jim ganin sabuwar number sai kawai ya share, aka ƙara kira rai ɓace ya ɗaga. "Muna kira daga nan asibiti, muna magana da Zameer ne mijin Ridayya Bilal Mansur Rano?" "Nine ya akai?" Daga cikin wayar aka ce "Muna buƙatar ganinka a emergency sashin gaggawa, matarka na cikin halin suma an kasa shawo kan lamarin....," Ƙit! Zameer ya kashe wayar can ya ja tsaki ya ce "To ina ruwana? Nina na ɗora mata ciwon ne mace sai laulayi komai ciwo kamar ni zan bata lafiya, mayya kamar dangin tattabara ko soyayyar Layler da majnun ba wata nasara mutuwa ce kema haka za ki yi ni kam ba haukacewar da zan yi" Shi kansa Zameer bai san mene ya same shi a yanzu ba, haka kurum ya samu kansa da yin faɗa can Khairy ta ce "Ka tashi ka je mana matarka ce fa" a fusace ya ce "Nikam bana so da gaske bana so ki daina yi mini shisshigi Khairy" Khairiyya ta juya baya tana gwalo sai kuma ta dawo ta marairaice fuskarta fara tas farin da Zameer ke mugun ƙauna ta ce "Matarka ce hakƙinta na kanta...," "Zan yafa miki yatsu a fuska Khairy da gaske zan sauke mini hannuna" A hargitse yake gabaɗaya, ya ture kanta ya miƙe domin ko wanka bai samu damar yi ba balle ya tsarkake najasar yana zuwa baƙin ƙofa ya ce. "Why Khairy me ya sa?" Da rashin fahimta ta ce "Mekenan kake magana?" A hankali ya ce "You, both of you are different, difference sweetness and tasty" kafin Khairy ta yi magana Meer ya fice daga cikin ɗakin. Tunani ta shiga yi mene bambancin me kuma ita da wa, Khairy ta kasa fahimta domin bai bata wata ƙofa da zata hasko abinda yake nufi ba, a hankali ta gyara zamanta jikinta duk ciwo yake mata wannan shi ne karonta na farko. Zameer na fita ɗakin Ridayya ya shiga ya zauna tare da yin shiru, tunani fal zuciyarsa wanda tunda yake bai taɓa zama ya yi akan Ridayya ba, kenan mata sun bambanta, kamar yar da a kamanni suka kowa da nashi? Me ya sa bai samu yar da yake so a wajan Khairiyya ba? Duk irin jiran rana da lokacin da kuma shirin da ya yi wa ranar, baya ƙaunar baƙar fuskar Ridayya ko kaɗan baƙar mace bata tsarin rayuwarsa hasalima idan yaga baƙar mace zuciyarsa tashi take, shi ya sa bai damu da zama kusa da Ridayya ba ko kallon fuskarta ba, but he lost his mind idan ya raɓeta, sai ya ji shi Allhamdulillah! Ba yar da ya zaci baƙar mace ba. Babban damuwar Zameer a yanzu ko rabin matakin Ridayya Khairiyya bata ɗauka ba a wannan ɓangaren, ya zacci yadda fuskarta ke da haske kamar hasken farin wata ɗan goma sha biyar haka sai samu nutsuwa a wajanta. A hankali ya miƙe tsaye ya shiga safa da marwa can ya ce "Me hakan ke nufi?" Kyan fuskar na banza ne? Munin shi ne abin so ganin ya gaza sanya ko wanne a mizani ya fice daga cikin gidan a ransa yana ayyana Allah ya sa ya samu nasara a caca ya ciwo miliyan biyun nan. Duk suna zaune a madaidaicin parlon gidan suna jiran shigowar Baba ƙarami tunda Abban sama baya nan ya je can Rano. Balkisu ta ce "Yanzu babu mai zuwa duba Ridayya a asibiti?" Zuhura ta ja siririn tsaki da zuwanta gidan kenan ta ce "Uwar me za a yi mata? Akan Idanunki ta ci mutuncinmu ta zaɓi mijinta fiye da dangi" "Yaya Zuhura hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, naka shi ne naka jininka wuya za shi, gobarar data kunno a gidan Ridayya muke da ruwan kashe mata ita, dole ace ita jininmu ce dole a ce ita ƙanwarmu ce, ko babu komai akwai hakƙinta akanmu na zumunci....," A fusace Amma ta ce "To uwar ƴan farsafa da tsara zance kamar wata marubuciya, daman da ɗan jarida da marubuci gindin ɗaya suke, muddin Ridayya bata ji tausayin kanta ba babu mai jin tausayinta, ni kai na ba kuga me ta yi mini ba?" A hankali Balkisu ta ce "Ki yi haƙuri Amma, Allah ya kiyaye" "Na gaba, domin wannan ya riga daya faru Balkisu ki raba kan ki da shiga shara ba shanu, yau ko yayyanka namanta wancan ɗan iskan marainin yaron zai yi ba mai hanawa" Bakinsu ta ce "Allah ya rufa asiri, Allah ya sauƙaƙa mata daman bakina kun riga kun yi wa aurenta tun kafin a yi ai" Balkisu na faɗin haka ta ja bakinta ta rufe ta fara danna wayarta. Duk abinda ake Mami na zaune ita da Zainura ba wanda ya tanka ƙasan zuciyarta ba abinda yake banda zafi. A hankali kowa ya dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya, Junaid, Aliyu, Usman, Umar sai Abubakar. Amma da Mami da Yaya Zuhura, Balkisu da Zainura sai Baba ƙarami mahaifin Bilal, baban Ridayya mijin su Amma daman baya gari ya je can asalinsu Rano. A hankali Baba ƙarami ya kalli kowa can ya ce "Bilal fa?" Aliyu dake zaune ya ce "Banga Ustaz ba yau gabaɗaya" Baba ƙarami ya juya da nufin tambayar Junaid don shi yake ɗan samun kusanci da Bilal kafin ya yi magana Junaid ya ce "Banga Ustaz ba Baba ƙarami, ni kam tun jiya idan har akan maganar Ridayya ne ai ina tunanin ba wani meeting ta zaɓi abinda ya kamata da ita ne" "Yaya Junaid Ridayya yarinya ce gabaɗaya bata rufe sha bakwai ba girma ne ba hankali da ruɗun ƙuruciya, idan mutum na matakin adolescence babu abinda ba zai iya ba, ko wanne bawa da kalar nashi ƙaddarar...," "Na bi adolescence da gudu ba wando, zan watsa miki tafi a nan wajan Balkisu, ina cewa gata duk muka je nema mata amma ta shafa wa idanunta kwallin rashin kunya ta baɗa masa ƙasa a idanu, idan na tuna abinda ta yi wa Ustaz kamar na zunduma ihu haka na ke ji ni da kai na kunyar haɗa idanu nake da shi" Balkisu ta ce "Ba haka nake nufi ba Yaya Junaid, abinda Ridayya ta yi bata kyauta ba amma ba tsana zamu nuna mata ba, ba zamu guje ta ba, tana buƙatar nutsuwa a kuma jata a jiki, ina cewa kaima akwai naka zanen ƙaddarar saboda matsalar Genotype har yanzu ba ka yi aure ba, duk wacce ka samu da sunan mata ana yin gwaji za a ga Genotype ɗinku bai yi daidai ba" Ganin abin na neman zama wani daban ya sa Baba ƙarami kiran Bilal a waya ya ce yana buƙatar ganinsa cikin gaggawa ya umarci kowa ta shigo. Sallamar Ustaz ya sa suka kalle shi baƙin wagambari ne a jikinsa, sai wata ƴar ƙaramar riga kamar top da wacce akaiwa aiki a jiki ya ɗora hula akan shi, ɗaya hannun rigar a tattare ga audiga a jiki gabaɗaya ya fi kowa girma a wajan hakan yasa ya yi kwarjini sosai. Kansa a ƙasa yana dafe kai saboda jiri jinin da aka ɗiba a jikinsa yasa jiri ke kwasar shi. Ya nemi waje ya zaune ya harɗe ƙafa da ƙaramin carbi a hannunsa can ya juya ya ce "Sannu Abba, gani" Yana faɗa ya yi shiru. "Na ganka, Ina ka shiga Ustaz?" Junaid ya ce "Baba ƙarami ba ina Ustaz ya shiga ba, cewa za ka yi me ya sameka Ustaz kalli hannunsa, jininka aka ɗauka?" Shi dai Bilal bai tanka kowa ba a ransa yake jin dole ya ci uban Junaid yaga raini na son shiga tsakaninsu. "To Allahamdulillah, yau zan ƙare magana ƙare kuma amsar ka shi ne zai kawo ƙarshen komai Ustaz muddin ka ce kana son Ridayya zan maka Zameer a kotu ya saketa na aura maka ita, shin da gaske kamar yar da Junaid ya faɗa kana son Ridayya?" "Shi ne kiran Abba?" Baba ƙarami ya ce "E, bani amsa" Ustaz ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa a hankali ya ce "Ridayya ƴata ce, kuma na san babu aure tsakanin uba da ƴarsa" Bai bawa kowa damar magana ba ya fice saboda jirin dake shirin yar da shi a wajan. Yaya Zuhura ta jinjina kai ta ce "Allah ya yi maka gyaɗar duguwa, daman mai ka ci na asham balle ka yi ramakon sallah? Me Ustaz zai yi da Ridayya yarinya duk da lalace ta zama tsohuwa, sai dugun baki da haƙora a waje, ni ɗin nan da nake yayarta na fita kyan gani hatta Amma tafi Ridayya kyan gani fa?" Balkisu girgiza kai kawai ta yi zuciyarta bata yi mata daɗi, sauran ƴan mazan ba wanda ya tofa tashi a ciki haka Amma. Mami ta kalli Baba ƙarami kanta a ƙasa ta ce "Zan iya tafiya Baba ƙarami?" Baba ƙarami ya ce "Tashi ki je Fatima Allah ya kyauta ya sauwaƙa" Ta miƙe tsaye ta ce "Amma bari na shiga ciki" "Mami tun yanzu? To shikenan" Zainura ta miƙe da sauri ta bi bayan babarta, da ƙyar Mami ta kai kanta ɗaki "Mami Yaya Ridayya kar ta mutu" Ta sauke numfashi ta ce "Babu abinda zai sameta, ko wacce kalar mace da kalar ƙalubalan da take fuskanta a gidan aurenta, na yi imani baƙin cikin ɗa namiji ba zai taɓa kawo ƙarshen rayuwar Ridayya ba kamar yar da bai kawo ƙarshena ba, da yawa wasu burinsu kawai su yi aure ba tare da tunanin kalar rayuwar da zasu fuskanta a gidan miji ba, Zainura babu soyayyar har abada fa, da yawa wasu matan haƙurin su yasa ake ganin kamar basu da matsala a gidan aurensu" Kwana biyar da yin rigimar asibitin, amma Zameer sau ɗaya ya leƙa shima a gigice cikin dare da buƙatar kai da kai ta kaishi, duk yar da yake son samun nutsuwa da Khairy sai ya ji ba kamar Ridayya ba, baya buƙatar komai a wajan Ridayya sai wannan abun. Tana kwance sai numfashi take da ƙyar kamar daga sama ta ji mutum ya faɗa mata ka, za ta yi ihu ya ce "Kee nine Rayuwarki ne, mai sona" Numfashi ta sauke tana rufe ido "Ina ka je?" A taushashe ya ce "Aiki nake domin rufin asirinmu da gujewa raini" Ta yi shiru can ta ce "Kwanaki na kira ka cikin dare na ji surutai da wata murya ana cewa a yi a hankali ban saba ba" Dam! Kirjinsa ya buga sai kuma ya ce "Ƴan fashi, wallahi ƴan fashi ne Ridha wuƙaƙe sun fi talatin akai na" Tunda daga sama har ƙasa ta dinga kallonsa ba ta yi magana ba irin kallon da take masa yasa shi faɗin "E, dake na sha maganin tauri ai wuƙa bata yankata da tuni sun kashe ni" Gabanta ya faɗi ita kam aka kashe Zameer bata da wani saurin gata a hankali ta ce "Na ji sai ihu kake kam" Cikin rashin sani ya ce "Ihun daɗi ne" "Daɗi kuma" Ya haɗe fuska tare da mitsi mitsi da ido ya ce "Bala'in daɗi ma, saboda wuƙa bata shigata kuɗin da kika bani kawai suka kwashe ai" Ganin yana sauya salo ta riƙe hannunsa ta ce "Bani da kuzari, yunwa na ke ji ka bar ni" Zameer ya ƙara haɗe fuska da kyau ya ce "Ridayya na bar ki hakƙin nawa?" Idanunta na zubar da hawaye ta ce "Shi kansa tarayya sai da nutsuwa da cima mai daɗi Meer, bani da nutsuwar hakan ba zan iya ba" Ya miƙe tsaye ya ce "shikenan ba komai kwanta na haƙura ko zan mutu ban taɓa ki" Tausayinsa ya kamata tasan hakanma soyayya ce ta ce "Bismillah" Kuka take sosai saboda tsananin azaba kamar ta yi amai, Zameer ko a jikinsa buƙatar maje hajji sallah ya miƙe yana goge zufa sai yanzu yake jin damuwarsa duk ta kau Ridayya bata da wani amfani gare shi bayan wannan. "Tafiya za ka yi ka bar ni?" Ya haɗe fuska ya ce "Ina da uzuri" yana faɗin hakan ya fice ta kifa kanta ta saki wani irin kuka mara sauti. Washegari da yamma Baba ƙarami ya zo duba Ridayya ganin ko zama ba ta yi ya sa shi buɗe mata ido tare da kwasarta zuwa gida a cewarsa ba zata koma gidan Zameer ba sai ya gyara halinsa. Babu wanda ya san Ridayya na gidan ya gargaɗe ta kar ta faɗawa Zameer inda take yana fita daga ɗakin ta masa message ya yi haƙuri ya yafe mata kar ya zo asibiti bata nan tana gidan Baba ƙarami. Sanda saƙon ya isa Zameer na ɗaki Khairy kwance a gefensa tsaki ya ja don tafiyarta bai dame shi ba muddin ba hakƙinsa yake buƙata ba. Cikin dare Ustaz ya shigo domin ya jima a waje saboda a gobe ne zai koma Lagos har ya shige kitchen ya ji kamar motsi, ya dinga mamakin waye a kitchen kuma cikin dare? Har zai juya sai kuma ya juyo ihu da da kuma ƙarar faɗuwar kwanoka da sauri ya nufi kitchen ɗin domin ganin waye a ciki.... Kar a manta da sharing da comments free book ne 🤙🏼🤙🏼👯🏻‍♀️ 08164069385. *🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝* *MTN* . *Airtel* 1GB = ₦300. 1GB = ₦300 2GB = ₦600. 2GB = ₦600 3GB = ₦900. 3GB = ₦900 4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200 5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500 *GLO* . *9MOBILE* 1GB = ₦300. 500Mb ₦250 2GB = ₦600. 1GB ₦500 3GB = ₦900. 2GB ₦1000 4GB = ₦1200. 3GB ₦1500 5GB = ₦1500. 4GB ₦2000 VALIDITY: 30:DAYS My whatsapp number 08066268951 *✿ MUNAFUKIN MIJI ✿* Nimcyluv@Arewabooka BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Page 5 Idanun Ustaz ya sauka akan abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwarsa, ya yi zaton wani a cikin kitchen ɗin, amma mummunan ganin da ya yi ya sanya ya ɗan yi baya a tsora ce tare da rufe idanunsa can ƙasan zuciya Ustaz Bilal ya ce "Ya subuhanallahi! Asstagafirullah" Ridayya ya gani da Zameer kwance a ƙasan kitchen ɗin, turmi da taɓarya, ya saka hannu ya shaƙe mata wuya sai shure shure take tana kakari tamkar na fitar hayyaci ko zarar rai. Ustaz da ƙyar ya ja ƙafafuwansa da nufin barin wajan domin jiri ne ya ji ƙoƙarin yasar da shi a ƙasa, al'amari Ridayya kullum girmama yake yana sake lalacewa. Karo suka ci da Baba ƙarami daya fito hakan ya sa Ustaz tsayawa tunda ya ga lokacin assalatu bai yi ba, balle ya yi zaton Baba ƙarami sallah ya fito yi. "Ustaz ba dai ya zo kake dawowa ba?" Ustaz ya kalli baban nasa a hankali ya ce "E, dawowar kenan" Cikin gamsuwa ya jinjina kai yana mai faɗin. "Ai tun ɗazo nake jiranka mu yi magana, har dare ya yi shiru ka jira ni a parlo zan duba naga ta'addin me nake ji tun a shashin baya har hanyar kitchen" Kafin Ustaz ya yi magana Baba ƙarami ya nufi hanyar kitchen ganin da gaske can ya nufa, kuma baya fatan ace mahaifinsa yaga abinda nasa idanun ya gani da ɗan saurin harshe ya ce "Abba, ni ne fa" Baba ƙarami ya tsahirta da tafiya ya ce "Kai ne me?" Kan Ustaz a ƙasa "Ruwan zafi na haɗa, na ɗan zaga baya ne" "Ruwan zafi a daren nan Mai babban suna? Kamar wani ƙaramin yaro kake suntiri da ɓuruntu?" Shi dai Bilal bai ce komai ba, domin baya buƙatar sake shimfiɗa wata ƙaryar akan kare Ridayya, ya nufi hanyar parlour. Yana zama Baba ƙarami ya zauna yana ƙarewa ɗan nasa kallo a nutse ya ce "Bilal?" Da Idanu kawai Ustaz ya amsa Baba ƙarami ya ɗora da faɗin "Ridayya tana gidan nan, na ɗakkota daga asibiti rayuwar yarinyar nan abar dubawa ce, bai kamata a ƙarancin shekarunta a ce tana fuskantar ƙalubalen gidan aure da matsalar miji ba, kasan rayuwar Ridayya ka fi kowa sani da halin data tsinci kanta a baya, me ya sa ba zaka aureta ba?" "Aure Abba?" Baba ƙarami ya yi murmushi ya ce "Shi fa, naga ba haramun bane" Ganin Ustaz na shirin miƙewa ya saka cikin bada umarni Baba ƙarami ya ce "Kar ka kuskura ga tashi, ko baka son Ridayya zaka aureta" "Mahaifi da auren ƴarsa ina aka taɓa haka? Asstagafirullah Allah ka ya fewa Abbana" Baba ƙarami ya saki baki kafin ya ce "Zan sassaɓa maka yanzu, idan ranka ya yi dubu to zai ɓaci, ka kuma gaggauta cire abin da ke yawo a zuciyarka ka daina haramtawa kan ka abinda yake halak ne zaka iya jahadi ne" Ustaz ya miƙe tsaye idanunsa jajur ya ce "Abba kai na ciwo yake nikam ciwo kai na ke mini, Matar auren kake jingina mata auren wani Abba haza haramun Ya Rasulullah Asstagafirullah!" Yana faɗin hakan ya fice shi kansa bashi da tabbaci akan maganganun da yake furtawa. Washegari wajan shi da na safe Baba ƙarami ya saka a haɗa abin karyawa zai kaiwa Ridayya ta sha, ta ci abinci ta ƙara hutawa sai a sauya mata asibiti domin wani abun da yake damun Ridayya hadda sakacin iyaye da rashin kula da al'amarin yaran su. Da sallama ya shiga ɗakin amma shiru ba amsa ya dinga bin ko'ina da kallo ba Ridayya babu mai kama da ita, yana shirin fita idanunsa ya a kan takardar da aka ajjiye saman gado ya saka hannu ya ɗauka, saƙon daya gani ya gigita shi tare da sauya masa lissafi da jin komai zai yi a rayuwa dole ya kashe auren Ridayya Ustaz ya aura, Ubangiji shi ne shaida bai aikata hakan domin ya ci mutuncin wani ba, ko ya lalata mata auren ta ba, zai yi ne domin taimakon rayuwar ƴar ɗan'uwansa. Ya sake ware farar faifa ɗin idanunsa ya sauka a kan rubutun nata. _Ni na san ban kasance alheri a zuri'armu Abba zan so ka cire hannu a cikin al'amarina kamar yadda Baffana ya cire, na gode da taimako daga yanzu har zuwa ƙarshen rayuwa bana buƙatar ko wanne taimako mijina ya tsaya mini, ya share mini kukana, daman kune baku fahimta ba amma nasan ba wata mace da Zameer ke so kamar mata ni Ridayya, zan yi nisa daku domin na fahimci za ku iya raba aurena, Abba kar ka yi mini kuskuren fahimta Zameer ya zo na bi mijina gidan aurena na sunna ya ce muddin ban bisa ba to zai sake ni, ba zan iya zawarci ba, ba zan iya barin Zameer ya rayu da wata mace bayan ni ba, wallahi ina son mijina shi ne rayuwata_ Murmushin takaici kawai Baba ƙarami ya yi tare da yaga saƙon, ƙiri-ƙiri Ridayya ta watsa masa ƙasa a ido? Allah ya sa banda Bilal babu wanda ya san da zuwanta nan daman mahaifiyarsa Bilal bata nan ɗin. Ya juya yana kiran ɗan'uwansa a waya domin akwai buƙatar ya baro Rano zuwa Kano. Ustaz a gida ya bar motarsa kasancewar aljihunsa da ɗan nauyi tunda an yi albashi ya biya kuɗin jirgi daga Kano zuwa Lagos ɗin. Suna tafe a mota zuwa airport Junaid na driving Ustaz na zaune idanunsa rufe ya ce "Baku daidaita da Batool ba?" Damuwar Junaid ta bayyana ya ce "Kowa da ƙaddarar shi, itama Batool an yi Genotype jikinta AS ne dole za mu haƙura da juna ne, idan ban manta ba Batool ita ce mace ta shida" Ustaz ya ce "Ikon Allah, to Allah ya shiga lamarin" Junaid ya ce "Amin, yaushe zaka dawo Kano idan ka tafi?" Ustaz ya yi shiru can ya ce "Shekara war haka" Jinjina kai kawai Junaid ya yi domin shi na zai so ace Bilal ɗin bai dawo ba balle ya ci-gaba da taimakawa Ridayya. "Na manta wayata ɗan bani a ron wayarka" Kamar Ustaz ba zai bayar ba sai kuma ya miƙa masa, Junaid ya matsa can gefe ya shiga lalubar number Ridayya da ƙyar ya gano ta yaga an yi saved da _Ustaza_ Number ya saka a black list ya yi blocking gabaɗaya kana ya dawo yana cewa. "Nama tuna inda na ajjiye wayar tawa, daman ita zan kira na bar ta a parlon Mami wajan Zainura" Bilal bai ce komai ba har aka kira su ya shiga jirgi kana Junaid ya juya zuwa gida zuciyarsa cike da tausayin Ridayya amma dole ta gane kuskurenta yanzu zata fahimci muhimmancin Ustaz a cikin rayuwarta. Ridayya na kwance tun cikin dare da Zameer ya je ya biya buƙatarsa wanda a lokacin ta ɗauka mutuwa za ta yi saboda wahala amma shi ko a jikinsa, tunda ya fita bai dawo gidan ba har gari ya waye, ko ƙwayar abinci bata kai bakinta ba balle kuma a yi batun maganinta ga ɗinkin da akai mata yana neman farke wa dalilin abinda Zameer ya yi mata a asibiti da kuma gida sai ruwa wajan yake. Kai ta ɗaga ta kalli lokaci ƙarfe 1:56 so take ta tashi ta gabatar da sallar zhur wato azahar amma ta kasa jikinta duka ciwo yake mata jijiyar bayanta ta riƙe sosai, ta ci kuka son ranta har ta ga ji. Khairy ce ta shigo daga ita sai ɗaurin ƙirji da towel ya tsaya iya cinya, kamar daga sama kuma taga Zameer ya shigo shima gajeren wando ne a jikinsa ruwa na zuba alamar wanka ya yi ko kuma sukai tare da Khairy ɗin. Farar fatar Khairy sai ɗaukan idanu take a barka da kyakkawa kuma mai diri da kyan fuska, hakan ya ƙara sawa Zameer jin komai ya dawo masa sabo fil dan gane da abinda yake ji game da Khairy. Ridayya ta dinga kallon su tana haɗiye yawun daya taro a bakinta ƙirjinta na bugawa numfashinta na ƙoƙarin tsayawa, kallon Khairiyya take kamar bata taɓa ganinta ba tana ƙoƙarin magana Khairy ta saka hannu ta ja gajeren wandon Zameer ta ce "Kai Yaya tun safe nake nemanka zani wajan Mama yau zuwa dare na dawo" Zameer ya kasa kallon Khairy duk yar da zuciyarsa ke kwaɗaituwa da son haka, haka kuma ya kasa kallon Ridayya ganin yar da take binsu da kallo sai kuma ya haɗe fuska ya ce "Ridayya jikin ne ya sa ba ki iya sannu ba? Sai bina kike da idanu da kuma dugun baki?" A hankali ta ce "Ka yi haƙuri" Niyyar ƙorafi take amma ganin fushinsa ya saka ta haƙura da nata domin ko da wasa bata ƙaunar taka sauyi a fuskarsa. Khairiyya ta ce "Laa matar taka kake cewa mai dugun baki? Daman gashi duk ta zama tsohuwa" Caraf ya saka hannu da nufin make Khairy sai ya hau yi mata cakulkuli ta shiga dariya tana guduwa yana binta suka shiga tsere a parlon Ridayya suna zagayeta ba kunya da tsoran Allah. Suna cikin gudun towel ɗin Khairy na faɗuwa ƙasa, sarai Khairy ta san towel ɗin ya faɗi ta rufe idanunta tare da juyowa inda Zameer yake tana girgiza ƙirji da banƙaro ƙirji haɗe da faɗin "Hooo bai kamani ba, a yi masa gwalo wulwul bai kamani ba" Ta sake faɗa tana tura ƙirji gashi daman ba komai a jikin nata sai towel kuma ya faɗi. "Kau!" Ridayya ta ɗauke Khairy da mari tana shirin ƙara mata wani kamar daga sama ta ji an ɗauketa da wasu tawayen maruka wanda sai da taga wuta ta gilma ta tsakanin idanunta, daman ba ƙwari gare ta ta yi bata zata faɗi ta yi Khairy cike da makirci ta tare Ridayya ta ce "Haba yaya me ya sa zaka mata wannan jahilin marin? Ka manta bata lafiya? Ya kake abu kamar baka damu da matarka ba" Zameer ya yi mitsi mitsi da Idanu ya ce "Shiru a nan Khairiyya, shiru na ce, ke me kika yi mata da zata saka hannu ta daki lafiyayyiyar farar fuskarki? An faɗa mata ko wacce fuska ake mari?" Khairy rai fes ta ce "Babu mamaki tana da hujjar marina ko na yi mata laifi ban sani ba" Ridayya kishi ya turnuƙe ta kenan suna nufin daga Khairy har Zameer ba wanda ya fahimci me sukai? Idanunta ya rine jiri na ɗaukan ta ga ɗinkin jikinta dake amsawa ta ce "Rayuwata mari na ka yi? Mari har biyu?" Ya juya yana kallonta ya ce "Zan miki mahaukacin duka ba mari ba muddin za ki taɓa jinina bana wasa da ƴan'uwana" Ta runtse idanunta ta yi tana kiran sunan Allah kafin ta ce "Yanzu ya dace ka dinga bin baligar mace da cakulkuli a gabana Meer? Har towel ɗin jikinta na faɗuwa kai hakan duk bai dameka ba? Tsaraicinta shi ne abin kallo Meer?" Zameer ya yi kan Ridayya zai daka Khairy ta yi saurin tare shi tana haɗe jikinsu waje guda ta ce "Haba yaya Anti Ridayya gaskiya ta faɗa ɗan miƙo mini towel ɗin na rufe jikina" Zameer ya juya tare da ficewa yabar wajan, Khairy ta ce "Ki yi haƙuri ban san towel ɗina ya faɗi ba, bada gangan na yi hakan ba, amma kar ki sake gangancin marina domin amana Mama ta bawa Zameer ni zai iya komai a kaina" Ridayya ta kasa furta komai takaici ya mamaye ta, kenan ita data bar kowa nata saboda miji hankali ne bata da shi kome? Yau Zameer ita ya mara a kan ƙanwarsa? Saboda suna aikata abinda bai dace ba? Ko kuma laifi ne don ta nuna kishi akan abinda take mutuwar so?. Kuka ta dinga yi ita kaɗai domin hakan sabon abu ne a wajanta, ga yunwa ga ciwo ga takaicin da miji ya ƙunsa mata, ga matsalar ciwon zuciyarta na soyayyar Zameer. Da ƙyar ta miƙe ta gabatar da sallah ta haɗa azahar da la'asar, Zameer na fita ya shige ɗaki Khairy ta bi bayansa suka kulle ƙofa bata tare da yin shiru. Ridayya bata san meke faruwa sai jin sautin waƙa ta ji yana tashi daga ɗakin Zameer ta rufe ido tana jiran taga ta ina mala'ika azara'ilu zai fito? Domin mutuwa ita ce abar da take fata ta risketa. Sallamar Zainaba da yar da take bubbuga kafaɗar Ridayya ya fahimtar da ita ce ita da rayuwa sun ƙalla aminci ne, haƙarta sam bata cimma ruwa ba, ta bi Zainaba da jimammen idanunta ta kasa cewa komai. "Mai ƴar tsala tunanin me kike haka? Ashe da gaske daman Usman yake kin dawo cikin dare ke da Zameer?" Ridayya ta jinjina gulmar Zainaba da mijinta ta ce "E, an wuni lafiya Maman Hajjo?" Zainaba ta ce "Lafiya ba lafiya ba, ina can ƴar nan da tunaninki, to Masha Allah jiki ya samu" Ridayya ta ɗan yi yaƙe haƙora suka bayyana muninta ya sake fiddowa fili. "Abinci na kawo miki, sai kuma kika ji daga tafiyarki Mai ƙosai ta fara yin ƴar tsala? Mutane babu ko kara" Ridayya ta ce "Allah sarki kowa rabonsa zai samu ai, ni ina tunanin ba zan sake ƴar tsalar ba" Zainaba ta riƙe baki ta ce "Ke kowa saboda me? A'a wallahi ai jama'a nata cigiyar mai ƴar tsala" "Ba kuɗi a wajena, ba jari" Zainaba ta yi ƙasa da murya ta ce "Ina adashin da kike yi to? Ki karɓa bayan ƴar tsala sai ki fara siyar da kayan miya ma ai zama haka ba naki bane tunda kalar naki ƙaddarar kenan" Ridayya ta yi murmushi ta ce "Ai na amshi kuɗin yau da safe har sun ƙare a magani" Baki sake Zainaba ke kallon Ridayya zata iya rantsewa da Allah mijinta mai zaman banza ta ba wa kuɗin. "Shikenan akwai wata dubu biyar waje na sai na ara miki ki ɗora jarin idan kin manshe da kuɗin kya bani ko?" Ridayya ta ce "Na gode sosai Maman Hajjo Allah ya saka" Ta kunce bakin zani ta ba wa Ridayya kuɗin kana ta yi mata sallama ta ce "Zan aiko hajjo ta amshi kwanon abincin" Da sauri Zameer ya koma ɗaki jin Zainaba ta fito, daman ya fito da nufin karɓar hakƙinsa wajan Ridayya tunda duk nacinsa da Khairiyya ya kasa samun nutsuwa da ita. Ridayya ta jawo kwanon abincin kenan Zameer ya shigo yana ƙamshi ya sha shadda daman ba dai iya ɗaukan wanka ba, ya san takan gayu sosai. Ridayya bata kalle shi ba ba kuma ta saka hannu cikin abincin ba. Meer ya tausasa murya cikin salo na makirci kamar mace ya ce "Fushi kike dani mai sona? Idan kikai fushi dani ai na shiga uku bani da wani sauran gata" ko tari ba ta yi ba. Sai kawai ta ji ya fashe mata da kuka yana kifa kansa a cinyarta a hankali kuma ya toshe hanci gudun kar ƙarnin ruwan ciwonta ya saka shi a mai. Ya dinga kuka kamar amaryar da aka ɗaurawa lallai. "Ki yafe mini kada ki tarwatsa zuciyata da shirun nan naki, nasan na miki laifi Ridha amma kin san halin Khairy yarinya ce ita ba hankali kuma mun saɓa ƴar tsere da cakulkuli da ita, yanzu da kika mare ta da ban rama mata ba zuwa za ta yi ta faɗawa Mama kuma a kan Khairy Mama na iya tsine mini" Ridayya dai bata ce komai ba ya ce "To shikenan rama marin tunda ba za ki yafe mini ba" A hankali ta ce "Ina zaka?" "Ke na yi wa kwalliya, nikam ke na yi wa ki yi ta kallon rayuwarki ki na jin daɗi, ina tsananin son ki matata farin cikin rai na, mayyar Zameer i love you!" Nan da nan Ridayya ta mance komai daya faru ta ce "Ka ci abinci?" Ya ce "Ta ya zan ci na hanaki bani kuɗi, nema dai zani" Ta tura masa kwanon abincin da Zainaba ta kawo mata ta ce "Ga abinci nan, kuma ka bawa ƙanwarmu Khairy haƙuri kishinka da son ka ya sa na yi abinda na yi" "Uhm" ya ce yana jan kwanon. Shinkafa da miya ce da kuma yankan nama guda huɗu ga haɗin salak, Ridayya sai haɗiyar yawu take sai daya cinye tas sannan ya ce "To ke kin ci?" Ta yi murmushi ta ce "E" Ya dinga kallonta gabaɗaya ta zama tsohuwa ya ce "Mai sona aron kuɗi nake so zan biya a yi mini printing na wasu takardu zan kaiwa Alhaji Muttaƙa ya nema mini aiki, da zarar na samu aikin zan fashe gidan nan na yi miki sabo ke da yaranmu, domin har miliyan biyu za a fara bani cikin satin nan muddin yau na kai takardun nan" Daɗin ya kama Ridayya domin da zarar Zameer ya samu aiki zata fita daga wannan wahalar kuma zai siya mata kayan ɗaki "Har nawa kake so?" Ya ce "Dubu goma haka" Ta ware ido ta ce "Tab sai dai dubu biyar yanzu aka bani aronta na ɗora jarin ƴar tsala, kuma ka san na faɗa maka yar da mukai da Baba ƙarami na cewa Bilal kuma kar ya sake turo mini kuɗi bana buƙatar taimakon shi" Zameer ya zare ido ya ce "Amma ba ki da hankali ai ban hanaki kar ɓar kuɗi wajan shi ba, taimako ne maza ki bashi haƙuri ya dinga tura miki" Da mamaki ta ce "To tunda bana son shi me zan yi da kuɗinsa? Duk wanda zai wulaƙanta ka wallahi bana son shi" Zameer ya ce "Ai ana iya zuciya da komai ban da kuɗi, matsalarku daban taimako daban, bani kuɗin" Ta ɗakko dubu biyar ɗin ta bashi. Daga nan kuma ya dinga kallonta can ya ce "Ina buƙatar ki" A tsorace ta ce "Bani da lafiya ka yi mini afuwa, wallahi wannan abun baya gabana" A ransa Zameer ya ce "Banda wannan dalilin ni ma ko inda kike ba zuwa zan yi ba, wannan shi ne kawai dalilin daya sa ba zan rabu dake ba" A fili kuma ya ce "Shikenan na gode" Ta girgiza kai ta ce "Zameer ka yi mini uzuri, bani da lafiya ba cima mai kyau balle abin ƙara lafiya da kuzari" Ya ƙanƙance ido "Ohho ƴan'uwanki za ki bi kenan Ridha, ni kike wa gori? Ridha ni mijinki aljannarki na tafin ƙafata? Kike cewa ba cima mai kyau sata zan yi na ba ki? Ko ni zan zo ki cinye ni, to wallahi hakƙina ko kina so ko bakya so sai kin bani ai sadaki na biya" Kafin ta yi magana ya cimmata tana kuka da ihu saboda ba daɗin abin take ji ba tsananin a zaba kawai take sha, gashi kamar mahaukaci haka zai shaƙeta idan zai nutsu, wani ihu Ridayya ta yi wanda ya yi daidai da ƙarar ƙarar zagewar wani abu keeeetttt hakan ya yi daidai da ɗaukewar numfashi Ridayya tare da yin ƙaura daga jikinta wanda yake bayyana suman da ta yi. 08164069385 Duk mai so daga farko ya yi following channel ɗita dake WHATSAPP🥰 *✿ MUNAFUKIN MIJI ✿* _Nimcyluv@arewabooks_ BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Page 6 Ruwan da Ridayya ta ji ana sheƙa mata mai sanyi ya haddasa farfaɗo war ta daga suman hucin gadin da ta yi. "Ɗinkina zai farke, ka tausaya mini ba zan iya ba wayyy...," Zainaba ce ta jijjiga Ridayya da ƙarfi ganin kamar bata gama dawowa cikin hayyacinta ba cike da tausayi na halin da yarinyar ta saka kanta ciki ta ce "Ridayya lafiyarki lou? Me ya sameki na gan ki a yashe kamar gawa? Ina shi mijin naki ya bar ki haka? Wacce kalar rayuwa ce wannan?" Maganar Zainaba ya dawo da Ridayya cikin nutsuwarta ta fahimci ba Zameer ne a kusa da ita ba balle ta saka ran samun kulawa daga wajan shi tunda shi ya cillata halin da take ciki a yanzu. A karo na farko tun kafin auren su, da bayan auren su ta ji wani irin mummunan faɗuwa da ladamar abinda ya shuɗe sun dirar matar a zuciya ta ji babu abin da bata ƙauna irin tarayyar aure, rashin mafita da yar da zata fahimtar da Zameer ɗin ya saka take biye masa ba son ransa ba, yana nuna mata ƙarfin ikon shi akan ta matsayin miji. "Allah na tuba, na tuba Allah ka yafe mini zunubin dana aikata a baya yake bibiyata na ji a jikina, idan har haka ne gwara mutuwa da rayuwa a gare ni" Zainaba ta yi saurin rufe mata baki, ita ma hawaye ne ke sauka daga cikin idanunta kamar yar da Ridayya ke kuka mara sauti mai cin zuciya. "Komai ya yi zafi maganinsa Allah, Ubangiji baya taɓa ɗorawa bawa abinda ba zai iya da shi ba, ba kuma ya ɗorawa bawa ƙaddarar a domin baya son shi ba, sai dai gwada imaninsa da Tauhidi" Ridayya bata fahimtar maganar Zainaba saboda tsoran daya rusketa da jin yar da ruwa ke gudu ta ƙasan cibiyarta. Zainaba ta yi saurin toshe hanci ta ce "Ridayya warin mene wannan?" "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Shikenan" Ridayya ta furta a raunace ganin yadda ɗinkin ya farke wajan ya yi jajur kamar yanzu ne aka yankata, ruwan dake zuba na fidda warin. Zainaba ta miƙe ta ce "Zama ai bai kama mu ba, dole a koma asibiti ki kira ƴan gidanku ki shaida musu" fahimtar kuka a rahama yake ya sa Ridayya bata damu da yadda hawayen ya tsaya mata ba, zuciyarta ta bushe tana mata wani irin suya, ta ƙura wa wajan ido numfashinta na fuska. "Babu wanda zan iya kira, domin na bar su" "Kin bar su kamar ya?" Ridayya ta girgiza kai ta ce "Aurena za su kashe mini ta ƙarfin tsiya, suna son bawa Abbiey ni, na zaɓi mijina domin shi ne Aljannata" Baki sake Zainaba ke bin Ridayya ta ce "Kuma kin tabbata lafiya kike, ma'ana babu Aljanu a jikinki" Murmushin takaici wanda ya fi kuka ciwo Ridayya ta yi. "Idan ina da aljanu kawo yanzu da kin sani" Zainaba ta ƙara cewa "Kuma babu wani asiri da tsinannan can ya yi miki?" Ridayya ta ɗaure fuska duk da halin da take ciki ta ce "Ki dai na zagin mijina cin mutunci ne wannan" "Na ci uwar mijin ba mai ha ya ji, na ci shi ƙandas, na bisa da gudu aikin banza aikin wofi yanzu na ƙara tabbatar da bayan ƙuruciya har da rashin komawa ga Ubangiji da bijirewa iyaye" Zainaba ta ce "Kin taɓa ganin inda iyaye suka mutu aka sauya wasu? Zaka iya sauya komai banda iyaye da dangi, hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, iyaye ba abin wofintar wa bane Ridayya, a yau kika faɗi kika mutu jimawar duniya shi ne ki arba'in, zai yi sabuwar amarya ta tare a ɗakin da kike gadara da sunan ɗakin miji, gidan aure" "Duk lalacewa GIDAN AURENA NE" Zainaba ji ta yi kamar ta yi wa Ridayya mugun duka, sai dai tausayinta ya danne haushin da take ƙunsa mata ta ce "Kira wannan kamilin ko shi ne ya kai ki asibiti" Ridayya ta yi shiru yanzu ta kira Abbiey ta ce masa me? Ustaz ina son ganinka?. "Kira shi mana Ridayya ba lokaci idan ba haka ba kina kallo za ki ruɓe" Ridayya bata da zaɓin daya shige kiran Abbiey ɗin nata, idan kowa zai guje ta babu shi. Abin mamaki wayar baya tafiya tunda take bata taɓa kiran layinsa ya dawo mata ba sai yanzu. "Kiran baya tafiya" Zainaba ta yi shiru ta ce "Gashi babu kuɗi wajena, amma ina dubu biyar ɗin dana ba ki?" A hankali ta ce "Ya amsa?" "Waye?" Cewar Zainaba duk da ta gane ta ce "Rayuwata" wata lailayayyiyar ashar Zainaba ta ƙunduma ta ce "Lahirar ki dai makashinki shege da munafukan idanunsa, dake ke makira ce uwar son miji shi ne kika kwashe kuɗin kika bashi? Ohhho ni Zainabu Abu ina ganin rayuwa a wannan gidan Munafukin mijin, Allah ka nuna mini sanda Ubangiji zai jarabci wannan mugun ya nuna mini ranar da zai ga amfanin matarsa" Ridayya jin Zainaba take, ba don ta yar da ba ta ce "Akwai wata Atamfa valisco da super was a akwatina idan za a samu masu siya, ki siyar mu je asibitin" Zainaba ta miƙe. Neman duniya babu atamfofin nan sun yi ɓatan dabo hankalin Ridayya ya tashi domin sune kawai kadarar daya rage mata sai katifar da take kwana akai. Duk atamfa ɗaya ta kusa dubu hamsin haka Abbiey ke bata baya mata ƙaramar suttura. Waye zai ɗakko har ɗakinta. Zainaba ta ce "Uhm, lokaci" Fita ta yi babu jimawa ta dawo da kuɗi a wajanta ta dafawa Ridayya ruwa ko zani baya zama jikinta haka ta rufe wajan ɗinkin dauɗa na taso mata ta yafa ruwan. Ruwan shayi mai kauri Zainaba ta bata ta kasa sha ganinta take kamar kayan cikinta zai fita, ta dinga kiran Zameer a waya shiru baya ɗauka Maman Hajjo ta kwace wayar ta ce "Uwar me zai mana banda ƙaryar da zai shirya miki, napep na waje mu je" da ƙyar ta shiga napep suka rufe gidan tare da nufar asibiti,suka samu Nas Hajjara cikin sauri aka yi wa Ridayya komai a account ɗin Nas Hajjara aka cire kuɗi, a nan kuma Ridayya ta kwana washegari da dare aka sallame su da zummar nas Hajjara zata dinga zuwa duba ta, har sannan Zameer bai kira waya ba. Gama shan shayinta kenan bayan sun yi sallama da Zainaba Zameer ya shigo a gigice yana zuwa ya saka hannu ya ɗauke Ridayya da mari za ta yi magana ya sake ɗauketa da mafi ya ce "Ni kika mayar mahaukaci a unguwa? Kika rufe gida kika ta fi yawon duniya abinki? Har ki kwana ki yini bin maza kika fara?" Ta kasa magana balle kuka bakinta ya kumbura tare da ƙara tsine ya sauya mata kama abinka da baƙar mace mai rangwamen kyan halitta muninta ya fiddo fili. Ganin yar da take jan numfashi jikinta ya fara rawa kamar mai jijjiga ya saka Zameer yin ƙasa da murya ya ce. "My love, ban yi da niyya ba, na gigice na zama mahaukaci a wajan nemanki da gudun kar na rasa ki, tsananin farin ciki ya saka na mare ki ba tare dana tuna ba ki da lafiya" Rana ta farko da ya ce "My love, masoyiyata" sai ta nemi duka zafin marin ta rasa ta kasa cewa komai. Ya tausasa murya ya ce "Haba mana, ki rama idan ba ki haƙura ba" Ridayya ta ce "So kake Allah da mala'ikunsa su yi fushi dani?" Ya kashe mata ido ya ce "Well is allowed" "Baka tambayi ina na je ba, baka kuma ka neme ni a waya ba ai kasan tana wajena" Ya shafa kai ya yi mitsi mitsi da ido kafin ya ce "Ohh ina kika je?" Ta ce "Asibiti, daka gamar biyan buƙatar rai ka fita ka bar ni yashe a sume" Kamar bai sani ba ya zare ido ya ce "Suma kikai? Ayya" Kafin ta yi magana sun ji an ce "Sweetheart" da sauri Ridayya ta ɗaga kanta taga Khairy tsaye daga ita sai three qauter na Zameer da kuma half vest iya ƙirji. "Me kika ce Khairiyya?" "Sweetheart na ce" "Yayan naki ne sweetheart? Wandonsa ne a jikinki fa? Kalli rigar da kika saka ai da haka kika fito zai fi" Khairy ta fara yunƙurin cire vest ɗin tana faɗin "Ok bari na cire idan hakan zai fi" Zameer dai na zaune yan ta son ya juya ya kalli Khairy kaifin idanun matar tasa ya hana "Fitar mini daga ɗaki" Khairy ta ce "Su ɗaki manya, kar fa ki manta gidan miji ne wannan ba gidan uba ba, a yanzu zai iya tafa miki rasit ki yi gaba ni kuma zama daram mai naƙuda ta samu katifa don haka ki saurara mini kar ki nemi ɗaga mini hankali" Ridayya ta kalli Zameer ta ce "Kana jin mai ƙanwarka ke faɗa mini?" Ya juya ya kalli Khairy daidai lokacin data kammala cire vest ɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Wanne irin tashin hankali ne "Na shiga uku Khairiyya kina da hankali? Kalli ƙirjinki a bayyane kalli yar da yayanki ke binsu da ido" Kasa magana ya yi ya miƙe tare da ficewa daga cikin ɗakin, wani irin kishi ya turnuƙe Ridayya ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta ta haƙura har lokacin bacci ya yi bai shigo ba, ga sauro kamar ya cinye Mutum. Ganin ba a kawo nepa ba ya saka ta kunna hasken wayarta domin rage sauro. Cikin bacci kamar kuma ido biyu taga an zuro hannu tare da ɗauke wayar kafin ta motsa an yi waje da gudu ta laluba bata ji Zameer ba ta saki ihu tana faɗin "Wayyo jama'a ɓarawo..... *Ku yi haƙuri da jina shiru bana jin daɗi ne, wannan ma da ƙyar na yi ya ɗan yi short da yawa.A ci-gaba da bibiyar labarin RIDAYYA na MUNAFUKIN MIJI😢😭 Bright pens na godiya da karɓar su hannu bibbiyu da kukai* *✿ MUNAFUKIN MIJI ✿* Nimcyluv@Arewabooks Page 7 BRIGHT PENS🤙🏼 free batch A kiɗime ta ƙara cewa "ɓarawo, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un ɓarawo a ɗakina, Meer rayuwata ɓarawo ya shigo mana" Babu wanda ya amsa Ridayya balle kawo mata ɗauki ta tashi zaune tare jingina da jikin bango, abu goma da ashirin ya haɗe mata. Ƴar raguwar wayar da ta yi mata saura a kadara itama an rabata da ita wai meke shirin faruwa ne. Daidai ɗaga labulen ɗakinta sa'arda nepa suka kawo wuta, hasken wutar ya haska fuskar Zameer da yake ɗan mustsike Idanu alamar bacci cikin kulawa ya ce "Sama-sama ina bacci na ji ihunki lafiya?" Ya tambaya yana daga tsaye, domin baya jin zai iya zama a ɗakin. Ridayya ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Kana gidan ashe?" Ya ware Idanu kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru kawai. "Ina bacci ne ɓarawo ya shigo, ya ɗauke wayata" Zameer fuskarsa shimfiɗe da damuwar daya ƙirƙira a lokacin ya ce "Waya kawai aka ɗauka?" ta jinjina kai alamar "E" Ya ja tsaki a fili ya ce "Shi ne abin ihu a kan ɗaukar waya? Ke dai Ridayya ba ki da tawakkali Kwata-kwata, kece raki idan babu lafiya, kece surutun yunwa kamar za ki yanki naman jikina ki gasa kici, duk abinda na yi miki baya birgeka bana miki gwaninta daman kece kika zubar mini da ƙima da girmana a idanun ƴan'uwanki, ni kam na auri matar ƙaddara!" "Matar ƙaddara!?" Ta maimaita a fili idanunta tsaye cur cikin na Zameer domin a ko wanne yanayin a duk halin da zata tsinci kanta bata shayin sanya idanunta a cikin nasa. Muryarta na rawa laɓɓanta na karkarwa saboda ciwon ciki ta ce "Ni kake kira da matar ƙaddara Rayuwata? Ni Ridayyanka?" Ya ɗaga kafaɗusa duka biyun yana ƙanƙantar da idanu murya ƙasa ya ce "Kar ki mini gurguwar fahimta, kar ki mini, ai ba kece ƙaddarar ba, ƴan'uwanki da auren sune, tunda na aureki ban hutawa raina ba, Allah ya ƙara mini haƙuri, shi ya sa magabata suke cewa Allah ya saɓa halayya" Ikon Allah kawai Ridayya ke kallo ko dai mijin nata wani abu ya sha yau? Bai taɓa mata furuci makamancin wannan ba a hankali ta ce "Don na bar ƴan'uwana baya nufin bana son su ai" Ya riƙe ƙugu ya ce "Ba shakka, idan tururuwa ta so lalacewa, daman fiffike take yi ta tashi ai" Idanunta suka cika da hawaye fal idan da sabo ta saba da kuka tun a daren amarcinta ta ce "Meke damunka na rayuwata? Me na yi da zafi har haka? Don Allah ka yi haƙuri ka yafe mini" Ya ja tsaki yana juyawa. Kasancewar a waje ya yi shimfiɗe tunda ya kammala buƙatarsa da Khairy. Juyi ya dinga yi akan tabarma shi sam ba haka ya tsara gani a auren Ridayya ba, duk abinda yake buri bai samu ba sai masifa kala-kala da auren ya jefa shi. Ridayya ta share hawayen da yaƙi tsaya mata, tana nan jingine da jikin bango, da tana da ikon tariyo rayuwarta ta baya babu shakka da ta yi hakan domin gyara ƙazantar data aikata wacce babu mamaki warinta ke bibiyarta a yanzu. "Ƴar baƙata" Ta ji ya kirata jikinta na rawa ta miƙe zani na faɗuwa ɗuwawu a waskace saboda masifar zama waje guda ta zama tsohuwar gaske wacce masifaffiyar wahalar gidan miji ya mai da ita, daman ba kyakkawa ba domin Ridayya ko a kwatance tana cikin mutanen da za a yi kwatance da girman munin halittarsu. Domin saboda wannan yanayin nata zubin halittar ko a makarantar da aure ya datse mata ita Duduwa ake ce mata. Kamar zata yi masa sujjada haka ta tsuguna a gabansa jikinta na rawar ɗari kar ya taɓa lafiyarta. A hankali ta ji ya ce "Sorry ƴar baƙa, raina ne a ɓace mece waya? Ni da nake saka ran siya miki zuƙeƙiya kalar ya yi, kin san komai na samu naki don ke nake fafutuka da ba ke, da tuni ina Lagos wallahi" Ta yi shiru ya ce "Ki manta da faɗan ɗazo, zan yi miki swapping na sim ko?" A nutse ta ce "Allah ya baka iko" Tunawa da cewa bai tsarkake jikinsa ba ya ce "Ɗan dafa mini ruwan zafi" Ta kalle shi da sauri "Me za ka yi da ruwan zafi a wannan tsakiyar daren?" Ya haɗe fuska da kyau yana nutsa idanunsa a nata bisa dole ya ce "Wanka, zafi ake yau" Ta dinga kallon shi haka kurum gabanta ya dinga faɗuwa ta ce "Ba gawayi ai" kai ya bata amsa da "Amma akwai ita ce ko Ridayya?" Muryarta a sanyaye saboda rashin ƙwarin jiki da yunwa da gajiya da surutun Zameer domin wuta take buƙata. "Duka manya ne, babu faskararre" A zuciye yana ɗaga murya ya ce "Kuma Allah bai azurtaki da hannu ba? Bayan rashin fasali har da nakasa ko? Ina cewa akwai gatari a gidan nan, aure ba abin wasa bane dole ki yi bautar gidan miji, da ake cewa Aljanna da wajan miji ai ba banza ba, bauta kawai aka san mace da yi a gidan miji ta yi ta wahalarta masa yana saka mata albarka, idan albarkarce bakya so sai na ji ba'asi" Miƙewa ta yi a tsakiyar daren ta tattare zaninta shi kuma ya ɗauki wayarsa yana ƙarasa kallon wani blue film yana rufe ƙananun idanunsa. Da ƙyar ta ja itacen zufa na yanko mata haka take ɗaga gatarin tana yin faskaren ana ƙarshe tana ɗagawa ruwan gatarin ya zare ya sauka a yatsan ƙafarta wani ihu da kururuwar azaba, zafi da raɗaɗin daya ratsa jijiyar kanta ya shiga rabawa sauran jijiyoyin jikinta, ƙofofin fatar jikinta ta mimmiƙe wani zazzaɓi mai zafi ya kunno kai ya ratsa jikinta, kuka take majina na fita daga hancinta ga jini na zuba sosai. "Ke kam an yi raguwa kamar ba mace ba? Ba har haihuwa mata na yi ba kuma su jure gabaɗaya ruwan gatarin nawa yake?" Bata gane saboda ji take kamar ranta za a zare ya haska yatsan da wayarsa yaga farcen saura kaɗan ya cire, ya ware ido ya ce "Tab, ɗan wannan abin?" Kafin ta farga ya saka hannu ya fisge sauran farcen bata ƙara sanin meke faruwa ba sai da ta ji ana zuba mata ruwa ta sauke ajjiyar zuciya, lokacin ko kuka ta kasa sai jan numfashi ya ce "Ai suma kikai wai? Ke komai na suma ne kamar mai cutar suma?" Ta cure waje ɗaya saboda bata ƙaunar tsawa sam ya ce "To ɗoran ruwan tunda Allah ya nufa ba ki shige ƙiyama ba" bata iya cewa komai ba ta ɗora ruwan har ya yi zafi ta juye masa. Lokacin yatsar har ya kumbura. Cikin bacci ta ji ya ce "Ridayya ke Ridayya" Yana saka ƙafa tare zungurin gutaccen kwankwasonta ta farka a firgice tana "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un don ka yi haƙuri zan dafa ruwan yanzu wallahi zan dafa" Takaici ya cika Zameer ya ce "Au ke nan har mafarkina kike? Saboda ga mugu azzalumi yaushe muka fara haka dake ina soyayyar tawa Ridayya ina zaluntarki ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a mafarki ne kawai da rayuwata" Ya sauke numfashi ya ce "Firfita za ki yi mini har na yi bacci zafi ya addabe ni" Matsawa ta yi inda ya kwanta ta fara masa firfita bacci na ɗaukarta idan ta yi kamar zata kifa sai ya zunguro ta iska na busa shi a haka har ya yi bacci tana zaune. Washegari Zameer ya shirya tsaf cikin wata shadda ash ta amshi jikinsa ya fito yana banza ƙamshi tare da murza hula, hannunsa zube cikin aljihu. Ridayya dake tsaye ta ce "Fita za ka yi?" Kai kawai ya jinjina mata bai ma kalleta ba a hankali ta ce "Babu ko hamsin ce na jiƙa kwaki?" Yana yin gaba ya ce "Sai dai ki jiƙani Ridha, neman kuɗi zan fita" Ta ce "Allah ya tsare ya bada sa a, sharrin mutum da Aljan Ubangiji ya kare ya baka halak Ubangiji ya rabaka da haramun mijina" Bai amsa ba ta ce "Don Allah kar ka kalli ko wacce ƴa mace ina jin kishinka har ƙasan zuciyata ina tsananin so da ƙaunarka Rayuwata" Zameer shi dariya ma ta bashi mace duk a jeme wai kar ya kalli kowa? Ya saka kai ya fice abinsa. Kai tsaye wajan cacarsu ya nufa, yana tafiya ɗaiɗai duk ya samu team ɗinsu suna zaune A.y ya ce "Ango mijin Ridayya bada kanka a sare ka je gida kace ya faɗi, wuya ina wuya a gidan Ridayya daɗi a ina daɗi a gidan Ridayya ɗan'gatan Ridayya farin cikin Ridayya shalelen Ridayya kuma rayuwar Ridayya" "Zan ci ubanka zan ci mutuncin ka A.y" A.y ya sheƙe da dariya sosai ya ce "Amma fa mutuina kaci uwar shadda dole mata su yi crushing a kan ka yarinya ta mace kana da kyau da zubin nagarta sai dai kai shaiɗanin ɓoye ne" Zameer ya fara jan ajinsa da haɗe fuska. Gaza dake jinsu ya ce "Zameer akwai caca mai kyau ƙila kana da rabo" Zameer ya ware idanu yana jiran ƙarin bayani, Gaza ya ce "kuɗaɗe ne za a samu wanda mutum da talauci sun yi hannun riga, a ƙalla ba a samu kuɗi ba shi ne miliyan 500 kai fima, mu ma duk mun shiga cacar babbar harka ce" Zameer ya ce "Kai me ka saka naka?" Gaza ya ce "Motata" Zameer ya ce "Na saka gidana" Duk suka zare ido suka ce "A'a banda gida ne idan aka cinyeka ina zaka saka Ridayya ɗin?" Ya ƙanƙance ido ya ce "Babu ruwanku da inda zan saka matata ni dai na shiga caca kuma na saka gidana" gabaɗaya suka amince Zameer ya ji cewa tabbas a wannan karan mafarkinsa zai cika akan nasarar caca. "Wai yau wasan Barcelona da Real Madrid" A.y ya ce "Wacce match?" Gaza ya bashi amsa da "Afcon 2024" Zameer ya ce "Madrid ne ma za su ci, su Barcelona uwar me suka iya?" Gaza ya ce "A'a fa, wallahi Barcelona za su ci wasan bana fatan gidan madara su ɗauki cup" Zameer ya zaro waya daga aljihu ya ce "Na saka wannan wayar idan Barcelona suka ci ka riƙe" Ya dinga juya wayar domin yasan ba wayar Zameer bace. "Na saka Dubu hamsin" Hira sukai sama-sama domin dukkansu zaman banza suke babu mai aiki arziƙi, sun fi ƙarfin aikin ƙarfi saboda sun yi degree aikin office suke jira sun ce amfanin karatun kenan. Daga nan Zameer gidansu ya shige Lagos A hankali yake danna system ɗin gabansa lokaci zuwa lokaci yake ƙara danna number Ridayya amma sai ya ji baya going, ya ajjiye wayar yana sauke numfashi. Daga bakin ƙofa aka yi knocking Ustaz ya dinga kallon ƙofar haka kurum ya ji baya buƙatar ganin kowa jin knocking ya yi yawa a hankali ya ce "Uhm" Buɗe ƙofar akai tare da shigowa. "Assalamu alaika Ustaz Bilal" Ustaz ya ɗan ware Idanu sai kawai ya jinjina kai, laɓɓansa da suka motsa ya bada tabbacin ya amsa. Nasir ya ce "Ai tunda na shigo nake tambayar Md aka ce baka samu damar zuwa ba, ina can ɓangaren customers care naga shigowarka ta baya, fatan ka zo lafiya Ustaz" Ustaz bai ko tari ba Nasir ya ce "Yaushe ka shigo Lagos ne? Har hutunka ya ƙare?" "Nasir" Ustaz ya kira kamar baya son magana, Nasir ya yi dariya ya ce "Da alama yau kaɗaici kake ji ka yi aure kaƙi ƙaton gauro babu mai aurenka yanzu ai" Ustaz da idanu ya bi Nasir idan suna maganar aure mamaki suke bashi suna ɗaukar kalma kamar wasa, bayan yana da kyau kafin namiji ya yi aure ya tsaya ya yi karatu guda akan sanin ma'anar aure da haƙƙoƙin auren, amma daga maza har mata auren kawai ake domin nishaɗi da magance abinda suke kwaɗayi. Nasir zai sake magana Ustaz ya lumshe fararen idanunsa wanda suke ɗauke da dugwayen gashi sukai kwance luf saman matar idon cikin muryarsa ta ustazanci ya ce "Ya isa, ya isa Nasir" Nasir ya kwashe da dariya ya ce "Yanzu zaka fara Asstagafirullah, Hasbunallahu kamar an yi kalmar ɓatsa ustazan nan kuna yin abu kamar baku san komai ba, bayan kun fi kowa iya shege a gidan aure" Ustaz Bilal ya juya tare da ɗaukan gwangwanin Malt ya cillawa Nasir, da sauri ya miƙe yana cafe gwangwanin ya ce "Ohho dai nasan kai ba waliyi bane" Ganin Ustaz ya miƙe yasa Nasir ya kwasa da gudu ya yi waje, girgiza kai kawai Ustaz ya yi yana zama saman kujerar dake office ɗinsa. Wayarsa ta fara ringing ganin sunan Abban sama mahaifin Ridayya ya sa ya ɗauka ya ce "Baffa" Ya yi shiru can ya numfasa ya ce "Allah ya sauwaƙe ku je kawai ban jin zuwa Rano" Yana faɗin haka ya kashe wayar idanunsa ya lumshe a hankali ya shafa ƙirjinsa dake harbawa ya miƙe ya shiga zagaye office ɗin ya ƙara komawa ya zauna a taushashe ya ce "Ustaza" Da sauri ya ce "Asstagafirullah!" Baffa ne ke kaiwa yana dawowa sai sura masifa yake Mami kan ta a ƙasa Amma ke bashi haƙuri Junaid dai bai tanka ba. Ya ce "A zuri'a ta jinina har na haifi ƴar da zata nuna tafi ƙarfinmu? Wallahi ba a haifeta ba idan har ni uban Ridayya ne kuma ta haifu wallahi tallahi sai na raba aurensu da yaron nan gwara ta zauna a gabana har ta mutu babu aure" ya juya kan Mami ya ce "Babu shasha wacce bata san darajar ƴarta ba irinki Mami, ni ba haka na tashi naga ko wacce uwa na yi ba, amma kin zuba idanu ba ki da wata asara ko gawarta za a kawo miki sbd ba ki san wahalar rainonta ba" Mami kanta a ƙasa Zainura sai kuka take ganin yar da ake wa babarta faɗa kamar za a dake ta. Baba ƙarami ya ce "Saurara Bawan Allah Fatima bata da wani laifi, a haka kuka ɗora ta tun zuwan Ridayya duniya,kuma da kake hayaƙin baki a kan taƙi ɗaukan mataki daman hakƙinka ne kwatarwa Auta ƴanci" Baffa ya ce "To wallahi idan har ina raye sai na kashe auren Ridayya" Ya ɗauki waya ya shiga kiran layin Ridayya ba jimawa aka ɗauka Zameer ya ce "Barka da yamma Baffa" "Ina ƴata? Ka ce ina buƙatar ganinta yanzu yanzu a gida" Zameer ya ce bari na bata wayar ya cire wayar daga kunnensa ya fara cewa "Wife... Wife sweetheart Baffa yana kira" ya ɗauki seconds kafin ya mayar da wayar kunne ya ce "Baffa wai bata buƙatar magana daku, ta haƙura daku kuma ta yi nisa daku kamar yar da ta yi muku alƙawari" Wani tari ya turnuƙe Baffa da sauri Mami ta ɗauki ruwa ta bashi ya girgiza kai yana ture hannunta ya ce "Ni mahaifinta? Ni Ridayya take faɗawa haka ashe girman haukanta ya kai haka?" Idanuna ya sauya Baba ƙarami ya ce "A kul ka zubar da hawaye saboda ita, idan ka yi hakan to ka bata lasisin ƙara lalacewa ka yi addu'a sharrin soyayyar zamani ne kawai" Ya jinjina kai ya ce "Ku shirya gabaɗaya a yau ɗin nan zamu tafi Rano duba Hajiya Junaid harku gabaɗaya ku shirya a faɗawa Balkisu, Zuhura Ustaz ya ce zai bimu daga can Lagos ɗin zamu bar wa Ridayya garin na wasu lokaci. Nan da suka fara shirin tafiya Rano a gaggauce gabaɗaya familyn banda Ridayya da Ustaz. Mami kuka take sosai ta cikin waya ta ce "Haba Yaya A'isha ya ake so na yi, ni da Ridayya bamu da wata shaƙuwa ina buƙatar ƴata ina buƙatar tattaunawa da ita" "Ki je gidan nata kafin ku shige Ranon" Tana kuka ta ce "Baffa ba zai barni ba, ya ɗauki zafi ban san me mijin Ridayya ya faɗawa masa ba" Yaya A'isha ta ce "Fatima tun farko kin yi sake a yanzu kuma kafin ki gyara kuskurenki abu ne mai wahala raina ɓaci yake idan na zo gidanki amma ni zani gidan Ridayya ɗin ki kwantar da hankalinki" Mami ta ce "Idan har ban mutu saboda baƙin ciki ɗa namiji ba, to tabbas Ridayya ba zata mutu ba, hakƙina akan ubanta ke bibiyar tata rayuwar ina mata fatan alheri a rayuwarta Ubangiji ya kawo mata sassauci" Ridayya kamar an tsikare ta haka ta miƙe tana saka hijabi Zameer ya kalleta ya ce "Ina za ki" Kai tsaye ta ce "Wajan Mami ina buƙatar ƙarin haske ina son ta fahimtar dani abinda na gaza fahimta" Ya dinga kallonta mamaki ya cika shi jin yau ta ce Mami ba Amma ba, ya ce "Tab, Baffa ya dawo na je gaishe shi ba, amma ba kiga korar karen da ya yi mini ba, cin mutunci ta uwa ta uba kuma ya ce ko da wasa ya ganki a gidansa wallahi sai ya tsine miki" Zaman ƴan'bori Ridayya ta yi kanta ya kulle ta rasa wanne irin hali take ciki ne? Tana buƙatar zama a fayyace mata ma'anar so da ƙauna, so da birgewa da kuma soyayya ta gaskiya tana buƙatar ta fahimci mene take na kuskure. Kuka ta rushe da shi kamar ta yi hauka "Na shiga uku Baffa don Allah kar ka tsine mini zan dawo gare ku wayyo Allah na" Ficewa ya yi. Zainaba ta shigo da kwanon abinci ta ce "Ridayya don Allah don girma ki bani tarihinki wacece ke? Ki bani labarin rayuwarki da aurenki da Zameer don Allah kullum da kwaɗayin jin hakan nake kwana" Cikin kuka Ridayya ta ce "Babu komai a rayuwata sai tarin baƙin ciki da takaici sai baƙin cikin labarina ya haddasa miki ciwon zuciya ku yi mini uzuri a duk abinda na aikata wallahi ina cikin hankalina ko a mafarki bana ƙaunar tuna rayuwata ta baya" Kuka itama Zainaba take sosai ta ce "Wallahi ina tausaya miki ina jin tausayinki kayan haushinki da takaicinki ke mini yawa yana danne tausayin ji nake kamar na jaki na lakaɗa miki mugun duka wallahi, don Allah ki bani labarinki" Ridayya ta ce "Zan ba ki amma gobe da alƙawarin za ki riƙe mini sirrina" Zainaba cike da gulma da son jin zance ta ce "Kin yi alƙawari? Gobe da yaushe kuma kyan alkawari cikawa" Ridayya ta jinjina kai, a yanzu burinta bai shige ganin Mami da Baffa tana jin ko za a kasheta gobe sai ta je gida sun gana da Mami... Tunda suka ɗauki hanyar Rano babu mai magana a babbar mota suke ciki gabaɗaya family guda ɗin, daga Kano zuwa Rano tafiyar 1 hr 18 min (68.7 km) ce kuma cikin dare suka tashi, a karo na farko Baffa ya ji wani matsanancin tausayin ƴarsa zuciyarsa ta shiga zullumi da zarar ya dawo zai dawo mata da duk abinda ta rasa a rayuwa. Junaid dake driving ya ce "Ustaz fa ba za shi wata Rano ba Baffa dabara kawai ya yi maka" Yaya Zuhura ta ce "Kai kam Junaid ka sakawa Ustaz idanu kamar wani sa'anka" Gabaɗaya cikin motar suka saka dariya banda Mami da Baffa Zainura na jikin Mami idanunta, Junaid ya shiga duba lokaci a wayarsa ɗaguwar da zai yi yaga wata ƙatuwar tirela tayo kan motarsu gadan-gadan tirelar na ƙoƙarin kaucewa motar su Baffa na ƙoƙarin kaucewa a ƙoƙarin Junaid na tsayar da motar a tsakiyar titi, gabaɗaya ya danne giyar motar kai tsaye ta yi ƙarƙashin tirelar Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Gabaɗaya tirelar ta bi ta kan motar ta danne jama'ar ciki baka jin komai sai salatin da jama'ar motar ke yi wasu na ihu a hankali aka daina jin motsin kowa sanda tirelar ta mirgina ta ƙarasa danne kan motar su Baffa.... Don Allah idan kun karanta a yi sharing please saboda masu nema a kuma yi comment kar ku manta free book ne. 08164069385 Na'ima Sulaiman Sarauta08164069385 *✿ MUNAFUKIN MIJI ✿* Nimcyluv@Arewabooks Page 8 BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Yau duk wanda ya karanta ina son ya shiga Tiktok ya yi mini comment ta can👇🏼👯🏻‍♀️ Hatsari ne wanda duk wanda ya gani sai ya girgiza, wasu su kuka da faruwa mummunan al'amarina na yiyuwar rasa rayuka da dama, masu matsanancin tsoro ta iya yiwuwa su yi mafarkin yar da babbar motar ta bi ta kan, ta su Baffa. Titin ya cika da jama'a aka dinga parking da abeben hawa, da ƙoƙarin ceto wanda Allah ya nufa suke raye. Da ƙyar aka samu damar zare motar jini na zuba sosai daidai ambulance suka danno kan motarsu, basu tsaya tantance akwai masu rai ko duk sun mace ba duka aka kwashe su zuwa mota aka nufi asibiti mafi kusa da wajan da hatsarin ya afku. Tsoran Allah ya ƙara shigar wasu. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yanzu haka ahhali guda ne irin tafiyar da ba'a so, duk wanda ya yi saura a dangin ji zai yi kamar shi ma ya mutu ya huta, sun fito lafiya babu wanda ya taɓa tunanin lokacin mutuwarsa ya yi, kana tafe ne baka san kwana ya ƙare ba, Allahu Akbar wayyo Allah!" Wata mata dake gefen mota ta dinga faɗa kuka yaƙi tsaya mata hankalinta ya tashi ainun. Mijinta ya riƙe ta ya ce "Ki kwantar da hankalinki Madam, kar ciwonki ya tashi kuma, shi ya sa a kullum a kodayaushe ake son bawa ya dinga aikata abin arziƙi domin mutuwa bata sallama balle kasan ranar tafiyarka lahira. "Allah sarki ni fa sai naga hannun wata kamar ya cire ga kan wani ya yi daga-daga wallahi zai wahala idan duk basu mutu ba" Nan da nan hankalinta ya ƙara tashi ta rushe wa mijinta da kuka da ƙyar ya lallaɓa suka shiga mota. Ana ta rai da neman taimako, a gefe guda kuma wasu sun taro sun sace kayan mamatan babu tsoran Allah da tunanin suma za su je inda sauran suka je. Emergency ɓangaren ƴan hatsari aka nufa da su, aka shiga duba wa ko akwai sauran masu rai, aka bar likitoci su yi aikinsu, ƴan'sandan kuma suka shiga fafutukar inda za su gano ƴan wanne gari ne mamatan, da inda za su samu wani nasu amma har gari ya waye babu wani Information da zai tabbatar da su waye su, har lokacin ba'a samu cikakken bayani na kasancewar wasu a raye ba, ko duk babu. Kwana biyu da faruwar lamarin Ustaz na zaune a parlon gidansa ko wajan aiki ya kasa zuwa, haka kurum ya ji faɗuwar gaba na ruskarsa, fargaba da tsoran da basu da masaniyar komai a kan wanzuwar su a zuciyarsa suka shiga ratsa shi. Ya rufe idanu sai ya buɗe da sauri shi kaɗai amma duk a firgice yake dukda ƙoƙarin riƙe kansa da yake da kyau da gudun hana faruwar tashin ciwonsa. Wayarsa ya ɗauka yaga Baffa ne last wanda ya kira shi sai kuma a lokacin ya lura da saƙon Baffa dalilin notification dake alamta masa zuwan saƙon. Kai tsaye number Baffa ya kira amma baturiyar wayar na zayyana masa wayar a kashe take. Ustaz ya yi shiru yana sauke numfashi can ƙasa zuciyarsa kuma sunan Allah yake kiran a kan ya sassauta masa fargabar dake shirin tarwatsa masa zuciya ya miƙe tsaye a hankali ya ce "Ya Allah, Rabbi inni lima anzalta min khairin faƙir..." Number Baba ƙarami ya kira itama ƴar'uwar ɗayar ce duk a kashe ya koma da baya kamar zai zauna sai kuma ya tsaya saƙon da Baffa ya tura masa ya buɗe, ya ware idanu ƙirjinsa na dukan tara-tara a hankali ya fara bin abinda saƙon ke cewa. _Muhammad-Bilal zan so wannan maganar na yi ta ga-ni ga-ka babu mamaki zaka fi fahimtar hali da raunin da zuciyata take ciki, faɗar kalmar ban yi wa Ridayya adalci a rayuwa ba wannan kuskure ne, ina tunanin ta zaɓi rabuwa dani ne bisa ga abubuwan da suka faru a baya, Bilal girma muke nasan cewa mutuwa da rayuwa na Allah ne, amma babu tabbacin ganin gobe balle jibi balle kuma sanda zamu dawo daidai da Ridayya, Kullum Baffa take ce mini bata taɓa guduna ba, a wannan karan Ridayya ta zaɓi rayuwa da mijinta a kaina, bata ƙaunar ganina ta ce kar mu sake nemanta, ba zan wa Ridayya baki ba balle hakan ya haddasa ƙara lalacewarta. Muhammad-Bilal, Abbiey kullum Ridayya ke kiranka tun tana ƙarama har ta girma, sai daga baya ta fahimci ba kai ka haifeta ba...,_ Kasa ƙarasa karatun Ustaz ya yi saboda ƙafewar da yawon bakinsa ya yi, ruwa mai sanyi ya ɗauka ya sha kana ya kira number Junaid itama a kashe a fili ya ce "Ya Allah!" Ya koma tare da ci-gaba da duba saƙon Baffa wanda yake tamkar wasiyya ce ga Ustaz ɗin _Ka ci-gaba da zama a matsayin Uba kuma jigo a rayuwarta, Bilal don Allah don Allah ka duba girman Allah ka bawa Mamana rayuwa mai kyau idan har mijinta bai kasheta ba, ka bata karatun data rasa a baya ka tabbatar bata sake kuka ba, sai yanzu na fahimci ba Ridayya ta yi kuskure ba, mune mukai muna muka bata lasisin zaɓar wanda ya fi mata muhimmaci a rayuwarta, Bilal, Muhammad-Bilal, Ustaz Ridayya taka ce amace yanzu a wajanka na bar maka ita halak malak har abada, da zarar mun dawo daka Rano duk zan raba auren su wanda bai yi mini wata rana ba, zan bata mijin da yanzu fitila ta haska mini da cewa; shi ne ya fi cancanta da rayuwarta, ba zance umarni nake baka ba, ba kuma zance saƙon zuciya zuwa zuciya bane, ina da yaƙinin cewa wannan ɗin tamkar WASIYYA ce, rashin tabbaci kawai nake da shi, Na barka lafiya yanzu zamu ɗauki hanyar zuwa Rano duba kakarku_ Tunda Ustaz yake a rayuwa bai taɓa shiga halin daya shiga irin yanzu ba, rana mafi dana sani a rayuwarsa shi ne ranar auren Ridayya, sai yanzu da wannan ranar take bin bayanta suka zama tagwaye. Zufa ta dinga yanko masa jiri ya shiga ɗaukarsa. Da sauri ya fara dubawa ko zai samu jirgin da zai kai shi ya isa Ranon? Cikin dare ko gama kimtsa wa bai yi ba ya nufi garin Rano. Mamakinsa bai shige ganin babu wani ahhali ko guda ɗaya ba, sai Hajiya wacce jikin nata yake da sauƙi ta sa shi gaba da tsokana ya fara tsofa babu aure. "Hajiya su Baffa?" Ta ɗan yi sak sai kuma ta ce "Mun yi waya da su, tun kwanaki biyu baya ya ce sun taho amma har yanzu shiru" Mai ran ƙarfe ya ce "Babu mamaki ɗaga tafiyar sukai domin umarni na bayar a tattaro mini kowa a zo da shi, har da wannan yarinyar mai kama da baƙar tukunya rabo na da ita tun tana shan nono babu wanda nake kwaɗayin gani sai ita" Ustaz ya ce "Baku sake waya ba?" Ta ce "A'a, mene damuwar wai suna nan tafe In sha Allah" Ustaz ya girgiza kai sai kuma ya miƙe ya fice, number maƙocinsu ya kira ka ce ai kwanansu biyu da yini da tafiya, tashin hankali ya ƙara shigar Ustaz duk inda zai bincika labarin hatsari wanda baya fatan ace haka ɗinne ya yi amma ba wani labarai da suke yawo ba hatsari daga Kano zuwa Rano, Asibiti zuwa asibiti ya dinga dubawa har mutuware amma shiru. Watan uku da yunƙurin zuwan Ridayya gida wanda Zameer ya yi munafurci ta fasa kenan. Tana zaune banda mugwayen mafarkai babu abinda take yi. Kwaɗon kwaki ne a gabanta wanda ta baɗa masa gishiri ta kasa ci, Zameer ya ɗaga labule daga waje yana ƙare mata kallo ya ce "Ga kayan wanki na nan" Kai kawai ta jinjina ya ƙanƙantar da idanunsa cike da masifa ya ce "Ba'a yi mini magana da kai, nikam ba a yi mini ban so" A hankali muryarta bata fita sosai ta ce "To, kuɗin Omo da ruwa" Ya ɓata fuska ya ce "Nan fa ɗaya, ki ranta mini ruwa kuma ki shiga gidan matar can ki ja a rijiya" Da jemammun idanunta kawai take kallonsa magana ma bata ƙaunar yi ko kaɗan "Kana gani bani da lafiya ka tausaya mini mana, Khairiyya ta ja ruwan" Ya zaro idanu waje sosai ta ce "Tamɗijam! Lallai kin samu matsala ki duba fatarki ki duba da baby Khairy ɗaya ce? Farar fata ai bata san wahala ba, kuma ke aure kike bautar aure za ki fa Ridayya ladanki yana wajan Allah" Ya girgiza kai yana riƙe ƙugu ya ce "Kambu to na saka Khairy jan ruwan guga ai Ubangiji ba zai yafe mini ba, saboda na ci zarafin kyakkawar halitta, ko aure ta yi mijinta ya ce ta ɗakko wallahi ubansa zan ci" Yar da yake magana haka take binsa da kallo zuciyarta fal mamakin abu biyu, baby Khairy, ko aure ta yi zai ci uban miji cike da damuwa ta ce "Aure baya nufin bautar da mace Rayuwata, biyayyar gidan miji ai ba bauta ba ce" Ya ɗaga kafaɗunsa ya ce "A to!" Ya zuciya sai fita ta ce "Ashe Khairy baby ce kuma yanzu?" Ya tsaya turus gabansa na faɗuwa ya ce "E, haka babanmu ke ce mata baby saboda mugun kyan da take da shi, she's so romantic" Duk da ilimin Ridayya bai yi zurfi ba ta fahimci me yake nufi ya ce "Ki aro iron ki goge mini" Ya fita domin burinsa bai huce ya ciwo maƙudan kuɗaɗen da aka zuba a caca ba. Zanin wata atamfarta ruwan huda ta yafa ta ɗauki bokici ta shiga gidan Zainaba. Zainaba na zaune tana kaɗa miyar abincin dare ta ce "Wai ikon Allah yau kuma" murmushi Ridayya ta yi dugun bakinta ya washe haƙora suka fito kamar ƴar shekaru 50 don tsofa. "Mara ba lallai yanzu muke maganarki ni da Baban hajjo, yana jira ki bani labari na je na bashi har da mafarki na yi jiya" Ridayya ba ta yi magana ba. Can ta ce "Ruwan zan ɗiba" Zainaba ta ƙura mata ido sai bata ce komai ta ce "Zan saka Almajiri ya kawo miki, zauna kici abinci" Ta girgiza kai "Allhamdulillah na ƙoshi" Zainaba ta miƙe ta zuba mata tuwon samo har da bushsshen kifi ta shimfiɗa tabarma ta ce "Yau banga abinda zai saka ki fita kibar gidan nan ba" Dole Ridayya ta zauna ta fara cin tuwon hannu baka hannu ƙwarya ta kawo mata kwaɗon zugala domin jinin jikinta ya dawo harda yanka mata dafaffen ƙwai kafin ta gama ci Almajiri ya fara kaiwa Ridayya ruwan. "Ciki ne dake Ridayya" Ridayya ta zaro Idanu waje ta ce "Ciki kuma?" Murmushi kawai Zainaba ta yi ta ce "Wallahi ciki gare ki na jima da fahimta, kamar yar da na fahimci Khairy ma ta haɗiyi wake" Ridayya bata gane irin wannan maganganun ta ce "Haɗiyar wake kuma? Kamar yaya" Zainaba ta ce "Za ki gani ai shi ɗan duma ne watarana zai fallasa kan shi, ƙwai zai fashe warinsa ya adabin uban kowa musamman mamallakinsa" Ridayya ta yi shiru "Ki bani labarin tunda kin shigo mini yau" "Wannan labari" Zainaba ta ce "Shi fa, wallahi na ƙagu" Ridayya ta lumshe idanunta hawayen dake ciki ya sakko a nutse ta ce "Ta ina zan fara? Labarin Ridayya mai girma ne, girman da ko wacce ɗiya mace musamman budurwa da matar aure jinsa zai yi mata amfani" Ta yi jim "Rayuwata a wajan Amma zan faɗa miki? Ko zamana da Abbiey zan labarta miki? Ko kuma juya mini baya da mahaifina ya yi ne zai zama farkon labarin ko haɗuwata da Zameer?" Zainaba ta kawo kujera ta zauna ta yi taƙumi ta ce "Fara mini ta farko yadda zan fahimta" murmushi kawai Ridayya ta ce "Taya zan ba ki labarin abinda bana duniya ya faru sai dai abinda aka bani labari zan iya" Zainaba ta ce "Yawwa ai farkon zai fi citta ƙila shi ne soyayyar Baffa da Mami ko?" Ridayya ta ce "Da farko dai...." Da sauri ta yi shiru zumbur kuma ta miƙe jikinta na rawa da ɓari ganin Zameer a kanta Zainaba ta ce "Ya zaka faɗo mini gida babu umarni kamar ana zaman bariki" Bai kula Zainaba ya finciki hannun Ridayya tana turjewa ya fara janta a ƙasa, maƙota duk suka fito har da mazajensu babu wanda ya iya dakatar da Zameer, Zainaba ta dinga ƙundumawa Meer zagi tana faɗin "Tsinanne haihuwar asara Allah ba zai bar ka ba, In sha Allah Ridayya ta kusa rabuwa da kai faƙirin banza cima zaune" Maganganun Zainaba kamar saukar dalma haka Ridayya take jinsu a zuciyarta, jin yar da take tsinewa mijinta da yadda take fatan aurenta ta mutu baƙin cikin haka ya saka Ridayya rushewa da kuka. Zameer ya rufe ƙofa baka jiyo sautin komai sai ihun Ridayya da saukar bulalar wayar caza "Iskancin banza da wufi ni za ki kawowa ɗan iska har gida, wato kema Idanunki ya buɗe abinda na gudu kenan na datse karatunki, shi ne za ki shigo mini da kwarto har cikin gidana?" Ridayya tuni numfashinta ya tsaya Khairy na tsaye ta ce "Shi ya sa ban taɓa faɗa maka ba ai wallahi kar ta ce sharri nake mata, yanzu ai ka gani da Idanunka" ran Zameer ya ɓaci domin baya wasa da duk wani abu daya shafi alaƙar gado tsakaninsa da Ridayya cikakkiyar gamsuwa a wajanta yake samu dukda bata tsinana masa da uwar komai, kamar ruwa haka take zama, she's not romantic at all. Amma baya jin zai iya sharing ɗinta da wani banza ya shige ɗaki Khairy ta bi bayansa suka rufe ƙofa Ridayya na shimfiɗe kamar gawa. Hajiya da Mai ran ƙarfe ne suke jijjiga Ustaz amma ina ya jima da fita daga hayyacinsa, a gigice Bintalo ta shiga yayyafa masa ruwa amma ko motsi bai yi ba, Hajiya ta fara kuka wiwi don a duniya tana ƙaunar Ustaz ta jima bata taɓa ganin mutum mai zurfin cikinsa ba, taurin zuciya kafiya da na ci da kuma haƙuri da kawaici. Firfita take masa tana shafa kansa "Innalillahi! Mene shirin faruwa ne mun shiga uku" Mai ran ƙarfe ya ce "Maganin shiga uku Allah, ciwon Ustaz ne ya tashi yi ta yi masa firfita, Bintalo ci-gaba da zuba ruwa a kansa" Gabaɗaya suka rufo akan Ustaz su shafe mintuna kafin ya sauke ajjiyar zuciya idanunsa rufe bakinsa na motsa wa shi kaɗai ya san me yake cewa "Bilalu lafiya,ina dalilin wannan ciwo naka?" Ya sake rufe idanu da tunani inama ya buɗe idanu yaga mafarki yake. Hajiya ta riƙo fuskarsa ta shiga girgiza shi ta ce "Yi magana Bilal buɗe Idanunka" "Baffa, Abba, Mami, Amma, Junaid, Balkisa, Zuhura, Zainura, Aliyu, Usman, Umar, Abubakar...," Ya kasa ƙarasa maganar Hajiya ta ce "Mene ya same su? Suna ina yi mana bayani Ustaz" Nutsuwa ya tattaro ya aza bisa gangar jikinsa ya daure ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" "Ustaz wai mene haka?" A hankali yana fusgar numfashi ya ce "Ba a gansu ba, suna mace suna raye tsayin watanni..." Kafin ya ƙarasa faɗa Hajiya ta yanke jiki ta faɗi. Zameer na zaune shi da Gaza ya ce "Zameer baka son yarinyar nan ka sakar musu ƴarsu?" Wani irin murmushi ya yi ya ce "Hauka ma kenan" "Kamarya Hauka mene fa'idar zamanku aure ba soyayya ba kulawa" Zameer ya gyara zama ya ce "Tunda nake a rayuwa ko da second guda ban taɓa jin son Ridha ya gitta ta zuciyata ba, ban taɓa ji ba" "Than, you have to divorce her" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Shi ne ba zai iya ba, domin akwai amfaninta yana nan zuwa musamman yanzu dana fahimci ciki gare ta" Gaza ya ce "Ikon Allah, mene shirinka sanar dani please" Murmushi kawai ya yi ya ce "Babar Ridayya na da kuɗi sosai da wanda aka bar mata gado da wanda ta mallaka nata na kanta, na saka an duba mini wajan ƊAN GADO, Malamin ya iya aiki" "Kenan asiri ka yi wa ƴar mutane" Ya girgiza kai ya ce "Ko kaɗan wallahi ban taɓa yi wa Ridayya asiri ba, ai ba zan ɓoye maka komai ba nasan dai ina zuwa ana yi mini duba, plan ɗina shi ne da zarar iyayenta sun baza zata mallaki kadara nai yawan gaske, zan buƙaci ta bani na juya mata amma ko wanne ta yi sa hannu da sunana" Dariya Gaza ya yi sosai ya ce "Saboda ita bata da ilimi" kai tsaye ya ce "Ina ta ganshi, ai dabara na yi na datse mata karatu saboda karma idanunta ya buɗe ta ce zata iya juya kadarorinta, tana gama secondary a ajinta na farko na jam'i na datse karatun idan ina raye ai ba zan bar Ridayya ta yi ilimi ba balle ta mallaki wani abu nata na kanta, soon rabata da garin nan" "But You don't love" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Ita ai tana so na, zata iya mutuwa saboda ni soyayyarta a gare ni ita ce rauninta na fahimta, yanzu ma goga take mini" Sallama sukai yi tare nufar gida. Kasancewar bata samun bacci sosai ya sa tana tsaka da goga bacci ya ɗauketa. Hayaƙi ya cika ɗakin da sauri Zameer ya shigo gani ya yi sabuwar shaddar shi ta babbake Allah ya sa dutsen bai buga ba. Ya kalli Ridayya ya kalli kayan cikin ɓacin rai dutsen da ya yi jajur da wuta ya ɗauka ya manna mata shi a fuska. Ihun a zaba ta saki da sauri ta shafa fuskarta sai fata ta biyo hannunta rabin fuskar ya kwailaye kafin ta dawo hayyacinta ya yi ball ta ita ya taka mata ruwan ciki azaba ta saka ta saki fitsari da tusa a wajan ya juya ya fice daga cikin gidan, kuka ta kasa ta riƙe cikinta sai birgima take a wajan har gari ya waye tuni kamanninta suka sauya. Ta fito da ƙyar zata shiga banɗaki ta ji Khairy na waya tana cewa "Na je likita ya tabbatar mini ciki ne dani" Ridayya ta nemi ciwo ta rasa ta saki butar hannunta ta nufi kitchen wata sharɓeɓiyyar wuƙa ta ɗakko kai tsaye ta nufi ɗakin Khairy da wuƙar a hannunta.... Idan naga comment gobe kuga posting da wuri. Muna godiya da zaɓar BRIGHT PENS🫶🏼🤙🏼 *✿ MUNAFUKIN MIJI ✿* Nimcyluv@Arewabooks Page 9 BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Khairy na kwance akan gado daga ita sai gajeren wandon Zameer, tana danna waya tare da ƙyaƙyacewa da dariya. Kamar daga sama taga Ridayya ta faɗo cikin ɗakin tana huci kamar wata mahaukaciya, jiri sai neman ka da ita yake neman yi amma ta turje. Tsirarar wuƙar ta nunawa Khairy tana nufar wuyanta da ita, idanunta jajur hawayen baƙin ciki na zuba daga cikin idanunta, na tsananin kishi da soyayyar Zameer, imagining take ita cikin ya tabbata yana da kusanci da Zameer, to; a cikin biyu za a yi ɗaya, ko dai ta kashe Khairy ko kuma ta kashe kanta ta huta. "Kar ki mini ihu a ɗakin nan, daga ni sai ke ba ki da wani mataimaki" Ridayya ta furta tana sake nunawa Khairy wuƙar. Ganin haka yasa Khairy rikicewa tsoro ya ɗarsu a zuciyarta. Bakinta na rawa da ɓari ta ce "Na shiga uku me na yi miki da zafi haka Anty Ridayya? Me ya sa kika tsane ni?" "Riƙe kalamanki marasa daraja a wajena Khairy, bana buƙatar duk wasu shaci faɗe naki, idan yau ki kaga ban kashe ki ba, to wallahi gaskiya kika faɗa mini" Ganin al'amarin Ridayya da gaske ne domin ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta, maganganun fitar da kansu kawai suke ba tare data shirya ba ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Kisa kuma? Kashe ni za ki yi, me na yi miki kina cikin hankalinki kowa?" Ridayya ta yi dariya sosai dukda cewa bakinta a waskace yake, fuskar ta tattare saboda ƙona ta da Zameer ya yi, muninta ya sake bayyana ƙarara idan ka kalli fuskar Ridayya ba za ka so ka sake kallo ba. Ridayya ta ce "Idan na yi miki lahani, na saɓa miki kamanni tare da ji miki rauni na kashe ki za ki gane ban haɗa hanya da dawanau ba balle a laƙaba mini sunan mahaukaciya, Khairiyya ki faɗa mini cikin waye a jikinki, mene ya haɗaki zama da ɗakin mijina bayan ga naki can? Ina dalilin sanya sutturar mijina bayan ta haramta a gare ki, gajeren wandonsa, tsaraicinsa ne" Lallai daman an ce; mai haƙuri bai iya fushi da tara mutum ba. Khairy ta rikice ta rasa da wanne kalamai za ta yi amfani da su wajan shimfiɗa ƙaryar da zata tseratar da ita, daga haukan Ridayya domin ta gama tattarawa tare da azata a gurbin sabbin masu taɓin hankali. "Ci...ci...ciki kuma? Ni mene haɗina da ciki? Wallahi....," Kafin ta ƙarasa maganar Ridayya ta sauke mata wuƙa a gefen hannunta, nan take wajan ya dare jini ya fara zuba. Khairy ta zunduma ihu tare da faɗin. "Wayyo Allah, mahaukaciya ce wallahi mahaukaciya ce jama'a a kawo mini ɗauki" Ridayya ta sake sheƙewa da dariya ta ce "Ai na faɗa miki, kashe ki zan yi muddin ba ki faɗa mini cikin waye a jikinki ba" Suka shiga zagaye ɗakin, Khairy na riƙe da hannunta tana ihu a kawo mata ɗauki, amma tsit kake ji, tamkar malam ya ci shirwa. "Khairiyya kenan ki daina ɗauka ban san me nake ba, na sani ni yarinya ce, you're smarter than me, tunaninki da nawa ba ɗaya bane ba komai nake ganewa ba idan, idanuna suka makance, wallahi a yau ko za a kashe ni, ko zan tafi gidan yari sai kin faɗa mini gaskiya ko na kashe ki a nan, idan ya so a yi jana'izarmu tare Ubangiji ya yi mana hisabi ya kuma tantance mai gaskiya" Khairiyya na kuka sosai, bawai don Ridayya ta fi ƙarfinta ba, saboda makamin dake hannunta ba a wasa da mai wuƙa. "Bani da ciki, mene zai haɗani da ciki kuma? Ki yi mini rai ni gidanki ma zan zo na tattara na bar miki, idan hakan zai zama farin giki a gare ki, da nutsuwar zuciyarki" "Hehehe ki je ina? Ai ni dake mai ƙarfi yau shi zai ƙwaci kansa lashakka, ki bar gidan Ridayya matar mijin Zameer ban miki lahani ba? Ai ƙarya kike, Har ka tuna mini, an ce da mahaukaci ba ka duka, har ke ce kike cire kaya a gaban mijina ko? To bari na cire miki nono ɗaya sai naga gobe me za ki nuna" A gigice Khairiyya ta ce "Na shiga uku wallahi kin haukace, banda haka ni da nake ƙanwar miji meye na ɗora zargin naki akai na?" Ridayya ta ware idanu ta ce "Au, ba rami mene ya kawo rami? Kin ji na Amjat zargi? Haka tara, in ji kishiyar mai mageduwa, ai shi ɗa na kowa ne, ƙanwar miji ai ƙanwa ce, dole na ba ki tarbiyya saboda gudun bakin jama'a" Khairy ta ce "Don Allah ki barni na fita, na je gidanmu babu wani ciki a jikina" Ridayya ta ce "Kin san Allah, wallahi ba zan barki ba, kowa ya yi maka kan kara, yi masa na itace" Da gudu Khairy ta juya ta nufi wajan ƙofa ta sunkuya zata buɗe, Ridayya ta sauke mata wuƙar a wuyanta ta ƙara sauke mata a damtsen hannu, Khairy ta gantsare tana kare cikinta don a duniya yanzu ba abinda take so dama da cikinta. "Jama'a wai ba kowa a gidanne? Zata kashe ni wallahi kashe ni za ta yi matar yayana ta haukace ku kawo mana a gaji" A guje ta buɗe ƙofa ta fita Ridayya ta bita da sauri, daidai nan Zameer na shigowa da Zainaba idanun Ridayya rufe kallon Zameer take tamkar Khairy ce a gabanta. Yana zuwa ya kifa wata wasu lafiyayyun maruka guda biyu sau biyu a jere ta yi taga-taga zata faɗi ta cake waje guda. Khairy itama wuƙar ta ɗakko ta ce "Wallahi ba ki jimi ciwo a banza ba, ƴar ta'adda kawai" Ridayya ta yi murmushi hawaye na fita daga idanunta bakinta na rawa ta ce "Haka nake so daman, ko dai ki kashe ni ko kuma na kashe ki" Khairy ta ɗaga wuƙar zata kwaɗawa Ridayya a gigice Zainaba ta hankaɗa Zameer tsakiyarsu daidai nan Khairy ta sauke masa wuƙar a mara, ya fasa ihu yana riƙe gabansa saboda wani azaba daya tsarga masa jini ya fara zuba, ya faɗi ƙasa Khairy ta shiga ɗaki ta rufe ta fara haɗa kayanta. Ganin Zameer kwance a ƙasa cikin jini ya dawo da Ridayya daga hayyacinta, ta rarrafa ta nufi inda yake ta fara jijjiga shi tana kuka tare da furta "Ka tashi rayuwata, ka yi mini rai kar ka barni a cikin wannan halin da nake ciki" Zainaba ta ce "Ridayya mene ya sameki a fuska? Gobara kukai ta cinye rabin fuskar ko annoba ce ta faɗa miki? Zameer kuma ina ruwanki da shi, ai bake kika ji masa ciwon ba ki yi ta kan ki kawai" Wani irin kallo Ridayya ta yi wa Zainaba ta ce "Ki fita daga rayuwata ki barni haka, mene rayuwarki da gidan aurena da mijina kuma? Kin saka mini ido kin takura ni" "Ridayya ni kike faɗawa haka saboda kina son maso wani? Makauniyar soyayyar da bata da wata riba wajanki, munafukin mijin naki cima zaune wahalalle maƙaryacin" kuka kawai Ridayya take kafin ta ce "Kima siyar da rayuwa take, soyayya kuma bada rayuwa take, ki saurara mini ki barni ki tsahirta mini...," Saukar bulala ta ji ta ko'ina a jikinta, tun yana dukan ta da bulala har ya fara saka ƙafa yana ball da ita tare da taka mata ruwan ciki, daman buta ta ɗauka zata shiga banɗaki ta fasa, azabar bugun mararta da ya yi ta saki kashin wahala a kiɗime take cewa "Na tuba ka yafe mini tausayi ne, don Allah ka da ka kassara mini ɗan cikina" Bai kulata ba, dukanta yake da ko'ina tana ihu da ƙoƙarin guduwa har ta kasa motsi. Zainaba mutanenta na kusa jikinta ya fara rawa da ɓari ta ƙura wa Zameer idanu kafin ta yi ihu ta zube a ƙasa tana surutai. "Tsinanne maciyaci, mugu macuci ba za mu barka ba, ka zalunci yarinyar jama'a ka ajiyye karuwa a cikin gidanka ƙarya yake ba ƙanwarsa ba ce zaman cin amana suke bashi da kowa a garin nan" Da sauri Zameer ya ce "Munafukar banza na ci uwar aljanun" Domin ya ɗauka aljanun ƙarya ta yi. Baban hajjo Usman ya yi sallama Zameer ya ce "Yawwa! Babu matarka babu tawa duk abinda na yi mata zunubinta ya ja mata, ba zata raba mini aure na kasa gane kan matata ba" Usman ya ce "Ai kowa ya yi na gari kansa, daɗin abin ba a duniya za mu tabbata ba" Yana faɗin haka ya kinkimi matarsa sukai waje, Zameer ya shige banɗaki sosai gabansa da mararsa ke masa ciwo har ɗingi shi yake. Yana fitowa ya shiga ɗaki ganin Khairy ya yi tana haɗa kayanta da sauri ya ajjiye wayar hannunsa ya nufi inda take, ta yi saurin kauce wa ta ce "Kar ka taɓa ni, kar ka fara" Zameer ya sauke numfashi yana yin ƙasa da murya. "Haba dear, ki sassauta hukuncin nan" Khairy ta ce "Wato ni ba ƴa bace saboda ina zaman bariki da kai ko? Wallahi idan kaga ba haƙura ka bi mini hakƙina" Riƙota ya yi gabaɗaya ya haɗe ta da jikinsa yana sauke mata numfashi a wuya idanunsa a saman kyakkawar fuskarta, a nutse daidai kunnenta ya ce "Za ki iya barina ashe?" Ya faɗa yana fesa mata iska a kunne. Jikinta ya saki sai kawai ta fashe da kuka ta ce "Ka sauya mini matsayi, ka mayar dani matarka, zan yi istibira'i mu yi aure mu huta da wannan rayuwar na san cewa zaman kishi nake da tsinanniyar matarka mai zubin aljanu" Hannu ya sa ya matse bakinta a hankali ya ce "Kar ki mini tsiwa, ke kika bari har tasan da cikin amma nasan me zan yi" daga nan rufe ƙofa sukai abinsu tare da barin Ridayya yashe a ƙasa. Usman ya ce "Kema Allah ya ƙara ya daɗa, kafirin iyayinki ne ya ja miki wahala" Zainaba na kuka ta ce "Baban hajjo ba zaka gane ba, jin Ridayya nake kamar ƴar'uwata wallahi tausayinta nake ji sosai" Bai ce mata komai ba don baƙin ciki yana jin da shi mai kuɗi ne babu abinda zai hana shi maka Zameer a kotu ko kuma ya kaiwa hisba ƙara. "In sha Allah Zameer sai ya wulaƙanta ba zai taɓa ganin daidai ba, ba kuma zan bar shiga gidan nasa ba" "Azzalumi ba fa dole sai ya wulaƙanta ba, muddin zai tuba wajan Ubangiji" a fusace ta ce "Banda munafiki irin Zameer wanda shaiɗan ya yi wa fitsari aka". Sanyin yamma ne ya dawo da Ridayya daga suman da ta yi, ta motsa kaɗan tare da yin ƙara saboda wani nauyi da hannunta ya yi mata, da ƙyar ta miƙe zaune sai a lokacin ta farga da kashin da ta yi, ta runtse idanunta zuciyarta na zafi da raɗaɗi na rashin mafita da abin yi. Ba zata iya tashi ba don haka ta dinga jan jiki zuwa banɗaki ta wanke jikinta tas, kana ta daddafa ta fito tare da haɗa kai da qwiwa ta shiga sauke ajjiyar zuciya wani irin matsanancin tsoran Zameer ya kamata, haka kurum ta shiga razana ita kaɗai, ga ciki a jikinta, ga duka ga wata kafurar yunwa dake mata barazanar raba mata hanji. Tunaninta ya tsaya kwakwalwarta ta gaza yin aikin komai da sarrafa wasu kalaman na Zameer. Bata da burin daya shige zuwa gidansu wajan Mami. A hankali ta miƙe ta saci jiki ta fice daga cikin gidan. Duk inda ta gilma kallonta ake ana nunata, domin kawo yanzu a wannan sabon zamanin da muke ciki ba kowa zai kai Ridayya gidan miji ba, amma a yarda ake kallon nata da yawa sun ɗauka wata dattijuwar ce. Turus ta yi lokacin da taga gate ɗin gidansu a garƙame, gabanta na faɗuwa wani yaro ta gani, ta ya fito shi da hannu da gudu ya runtuma yana "Wayyo mahaukaciya" Ridayya ta dinga kallon kanta can wata yarinya ta fito daga gidan dake kusa dana su Ridayya, ta ce "Don Allah masu gidan nan fa?" Yarinya ta kalli Ridayya tana ja da baya ta ce "Sun tafi Rano, sun daɗe da tafiya na ji ana siyar da gidan za a yi" "Siyar da gida? Rano?" Ridayya ta maimaita a fili, yarinyar tuni ta juya, zama ta dinga yi a wajan abin mamaki duk wanda suka zo shigewa sai su ajjiye mata kuɗi a gabanta, wani irin hawayen baƙin ciki ya ziraro mata a ƙofar gidansu ake bata sadaƙa? Ganin tana samun kuɗi taƙi tafiya har aka kira magriba, ta rarrafa ta miƙe a hanya ta siyi taliya guda ɗaya, da kayan miya da magi da mai. Tana zuwa ta fassakara itace tare da dafa jallof ɗin taliya ta saka daddawa. Zameer da Khairy suna ɗaki suka jiyo ƙamshin abinci nan da nan kwaɗayin masu ciki ya addabi Khairy ta ce "Baby matarka ke girki?" "Ina ta ga kuɗin?" Saboda basu san ta fita ba ta ce "Ka duba please wallahi hankalina duk ya tashi" Ya yi murmushi yana cireta a jikinsa ya ce "Idan ma ita ce dole zata bani ba zata iya cin abinci banci ba, idan ta bani zan kawo miki" Yana fita ya samu Ridayya na juye taliyar a faranti daman rabi ta dafa, ya tsaya tare da sassauta murya ya ce "Ridayya mai sona girki kike?" Shiru ta yi masa don magana yanzu sai dole ga zugin fuska gana hannu da ƙyar take motsa shi. "Fushi kike dani? Bari na yi sallah na dawo mu yi magana ki jira ji" A hankali ta ce "To" Yana fita ta saka hannu a faranti ta fara cin taliyar ta cinye tas, saboda baƙar yunwa ta suɗe farantin kana ta yi alwala tare da yin Sallah, hannu ta ɗaga ta rasa wacce kalar addu'a za ta yi sai kawai ta yi shiru. A zaune ta sameta ya ce "Ba dai kin cinye abincin ba?" Ta ce "Wanne abinci?" Ya ce "Wanda kika dafa" ta yi shiru ya sake magana shiru, ji ya yi kamar ya zabga mata mari amma ya daure "Fushinki a zama ce mai raɗaɗi a gare ki wife, zan jure shurin kowa banda naki" Nan ma ta yi shiru. Cike da makirci ya fashe da kuka yana riƙe hannunta ya ce "Saboda Allah ya jarabce ni da son ki, kike wulaƙanta ni Ridayya? Laifi ne don na so ki? Mene laifin zuciyata kar ki hukunta ni ta haka, nikam kar ki mini wannan azabar zan zutu da yawa" Kuka yake sosai ya ce "I love You Ridha, wallahi ina son ki, ki yafe mini abinda na yi miki jiya" "Me ka yi mini?" Ya ce "ƙona ki da dutse, wallahi lemo aka bani na sha ashe akwai ƙwaya a ciki ita ta buge ni, har na ci zarafin matata ƴar aljanna, ba zan taɓa yafewa wanda ya sa na yi shaye-shaye ba" Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ba komai" Ya rirriƙe hannunta ya ce "Hankalina ya tashi gudun kar ki yi kisan kai a kashe mini ke ya sa na dake ki, bawai saboda kin jiwa Khairy ciwo ba" Ya sauke murya ƙasa yana tausasa kalami ya ce "Wanne irin miji ne ni? Ridayya ban cancanta da rayuwarki ba ina zaluntarki, ki bari na sawwaƙe miki" Ya faɗa yana bugar cikinta. "A'a, ka rufa mini asiri bani da kowa yanzu sai kai" Ta faɗa tana girgiza masa kai, ya ɓoye dariyarsa ya ce "Me ya sa kike zargin Khairy dani? Saboda ban taɓa faɗa miki Khairy nada aure ba? Laifina ne ƙanwata Khairy nada aure saɓani suka samu da mijinta shi ne ta nufi gida, a gida aka hanata zama ana ganin laifinta ne, ganin hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ya saka na dawo da ita gidana kafin Allah ya daidaita labarin auren" "Kuma ciki bai bayyana ba sai yanzu?" Da sauri ya ce "Kwanciya ya yi, ai kwantawa cikin ya yi amma gobe zan je na same shi zata koma ɗakinta shikenan?" Ta jinjina kai kawai ya ce "A'a ki ce kin yafe mini" Ta ce "Ya shige ba komai ka bata haƙuri" Ya yi sai kuma ya ce "To ɗakko mana abincin muci mai sona" Ta ware idanu ta ce "Bani da abinci,nima bata ishe ni ba" Wata uwar ashariya ya narka Ridayya a zuciyarsa ya fice. Yana fita Khairy ta shigo ta ce "Yanzu kin fahimta ko?" "Ki yi haƙuri ban ɗauka haka ba, Allah ya daidaita tsakaninku" Khairy ta ce "Wannan turaren naki da maganin matan za ki sammin please" Ridayya ta nuna mata lafiyayyiyar humra ce da kwalacca, tun kafin ta buɗe suka cika ɗakin da ƙamshi ita kanta Khairy ta san humra ɗin ta musamman ce ba a ko'ina ake samun irinta ba, tafiyayyiya ce, sai ka wanke kaya sau nawa ƙamshinta bai fita ba. Ta duba maganin matan duka ta kwashe ta yi waje Ridayya sam bata damu ba hankalinta ya kwanta bata da matsala da Khairy bata damu da sanin me za ta yi da kayan matan bai tunda ba a gidan miji take ba. Cikin dare Ridayya ta kasa bacci hannunta ya kumbura, fuskarta sai jini take. Kamar an cillo Zameer haka ya faɗo ta kalle shi ya ce "Ina buƙatar ki" "Bani da lafiya, marata ciwo take hannuna haka ga fuskata" Rai ɓace ya ce "Nina ɗora miki ciwon? Sanda na biya sadakinki kin faɗa mini ba ki da lafiya ne? Bayan ba uwar tsiyar da kika iya sai dai ki kwanta kamar ruwa? Allah ya ƙara mini haƙuri, ga babu gyara ɗan ƙamshin nan na zamani ɗan farin da mata suke" "Dame zan yi kwalliyar? Duk abinda na mallaka wana bawa ina cewa kai ne? Ya kake so na yi wai me ya sa duk ka sauya?" Ya ce "Bai dame ni ba, hakƙina na zo amsa" Mamaki ya cika ta ganin yana rufe fuska da face mars, daman tunda suke irin sumbatar nan ta Zameer bai taɓa yi mata ba, tamkar yana ƙyanƙyamin bakinta "Idan har da yarda ta ce to I'm not in the mood" Ƙafa ya saka ya maketa ta faɗi ƙasa kamar mahaukaciya babu tausayi yana ya haike mata babu kulawa ba soyayya, ya yi forcing nata ne tunda bada yardar ta ba, haka ya shaƙe mata wuya tana kakari gabaɗaya bai san me yake ba kamar zai kasheta... Kuka ta dinga yi ta kasa motsi saboda wahala wuyanta duk shacin yatsunsa saboda shaƙa. Washegari bayan Zameer ya fice Khairy ta shirya ta fice wajan samarinta. Mai gyara Zainaba ta kira ya duba hannun Ridayya ashe karyata Zameer ya yi tana kuka sosai da muryarta mai sanyin nan kamar shagwaɓa, saboda bata da hargowa sam. Bayan an gama Ridayya ta kwaɓe fuska ta kasa kallon Zainaba, murmushi kawai Zainaba ta yi ta ce "Alkawari na zo ki cika mini, ki bani labarin rayuwarki kafin aure" Ridayya ta lumshe idanunta ba dan ta so ba ta soma bawa Zainaba labarinta kamar haka..... *Ga duk mai buƙatar humra da kwalacca lafiyayyun sa mai gida magana ka hanzarta neman wannan number 08164069385 suna aikawa ko'ina, akwai ta masu ƙarfi akwai ta masu ƙaramin ƙarfi, ba za ku taɓa ladamar siya ba muna maraba da masu siyan ɗaiɗai ko sari🥰🥰🤙🏼🤙🏼* *✿ MUNAFUKIN MIJI ✿* Ridayya's story Page 10 BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Please ku yi following nawa a facebook🫶🏼👇🏼 https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL *PAID ADVERT* https://chat.whatsapp.com/LvflCjMI3U5IfUHobHzudk *HAUSA AFFILIATE MARKETING (HAM COURSE)* Yadda zaka samu kuɗi a ƙalla 50k- 100k a wata online da wayarka ta hannu (Smartphone) Matan aure, Ma'aikata, Ɗalibai, Ƴan mata e.t.c 07063194432 *Ta ina zan fara ne? Ta haɗuwar Ridayya da Zameer a jami'a ko kuma ta amintarta da ƙawarta Mardiyya? Ko dai na fara ta riƙon da Ustaz Bilal ya yi mata, girman ƙaddarar nada faɗi, al'ajabinta na da girma, dafin ƙaddarar kan iya harbar kowa, babu kuma wanda akai wa shamafiki da zubar hawaye. lissafin ƙaddarar zai fi tafiya daidai, idan muka fara da tubalin ginin, ya sanya zan fara da sanda Ridayya Bilal Mansur Rano ta zo duniya!* Gabaɗaya suna tsaye sun yi carku-carku yanayin sauyin fuskokin kowa zai labartawa mai kallon su akwai lauje cikin naɗi, abu biyu ya sanya zuƙatansu cikin halin da suke, dukda bai cancanci ace akwai damuwar da kan iya hana fara'ar fuskarsu bayyana ba, duba da tagomashin abin alherin daya samu zuri'ar Mai ran ƙarfe a safiyar yau ta juma'a. A kuma unguwar Darmanawa dake Jihar Kanon Nigeria. Ciwo ɗaya idan ya samu mutum ɗaya a familyn, to kamar ya shafi kowanne daga cikin ahhalin ne kasancewar su, marasa yawa da girma, kowa a hargitse yake idan ka ɗauke Alhaji Mansur Rano, wanda ko zuwa cikin asibitin bai yi balle a san halin da yake ciki. Shekaru aru-aru bai taɓa nuna rashin kulawa akan jininsa ba sai yau, ranar da kowa ya girgiza ya kuma ji a jikinsa tare da shakkar Alhaji Mansur Rano, jinkimarsa da ainahin ɓoyayyiyar siffarsa ta bayyana, wacce ta nuna asalin halinsa wanda inuwarsa ta lulluɓe tare da yi wa jama'a katanga da ita. Reception ɗin asibitin a cike yake idan ka ɗauke wanda baya garin ma. Dr ya fito da sauri yana goge zufar data yanko masa, cikin sauri kuma Hajiya ta miƙe tare da tarar shi tun kafin ya ƙarasu. "Likita ya ake ciki? Yarinyar nan har yanzu, ba amo ba labari wacce kalar naƙuda ce wannan?" Dr ya yi jim sai kuma ya ce "Sai haƙuri Hajiya..," Jikin Hajiya ne ya fara rawa nan da nan ta nemi rikicewa zuciyarta na bugawa ta ce "Ka...ka.. kamarya sai haƙuri? Kada ka kuskura ka ce mini Fatima ta rasu, kar ka ce mini na rasa surukata da abinda ke cikinta?" Ƙoƙarin yi mata bayani yake amma bashi da zarafi da ƙarfin qiwwar yin haka, shi kansa bashi da tabbaci wacce ake magana tana raye ko ta mutu ne. Amma ce ta share hawayen dake gudana a idanunta ta miƙe da ƙyar ta nufi inda Hajiya ta cakume Likitan tana surutai. "Hajiya ki sake shi please, ki bari mu ji me ya zo da shi, allow him to talk" ta rarrashi Hajiya kana ta dubi likita ta ce "Dr meke faruwa? Ya jikin Fatima?" A karo na wajan uku ya ƙara girgiza kai ya ce "Tsakani da Allah tun yaushe ne ta fara naƙuda?" Amma ta yi jim ta ce "Bana ce ba gaskiya, Fatima ai zurfin ciki gare ta, kodayaushe cewa take lafiya lou take meke faruwa?" "Follow me Maaa" Amma ta ce "A'a batun na biyo ka bane, bani da kuzarin hakan ma kawai ka faɗa mini halin da ƴar'uwata ke ciki" Dr ya yi jim sai kuma ya ce "Har yanzu bata sauka ba tun jiya da kuka kawota, maganar da ake mun fidda rai da ita, wasiyya take bayar wa kuma tana buƙatar ganin mijinta, don Allah ku kira shi tana cikin wani hali" Amma ta yi baya tana shirin zubewa Zuhura ta yi saurin tare ta ta ce "Subuhanallahi, take it easy Amma In sha Allah babu abinda zai faru sai abinda Ubangiji ya ƙadarta" Da dugu Amma ta nufi Emergency room hankalinta baya jikinta, kai tsaye ta hankaɗe likitocin da suke wajan tare da faɗawa cikin ɗakin. Abinda idanunta suka gani ya yi matuƙar gigita ta, ta nufi gadon tana cewa "Ba mu yi haka dake ba Fatima, kar mu fara ba ki taɓa ce mana mutuwa za ki ba, mata nawa suke aure su ɗauki ciki, su yi rainonsa kuma su haife lafiya su shayar da abinda suka haifa? Ba za ki mutu ba, da gaske ba za ki mutu ba Fatima" Amma kuka take sosai domin bata taɓa ganin naƙuda irin ta Mami ba, jijjiga take idanunta ya zazzaro waje harshenta ya zazzago sai fisga take kamar mai aljanu, likitoci ne suka fitar da Amma ta nufi reception hankali tashe, Junaid ya tari Ammi da cewa. "Ammi ya kike kuka haka? Kar ki ce mana wani abu ya samu Mami don Allah" Ammi ta dake ta share ta ce "Junaidu kira mini Baffanku kada ƴar mutane ta rasu na shiga uku" "Kamarya ki shiga uku Ammi?" Amma ta kalli Zuhura ta ce "Wallahi idan Fatima ta mutu na shiga uku, ba za a taɓa ganin laifin Alhaji ba nawa za a gani, duk duniya gani ake kishiya azzaluma ce, ban san meke damun mahaifinku ba Zuhura wallahi ban sani ba" Hajiya rai ɓace ta kalli Junaid ta ce "Wa kake da suna? Mu je can wajan uban naku" Ya yi sururu sai kuma ya bi bayanta, mota ya buɗe mata ta shiga, shi ma ya shiga ya nufi gida da ita. Alhaji Mansur Rano na zaune a parlon ya rasa meke masa daɗi, tun asubar fari ta wayewar garin yau yake jin damuwa a zuciya, ga wani masifaffen ciwon kai dake shirin haukatar da shi, da ƙyar yake buɗe idanunsa saboda nauyin da sukai masa. Rana ɗaya tal a rayuwarsa da komai yake shirin jirkice masa tare da ƙoƙarin raba duniyarsa zuwa biyu ta ƙarfi. A hankali ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Allahumma inni lima anzalta min khairin faƙir" Ya lumshe idanunsa zuciyarsa na bugawa, tunanin Fatima ne a ransa da son sanin halin da take ciki, da zarar ya yi ƙoƙarin ambatar sunanta yake jin kamar zai mutu ko zai haukace, ransa ya ɓaci. A hankali ya miƙe da nufin tattara files ɗin gabansa yabar garin ya koma wajan aikinsa, yana miƙewa sai ya ji kansa ya sara da zarar ya rufe idanu kuma Amma ke zuwar masa cikin idanu ya ji kawai ita yake son gani a gefensa, wayarsa ya ɗauka yana shirin kiran Amma sai ga su Hajiya sun shigo, ya faɗaɗa fuskarsa tare da ƙoƙarin shimfiɗa fara'a ta maye gurbin damuwar akai. A nutse ya koma ya zauna idanunsa a ɗan zube kan Junaid domin ya kasa kallon Hajiya haka kurum. "Ni zaka ka kalla ba Junaidu ba, ni ce nan wacce zaka kafe da kallon tuhuma Mansur" Baffa ya juya cikin ladabi ya ce "Wani abun ya faru?" Ta miƙa masa hannu tare da yi masa daƙuwa ta ce "Ubanka ka yi yana can yana dogara wa da sanda, ni zaka kalli tsabar idanuna ka tambaye ni mai ya faru? To ai kafi ɗan dako sanin ta sha Mansur, wallahi wahainiyarka ta kiyayi ramata, karka kuskura na nuna maka ɓacin raina" Baffa kansa a ƙasa saboda juyawar da yake masa ya ce "Afuwan, ki yafe mini Hajiya" Ta gyara zama ta ce "Faɗa mini wanda ya tilasta maka wajan auran Fatima?" Jin sunan Fatima ya sa ya riƙe kai da sauri yana mai ambaton sunan Allah ya jima kafin ya ce "Fatima? Fatima wace haka" Hajiya ta saki baki tana kallon Baffa, ta juya ta kalli Junaid shi ma da mamaki yake kallon Baffansa sai dai bashi da ikon saka baki cikin zancen manya. "Ni kake tambaya wace Fatima? Ni zan faɗa maka matsayin Fatima a wajanka Mansur?" Hankalinta duk a tashe yake ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ce "Da gaske na yi makkuwa wacece Fatima?" Hajiya ta fashe da kuka ta ce "Idan tururuwa ta so lalacewa sai ta yi fiffiken tashi, lafiya ƙalou kake Mansur ko dai shaye-shaye ka fara bamu da labari?" Ya girgiza kai ya kasa cewa komai idanunsa ya yi jajur, kukan mahaifiyarsa na taɓa shi. "Bari na tuna maka shuɗaɗɗen tarihin daka manta, Fatima matarka, wacce kukai auren soyayya da ita, kuma ita ce soyayyar farinka akan bata isa aure ba ka jirkinta da aurenta ka fara soyayya da Maryama, matarka ta farko ita ce Maryam uwar su, Zuhura, Balkisa, Junaid, Aliyu, Usman, Umar, Abubakar, soyayyarka ta farko kuma ita ce Fatima, soyayya gaskiya ce musamman first love, har cewa ka yi a aura maka Fatima da ƙuruciyarta kasancewar iyayenta wayayyu ne sun san illar haka suka hana, tana budurwa aka yi mata kishiya duk wani a duniya daka tara kake alfahari da shi sanadin Fatima ne, kada ka manta kuma da Babar Fatima da babbar Maryama aminan juna ne, silar auren Fatima da samuwar cikin da take da shi ya taka rawa wajan samun cigaban kasuwancinka zuwa matakin da kake a yanzu, soyayyar duniya ka ɗauka ka ɗora wa wannan cikin, dukda cewa bata samu ciki da wuri ba, babu wanda ya taɓa jin kansu da abokiyar zamanta, baka taɓa kawo mini ƙarar Fatima ba, yarinya mai haƙuri da ɗauke kai da zurfin ciki, albarkacin Fatima wanne kalar ci-gaba ne baka samu ba? Sai yanzu kwatsam sanda take buƙatarka sanda rayuwarta take tsakanin abu biyu zaka juya baya ka bijiri da abinda ba shikenan ba? Anya kama kan ka adalci? Kasan me kake kowa Mansur? Ko akwai abinda ya haɗaku ne, naga kai da kanka ka kai ta asibiti jiya" Baffa kuma Abban sama ya yi wa Hajiya ƙuri da idanu kamar mai son tuna wasu abubuwan a hankali murya bata fita sosai ya ce "Na tuna ta, Fatima matata mene ya faru yanzu Hajiya?" Hajiya ta ce "Likita ya ce ta shafe sati tana naƙuda, ƙarfinta ya ƙare bata da wani kuzari ba zata iya haihuwa da kanta ba, ga yawon ciwon kai da zazzaɓi da take sun haifar mata da jijjiga babu mamaki ta shafi abinda yake cikinta, bama fatan haka" Baffa ya ɗauki waya ya ce "Allah ya kyauta" "Ma ma'anar Allah ya kyauta kar ka saka ni saɓo Mansur tashi za ka yi mu je" Ya numfasa kamar zai yi kuka saboda ciwon kai ya ce "Na je ina kenan?" "Asibiti, Fatima na barin wasiyya tana buƙatar ganin ka" Ya runtse idanunsa kamar kansa zai tarwatse ya ce "Allah ya bata lafiya, idan ta tafiya ce Allah ya jiƙanta na yafe mata" "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Masur, Mansur ka ji tsoran Allah ka tuna duk abinda ka yi wa ƴar wani a rubuce take sai an yi wa taka, shi alhaki kwikwiyo ne, kada ka gina ramin muguntar da zaka rufta kanka a ciki" Baffa ya kasa cewa komai ya kara waya a kunensa ana ɗagawa bai tsaya jan zaren zancen ba ya ce "Maryam na ba ki mintuna goma ki dawo gida yanzu, minti ɗaya kika ƙara a bakin aurenki" Yana faɗin haka ya kashe wayarsa. Hajiya ta ce "Wannan ba Mansur ɗina bane akwai alamar tambaya, Allah ya shiryaka ya dawo da kai hanya madaidaiciya" Baffa ya miƙe tsaye sai haura sama ta ce "Idan ni uwa ce, kuma ni na haifeka ka zo mu shige kaga halin da matarka take ciki" Baffa ya ce "Ki yi haƙuri Hajiya nikam ki yi haƙuri ban iya zuwa, wallahi ana takura ni zan iya sakinta" Kuka sosai Hajiya take Junaid na bata haƙuri ta ce ya kira mata Yaya A'isha wacce ta kasance yayar Mami, Junaid na kira ta ce ai sun jima cikin asibitin. Suna zuwa asibitin suka tarar da ƴan'uwan Mami manyan mutane masu ilimi da hankali, da zarar Yaya A'isha ta yunƙura za ta yi magana sai Dada ta hanata, Anuty Kaltum kowa idan ranta ya yi dubu ya ɓaci masifaffiya ce ta ajin ƙarshe. "To, da alama zaman haƙuri kawai Fatima take a gidan Mansur bamu sani ba sai yanzu, ashe mutumin banza ne bamu da labari" Yaya A'isha ta ce "Uhm, ni fa ban yarda da kishiyarta ba haka kurum jikina yake bani akwai wata a ƙasa" Tsaki Anuty Kaltum ta yi ta ce "Sune asararru, kuma banda abinsa ai ɗauɗar gora, ciki kan shata ruwan daya dake ka shi ne ruwa, duk lalacewar goma ai tafi biyar albarka kuma ko yanzu kura ta faɗi tafi ƙarfin Allah wadai" Duk maganganun da su ke Zuhura na jinsu. Ita kanta Anuty Kaltum da biyu take, jira take Zuhura ta tanka ta ci uwar yarinyar hankali kwance. Dr ne ya fito ya ce "Ina mijin nata muna buƙatar yi mata c.s yanzun nan, za mu cire abinda ke cikinta" Anuty Kaltum ta ce "Dr me ake buƙata" "Sa hannun mijinta ko uba" Ta ce "Duka basa kusa bari na saka hannun" Dr ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya miji muke buƙata ko uba" Ana kiran Baffa ya ce ina ruwansa ne? Duk an addaba masa akan wata Fatima? Duk yadda sukai daidai ne bashi da wata damuwa. Yana gama wassafawa Anuty Kaltum ta ce "Kan uba, wannan mutumin bai san wacece ni ba har ya manta sanda yake bina da Allah da Annabi a bashi auren Fatima? To zan ci kaza-kazan duk tsinannan da yake da hannu a kan wannan abun, shegu gayyar tsiya" Suka rasa yadda za su yi. "Zan saka hannun madadin Baffa" Su ka ji an faɗa. Juyawa sukai gabaɗaya a hankali yake tafiya kansa a ƙasa, hannayensa a baya, farar jallabiyya ce a jikinsa bai taushi, ga nutsuwa da haibarsa ta bayyana a fili. Dr ya ce "Ashe kana gari?" Bai yi magana ba, bai kuma ɗago kansa ba ya amshi biro ya saka hannun. Yana kammalawa ya yi gaba Dr ya bi bayansa, yadda yake gudanar da abubuwan shi tamkar shi ne jagoran gidan. "Babban mutum zuwan yaushe?" Nan nan bai tanka ba, shi bai ga dalilin tambayar ba idan zai zo daman sai ya nemi shawarar wani ko umarnin zuwa wajan wani? Addu'a ya yi wa Mami kana aka shigar da ita C.s kamar daga sama haka su kaga Baffa yana zuwa ya kalli wanda ke zaune can nesa hannunsa maƙale da carbi idanunsa rufe ya ce "Da izinin wa ka saka hannu Bilal?" Sai a lokacin ya buɗe ido ya kalli jama'ar wajan sai kuma ya yi kicin-kicin da fuska don bai son kallo ya ce "A ceton rai ai ba buƙatar izini Baffa" Baffa zai yi magana Bilal ya miƙe tsaye ya ce "Kar ka yi mini ihu Baffa, karka mini faɗa a gaban yara" Baffa ya ce "To tunda har ka yi abinda ba shikenan ba, ka zuba ido za ka gani" Bilal ya ce "Alheri Baffa, alherin ALLAH muke nema" Daidai nan kuma aka fito da Mami sai wata nurse hannunta riƙe da Baby, Baffa ya bi fuskar Fatima da kallo yana jin kamar ya je ya ɗauke matarsa saboda soyayya da zarar ya yi wannan yunƙurin sai ya ji kansa ya sara ransa ya ɓaci, Nurse ta bawa Anuty Kaltum baby ta amsa tana murmushi Dada ta ce "Ma sha Allah, ki bawa angon ƙarni ya yi mata huɗu ba" Ana bawa Baffa Babyn da basu san me aka haifa ba ya ƙura mata idanu sai kuma ya yi murmushi yana mai sakin jaririyar ya ce. Banko ƙofar da aka yi da ashar ɗin da aka zunduma ya katse Ridayya daga bawa Zainaba labarin, ta miƙe da sauri jiki na rawa take kallon Meer, shi kuma yana kallon Zainaba ya ce "Ke wacce uwar ce ta kawo ki cikin gidana?" Zainaba ta yi dariya sosai ta ce "Au ina abin yake? Ina ƙoda ina romansa? Wannan abin shi kake kira da gida?" Zameer ya ce "Fita munafukar wallahi zan yi maganinki soon, kuma ba ke babu matata" Ta ce "Wallahi tallahi ni da Ridayya mutukaraba, duka kuma shege ka fasa nima tsohuwar ƴar tasha ce ni wallahi ka kiyaye ni" Zainaba bata da burin daya shige ta ji ci gaban labarin, keke faruwa a cikin asibitin me Baffa ya ce da yaga Ridayya a zanin goyo? "Ki kwashe kayanki za mu bar wannan gidan" A rikice Ridayya ta ce "Ba dai sakina za ka yi ba?" Zainaba ta ji kamar ta dannawa Ridayya ashar ta dinga zabga mata harara ya ce "Ban sani ba, gidan ba nawa bane yanzu, kai kima nemi wajan kwana yau kafin gobe da safe yanzu masu gidan za su shigo" Yana faɗin hakan ya fice yasan dole ta neme shi, Ridayya ta rasa me zata ce ta dinga sakin ajjiyar zuciya, Zainaba ta kwashe mata abin kwasa ta zuba a gidanta daman babu uwar komai, sanadin caca Zameer ya siyar da duk abinda ta mallaka. Daga nan Ridayya a ƙafa ta nufi gidansu Zameer wajan Mama domin ta kwana a can. Sheƙeƙe Mama take kallon Ridayya kafin ta ce "Ai bamu da wajan kwana wallahi ki yi haƙuri ki nemi wani wajan" Ridayya ta ce "Mama Meer ɗan'kine ni surukarki ce idan ba ki wani wajan kwana ba waye zai bani?" Mama ta yi dariya ta ce "Yau dai bari na faɗa miki gaskiya, bani da alaƙa da Zameer ban san waye shi ba, kamar yadda kika ganshi haka nima na ganshi, asali Almajiranci ya zo Kano shi ne yake mana aike daga nan muka riƙe shi kamar ɗan'mu saboda yana ɗan taimaka mana kuma kwana biyu ba uwar da yake bamu, ke yanzu kina nufin kafin ku yi aure iyayenki ba su yi bincike ba? Wallahi ban san waye Zameer ba, ban san kuma iyayensa ba don Allah fice mini daga cikin gida...... Ina jiran comment ɗinku, a duk inda kuke🥰🫶🏼 #Munafukinmiji #Labarin Ridayya #Masur&Fatima #Ƙaddara #Rashin bincike #Baƙin kishi #Son zuciya #Kishiya Na'ima Sulaiman Sarauta 08164069385 *✿ MUNAFUKIN MIJI 11 ✿* BRIGHT PENS🤙🏼 free batch A rikice Ridayya take kallon Mama, da alama ta kasa yarda da kuma fahimtar zancen nata. Mama ta ce "Wallahi tallahi bani da haɗi da wani Zameer, ba dangin iya babu na baba, ai asali da tushen shi yana ƙauye da ina jin? Almajiri ne sosai a nan makarantar almajirai ta Malam Iro, tun yana ƙarami dai da kashinsa a gindi aka kawo shi, ba kowa zai san ba ɗan Kano bane, tunanin kowa mune iyayensa" Bakin Mama Ridayya ke kallo, ta kasa sanin ainahin inda zata zuba kalaman nata, har ta fahimta daidai. Da ƙyar ta buɗe baki ta ce "Mama kin gane wa nake magana akai anya? Mijina fa Zameer ɗan'ki" "A'a gyara kalman bakinki, ban yi cikinsa ba balle na haifa na ba ki shi ki aura, bai kuma sha nonona ba, lafiya ras nake da alama kece tunaninki ya yi ƙaura daga kwakwalwarki, nutsuwarki ta bar gangar jikinki, Zameer Almajirin Malam Iro ne" Ridayya ta fara kallon Mama dishi-dishi hawayen da suka jima da yin hijira daga idanunta suka fara bin fuskarta ba tare data shirya zubar su ba, bakinta na ɓari da ƙyar take iya motsa bakin saboda ƙonan fuskar daya kame tare da tattare wa waje guda. "Me ya sa Mama? Me ya sa kika ɓoye wa iyayena gaskiyar al'amarin? Kun rufe ni kun cuce ni" Mama ta buga cinya ta ce "A'a a hir ɗinki wallahi kar ki kuma cewa mun cuce ki, idan akwai wanda ya cuce ki bai shige iyayenki ba, da suka kasa yin bincike a kan wanda za ki aura, sai kuma zuciyarki data zama kurma akan Zameer ɗin, don me ake cewa a yi bincike kafin aure? Ai saboda irin haka ka je ka auri ɗan fashi ko kidnapa babu uban wanda ya sani, kinga ni fice mini daga gida kada ki saka bakina ya yi tsini" Kuka Ridayya take kamar ranta zai fita wannan wanne irin lamari ne? Ikon Allah da ƘUDIRAR ALLAH ke riƙe da rayuwarta a yanzu. Waye Mijinta? Ina ne garinsu mene mafita? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un. "Mama kin cutar da rayuwata ki sani Allah ba sai bar ki ba, na san ba za ki so a yi wa ɗiyarki dake gidana haka ba, domin aure ba abin wasa bane" Sheƙeƙe Mama ke kallon Ridayya kafin ta ce "Wacce ƴar rawa ce a gidan ki?" "Khairiyya!" Ta bata amsa a raunace ƙirjinta na ɗaga wa sama, kamar wacce Asthma ke shirin kama ta. Mama ta ce "Tab, wata aba ce haka kuma? Bani da wata yarinya mai irin wannan sunan nikam" Dam! Ƙirjin Ridayya ya bada sauti juwa na ɗaukar ta, ta sulale a wajan tana riƙe da ƙirjinta sunan Allah take son kira ta gagara furta komai. Ganin haka ya saka Mama figar hannunta ta ce "A'a ba za ki mace mini a gidana ki ja mini jarfa da zunɗe, ke da can ba ki yi tunani da nazarin wanda kike tare da shi ba sai yanzu da masifa ta faɗa miki? Ni duk wani Almajiri nawa ne ba ruwana da sanin waye shi" Ta hankaɗa Ridayya waje ta rufe ƙofar gidan. Tana faɗin "Yaran zamani da masifar kwaɗayin abin hannun samari, da shegen iyayi da kinibibi da kunga namiji yana murza shadda ya kafa hula kyakkawa da shi sai ku liƙe masa? Ba kusan kura ce da fatar a kuya ba, yawanci cima zaunane masu burin tsiya, su kuma iyayinki ganin Allah ya rufa musu asiri suka bashi ke da tunanin ya cancanta, ko kuma tunaninsu arziƙi gare shi?" Ta yi ƙwafa tana komawa tare da zama ta ci-gaba da yanka albasa da kabejin awarar daren da take yi almajirai da ƴan unguwa na siye, ta girgiza kai ta ce "Ai bada kuɗi ne kawai arziƙi ba, hadda miji na gari a wannan zamanin arziƙi ne, ni kuma mene nawa? Kuɗi kawai ya biya ni ya ce na yi masa komai a matsayin uwa" Haka kurum ta ji kamar bata kyauta ba na ɓoye gaskiyar waye Zameer da ta yi, kila a kyau masu sonta wanda suka fishi nagarta da komai, idan ta tuna kuɗi ya bata fa sai ta ji ko a jikinta. Ta share batun Ridayya tare da ci-gaba da aikin gabanta domin a yanzu bata da wani abu daya dameta. Ƙafafuwanta kawai take cillawa ba tare da sanin inda take saka su ba, wani irin duhu ne ya mamayewa idanunta jiri na ɗaukar ta tare da ƙoƙarin yasar da tsamurarren jikin nata, har ta ƙarasa tsakiyar titi bata sani ba, dukda irin horn da masu abeben hawa suke mata. Wawan burkin da aka ja, da kuma sauke mata lafiyayyen marin da aka yi ya saka ta dawo cikin hayyacinta mutumin daya fito daga cikin mota ba shiri ya ce "Ke wacce irin mara tunani ce da za ki zo tsakiyar titi kamar kin samu hanyar gidan ubanki, e?" Wani ya leƙo daga mota ya ce "Da ka yi mata afuwa bana jin data da cikakken hankali fa, ko babu komai a girme ta girmeka sai ta ci albarkacin hakan" Cikin kumfar baki ya ce "Matsalar ta ce wannan kuma hauka ai bani na ja mata, irin su ne masu yawa mutane bala'i" Murmushi Ridayya ta yi idanunta akan mutumin ta ce "Rashin adalci da ka yi mini daka hana motarka bi ta kai na, wallahi farin cikina a yanzu bai shige mutuwata ba, inama baka dakatar dani ba? Ina ma ka take ni ka yi gaba abinka, babu mai ce maka don me, mai gata shi ake nema wa ƴanci" Ya yi tsaki yana komawa mota ya ce "zafin talauci hauka ne? Kowa idan masifar yunwa ta masa yawa sai ya nemi kashe kansa aikin banza aikin wofi, wahala ku ta ganku" Ya yi wa matarsa key tare da barin wajan, Ridayya ta bisa da kallo domin kamar ba Hausa yake mata ba, laɓɓansa kawai take kallo ta kasa fahimta. Ɗaya mutumin mai bawa Ridayya wancan haƙuri ya dinga kallon Ridayya, yarda maganarta ke fita a hankali a kuma taushashe da yarda take marairaice fuska a shagwaɓe ya saka ya fahimci yarinya ce masifar wahalar rayuwa ce ta mayar da ita haka. Daga gefe guda yana mamakin wasu mutanen da basu iya taimako ba sai gori da arziƙi kamar iyalan ƙaruna. Ya fito daga motar ya ce "Sannu baiwar Allah kamar kina buƙatar taimako?" Ta yi masa ƙuri da idanunta ta kasa furta komai saboda kwarjinin da ya yi mata. A hankali ya zaro kuɗi a aljihu ya miƙa mata ya ce "Gashi kya ci abinci" Kamar ƙaramar yarinya ta maƙale kafaɗa, ita yanzu ba kuɗi take buƙata ba, wanda zai ja ta ya rungume ta ya rarrashe ta, shi take so. Yin duniya taƙi amsa, sai kallonsa take kamar zata bisa, ya zaro card ɗinsa da number shi ya ce "Ki kira ni, when you need my help ok?" Ta amsa ya juya a hankali ya ji ta ce "Abbiey!" "What? What did you say?" Ta juya da sauri ta bar wajan, ya yi murmushi a fili ya ce "Ikon Allah" kuɗin daya fito da su ya bada sadaƙa da nufin Allah ya bata lafiya ya kawo mata sauƙi cikin lamuranta. Mota ya shiga daman akan hanyar barinsa garin yake. Ridayya bata nufi hanyar gidan mijinta ba, tafiya ta cigaban da yi bakinta na motsa wa kamar bai magana, harta ƙarasa gidan Baffa, yanayin yadda taga gidan ya saka ƙirjinta bada wani ƙyakƙyawar sauti, bai yi kama da gidan da mutane suke rayuwa tare da wanzuwa a cikinsa ba, ya dinga kallon cikin gidan daga waje babu mota ko ɗaya sai uwar ƙura duk flowers ɗin sun bushe sun mutu murus ya zama kamar kofai. Ta runtse idanunta sunan Allah take son kira amma ta kasa, me ya sa sai yanzu take buƙatar jin ra'ayin Mami a kan lamarin aure da yardar ta? Me ya sa Mami bata taɓa janta a jiki ba? Me ya sa sai yanzu take son rayuwa da Maminta. _When all is gone...!_ Hannu ta sak ta dinga bubbuga ƙofar gate ɗin a raunace ta ce "Baffa ka buɗe mini ƙofa na dawo, Mamina na dawo gani na zo ba zan ƙara zaɓar kowa a kan ku ba, Mamina buɗe mini ni ce Ridayya" ƙofar take bubbuga wa sosai ta ce "Bakwa jina ko? Yunwa na ke ji Mami shi ya sa muryar tawa babu ƙarfi, Mamina zan ƙara haihuwa za ki samu jika, Baffana wai ka dawo ashe kana nan" Shiru ba amsa, ta dinga buga wa da iyakar ƙarfinta. Ta matsa ɗaya ɓarin ta ƙura wa side ɗin Ustaz idanu tana tuna sanda yake bata abinci ya goyata tana tuna yadda duk wani motsinta yake kan idanunsa. Ta rufe ido tana sauke ajjiyar zuciya a cikin raunatacciyar muryarta mai tsananin sanyi ta ce. "Abbiey, i miss You" Waje ta nema ta zauna da nufin ta jira su dawo ko unguwa suka je, sai dai Ridayya bata san sun yi tafiyar da babu waiwaye balle batun dawowa a cikinta ba, sun je inda ko wanne mai raye sai ya ke ko baya su, sun je gidan gaskiya. Tana ta zaune ko motsi bata yi saboda galabaita ga cikinta daya fara motsi alamar yana cikin wata na huɗu yanzu yana buƙatar ɗaukin gaggawa, a nan wajan bacci ya ɗauketa. Ita yanzu ba kowan kowa ba ce, but an unprivileged woman Lagas/ Ikeja Birnin Legas, ko kuma Birnin Ikko, shi ne babban birnin Jihar Legas da ke Najeriya. Legas yana ɗaya daga cikin birane mafi girma da yawan jama'a a Afirka da ma duniya bakiɗaya. Legas ne birni na biyu mafi girma a Afirka, kuma na bakwai a duniya. Government Residence Area (GRA). Unguwa ce babba mazuna manyan mutane. Idanunsa a lumshe yake sauraran maganganun da ake yi ta cikin wayar dake saman kujera wacce ya sanya a handsfree. Yadda yake sauke ajjiyar zuciya a hankali yana tura hannunsu cikin kansa za a ɗauka bashi ke yin wayar ba, ɗan gajeren tsaki ya ja a fili yana haɗe yatsun hannunsa wanda suka bada wasu sauti kafin a hankali ya buɗe sanyayan idanunsa masu kaifi da wani kwantaccen sirri a cikin su. Cikin gajiya da maganar mutumin ya ce "Enough" Ya faɗa cikin kakkausar murya yana mai sauke numfashi da ƙyar saboda nauyin ƙirjinsa da yake ji. Ta cikin wayar aka ce. "Be patient Ustaz Bilal, ka ɗauki ƙaddara watanni nawa da faruwar hatsarin nan mun yi iyinmu mun faɗa maka gabaɗaya mutanen ciki sun ƙone" Ustaz Bilal ya manta da waye yake waya cikin hargowa ya dakawa DSS (Department of State Security) tsawa ya ce "Liar, wanne irin hatsari ne a ce kowa ya rasu, my own family? Kana nufin na rasa kowa, e? Mene amfanin (IPO) a cikin police ne?" DSS ɗin ya ce "Investigating Police Officer" Ustaz ya jinjina kai ya ce "Good, to ya ƙara bincikawa familyna suna raye kar ka sake kira na muddin bada Baffa za ka haɗa ni ko Junaid ba" Ya kashe wayar yana miƙewa tsaya, Nasir ya dinga bin Ustaz Bilal da kallo a ɗan tsorace domin bai taɓa ganin zallar masifar Ustaz irin yau ba, ana cewa masifaffe ne bai taɓa gani ba amma yau shi kam zai bada labarin haka. Ya miƙe ya ce "Md komai ya yi zafi maganinsa Allah, ka yarda da ƙaddara ka yarda cewa dukkan mai rai mamaci ne, ka yarda cewa aljalinsu ne ya zo lokacin ɗaya, mutuwa wajibi ce hisabi gaskiya ne, rayuwa ƙarya ce kuma wa'adi ce, ina iliminka ina da tauhinka" "Yana gidan ubanka, na ce yana gidan Ubanka Nasir tsahirta mini" Nasir ya ja baya yana gwaloido ya ce "Asstagafirullah, yau Ustaz da zagi? Wallahi dole na saka Hajiya ta yi maka aure" Ustaz Bilal ya yi kamar zai shiga ɗakinsa yana zuwa dab da Nasir ya saka hannu ya damƙo shi tare da jansa har bakin ƙofa, ya cilla shi tare da rufe ƙofar yana dafe kansa ya ce "Haihuwa za ka saka a yi mini ba aure ba, stupid". Nasir ya dinga dariya, koba komai yau ya ja Ustaz da magana a ƙasan zuciyarsa kuma yana mai tausayinsa domin duk wani bincike ya nuna Ustaz Muhammad-Bilal ya yi rashin ahhalinsa yana buƙatar mai kula da shi, ba kowa yanzu Ustaz ke buƙata ba face Mata wajan zata kula da shi, amma shi ganin kansa yake tamkar waliyyi bai taɓa jin ko da wasa Bilal ya yi maganar mace ba, balle kuma aure ko bashi da lafiya ne Ohho ko irin first love ɗin nan bai taɓa gwada yi ba. Nasir yana ƙoƙarin ficewa mota na shigowa cikin gidan, ya ware Idanu ya ce "Wonder shall never ends, wa nake gani kamar Baita?" Murmushi ya yi yana buɗe idanu tare da watsa hannu alamar oho maka. Nasir ya daki kafaɗar Baita ya ce "Let's keep a joke aside, when did you came?" "Jiya" Baita ya ce a taƙaice yana kallon Nasir, sai kuma ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na tashi, wani abu na son fusgarsa da son ɗarsa abun da bai shirya ba. Allah Allah yake ya ƙarasa wajan Ustaz babban amininsa ya yi sharing damuwarsa da shi. "Shi ne ba waya? Ko chat?" Baita ya ɗaga kafaɗa ya ce "Bazata" gaba ya yi abinsa ya ce "Ustaz fa? Md" "Kamar ka shiga, don baya cikin nutsuwarsa wallahi yau ko Bank bai je ba" Baita ya tsaya cak tare da jin abinda yake faruwa da Ustaz ɗin, don dama yana ta kiran wayarsa bai ɗauka ba. Nasir ya san Baita ba zai magana ba hakan ya sa ya ce "He lost his entire family in an accident" Baita ya zaro ido sai kuma ya runtse da kyau yanzu da me zai ji da rarrashin Ustaz Bilal ko kuma da matsalar yarinyar da ta tsaya masa curr a rai? Iskar hadarin dake kaɗawa ya sanya Ridayya farkawa daga bacci wahalar daya ɗauke ta, ba tare data shirya ba. Ta miƙe da sauri tana murza idanunta tare da kallon gate ɗin gidansu har yanzu basu dawo ba? Ta juya taga duhu ya fara a hankali ta ce "Ko sai yaushe za su dawo? Mamina, Baffa gobe zan dawo na ganku kun ji?" Ta ja ƙafa ta nufi gidanta ta mance da cewa yanzu ba mallakin mijinta bane. A ƙofar gida ta samu Zameer a zaune ya wanka wani voyel mai laushi har farar singlet ɗin ciki ana gani ya yi kyau, gefensa kuma leda ce sarai ya ganta ya share ya ta nufi ƙofa sai ta tsaya ganin gidan a garƙame da kwaɗo. Ta juya ta kalle shi ta rasa dalilin daya sanya yau ko kyansa bata gani ba, duk yadda ta kai da danne zuciyarta wajan ganin bata ji zafinsa ba. "Ka buɗe mini?" "Daga ina kike?" Ya tambaye ta yana miƙewa tsaye tare da mayar da wayarsa zuwa cikin aljihu, ta kafe shi da ido taƙi magana. Daram! Ya ji zuciyarsa ta buga, ba tare da sanin dalili ko hujjar hakan ba, abu ɗaya ya fahimta, rashin tsoro da tausayin da suke shimfiɗe a idanun Ridayya yau babu su, tarwai yake kallon cikin idanunta, ya rufe ido ya buɗe wannan kwantacciyar soyayyar babu ita idan har yaren soyayyar daya karanta idanunsa sun faɗa masa daidai. "Daga ina kike? Kar ki bari na maimaita maganata idan ba haka ba, za ki mamamkina" "Mamaki na nawa kuma ZAMEER?" Ya zaro ido jin ta ce Zameer yau Ridayya ta kalli cikin ƙwayar idanunsa ba shakka ba tausayi, da wannan soyayyarta ta, kai tsaye gatsal ta ce Zameer? "Sunana kika kira Ridayya, sunana Ridayya" Still idanunta a cikin nasa ta ce "Kenan daidai na faɗa ashe, Zameer ko?" Ya shanye mamakin ya san fushi ta yi yana mata daɗin baki zata sakko, sai dai ko a fushi Ridayya bata taɓa tsare shi da wannan rikirkitattun idanun nata ba sai yau. "Daga ina kike?" Kai tsaye ta ce "Gidan iyayena, gobe ma zan koma don ban tarar da su ba" Ya yi wani murmushi ya ce "Opps sorry, ai na manta ban faɗa miki ba iyayenki duka sun mutu babu kowa da ya yi saura hatta wannan farin mutmin Bilal ko? Shi ma ya mutu?" Murmushi ta yi dukda jiriri ta ji yana kwasarta ta ce "Tom, buɗe mini gidan" Don ita ta san babu yadda za a yi kowa nata ya mutu yabar cikin wannan rayuwar. "Na faɗa miki Baffa mota ta bi ta kansu ta, an ce ma kansa ya gutsire kuma huta ta babbake su kamar yadda ake babbaka taya....," Saukar wani lafiyayyen mari Zameer ya ji a fuskarsa, tunda yake a duniya ba a taɓa marinsa ba, marin daya shige shi irin yau ba, ya juya ya sake juyawa yaga babu wanda wake gani a gabansa sai Ridayya. "Ke! Wa kika ga ya mare ni ya gudu?" Kai tsaye ta ce "Ni ce, kuma ban gudu ba" Ta faɗa tana shigewa gidan Zainaba. Zameer ya bi Ridayya da kallo domin ya san ba zata taɓa marinsa ba, ƙarya kawai ta yi kansa har wani za fi ya ɗauka. Zainaba na zaune kamar daga sama taga Ridayya ta shigo a rikice domin ta ɗauka Zameer ya biyo ta, bata taɓa tunanin zata yi wa Zameer ko da tsawa ba amma sai gashi har mari, ba zata taɓa cewa ga sanda ta mari Zameer ba. A gigice Zainaba ta bawa Ridayya ruwa ta sha, ta bata abinci amma taƙi ci hannunta ƙanƙame da card ɗin da mutumin ya bata. "Tunda ba za ki ci abincin ba, kwanta ki huta idan kin tashi sai ki yi wanka" "Ina son Zameer ya sake ni, hallayarsa bata irin mijin da nake so ba ce" Wani farin ciki ya mamaye zuciyar Zainaba amma ta ɓoye ta ce "Saki kuma? To idan ya sake ki ina za ki?" Ta ce "Wajan Baffa da Mami ko Abbiyena" Zainaba ta jinjina kai ta ce "Kuma zai sake kin?" Wani irin kallo Ridayya ta yi wa Zainaba sai kuma ta yi murmushi ta ce "Wallahi wallahi Allah na gama zama da Zameer wallahi sai ya sake ni" Zainaba ta yi hamdala tana ƙoƙarin tashi Ridayya ta ce "Zauna na ƙarasa miki labarina wanda na fara, zan baki gabaɗaya labarin a daren nan, domin daga gobe ba za ki ƙara gani na ba" Zainaba ta gyara zama sosai, Usman mijin Zainaba da sauri ya dawo ƙofar ɗaki ya zauna cike da zumuɗin jin cigaban labarin Ridayya. Ridayya ta lumshe idanunta a hankali ta ci gaba da bawa Zainaba labarin..... Back to story Baffa ya saki babyn tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa, Bilal ya yi saurin tare ta, ta faɗa hannunsa ya yi saurin rungume ta a ƙirjinsa saboda jin ta tsala ihu. Gabaɗaya suka kalli Baffa wanda har lokacin babyn yake kallo wacce take ƙirjinsa ya yi girgiza kai ya ce "Bana ƙaunarta wannan ba ƴata ba ce a kaf zuri'ar Mai ran ƙarfe babu baƙin mutun babu mai munin wannan jaririyar, ni Alhaji Mansur Rano bani na yi cikin wannan yarinyar ba a nemi ubanta wani wajan.... * Na'ima Sulaiman Sarauta 08164069385 *✿ MUNAFUKIN MIJI 12 ✿* BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Anuty Kaltum ta ce "Alhaji Mansur me kake nufi da jaririyar ba ƴarka ba ce?" Baffa ya yi wa Anuty Kaltum kallon ki shiga hankalinki kafin ya ce "Ina nufin abinda na faɗa, wannan yarinyar da Fatima ta haifa a nemi ubanta wani wajan, bani da haɗi na jini ko gamuwar ƙwayar halitta, ita ɗin ba jinina na ba ce, I'll never accept her as my biological daughter, kuna iya neman ubanta wani wajan" "Kam bala'i, wa kake da suna Mansur ko wa? To wallahi ƙarya kake idan ma shaye-shaye ka fara ka zo zaka mana maye a nan to yanzu zan dawo da kai cikin hankalinka, kana da yaƙini da tabbacin Fatima bata taɓa yin wani saurayi bayan kai ba, balle ka ce wani abu ko ka saka kalmar zargi a ranka, wannan kuma jaririya bata da wani uba daya shige kai Alhaji Mansur Rano, kamar yadda su Junaid su Zuhura suke ƴaƴanka, wanda ka yi cikinsu to haka wanann jaririya" Anuty Kaltum ta ƙare maganar cikin masifa da kumfar baki, ita daman faɗa ba nata bama siya take balle ya shafi jikinta da suke uwa ɗaya uba ɗaya?. Baffa ya yi kicin-kicin da fuska kana ya juya ya kalli yaransa da suke tsaye a wajan ya ce "Wa kika gani baƙi ko mummuna a nan cikin jerin yarana? Tunda nake haife-haife ba a taɓa haifar mini jariri mai munin halitta da baƙin kamar kalwa ba sai wannan mummunar jaririyar, babu ta inda na zama ubanta ba zan taɓa zama ba" Anuty Kaltum ta ce "Ok sai ka faɗa mana waye ya amshi budurcin Fatima a daren aurenku?" Baffa ya ɗaga kafaɗa ya ce "I am the one, but this baby will never be my daughter" Yaya A'isha dake tsaye itama ta ce "Sai a yi DNA TEXT, a nan gaskiya zata fito" Baffa ya ce "Ba DNA TEXT ba, ko cikin yarinyar zan ƙara a sake haifar ta, ba zan taɓa amsar ta, ku je ku nemi ƴar'uwarku ta yi muku explanation uban yarinyar sai a kai masa, amma....," Maruka aka shiga saukewa Baffa ta ko'ina, ya runtse idanunsa ganin yadda aka mare shi a kan idanun yaransa. Rai ɓace Hajiya ta ce "Ba shakka, dole ka nuna mini ka isa wannan shi ne kalar adalci da halaccin da zaka yi wa Fatima? Yarinyar da sadaukar da soyayyarta ga ƴar aminiyar babarta, ta haƙura har sai ta girma ta kai shekarun da iyayenta suka ɗiba na girmanta, a bayanka; wanne kalar samari ne Fatima ba ta yi ba, wanda suka fika kyau, arziƙi na saba, cancanta? Amma duk ta saka kamar ta share su, tana ganinsu tamkar mata kai kaɗai ta kewa kallon namiji, wanda zai wadata mata da komai? Zai bata farin ciki, ta dinga jin kalaman soyayyar su, kamar busar sarewar Audu" Hajiya ta share hawayen idanunta ta ce "Cikin daka ƙwallafa rai a kan shi, ka ɗauki burin duniya ka saka wa cikin, har kake cewa duk abinda Fatima zata haifa maka tabbas mai ƙashin arziƙi ne, Mansur yau a gaban iyayen Fatima akan idanun surukarka kake aibata abinda ɗiyarta ta haifa? Kake ƙoƙarin liƙa wa ƴarta kalmar zina? Ina tunanin ba abinda Fatima ta haifa ba ko wata ta ɗakko daban zaka saka hannu bibbiyu ka riƙe, Mansur! Mansur! Wallahi ka haukace" Baffa ya ce "Lafiya lou nake, wallahi Hajiya ina cikin hankalina a nemi uban yarinyar, matata Fatima kuma a mayar mini da ita gidana" Jama'ar wajan sun fi yarda Baffa ya samu matsala da tunaninsa, duk wani wanda ya san Baffa ya san labarin soyayyarsa da Fatima-zahrah bashi da wani sukuni sai nata, har ya yi aure jinsa yake empty without his Fatima Batool. Ammi har cewa take ya je ya ganota kar tunaninta ya haukata mata miji cike da zulaya take furta haka, sai kawai ya harereta irin ai na fiki sanin me nake. Baba ƙarami yayan Baffa ya jinjina kai ya ce "To ya kake so a yi kenan Mansur?" Kai tsaye ya ce "Kawai a nemi uban yarinyar, wallahi tamkar na saka hannu na murɗe wuyanta haka nake ji, wannan ai baƙar kadara ce, annoba, kuma wake ɗaya mai ɓata miya Fatima fara ce tas, ni ma fari ne tas, yarinya kuma da sharɓeɓan leɓe harshe a waje? Hanci zai yi goman nawa? Jibi suma duk saman fatarta? Wallahi ƙila aljana ce ba" Murmushi kawai Baba ƙarami ya yi ya ce "To wa za a nema matsayin uban nata? Ko zaka taya mu lalube ne Mansur?" Baffa ya yi shiru. "Wanne suna kake so a saka mata?" Aka faɗa a taushashe cikin sanyin murya, Anuty Kaltum ta kalli wanda ya yi maganar domin tunda ya zo wajan gabaɗaya maganar da ya yi ba takai huɗu ba. Rai a matuƙar ɓace ta ce "Tambayi mahaukacin ubanta gashi nan" A fusace Baffa ya ɗaga hannu zai kifawa Anuty Kaltum mari, Mai ran ƙarfe ya yi saurin riƙe hannun. Anuty Kaltum ta fashe da dariya tana tafa hannu ta ce "Basshi, basshi ya taɓa ya taɓa wa kansa masifa da bala'i, da matar soja kake magana, wallahi sai na saka a ɗaure ka ka yi life in prison, kaf zuciyarmu babu faƙiri matalauci, kuma mai ƙarancin ilimin addini, aikin banza nifa daman tun farko wannan mutumin bai mini ba" Ganin hayaniyya na neman tarwatsa masa kai, da kuma yadda jaririya ke saurin firgita ya sanya ya ƙara rungume ta a ƙirjinsa a hankali numfashinta mai zafi ke sauka, bakinsa ɗauke da addu'a yake ɗan tofa mata sama-sama. "Muhammad-Bilal" Baffa ya kira sunan Bilal a harzuƙe, cak ya tsaya kamar ba zai juya ba sai kuma ya ɗan yi baya tare da kafe Baffa da kallo na ya akai? Wannan tsawar fa? "Ka basu tsiyar su, su nemi ubanta" "Ni ne ubanta, yarinyata ce, zan kula da ita a matsayin uba" Bilal ya faɗa idanunsa cikin na Baffa. Wata dakakkiyar tsawa Baffa ya yi wa Bilal ya ce "Ka basu ƴar su na ce" "Ka dai na yi mini tsawa, nikam ka daina bana so, a gaban yara Baffa kalli yara kake mini tsawa a gabansu?" Babban ɓacin ran Bilal har da mutanen da bai taɓa ganin su ba sai yau, amma Baffa zai masa tsawa a kan idanunsu salon su raina shi? Bayan kowa ya san da shekarunsa a ka. Baffa ya ce "Sannu gyanbo, Bilal ka basu shegiyar ƴar su na ce" Idanun Bilal ya shige ciki saboda ɓacin rai, suka yi jajur jijiyoyin kansa duk suka fito, ba matsalar ƴar ce gabansa ba, damuwarsa faɗan rainin wayo da rashin tubalin yinsa, shi ba wanda ya yi masa faɗa sai shi za a yi wa? For God sake! "Bilal ni Baffanka ka ke yi wa haka? Ni?" Bilal ya ƙara nutsa idanunsa a cikin na Baffa ya ce "A kan idanuna kake musayar yawo da Hajiya, Hajiya fa, ashe ba daɗi?" "Me kake nufi da ɗaukan yarinyar nan?" Kai tsaye ya ce "Rainonta zan yi, zan kula da ita, kyautar da ubangiji ya baka ka wofintar ni ina so, zan kula da ita da izinin Ubangiji zan kuma aurar da ita da ƙudirar Allah" Murmushin takaici Baffa ya yi ya ce "Ok, bada kuɗina ba, ba kuma da abinda na mallaka ba zaka ciyar da ita ba, kuma ka tattara kayanka ka bar part ɗina" Bilal ya jinjina kai don baya jin zai iya magana har yanzu idanunsa cikin na Baffa, ganin yana shirin juyawa ya saka Baffa cewa "Ka basu ƴar nan na ce, Muhammad-Bilal" "Baffa?" Bilal ya faɗa a rikice yana jin tsawar har tsakiyar kansa, ya taka har inda Baffa yake ya kama hannunsa ɗaya ya damƙe sosai ya ce "Na roƙe ƙa da ka tsahirta haka nan, ban so da gaske ban so, nikam ban son tsawa, ka bar daga ni sai kai ka yi mini" Baffa ya ce "Sannu ubana" Bilal ya sake runtse idanunsa gam kamar ya nutse a wajan ganin yadda Baffa yake shirin zubar masa da girma "Kashe ni kawai Baffa zai fi wannan" sanin Bilal da masifar taurin kai da son girma ya saka Baba ƙarami cewa "Babban mutum jeka, Allah raya maka ɗiyarka ya sanya mata albarka" Bilal ya lumshe jiƙaƙƙun idanunsa da sukai laushi ya jima kamar ba zai magana ba ya ce "Amin Ya Allah, na gode ƙwarai Baba ƙarami" "Wanne suna ka saka mata?" Ya yi sak domin bai yi mata huɗu ba sam, yana buƙatar tantance sunan da zai saka mata a hankali ya ce "Zuwa gobe zan saka mata suna" Baba ƙarami ya jinjina kai ya ce "Allah ya kaimu" Yaya A'isha ta ce "Babba mutum kawo ta, zuwa anjima sai ka amsheta" Bai kalli Yaya A'isha ba, ya ɗan kalli fuskar jaririyar yana sake ƙanƙameta a ƙirjinsa ya jima sai kuma ya miƙa mata ita da ƙyar yana bata yabar cikin asibitin. Yaya A'isha ta juya zuwa cikin room ɗin da Mami take kwance tana hutawa hannunta ɗauke da baby. Anuty Kaltum kuma ta kalli Baffa ta ce "Muna jiran takardar sakin Fatima, domin gida zamu shige da Ita" "Ban niyya ba, ban shirya rabuwa da matata ba, kuma kar a kuskura a tafi da ita idan har nine mijinta" Yana faɗin haka ya fita, Anuty Kaltum za ta yi magana Dada ta hana. Kuka sosai Hajiya ke yi Baba ƙarami na bata haƙuri, kana suka dinga bawa su Dada dangin Mami haƙuri akan komai zai shige. Zuhura da sauran yaran suka tafi gida. Zuciyar Baba ƙarami babu daɗi takaicin abinda ɗan'uwansa ya yi, ya masa tsaye a zuciya. Har kwana biyu jikin Mami bai yi daidai ba saboda jijjigar da ta yi, sai a kwana na uku ta dawo hayyacinta bayan ta buɗe idanu ganinta ya sauka a kan Dada dake zaune hannunta riƙe da azkar, motsin da Mami ta yi ya saka Dada juyawa cikin farin ciki ta ce "Ma sha Allah autata ta farka" Ƙuri Mami ta mata kafin ta ce "Me na haifa?" Kai tsaye ta ce "Ɗiya mace Allah ya ba ki Batool ɗina" Mami ta yi ajjiyar zuciya ta ce "Ki yafe mini Dada haihuwa akwai wahala, Allah ya saka miki da alheri da kika haife mu kika kula da mu, bamu da abin saka miki wallahi na ɗauka mutuwa zan yi haihuwa da wahala Dada" Dariya Dada ta dinga yi ta ce "Su Autana an girma an son zafin haihuwa da ciwon uwa, ba ki mini komai ba Allah ya raya mini ke da jikata cikin aminci da kwanciyar hankali" Mami ta yi murmushi, sai rarraba Idanu take taga ta ina za a bata babynta? Ta faɗa mata azabar data sha kafin samuwar ta. Ta kasa haƙuri ta ce "Ina babyn?" Daga bayanta aka ce "Kima cire ranki daga ita Fatima" a rikice ta kalli Anuty Kaltum ta ce "Saboda me Anuty Kaltum?" A fusace ta ce"A saboda ubanta ya ce shegiya ce ita, bashi ne mahaifinta ba, ki nema mata uba wani wajan" Mami ta dinga kallon bakin Anuty Kaltum kamar zautacciyya, hawaye na zuba daga cikin idanunta ga wani azabar ciwo da nononta ke mata ya cicciko alamar babyn na buƙatar abincinta "Ban gane ba ƴarsa ba ce? Wallahi tallahi tunda nake a duniya babu namijin daya taɓa riƙe hannuna, Baffa ne wanda ya raya daren aurenmu, me na yi masa da zai haɗani da wannan masifar? Anya Baffa ne?" Kuka take kamar ranta zai fita ga ɗinkin dake cikinta nan da nan jikinta ya nemi rikicewa, Dr ne ya shigo yana yi wa su Anuty Kaltum faɗa da ƙyar akai mata allura bacci ya ɗauke ta. Faɗa Dada ta shiga yi wa Anuty Kaltum a kan a matsayinta na babba don ranta ya ɓaci ba haka ya dace ta yi ba, idan bata kwantar wa da Mami hankali ba waye zai taushe ta? Bilal na zaune idanunsa ƙuri a kan yarinyar fuskarsa baka tantance yanayin da take ciki. Mahaifiyarsa kallonsa kawai take yi har yanzu bata ce masa komai a kan al'amarin daya faru ba, domin ya tattara ya dawo shashin iyayensa da zama. Ya ɗago idanunsa wanda kullum suke a ƙasa a nan yaga kallon da Baba ƙarami da babarsa suke masa, ya yi kicin-kicin da fuska "Baban baby har yanzu baka faɗi sunan ƴar taka ba" Bilal ya zubawa yarinyar ido can ƙasa ya ce "RIDAYYA" "Ridayya" Baba ƙarami ya maimaita kana ya ce "Ma'ana?" Bilal ya miƙe tsaye ya ce "Zuciya, shi ne ma'anar sunan" Ɗakina ya koma ya dawo da wasu ledoji manya manyan guda biyu ya ce "Kayan dana siya nata, gobe za a kawo rago" Baba ƙarami ya ce "Kai, Ma sha Allah har da Ragon yanka? Lallai uban Ridayya mai zuciya ne, ina ka samu kuɗi?" "Aiki na yi, zan nemi aiki saboda ita tunda na kammala karatuna" Baba ƙarami ya jinjina kai. Ya miƙe tsaye zai shige ɗaki sai a lokacin mahaifiyarsa ta ce "Ina zaka da ita? Ko kana da nonon shayar da ita, ka kaiwa A'isha ita" Sak Bilal ya yi domin ya manta da batun shayarwa ya dinga tunanin wanne nono kuma? "Zan siyo a kanti" "Shi nonon kenan? Riƙon yarinya na neman sawa ka zauce Babana? Daman nonon a kanti yake ko a jikin uwarta? Bilal ya gwalo ido ai shi ya mance da wani abu a jikin mace kuma a ce da shi ake shayarwa? Juyawa ya yi ya fita kawai tare da barin parlon don yau da yarinyarsa yake son kwana ta ji ɗomin uba kamar ko wacce jaririya. Washegari da safe Ammi na zaune sai kuka ta ke a kan Baffa ya ji tsoron Allah ya amshi Ridayya, ko ita ce ta amince zata riƙe ta da amana zata kula da ita kamar su Zuhura da Junaid. Tausayin Ammi ya kama Hajiya wacce take shirin tafiya Rano, bata taɓa ganin kishiya mai tausayi kamar Ammi ba, har tattara kayanta ta yi ta ce zata bar masa gidan tunda haka ne. A haukace Mami ta shigo gidan kai tsaye ta yi wajan Baffa ya ce "Baffa ina soyayyar? Ina tattalin ina yardar? Ka tausaya mini kada ka aibata ƴata, bayan ita halastacciya ce, ka da ka yi mata baƙin tabon da zai dinga bibiyar rayuwarta, kada ka yi abinda za ka yi ladama, wallahi ban taɓa kusanta kai na da zina ba, ban taɓa ganin wani namiji bayan kai ba, shin Ubangiji ba shi ke halittar bawa a yadda ya su ba? Baka halitta bana halitta balle mu zaɓi kalar yaran da muke so mu haifa, kalar halittar Ridayya har ya kai ka nisantaka da jininka? Har ya kai ka laƙaba mata kalmar shegiya? Kada ka gurɓata rayuwar ƴarka tun ƙuruciya Baffa ba roƙe ka" Tana kuka Ammi na yi kuka, Anuty Kaltum ta cika ta yi fam ganin kukan Ammi take tamkar na munafurci. "Fatima wallahi tallahi na rantse da Allah ba zan amshi yarinyar nan ba, bana buƙatar sanin uban nata ki shige cikin ɗakinki ki zauna" "Ɗakin ya ci uwarsa da ubansa, wallahi wallahi Fatima ba zata zauna da kai ba, ka sauwaƙe mata" Baffa ya jinjina kai ya ce "Na sauwaƙe miki?" Mami ta ce "Muddin ba zaka amshi yarinyar da Ubangiji ya halatta maka ita matsayin jininka ba, ni kam ka sauwaƙe mini zan raini yarinyata in sha Allah, Ubangiji zai mini sakayya" Baffa ya jinjina kai ya kalli Ridayya dake hannun Bilal kana ya kalli Mami ya ce "Tunda haka kika zaɓa shikenan, na sake ki saki ɗaya Fatima na sauwaƙe miki" Saki babu daɗi musamman idan da soyayya, ta dinga kallon Baffa sai ta ji komai na yayewa na soyayyar da take masa daga ƙirjinta, wani abu ya tsaya mata sai kuma ta miƙe tsaye ta ce "Babban mutum bani Ridayya" Kafin ta amsheta Baffa ya yi caraf ya amshi Ridayya daga hannun Bilal ya juya ya damƙawa Ammi ya ce "Riƙe ta na bar miki ita halak malak Maryama, na bar miki ita Ammi" Cikin tashin hankali Mami ta ce "Kamarya ka bata ƴata? Ina saboda ita na zaɓi ka sauwaƙe mini domin rayuwa da ita? Da raina ina raye ƴar dana haifa zaka ce mini ka bawa kishiyarta Baffa, kishiyata ita zata raini ƴar dana haifa, ƴar da ka ce ba taka ba ce?" Baffa ya ce "E, yanzu kuma na amsheta matsayin ƴata, kuma na bawa Maryam ta raineta bana buƙatar ku rayu tare tunda kika ɗanɗana mini baƙin ciki, to kema za ki ɗanɗana naga kina mugun son waccan mai kama da dalma ɗin ko? To na raba uwa da ƴa na zaɓi kishiya ta kula da ita, ke kuma ki bar mini gidana yanzu yanzu?" Jiri Mami ta fara gani a idanunta kanta na juyawa ta nuna Baffa da hannu kana ta miƙawa Ammi hannu ta ce "Bani ƴata Maryam" Ammi ta yi murmushi ta ce "Zan bi umarnin mijina zan kula da ita tamakar ke" "Ƙarya kike baƙar munafuka makira, macuciya azzaluma" Anuty Kaltum ta faɗa tana yin kan Ammi, Ammi ta fashe da kuka,jin kukan Ammi ya saka Baffa rikicewa kansa ya fara juyawa baya ƙaunar jin kukan nata kafin Anuty Kaltum ta ƙarasa wajan Ammi Baffa ya fincikota tare da sharara mata maruka wani ihu Mami ta yi sai kuma ta sulale a wajan babu numfashi..... Imagining kana raye a duniya kana numfashi mijinka ya ɗauki jaririyar da ka haifa ya bawa kishiya ta raina, anya? *✿ MUNAFUKIN MIJI 13 ✿* Mikiya Writers Ass..... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Masu tambayar ko ina yin paid Advert? Ina yi ga wanda suke buƙata su yi magana 08164069385 Yaya A'isha ce ta nufi kan Mami dake zube a sume tana kuka da ihu domin zaton ta Fatima Batool ta rasu ta ce "Anuty Kaltum ki rabu da su ki zo Fatima, ina jin ta rasu Fatima ta mutu Anuty" Idanun Anuty Kaltum jajur a haka take bin Baffa da kallo dafe da kuncinta, zuciyarta na yi mata zafi da raɗaɗi ta ce "Alhaji Mansur ni ka mara a kan wannan azzalumar wacce daka gani babu Allah a ranta? Ni matar General ka daka?" "Zan miki abinda ya fi duka, muddin za ki shiga hurumin da bai shafeki ba, ƴa dai na ce bana so, yanzu kuma na amsa na yarda ƴata ce, na kuma dawo na amshi ƴar daga hannun uwarta na bawa kishiyarta ta raina, ita na fi gamsuwa data raini yarinyar idan kuna ganin hukuncin dana yanke bai yi ba, sai ku yi abinda kuke ganin shi daidai" Ya ƙare maganar cikin ƙonar kaifin ya juya ya kalli Ammi ya riƙe hannunta ya ce "Sorry, bata dake ki ba ko? Bata ji miki rauni ba?" Kuka Ammi ta fashe da shi tare da zubewa gaban Baffa ta durƙoshe ta ce "Baffa nikam na yafe wallahi ba zan iya rainon Ridayya ba, kana kallon kallon zargin da ƴan'uwan Fatima suke mini, ba zan taɓa cutar da wani rai dake numfashi a duniya ba, balle kuma na cutar da jinin Mami, ban taɓa ɗaukan Mami matsayin kishiya ba, saboda ta yi mini karamci a rayuwa, ta bani kai na aura ba tare da ƙyashi ba, na haifi Junaid ta kula da shi ba cuta ba cutarwa, don Allah don Annabi ka bawa Mami Ridayya ta kula da ita ta ji ɗumin jikin uwa mahaifiya, kar ka raba soyayyar gaskiya raba uwa da ƴa tamkar ka kashe mutum wa'adinsa bai yi bane ka tausaya mana, ba lallai ka fahimci haka ma amma ni ma uwa ce na san zafin haihuwa" Anuty Kaltum kallo Ammi kawai take, Hajiya ma haka hatta Mai ran ƙarfe tausayin Ammin ne ya kama shi. Muhammad-Bilal jingina ya yi da jikin bango idanunsa zube a kan Ammi, tunaninsa ya bambanta dana sauran jama'ar dake wajan, a hankali ya girgiza kai a zuciyarsa ya ce "New Episode" Ya harɗe hannunsa zuciyarsa na bugawa na rashin sanin haƙiƙanin hujjarta ta yi hakan. Baffa ya kalli Ammi sosai da kyau cikin kakkausar murya ya ce "Maryam ke na yi niyyar ki raini Ridayya, ke nake da muradin ki yi hakan, ai ita ma ta yi miki rainon ɗan'ki Junaid, sai a ramawa kura aniyyarta" Ammi ta girgiza kai sai kuma ta sunkuyar da kan ƙasa ta ɗan jima can ta ɗago ta ce "Ba zaka fahimci kuskuren da kake shirin yi ba sai gaba, Allah yana kallo tun kafin Mami ta haihu nake ƙaunar abinda ke cikinta, bana jin zan iya cutar da jikinta, idan ni na san haka ai ƴan'uwanta ba za su lamunta a ce kishiya ta yi rainon ƴar'ƙanwarsu ba, ita kanta Fatima ba zata aminta ba, Ridayya ita ce jininta ita ce haihuwarta ta fari ka bari su rayuwa tare" Baffa ya ce "Kar ki mini haka Maryam, muddin ba ki amshi Wannan ƙazamar yarinyar ba, to wallahi tallahi za ki sha mamaki na, kuma ba zan taɓa bawa Fatima ƴar ba" Sunan Fatima da Baffa ya kira sai ya ji kamar an saka guduma an daki tsakiyar kansa, ya yi baya da sauri yana riƙe kansa. "Ni ma ka sauwaƙe mini kamar yadda ka sauwaƙe wa Mami, sai ka zauna da yaranka kawai" A gigice Baffa ya zube gaban Ammi idanunsa a ƙanƙance yana riƙe ta kamar zai yi mata sujjada ya ce "Na tuba, na bi Allah na biki Maryama kar ki kuskura ki sake furta kalmar saki, azaba kike gana mini a zuciyata, aure na dake kamar auren zobe ne, auren alƙawari, auren yarda da juna da aminta muddin na barki zan iya rasa raina" Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Ammi ta sauke. Hajiya dake tsaye ta ce "Duk ba za a yi haka ba, matsalarmu ɗaya ce shi ne, sheganta yarinya da Mansur ya yi. Allahamdulillah yanzu kuma ya amshi ƴarsa da Maryam da Fatima duka ɗaya ne, ko a wajan wa Ridayya ta tashi ba za ta yi assha ba, Ke Maryam ki riƙe Ridayya Allah ya rayata har zuwa lokacin da Mansur da Fatima za su daidaita kan su, ta dawo gidan" Anuty Kaltum ta ce "Ai da salihar kishiya gwara muguwa, da makira gwara annamimiyya, green snake in the grass, Fatima Batool ba za ta taɓa dawowa gidan nan ba, idan kun ga dama a daren nan ku saka wuyan Ridayya gabas ku yanka" Hajiya ta ce "Ki yi haƙuri Kaltum, ɗa na kowa ne bawa sai mai shi, ɗan Fatima ai ɗan Maryam ne, tunda kike kin taɓa gani saɓani ya haɗa su? Kuma duk runtsi da Uba ake ado bada riga ba" Kai tsaye Anuty Kaltum ta ce "Hehehe tab, ba girin-girin ba, ta yi mai wallahi da wata kishiyar gwara gidan marayu, Ridayya kuma Allah zai kula da lamarinta, sara da sassaƙa baya hana ganji toho" Tana faɗin haka ta juya suka kama Mami tare da ficewa daga cikin gidan domin daman farkawar ta kenan daga allurar baccin da likita ya yi mata ta fito a haukace da ƙyar suka gano ita ta nufa, dukda ikon Allah da ƙudirarsa ce ta kawo ta gidan. Bayan fitar su Anuty Kaltum, Baffa ji ya yi ciwon kan da yake masa ya ragu ya samu peace of mind, ko minti ɗaya bai tsaya yin nazarin cewa Mami fa ya saka? Hakan na nufin za ta yi nisa da ganinsa, gefensa zai rasa komai nata sai ya ji tamkar daman bai taɓa auren wata mace ba face Ammi. Hajiya ta kalli Ammi da kuma Ridayya dake hannunta ta ce "Ke kuma Maryam na dawo kan ki, ki ji tsoron Allah ki riƙe wannan jaririyar tsakani da Allah ki ɗauke ta tamkar su Zuhura, idan har kika cutar da ita bayan a kan Idanunki aka raba uwa da ƴa to wallahi Ubangiji ba zai bar ki ba" Ammi dai bata kalli Hajiya ba sai cewa ta yi "In sha Allah" "Mansur mu za mu shige, daga nan zani gidansu Fatima na sake basu haƙuri kuma In sha Allah watan gaba zan dawo gani Ridayya" Baffa ya ce "To" Ya miƙe ya ce "Allah ya tsare ya kiyaye, Junaid zai kai ku ko kuma driver?" "A'a Junaid zan aike shi ga Muhammad-Bilal nan" Cewar Ammi tana miƙewa tsaye idanunta kuma a kan Bilal ɗin daya kafe ta da Idanu. Ya ɗan taka har tsakiyar parlon kafin ya tsaya ya ce "Nikam ban so, tsahirta miki nake idan ba za ki ce Yaya Bilal ba ko Babban mutum ki barshi" Ammi ta riƙe baki ta ce "To ba zan ce Yayan ba ba kuma zan ce Babban mutum ɗin ba, Muhammad-Bilal zan faɗa tunda haka aka raɗa maka" Bilal ya ƙanƙance idanunsa rai ɓace ya ce "Baffa ka yi wa matarka magana yanzu ni idan na ce Maryam za ta ji daɗi"Ammi ta saki baki sai kuma ta nufi kan Bilal ta ce "Ungu wannan dan ubanka ka rama ka ji daɗi, ni kake cewa Maryam?" Bilal ya yi kicin-kicin da rai fuskar nan a ɗaure kamar zai ce ya shiga uku. Baffa ya kalli Bilal kawai sai bai ce komai ba, Hajiya ce ta ce "Kai Babban mutum Maryam ai matar ƙanin mahaifinka ce, kar ka kuma ambaton sunanta mahaifiyarka ce ai" Ya yi gaba cikin kamilalliyar nutsuwarsa yana bada faɗi har ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce "Ita ma ta dinga ce mini Yaya Bilal, idan ba zata iya ba ta kalle ni ta shige" Hajiya ta rafka salati ta ce "Uwar taka ce zata dinga ce maka Yaya?" Har ya buɗe ƙofa ya dawo da baya yana riƙe kansa dake juya masa sosai da sosai ya ce "Ta faɗi sanda ta yi cikina ta haifa, nikam bana son haka raini ne da gaske raini ne Granny" Ya fice yana banko ƙofar, Ammi ta yi ƙwafa a ranta ta ce "Zan ci ubanka ne, shegen yaro me uban son girma ma rainin kowa da taurin kan tsiya" A fili ta ce "Ai kar ki damu Hajiya haka halinsa yake sai mu dinga cewa Yaya Bilal ɗin muna bashi girma kamar yadda yake so" Sallama sukai Hajiya ta fita zuwa harabar gidan, ta nemi Bilal ta rasa domin ya ji haushin yadda ta ce Ammi babarsa ce. Wani irin shu'umin murmushi Ammi ta yi tana girgiza ƙafa wacce ta harɗe su ɗaya kan ɗaya kafin ta miƙe tsaye ta ce "Ni za a bawa rainon ƴar kishiya? Ni Maryam ko a gidanmu ba kishiya, na zo nan na yi zaman bora sannan a haɗani da rainon ƴar kishiya?" Dariya ta kece da ita sai da ta yi mai isarta kafin ta juya ta ƙura wa fuskar Ridayya kallo kana ta ce "Barka da zuwa hannun kishiyar uwa, barka da zuwa uƙubar kishiyar uwa, zan fanshe duka haushin da ubanki ya gana mini da cikinki, zan fanshe fifikon soyayyar da ubanki ya nuna a kan majaifyarki, na rantse da Allah duk abinda na haɗiya na ɓacin rai da kishi a yanzu zan amayo da shi a kan ki, zan tabbatar muguwar azabar da zan miki sai ta ƙarasa rayuwarki, kamar yadda Mansur yake mugun sonki tun kina ciki, gashi yanzu a ranar da kika zo duniya tsana mai tsanani ta maye gurbin soyayyar, ai ɗan halak shi ya san idan an yi masa ya rama, tuwon girma, miyarsa nama" Ammi ta girgiza kai tare da kaɗa hannu ta ce "Ɗan kishiya ba zai taɓa zama ɗa ba, kamar yadda kishiya ba zata taɓa zama ƴar'uwa ba" Hannu ta saka ta ɗauki Ridayya sai kuma ta saka zaftara-zaftaran faratanta ta gantsarawa Ridayya mintsini a cinya har sai da fatar wajan ta sutale, tunda a ka haifi yarinyar ba wanda zai ce ya ji kukanta banda wanda likitoci suka saka ta yi, sai kawai ta dinga zabura ita kaɗai. Tsananin azaba da yadda mintsinin ya ratsa jaririyar ƴar kwana biyar zuwa shida a duniya wacce bata san meke faruwa ba ya saka Ridayya sakin wata ƙatuwar shaƙuwa ita kaɗai gumi zai yanko mata yake, ta dinga zabura kamar wacce ake kaɗa mata gangi, dukda irin azabar da Ammi ta yi mata bai daka Ridayya yin kuka ba. Ammi ta duba taga fatar wajan ta sutale jini na zuba ta ƙarasa kitchen ta kwashi gishiri ta manna a wajan, ta kwashi ya ji shi ma ta manna, yarinyar ta dinga sakin ajjiyar zuciya fuskarta ta yi sharkaf da gumi. Ganin har yanzu ba ta yi kuma ba ya saka Ammi cewa "Tsinanniya gayyar tsiya, yadda ban taɓa ƙaunar uwarki ba wallahi ba zan ƙaunace ki ba" fuuu ta yi part ɗinta a tsakiyar parlo ta shimfiɗe Ridayya bayan ta cire mata kayan da Bilal ya saka mata ta ƙure a.cn dake cikin parlon kana ta yi cikin bedroom ɗinta. Wata number ta kira ana ɗagawa ta ce "Ki tura masa raguwar kuɗin, ki zo ina buƙatar ganinki" Tana faɗin haka ta kashe wayar. Muhammad-Bilal na fita ya nufi ɓangaren iyayensa ya samu Umma zaune tana kallo, yanayin yadda ya shigo ya sa bata kula shi ba, duk da mutum ne shi mai zurfin ciki bai fiya shiga sabgar da babu ruwansa ba, sai a yi abu sau naya bai tanka ba ta rasa dalilin daya sanya ya damu da lamarin Ridayya? Ta girgiza kai tare da ci-gaba da kallonta. Wanka ya yi ya shirya cikin wata blue black ɗin jallabiyya mai kyau da taushi sai zabga ƙamshi yake komai na ɗakinsa a tsaftace yake, drawer ɗin littafansa daban tari guda duk na addini ne, Alkur'ani, hadisi, tafsir, azkar, ƙawa'idi, Dala'ilu, umdatul ahkam, zajidul zauj, hakƙun mubin littafai na addini kala-kala. Yana tsaye hannunsa ɗaya goye a bayansa takardun kammala karatunsa yake gani, bai taɓa sha'awar neman aiki ba sai yanzu. Kasancewar ɓangaren Accounting ya karanta fannin business, finance, and accounting ya sanya ya fita da sakamako mai kyau, baya wasa da duk abinda zuciyarsa ke so da muradi yana da naci, da ƙwallafa rai ga taurin kai ga duk abinda zuciyarsa ta kwaɗaitu a kai, ya dinga kallon takardun yana tunanin ta ina zai samu aiki? Ko bai samu ba, ta wacce hanya sai dinga neman kuɗi? Wayarsa ya ɗauka da takardun ya fita bakinsa ɗauke da addu'a ya haɗe rai sosai a dole baya son raini gani yake yawan magana da sakin fuska shike kawo raini. Makarantar islamiyyar da yake koyarwa ya fara zuwa, ɗalibai na ganinsa suka shiga hankalinsu ya nufi aji shida ajin ƴan sauka gabaɗaya ƴan'mata da samari ne a ciki waje ya nema ya zauna suka gaishe shi, ɗaya bayan ɗaya suke bashi haddar Alkur'ani har aka zo kan Muwahif, duk sanda zata bawa Bilal karatu sai ta samu matsala gabanta ya dinga faɗuwa saboda tsananin kwarjininsa, haiba da mazantaka ta cikakken namiji. A hankali ya tsaya da danna wayarsa ya yi mata kallo ɗaya jin haukan data rafka masa kowa ya yi nisa amma har yanzu a izu biyar take bata jima da zuwa Ali'imran ba. Kallon da ya yi mata da nufin ta gyara sai ya ga ta ƙura wa fuskarsa Idanu da kuma tsayayyen gemunsa mai kyau da sheƙi. "Keee" Ya kira sunanta amma ta shagala wata ta zungureta ta ce "Wahif Ustaz yana magana, Wahif" Firgigit ta dawo hayyacinta tun kafin ya yi magana ta fashe da kuka tana ƙoƙarin cewa "Ustaz ka taimaka mini wallahi ina...." "Out" Ya faɗa a tsawa ce da gudu ta miƙe tare da yin waje tana rushewa da kuka, bayan gama karatun ya fita ya nemi aiki ko na hannu ne bai samu ba da ƙyar ya samu aikin jiran wani babban shago na wani Alhaji. Sai magriba ya dawo gidan. Dr ne tsaye yana ƙare wa Dada kallo kafin ya ce "Mu je office" bayansa ta bi ita da Yaya A'isha ya ja kujera ya zauna idanunsa a kan Dada kana ya sauke ajjiyar zuciya yana zare glasses ɗin idanunsa a hankali ya ce "Mun sauya mata ɗaki zuwa ICU" Yaya A'isha ta zare ido ta ce "ICU Dr? But why?" "Eclampsia, dalilin jijjigar da ta yi kafin a yi mata Cs, binciken da mukai ya tabbatar tana da hawan jini kuma ta ɗauki lokaci tana naƙuda wacce ya haifar mata da zazzafan zazzaɓi da ciwon kai, sanda ta fara jijjigar mun su yi mata Loading dose mgso4 amma babu hali hakan yasa mukai aiki aka cire babyn" Likitan ya yi shiru can ya ce "Ta farfasa bakinta sosai sanda ta yi jijjigar, babbar damuwar ta yi saurin farkawa daga coma da wuri kuma hakan hatsari ana iya samun rasa rayuwa ko hankali gabaɗaya" Yaya A'isha ta fashe da kuka sosai ta ce "Amma dukda wannan baƙar azabar da Fatima Batool ta sha wajan haihu aka iya ɗauke jaririyar a bawa kishiya? Ko zafin haihuwar da wahalarta bai gama sakinta ba, ga saki ga ƙwacen dole da raba soyayya ina Alhaji Mansur zai kai wannan hakin don Allah?" Likitan ya ce "Pardon, bangane ba an karɓi baby ba, kuna nufin babyn baya cikin asibiti under special care na likitoci? Ba kusan cewa Eclampsia na iya taɓa jariri ba?" Hajiya ta yi jigum saboda wannan tashin hankalin ta kuri Anuty Kaltum ta ce "Jijjiga na taɓa jariri ne Dr?" Ya jinjina kai ya ce "Sosai ma, suna samun Cerebral palsy irin yaran nan Abnormal dolaye irin galahanga ɗin nan, babyn ma na iya rasa ransa, ko a haife shi yaƙi kuka kamar yadda itama babyn taƙi yi, idan baby ya samu Cerebral palsy akwai matsala, wasu suna kurmancewa ne, wasu basa gani sosai, ko kuma kaga gabaɗaya yaro baya gane karatu" "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Shi ne abinda Dada take faɗa Yaya A'isha kuka kawai take ta ce "Don Allah don girman Allah Dada a dawo da Ridayya wajanmu, yarinyar ba cikakkiyar lafiya ta cika ba" Godiya Dada ta yi wa Likitan tunda ba za su samu damar shiga wajan Mami ba sai zuwa safiya tana addu'a a ranta Ubangiji ya sa kada sanadin haihuwa Mami ta rasa tunaninta ko ta haukace. Wajan ƙarfe goma Ammi ta ruski Baffa a ɗakinsa yana ganinta ya ɗan saki murmushi ya ce "Uwar gida ran gida, idan ba ke ba gida" Ammi ta juya idanunta ta ce "Yau kuma kirarin na uwar gida ne, ina na amarya Fatima?" Nan da nan annurin fuskar Baffa ya ɗauke domin baya ƙaunar jin sunan Fatima ko da wasa. Ya riƙe kafaɗun Ammi idanunsa cikin nata wanda suke ƙara rikita shi ya ce "Maryama kar ki kashe ni da raina don Allah" Ta ware idanunta kafin ta ce "Rufa mini asiri na kashe mijin Fatima baban Ridayya Uncle ɗin Bilal" ai gabaɗaya Baffa ya ji ɗakin na juya masa yana jin kamar ta caka masa wuƙa a zuciya ne ya riƙe ta da ƙarfi ya ce "Ki tausaya mini Maryam, sunan Fatima azaba ne a gare ni ban so koda wasa,na tuba; na bi Allah na biki matata Maryam" Ta yi murmushi tana kashe mata ido ta ce "An gama ranka ya daɗe, angon ƙarni" Juice ta bashi ya kalli ruwan lemon jajur da shi kamar an kaɗa jini, bisa umarnin zuciya da abubuwa dake fusgarsa ya damƙi hannunta gabaɗaya mai ɗauke da kofin ya shanye lemon. Bayan ya shanye yana tsaye ta ce "Zauna mana Baffa?" Ya kalleta sai ya ce "Na zauna Maryam?" "Zauna Baffana" Ya nemi ƙasan kujera saman carpet ya zauna ta yi wani kalar murmushi ta ce "A'a koma kan kujera magana za mu yi" Ya yi jim ya ce "Na zauna a kujera Maryam? Na zauna ba matsala?" Ta jinjina kai ya miƙe jiki na rawa kamar mazari ya zauna a kujera ta harɗe ƙafa ta ce "Mansur kuɗin rainon ƴarka za mu yi magana, duk wata zaka bani dubu ɗari, dubu ɗari da hamsin kuma kuɗin siya mata madara da kaya" Ya kalleta ta ce "Ka ji?" Ɓarin da jikinsa yake ya tsananta ya ce "Shikenan koda saura? Yanzu zan tura miki kuɗin ko sai anjima?" Ta yi murmushi ta ce "Da safe, sai abu na gama ko da wasa kar na ganka a ƙofar gidansu Fatima da niyyar zuwa biko" Ya girgiza kai ya ce "Ba zani ba" Ta ce "Good, bacci na ke ji yanzu da safe zan zo ka faɗa mini duka abubuwan daka mallaka, ka faɗa mini me da me ka mallakawa Ridayya tun tana ciki, ka faɗa mini irin abubuwan da Fatima take maka wanda kake so" Ya jinjina kai ta ce "Ka ji ko?" "E, na ji Allah ya kaimu" Waje ta yi bita da sauri sai da sukai nisa ta tsaya ta ce "Ya kake bina Baffa salon ka ja mini masifa?" Ya marairaice fuska ya ce "Tambayarki zan yi daman zan iya kwanciya a gado na yi bacci?" Ta ce "E mana jeka" Ya ce "Thank you" Ya juya. Tana komawa part ɗinta ta samu Ridayya kwance inda ta barta ƙafa ta ɗaga zata taka mata ciki sai kuma ta girgiza kai ta ce "Idan na kasheta mene ribata?" Sai ta ɗauki Ridayya ta yi mata tumɓur har pamper ɗin ta cire ta zaga can baya wajan bola ta saka ɗan'kwali a ƙasa kana ta ɗora Ridayya a kai cikin bolar shirgin gidan ta juya, dare ya raba kafin ka ce me cinnaku sun yayyame saman fatarta sai gantsara mata cizo suke, sun cika gabanta hancinta saman laɓɓanta har cikin idanunta cinnaku ne sai gatsa mata cizo suke ga tsanyin dare tsananin azaba ya sanya jaririyar daddagewa ta yantsara uban ihu cikin tsakiyar daren sakaliyya.... Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv *✿ MUNAFUKIN MIJI 14 ✿* Mikiya Writers Ass..... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Nimcyluv Fitowarsa kenan daga shashinsu domin yin shur na azumin Alhamis, tunda ya fito yake jin zuciyarsa babu daɗi, ya yi shiru yana jin yadda iskar gari ke kaɗawa tana bada wata amintacciyar ni'ima mai saukar da nutsuwa a zuciya. Saukar kukan jaririyar ya yi daidai da lokacin da ya ji kansa ya sara, ya yi jim yana son tabbatarwa da kansa abinda kunensa ke jiyo masa. Da sauri ya miƙe tsaye carbin hannunsa na ƙoƙarin faɗuwa zuwa ƙasa, gashi farar jallabiyya ce tas a jikinsa. Direction na inda kukan ke fitowa yake bi, a haka har ya isa daidai inda bolar gidan take ya waiwaya a hankali, amma bai ga kowa ba zatonsa ya bashi yau ko rashin sa'a ya yi mutanen ɓoye ke son buɗe masa ido? Ya ci-gaba da tasbihi a zuciyarsa. A bin mamaki kuma lokacin jaririyar ta daina kuka, yana ƙoƙarin juyawa ya sake jin saukar kukan nata wanda yake shirin rusa nutsuwar daya gino a kanta, cikin sauri ya fiddo wayarsa ya kunna torchlight tare da haskawa. Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! A gigice ya saki wayarsa dukda ƙasan zuciyarsa bai gama tabbatar masa daba gamo ya yi ba, ya saka hannu a fili kuma cikin kamilalliyar muryarsa ya ke azakar na neman tsari da kariyar Ubangiji. Da duka hannu biyun ya ɗauki jaririyar yana matsawa wajan haske, ya runtse idanunsa da sauri lokacin da ya yi tozali da Ridayya, fatar jikinta ta kumbura jini sai zuba yake tako'ina a jikinta, da sassarfa ya nufi ɓangarensa ya shiga bedroom ya rasa abinda zai yi duka wannan abubuwan bai san su ba, sai jaririyar ya gama sha'aninsa a gidan bai kalle shi ba, balle ya san yadda ake kula da su. Ruwan shower ya kunna yana ƙoƙarin zuba mata sai kuma ya girgiza kansa ya koma ya kunna hiter kafin ruwan ya yi zafi ya nufi saman gado, ya ɗora Ridayya a ciyarsa. a hankali yake bin fatar jikinta da kallo, dukda kasancewarta jaririya amma sam bata da hasken fata gashi da cinnakun da fatar suna neman zama ɗaya ga jinin dake fita duk ya dagule fatarta. Audiga ya ɗakko ya dinga share jinin yana marmasar da cinnakun amma tamkar na asiri sun kafe gashi sai tsala ihun azaba Ridayya ke yi. Ustaz ya inda zai saka kansa idan ya tsora mata idanu sai kawai ya sauke ajjiyar zuciya, da ace shi ma'abocin kuka ne da karaya da lamarin rayuwa da tuni ya raunata. Ya ci-gaba da gogewa har jinin ya fita a hankali ya dinga kaɗe cinnakun wasu su fita wasu kuma suna nan. Ya ajjiyeta sai kuma ya dawo ya ɗauketa gani yake tamkar wani abu ne zai sameta idan ya bar ta. Ruwan zafin ya haɗa daidai wa daida, ya saka detol a ciki. Zabura Ridayya ta yi sanda ruwan ya ratsa ta, ga sabuwar fata ga ciwo ga zafin ruwan wanda Ustaz ya kasa fahimta ya ɗauka duk ciwonne ya sata kuka, ya dinga wanke mata jiki a hankali kamar ƙwai ya gama ya sake haɗa wani ruwan ya mayar da ita har fatar ta ɗan washe cinnakun suka fita a towel ɗinsa ya naɗe ta, tare da fitowa. Farar jallabiyyar Ustaz ta ɓaci da jini ya ajjiye Ridayya saman gado zai juya ta canyara ihu ya yi saurin dawowa ya ɗauketa ya sata a kafaɗa. Fatar wuyansa ta fara tsotsa kamar ta samu nono. Murmushi ya saki mai taushi jin yadda take ƙoƙarin neman abinci ido biyu, sakkota ya yi sai ta fara motsi da nishin kuka ya saka mata yatsarsa a hannu da sauri ta fara tsotsa tana sauke ajjiyar zuciya. Ustaz ya lumshe idanunsa wani irin tausayi ya kama shi, bai taɓa ganin wannan rashin imanin ba ko a fina-finai Hausa da littafan Hausa ta marubuta suke yi. Ruwan zam-zam ɗin daya jiƙa tare dabinon ajwa ya ɗakko ya yi kauri sosai ya bata ta dinga sha, sai ta sha sosai kana ya cire. Jin ta yi shiru ya miƙe ya watsa ruwa a jikinsa ya sauya kaya daga jallabiyya zuwa three qauter Ustaz baya son kaya masu nauyi shi ya sa ba kowa ke shigowa bedroom ɗinsa ba, idan har shi kaɗai ne za ka iya samun shi daga shi sai trouser. Sai a lokacin ya samu damar ƙare wa yarinyar kallo, idanunta rufe har yanzu babu wanda zai ce ya taɓa ganin su. Idan ka ce real definition of blac skin kai tsaye Ridayya ce, baƙin mai duhu sai da yana haske za kaga har ɗaukan idanu yake, yanayin shi bama mai irin maiƙo ɗin nan bane ya fi kama da baƙi irin na ƴan Ethiopia. Laɓɓanta jajur suke duk da suna da girma da kauri amma kamar a tsaga jini ya fita, gashin gira a cunkushe suna neman haɗe wa waje guda, ga gashin ido zara-zara sumarta har ta shige goshi ko'ina na jikin Ridayya suma ne. Ya kai hannu ya taɓa lips ɗin da sauri ya ɗauke hannun yana yarfe wa jin kamar fatar wajan zata ciro saboda laushi ya rufe ido kamar mai koyan magana ya ce "Ya subuhanallahi!" Yana faɗin haka ya yi shiru, har gari ya yi shiru dab da subhi Ustaz na zaune ya saka Ridayya a gaba da kallo a hankali ya zunguri cibiyarta. "Open your eyes shalele" Kamar tana jinsa haka Ustaz ya ga idanunta sun buɗe ta kalli sama da sauri ta rufe saboda haske, can ta ƙara buɗewa ta ƙura wa waje guda da kallo, Ustaz sai yaga kamar shi take kallo bai san kallon ƙoda bane. "Allahu Akbar, Ma sha Allah laƙuwata illabillah" Idanun Ridayya irin su a kaf gidan, tsarin halittar da Ubangiji ya yi mata daban yake, kamar yadda kamanninta ya sha bambam dana jama'ar gida haske tas da su kamar ƙwalla ta kwanto manya wanda idan ta kafe ka da su sai ka firgita, akwai wani irin sirri a cikinsu. Ya kwanta gado ganin kamar tana jin sanyi ya saka ya cire towel ɗin ya ɗora ta a saman ƙirjinsa ya rufa mata towel ya rungume ta, a ransa yana so ita ma ta ji ɗumin jikin uba mahaifi. "Babana" Ya ji kiran sunan a saman kansa, bai buɗe ido ba ya sake bubbuga pillown da yake kai ya ƙanƙame abu a ƙirjinsa ƙafarsa ɗaya a ƙasan gadon wacce yake jijjiga wa har bacci ya ɗauke shi. "Za ka yi missing jam'i ka ɓatawa mutane lokaci" Bakinsa ɗauke da addu'a ya buɗe ido, sai kuma ya ƙanƙance su ya kalli Umma ta ce "To Babana kar ka mini faɗa, mutum kamar rainon iska ya ce wai baya son magana a saman ka? Baya son faɗa baya son tsawa?" Ya sake shigar da idanunsa ciki ya kalli Umma can ya girgiza kai a hankali ya ce "Faɗa da asubar nan faɗa Umma? Kai na zai cire nikam zai cire" Idanunsa sukai jajur. Umma ta riƙe haɓa ta ce "Me kake ƙanƙame wa ne haka Babana?" Ya shiru ta miƙa hannu zata cire towel ya yi saurin riƙe wa ya kalli Umma yana kicin-kicin da fuska ya ce "Tsaraici na, umma tsaraicina za ki yaye?" "Gidanku kai da tsaraicin, ni uwarka ce har wanka na yi maka ko yanzu ta kama ki tas zan wanke ka" A gigice ya ɗago Ridayya daga ƙirjinsa da numfashinta ke sauka a hankali ya leƙa, wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke shi kam da idanun Shalale biyu ai Umma ta gama zubar masa da girmansa wallahi. "Matata kawai ke da ikon ganin tsaraicina, ki tausaya mini a rufe maganar nan nikam" "To da za ka yi auren ma ni ba haka ba? Ni tun da ƙuruciyarka nake ganin matarka" Ta faɗa tana mamakin abinda Muhammad-Bilal ke ɓoye wa a ƙirji. "Ni fa ba zan aure ba" Gaban Umma ya faɗi ta ce "Me kake nufi" Ya yi shiru bai tanka ba, yaƙi motsa wa, tana kallon yadda jijiyoyin kansa duk suka fito ƴar wannan maganar da ya yi ta ce "Idan ba zaka samu damar yi wa jama'a jam'i ba a sanar wani ya yi" Tasan ko zai makara ba zai taɓa tashi ba, duk duniya Ustaz ya tsani wani yaga surar jikinsa. Fita ta yi tana jan ƙofar ya bi bayanta da kallo. Ya miƙe yana ajjiye Ridayya ya rufe ta ruf, wanka ya yi ya shirya cikin jallabiyya mai taushi kana ya ɗauki carbi ya rufe ƙofarsa da key ya nufi masallaci. A nan ya samu shi kaɗai ake jira, son girman Ustaz ya saka suke girmama shi hakan yana masa daɗi uwa ub kaifin tunani da basira bayan idar da sallah suka jero da Baffa da Baba ƙarami ya gai da su bai tsaya jin me Baffa ke faɗa ba ya yi gaba. Wani wankan ya yi Ridayya ya saka mata fararen kaya tare da hula wanda ya siya mata ta yi luf har yanzu fatar kuma a kumbure take, ba tare da kowa ya sani ba ya nufi asibiti da ita. Ustaz na zaune gaban Dr yana jin bayaninsa da yake cewa "Kawo yanzu bamu da tabbaci da zubin hankalinta, amma ganinta lafiya yake matsalar bakinta kuma da hanci ya faru ne dalilin jijjigar daya taɓa ta tana ciki, zamu ɗora ta a magani kuma zamu ajjiyeta a wajan mu, komai zai daidaita In sha Allah" Ustaz idanunsa rufe ya jinjina kai. "Cikakken sunanta?" "Ridayyerh Muhammad-Bilal Rano" Dr ya kalli Ustaz da kyau, ya san Ustaz amma bai taɓa ganin mutum mai bala'in jinkima da rashin damuwa da abubuwa ba sai shi. Ya cike komai kana ya ce "Ustaz yarinyar nan idan na ce bata buƙatar kulawa na yi ƙarya, domin cinnakun da suka shiga gabanta sun yi mata illa sai yanzu muka cire wasu, fatar wajan.....," "Faɗi wani abu, ba wannan ba" Dr ya ce "Tana da ƙarancin lafiya a nutsu a tsaya a kanta a bata kulawa sosai da sosai, bayan mun sallame ta zan rubuta madarar da za a bata da yadda ake amfani da ita, dukda na so ta samu ishasshen nonon uwa ko dan kaifin basira amma kowa da nasa ƙaddarar" "Ni zan shayar da ita" Dr ya zaro ido waje sosai sai kuma ya yi dariya ya ce "Shayarwa ta iyaye mata ce" Ustaz ya miƙe tsaye can ya ce "Maza ba sa yi?" Yana yatsuna fuska kamar me. "Halittar maza data mata ai bambancin su a bayyane yake, ban taɓa ganin namiji ya shayar ba, tunda Ubangiji daya halitta nono a ƙirjinsa bai halitta shi da ruwa a ciki ba, wannan ƙudirar da bowayar mata iyayenmu Ubangiji ya bawa, Allah kuma ya saka musu da fificin alheri domin bama da abin da za mu biya su, za su shayar damu tsayin watanni ashirin wasu shekara biyu ba, ba tare da gajiyawa ba, ba tare da tunanin sun ci ko ba su ci ba, ko uwa zata yini bata ci komai ba; ba zata fasa shayar da ɗan ta ba, ai uwa ta musamman ce shi ya sanya Ubangiji ya fifita ta fiye da uba, duk wanda bai ni mahaifiya ba wallahi ya shiga uku" Ustaz ya yi jim tunani fal ransa, taya zai zama uba kuma uwa a wajan Shalale? Da wannan tunani ya fita wajan biyan kuɗi tare da barin asibitin ko ɓangaren su Mami bai je ba, tunda bashi da masaniyyar sun koma ICU. Gabaɗaya Ammi ta manta da batun wata jaririya domin ba ita ce a gabanta, har wajan ƙarfe 11 na safe tana Hakimc ce a parlon tana jiran zuwan Biba, 11:30 daidai ta ƙarasu duk suka zauna a parlo tun kafin su gaisa Biba ta ce "A haɗa mini breakfast please, lafiyayye da naman kaza" Ammi ta ce "Biba kamar wacce ta yi kwanan yunwa?" "Uhmm Zawarci masifa ne Maryam, bani da kuɗi gida kuma a wulaƙance ake kallona wai saboda na kashe aurena" Ammi ta girgiza ƙafa cikin izza ta ce "Lallai, ai laifin ki ne Biba wake wasa da gidan miji? Ai idan ba ki kori ta ciki ba, bata isa ga kora ki ba yanzu ai ta ci bulus" "A'a fa, na fita ne kawai amma babu abinda muka fasa yi da Muktar wallahi ko ƙwayar shinkafa sai bawa iyalinsa sai da umarni na, ai lafiyayyar mallaka aka yi mini a kansa, wai a haka bana wani son shi,da son shi nake ko uwarsa sai da izinina sai gaisar" Ammi ta miƙe "Makira ce ke, shu'umancinki ya girmami nawa Biba ajina bai kai naki ba" Biba ta cire mayafi ta yar, tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ce "Ai gida yanzu ya zama namu, dole na zo na ci rabona bati available" Ammi ta dawo ta zauna ta ce "Yanzu za a kawo miki, to ya ake ciki kin tura kuɗin?" "Na tura, ya kuma ce dole ki zage damtse domin akwai wani rabon mai ƙarfi tsakanin Mansur da Fatima, iyayenta malamai ne a kodayaushe aikinmu zai iya lalacewa" Ammi ta miƙe tsaye ta ce "Tab ɗin, to wallahi tallahi Fatima ta yi kaɗan, ita da gidan nan har abada komai nata sai na mallake shi" Biba ta girgiza kai ta ce "Maryam shi fa yaƙi ɗan zambo ne, idan ba ki iya ba sai a tashi dake, kamar wasan ƙwallo ne mai tunani da kaifin basira shike da nasara, cin nasarar ki da Maryam dole a sauya taku" Ammi ta dawo da baya ta ce "Ya zan yi yanzu?" "Ki zauna" cewar Biba, ta girgiza kai ta ce "Bana jin zan iya zama, ba ki san yadda Mansur yake mutuwar so da ƙaunar Fatima ba, ba ki isan irin burin daya ɗauka a kanta da abinda zata haifa ba, komai ya samu Fatima baya ɓoye so da ƙaunarta a kan idanuna, ya ɗanɗana mini azaba, ko a kwance muke idan zai kira sunana Maryam wallahi Biba na faɗa miki sunan tsinanniyar yake kira, a plan ɗina babu kishiya ko dana barshi ya aureta baya nufin da zuciya ɗaya na yi hakan, na rasa uwar da Fatima ke bashi" Biba ta ce "Biyayya, soyayya" Ta faɗa tana zuge cinyar kaza a bakinta ta ɗora da "Kin san biyayyarku ba ɗaya bane, Fatima ta iya soyayya ta iya zama da mijinta, kuma ba ki san wani abu ba, soyayyar gaskiya bata da dalili ko hujjar yinta musamman first love, shi kansa bai san dalilin daya saka yake son Fatima ba" "Mene mafita? Ko mu kashe yarinyar ya zama babu wani abu daya yi saura tsakaninsu" Biba ta ce "Matsalata daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa ce dake wallahi, ai da yarinyar za ki yi amfani kina kwashe komai daya mallaka kafin tunaninsa ya dawo, daga nan sai mu je plan ɗinmu na gaba" Ammi ta jinjina kai daga waje suka ji Junaid na ƙwalla kiran sunan Ammi ta miƙe ta nufi hanyar fita. Baba ƙarami ta gani zaune a parlo shi da Junaid sai kuma Zuhura, fuskarta ɗauke da fara'a ta zube a kan ƙafafuwanta ta ce "Baba ƙarami an yini lafiya? Ya Umman Ustaz?" "Allahamdulillah" Ya bata amsa ta ce "Ma sha Allah, Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya ƙara lafiya da nisan kwana, Baffa bai fito bane?" Ya ce "Ba wajan Mansur na zo ba, ƴa ta na zo gani" "Ƴa kuma?" Ya ce "E, ƴar gidan Muhammad-Bilal" Gaban Ammi ya faɗi sosai domin ta manta da batun wata Ridayya sam ta ce "Au ai yanzu na yi mata wanka har ta yi bacci wajan Baffa" Sosai Baba ƙarami ya ji daɗi ya ce "Ikon Allah shi Mansur ɗin ya ɗauke ta?" "Sosai Baba, daman rashin fahimta ne kuma yanzu Allahamdulillah na fahimtar da shi idan ta tashi zan zo na kawota ba ruwanta ai bata rigima sam" Ya miƙe ya ce "Sannu Maryam, Sannunki Allah ya saka miki da alheri yadda kika kula da Ridayya Allah ya kula dake" Fara'a kamar zata yi magana a fuskar Ammi ta ce "Ba komai ai ɗa na kowa ne, bamu san wanda zai ji ƙanmu ba, Fatima ta fi ƙarfin komai waje na" Sallama ya yi mata ya bar gidan. Ta samu Baffa zaune a kujera ya yi shiru idanunsa a sama "Baffa" A tsorace ya miƙe jiki na rawa ya ce "Ranki ya dade an yini lafiya?" "Lafiya lou, ni fa ban ga Ridayya ba" Ya ce "Wace haka?" Ta ce "Ƴar Fatima daka maƙala mini riƙo ita nake magana" Ya taɓe fuska ya ce "And so what? Ki share kawai" "Mansur!" Ta daka masa tsawa ya ɗimau ce ya zube gabanta ya ce "Na tuba ki yafe mini" "Kar ka bar su Hajiya su dawo ganin Ridayya ka ce kun daidaita da Fatima ta dawo ka ji ko? Kuma ka fita neman ƴarka wallahi kai hukuma za su rufe bani ba" A ɓangaren Mami jiki sai addu'a domin bata san idan kanta yake ba tunda da aka kai ta ICU. General ya dawo Anuty Kaltum ta zayyana masa komai ya ce Baffa zai ci Ubansa sai ya karya masa hannu sai ya sauya masa kama zai kuma kulle shi, idan shi mahaukaci ne zai nuna masa ƙarshen hauka, idan mugu ne shi zai nuna masa shi a iya mugunta babansa ne, zai maka shi a court zai yaɗa har Human rights su Unicef duk sun shigo Maganar a ina ya taɓa ganin uwa na raye an bawa kishiya riƙo? Kuma ya ƙwace jaririya ai ko yana da iko yin haka banda a kan jaririya. Ko da Dada ta ji abinda Anuty Kaltum da General suke shirin yi ta dinga masifa ita yanzu ta lafiyar ƴarta take tana sane da komai, kuma za ta yi taking action on it, but not now har sai Mami ta samu lafiya, kuma ko da wasa ta ji labarin Anuty Kaltum ta je gidan to wallahi bada yawonta ba sai ta sassaɓa mata idan ranta ya yi dubu sai ya ɓaci, banda zafin rai babu abinda ta iya. Anuty Kaltum ta fusata ta tattara kayanta ta bi mijinta suka bar ƙasar bakiɗaya. Lokacin da Ustaz ya dawo da Ridayya daga asibiti ƙaramin yaƙi a kai a gidan, har Baffa na cewa wallahi sai ya ɗaure Ustaz muddin ya ƙara taɓa Ridayya idan kuma da gaske shi ne ya cikinta basu da labari sai a faɗa. Ranar kukan makirci Ammi ta dinga yi tana iƙirarin zata bar wa Baffa gidan, sosai Baba ƙarami ya ji zafin maganar sai bai nuna ba, Umma kuma ta ce idan har ita ta haifi Ustaz wallahi ta sake ganin da yarinyar sai ya san true color ɗinta, ya fusata ya tattara kayansa ya bar garin daman karatu zai je ƙaruwa na shekara huɗu duk a kan Ridayya domin ya bata rayuwa mai kyau, riƙon Ridayya ya dawo hannun Ammi, ta kaɗa ruwan gasara ta ɗora mata cikinta ya kumbura kuma ta hanata ruwa, izaya kala-kala Ridayya ta tashi wata gala-gala sai a kira sunanta bata san ita ake kira ba, kullum tana naɗe kanta yaƙi tsayiwa. Daga ƙarshe maganin bacci Ammi take bata yarinya ta yi ni guda cur tana bacci tana farkawa zata sake bata, har ya yi effecting nata, bata taɓa yi bacci idan ba a bata maganin ba, ta zama ƴar maye wanda ƙarfin maganin ya girmeta ya fara taɓa tunaninta yanzu za ka yi magana yanzu zata manta me ta ce. da ƙyar aka samo ta fara tafiya yi ɗaya biyu zata faɗi ko abinci aka bata ci idan ba gasara ba sa maganin domin su ta sani matsayin abinci sai gayen tuwo. Sanda ta isa saka makaranta Ammi ta ce ba yanzu ba, a tausaya mata ai yarinyar ba wani wadataccen hankali gare ta ba, karatun ma ba lallai ta fahimta ba, dukda cewa akwai makaranta irin ta su ta samu rangwamen hankali. Ustaz har tsayin shekaru huɗu bai dawo ba, ya tafi ta biyar farin ciki ya kama Ammi lokacin ta mallake gida da ita sai yaranta. Baba ƙarami ya daina shiga part ɗin saboda Baffa bai fiya zama ba, arziƙi ya ci uban na da ta ko'ina alheri zuwar masa yake. Shuɗewar shekaru shida. (After 6 years) A hankali ta lallaɓa kitchen ta leƙa tukunyar da ta hangi nama, sau biyu ta taɓa ci amma a rayuwarta tana son nama hannunta na karkarwa saboda rashin ƙwari idanunta na yi mata yana-yana saboda yawan bacci. Wani kyakkawan murmushi ya suɓuce mata lokacin da hannunta ya isa kan tsokar nama ɗaya. "Ihee Mama, Abbiey" Domin komai a wajanta Abbiey idan Baba ƙarami ya kira Ustaz sai ya haɗa su, bata iya cewa komai, Ustaz ne yake cewa "Shalale ce Abbiey" da haka ta haddace sunan raɗau a bakinta komai Abbiey. Tana saka naman a baki Ammi na shigowa Ridayya ta yi wuƙi wuƙi da manyan idanunta, tun tuni ta daina kuka ya zama jikinta, a tsorace ta yi baya tsautsayi tukunyar naman ya kife gabaɗaya a ƙasa, Ammi ta ƙunduna ashar ta ce "Ƴar banza mayya nakashsshiyya tsinanniyar ƙarshen muni mara amfani a cikin mutane wallahi yau za ki san ni ki kai ma ta'addi, daman kin kashi ɗazo a wando" Biba ta leƙo ta ce "Lafiya Maryam?" Ta ce "Wanne lafiya? Farfesun da na yi wa Alhaji Mansur wanda na haɗa da jinin al'adata ta kifo da shi" Biba ta ce "Kutimelesi ina ganinta a murguɗe ashe muguwa ce?" Ammi ta finciko Ridayya ta ce "To da fa? Kwana biyu daman bana gane kan Alhaji Mansur cikin bacci zai fara kiran Fatima, Zarahna" "Riƙe mini ita Biba" wuƙa Ammi ta ɗakko ta ɗora a saman gas, wuƙar nan ta yi jajur da ita kamar a maƙera sai ka ce mai shirin yin walda "Fito mini da harshenta, buɗe bakin nata ki riƙe kafura mahaukaciya da kyau" Biba ta buɗe bakin Ridayya tare da zaro ɗan ƙaramin harshen yarinyar duk miyar data shafi wajan tana nan, babu tsoran Allah babu tunanin zata mutu tabar yaranta a duniya cikin rashin tausayi da imani Ammi ta ɗakko wuƙar nan daga gama yin jaa a wuta ta manna wa Ridayya a harshe...... *Wannan page ɗin na ku ne stepmother Jama'a mutuna a kodayaushe mutuwa na kusantarmu, yanzu ne, anjima, gobe ne jini. Only God knows. Uwar gida da amarya ku ji tsoron Allah, babu amfanin cutar da ɗan kishiya, matsalarki da kishiya daban, babu ruwan yaranku ciki, wallahi wallahi duk wanda ya wulaƙanta ɗan wani sai Ubangiji ya musu hisabi. A cikin Alkur'ani Ubangiji da kansa ya bawa maza damar auren mata huɗu cif, banga dalilinki na shigowa ki kori wacce take gidan ba, maza sun bar mu da wahala, saboda kawai ki mallaki miji sai ki haukata kishiyarki ko ki sabauta ta, ko kuma kai saka tsanarta a zuciyar miji ko ki saka mata warin jaɓa, ko ki musu farraku da ɗa da dukiya Allah kaɗai ya san mai morar su wallahi. Ku ji tsoran Allah ku ji tsoron wallahi cases ɗin da muke karɓa wajan aikinmu Allah ya yi yawa da su mene amfanin yin abinda ba zai maka amfani a lahira ba😭😭🤲🏻* *✿ MUNAFUKIN MIJI 15 ✿* Mikiya Writers Ass..... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Nimcyluv _Wannan shafin naku ne masoya Munafukin miji masu ƙaunar Zameer da shalalen Ustaz🤓 Drama section, Munafikin miji fans, Sarautar's Library gidan da aka kusa ƙwace shi daga hannuna🤣su Oum Safna,su Balkisa su Oum shaheed su Mom sani writer ɗin Surukata. Ga na musamman ajin tubarkalla Nimcy paid library, da jama'ar Nimcyluv readers hub. My WhatsApp channel people🥰🥰 much love Bright pens na godiya_ "Biba sake riƙe mini tsinanniya gayyar na ayya gayyar assha, wato ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu ko? Yadda uwarki ke son kwace mini miji, haka kike so wargatsa mini plan na yi biyu babu,uku ba ko ɗaya? Ki zame mini ƙarfen ƙafa mai wuyar fidda wa?" Ammi ta faɗa tana sake ɗora wuƙar a saman wutar gas ɗin. Biba dake riƙe da Ridayya, kamar wacce ta riƙe sa'arta sai haki take saboda wahala ta ce "Ina ganin ki rabu da ita haka, she's to young da wannan azabar taki Maryam, matsalarki da uwarta daban, matsalarki da yarinyar daban, look at her? Shekara shida amma kamar ƴar shekara huɗu duk ta tsamure kodan rangwamen hankalinta kya saurara mata please" "Na saurara mata? Kin san me kike cewa Biba, kin san baƙin ciki da takaicin dana ɗanɗana dalilin uwar yarinyar? Kin san halin dana shiga sanadin Fatima? Ai wallahi ko zan ƙarar da komai nawa ba zan saurara ba sai na kai ga gaci, this is my promise" Biba ta girgiza kai domin haka kawai tausayin Ridayya ya kamata, ita kanta ta tsani kishiya ko a mafarki bata fatan ace yau gata da kishiya balle a zahiri? Kuma burinta ta rayu daga ita sai ranta banda ƴaƴan kishiya. Ta kalli Ridayya da wani irin yawu mai kauri ke dalala daga cikin bakin nata,bata zaro harshenta da ya yi jajur yana tsastsafo da jini, fatar wajan ta ciro, idanun yarinyar kamar zai faɗo ƙasa saboda masifar azabar dake ratsa mata jiki, tana kaiwa gurɓatacciyar kwakwalwarta ziyara tare da game dukkan wani sassa na jikinta da suke motsa ji da gani. "Ba kyau azaba da wuta, Ubangiji kawai ke da ikon haka, kurman da ita kike son yi ne?". "Ta kurman ce mana Fatima ke da asara bani Maryam ƴar Alhji Shitu ba" "Malam Shitu dai, don bani da labarin Malam ya je makka, ke fa matsalar dake damunki hadda talaucin daya yi miki katutu a gindi" Ammi bata kula Biba don taga alama tunan silili take ƙoƙarin yi mata. Ta cafko harshen Ridayya tana ƙoƙarin manna mata wuƙar suka ji an ce. "Ammi, Ammi me kike ƙoƙarin yi haka" Ta yi saurin cillar da wuƙar tana haɗe rai kafin ta ɗauki Ridayya idanunta zube a kan Junaid ta ce "Daga ɗora girki fa na nemeta na rasa, sai ihun ta na ji a kitchen, kasan ta da kwaɗayin nama kamar jikar mafarauta shi ne ta kifo da tukunyar ta ƙona kan ta" Junaid ya kalli kitchen ɗin, kana ya kalli Ridayya dake miƙo masa hannu tana sauke ajjiyar zuciya idanunta ya ƙafe sun ƙara girma, harshen data zaro yake kallo da sauri ya matsa yana kallon wajan ya ce "Me kuma ya sameta a baki?". "Ƙonar da nake faɗa maka ce ai" "Bai yi kama da wacce ta ƙone ba, sai dai ƙona ta a kai, kalli shatin wani abu fa?" Ammi ta kalli Junaid gabanta na faɗuwa sosai ta ce "Me kake nufi? Ni zan ƙona ta ko kuma Biba data taimaka mini na ɗauke ta? Yarinyar daba hankali gare ta shi ya sa na ce babu mai saka ta a makaranta yanzu, ni zaka ɗora wa alhakin hakan Junaid?" Ya girgiza kai murya a ƙasa ya ce "Ki yi haƙuri Ammi, bana nufin haka" Yana faɗa ya fice, ta leƙa ganin ya fi ta ta dungurar da Ridayya a wajan tare da yin part ɗinta, Biba ta bi bayanta a ranta tana jinjina abubuwan da suke mata yawo a kan ta. Suna fita Ridayya ta miƙe tana yarfe hannunta, tare da fito da harshen waje domin samun sauƙin abinda take ji, da zarar iska ta kaɗa sai ta ji kamar yanzu ne Ammi ke manna mata wuƙar, majina, yawu suka haɗe mata sai kuma a lokacin ne ta fara neman hanyar gudu inda bata taɓa yi ba a gidan ta nufa, rashin ƙwari da ƙarfin jikin da bata da shi suke neman yasar da tsamurarren jikin nata. A jikin bishir zugale ta raɓe hawaye na bin idanunta sai nishi take da haki tana son yin kuka a fili ta kasa. Shigowar shi kenan cikin gidan, tunda ya shigo ya samu kansa da faɗuwar gaba mara dalili. Ya yi jim a daidai mararrabar data haɗa shashin biyun, na Baba ƙarami dana Baffa. Yana ƙoƙarin nufar part ɗinsu ya ji saukar siririn muryarta a cikin kunensa. "A...aaa.. Abbiey, Abbiey" Furucin ya yi fitar gurbi daga cikin bakinta, ba tare data san waye a wajan ba, azaba ta saka babu sunan wanda ya zo bakinta da tunaninta sai na Abbiey. Ustaz ya juyo da sauri har hiramin kansa na faɗuwa, idanunsa da suke kodayaushe a rufe ya sauka a kan Ridayya, ya zuba mata ido ganin sai murza harshe take. "Shalele" Ya kira ta, cikin sauri ta buɗe idanunta ta kalli wanda ke tsaye a gabanta, bata hawaye da shi ba, amma tabbas muryarsa ta zauna a tunaninta raɗau. Ta shige ƙifta idanunta a karo na farko cikin murya ta sangarta ta fashe da kuka har lokacin kallonsa take. Ustaz ya durƙosa a gabanta ya kasa magana a tsayin shekaru shida ɗin da suka samu basa tare abubuwa da yawa sun faro har girman Ridayya, da kuma yanayin daya rusketa a yanzu. Tattausan hannunsa ya saka ya cira ta saba, tare da ɗora ta a kafaɗa ɗaya hannun kuma ya ja trolley ɗinsa kai tsaye kuma part ɗin Baba ƙarami ya nufa, shiru komai an yi mutuwa ba kowa, ko sallamar da ya yi cikin kamilalliyar muryarsa babu wanda ya yi balle ya amsa bedroom ɗinsa ya nufa da ita, yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya a bayyane. Ammi dake zaune tana jinjina girman asarar da Ridayya ta saka ta, ta yi ƙwafa ta ce "Wallahi na tsani yarinyar nan, da dukkan alamu uwarta ma malamai take bi gashi nan komai na neman jirkice mini" Biba ta yi murmushi ta ce "Me ya sa kike tunanin Fatima za ta yi miki asiri?" Ammi ta ce "Me ya sa ba zan yi tunanin hakan ba, tunda tana son mijinta dole ce ta saka suka rabu, gashi da baya ƙaunar ko jin sunanta babu wanda yake magana a kan al'amarin auren yarinyar da kuma neman hakƙin Fatiman, kwatsam yanzu Mansur ya tsiro mini da wata ɗabi'a" "A moral person doesn't lie, cheat, or steal, Fatima ba zata taɓa miki asiri ba wallahi zuciyarta ai ba irin taki bace, matsayin ƴar'uwa take kallon ki ba kishiya ba, babu laifi don ta so mijinta tunda ai sun gina tsaftatacciyar soyayya tun kafin aure, shiga kika yi wajan ganin kin raba su, ki ka yi musu farraƙu kuma kika raba uba da ƴarsa" Ammi ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Yanzu Biba mene abin yi?" Biba ta yi murmushi ta ce "Nasan bayan na yi tafiya kin je wajan Malam right? Wanne aiki ya yi miki?" "Kin san wannan yayar Fatimar Kaltum take kowa? Ƴar ta'adda ce wallahi da ƙyar idan bata taɓa yin dabanci ba, gashi mijinta soja ne muƙamin General gare shi, ni da abinda ya shafi hukuma bana son shi, to kuma tana iƙirarin zan gane kure ne" "Kawai ki faɗa mini wanne aiki malam ya miki, ki riƙe bayaninki" Ammi ta ce "Ok. Na saka ya garƙame mini bakin jama'a da dama, ya kuma ɗauke hankalin kowa daga tunanin samawa Ridayya ƴanci, an rufe bakin Kaltum da mijinta, haka na mahaifiyar Fatima, an rufe bakin Baba ƙarami da matarsa ke dukkan wanda ya shafi Ridayya kuma yake da ikon yin magana a kan lamarin na kai sunansa wajan Malam, na saka an ɗauke hankalin Hajiya da Mai ran ƙarfe daga zuwa Kano, tun ranar basu ƙara zuwa ba, balle kiran waya, ke hatta yarana na rufe bakunan su kuɗi kawai nake kwasa wajan Alhaji Mansur" Murmushi sosai Biba ta yi ta ce "Wow! That's good dear, amma kin manta malam ya ce Ridayya mai ƙashin arziƙi ce? Ko alherin da Alhji Mansur ke samun albarkacin haihuwarta ne, kuma ya haska mana goben mun gani, ga baiwa da tarin hikima" Ammi ta miƙe tsaye ta ce "Shi ne abinda ba zai taɓa faruwa ba, idan har ina raye Ridayya ba zata taɓa zama wata a duniyar nan ba, shi ya saka nake bada maganin mayen nan ƙwaƙwalwar ta ƙara sa juyewa, ta yadda ba za ta taɓa fuskantar karatu ba, yadda ban hango future mai kyau a tawa zuri'ar ba, babu abinda zai saka na zuba idanu ƴar kishiya ta zaba wata, zan tabbatar bata samu ilimi ba idan har ina raye" "Idan haka ne, kar ki sake ki bari Fatima ta dawo cikin gidan nan har abada" Biba ta faɗa tana cewa "kawo kunnenki" Duk suna zaune a babban parlour mai zaman kansa, banda ƙira'ar Sheikh Afif Taj babu abinda ke tashi, ƙamshin Air-freshnerh ke tashi tako'ina. A hankali ta ɗaga kai tana kallon wacce ta fito daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa ta ajjiye azkar ɗin hannunta tana sakin murmushi ta ce "Autana ta fi ta kowa ya aka yi?" Mami ta ɗan juya idanunta sai kuma ta miƙa wa Dada wayarta idanun Dada ya sauka akan number da aka saka "Zaujina" "To ki ɗaga mana" Mami ta zauna kusa da Dada ta ce "I won't pick it, six years bai kira ni ba sai yanzu?" Murmushi Dada ta yi ta ce "Ikon Allah, Autana shin sau nawa zan faɗa miki ki wa Alhji Mansur uzuri ne? Ita addu'a bata taɓa faɗuwa a ƙasa dole akwai ranar da za ta yi aikin ta, ki ɗauka yanzu ne ta yi nata aikin ɗauki wayar mijinki Fatima" "Dada please" "Just pick up dear" Mami ta ɗauki kiran tare da saka wayar a handsfree ta cikin wayar Baffa ya sauke wani wahalallen numfashi mai nauyi ya ce "Batuluna kin azabtar dani, kiran waya ba ɗagawa kamar na miki laifi?" Mami ta yi saurin kallon Dada, Dada kuma ta yi murmushi tana ci-gaba da duba azkar ɗin ƙasan zuciyarta tana hamdala ga Sarkin sarakuna Ubangijin talikai, Ubangijin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ta wanzar da ƙudira da buwayarsa a lokacin da suke tsananin buƙatar taimakon shi. "Kin yi shiru? Wallahi ɗan tafiyar da na yi a kan kwangilar da mukai magana last month ji nake kamar na yi shekara ɗari bakya kusa dani, i feel nothing but empty without you Zahraahna" Mami jin abin take kamar a mafarkin data saba yi na mijinta da tilon ƴarta, dukda babu wanda take nunawa abin yana damunta tasha wahala ƙwarai da gaske har kukan mutuwarta an fasa, amma dake mai dokin rai ce ta miƙe jijjigar da ta samu bata sake ta har yanzu. "Fatima, are okay?" Ta yi shiru can ya ce "Ok fine ki yi mini tuwon shinkafa miyar kuka ki tanadar mini man shanu, ki yi mini wannan kyakkawar shigar taki" Nan ma murmushi Mami ta yi idanunta na cikowa da hawaye a hankali ta ce "Kamar baka cikin hayyacin ka naga alama, har ya sa ka manta cewa ni ba matarka bace ko?" A rikice ta ji muryarsa yana buga tsawa ya ce "What kamar ya? wanne irin mummunan furuci ne wannan wanda girman dafinsa na iya tarwasa zuciyata na roƙe ki da ki daina" Mami ta ce "Wallahi tallahi ni ba matarka bace, shekaru shida da suka shige ka sake ni ka rabani da jaririyata" Cikin sauri shima ya ce "Na rantse da girman Allah ke matata ce ban sake ki ba" Sai kawai ta kashe wayar tana kifa kanta a cinyar Dada tare da rushewa da wani irin kuka mai cin rai. _So the real love is never gone..?_ Dada ta dinga shafa kan Mami tana ganin yadda Baffa ke kira ba tsahirta wa wani na korar wani har number Dadan ya kira suke suka ƙi ɗagawa. Ustaz ya dinga bin Ridayya da idanunsa masu laushi ganin yadda take ta murmushi a bawon wankan daya saka ta a ciki, ya ɗaure mata ƙugu da towel ƙarami ya jiƙe ta shakaf da ruwa, hakan ya yi ma Ridayya daɗi tana wasa irin wannan yadda ta nuna tamkar ba a yi mata wanka. She's so happy. "Shalele, fita dai" Ta yi murmushi mayan dimples ɗinta suka loma duka lokaci ɗaya, ta fiddo masa da manyan idanunta masu zara-zaran gashin Idanu, baƙin fuskar nan kamar a saka ruwa da audiga a laso tamkar ya yi magana, yanayin farin idonta ke ƙara fidda baƙar fatarta ta a fili, a zahiri babu wani abu mai jan hankali a fuskar Ridayya duba da yadda bakinta ke tamkar a karkace ga yawu na fita ta gefe. "Abbiey" Ta ce tana ƙifta masa ido, ya mata ƙuri a hankali kuma ya kai yatsa yana taɓa dimples ɗinta both sides. "Ƴar gidan Abbiey" Ya furta a kasalance hana rufe ido, shekarun Ustaz 25 yayinda Ridayya take shekara 6 a duniya. Tafiya karatunsa ya sauya sosai da gaske daman yana da girman jiki, wannan dalilin ya sa yake ganin idan aka faɗi shekarunsa jama'a za su raina shi, yanzu komai nasa ya sauya girma, nagarta, nutsuwa miskilanci da rashin son magana, baya damuwa da komai kamar yadda baya ɗaukan raini daga wajan wanda ba zai lamunta ba. Ya ajjiye ƙasumba mai kyau wacce ta yi daidai da tsayayyen gemun da Ridayya ke yawan jaa masa tana murmushi. Yana cireta daga cikin ruwan ta haɗe fuska ita ba haka ta su ba, ya shafe ta da Rob, ya ɗauki kaya masu nauyi yasa mata, da zai cire towel ɗin jikinta sai daya rufe ido yana faɗin "Haza haramun" bayan ya kammala shiryata cif ya kalleta ya kalli sumar kanta, bai ma iya tazar ba sai kawai ya ƙuƙƙulle ya saka mata hula. Ruwan zam-zam da rubutu ya ɗauka ya yi addu'a ya bata kana ya bata ruwan bagaruwa da zaiton yana jin tana da ajjiyar zuciya. Bacci ne ya ɗauketa ya shirya shima cikin jallabiyya mai taushi ya naɗe kansa da hirami kana ya kunna karatun Alkur'ani mai girma ya rufo ɗakin. A parlour ya samu Umma da Baba ƙarami ta ce "Ikon Allah saukar yanzu hala?" Ya jinjina mata kai yana zama saman kujera kana ya lumshe idanunsa hannunsa ɗaya yana murza goshinsa da gumi ke yanko masa da ƙyar ya iya cewa "Umma, Abba sabahur khair" "Sannu da hanya Babban mutum ya karatu? A zo lafiya" Ya jinjina kai. "Baka ce kana zuwa ba, gashi bani da abinci" Ya girgiza kai ya ce "Nikam yunwa ina ji, da gaske yunwa Umma" "To Babana girki ya kamani, Ustaz guda da jin yunwa?" Baba ƙarami ya yi murmushi kawai. "Ustaz bani ruwa a fridge mana" Miƙewa Ustaz ya yi ya ɗauki ruwan gorar kana ya nufi ɗakinsa ruwan rubutu ya zuba a ruwan ya girgiza kana ya koma parlour ya bawa Baba ƙarami ruwan, tunda ya sha yake jin zufa na yanko masa jikinsa ya yi sanyi ya ce "Ka dage sai ɓangaren banki, yanzu gashi ka kammala karatun wanne banki kake tunanin za su karɓe ka?" Ustaz ya yi shiru, ganin haka ya sa Baba ƙarami cewa "Sai kuma maganar aure, yana da kyau ka ajjiye zuri'a" Ustaz ya yi saurin buɗe ido sai kuma ya ce "Aure? Asstagafirullah Allah ka yafewa Abbana" Yana faɗin hakan ya fice daga parlourn. Da mamaki Ammi ke bin Bilal da kallo irin yaushe ya dawo ɗin nan? Sai kuma ta dake tana kallon Biba data sake zuwa za su wajan Malam domin ƙarasa aiki. Tunda Biba ta kalli Bilal ta ji wani abu ya saukar mata komai nata ya nemi kuncewa ta jima ba taga mutum mai kwarjinin Bilal ba. Ustaz ya juya ya kalli Zuhura wacce gaba take da shi, ganin kallon da yake mata ya sa ta ce "Ina yini Ustaz?" "Ina Balkis?" Ta ce "Ta fita makaranta" Ya haɗe fuska ganin Junaid ya ce "Kai don ubanka jira kake na gaidaka?" Junaid ya ce "Afuwa kai na ƙasa, barka da zuwa Babban mutum, zuwan ba zata haka?" Ammi ta yi murmushi ta ce "Ustaz ya hanya, ashe kana tafe kana lafiya?" "Ƙalau, Ridayya fa?" Junaid ya juya ya ce "Ammi ina Ridayya? Ni tun jiya ban sata cikin idona ba" Ustaz ya nufi kitchen haka kawai ya samu kansa da duba CCTV ɗin daya saka ba tare da sanin kowa ba, ya shiga dubawa abubuwan tashin hankalin daya gani sun girmimi tunaninsa jikinsa har wata kakkarwa yake na ɓacin rai zuciyar ta motsa, idanunsa suka juye tare da rikiɗe wa tamkar bashi ba. Daidai lokacin kuma motar Baffa ta sauka a gidan, zuwan Baffa da fitowar Ustaz daga kitchen ɗin sukai daidai. Bilal na zuwa ya ɗaga hannu ya wankawa Ammi mari ta yi baya tana zare ido "Bilal are you out of your sense? Mari fa" Bai yi magana ba saboda gabaɗaya jikinsa rawa yake, ya sake ɗaga hannu ya sauke mata wani mai lafiya ta yi bata zata kifa ta juya ta kalli Baffa ta ce "Kana kalli a kan Idanunka ya mare ni....," Kafin ta ƙarasa magana shi ma Baffa ya sauke mata wasu tagwayen maruka a fuska, da sauri Ustaz ya juya da nufin ɗakko Ridayya daidai nan kuma Anuty Kaltum ta sauka a gidan tare da mijinta General. Ustaz na zuwa ya kalli Ridayya ya san idan ya nufe ta a haka zata firgita wannan yanayin nasa ba nata bane, ba zata ɗauke shi ba, dole ya fara samun nutsuwa kamar yadda yake idan ransa ya ɓaci, ya nufi bathroom ya mance bai rufe ƙofar ba, ya cire duka kayansa gabaɗaya ba abinda ya bari ya tsaya a tsakiya tare da sakarwa kansa shower idanunsa ya juye ya daddafe hannunsa da jikin bango ruwa na dukan tsakiyar bayansa. Ba zato ya ji an turo ƙofar ana faɗin "Abbiye.... Abbiey" A gigice ya juya yana cewa "No, Shalale haramun ne jikina stop amma ina...... BRIGHT pens na godiya *PAGE 16* Bright pens🤙🏼free batch Duk saurin Ustaz wajan dakatar da Ridayya daga shigowa cikin toilet ɗin, haƙarsa bata cimma ruwa ba. Ya dafe kai yana murza goshinsa da zufa ke fesu wa ta tsakiyar wajan. Cikin saurin kuma ya saki labulen dake tsakanin jacuzzie da mirror wajan shigowa. Ridayya ganin bata ga Ustaz ba ya ɗan leƙa kanta cikin sanyin muryarta ta ce "Abbiey, nine, gani" Ta furta idanunta na rufe wa sosai srup ɗin da Ammi ke mata ya yi matuƙar tasiri a kwakwalwarta, she's always sleeping. "Abbieynaa!" Ridayya ta furta tana mai janye idanunta ta buɗe su da ƙyar, saboda wani irin maganaɗisun bacci dake ribatar idanunta. Ustaz dake tsaye dafe da kansa gabansa sai tsananta bugawa yake, da ƙyar ya samu ya zura jallabiyya a jikinsa ko hiramin bai samu zarafin ɗaurawa ba ya ɗaga laubulen ya fito, idanunsa ya sauka a kan ta, ganinsa tsaye a gabanta ya saka ta buɗe bakinta tare da yin murmushi. Ya girgiza kai a hankali ya sunkuya ya ɗauketa a kafaɗa suka fice daga toilet ɗin zuwa bedroom ɗin Ustaz. Ƙoƙarin kai hannu take zata taɓa tsayayyen gemunsa dake zubda ruwa ya yi saurin riƙe ɗan mitsitsin hannun nata, idanunta zube a kanta ya ce "Na roƙe ki Shalale ki ce ba kiga Abbiey yanayin haramci ba..," Ta yi shiru tana kallonsa ya janye idanunsa sai kuma ya juya da sauri bayan wani abu ya zo ransa ya cafke hannayenta muryarsa a daƙushe ya ce "Me hakan ke nufi Shalale? Da gaske ban fahimta ba, nikam ban fahimta ya zan yi da al'ƙawarin dana ɗaukar wa kai na? Kin rusa komai kin rusa tunanin Abbiye Shalale" Ya yi baya tare da kwanciya yana rufe ido, kokawa yake da tunaninsa wanda ya rabu kashi-da-kashi. "Babu mai ganin tsaraicina sai matata!" Kalaman suka dawo masa, koda wasa ya faɗi abu to gaskiyar kenan, ya zai yi da wannan jirkitaccen al'amarin? Ya miƙe tsaye kamar zai fita ya dawo ya durƙosa daidai tsayin Ridayya duk ya gaji da magana, kuma da taimakon shi dole bakin Ridayya zai buɗe, ya kalli cikin idanunta da suke sauya masa kala a kullum a kodayaushe a taushashe ya ce "Shalale kin ga abin a halin da matarsa ce kawai zata gansa?" Cikin rashin fahimta Ridha ta kalli Ustaz, jin ya ambaci sunan Abbiye ya saka ta yi murmushi dimples ɗinta na lomawa kana ta ɗaga kai, Ustaz ya yi saurin girgiza kai yana runtse gajiyayyun idanunsa masu laushi, faɗuwar gaba na wanzuwa a ko wanne lungu da saƙo na ƙofofin zuciyarsa, ya tsune laɓɓansa a nutse ya ce "Subuhanallahi! Hakan na nufin...?" "Zata zama Matarka idan har da gaske al'ƙawarin zuciya ne, kuma zuciyar ta Ustaz Muhammad-Bilal" Ustaz bai juya ba, domin ya fi kowa sanin mamallakin muryar. Umma ta ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin ta juya ta kalli Ridayya ta kuma kalli Ustaz kana ta ce "Sai ka ce rainon matarka kake bamu da labari" Ya yi shiru ta taɓe baki kana ta ɗora da "Da sake an bawa mai kaza ƙafa, ka gaggauta sauya tunani" Sai a lokacin Ustaz ya kalli Umma kamar ba zai yi magana can dai ya girgiza kai ya ce "Umma please, kai na ciwo yake" Domin bashi wata magana bayan wannan ɗin, bayan ita kuma bai san wacce magana zai furta Umma ta gane tsakaninsa da Ridayya zumunci ne kawai. Umma ta ce "To, ta dai haramta a gare kuma, she's not your type, kwailar ma?" Ya kalli Ridayya sosai kana ya kalli Umma ya ce "Mene kwaila?" Ta ce "Baka sani ba?" Ya yi shiru ta yi murmushi ta ce "Kwaila ana nufin ƙaramar yarinya, ƴar mitsitsiyya wacce bata fara irgan dangi ba, balle batun al'ada" Ya sake juya idanunsa duk a gajiye yake daga jiya zuwa yau "Irgan dangi?" "Nono irin na ko wacce ɗiya mace nake nufi Ustaz" Ustaz ya yi saurin rufe ido yana miƙewa tare da toshe kunnensa ya ce "Ya Rasulullah Asstagafirullah, ba a kunnen Muhammad-Bilal ba" Umma ta ce "Tunda na yi saƙo ba? Shekarar ta shida kai kuma shekara ashirin da biyar, ƙanwarka ce babu wani zance bayan wannan" Har ta fita ta tuna abinda ya kawo ta, ta ce "Ana kiran ka a sashin Baffa" Tana furta hakan ta yi waje tana jan tsaki, halin Ustaz gabaɗaya a bauɗe yake ta rasa waya gado? Tana fita Ustaz ya juya ya kalli Ridayya da ta yi shiru idanunta a kasalance ya saka ƙafa tare da zungureta ta buɗe ido a gigice jikinta na rawa da ɓari tunaninta Ammi ce, domin komai yana zaune a ranta daram kamar yadda al'amarin ya nuna a karatu, haddar ƙaramin yaro, kamar rubutu ne a kan dutse ganin Ustaz ya saka ta kwaɓe fuska za ta saki kuka. "Ni zan yi kuka ba ke ba Shalale, kin ga abinda kika jawo, zan nema miki gafarar Ubangiji ƙuruciya ce da rashin sani" Ya miƙe tare da ɗaukan ta ya nufi ɓangaren Baffa cikin takun nutsuwa da zallar kamala, dab da zai ƙarasa annurin fuskarsa ya ɗauke ya yi kicin-kicin da fuska tamkar ya ce ya shiga uku, ya tsuke girarsa har haɗe wa take saboda tsabar baya son raini. Yana zuwa Ammi dake dafe da fuska domin marin Ustaz ya gigita ta, kunya take ji ya sauke hannunta a ga zanen yatsun shi daya kwanta a fuskarta. Baba ƙarami ya kalli Ustaz ya ce "Muhammad-Bilal mene hujjarka na marin matar ubanka?" Ustaz ya yi shiru domin haka nan ya ji baya buƙatar wani surutu, ya tsaya iya shi da ita Ammin. "Ina magana ka yi shiru?" A hankali ya ce "Abba!" Ya faɗa yana nutsa idanunsa cikin na Baba ƙarami "Ba'asi nake tambaya, domin ba zan lamunta ba" Ustaz ya yi shiru Baffa ya juya kan Ammi ya ce "Ke me ki ka yi masa, ya ake neman haukata mini tunani ne a cikin gidana?" Ammi ta ce "Ni ni ni ce da laifi, amma ya shige ba komai na yafe masa" Anuty Kaltum ta buga shewa tare da yin tafi ta ce "Ai daman duk ɗan tauren da ya je barbara ya kwana da sanin da ciki zai dawo" Baffa kansa sai juyawa yake ya rasa meke masa daɗi ya juya ya kalli Anuty Kaltum da mijinta General ya ce "Anuty Kaltum wai meke faruwa ne, can you help me?" Ta yi dariya ta nuna jin daɗi da Allah ya gwada mata wannan rana ta ce "Me kowa yake faruwa banda girbar abinda ka shuka? Ai duk wani rami daka tsinci kanka a ciki yanzu, to kai ne ka haƙa abinka da kan ka Alhji Mansur" Baffa ya girgiza kai tamkar zai yi kuka ya ce "Bari na kira Fatima a ɗakinta nasan ba zata bar ni a duhu ba" Anuty Kaltum ta ce "Hanzarta" Baba ƙarami dake zaune ya girgiza kai ya ce "Dawo nan ka zauna Alhji Mansur babu Fatima a gidan nan" Komai na Baffa ya tsaya cak, domin bai fahimci Fafima bata gidan ba, ko ya ji bata taɓa yi ba, ina zata bada izinin shi ba? "Shekaru Shida da suka gabata, ka saki Fatima a kwana biyar da haihuwar yarinyarta, bayan ka aibata yarinyar ranar da aka haifeta ka ce ba kai ne ubanta ba, ba kuma zaka taɓa zama uban jaririyar Fatima ba,ka ce a je a nemi ubanta" Zufa ta dinga yankowa Baffa jiri na neman kada shi wanwar a ƙasa. Anuty Kaltum dake tsaye ta ce "A shawar ce daka nemi wajan zama, don zaka iya yanke jiki ka faɗi babu mamaki daga nan ka samu shanyewar ɓarin jiki tun a nan duniya" Zuhura dake tsaye zuciyarta kamar zata fito don baƙin ciki, ga marin da Ustaz ya yi wa mahaifiyarta, ga cin mutumcin mahaifinta da Anuty Kaltum ke yi, cikin masifa ta ce "Babu abinda zai same shi, kuma Mala'iku suna cewa walaaká ga duk abinda ka roƙa wa waninka" Anuty Kaltum dake jiran kaɗan ta ce "Ji banza shasha, ki bari ki samu cikakken ilimin kawo fatawa, kuma idan har haka ne ki shirya ganin abinda kema zai same ki ta dalilin babarki" Zuhura zata sake magana ta ji an daka mata wata razananniyar tsawa a kiɗime ta juya ta kalli Ustaz da jijiyoyin kansa suka gama bayyana suna harbawa ya ce "Out!" Da sauri ta fice daga parlourn zuciyarta na faɗawa cikin ƙiyayyar Ridayya domin ta san all this happened because of her, ita ɗin annoba ce! Baffa ya kalli Anuty Kaltum ya ce "Anuty Kaltum da gaske na saki matata Fatima, kar ku yi mini wasa da hankali" Anuty Kaltum ta ce "Ya shige wai, amma ai ya zama tarihi domin Fatima tuni ta samu mijin aure, mun zo batu a kan Ridayya a bamu ita mu tafi, a wannan karan babu ɗaga ƙafa ina tare mijina General Buba Manti" Baffa bakin Anuty Kaltum kawai yake kallo kamar wacce ba Hausa take furtawa ba ta ce "Faɗi ko wanne yare kake ji, ina da ƙarfin qiwwar yi maka shi ni ba irin makirar matarka ba ce empty head" Ammi ta ce "Kaltum ya ishe ki haka nan, Ridayya kuma babu inda zata ƴata ce har abada kamar yadda mijina ya bani ita" Junaid dake tsaye ya ce "Ammi ki bar wannan maganar ki bari a tafi da ita" Ammi ta ce "Zanci Ubanka Junaid idan manya na magana kana saka baki, kai ki damuwa bakya yi za a tafi da ƙanwarka?" "Kin nuna masa damuwa da ƙanwar ta shi ne? Maryam bata wajanki na zo ba, karki nemi tunzura ni, ƴar masifa ce ni babu wani kalar tijira da ban iya ba, da matar General Buba Manti kike magana ko a sojojin sanin irinsa zai yi matuƙar wahala" General dake tsaye ƙiƙam! Kamar gunki ya dakawa Baffa tsawa ya ce "heyyy where is the baby?" Baffa ya yi shiru domin shi bai ba san a kan wa ake magana ba, shi tunaninsa da dukkan wata nutsuwarsa yana ga matarsa FATIMA ZAHRAAH. "Zan cire maka yatsun hannu a nan wajan, I said where is the baby?" Junaid ya ce "Ka yi haƙuri, za a kawo Ridayya" Hankalin Ammi ya tashi domin tafiyar RIDAYYA MUHAMMAD-BILAL RANO tamkar rushewar plan ɗita ne. "Ni ban ma san inda wa ma kuka ce?" A zafafe General ya ɗaga hannu zai kifawa Baffa mari a hankali Ustaz ya ce "No please" General ya juya domin bai san da zaman Ustaz a wajan ba. "Ridayyerh na waje na, zan riƙe ta In sha Allah" Da ƙyar Baba ƙarami ya shiga cikin rigimar ya bawa General Buba Manti haƙuri tare da Anuty Kaltum. Hankalin Baffa ya tashi shikenan suntirin gidan su Fatima, ita kanta idan ta ce bata zumuɗin ganin ƴar cikinta ta yi ƙarya, ko a baya bata san mene ya hanata zuwa ganin Ridayya ɗin ba. Anuty Kaltum sai da ta rahama duk wani ta'addaci da Baffa ya yi mata, har yana cewa sun raba shi da matarsa ba wani laifi, shi kam ko haka ai sun gasa shi idan ma haukata shi za su yi ba. Ya kuma mayar da Fatima tuni, Dada ta shiga maganar a nan akai addu'a Baffa ya sauyawa Fatima komai na part ɗinta, jinsa yake kamar sabon aure zai yi har magani ya sha ya fam abinsa. A daren da Fatima ta dawo ko inuwarsa bata ishe ta kallo ba, wani abun ban malak duk yadda take zumuɗin ganin Ridayya da rungume ta a jikinta ta faɗa mata yadda take so da ƙaunar ta, amma Mami ta kasa har mance wa take tana da wata ƴa a gidan tsakaninta da ita idan ta ganta a parlour shima idan sun zo tare da Ustaz ne. Ridayya ko inda Mami take bata taɓa zuwa ba, ko gaisuwa sai Ustaz ya ce Shalale a gaida Mami sai ta maƙale kafaɗa. A ɓangaren Ammi farraƙu ta saka aka yi mai tsanani tsakanin uwa da ƴar, ya zamana ko wuta Mami za taga Ridayya zata faɗa ba zata taɓa yin magana ba, haka kuma Baffa sam bai damu da Ridayya ba komai zai lissafa na yaransa babu ita, Ammi ke nan nan da ita ta nuna mata soyayya kamar zata cinyeta a gaban mutane har lokacin kuma bata bar bawa Ridayya maganin maye ba. Rayuwa na juyawa komai na sauyawa, Baffa ya dawo da halinsa a kan Mami sam bai damu da ita ba, itama rayuwar haƙuri kawai take biyar tasa ya daina shiga hannunta, lokacin zuri'ar ALHAJI MANSUR ta ƙara yawa, Mami nada Zuhura, Junaid, Balkisa, Abdullahi, Khaliperh, ta yi ƴan uku su ne Usman, Umar, Abubakar, sai autanta Aliyu. Daman kuma duk sun girmewa Ridayya Aliyu ne kawai ta girma. Ridayya nada shekaru goma a duniya Mami ta samu ciki, ba wanda ta faɗawa ko Baffa bai sani ba. Muhammad-Bilal Ustaz ya dage komai na rayuwa shi ne ya kewa Ridayya, tuni ya kaita asibiti tana amsar magani, shigar Ridayya makaranta ya zama sabon babi na rayuwa a gare ta, bata fahimtar karatu sam, kullum cikin bacci take sai ta gama yini a makaranta bata fahimci komai ba, dalilin hakan ran Abbiye ba ƙaramin ɓaci yake ba sai ya yi kamar zai dake ta sai ta fashe da kuka tana faɗawa jikinsa tare da bashi haƙuri, ya zage yana koya mata wani ta fahimta wani sai addu'a. Suttura komai na rayuwa Ustaz ne duk wanda ya tambayeta waye babanta sai ta lumshe idanu ta ce "Abbiey" Bata da ƙawa kowa gudunta yake wai daƙiƙiya ce kar ta shafa musu, gashi wata jarrabawa ita kaɗai sai a ga ta faɗi tun ba a fahimci menene ba har aka gane ai Farfaɗiyya ce ke damunta. Mami na zaune Abdullah ya shiga part ɗinta ya sameta a parlour ta yi shiru tana tunani ya kalli yadda ta caɓa kwalliya ko'ina na sai ƙamshi yake "Mami" Ya faɗa da ƙarfi ta yi saurin buɗe ido ya ce "Ina ta sallama lafiya kowa? Ko wani abun ne?" Ta yi murmushi ta ce "Lafiya Abdullah, zauna mana?" Ya ce "Ba sai na zauna ba ai, Ridayya ce ta faɗi" Ta ƙura masa ido sai ta ce "Ina zuwa" Yana fita ta miƙe tare da shigewa bedroom ta kwanta tuni ta manta da babin wata Ridayya. Cikin jikinta ya saka mata wata irin kewa da so da ƙaunar kasancewa da mijinta. Ta duba lokaci taga wajan 10 na dare kuma ita ce da girki,ta miƙe tana nufar part ɗin Baffa da nufin kai masa ziyara ta sauke wani jan aji na ɗiya mace, tana shiga ta ji tsit sai ta nufi bedroom da sauri ta yi bays zuciyarta na bugawa da ƙarfi ganin Baffa tare da Ammi kuma a ranar girkinta babu abinda ya fi ɗaga hankalin Mami sai furucin Baffa da yake cewa "Dake kawai nake kasancewa na ji daɗi Maryam, Mairamu, Mero na, jin Fatima nake tamkar gidan biredi, ji nake kamar ana gasa ni, gabaɗaya azaba nake sha, Maryam kece mace ɗaya tamkar da dubu na baki naira dubu ɗari" Ammi ta ce "Fatiman ce kamar gidan biredi?" A gigice ya ce "Tama fi, haƙuri kawai nake da ita yadda kika san ruwan sha, Maryam na ƙara miki wata dubu ɗarin" Ammi ta ce "Ba dubu ɗari nake so ba, furnitures ɗin part ɗin Mami nake buƙata, da duk wani abu daka mallaka nata" "An gama yadda kika ce haka za a yi" Wannan maganganun ya rusa duk wata sauran yadda da ta yi wa Alhji Mansur Rano, ta rasa me yake mata daɗi wani irin kalar cin mutunci ne wannan? Ta durƙushe a wajan tana kuka. Ammi ta gyara zaman jigidar data siya a ƙugunta ta shirya ta nufi hanyar fita, a parlour ta samu Mami, fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Mami kina nan?" Idanun Mami a kan wayarta ta jinjina kai, Ammi ta ce "Nima zuwana kenan ban samu Baffa ciki ba" Mami ta ce "Ayya" kamar an cillo Baffa ya fito daga bedroom ɗinsa zai nufi ɗaya ɗakin idanunsa ya sauka a kan Mami data kafe shi da idanunta sai ta yi murmushi ta ce "Ikon Allah kaga kamar Aljani, yanzu Ammi ke cewa baka ciki, da alama kamar babban aiki ka gama?" Baffa yana inda-inda ya ce "E....eh...eh haka ne ina ciki, ina nufin ina bayan gado kamo ɓera..... (Wata kishiyar Alheri ce wata kuma sharri mata a dinga jin tsoran Allah, bana son labarin nan ya ja ni da tsayi amma yanayin comment da supporting naku shi ne ƙarfin qwiwata. Bright pens na matuƙar godiya). Domin gyara ko sharhi sulaimanshuaibunaima@gmail.com Ko WhatsApp 08164069385 *✿ MUNAFUKIN MIJI 17 ✿* Mikiya Writers Ass..... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Mami ta tsare Baffa da kallo zuciyarta na yi mata soya, ta girgiza kai tare da miƙewa zata fice. Baffa ya tare ta faɗin "Yawwa na ce ki tattara dukkan furnitures ɗin dana siya miki, na bar wa Ammi su" Maganar ta doki zuciyar Mami ta juya a sanyaye ta ce "Ban gane na tattara kayan ɗakina na bar wa kishiyata su ba, explanation please?" Cike da faɗa Baffa ya ce "Ba wani explanation Hausa ce dai na san kina ji ko Fatima?" Ta jinjina kai alamar E, kafin ta ce "Bana tunanin akwai wani yare da ka iya wanda ban iya shi ba, ma'ana da hujjar tattara furnitures ɗina na bawa wata ne ban wani ba Alhji Mansur, cikakken bayani" Kamar zai make ta haka ya tunzura ya ce"Maryam ɗin ce wata? Abokiyar zaman ki ce fa. Ok fine zan maimaita ki tattara komai na ki na bar wa Maryam su ina nufin Ammi, kawai yanzu nake ganin ita ta cancanta da kayan bake ba, kuskure na yi wajan siya miki su wallahi tallahi" Mami ta dinga kallon Baffa ta kasa cewa komai ta fice idanunta na cika da hawayen baƙin ciki. Mami na komawa bedroom ɗinta ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, damuwar zuciyarta gabaɗaya ta addabe ta, duk yadda tasu ta yi sharing ɗinta ta wani ta gagara, gashi babbar damuwarta a duk sanda ta buɗe baki da nufin yin addu'a wajan faɗawa Ubangiji halin da take ciki, sai ta ji kamar an rufe mata baki ta kasa ambaton sunan Allah da nufin neman taimako. Ga wani irin masifaffen yanayi da cikin ya saka ta, na buƙatar mace zuwa ga mijinta babu abinda take so irin kasancewa da Alhji Mansur da shaƙar ƙamshin turaren shi. Ta share hawayenta komai yaƙi ƙare wa kamar cin ƙwan makauniyya. Washegari da sassafe ta kwashe komai nata, ta ce a zo a kwashe Alhji Mansur Rano wato Baffa da kansa ya kira yara suka kwashe tas, ya ce ita kuma a mayar mata da furnitures ɗin Ammi ta ce ta gode. Kwana biyu da yin haka aka shigo da sabbin kaya ƴan Turkiyya masu masifar kyau lokacin suna zaune a parlour Umma ta shigo. Ammi ta dinga kallon zubin kayan da tunanin ko Baffa ne ya siya masa sabo fil tana girgiza ƙafa cike da taƙama ta ce "Kayan ne?" Wani matashin saurayi ne ya ce "E, Hajiya sune ina za a saka" Ya ce yana danne dariyar data kama shi "Ok ku haura da su upstairs" cewar Ammi. Mami ta dinga murmushi kafin ta juya ta ce "Hilal har kun ƙarasu?" Ya ce "E Mami, Mimi na gaishe ki ma" Mami ta miƙe tana murmushi har lokacin ta ce "Zan kira ta kam, amma kayan sun yi ma sha Allah". "Mami a wajan fa kaf babu irin su kin san kuɗin da Grandfather ya tura? Ai arziƙi ya yi idan kana da kuɗi ka shige duk wani raini da wulaƙanci wlh Mami" Murmushi kawai Mami ta yi Hilal ya ce "Talk Mami, ai gaskiya ce duk wata mugunta a wajan ɗan talaka aka santa musamman idan ka samu gidan miji ba fus ba ass sai dai a shimfiɗa dugwayen ƙafafuwan na cin banza da damfara, ga mugun abu kamar haihuwar Katsinawa" "Wallahi Allah ya shirya ka Hilal Yaya A'isha bata gasa maka baki ba halan?" Ya ɗan kashe murya ya ce "Surprise....." "What?" Ya mirgina kai ya ce "Na ba ki gari" Ta girgiza kai ta ce "I'm not good da cankar Surprise but i like surprises, just giss me" Hilal ya ce "Aure zan yi" sai ya ɓata fuska ya ce "Mimi ta ce na yi ƙanƙanta don Allah mene abin ƙanƙanta a nan? Shi aure ai raya sunan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, kinga haihuwar fari sai na saka sunan Mamina" Mami ta ce "Kuma kana da gaskiya, amma auren RUƊIN ƘURUCIYA ne" "Mami Ridayya fa?" A wannan lokacin ita kan ta Umma mahaifiyar Ustaz kallon Mami ta yi tana jira ta ji me za ta ce? Amma ta haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba, ganin hakan yasa Hilal yin shiru. Ammi kunya ta kama ta ganin yadda ya kwafsa, a ranta tana mamakin kuɗi irin na mahaifin Hajja Fatima wato Mami. Hilal suka fara gyara kaya, Mami kuma ta haɗa musu lunch. Hira suke sosai da Umma tana mata murnar kayan data siya ta ce "Hajja Fatima yaushe aka zuba miki kaya har kika sauya wasu?" Caraf Ammi ta ce "Lallai fa, cewa ta yi bata so tunda kinga ai haihuwa za ta yi shi ne Baffa ya ce ta bar mini su, da gudu na karɓa ina godiya" Girgiza kai kawai Mami ta yi tana jinjina munafurcin Alhji Mansur Rano. A ranta tana mamakin yadda Ammi ta gane tana da ciki domin kullum cikin hijab take a gidan, kamar wacce take duba? Ustaz Bilal sai raba Idanu yake a harabar makarantar su Ridayya, a hankali ya dubi a gogon hannunsa ganin ai tuni lokacin tashi ya yi wasu sun jima a gida ma. Ya miƙe daga jinginen da yake a hankali cikin nutsuwa da kamala, tare da zallar haiba da nagartar dake siffanta ainahin Ustazancin shi, ya nufi office ɗin Headmaster a ransa yana ayyana rashin dacewar haɗa mata da maza a makaranta. Da fara'a Headmaster ɗin ya tarbi Ustaz Bilal. "Irin wannan zuwan bazata haka? Fatan lafiya" Ustaz ya yi shiru yana haɗa kalaman da zai faɗa a gajarce. "Kamar kullum karatun Ridayya sai addu'a, domin tafi gane naka karatun fiye da na mu, babbar damuwar ma kullum cikin bacci take a aji, bata wasa da yara she feels uncomfortable" Ya fiddo da duka littafan ta na makaranta wanda ya amsa wajan class teacher ɗin su, ya nuna wa Ustaz kana ya ce "Za a Iya magance matsalar ta, ta hanyar cire mata tsoran dake addabar zuciyarta a saka son karatu da nuna mata itama ƴar ce kamar kowa mai gata da ƴan cin zama duk abinda take da buri a duniya, a nuna mata watarana ita uwa ce a nuna mata cewa Ubangiji ke yin halitta ba kuɗi ake bayar wa a kasuwa a siyi mutum ba, buwaya da ƙudirar Allah da girman zati da kaɗaitar shi ce, a nuna mata Ubangiji yana son duka bayinsa kuma babu mummuna a cikin halittun daya halitta, a saka mata ya ƙini da hope na cimma buri, a nuna mata cewa ko wanne mutum yana da nasa raunin cikakken mutum mai asalin kyau shi ne wanda ya yarda da Ubangiji ya kuma yar da ƙaddara. Dukda ba lallai ta gane yanzu ba, amma ya zama na wannan shi ne nata karatun kafin mu ga mai zai faru next" "Yaa Rabb" Ustaz ya furta a taushashe yana lumshe idanunsa, Headmaster baya iya tantance yanayin sauyin fuskar Ustaz Bilal don haka bai fahimci damuwa ko akasarin hakan ba ya ce "Karka damu fa, ina ji a jikina Ridayya zata zama wata a nan gidan duniya, yawanci yara irin wannan suna da baiwa ta musamman" Jinjina kai kawai Ustaz ya yi da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce "Ta na ina?" Da mamaki ya ce "Ai mun tashi, ka duba za ka ga babu students a compound" hankalinsu ya tashi a ka shiga neman Ridayya babu ita babu mai kama da ita, har class teacher ɗin su sai da aka kira. A ɓangaren Ridayya sai rarraba manyan fararen idanunta take yi tana jin me suke faɗa. "To ko dai Aljana ce ke ko kuma babanki kika gado a muni ko?" Ridayya ta kalli Nimra wacce ta kasance class mate ɗinta a makarantar masu kuɗin dake nan unguwar Darmanawa. Ɗaya daga cikin students ta fashe da dariya ta ce "Help me as Nimra, oh oh muni ko wahala?" Nimra ta yi fari da idanu tana riƙe maƙalallen ƙugu idanunta kamar ya fado cike da azaba ta ce "Yapp, ga idanu kamar na mujiya gata daƙiƙiya sai tsinanen bacci kamar kasa, kullum sai ta yi mana fitsari a class" "Ohh Goodness! Fitsari?" Jidda ta faɗa a ruɗe. "Ai yawan sai na ci uwar ta wallahi, baƙa mummuna mai baƙin zunubi ji Idanu kila mayya ce" A sanyaye Ridayya ta ce "Ai dai ɗakin Allah ma baƙi ne" Da sauri Nimra ta doke bakin Ridayya ta ce"Uban me kika sani? Ke ina kika taɓa ganin ɗakin Allah ɗin? Wannan dama gidan zoo aka kai ma da ita da sallah mu je mu ga daƙiƙiya" Idanun Ridayya ya yi rau rau sai ya fidda wani shiny. "Ai dabbobi ake sawa a zoo road" Jidda tana dariya sosai ta ce "To ke ɗin me ce? Wallahi dabba ce ki je ki tambayi Babanki ki ce a dabbobi da wacce kike kama zai faɗa miki" Suka haɗu sukai mata dukan tsiya da bulala wai ba za su saka hannu ba kar su shafi baƙin zunubi. Haka kurum suka tsane ta. Ridayya na son wasa da zarar ta nufe su idan an fita break sai kowa ya daka mata tsawa ya ce ta tafi, daga nan sai ta fi wajan bishiyoyin makarantar ta dinga wasa Ita ɗaya, a lokacin kuma sai ta dinga karatu ita ɗaya ita bata iya gani ta karanta muddin zaka takura mata ta yi karatu to ba zata iyi ba ko a exam ne. Idan ita kaɗai ce kuma sai ta dinga yi tiryen-tiryen a nutse take komai nata. "Shalele" Da sauri ta ɗaga kai tana kallonsa dukda hawayen dake idanunta bai hana Ridayya sauke ajjiyar zuciya ba, ta nufi wajansa da gudu kafin ta ƙarasa ya ware hannayensa tana zuwa ya ɗauketa ya cira ta sama yana furta "Shalelen Abbiye, You scread me" Ta yi shiru. Jikinta ya ji zafi sosai yana ɗaga rigarta ya ga shatin bulala duka jikinta, ya kalleta tambayar duniya taƙi faɗa masa waɗanda suka dake ta. Kamar kullum yau ma Ustaz da kansa ya yi wa Ridayya wanka bayan ya naɗe ta da towel ya shirya ta cif cikin wasu sabbin kaya ƴan kanti daya siya mata, ya ɗaure tulin sumar da ribbon yana hakki, yana gamawa ya yi baya tare da kwanciya ta haye ruwan cikinsa tana dariya ta ce "Abbiye gajiya" Idanunsa rufe domin yanzu Ridayya ta zama ƴar lukuta saboda kulawar da yake bata. Ya yi murmushi ta ƙura masa ido, ganin kumatunsa ya loɓa _Beauty points_ ta danna yatsa a wajan ya ce "Shhhh, Shalale mu je ki yi bacci ko?" Ta maƙale kafaɗa ya rufe ido tana zaune bacci ya ɗauke shi da sauri ta fice ta nufi part ɗin iyayenta. Lokacin data shiga ba kowa a parlour sai Mami wacce cikinta ya girma kawo yanzu kuma kowa ya san da zamansa hatta shi mai gayya da aiki Alhji Mansur Rano. Jin motsi ya saka Mami juyawa idanunta ya sauka akan Ridayya itama Mamin ta ke kallo. "Lafiya ke kuma?" Ridayya ta girgiza kai sai kuma ta juya zata fita aka ce "Daughter come back" Ammi ta faɗa cike da fara'a da sauri Ridayya ta juya tana murmushi don yanzu ta daina jin tsoran Ammi tunda ta fara nuna mata kulawa da soyayya. "Yawwa ƴar baba mai iyaye maza biyu ta gaban goshin Abbiey ɗinta Muhammad-Bilal Ustaz" Ridayya ta yi murmushi ta ce "Zauna na baki abin daɗi daughter na" Mami dai ko motsi ba ta yi ba, Kwata-kwata bata damu da Ridayya ɗin ba, bata taɓa ɗaukar ta ba, tunda take a duniya bata taɓa hira da ita ba ki na seconds ba, sai magana sama-sama. Farfesun nama ta zubo mata hakan ya yi wa Ridayya daɗi tana son nama kuma gashi yanzu Ustaz ya saba mata kullum sai ya siya mata balango ko tsire ko kaza. Ta cinye tas kana Ammi ta ce "To zo mu je na baki ɗaya abin daɗin" Hannunta ta kama suka nufi cikin bedroom ɗinta, a zuciyarta tana tsinewa Ridayya tana kuma jin daɗin yadda Mami ke nuna rashin kulawa a kan Ridayya ɗin. Maganin mayen da take bata a kullum, yanzu ma shi ta ɗauka. "Yawwa ungu wannan shanye tas kin ji ko?" Ridayya ta jinjina kai kana ta amsa ta shanye tas kusan cikin kwalba ɗin, kama hannunta ta yi ta ce "Kinga yadda nake son ki ko? Ko me kika ce ina miki haka ne? To Mami da kike gani ba ƙaunar ki take ba, cillar dake ta yi ta ce bata son ki ni kuma na ɗauke ki, ki daina ko gaishe ta kina ji?" Ridayya ta jinjina kai ta ce "Ai shi ne take mini haka...," Ta yi maganar tana yin harara da taɓe baki ta ce "Yaya sunan wannan abin Ammi?"Ammi ta ce "Yana nufin na tsane ki, kuma sai na kashe ki" "Ta kashe ni na bar ganin Abbiey?" Ammi ta ɓata fuska ta ce "Abbiey kawai bani?" Ta yi shiru kan ta a ƙasa can ta ce "Ni ma na tsane ta, zan ɗauki wuƙa na caka mata" BATSARI /KATSINA. Yanayin duhun samaniyya da yadda daddaɗar iska ke kaɗawa, gari ya yi shiru sai kukan tsuntsaye da tashin ledoji zuwa sama zai tabbatar maka a tsakiyar watan Agusta ake. Yau ruwa gobe ruwa, hakan ya yi dab da shigowar watan azumin Ramadan. Yau ma kamar kullum garin ya yi baƙiƙƙirin gajimare sai gudu yake, ana wata kalar walƙiyya da iska mai ƙarfi dake tashi tana yaye gutsirarrun rufin saman wani gidan mai ƙarar kwana. Hankulan jama'ar ƙauyen Nahuta dake yankin ƙaramar hukumar Batsari, ya fara tashi ganin hadarin yau na musamman ne, wanda suke gonaki suka fara shirin dawowa gida, wanda suka fita bara suka fara tattaro tarkacansu suna ɗaukar hanyar gida, matan da suka fita garuwa suma duk suka yo hanyar gida, aka dinga kama awakai da shanu ana ɗaure su. Kamar yadda Hausawa ke yin lakabi da sunan “Katsinawan Dikko, kunya gare ku ba dai tsoro ba” Gefe guda kuma wasu su ce “Ta Dikko ɗakin kara" Hakan ɗin ce ta kasance a cikin wani fafakeken gida, wanda zubi da tsarin shi bashi da mara da gidan gandu. Gida ne mai rangwamen ƙarfi, ga tarin yara manya da ƙanana kasancewar mata huɗu ne a gidan, idan ka ɗauke surukansu da duk suke tare waje guda. A daidai sanda ruwan saman ya fara sauka a sannan ne ya fito daga ɗan ƙaramin ɗakin da take ciki mai kama da Bukkar Fulani mita take kamar ta ari baki "Ni wannan masifa da bala'in na cikin gidan nan ya ishe ni, masifa kamar ana tuttula mata man fetir, hoɗijam!" Ta faɗa tana yin turken awakai tare da kama gudu wacce ta kifo mata da ƙazon data shanya,sai ta yi wa akuyar dokan kawo wuƙa kana ta ɗaure. Ta kalli sama ganin yadda cita ke ta gudu ta ce "Ko a ina Gaaji ta samu gindin zama?" Kafin ta shige ɗaki yariyar ta shigo da gudu tana haki saboda ruwan daya fara dukan ta. Kallon tsaf ta yi mata kafin ta ce "Hala kin kwana turo? Hakin ga na lafiya?" Gaaji ta ce "Iya don ki ji Gidaɗo ya zo, ya dawo daga birni" A guje sauran yaran suka fito daga ɗaki suna murna yau za su ci abu mai daɗi da kyau. Iya ta ce "Ke ƙarya, Gidaɗo nawa? Yaushe ya zo babu labari" "Yana bisa hanya" Rufe bakin Gaaji kenan ya faɗo gidan yana cin magani sai taɓe baki yake yana kakkabe jikinsa. Jikin Gaaji na rawa ta ce "Ina taimaka maka kawo jakar tafiyar" Tana zuwa ya saka hannu ya sakar mata ranƙwashi ya ce "Kina ƙara taɓa mini kaya sai na ci ubanki, ƴar ƙauyen banza" Da sauri ta matsa tana sosa kan ta. Iya ta ce "Sannu lale me ka zo mana da shi? Kawo jakar naga?" Ya haɗe fuska tamau ya ce "Ke Iya nan kamar kin bani ajjiya, wai karatu na je yi ne ko neman kuɗi?" Ta riƙe baki "Kake faɗa mini haka Gidaɗo?" Ya ce "Gaskiya ce ai, ba ki ce Gidaɗo ya karatu ba sai me na zo da shi, ko tunanin na mutu a can bakwa yi kun kai ni gari kun zube babu mai zuwa, sai ni nima daga sallah sai sallah ko idan na yi wata ƙaryar" "To zage ni ka huta Gidaɗo, ni dai bani burodi" Ya ƙara yin kicin-kicin da rai ya ce "Point of correction, biredi ake cewa Iya" "Bari na je na faɗawa Hanne ka zo" Iya ta ce "Maza ki faɗa mata, a zo a yi maganar aurenku" Gidaɗo ya kalli Gaaji ya ce "Wallahi kika fita kika gaya mata sai na yi miki shegen duka ƴar banza da baki kamar na aku" Haka daga shigowarsa suka fara yi da baki daman babu kowa namiji a gidan sai Jafar shekarar shi Bakwai shirin kai shi Maiduguri ake wajan sauran yayyensu da suke can. "Ka je gona, lokacin girbi ya kusa za mu samu albakar noma na hatsi sosai" Gidaɗo ya miƙe ya ce "Ku za ku iya cin hantsi ni na yi hannun riga da shi, noma kuma a yanzu gaskiya Iya sai dai ku yi haƙuri na fi ƙarfinta" Kafin Iya ta yi magana an tsuge da ruwan saman, da gudu Gaaji ta fice daga cikin gidan ta nufi gidan su Hanne ta shaida mata Gidaɗo ya dawo. Gidaɗo na zaune a ƙofar gidansu ya ci wani uban yadi yellow ful da shi, da ƙaton takalmi ga wani irin glasses daya saka a fuskarsa ya haɗe rai, kasancewar fari ne jajur da shi irin farin Fulanin usul kuma Katsinawa ya yi wani irin kyau da shi, yara sun zagaye shi ƴan mata nata leƙo katanga suna kallo Giɗaɗon birni, hatta matan aure kallonsa suke wasu da alwashin tattara yaransu sukai su Almajiranci don kallo ɗaya za ka yi wa Giɗaɗo kasan yana saurarawa. "Giɗaɗona" Ya cira kai da ƙyar yana kallonta, haka kawai ya ji ransa ya ɓaci tas, saboda kwalliyar da yaga ta yi ta ci uban jambaki har ƙasan leɓe haƙoranta jajur nan da nan ya ji zuciyarsa na tashi. Hanne ta washe baki ta ce "Giɗaɗo ni ce Hannenka, ta Giɗaɗo ikon Allah dole mu saka maƙiyanmu dariya" Ya ɗaga kafaɗa a dole shi wani shege ne ya ce "Ni daman na jima da saka su kukan, tunda na je birni ko ba kiga yadda ake ta kallona ba, saboda na celeborotin a ƙauyen Nahutun Batsari" Hanne ta yi fari da ido sosai ta ce "Sai ni Hannen Giɗaɗo, mijina da izinin Allah, na haifa maka ƴa ƴa kallo su karime su Baɗejo duk an yi musu aure don ka ji" Giɗaɗo ya taɓe baki sosai yana kallon Hanne sosai da ne take burge shi yake mutuwar son ta amma tunda ya fahimci inda mata suke ya gane Hanne ba komai bace "Dube ki da kyau Hannen Nahutun Batsari, gaskiya bana miki kallon mace a yanzu, infat ma ba zan iya auren ki ba" Shi a dole a iya turanci haka Giɗaɗo yake jin kansa, babu shakka da sarauniyar Ingila za ta jisa sai ta yi masa kukan baƙin ciki. "Me kake nufi? Ni ce Hannenka fa? Ka manta kalle ni" Ta faɗa tana jujjuya wa. Tas ya kalleta sai ya yi miskilin murmushi ya ce "Hanne ƙuruciya, Hanne kwaila, Hanne wawta, Hanne ƙauyanci, Hanne daƙiƙanci, Hanne no no no kai Hanne ba zan iya ba" Idanunta ya cika da hawaye gabaɗaya shekarunta Goma sha biyu ne a duniya amma tana da jiki kyakkawa da ita, amma tasan soyayya ta san aure tunda tun suna yara ake aurar da su."Ban fahimta ba?" Giɗaɗo ya ce "Kalli ƙirjinki, idan na haɗa na cure su a tafin hannu ba su fi curin tumatir ɗan biyu biyar ba a birni, mazaunanki kam sai addu'a, ina taɓe su ba zai shige yankan biredi ɗan hamsin ba, ki je kiga matan birni yadda suke da kaya murguza murguza kamar sun ɗora ai zan nemi wata kawai" Kuka Hanne ta fashe da shi don a duniya ba wanda take ƙauna sama da Giɗaɗo fari ɗan kyakkawan saurayinta haka tana kiran sunansa ya yi burus yana ji a ransa yanzu Hanne ba tsarar auren shi ba ce. Haihuwar Mami ta yi daidai da samun aikin da Muhammad-Bilal Ustaz ya samu a wani Lagos. Aikin banki ne a Fidelity bank plc, dake Kofo Abayomi street victoria Island Lagos. Haihuwar Mami ya ƙara kawowa Alhji Mansur Rano buɗi, sosai ya nuna farin ciki da samun fara yarinya mai tsananin kama da Mami, kyakkawa asalin kyau na ban mamaki fari kamar ya yi magana. Baffa ya ɗaga babyn da tuni an yi suna ya ce "Sai yanzu kika haifo kalar zuri'ar Mansur Rano, yarinya kalar kyau ina alfahari da samun Zainura ita ɗin cikon farin cikina ce" Ridayya dake gefe ta yi zuru da Idanu ya kalle ta ya ce "Da an haifo mai kama da jakin dawa na gidan zoo, baƙi kamar zunubi Idanu daƙwa-daƙwa gabaɗaya suffar Aljanu ce da ita, ji nake dama ta mutu domin bata da wani amfani" Mami ta yi shiru idanunta a kan fuskar Zainura. Ammi ta ce "Haba Baffa wannan cin mutunci ne, duk lalacewar goma ai tafi biyar albarka, kafin Zainura Ridayya ce ta fara zuwa duniya" Ya yi murmushi ya ce "Maryam kenan, ke kin fi uwar yarinyar sanin ciwon ƴar banda kina son ta da tuni na cire ta daga cikin zuri'a ta don ina kokwanto da ƙyar idan ba ƴan ruwa bane suka sauya ta a ciki, domin da yaran Aljanu take kama" "Alhaji Mansur idan fitsari banza ne kaza ta yi mana, kana da kasuwar samun kamar Ridayya ɗin? Ko zaka iya ƙera irin ta ne? Ai ko yanzu kura ta faɗi tafi ƙarfin Allah wadai" Baffa ya ce "Bana son kina mini haushi kamar na kura Kaltum ba ruwana dake" Ta yi murmushi ta ce "Ai kura haushi ɗaya take yi wanda ka ji yau shi zaka ji gobe, ina son ka fahimce cewa ko yanzu ka mutu babu abinda zai hana Ridayya cin gadonka, daɗin abin kai ka kawo kan ka ma, idan ka ga dama ka tafi ruwan, domin Ridayya bata ɗauke ka matsayin uba ba" Tana faɗin hakan ta miƙe ta kalli Mami ta ce "Ke kuma shasha wacce bata san daraja da kimar kanta ba, yadda kike nuna ko in kula a kan Ridayya ki sani akwai ranar da za ki yi ladamar hakan ƙwarai da gaske" Rayuwa ta juyawa Ridayya domin har Zainura ta tashi ta fara wayo bata kula ta, cikin lallami da dabara Ammi take nunawa Zainura Ridayya ƴar tsintuwa ce a gidan kuma mayya ce kar ta yadda ta dinga kula ta wannan dalilin yasa Zainura ta kewa yayar tata kallon hadarin kaji, ba ruwanta da Ridayya wani lokacin har hana ta zuwan gidan take kullum tana part ɗin Baba ƙarami wajan Abbiey. Zahura ta yi aurenta daman ita karatun bai dame ta ba, Balkisa ta karanci ɓangaren jarida tana aiki a gidan rediyon Liberty itama haihuwarta uku. A gajiye Ridayya ta shigo idanunta lumshe saboda gajiya shekarunta Goma sha biyar ciff a duniya amma jikinta ya buɗe saboda tsananin kulawar Abbiey komai ya samu ita komai Shalale shiga matsala da damuwa da yawa sabo da ita amma ba wanda ya sanni ya ci bashi daga wajan jama'a saboda ya kula da ita nan ma babu wanda ya sani daga shi sai Allah sai mutanen. Kasancewar ta san Abbiey baya gari ya saka ranta duka a ɓace yake ta cire hijab ɗinta gashinta ya baje ta gire skirt ɗin makarantar sai ɗan ƙaramin gajeren sabon wanda da Abbiye ya siya mata ya zauna daidai da cibiyoyinta da suke da kyalli saboda baƙi ko'ina luff da gargasa ta miƙe tsaye. Madaidaicin ƙugunta a buɗe yake zaune daram Ubangiji ya bawa Ridayya dirin da surar jiki waist ɗinta tamkar ya yi magana har yanzu dai bata fara Irgan dangi ba. Ta ƙura wa kanta Idanu ta cikin madubi sosai take kallon kamar ta sai ta yi murmushi while hawaye na zuba a idanunta a hankali tana kwaɓe fuska cikin siririyar muryarta ta ce "Da gaske dai ni mummuna ce, me ya sa duka ni kaɗai ce baƙa mummuna a gidanmu? Me ya sa na girmi Zainu amma ita fara kyakkawa,me ya sa? Me ya sa?" Ta faɗa tana fashewa da kuka. Tunda Ridayya ta samu lafiya take so da ƙaunar farar fata da kwalliya gayu da ƙwalisa mutum irin haka yana masifar burgeta tasha yin kwalliya amma ita bata yin kyau. "Ya kamata ki yi farin ciki Ridha kin kammala final exam na secondary school" Wata zuciyar ta furta hakan domin Ustaz da kansa ya saka a yi wa Ridayya tsallaken aji saboda girman jikinta kuma ya samu kwakwalwar ta buɗe tunda ya bi shawarar Headmaster ya firgitar da Ridayya ya ce ai mutuwa zai yi yau ya kwanta a gado yana kakari har ya daina motsi ranar har suma sai da ta yi sai da ya yi ladama ya rungume ta a jikinsa yana jijjigata hankali tashe. Tunda daga ranar ta samu nutsuwa idan ta tuna da zarar bata karatu Abbiey zai mutu ta miƙe sosai. "Abbieyna ka dawo kaga na yi karatu an bani gift ka ji Abbiey" Ta faɗa tana lumshe idanunta tana jin duk gashin kanta ya dame ta. Ba tare data damu ba ta saka slippers ta nufi parlour wajan Umma ta ce mata ta dawo yunwa take ji. Cak ta tsaya jikinta na rawa da ɓari idanunta ƙuri a kan Abbiye ɗinta wanda ya hakimce a saman kujera hannunsa riƙe da kofi yana shan black tea. Jallabiyya ce a jikinsa yau sumar kansa duk a cuccure kamar baya cikin nutsuwarsa. A hankali ya saka hannu ya mayar da sumar kan nasa zuwa baya yana ɗauke hannun ta ƙara dawowa gaban goshin, ya ɗan ɓata fuska a jikinsa ya ji ana kallonsa, yanayin yadda tsigar jikinsa ke tashi ya fahimci ba kowa ke kallonsa ba sai Shalale. "How long will it take you to stop looking at me?" Murmushi ta yi idanunta na rufe wa sai kuma ta nufe shi da sassarfa domin mamakin ganinsa ya hanata motsi gabaɗaya kwanan shi biyu ta tafiya Lagos ɗin. Tana zuwa kusa da shi ya ajjiye kofin yana miƙewa tsaya tare da ƙoƙarin yin baya zai juya yabar parlourn. Ridayya ta yi saurin rungume Abbiey fararen haƙoranta na bayyana ta ce "Oyoyo Abbieyn Shalele i miss You mardly" A kasalance ta fara idanunta da suke cike da maye a rufe. Ustaz ji ya yi ta sakar masa nauyi ya saka hannu ya ciro ta daga jikinsa ya riƙe kafaɗunta tare da jijjigata. "Yes Abbiey.... Yes yes Wlcm back" Ta faɗa a rarrabe ganin ko idanunta ta kasa buɗewa ya saka Ustaz taɓa kumatunta wanda yake da laushi kamar audiga da ƙyar ya ce "Ustaza, open your eyes Ustaza" Dake tunda ta yi sauka yake ce mata Ustaza. Kafin ya yi motsi ya ji ta yi baya tare da faɗuwa ƙasa tim kamar saukar buhun siminti nan take gefen kanta ya fashe jikinta ya fara da kakkarwa ta shiga cuccure wa da kanannaɗewa tamkar maciji. Ku yi haƙuri bisa jina shiru da kuka yi ayyuka ne sukai yawa😢🥹A yafewa Mar'atussaliha Saliha idan naga comment da yawa sosai da sosai birjik zuwa anjima za ku ga new update. *✿ MUNAFUKIN MIJI 18 ✿* Mikiya Writers Ass..... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Ustaz ya bi Ridayya dake kwance a ƙasa tana juyi da mummurɗewa zuciyarsa na ƙoƙarin tsinkewa ganin kumfa na fita daga cikin bakinta ta abu kamar bugun jinnu "Ustaz ya haka ka zubawa yarinya ido cikin wannan hali, haba babban mutum" Umma ta furta tana ƙoƙarin kai hannunta jikin Ridayya. Ya furzar da iskar bakinsa ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya kafin ya ce "Karki taɓa ta" "Kamar ya?" Ya ɗan marairaice fuska kamar an yi masa dole ba tare daya kalli Umma ba ya ce "Hausa fa na yi, da gaske Hausa ce Umma" Ta girgiza kai ya juya a hankali tare da ɗakko hiraminsa ya rufe jikin Ridayya da shi, bakinsa na motsa wa a hankali yana mai yin addu'a tare da tofa mata. Can ta saki fitsari a saman carpet yana bin cibiyoyinta. Ustaz dai na tsaye haka Umma na kallon abin al'ajabi domin ba'a taɓa yin farfaɗiyya a gabanta ba sai yau. "Ikon Allah, Allah ya sauwake daman haka take yi kenan? Baiwar Allah" Tausayin Ridayya duk ya mamaye mata zuciya bayan matsalar gidan uba gata zubin halitta, gata gorin kalar munin da ake mata, ga makarantar babu daɗi. Uwar data haifeta ma sam bata damu da ita ba, balle kuma uba, wata sabuwar ƙaddarar na lalura ita kanta ba ko wanne namiji ne yake ƙaunar mace mai farfaɗiyya ba, ga shi ƙanwarta Zainura kamar ba jini ɗaya ciki ɗaya suka fito da Ridayya ba haka take nuna mata. Da ƙyar ta buɗe idanu saboda tsananin kunyar Umma da Abbiey wanda yake tsaye har yanzu, ita bata san lokacin data faɗi ba gashi duk sanda ta yi hakan sai ta yi fitsari a kwance. Basu san ta dawo hayyacinta ba sai sautin kukanta suka ji wani irin raunataccen kuka bai taɓa zuciya. Ustaz ya runtse idanunsa saboda wani irin dokawa da zuciyarsa ke masa, a hankali komai na jikinsa yake sage wa kansa ya fara sara masa da wani irin ciwo. Ya saka hannu yana dafe kan tare da furza goshinsa. Can ya juya a ɗan fusace kamar zai yi faɗa sai kuma ya tausasa murya, daga ƙarshe ma ya rufe bakin ya fasa faɗar abinda ya yi niyya. Yatsu ya kaɗa mata yana gyaran murya ta miƙe da sauri tana bin bayansa da sanyin jikin daya zame mata jiki komai nata a sanyaye yake yadda take tafiya kamar bata so haka take yi ko gudu bata iya ba, muryarta kodayaushe a ƙasa ba hargagi so silent, innocent gril. Ta yi jim tana leƙen bedroom ɗin can kuma ta shiga tana furta "Assalamu alayka" Babu tabbacin ya amsa kawai tana da yaƙi nin dole zai amsa idan har ba ta yi sallama ba baya kula ta duk kalar zancen da za ta yi masa. Ganin yadda ya yi tsaye a bakin wardrobe bai kula ta ya saka Ridayya ƙara fashewa da kuka tana yarfe hannunta "I am sorry Abbiey, ban san na faɗi ba, ban san na yi fitsari ba Allah" Ustaz ya juya ya kalleta idanunsa duk ya shige ciki sai ya girgiza kai a hankali ya ce "Yaushe Ustaza za ta girma?" Da sauri ta ce "Yau Abbiey" Sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ai ba zan girma ba, ai dabbobi basa hankali ni ma ba zan yi ba" A rikice Ustaz yana riƙe jarumarsa ya juya ya kalleta da kyau kana ya yi baya a taushashe ya ce "You said that?" "Zainura ce Abbiey" Ya yi shiru tana shassheƙar kuka sosai ta kama hannun Ustaz ta ce "Abbiey da gaske wai tsinto ni a kai ba nan ne gidanmu ba? Abbiey you're my father ko? Ammi ce Ya haife ni ko?" Ustaz ya rasa wacce amsa zai bawa Ridayya wacce za ta yi daidai da tunaninta ya fahimtar da ita ƙaddarar ta ce ta zo a haka? Ya nuna mata babu wanda ya isa ya ja girman ƙaddara, komai lokaci akwai sanda za ta shige. Bai dawo daga tunanin da yake ba ya ji ta saki ajjiyar zuciya. "Abbiey mene kwaila kuma? Yau da muna yin final exam ina murna wata ce mini wai na daina murna jss 1 a dawo dani saboda ni kwaila ce kuma Kangaroo basa zuwa University. Abbiey mene kwaila kuma mene Kangaroo?" Ustaz ya yi shiru yana son Ridayya ta fahimci abubuwa da dama amma babu mai faɗa mata, babu mai nusar da ita shi ya sa wani lokacin idan ta yi magana yake girmama wawtar ta, da tunanin har yanzu ita ɗin yarinya ce gata ƴar'fari ga lalura abin ya yi mata yawa. Jin ya yi shiru ta sake marairaice fuska ta ce "Abbiey mana, please" Ya kama hannunta tare da janta saman kujera bayan ya zauna ta, zauna a ƙasa wajan ƙafafuwansa kan ta a ƙasa shi kuma ya zuba mata ido, yana jin yadda zuciyarsa ke dokawa da ƙarfin gaske abubuwa da yawa na farmakar shi. "Ustaza" A sanyaye ta ce "Abbiey" Ya yi shiru ya ce "Kina bari ana raina ki ta hanyar nuna ƙuruciya Ustaza, da gaske ba za ki girma ba har yaushe zan kasance dake haka?" "Kasancewa kuma Abbiey?" Ta tambayata cikin rashin fahimta. Ya fasar ya ce "Wai suna nufin ba ki fara irgan su Zainu su Junaidu su Abdullah ba" Ta yi ƙuri ya ce "Wai fa nono suke nufi Ustaz idan mace nada shi ta girma if not kuma she's still a baby, kwaila ce ita" Ridayya ta zare ido sai kuma ta yi ƙasa da kanta. Ustaz ya tallafo haɓarta yana zubawa fuskarta Idanu ya nutsu yana nutsa ganinsa da kyau wai ko zai yi dace ya hango ta inda Ridayya ta samu tawaya amma ya kasa. Yasan idan ana neman asalin baƙar fata ta ƴan arewa to Ridayya ce a fusge kuma yanajinta kamar haihuwar ƙasar Ethiopia ko Mali. "Kin fahimta?" Cike da rashin sanin me take cewa ta ce "Ni ina ruwana da wani nono Abbiey? Ai ɗan Iska ake gani da shi nikam bana so" Ya ɓata fuska ya ce "Saboda me bakya so?" Ta ce "Ai yarinya ce ni shiyasa" A ransa ya ce "Allah ya sa motsin gado ce ke Ustaza" A fili ya ce "Allah ya shirya mini Ustaza" Ta yi murmushi tana lumshe idanunta a hankali ya ce "Congratulations an gama school sai University daga nan kuma sai.....," Ya yi shiru ta miƙe ta ce "Sai auren Abbiey in ji Umma" Bai kalleta ba sai girgiza kai da ya yi kawai yana sauke numfashi domin tun ɗazo a takure yake jinsa ya kasa nutsuwa da zuciyarsa bai bama ga dalilin dawowarsa Kano ba a daidai wannan lokacin. Da sauri ya shiga shagon yana duba lokaci can dai ya tsaki yana gyara sajensa daya zaune a fuskarta ya yi masa kyau, ga farar fatar nan ta shi gwanin sha'awa kyakkawa ne ajin farko, san kowa ƙin wanda ya rasa ga aji da masifar ɗaukan wanka. Ya sake yin tsaki a karo na biyu yana cije laɓɓansa. "Ni da wajan sana'a ta ba za ka zo kana mini tsaki ba a gaskiya, kuma yau ko asirinka zai tuno ba zan baka aron kayan kowa ba. Haka kurum kaja mini jarfa jiya fa da zaka je dinner ɗin Farouk wallahi saura kaɗan mai kayan dana ɗauka na baka ya ci ubana, to neman halak ɗina nake wanda zan rufawa kai na asiri da iyayena ban ja magana ba, to ka yi kaɗan ka yi tsararo ka ja mini ita wallahi" Rai ɓace ya kai ƙarshen maganar yana ɗauko wata dakakkiyar shadda gezner blue black ta ji ɗinki sai ɗaukan idanu take ga ƙamshin turare na tashi a jikinta. Ya shimfiɗa rigar shaddar yana yayyafa ruwa zai goge domin mai ita ɗan bala'i ne. Ganin yana ta tsaye ya saka shi kada baki ya ce "Zai fi maka kyau kasan inda dare ya yi maka, tunda ka ɗauki rayuwar da Allah bai baka ita ba ka ɗorawa kan ka, banda ƙarya da yaudarar yaran jama'a babu abinda ka iya, ba fus ba ass sai zaman kashe wando idan mota Benz ta shigo shigewa a ɗora buri da lissafin duniya a kanta, bayan ana fama da dattin aljihu" Sai a lokacin wanda ya shigo shagon ya ce "Kasan dai zan yi arziƙi kuma zan zama millionaires?" Mai gugar ya saki dariya ya ce "Ina fa? Nasan dai watarana zaka ci ubanka ka kuma koma Nahutun Batsari" "Shikenan daga na faɗa maka sirrina sai ya zama abin gori Mujahid? Mene ya kawo maganar Batsari kuma?" Mujahid ya ce "Babu laifi a tunawa mutum asalinsa, ai arziƙi ne ka yi baƙo ya kashe ka" Mujahid ya sake yin dariya ya ce "Wallahi ka ji tsoron Allah ka daina rayuwar ƙarya" "Idan ban ji tsoron Allah ba, Mujahid kai zan ji tsoro duk abinda nake yi bashi ne zan biya ka dana amsa sunan mijin Hajiya" Mujahid ya riƙe guntun gemunsa ya ce "Ba shakka, wannan shi ake kira da kunne ya girmi kaka, duniyar rawar ƴan'mata na gaba ya koma baya, kai a ɗan iska ba labar farko ne" "Ka rufa mini asiri" Mujahid ya ce "Allah ya rufa mana, ai duk duniya babu mai jin wannan zancen ka huta ka sarara" Ya yi murmushi yana ƙanƙance idanunsa cike da iskanci wanda suke fusgar ƴan'mata ya ce "To ya Opay na zo yi, ka bani wannan shaddar awa ɗaya zan yi kawai ka haɗa mini da hula zanna bukar ka bani aron air-pies ɗinka na Iphone or bluetooth ake ce masa ko? Sai kuma takalmi" "Duk a nawa? Domin masu kayan anjima za su zo amsa karka bar ni a ruwa don ubanka zan ci" Yana jingina da jikin bango hannunsa ɗaya a cikin aljihu ɗaya yana shafa sajensa ya ce "1hour ya yi yawa zan dawo, wani get-together zani ne a group ɗinmu na Kano celebrities". "Yaushe Bakatsine ya dawo Bakano? A gaskiya idan ajeboters suka ji abin ba zai yi kyau ba" Tattara harɗaɗɗiyar shaddar ya yi, ya ba shi yana karta masa warning sosai ya ce "Dubu biyu za ka bani" Ya ce "Na ƙara maka da ɗari ɗaya" Mujahid ya girgiza kai ya ce "Ɗan iskan Almajiri" Kamar yadda a rayuwa baka san mene zai faru da goben ka tunda al'amarin na kasancewa kamar karatun littafi, abinda ka karanta a wannan shafi ba shi ne zaka ruska a shafin gaba ba, haka kuma bangon littafi bashi zai fasalta yadda labarin ya gunsa ba. Yau fari ne gobe baƙi, yau dariya gobe kuka, yau zuma gobe maɗaci. Rana ta juya zuwa kwanaki, sannu a hankali kwanaki ke mirgina wa suna rikiɗe wa zuwa satutttuka, sati ya zama watanni daga sai a yi maganar cikar shekara. Tafiyar Ustaz zuwa Lagos ya dawo da rayuwar Ridayya sabuwar fil, ta koma ruwa. Damuwa da ƙunci sune abokan hirar ta, bata jin daɗin zaman gidan domin hatta Umma bata wani damu da ita ba, hakan baya rasa na saba da sabon Malamin da Ammi ta sauya, asiri gaskiya ne sai dai ya zo maka da sauƙi idan kana da kariyar Ubangiji. Bayan rubuta Jam ta samu maki na ban mamaki wanda ya yi daidai da kalar makarantar da Ustaz yake muradin sanya ta ciki wato B.U.K _Bayero University Kano_ A baya basa ɗaukan under 18 amma dake abu na manya ne an shiga an fita aka samar mata da Admission ta samu gurbin shiga a shekarunta daya kasance 16 amma jikinta ya ƙaryata ƙanƙantar shekarun. "Ridayya tun ɗazo kikai shiru, wai a hakan bama ki fara attending lectures ba?" Ridayya ta yi shiru zuciyarta na bugawa da abinda zata ruska yau a gida, Baba ƙarami baya garin ya je Rano gashi Hajiya Grandmother ɗinta ta je Umra tunda suna cikin watan Ramadan ne. Tsaki wacce suke tare ta yi ta ce "Matsala ta dake wulaƙanci da raini" "Haba mana Mardiyya" Ridayya ta furta a sanyaye idanunta na cikowa da hawaye. Mardiyya ta ce "Mtwsss mene na kuka to? You looks so doll mene?" "Nothing, babu" Ta faɗa tana share hawayen idanunta daya kasa tsaya mata. Diyya ta ce "Ni bana son irin haka, sai na faɗa miki damuwata amma ni kiƙi faɗa mini meke damunki ko Abbiey ne?" Jin sunan Abbiey ya saka Ridayya ɗan lumshe idanunta tana kokawa da numfashinta daya gama tsaya mata a maƙo shi "A'a" A fusace Diyya ta ce "To banga amfanin zama ƙawa a wajanki ba, daman nike tuttura kai na ina miki shisshigi a rayuwa, na yi hakan ne saboda conditions ɗinki" Ridayya ta marairaice ta ce "Kema na ishe ki?" Sai kawai ta fashe da kuka har da shassheƙa ta ce "Don Allah na dawo gidanku da zama kafin Abbiey ya dawo Mardiyya?" Tausayin Ridayya ya ƙara kama Diyya ta ce "Komai ya zafi maganinsa Allah, ita ƙaddara tana da nata lokacin ki rubuta ki ajjiye watarana zai zama tarihi" Ridayya tunani take a zuciyarta yaushe za ta yi murmushi irin na Zainura? Irin na su Junaid yaushe zata zama cikakkiyar ƴa kamar kowa a gidansu? Ita da gidan ubanta amma ya fi ƙarfinta? _How long_ zata kasance haka? Sai yaushe komai zai zama daidai a rayuwarta? "Don Allah na tambaye ki Mar" "Allah ya bani iko" Ridayya ta ce "Da gaske ba zan taɓa yin aure ba wai? Ba zan taɓa samun wanda zai ce yana so na ba? Wai zan ƙare a gidanmu har abada kamar baiwa" Diyya ta ce "Ki daina faɗar haka, shi aure ai lokaci ne da shi da mutuwa ba a saka musu rana, da shi da haihuwa ba a yin gorin su babu maki ki yi auren ki bar ni, ki manta ki saka karatu a gaba ki yi achieving abubuwan da kike da buri" Ridayya ta yi shiru tana sauke ajjiyar zuciya hawaye yaƙi tsaya mata gashi idan tana kuka leɓen ƙasa ya yi sharɓeɓe ya sakko ƙasa hancinta ya bubbuɗe. Ganin tana sauri ya saka Diyya riƙe ta sosai "Wannan saurin fa? Kar ki faɗi fa" Gabaɗaya ta tsangwami kan ta ji take ko'ina a makarantar gulmarta ake gashi ta hango wasu matasa tsaye a jikin mota sai kallonta suke kamar ta kurma ihu ita kam idan haka ne bata jin zata iya karatun. A haka suka gilma ta gaban samarin suka shige wani ya yi saurin toshe hanci ya ce "Smell wannan kill me oh gosh!" Wani matashin saurayi ya faɗa yana rufe hanci da hanky. Moo Ya ce "Ban son sharri kana nufin mun yi tusa ne?" Khalil ya ce "No, I don't mean that, that black girl data shige ita ke yin warin" Duk suka juya suna kallon bayan Ridayya abaya ce a jikinta mai ɗan faɗi ta ɗaure igiya a ƙugunta, yadda abayar take baƙa ƙirin haka jikin Ridayya suka yi anko haƙonta ne kawai da idanunta masu haske a jikinta. Haɗa baki sukai wajan furta "Rabbi ya yi halitta, halitta, halitta...," Shaba ya ce "Asnanic ya yi basira wajan yin waƙar nan, wlh ban taɓa cin karo da baƙar mace irin wannan ba, tab kwalta" "Ga leɓe ina ruwan Dandamali" Moo ya ce "But she's arrogant, i like the way she's act" Tunda suke surutun su, bai ɗago ba bai ma san a kan wa suke magana ba, saboda ba kowa ya sani a school ɗin ba. Sai baza ƙamshi yake mai ɗaukan hankali kaf cikin haɗaɗɗun matasan babu wanda ya kama yatsarsa a kyau da haɗuwa Ubangiji ya yi halitta, fari tas har ɗan yellow yake ga sajensa daya gewaye fuskarsa ya yi daidai da gemunsa mai kyau. Wagambari ne a jikinsa brown colour ya ɗora hula zanna bukar ya bluetooth a kunnensa ya riƙe waya iphone a hannunsa yana dannawa. Kan shi ya ɗaga ya kalleta idanunsa a sauka a faffaɗan ƙugunta dake juyawa ta cikin abayar, ya jima kana ya ɗan taɓe baki ya juya. Khalil ya ce "Meer ka san ta ne?" Ya ɗaga shoulder duka biyun alamar "No" "Bama zata kula ka ba, ba hannunka ba ce?" "A saboda bani da qualities da zata kula ni? Mu ai sai dai mu saka mace kuka mu ɗora mata hawan jini, har yanzu banga kala ta ba" Moo ya ce "Na santa fa" Duk suka juya suna kallonsa da alamar ƙarin bayani ya ce "Ridayya Muhammad-Bilal Rano is her name, babanta a yanzu mai arziƙi ne sosai da sosai yana da kantuna a katin kwari da sabon gari, gashi yana kwangila kala-kala business yake na ban mamaki, sai babban yayenta mai suna Muhammad-Bilal Tahir Rano ana ce masa Ustaz shi ne Md a fidelity bank dake Lagos yana mugun son ta, hatta aikin da ya ke yi domin ita ne. Babban mutum ake ce masa a familyn saboda ya girmi kowa kasancewar basu da wani yawan ƙwarai duk abinda ya mallaka sunan Ridayya ne a jiki, sai dai ita kuma kaf dangin basa son ta hatta babanta wai ya ce ba ƴarsa ba ce shi ne shi kuma Ustaz ya raineta tun tana ƙarama, yarinyar nan da kake gani ba hannun kowa ba ce dukka da muninta kamar a yanka a ɓoye wuƙar ko a haɗata da su Dila a kejin zoo road" Meer ya ce "Wow interesting, kawai ka ce kadara ce" Moo ya ce "Meer kai me za ka yi da ita ai Daddynka ba zai bari ka auri ugly ba" Meer ya jinjina kai ya ce "Zai bari mana, matsalar na tsani abu mai muni gaskiya bana ƙaunar baƙar mace yadda nake fari na samu fara mu dinga haifar farare" "Ba zata taɓa sauraran ka ba" Cewar Moo. Da sauri Meer ya ce "Hujja?" Kai tsaye ya ce "Ta yi sati tana shigowa School fa, kuma ina bibiyarta duk wasu gulma na ƴan mata ni nake kawo muku, to ko mata bata magana da su balle namiji, kullum cikin kuka take sai dai tana da diri fa idan ka nutsu ka kalleta wallahi" "Ko soyayyar minti ce sai na rinjaye ta mun yi, na ci moriyar ganga na yar da ƙwallon mangoro na huta da ƙuda kuma" Khalil da babansa ya fi na kowa kuɗi a wajan ya ce "Caca" Gabaɗaya sukai shiru Meer ya ce "Ina ciki" Khalil ya ce "Idan ka nemi soyayyar yarinyar nan, kuma ka sami abinda kake so kana da 5 Million kassh" "Are you sure?" Khalil ya ce "Ai idan maganar caca ne ba a wasa, idan kuma bata amince maka ba zaka bani wani abu dana jima ina buƙata a wajanka, na baka nan da wata biyu" Duk sukai ihu Meer ya dinga tunanin miliyan biyar ko dubu ɗari ta kansa bai taɓa riƙe wa ba, hatta yadin jikinsa wajan Mujahid mai guga ya yi opay ɗin su, wayar ma ta Mujahid ce amma kaf cikin abokan nasa babu wanda ya san asalin Meer ganinsu yake kamar duka masu kuɗi shi ne kawai ɗan gidan Malam Ɗan'lami ya ji a ransa dole ya bi salo mai kyau na burge Ridayya kafin furta soyayyar. Ridayya na komawa gida ganin Umma bata nan ita kuma ba zata iya yin girki ba saboda ciwon cikin dake damunta, gashi ko azumin ma bata yi, ya saka ta cire hijab ɗin kanta daga ita sai duguwar rigar da ta bi jikinta ta yi luf ita na maiƙo rigar na maiƙo. Ita ko powder bata taɓa shafawa ba bata kwalliya bata san yadda ake ba karatu kawai ta saka a gaba don tana da buri mai girma da take son cimma, dake ɓangaren Mefa take son karanta Medicine, daga ta zama Medical Doctor sai ta nufi Gynea. Bachelor of Medicine (MB) of Surgery (BCh) and of Obstetrics (BAO). Idanunta rufe take son buɗe cooler ɗin ta ji an ce "Wallahi kina taɓa wa zan faɗawa Mami" Ridayya ta kalli Zainura tunu idanunta ya sauya ta ce "Yunwa nake ji" "To cinye ni, ko me kika taɓa a gidan nan najasa ce wallahi" Ridayya ta kalli Zainura bata kula ta ba ta fara ƙoƙarin ɗora tukunya zata dafa Indomie "Wannan kuma ki ɗauki mai kama dake Allah ya sauwaƙe ki zama yayata kila ke fa shegiya ce zina aka yi aka haife ki" "Zainura!" Ta ji Mami ta daka mata tsawa tana juyawa ta ce "Mami wallahi na tsane ta ai ƴar tsintuwa ce kuma mummuna duk gidan nan ita ce baƙa" Ammi na zaune ba ta yi magana ba Mami ta ɗaga hannu ta zabgawa Zainura mari idanunta na sauya kala har ƙasan zuciyarta ta ji zafin maganar amma koda wasa ba za ta yi kusantar kan ta da Ridayya ba. Kafin ta ɗauke hannunta Mami ta ji an zabga mata mari da sauri ta ɗaga idanu kallonta ya sauka a kan Baffa ashe tun jiya ya dawo bata da labari dukda cewa girkinta ne "She is right, Zainura nada gaskiya wallahi kika ƙara taɓa mini ƴa a kan wannan shegiyar mujiya sai na yi maganinki Fatima, kuma waye ya hanata yin azumi ma?" Kuka Ridayya ta fashe da shi sosai ta kalli Baffa ta kalli Mami ta ce "Baffa, Mami yau ɗaya ina neman alfarma don Allah don girman Allah ku nuna mini iyayena na gaskiya na koma wajan su, idan ni tsintata a ka yi a faɗa mini gaskiya ko gidan marayu ne na koma, idan kuma da gaske ni ƴar ku ce don Allah ku faɗa mini shin da aure kuka haifeni? Ko kuma zina ta samar dani, shin ni na yi kai, Ubangiji daya baku Zainura shi ne ya halicce ni don.....," Kau! Mami ta sauke wa Ridayya mari kalmar zina ta gigita Mami sai kawai ta fashe da kuka tana yin bedroom ɗinta. Baffa ya ce "Ni kik faɗawa haka?" "Ka yi haƙuri Baffa, wallahi zuciyata bugawa za ta yi na kasa jurewa" Cafko tufkar kanta ya yi ya shiga jaa tana ihun a zaba tana kiran sunan Abbiey da Ammi Baffa ya shiga dukanta kamar jaka ya saka ƙafa ya murje mata yatsun hannu azaba ta saka ta saki fitsari. Addu'a take inama a wannan dukan Ubangiji ya amshi ran ta? Inama mutuwa zata ruske ta? Sai da ta gama dakuwa Ammi ta miƙe ta ce "Ya isa haka Baffa" Cak kamar cirar ƙaya ya daina dukan Ridayya da sauri ta miƙe ta faɗa jikin Ammi tana kuka jikinta sai ɓari yake ko'ina ciwi yake mata. Baffa ya haura sama Ammi ta saki murmushi kana ta ce "Jeki Ki kwanta Ridayya ki yi shiru haka nan" Da ƙyar ta nufi waje. Ammi ta yi murmushi ta ce "Allahamdulillah, sannu hankali ku yi ajalin ƴar ku da kan ku daga nan na dawo kan Zainura ai ba zan taɓa ƙaunar kishiya kuma na ƙaunaci ƴaƴanta ba" Kuka sosai Mami take ta rufe kan ta a ɗaki a lokacin na farko da ta ji bakinta ya buɗe ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Rabbi inni lima anzalta min khairin faƙir" Ta ji tana son kaiwa Ubangiji kukan ta. Zainura ta dinga dukan ƙofar tana kiran sunan Mami ta ji kuma tausayin Ridayya sosai a karo na farko na dukan da Baffa ya yi mata. Kuka sosai take a corridor har lokacin kiran shan ruwa ya yi ta ji dama kawai azumin ta yi ta huta anya ba zata gudu tabar gidan ba? Ai ta san inda ake kai marayu kuma ta san gidan karuwai ba dai sabon gari bane bata taɓa zuwa ba amma zata tambaya tana da raguwar kuɗin da Abbiey ya bata. Hijab ta saka da slippers ta goge hawayen fuskarta tas ta nufi hanyar fita da Usman sukai karo ya kalle ta ya shige abinsa tana ƙoƙarin buɗe gate ne Junaid ya shigo ya ce "Ke ina zaki?" Da ƙyar tana rarraba Idanu ta ce "Wajan Diyya zani" "Ba ki ji ana kiran magariba ba? Za ki shige ko sai na yi ƙwllo dake" Ta juya ganin ta koma ya nufi cikin gida yana shigewa ta fito daga bayan corridor da gudu har tana yin tuttuɓe ta fice daga gidan kai tsaye titin Darmanawa ta nufa inda zata samu napep..... *✿ MUNAFUKIN MIJI 19 ✿* Mikiya Writers Ass..... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Nimcyluv KULIYA HAUSA NOVELS za mu shirya kowa? Ni banga alamun kuna karatun ba a gaskiya idan banga 500 comment ba, ba zan ci-gaba da yin posting ba. Tunda ta fara tafiya bata waiwaya ba, cikin kasalar da take tunanin sauri take yi haka ta nufi titi ba tare data san inda take cillar ƙafafuwanta ba. Tana tafe tana share hawayen da yaƙi tsaya mata, ga wani masifar ciwo da jikinta yake yi mata, hannunta jinsa take tamkar ba a jikinta ba saboda karayar data samu lokacin da Baffa yake haɗa mata na jaki. "Ɗitt, ɗitt, ɗitt" Haka wata dakakkiyar mota ke danna mata horn amma ina, Ridayya babu abinda take ji da matukin motar zai mata adalci da ya bi ta kan ta, kilan farinciki da jindadinta yana Aljannar firdaus. Tana ƙoƙarin shiga tsakiyar titin ta ji an saka hannu tare da fincikota zuwa baya rai ɓace mutumin ke magana idanunsa rufe "Ke wacce kalar yarinya ce? Kurma ce ke da ana horn bakya ji? Who do you think you are? Eh? Salon ku jawa mutum bala'i a wannan rayuwar da ta tsada kuɗin diyya ma da ɗuwawun shi yake zaune, banda azumi sittin" Kasa cewa komai ta yi kanta ƙasa jikinta duk rawa yake don fargaba ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, musamman da ya ga taƙi kallonsa. Inda take fuskanta ya koma Ridayya ta yi saurin sauya direction ita bata so ya kalli fuskarta don bata san da wacce kalar dabbar zai haɗata shi kuma. "Kurma ce ke da ina magana za ki yi ignoring nawa? Wace ke?" Ya faɗa yana sake kai hannu zai fusgota ta yi saurin juyawa tana haɗe hannunta biyu idanunta har yanzu hawaye yake fiddawa muryarta na rawa ta ce "Ka yi haƙuri don Allah" Zaka ɗauka iyayi ta yi wajan maganar saboda a sanyaye muryar ke fita, ga kukan da ya zama abokinta kodayaushe. "Goodness!" "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Wa'innahu Sulaimanu wa'innahu Bismillahir.....," Da sauri ta buɗe dara-daran idanunta farare tas ta ƙura masa ido irin me kake nufi ɗin nan? Shi kam murya na rawa ya ce "Oh.... Shi.... Shikenan it's okay" Ya juya da sauri zuwa cikin mota ɓangaren direba yana addu'ar data zo bakinsa. Yana shiga motar ya kurma ihu ya ce "Aljana ce, mun shiga uku na yi gamo" Duk ya gigice saboda har zuciyarsa ya ɗauka gamon ya yi dalilin duhun magaribar daya kunno kai ga baƙin Ridayya gami da baƙar abayar data saka a jikinta. Wanda yake zaune a gefe ɗaya hannunsa riƙe da jarida yana dubawa don shigowar su garin Kano kenan tafiyayyiya sukai. "What nonsense, Mahmud?" Wanda aka kira da Mahmud ya ja numfashi idanunsa waje ya ce "Aljana ce, Aljana na gani?" Ya ware Idanu da mamaki can ya taɓe baki tare da yin shiru. Mahmud ya ce "Tajj da gaske Aljana ce wacce mu ke wa horn fa" Ya sake ɓata fuska ya ce "In Ramadan period?" Ya ce "Wallahi Tajj" Tajj bai sake magana ba don baya ra'ayinta da ƙyar Mahmud ya iya jan motar suka ɗauki hanya a ransa yana mamakin mugun halin Tajj Baita ko jajinta masa bai iya ba. Ridayya kowa itama a tsorace ta matsa daga wajan domin ta ɗauka wani mugun abu mutumin ya gani, a hankali ta ja jiki waje guda a bakin titin banda ƙugi babu abinda cikinta ke yi mata, ga wani azabar ciwo da murɗawa da mararta ke yi mata tun safe sannu a hankali ciwon ke ratsa ta yana cin jikinta. Ta rufe idanunta bakinta ɗauke da sunan Allah, da sauri ta buɗe idanun ganin a wannan karan ma kamannin shi ya ƙara gittawa ta cikin idanunta. Ta marairaice fuska da gaske ya takura ta, bata san waye shi ba amma tunda ta fara shiga B.u.k kullum sai taga rukunin su _who is he?_ Ta ɗan yi murmushi kaɗan sanda ta runa farar fatarsa da idanunsa da kuma abin kunnensa, tana son ganin namiji ɗan gayu yana burgeta haka kurum. Sai kuma ta ɓata fuska sanda ta tuna Abbiey kullum cikin jallabiyya da hirami, wanda ta gani yana da bambanci da Abbiey ɗinta ƙwarai ko dan shi babba ne ya manyan ta? Ƙara rufe ido ta yi kamar alamar fuska ta ƙara gilmawa ta idanunta ta marairaice ta ce "Kar ka hanani bacci, Uhm waye kai? Shaddarka mai kyau" Tunani ta fara to ina za ta je yanzu? Ga dare ya yi idan ta tafi Abbiey fa? Zai shiga damuwa saboda shi kawai zata koma gidan don shi ɗaya ta miƙe tana juyawa har zata shiga sai ta fasa ta nufin gidansu Mardiyya dake kusa da su. Tana shiga ta gaida babbarsu Mardiyya lokacin ana sallar isha'i kwanciya ta yi saman carpet idanunta rufe, sai juyi take a yanzu ba yunwar ke damunta ba tunaninta wanda ya yi tsaye a zuciyarta shi ne matsalar gashi bata san ainahin abinda ke faruwa da ita ba, ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Yin duniya Mardiyya ta yi a kan Ridayya ta ci abinci amma ta ce Allahamdulillah ta son bawa Mar labari amma tana shakkar abinda hakan zai haifar. Sai ashirin ga watan Ramadan Ustaz Bilal ya dawo daga Lagos shigowar dare ya yi don haka ba wanda ya san da zuwan shi. Bayan ya nutsu ya huta sosai a hankali ya miƙe kamar kullum yana tafiya cike da izza nutsuwa kama da haiba faffaɗan jikinsa na motsa wa, he looks so good amma ya ɗan faɗa sosai ba hirami a kansa sumar ta yi baya kamar Balarabe jallabiyyar ta kwanta. Yana tafe yana karatu cikin kamilalliyar muryarsa har ya isa bedroom ɗin dake kusa da na shi ya saka key tare da buɗewa ya shiga. Kasancewar dare ya sa sallamar can maƙoshi ya yi ta. A tsakiyar gado ya hango ta, ta cure waje guda alamar sanyi take ji, bargo daban ita daban, haka rigar baccin daban ya jima tsaye yana tasbihi a ransa a fili ya ce "Mugun gani Ustaza" Ya furta yana zama a gefen gado, a hankali ya kai duban shi ga fuskarta duk ta marairaice saman idanunta ya kumbura sai ajjiyar zuciya take saukewa na wahala da ƙyar ta yi bacci saboda ciwon ciki ita kaɗai a ɗaki kamar mayya. "Allah ya yafe miki Ustaza, bani da laifi" Ya faɗa yana ja mata rigar ta rufe mata cinyoyinta ya ja mata saman ƙirjinta yana mai neman ya fiyar Ubangiji. Caraf ya ji ta riƙe hannunsa tana fashewa da kuka. "Abbieyna ka dawo zan mutu bafii cikina Abbiyena" Ya ɗauka mafarki take ganin yadda jikinta ke rawa ya sa shi fahimtar zahiri ya sauke numfashi yana mai lalubo kalamar "Shalale... Ustaza" Da sauri ta buɗe ido wanda ya kumbura ganinsa ya saka ta sauke wata ajjiyar zuciya tare da mirgina wa ta ɗora kanta a cinyarsa tana marairaice fuska "Abbiyena cikina zan mutu wayyo Allahna" Addu'a ya fara yi mata yan shafa sumar kanta, da ƙyar yake motsa hannunsa saboda yadda gargasar jikinsa ke mimmiƙe wa tana zubewa, zuciyarsa na doka masa da tsananin ƙarfi tunaninsa na neman gurɓata, kokawa yake da zuciyarsa yana ambaton sunan Allah zufa sai yanko masa take kyakkawan bugun da zuciyarsa ke yi masa ya tsananta, ya yi saurin matse hannun Ridayya. Da ƙyar ya iya tattaro jarumta ya aza bisa gangar jikinsa. Kuka Ridayya ke yi sosai tana jin kamar zata mutu gashi ta bi ta shige masa jiki kamar anan zata samu sauƙi, jikinsa mahaifi daɗi gare shi kuma an ce mutuwa na jin kunyar idon mahaifi wannan dalilin yasa Ridayya riƙe Ustaz da kyau tana kuka "Abbiey zan mutu cikina" Da ƙyar ya ce "Ba za ki mutu ba Ustaz, sorry" Bashi da wani zaɓi haka ya rungume ta a jikinsa yana yi mata addu'a hannunsa ɗaya na shafa sumar kanta. Iddar da sallar ƙiyamul laili ya yi daidai da lafawar ciwon bacci ya ɗauke ta a jikinsa tana sauke numfashi mai zafi ya ƙura mata Idanu a fili yana girgiza kai ya ce _"When?_ Sai yaushe ne?" Kwantar da ita ya yi yana rufe ta da bargo ya miƙe tare da nufar waje. A parlour ya same su suna shur Umma ta ce "Babban mutum saukar yaushe?" Ya nemi waje ya zauna Baba ƙarami ya ce "Jiya ko?_ "Na rasa sunturin da yake bashi Kano bashi Lagos shi kuma ba auren ba" Nan da nan ya kame fuska a nutse ya ce "Abba, Umma ya ibada?". "Allhamdulillah!" Suka amsa lokaci ɗaya Umma ta kalle shi ta ce "Rashin lafiya ka yi a can ne naga duk ka rame idanunka zuru-zuru?" Ya ɗan gyara fuska ya ce "Haba mana Umma haba, kin ce rama kin ce sunturi kamar mota, haba mana" "To Ubana na yi shiru" Baba ƙarami ya yi murmushi ya ce "Kowa lafiya ta yi wa daɗi ba kamar mai ita ba, sannu sannu ai bata hana zuwa sai dai a jima ba a je ba, ki daina gaigaye za ki ci tumu ne" Umma ta ce "Gwara na yi shiru yanzu sai ya ce bana son tsawa da gaske ban son tsawa Umma" A ɗan fakaice Ustaz ya yi murmushi yana shafa kansa zuwa gemunsa "Tea please" "Shur da tea?" Ustaz ya ce "With lemon" ya ƙare yana lumshe idanunsa Umma ta miƙe ta nufi kitchen. Baba ƙarami ya kalli Ustaz ya ce "Muhammad-Bilal" Ustaz ya runtse idanunsa sosai jin sunan ya yi har tsakiyar kansa ya juya ya kalli Baba ƙarami dake cewa "Yaushe za ka yi aure? Tun ƴan'matan na marmarinka sai ka tsofa a idanun nasu? Kasan shekara nawa kake a yanzu, me kake nufi Muhammad-Bilal" "Ina nufin lokacin Abba, sai na fara aurar da Ustaza" Ya runtse idanu sam maganar ba ta yi masa daɗi a zuciya da kuma baki ba, gudun kar Baba ƙarami ya sake magana ya miƙe yana bin Umma kitchen. Ta farka jikin da sauƙi ta yi wanka ta shirya cikin milk ɗin abaya ta ɗora mayafi fuskar ta faɗa sai maiƙon da take idanun sun ƙara girma laɓɓan sun yi jajur saboda kuka. Bisa umarnin Ustaz ta nufi part ɗin Baffa lokacin 12 na rana ta samu Baffa a parlour shi da Ammi suna maganar kayan sallah ta durƙusa ta ce "Ina yini Baffa, Ammi?" Ko inda take Baffa bai kalla ba Ammi na yin murmushi ta ce "Lafiya lou ƴar University, ya karatu?" Cikin cool voice ɗinta ta ce "Yau ne zan fara attending lectures" "Oh i see" Ta kalli Baffa sai kuma ta ce "Yanzu nake cewa Baffanku ya bada kuɗin kayan sallarki amma fur ya ƙi ya bawa kowa, Zainura kala kusan goma ya yi mata" Ridayya bata ce komai ba ganin yadda take ta kallon Ammi ya sa ta ce "Saƙon ki yana kan mirror" Ta miƙe ta nufi best ɗin Ammi. Baffa ya ce "Maryam ki daina haɗa ni da wannan yarinyar zan miki abinda ba ki yi za to ba" "Jinka wuya za shi. Kuma ai duk lalacewar goma ta fi biyar albarka dole a kira Ridayya da ƴarka, idan baka so kawai ka kure ta a gidan gabaɗaya ko kuma ka tsine mata" Kalmar ta daki Baffa haka kurum a ransa yana jinjina kalmar tsinuwa. "Kuma ka tura mini kuɗin kayan sallar nata yanzu umarni nake baka" A sanyaye ya ce "Nawa?" Ta ce "Kala sha biyar zan mata, ka bada 250k" Bai yi magana ba a nan take ya tura mata kuɗin ita kuma ta turawa Biba ta ce ta haɗa mata a kan sauran. Ridayya sam bata lura da wanda yake zaune a ɗakin Ammi ba tana ƙoƙarin ɗaukar kwalbar ta ji an ce "Wow irin wannan diri haka?" A firgice ta juya idanunta ya sauka a kan garjejen dake kwance saman gado. Ƙanin Ammi ne don ta gane shi ya miƙe ya ce "Kin yi mini da harka ƴan'mata" Ridayya jikinta ya fara rawa sosai ko maganin bata sha ba ta nufi hanyar waje ya yi saurin tare mata hanya ya ce "Ke cika yane, ki gane mana ki zo mu sarara kafin na sata" Bakinta na rawa ta ce "Ka yi haƙuri" "Hahaha ji gaja, mu saya za mu yi, na baki gishiri ki ban manda kin ji ƴar baka ƴar duma duma jin ki ya fi ganinki" A tsorace ta ja da baya ganin yana ƙoƙarin kamo ta "Ka bari bana so, wannan iskanci ne" Burhan ya ce "Ai daman Iskancin zan miki, ki bani dama ki ware ki ci duniyarki da tsinke, domin idan kina tunanin aure ki daina. Wallahi babu mijin da zai ɗaukar wa kansa jaraba da bala'i da ƙaddara, duk matan duniya sai ke? No no Animals" Kalmar Animals ya daki zuciyar Ridayya ko dai babu wanda zai aure ta ɗin kenan? Ba namijin dake son ta sai Abbiey? "Thinking? Kar ki wahalar da kan ki sai ki mace a tunkuɗaki kabari a narka gasa, aure sai dai a mafarki wanda za ki yi sai kuma ki yi wanka, amma har gaban abada ba za ki taɓa samun mijin aure ba, ki rubuta ki ajjiye idan ma an yi dace sai dai wulaƙantacce amma ko shela a ka yi ba za ki samu ba, gwara ki zo mu shaƙata ita Maryam ɗin ce ta bani dama ta ce mu yi awa biyu ba wanda zai sani zata ɓoye mu ki zo na dandali roman daɗi na farke wannan rufin kafin wani ya ruga ni don tabbas ƙarshen budurcinki a waje ne ba dai gidan aure ba, kar ki mini asara" Hawaye ya ɓalle a fuskar Ridayya domin yanzu tana fahimtar komai albarkacin karatun littafan Hausa da zama da Mardiyya. Burhan ya ce "wallahi na kwaɗaita zan sarara dake zan rufa miki asiri ba wanda zai san na yi tarayya dake, mu maza duk mai mukai ado ne kune zai zame muku gori, gashi kin nuna sosai kaya iya kaya" Fita za ta yi ya damƙo ta ta daddage ta gartsa masa cizo ya sake ta yana ƙara ta fice a guje. Ammi na zaune a parlour bayan ta damfari kuɗaɗe tana jiran taga fitowar Ridayya tana jirga ƙafa jini na bin ƙafarta haka shi ne zai bata tabbacin plan ɗinta ya yi. Ta miƙe da sauri ganin Ridayya ta fito ta ce "Ke lafiya lafiya?" Daidai nan Mami ta fito zata kasuwa ita da Zainura kai tsaye Ridayya wajan Mami ta nufa tana zuwa ta faɗa jikinta ta fashe da kuka, wani irin kuka take wiwi kamar wacce aka ce Ustaz ya mutu a hankali kuma ta ji wani sanyi na ratsa zuciyarta, jikin uwa daban ne wani irin abu wanda bata taɓa ji ba shi ne yake ratsa ta. Mami ta yi shiru ta kasa taɓa Ridayya daman ita ta san Mami ba zata taɓa jan ta a jiki ba, itama kwaɗayin uwa ne da kuma neman inda zata zubar da hawayenta. Da sauri ta saki Mami ta nufi part ɗin Baba ƙarami kai tsaye bedroom ɗin Ustaz ta nufa. Mami ta tsaye da sauri kuma ta ɗauke kanta tana goge hawayen idanunta babu shakka addu'a daban take tasan kusancin ta da Ridayya yau addu'ar data jima ta na yi ce cikin watan mai falala. "Fatima bani kuɗin dana baki na kayan sallar ki na fasa ban niyya ba" Baffa ya faɗa yana haɗe fuska. Mami ba ta yi magana ba ta ciro cash ɗin kuɗi dubu hamsin ta bashi. Ya ce "Fitar ma bana da ra'ayi" Ta yi sak ta ce "Nan kuma ɗaya, kuɗinka na baka daman ban damu da su ba domin ba a wulaƙance ka ganni ba, fita kuma babu fashi" Zainura ta ce "Siyaya za ta yi mini fa Baffa" Bai kula Zainura ba ya ce "Wallahi kika fita a bakin auren ki" Mami ta ce "Ka ji tsoron Allah Alhji Mansur, ka tuna Ubangiji yana kallon ka" "Bari na ji tsoran ki Fatima tunda ba zan ji tsoron Allah ba, auren ki gabaɗaya ƙaddara ce" Ammi ta ce "Haba Baffa me kake cewa haka bana son irin wannan ya dinga faruwa wallahi" "Kyale ni Maryam ni na san kalar baƙin cikin da nake shaƙa da ita, ladabin babu kwalliyar babu idan muna gado jina nake kamar a gidan biredi babu komai a fafake take wallahi tamkar ruwan rijiya" Da sauri Mami ta ce "Zainura out" Zainura ta fita tana kuka. Wani irin kuka Mami ta fashe da shi sosai ta ce "A kan idanuna a kan idanun ƴata kake ci mini mutunci? Me na yi maka Baffa me na yi maka?" Ya kaɗa Babbar riga ya ce "Ohho ai gaskiya ce na faɗa banda kurje ni ba abinda kike kamar murhu don azaba" Ammi ta juya tana yin dariya kamar ta taka rawa don farin ciki "Akwai Allah" Mami ta ce tana komawa zuciyarta babu daɗi ta ga ji da gunsar baƙin cikin Alhji Manur Rano. Ta yi ladamar auren shi bata taɓa tunanin hakan zata faru a yadda suka gudanar da soyayyarsu har zuwa aure ba, tun haihuwar Ridayya komai ya sauya. "Bani kuɗin" Ammi ta ce tana hararar Baffa dubu hamsin ɗin ya bata ya ce "Ki bawa Burhan ya siyi takalmi" Burhan nata takaici yadda Ridayya ta suɓu ce masa ya gama kwaɗaituwa da surarta kuma no matter what happens sai ya same ta wallahi wannan al'ƙawarin zuciyarsa ne. Ammi ta shigo ta ce "Ya plan ɗin mu ya wargatse Burhan?" Yana cije baki ya ce "Yarinyar ce ta kwafsa, amma Maryam yarinyar akwai ehhhh kaya". "Sai nawa zan ce ka daina ce mini Maryam yayarka ce fa ni" "Ki dake kawai, yanzu mene abin yi ko na duƙo cikin dare ne?" Ammi ta ce "Ka rusa mini plan so na yi ka riba ce ta, ka yi mata fyaɗe Burhan a yau ɗin nan, mene matsalarka ga gado na nan ka ɗaki na nan ga kuma banɗaki, baka da lafiya ne?" Ya ce "Dake kwana biyu na ɗan kwanta dama ne sai a hankali baya going, amma yarinyar nan na zam da ita wallahi kin san albakar baƙar mace kenan" Ta ce "Mtwsss zan baka magani, ita kuma zan aike ta gidan Biba sai ka bita daga nan zan faɗawa Biba komai sai ka rutsa ta a can, idan ta samu ciki dole zan saka a yi muku aure ne ko ta ki ko ta so, ni kuma zan saka Baffa ya mallakawa Ridayya dukiyarsa kaga shikenan komai ya dawo wajan mu" Burhan ya ce "Ƙirittt kenan kema dai jar wuya ce Maryam kina kawo wuta daman ƴan matan duk sun gu je ni bani da ko sisi yanzu ciki nawa zan mata idan ta je gidan Biba?" "Wallahi Shaye-shaye ya fara haukatar da kai Burhan bari na duba idan ba kowa sai ka zo ka fita, Junaid daman baya gari su Khaliperh na wajan aiki duka, zan kira ka ga wannan" Ta ɗauki tablet ɗin da take bawa Baffa ta bawa Burhan. Daga nan ya bar gidan. Tunda ta shigo yake kallonta ganin sauyin da ta samu yanayin bugun zuciyarsa da yadda take fusga daga ƙirjinsa zuwa gare ta ya tabbatar Ustaza tana cikin matsala. "Ina yini Abbiey" Ta faɗa kan ta a ƙasa ganin ba haka suka saba gaisuwa ba ya zungure ta da ƙafa ta ɗago kan ta bayan ta share hawayen, hannu ya miƙa mata itama ta miƙa ɗan ƙaramin hannunta da yatsun suke zara-zara farare tas musabaha sukai ya ce "Kin yi sallar zhur ne?" Ta girgiza kai tana yin ƙasa da kan ta zuciyarta tsananta bugu take idan ta kalli Abbiey wani abu na yi mata kwance a zuciyar a hankali yana sakin hannun ya ce "Kar ki yi" "Me ya sa?" Ta faɗa da mamaki tana mai kallon gefen idanunsa don bata iya ganin cikinsu, da gaske ko da wasa hakan ya haramta wani kalar abu take ji idan idanunsa suka nutsa cikin nasa. "Kin fara Al'ada Ustaza dubi kayan ki, ok." da sauri ta duba rigarta jini ta gani kunya ta kama ta ta yi saurin sunkuyar da kanta. Ya girgiza kai yana riƙo haɓarta ya ce "Kunya Ustaza?" Ya girgiza kai ya ce "Shi ne abinda ba zan ɗauka ba, kina da wanda ya fini ne?" Ya sake ta yana miƙewa ya ce "Zo" Bayansa ta bi har zuwa wasu kayan data gani cikin wata sabuwar akwati ya buɗe ya dinga fito da kaya har ya ɗakko pant da pad fari ne wandon sai ladycare ya ɓare ya saita a saman wandon ya bata ya ce "Shiga toilet ki wanke jikinki sai ki using wannan ok" hanyar fita zuwa bedroom ɗinta ta nufa ya damƙo hannunta ya tura ta cikin toilet ɗinsa yana tsaye ta fito sai raɓe raɓe take. "I have been waiting for this day Ustaz ki kula, kina sauya kayan jikinki a kan lokaci, banda ƙazan ta ai kin san komai?" "E, Abbiey" Cike da kunya dukda ba wani nauyin shi ta ke ji sosai ganinsa take babanta kuma babarta kuma abokinta kuma ƙawarta kuma Bestfriend ɗinta. "Lecture ɗin ki gobe ne zai fara, ki kwanta yamma zan nuna miki wani waje" Ta yi sauri ta batsa kusa da shi ya mata tsayi sosai ta kama hannunsa ta ce "Na gode sosai Abbiey uba na gari farin cikina, Allah ya saka da alheri ya ƙara buɗi" Kallon ta yi sai ya jinjina kan shi. Da sauri kuma ya ce "Ki mini alfarma Ustazana kin zama babba ki nisanta kan ki daga maza please" Ta ce "In sha Allah, Abbiey me ya sa baka saka shadda kai ka saka bluetooth da irin kayan nan na ƴan gayu? Kullum hirami i doesn't like it" Ya haɗe fuska nan da nan ta shiga hankalinta bayan ya nuna mata sabbin kayan sallar da ya yi mata rabi duk abayas ne masu mugun tsada shoes backs atamfa lace kamar bashi da matsala haka ya zage ya yi mata siyaya daɗi ya ishe Ridayya ta faɗa jikinsa tana kuka "Thank You! Thank you!" Washegari da kansa ya kaita makarantar a sabuwar motarsa ta zamani, tun shigowar su Moo ya daki kafaɗar Meer ya ce "Hee look" Meer ya juya iya motar kawai ta ja hankalin Meer lallai wannan mai kuɗi ne. Nasiha sosai Ustaz ya yi mata kana ya ɗauki sabuwar waya da sim ya bata saboda karatu ta fita ya juya yabar makarantar. A hankali take tafiya saboda hijab ɗin da Ustaz ya ce ta saka jakarta a hannu sai yatsuna fuska take kan ta a ƙasa, yadda take tafiya zaka ɗauka yanga take da ƙibar ta da tsayin ta daidai wadaida. Kamar an ce ta ɗago kan ta idanunta ya nutsa cikin na shi yana tsaye yana kallonta hannunsa zube cikin aljihu, wata harɗaɗɗiyar shadda ce ya saka a jikinsa Amy color iya haɗuwa ya haɗu sai kashe mata ido yake yana ɗan rausayar da kansa gefe hakan ya ƙara masa kyau a idanun Ridayya ita kam kwalliyarsa na matuƙar burgeta. Jin numfashinta sai tsaya ya saka ta yi saurin sunkuya wa zata ɗauki jakarta data faɗi ƙasa gabaɗaya jikinta rawa yake kokawa take da zuciyarta wajan ganin bata sake kallon shi ba. Ta ɗauki jakar ɗaguwar da za ta yi ta ganshi tsaye a gabanta...... Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv Share Comment🌚🧚🏻‍♀️ *✿ MUNAFUKIN MIJI 20 ✿* Mikiya Writers Ass... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Nimcyluv Saurin ka baya ta yi jin numfashi da ƙamshin shi na sauka a fuskarta, ta kakkaɓe jakar tana juya idanunta, zuciyarta sai dokawa take saboda tsaiwar shi a wajan. "Most beautiful lady in the world, what pretty!" Da sauri Ridayya ta ɗago idanunta ba tare data shirya ba, jin kalaman da suka daki zuciyarta, wanda ba a taɓa danganta ta da su ba, ita da ake ce mata Zoo ko Kangaroo? _Most beautiful lady in the world?_ ta maimaita a zuciyarta Yana sakin murmushi mai taushi idanunsa a ciki ya ce "Yes you're, please ko sau ɗaya ki fito takara ta Miss Nigeria" Ya ƙare maganar yana kashe mata Idanu ɗaya, tare da gyara tsaiwar shi da kyau fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi wanda ya ƙirƙira bisa dole ya aza mata. Ridayya kasa magana ta yi domin ba ɗabi'arta ba ce musamman yadda rikicewar al'amarin da afkuwar shi ya wanzar da wani irin sabo abu daya gitta tare ɗar suwa a jaririyar zuciyar da bata san komai ba sai Abbiey. Haɗuwar wasu ƴan sakanni na shirin shafe alaƙar shekaru masu yawa da sanya almakashi ta ƙarfin tsiya wajan yanke alaƙa da zumunta mai cike da shaƙuwa soyayya da kulawa haɗi da al'ƙawarin zuciya kuma halastacciya. "Kar ki saka na dinga mafarkin waɗannan sexcy eyes ɗin, pretty" Meer a ransa ya ce "Kutumar uba, ji yarinya kamar irin gumakan Indian nan sai masifar girman kai" bai gama tunani ba ya tsinkayi muryarta cike da sangarta kamar mai shirin kuka ta ce. "Thank you" A ranta tana jinjina sabon kalaman cin mutumcin data ruska yau, tare da sanya ƙafa ta shure su nan take, babu inda ta ɗarsa zancen balle ya kwaɗaita mana wani abun. Gabaɗaya ta mayar da maganganun nasa amshin shata, tamkar kuma busar sarewar Audu haka muryarsa ke mata amo a kunne. Meer ya girgiza yana ɗaga shoulder ya ce "Wow! Gaskiya muryarki akwai daɗi ma sha Allah, new student?" "E, haka" Ta faɗa tana ƙoƙarin barin wajan domin da ƙyar take fusgar numfashi, ita kam hundred percent mutumin nan ya gama burgeta, his voice, his dress, the way he's talking, komai nasa daban ɗan gayu sosai da shi. Ya yi saurin shan gabanta ya ce "Uhm kuma za ki bar ni bayan ban ga ji da kallon wannan black beauty ɗin nan fa" Sai a lokacin ya ɗan kalli idanunsa a ranta tana mamakin yadda bata iya nutsa ganinta a ƙwayar idanun Abbiey amma yanzu kai tsaye take kallon cikin idanun Meer. Kamar za ta yi kuka tana rausayar da kai ta ce. "Don Allah kar ka ci mutuncin HALITTAR ALLAH, nasan tsananin munina ya sa kake cewa na zama Miss Nigeria, bani na halicci kai na ba, BAƘAR KALA da launin halitta na muni shi Ubangiji yaga ya cancanta dani, kuma na gode da ni'imar shi" "Subuhanallahi!" Cewar Meer yana sauya fuska tare da jujjuya kai daga hagu zuwa dama, daga kudu zuwa arewa, daga gabas zuwa yamma ya ce "Who told you cewa ke mummuna ce, yanzu na zubar masa da haƙura, keep a joke aside Black beauty ban taɓa ganin colour mai kyau da ɗaukan hankalin mutum nan take kamar na ki ba" "Uhm" Meer ya ce "Ban son Uhm ɗin nan, ina nufin abinda na faɗa i never lie to you" "Stop kidding me" _Ka daina tsona ta_ Ya girgiza kai yana ɗaga gira ya ce "Ko tsokar da kan ta, ta yi kaɗan ta tsoka ne ki" Murmushi kawai ta yi tana bin gefen shi zata shige ya bi bayanta, gabaɗaya Ridayya jin ta take wata uncomfortable duk duniya banda Abbiey ba wani namiji daya nuna mata kulawa ya faɗi kalaman masu daɗi a kan ta sai wannan mutumin da ko sunan shi bata kai ga sani ba. Ya sha gabanta idanunsa zube a kanta yana bin yadda jikinta ke motsa wa dukda ta saka hijab, da baya da baya yake tafiya ya lumshe idanu ya buɗe ya ce "Kuma ba ki tambayi sunana ba?" Nan ma ba ta yi magana ba ya sassauta murya cike da salo na yaudara wanda yake ƙara nutsar da zuciyar Ridayya na daga cikin abubuwan da suke burgeta da shi. "Iyee irin wannan jan a ji? Well is allowed sunana ZAMEER MAHBOOB DOLLAR" Ta dai yi murmushi kawai wanda ya tabbatar da ta ji sunan. Ya ɗaga kafaɗa duk biyun yana ƙara yin baya ya ce "Sunan ba daɗi ko? Ai shikenan bari na gudu tunda am not welcoming" Ya juya abinsa. Sai Ridayya ta ji duk ba daɗi tunda shi ne first person a maza daya fara nuna kulawa a gare ta, gashi yana da sauƙin kai da fara'a da kuma wasa bata kammala tunanin ba ta ji ya ce "Ok see you later RIDAYYA" ya faɗa yana nufar inda ya faka motar shi. Mamaki ya cika ta a ina ya san sunanta? Me ya sa kuma zai ta fi? Ko ba a makarantar yake ba? Sai ta ji gabaɗaya kamar ya tafi da ƴar nutsuwar data fara samu. Daman ta riga ta san a Department ɗin da zata ɗauki lecture yau ɗin kai tsaye ta nufa kan ta a ƙasa saboda kar wani ya ganta ya ƙara razana domin abinda Mahmud ya yi a kanta yana nan zaune a ranta bata manta ba. Tunda ta shiga cikin hall ɗin ake ta kallonta sai a tuntsire da dariya nan da nan idanunta ya cika da hawaye ta na jin wata na cewa "Ba za ki daina kallonta ba sai kin yi mafarki? Kila irin mayun dajin nan ne ko ƴan ruwa ai duk haka suke fa" "Wallahi Ilham mamakin yadda aka samu mutum bai wannan baƙin nake, kima ture munin baƙin ya yi over zan sauya wajan zama gaskiya wannan ai illa za ta yi wa mutum" Hankalin Ridayya ya tashi ainun wannan shi ne ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu. Yadda ake aibata halittar da Ubangiji ya yi mata ya sanya babu abinda ta fahimta har lecture ɗin ta zo ƙarshe, zaman ya gundure ta sai kuka take na zuciya wanda ya fi cin rai. Ta riga kowa tashi ta fita ta yi nisa sosai har ta zauna kan kujera ƙasan wata bishiyoyi tunanin rayuwarta da yadda babu farin ciki ko kaɗan a ciki ya shiga kai kawo a ranta, tun daga haihuwa a yadda aka bata labari, fitar mahaifiyarta zaman ta wajan stepmother ɗin ta wacce tasha azaba kala-kala wanda shiru da miskilancin Ridayya yana daga cikin ƙona ta da a ka yi a saman harshe, tsanar mahaifi rashin jan jiki da Mami ke nuna mata dukda lukuta da dama ana ce mata wai don ita ƴar'fari ce a ranta ta san ba haka bane. "So You are here?" Ta yi saurin ɗago kan ta domin ta gane muryar. Suna haɗa ido ya kashe mata nasa idon ɗaya tare da langwaɓar da kai gefe "Wai guduna kike yi? Yasin to ba ki isa ba don ni naga wajan zama" ganin idanunta sun sauya sun kumbura ya yi ƙasa da murya ya ce "Kuka? Kuka ki ka yi pretty?"Ta ce "A'a" "Kuka ne mana ya zaki ce a'a bayan ga gaskiya nan a kan fuskarki, waye ya saki kuka wlh sai ya ci ubansa" A sanyaye a yanayin muryarta na zan yi da shagwaɓa ta ce "Kai ne ke mini ciwo, thanks" Mamaki ya kashe Meer jin yadda ta ce wani _thanks_ a wulaƙance ya ce "Oh sorry, kin sha magani?" "Azumi" Ya ɗan shafa kai ya ce "Oops yhhh haka ne, sannu kyakkawa" Ta miƙe tana shirin tafiya ya miƙe shima ya ce "Kuma shi ne ba ki tambayi sunana ba, jan ajin ya yi yawa haka". "Ka faɗa mini ai" "Na ce miki me?" A sanyaye ta ce "Zameer" Ya lumshe idanunsa cike da gwaninta ta samarin zamanin yanzu ya ce "Oh my dear lord, za ki kashe ni da golden voice Ridha" ta yi shiru har sukai nisa cak ta tsaya ganin motar Abbiey jikinta na ɗan rawa sosai ta ce "Don Allah ka daina mini ga Abbiey na can zai ganni" Meer ya taɓa fuska yana laɓɓansa ya ce "Na je na gaida Abbiey na nemi ta barraki da albarka saboda watarana" Ta yi rau rau da Idanu wanda suka cika da hawaye ta ce "Faɗa zai yi mini fa, please ka tsaya nan" Ya ce "zan tsaya muga wayarki?" Kafin ta yi magana ya amshi wayar ya saka numbersa kana ya kira ashe har credit duk Ustaz ya saka mata bata sani ba, ya bata wayar ya ce "Matsoraciyya kawai, bye ki kula kar ki yi kuma ki taimaka mini" Bata kula shi ba ya zo daidai kunnenta ya ce "Take care of yourself for me, only me pretty" Ta runtse idanunta tana jin wani irin, ban bara kwai wai namiji da suna Hajara haka take ganin al'amarin Zameer lokaci guda ya yi zaune daram a zuciyarta ko iya haka ne ita kam ba zata mance da shi ba, ya faɗa mata kalamai masu daɗi a lokacin da take tsananin buƙatar hakan, dukda ko sau ɗaya bata taɓa jingina kan ta da wani namiji ba balle ta yi kwaɗayin rayuwar aure da shi, babu lissafin hakan a ranta. Burinta ta yi karatu ta yi achieving muradanta, ko sauya ɗaya ta samu kusanci da iyayenta su jata su rungume ko da basu kira ta da sunan ƴa cikakkiya wacce kwayayayen halittarsu ya samar da wanzuwar ta a duniya ba. Daga nan kuma ta jirayi lokacin da ruhinta zai koma ga mahaliccinta. Sauyin bugun zuciyarsa ya samu asali tun kusanto shi da ta yi, sannu a hankali zuciyarsa ke buɗewa wani abu na shiga tare da wanzuwa a zuciyarsa. Ƙoƙarin hana idanunsa abinda zuciyarsa le buƙata da muradin gani a kodayaushe, haƙar shi bata cimma ruwa ba, tsintar idanunsa ya yi kwance a kan ta. Ya zame idanunsa yana mai yin tasbihi har ta buɗe ƙofa ta shigo kan ta a ƙasa ta ce "Sannu da hanya Abbieyna na kaina" Bai yi magana ba ya tayar da motar suka fice a hankali kuma yake driving ɗin. "Ridayya" ta yi saurin cewa "Na'am Abbiey" "Kin tuna girman alƙawari Ustaza" ta kalli gefen fuskarsa yadda sumar sajan ya yi kwance yana ta kyalli sai duk ta ji ba daɗin ganin jallabiyya a jikinsa, da yadda ya naɗa hirami sai ta ɗauka kamar tsofa ne ya saka ko rashin waye na ohho. A hankali ta ce "Al'ƙawari Abbiey?" "Ustazana ke fa baushiya ce, na maimaita wa wasu magana kema, da gaske kema maimaici kike so shalale?" Ta girgiza kai ta ce "Ka yi haƙuri Abbiey ba zan karya ba" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya yana jin kamar ganganci ya yi a hankali ya ce "Mene al'ƙawarin?" "Ka ce University ba irin primary school bane ta sha bamban da secondary school na riƙe mutuncina, na yi maka alfarma zuwa sanda zan kammala karatun, na jingine batun samari har zuwa lokacin, zaka share mini tantama a wannan zaka bani mamaki zaka tabbatar da sauyin matsayin dana samu" Ya yi shiru yana hamdala a ransa ganin maganganun shi sun yi zaman tishin hadda a kanta jin ya yi burus ta ce "Mene matsayin Abbiey?" Ya juya sai a lokacin ya kalleta da kyau a hankali ya ɗauke Idanu kafin kamar an yi masa dole ya ce "Ba zan su furta su a yanzu ba Ustaz, kar ki tilasta mini faɗar hakan da gaske ba za ki ɗauka ba, bar lokaci" Bata sake magana ba, har suka je gida bayan ya yi parking shi ne ya fara fitowa ya matsa yana buɗe mata ƙofa tare da kallon ta, ta marairaice ce fuska cike da gajiya ta ce "Wassh Abbiey na, ka ɗauke ni na ga ji" Ya girgiza kai ta sake cewa "Ƙafana bayana cikina Abbiey ka taimaki ka ɗauke ni na ga ji" ya kame fuska da kyau yana gyara tsaiwa ya ce "Allah ya yafe miki Ustaza watarana haihuwa za ki fa, ki daina raki yanzu ai ba zan iya ɗau kar ki ba" "Yee na zama ƴar lukuta Abbiey ba zai iya ba" Ganin ya nufu ta ta yi saurin fitowa tana gudu ta ce "Yanzu sai ka ɗauke ni Abbiey" "Gudanawa kike? Goyaki zan daga nan har bedroom" Ta yi dariya tana jerawa da shi ta ce "Kuma na yi missing bayanka da gaske Abbieyna mai laushin nan" Girgiza kai kawai ya yi suna shiga ya nufi bedroom ɗinsa, ita ta fara zuwa ta gaida Umma da Baba ƙarami. Wanka ta yi tare sauya kaya, bata son ɗan kwali gabaɗaya ta ɗaure kanta har baya ta fito parlour taya Umma yin abin buɗe baki, lokacin ta samu Abbiey suna ɗan magana da Baba ƙarami a hankali kalli ɗaya ya yi mata tare da haɗe fuska da sauri ta juya ɗakko hirami Baba ƙarami yana kallon yadda Ustaz ke zare Idanu da haɗe fuska. Bata sake fitowa ba sai da aka yi buɗa baki ta sha kunun gyaɗa da ƙosai sai fruits komai take tunaninta yana kan Zameer yadda yake lumshe idanunsa sa zubin halittarsa da adon da yake musamman yadda yake murza shadda _Pretty_ sunan ya yi mata wani irin it was so special to her. Ƙarfe 12 Ustaz ya kira ta bitar karatun Alkur'ani sosai yake mamakin baiwar iliminta abu ne mai matuƙar wahala ka ji ta kuskure amma yawan ya mata tilawa har sau biyu gashi tunaninta ya kaɗai ta tabbas akwai abinda yake faruwa a rayuwar shalalensa. Har aka kammala azumi a B.u.k dai kullum suna tare da Zameer abinda ya bawa Mardiyya mamaki sosai, sai ta ce ta daina kula shi amma fur ta ƙi ita ba taga dalilin barin Zameer shi ne namiji na farko daya bata kulawa bayan Abbiey ya nuna mata itama mutum ce, ya bata lokacinsa ya nuna muninta is nothing tunda ba ita ta yi kanta ba, kuma shi colour ɗinta ya yi masa hundred percent. Aka sallame azumi akai sallah Mami ta dinga mamakin kaya masu tsadar gaske da Ridayya ke sawa domin ko Zainura albarka. A zaune a parlour Ridayya ta samu Mami tana mai yin ɗari-ɗari ta tsuguna ta ce "Mami Zainura ta ce kina kira na" Mami ta jinjina kai tare da zubawa Ridayya Idanu, da sauri kuma ta share hawayen daya zubo mata har za ta yi magana sai Ammi ta fito ganin haka ya sa Mami miƙewa ta ce "Zo mana" Abin ya bawa Ammi mamaki yau Fatima ke kiran Ridayya? Aikinta ya lalace kenan ko me? Ridayya ta bi bayan Mami har ɗaki ta tsaya bakin ƙofa. Ganin inda ta tsaya Mami ta ce "Shigo mana" Ridayya ta ƙarasa ta nuna mata leda ta ce "Ɗauki naki ne" haɗaɗɗan lace mai kyau da tsada blue and white ɗinkin riga da skirt "Gobe akwai taron family, ki saka" "Na gode Allah ya saka da alheri" Zainura ta ce "Wannan abayar ta yi miki kyau Ridayya" Ta ɗan murmusa ta ce "Bari na cire na ba ki, Abbiyena ya siya mini da yawa" Kan Mami a ƙasa ta ce "Rabu da ita, ki je kar Abbiey ɗin ya jiki shiru ya yi faɗa" Ta ce "Ai baya nan" Fuskar Mami a ɗaure ta ce "Na ce ki je ko?" Jikinta na rawa ta fita domin har ta fara farin cikin jin muryar Mahaifiyarta. Tana murna ta nunawa Ustaz kayan ya dinga kallon kayan ya ce "Mun godewa Mami" Taron familyn kowa ya bayyan har su Hajiya da mai ran ƙarfe, Zuhura da Balkisu kowa yana nan Alhji Mansur Rano da Baba ƙarami, sai yaran su. Ammi, da Mami. Farin ciki sosai a zuciyar Mami ganin Zainura da Ridayya cikin kaya iri ɗaya. A ka ci aka sha za a fara tattaunawa Baffa ya ce "Ke tashi kibar nan" Tasan bada kowa yake ba sai ita, ta miƙe hakan yasa Ustaz miƙewa Baffa ya ce "Ya zaka tashi?" "To bari na dawo na zauna, Ustaza jinin jikina ce, nima na yafe" Mami ta miƙe zata bar wajan Ammi ta ce "Fatima lafiya za ki tashi?" "Lafiyar kenan" "Ikon ko na yi miki laifi ne Fatima? Kwana biyu kamar gaba kike dani ma wallahi, me na yi miki? Bafa ni na sheganta miki yarinya ba, bani nakar zomon ba rataya aka bani" "Don Allah kin ishe ni Maryam, na ce miki wani abu? Rayuwa ce fa kowa ya tashi gina ramin mugunta sai ya gina daidai da shi gudun watarana" a zafafe Baffa ya ɗauke Mami da mari kafin ya sauke hannunsa ya sauke wa Ammi lafiyayyun maruka guda biyu tunda ba zata iya marin mijinta ba ta ce "Ki saurara mini, kin hana ni sukuni kin takura ni haba Maryam me na tsare miki ne? Me na yi miki don Allah kishi hauka ne?" "Ban taɓa ganin inda abin alheri ya zama sharri ba, ni kika mara Fatima duk ƙoƙari na wajan gina rayuwar Ridayya, kin watsar da ita ko kallo bata ishe ki ba" kuka sosai Ammi take na kissa hakan yasa Hajiya ta ji ba daɗi nan suka ɗorawa Mami laifi ba ta yi halacci ba ta riƙe mata jaririya har girma amma duk a banza ashe take gani. "Hajiya ki yi mini uzuri, babu inda uwa zata haifi ɗa kuma ta bar shi ya wulaƙanta, ku ke a gwada Ridayya cikakkiyar ƴar maye ce ƴar srup duk sanadin Maryam idan kuma hakan shine soyayya babu laifi" Tana faɗin ta fice rai ɓace haƙurinta ya je ƙarshe hakan kuma baya rasa nasaba da kukanta da ta kai wajan Ubangiji. Ustaz ya dinga kallon Ridayya yana jinjina kalmar shaye-shaye sai yanzu ya fara fahimta wasu lokacin da take masa magana ba kai ba kan gado yawan bacci ko idanunta biyu sai ta dinga lumshe Idanu. A fusace ya damƙi hannun Ridayya ta fara kuka Umma za ta yi magana Baba ƙarami ya dakatar da ita "Ba ruwanki bake kike masa tarbiyyarta ba, ki bar shi" Kuka take sosai tana "I am sorry Abbiey ka yafe mini don Allah.....," Hannu ya watsa mata a fuska a karo na farko a rayuwarsa idanunsa suka firfito waje fuskarsa ta yi jajur, masifar zafin hannu ne da shi hannu ya ɗaga zai ƙara zabga mata wani marin ya ji ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi a rikice daga nan kuma ta zube a ƙasa jikinta na rawa da ɓari tana cuccure wa waje guda. Ustaz ya lumshe idanunsa yana murza goshinsa sosai da kyau a hankali ya ce "I am sorry Ustaza...!" "Gayu an sanku ba a san makwantar ku ba, kaga samarin ƙauyen Nahutun Batsari Giɗaɗo ikon Allah" Zameer ya haɗe fuska ya ce "Wanne cin fuska ne haka Mujahid?" "Gaskiya dai, bani hakƙina" Zameer ya ciro gudar ɗari biyar ya bawa Mujahid ya ce "Mene wannan ai dubu uku zaka bani, kayan da ka yi opay sababbi ne ko mai shi bai saka ba wlh" "Sune dani" Mujahid ya ce "Tab, sunanka Zameer Mahboon Dollar fa? Kai da zaka bani dollar naga Naira, Naira ɗin ma ɗari biyar ba girman ka bene" tsaki Zameer ya ja ya fice daga wajan ya nufi makarantar allon domin yamma ne yana zuwa malam ya haɗa shi kula da almajirai yana fita ya tashi ya nufi gidan Mama ta dinga murna data gansa ta ce "Ɗana na kai na, kwana biyu na ji ka shiru na ɗauka ka koma ƙauyen naku?" "A'a" Ta ce "Wai wanne ƙauye ne?" Ya ce "Ni fa ina da wani deal bana son kina nunawa bake kika haifan ba, zan kawo wata gidan nan ki nuna gyara ake mana sabon gida shi ne muka dawo nan ki nuna yadda nake da nutsuwa hankali da dukiya" Ta ce "A nawa?" "Kin ji matsalarki ai, ana maganar yadda za a samu miliyan goma kuɗi zan ba ki sosai" "To shikenan" Kyakkawar mu'mala ke wanzuwa tsakanin Meer da Ridayya, ta daina ganin kyan Abbiey ta janye jikinta yanzu ganinsa take koma baya cikin maza bai iya wanka ba, gashi yanzu yana ɗan haɗe mata fuska sai dai tasan Abbiye mutum ne mai tsananin kwarjini, nutsuwa kamala da haiba kyakkawa ne shi mai tarin baiwar ilimin addini dana boko. Ita kam Zameer yana tsananin burgeta gashi a iya magana kullum suna maƙale a waya. Babban kuskure wanda da shi Zameer ya gina tarko yadda Ridayya ta fara furta masa kalmar Soyayya, ya shure kimar da Ubangiji ya yi mata na ɗiya mace ta nuna ƙaunar ta ga namijin da bama ɗigon soyayyar ce a ran shi ba. Sanda ta faɗa masa tana mai cewa "Ka taimaka mini an ce ba zan taɓa samun mijin aure ba, ni kuma hankalina ya kwanta da kai komai naka yana burgeni" Kasa magana ya yi, sai da ya kira Moo ya ce "Done, she said it, she said she love me wow!" Moo ya ce "Kana da sauran aiki" Ganin kiran ta ya saka ya ɗaga "Muna magana ka kashe" Ya ce "Ridayya dole na kashe na jima ina son ki amma sai naga tamkar hakan ba mai faruwa bane, kina da kyan da zamanki mata a gare ni zai an tona" "A'a wallahi zan aure ka, ka amince mini please, kai ne ma kafi ƙarfina duk gidanmu babu mai so na sai Abbiey da iyayensa Kullum Baffana ai ban tani yake....," Daɗin soyayya da shauƙi ya saka Ridayya kwasar komai na sirrin rayuwarta dana gidansu ta faɗawa Zameer ya ce "Ina son ki ni ma Baby pretty na" Ta ce "Na gode sosai da amsar ta yi na" A hankali ya tsuke bakinsa ta cikin speaker wayar ya ce "Mu'ahhh take this as my appreciation" Ta yi murmushi kiss ɗin har cikin zuciyarta ya ce "Wannan na waya ne kafin gobe ai haka ake soyayyar" WhatsApp suka koma ta ji ya ce "I love You Mrs Zameer, i so much love you Baby" "I love you too" Huci da fusgar wayar da aka yi ya saka Ridayya juyawa a ruɗe jikinsa taga yana rawa kamar ana kaɗa masa ganji gargasar jikinsa duk sun mimmiƙe a karo na farko taga sauyin yanayin idanun Abbiey ya yi jajur ta miƙe zata kwasa da gudu tako ɗaya ya yi ya damƙo ta "Don Allah Abbiey kar ka dake ni i am sorry please...," Kai kawai yake girgiza wa ya kasa magana ya damƙe hannayenta duka biyun cikin nasa, yadda jikinta ke ɓari haka nasa ke yi da ƙyar ya fusgi maganar "Soyayya? Wani kike cewa i love You Ustaza?" Ya Girgiza kai ya ce "Ba haka mukai dake ba, kin ƙarya al'ƙawari Ridayya ban shirya hakan a gare ki yanzu ba, karatu nake son ki yi ba Soyayya ba" Ta kasa magana ya sake matse hannunta yana jawo ta dab da shi muryarsa bata fita saboda rawar da take ya ce "Soyayya Ustaza? Mene laifina da za ki hukunta ni ta wannan hanyar?" "Aure nake so ba karatu ba Abbiey ka tausaya mini ina......," A bazata ya tsinkayi maganarta gane abinda take ƙoƙarin faɗa wanda faruwar hakan daidai yake da tarwasa zuciyarsa ya saki hannunta ya matsa kafaɗunta yana sake kusanta kan shi gare ta a fusge ya ce "Karatu nake so ki yi ba soyayya ba, idan soyayyar kike shi ma za ki iya, idan auren kike so ba gani ba? Ustaza idan auren kike so ba gani ba? Nine ya dace dake ni ne kuma zan aure ki..... As your wish as my own wish ga update ne🥹🧚🏻‍♀️ Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv *✿ MUNAFUKIN MIJI 21✿* Mikiya Writers Ass.... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Nimcyluv Ustaz ya kasa magana sai kafaɗun Ustaza daya sake matse wa yana jijjigata idanunsa har wani ruwa ke kwanciya a cikinsu. "Ustaza why? Ni na ce ba zan iya aurenki bane? Kar ki hukunta ni ta wannan hanyar Ustaza, na yafe miki ki janye maganar nan" Zuciyar Ridayya ce ta yi wani irin tsalle da ya tilasta mata rufe idanunta tare da ware su da kyau ta watsa a kan rikitacciyar fuskar ta Abbiey ɗin nata, bata san mene a idanunsa ba da yake mata shamaki wajan nutsa ganinta cikin nasa, ta kasa bisa dole ta janye idanunta na zubar da hawaye ta ce "Me kake nufi Abbiey, ban gane ba wa zaka aura? Wani laifi ka yi mini Abbiey?" Ustaz ya runtse idanunsa takaicin yadda maganin shaye-shayen nan ya dauɗar mata da kwakwalwa ke ƙuntata zuciyarsa a hankali ya ce "Kin gane mana Ustaza, bambancin ko wacce rana shigar ta da fitar ta, na ƙara kusanta ni dake, ki yi mini alfamar a bar maganar haka nan" "Ina son auren shi bana son karatun aure nake so nikam" ta faɗa hawaye na sake wanke mata fuska zuciyarta na yin ƙaura zuwa ga tunanin Zameer ɗinta. "Ok zan miki aure, zan haɗa ki da miji na gari Ridayya" Kuka take sosai ganin yadda Abbiey ya kasa fahimtar ba kowa take muradin aure ba sai mutum ɗaya wanda a duniyar Ridayya babu wanda ke burgeta sama da shi domin har yanzu bata san ma mene soyayya ba, ta ɗauki alhakin yadda take jin a kan shi da yadda komai nasa yake Unique matsayin SO. Bata da hankali da nutsuwar tsayawa ta gane bambancin dake tsakanin SO da BIRGEWA. "Shi ma na gari ne, wallahi Zameer na gari nikam shi zuciyata shi ta ke da muradi" A wannan karan wata tsawa Ustaz ya daka mata amma ko gezau ba ta yi ba, sai ma haɗe fuska da ta yi tana sake ci-gaba da kukanta. "Shin ni bani da Qualities ɗin zama miji na gari a wajanki Ustaza? Ki yi tunani shekaruna nawa, mene ya hanani kasancewa da wata ɗiya mace, just because _I love you_" Da sauri ya sake ta, jin yadda kalaman sukai futar da kan su tare da zama daram a kan shi bai shirya ba, bai san yadda akai ya saki abinda zuciyarsa ke danƙare da shi ba. "Kashe ni kawai Ridayya" Muhammad-Bilal Ustaz ya faɗa yana jin alamun zufa na yanko masa daga tsakiyar goshi zuwa bayan wuyansa, idanunsa na lumshe wa har wani dishi-dishi yake gani tare da wata yana-yana. Ta durƙushe ta ce "Wallahi ban taɓa mafarkin ganin kai na a matsayin matarka ba, kai ɗin uba ne, babu wani tarihi da zai zo ya sauya sunana daga matsayin Ridayya Muhammad-Bilal Rano, bana son ka Abbiey komanka baya burgeni kana da tarin bambanci da Zameer wallahi.....," "Ya isa! Allah yafe miki Ustaza nikam na yafe miki" Yana faɗin hakan ya juya da sauri ya fice daga cikin ɗakin. Rasa inda zai nufa ya yi, baya da wani da yake sharing damuwarsa da shi, baya son mutane sam mutane basa ɗaukar hankalinsa. Ya tsani ƙarya magana biyu cuta ha'inci uwa uba rainin hankali wannan dalilin yasa ya ware kansa. Yana shiga bedroom ɗinsa ya dinga safa da marwa zufa ta gama wanke shi tas hannunsa goye a bayansa maganganun Ridayya na amsa kan su da kan su a kunnensa. Da sauri ya fice daga ɗakin ya nufi bedroom ɗin Baba ƙarami domin Umma bata nan. Baba ƙarami na zaune saman laddumar dake shimfiɗe a carpet yana duba jarida. Idanu ya ji a jikinsa ganin daya bambanta dana ko wanne lokaci ya ɗago kai a hankali idanunsa ya sauka a kan na Muhammad-Bilal Ustaz. Rabon da yaga yanayin mai firgitar wa a tattare da Ustaz ya manta wannan shi ne karo na farko daya taɓa shiga irin wannan situation ɗin, tun yana ƙarami sai kuma yanzu. Kafin Baba ƙarami ya yi magana Ustaz ya ƙarasa ciki da sauri kuma ya kwanta yana ɗora kan shi a cinyarsa mahaifin nasa. "Subuhanallahi! Babban mutum lafiya kar ka rikitar dani da wannan yanayin mene ne? Ridayya ce babu lafiya mene ya same ta?" Domin a ransa yake jin babu wani abu da zai iya saka Ustaz shiga wannan halin sai Ridayya ko ciwon nata ne ya motsa? Mene ya samu Ridayya? "Babban mutum bar rufe ido faɗa mini ne kar ka yi give up da wurwuri kana da rayuwar muradan daya kama ta ka cimma" "Abba ka yi mini addu'a" Da ƙyar yake maganar saboda wani zazzafan zazzaɓi da ya cimma shi lokaci guda. Ya damƙe hannun Baba ƙarami ya ɗora a saitin zuciyarsa dake dokawa da matsanancin ƙarfi kamar zata fito ta ratso ta tsakiyar ƙirjinsa. Jijiyoyin kansa sai harba masa suke ciwon kan shi ya tashi nan da nan idanunsa ya fara rufewa. Jikin Baba ƙarami ya fara rawa ganin yadda jikin Ustaz ya saki ya ɗauki waya ya kira Baffa ya sanar da shi kana ya kira mahaifiyar Ustaz ya faɗa mata. Ustaz bai san yaushe ne ba, kuma san ya akai ba kukan da ya addaba masa yake shirin fasa masa kai shi ne ya saka shi buɗe idanu, tashin farko ya fahimci a gadon asibiti yake ga ruwa na bin jikinsa meke faruwa? "Sannu Babban mutum ya jikin?" Cewar Ammi ya haɗe fuska tamau yana shigar da idanunsa ciki, a hankali ya dinga bin mutanen ɗakin. Baffa na zaune a gefen Ustaz idanunsa sun faɗa sbd fargaba, sai Baba ƙarami da baya cewa komai, sai Umma da kuka take, sai Ammi, sai kuma Mami data rufe idanu tana jan carbi Zainura a gefenta sai Zuhura Balkisa. Sai kuma sauran mazan gidan ga Junaid ma. Mutum ɗaya ce babu wato Ridayya to me ma yake a asibiti mene ya samu Ustaza da babu ita? A nan ɗin. "Sannu Yaa Bilal" Ya kame fuska ya ce "Wai wani ne ya mutu ne da naga gabaɗayan ku?" "Wani ne dai yake jinya" Junaid ya bashi amsa Zuhura ta ce "Kenan bamu kyauta ba da muka damu da ciwonka kake ta haɗe fuska?" "Ban sa dake ba, daga ɗan yin ciwon kai na kwanta bacci sai na ganni a asibiti?" Junaid ya riƙe haba yana jinjina wulaƙancin Ustaz ya ce "Gafa ciwon kai nan mun gani, kama ce da ƙafar ka zo kwanan ka biyu a sume fa, wai mene ya same ka har haka" "Ubanka ne" Baffa dake kusa da Ustaz ya ce "Gani nan ina godiya kuma" Ya yi saurin rufe ido sai kuma ya sakko "Ina zaka?" "Ko second ba ƙara yi cikin asibitin nan ba" Kafin sun yi magana ya fice yana jira yana mai dafe kansa da ƙyar ya shiga napep ya yi gida ko kuɗi bai bawa mai napep ɗin ba ya nufi cikin gidan kai tsaye bedroom ɗin Ridayya. "Allah ya baka lafiya" Cewar mai napep ɗin yana jan a bar shi ya bar wajan. Domin tunaninsa zafin ciwo ne ya sa bai bashi hakƙinsa ba. Sautin kukanta ne ya fara sauka a kunensa ya shiga da sauri ya ganta kwance ta yi zuru daga ita sai body short ya zauna a gefen gadon dab da ita ya ce "Kuka Ustaza? Mene haka?" "Abbiey don Allah don Annabi ka tausaya ka aura mini Zameer wallahi ni bana son ka, ba ka yi mini matsayin miji ba" Maganar ta daki Ustaz jin kai tsaye yadda Ridayya ke jin gina kalmar rashin so a gare shi. Ya sunkuyar da kan shi sai kuma ya ɗago fuskarsa ba yabo ba fassala ya ce "Babu laifi, ki turo shi ina neman shi ok?" Nan da nan murmushi ya mamaye fuskarta tana ƙoƙarin shigewa jikinsa tare da yi masa godiya kamar yadda ta saba ya yi saurin miƙewa. "Na gode sosai Abbiey ubana maganin kukana thank you" Bai ce komai ba ya fice daga ɗakin sai ya ji kanon ta yi masa zafi sosai da sosai yana son samun kaɗai ta baya son a fahimci rauninsa ko kaɗan gashi gab yake da bayyana. Cikin farin ciki Ridayya ta kira Zameer lokacin yana kwance a ɗan ƙaramin shagon sa suke kwana su wajan goma, banda tsami da warin kayan Almajirai babu abinda shagon ke yi ga allo kala-kala da rubar bara ta almajirai. Wayarsa mai ƙirar Vivo ta fara ƙara ya duba yaga an saka "My target" Tsaki ya yi a fili domin baya son yadda take takura shi da kira sosai idan ya tuna target ɗinsa da plan ɗin da yake da shi a kan ta sai ya daure. "Hi baby" "Abbiey ya amince ya ce ka zo yana son ganinka" Zameer ya ɗan taɓe baki a fili kuma ya sauke wani irin numfashi ta cikin wayar murya can ƙasa ya ce "Wow har na fara hango kai na matsayin mijin My pretty babyna" Ta yi murmushin ta mai sauti ba tare da ta ce komai ba. Ya ce "Yanzu bana ƙasar Daddy ya aike ni zuwa Switzerland a nan zan haɗo miki lefe ma, kuma gidanmu ana ta gyara ne" Kai tsaye ya ce Switzerland ɗin ba tare da ya san wacce ƙasa ce ba, kawai da ya yi searching na best country in the world sai suka nuna masa Switzerland ɗin matsayin ƙasar da ta fi ko wacce shi ya sa ya faɗa mata. "Oh Allah ya dawo da kai lafiya" Ya ce "Cewa za ki Allah ya dawo mini da mijina lafiya, ki daina jin kunyata fa" Ta yi murmushi kan ta a ƙasa ta ce "To na ce" "Ridayya" "Na'am" Ya yi jim sai ya ce "Me ya sa mutane basu da uzuri ne? Suna manta Ubangiji ke yin halittar bawa a yadda ya so, bana jin daɗin yadda friends ɗina ke nuna mini wai bai dace na aure ki ba" A rikice ta ce "To saboda me?" Ya ce "Saboda yanayin halittarki wai muninki ya yi yawa, nikam cin uban shegu nake ai basu san daraja da alfanun baƙar mace ba wlh, kuma ina ce musu you're the first person da kika nuna kina so na kuma na yi supporting tare da accepted naki a yadda kike" Jikinta ya yi sanyi kar a raba ta da wanda take ganin tuni ya zama miji gare ta, tana tabbacin idan ta rasa Zameer to babu wani namiji da zai ƙara ce mata hello ko da wasa balle maganar soyayya tabbas ita ta fara cewa tana son Zameer kuma ya amince ba tare da san aibun hakan ba, ta shure duk wanda girma, daraja, baiwa, ni'ima da Ubangiji ya yi mata. A sanyaye ta ce "Don Allah ka riƙe ni amana ka zauna dani tsakani da Allah nasan ba zan taɓa yi maka laifi ba, kar ka ce ka fasa aure na, kar ka ce zaka rabu dani kar ka ce zaka sake ni bana son zaman gidanmu ko kaɗan wallahi.....," Sai ta fashe masa da kuka a ransa wani farin ciki ya ji ya samu weakness nata available a fili ya ce. "If you are never fallen madly in love, understand that God has done you a huge favour. Wallahi na masu na tabbatar dake matsayin matata kuma wannan Abbiey ɗin naki yana neman yi mana shamaki amma idan muka bi hanya ɗaya ba shi ba ko Baffa ba zai hana ba" Ridayya ta ce "Shi Baffa da mai damu dani ba ya ce ni ba ƴarsa ba ce kaga ai ba zai hana ba" Zameer ya ce "To kice ba ki da wani gata ma kar ki damu zan maye miki gurbin kowa da kowa kin ji? Za ki yi farin ciki sosai Mrs Zameer Mahboon Dollar" Ta yi murmushi ta ce "Na gode" Ya kashe murya ya ce "I love you so so much my wife matata, ki zo makaranta gobe da wuri ina son ganinki" "Ka ce baka ƙasar?" Ya yi saurin zare ido jin ya kwafsa ya ce "Ai soyayyarki ta motsa ta yi bake-bake a zuciya zan dawo da sassafe" Sallama sukai Ridayya na ji wata nutsuwa a ranta. Sama da sati Ridayya bata saka Ustaz a idanunta, hankalinta duk ya tashi gashi Zameer yana ta tambayar yaushe zai ga Abbiey ɗin a lokacin sai ta ji bata damu da wayar Meer ɗin ba tunda tana da tabbacin zai aure ta ɗin. Nufar part ɗin iyayenta ta yi ta kuma ci sa a duk suna nan dake weekend ne har da su Zahura suka dinga kallonta haka Mami Zainura ta ce "Yaya Ridayya" Ta juya ta kalli Zainura a tsawa ce Baffa ya ce "Lafiya kika faɗo mana gida?" "Aure nake so a yi mini Baffa" Maganar ta gigita kowa musamman Mami amma ta yi shiru hankalin Ammi ya tashi ganin plan ɗinta na aurawa Burhan Ridayya zai lalace "Aure wanne iri? Idan aure ne ki je ki yi magana da Babban mutum mana" In ji Balkisu domin ta jima da fahimtar tsananin son da Ustaz ke yi wa Ridayya ɗin ta ce "Na faɗa bai yarda ba, ni kuma aure za a mini bana son zaman gidan nan" "Tab amma wannan yarinyar ba ki da hankali, yaushe kika san soyayyar wanne mara hankalin ne zai aure ki kuma? Ya taɓa ganin fuskarki?" Ridayya ta ƙi kula Zuhura domin ta san ba ƙaunarta take ba. Junaid ya ce "Kuma kika kasa yi wa Yaa Bilal ɗin biyayya ki jira yi uzurin shi?" Ridayya ta ce "Bashi da wani uzuri fa, kamar yadda Yaya Zuhura ta ce babu mai iya aure na to yanzu na samu aure nake so" Baffa ya miƙe tsaye ya ce "Allahamdulillah ni na ji daɗi gwara na aurar dake na huta wallahi" Da sauri Ammi ta ce "Wannan ɗin zaka aurar? Me ta sani dangane da soyayya balle zaman aure wallahi ba za a aurar da ita ba ban shirya ba, ba kuma haka na tsara ba" Baffa ya ce "Zan aurar da ita sai dai idan yaron ne ya ce baya so ban kuma damu da dukkan wanda zata aura ba koda zai dinga taka ta a turmi ne" "Kar ka yi wa aurar baki Baffa ka sanya albarka" Baffa ya ce "Ki rawo mini yaron" Da sauri Ridayya ta kira number Zameer ya ce gashi nan zuwa. Gabaɗaya wanda suke wajan sai la'antar auren suke musamman Baffa da Ammi da Zuhura Mami bata cewa komai tunani take wanda ya sha bambam da nasu. A lokacin har Baba ƙarami yana wajan da Umma kowa ya hallara Zameer na zaune ya ci uwar shadda ta babbar riga ga ɗan makulin mota ga iphone a hannunsa. Balkisu sai kallonsa take ita da Mami haka kurum suka ji bai kwanta musu ba. "Kai ya sunanka? Waye ubanka a garin nan? Mene matakin karatunka?" Sai kuma Baffa ya sake cewa kodayake ban damu ba idan zaka aure ta ɗin dukda na yi mamaki. Zameer mamakin yadda ake ta wulaƙanta Ridayya a kan idanunsa a cikin gidansu ya kama shi ya ce "Sunana Zameer Mahboon Dollar, ina GRA dake Nassarawa da zama Daddyna bai fiya zaman ƙasar nan ba, na yi degree a Bayero University a nan na haɗu da Ridayya ƴarka, kuma ta kwanta mini kuna iya yin bincike domin ku tabbatar" Baffa ya ce "Ba wani bincike da za a yi, kawai ka turo a magabatanka sai a ɗaura aure ka ɗauki matarka" Zameer ya yi hamdala Baba ƙarami kallon Zameer ɗin yake shi da Mami da Balkisu harda Junaid. "Yanzu kenan ka yi degree aikin me kake?" A ransa ya ce "Zaman banza mana" A fili kuma ya ce "Ina Business a wajan ƙasar nan ina tafiyar da harkokin mahaifina" Da gaske ya yi degree domin ya dage yaga ya yi karatu domin ƙarya da shiga sabgar manya sai da ilimi kawai ya yi alƙawarin idan ba aikin Gwamnati bane da zai dinga ganin kansa a office mai A.c yana juyawa yana saka hannu a manyan files na harkar maƙudan kuɗaɗe to zai taɓa wani aiki saɓanin wannan ba. "Na baka ita" "Ban amince ba, sai mun yi bincike a kan ka" Da sauri Baffa ya kalli Baba ƙarami Ammi ma ta ce "Ban amince nima" Haka Balkisu. Nan da nan Ridayya ta fara kuka hankalinta ya tashi "Ka je zan kira ka ko?" Cewar Baba ƙarami. Kwana biyu tsakani Ridayya ta dinga neman Abbiey ɗin nata baya nan ta san shi kaɗai ne kawai zai ji tausayinta,number shi a kashe bedroom ɗinsa a rufe. Baba ƙarami ya dinga neman Ustaz shima domin abin ya zo saɓanin tunaninsa shin daman ba son Ridayya yake ba all this time?. Abinda basu sani ba Ustaz na gidan ya rufe kansa a ɗaki shi kaɗai sai rubutu yake a cikin diary ɗinsa cikin kwana biyu ya faɗa ga wani ciwon ƙirji komai ya dai na yi masa daɗi ya ƙara zama shiru-shiru Ridayya ta bashi mamaki ta gigita shi da kalamanta. Yau tunda ta je makarantar ba taga Zameer ba yanzu ne kuma suka shiga second semester. Mardiyya ta ce "Dole na kalle ki ban ɗauka haka kike ba, wallahi za ki yi ladama idan kika auri Zameer I'm telling you Ridayya" "Ki samun albarka kawai Mardiyya" Diyya ta ce "Ba kya tausayin Abbiey wallahi yana son ki duniya ma ta san haka" "Ki aure shi mana Mardiyya, ai ke kina jin tausayin shi ko?" Da mamaki Mardiyya ta ce "Haka kika ce? Ni fa aminiyarki ce idan ban faɗa miki gaskiya ba waye zai faɗa miki? Ki nutsu sosai ki gane dalilin daya saka kike son auren Zameer na tabbatar ba soyayya ba ce, kamar yadda shima ba son ki yake ba, soyayyar gaskiya tana wajan Abbiey" Ridayya ta miƙe ta ce "Mardiyya me kike nufi? Jallabiyya zan aura ko hirami ko carbi, ki auri Abbiey mana wallahi zan fi kowa murna idan na gan ku tare as husband and wife ni bana son shi ke kuma ya yi miki sai a haɗa bikinmu rana ɗaya ki zauna kullum ya dinga faɗa miki Asstagafirullah subuhanallahi ko kuma ya yafe miki" kalaman Ridayya kamar ka yi musu dariya amma gaskiya take faɗa. "So kina so ki ce he's not romantic? Jallabiyya baya burge ki ko? Kin san wani abu baki san su waye ustazai ba Ridayya lokaci ko na ce rana ɗaya idan ki kai soyayya da su wallahi sai kin hauka ce, su ɗin daban suke ba a banza ake kiran su da Ustazai ba sun karanta sun gani sun san mene soyayya da aure, ki rubuta ki ajjiye wallahi tallahi sai kin yi kuka akan Abbiey" "Kuka? Duk kukan da na yi a rayuwa? Bari ki ji Abbiey ba irin mutanen ne ba daban Allah ya yi mini Abbiey na, kuma da na ke cewa ki aure shi wasa nake miki shi ba zai yi aure ba ai faɗa mini, kuma uba ne a wajena har abada ba kuma yadda za a yi ya sauya mini ba zai taɓa barina na yi kuka kuma ni ma bana son damuwarsa, ni kawai bana son shi kuma shi ma bai taɓa cewa yana so ba idan kina tunanin na yi ba daidai ba don Allah watarana na ji labarin aurenku ke da shi" Tana faɗin hakan ta ɗauki jakarta ta bar wajan. Mardiyya ta bi Ridayya da kallo tunda suke yau ta taɓa jin Ridayya ɗin ta yi magana mai tsayi dukda faɗa take amma sanyi ne a muryarta sosai idanunta da maganganunta na ƙarshe sun nuna zallar kishin Abbiey. Idan ta fahimta SO shi Ridayya ta ke wa Abbiey, BURGEWAR da Zameer ke yi mata ya danna son take ganin kamar shi zuciyarta ke buƙata da yawan lokaci ganganci da mata ke yi kenan da zarar anga farin namiji yana murza shadda za a ɗauki soyayya a aza masa. Ridayya ta sake kiran number Ustaz cikin sa a ta shiga kuma aka ɗaga sai dai ba magana. Shirun Abbiey na taɓa zuciyarta ainun muryarta na rawa ta ce "Abbieyna don Allah kar ka yi fushi dani ka taimaka ka saka baki su Abba su amin na yi auren nan" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta ce "Baka da lafiya? Please kar ka yi ciwo ka taimaka mini" "Shalale just think about me, kar ki cutar dani please" "Abbiey wallahi bana son ka wallahi baka taɓa burgeni ba ka tausaya mini" Ba zata tantance yanayinsa ba sun jima kafin ya ce "Ki yi tunani iya yau, a yanzu ba ruwana Ustaza" Ya kashe wayar. Ta yi ta kuka ta dinga neman Zameer da ƙyar ta same shi cikin tawagar su. "Meer ga mayyarka can" In ji Moo ya ce "Wallahi duk ta daman gashi bana son Khairy ta fahimci da ita, kasan halinta amma yau zan kawo ƙarshen komai" Ta tsaya daga nesa da tunanin zai zo amma ya yi burus ya haɗe fuska ta ƙarasa kan ta a ƙasa ba wanda ta kuma sai shi ta ce "Ina son magana da kai" Suka matsa ya haɗe fuska ya ce "Ki rabu dani kawai tunda bakya tausayina ba ki damu dani ba, kina kallo za a rabani da ke" Ta girgiza kai ta ce "Ba zan bari ba" "Me za ki? Ai wannan Abbiey ɗin baya son farin cikin ki daya bari mun yi aure amma zan nemi wata kawai" Jikinta na rawa ta ce "A'a don Allah idan ka bar ni ba zan samu wani mijin ba" "Kina so na?" Ya tambaya idanunsa cikin nata, ita ma cikin idanunsa take kallo kamar yadda yake kallon nata. "Ina son ka" "Ki tabbatar mini da wannan son Ridayya ki bani dama mu raya yau, muddin na same ki yau babu wani abu da zai yi mana shamaki da aure, ki mallaka mini kan ki budurcinki yau ɗin nan idan ba haka ba kawai zan rabu da ke" "Kana nufin mu yi iskanci?" Ya ce "Oh C'mn auren ki zan yi so babu wani batun kalma mai kama da iskanci, amince mini shi zai tabbatar da kina so na za ki iya yin komai domin ni, kamar yadda ni ma zan iya ka kalli yadda na rame ki duba ko abinci bana ci saboda tunaninki, idan na bar ki ba za ki samu mijin aure ba" Ridayya ta fara tunani da gaske idan Zameer ya rabu da ita babu wani da zai zo mata da kalmar Soyayya balle aure, domin har yanzu kalaman Burhan yana zaune a zuciyarta. "Idan ban amince ba wata zaka aura?" Ya kashe ido yana kwantar da kai ya ce "Bisa dole, domin tun yanzu zan fahimci ba za ki iya sadaukar da abi domin ni ba, kuma ai daman haka ake soyayyar yanzu don dai ba ki taɓa yi ba, ni kam idan ba ki amince ba daga yau babu ni ba ke" "Na amince" Ta faɗa ba tare da tunanin komai ba. Zameer ya zage ya dinga mata kalamai masu daɗi da sanyaya zuciya ya tabbatar mata ita da shi mutukaraba takalmin kaza. Haka ya ɗauketa zuwa hotel ta na ji tana gani ya yi fatali da budurcinta ya mayar da ita cikakkiyar mace a waje tun kafin ta je gidansa, ba tare data sani ba duk abubuwan da suka wakana a lokacin Zameer yana yin vedion komai a wayarsa tun daga zuwansu hotel ɗin har sanda ya rabata da budurcinta.... Ku jira ni zuwa dare idan naga comment. Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv *✿ MUNAFUKIN MIJI 22 ✿* Mikiya Writers Ass..... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Nimcyluv Ya juya ya kalleta jin yadda take ta kuka, zuciyarsa fes ya samu miliyan goma a caca ta sanadin yarjejeniyar soyayya ta samu budurcin Ridayya. "Kukan na mene kuma? Bafa dole na yi miki ba" Kukan da bata san dalilin yin sa ba shi take a lokacin da ƙaddara ta yi fatali da dukkan wata kima da darajarta na ɗiya mace saboda ƊA NAMIJI, da soyayyar da bata tabbacin zahirin ta a cikin zuciyarta, ta wofintar da duk wata kulawa tarbiyar da Abbiey ya bata sun zama tarihi a yanzu. Shigowar Zameer cikin rayuwarta tsakanin wasu ƴan watanni ya rusa tarbiyyar shekara goma sha shida da watanni. "Haba Pretty idan kina kukan nan ina jin kamar ban dace da ki mallaka mini komai a matsayina na wanda kike so kuma kike shirin aure ba" Ta kasa magana sai sautin kukan dake tashi a hankali tana naɗe jikinta a bargo, haka kawai fargabar Abbiey ya san wannan abin mai shirin tarwatsa zuciya ya rusketa. Ta tsinkayi muryar Zameer dab da kunnenta yana kama hannunta da yanzu bashi da shamaki da shi ya ce "Look into my eyes Ridayya, na yi miki dole? Ita fa soyayyar zamani haka take kina so na yi believing da haka, kuma wannan abin daya faruwa babu komai sai ƙauna kin bani kyauta mai muhimmanci wacce ba zan mance da ita ba, zan dinga tunawa a kullum, kin bani budurcinki na ba ki nawa kinga 50/50 kenan ko?" "Idan har zaka aure ni shikenan hakan shi ne muradi na, i know nothing about the love.....," "Shi ya sa na fara nuna miki yadda soyayyar take yanzu ai, cikakken masoyi shi ne mai yin haka idan ban yarda da ke babu ta yadda za a yi na yi tarayya dake Ridayya" Ta jinjina kai a hankali ba tare da ta ce komai ba a hankali maganganun Zameer na yaudara ke ratsa zuciyarta ya ce "Ki yi wanka na yi dropping naki gida baby" Da ƙyar ta ja ƙafafuwanta tana rufe Idanu saboda tsananin azabar dake ratsa gaɓoɓin jikinta yana kai wa zuwa jijiyar dake sadar da yanayin mutum a kwakwalwa. Yana tsaye ya sauya kaya zuwa wani milk ɗin voyel mai manyan zane iya kyau da ɗaukar hankali Zameer ya yi, ya taje sumar kan da comb sai ɗaukar ido take komai nasa dabanne a idanun Ridayya ta yi tsaye tare da shagala da kallon shi. "Ya dai? Wannan kallon fa Mai so na?" Ta ɗauke idanu sanyaye ta ce "Ka iya kwalliya ko wanne kaya na yi maka kyau ina son yadda kake dressing" Ya ɗan taɓe fuska yana lumshe idanunsa can ya riƙe ƙugu ya ce "Oh hello na fahimci ke kalmar _I love you_ wahala yake miki ban taɓa ji kin ce Zameer i love You ba, sai dai a ce na yi kyau? To ki riƙe yabon nikam yau kalmar soyayya nake buƙata wajan ki" Cikin yanayin da ya zame mata ɗabi'a ma rashin son magana da sanyin jiki ta ce "To ai ban san me zan ce ba, Abbiey kawai nake iya cewa ina son shi" Ya watsa idanunsa cikin nata can ya ce "Say something different....," "Rayuwata" Ya juya da sauri jin sunan da ta ce ya dinga binta da wani irin kallo can ya saka hannu ya cira ta sama yana zagaye da ita ya ce "Oh wow gaskiya I'm lucky person, irin wannan suna haka say it again" "Rayuwata" "Mai sona" Ya faɗa yana kallon idanunta da suke a lumshe komai nata a nutse yake hatta muryarta golden voice Ubangiji ya bata, idanunta sexcy eyes ne irin nasu kyau da tsari shi sam har lokacin a gigice yake da lamarin Ubangiji, yadda take da muni daban yadda Allah ya sanya ni'ima da baiwa a jikinta daban, ya kasa mance irin tagoma shin lagwadar daɗin daya kwasa, sanda ya fara kai hannunsa zuwa jikinta ya girgiza the real definition na jin daɗi fata mai kyau ita ce Ridayya's skin bashi da ƙarfin qiwwar faɗar taushi da laushi fatar ta, ko'ina ya taɓa lutsum yake nutsa hannunsa babu rama ko misƙata zarratan a jikinta. Lafiyayyen diri mai ɗaukan hankalin namiji gata a sangarce take komai kuka Abbiey ya riga daya lalata Ridayya a ɓangaren shagwaɓa ko tari baya so da ƙaunar yaga tayi hakan bai rufe masa ido wajan tsawatar mata ba idan ta kuskure. Da ƙyar take jan ƙafar tana tafiya a hankali cikin ikon Allah ta shige bedroom ɗinta, tare da faɗawa kan gado ta kwanta idanunta lumshe, abinda ya faru tsakaninta da Zameer ba komai bane sai soyayya kuma zai tabbatar zata iya komai domin shi. Amma ta sha jin ana cewa cikar kima da darajar mace shi ne ta kai budurcinta gidan miji? Mene bambancin wacce ta bawa saurayi a waje da nufin nuna masa soyayya da wacce takai gidan miji? Ta mirgina wani irin zafi ƙafafuwanta ke mata wa zata faɗawa? Me zata saka ta daina jin zafin? Nan da nan zazzaɓi kuma ya rufe ta ta rufe jikinta sai rawar san yi take hawayen da bata da masaniyyar dalilin taruwar su suka shiga wanke mata fuska. A hankali ya turo ƙofar domin ya kasa jurewa idan wani zai faɗa masa zai iya yin kwana biyu a gidan bai ga Ustaza ba zai ce ƙarya ne, sai gashi ya shafe sati bai nutsa ta a idanunsa ba. Yadda ta rufe jikinta ya tabbatar masa akwai matsala a ƙarasa a nutse hannunsa a bayansa, kansa ko hirami babu duk ya hargitse gashi da yalwar suma kamar ita. Ya zauna gefen gadon ya jima kafin ya saka hannu ya janye bargon zuwa ƙasa ƴar body short ce a jikinta wacce ta sauya da ƙyar ya ɗan zame idanunsa daga kan cinyoyinta ya watsa saman fuskarta ta yi saurin rufe haka kurum kunyar Abbiey ɗin ya kamata sosai... "Tashi zaune" Nan da nan idanunta ya kawo ruwa ta ce "Abbiey ba zan iya ba" Ya yi jim sai kawai ya saka hannu ya ɗago ta zuwa jikin gadon ya kalleta idanunta a rufe yana damƙe hannayenta cikin nasa ya ce "Kalle ni Ustaza, kalli cikin Idanuna" "Ba zan iya ba, Abbiey wasu abu ne a cikin idanunka ina kalla sai tsigar jikina ya tashi na ji wani abu daban" Ta faɗa da iyakar gaskiyarta ya girgiza kai maganar ma azaba ce a tattare da shi ya yi miskilin murmushi bisa tilas a nutse ya ce "Kallon idanuna su ne zai ba ki damar mallakar wanda kike da buƙata a rayuwarki Ustaza, just look at into my eyes" Ta ɗago a hankali ta kalli idanunsa kamar yadda yake kallonta, kallon kallo ake tsakanin Ustaz da Ustaza, abubuwa da yawa yake ganowa cikin maganganun da idanunta suke, yayinda ita kuma ta kasa me nasa Idanun yake faɗa jikinta ne dai ya fara rawa bata ankara ba ta ji fuskarta cikin tafukan hannunsa ya ce "Ki tabbatar mini mafarki nake a yanzu Shalale" "Ba mafarki bane ba Abbiey ka taimaka ka yi mini abinda nake so idan kana so da gaske, ka faɗawa su Abba Zameer nake buƙata, Abbiey kalli sumar kan ka ba haka ta Zameer take ba, Abbiey kalli jallabiyyar jikinka shi kullum shadda yake sawa, yadi voyel masu kyau, nikam ka yi haƙuri" "Idan na amince shikenan?" Ta jinjina kai ya saki fuskarta yana yin baya idanunsa rufe tana ganin yadda ƙirjinsa ke ɗagawa jijiyar kansa duk a bayyane. "Na Amince Ustaza Allah ya sanya albarka ya ba ki farincikin da kike nema a can" "Na gode sosai na gode Abbiey best father in the world, i love You" Cikin kulawa ya ce "Ban san yaushe ne har kika zama haka ba, shigar ki University ko kafin nan? Babu tabbaci. Allahamdulillah farin ciki na ɗaya iya yina na ba ki tarbiyar da ya dace a bawa ɗiya mace kuma na yi alfahari da mutuncinki za ki shiga gidan miji, babu wani abun aibu da miji zai goranta miki Ustaza dukda cewa soyayyar gaskiya bata da wani dalili, nutsuwar hankali da samun sauƙin zuciyata yadda kika kula da darajar ki na mace, za ki gidan miji da budurcinki Ustaza na yi ma Ubangiji godiya. Kema na gode da riƙe kan ki da kikai" Ya miƙe ya nufi waje sai kuma ya tsaya cak "Ki sha magani, zan turo miki Zainura ta ba ki" "Abbiey baka taɓa mini haka ba, kai kake bani magani fa? Kake tsefe mini kai ka yanke mini farce ka wanke mini sumata. Abbiey kai ne kake zaɓa mini kayan sawa kake mini magana a hankali me ya sa yanzu Zainura?" "Ke kika zaɓa mana haka Ustaza" "I am sorry Abbiey" Ya juya tare da ficewa. Ustaz ya fahimtar da Baba ƙarami muhimmacin auren da Ridayya ke so, tunda ya fara magana kawai yake kallonsa kafin ya ce "Ok daman ba son ta kake ba?" "Abba Allah ya yafe maka akan wannan maganar, ni mahaifi ne" Wani kallon baka da hankali Baba ƙarami ya yi masa kafin ya ce "Ya yafe maka dai a kan ƙaryar da ka yi wacce baka taɓa yi ba, Ubangiji ka yafewa Muhammad-Bilal Tahir Rano" Ustaz ya yi shiru fuskar Baba ƙarami babu walwala a ciki ya ce "Babu laifi, na ji na kuma yarda baka son Ridayya a je a haka. Daman na zuba maka idanu ne da tunanin kana kiwo da kuma rainon matarka ne ashe wani kake wa, well is allowed ba zan zuba maka idanu haka ba shekara ɗaya ɗaya har shekaru arba'in kana gabana, yanzu ina buƙatar sarari da space ina son ganin jikoki burjik tunda kai ɗaya Allah ya bani, ka gaggautar fitar da matar aure Muhammad-Bilal tun muna mu biyu" "Gori Abba, haba babu kyau gori fa ina buƙatarka sosai a yanzu Abba ka ɗan tsahirta mini da maganar aure" Baba ƙarami ya zame kan Ustaz a kafaɗar shi ya ce "Ba wasa nake maka ba, idan baka fitar ma a lokacin zan nuna maka ni na haifeka kuma kana amsa sunan Muhammad-Bilal Tahir" "Allah ya bani iko" Ustaz ya ce yana kwanciya cinyar Baba ƙarami ya rufe idanunsa a yanzu iyayensa kawai yake buƙata hakan zai sanya ya ji sauƙin dake ransa. Ya tuna al'ƙawarin zuciyarsa duk macen data kalli tsaraicin shi babu shakka matarsa ce yanzu ya zai yi da Ustaza? Hankali tashe Ammi ta isa wajan bokanta ta tarar ya yi mushe ba wanda ya sani gabanta ya faɗi domin ya faɗa mata watanni bayan mutuwarsa ko shekara duk wani abu da ya yi mata zai zama tarihi. Ta je wajan Biba ta nema mata wani malamin aiki cikin gaggawa amma Biba bata ƙasar tana can saurarawa abinta. Wani abin mamaki kamar an rufe bakin jama'ar babu wanda ya tsaya bincike a kan Zameer da sanin waye shi, asalinsa dama iyayensa. Duk suna tsaye suna kallon Vedion Moo ya girgiza kai ya ce "Amma mene amfanin yin vedion please?" "evidence na amsar budurcin wacce ake ganin ba zan iya soyayya da ita ba" Moo ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ban ji daɗi ba, kuma har ka zo cikinmu kana nunawa? Yanzu tamkar tsirara haka muke ganinta innocent gril irin Ridayya ka wulaƙanta haka saboda kaga tana son ka? Ina da tabbacin itama bata san mene soyayyar ba tunda burinta kawai ka aureta" "Ai matsalar ta fara cewa tana son namiji kenan, ya yi amfani da rauninta sosai. You see that madly in love situation is actually a mental health condition wallahi tallahi, birkita ƴan mata yake sosai, Balle kuma idan ya ketara obsession it comes with anxiety,depression, delusion. When God wants to test you, he makes you fall madly in love with an emotionally unavailable GAYE, your own don finish. Wallahi tallahi ina tausayin mace a zamanin yanzu wajan yi soyayya zuciyar mace mai rauni ce, ko yanzu da rauninta ka amfani wajan cimma burinka" Zameer ya cije laɓɓansa ya ce "To Babana Shaba" Shaba ya ce "Idan na haifi ɗa irinka na tabbatar ban aikata abu mai kyau ba wallahi, Allah ya yi mini tsari Daddynka na Switzerland" Duk suka saki dariya Khalil ya ce "Muga vedion ko?" Zameer ya miƙa masa Khalil ya dinga danne danne a wayar ya shiga WhatsApp ya tura vedion ta number shi yana gama shiga ya saka delete for me yana murmushi ya ce "Oh" Ya miƙa masa wayar kana ya nufi bayan motarsa ya ɗakko ƙatuwar jaka a gabansu ya buɗe kuɗi masu jikin Zameer ya dinga ɓari ganin yawan kuɗaɗen kamar a mafarki ko sanda yake Nahutun Batsari ai bai taɓa ganin kuɗi haka ba, har su yi noma a girbe albarkar noman Khalil ya ce "Ga kuɗinka" Zameer ya amsa Khalil sai cije laɓɓansa yake suna tsaye kuma aka kira Zameer a kan an bashi auren Ridayya ya ture iyaye. "Auren ta za ka yi bayan ka gama nuna mana tsaraicin ta?" In ji Moo "E zan aure ta In sha Allah" Zameer tunda ya fahimci Ridayya nada wata kalar baiwa ta musamman wacce ba ko wacce ƴa mace Allah ke bawa ita ba, ya sanya a ransa zai aure ta, kuma zai yanke karatunta baya buƙata domin idan ta yi zurfi a karatu ilimin zai bashi matsala. Tunda Ustaz ya siyi komai da sunan Ridayya sannu a hankali zai dawo wajanta, kuma duk sanda iyayenta suka mutu Ridayya nada kaso mai girma daga ɓangaren babanta zuwa babarta, zata zama jarinsa ƙwarai da gaske. A cikin kuɗin ya cira aka kai kuɗin na gani ina so hadda sadaki, da Mijin Mama gidan iyayen gidansa da wasu mutane sune suka kai kuɗin Zameer bayan sun yi shiga ta alfarma wacce Zameer ya basu. Ba a tsaya lissafi da tambayar su waye su aka amshi kayan aka saka aure sati huɗu masu zuwa. A cikin sati aka kawo lefe na gani na faɗa masu a zabar kyau, Mami kallon komai take kuma ta ƙasa faɗawa ƴan'uwanta. Cikin satin bikin Ridayya ta samu Mami a ɗaki ta ce "Mami zan yi aure lokaci ɗaya ki saka mini albarka a rayuwarta ba ki ce komai dan gane da auren ba, mijin ya yi ko bai yi ba ki faɗa mini komai ba" "Allah ya sanya albarka" Shi ne abinda Mami ta ce tana ɗauke kai. "Contractions Yaya Ridayya" Zainura ta faɗa tana murmushi jinjina kai kawai Ridayya ta yi ta miƙe ta nufi bedroom inda Mardiyya take. Ita dai ta san banda darajar Abbiey da bata auri Zameer ba tabbas shi ne ya sama mata wannan farin cikin. "Amarsu ta ango su Ridayya za a san kan duniya, dole Zameer ya yi farin ciki da tarbiyar Abbiey ya kare masa mutuncin matar daya aura" "Uhm" Kawai Ridayya ta ce har yanzu ta kasa faɗawa kowa abinda ya faru Mardiyya ta miƙe ta ce "Bari naje tunda ba wani event sai ɗaurin aure ko? Allah ya sa albarka" Tana fita suka kusa cin karo da Ustaz wanda ya fito riƙe da trolley ta yi saurin ja baya ganin hannunta ya shafi nasa ya haɗe fuska sosai yana yarfe hannu ta ce "Ka yi haƙuri Abbiey ban gani ba" Bai kula ta ba ta ce "Tafiya za ka yi? Ba zaka tsaya ɗaurin auren Ridayya ɗin ba?" Bai kulata ba ta ce "Bari na faɗa mata za ka tafi" Hannu ya saka ya figo gefen hijabinta ya kafe ta da Idanu hasken fatar jikinta yana damun idanunsa ta masa haske da yawa da yatsa ya saita mata hanyar waje ta yi saurin ficewa daga cikin gidan. Ustaz ji ya yi ciwo na neman kwantar da shi domin ko tsaiwa ya gagare shi hakan ya sa zai bar Kanon bakiɗaya. Ana saura kwana ɗaya ɗaurin auren Anuty Kaltum ta diro gidan ita da Yaya A'isha faɗa suke kamar za su daki Mami sai kuka take ranar an yi tashin hankali a gidan Alhji Mansur Rano ya ce idan har yarinya ta shi ce babu abinda zai hana a ɗaura mata aure gobe. Ya shiga ɗaki ya fito da tulin files ya damƙawa Ridayya ya ce "Riƙe nan wannan kyautar da na yi miki ce" Yana faɗin hakan ya juya gaban Ammi ya faɗin ganin takardun abubuwan daya mallaka ya saka hannu tare da mallakawa Ridayya su ta bisa da sauri ta ce "Baffa ban gane ba, kasan me ka yi kowa?" "Kina da tarihin ban taɓa yin hauka ba ko Maryam? Abubuwan dana mallaka na raba gida uku na bawa Ridayya biyu ya riƙe ɗaya shi ne mana" "Ita kaɗai ce ƴa?" Ya ce "A'a, kawai haka nan na ji ita zan bawa" Za ta yi magana ya daka mata tsawa ya ce "Maryam fice mini a ɗaki kar ki ƙara mini ciwon kan da ban san dalilinsa na addabata ba shekara da shekaru" Ta fice a zuciya. Anuty Kaltum da Yaya A'isha har Mami suka dinga mamakin abinda Baffa ɗin ya yi a yanzu. Washegari aka ɗaura auren Ridayya Muhammad-Bilal Rano da Zameer Mahboon Dollar auren da babu gata a cikinsa tunda babu Ustaz. Anuty Kaltum ta yi mata furnitures ƴan waje masu tsada haka Baffa da kayan kitchen an narka dukiya gashi kayan lefen ba abinda aka taɓa Ustaz ya bawa Umma komai da komai wanda Ridayya ɗin zata saka har kuɗin furnitures ma ya bata Baffa ne ya ce Umma ta bar shi duk abinda uba ya dace ya yi Ustaz ya ma Ridayya kafin ya tafi ta wajan Umma. Aka kai kaya cikin wani dakakken gida tare da amarya sai santin gidan ake gwanin sha'awa iyakar haɗuwa ya haɗu. Mardiyya tare da amaryar sai Zainura a haka Zameer ya shigo shi ɗaya bayan sun gaisa ya ce "Ikon Allah har jere akai na manta ban faɗa musu ƙasar zamu bari ba yanzu haka" "Ƙasar kuma?" Ya ce "E, a can zamu raya daren farko haka na tsara wa rayuwarmu ni da Mai sona" Mardiyya ta jinjina kalmar _Mai sona_ "Zan saka a kwashe kayan a kai ajjiya wani gidan idan mun dawo sai a dawo dasu yanzu haka a airport zaman jiranmu" Mardiyya ta miƙe tsaye ta ce "Za mu yi rakiya kenan?" "No please hakan ma mun gode sosai" Ta kama hannun Zainura suka bar gidan Zameer ya sa aka kwashe kayan zuwa can wata unguwa wani ɗan ƙaramin gida aka jera kayan kitchen ɗin aka ƙulle. Ita da aka ce za a tafi airport sai ta gansu a wani gida ta dinga kallon gidan tana kallon Zameer ya haɗe fuska ya ce "Zan fara jarraba imaninki za ki iya rayuwa dani a duk yadda nake ko a'a shi ya sa na kawo ki nan idan kin cinye jarrabawa sai mu bar ƙasar" "Idan har kana tare dani ai bani da wata matsala" Ta faɗa murmushi tana shiga gidan ta tarar da wata budurwa fara tas da ita sai danna waya take ya ce "Yawwa ƙanwata ce sunanta Khairiyya ana ce mata Khairy zata ɗan zauna damu" "Sannu?" Cewar Ridayya Khairy ta ce "Sannu amarya zance ko bazawara ko budurbazar" Ridayya ta kalli Zameer ya kashe mata ido ɗaya ya ce "Tana da wasa sosai don mind her" Cikin dare Zameer ya matsa gefe ɗaya yana tsaki sosai ta ce "Lafiya?" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Amma dai bakya kula wasu samarin don tsoro ya kamani yadda kika bani budurcinki suma za ki iya basu" Ta dinga kallonsa nan da nan idanunta ya cika da hawaye ta ce "Shiyasa ka matsa daga kusa dani?" "To uban me zan yi idan ban matsa tunda ba wani ɗokin ki nake ba, abu ne ya yadda jiki an bani tun a waje yanzu bani da ra'ayi na riga na san shi, ai ba wani saura kin bani budurci tun waje" "Me kake nufi?" A ɗan fusace ya ce "Ina nufin na gode mana, Allah ya sa ya tsaya iya ni kuma" Bata ce komai ba, a daren ta yi kuka mai isarta ya ce kuma ya na da vedion abinda sukai ta yi a hankali. Cikin dare aka hauro tare da kwashe kayan lefen tas abu ɗaya ba a bari ba Ridayya ta dinga kuka, Zameer ya jata a jiki ya ce "Suna wahalallu ai talaka haka yake al'amarin shi akwai mugunta, zan mu je ƙasar waje ki zaɓi komai ta ɗauka ƙaddara ce" bayan ta kwanta ya ɗauki waya ana ɗagawa ya ce "Na gode da aron kayan lefe na gode sosai ka duba da kyau babu abinda aka taɓa" Ya kashe wayar. Gari na wayewa babu abinci ya baza wanka tare da yin waje daman ta zo da kuɗi ta yi cefa ne ta aza wuta idanunta sai hawaye yake sosai. A cikin watanni biyu bayan auren Ridayya aka dawo da Ustaz gida rai a hannun Allah ciwon yau daban na gobe daban ya yi jinya zuciya data jiki kamar zai mutu hankalin family ya tashi aka faɗawa Ridayya Zameer ya ce ai basa ƙasar sai dai idan sun dawo. Ya yi haka ne domin baya so ya san halin da Ridayya ke ciki da gidan da take. Ta kira Ustaz a waya a ɓoye ta yi masa sannu bai iya magana ba kawai ya kashe wayar nan take ya tura mata kuɗi a Account ɗinta naira dubu ɗari. Bishasha ta samu Zameer sai da yaga bayan kuɗin. Komai ta samu Zameer gani take tana kuskurewa zai saki vedion ta ga al'umma ya ɓata career ta. Ya kwashe kayanta ya siyar wai sabbin zai kawo mata ashe caca ya shiga da su bata sani ba, ganin hakan wahala ya yi mata yawa ta kira Mardiyya ta ce sun dawo sanda Mardiyya taga Ridayya hankalinta ya tashi amma basu ƙare lafiya, Mardiyya ta kwashe ta faɗawa su Ammi akai faɗa sosai Ridayya ta murje idanu ta ce babu abinda mijinta ke mata kuma. Ustaz bai ce komai ba domin ya jima da sanin inda Ridayya take rayuwa kawai ya zuba Idanu kuma shi ne dalilin daya saka yake tura mata kuɗi duk wata. A haka ta fara yin ƴar'tsala suka saba da Zainaba kullum ta yi zata bawa Zameer da Khairy. Lokaci ɗaya ta rame duk ƙibar nan ta zabge saboda wanki da gugar Zameer har ciwon baya ta fara, ba ci ba sha babu suttura sai dai idan buƙatar shi idan ta tashi ya neme ce a haukace haka zai faɗa mata tamkar dabba, bayan ya gama ya magance ta da kalamai masu daɗin gaske da nuna ita ce mace ɗaya tamkar da dubu duk wannan abun bai taɓa haɗa baki da ita a cewar shi wannan zuntumemen leɓen babu uwar da zai tsinana dai wari. Kwanci tashi ta samu ciki a lokacin kuma duk abinda ƴan'uwanta suka faɗa dangane da Zameer zai ta kwashe ta faɗa masa, hakan yasa Zameer ya haba uban kowa zuwa gidansa hatta Yaya Balkisu zuwanta biyu Zuhura sau ɗaya a lokacin Ridayya ta hana su shiga cikin uwar ɗakinta. Takaici ya saka Anuty Kaltum da Yaya A'isha ƙin waiwayar Ridayya kefe ɗaya kuma Ammi bata da burin daya shige taga auren Ridayya ta mutu ta haɗa ta da Burhan saboda kadarorin da suke wajanta. Zameer na ya san da kadarorin amma bai taɓa sanin inda ta ajjiye ba idan ya tambaya sai ta ce suna nan. A lokacin Baffa baya zama sosai kullum cikin tunani Ridayya yake kuma ya sakko akan Mami ita ko kallo bai ishe ta. Huɗuba sosai Zameer ya yi mata a kan ƴan'uwanta ya ce ko gidan basa barinsa shiga wai shi talaka bayan karayar arziƙi iyayensa suka samu. Har cikinta ya tsofa bata taɓa zuwa asibiti ga rashin abinci ta kwana da yunwa ta yini da ita ko abincin ta samu sai ta bawa Zameer wani lokacin kuma tana kallon sai su kwana ɗaki ɗaya da Khairy ta yi magana ya ce ai ƙanwarsa bai zarge ta ba sai shi zata zarga? Ta kira Mardiyya a waya a lokacin shi ne suka faɗa kaca-kaca a kan ta ce namiji ba ɗan goyo bane musamman Zameer kuma Khairy ba ƙanwarsa bace farkar shi ce ta ce babu ita ba Mardiyya har abada, a ranar ne kuma da daddare ta samu Zameer a ɗaki shi da Ridayya turmi da taɓarya har ta nemi kashe kanta da fiya-fiya WANNAN KENAN. BACK TO STORY Kuka sosai Zainaba ke yi haka Ridayya, Usman mijin Zainaba ya rushe da kuka har da face majina aka rasa wanda zai rarrashi wani da ƙyar Ridayya ta ce "Duk abinda kuke faɗa na sani bani da wani option wanda ya shige watsar da maganganunku na riga na bawa Zameer mutuncina, kuma a duk sanda na yi yunƙurin rabuwa da shi ya ce zai saki vedion a duniya" "Tsinanne matsiyaci ce *MUNAFUKIN MIJI* wutar Allah ta ci shi" Ridayya ta goge idanunta ta ce "Amma wallahi tallahi sai ya sake ni na koma wajan Abbieyna, ko da zai saki vedion zinar da mukai ne....... Share and share please Ina godiya da comment da goyan baya masu zagen Ridayya ku yi mata uzuri please Allah ya yafe mata. Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv *✿ MUNAFUKIN MIJI 23 ✿* Mikiya Writers Ass.... BRIGHT PENS🤙🏼 free batch Nimcyluv "Yanzu kina nufin Ustaz bai san kin watsar da tarbiyar da ya yi miki ba, ba shi da labarin kin bawa saurayi budurci tun a waje saboda soyayya da ganin idan ba ki ba shi ba zai aure ki ba?" Ridayya ta kasa magana sai wani irin ajjiyar zuciya da take saukewa, a kawo biyar na damuwa da ƙuncin data wanzu da shi tun haɗuwar ta da Zameer yau babu kaso ɗaya. Zainaba ta girgiza kai kawai har yanzu kuka take ita har yanzu tana ɗorawa Ridayya laifi, dukda cewa rayuwa da ƙaddara suna tafiya daidai ne kamar shaƙar numfashi ne da bugun zuciya. "Wallahi ji nake kamar na ja ki ka zaune na yi miki mahaukaciya dukan kawo wuƙa, to kar na ƙarasa gawar da bata wa ba, amma Ridayya ba ki wa kan ki da Ustaz adalci, ba ki wa zuciyoyinku halacci ba, ina da tabbacin duk sanda Ustaz ya yi baki babu shakka sai ya biki, ya yi miki abinda uba da uwa ba su yi ba, ya raine ki da tafukan hannunsa, ya ciyar dake daga dukiyarsa, ya ba ki ilimi daga baiwarsa, ya ba ki tarbiyya daga cikin abinda ya sani, ya nemi aiki domin ya kula da rayuwarki. Ya yi miki wanka, ya yi miki tsifa ya gyara wannan sumar kan naki mai kama da bishiya, ya goya ki kin zama tamkar bakwaini amma haka zai yi amfani da ɗumin jikinsa domin ki ji shi tamkar cikin uwa mahaifiya, kin yi babban zunubi Ridayya. Da na san abinda kikai masa kenan wallahi tallahi ba zan barshi ya kai ki asibiti gwara kawai ki mutu ya yi jinyar zuciya da kuma mantawa dake bakiɗaya" Shassheƙar kukan da sai yau ta samu damar yin mai isarta ta ci-gaba da yi tasan ba kowa zai yi mata uzuri ba, ba kowa zai fahimci dalilinta ba. Zainaba ta ja tsaki tana zabga mata harara ta ce "Wallahi hannuna rawa yake ki daina wannan kukan banzan ko ka kwasa miki mari mtwsss" Ta girgiza kai ta ce "Samarin yanzu? Wannan gantalalliyar soyayyar da kalaman da mazan zamani ke amfani da shi haka yake ruɗa ƴan'mata fa, musamman a ga namiji fari tas da shi yana saka suttura a tsayar da gemun da wani mai yake shafawa na bana Allah da Annabi bane, da kalaman ƙarya na bugi da zarar ya samu nasarar a kan mace kuma shikenan fa, wata mara kan gadon ma ki na da saurayi amma ba ki san tuni an yi masa baiko da wata ma. Uhm! Soyayya har haukata ɗiya mace na yi tafi talauci barazana ga rayuwar yara mata......," "Ai ita ma a haukace take, ta haukace a lokacin" Usman mijin Zainaba ya katse maganar matarsa ta hanyar ɗaga labulen ɗakin ya zuro kai yana faɗa tare da face majina. "Kai fa Baban Hajjo ba zan taɓa yi wa Ridayya uzuri ba, Allah ɗaya kawai za ta ce mini na yarda. Ka yi tunani idan har Ustaz ya ji labarin abinda ta aikata na yin iskanci da wani ya sai tsinci kan shi? Tsaf zuciyarsa zata buga kwarankwasa" Ras! Zuciyar Ridayya ta bada sauti ita koda wasa bata taɓa zama ta yi tunanin abinda hakan zai haifar wa Abbiey ba, bata taɓa tunanin kuskure ta aikata ba domin a lokacin mahaukaciya ce ita, ta samu makantar zuciya data kunne aure, soyayya, da Zameer ɗin sune kawai a idanunta. "Don Allah mu bar maganar nan Maman Hajjo, ki ɗauka ban taɓa faɗa miki ba, don girman Allah kar ki kalle ni da wannan sigar" "Wannan zunubi kike faɗa kina wasa ne don ba ki san yadda nake jin zuciyata ba, uwa ce ni fa? Wallahi ina miki kallon wacce ta wofintar da kan ta a waje tamkar tsirara haka kike a idanuna" Wani abu ya caki zuciyar Ridayya ta runtse idanunta zuciyarta na yi mata zafi da raɗaɗi na maganganun Zainaba ta san kuma ba ita kaɗai ba duk wanda ya yi da kalar maganar da zai jefe ta da ita take, ta yi kuka har ta gaji a ranta tana karkarta tubalin ginin ƙaddararta da Ahlinta. Da ƙyar ta miƙe ta yi sallar asuba domin daman ba bacci ta yi ba. Zainaba ta lallaɓa ta tare da cewa ta yi wanka da ƙyar da ta yi domin ita yanzu tana jin bata wata wani saura banda jiran ranar da mutuwarta zata rusketa. Bata tsaya ta ci abincin da Zainaba ta bata ba ta lallaɓa tare da ficewa daga cikin gidan. Tunda ta fara take tafiya ta ji faɗuwar gaba na tsananta a ƙirjinta, ta dinga addu'a tana jin komai ya kusa zuwa ƙarshen ta kusa isa gida babu mamaki ma ta tarar da Abbiey yana ciki. Ta faɗaɗa murmushinta ganin gate ɗin gidan abu tare da ƙara tafiyar da take zaton sauri take har ta shiga cikin gate ɗin lokacin Maigadi yana cikin ɗan ƙaramin ɗakinsa. Ridayya ta wanzu tana tunanin ina zata fara zuwa wajan Mami? A hankali ta girgiza kai ta nufi ɓangaren Baba ƙarami kai tsaye bedroom ɗin Ustaz ta nufa da siririyar muryarta tana faɗin. "Abbiey.... Abbiey.... Abbieyna" Babu magana sai tashin kiɗa dake tashi a hankali, direction ɗin da ta ji sautin kiɗan ta bi da kallo a tsaye ta gan shi gaban madubi ya zage yana taje gemu da mataji farar fatarsa ta sauya sosai daga yadda ta santa a baya ta sake yin fresh. There is a difference between her previous Abbiey and this Abbiey. Domin wannan riga Armless ce a jikinsa ta kama shi, ga gajeren wandon dake jikinsa, idan ya yi tazar sai ya fara goge tsakiyar goshinta kamar Abbiey. "Abbiey ina ta magana" Ta faɗa tana matsa wa inda yake tsaye amma har lokacin bai juyo ba, da alama bata san yana yi ba ta buɗe iyakar muryarta ta ce "ABBIEY!" A hargitse ya juyo yana gwalo Idanu waje saboda tsoro, ta ƙwalla ƙara saboda razana ta yi baya jikinta sai rawa yake tamkar mazari daman ba wani ƙwari ne ita ba. Ya riƙe ƙugu daman tun safe ransa a ɓace yake ya kalleta sosai ya ce "Lallai ji mini wata tsohuwar kilaki da alama kece iyar da aka ce za a kawo ƴar'aiki sabuwa ko?" Ridayya ta saki baki Iya? Ta maimaita kalmar a zuciyarta kenan burin Zameer ya cika bai barta da komai na ɗiya mace kuma budurwa ba? Ya tatse komai na albarkar jikinta har ta yi kama da tsohuwar da za a cewa Iya? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!. "Wait wai mene ya kawo ki bedroom ɗina? Na faɗawa Alhji ban buƙatar maid duk ƙazamai ne kamar ke ɗin nan" "Ina Abbieyna?" Ridayya ta faɗa muryarta na rawa sosai. Ya sake riƙe ƙugu ya ce "Ji rainin wayo waye kuma Abbiey ki shigo har gidan uban cikin ɗakina ki kuma tsare ni da wani ido kina tambayar wani? How dare you?" Ridayya dai kallon yadda yake zuba masifa hankali kwance take shi kaɗai duk ya hargitsa kan shi. Da sauri wata ta shigo ɗakin Matashiyar mata mai zubin haƙuri da nagarta ta ce "Lafiya meke faruwa ne tun daga parlour na jiyo wannan muryar taka kullum cikin faɗa baka gajiya kamar Dage?" Ya ɗage gira ɗaya cur kuma ta tsaya dake cikakkiya ce ya ce. "How can i know mother? Kawai ta shigo ɗakina wai ina Abbiey nata? Na bi Abbiey da gudu ba wando wai banda lalacewa maid ce zata shigo kai tsaye ɗakina without my knowledge?" Wacce aka kira da mother ɗin ta kalli Ridayya tun daga ƙasa har zuwa sama take kallonta kafin ta girgiza kai ta ce. "Zafin rai Sadauki? Ka dinga yayyafawa zuciyarka ruwa kana shan ruwan alwalar sallar asar" Sadauki ya dafe kansa ya ce "Kawai ta faɗa miki wace ita duniyar nan babu gaskiya mother" "Wacece ke wa kuma kike nema ƴar nan?" Sadauki ya yi caraf ya ce "Wacce ƴar? Tsohuwa ce wannan....," "Ya isa ya isa Sadauki kar na ƙara jin bakin ka nan wajan" Ya yi shiru kawai yana jijjigata kan shi "Ya sunanki?" "Ridayya" Hajja Azizat ta ce "Ohh wakike nema? Kin shigo har cikin gidanmu kin taho ɗakin ɗana kin san shi ne?" "Wallahi bata sanni ba, kawai ki tambayeta me ta zo yi mini" Hajja Azizat ta girgiza kai daman ta san ba shirun zai yi ba, ƴar banzar mita gare shi. "Ina jin ki baiwar Allah" "Abbieyna na zo nema ai gidanmu ne nan ɗin kuma nan ne ɗakin Abbiey" "Kutumar u....," "Kar ka ƙarasa ta a kunnena Sadauki" Idanunsa har hayaƙi yake, ya yi ƙwafa yana ɗauke kan shi zuwa gefe. Hajja Azizat ta ce "Ikon Allah gidanku? Allah sarki to saɓani aka samu domin mijina ne ya siye wannan gidan gabaɗaya idan kin lura mun yi gyara sosai kafin mu tare, wannan ɗin ɗana ne sunansa....," "No please mother" Ya faɗa yana haɗe fuska tare da girgiza mata kai alamar baya son a faɗi sunansa mene haɗinsa da ita, wayarsa ta fara ringing ya ɗauka da sauri a hankali yana cewa. "She is already here, yes Nadiya" iya abinda ya faɗa kenan a ɗakin ya fice. Kuka sosai Ridayya ke yi tana durƙushe wa a wajan hannunta bibbiyu ta haɗe ta ce "Don Allah don Allah karki kure ni a gidan nan wallahi gidan Baffana ne kuma nan ɗin ɗakin Abbieyna ne, ki ji tausayina ki faɗa mini inda Baffa Mami Abbiey suke don Allah" Jikin Hajja Azizat ya yi sanyi tausayin Ridayya ya kamata amma tasan halin mijinta baya ƙaunar kowa cikin gidansa idan ba su ba. A sanyaye ta ce "Babu shakka da ina da hali zan taimaka miki da inuwar da za ki shiga ki samu sanyi, ni ma zama nake a ƙarƙashin wani bisa umarninsa nake komai" Ta tausasa harshe ta ce "Komai ya yi zafi maganinsa Allah, ki ɗauka gobara ce ta tashi a cikin kogi Ubangiji ne kaɗai zai yi maganin al'amarin" Ridayya ta miƙe idanunta ya kumbura sosai jiri na kwasarta don yunwa. Hajja Azizat ta ce "Amma ke kina ina iyayen naki suka bar gidan? Ki kira number su mana idan suna kusa sai ki je" Ridayya bata ce komai ba can ta ce "A wajan wa kuka siyi gidan?" "Gaskiya bana ce ba domin mijina ne ya san mutumin. Ki tsaya ki yi ƙarya sai ki tafi" "Na gode" Zuciyarta babu daɗi ta nufi hanyar waje yau ita ce ta shigo gidan ubanta amma bata da iko da shi,duk yadda take ƙoƙarin goge hawayen sai kallon gidan take rayuwarta ta baya na dawowa fes cikin tunaninta rayuwar gidan da a yanzu ita take buƙata fiye data gidan miji. Yana ganin ta fito ya kashe wayar da yake ya diro daga kan motar hannunsa ɗaya riƙe da ball yana juyata tare da binta da kallo can ya girgiza kai ya ce "Who are you? Wace ke?" Ridayya ta yi shiru kan ta a ƙasa ya matsa yana ja da baya tare da leƙar fuskar ya ce "Sai fa kin faɗa mini mene ya kawo ki bedroom ɗina fi not" "If not zaka dake ta ne?" Ya kame fuska ya ce "Kar ki shiga faɗan nan Mother ki bar ta mini bayanin kan ta da wannan bakin nata" "Sadauki wallahi baka ɗauki halin mai sunanka ba, kasan daraja da kimar sunan da a sanya maka" Ya turɓune fuska ya ce "Na sani" Ta ce "Bari na tuna maka Hamza sahabin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, cikakken sunan shi Hamza Ibn Abdul mutallib,ya kasance sahabin Manzon Allah (SAW) ne kuma kawu ne na Manzon Allah Muhammad (S.A.W), jarumi, mai farautar zaki" "E to tunda ni ban samu zakin ba ga zakanya nan a bar ni na farauce ta, sai fa ta faɗa mini wacece ita" Gabaɗaya ya Sadauki ya tare hanyar tare da babbake ta, ba ruwansa da yadda yake acting shi bai ƙi ya cire a daku ba, daman ɗan rigima ne kuma shi ne ɗaya tilo ɗan fari kuma ɗan auta abin ya haɗe masa gashi ƙato da shi saboda ɗaga ƙarfe. Sai yanzu ta ɗago ta kalle shi, shi ma ya kalleta da sauri ta zame idanunta sanda ta tuna akwai igiyar aure a kan ta. Sadauki bai damu da yadda take ba kawai yana mamakin ashe duk baƙinsa akwai wacce ta ci ubansa a baƙi. "Ka bani hanya please" Sadauki ya muryar Ridayya ta amsa a kunnensa ya runtse ido ya buɗe yana girgiza kai tare da tattara hannu ya ce "Kin ji ba mother? Muryarta kamar kamar ana busa irin jita ta amma kalle ta tsohuwa? Yasin da akwai abinda ke tattare da ita" "Yi tafiyar ki kin ji" Sadauki ya yi sauri zai bita Hajja Azizat ta riƙe shi tana murɗe kunnen shi. Ya juya ganin Ridayya ta ɗan fara nisa ta kusa gate ya ɗaga murya ya ce "Kuma sai na rama ko ba yanzu ba, sai na shigo miki ɗaki ki ji idan daɗi, ki saka a ranki zan sake ganinka Sadauki baya mantuwa" Da sauri ta fice don ba zata iya da masifar wanda aka kira da Sadaukin ba. Bata taɓa zuwa gidan Dada ba, balle gidan Yaya A'isha Anuty Kaltum daman ba mazauniyya ba ce. Ta rasa inda zata saka ranta ta ji daɗi a rayuwarta, zuciyarta wani irin zafi da raɗaɗi take mata ga wani irin ciwon kai dake damunta tana jin abinda ke cikinta na juyawa yana sanar mata shi ma yunwar yake ji. Mardiyya ce ta faɗo mata ta mance ma da abinda ta yi mata tana zuwan gidan ta ruski sun yi tafiya zuwa biki sai wata wacce take haya a gidan da alama bata jima da tarewa ba ganin bata da mafita wacce ta shige komawa gidan Zameer ta ji ta bakinsa ya saka ta nufi gida. Tana ƙoƙarin shiga layin aka ce "Ridayya" Gabanta ya faɗi ta yi saurin juyawa wani matashi ta gani tsaye a gabanta jikinta na ɓari ya ce "Kar ki ji tsoro, matar Zameer ko?" Nan da nan ranta ya ɓaci jin sunan Zameer take kamar saukar dalma a zuciyarta ya gyara tsaiwa ya ce "Zan faɗa miki wani abu da ba ki sani ba game da mijinki Zameer. Ya yi auren caca dake da niyyar idan kikai soyayya da shi kuma ya samu budurcinki yana da Naira miliyan goma, sai ya ci sa a kece kika fara furta cewa yana son ki, ya dinga amfani da soyayyarki da kuma rauninki na cewa kar ya barki saboda ba za ki samu mijin aure ba. Zameer bai taɓa son ki ba koda da rana ɗaya ne. Ya yi ƙoƙarin barin ki bayan ya cimma burinsa sai ya ga wata sabuwar damar, kin faɗa masa an mallaka miki kadarori wannan dalilin yasa yake zaune dake saboda su zama mallakinsa one day" Ƙoƙarin faɗuwa take ta riƙe jikinta sosai ta shiga girgiza kan ta. Gaza ya ce "Ba iya wannan ba ai, gidan daya fara kai ki ara ya yi ba nasa bane, plan ne da ƴan kai amarya sun tafi zai kai ki asalin gidan daya tanada domin ki, lefan da aka sace naki shima haya ya yi da niyyar kai musu bayan biki shi ne akai plan a zo a ɗauke kamar ɓarayi duk shi ya shirya. Uhm! Sai furnitures ɗinki daya siyar ya ce kasuwanci zai yi ko? To caca ya shiga da kuɗin wanda ya ci yana da miliyan kusan 30 ya yi hakan ne idan ya samu ya auri budurwarsa da yake mugun so, ya sace atamfofinki ya shiga caca, ya sace wayarki ya shiga caca maganar da ake yanzu hatta gidan da kuke ciki ya shiga caca da shi kuma an ciye yanzu ba mallakinsa bane shi ne ya ce ma za ku tashi right?" Jin Ridayya bata ce komai ba ya sanya Gaza ɗorawa da faɗin. "Zameer bai taɓa so da ƙaunar baƙar mace ba, ki yi tunani tunda kuke sumbata ta taɓa haɗa ki da shi? Saboda yana tsantsamin wai dugun bakinki, yana sane ya daƙile miki karatunki saboda kar ki zama wata idan har kikai ilimin mai zurfi za ki hana shi samun abinda yake kwaɗayi wata dukiyarki, ki nazari akwai baƙar macijiyar da kike rayuwa da ita ki gaggauta yin maganinta dukda kin ɗakko hanya" "Ya isa zuciyata dab take da fashewa don Allah ka ce mini ba gaskiya bane, ka ce mini mijina yana so na wallahi zuciyata zata buga" Gaza ya ce "Bai kamata ta buga tun yanzu ba, ai kina da rayuwa mai tsayi da muradan daya kamata ki cimma ki yi achieving nasu tas. Wannan kenan abi na gaba shi ne iyayenki" A gigice Ridayya ta damƙe hannun Gaza ya ce "Su nake nema sune suka rage mini a yanzu ina gama ka da girman Allah ka kai ni wajan su" "Abu ne mai wahala gawar dake cikin kabari ki ga ta tashi, kamar yadda yake abu ne mai wahala buduwar da bata da mijin kiga ta samu ciki sai dai idan ƴar'iska ce. Ridayya ki yi haƙuri da abinda zan faɗa iyayenki su duka basa raye sun mutu daga ciki kuwa har wannan Manajan Bankin....," Wata shaƙa Ridayya ta yi masa idanunta ya firfito waje kamar mahaukaciya ta ce "Ƙarya ne Abbiey ya mutu ya barni, ƙarya ne na rasa kowa nawa suna nan a raye ka ce mini suna nan basu mutu ba" Cak kuma numfashinta ya tsaya ta sulale tare da yanke jiki ta faɗi a sume. ____ Kuka take sosai kamar ranta zai fita ya kifa kanta a kafaɗar shi tare da damƙe hannunsa dake cikin nata, yadda take kukan zaka ɗauka ƙaramar yarinya ce tsananin damuwa ne ya yi mata yawa a zuciya. A hankali yake shafa bayanta tare da ɗan bubbuga wa alamar rarrashi amma kamar yana zuga ta ganin kukan ba mai ƙare bane ya sanya ya jawota ya rungume ta a jikinsa, da sauri ta ƙanƙame shi domin da gaske tana buƙatar wajan da za ta yi kuka, kuka mai yawa ko hakan zai sassauta damuwar zuciyarta. A hankali ya ce "Shhh ya isa haka, daina haka nan ni ma za ki sani kuka" Ta ɗaga masa kai kawai tana sauke ajjiyar zuciya Ɗago kai ta yi ta kalle shi idanunsa sun yi jajur shima ta buɗe ba ki za ta yi magana ya saurin rufe mata bakin ya ce "Yi shiru, na san me za ki ce yau dai ki kwanta ki huta ki kuma samawa kan ki nutsuwa kin ji?" Ta ɗaga kai a hankali ta kwanta ya ɗora kanta a cinyarsa har lokacin hannunsa na cikin nata ta riƙe da ƙarfi a haka ya shiga shafa kanta shi ma yana sauke ajjiyar zuciya. Kasancewar azumi dab yake da shigowa domin bai fi saura kwana ashirin da wani abuba ya saka ya nutsa tunaninsa ga mutanen da ya dace a bawa zakka wannan shekarar. Kodayaushe tunanin inda zai sameta shi ne burinsa dukda yana son ya samu zuciyarsa ta kaɗaita da tunaninta al'amarin ya girmame shi ita ɗin kula da ita hakƙinsa ne kuma wasiyya ce a gare shi, babu wanda ya rage masa a duniya sai ita ɗin INA ZAI GANTA? Bai ji ƙarar buɗe ƙofa ba sai sautin murya ya ji a bayansa a hankali ya juya da kyau a kan ƙafafuwansa walwalarsa ta ragu faɗan shi ya ƙaro fiye da kima. Ya rame ya faɗa amma kamar ana ƙara masa kyau da hasken fata ne. "by now it is appropriate that you stop thinking" Ya faɗa yana jan kujera ya yi wa kansa mazauni har lokacin wanda yake magana da shi ɗin bai kalle shi ba, bai kuma tanka maganar shi ba "Na yi magana da Hajiya akan dawowar su Legas" "Why?" Baita ya watsa hannu ya ce "Haka na yi niyya, have a seat" Zama ya yi saman haɗaɗɗiyar kujerar shi idanunsa a lumshe sosai ga wani irin ciwon kai daya kasa barinsa Baita ya ce "Yau ka yi niyyar shigowa office kenan?" Bai yi magana ba sai hannunsa da yake kaɗawa yana matse yatsun alamar yana azabtar da kansa ta haka ne duk miskilancin Baita amma Ustaz ya ce shi babansa ne a wannan ɓangaren "Kwana biyu na shigo na baka labari friend na sameka cikin wannan yanayin, naga kuma bai dace ba koda na je gidanka da ƙyar ka saurare ni kuma ka ji rarrashi na" "Baka gajiya da magana Tajj?" Baita ya ɗaga gira ya ce "Saboda Ubangiji ya bani bakin, kuma kai dai baka isa ina maka magana ka yi mini shiru ba, serious magana nake da ita" "Ina ji" Ustaz ya faɗa yana ɗora ƙafarsa ɗaya saman table ɗin dake gabansa, can kuma ya miƙe ya nufi duguwar kujera ya kishin giɗa a kai. Baita ma ya tashi ya dawo kusa Ustaz, takaici ya saka Ustaz kasa magana domin ba zai iya da neman maganar Baita ɗin ba. "Ina cases ɗin da nake maka magana akai? Mun kusa yin nasara domin mun samu an yi tracking number ɗaya daga cikin yaran" Ustaz ya jinjina kai sosai yake jin maganar amma idan aka kalle shi zaka ɗauka bai ma san abinda Tajj Baita ke faɗa ba. "Na je Kano na yi kwana biyu gida a hanyata ta dawowa Legas na haɗu da wata" "Maman Nadra za ka yi wa kishiya kenan?" Baita ya haɗe fuska ya ce "Ka taɓa ganin an yi wa wanda baya raye kishiya?" Ustaz ya ɗaga kafaɗa tare da juyawa baya Baita ya ce "Tana buƙatar taimako na tsaya, ka sanni bana ƙaunar ganin mace cikin wani hali ina da tausayi sosai a kan mace wallahi tunda na ganta na ji ina son taimakonta, zafa ka ɗauka tsohuwa ce irin sosai ɗin nan amma wallahi yarinya ce kasan ina da fahimtar abu ba a banza na shiga police ba, ina son taimaka mata" "Ka yi mana" "Ban san ina take ba, taƙi saurarata sam wallahi" Tsaki Ustaz ya ja yana miƙewa tsaye a hankali ya ce "Yanzu ka zo ka faɗa mini naje na nemo maka ita ne? Tajj ka ɗan saurara mini ba ruwana da ita taimako ko ni zan iya taimakawa amma ka daina mini maganar ko wacce mace" Baita ya riƙe baki ya ce "Wonderful! Ai wallahi sai na saka an yi maka aure da zarar ka san mece soyayya zaka riƙe mace hannu bibbiyu" "Uhm soyayya, kune baƙin ta, daɗi da zafinta ba wanda ban sani ba" Ustaz na faɗin hakan ya fice daga office ɗin da sauri Baita ya bi bayansa yana cewa "Wait, tell me something about your first love kasa ka a kai wa ka taɓa so? Ka zama ragu a soyayya kenan?" Ustaz bai kula shi ba ya yi waje abinsa. Tunda ta sulale ta suma a wajan bata san mene ya sake faruwa ba, bata san adadin data ɗauka ba a hakan balle kwanaki sautin muryar data tsana a rayuwarta fiye da komai ita ta firgitar da ita ta buɗe ido da ƙyar tana dafe kanta idanunta sun yi mata nauyi saboda kumburi da jimawa da ta yi da rufe su. "Tashi mun ƙara su" Ya faɗa yana yin wani irin murmushi ganin hakan shi ne kawai damar data rage masa. Kafin ta sake buɗe idanunta ta ji ana faɗin "Giɗaɗon ya zo Giɗaɗo ya zo, yee mijin Hanne ya dawo sannu da zuwa Giɗaɗo" Yaran da suka baibaiye motar suka shiga faɗa tsakar kuma basu taɓa ganin mota ba haka suke shafa ta ana leƙuwa tare da kallon Ridayya. "Waye kuma Giɗaɗo?" Ta tambaya a zuciyarta "Ki fito" Ta ce "Ina ne nan ɗin?" Kai tsaye ya ce "Katsina. Ƙauyen Nahutu dake yankin Batsari" "Me za mu yi a Katsina mene ya kawo mu ƙauye" "Saboda nan ne mahaifata cibiyata kuma daga yau zai zama garin mijinki" Ridayya ta girgiza kai bayan ta fito daga motar ta ce "Wallahi ƙarya kake ba zan taɓa zama a nan ba ina gidan Alhji Mahboon Dollar ɗin?" Sai kuma ta miƙe da sauri da sauri ta ce "Munafiki macuci azzalumi wanda baya tsoran Allah bambancinka da shaiɗan kaɗan ne" A gigice Zameer ke kallonta koda wasa aka ce masa Ridayya zata ɗaga masa murya ba zai taɓa yarda ba, yau Ridayya shi take kallon cikin idanunsa babu tsoro balle shakka bata tunanin gargaɗinsa. Wani abu mai kama da faɗuwar gaba ya gitta masa ganin komai na yayewa a idanun Ridayya Mai son shi, babu son, babu tsoron, babu biyyar babu tattali da wannan tausayin nata zuwa gare shi lokacin na farko wani abu mai kama da fargaba ya matse zuciyarsa kar dai ta daina son shi? Ya girgiza kai da sauri a fili ya ce "Never!" "Ridayya ni kike jefa da wannan maganganun?" "Na faɗa waye kai banda MUNAFUKIN MIJI? Ka aure ni a caca ka ce kana so na saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, ka kwashe kayan ɗakina ka siyar ka ce kasuwanci za ka yi saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, ka ce a kano kake sai gamu a Katsina saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, mene laifina da zaka munafurci ni har haka? Laifi na kawai don na nuna maka soyayya? Ashe haramci ne nuna kana son mutum ka wulaƙanta ni ka wulaƙanta rayuwata ka gaggauta mayar dani Kano, wallahi ko zan kwana bola ban zama tare da kai" "Idan kina da kuɗin mota ki koma tunda ai na san kin san hanya" Ya faɗa a dage amma zuciyarsa wani kalar tsinkewa take kar dai Ridayya ta sauya "Gidaɗo ka zo ashe? Meke faruwa nan ne ake ta ɗaga haƙarƙari?" "Gidaɗo? Wani munafurcin sunanka Giɗaɗo?" Ridayya ta ji gabaɗaya ta sare da al'amarin maza kuma da tsani ko wanne namiji gani take zai zama kamar Zameer ya kasance MUNAFUKIN MIJI. Da ƙyar aka rarrashe ta tana kuka sosai ganin kuma yadda yaran ƙauyen suka baibaiye ta kamar za su cinye harda masu leƙowa ta katanga babu ɗaurin ƙirji. Ta yi kuka mai isarta taƙi fitowa daga ɗaki komai aka bata bata ci bacci ya gagari idanunta ga wani irin ciwon kai kamar kanta zai rabe gida biyu da gaske bata da kowa bata da sauran gata ita fa dole Zameer Giɗaɗo ya saketa. Cikin dare tana kwance ba bacci take ba sai juya kanta dake bala'in ciwo yake kuma ta dinga ganin Abbiey yana mata gizau yana kuka sosai sai taga wani ya zo ya janye shi. Kamar daga sama ta ganshi ta yi masa banza ya ce "Hakƙina za ki bani na kasa jurewa na fahimci ke kaɗai nake samun nutsuwa a tare dake" Ridayya ta cije bakinta ta ce "To Bismillah" Ya yi watsi da suttura shi kamar dabba haka ya faɗo idan take ta yi saurin ta shi ya ce "Ya haka ina jin kamar zan mutu" Ridayya ta waiga can ta hango fatanya ta ɗauka ta zage iya ƙarfinta ta maka masa akan abar........ Share and share and share as you can! Giɗaɗon Batsari da alama za mu je Nahutu jinya🤣🤣🤣 Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv 08119237616 *✿ MUNAFUKIN MIJI 24 ✿* Mikiya Writers Ass.... BRIGHT PENS🤙🏼free batch Nimcyluv Mirgina wa ya yi gefe jikinsa na rawa yana ƙoƙarin kurma ihu ya ce "Akan hakƙina za ki nakasa ni? Ki cuce ni ki cuci kan ki?" Gabaɗaya muryar Zameer rawa take ganin yadda har yanzu take riƙe da fatanyar idanunta sun yi jajur jikinta na wani irin ɓari kamar mai shirin tayar da aljanu. Ya dake ya ce "Ki bi a hankali, ni mijinki ne kuma zan ci gaba amsa sunan hakan har gaban abada, idan kina tunanin wani abu saɓanin nawa kin yi kuskure" Ridayya da ƙyar take riƙe kanta, ji take kamar za a wurgar da ita ne, duk da gabanta dake faɗuwa da kuma girman igiyar auren dake kanta bai hana ta nutsa idanunta cikin nasa ba ta ce "Giɗaɗo" "Giɗaɗo kuma? Ina kika ji sunan nan? Mene haɗina da Giɗaɗo?" Har lokacin yana damƙe da jikinsa da Ridayya bata samu damar idda nufinta akan shi ba sai gefen ƙafarsa data makawa. Jikinta duka rawa yake gani take tamkar babban zunufi zata aikata faɗawa miji magana, mijin da a yanzu komai da take ji game da shi yake yayewa. Da ƙyar tana riƙe jikinta ta ce "Giɗaɗo ba shi ne sunanka ba? Giɗaɗon ƙauyen nahutun batsari ko?" Ta girgiza kai ta ce "Daga Almajiranci ka dawo Zameer?" Ta zube a kan ƙafafuwanta zuriyarta na yi mata wani irin zafi da tafasa ta haɗe hannayenta biyu ta ce "Yau ɗaya ka faɗa mini laifina a gareka don Allah, soyayyar dana nuna maka? Zaɓarka da na yi na watsar Abbieyna? Ko fara furta maka kalmar Ina son ka? Ko kuma budurcina daka amsa kafin aure shi ne laifina? Ko kayan ɗakina daka kwashe ka siyar shi ne nawa laifin? Ciyar da kai da nake yi kullum, ko kuma fifitaka a kan iyayena shi ne laifina? Ka faɗa mini laifina dana cancanci irin wannan cin mutumcin wulaƙanci da ƙasƙanci a gidanka, me na aikata har haka daya dace ka zame mini MUNAFIKIN MIJI? ka faɗa mini mana" Miƙewa ya yi ta yi saurin miƙewa dukda rashin ƙarfin jikinta ga ciki. Zameer bai bari kalaman Ridayya sun yi tasiri a zuciyarsa ba ya yi murmushi ya ce "Wane ya faɗa miki haka? Wanne munafukin ne har haka Ridha tsakanina dake za a shiga?" Kallonsa kawai take da juyayyun idanunta ba tare da ta ce komai ba. "Ridayya kar ki bari zuciyarki ta yaudare ki, ba ki da wani waje da yafi wajena, ba ki da wanda ya fini a yanzu dole ki yi mini biyayya domin Batsari kike ba Kano ba" Ya nufi inda take domin baya jin zai iya rabuwa da ita, abubuwan da yake ji game da ita ƙara fusgarsa suke, a gare ta ɗinne kawai yake jin haka dukda wani irin tsoro da yake shirin ruskar shi a yanzu. Ya gyara tsaiwa ya ce "Ni tamkar ƙadangaren bakin tulo ne, a gare ni a ɓata ruwa, a bar ni a ɓata ruwa, ni ɗin dai ya zame miki dole. Na tuna miki da babban murya iyayenki sun rasu baki da kowa a duniyar nan sai ni, kuma ki hanani abinda nake so ki gane Allah ɗaya ne" Kallonsa kawai take duk yadda hawaye ke ƙoƙarin fita daga cikin idanunta ta kasa saboda kada ya gane a yanzu iyayenta sune rauninta da rashin gatan da take da shi. Hannu ya saka ya fusgota kamar yadda ya zama yi mata wanda hakan ya zama tamkar Sexual violence a gare ta ko shi mijinta ne idan ba da ra'ayinta bane to tamkar zalinci ne, CUTARWA ne. Kokawa suka shiga yi duk ya gigice da tsananin buƙatar ta ita kuma ta yi alƙawarin har gaba da abada idan akwai ba zai ƙara morar jikinta ba. Ta zage iya ƙarfinta ta gantsara masa cizon daya kusan kwashe masa fatar wuya ya saketa ta yi saurin fitowa daga ɗakin tana nufar ɗaya ɗakin da yake da wata mata a ciki. Wani baƙin ciki ya tukare a wuyan Zameer ganin yadda ya ga samu kuma ya ga rashi amma ko zata mutu sai ya fanshe duka sauran ranakun daya biyo ta bashi. Ya yi tsaki ya fita. Kuka take tamkar ranta zai fita numfashinta na tsarƙewa saboda yadda zuciyarta ke mata zafi da raɗaɗi, idan ta tuna bata da kowa bata da wanda zata raɓa balle ya ƙwatar mata ƴanci sai ta ji komai ya sare mata ta ji tamkar ta yi giving up ko ta ji kamar ta kashe kanta. Rana zafi inuwa ƙona, ruwan daya dake ka shi ne ruwa ta yarda rayuwa da ƙaddarata a tare Ubangiji ya samar da su kuma sun zama jinin jikinta yadda ba zata taɓa iya guje musu ba. Ridayya ta yi kuka mai isarta gashi tun tayin abincin da aka yi mata taƙi ci babu wanda ya sake sauraren ta da wani abinci tamkar gudunta suke haka suke mata acting. Kasancewar su gabaɗaya fulani kowa kyakkawa farin tas da shi zai ya zama ta kasance kamar baƙar tukunyar da aka tuƙa farin tuwo a cikinta. A hankali ta lumshe idanunta tana shafa cikinta da yake ta zungurar mata mara wata iriyar ƙauna mai ratsa fata, jini da ɓargo ke ratsa zuciyarta ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗorawa cikin tana jin shi ne kawai ya rage mata a yanzu. "Idan kin gama kukan tashi ki fita daga ɗakin baiwar Allah" Ridayya ta kalli matar, wacce ta yi saurin ɗauke kai tana cewa "Bismillahir Rahmanir Rahim" A sanyaye ta miƙe tana dafa bango ta fita ta nufi ɗakin tunda tana da tabbacin Zameer ɗin ya fita. Tana fita Iyatu ta ce "Shatu maza ɗakko turaren mayun nan ki turara a ɗakin nan" "Mayu kuma Iyatu?" "Su fa, au wai ba ki san mayya Giɗaɗo ya auro daga Birni ba can? Ayya ai mayya ce saura ƙiris ta ci ɗari ba ɗaya shi ya sa kika ganta baƙa ƙirin wallahi tallahi" Shatu ta yi zuru don a duniya tana jin tsoron maye an ce cinye mutane suke tare da soye naman shi su cinye. "Mun shiga uku Iyatu kar ta suɗe mu" "A'a kurwa kurr namanku ɗaci gare shi, da kun ganta ku gudu ai kuna ji ko? Kar ma ta kira ku kuje" Giɗaɗo na fita ya yi waje can dandali jikin Hanne na rawa ta zo wajansa ta ce "Masoyi ka dawo wai da matarka? Da gaske ba zaka aure ni ba?" Kallon tsaf ya yi mata kana ya ɗauke kai yana danna wayarsa hankali kwance tunanin yadda zai amshi takardun wajan Ridayya kawai yake domin sune plan ɗinsa da burinsa a yanzu. Hanne ta fashe da kuka Allah yana gani tana son Giɗaɗo tun tana ƙarama kuma shi ma yana sonta tunda ya je birni ya dawo ya wargatsa duk wata shaƙuwa da sukai. Ta zube ta ce "Giɗaɗo ka tausaya mini ni ce Hannen Nahutun Batsari ni ce Hanneka fa Giɗaɗo ko ka manta ne?" Ya ja tsaki ya miƙe tsaye ko inda take bai kalla ba ya yi gaba a wajan gani yake gabaɗaya ƴan'kauyen ba sa'aninsa bane shi ɗin dabanne a cikin su. Rayuwa ta yi wa Ridayya zafi duk ana ɓoye mata har ta fahimci kallon da suke mata na mayya bata uhm bata un'uhm bata walwala bata sukuni damuwa sun yi mata tsaye a zuciya ko bacci bata iyawa yadda taga rana haka take ganin dare idan an sammata abinci ta lasa wani lokacin ta kalle shi a Idanu ta nutsu ta gane mene asalin so ya ake jinsa a ƙirji da zuciya? Amma kwakwalwarta ta gaza bata damar yin hakan. Ta zama tamkar wata sauna gashinta kullum ƙara yawa yake kamar buzuwa. Yatsarta da take sha tun tana ƙaramar yarinya shi ta dawo sha yanzu. A haka watanni suka shura mata har zuwa wajan wata uku da zuwanta cikinta ya shiga wata na takwas. Da sassarfa ya shiga sakkowa daga strains ɗin benen idanunsa a ɗan lumshe daga shi sai gajeren wando da wata milk ɗin Armless daya buɗe zip ɗin gabanta a ɗan gurguje yake sakkowa ɗin bakinsa kuma bai fasa ƙwalla mata kira ba. "Mother mother mother" Tunda daga kitchen take jiyo muryarsa a narke rikicinsa bata tsoro da mamaki yake hannunta duk fulawa ta fito a ɗan gigice tana mai tsayawa ganinsa zaune a ƙarshen step ɗin benen ya tanƙwashe ƙafa ta ce "Sadauki lafiya kake? Wannan kiran fa?" Ya ƙura mata Idanu "Magana za ka yi Sadauki ba kafe ni da wannan idanun naka ba" Hajja Azizat ta faɗa tana kallon tilon ɗan nata wanda take ji har ƙasan zuciyarta zata iya sadaukar da komai nata akan shi. Ta rikice ganin yaƙi magana ta ɗauka ko bashi da lafiya ne? Tunda yake bai taɓa cewa wassh saboda ciwo ba... Ta koma kitchen ta wanke hannunta tana bawa Dija umarnin ƙarasa wanke-wanke ta dawo gani ta yi baya parlourn da sauri ta nufi bedroom ɗinsa nan na baya ciki daga can ta ji sautin kiɗan jitan shi ta nufi wajan, ta tsaya saroro tana kallonsa ya tuɓe rigar sai training yake a gym ta ce "Sadauki" Ya juya ya kalleta yana ɗaga mata hannu tare da juya yatsunsa alamar "What Mother?" Ta kashe sautin jitan kana ta rage gudun injin ya marairaice fuska sosai yana kallonta ta ce "Ka bani tsoro Sadauki ba ka ji zuciyata ba, baka da lafiya ne? Mene ya sameka? Are you okay?" "Mother" Sadauki ya faɗa yana sauka ya ce "Kin taɓa ganin Sadauki ya yi rashin lafiya?" "To wannan kiran gaggawar na mene?" "Just to see you Mother, na farka na leƙa bedroom bakya nan shine na biyo ki fa" Ta dinga kallon shi ya ɗaga hannu ya ɗora a kafaɗarta suka fita waje ta ce "Yaushe Sadauki zai girma ne ni Azizat?" "Sanda na yi aure, ko na yi aure ban taɓa girma wajan Babata da Matana Allah idan ban muku shagwaɓa wa zan wa?" Waje ta nema ta zauna ta ce "Wallahi da za ka yi auren da na ji daɗi sosai na samu jikokai kaga kai kaɗai Allah ya bani" Ya girgiza kai yana ɗaukan ƙafa ya ɗora saman table yana mai sauya channel zuwa kallon ball ya ce "Da kowa zagewa zan yi nai ta haihuwa, matana ta haihu nima na haifa" "Ikon Allah. To ka fito da matar auren mana" Ya ɗan ɓata fuska sai kuma ya girgiza kai ya ce "To har yanzu babu ƴan'matan" Mother ta ware Idanu sosai ta ce "Duk tarin ƴan matanka Sadauki? Kiran yau da ban na gobe daban" Ya yi mata shiru kawai don hankalinsa ya koma kan ball wasa ake bugawa sosai tsakanin Hala Madrid da Bercelona. Ta ce "Ina magana fa" Ya juya ya kalleta sosai tasan lissafin abinda zai faɗa yake can a nutse ya ce "Su duka ƴan matan suke so na, ina son samun wacce zuciyata ta nutsu a kanta Mother, ina son soyayya sosai, ƙauna, tattali da kulawa ina son macen da ni zan koya mata mene soyayya da yadda zata so ni, wacce zan sha wahala a kan ta sosai. Sadauki na son soyayya" Ya faɗa hankali kwance don har a ransa yake jin normal ne Hajja Azizat ta riƙe haɓa ta ce "Naga abinda ya dame ni" Sadauki ya ce "A'a fa ki daina salati kamar na faɗi mugun abu, a duniya babu abinda yafi daɗi irin zama da wanda zuciyarka ke tsananin so" Tana ƙoƙarin magana ya buga ihu ya miƙe yana "Go goooo!" Daidai nan wani ya shigo cikin parlourn Sadauki ya tafi da sauri ya bawa mutumin hannu ya ce "Gooo Daddy mun cinye ku goo" Daddy ya girgiza kai kawai ya ce "Yau ɗaya Madrid sun abin ƙwarai" Sadauki ya ɗan rusuna sosai har ƙasa ya ce "Good morning Daddy" "Morning Friend, ya jita? Ya kuma business?" "Good" Daidai nan wayar Daddy ya fara ringing aka saka secretary a number bai ɗauka ba sai da yaga Hajja Azizat na kallonsa ya ɗaga ya ce "Laminu ya akai ne?" Ya yi shiru can ya ce "Oh waje mai kyau please, ya yi tsari da ƙawa a shirya sosai don na daɗe ban yi ba, a fa shirya?" Ya kashe wayar Hajja Azizat ta ce "Sannu da shigowa Prof" "Yawwa wife, ya rigimar ɗanki Sadauki" Ta yi murmushi Ƙara wayar Prof ta yi notification ya shigo Sadauki ya kalli screen ɗin wayar ya ce "Daddy wannan secretary ɗin baya ga jiya da turo maka pictures? I noticed that" Prof ya miƙe ya ce "Yhhh pictures ɗin motoci ne sababbi da zan siya na bawa secretary aikin hakan yanzu ma can zani" "Yanzu ka shigo tunjiya kuma yanzu zaka sake fita?" Ya ce "To ya za a yi ni kaina ina buƙatar iyalai na kusa dani, na yi kewarku sosai wallahi" Jikinta a sanyaye ta ce "To Allah ya tsare ya kiyaye ya bada sa a" Prof ya ɗan bawa Hajja Azizat side hug ya ce "Love you wife soon zan dawo" yana ƙoƙarin fita Sadauki ya ɓata fuska ya ce "Daman baka so na ka fi son Mother" "Banda ciwon baki me kake saka mutane Sadauki? Shekaru 30 ciff kake wannan shekarar fa, and idan ban so matata ba wakake tunanin zan so?" Ya haɗe rai shi dai ganin hakan ya saka Prof rungume Sadauki ya ce "Stubborn friend i love You" Sadauki ya ɗage gira shi ma. Bayan Prof ya shiga mota driver ya ja ya kira number secretary ɗin a hankali bayan an ɗauka ya ce "Sweetheart Lina ina bisa kan hanyar hotel ɗin...." Zuwan Ustaz Kano uku bayan tafiyar Ridayya yana zuwa gidan Zainaba ta shaida kaf halin da Ridayya ke ciki amma ta ɓoye labarin data bata don gane abinda suka aikata tare da Zameer, ta kuma ce tun ranar da aka faɗawa Ridayya kowa ya mutu daga ciki har da Ustaz ɗin ta sulale a wajan ta suma, Zameer kuma ya saka aka yi mata allurar bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta ya koma garinsu. Ta shaida masa bata san garin ba sam sai dai ya tambaya a lokacin kuma Malam iro Allah ya yi masa rasuwa kaf Almajiran ba wanda ya san asalin sunan Zameer balle garinsu hankalin Ustaz ba ƙaramin tashi ya yi ba. Ya je ya tambayi gidansu da Sadauki ya fara cin karo yana wasa da wani ƙaton kare. Haka kurum Sadauki ya ji mutumin ya yi masa kwarjini ya tsaya yana kallonsa Ustaz ya faɗa masa dalilin zuwan Sadauki ya ja baya da sauri ya ce "Thank you dear Lord, nemanta nake ido biyu ta hanani runtsawa so kai ne Abbiey ɗin da take magana?" "Ta zo?" Ustaz ya faɗa a hankali yana cin surutun Sadauki har tsakiyar kansa ya ce "Wacece ita? Muryarta daɗi amma kamar bata da lafiya?" "Ta zo ne?" Ustaz ya sake tambaya cikin damuwa ganin yadda Ustaz ke ɗaga kai kamar ana masa dole Sadauki ya dawo da asalin halinsa ya ce "Ban sani ba" Don a rayuwa ya tsani ɗagawa da faɗin rai yana sane ɗin kuma ya share Ustaz ya yi tafiyarsa. Duk inda Ustaz ke tunanin neman Ridayya ya fassakara Wasiyyar Baffa kawai yake son cikawa ba wai wani dalili ya saka yake neman nata ba. Bayan ya shiga mota a hankali wanda yake ciki ya yi mata key suka fara tafiya ya ce "Babu labari?" Ustaz ya lumshe idanunsa zuciyarsa na dokawa da matsanancin ƙarfi ga wani irin matsewa da zuciyarsa ke yi tana tattare masa waje guda a ƙirji tana ƙoƙarin haifar masa da wani irin ciwo. "Ka bani dama na baka labarin matar dana gani mana please wallahi kullum da abin nake kwana a rai nake tashi" Ustaz ya yi shiru yana sunkuyar da kansa ƙasa wani irin numfashi numfashi yake futarwa da ƙyar, zanen photon abun ya kasa gogewa daga idanun zuciyarsa gani yanke tamkar yanzu idanunsa sukai masa mummunan ganin da har ya koma ga Ubangiji ba zai manta ba. Gefe guda sunan BILAL da Ridayya ta furta yana masa amsa amo! A kunne tamkar yanzu ne take faɗa "Bilal ka taimaka ka saurare ni, idan na fasalta maka ita babu mamaki mu sameta gidan mahaukata" "Tajj...please" Ustaz ya faɗa da ƙyar yana ƙanƙame jikinsa tare da rirriƙe kansa yana jin kamar zai cire maimakon su shige airport kai tsaye sai ya nufi asibiti da Ustaz ciwon kan nasa yana bashi tsoro. Tamkar mujiya haka Ridayya ta tsinci kanta a ƙauyen Batsari mai cike da tarin ni'ima da albarkar noma ga yalwar bishiyoyi da ƙoramaiw gwanin ban sha'awa. Da yawan lokaci barin gidan take ta yi nisa ga cikin ƙauyen ta zauna bakin ruwa ta ci kuka ta ƙoshi ta yi bacci a wajan ta tashi ga girman da cikinta ya yi haihuwa yau ko gobe. Bata da abokin hira sai cikin jikinta gefen zuciyarta kullum tana son tambayar Zameer ina ƙanwarsa Khairiyya? Tunda ya ce ya mayar da ita gidan mijin bata ƙara ji ya yi maganarta ba ko ba a garin take da zama ba? Ganin yamma ta yi sosai ta miƙe ciki a gaba tana tafiya a hankali tana shigowa cikin mutane aka fara darewa ana cewa "gata nan gata nan" domin tuni ƙauyen ya gama ɗauka ita ɗin mayya ce kowa kaffa kaffa yake da yaronsa da an ganta za a tsiri kunna turaren mayu ita dai bata kula kowa hakan bai taɓa damunta ba, babu kalar tsangwama da tashin hankalin da bata shiga ba a rayuwa, daga iyaye ƴan uwa al'umma gari da miji. Yanzu kuma dangin miji da ƴan ƙauyen su duk dalilin Soyayya da kuma halittar da Ubangiji ya yi mata. Ƙauyen Batsari daman ba wani ilimi ne da su ba balle wayewa kowa ya yi believing cewa ita ɗin mayya ce. Tunda ta ƙarasu take jin hayaniyya ƙofar gidan kuma cike da mutane ana ganinta aka dare ta shige dafe da ciki turus ta yi ganin Khairy tsaye ta tura ɗauri a gaban goshi ga Zameer ga Iyatu ga baban Zameer da babarsa da tarin yaran gidan da kuma Hanne dake ta kuka. Ridayya ba ta yi magana ba don ta ɗauka Khairy gida ta zo gani sai dai kukan da ta ji da kalaman da suka sauka a kunnenta suka haifar mata da murɗawar mara ƙafarta ta riƙe sosai, haka bayanta da ƙyar ta juya idanunta ya sauka a kan wata halitta wacce Ubangiji kawai ke da ikon samar da ita. "Ni ba wahalalliyar matarka ba ce Zameer ga tsiyarka nan munafukin banza da wufi, wato ka ɗirka mini ciki shi ne ka watsar dani? Allah ya yi na haife ga kuma ɗanka nan" A gigice Zameer ya ce "A'a Khairy wallahi ke nake da muradin aure kece kala ta kuma ina da abinda nake jira dana samu za mu yi aure mu rayu da ɗanmu" "Wa? Ni Khairiyya na aureka Allah ya kyauta mini idan duk duniya kai ne saura wallahi ban taɓa aurenka na faɗa maka" a gigice Ridayya ta ce "Khairiyya wannan kalaman fa? Wannan maganganun fa ina shi ɗin yayanki ne?" "Tofar da yawon bakinki ni ba ƙanwarsa bace raina miki hankali kawai yake wallahi, ni budurwarsa tun muna University shi kuma ya ce na dawo gidansa da zama cikin da ya ce miki na mijina ne to nasa ne" Ridayya ta juya ta kalli jaririn baƙin shi har ba a magana ga ƙaton goshi hanci kamar bana mutum ba suma ɗa babu a kan shi, ɗan tamkar bakwaini ta kalli Zameer da Khairy duka farare ne su gashi sun haifi baƙi kuma mummuna munin daya zarta na Ridayya. Juyawa Ridayya ta yi ta kasa gane wanne yanayi take ciki tana Khairy na cewa "Gashi nan sunan shi Harazimi" Kafin wani ya yi magana suka jiyo salatin Ridayya tana durƙushe jini na zuba ta ƙasan ta cikin ikon Allah kafin su ƙarasa sun ji kukan jariri amma ba wanda ya taɓa Ridayya wai kar ta cinye shi. Ga wani jini ɗaya ɓalle mata idanunta ya fara rufewa ta fara ƙoƙarin danne jaririn dake kuka ta ƙasanta. Hanne ce ta ƙarasa tana kuka ta riƙe Ridayya ta zaro jaririn ta goge masa jinin jikinsa tas ta yanke masa cibiya. Hanne ta damƙawa Ridayya jaririn ta buɗe ido da ƙyar wani irin hawaye ya zubo mata abinda bata taɓa zato ko tsammani ba, abinda ko mafarki bata taɓa hasaso hakan ba. Kyakkawar halittar dake ƙirjinta kawai take kallo hasken fatarsa har kashe mata ido yake babu abinda ya firgitar da ita yadda take hango tsantsar kamannin Muhammad-Bilal Ustaz a kan fuskar jaririn data haifa kamar su ɗaya sak da Abbiey ɗinta. "Allahamdulillah" Jikinta ya fara rawa saboda jinin daya ɓalle mata idanunta ya shiga ƙaƙƙafewa ta damƙi hannun Hanne ta ce "Ban san ki ba amma na yarda dake, na bar miki wannan ɗan nawa don Allah ki bawa Abbiey shi ki tambayi Giɗaɗo ya faɗa miki waye Muhammad-Bilal Ustaz na bar miki shi wallahi na bar miki Allah ya yi masa albarka" Idanunta ne ya rufe hanne ta riƙe jaririn ta fara salati cikin ikon Allah Ridayya ta amshi salatin da ƙyar tana mimmiƙewa tana faɗin "La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah...... Idan an yi comment zuwa dare a yi new posting M. SHAKUR ‎KISSA TRAINING CLASS📢 MASU SO SU KOYI KISSA🎊 MASU SO SU IYA KISSA🎊 MASU SO SU SAN KAN KISSA🎊 MASU SO SU ZAMA HATSABIBAI AKAN KISSA🎊 GANE IDAN AN SHIRYA MIKI KISSA🎊 KISSAN IYA KWACE DANGIN MIJI🎊 KISSAN IYA KWACE MIJI🎊 BA BOKA BA MALAM BAKUMA MAGANI KAWAI KISSA KADAI🎊 ZOKI SHIGA AJIN KISSA DA NAIRA DUBU KACAL!!! 5DAYS TRAINING CLASS WANDA BABU YANDA ZA’AYI KIYI TRAINING DIN NAN BAKI IYA KISSA DA KISISINA BA. KISSA SHİNE BABBAN MAKAMIN MATAR AURE❤️ ZOKI SHIGA KAFIN KISHIYARKI TARIGAKI SHIGA💃🥳 KISSA CLASS PAYMENT IS 1k GUESS WHAT 5 LUCKY ACTIVE MEMBERS ZASU CI NAIRA DUBU ASHIRIN EACH💃💃💃 20k EACH ANOTHER 5 LUCKY MEMBERS ZASUCI KYAUTAN SET NA TURAREN WUTA BY RUKY ANOTHER 5 LUCKY MEMBERS ZASUCI KYAUTAN KAYAN MATA FROM HONEYDROPS KAYAN MATA JOIN YANZU YOU MIGHT BE THE LUCKY WINNER You can make payment here 3107021073 Aisha Muhammad first bank KO 0895672695 AISHAT MUHAMMAD GT BANK Send evidence of payment to 07032934950 MUNAFUKIN MIJI 25 Mikiya Writers Ass... Bright pens free batch Nimcyluv Writer of Moon Mijin Malama Idan ba ke Sirrinmu Uncle ne Jidda Zain Abeed Kwaila ce e.t.c *Masu son MUNAFIKIN MIJI daga farko ku je wattpad don Allah🥰* https://www.wattpad.com/1425100722?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv "A'a ke za ki raini ɗanki ba za ki mutu ba, kin ji?" Cewar Hanne wacce ke riƙe da babyn. Ridayya ta rufe idanu ita kaɗai tasan zafin da zuciyarta ke yi mata ga jinin da yaƙi tsaya mata da ƙyar ta riƙe hannun Hanne ta ce "Mene ya yi saura a rayuwata? Gwara na mutu maybe nawa farin cikin sai a lahira zai tarbe ni" Idanunta rufewa suke sosai jikinta na rawa har yanzu tana riƙe da hannun Hanne. "Matar Giɗaɗo... Matar Giɗaɗo" Shiru Ridayya bata amsa ba, hakan yasa hanne rikicewa ta kurma ihun daya jawo hankalin jama'ar gidan da suke ta ɗauki babu daɗi su da su Khairy. Abinda tunda yake bai taɓa ji ba a tsakanin shi da Ridayya shi ya ruski Zameer, mummunan faɗuwar gaba wani abu dake nuna ban shirya rasa ki ba shi ne yake ji yana matse masa zuciya. Ganin idanunsa ya sauka a kan jaririn dake hannun Hanne ga Ridayya a kwance ga jinin dake zuba ta jikinta ya saka ya ƙarasa wajan da sauri ƙuri har lokacin yana kallon halittar Ubangiji wacce kamar a kan Jaririn na Ridayya aka gama kyau, wannan shi ake kira da baƙar tukunya mai fidda farin tuwo. "Ke Hanne wannan yaron fa? Ina kika same shi?" Domin shi zaton shi ko jaririn da Khairy ta kawo ne ya yi masa kallon tsoro da farko? Wancan baƙi ne yanayin halittarsa har ta ɓaci sosai ga shimfiɗeɗen baki ƙaton goshi kamar irin yaran ruwan nan wannan kuma zaka iya cewa haihuwar Larabawa ne irin usul ɗin nan. "Matarka ta haife shi yanzu fa Giɗaɗo, kaga da mun yi aure da tuni ni ce na haifa maka wannan kyakkawan babyn" Mamaki ya kusa kashe Zameer sai ya dake ya kama Ridayya ta yi saurin ƙwace hannunta da ƙyar ta buɗe baki ta ce "Karka taɓa ni, Hanne kar ki kuskure ki bashi ɗa na don girman Allah" Zameer ya ja tsaki sosai bai tsaya jiran me zata ƙara cewa ba ya sunkuce ta ya yi waje da ita zuwa can shargalan asibitin da suke da shi a gefen ƙauyen Batsari. Hanne ta rungume jaririn a ƙirjinta tana jin ƙaunar yaron na ratsa ta, dukda ta san zafin ciwo ya saka Ridayya cewa ta bar mata shi amma da gaske take ji inama ta bata shi? Amma ya za a yi mummuna kuma baƙar mace ta haifi wannan yaron? "Ikon Allah" Hanne ta furta a fili. Ta juya ta kalli yaron da aka yasar a ƙasa yana ta tsala ihu da alama shima bai jima da zuwa duniya ba, ta juya ta kalli Iyatu ta ce "Haba Iyatu kun bar yaro yana kuka a ƙasa? Akwai karara a gidan nan fa" a harzuƙe Iyatu ta ce "Me ɗin zan taɓa? Wannan halittar Allah ya sauwaƙe, uwar Giɗaɗo ma bata taɓa shi ba sai ni da nake kishiyar uwarsa? Ai idan kin ganni a lahira wallahi kai ni a kai, gidan da kowa gashin kansa ya ke ji ya je can ya gama ta zubar ɗinsa a kawo shege ki ce na taɓa? Zunubin zan taɓa Hanne kema da zan ba ki shawara da kin haƙura haka nan kin yi auren ki, domin Giɗaɗo ba irin arziƙi bane tun yana ɗanƙaramin shi yake ƙoƙarin hakkewa yaran ƙauyen nan da gayya Malam ya kai shi bara ba? Ashe iskanci kawai yake zubawa a can birnin Kanon" Wuff iya mahaifiyar Giɗaɗo ta fito daga ƴar bukka tana riƙe zani dake neman kuncewa ta ce "Baƙin ciki kike da ɗaukakar Giɗaɗo ya je birni ya yi ilimi na boko ya nemo mace mai ƙashin arziƙi ai ya bani labarin komai nan da ɗan ƙaramin lokaci jirgina zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki" Sai kumfar baki take yi ita ɗaya. Iyatu ta buga cinya tana ajjiye abin kaɗin adudiga tare da yin shewa da tafi ta ce "Anzo wajan daidai wajan ma, ai ba girinrin ma ta yi ma, idan kuma kaga baƙin maciji ko baƙar leda ka gani ka shafawa hanyarka lafiya,ina ƙoda ina romansa?...," Wata shewa Iyatu ta sake yi tana juya ɗuwawu ta ce "Riiiiiiii arziƙi kashi idan irin wannan arziƙin dana gani yau an kawo muku shi ne arziƙi to umma ta gaida assha, wai shi ɗan gidan mai dallla ne ko me?" Kafin ka ce me tuni sun hargitsa ɗan gidan nasu Hanne ta lallaɓa ta gudu da jaririn Ridayya zuwa gidansu domin ba zata iya da wannan azabar tasu ba, ko kunyarta sam basa ji. Da ƙyar jinin ya tsaya aka ce za a ƙara mata wani dukda bata cikin hayyacinta furr cewa ta yi bata buƙatar jinin Zameer a jikinta bisa dole Dr ɗin ya haƙura akai mata allura ya bada magani kasancewar asibitin komai na masu haihuwa kyauta ne a haka bacci ya ɗauke ta. Dr ɗin ya dinga kallon Ridayya ko mutuminta ke bashi mamaki ko tsofan da ta yi shi kaɗai yasan abinda yake masa yawo a zuciya. Kwanan ta biyu cikin asibitin aka sallame ta ko inuwar Zameer bata marmarin kallo balle fuskarsa, sai yanzu kuma yadda ta samu Zameer ɗin shi da Khairy matsayin turmi da taɓarya ya dawo cikin tunaninta kamar mai cutar mantau haka abin ya kwanta a ranta sai dai wani irin zafi da ciwo da zuciyarta ke yi mata. Tana shiga gidan sukai karo da Shatu, Shatu ta faɗi ƙasa tana birgima da ihu a gigice Iyatu ta fito daga ɗakinta ganin Shatu a kwance ga Ridayya a tsaye a gefe ta fasa kuka ta ce "Ta kama mini yarinya mayya ta riƙe mini kurwar Shatu" "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Shi ne abinda Ridayya ta faɗa a zuciyarta shin wacce kalar rayuwa take ciki ne? Me ya sa al'umma da mijinta da ƴan'uwanta suka kasa yi mata uzuri ne me ya sa har yanzu bata ganin daidai ne? Yaushe za ta yi farin ciki kamar kowa yaushe za ta samu ƴan'cin kanta ne yaushe zata bar wannan rikitaccen ƙauyen dake neman kashe da ranta da nasu kalar ƙazafin. Iyatu ta finciko Ridayya ta ce "Wallahi sai kin sakar mini kurwar ɗiyata shegiya mayya baƙar muguwa mai baƙar aniyya" Ridayya ta kasa kuka ta kasa cewa komai sai kallon Iyatu take tamkar zautacciyya ta saka hannu ta tsinka mata mari ta ce "Dai na kallona makira danginki ma sun guje ki balle mu? Mayya kawai" "Wallahi ni ba mayya ce" "Ƙarya kike ai mu da baƙin mutum muke gane maye" Sai a lokacin Iya ta fito hannunta ɗauke da Harazimi dake ta wangale baki yana tsala ihu Ridayya ta kalli yaron ta ce "To kenan bani kaɗai bace mayya ga wani nan ma" Iya ta ce "Jikina ba maye bane, ki ne mi can maye kuma ki zo ki faɗi uban ɗan da kika haifa ni nafi zaton ma mu can muna surutu kikai mata sauyin yaro ko aljanu sukai muku musaya" Zameer dake tsaye ya jingina da jikin garo ya ce "I was thinking the same thing Iya, Ridayya baƙa ce kuma mai muni kamar dai ɗan hannunki, ni kuma fari ne kyakkawa haka ma Khairiyya fara ce tas haka iyayenta to tayaya za mu haifi wannan ɗan? No way ki bata wannan Harazimi yake ko waye? Ki amshi farin ɗan wajanta domin babu yadda za a yi ta haifi ɗa kyakkawa" "Amma ban taɓa ganin zalunci irin wannan ba, a kan idanuna ta haihu na yanke cibiyar kar ku rabata da yaronta wallahi zan tuna muku asiri" Ta fashe da kukan tausayin Ridayya kamar jininta. Zameer ya dakawa Hanne tsawa tare da ƙwace ɗan daga hannunta ya ce "Ki dai na yi mini shisshigi cikin iyalaina Hannatou" "Su waye iyalan naka? Ni da nake matarka ko fasiƙar da kuka haifi ɗa babu aure kuma ta hanyar zina? Ko kuma ita data kasance tana son ka kuma budurwar daka yaudara waye iyalin naka daga cikinmu Giɗaɗo?" "Ki daina ce mini Giɗaɗo ban so zan watsa miki tafi wallahi" Iya ta ce "Saurara ita kanti take ko kairi ai matarsa ce kamar yadda kike matarsa cewa ta yi dole sai an raba auren ba zata iya rayuwa a ƙauye ba shi ne yanzu data haihu ta kawo ɗan" Ridayya ta kalli Zameer ya haɗe fuska ta kalli Iya ta ce "Ban yi mamaki ba tunda shi ɗin Munafikin miji ne, amma wallahi ba matarsa bace" Nan da nan Zameer ya sauya fuska ya ce "Sharri Ridha? Duk zafin kishin ne za ki haɗa ni da laifin aikata zina?" Ya zaro wayarsa ya shiga nunawa Iya pictures ɗinsu da Khairiyya wasu a kwance wasu suna rungume da juna wasu suna kiss abubuwa dai na ma'aurats ya ɗora da cewa "Wallahi matata ce sharri zata ƙulla mini" Ridayya ta kasa magana Iya ta hau masifa tana cewa "Ke dai ba matar rufin asiri bace ki dinga aibata mijinki, ai ya faɗa miki komai da Allah da Annabi kika haɗa shi domin ya aureki kin rasa mijin aure to Allah yasa yana raye balle ki yi masa sharri, wannan tsinanen baƙin ɗan naki kowa ba lallai ya yi albarka ba kuma ba zan taɓa amsar shi matsayin jikina ba wallahi, gona ɗaya tal Malam yake da ita idan ya mutu ita Giɗaɗo zai mallaka ko Giɗaɗo ya mutu ki rubuta ki ajjiya bashi da gado, mai farar ƙafa" Ta taga Iyatu ta leƙo ta ce "Tunda shi kaɗai Malam ya haifa dole ki ce gonar gantalallen ɗan ki zai mallake ta" Faɗan ya koma tsakanin Iya da Iyatu Ridayya ta shige ɗaki wani abu ya tukare mata. Tun daga ranar bata da walwala damuwarta ta tsananta tsakaninta da ɗanta wanda har yanzu bata san sunan da aka saka masa ba sai kallo daga nesa ko kuma idan zata bashi nono, a ranta ta jima da bawa ɗan suna Muhammad-Bilal. Harazimi kowa yana ɗan girma muninsa na ƙara bayyana bisa dole take shayar da shi domin ba zata iya barinsa da yunwa ba. Watarana iya idan ta ɗauke shi sai ta daddoke mazaunansa ta tallaƙe masa ƙewa, tana ji za a dinga yi wa Little Bilal waƙa ana irin arziƙi irin albarka haihuwar farar mace ko da ka sha nonon baƙar mace sai ka ƙara fari gwanin ban sha'awa. Iye iye kamo mini shi nan. Irin wannan waƙen ya kan sanya Ridayya ɗan mursawa kaɗan. Har yanzu kuma tabon ƙonar da Zameer ya yi mata yana nan wani lokacin ya yi kamar zai tashi wani lokacin kuma ya addaba mata da ƙaiƙayi. Hanne ta ɗauki ragamar dafa mata zugala ta ci ta sha ruwan. Tana zaune Zameer ya shigo hannunsa ɗauke da Little Bilal kamar ana ƙara masa girma sumar shi babu inda ta bar ta Ustaz yadda kasan Ustaz ne ya yi cikin ɗan ko kuma ya yi kaki ya tofar ba inda ya ɗauki kamar Ridayya sai ta Idanu, amma girma faɗi hanci baki dimple sumar kai da jerin yatsun hannu gabaɗaya irin na Abbiey ɗinta ne Muhammad-Bilal Tahir Rano. Ta ƙura wa yaron Idanu wanda yake ta kallonta gashi da ƙiriniyya hannunsa baya zama waje ɗaya duk sanda Zameer ya ɗauke shi ya dinga kuka kamar zai mutu. "Ridayya ki faɗa mini gaskiya ni na san da gaske wannan ɗan ki ne, kawai na yi hakan ne domin ki san har yanzu ni nake da iko a kan ki kuma ba zan taɓa bari ki zama wata ko ki ji daɗin rayuwa ba muddin ba ki mini yadda nake so ba" Ya yi shiru can kuma ya ce "Me ya sa kika haifi ɗa mai kama da wannan Ustaz ɗin? Ko akwai wani abu saɓanin abinda na sani kullum cikin firgici nake kwana kamannin Muhammad-Bilal dana wannan yaran kullum ƙara bayyana suke a Idanuna, kin taɓa tarayya da shi ne?....," "Zameer!" Ridayya ta kira sunan Zameer tana jin sunan har tsakiyar kan ta, jikinta na wata kalar Jijjiga da ɓari bata so tunaninta a kullum da kuma maganganun Zameer su samu tasiri da gasgata zuciyarta. "Ai yadda kika iya bani kan ki a waje babu mamaki da auren naki ba za ki iya" Ridayya kallon Zameer kawai take ta kasa cewa komai, idan shi ɗan iska ne to Abbiey ɗinta mai tsafta ne ba zai taɓa shiga gonar da bashi da hakƙi a kanta ba. Ya gyara murya tare da fara zubar kalamai masu sanyawa ka yarda da mutum haɗi da kalaman soyayya "Bana jin daɗin yadda muke ba haka nasan ki ba, kina faɗar sunana kai tsaye saboda Kinga ina son ki ko? Ki bari mu dawo da rayuwarmu ta baya please ki bani wannan kadarorin na fara juya miki" "Idan na baka zaka sake ni?" Domin sakinsa da warware igiyar auren kawai take muradi. Zameer ya yi tunani ai sai ka rubuta takardar sakin a rubuce ya zamana an yi sakin na halak bari ya yi da baki ya mata wasa da sakin, domin har ransa yake ƙaunar Khairiyya kuma yana da tabbacin ta yi masa nisa ba zata taɓa auren shi ba. Hanne kuma so yake kawai ta fahimce shi suyi rayuwa irin wacce sukai da Khairiyya. Ridayya kuma zata zama lover bed ɗinsa har abada ko baya sonta zai ci gaba da zama da ita yana samun ni'imar dake tattare da ita, ga dukiya ga farar mace a waje ta sawa a gaban mota, ga abokiyar gado shikenan. "Idan sakin kike buƙata zan yi miki dukda ba a son raina ba rabuwa dake azaba ce a zuciyata" Ta miƙe ta warware wata atamfa tare da ɗakko takardun ta ajjiye a gabansa ta ce "Ka bani ɗana ka sake ni ga takardun nan, ka sani dai dukiyata ce" "Na sani ai juya miki ita zan yi dukda ba ki da wani ilimi balle qualifications masu kyau" Ya miƙa mata Little ta rungume shi tana sakin ajjiyar zuciya tana jin kamar Abbiey ɗinta take gani a gabanta. Zameer ya kwashe takardun ya ji daɗi babu wasu shaidu balle suga lokacin sakin da lokacin bada takardun. Ya miƙe zai fita ta ɗan yi gyaran murya alamar tuni. Ya tsaya haka kawai faɗuwar gaba ta tsananta a zuciyarsa yana jin kamar wani abu mai mugun muhimmacin zai rabu da shi a rayuwarsa a hankali kamar zai yi kuka ya ce "Na sake ki saki ɗaya" Ya nufi fita sai kuma ya tsaya ya ji bari ya ƙara ɗaya kawai ai duk cikin wasa ne "Na ƙara miki ɗaya, biyu kenan ki ke na sake ki Ridayya sai naga inda za ki je ki zaune wanda ya fi nan, naga wanda zai taimaka miki kuma ya zama jagoranki duk inda za ki dole waje na za ki dawo ni kuma na zama dolen ki my dear Ridayya! Ni ɗin nan ne ya zame miki dangi, ba za ki taɓa zama wata ba a duniyar ba za ki taɓa samun mijin daya kai ni kyau ilimi nagarta mai kuma jure zama dake ba" Da sauri Hanne data raɓe a bakin ƙofa ta dafe ƙirji hawaye na zubo mata sai kuma ta yi waje da sauri daman jama'ar gidan duk suna gona. Tana fita Zameer ya fice zuciyarsa fari tas mafarkinsa yau ɗin ya cika. Ko wacce mace na jin zafi da baƙin ciki da wani irin wani abu a zuciya idan kalmar saki ta gitta a tsakanin aurenta. Amma Ridayya zuciyarta fes dukda tana mai tunanin inda zata nufa idan bata da hakƙi tabbas Ubangiji zai nuna ikonsa zai bata miji nagari amma gabaɗaya a yanzu ta tsani MAZA gani kowa take tamkar Zameer kuma zai kasance MUNAFUKIN MIJI. Daman ita babu wani abu data sani don gane da so balle har ta ji ba zata iya rabuwa da miji ba. Bata san mene so da yadda ake gane shi ba, ba kuma tasan wanne namiji ne zai iya bata hakan ba koma waye dai bata buƙata wajen Abbiey ɗinta kawai da yana raye take son komawa. Suna zaune cikin haɗaɗɗan gidan da suka sauya ya ɗan gyara zama fuskarsa a dame ya ce "Na yi wawta ban ɗauka haka ce zata kasance ba, na yi tunanin wannan plan ɗin shi ne zai dawo da rayuwarta cikin ta Babban mutum, na jima da gane su ɗin tamkar rayuwa da mutuwa ne, kamar kuma numfashin juna su ɗin ƙaddararsu tana tafiya ne da rayuwar ko wannen su, kamar yadda nake bibiyar rayuwar Babban mutum haka ta Ridayya sai dai na yi sake ta zilla mini garin gyara kuskuran da na yi na ƙara cilla rayuwarta cikin wani hali....," Kasa ƙarasa maganar ya yi saboda zafin da zuciyarsa ke yi masa ya sunkuya yana haɗe yatsun hannunsa. Can ya miƙe yana safa da marwa ya ce "Ban zama uban ƙwarai ba, na yi dana sani a rayuwa wacce bata da wani amfani where is she?" Abokin nasa ya ce "Kar ka ce haka Alhji Mansur ni na yarda plan ɗin nan zai yi working Ridayya zata neme ku da kan ta kamar yadda ta kuje muku, zata nemi Ustaz idanu rufe kamar yadda ta watsar da shi a baya, zata gane danginta da iyayenta sune gaba da miji a rayuwa, zata gane babu wani da yake son ta da gaske tsakani da Allah irin Ustaz" Alhaji Mansur ya sauke numfashi ya ce "You are right Barrister, amma sai yaushe ne komai zai yi daidai wake da hannu wajan rabani da ƴata? A ina take yanzu ina tunanin zan nemi Babban mutum na bayyana a gare shi" Da sauri Barrister ya ce "Mekenan akai? Baya ta haihuwa ai no no please don't do this. Idan Babban mutum ya san You are still alive ba zai saki jiki da dukkan zuciyarsa ya nemo Ridayya ba, kuma ba zai amince da ya aure ta ba, musamman da ka ce tunda yake bai taɓa faɗawa kowa yana son Ridayya ba ko?" Ya yi maganar yana kallon Alhji Mansur ɗin da ya yi can ya ce "Haka ne" "Ka yi haƙuri kamar plan ɗin mu ya yi going please na san da zafi but ka daure" Sallama sukai da Barrister shi daman Baba ƙarami bai ce komai ba jinsu kawai yake. Alhaji Mansur ya mance ma wani girkin Ammi ne ya nufi ɓangaren Mami ya sameta zaune ta yi wanka ta shirya hannunta riƙe da azakar idanunta ya yi jajur kamar kodayaushe ya nemi kusa da ita ya ce "Kukanne?" Ta girgiza masa kai ya saka hannu ya kamo fuskarta a tafin hannunsa ya juyo da ita suna shaƙar ƙamshin da numfashinta juna ya ce "Haba Zara'una ya kike so na yi ne? Ni ma na yi kukan ne?" Ta kama hannunsa ta ɗora a ƙirjinta ta ce "Baffa bana jin daɗin zuciyata ina son ganin Ridayya na bata soyayya da kulawar data rasa ka taimaka mini" Hawayen ya shiga goge mata ya rungume kawai ya kasa cewa komai a hankali ya yi magana a kunnenta ta yi saurin dukan ƙirjinsa ta ce "Uhm ni ka bari" Yau tunda ya shigo gidan ba sauƙi ko abinci bai ci ba, ya juya ya sake juyawa ya miƙe zaune a tsakiyar gadonsa ya koma ya zaune ya sake tashi ya nufi gaban madubin bedroom ɗin nasa. Ya zubawa kan shi idanu sai kuma ya langwaɓar da kai yana marairaice fuska da sauri kuma ya juya fara sakkowa daga strains ɗin benen mother da wata mata suna zaune ganin ba ita ɗaya bace nan da nan ya haɗe fuska ya koma armchair ya numfasa "Sadauki ya aka yi ne? Yaushe ka shigo?" Ya yi shiru bai yi magana ta juya ta ce "Atika ki dawo gobe mu yi magana ok?" Sallama Atika ta yi wa Hajja Azizat Sadauki ya zauna yana ɗora kansa a cinyar Hajja Azizat ya ce "Ta ƙi barin idanuna me ya sa kullum take zuwa ne?". "Wakake magana ne?" "Na san dole ta faɗa miki wace ita dole ne mother ki bani address na je ta faɗa mini dalilinta na shigowa bedroom ɗina?" Hajja Azizat ta saki baki ta ce "Sadauki wata nawa da yin hakan baka manta ba?" "Sai na rama zan manta fa" Ya koma ya kwanta a cinyarta yana tuna ɗazo kamar motar Prof ya gani ta shiga Bristol hotel ya share domin ai Prof ɗan business ne za a iya ganinsa a ko'ina. "Ɗaga mini cinya malam" ya juya yana cewa "Allah ya kawo wacce zata kula da Sadauki" "Amin. Domin na ga ji sosai da ganin haka kai baka girma kullum rikici da rigima da jama'a sai zuciyar masifa ga ɗan banzan kishi gwara ka yi auren macen ta lillisa mini kai ko ka nutsu" Tun safe sai yanzu Sadauki ya yi murmushi wai mace ta lillisa shi ya lumshe idanunsa ya ce "Duk sanda na yi aure ban ƙara kwanciya a cikiyarki sai ta matana, kike ta mini gorin haihuwa and kuma soyayyar da zan nunawa matana shi kaɗai ya isa ta nemi yafiya waje na ban iya son abu ba Mother ki mini addu'a ina da matuƙar kishi a kan abinda nake so" Ta shafa kan shi ta ce "Allah ya yi maka albarka Hamzana Sadauki jarumin jarumai mai tarar zaki cikin dokar daji" "E na tari zakanyya kin hanani mother. Amin Ya Allah love Allah ya ja da ranki kiga zuri'ar Sadauki" "Allah ya amsa. Commissioner ya shigo Nigeria kasan watansa biyu baya nan, mun yi waya ya ce yana nemanka" Nan da nan Sadauki ya haɗe fuska ya ce "Gaskiya ba zani ba, ƴarsa masifar surutu ne da ita kuma ni bana son ka nemi juya ni" A can ƙauyen Batsari yamma sakaliyya wasu mutane a babura sukaiwa ƙauyen tsinke kamar yadda suka saba hankalin jama'ar ƙauyen ya tashi domin sun san ƴan kidnaping ne ko masu kwashe musu shanu. Gida bayan gida suka dinga shiga suna kwaso yara da mata duk wanda ya yi yunƙurin hana su nan take suke kashe shi. Cikin rashin sa'a suna tsaka da al'amarin da kwashe jama'a manyan motocin jami'an tsaro sukaiwa ƙauyen tsinke suma daman sun zo bincike ne da kuma kawo musu taimako wanda kuma Commissioner da kansa ya buƙaci zuwa da jagorancin tawagarsa. Musayar wuta aka fara dukda ƴan sandan sun yi nasarar kashe wasu da kama wasu amma kidnappers ɗin suma sun yi nasarar tafiya da wasu. Daga can kuma Zameer ne ke cewa "To ai sakin wasa ne bada gaske nake ba, BAN SAKE KI BA" kallon baka da hankali kawai Ridayya ke yi masa Allah ya bata iko ya riƙe Little Bilal a hannunta dukda jirin dake kwasarta saboda rashin jini ba ta yi ƙasa a qiwwa wajan barin inda Zameer yake ba da gudu. Ya mara mata baya "Wallahi ban sake ki ba duk inda kika je za ki dawo ne sakin wasa ne ba" Kasancewar bata gani yasa gudu kawai take ta ƙanƙame ɗan ta duk yadda suke mata horn bata ji ba. Driven ya yi ƙoƙarin kauce mata amma ina bai ankara ba sai ihu da ƙarar faɗuwarta suka ji. Ya ajjiye wayarsa da yake tura information na gaggawa ya ce "Ya akai?" "I am sorry DCP TAJJ MUJID BAITA mun kaɗe wata mata ne... Nimcyluv sarauta *MUNAFUKIN MIJI 26* Mikiya Writers Ass Bright pens free batch Nimcyluv *Masu wattpad a dinga following ɗin Account ɗina (profile) a kai ni 5k follower🌚 kunga ai kwana biyu ina ƙoƙarin posting* https://www.wattpad.com/1425391962?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv "Accident? Mace da yaro?" Tajj dake bayan mota ya furta hakan, haka kurum gabansa ya faɗi bai tsaya an buɗe masa motar ba. Ya ajjiye wayar hannunsa ya fito da sauri yana gyara zama suit ɗin jikinsa ya ce "Subuhanallahi garin yaya aka bugeta? Is she alive?" "Sir mun yi ƙoƙarin kauce mata amma mun kasa, da gudu ta shigo gabanmu kamar mahaukaciya ce ma ga baby a hannunta" Tajj ya dinga kallon wacce ke kwance dukda abin bigeta amma tana ƙanƙame da yaronta wanda ya haska baƙar fatar jikinta. Ya ɗan juya kafin ya kalli sergeant Tukur ya ce "Katsina to Kano awa ne zai ɗauke mu ne?" "3 hr (176.0 km) Sir" Ya yi jim sai kuma ya ce "Zata wahala har tsayin awa uku, ina tunanin za a yi booking Flight ni da ita da babyn kafin ku ƙarasa mun je asibiti" Cikin girmamawa Sergeant Tukur ya ce "Yes sir" Tajj bai tsaya tunanin wani abu ba ya ɗauki Ridayya ya sanya ta abayan mota, har lokacin bai ga fuskarta ba kawai ya samu kansa cikin mummunan faɗuwar gaba ne. Little Bilal kuma yana wajan sergeant a haka suka nufi masaukinsu kafin a samu booking Flight ɗin ya zama ready. Cikin sa a suka samu jirgin da yake shirye da tashi har airport suka kai su a kan idanunsu suka shiga jirgin kuma basu bar wajan ba har jirgin ya tashi da D.c.p Tajj Mujid Baita da Ridayya da kuma babynta, sai sergeant da aka sanya shi cikin tafiyar saboda yaron, lokaci zuwa lokaci Tajj Baita ke kallon Ridayya da fuskarta take a rufe mamakin hakan ya cika sergeant domin ya fi kowa sanin waye Dcp ɗin baya shiga lamarin mace da sai dai idan harkar taimako ne yadda ya nuna tausayi da attention ɗinsa lokaci guda a kan Ridayya shi ne ya fi bashi mamaki sosai. Aminu Kano Teaching hospital a nan aka kwantar da Ridayya nan da aka sanya mata ruwa tare da yi mata gwaje-gwaje bayan kammala komai Dr ya kalli Tajj ya ce "Office please" "Ok" Tajj ya faɗa yana rufawa Dr ɗin baya jikinsa a sanyaye ya shiga ya zauna sosai kafin Dr ya kalli Tajj ya ce "Allahamdulillah mun kammala bincikenmu a kan wannan yarinyar?" "Yarinya Dr?" Dr ya jinjina kai ya ce "E, yarinya zai wahala idan ta cika 17yrs daidai ma. Akwai abubuwan da take buƙata sosai" Tajj ya yi shiru jin hakan ya saka Dr gyara zama yana zame gilashin idanunsa ya fuskanci Tajj sosai ya ce "Sir da farko tana buƙatar jini a ƙalla leda huɗu kenan,abu na biyu ta samu ƙari a wajan haihuwar da ta yi amma ba a kula ba domin wajan ya ɗan fara kamar ruwa zamu wanke kuma a yi mata ɗinki, a ɗinke wajan tas. Tana buƙatar hutu domin samun nutsuwar zuciya data kwakwalwa idan ba haka ba tunaninta na iya gurɓata ainun ko Depression ya kamata saboda bincike ya nuna mana tana cikin damuwa da ƙuncin zuciya duk wasu alamomin cutar damuwa sun gama bayyana tattare da ita" "Dr na ji ba damuwa, a yi komai kawai" dr ya girgiza kai ya ce "A'a sir maybe da kwai wani abu ka fara shiga wajan yarinyar ka ganta ko?" Ya ɗan ɓata fuska yana jan kujerar baya domin duk a gajiye yake ga wani irin bacci dake damunsa a kasalance ya ce "Ba sai na je ba ina tunanin ka tattara baya nan kuɗin ka bawa sergeant" "Ka dai shiga" Ganin yadda dr ya takura ya miƙe ya nufi ɗakin da aka ajjiyeta na musamman. Tunda ya ɗora idanunsa a kan fuskarta jikinsa ya yi sanyi ya ƙura mata idanu a hankali kuma ya ci-gaba da takawa zuwa gaban gadon zuciyarta na harbawa da ƙarfin gaske "You?" Ya furta daidai da kunnensa a zuciyarsa yake cewa "Finally i got you" Wani irin tausayinta nan take ya mamaye zuciyarsa baya son mace cikin wahala da rashin kwanciyar hankali, hankalinsa tashi yake sosai musamman irin yarinyar da a shekarunta ba zai shige ace tana makaranta tana karatu ko gaban iyayenta ba, yana buƙatar sanin wacece wannan yarinyar, daga ina ta fito ina zata, last time ya ganta a Kano yanzu kuma ya ganta a Katsina meke faruwa? Dole akwai wani ɓoyayyen al'amari a cikin rayuwarta wacce ita kawai tasan hakan. Ya ɗan haɗe rai a fili ya ce "Ba na ce miki ki kira ni ba when you need my help? Shi ne kika ƙi ko gashi nan na same ki ba zan ƙara barinki ba sai na taimaka miki" daidai da kunnensa yake maganar kafin ya juya ya kalli dr ɗin cikin nutsuwa yake masa wani bayanin yana mai ɗan matsa hannunsa "Zan je gida na dawo kafin nan ka gwada jinina idan zai yi daidai da nata sai a ɗauka ga fuskarta ma kafin wani abinne ya sameta ko?" "Ƙona ce" Laboratory suka shige aka ɗauki jinin Tajj Baita domin a gwada ko zai yi daidai dana Ridayya daga nan sukai sallama ya nufi reception na asibitin kai tsaye ya samu driver na jiran shi ya shiga bayan mota aka nufi da shi gida. Kasancewar a gajiye yake ya saka ana parking ya fito yana zame ƴar saman rigar tashi a hankali yake tafiya kamar baya so har ya nufi ƙofar farko ya buɗe ya shiga ya sake tura ta biyu ya shiga babban parlourn gidan. Da gudu wata ƙaramar yarinya kyakkawa da ita ta tashi tana faɗin "Daddy daddy" Ya sunkuya ya ɗauketa yana cewa "Iyee ƴar Daddy kullum tana zaman jiran daddynta" Murna ta kama yarinyar ta ce "I miss You Daddy jiya na dinga kuka a kai ni wajanka amma Mahmah taƙi ya" Mahmah dake fitowa daga ɗaya parlourn ta ce "To farfesa komai a kai kamar kina kira ubanki ya dawo ki wassafa masa ko gulmarsa mukai a banza mukai" Yarinyar dai ta yi shiru ta lafe jikin babanta. Mahmah ta nemi waje ta zauna, shi ma Tajj ya zauna kusa da Mahmah ya ce "Barka da rana Mahmah mun same ku lafiya?" "Allahamdulillah Tajuddeen ya aiki? Ka zo lafiya" ya ɗan gyara fuska ya ce "Aiki sai addu'a kawai Mahmah ko jiya an kai hari Katsina fa sun kwashe ƴan mata wallahi" "Wannan ƙasata mu ko yaushe komai zai zama daidai? A dinga sace jama'a musamman ƴan'mata ga kashe al'umma ba gaira ba dalili idan zaɓe ya ƙaratu an dinga abubuwan da basa tafiya daidai" rufe idanunsa yana shafa kansa sosai. Jin ya yi shiru ya sa Nadra cewa "Daddy Uncle ya zo yana nan" Idan ta ce Uncle ya san wa take nufi kuma bai yarda da maganar ta Nadra ba, yasan halin surutunta Uncle ba zai taɓa shigowa Kano ba saboda ya tsani kano a yanzu ɗin kuma daman rabon Uncle ɗin da gidan su Tajj har ya manta. Don haka ya share maganar ta Nadra ya rufe Idanu yana ji tana jan samarsa. Mahmah dake zaune ta ajjiye remote ɗin hannunta ta ce "Ustaz bari a ƙarasa kammala maka tuwon ko?" Shiru kamar ba zai yi magana a hannun Tajj ya ji saukar muryarsa a nutse cikin kunnensa ya ce "No" Ya buɗe idanu sai kuma ya juya kallonsa ya sauka kan Muhammad-Bilal Ustaz dake zaune a saman kujera ya kishingiɗa a gefe kamar mai yin bacci fuskarsa a haɗe sosai tamkar bashi ne ya yi magana yanzu ba, dukda maganar bata arziƙi ba ce. Sosai Tajj ke kallo Ustaz ganin yau gwarjininsa ya fito ga wani irin kyau da ya yi ko dan bai taɓa ganinsa cikin wagambari ba? Getzner wagambari brocade ce a jikinsa sai ɗaukan Idanu take kana gani kasan an kashe kuɗi wajan siyan shaddar. Blue green ce ta yi wa farar fatarsa masifar kyau gashi saje da ƙasumba sun ƙara cika fuskanta ya gyara sosai sukai ma fuskar kyau nutsuwa da haibarsa ta sake bayyana ƙwarai a fili. Ya ɗan ɓoye shekarunsa ta hanayar tsare gira kodayaushe baya ƙaunar raini. Tajj ya haɗe fuska shima ya ce "Lallai Babban mutum kana ciki na shigo amma ba magana?" Ustaz bai ɗago kansa ba balle ya kalli Tajj ko ya kula shi a nutse kawai yake danna wayarsa shi bai ma san me yake dannawa ba kawai rashin sabo da yin maganar ne ya saka ya fara danna wayar. "Lallai ya yi maka kyau, ina yini ka zo lafiya zuwa yaushe?" A hankali ya ɗago idanunsa ya kalli Tajj sau ɗaya sai ya zame ganinsa ya yi shiru wasu daƙiƙo a shirun nasa can ya numfasa ya ce "Kana lafiya Tajuddeen?" Tajj ya watsa hannunsa ya ce "Lafiya lou nake Babban mutum ya leges kuma? Ban yi tsammanin ganinka a Kano ba, ka ci sa a ni ma yau na shigo gari" Ustaz bai yi magana ba don zancen na Tajj ya masa yawa "Mahmah a kawo mana abincin nan ki kawo man shanu daban ni ban so Friend dai yana so" "Ai da yake kai ne maybe ya ci, amma daman shi idan an ce abinci sai ya ce I'm full" Tajj ya yi dariya sosai ya ce "He is always full daman amma banda yau" bayan tashin Mahmah Nadra ta bi bayanta tana tsalle Daddy ya dawo, ta ƙasan idanu Ustaz ya bi Nadra da kallo yana so da ƙaunar yara a hankali ya lumshe idanunsa yana tunanin yaushe zai samu nasa ne? Me ya sa ƙaddara ta yi masa kutse tare da yi masa tabo a zuciya me ya sa a kullum ƙaddara ke bibiyar rayuwarsa ne? Ya san hakan tabbatacce ne kuma al'amarin Ubangiji ne, tarihinsa ba zai taɓa cika daidai ba dole sai da sunanta rayuwa da ƙaddara abu ɗaya ne kamar yadda karatun littafin yake abu ne mai wahala na rashin sanin meke ƙunshe a cikinsa, idan ka karanta wannan shafin ba zaka san mene a shafin gaba ba dole sai ka buɗe to lissafi haka ne yaƙini da wanzuwar karatun littafin ƙaddararsa dole idan anga sunansa a gaba kaɗan za a ga nata bashi da tabbacin da numfashi da tunaninta wani ya fi yawa a ƙirjinsa. Ya ɗan sauke ajjiyar zuciya a sauƙaƙe yana riƙe yanayin da yake ji wanda ganin Nadra ya dawo masa da shi. "Ga abincin fa ina ta magana". "Azumi" Ustaz ya furta a taƙaice yana ɗauke ƙafafuwanta ya tanƙwashe saman kujerar parlourn Mahmah da shi wani ɗan gata ne tausa yake buƙata a gajiye yake sosai, ba uwa ba uwa ba ƴan'uwa ba mata ba ƴaƴa Maybe bashi da wani rabo ne. Tajj ya ce "Me ya sa kullum cikin azumi kake ne Ustaz? Ba a gane azumin lada dana kai da kai? Kalli yadda ka rame ka saurara da yin azumin nan" "Kana da matsala da azumi na ne Baita?" Da sauri ya ce "Of course ina da shi ko dan lafiyarka" Ustaz bai sake magana ba sai da Tajj ya yi surutunsa shi kaɗai ya ga ji ko tari ya ji Ustaz bai yi ba kamar daga sama ya ji ya ce "Labarin yarinyar na zo ka bani, ka sameta? Wace ita?" Ya yi maganar ɗaya bayan ɗaya yana mai jan gemunsa Tajj ya ce "A'a, nama manta da ita wannan ne dalilin zuwan naka?" Kafin ya yi magana an kira Tajj an sanar da shi jininsa bai yi daidai dana Ridayya ba. "Shikenan zan zo" "Wai wanne labari kake da shi a kan Ridayya ne? Nifa bulayi nake bara a kofai ko ganinta na yi i can't recognize her saboda ko a picture baka taɓa nuna mini ita ba, kasa na fara tunanin ko dai son ƴar rainon taka kake yi labarin rainonta kawai na sani ba ita ba please ka nuna mini ita maybe ma na taɓa ganinta rashin sani ne" Ustaz ya miƙe ganin yana ƙoƙarin fita ya sa Tajj miƙewa ya ce "Ɗan jirani" Ustaz ya fita zuwa waje ya shiga motarsa mai kyau blue black ce mai baƙin glasses ya ɗan jima kansa kife a jikin hannun motar kafin Tajj ya shigo ya ce "Muje" a hankali Ustaz ya yi bismillah ya yi wa motar key suka fita daga babban gate kai tsaye Tajj ya ce "Aminu Kano hospital please" Ya sauya direction mamakin shirun Ustaz da miskilancin shi yake bawa Tajj mamaki. Suna ta ce ya ce "Mun yi magana da Hajiya ai ta ce lallai nasa ka nemo matar aure ko kuma duk wacce ta yi mata wallahi ta aura mata cikin watan nan, kuma ni na yarda ta maganarta wallahi ka nemo matar aure ko na ce ka bata zaɓi" "Ina ta magana ka yi shiru" Gabaɗaya Ustaz ya saki kan motar ganin yana neman kashe su jikin Tajj na rawa ya riƙe motar ya ce "Babban mutum mene haka kashe mu za ka yi saboda ka ga ji da rayuwarka?" "Wallahi zaka fita daga motar nan da gaske zaka fita mtwsss" "Commissioner guda kake wa haka? Tsawa fa yau guda yafiyar da kake nema wa jama'a bari na nemaka Allah ka yafewa Ustaz kar na kama shi na kai bayan kanta" har suka ƙarasa asibitin kamar an ɗinke bakin Ustaz yana kallo aka ɗauki jininsa leda biyu amma bai tambayi dalili ba, tambayar ma wahala take masa. Jiri na ɗan ɗaukar shi ya kifa kansa tsakanin cinyoyinsa. Mintina wajan goma ya ji muryar wani na mita.. "Tab gaskiya Yaya ka yi haƙuri i can't, jinina fa? Daman shi ne kiran da kake ta mini kamar zaka fasa mini dodon kunne" "Ni kake cewa zan fasa maka dodon kunne? Zauna a ɗauki leda biyu ai aikin lada za ka yi banda rigima da rikici mai ka ajjiye har cewa na yi ina nemanka ka ƙi zuwa wai kar na juya ka?" Ya haɗe fuska sosai "Da tausayi ɗaukan jini har leda biyu a wannan zamani salon ka saka wacce zan aura hasara, ni a faɗi nawa ne kuɗin na biya a siya kuma taimako ba sai mutum ya yi niyya ba" Tajj ya juya ya kalli dr ɗin dake ta dariya yana mamakin ƙarfin halin mai maganar commissioner guda yake faɗawa haka shi kuma Tajj ya san matsalar baya son allura ne duk wannan hanya-hanya ɗin "Lallai yaron nan au matarka? Oya zauna a ɗauki before i shoot your legs" ya ƙara yin kicin-kicin da fuska kamar ya ce ya shiga uku shi ya ɗauka ma bashi da lafiya ne da har ya kira shi zuwa asibiti ya zo "A'a kafa daina ce mini yaro shekara 30 ba kwana uku bane ni kaga ma bana jin daɗi na ci maiƙo yau Olser ta mini mugun kamu" Tajj ya dake ya ce "Dr ɗauki jinin please kar ka saurari maganarsa" Ya girgiza kai tuni ya rikice ya ce "A'a dole a ji reason ɗina idan ba gado kake so a bani a nan ba, kuma a bari na shirya" Kamar an tsikari Ustaz ya miƙe tsaye yana daddafe kansa yana jin kamar kansa zai rabe har tsakiyar kansa ya ke jin musayar yawun nasu ga wani jiri dake ɗaukarsa da ƙyar ya riƙe jikinsa ya fice. Da ƙyar ya bari aka ja jinin yana ta mita tunda aka soka allurar ya yi tsit fuskarsa ta sauya ana gamawa ya miƙe ya yi luuuu zai faɗi Tajj ya riƙe shi ya ce "Be careful" a ƙasan maƙoshi ya ce "Cika ni" muryarsa ba wasa ya haɗe rai tamau kai ka ce shi ne gaba da Tajj Baita ɗin ya nufi ƙofa sai da ya je ƙofa ya tsaya ya ce "Kuma wallahi sai ka biya ni ko na kwasa a kuɗinka" Yana faɗin hakan ya fice mamakin ƙarfin jininsa ya cika Tajj domin kamar bashi ne aka ɗauki jini har leda biyu a jikinsa ba. Nan da nan aka ɗaurawa Ridayya jinin Ustaz ya fara shiga jikinta bayan sun keɓe Tajj ya ce "Dr matsalar fuskarta da kuma fatar jikinta fa?" "Ina tunanin sai dai ku je asibitin Bela nan za ku samu likita mai kyau" godiya ya yi masa kafinwya fito daga Ustaz har mai mitar kowa ya shiga mota ya fice da ra'ayi iri ɗaya a zuciyoyinsu. Sanda Tajj ya ga Little Bilal mamaki ne ya cika shi banda yasan waye Ustaz babu shakka da ya ce wannan jininsa ne ko kuma ɗansa ya ɗauki yaron ya koma gida Mahmah ta yi masa wanka ta sauya masa kaya nan da nan Tajj ya shiga yi masa pictures da video yaron sai dariya yake yana lumshe idanunsa ya ɗora shi a status da caption ɗin _My lovely son_ Zirga zirga take yi hankalinta yaƙi kwanciya ta juya ta kalli Zuhura ta ce "To yanzu da kika dawo gida da zuƙar yara uwar me zan yi miki? Kina nufin kashe aurenki za ki yi ki zo ki tare mini a gaba ko mekike nufi" "To Ammi ni ya zan yi ne baya bamu abinci kullum cikin wahala nake gashi ni bani karatu na yi ba balle na samu aiki haka kurum yunwa ta kashe mu" Ammi ta ce "To ba kece ba tun ina lallama ki ko ƴar diploma ki haɗa amma karatu baya gabanki yanzu wa gari ya waya ki barni da abinda yake damuna mana" Zuhura ta fashe da kuka ta ce "Wallahi don ba ki san wulaƙancin da Nura yake mini bane a cikin gidan nan kamar wanda ya fara neman mata. Kwata-kwata bana jin daɗin zaman gidan mijina" "To dan ubanki ni daɗin zama nake a gidan uban naki, kina kallo yadda komai yake neman fin ƙarfina sai na yi kwana biyar a cikin gidan nan ban saka Alhji a Idanuna ba, sisi ta daina haɗa da shi ya tattara komai ya liƙe a gindin wancan shu'umar matar wacce ta gama a sirrice shi, ki duba ki gani wai don duk ya daidaita abubuwan da suka faru tsakanin Babban mutum da mummunan wannan yarinyar ya liƙa mana hatsarin ƙarya" Zuhura ta ce "Ammi ai ba hatsarin ƙarya bane kawai dai Allah ya kiyaye muna da raguwar numfashi da motar da akai hatsarin da ta mu iri ɗaya ce muna baya ɗaya motar na gaba ta mu ta shiga cikin jeji ki duba yatsan Khaliperh kusan cirewa ya yi, kuma ni ina maganar gidan mijina mene nawa da nan gidan fisabilillahi" A harzuƙe Ammi ta ce "To ba dole sai ina da kuɗi zan ji da matsalarka ba, addu'a nake Allah ya rusa farin ciki da daidaito ɗin dake tsakanin Baffa da Fatima, kuma muddin ina raye wallahi tallahi ko Ridayya na duniya ba zata taɓa zama wata a duniya ba kuma dole ne mu mallaki wannan kadarorin da aka bata gabaɗaya haihuwarsa yarinyar nan masifa ta zame mini" Zuhura ta cika ta yi fam ta ce "wannan mayyar mijin kike tunanin zata iya rabuwa da shi? Kila ta tattara ta mallaka masa dukiyar" "da kowa na yi ɗaiɗai da rayuwarta wallahi Ridayya ba zata taɓa zama wata a duniya ba, ai daman sai dai shi Zameer ɗin duk yadda naso kashe auren Burhan ya aureta abu ya gagara ni addu'a nake ma plan ɗin Alhji ya yi daidai dukda yaƙi faɗa mini komai ta dawo ta auri Burhan ai daman shi ne ya zama dole a yadda take uban wanne namijin ne zai aure ta ko shela akai matsayin kyauta babu mai amsar ta yin" Miƙewa Zuhura ta yi ta ja hannun yaranta a ƙalla ta yi ya ji sama da biyar gashi igiyar auren nata saura ɗaya tal da take lilo. "Kee Zuhura" Baffa ya kira sunanta ta tsaya ta ce "Na'am Baffa ina yini?" Bai amsa ba ya ce "Me ya kawo ki gidan nan? Asiri kike son tuna mana? Bana gaya miki bana son a san wani daga cikin ahlinmu na raye ba? Shi ne kike ta mini zurga zurga?" "Baffa ka yi haƙuri wallahi daman Nura.......," Caraf Ammi ta ce "Nuran ne baya gari ya ce ta zo gida kafin ya dawo" Baffa ya juya ko Ammi bai kalla ba ya ce "To ki kiyaye zan yi magana ta Nuran idan ba zai iya haƙuri har mu kammala ba kawai ya barki a gidan nan har zuwa sanda komai zai zo daidai" Yana faɗa ya yi sashin Mami. Ammi ta cije bakinta ta ce "Kin gani ko Zuhura ko inuwata Baffa baya son gani? Na zama mujiya to ni me na yi masa duk yadda na riƙe yarinyar nan tsakani da Allah?" "Ammi kin fiya mita shi Baffa kin taɓa ji ya miki maganar Ridayya ne? Duk kin damu kan ki" Miƙewa ta yi ta nufi ɗaki number Biba ta kira tana ɗagawa ta ce "Biba ko ba za ki dawo ƙasar nan ba ki turo mini kuɗina na wajanki ko miliyan biyar ne" daga cikin wayar Biba ta ce "Maryam babu kuɗin nan fa wallahi an sace" Wata uwar ashar Ammi ta ja ta ce "Kan uba ni za ki cewa ba kuɗi last kuɗin dana tura miki a ƙalla ya yi miliyan huɗu da rabi kuɗina a wajanki ban san adadi ba shi ne ki ce mini an sace na bi sata da gudu ba wando....," Ƙittt! Biba ta kashe wayar nan take kuma ta saka number Ammi a Black list. Satin Ridayya biyu cikin asibitin ta warke sosai aka sallame ta Tajj ya dawo da ita gidansu saboda ita yaƙi komawa wajan aiki dukda yana son zuwa wajan Ustaz can leges ɗin rabonsa da shi tunda aka ɗauki jininsa ko wayarsa ya kira a kashe yake jinta. Kulawa sosai yake bawa Ridayya Mahmah da kanta ta saka aka kawowa Ridayya sabbin abayas masu kyau da tsari wando da riga su english wears mayuka wanda aka rubuta mata a asibitin Bela bana saka fari bane amma nan da nan fatarta ta yi fresh daga tattarewar da ta yi ƙashin wuyan ya fara cikowa ta fara miƙewa sosai a kan ƙafafuwanta daga ɗan ranƙwafawar da ta yi hips ɗinta ya fara buɗewa zuwa asalin yadda yake. Tajj yana ƙoƙarin janta a jiki da son jin muryarta amma ko daga bedroom bata fitowa gaisuwa ce kawai ke haɗata da shi kullum cikin tunani take ko ta shagala da kallon Little Bilal. Gashi abinci mai kyau da gina jiki ake bata bisa tsarin likitoci ba a bata mai ya ji saboda bata son ya ji Kwata-kwata. Wajan watanta guda kenan sati biyu da tafiyar Tajj tana zaune a gaban madubi Little Bilal ya maƙale bayanta sai rigima yake mata ya hanata sakat kamar mai zazzaɓi dai kokawa take da gashinta da take son ɗaurewa take gashi wata ƴar ƙaramar riga ce a jikinta sai wani wando iya qwiwa tunda tasan daga ita sai Mahma ta saki gashin ta kalli kanta a madubi gabaɗaya babu tabon ƙonar fuskarta ta yi fresh asalin baƙinta mai kama da chocolate ya bayyana ashe duk wahala ce ta dafar da ita da rashin kula gashi yanzu data samu hutu da abinci mai kyau ga gado da a.c ga mayuka bisa yardar likita sai baƙin wahalar ya kai fatar sai glowing take baƙin gwanin sha'awa ga gargasar a saman fatar da sukai kwance luff gashin girarta kamar su haɗa dana juna, laɓɓanta yirrr jajur da su idanunta farare tas kamar tana ɗiga musu wani abu. Idan ka kalli fatar ta a time ɗin ba za ka yi sha'awar farar fata ba domin irin skin ɗinsu ke wahala a wannan zamanin. Sumarta har gaban goshi ta langwaɓe kai cikin siririyar muryarta ta ce "Abbiey me kake so ne?" Ta faɗa tana ɗaukar shi ta ɗora saman mirror sai ya fashe da kuka ta taɓa jikinsa ta ji zafi nan da nan idanunta ya cika da hawaye "Ka daina kuka please" Idan duk bata san me za ta yi wa yaron ba daman Tajj ke rarrashinsa idan yana rigima sai kawai ta fashe da kuka tana kifa kanta. Mamaki ya hana Tajj dake tsaye bakin ƙofa magana mene na kuka ita sam shagwaɓa baya yi mata wahala ne? Kodayake ai yarinya ce babu mai cewa ta haifi Little Bilal jikinta ya dawo ɗanye shi kansa ya san yana kashe kuɗi a kan ta. Ya ƙarasa kusa da madubin ya ce "Like mother like son, mrs crying" Ta kasa ɗago kan ta saboda kunyar kayan jikinta Tajj ya ɗauki Little ya rungume shi ya zauna bakin gado ya ce "Ka saka Mimi kuka ko? Mimi a taimaka a yi haƙuri kar a saka Daddyn Bilal kuka" Kamar ya ce ta ƙara sautin kukan nata ta sake fashewa da kuka Tajj ya miƙe ya nufi inda take ya zauna saman mirror ya ce "Mimi wannan kukan fa" ta yi shiru ya ce "Ɗago kan ki muga" Kasancewar ta ɗauke shi matsayin yayan data rasa a baya ya saka ta ɗago kanta ta kalle shi fuskarta jage jage da hawaye ya ce "Tsakani da Allah Mimi wannan kukan na shagwaɓa ne wannan ai ni za ki illata" Ta marairaice fuska a hankali cikin sanyin murya ta ce "Abbiey ke ta kuka shine na yi nima" Tajj ya yi saurin ɗauke abinda ke zuciyarsa a taushashe ya ce "Saboda ke ƙaramar yarinya ce ko? Waye zai rarrashi wani?" Ta yi shiru Ya sake rage murya ya ce "Ki daina ban so kukan nan, akwai sanda za ki yi na shagwaɓar ba yanzu ba" Ya ɗago wani magani ya bata ya ce "Kullum da daddare kina shafawa a lips ɗinki na ƙasa, wannan kuma Dynewell safe da rana za kina sha saboda na lura baki son cin abinci" "Na gode Yaya" Ya ta zaune ya yi yi wa Little Bilal pictures wani mai masifar kyau ya ɗora a status tare da emojin na love. Tun kafin ya fita yaga Ustaz ya yi viewing can yaga ya yi masa reply da. "Ɗan waye?" "Ɗa na ne mana, bani kaga na saka shi a status ba?" A taƙaice Ustaz ya ce "Bana son wasa ɗan waye wannan? Ka cire shi a status" Tajj ya ce "Me ya sa kake son jin ɗan waye?" "I just seen my photocopy, we look alike" Ustaz ya bashi amsa Tajj a fili ya ce "Ikon Allah" Kiran wayar Ustaz ya shigo wayar Tajj ya ɗauka ya ce "Wai ya naga duk ka damu ne tunda ka buɗe WhatsApp baka taɓa mini magana ba, sai yanzu? Abinda baka sani ba takwaranka ne wallahi sunansa Bilal" Tsit Ustaz ya yi can ya ce "His mother please? Kirani vedio call ka bani yaron mu gaisa" Tajj ya ce "Ba zan nuna maka ɗan mutane ba kuma.....," "Yaya Yaya Yaya" Ya ji ana kwaɗa masa kira ya ajjiye wayar saman mirror ɗin ya fita tsaye ya ganshi hannunsa riƙe da jita ya ce "Wannan kiran fa?" "To ka je ka wani shige ɗaki tun ɗazo na zo ni bana son jiran gaskiya ka sani ni sai naga me kake a ɗakin" kafin Tajj ya yi magana Sadauki ya shige cikin bedroom ɗin lokacin Ridayya na tsaye tana ta kallon wayar Tajj da ake kira a jiki an rubuta friend haka kurum ta ji tana son ɗaga kiran hannunta na rawa ta ɗaga tana kai kunnenta tare da yin shiru tana jiran a yi magana. A hankali Sadauki da yake tsaye riƙe da ƙugu ya ce "You?" "Sadauki zo ka fita" cewar Tajj ya faɗa idanunsa sun yi jajur Sadauki ya juya ya kalli Tajj fuskarsa a haɗe shima baya son Ridayya ta san yana ɗakin don sai ya rama yadda ta yi masa ya damƙi hannun Tajj kamar za su fita tare yana zuwa baƙin ƙofa ta tura Tajj waje ya rufe ƙofar tare da sanya mata key ya cilla makullin cikin Aljihu ya nufi inda take tsaye tana jin sautin bugun zuciyar Ustaz ta cikin wayar..... Share and share and share as so much as you can! Saboda masu tambaya sulaimanshuaibunaima@gmail.com 08164069385 *MUNAFIKIN MIJI 27* Mikiya Writers Ass Bright pens free batch Nimcyluv Sosai numfashinsa ke sauka a kunnenta ta cikin wayar dukda bata san waye ba amma tsigar jikinta ce ta shiga mimmiƙewa tare da tsastsafo mata da wasu zufa daga ƙofofin gargasar. Ta zame wayar a hankali ta tunanin ko an kashe kiran? But his still on the line, ta sake bin jerin haɗaɗɗun 11 digits ɗin da kallo ta mayar da idanunta kan sunan da aka sanya wa. “Friend” A sanyaye ta sake mayar da wayar tana tunanin ko za a yi magana amma har lokacin shiru yanayin sautin da take ji kamar mai wayar ya sauya muhalli na asalin inda yake ta ɗan marairaice fuska sai ta ajjiye wayar ba tare data kashe ba ta ƙara zubawa kan ta idanu ta cikin madubin. Tarin sauyin data samu daga barinta Batsari take kallo sai dai har yanzu babu farin ciki a fuskarsa ta zuciyarta kawai ƙoƙarin danne komai take kar ta nuna musu gazawarta dole akwai abinda take buƙata mai matuƙar amfani at least ko ba ta yi farin ciki ba a rayuwa a ce zuciyarta ta kusanta da wannan abun. Ta yi rolling fararen idanunta manya da su wanda suka sake yin sheƙe saboda kwantaccen ruwan hawayen daya cika su. Kamar daga sama ta ji an ce "So you're here all this time?" Duk wannan lokacin kina nan? Da sauri ta juya tana mai ƙoƙarin ɗaukar hijabi domin kai tsaye ta san ba muryar Tajj ba ce ya yi saurin ƙara sawa inda take tsaye ya riƙe hijab ɗin yana zuba mata rikitattun idanunsa a saman fuskarta. Ridayya ta sauya fuska domin sarai ta gane shi ta sakar masa hijab ɗin kunya duk ta gama cikata ita bada burin kowa ya ga jikinta ta juya zata shige bathroom ya saki hijab ɗin ya sha gabanta. "Ka bari" Muryarta can ƙasa ta yi maganar Sadauki ya haɗe duka girarsa guda biyun ya haɗe su waje guda tun daga sama har ƙasa yake kallonta zai iya cewa ba ita bace ganin yadda ta sauya lokaci guda jikinta ya buɗe fatarta ta yi fresh tana ɗaukar Idanu ga sumar kanta kamar ta Aljanu har ta yi mata yawa lips ɗinta ya rage girma. Muryarta da manyan fararen idanunta sune suka tabbatar wa Sadauki cewa ita ce babban dalili kuma shi baya mantuwa. Ya jima yana kallonta bai ce komai a hankali ya matsa gefe ya bata hanya ta shige bathroom ɗin da sauri kamar ta tashi sama. Ya zube gefen gado yana riƙe da kansa idanunsa rufe kamar yanzu ne ta shigo ɗakinsa tana tambayar wani yanzu kuma shi ne a ɗakinta ya kasa rama duk abubuwan daya shirya ya ƙudurcin niyyar yi mata ɗin bai san lokacin daya shafe yana zaune ba sai da ya ji muryar Mahmah a bakin ƙofa tana cewa "Hamza buɗe ƙofar nan ka ji ko?" Ya miƙe tare da nufar wajan ƙofar ya ciro key ya buɗe. Mahmah ta kalle sauyi ta gani sosai a tattare da shi, ya shigo da karsashi fuskarsa wasai yanzu kuma jikinsa ya yi weak fuskarsa a haɗe ya yi kicin-kicin. Ya shige Mahmah ya nemi waje ya zauna ita kuma ta shige cikin bedroom ɗin Ridayya. Tajj ya jujjuya cup ɗin hannunsa kawai yake yana jiran ya ki Sadauki ya yi magana ya ci ubansa ko ya juye duka abinda yake ji a ransa a kan Sadauki ɗin sai ya lura yaron ko inda yake bai kalla ba sai zama da ya yi ya manne jikin kujera yana rufe idanunsa. Tajj ya kasa jurewa ya ajjiye cup ɗin ya ce "Me ka shiga yi cikin ɗakin? Me ka yi mata" Sosai Sadauki ya ji tambayar sai kawai ya basar ya zaro wayarsa ya fara dannawa a ƙufule ya miƙe ya ce "Wai Sadauki ba da kai nake magana bane raini ko?" Ya ɗaga manyan idanunsa yana gyara zaman rigarsa da take a ɗan buɗe kallon Tajj yake bai ce komai ba. "Ina magana kana tsare ni da Idanu yaushe na zama abokin wasanka?" Ya girgiza kai ya ce "Ko mother bata mini faɗa mara dalili to a kan me kamar ka haifan daga shiga ɗaki za ka hau ni?" "Ni kake faɗawa haka?" Sadauki ya haɗe fuska bai ce komai shifa shiyasa bai damu da zuwa ba idan yana nan, saboda Mahmah kawai yake zuwa gidan. "Kadai san ko babu komai na girmeka kuma ni uba ne dole ka girmama shekaruna ko tashen girma kake ji sai na yi maka duka a nan wajan bama iya nan ba har gidan mother ɗin sai na je idan kuma Prof ke ɗaure maka gindi to" Sadauki ya miƙe tsaye saman ƙafafuwansa ya ajjiye wayarsa a saman kujera ya matsa kusa da Tajj ya ce "To bari kawai na zo ka dake ni mu gani" Har hucin juna suna juyowa daidai nan Mahmah ta fito tana rafka salati ta ce "Mene haka ne zan gani kuma ni Hajjara? Faɗa kamar wasu sa'annin juna ko abokan gaba" Sadauki ya juya idanunsa tuni sun sauya wani irin numfashi yake fesarwa dan dai ba zai iya taɓa Tajj bane amma da tuni ya watsa masa yatsu biyar a fuska. Har wani rawa jikinsa yake saboda ɓacin rai ya ce "Ya ce zai iya dukana ba tunda shi ya haife ni, bar shi ya dake ni" Mahmah ta yi salati ta ce "Wanne irin duka kuma Hamza? Shi Tajuddeen ɗin ya ce" Tama rasa me zata ce dalilin wannan rikicin take son ji amma babu alamar za su faɗa. "Nemi waje ka zauna Sadauki maganar ya shige bana son ji ai Tajuddeen gaba yake da kai" Ya cije lips ɗinsa ya tsune da alamar yana huce zafin zuciyarsa a kan su a hankali ya juya ya hango wani zare ya je ya ɗauka ya nufi Tajj ya ce "Ba ka ce Daddy yana ɗaure mini gindi ba ko? To gashi kai ma ɗaure ka ɗaure na ce" "Sadauki wai ba nace a bar maganar hakan nan ba? Ta shige" Ya runtse idanunsa ya buɗe ya tura hannunsa cikin sumar kansa ya girgiza kai ya ce "Ba zan samu nutsuwa ba sai ya ɗaure mini shi ma, idan kuma gadarar ka haifi Nadra ne ka zuba Idanu wallahi ni ma yarana sun kusa zuwa duniya" Bala'i kawai yake zubawa idanunsa na yin wani ruwa ruwa idan ya yi kamar zai daki Tajj sai ya yi saurin dunƙule hannunsa. Tajj kallon ikon Allah kawai yake shi ne mai laifi kuma shi yake yi wa wani faɗa yama kasa cewa Sadauki komai don takaici a ransa ya ɗauki niyyar dole ya yi amfani da uniform ɗinsa wajan tanƙwara Hamza ɗin. Kamar ɗaukewar ruwan sama haka muryar Sadauki ta ɗauke daga parlourn ya yi kicin-kicin don bai yi zaton za ta fito ɗin ba cikin ikon Allah kuma Ridayya bata ji ko kalma ɗaya ba ta ƙarasa shigowa cikin parlourn. A hankali ya nemi waje saman kujerar ya zauna yana harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya ya fara buga game a waya, ko inda Ridayya take bai kalla ba. Mahmah tana murmushi ta ce "Yawwa Mimi ai gwara kina fitowa sai ki yini a ɗaki kamar matar mamaci" Ridayya dai ba ta yi magana ba kanta a ƙasa Tajj ya kalli Sadauki ganin yadda ya yi ya sanya ya sauke ajjiyar zuciya ko babu komai ya san ba lallai Ridayya ta zama daidai da ra'ayin Sadauki ba domin zai iya shaidar Sadaukin duk abinsa mata basa gabansa sai dai su ɗinne suke liƙe masa. "Ridayya nikam mijinka ba zai neme ki ba kar hankalinsu ya tashi kina zama a gidan nan da auren wani a kan ki tunda kin ji sauƙi ko number mijin naki ne ki bayar sai a faɗa masa halin da kike ciki" gaban Ridayya ya faɗi domin ita bata ƙaunar koda wasa ta tuna da wani Zameer balle ta tuna zaman ƙuncin da ta yi a cikin gidansa da wahala da tuzarcin data fuskanta a tattare da jama'ar ƙauyen Batsari nan da nan idanunta ya cika da hawaye sosai Mahmah ta ce "Duk sanda na yi miki maganar mijinki sai ki fara kuka ko mutuwa ya yi ne akwai alamar tambaya a tattare dake, waye mijin naki" "Mtwsss" Sadauki ya ja siririn tsaki shi kansa bai san ya yi ba maganar damunsa take. Maganar Ridayya ta share abinda yake tunani faɗuwar gaba ta ruske shi inda take cewa "Mahmah ki mini alfarma a bar maganar zuciyata bugawa take" Muryarta ita kanta rawa take sosai kamar yadda jikinta ya ɗauki rawa tsoro take kar su ce za su mayar da ita Batsari ta ci-gaba da rayuwa da Zameer. Mahmah ta miƙe ta dawo kusa da Ridayya ta riƙe ta ta ce "Ridayya what are afraid of? Ki faɗa mini matsalar in sha Allah maganar zata zama confidentiality tsakaninmu" "Mahmah ki barta" Ya faɗa a taushashe ta ce "Sadauki an barta, amma ta faɗa mini ina mijinta" "Mun rabu, wata guda kenan" Ridayya ta ce tana runtse idanunta ta na jin hakan kamar sirrinta ne sai wanda ya zama dole ya sani Lokaci ɗaya Tajj da Sadauki suka kalli Ridayya With difference feelings. "Kina nufin ya sake ki? Zaman idda kike yi yanzu?" Ridayya ta yi shiru hakan ya tabbatarwa da Mahmah haka ɗinne ta girgiza kai ta ce "Allah alhakkamu sarki buwayi gagara misali yarinya dake ƙaddara ta sa kin san mutuwar aure? To Ubangiji ya sa kafin ki yi idda ya mayar dake ɗakinki Ubangiji ya takaita y rufa asiri mutuwar aure babu daɗi" Ridayya a zuciyarta ta ce "Ba amin ba" Gabanta ya faɗi sosai domin tasan idan har Zameer ya ce yamar da ita kafin ta yi idda to fa ta mayu ɗin har abada. Damuwa da ƙuncin zuciyarta ya ƙaru wani irin zafi da raɗaɗi take ci a ranta. Sadauki ya miƙe tsaye yana gyara zaman rigarsa Mahmah ta ce "Sadauki tafiya za ka yi?" Ya jinjina mata kai tare da ficewa Ridayya ta ji kamar an kunce mata jijiyoyin jikinta Tajj ya kasa cewa komai a ransa yana wassafa raguwar watanni daya ragewa Ridayya. Washegari da safe Tajj ya gama shirin zuwa Bampai duba bayan ya fito parlour ya tarar da Mahmah zaune tana gyarawa Nadra zoben hannunta ya ce "Mahmah ina Little ne?" Ta ce "Ai zazzaɓi yake fama da shi ya mannewa Mimi sai rigima yake" Ya zaro waya a Aljihu ya bawa Mahmah ya ce "Ki bata an saka mata sim da komai idan da matsala tana iya kira a gaida Junior" "To an gode Allah ya saka da alheri Tajuddeen" "Daddy zani" Ya kalli Nadra ya ce "Maza jeki ɗakko mini Junior ku zo kin ji" Ta tafi bedroom ɗin da gudu ba jimawa sai gata ɗauke da Bilal tana ta nishi domin ya fi ƙarfinta a haka ya ɗauke su pictures akan ya ajjiye Little Bilal ya dinga masa vedio yana ƙaunar yaron yana gama yi masa ya ɗora a status ya sa "Tubarkalla ahhasanulkaliƙin" Ya sanya emojin na crush da love kana ya sauka daga internet. Tun bayan wayar da Ustaz ya yi da Tajj da kuma sake kiran da ya yi a karo na biyu aka ɗakka babu magana sautin da zuciyarsa ta buga a lokacin ya bambanta da irin bugawar da take masa a kullum a kodayaushe. Baya son ya gasgata abinda zuciyarsa ke faɗa masa, domin babu shakka ko tantama dokawar da zuciyarsa ta yi irin bugawar da zuciyarsa ke masa ne a duk sanda ya yi Ustaza irin abinda yake ji kenan shi kuma ya ji a lokacin, ya yi shiru ne da zaton za a amsa a yi magana sautin numfashinta da ya ji ta cikin wayar ya sanya dukkan wata suma da take jikinsa ta mimmiƙe irin miƙewar da sai Ustaz ta raɓe shi yake jin haka, miƙewar data tuna masa har yanzu yana da sauran cikakkiyar lafiya irin ta ɗa namiji. A hankali ya mirignawa gefe idanunsa rufe a kan bed a hankali ya buɗe ido yana mai sake ɗauke zancen a ransa yana cewa “Asstaafirulla" domin azuminsa neman lalacewa yake haka kurum. "Ba ki mana adalci ba Ustaza" Knocking ake a bakin ƙofar bedroom ɗinsa tun ɗazo amma ya kasa tashi ya buɗe ƙofar can ya ji an daina babu jimawa kuma aka buɗe ƙofar aka shigo. Ya juya yaga Hajiya bisa dole ya haɗiye abinda ya yi niyyar domin ɗakinsa tsaraicinsa ne ko boxer ɗinsa aka gani ai kamar shi aka gani haka yake ji a ransa ta lalle shi sosai ta ce "Babban mutum na aiko Bintalo ta kira ka kaƙi buɗe ƙofa kuma kai kace a daina shigo maka kai tsaye gaba-gaɗi" Ya dai kalleta bai ce komai ba ta ɗora da "To wai wannan zufar ta magani da mece?" "Ta magani da kece mana" Ya faɗa yana haɗe fuska tsohuwar rikici da neman magana ya yi mata yawa ta ce "Ka yi baƙuwa ne, ka fito idan ba haka ba na shigo da sanda ya kura ka" Ta yi waje tana ƙoƙarin fita ya ce "Black tea da lemon please" Ta juya ta ce "Kamarya azumin fa?" Ya juya mata baya abinsa yana jin yadda zufa ke ƙara wanke masa kyakkawan jikinsa kamar mai shirin yin zazzaɓi. Ya ɗauki wayarsa da tun safe bai duba ba, dake akwai WiFi a gidan kai tsaye WhatsApp ya shiga yaga status ɗin Tajj yana shiga ya ci karo da video Little da ya yi murmushi dimples ɗinsa sun lotsa ya lumshe idanunsa irin na Ridayya ya ɗan shagwaɓe fuska a hankali Ustaz yanayinsa na sauka damuwar daya tashi da ita yau ta fara yayewa ya jima yana ta kallon yaron kana ya yi saving a wayarsa ya sauka. Sun fitar da rai ta fitowarsa sai ya fito ta ɗaga kai ta kalle shi hannunsa goye a bayansa yana juya idanunsa ash ɗin jallabiyya ce a jikinsa mai gajeren hannu, ita idan aka ce mata Ustaz ya haɗa jini da Larabawa wallahi ba za ta yi musu ba musamman yanzu daya ƙara girma shekaru suka ƙaru hutu da jin daɗi da kuɗi suka ɓoye shekarunsa gashi baya barin duk wani abu da zai nuna ya mayyanta ko'ina na jikinsa luff yake da gargasa ga yatsunsa dugwaye. Ganin wacce ke zaune ya sanya Ustaz haɗe fuska sai kuma ya ɗan zaƙu da son jin me yake tafe da ita ya akai ta san gidansa dake Lages ɗin? Ya nemi waje saman kujera ya zauna yana harɗe ƙafa idanunsa zube a kan plasma "Ina yini Abbiey?" Bai kalleta ba bai kuma amsa ba t.v kawai yake kallo sun fi seconds a haka kafin ya ce "Mardiyya ko? Kar na sake jin Abbiey a bakinki kin san sunana ai" "In sha Allah Yaa Bilal" ta faɗa da ƙyar saboda masifar kwarjinin da ya yi mata ta buɗe jakarta ta ɗakko wasu takardu ta tsuguna har ƙasa ta ce "Gashi kafin a yi auren Ridayya ta bani ajjiyar takardun nan ta ce ranar za a kaita zata amsa, ni kuma ba tare da saninta ba na yi photocopy dana bashi bata sai na bata photocopy ɗin na riƙe original ɗin, ganin yadda ta mini da yadda ta wulaƙanta ni bata buƙatar ganina har tana iƙirarin na auri mijinta ya sanya na rabu da ita, kullum ina addu'ar Allah ya haɗani da wani nata na bashi cikin saa kuma mun zo Lages ɗin shi ne nake tambayar inda kake ta hanyar zuwa bankinka" Jin ya yi shiru ya saka Mardiyya ta ɗago kai taga gabaɗaya ba ita yake kallo ba t.v yake kallo ba zaka taɓa ɗauka ma da shi take ba. "Babban mutum ana magana" cewar Hajiya ya nuna mata ƙasan carpet alamar ta ajjiye a nan ta ajjiye zuciyarta babu daɗi ganin yadda ya nuna kamar bai santa ba, ta miƙe ta ce "Hajiya bari na shige" Da sauri Hajiya ta miƙe da yake tana da ɗan raguwar ƙarfinta ta ce "Bari na saka driver ya kai ki can unguwar da kuka sauka ko?" Suna fita Hajiya ta ɗauki card ɗin Ustaz ta bawa Mardiyya ta ce "Riƙe wannan kina kiran shi kullum kila shi ne rabonki tunda kinga ba ki yi auren ba" "Hajiya ba za a yi haka ba ni daban wacce yake buƙata daban" "Ni dai ke kika kwanta mini ba zan je rashin aure ya haukata mana shi ba, shi ne kawai ya yi mini saura ina tsoran matan zamani kar su lalata mini jika" Tsoro da fargaba suka wanzu a zuciyar Mardiyya lokaci guda kuma kwaɗayin auren Ustaz ya ɗarsu a zuciyarta amma tana ganin kamar abu ne mai wahalar gaske tunda ta san waye Ustaz ɗin baya ɗaukan wasa da kuma raini a rayuwarsa. "Amma Hajiya ba lallai ya amince ba" Hajiya ta ce "Kin jiki kuma kamar ba mace ba? Ai salo za ki zo da shi da kissa ki siye zuciyarsa kuma nima zan tursashi na nuna masa ni nake buƙatar hakan kuma alfarma na nema wajanki" Farin ciki ya cika zuciyar Mardiyya idan ta samu miji kamar Ustaz to babu wata ƴa mace da zata iya barinsa ya kalla duk wannan samartakar da tuzuruntakar ta ji ta gani zata iya ɗaukarsu, wani irin so na ban mamaki ya wanzu tare da mamaye zuciyarta nan take ta nufi gida da buri da kuma ƙudiri na samun Muhammad-Bilal Tahir Rano a matsayin mijinta. Wajan sati guda kullum sai Mardiyya ta kira Ustaz da ya ji muryarta yake kashe kiran. Yau sai issha ya shigo a gajiye yake sosai tun kafin ya shige part ɗinsa Hajiya ta tsayar da shi, Mai ran ƙarfe kowa baya ce mata komai ya nemi waje ya zauna ta ce "Babban mutum a ranka za ka ji kamar ina takura maka wallahi ba haka bane kwaɗayin ganinka cikin fari da kuma kwaɗayin samun wata zuri'ar da muka rasa sune suke jana zuwa hakan, ka ɗauki hakan matsayin ƙaddara wacce ta ruga fata, rabonka baya taɓa huce ka. Ka ɗauki hakan matsayin wani sabon babi na lissafin zanen ƙaddararka ka ɗauka Mardiyya ita ce matar da Ubangiji ya ƙaddara zaka aura wallahi idan da aure tsakaninku ka bijire to wannan rabon ko a titi ne sai an same shi, Asstagafirullah! Kuma bama fatan hakan don Allah don Annabi ka duba girman Allah ka amince" Ustaz jikinsa ya yi sanyi ya rufe idanunsa ya buɗe baya son ana gama shi da girman Allah ita kanta Hajiya ta sani. "Zan durƙusa a saman ƙafafuwana idan hakan zai saka ka amince da auren Mardiyya bana son a dinga maka kallon tuzuru shekaru wajan na 41 kake fa?" Ya numfashi ya kalli Hajiya ya ce "Idan na faɗa miki gaskiya za ki aminta?" Ta ce "Sosai ma ko shakka babu" Ya cije baki kana ya yi miskilin murmushi ya ce "Wannan jikokin da kike kwaɗayi ba za ki same su ba ko na auri Mar" "Assha saboda me Babban mutum? Haihuwar ce baka so?" Ya miƙe tsaye yana juya baya ya ce "Saboda bani da lafiya tarayya da ko wacce mace sai......," Ya fasa faɗar abinda ya yi niyya ya sauke numfashi ya ce "Ni nakasashe ne" Duk sati sai Sadauki ya je gidan Mahmah magana bai taɓa haɗa shi da Ridayya ba, idan Allah ya yi sun haɗu ta gaishe shi wani lokacin ya amsa wani lokacin ya share. Gefe guda kuma kullum cikin bawa mother labarinta yake haka karum cikin dare zai tashi mother ya ce ta yi masa addu'a dole ta miƙe ta yi sallah ya dinga masa addu'a. Prof ma abin har mamaki yake bashi zai wahala kaga ya yi kwana uku cikakke a gida kullum yana da meeting da ma'aikata ko marketing manager ko secretary bashi da aiki sai danna waya da duba pictures ana magana ya ce wani aikin kwangila yake gani. Mother na zaune taga Sadauki ya fito sai kallonsa take tana murmushi ganin inda ya yi wani irin kyau ya nutsu sosai ya sanya shadda shampoo sky blue bai saka hula ba ya taje gashin kansa ya sanya baƙin glasses a Idanunsa sai baza ƙamshi yake ya ƙarasa ya durƙusa kusa da mother ya ce "A sanya mini albarka zan je neman matar aure" Hajja Azizat ta yi murmushi ta ce "Ma sha Allah Ubangiji ya yi maka albarka ya baka sa a, ya ɗora ka a kanta lokaci guda ta amince" Ya lumshe idanu ya ce "Amin love" Ya yi shiru can ya ce "Zuciyata bugawa take sosai" "Tsoro mace kake Sadauki?" Ya shagwaɓe fuska sosai sai kuma ya miƙe tsaye ya ce "Why should I?" Ta yi masa dariya ya fita ya ɗauki wata farar motarsa ya yi waje kafin ya isa gidan Mahmah ya yi sadaƙa babu adadi bai san nawa ya bayar ba, kuma yau kwanan Ridayya uku kenan da yin idda yana lissafe da komai shi ya sa bai taɓa kulata ba wannan ranar yake jira. Mahmah na zaune a parlour tana kallon tafsir ta ji sallamar Sadauki ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce "Ikon Allah da alama taurarin sa'ata ne suke haskawa a kan ka Hamza, irin wannan ziyara haka?" Ya basar yana zama ya ce "Mahmah ai na girma aure ma zan yi daman ana kawo miki ƙarata" Ta ce "Au Hajja Azizat ɗin ce mai kawo ƙarar taka?" "Uhm na san komai fa, ni unguwa zani kuma ɗan rakiya nake nema" kafin ta yi magana ya miƙe ya nufi bedroom ɗin Ridayya ta girgiza kai ta ce "Ban hango maka rakiya a nan ba, rikice dai kawai Sadauki matar wanin??" "Thank God ki ce wani, kuma ai ta yi Idda" "Idda kuma kai ina kasan ta yi Idda ɗin?" Bai yi magana ba ya shige cikin bedroom ɗin Ridayya na zaune a gefen gado tana ta yi wa Little Bilal wasa Sadauki ya shigo. Ta yi saurin rufe jikinta ya taɓe baki ya ce "Tashi zaune" Ya faɗa babu wasa ta miƙe tana riƙe da Junior. "To kibar nannuƙewa unguwa za ki rakani" Ta yi sauran kallon shi ya ɗaga mata gira yana kashe mata ido kamar ya shiga ranta ya ce "Da zan rama abinda kikai mini da tuni na yi fa, so get down" Ba zata iya masa musu ba domin a muryarsa ta ji ba wasa kuma ya cika mata Idanu ta miƙe tsaye zata ɗauki vail ɗin abayarta yana juyawa ya ce "Hijab please" Ta ajjiye mayafin ta ɗauki hijab ta yi covering jikinta ta saka flat shoe ba ƙaramin kyau blue ɗin hijab ɗin ya yi mata ta fito parlour tana rarraba Idanu Mahmah ta ce "Saki jikinki Sadauki bashi da matsala ɗan'ƙanwata ne Hajja Azizat, ki je ki raka shi ku dawo ki nutsu dai kar ki biyewa rigimar shi" Ridayya ta jinjina kai "Muhammad-Bilal zo nan na goya ka" Ya tafi da gudu wajan Mahmah ita kuma Ridayya ta yi waje. A cikin mota ta samu Sadauki yana ta danna wayarsa taga yana bawa waya muhimmaci sosai. "Ba mayen waya bane, business nake rufo ƙofar" Rufe ƙofar ta yi a hankali ya yi wa motar key yana kallon hanya ya miƙa mata wayarsa ta kalli wayar a hankali a taushashe kamar mai raɗa ya ce "Kina so ne? Ba bar miki zan ba" Ta yi shiru da zata iya murmushi da ta yi amma ita a yanzu babu wani dalili da zai zo wanda zai sanya ta yi murmushi sun jima kafin ya yi parking a gefen titi ya yi shiru can ya juyo gabaɗaya ya ce "Bana jin daɗin shirun damuwa ce dani ki bani shawara" ta juya sexcy eyes ɗinta ba ta ce komai ba ya marairaice fuska ya ce "Shanshan please do something" "Allah ya kawo sauƙi" Ya girgiza kansa a hankali ya ce "Juyo ki kalle ni" Ta girgiza kai ya sake narkar da murya yana ɗan fesa numfashin bakinsa dake fitar da mouth freshner ya ce "Bana iya magana bana kallon cikin idanun mutum, but lemme try. Ridayya ni ɗaya ne wajan Mama da Daddy, Daddyna ɗan kasuwa ne kuma ɗan siyasa yanzu haka shirye-shiryen fitowa takarar house of assembly, kuma ya ja kunnena wai dole na fito da matar aure ni tsoran matan yanzu nake yaudara da cin amana sun musu yawa, amma na ga guda ɗaya wacce take tamkar zara a cikin taurari da gaske na ji ina son amma ban iya soyayya ba, ina so sai na iya kafin na fara zuwa wajanta" A sanyaye Ridayya ta ce "Ayya to Allah ya bada sa a" Sadauki ya marairaice ya ce "Help me" "Tayaya?" "Ki bani dama ta sati ɗaya kawai na gwada soyayya dake idan na ji na iya sai na je na faɗa mata ko?" Jikinta ya yi sanyi ranta ya ɓaci domin ita ba wannan a ranta da iyakar gaskiyarta ya ce "Ni na tsani maza" "Nima bana son matan ai, kawai dake na yarda kinga ni ɗaya ne a gidanmu gidan Mahmah babu mace ni ba cewa zan yi ina son ki ba" "To ai nima ban iya soyayya ba" Ya ɗan miƙe daga jikin kujerar ya saka hannunsa ya juyo da fuskarta zuwa inda tasa yake a hankali ta ɗago ta kalle shi,cikin saka idanunsu ya haɗe waje guda sun ɗan jima haka Sadauki na jin zuciyarsa kamar zata fito cikin kasala ya ce "Za ki iya Shanshan, just trust me mu zama true friends komai ya zama confidentiality between us ok?" Za ta yi magana ya ɗora yatsarsa guda a laɓɓanta ya ce "Shhhhhh kar ki taurin kai Shanshan" Ta jinjina kai ya miƙa mata hannunsa ya ce "To mu yi musabaha mu ƙulla kuma" Tana kallon shi ya kama hannunta ya ce "Assalamu Alayki Hamza Hamdan Hamish ana ce mini Sadauki, but ke ki ce Sahibi zan amsa" Ta ɗan lumshe gajiyayyun idanunta ya matse hannunta ya ce "You?" Cikin sanyin muryarta mai kashe jiki ta ce "Ridayya" "I knew. Soyayyarmu ta fara yanzu sati ɗaya kawai. Ridayyerh yanzu ke tamkar budurwata kuma matar da zan aura a haka nake kallon ki, ki yi haƙuri da halina ina da naci da taurin kai. Ridayyerh ban miki al'ƙawarin farin ciki har abada ba, abu ɗaya Sadauki ya sani ba riƙon amana ba zan taɓa bari ki yi kuka ko shiga damuwa ba, zan zama ɗan halak a wajanki ki sanyawa ranki Sadauki na ki har abada Shanshan" Kallonsa kawai take ya saka baki ya hure mata idanu da iskar bakinsa, ta yi saurin ƙifta idanu sai kuma ta ɗan turo bakinta da suke jajur. Sadauki ya kalli laɓɓan data tura sai kawai ya girgiza yana sakin hannunta ya ce "Nifa kwaɗayi nake ji ice cream za ni sha hope ki sha ko Saheeba?" Kallon da yake mata ya sa bisa dole ta ce "Eh" "Eh wa?" Ta kwaɓe fuska sosai ta ce "Zani Sahibi" "To Allah ya yi miki Albarka" Ta ce Amin. Surutu ta gani kala-kala wajan Sadauki bisa namanki taga mata sai magana suke masa haka kawai kuma ta ji ranta ya ɓaci yana lura da ita bata sha komai a wajan ba. Yana gama yin parking ta buɗe ta fito ta yi cikin gida kai tsaye kuma kitchen ta nufa, Sadauki ya zauna a parlour sama da minti goma ya ji murya mai taushi ta yi sallama a palroun ya ɗago kai Sadauki mamakin ganin mutumin ya cika shi wai mai yasa suke yawan haɗuwa ne? Ya amsa masa ya nemi waje ya zauna. Mahmah ta fito ɗauke da Little Bilal ta ce "A'a Babban mutum saukar yaushe?" A hankali ya ɗago idanunsa maimakon ya yi magana idanunsa ya sauka kan Little Bilal wanda shi ma kallonsa yake yana ɗago masa hannu yana tsalle kallon yaron kawai Ustaz yake da wani irin firgitaccen yanayi ya kasa furta komai kamar yadda ya kasa daina kallon Little kamar daga sama suka fara jiyo tari daga kitchen ga hayaƙi na tashi a gigice Mahmah ta ce "Nadra ce a kitchen" Jin haka ya saka Ustaz ajjiye wayarsa ya miƙe tsaye babbar rigar jikinsa na ƙara saboda sabbinta dukda dokawar da ƙirjinsa yake na rashin dalili bai hana Ustaz nufar kitchen ɗin ba kai tsaye.... Share and share as so much as you can! Sorry Ustaz🥰 Shanshan tana wajan Sahibi Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv 08164069385 *MUNAFUKIN MIJI 28* Mikiya Writers Ass... Bright pens free batch Nimcyluv Duk yadda zuciyarsa ke bugawa bai hana Ustaz nufar kitchen ɗin kai tsaye ba, ga wani irin hayaƙi da yake fitowa ya turnuƙe cikin kitchen ɗin gabaɗaya, hakan bai dame shi ba sai na zuciyarsa data ƙarfafe shi ta hanyar ƙara masa ƙwarin qiwwar shiga ciki ɗakko Nadra kamar yadda tunaninsu ya wanzar musu ita ce a ciki. Yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarsa da nufin shiga ya ji an riƙe masa babbar riga ana faɗin "Uncle ƙani na kuka ƙani yana kuka" cak Ustaz ya tsaya ƙafar daya shigar cikin kitchen ɗin a nutse ya zaro ta, tare da mayar da ita baya yana juya idanunsa sosai da suke zube a kan yarinyar ba tare da ya ce komai ba. Mahmah ta ce "Babban mutum dawo ka zauna ashe Nadra na bedroom ɗina tana mini wasa da bagaruwa, nasan baka son hayaƙi saboda ciwon kan ka, Sadauki shiga ka duba mene ya haddasa wannan hayaƙin idan dai gas ne sai dai mu fita daga gidan don sharrin shi yawa ne da shi" Ustaz ya dawo da baya jarumta kawai ya nuna amma zuciyarsa ba ƙaramin tsalle take masa ba tana matsewa waje guda a ƙirjinsa tuni jijiyoyin kansa sun fara bayyana ya zauna saman kujera, ya kasa yin alkunyar ɗauke ganinsa daga kan Little Bilal. "Mun same ku lafiya? Yara gida da ayyuka?" Ya faɗa a rarrabe bayan ya gama samun daidaito da tafiyar numfashinsa. A hankali ya saka hannayensa biyu ya ɗauki Little Bilal. Mahmah ta murmusa cikin jin daɗin yadda ya ɗauki Little ta ce "Lafiya lou Babban mutum, kwana biyu zuwa kano baya yi maka wahala" Ya lumshe idanunsa ya buɗe bai ce komai ba, sai nutsuwa da sanyin da yake samu deep down na zuciyarsa yana mamakin baiwa da ƙudirar Allah dake samar da mutane masu kamanni iri guda kuma ma bambanta jini, toshe da ƙwayar halittar haihuwa. Sosai ƙaunar Little ta zauna daram a zuciyarsa. Mahmah ta ce "Sadauki ta shi mana, kana ganin baƙo babu gaisuwa?" Baya son nuna halinsa da yi wa Mahmah gardama ya kalli Ustaz ya ce "Ina yini?" Tamkar Ustaz bai jima, haka ya yi shiru kai bama zaka ɗauka da shi Sadauki yake ba, can ya nisa ba tare daya ɗago kai ba ya ce "Sannu" Wani baƙin ciki Sadauki ya ji zuciyarsa kawai ya miƙe ya nufi kitchen ɗin a ransa yana mamakin waye shi a wajan Mahmah? Mene ya sanya yake yawan haɗuwa da shi? Kuma shi ne wanda yaje gidansu yana neman Ridayya kuma ga Ridayya ga shi what's going on? Bayan tashin Sadauki Mahmah ta kalli Ustaz ta ce "Muhammad-Bilal ya kamata ka yi haƙuri da dukkan abubuwan da suka faru ka ɗauki ƙaddara, Ubangiji shi ke rayawa kuma shi ke kashewa, shi ke samar wa kuma shi ne ke kwacewa, shi ke tadawa kuma shi ne sarkin dake kashewa. Ka ɗauka Ubangiji ya fi ƙaunar su Baffa da iyalanka shi ne yasa ya amshe su, suka koma gare shi dole ka yi haƙuri ka ɗauki ƙaddara ka sakawa ranka cewa kaima ranarka na zuwa. Ka yi amfani da damarka ka ribaci lokacinka..." Ta ɗan yi shiru, ta ɗora da faɗin "Aure! Ka yi aure Ustaz don Allah ka raya sunnar ma'aiki sallahu Alaihissalam, ka tara zuri'a yadda Ubangiji zai yi alfahari da kai wannan zaman da kake babu mace a gefenka is not good rashin aure ga baligi babban mutum irinka babbar matsala ce, shi aure ni'ima ce yana ƙarawa mutum nutsuwar zuciya da ɗauke damuwa rashin yinsa kuma yana taɓa kwakwalwa da gurɓata tunanin mutumin daya isa yin shi. Don Allah don Annabi Muhammad-Bilal ka yi aure kar ka tsufa a gida ƴan'matan su dinga gudunka nasan ba rasa matar aure ka yi ba, a taimaka a daure" Ya kalli Mahmah sai kawai ya jinjina mata kai alamar “In sha Allah” don baya jin zai iya magana ya miƙe da Little Bilal a jikinsa wanda ya rungume Ustaz ya kwanta jikinsa tamkar jikin babansa, ya kama hannun Nadra yana ta tsaye bai ce komai ba. Fahimtar hakan yasa Mahmah cewa. "Za ku fita kenan? Allah ya tsare Nadra banda ƙiriniya domin nasan halinki" nan ma jinjina kai kawai ya yi kana ya nufi waje da yaran a ransa yana ayyana inama yaran shi ne. Mahmah ta raka Ustaz da idanu ta ce "Ikon Allah Ubangiji ka kawowa wannan bawa naka sauƙin rayuwa, a yi mutum magana ma wahala take masa? Sai ya ƙaraci zaman shi tari bai yi ba?" Da sauri Sadauki ya saka ƙafa ya daki ƙofar ta buɗe ya kutsa kai ciki. Kwance ya ganta yashe a ƙasa jikinta nata rawa sai kakkarwa take ga abinda ya ɗora yana kamawa. Ya kashe gas ɗin ya sauke tukunyar ƙasa zuciyarsa sai harbawa take ya tsuguna gabanta muryarsa a harɗe yake faɗin "Shanshan lafiya? Me ya sameki?" Shiru bata amsa ba. Ya tattare bakin hannun rigarsa yana ƙoƙarin ɗaukarta yaga ta saki fitsari ya fara gangarawa zuwa bakin kitchen ɗin. Sadauki ya tsaya yana kallon ikon Allah domin bai taɓa ganin mutum kuma mace rana tsaka da fitsarin kwance ba. "Hamza wai lafiya ne na jika shiru?" "Mahmah" Shi kawai Sadauki ya iya cewa Mahmah ta leƙo ta kalli Ridayya da tunda ta yi fitsarin ta dawo hayyacinta, tsananin kunya ne ya saka ta kasa motsawa tunani take mai ya saka ciwon ya motsa mata a gidan da bata iko da shi? Me ya sa ta yi fitsarin a gaban wanda ba muharraminta ba? Ta ƙara cure wa waje guda tana jan wani irin numfashi. "Mimi fitsari? Sadauki jeka ko? Sai mun yi waya da Hajja Azizat" Ya yi tsaye jikin sink hannunsa harɗe a ƙirjinsa abubuwa da yawa suna wanzuwa a zuciyarsa can ya juya tare da ficewa daga cikin kitchen ɗin. Yana fita ya shiga motarsa ya nufi gida zuciyarsa cike da tunani kala-kala. Ridayya kasa cewa Mahmah komai ta yi ta miƙe ta nufi bedroom ta wanke jikinta tare da sauya kaya, kuka ta yi sosai mai isarta wani irin kewar dangi da son ganin Abbiey ɗinta ya addabi zuciyarta, shi kaɗai ya san yadda zai kula da ita idan ciwon ya tashi shi kaɗai ya san hanyar yayewar damuwarta shi ne kawai baya damuwa data amsa shi ko ta yi shiru. Ta dawowa a lokacin da komai ya ƙare. Ta miƙe ta nufi gaban mirror ta zubawa kanta idanu, hawaye ya cika mata Idanu sumar kanta duk ta dameta daman Abbiey ke kula mata da ita ji take tamkar ta aske ta wuta bata son gashin ya dameta duk wani abu da zai saka tana tunawa da Abbiey ɗinta bata ƙaunar ganinsa. Ta fashe da wani irin raunataccen kuka kamar yarinya ta saka bayan hannunta ta share idanunta "Shikenan ka yi nisa da duniyata? Shikenan ba zan ƙara ganinka ba Abbiey, ba zan nemi yafiyarka ba, ko bamu dawo daidai ba ka yafe mini nasan abu ne mai wahala ka yi mini uzuri ka amshi ƙaddarata matsayin kuskure irin na kowanne bawa. Me ya sa kai ma ka mutu Abbiey kai ne kaɗai kake so na, me ya sa za ka bisu zuwa inda suka je don Allah ko a mafarki ne ka zo Abbiey ka tafi na rayu" Jikinta ya ɗauki rawa ta durƙushe a wajan tana wani irin kuka "Zan yi karatun yanzu zan zama abinda kake so na zama, babu ruwana da maza hasalima na tsani namiji ba zan sake yarda da kowa ba, zan tsaya tsayin daka wajan karatu da yi maka biyayya ko da za a kira ni da _Feminist_. Abbiey soyayya guba ce na sha ta kusa illata ni, Abbiey namiji ba ɗan goyo bane, na goya shi ya nakasta baya na, Abbiey namiji ɗan kunama ne wallahi tallahi Abbiey na tsani maza, kai ne ubana kai ne yayana you still be...." "Ridayya" Ta yi saurin goge hawayen idanunta, duk kukan da ta yi amma idanunta tar suke babu ja sai ruwan daya kwanta a cikinsu wanda ya ƙara musu haske sosai. Mahmah ta ce "Tun ɗazo nake buga ƙofa shiru are you okay?" "Eh" Ta furta a hankali kanta a ƙasa zuciyarta babu daɗi "Ki fito ku gaisa da Uncle ɗin Nadra zai tafi, ai ya shigo kina kitchen ma" "Ba zan iya ba" Mahmah ta kalleta sosai sai ta jinjina kai ta ce "Babu matsala ki kwanta ki yi bacci idan kin farka za ki samu nutsuwa, daman naga Little ya maƙale masa ne yana kuka gashi hadda ɗawainiyya ya yi musu shatara ta arziƙi" "Ayya Allah ya ƙara arziƙi ki ce masa an gode" "La ba'asa" Mahmah ta fita, Ridayya ta kwanta kan gado ta rufe jikinta har fuska kanta da ƙirjinta na yi mata ciwo sosai tana jin Mahmah tana magana ita ɗaya a parlour a haka har bacci ya ɗauketa. A can parlour Mahmah ce kawai ke hira Ustaz yana zaune saman kujera ya harɗe ƙafafuwansa, mamakin yadda gudun zuciyarsa ke ƙara hauhawa idan ya shigo cikin gidan yake. "Ai Tajuddeen baya garin ya koma can Katsina saboda abubuwan da suke faruwa, kasan ƙasar nan ta mu sai dai kawai aja mata li'ilafi cin kashin da ake mata ya yi yawa. Can kwanaki an sace ɗaliban makarantar kwana har yanzu shiru kake ji shawo ya saci shirwa, yanzu haka fa an ce an lalata ƴan'mata da yawa wasu ciki nema da su yanzu don girman Allah Ustaz wa kake ganin zai auri yarinya ba budurwa ba?" Ustaz ya girgiza kai a ransa yake cewa "Idan har yana son ta, to budurci ba wani abu ba ne, so na gaskiya bashi da dalili Mahmah ki gagauta tuma da neman yafiyar Ubangiji allahumma yahdiki Mahmah zancen ya yi girma" "Abun ya yi wani iri ko ki ba lallai na bari ba zamani na ciwoka annoba kala-kala" Ustaz ya miƙe yana gyara zaman rigarsa domin hirar a saman kan shi yake jinta. Nan da nan Little Bilal ya saka kuka da rigima yana miƙa wa Ustaz hannu a dole sai ya ɗauke shi. "Wannan yaron ba dai son gantali ba, uwarka na can tana kuka kamar ƴar yaye". Ustaz ya rungume Little yana ɗan jijjiga shi a kafaɗa kamar yadda ya yi wa babarsa har bacci ya ɗauke shi ya ɗan faki idanun Mahmah ya sunbaci goshinsa kana ya miƙa mata shi. "Zaka tafi kenan?" "Uhm" ya ce yana nufar waje ko ruwa yaƙi yarda ya sha ta bisa da idanu tana "Miskilin mutum ko ƙaddara, Allah ya baka mace daidai kai amma wannan shirun ni kai na ya kusa kassara ni" Ko da Ridayya ta farka ta ji ƙamshin da ko a mafarki ba zata manta ba, bawai ƙamshin turare bane ƙamshin Abbiey na musamman ne daban yake ta dinga kallon Little Bilal sai ta marairaice fuskarta a hankali tana tura baki ta ce "Haba Abbiey komai sai ka ɗauke mini na uba?" Shi kuma yaron ya washe mata baki yana lumshe idanu ta cire masa rigar ta ɓoye ta saka masa wata ta yi shiru tana kallonsa ya zama tamkar t.v a gare ta. Duk yadda Ridayya take ƙoƙarin gujewa buƙatar Sadauki abin ya gagara, ya san duk hanyar da zai bi ya rutsa ta kuma bata da wani dalili mai ƙarfi ita babu kalamai ma a bakinta. Yanayin yadda yake gudanar da abubuwan shi mamaki abin ke bata, yana ƙaunar yin sadaƙa yana son kayan kwaɗayi ta dinga mamakin inda yake samun kuɗi har yanzu kuma bai yi mata magana a kan fitsarin da ta yi ba, ya yi burus da batun ko a chat daya buɗe mata bata fiya magana ba sai kawai ya ce ta yi masa voice kuma kawai ya kirata kafin ta yi magana ya zai ce Shanshan shhhh numfashinki na kira na saurara yana gama ji zai kashe kiran. Abubuwan Sadauki hadda almara ta ɗan saki jiki da shi har ta yi masa murmushi ko dariya a kwana na biyar ke zancen ya sauya ya ɗauketa zuwa wani waje suna tsaye wata ta zo ta rungume Sadauki. "Wow ashe da gaske Sadauki ne baby Idanunka kenan?" Sadauki ya juya ya kalli Ridayya yaga ta juya baya tana danna waya kamar mai sanin me take amma dannawa kawai take. "Zubby ya kike?" "I'm good, ina ka ɓoye ne ko'ina na duba ka baka nan ka bani number ka" "No, ina tare da matata ne" Zubby ta zare Idanu ta ce "Mata fa ka ce? Sadauki aure ka yi babu labari? Shi ya sa ka sauya number" bai kulata ba. "Wace matar?" Da hannu ya nuna mata Ridayya bai ce komai ba. "Hi" Ridayya ta juya ta kalli Zubby sau ɗaya ta ɗauke kai. Zubby ta zare Idanu tana kallon Sadauki ta ce "Goodness! Sadauki wannan abar zaka aura? Kuma a gida za a barka wannan halittar? Yaaakkkk" Ya gyara tsaiwa sai kuma ya ce "Wakike da suna?" "Sunan nawa ka manta?" Ya ɗage gira ya ce "Sunan na uwata n da ba zan manta ba? Ke fara ita baƙa ko? Na yi rejecting ɗinki na yi accepting nata shi ne ya ba ki ƙarfin qiwwar cewa haka" Ya juya ya damƙo hannun Ridayya wacce tuni idanunta ya cika da hawaye ta kalli Sadauki ya yi saurin matse hannunta ya ce "Wallahi kika bari hawaye ya sauka a gaban kowa zan share su da bakina Ridayya, na tsani kuka mara dalili" Ta sunkuyar da kanta ƙasa. Zubby dariya kamar me ta ce "Yanzu duk wayewarka da zagaye-zagayen da ka yi a nan ka yar da zango Sadauki? Wallahi kai ka yi abin ni ce kuma da kunya wanna baƙar da kayan idanun za ka kwasa village girl domin babu alamar hawaye a tattare da ita" Sadauki ya ce "Ridayya ki rama abinda take faɗa miki i can't take it anymore, wallahi idan ki ka yi kuka ni na san me zan miki" gabaɗaya jikinta rawa yake domin bata saba da wannan tashin hankalin ba. Ya jata fuuuu zuwa mota ya buɗe ya dannata ciki ya saka key ya rufe ya dawo wajan zubby idanunsa jajur. "Kin ci sa a Sadauki baya taɓa jikin ƙazamai kuma baya dukan mata, ita waccan ƴar ƙauyen ita ce zuciyar Hamza Sadauki gabaɗaya ita ce numfashina, abinda baki sani ba irin colour ɗinta nake buƙata mai wahalar samu domin yanzu baƙaƙen mata wahala da tsada suke sadakinsu daban suke, kalar kulawar da za a basu ta musamman ce. Idan za a biya sadakinki da naira na Shanshan da dallors za a biya, ki duba komai na jikinta natural ne halitta da Ubangiji al'arshi ita maza ma tsoro suke bata, ba ke da kika mayar da kan ki ƙaryar kowa ba, ita tana ƙaunar fatarta bake da kike shafa na kan ti ba. I love her the way she is, i love her so much i love her to the square of infinity💕 mother of my childrens" "Ban yarda za ka aure ta ba" Zubby ta faɗa idanunta na sauya dauriya kawai take na cin mutuncin da Sadauki yake mata. "Idan ban auri Ridayya ba ki ƙaddara Sadauki baya duniya, ni na san saboda ita ne har yanzu ban taɓa budurwa ba, babu macen data isa ta yaudare ni ba a haifeta ba, Sadauki bai yarda da asara ba baya kuma give up zan aureta kuma zan tabbatar miki da haka, useless" Bayan ya shiga motar ya kasa driving ya cije laɓɓansa cikin zafin nama ya daki kan motar jin kansa yake yana yi masa wani irin hayaƙi, zuciyarsa na tafarfasa bai san dalilinsa na zuwa wajan nan da Shanshan ba, yasan ƙaddara ce wacce ya riga fata ya rasa wanne kalar love words masu taushi da zai yi amfani da su wajan rarrashinta, shi kansa zuciyarsa wata kalar rawa take masa ya buɗe baki zai yi magana ya kasa ya sake buɗewa da nufin magana ya kasa maimakon hakan wani irin sauti ne mai ƙarfi ya maye gurbin maganar da zai yi hakan ya tabbatarwa da Ridayya Sadauki ya fita shiga cikin tashin hankali ainu ta ɗago idanunta daya gama jiƙewa da hawaye ta kalle shi a tsorace yanayin rinewar da idanunsa ya yi shi kaɗai ya bata tsoro ya janye idanunsa murya a daƙushe ya ce "Can you help me with drive?" "Ban iya ba" Bai ce komai ya kifa kansa ya ɗauki lokaci kafin ya ja motar suka bar wajan. Ita ce farkon fita ta yi gida da gudu bai bita ba domin yanayin da yake ciki ba nata bane ya nufi gida kawai. Ridayya har dare kalaman Sadauki na yi mata yawa ashe haka soyayyar take? Ashe haka ake faɗawa masoyi? Mai yasa ita sam bata taɓa jin daɗinsu ba, ta rufe idanu ta mirigna she wish a ce ita Sadauki zai mallakawa wannan kalaman domin bata hango ƙarya cikin idanunsa ba, bata da kowa a yanzu har a zuciyarta take gasgata cewa Ustaz ya rasu da yana raye dole zai neme ta. Ta samu kanta da lissafin kwanakin da suka rage da game ɗin soyayyarta da Sadauki. "Kina yin hawaye zan share su da bakina?" Gabaɗaya tsigar jikinta ta mimmiƙe wani yarrr ita tunda take a duniya ko kiss bai taɓa haɗata da Zameer ba balle irin romantic abun nan, ko idan aka yi kiss ya mutum yake ji?. Da sallama ya shigo parlourn idanunsa maƙale cikin glasses fitowarsa kenan daga Library yana research a kan wani abu. Jallabiyya ce a jikinsa mai taushi, laushi, santsi kasancewar weekend ne yana gida. Yana ƙoƙarin shigewa ya ji an ce "Muhammmmd!" Cak ya tsaya domin Hajiya bata taɓa yi masa irin wannan kiran ba, irin kiran yaran nan. "Dawo ka zauna" Ya nemi waje ya zauna ya ajjiye wayar hannunsa da diary ɗinsa da yake ajjiye muhimman abubuwa. Babu wasa a fuskarta ta ce "Wacece ni? Mene matsayina a wajan mahaifinka dama kai kan ka?" Ya dinga kallonta "Ba kallona za ka tsaya yi ba, yau dole na kawo ƙarshen abubuwan da suke faruwa" "Kaka, wacce ta haifi Abba" Yana faɗin hakan ya miƙe ta ce "Ban gama ba" ya koma ya zauna. Ta kalle shi sosai ta kalli Mai ran ƙarfe ta ce "Ka kawo mini dalilinka kuma na karɓa na amsa matsayin hujja mai ƙarfi, saboda yaran zamani ba ko wacce mace ce zata iya zama da namiji da ba zai sauke hakƙin aure ba. Na kuma yi wa ita Mardiyya bayanin komai amma ga mamakina ta ce mini ta amince zata zauna da kai a haka, ba zata taɓa kokawa ba, babu gori babu tashin hankali ba zata taɓa magana akan hakan ba. Wannan yarinya ƴar halak ce gaba da baya irinta kuma ake buƙata a aure ba riƙe sirrin miji dana aure" "Muhammad idan har ka yarda ina da iko da kai ina son ka amince da batun auren Mardiyya, rashin amincewar daidai yake da cewa aurenne baka buƙata kuma wallahi zamu tattara mu bar maka gidanka in sha Allah" Babu mai iya gane yanayin Ustaz balle ka fahimci yadda ya ɗauki zancen fahimtar halin da yake ciki daidai yake da fahimtar abinda mace mai ciki zata haifa mace ko namiji ya ɗauki daƙiƙo kafin ya fesar da iska yana kuma jan wata ciki zuwa ƙirjinta dake masa raɗaɗi a hankali ya ce "Allah ya sa albarka" "Amin Amin. Kuma ka dinga amsa kiranta kuna hira ku fahimci juna tunda babu wani babba jagora Mai ran ƙarfe zai je da kansa Kano wajen iyayenta ya nema maka aurenta ai yarinyar nutsastsiyya ce kyakkawa da ita" Da ƙyar ya ja ƙafafuwansa zuwa cikin bedroom ya yi shiru yana kallon abun tamkar a mafarki taya zai fara iya magana da mace shi yanzu? Balle zama gida ɗaya da ita, ɗaki ɗaya gado ɗaya bashi da wannan confidence ɗin dole ya nemi Mardiyya su yi magana important kuma confidentiality. Maganar Tajj ya gani a WhatsApp. "Ka zo kano bana nan, wai zaryar me kake ne giss me" ya karanta sai bai bashi amsa ba. "Munga abin arziƙi da ka yi wa takwaranka muna godiya, kasan Mimi bazawara ce ta yi idda kuma na ji hankalina ya kwanta da ita in sha Allah zan aureta amma har yanzu ban furta mata ba, bana son na yi mata dole ko kuma taga saboda na yi ɗawainiyya da ita" Sosai Ustaz ya karanta ya kuma karantawa. Can ya fara typing sai kuma ya tsaya "Say something please" Nan ma Ustaz ya ci-gaba da typing sai ya tsaya. "Talk mana bani da aminin daya shige kai Mohd" "Ka rabu da ita" Shi ne kawai abinda Ustaz ya turawa Tajj duk tsayin typing ɗin. "But i love her" "Ok" Ustaz ya rubuta yana fita daga whatsapp ɗin yana ganin kiran Tajj ya share. Ta juya ta sake juyawa sai kuma ta kasa daurewa ta ce "Yanzu mene tunaninka idan Ridayya ta bayyana ana nufin haɗata aure da Babban mutum ne?" "Haka ne" Umma ta ce "Bana tunanin zan amince a gaskiya gabaɗaya yarinyar ta siri mini duk irin wahalar da ya yi da ita ta rabu da shi ta auri wani, sai ta jeme ta lalace take ƙoƙarin tashi daga aiki sannan za a haɗa auren?" "Ya taɓa ce miki yana son ta ne?" Baba ƙarami ya faɗa yana ajjiye jaridar hannunsa. Umma ta haɗe fuska tana kaɗa ƙafa ta ce "Ko da wasa amma ai wawa ba mahaukaci bane ni fa uwa ce ina fahimtar abinda ba kowa zai fahimta daga wajan Ustaz ni bana ra'ayin haka ya samu wata ya aura kuma na fara gajiya da ɓoye kai na daga wajan ɗana" "To ba shakka sannu uwa, idan Ustaz na raye Ridayya na raye kuma bata da auren wani a kanta ita da Ustaz tamkar sun zama miji da mata ne wannan rubutaccen al'amari ne daka rubutacciyar ƙaddara" "To wallahi idan har ina raye hakan ba zai faru ba, ka rubuta ka ajjiye" ta miƙe fuu ta yi ɗaki. Baba ƙarami ya girgiza kai yana mamakin sha'anin mata duk abinsu wani lokacin zai su shafawa idanunsu toka. Tajj ya sake ɗaukan Ridayya zuwa asibitin bela suka ƙara duba fatarta suka sauya mata mayuka daidai da kalarta, na wanka na shafawa da kuma na sha. Kasancewar sun ga ji ya sa kai tsaye yayu gida da niyar da yamma ko zuwa dare ya je ko ya aika asiyo mata mayukan. Wanka ta yi ta shirya Washegari Tajj ya ce zai yi baƙo sa fita gobe ta cire abayar jikinta ta bar wata ƴar top mai ƙaramin hannu da wando a jikinta iya qwiwa kayan sukai mata ainahin kyau sai baza ƙamshi yake ta sanya man leɓe a baki ta tattare sumar kan nata zuwa tsakiyar kan ta ɗaure da ribbon. Gaban goshin duk sumar ta kwanta ɗan faffaɗan ƙugunta ya zauna das ƙirjinta daidai dana ko wacce budurwa domin Little bai damu da shan nono ba. Tasan yau dole Sadauki zai zo ya kwana bakwai ciff da fara game ɗin. Bayan ta gama shiryawa ta nemi waje ta zauna kiran Sadauki ne ya shigo taƙi ɗagawa a kira na uku ta ɗaga Ya sauke numfashi ya ce "Shanshan za ki zautar dani" Ta kwaɓe fuska "I don't know amma kullum ƙara son ki nake" ta yi shiru "Ridayyerh" A sanyaye ta ce "Na'am" "I don't know why I love you, but I do I don't know why I cry so, but I do I only know I'm lonely and that I want you only I don't know why I love you, but I do....," "Sadauki" Ta yi saurin faɗa a karo na farko ya yi shiru "The game is over ka je ka faɗa mata" A hankali ya ce "ko?" "Eh" ok kawai ya ce ya kashe wayar. Sai ta ji babu daɗi ta kira shi ya ce "Ya akai?" "Zuwa za ka yi ka faɗa mata kenan?" "E, da matsala ne yau in sha Allah zan faɗa mata ki taya ni da addu'a Shanshan" Sai kawai ya ji ta fashe da kuka ta yi saurin kashe wayar ta cillar. Ta jima tana kuka kafin ta ji Nadra ta kinkimi Little Bilal dake bacci ta yi waje.. Da sauri Ridayya ta miƙe gudun kar ta yar da shi tunda ai yafi ƙarfinta ko takalmi bata saka ba riga da wando ne kawai a jikinta ta nufi waje tana kiran Nadra amma ina yariyar gudu take ta ƙanƙame yaron. Idanun rufe Ridayya ke bin Nadra ta marairaice fuska duk ta ga ji yariyar ta wahalar da ita idanunta ya yi raurau da hawaye daman zuciyarta a kusa take tuntuɓe ta yi da ƙafar mutum ta yi taga taga zata faɗi ta yi saurin riƙe jikinta muryarta na rawa ta ce "Haba Nadra ki kawo Abbiey na ga ji" ta saka hannu tana goge idanunta. Ganin har yanzu wanda ta buge da ƙafarsa bai motsa ba, bai kuma janye ba fararen jerarrun yatsun ƙafarsa da suke shimfiɗe take kallo. A hankali ta fara bin jikinsa da kallo. Kyarma da ɓari jikinta ya ɗauka zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi sai da ta yi amfani da dukka ƙarfi hali da jarumta wajan sake ɗora idanunta a kan fuskarsa wacce take kwance a kan waya yana dannawa. Ji ta yi gabaɗaya wasu abubuwa na yi mata yawo he just confusing herself me ya sa yake mata gizau. Inuwar da ya gani ta cikin wayarsa ya sanya shi kashe wayar domin shigowarsa Kano kenan kai tsaye nan ya nufi ko minti uku bai yi da shigowa parlourn ya tsaya duba wani saƙo ko zarafin zama bai samu ba. Ya kashe wayar tare da ɗago kansa was the first abinda ya a fara gani RIDAYYA tana tsaye tana kallonsa bai san yaushe ne jikinsa ya saki ba har wayar hannunsa ya zame ta faɗi ƙasa duk ƙoƙarin da ya yi amma zuciyarta da gangar jikinsa suka ƙaryata Ustaz, jikinsa ya ɗauki rawa da ɓari naman jikinsa dana zuciyarsa gabaɗaya karkarwa yake. Mahmah da Tajj suka tsaya kallon ikon Allah ganin abinda ke ƙoƙarin faruwa a kan idanunsa rawar da jikin Ustaz yake shi ne ya fara basu tsoro zufa ta wanke shi tas hatta Nadra tsayawa kallo Uncle ɗin nata take. Hawaye ya gama wanke fuskar Ridayya idanunta har yanzu a kan fuskar Ustaz. Bai sai yaushe ya ɗaga ƙafarsa ba samun kansa ya yi kawai ba gaban Ridayya ganin abinda ke shirin faruwa ya saka Sadauki saurin juyawa ya bar palroun hannun Ustaz na rawa ya miƙa tare da riƙo ƙafaɗun ya kasa magana sai kawai ya kifa fuskarsa a saman tata tare da.... Idan kin karanta danna share bayan kin yi comment🥰 ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *MUNAFUKIN MIJI 29* Mikiya Writers Ass Bright pens free batch Nimcyluv Ganin abin na Ustaz azumin ne ya saka Mahmah kama hannun Nadra ta ce "Mu je ciki" "Ki haɗa da Junior" Tajuddeen ɗin ya furta da ƙyar yana jin wani abu mai zafi na tsaya masa a ƙahon zuciya, mene ya shiga tunanin Ustaz har haka? Mene tsakaninsa da Ridayya girman tuzuruntakar tasa har ya kai ya fara kama yaran mutane? Gabaɗaya tunanin Tajj ya tsaya wani abu mai kama da zullumi ya fara kawo masa ziyara. Miƙewa ya yi tare da yin waje ya bi bayan Sadauki domin ya lura da shigowar tasa da kuma sauyin daya gani tattare da shi ɗin. Bakin Ridayya ne ya fara rawa idanunta a fuskar Ustaz har yanzu ta kasa kallon cikin idanunsa wanda kuma hakan shi yake buƙata, jininta na rawa tana jin saukar numfashinsa a fuskarta yana saukar mata saboda fuskarsa dake ɗan rakaɓe da nata ya kasa furta komai. Da sauri kuma ta yi saurin zame fuskar tana yin baya tare da ƙare masa kallo. Sai kuma ta shiga girgiza kai while hawaye running down on her face. Ta buɗe baki cikin firgitaccen yanayi ta ce "Mafarki nake da gaske mafarki ba kai nake gani ba, irin mafarkin dana saba yi ne a kullum a koyaushe ba zaka taɓa zuwa gare ni bakai bane you're not my father...... My Abbiey is dead, he is in the grave" Baki Ustaz ya buɗe zai yi magana ya kasa ta yi saurin cewa "Me zaka ce? Shiru ko na san mafarki nake ni kaɗai ce bani da kowa sai wanda yaga Allah ya taimaki rayuwata me ya sa zaka bar ruhinka ya fito domin ya firgitar dani Abbiey why why why?" "Don Allah ka yi magana ka ce kai ne ka dawo gare ni baka mutu ba, wayyo Allah wayyo ni Ridayya na shiga uku" Ji ya yi kamar an saka sofa glue tare da manne masa laɓɓansa ya kasa buɗe baki balle furta komai ya kasa nufar inda yake da tunanin idan ya riƙe ta da hannayensa zata dawo cikin hayyacinta da nutsuwarta. Duk dauriyarsa da yadda ya so riƙe kansa kasawa ya yi jikinsa ya shiga ɓari hatta laɓɓansa rawa yake baya son tunkararta kai tsaye domin a farkon ma, tsananin ta'ajjuji ya saka shi yin hakan da son fahimtar da gaske ita ɗin ce tsaye a gabansa shekaru nawa? Wata nawa? Kwanaki nawa? Mintunawa nawa? Daƙiƙo nawa ya shafe yana jiran wannan ranar? Abu biyu ne zai faru idan ya ƙarasa wajan wanda kuma a yanzu bai isa ya hana zuciyarsa da gangar jikinsa hana afkuwar hakan ba, domin baya da iko da su a yanzu sune suke jan ragamar shi. Idan bai riƙe Ustaza ya sanyata cikin jikinsa ta jiyo ɗuminsa wanda ta saba da shi tun tana ƙaramar, to idan bai hakan ba yasan sauran abinda zai biyo baya shi kansa bai sani ba yana tabbacin sahihiyar runguma ce zata samu matsayin tarba a gare shi. Yana kallo ta juya tare da shigewa ɗaki ta rufe ƙofar kai tsaye kuma zaman dirshen ta yi saman carpet ta saki wani irin raunataccen kuka na ƙuncin rayuwarta. Tunanin Abbiey har ya kai ya dinga zuwar mata idanu biyu? Ya fito daga kabarinsa yana wasa da tunaninsa tasan tunda ya kasa furta komai to wannan mutum mutuminsa ne kuka take da iya ƙarfinta har sai da ta ga ji ta fara shassheƙa tare da kwanciya saman carpet ɗin duniyar ta mata zafi cikin wani irin sounds na fitar hayayci ta ce "Allah ya isa Zameer Allah ya isa ka rusa mini rayuwata ka hanani sukuni da jin daɗi na yi regretting sanin ka a rayuwa, ka yi amfani da rashin gata na, rashin farin ciki, kushe da zunɗen da ake mini a kan halittar da Ubangiji ya yi mini ka yi amfani da son da nake maka ka rabani da jin daɗina ban san haka ɗabi'unka suke ba ashe kura ce da fatar akuya ashe kyan ɗan'maciji ka yi ka zame mini ƙarfen ƙafa bani da sukuni sai na fargabar abinda za ka iya yi mini. Ka zame mini MUNAFUKIN MIJI ba tare dana fargaba ka yi mini illa ka yi mini shamaki da dukkan wani ɗa'namiji babu mai dubana idan ya ji zumubin dana aikata saboda soyayya!" Wani irin ɗaci take ji a duk sanda ta tuna lokacin data bawa Zameer kanta wai saboda kar ya daina son ta ya koma wajan wata ko ya fasa aurenta. Batun bidiyon da ya yi musu ya fi komai ɗaga mata hankali video ne da zai iya taɓa career ɗinta dana iyayenta da suna raye a ranta take jin ko zai yi sanadin da kowa zai guje ta; ta zama mujiya ba zata taɓa komawa auren Giɗaɗo ba. A tsaye nan Mahmah ta fito ta ruske Ustaz ya gama haɗa zufa fuskarsa ta yi jajur wanda yau ne kaɗai ta taɓa ganinsa cikin hakan, dukda ba komai ta sani game da Muhammad ɗin ba. Ta kalle shi ta ce "Babban Mutum ka zauna mana, ina fatan yau zaka tsaya kaci abinci ko?" Numfashi ya haɗiye zuwa cikin bakinsa kafin ya yi magana Tajj ya shigo ya nuna kamar bai ga komai ba ya ce "Saboda Allah ka mayar da hanyar Leges da Kano kamar wajan wasan yara? Kodayake kuɗi ke ake shiga jirgi baya yi maka wahala" "Ni ai na ji daɗin hakan ya fi samun nutsuwar zuciya gabaɗaya ya sauya tamkar ba shi ba" cewar Mahmah. Ustaz ya tattare nutsuwarsa yana juyawa zai fita, sai da ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce "Zan buɗe baki a nan in sha Allah Mahmah, Bari na je muga?" " To to ma sha Allah babu laifi a dawo lafiya, yau na tarki sa a" Murmushin yaƙe kawai Tajj ya yi yana bin Ustaz da idanu tare da mamakin abubuwan da suka faru a yanzu ɗin kamar gilmawar walƙiyya. "Wacece Ridayya mene haɗin ta da Bilal abinda ya faru ya yi confusing ɗina, dana juya naga Little na ƙara kallon Ustaz sai tsoro ya kamani kamannin Muhammad-Bilal nake gani kwance a fuskar Little hakan ya tabbatar mini akwai alaƙa mai ƙarfi ta jini a tattare dasu duka biyun, da Ustaz ya yi aure zan iya cewa wannan yaron jininsa ce ya fito ne daga ƙwan halittar Ustaz na haihuwa" "Tajuddeen ina magana" Mahmah ta faɗa tana taɓo Tajj daya zurfafa a tunani, ya tuna sanda Majnun yake cewa Ridayya ita ce wacce ta bashi tsoro a lokacin a area ɗin su Ustaz ne, ya tuna sanda ya yi mata gani na biyu furucin data faɗa ta kira sunan “Abbiey” abu mai muhimmanci kamannin Ustaz da Little da yadda Ustaz ya riƙe fuskar Ridayya ɗin banda yana da kusanci da ita ko farcenta ba zai taɓa ba. What is going on? Meke ɓoye? Ya miƙe tsaye yana ƙara zurfafa tunaninsa a matsayinsa na police mai rang ɗin DCP a firgice yana dafe kansa ya ce "Bilal's adopted daughter?" "No! But how ya akai ban taɓa tsayawa na yi tunani a kan haka ba? Why Tajuddeen mene ya saka duk wannan wahalar da Ustaz yake sha na neman yarinyar nan ashe ina tare da ita? No wonder Ustaz ya damu da batun Junior ashe jininsa ne tsatson shi" Tajj ya shiga damuwa lokaci guda amma daya tuna wani abu sai ya ji damuwar ta kau babu ita dole ya idda nufinsa a kan buƙatar zuciyarsa. Zama ya yi tare da yi wa Mahmah bayanin komai ta jinjina kai ta ce "Allah Alhakkamu sarki gagara misali Ubangiji ya sa ƙarshen wahalar kenan, Allah ya jiƙan iyayensu da rahama gaskiya na yi wa Muhammad murna da farin ciki dole ya ruɗe sosai shekarun da yawa kuma akwai shaƙuwa tsakanin zuciyoyin guda biyu" Ustaz na fita motar da yake amfani da ita idan ya zo Kano ya shiga, ya jima yana sauke numfashi da tunanin ta inda zai ɓulluwa lamarin Ustaza da kalaman da zai yi amfani da su wajan rarrashinta na nesan ta kansa da ya yi da ita, zai ɗauki duka laifi ya ɗorawa kansa ita ɗin yarinya ce kuma macace mai tarin rauni da ƙalubale bata da wani zaɓi zai amshi laifin da hannu bibbiyu. Ya miƙa hannu da ƙyar ya daɗo gudun a.cn motar tare da kunna karatu duk dan ya samu nutsuwa zai ciccije bakinsa yake komai na Ustaz special ne daga yanayin kallonsa zuwa buɗe baki da sarrafa harshensa. Ya ɗauki lokaci kafin ya zame hular kansa ya ajjiye a gefe sumar kansa ta baje ta sakko wacce ta sha gyara da saloon ya yi key tare da yin Bismillah ya bar gidan bakiɗaya. Har bayan la'asar Ridayya bata daina kuka ba, kewar Abbiey ya dame ta domin da gaske bata yar da shi ta gani a ɗazon ba. Tana zaune ta idar da sallah tana karatun Alkur'ani ko ta ji sauƙin raɗaɗin da zuciyarta ke yi mata wayarta ta fara ringing ta duba a hankali taga an saka “Sahibi” Ta lumshe idanunta ƙofofin zuciyarta na buɗewa ba zata manta ba shi ne ya yi saved number a haka ta ɗauki kiran tana manna wayar a kunnenta. "Hello" "Amincin Allah ya tabbata ga ruhin Hamza Hamdan Hamish barka da yamma Shanshan" Ya faɗa a kasalance ta cikin wayar yana sauke ajjiyar zuciya. Ridayya ta ɗan juya idanunta a nutse ta ce "Ina yini ya mother?" "Ni ba ki tambayi ya nake ba sai mother, ni da mother waya fara saninki Shanshan?" "Yi haƙuri to ya kake?" Ya mirigna daga hagu zuwa dama yana rungume pillown kusa da shi a hankali muryarsa very slowly and sadness ya ce "Cewa za ki Mijina ya zuciyarka take ba ya nake ba" Ta yi shiru. Cikin serious magana ya ce "Ridayya" "Na'am" "Waye naga ya riƙe ki ɗazo? Ya riƙe miki kafaɗu?" Ta ɗan yi jim tana tunani ita kam ai babu wanda ya riƙe ta yaushe ma ya zo gidan? "Ina magana" a hankali ta ce "Babu kowa" Wata razananniyar tsawa mai lafiya ya daka mata ta cikin wayar wacce ta kaɗa hantar cikin Ridayya tana mugun tsoron tsawa ko ihu a ka yanzu zata gigice. Nan da nan ta ruɗe tana ƙoƙarin kashe wayar a hargitse kuma a kasashe ya ce "Don't try it" kuka ta fashe da shi sosai ta kasa magana yana ji tana kukan bai ce komai ba can dai ya kashe wayar. Tsakanin minti biyar da kukan ya kira taƙi ɗagawa saboda tsoro ya yi mata DM da _"Idan na ruske ki gidan Mahmah abin ba zai mana kyau ba ni da ke Shanshan. So pick my call"_ Tana gama karantawa ya kira hannunta na rawa ta ɗauka ta kasa magana bisa mamakinta sai ta ji ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya mai ƙarfi kuma muryarsa can ƙasa kamar ba Sadauki ba ya ce "I am sorry Shanshan kar ki yi fushi dani" Ta yi shiru ya ce "Ridayya ina da zuciya a nan ɗina" Ya nuna saitin ƙirjinsa dukda bata ganinsa "Yeah! Ina da zuciya kuma ina da masifar kishi a kan abinda nake so, idan da akwai abinda Ubangiji ya jarabce ni da shi a kwanakin nan bai shige ba, ke ɗin ƙaddarata ce kuma wallahi tallahi ba ki isa ki zama ƙaddarata ba sai dai mu zama ƙaddara juna. Ki saka a ranki duk inda kika sanya ƙafa za ki ga Sadauki a wajan, kuma ni na fi ƙaunar duk abinda yake bani wahala ko yake nuna mini ƙi so don't ever trying to reject me kar ki ce za ki bani wahala don sai dai mu wahalar da juna, yadda bana iya bacci ba zan barki ki runtsa ba sai dai idan ya kasance kina gefena ina jin saukar numfashinki a ƙirjina ina riƙe dake yadda na san ba za ki guje mini ba" Tsoro ya kama Ridayya da ƙyar ta ce "Me ya kawo maganar nan Sadauki i think it's over between us, everything is over between us.....," "Uhm ko?" Shiru ta yi zuciyarta na bugawa dukda bata ganinsa tsoro da fargabar abinda zuciyarta ke ƙoƙarin ɗarsa mata a kan Sadaukin ya fara gigitata dukda ƙoƙarin da take na danne hakan bata son yarda ko gasgata hakan bata so bata shirya ba, ha dan komai ba sai dan illar da namiji ya yi mata a rayuwa a cikin kunnenta ta tsinkayi kalmar daya faɗa “I have a feelings for you Ridayya no fall in love with you" "Sadauki please, the game is over ka je wajanta ka faɗa mata" A hankali cikin muryar tausayi ya ce "E zani, amma ke za ki rakani na faɗa mata yanzu ma ai ina rihazal ne" Ta sauke numfashi ya ce "Ki yi haƙuri please na miki tsawa ban so ba" nan ma ta yi shiru ta ɗauka ba zai sake magana ba ne sai ta ji ya ce "Zan zo fa, ba rana kawai ki jira zuwana bye ki kula mini da kan ki Shanshan ki shafa mini kan Son" "To" kashe kiran ya yi ta jingina tana lumshe idanunta gabaɗaya abinda bata taɓa ji ba shi ke ƙoƙarin mamaye ta tare da yi mata shigar saurayi Sadauki yana da rigima kuma da saurin shiga rai don dole tana jin daɗin yadda yake ƙaunar Little har zuciyarta. Sadauki na gama wayar ya miƙe ya nufi down stairs ya iske mother zaune tana kallo ya ƙarasa kusa da ita ya yi shiru yana kallon waje guda abu ne mai wahala Sadauki ya zo kusa da mother ya mata surutu ba shirun nasa ya bata mamaki ta ɗan taɓa jikinsa ta zare ido ta ce "Baka da lafiya Sadauki?" Ya girgiza kai kawai bai ma san me yake ba "Ya zaka girgiza kai bayan ga jikinka nan ya yi zafi, daman tunda ka shigo ka shige ɗaki na lura ko abinci baka ci ba what is the matter? Meke damun Sadaukina?" "Ki yi mini addu'a mother ki sani cikin addu'arki don Allah" Ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da ɗage girarsa kansa na yi masa wani irin ciwo ga zazzaɓin daya rufe jikinsa lokaci guda "Addu'a kullum cikin yi maka nake ita Sadauki shi ya sa bana son ka saka abu a rai ka ƙwallafa na ci a kai. Ka yi ta addu'a ka ji ko komai ya yi zafi maganinsa Allah duk wata jarrabawa tana tare da nasara" "In sha Allah love thanks" Da daddare bayan sallar issha Ridayya na kwance a kan gado damuwarta ta dawo sabuwa fil ga tunanin rashin gata da iyaye ga tunanin Zameer da fargabar abinda zai iya aikatawa a kanta. Ga tunanin video idan ya fita da wanne idanu zata kalli Junior? Ta yi masa bayani ga al'ummar gari da suka shayar da ita maɗaci ga tunanin Sadauki da rigimarsa da sauyin da ya yi na lokaci guda idan ta tuna kalar rayuwar da ta yi a gidan aurenta sai ta ji a duniya ba abinda data tsana irin namiji da kuma aure idan ta tuna ƙauyen Batsari sai ta ji ko sunan Katsina bata ƙaunar ji. A hankali take jiyo sautin muryar Tajj yana magana yanayin yadda yake shiru ya bata tabbacin bashi kaɗai bane a parlourn koma shi da waye muryar Tajj ɗin ita ce a sama wancan ɗin kuma maganar tasa gajeriya ce domin sai Tajj ya jima yana magana kafin ta ji ya yi shiru. Yunwar da ta ci ƙarfinta ne ya sanya ta miƙe bisa dole ta sanya slippers tare da ɗora hula ta fito duguwar rigar bacci ce a jikinta wacce ta kwanta ta haska dark black skin ɗinta hasken idanunta da jajayen laɓɓanta kawai ake gani sai tulin gashin girarta. Magana yake a nutse hannunsa riƙe da cup yana ɗan juyawa kaɗan saboda zumar dake ƙasan kofin fararen ƙafafuwansa gabaɗaya ya zuba su saman table ɗin da aka jera masa abin buɗe baki daman haka ɗabi'arsa take ko ya tanƙwashe ƙafafuwansa ko ya miƙar dasu saman abu. Kaɗa ƙafar yake a hankali yana jin Tajj na cewa "Ai ni dole ya zame mini na yi maka biyayya babban yaya duk yadda ka ce haka za a yi amma nasu ka bari ba yanzu ba ko zuwa next week ne" "Tajuddeen ina buƙatar hakan da ganin gilmawarta, ita ɗin wasiyya ce so a yi hakan" "Ba zaka barta ta ƙara satin guda ɗin ba?" Wani irin kallo Ustaz ya yi wa Tajj irin ai ko kwana guda ban ƙara barin Ustaza ta yi a Kano. "Akwai aikin da zan gabatar na kwana uku zuwa huɗu haka. Zan jira bisa dole na gode da ɗawainiyya Allah ya yi maka Albarka" Tajj ya yi dariyar dole ya ce "Amin Babana Abbiey" Tsit ya yi kamar ruwa ya cinye shi bai san ta fito ba sautin da ƙirjinta ke bayarwa ya alamta masa hakan. Ya miƙa hannu ya kashe hasken ɓangaren shi tare da yin baya ya kwanta jikin kujerar idanunsa zube a kanta ganin yadda take tafiya kamar bata so Tajj ma ya bita da Idanu da kalar nasa tunanin ba jimawa ta fito ɗauke ta kofin shayi mai madara sosai ta nufi cikin bedroom ɗin da ƙyar ta ƙarasa domin ta kusa kifawa a jikinta ta ji kallonta ake. Sun jima dukda tun tafiyar Ridayya ko tari Ustaz bai kuma yi ba. 12 daidai ya miƙe hannunsa riƙe da babbar rigarsa da key ɗin mota hular ma a hannunsa ya riƙe sumar kansa nata lilo a gefen fuska da wuyansa. "Ba a nan zaka kwana ba dama? An gyara ɗaya part ɗin" Ustaz ya yi kicin-kicin da fuska yana ƙanƙance idanunsa a hankali ya ce "Ubangiji ga Tajuddeen ka yafe masa da tunanin Muhammad-Bilal zai kwana gidan mutane" "Ya yafe maka dai Babban yaya kuma babbanmu" Ustaz bai kula shi ba ya nufi bedroom ɗin da Ridayya ke ciki bakinsa ɗauke da sallama can ciki yasan abu ne mai wahala ba ta yi bacci ba, bata kaiwa haka ido biyu. Haske ya gauraye ɗakin tana tsakiyar gadon ta rungume Little ya ƙarasa jikinsa na yin sanyi bai kalli fuskarta ita ɗin dai yake kallo ya kalli shayin data ajjiye ya ɗauka ya kurɓa da ƙyar ya haɗiye yana runtse Idanu "Iyayi dai Ustaza iyayi ne hakan da gaske suger ya miki yawa" Ya dinga bin ɗakin ko wacce kusurwa da addu'a bayan ya gama ya saka hannu ya rage mata sanyin ɗakin yana jinjina wawtar Ridayya da bata san illar sanyi ba ya ja mata fargo a hankali ya durƙusa dab da fuskarta sai kuma ya janye jikinta yana kashe hasken ɗakin. Washegari kiran Sadauki ne ya fara shigowa wayarta ta ɗauka da ƙyar kafin ta yi magana ya ce "Subhi ce Shanshan kina ta bacci abinki" "Abbiey" ta furta domin shi ne ya zo bakinta saboda ƙamshin shi ta ji "Mijinki ne wannan ba Abbiey oyya wake up sweetheart" "Oh bari na yi sallah" "I'll call you later ki yi mana addu'a Allah subhanahu wata'ala ya ji tausayin Sadauki ya mallaka miki ke matsayin mata" Murmushi kawai ta yi ta kashe wayar. Manyan mutane ne a cikin haɗaɗɗen parlourn duk wanda ka gani kasan sunansa ya yi amo ko wani shi a jihar. Zama suke na musamman wanda ya shafi yaran jam'iyya da shugaban jam'iyyar gabaɗaya. Ya gyara zama cikin nusa iko da jin daɗin abinda yake faruwa ya ce "Mu hakan ya yi mana kyau, su yi ta gwara kansu ya su ya su, za mu yi amfani da wannan damar wajan cimma manufarmu" Hon. Mubarak Nas ya numfasa ya ce "Mene manufar ta mu madugu? Kaga kawo yanzu sun fi mu ƙarfin jam'iyya tun da ba mu jima da sauya wannan jam'iyyar ba" "Na gode Allah da ka ce ƙarfin jam'iyya suka fi mu ba masoya da magoya baya ba, za mu yi musu kwantar ɓauna mu fid da ƴan'takarkaru kama da ga Gwamana mataimaki ɗan'majilissa na jiha dana tarayya, ƙasar ai ta mu ce ƴan'uba muka samu dole kuma zata dawo hannunmu" Hon Iyantama ya ce "Wannan haka yake kuma za a samu ƴan'anti fati kawai mu tsayar da kyakkawar manufa kar mu yi lako lakon da za a yi mana irin ta shekarun baya a ƙwace mana mulki mu shiga court a banza tunda kaga har koton ƙoli mun shiga amma result ɗin ɗaya ne, Shitu Bala shi ne Gwamna talakawa an saka musu tsoron fitowa sake bin wani layi domin kaɗa kuri'a" Madugu ya ce "Wannan tsoron za mu cire musu mu tabbata sun tsaya akan a ƙidarsu da kwatar ƴan'ci ba wani dalili da zai zo a watsa musu hatsi kamar kaji su bi su tsince" Hon. Mubarak Nas da Hon Iyantama duk sukai ma'ana da maganar uban jam'iyya madugu. "Prof ana ta magana ka yi shiru?" Prof Hamdan Hamish ya ce "Gare ni komai yana going well" "Prof ai shi ne ɗan'takararmu na ɗan majalisar Jiha ina fatan baka da wani abu a ɓoye wanda zai kawowa kujerarka tsaiko yana da kyau mu kawo ko wacce kujera" Prof ya yi shiru sai kuma ya ce "Ba wata matsala, yanzu waye zai zama ɗan'takarar Gwamna a jam'iyya T.D.A?" Madugu ya miƙe tsaye yana ɗan takawa cike da ƙarfin qiwwa kafin ya ce "Wanda za mu bawa kujerar Gwamna ba lallai ya amince ba, amma dole mu sanya masa ƙaunar hakan a zuciyarsa yana da farin jinin al'umma kuma bashi da wani tsaiko ko mugun halin da zai kawo barazana a kujerar da jam'iyya bakiɗaya ganinsa zan binka ai yana gari dole ya dawo mahaifarsa ya ceceta" Da haka taron ya watse Prof na hanyar zuwa gida saboda kiran da Sadauki ya yi masa secretary ya tura saƙo kamar yadda yake nuna musu namiji da sauri ya juya kan motar zuwa hotel ɗin da suka saba haɗuwa. Hajiya ta tashi Mai ran ƙarfe shi da wani mutumin nemawa Ustaz auren Mardiyya bayan sun je kawun Mardiyya ya yi mamakin jin Ustaz na son Mardiyya ya yi farin ciki da hakan domin ya san waye Ustaz girmama mutane sadaƙa da tausayi da ƙare hakƙin addini. Ya ce su je za su yi bincike kuma su zauna da yarinyar domin jin ta bakinta. Haka aka yi nan take Mardiyya ta ce tana son Ustaz kamar rai kuma ta amince. Suka ce za su kawo kuɗin na gani ina so da sadaki da lefe lokaci guda kuma a baki sun saka aure sati uku kacal as soon as Ustaz ya dawo Legas zai zo gaishe su kuma za a haɗu da komai na biki kawai yarinya ta zama cikin shiri ta faɗi duk mai take buƙata shi Ustaz na can Kano bai san meke faruwa ba. Kwana huɗu Ridayya bata kuma saka Ustaz a idanunta ba tama manta da hakan tun abinda ya faru shima Ustaz tun daren bai ƙara zuwa ba abubuwa sun ɗan sha masa kai ƙoƙarin ajjiye matsayin Md yake a fidelity bank ɗin. Yana zaune wani baƙin yadin kaftani ne a jikinsa mai kyau da laushi ya kwanta a jikinsa sosai ya ƙara haska farar fatar da har wani yellow take saboda haske. Babu babbar riga yau hannun rigar ma half ne saboda ciwon da kansa yake masa ya saka ya ajjiye zanna bukar ɗin a gefe sama-sama yake jin maganar Tajj suna zaune har a ka yi sallama. "Sadauki wai yaushe gidan Mahmah ya zama gidan zuwanka?" Sadauki yana kaɗa ɗan'mukullin motarsa brown ɗin wagambari ne a jikinsa ɗinkin 3 fisis na maza an jera masa bottles a tsakiya ya ɗora jaddara a kansa ya yi miskilin murmushi ya ce "Uhm Commissioner kenan" "Kira ni da sunan Hamza ai kaɗan daga cikin aikinka" Sadauki ya girgiza kai ya ce "Ni yau ba faɗa na zo yi ba, unguwa za a rakani" "Ikon Allah Mahmah ɗin ce zata rakaka unguwa ko Nadra?" Sadauki ya gyatsina fuska ya ce "Me zan ɗauka da wannan ƴar'taka mai surutun tsiya, kuma ai ba su kaɗai bane Ridayya na zo ta rakani" Cak Ustaz ya tsaya da danna wayar da yake yana nanata sunan wacce yaron ya kira yaushe Ustaza ta zama haka? Har take wa maza rakiya? A zahiri ba zaka taɓa cewa Ustaz ya san me suke cewa ba. Tajj ya kasa cewa komai. Sadauki ya ɗauki waya ya kira numberta tana ɗakko ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Shanshan ina parlour ina jiranki, magana za mu yi very important a hanya, na nemi izinin Commissioner karki ji tsoron wannan bogin bindigar tasa, waiting for you" Kashe wayar ya yi babu jimawa sai ga Ridayya ta fito cikin wata pink ɗin abaya mai kyau ta yi rolling kanta da vail ta yi ƙiba amma kana ganinta kasan bata cikin nutsuwa. Tajj na jin lokacin da Sadauki ya sauke numfashi ya ce "Rest of my life, i so much love you my ride or die" Kanta a ƙasa ta ƙarasa tana ta wasa da yatsun hannunta "shall we?" Sadauki ya faɗa "Abban Nadra zan raka S....." Tajj ya yi murmushi a ransa yana cewa wannan faɗan da umarnin ba nawa bane. Ridayya kowa maganar ce ta tsaya mata lokacin da idanunta ya sauka a kan Ustaz so da gaske shi ɗinne? Ta dinga kallonsa jikinta na rawa Sadauki ya ja mata masifa gashi ko inda take Ustaz bai kalla ba kuma tasan sarai ya ji muryarta. "Mu je mana?" Cewar Sadauki ya faɗa yana miƙewa tare da kallonta Ta kasa motsawa kanta a ƙasa a ɗan hargitse Sadauki ya ce "What are you afraid of.......,?" Jin Sadauki na neman fasa masa kai ya saka Ustaz ajjiye wayar tare da ɗaga fararen idanunsa yana shigar da su ciki ya kalli Ridayya sosai da kyau sai ya ɗauke ganinsa "Koma ciki" Ya faɗa cikin nuna umarni da sauri ta juya Sadauki takaici kamar ya fashe waye wannan ɗin da zai nuna masa iko da Ridayya?. Ustaz ya miƙe yana ajjiye wayarsa ya nufi ɗakin Ridayya ya murɗa ya shiga tare da saka key ya zare ya cillar saman wardrobe. Jikin Ridayya sai rawa yake da ɓari bakinta na karkarwa "Abbiey da gaske kai ne? Ko mafarki nake yi Abbiey nane?" Kallonta kawai yake yana nufar inda take tsaye bai san me yake ba shi dai ya tsinci kansa a gabanta ne hawayen fuskarta sun jiƙa masa tafin hannu kuka ta fashe da shi tana yin baya gani take har yanzu mafarki ne "Daman nasan mafarki ne ba Abbiey bane me ya sa kasan ba kai bane zaka kora ni ka hanani bin Sadauki?" Sai a lokacin ta girgiza kai yana jin kalamar Sadauki a kansa a fili ya ce "Ba ki da kai Ustaza" "Innalillahi wai mafarki nake ko Idanu biyu muryar Abbiey nake ji Abbiey..m.," bata ƙarasa maganar ba ta ji ya cafko hannunta tare da haɗe ta da jikinsa ya riƙe ta gam a ƙirjinsa ba daidai kunnenta yana sauke numfashi ya ce "Ustaza Oum-Bilal" ya faɗa yana yi mata wata kyakkawar rungumar da shi kansa bai san ya yi ba. Karanta ki yi comment ki danna share to all your groups *MUNAFUKIN MIJI 30* Mikiya Writers Ass... Bright pens free batch Nimcyluv sarauta Zazzare Idanu ta yi sai ta ji wani iri ta kasa kallonsa sunan Oum-Bilal ya yi mata wani iri. Sakin ta Ustaz ya yi bayan ya gama zuge mata zip ɗin data mance bata rufe ba, wanda shi ne dalilin biyo bayanta da kuma kusancin da suka samu wanda a tunaninta rungumeta zai yi. Ya ja baya tamkar bashi ya yi magana ba ya ce "long time Sayyada, irin zuba kyau haka?" Ridayya ta kasa ɗago kanta dake ƙasa tsoro da kunyar Abbiey ɗin ya mamaye mata zuciya, tunanin hukuncin da zai yi mata a kan Sadauki kawai take yi, daman yasan tana nan amma ya kasa nemanta cikin shekarun nan ko watanni? "Zo mana" Ustaz ya furta a taushashe bayan ya gama daidaita zaman shi a saman gefen gadon ɗakin nata idanunsa a kan wayarta dake ringing an rubuta “Sahibi” Ta ƙarasa tare da zubewa a gabansa ƙasan ƙafafuwansa ko zama ta kasa bakinta na rawa ta ce "Ina yini Abbiey?" "Allah ya yafe miki Ustaza ba haka muka saba ba kin ji ko" Hannunsa na dama ya miƙa mata a hankali ta ɗago kanta tare da cira hannunta na dama ta miƙa masa sukai musabaha ya riƙe ɗan mitsitsin hannu idanunsa zube a fuskarta ya ce "Assalamu'alaiki" "Wasallamu'aika Abbiey" "Sannu Oum-Bilal kina lafiya dai? Komai ƙalau?" Ta jinjina masa kai ya zame hannunsa yana yin baya ya jingina da jikin frame wasu sakanni ya ɗauka kafin ya ce "Masha Allah. Rabbi ya yi miki albarka" "Amin" Ta yi shiru na rashin abin faɗa banda harbawa da ƙarfi babu abinda zuciyarta ke yi mata, a kullum Ustaz na yi mata kwarjini amma na yau na musamman ne ya sauya mata gabaɗaya babban abin ba wani sauyin kamanni a fuskarsa banda shekaru da ƙasumba daya ƙara da yawan sumar kai, sa nutsuwarsa da tarin kamalar daya sake mamaye gangar jikinsa ga wata Ilham ta musamman. Haka kawai ta ji ranta ya ɓaci da ransa da lafiyarsa hankalinsa kwance yake gudanar da mu'malarsa babu damuwa da tunanin yarinyarsa bata tare da shi bai san hali da ƙuncin data shiga ba. Baya kallonta a zahiri sai sai dai da idanun zuciya yake kallon yanayinta shi bai ma san yaushe ya riƙe ta taɓa ɗazo kawai yasan ba zai zuba Idanu ta fita riga a buɗe ba. Duk suka yi shiru kowa ya kasa magana sai bugun zuciyarsu dake aiki so yake ya tambayeta ina mijin nata? Ya akai ya neme ta ya rasa. Mahmah ce ta shigo ɗauke da Little dake kuka sosai tana faɗin "Mimi gashi ya addabi jama'a da kuka kin san halinsa idan ya fara kuka sai kin bashi ya sha hankalinsa yake kwanciya" Ridayya ta kasa amsar Little ita kunyar Abbiey take yaga wai wannan ita ta haife shi kenan ya san me ta yi ta samu ɗan? "Ina magana kina jin yaro zai fasa kunnen mutane?" A marairaice ta ce "Mahmah ki riƙe shi zai yi shiru fa" Daƙuwa ta yi mata ta ce "ungu wannan dan gidanku idan ke ba ki sha nonon uwa ba sai aka ce shi kar ki bashi? Saboda wa Allah ya hallici nonon banda yaranki? Bafa don a do aka mallaka miki su ba. Naga kullum kina bashi yanzu iyayi ne ko san a sani? Karɓe shi ni" Idanunta tuni ya yi raurau hawaye ya cika su wacce kalar mafisa ce Mahmah ke shirin janyo mata don abin kunya? "Don Allah Mahmah wallahi....," Ustaz dai da kunne yake ji ko ɗaga kai bai yi, he just pretend kamar bai san mene faruwa ba. Ajjiye mata shi ta yi a cinya Mahmah na fita da halin yaran yanzu ta yi waje abinta don ita har zuciyarta bata ɗauka ta yi wani laifi ba. Little ya dinga kuka yana zura hannunsa cikin rigar Ridayya alamar dai a matse take har da haura ƙafa kukan ya yi wa Ustaz wani iri a ka domin har ƙasan zuciyarsa yake jin kukan na Little ya ɗago kai yana haɗe fuska ya ce "Ba haka na yi miki ba Ustaza da gaske ban raineki haka ba, ko sau ɗaya a ta dalilina ba ki taɓa kuka ba" Ya faɗa yana gyara zama tare da kafe ta da Idanu babu kuma wasa a fuskarsa don shi bai ga wannan dalilin ɗaukan alhaki da zunubin ba. Ta tura baki taƙi cewa komai ita haka kurum haushinsa ya kamata me ya sa bai taɓa nemanta ba ta kuma yi alƙawarin ba zata yi magana ba amma tuni hawaye sun fara sauka daga idanunta saboda zallar sangarta da ganin kuma Ustaz ɗin a gabanta. "Ko dai ki bashi abinda ya kewa ko kuma ni na zo na bashi, ko kuma dai ki cire su tunda basu da wani amfani" Ganin ya miƙe ya saka ta yi saurin riƙe Little ta fara ƙoƙarin fito da shi cikin sauri kuma mai kama da nutsuwa Ustaz ya yi hanyar ƙofa yana jin kansa na sarawa. Sanda ya fito daga bedroom ɗin Ridayya ya samu Tajj zaune shi da Sadauki daya gama rikicewa ya daddafe kansa da yake masa wani irin ciwo. Shi fa dole yau sai ya fita da Shanshan duk wahala yadda ya nuna masa iko shi ma dole ya nuna masa ya fisa dabara kuma ɗan'yau ne shi. Ya miƙe tsaye ya ce "Please i want to talk to you Brother" Tajj ya nuna kansa ya ce "Ni?" Ya jinjina kansa tare da ficewa ya yi waje. Tajj ya miƙe ya bi bayan Sadauki. "Wannan kiran fa Hamza?" Sadauki ya riƙe hannun Tajj tare da ɗorawa a zuciyarsa ya ce "Ka ji ko? Ka ji yadda zuciyata take yi to wallahi gab take da bugawa kuma na san ba za ka so na mutu yanzu ban yi achieving komai ba, ban yi aure na haifi kamar Nadra ba, ban san mene daɗin aure da daɗin zama da macen da kake tsananin so ba, ina so aure sosai" "Duk ɗan sunna ai ba zai ƙi sunna ba Sadauki" Sadauki ya jinjina kai yana ƙasa da murya har ɗagawar ƙirjinsa ana gani ya kama hannun Tajj ya damƙe cikin roƙo da neman iri ya ce "Kai ne tsanin da zan hau na cimma gaci, gina soyayya a tubalin zuciyar daya dace da Hamza Sadauki wannan ba matsala ba, magance abinda zai iya kawo shamaki a rayuwar Sadauki da matar da yake da burin rayuwa da ita shi ne matsalar, Yaya help me please allow me to go with her" "Ita wa?" Sadauki ya hargitsa kansa kamar ya make Tajj haka yake ji ya ce "Haba Yaya haba Baban Nadra ya kake haka ne ka fahimta mana" Tajj ya girgiza kai ya ce "Ban fahimta ba Sadauki" "Ka fahimta mana da Hausa nake magana bada yaran Jamus ba, balle ka ce don na rayuwa a canne. Ka bani izini na fita da Ridayya akwai magana mai muhimmanci da zamu tattauna da ita ka tausaya mini" "Wacce magana bisa wanne dalili kake son fita da ita?" "Saboda ina son ta, ina son ta, ina son Ridayya Yaya kuma aurenta nake son yi" Tajj ji ya yi jiri na neman yar da shi zuwa ƙasa ya yi saurin jingina da motar Sadauki yana karanto Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! A zuciyarsa ga Amini da ɗan'uwa ga kuma shi shi bai tsaya ya nutsu a kan qualities ɗin Ridayya ba kawai ya ji yana son rayuwa da ita ko dan yadda Nadra ta samu farin ciki, yana tsananin tsoron macen da zai aura wacce zata riƙe masa yarinya saboda Allah.. "Ka yi shiru, akwai matsala ne?" Tajj ya girgiza kai ya ce "Gare ni babu, amma wanda ya ce ta koma cikin nan shi ne problem ɗin. Shi ne komai nata shi ne yake da ikon baka ita da amincewa da kai, idan ka ji ance Ridayya Muhammad-Bilal Rano to ita ce sunansa ne maƙale a nata. Idan na faɗa maka halin da Ustaz ya shiga da babu ita zaka ƙaryata domin tamkar ƴa haka take wajansa" "Da sauƙi ai ka ce kamar ƴa ina tunanin problem kaɗan ne" Murmushi Tajj ya yi yana taɓa kafaɗar Sadauki ya ce "Soyayya gaskiya ce Hamza, kuma dukkan inda soyayya ta gaskiya take tana nuna kan ta duk yadda mutum ya kai ga zurfin cikinsa, wani irin abu ne da yake fitar da kansa ba tare da mutum ya shirya ba. Akwai bambanci tsakanin _i have a feelings for you ko you're my crush da i have falls in love with you_. Sadauki ba kasancewar Muhammmmd uba a wajan Ridayya ne matsala ba, Ridayya ita kanta ita ce rayuwar Ustaz wallahi Allah ba zan yi san zuciya ba, ko dan kasancewarka jinina. Ustaz yana tsananin so da ƙaunarta bai taɓa faɗa mini amma halin daya shiga ya nuna, yanayin daya samu kansa daya ganta ya fallasa sirrin zuciyarsa ina tunani ka yi haƙuri ka nemi wata ko a family ne" Wata kalar dariya Sadauki ya yi yana fesar da iska daga bakinsa yana dinga tafiya yana dawowa sai kuma ya girgiza kai ya ce "Idan shi yana son ta ita tana son shi ne? Idan yana son ta mene yasa ya barta ta auri waninsa? This is unbelievable" "Ƙaddara ita ce silar faruwar komai, ƙaddara ita ta sanya Ridayya yin aure kuma har ta haihu kuma ƙaddara ita ta saka mijin ya sake ta. Kasancewar littafin da zanen ƙaddararsu ɗaya ne ya saka shima bai yi aure ba har yanzu, kuma ƙaddara ta ɗauki rayuwar iyayensu ta bar su, su kaɗai a duniya, ƙaddara ita ta saka muka buge Ridayya kuma na kawota gidana zuwan Ustaz nawa bai taɓa ganinta ba, kuma ƙaddara ita ta haɗa su yanzu bana son wannan ƙaddarar ta yi silar rayuwarka Hamza You are my young brother kabar maganar iya mu domin ko Ridayya bata so a wannan karan bata da zaɓin daya shige Muhammad-Bilal" Sadauki ya zame hannun Tajj ya ce "This is serious. Ni kuma na ɗaukar maka alƙawari ƙaddarar aurena ita ta rabata da mijinta, kuma wallahi ba zan taɓa haƙura ba, bana faɗuwa ko a makaranta ba kuma zan faɗi a Soyayya ba, ko zan rayu da Ridayya na kwana ɗaya a matsayin miji da mata wallahi sai na aureta kuma zan tabbatar mata a yanzu soyayya take buƙata ba zaɓin wani ba, dole ta bi abinda zuciyarta yake so" Tajj ya yi murmushi ya ce "I wish you all the best Romeo" "What ever; na ji na yar da kuma zaka sha mamaki Commissioner" "Commissioner? Yayanfa?" Sadauki ya haɗe rai ya ce "Ba zan faɗa ba, tunda ka kasa taimakona bana ma buƙata kuma duk sanda ka ji an ce alfatiha ni da Shanshan daga ranar ni ne babba" Ciki ya koma ya samu Ustaz riƙe da Little yana jijjiga shi ya kalli Mahmah ya ce "Mahmah please za mu fita tare da Ridayya" "To Allah ya tsare ya kiyaye" Sosai mamaki ya cika Ustaz jin furucin Mahmah sai ya share kawai. Yana zaune yaga sun fito tare da Ustaz kafin ta yi magana Ustaz ya miƙe fuskarsa kamar an yi masa wahayi da ranar mutuwarsa ko an ce masa Hajiya ta rasu ba walwala jijiyoyin kansa duk sun fito ya ajjiye Little ya kalli Sadauki dake bisa hanya. Hannun Ridayya ya damƙa tamkar zai ɓalla shi biyu ya yi ciki da ita suna shiga ya ɗauki akwati ya fara zuba kayanta ciki sai kuma ya fasa ya cire mayafin kanta ya jawota gabansa ya saka mata hijabi ya sake damƙo hannunta ya sunkuya ya ɗauki Little. "Lafiya Ustaz?" Wayar hannun Ridayya ya amsa ya bawa Tajj ya ce "Tajuddeen Allah ya yi maka albarka mun gode" Ya juya ya kalli Mahmah ya ce "Mahmah tarbiyar ƴa'mace akwai wahala musamman lokacin ƙuruciya da matakin girma bai cancanci ana barinta fita ba, ban yi zaton haka ba" "Ayya Ustaz ai naga Sadauki ne shi ɗin kuma ɗa ne a waje na shi ya sa" "Muharraminta ne? Ba haka na raini yarinyarta ba, ki yi haƙuri Mahmah amma ban ji daɗi ba Ustaza bata taɓa fita da wani ba sai lokacin da aka yi mata aure, ina son ruɗin samarin da yaran zamani na yanzu kar su lalata mini ita. Dole za ki ji ba daɗi amma gaskiya ce bana barinta, a kiyaye hakan ko dan Nadra maza basu da tabbas haka ɗiya mace bata da tabbas akan soyayyar zamani, ni na yarda da yarinyata. Babu komai na yafe miki Allah ya kankare zunubanki" Tajj ya girgiza kai abin dariya abin takaici. "Ni ba zan taɓa lalata Shanshan ba, ka bani dama a matsayinka na uba mu fita tare da ita zan dawo maka da yarinyarka cikin salama kawai Restaurant za mu, mu yi abu very important.....," Wani irin mari Ustaz ya saukewa Sadauki a fuska yana nuna shi da yatsa zuciya ta ɗauki Sadauki ya dunƙule hannu zai naushi Ustaz Ridayya ta yi saurin dakawa Sadauki tsawa "Mene haka? Dukansa za ka yi?" Ya sauke hannun ƙasa idanunsa jajur jikinsa na rawa ƙwayar idanun Ridayya yake kallo kuma ya fahimci komai ba. "Shanshan ya zan yi? What do you want me to do? Kin mini alƙawari Shanshan" Juyawa ta yi zata shige ɗaki Ustaz ya riƙe ta ya ce "Mu je" Da wani irin expression Ridayya ke kallon Ustaz hawaye ya cika idanunta ta ce "Ba zan bika ba, ba zan taɓa binka ba" sai kuma ta fashe da kuka sosai. Ustaz kallonta yake yana ɓoye tashin hankalinsa. "Ustaza gidana zan kai ki mu zauna tare" "Bana son zama da kai bana son ganinka Abbiey baka damu dani ba, baka damu da halin da nake ciki ba, kalle ka ka yi kyau ka ƙara fari ka yi ƙiba kana zaune cikin kwanciyar hankali ka kwanta ka yi bacci, babu mai hattararka babu mai saka abu ya ƙona ka babu mai hanaka abinci babu mai zagin halittarka babu mai ce maka maye, baka taɓa nema na ba ko sau ɗaya babu inda ban shiga ba akan nemanka Abbiey ban ganka ba, bana da kowa bana da dangi babu mai kulawa da maraicina babu wanda zai faɗawa damuwata. Sai yanzu sama taka ka zo ka ce na bika? Ka barni ka rabu dani na ƙare rayuwarta a rashin gata da ƴanci kamar yadda na fara ka bari na mutu ka zo ka ɗauki gawata" Ba zai ce ƙiyayya ya hangu a idanun Ridayya ba amma ya hangi rashin yarda damuwa tsoro ransa abu, haushi, takaici uwa uba kewa. Fargaba ta kama Ustaz ya rasa me zai ce. Ridayya na kuka ta ce "Ka kai ni gidanka? Abbiey kenan aure ka yi ban sani ba? Shikenan ka je ka zauna da matarka bana son ƙara ganinka wallahi wallahi Allah ba zan bika ba" Tajj ya ce "Ridayya You misunderstanding babu..." "No Tajj" Ustaz ya faɗa a hankali yana miƙa mata Little ta amsa ya juya ya fita daga gidan bakiɗaya. Ikon Allah ne kawai ya kai shi masaukinsa wani irin kuka Ridayya take wanda ita kanta bata san dalili ba. Mamakin wawta da rashin hankalin Ridayya ya gigita Tajj taya tunaninta ya bata Ustaz bai neme ta ba? Har ta kafa hujja a kan haka, ko Ustaz zai yi fushi dole ya faɗawa Ridayya halin da ya shiga. Ganin abinda ke faruwa ya saka Sadauki fita hankali tashe ya nufi gida. Sama da kwana uku duka wayoyin Ustaz a rufe suke kuma Tajj bai san inda ya sauka ba domin Ustaz mutum ne mai sirri da son rayuwar sirri da keɓewa waje guda. NAHUTU/BATSARI Kallon yaron yake cike da damuwa da takaici ganin babu wanda yake ɗaukan shi saboda tsananin muni da ƙazanta, ya ƙara yin wani irin baƙi idanunsa daƙwa-daƙwa ga wani rafkeken hanci gashi gashi ko ɗaya babu a kansa kamar an yi masa ƙwal kwabo tamkar ɗan'ruwa. Ga masifar kashi a wando kuma babu mai ɗaukar shi shi fa duk inda Ridayya take dole ta zo ta amshi ɗan'ta ta bashi nata yana da tabbacin Little shi ne yaron da suka haifa da Khairiyya Harazimi kuma Ridayya ta haife shi, saboda babu yadda za a yi baƙa mummuna kamar Ridayya ta haifi yaro kamar Balarabe. Ya sauke ajjiyar zuciya saboda masifar yunwar dake cinsa Iya ta ce "Ka yi hamma ta yi dubu har wannan kar ka cinye ni idan iya ɗan'ka za ka ci da sauƙi, ai muddin ba zaka shiga gona ka taya babanka aikin gona ba ko kayo ita ce kana cikin garari wallahi tallahi yunwa yanzu ka fara zama da ita. Abin tausayi ka saba da cin lemo zubu da biredi da jar miya" "Giɗaɗo magana nake" "Haba Iya sau nawa na ce miki Zameer sunana ko Meer? Yunwa nake ji sosai" "Sai dai kaci kanka ƙandas wallahi dan ko ƙwayar gero babu balle mu yi gero da wake" Ta faɗa tana ƙarasa watsar garin hannunta zuwa baki. Wani irin yanayi ya ji saboda tunanin Ridayya, ko ta ci ko bata ci ba haka zata ɗauki abinci ta bashi ya ci ya sha ruwa, amma gashi uwar data haife shi ta gaza bashi abinci, Ridayya ta yi masa wanki guga ta dafa masa ruwan wanka haka kuma zata faskara ice a fili ya ce "Da sake" "Wanne saken? Wai ba zaka nemo yarinyar nan ba? Nifa hankalina yana kan zuwa makka ɗin nan na shiga sararin subuhana na sauka ƙasa mai tsarki, gashi ka ajjiye takardu" "Iya dole duk inda Mai sona take zata dawo domin bata da wani zaɓi daya shige rayuwa dani, bata da kowa babu kuma wanda zai ce yana son ta domin ta tashi daga aiki ni na fara kuma ni zan ƙarar bata da wata marmora ai na faɗa miki tun kafin na aureta ta bani a kanta, tana masifar so na ba zata iya rayuwa babu ni ba dukda abinda na yi mata, balle yanzu da bata da wani gata duk iyayenta sun mutu har mariƙin nata ko tana da gatan ma ai basa son ta, kinga dole mu mayar da aurenmu a lokacin ma idan ta zo sai na ja ajina" "Sakinta ka yi ne Giɗaɗo?" "A'a ba wani saki guduwa ta yi na san Khairiyya ba zata dawo gare ni ba zan lallaɓa na je wajan Hanne kafin Ridayya ta dawo, kuma zan ɗauki takardun kadarorin nata a satin nan na shiga Kano na fara siyar da fili ko guda uku ne" Ya miƙe da ƙyar ya fita yana jin Harazimi na kuka. Iyanti ta ce "A yi dai mu gani idan tusa zata hura wuta" Iya ya leƙo ta ce "Zata hura mana sai dai ba daga Babban ɗuwawu ta fito ba" Zameer na fita gona ya nufa Moo ya kira shi ya ɗaga ya ce "Haba Zameer tafiya shiru shiru har yanzu daga Germany ɗin?" Zameer ya fara hura iska ta cikin wayar ya ce "Daddy ɗina abubuwa sun masa yawa yanzu ma muna airport daga Germany za mu shige England a duba lafiyarsa nan da sati za mu dawo" Moo ta cikin wayar ya ce "Ayya Allah ya bawa Daddy lafiya Gaskiya ne ajeebo kana saurarawa" Kafin Zameer ya yi magana Moo ya ji ta cikin wayar an fasa ihu ana faɗin "Giɗaɗo wai ka zo maciji ya sari Baffa" Ganin an haura sati ya saka Hajiya zuwa Rano ta siyar da gona ta saka aka haɗa kayan lefe ta ware kuɗin sadaki da komai da komai. "Goben nan idan kun je wajan iyayen Mardiyya kawai a ɗaura auren sai na fi samun nutsuwar zuciya ina tausayin Ustaz burina bai shige ya yi aure ba" "Matar anya ba ki yi gaggawa ba? Ki bari ya dawo" Ta ce "A'a ba wata gaggawa ni ban santa ba, In sha Allah sai dai ya dawo yaga matarsa a ɗaki zamansa ya fara dundirata haka" Hajiya ta kafe Mai ran ƙarfe da wasu mutane suka nufi gidansu Mardiyya nan take kamar auren bazawara aka ɗaura auren Mardiyya Salis da Muhammad-Bilal Tahir Rano a kan sadaki dubu hamsin bisa tsari na Muslunci aka raba alawa da goro. Mardiyya har sujjudul shukri ta yi ta mallaki Ustaz cikin ruwan sanyi miji na kere sa'a ta ce ita ko ba'a gama haɗa kayan ɗaki ba zata bi su Mai ran ƙarfe gidan mijinta ta yi masa kyakkawar tarba gabaɗaya ta mance da cewa ya ce bashi da lafiyar ɗa'namiji. Kullum Ridayya sai sun yi waya da Sadauki ta cikin wayar yake shaida mata ita ce wacce yake so ta bashi dama. Har yanzu bata ce ta amsa ba, ba kuma ta san mene matsayin Sadaukin a ranta ba kullum sai ya yi kamar zai yi mata kuka kalaman soyayya na musamman ke fita daga bakin Sadauki baya tsoron Ustaz ko kaɗan. Kwana goma kenan da faruwar hakan misalin 11:43 Ustaz ya shigo gidan babu mai cewa shi wata kakkaurar black ɗin jersey ce a jikinsa sai trouser babu ko hirami gabaɗaya a ɗan hargitse yake, babu kowa a main parlour ya nufi bedroom ɗinta ya ɗauki Little ya fita da shi ya kwantar a bayan mota ya dawo cikin ɗakin yaga bacci take sosai ya san baccinta da nauyi, daga ita sai rigar bacci ya sunkuya ya cicciɓeta ya nufi mota da ita yana shiga rufe yana ƙoƙarin yi wa motar key tana farkawa ganinsa ya saka ta buɗe baki za ta yi magana fuskarsa babu walwala ya saka hannu ya riƙe bakin nata tare da murɗe shi da sauri kuma ya ja motar ya fice da wani irin gudu.... 🥰🧚🏻‍♀️ Sannun ku Mar'atussaliha na yaba muku wajan comment da sharing Ubangiji ya raya zuri'a. 👉🏼🤙🏼🤙🏼 Zazzafar muhawara team Sadauki da Ustaz Ridayya dai second hand ce. *MUNAFUKIN MIJI 31* Mikiya Writers Ass... Bright pens free batch Nimcyluv Hotel ɗin da yake sauka tare da yin rayuwarsa secret and privacy a Kano ɗin nan ya nufa da ita, a jikinsa yake jin idanuwanta na yawo a kansa ya share fuskarsa babu walwala ta yi jajur a haka driving da gudu dukda kasancewarsa Ustaz baya ƙaunar yin tuki a hankali. Ustaz ya yi parking a harabar hotel ɗin a hankali ya kifa kansa a kan sitiyarin motar yana fid da numfashi wani irin zafi zuciyarsa ke yi masa, ciwon da ya yi na kwana biyu bayan faruwar abun shi ya hana shi dawowa, so yake ya zama mutum mai uzuri baya son nuna zafin zuciyarsa a kan Ridayya akwai tarin abubuwan da idan ya duba ya ke yi wa Ridayya uzuri. Yanzu ma a hargitse ya fito kuma baya son taga fushinsa domin ya fahimci idan ya nuna damuwarsa kamar hakan take so shi ne abinda take buƙata. Fitowa ya yi daga cikin motar wani ya zo wajansa da sauri ya ɗan jingina da motar yana sauraren bayanin mutumin wanda tsayin lokaci ya kasa zama ya ji bayanin sai yanzu. "Da gaske depression yana neman cin ƙarfinka damuwa ta yi wa zuciyarka yawa baka samun yin bacci cikin dare haka da rana ba yi kake ba, zuciyarka a ƙuntace take sosai hatta yawan ciwon kan da kaɗaitar da kake buƙata duk alamomin depression da rashin son maganar ka yi ƙoƙari ka samu nutsuwa ka ɗan ɓata lokacinka a kan wani abun da zai ɗauke maka kewa gudun kar kwakwalwarka ta samu matsala" Ustaz ya yatsunsa fuska yana jan gemunsa dake yi masa ƙaiƙayi saboda sauyin yanayi baya son zafi weather ɗin Kano dana Lagos are different. Ya jima kafin ya ce "Ina jin kamar ana kiran sunana ko ana jana wani wajan idan na rufe" "Dole za ka ji hakan, amfanin zuwa asibitin kenan idan wasu ne cewa za su yi mutanen ɓoye ne ai cutar damuwa haka take signs and symptoms na depression yake you have to be very careful Sir, symptoms ɗin suna da yawa. Feelings of sadness, tearfulness, emptiness, or hopelessness Anxiety, agitation, or restlessness Behavior that looks like extreme laziness, rudeness, or disregard for others. Ɓacin rai da kulawa da lokaci, takaici, jin rashin fahimta da rashin kulawa, jin rashin sha'awa da wasu ayyukan al'ada, janyewa daga jama'a rashin mayar da kira rubutu da saƙon imel. Soke wasu tsare-tsare gajiyawa da rashin kuzari rashin samun wadataccen bacci,Jinkirin tunani, magana, ko motsin jiki. Feelings of worthlessness or guilt Fixating on past failures or self-blame Trouble thinking, concentrating, making decisions and remembering things" Dr ɗin ya jinkirta kafin ya ce "Kai namiji ne wanda bai kamata a samu haka daga gare ka ba, i wonder why har ka samu kan ka cikin cutar damuwa dole ka kula kuma.....," "Enough!" Ustaz ya furta yana runtse idanunsa ya girgiza kansa kaɗan sai kuma kawai ya jinjina wa Dr ɗin kai tare da bashi damar tafiya. Gabaɗaya ji ya yi jiri na neman ɗaukar shi, yana ganin mutane bibbiyu a idanunsa ga wani irin sabon ɓacin rai dake wanzuwa a zuciyarsa me miliyan yake nufi? Mahaukaci zai zama ko me sunan Allah kawai yake ambata har ya ɗan samu sassauci ya buɗe bayan motar ya ɗauki Little da har yanzu bacci yake, a nutse ya nufi ɓangaren ɗaya ƙofar ya saka key ya buɗe ya ganta ta kifa kai tana shassheƙar kuka ga rigar jikinta duk ta manne mata a fata da yatsunsa ya fara mata magana taƙi ɗago kanta shi ba zai iya tashin hankali ba ko buɗe baki ya yi zai yi magana har tsakiyar kansa yake jin wani irin dokawa. Ta ɗago kai ta kasa kallonsa domin duk abinta bata iya kallon idanunsa, a hankali ta fito daga motar Ustaz ya bita da kallo yaga rigar sam ba ta yi masa ba "Riƙe shi muga" Amsar Little ta yi sai cin ɗaci take tana ɓata rai jerseyn jikinsa taga ya cire ya zama sai farar singlet a jikinsa da trouser ya zama ƙato a gabanta ya miƙa mata ta tura baki ta ce "Ni ka mayar dani" Ya girgiza kansa bai ce komai ba ya gyara tsaiwarsa tare da marsad ya saka mata jerseyn ta rufe mata kirji ya ɗan sauke numfashi maganar ita kanta ba komai take ji ba kamar mai raɗa ya ce "Za ki komai na ɗauka, banda nuna tsaraici da sura Sayyada" Ta tura baki ya kalli lips ɗin kansa na juyawa da sauri kuma ya ɗauke kai ya amshi Little yana tafe tana binsa domin ya san halinta babu inda ta sani kuma ba zata iya komawa ba. A ƙofar wani bedroom ya tsaya ya saka key ya buɗe, yanayin wajan na mutum ɗaya ne komai da komai yana shiga ya kwantar da Little har ya je bakin ƙofa ya ce "Ina zuwa" Ta bi shi da kallo ya jima kafin ya dawo, yana shigowa taga idanunsa sun rine ba kuma ja sukai ba tsananin azabar ciwon kai ne. Ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito sanye da islamic jallabiyya mai ƙaramin hannu banda ita ba da haka zai kwanta zafi yake ji sosai. "Abbiey jallabiyya dai wannan jallabiyyar sai na yayyanka su" Sarai ya jita amma ko kallonta bai yi ba, ya daddafa ya yi sallah ya yi azkar ya miƙe kamar zai nufi gado ta yi saurin tashi bai kalleta ba ya ce "Ba ki da kai Ustaza, me kike tunani?" Ta yi shiru, shirun nata kuma damunsa yake ko bai tanka mata ba yana son jin maganarta ya ji kalar tsraiwar data sake "Sallah zan yi" Ta faɗa kai tsaye ita idan ta yi wa Ustaz ƙarya har cikin zuciyarta bata jin daɗin hakan "Kwanan wata 15 yau, yaushe al'adar ki ta rikiɗe?" Wata kunya ce ta kama Ridayya komai nata ya sani, da gaske bata sallah tashi kawai ta yi da tunanin kwanciya zai yi a gadon "Uhmm Ustaza kenan akwai matsala a kwakwalwarki ban miki komai ba a baya sai yanzu? Lokaci dai" "Ni kawai Abbiey ka mayar dani gida na ce ba zan bika ba, ba zan je gidan matarka ba" Ya nemi waje ya zauna yana tanƙwashe ƙafafuwansa sosai ya dube ta yana jin ciwon kansa na sauka ya daɗe kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Kina da matsala da matata ne?" A hassale kamar ba Ridayya ba ta ce "E, ina da ita mene ruwanta da kai zata aureka? Kuma ni ba zan je na dinga ganin yadda kuke rayuwa ba" Nan da nan idanunta ya cika da hawaye sai yanzu Ustaz ya fahimci da biyu ta yi masa abinda ta yi kwanaki idan ya fahimta daidai ya haɗe da fuska sosai kamar ba shi ba a kasashe ya ce "Oum-Bilal buɗe kunne zuwa gidana da rayuwa dani dole ya zame miki domin ina buƙatar, ina ƙaunar matata kuma ƴar'uwata bisa umarninta na zo gare ki, soyayya da ƙaunarta a zuciyata ya saka nake mata uzuri, idan kika bari ta yi kuka saboda ke za ki ga me zan miki, bana son fushinta kuma rayuwa gidana daban take wacce baki taɓa ganin irinta ba ko a mafarki" Numfashinta ta ji yana tsayawa ta saka hannu ta ɗan riƙe rigarta bakinta na rawa ta ce "Da gaske wai ka yi aure Abbiey? Waka aura?" Haɗaɗɗiyar girarsa ya ɗage mata alamar eh don ba zai faɗi abinda bashi kenan ba ya juya a hankali ya ce "Aure lokaci" Wani irin kuka ta rushe masa da shi tana durƙushe wa a ƙasa "Amma ƙatuwa dani a ga babana ya yi aure? Kuma soyayya kuke kuma ta haihu?" A ransa ya ce "Babbar magana" a zahiri ya ce "Laifi ne idan matata ta haihu? Ke dana aurar dake kika haihu laifi ne? A'a ƙiyayya muke kema mu je ki faɗa mini inda kika baro mijinki a daidaita na ba yar dake, matata jinina ce" Daga nan bai ƙara cewa komai domin daman dauriyar maganar yake yana ji tana ta kuka ya rasa dalilin kukan nata a haka har bacci ya ɗauketa. Ya tashi ya bi ko'ina da addu'a ya ƙure gudun a.c ya gyara mata rufa bayan ya cire jerseyn ɗin yana ji tana ta sakin ajjiyar zuciya hawaye ya nashe da baƙin fuskarta. Can cikin dare Ridayya ta ji kamar ana buga abu da sautin fitar numfashi sama-sama ta buɗe idanunta daya kumbura a tsaye ta ganshi daga shi sai single ya cire jallabiyya ɗin bata taɓa tsayawa ta yi masa kallon tas ba, gabaɗaya Abbiey ɗin yanayin kamar ruwa biyu haka Ubangiji ya yi masa kalar tashi halittar kamar Balarabe kamar Bature fatarsa har yellow take ta ɗauka Zameer ne kawai mai yin murɗaɗen jikin nan amma sai taga naga Ustaz ya ci uwar na Zameer ko dan kullum cikin jallabiyya yake ne? Baya ya juya mata amma six packs ɗin shi a buɗe yake ko'ina ya rabu ga wasu muscles dake rawa a jikinsa kana ganinsa kasan yana cikin wani hali ji yake kamar ana tsaga naman jikinsa kansa ana sara masa gida biyu gashi ya kasa runtsawa ko kaɗan sama da sati baya iya bacci tsananin azabar ciwon ne ya saka yane buga kansa da bango kaɗan-kaɗan har ya fara da sauri. A tsorace Ridayya ta miƙe tsaye bakinta na rawa ta ce "Abbiey?" Cak ya tsaya da sauri kuma ya saka hannu ya kashe hasken ɗakin kafin ta kunna ya yi saurin shigewa bathroom zata iya cewa zata taɓa shi a wawtar Ridayya domin ya lura ba ta yi girma da hakan ba. Ta yi jigum ƙasan ranta kuma tunanin Sadauki take da halin da zai shiga. Dab da asuba wayar Ustaz ta fara ringing taga baƙuwar number tunaninta ya bata maybe matarsa ce. Can kuma aka kira da wata number an saka “Friend” "Babban mutum" "Yaya ni ce, Ridayya ce Abban Nadra Please ka zo ka tafi dani wallahi ba zan bisa ba" Tajj ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Bake kika bisa ba?" Ta kasa cewa shi ya zo ya ɗauketa. "Listen Mimi, ina Ustaz ɗin?" Ta tura baki ta ce "Na farka na ganshi tsaye yana buga kansa kuma ya shige toilet" "Subuhanallahi, Innalillahi! Ciwon kanne? Abbiey ɗinki bashi da lafiya Mimi yaƙi bari a faɗawa Hajiya ciwon kai ne wanda yake shirin ɗaukan rayuwarsa ki gaggauta zuwa wajansa ki riƙe masa kan ki yi masa addu'a" "Yaya Sadauki fa?" "Ridayya wai wanne kalar tunani ne dake? Me ya sa kwakwalwarki bata faɗa miki daidai ga halin da Ustaz yake ciki kina tambayata a kan wani" "Bai san na tafi bane, Yaya shi Abbiey bai taɓa nema na ba tunda nake kana ji ma wai ya yi aure ai ya jira dawowata a yi bikin ina nan?" A nan Tajj ya warware mata komai na irin neman da Ustaz ya yi mata tare da cigiyarta "Ke a iya tunaninki Ustaz zai iya zuba idanu ba tare da ya san inda kike ba? Idan ke za ki iya aikata abinda kika aikata kina tunani shi zai yi, Ridayya kin san waye Babban mutum kowa? Ki yi tunani da kyau ki nutsu ki fahimci shirun shi, kallonsa idan ke ba ki fahimce shi ba waye zai fahimce shi ba, idan ke ba ki zama silar farincikin shi ba da yayewar ciwonsa ba waye zai zama wa yake da shi? Ko biyu ne kawai kuka rage a duniya daga ke zai shi nasan kina sane da cewa iyayenku basa raye, Hajiya ta rage da Mai ran ƙarfe su kuma ba za su iya kulawa da ku ba, idan ke Ustaz ya kula dake shi waye zai kula da shi? Kin san zurfin cikinsa rashin damuwa da abu, sadaukarwa. Kin san adadin matan da suke ƙaunar Ustaz dukda shekarun shi? he is blessing ni da kai na ina ƙaunar zama kamar shi da Nadra ta isa aure ko kuma babba ce wallahi shi zan aura mata ko ta na su ko bata so.....," Ya yi shiru yana sauke ajjiyar zuciya kafin ya ce "Every girl deserves a guy that can make her smile, even when she doesn't want to. Ki buɗe zuciyarki ki ji sunan waye idan kika tuna ko kika ji yanayinki ke sauyawa? Waye bakya jure ganin ƙwayar idanunsa? Waye bakya gajiya da ɗabi'unsa waye za ki iya sadaukar da farincikinki saboda shi? Waye idan ya taɓa jikinki yanayin yake kaiwa har kwakwalwarki? Waye kike jin kishin shi? Waye bakya ƙaunar ganinsa da ko wacce mace sai ke ɗaya? Who sacrificed many things for you?" Ya yi shiru a hankali Ridayya ta ce "Mene amfanin haka?" "Idan kika nutsu kika gano waye wannan mutumin to shi ne the best for you shi ne wanda kike so kuma kika cancanci rayuwa da shi" "To idan na gano fa sai na yi me?" "Ki faɗa mini waye wanda fitilar ta haska miki, sai ki fara tunanin rayuwa da shi" Ta yi saurin girgiza kai ta ce "Wai da gaske Abbiey ya yi aure?" Tajj ya yi shiru ya san ba haka bane sai kawai ya ce "Oh ba ki sani ba ko? Ai ya yi aure kama yana matuƙar son matarsa komai ya ce ita komai ita ba kiga yadda itama take son shi ba, ina tunanin ma ciki gare ta kuma....," Ƙittt! Ya ji Ridayya ta kashe kiran ya yi murmushi a ransa yake addu'ar ranar da zai ga Ustaz da Ridayya matsayin mata da miji dukda damuwar dake ransa shi ma amma ganin wannan ranar kamar abu ne mai wahalar gaske. Ridayya ta kifa kanta tana rufe idanunta "Ciki?" Ta maimaita kalmar haka kawai abin ya zauna a kanta kenan duk abinda Zameer ke yi mata shi Abbiey ya kewa matarsa har ta samu ciki? Wani abu ya tsaya mata a maƙoshi. Washegari kafin ta farka Ustaz ya yi wanka ya shirya cikin shadda ruwan makuba ta amshi jikinsa ya ɗora zanna bukar a kansa ya yi wani irin kyau amma idanunsa ya faɗa. Yana parlour ya zaune can ta fito sanye da baya mai hijabi ta amshi jikinta idanunta ya kumbura Little na ganin Ustaz ya fara dariya yana zillo tare da miƙa hannu ya ɗauke shi. Kanta a ƙasa ta ƙarasa ta tsuguna gaban Ustaz da ƙyar ta iya cewa "Ina kwana? Ya jiki?" Bai kalleta ba, bai kuma amsa ba ya amshi Little ya miƙe ya yi waje ta bi bayansa da kallo kana ta bisa a jikin mota ta ganshi suna magana da wani ganin ta kusa ƙarasuwa Ustaz ya sallami mutumin ya shiga bayan mota yana rungume da Little itama ta shigo drive ya ja zuwa airport basu ɓata lokaci ba wajan shiga jirgi daga nan suka nufi hanyar Lagos lokaci zuwa lokaci tana kallonsa kamar bashi ba a ranta tana makami daman haka shadda ke yi masa kyau? Yadda Little ke bacci a jikinsa zaka ɗauka uba da ɗana kamar Ustaz ya yi kaki ya tofar. Da farinciki ya shigo parlourn yaga bata ciki ya kalli Zainura ya ce "Daughter where is your Mom?" Zainu ta ce "Baffa kullum idan ka zo sai ka ce ina Mami ni baka cewa ina nake?" "Ke me za ki yi mini me kuma za ki bani banda surutu da amsar kuɗi" Ta rausayar da kai ta ce "to ai kowa yau ba zan faɗa maka inda take ba" Baffa ya zaro idanu ya ce "Haba mana daughter rufa mini asiri kar ki ga yanzu na sume muku" Ta dinga dariya ta ce "Yanzu ta shiga bedroom tana waya ne" Ya nufi bedroom ya hango ta tsaye gaban madubi sai kanshi ke tashi a room ɗin ta sha kwalliya waya ce kare a kunnenta sai kuma ajjiyar zuciyar da take saukewa ya ƙarasa ya rungumo ta, ta baya yana ɗora kansa a kafaɗarta "Zan kira ki anjima Yaya A'isha" ta katse wayar tana juya Baffa ya rungumeta ya ce "Lovely ke kullum kamar wahainiyya" ya sunbaci goshinta da kumatu yana kallon bakinta ya ce "Albishirinki" Ta ce "Goro" ya girgiza kai ya ce "Canki kawai ma" Idanunsa akan jakar wata zuma. "I have no idea, ka faɗa mini mana" "Idan na faɗa miki me za ki bani? Idan kin yarda mu ji daɗin wannan zumar tare da ake cutata da ita" Ya kai zumar bakinsa yana sha kallonsa kawai take tana murmushi tamkar ba Alhaji Mansur Rano ba, wanda ya gana mata azaba ita da yarinyarta "Kin san me? Wahalarmu ya ƙare ba, they are together kuma i have a plan in sha Allah" Wani irin rungume Baffa ta yi tana fashewa da kuka ta ce "Allahamdulillah na gode Allah da ban mutu ba zan ga Ridayya Allah ka bani ikon nuna mata soyayyar data rasa Allah ya sa ta amshe ni matsayin uwa ta haife mini" Dariya kawai Alhji Mansur ke yi mata ya ciro alawa da dabino da goro ya ce "Amshi naki rabon ki saka albarka" Ta kalli abinda ya bata ya ce "all this for?" "Idon matambayi ki yi addu'a na ce" Fita ya yi ya bawa Ammi itama da Junaid ya ce duk su yi addu'a abin farin ciki ne Ammi ta yi, ta yi ya faɗa mata ya yi shiru Junaid ya ce "Ki yi addu'a kawai Ammi" Baba ƙarami yana zaune fuskarsa ɗauke da farinciki Umma ta ce "Wai wannan tulin alawar ta mece?" "Ta abin alheri ce mana sai da kika shanye za ki tambaya?" Ta share ta ce "Ina buƙatar ɗana kusa dani na fara gajiya da wannan tsarin a gaskiya zan je wajansa, ni ina kan ƙudirina wallahi tallahi bana ƙaunar a haɗa mini yaro da wannan yarinyar tunda bata da halacci gabaɗaya na tsane ta a nemo ko wace a bashi da ita wallahi idan kaga an yi auren sai dai idan bana numfashi" Bai kulata ba yana ta murmushi "Ina magana ka mayar dani sauna?" "Bani da lokacinki ne Hadiza" Farin cikin da Hajiya ta yi na ganin Ridayya ya ɓaci ta rasa inda zata saka kanta don farinciki ashe zata sake ganin wani nata? Jikinta kai Allahamdulillah komai ta ce jikata Mai ran ƙarfe ya dinga murna. Ridayya ta yi farin ciki sosai bayan ta huta ta ce "Granny ɗan bani aron wayarki" "Riƙe ƴar'nan na baki ita duka ma" number Sadauki ta kira yana ɗagawa ta miki a hankali ta ce "Sahibi" Ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Na azabtu Shanshan don Allah kar ki sake mini haka karki hukuntani ta wannan hanyar" "Ka yi haƙuri" "Uhm kina ina?" Ta faɗa masa sosai ya yi mamaki "ki tura mini address via email, zan zo gobe" "A'a mu yi waya ba sai ka zo ba" cikin zafin rai ya ce "Yakike so na yi? Har yanzu ba ki amsa mini ba, kina so na ko a'a kin guje mini kuma yanzu ki ce kar na zo what do you mean by that eh?" "Shikenan zan tura maka" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya a hankali ya ce "I'll call you later" "To" cikin wata kalar murya yana sauke mata numfashi ya ce "I love you Shanshan, i love You till the end of my life, i love You to square of infinity mu'aaah" Da sauri ta kashe wayar jikinta na amsawa tana rufe Idanu. Duk suna zaune a parlour tun bayan dawowarsa bai fito ba sai yini cikin bedroom da ƙyar ya samu ya fito ya zauna saman kujera ya rufe Idanu abubuwa sun masa yawa Hajiya ta ce "Ango ango kaga ango mijin amarya" Ya yi saurin buɗe idanu. Kafin ya yi magana Mardiyya ta fito daga wani part sanye da lemon ɗin lace sai baza ƙamshi take ta kafa ɗauri tana taku ɗaiɗai. Lokaci guda Ustaz ya haɗe rai ƙasa-ƙasa kuma yake kallon Mardiyya ɗin "Barka da gida Hajiya" "Yawwa Mardiyya kin fito ya gajiyar hanya?" Ta yi murmushi kawai ta nemi waje kusa da Ustaz ta zauna cikin iyayi ta ce "Na shiga dubaka kana baccin gajiya, ya hanya Yallaɓai?" Ganin wani irin kallo da Ridayya ke yi masa shi da Mardiyya ya saka shi daurewa ya ce "Lou" Wata irin zufa ke yanko masa ta ciki tashin hankali ya bayyana daga ta cikin zuciyarsa me Hajiya ke nufi? Me ya kawo Mardiyya gidan nan?. Ridayya kuma cike da mamaki take kallon Mardiyya daman ita Abbiey ya aura ya rasa wacce zai aura sai aminiyarta? Ita Mardiyya za ta ci amana kenan don ta ce ta je ta auri Abbiey ɗin shi ne ta aure shi? Wani irin ɗaci ta ji a ranta har wani duhu take gani a idanunta. "Barka da hanya ƙawata aminiyyata kuma ƴata ya rayuwarki kuma?" Miƙewa Ridayya ta yi daidai nan suka haɗa Idanu da Ustaz ta auna masa wata harara idanunta cike da ƙwalla ta yi cikin ɗaki. Tana barin wajan ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa, Hajiya ta bishi ta wassafa masa komai da yake faruwa. "Ba ki kyauta mini ba, kin haɗa ni da aiki duk abinda na yi wallahi zunubi a kan ki" Ta riƙe baki ta ce naga kana ƙifta Idanu kana girgiza kai "Ohho maka aure dai an ɗaura nan da wata tara na ji kukan jariri ai nasan ƙarya kake lafiya lou kake" "Sai ki je ki yi mata cikin ai" Ya shige toilet abinsa. Washegari da safe Hajiya ta ce Ridayya ta je ta kira Ustaz ya yi breakfast. Gudun faɗa yasa ta miƙe ta nufi ɓangarensa tana shiga ta ganshi tsaye a gaban madubi ga Mardiyya a gefe. Ganin Ridayya ya saka Mardiyya saurin rungume Ustaz ta ce "Abbiey ka bari na zaɓa maka kayan sawa" Ai gabaɗaya maganar Ridayya ta maƙale jikinta ya ɗauki rawa ta yi saurin juyawa Ustaz ya kalli Mardiyya ta yi saurin sakinsa wani irin kallo mai kama da “Last warning” Bayan ya gama shiryawa tsaf ya nufi bedroom ɗin Ridayya da niyyar tambayarta abubuwan da suka faru da yadda akai ta haɗu da Tajj. Yana shiga ya ganta tamkar mahaukaciya tana zaune a saman gado gashinta ya sauka har baya ta ci kuka son ranta ga Little nata kuka taƙi kula shi. Ya kasa magana sai tsayawa da ya yi kawai a kanta ƙamshinsa da ta ji ya saka ta ɗago idanunta, ganinsa ya saka ta ji wani irin abu yarr a jikinta ta miƙe tsaye zata shige parlour ya ɗan sha gabanta "Ina kwana?" Bai amsa ba ya saka hannu ya tallafo haɓarta yana ƙare mata kallo sosai kafin ya ce "Kukan na mene?" Ta kasa magana sai kawai ta rushe da raunataccen kuka gabaɗaya ta nufi kan Ustaz shi kuma ya ɗan yi baya tana zuwa ta faɗa jikinsa kamar yadda ta saba a baya ta ƙanƙame shi tana wani irin kuka kamar ranta zai fita kuka take da dukkan zuciyarta da ƙarfinta wani irin kuka take wanda bata taɓa yinsa ba a rayuwarta, kuka take wanda ko sanda aka ce su Baffa sun mutu ba ta yi irinsa ba, har wani irin shiɗewa take jikinta na rawa da karkarwa babban tashin hankalinta bai shige zunubin data aikata ba ko rufe Idanu ta yi tana hango ranar data bawa Zameer kanta. "Abbi..... Abbiey" Ta kasa magana tana neman zubewa a ƙasa saboda yadda jikinta ke rawa magana take son yi ta kasa ta haɗa zufa shi kansa Ustaz sai da ya ji tausayinta. "Ka yafe mini Abbiey don girman Allah ka ya....," Maganar ta tsaya sanda ta sake fashewa da kuka gabaɗaya ta ɓata masa farar shaddarsa he could feel yadda hawayenta ke sauka a jikinsa. Ya riƙe ta da kyau bashi da wani zaɓi dole ya bata damar kukan ko hakan zai sanya ta ji sauƙi "Abbiey an ce ni mayya ce an ce bani da gata" Ustaz bai san lokacin daya rungumeta a jikinsa ba idanunsa ya yi wata kala ƙirjinsa na buga ta yi luff tana kuka sosai "Da gaske mayya ce ni Abbiey?" "Shhhh" ya faɗa daidai kunnenta yana ɗan bubbuga bayanta, Ridayya ta juya fuskarta tsakiyar ƙirjinsa da sauri Ustaz ya ce "Ya Rasulullahi Manzon Allah..... Karku yanke hukunci sai an sauke littafi *MUNAFUKIN MIJI 32* Mikiya Writers Ass.. Bright pens free batch Nimcyluv Ustaz ya girgiza kai ya kama hannunta suka zauna bakin gado, har lokacin kuka take ta ɗora kanta a ƙafarsa tare da zamewa zuwa ƙasan carpet, sosai take kukan ta riƙe ƙafafuwansa gani take kamar zai gudu ya sake barinta rashin gatan ya tabbata a gare ta. Sai da ta yi mai isarta ta fara sauke ajjiyar zuciya nan da nan kanta ya fara ciwo ta ɗaga kai ta kalli Ustaz shi ma ita yake kawai yake kallo. "Kin gama?" "E, ina jin kamar na yi ta kuka" ya miƙe tsaye ya nufi wajan fridge ruwa mai sanyi ya ɗakko ya ɓalle murfin gorar ya dawo ya miƙa mata yana mai sake zama inda ya tashi. Ta tsare shi da idanu dukda gefen fuskarsa kawai take kallo. Ruwan ta sha sosai kana ta ajjiye tana sauke ajjiyar zuciya mai nauyi. "Ki kwanta, bacci ko za ki ji daidai" Ta girgiza kai tana ƙoƙarin sake ɗora kanta a ƙafarsa ya zame yana kame fuska ya san tuni ta saba, ko bacci wani lokacin a kan ƙafafuwansa take yi, ta ɗauke shi uba, aboki, uwa, amini bata shakkar faɗa masa komai da zama a duk yadda ta so idan yana wajan. "Abbiey magana zan yi maka" "Ki kwanta" "Ko na kwanta ba zan iya bacci ba, ka bari na faɗa maka ka ji" ta ƙare maganar tana marairaice fuska ta ɗan tura bakinta gaba. Jinjina mata kai ya yi ta sauke kan ta a ƙasa "Abbiey don Allah yau ɗaya ka faɗa mini me ya sa Baffa da Mami basa so na? Me ya sa Mami take son Zainura ni bata so na, me ya sa Baffa yake son kowa ni ban dani, me ya sa nake amfani da sunanka a makaranta maimakon na Baffa? Me ya sa kuma kowa na gidanmu fari ne ni kuma baƙa mummuna? Me ya sa ko a makaranta kowa ke guduna? Me ya sa mutane suke cewa ba zan taɓa samun mijin aure ba saboda ni mummuna ce ina da manyan idanu, da babban leɓe kuma ina da jiki da gashi me ya sa fatata take maiƙo kamar an shafa mai? Me ya sa kowa baya sona kowa yake guduna kai kuma kake so na Abbiey?" Ustaz ya yi shiru ta ce "Ka faɗa mini mana kamar na so na gane" "Ustaza ba za ki gane bane, ki na ta harbo tambayoyi" Ya miƙe ya nufi gaban madubin ɗakin da hannu ya nuna mata ta zo, tana zuwa ta yi ƙoƙarin jingina da jikinsa ya yi saurin zamewa kan hakan ya faru ya yi baya ya nuna ta tsaya gaban madubin a hankali ya saka hannu ya yaye labulen gabaɗaya suka fito a cikin madubin tana gaba yana baya da ta zara "Bani za ki kalla ba, dubi kan ki sosai" Ta ƙura wa kanta Idanu dan baƙi da gaske ita ɗin asalin baƙar fata ce, asalin Bahaushiya ƴar'hausawa cikakkiya kuma. Idanunta farare tas sai dugwayen gashin Idanu har kwanciya suke, girarta a haɗe suke sai yalwar gashi gaban goshinta ma haka, lips ɗinta su ba jaa ba kuma ba pink ba sun yi wani colour yirrr da su ɗaya ƙarami ɗaya mai ɗan faɗi ya bada wani shap tana da Oval face kawai tsananin baƙi da duhun fatarta ya saka ake ganin muninta. Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Na gani ni dai ban gane ba" "Ki gode Allah ki gode Annabi irin ku, ku ne ya yi yin zamani. Farin mutum har abada ba zai iya komawa kalar fatarki ba, ke kuma kina iya komawa fara idan ba ki gode Allah da irin zubin halittar da ya yi miki ba...," Ya sauke numfashi yana ɗan hutawa. "Idan kowa baya son ki ai ni ina son ki ko?" Ta yi shiru ya ce "Idan Allah da kansa daya halicce ki ya samar dake a duniya yana son ki kuma ya amince da ke to babu damuwa kowa ma yaƙi ki, mutanen ƙwarai Ubangiji yafi jarraba imaninsu Ustaza ki kasance mai haƙuri da gode Allah da ni'imar da ya yi miki. Mutane da yawa sun lalace da yi wa mutum ba'a na daga halittar da Ubangiji ya yi masa, amma tunda kike kin taɓa ganin mutum ya yi halitta?" Ta girgiza kai ya kalleta ta madubin ta yi saurin cewa "A'a" "To bai kamata ki yi fushi ba, yin hakan kamar kina nuna rainuwa ga Allah da nuna masa bai iya halitta ba, ki saka a ranki ke mutum ce kamar kowa mai tarin marudai wanda kike shirin cimma, ki yi ƙoƙarin bawa masu faɗar hakan kunya, ki zama mai ƙwatarwa kan ki ƴanci a ko'ina kar ki bari a wulaƙantaki kuma kar ki wulaƙanta kowa, Allah da kansa ya ce wáakaramna bânii adama" "To idan mutane sun guje ni me ya sa su Baffa za su yi mini haka?" "Ki manta da abinda ya shige, mutanen kuma da basa raye wanne ƙorafi Ustaza? Ki yi addu'a ki yafe musu ki zama mai uzuri" A sanyaye idanunta na cika da sabbin hawaye ta ce "Allah ya jiƙansu da rahma na so ko sau ɗaya Baffa ya kira ni da sunan ƴa, ya saka mini albarka kamar su Zainura su Yaya Khaliperh" Ustaz bai sake kallonta ba ya fara shirin barin wajan ta ce "To baka faɗa mini me ya sa kai kake so na?" "Ban sani ba" "Ina son sani Abbiey Dole ya kai Ridayya a duba lafiyar tunaninta da kyau domin yana kokwanto ta marairaice sosai "Ka faɗa mini" "Saboda you're lovely ke bar so ce" "To ni da matarka wa ka fi so? Kuma me ya sa ka aureta maimakon wata? Abbiey ka taɓa ce mini aure ba dole bane daka haƙura" "To ni dai ina son matata" Sai kawai yaga ta fashe da kuka sosai tana cewa "Amma ba zata haihu ba ko?" "Ke za ki haifa mini idan ita bata haihu ba? Idan kin yarda duk shekara za ki bani baƙaƙen yara kamar ki to" "Ga Little na baka kyauta, kuma me ya sa Little yake fari kyakkawa kamarka?" "Saboda abin cikin ƙwan ya fi ƙwan daɗi, Little ya mini kaɗan zuri'a nake so mai yawa kinga da gani sai ke muka rage sai ki yi ta haihuwa, idan kuma ba zaki haifa ba nan da wata tara za ki ga Mardiyya ta haifa mini" Wani abu ta ji ya tukare mata zuciya kanta a ƙasa ƙirjinta na ɗagawa, shi ɗin babanta ne taya zata iya haifa masa yaro wannan ai iskanci ne kawai. "Ustaza ban yi zaton zan sake ganinki ba, bana faɗar abinda ya shige a baya amma kaɗuwar ganinki gidan Mahmah ya kasa barin tunanina, gani nake kamar a mafarki na fita daga gidan saboda tashin hankali da mamaki kuma zan iya abinda bai dace ba, yanzu haka ina ganin kamar idan na rufe idanu na buɗe ba zan sake ganinki ba, ke ɗin ƙaddarata ce tamkar inuwata haka kike ban iya guje miki, ba zan iya zama hankali kwance ban san ya rayuwarki take ke ɗin amana ce. Ban taɓa nunawa Tajuddeen photonki ba balle na ce yana sane ya ajjiyeki a gidansu, a labari dai ya sanki banda kamanni ya akai kika je? Ina mijinki?" Wani irin miki ne ya taso mata bata ƙaunar tuna Giɗaɗo gabanta faɗuwa yake tana yawan manta abubuwa amma ba zata manta rayuwarta gidan Zameer ba. "Abbiey shi ɗin MUNAFUKIN MIJI ne, ba don Allah ya aure ni ba, ashe ba ɗan kano bane a Katsina yake ya zo Kano Almajiranci sunansa Giɗaɗo. Baya bani abinci, baya yi mini ɗinki babu magani ba sabulun wanka babu man shafawa, ya kwashe kayana ya siyar ya ce aiki ya samu da yake buƙatar kuɗi, ashe caca yake yi komai nawa ya siyar ya sace wayata ya siyar ya sace atamfofina ya siyar, na yini na kwana banci abinci ba baya barin kowa zuwa gidana baya barina fita, lefen da ya yi mini ashe na haya ne ranar da aka kai ni ya saka aka sace su, na fara yin ƴar'tsala mutane suna siya da kuɗin nake cin abinci na siyi omo na kwanka da kuɗin kuma shima yake amfani, duk kuɗin da kake tura mini tura mini shi yake amfani da su. Na yi faskare na dafa masa ruwan wanka na yi masa wanki da guga ya ƙona mini fuska da iron ya karya mini hannu, kuma ya dinga shaƙe ni a wuya idan zai....," Ta kasa faɗa haka kurum ta ji nauyin faɗawa Ustaz abinda Zameer yake mata a gado, kuma ta kasa faɗa masa zaman Khairy a gidan tana ganin kamar sirrin aurenta ne wannan ko dan ɗanta Little ba zata tunawa ubansa asiri a wannan ɓangaren ba. Ustaz ya kasa cewa komai kallonta yake yana jiran jin me zata ce kuma?? Yadda zufa ke yanko masa da yadda jijiyoyin kansa suka tashi kaɗai zai saka mutum yasan ran Ustaz ya ɓaci zafin zuciyarsa ya motsa. "Abbiey ka yafe mini don Allah kar ka ce na koma gidan Giɗaɗo kashe ni zai yi kuma ya ƙwace takardun da Baffa ya bani please forgive me Abbiey" Ustaz ya taka zuwa gabanta yana riƙe numfashi ya jima sosai sai kuma ya ce "Ya zama kukanki na ƙarshe, ban taɓa fushi dake ba ya isa haka nan, fatan za ki nutsu ki gane kuskurenki ki buɗe zuciyarki kin san wanda ya dace dake a rayuwa a matsayin miji....," "Sadauki Abbiey" A sama Ustaz ya ji sunan Sadauki shi har ya mance ma, da wani irin expression na mamaki yake binta da kallo gabaɗaya naman jikinsa rawa yake ya kasa cewa komai ya juya tare da ficewa tabi bayansa to me ya sa ya yi shiru kuma? Fasa fita ya yi ya koma bedroom ɗinsa ya kwanta yana kallon sama tunaninsa ya tsaya cak bakiɗaya ma ya rasa wanne Irin tunani ya kamata ya yi wanne kuma irin tunani ne da Ridayya? Har akai zhur yana kwance Hajiya ta shigo ta ganshi zaune saman ladduma ta ce "Wai daman kana gidan nan? Babban mutum sallah a ɗaki ban taɓa gani ba" Ya kalleta bai ce komai ba ta zauna kusa da shi ta ce "Lafiya dai? Meke damunka Babban mutum?" "Hajiya bani da Nagarta da za a so ni ne? Ko ni ba mijin ƙwarai bane ko ba zan iya kula da mace bane?" Ta sauke numfashi jikinta a sanyaye ta ce "Injiwa? Wane ya faɗa maka hakan Muhammmmd wallahi kwaɗayin halinka ya saka na karfafa aurenka da Mardiyya, kai ɗin mutum ne mai ƙoƙarin kyautatawa mutane da neman na kansa kuma hakal da zuciyar neman addini riƙon amana da gaskiya, na saba cancanta gaka kyakkawa son kowa ƙin wanda ya rasa ma macen da zaka tunkara ta yi fatali da soyayyarka ka bawa Mardiyya dama ban sani ba ko akwai wacce kake so ka yi haƙuri ka yafe mini na yi kutse a rayuwarka da tunanin na isa na yi hakan ba dan na baƙan ta maka rai ba, tausayin halin da kake ciki nake, ka rungumi Mardiyya hannu bibbiyu" Daidai nan Mai ran ƙarfe ya shigo. Ustaz ya riƙe hannun Hajiya da kyau ya ce "I was depressed, ƙofar da kuka saka a ɗakina bai wa ɗakin kyau ba, ba haka na tsara ba kada ku saka na zama mai karya alƙawarin zuciya" Hajiya da Mai ran ƙarfe suka saka Ustaz tsakiya domin suma ɗin shi suke kallo matsayin mataimaki. "Muhammad ka faɗa mini wacce kalar ƙofa kake so, wacce zata haska ɗakinka ko a ina take zan yi iya ƙoƙarina wajan ganin ka mallake ta, ko bata son ka zan saka ta soka" Ya yi shiru kansa na harbawa, baya son yi wa Ridayya dole ko kuma amfani da damar shi. "Babban mutum ka yi magana shiru baya magani" Mai ran ƙarfe ya faɗa yana riƙe kan Ustaz shi kansa ya firgita da yadda jijiyoyin suke harbawa. "Zurfin ciki ba shi ne mafita ba, wacece? Ka faɗa, yi magana" "Oum....," Sai kawai ya girgiza kai ya miƙe yana shigewa toilet. Hajiya ta fashe da kuka ta ce "Mun shiga uku wanne irin hali ne wannan? Miskilanci da riƙe damuwa kar zuciyar yaron nan ta buga" "Ba zata buga ba in sha Allah. Ƴar rainonsa yake so na jima da fahimta musamman a dawowarsu na so ya furta ya ce Ridayya yake so da wallahi tallahi a yau Ridayya ba zata kwanta ba sai da igiyar auren Muhammmmd a kanta". "Babbar magana wannan shirgegen ai ya mata girma, kuma duk shekarun daya kwashe sai ya auri bazawara kuma mai haihuwa? Ina masa kwaɗayin samun budurwa" Mai ran ƙarfe ya ce "Mata mata ku dai tunaninku na musamman ne, shi so na gaskiya ba ruwansa da wannan idan kuma don wannan yake sonta ai daya haƙura yanzu. Ko a baya dan dole ya aurar da ita" Hajiya ta ce "To yanzu mene mafita? Kawai tunda mu mun fahimta a aura masa ita mana ai ɗan'uwanta" "Bana son Ridayya ta fahimci alfarma ta yi wa Babban mutum, ita a yanzu bazawara ce tana da ikon zaɓawa kan ta wanda take so ne, kuma ina son Muhammmmd ya san ba a komai zurfin ciki yake da amfani ba, mutum kan iya rasa abubuwa da dama idan har ba zai buɗe zuciyarsa ba, ki bari sai ranar daya furta da bakinsa ni kuma a ranar zan nuna masa gata kuma ya je ya gina soyayyarsa a zuciyarta, ya fara nuna mata akwai halarcin aure a tsakaninsu ya kuma nuna mata bashi ya haifeta ba" Tun ranar Ustaz ya ƙauracewa ganin Ridayya baya zama a gidan sosai ita kuma kullum sai ta fito ko zata ganshi abin ya fara damunta ta yi ta kuka ita kaɗai saboda ya yi aure ya daina son ta? Ashe mata tafi ƴa daman? Wani irin zafin Mardiyya take ji a ranta ita har yanzu ta kasa yarda cewa matarsa ce wannan ai cin amana ne kuma tun ranar data gansu rungume da juna bata sake yarda taga Mardiyya ba, bata da abin faɗa mata. Gefe guda kuma suna waya da Sadauki sosai a wayar Hajiya. Ustaz ya fara neman appointment da likitan kwakwalwar domin a tabbatar ko tana da Mental Illness. Hakan yasa cikin gaggawa ya fara neman hanyar zuwa asibitin Psychiatry domin samun ganin Neurologist a san mene matsalar. Rana tsaka ya saka Hajiya ta kira Ridayya bai ce mata komai ba ko gaisuwarta bai amsa ba. Bayan tambayoyin da likitan ya yi mata ya buƙaci yi mata photo na ka da yin gwaje-gwaje na kamar su CT scan (Brain hemorrhage) MRI (Stroke, Brain tumor) da EEG (Epilepsy) bayan duk an yi komai ya ce Ustaz ya dawo shi ɗaya washegari Ridayya dai da idanu da kunne take jin komai, ya shige da ita shopping ta baza idanu tana kallon garin Legos gwanin sha'awa abayas ya siya mata underwears komai size ɗinta perfumes, kalar man da aka rubuta mata a bela dake ya ganshi a ɗakin dake gidansu Tajj ribbons, flat shoes. Har sun gama komai taga wasu saitin kaya na maza masu kyau amma ƙanana ta ce "Abbiey ka siyi wancan zai maka kyau" ya kalli kayan kafin ya yi magana ta ɗakko ta haɗa da wata hula p.cap da wani baƙin glasses ya fahimci Ridayya ita kyalekyale kawai ta sani bai kulata ba ya biya kuɗin. Har bayan mota aka kai musu ya nufi gida ko ciki bai shiga ba ya juya ya fita yana buƙatar shan iska da samun nutsuwa. A can Batsari mahaifin Zameer Giɗaɗo ya nema masa auren Hanne cikin ƙaramin lokaci aka ɗaura aka ware mata ɗaki a cikin gidan ta tare kasancewar Allah ya jarabceta da son shi amma duk ya siri mata auren ma fin ƙarfinta akai kullum cikin dare rufe ƙofa take. Da ƙyar cikin sa a ya samu ƙofar a buɗe, jiki na rawa ya nufeta ta yi saurin ja baya ta ce "Saurara meye haka kamar wani daƙiƙi zaka yo kai na haka dabba ce ni da zaka faɗo mini?" "Ke kisan da wanda kike magana dole ta saka zan raɓeki a rashin matata ne" Hanne ta yi shewa ta ce "Wacce matar bayan wacce ka saka kana da wata mata ne ko jikin karuwar taka kake marari? Ashe zuwa birnin na banza ne" Ya haɗe fuska gabansa na faɗuwa ya ce "Yaushe na saki matar tawa? Kuma ko ki yarda ki karki yarda dole na amshi hakƙina sadaki na biya, ki yi a hankali kafin na tafa miki rasit" "Ai na zame maka ciwon ido wallahi zama dani dole mutukaraba takalmin kaza, na zama ƙadangaren bakin tulo, ni ba irin Ridayya bace ina da gata yanzu za a ci ubanka hankali kwance" "Zagina ki kai fa?" "Allah ya yi mini tsari da zagin mijin karuwa" Ya sauke murya ya ce "To na ji, amma mu je mu raya daren aurenmu, haba Hannene Hanneta" Gabaɗaya laɓɓanta ke fusgarsa yadda suke jajur kuma bakin ƙarami sai ya ji yana sha'awar sumbatar bakin. Hanne ta ce "Ni wanka zan yi ma kuma ina buƙatar cin kaza" Kaya ta cire gabansa ya faɗi Hannen da yake rainawa ita ce haka? Har wani yawu yake haɗiyewa daman a matse yake kullum sai ya yi mafarkin Ridayya da yadda yake jinta zam idan yana tare da ita sai ya ji kamar ba ita bace baƙa mummunan ba. Kawai baya ganin darajarta tun ranar data bashi kanta kuma daman ba wani sonta yake ba. Hanne ya juya ta sake juyawa tana ƙara rura wutar dake tashi a jikin Zameer idanunsa a rine ya ce "Bari na je na kawo miki kazar, amma ki bari ko ɗan bakinki na sumbata" Ta zare Idanu ta ce "Hoɗijam! Ni na haɗa baki da kai Allah ya sauwaƙa maza ka kawo kazar dai na baka hakƙinka" a gurguje ya je ya kawo kazar bayan ta cinye tas ta ce "Ya leɓo mata ruwa a tulo ya ɗan fi san yi" Kafin ya dawo ta rufe ƙofa ta sha ruwa abinta kaza ta kwanta ta bi lafiyar katifa sai bacci. A daren Zameer kasa bacci ya yi kamar ya haukace ciwon ciki dana mara banda gizau babu abinda jikin Ridayya ke masa, yasan kuma duk inda take tana hanyar dawowa gare shi. A suba ya haɗa takardu da nufin zuwa Kano siyar da ko filaye uku ne daga cikin filayen Ridayya tunda yanzu shi ne yake da iko da su. Bayan ya shirya ya baza shaddar daya zo da su ya haɗa komai ya duba inda ya ajjiye kuɗin mota suka je nemi inda ka ajjiye ba kuɗi babu alamar su sama sukai ƙasa sukai sai Allah gashi bayan su bashi da ko taro. Gabaɗaya parlourn ya cika da mutane kowa na familyn yana nan banda mutane huɗu, Ustaz, Ridayya, Hajiya, Mai ran ƙarfe. Cikin fara'a da farin ciki Baffa ya ce "Allahamdulillah komai ya yi farko yana da ƙarshe, na so ba yanzu zamu bayyana ba amma na kasa jurewa ina buƙatar ganin yarana gabaɗaya su biyun, farin cikin haɗuwar su waje guda ya saka na sa a ka yi mini saukar Alkur'ani akan Ubangiji ya kawo mana ƙarshen komai ya daidaita tsakaninmu har na rabawa kowa alawa da goro to bana komai bane sai na farinciki. Kuma gabaɗayanmu zamu haɗu muje Lagos zuwan bazata" Junaid ya ce "Baffa ai bamu san ina suke a Lagos ba" Alhji Mansur ya ce "Tajuddeen ya sani" Gabaɗaya suka kalli Tajj dake shigowa da mamaki Yaya Balkisu ta ce "Tajj ya san komai?" "Babu abinda ya sani, infact bai san Ridayya ba bai kuma san muna raye ba, daga baya na buƙaci ganinsa da neman taimakonsa. Ni na bashi picture ɗin Ridayya a nan yake ce mini ya taɓa ganinta sau ɗaya mota ta kusa bugeta, har ya bata kuɗi taƙi amsa daman ita ce Ridayya ɗin? Shima ta tsaya masa a rai haka kurum yana son taimaka mata tun daga ranar ya tsananta bincike a kan Ridayya har zuwa sanda ya je Katsina ya bigeta nine farkon wanda ya faɗawa, kuma na shaida masa kar ya nuna ya santa ko yana da alaƙa da wani nata, duk kuɗin daya kashe mata ni na bayar har wayar daya siya mata domin ina buƙatar na fara ɗaukar ɗawainiyyarta tun yaushe, kuma na hana shi faɗawa Ustaz, nine da kaina na saka ya dinga ɗora photon ɗanta mai sunan Babban mutum a status, kuma ta hanyar ɗora photon muka jawo tunaninsa zuwa Kano akai-akai har mutuwar aurenta na sani, ban san dai abinda ya kaita Katsina ba shi ma Tajj bai sani ba, kuma shi ne ya faɗa mini Ustaz ya ɗauketa sun tafi Lagos to in sha Allah a gobe muma zamu ɗauki hanya gabaɗaya kuma ta jirgi domin ina fargabar shiga mota tafiya irin wannan akwai ban tsoro iyali guda" Barrister ya ce "Wannan haka ne kuma na yabawa ƙoƙarin Tajuddeen sosai samun aminin ƙwarai kamarsa yana da wahalar gaske mun samu taimakon ƴansanda na rashin binciken mutuwar taku" "Yanzu a kan ganin Ridayya zaka kashe maƙudan kuɗaɗe na jirgi har wajan mutum goma sha?" Baffa ya kalli Ammi ya ce "Wai Maryam lafiyarki lou ya ci a ce kinfi kowa murna da dawowar Ridayya tunda kunfi kusanci da ita a kan mahaifyarta, kuma ko nawa na kashe a kan Ridayya ban faɗi na yi mata abinda ba lallai ta yafe mini ba, kuma Ubangiji ya hure mini donna kyautatawa iyalina ba laifi bane" "Haka ne murna ce ta mini yawa Allah ya ƙara arziƙi da wadata, na ce ka haɗa da Burhan shima zai yi farin ciki idan yaga Ridayya". "Babu komai a je da shi ɗin" Tajj ne ya kira Ustaz ya ce gobe kar ya fita zai zo da mutane masu muhimmanci. Ustaz ya shaidawa Hajiya zuwa Tajj don bai ɗauki baƙin wasu serious ba, bashi da appointment da kowa a ranar ma yake ƙoƙarin zuwan jin sakamakon gwajin da akaiwa Ridayya. Yana zaune saman kujerar parlourn ɓangarensa system ce a gabansa yana ɗan operating ɗinta Mardiyya ta shigo sai baza ƙamshi take ya sha atamfa Valisco da ɗauri ta yi sallama bata da tabbacin ya amsa domin bata ji ba, amma ta san ba zai wofintar da sallamar ba. Ta ƙarasa ta zauna tana cewa "Barka da yamma ka shigo ashe?" Ya jinjina kai bai kalleta ba. "Na kawo maka abincin nan? Tuwon Alkama ne idan ba zaka ka ci ba to ka faɗi abinda za a dafa maka" "No" Kawai ya ce mata a hankali itama idanunsa har yanzu a kan system Wani irin Mardiyya take ji ta ce "To shayi fa? Ko fura naga kana so" "Injiwa?" Sosai ta ji daɗin maganar tasa har ƙasan zuciyarta ta ce "Ai nasan duk abinda kake so a wajan ƴarka Ridayya na ji tun kafin ma ta yi aure kullum sai ta bani labarinka da abinda kake so na abinci da kayan sawa, ka san har cewa ta yi shigarka bai taɓa burgeta ba, kullum kana saka jallabiyya da hirami kana carbi Ustazai basu san komai a soyayya ba, gabaɗaya baku san mene soyayya ba shi ya sa ba zata iya auren Ustaz kamarka ba" Ya ɗago kai ya kalleta sai ya ɗauke ganinsa zata sake manana ya nuna mata hanyar waje "Idan ina buƙatar abincin zan sanar" Sai ta ji ba daɗi ta ce "Don Allah ko baka so na ka yi ƙoƙarin kallona a matsayin matarka Ridayya kake so kuma kaga yanzu ai ita bazawara ce, ka ji tausayina da gaske ni ina sonka" Ya kashe system ɗin ya ture yana jingina da kujerar ya kalleta gabaɗaya ji ya yi hasken fuskarta yana shigar masa idanu ta masa dau da yawa ta saka wani jan jambaki ya ƙara haska fuskar baya son irin haka amma kalar nata halittar kenan. "Kuma daga faɗa miki sai ta ce ki faɗa mini? Ko kin faɗa ne domin samun fada ko na ji zafinta? Look Mardiyya kar mu fara haka dake ok, kuma da ban yi accepting naki as my wife ba da kin jima a Kano na dai faɗa miki bani da lafiya ba zan iya amfanar ki da komai ba, na gode da soyayya i appreciate it" Miƙewa ta yi zata durƙusa daidai nan Ridayya ta shigo hannunta riƙe da wayar Ustaz daya manta kuma a lokacin ta saka sabuwar abayar daya siya mata ta yi rolling ta yi kyau. Da sauri Mardiyya ta zauna saman cinyar Ustaz tana ɗora hannunta a ƙirjinsa dake buɗe. Kalmar A ce ta maƙalewa Ridayya hannunta ya shiga rawa wani irin abu mai zafi ya shiga yawo a ƙirjinta numfashinta ya tsaya cak. Tuni idanunta ya cika da ƙwalla sai ta ji wani irin haushin Ustaz ya kamata daman tuni ta ji bata ƙaunar ganin Mardiyya, zata juya ya ce "Ridha..." Ta tsaya ta kasa juya ji take kamar zuciyarta ce zata fashe ganin Mardiyya zaune a cinyar Ustaz wacce rashin kunya ce wannan? "Ridayya ƴarmu kina ji Abbiey ɗinki na kira?" Ta juya Ustaz yaƙi kallonta ita kuma shi take kallo Mardiyya ta miƙe tana shafa sumar Ustaz tare da sumbatar gefen fuskarsa ta ce "Bari na baku waje Baby ƴarka kunyar ganin babanta take haka, idan kun gama na dawo na shafa maka mai nima bari naje na sake sabon wanka" Ridayya bata san yaushe Mardiyya ta fita ba, to daman idan aka yi auren haka ake? Ya ita bata taɓa sani ba kuma ba haka Zameer ke mata ba. "Kawo mini wayar ki je, kin kuri matata" Wayar ta ajjiye saman madubi ta juya tana sakin kuka ya girgiza kai ya ce "Rigimammiyya" Tunda ta fita take kuka da ƙyar Sadauki ya rarrashe ta ya ce "Haba Shanshan kamar wacce a ka yi wa mutuwa?" Ta share ta ce "Ka zo lafiya? Ya mother da hanya" "Allahamdulillah hanya kuma kamar wanda ya yi tafiyar mota?" Ta yi murmushin yaƙe ya zuba mata Idanu ya ce "Wani ya taɓa ce miki colour ɗinki me kyau ce?" Ta yi jim sai ya ce "Kamar an taɓa faɗa na manta dai" Ya kashe mata Idanu ya ce "Ko an faɗa bari na maimaita i love your skin colour Shanshan, na jima ina sha'awar kalarki kin san yanzu mata duk sun lalace da shafa mai su yi ta wari sai ka rasa baƙa kuma ka fara farar asali amma ke normal komai naki abin so ne natural halitta ba fake ba, i love You my fiance" "Na gode" "Meye wani kin gode, ku Hausawa kuna da matsalar you can't say you love me too?" "Kunya nake ji" "Ridayya" ta amsa ya ce "Ban san yaushe ne ba amma san nasan kawai ina son ki ina buƙatar rayuwa dake har ƙarshen numfashina kar ki mini wasa da hankali domin dana rasaki gwara kowa ya rasaki, na rantse miki da Allah sai na mallake ki" Gabanta ya faɗi ta ce "To mene abin rantsuwa kuma?" "Ki faɗa mini kina so na, zaki aure ni? Zan turo Daddy wajan Abbiey ɗinki" "Kai ba naka bane" Ya yi shiru ta ce "Uhm" "No karki mini wata fassara fa, nawa ne mana ai wajansa zani neman aurenki just tell me kina so na?" Ta miƙe zata gudu saboda kunya ya yi saurin riƙo ta yana tashi tsaye hannunta duka biyun ya kama kamar za su haɗe daidai nan Ustaz ya fito da waya a hannunsa saboda Tajj da yake cewa suna bakin gate mai gadi ya hana su zuwa. Ustaz ya nemi iskar shaƙa ya rasa ya ja numfashi ya kasa wayar hannunsa ya suɓaci zuwa ƙasa idanunsa a kan hannayensu da suke riƙe da juna. Tari ya fara sosai yana riƙe ƙirjinsa yana ganin yana-yana a idanunsa hannunsa ya saka da niyyar rufe baki yaga jini ya ɗigo hannunsa tsoro da tunanin kar zuciyarsa ta buga ya saka ya yi ƙoƙarin nufar gate ɗin da ake ta horn babu adadi har lokacin kuma Ridayya bata ji tarin na Ustaz ba, ya nufi gate ɗin amma jiri ya kama shi tari yaci karfinsa ya riƙe ƙirjinsa da yake jin kamar wuta na tashi ƙoƙarin kiran sunan Ridayya yake yana ɗaga mata hannu amma ya kasa abu mai danshi ya biyo ta hancinsa sunan Allah kawai yake kira ji ya yi kawai yana buƙatar Ridayya kusa da shi ko mutuwa ce ya mutu a cinyarta ya samu damar faɗa mata abinda yake ransa tsayin shekaru amma ina ya gagara daidai sanda aka buɗe ƙaton gate ɗin ya yi daidai da sanya Ustaz ya sulale ya zube a ƙasa jini gabaɗaya ya ɓata farar shaddarsa a lokacin kuma Ridayya ta ji ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske komai nata ya tsaya.... *Soyayya gaskiya ce! Zurfin ciki halitta ne, ƙaddara zane ce. Kowanne bawa yana da marudai wanda yake son cimma, haka ko wacce zuciya da abinda take so, da kuma son kasancewa da shi. Ba komai kake nema kake samu ba a rayuwa, wani baya gane kuskuren da yake sai ya sake making mistake the same, wani rashin wanda zai fahimtar da shi abu shi ne matsalar shi. Rashin tarbiyyar uwa na taka muhimmiyar rawa wajan rugujewar yara, kuma ɗa baya taɓa girma a gaban iyayensa. Rayuwa da ƙaddara abokan juna ne, soyayya tafi talauci illa a zuciya rayuwa da wanda kake masa kallon uba mahaifi matsayin miji abu ne mai wahalar gaske* Ku bi a hankali ba sauri muke ba komai a tsare yake waye zai zama RABAGARDAMA? A rayuwar RIDAYYA? Uba ko Sadauki ko kuma kome za ta yi gidan tsohon mijinta? Share and share as so much as you can *MUNAFUKIN MIJI 33* Mikiya Writers Ass Bright pens free batch Nimcyluv Koda ya je ƙasa bai bari ya sare ba, baya son ciwo Ustaz ya dinga ƙoƙarin tashi ya kasa jinin zai zuba yake ta hancinsa. Ridayya kam ji ta yi gabɓanta sun yi sanyi duk maganar da Sadaukin yake bata fahimta kamar almara ta kasa juyawa kuma. Tajj tun shigowarsa harabar gidan idanunsa ya sauka a kan Ustaz da sauri ya fito ko kashe motar bai ba cikin wani irin tashin hankali ya kira sunan Ustaz. "Bilal Innalillahi Bilal" Kiran sunan ya saka Ridayya juyawa da wani irin firgitaccen yanayi ta kwace hannunta daga na Sadauki har tana bangaje shi ta nufi inda Ustaz yake wanda Tajj ke ƙoƙarin riƙe shi amma ya hana a dole shi zai miƙe. Tuni hawaye sun wanke mata fuska kamar yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke yi daga kusa da ita ta ce murya mai ɗauke da tashin hankali ta ce "Abbiey" Kallon da ya yi mata ya saka ta fahimci zuciyarta ce ta kira shi, raguwar halittar daya ya yi saura a cikinta shi ne ya kiranye shi. "Kar ki zo mini nan kar ki taɓa ni" Ya furta da ƙyar yana numfashinsa na riƙewa zuciyarsa na tarwatse. "Please Ustaz not here akwai Sadauki a wajan, ka bari mu je asibiti" "Sadauki? Ka faɗa masa ya zo ya nemi aurenta waje na" Yadda Ustaz ke maganar kamar baya nutsuwarsa kuma shi kansa bai san me yake cewa ba, taurin kai kuma ya hana shi ya kwanta yana miƙewa jiri kwasar shi. Ridayya kuka take ganin yadda Ustaz yake abu kamar zautacce Tajj ya ƙarasa wajan Sadauki ya ce "Hamza jeka za mu yi magana" "Where? Kana ji ya ce na zo na nemi aurenta a wajansa" "Na ce ka je za mu yi magana ko Sadauki" idanun Sadauki ya yi jajur ya ce "Ba inda zani domin ba wajanka na zo ba, kai na nemi taimakonka ka share ni, bare ya fini...," Wani mari Tajj ya saukewa Sadauki a fuska ya ce "Ka shiga hankalinka kuma zanje wajan Daddy na ji da wanne irin abokai kake yawo" "Babana babana ne ni ɗaya ka ce Prof zai fi daɗi a rai, daka ɗauke shi matsayin uba ba zaka wulaƙanta ni a kan wani ba, kuma ba zaka bari na rasa abinda nake so ba, so please stay away from me" "Ok fine ka fita" Sadauki ya nufi wajan Ridayya ta yi saurin yin baya idanunta a kan Ustaz da kansa ke ƙasa ya ƙarasa har gabanta idanunsa na zubar da wani rin hawaye mai zafi ya ce "Zan tafi ba zan dawo ba sai da Daddy, i love You Ridayya don't ever ever trying to break my heart" Ya runtse idanunsa "Wallahi ina son ki, idan kika rabu dani abin ba zai mana daɗi ba ki saka a ranki bana yafiya saboda tsakani da Allah nake tsananin ƙaunarki duk abinda nake ina sane na san me nake yi, don Allah karki barni" Sai kawai ya fashe da kuka abin har tsoro ya bawa Tajj don bai taɓa ganin Sadauki ya yi ko hawaye ba balle kuka, ko abu ne sai ya ce ya fi ƙarfin ya saka wannan ɗan abun a rai shi ya sa bai taɓa gwada yin soyayya ba. "Ridayyerh i love You. Love isn't something you find. Love is something that finds you, ban san yaushe nake miki wannan son ban" "Sadauki get out, ka rabu da ita ko?" "Tajuddeen Baita shut up ok, ka rabu dani kai baka san komai ba tunda Maman Nadra auren zumunci ne haɗa ku akai, baka san ya mutum yake ji a zuciya ba idan hakan ya kasance" Tajj ya jinjina kai ya ce "Ok" wayarsa ya danna magana biyu ya yi ya kashe sai ga wasu ƴan'sanda sun shigo cikin gidan sukai kan Sadauki da mamaki Sadauki yake kallon ɗan'uwan nasa ya juya ya kalli Ridayya wacce itama a ruɗe take gabaɗaya ta kasa fahimtar mene hakan? "Ku je da shi" Har aka fita da Sadauki idanunsa yana kan Ridayya yana jin kamar yanzu ne ma ya santa kuma ya fara sonta a cikin zuciyarsa. Jansa ƴan'sandan suke yana ji kamar ana saka abu ana cakar masa zuciyar gabaɗaya ji ya yi he just left himself wajan Ridayya there are millions of people in this dunia but all what he see is RIDAYYA no one can make him feel like her, and he will do anything to keep this feeling safe dole zai dawo kuma da iyayensa. Sadauki na kallonta ita tana kallon Ustaz shi kuma Ustaz na kallon ƙasa Tajj kuma yana wayar a gaggauce. "Abbiey jini a jikinka mu je hospital ka ji kar ka yi ciwo" Kallonta ya yi, wanda sai da hantar cikinta ta juya sai da ta yi ƙarfin hali wajan sake kallon cikin idanunsa amma abinda ta gani ya nemi ɗauke numfashinta, jinta ganinta murmushi taga ya yi tare da yi mata nuni da ta zo. Jikinta na ɓari ta ƙarasa ya yi saurin dakatar da ita ɗan nesa da shi ya ƙarasa miƙewa tsaye daman yana ɗan durƙushe ne gudun kar ya faɗi. A daidai inda take ya tsaya ya dinga murmushi sai kuma ya haɗe fuska ta ji muryarsa a saman kanta na faɗin. "I don't hate you for not loving me anymore, but I hate myself for still loving you." Ya sake yin murmushi idanunsa jajur komai na zuciyarsa na buɗewa dukda ta gama yin rauni ya kuma sare da al'amarin bata isa ya mutu saboda ita ba "Abbiey don....," "Shhhh!" Ya faɗa yana ɗora yatsarsa a bakinta yana jin dukkan wasu feelings and emotions ɗin zuciyarsa suna tattarewa zuwa wuya ya ce "I've lived all this while for your happiness, but now, it is time I'll have to live for my own. I hope someday karma makes you suffer very much for betraying my trust. I hate you." Komai na kan Ridayya ya zama fresh kuma new kamar an yi updating ɗinta da kwakwalwarta da tunaninta to the latest version ba a taɓa furta mata kalma mai zafi da ɗacin wannan ba, har maƙogaronta take jin ɗacin maganar ta dinga girgiza kai ina ma zata iya faɗa masa gaskiyar abinda take tsoro kuma take shakkarsa? Me ya sa rayuwarta take zuwa a haka ne ta ji dama bata zo duniya ba. "I just hate you Ustaza" Fitowar Mardiyya ya saka kai tsaye Ustaz ya nufi wajanta da yana da iyaye babu shakka wajansu za shi ko ya samu sauƙi yana ƙoƙarin ƙarasawa inda take ya yanke jiki ya faɗi ga wani dutse a wajan kai tsaye kuma mararsa ta sauka a kan dutsen. "Abbiey!!!" Ridayyerh ta faɗa shout and soundly daidai nan itama ta yanke jiki ta faɗi a sume kafin Tajj ya motsa motoci wajan guda uku suka shigo. Da sauri Alhji Mansur ya fito bayan Junaid ya yi parking suka, daga nan kowa ya fito hadda Barrister jikin Mami na rawa ta nufi wajan Ustaz Ammi kuma ta tsaya tana addu'ar Allah ya sa Ridayya mutuwa ta yi uban kowa ya huta don kar a ganota ta yi saurin nufar wajan Ridayya Baba ƙarami kallon tilon yaronsa ɗaya tal a duniya yake zuciyarsa na tsinkewa bai yi zaton a haka za su ruski yaran nasu ba. Tsoron rasa Muhammmmd ya saka shi rikicewa dukda kawaicinsa a kan Ustaz ɗin. Umma ta rushe da wani irin kuka tana cewa "Shikenan ta kashe mini yaro ta kashe shi wallahi idan Muhammmmd ya rasu a kan ta ba zan yarda ba itama sai an kashe ta innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Babana baban mutum" kuka take tana jijjiga shi hankali tashe. Barrister ne ya yi ƙoƙarin cewa "Asibiti ya kamata mu tafi da su ba mu tsaya kallon su ba" Alhaji Mansur ya ce "Tajuddeen Junaid ku saka Babban mutum a mota" Suka kama Ustaz tare da sa shi a mota Baffa da kansa ya ɗauki Ridayya da hannunsa abinda bai taɓa yi ba tunda aka haifeta yana jin wani danshi na bin fuskarsa ya saka ta a mota, gabaɗaya basu lura da Mardiyya dake ta kuka kamar ranta zai fita ba. Ta ƙasan Idanu yake kallon tafin ƙafarta da sukai fari tas ga dugwayen yatsunta gwanin sha'awa yadda aka gigice a kanta abin har mamaki yake bashi. Ya taɓe bakinsa tare da ɗaga kafaɗunsa cikin ko in kula ya zaro mandula yana murzawa tare da kunnawa ya shiga bata hayaƙi. Ammi data lura ta yi saurin dawowa baya ta ce "What rubbish? Mene haka shaye-shaye za ka yi anan wajan?" "And so what? Ni fa gaskiya ba zaki kawo ni nan kuma ki takura ni ba" "Amma Burhan kasan plan ɗinmu ko? Kai gabaɗaya kwakwalwarka bata faɗa maka gaskiya haka fa jiya na ji ance kun yi faɗa da wani ka saka wuƙa ka yayyanka shi yana asibiti da ban zo da kai nan ba da tuni police sun kama ka" "Uhm" kawai ya ce yana girgiza kansa yana jin hayaƙin mandulan har tsakiyar kansa ga wani lafcecen yanka a ƙasan wuyansa. "Ina magana kana sake hura mini hayaƙi bana son warin abar nan" zuƙar ƙarshe ya yi mata ya cillar a ƙasa ya saka ƙafa ya take sai yanzu yake ganin mutane tarr kuma daidai. "Muje asibitin" Burhan ya girgiza kai ya ce "Kuje kawai" ya nemi waje can kusa da Maigadi ya zauna Maigadin duk a tsorace yake da Burhan. Emergency a nan aka amshi Ustaz shi da Ridayya aka sanya su a ɗaki ko wanne daban nan da nan aka shiga kulawa da su har yanzu Umma kuka take Mami ta kasa cewa komai kasancewarta mace jaruma mai shanye abubuwa da yawa. Alhaji Mansur ya ce "Ban yi tsammanin ganin hakan ba, na ɗauka zanga Muhammmmd da Ridayya cikin farinciki suna tare ina jin kamar na yi kuskure wajan ɓoye gaskiyar komai akan cewa mun mutu, ban kyautawa kaina na ji ban cancanci zama uba a wajan Ridayya ba, na wulaƙanta ta na aibata ta, ta nuna wa duniya bata da wata daraja irin ta ɗa, ina tsoro kar ta mutu ban kyautatawa rayuwarta ba tunda aka haifeta bata yi farinciki ba...," Barrister ya riƙe hannun Baffa ya ce "Alhaji Mansur mu bar maganar nan, fatanmu Allah ya basu lafiya bakiɗaya. Za su yi farinciki in sha Allah za a zama one big family" "Na rasa wake da saka hannu wajan rusa farincikin iyalina, dole akwai dalili wannan dalilin bai shige ni ba" "Kai Munafikin miji ba, daka fifita yarinya tun tana ciki ka nuna kamar ba a taɓa yi maka haihuwa ba, munafurcinka ya ja komai" Cewa akai duk su tafi gida har zuwa sanda wani daga ciki zai farfaɗo Junaid ya kasa tafiya yana masifar ƙaunar Yaa Bilal kamar rai yana tausayin ƙaddararsa kamar yadda yake tausayin nasa ƙaddarar wacce har yanzu ta hana shi aure. Suka koma gidan Ustaz aka bar Junaid da Tajj da kuma Yaya Balkisu. A can suka samu Mardiyya mamakin ganinta ya cika masu rai, Hajiya tana ta kuka itama Mardiyya haka. Farincikin ganin Alhalin Mai ran ƙarfe ya saka Hajiya da Mai ran ƙarfe yin kukan da basu taɓa yi ba, daman komai cuɗe musu sun kasa aiwatar da abinda ya dace, sun yi kuka har sun gaji bayan Baffa ya basu labarin komai. Ammi ta juya ta kalli Mardiyya ta ce "Mardiyya tare kuka dawo da Ridayya ne domin idan anga zara za a ga wata, to ai ba kuka ya dace ki yi mata ba addu'a ya kamata ki yi ko?" Hawayenta yaƙi tsayawa ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta wajan Ustaz. Hajiya ta ce "A'a ai matar Ustaz" Da wani irin shock Baffa da Baba ƙarami suka kalli juna hatta Barrister ya razana da jin furucin na Hajiya Yaya Zuhura ta ce "Matarwa kika ce Hajiya?" "Matar Muhammad-Bilal matarsa ta sunna" "Tamɗijam! Kuma ya san an yi auren shi ya ce yana sonta wannan dai haɗinki ne" A fusace Hajiya ta ce "Dam ƙundun ubanki haɗin nawa ne, ba zuba idanu ya tsofe babu aure ba masifa ta ci ta cinye shi" Yaya Zuhura ta ce "To a gaskiya ba ki kyauta ba, ita kuma ya yarda ta aure shi har da shimfiɗe ƙafafuwa?" Baffa dai ya kasa magana ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu rikici kan rikici Allah ne kaɗai ya san manufar faruwar hakan. "To yana can Kano aka yi komai, kuma Allahamdulillah ya aminci bai bani kunya ba dukda har cewa ya yi bashi da lafiyar zama da mace wai nakasashe shi, bayan nasan ƙarya yake ni zai mayar karfa kullum yana cikin azumi ai tarr nake kallonsa lafiya lou yake itama yarinyar na faɗa mata ta kwantar da hankalinta" Wani sanyi Mardiyya ta ji at the end zata san mijinta, za su yi tarayya matsayin miji da mata hope ɗinsa a kanta ya ƙaru tare da wata kalar soyayya mai zafi dole ita kaɗai zata kasance da shi babu wata ƴar mace da zata yi musu shamaki ko ta zama labule tsakaninsu. "Alhaji Mansur mun makara" Baffa ya girgiza kai ya ce "Ya ce haba kafi kowa sanin komai" "Ma sha Allah, na ji daɗi Allah ya sanya albarka ya basu zama lafiya daman Babban mutum mace ɗaya yake da muradi a rayuwarsa tunda an masa aure da Mardiyya magana ya shige su zauna lafiya su biyu abinsu ni kam Hajiya kin kyauta mini sosai" Daga Baffa har Mai ran ƙarfe sun gane manufar Umma suka share. Ammi hamdala ta yi tunda Ustaz ya yi aure yanzu dole Burhan ya zama zaɓin Ridayya. Mami bata cewa komai tana jin zafin yadda Umma take nuna tsanar Ridayya idanu biyu Zainura ta yi shiru. Can dare aka kira su Ustaz ya farka kuma Allahamdulillah da sauƙi amma akwai matsala zuwa safe suna iya zuwa a yi musu bayani. Har kuma gari ya waye Ridayya ko motsi ba ta yi suka fara shiga fargaba har likitoci har kawo lokacin Ustaz bai san su waye suke tare da Tajj ba. Kokawa suke sosai shi da Hanne yana haki tana haki ta ce "Ba jaka bace ni da zaka dinga faɗo mini kamar dabba ko dabba ta san soyayya" "Karki kuskura ki zage ni kuma ai ke matata ce ina da hakƙi a kan ki" "Baka bani ci ba balle sha uwa uba abin ƙara lafiya da kuzari to baka isa ka zo mini da wata buƙatarka ba, shi ne ka wani kwaso ƙafa abujajen kai kaga mai mata ko? To wallahi ƙwalelenka malakar kare da hanzar kura, na farko dana bari na yi niyya ne" "Don Allah don Annabi Hanne ki tausaya mini ni kaɗai na san yadda nake ji, ni ba haka na saba da matata ba, ita kullum bata gajiya dani baiwar Allah ce" Hanne ta yi shewa tana tafa hannu ta ce "Haka na gani a ƙasa, daman taya zata ga ji da kai tunda ka zame mata munafikin miji banda ƙarya da haɗata da dangi ba abinda ka iya, ni daban Ridayya daban" "Wallahi ita baiwar Allah ce ga haƙuri da tausayin miji ko na lokaci ɗaya ne ki bani dama ba zan sake tambayarki ba, da zarar matata mai sona ta dawo shikenan na miki al'ƙawarin ba zan sake tambayarki ba, kin san ina son ki you are my first love" Zameer ya zage yana kwararawa Hanne kalaman soyayya masu ratsa zuciya nan da nan ta ji wani irin buƙatar mijinta Ubangiji ya bawa Zameer baiwar tsara mace gashi kyakkawa da iya ɗaukan wanka. "Na ji amma ka fara wanke mini kaya ka kai mini ruwan wanka banɗaki ka kuma kawo mini tsiren Ayuba mai zafi sai ka zo mu satata" Ta faɗa tana fari da idanu tare da kaɗa jikinta Jikinsa na rawa ta wanke kayan tas ya kai mata ruwa, ya saka Iya a gaba kalamai akan zai je ya siyar da fili ta bashi aron kuɗin mota "To ni bani da kuɗi amma a ɗaga shanuwa ɗaya a siyar na baka rance" Nan da nan ya je ya amso zazzafan tsire na dubu biyu da biredi yana dawowa ya tarar Hanne ta caɗa ado daidai yanayin ko wacce mai wayewa ta ƙauyen Nahutun Batsari. Ta ci ta ƙoshi ta yi gatsa Zameer jikinsa har rawa yake domin sai daya tsaya ya sha tsumi a hanya yana ta faman baza riga. "To jeka ka yi wa iya sallama" Babu musu ya fita kafin ya dawo ta rufe ƙofa ta ce "Zaka gane baka da wayo Munafuki" Zameer bai iya bacci ba ya kwana tsaye yana firfita wando daga ƙarshe ya cire ya saka babbar riga ji yake kamar ana jan shi ya haɗa uwar zufa tsumin ya gama ratsa shi. Yana fita yaga ƙofar Hanne a buɗe ta manta sanda ta yi fitsari cikin bacci ta ji an faɗa mata kamar doki, ya fi ƙarfinta dole ta haƙura burinsa ya sumbaci bakinta ta datse taƙi bashi daman. Sanda ya ji daidai ya shaƙe mata wuya tamakr zai kasheta shi haka halittarsa take ta dinga kakarin mutuwa amma yaƙi sakinta faratansa duk sun shata a wuyanta sai dai ya ji daidai ya saketa ganinta a shimfiɗe kamar gawa ya saka nan da nan ya rikice tunaninsa ta mutu domin kullum haka yake wa Ridayya ya shirya ya kwashi kayansa da kuɗi da takardu sai tasha ya shiga motar Kano. Suna hanya ya kira Moo yake cewa nan da lokaci kaza jirginsu zai sauka a airport sun dawo daga Cameroon shi da Daddynsa. Sanda labari ya je wa Prof Tajj ya kama Sadauki lokacin yana tare da wata sabuwar yarinya da ya yi Asabe reza tana ta masa yauƙi bai wani damu da iyalinsa idan ya sakar musu kuɗi gani yake basu da damuwar komai. "Prof zan ce ko Hon?" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Ko wanne zan amsa, ai da secretary ya tura mini pictures ɗin ƴan'matan na ji ba wacce ta yi mini sake" Ta yi fari da idanu ya tura mata kuɗi masu yawa ta ce "Thank you zama Ɗan'majalissa dole my professor" "Anything for you baby" Yana ta ganin kiran mother ya share can ya ɗauka ya ce "Sweetheart matata uwar Hamza Sadauki ya aka yi ina ta missing naki aiki ya sani gaba yanzu haka ina office" Cikin kuka ta ce "Ba cewa zan yi ka dawo ba, Sadauki yana wajan ƴan'sanda ko ba zaka dawo gida ba ka taimaka ka shiga maganar" Cikin basarwa ya ce "What? My son mene haɗin Sadauki da ƴan'sanda kuma ni ina nan ina ta fafutukar neman abinda zan rufa mana asiri shi kuma zai ɗakko magana? Aiki nake amma gabaɗaya tunaninku ya hanani sakat ji nake kamar na haƙura da komai na zauna daku idan na tuna ina son rayuwarku ta yi kyau sai na dage wajan aiki" Ya ƙare yana shafa hannun Asabe reza. "Ka yi haƙuri Prof na san kana ƙoƙari shi ya sa bana damuwa da rashin kwananka gida ka shiga maganar" ya rausayar da murya ya ce "Oh ni ke haukana bama ki damu dani ba Hajja Azizat? Kin san yadda na yi kewarki kowa? Sadauki yau zai dawo babu abinda zai same shi" Wani sanyi ta ji ta saki jiki ta fara masa ƴar shagwaɓa ya ga ji ya fara hura iska "Hello Hello wifey network problem zan kira ki" Ya kashe wayar yana jan Asabe reza ya mance da batun Sadauki. Hajja Azizat ta yi murmushi ta ce "Allah sarki My man neman na kai akwai wahala Ubangiji ya dafa maka ya baka wannan kujerar ta Ɗan'majalissa" Cikin dare Sadauki ya shigo da wani irin mugun ciwon kai yana shiga ya nufi wajan Mother tana ganinsa gabanta ya faɗi kafin ta yi magana ya zube gabanta "Mother ina buƙatar Shanshan ku nema mini aurarta kafin zuciyata ta samu matsala" "Subuhanallahi wacce irin matsala ni ƴar nan, bari Prof ya dawo in sha Allah za a je a nema maka aurenta ai mahaifinka ba ɓoyayye bane suna yin bincike na tabbatar za su baka aurenta" Ya sauke ajjiyar zuciya "Yaushe zai shigo? Yana wanne office ɗin?" "Ban san wanne office ɗin yake ba, tunda secretary ya tura masa pictures ɗin sabbin kayan da aka kawo musu ya fita amma na tabbatar a gida zai kwana. Ai yarinyar na son ka ko?" "Tana so na sosai, zan jira har ya shigo" Sadauki ya kasa bacci kansa a cinyar mother ko ruwa yaƙi sha tun yana duba lokaci har bacci ya ɗauke shi a ƙasan carpet wajan ƙarfe 3 na dare. Ustaz ya kasa yarda iyayensa ne a gabansa wani irin daɗi da sanyi ya ratsa zuciyarsa da yana da ikon tashi da tuni ya yi hakan ya dinga kallon Baba ƙarami da Umma ya dawo ya kalli Baffa da Mami da Junaid da sauran yaran amma ko inda Ammi take bai kalla ba ya runtse idanunsa da sauri kuma ya mayar da abinda yake ji suna taruwa a idanunsa "Allahamdulillah!" "Allah shi ne abin godiya Babban mutum ai ba zaka taɓa mutuwa ba muga zuri'arka ba" "In sha Allah akan wata ba zai taɓa mutuwa ba, sai naga jikokina sai naga yaransa shi da Mardiyya kyakkawar yarinya kuma budurwa" Mardiyya ta yi murmushi tana sake gyara zamanta a gadon da Ustaz yake, rigar asibiti ce a jikinsa ƙafarsa biyun duk a ware an saka masa abu a tsakiya. So yake ya tambayi Ustaz amma ya kasa a yaransa yana tunanin ko haka kurum taƙi zuwa wajansa. "Yadda Babban mutum ya farko Allah ya sa Ridayya ta farka abu kwana uku? Shiru" zuciyar Ustaz ta buga ya kasa cewa komai. Bayan ganin jikin Ustaz ya buƙaci a bashi waje zai gana da likitan da ya yi Ridayya gwaji. Dr ya numfasa ya ce "Bari na fara yi maka bayani. Neurology: wannan ɗaya daga cikin ɓangaren likitanci ne wanda ya keɓanta da cututtuka kaɗai. Ita kuma Nervous system wata hanyar sadarwa ce wanda take kula da aiwatar da aikin jiki na motsi da ji (Sensation) da tunani (Thought & emotion). Nervous system ta ƙunshi kwakwalwa da ɓargon ƙashin baya (Spinal cord) da kuma dukkanin sauran jijiyoyin da suka haɗa da sauran jiki da kwakwalwa ko ɓargon ƙashin baya. Ga kaɗan daga cikin ire-iren cututtukan da ya shafi Neurology" Buɗe system Dr ya yi Ustaz na binsa da idanu yana jin tsoron abinda zai ji na game da binciken. Dr ya ce "Ciwon kai mai tsanani (Migraines & headaches) farfaɗiyya (Epilepsy & Seizures) da kuma rashin iya sarrafa gaɓɓai yadda ya kamata (Cerebral palsy). Yawan karkaɗuwar hannu, ko ƙafa ko kai (Parkinson's disease). Ciwon tsufa wanda yake sabbaba ko na ce haddasa mantuwa da ruɗani tare da rikicewa (Dementia ko Alzheimer's disease). Shanyewar wani gaɓa (Stroke) Jin tsananin zafi a hannu ko ƙafa tare da sauran cututtukan jijiyoyi (Neuropathy and nerve damage)......," Dr ya yi shiru yana kallon Ustaz ganin ya rufe idanu a hankali ya ce "Continue" "Naga ai kamar bacci kake ne" Ya girgizawa Dr kai alamar “A'a” Dr ya ɗora da faɗin. Cututtukan da suka shafi kwakwalwa kamar zubar jini a kwakwalwa (Brain hemorrhage) ko kuma dajin kwakwalwa (Brain tumor) waɗannan cututtukan ana kiran su da “_NEUROLOGICAL DISCORDERS_” sannan kuma waɗanda suka shafi kwakwalwa kawai a kira su da BRAIN DISORDERS. A wasu lokuta likitan daya ƙware akan yin fiɗa a ɓangaren Neurology Neurology wato Neuro-surgeon ya kan yi tiyata wato ya buɗe kwakwalwar mara lafiya domin magance matsalar dake damun sh. Daga bayanin da na yi maka zaka fahimci Neurologist shi ne asalin likitan kwakwalwa da ɓargon ƙashin baya da kuma jijiyoyi. Shi kuma Psychiatrist shi ne likiyany ciwon halayya da ɗabi'un Ɗan Adam (Mental Discorder). Sauran sunayen da za a iya kiran Mental Discorder sun haɗa da Mental Illness, Psychiatric Disorder da Psychological Disorder. Yanzu zan maka bayanin menene Mental Health da Mental Discorders Yadda za kafi fahimtar matsalar ƴar taka" Dr ya sauke numfashi domin bayani ne mai wahalar ganewa kuma sai ka jima da mai irin halayyar baka san yana da matsalar kwakwalwa ba ya ce "Mental Discorder yana nufin tattarawar wasu alamomi waɗanda suke iya jirkitarda yanayin da mutum yake tsinkayan abubuwa da kuma yadda yake tunani da mu'amala da mutane. Irin waɗannan alamomin suna saka mutum ya shiga cikin matsanancin damuwa (Subjective distress) Sannan kuma suna janyo matsala ko nakasa (Impairment) a game da yadda mutum yake mu'amala da iyalin shi ko ƴan'uwansa a gida da abokan aiki ko kuma abokan karatunsa (Pervasive) Irin waɗannan alamomin za su iya jimawa mutum yana fuskantar su (Persistent) ko kuma a wani lokaci sai su zo gadan-gadan kamar saukar ruwan sama (Relapse) daga baya kuma sai su yi likimo kamar an yi ruwa an ɗauke (Remission) a wani lokacin ma su tsaya cak (Single episode)" Dr ya yi shiru ya ce "Manyan abubuwan da suke kawo Mental Discorders sun haɗa da Gado (Genetics) yanayin muhallin da mutum ya taso (Environment) ɗabi'un yau da kullum da aka ɗora ko gina mutum akai (Daily habits) da kuma yanayin halittar mutum (Biology) ko kuma yawan ƙarancin sinadarin kwakwalwa (Neurotransmitters) da kuma yadda suke aiki (Brain Chemistry) da kuma Shaye-shaye (Drugs) irin waɗannan Neurotransmitters ɗin sun haɗa da Serotonin (OCD) Dopamine (Schizophrenia, ADHD) da kuma Norepinephrine (Anxiety Disorders) da kuma sauran Brain Disorders ba waɗanda ake iya gano su ta hanyar yin gwaje-gwaje a asibiti kamar MRI ko CT scan har ila yau babu tabbatacciyar gwajin asibiti da ake iya yi domin gano Mental Discorders. Waɗanda suke da alhakin gano hakan sune Psychiatrist, Psychologist da kuma Clinical social worker amma an fi so Psychiatrist ya ja ragamar binciken duk wani Mental Discorders ciwon kuma shi ake kira da Mental Health Professionals" Ya rufe system ya ce "Kai kake tare da mara lafiyan yana da kyau ka gaggauta zuwa wani likita domin a tattauna da ita da iyayenta da yin sabon gwaji amma nawa binciken tabbas ta jima tana shan kayan maye kuma ta rasa sinadarin kwakwalwa tun tana jaririya maybe ta hanyar jijjiga ko wani abu, dole zata dinga ganin abu somehow abinda yake daidai a rashin daidai zata ganshi na kuskure kuma a daidai zata ganshi zata dinga yawan mantuwa musamman abu mai muhimmanci, kuma kwakwalwarta ta samu shock na ganin wani mummunan abu ko ana tilasta ta yin abinda bata so wannan shi ne nawa binciken" Ya miƙe Ustaz ya miƙa hannunsa mara ƙarin ruwa ya ce "Thank you Dr na gode da zuwa da kuma bayani zan kira ka" "My responsibility Allah ya bata lafiya kai ma haka" Dr na fita Ustaz ya sauke numfashi mai zafi ko Ridayya bola yake bi shi kam zan iya rayuwa da ita dukda yanzu wani irin zafinta ya ke ji rai amma dole ya yi mata uzuri ya buɗe mata dukkan zuciyarsa ya bayyana mata abun a fili ya kuma shayar da ita abinda ta rasa kuma take buƙata. Da sauri Baba ƙarami ya shigo ya ce "Babban mutum maza ta so Ridayya ke kiranka ta yi suma babu adadi sai buga kanta take tana kiran Abbiey" ba zai iya tashi ba saboda aikin da akai masa a mara amma haka ya fisge ya tashi nan da nan jini ya fara bin ƙafafuwansa "Wallahi ko ƙofar waje ka fita ni da kai ne ta mutu mana wallahi ka fita domin ganin wata Ridayya sai na yi maka Allah ya isa" Umma ta faɗa tana kumfar baki Mardiyya ta shigo haka Dr ta Junaid da Baffa hankali tashe domin yanzu likitan ya gama yi musu bayanin matsalar Ustaz "To a kan me yaro da matarsa a tsiri liƙa masa bazawara kuma baƙa ban shirya ganin munanan cikoki ba" Baba ƙarami ya ce "Ba kuma za ki taɓa ganin jikokin ba har abada" "Wallahi gani kamar na gansu domin ina zargin Mardiyya ciki gare ta, idan kaga Muhammmmd ya auri wannan yarinyar sai dai idan mutuwa na yi kuma ko mutuwa na yi bashi da matar data shige Mardiyya" Baba ƙarami ya ce "Ko? Bari mu gani idan soyayyar gaskiya take masa ita Mardiyyan domin har abada Ustaz ba zai iya tarayya da ko wacce mace ba a duniya kuma ba zai haihu ba, sakamakon faɗuwar da ya yi mararsa ta sauka akan dutse wannan jinin da kika gani yana bin ƙafarsa to aiki akai masa amma ba a yi nasara ba shi da mace dai dai kallo, kuma abinda baki sani ba Muhammmmd and Ridayya they're couples husband and wife suke kamar dai ni dake, tun a Kano kika sha alawar ɗaurin auren Muhammad-Bilal Tahir Rano da Ridayya Muhammad-Bilal Tahir Rano yanzu Ridayya matarsa ce hallaka ɗinsa halinsa ce.... Idan an karanta ayi comment a kuma danna sharing🤓🧚🏻‍♀️ Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv 08164069385 *SARAUTA CHARITY FOUNDATION* TAIMAKO DOMIN ALLAH Allhamdulillah! Kamar yadda mu kaga azumin daya shige lafiya gashi muna ƙoƙarin ganin wani da izinin Allah. Mun saba yin taimako domin Allah ga mabuƙata musamman Almajirai, nakasassu da wasu bashi da shi. Duk azumi muna yi musu abinci, ƙosai, kunu da ruwan sha mai sanyi. Yanayin rayuwa ya sauya jama'a sun ƙaru gari kuma ya yi zafi abinda muke da shi a Account ba zai isa mu yi abinda muka saba. *KIRA GA JAMA'A* Akwai wanda suke da halin bada ko dubu ɗari, wasu kuma ƙarfin hali, akwai ƴan'kasuwa da ma'aikta maimakon ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi, mai zai hana ba zaka taimaki mara shi ba. *SARAUTA CHARITY FOUNDATION* Na neman taimakon Al'ummar musulmi mai 500, 1000 har 200 zuwa abinda Allah ya baka su bayar domin a ciyar da mutane a cikin watan Ramadan. Ana saka alheri da alheri wannan alherin ranar ƙiyama za kaga samakonsa muna buƙatar yin abincin mutum 100 a kullum dole sai jama'a sun saka mana hannu😰🥰 Target: Target ɗinmu 200k ne yanzu muna da 20k da wani bawan Allah ya tura jiya ga wanda ya shirya taimako domin Allah ga Account number 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank Ko kuma 8164069385 Na'ima Sulaiman Shu'aibu Opay Ku yi zuwa ga ƴan'uwa da al'ummar Musulmi🥰🥰🥰 Allah ya haɗamu a ladan ya biyawa dukkan wanda ya taimaka bukatunsa na alheri. *MUNAFUKIN MIJI 34* Mikiya Writers Ass.. Bright pens free batch Nimcyluv Jikin Ustaz ne ya ɗan fara rawa, ya yi baya kamar zai faɗi Junaid ya tare shi jin maganar ya yi kamar tatsuniya, ta sauka a tsakiyar kansa baya son gasgata abinda ba haka bane, abinda kuma ya fid da rai da samun shi. Ko shakka babu an faɗa ne kawai domin ganin matakin da Umma zata ɗauka. Zuciyarsa ce ta ci-gaba da matsewa a ƙirjinsa komai nasa na ƙoƙarin tsayawa zafin da ƙirjinsa yake masa ya danne wanda yake ji a mararsa dukda jinin dake bin ƙafafuwansa saboda miƙewar da ya yi tsaye. "Ka samu nutsuwa Babban mutum, take heart please" Junaid ya faɗa yana zaunar da shi saman gadon amma ya ƙi kwanciya bakin Baba ƙarami yake kallo yana son sake jin maimaicin furucin koda a sigar wasa ne. Umma dake tsaye ta ce "Ohho dai batun aure abu ne wanda ba zai taɓa faruwa ba idan ina raye, ko ya aureta wallahi sai ya saketa tunda shi sakarai ne mai san ƙima da darajar da Ubangiji ya yi masa ba, ya zauna ya lalace akan wata yarinya ƴar cikinsa ma bazawara raguwar wani mai haihuwar yara biyu, baƙa mummuna a yadda ta saka a garari wallahi itama sai ta shiga" Ta yi ƙwafa sosai zuciyarta na yi mata zafi idan ta tuna yadda Ridayya ta watsar da Ustaz a kan wani, ta saka ƙafa ta shure duk wani gata da kulawa da yake mata bayan shi ne ya mayar da ita mutum mace kamar kowa amma abinda ta zaɓi ta saka masa da shi kenan. Ta ɗora da cewa "Ka yi zaton ban san komai ba ko? Yarinyar daka kusa mutuwa a kanta sanda ta ce bata son ka, ka zauna tsayin shekaru 42 zuwa 43 yanzu babu aure bayan Ubangiji ya baka ikon auren mata huɗu ka liƙi a ɗaya? Ɗayar ma wacce iyayenta basu nuna mata gata ba, ɗayar ma wacce ake tantama a kan waye ubanta.....," "Shut up! Saurara ya isa haka. Me kike nufi?" "Ina nufin abinda ka ji mana Alhji Tahir? Ba Alhji Mansur da kansa ya ce ba shi ne ubanta ba, ba shi ne ya haifeta ba ai wanda ya mutu shi a kewa ƙarya, na gode kuma saboda duk kuna wajan hakan ta faru" Baffa ya rasa abinda zai ce bai taɓa yin ladamar abubuwan da suka faru ba irin yanzu, ya san ya yi kuskure ya shafawa Ridayya baƙin fentin da ba zai taɓa gogewa ba, ya ɓata career ta da kansa a matsayinsa na uba. Ustaz ya runtse idanunsa tare da tsune leɓensa na kasa ba tare da tunanin har ya fashe ba, sai da ya ji ɗanɗano ya fahimci jini ke zuba a lips ɗin na shi a tsakiyar ƙirjinsa ko wanne kalamai na Umma yake sauka bai taɓa zaton akwai ranar da Umma za ta ƙi Ridayya ba ko taƙi abinda ya nuna yana son kasancewa da shi. Jijiyoyin kansa duk suka fito waje suna har bawa da fallasa raunin zuciyarsa da ƙyar ya cira idanunsa ya kalli Mardiyya dake tsaye tana jin yadda ake ciwa Ridayya mutunci ta samu lasisin yi mata gori. "Keee" ya ce a wahale yana lumshe idanunsa ta kalle shi cikin yauƙi ta ce "Ruwa za a baka?" "Out!" Ya faɗa yana nuna mata hanyar waje alamar ta fice kuma sai runtse idanunsa yake yana dafe kansa wanda yake ji kamar zai cire. "Da kai da out ɗin kun ci gidanku na bi out da gudu ban tsaya ba, matarka ce ta sunna kuma budurwa wacce bata taɓa haihuwa ita ce daidai kai ita kuma nake da burin ka zauna da ita har abada" Wata dakakkiyar tsawa Ustaz ya dakawa Mardiyya da gudu ta fice jikinta na rawa don ta ɗauka dukanta zai yi shi da kansa tsawar ta bashi tsoro ya yi baya yana jingina da frame ɗin gadon idanunsa lumshe kaɗaici yake so ya samu da zuciyarsa. Bayan fitar Mardiyya Baba ƙarami ya kalli Umma ya ce "Kin kyauta kuma kin yi yadda kike so, amma hakan ba zai hanani yin yadda na so ba, kece uwar Muhammad nine ubansa kina son Mardiyya ina son Ridayya domin jinina ce, ko babu aure ta zame wa Babban mutum dole hakƙinsa ne na kulawa da ita. Sai dai kin yi a banza domin sara da sassaƙa baya hana ganji toho, kamar yadda Mardiya take matarsa haka Ridayya take matarsa ta sunna babu mamaki ya zama na ita ce uwar gida domin idan aka bincka nata auren aka riga ɗaurawa" "Can ta matse muku da kai da masu ɗaurin auren, da munafukar uwarta data goyi baya. Ko a cikin hadisi an ce ka bi uwa har sau uku kana uba, maganata kamar yankan wuƙa haka take a kan Bilal, ba shawara nake bashi ba umarni ne kuma zan ga wanda zai tilasta ya zauna da wata bazawara muguwa butulu wacce bata san halacci ba, balle ban yarda an ɗaura auren ba I'll never accept her as my daughter-in-law" Tana faɗin hakan ta fice daga room ɗin, Baffa ya bita da kallo yana jin haɗin da sukai na neman sare masa tunda yana ƙoƙarin taɓa zumunci kuma ahli ɗaya. Kasa cewa komai ya yi sai ficewa daga room ɗin ya koma wajan Ridayya yaga halin da take ciki. Junaid ya kalli Ustaz da jikinsa har yanzu rawa yake ga wani irin zafin zazzaɓi dake farmakar shi a hankali ya ce "A kira Dr Abba" "Ba Dr Ustaz ke buƙata ba, ka je can wajan Baffa ka kula da ƴar'uwarka Junaid lokaci ne na bata gata da bata dukkan wani support da take buƙata kune yanzu muke buƙatar ku haɗe kan ku, mutuwa bata san inda rai yake ba, bata san inda ciwo yake ko shekaru yake ba, amma mu a kodayaushe ta Allah zata iya kasancewa da mu, kuma Allahamdulillah mun yi wa zumunci hidima dukda bamu da yawa. Jeka Junaidu maza jeka" Junaid ya miƙe yana jin ƙarfin qiwwa a maganar Baba ƙarami bayan fitarsa ya rage daga Baba ƙarami sai Ustaz da har yanzu idanunsa a rufe suke. Waje ya nema kusa da Ustaz ya zauna, tare da kama hannunsa ya riƙe cikin nasa lokaci mai yawa basu samu kusanci da ɗan nasa haka ba, rauni irin na uba ya mamaye zuciyar Baba ƙarami ya san zurfin cikin Ustaz tun yana ƙarami mamakin yadda zafin zuciyata ya ragu sosai yake. "Babban mutum buɗe Idanunka" A hankali ya buɗe sun yi wani irin jirkicewa yanayin da Baba ƙarami bai taɓa gani ba, ƙwayar idanunsa tamkar ba tasa ba, wani irin jan abu ya kwanta ciki tun ɗazo yake ƙoƙarin yin magana sai ya ji tamkar hayaƙi ne zai fito maimakon furuci. Baba ƙarami ya sake riƙe hannun Ustaz sosai a taushashe cikin kulawa ya ce "Duk inda ake neman jarumin mutum kuma sadauki mai bada farincikinsa saboda wani ya yi murmushi to a nemi jarumin ɗana. Muhammad baka buƙatar damuwa a yanzu ƙarfin qiwwa kake buƙata ka yi haƙuri ka daure abinda kake ji karka bari rauninka ya fito, a wannan karan kar ka yi faɗa domin Ridayya ka yi faɗa domin abinda zuciyarka ke so, kuma take son rayuwa da shi. Bani da tabbacin mene a zuciyarki game da ƴar rainonka abu ɗaya zan faɗa maka ka kula ka yi ƙoƙarin ganin ta zama taka ka yi hakan ƙarfin qwiwarka yana ga abinda kake so" A hankali ya shiga girgiza kansa yana matse hannun Baba ƙarami dake cikin nasa bakinsa na rawa ya cec "Bana jin zan iya Abba zuciyata a matse take bana fahimtar komai" "Be strong; ka yi abinda ya fi haka idan abu ya ƙare baya nufin rayuwarka ce ta ƙare, something is over doesn't means yourself is over. Har yaushe zaka zauna haka? Shiru baya maganin matsala ciwo yake haddasawa a zuciya da kuma dana sani mara iyaka ba zan ci-gaba da faɗa da mahaifyarka ba, ba tare dana san kana son Ridayya ko a'a ba?" Ustaz ya ware idanunsa a lokacin ya kalli mahaifinsa ya kasa furta komai sai zufa da take yanko masa shi gani yake me ya sa dole sai ya furta ba za su gane bane? Me ya sa ake son fallasa masa asirin zuciyarsa "Ka faɗa mini ina jiranka, mene matsayin Ridayya?" "Abba please" "Please what?" Ya yi ƙasa da idanunsa zuciyarsa kamar ta fito waje. "Look Muhammmmd the most important thing is to be yourself. Ni mahaifinka ne don ka fiddo mini sirrinka ka buɗe sirrinka ba wani abu bane, idan kana son Ridayya i most be by your side, idan baka son ta shikenan I'll let her go ta zama free" Da sauri ya matse hannu Baba ƙarami hatta tsokar jikinsa rawa take ya shiga girgiza kai laɓɓansa na rawa "Say it Muhammmmd" "Ni daban Abinda ke zuciyar Ustaza daban Abba" "Ko hakan yana nufin ita ɗin tana amsa sunan matar Muhammad-Bilal Tahir Rano ne?" "A'a Abba babu kyau kar ka fara wannan zunubi ne na yafe maka kuma" Baba ƙarami ya ce "Zunubi ko? A wannan lokacin kai Allah zai yafewa bani ba Babana, da gaske nake ina nufin abinda na faɗa. Ridayya Mansur Rano is your halal wife matar sunna" Ustaz ya kasa tantance halin daya shiga kallon Baba ƙarami kawai yake da wani irin firgitaccen yanayi da shakku dukda a zaune yake amma tun daga kan babban yatsarsa har zuwa saman jikinsa rawa yake fuskarsa ta fara sauyawa zuwa wani launi kamar ba Ustaz ba. "Allah ya yafe maka Abba Allah ga Abbana" Baba ƙarami ya yi murmushi ya fahimci Ustaz har yanzu bai yarda ba, ya ciro wayarsa ya kunna video recorded ɗin da aka yi na ɗaurin auren. Play ya danna Ustaz ya zubawa video Idanu ya Baffa ga Baba ƙarami ga Tajj har da Junaid ga Barrister ga kuma General mijin Anuty Kaltum. Sanda ya ji liman ya ce “An ɗaura auren Muhammad-Bilal Tahir Rano da Ridayya Mansur Rano a kan sadaki dubu ɗari biyu” Tsigar jikinsa ce ta fara mimmiƙewa yana jin wani emotions wanda baya kaiwa ƙasan mararsa a iya zuciyarsa yake tsayawa da gangar jikinsa ƙofofin gargasar jikinsa suka buɗe wani irin sanyi yana shigarsa, zuciyarsa ta buɗe hannunsa ya shiga rawa duk jarumtarsa ta kau ikon Allah kawai yake gani mai yin yadda ya so a lokacin daya ga dama, Hausawa sun yi gaskiya da suke cewa kana iya aurar matar wani amma ba zaka iya haihuwar ɗan wani ba, matar mutum kabarinsa. "Abba gaske kake?" "Da gaske nake Babana hukuncin Ubangiji ne ba namu ba, kuma tsarinsa ne Ridayya matarka ce" Ustaz kasa magana ya yi sai halin ɗan fari dana autar ya bayyana ya ɗora kansa a cinyar Baba ƙarami wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya ya sauke a ransa yana yin hamdala ga Ubangiji daya ara masa ganin wannan ranar. Bai taɓa fitar da hawaye a rayuwarsa ba bai suna zuba ba sai da Baba ƙarami ya riƙo fuskarsa yana share masa hawaye ya ce "Kuka? Al'amarin har ya kai haka Babban mutum baka tunanin ka girma?" Ya ɗan marairaice fuska ya ce "Allahamdulillah!" "Shi ne abin godiya, zan yi magana da kai idan ka samu nutsuwa" Ustaz ya kasa tantance wanne kalar farinciki yake ji, tsoron abinda Dr ya faɗa ya wanzu a zuciyarsa anya zai iya? Me ya sa bai samu Ridayya ba sai yanzu da ƙaddara ta faɗa masa ƙaddara mai zafi da munin gaske Ridayya ta saba da rayuwar gidan miji ba zata jure halin da yake ciki ba, domin ba zai amfana mata da komai ba shi ɗin kamar photo haka zai zama. Idan ya ture wannan taya zai fara rayuwar aure da Ridayya? Ƴar cikinsa yarinyar daya raina kuma yana jin ya mata girma, shi da kansa kunyar wannan al'amarin yake yana jin son rayuwa da ita har bayan abada idan akwai amma bai taɓa hango wani nauyi na musamman ba, taya zai iya kwana da ita gida ɗaya ɗaki ɗaya gado ɗaya matsayin matar, su kwana matsayin mata da miji? Ya rufe idanu a hankali yana sauke numfashi nauyin zuciyarsa na raguwa kamar a mafarki haka yake jin batun auren nasu gefen zuciyarsa Ridayya ɗin kawai yake son gani, a wannan karan zai yi mata kallo ne na matarsa kuma halalinsa. "Tsuguno bata ƙare ba" Ridayya Sadauki ne a ranta, shi kuma Ridayya ce a ransa Mardiyya kuma Ustaz ne a ranta ga matsalar rashin mazakuta ga matsalar Umma wacce tafi ko wacce illa a zuciyarsa ga matsalar Sadauki ga matsalar ciwon Ridayya ɗin _“What should I do?_” Allura aka sake yi wa Ridayya mai nauyi ta fara bacci al'amarin ya ƙara hargitsa kwanyarta wacce take a gurɓace har yanzu shocked ɗin ganin Ustaz zube a ƙasa ne bai yar kanta ba. Kwana biyu a tsakani ta farfaɗo cikin hayyacinta kuma babu abinda ke damunta sai ramar da ta yi ta ƙara yin zuru-zuru ta yi ɗan duhu a kan na baya saboda kwanciyar asibiti. Lokacin da idanunta ya sauka a kan Zainura firgicewa ta yi ta hau salati da addu'a "Yaya Ridayya ni fa ba fatalwa ba ce ki bar addu'a" Ridayya ta girgiza kanta ta fara yunƙurin guduwa Baffa ya ce "Fatalan suna da yawa" Da wani irin sabon tashin hankali take kallon Baffa sai kuma Mami ta dinga nuna su da hannu "Kun kun mutu an ce kun mutu ko kun zo tafiya dani ne, kar ku bar ni zan biku lahira ɗin an ce...," Sai kuma ta sulale jikin Mami a sume daman sun zan za a rina an saci zanin mahaukaciya bayan ta farfaɗo ta fasa wani ihu Mami ta riƙe ta gam a jikinta ita kanta kuka take Zainura ma kukan take Baffa ya sunkuyar da kansa. "Mami da gaske kece? Kece a gabana kike riƙe ni baku mutu ba aka ce kun mutu? Ashe ƙarya ya yi mini mugu azzalumi ba zan taɓa yafewa Giɗaɗo ba ya saka na dinga wahala ashe kuna raye Abbiey ma ya ce kun mutu to babu ruwana da shi tunda ya yi mini ƙarya" Ita tana kuka Mami na kuka "Shiitttttt ya isa haka kinga ba ki da lafiya ki bar kukan haka" "Lafiya lou nake ai tunda na ganku na warke Mami za ki dinga yi mini magana yanzu? Za ki dinga hira dani? Kuma za ki dinga siya mini abu irin n Zainu kin daina bari na cin mutuncin halittata?" "Ina tare dake Ridayya ki yafe mini na yi kuskure ka cutar dake" "Na yafe miki ba ki mini komai ba" daɗi ya ishe Ridayya tana tuno maganar Zameer da yake cewa bata da kowa bata da gata to ya zo ya gani iyayenta suna raye. "Baffa don Allah yau ɗaya ka ce ni ƴarka ce bani na yi kai na da na san inda zan samu farar fata da kyau irin na Zainu dana samu" "Shalalen Ustaz you're my darling daughter my love you're my favorite person. Na yi laifi da kuskure ban san yaushe ba kuma ba zai daina kukan hakan ba duk wanda yake da saka hannu a kan faruwar komai ba zan taɓa yafe masa ba" Baffa ya rungume Ridayya yana jin wani tausayinta soyayyar da yake mata tun tana ciki wacce ita ta yi sanadiyyar lalata komai ta dawo masa sabuwa fil a zuciya. Mami kuka take da dukkan ƙarfinta raba uwa da ɗa akwai ciwo kuma dafini mai girma a zuciyar ko wacce mahaifiya idan ta tuna bata bawa Ridayya tarbiyya sai ta ji hankalinta ya tashi shi ya saka wani lokacin komai take yinsa da ka, dukda Ustaz ya taka rawa iya karfinsa wajan gina ta a kan turbar arziƙi. Addini, biyayya, tsare mutunci, suttura da ilimin zaman rayuwa amma tarbiyyar uwa daban take role ɗin uwa is best a rayuwar ko wanne ɗa. "Mami ni ma ina son kayan irin na Zainu" "Ridayya ke dai kishi halittarki ne ƙanwarki ce fa, ke ga Little kin ajjiye da abinda kika haifa na fari yana nan da tuni ya yi wayo fa amma kina acting like a baby" Cewar Yaya Balkisu tana dariya. "Mu dai yanzu baby ce a wajanmu dole ta nuna mata wawta irin ta ƴaƴan fari da kuma sangartata Ustaz ya yi" Cak Ridayya ta tsaya da murmushin da take sai kuma ta miƙe ta ce "Baffa ina Abbieyna?" "Ki ce ina Yaya Bilal ko Ustaz ki daina cewa Abbiey Ridayya" "Shi Babana ne, yana ina?" Baffa ya sauke numfashi ya ce "Kusa da ɗakin nan ki fita a hankali" da ƙyar ta jira ta saka wula duguwar riga ce a jikinsa wacce komai nata ya fiddo ta yi mata kyau ko slippers bata saka ba ta fita tana ƙoƙarin shiga room ɗin Umma na fito wa "Ina yini Umma?" Da faɗa bakinta na rawa saboda kallon da Umma ke yi mata. "Ina yini ban ganshi ba, umma kuma ke neme ta idan kin zo don ganin Ustaz ne to ki koma domin babu ke babu shi" Jikin Ridayya ya yi sanyi idanunta ya cika da hawaye ta ce "Abbieyna ne fa don Allah ki bar na shiga" "Zan ga uban wanda ya isa ya saka ki shiga" A sanyaye ta ce "Me na yi miki Umma ki yi haƙuri idan na miki laifi" "Ai kinfi ɗan dako sanin tasha. Ba ki mini komai ba kawai na tsane ki bana son ganinki tare da Muhammmmd" Mardiyya ta ƙara su wajan ta ce "Umma the car is ready likitan ya bada sallama" Umma ta ce "Ok ƴar arziƙi irin albarka wanke hannu ka taɓa farar mace alkyabbar mata haske mai haska ko wanne duhu, farar mace baku da yawa a duniya dai a Aljanna, idan mutum bai auri farar mace ba kuɗinsa ne bai kai ba" Mardiyya ta yi wani irin fari da idanu ta ce "Na gode Ummana" Ridayya ta ji ta muzanta jikinta ya ɗauki rawa ta juya da gudu ta tsaya wani corridor ta yi kuka kamar ranta zai fita sai kallon baƙar fatarta take me ta yi wa Umma haka ne? Idan ta yi mata laifi to a kan me zata hanata zuwa Abbiey? Kukan da ta yi mai yawa ya saka kanta sarawa tare da fara ciwo. Duguwar jallabiyya ce a jikinsa ta maza saboda aikin da yake mararsa an bashi da wani ɗan sanda yana takawa da shi, fuskarsa a kame baka gane halin da yake ciki furr Umma ta hana shi shiga wajan Ridayya a haka suka shiga mota Junaid ya kai su can gidan Ustaz ɗin. Ustaz hankalinsa yana kan Ridayya a haka ya bar asibitin. Ridayya tana komawa ciki suma aka sallame su ta zama wata so silent maganganun Umma na yawo a kanta lokaci zuwa lokaci tana kallon baƙar fatarta. Zameer ne jingine da cikin wata jibgegiyar mota ya sha shadda sai ɗaukan Idanu take kamar kodayaushe waya iphone ce a hannunsa ya manna bluetooth magana yake kamar an yi masa dole idanunsa a kan Alhajin ya ce "Idan ka siyi filin haka to idan bai ba ka bar shi akwai masu siya da yawa" Mai siyin filin ya dinga kallon makeken filin da girman gidan da zai samar bai ɗauka kuɗin da Zameer ɗin zai buƙata kenan ba domin ya yi sauƙi fiye da yadda ya zata ya ce "A'a nikam filin ya yi mini idan miliyan 25 ɗin ne matsayarka shi kenan sai ka bani takardun fili ga shaidu ga dillali ni kuma na baka takardar banki ko transfer ko cash" Zameer ya ɗan taɓe baki yana danna waya a nutse ya ce "No transfer ɗin zai fi" Ya ce "Ok takardun filin?" Mota Zameer ya je ya buɗe ya ɗakko takarda ɗaya ya dawo ya bawa mutumin shi kuma ya shiga duba takardar can ya ce "Kace sunanka Zameer Mahboob Dollar?" "Sure; ya akai?" "This land is owned by Ridayya Muhammad Tahir" Zameer ya ce "Inji uban wa? To nawa ne halak malak idan zaka siya ka siya idan ba zaka siya ba ka bani takarda ba dole" Dillalin ya ce "A'a ai ba a yi haka ba kasan duniya ta lalace da ɓata gari masu satar filayen jama'a, ko ka mance ba wannan takardar zaka bamu ba? Domin wannan ma ai original ba ce" gaban Zameer ya faɗi jin ance ba Original bace fake ce kenan ko ya? Me ya sa ya yi gaggawar barin Ridayya ta gudu ne? "Eh maybe mantuwa na yi kawo kawai" "A'a ba a yi haka ba ina zuwa" Dillalin ya faɗa yana kwafe wasu numbers daya gani a jikin takardar kira uku ya yi kafin a ɗaga ya yi wa Alhaji alama daya kira police. "Assalamu alaikum kuna magana da Bello dillalin filaye, an kawo wani fili dake unguwar jan bulo kuma an saka Ridayya Muhammmmd Tahir" Shiru ya yi yana jin me ake cewa ya ce "To babu matsala nima naga alama bari a yi hakan" Zameer na tsaka da danna waya yana jira ya ji shigowar maƙudan kuɗaɗe ya an riƙe shi ya ɗago kai ganin police ya saka shi binsu da Idanu kafin ya yi magana ɗaya daga ciki ya ce "You are under arrest" "Arrest akan me kasan waye ni kowa officer kasan waye babana?" "Sorry sanin waye babanka baya cikin aikina, idan mun je office za ka ji bayani" Tija ƙeyar Zameer sukai zuwa police station. Suna zuwa suka bashi damar kiran babansa kuma suka zayyana masa laifinsa na sama da faɗi da yake shirin yi da filin wani. "Wani kuma? Filin na matata ne matata kuma hakƙina ce komai nata mallakina ne" "Ina matar taka take yanzu? Ta zo ta bamu tabbacin kai mijinta ne sai mu sake ta, ku saka shi a ɗaki" Zameer bai san ta ƙamaimai inda Ridayya take amma dole zata dawo gare shi bata da zaɓin daya shige zama ƙarƙashin inuwarsa haka ya saka a ransa kwana biyu ya yi ya fita daga hayyacinsa ko hauka yake ai ba zai kira gida ba, kuma bashi da ƙarfin qiwwar kiran Moo ko Khalid. Ridayya kawai yake nema idanu rufe. Sadauki na zaune shi da Prof da Mother sai secretary daya shigo yanzu cikin rashin sa'a files ɗin hannunsa suka kwace pictures ɗin zuƙa zuƙan ƴan'mata suka bayyana tare da tarwatse wa a parlourn. Sadauki ya dinga kallon pictures ɗin da mamaki haka mother. Prof hankalinsa ya tashi ya yi wa secretary alama da idanu cikin faɗa ya ce "Wai secretary how many times zan maka warning akan ka daina bina da photonan masu neman taimakon nan eh? Gabaɗaya baka san aikinka ba ana bata taimako dole ne na ce maka marayu kawai dana kasassu nake bawa tallafi" secretary ya ce "Afuwa ranka ya daɗe wallahi sun takura ne gabaɗaya bikinsu za a yi ke suna buƙatar taimako shi ne suka rarraba pictures nasu, wannan sun fi wata waje na yau na gaji na ce bari dai na yi maka bayani" "To i can't ba zan iya ba kasan takara nake bana son problem" "Muga" Sadauki ya faɗa yana amsar pictures ɗin yanayin kayan jikin ƴan matan su kaɗai abin mamaki ne ba su yi kama da masu neman taimako ba shi damuwar neman auren Ridayya ce a kan shi ya bawa secretary pictures ɗin mother ta ce "Daka taimaka shi taimako ba sai an ware wani ɓangare ba, kuma hakan zai taimaka wajan dasa soyayyarka wajan mutane shi ma campaign ne" Prof ya miƙe tsaye ya ce "Mu je" fita suka yi shi da secretary suna fita ya ce "Ka kusa kwafsawa wallahi idan Sadauki ya sani na banu" Secretary ya ce "Wallahi ban san ya aka yi ba" Prof ya lumshe idanunsa yana sake kallon pictures ɗin hankalinsa duk ya tashi ya ce "Wallahi duk ka firgitar dani a gida na yi niyyar kwana amma ka zaɓa mini guda biyu a yi booking hotel da ɗaki a kula da su ya zama confirmation please i trust you" Suna gama maganar ya koma ciki ya ce "Yes son ina ne address ɗin yarinyar gobe za mu je in sha Allah kar ka damu har da sadaki zamu tafi" Murmushi Sadauki ya yi ya ce "Best father thank you darling" "Anything for you dear, iye angon Ridha" Tashi ya yi mother ta ce "Badai fita za ka yi ba na haɗa maka abinci" "No meeting ne dani zan dawo nan da 2hrs love you wife" kafin ta yi maganar ya fice. Sadauki ya kalli mother yaga duk ta sauya ya san akwai damuwa a ranta, mother tana buƙatar mijinta a kusa da ita kewarsa take sosai ta manta yaushe rabonta da shi matsayin miji da mata Sadauki zai yi magana ta ce "Wanne gida ka ce ka zaɓa ne? Kuma zan tura a fara haɗa lefe" "Mother nrml fili nake so gidan da zan ginawa Shanshan na musamman ne" Ta yi murmushi ta ce "Oh Allah ya nuna mini wannan rana" "Wallahi mother ina tsananin son Shanshan Allah ne shaidata i love her with all my heart I so much loves her" "Allah ya baka ita" da sauri ya ce "Yama bani" Duk suna zaune a parlour banda Ridayya wacce kullum kuka take sun rasa gane kanta rabonta da Ustaz tun ranar da Sadauki ya zo. Idan ta fara tunanin Sadauki sai tunanin Abbiey ya danne na Sadaukin tunanin yadda zata zama fara shi ne kawai a ranta. Baba ƙarami ya ce "Allahamdulillah komai ya yi farko yana da ƙarshe kuma in sha Allah zamu tattara mu koma Kano da zama a Babban gidan da aka sauya. Kuma zamu tara mutane a yi addu'ar ɗaurin auren Ustaz da Ridayya kana a yi walima dole jama'a su shaida kuma aurenta ya zama mai ƴanci ba kamar wancan ba. Babban mutum zai gina gidansa da zai zauna da iyalinsa zamu bayyana ga wanda suke zaton mun mutu. Aure rai ne fa shi duk wanda yake ƙoƙarin ganin bayansa idan akwai rabo mai tsanani sai Ubangiji ya raba shi da duniyar bakiɗaya, auren Ustaz da Mardiya nufin Allah ne haka auren Ustaz da Ridayya rubutacciyar ƙaddara ce wacce ta jima a zane, kuma a bayanin Hajiya na fahimci Ridayya ita ce uwargida an riga ɗaura aurenta akan na Mardiyya domin mun jima da hakan mun su rufewa sai kuma aka yanke hukuncin rabawa dangi alawa da goro su saka albarka, ba wani wa'azi da zan yi sai ranar da aka yi biki Ridayya zata tare zan haɗa na yi musu wa'azi" Hajiya ta ce "Hakan ya yi Allah ya saka Albarka a wannan auren ya tsole idon maƙiya. Oh ashe zanga wannan ranar jikokaina aka haɗa aure Allahu Akbar" Ustaz ya watsa mata harara Junaid na kallonsa ya yi murmushi kawai. Baba ƙarami ya zaro kuɗi ya ce "Zainu kira mini Yaya Ridayya na bata sadakinta" Sai a lokacin Ustaz ya ce "Sadakin baƙar mace daban yake Abba ka bari zan bayar" "Gaskiya ne yanzu samun baƙar mace sai an bincka bincike mai tsanani" Mardiyya ta zo wuya. "To In sha Allah gobe zamu koma tunda jikin da sauƙi sai ku zaba cikin shiri" Ustaz ya gyara murya ya ce "Don Allah kar a sanar da Ustaza maganar auren nan zan faɗa mata da kaina" Duk suka yi na'am Mardiyya ta tashi fuu ta nufi ɗaki zuciyarta sai wasiwasi take mata babu mamaki ciwon Ustaz ƙarya ne kamar yadda Umma ta faɗa mata plan ne don a raba auren a bashi Ridayya. Ta fara tunanin mafita dole a yau ta saka Ustaz ya kusanceta but how? A fili ta ce "Maganin saka feelings" da sauri ta ɗauki jaka da mayafi ta fice ba tare data tambaya ba. Mami ta shigo ta samu Ridayya tsaye tana kallon madubi ta yi murmushi tare da kama hannunta suka zauna bakin gado ta ce "Bakya gajiya da kallon madubi? Ko kina shirya wani abu ne, Ridayya ke ta musamman ce ba za ki gane ba sai nan gaba" Ridayya dai ta yi shiru domin bata saba da Mami ɗin ba. "Mene matsayin Ustaz a wajanki ne?" A hankali ta ce "Abbieyna" "Baffa kuma fa?" "Babana" Mami ta ce "To waye uban na gaskiya kenan Ridayya ga Ustaz ga Baffa kowa kuma uba dole akwai wanda yake amsa sunan daba nashi ba. Baffa shi wanda ya yafe miki kuma biological father naki, Ustaz kuma yayanki ne wanda ya raine ki" "Kuma me ya sa ake kira na da sunansa?" "Saboda shi ya buƙaci haka. Ridayya buɗe kunnenki Ustaz ba mahaifinki bane a rashin uba a kan yi ubanɗaki a rashin gata da uba kika samu Ustaz. Kamar yadda Junaid yake haka Ustaz yake a wajanki bambancin shi ne Ustaz nada ikon aurenki ki zama matarsa domin ɗan gidan Abba ne ke kuma ƴar Baffa ce akwai aure a tsakaninku" Ridayya ta zare idanu tana rufe baki tana jin maganar wata kala ba tsari taya Abbiey zai zama mijinta? Wannan shafi abin kunya ne "Yanzu kika fara rufe baki na yi tunanin za ki fahimci cewa Ustaz yana son ki?" "Mami na sani fa, i knew everything ina jin wani lokacin ai matsayin uba ne wani lokacin kuma sai na manta abubuwa ban taɓa kawo shi a matsayin miji ba. Mami Abbiey bai cancanta dani ba na yi zunubin da ba zai taɓa yafe mini ba idan ya ji, wallahi ba zan iya kallon Abbiey matsayin miji Mami ban dace da shi ba" "Ya taɓa faɗa miki yana son ki?" Ta yi shiru koda ta nutsa tunani sai kanta ya fara ciwo Mami ta miƙe ta ce "It's okay. Mimi babu abinda yafi rayuwa da wanda yake sonka daɗi, ki tuna wanda ke zuciyarki wanda kike jin kishinsa idan kin ganshi da wata macen wacce kike jin dake kawai kike son ya rayu" "Abbiey ne Mami bana son ganinsa da Mardiyya" Mami ta yi murmushi ta ce "Sai ki ƙoƙarin maye gurbin Mardiyya a zuciyarsa ki zama kamar ita da matsayinta a wajansa" "To ki bani shawara, amma Sadauki fa?" "Shawara kike irin ta uwa ko kuma irin ta Aminiyya? Sadauki ban ce ki daina tunaninsa ba nima" "Aminai mugwaye ne, abokina ɗaya Abbiey ki bani irin ta uwa" ta faɗa tana kwaɓe fuska "Da farko dole ne kina hira da Ustaz, ki kula da shi daga abincinsa har ruwan wanka kayan sawa ki dinga nunawa kina son shi hakan zai saka Mardiyya ki shi, kinga dai kin girma amma a wajansa ki nuna ke da Little ɗaya kuke idan kun yi faɗa kar ki bari Mardiyya ta gane, duk abinda zai ɓata ran Ustaz kar ki yi kina kwaliyya kina zuwa kuna hira amma kar ki kwana wajansa" Ta yi saurin cewa "Ai ba zan iya bama tunda kika ce zai iya aure na nake jin kunyarsa" Mami ta miƙe tsaye ta ce "Sannu Mimi ke kam ko Zainura ta fiki wayo ki je yanzu ki yi masa sannu" Fita Mami ta yi Ridayya ta miƙe daman ta yi wanka ta gyara sumarta ta ɗaure dake dare ya fara ta saka riga body short ta saka slippers ba zaka ce ita ta haifi Little ba domin jikinta har ya fi na Zainura kyau balle kuma na Mardiyya. Burhan na zaune a parlour ta zo ta shige ya bita da kallo yana hura hayaƙin tabar shi a parlourn. Shiga ta yi bedroom ɗin a hankali bakinta ɗauke da sallama shiru babu kowa bedroom ɗin sai ƙamshi yake komai a gyare ta dinga kallon ko'ina ta nufi gaban madubi ta tsaya idanunta ya sauka a kan diary ɗin Ustaz ta buɗe ta ɗauka ta dinga dubawa ta buɗe shafin Farko idan aka saka _FIRST LOVE_ da mayan baƙi. Tana ƙoƙarin karantawa ta ji an ziro hannu ta saman kafaɗarta an ƙwace an dafa kafaɗarta da ɗaya hannun. Ta cikin madubin ta gan shi yanzu ma dai jallabiyya ce a jikinsa mai ɗan faɗi ya faɗa ya ƙara fari ya cika mata Idanu ya mata kwarjini sosai sai duk kunya ta kama ta ta fara ƙoƙarin matsawa ya ƙara faɗi bakinta na rawa ta ce "Abbiey ya jikinka? An ce ka ji ciwo a mara ko?" "Injiwa?" Ta tura baki ta ce "Haka na ji wai ƙafarka nata jini yanzu ya daina ko? Da zafi wajan ciwon da yawa ne? Mu gani nuna mini wayyo Abbiey" Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga jallabiyyarsa zuwa sama ya yi saurin durƙusawa ya riƙe hannunta yana rufe Idanu saboda zafi ya kame hannayenta duka ya haɗe waje guda ya ce "Ustaza ba ki da kai sam, kin san me za ki gano?" "Mararka zan gani mana wajan ciwon sai na yi maka addu'a" bashi da wani ƙwari gashi neman fin ƙarfinnsa take a dole sai taga wajan ciwon sai ƙoƙarin ɗaga jallabiyyarsa zuwa sama take. Cikin dabara ya janyeta yana tsayar da ita gaban madubi idanunsa a ɗan lumshe yake kallona yau Ridayya ce a gabansa take amsa sunan matarsa? Taya zai fara godewa Allah? A hankali ya ware hannunsa ya ce "Zo ki ji wani sirri" Ta ƙarasa har tsakiyarsa taƙi kallonsa a hankali ya zagaye hannunsu ya yi covering ɗinta tare da yi mata halal hug ya rungumeta a tsakiyar ƙirjinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar na rashin sabo ya sauke ajjiyar zuciya mai nauyi ya ce "Allahamdulillah ya rabbil alamin" Za ta yi magana ya damƙe hannunta tare da sumbatar tsakiyar goshinta irin na larabawa idanunsa a lumshe ta ji abu mai zafi na zuba a fuskarta kafin ta ɗaga kanta ya juyar da ita yana zama saman gado ya nuna mata lemon da Mardiyya ta kawo masa ya ce "Miƙo mini" jikinta a sanyaye ta ɗakko lemon ta ji san yi sosai ta ce "Abbiey na ɗan sha mu ji?" Ya kalleta da kyau tana yin komai kamar yarinya shi bai ba san ame ta ɗauke shi ba. Mijin ko aboki ko kuma uba? "Na sha kar ka mini rowa" "Sha" kawai ya ce kurɓa ɗaya ta yi ta ji daɗi sai ta zuƙe duka daga ƙarshe ta ji wani ɗanɗano nada ban ya ware Idanu ta kalli kofin shi ma kallon kofin yake kishin giɗa. "To wallahi daɗi ya yi" "Allah ya yi miki Albarka Ustaza ya ba ki lafiya daga miƙo mini lemo sai shanyewa?" Da sauri ta ƙarasa ganin ya lumshe idanunsa ta yi saurin kame ƙafarsa ta ce "Yawwa ai wallahi sai naga wajan ciwon inda ka yi maka aikin..... Karanta ka yi share 08164069385 *YI DOMIN ALLAH* *SARAUTA CHARITY FOUNDATION* Ciyar da marasa ƙarfi da almajirai lokacin azumi. Ta hanyar yin abinci, kunu, ƙosai da ruwan sha tun daga kan 200 zuwa sama na abinda Allah Ya a hure maka. *Saboda wasu dalilai da kuma yadda wasu suka nuna basa so, a daina saka sunan wanda ya bada kuɗi saboda sun yi ne domin Allah* Saura kwana biyu azumi har yanzu ba mu kai ga samun abinda muke so ba jama'a a taimaka. 1. Sa'idu Hafsat 1k 2. A'isha Gadanya 3k 3. Maman Khalid 1k 4. Someone 2k 5. Received from pos 1k 6. Fatima Kabir 500 7. Unknown 2k 8. Murtala Maimuna 500 9. Fauziyya Abdulsalam 500 10. Unknown 1000 11. Unknown 500 12. Unknown 500 13. Unknown 500 Total 14k 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank Ko kuma 8164069385 Na'ima Sulaiman Shu'aibu Opay Ku taimaka saboda Allah kuma ku yi sharing *MUNAFUKIN MIJI 35* Mikiya Writers Ass Bright pens free batch Nimcyluv sarauta *Ba zan ce na tafi hutu ba, ba zan ce ban tafi ba duk mai son jin ƙarin bayani ya duba ƙarshen page. Zan cigaba da posting iya wattpad da channel ɗina. Wanda suke buƙatar ci-gaba da karatu su yi following channel ɗin tawa, wanda baya buƙata shi ma yana iya joining bayan sallah ya karanta* Follow my WhatsApp channel👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T Sakin ƙafarsa ta yi ta fasa abinda ta yi niyya jin kanta ya sara da ƙarfi Ustaz ya kalleta kamar zai share sai ya ce "Sai dai fatan Allah ya bawa ƴar rainota lafiya, amma Ustaz tuni kin ci kai bayan tsaraicina da kika gani kina ƙarama yanzu kike son sake gani? Zunubi har haka Ustaza?" Ta tura baki taƙi cewa komai kanta a ƙasa maganganun Mami na mata yawo a kunne kamar yanzu take faɗa mata. "Abbiey wai zan iya zama matarka?" Ya ware idanu da kyau yana mai gyara zaman shi ya ce "Kuma injiwa?" "Haka na ji" girgiza kai ya yi yana sauke idanunsa a kanta a nutse ya ce "Kina son zama matar tawa ne?" Ta tura baki ta ce "Ni dai kawai na tambaya ne, kaga ni ai ba zan iya haɗa Idanu da kai ba idan ka zama mijina" "Jiki ma za ki haɗa dani soon Ustaza" "Ma ka ce Abbiey?" "Ke na ce mana" ta fara lumshe idanunta da suka fara yi mata laushi ga wani abu dake mata yawo saman fatarta. "Ni ban ji ba ka sake faɗa" ya miƙe daga kishingiɗan da yake zuwa zaune ya gyara da kyau hannunsa ya miƙa masa ya ce "Zo mu yi sirri" ta ɗauke kanta sai kuma ta runtse idanunta ta miƙe da ƙyar tana ƙoƙarin zama ƙasan carpet ɗin wajan ƙafafuwansa ya yi saurin tare ta, ta hanyar kama hannunta ya zaunar da ita a gefensa kafaɗarsu na gogar ta juna. "Wassh Abbiey jikinka ya jani" wuyanta ya bi da kallo da mamaki domin bai taɓa lura ba sai yanzu wasu yanka yanka ya gani kamar wacce aka saka reza aka tsatsaga mata fata ko aka karce ta, ta kasa kallonsa ya saka hannunsa masu taushi a saman haɓarta ya juyar da fuskarta ɗaya gefen wanda ya ƙone ga ɗan raguwar tabo nan ga wani karcewar ne. Ya saka yatsunsa biyu ya fara shafa wajan da son tantance mene. Ridayya kamar wata wuta haka take jin yatsun Ustaz jikinta ya fara rawa ɗakin ya shiga juya mata ga wani murɗawa da mararta ta yi ta kumburu nan ta nan ta fara fitar da numfashi. "Ya aka yi kika samu wannan ciwon Mimi?" Baki ta buɗe da nufin faɗa masa cewa Zameer tsohon mijinta ne silar komai shike shaƙe mata wuya a duk sanda suke tarayya. Nauyin Ustaz da girman shi da yadda kullum yake cika mata idanu da kwarjininsa yasa ba zata iya faɗa masa cewa mijinta na baya ke shaƙe mata wuya ba idan zai nutsu har suma take wani lokacin, ta yi ƙasa da kanta zuciyarta na bugawa. "Bana son tabo bana so ko kaɗan ina kika same su?" Ya faɗa yana juyo da fuskarta zuwa dab da tasa numfashinsa na sauka a kan tata fuskar. Kasa bashi amsa ta yi jikinta na rawa ta fashe da kuka tana kifa kanta a cinya tare da yarfe hannunta kuka take sosai ɗaya hannun tana riƙe mararta. Ta kasa daurewa da abinda take ji bata saba da wannan sabon yanayin ba ji ta yi akwai abinda take buƙata idan bata samu ba zata iya mutuwa. Ustaz ya zuba mata Idanu shi dai babu abinda ya yi mata ya miƙa hannu zai ɗago ta a firgice ta ce "Don Allah kar ka taɓa ni Abbiey ƙara mini azaba kake" Ya jinjina mata kai ya rasa mai ma zai ce bai ɗauka taɓarar Ridayya ta je har haka ba. Ya zame a hankali zuwa ƙasan carpet kansa daidai cinyarta a hankali ya ce "Ok meke miki ciwo? Jikin ne? Mu je asibiti" "Abbiey wallahi mutuwa zan yi na shiga uku, wani abu ke mini yawo a jiki marata ƙirjina wani iri Abbiey" Kuka take har da majina ta fita daga hayyacinta nan da nan kanta ya fara ciwo wani irin zazzabin ya fara rufe ta saboda abin yawa jininta girma ya fi ƙarfinta. Shi kansa Ustaz ya fara rikicewa bai kulata ba yama mance bashi da lafiya ya saka hannunsa duka biyun ya jawota zuwa ƙasa saman cinyoyinsa ta riƙe hannunsa da kyau jikinta kamar an jona mata wutar lantarki ga wata uwar zufa data gama wanke mata jiki. Addu'a ya fara yi mata yana ɗan buga kumatunta "Wifey, Little Mama, Angel buɗe Idanunki" Buɗe Idanunta ta yi ta zubawa fuskarsa Idanu musamman laɓɓansa ta saki wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta yi saurin rufe idanun "Ban san meke mini ciwo ba Abbiey ka taimaka mini ƙirjina marata, Abbiey ina son....," Idanunta da ya yi jajur yake kallo da kuma gargasar jikinta da suka mimmiƙe sai haɗe ƙafa take waje guda ya girgiza kai kawai ya jata jikinta kamar jira take ta yi saurin ƙanƙame shi tana jan numfashi jikinta ya yi zafi sosai. "Shhhh ya isa it's okay" Ta jinjina masa kai ta ce "Ka ƙara riƙe ni Abbiey wani abu ne yake mini yawo a jikina" "Bari na duba jikin mu gani, can i?" Kunya take ji amma gwara a duba mata kawai kar abin ya kasheta tana da sauran burika a rayuwarta. Ya ɗago ta ta dinga kallon bakinsa ya ɗage mata gira ya ce "Go on; fell free to ask Little Mama" Ta yi shiru ya mirgina ta ya fara ƙoƙarin zuge ziff ɗin zuwa ƙasa baƙar fatarta ta bayyana a fili fresh and natural skin ɗinta yake kallo sai kyalli yake daya taɓa fatar bayanta taushi da laushinta har tsoro ta bashi kamar ta yage bai ga komai a bayan ba ya ɗora hannunsa a saman bra zai yi unhooking ya ji an zabga salati. "Me zan gani ni ƴar nan? Wacce ƙaniyyar ce haka" Har lokacin hannun Ustaz yana wajan ya kasa ɗago kai ya kalli Umma kuma ya kasa ɗauke hannunsu, Ridayya kuma azaba ce ta yi mata yawa ta kasa tashi. "Bariki a lalan gero an saba da gidan miji daman yaushe za a jure? Har kika kawo kan ki tare da sakar wa ɗa namiji jiki uwar mai zai tsinta a jikin bazawara, sai baƙar fata da mugun baƙi kamar kwal za ki tashi ko sai na yi ciki dake kika kwanta kamar ruwa" Ustaz da idanunsa sukai wani irin sauya kala tun kafin Umma ta shigo ya ɗago ya kalli Umma cikin wata kalar murya ya ce "She is my wife Umma, kar ki yi haka bata da lafiya" Ta zabga salati ta ce "Muhammmmd ya na ji kana magana da ƙyar, to banga dama ba tunda kai baka san meke maka ciwo ba ga matar arziƙi zaka zauna ka ƙare a fanko" Ya yi mata shiru ya riƙo fuskar Ridayya data gama caɓewa da hawaye ya saka yatsunsa ya share mata hawayen tas wasu na sake sakkowa ya ce "Mu je asibiti?" "Uban uban uwar asibiti za ku" Ta saka hannu ta fisgo Ridayya ta tura ta waje ta ce "Li'ilafi kurash" "Kai kuma shanyaye kake son zama har ni zan dinga magana kana mini kunnen uwar shegu Babana?" "Wallahi ban ji me kike cewa ba" Ta dinga kallonsa ta ce "To tashi ka fito waje" ya yi shiru ta ce "Zaka tashi ko sai na zo na miƙar da kai? Ka daina ganinka wani gansameme mai shekaru 43 wallahi ganinka nake kamar yanzu na haifo ka" Yana daga zaune ya juya kama zai duba abu ya juya mata baya ya miƙe tsaye ba tare daya juyo ba ya shige bathroom yana dafe kansa. Ta saki baki tana binsa da kallo ta shiga uku kar fa ɗanta ɗaya tal ya zama bita zai-zai. Ta yi ƙwafa dole ta kawo karshen wannan auren. A gigice Ridayya ta fito daga part ɗin Ustaz idanunta rufe karo ta ci da abu warin taba ya daki hancinta cikinta ya hautsine ta shiga kwarawa amai a wajan kamar zata amayar da abinda yake cikinta ta tsani warin taɓa zata iya lissafa sanda ta taɓa jinta. "Kan uba!" Ya faɗa yana daka mata tsawa da sauri ta buɗe idanunta ganin Burhan tsaye a gabanta daga shi sai gajeren wando yana busa taba gabaɗaya ta wanke masa jiki da amai ta dinga kallonsa ta kasa magana ya ce "Ke wacce irin mahaukaciya ce za ki mini wannan abun a jiki? Kin manta waye ni ko?" "Ka ka yi haƙuri don...," Kafin ta ƙarasa ya saka hannu ya zabga mata mari wanda ya saka ta ƙara gigicewa kafin ta dawo hankalinta ya ƙara zabga mata wani marin wata ƙara da ihu ta fasa tana kifawa ƙasa daidai nan Mami ta ƙarasu wajan ta ɗago Ridayya dukda kasancewarta baƙa bai hana yatsun Burhan fitowa ba, duk kawaicin Mami sai da ta ji ranta ya ɓaci sosai domin ba zai kassara mata yarinyar da bata mori komai na rayuwa ba. "Burhan me ta yi maka da zafi haka?" Ya yi shiru yana bin Ridayya da kallo saboda yadda ta lafe jikin Mami tana kuka kamar ranta zai fita ga wani irin haushi Ustaz daya kamata yana kallo Umma ta ci mata mutunci gashi a ɗakin ta samu ciwon ya yi shiru. Mami ta kama Ridayya har zuwa ɗaki ta zaunar da ita ranta ɓace ta nufi inda Baffa yake domin ya shiga tsakani. Mardiyya na tsaya ta caɗa uwar kwalliya sai feshe jiki da turare take yau zata zama mace mai ƴanci ta fita daga layin ƴan'mata waya take yi tana cewa "Kamar yadda kika bani shawara ne, na siyo maganin na haɗa masa a juice, amma fa naga both gender ne maza da mata" Ta cikin wayar aka ce "Da za ki siyo wannan kema sha za ki yi ne?" Ta ce "A'a ya ce yafi aiki ne da wuri kuma yana da mugun ƙarfi yana iya yin kwana biyu jikin mutum yana aiki, kuma gabaɗaya na juye" Ta saki salati ta ce "Innalillahi kin kashe ɗan mutane wallahi kaɗan za ki saka fa shi ne kika juye duka zai iya yi masa illa fa" Mardiyya ta saki dariya tana duba gidan maganin ta ce "Kar ki damu yanzu zan je nasan idanunsa ya rufe ni kawai yake jira, ai Umma ta ce daman lafiyarsa ƙalau kiga dole na ja masa aji" sallama sukai ta yi dropping wayar saman mirror ta nufi banɗaki wanke baki. Tana shiga Ustaz ya shigo kai tsaye idanunsa ya sauka akan gidan maganin ya ɗauka ya dinga juyawa kenan shi ne dalilin kawo masa lemo? Kenan shi Ridayya ta sha? "Ya Allah!" Dole Ridayya ta gigice a ransa ya ji dole su yi wannan game ɗin 1-1 yaga lemon da take sha a saman stool ya zazzage mata raguwar ciki ya juya ya nufi bedroom ɗin Ridayya. Kwance ya sameta saman carpet tana ta birgima da kuka gefen fuskarta har ya kumbura ya ƙarasa ya ɗago ta zuwa tsaye ƙafafuwanta rawa suke sosai ta ce "Abbiey ka daina taɓa ni ka bar ni haka" ta faɗa tana shagwaɓe fuska "Ni ne maganin ciwonki Ustaza ki yi haƙuri bani da iko but i can help ki samu nutsuwa" Ya riƙo fuskarta shatin yatsu ya gani da mamaki ya ce "Waye? Waye da wannan aikin?" Tana kuka ta ce "Ba abinda na yi masa warin taba na ji shi ne na yi amai ya mare ni" "???" Alamar tambaya ya yi mata da hannu akan waye? Ta ce "Burhan" Bai ce komai ba amma tana ganin yadda jijiyoyin kansa suka fito bakiɗaya har wani huci yake futarwa ƙirjinsa na harbawa ganin bashi da lokacin magana baya kuma son gardama ya saka ya ɗauketa gabaɗaya zuwa bathroom ta tsayar da ita tsakiyar shower ya sakar mata ruwan sanyi wanda ya sauka har jikinsa. Ta yi saurin ɗauke kanta saboda wata kunya sosai daya kamata, shi da kansa MB USTAZ a tsorace yake domin bai taɓa ba, bai san ya ake yi ba bai taɓa kusanta kan shi da ko wacce ƴa'mace ba sai yanzu, ita kanta Ridayya sauyin data gani a idanunsa Abbiey ɗin nata ya bata tsoro ya damƙe hannunta ɗaya ɗaya hannunsa kuma ya riƙe ƙugunta mai faɗi. RIDAYYA bata san meke faruwa ba ta tsinci kanta da kallon cikin ƙwayar idanun MB USTAZ ɗin da kyau wani abu mai kama da feelings na tattaro mata wanda a kansa ne kawai take jin hakan. Ruwan ya ci gaba da sauka a jikinsu ba zai iya ganinta ba domin bai shirya ba, ganin kuma bashi da wani amfani a tare da shi, bai taɓa jin zafin sabuwar wannan ƙaddarar tashi ba sai yanzu, akwai lokacin da dole sai ta ɓukaci hakƙinta na aure musamman ita data riga ta saba ta san kan abun, yanzu na ya san alkuya kawai take da yadda bata ɗauke shi matsayin miji ba, da kuma yadda bata samu labarin auren nasu ba. Rashin lafiyarta ya taimaka wajan rashin fahimtar abinda yake mata a yanzu ba iya matsayin uba bane ya shige hakan. Ya rungumota jikinsa ya riƙe ta da kyau yana ji tana sauke ajjiyar zuciya ya ce "I am sorry Little Mama, ki yi mini uzuri" "Me ya sa ka ce ka tsane ni Abbiey idan baka so na waye zai so ni?" "Me kika sani game da so ko ƙi? Kin yi rayuwar aure dai kawai Ustaza ba tare da kin san mene auren ba, wahalarsa kawai kika sani am soon za ki san waye mijinki mene kuma aure da daɗin dake cikinsa. Ni ban yi mini al'ƙawarin babu ƙalubale ba domin ko harshe da haƙori ana saɓa wa kuma ko wanne aure ɗan haƙuri ne, ina da yaƙini za ki yi farinciki za ki samu freedom, soyayya, tattali, kulawa zan share miki takaicin da kika wanzu da shi zanja ragamar komai na rayuwarki" Ta kalli gefen fuskarsa ya mintsini kumatunta ya ce "ba gemuna za ki kalla ba cikin idanuna za ki kalla" "To me ya sa kake ce mini haka?" “I dreamt that you were mine, and then I woke up smiling because I realized it was not a dream. You are already mine!” Ta tura masa ba ta yi aune ba ta ji saukar bakinsa a gefen nata ya yi mata light kiss ya ce "Love you my dearest wife Mimina! ƴar lukutar Abbiey" Jikinta ya saki tana ganin zunzurutun iskanci yau yarr haka ta ji bata taɓa sanin akwai wani abu mai kama da haka ba nauyi da kunyar Ustaz ya kamata. Jin tana atishawa kuma yanayin ya ɗan sauka ya kashe shower ɗin ya jata gefe ya ce "Cire kayan kar sanyi ya kama ki" Fita ya yi a parlour ya same su Baffa yana ta faɗa Mami kuma har kuka ta yi Ustaz na zuwa yama mance jikinsa a jiƙe yake kai tsaye kan Burhan ya nufa lokacin ɗaya ya sauke masa lafiyayyun maruka biyar a gefe ɗaya gefen bakinsa ya fashe ya shaƙe masa wuya ya ce. "Na rabu da kai saboda babu ruwana da kai, amma yanzu ka shiga hurumina ka taɓa iyalina zaka san ka taɓa matar Muhammad-Bilal Tahir Rano, kuma daga kan ka babu wani zai yi gigin dukan Matata" Hannun Burhan ya kama ya ce "Bada wannan hannun ka mare ta ba? To daga yau ya tashi aiki" Lanƙwasa yatsun hannun ya yi suka bada sauti Burhan ya yi ƙara saboda jin yatsun sun karye Ammi ta ce "Wai mene haka akan ya mare ta zaka masa haka ba ita ce ta yi masa amai a jiki ba?" Ustaz ya kalli Ammi ya ce "Shhhh ban saka dake ba, akwai ranar da zan waiwaye ki kuma ko ke yanzu kika dakar mimi mata wallahi sai na watsa miki yatsuna a fuskarki, kuma ki shirya amsa duka tambayoyin da suke jiranki sonna or later, zalincin da kukai mata tun tana ƙarama bai isa ba ko? Waye bai zalunce taba a cikinku duk da kuke tsaye?" Baffa ya yi ƙasa da kai domin yasan wannan faɗan har shi. MB USTAZ ya murza hannu ya ce "Na yi shiru ne saboda ba ku ɗinne a gabana ba duka, amma yanzu duk wanda zai taɓa mini mata wallahi shari'a ce zata raba ni da shi for sure idan duk babu mai son ta ni kaɗai na ishe ta,ita ce ni; nine ita so stay away from my darling wife" Yana faɗin hakan ya juya zuwa part ɗinsa ransa a ɓace kwance yaga Mardiyya a kan gadonsa tana ta juyi tana ganinsa ta miƙe tsaye zata ƙarasa wajansa ya dakatar da ita da hannu "Don Allah ka taimaka mini ina buƙatarka" "Ba ki yarda bani da lafiya ba? Shi ya saka kika saka mini abu a lemo? Yanzu da kika saka mini mene ya same ni?" Za ta yi magana ya ce "Bana son na yi insulting naki in any way just leave my room" MB USTAZ ya nemi hutu wajan aiki suka koma Kano har lokacin Ridayya bata bari ta sake haɗuwa da shi ba, kunyarsa take ji da kansa deep down na zuciyarta tana tunanin Sadauki. Kwanan su biyu da komawa Anuty Kaltum ta zo ita da Yaya A'isha sun jima suna nusar da Ridayya kana Anuty Kaltum ta yi wa Ridayya wasu picture ta turawa wata ta WhatsApp tana gamawa ta yi voice ta ce "Yamara ga pictures ɗin nan don Allah ki haɗa kayan dana kawo ta a fara komai kafin Ramadan kun kammala na tura kuɗin komai, gyaran ciki da waje" Yamara yana nufin Hafsat a kanuri mazauna barno a Maiduguri. Kiran Yamara ɗinne ya shigo wayar Anuty Kaltum ta ɗaga ta saka handsfree ta ce "Ridayya ɗan jeki waje" "Ashe haka abu ya faru da ƴar wajan Botula? Ɗazo muke magana da Falmata fa" Anuty Kaltum ta ce "Wallahi shi ne dalilin daya saka na kira ki, aure ya mutu kuma an sake ɗaura wani kuma yarinyar tana buƙatar ilimin ɗa namiji da rayuwar gidan aure, infact she knows nothing about it kin gane me nake nufi?" "Ai kar ki damu Kaltum dole mijinta ya san ya auri jinin Kanuri kuma ya san daga wacce jiha dangin uwarta suke, domin ita kanta bata san cewa Dada kakarta asalinta ƴar Barno bace ba hala?" "Alamu sun nuna haka, ai babu wanda ya taɓa zama ya faɗa mata Dada Ƴar Barno bace a can kakanninmu na wajan uwa suke a can aka haifi babar Dada itama Dada acan aka haifeta ita kuma ta haife mu a Kano ƙaddara kowa da kalar tasa zanen jarrabawar" Yamara ta ce "Kar ki ji komai zata zama mutum zata dawo new Ridayya in sha Allah kin san komai ba sai na miki bayani ba, babu buka ba malam kawai dai mijinta ne abinda tausayi kuma ayi mana afuwa domin sai mun wana shi sai kuma ji a jikinsa" Sai duk jikin Anuty Kaltum ya yi sanyi domin an faɗa mata matsalar Ustaz da halin da yake ciki, kawai Ridayya za ta yi sacrifice farincikinta da ƙuruciyarta just to be with him da kuma abinda ya yi mata na alheri, kinga an saka alheri da alheri a inda ya dace ga matsalar uwar miji sai gorin baƙar fata take mata da muni wai kuma ita bazawara ce" Yamara ta saki dariya sosai ta ce "Kan uba ji wani zunubi za ta yi wa kanta domin wallahi soon zai fara bijire mata, wake tsayawa tunani idan zai faɗa soyayya ita take ganinta a bazawara amma shi kallon yarinya budurwa yake ba, so na gaskiya baya buƙatar dalili ko hujjar yinsa, idan don haka yake son ta to tabbas kawo yanzu daya daina amma ya fasa? Wallahi ta kiyaye zuciyar data kamo da matsananciyar soyayyar mace domin ta fi komai illa kuma bazawara za taga aikin zawarawa" Anuty Kaltum ta sauke ajjiyar zuciya Mami ta yi kamar bata san me ake cewa ba, domin daman ita magana bai wani dame ta ba Yaya A'isha ce take ta dariya ita kaɗai. "Ke dai Allah ya kyau don ma na bugi cikin yarinyar data haifi Little an yi mata ɗinki ita fa empty head ce a ɓangaren soyayya da zama da miji karatu na musamman nake so ki yi mata idan mun zo Barno" Sun jima suna tattaunawa sukai sallama Yaya A'isha ta ce "Wallahi ina jin tausayin Ustaz wannan a corner zaku saka shi" "Bari uwarsa ta ja masa wallahi kwana nan zai zama Munafukin miji akan Ridayya don wallahi zai ta share masa wannan tuzuruntakar tashi zai yi alfahari da ita" Kafin su tafi Anuty Kaltum ta je ta samu MB USTAZ a part ɗinsa na gidan domin tuni ya tsara yadda yake so a yi masa ginin gidansa Mardiyya tana nan tare da shi Ridayya kuma ta gudu wajan Mami yana zaune saman kujera ya kame nutsuwarsa da ilhmarsa ta bayyana bayan ya gaishe ta, ta numfasa ta ce "Alfarma nake nema za mu ke je a nuna matarka a dangi tunda ba a santa ba" "Ina?" Ya ce a taƙaice ta ce "Nan cikin garin Kano mana" Ya dinga mamaki bayan su daya sani Mami na da wasu dangin kenan Jin ya yi shiru ta ce "A bamu permission ba riƙe maka mata za mu yi ba" Ya duba agogo ya ce "Ok kar ta yi dare" "Wanne dare kuma ai kwana za ta yi wata guda ma za ta yi ai dangin da yawa wasu basu taɓa ganinta ba, to kafin ayi bikin muke buƙatar su ganta basai an kai musu katin bikin ƴar wajan Fatima ba su ga ba a kyauta musu ba" Ya miƙe tsaye yana gyara zama babbar rigarsa idan ka kalli Ustaz zaka ɗauka yana da tarin zuri'a saboda tunaninsa da kamalarsa da kuma tsare gira banda tsantsar kishin tafiyar babu abinda take gani a idanunsa. "Wannan cutarwa ne ai haramun kuke son aikatawa" "Subuhanallahi haramun kuma?" "A'a kifa daina salati kamar ba ki gane ba, yanzu don Allah ya General zai ji ki tafi ki barshi har wata guda?" Anuty Kaltum bata taɓa tunanin ya san sunan mijin nata ba sai yanzu furr ya sakawa idanunsa toka yaƙi yarda. "Wannan mijin na Ridayya akwai taurin kai da miskilancin tsiya kinga yadda yake mitsi-mitsi da Idanu wai idan ni ce zan tafi wata guda ya General zai ji kamar wanda ya san daɗin mace" Murmushi kawai Mami ta yi ta ce "Babban mutum kenan zai aikata" Washegari ya shirya tsaf cikin wagambari mai tsadar gaske zai je meeting ɗin da aka yi inviting nasa na Madugu daga nan sai ƙarasa police station. Fuskarsa fau tana wani yellow saje da ƙasumbarsa sai kyalli suke da sheƙi suke ya yi wani irin kyau ya rusuna ya ce "Abba Umma barka da safiya" "Barka Babban mutum an fito?" Ya jinjina kai Umma taƙi amsawa "Sai ina?" "Zan ɗauki Ustaza za mu ɗan je wani waje" "Bada yawo na ba, idan har nono na kasha wallahi babu inda zaka fita da ita" Ustaz ya kalleta ya ce "Asibiti za mu ga? Hakƙina ne kula da matata idan ba Ubangiji kike so ya yi fushi dani ba, wallahi Umma ba kyau shiga tsakanin ma'aurata" "Ni kake faɗawa haka? Ina faɗa kana mini bita tare da ɗora mini hadda? To wallahi sai ka sake ta a yanzu maza ka sauwaƙe mata" Baba ƙarami ya tashi ya ce "Hadiza ban hanaki kar ki tursasa Babban mutum wajan sakin matarsa ba, amma ki sani sai dai ku yi zawarci tare da Ridayya yana sakinta zan ɗora miki naki saki ukun, kuma zan buɗe idanu na zaɓo kyakkawa budurwa dal na aure ki daina ganina da furfura kyakkawa ne ni domin a waje na Muhammmmd ya kwashi rabin kyau, wallahi da gudu za a fara rububina zan auri budurwa mu sha soyayya, idan wacce zata ƙwace ni har abada ne sai na nemo ƴar Maiguduri, idan ilimi nake so na nemo ƴar Abuja idan wayewa ne na ɗauki ƴar kaduna, idan soyayyar ce ƴar Kano,idan biyayya ne Zamfara idan kishi ne Sokoto ko Katsina don haka ki bi a hankali, wallahi wallahi Allah kika saka ya saki Ridayya sai na sake ki kuma na auri budurwa sai ki zaɓa zawarci tare da surukarki ko haƙura da ƙaddarar Ubangiji" Baki Umma ta saka Baba ƙarami ya ce "Jeka Allah ya tsare Babban mutum" MB USTAZ ya sauke numfashi ya nufi ɓangaren Mami lokacin suna zaune a parlour Zainura sai ƙoƙarin haɗa breakfast take ya shigo ta ce "Yaya Bilal good morning?" Bai kalleta ba bai amsa ya nufi wajan Mami yana durƙusawa ya ce "Barka da safiya Mami" "Barka Babban mutum ka wayi gari lafiya?" "Cikin aminci Mami" kunyar surukai duk ta kamata shi kam ko a jikinsa ya juya yana miƙewa ya ce "Ustaza bata shirya ba?" "Tab ai dai ka je ka taso, da alama ka sangartata da baccin safe tun ɗazo nake abu ɗaya" MB USTAZ ya zaro idanu yana duba agogo ta nuna masa direction ɗin bedroom ɗin ya tura yana yin sallama underneath his breath. A kanta idanunsa ya sauka tana tsaye gaban wardrobe tana ƙoƙarin maƙale bra ɗinta bata ji sallamar ba balle ta ji zuwan shi, sai saukar lips ɗinsa ta ji a tsakiyar bayanta da laɓɓansa masu sanyi ta yi saurin sakin rigar tana juyawa a tsorace bakinta na rawa ta ce "Abbiey" ya yi saurin ɗora yatsarsa a bakin "Why Ustaza? Ni kike gudu" ta yi narai narai da Idanu ya sunkuya ya ɗauki rigar ya juyar da ita ya saka mata yana ɓalle ɓallin ta ce "Ba kyau fa Abbiey" idanunsa duk wani ya kala ya ce "Mene babu kyau?" Ta ce "Ganin jikina da gaske ba kyau haramun ne" A taƙaice ya ce "Bari na yi abinda yake mai kyau kuma halal" zillawa ta yi ya girgiza kai ya nufi waje ya zauna yana danna wayarsa shiryawa ta yi cikin brown colour ɗin Abaya mai ɗan faɗi ta saka igiya ta ɗaure ta yi rolling kanta ta saka pech ɗin lipstick ta yi fresh da kyau a hankali ta dawo ta tsuguna ƙasa ta miƙa masa hannu ya ajjiye wayar ya miƙa mata nasa hannun sukai musabaha ta ce "Good morning Abbiey" "Kin tashi lafiya?" Ta ce "Lafiya lou, ya jiki?" "Uhm bakin ki ne jikin zan gwada miki ƙalau nake" Ta kasa kallonsa ya ɗagota ya ce "Zo mu yi special gaisuwa" a kan ciyarsa ya ɗora ta ya juyo da ita ya sunbaci goshinta da kumatunta a hankali ya ce "Allah ya yi miki Albarka Ridherh" Ta yi ƙasa da kanta ya ce "Ki faɗawa wannan masifaffiyar Anutyn taki ta zo ta ɗauke ki ku je unguwar za ki bani address wata ɗaya ya yi yawa, daga nan zamu je asibiti idan mun dawo za a yi bikina da matata" "Wanne asibitin?" "Za ki gani ne, sati biyu za mu a asibitin bana son a sani fa appointment nake jira na asibitin" "To wa za a kai?" Da yatsa ya danna ƙirjinta tsakiya ya ce "Mijin Ustaza" "To bikin naka Mardiyya ce matarka?" Ya ɗage mata kira sai ta shagwaɓe fuska ta fara kuka wiwi "Wallahi ka nemo wata matar ni bana son ta ka zauna kawai babu aure" Ta dinga kuka tana yarfe hannu tana diddire ƙafa ƙugunta sai rawa ya zubawa ƙugun idanu sai kawai ya miƙe. Da ƙyar ta yi shiru a parlour ya ɗauki Little Bilal daman tuni ta daina bashi nono police station suka fara zuwa Ustaz ya cike komai. Ridayya na zaune ɗauke da Little taga mutum tsaye ta yi baƙi da duhu ta ji an ce "Mai sona?" A razane ta ɗago kai jin muryar da ba zata taɓa mantawa da ita ba a rayuwarta sukai Idanu huɗu da Zameer a gigice yake kallonta ganin kamar ba ita ba, ya ji duk wahalar daya sha a rufe ta kau ya ji wani abu da bai taɓa ji ba yana motsa masa a zuciya wani abu mai kama da zahirin so sadidan na gaskiya ya tsirga masa Ridayyan daya ce ta tashi daga aiki yaga kamar yau ya fara ganinta babu alamar ta yi aure ba balle a san da zaman Little ta yi ƙiba ta zama ƴar lukuta ya dinga kallonta zuciyarsa kamar zata ratso ta ƙirjinsa. Ridayya ta yi saurin ɗauke kai da sauri ya nufe ta BM USTAZ ya tare shi "Yawwa matata mai sona ke nake ta jira lovely mu koma gidanmu ga ɗanmu ya yi wayo" gabanta ya faɗi kar dai Abbiey mayar da ita zai yi? Officer ya ce "Hajiya kin shi? Wannan mijinki ne?" Ridayya ta haɗe rai ta ce "Gaskiya ban taɓa ganinsa ba sai yau bani da haɗi da shi" Gaban Zameer ya faɗi muryarta na rawa ya zube gaban Ridayya kamar zai yi mata sujjada bai taɓa jin abinda ya taɓa jin irinsa ba "Wallahi ke matata ta ce ga ɗana nan wajanta, ni ba ruwana da filayen ma matata kawai nake so" Officer ya ce "Hajiya kin ji?" "Ban san shi ba, officer kaga wannan?" Ta nuna Ustaz dake zaune yana danna waya ta ce "Shi ne mijina kuma ɗana bashi da alaƙa da wannan mutumin ka duba kamannin ɗana ka duba na mijina Ustaz kaga ana zaka tantance ɗan waye, ku amsar mini takarduna ku sake shi kawai" Tana faɗin hakan ta ɗauki Little ta bawa BM USTAZ ya amsa ya miƙe a hankali ya ce "Officer let him go" Suka saki Zameer a gigice ya bi bayan motar su BM USTAZ amma ina bai gansu ba kuma bai san wanne gida suka sauya ba. Anuty Kaltum ta shirya kayan Ridayya cif sai a lokacin Mami take faɗa mata kuɗin da BM USTAZ ɗin ya tura ta Accout ɗin Ridayya na tafiyar wai ta yi tsaraba sosai Anuty Kaltum ta yi mamaki ta ce "To Allah ya ƙara arziƙi da wadata ya bashi lafiya" "Ridayya je ki yi masa sallama mu tafi ko?" "Ai ba sai na yi masa sallama ba Anuty" Watsa mata harara Anuty Kaltum ta yi ta ce "Ji wawta za ki tashi ko sai na ci ubanki?" Ta miƙe da sauri ta nufi ɓangaren Ustaz lokacin Mardiyya na parlour ta ce "Ɗiyarmu da kin tsaya yanzu na taya shi yin wanka yana shiryawa ne" Ridayya ta kalli Mardiyya zuciyarta na yi mata wani irin zafi sosai ta ce "Na san wanka ya yi ai mun yi vedio call da shi har yake nuna mini wajan ciwon shi yanzu na wajan zan gani, karki damu uwata ai Abbiey nawa ne ba wani sirri tsakanina da shi" Tana faɗin hakan ta buɗe ta shiga ta fashe da kuka a kwace yake tsakiyar gadonsa daga shi sai boxer ko riga babu sai farar fatarsa dake ta ɗaukan idanu ya juya ya kalleta ta tura masa baki taƙi kallonsa tana kuka ta ce "Anuty ta ce na zo na yi maka sallama zamu tafi" Sai ta sake rushewa da kuka idan ta tuna abinda Mardiyya ta ce ya dinga kallonta ya ɗauke kai ya ce "Miƙo mini wayata can" ya nuna mata saman stool ta ɗauki wayar ta miƙa masa wayar ya amsa ya cafke hannunta tare da fusgota saman gadon ya mirgina ta koma ƙasan shi fuskarsa a saman tata ya ce "Ni kikewa tsiwa haka ake sallama da miji?" Cikin rashin fahimta ta ce "Miji kuma?" Ya share ya ce "Ni bari na sallame ki my crazy darling wife" Baki ta buɗe za ta yi magana ta ji saukar nasa cikin nata ya saka hannu ya kashe hasken bedroom ɗin...... *ALLAHAMDULILLAH* Ubangiji ya sanya muna ɗaya daga cikin wata zasu lazumci wannan wata, yadda za mu ga farko Allah ya sa muga ƙarshe lafiya. Ubangiji ka yafe mana zunubanmu ya sa mu yi karɓaɓɓe. Bana son labarin ya kai ni bayan sallah wannan dalili ya saka lokaci zuwa lokaci zan dinga posting a channel da wattpad wanda ya karanta yana iya zuwa group ya yi comment ko prvt ko ta can wattpad. A daure a yi sharing domin kowa yaga sanarwar🌚🥰ONE LOVE HABIBATIES. *YI DOMIN ALLAH* *SARAUTA CHARITY FOUNDATION* Ciyar da marasa ƙarfi da almajirai lokacin azumi. Ta hanyar yin abinci, kunu, ƙosai da ruwan sha tun daga kan 200 zuwa sama na abinda Allah Ya a hure maka. *Saboda wasu dalilai da kuma yadda wasu suka nuna basa so, a daina saka sunan wanda ya bada kuɗi saboda sun yi ne domin Allah* Saura kwana biyu azumi har yanzu ba mu kai ga samun abinda muke so ba jama'a a taimaka. 1. Sa'idu Hafsat 1k 2. A'isha Gadanya 3k 3. Maman Khalid 1k 4. Someone 2k 5. Received from pos 1k 6. Fatima Kabir 500 7. Unknown 2k 8. Murtala Maimuna 500 9. Fauziyya Abdulsalam 500 10. Unknown 1000 11. Unknown 500 12. Unknown 500 13. Unknown 500 14. Unknown 2k 15. Unknown 500 16. Unknown 3k 17. Unknown 1k 18. Unknown 1k 19. Unknown 4k 20. Unknown 1k 21. Unknown 1k 22. Unknown 500 Total 28k 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank Ko kuma 8164069385 Na'ima Sulaiman Shu'aibu Opay Ku taimaka saboda Allah kuma ku yi sharing *RAMADAN FEEDING* Sarauta Charity Foundation. Re-post and support. Share saboda Allah THE LAST DAY. KA SANYA KO BIYAR NE ALBARKACIN WANNAN WATAN YA ZAME MAKA MAFARKIN BUƊIN AYYUKANKA NA ALHERI A WANNAN WATAN. CIYAR DA WANDA BASHI DA SHI WANNAN SHI NE ABIN FARIN CIKI. KA YI SHARING SABODA WANNAN WATAN SABODA ALLAH *MUNAFUKIN MIJI 36* Mikiya Writers Ass Bright pens free batch Nimcyluv “coward” ya ce yana ɗage mata gira da kashe Idanu ganin yadda jikinta ke rawa kamar ba a taɓa ya yi mata abinda ya yi yanzu ba, he just gave a little light kiss. Amma ya lura jikinta sai rawa da ɓari yake ta rufe Idanu kamar bata taɓa jin abu makamancin wannan ba. Ya dungure mata kai ya ce "Lazy wife, buɗe idanun" Ridayya ta kasa saboda da wani dake masa yawo saman jikinta yana kai mata saƙo na musamman da ban kuma. Wanda a duniyarta bata san da shi ba, hatta babban yatsarta rawa yake wai Little? Abinda ya yi mata ya fi ƙarfin a kira shi da haka yin duniya Ustaz ya yi ta buɗe idanunta amma taƙi sai wasu hawaye da bata san na menene ba suka fara bin gefen hawayenta. "Kuka Ustaza? To shikenan a fasa tafiyar" Ta yi saurin girgiza masa kai tana ci-gaba da shassheƙar kuka na rashin dalili abinda ya yi mata ya tsaya mata curr a zuciya. Ya ɗagota zuwa gefensa tare da riƙe hannayenta duka biyun ɗayan ya tallafo haɓarta yana zubawa fuskarta Idanu da gajiyayyun idanunsa a hankali ya ce. "Kukan fa? Na mene?" "Why Abbiey?" Ya juya Idanu yana ƙara mutuwa da kyau gudun kar ƴar mitsitsiyyar yarinya ta birkita masa lissafi. Dukda ya gane sai ya basar ya ce "Me?" "You ki....," Sai ta yi shiru tana shagwaɓe fuska still taƙi kallonsa kamar yadda yake son nutsa ganinsa cikin ƙwayar idanunta da son gano ai nahin abinda ta ji game da hakan. "Uhm za ki me dalili" "Me ka ce?" Ya matse hannunta dake cikin nasa tare da yin ƙasa da bakinsa daidai kunnenta numfashinsa na sauka ya ce. “Play the role of my wife and be my children's mom Mimi” Ta yi shiru sai duk ya damu da shirun nata, kuma a ɗabi'ance hakan ya yi mace mai alkunya a kamata kuma hakan damuwa ce a gare shi, ko ABBIEY ɗin zata ce yana son jin muryarta. Da ita ɗinne kawai ƙofar zuciyarsa ke buɗewa yake jingina da ita ya yi hirar daya jima bai yi da ita, shi kawai yana son ta kama hannunsa ta ja shi zuwa rayuwarta da kanta, samun damar haka zai bashi ƙarfin qwiwar share dukkan wani damuwa da baƙin cikin data wanzu da shi tsayin shekaru, zai bata cikakkiyar dama a matsayinta na matarsa, zai share mata hawayen data daɗe tana zubar wa. Babban rainonsa yadda zuciyarsa taƙi masa adalci wajan buɗewa ta faɗa mata ainahin menene SO da ƘAUNA da kuma bambancin da suke tattare da shi game da BIRGEWA so yake ya samu damar da zai faɗa mata dukkan abinda yake ji a zuciyarsa game da ita, sai dai ƙaddarar shi kenan zurfin ciki kuma a kan abinda ya fi so da bawa muhimmacin ya fi ganewa ya yi komai a zahiran ce ko za a fi fahimtar yaran nashi. "Can you? Za ki iya?" Ya maimaita a hankali ta buɗe idanunta ta kalli gefen fuskarsa ya riƙo ta ya ce "Ƙwayar idanuna za ki kalla" Ta girgiza kai. "Ok fine an fasa zuwa ko'ina ma" "Ka yi haƙuri Abbiey ban iya ganin Idanunka" ta faɗa a kasalance wani abu na yunƙuro mata. "Za ki iya Ustaza nutsu" Ya riƙe kafaɗunta duka biyun yana gyara zaman shi a gadon daya gama cukurkuɗa shi da ita. Ya matsa gare ta sukai kusa da juna speaking calmly ya ce "Rufe idonki" Ta yi yadda ya ce "Ja numfashi" Nan ma ta yi ya ce "Ok breath out" a hankali ta sauke numfashi zata buɗe idanun ya ce. "Noo, wait a moment ɗan jira" Ustaz ya jima yana kallon fuskarta ƴar jaririyarsa yau ta girma har ta haifi Bilal, wanda da Allah ya ƙaddara a ɗan shi zai zo, lallai wani baya haifar wani rabo kuma ajali. Idan rabo ya rantse sai a rabo da juna a je wajan wani a haifa masa, Ubangiji ya sanya yana da rabon samun zuri'a da Ridha. "Buɗe Idanunki, kai tsaye ki kalle ni Ustaza" ya ce yana riƙe fuskarta da duka tafukan hannunsa. Kamar mai shirin ganin sabuwar halitta haka ta buɗe idanunta wanda kai tsaye suka samu gurbin sauka a cikin idanun Ustaz, wani abu ta ji ya tsarga mata a zuciya wanda ya sanya halittar ƙirjinta buɗewa da kyau tana fahimtar wani abu na musamman, wasu launi idanun Ustaz ke dasu, wanda ta kasa tantance ko na mene a karo na farko da take son ganin jallabiyya a jikinsa domin taga kamar ma ya fi kyau da ita, kallon ido cikin ido suke Ridayya ta dinga gani kamar ba Abbiey ɗinta ba, ya sauya ya ɗan birkice ya kuma rame sai nutsuwa da kamala haɗi da daddakonsa suna nan. “Love is not by meeting eyes but by uniting hearts Ridherh, ki nutsu ki cire ƙuruciyar nan you are no longer a child, ke ɗin Oum-Bilal ce, haba jaririyata ya kike so na yi?" "Me zan yi Abbiey" "Be my wife" Runtse idanunta ta yi sosai lokacin data tuna kalaman Zameer sanda ya ce yana son ta zama matarsa ta har abada sai dai mutuwa ta raba, ya yi mata al'ƙawarin hakan, Had all his promises been nothing but lies. Datse bottom lip ɗinta ta yi bata san ya fashe ba sai da ta ji taushin yatsarsa ƴar manuniyya yana goge mata jinin dake fitowa. "What about me? If i ware to ask you to marry me, what would you say?" Ustaz ya yi shiru yana binta da idanu zuciyarsa na bugawa da ƙarfi amma bai bari rauninsa ya bayyana ba sam. Ya kasa ce mata komai. Ta girgiza mai hawayenta na sake yawa muryarta na rawa ta ce "What if i don't want you to love me? Abbiey....," Yatsarsa ya ɗora a lips ɗinsa alamar ya isa ya kasa maganar. Kukan Ridayya ya tsananta ta ce "Kallon mahaukaciya ake mini, na yi mamaki daya kasance har da kai amai yi mini wannan kallon. Wallahi ina da hankali Abbiey ni ba mahaukaciya ba ce, kuma Umma ta yi maka zaɓan da ya fi ni ta baka budurwa fara kyakkawa, bana jin aure Abbiey ko zan yi aure Sadauki ne zaɓina Abbiey ka yi mini uzuri please" Ta kasa ƙarasa maganar saboda kuka ta ɗora kanta a cinyarsa kuka take mai cin rai, duk wanda ya ce bata fahimtar shirun Ustaz, da kallonsa ko tarinsa ko maganarsa ya yi ƙarya, sam Abbiey bai dace da ita ba yadda ya ƙare rayuwarsa haka yana da kyau ya samu kyakkyawar mata budurwa mai budurci, ba ita data watsar da nata tun a gabansa ba, tun kafin ta yi aure ba, ba ita data aikata zina ba. Wannan dalilin ya sanya take masa fatan samun macen data fita komai na rayuwa, Sadauki ya sota ne a yadda take ya kuma san ta yi aure ta haihuwa ko gaskiya ce ta bayyana ba zai ji zafi da baƙin cikin da Ustaz zai ji ba, shi ne ya bata rayuwa, ya kula da maraicinta dukda tana da Iyaye a raye ya bata tarbiyya daidai gwargwado tsakani da Allah amma ta saka ƙafa ta shure hakan ruɗin shaiɗan da uƙubar gidan uba, da mugun fata na Burhan da tsangwamar jama'ar gari ya sanya ta ji barin gidan shi ne mafita a gare ta, ta yi believing idan Zameer ya bar ta ba zata taɓa samun mijin aure ba ta yanke hukuncin bashi abinda ya buƙata tunda ta yi imani idan ta yi hakan zai zama miji a gare ta, mai share mata hawaye sai dai kash! Aka yi rashin sa a ashe MUNAFUKIN MIJI ta aura. Ranar data bawa Zameer kanta ya dawo sabo a tunanin a hankali shuɗaɗɗun abubuwa suka dinga maimaita kansu a idanunta da zuciyarta dama kwakwalwarta suka zama sabbi a gare ta. "Shhhh ya isa" Muryarsa bata ma fita har yanzu sunan Sadauki ne a kansa zaune. Ya ɗagota yana murmushi ya ce "To maganar ta shige ok? Bana son mu yi irin wannan sallamar" Ta jinjina masa kai wayarta ta fara ringing ganin sunan Anuty Kaltum ya saka Ustaz ɗaga kiran ya yi shiru. "Wai uwar me kika tsaya yi ne daga zuwa sallama?" "Hakƙin mijinta ta tsaya saukewa" Ƙitt Anuty Kaltum ta kashe wayar Ridayya ta zaro Idanu ya haɗe fuskarsa yana goga mata hanci a hankali ya sunbaci goshinta ya ce "Blessing women" Ya sauka daga kan bed ɗin ta bisa da kallo wallahi ƙato ne shi bata taɓa ganin girmansa ba sai yau, abinda ya fi ɗaukar hankalinta farar fatarsa ga suma luf luf kuma daga shi sai boxer. "Abbiey ciwon ya warke ne kake saka ɗan mitsitsin wandon nan?" Ya juya ya kalle ta ba yabo ba fassala sai ya ɗauke kansa ya share kamar ba zai magana saboda ya ja lokaci ta ji ya ce. "Maybe ke yake jira, do you like it?" Ta ɗauke kai da sauri sai kuma ta sakko ta fara gyara masa bed ɗin bai kulata ba ya buɗe drawer ya ɗauki wasu abubuwa kana ya rufe. Yana tsaye har ta gama gyara masa gadon ta saita komai tunda ta saba bayan ta gama ya ce "Jazakhilla bil khair Jaririyata, Allah ya yi miki albarka" Kanta a ƙasa ta ce "Amin. Abbiey na bar Little a wajanka" "Shi wai ba a shirya yi masa ƙanne bane?" Ta yi murmushi kawai ta nufi waje ya bi bayanta suka jera a tare. Zaune suka samu Mardiyya da sauri ta goge hawayenta tas amma idanunta ya yi jajur har ya kumbura domin ta laɓe ta ji komai hankalinta ya tashi sosai wani irin son mijinta da kishinsa ne suka dinga damunta. Ta fara yarda Ustaz bashi da lafiya idan hakan ya tabbata akwai matsala amma dole ta sake gwada shi domin gano gaskiya. "Kaga ƴar Abbiey ɗinta kun fito?" Ridayya ta share ta yi kamar bata ji ba, Ustaz ya san mene hakƙin iyali baya son Ubangiji ya kama shi da wannan laifin ya fahimci Diyya da kyau a kame ya ce "Lafiya? Akwai damuwa?" "Babu kawai bacci nake ji ne ina jiran kuma mu yi sallama da Ridayya" Ridayya yunƙurin tafiya ta yi Ustaz ya yi mata wani kallo da sauri ta tsaya jikinta na rawa. Mardiyya ta fara ƙoƙarin haɗa jikinta dana Ustaz sai suka ji Ridayya ta fasa ihu ta zube tana riƙe ƙafarta hakan yasa da sauri Ustaz ya matsa daga kusa da Mardiyya ya ɗan rikice da tambayar Ridayya lafiya mene meke mata ciwo wani abu ne? "Abbiey ƙafana ya maƙale ba zan iya tafiya ba ka ɗauke ni" Kuka take sosai hankali kuma tashe take riƙe ƙafar Mardiyya ta tsaya kamar statue. Ustaz ya ɗauki Ridayya cak ya nufi main parlour da ita. Tun daga nesa Umma ta fara salati tana "me zan gani ni Hadiza wai ɓatan nono a ƙirjin budurwa" Hankalin Ustaz baya jikinsa balle ya fahimta kukan Ridayya kawai yake ji, Umma ta yi saurin shan gabansa ta ce "Sauke ta almura munafuka uwar ƴan iya mitsitsiyya dake kin iya kissa daman zawarawan nan haka suke da nacin miji" Ustaz ya kalli Umma ta ce "Yanzu zaka fara Allah ya yafe mini ko? Ka zama shanyaye na mace nan gaba ɗan Daudu zaka zama kama maƙale hannu da kashe murya duk a sanadinta sauketa ka juya" "Bana gane komai Umma ki mini uzuri Ustaza ba lafiya" "Ta mutu mana? Idan ta mutu ni na mutu" Da wani tashin hankali ya kalleta ya ce "Gwara ni na mutu Umma" Yana faɗin hakan ya yi gaba tana kwaɗa masa kira ya share. Baba ƙarami murmushi kawai yake yana mamakin Hajiya Hadiza da bata san mene mayen so ba. Anuty Kaltum ta dariya domin taga komai a ranta ta ce "Za kiga aikin bazawara soon domin ba kiga komai ba sai Ridayya ta ke Maiduguri ta dawo ganin ɗanki sai ya gagare ki tunda kina jayaya da hukuncin Ubangiji" Suna nufar hanyar harabar gidan Ridayya ta yi saurin cewa "Sauke ni" da mamaki Ustaz ya kalleta ganin ta zame ta sauka tare da tsayawa a kan ƙafafuwanta ya dinga binta da Idanu ya kasa furta komai. Anuty Kaltum ta ƙarasu wajan ta ce "Mu je ko ana ta jiran mu" Ridayya ta ɗan ji ba daɗi ta juya ta kalli Ustaz shi kam ya share ya yi kamar bai gani ba "Abbiey zan tafi" Ta faɗa idanunta yana cika da hawaye ya juya yana riƙe kansa da yanayinsa da kyau a ɗan kame kamar koyaushe murya a taushashe ya ce "Mene na kuka?" "To za ka zo ne? Zaka kira ni a waya?" "To ki haƙura mana Ustaza" Ta girgiza masa kai ya ɗan matsa kusa da ita ya ce "ki kula da kan ki, ki girmama kowa banda raini banda surutu da maza, be careful" Ta jinjina kai ya shafa kanta ya ce "Allah ya yi miki Albarka, Little fa?" "Wajan Mami zai zauna" ya sauke numfashi yana ta kallonta taƙi yarda ta kalle shi sai ya sake ta ya ce "Take care of yourself Ustaza" "To Babban mutum za mu shige mu duk ka cinye mana lokacin" Bai kalli Anuty Kaltum ba ya miƙa mata robar hannunsa ya ce "Duk dare ta sha, ki kula da ita please" Yana faɗin hakan ya juya zuwa cikin gidan su kuma suka shiga mota zuwa wacce zata kai su Maiduguri driver ɗin sai mita yake musu. Ridayya bata saba tafiya haka ba tun tana ware idanunta na kallon hanya har bacci ya ɗauke ta. Anuty Kaltum tana ƙara jinjina girman so da ƙaunar da Ustaz ya kewa Ridayya ta ɗauki niyyar ko komai nata zai ƙare a wannan karan za ta yi zumunci aiki Ridayya zata share masa damuwarsa zata zame masa irin matar da yake so, bazawara zata ɗauke masa dukkan buƙatunsa koma zata saka Umma ta dawo cikin hayyacinsu ta fahimci zawarawa suma mata ne. Balle irin Ridayya sauta ga wawa? Sanda Ridayya ta farka ta samu Anuty Kaltum na waya da General yadda ta ji ana musayar kalaman soyayya ya bata Maman ƙwarai da gaske, har take ganin wannan rashin kunya ce ta yi zuru tana kallonta. Ridayya ta yi mamakin ganin ƴan'uwan kakarta wacce ta haifi Mami wato Dada kusan ita ce ta ɗauki yalwar suma irin nasu, asalin kanuri cikakkun mazauna garin Maiguduri yawanci sun saka lafaya ga wani irin kitso a kansu gwanin sha'awa kowa ka ganni akwai zanen lalle a ƙafarsa so ma sha Allah. Dangi aka yi ca ana ganin cikar Dada ta wajan Fatima Batula aka sauke su da shatara ta arziƙi tun a lokacin Yamara ta fara fito da kayan gyara tsofaffin ajjiya aka haƙa rami aka fito da wasu itatuwa da tsumammun turarruka aka wanke ramin tsugo tas. Tun a daren data bawa Ridayya wani magani tasha wani irin ruwa ya dinga fita daga jikin Ridayya mai yauƙi yauƙi kwana ta yi ba tai bacci ba sai sauya zani take. Kwananta biyu tana shan maganin sanda aka zo gyaran fata har kuka ta yi saboda azaba sai ta ji kamar fatar jikinta zata kwailaye kafin ka ce baƙar fata da dawo wani special colour na musamman ita ba za a ce baƙa ba, kuma ba za a ce chocolate ba. Idan ta hau ramin tsugo kowa ba a magana sai jikinta ya gaya mata, ta ji ta matse da kyau kamar ba ita ba, ko sanda aka yi mata wannan ɗinkin na haihuwar Little bata ji ba domin tunani take anya zata iya fitsari? Bayan ta yi turare sai a haɗa ruwa a babban baho mai ɗauke da kaya kala-kala ace ta zauna ciki sai ta yi awa guda, idan dare ya yi sai a bata na shafawa kala biyu dana fata da wanda zata shafa a gabanta. Yamara da kanta ta haɗa mata mai na amfani iya fuska mai ɗauke da aloe vera da honey da ƙwai cikin sati guda jikin Ridayya ya dinga wani glowing duk inda ta zauna kuma sai ta bar alama ko waje ya jiƙe ga wani mafifaffen ƙamshi daya zauna a jininta na musamman. Aka dawo kai kullum sumar sai an wake da karkashi da wasu tarkace ashe duk tsayin gashin ba iya haka yake ba, daman gashi da laushi sai ya zamana ko kalba akai baya zama ware wa yake. Ridayya duk da gyaran ne a gabanta ba yadda Yamara ke yi mata wani karatun ne bata ganewa idan ta faɗi wata maganar sai Ridayya ta runtse idanunta sannan ta sake fahimtar lallai akwai wani abu da take ji game da Ustaz, ga tsoran kasancewarta bazawara ga babban zunubin data aikata idan ta tuna wannan sai ta share domin har lokacin bata san Ustaz mijinta bane, a ranta take jin abinda yake mata ya shige misali kuma babu kyau ba zata bari hakan ta kasance ba. Ga wani baƙin cikin Mardiyya da take ji idan ya tuna ta sai ta ji gabaɗaya haushin Ustaz ɗin ya kamata. Satin ta biyu tana zaune kamar sabuwar halitta hannunta riƙe da tsumi tana ta kwaɓe fuska kira ya shigo wayarta ta dinga bin number da kallo tunaninta Ustaz ne tunda har yanzu bai neme ta ba. Ta ɗaga wayar ta kara a kunne muryarta a kasalance ta ce "Hello" Ajjiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya ce "So is true" Gabanta ya faɗi jin muryar Sadauki a hankali ta ce "Sadauki" "Why Ridayya? Why why kashe ni kike son yi ko so da gaske kin yi blocked number na?" "Kamarya" A raunace ya ce "Kamar yadda na faɗa miki Shanshan sau nawa zan kira number ki baya tafiya, na shiga damuwa da tashin hankali gashi ban san gidanku ba, yin duniya Tajj ya faɗa mini yaƙi wallahi na kusa mutuwa a kan yanzu haka drip ne a hannnuna Shanshan" Kamar zai yi mata kuka yadda yake marairaice murya can ƙasa "Ayya sannu ya jikin me ya same ka" "You are the reason behind anything, kin guje wa ganina, na rasa kallonki da muryarki da jikin nan naki mai ƙara sawa na ji babu wata mace a duniya sai ke, Ridayya Allah ne shaida ina tsananin son ki" "Uhm be patient Sahibi" "Where are you zan zo na ganki" Ta ce "Kai da baka da lafiya?" "Zan iya, idan na ganki zan warke daman rashin ki n Shanshan" "Ka bari ka ji sauƙi mana" Sadauki ya zare ruwan hannunsa yana miƙewa daga cinyar mother data gama cin kuka sosai ya ce "Uhm just tell me kina ina? I'll be there for you" "Maiguduri" Ya zare idanu sai kuma ya ɗan yi baya ya zauna, yana dafe kansa dake matuƙar sara masa ya jima kana ya sauke numfashi ya ce "Yaushe kika je, when za ki dawo kuma?" Tana ɗan kallon Anuty Kaltum ta ce "Sati na biyu sai na yi wata a can, idan na dawo zan faɗa maka" tun kafin ta ƙarasa maganar Sadauki yake girgiza kai ya ce "I can't wait any longer Shannn, ba zan iya zaman jira ba ki bani address zan zo na ganki mu tsayar da magana" "Please mana ka bari ka ji sauƙi" Sadauki ya nace sosai ta ce "Shikenan to ko na faɗa maka ka zo ba zan fito ba" "Shikenan Allah ya dawo mini dake lafiya, but promise me kina dawo za a tsayar da maganar auren mu already na faɗawa Prof da Mother" "Na yi" Ya sauke numfashi mai ƙarfi yana ƙanƙame wayar ya ce "Thank you Shannn shaaa. Zanna kiran ki ok ki kula" "Tom" “I love you” "Thank you" Ya sake cewa "I love you" ta ce "Thank you" “I LOVE YOU JAANN” Cikin jan aji ta ce "Really appreciate Sahibi" “Mu'ahh💋" Ya sakar mata ta cikin wayar tsigar jikinta ya tashi ta yi saurin kashe wayar tana lumshe idanunta tare da ƙanƙame wayar a ƙirjinta, ta jima a haka sai kuma ta ɗauki wayar ta kira number Ustaz da aka saka Abbieyna ana ɗagawa ta fara jin ruwan ashar kwando kwando kuma muryar Umma ce. "Haihuwar tsiya mai raba ɗa da uwarsa Allah ya fiki kuma ke da shi har abada sai dai ki hange inuwarsa in sha Allah, bazawarar kawai baƙa gayyar muni ai kin yi kaɗan ɗana ya dinga wahala a kan ki mai baƙin jini wacce ta rasa mijin aure mijin nata ya kure ta....," Da sauri ta kashe wayar Anuty Kaltum kuma ta ji komai Ridayya ta fashe da kuka ta ce "Na shiga uku wallahi Giɗaɗo ba kura ta ya yi ba, ni ce na ce ya sake ni bana son zama dashi, don Allah Umma kar ki raba ni da Abbiey zan jure komai banda haka ni ban masa asiri ba ban san yaya ake yi ba" Kuka take kamar ranta zai fita babu abinda ta tsana irin a ce ta rasa miji bata so, ta tsani gorin aure ko da sigar wasa ne sai ta yi mai isarta Anuty Kaltum ta bata ruwa ta sha kana ta ce "Mene damuwar don an rabaki da Ustaz?" Da mamaki Ridayya ke kallon Anuty Kaltum "Yi ta kallona ba yanzu kuke waya da wani ba har yake miki kiss kina tunanin idan kika aure shi zai jure ganinki da Ustaz ne? Duk da muharraminki ke amma ai akwai aure tsakaninki da shi, idan bakya son rasa Ustaz so be with him, a yanzu ne yake buƙatarki bari na faɗa miki abinda baki sani ba Ridayya. Ai kin tuna sanda ya faɗi a Lagos ko?" Bata amsa ba kallon Anuty Kaltum take kawai ta ɗora da "To tsautsayi ya saka Ustaz ya faɗa saman dutse ina nufin mararsa ta sauka akan dutse har aka yi masa aiki a mararsa, abinda ba ki sani ba ake ɓoye miki Ustaz ba zai taɓa haihuwa ba, kuma ba zai iya tarayya da mace ba a duniya saboda ya nakasa kinga kenan babu yadda za a yi ya samu macen da zata zauna da shi tsakani da Allah sai dan kuɗinsa, tunda da shi za fankon ashana duka ɗaya suke. Idan ke baki amshe shi ba waye zai amshe shi? Ki yi amfani da damarki kafin ta ƙwace miki, kina ji kina gani ganinsa zai yi miki wahala kina yawan ƙaryata abinda zuciyarka ke ƙoƙarin bayyanawa amma ba za ki iya ba, domin soyayya gaskiya ce yanzu ya rage naki ki rungumi Ustaz da ƙaddararsa ki taya shi share hawayen idanunta kamar yadda ya yi miki sanda kike neman mataimaki, soyayya bata ɓangare ɗaya bace kuma ƙarfe ɗaya baya amo!" Tashi ta yi ta bar mata wajan cike da takaicin Ridayya da uwar Ustaz Umma kenan. Ridayya ta dinga juya maganganun Anuty Kaltum a kanta. *** Tun bayan tafiyar Ridayya Umma ta saka Ustaz a gaba da masifa a kan ya saki Ridayya tun kafin ta dawo idan kuma har ta isa fa kenan. Ta ƙwace wayoyinsa gabaɗaya kamar yaro komai ta ce biyayya yake mata amma yana cikin azaba ya san ko yanzu ya faɗi ya mutu Umma ce sila a wannan lokacin ba Ridayya ba. Mardiyya aka samu abin yi Umma ta ƙara tabbatar mata Ustaz lafiya yake ta yi ƙoƙari su fahimci juna kafin mayyar ta dawo ta suɗe masa kurwa ko kunyar Baffa da Mami bata ji. Ustaz ya samu meeting da Madugu kai tsaye Magudu da secretary na Jam'iyya suka faɗawa Ustaz ƙudirinsu na son tsayar da shi ɗan takara a matsayin gwamna a ƙarƙashin jam'iyyarsu. A nan take ya nuna he is not interested siyasa ba ita ce a gabansa secretary ya fara lallaɓa shi meeting ɗin ya ƙare babu daɗi amma Madugu ya kafa na ci. Alhji Mansur da Alhji Tahir suka tsayar da biki wata uku masu zuwa ya yi daidai da kammala ginin Ustaz na gidansa Mami ta shiga shirye-shirye ita da su Yaya A'isha. Ammi ana ta ɓangaren tana ta haɗa plan B ɗinta ita da Burhan ba wanda ya san me take yi. _Only God knows!_ Ga Anuty Zuhura mijinta ya sake halin ta yi ya ji ta dawo gida. Ustaz ne durƙushe gaban Umma hannunta riƙe da farar takarda da biro ta ce "Muhammmmd" Ya ɗago kai ya kalleta ya kasa magana ta ce "Well is allowed ai kana ji, idan ni ce uwarka na yi cikinka na kuma na raini cikin tsayin wata tara, na yi nishin naƙudarka na shayar da kai nono na shekara biyu ciff wata ashirin da huɗu to ka gaggauta rubatawa Ridayya sakinta a wannan takardar idan ba haka ba wallahi wallahi sai na ɗaga maka nono kuma na yi maka Allah.....," Jikinsa na rawa ya amshi paper ɗin gumi na yanko masa all over himself idanunsa ya jirkice ya ce "A'a kar ki mini Allah ya isa zan yi yadda kike so" Rubutu ta fara a takardar yana gani dishi-dishi ya gama ya ninke sosai ya miƙewa Umma duk abinda yake faruwa Baba ƙarami yana kallo shigowarsa kenan cikin gidan. Umma ta yi murmushi ta rangaɗa buɗa ta ce "Allahamdulillah yadda yarinyar nan ta baka wahala albarkacin Annabi sai ta wahala a kan ka, ai daman na san ba za ka ƙi yi mini biyayya ba yanzu ka rungumi matarka baka da mace sama da Mardiyya" Ustaz tunda ya miƙe tsaye jiri ya fara ɗaukar shi idanunsa baya buɗewa, yana jin idan har ya samu zarafin fita to ƙasar zai bari gabaɗaya kuma sarai ya san inda Ridayya take domin Zainura ta faɗa masa, ya ji a ransa ba zai ƙara kwana a gidan ba, ba zai ƙara kwana ɗaya a kano ba kuma ba zai sake yin sati guda a Nigeria ba. Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yana riƙe jikinsa a haka ya nufi hanyar waje Umma ta ce "Maza jeka sha iskar ƴan'ci ka dawo wajan matarka Allah ya yi maka albarka ba dai biyayya ba" Ustaz ya juya ya kalli Umma sai ya ce "Ki yi haƙuri na yi miki abinda kike so wanda ya sanya zuciyata cikin ladama da fargaba ba kuma zan taɓa yafe wa kai na, tunda kika saka na saki Ridayyerh ni ma ba za ki sake ganina ba" Yana faɗin haka ya fice yabar gidan gabaɗaya kai tsaye da niyyar zuwa Maiguduri ya fita daga gidan. More comment more update RAMADAN MUBARAK *MUNAFUKIN MIJI 37* Mikiya Writers Ass... Bright pens free batch Nimcyluv Bayan ya fita daga gidan bai samu zarafin shiga motarsa ba, texci ya shiga zuwa tasha suna tafe Idanun Ustaz rufe zuciyarsa na bugawa da matsanancin ƙarfi. A hankali a fili cikin sautin da shi kaɗai zai iya ji ya furta. “Ridha, you are my choice, always. Even if fate brings me a fated mate, my heart will remain yours” Ya sauke numfashi yana jin komai na fice masa a rai,hukuncin da Umma ta saka ya yanke daidai yake da tsaiwar numfashinsa wanda hakan ke nufin rayuwarsa na dab da zuwa ƙarshe. Love is nothing but a destiny; dole kowa ya yarda soyayya ƙaddarar ko wanne mai rai mai zuciya ne a ƙirji. Ƙaramar wayarsa ya ji tana ringing ya kasa motsawa balle ya duba yaga waye? Kawai ƙasar yake son bari amma komai nasa yana gida bai san ya zai yi ba, ya koma ne ko ya tafi haka? Wayar ya zaro ganin Baba ƙarami ya saka cikin nutsuwa da ladabi ya ɗauki kiran, yana mai yin shiru tare da sauraren abinda Baba ƙarami yake cewa can ya nisa ya ce . “Huh! In sha Allah” "Turn the car driver" Cikin sauri driver ɗin ya juya lokaci zuwa lokaci yana juyawa tare da kallon Ustaz ganin yadda fuskarsa ta yi jajur har wani ruɗi-ruɗi take gabaɗaya jijiyoyin kansa sun tashi. Yanayin shi bai bari an gane ya yake ciki ba zafin ransa dai a bayyane yake. Umma ta miƙe tsaye tana juya farar takardar dake naɗe a hannuna ta ce "Allahamdulillah! Allah abin godiya sai yau zan yi cikakken bacci tun bayan auren ƙaddarar nan bana runtsawa da kyau. Yadda ka yi shekaru har 43 ba zaka ƙare rayuwarka a bazawara ba, ina son ka yi aure na ƴanci ka bawa zuciyarka da gangan jikinka abinda ko wanne namiji yake buri, buƙata, da kwaɗayin samu. Yaro gabaɗaya ya gantalar da rayuwarsa akan bautawa yarinyar da bata son ciwonsa ba, bata san damuwarsa ba, sai da ruwa ya ƙare wa ɗan'kada za a ƙallaga masa ita banda ƙaddara da naci da kuma maitar soyayya wallahi Babban mutum ya fi ƙarfin auren Ridayya ta ko wacce siga" Ta faɗa rai ɓace fuskarta kuma na bayyana tsantsar farincikin da take ciki. Baba ƙarami ya ƙarasa shiga ciki jikinsa duka a sanyaye tunanin makomar Muhammmmd kawai yake domin Allah ne shaida yana yi wa Ridayya son da shi kansa bai sani ba tun yana rufewa da murfin zuciyarsa har murfin ya gaza ɗaukan girman al'amarin rauninsa a kan ta ya fid da kan shi. "Kin yi farincikin?" "Kamarya?" Baba ƙaramin ya zauna ba wasa a fuskarsa ya ce "E, you have to tunda kin yi abinda kike so yana da kyau ki zuba ruwa a ƙasa ki sha ko kuma ki kunna kiɗa ki taka rawa, kin saka an saki ƴar ƙanina kin mayar da ita bazawara" "Wannan shi ake kira ga fara sa banga ƙaho ba, bazawara ta nawa kuma? Ba a zawarcin aka maƙala masa ita ba? Sanda take budurwa wane a cikinku ya yi tunanin haɗa auren su? Sai yanzu ta yi aure ta sha baƙar wahala miji ya ci ubanta son ran shi ta haihu ya gama kwashe albarka da ni'imar jikinta sannan kuka tuna da Muhammmmd ko? Uhm ni da bana ƙwai na sai da zakara kuma wallahi Babban mutum ya zama kwankwason jimina mai wuyar shafawa, ya ma ƴarku nisa" "Ni kike zagi Hadiza?" "Ni? Yaushe?" Umma ta ce tana gwalo Idanu. "Ridayya bata da uban daya shige ni, kamar yadda Muhammad-Bilal ba shi da uban daya shige ni Alhji Tahir Rano. Kin yi playing role ɗinki da kyau amma ki sani Ridayya ba za ta yi zawarci ita kaɗai ba, dole ne su yi tare da surukarta idan kuma ta samu miji ta bar ki a titi mafi mushkila" "Me kake nufi Alhji Tahir?" "Ina nufin abinda kika ji Hajiya Hadiza. Bani takardar domin nasan saki nawa zan iya miki" Tana karkaɗa ƙafa ta miƙa masa cukurkuɗaɗɗiyar takardar dukda ƙasan zuciyarta fargaba ce fal ita kam ina takama tsofe-tsofe da ita da yin wani zawarci?. Baba ƙarami ya buɗe paper ɗin a hankali ya fara dubawa gumi na yanko masa all over himself bai taɓa zato ko tunanin hakan ba, bai taɓa kawowa a ransa Ustaz zai yi saurin saduda ba har haka, girman abin da yake karantawa tamkar zunubi ne a wajan shi hakan ya saka Baba ƙarami rufe paper ɗin ya yi shiru na wani lokaci yana jan numfashi. A wannan karan cikin muryar rauni ya kira Umma ya ce. "Me kika ɗauki bazawara ne?" "Ni ban ce na ɗauketa wani abu ba, amma yana da kyau ko wanne saurayi ya auri budurwa don Allah ka yi mini adalci" Sai ta fashe da kuka sosai ta ce "Ni da kai na faɗa maka Babban mutum yana son Ridayya, ka ce mini taya na sani, ka sani ni uwa ce a cikina ya fara rayuwa kafin ya zo duniya dole zai fi kowa sanin waye Ustaz halinsa da ɗabi'unsa duk uwar da zata ce bata halin ɗanta ba wallahi ƙarya ne, idan yaranka goma ka san halin kowa, i told you abaya kan ka yi wani abu, tun kafin alaƙar su biyu ta yi zurfi but you refused ka ƙi ka share, shikenan bashi da aiki sai ƙarar da lokacinka a kanta, wayyo ta ce yanzu zai yi zumbur, sanda ta fara girma ba shi da nutsuwa tunaninsa kar shukar da ya yi wani ya zo ya girme kar ginin daya jima yana yi wani ya rusa, shikenan zarya from Lagos to Kano daga Kano sai Lagos saboda Ridayya, ya ƙarar da ƙuruciyarsa samartakarsa duk saboda farincikinta. A karo na biyu na zo maka da maganar ka gagauta haɗa auren domin yarinyar ta sauya, na san komai fa har irin wulaƙancin da ta yi masa da dalilin ciwonka, da rashin lafiyar da ya yi aka kawo mana shi kamar gawa daga Lagos, amma ba ku ɗauki hukuncin komai yana gani ya sadaukar da soyayyarsa saboda ita shi kuma ya wahala sai yanzu da komai ya ƙare mata za a haɗa su aure? Wallahi muddin ina numfashi ba zan bari ba, dole ta wahala kamar yadda ta wahalar da shi, Ridayya ita ta saka mini tsanarta da kanta ban jin kuma akwai dalilin da zai saka na yi accepting nata as my daughter-in-law" "Ke kuma a matsayin ki na uwa kina son kashe ɗanki da kan ki ne, kuma duk ranar da hakan ta faru ba zan yarda ba wallahi Allah" gabaɗaya ransa ya gama ɓaci dole ya fito mata a mutum ganin yana mata shiru zata ɗauki kamar bashi da ƙarfin qwiwar yin magana da tsawatar da ita ne. Ya gyara zama cikin dakakkiyar muryar ya ce "Akwai bambancin na abinda idanunmu ya nuna mana da abinda zuciyarmu ke zargi akai, ba a yi wa ƴa mace gaggawa cikin rayuwarta da tarbiyyarta, haka ba a yi wa ɗa namiji katsalandan a cikin rayuwarsa musamman irin Muhammmmd. Na fiki sanin yana son Ridayya na share shi ne tunda yana ganin hakan shi ne daidai, kuma babu inda zurfin ciki yake da magani ko mafita, yasan mene daidai shi tunda ya ja bakinsa ya yi shiru hakan yana nufin wani abu. Harkullum mu iyaye nutsuwa da fahimtar yaranmu shi ne abinda ya fi dacewa a gare mu, ba wai mu yi musu kutse ba, Allah da kansa ya ce yara amana ce a gare mu kuma kiwo ne, zai tambayi yadda muka kula da wannan kiwon idan mun koma gare shi. Ki faɗa mini wani abu mana Hajiya Hadiza, Ridayya ta ce aure take so kamar yadda kika ce, ya ce zai aureta ta ce a'a tana da wanda take so, me kike so Ustaz ya yi ko kuma ni na yi? Saboda ya kula da ita sai ya tursasata yin abinda ba ta yi niyya ba? Ko kuma ta yi masa halacci na abinda ya yi mata? Shi abin alheri ana yi ne domin Allah kuma masoyin gaskiya shi ne zai sadaukar da nasa farincikin domin wanda yake ƙauna ya yi farin ciki. Ba kisan komai ba game da so tunda kina kwaila na je garinku aka bani ke, ni na kula dake na nuna miki mene so har kike jin idan bani ba za ki iya rayuwa ba, ki saka a ranki tarihi ne zai maimaita kansa" "Ok gori za ka mini kenan? Amma ita Ridayya ɗin ai ta san halacci ko?" "Wanda ya faɗa soyayya mai zafi ko jarrabawa ta saka ya faɗa soyayya baya buƙatar neman dalili ko hujja, wanda yake so ɗin nan shi ne kawai a gabansa, da idanun zuciyata. Duk abinda ya faru dalili biyu ne ƘADDARA kamar yadda zanenta ya bayyana ƙarara a rayuwar yarinya da bata ji ba, bata gani ba, idan soyayya kike so mai zafi da sanin masoyin gaskiya da faɗa akan masoyi na bin abinda zuciya ke so, ki je ki karanta littafin *DIYAANA*. Zurfin cikin Ustaz ya ja masa rasa Ridayya da son nuna mata ikon uba, ita kuma ƙaddarar data faɗa na ƙiyayyar uba da damuwa na aibata halittarta ya saka ta faɗa tarkon MUNAFUKIN MIJI, a lokacin ba soyayyar ce a gabanta ba yadda zata bar gidan mahaifinta ta rayuwa inda babu duka, ba zagi ba tsangwama shi ne fatanta, ƙaddara kuma ta raba ta da mijin ta kuma sake dawo da ita hannun Ustaz" Baba ƙarami ya nuna Umma da yatsa ya ce "Wallahi wallahi idan kika ce za ki ja-in-ja da wannan ƙaddarar to ranki zata ɗauka, ki sani Babban mutum ya yi nisan da ba zai ji kiran ki ba yanzu a shirye yake ya yi faɗa a kan abinda yake so, kuma ganinsa zai miki wahala zai miki abinda za ki yi kuka da kan ki I'm telling you ba a yi wa ɗan yau haka musamman akan soyayya a wannan gaɓar kurame suke zama" "Yanzu dai saki nawa ya yi mata Allah ya sa ukunne kawai" "Ba matsalarki bane wannan tunda kin saka ya yi sakin ya kuma bar miki gidan shikenan" Ransa ɓace ya bar parlourn ya rasa meke damun matar tasa bai santa haka ba bai kuma san yaushe ta lalace ba. Sashin baya ya nufa inda bai fiya zuwa ba, daga nan kuma akwai ƙofar dake kai mutum kai tsaye zuwa bedroom ɗin Ustaz ba tare da kowa ya sani ba, tun kafin ya ƙarasa ya kira Tajj ya ce yana buƙatar ganinsa Allah ya sa kuma yana gari. Tsaye ya samu Ustaz ya yi shiru idanunsa buɗe kansa kuma a ƙasa ya kalle shi na wani lokaci kana ya nemi waje ya zauna ya ce "Muhammad-Bilal Tahir Rano dawo nan" Kamar baya son ɗaga ƙafarsa haka ya jata ya zauna ƙasa wajan ƙafafuwan Baba ƙarami wani hucin zafi ke fita ta cikin bakinsa da hanci. "Babban mutum me ya sa ka yi haka? Kar ka bani kunya har ka sare da wur wuri ashe daman soyayyar tatsuniya kake ma shalalen ko?" "I have no idea father, bana shiga shiga fushin uwa" "Kuma saki ba kyau, halak ne amma Allah baya son shi. Babu zunubi ko kaɗan a aurenku babu abinda ƴar'uwarka ta yi maka, a zahirance ma bata san matsayinka wajanta ba" Ustaz ya yi shiru Baba ƙarami ya ce "Do something Abokina ɗaya tal, ka yi abinda zai bawa kowa mamaki ni dai ba zan ce ka rabu da Mardiyya ba domin tana da hakƙi akan ka, haka ba zan lamunci abinda ka yi ba" A hankali ya jinjina kai don baya jin zai iya magana rauninsa gab yake da gama bayyana. "Ina zaka?" "Bana son zaman nan, zan je wani waje daban idan akwai alheri tsakanina da Ustaz tabbatas Ubangiji ya ba zai bar mu haka ba" "In sha Allah. Ka je ka ɗauki abinda ya dace Tajj yana waje zai yi dropping naka, nasan ba zaka iya driving ba" Part ɗinsa ya shiga ta bayan ya ɗauki atms ɗinsa files ducoments da abubuwan da zai iya buƙata ya haɗa kaya cikin luxury trolley ya nufi waje. A tsaye ya samu Tajj shi da Zainu yana ta tsokanarta tana tura baki. "Tab Yaya Ridayya ɗin ce ta fini kyau, ana ta cewa ni kyakkawa ce" Tajj ya buɗe ido ya ce "Subuhanallahi amma masu faɗa tsoran Zainura suke, ai colour ɗinku sun yi yawa gari da society namu yanzu baƙar kala ake ya yi" "Tamɗijam! Kawai ka fi son Yaya Ridayya kai da Yaya Ustaz" "Yes we love her, saboda she is a durlin.....," Wani irin kallo Ustaz ya yi wa Tajj fuskarsa ta haɗe ta yi jajur Zainura ta ce "Ina yini Yaya Ustaz" Wata tsawa ya daka mata ita da Little dake hannunta suka firgita nan da nan Ustaz ya rikiɗe kamar ba shi ne fara'ar sisi babu a fuskarsa kamar an yi masa mutuwa. "Mu je na sauke ka" Ya yi masa banza ya buɗe bayan mota ya saka kayansa ciki ya nufi ƙofar motar. "Ya ina ta magana ka yi shiru, ka bani key ɗin ko ka shiga motata ban fito da securities ba" "Ka tsahirta mini kafin na watsa maka yatsu" "Ikon Allah me na yi kuma ni ka zo ka yi wa yarinyar tsawa har yaro yana ihu ka zo kana mini faɗa? Daga zuwa aikin lada" Tajj ya ƙwace key ɗin ya juya yana buɗewa MB USTAZ motar, kamar ba zai shiga sai kuma ya shiga ya yi wa motar key. Tajj shi kaɗai yake maganarsa Ustaz ji yake kamar ya yi bindiga a haka suka ƙarasa airport sai a lokacin ya juya ya kalli Tajj shi kuma ya ɗaga masa gira ya ce "Dole haka za a yi fa" Hankalin Umma kwance tunda ta san aure dai babu shi ta zaunar da Mardiyya ta yi mata bita da zarar Ustaz ya sauka daga fushi ya dawo ta yi duk iyakar yinta wajan ganin sun samu daidaito kafin ƴar mayun ta dawo. Har sama da sati kuma babu alamar BM USTAZ numbers ɗinsa duka a kashe suke. Umma ta share tasan dole duk inda yake zai dawo ya sameta ne for sure. Mami na zaune da yammacin ranar ita da Yaya A'isha da suke magana ta ce "Ina jin tsoro Yaya A'isha Ridayya har yanzu babu kulawar uwa a tare da ita, bata san ya kamata ba, ta rasa abubuwa da dama" "Me kike tsoro ne Fatima?". "Aurenta da Ustaz bata san komai akai ba yana da kyau ta sani, gashi Umma bata ƙaunar Ridayya ko kaɗan ga Mardiyya ta fi Ridayya buɗewar ido wayo da ilimi da sanin kan duniya ina tsoro Ustaz ya rabu da Ridayya ina tsoran wannan ranar" Yaya A'isha ta yi murmushi irin na manya ta ce "Bari na fara da magana mai muhimmanci ki daina mafarkin Ustaz zai rabu da Ridayya, su ɗin tamkar ruwa da iska ne, kamar Inuwa haka suke, haka kamar rayuwa da mutuwa haka su duka biyun suke, ƙaddararka zane suke dana juna. Ridayya matar so ce, Mardiyya haɗin Hajiya ne a kuma rashin Ridayya aka bashi Mardiyya, auren Mardiyya da Ustaz kamar auren cin amana ne ta yi shi wa kika taɓa gani ya ci amana kuma ya zauna lafiya? Ilimi kuma Ridayya za ta yi shi, za kuma ta waye ke kan ki zata ba ki mamaki musamman ta zama her Excellency" "Her Excellency kuma?" "Uhm ai abin duniya baya ɓuya tuni zance ya zaga ana son tsayar da BM USTAZ takarar gwamna" Mami ta ce "Ikon Allah" Yaya A'isha ta ɗauki waya tana buɗe furnitures ɗin da dukai order na gidan Ridayya ta ce "Ai da ruwan ciki ake jan na rijiya, abinda ya taɓa hanci dole ido ya yi kuka idan ta yi yunƙurin raba Ustaz da Ridayya to ɗanta zata rasa, ƙoƙari ɗaya za mu yi mu fahimtar da Ridayya Ustaz fa ba ubanta bane mijinta ne, idan har tana masa kallon uba to kunya ce zata shiga tsakani ta zama hijabi namiji kuma baya son kunya a zaman aure, balle kuma wannan Babban mutum ɗin daka gani ɗan Soyayya ne kuma za ku ce na faɗa" "Kai Anuty shi da yake Ustazu malami" "Zainura get out, sai nawa zan ce idan manya na magana ki daina saka baki ne?" Miƙewa ta yi ta fice. Yaya A'isha ta ce "Wannan ƴar autar taki ta cika kanzagi, da alama kuma kamar kin haɗiyi wake" "Rufa mini asiri Yaya, Ridayya na haihuwa ni na haihu ai da kunya" "To za mu gani ai ɗan duma ne dole zai bayyana kansa, wannan karan maga haukan da kishiyarki za ta yi" Murmushi kawai Mami ta yi suka ci-gaba da duba furnitures ɗin da sauran kayan da za su yi Ridayya da kayan sawa komai da komai daga ɓangaren dangin uwa. Bayan sun gama ta fito raka Yaya A'isha suka tarar da yaya Zuhura zaune tana rusar kuka kamar ranta zai fita Ammi sai masifa take mata ganin su Mami ya saka ta yi shiru cikin sakin fuska da yaƙe ta ce "Hajiya A'isha kin fito ashe sannu da zaman ɗaki" "Yawwa sannunki da zaman gadi ana shan A.c" Yaya A'isha ta faɗa tana dariya tare da mayar wa da Ammi raddin maganarta. Murmushi ta yi ta ce "Ke kuma tashi wai fa surukar ta ce babu lafiya shi ne take wannan kukan kamar ni na mutu, ke kam an yi sakarar wofi" "Allah sarki idan da kima uwar miji ai uwa ce" Yaya A'isha na faɗin hakan ta shige abinta Mami daman bata ce ƙala ba wayarta kawai take dannawa gabaɗaya nutsuwar Mami Ridayya ta ɗauke ta ciff ba abinda ta manta bata ɗauka ba a wannan ɓangaren. Suna barin wajan Ammi ta ce "Wallahi tallahi sai kin koma gidan mijinki magana ɗaya ki dako ya ji ki dawo gida so kike a samu abin magana a kai na kenan ko? Ko Ridayya data auri miji mara kirki bata taɓa yin yaki ba sai ke da kikai auren soyayya miji na gaban kwatance, to Allah kar ya nuna mini ranar da zanga ƴata na zawarci" "Haba Ammi ni kaɗai nasan wahalar da nake sha ba, tun yana waya da ƴan mata a ɓoye har ya zamana baya jin tsorona, baya bani abinci yanzu haka dukana ya yi a gaban ƴaƴana kuma ya ce na bar masa gidansa ni kuma kamar mayya sai na zauna don Allah?" "Ai wallahi sai kin koma tun kafin kowa ya ji ni zan zo na samu mijin naki gantalalle shi ma" Bata bar Yaya Zuhura ta zauna ba ta mayar da ita da masifa da komai. Koda Ammi ta ce gidan Yaya Zuhura ta iske mijin ya zage yana nanawa Yaya Zuhura wuƙa a wuya gabaɗaya ya ƙona mata wuya da wuƙa nan take abinda ta yi wa Ridayya ta faɗo mata ta hau masifa da bala'i. Ya kalli Ammi ya juya mata baya tare da cewa "Na ki rududu wannan faɗan ba zai mini ba, ƴarki ce bana so bana ƙauna a yanzu" "Ashe baka da mutunci ɗan wahala ne kai gayyar tsiya? Ashe ɗan kwalta ne kai?" Ya ce "Yanzu zan yanka miki rashin mutunci wallahi ki ɗauki yarƙi ku bar mini gida immediately" A gigice Ammi ta riƙe hannun Yaya Zuhura ta ce "Ɗan'tadda ne ashe mijin naki na san maganinsa da Burhan zan haɗa shi wallahi" banda kuka babu abinda Yaya Zuhura take kuma ya hana ta ɗauki yaro ko ɗaya har wacce take shan nono ya kwance ta. Sadauki ya samu relief daga nauyin da zuciyarsu ke yi masa dalilin wayar da suke yi da Ridayya ta tabbatar tana dawowa z a yi maganar komai a shige wajan. Yanzu ma yana cikin mota yana driving bluetooth maƙale a kunnensa farin yadi ne a jikinsa mai laushi ya ɗora hula kasancewar yau juma'a ya je masallaci juma'a daga nan ya leƙa wajan aiki yanzu kuma ya ɗakko hanyar gida. Ya lumshe idanunsa da suke zube a kan titi cikin kasala ya ce "Allah Shanshan sai na dinga jin faɗuwar gaba, please come back ko sbd ni ne" Murmushi kawai ta saki ta cikin wayar ya marairaice mata ya ce "To ki bani address zan zo na gaji da rashin ki ba ki san yadda nake jin ki a zuciyata bane, i so much loves you sweetheart" Muryarta bata fita sosai ta ce "Ka jira lokaci banda gaggawa Sadauki" "Yaushe za ki dai na kira da Sadaukin nan ne? Well is allowed ai ni ɗin Sadaukin ki ne ko ruwa ban bari ya taɓa mini ke i swear" Ta yi shiru shi ma shirun ya yi haka kawai ya ji kamar tana cikin damuwa kuma tsoro a kama shi ya ce "Ridayya" Ya kira da murya mai rauni bayan ta amsa a ƙasan maƙoshi ya ce "You are the most beautiful person, both inside and out. I am so lucky to have you as my girlfriend. Ina son ki Ridayya don Allah kar ki cutar dani idan na rasa ki ban ya zan yi ba, i don't know what to do seriously" "Addu'a" Ya ware idanu kamar tana gabansa ya ce "Oh kina nufin zan rasa ki?" Ta yi saurin girgiza kai kamar yana gabanta ya fahimci hakan ta yi ya ce "Shikenan bari na ƙarasa gida zan duba ki online take care" "Send my regards to your family" "I will. I love you" "Thank you" a fili ya maimaita “Thank You” mai yasa Hausawa suke haka ne, kunya ce ko rashin damuwa? A muryarsa ta ji bai ji daɗin hakan ba. "Uhm ki riƙe alƙawari" ya faɗa yana kashe wayar bakiɗaya. Kuka Ridayya ta saka bayan ta ajjiyar zuciya zuciyarta babu daɗi sam Anuty Kaltum ta ce "Mene abin kuka kuma?" "Anuty tausayin Sadauki nake idan na ji labarin Abbiey ya aure ni ban san ya zan yi ba" Anuty Kaltum ta sauke ajjiyar zuciya domin ta yi wa Ridayya bayanin komai da matsayin MB USTAZ a wajanta kuma ta yi accepting ɗinsa matsayin miji sai dai bata san a wanne gurbi yake a zuciyarta ba, abu ɗaya ta sani tana jin wata matsananciyar kunyar Abbiey ɗin nata, ba zata iya haɗa idanu da shi a matsayin mijinta ba na sunna. Jin daɗinta ɗaya tunda bashi da lafiya dukda bata taɓa kawo wani abu a ranta ba, first kisses ɗin daya wanzu tsakaninsu ta bar shi matsayin kuskure, kullum yana maƙale a zuciyarta wani lokacin har shafo lips ɗinta ta ke yi tana tunawa tsigar jikinta zata mimmiƙe wani lokacin har rufe jikinta take da bargo bata taɓa tunanin akwai wani abu a zaman aure wai shi “Kiss” ba. "Ridayya kin mini al'ƙawarin daga yau ba za ki ƙara waya da Sadauki ba, kuma kin ɗauki karatun duk da muka yi miki ni da Yamara, ki nutsu ki rayuwa mai kyau da tsafta ke da mijinki" Ta kama hannun Ridayya ta ce "So na gaskiya yana tare da mutanen ƙwarai ne kawai. Shi yasa duk yadda za ayi just be with the right person in sha Allah za a dace, ba wai following soyayya ko sharholiya ba" "Kina ganin Sadauki zai haƙura?" "Yeah but not really. Saboda if one of them got another man or lady and the other is such a jealousy he can't absorb it. Dole zuciya ta tsaya a iya ɗaya na san Ustaz yana da kishi kuma soyayya ba zata rufe masa ido ya kasa hukunta ki ba. Mafi girman dace ko kuskure shine na zaɓar aboki/abokiyar rayuwa. Shi yasa a irin wannan lokacin ga samari da ƴan mata yake da matuƙar haɗari musanman a zamanin nan, ki tsayar da zuciyarki ga Ustaz" Idanunta ta lumshe ƙofofin zuciyarta ya buɗe maganganun Anuty Kaltum suka shige ta sosai ta ji Abbiey ɗinta take son gani. Wayarta ce ta fara ringing ganin sabuwar number ya sa ta ɗaga ta cikin wayar aka rangaɗa buɗa nan da nan hankalin Ridayya ta sha can kuma ta ji saukar muryar Mardiyya ta ce "Yadda kika aure mini miji da sunan aure da haɗi na iyaye bayan mijin ba son ki yake ba, to yau an sake ki uwar da ta yi nishin haihuwarsa ta ji zafin naƙudar shi ta saka ya miki saki har uku. Bashi da mata sai ni don haka stay away from my husband idan ba haka ba zan miki abinda ba ki yi tunani ba. Banza baƙa mummuna mai auren mijin wata kuma bazawara a karo na biyu" Ƙitt ta kashe wayar Anuty Kaltum ta ji komai Ridayya ta kasa kuka wani abu ya tsaya mata a wuya zuwa ƙirji she needs a shoulder to cry on wanda zai fahimci kukanta. Miƙewa kawai Anuty Kaltum ta yi ita kanta jikinta ya yi sanyi. Ridayya ta zama so silent ashe sakinta ya yi shi ya sa baya nemanta. Washegari suna zaune a parlourn an gama yi wa Ridayya kitso wasu manya kamar doka jelar ta sauka har hannu aka saka mata stone yatsunta sun sha zanen lalle da ƙafa. Kamar daga sama suka ji sallamar mutum kasa ɗago kanta ta yi jikinta ya ɗauki rawa ta gane muryar Abbiey ce. Wata riga ce a jikinta iya qwiwa gashi a ranar ta sha gyara ta kasa motsi tana ji ana ga gaida shi bata sani ba ko ya amsa tunda bata jin muryarsa. "Ashe kana tafe?" Ya ɗan kalli Anuty Kaltum ta gefen ido sai ya jinjina kai kawai kafin wani lokaci an jere masa abinci kala-kala Anuty Kaltum ta ce "To bari idan ka gama ma gaisa da kyau ko?" "No, zan ɗan je unguwa da ita ne yanzu ta shirya ina waje" Ya miƙe ya nufi waje har zai fita sai ya tsaya ya ce "Ta ɗakko wayarta,abu mai muhimmanci banda kaya" Ajjiyar zuciya Ridayya ta sauke shi kansa ya ji bai dai kula ta bane bashi da lokacin shirmanta. Da ƙyar ta shirya cikin wata lafaya mai kyau da taushi zanen kitson ya fito Yamara ta yi mata wani turare ta mata wasu magani ta sha kana ta yi waje tana tafe tana harɗewa da lafaya ɗin. Tsaye ta same shi jingine da mota shi da Khamis ɗan gidan Yamara tana ƙara sawa Ustaz ya yi shiru sai kuma ya buɗe manya mata ganin ta tsaya ya saka ya zuba mata narkakkun idanunsa da sauri ta shiga shi ma ya shiga, Khamis ya ja su zuwa airport. Kwanan BM USTAZ biyu a garin bai zo sai da komai na tafiyarsu ya zama ready daman yana da komai nata suna zuwa airport minti ashirin sukai suka shiga jirgi shi ya ɗaura mata igiya duk a tsorace take shi kuma ko tari bai mata ba, sanda jirgi zai tashi ya kama hannayenta biyu ya damƙe cikin nasa dukda haka bata nutsu ba sai ya ɗora kanta a ƙirjinsa ya ɗora nasa kan saman kafaɗarta ya ɗan riƙe ta da kyau a jikinsa jirgi na sama ta ƙanƙame shi tana rufe fuskarta a ƙirjinsa Ustaz rufe idanunsa ya yi a ƙasan zuciyarsa yake furta "Ya subuhanallahi banda kisa Ustaz" Bata san wacce ƙasa suka ta fi ba, ta farka dai ta ganta still kwance a jikinsa ya rungumeta very tight hannunsa riƙe da nata yana kallon red henna ɗin ta kasa kallonsa ganin ta motsa ya saka Ustaz ɗago ta ya kalli fuskarta idanunta rufe a hankali ƙamshin bakinsa na sauka a hancinta ya ce. "Kin danne mini ƙirji" Ta ɗan turo baki a ransa yana Maman rufe idanun a hankali ya ce "Baccin za ki koma?" Ta girgiza kai a nutse ya ce "Za ki ci abinci Baby?" Jin sunan Baby ya saka Ridayya saurin buɗe idanu kunya ta sake rufe ta, sunan babyn ya yi mata wani iri a ranta tana mamaki Abbiey da zai ce mata baby sai taga babu Ustaancin a fuskarsa yau. Kafin ta yi magana ta ji saukar hannunsa a flat tummy ɗinta daya shafe a daidai kunnenta ya ɗora bakinsa ya ce "U need a food Baby" Ya ce shortly yana kiss ƙasan wajan very lightly da lips ɗinsa da suke softly. Ridayya ji ta yi komai na shirin ƙwace mata mene ya damu Abbiey yau?. Kayan fruits ya jawo ta fara ƙoƙarin zame wa daga jikinsa ya hana ta ya ɗakko kankana ya kai bakinta ta girgiza baki ta buɗe za ta yi magana ya ɗora yatsarsa ya ce "Shhhh, buɗe bakin" a hankali ya fara bata fruits cikin nutsuwa jirginsu na ta yawo saman gajimare. Sosai hankalin Mami ya tashi jin batun sakin Ridayya nan da nan Baffa ya haɗa meeting ɗin gaggawa kowa ya hallara bayan addu'a Alhji Mansur ya cec "Yaya yaushe aka saki ƴar wajan Babban mutum bani da labari?" "Alhaji Mansur ai baka gari ne ina son a samu daidaito....," "Ba wani daidaito Allah ya ƙara rusa wannan auren na ƙaddara" Baba ƙarami ya kalli Umma bai ce komai ba. Baffa ya ce "Ikon Allah to saki nawa ne?" Baba ƙarami ya zaro takarda ya miƙawa Baffa. A hankali Baffa ya fara ware takardar abinda idanunsa ya sauka a kai ya bashi mamaki ya sake dubawa yaga an saka _“Ba zan iya rabuwa da jaririyata ba, yin hakan kamar mutuwa ce bayan ina numfashi, ba kuma zan saki Mardiyya ba domin babu saki a rayuwata zan je ba zan dawo ba sai Ridayya nada turtsetsen cikin da na yi mata in sha Allah. I love my wife ina son jaririyata Umma ki yi haƙuri bye daga Mijin Ridayya Muhammad-Bilal Tahir Rano na Ridayya”_ More comment more update A yi haƙuri da errors Ramadan mubarak [4/30, 3:46 PM] null: *MUNAFUKIN MIJI 38* Mikiya Writers Ass... Bright pens free batch Nimcyluv Follow my tiktok Account https://www.tiktok.com/@nimcyluv?_t=8lxgsAjuU0z&_r=1 Allahamdulillah Channel ɗina ya je 2k followers keep following my people❤‍🔥🥰 “Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa? Wai da gaske babban mutum ya saki Ridayya? Ku karanta mana takardar a fili mana" caraf Ammi ta karɓe zancen da faɗin "Wallahi Hajiya kema kya faɗa, su kawo takardar na karanta a fili kowa ya ji, ai saki ba kan Ridayya farau ba, ba kuma za a ƙare a kanta ba. Allah ya ƙaddara ita ɗin matar Burhan ce" "Burhan kuma?" Junaid ya furta da mamaki kwance a fuskarsa ita nata allon sai ya haska mata Burhan matsayin mijin Ridayya? Ai kowa da ƙaddara sam ba ta yi wa Ridha adalci ba, duk lalacewarta ta fi ƙarfin mashayi. Ammi ta zarewa Junaid Idanu ta ce "To uwar mece da Burhan ɗin har kake maimaita sunansa, ai daman ya jima yana son ta, kawai babu yadda zai yi ne ni ce nake tanƙwara shi" Kowa kallon Ammi yake banda Baffa da Mami, wacce ta yi kamar ruwa ya cinye ta wani irin zafi zuciyarta ke yi mata yaushe ne Ridayya za ta yi farinciki? Yaushe ne damuwarta za ta zo ƙarshe? Mene laifinta? Wani abu ya tukare maƙoshinta nan da nan abinda ke kwance a mararta ya motsa tare da tabbatar da lafiyarsa ras. Baffa ya sauke numfashi bayan kammala karanta abin da takardar ta ƙunsa ya yi shiru domin bashi da wani abin cewa tsananin kunyar abinda ke zane a takardar shi ya addabi ransa ya kuma jin daɗin kalaman Ustaz har ransa, tantama da mamaki suka mamaye zuciyarsa at the same time kuna ya hasko irin zuri'ar da Ridayya da Ustaz za su samawa Rano families. Ya ɗaga kansa yana kallon Hajiya ya ce "To daman ba wani abu bane face.....,' Abba ya yi saurin tarar numfashin Baffa yana me riƙe hannunsa ya ce "Saki ne kamar yadda kowa ya ji sai fatan Allah ya daidai tsakani. Aure daman rai gare shi na wasu ya ɗore na wasu akasin hakan ƙaddara kuma yaɗo take idan an san farko babu wanda ya san ƙarshen ta, wata ƙarshen ya zo me kyau wata ba yadda muka yi tsammani ba, idan akwai rabo tsakanin Muhammmmd da Ridayya babu shakka wanda ke da tawaye da auren rabo zai yi ajalinsa kowa ya sassauta buri" saurin yin shiru ya yi jin Umma ta rangaɗa uwar buɗa da faɗin. "Ayy yiri-yiriri. Na gode Allah na kuma ji daɗin wannan rana don murna kamar na zuba ruwa a ƙasa na sha haka nake ji, ina roƙan Allah ya ɗorawa muguwar ƴarku son ɗana wanda zai kwantar da ita har gadon asibiti ta ji irin abinda ya ji, kuma tsakaninta da shi sai kallo daga nesa Mardiyya ita ce matarsa ta nan gidan duniya da kuma lahira, na tsaneta bana ko ƙaunar buɗe idanu na ganta ina fata idan rabon ya tashi kisa ya kasheta ita" ta sake sakin dariya. "Ahhayeee cas raina fari tas idan ma mata biyu yake so ni zan nema masa wata in sha Allah ko a cikin yaran ƴan'uwana ne na Zamfara, kuma Muhammmmd dole ya dawo gida ya kuma bi umarnin uwarsa" "To bari mu gani umarni uwa zai bi ko na mata? Ko kuma soyayya" Abba ya faɗa a fili ta ce "Me ka ce?" "Cewa na yi ki saurin nema masa matar auren nima zan fi son hakan, kuma ki dinga sara kina duban gatari ki buɗe kunne da idanun zuciyarki kuma ki tuna cewa ɗanki nakasashe ne banga lafiyayyiyar yarinyar da zata zauna da shi baya amfana mata da komai ba, musamman yaran zamani da idanunsu yake a buɗe. Babban dalili babu iyayen da za su amince su bawa Muhammmmd auren ƴarsu bayan sun san ba zai taɓa haihuwa ba. Itama Mardiyya zan nemi makusanta na labarta musu komai" Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da barin parlourn ransa babu daɗi, ana zaton wuta a maƙera sai gata a masaƙa bai yi zaton Hajiya Hadiza zata kawo masa tsaiko ba. Mami ma miƙewa ta yi ta nufi part ɗinta zuciyarta tuni ta raunata ainun. Hajiya ta ce "Allah shi daidaita al'amarin nan duk auren da ake tsiya haka fa ya fi tsayin rai, mutane suyi ta ƙoƙarin kashe aure kamar sune suka halacce shi, Ubangiji ya kawo musu da sauƙi" "Amin" Anty Zuhura ta ce Ammi ta watsa mata muguwar harara tana ƙwafa. Baffa ya miƙe Ammi ta yi saurin cewa "Baffa idan ba damuwa ina son magana da kai" ya dube ta can ya ce "Ina ji" "Kamarya kana ji nemi waje ka zauna" da wani irin expression Baffa ya juya gabaɗaya yana kallon Ammi a kasashe ya ce "Maryama kin haife ni ne? Yaushe muka saba haka dake? Ko Junaid kya faɗawa haka balle ni ubansa kuma mijinki?" Ta yi shiru domin ta kwafsa wai tana gwada aikin sabon malamin data samu ne sai dai taga har yanzu da saura. Rai ɓace ya juya ya nufi ɓangaren Mami dukda cewa girkin Ammi ne. "Uhm ka yi lokacinki na, ka mure shi ina nan zuwa daga kai har Fatima za ku gane shayi ruwa ne" Junaid ya kalli Ammi ya ce "Ammi wai meke faruwa ne?" A tsawa ce ta ce "Ubanka da uwarka sune suke faruwa, ka fita daga sabgata Junaid kuma wallahi ko ka fito da matar aure ko na zaɓa maka duk wacce ta yi mini" Ya miƙe zai fice ta ce "Ina magana kana mini banza? Do i look like an idiot to you?" Ya girgiza kai ya ce "Me zan ce Ammi? Kin san matsalata genotype ɗina AS ne duk wacce na gani ina so da zarar mun je gwaji sai itama aga AS ne dole aure ba zai yiwu ba" tausayin Junaid ya kama anty Zuhura amma Ammi ta saka ƙafa ta shure ta ce "Duk fa ƙarya ce kawai irin ta likitoci ba wani ciwon sikila da sanda ake auren uwar wa ya samu mutane? Sai yanzu to ni zan nema maka mata kuma dole ka aura tunda kai baka ganin me nake faɗa maka, bari su Aliyu, Abubakar, da Khaliperh su shigo suma" Junaid dai bai ce komai yana fice daga gidan bakiɗaya. Baffa ya samu Mami tsaye a baƙin ƙofa ta yi shiru ya shiga yana murmushi ya ce "Waya ɓata mini ran Sahiba? Shi ma yanzu nasa ya ɓaci" Ta juya gabaɗaya hakan ya bawa hawayen idanunta damar sakkowa zuwa saman kumatunta. Muryarta na rawa ta ce "Baffa da gaske ne Babban mutum ya saki Ridayya?" Ya yi shiru yana kallonta sai kuma ya saki dariya ta kwaɓe fuska tana dire ƙafa ta ce "Ba maganar wasa bace hankalina duk ya tashi, tsoran sanin gaskiyar abin ya addabi zuciyata" "Yaushe na yi miki ciki Batool? Ciki nake gani a jikinki fa?" Gabaɗaya hankalinsa yana kan cikin ta yi saurin juyawa ya kamota ya saka hannu a cikin muryarsa na fidda sauti na farinciki ya ce "This is serious, please when?" "I have no idea, ni ba maganar ciki nake yi ba" "Ni kuma ita nake so mu yi Zarana ɗa za ki haifa mini wannan karan. Allahamdulillah" gabaɗaya ya kamota jikinsa ta yi shiru can ta ce "ina son Ridayya ta rayu da Ustaz Baffa ina son haka shi kaɗai na aminta da shi, bana son ta sake shan wahala a rayuwarta" "In sha Allah,ki kwantar da hankali ba wani saki fa? Bai sake ta ba kawai muna pretending ne zuwa sanda ƙaddara zata sauya komai, ya isa kin ji?" Ta jinjina kai... Yana shafa cikin ya ce "Mu je ki ji akwai batu fa ƴar nan" ya ce yana raɗa mata a kunne. ***** Numfashi ya sauke a karo na biyu yana sake ware idanunsa da nutsa su cikin photon da kyau "why? You have been far away from me and you have tortured my heart a lot?" Ya cije bakinsa tare datse bottom lip yana jiwa kansa ciwo, zafin da zuciyarsa ke masa tamkar ciwon daya ruski mace mai ciki. “Ban taɓa ganin inda so ya zama aibu ba, I love you, i just loves you kina yi kamar ba ki san komai ba, kina wasa da feelings ɗina, I don't care what will happen, I don't care what you will say, I only know myself and my heart, dole na raba ki da ko wanne namiji na kasance dake, ba zan yafe miki ba muddin kika saka bakin almakashi wajan datse alƙawarin zuciyoyinmu, dole; tabbas ne hakan" "Sadauki what is this? Mene haka Sadauki kana cikin nutsuwarka kowa?" Ya juya da jajayen idanunsa ya kalli Mother laɓɓansa sai rawa suke ya kasa furta komai har ƙanƙance Idanu yake, ganin yanayinsa ya saka Mother juyawa zuwa wajan fridge ta ɗauki ruwan gora mai sanyi tare da tsiyayawa a farin cup ta ƙarasa kusa da Sadauki tana cewa "Drink, sha Sadauki" Bai yi magana ba sai tsare Mother da kallo da ya yi, a hankali ta kama hannunsa tare da saka masa glasses cup ɗin hannu, ya amsa still he looks at into her eyes ya matse hannunsa cup ɗin ya yi ƙara tare da fashewa a hannunsa jini ya fara zuba hankali tashe Mother ta ce "A kan mace kake neman kashe kan ka Hamza? Baka tunanin ni da kuma Prof?" Murmushi kawai ya yi mata idanunsa na ƙara rinewa a hankali kuma underneath his breath ya maimaita sunan “Prof.....” Irin bai gane ɗin nan ba can ta ce "Baka tunanin halin da za mu shiga ni da mahaifinka? Kai kaɗai muke da shi fa" ya yi baya yana tura hannunsa cikin suma har yanzu jikinsa rawa yake musamman tsokar ƙirjinsa ta cikin zuciyarsa "Oh your husband?" "What?" Sai kawai ya girgiza kai ya juya baya yana ɗaga kansa sama tare da ƙurawa waje guda kallo. Tsoro ya kama Mother kar wani abu ya taɓa tunanin Sadauki ta sakko daga upstairs da sauri tare da ɗaukan wayarta. 3 miss calls ta yi Prof amma ba a ɗagawa ana huɗu ta samu aka yi picking muryar da ta ji ya saka ta yin baya tare da neman waje ta zauna bisa tilas, wani irin bugawa ƙirjinta ke yi ta kasa furta komai sai da aka ce. "Hello who is on the line?" Hajiya Azizat ta haɗiye yawo mai yauƙi daya tsaya mata can ciki ta ce "Matar me wayar ce, You can give the phone owner his phone?" "Baya kusa yana kan......," "Hiiii stop this nonsense, mijina nake nema bake ba, and lemme warn you first; idan na sake kira kika ɗaga mini waya I'll show you the other side of me, har ina ki bani mijina kina tsayawa yi mini rubbish? Who are you? How dare you eh?" Faɗa sosai Hajiya Azizat ke yi daman mai haƙuri bai iya nuna ɓacin rai ba, ƙitt ta ji an kashe wayar. Tunani ya shiga kanta who is she? Mene haɗin ta da Professor? Har take ɗaukan wayarsa kai tsaye wacce ko ita bata da damar hakan?. Ta miƙe tsaye ta fara kai kawo can wayarta ya fara ringing line ɗinsa ta gani ta ɗauki wayar tun kafin ta yi magana ta ji ya sauke ajjiyar zuciya mai nauyin gaske ya ce. "Sorry wife wallahi wata....," Hajiya Azizat ta katse shi ta cewa "It's okay. I trust you ban taɓa saka zargi a aurenmu ba tsayin shekaru" "But wife at least ki tsaya na miki explanation who is she to me?" "Sweetheart bana buƙata ko wace na san bata da wani important a wajanka, kuma duk lalacewar abu matarka ai matarka ce" Ya sauke numfashi ta wayar ya ce "Haka ne that's why i always Madam, ya akai?" "Ni da ɗanka Sadauki muna buƙatarka don Allah don Annabi don darajar iyayenka ka bamu lokacinka professor, muna da damuwa muna da matsala muna tsananin buƙatarka kusa damu amma kodayaushe kana nisanta kan ka damu why? Aiki ya fi mu ne? Sadauki na cikin matsala Prof na kasa jurewa kullum baya bacci yana jiran zuwanka amma kodayaushe baka dawowa kai ne meeting kai me secretary ya kira ka, kai ne Md ya nemanka ga shi ka cusa kanka a siyasa, ya kake so mu yi da ranmu? Bamu da abokin hira kai ba barina fita kake ba ko wajan ƴar'uwata da muke gari ɗaya you didn't allowed me to go? We need you dear..... Bama buƙatar kuɗi ko wani abu kai kawai muke so kusa damu ka yi mana wannan alfamar" Ya yi shiru ya kasa magana, yana tsananin kishin matarsa da masifar son ta, yana jin tsoro ta fita wani ya ganta gani yake tamkar zata aikata abinda yake yi itama. Shi kansa bashi da wani dalili na tarayya da wasu matan, matarsa bata rage shi da komai ba ya ɗauki hakan matsayin babin ƙaddararsa, tsananin kunyar ta ya saka Prof kasa magana ta ce "Can you? Za ka iya?" A hankali ya ce "Ina kan hanya zan zo yanzu" Kashe wayar ta yi, lokaci zuwa lokaci sai ta duba agogo ga Sadauki ya daina fita wajan aiki walwalarsa ta ragu baya magana duk barkwancinsa ya kaɗaita da kowa, tun yamma har aka yi magariba babu Prof. Number Tajj ta kira ta ce tana son ganinsa ya taho mata da ƴar wajansa yana dariya ya ce "to shikenan Anty, amma zuwa gobe" "Ba damuwa, za mu yi ko chat ne Allah ya tsare ya taimaka" Ya amsa da "Amin" Har ƙarfe 2 na dare Prof bai dawo ba, ta sake nufar upstairs zuwa part ɗin Sadauki ta same shi a rufe wayarsa a kashe ta rasa yadda za ta yi tana sake kirab number Prof ta ji a kashe kawai ta durƙushe a wajan tare da fashewa da raunataccen kuka. Professor bayan kammala wayarsa ya juya ya kalli Talatu ƙarin kunama ya ce "Sau nawa zan ce miki kar ki kuskura ki ɗauki wayata?" "Au haba? Nima na yi maka warning idan ina tare da mutum bana buƙatar ya kula ko wacce mace" Ya ware idanu ya ce "Even my wife?" "Ko ma wacece ai kasan da matar taka kake kula karuwa" da shock ya ce "Da kan ki kike kiran kan ki da karuwa?" Ta wani waskace ƙugu tana kaɗawa ta ce "Ba ka ji take na bane? Talatu ƙarin kunama? Ai guba ce ni idan na kafawa mutum ƙarina dole ya lalace ka bi a hankali kar ka ja na yi maka asarar kujerar ɗan majalisa ɗin da kake nema, kuma ba naga kana ruwan jiki ba muna tare dakai gabaɗaya weekend ɗin nan, da kake cewa ina kiran kai na karuwa ai ɗan'iska baya tsoran a kira shi da ɗan'iska mufa wannan harkar shi ne kasuwancinmu kune kuke ɓoye kan ku, but ni a yi shela a kira ni da Talatu karuwa ko a yatsana" Nan da nan ta sauyawa Prof lissafi ya mance da batun Hajiya Azizat da ɗansa ɗaya tal a duniya daya kasa bashi lokacinsa har dare suna tare ƙarfe uku ya shige Dubai wajan Anita uwar shegu sai da gari ya waye ya haɗa haɗaɗɗan messages na ban haƙuri da kalamai masu sanyaya zuciya zuwa ga Hajiya Azizat cikin sa'a wayar hannunta ta gani sai ta ji tausayin mijin nata, komai ya ke yi saboda su ne yana yi don kyautata gobensu. A taƙaice ta masa reply da; “Take care” JAPAN.... A hankali ta juya tana sake shigewa cikin lallausan duvet ɗin saboda wani sanyi da yake ratsa mata jiki, kwanan su uku a ƙasar Japan ɗin amma ta kasa sabawa da weather ɗinsu kullum ƙasar cikin ruwan sama suke da zubar dusar ƙanƙara. Bata son ruwan sama hakan yasa kullum tana cikin bedroom dukda cewa gidan ko alamun saukar ruwan saman ba za ka ji ba, sai dai ka gani ta window, jin shigar sanyin ya tsananta gargasar jikinta na zubewa tana mimmiƙewa ya saka ta yaye duvet ɗin tare da yin miƙa bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, dim light ne hakan yasa ba sosai take gani ba, ta sakko da ƙafarta duba kayan baccin jikinta ta yi sai kuma ta yi baya tana lumshe idanunta da ƙanƙame jikinta a hankali ta ware laɓɓanta ta ce "Uhm Abbiey" Idan ta tuna kokawar da suka sha wajan sauya mata kayan har ta cije shi a wuya abin dariya yake bata, musamman yadda tana sane ta dinga bashi wahala. Wani flip flops slipper ta saka a hankali ta nufi parlour wanda ta ji ya ɗauki ɗumi tun daga nesa ta hango fararen ƙafafuwansa ya lanƙwasa su a saman glasses table zoom meeting yake don haka bai ji motsin fitowarta ba, Ridayya kuma haɗe rai ta yi ganin still jallabiyya ce ya kuma sakawa ita ta rasa dalilinsa na saka wata jallabiyya. MB USTAZ idanunsa da suke lumshe ya buɗe yana sauraren mai maganar da yake cewa. "Kafin tsayawa takara dole ne ka ajjiye aikinka, domin ana da wata uku tsaida ɗan takara ake ajjiye aiki, kuma har yanzu baka amsa cewar ka amsa ba ko aka sin haka" Ustaz ya jinjina kai da gaske magana yake son yi da kuma bayani amma laɓɓansa sun yi nauyi ya rasa ta ina zai fara sai juya idanunsa yake yana datse leɓe ga gashin goshinsa dake reto a gaba. "Sir please ko dan al'umma ka ceci wannan jiha ta mu daga hannun ƴan kama karya, domin ana mana kashin dankali ne, wahalar fetur, babu nepa, babu abinci, securities, abubuwa da yawa muna da tabbaci a kan ka ne" "Allah subhanahu wata'ala shi ke da ikon ceto Jiharmu ba Ustaz ba, Allah ya yafe maka da kalamanka. Ba zan iya mulki ba, shugabanci yana bani tsoro ban san me zan cewa Ubangijina ba, ko shugabancin cikin gidana sai an tambaye ni balle na dubban al'umma ka yi....," Wanda suke meeting ɗin da shi kai tsaye ne Ustaz yaga ya yi shiru ya kuma zubawa bayan Ustaz idanu, cikin sauri Ustaz ya rufe idanunsa sai yanzu ne ya ji bugun zuciyarsa ya sauya cikin sauri ya katse meeting ɗin yana rufe laptop ɗin. Wani irin nauyi ƙirjinsa ya yi masa, ya ji wani abu mai tudu ya tukare masa ya dunƙule hannunsa waje guda waje guda karan hancinsa ya yi jajur. Bai juya ba sai a hankali ya yi baya tare da ɗaukan ruwa ya shanye tas. Ridayya kuma a hankali ta fara tafiya zata shige ɗaya part ɗin domin tunaninta bai ganta ba, shi ma ɗin ya rabo da ita ne yaga ƙarshenta ta yi sauri ta shige ya girgiza kai kawai, ya rasa dalilin wannan kunyar da ba haka take masa ba, tunda aka ce shi ne mijinta kuma ta yi accepted shikenan take jin kunyarsa addu'a ɗaya yake Ubangiji ya sa ba kallon uba take masa ba. After 15 minutes ta fito sanye da riga body short da wani wando mai kauri iya qwiwa ta ɗora hula a kanta zanen ƙunshinta raɗau da shi, ta yi fresh baƙar fatarta ta sake fidda asalin kalarta wani irin baƙi ne mai masifar kyau. Ta ƙarasa wajansa ta zauna dab da ƙafafuwansa ta zubawa yatsun ƙafarsa idanu a hankali kuma tana danne nauyin kunyarta ta ɗaga kai suka haɗa Idanu ta yi saurin ɗauke nata ashe ita yake kallo ta miƙa hannunta na dama ta ce. "Good morning Abbiey?" Jin bai saka hannunsa sun yi musabaha kamar yadda suka saba ba ya saka ta turo baki tana shagwaɓe fuska ta ce. "To ni me na yi maka ne? Ka yi haƙuri don Allah Abbiey" Ya yi shiru ta juya gabaɗaya ta ga waya yake dannawa tunaninta ya bada ƙila Mardiyya ce suke chatting. _“Lovely, and sweetness”_ Da sauri ta miƙe tsaye tana fashewa da kuka, ya bi bayanta lallausan murmushi ya saki yana miƙewa tsaye tare da bin bayanta ya same ta sai sharɓar kuka take tana tsaye gaban madubi, gently ya ƙarasa inda take ya tsaya zata gudu ya yi saurin riƙo ƙugunta da tafin hannayensa ya jawota tare da haɗe bayanta da ƙirjinsa ya riƙe ta a jikinsa tare da rungumota tsam a ƙirjinsa, murya can ƙasa yana goga mata sajensa da hancinsa ya ce "Allah ya yafe miki Ustaza, wake fushi da miji?" "Uhm a'a um'um ni" "Kuma haka ake gaisuwa? Kina neman rabauta a ƙarƙashina?" "To ba kai ne ba" ya juyo da ita, tare da zuba mata idanu ya dinga kallon ta sai kawai ya ɗaga ta ya ɗora saman madubin ya shiga dudduba mayukan wajan ta ce "Me kake nema?" Ya mata shiru sai da ya gama hargitsa wajan ya ɗago ya sake kallonta can ya ce "Wanne mai da turare kike using?" Da yatsa ta yi masa pointing wani mai na Aloe vera. Ya girgiza kai sai ya matsa ya sake riƙe kafaɗunta ya shafa da sauri ta rufe idanu saboda amsawa da jikinta ya yi, ya sake murza fatar wajan wani irin laushi da santsi haɗe da taushi yake ji, bai taɓa jin abu mai laushi kamar fatar jikinta ba, gata dai baƙa amma fatarta na shirin sa shi abinda bai niyya ba. Ita dai kanta a ƙasa bata san halin da yake ciki ba muryarsa bata fita sosai ya ce "Uhm" har zai juya sihirtaccen ƙamshin na asalin haɗaɗɗiyar kwalaccar Nana da wata shekararriyar humra ta Nana ya shiga hancinsa ya shaƙe shi da kyau ya damƙi hannun Ridayya ya sakko da ita ƙasa cikin sauri a kamalance kuma ya zura hancinsa da kyau a wuyanta ƙamshin ya zauna masa sosai ya yi masa wani irin daɗi, so yake ya tantance ƙamshin wanne turare ne amma sam ya kasa ya ƙara ɗora hancinta saman ƙirjinta ta yi saurin riƙe kansa ta ce “Abbeee....," Sauran abinda ta ji ya saka ta ja sunan nasa tana riƙe shi, jininta ya ɗauki rawa da kakkarwa bata taɓa zaton haka ba, sai gashi Ustaz ya rikiɗe mata zuwa Simba ta fara shassheƙar kuka tana yarfe hannu ya ɗago kansa ya dube ta, ya dake shi kansa ya ji kunya ganin abinda ya yi wa jaririyar tasa ta dinga yarfe hannu tana ɓoye ƙirjinta ta mayar da rigar. "Kin bar ni da yunwa" ya yi saurin ficewa da bashi da abin faɗa, ji ya yi ma kamar zai yi zazzaɓi wallahi bai taɓa tunanin hakan al'amarin yake ba. Yana ta zaune saman kujera can ya miƙe ya nufi bedroom ya shiga bathroom wanka ya yi mai kyau kuma da kyau, ya saka armless da wando iya qwiwa samun kansa ya yi da ƙarewa kansa kallo sai ya ji yana son saka turare ko Ridayya zata shaƙa watarana. Ya fito fuskarsa wasai kamar bai yi komai ba, ya samu Ridayya zaune ta jera breakfast ɗin ya zauna saman kujera. "Bani abinda ki ka yi?" Ta buɗe plate ƙwai ta soya mai yawa da kuma soyayyen dankali ta haɗa masa green tea ta saka spoon ta miƙa masa da hannu biyu ya amsa ya ɗora a cinyarsa. A hankali ya dinga cin abinci yana ratsa shi sukai shiru can ta ji ya ce "Zo mu gaisa mana Oum-Bilal" ta miƙe tana ƙoƙarin zama ya jata saman cinyarsa ta ce "Ina kwana?" "Yana kwano" Murmushi ta saki domin basa ƴar haka dashi ya ce "Ya baƙunci? Kina cikin aminci?" "Abbiey wai ina ne nan" yana bata ƙwan a baki ya ce "Japan" ta sake yin murmushi ta ce "Zaka saka ni a jirgin ruwa irin na ƴan India?" Zuba mata idanu ya yi tana cin abinci tana masa surutu da yaƙi tankawa ta shiga wasa da gemunsa, mamakin ƙuruciyarta da saurin manta abu kawai yake, ɗazo ya yi mata abu har ta kasa haɗa Idanu da shi amma yanzu ta manta. "Iya jirgin ruwan? What about the babies?" "Ka siya mini teddy babba mai irin tsayin Little" ya yi murmushi yana girgiza kai ta saka cewa "Wai baka da lafiya ko Abbiey?" Ya ɗage mata duka girarsa biyun ya ce "Haka na ji" ta shiru can ta ce "Abbiey ka amshi kujerar da suke maka magana saboda Allah, da kuma al'ummar Musulmi. Ina da tabbaci da kyakkawar zuciyarka kuma ina da yaƙinin za ka yi nasara, kawai ka saka Allah a ranka ni zan tsaya maka ai kaga na isa yin zaɓe kuma ina da voters card zan zaɓe, I'll be by your side zan yi supporting naka kuma da ina da ƙawaye sai na saka duk su zaɓe ka amma bana da su, nasan za a dace. Ubangiji yana bayan mai gaskiya kuma kana da ita ai kaga zaka zama Gwamna ka yi aiki mai kyau wanda ko bayan baka nan za a yi alfahari da kai, please say yes" Ta faɗi yes ɗin a shagwaɓe tana narke murya ya juya ya kalleta can ya ce "A matsayinki nawa a wajena kike bani shawara?" "Matarka" "To, stop calling me Abbiey" "Zan daina to ka ce ka yarda" ya shafa kansa yana zamewa tare kwanciya a cinyarta ya ce "I'll think about it...," "Yaushe?" "Idan kika bani baby" shiru ta yi kawai ya sake mata dukkan nauyinsa ya juya fuskarsa zuwa wajan cikinta... Ya jima sosai tsaye a ƙofar gidan yana jin kamar ya shiga ciki kamar kuma ya tsaya,he can't go without talking to Ridayya, mai son shi da ƙaunar shi bai taɓa jin abinda yake ji game da ita ba a yanzu, bashi da sukuni bashi da wani lokaci sai nata kullum cikin tunanin muryarta yake, bai taɓa zaton Ustaz na raye ba da ba zai yi gangancin da ya yi ba, ya zama dole ungulo ta koma gidanta na ainahi. Yana tsaye Zainura ta fito kyakkawar yarinya fara tas sai ya ji farin bai wani birgeshi ba ƴar baƙarsa yake son gani. Kallon sama da ƙasa ta yi masa dukda kwarjini irin na Zameer ta ce "Kai kake neman Yaya Ridayya?" Hadda murguɗa masa baki ta yi Little yana tsaye kusa da ita hannunsa riƙe da chocolate ya ce "Ba ki gane ni ba ne Zainu?" "What? Na haɗe dangi da kai ne da zan gane ka? Ko kuma ce maka a yi gantalalliya ce ni? Ko da yake ai babu mamaki Bakatsine haka yake" da mamaki Zameer ya ce "Ni kike faɗawa haka? I'm older than you..." "Matse maka ta yi kai da older ɗinka wani guntun turanci irin na fulanin katsina, kuma kar ka sake zuwa ƙofar gidan nan domin bamu da haɗi da kai" Takaici ya kama Zameer ya kalli Little ya ce "Come my boy" ya maƙale ka faɗa da Zameer ya yi ƙoƙarin ɗaukarsa ya saka ihu yana riƙe Zainura. Suna haka Junaid ya fito cinin shigar yadin voyel ya kalli Zainura ya ce "Shiga ciki" Har ƙasa Zameer ya durƙusa ya gaida Junaid abinda bai taɓa yi ba, Junaid ya ce "Lafiya Malam?" Zameer ya shafa kai ya juya ya kalli gidan sai kuma ya kalli Junaid ya ce "Daman matata Ridayya na zo gani" "Matarka? Daman baka sake ta ba?" Ya zaro ido yana girgiza kai ya ce "Cewa ta yi na sake ta? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ashe ƙiyayyar da Habibty ke mini da gaske muna zama lafiya ta ce dole sai na sake ta, na ce ba zan iya ba domin ina son ta da gaske masifar yau daban ta gobe daban sai wayagari muka yi ta gudu, to; ta mance da takardun filayenta na yi yunƙurin siyarwa da gangan na san dole sai wani nata ya bayyana cikin sa a na samo gidan nan" Mamaki ya cika zuciyar Junaid kenan Ridayya AURE TA YI KAN AURE? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un dole duk inda take ta dawo haka Ustaz. Yana ƙoƙarin magana yaga an fito da Mardiyya tana kelaya uban amai kamar zata mutu, Umma sai murna take a tunaninta ɗanta Ustaz ne ya saka ƙwallo a raga ganin hakan ya saka Junaid bawa Zameer haƙuri ya bashi uzurin gobe ya dawo. A can Japan dukda babban gidan da suka sauka a gyare yake kuma gida mai tsari irin na turawa bai hana Ridayya ƙara share ko'ina ba ta yi mopping kana ta ɗora musu dinner domin bata iya cin abincin ƙasar, shi kuma abinda ta ci shi zai ci. Ta gama komai ta yi wanka ta saka riga da wando amma wandon iya qiwwa ne rigar kuma mai faɗi ce tana da kauri ta kunna hiter ta ɗumama gida. Misalin 8:2 daidai ya shigo cikin main parlour ɗin wanda yake a zagaye ya haɗu sosai, yana shigowa ya lumshe idanunsa yana mai tasbihi a ransa a hankali ya buɗe idon daidai fitowarta da sauri ta ƙarasa tana "Oyoyo Abbiey, na yi ta jiranka ina jin tsolo" riƙe kansa ya yi da kyau ta amshi kayan hannunsa ta dinga mamakin shigarsa wasu jersey ne masu bala'in kyau kuma duka baƙaƙe sai hula daya jata har kunne sumarsa ta sauka, yana yin numfashi hayaƙin snow ke fita daga bakinsa da hancinsa. Ganin bai yi magana ba ta fara ƙoƙarin kama hannunsa ya yi saurin zamewa yana waro mata idanu ya ce "uhm a'a" "Kar na taɓa ka?" Ya jinjina mata kai kamar yaro da sauri kuma ya shige part ɗin da yake. Tana zaune shiru shiru bai fito ba, shi kuma yana can saman gado sai juyi yake ya yi nan ya juya nan, bai taɓa jin zafin ƙaddararsa ba sai yau, gani yake jaririyarsa ta yi muguwar ƙanƙanta da ɗauke buƙatunsa bai kuma saba ba, bai san yadda ake ba, wata kunyar ƴar tashi yake jaririyarsa ƴar rainonsa. Daga shi sai boxer amma duk sanyin garin zufa ke tsasstafo masa yana tsananin buƙatar matarsa shekaru wajan arba'in ba wasa bane. Wayarsa ya jawo ya nemi numberta daman ita ce last kira tana ɗaga kiran ya ce "Come" yana faɗin hakan ya kashe ya kifa cikinsa idanunsa rufe, yana a haka ya ji ta shigo da sallama bai amsa ba ta ƙarasa ta ce "Do you need something?" Ya yi shiru "Abinci za ka ci? Ko baka da lafiya ne?" Duk ya yi mata shiru ta miƙa hannu zuwa wuyansa ta ji zafi sosai kafin ta ɗauke ya damƙota tare da fincikota zuwa saman gadon ta faɗa jikinsa ya riƙe ta gam, idanunsa rufe ya miƙa ya kashe hasken ɗakin magana yake son yi amma ya kasa laɓɓansa sai rawa da ƙyar ya furta. "Yes; i need you, i need to feed on you....., Ya kasa ƙarasa maganar tsoro ya shiga zuciyar Ridayya ta mance yadda ake ta manta sam kuma bata shirya ba, uwa uba ga ɗinkin da akai mata ga kuma gyaran data sha a Maiguduri. Hankalinta ya tashi ta fara shassheƙar kuka Ustaz bai ma san me take yi ba yana ƙoƙarin maida Ridayya matarsa ta halak kuma ta sunna kamar gilmawar walƙiyya haka photon Zameer da Ridayya ya faɗo masa a cikin idanunsa sanda ya gansu turmi da taɓarya cikin hanzari ya miƙe tsaye yana dafe bango ya fice daga ɗakin bakiɗaya.... Barkanmu da sallah🤓 Ku yi haƙuri na jina shiru, wallahi ayyuka ne suka sake ƙaruwa. Kun san me rai da buruka wani aiki da na yi apply tuntuni shi ne na samu aikin yanzu nake ta jigilar zuwa seminer. Bana son fara typing na tsaya, but yanzu Allahamdulillah da taimakonku da haɗinku za mu kai zuwa gaci a ci-gaba da yin comment da sharing. A kuma yi haƙuri da abinda za a karanta marubuci baya fara labari ba tare daya tsara shi ba komai aka karanta daman a haka yake dole zai kasance. Comments Share fisabilillahi. [5/4, 1:10 PM] null: *MUNAFUKIN MIJI 39* Mikiya Writers Ass Bright pens free batch Nimcyluv *Masu buƙatar Munafikin miji daga farko ku yi following channel ɗina👇🏻*https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T Muna yin tallah don ƙarfafa kasuwancin jama'a, a saka maka a status mai 1k to above viewers muna sakawa channel mai 2k zuwa sama followers sai kuma a littafi. Idan kayan mata kake shiryawa muna yi mun sanya shi a kayan da tauraruwa ke using dashi, idan bags ne, shoes ne anything... Ku yi magana ta wannan number 08164069385 Ajjiyar zuciya Ridayya ta sauke tana wurƙila idanunta ƙirjinta sai ɗagawa yake ta jima kafin ta dawo daidai ta ce "Na shiga uku Abbiey me kake shirin yi?" Can ƙasan zuciyarta ta ce "Ke ɗin fa matarsa ce, yana da iko dake Ridayya, idan bake akwai Mardiyya" Tunawa da ta yi tana da wata wai kishiya hankalinta ya yi masifar tashi, tsoro ya wanzu a zuciyarta yanzu idan ya barta zai iya zuwa wajan Mardiyya yana da wannan ikon, ƙirjinta ya motsa wani abu mai kama da tsoka ya motsa a gefen ƙirjinta hakan ya bata tabbacin bata mace ba, tana da raguwar zuciya a ƙirjinta wacce babu shakka soyayyar Ustaz ce ta mamaye cikin tsokar da wajanta wacce ta haddasa bugawar ƙirjinta da ƙarfi fiye da bugawar agogo. Sakkowa ta yi jikinta a sanyaye sai yanzu fitarsa ya dame ta, domin har zuciyarta bata da tabbacin abinda ya hana shi idda nufinsa a kanta, tana tsoro da shakka ƙwarai. Jiki a sanyaye ta nufi parlour amma the parlour is empty ba kowa a ciki, sai ɗumin hiter saboda sanyi. Ta bishi? "A'a Ridayya kar ya yi miki faɗa" zuciyarta ta yi saurin faɗar hakan. Ta marairaice fuska bata sake bada ƙofar wani tunanin ba, kai tsaye ta nufi ƙofar da take da tabbacin yana ciki. Ƙarar saukar ruwan shower da ta ji ya sa ta san yana ciki da alama kuma wanka yake ta yi can ta zauna. Ustaz ya sauke numfashi sai a lokacin ya lura bai kyautawa kansa da zuciyarsa ba, kokawa yake ta yi da zuciyarsa amma wani irin zafi da yaji-yaji yake ji a tsakiyar ƙirjinsa ɗanɗanon bakinsa ya sauya, bai san me ya sa tunanin abub ya faɗo masa ba, tunda ba zina ya rusketa tana aikatawa ba, sunna ce, sunna mai ƙarfi tunda mijinta kuma koba komai Ridayya ba zata taɓa wofintar da tarbiyyarta ba. Ya buɗe idanu wanda suka shige ciki a fili ya ce "Allah ka yafewa Ustaz, na yi rashin uzuri ka yafe mini bisa tunanina" Gyara zaman bathrobe ɗin ya yi ta zauna da kyau a jikinsa, ƙamshin shower gel na fita daga jikinsa, a baƙin ƙofar toilet ɗin ya cire bedroom slippers ɗin ya saka normal slipper na ɗaki yana fitowa zuciyarsa ta doka da ƙarfi ganninta zaune idanunta cike da hawaye, idan da akwai abinda ba zai jure ba shi ne zubar hawayenta. Kasancewar shafa baya cikin ɗabi'arsa ya saka ya ƙarasa bakin gadon ya zauna, kamar zai yi shiru sai kuma ya juya ya kalleta a taushashe cikin lallausan harshe da murya mai nutsar da sabuwar zuciya a shiga soyayya ya ce "Mene? Are you okay? Lafiya kike?" Ta yi shiru ya kama hannunta ya damƙe cikin nasa "The tears? Hawayen mene? Nine? Laifi na yi? A nutse yake magana, laɓɓansa na ware wa ɗaya bisa kan ɗaya amma zuciyarsa rawa take, bai san me ya sa bashi da ƙarfin qwiwa ko kaɗan akan Ridayya ba, tsoro ne hakan? Ko kuma tsananin soyayyarta ce ta hadda masa, ko raunin dake tattare da yarinyar ne? "Abbiey me ya sa ka juya mini baya?" Ya waro manyan gajiyayyun idanunsa masu cike da bacci da kuma abinda ke kai kawo a jikinsa, ya sake shigar da hannunta cikin nasa yana raba musu ɗumin ruwan wankan, ya ware idanu a kanta ya kasa cewa. "May be i was wrong da nake tunanin zan samu farinciki wajanka Abbiey" "Shhhh Ridherh" Ya ɗora yatsarsa a laɓɓanta baya son jin komai, hawayenta ya sake sakkowa bai yi magana ba ya miƙe tsaye ya kashe hasken bedroom ɗin ya dawo ya kwanta tsakiyar gadon, yana daga kwancen ya miƙa mata hannu ta yi saurin cewa "Ba za ka yi mini komai ba?" Ta cikin zuciyarsa ya ce "Jaririya ba ki da hankali, ke ɗin halaliyyata ce" A fili kuma ya lumshe idanunsa ya buɗe alamar “Eh" Gadon ta hau ya ɗora kanta a ƙirjinsa ya rufe ta da hannayensa, babu wanda ya yi magana cikinsu sai shi da hannayensa suke shafa sumar kanta, ya kasa daurewa saboda ƙamshin turarenta wanda bai taɓa jinsa ba ya addabe shi, haɗin turaren amare ne daga (Hajiya Nana). Misalin 3 daidai ya zame ta daga cikinsa yana ji tana motsi saboda raba jikinsu da ya yi, ya ja mata pillow. Ustaz bacci ya ƙaura ce masa ya yi alwala ya shimfiɗa ladduma Nafila yake ta yi har lokacin yin Assalatu ya yi. Samun kansa ya yi da yin addu'a tsakaninsa da Ridayyerh, ya ɗora goshinsa a ƙasa yana kallon Alƙibila da murya ta neman taimako da ɗaukin Ubangiji ya ce. "Ya Ubangiji ga Muhammad-Bilal Tahir na neman taimakon ka, ni ɗin bawa ne gare ka, mai rauni, mai damuwa, na san ka fini sanin damuwata, ban kuma raina ni'imar da ka yi mini ba, ni Ɗan'Adam ne mai buri da sanya abu a zuciya, ni almajiri ne kuma bawanka mai tsananin tsoron haɗuwa da kai saboda rashin tabbas. Ya Mujibudda'awati ka sanya hannu cikin lamarina. Ina tsananin son matata Ridherh, bana son ya kai ni ga halaka, ina tsoran soyayyar zamani, Allah ka tabbatar da dukkan alheri ga rayuwar aurenmu, idan aure na da Ridherh alheri ne kuma akwai rabo, Ubangiji ka cire mini abinda ke mini yawo a zuciyata, ka rage mini kishinta, ka tsayar mini da zuciyata waje guda, idan alheri ne auren nan namu ka bani ikon mayar da ita cikakkiyar matata ta sunna, ka yi mana tsakani da sharrin mutum dana aljan, ka sanya farinciki da walwala a rayuwarmu, ka sanya mana nutsuwa yarda da juna, ka kaɗe mana fitina, ka sanya matata ta soni ko kwatan son da nake mata ne, domin ba zata mini irin soyayyar da nake mata ba. Idan aure na da Ridherh babu alheri Ubangiji ka fini sanin komai ka mayar mini da mafi alheri ya zuljalalu wal ibkar. Allah buƙatar al'ummar jihata akan zamana gwamna idan alheri ne ke kirana ka tabbatar mini dashi,, idan ba alheri ka nisanta ni daga wannan al'amarin, gani gabanka ya Allah ka taimake ni, ka tausaya mini, ka sanya hannu cikin lamarina" Ya jima yana addu'ar har sai da ya ji damshi a fuskarsa ya gamsu kana ya ɗago ya shafa ya fara azkar idanunsa a kanta. Kamar yadda aka ce dukkan wani musulmi idan har Assalatu ta yi dukkan baccin da yake sai ya motsa hakan ce ta kasance ga Ridayya, bakinta ɗauke addu'a da salati ta shiga motsawa har ta buɗe ido, ta shafa ta ji ta ƙanƙame pillow ta kwaɓe bakinta. Zamewa ta yi daga cikin duvet ta sakko ƙasa, mamakin ganin kayan bacci ya kamata kullum Abbiey baya gajiya da sauya mata kayan bacci? Kenan yana kalle mata jiki? Innalillahi ta yi saurin rufe ƙirjinta. Bata san yana ciki ba ta ji ya yi gyaran murya ya ce "Sai dai ki ɓoye wani abun ba wannan daya zama t.v ɗin Muhammmmd ba" Ta tura baki "Kai Abbiey ba kyau" Ya cije laɓɓansa yana duba lokaci "Uhm Ustaza manya, bari na je masallaci" "To Allah ya tsare mini kai" Ya yi saurin Juyawa ya kalleta ya ji me ta ce fuskarsa ta faɗaɗa duk da haƙurinsa bai bayyana ba. Ya juya ya nufi masallaci. Alwala ta yi itama ta gabatar da raka'atul fjr kana ta yi sallar asuba, ta yi wanka cikin sauri ta haɗa turaren zama wanda Hajiya Nana ta bata da Anuty Kaltum ta yi mata bayani tare da mata order nasa. Sosai take jin daɗin turaren aduk sanda ta yi sai ta ji jikinta ya sake haɗewa nan da nan kuma za ta ji sauyi bayan ta kammala, ta kunna kwal mai ƙwalli ɗaya ta saka turaren icce ta yi durƙuso ya shiga jininta sosai, cikin sauri ganin har 6 ta kusa ta ɗauki halin oil ɗin da aka yi mata na musamman wanda ke ƙarawa fata laushi da santsi kamar ta jarirai idan kana shafa shi babu buƙatar kana yin dilka duk a haɗin kayan Hajiya Nana yake, bayan ta shafe jikinta ta ɗauki kwalaccar Nana ta shafa, ta ɗauki humura ta shafa, ta haɗa wani magani a cup mai ɗauke da hulba ta ruwa data gari saboda tsaiwar ƙirjinta tunda ta shayar kuma Allahamdulillah maganin na musamman ne domin a sati guda ta yi da fara amfani da maganin abin har tsoro yake bata idan ta kalli ƙirjinta lallai a gaida Hajiya Nana mai da tsohuwa yarinya, duk yadda Zameer ya wulaƙanta mata jiki amma yanzu tamkar ba ita ba. Idan ta tuna yadda ta komaɗe ta nemi zama tsohuwar ƙarfi da ya ji a gidan Zameer sai ta ji a rayuwa babu namiji da ta yi wa muguwar tsana sama da shi, ya cuceta ya ruguza mata rayuwa, ya rusa gobenta yana son lalata mata career ɗinta, idan haka aure yake zata bugi ƙirji ta bawa ɗiya mace shawarar kar ta sake ta yi aure. But now rayuwarta Allahamdulillah tana rayuwa cike da kwanciyar hankali da mutumin da tun fil'azal ya dace ace shi ne zaɓinta na farko, amma ƙaddarar auren MUNAFIKIN MIJI ya sanya bata fahimci hakan ba. "Ridayyerh yana da kyau ki nutsu ki rayuwa mai kyau da tsafta da mijinki, hakan ne zai ba ki damar janye hankalinsa daga kan Mardiyya,da kuma macen dake kwaɗayin zama da shi" Kitchen ta nufa ta tafasa black tea domin tasan dole ya nema, bayan ta kammala ta haɗa zuma cikin cup da dafaffiyar madarar shanu mai zafi ta shanye a kitchen ɗin duk ƙaunarta da son shan ruwan sanyi haƙura ta yi saboda maganin da take akai yanzu. Parlour ta koma ta sanye da plazo da kuma t.shirt mai babban hannu ɗaya a zame wajan kafaɗa ɗaya daidai ta ɗora hula ta rufe kunnenta, tana zaune tana azkar wajan 6:34 ya shigo ciki bakinsa ɗauke da sallama muryarsa a nutse wajan ta nutsar da zuciyar Ridayya sosai da kyau. "Good morning Abbiey" Ta ce bayan ta durƙushe har ƙasa ta miƙa hannunta, ya yi murmushi mai taushi yana lumshe idanunsa "Oh Allah na, yaushe za ki bani wani gurbin ne Ustaza?" Ta yi murmushi ya kama hannunta tare da ɗagota saman kujerar ya zaunar kusa da shi, sukai kusa very close numfashinta na sauka a wuyansa ya kama kanta tare da sumbatar goshinta, ya sake sumbatar ƙuncinta a hankali yana kallon fuskarsa dake cikin tafukan hannunsa ya ce "Kina lafiya Mar'atussaliha?" "Cikin amincin Abbiey" Ya jinjina kai yana ta kallonta for long a hankali ya sauke breathing numfashinsa calmly ya ce "Kin san me?" "Sai ka faɗa Abbiey" "Za ki iya rayuwa dani for life? Na dindin ba na wani lokaci ba?" "Abbiey zan rayu da kai na har abada, zan rayu da kai zuwa ƙarshen numfashina da zan yi a jikinka koda mutuwa ta ruskeni" ya matse hannunta wanda shi ke nuna mata magana ta shige shi da kyau "Allah ya yafe miki Ustaza ya taƙaita miki haka nan" "Why? Mardiyya kake so? Da ita kake son rayuwa? Baka so na bayan na kasance matarka ko akwai wani abu daka riƙe a zuciyarka Abbiey wanda kake ƙoƙarin hukunta ni da shi, why not me sai Mardiyya? To why i am here? Me ya sa ba Mardiyya ba?......," Caraf ya cafke bakinta da yatsu biyu yana juya mata idanu, amma ina idanunta zallar ƙaunarsa suke nunawa, sai ya ji zuciyarsa na matsewa tana tattarewa waje guda a ƙirjinsa wani irin emotions na yunƙuru masa gabaɗaya ƙofofin gargasar jikinsa suka buɗe ya kasa furta komai sai ƙwayar idanunta da yake kallo. Hakan da ya yi mata ya ƙara tabbatar mata zuciyarsa naga Mardiyya sai ta fashe da wani irin makirin kuka wanda ya gigita Magidancin mutumin, Ustaz ya rasa me zai yi sai kawai ya zame ƙasa ya durƙushe gaban Ridayya a saman qwiwowinsa. A can ƙasa Nigeriya Ammi ce zaune a parlour ta saka Yaya Zuhura a gaba da mita tana faɗin "Ba zan zauna dake a cikin gidan nan ba Zuhura, kina kallo na lallaɓa ɗan wulaƙancin mijin nan naki amma shi ne kika sake dako wani yajin ko? Kina so a yi mini dariya kin kasa zaman gidan miji" Yaya Zuhura ta yi shiru wani irin haushi kalaman Ammin ke bata wato ta zauna ya kashe ta? "Dan ubanki ina magana kina mini shiru? Shegiya uwar taurin kai" "Ammi idan kika yi mini baki wallahi ke zan lalacewa ba wani ba, domin sanda muke zuwa wajan malamai ana siye zuciyar mijina yana bani kuɗi Baffa bai sani ba, kuma ni da za ki sani a gaba kina mini mita so kike na koma ya yi ta dukana ya samu jaka?" "Jakar ce mana tunda ba za ki iya haƙuri da zaman gidan miji ba, tunda kike duk wahalar da Ridayya ta sha kin taɓa ganin tayo ya ji a gidan? Ba kalar uƙubar da bata shiga ba, yarinya ta zama kamar dabba don azabar gidan miji...," Yaya Zuhura ta miƙe tsaye ta ce "Ni da ban Ridayya daban, ba zan iya ba kuma ba zan jura ba, ya ce a biya shi kuɗinsa daman duk kuɗin da nake amsa ke nake bawa, wallahi ki nemi kuɗinsa ki kai masa babu ruwana ficika ban ci ba" a fusace Ammi ta miƙe tsaye zuciyarta na tafasa ganin Junaid a tsaye da kuma Zainu ta ce "Zuhura har wuyanki ya yi kaurin da ina uwarki za ki dinga faɗa mini haka? To oya zoki shige ki tafi gidan mijinki kafin na yi miki baki yanzu" Ƙunƙuni Yaya Zuhura ta fara ta ce "Duk wata masifa bake kika ja mini ba, idan don ina kwana a gidan nan ne sai na daina kima daina ganina bakiɗaya a gidan, sai na daina kulaki mu daina magana da juna" Junaid ya ce "This is serious, kin san me kike cewa kowa?" "Ina cikin hankalina ba hauka na yi ba, ni wallahi ban san me ya sa ba amma ji nake inama ba Ammi ce uwar data haife ni ba, dama ace Mami ce" Wani irin mari Ammi ta kaiwa Yaya Zuhura ta yi saurin kaucewa Ammi ta yi luuu ta kifa zuwa ƙasa bakinta ya daki jikin kujera nan take bakin ya fashe, ya fara fidda jini haƙori ɗaya ya gutsire. Da sauri Yaya Zuhura ta tattara kayanta tas ta koma part ɗin Mami da zama, Junaid da Abdullahi ne suka kama Mami tare da kiran family Doctor. A daren bakin Ammi ya haye ko magana bata iya yi, wai yau ƴarta da duk duniya ta fi ƙauna cikin yaranta ita ce ta yi mata haka? A gaske hakan ya faru ba zahiri ba? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un babban tashin hankalin Ammi bai shige tunani wai Yaya Zuhura ta koma part ɗin Mami gabaɗaya ba, ta daina mata magana gaba take da ita suna rayuwa kamar Musa da fir'auna. Ammi ta manta yadda ta raba ƙaunar dake tsakanin uwa da ɗiyarta tun tana jaririya ta raba ganawa, ta yi musu farraƙu gida ɗaya suke amma Mami taba iya ganin Ridayya ta yi mata magana kamar ba yarinyar da ta yi dakon cikinta ba har wata tara da wasu kwanaki, yarinyar data kusa mutuwa wajan haihuwarta. Wataƙila shukar da Ammi ta yi ce ta fara girba amma duhun dake cikin kanta ya mamaye ƙwaƙwalwarta har ta kasa lura da hakan. Daman Zainu jininta bai haɗu da Ammi ba, wani lokacin a dole take gaishe ta. Mami dake zaune cikin baƙar abaya wacce ta rufe mata tsohon cikinta, mace mai tsananin haƙuri, kawaici ɗauke kai, da nuna damuwa akan damuwar wani, ga kyau ga kyan hali ga kula da miji da tsantsan biyayya ta dubi Zainura ta ce "Mr tsiwa je ki duba abinci idan ya nuna, ki shirya dinner ok?" Zainu ta kwaɓe fuska tace "Mami wai tsiwar me na yi ne haka, Allah ki daina mini wannan shaidar ba kyau ke uwa ce" "Na ji uwar ƴan tsara zance" "Mami" Mami ta ɗaga Idanu ta kalli Zainura sai bata ce komai ba, Zainu ta ce "I love u Mami, u looks so young na matso a yi mini ƙani kowa yana da ƙani ban dani" Mami ta zare idanunta da suke farare ta ce "Na shiga uku, waye zai miki ƙani?" Da hannu Zainu ta nuna cikin Mami ta ce "I saw it, wallahi cikin haihuwa ne bana abinci ba" "Get out Zainu" Fita Zainu ta yi da gudu saboda ta san halin Mami bata ɗaukan nonsense akan abu, musamman tarbiyya ta yara, Zainu akwai karabbani bata ɗaukar raini kana yi mata zata maka nan take tana da wani irin kishi da uwarta da ƴar'uwarta Ridayya. Mami ta girgiza kai kawai ta sauke ajjiyar zuciya how long zata kasance tana ɓoye cikin? Bayyanar cikin na nufin abubuwa da yawa ta gwammace ta yi ta ɓoye wa har zuwa haihuwa tunda tana da jiki da tsayi cikinta baya bayyana sosai. Waya ta yi da Mahaifiyarta Dada tana ta yi mata taɓara irin ta auta. Tana zaune taga new number kuma special ta yi ta kallo haka kawai jikinta ya bata, a hankali ta ɗauki wayar danna answering call ɗin ta cikin wayar aka sauke ajjiyar zuciya. "Ridayyerh" Mami said; tana sakin murmushi da kunyar ƴar fari tattare da ita, Ridayya dake zaune ta ce "Mami ina yini" "Allhamd ya kike? Ya mijinki?" "Uhm lafiya lou, Mami ina Baffa da Zainura na yi kewar su sosai" "Zan basu numberki sai su kira" Mami na son tambayar Ridayya tana ina amma kunya take ji, Ridayya ta ce "Mami ina Japan tare da Abbiey, ki yi mini addu'a please" "To Allah ya tsare ya yi muku albarka, ki iya bakinki kinji, ki kira Ammi ko gaisa" "Uhm Mami kenan, sai anjima" Mami ta yi saving number Ridayya da Ƴar Abbiey ta saka emojin na love a gaba kana ta ajjiye wayar ta nufi bedroom ɗin da Yaya Zuhura ke ciki, faɗa ta yi mata sosai tare da nasiha mai ratsa jiki a ranar Yaya Zuhura ta koma gidan mijinta ba dan tana so ba. Abinda ta guda shi ta tarar ya dinga dukanta kamar jaka ya yi mata jina-jina ya tura ta waje a tsakiyar daren nan, gashi ƙofar gidanta tarin bola ce haka ta kwana cikin bola ga uban sauro tana zaune ta ji ƙatuwar kunama na yawo a jininta duk inda ta matsa sai ta sakar mata harbi ta dinga ihu ta kururuwa tana bugan gidan amma ya yi burus, makota ba wanda ya leƙo da ƙyar ta samu kunamar ta fita ta yi kamar zata zauce. Cikin weekend ɗin MB USTAZ Ya sauka a Nigeria ba tare da kowa ya sani ba, hatta Ridayya bata san Nigeria ya nufa ba, muhimmin zama ya kawo shi da ƴan jam'iyya. Tajj ne ya yi ya ɗauke shi zuwa keɓantaccen waje wanda yake prvt da securities sosai a wajan. Ustaz bai samu damar yin magana da Tajj ba saboda gajiyar dake jikinsa da kuma kewar rigimar matarsa, ya yi missing jaririyarsa so much. Meeting suka yi wanda a nan ne MB USTAZ ya amshi takarar, ya kuma yi sign ya yi hakan ne Only for his wife saboda ita, Only her. Sosai ƴaƴan jam'iyyar sukai farinciki nan akaiwa BM USTAZ photona wanda za a yi using dasu for posters. Dukda sun buƙaci ya tsaya ya yi magana da ƴan jaridu ya yi musu bayanin tsayawa takarar ya yi burus ya ce shi fa babu takura cikin lamuransa. Bayan ya yi wanka ya shirya cikin Robe Pyjamas ash ƙafarsa sanye da Zizor Men's Lightweight House Slipper. Gyara zamansa ya yi wayarsa a hannun bai samu cikakken lokacin kiran Ustaza ba, sai ya tura mata da saƙo na kalmomi kaɗan a taƙaice. _Ki saka kayan sanyi, ki kula da kan ki da kyau, take care baby_ Kafin ya ajjiye wayar yaga reply ɗinta very shortly ta ce _I miss u_ Murmushi ya ƙwace masa ya ɗan yi na gefen laɓe saboda Tajj dake gabansa, ganin ya shagala ya saka Tajj cewa "Shayar daka shanya ta bushe fa" Sai a lokacin ya ɗago kai ya kalli Tajj Baita sai ya ɗauke kai can can ba magana kafin ya nisa ya ce "Why?" "Me?" Ya ɗaure fuska ya ce "Tajuddeen don't pretend, why? U lie to me" "Taimako dai, ai gode mini ya kamata ka yi fa, saboda nasan duk duniya babu wata ƴa mace da zaka iya tarayya da ita idan ba Ridayya ba, shi ne ya sa na nemi ganawa da Dr na ce ya faɗi result ɗin test da aka yi maka cewa ka nakasa ba kuma zaka taɓa haihuwa ba" "Mugun abu" Ustaz ya ce idanuna still zube akan message ɗin Ridayya da ta ce I miss u. Umma da mamaki ta dinga kallon Dr ta ce "Ko ban ji daidai bane?" Dr ya ce "Haba Hajiya your daughter in-law is pregnant, kuɗin albishir kawai za ki bani" Wata uwar guɗa Umma ta rangaɗa tana fito da bandir ɗin kuɗi ta bawa Dr ta ce "Allahamdulillah, daman nasan lafiyan yaro na ƙalau kuma yana son matarsa kai na ji daɗin wannan labarin Ubangiji ya sanya namiji zata haifa yau zanga jinin Muhammmmd ashe ina da rabon gani" Mardiyya dake kwance wacce aka gama cire mata drip ta dinga zare Idanu tana shafa cikinta, zufa sai yanko mata take ciki kuma? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un. Ita dai Umma farinciki take yanzu dole Ustaz ya dawo gida ya zauna da matarsa su raini cikin tare tunda shi ya yi ya gudu. JAPAN.... Saukar cikin dare ya yi don haka yana fitowa daga mota ya nufi cikin gidan domin ya san dole ta yi bacci, abubuwa da yawa sun masa yawa, yana son yin magana mai muhimmanci da Ridayya yana son magana da Baba ƙarami and Umma too but bai shirya ba, ba haka ya tsara plan ɗinsa ba. Wanka ya yi ya sanya kayan bacci yana buƙatar green tea da dafaffiyar madarar shanu ga wani bacci dake cin idanunsa, a hankali ya murɗa handle bedroom tare da tura kansa ciki, wani ƙamshi ne mai sanyin gaske da nutsar da zuciya ya shiga hancin Ustaz, a hankali ya buɗe hancin yana shaƙa da kyau, cikin nutsuwa sabon yanayi ya fara maye gurbin gajiyarsa ya buɗe zuciyarsa da kyau domin bata damar tabbatar abinda take buƙata. Kwance can gefen gado ya hangota, ta ja pillow ta manne a jikinta, ta cure waje guda alamar sanyi na damunta, ya ƙarasa jiki babu ƙwari zuwa inda take,guntun hawaye ya gani ya bushe a fuskar ya girgiza kai yana jinjina rigimar Ridayya mara dalili da tushe, yanzu idan taso a zauna lafiya yanzu kuma ta botse gashi kullum sauya masa take ko dan kullum tsumin ƴan Maiduguri ƙara zama yake a jininta? Hannunsa ya kai zuwa cinyarta da niyyar tashinta sai dai me? He lost his mind ya kasa control kansa gabaɗaya, a firgice ta fara saboda zuwan abinda bata taɓa ji ba ta shiga kokawa amma taga Abbiey ɗin uwa baya cikin hayyacinsa wani gurnani yake yi a hankali. "Ka yafe mini Abbiey ban kumawa ban shirya ba, ka barni" Kuka take sosai ta fita hayyacinta domin ko a tarihi bata taɓa tunani wannan ranar ba, musamman da Abbiey ɗinta abubuwan da yake mata was very different da abinda Zameer ke yi, wannan with love and care yake da tsantsar soyayya, kulawa with romantic styles wanda shi kansa bai san ya iya ba, tsoro ne fal zuciyarsa a raunace yake komai. Ridayya rikituwa ta yi zuwa ƙasa saboda ta kasa ɗaukan al'amarin ya bita zuwa saman carpet ɗin. "No please Abbiey" "Yes Ustaz, kar ki shiga fushin ma'aiki allow me" "Abbiey am scared, ban shirya ba" "I didn't too,nima ban shirya ba tsoro nake ji kuma dr ya ce na gwada I'm just trying ba yi zan ba....," Tun tana kuka har dana shagwaɓa ta dawo zubar da hawaye wani irin kunyar Abbiey ɗinta ya mamaye zuciyarta ta kulle idanunta tana saurare zuciyarta dake buɗe tana ƙara ninka son da ta kewa Ustaz. Lokacin da komai ya faru Ridayya da Muhammad-Bilal Tahir Rano suka zama abu ɗaya, masoyan juna, ƴan'uwan juna, ma'aurata ya mayar da ita cikakkiyar matarsa ta sunna Ustaz bai san bakinsa ya buɗe ya ce. "Allahu Akbar, Allah ya yafe miki Ustaza na yafe ni Ustaz na yafe miki....... Ku yi comments tare da sharing❤‍🔥❤‍🔥🫶🏻 [5/8, 12:45 PM] null: *MUNAFIKIN MIJI 40* Mikiya Writers Asso.... Bright pens free batch Nimcyluv *A yi FOLLOWING CHANNEL ɗina domin samun update akan lokaci na Munafikin miji da wanda suke buƙata daga farko, ƙofa a buɗe take ga masu buƙatar ayi musu tallah* https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T Ustaz ya sauke numfashi mai huci ji yake kamar ya buɗe baki ya kurma ihu tare da kabbara ga Ubangiji, amma abinda ya ke ji ya danne duka wannan yanayin ya fi gaban ihu, balle magana domin ji yake kamar wutar lantarki ke jan shi tana fisgarsa tunda Umma ta haife shi har kawo yanzu bai taɓa jin abu makamancin haka ba. Tun daren jiya har wayewar gari sabo yake jin kansa, yana ta son furta ko kalma ɗaya ne,amma idan ya kalli Ridayya da abinda ta bashi sai ya ji duk abinda zai faɗa ya yi kaɗan, Ridayyansa ta fi karfin hakan. Ya sauke numfashi a karo na babu adadi ya juya a hankali ya zuba idanunsa akan ta, ta kwaɓe fuska busassun hawaye duk a fuskar saman idanunta ya kumbura sosai. Ganin tana ɗan firgita ya saka shi miƙa hannunsa zuwa wuyanta ya ji zafi sosai. Ba ki ya buɗe zai yi magana maimakon furta abinda ya yi niyya sai furucinsa ya zauya zuwa. “Allahu Akbar, Ma sha Allah walihamdulillahi wallahu Akbar. Allahamdulillahi godiya ga uwar mataye, godiya ga baƙar mace godiya ga Ustaza data amshi budurcin Muhammad Bilal ta mai da shi mijin aure na sunna” Sarai Ridayya ta ji shi amma ta yi shiru, wani irin kunyarsa ta fara ji,nauyinsa da kimarsa sun ninku fiye da kima a zuciyarta da idanunta. Ta sha wahala ƙwarai a wajan Zameer idan har zai yi tarayya irin haka da ita sai ya shaƙe mata wuya, kafin yanzu gabaɗaya shatin yatsunsa ne a wuyanta wani lokaci har hijira numfashinta ke tafiya. Bata taɓa jin wani abu ki sani wani abu wai shi emotions or feelings ba sai a daren jiya. Abbiey ɗinta ya nuna mata mene duniyar soyayya da rayuwar auratayya ya bambance mata ƙauna da biyan buƙatar kai da kai, bata cikin haiyacinta amma ta ji muryarsa a jiyan bayan faruwar komai yana tambayar ta a hankali daidai kunnenta yana shafa kanta. "Are You okay with me? Kin gamsu or do you need more? Are u happy with me? Is there any problem with? Or am not romantic man, banda kunya Ustaza rayuwarmu ce wannan" Sanda yake furta hakan ji ta yi kamar ta nutse, ta ko'ina Ustaz ya sha bambam bai yi son kai ba, bayan ya nutsu da ita yake tambayar ko ta gamsu saɓanin wasu mazan kansu kawai suka sani da son samu biyan buƙata shikenan. He is so lovely! Her world. Ya kasa fita daga ɗakin dukda yunwar dake damunsa ainun tsoro yake ko ya yi mata wani, kar Ustaza ta yi fushi da shi shi kam ya bi Allah da Manzonsa kuma ya bi Ridayya sau da ƙafa. Motsin yatsun ƙafarta da suke riƙe a hannunsa ya ji, yana juya ta yi saurin rufe idanu daga kallon bayansa ya girgiza kai shi a duniya yanzu bai san mene bai sani ba don gane da ita idan har baccin ƙarya take yana ganewa. Ya matse yatsun tare da girgiza ƙafar sai ta fashe da kukan ƙarya tana murza idanunta. "Wayyo Baffa zai cire mini ƙafa, Auchiii" "Sharri Ustaza" Ya furta a hankali kuma a nutse yana matsawa daidai kanta inda take kukan wiwi. Ya dinga kallonta can ya ce "Ki gasa jikinki" Ta tattare duka duvet ɗin a jikinta ta fara ƙoƙarin sauka ya riƙe ta marairaice ta ce "Uhm ta ba zan wankan ba" Ya sake ta yana ƙoƙarin tashi ta yi saurin shigewa toilet dukda ciwon da kwankwasonta ke yi mata hatta ƙirjinta a zabar zafi yake. Bayan ta shiga Ustaz ya tattare gadon ya gyara ya fito mata da wata blue ɗin riga iya qiwwa mai sauƙin nauyi a jiki. Fita ya yi zuwa sashinsa sai a lokacin ya ji gajiya ta saukar masa ainun shi kansa nasa kwankwason ciwo yake he wonder why? Maybe don ta amshi budurcinsa ne. Wanka ya yi sosai ya shirya cikin English wear black colour suka ƙara fidda hasken fatarsa irin ta larabawa hannunsa rigar half damtsensa ya fito sosai wandon iya qiwwarsa gargasar jikinsa har ta yi yawa amma tai wa fatarsa kyau sosai da gaske ta yi kwance luf luf ya samu kansa da ɗaukan turaren daya siyo for the first time a rayuwarsa, ya dinga kallon turaren na ROJA DOVE AOUD a hankali ya dinga fesawa har su ƙasan wuyansa bayan kunne gashi kamshin na musamman ne, sai a lokacin yake duba price ɗin turaren lallai ya kashe kuɗi. Ya tattare sumarsa zuwa baya a karo na farko ya saka abu ya ɗaure dukda haka sai da wata ta kwanta gaban goshinsa ya dinga sakin murmushi shi kaɗai gabaɗaya wankansa na Ridayya yau. Ya kalli kansa sosai. Sanda ya koma bedroom ɗinta ya sameta zaune a kan stool na gaban madubi tana ganinsa ta yi saurin ɓoye zuma da kwalaccar wajan Hajiya Nana. Ya buɗe idanunsa a bayanta dake ta glowing na baƙar fata. Gently a hankali ya ƙarasa ya ɗora hannunsa a kafaɗunta ta yi saurin ɗago kai ta cikin madubin suka haɗa idanu ta saki baki tana kallonsa wallahi idan ba magana Ustaz ya yi ba, ba zata taɓa cewa yana jin Hausa ba. "Uhm cikakken Bahaushe ne mijinki bar tunani" Ta yi mamakin yadda ya fahimta, ƙarasa shiryata ya yi kanta a ƙasa ya dakko kaya ta yi saurin cewa. "Zan iya sawa fa" "Are you sure?" Kin tabbata? Ta ɗaga masa kai ta ɗauki rigar zata saka ya yi saurin amsa ya ɗage hannayenta ya zura mata ta yi baya kamar zata faɗi ya yi saurin jawota gefensa a kunne ya ce "No more secret between us Baby " Ita dai Ridayya yau ba Ustaz take gani ba, ba kuma Abbiey ba yau Yaa Bilal ne da kansa kuma Md na bankin Fidelity dake Lagos. "Bacci zan yi ni" "No, jikinki zai ciwo ki sha tea da paracetamol ko?" Ta maƙale kafaɗa idanunta ya cicciko da hawaye te nemi rikice masa, sai ya kama hannunta a hankali ya jata wani ƙaramin parlorn da yake can gefe amma yana da sanyi saboda gabaɗaya taga da ƙofar na glasses ne hakan ya saka suke ɗaukan sanyi sosai duk snow a jikinsu, suna shiga ya kunna heater ta zafi. Sanyin ya rasa Ridayya ta yi saurin maƙale wa a gefen shi tana juyar da fuskarta ya zaunar da ita a kujera mai tsayi, wayarsa ya fara danna ba jimawa door bell ya fara ƙara ya ajjiye wayar a cinyarta ya nufi ƙofa ta bi bayansa da kallo tana lumshe idanunta. MB USTAZ ya dubi baturen saurayin da yake masa magana cikin harshen turanci, Ustaz bai ce komai ba yana tsaye hannunsa zube a aljihu jin surutun mutumin ya yi wa ya saka Ustaz jan breakfast table ɗin tare da rufo ƙofar. Yana juyawa Ridayya ta yi saurin rufe idanu tana shassheƙar kuka ya ja table ya ajjiye tare da rage tsayin shi daidai su. Ya kalleta murya ƙasa a taushashe cikin kulawa ya ce "Ƴan mata ya dai?" "Abbiey jikina ciwo, bayana,ƙafata, ƙirjina wayyo Abbiey na mutuwa zan yi" Nan da nan ya rikice Ridayya ko tausayin Dattijon Abbiey ɗin nata ba ta yi daman haka soyayya take tsakanin yarinya da babba, kuka take sosai duk ta ɓata fuskarta hadda jinjigar zazzaɓin ƙarya. BM USTAZ ya rikice duk da ƙoƙarin riƙe kansa da yake wajan ganin ya ja girmansa amma zuciyarsa ta yi masa gardama ya kama hannunta ya ce "Na bi Allah na biki Babyn baby ki bar ni haka nan Please" Ta yi shiru ya matsa sosai yana rarrashinta "I lost my words, i have no words wajan magana tunjiya ki bar nutsuwa ta ta dawo" "To ni yunwa nake ji" "Oopps" Tea ya haɗa mata mai kaurin gaske yana zafi ya zuba mata roman naman da aka dafa mai ruwa-ruwa ya saka cokali a shayin ya nufi bakinta ta ɗauka kai tana kumbura fuska. Ustaz a ransa yana jinjina shagwaɓar Ridayya dukda daman ya san halinta idan ta samu sake wajansa tun tana ƙarama "What?" Ta ɗauke kai ta ce "Ni a bulunbuti nake so" Da wani irin yanayi ya zaro idanu waje cike da tashin hankali da fargabar inda zai nemo wata bulunbuti. A gida Nigeria Umma ce tsaye a kan Mardiyya ta gama kwara amai sosai take laulayi ta jigata ainun Umma kuma baki har kunne ta kusa samun jika sai kashe uban kuɗi take komai ta ɗauka ta ce Mardiyya matar Babana zata haifawa Bilalunta ɗa. Yanzu ma tana riƙe bowl wanda ta haɗa kwaɗon rama a ciki ya sha tumatur ta ce "Oh ni Hadiza yanzu a yi ace komai mutum ya ci sai ya dawo da shi? Ki daure ki ci wannan" "Umma wari abin hannunki yake zan yi amai" Umma ta ce "Ikon Allah, shi ma bakya ci? To me kike so?" Mardiyya ta lumshe idanunta abubuwa da yawa ke mata yawo a rai babban burinta bai shiga Ustaz ya dawo ba. Ta sauke numfashi ta ce "Farfesun kai da ƙafa nake so, shi ma na ɗan taure irin me warin nan" Umma ta tafe ƙirji ta ce "Wanne irin ɗan taure ina za a iya tantancewa ni Kubura" ita dai Mardiyya shiru ta yi Umma ta yi murmushi ta ce "Ai shikenan duk ranar da mijin nan nawa ya zo duniya sai na dungure masa kai da hanci na wahalar daya saka ni, nasan fari jajur za ki haifo tunda ma sha Allah daga ke har Babban mutum farare ne tas a wanke kuke, Ubangiji ya ƙara nisanta shi da waccar munafukar mai baƙar fuska kamar zunubi, gwara da Allah ya raba wannan matsiyacin auren na ƙaddara da babu Makka duk ta haifa jama'a munana yara masu kalarta da ba zan taɓa amsar su matsayin jikokina ba" Ta ja ƙwafa rai ɓace haka kawai ta tsani Ridayya Mardiyya ta ce "Umma amma Mai sunan sweetheart kyakkyawa ne kalli kama suke da Ustaz fa" "Allah ya yi mini tsari Ridayya ta haifi mai kama da jinina can ta gwale mata wallahi, kune yaran zamani amma babu mamaki shi ma Bilal ɗin data haifa shege ne bai yi kama da uwar ba, bai yi kama da mijin ba Zameer yake, wallahi ba mamaki shege ne suna can suna ta ɗawainiyya da ɗan haram Allah dai ya tuna mata asiri" Mardiyya ta ɗan yi shiru ta ce "Umma yaushe Ustaz zai dawo duk na damu, kunya nake ji na yi ta zama kina ɗawainiyya dani,kuma a gida sai tambayarsa ake yi sai dai na yi ƙarya na ce tafiya ya yi wajan aiki. Bansan muhimmancina a wajan shi ba, wallahi ke na kewa biyayya" Umma ta sauke ajjiyar zuciya a ɓoye ita kanta bata san inda Babban mutum yake ba. A zahiri ta ce "Ki kwantar da hankalinki, matsayi kuma ai kin sani karki manta cikin Bilal ne a jikinki, duk na mijin da ya ti tarayya da matarsa yana nufin ya aminta da ita kuma yana son ta. Kar ki saka haka komai a ranki ki raini cikinki kuma zan kula da ke Babban mutum kuma na miki alkawarin dawowarsa da wuri haka" "Shikenan Umma na gode amma ko numbersa babu?" "Zan bincika miki, bari na je a nemo kai da ƙafa" Mardiyya ta yi saurin toshe hanci ta ce "Don Allah umma ɗan matsa wari kike,ina nufin warin rama" kafin Umma ta yi magana ta fara kelawa amai a saman gadon ko tashi ba ta yi ba. Umma da kanta ta dinga bulayin neman kai da ƙafa na ɗan taure. Bayan ta gama komai ta kawowa Mardiyya taƙi ce ta ce daman wurin ɗan tauren kawai take son ji. Baba ƙarami ya manta wayarsa a ƙaramin parlorn da yake sashinsa Umma na zuwa ta fara bincike cikin sa a ta samu wata sabuwar number da aka yi saved da Aboki. Ta san Babban mutum kawai baba ƙarami yake cewa. "Me kike nema ne haka Hajiya Hadiza?" "Ba komai, cewa na yi baka ce komai akan cikin Mardiyya ba?" Ya kalleta ya yi murabus bai ce komai ta ce "To murmushin mene kake? Ina tunanin daman babban mutum rabonsa a tattare yake da Mardiyya ya kamata ka ce ya dawo gida haka, tunda ita muguwar mai baƙar aniyyar ba zata dawo ba saboda tana baƙin cikin ta ganshi tare da Karfi in sha Allah sai Ubangiji ya ɗorawa Ridayya soyayyar Ustaz kuma a banza ya mata nisa" "Amin, hakan muke addu'a " "Me? Yanzu dai ka faɗa masa" "Ki faɗa masa da number da kika ɗauka" yana faɗin hakan ya fice ya bar mata wajan. Ammi abin duniya ya yi mata yawa Junaid ya kasa samun matar aure saboda matsalar Genotype, ga Balkisa ta dawo gida ba lafiya ga Yaya Zuhura miji ya yi mata dukan mutuwa har kwanciya ta yi a asibiti Mami ce ta kula da ita, ko kallonta ta lura Yaya Zuhura bata son yi yarinyar data fi karfin fiye da kowa a yaranta amma yanzu wai gaba da ita, kamar am musu farraƙu ta ɗauki alhakin hakan ta tattara akan Mami ita ce ta yi mata asiri. Gashi ta kwace gida abinda bata ƙauna kenan ga Baffa ya juya mata baya kwana biyu komai cuɗe mata. Ta juya ta kalli Burhan da baya cikin haiyacinsa ta ce "Yanzu tunda ba Ridayya ga wani sabon plan, Zainura ita ce target ɗina ka san duk yadda ka yi ka samu kusanci da ita, idan har tsarinmu ya yi daidai sai a nan gab da bikinku ka ɗirka mata ciki ka gudu yanzu ba kuɗi ne a gabana ba, kawai rayuwar yaranta nake so na wargtsa kamar yadda komai nawa ya juye na yi nasara akan Ridayya na bata wahala tun tana zanin haihuwa na rabata da iyayenta, na juyar mata da tunani bayan n bata maganin shaye-shaye na ƙona mata harshe da wuƙa, ni ce na dinga assasata akan Zameer wannan shi ne babban abinda ba wanda ya sani, na dinga ƙarfafa mata qiwwa. Daman na ce ba zata taɓa zama wata a duniya ba gashi ba inda ta je ta rabu da mijinta, Bilal ya aureta uwarsa ta saka ya sake ta kaga an fara lissafa mata aure kenan, in sha Allah haka zata dinga aure tana fitowa ko wanne ta je kuma ta haifi ɗa ɗaya, kuma duk ta haifi lalatattun yara" Ta juya ta kalli Burhan da yake busa sigari ta ce "Wai kana jina ma? Idan kana busa shegiyar abar nan ba komai kake fuskanta ba" "Na ji, ni ban iya wata soyayya ba" "To daman ina mashayi ina soyayya ka nutsu ka tambayi abokai" Ya miƙe bayan ya ɗauki wayarsa ya ce "Bari na doƙa yanzu abinda za a yi ki nemi jauwalarta ki bani shaɗayanta ko?" "Mene shaɗaya kuma?" "Ke ciki ce fa, ana miki inkiya bakya ehhh, number wayarta nake nufi naka yarinyar mai ƙirice matsalar kawai yama sunanta kika ce ta fita haɗewa" Ammi ta ja tsaki ta ce "Ji wawa ba maganar yayar muke ba ta ƙanwar muke" "Ohh sure zahabu zahabu ya sunan beb ɗin?" "Zainura" Burhan ya lissafa faɗar Zainura ya kasa sunan ya masa wani iye yane. Sai kawai ya ce “Zinu" Cikin sa a yana fita ya yi karo da ita ta dawo daga makaranta dake weekend ne ana ta kiran sallar magriba tana ganinsa ta haɗe rai bai taɓa tsayawa ya mata kallo sosai sai yanzu ba ya tsaya a hanya ya cake ta haɗe fuska cikin muryarta ta tsiwa ta ce "Malam ka tsaya mini a hanyar shiga gidan ubana?" Ya yi mata shiru sai warin sigari yake ta yi saurin rufe hanci Zata shige ya yi saurin kama hannunta tana juyawa ta ɗaga hannu ta kifa masa mari ta ƙara kifa masa wani ta ce "Sakarai shashasha ko an faɗa maka ni irin ƴan iskan da kake bi ne? To ɗabi'ata ta sha bamban da taka jikina mai tsarki ba irin naka ƙazami...." Hannunta ya fisga da ƙarfi ta yin saurin matsawa kusa da shi saboda yadda ta ya jawo hannunsa idanunsa jajur sai huce yake yatsun hannun Zainura raɗau a fuskarsa ya zaro wuƙa a aljihu nan Zainura ta firgita amma ta dake jiran yadda zai soka mata kawai take. Idanunta rufe ba zato ta ji ya ce "Ina son ki Zinu ki koyi so na dole" yana faɗin hakan ya sake ta ya fice kamar walƙiyya. Junaid bai samu faɗawa Baffa uzurin Zameer ba yama manta shaf dake baya yawan zama always yana wajan aiki. A ɓangaren Zameer baya iya bacci ya zama kamar sauna matarsa Ridayya kawai yake muradin gani kusa da shi duk duniya babu wata ƴa mace dake gabansa sai Mai son shi Ridayya kuma zai yi komai saboda ya mallaketa shi kaɗai zai rabata da ko wanne namiji. Ya shirya cikin shadda skyblue ya nufi gidansu Ridayya da addu'ar Allah ya sa ya haɗu da Baffa ko Junaid ko ita kanta Ridayya ƴar Aljanna. Sadauki ya zama sai addu'a ya kaɗaita sosai sai ya yi kwana da yini a ɗakinsa sosai suma ta taru a kansa da fuskarsa kamar mahaukaci ya daina walwala ko da Mother ne. Tajj ya zo har gidan shi kansa ya firgita da yanayin Sadauki ya faɗawa Hajiya Azizat gaskiyar Ridayya ta yi aure amma kar ta faɗawa Sadauki idan lokaci ya yi zai sani. Takarar BM USTAZ ta kankama ko'ina an sanya poster ɗinsa da inkiyar Fari mai farar aniyya ya samu karɓuwa wajan jama'a dukda ba a ba a bada damar fara yin kamfen ba. Al'amarin daya ƙara gigita Mardiyya soyayyar Ustaz ta dawo sabuwa fil a ranta gefe guda mata suna fara crushing akan shi. Yayinda shi kuma yake ƙasar Japan zaune da matarsa ko wanne meeting ta zoom yake halatta sai ya sauka a Nigeria har ya koma ba wanda ya sani. Har yanzu Ustaz ya kasa furta komai akan first night ɗinsa da yake cewa Ridayya ta amshi budurcinsa, duk abinda ya lissafa sai ya ga bai dace da Ridayya ba. Bai jima da shiryawa ba suna zaune akan duguwar kujera daga shi sai wata haɗaɗɗiyar rigaw armless amma mai kauri ya zuge zif ɗin gaban rigar saboda yanayin da yake ciki a yanzu ke haifar masa da zafi a ƙofofin gashin jikinsa. Ridayya kuma na kwance a jikinsa ta miƙe ƙafarta a saman tashi tana wasa da wayarsa shi kuma ya yi shiru yana shafa samar kanta data kunce kitson. Ta ji yana shige gona da iri ta yi masa banza a hankali ta ji ya ce "I am very lucky" "Dame?" Ta tambaya hankali ya ɗago ta bayan ya kalli cikin idanunta ya ce "Ko wanne namiji yana amsar budurcin matarsa ni kuma matana ta amshi nawa dole na yi wa Ubangiji godiya" Ta ɗaure fuska ta ce "Magana kake faɗa mini idan na fahimta ka auri bazawara" Nan da nan fuskar Abbiey ta yi jajur fushinsa wanda bata taɓa gani ba ya bayyana ya dinga kallonta da wani irin firgitaccen yanayi goshinsa ya fara fidda zufa ya kama hannunta duka biyun kamar zai yi faɗa sai ta ji muryarsa a ƙasa ya ce "Ridha" ya yi shiru ta kasa kallonsa "Ɗago idanunki ki kalli cikin idanuna" a hankali ta kalle shi abinda ta gani a idanunsa was very different yanayi ne da babu wanda zai iya ganewa amma zuciyarta tuni ta buɗe wani irin son Abbiey ɗinta ya dunga huda mata ƙirji yana shiga zuciyarta "Na taɓa miki maganar mijinki ko aurenki na baya? Kin taɓa ji na yi magana akan surarki ko wani abu? Balle budurci ko bazawara?" Ta girgiza kai "Buɗe baki ki yi magana" ta yi shiru cikin faɗa ya ce "Zan watsa miki yatsu a fuska Ustaza, gaggauta magana Ustaz na jinki" Muryarta na rawa ta ce "A'a Abbiey" Yana riƙe da hannunta ya matse alamar hukunci yake mata can ƙasa daidai yadda za ta ji cikin wata kalar murya ya ce "Ban taɓa damuwa da wannan ba, ba kuma don shi na aureki ba, ba don shi ya sa nake son ki ba. I'm just love you for the sake of Allah for the sake of love Ustaza, ina ta laluban dalilin daya sa nake son ki tun kina jaririya ina goya ki har kika girma na ji ina son rayuwa dake na kasa, nasan soyayyar gaskiya bata da wani dalili" ya yi shiru ya murza tsakiyar tafin hannunta "A shekeran jiya na samu amsar tambayata, Ridha bayan son tsakani da Allah da nake miki na ji a raina tarbiyyarki kawai na yarda da ita a cikin ƴan matan duniya, saboda ni na tarbiyantar dake na kare mutuncinki har zuwa gidan aurenki, matan yanzu abin tsoro ne wayewa ta musu yawa wasu soyayya da suke abin tsoro ce, Ridha ba kunya za kiga mace tana bari namiji yana riƙe mata hannu. Innalillahi Allah ka yafe musu Allah ka yafe masu wallahi da na auri Iran matan nan gwara na zauna haka, ke kam ina alfahari dake kin riƙe mini kimarki da mutuncinki na ɗiya mace" Gaban Ridayya ya yi mummunan faɗuwa ƙirjinta ya duka da ƙarfi, wani tashin hankali ya mamaye ta nan take jikinta ya yi sanyi tausayin Abbiey na yardar da ya yi mata ya kamata idanunta ya cika da hawaye. Ustaz ya saki murmushi har dimple ɗinsa na shigewa yana riƙe da hannunta a hankali ya kai yatsunta zuwa bakinsa ya tsotsa tare da sumbata ya ce "A gare ni babu wani abu da nake ɓoye miki, babu shi don Allah idan akwai abinda ya kamata na sani tun yanzu ki faɗa mini na san yadda zan fuskance shi, bana son rayuwar ɓoye abu idan na miki abu kawai ki faɗa mini ok?" A hankali ta ce "Ba komai" ya tsora mata idanu kamar mai fahimta "Are you sure?" Ta jinjina kai ya jawota jikinsa ya rungume yana jin yanzu abinda ya yi masa saura gashi ga muradin ransa "Thanks for the gift, thanks for the virginity, i appreciate it. Ubangiji ya yi miki albarka ya ba ki aljannar firdausi, u make my day kin mai dani cikakken mutum" Idanunta cike da hawaye ta ce "Ka yafe mini Abbiey, bana jin na cancanta godiya ƙaddara ta zo ba yadda muke tunani ba ban baka.....," "Shhhh!!" Ya ɗora yatsarsa a bakinta "Ni budurci na amsa da gaske Ustaz i feel very comfortable with you ban yi zaton haka ba, ke ta musamman ce Sayyada ki saki jiki Allah yana kallo ina son soyayya ina son romantic love, ba zan ɓoye miki me na ji idan na gamsu baya nufin kema haka karki cuci kanki if u need more, all you have to do is ask I'll be the best husband for you bani da bakin gode miki ba kuma zan yafewa kai na idan zuciyata bata cika da soyayyarki ba" Kunya duk ta kama Ridayya ta ɗaga kai ta kalle shi ya kashe mata ido ɗaya yana ɗage mata curin girarsa "Na gode" "Mu je ki kai ni asibiti" "Baka da lafiya?" Ya dubeta yana sauya yanayi sosai ya ce "Tun first night ɗina da kika amshi budurci jikina ke ciwo ba ki gasa ni a ruwan zafi ba ban sani ba ko na ji rauni " "Uhm uhm kai Abbiey " "Serious Ridha a lokacin ihu nake ta cikin zuciyata" ta yi saurin kifa kanta a ƙirjinsa ya rungume ta sosai da kyau a jikinsa yana shaƙar ƙamshinta a hankali yake sake shigar da ita jikinsa sukai shiru for some minutes zuciyoyinsu na dukawa a tare suna buɗewa tare da amsar yanayin iya wahala Ridayya ta wahala sosai domin ji ta yi kamar bata taɓa sanin ɗa namiji ba, amma dole ta gyara jikinta ta daure tunda ita ba matar novel mace da za a ce miji ke yin komai. “Ridherh...," “Abbiey" ta amsa a nutse tana wasa da dugun gemunsa mai kyau. “I love you!” Ya ce a cikin kunnenta ya hura mata iska a kunne daidai lokacin wayarsa ta fara ringing bisa tsautsayi hannun Ridayya ya danna amsa kiran dake wayar nada speaker sosai suke jin me ake cewa banda Ustaz daya ya tafi love world. Ridayya har tsakiyar kanta ta ji kalmar names ya sha faɗa mata sanda suke University bata taɓa jin tasirin kalmar ba sai yanzu,ta ƙara bambance so da birgewa jikinta ya saki ta kasa ɗagowa a hankali wani yawo mai ƙamshi ya fita daga bakin Ustaz ya sauka a kunnen Ridayya muryarsa bata fita sosai kamar zai yi kuka ya ƙara cewa “I love you ” Daidai lokacin ta cikin wayar suka ji an ce "I love you too sweetheart, na kira na yi maka albishir da cewa ina juna biyu ma'ana ka tafi ka bar ni da cikinka...... 08164069385 Ga masu buƙatar ayi musu tallah . [5/12, 12:42 AM] null: *MUNAFIKIN MIJI 41* Mikiya writers asso... Bright pens free batch Nimcyluv *A yi FOLLOWING CHANNEL ɗina domin samun update akan lokaci na MUNAFIKIN MIJI da wanda suke buƙata daga farko, ƙofa a buɗe take ga masu buƙatar ayi musu tallah* https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T Ƙoƙarin tashi Ridayya ta yi cikin sauri a nutse kuma Ustaz ya damƙe hannunta yana ƙara kame fuska saboda saukar muryar Mardiyya da ya ji. Ta cikin wayar Diyya ta ƙara cewa "Baby na yi kewarka sosai na yi kewar mijina, ya kamata ka dawo tunda mayyar data na ce maka ka sake ta, kuma kai ma ka tabbatar mini baka son ta" da mamaki Ustaz yake jin furucin na Mardiyya ya lumshe idanunta zuciyarsa na matsewa yana jin yadda hannun Ridayya ke rawa wanda yake da tabbacin ba iya hannun bane hatta zuciyarta rawa take. Mardiyya ta gyara zama idanunta akan wata ƙawarta data zo gidan ta ce "Ni daman na san bakai ka zaɓi Ridayya ba cusa maka ita aka yi,kuma gashi Umma ta saka ka rabu da mugun iri. Da ina cikin damuwa yanzu na samu nutsuwa ganin ka zama nawa gani ɗauka da cikinka wanda nake ƙoƙarin haifa maka, baby naga ka fito takara ashe kaga zan zama matar gwamna her Excellency na ji na ƙara son ka" Barin ta ya yi ta yi magana son ranta don baya katse mutum a tsarinsa ya sauke numfashi kamar zai yi magana sai kuma ya kashe wayar domin ba ita ɗince a gabansa ba yanzu. Ridayya da sauri ta ƙwace hannunta ta miƙe jikinta na rawa kuka ne ke ƙoƙarin kwace mata amma ta hana faruwar hakan, sosai batun cikin Mardiyya ya saka ta cikin firgici da kaɗuwa da kuma jin ta furta wai Ustaz baya son ta, Umma ta saka ya sake ta duka wannan abubuwan mene gaskiyar batun? So da Abbiey ke cewa ta amshi budurcinsa faɗa kawai ya yi don ta yi farin ciki ko mene? Kar dai ya munafurce ta ne? Ta rabu da MUNAFIKIN MIJI kuma wannan da take saka ran ya zame mata bango abin jigina ya zama silar yaye war baƙin cikin data ƙunsa a gidan Zameer shi ma ya kasance MUNAFIKIN MIJI. Innalillahi wa'inna ilahir raji'un dunƙulewa zuciyarta ta fara yi tana matsewa waje guda ɗacin da ranta ke yi mata har saman harshenta take jinsa. Ustaz ya yi shiru shi kansa maganar Mardiyya ta jikkita masa zuciya yana son rikicin Ridayya bai kuma shirya rufe ta ba, babu ƙarya a zaman su. Yana ƙoƙarin miƙewa ya bi bayanta ya ji ƙarar faɗuwar abu dimmm! Yana juyawa ya ga Ridayya kwance a ƙasa goshinta ya daki gefen center table nan take ya fashe glasses ya caki gefen goshinta jini ya fara zuba. Idan ta yi yunƙurin tashi sai ta sake yanke jiki ta faɗi, jikinta ya fara karkarwa tana kanannaɗewa kumfa ya fara fita idanunta rufe amma hawaye ne ke fita sosai nan da nan ta fita cikin haiyacinta rabon da farfaɗiyya ta tasar mata har haka shi kansa Ustaz ya mance yama ɗauka ko ta daina. Ya riƙe kansa da kyau cikin sauri ya kunna karatun Alkur'ani ya ɗakko ladduma ya rufe ta gabaɗaya bai san wanne irin mataki zai ɗauka akan Diyya ba, ba zata ja masa masifa kullum rabin ransa tana faɗuwa ba. Ya jima durƙushe a gefenta idanunsa ya sauya ƙirjinsa ya ƙara buɗewa a hankali ya ga fitsari na jiƙa laddumar can ya ji ta saki ajjiyar zuciya bacci ya ɗauke ta. Bata san adadin lokacin data ɗauka tana bacci ba, ba kuma ta san mene ya saka ta bacci har haka ba ta farko tana buɗe idanunta da suka mata nauyi sosai ɗakin duhu sai ɗan ƙaramin haske ta miƙa hannu ta kunna haske a hankali ta jikin gina da jikin frame fuskar gadon sai a lokacin ta lura da sauyin kayan jikinta ga ƙamshin Abbiey ya mamaye ɗakin wanda hakan ke tabbatar mata bai jima da barin wajan ba. Bata son tunawa amma kamar yanzu furucin ke fita ta ci kuka son ranta wataƙila bata cikin matan da suka yi dace da gidan miji wataƙila bata cikin mutanen da za su rabauta da farinciki a nan duniya. Zuciyarta ce ta ce "Kar ki zama mai butulcewa rahamar Ubangiji, gode masa da iya abinda ya ba ki da kuma abinda kike dashi, ki tuna rayuwar da kika yi a gidan iyayenki babu mai son ki sai Abbiey, kin zama mujiya gidan ubanki, mahaifinki ya ce ke ƴar zina ce, matar uba ta shayar dake uƙubar da ba za ki manta da ita ba, wacce ta haife ki bata son haɗa inuwa dake, ko wanne yaro gudun ki yake saboda kasancewar ki baƙa mummuna. Ridayya kin faɗa tarkon ɗa namiji saboda ki gujewa azabar da masifar gidan iyayenki, kin nuna masa so sa tunanin ya dace dake da tunanin kina son shi ba ki san birgeki kawai yake ba, kin yi amfani wahalar da kike sha wajan ganin kin bar gidan hakan yasa kika amincewa MUNAFIKIN MIJI, ruɗin zuciya, dana kalaman soyayya da tunanin idan Zameer ya bar ki ba za ki samu wani ba, ya saka kika amince kuka ai bata abinda a yanzu yake ƙoƙarin tarwatsa rayuwarki. Kin yi rayuwar aure a gidan Zameer kin zama baiwa kina rayuwa da karuwar mijinki da tunanin ƙanwar mijinki ce, kin sami mijinki turmi data ɓarya, ya aure ki a caca ya raba ki da kowa naki ya miki duka ya karya ki ya ƙona ki a fuska. Ƙaddarar auren MUNAFIKIN MIJI bai barki haka ba, ya mai dake mahaifarsa kika fuskance wulaƙancin ƴa ƙauyen Nahutun Batsari, suka jingina ki da sunan Maita saboda halittar da Ubangiji ya miki, wannan bai gamsu ba aka wayi gari an kawo ɗan shege da mijinki Zameer ya haifa. Ki duba girman abubuwa nan duk kika jure kika shanye saboda kina neman rabauta da Aljanna, kuma kika ɓoye wasu hallayen namijinki saboda ɗan da kuka haifa da shi da kare mutuncinsa har zuwa girma, ba ki da laifi Ridayya ƙaddara ke ɗawainiyya da rayuwarki kuma babban abin farinciki Ubangiji ne ya hallace ki ni'imomin da ya yi miki suna da matuƙar yawa....." Miƙewa ta yi jin yadda zuciyarta ke faɗa mata abubuwa ta zubawa kanta idanu ta cikin madubi wasu hawayen na sake biyo saman fuskarta a fili ta ce "Kenan ba zan yi farinciki ba? Komai yake faruwa dani ƙaddara ce ko kuma don na kasance mummuna?" "Mu kira hakan da ƙaddara" rufe idanunta ta yi da saurin tare da ƙoƙarin shigewa cikin bedroom ya kama hannunta ɗaya ta juya masa baya ya saka hannu ya juyo da ita suka fuskanci juna idanunsa zube a kanta yana ƙanƙantar dasu ya nutsa ganinsa sosai da kyau "Fushi Ustaza akan wannan abin?" "Wannan abin?" Ta sake maimaita wa a zuciyarta ƙoƙarin shanye hawayen take muryarta na karkarwa ta girgiza masa kai, kanta a ƙasa ya tsare ta da manyan gajiyayyun idanunsa masu kaifi da sawa ta manta wasu abubuwan ta san baya amsa magana da ka "A'a ba komai ni ba.....," Sai kawai ta fashe da kuka da sauri kuma ta shige bathroom tana sakin wani irin raunataccen kuka shikenan wanda ta saka ran zai bata farinciki ana shirin rabata da shi. Tana buƙatar mai bata shawara tana buƙatar wani kusa da ita ji take at anytime zuciyarta zai iya bugawa. Ustaz ya ja baya ya zauna saman gadon yana mai sakin yalwataccen murmushi abubuwan daya gani cikin idanun Ustaza sun saka zuciyarsa nutsuwa, he didn't see anything yet but an enternal love da wani irin pure heart zuciya cike da kishi. Ta shi ya yi yana rage kayan jikinsa. Ridayya bayan ta yi kuka sosai har zuciyarta ta yi sanyi ta fara saukarwa da kanta ruwa a shower mai zafi daidai jiki ta saɓa sabulu kenan ta ji tsaiwar mutum a bayanta. "Innalillahi Abbiey please out" gabaɗaya jikinta ya ɗauki rawa tunda take a duniya bata taɓa sanin sa irin wannan lamarin ba, jikinta ya dinga rawa kamar ta yi ihu tai ta kurmawa haka take ji "Don Allah ka fita ba kyau ganin tsaraici Abbiey" "Ko?" Ta yi saurin ɗaga masa kai a hankali daidai ita ya ce "Today is the most suitable day for you to fulfill your heart's promise" "What promise Abbiey?" Ya mata shiru yaƙi magana ita kanta shiru ta yi tunani take anya wannan Abbiey ɗinta ne ba a sauya mata wani ba, baki ta buɗe da niyyar yin ihu jin wani abu ya yi saurin rufe bakin ya ce.. "Tukunna akwai sauran time, remember? Sanda kike ƴar mitsitsiya kin leƙa ni a toilet tun daga ranar na sawa raina da zuciyata na samu matar aure, na ɗauki hakan matsayin promise of the heart, yanzu ke ɗin tsagina ce" Ta runtse idanunta kunya mai tsananin girma ta kamata dukda da ya hanata wanke sabulun ta dinga jan numfashi ba ƙaramin jarumta ta nunawa Ustaz ba, har mamaki ya yi for some minutes ya wanke su tare sai a lokacin ta buɗe idanu kanta na zubar da ruwa ya tallafo haɓarta "Allah ya yi miki albarka" "Uhm uhm ka yi shiru ni" "Da na yi magana ne? Tsayin shekaru nawa ina rufe da bakina da zuciyata? Ki bar ni na faɗa kin ji ina da abubuwan cewa" Ta maƙale kafaɗa tana narke fuska ta ce "Abu ɗaya" “I LOVE YOU ” kalmar ta saukar mata har cikin ƙasan zuciyarta,ta dinga jin wani iri kanta a ƙasa ya girgiza kai kawai yana ficewa bakinsa ɗauke da furucin "Ustazu mijin ƴar baƙa" Zameer na tsaye shi da Moo da Shaba sai Khalid kowa cikin shadda matasa masu jini a jika Shaba ya kalli Zameer ya ce "Na yi mamaki fa?" "Name?" Cewar Moo idanunsa akan wata kyakkyawar yarinya dake cikin kyakkyawar shiga abaya ce jikinta amma ta saka irin baby hijab ɗin nan,sai wani mayafi ta yi covering jikinta tafiya take fuskarta a haɗe babu alamar wasa. "Ban taɓa ganin Daddyn Zameer ba always baya ƙasar nan, mu a cikinmu waye ba a san dadynsa ba don Allah?" "To mene matsalarka ne wai Shaba?" Shaba ya ɗaga kafaɗunsa ya ce "Kawai ina son ganinsa naga how rich he is yadda Zameer ke feeling kansa wani daban a cikin mu da alama Alhaji Mahboob Dollars is richer than my father, don haka ina neman appointment please Zameer" Zameer dai bai yi magana ba, Khalid girgiza kai kawai ya yi yana murmushi hankalinsa na kan waya Moo ya ce "Akwai ƙamshin gaskiya sai ka ƙara girmama Zameer akan wanda kake" gabaɗaya suka saka dariya wasu na saman mota wasu jingine da mota Zameer gabansa sai faɗuwa yake yanzu babu mamaki Baffansa yana can gona ma, ga Hanne matarsa ta can ko ta haihuwa ohho ma ko ta kan lamarin baya bi Ridayya ce kawai a gabansa ita ke masa yawo a zuciya. "Kunga wata Beb" Gabaɗaya suka kalli direction ɗin da take hankalin Khalid ya karkata sosai a kanta "Wannan hannuna ce" "Amma kamar babyn can nata ne ka duba hasken fatarsu mana" cewar Shaba. Cikin sauri Zameer ya cewa "Zainura? My son" "Ɗanka ne?" Ya jinjina musu kai ya ce "Ɗan da Ridayya ta haifa mini ne Zainura kuma ƙanwar matata ce" Gabaɗaya suka kalli little Bilal wanda yake tsananin kama da MB USTAZ kyakkyawan yaro mai shiga rai ga wayo kamar ba haihuwar Ridayya ba, ga baki irin na Zainura magana yake sosai hatta sumar kansa irin ta Bilal ce. A wannan karan Khalid ne ya ce "Karka raina mana hankali tayaya wannan baƙar matar taka mummuna zata haifi wannan yaron?" Kalmar baƙa mummuna ya caki zuciyar Zameer ya ce "Idan ka kuma cewa matata mummunan sai na ci uwarka a wajan nan" "Me za ka yi? Na faɗa baƙa mummuna wacce baka taɓa yi wa ko kiss ba, wacce ka tsana saboda ta baka budurcinta" da sauri Shaba ya rufe bakin Khalid ya ce "Haba Khalid this is not good, bai kamata kana aibata masa matarsa ba, kuma ai ba zai ga yaro ya kira sunansa ba Ubangiji ke halitta fa, don uwa ta kasance mummuna kuma baƙa ƙirin ba shi yake nufin ɗanta zai zama kamarta ba" "Ikon Allah, baƙar tukunya mai fidda farin tuwo" cewar Moo ya kalli Zameer sai kawai ya girgiza kai, Zameer wani irin ƙaunar ɗansa ya matsa masa amma shakkar yi wa Zainura magana yake ya lura suna da bambanci da Ridayya mai son shi. "Hi jimana" Khalid ya ce yana shan gaban Zainura ta ja ta tsaya tana tsare shi da idanu ta juya ta kalli Zameer ta ce "Oh sawa ka yi a tare mini hanya ko me? Saboda na faɗa maka cewa karka ƙara zuwa ƙofar gidanmu? Wai kai wanne irin mutum Please?" Ta yi dariya tana cije bakinta Zameer ya ce "Me ya sa ke baki da kunya ne? Ki koyi haƙuri da kunya da kawaici irin na ƴar'uwarki mana" "Zameer kake ko? Koda yake bari na kira ka sa sunan da zaka gane Giɗaɗon ƙauyen Nahutun Batsari ta garin Katsina" Shaba, Moo, Khalid da mamaki suka kalli Zainura ta riƙe ƙugu tare da yin fari da idanunta ta ce "Meye kuka tsare ni da idanu kamar yau kuka taɓa jin sunansa ba, ko kuna nufin yau kuka taɓa ji?" A gigice Shaba ya ce "Wait; keep a joke a side Giɗaɗo kika ce fa?" "Yes haka na ce, oh baku san cewa Almajiranta ya zo Kano ba daga Katsina shi ne ya zama ɗan fake life? Ku je ku yi tunani ko kuma baya ku yi nazari da kyau" Wata zufa ce ta shiga yankowa Zameer kana ganinsa kasan ƙarya ta ƙare buri ya kar boka da tashin hankali yake kallon Zainu ita kowa sai murguɗa baki take hankalinta kwance, Khalid ya dinga murmushi Moo ya kasa cewa komai Shaba kallon Zameer yake from head to toe ya ce "Amma da gaske wannan cute boy ɗin nasa ne? Ni kama yake mini da wanda ya fito takarar Gwamna ɗin nan Muhammad Bilal Tahir kamar ya yi kaki" Watsa masa harara ta yi "E ai duk inda magana ta je ta dawo gaskiyar ba zata ɓoye cewa bashi ya haife shi ba, Muhammad Bilal Giɗaɗo sunansa muna ce masa Little, amma a yanzu na raba wannan alaƙar ya je can ya nemi ɗansa, little ko zaka je wajansa?" "No Abbiey" ya ce yana maƙale kai "Well-done my son za ka yi albarka irin ta uwarka" Duk wannan tashin hankalin Zameer bai dame shi ba, ganin yadda ɗansa yake ƙoƙarin gudunsa da gaske shi ke firgitar da shi, kar dai Ridayya ta karantar yaron nan komai? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ya shiga uku ga wani masifar son Ridayya dake ƙoƙarin haukatar dashi tattausan laɓɓanta ranar da ta je police station yaƙi barin idanunsa ya biyo bayan Zainura da sauri ya ce "Ki faɗa mini Ina matata take ina mai so na, ni ne rayuwarta Please Zainura ina kika ɓoye mini matata?" "Tana cikin Aljihuna na ce gata cikin Aljihuna wai kai wanne iri ne, Yaya Ridayya ta maka nisa har gaban abada muna nan da kai akan son ta zai zuciyarka ta buga,kuma idan baka rabu dani ba Wallahi zan saka a sassaraka a mayar da kai Nahutu a ƙarye useless useless" baki sake ta bar Zameer ga kunyar su Moo ga zuciyarsa da take masa wani irin tsalle ko wacce gargasar jikinsa idan ta buɗe da muradin samun Ridayya take yin hakan baya iya bacci wani irin MAHAUKACIN SO ne ya kama shi. Bai tsaya ba ganin Shaba na zuwa inda yake ya saka cikin sauri ya faɗa cikin wata napep dake harabar jami'ar. Zainura na zuwa gida ta tarar parlorn Mami cike da su Anuty Kaltum da Yaya A'isha da sauran jama'a ana ta hira ta dinga mamaki cikin sauri ta shiga bedroom baki ta sake ganin Baffa zaune hannunsa ɗauke da jariri ta juya ta kalli Mami, Mami ta watsa mata harara tana ɗauke kai daga ita har little Bilal wajan jaririn suka nufa, ta taɓa babyn taga yana motsi ta fasa wani ihu ta faɗa kan Mami ta ce "Is true Mamina ta mini ƙani wow Zainura you are so lucky" Ta ƙanƙame Mami Baffa ya ce "Maza yi ƙoƙarin danne mini matata sahibata" "Haba Baffa murna ce fa, Mami ko na ji miki ciwo ne" Mami ta ranƙwashe ta ita kam ta riƙe Mami so take ta ƙara taɓa Babyn Baffa ya ce "Idan ba ki ɗaga mini mata ba idan na zo ni da ke ne, ga wahalar haihuwa ga taki ke bakya girma ne" Little ya ce "Baffa wannan" Baffa ya ce "Ɗan kyakkyawan jikina kalli Madam ce ta mini kyautar baby say thank you granny" "Thank you granny" Mami ta yi murmushi ta ce "Wato little surutun uwarsa Zainura ya ɗauka" Baffa ya ce "I see, like son like mother kenan" "Uhm ai yau na sake ganin tsohon mijin Yaya Ridayya wai ina matarsa ji banza fa? Na kowa ci masa mutunci ya ɗauka ban san shi ba, Giɗaɗo sunansa fa a Katsina yake can ƙauyen Nahutu daga yankin Batsari ai Almajiranta aka kawo shi nan kuma.....," "Zainura!" Mami ta kira sunanta da ƙarfi har sai da ta ji tsoro ta ce "Zameer ɗin kika faɗawa haka?" "Mami to mene? Wallahi na tsane shi criminal ne gabaɗaya ya wahalar da Yaya Ridayya" Mami zata ƙara magana Baffa ya ɗaga mata hannu ya ce "Baya saki Ridayya ba? Meye na kiran ta da matarsa " Zainura ta tura baki ta ce "Ɗan wahala ne hadda rantsuwa bai sake ta wai guduwa ta yi matarsa ce yen yen yen ni ko jin zancen ban yi b saboda warin bakin ƴan ƙauye yake ai yama faɗawa Yaya Junaid everything " Hankalin Baffa dana Mami suka tashi bada aure akan aure Ridayya ta yi ba? Nan da nan Baffa ya kira Junaid ya ce duk inda yake ya je. Ammi kusan zaucewa ta yi bata taɓa ganin cikin Fatima ba sai kukan jariri ta ji? Ya akai bata taɓa lura ba mai ya ɗauke hankalinta har haka? Kenan Mami zata ci-gaba da haihuwa har ta kamo ta a raba gado daidai kenan gashi wannan karan namiji rawar kan da Baffa yake akan haihuwar har ya ɓaci ta rasa ya za ta yi koda ta samu Yaya Zuhura ta mata magana cewa ta yi "Ammi matar na da zuciya ɗaya take zaune dake idan kika ce za ki mata baƙin ciki mutuwa za ki yi a tsaye bayan kin aure mata miji tun kafin ta aura amma ki dinga ƙoƙarin rabata da mijinta, abinda ka yi wa ɗan wani shi za a yi wa naka ni kin cucu ni ji nake dama bake ce uwata ba mugun abinki ya miki yawa" "Ni kike faɗawa haka Zuhura " Yaya Balkisa girgiza kai kawai ta yi wannan shi ne ƙaiƙayi koma kan masheƙiya. Mardiyya burinta bai shige Ustaz ya dawo ba, ta samu tarayya da shi ko sau ɗaya ne kuma ta yi evidence, wanda zai tilastawa Ustaz amsar cikin jikinta wannan shi ne plan ɗinta kuma ko kiranye ne zata saka a yi masa domin ya dawo ta cimma burinta. Gefe guda kuma Umma sai ɗawainiyya take da cikin Mardiyya ta fara siyan kaya tana ajjiyewa har fili ta bawa Ridayya akai shaidu da saka hannu matsayin tukuci na cikin da haifa mata jika da zata yi a ƙalla kusan kullum tana kashe kuɗi sama da dubu goma zuwa sha biyar na kayan kwaɗayi ga yawan fita da take wai asibiti take zuwa. Kuka sosai Hajiya Azizat ke yi tana kallon Prof ta ce "Yanzu ya zan yi da damuwarka zan ji ko data Sadauki? Anya Prof wanne kalar rayuwa ne na kasa gane maka dani da photo ɗaya muke a wajanka a matsayina na matarka yaushe rabon daka sauke mini haƙƙina? Ci da sha ba shi ne aure ba Professor al'amarin naka kullum ƙara girma yake sai ka yi wata baka gida? Prof ya girgiza kai yana tattaro kalamansa ya ce "Madam plates try to understand me, ke shaida ce ina son ki kuma duk abinda nake yi ina yi ne saboda ku, bani da burin daya shige zama daku yanzu muna maganar fara kamfal ne takara ta sako ni a gaba addu'arku nake buƙata" "I wish you all the best dear amma ka je wajan Sadauki talk to him ka ji damuwarsa" "Right now my love" Kwance ya samu Sadauki daga shi sai gajeren wando idanunsa yana kallon sama faffaɗan ƙirjinsa a buɗe ya rame saboda sam tunda yake bai taɓa saka damuwa a rai ba, bai taɓa tunanin a duniyarsa akwai abinda zai raunata zuciyarsa ba sai gashi Shanshan na neman kashe shi da ransa. Prof ya kalli kwalbar srup ɗin dake kusa da hannun Sadauki a karo na farko ya ji bai kyautawa ɗan shi ba. "My love tashi mu yi magana" Sadauki ya share shi ya shanye kwalbar srup har uku saboda ya samu bacci ya ɗauke shi daman mai jima da tashi ba. "Akan wacce ka shiga halin nan za mu yi magana, zan tabbatar data zama martarka idan har Ridayya ce" Da sauri Sadauki ya juya ya kalli mahaifinsa Prof ya ce "Da gaske i am with you wannan karan ba zan bari soyayya ta kashe mini kai ba, yaran yanzu akwai saka damuwar soyayya musamman irin madly love ɗin nan yana rusa muku rayuwa, da yawa wasu na samun depression idan sukai heartbroken, wasu ma su fara shaye-shaye duk a sanadin soyayya" Ya kama hannun Sadauki ya ce "Please my son ka kwantar da hankalinka ban san mene Hukuncin Allah ba, amma tabbas kai da Ridayya zaku kasance ma'aurata" Ya kalli mahaifinsa sosai a raunace ya ce "Prof Shanshan bata tsautsayi na me na yi ba? Kullum cikin bata haƙuri nake, mace ƴar rarrashi ce da kulawa suna buƙatar a dinga supporting nasu komai ta ce zan yi obey, but bata so na she doesn't love any more, i love Ridayya Daddy" "Na da kai na shaida hakan kuma na samu ganawa da mahaifinta" "Are you sure Daddy?" "Of course my son amma ban faɗa maka komai sai ka kwantar da hankalinka ka dawo asalin Hamza Sadaukina" "Abba Ridayya fa?" "Oh Sadaukin Ridayya, makaranta ta koma kamar yadda aka shaida mini kuma bata mance da kai ba, tana buƙatar ta kammala karatu yadda idan kun yi aure zata samu ciakken kula da kai as she said. Ridayya loves you Hamza bai kamata ka damu ba ka yi mata uzuri ka ji ko" Sadauki ya yi shiru can ya ce "Kamar na yadda kamar ban yadda ba, well is allowed zanta yi mata uzuri zan ci-gaba da sonta kuma zan jira rata har zuwa ƙarshen numfashi zan bata lokacin da take buƙata, i love Ridayya Daddy help me ko gidansu na je na gaisa da iyayenta Tajj mugu ne ya hanani da ƴarsa ce Nadra ba zai bari ta dinga wahala ba ya san yana da maganin damuwarta" Prof ya yi murmushi ya ce "Babba babba ne my dear respect your cousin brother ka ji? Yanzu ba wata damuwa" "Sure Prof " "Baka buƙatar kuɗi? New car, kayan sawa abubuwa dai" "Kawai ka bani soyayyarka da addu'ar ka ka taimaka mini na samu Ridayya shi ne kawai abinda nake buƙata ka san ai ina da kuɗi ni fa ba lusari bane da komai sai iyaye sun mini now I'm going back to my business" Hira sukai sosai Mother ta ji daɗi a lokacin tana buƙatar mijinta ta shirya tarɓarsa amma ana kiransa a waya jiki na rawa ya fice ya ce meeting ya tashi na gaggawa a jam'iyya. Baba ƙarami ya dinga neman MB USTAZ a line ɗinsa na JAPAN amma baya samu hatta number da Ridayya ta kira Mami ba a samu suka rasa ta inda za su ɓulluwa lamarin. Akai suna jaririn Mami ya ci sunan Baffa Mansur ana ce masa Junior shagali akai wanda ba a taɓa yi ba, Mami ta dinga shiga tana fita Baffa ya yi bajinta sosai har kuka Mami ta yi Ammi ta ja ta yi gum plan ɗinta kawai take so ya cika a kan Zainura. Watannin MB USTAZ ciff a Nigeria ana kamfel amma bai taɓa zuwa ba, ƴan jam'iyya da wanda aka fitar matsayin mataimakin Gwamnan jihar Kwamred Muhammadu Hassan da sakataren jam'iyyar Dr Gali Uba suke yin komai na kamfal ɗin, suna zagawa local government zuwa local government da ƙauyuka bisa mamaki an karɓi buƙatar su, dukda suna samun barazanar wai jam'iyya sabuwa ce inec bata san da zamanta ba. Tajj tsaye yake ana masa tambayoyin ƙare dangi, MB USTAZ ta cikin Camera ya hango Tajj Baita ya danna wani layi ana ɗauka ya yi shiru ya dinga tunanin me zai ce ya jima kafin ya ja numfashi a takaice ya ce "Allow him to come" Ajjiyar telephone line ɗin ya yi yana zaune hakimce cikin wata dakakkiyar shadda fara tas jamper da babbar riga ya ƙara yin wani fresh ya yi ƙiba da wani irin haske da kumatu kamalarsa ta sake bayyana. Yana jin Tajj na mitar kamar shi sai an tsare shi amma ya yi masa banza yana duba jarida wayarsa ce ta yi haske yaga message ne daga Ridayya ya buɗe short note ne ta ce "I need you, i miss you, i love you Abbiey" Wani kwantaccen murmushi ya yi har sai da dimples ɗinsa suka shige ya ji ita kawai yake son gani ya azabtu kwarai da gaske da rashinta reply ya yi mata da “take a kiss Mu'ahhh" Tajj Baita leƙawa ya fara ya ji an kai masa duka ya goce"zan watsa maka yatsu Tajjudeen Baita za ka ci gidanku" "Allah ga Ustaz ka yafe masa" MB USTAZ murmushi ya yi kawai wato komai ka zama a rayuwa akwai wanda ba za su taɓa girmamaka ba. "Zameer ya matsa wai bai sami Madam ba, shi ya sa na ce ka sauke layukanka na san Baba ƙarami zai matsa ka dawo,kuma Umma still tana kan bakanta, ni na san Madam ba zata taɓa yin ƙarya ba da iliminta" Shiru MB USTAZ ya yi idanunsa akan Tajj hakan yasa Tajj fahimtar Ustaz ba zai magana ba. "Little yana nan cikin lafiya, babu inda ya barka shi kuma ana yin magana zai runtse idanu ya ce Assatagafirulla!" Nan ma Ustaz bai magana ba can dai idanunsa lumshe ya ce "Zaka iya tafiya ka saka idanu akan Mardiyya ok?" "In sha Allah " A lokacin ya nemi airplane zuwa JAPAN. Domin tuni ya samawa Ridayya makaranta ta fara zuwa a ɓangaren medicine kuma ta mayar da hankali sosai dole ya tayata cika muradanta idan lokacin komawa gida ya yi za su koma ne. Shigar tsakiyar dare ya yi saboda ƴan jarida tafiyarsa a sirri take. Cikin bacci ta ji yanayinta ya sauya ga gamshi sosai dake ratsa hancinta ta buɗe idanu da kyar ta ganta kwance a ƙirjinsa ya rungume ta sosai numfashinsa na sauka a hankali alamar ya gaji wata uku kamar shekara uku Ridayya ta ji Abbiey ya sauya mata sosai ya ƙara mata kwarjini. Ta kunna fitila tare da tsora masa idanu a hankali ta zura hannunta a sumarsa mai laushi ya ta nutsa taga da gaske bacci yake a nutse cike da tsoro ta sumbace shi ta ce “I love you Abbieyna” “Love u too habib Albi” Ta zare idanu tana ƙoƙarin matsawa ya riƙe ƙugunta da hannu ɗaya yana shagwaɓe fuska wacce ita kawai ke ganin baɗininsa ya ce "I need more" ya nuna lips ɗinsa ya ce "The kisses" Zameer zube gaban su Baba ƙarami da Baffa da Junaid ya dinga kuka yana masu bayani ya ce "Ku taimaka mini Ina son matata wallahi Allah na rantse da Allah ban sake ta ba..... Ku yi sharing saboda sauran ƴan'uwa🥰👏🏻 [5/16, 2:30 PM] null: *MUNAFIKIN MIJI 42* Bright pens free batch Nimcyluv "Innalillahi baka sake ta ba ka ce fa ɗan nan?" Zameer ya girgiza kai idanunsa cike da hawaye ya ce "Da gaske nake Baffa ni ban saki matata ba, guduwa kawai ta yi ta bar ni babu inda ban nemeta ba har gidan rediyo" ba iya Baffa ba hatta Junaid da yake zaune maganar Zameer ta jijjiga shi. "Kenan Ridayya aure ta yi akan aure?" Baffa ya miƙe tsaye ya shiga zirga-zirga a tsakiyar parlorn can ya juya ya ce "Na kasa yin tunanin komai akan wannan al'amarin,abu kamar a wasan kwaikwayo da labaran hausa na tatsuniya?" "Alhaji Mansur zo ka zauna" Baba ƙarami ya kira sunan Baffa yana nuna masa wajan zama domin ya lura gabaɗaya hankalinsa a tashe yake tsoro da firgici sun shige shi sosai ainun da gaske. Junaid ya kalli Zameer yadda yake ta share hawaye tunda yake ko ada can baya bai taɓa ganin ladabi da tsantsar tsoro a fuskar Zameer ɗin ba sai yau bai kuma taɓa ganin hawaye akan fuskarsa ba, rashin yadda ya gitta a zuciyar Junaid ya ce "Idan baka saki Ridayya ba, to akwai wani abu a ƙasa tunda da can bata taɓa yunƙurin fitowa daga gidanta ba, ta dawo gida a saboda ka saɓa mata ba, balle a yanzu da take tunanin bata da kowa tunda Ridayya ta dawo ne kafin ta san cewa muna raye. Me ka yi mata? Me kaiwa Ridayya da har ta baro inda kake ta gudu? Me ya sa baka biyo bayanta ba sai yanzu?" Da wani kalar shock Zameer ke kallon Junaid da kuma sauraren shi, ganin yadda zai rutsa shi ya saka ƙaryar shi ƙarewa Zameer ya ce "Yaa Junaid ai kasan ba zan yi ƙarya ba, go and ask her ta san komai she knows everything wallahi tallahi" "Da mamaki wannan lamarin, ba a rabu da Bukar ba an haifi Babu, wacce irin ƙaddarar ke bibiyar rayuwar Ridayya" Cikin fusata Junaid ya ce "Karku yadda da shi, domin tun farko shi ɗin ba abin yadda bane ina da tabbacin Ridayya bata taɓa cutar da kai ba, balle ta aikata wannan babban lamarin" "Ya isa Junaid please" Zameer ya sake sauke kansa ƙasa cike da ladabi kamar zai yi sujjada muryarsa a raunace ya ce "Ita ta ce na taɓa cutar da ita? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lallai a bar mace da kaidinta amma ni ba zan ce komai ba, idan kana ganin ta dinga yawo da aurena a kanta shi ne daidai to babu damuwa I'll let her be tunda kana ɗaurewa ƙanwar gindi" Junaid ya kalli Zameer cike da ɓacin rai yana tuna abubuwan da suka shiga tsakaninsa da Yaa Bilal musamman a cikin asibiti a kan Zameer Ridayya ta yi wa Ustaz Allah ya isa kuma ta kira shi da sunan da ko a family shakkar kiransa ake da shi. Idan Junaid ya tuna ranar sai ya ƙara jinjinawa Ustaz na irin so da ƙaunar da ya kewa Ridayya. Baba ƙarami ya yi murmushi irin na manya mutum mai tunani da girmama zumuncin Allah da bawa kowa haƙƙinsa ya ce "Ɗana Zameer kana ina Ridayya ta gudu garin yaya hakan ta kasance ka yi wannan sakacin?" "Abba muna nan Garin Kano ba sakaci na yi ba cikin dare ta gudu wai ta gaji da zama dani saboda kuskuren dana tafka a rayuwa, na mata laifi ni ɗin mai kaifi ne Abba amma girman laifin bai ka ga Ridayya ta gudun daga cikin gidanta na sunna ba kuma tare ɗana. Abba kai mai fahimta nasan zaka fahimce ni" Zameer sam bai kula da Tajj daya shigo ya zauna ba, yana sanye da black suit irin ta manyan ƴan sanda sai baza ƙamshi yake idanun Tajjudeen Baita zube akan Zameer shi ma yana sauraren shi. Tajj zai magana da hannu Baffa ya yi masa alama da ya yi shiru. "Karka wani damu ɗana ka ɗauka ni ɗin tamkar uba mahaifine a gare ka zan saurareka kamar yadda zan saurari ɗan dana haifa kuma na maka alƙawarin wallahi wallahi wallahi uku kenan idan har kai ne da gaskiya to zan dawo maka da Ridayya cikin gidanka da yaronka matsayin matarka" Da sauri Baffa da Junaid da Tajj suka kalli Baba ƙarami da yake ta murmushi, firit Umma t fito daga laɓewar da ta yi ta ce "Kai Allahamdulillahi idan hakan ta faru zan fi kowa murna da samun nutsuwa a zuciya, Babban mutum ya rabu da kwallon mangoro ya huta da ƙuda har abada. Na daɗe ban ji tsanar da na yi wa mutum irin ta matsiyaciyar ƴar nan Ridayya ba, ba zan taɓa ganin farinta ba wallahi mummunan mai baƙar zuciya mai kama da Alade kawai" Baffa har ƙasan zuciyarsa yake jin zafin maganganun Umma amma babu yadda ya iya matar yayarsa ce dole ya zuba mata idanu. Mami data fito hannunta ɗauke da Junior ta tsaya cak saboda furucin Hajiya Hadiza karamcin Ustaz ya shige ta faɗawa babarsa magana wallahi Anty Kaltum ta ji maganar itama niyyar tafiya ta yi amma kawai ta juya cikin ɗakin Mamai ta yi alwala tare da gabatar da sallar asar. Baba ƙarami bai kula Umma ya dubi Zameer ya ce "Wanne laifi ka yi wa Ridayya da kake neman yafiya?" "Abba i was wrong i was totally wrong ban san da wanne harshe zan maka bayani ba komai zan ce komai zan furta ba lallai na ƙara fari a idanun Ridayya ba" "Tunda you are already knew dat why are wasting your time here? Me ya sa za ka zo nan ne ma?" Da ƙarfi Baba ƙarami ya ce "Abubakar Sadeeq!" "I am sorry Abba" "Ina jinka Zameer" Zameer ya sassauta murya ya ce "Abba farkon fara haɗuwata da Ridayya a makaranta ne, na sameta tana ƙoƙarin kashe kanta ta hanyar rataya a ƙarƙashin bishiya, Allah ya kawo ni wajan domin na ceci rayuwarta Abba just to save her life. Ban tambayi Ridayya komai ba amma sai ta fashe da kuka ta fara zayyana mini halin da take ciki, ta ce mini mahaifinta ya tsaneta haka mahaifiyarta kowa na gidan baya sonta ƴan unguwa da ƙawaye haka a makaranta kowa na aibata halittar da Ubangiji ya yi mata sannan ta ƙara da cewa...," Ya yi shiru kansa a ƙasa yana girgiza kai ya kasa cewa komai. Baba ƙarami ya ce "Go on my dear ina jinka ka faɗa mini komai tsakaninka da Allah" Hawayen da yake ta rikewa ne ya sake gangaro masa ya ce "Abba ka yi mini uzuri abar maganar domin zata iya rusa wannan zumuncin naku magana ce da zata iya sawa zuciyar kowa ta buga daga ciki kowa har kai Abba ko kuma Abban Ridayya just let bygones be bygones Abba" Baba ƙarami ya miƙe tsaye ya ce "Ya zama dole ka ƙarasa faɗar abinda ka yi niyya ba a mini haka ba zaka fara mini ba kuma" "To Abba ya zaka ji idan na shaida maka cewa Ridayya ta faɗa mini saboda ɗan'uwanta Ustaz wanda ya zama kamar uba a gare ta take son kashe kanta? Ya zaka ji idan na faɗa maka cewa sanda Ridayya ta je gidana ta je da shigar cikin da Ustaz ya yi mata? Ta shaida mini tun tana yarinya yake lalata rayuwarta kuma ya yi mata barazana da faɗin muddin ta faɗawa wani sai ya yankata da wuƙa? Me ya sa ba ku taɓa tunanin ƙin auren shi da ta yi a fari ba? Me ya sa ta zaɓe ni ta barsa? Abba da farko bani na fara cewa ina son Ridayya ita ce ta buƙaci hakan ni kuma na tausaya mata a haka har na fara son ta, Abba laifina a nan shi ne na ɓoyewa Ridayya gaskiyar waye ni maimakon Zameer sunana Giɗaɗo ɗan asalin Garin Katsina can ƙauyen Nahutu yankin batsari na zo Kano Almajiranci ne, ban yi haka don na cutar da mai so na Ridayya ba, na yi ne saboda kar na rasa ta na yi ne saboda na rufa mata asirin da ɗan'uwanta yake ƙoƙarin tuna mata na yi kuma da tunanin idan kun ganni talaka zaku hanani auren Ridayya, bayan ta gano gaskiyar dana ɓoye mata shi ne ta ce dole sai na rabu da ita" Tunda ya fara maganar tasa Baba ƙarami zufa ke yanko masa jikinsa ya ɗauki rawa dukda cewa a zaune yake amma ƙoƙarin faɗuwa yake wani abu mai kama da tashin hankali da fashewar bom ya ji a zuciyarsa da gangar jikinsa kansa ya fara juyawa maganar Ridayya ta yi aure da cikin da Ustaz ya mata ita kaɗai ke gigita masa lissafi da ƙoƙarin saka zuciyarsa bugawa. Ya kama hannun Zameer ya damƙe idanunsa na fitar da ƙwalla ya ce "Yaro ka ji tsoron Allah ka tuna zaka mutu da gaske ne abinda kake furtawa akan Bilalu ɗana? Babban mutum fa? Ka ji tsoron Allah karka goga masa baƙin fentin da ba zai iya shafewa daga jikinsa ba, ko ka yi ne don matarka ta dawo gare ka?" "Haba Abba haba Abba ina dalilin wannan furucin naka? Mene ribata idan na wulaƙanta mutum kamar Muhammad Bilal? Gaskiya ɗaya ce kuma ita na faɗa" "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Hasbunallahu wani'imal wakil Muhammad Bilal? Babban mutum Allah ya...." "A'a yaya don Allah, don't say that karka ce haka" "Me kake so na ce Alhaji Mansur? Ɗana na cikina ya wulaƙanta ƴarka tun tana ƙanƙanuwa? Ta ina zumuncin Allah zai bar ni? Wannan shi ne dalilin daya saka ya ƙiyin aure? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un" nan da nan Baba ƙarami ya gigice ya riƙe ƙirjinsa hankalin Junaid dana Tajj Baita ya yi mummunan tashi wacce lukutar masifa ce wannan? Anya Muhammad Bilal zai aikata haka? Mene gaskiyar lamari? Only God knows! Likita aka fara ƙoƙarin kira Baba ƙarami yana cewa a bar shi haka nan "Idan har maganar nan gaskiya ce wacce Zameer ya faɗa wallahi Allah sai na ɗauki hukunci sai na ɗaukarwa Ridayya fansa wallahi sai na ɗaure Muhammad Bilal da hannuna" Da sauri Zameer ya ce "Ai gaskiya ce ma Abba kaɗan kenan daga abubuwan da suka dinga faruwa" wani irin hawayen baƙin ciki dana tsanar Ustaz Baba ƙarami ya dinga zubarwa deep down na zuciyarsa yana ƙoƙarin ƙaryata lamarin. "Kai out of this house before i count 1" Junaid ya cewa Zameer miƙewa ya yi with confidence ya bar parlorn ya yi waje a zuciyarsa yana jin cewa wannan shi kaɗai damar da yake da ita wajan sawa Ridayya ta dawo inuwar aurensa yana jin wani iri idan ya tuna ta, he feel very comfortable without her, her love,her voice, her.... He miss everything about her more especially her soft skin ga kullum lips ɗinta dake masa barazana ga Black skin ɗinta sai ya ji gabaɗaya baya son farar mace baƙar matarsa kawai yake da interested akan ta wannan shi ake kira da LOVE! "Good job Zameer ka yi abu cikin sauƙi u are smarter than everyone! Smart smarter smartest u are so lucky ka yi komai muddin Ridayya zata dawo kanka, ka so kanka fiye da kowa karka zama mai yadda da faɗuwa da karaya akan abu" Murmushi ya yi yana shafa samar kansa da lumshe idanunsa he is more than okay gani yake dawowar Ridayya ya zama dole ne. Tafiya ya fara yana barin entrance ɗin gidan. Sosai Tajj Baita ya shiga tashin hankali fitar maganar nan waje yana nufin komai zai taɓa career MB USTAZ zai taɓa takararsa da jam'iyyar da yake ciki musamman ƴan jarida da ƴan media suka samu labari. "Abba calm down please jikinka na girma ne kai hakan ya haifar maka da hawan jini ka ciwon ɓarin zuciya ka kwantar da hankali abi komai a sannu don Allah" "Tajjudeen kasan zafi da raɗaɗin da nake ji a zuciyata? Idan na rufawa ɗana asiri Ubangiji zai yafe masa wannan zunubin ne?" "Abba ba kyau karka yanke hukunci akan abun da babu tabbas ba evidence mu fara bincike.....," "Kai Tajjudeen! Na san ka san inda zaka samu Muhammad Bilal ka faɗa masa idan har ni na yafe shi ina buƙatar ganinsa nan sa kwana biyu" kana ganin Baba ƙarami kasan he's out of his sense he lost ciwo kawai zuciyarsa ke masa. Junaid ya ya jugum shi kansa kan nasa hayaƙi yake yana buƙatar ruwan sanyi. Tajj Baita ya ce "Abba ina zanga His Excellency yanzu?" Wani kallo da Baba ƙarami ya yi wa Tajj ya sanya shi yin shiru tare da yin waje a ransa yana jin dole zai saka a kama Zameer bayan election a sake shi sannan komai ya yi daidai samun nasara ko faɗuwa. Yanke jiki Baba ƙarami ya yi ya faɗi Baffa da Junaid da Abubakar suka rufu a kan shi nan da nan aka ƙara kiran Dr gabaɗaya matan gidan basu san wainar da ake tuyawa ba hakan kuma ya yi wa Baffa daɗi a rai. Japan Dawowarta daga makaranta kenan saboda karatu ya ɗauki zafi shirye-shiryen exam suke ta first semester zangon karatu na farko a jerin sabbin ɗaliban da jam'iyyar Japan ta ɗauka a Kyoto University. Kyoto University is a Japanese national university that was founded in 1897. Ta ƙara samun gogewa da ilimin zaman rayuwa musamman data haɗu da mutane kala daban-daban kuma ƙabila daban-daban ta samu rangwamen tsana daga idanun mutane wasu kuma saboda baƙinta ya yi yawa sai su dunga guduwa tamkar zata shafa musu baƙin zunubi hakan baya damunta a yanzu tana da confidence na fuskantar ko wacce matsala da zata ƙalubalanceta ta samu ƙarfin zuciya da abinda ake kira Self-confidence ga mijinta wanda baya gazawa he is always supports her akan dukkan lamuranta yana nuna mata ita ma mutum ce kamar kowa tana da ikon yin dukkan abinda take so wanda bai saɓawa addinin Muslunci ba. Zamanta da mijinta MB USTAZ babu komai face farinciki da kwanciyar hankali, dukda akwai samun saɓani irin na ma'aurata wani lokaci duk wacce ta ce bata taɓa faɗa da mijinta ba ko misunderstanding ya shigo ciki ƙarya take, aure ibada ne kuma sunna zama ne na dindin wanda ake fatan sai dai mutuwa ta raba. Da farin ciki ta shigo tun a parlor ta zare safar hannunta dana ƙafa ta cire madaidaicin hijabin wata takarda kawai ta ɗauka ta nufi babban part ɗin data tabbatar yana ciki a hankali ta murɗa ƙofar ta shiga parlorn farko mai ɗauke da haske ta shiga na biyun shi kuma duhu ta ƙarasa har cikin bedroom tana shiga ta hango shi kwance tsakiyar gado ya shiga cikin duvet yana bacci hankali kwance Ridayya ta saki murmushi mai sauti ta zauna kan gadon idan ta kalli MB USTAZ da kyau ta tuna shi ne wanda Ubangiji ya bata shi matsayin miji sai ta ji damuwar da ta yi shekaru da ita duk ta kau daga zuciyarta, ganinsa take tamkar ba a cikin zuri'ar Mai ran ƙarfe yake ba, shi kaɗai daban Ubangiji ya yi masa tsarinsa kaf familyn. "Now is my turn Abbiey" Sai tana bacci mai daɗi zai fara damunta bata bacci ya isheta yanzu ganin yana jin daɗin baccin sosai ya saka ta fara tashinsa ta hanyar zura hannunta cikin sumar kansa data rufe masa fuska a hankali take ya motsa masa kan tana murza tafin hannunsa daidai kunnensa ta ce "Abbiey Abbiey Abbiey" Amma ina bacci yake sosai saboda gabaɗaya satin bai samu ciakken bacci ba Ridayya ta dinga takura masa "Abbiey mijin" Duka yana jinta ya yi luf can ya ɗan mirgina ya ɗauki pillow ya rufe kunnensa data miƙa hannu ta fara taɓa shi can zai make hannun yana sake mirginawa abubuwa biyu ke damunsa ba lallai ta fahimta amma yanzu baccin shi ne gaba da komai. Sake hayewa gadon Ridayya ta yi saman jikinsa numfashinta na sauka ta fara bugunsa da ƙarfi cikin magagin bacci ya ce "Haramun Ustaza haramun zunubi kike ɗauka" "Nima haka kake mini please ka tashi i want...." "Are you sure u want this?" Ya faɗa yana nuna mata wani abu ta yi saurin rufe idanunta a hankali shi kuma baccinsa ya fara warware wa wani abu ya danne baccin ya ɗan cije lips cike da mugunta yana juyata ƙirjinsa na matsewa sosai da kyau jikinsa na buɗewa yanayin na shigarsa da kyau yana ɗago kanta ya ce "Because once it is in, you will officially belong to me" Ta zazzare idanu domin ita kwana al'amarin fitar mata yake daga kanta tana ɗan narke fuska murya shagwaɓe ta ce "Koma bacci abinka bari na gyara maka duvet ɗin" Ya buɗe idanunsa da kyau yana rungume da ita suna daga kwancen ya lumshe ido ya buɗe magana yake son yi kuma ya kasa Ridayya ta ce "Allah ya yafe miki Ustaza ke yarinya ce" Ya ɗaga mata kai alamar “Good” Ridayya ta gyara kwanciyar ta a jikinsa ganin ya mata shiru ta ce "Kasan me Abbiey?" Ya zuba mata gajiyayyun idanunsa sosai mai ɗauke da abubuwa da yawa ya kasa cewa komai ta ce "Karatun daka koya mini shi ne aka yi mana a test kuma na cinye Assignment ɗin nan" Ya buɗe ido zai magana sai ya fasa ya yi kissig kumatunta muryarsa bata fita sosai da wani irin romantic voice ya ce ""أنا أحبك" Murmushi kawai ta yi ita har yanzu nauyin faɗa masa kalmar soyayya take nauyinsa take ji sosai shi kuma baya takura ta yasan soyayya ba dole sai an furtata da baki ba wani a aikace yake yin komai "Black tea Zauja ok" "Right now Abbiey" Ya sake ta can ciki ya ce "Barakallahu fiiki" Gani yake komai ta yi yarinya ce ita tana buƙatar uzuri shi ya sa yake sassauta yanayinsa da fushinsa a kanta. Fita ta yi da niyyar nufar kitchen ta haɗa masa tea ɗin sai ta ji telephone line ɗin gidan na ƙara ta jima bata yi ba da tunani Abba ne ko Baffa ta ɗauki kan wayar muryarta a sanyaye ta ce "Assalamu alaika/ki" "Allahamdulillahi! Ridayya are u alone oh sorry her Excellency" "Daddyn Nadra ina yini" "Ajjiye gaisuwa a gefe are u alone magana za mu yi ta fahimta bana son mijinki ya sani" Tabbaci ta bashi ita kaɗai ce lafiya? "Ridayya daman Tsohon mijinki bai sake ki ba? Guduwa kikai daga gidansa?" Mararta ta ji ta ɗaure mata wani abu ya yi zillo ta ƙasan marar jikinta ya ɗauki rawa ta ce "Ka...ka...ka kamarya bangane ba" Tajj Baita ya ce "Nima dai ban gane ba, ta bakinki nake son ji, ya ce daya aureki kina da ciki ba kowa ya yi miki ba sai His Excellency MB USTAZ kuma tun kina ƙarama yake lalataki ya rantse da Allah bai sake ki ba, shin Ridayya da gaske kin yi aure da ciki kuma na Ustaz ne?" Tajj Baita bai san meke faruwa daga ɓangaren Ridayya ba sai ji ya yi ta fasa gigitacciyar ƙara kiran kuma ya katse. Ustaz dake zaune da laptop a gabansa yana duba wani muhimmin saƙo da Muhammad Hassan ya tura masa ta email ya ji ihun matarsa cikin sauri ya miƙe a ɗan gigice yana addu'a ya nufi waje kwance ya sameta bata ko motsi jini na zuba ta ƙasanta bai tsaya jiran komai ya shiga kiran ambulance kafin su ƙarasa ya zura kaya ya sunkuceta sai ambulance. Some hours left Girgiza kai kawai yake idanunsa da suka nutsa ciki sosai da maka tantance yanayin su ne zube akan wanda yake tsaye a gabansa, shi kansa wanda yake tsaye ya firgita da yanayin Ustaz ya san halinsa idan ransa ya ɓaci "Try to understand me ni ban san me ya saka Madam shiga halin da take ciki ba, kawai na san ana buƙatar ganin ka a gida" "I hate liars, why?" "Yanzu muje asibitin muga halin da take ciki" "Tajjudeen Baita ka jima ba kaga rikicina ba, matata tawa ce ba ruwanka da na je wajan ta ko akasin haka. Firstly ka kira matata without my permission, secondly ka ce mata wani abu wanda ya saka ta shiga firgici, lastly ka shigo jirgi ka zo mini nan? Explain why? Menene?" "Calm down please" "Calm down? Assatagafirulla Allah ya yafe maka Ubangiji ka Tajjudeen" muryar Ustaz har shaƙewa take Tajj ya buɗe baki zai yi magana ya ji saukar wani mari a fuskarsa ya ƙara jin wani muryar daya jima bai ji ya ji ta masa amo! Da amsa kuwwa a kunne "What is going on? Meke faruwa don't let me to repeat myself". "Your wife's ex-husband" Tajj ya ce yana riƙe fuskarsa sosai marin ya ratsa shi saboda a hagunce ya mare shi shirun Ustaz na nufin ƙarin bayani nan da nan Tajjudeen Baita ya zayyana masa komai da yake faruwa. Kan Ustaz a ƙasa murmushi kawai ya yi ya nufi wajan freezer ya ɗauki ruwa mai sanyi sosai ya ɓalle gorar kai ya shanye tas ya cillar Murmushi ya sake saki ba za ka taɓa cewa ya damu ba ko maganar ya shige shi musamman furucin Baba ƙarami na cewa zai ɗaure shi, wai ciki? Ya lalata ƴar jaririyarsa shi kuma nasa salon kenan? Ta cikin cikin zuciyarsa naman wajan rawa yake gumi ya lullube zuciyar har hucinta ya ke jin da maƙoshinsa wani irin firgitaccen yanayi ya ruftu masa zazzaɓi ya nemi rufe shi ya sake duƙar da kansa ganin idanunsa na rikiɗewa muryarsa na rawa ya ce "Leave" "Ta ya ya zan barka cikin wannan yanayin?" Gabaɗaya Ustaz ya juya kan Tajj yana sake yin murmushi tare da ɗage girarsa duka biyun ya girgiza kai ya ce "Allahumma yahdiìka, Allah ya yafe maka" Tafiya suke har entrance kana suka nufi hanyar emergency daga nan suka nufi sashin ICU ɗaki na musamman a baƙin ƙofa suka tsaya shi kuma ya shige ciki. Idanunsa ya sauka a kanta tana kwance bacci mai nauyi ya ɗauke ta ga drip a jikinta kuma ga ƙarin jini ya sauke ajjiyar zuciya so wannan tashin hankalin ya sana Shalele shiga wannan halin? Dr Lin daya shigo tun ɗazo ya ce "Karka damu she will be fine by the grace of God ɗan cikin yana mararta lafiya lou" Da rashin fahimta MB USTAZ ya kalli Dr Lin gane hakan yasa Dr Lin cewa "Sir Allah ya kiyaye cikin bai bi jini ya gudu ba, babyn yana lafiya itama matan ki she will soon recovering" Kallonsa kawai Ustaz yake Dr Lin ya bawa Ustaz wani file ya ce "Your wife is pregnant" A zaune yake amma bai san lokacin daya miƙe tsaye ba, da wani irin yanayi na farinciki yake duba wajan positive ya dubi Dr Lin dake murmushi baturen likita duk hasken shi amma Ustaz ya ɗara shi haske tunanin Dr Lin ko baya jin irin nasa turancin ne ko larabci yake ji? Ustaz ya damƙe hannun Ridayya sosai ya haɗe fuskarsu waje guda ya kasa magana sai wani light kiss da ya yi mata a gefen lips ɗinta wani irin hawayen farinciki running down to his face ya sake sumbatar goshinta da kumatunta da ƙyar ya ce "I love you Mintyna. Allahumma barik" "What a love!" Murmushi USTAZ ya yi ya mance damuwarsa ya rungume Dr Lin wani irin farinciki yake ji a ransa yana shiga dukkan ƙofofin zuciyarsa. ALLAH alhakkamu wanda komai nasa yake a tsare ya ƙara tabbatar rabon Little Bilal ya haɗa Zameer da Ridayya haka kuma wannan rabon ya saka su rabuwa ta dawo gare shi, rabo ajali haka ko mutuwa ce duk inda ya je sai ya dawo wajan mutum indai rabonsa ne. Wata bata haifar ɗan wani amma tana auren mijin wata hakan rubutacce ne a lauhil mahfuz Allah kaɗai ya san abinda ya ɓoye a aurensa da Ridayya koma mene yana fatan akwai zama tabbatacce wanda mutuwa ce zata raba. Ustaz ya dinga murmushi shi ɗaya hannunsa riƙe dana Ridayya ya mance batun Tajjudeen Baita dana Zameer komai ya shafe a zuciyarsa sai Ridayya da abinda yake cikinta idan ya lissafa daidai babu mamaki tun a ranar budurcinsa Ridayya ta samu rabo ƙwallonsa ya isa ga raga haƙarsa ta cimma ruwa. Cikin dare ta farko jikinta lafiya lou amma da kuka ta farko Ustaz dake ƙasa saman ladduma yana Sallah da addu'oi ya miƙe ya nufi wajan ta tana jinta kusa da shi ta fisge ƙarin jinin ta ƙanƙame Ustaz tana kuka sosai kamar ranta zai fita magana take son yi ta kasa ganin haka ya saka shi shigar da ita jikinsa ya rungume yana bubbuga bayanta. "Abbiey ka yafe mini ka yafe mini Abbiey" "Shhhh it's ok Mintyna" "Na maka laifi Abbiey ka yafe mini ka ji tausayina" A banza yake jin maganarta ya ci-gaba da rarrashinta ta fara sauke ajjiyar zuciya ya ɗago fuskarta ya ɗora tasa akai yana mata murmushi ya ce "I love you" Ya shafa cikinta ya ce "Kin ji kyautar Allah ko Minty? Za ki bani babies ranar da nake jira ya zo tsayin shekaru babu adadi abinda nake fata da buri da kwaɗayi shi ne ki tabbatar ke jaruma ce baki amshi budurcina a banza ba, now let celebrate together wife" Ta lumshe idanunta tana jin ɗumin tafin hannunsa a hankali ta zame ta kwanta a jikinsa tana sauke ajjiyar zuciya "Abbiey" Ya ɗaga mata gira "Ka yafe mini ko?" Ya yi kissig nata ya ce "Allah ya yafe miki Ustaza" Ta yi shiru can ya matseta a jikinsa ya ce "Thank you" Nigeria Sosai hankalin Baba ƙarami ya tashi amma bai nunawa Umma ba, shi kansa Baffa ya ɓoyewa Mami komai a ɓangaren Umma ta ci-gaba da kula da Mardiyya har wata ramewa ta yi kamar itama laulayin take yi bata san nawa ta ƙarar ba burinta kawai jikanta ya zo duniya a ranar zata zuba ruwa a ƙasa kuma ta je ya direwa Ridayya ta kalli jinin Ustaz a duniya ta san jaririn dole ya kasance kyakkyawa Diyya fara tas haka Babban mutum tun yanzu ta fara nemawa yaro maganin baki. Da Biba da Baffa kusan tare suka shigo cikin gidan kamar zata bige shi ta buɗe murya ta ce "Ina kike ƴar matsiyata wacce bata san halacci ba wallahi kin yi kaɗan kuma kin jawowa kanki masifa" da Ammi da Umma kusan tare suka fito Ammi ta yi tsalle ta dire ta ce "Huhuhu ai daman na san za a-rina an saci zanin mahaukaciya har Ni za ki ci amana? Na baki ajjiyar kuɗi ki turmushe dake na kyatuminki ne?" "Daɗin kuɗin ba naki bane kuma na cinye na ci banza" Ammi ta daki cinya tana tafi da juyi ta ce "Ahhayeee riiii ai yanzu kinga me gari ya waya" Biba na huci ta ce "Ai ba ki ci lalas ba har ni za ki kira wanda zai aure ni ki ce masa wai zaman kaina nake yi? Banza mai kwacen saurayin wata annamimiya" Magana Mami za ta yi Baffa ya hanata ya nemi waje ya zauna watching all of them da yadda dramar zata kasance. Zagi suka dunga ƙundumawa junansu da tunawa kai asiri kafin dambe ya ɓarke aka fisge ƙarin gashin Biba, itama Biba ta tsalle ta damƙo zanin Ammi sai ga ɗan tofi ya faɗo ta zaga rigar sharaf abubuwan suka bayyana kamar nono ya zube a kwalta. "Za ki ci kaza kazanki ni za ki wa tsirara mai yawo hotel hotel" Junaid ya yi saurin juyawa Yaya Zuhura dariya kawai ta yi mai ciwo Mami na riƙe da Junior Zainura ta ce "I have never watch a beautiful movie like this perfect drama in season finale" Biba ta juya ta kalli Baffa ta kalli Mami ta ce "Ita ce nan ta yi asiri ta aureka kuma ta yi asiri ka tsani Ridayya saboda ta ji labarin zaka mallaka mata dukiya tun tana ciki wai ka zama Munafikin miji. Sannan ta yi asiri ka saki matarka Hajiya Fatima ka kwace Ridayya ka bata a ranar da ka bata jaririyar ta ajjiyata a bula ta kwana Muhammad Bilal ne ya ɗauke ta a wajan, kuma ta ƙonawa Ridayya harshe da wuƙa bayan ta gasata a gas ta yi jajur sannan ta fara bata maganin bacci har ya zame mata jinin jiki ta fara maida maganin na shaye-shaye shi ne ya taɓa mata ƙwaƙwalwa ta dinga amsar dukiya a wajanka kuma ita ta ɗauke tunanin Hajiya da Mai ran ƙarfe....," Sharaf suka ji faɗuwar abu da sauri Baffa ya miƙe ganin Mami zube a ƙasa Ammi ta dinga tsinewa Biba tana cewa ƙarya ne. Fitowar ta kenan daga lecture fuskarta ɗauke da farinciki yau Abbiey da kansa zai zo ɗaukarta da ya yi mata text ɗazo kasancewar ya ji Nigeria ya yi wata guda a can abubuwa da yawa sun faru a can amma bai faɗa mata ba. Inuwar mutum ta gani a gabanta tun daga shap ɗin mutumin ƙirjinta ya duka abin cikinta ya juya gabaɗaya watan cikin shida sai ka ɗauka ta kusa saukewa hakan yasa Ustaz baya barinta iya ɗaya karatun ma don ya zama dole ne hatta Tajj bashi da labarin cikin Ridayya daga ita sai MB USTAZ. Da ƙyar ta ɗago kanta numfashinta na riƙe wa idanunta ya sauka akan Sadauki dake tsaye cikin Black suit ya yi kyau ainun fuskarsa yalwace da wani irin murmushi na zallar so da ƙauna wanda yake nuna tsantsar kewa wani abu na fisgarsa zuwa gare ta ya azabtu ainun da rashinta ashe sa a ce ta kawo shi Japan har yana complain ba zai zo ba. Ridayya komai nata ya tsaya zuciyarta take ji kamar tayo sama zata fito da maƙoshinta Sadauki ya matsa yana kashe mata idanu ya ce "I so much miss....., shiru ya yi kalaman suka tsaya ganin turtsetsen ciki a jikinta. A yi haƙuri idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi 😥🥰👏🏻 [5/29, 12:08 PM] null: _*MUNAFUKIN MIJI*_ Nimcyluv 43 "Beloved" Sadauki ya furta idanunsa zube a kan ta, ganin tana jan baya hannunta dafe da cikinta daya girma sosai ya saka ya ƙara kusan ta kan sa zuwa gare ta, tana ƙokarin juyawa ta gudu ya saka hannu ya jawota zuwa jikinsa, abinda ya yi masa iyaka tare da yi masa shamaki daga rungume ta ya saka shi saurin sakin hannun Ridayya. Ciki! Shi ne abinda Sadauki ya gani har ya girma cikin haihuwa ko nacin abinci? mene ya haɗa his fiance da ciki? Innalillahi! Zuciyar Sadauki ce ta fara rawa tana wani irin yunƙuru masa har maƙoshinsa yake jin numfashinta, ya sake buɗe idanunsa da sukai laushi ya zuba akan cikin dake maƙale a jikin Ridayya,what does that mean? Did she cheat or what? Hatta ƙafafuwansa rawa suke suna neman gaza ɗaukar gangar jikinsa a karo na farko kuma kusan na biyu. Murmushi ya suɓuce masa dukda cewa idanunsa a rine suke tana iya hango yadda ƙirjinsa ke ɗagawa. Kallon Ridayya kawai yake irin kallon dake nuna, I love you so much, the kind of crazy love that even in Ustaz's eyes she has never seen that. Har ya juya sai kuma ya sake tsayawa irin me ya sa zan tafi? Why should i do that? Ridayya ce fa? Ba zata taɓa cin amanar shi ba, ya aminta da ita aminta mai yawa amintar da har zuciya da gangar jikinsa sai da suka shaida hakan, murmushi ya dinga yi shi kansa bai san dalilin faruwar murmushin nasa ba. "Wow! U look so beautiful shanshan kin sauya a idanuna sosai" yana magana yana ɗan hargitsa sumar kansa alamar ya fara fita daga yanayin da yake na Hamza zuwa na Sadauki. Ya zubawa cikin Ridayya idanu domin tabbatar da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, idan cikin gaske ne mene haɗin budurwar da zai aure da cikin haihuwa? What bring her here? Me ta ke yi a Japan? Ƙara matsawa ya yi wajanta ta girgiza masa kai irin ya dakata ɗin nan, he just trying to get more close to her a gigice Ridayya ta ce "Stop it, Stop it Stop it Sadauki" jikinta duka rawa yake tsoro da fargabar yanayin Sadauki ya saka mararta riƙe wa, idan ta tuna cewa Abbiey na hanya kamar yadda ya ce sai ta ji kamar abinda ke rayuwa a cikinta zai fito zuwa duniya ne, bata san hawaye ke fita daga cikin idanunta sai da ta ji saukar yatsar Sadauki manuniya ya sharce hawayen ta ɗago ta kalle shi ya mata murmushin a hankali nunfashinsa na sauka da kyar a fuskarta ya ce "Wai Shanshan wannan sabon yanayin fa? Bai dace dani ba na miki wani abu ne?" A taushahe ya yi maganar Ridayya ta kasa cewa komai bata san haɗa idanu da shi tsananin tausayinsa ke addabar zuciyarta, ta san ta masa laifi kuma laifi mai girma "Sadauki ka fahimta mana!" Ta furta a fusge tana ja baya ya bita ya ce "Me zan fahimta bayan abinda na fahimta yanzu? Ki barni kin wofintar dani saboda muradin ki yi karatu? Tunaninki ba zan bari ki yi karatu ba ko mene? And wannan guje-gujen na mene eh?" "I am sorry very very sorry Sadauki " "Sorry for what? Zan jira ki zan dinga dakon soyayyar ki a nan ɗina" ya nuna tsakiyar ƙirjinsa da hannunsa ya ce "Har zuwa ƙarshen numfashina, bani nake son ki ba Ridha ruhi da zuciya da gangar jikina ke ƙaunar ki, bana son komai sai rayuwa dake kawai so nake ki riƙe hannuna mu yi rayuwa tare.....," "I am sorry Sadauki ka yi haƙuri don Allah...," matse kafaɗunta ya yi idanunsa a rine ya ce "What wrong with Shanshan? Hakurin mene na miki uzuri na fahimci cimma muradinki zan jira da gaske zan jira ki, so halitta ne kuma jarrabwa ce na jarabtu akan ki Shanshan kawai ni ina son ki" "Ciki gare ni Sadauki ciki ne dani haihuwa zan yi, na haramta a gare ciki gare ni Hamza Sadauki " Ba kansa ne kawai ya harba ba hatta zuciyarsa sai data girgiza tana neman rabewa biyu a tsakiyar ƙirjinsa, kalmar CIKI kawai yake masa yawo komai nasa yana warware ƙirjinsa na matse masa guri guda, murmushi ya yi mai kama dana masu jin tatsuniya a fusge ya ce "Ciki? Wasan banza kenan" Ta girgiza kai ta ce "Da gaske nake" Ya tausasa murya ya ce "How? A gida an sani? A ina kika same shi? Kin san uban cikin?" Ta yi shiru kawai domin tana da yaƙinin Sadauki ba zai fahimce ta ba, tana kuma shakkar faɗa masa cewa ta yi aure ne, cikin sunna ne maƙale a mararta. Sadauki yana da naci da taurin kai kafin ta gama yanke shawarar abin yi ta ji ya damƙo hannunta ya ce "Ciki Ridayya? Abinda ya kawo ki makaranta kenan?" "Ba zaka gane ba Sadauki Please let go of me kar ka saka na shiga fushin Ubangiji" "Fushin Ubangiji na nawa Ridayya? Kin san me kika aikata zina? Har da cikin shega" a gigice ta ce "Ba cikin shege bane Sadauki, i am a married woman, am married and live with my husband in this country, ba abinda kake tunani bane wannan dalilin yasa nake baka haƙuri" Sakin ta ya yi a karo na farka na rayuwarsa a gaban mace idanunsa suka zubar da hawayen da bai shirya zubar su ba, yin kansu kawai sukai ba kuma iya idanunta ke hawayen ba hatta idanun zuciyarsa kuka take ya dafe kai ya shiga kaiwa da kawowa ganin tunaninsa ya yi hijira ya saka Ridayya ɗaga ƙafafuwanta da ƙyar ta bar wajan tsakanin gittawar mintuna ya juyo yana cewa "stop kidding me dear kina son zuciyata ta buga da gaske na san ba za ki iya karya alƙawarin da kikai mini ba, idan na yi magana ne ki yi yafe mini na tuba na bi Allah na biki Ridayya....," Shiru! Shi kaɗai yake kiɗan shi da rawarsa babi ita babu ko inuwarta da sauri ya rufa mata baya domin yasan wasa take masa. Bata ko ganin gabanta a haka take tafiya hannunta duka biyun riƙe cikinta hawayen tausayin Sadauki yaƙi tsaya mata, sama sama take jin ƙarar horn a bayanta a hankali kuma motar ke tafiya tana bin sahun ƙafafuwanta jin haka ya saka Ridayya matsawa gefe domin bawa motar hanya itama motar tsayawa ta yi a gefe. Bai jira an buɗe masa ba ya buɗe da kansa ya fito, jikinsa sanye brown ɗin suit mai kyau ya fito da ƙafarsa ya fito hannu ya ɗagawa wani ya dakata slowly yake tafiya har ya cimmata. Ƙamshin turarensa ta ji ta tsaya ba dai ta juyo ba sai da ya ƙara su ya ɗan taɓa kafaɗarta da sauri ta juya tana goge hawayen fuskarta ta ce "Abbiey" Ya ɗaga mata gira biyu idanunsa nutse a kanta da ƙyar ta yi yaƙi da zuciyarta wajan dakatar da kukan ta ƙirƙiri murmushi ta aza a fuskarta tana matsawa wajan kusa MB USTAZ ganin a gaban jama'a tana neman shige masa ya yi saurin kama hannunta yana bata side hug tare da tafiya da ita a hankali har zuwa wajan mota key ɗin dake hannun John ya amsa yana basa umarnin neman abin hawa ya buɗewa Ridayya gaban motar ta shiga kana shi ma ya shiga bakinsa ɗauke da addu'a ya fara driving zuwa direction da zai kai su gidan da suke a nan Japan ɗin. "Ni fa ban ɗauka da gaske yau zaka dawo ba Abbiey" bai ce mata komai ba ya dai juya ya kalleta ganin yau halin ya motsa ya saka ta yi shiru can ta ce "Ya hanya ka dawo lafiya? Ya su Umma, Mami, Baba ƙarami da Baffa?" Bai amsa ba sai sautin karatun ban daya ƙaro yana lumshe idanunsa a hankali yake kuma tuna yadda ya ruski Sadauki da Ridayya domin ya gane Sadauki sosai tun a gidan su Tajj da yadda ya riƙe mata hannu da ƙoƙarin rungume ta da ya yi ya cije lips underneath his breath ya ce "Allah ya yafe miki Ustaza" Sadauki ikon Allah ne kawai ya kai shi hotel ɗin da yake zaune ko wajan abokinsa Riyad su yake ya auna maganar Ridayya a ma'auni na hankali amma sam yaƙi samun gamsuwa da maganar ya ji yaƙi yarda dole ne ya sake ganin Ridayya domin this time around ƙafarsa ƙafar Ridayya zuwa Naija zuciyarsa gabadaya ciwo take masa, he feels like uwa wani abu ke shirin faruwa dashi. Wayarsa ya dauka shiga duba picture ɗinta a hankali yake bin baƙar fuskarta da kallon fararen idanunta masu kyau da tsari ga wasu irin abubuwa na musamman a cikinsu ya yi murmushi yana manne wayar a ƙirjinsa a hankali ya ce "Rest of my life" ya sake lumshe idanunsa underneath his breath ya ce "Shanshan my love" Number hajiya Azizat ya kira ta jima kafin ta ɗaga ya yi shiru itama ta yi shiru can Sadauki ya ce "Are you still crying mother?" Ta cikin wayar ta ce "Kuka kuma? Do i look like a baby to u Hamza?" Zai yi magana ta ce "Ya isa now tell me ya Japan yaushe zaka dawo kuma" Ya cije lips "guess what?" "No idea son" "I meet Ridayya" Da sauri kuma cikin ɗaga murya Hajiya Azizat ta ce "What! Ka yi mata magana a can kuma Japan ɗin?" Cikin rashin fahimta Sadauki ya ce "Me ya sa ba zan mata ba? Bayan da tunaninta kullum nake kwana da tashi, i meet her i talk to her ta sauya sosai na ji kuma na ƙara son ta fiye da ko wacce rana data shuɗe" "Innalillahi wa'inna illahir raji'un!" "Wannan salatin fa?" A kasalance ta ce "Stay away from her" Shuuuuu! Ya ji abu ta cikin kunnensa yana shigewa ya kasa cewa komai sai kawai ya kashe wayar gabadaya ya kasa yin wani ƙwaƙƙwarar tunani. Riyad ya kira ya ji yaushe zai shiga makarantar su Ridayya ya faɗa masa sai basa wani secret abu yana buƙatar information akan haka. Ridayya na zaune hannunta riƙe da honey ɗin da maid ɗinta Ilhas ta haɗa mata, matar ta jima a gidan MB USTAZ ne da kansa ya saka aka nemo masa mace mai hankali wacce zata kula da Ridayya da abinda yake cikinta, shi kansa da yake namiji bai taɓa ganin ciki mai girman na Ridayya ba, ga tafiya ta saka shi gaba kuma yana tsananin tsoron barinta ita ɗaya, komai yake hankalinsa yana kanta. Mai aikin ta ce "Madam kina huta sosai ƙafafuwanki sun kumbura ga ƙirjinki yana yawan ɗagawa kamar mai matsalar numfashi, cikin ya yi girma dukda da bai shiga matakin haihuwa ba" Ridayya ta ja ajjiyar zuciya tana shafa cikin har yanzu Sadauki ne ke yawo a zuciyarta cikin sauri jima take yin Assatagafirullah! A gajarce ta ce "In sha Allah zan kula" "Me za a tafa muku naga Alhaji ya shigo" "No; kar ki damu da abinda za mu ci zan kula da wannan ki yi abinda kike so kawai" Ilhas ta jinjina kai domin bata jin daɗin jikin nata amma tabbas Ridayya na buƙatar kulawa ta musamman. Fita ta yi domin iyaka cin ta ƙaramin parlon gidan ganin hakan ya saka Ridayya miƙewa bayan ta kammala shan zumar ta nufi shashin da ta san gwarzonta na ciki, ƴar ƙaramar riga ce a jikinta silver mai sauƙin nauyi domin zafi jikinta ke yi mata dukda weather na ƙasar, rigar iya cinya jikinta duk a bayyane ga cikinta a gaba sumar kanta a tufke har baya gwanin sha'awa. Tura ƙofar ta yi sallama ta yi cikin siririyar muryarta mai cike da nutsuwa da tarin rauni tana shiga yana fitowa daga wanka murmushi ta yi ta ƙarasa bakin gado ta zauna tana miƙe ƙafa ta ce "Yau me ya samu Yaa Bilal ne?" Showel ɗin hannunsu ya miƙa mata ta gane me yake nufi ta maƙale kafaɗa ta ce "Ni ma na ga ji fa" "To tasar mini a ɗaki" Ta dinga dariya tana kallonsa ganin yadda ya kame fuska sam bata san fushin me yake ba, dukda bai nuna ba amma ta san dole akwai wani abu a ƙasa tana kallonsa ya gama shirya wa tas sai baza ƙamshi yake ya fito a cikakken mutum mai cikar zati gwarzon Ridayya mijin Ridayya yayan Ridayya jigon Ridayya ta ko wacce fuska, kusurwa ko wanne sashe. Jallabiya ya ɗakko zai saka yana sane ta yi saurin miƙe fuska a shagwaɓe ta ce "Abbiey Please na" Tana taɓa shi ya yi saurin damƙo hannunta ya haɗa ta da jikin wardrobe ta fara zazzare ido ya dinga kallonta ya ce "Wana kama?" "Ni ni.... A a bani ba" Yanayinsa ya bayyana tuni shiyasa ko magana baya son yi ya sauke mata numfashi a ƙirjin "Ke kina tura mini stickers da emojis na kisses, a hall meeting" "I am sorry" "Nooo!!" Magana za ta yi kawai ya kashe hasken ɗakin bisa sunna ya nufi bedroom....... Ƙafarta yake danna mata a hankali kumburin na sauka tana kwance gefensa karatun kur'ani suke saurara duka suna bi a hankali wayarta a hannunta ta shiga X tana rubutu can ta ji ya kashe karatun ya rungume ta very tight a jikinsa zuciyarsa na bugawa sun jima kana ta zuba masa ruwa mai sanyi ya kalli ruwan ya saka hannu ya amsa ya ajjiye ta ce "Kasha mana" "ban so" "Me kake so" "You!" Ta zuba masa ido yana ƙara riƙe ta a jikinsa "You Ustaza i want you Ridherh, I need u jaririya i want u always to be by my side I love you, I really really loves u Nisful hayaat" ya sumbaci kuncinta bayan ya gama maganar. Gaban Ridayya ya faɗi akwai abubuwa da Abbiey ya kamata a ce ya sani amma ba zata taɓa iya faɗa masa ba, ba zata iya ba ita haka ƙaddararta take zama da MUNAFUKIN MIJI ya rusa dukkan wani jin ɗaɗinta ya taɓa career ta. Kallon juna sukai ta ce "About yesterday a makaranta" ya yi shiru ta ce "Sadauki Abbiey..." Ya yi saurin rufe mata baki da yatsu biyu ya ce "It's ok" "Ya zo wajena....," ya watsa mata wani kallo jikinta ya yi sanyi calmly ya ce "I trust you ok" Ta jinjina kai tana komawa jikinsa ta kwanta “I love you” da sauri ta miƙe tunawa da zata ɗora girki ga dare na yi ta kusa faɗuwa ya riƙe ta ya ce "Zauna" "Abinci zan yi fa baka ci komai ba" "Na sani, akwai maid za ta yi" ta maƙale kafaɗa ta ce "Bana son mai aiki ta yi maka salon ta barbaɗa wani abu" "Kina tsoran snitching" Gwalo ta yi masa har ta tafi ta dawo kamar zata ɗauki wani abu ta yi masa kiss ya girgiza kai kawai yana lumshe idanunsa. Ridayya taƙi komawa makaranta saboda tsoron gaminta da Sadauki sosai take jinsa a zuciyarta da shakkar haɗuwa da shi. Soyayya suke mai cike da kwanciyar hankali da fahimtar juna gashi kullum sai Ustaz ya bata magani ya kuma yi mata addu'a wani lokaci kuma ya sauya mata hira don ya fahimci aikin maganin, ya gujewa zuwa Nigeria yana buƙatar zama kusa da iyalinsa da bata kulawar daya dace ita da abinda ke cikinta. Suna da fahimtar juna amma hakan baya hana su samun saɓani wani lokacin Ridayya ta dinga kuka tana ita gida kawai zata koma shi kuma ya birus da ita idan ya gaji da jin kuka ya dafe kumatu ya ce "Oh ni mijin kwaila naga ta kaina, wanne zunubi ne wannan Ustaza?" bata yin komai sai girka musu abinci da wanke kayan Abbiey na sirri domin ta ce gajerun wandonansa sirrinta ne. MB USTAZ a zuciyarsa yake tsananin haɗuwa da Ubangiji akan hakkin Mardiyya ya kasa sauke nauyinta dake kansa har zuciyarsa kuma babu saki a tsarin rayuwarsa yana jin da zarar Ridayya ta sauka za su koma ya daidaita kan matansa ya yi addu'ar Allah ya bashi ikon kamanta adalci a tsakaninsu gashi daman an ɗaga zaɓe sai zuwa watanni bakwai masu zuwa... Umma na zaune a parlour look so worries tunanin inda za taga Babban mutum kawai take ta ji a ranta fushi ya yi saboda ta saka ya saki shegiyar yarinyar can wacce bata san wacce duniya take ciki ba, gashi abubuwan hannunta na neman gazawa ta yi siyayyar haihuwar Mardiyya gashi da sauran rina a kaba Diyya ta ce kayan fitar suna kala ashirin take buƙata, filin da ya yi saura wajan Umma ta mallakawa cikin Diyya ta saka sunan Mardiyya har da shaidu abin duniya ya fara yi mata zafi ita hakan duk bai dame ta ba ɗanta kawai take son gani, gashi har mujiyar yarinyar ba labarin su ta kalli Baba ƙarami ta ce "Ka yi wa Allah ka faɗa mini inda yarona yake ina so na ganshi ga matarsa na dab da haihuwa duk wasu responsibility nata yana kansa ka ji tsoron hakki Abba" "Responsibility?" Baba ƙarami ya maimaita ta ce "E, hakkina na uwa dana matata dana cikin dake jikinta nasan kasan inda yake duk duniya bashi da wacce ta fini wallahi" "Hajiya Hadiza kenan ashe kin san ya sauke hakkinki na uwa ke kuma ba ki san ki sauke nasa ba ko? Ko a naki tauhidin babu haka halan? Ke da kan ki kika saka ya saki matarsa dukda kin fi kowa sanin irin son da yake mata, kika zana masa kashaidin zama da wacce kike ganin ta dace da shi, while ya miki abinda kike so shi ma soyayya ta saka ya yi abinda yake ganin daidai ne 50/50. Bari ki ji duk abinda ya faru ki kuka da kanki babu wanda ya ja miki sai ke, kin ɗauki son zuciya ki sawa ranki ki kasa yadda da ƙaddarar Ubangiji ki kasa tunanin dukkan abinda ya faru muƙaddari ne daga Indallahi, wallahi tallahi sai Allah ya tambaye ki hakƙin Muhammad domin raya kiwo ne a gare mu" Cikin fusata ta ce "Na gaji Alhaji Tahir na gaji ni duk ba kaga irin baƙin cikin dana haɗiya ba? Wacce uwa ce zata zuba idanu ɗanta yana wahala akan abinda nake tunanin yafi ƙarfinsa? Ka duba ƙaunar daya nuna mata ya sadaukar da farincikinsa samartakarsa just because of her? Who is she in the whole world? Ƙiri-ƙiri ta kalli tsabar idanunsa ta ce masa Allah ya isa ta tsane shi saboda mijinta Zameer ta kalli idanunsa ta kira shi da sunan da ko ni shaƙar faɗa masa nake, tun tana zanin goyo yake ɗawainiyya da ita komai ya samu ita, sai yanzu da komai ya ƙare mata zata dawo wajansa don taka bashi da zuciya a kanta, to wallahi tallahi ba a haifi wacce zata wulaƙanta mini yaro ɗaya tal a duniya ba, kuma ina kan bakata bana son Ridayya bana ƙaunarta gwara da Allah ya raba su balle baƙin cikinta ya kar ni" "Idan baƙin cikinta bai kashe ki ba, rabo zai kashe ki" "Me kake nufi what do you mean by that eh?" Ya miƙe tsaye ya ce "Kin ji ai, ki raba kanki da rabo ki ji tsoron rabo tun wuri ki amshi ƙaddara, daga ƙarshe ƙofar da kika saka a ɗakin babban mutum sam bai bata dace da ɗakin ba" Ta yi ƙwafa ta fice little ya shigo kenan ta saka hannu ta kwaɗe keyarsa ya juya da gudu yana kuka tare da yarda da chocolate ɗin hannunsa. "Mimi mimi mimi" little ke faɗa a gigice yana fasa ihu sosai dukan ya shige shi daman ita da Mardiyya da Ammi ke zane shi idan ba idanun mutane har ya gane ya daina zuwa wajan su. Zainura ta matsa da sauri bayan ta gama ciwa Burhan mutunci ta ce "Sweetie kai da waye" Hanyar part ɗin Umma ya nuna mata ta gane sarai ta murguɗa baki a zuciya ta ce "Allah ya isa wallahi" Ta rarrashe shi da ƙyar ta juya kan Burhan dake cewa. "Ki dube ni na sauya sosai Zinu ba da niyyar soyayya na zo wajanki ba, amma na ji ina son ki wallahi auren ki zan yi" "Kanbu! Ka raina mini wayo raguwar wiwi zan aura kenan? Allah ya suttura mini Zainura ta fi ƙarfin ka ta ko wacce siga" Ya juya kai ya ce "Zan sauya yadda kike so Zinuna kuma ma ai na fara daina shan komai kuma ina sallah 5/daily" Ta ɗauke idanunta domin yana da murya mai sanyi gashi daman rashin kulawar iyaye da masifar talauci ya saka ya shiga halin da yake ciki "Mene gaskiyar lamarin?" Nan take ya warware ko wanne ƙulli da Ammi ta ƙulla bai ɓoye komai ba, domin yana da faɗar gaskiya bashi da tsoro Baffa yana jin komai sai jiri ya fara ɗaukar shi ya saurin riƙe kansa da sauri ya juya zuwa part ɗin Ammi tana zaune ta yi zuru-zuru tun bayan faruwar tunan asirinta Baffa bai ce komai ba, tana tsoron matakin da zai ɗauka da sauri ta miƙe tsaye ta ce "Baffa lafiya?" Wayarsa kawai ya danna yana ta tsaye idanunsa akanta wajan mintuna 15 aka kira shi ya ɗauka ya ce "Su shigo" Polices ne mata guda huɗu ya kalle su ya ce "Arrest her" Ammi ta ce "Baffa police ne fa me na yi matarka ka saka a kama?" Ya juya baya ya ce "Take her out please na sake ki Hajiya Maryam, ta faɗa muku abubuwan data aikata mini nida yarana idan taƙi ku yi ta dukanta" Yana faɗar hakan ya fice Ammi ta zumduma ihu sosai tana kuka ihu da kururuwa kafin ta sulale a ƙasa ba numfashi haka suka ɗauke ta zuwa waje Baba ƙarami bai san meke faruwa ba haka Mami Yaya Zuhura daman ba ruwanta da Ammi Burhan ko a ƙafarsa ta Zainura kawai yake Baffa ya nufi ɗakin Mami tana riƙe da junior Baffa ya shigo kafin ta yi magana ya rungume ta tare da fashewa da kuka mai tsanani. Mardiyya ta dinga tunanin yadda BM USTAZ zai dawo har ta samu kusanci da shi kuma ta dangana masa alhakin zama uban cikin jikinta, dabara ta ƙare mata gashi tana gab da haihuwa ne a ranta kuma take jin yanzu ta fara zama da Muhammad Bilal ba zata ta bari kowacce mace ta raɓe shi ba. Suna tsaye gabaɗaya a harabar makarantar Zameer na gujewa ganin Tajj burinsa ya sake samun dama ya koma wajan Baba ƙarami ya lafta masa wata ƙaryar da dole zai saka Baba ƙarami ya bawa Ustaz umarnin sakin Ridayya shi kuma ya saka ta dawo gidansa zai lallaɓata da soyayya irin wacce ya saba yi mata a baya. Daga nesa suka ji ana cewa "Gashi can aradun Allah hene mijina ne Allah ya kawo ni Kano" Ta faɗa tana tisu kewar wani yaro wanda suke shekaru ɗaya da little Bilal ga wata yarinyar itama a baya ta yi yarkace kace zani na neman faɗuwa Moo ya ce "Wancan fa kika ce wancan ai mijin Ridayya ne" Ta zabga salati tana yagalo yarinyar daidai nan Zameer ya fara ƙoƙarin guduwa ya ji an tare shi ta gaba ya buɗe idanu ganinsa ya sauka akan Khairy itama hannunta riƙe da wata baƙar yarinya ta sha bille taya-taya a fuska ga leɓen yarinyar ya sakko ƙasa suka saka Zameer a tsakiya...... A yi haƙuri a yi haƙuri Please...... A tsitsita haka nan a tausasa zuciya 🤓 ko editing ban ba bear with the errors and spelling mistake. [6/5, 1:31 PM] null: *_MUNAFUKIN MIJI_* ..... Nimcyluv 44 Ya kalleta ya ce "what brought you here Khairy?" Ta juya idanunta tana nuna shi da hannu ta ce "Lallai so are you questioning me? Ba ka yi expecting ganina ba ko?" Ya haɗe fuska ya ce "I have no reason da zan buƙaci ganin ki balle na yi expecting zuwan naki" Khairy ta yi wani irin ciji baki jin wani rainin wayo na Zameer ta ce "Oh really? Is that so haka ma za ka ce kodayake ban yi mamaki ba mutumin ƙauye kuma bakatsine ɗan Fulani ba tsiyar da ba zai iya tufkawa ba, musamman ta wajan mugunta" Ta juya ta kalli Hanne dake tsaye yarkace kace ta kalli ɗanta Harazimi wanda duk ya fice daga hayyacinsa ba zaka taɓa cewa rana ɗaya aka haife su tare da little Bilal ba. Yarinyar hannunta ta dire masa a gabansa ta ce "Kaga dalilin zuwana, bayan na haifeta ba zan iya ci-gaba da zama da ita ba, domin ko nono bata taɓa shaba ba zan iya dakon wahala ba" da wani irin expression Zameer ya dinga kallon Khairy without saying a single words, sosai kalaman Khairy suka saka masa wani irin gigita ya fara goge zufa domin shi rabon shi da ita tunda ta taka tun daga Kano ta iske shi har garin Katsina ƙauye Nahutu dake Batsari, amma shi ne zata kawo masa wata yaƙunanniyyar yarinyar kamar ƙarshen duniya ta ce ƴar shi ce? Mahaukaci ta mayar da shi kenan. Ya yi murmushi ya ce "Khairiyya Please ki faɗa mini mene ya kawo ki bani da lokaci" "Hehehe sai ka ce mai aikin gwamnati ko wanda yake rolling babban kamfanin babansa, banda aikin banza da zaman kashe wando babu tsiyar daka iya, sai shegiyar ƙarya kamar me ga fake life kamar jinin ƙaruna, wai Zameer Mahboob Dollar ai kowa naga dollars ganin idanuna a gona, wallahi ka kiyaye ni ba Khairy daka sani bace, kuma ni ba irin Ridayya ba ce for sure don ma ka ji" Zuciyarsa ta buga tana neman tarwatsewa a ƙirjinsa da ƙyar ya iya controlling kansa domin bashi da wata power ga yadda friends ɗinsa suke kallansa ya ce "Ki yi komai ki ce komai amma karki sake sako sunan matata a nan wajan, domin ita ba irin ki bace Khairy kuma kika yi wasa yanzu zan sauke miki yatsun hannuna a fuskarki" Khairy ta ware idanu ta ce "Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa wanne dare ne jemage bai gani ba? Wanne kalar cin mutumcin da cin fuska ne ba ka yi wa Ridayya ba saboda ni, ka dake ta, ka ƙona mata fuska, ka karyata a hannu saboda ta gane ina ɗauke da cikin da ka yi mini kuma a cikin gidan aurenta na sunna,har na gama zamana a gidan ta rayu ne da tunanin ni ƙanwarka ce, ranar da na kai maka shegen ɗanka dana haifa a Katsina ta san komai a take ta yanke jiki ta faɗi naƙuda ta kama ka, ina cewa a garin naku ma mayya suke ce mata saboda muninta da baƙar fatarta, wanne mataki ka ɗauka eh? Ai wallahi tallahi masifu yanzu ka fara gani ita kuma mayyar bata san darajar kanta bane shi ya saka ta manne maka har yanzu" Tana faɗin haka ta sake tura masa yarinyar dake kuka tana share majina baki har kusan kunne ga uban leɓe an yi mata wani tsagu a fuska fuskar nan sai naso take tamkar an shafa mata soda ta ce "Ƴarka ce uwarka na yi takwara gata nan ana ce mata Deluwa, and please daga yau babu ni ba kai har gaban abada bana son yaran ciki daman kai ka yi shi ina son na yi free domin ban son ƙaddararka ta shafe ni Giɗaɗo" Kamar statue haka Zameer ke kallon Khairiyya yama kasa tunanin komai da ƙyar ya ce "Ki ji tsoron Allah Khairy na san cewa namijin ɗana ne amma wallahi tallahi bani ne uban yarinyar nan ba, ki dube ta ki dube ni babu ta inda mukai kama da wannan yarinyar, wallahi ki nemi ubanta tuntuni" Ta juya idanu ta ce "Matse maka ta yi wallahi ina da abinda zai saka ka tafi gidan yari for life har mutuwa, ba wai blackmailing naka zan ba, and this is my final decision bani ba kai" Zufa ce ta dinga yankowa Zameer ganin gininsa na neman rushewa shegu har biyu ya shiga uku ya zai yi dasu? Ya dinga kallon yarinyar da ƙyanƙyami a fuskarsa gashi kamar wacce ta san shi sai manne masa take Harazimi ma ya matsa kusa da shi, ga yarinyar wajan Hanne ya shiga uku! Yara har uku amma babu na zaɓe gashi yana ji yana gani an ƙaƙaba masa yarinyar da bashi da alhakin samar da ita. "Wai Zameer meke faruwa? Daman abinda kuka aikatawa Ridayya kenan kai da Khairy? Taya Ubangiji ba zai jarabce ka ba, na sha baka shawara akan abubuwa da kake gashi yanzu wankin hula na neman kai ka dare, a cikin gidan aurenka ka yi zina da wata matarka ta sameka turmi da taɓarya har ta rufa maka asiri kuma ka ci-gaba da zaluntar ta? Akan karuwarka ka fifita matarka ta sunna? Yanzu ka dubi yaran da suke gabanka da sunan naka? Wacce kake ganin matsayin mujiya bora a cikin mata mummunan ita ta haifa maka kyakkyawan yaro, wanda kake ganin sun fita kuma ka abinda ka shuka nan ka girma, ba a kushe halittar Ubangiji wannan ya zama izina gare ka" Khalid ya ce "Wannan shi ake kira da baƙar tukunya mai fidda farin tuwo, ƴar baƙa mummunan da haifar kyakkyawa, sai na ji ni baƙar macen wallahi ta fiye mini fararen nan sosai" idanun Zameer ya sauya ya rini maganganu Shaba sun masa zafi kamar ya watsa wuta a ƙirji ya ce "Khalid karka sake aibata mini mata wallahi zanci uban daya kawo ka duniya yanzu"... "Ni kake zagi akan gaskiya? Ina cewa kai ka fara aibatata a gabanmu eh? Da sanda ta fara cewa tana sonka wanne kalar zagi ne baka yi mata ba? Kuma...," bai ƙarasa sauran maganar ba Zameer ya kai masa naushi a baki tuni bakin ya fashe jini ya fara zufa ya ƙara kai masa duka "I love my wife, ina son matata Ridayya har gaban abada yanzu na fara son ta, ina jin kuma son ta ne zai zama ajalina wallahi akan ta sai na iya kashe ka muddin zaka ci-gaba da abinda kake faɗa a kan ta" "Ni ka daka?" Zameer ya ɗaga shoulder ya ce "Na daka ɗin ka ƙara cewa uffan akan mai sona" Khalid ya wani irin murmushi yana tare jinin dake zuba ya ce "Ka yi kuskure baka san waye ni ba, you have no idea na abinda zan maka amma wallahi tallahi sai na yi bugu, bugun da zai taɓa zuciyarka ta fashe nan take ka mutu zaka san waye Khalid" "A'a guys karku ɓata zumuncinku akan macen, kai Khalid ka yi kuskure kaima Giɗaɗo ka yi " Shaba ya faɗa yana riƙe dariyarsa musamman idan ya juya ya kalli yarinyar wajan Khairy ya dubu Hanne da har yanzu take tsaye. "Ba ruwan ka Shaba karka shiga abinda ba bai shafe ka ba" Khalid na faɗar ya yi gaba zuwa motarsa. Moo dai couldn't speak saboda al'amarin ya fi ƙarfinsa tunanin rayuwa kawai yake. "Kece matarsa baiwar kenan ke kishiyar Ridayya ce?" "Sharri! Kwarankwasa ƙarya ne a gabana a kunne na akan idanuna ya saki matarsa Ridiyya, bayan sun yi yarjejeniyar zata bashi takardun da aka bata na filaye shi kuma ya ce zai sake ta, yasan wai dole duk inda ta je ta dawo wajansa sata komo tunda bata da kowa a duniya sai shi iyayenta sun mace tuni, ita kuma ta ce aradu ta yadda ya sake ta, ya ce ya sake ko sako ɗaya ne? Na rantse da Alkur'ani mai girma ya saki Ridiyya ba tare da idda ba domin tana haihuwa hakan ya faru ji munafukin miji?" Salati kawai Moo yake yana kallon Hanne zuciyarsa na tsinkewa tana wani irin rarrabewa a ƙirjinsa, ya yi saurin cewa "Haba Hanne ki tausaya mini wanne ce kaɗai hanyar da zan dawo da Ridayya zuwa duniyata wallahi ina son ta, ban san har haka son ta ya addabi zuciyata ba sai yanzu, zan iya rasa raina da ita kawai nake samun nutsuwa, ina jin zan rayu da Ridayya ko zata mini iyaka da taɓa yatsanta ne, bana iya bacci kullum sai ta mini gizau ki taimaka mini, karki bari ahhalin Ridayya su ji wannan batun" Kallonsa kawai Hanne take tana girmama son zuciyarsa ta ce "To shikenan mu je ka bamu wajan zama da abinci" da sauri ya ce "Ok jira ni a nan na samu napep ok" ya yi bakin gate ɗin makarantar da sauri. Moo tausayin Zameer ya ji amma ya san shi da Ridayya har abada. Zainura na tsaye gefen motar driven gidansu watching them ta kalli komai da komai ta yi saurin yin saving VR ɗin na wayarta, ta nufi wajan Hanne cikin sauri tana mata magana. Japan.... Kallonsa ta yi a hankali ta ce "Abbiey sai yaushe zaka dawo ne?" Ya dube ta ya ce "Soon" Ta marairaice sosai ganin yanayinta ya saka ya kama hannuna ya ce "What? Ba mun yi sallma ba daga nan airport zan shige" "I will go with you" Ya kalle ta da kyau sai ya nuna mata cikin jikinta ya ce "Sai kin haife mini wannan babin ɗin, na ƙara miki wani cikin ko ki mini" Ta tura baki cikin shagwaɓa ta ce "Tab, ni daga wannan ban kumawa ɗaukan ciki wahala dakon shi haka haihuwa kai duk me ka sani" "Daɗi" "Me ka ce?" "Na san daɗi mana, kema haka ɗaukan ciki dai daɗi gare shi Ustaza" Cikin jin kunya ta ɗauke kanta gefe ya kai tafin hannunta zuwa bakinsa ya yi kissing so lightly in a romantic style "I need u" ta yi masa gwalo ta ce "Abbiey" Ya yi ƙasa da murya sosai yana sake damƙe hannuna ya ce "Are You okay with me? Please Mintyna open ur heart ni mijinki ne kuma sirriki muna samun saɓani wannan duka nrml ne ga ko wanne ma'aurata but ban san zaluntarki ta wannan ɓangaren na san akwai alkunya" Ridayya ta sake yin ƙasa da kanta tana murmushin ya ce "Talk Ustaza" "You are the best Abbiey, na gamsu sosai" ya saka hannu ya dungure mata kai ta ce "Auchhi" "Allah ya yafe miki Ustaza ba ki taɓa appreciate ƙoƙarina ba, kin san ni ba inji ba, ur words make me feel enough and encourage my energy" Ta yi saurin ɓoye kanta a should ɗinsa tana dukan ƙirjinsa a hankali kuma ta fara shafa sumar da ta yi kwance jikinta ya saki ta ji mijinta kawai take buƙata wani irin son Abbiey take kamar rai kuma har yanzu bata taɓa mayar masa da raddin he loves him ba, tana jin kamar bata cancanci zama matarsa ba still har yanzu kuma hankalinta a tashe yake kullum cikin fargaba yake. Tana jin yana jan hancinta underneath his breath ya ce "I love you Ya Rouhi" Ta yi shiru can ta ɗago kanta, ya zuba masa idanu with different emotions dake cin ranta da zuciya, for the first time a rayuwarta ta matsar da fuskarta zuwa gare shi, hakan ya sa ya gyara zuwan al'amarin da kyau..... She just give him a hot and deep kiss on his lips sai kunya ya kamata tunda wannan shi ne karon ta na farko, sosai take jin kunyar Abbiey a wannan ɓangaren tana ƙokarin matsawa ya yi saurin riƙe fuskar nata ya shiga bata sumbata halattacciya ƴar sunna irin wacce aka halatta wacce kuma ya karanta. Sai abin ya zama na su biyun ita ma ta cire kunya aka koma ban gishiri na baka manda da sauri ta yi baya ta ce "Zan yi test" Ya yi miskilin murmushi ya kasa cewa komai can dai ya nisa ya ce "Thank you, Allah ya yi miki Albarka Ustaza, ya sauke cikin aminci ya kare ki bisa kariyarsa.... Jazakilla bil khair Nisful hayaat, i love you Miftaahu qalbiy" Sosai ta ji daɗi ta kama hannunsa ta ce "Wasiymna, Allah ya kare ka da kariyarsa ya kare ka daga sharrin mutum da aljan, ya ƙara baka buɗi da arziƙi mai amfani ya wada taka da kyakkyawar zuciya ta taimako, ya kiyaye ka daga sharrin ƙarfe, Allah ya raba ka da haram ya haɗa ka da halak Allah ya tsare mini Qalbiy" Bashi da wani option wanda ya shige rungume ta sosai zuciyarsu ke bugawa da ƙyar ya cire ta, ya fita ya buɗe mata mota ta fito jingina ya yi da motar yana kame kansa da kyau fuska a kame ta ce "Abbiey zan shiga Allah ya kiyaye" Kai kawai ya jinjina mata idanunsa na yawo a harabar makarantar kamar mai duban wani abu, har ya juya sai kuma ya tsaya kamar bai son magana ya ce "Ki kula ok?" Ta ɗaga masa kai tana tsaye har ya bar makarantar..... Hankali kwance ta gabatar da karatu da kuma test ɗinta sallah ke tayar da ita jikinta ya mata nauyi sosai ƙafarta ya kumbura ainun, ƙarfe biyar ta fito tana kiran number drive kamar daga sama ta ganshi ta yi saurin ja baya, sosai ta razana ganin kamar ba shi ba ya yi duhu sosai ya rame. " I couldn't sleep shanshan, don Allah ki tsaya muyi magana idan tsoro kike sbd cikin nan ni ban ɗauki hakan a komai ba sai ƙaddara kuma ke ɗin nake so ba wani abu naki ba" Ta yi shiru Sadauki ya matso gabanta ta yi baya da sauri ya cafko hannunta a gigice ta saka hannu ta zabga masa mari ta ce "Ka dawo hayyacinka Sadauki ba cikin shege na yi ba, ina da aure ina da aure matar aure ce ni, cikin sunna ne a jikina" Dumm!! Haka Sadauki ya ji a kansa tamkar a duka masa wani abu, ya dinga kallon Ridayya can ya ce "Zan so ki ƙara marina ko zan farko daga mafarkin da nake, wannan kalman naki na banza ne wasa kike mini, day by day haka nake rayuwa da tunaninki, soyayyarki, ƙaunarki a zuciyata ba za ki iya auren wani ki bar ni ba, ba cancanci hakan ba" Kuka ta fashe da shi sosai tana girgiza kanta ta ce "I am sorry i am sorry Sadauki " da ƙyar ya ce "Is like something wrong with you?" "Yes seriously I have something to tell you, i want to apologize for my actions. I realize now that i made mistake by prioritizing financial status over our relationship. I deeply regret hurting you and i understand if it's difficult for you to forgive me". "Me kikai?" "I choose someone over you " "After a year? Duka wanna Ridayya da wanna maganar gwara ki ɗauki wuƙa ki caka mini a ƙahon zuciya Ridayya, gwara tun Fil'azal ki ce bani kike so ba da ki dinga wasa da feelings ɗina, me ya sa?..." Wani irin hawaye ne ya fara zuba daga cikin idanunsa wanda bai shirya musu ba, ƙirjinsa ya dinga ɗagawa jijiyoyin kansa suka firfito magana yake son yi amma ya kasa ya riƙe saitin zuciyarsu da ƙyar ya ce "You broke my heart Ridayya, ki tausaya mini don girman Allah.... I love you Shanshan Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun! Wasbunalallahu wani'imail wakil Ubangiji ka ɗauki raina my heart hurts my chest is burning Ridayya why? Why don Allah why are you doing this to me?..." Cikin kuka tana durƙushewa ƙasa dafe da cikinta ta ce "Sadauki stop all this forgive me don Allah" Ya girgiza kawai tears running down to his face wasu na korar wasu ya ce "I just forgive.... But will never forget" Kuka gabaɗaya suke da ace zata iya auren maza biyu tabbas data auri Sadauki ta haɗa biyu shi da Abbiey amma bata da wannan ikon. Tari ya fara da ƙarfi jini ya fara zuba hanci da baki yana ƙoƙarin miƙa hannu ya taɓa ta, da ƙyar ya ce "I will die for your love Ridayya Ubangiji shi ne shaida, stay with me please hold my hands ko sau ɗaya" Girgiza kai ta yi ta ce "I can't i can't Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun na shiga uku wai meke damuna mene ya yi coursing problems ɗin nan a rayuwata why all this happens to me, forgive me please Sadauki a gigice ta yunƙuru tana nufar kansa ganin idanunsa ya yi sama zuciyarsa ta daina bugawa ta fasa ihu ta ce "Karka ka mutu Sadauki don Allah karka mutu i love you....." Ta girgiza shi ta taɓa zuciyarsa bata bugawa ta taɓa agogon hannunsa baya harbawa wani irin ihu ta yi ta ta ce "Nooooo karka mini haka Sadauki don't leave me Daga yau in sha Allah kullum za a dinga yi har a kammala babu jira kuma kafin sallah mu idda ai alamu ya nuna ma... A yi comments a yi sharing 08164069385 [6/10, 11:23 AM] null: *MUNAFUKIN MIJI* Nimcyluv...... 45 *Masu arewabooks ku yi following account ɗina domin samun duka books ɗin 👇🏻* https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv Ba ƙaramin gigicewa Ridayya ta yi ba ganin gawar Sadauki a gabanta, a ƙasar da babu kowa nasa ba uwa ba uba, ba ƴan'uwa hatta ita kanta bata da kowa wanda ya shige Ustaz gashi kuma yabar ƙasar ya koma Naija? Ta rasa mafita sai kuka take tana girgiza shi ta fita hayyacinta sosai gani take tamkar ita ce silar mutuwar Sadauki "Don Allah ka tashi karka zama ragu a soyayya shin ba ka ji sunanka bane Sadauki? Ya zan yi dakai a ƙasar da bamu da kowa ka farka don Allah na san suma ka yi soyayyata ba zata taɓa zama ajalinka ba..." Sosai take kuka ga wani abu daya tukare mata a ƙirji. A kusan tare wasu manyan motoci guda biyu sukai parking a gefen Ridayya da kuma Sadauki dake kwance baya ko motsi, ta cire idanunta gabanta ya faɗi ganin bata gane mota ko ɗaya ba, a hankali aka buɗe motar farko wacce ta kasance ash wani matashi ne wanda zai iya girman Sadauki ya fito daga motar, fuskarsa sosai ta nuna tashin hankali ya ƙarasu wajan yana kallon Ridayya da Sadauki kafin ya ce "Me ya sa ya kwanta a ƙasa what happened to him?" Ridayya ta kasa cewa komai idanunta duk ya jime saboda fargaba Riyad ya nisa ya ce "Kece Ridayya? Naga lafiya ya fito ya ce wajanki zai zo, daman hankalina bai kwanta ba tunda kwana ya yi jiya bai runtsa ba, ya kira number Mother sun yi magana, ya kira mahaifinsa kuma more than 30 miss calls bai ɗauka ba, don Allah ki sassauta kukan ki mini bayanin abinda ya faru in briefly" da ƙyar ta ce "Ka fara duba nunfashinsa ka ji ko yana raye" sai a lokacin Riday ya lura da rashin bugawar zuciyar Sadauki ya nufe shi kasancewar shi Dr ya fara duba shi hankali tashe. Tsaye ya yi a kanta tun bayan fitowar shi daga motar, hankalinsa ya ji yaƙi kwanciya har ya je airport kawai ya saka aka dawo da shi, sai dai bai yi tsammanin ganin abinda yake gani ba, ya shanye damuwar dake ƙoƙarin bayyana a fuskarsa ya ce "Ridha.." jin muryarsa ya saka ta miƙe har tana ƙokarin faɗuwa ya yi saurin taro ta gefensa tana ganinta kusa da shi ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka sosai "Abbiey na shiga uku na shiga uku Abbiey na kashe Sadauki" Ustaz ya kasa cewa komai sai bayanta da yake bubbugawa a hankali alamar rashin, deep down na zuciyarsa addu'a yake ta yi ga Ubangiji ya tashi kafaɗun Sadauki sosai al'amarin ya shige shi ya kasa furta komai Dr Riyad ya goge zufa ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Allah gare ka muke kuma gare ka zamu koma Ubangiji ya sanya can tafi nan sannu da aikin bauta Hamza Allah ya yafe maka" kalaman shi suka daki Ridayya da Abbiey ta ƙara rikicewa ta riƙe Ustaz da kyau shi ma ɗin riƙe ta ya yi gudun kar a yi biyu babu. Abbiey wayarsa ya ciro ya kira number gidansa wacce ta sada shi da Maid Ilhas, magana ya yi a gajarce kana ya kashe kiran. Hannun Ridayya ya kama zuwa mota ya yi wa Dr Riyad alamar ya jira shi a nan wajan, rarrashin Ridayya ya fara cikin kulawa da soyayya dukda kasancewar jinta a jikin Ustaz yana yaye mata abubuwa da yawa amma yanzu ta gagara nutsuwa gani take idan Sadauki ya mutu tamkar ita ta kashe shi. Addu'a ya shiga yi tana maimaitawa suna a haka mota ta sauke Ilhas ya fito ta yi saurin cewa "Good day sir!" Ya jinjina kai yana ɗauke idanunta can ya ce "Ki kula da ita, ku kasance tare ok" "Yadda ka ce in sha Allah" motar ta shiga driver ya ja su zuwa gida shi kuma kai tsaye ya nufi wajan Dr Riyad ya ce "Me kake son cewa? Who are you?" "Sadauki's friends" Dr Riyad said yana goge hawaye ya ɗora da "Allah ya yi masa cikawa kuma ina da tabbacin bugawar zuciya ce na farat ɗaya amma zamu je asibiti na ƙara bincikawa" MB USTAZ ya ja numfashi ya fesar "No need, zamu shige Nigeria yanzu" daga nan ya fara neman number wayar Tajj Baita gabaɗaya bai san yadda iyayen Sadauki da shi kansa Tajj za su fahimci wannan al'amarin ba. Kasancewar abu ne na manya ya sanya cikin awa guda suka samu jirgin da zai ɗaga dasu, da BM USTAZ da Dr Riyad sai gawar Sadauki daman tuni ya yi waya da Tajj ya masa bayanin komai kasancewar Abbiey bai iya ƙarya ko ɓoye magana ba, yana da zurfin ciki amma ba a komai ba. Hajja Azizat na zaune ta yi zuru tana sauraren yayarta mahaifiyar Tajj tace "Yaya ban san meke damuna ba, kawai na ji bari na kira ki ko zan ji sanyi a raina, gabana faɗuwa yake sosai wallahi, gidan ya mini girma idan na kira Professor bana samun shi sama da sati ina son na faɗa masa al'amarin Sadauki" daga can ɓangaren Mahmah ta ce "Hajja Azizat ki yi haƙuri komai zai zama tarihi in sha Allah, yaushe Sadaukin zai dawo I'll talk to him zan masa bayanin yadda zai gane ya fahimta ya kuma yi tawakkali" Mother ta sauke ajjiyar zuciya tare da goge hawayen idanunta ta ce "Nothing goes well Yaya, Sadauki yana da ƙulafuci, kafin ya fita sai da ya bi mahaifinsa office domin ya ji matsalarsa da rashin son zama cikin iyalansa, lafiya ya fita amma daya dawo ban gane kansa ba, ya dinga ce mini na yi haƙuri da rayuwa da amshi ƙaddara a yadda ta zo mini da Prof da babu duk zan iya rayuwa, kuma karna bari wani abu ya sake shiga tsakanina da Prof, Yaya hankalina ya tashi na rasa gane me Sadauki yake nufi ban san kuma mene ya je ya gani wajan mahaifin nasa, main reason ya haɗu Ridayya kuma kin san tana da aure, ina guje masa fushin Ubangiji Yaya kuma ina jin tsoron faɗa masa gaskiyar lamarin na gaji na gaji Sadauki shi ɗaya nake da shi, zaman gidan babu daɗi" Sosai Mahmah ta tausayawa Hajja Azizat ƙanwarta cikin rarrashi take ce mata "Azizat kin yi haƙuri komai zai shige kowa da tasa ƙaddarar mumunin mutum Ubangiji baya barinsa haka nan. Ni da kaina zan fahimtar da Sadauki da zarar ya dawo Prof kuma ki masa uzuri ai kince ayyuka sun masa yawa, ga sabgar siyasa banda an ɗaga Elections ɗin da tuni an yi komai mai rabo ya samu, ba ki rasa komai ba" "Yaya buƙatun ƴa mace ba iya ci da sha da suttura bane, kawai dai abar tunawa zan ta addu'a shi kuma Hamza Allah ya yaye masa son Matar auren, ai masifa ce wannan kuma jarrabwa babba" Mahmah daga nata ɓangaren da take zaune a saman kujera Nadra na kusa da ita tana bacci, ƙoƙarin magana take kamar daga sama taga Tajj ya shigo yanayinsa ya mata daban ta ce "Ya zaka faɗo mini a gigice kamar kurarre lafiya? Wani abun ne kuma Deen?" Ya kasa magana sai zufa yake sharewa idanunsa sun yi jajur, dukda rashin jituwa da suke da cousin brother ɗin nasa amma sosai yake jin Sadauki a zuciyarsa, ya sha ɗaukar waya da niyyar kiransa just to find out if he is ok, daya tuna rikicin shi sai ya fasa, babban dalili a maza bashi da ɗan'uwa wanda ya shige Hamza, taya zan iya fuskarta Anty ya ce mata Sadauki ya rasu sanadiyyar bugawar zuciyar farat ɗaya, dalilin mace kuma a ƙasar daba ta shi ba? Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun! "Wai lafiya ina magana zai zufa kake ji idanunka kamar zasu shige don tashin hankali" "Ƙaddara ce ta same mu wacce daman tana kan kowa Mahmah" "Ƙaddara? Aikin ka rasa ko asarar dukiya ka yi" a rauna ce ya ce "Gwara na rasa aiki da dukkan abinda na mallaka da na rasa abinda na rasa a yanzu Mahmah, iya faɗan da muke da Sadauki ya wadatar dani yanzu dawa zan dinga yi?...," Mahmah ta ji cikinta ya juya gudawa na neman zubo mata ta yi baya kamar zata kifa ta ce "Mene ya samun Sadauki" "Allah ya amshi abinsa, a inda bashi da kowa sai wani jinin nada ban, mun rasa Sadauki Mahmah Sadauki ya rasu" Salati kawai Mahmah take idan ta kamo wannan sai ta saki ta gigice ta fita hayyacinta lokaci guda, Tajj ya rasa ya zai yi ya ce "A'a Mahmah wannan bai dace da Sadauki ba, addu'ar da kika fara ita za ki ta yi in sha Allah yana cikin aminci zai kasance ɗaya daga cikin samarin Aljanna wanda Ubangiji yake alfahari da su" Ta share hawayen da yaƙi tsayawa ta ce "Taya zan faɗawa Azizat wannan al'amari? Ya za mu yi?" Tajj ya ce "Faɗa mata ya zama dole, amma nima ba zan iya ba wallahi tsoro kallon idanunta nake na ce Hamza ya rasu" Da ƙyar Mahmah ta iya controlling kanta ta kira Mother tana ɗagawa ta ce "Ki zo gidana yanzu" "Yaya lafiya?" "Ki zo na ce" "Ban tambayi Prof ba Yaya, bari na kira shi idan ya barni sai na zo" "Ƙarama meke damunki ne? Wacce kalar biyayya ce haka? Kin san girman dalilin daya saka na kira ki? Sai kin tsaya kiran Prof?" "Yaya you are always telling me cewa Aljannata na ƙarƙashin mijina, biyayya kuma ke bada ita, kin ce mini haƙurin shi ne maganin komai a rayuwa, abinda haƙuri bai baka ba, rashin shi ba zai baka ba, yaya na gino akan wannan kalaman naki. Na tuna keda kan ki kike bani wata kissa lokacin Annabi Muhammad S.W.A kin ce; wata mata mahaifinta ne ko mahaifiyarta babu lafiya, amma taƙi zuwa dubiya saboda mijinta baya gari kuma babu al'amarin waya a zamanin, har daga ƙarshe kika ce an aiko mata cewa mahaifin nata ya rasu, ta yi aike wajan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce mata ta yi haƙuri ta nemi izinin miji, haka ta haƙura ta yi wa mahaifin nata addu'a tana daga gida, a kaiwa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama wahayin cewa wannan matar Ubangiji ya bata Aljanna.... Me ya sa ba za mu yi koyi da mutanen ƙwarai ba, da bana haƙuri ba zan kawo yanzu cikin gidan Prof ba Yaya ki yi haƙuri na nemi izinin shi" A sanyaye Mahmah ta ce "Okkk" Ta juya ta kalli Tajj ta ce "Yaushe zasu ƙarasu da gawar?" "Not too long, don sun jima da tashi bari na faɗawa wanda ya dace" ta jinjina kai ta ɗauki hijabi ta saka ta gyara parlon da za a saka gawar Sadauki. Tajj ya kira Baffa da Baba ƙarami da Junaid duk ya sanar musu, ya kira ƴan'uwansu na kusa da kuma na nesa ya kira abokan mahaifinsa ya saka aka wallafa rasuwar Sadauki a social media da gidajen rediyo. Da kansa ya kira Prof amma bai ɗauka ba ya masa kira sautarin shurin masaƙi but not respond. Cikin ƙaramin lokaci gidan Murgayi Alhaji Baita ya cika da jama'a ƴan ta'aziyya hatta Mami da Sisters ɗinta suna gidan da kuma Dada, hadda Zainu da little. Daga baya Balisa da Yaya Zuhura suka shigo tare dasu Abdullahi da Khaliperh su Usman har lokacin kuma Hajja Azizat bata ƙarasu ba. Gida ya cika zuwa su BM USTAZ kawai ake jira. Sama sama ya fara jin news dalilin breaking news da aka fara sanarwa nan take Allah ya yi wa Hamza Sadauki rasuwa ɗa a wajan Professor ɗan takarar ɗan'majalissa ya rasu ne a ƙasar Japan kamar yadda sanarwa ta je musu, za a yi jana'izarsa idan jirgin dake ɗauke da gawarsa ta ƙarasu aka maƙala photon Sadauki da yake tsaye da voyel fari tas ya yi murmushi idanuna na kallon wani direction ɗin daban ba camera ba. A gigice Prof ya yi cilli da wacce ke kusa da shi ya jawo jallabiya ya saka jikinsa sai rawa da ɓari yake yana ƙokarin ɗaukar key ya fita ta riƙe shi ta ce "Malam ina kake ƙoƙarin zuwa ai ha haka mukai alƙawari da kai ba" idanunsa na shigewa ciki ya ce "kina da hankali kowa? Kina jin ana news cewar ɗana gudu ɗaya tal da na mallaka ya rasu maimakon ki mini jaje sai ki kawo mini rubbish?" "And so what don ɗanka ya rasu? Ba zai taɓa zama ciwon kaina ba" wani irin mari ya sauke mata yana kaiwa bakinta naushi ta fasa ihu ta ce "Wallahi ka yi kaɗan ka dage ni kamar baka san wacece Ladi ƙarin kunama ba, da kuma abinda zan iya yi?" Idanuna rufe ya zare Belt ya shiga lafta mata tana kururuwa itama ta shiga kai masa duka, suka fara dukan juna kamar rayuwa bariki kodayake bambancin kaɗanne ya mata lilis tare da mata jina-jina ya zari wayata da key ya fita. Duk a hanyar ya fara duba miss calls na jama'a babu adadi ya yi mamakin ganin Hajja Azizat ta kira kuma har an ɗaga yaushe to? Bayan ya san yau gabaɗaya bai waya da ita ba? Yaga kiran Tajj dana shugaban jam'iya har kiran yan'uwansa kiran kowa ya share ya kira number Hajja Azizat yana kira ta ɗauka ta ce. "Thank God, ina kiranka ka yi mini izinin zuwa gidan yaya ta mini kiran gaggawa ban san meke faruwa ba" Wani irin tausayin matarsa ya kama shi, innocent mace ya cutar haka? Har ɗanta ya rasu amma ta kasa fita ji ya yi hawaye ya cika idanunsa wani irin sonta ya ninku a zuciyarsa da ƙyar ya ce "Jeki yanzu Azizat, Allah ya yi miki Albarka" Tana shirin fita notification na shigowa wayarta dake gidan nasu akwai Wi-fi bata tsaya duba pictures ɗin da aka turo mata ba da sabuwar number a WhatsApps ta shiga mota, da kanta take driving tunani fal zuciyarta hannunta kuma sai rawa yake. zuwanta da yin parking ɗin motarta ya yi daidai da shigowar motar Ambulance ta tsaya tana kallon ikon, akan idanunta aka fito da gawa rufe da farin yadi a kan wani gado, can taga Dr Riyad ta gane shi sarai babu jimawa wani magidancin mutum ya fito fari tas dashi farinsa ya shige misali ko'ina na fatarsa lub yake da gargasa fuskarsa rufe da mask ya saka baƙin glasses a idanunsa, da kansa ya ja gawar Sadauki zuwa cikin gidan Mother ta bi bayansa da kallo ta kasa tunain komai da ƙyar ta ja ƙafarta zuwa cikin gidan, tana shiga parlo ya ruɗe da koke koken jama'a ta dinga bin kowa da idanu sai kawai ta shiga cikin bedroom ɗin Mahmah ta kwanta Mahmah da Tajj suka biyo bayanta nasiha sosai sukai mata can ta ce "Me ya faru ne?" "Allah ya amshi Sadauki, Ubangiji ya amsa ran Sadauki ya rasu" Mother ta rasa gane waye Sadauki wacce kalar mutuwa kuma "Sadauki? Wanne Sadauki?" "Hamza Sadauki ɗanki Azizat" "Kamar bani da ɗa mai suna Sadauki Yaya, wanne Sadauki yaya take nufi Deen?" Tajj ya ce "Ki yi haƙuri don Allah Anty Sadauki dai ɗanki ɗaya tal ke da Prof" Ta jinjina kai a hankali ta yi baya ta ce "Allah ya jiƙan shi ya yi masa rahama" daga haka bata kuma cewa komai ba, ta juya baya tare da kwanciya saman gadon babu hawaye ko tashin hankali a tattare da ita amma zuciyarta cak take kwakwalwarta nata processing tuna waye Sadauki? Mene haɗin ta da shi nata sadauki dai baya ƙasar gabaɗaya ai. Haka al'amarin Ubangiji yake komai da lokacin shi, haka kuma mai rai dole ya ɗanɗani ɗaci mutuwa. Har akai arba'in ɗin Sadauki babu wanda ya ji kukan Hajiya Azizat ta kaɗaice daga cikin jama'a bata son kowa ya raɓe ta. Sau ɗaya suka ji ta fasa ihu a gigice Tajj ya shiga ɗakin ya ganta tana fisge-fisge ta fita hayyacinta idanunta rufe jikinta na rawa Tajj ya ƙarasa wajanta tuni ta doka wayarta da ƙasa wayar ta fashe ta yi fari baka ganin komai, kokawa suke sosai da Tajj da ƙyar ya rungume ta a jikinsa yana hawaye tare da kiran sunan Allah ya fara mata addu'a yana tofa mata, Mahmah ta yi tsaye ta kasa cewa komai makamin yadda Hajja Azizat bata ƙaunar Prof ya zo kusa da ita take, ko ta'aziyyarsa taƙi amsawa ta tambayi dalili ta ce "Me zata cewa wanda ya kashe kiran yaro?" Tun daga lokacin bata kuma cewa komai ba sai sanda ta yi ihun a hankali ta sauke numfashi jikinta ya saki a jikin Tajj ta riƙe shi da kyau kuma. Gabaɗaya sun rasa meke damunta mai kuma ta gani? Suka kira Malami ya fara mata rubutun don gana amma abu ya ci tura. Umma ta kalli Mardiyya da duk ta yi wani zuru-zuru sai ciki a gaba ta dire mata kuɗi ta ce "My daughter gashi 200k ne ki ƙaro abinda kike so na fitar suna, tunda haihuwa ta zo gab gamu cikin watan haihuwar edd kawai muke jira" Mardiyya ta kalli kuɗin ta ce "Ok thanks" Ta ce a yatsune kafin ta ce "Hadda Ustaz a masu zuwa ta'aziyyar Sadauki amma kin kasa dawo da shi gida, bakwa tsoron haƙƙina rabona da shi tun ina amarya tun kafin na samu ciki?" "Kamarya kenan kafin ki samu ciki kuma? Ko dai bayan kin samu ciki?" Cikin inda-inda Mardiyya ta ce "A'a ina nufin kafin nasan da cikin a wajena" murmushi Umma ta yi ta ce "To albishirin ki wannan kuɗin shi ne ya turo da su ya ce a ba ki kuma yana nan kan hanya soon" cikin farinciki Diyya ta ce "Da gaske ko dai ƙarya kike mini Umma?" Da wani mamaki Umma ta ce "Ƙarya kuma Mardiyya?" "Opps sorry na ruɗe ne, bedside kin jima ai kina ce mini yana hanya, amma dai kafin na haihuwa zai dawo" Umma ta jinjina kai cikin ya yi laushi ta ce "In sha Allah" daga haka ta juya cikin sauri Mardiyya ta kira ƙawarta ta sanar mata komai ta cikin waya ta ce "Saura ki ƙara jakanta irin na baya, tunda brain ɗinki a tushe yake kamar na kifi bayan maganinsu sha'awa ki saka masa wanda zai zama kamar na maye, sai ki yi bidiyo shi zai zama hujja ni kuma zan bayar a yi editing na bidiyon a cire cikin jikinki shi kuma a ɗan rage masa ƙiba, don na lura ya ƙara tumbi da kyau da haske wallahi irin yana cikin kwanciyar hankalin nan" Diyya ta haɗe fuska ta ce "Ban gane ba, mijina ne fa kuma kike yabon ƙyan shi" "Dilla to mene? Ai kyakkyawa ne" "Kambu saurara akan shi zan iya rabuwa dake tuni wallahi aikin banza daman haka ku ƴan'matan da kukai kwantai a gida kuke, guzuma" ta ce "Ni kikewa gorin aure Mardiyya? To shikenan kya zauna da Ustaz ɗin na gani" tana faɗin hakan ta kashe wayarta. Baba ƙarami ya dinga ladamar aibata Ustaz da ya yi daman a lokacin ya kasa fahimtar meke faruwa da shi har ya yarda, ya samu nutsuwa ya kuma tambaye shi ya jikin Ridayya da yanayinta ya sanar masa tana lafiya. Baba ƙarami ya ce "Babban mutum ya kama ka dawo gida haka nan domin asan kana tare da matarka" Ustaz ya sauke ajjiyar zuciya yana janye idanunsa da lumshe su hannunsa ɗaya yana shafa sumar Ridayya dake bacci akan cinyarsa hankali kwance ta zama wata ƙatuwa da ita jikinta ya buɗe sosai kamar an hura ta, ta fresh da ita laɓɓanta jajur dasu ya kasa cewa Baba ƙarami komai. "Muhammad yaushe haka zata ci-gaba da kasancewa ne? Akwai rikici mai yawa muna buƙatar ka, hakƙin matarka dana mahaifiyarka ga matsalar kuma ta cikin Mardiyya, gashi kai kaɗan zaka iya tanƙwara surukinka ya saka a saki mahaifiyarsu Junaid ai abin kunya ne" "Cikin Mardiyya?" "E, ai tama kusa sauka" Ustaz ya taɓe baki yana murza lips ɗin Ridayya can ya ce "Oh, cikin gaske ne ashe?" "Baka da labari ne? Bayan jininka zata haifa" "Ina da shi, amma Ridayya ce kawai ta amshi budurcina Abba, ita kawai ta san baɗini na, kuma Mardiyya ta sake ta furta haka a kan idanuna zan watsa mata yatsuna biyar a kuncinta, kawai ina addu'ar Allah ya yafe mata zunubanta da kurakuranta ne Abba" Baba ƙarami ya ce "Ikon Allah, to Allah ya yafewa Babban mutum da sakin bakin sai anjima" Ustaz ya dinga tunani mai ya ce wanda bana daidai ba? A hankali ta juya suka haɗa idanu ya ɗaga mata gira ta yi murmushi ta ce "Ba ka yi bacci ba?" Ya sake jinjina mata kai ta miƙe tare da jingina a jikinsa a sanyaye ta ce "Abbiey" ya yi shiru ta sake cewa "Abbiey?" "Kina buƙata ta ne jaririya?" Ta girgiza masa kai ya lumshe idanu. "I am sorry, ni kaina na kasa yafewa kaina tsananin ruɗewa ne ya saka na aikata abinda na aikata, amma bawai don ina son murgayi bane, na faɗa ne da tunanin ko kalamai na za su saka ya dawo hayyacinsa amma wallahi ba kowa a raina kuma....," bakin dake ta juyawa ya kame ta yi saurin yin tsit bisa tilat some minutes ya sake ta yana jan numfashi. Ta zare idanu ta ce "Yawon bacci fa Abbiey" ya juya ya harareta ba tare da ya ce komai ba, fuskarsa a haɗe dai ta yi ta magana ya yi banza da ita can ta fara masa cakulkuli ya juyo gabaɗaya ya ce "Wa'auzubillah yake Ustaza wasan banza ne wannan ai" ci-gaba ta yi ya fara murmushi tun yana daurewa ya fara dariya sosai wacce bata taɓa ganin ya yi ba, ya jata ya rungume sosai yana shafa cikin jikinta dake gab da zuwa duniya. "Tab Mimi kalli hancinki ya yi kamar funkaso wlh" Ta haɗe rai ya girgiza kai ya ce "Serious wannan cikin ya saka ki zama Mama boss kin fi ƙarfin bayana" bata kula shi ba ta miƙe tana juya masa mazaunai ya girgiza kai kawai ya san tsokana ce. Zameer ya shiga tashin hankali cikin bacci zai farka a gigice yana kiran sunan Ridayya ya azabtu ya rame ya fita hayyacinsa da kamaninsa wanka da gayun tuni babu daman ya tattara ya koma Batsari, ba sana'a sai dai ya ɗauki fatanya da magirbi zuwa gona ga yara har uku har tsora tashi suke cikin dare sai ya gansu kamar yaran aljanu. Idan azabar kasancewa da Ridayya ta tasu masa yaje wajan Hanne haka zata raraka shi ya kwana yana birgima yana son komawa Kano ko Ridayya ta dawo ya san zata ji tausayinsa ta dawo gare shi amma yana tsoran Tajj da kuma ƴan'sanda ya susuce. Sosai yake saffa da marwa a harabar wajan ya kasa zaune balle tsaye yana cikin halin Dr ya fito da sauri ya ce "Sir dole sai dai ka saka hannu mu yi mata c.s ba zata iya haihuwa ba" Ya ja wani irin numfashi da ƙyar da ya ji ya tukare masa maƙoshi a hankali ya ce "Ok" ya amsa ya saka hannu har Dr ya tafi sai kuma ya ce "I love my wife dr please...,.," ya kasa ci-gaba likitan ya ce "Idan baka nutsu ba, zaka iya shigowa ka kasance da ita lokacin aikin" Ya jinjina kai. Cikin ƙaƙanin lokaci aka shirya aiki kasancewar babban asibiti ne kuma na kuɗi komai nasu daban yake. BM USTAZ na zaune saman kujera ya damƙe hannayenta biyun idanunsu maƙale da juna, yayinda aka saka labule ya raba tsakanin cikin Ridayya na wajan likitocin ƙirjinta da kanta yana wajan Ustaz. "Abbiey" Ya ware idanunsa har lokacin bakinsa ɗauke yake da addu'a ta ce "Me ake mini ne? Na ji ƙafana ya sake kamar ba nawa ba" Ya shafa kanta yana murmushi can ya ce "Za ki zama Big Maama jaririyata Little zai samu sister" ta ɗan yi murmushi ta ce "To bani labari" Ya ɗan yi jim a taushashe ya ce "Me zan ce wanda ya shige labarta miki yadda nake son ki tun kina zanin goyo ina goyaki a bayana? Ridayya da gaske ban taɓa shan a zaba wacce ta shige ta soyayyarki ba, har mamaki nake da zuciyata bata buga ba, ke wata irin macace da duk wanda ya kasance dake zai ji kin fiye masa mata da dama, ba kowa ke bawa ni'imar daya ba ki ba. Ina tsananin son ki da ƙaunarki akan ki nasan cewa ni mutum ne lafiyayye, sanda kika zaɓi wanina da tunanin ya fini qualities I just hate myself, na fara ƙoƙarin ganin na sauya na zama yadda zaki iya sona amma it's too late to cry, kin wahalar dani da zuciyata da gangar jikina. A hankali na fara fahimtar hakƙin Muwaheeb ke bibiyata ta so ni sosai amma na yi kamar ban sani ba, ta sha tara ta tana kuka akan na taimaka mata na kunnen uwar shegu...." Ridayya ta sauya fuska kishinta ya fito sosai Ustaz ya kashe mata idanu kana ya sumbaci goshinta ya ce "Da ne not now, you're the only one i love you Miftaahu qalbiy" Sosai ya zage yana faɗawa Ridayya abinda ita kanta bata sani ba, ya buɗe zuciyarsa a haka suka wanzu suna kallon juna bata cewa komai sai shirunta ya yi yawa ta lumshe idanu ya ɗan bugi kumatunta ya ce "What?" Ta girgiza masa kai yana lura da yadda fuskarta ke ɗan sauyawa ta yatsuna fuska ko ta marairaice ce a hankali ya ce "Repeat after me" Yana addu'a tana maimaita hannunta har lokacin yana cikin nasa fuskarsa a kan tata. Basu ankara ba Dr ya ɗorawa Ridayya baby a ƙirjinta sai kuka yake, ta dinga kallon babyn shi kansa Ustaz kallon babyn yake, zai magana Dr ya sake ɗora wani babyn suka buɗe idanu lokaci guda"Dr.....," maganar ta tsaya ganin na ukun Dr ya ce "Wannan kuma kai na bawa ka riƙe" bai damu da jinin ba ya amshi yaron ya riƙe a ƙirjinsa Ridayya idanun take ta rarrabwa suna ta hira ashe abinda ake ciro mata kenan? Abinda suka rayu a coming kenan ashe wani irin hawaye ta ji ya zubu mata ya fahimci rabo masifa ne musamman idan ya rantse, ta dinga kallon yaren shi kansa Ustaz girman zatin Ubangiji yake girmamawa likitan ya ce "Madam yara nawa kika haifa?" "Uku" ta furta hawaye na bin fuskarta sosai ya ce "Mata ko maza?" "Ban sani ba" ya girgiza kai ya ce "A'a duba da kyau" Ta juya ta kalli Ustaz ta ce "Abbiey" Ya yi mata tattausan murmushi ya ce "Gabaɗaya boys ne Mimi" Ta jinjina masa kai. Ya ajjiye jaririn Norses suka ɗauke su aka fara shirya su. Ustaz ji yake kamar ya gama samun komai a rayuwarsa ya dinga sawa Ridayya albarka da addu'a ya rungume ta sosai ya dinga sumbatar fuskarta ta yi shiru a jikinsa. Labarin haihuwar ƴan ukun masu matsanancin kama ɗaya ya wanzu a asibitin sai labari ake wasu na zuwa ganinsu sosai kuma Ustaz ya musu addu'a da huɗu ba. Ɗaya ya amsa sunan Baffa ɗaya kuma Baba ƙarami na ƙarshe ya amsa sunan Hamza Sadauki. Da sauri Ridayya ta kalli Ustaz jin ya ce Sadauki ta kasa furta komai sai gdy take a ranta. A can gida Nijeriya fitowar Umma kenna daga ɗakin Mardiyya sbd har ta shige Edd nata amma shiru. Turus ta yi ganin wani abin mamaki makeken photo ta gani an saka shi a Frame yara har uku jere farare tas jajur tasu suma har gaban goshi kamar su guda baka iya bambance ɗaya a ciki. Nan take son yaran ya kamata ta sake kallon frame ɗin da manyan baƙi aka saka “WELCOME TO THE RANO'S FAMILY, TAHIR, MANSOOR, HAMZA” Baba ƙarami ya yi kamar bai san me take ba, ta sake juya can da sauri ta ce "Yaran waye waɗannan?..... More comments more update 08164069385 Na'ima Sulaiman Sarauta *MUNAFUKIN MIJI* Nimcyluv...... 46 *Follow my account AREWABOOKS* https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv Jaririn shima ya zubawa idanu ya ce "Sun miki kama da wani ne?" Umma ta girgiza kai ta ce "Bana jin kaf RANO'S FAMILY akwai mai kyawun halittar jariran nan, Ustaz ne kyakkyawan ciki kuma sun ninka shi a kyau da komai yana jariri bai samu kyansu ba wallahi wannan girmansu abin kallo ne" Baba ƙarami ya jinjina kai ya ce "They're blessed, Allah ya yi musu albarka ya ƙare haɗa kan iyayensu ya kau da idanun maƙiya akan su" "Amin, yaran waye?" Umma ta tambaya cike da zaƙuwa saboda kyawun yaren ya gigita ta ainun ya sake murmushi ya ce "Ki fara saka musu albarka tukunna tunda kin yaba" Umma da take jin wani irin matsananci daɗi ga wani farinciki daya saukar mata lokaci ɗaya wanda hakan ya faru ne sanadin ganin zuƙa-zuƙan jaririn guda uku sanye da kaya iri guda kuma kamanni guda ta ce "Wallahi tun kafin na furta komai na sanya musu addu'a tare da addu'ar Allah ya tsone idon maƙiya ya yi musu albarka, ya ƙara so da ƙauna a tsakanin iyayen su, ma sha Allah tubarakallah har cikin zuciyata nake jin ƙaunar yaren" yadda take nuna farinciki a fili zai nunawa mutum zahirin gaskiyar da take faɗa tsakani da Allah take son yaran kamar yadda ta furta. Baba ƙarami ya sauke numfashi idanuna akan matarsa yana jinjina girman rabo, kuma duk inda jininka yake sai jikinka ya baka ya kasa furta komai deep down na zuciyarsa addu'a yake Allah yasa haihuwar yaran nan ya kawo daidaito tsakanin uwar yaran da kakarsu ya zama silar kwanciyar hankalin duka familyn bakiɗaya. Ya nemi waje tare da zama saman kujera yana girgiza ƙafa shi kansa yaran Ridayya da Ustaz sun jijjiga shi kyan yaran ya bashi mamaki dukda ba'a mamaki da ƙudirar Allah. "Baka faɗa mini yaran waye ba? Ni dai na gama tunani daga dangina har naka babu mai haifar kyawawan yara kamar su" Baba ƙarami ya juya ya sake kallon yaran a hankali ya ce "Ko?" Ta ce "Wallahi fa, Mardiyya kawai nake saka ran zata haifawa Muhammad kyakkyawan yaro kamar shi ko fiye da shi" "Me ya sa kike tunanin namiji zata haifa kuma kyakkyawa kamar gwarzon ɗana" ta matsa kusa da shi ta ce "To ai haka ne kuma juma'ar da za ta yi kyau Hausawa suka ce tun daga Laraba ake gane ta, Mardiyya nada kyau haka Babban mutum kuma an ce abin cikin ƙwai yafi ƙwan daɗi kaga dole ɗan za su haifa shi da Mardiyya ya zama kyakkyawa" Baba ƙarami ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "Haka ne kam, kina da taki gaskiyar" "Ni sai naga kamar baka ƙaunar yarinyar nan baka mayar da hankali akan lamuranta karka manta daughter-in-law ɗinka ce fa" Cikin sauri ya juya ya kalleta yana waro idanunsa waje ya ce "A'a karki mini sharri matar, ai jinin ka wuya za shi you're just like a drive mu duka passengers ne a tafiyar nan sai inda kika ajjiye mu, nina isa naƙi zaɓin uwar gidan Tahir" ita dai duk bata gane me yake son cewa ba, don haka ta tattara maganar ta ajjye waje guda. "Ki mini wata alfarma ɗaya mana Hadiza" "Wacce alfarma?" Ya fito da A.t.m guda biyu ya ajjiye mata kana ya nuna mata jariran ya ce "Haɗaɗɗun kayan barka nake so ki haɗu na Triplets masu kyau na gani na faɗa, komai da kika sani na yara ki haɗu" Umma ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Wannan kam ai ba alfarma bace ko su waye waɗannan na san suna da muhimmanci a rayuwarka sosai. Zan wa wata friend ɗina magana da take kawo kaya irin wannan daga waje sai na yi mata list na duka abinda muke buƙata, sana'arta kenan ai" "To madallah ba damuwa a yi hakan" "Uwar yaran fa?" Ya ce "Me fa?" Ta ce "Ina nufin me za a siya mata?" Baba ƙarami ya yi shiru can ya girgiza kai ya ce "Iya yaran dai kawai" "A'a ba za a yi haka ba, uwar kam ai ta cancanci a yi mata ni zan haɗawa uwar da kuɗina kaga sai na kai daga nan naga yaran so ma sha Allah" Yana miƙewa saboda kiran sallah ya ce "Lallai to muna godiya" har zai tafi ta ce "Don Allah yaushe ɗana zai dawo gare ni ne? Idan fushi yake wallahi hukuncin daya ɗauka ya yi yawa ina jiye masa fushin uwa Baba ƙarami, yana da kyau ya dawo kafin matarsa ta sauka ga kuma hakƙin matarsa" A hankali ya ce "Zai ba ki mamaki ne soon zai dawo ki shirya tarɓa ta musamman domin ya yi aure a inda yake" Da wani irin tashin hankali Umma ta ce "Aure kuma? Shi babban mutum ne ya yi aure ba tare da mun sani ba, a wani gari? Waya aura? Ƴar waye?" Duk hankalinta a tashe yake wani gefen kuma tana jin hakan ba komai bane idan har ba Ridayya bace kuma daman tuni ta raba shi da ita, tana mace tana raye wama ya sani ne? "Zan je sallah zan miki bayani idan na dawo ki haɗa mini tuwon nan ki saka man shanu" jiki a sanyaye ta ce "Tom" Baba ƙarami na fitowa Main parlor ya ci karo da Junaid ya fito yana gyara hannun riga alamar ya yi alwala ya ce "A'a Junaidu dawowar yaushe?" Yana murmushi ya ce "Yanzu ne Abba" "Lalle kaga ina son magana da kai kowa idan mun idar da sallah" Junaid ya jinjina kansa suka jera tare da nufar masallaci sosai Junaid da Khaliperh sukai mamakin ganin Burhan a masallacin kusa da Baffa sahun farko har aka idar kuma basu ce komai ba. Baffa ya gai da yayansa yaran suka gaida shi Burhan dake ɗan janye jiki ya ce "Barka Abba" "Yawwa Burhan" Burhan bai kalli inda su Junaid suke ba ya yi shigewar shi cikin gidan da mamaki Abdallah ya ce "Baffa me wannan yake a gidanmu kuma?" Cikin ko in kula Baffa ya ce "Nina kira shi?" Ya faɗa fuska a kame ba alamar wasa suna shigowa parlour suka samu Zainura tsaye ita da Mami suna kallon tafkeken frame ɗin ƴan ukun wanda aka maƙala a main parlour gabaɗaya bata lura da Burhan dake zaune saman kujera ya zubawa bayanta idanu hatta Mami bata lura dashi ba Zainura ta ce "Mami yaran waye waɗannan don Allah i love them wallahi" Mami ta zubawa yaran idanu musamman na tsakiya ta juya ta kalli little Bilal ta ce "Waya saka frame ɗin nan?" Zainura ta ce "Ni ma a haka na gani kuma akwai a ƙaramin parlonki ma akwai ana Baffa" Kafin Mami ta yi magana sun ji sallamar Baba ƙarami cikin sauri Mami ta shiga part ɗinta domin babu ko mayafi jikinta Zainura ce ta uzzura mata ta fito. Baffa ya dubi ƴar rigar dake jikin Zainura iya qwwia cikin sauri ya ce "Zainura wanne shirme ne nan za ki fito haka?" Ta yi narai narai da idanu ta ce "Baffa naga dama haka nake zama" ya lura dai ba zata fahimta ya nuna mata hanyar part ɗin babarta ya ce "Leave" wajan ta bari cikin sauri Burhan daman tuni ya ɗauke ya fara danna wayarsa da bai jima da siya ba sbd zaman shagon kati da yake yi yanzu. _You look so beautiful Zinu, and please save ur dress for me...... I love you_ Tsaki ta yi sanda taga saƙon ta rufe idanu da sauri ta buɗe jin tsigar jikinta na tashi da kuma tunanin Burhan data fara. Mami ta ce "Lafiya?" A hankali ta ce "Ba komai" sai kuma ta miƙe ta ce "Mami nifa babyn nan na tsakiya yana mini kama da little Allah, yaran waye don Allah?" Abinda Mami ta hango kenan har ta juya ta kalli little itama taga kamar a fili ta ce "Allah yaye miki wannan tambayar Burhan dai ya haɗu da aiki" cikin sauri ta ce "Why Burhan Mami, wanne Burhan" Mami ta haɗe fuska ta ce "Wanda kika baro a parlour yanzu da yake mana sunturi" nan da nan hankalin Zainura ya tashi ta fara hawaye ta ce "To ni mene haɗina da shi kuma don Allah Mami?" "Oh zan sanar masa ya tattara ya bar mana gida muna da wanda zamu bawa auren ki is that clear baby?" Zainura ƙirjinta ya buga ta kasa magana Mami ta yi murmushin ta ce "To ko dai na bari kya faɗa masa da kan ki?" "Eh Mami zai ma fi fahimta" Murmushi kawai Mami ta yi a ranta tana jinjina ta ɓarar Zainura. Har Baba ƙarami ya gama cin abinci bai cewa Umma komai ba, ita kuma ta kasa sukuni burinta ta ji ya faɗa mata iyayen yaran amma ya yi gum da bakinsa. Sanda ta shiga bedroom ɗin Mardiyya ta same ta zaune tsakiyar gado da ƙaton ciki gaba Umma ta kalli cikin ta ce "Kila kema dai yara biyu za ki haifa gashi har kin gota Edd naki Daughter" Mardiyya ɓata fuska ta ce "Wai yaushe Mijina zai dawo ne ni sam na gaji na kasa tantance ke nake aure ko shi?" Da wani irin yanayi Umma ta ce "Rashin kunya za ki mini Mardiyya ni za ki mannawa wannan maganar mai ɗaci a zuciya?" Fashewa da kukan munafurci Mardiyya ta yi ta ce "Kalamanne suka kwace mini bana nufin hakan, amma ko dutse aka ajjiye da buƙatar a sauya masa wajan zama balle mace kuma mai ciki, akwai haƙƙina da yawa a kan mijina, yanzu ba'a tunanin halin da zan shiga da raina da lafiyata amma babu miji a kusa dani? Yanzu kuma idan na aikata wani abun sai ace mini na aikata zunubi da wannan abin gwara ya sake ni kawai nasan ni ba matarsa bace" ta faɗa gabanta na faɗuwa domin kalaman iya laɓɓanta ne ita kam idan Ustaz ya sake ta ai ta shiga uku balle yanzu da arziƙinsa ya buƙasa. Umma ta ce "Haka ne an yi miki laifi maganar dana shigo na faɗa miki kenan cewa yana hanyar dawowa" cikin hanzari ta ce "Don Allah da gaske Ustaz na hanya kai na ji daɗi in sha Allah idan zai koma tare zamu tafi" "In sha Allah " Kawai Umma ta ce amma ƙasan zuciyarta kalmar da Mardiyya ta faɗa ke ta yi mata yawo a zuciya babu kunya ko ɗa'a a furucin Baba ƙarami ta samu yana waya a hankali ya ce "Tajj ya mai jikin?" "Da sauƙi Abba, ita ta sani kiranka ma" "Ikon Allah lafiya?" Tunanin Umma ya bata Muhammad ne hakan ya saka ta nemi waje kusa da mijinta ta zauna, ta cikin wayar Tajj ya ce "Ban san me take buƙata ba Abba, ta dai matsa tana son magana da kai wai akan Shari'a na faɗa mata ai ka daina ka yi ritaya amma dai ta saka rigima ka san yadda ta dawo yanzu abu kaɗan kuka kuma har yanzu taƙi ce mana komai" Baba ƙarami ya juya ya kalli Umma kamar zai tashi sai kuma ya ce "Bata wayar?" Tajj ya kalli Hajja Azizat dake cikin baƙar abaya ta yi rolling kanta sai idanunta dake a jeme saboda kuka duk ta rame damuwa ce take ta cin ranta hannunta ta zura tsakiyar cibiyoyinta tana girgizawa a hankali kamar wata Balarabiyya ta zubawa Tajj idanu ya yi murmushi ya ce "Anty gashi ki yi magana" yana bata wayar ya miƙe jin sallamar Nadra wacce ta yi wayo ta girma kuma sosai ya ɗaga ta sama ya ce "My queen my happiness an dawo?" Peak ta yi masa ta ce "Yes Daddy, ina abokina ne?" "Anjima za su zo shi da Zainura" Nadra ta dinga murna little zai zo. Hannunta ya kama suka nufi bedroom ɗin Mahmah. Tajj na fita Hajja Azizat ta damƙe wayar a hannunta kana ta kai kunne, Baba ƙarami ma shiru ya yi yana jiran me za a ce masa, Umma kuma ta zubawa masa idanu musamman wayar data kasance a speaker. Can a ƙasa a taushashe kamar dirar mikiya ya ji muryarta ta sauka a kunnensa.... “Abbaa” Hajja Azizat ta ce muryarta na rawa domin bata da wani suna da zata iya kiran shi da shi sai Abba ɗin da ta ji Tajj na faɗa as always. Lokaci ɗaya shi da Umma suka kalli juna fuskar Umma ta sauya, Baba ƙarami kowa ƙirjinsa ya doka da ƙarfi kansa ya juya gargasar jikinsa suka mimmiƙe ba zai iya tuna rabonsa da jin wannan yanayin ba sai yau. Kashe wayar kawai ya yi ya ajjiye a gefensa yana ɗaukan jarida Umma ta ce "Ai dole ka kashe saboda kar ka yi waya da budurwarka a gabana" Da mamaki ya ce "Budurwa kuma Hadiza?" "E, idan ba budurwa bace ka amsa mana? Ji yadda ta narke murya fa wai Abbaa yaushe ka haifeta da zata ce haka? Yadda ƙirjinka ke bugawa ya ƙara tabbatar mini da haka" Ya girgiza kai kawai a hankali ya ce "Na ajjiye yaro mai shekaru wajan 40 da jikoki amma ki dube ni ki ce wai budurwa? Ai kece matata kuma kece budurwata" "Ai ko maza ne baku da wani tawadiƙu akan mace wallahi, ni dai idan ta sake kira wallahi ban yafe ba" "To Hajiya mai ran ƙarfe" Tajj ya ce "To mene abin kuka kuma?" Ta ɗan girgiza kai tana cewa "Bai amsa ni ba fa, kuma ya kashe wayar, ya kashe wayar fa son" Cikin rarrashi Tajj ya ce "A'a maybe yana cikin jama'a amma zai kira ne" "Ka kai ni gidansa mana" Tajj ya kalli Mahmah ta yi saurin girgiza masa kawai ya ce "To zan kai ki amma ki kwantar da hankali Anty shi baya magana da wanda suke yawan kuka da riƙe damuwa" ta ɗauke kai taƙi cewa komai. Gefe guda Baffa ya bawa Burhan sanda ya tabbatar ya daina dukkan abinda yake kuma hakan ya faru ne dalilin son da ya kewa Zainura daman so babu abinda baya sawa, bayan bincike da tabbatar da cewa Burhan halin rayuwa ne ya saka shi lalacewa tun farko tun yana ƙarami ba'a bashi ilimi ba, babu abinci yabi abokan banza suka fara bangar siyasa daga nan ya tsallaka zuwa Lagos a can ya koyo turanci da dukkan wani tantiranci Ammi kuma ba ruwanta bata nemansa zai yi bata wani abun hakan ya saka Baffa dawo da Burhan gidan ya tabbatar ya zama mutum kamar kowa... Prof ya shiga tashin hankali duk hanyar da zai samu ya yi magana da matarsa Hajja Azizat ta toshe ta, gefe guda kuma tashin hankalin ya fi gaban kwatance Talatu ƙarin kunama ta tura masa wasu bidiyo da hotuna wanda ta ɗauke su tare suna tsaka da sheƙe ayar su, kuma tsirara ta umarci ya bata miliyan 50 ko ta saki bidiyon a yanar gizo ita daman ko a jikinta, ta bashi kwana biyu tal ba kuɗinne matsala ba fitar da bidiyon tsayin shekaru Hajja Azizat bata taɓa sanin wata aura ba, kuma wa take aure ba. Zameer kamannin yaransa suka ci-gaba da firgita shi cikin dare, ƙiri-ƙiri zai je da buƙatar shi wajan Hanne amma ta yi masa fur ta ce ba jaka bace ita da zai dinga shaƙe mata wuya kamar dabba, ta ci masa uwa ta tattara duka kayanta dana yaran ta bashi haka zai wanke, ya tuna sanda Ridayya ta tsohon ciki take masa wanki ya tuna sanda ya ƙona mata fuska saboda ta ƙona masa kaya, da sanda ta datse yatsa a garin yin faskare, bai bata ci ba ba suttura amma kodayaushe ya je da buƙatar shi haka zata saurare shi babu wata mace da zata iya haƙurin zama da shi sama da mai son shi Ridayya ya yi believing yana haɗa idanu da ita dukkan wata soyayyar shi data narke a zuciyarta zata dawo ta zama sabuwa fil. A can ƙasar Japan kowa Ridayya ce zaune ta zubawa yaran nata idanu da suke bacci cike da nutsuwa cikin kyakkyawar tofa har sun zarta sati guda a duniya yanzu. Ta juya ta kalli MB USTAZ dake zaune saman kujera ya tattara hankalinsa guda akan laptop ɗin gabansa, wando ne trouser a jikinsa wanda ya kama shi fari tas da shi, jikinsa kuma babu riga gabaɗaya gargasa ce a saman farar fatarsa ta yi luff sai sheƙi take dalilin farin daya ƙara, ta ɗan kalli damtsen hannunsu da yake a ɗan murɗe kamar mai ɗaga ƙarfe a hankali ta mayar da kanta wajan sumar shi, tana mamakin yadda kullum sumar kansa ke ƙaruwa ta sakko harta zarta kafaɗa ya ɗaure da wani abu kamar ribbon, gash ta wani cuccure kamar indomie Saboda yawan saloon da yake mata, girarsa tamkar zasu haɗe da juna gasu baƙa ƙirin gabaɗaya ta rasa wa Abbiey ya ɗakko a kama? Da zai shiga cikin Larabawa babu shakka zai iya fin wani balaraben kyau da hasken fata, gashi a dire yake dogo da shi faffaɗa yana da jiki ba can ba ga kuma Brest ɗinsa da suka ƙara girma alamar lafiyayye ne shi gaba-da-baya. Ganin baya kallon ta saci kallon yaron dake tsakiya wanda ta yi masa alamar baƙin zare ta taɓa hancin yaron har zuciyarta take jinsa ba ƙaramin kima Abbiey ya ƙara a idanunta ba daya saka sunan Sadauki kulawa ta musamman take son bash da nuna masa soyayya tare da muhimmancin mai sunan. "Ba sai kin yi haka ba za ki tantance Sadauki a ciki ba Mimi" ta zaro idanu ta yi saurin matsawa ya miƙe da laptop gabaɗaya ya ƙarasa inda take hannu ya miƙa mata ta ce "Me za zan baka" hannun data miƙa masa ya doke yana harararta speaking calmly ya ce "Wajan za ki bani" Ya cafke yatsu biyar ɗin hannunta ya ɗago ta bakiɗaya ɗaya ya koma inda ta tashi ya zauna, ta saki baki tana kallonsa duk faɗin wajan nan sai nan ne ya yi masa? "Zauna" "Kafa tare mini waje Abbiey ina zan zauna" bai ce mata komai ba ya jawo ƙugunta da ya yi wani faɗi ya buɗe har rawa yake ya zaunar da ita a cinyarsa, ya ɗora laptop ɗin a cinyarta a hankali ya zuro da hannayensa ta ƙasan hammtarta ya ɗora tafukan hannayensa a saman nata, ya fara shafa keyboard ɗin jikin laptop ɗin yana yi yana shafa mata ƙwantaccen gemunsa mai laushi tare da manna mata laɓɓansa masu sanyi a ƙasan wuya ta runtse idanunta "Abbiey.....," Ta ce da ƙyar saboda wani abu daya tsarga mata bai ce komai ba sai da ya sauke numfashi ya ce "Look!" Can ƙasan maƙoshi manyan Haɗaɗɗun gidaje ne na kice raini har guda uku ta dinga kallon pictures ɗin gidajen kafin ta ce "Na mene wannan?" "Wanne kike so mu zauna?" "A ina?" "Nigeria" Cikin wani farinciki ta juya gabaɗaya itama ta zura hannunta kamar yadda ya yi mata tana kallon cikin idanunsa ta ce "Abbiey da gaske gida zamu koma? Kuma ba zamu sake dawowa nan ba?" Ya dinga kallon laɓɓanta masu taushi da ɗan tudu yaƙi cewa komai sai idanu yake bin ta da shi ta ɓata fuska ta ce "Uhm'uhm" "Kin gaji da ni?" Ta waro manyan idanunta tare da ɗora hannunta akan wajan brest ɗinsa ɗaya ta girgiza ta ce "Ka zama jinin dake yawo a jikina Abbiey, gajiya da kai har abada" "Show me" Ta yi shiru ya kama hannunta ya ƙara manna shi a wajan ƙirjin ya ce "Mimi" "Abbiey" "Hug me and kiss my lips" Ta tura baki ta ce "To rufe idanunka" "Barshi kawai.....," kafin ya ƙarasa ta yi saurin riƙe lips ɗinsa tare da bashi wani irin deep and hot kisses idanunta cikin nasa ya saki laptop ɗin ganin zata faɗi ya yi saurin manne Ridayya da ƙirjinsa ya riƙo laptop ɗin....... Ƙauna ce mai tsayawa a zuciya ta wanzu a lokacin cikin sauri ta matsa ta ce "Yaranmu Abbiey" Ya girgiza kai kawai yana kallon ta da wani irin yanayi mara misaltuwa a hankali underneath his breath ya ce “I love you Mimi" "I love you Abbieyna" Ya yi murmushi mai taushi ya ce "To zaɓi" "Wannan farin yafi kyau Abbiey" Ya jinjina kai take ya yi order na furnitures na gabaɗaya gidan tare da biyan kuɗi ya kuma tura kalat decorations ɗin da yake buƙata. "Ɗaga ni to" "Wallahi cinyarka laushi Abbiey" bai kula ta ba ya san tunda ta ce haka ba zata tashi ba, ya ɗauki Sadauki dake kuka ya ajjiye a cinyarta ya ce "Ki duba yatsunsa yana da cindo a gefen na dama, babu buƙatar tantance shi da zare Mimi, Baffa kuma yana da cindo a ƙafarsa na hago Baba ƙarami kuma duk ciki shi ne tawadar Allah a saman leɓen shi" "Abbiey ya akai ka gane?" "Kece malamar yaranki ke ya kamata ki fara gane hakan Mimi, yanzu you're no longer a child na fita daga rainonki da tarbiyyarki dukda cewa tarbiyyar mace bata ƙarewa, ke yanzu uwa ce Mother of her childrens mother of 4 Childs Mimi, tun yaranki suna yara za ki kula da takun kowa muradan su, da abinda suke so hatta kukan su yana da kyau ki bambance su, ki tsaya a kan tarbiyyarsu da girmama junansu addininsu Mimi bana son rashin kula akan ibada kema ban ɗora ki haka ba, ina miki uzuri a baya amma idan kika nuna rashin kulawa da sake da tarbiyya za ki san wa kika aura" "Duka na za ka yi?" Ta faɗa a raza ne kuma da gaske har zuciyarta ya kame fuska sosai ya ce "Ai saboda haka na nemi dorina" Nan da nan idanunta ta sauya ta ƙasa magana "Idan kika nuna bambanci a yaranki za kiga bambanci, ina tunanin wannan zai zama aya ma a gare ki, domin nuna Banbancin da Baffa ya yi akan ki tun kina ciki shi ne ya yi sanadiyar samuwar ƙaddarar data same mu duka, domin na azabtu sanda na tabbatar kin zama matar wani i cry Ridayya...." "Abbiey please abinda ya faru ya faru" Ya ɗage mata gira duka biyun alamar YES a fili ya ce "ƙila idan na faɗa zan mata" Hawaye ne ya fara sakkowa daga cikin idanunta ta fara shassheƙar kuka ya ce "You broke me" Kawai sai ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi tana fashewa da kuka, tare da ɓoye kanta a ƙirjinsa tana kuka sosai da dukan ƙirjinsa ƙanƙame ta ya yi da kyau a ƙirjinsa yana dariya sosai dimples ɗinsa na lotsawa idanunsa suka sauya a daidai kunnenta ya ce "I am always in pain i've never cry for love but you make me cry, my heart hurts my chest is burning i beg you to stay with me amma.....," cikin sauri Ridayya ta hankaɗa Abbiey kan gadon ya yi saurin gocewa zuwa gefe gudun karya danne yaran tare da ƙoƙarin miƙewa zai gudu amma Ridayya ta yi namijin ƙoƙarin hana shi ta hanyar rufe bakin maganganun da yake ɗarsa mata masu zafi a zuciya ta shiga yi masa sumbata ƴar sunna kamar yadda ya koyar da ita.... Abbiey na zaune idanunsa zube akan waya Ridayya kuma hannunta riƙe da Al'hassan mai sunan Sadauki ta yi kwalliya cikin shigar atamfa ta murza ɗauri itama pictures ɗin take kallo "Amma ya akai ka fini kyau a nan Abbiey?" Ya murguɗa mata baki picture ɗ [7/1, 5:40 PM] null: *MUNAFUKIN MIJI* Nimcyluv 47 Mikiya writers Association..... *Masu tiktok kuje ku yi following profile ɗina domin mu dinga tattaunawa daku a can...* https://vm.tiktok.com/ZMrhYsBQE/ Cikin tashin hankali Umma ta ce "Bakin jariri kika ce fa Balkisa? Leɓe na jin baki irin nawa da nake magana kike nufi ko kuma wata tsoka ce ta yi tozo take neman faɗuwa ƙasa haka?" Ita kanta Balkisa mamaki da kallon baiwa da hikimar Ubangiji wajan iya tsara halitta shine ya cika mata zuciya da ƙyar ta zame idanunta akan jaririn ta ce "Zai fi kyau ki nutsu Umma jaririn na hannunki ki duba da kyau sosai" "Wannan ba dai jariri ba, sai dai idan ɗan aljanu kawai Mardiyya ta haifa, na rantse ban taɓa ganin jariri mai munin wannan ba, kalli hanci a bulaƙe kuma ya nane ta fata kalli halitta a jikin baki wai leɓe ce ko fa irin hasken jarirai babu a tattare da wannan jaririn" yadda Umma ke magana zai tabbatar da tashin hankalin da take ciki da gaske bata taɓa tsammanin jinin Babban mutum zai kasance haka ba, tana da yaƙinin jinin Muhammad mai ƙarfi ne duk yaron da zai haifa tabbas kamanninsa zai ɗauka. Balkisa ta juya ta kalli Mardiyya da ko zafin haihuwar bai gama sakinta ba, fama ake ta yi ta mahaifa ta faɗo amma abu ya ci tura, dukda an ɗaure amma neman yin sama take wajan ƙirjinsa, hakan ya saka innar Mardiyya ta fara shiga tashin hankali domin tas mahaifa kan kashe mutum jini take sha sosai. Innar ta kalli Umma ta ce "Haba baiwar Allah ke baki da imani da tausayi ne, kamar ba ki san ciwon haihuwa da zafin naƙuda ba zai yarfawa yarinya magana kike ina laifin ki yi lale da zuwan mai gidan naki? Halitta ɗaya ce dai kuma an haifa" Wani banzan kallo Umma ta watsawa Inna ta dire jaririn da take jin ranta yana ɓaci a kansa, amma bata isa ta nuna masa ƙi ba saboda jininta ne amma har ƙasan zuciyarta take mamakin yadda yaron sam bai kwanta mata ba. "To Allahamdulilah mahaifa ta faɗo mun gode Allah an rabu lafiya" "Ma sha Allah, sannu Mardiyya" cewar Balkisa ta shiga goge jinin wajan. Mardiyya ta sauke ajjiyar zuciya idanunta akan jaririn ganin babu inda ya bar mahaifinsa ta runtse idanunta tana jin fargaba mai tsanani na ratsa mata zuciya haihuwarta sa zuwan yaron duniya na nufin abubuwa da dama. "Me na haifa ne Inna?" Ta furta da ƙyar Inna ta ce "Jaririya ce mace kika samu Mardi" A firgice Umma ta ce "Mace kuma ke Balkisa ba namiji kika ce ba? Ai da maza jaririn ke kama" "A'a Umma mace daman na ce miki ai" Umma dai ta kasa furta komai sai girgiza kai take Mardiyya ta ce "Na yi wa Umma takwara a sakawa babyn Hadiza" zanin Umma na faɗuwa ta ce "Wacce Hadizan za a yi takwara? Ba dai ni kike nufi ba Mardiyya" "Umma mene laifina idan na saka sunanki jikarki ce fa? Ai farinciki ya kamata ki yi ko?" Umma ta girgiza kai ta ce "A'a na yafe idan an haifi wani a saka, ga innarki nan a saka ko" Kafin su yi magana Yaya Zuhura ta shigo cikin murna ta ce "Umma albishirin ki?" Ta haɗe rai ta ce "Goro" "Babban mutum ya dawo yanzu, Yaa Bilal is now at home" ba Umma hatta Mardiyya ba ta yi tsammanin jin hakan ba, ta sauke ajjiyar zuciya mai nauyi na farinciki da kuma na tashin hankalin da take tunanin yana gab da rikito mata. Farinciki ya saka Umma ta kasa cewa komai ta riƙe Yaya Zuhura ta ce "Da gaske kike Zuhura?" "E Umma, yana main parlon ma" Umma ta juya zata fita Mardiyya ta ce "Umma ki tafi masa da babyn na san zai yi farinciki" Ita dai Umma ko ta kan Mardiyya bata biba ta nufi hanyar fita Yaya Zuhura ta rufa mata baya, Balkisa ta miƙe ta ce "To Mardiyya bari na je na gaisa da ɗan'uwan nawa nima kafin ya shigo" Inna dake satar kallon Balkisa ta ce "A'a kekam ai sai son barka sannu da ƙoƙari, uwar mijin dai ce naga ta na yi wa jinjirar wani gani-gani ai halittar Ubangiji ce" Bayan Balkisa ta fita Inna ta ce "Mardi anya ba ki yi gamo da aljanu a wannan cikin ba? Ko kin watsawa ƴaƴan aljanu ruwan zafi ba ki sani ba?" "Inna me kika gani?" "Uban uban me na gani, ga abinda na gani nan a cinyarki ki dubi yarinyar nan har wani maiƙon baƙi take yi ke fara ubanta ma jaririn da shi haka kakannin nata" cikin runtse idanu Mardiyya ta ce "Ai Ubangiji da yadda ya kewa kowa tashi halittar" "Haka fa, na ga alama to Allah ya raya miki" A can main parlour Ustaz na kishin giɗe yana ɗan lumshe idanunsa hannunsa ɗaya riƙe da hular kansa little Bilal na cinyarsa sai Junaid dake kusa da shi, dukda cewa Ustaz ba ma'abocin yin fara'a bane amma fuskarsa ɗauke take da lallausan murmushi wani daɗi ya ke ji da nutsuwa na saukar masa, musamman yadda yake ganin farinciki a fuskar kowa dalilin zuwansa da zuri'arsa,bai taɓa zaton haka ya yi kewar gida ba sai yanzu daman Ridayya tuni ta shige part ɗin Mami saboda jininta bai gama ƙwari ba, ƴan'uwan Mami sun yi caa a kanta ita dai sai murmushi take gashi kowa burinsa ya ɗauki su Al'hussan, hawayen farinciki ke ƙoƙarin zuba daga cikin idanunta ta sauri juyar da fuskarta ganin sun haɗa idanu da Mami Anty Kaltum ta saka a haɗawa Ridayya farfesu wanda ya ji daddawa da kayan ƙamshi tare da kunun kanwa. Jikin Ustaz har rawa yake wajan miƙewa lokacin da Umma ta ƙarasu parlourn tsayawa ta yi tana ƙare masa kallo ta kasa yadda babban mutum ne ya zama haka, tamkar ba jikinta ya tsaga ya fito ba, hatta kwantaccen murmushin dake shimfiɗe a saman fuskarsa is very different dana baya, bata san hasken fatarsa ya kai har haka ba sai yanzu, har wani yellow fatarsa ke yi saboda tsananin hutawar da yake yi, zagayayyiyar fuskarsa ce kawai a bayyane da manyan idanunsa da suke farare tas sai kwantaccen sajen fuskarsa ya zagaye ya sauka tare da haɗewa wajan gemunsa, a hankali ya sauke hular kansa ya riƙe sumarsa ta sauka don dama tuni little Bilal ya zare masa ribbon ɗin. Ustaz ya kasa kallon Umma saboda ya san shi ɗin mai laifi ne, ya ƙarasa gabanta da tsananin girmamawa yana ƙoƙarin tsugunnawa ta yi saurin riƙo hannunsa ta damƙe a nata ta kasa cewa komai ta kasa jurewa kawai ta rungume shi cikin farinciki ta ce "Your welcome Son, barka da zuwa" ya kwantar da kansa a shoulder ɗinta tunda ya mata tsayi da yawa a hankali ya ce "I am sorry Umma Please...." "It's okay, zuwanka alheri ne Muhammad domin kana zuwa jininka na zuwa duniya" ya ware idanu da tunanin ko ta samu labarin su Sadauki yaransa ne? Kafin ya zurfafa tunani ta ce "Mardiyya ta sauka lafiya yanzu, kaga sai ka shigo ka yi mata sannu da samun kai ka yi wa baby huɗuba" da wani irin expression yake kallon Umma sai bai ce komai ba ta ce "Akwai matsala ne?" Ya girgiza kai a hankali ya ce "Zan zo" Ta yi murmushin sosai yanzu hankalinta ya kwanta ta ce "Bari na shirya maka favourite ɗinka yanzu, ka shiga ɗakinka ka huta yanzu sosai" ya ɗan juya agogon hannunsa ya ce "Ok tom" kafin ta yi magana Yaya Zuhura ta fito da sauri ta ce "Zuhura zo mana kawo mini wannan kyakkyawan babyn mana" "Umma ai ƴan uku ne bari na kawo miki sauran" da sauri ta ce "Ba dai wanda Baba ƙarami ya saka mini frame nasu a parlour ba?" "E, sune wallahi" "A'a Ikon Allah, yi sauri Please Zuhura" Har Ustaz zai tafi sai ya tsaya tare da jingina da jikin bango ya harɗe hannayensa a ƙirji waiting to see Umma's reaction Umma tunu ta zauna saman kujera tana riƙe da Sadauki da yake buɗe idanu yana rufewa alamar baya son haske tana zaune Yaya Zuhura da Zainura suka kawo mata sauran suka ajjiye a cinyarta, ita kanta Umma bata san meke damunta ba, wani daɗi ta ji yana ratsa mata zuciya ta ce "Ma sha Allah, fatabarakallahu ahsanunl kaliƙin Ubangiji ya raya wannan yaran ya yi musu albarka ya kau da idanu a gare su" Yaya Zuhura ta ce "Amin" Zainura kallon Umma kawai take Ustaz dai na tsaye shima idanunsa akan yaran idan kuma ya tuna daga jikin wa yaran suka fito yana samun tsoro a zuciya na rashin matakin da Umma zata ɗauka a wannan karan kuma. Umma ta kalli Yaya Zuhura ta ce "To ina ruwar yaran na yi mata barka" "Ridayya ce Umma" cewar Zainura Umma ta juya sai a lokacin ta kalli Zainura don ba wani shiri suke ba ta lura yarinyar surutu gare ta da rashin kunya "Wacce Ridayya kuma?" Zainura ta ce "Ridayya dai ƴar Abbiey yayata kuma yaranta ne ita ya haife su" cikin rashin fahimta ta ce "Zuhura me yarinyar take cewa ne?" "She is right Umma, they are Ridayya's children yaranta ne ai tana part ɗin Mami" Umma ta yi jim ta kasa cewa komai sai kallon yaran take da wani irin shock ya akai Ridayya ta haifi wannan kyawawan yaran? Masu kama da larabawa? Ta tuna yadda little Bilal yake ita kenan jininta na haifar fararen yara ne masu kyau? Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Daman ta yi aure ne?" "Kai ai bata bar gidan nan ba sai da ta yi aure Umma" Umma ta yi shiru bayan ta ji abinda Zainura ta ce shi dai Ustaz na tsaye lokaci zuwa lokaci yake ɗan goge goshinsa Yaya Zuhura ta ce "To kawo su a mai dasu" "A'a ki bar su mana, ɗauki wannan mai tsotsar hannun naga yana da rigima" Ustaz ya kalli wanda ta ce yaga Sadauki ne bai san ya akai maganar ta fita ba sai ji ya yi ya ce "Sadauki ko? Daman shi ne baya baccin dare haka muke ta fama" Umma ta ce "Me ka ce?" Ya saurin lumshe idanu tare da tafiya zai bar wajan ta sake cewa "Taya ka sani kai to?" "Saboda yaransa ne su ɗin ai" Gabaɗaya suka kalli mai maganar Baba ƙarami ya ƙarasu fuskarsa ɗauke da murmushi cikin sauri Babban mutum ya rungume Abba ya ce "Abba....," Baba ƙarami ya ce "Barka da zuwa babban abokina uban ƴan uku" Ustaz ya lumshe idanunsa kawai ya gaida Abba kana ya matsa for the first time ya ji nauyin Baffa ya ce "Sanniyda zuwa Baffa" Baffa ya ce "Kai ne da sannu Babban mutum, an samu ƙaruwa Ubangiji ya raya ya saka musu albarka" Kai tsaye Ustaz ya ce "Amin Baffa, thank you" Tajj dake shigowa ya ce "Shugaban marasa kunya ta duniya" Ustaz ya yi masa banza ya kame fuska musamman ganin su Zainura da su Khaliperh a wajan, amma dole sai ya ce uban Tajj akan irin haka. Umma ta kalli Baba ƙarami da tsananin mamaki ta ce "Abba ka yi magana ka yi shiru kuma ban gane yaran Babban mutum bane, yaushe ya samu yaran? Bayan yarinyar da aka haifa masa yanzu?" Baba ƙarami ya yi murmushin jin daɗi kuma irin na manya ya ce "E, Hadiza Al'hussan, Al'hassan, Gambo yaran Muhammad Bilal Tahir Rano ne da Ridayya Muhammad Bilal Rano, bi ma'ana Ridayya Mansur Rano" Tashin hankalin Umma ya girmama zufa ta dinga yanko mata baki buɗe take kallon Ustaz irin You disappointed me ɗin nan bani da alfamar da zaka iya mini biyayya ko bin umarnina idanunta ya sauya da ƙyar ta ce "Sakin da ya yi mata fa?" Ta faɗa a raunace labɓanta har rawa suke tana datse su. Baba ƙarami ya zura hannunsa ya ɗakko takarda ya ware ya ƙarasa wajanta tare da kamo hannunta ya damƙa mata ita ya ce "Read it Hadiza, ka karanta da kyau Hadiza ya rubuta miki takarda bisa umarnin da kikai masa sai dai baki karanta ba na amsa, wannan shine abinda takardar ya ƙunsa, nutsu ki karanta" ta buɗe; tunda ta fara karantawa take jin ƙirjinta na yi mata wani irin nauyi bayan ta kama ta miƙe tsaye hannunta ɗaya riƙe da Sadauki haka ta shige part ɗinta without say a single word. Ustaz trying to follow her Baba ƙarami ya riƙe shi ya ce "Ba yanzu ba, ka bata lokaci ka kalli waye a hannunta ta bar parlon, in sha Allah komai zai daidaita yanzu ka huta ka ci abinci ka ji ko?" Jinjina kai ya yi kana ya juya zuwa asalin part ɗinsa dake gida walking slowly yana ɗan buɗewa sai goge goshinsa yake, Tajj ya biyo bayansa Ustaz ya zauna saman doguwar kujera yana ɗan ɓalle botiran gaban rigarsa. "Japan ta yi maka mugun sabo duk a.cn nan ji yadda kake goge fuska" Tajj ya faɗa bayan ya ɗauki remote ya ƙaro gudun A.cn kana ya zauna yana kallon Ustaz ya ce "Ya hanya ka dawo lafiya?" Shiru Ustaz ya yi kamar ba zai magana ba, a hankali ya ce "Kana lafiya Tajjudeen?" "Allahamdulilah, an samu ƙaruwa Ubangiji yasa albarka munga kara thank you?" "For? Kara?" "Sunan Sadauki da aka saka" siririn tsaki Ustaz ya ja yana watsawa Tajj harara ta watsa bai ce komai ba can ya nisa ya ce "I love Ridayya Tajj" Sosai Tajj ya yi dariya ya ce "Sai yanzu Emotions ɗin ke ɗibarka? Da zurfin cikin fa?" Cije lips kawai Abbiey ya yi yana sauke nunfashi tunaninsa ya bambanta, ga Umma, ga Zameer, ga Mardiyya da abinda ta haifa ga matsalar siyasa sam baya son siyasar ƙoƙarin janyewa ma yake yi. Sun ɗan taɓa hira dukda rabin hirar Tajj ne Ustaz da kunne ya ke ji a haka Mami ta aiko musu da abinci, Ustaz ya kalli abincin sai ya ɗauki wayarsa ya kira number ba jimawa aka ɗauka. A hankali a kuma taushashe ga ce "Waye ya yi girkin?" "Mami" ya yi shiru yana lumshe idanunsa, daga can ɓangaren Ridayya ta miƙe bayan Yaya A'isha ta amshi Al'hussan ta shige bedroom ɗin Zainura murya can ƙasa ta ce "What happen?" Still ya yi shiru, Tajj kowa ko a jikinsa abinci kawai yake ci hankali kwance domin sakwara ce da miyar akusi ta sha nama sai tuwon shinkafa da miyar wake wacce ta ji kifi Abbiey yaƙi magana kamar za ta yi kuka ta ce "Talk, do you need something" "Mimi" ya kira sunanta a ɗan shagwaɓe wanda ya saka Tajj kallonsa cikin sauri domin tabbatarwa da kansa Ustaz Bilal ne mai narkewa mace haka? Suna haɗa idanu Ustaz ya buɗewa Tajj idanu murmushi kawai Tajj ya yi. "Abbiey mene? You scared me" "Ki zo mu tafi gidanmu" ya ce ƙasa ƙasa yana ƙara lumshe idanunsa sosai ya takura da haniyar gidan da kallon da ake yi masa ta ce "Wanne gidan kuma Nurul hayat?" "My house, our house" Ita abin dariya ya bata ma tai ta dariya a hankali ya ce "Come" Yana faɗin hakan ya kashe wayar. Hannunsa ya wanke tas ya zame ƙasa saman carpet tuwon ya saka da kansa sai marairaice fuska yake da sun haɗa idanu da Tajj kuma sai ya sha kunu ya saka malmala ɗaya tare da yin Bisimillah ya saka yatsu ya fara ci. Har wajajen magariba Umma bata fito ba, ko da Sadauki ya yi kuka rarrashinsa ta yi har ya yi shiru ya koma bacci, tana zaune da tunani kala-kala a ranta wato rabon yara har uku kuma duka maza ba wasa bane, rabo ya saka Ustaz ƙin yi mata biyayya, rabo ya saka ya bar ƙasar rabo ya kashe Sadauki, rabo ne ya saka ta gudu daga Katsina, lallai rabo abune mai girma yarinyar da take aibata muninta ita ta haifi waɗannan zuƙa-zuƙan yaran? Allahu Akbar, gabaɗaya ta rasa me za ta yi ita kunyar fita take tun bata san uwar yaran ba ta ji tana ƙaunar su sosai, hawayen tausayin Ustaz ya shiga cika mata idanu tana zaune aka buɗe ƙofar tare da shigowa. Inna ta ce "A gaskiya ba zan ɓoye miki ba an wulaƙanta yarinya kuma anci mutuncin furfurata, ban taɓa ganin haka ba tunda nake a rayuwa wannan cin mutuncin haihuwa ne, da ya yi ciki ya ɗora mata ya kama hanya ya yi tafiyarsa yanzu ya dawo amma ko ya shigo ya ce me aka samu? Saboda ga mara galihu ta haihu ko? Ai yau Mardi ki ƴar iska ce tunda ta haifa muku a ce mata sannu, balle kuma tsarkakkiyar yarinya ce mai haƙuri, ko kuma saboda bake ce kika wage ƙafafuwa kika haihu ba shiyasa kike mana haka ohho" Da mamaki Umma ta ce "Muhammad ɗin bai shigo bane?" A fusace Inna ta ce "Ya shigo gashi cikin rigar mamata, ji wulaƙanci ƴar dabar ina ce ni daya shigo zan masa ƙazafi haka?" "Ki yi haƙuri bari ina zuwa" ina ta dinga satar kallon Sadauki dake motsi kana ta fice Umma kuma bata san mene yake faruwa da ita ba, bata son fita bata kuma son ƙara kallon babyn da Mardiyya ta haifa dukda cewa Ridayya da yaranta sun zame mata ishara akan tsarin halittar Ubangiji. Number Ustaz ta kira bai ɗaga ba, tana ƙoƙarin kira ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ta amsa ya nemi waje ya zauna ta ce "Yanzu nake kiranka" Ya ɗaga kai ya kalleta sai kuma ya ce "Ina kusa ai" a hankali ya ce "Barka da hutawa" "Yawwa. Amma na faɗa maka Mardiyya ta haihu ko? Tana hakƙi a kanka fa babban mutum, ashe daman baka shiga ba balle kaga yarinyar data haifa" shi dai ya yi shiru yana kallon ta idanunsa tuni suka shige ciki Gambo ta ɗauka ta miƙa masa ta ce "Tun ɗazo yake kuka ko abinci yake so" Ya miƙe ya amshi Sadauki ya rungume shi, sosai yake da rigima kuma ya fi son a ɗauke shi ko irin kwanciyar jarirai bai so, saɓanin ƴan'uwan shi sam baya son haske yana buɗe idanu yake rufewa ɗan duhun daya gani a jikin Ustaz ya saka buɗe idanu yana gurun-gurun da baki. "Bari na je" "Yawwa sai ka yi wa yarinyar huɗuba" sai da ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce. "Zani saboda je da kuma kasancewar ta matsayin matata, amma bani ne uban yarinyar ba" yana faɗin hakan ya fice Umma ta ji kamar Hausa kamar ba Hausa ba ta dinga maimaita furucin nasa a zuciya da fili. Mardiyya na zaune bayan ta yi wanka ta shirya ta murza ɗauri tayi kyau ƙwarai abinta sai ƙamshi take wani irin daɗi take ji za ta yi tuzali da mijinta tana jin abinda Inna ke cewa ta ce "Ai kin san tun ina yarinya ba wani kirki ne dani ba, zuwa na yi fa nai mata tas ta dinga kuka tana bani haƙuri idan na yi shiru da baki aka wulaƙanta ki ai ban ma uwarki adalci ba" Murmushi Mardiyya ta yi ta ce "kin yi maganinta ai yanzu" "Amma naga wani kyakkyawan jariri a hannunta tubarakallah wallahi aka haɗa jaririn da wannan ƴar taki to cewa za a yi ba mutum kika haifa ba, to daman na ji ƙishin ƙishin wai mijin naki ya dawo tare da matarsa kuma ita ta haifa masa wannan yaran" Inna ta ce tana ƙifta idanu sai kallon ƙofa take. Diyya ji ta yi cikinta ya zuciya abu ya tukare mata a ƙirji idanunta ya yi jajur sai nishi take yi ta ce "Anya Inna daidai kika jiyo?" Inna ta ce "Habawa ji ne dani kamar maciji wallahi haka akai kuma yara uku aka haifa duka farare idan haka ya tabbata kinga wancan ita ce da gida tunda maza uku ba wasa bane, ki dai kwantar da hankalinki kar jininki ya yi hawa 200 wallahi, kwana nawa ne ya yi miki wani cikin tunda naga baiwarsa kenan" Hawaye ya cika idanun Mardiyya bawai tabbatarwa ta yi ba, kawai tana tunanin yadda zata iya haɗa Ustaz da wata ƴar macen. Tuna tana tunanin zuwan shi har ta fidda rai kuma Umma bata shigo ba, Balkisa kawai ta shigo sai Baba ƙarami da ya yi mata sannu. Washegari duka suna Main parlor hadda Ridayya da ta yi wanka cikin wani dakakken lace ta yi masifar kyau, tai fresh sosai sai murmushi take tana kallon Little Bilal da suke ta faɗa da Zainura tana cewa "Ba za ka yi mini zaman ɗakin ba, tunda babarka ta dawo ita zaka bi" Shi kuma sai ya maƙale kafaɗa ya ce "Uhm'uhm zani" "Wai waye surukin namu ne?" Cikin Sauri Abdullah ya ce "Wai Burhan" "Burhan?" Ridayya ta maimaita tana sake kallon Zainura, Zainu ta haɗe fuska Khaliperh ya ce "Ta kwafsa ai yarinyar nan, kuma na fahimci Tajj ma son ta yake ga mutumin kirki ta je ta ɗakko ɗan shaye-shaye" "Wallahi ba ɗan shaye-shaye bane, kuma yana da kirki" ƙafa Aliyu ya kawo zai haure ta, ta kwasa da gudu ta bar wajan. Shiru duk sukai ganin Ustaz ya fito cikin wani voyel mai laushi da manyan zane ya ɗora baƙar dara a kan shi ta ƙara fiddo kyawunshi Ridayya ta gefen idanu ta kalle shi ta ɗauke kai, Little ya tafi da sauri yana "Abbiey, Abbiey" Ya ɗauke shi yana shafa kansa kamar zai shige ya dawo ya ɗauki Al'hussan a cinyar Ridayya, numfashinta na ɗauka a fuskarsa ya ɗaga kai suka haɗa idanu ɗan matsawa ya yi ganin kamar duk t.v suke kallo a hankali ya manna mata kiss a kumatu "Morning Mimi" Ta yi saurin ware ido da sauri ya ɗago kansa suka haɗa idanu da Baba ƙarami, bai yarda ya sake kallon wajan ba ya nufi part ɗin Mardiyya ganin inda ya nufa ya saka Ridayya jin wani abu a ranta mood ɗinta ya sauya. Mardiyya na zaune cikin kwalliyar atamfa gilita babyn na hannunta ta ji ƙamshin Ustaz cikin sauri ta ɗaga kai ta ganshi tsaye bakin ƙofa hannunsa riƙe da baby, ta yi murmushi tana ajjiye jaririyar ta miƙe ta ce "Oyoyo sweetheart barka da zuwa" kafin ta rungume shi ya gefe tare da shiga cikin bedroom ɗin nata, ya zauna saman stool ta ƙarasa ta zauna ta ce "Good mrng" Shuɗewar wasu seconds ya ce "Sannu, ya jiki?" Ta ce "Alhamd, ya hanya kana dawowa babynmu na zuwa duniya" ya ɗan yi mitsi-mitsi da idanu ta ɗakko yarinyar ta miƙa masa ba musa ya ɗora Al'hussan a cinyarsa ya amshi yarinyar ya zuba mata idanu can ya ce "Allah ya sa mata albarka" "Sweetheart ya naga kamar baka farinciki, first born ɗinka ce fa kuma ba wani gift na haihuwa" tunda take bata taɓa ganin murmushin Ustaz irin yau ba, sai hakan ya yi mata daɗi sosai ya yi murmushi ya ce "Zan bada gift ai kin cancanci hakan ko dan riƙo da tarbiyya" bata kawo komai a ranta ba ta ce "Haba sweetheart ai ba komai don na haifa maka baby" Ya miƙe tsaye ya ce "Zan je abu, ga wannan" ya miƙa mata envelope mai ɗauke da kuɗi ya ɗora akan jaririyar, ta ce "But is true?" "For?" Ya tambaya yana ware mata idanu to be sure ya ji tambayar ya dai share ne ta ce "Da gaske wannan ɗanka ne? Kuma ka yi aure?" Ya ɗan lumshe idanunsa yana rungume Al'hussan a ƙirji ya ce "E, daman ai ina da aure yara kuma nawa ne Mardiyya" "Wace matar daka aura?" "Ridayya Mansur Rano, Ridayya ƙawarki aminiyarki tun kuna yara" yana faɗin hakan ya juya a firgice kamar zata jawo shi amma tana shakka ta yi saurin shan gabansa ta ce "Ridayya ka ce? Wace haka wanann mummunar yarinyar she can't be your wife bayan ka sake ta?" Ya dinga kallon ta duk yadda yake ƙokarin danne zuciyarsa yaga bai ci mutuncinta ba tunda da gaske tana hakƙi a kan shi kuma har zuciyarsa yayi niyya zama da ita idan ya so ya ji da rigimar Mimi shine take masa ihu aka, ko waye ya faɗa mata ana masa ihu a ka ya haɗe rai sosai a dake ya ce "Ke bana son shirme matsa mini" bai zata ba ya ji ta cakumi wuyan rigarsa ta ce "Wallahi ƙarya ni,ni za ku ci amana bayan kowa ya san cewa ka sake ta sai dai idan zaman kasuwanci kuke tare a inda ka ɓoye ta" wani kyakkyawan mari ya sauke mata wanda ya sanya ta fasa gigitaccen ihu hakan ya saka Inna farkawa daga bacci a razane tana "Wanne ɗan mara wulaƙancin ne wannan" Daidai nan Baba ƙarami ya ƙarasu tare da Umma da har yanzu bata fita daga shock ba ta ce "Muhammad ka bar ni cikin duhu ban gane cewa ba ƴarka bace" Ya juya ya kalli Umma ya kalli Baba ƙarami kana ya kalli Mardiyya dake rusa ihu Inna na tsaye ya ce "To yaushe na yi cikin? Babu wata ƴa mace dana sani a duniya sama da Ustaz kuje ku tambaye ta ita ta amshi budurcina a can Japan, Ridayya kawai ta gani a halin daya kamata daman ace ita ta ganni, bayan tafiya ta da yaushe ta samu cikin? Ta muku bayani bani da lokacin hakan" Umma ta saki baki Baba ƙarami girgiza kai kawai ya yi ya san daman za a yi hakan ya ce "Mardiyya an yi yarinyar huɗuba?" Ta girgiza kai tana ta kuka fargaba ta cika mata zuciya tana fatan komai zai je ya dawo ta kasance da Ustaz har abada ta kuma raba shi da Ridayya da ta ci amanarta. Baba ƙarami ya amshi yarinyar bayan ya yi mata huɗuba ya ce "Wanne suna kike so?" "Sunan Umma na ce a a saka Hadiza Umma na yi wa takwara" "To ma sha Allah, Allah ya yara Hadizatul-kubra" Umma ta yi saurin cewa "Wacce Hadizan? Wallahi bana so a ƴar shegen za a saka sunana wallahi na yafe a saka sunan tata uwar ko wannan" Ta nuna Inna. Inna ta zare idanu ta ce "Ni Mero ina ruwana? Bake kikai ta ɗawainiyya da cikin ba" Baba ƙarami ya danne dariyar dake cinsa ya ce "Kina da gaskiya Inna, Umma ta yi ƙoƙari a cikin nan har fili ta mallaka masa fa? Ai dole a saka Hadiza" Yana faɗin haka ya sawa yarinya Hadiza Umma ta fashe da kuka ta ce "Allah ya isa wallahi, kuma ba ni Hadizan aka saka ba ki je ki fito mini da takardun filayena" "Wallahi Umma ƴarsa ce sharri yake mini, wa aka aura mini idan bashi ba yawo nake yi ne?" Sai kuka take Umma ta ce "Ke rufa mini baki a nan, Ustaz kalma ɗaya yake idan ƙarya ne kai tsaye zai faɗa haka idan gaskiya ne" Takaici ya haɗewa Mardiyya Inna dai na tsaye sai zare idanu take suna haɗa idanu da Mardiyya ta ce "Ashe tantiriyar ƴar iska ce ke?" Duk suna zaune kamar daga sama Ridayya taga mace a gabanta ta ɗaga idanu ta kalli Mardiyya da take cewa "Shegiya munafuka Allah ya tuni asirinki mai ƙwacen miji wallahi ba ki isa ba sai kin bar mini mijina domin nawa ne ɗaya har abada" Miƙewa Ridayya ta yi zata shige part ɗin Mami Mardiyya ta riƙo wuyanta, daman tun ɗazo zuciyarta ke yi mata zafi sosai bata tsaya jiran komai ba ta ɗaga hannu ta zabgawa Mardiyya mari ta ƙara sauke mata wani ta nuna ta da yatsa ta ce "Kul karki kuma, ki haukan ki kan wanda ya ajjiye ki ba ni ba, wahainiyyarki ta kiyayi ramata, ke har ni za ki buɗe baki ki cewa mai ƙwacen miji? How dare you? Ni kikaiwa ƙwace ko ni na yi miki?" "Idan kin manta na tuna miki, kin tuna sanda kika ce Abbiey ba tsarinki bane jallabiya za ki aura ko shi? Kuma kika ce idan ina da ra'ayi na je na aure shi? Ai tun daga wannan na sakawa raina sai na aure shi kuma ya zama nawa har abada, kin yar ni na ɗauka don haka dole ki bar mini mijina" Maganganun da Mardiyya ta tunawa Ridayya sun mata zafi ta dake ta ce "Ohho dani dake za a ga mai fitar da wani, zama da mijina yanzu na fara kuma yanzu na shirya zan cika gidansa da tarin yara masu kyau irin albarka, zan ci gaba da son mijina don haka kowa ya iya allonsa ya wanke, ina son Abbiey yana sona" sosai suke faɗa ba zaka taɓa cewa sun taɓa zama aminai ba, Mami na ji ta yi shiru shi kansa Ustaz yana tsaye Umma ta ƙarasu ta ce "To wallahi sai kin barwa Ridayya mijinta, domin ita ce irin albarka" kalaman Umma sunwa kowa daɗi kuma sun bawa kowa mamaki ganin jinin Ridayya ya fara rawa idanunta yana wani kala ya saka Ustaz yin murmushi ya ƙarasu tare da kama hannunta ya ce "No please Mimi" hannu ta saka ta doke hannunsa tana zabga masa harara ta suka ci-gaba da cacar baki "Banza wacce ubanta ya ce ba shi ya haifeta ba, wacce babarta ta gudu ta barta wajan kishiya uwar ƴar shaye-shaye kawai wacce ta auri ɗan caca.....," Caraf Zainura ta ce "E an ji ɗan caca ke kuma da kike yawan ta zubar fa? Mai shafe shafe kuma ita bata zalunci mijinta ba shi ne ya tauye mata hakƙi shi ya sa yanzu take ta ganin sauyi kala-kala, da kike maganar muni kuma ai ga ƙarshen muni nan kin haifa bayan ke ɗin fara ce kyakkyawa ita data kasance baƙa ki dubi nata kalar irin kiga? Ai babban goro sai magogin ƙarfe kuma da tsohuwar zuma ake maganin hakan kuma don tuwan gobe ake wanke tukunya" Burhan sai murmushi yake that's why she always love Zainura yana son mace mai tsiwa da baki wacce yana cewa ke zata ce kai ƴar drama like Zainura. Ustaz ya sunkuya ya sunkuci matarsa ya nufi part ɗinsa da ita sai rawar jiki take, Mardiyya ta juya fuuu bayan taci kuka ta ƙoshi addu'a take Allah yasa jaririyar ta mutu ma, ta dinga kiran number ƙawarta domin ita kaɗai tasan gaskiyar komai amma bata samu ta tuna gift ɗin da Ustaz ya bata hakan yana nufin yana son ta bai kuma yi fushi ba. Ta buɗe kuɗi ne ƴan 1k bandir uku sai ƙaramar takarda tana buɗe taga ya rubuta. _Wannan kuɗin kyauta ne daga ni a matsayin mijinki, da gaske na so zama dake tunda ni bana buƙatar saki a cikin lamarina aurena dake ƙaddara ne, amma zunubin da kika aikata ya saka na janye nawa ƙudirin ba zan iya zama da macen dake bin maza ba.... Mardiyya na sake ki saki uku kuma ki nemi uban yarinyar da kika haifa_ Wani ihu ta saka tare da sulalewa a wajan babu numfashi. Waya yake yi yana cewa "Na ji ya dawo gari, ba zan taɓa haƙura da cin mutuncin da Zameer Giɗaɗo ya yi mini ba dole ne na baza bidiyon da sukai a jam'i kafin su yi aure, kowa ya gansu tsirara babu abinda ya shafe ni ba'a cin bashina na yi haƙuri wallahi, so zan jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan, daman akwai wani ya bani kwangila ɓata shi Muhammad Bilal Tahir Rano ɗin domin jama'a suka baƙin shi, kaga yarinyar da sukai zina tare da Zameer ai matarsa Bilal ɗin ce da yake neman takarar Gwamna, kuma shi da kansa bai san cewa ta aikata abinda ta yi ba, so babu mamaki ganin bidiyon ya saka zuciyarsa bugawa ya mutu nan take" Khalid ya yi ɗan jim sai kuma ya ce "Ok bari na tura maka bidiyon yanzu da iPhone aka ɗauka ya yi clear sosai a fara posting a tiktok sai ya fi zama trending going in to viral ka yi hash tag sai a koma facebook da X da Instagram sai a turawa bloggers yawwa gashi nan zan tura bidiyon yanzu...... A yi haƙuri gobe zamu kammala 08164069385 [7/4, 9:31 PM] null: *MUNAFUKIN MIJI* Nimcyluv 48 Mikiya writers Association Fitowa sukai daga ɓangaren emergency ɗin kana ganinsa zaka san yana cikin damuwa ya ce "Dr yanzu ya za mu yi da gawar? Kuma ba a samu labarin wanda sukai masa wannan rashin ɗa'ar ba?" Dr ya kalli Shaba da Moo ya ce "Ambulance za a kira sukai muku gawar, and wanda suka aikata hakan i think that is not part of my work, an dai samu labarin cewa ƴan daba ne suka same shi a bakin hanya, sukai ƙoƙarin amshe wayarsa ya hana su, garin haka suka soka masa wuƙa a ciki sai data ɓullo ta bayan shi, bayan wayar har motarsa suka gudu da ita shi kuma suka yasar da shi a ƙasa, kafin ma a zo asibiti ya cika" Moo ya sauke numfashi shikenan sun rasa Khalid? Yaushe za a daina ƙwacen waya? Yaushe ne za a daina shaye-shaye? Yaushe ne za a daina daɓa? Abin kullum ƙara girmama yake kamar cin ƙwan makauniyya? Faɗan sai ƙara yawa yake ba mai cewa komai babu mai ɗaukan mataki? Meke haddasa shaye-shaye da kuma daba? (Find out on MUTALLAB). "Allah sarki Khalid Allah ya jiƙan shi bai so ya rasu bamu daidaita tsakaninsu da Zameer ba" cewar Moo kallon shi kawai Shaba ya yi without saying a single words. In few minutes rasuwar Khalid yaɗu cikin jama'a da kuma yadda ake Allah wadai da masu ƙwacen waya. Ambulance na zuwa aka saka gawarsa suka nufi gida, hankalin duka ƴan'uwa a tashe yake. Zagaye yake cikin parlon nashi zufa sai yanko masa take ya juya ya kalli wanda ke tsaye a gabansa a hankali ya nisa ya ce "Kuma da gaske bai tura maka bidiyon ba kafin rasuwar shi? Bidiyon nan shine confidence ɗina kuma shinr hope nawa na ɓata farinjinin Muhammad Bilal, da kuma kawo naƙa su a takarar shi" Guy ɗin ya girgiza kai ya ce "Oga bai tura mini ba, daman na baka shawara wannan aikin da mutum ɗaya kawai ya dace, baya tsoro, baya shakka baya damuwa da duk abinda zai biyo baya shi ɗin tamkar walƙiya haka yake, hagayi sa gabanka inda kake so, shi ɗin murucin kan dutse ne bai fito ba sai daya shirya, ɗan malam yaƙi halin malam, faɗa taka cikawa tashi kuɗi kawai shi ne a gabansa kaci amanar shi uwarka ta haifi wani, jan biro maganin daƙiƙin yaro..... Huhuhu kutumar uban nan wani aikin sai maza da an ganshi fitsari ake a wando, ya gagara matacce ne amma kullum firgita su yake mutum me aikin aljanu, mata maza wajan ƙin mata da sabgoginsu" Nan da nan jiginsa ya fara rawa ganin haka ya saka Sakataren jam'iyar su Muhammad Bilal Ustaz mai suna Dr Ghali Uba ya ce "to waye wannan ɗin da kake ta yi wa kirari haka?" Shazali ya kalli Sakataren jam'iya ya ce "MUTALLAB" "MUTALLAB?" Dr Ghali Uba ya maimaita sai kuma ta ce "Yanzu bamu da wani lokaci, amma idan ina raye ba zan bar Ustaz ya hau wannan kujerar ba, ni na nemi takarar kujerar wajan Uban jam'iyya amma saboda ya wulaƙantani ya ce ban dace da ita ba, ya je ya ɗakko wanda bai san darajar siyasa ba ya bashi? Na ci alwashin lalata jam'iyyar idan ya so na yi anti fati kawai" "Oga kenan zagon ƙasa kake musu, sun yarda da kai fa? Shi ne kake ɓallo musu ruwa ta ƙasa? Ka daga oga" Dr Ghali Uba ya ce "Shazali kenan siyasa sai ɗan siyasa, yanzu ka je ka yi bincike ka ji ko shi Khalid ɗin ya bawa wani kwafin bidiyon, kuma ka ce ina kiran shi yama sunan shi yawwa MUTALLAB TAHHB" "Da ƙirinka oga ai MUTALLAB ko appointment ka nema da shi baza ka samu ba, saboda shegan ƙaro ne, innalillahi wani aikin sai ɗan Amina oga shi fa TAHHB ɗan balaja'u ne ko a rukunninsa ba kowa ya san shi ba" da mamaki Dr Ghali Uba yake kallon Shazali a ran shi yana tambayar who is MUTALLAB TAHHB? Mardiyya ta yi tsuru-tsuru lokacin da ƙawarta ta shigo gidan daman shirye-shiryen kai Ustaz koto take yadda ta ƙarfi za a mallaka masa yarinyar. Umma ta juya ta kalli wacce ta shigo haka Baba ƙarami da Junaid da sauran mutanen wajan "Baiwar ke fa?" Cewar Aliyu kafin ta yi magana Umma ta ce "Na san wannan fuskar ƙawar wannan ƴar iskar ce" cikin sauri Mardiyya ta ce "Laa ni ban santa ba, ban taɓa ganinta ba sai yau" da wani irin mamaki ƙawar ta ce "Idan ba ki ce haka ba ai ba ki cika cikakkiyar munafuka ba, ke har ni za ki kalla ki cewa haka? To bari ki ji I'm not coming for this ga uban yarinyar da kika haifa can waje yana jiranki" gaban Mardiyya ya faɗi ƙirjinta na dukan saba'in saba'in ta ce "Ban gane ba" ta ce "Oh bari na yi yadda za ki gane" ta juya ta kalli Ustaz ta ce "Sanda Mardiyya ta aureka tana da wanda take so, kuma maganar aure ya shiga tsakaninsu ma, tunda ta je gidan Ridayya suka samu saɓani ta ɗauki alwashin sai ta aureka, bayan an yi auren ta cigaba da mu'amala da Yaƙub suna haɗuwa a hotel kala-kala har mu'amala ta gitta tsakani ta samu cikin, hankalinta ya tashi domin a lokacin ta ji ta fara sakon ka gashi kana ƙoƙarin zama Gwamna, tana ta neman hanyar da za ku yi tarayyar aure saboda ta ɗauki bidiyo ya zama evidence na cewa cikinka ne, domin bata taɓa kawowa ranta zata haihu baka kasance ta ba, domin tabbatar da abinda nake faɗa ka je waje ai za kaga Yaƙub ɗin" Ustaz ya kasa cewa komai jin abinda yake kamar a littafan Hausa ko dram na film, ya juya tare da barin wajan. Mardiyya ta durƙushe a wajan tana rusa kuka bata taɓa ladamar abinda ta aikata ba sai yau, gashi wani irin mugun son Ustaz take kamar rai ji take kamar ta haɗeye shi ta hutawa ranta. Zuwan Hajia kenan ta ce "Amma dai kin watsa mini ƙasa a idanu Mardiyya, na yi bake bake raina bai huta ba sai dana ga kin auri yaron nan ashe tsatsa tuni ta cinye zuciyarki, to maza maza haɗa kayanki ki ɗauki ku yi gaba zuciyata har nunfashi take wajan ganin na ci miki mutunci" Inna ta ce "Ni dai daman zaman wanka na zo tunda abin ya zama haka ya lalace sai dai na ce Allah ya baku haƙuri amma tabbas anci mutuncin aure an kuma taɓa martabar aure" Tana kaiwa nan ta ja jakarta ko inda Mardiyya take bata kalla domin zata iya ci mata mutunci naƙin ƙarewa. "Umma don Allah ki rufa mini asiri ka saka mijina ya mayar dani, wallahi na yi ladama ba zan kuma ba sharrin shaiɗan ne" Umma ta zare idanu ta ce "Wanne shaiɗan ɗin kuma? Ai kece shaiɗaniyyar kan ki wallahi kuma tsakanina dake Allah ya isa, ki yi gaggawar fito mini da takardar filin dana ba ki" ganin da gaske ta rabu da Ustaz rabuwa ta har abada ya saka Mardiyya miƙewa tana goge hawayen idanunta zuriyarta na yi mata wani irin zafi da ƙona ta ce "Ai fili na takwararki ne Hadiza, kamar yadda shaidu suka tabbatar tuni na siyar da shi na siya mata wata kadarar" "Kika siyar mini dame? Dukiyar tawa akan ƴar zina?" Mardiyya ta ce "Bafa nina ce ki bani ba, da hannunki kika ɗakko tare da mallakawa cikina shi, da saka hannunki da komai, idan ba ki yarda ba kina iya kaiwa koto" tana kaiwa nan ta ɗauki yarinyarta tana cewa "Ga Hadiza ga takwarar Hadiza" Umma ta dinga tsinewa Mardiyya albarka duk irin cin mutuncin da takewa Ridayya bata taɓa yin tari ba balle tai mata kallon banza, yau wacce ta zaɓa ta fifita ita ke kiran sunanta haka tsirara. Baba ƙarami ya dinga murmushi daman wannan ranar yake jira gashi lokaci ya yi yana danne dariyarsa ya ce "Sai haƙuri,surikar so kuma surikar gwal da kika fifita ce akan zaɓin da ƙaddara taiwa ɗanki ce fa? Mardiyya fa? Haba Umma a dinga sara ana duban bakin gatari" Umma ta sake fashewa da kuka ta ce "Daman ai kana sani ka sawa shegiyar yarinyar suna Hadiza,kuma wallahi bani Hadizan ba" Ridayya na can part ɗin Mami bata san meke faruwa ba sai da Zainura ta shiga take bata labarin komai, ita kam ko a jikinta haushin Ustaz ɗin ma take ji. A daren Ustaz ya saka Baffa a gaba akan ya yi haƙuri ya saka a saki Ammi haka nan tasha wahala da ƙyar ya shawo kan Baffa ya yi wa aka saki Ammi amma ya ce ba gidan shi ba, Junaid ya ɗauke ta zuwa gidan daya siya mata daman ya san zai wahala Baffa ya yafewa Ammi ta sauƙi. Ta dinga kuka tana bawa Junaid haƙuri da sauran yaran banda Yaya Zuhura ko wajanta ma bata je ba, domin ta ce ita ta sake uwa. Prof na durƙushe gaban Hajja Azizat idanunsa sun ɗauka tare da yin jajur saboda damuwa da tashin hankali, abubuwa sun masa yawa ga matsalar takara daya samu domin tuni an sauke shi an bawa wani, ga matsalar Talatu ƙarin kunama data ke shirin tattare arziƙinsa saboda barazanar da take masa akan bidiyon data ɗauka duk ya fita hayyacinsa, ya yi gurfane kamar mai neman ɗauki ya ce "Me ya sa kika kasance mai taurin kai ne? Mara yafiya da duba baya?" "Baya? Wanne bayan zan duba kenan Prof?" Hajja Azizat ta furta cikin yanayin mamaki dake cin zuriyarta lokaci guda kuma ta juya tare da zuba masa idanunta masu kaifi ya ce "Ki tuna ni ɗin mijinki ne zuri'a ta shiga tsakaninmu, karki duba kuskure na ki yafe mini ki dawo gidanki ƙarshen igiyar aurenki" ta cije baki tana girgiza ƙafarta ta kasa furta komai saboda yadda zuciyarta ke mata zafi, bata taɓa dana sanin auren Prof ba sai yanzu, ba shine irin mijin daya dace da ita ba, rabon Sadauki daya rantse shine ya ƙaddara auren nasu Sadauki ya rasu he is no more don haka dole auren ma ya rasu. Ya miƙa hannu zai kamo ƙafarta ta yi saurin zamewa ya ce "Ki tausaya mini sharrin shaiɗan ne, wallahi ina matuƙar son ki da gaske i don't know what come over me nake aikata zunubin da bai dace ba, i love you i so much love you Azizat" Mother ta yi murmushi tana miƙewa tsaye ta ce "You know what Prof? Fita a parlon nan kafin zuciya ta ɗauke na faɗa maka abinda har ka mutu baka mance ba" ya miƙe tsaye idanunsa sun ƙara jirkicewa ya ce "Don girman Allah ki tausaya mini Azizat do you know how much I love you, kin san yadda nake son ki kowa? Me ya sa ba zaki yadda da ƙaddara ba? Eh?" Rai ɓace ta juya zata shige cikin gidan daman a parlon farko suke ya yi saurin kai hannu ya jawota, kafin ya zame hannunsa ta ɗaga hannu tare da sauke masa wani gigitaccen mari a kunci da yatsa ta ce "Kul! Ko da wasa don't even try to do, jikina ba irin na karyan matan da kake mu'amala da su bane Prof, a tsarkake nake kuma na gode da tsayin shekarun daka dinga tauye haƙƙina ashe hakan alheri ne a gare ni, wallahi tallahi na yi ladamar aurenka na ji inama ban taɓa aure ba" ta share hawayen idanunta don kar rauninta ya danne zafin zuciyar da take ciki ta ce "Me kake tunani dukiya shine aure da jin daɗi da kwanciyar hankali? An faɗa maka dukiya na kewa, ana yin aure ne domin raya sunnar ma'aiki, tare da tattali da soyayya da kulawa, haɗe da kare mutuncin juna da martabar aure, ban yi zaton soyayyar da kake nuna mini iya ta waje bace, baka san ka zauna da matarka ku yi hira ba, baka san ka sauke haƙƙina da ke kan ka ba, baka son ka zauna a gida cikin iyalanka, kai maƙaryaci ne you're a liar, cheater, hypocrite, adulterer, you're nothing but my destiny, you kill your own child saboda rashin kulawa da tsoran Allah irin naka" Prof ya dafe kunci ya ce "Ni kika mara Azizat? Ni kike zargi da kashe ɗana Sadauki?" Murmushi ta yi tears running down on her face tana girgiza kai she couldn't feel yadda take jin zuriyarta a lokacin. "Zan iya yi maka abinda ya fi haka, wallahi na tsaneka kuma ka gaggauta rubuta mini sakina ba zan taɓa iya cigaba da zama da kai ba, daman can kasancewar mu tare zanen ƙaddara ne kuma yanzu ta sake rabawa" shi kansa Prof a sama yake jin maganganun nata, bai zacci girman son da ya kewa Azizat ya kai har haka ba sai yanzu da ƙaddara ke barazanar raba shi da ita, sakaci da son zuciyarsa sun takawa rawa wajan yin fatali da muradan zuciyarsa dana iyalansa ya duƙa saman ƙafafuwansa ya ce "Let by gone be by gone Hajja Azizat, wallahi ba zan ƙara bari mummunan zuciyata ta kwaɗaita mini wata sura ba face take, ki yafe mini na bi Allah na biki please ki yi komai zan ɗauka banda rabuwa da ke" kasa ce masa komai ta yi sai ta juya ya yi kamar zai bita ciki tana zuwa ƙofa ta ce "Mu haɗu a koto" Prof ya jingina da jikin bango yana dafe kansa ya bita da kallo har fa shige ciki. Tana shiga ɗaki ta ji kanta na sara mata ƙirjinta ya yi mata nauyi mutuwar Sadauki ya dawo mata sabuwa ta dinga kuka kamar ranta zai fita har bacci ya ɗauke ta. Kwanaki biyar da dawowarsu Nigeria Ridayya ta shirya zata asibiti a ƙara duba jikinta tana sanye cikin ash ɗin Abaya ta yi rolling kanta sosai ta yi kyau ta ƙara cika da buɗewa, hankalinta ya kwanta ga kulawar da take samu a wajan Mami da Yaya Zuhura da Anty Kaltum, domin sosai Anty Kaltum ta tura Maiduguri aka amso mata tsumin mai jego hakan ya saka Abbiey daƙulewa ya rasa abinda ke yi masa daɗi, har baya so Ridayya ta ƙarasu kusa da shi sosai yake gigicewa, gashi baya da sukuni a gidan yana ta sauri su koma gidansu domin an kammala komai na hadaɗɗan gidan. Dawowarsa kenan daga duba babban boutique ɗin da yake haɗawa da Sunan Ridayya, business yake sosai kuma Ubangiji ya saka masa albarka dukda cewa Fidelity bank suna ta masa requesting ya dawo amma ya nuna bai son aikin bankin yanzu. A hankali ya juya tare nutsa ganinsa a kanta ta yi masa murmushi shi kuma ya kame fuska sai kallon ta yake har ta ƙarasu kusa da shi ta zauna tana sake kyakkyawan murmushi a hankali ta saka hannu ta shafo gemunsa ta ce. "Barka da hutawa Abbiey" Ya ɗauke kai yana mayar da idanunsa saman laptop ganin hakan ya saka ta marairaice fuska ta ce "Me na yi kuma?" Still ya yi mata shiru wayarsa ce ta fara ringing suka kalli wayar lokaci guda sunan Muwahib ya fito, Ridayya tai shiru tana tunanin ina ta san sunan?. Ustaz ya gyara zama yana matsar da laptop ɗin tare da ɗaukan kiran a taushashe ya ce. "Kina lafiya Wahib?" Ya faɗa bayan amsa sallama ɗin, Ridayya gabanta ya faɗi who is Muwahib? Da har Abbiey ya bata dukkan attention ɗinsa haka? Bata san me take ce masa ba sai gani ta yi ya miƙe yana ɗan jan gemunsa ya ce. "Ohh, i will come" Ya kashe kiran kana ya kalli Ridayya da kanta ke ƙasa ta yi nisa cikin tunani sai ganin shi ta yi ya duƙa gabanta tare da tallafo fuskarta a tafin hannunsa taƙi yarda ta kalle shi ya kai baki ya sumbaci lips ɗinta ta yi saurin janye fuskarta "Ina za ki?" "Asibiti" Ya haɗe girar sama data ƙasa yana sake matsar da fuskarsa dab da nata tare da sauke mata nunfashi ƙamshin bakinsa na shigar mata hanci a hankali ya ce "Wa kika tambaya" Muryarta na rawa ta ce "I toot i told you" "Ko?" Ta yi sauri ta miƙe ta ce "To na fasa, ka je kiran Wahib ɗin" Ta juya zuwa bakin ƙofa ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofar zata fita hawaye tuni ya fara cika idanunta tana gani dishi-dishi saboda tsabar kishin daya mamaye idanunta tana tsaye ta ji ya zuro hannunsa ta baya ya saƙale ƙugunta tare da haɗe shi a nasa, ya rungume ta ta baya ya ɗan ranƙwafa ya ɗora kansa a kafaɗarta ya ƙi cewa komai sai kawai ta fashe da kuka tana doke hannunsa, ya sake matseta a ƙirjinsa da kyau, he just trying to explain to her, wace Wahib and who is she to him, taƙi yarda ta ji sai kuka take ai kowa ya nuna mata da wayo, ya kinkimeta gabaɗaya ai kowa da sauri ta riƙe shi ta ce "A'a don Please" Ya matse ta jikin bango ya ce "Ok listen" ta ce "Oh oh ok" Ya ƙura mata she just love her, yana tsananin son matarsa bawai tsoron ta yake ji ba ko shakkata ba, baya son damuwa da ɓacin ranta musamman abinda ya san shine da laifi, haka yanzu bai ma san dalilin daya saka zai yi mata explanation ba. "She is my ex" A gigice Ridayya ke kallon shi jin abinda ya ce, ya ɗage mata gira idanunta ya sake cika da haway yana shafa mata fuskarsa ya ce. "Ina son aurenta ne beb" kallonsa kawai take babu ko ƙiftawa ƙirjinta na ɗagawa kamar mai Asthma cikin sauri ya ce "Kee wasa nake miki, ɗalibata ce ta ma yi aure mijinta ne ba lafiya take neman taimako" "Ka aure ta mana" Ta faɗa zata shige ya ƙara damƙo ƙugunta ya haɗa da nasa idanunsa ya sauya "Da gaske nake miki Allah" nan da nan ta fashe da kuka kamar ranta zai fita tana yarfe hannu "To ka aureta mana ai ban hanaka ba ban isa kuma na ce a'a, daman na san ba sona kake ba, u just manage kawai daman ban cancanci ka aure ni ba, ƙaddarar su Al'hussan ya saka ka taimake ni ne kawai kamar yadda ake cewa ni dai na son ina son ka amma don baka so ni ba wani abu bane it's all my fault" Ba iya jijiyoyin kansa ba, hatta gargasar jikinsa ta gama miƙewa gabaɗaya ya jima tashin hankalinsa bai bayyana ba ƙarara irin yanzu ba, so daman auren under age haka yake? Mutum da girmansa da gemunsa da shekarunsa ƙaramar yarinya like Ridayya ta yi ƙoƙarin sukurkuta masa tunani da lissafi domin tashin hankalin daya shiga ya ninka nata. Ya dafe kansa kana ya kamo hannunta har zuwa bakin gado ya zaunar da ita saman cinyarsa ya riƙo tafin hannunta ya sarƙe da nasa ya kasa cewa komai ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana shassheƙar kuka wanda duk na ƙarya ne kukan banza ne kawai, ya sauke numfashi. "Ustaza" "Abbiey" Ya juyo da fuskarta ya ɗora goshinsa a kan nata ya ce "I am sorry ok?" Ta jinjina masa kai ya haɗe rai ya ce "Talk" "Na bar Al'hussan zazzaɓi yake" "Ok ki shirya I'll drop you off beb" ta jinjina kai tana miƙewa ya miƙe shima ya rungume ta. "I love you beb" "Thank you" Ya ware idanu "Are you still angry with me? Ni me zan yi da mace bayan ke? Kin isheni kin kuma wadata ni da komai, soyayya, biyayya anything Mimi ai ba wata bayan ke no one but you Mintyna" "Uhm'uhm" ta ce cikin shagwaɓa tana turo baki wanda ya sha lipstick. Ya girgiza kai "Allah ya yafe miki Mimi" "Amin" "I love you " Kutunsa ta sumbata ta ce "I adore you" Ita ta yi driving nasu zuwa asibiti ya ce sam ya gaji, yana riƙe da Sadauki Zainura na baya ita da little da Al'hussan a hannunta Al'hassan sai bacci yake a cikin wani ɗan ƙaramin gado. Bayan sun ga likita suna ƙoƙarin fitowa daga emergency Ridayya ta ji ana "Me haƙuri me haƙuri" da wani irin murmushi ta juya domin ba zata taɓa mance muryar ba, Abbiey na jingine da mota yana kallon su "Wa zan gani kamar Zainaba?" "Ni ce nan mai ƴartsala ikon Allah rai kan ga rai" Ridayya ta yi murmushi suka gaisa cikin farinciki ta ce "Ina mijin naki, wai da gaske kece haka mai ƴartsala?" Ridayya ta yi mata pointing ɗin Abbiey ta ce "Ga mijin nawa can da yarana" Da sauri Abbiey ya ɗauke kansa kamar bai gansu ba, Zainaba ta zare idanu ta ce "Lillahi wadihul ƙahhar Allah alhakamu, wancan ba shine kikaiwa iskanci kala-kala ba? Ina Zameer ɗin?" Ridayya ta haɗe rai ta ce "Kin jiki da wani zance?" Zainaba ta yi ƙasa da murya ta ce "To kin bashi labarin abinda ya faru da jami'a kafin aurenku da tsinannen nan?" Ta girgiza kai ta ce "A'a, ina so ya san komai amma" Zainaba ta zare idanu ta ce "A'a sam kar ki soma, idan Allah ya rufa maka asiri sai kace zaka tunawa kanka? Wallahi ki gode Allah Ubangiji ke son ki da Rahama tunda har ya rufa miki asiri ki yi shiru da bankin, ai idan Allah bai so kunyataka a idanun duniya ba babu wanda ya isa ya yi haka, Allah ya duba zuciyarki ribatarki akai bada sunan iskanci kika je ba" Ridayya ta yi murmushi ta ce "Ga numberta idan na tare a gidana sai ki zo" "Ai kowa in sha Allah za ki ganni faka-faka" "Mai sona" Da sauri ta juya ganinsa a wannan halin ya saka Ridayya waro idanu ƙirjinta na bugawa, kafin Zainaba ta yi magana ya zube ƙasan qiwwarsa ya ce "Don Allah ki ji tausayina ki yafe mini Mai sona, karki bari na zauce a tunaninki a zuciyata ki tausaya mini" Moo ya ƙarasu wajan ya ce "Wai Zameer mene haka? Ba zaka ɗauki ƙaddara bane kai? Aurenta zata kashe ta dawo wajanka?" "Ba wani aure da ta yi kawai an faɗa ne domin a rabani da ita, a hukunta ni akan kuskure da wawta tare da son zuciyar dana tafka" Zainaba ta taɓe baki ta ce "Jama'a yau ga Zameer a lalace? Ina ita shegiyar yarinyar Khairy take kowa?" Moo ya ce "Ai ita muka zo dubawa, ta yi hatsari ne ga matsala data samu har an cire mata mahaifa ba zata kuma haihuwa ba, shine ta buƙaci ganin Zameer ya yafe mata kan sharrin da ta yi masa na kawowa masa yarinya bayan ta san ba shine ubanta ba, ta buƙaci ya bata yarinyar shi kuma ya ce ba zai bayar ba ya dai yafe mata, kema ta roƙi daki yafe mata" "Ina ruwana da ita? Allah ya yafe mana bakiɗaya" "Ridayya don girman Allah ki dawo gare ni wallahi mutuwa zan yi" daidai nan Ustaz ya ƙarasu wajan hannunsa ɗauke da little Bilal, yana zuwa Zameer ya yi saurin buɗe idanu yadda kasan photocopy akai na Ustaz a fuskar little kamar ya yi kaki ya tofar, Zainura ta ƙarasu wajan hannunta ɗauke da Sadauki da Al'hussan. Zainaba ta gai da Abbiey ya jinjina kai ya kama hannun Ridayya suka bar wajan "Daman taya kake tunanin zata dawo wajanka kamar ita ta zalunce ka? Ai kai da ita sai dan irin wannan ganin daga nesa yasin" Zainura ta ce "Wallahi, wannan yaran nata ne ƴan'uku ta haifar jajur" tana faɗin hakan ta bar wajan itama. Hawaye ya shiga sakkowa a fuskar Zameer Hanne bata ganin girmansa ga yaransa sai addu'a musamman macen, ga babu aiki sai zuwa gona abokai duk sun guje shi Moo kawai ya rage da ace Ridayya na gefensa da komai mai sauƙi ne a gare shi, zaman Kano ya fi ƙarfinsa Ridayya ta fi ƙarfinsa a yanzu duniya ta tabbatar shi ne ya zalunce ta tunda Ubangiji ya yi mata sauyi a rayuwa. Wata biyar bayan dawowarsu suka koma hadaɗɗan gidan Ustaz, Umma sosai take ƙaunar Ridayya da yaran da sukai ƙima sosai da wayo aka haɗa Auren Junaid da wata yarinya Iklas sai Zainura da Burhan akai aure lokaci guda, tsakanin Mami da Ammi mutunci ne kawai Tajj ya samu ya yi aure shima da ƙyar Prof ya bawa Hajja Azizat takardar saki. Misalin ƙarfe tara na dare ta shigo parlon tana sabga ƙamshi uban ƙamshi kanta a ƙasa ta ɗora mayafi saman ɗaurin ɗan kwalin da ta yi na black and gloden ɗin lace sai walƙiya yake a hankali take ta kawowa har ta zo tsakiyar parlon, tunda ta shigo yake kallon ta da wani expression looking da emotions na shekarun baya da suka shege sai yanzu da suke motsa masa a ƙirji da zuciya ashe ba mutuwa sukai ba kawai dole ta saka suka kwanta. Ya ɗan yi tattausan murmushi irin na manya ya ƙarasa tare da buɗe mayafin kanta ta yi saurin yin ƙasa da kai tana murmushi, bata san cewa dattijon zamani bane sai da ta ji ya rungomo ta zuwa jikinsa ya ce "Allah Allahamdulilah daka mallaka mini Azizatuna..... Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcyluv 08164069385 *MUNAFUKIN MIJI* Nimcyluv 49-50 Mikiya writers Association. "Abba" ta furta cike da kunya shi kuma ya riƙe ta da tafukan hannayensa, dukda cewa ita ta yi requested auren a wajan shi, amma ji yake kamar ta shiga zuciyarsa, dukkan wasu ƙofofi na zuciyarsa a buɗe suke ƙara raya kan su suke da farfaɗo abinda ya kusa macewa a tsakiyar ƙirjinsa. Hajja Azizat ta ce "Congratulations" Baba ƙarami ya saki hannunta baya ya yi mata runguma ƴar sunna ya koma ya zauna a hankali ya ce "Allahamdulilah" ta nemi waje ta zauna ta ɗan buɗe mayafin kanta sukai shiru can baba ƙarami ya ce "When last rabon dana ganki haka kusa dani Azizat?" "Tun ranar ɗaurin aure na" ta furta cikin ƙasa da murya ya jinjina kai kamar yadda Abbiey yake idan yana son kawar da zancen addu'a ya yi sosai mai tsayi kana ya shafa ya ce. "Allah ya bamu zama lafiya" "Amin" "Am still on your mind kenan? Wanne qualities kika gani wajan tsoho mai tarin jikoki har kikai sha'awar aurena?" Ta yi masa wani irin kallo kafin ta ce "Tun qualities ɗin dana gani a baya na nace maka, shi ne dai" "And you left me, har yanzu ban san dalili ba" Ta ce "Destiny! Ƙaddara mana ita ce dalilin Abba ta raba mu and now we are together, za mu kasance har abada" Ya yi murmushi yana shafa gemunsa ya ce "In sha Allah" sai ya kalleta sosai ita dai still da garin ƙuruciyarta daman ba wani jikin kirki gare ta, a goge fatarta take ƴar daidai da ita. "Tahir ɗin da kika sani a baya yanzu fa bashi bane Azizat, ina da yaro mai shekaru wajan 40 gani da jikokai, anya zan iya sauke nauyin ki kowa? Ba ki yi kuskuren zaɓe na a karo na biyu ba?" Idanunta a kansa ta ce "I'll never regret in sha Allah Abba,in dai kana so na ai komai mai sauƙi ne" bai ce komai ba ya ɗauki wayarsa ya duba, daman tun kiran farko da ta yi masa ya san kwanan zancen yaƙi zuwa wajanta ne sai da ta gama idda, tana gamawa kuma ta masa text via mail kai tsaye, bai tashi zuwa wajanta ba sai da ya tabbatar igiyar aurensa ta hau kanta, bayan shaidu sun shaida. Ya miƙe tsaye ya ce "Zan shige ni" ta ce "Tun yanzu ango?" "Kina da wajan ajjiye ni ne?" "Sosai ma" ya girgiza kai ya ce "Kina buƙatar wani abu ne?" "Babu sai abu ɗaya" har zai tafi ya ce "Me?" "Bari kaga" ya tsaya ta ƙarasu wajan kafin ya ankare ta rungume shi tare da yi masa kiss a kumatu, ya hangame baki ya zama kamar statue ya ji kamar wani ke jan shi, ta yi masa bye bye yana dai tsaye bayan ya tabbatar ba wanda ya ga wannan abin kunyar ya sauke numfashi ya fice. Fitowa Abbiey ya yi bayan sun kammala magana da Ridayya ya nufo hadaɗɗan main da yake tsakiya yana gaba tana biye da shi hannunta riƙe da hula, ta dube shi ta ce. "To Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri" a nutse ya ce "Amin, shi ne ma tunda bana jin siyasar a raina" "Haka ne, kawo na saka maka hular" Ya rausayar da kansa gefe yana kallon yadda take ɗage amma ta kasa ta bashi hular kuma taƙi shi kuma yaƙi sunkuyo da kansa ƙasa "Abbiey please ka miƙo kan" yaƙi cewa komai sai kallon ta kawai da yake da wani irin yanayi mai fisgar zuciyar duk wata budurwa. Ta ɓata rai sai kawai ya saka hannunsa biyu ya ɗago ƙugunta sama "Saka" tana dariya ta saka masa hular tare da tattare gashin ta tura cikin hular. "Ka yi kyau sosai kamar karka fita ko'ina" ya lumshe idanunsa ya buɗe "Me zan taho miki dashi?" "A'a ba komai" Ya haɗe hannuwanta biyu ya riƙe "Allah ya yafe kiki Mimi, hakan kyautatawa iyali ne kuma koyarwar Annabin tsira ne, kawowa iyali tsaraba muddin akwai halin hakan" "To ka siyo mini vanilla ice cream" "Banda kayan sanyi" tai shiru tana tunani sosai sai kuma ta ce "Ok Gashasshen nama mai zafi da kuma L&Z" "An gama beb" "Thank you" ya rungume irin side hug ɗin nan ya ce "I love you" Ta ja gemunsa da yake mata kyau kullum ta ce "You mean the world to me Hayatee" ya ƙara 10 minutes akan yadda tsara zai fita ɗin. Umma dake sauraron baba ƙarami ba tare data fahimci me yake cewa ba ta ce "Aure kamar wasan yara kai ne ka yi auren ko dai wani?" Ya kame girka ya ce "Ni ke wasan kenan Hadiza?" Ta ce "A'a, abu ne na ji shi gaba-gaɗi" a hankali ya ce "To da gaske aure na yi wallahi Allah, kuma yau za a kawo amaryar kuma ƴar'uwarki" "Aure dai irin wanda iyayenmu sukai mana kake magana Tahir?" A fili ya maimaita “Tahir” sai kuma ya yi murmushi ya ce "Shi dai, ai ni mijin mace huɗu ne kuma ban taɓa miki alƙawarin zama dake ke ɗaya ba, ban kuma yi auren don na ƙuntata miki ba, ban yi kuma don bana son ki ba Umma Ubangiji ya ƙaddara auren ya kasance kuma ya kasance ɗin, ki bani ƙarfin qwwa please na shaideki a bayan idanunki kan cewa ba ki da wata matsala, tunda nake dake shekaru nawa ban taɓa bijiro miki da maganar aure ba, na aure ki don ina son ki kuma zan cigaba da son ki don Allah ki cire komai a zuciyarki ku zauna lafiya ita sam bata da matsala" Ta wani kalle shi tana murmushi ta ce "Waka aura? Ina nufin wace kishiyar tawa?" "Hajja Azizat, mahaifiyar murgayi Sadauki" Da wani irin firgitaccen yanayi mai ban tsoro da kuma tashin hankali, daya saka Umma miƙewa tsaye ba tare data shirya hakan ba, baki sake kawai take kallo Baba ƙarami kafin ta haɗiye wani irin yawu mai ɗaci ta ce "Now i understand, cewa za ka yi tsohuwar budurwarka ka aura domin ka nuna mini iyaka ta na cewa a rashin ta ka aure ni Tahir" ya dinga kallon ta ya ce "Amma tsakanin ki da Allah tunda muke kin taɓa ji na yi maganar ta?" "To bayan ta yi aure ta ya ka aure ta?" "She has been divorced" ya ce yana kame fuska. Umma ta rushe da kuka sosai ta ce "Mayya ai na sani wallahi tana sane ta kashe auren domin ta aure ka, kawai zan tattara na bar muku gidan domin sai abinda na gani kawai" Baba ƙarami ya yi murmushi ya nufi inda take yana cewa "Zo ki ji" 6 month later Kuka take sosai tana gogen hawayen da yaƙi tsaya mata shi kuma yana gefe yana ta yi mata dariya abinsa, ta juya ta kalli Al'hussan dake bacci gabaɗaya watan su shida, ta kalli takardar hannunta daya tabbatar tana ciki ta dube shi ta ce "Abbiey don Allah ka rufa mini asiri, na shiga uku wanne irin ciki kuma? Ni a haihuwa zan ƙare kenan" ya ajjiye wayar hannunsa cikin kulawa ya ce "Ba kowa Allah ke wa wannan ni'imar ba Mimi, ki yi farinciki this time around za ki haifa mini me kama da ke" cikin damuwa ta ce "Ai ba za kaga aibu ba, sai da na ce kar ka yi kar ka yi amma ka yi, gabaɗaya watan su Al'hassan shida ya kake tunanin za su lalace? Da wanne ido zan je gida a ganni da ciki?" "But ba iskanci kikai ba mijinki ne ya miki shi Mimi" ya faɗa a taushashe kawai ta sake rushewa da kuka, shi abin duk mamaki yake bashi mene a cikin yin kwanika to? Girgiza kai ta yi ta ce "Zan zubar da cikin nan gaskiya ka yi haƙuri" tana faɗa tana miƙe zata bar bedroom ɗin, daman dawowarsu kenan daga asibiti saboda zazzaɓin da take hannu ya saka ya fisgota yana wani irin nishi idanunsa sukai jajir ya ce "za ki zubar da me?" "Cikin" ta faɗa ba tsoro. Ya matse hannunta ya yi wani irin murmushi ya ce "Wannan shi ne abinda za ki yi har abada naƙi yafe miki" "Wallahi sai na zubar yarana watan su shida kawai sai a ganni da ciki? A saboda ba kai kake shiga cikin jama'a ba? Gashi ina tunanin ƙarasa karatuna" yadda take ɗaga masa murya ya fi komai bashi mamaki ya sake ta ya ce "Ridayya kenan, muddin ni na yi cikin nan wallahi tallahi kika zubar anan za ki san waye kike aure a nan za ki ɗaya fuskar tawa, ba maganar saki a tattare dani amma abinda zan miki sai kin gwammace kiɗa da karatu ni Muhammad Bilal Tahir zan ba ki mamaki" ya sauke numfashi yana jin kansa na sara masa ya ce "Idan kuma ke kikaiwa kanki cikin fine kina iya yin abinda kika ga dama" sosai suke cacar baki abinda basu taɓa yi ba, basu yi aune ba su kaga Little ya shigo cikin sauri Abbiey ya koma bayan Ridayya yana saita yanayinsa kana ya ɗan jawota jikinsa, Ridayya ta ɗan dake tana murmushi ta ce "Jarumi na ya akai? Shigowa ba sallama ba neman permission bana hana ba?" Little dai kallon su yake ya san dai ya yi sallama har babu adadi ya ce "Kuna ta faɗa Mimi da Abbiey" "Faɗa kuma?" Ya ɗaga kai ya ce "Kuna ɗaga murya kinawa Abbiey haka" ya miƙar da yatsar shi yana pointing wani waje, Ridayya ta yi murmushi ta juya ta kalli Abbiey ta ce "Abbiey ka ji wai faɗa muke?" Ustaz dai ya yi shiru don bai iya ƙarya ba idan muddin ya buɗe baki to e zai ce. Ta kalli little ta ce "Wani abu muke nunawa na Film, scane ɗin ya mini kyau na ce mu yi rihazal da Abbiey amma ba za mu kuma ba" cike da gamsuwa ya ɗaga kai ya ce "To malam ya ce idan an yi faɗa za a sasanta musabawa ake" ya kamo hannun Abbiey ya kamo na Ridayya ya haɗe, Abbiey ya damƙe hannunta dake cikin nasa yana shafawa ya zuba mata idanu, ya fahimci dole ya shiryawa wannan cikin domin ta tsiwa ya zo idan tana al'ada ta yi ƙunci taƙi magana yanzu kuma ciki ya zo mata da rigima dole ya tausasa zuciyarsa ya fahimtar da ita da kyau ya kuma iya controlling kansa ya ja numfashi ya sauke yana sake riƙe hannunta little ya ce "To ku gaisa" "Assalamu Alaika Abbiey" shi dai kallon ta yaƙe yaƙi cewa komai ganin yadda little Bilal ya kafe shi da idanu ya saka shi cewa "Sannu Mimi" little ya dinga tsalle yaro ne mai shegen wayo da surutu ya ce "Second Mimi ta zo da wata" Ridayya ta ce "Ka cire second ɗin Just say Mimi, idan da amana kuma duniya da gaskiya ai wajan Zainura zaka zauna" ya maƙale kafaɗa ta ce "And this is the last time da zaka shigo bedroom ɗina da Abbiey ba a baka permission ba, a good person never do this ok?" Ya ɗaga mata kai Ustaz dai kallon su yake, little ya fara ƙoƙarin shigewa jikinta ta ce "A'a wallahi muje" sai da ta je bakin ƙofa bayan little ya fita ta juya ta kalli Ustaz ta ce "Kuma da kake maganar saki an faɗa maka ko ka sake ni zan tafi ne? Rayuwa da kai yanzu na fara saboda ina son ka" girgiza kawai ya yi a zuciyarsa yana "Allah ya yafe miki Ustaza" wato idan baka da mace ƴar drama ma da sauran ka, ko babu komai za a saka bakinka ya motsa da surutu. A zaune ta samu Zainura da Zainab suka gaisa sosai nan da nan ta dafa musu taliya fara da mai da haɗin salad domin bata iya dafa komai. Ta kalli Zainura ta ce "Amarya bata lefi" Zainura ta ce "Sallama na zo miki zamu shige Lagos" "Lagos ke da wa?" "Da mijina mana yaya" Ridayya ta ce "Ikon Allah, to Allah ya tsare ya kai ku lafiya sai na tuna zuwana Lagos sai ki dage da sana'a garin neman kuɗi ne ba mugunta, ki fara business nima za kina turo mini da kaya" har compound ta raka Zainura sai a lokacin ta lura da Burhan tace "Kake ta zauna a mota? Ban san tare kuke ba" "No ba komai yaya" "To Allah ya tsare ya kiyaye" suna tsaye Ustaz dake balcony yana waya ya ƙarasu suka gaisa da Burhan kana ya musu fatan alheri ya yi Zainura faɗa sosai. A haka suka fice daga gidan "Baby lafiya naga ka ɓata rai?" "Kin bar marayan Allah a waje shi ɗaya haba sweet" ta juya idanu tana shafo fuskarsa ta ce "A yi haƙuri mazaje ba za a kuma ba" ya juya ya kalleta ya ce "Zinu....." Sosai Zainaba ta yi wa Ridayya faɗa na wawtar da take shirin aikatawa ta bata shawarwari masu kyau, da Zainaba zata tafi Ridayya ta haɗa mata goma ta arziƙi kayan abinci da kayan miya suna nama da kuɗi dubu hamsin ta saka drive ya kaita gida. That's how life is.... Har gidan Ridayya Ammi ta je ta bata haƙuri Ridayya ta ce ba komai ƙaddara ce, ta nuna har zuciyarta komai ya shige. Umma ta yi ƙunci sosai kafin ta sakko Hajja Azizat ta nunawa baba ƙarami soyayya irin wacce ta yi masa tanadi tun suna samari, ya kuma sha mamaki ainun har wani fresh ya yi ya ajjiye tumbi ta ce Abba ya ce Zauja kullum kuma sai ta gai da Ammi bata da matsala hankalinta ya kwanta bata taɓa sanin haka zama yake daɗi idan ka samu caring husband ta ji ita kamar bata taɓa soyayya ba, bata san mene auren ba ta fara business sosai bai kuma hanata ba. Mami hankalinta kwance ita da mijinta Baffa sai junior babu abinda ta nema ta rasa a rayuwa, sosai take kula da su Aliyu Yaya Zuhura tana nan tana zuba zawarci abinta Balkisa ta samu suka daidaita da mijinta. Junaid ma lafiya suke zaune da Iklas hankali ya kwanta kowa ya amshi ƙaddara da Ubangiji ya jingina masa da rayuwa. Ridayya ta haƙura ta fara rainon ciki Mami kuma ta amsu yaran gabaɗaya abin mamaki kuma basu wani lalace ba girma suke sosai, a haka ta ce zata koma makaranta Abbiey ya ce ta bari ta haihuwa sun kusa komawa Japan ai ya mata settling komai a can ta yi masa godiya, sosai arziƙinsa yake ƙara yawa business yake sosai na motoci da da gidaje ya gina ya siyar ya buɗe babban shago a kantin kwari ya saka hannun jari ta ko'ina abubuwa sai addu'a da godiya ga Ubangiji a yadda ya ce Ridayya ce ƙashin arziƙinsa tunda ya same ta komai yake buɗe masa. Basu da matsala sai irin na samun saɓani da ko wanne ma'aurata suke samu a zamantakewa. Mardiyya ta auri Yaƙub babban gidana wajan sama da mutane ashirin tukunya ɗaya ake ɗorawa sosai ta rame ta zabge ta shiga damuwa amma bata da wata mafita data shige zaman gidan mijinta. Prof komai ya ƙare a wajan Talatu ƙarin kunama ya zama bashi da komai komai ya lalace masa da ƙyar ya samu mace ya aura itama ƴar kanta yana fita take sakawa takalminta igiya ba ita zata dawo ba sai dare, tana dawowa ba maganar abinci za ta yi kwanciyarta idan ya tashe ta kan haƙƙinsa ta ce "wallahi kai kamar bunsuru haka kake, ba zan iya jaraba ba bacci nake ji" tana faɗin hakan take kwanciya abinta. Bayan shekaru goma sha biyar. Sosai Hanne ke kuka Zameer na tsaye a gefe ga tarin jama'ar da suka taro domin shaida auren ƴar wajan Zameer ɗin da Hanne ta haifa masa,bayan jama'a sun taro saurayin ya ce ya fasa auren a gaban bainar nasi koda aka buƙaci dalili ba kunya ya ce "Aje a tambaye ta" yana faɗin hakan ya ce a bashi sadakinsa aka bashi tun a lokacin ya bar garin gabaɗaya, a gida aka tsare yarinyar akan ta faɗi dalili ta fashe da kuka ta ce "Wai saboda likita ya ce masa ina da ciki" "Ciki?" Hanne ta faɗa tana dafe ƙirji yarinyar ta ɗaga kai ta ce "E, kuma ai shi ne ya yi mini cikin ko kwanaki da aka nemi aka rasa ai ina shagonsa a can na kwana, kullum sai mun yi" Hanne "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun! Hakƙin Ridayya ke bibiyar rayuwar ƴata a dalilin zunubin daka aikata" kuka Hanne take kamar ranta zai fita ko Ridayya ƙaddara ce ta hau kanta da kuma sharrin MUNAFUKIN MIJI Zameer, kuma ba ta yi ciki ba amma gashi saboda an ce alhakii ɗan aike ne kan me shi yake bi ga abinda zunubinka ya ja nan, Allah ya isa wallahi ni dai na yi iya abinda zan iya da wanne ido zamu kalli jama'a? Ranar ɗaurin auren ƴarmu a gaban kowa miji ya ce ya fasa kuma ya ɗauke ƙafa ya gudu yanzu za mu yi da wannan cikin?" Gani sukai Zameer ya sulale tare da faɗuwa ƙasa babu numfashi, daidai nan Ƙaramin Alhaji ya shigo gidan wato Muhammad Bilal Zameer. wanda tuni an nuna masa cewa Zameer ne mahaifinsa tun bai yarda ba ya kuma yarda, Abbiey ya yi masa faɗa da nisiha sosai akan muhimmacin yarda da ƙaddara da yiwa iyaye biyayya hakan ya sa lokacin zuwa lokacin yake zuwa Katsina, kasancewar Alhaji ƙarami yana da garin jiki da shi da sadauki halinsu ɗaya kodayaushe fuska a kame ba walwala, idan ka ganshi zaka ɗakka wani babban mutum ne baya ɗaukan wargi hakan ya saka ƙannen shi suke shakkar shi, magana ɗaya yake baya biyu. Ya ɗaga labulan ɗakin yana daga bakin ƙofa ya dinga kallon yarinyar da kuma mahaifin nasu dake kwance ga Hanne dake kuka hannunsa ɗaya zube cikin aljihu ya ce "Ya akai?" Nan take Hanne ta yi masa bayanin komai sai kawai ya saki labulan ya fita, ba jimawa ya dawo da bulalar darbejiya ya rufe ta da duka ya yi mata jahilin duka tas kana ya yar da bulalar ya ɗauki Giɗaɗo dake cikin kwance daman yunwa dukta cinye shi, ya nufi mota da shi yana zuwa ya samu abokinsa wanda tare daman suka zo ya buɗe motar suka saka shi a ciki, Muwab ya koma ɗaya gefen YAA B ya ja motar da wani irin sauri yabar unguwar. Bayan sun sauka Kano ya kai shi asibitin Aminu Kano teaching hospital, aka kammala komai tare da kwantar da shi ya nufo gida Muwab ya tafi gida shima. A main parlour ya samu Sadauki zaune shi ɗaya har ya yi sallama Sadauki bai ji ba, ya lula duniyar tunani Noor da suka baro a Japan suka dawo gida hutu, tun daga makaranta primary irin soyayyar nan ta ƙuruciya da wawta a ciki amma abin ya girmana komai yake Noor yake tunani. "Kai da ubanka ba magana nake ba" sai a lokacin Sadauki ya ɗago kai yana haɗe fuska sosai ya ce "Ban ji ba" "Tunani uban me kake da har nake magana baka ji ba" "A'a yaya kawai ban ji ba" daidai nan Al'hussan ya shigo da kayan ball a jikinsa, Al'hussan kuma ya fito daga direction ɗin kitchen hannunsa riƙe da plate ɗin indomie, sai lemo a tare suka ce "Wlcm yaya" Sadauki ya miƙe ya bar wajan abinsa yana shiga bedroom ɗinsu ya ɗauki jitarsa ya zaga zuwa lambu, Ridayya ta fito hannunta riƙe da farar riga irin ta likitoci ta saka glasses a idanunta, dake bayan su Al'hussan cikin data samu ta sake haifar tagwaye duka masa aka saka musu Jaheed da Junaid, ya sake samun wani cikin ta haifi namiji still aka kuma saka masa suna Talba, gabaɗaya yaran data haifa maza ne ake cewa mata uwar iyaye maza, Abbiey da har yanzu yake ɓoye shekarunsa ta hanyar kyakkyawan shiga da cima mai kyau da kwanciyar hankali shima ya fito daman sallama suka gama da Ridayya zata ta fi asibiti night duty gare ta, amma zata fara zuwa ta gaida Dada kakarta ta ƙara duba jikinta, kai tsaye Abbiey ya ƙarasa kusa da Alhaji ƙarami ya ɗora hannunsa a kafaɗarsa yana cikin tattausan jallabiya mai kyau da laushi hasken nan nasa har ɗaukan idanu yake, ya ɗaure sumarsa da ribbon ta sauka baya a hankali ya ce "Aboka nai ya kake?" Al'hussan ya yi murmushi ya ce "Abbiey ya zan tara gashi irin naka da YAA B kalle ku kamar wa da ƙani" Alhaji ƙarami dai bai magana ba sai kame fuska yake, Ridayya ta ce "Suma ina dawowa duk yanke shi zan yi ai musu kwalkwabo" a tare Abbiey da YAA B suka shafa kansu ta ce "And wannan fuskar taka ta yi kyau da yawa idan zaka fita shafa baƙi ai na ji labarin ƴan mata sun fara rushing akan ka, da kai da Sadauki kuna feeling kan ku wai ku samari ko? Karka fara saka ƴanmata suna mini sunturi a gida" ta juya ta kalli Al'hussan ta ce "And you too ba zan ɗauki ɗabi'ar ta ball ba zan bi duka na yayyaga kayan ball ɗin, karku manta nan gidan Ustaz ne ba gidan Professor ba. Ta juya ta kalli Al'hassan ta ce "Kai ba mace ba kai kenan a kitchen, ya kamata ka fara ɗaura zani ai da gayya daga yanzu azumin Alhamis da Litinin zaka fara" su dai duka kallon ta suke ta ce "Ina Sadauki?" "Ya shige bedroom" ta riƙe haɓa ta ce "Shi ban ma san layin daya ɗauka ba, banda nunƙufarci babu abinda ya iya ba zan ɗauki ba duk ranar da naga ƴan'uwansa a parlon ya shige bedroom zai San bashi da wayo" Abbiey ya ce "Saura ni" ta juya ta harare shi ya ce "kin haɗe kan yarana kin musu tas saura ni kawai, Kodayake ai an ce za a mini aski" ta yi murmushi sai a lokacin Alhaji ƙarami ya ce "Father is on the hospital" ya faɗa da fuska a dame duk sun fahimci wa yake magana akai, uba uba ne dole ya damu da mahaifinsa. Burin Ridayya na zama cikakkiyar likita musamman a ɓangaren mata ya cika, bata da sauran damuwa komai ya zama tarihi idan ba magana akai ba sam ita ta mance farinciki da walwala kawai take da mijinta, idan suna Japan a can asibitin take aiki, daman yaranta duk a can suke karatu, idan sun samu hutu su dawo Naija a ziyarci ƴan uwa. Zainura ta haifi kyakkyawar yarinya mace Burhan ya saka mata Zainura saboda soyayya matar Junaid kusan tare suka haiho da matar Tajj, rayuwa ta yi daɗi sosai har yanzu kuma Yaya Zuhura bata samu mijin aure ba, hakan ya fara damunta duk ta zama wata kala. Hajja Azizat ta yi wa Bilal ƙanwa aka saka mata Rusul ta zama ƴar shalele sosai kuma Abbiey ke son Rusul kamar rai. Gabaɗaya suna zaune a parlour suna jin labaran da yake trending a lokacin cewa ana neman wani TAHHB SCORPIO babu asalin photon fuskarsa sai wani da iya idanunsa ne sukai fito farare tas dasu "Allah ya shirya masa zuri'a, wannan ai abin tsoro ne shi a cikin al'umma" Sadauki ya ce "Kamar na san shi" Ridayya ta zare idanu ta ce "Wannan ɗan daban?" Ya sha kunu kamar shi ya yi magana ba can ya ce "MUTALLAB sunan shi...." Daidai nan Abbiey ya shigo ya tsaya ya ce "Mimi come" yana faɗa ya yi waje duk suka bisa zuwa compound, wata dalleliyyar baƙa ce a tsakiyar compound ɗin, ga decorations alamar na gift ne ta zaro idanu ya miƙa mata key ya ce "For me?" Ya ɗaga mata gira ya yi murmushi, ta yi sauri ta rungume shi Sadauki sai murmushi yake YAA B ma yana can tsaye yana musu bidiyo a hankali Abbiey ya ce "Today is our anniversary day, take this as a gift Mimi" tai ta masa godiya Sadauki ya ƙarasu ya ce "Mimi muga key" ta miƙa masa ya shiga motar ya fara gwadawa "I love you" ta ce "Na gode sosai man ban san me zan ce" kawai ta fashe da kuka ya rungume ta ya ce "Say Allahamdulilah" tana murmushi idanunta akan yaranta gata kusa da mijinta a hankali ta ce "Allahamdulilah!....." End Komai ya yi farko yana da ƙarshe babu wata ƙaddara da take tabbata, babu wata ƙaddara da bata da lokaci idan mutum ya yi haƙuri. Haƙuri yana da ribar kamar yadda Ridayya taga ribar shi a yanzu, duk baƙin cikin mutum hassadar shi idan Allah ya ce zai ka kai to tabbas zaka kasance, ku yi haƙuri da gidan mazajenku watarana sai labari mai haƙuri ya kan dafa dutse ya sa roman shi, a daina baibaita yara ƴaƴan kishiya ƴaƴa ne, baka san wanda zai jikan ka ba, da yara da dukiya daban suke a kuma daina aibata halittar Ubangiji domin yin hakan kana nuna Ubangiji bai iya halitta ba. Nan na kawo ƙarshen littafin MUNAFUKIN MIJI Domin yin gyara ku sharshi ƙofa a buɗe take 08164069385 Wattpad ina godiya da haɗin kan da kuka bani ina jiran last comments ɗinku😍 WhatsApp Arewabooks Facebook duka ina godiya ina jiran jin sharhi, a yi haƙuri a bisa rashin posting an samu matsala ne kuma hakan bai taɓa faruwa dani ba kuma daga wannan ba za a kuma ba in sha Allah. BRIGHT PENS na godiya da jimirin bibiyar littafanmu a karo na farko CUTARWA, YI WA KAI, MUNAFUKIN MIJI, ƘUDIRAR ALLAH. ku jira mu a second batch in sha Allah. Zan dawo cikin littafin *MUTALLAB* labarin Mutallab daban yake zan so ko wacce uwa ta karanta, zan so ko wacce budurwa ta karanta, zan su ko wanne namiji ya karanta. Bani da tabbacin zai yi daidai da ra'ayoyinku amma ina da yaƙinin kuka fara karantawa ba zaku daina ba, rubutun zanen ƙaddara a nan nafi ƙarfi da saka idanu zubar da hawaye. Amma wannan salon na musamman ne ban taɓa yin irin shi ba kawai ku biyo ni a labarin MUTALLAB ma'ana dai MUTALLAB TAHHB SCORPIO. ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************