*_Typing📲_* *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _Chapter 1_ *_Free pages_* ________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1 Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv _________________ A tsari da tarihin rayuwa ƘADDARA MADUBI ce. Domin tana sakaka kallon kanka a ɗan adam kuma bawan da rayuwarsa ba ikonsa bace. UBANGIJI ya halicci duniya da halittun dake rayuwa a cikinta daban-daban, wanda suke a zahiri, da wanda ya baiwa kansa ilimin sani shi kaɗai. Sai dai a dukkan halittunsa ya tabbatar mana ƊAN ADAM mai daraja ne. Musamman idan mukai dubi da ayoyi da suka zo cikin Alkur'ani mai girma.         Bawai hakan na nufin sauran halittunsa basu da muhimmanci ba, a'a kai dai DAN ADAM ya baka wannan darajar, ya kuma fifitaka, idan muka duba Suratul Baqarah. Yayin da ALLAH ya ce wa mala’iku zai halicci khalifa a ƙasa (wato Adam), kuma ya umurci su su yi masa sujada, abin da ya nuna fifikon mutum fiye da mala’iku (sujuda ta girmamawa ba ta ibada ba). Bai barmu a mutanen kawai ba, sai ya rabamu a jinsi guda biyu, NAMIJI da MACE. sannan ya yomu a BAƘIN FATA da FARAREN fata. Ya yomu a YANKUNA DABAN-DABAN. Ya kuma banbantamu a ADDINAI DABAN-DABAN. Ba iya nan kawai muke ba, yarukan bakunan mu ma daban-daban suke, ta yanda wani idan zai kwana magana wani bai san mi yake faɗi ba koda zaginsa yake kuwa. Ba'a nan kawai muka banbanta ba, yama wasu ARZIƘI, wasu DUKIYA, wasu ILIMI, wasu BAIWAR SARRAFA HARSHE ko yin AIKI tuƙuru daga gaɓɓansu da ƙarfin daya azurtasu da shi. Samun ɗaya daga cikin wannan bashi ke nuna maka kafi wane DARAJA ba. Dan zai iya yinka mai ARZIƘI a DUNIYA, ka tashi talaka a lahira, talauci irin na rasa ƙyawawan ayyuka da rashin samun ƙyaƙyƙyawar MAKOMA. Zai iya yinka TALAKA a DUNIYA a lahira ka tashi mai tarin arziƙi da AYYUKANKA da samun kyakkyawar makoma. Zai iya yinka mai ILIMI, a lahira ka tashi ILIMIN bai amfaneka da komai ba domin baka amfanar da kanka da shi ba bisa kyakkyawar hanyar data dace da iklasi a DUNIYA. Zai iya yinka JAHILI, amma ka tashi a ƙyaƙyƙyawar MAKOMA saboda baka cutar da kowa ba a duniya, baka kuma bi mummunar hanyar da zata RUGUZAKA ba wajen yin ayyuka saboda RIYA (Rahama ta ALLAH ce). Wannan kaɗan ne daga cikin RAHAMARSA ga bayinsa.       A yanda DUNIYA take kamar ƙwallon wasa a ido, haka RAYUWAR kowane ƊAN ADAM take a NASARA ko FAƊUWA. Yanda kwallon ke a hannunka kusa da idanunka babba, haka girman matsalolinka da damuwarka da nasararka suke a zahirin idanunka da ZUCIYARKA. Idan ka harbata nesa da kai takan koma ƙarama, haka idan ka yarda UBANGIJI shine mai ƙaddarawa da bada sakamako sai ka dinga kallon wannan damuwar taka da matsaloli da jarabawoyi ƘARAMA kamar yanda kwallon nan dake nesa da kai take ƙarama.      Banbancin kawai girma da ƙarantar kwallo a idanu muke ganinta ƙwaƙwalwa ta auna mana. Amma girman jarabawa da matsalolin rayuwa muna kallonsu ne a ZUKATANMU da KWAKWALWAR MU baki ɗaya.       Bara mu taƙaita domin ku fahimci inda ainahin shimfiɗar tamu ta dosa kai tsaye, dan karmu shagala lokaci na gudu ba kuma mu yake jira ba. Abinda kawai nake so mai karatu ya auna anan minene ainahin RAYUWA? WANENE SHI? MAI ZAI KOMA A WATARANA? MINENE ƘARSHENSA A ƘARSHEN RAYUWA?.      Ki yarda, ka yarda a cikin kowace RAYUWA akwai farin ciki, akwai jarabawa, akwai nasara, akwai faɗuwa, akwai ƙalubale, akwai mafari, akwai ƙarshe, akwai mina aikata mina bari a bayana?. Dukansu kuma suna ƙunshe ne a cikin wannan rayuwar taki ko taka guda ɗaya tak da ba'a hannunka take ba, yanda ba'ai shawara da kai yayin halittarka ba, sai da ka girma ma kasan wanene kai? Haka baza'ai shawara da kai wajen tabbatuwar waɗan can abubuwan na sama ba. Domin a dukkan ni'ima da rahamar da UBANGIJI ya baka babu wacce kake biyansa da KUƊI. Ibada ma idan kayi kai kakema kanka gata bazaka rageshi da komai ba, ba kuma zaka ƙareshi da komai ba. Dan haka mu tafi kai tsaye kawai a wannan labari mai suna KIƊA A RUWA! MAI MAGANIN DODO. da zaizo gareku a wannan lokacin, mu kuma hango darasin da yake mana hannunka mai sanda akai domin mu fahimta, mu ilimantu, mu nishaɗantu, mukuma wa'azantu idan hakan ta kama...... •>•>•>•>•>•>• .....17/5/20013.....       ......Motse-motse yake ɗan yi da surutai cikin barci, har takai wanda ke a kusa da shi yana iya jin komai. Gashi yayi sharkaf da zufa a goshinsa duk da ba yanayi ne na zafi ba. Hasalima wani ɗan karan sanyi ake zuwabawa irin mai hazo ɗin nan da iska mai kwaso ƙasa ta buɗe mutane.      Da mamaki wanda ke kusa da shi da littafi a hannunsa yana dubawa ya ɗan zuba masa ido, sai kuma ya kai hannu ya taɓa shi yana kiran sunansa amma ko motsi. Littafin hannun nashi ya ajiye, zuciyarsa na ƙara shiga ruɗani da tsoro. Ba wannan ne karo na farko da abokin nashi kuma amini ke shiga cikin wannan halin ba a cikin barci, wani lokacin har sai ka fara fassara al'amarin nashi kamar na mai aljanu, kuma sam ba aljanun bane ba, in dai har zai kwanta barci mai nauyi a ƴan shekarun nan da wahala ya tashi bai shiga wannan yanayin na mafarki ba, duk da bai taɓa faɗa masa irin mafarkin da yake yi ɗin ba shi ya fahimci mafarkine mai nauyi da ban tsoro....        Sosai ya girgizashi kam yanzu, bayan ya janye bargon da yake ciki kalar army green, tare da shafa masa ruwan gorar dake gefensa a fuska. Wani nannauyan numfashi ya kawo tamakar mai dawowa daga suma, sai kuma ya ɗan furzar ya sake jan wani kaɗan kafin ya buɗe idanunsa a hankali.       Masha ALLAH na ambata ganin wasu kyawawan idanu tamkar ba na namiji ba. Da farko abokin nashi da shima ke kallonsa ya zubama ido, sai kuma ya kauda gefe yana yunƙurawa ya tashi zaune yana jingina da jikin tantin da suke ciki. Riga ce armless data kama ginannen jikinsa kalar army green, sai wando 3-quater irin kakin sojoji. Duk da a zaune yake kallo ɗaya zai tabbatar maka da sojan ne na gaskiya kuma tsayayye, dan kuwa jikinsa irin na lafiyayyun tsayayyun jaruman sojoji ne da zasu iya tunkarar kowane harmutsi musamman na nuna ƙarfin ƙwanji.       Abokinsa da ya zuba masa ido ya ɗan girgiza kansa, sai kuma cike da kulawa ya ce, “Da ace ina da damar matse bakin nan naka da baya son motsawa yayi magana da nayi hakan dan sanin wane irin mafarki kakeyi a shekarun nan, dake saka ka a wannan yanayin, *_Zak-Shadow_* duba fa yanda kake zufa tamkar wanda yake a filin daga, amma kuma akan mafarki, wannan al'amari na bani mamaki da tsoro”.        Wani ɗan kallon fishaa yay masa slowly da idanunsa ya kuma janye, batare da yayi maganar da yake so yayi ɗin ba ya miƙe abinsa. Nace oh oh! Wato fa da gaske a sojojin ma akwai SOJA, akwai kuma SOJI. Kai daka kalla wannan kasan yaci sunansa na Zak-Shadow, har hamar ya dace a ƙara masa da ILIYA ƊAN MAI KARFI. Dan kuwa mazan faman ne fa a mazansu da kayar da su ƙasa sai an haɗa da babban shirin haɗin gwiwa. Cikin yanayinsa na rashin gaggawa da hayaniya ya saka tausasan slippers baƙaƙe dake a gaban gadon daya tashi, batare daya sake kallon abokin nashi da yay tagumi yana binsa da idanu ba ya nufi ƙofar tantin da suke ciki, sai da ya ɗan ranƙwafa sannan ya fice.     Babbar magana, jeji ne iya jeji da babu alamar wani gari ko motsin halittu na mutane a kusa. Idan ka cire ɗan sansanin da suka kafa nasu na sojojin mai Tanti biyar kacal. Uku manya ne sosai da zai iya cin sojoji da yawa. Guda biyun sune ƙananu madaidaita. Guda ukun manya da ɗanyan ƙaramin suna a kusa da juna ne, ɗayan da Zak-Shadow ya fito a ciki yana gefe guda ne a ware ƙarƙashin wata ƙyaƙyƙyawar bishiya ƙatuwar gaske. Sosai garin yayi hazo na yanayin sanyi har baka iya hango abinda ke ɗan nesa da kai da ƙyau koda bishiyoyi ne, a gurin yashine shimfiɗe mai ƙyau da ɗaukar idanun mai kallo, ga tsafta, dan gabansu kaɗan akwai ruwa kwance dake rayuwa a wajen, dan haka ya zama matattara dabbobin jeji dake zuwa shan ruwa, wani lokaci kuma harda masu haɗari amma suka zo suka kafa sansani a wajen saboda ƙarfin hali irin na soja.       (Sojojinmu ALLAH ya ƙara muku lafiya da nisan kwana a duk inda kuke🙏).      Babu yawan sojoji a waje, dan basufi a ƙirga ba dake ɗan kai-kawo da bindigu a hannu sai wasu a zaune, da alama ƴan jiran kota kwana ne.         Fitowar Zak-Shadow ya saka wanda ke jikin tantin daya fito nutsuwa da sauri, tare da ƙamewa yayi salute nashi cike da girmamawa yana sake risinar da kai ƙasa, dan da gaske Zak-Shadow zakine a wajen na sama da shi ma ba naƙasan kawai ba. Idanunsa kyawawa masha ALLAH ya zubama sojan na sakanni, sai kuma ya maida ga sauran da ƙamshinsa ya fargar da su, suma duk sun nutsu, wasu a cikinsu jikinsu har tsuma yake yi. Jin shakkar Zak-Shadow a jinin duk wani matashin soji daya sanshi yake, badan ya kasance azzalumi ba, sai dan kasancewarsa tsayayyen mutum da baya ɗaukar shirme akan aikinsa da gaskiyarsa, kana take doka ko gaskiya ya ɓallaka ya ɗora gaɓa-gaɓa wannan abu ne mai sauƙi a wajensa.      Sai da ya gama ƙare musu kallo tsaff batare da yace uffan ba yay wucewarsa cikin takun bajinta na ma'abota ƙarfin jiki. Numfashi suka shiga saki a hankali, dan tunda ya fito kowa ya riƙe nashi a maƙoshi gudun shiga tarko. Sai kuma suka shiga ɗan kallon juna suna gulma da idanu, dan buɗe baki dai ayi magana tamkar taro match ɗin da babu yawan ƴan wasa ne..........✍🏼      _(🤣To bana kuma wa muka kwaso ne? Nima fa masu karatun wannan Zak-Shadow ya fara razana ni🤭, kota yaya labarin ma zai rubutu oho🥱😆. Kudai kuyi addu'a kawai kar ku ji ana karya Bilyn ku gaɓa-gaɓa ana ɗorani🤥.)_     ________________👇 _Zaku samu wannan Littafi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER🇳🇪- (500 CFA)_(VIP 1000 CFA)* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899* *_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_* [02/10, 2:02 pm] Abue Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _Chapter 2_ __________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1 Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 ________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv __________________ ........A gaban ruwan nan da kowa yasan wajen zuwansa ne in har ba suna akan aiki ba ya iso, ya ɗan bi wajen da kallo cike da nazari, sai kuma a hankali ya furzar da huci mai ɗan nauyi da nuna damuwa. Dai-dai nan wani matashin soja ya iso wajen hannunsa ɗauke da roba cike da dawa. Ɗan kallonsa Zak-Shadow yayi, sai kuma ya miƙa hannu ya amshi roban dawar alamar baya buƙatar wata magana. Cikin girmamawa sojan ya bashi, ya juya yabar wajen. Tamkar tsuntsayen dake rayuwa a wajen sunji ƙamshin dawar ne, sai gasu suna sauka ɗaya bayan ɗaya a gabansa. Karo na farko yay wani ɗan murmushin gefen baki, tare da ɗibar dawar a hannunsa ya shiga watsa musu, ai kafin wani ɗan lokaci tsuntsaye kala-kala sun cika wajen, shiko yana cigaba da watsa musu dawar. Abin sha'awa harda masu sauka akan kafaɗarshi. Dan dai-dai nan ma wata ƙyaƙyƙyawa mai adon ja da blue a jikinta ta taso fiirrr ta sauka akan kafaɗarsa ta haggu. Juyawa yay a hankali ya zuba mata ido, kai da ganin kallon da yake mata kasan tunaninsa ya tafi wani waje ne kuma daban. Mafarkinsa ne ke dawo masa daki-daki tamkar Film da ake kallo zaune a cinema. Ba yau bane farko a garesa yin mafarkin, amma duk sanda yayi yana koma masa ne kamar sabo, kamar kuma a ranar ya fara yinsa, ga mafarkin a duk sanda zai yi shi cikin maimaita masa kansa yake abin kamar wani sihiri koma mi zai kirashi oho. Shekararsa bakwai da wasu watanni kenan da fara wannan mafarki, tun daga randa suka fara shigowa wannan jeji (2006) akan aikin da suke kai har zuwa yanzu lokacin yana ma a matsayin Major. Sun yo nisa sosai da jejin sukaci karo da wasu gayyar mata tafe da kayayyaki a kansu har da yara anata raira waƙar aure, ganin motocinsu da kayan jikinsu na kakin sojoji ga bindigu a hannu ya saka mutanen firgita suka shiga watsar da kayan kansu suka kwasa da gudu, masu ihu nayi masu kururuwa nayi. Sai mace ɗaya mai tsohon ciki data tsaya cak a hanyar, lallai itama a tsoracen take, sai dai da alama bazata iya gudun bane ba saboda ciki. Idanunta a rufe suke ga zufa ta gama wanke mata jikinta dake rawa. Duk abin nan dake faruwa kallo ɗaya yay musu ya maida kansa ga jaridar da yake dubawa, sai da abokinsa, koma ace amini da ya zama ɗan uwa na jini dake gefensa a motar da suke su biyu rak sai driver ya furta, “Ikon ALLAH irin wannan cin gudu kamar kunga dodanni! Ita kuma wannan halan cikin jikinta ne ya hanata gudun..?” A karo na biyu ya ɗan ɗago a hankali jin furucin Imran ɗin, akan matar dake tsayen ya sauke kyawawan idanun nasa da kullum suke a juye da sirkin ja kamar wani mai afa ƙwaya, baya ganin fuskarta saboda ta juya musu baya, atamface a jikinta kalar blue da zanen barewa yallow. Zanen atamfar shine a matsayin gyale data lulluɓa, sai fanteka madaidaiciya a kanta dake haɗe kusan guda goma. Ƙafarta takalman danƙo ne da ake kira ɗan-madina suma blue. Tunaninsa ya katse sakamakon fitar wani yaron sojansu inda matar take yana mata tsawar data sakata daburcewa har tana neman zubar da kayan kan nata. Shi kansa baima san ya ɓalle murfin motar ba ya fita, sai ganinsa yay kawai a gabansu. Yaron sojan ya ƙame da sauri yana salute nashi, sai kuma ya nuna matar cike da takaicinta zai fara masa bayani kawai sai yaga ya ɗan duƙa a gaban matar. Ba shi dake tsaye inda suke ba har waɗan da ke mota sai da suka firgita, ai tuni suka shiga rige-rigen fitowa a motocin harda Imran, yo oga kwata-kwata ya fito su ubammi zasu jira yi kuma. Zak-Shadow dake a gaban matar cike da tsigunnon ƙasaita kaɗan ya motsa lips ɗinsa ya ce, “Kiyi haƙuri”. Da wani kalar sauri ta ɗago tana kallonshi, dan gaba ɗaya ta gama ƙarasa susucewa tunda ya duƙunnu gabanta, sai taji ma ai gara na farkon da wannan mai kama da mala'ikan ɗaukar ran. Kalmar ‘Kiyi haƙuri’ daya ambata ta matuƙar jijjiga mata zuciya kwarai da gaske, dan ba abinda tai zato ba kenan. Numfashi ta sauke mai nauyi, sai kuma cikin sanyin murya da rawar baki ta ce, “Ku su waye dan ALLAH? Dan bamu taɓa ganin irinku a wannan yankin ba shiyyasa sauran ƴan uwana suka firgita”. Kallonta kawai yake baice komai ba, fin minti ɗaya kafin ya furta amsar da kowa baiyi zaton zai batan ba. “Mu sojoji ne, masu bada garkuwa ga al'umma da ƙarfin ikon ALLAH.” A mamakinsa sai yaga tayi murmushi mai ƙayatarwa tana ƙara sauke ajiyar zuciya da sharce zufar data jiƙeta da mayafinta. Ta ce, “ALLAH sarki, lale marhabun da shigowarku wannan yankin namu, dama haka sojojin da muke ji ana faɗa a redion Tanimu suke?. Lallai yau na yarda SOJA MAZAN FAMA, SOJA GA WUTA GA YAƘI. ALLAH ya ƙara kareku bisa ƙyawawan aikin ku, ya baku nasara da kariya daga duk wasu mugaye. Tunda na fara jin labarin aikin ku nake fatan ALLAH yasa na haifi ɗa namiji idan Tanimu zai tafi birni yaje da shi ya saka shi a makarantar sojoji shima ya zama soja. Amma tunda yau har gaku a wannan yanki namu in sha ALLAHU in dai namijin na haifa zan nemoku a wannan jejin ko badaɗe ko ba jima na baka amanar yarona ka koya masa wannan aiki na jarumai. Dan daga ganinka kai mutumin kirki ne jarumin kwarai ɗan gaske”. Karo na farko ya kai idanunsa akan cikin nata da yay girma sosai, sai kuma ya kauda kai batare daya ce komai ba, anutse ya miƙe gaba ɗaya yana mai tura hannayensa cikin aljihun wandon kakinsa na soji, daga sama kuwa riga ce baƙa t-shirt data kama ingarman jikinsa, yanda yay zanzaro da belt ya bama shafaffen cikinsa bayyana kwance a rigar luf. Tabbas suffarsa itace ta asalin Zaki da ake faɗa. “ALLAH ya saukeki lafiya, mun gode da addu'ar ki garemu. Zan zo da kaina amsar amanarki! Ku bata ruwa, a ƙarbi address ɗinta”. Yay furicin ƙarshe da umarni yana barin wajen. Ba ƙaramin mamaki abin ya bama sauran sojojin ba, hatta da aminin nashi Imran kuwa. Duk da dai kowa yasan Zak-Shadow a kallon nesa ne zakai masa ganin mugu, dodo mai firgitarwa koda a kallo ne, amma yana da tausayin na ƙasa da shi da sassauci ga mata, dan ko macen soja ce tai masa laifi yanda yake mata hukunci ba daidai yake dana namiji ba. Kamar yanda ya bada umarni sun bata ruwan roba da aka ɗakko a mota, sun kuma tambayeta garin da take ta faɗa suna rubutawa. Sannan suka taimaka mata ta tashi daga faɗuwar da tayi na firgita. Sojan da yay rubutun address ɗin nata ya miƙawa Imran cike da girmamawa, amsar takardar Imran yayi ya saka a aljihu kawai, sannan yay ma yaran umarnin su koma motoci, dan tuni shi mai gayya da aikin ya koma ciki abinsa. Haka suka wuce suka cigaba da tafiyarsu suka bar wannan mata mai tsohon ciki nabin motocinsu da kallo har sai da suka ɓace mata. Tun daga ranar bai sake bi takan zancen ba, sai dai a daren kwana goma sha shida da haɗuwa da su yay mafarkin ta haihu tana miƙo masa jaririn. Abin kamar wasa ya cigaba da maimaita wannan mafarki akai-akai, kuma koda yaushe irinsa yake maimaitawar babu canji. Gashi a ƙalla yanzu shekara bakwai kenan da wata har biyu..... _______________ FAZANAMS MULTIPURPOSE PLC. *_Ina masu neman ayi musu souvenirs Na bukukuwan su dana shagalin bikin birthday da dukkan wasu taruka?_* *_Ina masu son ayi musu abinci Na gargajiya da abin sha Don farin cikin taronku?_* *_Maza ku garzayo to ga Dama ta Samu a FAZANAMS MULTIPURPOSE PLC_* _Muna yin abinci Kamar: Masa, Dambu, Alkubus, Dashishi, Dan wake, Alala, Biski da sauran su da Miya Kala Kala 🍝🍜🍲🍛🥗🥘🫕💃💃_ *Sannan Muna yin: kunun Aya, Zobo Mai flavour Kala Kala, Kunun tsamiya, Kunun gyaɗa, Tamarind drink, Kunun Zaki da sauran su🥤🧋🧃🍸🍹🍷🥂💃💃💃 _Sannan Muna yin party packs na Yara da manya haka zalika Muna yin snacks Kamar samosa, spring rolls, doughnuts, cincin Mai kwakwa, Mai flavour Kala Kala da sauran kayan makulashe irin Aya Mai sugar da Mai gishiri, Muna yin kwakumeti, Muna alawar Madara, iloka, ridi da sauran su.🧇🥪🥙🌮🫔🌯🥐🥯🌭💃💃💃_ *_Muna yin abincin sadaka ga Mai bukata muna nan a area 2 Abuja_* kuna iya tuntubata a wannan lambar👇 *08094186230* _Whatsapp Ko Kira._ _________________ Ɗan motsin da wayarsa tayi ne ya sashi sake furzar da huci, sai kuma ya sauke hannunsa dake cikin dawar nan ya cirota daga aljihu yana dubawa. Kallon wayar kawai yake babu wani yanayi dake nuna kirane ke shigo masa ya kamata ya ɗaga, harta gama ta yanke, sai kawai yay ƙoƙarin maidata aljihun, amma hanzarinsa ya katse saboda sake motsawar data shiga yi a karo na biyu. Yanzu kam hannu ya kai ya wani murza goshinsa, kafin ya sake ɗaure fuska babu alamar wasa sannan ya kai wayar kunne alamar dai da gaske kiran nashi akeyi.. “Hallo. My D!”. Wata zazzaƙar murya mai sanyi da kwantar da kai ta faɗa daga can. Shiru babu alamar zai tanka, da sauri ta ce, “Oh I'm sorry dear. Assalamu alaikum”. “Wa'alaikissalam”. Karo na farko jarumar muryarsa ta bayyana cikin buɗaɗɗen sauti da ƙarfin lafazi irin na maza marasa son wasa da lokaci. Itama sai ta ɗan ƙara kwantar da murya ta gaisheshi. Maimakon amsawa tambaya ya jeho mata a kausashe. “Kiran na miye?”. Yanzu kam murya ta raunana kamar zatai kuka, ta ce, “Haba My D. Shike nan abu baya wucewa a wajenka, na baka haƙuri, na tura maka saƙo amma duk ka share ni. Dan ALLAH kayi haƙuri, nayi kuskure kuma na yarda nayi ina sake neman afuwa. Wlhy ni kewarka ma nake yi dan ALLAH kazo gareni, wata biyu fa ba sati biyu bace.” Shiru yayi bashi da alamar tanka mata, har sai da ta fara kuka ƙasa-ƙasa tana cigaba da roƙonsa da ban haƙuri sannan ya motsa lips da ƙyar ya furta, “Naji”. Baiwar ALLAH, dariya ta farayi cike da farin ciki, sai jera masa kalaman soyayya take masu zaƙi da taushi dake nuna tsananin kewa da begensa da take ciki. Shi ko yaƙi ya ƙara cewa komai. Cike da sake kwantar da kai ta ce, “Na faɗama Ummie?”. “No!”. “Ammafa itama tana kewanka D. Haka ma su Biebah kullum zancen ka ne a gidan nan, yau tunda na shiga hiranka kawai mukeyi”. “Uhmm!” Kawai yace. Bata damu ba ta cigaba da masa labarin ƙannen nasa, sai kuma ta koma na yaran dake tare da ita. Shi dai nashi saurare kawai, sai dai fuskarsa ta ɗan sassauta kaɗan ba kamar farko ba. Hakan na nufin koma wacece tana da muhimmanci a gareshi. Ya jima suna wayar kafin network ya fara rawa, kasancewar inda suke sai a hankali dama. Wayar ya maida aljihu, sai kuma ya ajiye robar dan dawar ta ƙare duka. Jejin ya shiga bi da kallo irin na nazari, kafin ya bar wajen gaba ɗaya ya koma cikin tantin da ya fito ɗazun..........✍🏼 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [02/10, 8:07 pm] Abue Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _Chapter 3_ __________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1 Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 _____________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ____________________ ........Ɗagowa Imran dake zaune a study table yana duba wasu takardu yay yana kallonsa. Shi ko kallo ɗaya yay masa ya ɗauke kansa, zama yay a bakin gado ya jawo takalma daga ƙasan gadon, batare daya kalla Abbas dake cigaba da kallonsa ba har yanzu ya ce, “Zanje gida”.         “Gida kuma? Lafiya dai ko?”.    “Kawai zanje ne!”. Ya faɗa a taƙaice. Abbas yasan amsar ke nan, amma sai yay shiru yana kallonsa da nazari. Eh yasan in dai yace zai je gida akwai dalili, sannan sai ya tabbatar babu wani ƙalubale da zai bari mai girma a inda suken, amma haka kawai shi sai a yau sai yaji kamar tsoro ya tsarga masa akan tafiyar tasa, sai ya kasa cewa komai. Dai-dai Zak-Shadow dake haɗa bindiga shima ya ɗan ɗago ya kalla Imran ɗin, ganin yanda ya zuba masa idanu sai ya sake tsuƙe fuska ya ɗauke kansa. Imran yayi murmushi, dan yasan ya tsani kallo. Cike da tsokana ya ce, “Anya ba kewar Madam bace ke tsikarin ka?”.       Bai kula tsokanar da yake masa ba, kansa ya ɗan girgiza kawai yana zuwa gab da shi ya ciri ƙaramar takarda ya ɗauki pen yay gajeren rubutu. Batare da yayi magana ba kawai ya tura gabansa ya nufi barin wajen, sai kuma ya juyo yana kallonsa, cikin ɗage gira sama ya furta, “Ka rage sa ido Imran, idan nayi kewar laifi ne?”.     Imran yayi dariya da faɗin, “A'a bakai laifi ba MAZAJEN FAMA, maza jeka ka ɗabbaƙa sunna abinka”. “ALLAH ya shiryeka”. Cewar Zak-Shadow. Imran ya amsa da amin yana ɗaukar takardar ya fara dubawa.         _“Bana son kowa yasan na fita, kamar yanda na faɗa maka 2 days ne, Kar abar ƙofar yamma a buɗe, dan haɗarinta yafi na sauran ƙofofi ka sani. Imran idonka ya zama sosai akan yaran nan da dukkan Captains ɗin kowanne sansani, sannan duk motsin da bai muku ba na sani, komai ƙanƙantarsa._      Takardar Imran ya ajiye ya juya yana kallonsa da faɗin, “Babu damuwa in sha ALLAHU. Amma dan ALLAH ka biya ka sayo min kilishi da gyaɗa. Zan sa a kawo maka saƙo daga gida ka taho min da shi..”       Wani kallo ya ɗago ya zuba masa, Imran daya san ma'anar kallon sai ya kwashe da dariya. “Maida wuƙar, ba ɗan aike zan maidaka ba ai ALLAH nace”.        A karo na farko Zak-Shadow ya ɗan saki wani murmushi gefen baki yana ɗauke kansa da ɗan girgizawa. Shima Imran ɗin murmushin sa ƙara faɗaɗa yayi. Yana matuƙar son aminin nasa, kamar yanda kowa yasan shima Zak-Shadow na sonsa matuƙar so ma kuwa. Dan shi mutum ne mai ra'ayin riƙau, idan baya yinka, baya yinka kawai. Idan ya soka kuma, to da gaske son naka yake. Mutum ne tsayyaye akan ra'ayi, kuma ɗan kai tsaye, baya iya kawaici akan duk abinda bazaiyi ba kuma baya buƙata. Idan har yace maka (eh) to ‘eh’ ɗin ce koda za'a kashesa, idan kuma yace (a'a) tofa ‘a'a’ ɗin ce. Zak-Shadow yasha baƙar wahala a lokacin da suke yaran soji saboda wannan taurin kan nasa a hannun manyansu. Dan a shekararsu ta biyu da fara aiki har zaman prison na sojoji yayi na wata shida saboda wata tirjiya da yayi akan umarnin wani ogansu. An azabtar da shi matuƙar azabtarwa a lokacin, dan bayan ya fito ma mutane da yawa sunyi zaton bazai sake rayuwa mai tsaho ba, amma da yake rayuwa ta UBANGIJI ce sai gashi ya miƙe, miƙewar data zama sanadin jajircewarsa a yanzu. Dan azabar da suka bashi sai ta zama kamar sun sake busar masa da zuciya ne ta yanda bai jin shakkar tunkarar kowane irin haɗari na rayuwa, daga nan kuma nasarorinsa suka fara bayyana har zuwa matakin da yake a yau.          Shi Dodo ne a idon wanda bai san ainahin halinsa ba, saboda a kallon fuska kai tsaye zaka kirashi mugu ne. Baida fara'a, bai san wasa ba koda da aboki ne. Duk wanda kaga yace maka yaga yana dariya lallai ya kai ai masa barka. Yana magana idan yaso, idan kuma bai so ba zaku iya kwashe awanni tare koma sama da haka bakinsa bai furta komai ba na hira sai dai kaji yana karatun Alqur'ani. Dan kuwa yana da addini sosai, hakama ilimin addinin. Tabbas da ace bai zama soja ba sai dai a kirashi malami, a yana sojan ma yana koyar da sojoji ilimin addini, kuma yana musu majalisi, sannan yana cigaba da neman nashi ilimin shi kansa.       Sai dai sirrin da mutane basu sani a kansa ba sai shi amininsa da mahaifiyarsa shine haƙuri. Zak-Shadow mutum ne mai haƙuri kwarai da gaske. Sannan mutum ne mai adalci da son tsayawa akan gaskiya komai ɗacinta. Yana da tausayi matuƙa musamman akan mata da yara. Zai iya saida rayuwarsa akan su. Sannan yana da kishin addini da yankinsa. Dan shi kai tsaye ma zai ce maka yana fara jin kishin yankinsa ne kafin ƙasa gaba ɗaya....         “Ka dinga tunani kamar wani mace”.     Buɗaɗɗiyar muryarsa ta dawo da Imran daga doguwar tafiyar tunanin da yayi. Cikin ɗan sauke numfashi yace, “Ai tunaninka nake yi”.        “Rashin aikin yi ne yay maka yawa da har zaka zauna tunani na halan?”.     Cewar Zak-Shadow yana ficewa a tantin. Tashi Imran yay yabi bayansa. Kamar ɗazun yaran sojin suka shiga kamewa da sake nutsuwa waje guda. Yanzu kam sunfi ɗazun yawa. Da alama wasu dama suna a cikin tantunan ne shiyyasa. Inda yake zaman yin alwala ya nufa, hakan ya tabbatar musu lokacin la'asar yayi, ruwa aka kawo masa shi da Imran, suma suka shiga haramar yin tasu musulman ciki kenan. Wanda ba musulman ba kuma suka amshi duty ɗin zagaye wajan. Koda suka idar da sallar shi da Imran sansanin suka bari gaba ɗaya, sun jima kafin can su dawo suna hirarsu. Wajen wani ɗan bukkan kara dake gefe suka nufa, koda ya buɗe buhun da akayi labule a bukkar wasu irin garƙama-garƙaman karnuka ne marasa ƙyawun gani, sai dai kallo ɗaya kai musu dole ne hankalinka ya tashi, dan babu tantama waɗan nan idan suka kama mutum sai kufan jinin jikinsa amma ko ƙashi bazasu bari ba, dan marabarsu da zakuna ƙalilanne. Aiko suna ganinsa suka fara zallo da haushi kamar wanda suke gaishe shi.     A mamaki na sai naga ya ɗaga musu hannu yana faɗin, “Good Afternoon my Boys”.        Wani haushin suka ƙara yi a tare kamar masu amsa masa. Imran yay dariya da faɗin, “Kama yaran nan naka training mai wahalar gaske. Idan suna wani abun sai ka rantse mutane ne”.      Ƙaramin Murmushi Zak-Shadow yayi da ɗan taɓe baki. Idan yayi murmushi ƙyau yake masa, maybe shiyyasa baya son yi. Sun jima a wajen karnukan sannan suka fito, lokacin duhun magriba yayi. Yanzu kam sojoji ne sosai a camp ɗin, gaba ɗaya sun fito daga tantunansu, ashe a ɗazun wasu basa wajen shiyyasa, wasu kuma na barci, dan maimakon barcin dare su na rana sukeyi saboda tsaro. Tunda Imran da Zak-Shadow suka fito gaba ɗaya wajen yay tsitt kamar an musu tsawa, kowa ya nutsu. Kallo ya bisu da shi kaf ɗinsu, a ƙalla sun kai su ɗari, dan wasu basa a cikin sansanin a yanzu suna kan aiki a cikin jejin tako wace kusurwa. Wanda ke nan tare da shi bazasu wuce ɗari ba. Wucesu yay ya zauna kan dutsin da yake zaman yin alwala akoda yaushe, ai da sauri wani ya kawo masa ruwa dan in dai kaga ya zauna a wajen alwala zai yi. Daga nan kowa ne ya fara ƙoƙarin yin alwalar, sai wanda ba musulmai ba suka sake amsar dutyn zama garkuwa a yanzu ma kamar dai ɗazun. Sanin yau zai bar jejin kuma baya son su fahimta sai ya ce yanzu ma Imran ya jasu salla. Hakan baisa sun zargi wani abu ba suma, dan yana yin hakan a kowane lokaci, ba oga Imran ba har a cikinsu yaran masu addinin kan jasu salla, duk da dai duk wanda ke a ƙarƙashin Zak-Shadow duk iskancinka da sakacinka ga ibada wlhy sai ya saita maka haukan kanka. Dan in har kana cikin tawagarsa bakai ba wasa da salla, ba kai ba shaye-shaye koda na sigari ne kawai, bakai ba zama da jahilci dole ka cigaba da neman ilimin addini, shiyyasa ma ya saka musu ranakun karatu, bashi kuma kaɗai bane malamin harda wasu a cikin yaran masu ilimi na koyarwa suma, sai dai in ana kan matsannacin yaƙi ne. Hakan yasa Alhamdullah hatta wanda ba musulmai ba a cikinsu zaka gansu a nutse. Dan in ma kace zaka bijire kayi jikinka ne zai gaya maka a hannunsa..      Bayan sunyi sallar magriba Imran yay musu nasiha kamar yanda suka saba, har zuwa lokacin isha'i. Bayan an idar kowa ya miƙe suka kasu group-group dan kowa da abokansa da kuma abokan maganarsa suka kunna wuta suna hira, wasu na cin abinci. A lokacin ne Zak-Shadow ya sulale ya bar jejin, barin da da yasan sakamakon da zai so da shi da bazai yi ba. Dan kuwa tabbas wannan barin shine mafarin wata babbar ƙaddara da alkalami ya jima da rubutata a cikin rayuwarsa tun yana cikin Ummiensa.........✍🏼    *_Wace ƙaddara ce wannan? Mizai faru? Mike shirin faruwa ne da Zak-Shadow 😭. Ya labarin mace mai ciki kuma? Wace rawa zata taka mana a wannan labarin?. Amsar ku na cikin labarin KIƊA A RUWA MAI MAGANIN DODO. Kada ku bari a baku labari. Dan ni kaina Bilyn ku labarin nan tsumani yake yi💃💃💃._* _Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER🇳🇪- (500 Fcfa)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899* *_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_* ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** [03/10, 12:31 pm] Abue Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _Chapter 4_ *_Free page_* _______________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1 Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃. __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ____________________ .........Gaba ɗaya hankalin yaran sojojin ya raja'a akan taɗi da jin ɗumin wutar da suka kunna. Amma shi yana gefe a saman wata bishiya ko tsoron dare baya ji balle wasu halittu daka iya fakewa a bishiyar koma aljanu. Shi ɗin ɗaya ne daga cikin amintattun yaran Zak-Shadow, dan haka duk wani motsinsa na yau da kullum zuwa yanzu ya haddace shi. Yakan fahimci yaren idanu daga Zak-Shadow, ya kan fahimci na gangar jiki harna ɗabi'a. Tun lokacin daya kai masa dawar daya zubama tsuntsaye ya fahimci akwai damuwa a tare da shi, dan haka ya laɓe yana nazartar shi, sai kuma akai sa'a aka kira wayarsa a lokacin, dan haka duk wayar da yayi acikin kunnensa take, duk da ba wani surutu ya zuba ba, amma da yake yana ankare da sai ya saka ma komai alamar tambaya. Sai kuma gashi da za'ayi sallar magriba yaga Major Imran Abbas ne yaja sallar, dan haka zuciyarsa ta bashi Lieutenant Colonel na shirin barin jejin kamar yanda ya saba fitar ɓadda sawu da tunanin basa fahimta. Eh tabbas basa fahimtar, dan a duk sanda suka daina ganin gilmawarsa kawai abinda zuciyarsu ke basu yana zagayen sauran sansanin ne ko meeting da sauran jagororin sansanin wato Captains, dan yakan yi hakan akai-akai. Dan kuwa runduna guda ce a ƙarƙashinsa dake rarrabe a cikin jejin da suka kai a dadin dubu ɗaya da wani abu, kuma shine Boss gaba ɗaya da suke ƙarƙashin umarninsa, Major Imran Executive Officer, sai Captains da su na ƙasa, duk da dai suma yaran hawa-hawa ne, kamar shi yana cikin Lieutenants. Akwai Sergeants na ƙasansu, akwai kuma Soldiers (rank-and-file). Tun asali tun fari shi dama ya shiga aikin soja ne badan kishin ƙasa ba, dan kamar an ƙirƙireshi ne saboda manufar da yake akai a yanzu, kafin ma ya shigo aikin an bashi horo na musamman ta yanda yake iya duk wani aikin munafunci da leƙen asiri cike da wayo, musamman akan Zak-Shadow a yanzu, kuma yana da tabbacin akwai ire-iren sa ma dan bashi ɗaya bane kuma suna tare da Zak-Shadow ɗin kusa sosai dama wasu manyan jami'ai irin Zak-Shadow ko na sama da shi harma dana ƙasa da shi batare da su sun sani ba. Koda yake kwanaki an taɓa kama ire-iren nasu aka kuma hukunta shi da hukunci mai girma, dan amanar gidan soja ta wuce tunanin mai tunani, su kansu a lokuta da dama suna wannan sheɗancin ne a tsorace, matuƙar tsoron gudun randa zata tashi musu. Amma maƙudan kuɗin da ake biyansu da shi na tunzurasu da assasa gurɓataccen tunaninsu da jagorancin shaiɗan. Balle shi dake a ƙarƙashin babban ZAKI, dan bafa a banza aka saka ma *_ZAK-SHADOW_* ɗin wannan sunan ba a gidan Soja, Zakin ne na gasken gaske da ya ciyo sunan tunma a asalin sunan yankan sa. Maybe shiyasa ma sunan ke da tasiri sosai a rayuwarsa da ɗabi'arsa. (ALLAH ya ƙara kare ku jami'anmu a duk inda kuke🙏. Kai mutane na ku ba MAZAJEN FAMA jinjinar ban girma mana💪😄, a haɗa musu da kirari na musamman kuma, ƙarshe a sara musu👍🏼). Waya ya zaro daga jikinsa, ƙarama ƙirar nokia, ya dannama wata number kira. Ba'a ɗaga ba sai da ta kusa tsinkewa. Murya ƙasa-ƙasa ya furta, “Good evening Sir!”.      Amsa masa da akai daga can ya sashi cigaba da magana cikin tsantseni da risinar da kai tamkar yana a gaban wancan ɗin.       “Sir! Yau ɗin nan ya fita. Dan sanda na kai masa dawar da yake zubama tsuntsaye bayan nabar wajen sai na laɓe, naji yana waya da matarsa kamar.....”      Sai kuma yay ɗan jimm alamar saurare. Kafin cikin yaƙini da son a yarda da shi ya cigaba da faɗin, “Tabbas na tabbatar baya jejin nan, dan yau ba shine yaja sallar magriba da isha'i ba. Na duba inda ake ajiye mashin ɗinsa kuma babu shi, na leƙa tantinsu oga Imran ne kawai a ciki, kuma in dai ba ana kan aiki ba baka raba su. Duk da haka na bincika dukkan sauran sansanin kuma an tabbatar min bai je ba”.     Sai kuma yayi shiru. Zuwa can ya sake cewa, “Yes Sir!”. Daga haka ya cire wayar a kunensa yana murmurshi, yasan yau account ɗinsa sai yayi rawar girgiza kwankwaso saboda manyan kayan da zasu shigo cikinsa akan wannan albishir ɗin. Sakkowa yay a bishiyar ya koma cikin ƴan uwansa, koda abokinsa da bai san ainahin shi munafuki bane ya tambayesa daga ina yake sai ya nuna ya zagaya ne yin uzuri, dan haka babu wanda ya kula suka cigaba da hirar su......        _____________   A can ɓangaren wanda ya kira kuwa yana yanke kiran wata number ya lalubo ya danna mata kira shima. Ana ɗagawa ko gaisuwa bai tsaya yi ba ya fara magana kai tsaye.        “Congratulations Aboki, yau dai mun samu damar da muka daɗe muna fako tun a watan jiya, dan na samu tabbacin barin yaron nan jejin yanzun nan”.     Daga can aka furta, “Woow Zak-Shadow!, damar da aka daɗe ana jira kace ta samu. Lallai yau rana ce ta musamman a garemu, dan kuwa na tabbatar zamuja kaya iya kaya akan wannan albishir. Ba damuwa yanzu zan sanar da oga kuwa ai ba zancen wasa faka-faka kawai Aboki”.        Dariya yayi irin ta nasara shima, sai kuma ya ce, “Okay hakan yayi,  amma abokina kadai tabbar babu matsala ko? Karfa mutanen nan su ci amanar mu. Bayan mun saida ƙasarmu sun sami biyan butarsu su zubar damu a banza batare da mun mori komai ba sai dukiya. Kasan fa halin ɗan Adam na wannan zamanin da wayo da iya cin amana, sannan mutanen nan a ankare suke komai nasu a tsare yake. Yaron nan yaron ƙasarmu ne na amana da kowa ke da hope a kan jarumtarsa, ba gidan soji da shugabanni kaɗai ba hatta al'ummar ƙasar nan ɗaukarsa suke kamar wani WALIYYIN SOJA”.         “Mtsoww!! Wato abokina wataran sai naji kana bani haushi. Wai miye damuwarka da batun wata ƙasa can, ƙasar data kasa gamsar da kai koda da albashin wahalar aikinka, su su minene ma kace duk basu suka so mu kasance a wannan hanyar ba, eh su suka so mana, tunda ai basai sunce muje mu aikata ba, sun gama tattare komai daga su sai ƴaƴansu da matansu dake ƙasashen waje. Muko an barmu da ɗumama kujera basir duk ya gama cinyemu”.        Dariya sosai wancan ya kwashe da ita, tare da faɗin, “Wlhy baka da dama, aiko bamace muna cikin masu ɗumama kujerar nan ba, dan mumafa tun farko karka manta munja kayan nan gwargwadon iko a gwamnati ta hanyar fakewa da ayyukan mu, kai dai a rufe rufau kawai. Ba lokaci faka-faka ka sanar dasu, kasan Yaron nan shegen kansa ne akwai wayo, komai a ankare yake yinsa”.       “Tabbas hakane. Ka bani 5minuts kawai, aikinka ya kammala a wannan gaɓar zakaji alert tare dana yaron shima”. “Okay yayi, byeee!”. Ya faɗa yana ajiye wayar fuskarsa cike da murmushi, sai dai can ƙasan zuciyarsa wani kalar luguden daka take yi. Tabbas yasan wannan halayyar tasu mummunar halayya ce kuma abar ƙyama da duk wani ɗan ƙasa na gari bazai aikata ba koda a wanne addini yake kuwa. Sun rufe jinsu da ganinsu saboda dukiya, sun manta da basu da inda yafi ƙasar a wajensu, anan aka haifi kakaninsu, haka iyayensu, suma haka, sun kuma haifi ƴaƴansu. Amma sam basa tunanin makomar ƴaƴan nasu da ƴaƴan ƴaƴansu, su dai kawai su tara kuɗi a kirasu masu dukiya. (Lallai UBANGIJI mai rufin asiri ne, dan tabbas da wani zai san wanene ai nahin kai a take zai danneka ya maka yankan rago koda da wuƙar yankan albasar gidansa ce. Amma wata hikima ta ALLAH sai kaita warkajaminka cikin al'umma ana girmamaka batare da ansan girman na riga bane kawai. Anya waɗan nan sunma kansu adalci kuwa?, summa shugabanninsu adalci da a kullum talaka ke ƙalubalanta da gazawa batare daya san ba laifinsa bane shi kaɗai, dan da yawan tsiyatakun da irinsu da ba'a tunanin zasu iya dasu ake haɗa kai ayi ba shugabannin da kullum ake kallo da zargi kawai ba. Yanzu kamar dai shi da abokinsa, ba shugabannin komai bane na siyasa, kawai ma'aikata ne a ƙasa da suka samu dama ake kuma amfani da damar tasu ake dama ƙasar saboda suna son suma su dama da kuɗaɗe. Anya kuwa bai kamata ace su zauna suma kansu faɗa ba, su tuna zuri'arsu dake rayuwa a ƙasar, dan duk iya ƙoƙarin su na su su barta ai iyaka dai su kwashe iyalansu ba wai zuri'arsu gaba ɗaya ba ko🤔? Wani lokaci irin waɗan nan sai kaga kamar kansu ya toshe. Basa tuna dukiyar a duk ma yanda ka tara sai duniyar daka nema dan ita ta maka tsirara tikk sannan ta turaka cikin ƙasa ta rufe ruf ta barka da azabar girbar abinda ka shuka. Dan UBANGIJI baya zaluntar kowa sai bawan daya zalunci kansa......) (Hummm kai dai ka sani zulwa, ni nayi nan🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️😏) >•<>•<>•<>•<>•<>•<             A ɓangaren abokinsa shima dai yana yanke kiran ya isar da nasa saƙon ne inda ya dace. Dan kuwa a cikin harkar gaba da gabanta ne. Buƙatar ganinsa da ogan nasu ya bashi ya sakashi shiga canja kayan jikinsa. Sauri-sauri ya kammala ya fice dan yana buƙatar ficewa karma matarsa ta ganshi. Aiko bata ganshi ɗin ba sai tashin motarsa taji. Cikin takaici taja tsaki, dan ita tunanin ta da manufarta daban ce kamar dai yanda kukasan mu mafi akasarin mata muke, kullum zargin baya wuce namiji na yawon banza ko huɗɗa da matan banza a waje kai tsaye idan yana fitar dare, sai dai abinda bamu sani ba wasu mazan ba hakan bane, wasu ɓarnar tasu ma tafi ta neman matan, ALLAH dai ya rufa mana asiri ya ƙara tsare mana mazajenmu. (😄👍🏼 Wannan jinjinar taku ce MAZANMU nagartattu, MAZAN ƘWARI kenan kuma MAZAN FAMA a wajenmu, ALLAH ya ƙara baku kariya da tarin ladar ƙoƙarin sauke hakkokinmu da kukeyi. ALLAH yasa mu da ku duk mu shiga aljanna. Ƴammata da zawarawa ALLAH ya baku mazaje na gari mazan fama a gidajen ku kuma. Kai a bama MAZA jinjina tare damu ma MATAN ƘWARAI RABIN ADDINI😘😘😀👍🏼❤️❤️💃)...........✍🏼                     _Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER🇳🇪- (500 Fcfa) (VIp 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899* *_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/10, 2:59 pm] Abue Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _Chapter 5_ *_Last free page_* __________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1 Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 ___________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ .......Falo ne babban gaske, sai dai gaba ɗaya an kashe fitulun cikinsa sai wasu candles da basufi uku ba kacal aka bari suna ci, suma a cikin kwalba suke dan haka haskensu baida tasiri mai yawa sosai. Yanayin duhun wajen ya ɓoye ainahin fuskokin mutanen dake zaune a cikin falon harma da sirrin tsarinsa, koda yake fuskokinsun ma a rufe suke da facemask ta yanda koda ace akwai hasken wutar baka isa tantance su wanene ba. Cikin wani ɓoyayyen harshe suke magana, harshen da babu makamncinsa a ƙasarmu. Sai ɗan ƙarar kofuna alamar akwai abinda ake sha, sai ko room hitter dake basu ɗumi saboda yanayin sanyi da ake ciki. (Waɗan nan sune manyan munafukan shaiɗanci, kowannen su nada laƙabin suna, dan babu mai amfani da sunansa na yanka balle kasan ainahinsa a addini ko yanki balle harshen yare. Hasalima gamayyace daga ɓangarori ta waje da cikin gida).           Ɗaya daga cikinsu ne ya ajiye kofin shayin hannunsa, tare da yin gyaran murya. Lokaci ɗaya abokan zaman nashi duk suka nutsu, tare da maida dukkan hankalinsu garesa. Cikin harshen da suke maganar ya furta, “Ya kamata muyi abinda ya tara mu, dan bamu da lokaci isashshe”.        “Tabbas haka ne Black Spider. Yanzu minene a teburin mu?”.      Zama Black Spider ya gyara, tare da nutsuwa sosai ya ɗauki remote yana dannawa. Hoton Zak-Shadow ne ya bayyana a jikin ƙaton majigin daya cinye kusan rabin bango, tsayayyen jarumin soja, da ko'a hoton kasan eh da gaske Gwarzan maza ne, dan kuwa a cikin uniform ɗin aiki yake, alamu kuma sun tabbatar yana kan aiki akai masa hoton batare daya sani ba, hakan kuma bai hanashi fita da ƙyau ba kuma tartar har kwarjininsa na dukan zukatan maƙiya koda basu bayyana a fili ba. Amma yanda duk suka ja numfashi a lokaci guda zai baka tabbacin hakan.       Black Spider ya fara jawabi kamar haka, “Wannan mutumin ya lalata shirye-shiryemu a gabashi da yammaci da yawan gaske da bazasu ƙididdigu ba koda a kintace. Mun ƙyaleshi badan yafi ƙarfinmu ba, sai dan bashi dama ya gama taka irin tashi rawar kafin mu canja masa salon kiɗa. Lokacin mu ya yi a wannan gaɓar. Duk da a baya Target ɗinmu Zak-Shadow ya ci gaba da zama cikas a shirye-shiryenmu. Dabarun mu da yawa sun durƙushe a gabansa. Amma yanzu, lokacin da muke jira ya iso garemu, wato dama ta dawo hannunmu.”       Cikin wata ƴar iskar dariya Viper ya amshe zancen da murya mai taushi amma cike da shaiɗanci irin ta shaiɗanun azzalumai, “Kamar yanda Black Spider ya faɗa a yanzun nan babu jimawa mun tabbatar da bayanin sirri ta hanyar yaran Dagger. Zak-Shadow ya bar sansaninsa na tsaro domin wata tafiya ta sirri a jejin, sai dai bamu san inda ya nufa ba, amma hakan mu ba damuwarmu bace kai tsaye, duk da dolene mu sani dan aikinmu ya tafi yanda ya dace akansa. Wannan shi ne gibin da ba zai taɓa tsammani ya bari ba a gaɓar da zai fuskanci illarmu mai muni, dan zamu zuba masa dafinmu mai ƙarfi da har abada babu makarin warkewarsa a zuciyarsa”.       Dariya suka kece da ita a tare, sai kuma suka koma tsitt kowa ya nutsu. Dagger da sam bai dara ba sanda ake dariyar, sai ma danna hannunsa da yake a kan tebur da ƙarfi cike da fusata, dan shi kaɗai yasan adadi tsanar da yayma Zak-Shadow a duniyar nan, saboda shine ya kashe masa ƙaninsa a wani hari na bayanan sirri da basu san yaya akai Zak-Shadow ɗin ya bankaɗo ba a kansu. Cikin kaushin harshe ya fara faɗin, “Sirs! Nayi muku alƙawari gamu mayaƙanku ba za mu bari wannan dama ta sulale ba! Dole mu kafa tarkon da zai karya ƙarfinsa gaba ɗaya. Zan jagoranci ɓangarena da ƙyau kuma da tabbatar cikar buri fiye da baya! Dan ina son da hannuna na gurfanar da shi a ƙasan ƙafafu na cike da ƙasƙanci da wulaƙantarwa. Dolene ya ɗanɗani fiye da abinda na ɗanɗana a wancan karon, da ace zaku bani dama bashi ba kaf ahalinsa sai na shafe babinsu a doron wannan ƙasar, na kuma........”      Mr Specter ya katse shi cikin jan girma, dan kuwa dukansu Dagger matsayin yaronsu yake, matsayinsa kawai shine shugaban mayaƙansu, hakan na nufin amfani ake da shi domin cimma manufa, kawai dai ita tunkunyar sharri ba'a banbance farfesun kayan ciki a cikinta, haɗawa ake har kashin dabbar da ruwan fitsari a dafe, shiyasa suka jawo Dagger ɗin jikinsu har haka, ahakan ma abinda suke buƙatar ya sani kawai suke tattaunawa da shi, sauran sirrinsu kuwa nasu ne..        “Ya isa haka mana Dagger. Abin da ya kawo nasarar Target Zak-Shadow a wancan lokacin har zuwa yanzu ba ƙarfin bindiga bane dabarunsa ne kawai da iya salon yaƙi, dan haka muma fusatarmu ba itace zata bamu nasara ba wayonmu ne da iya taku, ƙarfin makaman mu kariya kawai sunansu. Dan haka kai da yaranka zaku raba sojojin nasa da yankunan da yake tsarewa ne farko, rarrabuwa zai zama rauni a garesu ƙwarai da gaske musamman da shi ne dama ya fisu idon hangen nesa yanzu kuma baya kusa”.        Raven dake kusa da shi ya ƙyalƙyale da dariyar mugunta , “Hakane kuma fa Mr Specter! Dagger zaku tura labari na ƙarya a gabashi cewa za a kai hari. Captains ɗinsa za su tattara sojoji su nufi can. A lokaci guda, ku kuma ku tarwatsa yammacin ƙasa da ƙarfin ƙwanjin ku da dabaru.”        “Yesss! Tsarin Raven yayi shima, Dagger ruɗanin da zaku sakasu a ciki shine zai zama nasarar mu. Lokacin da jama’a suka ga sojojin Zak-Shadow sun kasa tsare yankuna, tsoro zai cika zukatansu. Kunga abin da tsoro ya fara lalatawa, baku da buƙatar harbi mai yawa akan yaransa, dan target ɗinmu ba'a kansu bane kawai, koma muce ba'a kansu bane, akan yankunan wajen ne da shi Ogan nasu”. Cewar Iron Fang kenan yana jingina da kujera cike da jin kai da ƙasaita, dan muryar tasa ma da nauyi take fita da isa, gashi ɗan tsirit kamar kazar mayu hegen.      Miƙewa tsaye Scythe yayi yana wani watsa hannaye da ɗagasu sama kamar sabon boka, gashi ƙaton gaske ɗan taran kamar buhun geron kakana. Cikin wagegiyar muryarsa mara daɗin ji ya ce, “Duhu zai mamaye su ƙwarai da gaske, Zamu haifar da tashin hankali daga gabashi zuwa Yammaci, daga dukanin karkarar dake zagaye da jejin da su. Lokacin da saƙo zai isarma Target yay tunanin dawowa daga tafiyarsa, zai tarar da ragowar ƙungiyarsa a cikin ƙura da jini, shi kuma zai faɗa ainahin tarkonmu. Dan a dai-dai gaɓar zai ɗaura ƙawance na gaskiya da handcuffs”.        Rafff! Raf!! Rafff!!! Kake ji tafi na tashi.      Oga kwata da baice uffan ba tun fara meeting ɗin sai a yanzu ya buɗe baki cike da isa ya furta “…Babu wanda zai tsira daga wannan shiri. Duk wanda ya tsaya a kan hanyar mu dama, zai bace cikin inuwar duhunmu ne, dan haka wannan ƙalubalen naka ne Dagger, kasani idan muka rasa nasara koda ɗaya ce kaima zaka rasa kanka, dan bamu shigo wannan ƙasar taku domin rera muku waƙoƙin yabo ko tatsuniya kuyita nishaɗi ba. Mune iyayen gidanku a jiya, a yau da gobe dole ku cigaba da zama ƙarƙashin zartarwar mu dan arziƙinku shine ƙarfinmu”.         Sosai zantukan oga suka soki Dagger, ashe dai duk da yake shege akwai ɓurɓushin kishin ƙasar a can ƙasan zuciyarsa. Amma saboda kuɗi da son duniya sai ya shiga jinjina kai irin na girmamawa.       Shiru sukayi na ɗan lokaci a karo na farko gaba ɗaya, sannan Eclipse ya miƙe cike da gadarar masu jin su sune manyan shegun duniya. Kai tsaye ya furta “An gama yanke hukunci. Operation Shattershield ya fara daga wannan dare. Duk ku shirya. Lokacin da Zak-Shadow ya sulale daga jeji, mu kuma za mu sulale da mulkinsa. Dagger zaka wuce ka fara aikinka, kaida duk yaranka zakuji alert”.         A tare suka ɗora hannayensu a kan tebur ɗin tsakkiyar falon, kowanne yana kiran laƙabinsa kamar alwashin ƙaddarar nasara da suke jin ta tabbata dole (Mahaukata)  “Eclipse! Specter! Dagger! Raven! Black Spider! Scythe! Viper! Iron Fang! Ashen! muna cikin duhu, kuma duhu ne zai mamaye Target ɗinmu Zak-Shadow!”.         Hummmm!! Zakuga duhu kuwa a lahira😭, kai tun anan duniya ma zaku cigaba da zama a duhun🙄. _______________           A lokacin da masu makirci ke shirya zalunci acan , anan Mazan fama ne ke isa gida gabannin asubahi. Ƙarfe huɗu da wasu mintuna ya tsaida ƙaton mashin ɗinsa ɓaki wulik ƙatoton gaske da a kallo ɗaya zaka san ba siyen yara bane sai dai manya, dan kuwa ƙirace ta musamman, sannan yana kiransa da suna na musamm *(Black Phantom)* shi da kansa.        A ƙofar wani baƙin gate ya tsaida shi, kasancewar anguwar da akwai wuta ko'ina da haskensa, hakan ya bashi damar bin street ɗin da kallo ta cikin hular matsin ɗin da gilashin ta daya sakaya idonsa. Sai da ya gama nazartar komai yanda yake buƙata kafin ya ciro wayarsa ya daddana ya kai kunnensa, cikin buɗaɗɗiyar muryarsa da ta ɗan shaƙe alamar iskar mashin da ya sha ya furta, “Taso ka buɗe min ƙofa”. Daga haka bai jira komai ba ya sauke wayar.      Cikakken mintuna huɗu ba'ayi ba wani ɗan saurayi da bazai wuce shekaru goma sha takwas ba ya buɗe ƙofar gate ɗin, cike da girmamawa ya ce, “Sannu da zuwa Dada”.      Maimakon amsa mishi mashin ɗin ya tayar, haskashi da yay da fitilar mashin ɗin ya bayyana yanda ya sako jallabiyar jikinsa a baibai alamar sauri. Ciki ya shige, shi kuma ya maida gate ɗin ya rufe. Duk da akwai haske na security light ya haska ko'ina na gidan babu abinda zan iya ƙararwa game da gidan face ganin flat biyu jere da juna. Sai motoci biyu dake fake a gefe inda yake ƙoƙarin faka mashin ɗin nasa, da mashin roba-roba guda biyu suma. Yana ƙoƙarin sauka a mashan ɗin bayan ya kafesa matashin saurayin ya ƙaraso inda yake, sannu da zuwa ya sake masa cike da nutsuwa da girmamawa, yanzun ma bai amsa masa ba sai da ya cire hular mashin ɗin kansa ya ɗan jujjuya kan sannan ya furta, “Ya kake?”. A taƙaice.      “Alhamdullahi Dada, ya hanya?”. Saurayin ya faɗa yana amsar hular, sai kuma ya sake miƙa hannu zai amshi bag ɗin dake goye a bayansa.       “Karka damu jeka kwanta zan shiga da ita”. Ya faɗa batare daya bashi jakar ba. Shima baiyi musu ba dan tsakaninsu babu wannan. Flat ɗin hannun dama ya nufa, saurayin ya wuce wanda ke gefen haggu ɗauke da hular mashin ɗin yana binsa da kallo da ɗan murmushi. A hankali ya furta, “Dodon gidanmu ya zo, gobe zakaji gidan nan kamar anyi mutuwa kowa yayi nutsuwar dole barema ƴan iskan yaran can da suka cika mana gida”.       Shi kam da bai san ƙanin nasa na gulmarsa a zuciya ba ɗaya daga cikin keys ɗin dake tare dana mashin ɗinsa dama wasu da yawa a jiki ya saka a ƙofar sashen ya buɗe, kai tsaye ya shige tare da maida ƙofar ya rufe. Fitilar falon a kunne suke haske fayau, dan tun kan ma ya shigo daga can waje ya fahimci hakan, sai tv da itama take a kunne tanata aiki. Kansa ya ɗan girgiza tare da jan ƙaramin tsaki, sai kuma ya shiga bin falon da kallo. Babba ne ba laifi, akwai kujeru masu ƙyau kalar ruwan toka ƙirar ƙasar waje. Hakama carpet ɗin tsakkiyarsu mai ƙyau ne, sai tvn bango, falo dai na dai-dai mai wadata ba masu arnan kuɗi ba. Centre table ɗin kujerun cike yake da plates da ledojin ruwa da aka sha, sai kwalaben lemon kwalba guda huɗu wasu ma ba'a gama shanyewa ba. A yanda fuskarsa ta sake tsukewa lokaci guda zai baka tabbacin baya son ƙazanta sam. Duk da kuwa bayan kwanikan babu wani datti da falon ke da shi mai nuni da rashin gyarawa ko ƙazatar. Da yake manya su manyanne ko fitilar bai kashe ba yay gaba abinsa zuwa wata ƙofar gilashi dake tacan ƙarshen falon. Hannu yasa ya tura gefe ɗaya suka haɗe a waje guda, kai daga ganin yanda gilashin yake ƙal-ƙal kasan ana kula da tsaftarsa sosai, koda ya shiga corridor ne mai tsaho ƙaɗan da ƙofa ɗaya tal a cikinsa, yaja ƙofar gilashin ya rufe sannan ya nufi ƙofar dake tabbatar da bedroom ɗinsa ne. Ilai kuwa hakan ne, dan yana buɗeta ƙaton bedroom ya bayyana sakamakon kunna fitilar ɗakin da yay, gado ne mai ƙyau 6-by-6, sai wadrobe ɗinsa da mirror, gefe kaɗan shiryayyun kujeru ne tamkar falo harda tv suma dai irin gadon sak. Komai dake ɗakin fari ne tas, in ka cire carpet ɗin dake malale a ɗakin gaba ɗaya kalar blue, suma labulaye fafare ne. Kaida kaga ɗakin kasan ana kula da tsaftarsa akai-akai, dan duk da babu kowa cikinsa ko ina tsaff ga ƙamshi mai daɗi na tashi, sai dai gadon babu bedsheed a kansa.       Kujerun kawai ya nufa ya zube a cikin 1sitter yana mai sauke  numfashi da ɗan dafe kansa, sai kuma ya jingina bayansa da kan gaba ɗaya a jikin kujerar ya rufe idanu ruff. Yafi mintuna biyar a hakan kafin ya buɗesu ya ɗago ya fara kunce zaren takalminsa, safar ciki ma ya cire sannan ya tashi yana cire maɓallan rigarsa da fara takawa a cike da nauyin jiki irin na mai doguwar tafiya zuwa ƙofar dake tabbatar da toilet ce. Ya jima a ciki sai gashi ya fito ɗaure da towel, da wani a hannunsa yana faman goge jiki, agogo ya kalla, sai kuma ya nufi wadrobe ya ciro doguwar riga. Babu ɓata lokaci ya shirya a cikinta ya saka sallaya a ɗan lungun gadon ya kabbara salla. Da alama yana son ƙarasa abinda ya rage na daren ne da ibadar daya sabarma kansa akowane dare, dan yana a wajen har akai kiran sallar farko, sannan ya miƙe zuwa wajen mirror ɗin ɗakin ya ɗauka turare ya saka ya fice a ɗakin gaba ɗaya.         Ana idar da sallar asuba daya fita yi massalaci ko ƙannensa bai bari sun ganshi ba ya dawo gidan, sashen dai ɗazun ya shiga, komai kuma na a yanda ya barshi babu alamar wani ya tashi yin salla ma. Haka ya sake wucewarsa ɗakin ɗazun, koda ya shiga saida ya sakama ƙofar key sannan ya wuce wadrobe ya fiddo wata leda babba mai ɗauke da zanen gado, fiddoshi yay da kansa ya shinfiɗa fari tas, ya saka rigar filo ɗaya ya cire jallabiyar jikinsa ya haye gadon daga shi sai boxer ya kwanta. Sai lokacin ya kai hannu ya kashe fitilar ɗakin duhu ya mamaye ko'ina............✍🏼      Hummm masu karatu, ga Zak-Shadow anan zai sha barci. Ga maƙiya can idonsu biyu suna shirya babbar ɓarnar tarwatsa komai harda shi kansa mai gayya da aikin😭. Su waye iyalan Zak-Shadow? Minene ainahin sunan Zak-Shadow? Su waye zuri'ar Zak-Shadow?. Wacece mace mai ciki da suka haɗu da su Zak-Shadow a shekarun baya har ta kasance cikin mafarkinsa saboda nauyin amana? Yaya su Major Imran Abbas babban amini kuma ɗan uwan Zak-Shadow zasu ƙare a jeji? Shin ƙungiyar DUHU zasu samu nasara kuwa?     Rigiji gabji, abubuwan fa da yawa suke, dan wannan labarin da kuke gani cakwakiyar cikinsa ta musamman ce. Akwai ɗan karan: ƙulli, makirci, gwagwarmaya, rikici, kitumurmura, nagartaccen zumunci, jajircewar wata JARUMAR UWA, JARUMTAR MAZAJEN FAMA, tsaftatacciyar soyayya mai narka zuciya da gaɓɓai, (kai ku kanku ko kun daina soyayya sai kun dawo ruwa a wannan gaɓar😂). Nasarorin masu gaskiya da sakamakon da zasu ɗauka.. Hoho abinfa ba'a cewa komai, dan ba lallai ku gane mi nake son sanar muku ba sai kun karanta KIƊA A RUWA MAI MAGANIN DODONNI💪. Wato labarin nan ko, hummm ni kaina fa..... To bari dai nayi shiru kawai🤭. Amma ku sani takowane fanni yazo da wani irin sabon salo ne da sai ka karanta kawai zaka gane. Ba cika muku baki nake ba, in sha ALLAHU da ƙarfin ikon ALLAH zakuga tabbacin fiye da abinda na faɗa muku. Ku dai ku kasance kawai a wannan tafiyar dan ta musamman ce😉🤤☺️☺️😋😋😀👍🏼. Free pages sun ƙare, masu buƙatar wannan labari sai ku garzayo.💃💃💃💃 ☺️Mutane na kuma masoyana ƴan bati dan ALLAH bana kar aci batin nan, kun san kuda Bilyn Abdull akwai amana soyayya take muku irin ta musamman ɗin nan. To kada ku bani kunya 500 ba komai bace ba, idan ka sauke haƙƙin wahalar wani kaima ALLAH bazai bar kowa ya cutar da kasuwancinka ba. Maza kuzo ku sayi naku, kuma in sha ALLAHU kasuwancinku zai yi albarka, ba kuma zaiba ƴan bashi damar riƙe muku kuɗaɗe ba da izinin UBANGIJI. Dan wannan kuɗin kaɗan da muke rainawa na littafi sai su zame mana ƙarfen ƙafa idan bamu sani ba. Babu wani hakki da yake mai sauƙi ga bawa koda na harar wani ne. Rubutu akwai wahala, bazaku gane bane, sannan muma business mukeyi kamar yanda kuke fitowa tallata hajojinku a media, dan ALLAH mutanena a daure kar a ci batin nan babu amfani🥰🥰🥰🥰❤️👍🏼. 😀Masoya abokan tafiya akoda yaushe jinjinarku ta musamman ne👍🏼, dan kuwa kuɗin na musamman ne a wajen bilyn Abdull, babu abinda zance sai godiya da fatan ALLAH ya haɗamu a aljannarsa muyita zumunci muna farin ciki. Yanda kuke ƙoƙarin sauke nauyi kuma ALLAH ya bama wanda suka ɗauki nauyin sayen kayanku damar sauke nauyi ta hanyar biyanku, ya sakama kasuwancinku albarka da kasuwa tako ina❤️❤️❤️❤️🥰🙏.           🙄Masu sauke mana littafi a arewa. Masu saka mana Littafi a website ɗinku bada izini ba, masu kai mana littafi YouTube bada izini ba su canja masa suna. Masu sayar mana da littafi a facebook ko WhatsApp su buɗe groups ko WhatsApp Channels suna amsar kuɗaɗen mutane kuzo ku saya a wajenmu da munyi posting ku ɗauka ku tura musu ku kuma alhalin bada izninmu ba, kuji TSORON ALLAH! KUJI TSORON ALLAH!! KUJI TSORON ALLAH!!!. Ku tuna zaku biya wannan hakkin da abu mai darajane a ranar da kuɗi basu da tasiri, a lokacin da ya ƙure na neman yafiyarmu, a lokacin da aikin lada keda muhimmanci a gareku, kuke gudun ƙarin zunuban wanda kuka zalunta. Bance ku daina ba, ba kuma zan roƙeku ku daina ba, amma ku shirya da shiri mai girman gaske, domin akwai ranar DANA SANI, zata zo ko ka yarda ko baka yarda ba, ƙilama tun a nan duniya zaka fara girba daga naka sakamakon. Idan kukazo garemu zamu iya tsara yanda zaku amshi lirtatanmu cikin mutunta juna ku saka a duk inda kuke so batare da kunci hakkin kowa ba. Dan haka shawara ta ƙarshe. Masu Website, masu kai books Facebook, masu buɗe group a WhatsApp suna saidawa. Dama masu bi da shi tako wace hanya kuna da damar zuwa garemu, in ba haka ba kuma zamu cigaba da kwana kan buzu😂 muna kaima ALLAH kukanmu a kanku🥲, abinda baku sani ba kowanne irin mugunta bata hana nasara, sannan baya hana mai nema samu daga abinda UBANGIJI ya ƙaddara masa, kuna ɗorama kanku nauyi ne batare da mu kun ragemu da komai daga abinda ALLAH ya ƙaddara garemu ba, dan nasara ma kuke ƙara mana kune baku sani ba wlhy, dan ALLAH karku bari hakan ta faru. Yanda bana fatan komawa ga ALLAH da hakkin kowa, haka bana fatan kowa ya koga ga UBANGIJI da hakkina, mu zama masoya na gaskiya musulman ƙwarai kuma ƴan uwan juna masu son cigaban kansu dana ƴan uwansu. Fatan alkairi a gareku a duk inda kuke😀🥰🥰❤️❤️❤️🙏👍🏼. _______________ _Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER🇳🇪- (500 Fcfa)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899* ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_*