********************** ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** ************************* ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ************************** [14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #bff#dimension#parallelworld#zombies apocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ^~^ Hello there beautiful souls..Good morning sweethearts❤️I know I’ve been gone for a long time buh I have gained more writing experiences I’m rewriting a lot of this..so I’m advising you to re-read this super story @wink ~* Chapter 1: The beginning of the beginning. 22nd October 1984 M.M Jalal Hospital 11:00pm Doctors ne wajen su biyar akan patient din saidai duk iyakan kokarin su da binciken su basu gano abinda ke damun matashiyar budurwar ba. Tana dauke da cikin wata bakwai da yan kwanaki wannan dalilin yasa doctors din basuyi tunanin haihuwa zatayi ba, kuma yau ne rana tafarko dasuka fara ganinta shima daya daga cikin nurses din ce ta ganta awaje cikin mawuyacin hali daga nan fa doctors sukayi kanta saboda ainahin mai hospital din ya budeshi ne saboda taimakon talakawa marasa karfi. Wani irin nishi tafara mai ban tsoro, cikin mintuna kadan tafara nakuda,nan da nan kukan jaririn yacika dakin su kansu likitocin mamaki sukeyi saboda cikinta bai isa haihuwa ba kuma wani abin mamakin yaron da girmanshi tamkar dan wata 9. Daya daga cikin doctor din ne ya karbi yaron da nufin gyarashi zuciyan shine ta buga ganin yaron kamar dariya yake masa mazewa yayi yafice yabar sauran suna gyara ta. Doctor Salim ne yafara gyara ta saidai cak ya tsaya jin tana wani irin gurnani gaba daya kanta sukayi tareda sauran nurses din kowa yana kokarin gano abinda ke damunta. Wani irin bakin amai tafarayi take idanunta suka sanja color yazama ja jajur, jikinta wasu irin jijiyoyi green da yellow suka fara fito mata, wani irin kalar sauti tafara marar dadin sauraro...likitan dake gefenta takama da wani irin sauri kafin yayi wani abu harta sa bakinta a wuyansa tana shan jinin sa,tareda cin naman wajen ganin hakan ya firgita sauran doctor's din kokarin guduwa sukeyi amma sam kofar taki budewa cikin karamin lokaci duk ta cije su. Bangaren Doctor Bilal kuwa bayan yakarasa dakin yara da baby din jikinsa yafara goge masa gani yayi yaron ya bude idon shi yazama dark red bakinsa wasu irin manyan hakora(fangs)suka bayyana, tsalle yayi yakama wuyansa,yasa bakin shi yana cizo tareda shanye jinin jikin shi. After 30mns. Duk wasu patients, doctors,nurses,metrons,guards,dake cikin asibitin sun zama zombies, mutum daya ne kadai yarage wato mamallakin asibitin Doctor JALAL. Shima saboda yana can cikin office din shi hankalinsa ba karamin tashi yayi ba ganin abinda ke faruwa a cikin CCTV camera,gaba daya asibitin ya hargitse harta karnukan dake asibitin sun sanja suma sun zama zombies din. Saboda tsabar masifa dakuma son shan jinin mutane saidai kaga suna cire jikinsu sunaci.... Waya ya dauka yakira wata number sun dade suna magana sannan yakashe wayan gaba daya kuma daidai lokacin ya farajin motsinsu a wajen kofar...Maida kallonshi yayi kan laptop din dake gabanshi cikin sauri yake typing bayan yagama ya kashe ta gaba daya yasa a cikin jaka sannan ya jefata can gefe guda..Wani irin sauti yafaraji alamun cewa sunzo inda yake cikin sanda yake tafiya harya isa babban kitchen din asibitin, sa’ar shi daya duk cooks din da suka zama zombies sunfice daga kitchen din,saidai ga jini nan yayiwa kitchen din shimfida. Katon gas din dake gabansa ya kunna duka guda bakwai din nan da nan yafara fita kuma daidai lokacin zombies din suka shigo kitchen din. Saida yabari duk sun gama shigowa sannan ya kunna lighter,cikin minutes gaba daya asibitin yakama da wuta. ~ * 30yrs later "My name is Hassana Musa Muhammad wasu suna kirana da Hassy. I always believed that life in another planet exists, babu abinda nafiso a rayuwata irin jin labaran Al'ajabi, ina bala'in son ganin abubuwan mamaki, kuma inason kafin rayuwata ta kare naga wani babban abin mamaki saidai bansan ta ina zanfara ba a cikin wannan duniyar tamu bansan ina zanje naga abin mamaki ba wannan shine babban burina,idan har.." bata karasaba taji ance "To idan kingama shashancin kizo Abbah yana kiranmu." Kallon system din gabanta tayi bayanta ta turo baki tace "gosh she’s so annoying," Daya daga cikinsu tace "wace ce ita?" Hassy tace "Aunty nace ita gani take wannan abin da nake fada shirme ne nikuma inaji ajikina cewa tabbas zanga wani abun mamaki a rayuwata.... so guy's I have to go now, see you later." Tana gama fadar hakan tayi disconnect call din ta mike ta tafi parlourn... Hassy kenan wadda take video call da friends dinta kuma duk lokacin dasukeyin video call saita fada musu burinta..wanda duk yake tareda ita yasan cewa wannan shine babban burinta...she wants to be in another world..and tayi believing cewa akwai wata duniyar bayan wadda take ciki yanzun. So here is the first chapter hope you like it!? @NM🦋♥️ [14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #bff#dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 2: Mom. Free Page *I assured you that bazakuyi danasanin siyan WANI GARI BA saboda labarin daban ne kuma salonsa daban ne* ~* Kallonsu yayi yace "Khadija, Hassanah, kubani hankalinku nan ku nutsu kuji abinda zan fada muku, da niyata shine na aurar daku amma yanzun nafasa saboda na lura cewa a wannan zamanin da muke ciki matan da basuyi karatu ba suna fuskantan matsala da wulakanci a gidajen aurensu, shiyasa muka yanke shawara nida Mom dinku akwai wata school da aka bude kwanan nan kuma tanada kyau, sosai saboda nayi bincike akan school din saidai ba a wannan state din take ba." Gani sukayi Khadija ta mikewa tafara kuka kamar wata yarinya tana cewa "nidai babu inda zanje banason rabuwa da gida banason rabuwa da Mom" Ita kuma Hassy wani irin sanyi taji aranta ko babu komai zata bar gida, sannan itama zata samu yancin kanta wataqilan idan taje school din zata samu ta cika babban burinta.... Mom ce ta shigo parlourn tace "aa hayaniyar me nikeji haka? Khadija lafiya kike kuka?" Da gudu taje ta rungume ta tana cewa "ba Abba bane ba wai boarding school zai kaimu nikuma banaso,banson rabuwa dake." hawayen ta goge mata tace "karki damu Dijan Mommy babu wanda zai takura miki tunda bakiso babu wanda zai kaiki aini tun farko ma bansan cewa school din ba anan garin take ba, banyi tunanin boarding school bace ba." kama hannunta tayi zama tayi akan kujera itakuma Khadija tazauna akasa sannan ta daura kanta akan kafar Mom din... Maida kallonta tayi kan Hassy "kefa kinaso ko bakison school din??" Da sauri ta gyada kanta... Bata rai tayi tace "magana za kiyimin bawai girgiza kai ba tayaya zan gane abinda kike nufi?" "Eh Mom inaso." wani kallon banza ta watsa mata taci gaba da cewa "to ai shikenan garama hakan masamu mu huta." Kallon Abba tayi tace "to kaji dai da kunnenka Khadija tace batason school din yawwa ka nemo mata wata anan cikin garin" bata jira amsarshi ba takama hannun Khadija suka bar parlourn.. Kallonta yayi yace "Hassanah karki damu daduk wani abu daza ayi miki a cikin gidan nan kiyi hakuri wata rana sai labari, karkisa damuwa aranki kinji?" smile tayi tace "babu komai Abbana karka damu" shima murmishin yayi yace "yawwa Allah yayi miki albarka, In Shaa Allah nan gaba za suyi alfahari dake." washe baki tayi sosai tace "Amin Abbanah nagode sosai." Bayan ta shiga dakinta kan bed ta kwanta zuciyanta yana mata wani irin zafi batasan meyasaba sam Mom bata sontaba indai kaga fara'arta to tana tareda Khadija ne koshi Abban zaman hakuri yake da ita... Wani tunani tafara kodai ba itane Asalin mom din taba? tunda ko a tarihi bata tabajin inda uwa ta tsani yar taba ai, wani irin kuka ne yataho mata nanta kife kanta taci gaba da kukan. Bude kofan akayi bata dago ba saboda tasan Khadija ce awani shekale take kallonta sannan taja tsaki tafice daga dakin, Bayan kmar 2mns sai gasu sundawo itada Mom. Jin Mom tana salati yasa Hassy dagowa, Daidai lokacin mom ta dafe kirjinta tace "nashiga uku mezan gani haka Hassana, Mene kika shigo daki kike kuka salon nayi baki ace ina musguna miki ko?" cikin dashewan mura tace "kaina ne ke ciwo shiyasa, amma don Allah Mom dagaskene kene kika haifeni?Dagaske ne cewa...." cikin fushi tace "Yimin shiru munafuka waima tsaya yaushe kika koyi iya tsara magana haka ai bansan cewa kin kai haka ba harkin kware a iya karya koh?? Bayan haka ma wato tsareni kikesonyi da tambaya koh? to bazan amsa miki ba, maza tashi yanzun nan kije ki daura girkin dare kuma karki kunna gas kije can waje ki hada ice." Hijab tasa cikin sanyin jiki ta fice daga dakin. Gaba daya ta hada zufa idanunta sai hawaye yakeyi saboda hayakin icen sam a rayuwanta bata iya hada wutan ice ba, kuma dama yawanci haka mom take mata bata bari ta hada wutan harsai taga tasha wahala sosai sanann take zuwa tace taje ta daura a gas saboda dama tun farko icen danye take bata. Yanzun ma saida taga ta wahala sosai sanann tace taje kitchen ta daura.... ~* Yau takasance ranan tafiyanta school duk wani abun da students zasu bukata an siyamata wajen mom taje domin tayi mata sallama itadai ba haka taso ba saboda saiyanzun take nadama dama tun karfo ta hana tafiyan amma yanzun batada mafita .... Saurin fitowa tayi daga dakin tace "tsaya anan karki shigomin daki" wani banzan kallo tayi mata taci gaba da cewa "to Allah ya kiyaye hanya" kunnenta takama ta murda tace "saura idan kinje karkiyi karatu kokuma kizauna kina wannan shashancin dakika saba wallahi idan baki kawo good result ba zakisha mamakin hukuncin dazan dauka akanki, wuce kibani waje." Sannan tayimata rankwashi akai, ficewa tayi jikinta a matukar sanyaye gefe guda kuma na zuciyanta cike yake da farin ciki. Bayan mota tashiga nan driver yaja suka tafi amma ita kadai saboda Abbansu baya gari wata muhimmiyar tafiya takamashi jiya da daddare... ~* YAMAN SCIENCE ACADEMIC Daidai school gate din motarsu tayi parking bayan anyi checking sannan aka bude musu babban gate din school din, Masha Allah Hassy tace aranta ganin kyau da tsaruwar school din... Direct Principal Office sukaje bayan angama mata komai nan aka bata Pink House a matsayin nan ne hostel dinsu. Nan principal tasa aka kaimata kayanta hostel din ita kuma ta shiga class. Bayan antashi daga class principal office takoma saboda batasan inane hostel din da aka bata ba, sawa tayi aka kira mata house captain din suka tafi tare. _School din hade take boys and girls_ Babban daki ne students sunkai su 50 wata kwana ta nuna mata tace nan ne kwananki gado ne saikuma locker a ciki duk ta jera kayan provision dinta. Da dare kasa bacci tayi wani irin kewan gida takeji duk tsanani da wahalar da mutum yakeji a gidansu tofa babu inda yakai nan muhimmanci, pillow tayi hugging tace I missed you Appa. Washe gari yakasance week end ne yau Saturday kuma duk ranan Saturday students suna zuwa sport field, takusa da itane tace "kisa sport wear dinki saimu tafi tare tunda naga ke new comer" ce smile tayi tace "thank you! sunana Hassanah Musa Muhammad Kefah?" "Zaynab Muhd nike, nice to meet you Hassy" Smile takarayi tace "I'm glad that I found you...nice to meet you too." _@Sport Field_ Zaynab tace "wani wasa kikeson yi?" Hassy kam tunani tayi kadan "inason volley ball kefah?" Zaynab tace "lah! nima shi nikeyi saimuje asa sunanki." _"Mega!"_ _"Mega!!"_ _"Mega!!!"_ Haka students din suke ta fada da karfi, wanda hakan ne yajawo hankalin Hassy kansu..she is curious shiyasa ta tsaya amma ga mamakinta sam wadda aka kira da Mega din bata juyo ba saima kara gyara tsayuwa takeyi half face dinta rufe da bakin kyalle sannan gashin kanta tayi parking dinsa sai wata transparent blue hula akanta, jikinta sanye da sport wear, navy blue color. she looks so beautiful. daya daga cikinsu ne yace "kutsaya! kutsaya!, badai so kuke taci wannan game din ba? to bari kugani" "MERAPATI!!!" Yace da karfi nan sauran students suka dauka *Merapati* *Merapati* Wani irin murmishi takeyi cikin wani salo tafara cire kyallen fuskanta sannan tacire ribbon din dake daure a kanta,take gashin kanta ya zubo zuwa kasan shoulder dinta,juyowa tayi nan fa students sukaci gaba da ihun kiran sunanta.. In a slow motion komai yafaru akan idon Hassy, kallon Zaynab tayi cikin mamaki tace "wacece Merapati? ,Kuma meyasa students suke ihun kiran sunanta haka?" Thank You For Reading My Story!! @NM__🦋♥️ [14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #bff#dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 3: Basma The Girl Who Love Watching Cartoons. Dedicated To Mega Aura Pangesti (Merapati). ~* Smile Zaynab tayi tace "asalin sunanta Mega Aura Pangesti, amma tafison akirata da Merapati she is the most popular student a cikin school din kowa da kowa sonta yake saboda tanada kirki sosai babu ruwanta kowa natane" tabe baki Hassy tayi tace "from your information,She is very arrogant. and rude girl, And I dont like such people's, wait waima meyasa muke magananta?" Zaynab tace "sam batada girman kai ko kadan saboda ta wuce duk yanda kike tunani amma da sannu zaki gane hakan..muje to" Nan suka tafi inda ake wasan volley ball. Bayan angama wasa kowa takoma hostel wanka sukayi sannan suka tafi dinning hall domin yin breakfast, Babban hall ne saikuma dinning table's mai kujeru guda shida hakan na nufin duk table daya mutane 6 ne zasu zauna. Bangaren maza da daban na mata daban amma kuma duk cikin hall din ne. Zaunawa sukayi bayan Zaynab ta gabatar da Hassy a matsayin new friend dinta. Hall din yayi shiru bakajin komai sai motsin spoon's, _"Ah-ah-oh-oh-ah-ah oh-oh-oh I can hear you but I won't Some look for trouble while others don't There's a thousands reasons I should go about my day.And ignore your whispers, which I wish would go away, oh oh oh..._ _"You're not a voice! You're just a ringing in my ear, And if I heard you, which I don't I'm spoken for, I fear, Everyone I've ever loved is here within these walls I'm sorry,secret siren, but I'm blocking out your calls I've had my adventure, I don't need something new I'm afraid of what I'm risking if I follow you.."._ _"Into the unknown Into the unknown Into the unknown Ah ah oh oh....."_ Cak ta tsaya dayin wakar ganin duk student's sun dago sun zuba mata ido, hannunta tasa akan bakinta alamun ta manta da karfi tace "oh my gosh I'm sorry guy's,,," nan fa students suka fara dariya dasauri ta tafi wajen data saba zama duk kunya yakamata.. Kallon Zaynab Hassy tayi tace "to ita kuma wannan wace? Gaskiya wanann school din taku akwai students kala kala." "Sunanta Fatima Salis Muhammad amma anfi kiranta da Basma,Kinga duk school din nan babu wanda yakaita iya waka kuma kinsan me wakokin ma irin na cartoons," kasa kasa tayi da murya tace "kuma batada friends ko daya." Dariya sosai Hassy takeyi tace "cartoon kuma? Yanzun wannan katuwar ce take kallon cartoon?" Cigaba tayi da cin abincin sannan tadago "nibansan mezata fahimta a cartoon ba saikace wata yarinya." dariya Zaynab tayi tace "kedai naga alamun babu wanda zai birgeki a school din." Bayan sunkoma hostel nan fa students kowa ta shiga harkokinta masu wanki nayi masu kitso nayi.. ~* Cikin sauri take shiryawa saboda tayi late nan tahau tattara books din ta dasu cleaners pencils tana zubawa a bag dinta,da sauri ta fito jitayi tayi karo da mutum duk paper's din dake hannunta sun zube a kasa tsugunnawa tayi tafara tattarasu itama Hassy tayata tafarayi sannan tace "I’m so sorry ki hakuri wallahi ban kula dake ba ina sauri nayi late ne" smile tayi tace "babu komai" ci gaba da tafiya tayi. Da sauri ta karasa kusa da ita tace "amma bantaba ganinki ba ke new comer ce koh?" "Eh ranan friday nazo," hannu ta mika mata tace "If you don’t mind inason ki zama kawata saboda duk school din nan banda kawa,They said I am ugly,freak,talkative, but I'm not,I love making new friends, I love talking to new people, I don't know why people's don't like me!" tace a hankali Hassy kuwa a ranta tace because you are talkative... amma a fili tace "babu komi karki damu" murmishi tayi tace "nagode sosai kuma naji dadi saboda wannan shine karon..." Saurin katseta tayi tace "babu komai." Shiru sukayi sukaci gaba da tafiya duk inda suka wuce saikaji ana kus kus ganinsu tare saboda kowa yasani kullum ita kadai take rayuwanta. "Oh my goshhhh I forgottt What's your name?" "Hassana M Muhd" tace a takaice, murmishi tayi tace "nice name nikuma sunana Fatima Salis Muhammad...you can call me Basma,,," Saurin kallonta Hassy tayi aranta tace ya akayi nakasa ganeta tun farko? Bayan sun shiga class gani tayi ta tafi can baya ta zauna hakan yasa Hassy cewa tadawo sit din gaba badan taso ba tadawo,saidai kafin ta zauna taji an fisge ta ta baya nan fa class suka hau dariya da shewa juyowa Hassy tayi ganin wata student daban kallo daya zakayi mata kagane cewa batajin magana wani banzan kallo tayi mata tace "who the hell are you? meyasa zakisa tadawo gaban sit? Kaf class din nan kowa yasani karshen bench nan ne wajen zamanta, saboda da can wajen ta dace" takarasa maganar cikeda da izza. Hassy kam da mamaki take kallonta wannan wace irin school ce? Hannu tasa da niyan jan Basma saidai kafin takarasa taji an rike hannun... Juyowa tayi taga Hassy ce ta rike mata hannun tace "karki kuskura ki tabata kuma tanada yancin zama a duk inda taso,, don haka baki isa kibata umarni ba." Janye hannunta tayi tafara clapping hands dinta tana cewa "wow..wow ina kuke yan group? Kuzo kuga abin mamaki yau acikin class din nan ansamu mai tankawa Ruky." nan fa gang dinta suka matso ciki harda maza kallonsu tayi "naga alamun tanason shiga abinda babu ruwanta don haka kuyi mata service" tana gama fadar hakan tasamu desk ta zauna. ganin hakan yasa Basma mikewa tashiga gabansu tace "please don’t touch her, saboda batasan komai ba rigimata iyaka..." kafin ta karasa akayi wurgi da ita gefe guda dasauri Hassy taje ta dagota tace "are you hurt?" Kanta kawai ta girgiza Hannu taji a kafadarta cikin bacin rai ta mike tana juyowa ta zabga masa mari sannan tasa kafanta tayi masa wani irin bugu a ciki nan ya baje a kasa.. Ganin hakan ya fusata sauran gangs din sukayi kanta saidai kowa naushi daya take masa saidai kaga sun zube a kasa. Nan fa class din suka hau ihu da tafi suna jinjina mata ko babu komai yau ansamu mai tankawa gang's dinsu Ruky saboda sam basajin magana ga shegen tsokana saboda suna ganin sunada karfi kuma they are popular and rich. Bayan antashi daga class suna tafiya Basma takalli Hassy tace "thank you,thanks for everything you..." saurin dakatar da ita tayi tace "kibar godemin since we are friends we have to help each other,And i just did that." murmishi tayi tace "yes you’re right duk da haka nagode." Tundaga ranan suka zama best friends,duk inda kaga daya to zakaga daya yanzun Basma ta sake babu mai takura mata kuma suma sun zama popular a school din. Bangaren su Ruky kuwa yanzun andaina tsoronsu suma duk jikinsu yayi sanyi so suke su kulla kawance dasu Hassy amma basuga fuskaba. Sosai suke shige musu yanzun ma indai sunje Hall saidai kaga su Ruky sundawo table dinsu duk dan su samu shiga. Gaba daya student's sun shiga busy saboda akwai wani shiri dasuke son gabatarwa a karshen term din kuma suna son abasu izinin zuwa wajen school saboda duk cikin school din babu inda yadace ayi shirin... Su Ruky ne kan gaba wajen zaben yan wasa mutane 50 sukesu amma sai Ruky tace abawa Hassy ta zaba itakuma tace batasan suwaye suka dace suyi participating ba kawai su zaba da kansu list din Ruky tabata tace "Dan Allah ko mutum daya ne tazaba" karba tayi tafara bin list din da kallo Idanunta ne yatsaya akan sunan Mega Aura Pangesti aranta tace Mss Arrogant kasa taci gaba dayi saikuma tadawo kan sunan Mega tayi tick mika mata tayi ganin sunan datayi ticking Ruky tace "Kai Merapati kika zaba? To Allah yasa taje don batason zuwa kowani excursion." Tabe baki Hassy tayi aranta tace "dama ta ina zataje tana fama da girman kai?" Bayan antashi daga evening prep a hanyarsu takoma hostel Hassy,Basma,Zaynab,Ruky tafiya suke suna labarin malamin maths dinsu dakuma yanda suke mamakin basa ganewa sam jisukayi ance "Ruky!" tsayawa sukayi dukansu suka waiwaya Merapati ce. Cikin nutsuwa take takowa harta iso kusa dasu daya bayan daya take kallonsu sannan ta tsaida idonta akan Ruky tace "meyasa kika sa sunana a yan zuwa excursion?kin manta cewa babu abinda na tsana kamar zuwa excursion how dare you put my name on the list?" Ruky kallon kinma rainawa kanki wayau tayi mata sannan tace "oops sorry mss bani nasa ba Hassy ce tasaka" kara kallonsu tayi tace "a cikin ku wacece Hassy?" kut jimin mata saikace wata boss Hassy tace aranta. "erm nice amma tunda bakiso za a cireki tunda babu lalle babu dole..." Shiru tayi tana kallonsu saikuma tace "kawai kubarshi tunda kunsa amma a kiyaye gaba, bakowani abu ne nike shiga harkansa ba." Tana gama fadar hakan ta juya tabarsu baki bude tsaki Basma tayi tace "bantaba ganin yar rainin hankali kamar wannan yarinyar ba, wasu ma nema suke asa sunan su amma basu samu ba sai ita dontaga ansa nata" mtsw takara jan tsaki. Hostel suka tafi zuciyoyin su cikeda mamakin Merapati Kamar yadda suka tsara hakan ne yakasance domin kuwa duk wasu shirye shirye sungama kuma kwana biyar zasuyi a inda zasuje din duk wanda za ayi tafiyan dasu kowa ta hada kayanta a suitcase saikuma school bag inda suka zuba su toothpaste and toothbrush,perfume,lotion,torchlight,dadai sauran abubuwan bukata. Principal Office sukaje anan takara ja musu kunne akan su kula saboda inda zasuje wajen babu mutane cikin daji ne sosai tsawon shekaru babu wanda ya zauna a wajen. Mota suka shiga sauran students sukayi musu fatan nasara....Daga nan driver yaja suka tafi.. Now The Story Begins. @NM__🦋♥️ [14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #bff#dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 4: Excursion. A kalla sunyi tafiyan 8hrs sannan suka isa ainahin inda za suje din, kowa a gajiye yake sallah ce kadai take tsaida su. Bayan kowa ya sauka da kayan sa nan fa mazan suka fara hada musu tent su kuma matan su ka fara yi musu girki kafin magrib sun gama komai kuma ko wani tent daya mutum uku ne nan fa akabawa Hassy Merapati da Basma tent daya, suitcases dinsu suka shigar ciki, masu wanka sukayi sannan sukayi sallah a jam'i. Nan fa suka fito wajen tent din gaba dayansu, dama tundazun mazan sun samo ice, decorating din wajen sukayi da wasu bulb sannan suka kunna icen a tsakiya bayan sun zagaye icen da kananun kujeru sosai wajen zai birge mutum, gaba dayansu kowanne ya samu waje yazauna. Kallon Hassy Ruky tayi tace "yakamata afara bawa kowa abinci tunda yanzun dare yayi babu abinda zamuyi gashi wajen bamu san yanayin saba gara kowa yaci abinci yaje ya kwanta." mikewa sukayi suna zuba abincin a plate wasu kuma suna mikawa na zaune tareda soft drinks. Harsaida kowa yasamu sannan suma suka zuba nasu. Bayan angama cin abincin Ruky ta kallesu taje "kowa yaje ya kwanta." Daya daga cikin students din mai suna Kabir yace "gaskiya bamajin bacci kuma a ganina bai kamata mu kwanta yanzun ba Let's make a lot of unforgettable memories,let's have fun guy's....." shewa suka fara suna cewa mun yadda da hakan, Kallonsu Kabir yayi yace a "cikinku wane kokuma wace ta iya waka?" Gaba daya kallon Basma sukeyi dagawo tayi a hankali tace "What?!" kamar hadin baki dukansu suka fara cewa "Basma!Basma!” Kallon Hassy tayi ita kuma tayi mata alama akan tayi wakan. Mikewa tayi tace shikenan zanyi muku...cikin melodious voice din ta tafara... _Someday this could be,this could be ordinary._ _Someday could we be something extraordinary?_ _You and me side by side yeah yeah out in the broad daylight if they laugh we'll say we're gonna be someday someday someday._ _So let them talk if they wanna, let them talk if they're gonna,we're gonna do what we wanna let them talk let them talk if they wanna they wanna._ _Someday this could be this could be ordinary, Someday could we be something extraordinary?_ _You and me side by side yeah yeah out in the broad daylight if they laugh we'll say we're gonna be someday we're gonna be._ _Someday someday someday we're gonna be someday we're gonna be someday.._ mikewa sukayi suna yimata tafi da karfi nan fa duka suka shiga filin kowa yana wakar datazo bakinsa kallo daya zakayi musu ka tabbatar suna cikin tsantsar farin ciki. basu kwanta ba sai wajen 12:30am. Bayan sun shiga tent dinsu Hassy tace "Gaskiya Basma kin iya waka sosai itakuma wannan wakar awani cartoon akayi ta?" murmishi tayi tace "no ba a a cartoon akayi ba sunan film din Zombies" Smile itama tayi tace "amma wakan tayi dadi sosai" kallonta tayi tace "ahaka ma ba duka nayi ba..its one of my favorite songs" Daidai lokacin Merapati ta shigo kallo daya tayi musu ta dauke kanta "anata ganin girman kai ne dasu" *LMAO 1-1 kenan.* Washe gari bayan sun kamalla abinda zasuyi nan suka shirya domin zuwa cikin dajin su duba inda yafi dacewa suyi shirin. Basuyi wata tafiya mai nisa ba suka ga wani tsohon gida kallo daya zakayi masa kagane cewa andade ba a shiga ba, nan wasu sukace a shiga a duba wasu kuma sukace aa kar a shiga saboda Principal tace su kula sosai ganin hakan yasa Merapati cewa "duk wanda yakeson shiga ya daga hannunsa " Hassy ce first aganinta wannan itane damarta taganin abun Al'ajabi. Mutum 25 ne suka daga hannu. Saikuma wanda basu so mutum 24 kallon Merapati Hassy tayi tace "saura ke wanne kika zaba?" Kamar bazatayi magana ba saikuma tace "nima na zabi kar... Saikuma tace Nazabi a shiga din, amma da zarar munga wani abu wanda baidace ba zamu fito sannan kuma gaba dayan mu awaje daya zamu tsaya ma'ana babu wanda zai shiga wani waje batareda damu ba idan kunyadda da wannan to idan kuma baku yadda ba bazamu shiga ba and that’s final" nan dukansu sukace sunyadda. Nan fa suka nufi cikin gidan bayan Merapati ta ciro camera dinta nan tafara daukan pics. Cikin gidan yanada duhu sosai ga yana duk ta rufe ko ina hakan yasa suka fito da torch suna haskawa, bayan kamar minti 5 basuga komai ba daidai lokacin Basma ta kwalla kara ganin skull💀 (kwarangal😂), Ruky tace "menene mekikagani" ajiyan zuciya tayi tace "wallahi na tsorata ashe skull ne." Bangaren Hassy kuwa zamewa tayi tabi wata hanya daban nan taci gaba da daukan pictures motsi taji a bangarenta cikin dakewa takarasa wajen haskawa tayi da torch nan taga wani abu bakin kirin,hannunta takai ta yaye yanar data rufe abin cikin mamaki tace "laptop bag??" cikin sauri ta dauka bayanta goge sannan ta rataya a hannunta,Sannan takama hanyar fitowa. Bayan sun fito daga gidan nan fa Basma ta lura Hassy bata taredasu cewa tayi "wait guys banga Hassy ba?" Merapati tace I don’t get it kamar ya baki gantaba?" Dafe kai tayi taci gaba da cewa "Aishh this girl bataji wato duk irin warning din danayi saida ta karya doka," Kafin Basma tabata answer gani sukayi Hassy ta fito daga gidan cikeda tuhuma duk suke kallonta... Smile tayi tace "why are you all looking at me like that...?" basu ce komai ba hannun Basma takama suka ci gaba da tafiya. Bayan sun isa inda suka kafa tents kowa ya shige saboda tsakar rana ce kowa ya debo gajiya...Kallon Basma tayi tace "zokiga abinda nasamo acan" sannan ta bude system din, Basma tace "amma kina ganin tanayi kuwa? Saboda wajen fa kamar anfi 30yrs babu wanda ya zauna gashi duk yayi yana.." Smile tayi tace "bari dai mugani Allah yasa takawo." Kunnawa tayi amma sam taki kawo wa cigaba tayi da danna switch din amma yaki kawowa tuni Basma tafara mata dariya tana cewa "aidama nina sani bazata kawo..." Saidai kafin takarasa gani tayi laptop din takawo..amma babu chargy sosai nan tafara bincike idanunta ne yasauka akan wata folder shiga tayi short note tagani cikin nutsuwa tafara karantawa a fili "Sunana Doctor Jalal Mahmud Muhammad inason duk wanda yaga wannan sakon nawa yayi gaggawar barin wajen saboda wajene mai cikeda hadari." Dariya Basma tayi tace "kujimin mutum kawai yanason bama mutane tsoro shiyasa zaice hakan," Hassy tace nikuma a ganina dagaske yake saboda a inda nasamu wannan system din wajen baki gani ba abin tsoro sannan gawasu irin bakaken abubuwa kamar mutane amma kuma sun kone da wuta...Dole nakoma wajen nan saina gano ainahin abinda yafaru.." Merapati ta kalleta tace "nima zan iya yadda da abinda yace saboda kalli nan kigani mika mata camera din tayi nan suka fara kallon pictures din data dauka indai mutum ya nutsu zaigane cewa tabbas mutane ne amma kuma sun sanja halitta, wani picture ta nuna musu tace kunga wannan shine gidan da mukaje amma kalli da kyau zakiga wata mata sanye da fararen kaya daga tsakiya gefenta kuma zakuga wani abu shi ba bat ba kuma shiba tsuntsu ba, duk yanda akayi akwai wasu halittun anan wataqilan ajlanu wata qilan kuma vampire's.." Hassy tace "bana tunanin vampires ne saidai aljanu din amma koma menene anjima zan koma saina gano mene acikin gidan can." kallonsu Merapati tayi tace "amma karku fadama kowa bnson nasa kowa a matsala,domin ni kadai zanje" Basma tace "kinsan kuwa hakan bazai yiwu ba bazan taba bari kije ke kadai ba komine saidai ya same mu atare." Nan fa suka fara sa'insa Hassy tana cewa bazata bita ba ita kuma tana cewa saita bita. "Both of you shut up!" Merapati tace da karfi da mamaki suke kallonta taci gaba da cewa "nima kuma bazan taba barinku kuje ku kadai ba" Basma tace "kekuma a mtsayinki nawa?" Wani banzan kallo tayi mata tace "A matsayina na wadda kuke sharing tent tare.." _1:00am_ Bakajin motsin komai sai kukan tsuntsaye dama already sungama hada kayansu cikin sanda suke tafiya harsuka fice daga ainahin inda suke. Direct gidan suka nufa saidai ga mamakinsu yanzun basuga gidan ba duk iyakan kokarin su nagano gidan amma sama ko kasa basu gani ba.harsun juya sun fara tafiya Merapati tace "ku tsaya,ku tsaya bakuji motsi ba?" Hassy tace "motsi kuma a ina?" "Shhh" tace sannan taci gaba da tafiya wasu flowers tagani kuma ta tabbatar daga nan motsin yake fitowa cikin karfin hali ta bude flowers din ajiyan zuciya tayi ganin cewa water fall ne, daidai lokacin su Basma suka karaso wajen, tunda suke basu taba ganin water fall mai kyau din wannan ba, ruwane mai balain hasken blue sannan a samanshi ga fure nan kala kala,ga wani kamshi na musamman yana fitowa daga cikin ruwan. Basma tace "kai gaskiya ruwan nan ya birgeni kujirani nayi wanka" tana gama fadar hakan ta cire kayanta underwear kadai tabari ta shiga cikin ruwan. Ganin haka yasa itama Merapati shiga cikin ruwan...dariya sukeyi dukansu,suna watsawa jikinsu ruwan. Hassy ma ruwan ne yabata sha'awa itama shiga tayi saidai ita can gefe daban taje...Bayan 5mns Hassy tafara ganin wani haske acan gabanta hasken yanata circling shi kadai juyowa tayi tace "Basma Merapati zoku gani," matsawa sukayi suna kallon wajen, nan take gaba daya ruwan yafara motsawa da karfi ganin hakan yasa su kokarin fita amma sam sun kasa nan take wani irin hadari ya hado gawata irin tsawa da walkiya da akeyi gaba daya ruwan ne yahau girgiza manya manyan igiyar ruwa suka fara fitowa... Wata irin tsawa akayi cikin seconds komi yakoma daidai tamkar babu abinda yafaru... I Hope You Guys Enjoyed This Story!!! @NM__🦋♥️ [14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #bff#dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 5: Something Happened. Free Page ~* Merapati ce tafara bude idonta a hankali harta bude shi gaba daya, da sauri ta mike daidai lokacin Basma ma ta bude nata idon nan suka hau dube duben Hassy can gefe suka hangota da sauri suka ka rasa wajenta Basma ce tafara girgizata bude idonta ta yi saidai dishi dishi take gani hakan ya sa takara rufe idon, girgiza ta takeyi tana cewa "please wake up! kitashi Don Allah..." Sai a lokacin Merapati ta lura da ciwon dake hannun Hassy kallon Basma tayi tace "Oh my God she's bleeding" mikewa tayi tafara duba bags dinsu can gefe ta hango su da sauri takarasa ta dauko karamar first aid kit. _It's important to have a well-stocked first aid kit a duk lokacin daza kuyi tafiya mai nisa kokuma a gida ma so you can deal with minor accidents and injuries._ Cikin karamin lokaci ta gama treating din hannun Hassy. _After 1hrs_ Dukansu suna zaune kowa da abinda ke ranta Basma tace "Merapati kina ganin zata tashi kuwa?" Merapati tace "Basma karki damu zata tashi saboda ciwon dataji bashida yawa kawai ta zubar da jini ne sosai shiyasa" Bude idon ta tafarayi fes ta sauke su akan su Basma da Merapati matsowa suka farayi suna yimata sannu dukansu tambayanta sukeyi yaya jikin nata yakuma takeji ajikinta? murmishi tayi tace "nagode sosai da kulawanku a gareni kuma yanzun banjin komai" Hamdala sukayi atare. Kallon wajen tafara cikin tsantsar mamaki tace "a ina muke? menene kuma yafaru damu?" Sai a lokacin suma suka lura da wajen da inda suke sam hankalinsu baikai kai ba saboda duk suna cikin damuwa ganin Hassy taji ciwo...Zagayayyen gini ne wanda saboda tsananin tsawon katangar mutum baya iya ganin karshenta sannan ga wasu irin manyan duwatsu a jiki....Basma tace "Ikon Allah nidai nasan lokacin da muke zagaya dajin nan babu wannan katangar kuma ni abinda yafi bani mamaki nakasa tuna abinda yafaru" Merapati tace "bana tunanin hakan saboda kinsan dajin yanada girma ba lalle hankalinmu yakai kaiba" Kallonsu tayi taci gaba da cewa "yanzun dai abinda zamuyi mu nemi hanyan fita daga nan nasan hankalin sauran students zai tashi idan basu ganmu ba gobe" Wayanta taciro saidai emergency yasa mata kwata kwata babu network gaba daya ya dauke tsaki tayi ta maida wayan. Basma tace "amma Hassy kizauna saboda ciwon hannun ki" Kanta kawai ta gyada saboda tanaji a jikinta tabbas wani abu yafaru dasu amma batasan mene ba. Nan fa suka fara bin katangar suna haskawa da torch saidai basuga alamun akwai kofa ba a bala'in gajiye suka dawo inda Hassy take a zaune kallonsu tayi tace "kun samu hanyan fita daga nan ne? " Atare suka girgiza kai. Tace "ina ganin kawai mu kwanta idan yaso gobe da safe saimu duba da kyau nasan bazamu rasa hanyan fita daga nan din ba" Blanket suka shimfida basuyi cikakken 2mns da kwanciya ba bacci yadaukesu, saboda ba karamin gajiya sukayi ba. Washe gari bayan sun yi sallah zama sukayi kowacce akwai abinda take tunani kallon su Hassy tayi tace "zaman nan fa bazai yimana ba gara mutashi mu nemi hanyar fita daga nan wajen" Mikewa sukayi suna duba ko ina. Tsayawa Merapati tayi ta zubawa rubutun jikin wani dutse ido, kwala musu kira tayi tace su zo sugani. Hassy ce takaraso wajen saboda ita Basma tana can daya bangaren bata karaso ba. Zubama rubutun ido sukayi amma sam basu gane komai ba saboda wasu irin kalmomine sam mutum bazai iya sanin me aka rubuta ba, daidai lokacin Basma ta karaso wajen bin rubutun tayi da kallo a fili tafara karantawa kamar haka: _Βόρειος_ _Νότος_ _Ανατολή_ _δυτικά_ Saikuma daga can kasa akwai wani rubutun kamar haka "_Αυτή είναι η διέξοδος"_ kallonta suke saboda ko kalma daya basu gane ba a cikin abinda data fada ba. Merapati tace "mene ma'anar wannan rubutun? Kuma kina ganin zai taimake mu mufita daga nan" Basma tace "wannan rubutun da greek akayi shi bari dai nayi muku bayanin rubutun" _Βόρειος(Voreios) Means North_ _Νότος(Notos) Means South_ _Ανατολή(Anatoli) Means East_ _δυτικά(Dytikq) Means West_ Saikuma rubutun karshe "_Αυτή είναι η διέξοδος (Afti einai I diexodos) Means This is the way out._" Cigaba tayi da cewa"anawa ganin wannan rubutun yana nufin tsakanin Gabas,yamma kudu,arewa tabbas akwai hanyar dazamubi domin fita daga nan wajen,saidai takamaimai bamusan wace hanya bace ba Yanzun dai mene shawaran ku? Wace kofa kuke ganin zamu bi?" Hassy tace "mubi yamma" Merapati tace "aa ina ganin mubi arewa" Basma tace "nikuma anawa ganin kofan gabas yakamata mubi, Amma fa sai mun duba inda key din yake wanda zamu bude kofan dashi." Kallonta sukayi suka ce "wani irin key kuma?" Smile tayi tace "bawai normal key dakuka sani ba ne ba zakuga wani rami a jikin kowace kofa to idan muka danna shi kofan zata bude" Merapati tace "tayaya akayi duk kika san wannan?" Basma tace "saboda ina karanta littafan tarihi so I know lots of things....let’s go girls bamuda lokaci." Nan dai suka tattara kayansu sannan suka duba daidai inda gabas take bin jikin katangar suke suna taba ko ina ajikin katangar harsun cire rai da samun kofar nan hannun Basma ya taba wani karamin rami cikin farin ciki tace "ina tunanin mun samu mabudin" dannawa tayi nan da nan wajen yafara girgiza kamar za a yi girgizan kasa. A hankali bangon yake budewa harya bude gaba daya take wata karamar kofa ta bayyana acikinta akwai wata matattakala mai tsayin gaske wanda mutum duk iya hangensa bazai iya ganin karshen stairs din ba. Cikin rashin tsoro suka shiga cikin kofar suna gama shiga kofar takoma ta kulle kanta. torch suka kunna saboda duhun wajen.. babu komi a ciki sai wasu irin zane kala kala kwata kwata na mutane da gidaje da kuma flowers kala kala. Merapati ce ta taka wani abu tsayawa tayi tace "Hassy Basma ku tsay..." kafin takarasa gaba daya wajen ya rufta fadawa sukayi dukansu banda ihu babu abinda sukeyi..wajen yanada balain zurfi gakuma wata irin iska mai karfi tana yawo dasu dalilin hakan yasa dukansu sumewa... Lokacin dasuka bude idon su a cikin dajin dasuka sauka suka gansu sosai suke farin ciki ganin sun dawo ainahin inda suke..Hassy ta dauko wayanta ta duba saidai itama babu network haka ya nuna mata kallon Merapati tayi tace "dan dubamin wayanki da network kuwa inason nakira Ruky naji ya ake ciki" Dubawa tayi tace "wallahi kinga tundazun ya dauke kuma har yanzun baidawo ba" Cigaba sukayi da tafiya har suka isa inda tents dinsu yake, gani sukayi sauran students din sunayi musu wani kallo kamar yau suka fara ganin su gashi kuma duk sun hada kayansu zasu tafi,driver din ne ya kallesu yace "Idan tafiya zakuyi ku shigo mutafi daku," Basma ce ta matsa kusa dashi tace "amma naga kwana biyar zamuyi meyasa za'a tafi yau?" kallon marar hankali yayi mata saboda tsabar takaici baice mata komai ba aranshi kuwa cewa yake "lalle yarinyar nan tacika yar rainin wayau wato duk kwanakin dasukayi bata gani ba shine yanzun zatazo dawani salon rainin hankali" Ganin yaki kulata yasata komawa kusa dasu Hassy ta tsaya. Nan fa duk suka cire tents din dasuka kafa sannan suka shiga mota.. Su dai su Merapati mamaki sukeyi ganin duk student's basa kulasu hatta Ruky ma nunawa tayi bata san suba sudai abin ya daure musu kai amma sunbar abin a zuciyansu idan sunkoma zasu tambaye su kowani abu sukayi wanda basa son kulasu? Daidai lokacin Idanun Hassy yasauka akan sunan school din *YAMAN SCIENCE ACADEMY* Tabo su Merapati tayi tace "Ikon Allah daga tafiyan mu har an sanja sunan school? wannan abu da mamaki yake gaskiya." Dukansu kowa mamaki takeyi..Bayan kowa yasauka suka nufi hostel saidai gaba daya sun tsargu saboda irin kallon da students ke musu wasu ma har nuna su sukeyi ganin hakan yasa jikinsu yin kara sanyi. Kebewa sukayi Basma tace "nifa nagama tsarguwa kodai munyi laifine?" Hassy tace "wallahi nima abinda nike tunani kenan meyasa suke kallon mu kamar wasu baki?" Merapati tace "Hmm kubari kawai nikuma abinda yafi bani mamaki meyasa basa kulamu meyasa suke mana kallon tuhuma?" Manage it please,been busy!! Thanks For Reading My Story!!! Mwah mwa sending warm hugs and kisses❤️ @NM__🦋♥️ [14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #bff#dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 6: Something Happened 2. Gabadaya mutane kallon baki sukeyi musu, tun bayan da suka koma school. Hassy ce ta je kwana din su Zaynab waje ta nema ta zauna a kusa da gadon. Kura mata ido Zaynab tayi tana mata kallon sabon halitta tamkar wacce bata taba ganinta ba, with full of surprise Hassy starts talking to her, Amma me shiru tayi mata bata ce da ita komai ba. Kallonta sosai ta yi tana ganin yanda mood dinta ya sanja tace "What's wrong with you? What did I do to you? Why are you treating me like a stranger now? If I wrong you unknowingly just tell me so that I will apologize to you.." "Nop ban sanki ba ta yaya za a yi kuma ki mun laifi? All I know shine bana kula wanda ban sani ba that's all" Ba karamin mamaki Hassy tayi ba da kyar ta iya budan bakinta tace "kaman yaya baki sanni ba after long that we are together?". "Excuse me young lady I swear I don’t know you..." Zaynab ta fada bayan ta tashi daga wajen, mamaki ne yakara kama Hassy, nan ta shiga tambayar kanta "me yasa tun lokacin da muka dawo daga excursion kowa yake mana kallon strangers? Ko dai wani abu ya same mu a can ne?." Tsayawa tayi takara kallon kanta ajikin mirror saidai sam bataga wata alama ba yanda take haka dai take haryanzun. Da sauri tabi bayan Zaynab don ita duk a tunaninta wasa takeyi mata. Jiki a sanyaye ta dafa kafadarta tace "Don Allah ki daina idan ma wasa kike yi zaki sani a rudani, kinsan dai banason irin wannan wasan" Hummmm ajiyar zuciya ta sauke tace "seriously ni ban san ki ba i swear tun da nake ban taba ganinki ba ma,kinga kuwa babu ta yanda za a yi ka san wanda baka taba gani ba after that kowa ya sani duniya ta baci ba ta yadda za a yi kizo kina mun magana haka kawai daga mun taimaka muku bayan mun ganku a cikin daji sai ace kin biyo ni kina cewa kin sanni Please! Leave me alone I don’t want any trouble” hannunta ta cire daga kafadarta ta bar wajen. Mutuwar tsaye Hassy tayi baki bude take binta da kallo gaba daya maganganun Zaynab sune ke mata yawo a kunne, babu abun da ya yi mata ciwo kaman cewa da tayi bata santa ba, wai yau har ita ce Zaynab zata ce bata sani ba? Rayuwa kenan! Jiki a sanyaye takoma dakin. Washegari ta kama Monday, da wuri suka shirya zuwa class, abun dayake kara basu mamaki shine yanda kowa yake kallonsu, sai kace an ga sabbin halitta, gaba dayansu tsarguwa sukayi,nan fa suka fara bin jikinsu da kallo ko akwai wani abun da ya sa ake kallonsu, amma basu ga komai ba. A haka suka shiga class desk din da suke zama suka zauna, shiru class din ya yi, mutane na ta binsu da kallo, su dai shiru suka yi ba su ce komai ba. Hassy gefenta ta kalla saidai bataga Ruky ba, bin yan class din take kallo amma babu ko daya daga cikin gang's din su Ruky aranta tace "to ina sukaje?" Bangaren Merapati kuma ganin su Ruky tayi a class din su wanda hakan ba karamin mamaki yabata ba tunda tasan cewa ba class din su daya ba... Monitorn class din ce ta tashi ta tafi office din principal ta sanar da ita ga sabbin fuska sun shigo class dinsu ba tare da sun san ko su waye ba, anan ta tarar da headgirl din itama tana shigar da report akan bakin fuska din dasuka shigo school din nasu, aikawa ta yi a kira su, jiki a sanyaye suka taho office dinta. Hassy ce a gaba sai Merapati a tsakiya sai Basma a baya. A can gefe suka takure a waje daya. Tambayarsu ta shiga yi "ku su waye? Daga ina kuke? Ya za a yi ku shigo mun makaranta ba tare da permission ba?". Hassy ta kalli Basma, Basma ta kalli Merapati, ba karamin mamaki maganar pc ta basu ba, Bama wannna ba gaba-daya principal din da suka sani ba ita bace wannan. "Mummy ta yaya za a yi kice mu ba daliban ki ba ne? Ki duba cikin list dinkin zaki ga sunanmu, har da mu aka je excursion din nan kuma tun da muka dawo sai mukaga ana mana kallon baki gaba daya abun ya daure mana kai". Merapati ta fada tana mai goge fuskarta da tissue. List students din aka dauko aka fara dubawa amma kuma abun mamaki babu sunansu gaba daya a ciki, ajiye wa tayi ta dauko na class dinsu nan ma babu sunan su a ciki, sawa tayi aka kira wasu daga cikin teacher's din nan fah suka shige bincike a system tun farkon fara bude school din nan ma abun mamaki babu ko alamun sunansu.... Tashi Principal din tayi cikin bacin rai tace "ku tashi ku fita mun a makaranta, babu ta yanda za a yi ku shigo mun makaranta har ku zauna ba tare da an dauke ku ba, kunbatamin lokaci a banza" security takira taci gaba da cewa "a tabbata sun kwashe duka kayan dasuka shigo dasu cikin school din sannan a fitar dasu daga school din cikin gaggawa saboda ba asan wani irin mutane bane ba su." Tana cikin surfa masifa taji an yi knocking din kofar office din, umarni ta bayar a shiga, kawarta ce wacce take Principal a wani private day school, tana shigowa idanuwanta suka sauka akan na Merapati, gabanta ne ya buga, mamaki ya kamata a take fuskar ya dawo mata tabbas ta san wannan yarinyar amma kuma ta manta a inda tasanta sosai take mata kallon sanni wanda Basma ta lura da hakan. "Ku fice mun daga office" jiki a sanyaye suka fita, bayan fitarsu ne kawar Principal din tace "nasan wannan yarinyar ta baya fa, amma kuma na manta a inda nasanta kawai abu daya nasani nasanta..." Shiru kawai tayi mata suka shiga hiran abun da ya kawo ta. Gaba daya rasa abun yi suka yi bayan sun fito, ga shi yamma tayi ga yunwa ta addabesu ko breakfast basu yi ba, gabadayansu babu yar gari, kowacce daga wani state aka kawo ta ba su san kowa ba,tunda basu taba fitowa cikin gari ba. Merapati taciro wayanta da niyan kira amma haryanzun no connection yake samata.gaba daya ma network din ya dauke... Tafiya suka shiga yi har suka ga wani restaurant, Basma ce tace su shiga su samu wani abu su ci, shiga su kayi, har bakin wajen, aka'idan restaurant din ba a cin abinci har sai an biya. Bayan waiter ya kawo musu order list sun yi ordern abun da suke so, kudi Hassy ta ciro tunda dama student ba a rabasu da pocket money daga bag dinta ta bashi. Karba ya yi yana kallon kudin da mamaki dauke a fuskarsa, kallonsu ya yi yace "wannan wani irin kudi ne? ai bama amfani da irin wannan kudin". Zuwa yanzu mamaki yagama kashe su,Hassy tayi karfin halin cewa "yaushe aka sanja kudin? bamu sani ba? yaushe aka daina amfani da wannan din?. Shima da mamaki yace "Kai! Aa gaskiya mu bamu taba amfani da irinsa ba a wannan kasar tun asali, dan zance miki tun da aka haife ni ma ban taba ganin irin wannan kudin ba kwata-kwata sai yanzu kuma a kalla shekaruna yakai 27" Dafe kai kawai suka yi, saboda basu san me za su ce ba,wani dake zaune a gefensu ne yace a basu abincin zai biya musu, kawo musu abincin aka yi suka ci, suka fita. A waje suka hadu da mutumin sosai suka masa godiya yace musu ba komai, kallon sani ya shiga bin Merapati dashi. Ita kuma ko kusa ma bata san shi ba duk da ta tsargu da kallon da yake mata. Wucewa sukayi suka bar wajen, tafiya kawai suke batareda da sun san inda zasuje ba, bakin magana ma basu da shi kowa da tunanin datakeyi aranta tabbas suna zargin akwai abinda yake faruwa dasu...basu dade suna tafiya ba sukaga wani katafaren hotel babban building ne dauke da more than 1000rooms reception sukaje nan ma still, kin karban kudin suka yi, saboda basa amfani dashi sosai hankalin su yatashi nan fa suka shiga rokonsu akan su taimaka musu basuda wajen kwana, baice komai ba yadauka telephone security yakira yace azo a fitar dasu..kin fita sukayi sosai suke rokonsu daidai lokacin manager din ya shigo cikin hotel din kallonsu yayi yace "release them" daya daga cikin guards din ne yace "but sir" hannu yadaga mishi yace "I dont wanna hear anything!" kallonsu Merapati yayi yace mata "Madam we are very sorry duka ma’aikatan sabbin zubi ne kiyi hakuri key ya mika mata yace VIP section room 102." Baki bude Merapati take kallonsa aranta tana maimata kalmar Madam? share zancen tayi tace may be haka suke treating din bakinsu. Hassy,Basma gaba daya mamaki ya ishesu, ko da suka shiga dakin tunani suke me yasa abubuwa suka sanja gaba-daya a cikin garin gashi mutane duk sun sanja, wanda suka sansu sun nuna basu sansu ba. Gashi kudi ma ance ba a sani ba kuma ba wai sanjawa aka yi ba to mene ya faru a kwanaki biyar din da sukayi basa nan bayan sunje excursion? Me yasa a kwana biyar kacal komai ya canza? Wani irin rayuwa kenan suke shirin fuskanta a yanzu? An ya babu wani babban kalubale a gaban su kuwa? . "You guys menene abun yi? Wani irin rayuwa muke shirin fuskanta?" Hassy ta fada. Ido suka zuba mata gaba daya sun yi tagumi. "We dont even know". "Ni kaina ya kulle" Basma ta fada. Merapati tace "tabbas akwai wani abu wanda bamu san shi ba da akwai wani abu daya faru damu ya zama dole mu san koma menene, tun kafin mutane su fara gudun mu". Ido kawai suka zuba mata kowa da abun da yake sakawa a ransa. Shiru sukayi sai can Basma ta kalleta "Merapati zaki tuno wadda muka gani a principal office?" Kanta ta gyada alamun eh cigaba tayi dacewa "the way she's looking at you kamar tasanki hakama wanda yabiya mana kudi a wancan restaurant din shima yana yi miki kallon sani and the Manager lokacin dayake miki magana muryansa cike takeda girmamawa shin duk cikin su babu wanda kika gane a ciki?" Kanta ta gyada "gaskiya bansan suba kuma bantaba ganin suba nikaina nayi mamaki danaji yakirani Madam! Koma dai menene yake faruwa zamu gano idan ma pretending sukeyi duk zamu gano..." Hassy ta kalle su "ni yanzun tunani na idan masu hotel din nan suka gaji damu fah?" Gaba daya shiru sukayi saboda basu da answer. *~ Washe gari dukansu suna zaune akan bed din kowa da abinda yake ranta Merapati ta mike wajen telephone din dake bed side drawer taje number din Dad dinta tayi dialing saidai ga mamakinta sam kiran yaki shiga daga karshe ma cemata akayi "Dear customer the number you are trying to reach doesn't exist... Please check the number and try again.." Tsaki tayi ta ajiye wayan. Kallonsu tayi tace "yanzun mene abin yi?" Basma tace "nidai yanzun yunwa nikeji" Hassy ta dafe cikin ta "wallahi nima haka gashi bamuda kudi yaya zamuyi?" kallon Merapati sukayi atare sukace "kimana order please tunda munga kamar sun sanki" Binsu take da kallo harsun cire ran zatayi magana saikuma ta mike takira tafadi duk abinda sukeso for breakfast... Ba a dauki lokaci ba aka kawo musu duk wani abin da sukeda bukata. *~ "Yanzun kuna ganin mene abinyi? ni abinda yafi damu na yanda duk numbers din da muka kira basa zuwa kuma network din mu duk ya dauke!" Kallonsu tayi ganin kawai abinci suke ci "Hassy,Basma I'm talking to you" tana nunasu da hannu amma kin bata amsa sukayi saima kara maida hankalinsu kan food din dake gabansu sukayi hakan yakara fusata Merapati her voice was full of anger "You stop fucking eating and talks to me" said Merapati angrily. Dagowa Hassy tayi calmly tace"What do you want me to say" Wani kallon banza tayi mata "kinfi kowa sanin abinda zakice" Cigaba tayi da cin breakfast dinta hankali kwance ganin hakan yasa Merapati mikewa taje ta zubar da abincin.. Hassy,Basma da mamaki suke kallonta... Basma tace "Mekikeyi hakan? why are you acting stupid have you lost your mind?" Hannu ta daga mata "you shut up! I am not talking to you...Maida kallon ta tayi kan Hassy taci gaba da cewa "this is all your fucking faults! tun farko dabakisa sunana a masu zuwa excursion ba da yanzun ina...." Saurin katseta Hassy tayi "naji laifina ne danasa sunanki a list din zuwa excursion,amma ke meyasa kikace dole zaki biyo ni?kawai don muna sharing tent daya? I didn't force you to come along with me,remember that you are the one who insisted to come,Stop blaming me..Stop acting stupid,stop embarrassing yourself for Pete’s sake Mega" Sosai suke sa insa tsakanin su ganin hakan yasa Basma shiga tsakaninsu janye Merapati tayi itakuma Hassy cikin bacin rai ta fice daga dakin... Tafiya takeyi saidai ita kanta batasan inda zatajeba tunda basu san kowa ba iyakan su cikin school cigaba tayi da tafiya harsaida tayi nisa da Hotel din dasuka sauka, sam hankalinta baya jikinta tayi zurfi a tunani wanda hakan yasa harta iso kan titi amma bata lura ba,, abu daya taji karar mota saikuma taganta a kasa dishi dishi take ganin mutanen da suka zagayetah saikuma idonta ya rufe gaba daya. *~ A hankali ta bude idanunta bin dakin take da kallo cikin seconds komai yadawo mata bin jikinta tafarayi da kallo Hamdala tayi ganin bata wani ji ciwo ba kawai kafantane shima ciwon ba sosai ba. Daidai lokacin aka bude dakin,Doctor ne agaba saikuma wata matashiyar budurwa abayanshi cikin Al'ajabi take kallonta A fili tace "Merapati? Ya akayi kikasan ina nan?" Bin bayansu suke da kallo saboda duk a tunanin su da wata take magana saidai basuga kowa ba Doctor ne ya duba jikinta "babu wata matsala anjima zan iya sallamanta" godiya tayi masa bayan ta zauna a gefen ta sannu tayi mata sannan ta mika mata hannu tace sunana "Sheenaz kefah mene sunanki? I'm so sorry about what happened earlier wallahi ina sauri ne hankalina bai kai kanki ba gashi..." Smile Hassy tayi "babu komi karki damu tunda banji wani ciwo sosai ba" godiya tayi mata sannan tace zataje tadawo kafin a sallameta harta fita saikuma tadawo ta kalleta "Amma baki fadamin sunankiba?" Her voice was low tace "call me Hassy,Amma bama saikin dawo ba tunda banji wani ciwo ba" kanta ta girgiza "don’t worry I will be back later" daga haka ta fice daga dakin.. A fili Hassy tace "Drama Queen let's see who is gonna win this game..." 4:30pm Doctor ne ya shigo bayan ya sallameta ya hada mata sauran medicines din da zatayi amfani dasu a karaman leda "Madam tana waje tana jiranki”.. Smile tayi batace komai ba yakira nurse yace su rakata. Lokacin da suka fito daga hospital din tana tsaye jikin wata mota ga securities nan masu yawa, sannan duk cars din sunan Sheenaz ne a jiki saikuma numbers 1to12 gani tayi an bude mata wata hadaddiyar mota shiga tayi itama Hassy aka bude mata dayan gefen nan fa suka fara tafiya duk inda suka wuce saidai kaga mutane suna basu hanya, Sheenaz ta dubi Hassy "inane gidanku? Nasan yanzun hankalin parent's dinki yatashi shiyasa nikeson maidake gida da kaina nakuma yi musu bayanin abinda yafaru," Smile tayi aranta tana cewa "let’s begin the game now" Cikin sanyin murya tace "ni bakuwa ce bansan kowa ba sannan kuma inda nasauka yanzu bazan iya ganewa ba" kallon tsab tayi mata "okay no worries zamuje gidan mu dake idan yaso gobe saimu san abinyi.." Lokacin da suka isa gidan Ma Shaa Allah Hassy tace saboda kyau da tsaruwar gidan ga maids nan kala kala kuma kowanne sanye da uniform amma different colors hatta masu bama flowers ruwa uniform dinsu daban ne hakika mamallakin gidan yakasance hamshakin mai kudi Hassy bata gama mamaki ba saida suka shiga Apartment din Sheenaz komi na ciki yanada tsada kallonta tayi tace ta saki jikinta tamkar tana gidansu wanka tace taje tayi shi kanshi bathroom din duniya ce ya hadu iyakan haduwa bayan ta fito lotion kawai tasa sai powder wardrobe ta bude mata ga kuma walk in closet su kansu kayan expensive ne masu tsada infact komi nata expensive ne tundaga kan inner wears zuwa su bangles _(lol komi dai some times im not good at explanation😂)_. Itadai Hassy mamaki takeyi ashe dama Merapati tana sane ashe anan garin take amma shine take nunawa batada kowa?to meyasa batason su san anan garin take? Saidai babu wanda zai bata answer din nan. A cikin kwanan dayan da sukayi Hassy tagane cewa Merapati tanada kirki sosai take maganganun Zaynab suka dawo mata gaskiyane Merapati sam batada girman kai. Washe gari bayan sungama breakfast sunyi wanka Sheenaz tace ta shirya ta maidata gida. Smile tayi tace saidai hotel din dana sauka. Sunan Hotel din tafada mata dariya tayi tace ainasan hotel din Hassy aranta tace aidole kisani.. Bayan sun isa hotel din kuma daidai lokacin Basma ta leko window din in shock take kallon su Hassy fitowa sukayi daga motan basu wani dade suna magana ba sannan ta bata Card dinta takuma ce zata kawo mata ziyara idan tasamu lokaci wata karamar bag ta bata godiya tayi mata sannan suka tafi. Basma takasa zama ta kasa tsayawa sai zuwa take tana dawowa gaba daya kanta ya kulle da abinda idanunta suka hango mata "amma tayaya? Tayaya hakan zai kasance alhalin ga Merapati kwance akan gado tana bacci?" Hassy ce ta shigo dakin kallo daya tayima Basma ta dauke kanta saboda haushin su takeji gaba daya saidai ganin yanda Basma take cikin damuwa hakan yasa komai ya wuce "Basma lafiya kike kuwa?" Girgiza kanta ta shiga yi "I’m not okay, Inaji ajikina wani abu yafaru tayaya hakan zai kasance yanzun fah naganki tareda Merapati?" Smile Hassy tayi "karki wani damu so take mu shirya shiyas...." Cak ta tsaya da maganan ganin Merapati kwance akan bed itama Hassy a zuwa yanzun tagama yadda akwai abinda yafaru kokuma akwai abinda yake kan faruwa kallon Basma tayi "You are right things are strange,something is going on,Something really bad is happening!!!." Daidai lokacin Merapati ta bude idonta fess ta saukesu akan su Basma maganan Hassy taji na karshe cikin sanyin murya tace "what's wrong? What is going on?" Basma look into her eyes and said "We are in a different world...." In shock suke kallonta Hassy tace "I dont understand! What do you mean?" Basma tace "You know what I'm talking about, we are in a different world,a different dimension, a parallel world..." Thank You For Reading My Story.!!! #Share #Follow #Comment Well I’m not uploading this on my wattpad account,buh may be soon I will change my mind hehehehe... [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 7: Doppelgänger Kallonta suke saboda sam basu gane abinda take nufi ba Merapati ce ta mike daga kwancen datake zama tayi sosai ta fuskanci Basma tace "Bangane abinda kike nufi ba shin ko zaki kara yimin bayani yanda zanfi ganewa na tabbatar itama Hassy tana cikin rudani kamar yadda nima nike ciki ayanzun haka." Zama tayi bayan itama Hassy ta zauna yazama cewa Merapati tana tsakiyar su, Kallon su Hassy tayi ta sauke ajiyan zuciya "gaskiya ne nasani zakuyi mamakin abinda nafada nikaina banyadda ba harsaida nayi tunani akan hakan, Tun bayan dawowar mu daga excursion abubuwa suka sanja nafarko yanda kowa yake mana kallon sabon halitta gashi wanda muka sani nunawa sukeyi basu san mu ba,Abin mamaki a yan zuwa excursion babu su Najlah amma kuma a wannan duniyar akwai su to idan ba tare mukaje dasu ya akayi muka dawo taredasu? Bama wannan ba ita kanta Principal din ba itane tamu ba sannan kuma vice principal dinmu namiji ne amma ita kuma wannan mace ce,kunsani nasani mune farkon zuwa school din amma abin mamaki kwata kwata babu sunan mu a cikin kaf students din tunda aka bude school din." Basma ta dago ta kallesu "Ina fatan kuna gane bayanin da nike muku?" Kansu kawai suka daga saboda suma sun fara yadda da abinda take fada musu. "Sannan Zaynab close friend din Hassy ce amma ta nuna bama ta taba ganintaba. Do you know why I believe that we are in a different world?" Basma asked them. A hankali suka girgiza kai. "Well let me explain it..The spelling of the school.." In shock suke kallonta Merapati tace "Mekike nufi? aini wannan ban daukeshi komi ba saboda zata iya kasantuwa an sanja sunan kafin mudawo." Basma tace "sam ba haka bane ba sunan school din mu _*YAMAN SCIENCE ACADEMIC*._ nan kuma sunan makarantar su *_YAMAN SCIENCE ACADEMY._* "Instead of IC sai sukayi amfani da Y. sannan idan kika kalli symbol din school yadade bazai yiwu ace daga kwana biyar din da bama nan ba aka sanja ba, sannan kudin da muke amfani dashi su anan bada irinsa suke amfani ba infact bama su taba ganin kudin ba,bakwa mamakin yadda kowa yake waya amma mu namu phones din gaba daya babu network? Sannan duk numbers din da muke kira basa zuwa..." nan taci gaba da kawo musu misali kala kala Kallon Merapati tayi tace "saikuma gashi dazun mun ganki... Hassy hartaje gidanku ta kwana" nan tabata labarin duk abinda yafaru. "Gidanmu?" Merapati ta maimata a fili taci gaba da "cewa gaskiya ba gidan mu bane ba saboda ni ba a wannan state din nike ba,tayaya zakuce kun ganni? Hmm Basma naga alama sokike kiyi wasa da hankalina kindauka kowa irin kine? Okay now I understand everything,saboda kina kallon cartoons shiyasa kikeson hada wata drama anan lemme tell you one thing,I will never ever believed you so please stop it stop this nonsense...." Tana gama fadar hakan ta shige bathroom. Binta kawai suke da kallo, Hassy tace "ni mamaki take bani tayita abu kamar wata yarinya she’s really annoying" Sai kuma ta kalli Basma "I’m still thinking how we ended up here,nifa nafi tunanin wannan water fall din da muka shiga ne, kintuno wannan circle din da muka gani? May be it was a gate to another world..." Ita sam ta manta da wannan waterfalls din tun lokacin da suka shiga ciki komai ya sanja "you are right Hassy ta nan muka zo wannan duniyar wadda bamusan ta yanda zamu iya komawa ba asalin duniyar mu." Tundaga ranan basu kara zancen ba Hassy tacewa Basma tabar zancen duk da cewa itama Hassy ta yadda daduk abinda Basma tace kuma taga sauye sauye a garin yanzun dai hanyan dazasu sa Merapati ta yadda suke nema saidai basu san ta ina zasu fara ba. Dama basu da matsalan food da duk wani abu da suke bukata. Basma tace "Hassy nikam ina jakar da Sheenaz ta baki? Ita gaba daya ma ta manta da ita mikewa tayi ta dauko bag din kudi ne masu yawan gaske sai perfumes masu kamshi saikuma wani karamin card shikuma phone number ne a jiki. Murmishi Basma takeyi Hassy kam kawai tsayawa tayi tana kallonta tace mene? Basma tace "ina tunanin lokaci yayi da Merapati zata yadda cewa muna wata duniya daban ne..." Hassy batace komai ba tazauna akan sofa bayan ta maida hanklinta kan Basma dama Merapati tana dayan bedroom din. Phone number din jiki Basma takira bata bata dade tana ringing ba aka daga cikin sanyin murya take answer duk maganan da Basma take fada mata bayan sunyi sallama ta kalli Hassy tace ta yadda yanzun saimu san yanda zamuyi musa Merapati zuwa wajen domin su hadu da Sheenaz. "Please don't say no..." Said Basma cutely wanda tundazun takeson Merapati ta yadda domin zuwa su hadu da wani dagowa tayi "nifa ba kin zuwa nayi ba kawai bansan mutum ba naje mu hadu dashi?" Hassy kam tana gefe ayanzun batason yin magana saboda indai tayi komi ya lalace cuz kwana biyun nan bawani shiri sukeyi da Merapati ba gani takeyi girman kanta yayi yawa bangaren Merapati ma kallon haka take yima Hassy (LMAO). Kanta ta dafe "Oh Allah kekam Basma idan kikasa mutum a gaba saikin sashi yayi abinda baiyi niya ba shikenan zanje." "Yay thank you sis" hugging din ta tayi taci gaba da cewa "ki shirya anjima za a zo daukan ki" Bayan tagama shirinta babu wanda zai kalleta yace ba Sheenaz bace ba saboda komi na jikinta yayi daidai dama Merapati akwai iya daukan wanka tana fitowa Basma tace "wow slay queen kinganki kuwa? you love adorable baby" Smile tayi in a low voice she said "Thank you darl". Batafi 10mns da zama ba telephone din room din tayi kara dagawa Basma tayi "okay tana zuwa" sai tayi hang up call din. Lokacin data fito Manager din yana tsaye cikin ladabi yake gaida ita sannan ya bude mata car ta shiga bayan yafadama driver din inda zai kaita wato _*Golden Gate Park.*_ Wajen ba karamin birge Merapati yayi ba,yahadu sosai VIP waje aka kaita bata dade da zama ba wani kyakkyawan saurayi yakaraso wajen, zama yayi adaya daga cikin kujerun amma ko kallonshi Merapati batayi ba saboda bata sanshi ba yau ne rana tafarko data fara ganin sa. Sallama yayi mata amsawa tayi saboda tasan muhimmancin hakan. Cikin kulawa yake mata magana amma ita duk jin ta takeyi a takure saboda bata sanshi ba shikuma a yanda yake mata kamar yasanta,Yanzun ma cewa yayi "You look beautiful,in blue the color really suits you darl." Dagowa tayi cikin takura dakuma gajiya da maganganunsa tace "What do you mean? Do I know you?" Smile yayi dama yasaba yawanci indai sukayi fada da ita haka take yimasa she always treats him like that every time when they had fighting.. "Look darl I'm sorry I'm sorry about last night" Mikewa kawai tayi don ita abin nashi yafara bata tsoro shikam da mamaki yake binta what's wrong with her? She is being really weird today..... Merapati bata wani dade tana tafiya daga can gefenta tafara jin sautin dariya hakan taji tanason ganin mai dariya din saboda saitaji tamkar ita da kanta keyin dariyan saboda yanayin da komai irin natane sak juyawa tayi she froze in an instant,Her heart was beating fast she felt paralyzed as she stared the girl....It was her.... Merapati...Cikin tsantsar mamaki take kallon kanta amma tasan ba itane ba tunda ita gata nan a tsaye...but how could that be? and how can it be possible.? Saidai babu mai bata answer cikin second's maganganun Basma suka dawo mata a fili tace "Basma? This means that she was telling the truth?" Da sauri tafice daga park din bayan ta rufe fuskanta da gefen veil dinta saboda batason a ganta komi zai iya faruwa a wajen.. Driver yana ganinta ya bude mata mota bayan tashiga ya rufe yaja suka tafi. Ko a cikin motan ma babu abinda datakeyi sai tunani dakuma auna duk wasu abubuwa dasuka faru tun bayan dawowan su daga excursion...Ashe shiyasa kowa yake girmamata? Sai yanzu tagane dalilin dayasa Manager din hotel ya yadda su zauna batareda da sun biya ko naira daya ba...babu tantama wannan saurayin dayazo wajenta yayi tunanin itane...yazama dole taci gaba da boye kanta indai har tanason suci gaba da zama a hotel din saboda ita kanta batasan inda zasuje ba suna da enough money amma kuma yatashi a banza tunda a wannan duniyar sam basa amfani dashi. Bata bari ya kashe motan ba tayi saurin fita kallo daya zakayi mata kagane cewa tana cikin damuwa sosai...da sauri sauri take hawa stairs din saboda a ganinta bazata iya hawa elevator ba. Basma Hassy zaune suna duba abu cikin phone din Basma, Merapati ta shigo kallo daya tayi musu take kunyan Basma yakamata saboda yanda ta fada mata maganganu a lokacin. Mikewa sukayi a tare Hassy tace "lafiya naganki a haka?" Basma ta matso ta kamata bayanta zaunar da ita sannan ta zuba mata ruwa a cup ta mika mata amsa tayi saida tasha rabi ta ajiye cup din a gefe kallon Basma tayi her voice is so slow "I’m so sorry Basma,,at first I don’t trust you buh now I agree with you! we are in a different world." In shock suke kallonta "What do you mean?" Hassy asked as she took a seat next to her.... Merapati looked at her "Um I mean I saw myself, amma kuma bani bace ba but it was me" Gaba daya shiru sukayi saboda sun tabbata cewa Merapati taga Sheenaz. Thank You For Reading My Story!!! @NM__🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 8: Apocalypse For more information contact this number 08084078727...feel free to message me I’ll reply ASAP thanks all "sending hearts" All the Characters place's event's in this story was all drawn from my imagination and are not based on any real life event's. Dedicated To Merapati♾ *** LastFreePage!! ~* Bangaren su Ruky kuwa washe gari hankalin su ba karamin tashi yayi ba ganin cewa basuga su Hassy Merapati Da Basma ba, nan suka yanke shawaran zuwa cikin dajin domin su dabasu wataqilan suna can din. kowa bag dinsa ya dauka sannan suka nufi cikin dajin. Basu wani dade suna tafiya ba sukaga gidan shiga sukayi bayan sun kunna torch saboda wajen yanada duhu sosai. Bin ko ina suke suna dubawa gashi gidan babban gida ne, ci gaba da duba ko ina sukeyi amma basu gansu ba. Wani babban daki suka gani budewa sukayi saidai gaba daya wasu irin halittu ne tamkar mutane amma kuma jikinsu yayi bakin kirin su kansu baza su iya tantancewa ba bi suke a hankali suna duba ko ina wani mai suna Abduljalal ne yataka wani abu mai tsini nan da nan jinin sa yafara zuba ganin hakan yasa su kamoshi suka fice daga gidan,bayan sun rufe gidan. Direct wajen tents din suka tafi. Abinda basu saniba akwai wata a cikin su Leemah ashe ita zamewa tayi tabi wata hanya daban sukam sam basu lura da itaba ganin yanda Abduljalal yaji ciwo.... Jin kamshin jinin yasa wannan konannun zombies din fara hade jikinsu cikin karamin lokaci gaba daya sun dawo ainahin siffarsu ta zombies kuma a lokacin babu abinda suke so sama da son shan jinin mutane. Leemah tana tafiya nan tafara jin motsi a bayanta juyowa tayi ta haska amma bataga komai ba cigaba tayi da tafiya still bata daina jin gurnanin ba cikin tsoro ta juyo da niyan komawa jitayi an kama hannunta nan take yasa bakinsa ya cijeta,dama hannunta akwai torch nan ta hau buga masa a kai take yafadi awajen da balain gudu itama ta fice daga gidan tana mai mamakin menene ya cijeta haka? Saboda ita sam bata taba kawowa akwai wata halitta a gidan ba,gashi kuma torch dinta ta mutu lokacin hakan yasa bataga komai ba. Bayan ta fito nan ta duba inda aka cijeta din,wajen yayi bakin kirin ga wani irin blood black yana fitowa tacikin wajen, karamin handkerchief tadauko daga bag dinta ta daure wajen. Tana komawa tent din su ta shige saboda sam batajin dadin jikinta,, ~* 15mns later Tent partner dintane ta shigo ganinta kwance cikin matsanancin hali yasata fita da gudu su Ruky ta fadama gaba daya kanta sukayi suna mata sannu kanta kawai ta iya dagawa saboda ita kadai tasan metakeji gashi color din idonta yafara sanja color Nasir Mukhtar Nasir shine yayi mata allura saboda jikinta yayi zafi sosai fita sukayi domin bacci yafara dauketa. _2:00am_ Partner dinta bacci takeyi hankali kwance kuma sai akayi rashin sa'a dayar da suke sharing tent tare bata nan sunacan tent din su Merapati itadasu Ruky anan zasu kwana tamkar a mafarki tafara jin wani irin sauti bude idonta tayi,ganin Leemah durkushe acan gefe tana wani kalar amai da sauri ta mike domin taimaka mata saidai lokacin dataga yanda kamanninta suka sanja hakan yasata sakin wata irin kara Leemah kam batayi wani tunani ba takamo ta sannan tasa bakinta a wuyanta....daidai lokacin su Ruky suka iso tent din in shock suke kallonta ganin yanda take shan jinin partner dinta gaba dayansu firgicewa sukayi cikin sauri suka dauki bags dinsu sannan suka nufi cikin dajin da gudu. Wannan gidan dai suka kara komawa anasu ganin nan ne kadai zasu samu su tsira da rayuwansu, saidai ga mamakin su yanzun gidan babu duhu gaba daya bulbs din sunkawo sai a sannan suka lura da cewa asibiti ne shiga sukayi bayan sun rufe kofar shiga ainahin cikin hospital din. Nan ma ko ina fess tamkar yau aka bude hospital din,jikinsu yagama basu cewa akwai wani abu a cikin hospital din saidai basu san mene ba ganin hakan yasa Ruky cewa "mu bar hospital din nan" juyawa sukayi amma abin mamaki babu kofan da suka shigo sama ko kasa basu gantaba. Kowa yarasa abin cewa nan fa aka hau kallon kallo,kuma kallo daya zakayi musu kagane cewa a tsorace suke tattarawa sukayi suka shige female ward dakin yanada girma sosai ga patient bed's nan masu yawa kowanensu yasamu bed daya suka kwanta amma babu alamun bacci a idon su kowa tunani yake wace irin masifa suka kawo kansu? Washe gari da suka tashi duk wannan hasken babu hospital din yakoma asalin yanda yake take hankulan su yakara tashi sudai sun san cewa ba mafarki sukayi ba jiya gaba daya hospital din da haske tayaya hakan tafaru? Kallonsu Ruky tayi cikin sanyin murya take magana "You already know what is going on,we must be very careful. This place isn't safe and secure...from now on we will be together.... Kar wanda yabar dakin nan duk da cewa bamusan ainahin abinda ke faruwa ba amma alamomi dayawa sun nuna cewa wajen nan akwai hadari...." ~* Leemah kuwa bayan tagama shan jinin partner dinta itama cikin karamin lokaci takoma zombies din a tare suka bar cikin dajin su kansu basu san inda zasuje ba a yanzun babu abinda sukeso irin shan jinin mutum daidai lokacin suka iso bakin titi,wata karamar mota ce ta tsaya a gabansu sam bai lura da yanayin su ba fitowa yayi yana tambayarsu shin zai iya taimakon su? Sai a lokacin ya lura da yanda kamanninsu suka sanja kafin yayi wani abu harta kamo hannunsa tasa bakinta hakama leemah itama bakinta tasa a kafanshi wani karfe ya dauko a motanshi ya buga musu da sauri ya shige motan. _8:30am_ *TRAIN STATION* Tsaye take jikinta sanye da wata black gown bin mutanen wajen take da kallo take idonta ya sanja color yakoma dark red,She felt her fangs coming out,ready to bite human. Right now she is hungry,hungry for blood, for a flesh to taste,for a body to consume... Kalle kalle tafara wani irin kamshi tafaraji tunda take bata taba jin dadin kamshin jini ba sai yanzun juyawa tayi idonta yasauka akan wata yarinya bazata wuce 18yrs ba binta take da kallo she's looking straight at her flesh,ganin hankalin mutane baya kanta kowa harkan gabansshi yakeyi yasata zuwa dab da ita Without a doubt she grab her close,and put her mouth on her neck,and starts sucking her blood. Kuma daidai lokacin ne wanda su leemah suka ciza yakaraso wajen cikin mawuyacin hali faduwa yayi awajen jama'ah sukayo kanshi ana tambayarshi lafiya? nakusa dashi yakamo ya yage cikin shi yanacin naman wajen,ganin hakan yasa sauran mutane kokarin guduwa amma a kalla saida ya ciza mutane sama da goma,,,,kafin cikar 2hrs gaba daya yan station din sun zama zombies take gari ya rikice mutane suka kulle kansu a gidaje domin tsira da rayuwan su. ~* _@Hospital_ "Gaskiya bazan zauna ina gani na rasa rayuwata a banza ba komine zai faru saidai yafaru amma saina nemo hanyan fita daga nan" cewar Abdul, wanda tun dazun yake musu mita akan cewa shifah saiya fita sukuma sun hanashi Ruky ce taja tsaki cikin bacin rai take magana "Kagafa Abdul naga sokake ka rainama mutane wayau don kawai kaga ana lallaba ka daga yanzun babu wanda zai kara hanaka fita Allah yabada sa'a," tana gama fadar hakan takoma kan bed tazauna ganin hakan yasa sauran ma komawa suka zauna akabar Abdul kadai tsaye baiyi tunanin komai ba yadauki bag dinsa sannan ya fice daga dakin. Saida yayi tafiya mai nisa amma baiga alamun kofa ba juyowa yayi da nufin yakoma inda su Ruky suke amma me cak ya tsaya sakamakon tozali da yayi da wani irin kare(dog) gaba daya jikinsa ya sanja kama, jikinsa babu gashi ko daya kuma rabin naman jikinsa duk babu wajen yayi wani irin abu tsoro bakinsa wasu irin zago zago hakora ne,sannan harshen sa yazama kalar abin tsoro sosai,,,, ga wani irin gurnani mai firgitarwa yana fitowa daga karen hatta color din idanunsa sun sanja sunkoma yellow and black, Juyawa yayi da niyan komawa ta baya nan ma arba yayi da karnukan su wajen biyar kuma gaba dayan su duk rabin jikinsu babu..wani irin tsoro ne yakamashi tunda yake bai taba ganin abu mai firgitarwa kamar wadannan karnukanba,,,Atake sukayo tsalle suka hau cin naman jikinsa wata irin kara yasaki wanda har sauran students din saida suka jiyo ihun nashi... ~* "Yanzun mene abin yi? Ni damuwa tama inasu Merapati suka shiga?" Zaynab tace tana kallon su. Suna shirin bata answer suka farajin motsi a jikin kofa...mikewa sukayi a hankali suka leka window din zombies ne su wajen 30 gaba daya sunzama abin tsoro don wasu ma fuskansu babu tsoka kuma jikinsu duk yazama ash while others have yellow colored skin... Idonsu ma kadai abin tsoro ne wasu nasu yakoma greenish blue,greenish black,orange,while others has yellow green eyes. "Shhh" Nasir frightened voice said, "don't make any sounds,keep quite, if they hear you, they will hunt you" alamu yayi musu akan su koma baya gaba daya a tsorace suke zama sukayi kowa da abinda ke ransu.... Duniya ta rikice yayinda zombies suka shiga cikin garin sosai yawancin rabin garin sunkoma zombies kuma bi suke ko ina duk inda sukaji kamshin jini saisunje mutum ko a cikin me yake sai sun shiga,yanzun kuma saiga tashin hankalin dayafi na zombies domin kuwa wasu irin halittu ne suka fara bayyana wanda har mutune suke tunanin gara suje zombies su cije su akan wannan halittun su gansu saboda su direct suke kashe mutum su dai wadannan hallitun sunada siffar mutane amma kuma ta bangare guda suna kama da bat,saboda sunada fuka fukai masu tsini hannun su ma wasu irin farce ne masu tsayin gaske bakinsu kuma manyan hakora ne (fangs) wanda idan suka saka bakinsu a wuyan mutum take suke rabashi da gangar jikin.....!!! @NM__🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 9: The Gatekeeper. Dedicated To Merapati🦋 Basma Hassy zaune suna duba abu cikin phone din Basma, Merapati ta shigo kallo daya tayi musu take kunyan Basma yakamata saboda yanda ta fada mata maganganu a lokacin. Mikewa sukayi a tare Hassy tace "lafiya naganki a haka?" Basma ta matso ta kamata bayanta zaunar da ita sannan ta zuba mata ruwa a cup ta mika mata amsa tayi saida tasha rabi ta ajiye cup din a gefe kallon Basma tayi her voice is so slow "I’m so sorry Basma,,at first I don’t trust you buh now I agree with you! we are in a different world." In shock suke kallonta "What do you mean?" Hassy asked as she took a seat next to her.... Merapati looked at her "Um I mean I saw myself, amma kuma bani bace ba but it was me" Gaba daya shiru sukayi saboda sun tabbata cewa Merapati taga Sheenaz. Basma tace "sai yanzun nagane abinda kike nufi kuma dama abinda mukeso kigani kenan ta hakan ne kadai zaki yadda cewa ba a duniyar mu muke ba muna wata duniya ce daban wanda mu kanmu bamu san ta yaya kokuma ta ina mukazo ba,,,kuma bamu san ta ina zamu koma ba,Kuma na tabbata yanzun kingane komai bakya bukatar wani karin bayanin! Yanzun abu uku ne a gabanmu na farko kota halin yaya ne karki bari masu hotel din nan suke ganinki saboda komai zai iya faruwa idan har suka gano bakene ainahin Madam din su ba...Abu na biyu dole ne musan hanyan daza mubi domin komawa duniyar mu sai kuma abu na karshe wanda shine yafi kowanne hadari kada mu nuna wata alama cewa ba anan duniyar muke ba cause people are dangerous now we must be very careful...." Maida kallon ta tayi kan Merapati taci gaba da cewa "karki damu kanki muma farko haka muka shiga rudani a lokacin da mukaganta sunanta Sheenaz" Kallonta suke gaba daya jikinsu yayi sanyi Hassy tace "dama hakan tana faruwa? do you think there is a different world like ours, and they live as we do?" "Yes, there are different worlds and in them there are different beings who live just like we do, just like you see in this world..There are different species and each species has its own way of life. One day I will tell you how a bee lives....you will see how it lives I am sure you will be amazed.." Basma continue with her explanation...... ~* Yau kwanan su 20 cif a sabuwar duniyar dabasu san tayaya sukaje ba,kuma tundaga ranan Merapati komai irin na Sheenaz takeyi wanda hakan yasa ba a ganeta. Suna zaune kowacce da tunanin datakeyi knocking akafara a kofan kallon kallo aka shiga saboda indai ba order sukayi ba babu mai shigo musu daki kuma yanzun lokacin Lunch baiyi ba bare suce sunyi order,Hassy ce taje ta bude kofan wata mata tagani sanye da black abaya saikuma face inta data sa nikab...Hassy looks at her,her face was full of surprise "who are you?what are you doing here? what do you need from us?" She just smile and say "please let me in i need to talk to you, and it's an important issue trust me." Juyowa tayi ta kalli su Basma kanta tayi nod alamun tabarta ta shigo.... Cikin nutsuwa take takowa harta iso cikin parlourn kallonsu take daya bayan daya akan Merapati ta sauke idanunta saikuma ta cire nikab din baki bude suke kallonta Merapati kuwa mutuwan zaune tayi zuciyanta yana bugawa da karfi ganin tsananin kamar ta da Sheenaz, komai da komai iri daya ne hatta tsawon su da hasken fatarsu, gefe guda kuma a tsorace suke ganin yanda suka shiga tashin hankali yasata sakin murmishi tace "ku kwantar da hankalinku banzo da niyan cutar kuba,nazo nan ne da niyan taimakon ku saboda nariga dana sani cewa ku baki ne a wannan duniyar tamu.... I know you don't exist in this world" Mamakin su yakaru to wai tayaya ma tasan cewa su baki ne a wannan duniyar? Zama tayi a daya daga cikin kujerun taci gaba da cewa "nasan kuna mamaki ta yanda akayi nasan ku baki ne ko? because I am the gatekeeper and no one can enter or leave without my knowledge! Tun ranan da kuka shigo nasani saidai a lokacin ina busy sosai shiyasa banbi ta kan lamarin ku ba, sannan principal din mu takira Dad dina tanayi masa complain akan cewa ta ganni a wata school din daban wanda nikuma nasan bana zuwa wata school idan ba wadda Dad yasani ba tundaga nan nafara tunanin akwai abinda ke faruwa...Saikuma Manager dina(Hotel Manager) yakirani yana bani hakuri akan abinda yafaru nan ma nakara tabbatar wa something's wrong saikuma kwatsam na hadu da Hassy Wanda harna bigeta nakaita hospital shima tundaga nan na kara yadda akwai abinda yafaru saboda yanda take kallona tamkar ta sanni saikuma naji ta kirani da suna Merapati....and ranan dana fara ganinki I was surprised when I saw you" she pointed at Merapati..."Tun farkon shigowata Park din naganki amma ke baki ganni ba shiyasa nabarki kikayi magana da fiancé dina saboda in tabbatar da cewa you’re me, cuz I know ta wani bangaren zamu iyayin abu iri daya ,sai gashi yazo yayimin complain akan cewa abinda nayi masa a park sam baiji dadi ba...and I was surprised yanda kikayi treating din fiancé na exactly haka nakeyi mishi duk lokacin da muka samu matsala! Jiya kuma ina zaune Manager yakirani akan cewa zaman da nikeyi a hotel bashida amfani gara nakoma gida don ya tabbatar da ace Dad dina yana gari bazan zauna a hotel tsawon kwanaki ba...Tundaga jin bayaninsa nagane kene wadda nagani a Park...kuma dama inason haduwa dake amma bansan ta ina zanfara ba Shiyasa yau na shirya domin zuwa nasa meku sannan kuma lokaci yayi dazaku koma gida ina nufin ainahin duniyar ku." Basma ta kalleta "amma tayaya kike ganin zamu iya komawa duniyar mu?" Smile tayi tace  "Three days before the rise of a blue moon" "Wait I dont understand,can you explain it?" Merapati ask her. She keep smiling and talking at the same time "Normally blue moons come only about every two or three years...you guy's are very lucky nan da kwana biyu zaku koma duniyarku." Hassy tace "yanzun a misali idan naje wata duniyar daban dole saina jira blue moon sannan zan iya komawa ainahin duniyar mu? Like saina jira shekarun fitowar blue moon?" Kanta ta gyada "aa gaskiya tunda ko wace duniya yanayin yanda suke rayuwa daban ba lalle bane ace komai zai zama iri daya." Basma ta sake jefo mata tambaya "kintaba zuwa wata duniyar ne bayan wannan?" Murmishi takarayi taci gaba da cewa "gaskiya bantaba zuwa ba tunda ana gargadin mu akan mu kula da inda muke zuwa...Some places are very dangerous." "Amma tayaya kika zama gate keeper? Naga bakida wasu shekaru" she just smiled and said "maybe I'm among the luckiest one's..." ~* Tundaga ranan komai tare sukeyi Basma Hassy Merapati Da Sheenaz sun shaku sosai har sunajin bazasu iya rabuwa da itaba tanada matukar kirki gata mace mai son jama'ah don yanzun haka ma suna tare a hotel din duk da Sheenaz taso suje gidan su amma sunki saboda suna ganin hakan kamar zai haifar da wata mtsalan daban.. Kuma a gobe suke shirin komawa duniyan su...dukkan su suna zaune shiru sam basason rabuwa da Sheenaz itama haka don jitakeyi kamar ta bisu su tafi tare amma hakan bazai taba yiwuwa ba ita kadai Allah yabama iyayenta.. Kamar wancan karon tafiyan 8hrs sukayi sannan suka iso wajen, tent aka hada musu sannan Sheenaz ta sallami masu hada tent din shiga sukayi dukansu shiru sukayi saboda aihinin rabuwa da juna.... _1:00am_ Hasken farin wata ne yafito sosai wanda ko allura ce ta fadi mutum zai iya ganinta saboda tsananin haske da girman moon din...Cikin dajin suka shiga daidai wajen dasuka tsinci kansu suka koma...Hugging dinta sukayi gaba daya kuka sukeyi sam basason rabuwa. Bayan sungama bankwana Sheenaz tafara fadan wasu magic words take wata irin iska mai karfi tafara kadawa cikin karamin lokaci suka daina ganin komai walkiya aka fara cikin second's komi yakoma daidai....Wani irin kuka ta Sheenaz takeyi mai tsuma zuciya! Lokacin dasuka bude idonsu a wannan wajen katangar suka tsinci kansu. Hamdala sukayi Merapati tafara duba inda Sheenaz ta kwatanta mata wanda ta nan ne kadai zasu iya komawa ainahin duniyar su...Ganin da gaske dai komawa zasuyi yasa Hassy cewa "Ku tsaya..." Juyowa sukayi suna kallonta Itama kallonsu tayi a hankali taci gaba da cewa "kuje niba yanzun zan koma ba." Wani banzan kallo Merapati tayi mata Basma tace "what the actual fuck! What do you mean?Anya kina cikin hankalinki kuwa Hassy? Kaman yaya ba yanzu zaki koma gida ba?” Hannu ta daga mata "dakata malama ba zai yiwu kisani a gaba kina fadar maganganu son ranki ba saboda niba yar ki bace ba kuma cewa nayi nibazan biku ba kokinji nace kiji rani?" ta karasa maganar cikeda masifa. Merapati ta kalleta "kamar ya bazaki bimu ba? Akan wani dalili kenan?" Dagowa tayi "saboda haryanzun banga irin abubuwan mamakin da na ke son gani ba, banga wani abin mamaki ba wanda zan iya bada labarin sa ba....nasan yanzu idan nakoma iyaka ince naga wata alkarya mutanen cikinta suna rayuwa tamkar yanda muke rayuwa saidai basa amfani da irin kudin mu sannan kuma naga mai......." "shut the fuck up! are you out of your fucking mind?duk irin abubuwan da muka gani acan bai baki mamaki ba? Anya lafiyanki kuwa?" Merapati ta katseta ranta a matukar bace. Hassy kam ranta yabaci itama cikin bacin rai take magana "Mega Aura Pangesti bance dole dole saikin biyo ni ba kuma ra’ayina kenan bazan koma gida ba, haryanzun bangama ganin abubuwan mamakin da nikeson gani ba wanda kullum nike mafarkin su,and alamu ya nuna cewa bakisan abubuwan mamaki ba,kutafi kawai aina san hanya..." Basma matsowa kusa da ita tayi cikin sanyin murya take mata magana amma sam taki saurarenta... Cigaba tayi da cewa "Nifah babu wanda zai sani tafiya nafada muku haryanzun banga abubuwan mamakin da nikeson gani ba..just fucking go, I know how to get back home" she shouts at them. Ganin bazata yadda ba yasa Basma kallon Merapati tace saidai ta tafi amma ita zata tsaya a wajen Hassy bazata taba barin ta ita kadai ba...Baki bude take kallonsu tsaki tayi tace "shikenan kuyi duk yadda zakuyi don kunga ina biye muku shiyasa..." bag dinta ta dauka sannan tafara tafiya ganin hakan yasa Basma kamo hannunta kallo daya zakayi mata kagane cewa tana cikin damuwa sosai kanta take girgiza wa a hankali ga hawaye yana zuba ganin hakan yasa jikin Merapati sanyi kamo hannunta tayi sannan tafara goge mata hawayen....Murmishi ta kakaro tace "shikenan kibar kuka zanbi ki amma wannan shine last dazan kara biyema wancan shashashar yarinyar..." Takarasa maganan tana hararar Hassy..Itakam bakinta ta tabe sannan ta daga kafada alamun she don't give a damn..... Direct Kofar Arewa suka nufa....Bayan sun lalubo key din Basma ta bude take kofan tafara budewa a hankali shiga sukayi suna gama shiga kofar takoma ta kulle kanta wanda idan mutum bai saniba zaiyi tunanin babu wata alamar kofa a wajen..... Kofar tana gama kullewa take wajen yazama fari fat ga snow suna zuba saidaga can gaban su wata kofa ce itama fara tass...Batareda da shakkar komi ba Hassy taje wajen kofar hannunta tasa ta bude kofar....Budewa take a hankali har tagama bude kanta shiga tayi nan suma su Merapati suka bi bayanta.... Da wata irin murya wanda bazasu iya tantancewa ba aka fara magana wanda har saida suka saka hannunsu akan kunnensu saboda tsabar rashin dadin muryan... Ga abinda muryan ke cewa: "Καλώς ήλθατε στον κόσμο της μαγείας και του θαύματος...(Kalós ílthate ston kósmo tis mageías kai tou thávmatos...)" "(Its greek means, Welcome to the world of magic and wonder....)" @NM__🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 10: A New World. Kofar tana gama kullewa take wajen yazama fari fat ga snow suna zuba saidaga can gaban su wata kofa ce itama fara tass...Batareda da shakkar komi ba Hassy taje wajen kofar hannunta tasa ta bude kofar....Budewa take a hankali har tagama bude kanta shiga tayi nan suma su Merapati suka bi bayanta.... Da wata irin murya wanda bazasu iya tantancewa ba aka fara magana wanda har saida suka saka hannunsu akan kunnensu saboda tsabar rashin dadin muryan... Ga abinda muryan ke cewa: "Καλώς ήλθατε στον κόσμο της μαγείας και του θαύματος...(Kalós ílthate ston kósmo tis mageías kai tou thávmatos...)" "(Its greek means, Welcome to the world of magic and wonder....)" Muryan tana gama fadar hakan wata irin guguwa mai karfin gaske ta fito nan take tafarayin sama dasu gaba dayan su ihu sukeyi saboda yanda guguwan take juyi dasu...Cigaba sukayi dajin muryoyin kala daban daban wanda sam basa gane abinda ake cewa.....Daidai lokacin komi yadawo normal...A matukar galabaice suka fado kasan wajen. A tare suka bude idonsu mikewa sukayi suna tattara kayansu bayan sun gama tsab nan suka fara bin wajen da kallo manya manyan duwatsu ne saikuma daga can gefe babban kogi ne amma wajen gaba daya snow ne ga snow flakes sunata zubowa amma kuma basajin sanyinta hakan ya tabbatar musu da cewa wannan duniyar tasha banban datasu Sheenaz...saidaga can gefe guda wani katon dutse ne wanda duk yafi sauran girma da tsawo....Saikuma kananun bishiyu masu kyau amma jikinsu duk snow ta rufe su hakan saiya kara musu kyau gakuma wasu red roses nan kasan kowace bishiya amma su jikinsu babu snow saima wani irin kyalli dake fitowa daga jikinsu a fili Basma tace "wow this place is very beautiful,,wonderful and amazing....." Gaba tafarayi nan tafara taba bishiyan gabanta..Kuma atake suka fara jiyo wani irin kalar gurnani... Wasu wolf ne suka fara fitowa ta cikin wannan katon dutse din ganin hakan yasa su Merapati hadewa a waje daya ja da baya sukeyi kuma abin mamaki duk inda suka taka saidai kaga sahun takalmin su ya goge tamkar babu wanda yataba taka wajen tsayawa sukayi saboda bayansu babu komi sai katon kogin nan, gashi wolf din kallo daya zakayi musu kagane cewa yunwa sukeji...Basma tace "mene mafita yanzun?" juyawa tayi ta kalli ruwan kogin shikanshi indai mutum yafada bazai rayu ba saboda wasu irin manya manyan kifaye ne a ciki.... Wata daga cikin wolf din ce tayo tsalle da nufin cinye Hassy saida tabari tazo dab da ita sannan tayi gefe guda ita kuma wolf din tafada cikin kogin hankulan su take yakara yatashi ganin yanda wasu kananun kifaye suka zagayeta kafin cikar minti daya harsun cinye ta...duk da cewa kananun kifaye ne amma sunfi manyan hadari su atake suke hallaka mutum dakuma duk abinda yafada cikin kogin...Basu gama tunanin mafita ba nan take wajen yafara wata irin girgiza tamkar za ayi girgizan kasa...Su kansu kananun wolf din neman mabuya sukeyi ganin hakan yasa su Merapati mamaki tabbas akwai wani abu wanda yafi wadannan wolf din hadari tunda gashi suma gudu sukeyi domin tsira da rayuwansu....Wannan katon dutsen ne yayi girgiza take yakoma wata irin katuwar wolf saikuma wasu kanana guda biyu suka fito Tunda suke basu taba ganin wolf mai irin girman wannan ba. Kallonsu farayi kuma daga irin kallon datake musu suka gane cewa da wahala idan za su tsira da rayuwansu...A yanzun sun riga dasun gama tabbatarwa mutuwa zasuyi...nan da nan nadama tazowa Hassy ina ma ace batazo nan ba inama ace zata iya maida lokaci da binsu Merapati zatayi sukoma gida..yanzun shikenan baza ta kara ganin Abbantaba? Yanzun shikenan baza ta kara ganin mom dinta ba Allah sarki Khady...sosai take nadama kallonsu Basma tayi cikin sanyin jiki take magana suma ganin hakan yasa jikinsu jin sanyi hugging dinta sukayi dukansu....A hankali tace "I'm so sorry! It’s all my fault.." Wolf dince tafarayo kasa da kanta sun riga dasun cire ran zasu sake rayuwa kuma suna ganin cewa bazasu taba komawa gida ba daidai lokacin wata tsuntsuwa(eagle) Ta bayyana a kusa da wolf din a hankali kasar wajen tafara girgiza....Suddenly the girl with the cape as red as blood appeared in front of them....Her voice is completely different, she look at the wolf and said "μην τους πληγώσεις (min tous pligóseis)" Tana gama fadar hakan wolf din takoma dutsen suma sauran duk suka bace Juyowa tayi tana kallon su "mekukazo yi nan? Mene dalilinku na shigowa wannan duniyar tamu mai hadarin gaske?shin bakwa tsoron wani abu yasameku?" shiru sukayi saboda basuda amsar bata "follow me" Kawai tace saikuma tafara tafiya akan Iska..... Ganin hakan yasa su daukan bags dinsu suka fara bin bayanta saidai tsayawa sukayi ganin kogin gabansu kuma babu wata hanya da mutum zai iya bi dole saita cikin kogin itama Juyowa tayi ganin sun tsaya dafe kanta tayi "oops sorry" saikuma tafadi wasu magic words...Dagowa tayi tace "kubiyoni...ta cikin kogin babu abinda zai faru daku." Hassy ce tafara sauke kafanta a kan kogin saidai ga mamakinsu Basma maimakon tafada cikin kogin saigani sukayi tana tafiya akan kogin tamkar akan kasa take tafiya....Wani farin ciki taji kobabu komai taga babban abin Mamaki wanda yafaru da ita...Bin bayanta sukayi saida sukayi tafiya mai Nisan gaske sannan suka iso cikin wani daji... Daji ne mai kyau ga bishiyu kala daban daban wadda ko wace bishiya tana motsi Sosai suke Al'amura tamkar yadda mutane sukeyi kuma duk lokacin dasukazo dab dasu saidai kaga suna bude masu hanya su Basma suna wucewa.. A jikin wata bishiya yarinyar ta tsaya ganin hakan yasa su Merapati tsayawa....Bin bishiyar suke da kallo idonsu ya sauka akan wata karamar kofa wanda ko mage bazai iya shiga ba amma ga mamakinsu sai yarinyar tace su shiga ta nan dariya suka fara mata Basma hada faduwa akasa saboda dariya Hassy tace "to wannan kofar ko mage bazai iya shiga ba bare kuma mutum." Merapati tace "sotake ta raina mana hankali kawai amma tayaya mutum zai iya shiga nan ai wannan gidan dana fairies yayi kama." Kanta kawai ta gyada tace "idan kungama shirmen na tabbata dakanku za ku shigo, well I will wait for you when you are done with your childishness" tana gama fadar hakan ta shige kofar...sudai su Basma bazasuce tayaya kokuma yaya akayi ta shiga ba tamkar walkiya haka ta bace bat... Zama sukayi akasan bishiyar gashi garin yafara duhu...Basu dade da zama ba suka fara jiyo wani irin takun sawaye tamkar dajin gaba daya zai rusa..Komai na cikin dajin girgiza yakeyi ga gurnanin yana kara kusanto su....Cikin kankanin lokaci suka fara hango wani irin duhu ya mamaye sararin samaniya, yana kusanto inda suke...mutum daga nesa zaiyi tunanin duwatsu ne manya amma saika kura ido zaka gane cewa wasu irin Giants ne masu tsananin muni,tsawo da girma, kuma duk abinda ke gabansu saidai kaga sunyi masa loma daya duk girman abun kuwa nan take tsoro ya kama zuciyoyinsu basu gama shiga tashin hankali ba saida sukaga wani daga cikin giants din ya nufo inda suke saboda yaji kamshin su....ai da wani irin gudu suka mike atare suke kokarin shiga karamar kofan duk da a tunanin su tayi musu kadan amma tamkar sun shiga cikin iska haka sukaji su domin kuwa lokacin da suka matso dab da kofan ji sukayi anyi sama dasu nan suka tsinci kansu a wani hadadden gida..Mai kyau da tsaruwa....Yarinyar tana zaune akan wani katon dinning table wanda manya manyan kujerun zinare guda goma sha biyu sukayima kawanya sannan ga abinci kala kala a jere akan table din sannan ga kyawawan yammata suna mata hidima dukansu Juyowa sukayi suna kallon su Hassy saboda yanda suka fado gidan tamkar jefo su akayi atare sukayo kansu take fuskan su ta sanja color daga ta mutane masu kyau zuwata munanan tsoffin aljanu gawasu irin hakora masu girma a bakinsu gaba daya jikinsu ya yamutse babu kyan gani...Hannayen su farce ne masu tsayin gaske kowaccen su tanada kusumbi wanda hakan yasa basa iya dagowa sosai saikuma gashin kansu duk babu baifi guda goma goma ba shima fari ne fat kuma a rarrabe suke wanda hakan yakara musu muni ainun....Kansu Merapati sukayi gashi suna fitar dawani sauti mai ban tsoro take idanunsu yakoma fari...Mikewa sukayi ganin duk sun zagayesu kallo daya zakayi musu kagane cewa akodayaushe zasu iya afka musu...Da murya daban daban take cewa "άφησέ τους (áfisé tous) leave them..." Take suka koma siffar mutane kyawawa, durkusan da kansu sukayi alamun girmamawa takowa take harta iso kusa dasu Hassy juyawa tayi ta kalli yammatan tace "su din bakin mune kubasu kulawa tamkar yadda zaku kula dani saboda sunada muhimmanci a rayuwata kuma ta sanadin sune zansamu nacika babban burin da nikeson cikawa." Nan wasu daban sukazo suka amsa bag's dinsu...Sannan aka zaunar dasu a babban dinning table din aka cika gabansu da kayan ciye ciye da kayan shaye2...yawunsu ya tsinke saboda abincine irin na alfarma wanda wani ma basu taba gani ba sosai sukaci suka sha..Sannan tace akaisu su huta suyi wanka abasu kaya masu kyau su sanya.... Baki bude suke bin wajen da kallo... Karamin kogi ne mai kyau da haske amma kuma hawa hawa ne kuma kowani ruwan ciki kalarsa daban ne duk lokacin da ruwan yayi motsi saidai kaga color din wajen yana sanjawa...ga furanni kala kala awajen sannan akwai wasu birds sune suke cirema mutum kaya kuma su dauko masa towel sannan sune zasu tayaka wanka..."Wow " Hassy tace tana shigewa gaba don su Merapati suna tsaye suna ganin abin mamaki ko a mafarki basu taba ganin irin hakan ba, Basma jumps for joy and say "wow just wow...this place is very beautiful and magical... I love itttt" Daya daga cikin kogin tashiga bayan ta cire kayanta ruwan yanada kamshi sannan bashida sanyi kuma babu zafi sosai yayi..wasu birds sukaje domin tayata wankan jinta take tamkar Cinderella a yanzu hakan... Merapati ma shiga tayi nan take ruwan yasanja color daga blue zuwa fari amma duk lokacin data motsa kafanta saidai taga ruwan wajen yakoma light blue in seconds kuma saiya koma daidai......wani murmishi tasaki aranta tana godema Hassy saboda badon ita ba bazata taba ganin wannan abin birgewan ba, kuma gefe guda tanajin haushin kanta akan cewa da tuni tayima kanta da ace bata biyo Hassy ba.... ~* *DRAKAINA: THE DRAGON KINGDOM* Babbar masarautace wadda ta amsa sunanta saidai ba kamar sauran masarauta take ba kodaga yadda aka tsara ginin masarautar mutum zai gane cewa lalle akwai wani babban lamari acikin masarautar.... Babbar katanga ce wadda ta zagaye ilahirin garin saikuma ginin masarautar a can sama wato duk sauran gidajen a kasan masarautar suke saidai kamar yadda kowanni gida yake a kasa to ita wannan masarautar ba a kasa take ba kuma ba sama take ba wato dai tana tsakiya ne wanda duk tunanin mai tunani bazai taba ganin ta inda zai shiga ba saboda babu wata matattakalar dazatakai mutum zuwa cikin masarautar sannan kuma gaba daya garin bakin kirine duk gidajen sunyi yana duk da cewa akwai mutanen dake rayuwa a ciki...Wanda idan mutum shi bako ne zaiyi tunanin shekaru sama da dubu babu wanda ke rayuwa a garin....Kaf cikin garin masarautar ce kadai batayi komi ba.....sannan abinda zai bama mutum mamaki yadda yan garin basa amfani da hannun su wajen yin aiki duk wasu bukatu nasu da magic sukeyi sannan basa sa kaya illah kayan fata kodaddu yamutsatstsu su kansu kayan sunyi bala’in tsufa yan gidan sarauta ne kadai sukeda Ikon sa kaya masu kyau saboda karfin magic dinsu kuma hakan yasamo asaline saboda wata annoba datake damun garin tsawon shekara da shekaru...... Saikuma daga can gefe katuwar majami'a ce (temple) inda a nan babban gunki su yake mai suna *NOVA* gunkin yanada siffar dragon ne... Kyakykyawar budurwa ce ta shigo cikin masarautar kallo daya zakayi mata ka tabbatar tana cikin tashin hankali dakuma fargaba saboda tsoron hukuncin da zata jama kanta muddin maganar data fada batayi tasiri a zuciyar Queen Drakaina ba..... Babban kofan shiga ainahin fadar aka bude mata fada ce mai kyau da tsaruwa wanda baxan iya kwatanta muku ba komai na cikinta shima da magic yake amfani.... Kyakykyawar Budurwace zaune akan wata throne jikinta sanye da kaya na alfarma saikuma kyakykyawar crown akanta..Jin an bude kofar yasata dagowa zubama guard din ido tayi ganinsu rikeda wata yarinya alamu tayi akan su sake ta...Matsowa tayi she fell on her knees and said "vasílissa mou éftasan "my queen they've arrived.!!" @NM__🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 11: Untold Story. Kyakykyawar Budurwace zaune akan wata throne jikinta sanye da kaya na alfarma saikuma kyakykywar crown akanta..Jin an bude kofar yasata dagowa zubama guard din ido tayi ganinsu rikeda wata yarinya alamu tayi akan su sake ta...Matsowa tayi she fell on her knees and said "vasílissa mou éftasan, my queen they've arrived...." Da sauri ta mike daga kan throne din kallonta take tamkar yau tafara ganinta saikuma ta zauna cikin muryanta mai dadin gaske tace "Are you sure,you're telling me the truth?" She nods her head and say "Of course my queen,I'm telling you the truth" Mikewa takarayi a karo na biyu..taci gaba da zagaye dakin...Juyowa tayi tace "yanzun Catrina tayaya kike ganin zansa su suyimin abinda nikeso?kin riga dakin sani cewa idan har basu taimake muba muna cikin tashin hankali tunda ko abin bautarmu ya tabbatar mana da cewa ta hanyar wadannan bakin ne zamu samu muyi maganin damuwar mu, saboda shima abin yafi karfinsa ga kuma babban tashin hankalin mu yau saura kwana goma ciff wadannan halittun su bayyana kuma kinsan illar su da hadarin su, I want to protect my peoples, my kingdom this time! I’m tired of loosing my people!!" Komawa tayi ta zauna kallo daya za kayi mata ka gane cewa tana cikin tashin hankali, damuwa da fargaba. Matsowa Catrina tayi cikin sanyi murya tace "My queen karki damu tunda har abin bauta ya tabbatar mana zasu taimake mu to kibar damuwa kuma zanje nakawo miki su har cikin masarautar nan nayi bincike a madubin tsafina nagano suna tareda Princess Mithian" dagowa tayi da sauri "poiá eínai aftí?,(Who is she)?" "Princess Mithian The Wolf Queen Tana can cikin kogon ta wanda babu wanda zai iya shiga harsai idan itane taso hakan," cikin girmama wa taci gaba da cewa "kuma dalilin daya sa ban kawo miki su ba saboda lokacin da suka shigo wannan duniyar tamu da ita suka fara haduwa kuma itama akwai wani burinta datakeson cikawa kuma ta hanyar wadannan bakin fuska din ne kadai zata iya cikashi! Ki gafarceni yake gimbiyatah naso ace kece kika fara haduwa dasu ba Princess Mithian ba!" Lady Catrina takarasa maganan tana durkuwa sa akan gwiwoyinta. Dagowa tayi ta zuba mata ido wanda harsun fara sanja color saboda tsananin damuwan data ke ciki...A hankali tafara magana "inason ahadamin keken doki yanzun amma banson kowa yasan zan fita daga ni saike kawai, as páme sto spílaio tóra, let's go to the cave now" "your wish is my command" tana gama fadar hakan ta fice daga cikin fadar... ~* Merapati Hassy Basma suna zaune a makeken bed din dake dakin shikan shi bed din ba kamar irin wanda kuka sani bane ba, Gado ne wanda akayi shi da fatar dabbobi sannan jikinsa anyi masa ado da gashin dawisu wanda hakan yakara masa kyau da tsaruwa sannan idan mutum yahau saboda tsananin laushin gadon mutum ji zaiyi tamkar zai lume a cikin sannan ga wasu irin kwari masu haske wanda sune a matsayin fitila din dakin kuma suna sanja color duk bayan minutes. Basma tace "nifa ji nike tamkar mafarki nikeyi" Merapati ma murmirshi tayi tace "nima haka, bantaba tunanin zan tsinci kaina a irin wannan wajen ba!thank you" ta karasa maganar idon ta kan Hassy, Da ido tayi mata alamun "for what.?" Kafadarta ta gyada alamun Bansaniba gaba daya dariya suka saka....Hassy tace "amma nifa da akwai abinda ke bani mamaki. Kun lura da cewa tunda mukazo gidan nan bamuga sunyi sallah ba,gashi kuma kamar wani Gunkin mace suke bautawa nikam abin yana damuna!" Suna shirin bata amsa aka bude dakin wannan yarinyar ce wadda har yau basu san sunan taba Zama tayi a kusa dasu tace "hiran me kukeyi ne?" Basma ta kalleta "kawai muna mamakin yadda komi yake faruwa tamkar a mafarki muke ganin hakan." Smile kawai tayi Hassy "gashi kuma haryanzun bamu san sunanki ba? Bamusan komi akanki ba" "Princess Mithian haka shine sunana sannan maganar baku san komai akaina ba lokaci nike jira a wannan lokacin zan fada muku ainahin ni wace dakuma taimakon da nikeso a wajenku.." Kallon kallo aka shiga Merapati tace "taimako kuma? wani irin taimakon kike bukata daga garemu? Kalleki fa sam bakiyi kama da mai neman taimako ba you have everything.." Kanta kawai ta gyada saidai kafin tayi magana sukaji wajen yafara motsawa kasar wajen ma tafara girgiza da sauri ta fito daga dakin suma haka. Wata budurwa ce sanye da kayan sarauta saikuma wata budurwan daban sanye da kayan fata amma sunyi bala'in yi mata kyau...Da Mamaki Mithian take kallon su saboda wannan shine karon farko da wata ta shigo har cikin gidanta batareda izinin taba hakan ya fusata ta take tafara karanta wasu magic words saidai kafin tagama taga wannan budurwan ta nuna su da hannu gaba daya sama sukayi kuma atake komai ya tsaya cak hatta ruwan dake zuba daga wani kogi suma tsayawa sukayi saidai kadan kadan dasukeyin circle nan suka fara zagayesu saikuma duk wani abu mai motsi shima saida yayi sama gashi sun kasa koda motsa hannun su...Kallonta tayi tace "Princess Mithian banzo nan da niyan fada dake ba na zo nan ne saboda mu hada karfi da karfi domin magance damuwar mu...." Su Hassy ta nuna taci gaba da cewa "Kinsani nasani wadannan bakin sukadai ne zasu iya taimakamana duk da cewa munada karfin sihirin da duk fadin nahiyar nan babu koda wanda yakama kafarmu a harkan tsafi dakuma iko saidai kash duk ya tashi a banza tunda bazamu iya magance matsalan muba....Ina rokon Alfarma kiyadda dani mu hada hannu da hannu nikuma nayi rantsuwa da darajar abin bautana bazan ci amananki ba....daga karshe sunana Queen Nimueh...Amma anfi sanina da Drakaina." Kara nuna su tayi da hannun gaba daya suka zubo a kasan wajen.. Dukan su zama sukayi saidai an rasa mai mgana can Hassy tace "shikenan zamu taimaka muku amma saimunji ainahin abinda ke damunku kafin nan muma akwai sharadin da mukeson kuyi mana kafin mu yadda da bukatun ku." Drakaina tadago ta kalli Mithian "yanzun ke mene zabin ki? Ina ganin yakamata kubiyoni zuwa masarauta ta domin muyi magana sosai...nasan kinada bukata amma kuma bansan wace iri bace ba kamar yadda kema bakisan tawa ba shi yasa nikeson mu zauna waje daya domin kowa taji bukatar kowa dakuma matsalan da muke ciki" shiru tayi harsun cire rai akan zatayi magana...Mikewa kawai tayi ta dauki wata jakar fata tacema su Merapati suma su dauka bag dinsu. Hakan yana nufin cewa ta yadda zata bisu kenan. Bayan sun fito a sannan suka lura cewa keken dokin yayi musu kadan, Princess Mithian batace komai ba, wata karamar tsuntsuwa ta fito da ita daga cikin bag dinta wasu magic words take fada saikuma ta jefa tsuntsuwan sama take ta bace cikin gajimarai ba ayi cikakken minti daya ba su Hassy sukaga sama tafara hada hadari gakuma tsawa ta cika dajin wata katuwar eagle ce ta bayyana, A gaban Princess Mithian...Baki bude suke kallon girman eagle din take mamaki ya gama cika su...Kan ta suka hau ta lula dasu can cikin sararin samaniya ganin hakan yasa itama Drakaina kallon Keken dokin ta nunashi da hannu shima yadawo wata katuwar dragon hawa sukayi suma suka shige cikin gajimaren.... @Drakaina Kingdom Dukan su suna zaune a babban parlourn bakin....Kowacce da abinda ke ranta....Gyaran murya tayi ta fara cewa "Mithian,Merapati,Hassy,Basma inason kubani hankalinku nan inason ku nutsu kuji labarin dazan baku saboda a cikin sane zaku gane irin matsalan da muke ciki dakuma irin taimakon dazakuyi mana kafin nan da cikar kwana goma." Mikewa tayi wani babban littafi ta dauko wanda saboda ajiya duk yayi kura da yana...Sukam su Merapati basu taba ganin littafi mai girman wannan ba tsab karamin yaro zai iya bacci akai saboda girman littafin. Anyi Rubuta da manyan harufa THE CHRONICLES OF NAINAH. "As I told you before dama wannan novel din zai tabo bangare biyu a ciki zakuji asalin labarin Nainah (Macijiya My first novel) wanda bansamu na karasaba Ma Shaa Allah the time has come let's go to another world...🤣 I hope you will enjoy this story Of *Nainah The Mysterious Girl*" Shafin farko ta bude zanen wata Kyakykyawar budurwa ce saidai rabinta mutum rabinta kuma maciji, cikeda al'ajabi suke kallon hoton Basma tace "who is she...??" "Her name was Nainah the most beautiful princess in the world she's a serpent...." Next page ta bude saidai babu komi sai wani rubutu baifi layi uku ba "Some time ago, over a thousand years ago, a baby girl was born the mysterious girl.....Let me tell you the complete story" ~* Mallam Habu Shine Asalin Sunanshi yana zaune a wani kauye duk karkashin Drakaina suke Talakane Futuk Domin Sana'ar gyaran takalmi yake bashida kowa a garin kuma babu wanda yasan daga ina yazo acikin haka yahadu da suwaiba yarinyar wani babban malami ne a wancan karnin...shine ya nemi aurenta suwaiba macece mai biyayya,kawaici,dakuma hakuri Sundauki tsawon lokaci basu haihuba saida suka kusan shekara goma sha biyu sannan tasamu ciki murna wajen Mal Habu ba a magana yakanyi kokarin ganin yafaranta mata duk da shi din talakane amma yanada zuciyan nema duk wani abu datake bukata yana siyo mata idan yashiga kasuwar Drakaina a wancan lokacin babu kasuwar data kai ta Drakaina saboda garin yanada ni’ima sosai...Saidai wani abu dake bama Suwaiba mamaki tun lokacin data samu ciki take mafarkin macizai amma abinda yafi daure mata Kai acikin macizan akwai wani fari ne tass wanda take gani yana wani irin kuka wani lokacin har magana yake mata amma da zarar safiya tayi saita manta abinda yake cemata Kwanci tashi asarar mai rai yau cikin suwaiba ya isa haihuwa wata ranan asabar cikin dare nakuda takama suwaiba nan MAL Habu ya fito domin kiran ungozoma yana fitowa yaganta a kofar gidansa batareda tunanin komiba yace ta shigo dama kiranta zaije itadai batace komai ba tabishi zuwa cikin gidan da taimakon wannan tsohuwar suwaiba ta haifo santaleliyar yarta nanda nan wannan tsohuwar ta gyara maijego da jaririyarta sannan tagyara wajen tas kamar ba ayi haihuwaba kunna turaren wuta tayi sannan tafice daga gidan batareda sanin kowaba washegari anata zuwa barka har ranan suna ta zagayo akasama yarinya suna NI'IMATULLAH suna cemata NAINAH Mal Habu Yayi komi daidai karfinshi..... Manage it please! Thank You For Reading My Story!! @NM__🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 12: NAINAH. Washe garin suna suwaiba tana bawa Nainah Tsotso saitaji kamar wani Abu Ya cije ta a Mamanta sosawa ta farayi sai kuma tafara wani irin amai yin aman take kamar ta amayar da kayan cikinta dasauri mallam yafito yana tambayanta "lafiya menene sameta?" kafin wani lokaci tuni ta fita hayyacinta Mal Habu ne yaruga aguje yakira wani Malamin gargajiya lokacin dasuka iso harta suma awajen da taimakon Mal suka kaita inuwa bayan wasu yan gwaje gwaje Malamin ya tabbatar masa dafin macijine ajikinta kuma irin macijin yanada babban hadari bare kuma ace ya zuba ma mutum dafin sa wata irin faduwar gaba Mal yaji "dafin maciji kuma tayaya dafi ya shiga jikinta alhalin Nainah Take bama nono?" Malamin yace yakawo yarinyan yagani Mallam Habu yaje ya daukotah tana kwance luf da ita tasa hannu a bakinta suna fitowa Malamin yatashi a firgice yana kallonta saikuma ya aro jarumta ya makalawa zuciyanshi mallam Habu ya zauna rike d Nainah sabanin malamin dayake mata kallon MACIJIYA Malamin ya fiddo wani magani daga jakansa yasa a garwashi take wannan macijiyan tafara mutsu~mutsu shi kam Mal Habu gani yayi Nainah tafashe da kuka saiyafara rarrashinta nantake tausayin Malam Habu yakama wannan malamin gargajiya din domin su suna mata kallon mutum shikuma yana mata kallon MACIJIYA Bayan wasu yan mintina yacema Mal Habu "wannan yarinyar ba mutum bace MACIJIYA Ce.!" Wani Kallon Bakada Hankali Malam Habu yayi masa sannan yace "kamar ya banganeba? yarinyantawa zakace MACIJIYA ce akan wani dalili zakacema ya'ta Macijiyace?" yana maganane cikin bacin rai danuna tsantsar damuwa ganin yanayinsa yasa malamin dafa kafadarsa sannan "kayi hakuri Mal Habu Iyakan gaskiyata nake fada maka yarinyan nan MACIJIYA Ce" ran Mal Habu ne yakara baci yace "fitarmin a gida bana son ganinka" fiewa Malamin yayi ransa yana masa kuna saboda yasan wannan macijiyar muguwace kuma saita sasu zubda hawaye.. Jikin Suwaiba yayi sauki wata ranan alhamis suna zaune Mal Habu yake cemata "wannan malamin dayayi miki magani haka yace Nainah macijiya ce bakiga rashin mutumcin danayi masaba dama nasan a garin nan kowa haushina yakeji akan Nainah saboda sunga yarinya kamar balarabiya duk fadin garin babu mai kyau dinta" Suwaiba dan jim tayi sannan tace "Mal yakamata aduba maganan nan domin tun lokacin dana samu cikin yarinyan nan nake mafarkin..." "keeeeee!!!" yadaka mata tsawa.."bantaba sanin bakya sonaba sai yau kema maganar makiyana zaki dauka ko? to bari kiji nafada maki Wallahi duk ranan dakika kwatanta irin wannan maganar to abakin aurenki!" ya fice fuuuu yanata masifa ...wata faduwar gabace ta ziyarci Suwaiba "meyasa Mal yakasa fahimtar ta tabbas akwai kamshin gaskiya a maganan wancan malamin ko itama shaidace yau kwanan Nainah ashirin cif a duniya amma duk dare idan ta farka bata ganinta.." Al'amarin wannan malamin kuwa bayan yakoma gida yana shiga daki yaga wannan macijiyar ko dar baijiba cikin bacin rai yace "meya kawoki gidana meyasa kika zabi cutar da bayin Allah nan alhalin su da zuciya daya suke zaune dake?Duk abinda sukayi miki basu cancanci haka daga garekiba" wata irin dariya ta kece da ita shi kanshi malamin saida ya firgita.. Saida tayi dariyan mai isarta sannan tayi shiru cikin wata irin murya mai ban tsoro take magana "shin wani tsautsayine yake rinjayar ka meyasa kakeson shiga hurumin daba nakaba? to kasani kasai ajalinka da kudinka" kafin yace wani abu tuni idanunta sun sanja color zuwa bakin kirin babu alamar digon fari a ciki, matsawa tayi kusa dashi hannun ta tasa duka ta kama wuyansa ta dagashi sama wani irin koren hayaki yafara fitowa daga idanunta yana shiga jikin malamin nan take jinin jikinsa yafara komawa jikinta....shure shure yafara anan rai yayi halinsa Batt tabace daga cikin gidan Mal Habu ne zaune yana rike da Nainah suwaiba kuma na cikin kitchen (waje ne aka zagaye kawai) tana dafamusu abincin rana dakyar take aikin saboda Kwana biyun nan duk batajin dadin jikinta haka take fama kamar ance ta kalli can gefenta na hagu saitaga wani irin koren maciji abun mamaki dariya yake mata irinta ta mutane gani tayi yayo kanta aituni tayi waya irin zarananniyar kara tafadi sumammiya Mal...ne yajiyo karar faduwarta cikin sauri yakaraso kitchen din yana maimaita "innalillahi wa inna ilaihir raji'un Suwaiba meyasa meki" ruwa ya debo ya zuba mata firgit ta tashi Sannu yafara mata yana tambayanta meke damunta?Amma sam takasa bude baki tayi magana sai nuna wajen take inda har yanzun macijin yana nan yanayi mata dariya....shikuma Mal yana cemata baiga komiba wasa wasa saida tayi sati daya ba magana kullum cikin firgita da ihu take ankira masu magani dayawa daga sauran kauyukan dake gefen Drakaina amma maganan dayace macijiyace take bibiyarta shikam Mal baya yadda saidai yace so suke suci kudinshi a banza....abu kamar wasa suwaiba takoma abin tausayi saidai a kwantar a tayar ciwo yagama cinye jikinta domin wasu irin kuraje ne suka firfito mata itakam Nainah Babu abinda yadameta sai kara qiba take kuma bata kukan yunwa don tuni an cireta daga tsotso saboda bata iya sha duk kuraje sun fito har akan nonon suwaiba din.... Wata ranan litinin cikin dare jikin suwaiba yayi tsanani domin wani irin yellow amai takeyi kafin cikar sa 'a daya tace ga garinku nan Tabbas mutuwar suwaiba ta tsara duk yan kauyen haka nan Mal Habu Yaji mutuwarta domin suwaiba macece mai tsananin hakuri da biyayya shiyasa Mal Habu yake ganin ba lallai yasamu kamar taba , mutane anata zuwa yimasu gaisuwa kowa da tausayin Nainah yake komawa gida ahaka har akayi sadakan bakwai baban suwaiba yace abashi Nainah tunda acan zatafi samun kulawa amma sam Mal yaki yarda yace abar masa diyarsa zai iya kula da ita dakyar aka lallabashi yabasu ita...Rayuwa kenan yau an wayi gari babu suwaiba kullum Mal yana dakinta yana fadar alherinta wani lokacin kuma yayitah kuka ahaka har akayi arba'in. Kwanaki suntafi lokaci yaja Al'amura da dama sun faru ciki harda girman Nainah yanzun haka shekaranta bakwai amma har yau Mal bai kara aureba suwaiba tana makale a ranshi yana ganin bazai samu kamarya itaba... Yau ranace mai cike da al'ajabi a gidan Baban suwaiba...yarane wanda duk sa'annin Nainah ne suna wasan kasa saiga maciji yafito daga rami yaran ne suka fara ihu suna cewa "maciji,maciji" baban suwaiba yafito dauke da katuwar sandarshi yana shirin buga masa yaji muryan Nainah tana cewa "Baffa karka kasheshi gurina yazo aboki nane." cak yatsaya yana mamakin jin kalamnta kafin yayi wani yunkuri tuni taje gaban macijin ta daukeshi ta dorashi kan cinyanta tana yi masa wasa cikin tsananin tashin hankali Baffa ya nufeta amma me dagowata tayi ta zuba mishi ido tanayi masa wani kallo idonta ya sauya color zuwa fari hakan yasashi jan burkin dabai shiryaba cikin wata irin murya mai ban tsoro take cewa "idan har wannan zancen yafita to kamar ka sanar d jana'izar kane" tuni yafara fitsari a wando....Ba shiri yaruga daki a guje ganin yafita a guje yasa yara da manya suka hau gudu suna fadawa dakinsu....nima tuni nafece daga gidan saboda naga tana hararatah Badamar dauko maku rahoto..... Short Chapter I Know..!!!:) @NM__🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger Dedicated to Merapati♡❥ ~* Episode 13: The Dream. Bayan kamar minti ashirin wannan macijin, ya sauka daga jikin Nainah yakoma ramin daya fito. Baban suwaiba kam yana shiga daki yafara goge zufan data ketomasa, can yaji ana kwankwasa kofan fadawa yayi kan gadon shi yana ihu yana cewa "Dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan fadaba,bazan fadama kowa ba natuba" muryan matarshi Tani yaji tana cewa "nice fa kabudeman" kara rudewa yayi saboda muryan Nainah yaji tana masa amo a dakin tana kara shaidamasa idan harya sake wani yaji wannan labarin to kamar ya yafad'a ma jama'ar gari mutuwarsa ne. Tani kam takara tsorota saboda ihun da Kaka yake yaki tsayawa can tayi dabaran kiran karamin danshi yashiga ta window yabud'e mata kofan, ganin Kaka tayi cikin bargo sai danna ihu yake yana cewa "ya tuba" itakam abin dariya ma yabata jin dariyanta yashashi bude bargon. Ganin Tani na dariya yasa Kaka mikewa cike da kunya borin kunya yafara Tani dariya taji ta ce "yaje yayi wanka saboda fitsarin dayayi duk yagama bata masa jiki.." Karfe 2:30 nadare agogon dakin yabuga kuma adaidai wannan lokacin ne yafara mafarkin wani dajine mai duhuwa yaganshi a ciki babu komi a cikin dajin sai wasu irin tsuntsaye wanda girmansu yawuce misali. kamar daga sama ya hangota tana nufoshi cikin wani irin yanayi wanda shi a zahirin gaskiya baiga tana taka kafafuntaba kawai yaga tana tahowa gareshi kafin cikar minti daya ta iso wajensa kamar koda yaushe,tana isowa tafasa wata razanniyar kara sannan tafadi kasa tana wani irin kuka,,,saiyaga takoma MACIJIYA Amma wannan lokacin rabinta mutum rabinta macijiya, cikin wata murya mai dadin sauraro tafara magana "Shin kanaso nazama ajalinka ko? meyasa kaki yarda da bukatata" cikin rashin tsoro yayi yunkirin bata amsa. Saurin matsawa tayi dab dashi hannunta tasa ta rike masa makwogaro take idanunta yasanja color zuwa bakin kirin saikuma kwayar idon tazama yellow cikin wata murya marar dadin sauraro tafara magana "kada kayi tunanin don inasonka shi yasa kake ganin bazan iya kashe kaba,,,kasani yanzun nan Zan kashe Ka kowa ya huta shake masa wuya tayi da karfi, yafara kakarin mutuwa idanunsa sukayi jaah saboda tsabar azaba...dogon harshenta ta fito dashi tafara bin fuskanshi tana lashewa...Cikin wani irin yanayi yafarka gaba daya gumi yagama rufeshi dafe kanshi yayi sam yakasa gane dalilin sa na yin wannan kalar mafarkin meyasa yarinyan takeson ganin bayanshi? shin wani laifi ya aikata mata ne? Shi dai a iyakar saninshi komai kama da ita baitaba gani ba.. Asalin sunan sa Umar baban sa kuma Khalil a wancan lokacin yana daga cikin wadanda ake sa ran bama sarautar Drakaina Su uku iyayen su haifa saidai shi musulmine saboda mamanshi ba yar kasar bace ba wanda a lokacin auren nasu ansha rigima saboda ganin babanshi zai auri wanda bata bautama gunki Nova....Dakyar dai akayi auren kuma sunyi yarjeniya akan cewa bazasu takura ma yaransu ba duk addinin da suke so shi zasu bi....Hakan ce takasance lokacin data haifi Khalil yaron yataso cikeda hazaka da nutsuwa kuma sai hankalinsa yafi karkata kan bautama Allah daya lokacin dasuka girma ya auri wata a cikin gidan take itama maisuna...Elena itama dai haka suka sake yarjeniya akan bazasu takurama yaransu ba duk addinin da sukeso shi zasuyi....Bayan ta haifi Umar shima yazabi addinin babanshi wanda hakan ba karamin batama ran sarkin wancan lokacin yayi ba.......yataso cikin so da kauna kowa a cikin Masarautar son shi yakeyi duk da wani lokacin yanason yin magana akan meyasa suke bautawa abinda suka kirkira da hannun su? Amma babanshi ya hanashi shikam yadauki kudurin koba yau ba saiyayi magana...Ranan daya cika shekara 25 a duniya tundaga ranan yafara mafarki da ita wanda duk iyakan tunanin sa baitaba ganin koda mai kama da itaba.... Nainah kam al'amarinta ya tsananta kullum saitasa Kakanta fitsari a wando daya gaji babanta yakira yace yadauketa sutafi gida Habu yaso sanin dalilin,, Amma fir Baban Suwaiba yaki fada masa yace shi kawai yagaji da rigimarta kullum sai an raba fada d ita. Tunda Nainah takoma gidan babanta abubuwa da dama sun faru ciki harda auren da babanta yakara. Ya auri wata bazawara mai suna Hajjo,sam batada mutumci ko kadan irin matan nan ne wanda suka gama yawo a duniya...yau kwananta uku da tarewa. Lokacin data tare da darene washegari da safe cikin isa taje ta taso Nainah waitayi mata aikin gida itakam tace baza ta iyaba, hayaniyarsu ce ta tada Habu daga baccin dayake, cikin sauri yafitoh yana tambayar "mene yafaru da wannan sanyin safiyar ake hayaniya haka?" Hajjo tace "yo wannan yar taka wai baza ya yimun aikiba" cikin bacin rai yace.. "Haba Hajjo da Nainah nawa take dudu shekaranta bakwai amma kice tayi miki aiki ae wannan rashin tausayine" cikin daga murya take cewa "ah lalle Habu!" tana magana tana tafa hannu "to wannan abin bazai yiwuba ace da wannan katuwar yarinyan a gida amma ni zanyi girki da shara? Wato saidai ta nemi waje ta zauna kenan inyi mata komi to wannan abin sam sam bazan yadda dashi ba yau ni naga lukutar masifa da sassafe" lol. tana maganan kamar ta rufeta da duka, Habu kam takaicine yahanashi magana daki yakoma yana mai nadamar aurenta....sam batada tarbiya... ~* Cikin nuna isa da gadara Hajjo tace "kee,Nainah badake nakeba magana ba" cikin tsananin tsoro tafito,tulu tabata tace taje rafi ta deno mata ruwa. jiki ba kwari tadauka tulun tana share kwallah,dakyar ta iya debo ruwan saboda bata saba ba Bayan tadawo tasata wanke-wanke da shara kafin tagama, tagama jigata dakyar ta shige daki domin ta huta. Darana ma haka tasha aiki,abin mamaki Babanta kam Kodamuwa baiyiba sam baya magana wani lokacin ma har sa baki yake idan tana mata fada, Hajjo tamaida Nainah baiwarta duk wani aiki itane takeyi tun bata saba ba harta saba kullum tasan aikinta duk tarame ta fita hayyacinta kallo daya zakayi mata kagane cewa tana cikin matsala. Ko abinci bata ci sosai...hakan yakara sawa tayi rama sosai. "Ni'ima.! Nainah!" Hajjo takirata cikin bacin rai tana huci kamar wata zakanya , dasauri ta karaso jikinta duk rawa yake saboda wani irin tsoronta takeji yanzun "wato dan iskanci kinaji ina kiranki shine kikayimn shiru koh" Cikin in'ina tace "uhm uhm banjiba shiyasa kiyi hakuri" rankwashi ta zuba mata sannan tarike kunnenta cikin fada take maganar "duk lokacin dana kara kiranki baki amsaba sainaci ubanki shegiya mayya,kitashi kikaimin nika kafin na zauneki anan" cikin sauri ta mike tadauka kwaryan tafita tana sharan kwallah. Tana fita suka hadu da Habu nan take yakara bata ranshi yaja tsaki yayi shigewarsa cikin gidan. Nainah kam tana can wajen nika sai can dare tadawo saboda layin dake wajen...bayan ta ajiye nikan taji muryan Hajjo a bayanta cikin tsoro taje wajenta nan Hajjo ta rufeta da duka,,tanayi tana masifa "taje ta zauna kamar wadda ta aika wata duniyar..." Sosai take kuka tarasa abinda dake mata dadi haka ta rarrafa tashiga dakin datake kwana.wani tunani tafara lalle yazama dole ta nemo mafita idan kuwa ba haka ba zata rasa rayuwanta a banza... Washe gari dasafe kamar kullum Hajjo tadauko kasko ta zuba wani garin magani aciki ta fito tsakar gida dashi, saida ta tabbatar ko'ina yasamu sannan ta ajiye kaskon, Sannan ta kira Nainah domin tayi mata aikin data saba. Kwanaki sunja yanzun haka Nainah shekaranta takwas kullum da irin sabon wahalan datakesha a wajen Hajjo, Habu kam yafita harkanta. gaba daya yamanta yanada wata diya wai ita Nainah saboda ko kallonta yayi wani irin bacin rai ne yake rufeshi jiyake tamkar yakasheta kowa ya huta.... Yauma kamar kullum Hajjo ce rike da kasko amma kana ganinta kasan bata cikin hayyacinta sai gumi take sharewa duk ta hargitsa dakin. Leka can,bude nan haka take fama tun karfe 6na safe haryanzun sha biyu na rana tana aikin abu daya. kamar daga sama tajiyo muryan Nainah tana cewa "maganin kike nema koh" dawata irin murya maiban tsoro, cikin tsurewa tace "a,a,,,ah ba magani nake nemaba." kutt,ta hadiye miyau. kana ganinta kaga marar gaskiya Wata irin dariya Nainah tafara can kuma tayi shiru ta zubawa Hajjo ido saikuma tafashe da kuka irin na jarirai,tuni jikin Hajjo yafara kyarma dama tasan wannan ranan tana nan zuwa. Bayan Nainah tagama dariyan saikuma ta hade rai, tafara magana cikin murya kala-kala sannan tace "kinsan nasan komi amma nafison kifada da bakinki" Cikin tashin hankali Hajjo tafara magana "dama,..dama... Uhm.... Dama lokacin dana hadu da babanki sai kawata jummai (kawar hajjo) tace yakamata naje wajen boka,,saboda babanki yana sonki sosae gara kafin na shigo na mallakeshi. Muka shirya sai wani kauye bangaren yamma da Drakaina mukaje dakyar mukaga bokan saboda tsabar yawan mutanen. muna shiga yafara wata irin dariya sannan ya murtuke fuska. Bayan mungama yimasa bayani saiyace tun farkon shigowan mu yasan komi akwai aiki babba agabanki,saboda wannan yarinyar MACIJIYA Ce" Cikin tsananin firgice ta dubeshi sannan tace boka "bangane ba kamar ya macijiya ce" Yace "kwarai kuwa amma nakasa gano komi akanta kawai abu daya nasani macijiya ce mai hadarin gaske.kuma tabbas baza ta bari ki auri babantaba" "To boka yaya Zanyi..?" Ta tambaya, "akwai wani garin magani dazan baki kullum da safe kinayin turare dashi shikadaine hanyan dazaki bi domin macijiyar batason warin maganin,amma fa duk ranan dabakiyiba kisani bazaki kara kwana a duniya ba, saikuma yabani wani kullin daban wanda da shine zan mallake Habu ko kallonki zaiji baison yi." Cikin kuka Hajjo tagama bawa Nainah Labarin Kuka take mai cikeda nadama tana rokon Nainah ta yafe mata. Kafin tagama rufe bakinta Nainah tayi kasa nan tadawo katuwar macijiya wanda saboda girmanta ta kusa cika dakin gaba daya...nannadeta tafarayi harsaida ta nade ta duka.....Sannan ta fito da harshenta take tafara zuke duk wani energy na jikinta......saikuma tafara sarin hajjo har a waje biyar take ta fadi kasa ba rai..gashi kuma jikinta yayi fari fat duk ta yamutse....,,,,, A hankali takeyin kasa harta dawo ainahin siffarta....sannan ta fice daga dakin ta bace bat. @NM__🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 14: Nainah 2. Nainah data bace a dakinta ta bayyana kwanciya tayi take bacci ya dauketa...Habu dama tundazun baya gidan sai yanzun yadawo Da sallama yashigo gidan amma shiru ba a amsaba "Hajjo! Hajjo!!" Yafara kiran sunanta amma babu alamun zata amsa. A fili yace "yanzun haka ta fice yawon data saba ace mace kullum tana yawo bazata zauna a gidan taba." Dakin yashiga gabansane yafadi ganin Hajjo kwance bakinta nafitar da wani irin farin ruwa,sannan gaba daya ta sanja kala kamar ba ita ba jikinta ma yayi fari fat ya yamushe cikin tashin hankli yafara kiran sunan "Nainah" wanda cikin bacci taji kiran da sauri tafito "Na'am baba lafiya kuwa" cikin tashin hankali yake magana "menene ya faru? Meyasamu Hajjo?" Cikin damuwa tace "Baba nima bansaniba dazun dai najiyo ihunta" Baice komiba yasa kai yafice daga dakin Nainah ajiyan zuciya tayi bayanta dafe kirjinta itama tafice da sauri. Gidansu Hajjo yaje yasanar dasu Hajjo ta rasu,babanta kamar yayi hauka saboda kaf cikin yaranshi yafison Hajjo saboda tana bashi kudi sosai.. Komawa yayi cikin gida ya sanar da iyayenta mata cewa Hajjo lokaci yayi...nan gidan ya rikice da koke koke...Kafin karamin lokaci mutuwan Hajjo ta tsara ko ina a kauyen... Bayan sun iso gidan dakinta suka Shiga cak baban Hajjo ya tsaya domin kallo daya yayi mata yagane cewa dafin macijine yayi sanadiyar mutuwar ta,baice komiba haka akayi mata wanka aka kaita gidanta na Gsky. Shikam mamaki yakeyi garin yaya hakan tafaru? Kara matsawa yayi yana kallon jikinta sosai a firgice ya mike saboda mamakin abinda yagani ba wani abu ne ya bashi mamaki ba illa ganin irin dafin macijin wanda a kaf fadin duniya duk wani masananin sirrin macizai yasan cewa wannan macijin yanada daga cikin mafi hadari domin yawancin su ma ba ainahin macizai bane ba iska ce take shiga jikinsu wanda hakan zaisa suna sanja siffa zuwa duk abinda sukeso. Bayan kwana Arba'in da rasuwan Hajjo babanta yakira Habu saboda yanason suyi magana ta fahimta lokacin dayaje yana zaune akan buzu na fata a kofar gida gaisuwa sukayi sannan yafara cewa "Hakika nasan zakayi mamakin wannan kiran danayi maka abinda yasa nakiraka saboda na shaida maka Hajjo macijine yasa mata dafi kuma shine sanadin mutuwanta...saidai bansa ta ina macijin ya shigo ba" yadanyi jim yana kallon Habu kuma yana karantar fuskarshi Cikin alamun rashin fahimta yace "kamarya banganeba a ina tasamu dafin maciji,,?" Baban Hajjo Yace "Kasan dai nidin tsohon mafarucine kuma nasan kowani kalar dabba tacikin daji kallo daya nayima farin ruwan da Hajjo take fitarwa nagane dafin macijine,sannan kuma ga jikinta daya sanja color alamu sun nuna macijin saida ya zuke duk wani jinin jikinta sannan ya sareta.." Kallon fuskar Habu yake saikuma yaci gaba da cewa "kuma alamu sun nuna cewa macijin agidanka yake saboda naji warinsa amma bansan ainahin inda yake ba kuma irin wannan macijin yanada matukar hadari kuma ina zargin yarka Nainah shawarata itace ka...." kafin Ya karasa fadan abinda zai fada Habu ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu "nagode" kadai yace yayi ficewarsa daga gidan. "Tabbas mutanen garin nan basa kaunata nida ya ta Nainah basuda burin daya wuce su daurawa Nainah sharri yakamata nadauka mataki bazan zauna ake yima yata irin wannan kazafin ba" Duk cikin zuciyanshi yake wannan zancen. Da sallama yashiga cikin gidan Nainah ta amsa tana mai yimasa sannu da zuwa, ya amsa cikin kulawa duk saiyaji tausayinta yakamashi yarinya karama akeson kalawa irin wannan sharrin? shikam baisan dalilin dayasa ake yi mata sharriba. Wata zuciyan tace saboda kaf garin nan babu mai kyau dinta.. "Baba nakawo ma abinci" muryan Nainah ce ta katseshi daga tunanin dayake,yace "eh Ni'imatullah kawomin" murmishi tayi harsaida dimple dinta ya lotsa tanason Babanta Yakira ta da wannan sunan. ~* Lokaci yaja yanzu Nainah Shekaranta goma sha shida a duniya sosai kyau dinta yakara fitowa wanda mutane sukan cemata anya kuwa ke mutum ce? Duk lokacin data fito waje domin zuwa aika to fa ranan mutane basa iya aikin komi saboda har layi akeyi maza da mata yara da manya domin kawai suga murmishinta Her smile is like summer moonlight-beautiful and magical, with a fire that could melt the night.She can kill with her smile, she can wound with her eyes,and her skin is as white as snow, she's damn beautiful and hot....Duk lokacin data fita sai ansamu wanda suke jika jikinsu da miyau wannan dalilin yasa babanta yahanata fita.... (Jajaja I laughed in Spanish),, Sai yanzu babanta yake shirin kara wani auren. Shirye-shiryen biki ya kankama Habu har fenti yakara yima gidansu duk da cewa gidan kasa ne kuma kasar baka ce yarinyar dazai aura acikin garin Drakaina take akasuwa suka hadu wajen kasuwancin sa soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu. Yau juma'a aka daura auren Habu da Amaryansa Sadiya. Saiwashe gari aka kawo masa amaryansa, bayan yan kawo amarya sunzo Habu yayi komi wanda duk wani ango yakeyi. Sannan yan kai amarya suka tafi akabar amarya da ango kawai...Wanda duk abinda ke faruwa Nainah ko lekowa batayi ba.. Bandaki yaje domin yayi alwala bayan ya idar yashigo dakin. maimakon yaga sadiya kan gado saiyaga wata katuwar macijiya wanda saura kadan ta cika gadon gaba daya, wani irin faduwa gabansa yayi yanason yayi addu'a amma sam bakinsa kamar ansa dan makulli an rufe masa bakin. Aebaigama tsorata ba saida yaga macijiyan ta taso tana tafiya irinta mutane tana nufowa gareshi sannan kuma tana fito da dogon harshenta... kafin takaraso yafadi kasa sumamme Labulen dakin na daga amma maimakon naga tsakar gidan Habu sainaga wata irin Hadaddiyar fada tunda nake bantaba ganin irin fadar ba iyakar tsaruwa fadar ta hadu Ko ina ya wadatu da haske kamar ba dareba. Wata kofa muka nufa tafiya muke amma ba alamun munkusa bayan kamar minti talatin mukazo wani gini,macizai ne kala-kala awajen, sannan gawani babban gunkin maciji nan wanda kasanshi duk macizai masu girman gaske can na hango Sadiya wani maciji ya nannade ta babu alamun tanada rai, Nainah wata dariya tafara saikuma tayi girgiza gaba daya ta bace bat saidai wani bakin hayaki wanda a cikin hayakin fuskantane kawai ake gani cikin wata irin murya tafara cewa "wannan shine hukuncin duk wadda ta auri babana" Habu kam sanyi asubane yafarkan dashi yana farkawa yaga Sadiya kan gadon amma fuskanta yana kallon bango take ransa yabaci yaji tsanarta sosai aranshi wato shi zata rainama wayau kenan..wani bakin ciki yakeji...yanajin dama ya shake ta kowa ya huta gaban gadon yaje ya sharara mata mari yace "Don ubanki tashi ki kwashe kayanki nasakeki saki uku" amma me? ji yayi tamkar dutse yataba gashi hannunsa yaji ciwo... Cak yatsaya sakamakon tozali da yayi da bakin abu yana fita daga bakinta,cikin tashin hankali yakare mata kallo tabbas bata motsi wata irin zufa ce take ketomasa shikam meke damunsa haka? meyasa duk lokacin dayayi aure baya samun nutsuwa saidai tashin hankli.?meyasa duk matar daya aura take mutuwa? A matukar sanyaye yafice daga dakin. Keken doki yahau yaje Drakaina yasanar da iyayenta tarasu bakin ciki tashin hankali al'ajabi duk sunganshi a wannan ranan, Nan aka kira wani mai maganin gargajiya saboda a gano dalilin dayasa take fitar da bakin ruwa din nan...maganar dai dayace macijine yayi ajalinta. wasa-wasa saida ya auri mata Biyar duk suna rasuwa dalilin dayasa kenan mutanen kauyen suka daina bashi auren "ya." Kuma duk wani mai magani cewa suke Nainah ce take ajalin duk matan dayake aure amma haryanzun yaki yadda da hakan shi kawai gani yakeyi hassada ake masa ganin irin kyawun datake dashi.... Kara bude wani page din tayi da niyan cigaba da karanto musu labarin Nainah Merapati ce tayi saurin katse ta tace "Lokacin sallan magrib ya gabato kibari zuwa anjima idan mukayi sallan saikici gaba da bamu labarin." Hassy tace "abinda zance kenan kika rigani" Basma tace "tunda nike bantaba jin labari mai cikeda al’ajabi kamar wannan ba lalle Nainah tanada abin mamaki nikawai so nike nasan dalilinta na kashe duk wanda ya auri babanta." Mikewa sukayi alwala sukayi sannan suka gabatar da sallan magrib wanda Princess Mithian, Queen Nimueh, Lady Catrina baki bude suke kallon su saboda tunda suke basu taba ganin ana bauta haka ba,, (in case of confusion basu san addinin islam ba sai a labari kawai, basu taba ganin yanda ake sallah ba cause yanzun babu abinda suke bautama idan ba Gunki Nova ba) Bayan sun idar sunyi addu'o'i sannan suka dawo wajen suka zauna da mamaki suke kallon su ganin yanda suke kallon su kamar yau suka fara ganin su Basma tace “what's wrong?" Lady Catrina tace "kawai muna mamaki ne shin wannan wani irin addini ne haka? Saboda mu duk fadin nahiyar nan babu masu bauta irin taku sama da shekaru dari biyu gunki nova muke bautama saikuma masu bautama wuta da taurari.." Smile tayi tace "karki damu lokaci na nan zuwa zanyi miki bayanin komi.." Kallon Queen Nimueh tayi tace "my lady we are waiting for you..." She just smiled and said "don't worry dear but before I continue the story,I have something to show you follow me" mikewa sukayi dukansu sukabi bayanta....basu dade suna tafiya ba suka tsinci kansu a wani babban garden wanda tunda su Merapati suke basu taba ganin garden mai kyau din wannan ba wajen saboda hasken shi kamar safiya ne sannan daga can sama akwai moon blue color wanda hakan shiya karama wajen kyau da haske sannan ga flowers nan kuma duk bayan 10seconds suke sanja color ga Rose's nan masu kyau kala kala duk wani abu dake cikin garden din yana motsi don wasu flowers din ma har heart shape sukeyi kuma suna fesawa mutum wani irin ruwa mai kamshi..."Wow" kawai suke cewa saikuma daga can gefe wata shimfida ce ta alfarma inda aka zuba kayan motsa baki kala kala dakuma abinci suma kala kala nunasu tayi da hannunta take wani green din haske yafito ya shiga jikinsu atare suka fara tafiya akan iska.... sama sukayi kadan yanda zasufi ganin garden din da kyau...Hassy hannunta tasa ta rufe bakinta saboda yanda garden din ya hadu ga wasu irin sparks lights suna fita daga jikin kowace flower wanda hakan yasa wajen kara shining.....The place is very beautiful, amazing,breathtaking and magical...Sannan ga karamin kogi mai haske sosai wanda a cikinsa wasu kalan kifaye ne masu kyau kala daban daban hakama jikinsu colors ne masu haske da kyau.... In a slow motion suke saukowa har suka gama sauka a kasa wajen shimfidar suka nufa dukansu zama sukayi sannan suka fara cin abincin.... Yanda suke hira dakuma wasa da dariya mutum zaiyi tunanin sun saba sun san juna tunda can... Bayan sungama komawa sukayi cikin gidan Hassy ce ta kwanta bayan ta dafe kanta tace "oh my gosh...I am very tired" Merapati ce ta matsa kusa da ita tafara yimata massage ganin hakan yasa itama Basma zuwa ta farayi mata..... Dagowa tayi tace "thank you babes " Bayan tayi musu wink* Mithian,Nimueh,Catrina cikin birgewa suke kallon su saboda suna kula da junan su sosai duk da wani lokacin suna fada...... @N__M🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 15: Friends Washe gari bayan sungama breakfast sunyi wanka Basma ta kalli Queen Nimueh "yaushe zaki karasa mana labarin?" Hassy tace "eh gaskiya kuwa don ni na matsu naji karshen labarin." Merapati ce tadawo kusa da Hassy tazauna dab da ita sannna ta daura kanta a kafadarta tace "wallahi nima haka please kici gaba yanzun tunda bama komai we are all free now" Mikewe Catrina tayi ta dauko book din ta ajiye agabanta sannna itakuma Drakaina tafara budo shafin har tazo daidai inda suka tsaya sannna tafara karantowa a fili kamar haka.... ~* "Al'amarin Nainah kuwa sai cigaba yake ko cikin kawayenta idan akayi musu koh fada da ita Toh daga ranan sunanka gawa,Ko makaranta duk malamin daya daketa shima saita kasheshi. Tun Abin baya damun Habu haryafara damunsa yanzu m shima yafara yadda da maganar mutanen gari cewa Nainah Macijiya Ce,saidai bashida hujjar hakan kuma bata nuna masa wata alamar ita din Macijiya Ce Shidai Abu daya yasani duk wanda yayi mata laifi washegari za aga mutum ya mutu. shawara ya yanke akan zaije ya tambayeta tafada masa gaskiya idan ita din da gaske macijiyace" "Nainah! Nainah!!" "Na'am Babana" "Zo nan inason muyi magana" Da sallama ta shiga dakin tace "Dada Gani" Kallon tsaf yayi mata sannan yafara cewa "Nainah!...hakika banjin dadin yanda mutanen kauyen nan sukeyi miki sharri da kazafi suna cewa ke macijiya ce.,kinsani kaf fadin kauyen nan bakida wanda yafini inason kifadamn gaskiyan lamarin! meyasa kike kashe mutane? meyasa duk wanda kukayi fada sai ya mutu washe gari? kuma dagaske ke macijiyace?" kuka tafara sannan tace "Duk duniya banida kamarka inason farin cikinka fiye danawa yakai babana kayi sani cewa niba Macijiya Bace ba kawai sunayiman sharri saboda surabani dakai sannan kuma duk wanda kaga ya mutu kwanan sane yakare bantaba kashe kowa ba kuma bazan iya kashe kowa ba" ta karasa maganan tana kara fashewa da kuka, take tsananin tausayinta yakara kamashi tabbas da alamun gaskiya a maganganunta tayaya zatake kashe masa duk matar daya aura alhalin tanason ganin farin cikinsa,akwai dai wanda yake binsa da sharri shine ake makalawa diyarsa kuma gudan jininsa cikin kulawa yace "yi hakuri kinji yar baba nidama nasani mutanen garin nan basa kaunata tunda harsuke dora mki irin wannan sharrin" Goge Hawayenta tayi ta kalleshi "Baba Dan Allah kayi hakuri banson kana damuwa da maganan mutanen garin nan saboda ina tsoron wani ciwon yakamaka kai kadai nake gani zuciyata tayimin sanyi idan narasaka bansan yaya rayuwata zata kasance ba a cikin garin nan saboda sam basa sona basa kaunatah" takara fashewa da kuka nan yaci gaba da rarrashinta dakyar tayi shiru ~* "Haba Umar wannan wace irin rayuwace ka zabawa kanka kai kullum cikin tunani duk kabi ka rame nayi nayi kafadamin abinda dake damunka amma ka ki fadamin ko?" tunda tafara maganar ya zuba mata ido cikin alamun damuwa yace "Ummieh babu abinda yake damuna" hannu ta daga masa "banason wani dogon zance idan babanka yadawo zanfada masa tunda shi kana tsoronshi zaka iya fada masa abinda ke damunka" mikewa tayi ta barshi nan zaune. Bayan kamar awa uku Abbanshi yadawo bayan ya huta yaci abinci suna zaune a babban parlourn su wanda yaji kayan alatu irin na gidan sarauta ga maids nan sunata aiki kallon su Ummieh tayi tace "ku ba mu waje" atare suka durkusa sannan suka fice daga parlourn. "Yawwa dama inason magana dakai" tana kallon Abban nashi "toh inajinki" "dama maganar Umar ce,yaron nan akwai abinda ke damunsa amma sam yaki fadaman,,Duk ya rame kamar bashiba" "Kiramin shi" Kawai yace,tashi tayi takirashi bayan kamar 5mns ya iso,guri nasamu ya zauna sannan yace "Abba gani" "Umar?" yakira sunanshi,"Umar meke damunka Umminka taceman kwana biyu ta rasa gane kanka? Shin akwai abinda ke faruwane wanda bamu sani ba?" "Abba babu abinda yake damuna fa" kallon tsab yayi masa yace "idan ma wani abu kake boyewa wata rana za muji kuma zamu gani" Ummieh ta kalle shi "yanzu iyakan abinda zaka ce kenan? baza kasashi a gaba yafadama damuwarsa ba.nifah duk na damu” Smile yayi yace "haba yazakice haka tunda yace babu abinda yake damunsa shikenan,tunda aishi ba yaro bane ba kuma bazamu takura masa ba kibarshi wata rana dakansa zaizo yafadama abinda ke damunsa.." Shidai umar bashida bakin magana yana jinsu,can yace "Abba zankoma ciki inason anjima naje gidansu Fadeel," "to kakula dakanka" Ummin sa kuma tace "ka gaisawummin fadeel din" ya amsa da "toh" sannan yamike yakoma dakinsa. Fadeel Abokin Umar ne tunsuna yara sun shaku sosae shima musulmi ne kamar Umar din kuma ta dalilinsa ya musulunta yanzun haka har Ummin Fadeel din sun muslinta Lokacin daya isa gidansu Fadeel sauka yayi daga kan keken dokin sannan yafitoh direct cikin gidan ya shiga a parlour yatarar da Ammin Fadeel gaisheta yayi Itakuma tana tambayrsa yan gidan,,,,yace duk suna lafiya ummieh ma tace nagaisheki,ina amsawa tace yaje fadeel din yana dakinsa to yace sannan yatashi ya nufi dakin fadeel dn. Da sallama yashiga dakin kwance ya ganshi da alamu yayi nisa a tunanin dayake "Fadeel!fadeel.!" Yakira sunanshi firgit yatashi ganin Umar ne yasashi ajiyan zuciya, “ya friend ashe kaine wallahi nadauka Ammi ce,." Hannu yamika masa suka gaisa kowa yana tambayar kowa ya aiki. Fadeel yace "gara dakazo wallahi ina cikin damuwa Umar" "meke damunka.?" Fadeel yace "Wallahi Abbane da rigima dole sainaje kauyensu kuma fa babu kowa nashi acan saboda anyi zaman mutumci da kakannina shine zanje nagaishesu" dariya Umar yake yace "shikenan saika samo mata acan koh,? shikam Fadeel abin ne yabata masa rai yace "Aa ka manta surika zanyi ba mata ba" wata dariyan Umar yakara kwashewa da ita yace "ai duk daya yaushe zan raka ka?" yakarasa maganan yana daga masa gira. Fadeel Yace "Aesaikaxo kakaini koh.?" Umar ne yataso yazo kusa dashi sannan "yace kaga friend dawasa nake yaushe zakaje? inason na raka ka saboda inason zuwa kauyen, dama nagaji da zama a cikin Draikana din nan" Wata harara Fadeel yayi masa sannan yace "ba rana,don banason zuwa" dakyar Umar yashawo kan Fadeel akan ranan asabar zasuje daga nan yayi masa sallama har bakin kofa yarakashi sannan yadawo cikin gidan. Umar kam lokacin daya koma gida ana kiran sallar magrib masallaci yawuce duk anan cikin gidan yake a wancan lokacin...baidawoba saida akayi isha abinci kawai yaci ya wuce dakinsa saboda yau yagaji sosae,saida yayi wanka sannan yakwanta. Can cikin dare kamar dai kullum yau ma yafara mafarkin daya saba amma wannan karon yasha banban dana kullum domin suna zaune cikin wani lambu mai kyau ga ya'yan itatuwa da furanni masu kyau da kamshi fuskanta fal fara'a tana sanye cikin wata hadaddiyar doguwan riga maroon color wadda tayi dai-dai da skin dinta hakan yasa kyawunta yakara fitowa bayan ta iso ta zauna a kujeran dake kusa dashi tanayi masa wani rikitaccen murmishi, wanda duk lokacin datayi smile hasken hakoranta har kashe ido sukeyi cikin murynta mai kamada busar sarewa tafara magana "Yakai masoyina kuma abin alfaharina hakika ina cikin farin ciki marar misaltuwa domin ka kusa zuwa gareni." Yace "Hakika kinyi babban kuskure dahar kike tunanin zan zama masoyinki babu wadda na tsana kamarki kiyi sani cewa..." kafin yakarasa ta daka masa wata irin tsawa wanda bakinta har fitar da hayaki yake kuma idonta sunfara sanja color ganin tana kokarin rasa control kawai saita bace bat..Wani irin gurnani yafara ji daga bayansa mutuwar tsaye yayi ganin wata irin katuwar macijiya a bayansa kafin yayi wani yunkuri tuni macijiyar tafara hadiyeshi....daidai wannan lokacin ya farka yana mai nadamar kwanciyarshi baccin Toilet yanufa yadauro alwala yana mai kaiwa ubangiji kukanshi akan ya saukaka masa abinda ke damunsa. ~* Habu zaune abin duniya yayi masa yawa saboda wani abu da Nainah ta tsiro kullum idan dare yayi baya kuma ganinta saikuma gobe da safe wannan abun yana damunshi. gashi jiya sunyi fada da yar gidan maigari yanzu haka yarinyan ta rasu itakuma Nainah hukuma sunkamata tanacan hannunsu. mutanen gari sunyi kokarin nuna masu ilar kama Nainah amma sunki, Adaren da suka kamata mutum dayane ya tsira gaba dayansu su biyar duk sun mutu. Itakuma ba agantaba ko ina anyi cigija amma babu alamarta. abubuwa sunyima Habu yawa yarasa inda zai sa kansa yaji sanyi mutanen gari kowa yafita harkansa,duk inda yaje saidai kaga ana gudunsa...yanzun haka ko kasuwa yaje ba a siyan kayansa wata tsohuwa ce kadai take siya kuma kullum duka take siyewa wanda hakan ba karamin mamaki yake bashi ba kuma baitaba ganin fuskanta ba... Yau takama asabar ranan dasu Fadeel zasu je kauyen su Nainah hakanan gaban Umar yaketa faduwa baisan daliliba,kuma duk jikinsa yayi masa nauyi. dakyar da tambaya suka iso kauyen kafin su iso cikin kauyen cikin ciyayin dake gefen hanya suka ga alamun ana daga musu hannu cikin sauri Fadeel yace a tsaya da tafiyan kallon Umar yayi yace "mutsaya mutaimaka masa koh" shikam tsaki yaja yace "duk yanda kagani." Murmishi Fadeel yayi sannan yafita yana zuwa gabansa yafadi cikin tashin hankli yake kiran "Umar....!!!" @N__M🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 16: The News. Cikin tashin hankali yaci gaba da kiran sunan Umar da sauri yafito wanda shikansa a lokacin ji yayi tamkar umarni ake basa akan yafito din yana karasawa wajen idanun sa yasauka akanta saidai baya ganin fuskan ta saboda ta juya can, kallon Fadeel yayi yace "to yanzun yaya zamuyi da ita?bamusan wace ba gaskiya bazamu taimak..." kafin yakarasa ta juyo da fuskan saidai haryanzun baya ganin ta saboda fuskanta duk jini ya rufe rabin... Fadeel yace "kawai mutaimaka mata inaga a cikin kauyen take itama" kamata sukayi sukasata a bayan keken dokin sannan sukaci gaba da tafiya... Lokacin dasuka isa kauyen gidan mai unguwa suka tambaya aka nuna musu gashi mutanen garin sai kallon su sukeyi ganin cewa yanayin shigar su ta banbanta datasu komi da komi ma ba iri daya bane ba saboda ba sosai ake ganin yan gidan sarautar Drakaina ba...shi yasa suka zama abin kallo a wajensu shikam Fadeel duk ya tsargu kara jan tsaki yayi saboda sam bayason takura bare kuma ayita kallonsa... Bayan anyi musu sallama dashi yace su shigo gaisawa sukayi kallon su yayi yace "daga ina kuke? Meya kawoku wannan kauyen namu don kallo daya za ayi muku a gane cewa daga gidan sarauta ko attajirai kuke" don shi bai gane suba Fadeel ne yayi masa kwatancen kakanninsa cikin fara’a suka kara gaisawa sannan suka ce a hanya sun hadu da wata yarinya wataqilan a nan take mikewa sukayi atare suka fita gaban sane yafadi saboda kallo daya yayi mata yagane cewa Nainah ce salati yafara saikuma ya tsaya da tafiyan kallon su yayi yace "kuyi gaggawar sauketa daga kan keken dokin saboda wannna yarinyar dakuke gani muguwa ce kuma macijiya ce duk wanda tsautsayi yafada akansa baya kara koda kwana daya yanzun haka ba a fi kwanaki ba takashemin yata saboda kawai sunyi cacar baki bama ita kadai ba hatta uwarta saida ta kashe kuma duk matar da babanta ya aura a ranan take mutuwa.." Baki bude suke kallon sa Fadeel ne yafara dariya saboda shi a ganinsa duk karya ne kokuma tsatsuniya ce kawai dagowa yayi yace "haba dai tayaya zata zama macijiya? wace shaida kukeda ita dahar zaku iya kulla mata wannan sharrin? yanzun dai ba wannan ba bani magani nasa mata saboda ta zubar da jini sosai" kanshi kawai ya daga cikeda takaici yakoma cikin gidan baidade ba yafito hannun sa rikeda wata jaka ta fata mikama Fadeel yayi bayan sun fito da ita shikuwa Umar cikin keken dokin ya shiga inda anan Fadeel yafara goge mata duk jinin daya bata mata fuska tasbihi yake aranshi saboda ganin irin kyawun datake dashi... Aransa yace "lalle nasamu matar aure." Duk wani ciwo saida yabi yasa mata magani amma baigama sa mata ba yaga duk inda yasa maganin yana cirewa dakanshi kuma babu ko alamun ta tabajin ciwo da sauri ya mike daga gabanta tunda yake baitaba ganin irin hakan tafaru ba amma tayaya? dama akwai irin wadannan mutanen wanda sunajin ciwo atake yake warkewa?tabbas akwai kamshin gaskiya a maganar mai unguwa koda ace ita ba macijiya bace ba akwai wani abun al’ajabi atareda ita juyowa yayi ganin mai unguwa yana mishi kallon "ai na fada maka" yasashi mazewa kawai yana sosa keya yace "yanzun ka yadda da abinda nafada maka? Ko haryanzun kana tantama?” kansa ya girgiza yace "dama akwai yan baiwa irin su ai." Wajen Umar yaje yace masa yazo yaga wani abun mamaki fitowa yayi saidai sama ko kasa basu gantaba Fadeel har hanya ya duba amma babu koda mai kama da ita but how is that possible?who is she? definitely there is something wrong with her...she's not a normal person, tunanin dayakeyi kenan aransa... Basu wani dade ba suka ce zasu tafi a hanyan su ta komawa bayan sun bar kauyen suka fara hango wani farin haske yana matsowa inda suke tsayawa sukayi da tafiyan saboda babu ta inda zasu iya wuce wa hasken ne yaci gaba da matsowa haryazo dab dasu kyakykyawar budurwace sanye da fararen kaya saboda tsananin hasken kayan shiyasa suke hango hasken tundaga nesa..baki bude suke kallonta tunda suke basu taba ganin mace mai kyau kamar wannan ba shikuwa Umar yayi nisa a tunaninsa tabbas yasan wannan fuskar amma kuma a ina? kwata kwata yakasa tuno inda yasanta hakan yasa shima maida hankalinsa kanta yazuba mata ido... Cikin hadaddan greek dinta tafara magana "Thélo aplós na sas efcharistíso, pou me voithísate, sas efcharistó polý! kai tha sas pliróso píso, párte aftó to koutí pou tha sas voithísei mia méra.....means (I just want to thank you,for helping me, thank you very much! and I will pay you back, take this box it will help you one day.)" Bayan ta mika masa wata karamar akwati mai kyau dakyar ya amsa saboda ya shagala da kallonta dakuma yanda take magana da greek tamkar dama can yaren saboda ita akayisa.... "her voice is so cute, and her accent was damn amazing when she is talking in greek.." *Oo I'm in love with you Nainah*wink Yana amsa ta bace bat da sauri sukabar wajen gaba dayansu a mugun tsorace suke...babu tantama aljana ce suka hadu da ita gashi kuma ko sunan ta basu sani ba sannan kyau dinta ya wuce misali.... Yau kwanansu biyu dakomawa gida shikam Fadeel jiyake kamar ya bude akwatin yaga mene a ciki amma kuma wani bangare na zuciyansa yana gargadinsa akan hakan wataqilan haryanzun akwai sauran lokaci..da wannan tunanin yake hakura kuma a yanzun yagama yadda cewa sonta yake yakamu dason aljana. Umar ma duk hankalinsa baya jikinsa kawai burinsa ya tuno inda yasanta amma yakasa tamkar wanda aka wanke ma brain kuma duk lokacin daya tsananta tunani take wani irin ciwon kai ke kamasa wanda harsaiyaji kamar zai rasa ransa...Yanzun haka yana gaban mirror kansa yake kallo ta cikin mirror din yafara hango wata mata jikinta tasa wata black abaya amma kuma lokacin daya waiwaya baiga komi ba juyowa yayi yaci gaba da kallon cikin mirror din still tana nan haryanzun kuma matsowa takeyi wajensa wanda shikawai akan iska yaga tana tafiya kuma abinda yakara bashi mamaki ganin bayansa a cikin wani daji suke amma duk lokacin daya waiwaya saiya ganshi a dakinsa..Dab dashi ta matso cikin sanyin murya tafara magana saidai bayajin abinda take cewa kalmar karshe kawai yaji "dama nace zakazo gareni masoyina inasonka" sama ko kasa ya nemeta baigantaba.... Saiyanzun yagane wace kwarai itane yarinyar daya hadu da ita a kauye...kenan aljana ce? amma meyasa take bibiyansa...jikinsa a matukar sanyaye ya kwanta bayan yayi addu'a.... ~* Next page ta bude saidai kafin tace komai wani guard ya shigo da sauri durkusawa yayi akan gwiwansa bayan ya sunkuyar da kansa cikin girmama yace "Akwai matsala yake shugabata wani babban al'amari yafaru a safiyar yau din nan domin kuwa an wayi gari duk ruwan dake kogin gabas ya kafe ga mutane can hankalinsu a tashe saboda duk ciki shine yafi kowanne yawan kifaye dakuma ruwa." Gaba dayan su mikewa sukayi wata hanya sukabi sai gasu a wani waje lekowa Nimueh tayi ganin jama'arta awajen amma kallo daya zakayi musu kagane cewa suna cikin tashin hankali da damuwa yawancin su kuka sukeyi kanta ta dafe cikin damuwa ta kali guards din ta "afada musu gani nan fitowa yanzun zamuje temple domin yin addu'a" tana gama fadar hakan takoma cikin gidan suma su Lady Catrina bin bayanta sukayi... Queen Nimueh Lady Catrina ne suka fito amma yanzun sun sanja kaya zuwa wasu kalar daban kallon su Hassy tayi tace zasuje su dawo sukam kansu kadai suka daga saboda mamaki inbanda ma bata tayaya zaka kirkira abu da hannunka kuma sannna ace shine abin bautarka? Merapati tace "Mithian ke mene abin bauta dinki?" shiru tayi batace komi ba ganin hakan yasa suma duk yin shiru. A hankali Hassy tace "I'm missing home...bansan awani hali mum take ba bansan yanda Abbah zaiji ba idan har yasamu labarin batan muba" kuka tafara a hankali Merapati ce ta matsa kusa da ita hannunta takama saikuma tayi hugging dinta tana rarrashinta ita kanta Basma daurewa kawai tayi.... ~* Mom din Hassy zaune tana kallon news innalillahi kawai take maimaitawa ganin abinda ke faruwa daidai lokacin Abbansu yashigo parlourn jin tana salati yasashi tsayawa yace "Aaa Mum din su mene lafiya kuwa menene yafaru? TV take nuna masa saboda sam takasa magana zama yayi bayan ya maida hankalinsa kan TV din news ne akan annobar data shigo garin ga mutane nan duk sunkoma zombies saikuma wasu irin halittu daban daban suma kuka tafara sosai take nadama ya rufeta akan abinda takema Hassy kallon Abbah tayi cikin kuka tace " Kira Principal din school din tasu Allah yasa abin bai shafe su ba" shikansa jikinsa yayi sanyi da kyar ya ciro phone din yayi dialing number din... Tana zaune ta buga tagumi ga duk staffs din nan a zaune saboda ganin irin abinda ke faruwa yasata tura driver domin ya dauko su Merapati amma saiyazo mata da labarin daya daga mata hankali nacewa baiga kowa ba awajen kuma alamu sun nuna bawai tafiya sukayi ba saboda akwai sauran kayansu anan saidai babu alamun student ko daya awajen.... Wannna dalilin yasa ta tattaro duka teacher's din domin asan abinyi inda wasu sukace akai report police station wasu kuma sukace aa abari dai ayi bincike a sirri saboda wannan babban case ne daidai lokacin phone dinta tafara kara gaban tane yafadi ganin cewa Abban Hassy ne ke kira dagawa tayi hankali tashe bayan sun gaisa nan yake tambyanta "amma su abin bai shafe suba ko saboda yanzun yake gani a news..." Hamdala tayi aranta da dukkan alamu baisamu labarin batan students din ba murynta ta gyara tafara magana "abin bai shafe mu bayanzun haka duk wasu students an tattara su waje daya da niyartama kowa tatafi gidansu amma aka hanata saboda fita waje a irin wannan yanayin da ake ciki abu ne mai hadarin gaske karya damu yarinyarsa tana cikin koshin lafiya saboda ansa security sosai...." Hamdala yayi sannan sukayi sallama gaba daya staffs din sun zuba mata ido lalle mata sun kware a komi dagowa tayi tace "mene kuka zubamin ido haka? wannna karyan danayi bani kadai ba harku ma zata taimaka yanzun dai menene abin yi?" ~* "Oh my gosh" tace tana dafe kanta zama tayi a gefen bed din taci gaba da cewa "guy's mene abin yi? kunsan dai bazamuci gaba da zama anan ba har karshen rayuwan mu yakamata mu nemo mafita I'm tired of this place...we can't just stay here forever dole mukoma gida nasan hankalin iyayen mu yatashi ni bama wannan ba shin inasu Basma suke?me zamu fadama Pc idan munkoma school?" Kallon su tayi ganin basu ce komai ba cikin bacin rai tace "mene hakan wai saikace bada mutane nake magana ba? Stop staring at me and open your fucking mouths! we need a plan on how to go out of this shitty place! Because I’m so fucking tired of being trapped in here!" tsaki taja sai kuma ta zauna ranta a matukar bace, Nasir ne yace "mekikeso muce kin riga dakin sani muma bamuda amsa din baki ai....koban fada miki ba kinsan cewa akwai zombies nasani dakyar idan zamu fita daga nan a raye saboda..." Hannu tadaga masa a zafafe Ruky tace "you shut up please! I don’t wanna hear your damn explanation,sam sam bakinka baya fadan alkairi tsskk" @NM__🦋♥️ [27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world) Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew? Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own? Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger ~* Episode 17: Sleeping Beauty. ^*^ Kallon su tayi ganin basu ce komai ba cikin bacin rai tace "mene hakan wai saikace bada mutane nake magana ba? Stop staring at me and open your fucking mouths we need a plan on how to go out of this shitty place! Because I’m so fucking tired of being trapped in here!" tsaki taja sai kuma ta zauna ranta a matukar bace, Nasir ne yace "mekikeso muce kin riga dakin sani muma bamuda amsa din baki ai....koban fada miki ba kinsan cewa akwai zombies nasani dakyar idan zamu fita daga nan a raye saboda..." Hannu tadaga masa a zafafe Ruky tace "you shut up please! I don’t wanna hear your damn explanation,sam sam bakinka baya fadan alkairi tssk! Saidai idan kaine bazaka fita a raye ba amma nasani we can make it!Yanzun dai abu nafarko dazamu farayi shine samun makaman dazamu kare kanmu dashi saboda dole mufita daga wannan wajen and let me tell you about zombies they are not like us cause they're dead already.To kill zombies,you need to destroy their brains,when their brain dead they can't do anything...wannan itane hanya mafi saukin kashe su indai ba brain din sune yadaina aiki ba to bazasu taba kyalemu ba secondly zombies are afraid of fire,indai kanason tsira da rayuwanka dole kasamo fireworks saboda bazasu iya zuwa inda kake ba,sannan main weakness dinsu shine stupidity,zombies have no intelligence,so they can be easily fooled..zombies cannot walk fast mu kuma da wannan damar zamuyi amfani wajen tsira da rayuwan mu...lastly try not to make any sounds saboda duk inda sukaji sounds sai sunje wajen koda kuwa ace nisan wajen yakai 100kilometers, ta wannan hanyan ne kadai zamu kauce sharrin su...hope I made myself clear?" tana kallonsu Adam ne yace "inada tambaya tayaya akayi duk kikasan wannan Ruky tayaya akayi kikasan abubuwa akan zombies haka?" Mikewa tayi saida taje wajen bag dinta kayanta tafara tattarawa tace "cause I'm watching zombies movies that's why I know lots about them but remember this isn't a movie, or kdrama this is real it is happening to us right here in this hospital we need to be very careful.... " ~* “Oh lord" tace a hankali kallon kanta take a madubi cikeda mamaki ganin yanda skin dinta ya sanja color ita dai tasani jikinta ba haka yake ba amma yanzun saiwani glowing yake and her eyes suma sun sanja color zuwa golden color to kenan dama idan mutum yayi rashin lafiya haka yake zama? Anya kuwa aikuma ba yau ne tafara yin rashin lafiya ba....Itadai tasani tun ranan nan a station wata mata tasa bakinta a wuyanta tundaga nan bata kara sanin abinda ke faruwa ba yau tsawon two weeks kenan saida tayi kwana goma a asibiti amma meyasa meyasa tunda tadawo gida abubuwa suke sanja mata? cigaba tayi da kallon kanta ganin yanda takara kyau da haske tsallen murna tayi amma ga mamakinta saigani tayi tayi sama sosai cikin tsoro ta sauko kasan lalle akwai abinda ke damunta babu ta yanda zata iya wannan tsallen...Knocking aka fara wanda hakan shiya tsaida tunanin datakeyi, zuwa tayi ta bude kofan Maid ce cikin girmama tace "Hajiya tace ki sauko ga breakfast can yana jiranki..." "Tell her I don’t wanna eattt!" daga haka ta rufe kofan.. Zama tayi a gefen gado gaskiya dole akwai abinda ke damunta komawa tayi gaban mirror din taci gaba da kallon kanta again knocking aka karayi "God meyasa mutane bazasu barni na huta ba?" tace ranta a bace zuwa tayi ta bude tana cewa "I said I don’t wanna eatt!!" Shiru tayi ganin Friend dinta ce tsaye itama kallonta take kamar wadda taga sabon halitta tace "Amara mezan gani haka? Mene yasamu idonki? And your skin is glowing wow that's really cute you just look Ah...may...zing Amara...mene sirrin? don na lura tunda kika kwanta a asibiti kikayi wani kyau.." Itakam takasa magana saboda ita kanta ta lura akwai sauyi a tattare da ita cikin sanyin murya tace "come inside we really need to talk!" Hannunta taja zuwa cikin bedroom din. ~* "I just want to go home,and I want to see my family again...am sick of being alone..I need my family, I really missed my daddy, I wanted to hug him again..." she can't control herself right now kawai saitafara kuka..."Oh no don't cry babe please I'm here for you,I'll comfort you in the difficulty and painful times, and I will never leave you alone!!" Merapati tace bayan ta zauna a kusa da ita kanta ta kwantar akan lap dinta sosai take kuka ganin hakan yasa Basma zuwa ta kira Nimueh itama hankalinta yatashi ganin yanda Hassy ke kuka zama tayi tsawon minti daya saikuma ta mike kallon su tayi tace su biyo ta Merapati ce takama Hassy suka bi bayanta harda Mithian ma, wani bangare suka bi daban wanda tunda sukazo gidan basu taba zuwa ba babban daki ne saikuma gunki kala kala na dragon's manya da kanana saikuma wata matattakala a karshen wajen wani babban kasko ne saman shi wani mulmulallen dutse ne amma yanada haske sosai wanda ya haska kusan rabin dakin wani ruwa ta dauko acikin wata karamar butar zinare zubawa tafarayi akan dutsen, ruwan maimakon ya zube saima shigewa dayakeyi cikin dutsen saida ta zuba rabi sannan ta maida butar mazauninta nan da nan hasken yafara zama color daban daban red blue pink purple white black orange brown duk wani color dakuka sani saida yakoma sannan a hankali wata kofa ta bayyana ajikin dutsen nan da nan wasu irin sparks suka fara fitowa saikuma dutsen yafara zagayawa da sauri sauri bayan yayi sama sosai....a hankali komi ya dawo normal saidai abin mamaki tamkar tv haka suke kallon jama'ar garin su sosai hankulansu yatashi ganin yanda garin nasu yazama....Ita kanta Nimueh ta firgita da ganin abinda ke faruwa nan take Basma Merapati suma suka fara kukan.... Hannunta tanuna dutsen wani green din haske yafito nan da nan komi yakoma yanda yake juyawa sukayi suka koma masaukinsu gaba daya kuka suke inda su Mithian Nimueh,Catrina suke rarrashin su.... Yau kwana daya da ganin abinda ke faruwa a duniyar tasu gashi bazasu iya komawa ba saboda yanzun ba lokacin fita daga duniyar bane ba, kallo daya zakayi musu ka tabbatar suna cikin damuwa da tashin hankali sannan bangare guda Basma akwai maganan datakeso suyi da Merapati... Kamar kodayaushe suna dinning area don cin lunch duk da bawani sosai suke ci ba saboda damuwan da suke tattare da ita... Su kansu su Mithian sun damu ganin yanda suke cikin damuwa sam yanzun basa hira saidai kowa tayi shiru gara ma Merapati tanayima Hassy hira duk da bata cika bata answer ba..Mithian ce ta debo abinci a hannunta ta watsawa Basma, da mamaki take kallonta ita kuma tayi mata gwalo ganin hakan yasa itama Basma ta debo ta watsa mata because she understand why she did it she wants to lighten up their mood...Catrina ta debo ta watsawa Merapati ita kuma ta watsawa Hassy...kafin cikar 15seconds gaba dayan su sun fara watsawa kowa Wasa suke tamkar wasu kananun yara saida suka bata komai na wajen sannan suka daina. Nimueh ta kalle su cikin murmishi "ina tunanin yau zamu fita kuga gari kusha iska na tabbata damuwar datake ranku zata rage sosai don haka kowa taje ta shirya ku wanke jikinku.." Tana gama cewa hakan ta mike wani part ta nufa daban, ganin hakan yasa su Hassy zuwa su shirya suma har suka dawo Nimueh bata dawo ba...kuma abin mamaki kaf wajen da suka bata dazun an gyara tsab tsab, zama sukayi suna jiranta ba a dauki lokaci ba saigata ta fito jikinta sanye da white and blue din kaya saikuma karamar dragon a samanta “wow" Basma tace kallon su tayi tace "ku taho akwai inda zamuje" Wani bangare daban sukaje na cikin masarautar anan suka ga dragons kala kala awajen guda uku tasa guard ya fito dasu Queen Nimueh Lady Catrina suka hau guda daya Basma Princess Mithian suka hau guda daya inda Hassy da Merapati suka hau guda daya.....Nan take suka fara tafiya akan iska saikuma suka shiga can cikin sararin samaniya. Basu wani dade suna tafiya ba suka gansu asaman gajimare inda agabansu wata babbar masarauta ta bayyana amma kuma wani circle ya zagayeta sannan ga dragons nan kala daban daban suna zagaye wajen kallon su Drakaina tayi tace "anan wajen Nainah take duk da har yanzun bata farfado daga dogon baccin da aka sata ba lalle dole ku kula da inda zaku taka dakuma abinda zaku taba saboda wajen yanada matukar hadarin gaske" A hankali dragon din suke saukowa tamkar walkiya haka suke shige cikin circle din saikuma gasu a gaban masarautar....Bayan sun sauko Merapati takama hannun Hassy tundaga wajen ginin mutum zaigane cewa lalle wajen yatara abubuwan mamaki da al'ajabi mutane ne manya da yara amma gaba daya sun kame jikinsu baya motsi kuma sun zama light brown wasu ma kamar aiki sukeyi amma a hakan suka kame wato jikinsu kamar tabo kamar kuma kasa... Kallon su tayi "duk abinda kuka gani karku tabashi domin hakan zai iya janyo wata matsalan daban" tana gama fadar hakan tafara tafiya suma binta sukayi zuwa ainahin cikin gidan. Tafiya suke cikeda kulawa saboda gudun janyo matsala nan take Basma tayi misplacing kafarta da sauri Queen Nimueh ta juyo "kowa ya tsaya a inda yake kada wanda ya motsa sabod.."kafin ta karasa aka fara zubo musu kibiya nan Mithian,Drakaina suka fara using da magic dinsu da kyar suka samu aka daina sannan takara cewa "this is just the beginning, you must be very careful idan kuma ba haka ba we will all died here saboda ba ko ina bane magic zai taimake mu ba.." Hannunta ta nuna zuwa kan wani kasko take wuta takama nan take duk wani kaskon wuta yakawo. Haka suka ci gaba da tafiya zuwa cikin gidan sanann suna mamakin yanda gidan ya kasance da duhu gaba daya ginin yayi bakin kirin tamkar wani bangare na garin Drakaina kuma duk inda suka wuce akwai mutane,macizai,halittu daban daban amma gaba daya basa motsi wani babban gunkin maciji suka fara hangowa Mace ce akan throne amma kuma kanta gaba daya na macizai ne sune a matsayin gashinta saikuma kafafunta suma irin na maciji amma kuma yayi kama da kafar mermaid tana zaune amma itama bata motsi kamar sauran dai.... Wani babban daki ta bude amma shi baiyi bakin ba mutum zai iya cewa ana rayuwa a ciki ganin komi tsab ga lu'ulu'u inda suka karama dakin haske...Makeken gado ne na alfarma irin na sarauta wanda bakowane yake iya mallakar saba acikin sarakan harsai wanda ya isa kuma yakai wata kyakykyawar budurwace kwance akan gadon kanta da crown mai shape din maciji tunda su Merapati suke basu taba ganin mace mai kyau da kwarjini kamar wannan ba a hankali Hassy tace "Nainah ko? Gaskiya ne sai yanzun na yadda da zancenki dakikace she's the most beautiful princess in the world..yes you're right she's damn beautiful...." Basma tace "what a sleeping beauty! Saina tuno wannan cartoon din buh ita only a true love kiss can wake her up..." tana maganar tana smiling, ganin yanda suke kallonta yasa ta jin kunya "you are such a baby Basma" Merapati tease her. Sai kuma suka maida kallon su kan Nainah Tana kwance hannunta daya akan daya jikinta sanye dawasu kaya na alfarma saikuma rabin jikinta rufe da wani irin bargo wanda da gashin dawisu akayi shi,duk wanda bai saniba zaiyi tunanin bacci take lalle tsafi gaskiyar mai shi kalleta tsab da ita alhalin tafi shekaru dubu ahakan? tabbas duk wanda bai shiga duniya ba yabar kallon abubuwan mamaki Hassy tace aranta.. Drakaina tace "ga Nainah the serpent wanda akasa bacci kuma kune kadai zaku iya tasota saidai ni kaina bansan tayaya ba harsai nagama karanta muku labarinta" Basma tace "nufinki baki taba karantawa ba?" Kanta ta gyada tace "kwarai kuwa bantaba karantawa ba kuma ka'ida ne duk wanda yake mulkin Drakaina yasan tarihin Nainah amma ni?" smile tayi taci gaba da cewa "sam bantaba sha’awar karanta labarin ba saboda a lokacin ma muna cikin tashin hankali shiyasa na yanke shawaran bazan taba karantawa ba harsai kunzo sannan....kuma wannan wajen babu mai iya shigowa a yanzun harsai mutum shi jinin Drakaina ne...kuyi sani cewa a tarihi kune mutanen farko dasuka fara shigowa nan harkuka samu daman ganinta...lalle kunada sa’a a rayuwanku kudin na musamman ne" Yanzun dai zamu bar wajen nan ficewa sukayi daga gidan inda kofar tamaida kanta ta kulle sanann duk kaskon wuta din suka kashe kansu... Bayan sun dawo gida ganin yanda suka saki ransu hakan yayima su Mithian dadi....Nimueh tace zuwa dare zataci gaba da basu labarin Nainah don ita kanta ta matsu taji karshen labarin... @NM__🦋♥️ ********************** ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** ************************* ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** **************************