HALYSAAH PAGE 104... DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Ajay ya gaida Hajja da ta fito daga dakinta rik da bowl a rufe tana kallon sa da Khaleesat, bayan ta zauna tace "Kai kuma daga ina kama an jefo ka?" sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kalleta cikin sanyin murya ta gaisheta, Hajja ta kalli direction dinta tace "Lafiya lau" Sai kuma ta kalli Ajay tace "Ita ce matar taka kenan" Shi dai Ajay bai ce mata komai ba, Haj tace "To Maa sha Allah, Allah ya sanya albarka ya baku zaman lafiya" Daga haka bata sake cewa komai ba a parlon, bayan yan mintuna ta mike ta dau bowl din da ta ajiye ta fita daga parion, Jay taje ta sama a daki, bayan ta kulle kofar dakin ta karasa ciki ta zauna kan kujera tace "Na dauko maka dambun naman kuma ban same ka a parlon ba" Shi dai bai ce mata komai ba, ta ajiye bowl din tana kallonsa ta kwantar da murya tace "Kayi hakuri Jawwad, nasan kai me hakuri ne, bazaı ji dadi ba idan ka kullaci dan uwanka akan wannan abu, kun taso tare cikin so da kaunar juna kamar yan biyu rana tsaka wannan abu mara dadi ya gifta, ka fi kowa sanin halin dan uwanka ni ina da yakinin bai san da wannan aure ba shima sai bayan da sarki ya daura masa, sannan kasan yanxu haka in kace zaka sharesa damuwa zai saka ma kansa, ni naji ma kwata kwata yarinyar bata min ba wallahi' Sai a sannan Jay ya daga kai ya kalleta yace "Me ta maki?" Hajja ta hade rai tace "Me ta maki?" Hajja ta hade rai tace "Me ta min? Yarinyar kamar er jaraba gashi ta dalilint zumuncin da aka gina tale tale na neman rushewa tana neman shiga tsakaninku da dan uwanka, to kuwa ina amfanin irin ta a al'umma? Ai ta zama abar tsoro kenan, dole n sai an aurota cikin Family tunda auren bai yiw da kai ba ba sai a hakura ba, na meye sai an maida aure kan wani Junaid kamar ita din er gwal ce?? Wallahi da sarki yayi shawara da ni bazai aura ma Junaid yarinyar nan ba ko don saboda kai, in ma yace shi bazai zama karami mutum ba to gwara can ya aura mata Walid ko kuma Mukhtar, ko ya nemi wani a dangi ya aura mata, gaskiya ban ga alamar alkhairi tattare da yarinyar ba tunda ta dalilinta komai ya cakude na rasa ta inda zan fara gyaran nan kuma naga ma kamar halarabiva ce ko Idona ne Jay dai bai sake cewa komai ba, cikin nutsuwa Hajja tace "Nasan halin ka na kuma san halin Junaid, nasan Junaid bazai ki yi maka magana ba Jawwad don Allah idan yayi maka kar kace zaka ki kulasa, kayi hakuri ka bar ma Allah komai, kuma ba kowa ya ja sanadin faruwan wannan al'amari ba sai Aseeyah, Aseeyah ita ta ja komai kuma bata kyauta maka ba, amma a yanxu dai ina son ka saka ma ranka salama ka malda lamarin ka ga Allah" Hajja ta fi minti sha biyar a dakin tana kokarin kwantar masa da hankali tana kara jadadda masa kar yace zai yi banza da Junaid, shi dai yaki ce mata komai daga karshe ta bar dakin ta koma parlon ta, tun bata karasa ba take jin kamar muryar Aunty a parlon nata, tana shiga kuwa ta sameta tsaye da Hajlya Aisha suna ci ma Ajay mutunci ya ki ko daga kai ya kaliesu sai danna wayarsa kawai yake karnar ba da shi suke ba, Suna ganinta duk suka yi shiru, da mamaki Hajja tace "Lafiya? Me ke faruwa haka?" Aunty ta zauna kasa don gaida Hajja, Hajja tace "Me ke faruwa nace?" Cikin bacin rai Aunty zata fara magana Hajja tayi wani tunani sai ta dakatar da ita tace "Bana bukatar jin komai yanxu, kawai ke da A'isha ku tashi ku je" Aunty ta mike ta fita daga parlon Hajiya A'isha na biye da ita a baya, ita dai Khaleesat na zaune kamar an dasata inda take mamaki yaki barin ta, she was really shock don bata ga alamar mutunci ba kwata kwata, sosai jikinta yayi sanyi da wannan abu, is it she that will leave with this kind of people in the palace? Auren da har yanxu ba amsan sa tayi ba amma take ganin wannan abu, Hajja na kallonta bayan ta zauna tace "To ban san sunan kishiyar tawa ba" Khaleesat ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Sunana Halysaah" Hajja tace "Maa sha Allah, sunan kishiyar tawa ta yan gayu kuwa" Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace "Amma sunana Jiddah" Hajja tace "Maa sha Allah, kin ga mu mun fi gane wannan ai, you are welcome to the family Jiddah" Mikewa Hajja tayi da kanta ta kawo kayan ciye ciye ta ajiye a parlon sannan ta fita, can main parlor ta tarar da Aunty, Hajja na kallonta tace "Ke yanxu Hafsat saboda rashin kamun kai a gaban surka za ki zubar da mutuncinki ki nerr ki zubar da na gidan nan?" Cike da damuwa Aunty tace "Hajja tun da aka kawo yarinyar nan masarauta Junaid ke bude mata kofofin raina ni, tun kawota har yau yarinyar nan bata taba bude baki ta gaida ni ba kamar yanda sh ma sai ya ga ubansa yake gaisheni" Hajja tace "To ke ma ba sai kin ga uban nasa kike amsa gaisuwarsa ba? Duka duka yaushe har aka kai ta gidan da zata waye ki? Yarinyar da ko kwana uku bana tunanin tayi" Shiru Aunty tay bata sake cewa komai ba wani sabon bacin rai ya lullubeta, Hajja tace "To ki kama kanki, ba ruwana da abinda ke tsakanin ki da Junaid kar ki kuskura ki ce zaki zubar da mutuncin gidanmu a idon duniya, a gaban yarinya babu kunya ki tsaya kina kalaman banza da hofi akansa? Idan matar Walid ce za ki yi wannan iskancin a gabanta?" Aunty tace "Matar Walid ma bazata min haka ba Hajja" Hajja tace "To zageni Hafsat, kare min nima yanda kika kare ma Junaid al ba sabon abu bane" Shiru Aunty tayl sai kuma ta fara bata hakuri kai a kasa, Hajja tace "Aikin banza aikin Hofi kawai, a ko ina ke sai kin malda kanki karamar mutum, gaban yarinya kin zubar da mutunci da girman ki, ina amfanin haka wai kuma matar sarki? Dama haka matan sarakunan su ke? To sam mu ba mu yi haka ba, bama son duk wani abu da zai taba reputation dinmu da na gidanmu komin kankantarsa, amma ke kam taka haye ce ma a jinin sarautar Hafsat" Daga haka Hajja ta juya ta bar parlon, Aunty dai sai huci take tunani iri iri na yawo a ranta, lallai ta gamu da aiki ja wanda ko bacci bai kamata tana yi da ido biyu ba yanxu. Throughout ranan haka Khaleesat ta yini daga ita sai Hajja a parlor, ga 'ya ya da jikoki da mutanen arziki na ta zuwa gidan yi ma Hajja sannu da zuwa, in an gaisa sai Hajja tayi masu introducing Khaleesat dake gefenta, Khaleesat dai duk a masu zuwa bata ga wanda ya wani bata attention ba, duk kuma a nan ne taga yaran Aunty uku, wata me sunanta da ake ce ma Baby that is just a teenager sai yayyinta Maryam da Khadijah, gaba daya ko bin ta kan Khaleesat basu yi ba, ita dai tana zaune parlon ne amma Allah kadae yasan damuwan da ya cunkushe mata a rai, har take jin da zat: samu wajen da zata yi kuka ta samu relief, Babban damuwarta a yanxu shine wannan aure da aka mata da Junaid, secondly Jay da ta garni shigowar su daxu ya kara destabilizing dinta komai ya dawo mata kamar yanxu yake faruwa, thirdly Aunty, har cikin ranta taji take tsoron matar don bata mance mahaifiyar Abdul ba da abinda tayi mata, she is so afraid of the woman, further more gashi ta lura duk familyn babu alamar akwal wanda zai so ta, kllan sai Hajiya Shafa'atu kawai, duk sai sha mata kamshi kawai suke suna daga mata kai kamar sun ga kashi babu wanda ya bata attention a parion, hatta Hajja is just being neutral babu yabo babu fallasa ce, kuma duk zamanta a parlon sae ya kama Hajja ke mata magana although cikin mutuntawa zata mata maganar, kuma ko ita aka kawo ma abinci sae ta fara dibar me Khaleesat kafin ta ajiye. and the least among damuwarta Junaid, she don't know why he is being treated this way a gidan nasu, she don't even know ko hakan tausayi ya bata ko kuma she is just feeling for him, but for now dai duk ba shi ne a gabanta ba, damuwarta kawal Jay.... HALYSAAH PAGE 105 Khaleesat na komawa cikin gidan Hajja ta tarar da Hajja zaune parlor da Jay tana masa magana cikin kwantar da murya, Hajja ta daga kai ta kalleta da mamaki, Jay dai sau daya ya kalleta ya dauke idonsa, Hajja tace "Halan kin yi mantuwa ne Jiddah?" Khaleesat ta kasa kallonta ta gyada mata kai kawai, Hajja tace "To je dakin ki duba...." Hanyar parlon Hajja ta nufa tana tafiya a hankali, tana shiga parlon hawaye ya gangaro fuskarta ta juya tana kallon entrance din parlon kamar tana jiran taga ya shigo, she stood for almost 3 minutes a parlon daga karshe ta goge idonta kawai ta fita ganin ba shigowa zai yi ba, she was so heartbroken and sad, da kyar ta koma main parlor tana kokarin ganin hawaye bai zubo mata ba, Hajja tace "Kin gani?" Ta gyada mata kai ba tare da tace komai ba don tana iya fashewa da kuka, bata ga Jay a parlon ba, a haka tayi ma Hajja sallama da kyar ta fita, Har suka koma masarauta Ajay bai kalli direction dinta ba ita ma haka, sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, suna isa bangaren sa taga ya bude daya daga rooms din dake bangaren ya shiga a maimakon part dinsa, ita dai tana tafiya a hankali ta shiga parlonsa ta zauna kan kujera wasu sabbin hawaye na zuba idonta, sai kuma ta kwantar da kanta kan kujeran tana kuka a hankali, Har aka yi Magrib Ajay bai shiga part din nasa ba, at this point, the whole situation is beginning to get him very angry, why is he even to be blamed? Shi adalci aka masa with this marriage? Yarinyar da is nothing but a burden to anybody around her..... Khaleesat na zaune parlor bayan ta idar da sallah kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai, tayi nisa tunanin da take taji an kwankwasa kofar parlon, a hankali ta juya daga inda take zaune tana kallon kofar bata dai amsa ba, bayan few seconds aka bude kofar Yakumbo ta shigo da sallama ta tsaya nan bakin kofar tana gaida Khaleesat cikin ladabi, Khaleesat ta sauke idonta ta gaisheta ita ma cikin sanyin murya, Yakumbo tace "Abinci ne za a shigo da shi ranki shi dade idan babu damuwa" Khaleesat ta gyada mata kai tace "To" Sai a sannan Yakumbo tayi ma ma'aikatan dake bayanta izinin shigowa parlorn with trays of different food a hannunsu, su ma duk suka gaisheta da ladabi sannan suka ajiye duk abincin har da kayan marmari bayan sun fita Yakumbo ta kara kwantar da murya tace "Babu wani damuwa dai ko ranki shi dade?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Ba komai, Nagode" Yakumbo tace "To maa sha Allah, sannan babu wani abu da zaki bukata da za a kawo maki?" Khaleesat tace "Eh ba komai" Yakumbo tayi mata sallama sannan ta nufi kofa ta fita, tsaye taga Ajay bakin kofar dakin da yake ciki don tun da yaji anyi knocking door din parlonsa ya fito don ganin waye a part din nasa, Yakumbo ta risina kai ta gaishesa ya amsa sannan yace "Idan kin gama ayyukan da kike zaki kwana nan bangaren tare da ita, akwai ɗan aikin da zan yi can anjima da daddare...." Da ladabi Yakumbo tace "To in sha Allah ranka shi dade" Juyawa yayi ya koma cikin dakin ya kulle kofa. Ana idar da sallahn Asuba Ajay ya shirya ya tafi gidan Hajja don tun ma ba ayi sallah ba kiranta ya shigo wayarsa don ta tunatar masa tana jiransa bayan anyi sallah, yana isa gidan bayan yayi parking ya fi minti goma zaune cikin motar daga karshe ya kashe ya sauka ya shiga gidan, direct ya nufi parlon Hajja ya sameta zaune tare da Jay, zaunawa yayi ya gaisheta calmly, Hajja ta amsa tana kallonsa, bayan kusan minti biyu tace "Ban ga ka gaisa da ɗan uwan naka ba Junaid" Ajay yaki ce mata komai kuma bai fasa kallonta ba, Hajja ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Jay dake danna wayarsa kawai, can ta sake kallon Ajay speaking with calmness tace "Junaid, you owe Jawwad an apology even though you are not at fault but for peace to reign you have to do that, don in batun gaskiya za a bi ba a kyauta ma Jawwad ba, things were never supposed to be done this way in an zurfafa tunani, bana son zumuncin ku ya taɓu akan mace, a ajiye duk wani circumstances da yayi leading to all this amma yana da kyau ku fahimci juna da ɗan uwanka, come to think of ur bond together, this is so pathetic...." Ajay dake ta kallonta yace "Apology for what in particular Hajja? Why is he trying to play the victim whereas nima tauye ni aka yi tunda ban bude baki nace ina so ba don ban hango future na tare da yarinyar ba, why is he playing the victim in this situation? Ni nace a aura min yarinyar?" Jay ya ɗaga kai ya kallesa calmly yace "That is a lie, idan da baka so babu ta yanda zaka yi accepting auren, stop fooling your self Man" Ajay ya mike yace "Then you do ur worst Jawwad, you think yanda ka nuna ma Mai martaba ba shi da 100% say akan ka sai yanda Mamin ka tace kana tunanin nima zan nuna masa haka, You think I can also disappoint him and make him look foolish in the eyes of people? Beside stick this to ur brain Jawwad... Abba bai yi shawara da ni kafin ya yanke wannan hukuncin da ya yanke ba tunda yasan ni ya isa da ni dari bisa dari" Mikewa Jay yayi ya nufesa yana kallonsa direct in the eyes carefully yace "Watch ur tongue, do not let me voice out all what is in my mind Junaid, do not push me" Ajay yace "So? Ya wuce kace idan naka Dad din ne bazai yi maka haka ba, ina ce iya abinda zaka fada kenan, wannan kuma ba ni zaka gaya ma ba kaje ka samu Mai martaba and tell him that, go meet him" Hajja ta hade rai ta mike ita ma tace "Bana son sake jin bakin kowa a cikin ku, ba wannan ne dalilin da yasa na hada ku a nan ba, what is all this nonsense???" A hankali Jawwad yace "There is nothing that will be said to me here da zai yi convincing dina or change my perspective of this whole thing Hajja, don haka kar ma ace min komai i am not interested, bana bukatar jin komai" Hajja ta saki baki tana kallonsa, zai fita daga parlon tace "Jawwad" Tsayawa yayi amma bai juyo ba, Ajay ya karasa har inda yake tsaye ya zaga gabansa yana kallonsa yace "Halysaah ko? Take a chill pill, she is urs.... It's just a matter of time, i am giving you my words" Yana kai wa nan ya fice daga parlon without turning back, Jay ya bi sa da kallo, Hajja was totally speechless a inda take tsaye baki bude, bayan few seconds tace "Allah ya sauwake, Allah ya tsare mu da wannan taɓara sai kace a garin gaɓa gaɓa, shi Jawwad din mahaukaci ne me kuma zai yi da matar da aka aura maka, ko kuma ita Halysaar er gwal ce? meye ma amfanin auro irinta cikin zuri'a tunda ta dalilinta gashi zumunci na neman samun tangarda, sam ni yarinyar ma bata min ba saboda abubuwan nan da ke faruwa babu kan gado, shi Jawwad din bashi da hankali ne? Me kuma zai yi da matar ka?" Jay ya juya ya kalli Hajja. Khaleesat ta fito daga Bedroom wajen karfe goma na safe jin sallaman Yakumbo a parlor, cikin kwantar da murya Yakumbo tace "Ranki shi dade yanxu Yarima ya kirani yace a sanar maki ki shirya za ku yi tafiya yau, ina fatan kin sani" Khaleesat tayi shiru tana kallonta, can tace "To" juyawa tayi ta koma Bedroom din, rabonta da ganinsa tun jiya da suka dawo gidan Hajja da yamma, ta zauna kan kujera tayi tagumi tana kallon babban plasma din dakin, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya saboda damuwa gashi har ta fara jin kirjinta na ciwo, tana ta zaune har bayan minti talatin ta ji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, bai ko kalli inda take zaune ba har ya shigo cikin dakin, ta bi sa da kallo har ya dau abubuwan da zai dauka zai fita daga dakin ta hade rai tace "Ina za mu je?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban sani ba" Daga haka yayi ficewarsa daga dakin, ta taɓe baki ta dauke kanta, bayan fitarsa babu dadewa sai ga Yakumbo ta zo sanar mata ta fito Yarima na jiranta, Khaleesat ta ɗan hade rai tace "To ai ni ban hada kayan ba" Yakumbo ta ɗan yi murmushi tace "To ranki shi dade idan babu damuwa ki bani izinin in hada maki, Sai ki dinga nuna min duk abinda zaki bukata" Khaleesat tace "A'a kar ki damu Mama zan hada yanxu" Daga haka ta juya ta koma dakin, sai da Khaleesat ta ɓata kusan minti talatin kafin ta hada duk abubuwan da tasan zata bukata a akwati, gaba daya jikinta a sanyaye yake duk da tafi zargin Maryland za su koma, But will she cope there without Jay?? tunanin hakan yasa hawaye ya fara sauka idonta, a haka ta fito daga dakin, Yakumbo ta fita da akwatin nata waje Khaleesat na biye da ita kamar warce aka zare ma laka, Mikewa Ajay dake zaune daya daga parlor din part din yana jiransu yayi, yana kallon Yakumbo yace "Ki bar akwatin a nan za a shigo a dauka" Da ladabi tace "To ranka shi dade" Ita dai Khaleesat sau daya ta kallesa ta sunkuyar da kanta, babu yabo babu fallasa yace "Mu je" Bin bayansa tayi fuskarta babu fara'a suka tafi har parlon Mai martaba don yi masa sallama, Mai martaba na kallon Ajay yace "Flight din karfe nawa ne?" Ajay yayi kasa da murya yace "Na dare ne ranka shi dade" Mai martaba yace "Toh Allah ya kai ku lafiya, idan kun koma sai ka fara mata processing visa din UK, kasan akwai occasion da za ku yi attending a can, if there is anything concerning the Visa processing you let me know" Ajay yace "To in sha Allah ranka shi dade" Ita dai Khaleesat kanta na kasa tun da suka shigo parlon, Mai martaba ya sa masu albarka suka bar parlon bayan yayi instructing Ajay yaje su ma Aunty sallama. Bayan sun fito bangaren Sarki Ajay ya nufi part din Aunty duk da bai so ba but he have no choice, ita dai Khaleesat na biye da shi tana jan kafa, Aunty na zaune parlonta tare da Walid sai Maryam warce bazata wuce 25 years ba Ajay ya shigo parlon tare da Khaleesat, duk suka daga kai suna kallonsu, sosai gaban Khaleesat ya fadi bayan sun hada ido da Aunty, ta zauna kasan carpet ta gaidata a hankali sannan ta gaida Walid da Maryam, Walid ne kadai ya amsa gaisuwar nata yana kallonta, Maryam kuwa sai danna wayarta take ta toshe kunnenta da Ear pod, Ajay ya zauna kan kujera ya gaida Aunty without looking at her, a takaice yace "We are leaving for Maryland..." Da mamaki Aunty tace "You are leaving for Maryland?dama ka saba zuwa yi min sallama ne idan zaka tafi ko kuma rashin kunya ka shigo yi min ka nuna min ai an maka aure?" Ajay yace "Mai martaba ne yayi instructing dina mu shigo mu yi maki sallama so i have no option than to obey his instructions...." Maryam ta kalli uwarta tace "Wai Aunty wannan ce Bazawarar matar da ake cewa dama? Na ganta gidan Hajja jiya na zata irin masu zuwa kawo kukan su suna neman taimako ne" Ajay ya daga kai ya kalleta, tana ganin haka ta mike daga inda take zaune tana yamutse fuska sanin sai ya iya wanke ta da mari, Aunty ta daure fuska tace "Ina zaki? Ai ba karya kika yi ba Bazawarar ce er matsiyata, sai ma kin ji history din ubanta..." Ita dai Maryam taki tsayawa a parlon ta nufi kofar wani daki tace "Tabbb wa yaga kwamacala, lallai akwai aiki babba, wai er matsiyata a gidan sarauta, how is that even possible" Daga haka ta shige cikin daki har da sa makulli, Aunty tace "To karen hauka ya sha da zai taɓa ki, meye na shigewa daki kuma, ubanki ne shi da zaki ji tsoronsa?" Walid dai kallon Khaleesat da ta sunkuyar da kanta kawai yake yi kamar ya samu TV, Ajay ya mike yana kallonta a takaice yace "Tashi mu je" Sai a sannan ta daga kanta hawayen da ya fara taruwa idonta ya gangaro ta mike tana kallonsa, bai kara second biyar a parlon ba ya fice Khaleesat na biye da shi, Aunty ta bi su da wani kallo me cike da tsantsan tsana. Hawaye kawai Khaleesat take bayan sun bar masarautan, Ajay dai bai ce mata komai ba a bayan motar cause he was also deep in his thought, bayan tafiyar kusan minti talatin driver din yayi horn bakin gate din wani gida bayan an bude gate din ya shiga yayi parking, Ajay ya bude motar ya sauka, Khaleesat ta bi sa da kallo kafin ita ma ta bude motar ta sauka tana goge idonta, building din gidan taga ya nufa yana making phone call, ta bi bayansa tana tafiya a hankali, suna shiga parlon gidan bayan few minutes sai ga Hajiya Shafa'atu ta sauko downstairs ta karaso cikin parlon da fara'a tana masu sannu da zuwa Khaleesat ta zamo kasa daga kan kujera ta gaisheta cikin sanyin murya, Hajiya Shafa'atu ta ɗagota ta zaunar da ita kan kujera kusa da ita tana amsa gaisuwarta da murmushi tace "Sannu da zuwa amarya" Sai kuma ta kalli Ajay tace "Ni fa duk tunanina za ku yi few weeks kafin ku koma Amurka, ko dai za ku zauna Abuja ne for sometimes before traveling?" Ajay yace "A'a, Flight din na karfe sha dayan dare ne yau in sha Allah" Hajiya Shafa'atu tace "Ikon Allah, yanxu baza ku jira ayi Walimar Jawwad da Hadiyah ba? It's taking place in few weeks time fa, Ina ga ya kamata ace kuna nan za ayi" Khaleesat dai sai kallon Hajiya Shafa'atu take babu ko kiftawa jin abinda tace, Ajay yace "She is resuming school this Monday, kuma final semester ne" Hajiya Shafa'atu tace "Gaskiya kuma ya kamata ku koma saboda wannan, to Allah Ubangiji ya kai ku lafiya nima nan da few weeks za mu je Canada idan an gama Waliman an kawo amarya, kaga in mun koma ko weekend sai ka dinga kawota tayi tunda daga Maryland zuwa Toronto ba nisa sosai garemu ba, Visa kawai zaka fara nema mata tun yanxu" Ajay yace "Haka ne" Wajen karfe uku suka isa garin Kano, Khaleesat taji ina ma ya kai ta gidansu taga Ummanta ko zata ɗan samu relieve din abubuwan dake damunta suka tunkushe mata a rai, tun da yayi lodging dinta a wani babban hotel sannan aka kawo mata lafiyayyen lunch bata sake ganinsa ba har sai karfe shidda da rabi na yamma da yayi knocking, Bayan ta bude kofar yana kallonta a takaice yace "Where are your Traveling document?" Khaleesat ta jingina da kofa tana kallon different direction kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Gidanmu" Yace "And you were quiet all this while, da hancinki zaki koma US din ashe" Ta wani kallesa tace "To ai ba a tambayeni ba, don har nayi zaton an fara tafiya haka ne babu document" Yace "I will give you a dirty slap, ni kike gaya ma haka?" Tura baki tayi ta juya ta bar wajen ta koma cikin dakin ta zauna gefen gado ta rungume hannunta, kullo kofar dakin taga yayi, ta harari kofar, tana ta baza ido ya dawo yace mata ta fito su tafi can gidan nasu ta dauko document din ko ba komai dai zata ga Umma amma shiru shiru bata ga ya dawo ba, sai karfe takwas saura ya dawo dakin yace "If you feel like leaving sai ki taso ki bar masu dakinsu" Da ido ta bi sa har ya fita sannan ta taɓe baki ta mike ta bi bayansa, yana zaune gaban mota sai drivern da zai kai su airport wanda dama shi yayi driving dinsu daga Bauchi, tana bude back seat ta shiga taga traveling document din nata a kan kujera har da wayarta da Charger da ta bari a gida sanda za a kai ta Bauchi, lkci daya hawaye ya cika idonta ta daga kai tana kallonsa a gaban motar, shi ne bai tafi da ita gidan ba taga Ummanta, a haka suka bar hotel din tana jin hawaye na sauka idonta wani mugun haushinsa ya cika zuciyarta kuma bata fasa masa wani irin kallo ba wanda bai ma san tana yi ba a bayan motar. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 106 Khaleesat na zaune Departure lounge waiting for their flight to America bayan sun sauka garin Abuja, once a while take daga ido ta kalli Ajay da ke ta danna wayarsa don separately suka zauna far away from each other, gashi ko kallon inda take baya yi kamar ma ba tare suke ba, a hankali ta bude handbag dinta ta ciro wayarta dake kashe ta kunna, rabonta da wayar tun bayan da aka daura mata aure da abun duniya ya isheta ganin bata samun Jay a waya, bayan ta kunna taga tana da sauran caji, tasan har Safiyyah ta gaji da yi mata WhatsApp message, kilan in ta ji shiru tayi ma Aunty Farida magana, subscription ta fara yi kafin ta bude WhatsApp dinta, last message din da Sophie tayi mata ta bude tana dubawa taga tana ma online at the moment, hawaye ne ya cika idonta bayan ta karanta message din, kawai tace mata hm, message din na tafiya sai ga WhatsApp call Safiyyah ta doko mata, picking tayi ta kai kunne cikin sanyin murya tace "Sophie" Cikin farin ciki Safiyyah tace "Yau ni naga ikon Allah wajen matar nan, daga yin aure sai kashe waya Coursemate?? wato don ma ki ci amarcin ki cikin lumana babu me takura ki da Housemate, shi dama angon is always not replying messages, wallahi nayi missing dinki sosai Khaleesat you won't understand, yaushe za ku dawo plss, kinsan fa Monday za mu yi resuming" Khaleesat dake ta sauraron maganganun Safiyyah ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Yau za mu taso in sha Allah Sophie, nan da few minutes za mu yi boarding plane din" Safiyyah ta zaro ido with excitement tace "Don Allah da gaske kike kawata, na zata fa sai nan da sati biyu za ku ce zaku dawo, toh Allah Ubangiji ya kawo min ku lafiya, har girki kuwa zan maku wallahi, i will even meet you people at the airport, Ina Housemate din? Plss ki ce ina gaishesa sosai" Khaleesat ta kasa cewa komai, lokaci daya taji hawayen da ya taru idonta na zubowa, Safiyyah tace "Hello are you der?" Da kyar Khaleesat tace "Za mu yi boarding yanxu, bye" Safiyyah tace "Toh shkkn, pls in layover za ku yi ki min magana a kasar da ku ka sauka, na ma san Layover ne, sai in san sanda za ku iso so that i will be at the airport" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Ohk, bye" Daga haka ta katse wayar ta mayar cikin jakarta ta daga kai tana kallon Ajay fuska daure. After some more minutes Khaleesat suka yi boarding jirgi and they were among the few first to board kasantuwar first class passengers ne su, sake kallon ticket dinta tayi da mamaki don duk tunaninta Business Class ne, this is her first time flying first class and it was strange to her ganin luxury din, Duk da comfort and premium luxury na first class ita kam she wasn't comfortable bayan tashin su Abuja da few hours saboda Motion sickness da ya taso mata wanda bata fiye yi ba ma a jirgi sai ko in tana cikin damuwa, sau uku tana zuwa lavatory in taji amai ya taho mata, Flight attendant din was trying all possible best to see she is comfortable don da ta tafi zata dawo still to check on her and see if she's okay, sosai ta bata kulawa Flight attendant din, har daga karshe Khaleesat tayi converting seat dinta into lie flat bed tace mata zata yi bacci sannan ta kwanta ta rufa har kanta da blanket, duk Ajay na kallonsu ko da ba kusa suke ba cause there is enough space separating them, bayan kusan awa daya Khaleesat taji an sauke blanket din da ta rufe har kanta da shi, bude ido tayi suka hada ido da shi, yana duke yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Are you okay?" Da hanci ta amsa masa sannan ta kara jan blanket dinta zuwa kafadanta ta juya masa baya ta rufe idonta, mikewa yayi ya koma seat dinsa ya zauna, har jirgin su ya sauka London for stopover Ajay bai sake ce mata komai ba a jirgin. A cikin airport din ma ko kusa da inda take bai zauna ba suna jiran connecting flight dinsu to Baltimore, ita dai taki zama sai Safa da marwa take a Departure Lounge, she looks so uncomfortable, lokaci lokaci take satan kallonsa duk da yaki ma kallon inda take kamar bai san Allah yayi ruwanta ba, can dai ta dake ta nufi inda yake zaune ta tsaya amma kuma taki kallonsa tana wasa da veil din jikinta, daga kai yayi ya kalleta dai dai sanda ta saci kallonsa, tana ganin sun hada ido ta ɗan turo baki ta sauke idonta a hankali tace "I am having issues" Kallonta kawai yake jin abinda tace, Tayi kasa da murya tace "I need sanitary pad" Ajay ya dauke idonsa yayi shiru kamar me nazarin abinda ta fada, after almost a minute ya daga kai ya sake kallonta yace "Do I look like a pad vendor?" Ita dai taki kallonsa har sannan kuma bata fasa wasa da gefen gyalenta ba, bai sake ce mata komai ba tsabar mamaki ya tallabi chin dinsa yana girgiza kafa, can dai ya kuma kallonta yace "So as the lady you are you don't even know ur Cycle to prepare ahead?" Nan ma dai Khaleesat taki kallonsa taki cewa komai, Gyara zamansa yayi yace "Thank God is ur self you are going to disgrace here not me, nayi maki kama da me siyar da sanitary pad da zaki ce min you need sanitary pad, ko kuma amfani nake da sanitary pad?" Kamar zata yi kuka tace "Ni dai don Allah ka duba min kafin a fara boarding...." Jin yayi banza da ita kuma babu alamar zai tanka mata don wayarsa ma ya hau dannawa, tana ta tsaye for almost 5 minutes a wajen, a hankali ta juya kawai ta bar kusa da shi ta koma can inda take tsaye ta ci gaba da tsayuwarta tana kallonsa, after some minutes ta ga ya mike, daya daga Lounge staff din dake wajen Ajay ya nufa for assistance or even a concierge service request if possible don bazai iya fita daga Departure lounge din just like that ba, not too long after sai ga shi an kawo masa sakon da ya bukata, tun da Khaleesat taga Ajay ya nufota rike da ledan Sanitary pad tayi saurin dauke kai kamar bata san yana zuwa ba, yana isa gabanta ya mika mata ledan, bata yarda ta hada ido da shi ba ta amshi ledan a hankali tace "Nagode" Kamar jira yake yace "Kazamar mace ce kawai bata san when her period is going to be due ba..." Yana fadin haka ya juya ya bar wajen, ta bi sa da wani harara tana turo baki, daga karshe dai suka yi boarding jirgin da zai kai su Maryland wajen karfe takwas saura na safe, after 8 hours trip kuma suka sauka airport din Baltimore, sosai Khaleesat tayi farin cikin ganin Safiyyah da ta zo tarbanta a airport har da tsadadden bouquet of flowers dinta, Khaleesat ta rungumeta tare da flowers din looking so happy, Safiyyah ta bi Ajay da ya wuce su da kallo baki bude, can ta kalli Khaleesat tayi kasa da murya tace "Shi kuma wannan fa? Har da shi ku ka dawo dama?" Sai kuma ta fara kalle kallen inda zata hango Housemate shi kuma, ganin bata ga alamar sa ba tace "Ina Housemate din?" Khaleesat ta kasa ce mata komai tana kallonta, lokaci daya hawaye suka cika idonta, da mamaki sosai Safiyyah tace "Kuka kuma? Me ya faru? What's happening?" Khaleesat ta rungumeta hawaye masu zafi na zuba idonta ta fara shesshekan kuka, Safiyyah was speechless at first ta ma rasa ta ina zata fara magana don duk zurfin tunaninta bata kawo dalilin kukan Khaleesat a ranta ba a wannan lokacin, ta dago kanta tana kallonta tace "Tell me what is happening mana pls Khaleesat? Ina Housemate din? Ko dai ba ayi auren bane tukunna? but ke kika ce min an daura ai, and that was the last time we chatted, da naga baki online since after then nayi chatting Aunty Farida tace min ai har an kai ki Bauchi" Khaleesat ta fara goge hawayen da ya ki tsaya mata, ganin ba magana zata yi ba kawai Safiyyah ta kama hannunta suka bar wajen, suna tafiya a hankali cikin sanyin murya Khaleesat tace "Sophie, Housemate isn't my husband!" Safiyyah ta tsaya ta juya tana kallon Khaleesat da sauri babu ko kiftawa tace "I don't understand" Khaleesat ta sauke idonta wasu hawayen na sauka idonta da kyar tace "Yes, he isn't" Safiyyah that was so confuse tace "Then who is the Husband? Don Allah ki gaya min Khaleesat...." Khaleesat ta kasa cewa komai hawaye sai kai kawo suke a idonta taki dago kanta, A hankali Safiyyah dake gwalo ido tace "Ajay?" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta with more tears rolling down her cheek ta gyada mata kai trying not to burst into cry, kallonta kawai Safiyyah take babu ko kiftawa kana ganinta kasan ba karamin girgiza tayi ba a inda take tsaye kamar warce ruwa ya cinye, they stood there for more than 3 minutes babu wanda yace komai cikinsu, Safiyyah was just staring at her kamar gunki don ko kwakkwaran motsi bata yi, ita kuwa Khaleesat sai share hawayen da yaki tsaya mata kawai take, daga karshe Safiyyah ta kama hannunta a hankali suka ci gaba da tafiya slowly, kana ganin Safiyyah kasan she is more than shock and speechless at the same time, tsaye suka samu Ajay jikin motar da zai kai su gida ya rungume hannu fuskarsa babu yabo babu fallasa alamar su yake ta jira, driver din da ya zo daukansu daga gida har ya gama saka traveling luggages dinsu gaba daya a bayan mota, Safiyyah na kallonsa with calmness tace "Ina yini, ya hanya?" Ajay yace "Alhamdulillah" Ta juya ta kalli Khaleesat da idanuwanta har sun yi jajir saboda kuka tana ɗan murmushin karfin hali tace "Kawata zan koma can gida in dauko abincin da na girka, i will call you to know where to bring the food for you" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Safiyyah ta kalli Ajay tace "To sai anjima, zan je in dauko mata abinci a gidanmu" Ba tare da Ajay ya kalleta ba yace "Ohk, you can get in the car and tell the driver ur Address" Daga haka ya zaga ya shiga front seat, Safiyyah ta ɗan yi jim, can kuma dai ta bude bayan motar, sai da Khaleesat ta fara shiga sannan ita ma ta shiga ta kulle motar, a haka suka bar airport din, dai dai gidansu Safiyyah Drivern yayi parking bayan ta nuna masa sannan ta kalli Khaleesat tace "Ina zuwa" Bude motar tayi ta sauka ta nufi apartment dinsu, few minutes later sai ga ta ta fito da warmers din abinci biyu Khaleesat ta bude mata door din motar ta amshi warmers din ta ajiye su tana kallon Safiyyah a hankali tace "To ki shigo" Safiyyah ta ɗan kirki murmushi bayan ta saci kallon Ajay ta gefen ido tace "A'a ki dai je gida ki huta, ko gobe sai in zo in sha Allah" Nan da nan hawaye ya cika idon Khaleesat tana kallonta pleadingly alamar ta shigo motar, Shi dai Ajay ko kallonsu bai yi ba, Safiyyah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ganin hawayen idon Khaleesat ta kara satan kallon Ajay, sai kuma ta zaga ta daya side din motar ta bude ta shiga ta kulle sannan driver ya ja motar suka bar unguwan, wajen karfe biyar suka isa gidansu Ajay, bayan driver yayi parking a parking lot Ajay ya bude motar ya nufi entrance din gidan, Safiyyah ta bi sa da kallo sai kuma ta taɓe baki tana gyada kai murya can kasa tace "Tabɗijam" Bude motar tayi ta sauka rike da warmer daya na abinci, Khaleesat ma ta sauka tana rike da handbag dinta da dayan warmer din, a haka suka nufi cikin gidan driver na biye da su da traveling boxes dinsu, suna shiga babban parlorn suka tarar da babu kowa ciki, but everywhere was sparkling clean ga wani daddadan kamshi da parlon ke yi, Safiyyah ta zauna kan kujera tana kallon Khaleesat tayi kasa da murya tace "Khaleesat how did you agree to this? Menene ya faru har haka ta kasance? Dama ana switching aure all of a sudden just like that? Bar masa ke Jay din yace yayi kenan? Kuma me ya janyo hakan? Cewa yayi yana son ki shi ma shine Jay ya hakura? Da wani bakin ya iya budewa ya fadi hakan? Bai ji kunya ba? Budurwar brother dinsa fa? Does this look normal at all? Ke da wani ido kike kallon Jay yanxu? Shkkn wannan ne makomar azababben soyayyar da ku ka yi da Jay kenan? Is this how everything ended? Ko dai kuskure aka yi gun daurin auren aka daura da shi cikin rashin sani sai kawai aka ce ayi hakuri aje a haka tunda aure ya dauru? Don Allah ni dai ki fahimtar da ni wallahi kaina bai taɓa kullewa irin yau ba, i am so confuse Khaleesat, Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta duk tana jin abubuwan da Safiyyah ke cewa tayi shiru hawaye na zuba idonta, Safiyyah ta kalli sama da sauri jin Footsteps, shiru tayi ganin Ajay ne ke saukowa downstairs, yana isowa cikin parlon ya kalli Khaleesat yace "Ai kinsan dakin da kike zama a gidan nan, so you can go accommodate your self there" Yana fadin haka ya nufi inda zai yi leading dinsa to the kitchen of the house, Safiyyah ta bi sa da wani kallo, can ta taɓe baki ta mike ta dau abincin Khaleesat tayi kasa da murya tace "Tashi mu je ki bani amsar tambayoyina, ta yaya kika yarda da auren nan" Daga haka ta kama hannun Khaleesat dake goge hawayen da ke zuba idonta suka wuce sama zuwa Bedroom din da take zama idan tana gidan, suna shiga dakin wanda shi ma was sparkling clean Khaleesat ta ajiye handbag dinta kan gado cikin sanyin murya tace "Wanka zan yi Sophie, na gaji sosai" Safiyyah tace "To je kiyi bari in shigo maki da sauran kayan ki, amma wanne ne akwatin ki a kayan kar in taɓo ma kaina masifa?" A hankali Khaleesat tace "Duk nawa ne kayan" Safiyyah tace "Atoh" Sannan ta fita daga dakin, Khaleesat ta cire kayanta ta shiga bandaki, ko da tayi wanka ta fito har Safiyyah ta ciro mata kaya mara nauyi a tsadadden akwatin lefenta, da kayan shafanta, Khaleesat ta gama shiryawa sannan ta kwanta gefen gado tana kallon abincin da Safiyyah ta zuba mata, Safiyyah tace "To ki yi sallah mana sai ki ci abincin kafin ki kwanta" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "I am not praying" Sai kuma ta sauko daga kan gadon ta zauna kan lallausan milk carpet din parlon ta jawo plate din abincin da Safiyyah ta dibar mata a hankali ta fara ci, ko da ta ci sake komawa tayi ta kwanta, ganin she looks so tired sai Safiyyah bata bukaci amsar tambayoyin da ta tula mata ba daxu ta kyaleta kawai, after some minutes bacci ya dauke Khaleesat. A hankali Khaleesat ta bude idonta ta fara kalle kallen dakin da take ciki, ita kadai ce a dakin bata ga Safiyyah ba, wuta mara haske sosai ne kunne a dakin which made her realize it's already dark, ta jawo handbag dinta a hankali ta ciro wayarta don ganin karfe nawa, ta ɗan bude ido ganin karfe goma saura few minutes, ajiye wayar tayi dai dai sanda aka bude kofar dakin, juya fuskarta tayi zuwa daya side din duk da bata san who open the door ba, after some seconds taga an kunna wutan dakin zuwa me haske tarr, zagawa yayi zuwa ta inda take facing a dakin suka hada ido, dauke idonta tayi, taji yace "Daki kike jiran a kawo maki dinner?" Without looking at him tace "Did I even say I am hungry?" Bai tanka ta ba ya juya ya nufi kofa ya fita daga dakin closing the door, mikewa tayi zaune tayi tagumi, ta fi minti talatin a haka sai kuma ta jawo wayarta ta bude WhatsApp, DM dinta da Jay ta shiga ta dinga kallon last message da ta ajiye masa da bai yi reply ba har yau, hawaye ta ji ya cika idonta, jiki a sanyaye tayi typing din sunan da take kiransa wato Housemate tayi masa sending, after a while ta kashe data dinta ta ajiye wayar don bata ga alamar yana online ba, komawa tayi ta kwanta tana goge hawayen dake sauka idonta. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence 07087865788* Thanks so much for prayers and patience, I am better now, nagode sosai. HALYSAAH PAGE 107 Washegari har karfe sha biyu da kusan rabi Khaleesat na daki bata fita ba, tun da gari ya waye leg cramps yasa taki sauka daga saman gado banda wanka kawai da ta daure taje tayi ta canza kayan jikinta, ta dade bata yi irin ciwon kafar ba idan tana period sannan ya hade mata da lower back pain, tana ta kwance tana jiran zuwan Safiyyah don tun da sassafe ta kirata don yi mata korafin jiya tayi tafiyarta tana bacci babu ko sallama, shine Safiyyah tace mata anjima zata shigo da rana, kofar dakin aka bude tayi saurin juyawa tayi backing kofar ta rufe ido don tun bai shigo dakin ba tasan shi ne saboda kamshin turarensa, ya zaga har inda take facing yace "Get up and leave this room Malama...." At first tayi niyyar yin kmr bacci take but jin intonation da yayi using yayi maganar alamar he is not joking ta bude ido a hankali tana kallonsa, sosai ya hade rai yace "Ko baki ji na ne? You think i will tolerate you stressing my life in this House? Ni kike nufin zan kawo maki breakfast daki ko kuma kin zo da cook or any worker from Nigeria ne da zai dinga girki yana kawo maki daki? Or are you a baby?? Who do you think you are here to stress with ur problem?" Ƙin cewa komai tayi, a fusace yace "Am i making any sense?" Dauke kai tayi ta tura baki tace "I am not feeling fine" Ya mata wani kallo yace "What is making you not to feel fine?" Shiru tayi taki cewa komai, yayi mata tsawa yace "Kee" Kamar zata yi kuka tace "To wai ba cramps bane, I am having leg cramps" Tana fadin haka hawaye ya cika idonta, yace "And who did you tell that? Baki da phone number dina ne? Since you are a type of person that is always problematic from this problem to that problem, anytime any of ur so called problem arise don't you have my number?" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, ya juya ya nufi bathroom din dake dakin wishing dama Yakumbo tana da Visa available da jirgi kawai zai biya mata ta taho ko zai samu rest of mind daga issues din yarinyar nan don bazai iya ba, gefe kawai zai koma ya zuba masu ido yana kallo a gidan, after a while ya fito daga bandakin yana kallonta yace "Ko tasowar ma baza ki iya ba zuwa bandaki?" Ta juya ta kallesa, ganin his face is very serious ta mike zaune ta sauko da ƙafafuwanta daga saman gadon a hankali, daurewa tayi zata tashi amma ta kasa mikewa tsaye, ya nufi inda take zaune ya hade rai ya mika mata hannu, dauke kai tayi giving him her hand ta daure ta mike tsaye with his help, daga nan kuma ta zame hannunta ta fara tafiya a hankali tana rike waist dinta zuwa bandakin, ruwa me zafi ba sosai ba ya cika mata a bath tub for Hot bath, suna hada ido bayan ta shiga bandakin ta kulle kofar, she felt so much relieve after the hot bath, after almost 40 minutes ta fito daga bandakin bayan ta maida kayan jikinta don kar ma ta fito daure da towel ta gansa a dakin, bata gansa dakin ba sai tray din abinci dake ajiye kan Carpet with some fresh fruits a bowl, wani kayan ta dauko a akwatin ta, bayan ta gama shafe shafenta ta saka kayan ta dau hularta ta saka, abincin da aka ajiye mata ta bude tana dubawa taga ko kadan ba shi da yawa kamar dai yanda turawa ke cin abinci, hakan ma yayi mata don da yana da yawa ma bata san yanda zata yi da shi ba tunda English breakfast ne da bai dameta ba, baked bean da aka yi micro waving sai omelette a gefe with few slices of bread da aka yi toasting and 2 sausage, sai hadin salad madaidaici a wani bowl wanda iya olive oil aka yi drizzling a kai, ta dau pain reliever dake kan tray din da goran ruwa ta ajiye su gefe sannan ta fara hada shayi don har da gwangwanin madara da Milo da cube din sugar ya ajiye mata, sai da tayi breakfast din sannan ta sha maganin, iya apple kawai ta ci a fruits din, after 15 mins ta mike zata fita da tray din don taji saukin cramps din ta samu relieve sosai, tana sauka downstairs ta gansa zaune parlor yana kallon TV at the same time yana operating wayarsa, bai kalli direction dinta ba har ta wucesa zuwa kitchen sannan ya juya ya bi ta da kallo har ta shiga kitchen din, bayan ta gama wanke utensil din da ta kai kitchen ta goge wajen sink din ta fito daga kitchen din dai dai sanda aka bude kofar parlon da sallama suka yi ido hudu da Safiyyah dake leko cikin parlon daga waje kamar mara gaskiya, sai kuma ta shigo parlon don sun hada ido da Ajay, Tana yake hade da sosa keya tace "Good afternoon" Sau daya ya kalleta ya dauke kai yace "Evening" Khaleesat taji dadin ganin frnd din nata ta karasa har inda take tace "Sannu da zuwa Sophie" Hannunta ta kama zuwa sama, ya bi su da kallon gefen ido yana ci gaba da danna wayarsa, suna shiga daki Khaleesat ta kulle tana kallonta tace "Kawai sai ki tafi jiya baki tasheni ba" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi da ke na kwana a rai Khaleesat, my head still can't process what you told me yesterday, ganin abun nake kamar Movie fa, dama ana migrating aure?" Khaleesat ta kamo hannunta murya a sanyaye tace "Don Allah kina ganin akwai mafitar da zaki bani akan wannan auren Sophie? Wallahi har cikin raina ni dai bana son auren, ni ban ce ina sonsa ba aka aura min shi, hasali ma ban sani ba don babu wanda ya gaya min sai bayan aure da aka kai ni Bauchi na sani, we can never be compatible with him Safiyyah cause he is not my type and i am not his type too, i wish gidan Abdul ma na koma da wannan auren, i am soo heartbroken...." Tana kuka a hankali ta kare maganar tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta rike haɓa tace "Gidan Abdul? Eh lallai har yanxu baki da hankali kuma bana tunanin zaki yi, wallahi ba don Housemate ba da dai ki koma ma Abdul gwara maki Ajay din ki lallaba kiyi maneji da shi duk da kusan jirgi daya ya kwaso su da Abdul din kawai shi dai nasan bazai jibge ki yanda Abdul ke yi ba, amma duk same categories ne su biyun birds of the same feather, shi wannan ga shegen renin hankali da maida mutum ɗan iska, kina ji fa yanxu nace masa Good afternoon ya mayar min da evening, karfe biyun rana ne evening idan ba walakanci ba? Sau uku kenan yana min wannan iskancin a garin nan ina lissafawa bai sani ba, To wai wani irin al'amari ne wannan ya ja har aka daura aure da shi ne Khaleesat don nasan ba haka nan aka maida auren kansa ba? Bai san cin amanar ɗan uwansa yayi ba accepting auren ki da yayi no matter the circumstance on ground? Ai ana barin halal ko don kunya kuma a yanda yasan Housemate na bala'in son ki bai kamata ya amince da auren ki ba in da zuciya daya yake zaune da shi, gwara ace guduwa ma yayi aka neme sa aka rasa a duniyar da wannan abun kunyan auren budurwar cousin dinsa, yanxu da wani idon daga ke har shi za ku dinga kallon Yaya Jawwad? Wataran in bamu yi hankali ba ma mu ganki da cikin Ajay, Tabɗijam an ci amanar kauna wallahi, jiya da shock din Ajay na kwana a raina, gashi na gansa comfortable as if it's normal yana kallon ki as his wife, don't tell me kun ma kwana daki daya da shi, Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.... Me yasa za ayi ma Housemate dinki haka bayan duk mun san irin azababben son da yake maki kema haka? Kai duk wanda ma ya assasa wannan auren da Ajay bai son ganin Jay ne a doron kasa kawai wallahi shine ya bi ta wannan hanyar don Housemate ya hadiyi zuciya ya mutu kinga ai baza ace shi ya kashe sa ba..." Khaleesat ta fashe da kuka sosai ta tafi gefen gado ta zauna ta kife kanta da Pillow tana rera kuka tana jin zuciyarta na mata zafi, Safiyyah ta zauna kan kujera ta rafka uban tagumi, wato shi yasa take ta yi ma Housemate Allah ya sanya alkhairi yaki kulata ashe ba shi ne mijin ba kaicoo, wani azababben ajiyar zuciya Safiyyah ta sauke tace "To meye amfanin kuka kuma yanxu? Ai it's too late to cry, cuta dai kam an cuci Housemate, ke ma in er halaq ce ai kamata yayi ki gudu ki shiga duniya ki nuna baki yi na'am da auren ba, ba dole a warwaresa ba in aka ga kin gudu ma'ana baki son auren, wallahi nasan har ke sai Housemate yaji haushin ki ba Ajay ba kadai don gani zai yi kin ma yi accepting auren tunda gashi har kun taho Amurka, and the way I am seeing Ajay he look like someone that is very comfortable with the marriage, ya amshi auren hannu bibbiyu abinsa wato ya samu tsuntsu daga sama gasasshe, dama wa zai kalle ki yaki amsan auren ki, tabbb" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba kuka kawai take sosai, da kyar Safiyyah ta samu ta lallasheta don sai da suka fi minti talatin tana zaune kusa da ita tana lallashinta, daga karshe ta dena kukan cikin rawan murya ta ba Safiyyah labarin duk abinda ya faru da dalilin maida aure kan Ajay, Safiyyah dai haka ta hangame baki tana kallon Khaleesat da mugun mamaki, can ta sauke ajiyar zuciya ta koma gefe ta kama kanta don bata ma san me zata ce ba kuma, ashe dai uwar Jay din er iska ce bata sani ba. Wajen karfe biyar da rabi Khaleesat ta raka Safiyyah zata tafi shima don Ya Musty ne ke ta doka mata uban kira, sosai idanuwanta suka kumbura saboda kukan da tasha, a dai dai bakin kofar fita daga parlon suka hadu da Ajay zai shigo, Safiyyah dai ta koma gefe taki yarda su hada ido tana sosa kai, Khaleesat ta wani dauke kai bayan sun hada ido da shi ta koma gefe fuskarta daure, sae da ya shigo parlon sannan Safiyyah tayi masa sai da safe tayi ficewarta daga parlon tana zare ido, ita dai Khaleesat na biye da ita a baya tana tafiya a hankali, after some minutes Khaleesat ta dawo parlor bayan ta rakata har gun Lyft da zai dauketa, tsaye ta samesa a parlon alamar ita yake jira, ya juya yana kallonta calmly yace "I don't want to see her in this house again, if you have anything to discuss with her, discuss it at school but not in this House" Khaleesat ta wani kallesa tace "Bayan ita ina da wani ne a nan Maryland? She is all I have in this state bani da kowa ni dai, don haka wallahi sai ta zo gidan nan, ae ba wajenka take zuwa ba and she is not coming because of you...." Tana kai wa nan ta nufi stairs kamar zata tashi sama fuskarta daure, ya bi ta da kallo baya ko kiftawa har ta haura sama, tunanin yanda zai yi maganinta ya fara yi, can ya zauna kan kujera kamar me wani nazari, Khaleesat na komawa dakinta ta dau wayarta ta kunna data ta shiga WhatsApp, kamar yanda tayi expecting Housemate bai mata replying message dinta ba, kuma har status update yayi a Whatsapp, kuka ta fara yi a hankali ta ajiye wayar ta koma can Edge din gadon ta rungume hannunta hawaye na ci gaba da zuba idonta, shkkn ita kuma haka rayuwarta zai kasance har abada bata da wani say din kanta sai dai a yanke mata hukunci ko yayi mata ko kar yayi mata, haka nan aka hadata da Abdul ba tare da son ranta ba, that not being enough ya turo ta makaranta wani kasa shi ma ba tare da tana so ba kawai she just have to obey, at the end aka daura mata aure dashi ba tare da ta sani ba sai da ta dawo ta tarar da hakan, after going through hell gidan Abdul Allah ya kubuto da ita, tun daga sannan tayi tunanin she now have her freedom and will be allowed to decide for her self and chose what she want, sai gashi an kara yi mata wani auren ba tare da an damu da ko zata so ba ko bazata so ba, kawai anyi depriving dinta yancinta na yi ma kanta decision din rayuwarta, tunanin hakan ya sa ta kuka sosai tana jin ba a kyauta mata ba, ba ayi considering din feelings dinta ba.... Sai wajen karfe takwas Khaleesat ta sauka daga saman gadon ta shiga bandaki don tayi wanka, bayan ta fito ta ciro kayan da zata saka, she wish zai kai ta apartment dinta kawai tayi zamanta ita kadai a can don ji take a ranta ko ganinsa bata son yi, fuska daure kamar irin tana ganinsa din nan ta gama shiryawa cike da jin haushinsa, bayan ta gama ta zauna gefen gado tana nazarin ko dai kawai ta gaya masa ita ya maida ita apartment dinta bata son zama a nan, tana cikin tunanin nan message ya shigo wayarta, ta jawo wayar tana duba message din taga numbersa ne, bude text din tayi taga content din, taɓe baki tayi ta mayar da wayarta ta ajiye, tafi minti goma zaune kamar bazata tashi ba, amma can ƙasan zuciyarta kuma tana shakkar ya shigo dakin ya sameta, Mikewa tayi daga karshe fuska a daure ta nufi kofa ta bude ta fita daga dakin ta fara sauka downstairs ko ina ruwansa da zai dinga sa ta sai ta ci abinci, tana tafiya a hankali ta shigo parlon, zaune ta samesa a parlor da Glass din juice a gabansa yana kallon football, ko kallonta bai yi ba, ita ma taki kallon direction dinsa fuskarta babu fara'a ta nufi hanyar kitchen, sai a sannan ya bi ta da kallo ya dau Glass din juice dinsa yana sipping, tana shiga kitchen din taga ba wani abinci, ta ma zata abincin ya siyo ya ajiye mata, taɓe baki tayi ta hada hot chocolate kawai ta debi cookies me tsada da ta gani sannan ta fito daga kitchen din, Da sauri ta juya zata koma kitchen din bayan ta hada ido da katon karen gidan, karen na kyalla ido ya ganta kuwa ya bi ta yana haushi fiercly kamar ya ga Alien a parlon, ta kurma wani ihu ta fasa shiga kitchen din ta nufi dinning area da sauri jikinta na rawa tana kallon karen ta ajiye cup din hannunta da cookies, ai ko ya bi ta da gudu yana ci gaba da haushi, gigicewa tayi ta fashe da kuka sosai tana kallon Ajay da idonsa ke kan TV yana shan juice kamar bai san abinda ke faruwa a parlon ba, zaga dinning din suka dinga yi da katon karen da bai fasa mata haushi mai gigita mutum ba, cikin kuka tana kallon Ajay tace "Wayyo don Allah Yaya ka taimakeni, wallahi cizo na zai yi idan baka zo ba" Ajay yaki kallon inda take yayi keeping serious face yana kallon TV yana shan juice, tsallen da taga karen yake kamar zai cakumota yasa ta tattara rigarta, shi dai Ajay kawai ganinta yayi a gefensa kamar an jefota tana neman hawa jikinsa don karen sai da ya biyota har nan, turata ya fara yi yace "Kee baki da hankali ne, meye haka" At the same time yana matsawa da sauri daga kusa da ita putting a throw pillow barrier between them amma bata fasa rike sa ba tana shige masa jiki, hakan yasa ya yunkura zai tashi daga wajen amma taki sakesa don gam ta rikesa tana rusa kuka tana kokarin hawa kansa shi kuma yaki barin tayi hakan, bai san sanda ya haure karen ba daga kusa da su ya kora sa, da gudu karen ya koma kusa da stairs ya tsaya yana kallonsu kuma bai daina haushi ba, Ajay ya dau throw pillow ya jefa masa instructing him to leave the parlor, da gudu kuwa ya bar parlon, sai a sannan Ajay ya kara turata daga jikinsa don she was still clutching onto him tightly amma taki yarda ta sakesa cikin kuka tana boye fuskarta jikinsa take cewa "Wallahi cizo na zai yi, don girman Allah ka rufa min asiri ka kaini sama kawai" Ganin ba sakesa zata yi ba ya kyaleta kawai ya dau remote ya kara volume din TV don ma ya dena jin muryarta, don kanta tayi calm don bayan ta dena jin haushin karen, a hankali ta dago kanta daga jikinsa tana bin parlon da kallo har sannan zuciyarta na bugawa da karfi, ta fara matsawa daga kusa da shi hawaye na bin kuncinta, cikin rawan murya tace "You are very wicked, I never knew you are this wicked, kuma ni bazan zauna gidan nan da karen nan ba ka maida ni apartment dina" Calmly Ajay ya ajiye remote din hannunsa yace "Legend...." Ta zaro ido ta fasa wani ihu ta kara shigewa jikinsa tace "Don girman Allah kayi hakuri, i am very sorry, wallahi wasa nake" Yayi mata kallon gefen ido, muryarta na rawa ta marairaice masa tana kara shige masa tace "Plss take me upstairs" *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* ur evidence via 07087865788 HALYSAAH PAGE 108 Cikin tsoro Khaleesat ke bin parlon da kallo jin bata sake jin haushin karen ba, nan taga karen ya bar parlon ya gudu saboda koran da Ajay yayi masa, a hankali ta fara matsawa daga kusa da Ajay tana masa wani kallo, shi ko yaki kallonta yana kallon TV, hararansa tayi ta sauka daga kan kujeran tayi wucewarta sama tana share hawayen idonta tana jin kamar ta fashe da sabon kuka don takaici, sai a sannan ya bi ta da kallon gefen ido ya dau Juice dinsa yana sipping, tana isa stairs ta sake juyawa ta kallesa suka hada ido, wani hararan ta jefa masa ta haura sama tana jin wani mugun haushin sa a rai. The next day da ya kasance Saturday har goma da rabi Khaleesat bata fito daga cikin daki ba, har cikin ranta ta tsorata da karen gidan, kiran Safiyyah ne ya shigo wayarta ta daga ta kai kunne, Safiyyah tace "Kin fasa zuwa apartment din naki ki dauko items din ki ne?" A hankali Khaleesat tace "Ai ba makulli a wajena Sophie, kuma tsoron ma fita ko nan da parlor nake" Da mamaki Safiyyah tace "Kamar yaya?" Khaleesat kamar zata yi kuka tace "Sophie he is frightening me with their dog in this House" Safiyyah tace "Dog kuma? Dama shegen karen na raye? Nuna masa kika yi kina jin tsoron karen?" Khaleesat ta fashe da kuka a hankali tace "Kinsan ai ina jin tsoron kare ni Sophie, kuma kin fa san karen kato ne and it's fierce, wallahi jiya suma ne kawai ban yi ba da karen ya biyo ni daga na je kitchen" Safiyyah tace "Tabdi, to shi kuma sai ya zuba ido shegen karen ya bi ki?" Khaleesat tace "Wallahi babu abinda yace kuma bai hanasa ba, kilan ma shi ya kira karen da ya ga na shiga kitchen don sanda na shigo parlon ni ban ga karen ba" Safiyyah tace "Ko wani salon mugunta fa Ajayn nan da kike gani ya sani, meye kuma na barin kare ya dinga tsorata ki a gida in ba iskanci ba, amma kece kika nuna masa kina jin tsoron karen tun farko shi yasa, ban da haka tun yaushe zan rotsa masa duk abinda hannu na ya kai, wallahi idan karen ya sake zuwa kusa da ke ko wani abu kika gani ki dauka ki buga masa a kai, ko kuma ki kira 911 sun tafi da shi, ta ya za a bar irin wannan kosasshen karen a gida yana firgita mutane karen da ya kamata ace yana gidan zoo saboda girmansa, bari ma ina zuwa gidan yanxu ni kin san ba tsoron karen nake ba, ki shirya kafin in karaso" Khaleesat ta ɗan bude ido bayan ta tuno warning din da yayi mata jiya, da sauri tace "Kin ga Sophie ki bari zan fara gaya masa zan je debo kayana sai mu hadu a can apartment dina kawai, kuma wallahi idan muka je bazan dawo gidan nan ba don i can't withstand living together with him, ba shi da tausayi kwata kwata" Safiyyah tace "To zai yarda ki zauna apartment din har ya siya maki foodstuffs da abubuwan bukatan gida kuwa?" Shiru Khaleesat tayi, kafin a hankali tace "Akwai kudi da yawa fa a account dina" Safiyyah tace "Ayya wanda Housemate ke tura maki ko?" Khaleesat ta sauke ido bata dai ce komai ba don duk kudaden da Housemate da Ajay din suke tura mata ne a account din, cause sanda Housemate baya nan Ajay ma ya tura mata kudi sosai, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "To Allah ya kyauta, Allah sarki Housemate, ko wani hali yake ciki oho an dai cuce sa kawai, ki shirya ki fito ina jiran ki" Khaleesat ta daga kai da sauri jin an bude kofar dakin, murya can kasa tace "Bye Safiyyah...." Daga haka ta katse wayar ta ajiye taki yarda ta juya ta kallesa, wani mugun haushinsa take ji har cikin ranta barin yanda ya bari kare yayi tormenting din rayuwarta jiya da daddare, yana tsaye daga bakin kofar ya hade rai yace "What did I tell you yesterday?" Kamar zata yi kuka ta rungume hannuwanta still not looking at him tace "Ta yaya zan fito in hadu da karen da ka bari yana yawo a gidan nan yana tsorata ni" Yace "Ina ruwanki da shi? Zamanki yake aka ce maki a gidan?" Ta hade rai tace "Ni wallahi tsoronsa nake bazan iya fitowa ba yaje ya cije ni, kawai ni dai ka taimaka ka maida ni apartment dina I can cope alone there, ai da can ni kadai nake zamana" Daga sama har kasa yake kallonta kafin yace "Kina da kudin biyan hayan apartment din kenan?" Shiru tayi, sai kuma ta juya tana kallonsa, Calmly yace "The driver in this house is purposely employed here because of u, don haka you have to be making breakfast and dinner with his ration, I can't be paying him for ur services at the same time buying him two square meals in this state, don haka kina da hannuwan ki biyu da za kiyi maku girki da ke da shi" Khaleesat ta dinga kallonsa kafin tace "To da wannan shegen karen a gidan nan ne zan dinga zuwa kitchen inyi girki? Didn't you see the way the dog is being fierce at me?" Sai kuma ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da pillow tace "Ni wallahi bazan iya zama gidan nan da karen nan ba" Yayi mata wani kallon sama har kasa sannan ya juya ya fice daga dakin, breakfast ya kawo mata har dakin, ita dai taki kallonsa, sai da taga ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. Khaleesat was more than eager taga Monday yayi ta tafi school don gidan wasn't a comfort zone for her, gaba daya ji take kamar a ƙaya take ga boredom da ya isheta, gashi a tsorace take da karen gidan, duk da tun ranan Friday da ta ga karen ya tsorata ta da daddare throughout jiya da yau bata ga ko gilmawan sa ba, kamar yanda Ajay yayi instructing dinta in dai tayi girki sai ta ajiye ma Driver nasa abincin don iya su uku ne kawai a gidan babu wani worker, wannan yasa yau lahadi taji jiki wajen gyaran babban gidan tun daga upstairs har downstairs, she made sure she cleaned everywhere, haka ta gama aikin duk jikinta na ciwo saboda gajiya, tunda ta tafi daki wajen karfe dayan rana bata sake sakkowa ba sai kusan magrib shi ma don ta dafa ko taliya ne saboda driver, kamar munafuka ta sauko downstairs tana bin ko ina da kallo incase zata hango legend amma taga babu shi, da mamaki take kallon boxes dinta na can apartment dinta da wasu items tare da laptop and reading materials dinta, taɓe baki tayi ta karasa tana duba items din daya bayan daya, after some minutes duk ta kai su sama zuwa daki sannan ta dawo kasa ta nufi kitchen tana yi tana waige waigen ko zata ga legend don ita dai a tsorace take har ta shiga kitchen din ta kulle kofa, shopping ta gani birjik a kitchen island din, tana tafiya a hankali ta tafi gun ledojin, daya bayan daya ta dinga fiddo kayan shopping din, she made sure she arranged everything a kitchen din wanda zata jera a babban fridge duk ta zuba su ciki, cookies iri iri ta gani da kayan ciye ciye masu tsada, su ma duk ta ajiye su, bayan kusan minti talatin ta gama setting komai a mazaunin sa a kitchen din, ta zuba wasu bottled water cikin fridge, daga karshe taga ledan abinci biyu a kitchen din yayi masu order, she felt relieved don dama in don ta ita ne shayi kawai zata sha bazata dafa komai ba don ta gaji, ta dau leda daya ta bar ma driver daya ta juya ta fita daga kitchen din ta koma sama...... Khaleesat na zaune ita kadai a favourite spot din da suka saba zama da Sophie idan suka fito lectures, Safiyyah kuma taje amso masu snacks da wani frnd dinta ya masu order, it's been weeks now da suka yi resuming school don har sun fara preparing for quizzes, har Safiyyah ta karaso Khaleesat bata san ta karaso ba don tayi nisa tunanin da take, Safiyyah ta taɓe baki ta zauna gefenta tace "Kina nan kina aikin naki kenan" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai a hankali ta kalli Safiyyah, Safiyyah tace "Kawai ki dora ma kanki tunanin da bazai fisshe ki ba, ni dai ina gaya maki semester din karshe ne dai wannan in ba so kike ki samu matsala ba and you know what that means" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Even if it is once ai da sai yayi min reply yaji ko me zan ce masa Sophie, you know how painful it is mutum yayi ta ignoring messages dinka bayan duk yana gani...." Safiyyah ta kalleta ta zaro mata ido tace "Ke... Ke fa matar aure ce yanxu Khaleesat, bar ganin auren naki da Ajay a gantale haka, to reply din me kike son Housemate yayi maki? so kike ya biye ki ku fara chatting ko me? salon ma aga chatting din zargi ya shiga dama irin wannan gidan nasu gidan kananan zance don duk gidan sarauta gidan zance ne don haka gwara ma kar ya biye ki ya kama kansa wallahi, sannan fa shi ma yana can da matarsa, may be ma yayi move on suna can suna cin amarci tunda babu yanda ya iya an hanasa ke kinga he will just make the available the desirable, ke kuma kina nan kin damu kanki da tunani ji yanda kika rame don Allah kamar warce bata cin abinci, shi dama Housemate ana zaune lafiya ma ya share mutum balle an masa laifi? Ai kar ma ki saka ran zai bi ta kan message din ki, ashe har kin mance halinsa kenan" a hankali Khaleesat ta share hawayen da taji ya kawo idonta, Safiyyah tace "Shi kuma Ajayn ya fitar da shegen Legend din a gidan ko yana nan har yanxu? Ni rainin wayonsa ne ma yasa kika ga bana cewa zan je gidan don na lura ya karo sabon walakanci yanxu, kar wataran ya gaya min maganar banza in masa rashin kunya" Khaleesat ta taɓe baki tace "Ke ni fa sai mu yi kwana da kwanaki bamu hadu a gidan nan ba, kin tuna wani time da na taɓa zama gidan sanda Aymaan ya biyoni har apartment dina?" Safiyyah tace "Eh" Khaleesat tace "Toh yanda bama haduwa da shi wancan lokacin a gidan yanxu ma haka ne, although he is around amma sai mu yi many days bamu hadu ba tunda kinga da safe nake tahowa school kuma bana komawa gida sai yamma sosai, ko bani da lectures kinga sai na shigo school har Saturday saboda bana son zaman gidan kwata kwata, so bama haduwa gaskiya, aikin gidan ma na dena yi because he makes sure everywhere is clean, ko nace zan yi gyara gyara da asuba sai in ga ko ina neat, kinga yana gyarawa kenan" Safiyyah ta rike haɓa tana kallonta da mamaki, can tace "Tabb, to ku kuma haka naku salon auren yake kamar yanda ake yi a film? Ba ruwansa ma ko kina lafiya ko otherwise a matsayinsa na mijin ki? Ko kun mance mata da miji ne ke da shi?" Khaleesat tayi ma Safiyyah wani kallo sai kuma ta kauda kai, Safiyyah tayi shiru tana ta kallonta kamar dai tana son yin tambaya amma bata san ta yanda zata fara tambayar ba, bayan few seconds kawai tace "So you mean ba ku ma taɓa kwana daki daya ba kenan har yanxu da shi?" Khaleesat ta juya ta kalleta tace "Daki daya kamar ya? Saboda me za mu kwana daki daya?" Safiyyah ta zuba mata ido tana kallonta, Khaleesat ta kauda kai fuska daure tace "For what reason za mu kwana daki daya?" Safiyyah tayi mata kallon gefen ido kamar dai tayi shiru sai kuma dai tace "Kin fi ni sanin reason din ai" Khaleesat taki kallonta tace "Ban san wannan reason din ba" Safiyyah tayi er dariya, bayan kusan minti daya tace "No matter yanda aka yi auren dai mijin ki ne shi ki ji in gaya maki, in ma ke kika ki yarda ku kwana daki daya nasan kin san repercussion din hakan, ba ruwan Allah da yanda aka yi auren ko kuma abubuwan da suka janyo aka yi auren, aure dai aure ne koma yaya yake, yanxun nan sai ya kai ki wuta idan baki yi hankali ba" Khaleesat ta fara harhada kayan karatun ta without looking at Safiyyah cause she finds the conversation nasty in her ears, a takaice tace "Zan tafi gida since we are done with today's lecture....." Safiyyah dai kallonta kawai take, can ta ɗan yi murmushi bata sake cewa komai ba, har sai da Khaleesat ta mike zata bar wajen sannan Safiyyah tace "Yau kuma da wuri zaki koma gidan kenan? ke da kike jin kamar ki dawo kwana cikin makaranta tsabar rashin son zaman gidan?" A takaice Khaleesat tace "Ehh, na gaji ne yau, bacci zan je gida in yi... Sai gobe" Daga haka tayi wucewarta tana dialing number driver dinta don yana nan area din, Safiyyah dai ta bi ta da kallo tana murmushi a ranta ta fara tunanin banda dai abubuwan da suka faru wacce mace ce zata samu irin Ajay tayi ta claiming bata son sa? Ai sai dai shi yace baya so cause he gat everything, ilimin ne, kyan ne, asalin ne, wayewar ne, ko kuma dukiya? uwa uba ga sarauta, ai sai dai macen ta yaudari kanta tace bata so, although tasan ita dai Khaleesat da gaske take har cikin ranta ba lallai duk wannan qualities din su yi freaking dinta ba tunda ita ga wanda zuciyarta ke so.... Khaleesat ta dade bata ji haushin Safiyyah ba kamar irin wannan rana, she was really angry at her cause bata yi expecting irin wannan maganar daga gareta ba, ta yaya zata gaya mata haka ita da bata taɓa kallon Ajay a matsayin wanda za su yi wani abu wai shi aure tare ba, status dinta da shi will remain the way it is, ba wani aure a tsakaninsu, shima kuma a wajensa tasan irin kalan tunaninta yake yi, bazai taɓa kallonta a warce za su yi rayuwan aure ba, basu hango wani abu wai tarayyan aure between dem ba, har ta isa gida her mood was really spoilt, ta bude motar ta sauka tayi wucewarta cikin gidan, Allah ya so gobe Saturday ba ma ta da lectures balle taje school ta hadu da Sophie taji sabon takaici, ita da kullum ke cewa an ci amanar Housemate menene zai kai tunaninta zuwa irin wannan tunanin da tayi yau, what came over her to think that way? wato so take a ci amanar Housemate din da gaske kenan, tsaki Khaleesat tayi ta shiga cikin parlor, as usual babu kowa parlon tayi wucewarta sama zuwa daki, wanka tayi ta canza kaya tayi sallah tayi kwanciyarta, sai wajen biyar da rabi ta fita daga dakin zata tafi kitchen ta dora girki yanxu dai kwata kwata ta dena ganin Legend, tun da ta sauko downstairs take kallon wanda ta gani zaune cikin parlon har ta karaso inside of the parlor sannan ta gaishesa, ya juya ya kalleta greeting her also, Ajay dai na zaune parlon yana danna wayarsa fuskarsa babu yabo babu fallasa, sauke kanta tayi ta nufi kitchen, tana shiga kitchen din da few minutes sai ga Ajay ya shigo ta juya tana kallonsa ya hade rai yace "Ke baki da hankali ne da kika ga mutum a parlon baza ki koma sama to cover ur self up properly ba?" Ita dai bata ce komai ba tana dibar vegetables da zata yi amfani da shi wajen girki, ya juya ya fice daga kitchen din, kusan awa daya tayi a kitchen din tana girki don ba iya ita da Driver ta dora ma girkin ba har da Walid da ta gani a parlor, bayan ta gama ta fito har sannan Walid na parlon, Ajay ma na zaune and none of them is saying anything kamar kurame, shi Ajay wayarsa kawai yake dannawa at the same time yana operating din laptop dinsa dake gefe, shi kuma Walid kallon TV yake ya ƙishingiɗa kan 2 sitter, Khaleesat ta wuce sama Ajay ya bi ta da kallon gefen ido. Sai a sannan Ajay ya juya ya kalli Walid yace "Oxford din nan garin suka maido convocation din nasu na wannan shekaran kenan?" Kamar Walid bazai ce masa komai ba, sai kuma dai yace "How will that be possible?" Ajay yace "Da na ganka a nan ne nayi tunanin a nan kasar za su yi convocation din" Walid ya kallesa yace "However, su Aunty ma idan suka ga dama nan gidan za su sauka not England, cause babu inda aka ce an siya gidan nan da sunan just one or two persons...." Daga haka ya mike yaki jiran yaji me Ajay zai ce yayi wucewarsa sama ya tafi dakin da yake sauka idan ya zo gidan, wanda rabonsa da Maryland yayi 3 years yanxu, after a while Ajay ya mike ya tafi sama shi ma ya nufi bangarensa. Khaleesat ta idar da sallan magrib ta fito sanye da hijab dinta har kasa ta sauka downstairs zuwa kitchen zata debi abinci, tana shiga kitchen din taga an ci abincin an bar plate da mug din da aka sha Coffee a sink, tunda take gidan bata taɓa ganin an bar used utensils unwashed a kitchen ba, sai da ta fara wanke plate din ta goge inda aka yi littering da abinci sannan ta dau plate ta fara dibar wanda zata ci kenan aka bude kofar kitchen din ta juya, Walid ne ya shigo ya kulle kofar, ta sauke idonta ta kauda kai ta ci gaba da abinda take, yace "Akwai abincin ne?" Kai ta gyada masa without looking at him tace "Akwai...." Ya dau plate ya karasa har inda take tsaye ya tsaya yana kallonta yace "Can i have some of it?" Bata yi tunanin zai karaso har wajenta ba hakan ya ɗan sa ta daburce ta gyada masa kai da sauri tace "Ga abincin nan...." wanda ta fara zubawa a plate ya dau spoon ya diba ya kai baki yana gyada kai yana kallonta kamar me kirga kalamansa yace "Waow, you are a great cook, the meal taste delicious, did you learn catering? Are you a chef?" Ita dai sai kokarin matsawa take daga kusa da shi don dab da ita ya tsaya, bata yarda ta dago kai ba ta fara zuba wani abincin a plate with confusion, hannu ya kai ya rike plate din har hannun nasa na taɓa nata yace "John Hopkins kema kike na gan ki big gal" Ƙin cewa komai Khaleesat tayi tsabar shock, kawai bata ankara ba taga ya kai hannu chin dinta ya dago kanta yana kallon fuskarta yace "Hey I am asking you a question" Daburcewa tayi ta fara gyada masa kai alamar eh, sai kuma ta sakar masa plate din ta juya zata bar kitchen din yayi saurin rikota yace "Kee, are you alright? Ina maki tambaya zaki fita" Warce hannunta tayi da sauri ta fice daga kitchen din zuciyarta na bugawa, sama ta tafi tana waigen ko ya biyota don duk ya tsorata ta, tana shiga Bedroom dinta ta kulle kofar ta tafi gefen gado ta zauna with shock tana processing abinda ya faru. *Halysaah is 500 via 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 109 Wajen karfe goma Khaleesat na kwance daki duk da yunwan da take ji taki fita ta zuba abinci saboda fargaban haduwa da Walid, har sannan mamaki da shock da tsoro sun ki barin ta, she couldn't believe her self, bude kofar dakin taji anyi ta mike zaune da sauri tana kallon kofar gabanta na faduwa, ganin Ajay ne sai da ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, ta koma a hankali ta kwanta, ya tsaya daga bakin kofar yana kallonta yace "Have you dish the food for you self ko katti kawai kika yi ma girkin dama?" He asked that question because sau hudu yana ganin Walid na cin abinci daga sanda ta gama girkin zuwa yanxu, ta sauke idonta murya can kasa tace "My waist is aching me, bazan iya zuwa downstairs ba kuma" Yace "To wa zai je maki downstairs din? Ke tsohuwa ce da waist din ki zai maki ciwo" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, jin bai sake cewa komai ba ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, ta sauke idonta, juyawa yayi ya fita daga dakin ya kullo kofar, after almost 10 mins sai gashi ya dawo dakin da plate din abinci da bottle water, ko kallonta bai yi ba ya ajiye abincin a gaban mirror ya fita daga dakin, ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta tafi ta dau abincin cause she was very hungry, a nan dakin ta bar plate din bayan ta gama cin abincin gudun ta fita da plate zuwa kitchen ta sake haduwa da Walid, ta tafi bandaki ta wanke bakinta don tayi wanka tun sanda tayi isha'i sannan ta dawo, kofar dakin ta nufa tana kallon kofar wishing me makulli ne amma keyless door ne, and she don't know the Code, kawai ta kashe wutan dakin tayi addu'a ta kwanta tunani iri iri na yawo a ranta, a haka bacci ya dauketa. Ajay na zaune parlor yana danne dannen laptop har kusan karfe sha dayan dare, Walid ma na parlon yana kallon TV ba me cewa kowa komai cikinsu, daga karshe Walid ya kwanta kan 3 sitter ya dora handkerchief dinsa a fuska, har karfe sha biyu da rabi Ajay na parlon, daga karshe ya juya ya kalli Walid don for an hour now same position yake alamar yayi bacci tun daxu, mikewa Ajay yayi ya kashe TV din da wutan parlor ya dau laptop dinsa ya wuce sama, kofar dakin da Khaleesat take ciki ya bude ya shiga ya kunna wutan dakin yana kallon saman gadon, tana kwance ta rufe har kanta da duvet tana bacci, duk da ba frequently suke haduwa a gidan ba amma kusan duk dare idan ya gama abinda yake yi yakan zo dakin ya tsaya daga nan bakin kofa ya dubata, wani lkcn karfe dayan dare wani lokacin biyu, duk ya bude kofar kuma zai ganta kwance ta rufe har kanta tana bacci, kashe wutan dakin yayi ya fita ya jawo kofar ya rufe sannan ya nufi bangarensa. Cikin bacci Khaleesat taji ana kokarin sauke duvet din jikinta, ta bude ido da sauri ta rike duvet din gam ta yunkura ta mike zaune duk da bata ganin koma waye saboda duhun dakin cikin firgici tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Muryar Walid taji yace "C'mon, why do u have to close ur face while sleeping, do you want to suffocate ur self?" Sosai hankalinta ya tashi ta fara komawa baya tana rike da duvet dinta taki barin ya sauke daga jikinta tace "Don girman Allah ka fitar min a daki, me yasa zaka shigo min daki? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Yace "Hum, just to compliment you Halysaah, you've got a beautiful glowing skin and a fine body structure....." in hankalin Khaleesat yayi dubu ya tashi a wannan moment din, muryarta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri ka fita plss" Yace "C'mon, meye big deal don na shigo dakin ki? why are you acting like a bush girl warce bata waye ba, sai kace ba a abroad kika yi karatu ba?" Kunna wutan dake kusa da gadon yayi yanda zai dinga kallonta da kyau, da sauri ta fara kokarin komawa daya bangaren gadon tana gyara hularta da ya kusa cirewa daga kanta, ya fixgota ya hau kan gadon yana rike da ita speaking in a low tone yace "Hey listen to me Halysaah, stop acting like you don't know where i am headed, this is just between i and you, beside i will even be more active then him ur so called husband, if you don't co-operate now i promise even without ur co-operation i will get what i want wallahi, balle gwara kiyi co-operating yanxu kawai a wuce wajen, just once, after this I won't bother you again...." Khaleesat bata san sanda ta kwala kara ba tsabar yanda ta gigice da kalamansa ta gatsa masa cizo da karfi a hannu don har sannan yana rike da ita yana kokarin cire duvet din da taki sakewa, tsabar tashin hankali har wani zufa da zafi take ji duk da Ac dake kunne dakin, lokaci daya ya saketa bayan ta kurma ihun ya mike da sauri ya ciro wata karamar wuka a aljihunsa yana nunata da shi cikin kakkausar murya yace "I will deal with you, kuma na rantse da girman Allah kika ce zaki gaya masa sai na hallaka ki kuma babu abinda zai faru wallahi, kin dai ji na rantse, kuma i will definitely get what I want" Yana fadin haka ya kashe wutan jikin gadon da ya kunna ya nufi kofa da sauri ya fice daga dakin ya kullo kofar in a haste ya sauka downstairs kamar yasan reaction din da zata yi kenan shi yasa sai da yayi wanka ya canza kaya don kar ma dakin ya dau kamshin turarensa sanin how sensitive his step brother can be, Khaleesat kuwa bata fasa ihun da take ba cikin firgici da tashin hankali, bude kofar dakin aka yi lokaci daya aka kunna wutan dakin, ya nufeta da sauri yana kallonta yace "Me ya faru?" Sosai ta fashe da kuka tana sauke numfashi, har lkcin kuma tana rike da duvet din jikinta gam gashi duk ta hada zufa, bai san sanda ya zauna kusa da ita ba yace "Bakya ji na ne? What happened?" Cikin rawan murya tace "I had a dream" Da wani expression yace "Dream? What dream?" Taki cewa komai tana kuka tana sauke ajiyar zuciya, bin dakin ya fara yi da kallo, sai kuma ya kalleta yace "Didn't you pray before sleeping??" Cikin shesshekan kuka tace "Nayi" Jawo pillow dinta yayi kusa da ita yana kallonta yace "Kwanta...." Ta fashe masa da sabon kuka ta matso kusa da shi kamar zata shige jikinsa muryarta na rawa tace "Ni wallahi bazan iya kwanciya a dakin nan ba" ya dinga kallonta, sai kuma ya cire duvet din jikinta ya mike yace "Come down" Da sauri ta sauka daga kan gadon tana goge hawayen dake sauka idonta, rigar bacci purple ne jikinta ya ɗan wuce gwiwanta, Ajay dai ya kauda kansa daga kallonta yayi shirun kusan minti daya, ita dai tana tsaye kusa da shi tana zare ido, can ya juya ya kalleta yace "Mafarkin me kika yi?" She look so afraid and confused tace "Kamar na manta" Wani kallo ya watsa mata, ta fara wani sabon kukan, yace "Mu je" Da sauri ta nufi kofa yace "Ke, ina hijab din ki?" Ta dawo ta tafi ta dau hijab din sallanta ta saka, kofa ya nufa ta bi bayansa da sauri, ya jira ta fito sannan ya kashe wutan dakin, ko jiransa bata yi ba ta nufi bangarensa shi dai ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, zaune ya ganta kan kujera a parlor ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka, ya karasa har inda take zaune ya zauna, a tsorace ta dago tana komawa baya jin mutum kusa da ita, sai kuma ta fashe da kuka a hankali, yace "Ke, gaya min mafarkin me kika yi?" Cikin rawan murya tana kallonsa tace "Tsoro nake ji" Mikewa yayi yace "Ta shi" ta sauka daga kan kujeran yayi leading dinta har zuwa Bedroom dinsa, tana shiga dakin bata jira yace mata komai ba ta cire hijab dinta ta ajiye kan kujera ta tafi saman gadonsa, dai dai inda yake kwance kafin yaji ihunta ta tafi ta kwanta ta jawo duvet dinsa ta rufa jikinta har kanta da shi, ya ɗan hade rai ya kauda kai, bayan few seconds kawai ya juya ya fita daga dakin ya kullo kofar, Ya tafi kan 3 seater dake parlonsa ya kwanta har sannan fuskarsa a daure, duk da kamshin turarensa da ya cika Khaleesat ta ko ina both kan gadon, pillonsa da bargonsa haka bacci me nauyi ya dauketa. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 110 Da asuba Ajay ya shiga Bedroom dinsa zai dau darduma ya kunna wutan dakin mara haske sosai ya juya yana kallonta, ya kusa seconds talatin tsaye yana kallonta, can dai ya karasa har kusa da ita ya duka to be sure of what he is seeing, ya kara kunna wutan bedside lamp still looking at her, da mamaki ya kai hannu yayi raising gashinta yana feeling texture din, can ya cire hulan kanta da kadan ya rage ya fita daga kan nata yana kallon gashin gaba dayansa, lokaci daya Khaleesat ta bude ido jin hannu a gashinta tayi wani ƙara tana kokarin mikewa zaunewa tana kallonsa a tsorace tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Sai kuma ta dafe kirjinta ta jingina da gado feeling so much relieve ganin shi ne, tayi saurin daukar hulanta ta saka, da mamaki yace "Ke?? ƙarin gashi ne wannan kika yi? Are you okay??" Ta wani kallesa sai kuma ta koma ta kwanta kan pillow taki cewa komai, ya hade rai yace "Ba magana nake maki ba? A gidan nan zaki yi ƙarin gashi ko baki da hankali ne? Take that off immediately" On a serious note ya kare maganar fuskarsa daure, ta daga idanuwanta ta kallesa bata dai ce komai ba, ya ɗaka mata tsawa yace "Am i making any sense?" Mikewa zaune tayi tace "Naji" Daga haka ta sauka daga saman gadon ta nufi bandakin dake dakin, ya bi ta da kallon mamaki don da gaske yayi zaton saka gashin tayi kuma har ya zargi Safiyyah ce ta bata gashin ta saka, ya dau pray mat dinsa ya fice daga dakin.... Karfe tara saura Ajay ya shiga Bedroom dinsa cause he was expecting her to come out of the room and go to her room tun da asuba amma yaga bata fito ba, bacci ya sameta tana yi comfortably ta nannade cikin Farin duvet dinsa ba ma ta da alamar tashi anytime soon, ya hade rai yace "Kee" A hankali ta bude ido ta kallesa da sleepy eyes, yace "Garin ki bai waye bane har yanxu? Zo ki fitar min a daki malama" Miƙa tayi tana kallon agogon dake dakin, sai kuma ta mike zaune tana sosa kanta, ya bude mata kofar dakin yana nuna mata hanyar fita yace "Come and get out" turo baki tayi ta jawo hijab dinta ta saka sannan ta sauka daga kan gadon, ta gefensa ta bi ta fita daga dakin ya bi ta da kallo, sai bayan da ta fito zuwa parlonsa jikinta yayi sanyi tuno incident din jiya da daddare, kasa ci gaba da tafiya tayi ta juya a hankali ta kallesa taga kallonta yake, ta marairaice tace "Ni fa dakin tsoro yake bani yanxu ban san me yasa ba" Ya mata wani kallo yace "Kina saka gashin kanti ya baza ki dinga mafarki kina yi ma mutane ihu cikin dare ba, c'mon go to ur room my frnd, what do you mean? Ni zaki yi inconveniencing a nan" Juyawa tayi ta nufi kofar fita part din jiki a sanyaye, cikin rashin kuzari ta dinga tafiya gabanta na faduwa, tana isa corridor ta tsaya tana tunanin abun yi, gaba daya ta gama tsorata da Walid da lamarinsa ga kuma wukar da ya nuna mata wai zai kasheta, after a minute sai ga Ajay ya fito, tana jin Footsteps dinsa ta ci gaba da tafiya tana wasa da fingers dinta shi dai yana biye da ita a baya, dai dai nan sai ga Walid ya fito daga dakinsa rike da akwatinsa karami yana sanye da kananun kaya sai baza kamshi yake, sau daya ya kallesu ya dauke kai ba tare da ya kalli Ajay ba yace "I am leaving for England, na gama abinda zan yi a Maryland" Ajay yace "Safe trip" Walid ya daga kai ya kalli Khaleesat da tayi saurin sauke idonta gabanta na mugun faduwa har sannan tana wasa da hijab dinta, Gaisheta yayi yace "Ina kwana Aunty" cike da karfin hali ta mayar masa da gaisuwan tace "Ina kwana" yace "Toh sai wani lokaci kuma, ni na tafi...." Khaleesat ta gyada kai kamar kadangariya tace "Allah ya kiyaye hanya" Yace "Ameen" Daga haka ya sauka downstairs, wani boyayyen ajiyar zuciya ta sauke ta nufi kofar dakin da take ciki ta bude ta shiga tana kallon Ajay da ya bi ta da kallo, kulle kofar dakin tayi. That same day da yamma Ajay na zaune parlor yana waya da Hajiya Shafa'atu wanda ba don komai ta kirasa ba sai don Khaleesat don babu wani bond na communication tsakaninsa da ita tunda yawanci a Turai take zama da Mai gidanta da yaranta kuma tana jimawa bata shigo Nigeria ba, mikewa yayi ya nufi kitchen yace "Tana kitchen bari in Kai mata wayar" Yana shiga kitchen din Khaleesat dake yanka Salad ta juya ta kallesa, ya karasa kusa da ita ya yagi babban tissue dake kitchen din ya daure fuska ya mika mata alamar ta goge hannunta bazata taɓa wayarsa haka ba, taɓe baki tayi ta amshi tissue din ta goge hannunta sannan ya mika mata wayar, yana tsaye har suka gama gaisawa da Hajiya Shafa'atu, duka bai wuce 2 minutes ba sannan ya karbi wayarsa ya fice daga kitchen din, Hajiya Shafa'atu tace "To yaushe za ku shiga England din naji satin nan da za a shiga ne convocation din ko? ni dai ba lallai ma in je ba don ina da wani babban uxuri, but idan na samu sarari sai in iya zuwan" Ajay yace "In sha Allah ranan zan je ni" Hajiya Shafa'atu tace "Kai kadai zaka je?" Yace "Eh in sha Allah" Hajiya Shafa'atu tace "Jiddan bata da Visa halan? Ai da kayi mata all this long while da aka dauka da komawar ku Amurka" Ajay yace "An mata ai" Hajiya Shafa'atu tace "To shi ne zaka je kai kadai kuma? A'a hakan bai yi ba Yarima, Ai yana da kyau ka kai ta duk ta hadu da yan uwanka su santa ta san su don nasan za su je ko ba duka ba, kuma ba kowa yasan ta ba kaga wannan wata dama ne da za tasan dangin ka, going without her isn't an option" Ajay dai yayi shiru, but to bring an end to the conversation sai kawai yace "To in sha Allah Mama, za mu je tare" ya fadi hakan ne ba don zai je da ita din ba don babu wannan niyyar tare da shi, a haka suka yi sallama da Hajiya Shafa'atu ya ajiye wayarsa, banda ma rashin zuwansa zai zama wani issue din shi me ma zai je yi wajen convocation din Hadiyah...... Karfe goma saura na dare Khaleesat ta gama karatun da take don ta gaji da karatun, ta kashe laptop dinta tayi plugging dinsa sannan ta dau wayarta don dubawa ko Umma tayi mata reply din message din da tayi mata tun da rana amma taga bata ma hau WhatsApp din ba, Sophie tayi ma reply din maganar da tayi mata few hours ago, sai kuma taga Ajay yayi updating status tun daxu, once a while yake uploading status or may be ita ce bata lura da ko yayi status din ko bai yi ba, ta bude status din nasa taga hoton Inteesar ne yana wishing dinta happy birthday, tayi ta kallon hoton da kamar ta masa reply tace ya tura mata numberta kawai dai ta fasa, sai kuma taga status din Jay, sai da gabanta ya fadi don it's been a while bata ga status dinsa ba, ta bude status din tana kallon IV da yasa na Convocation din Hadiyah that is taking place in Oxfordshire England on Tuesday, caption dinsa ne yasa taji hawaye ya kawo idonta and she wished bata ma bude status din ba, ajiye wayar tayi ta kashe wutan dakin ta kwanta tana jin hawaye me zafi na zuba idonta. Wajen 12 na dare Ajay ya gama abinda yake yi a laptop dinsa ya kashe wutan parlon ya wuce sama, har ya nufi part dinsa sai kuma ya dawo ya bude kofar dakin da Khaleesat take, Flash din wayarsa ya kunna yana haska ta, bacci take amma bata rufe har fuskarta da bargo ba kamar yanda ta saba yi, ya karasa kusa da ita har sannan yana haska ta da fitilar wayarsa ya kai hannu ya cire hulan kanta, gashin da yace ta cire ya gani still a kanta, ta kurma wani ihu a mugun tsorace jin hannu a kanta, ta fara kokarin tashi zata bar wajen jikinta na rawa kuma bata fasa ihun da take ba tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Yayi saurin rikota yace "Ke, meye haka?" hannunsa ta riko bayan da taji muryarsa ta fashe da kuka sosai har lkcn jikinta na rawa tana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Gaba daya ta gigice har zufa ya keto mata a goshi, yayi saurin zaunawa kusa da ita bayan ya ajiye wayarsa ya kunna fitilar gefen gado yana kallonta yace "Are you alright?" Kalle kallen dakin ta ke yi har sannan tsoro ne kwance karara a fuskarta ga wani heaving da kirjinta yake ta matsa kusa da shi, shi dai kallonta kawai yake, har sai da ta yi calm down after almost 2 minutes, and everywhere was very silent, a hankali ta daga kai tana kallonsa kamar zata fara sabon kuka tace "Me yasa zaka bani tsoro? What are you looking for?" Ya hade rai yace "What did I tell you about the hair?" Ta marairaice tace "Which hair? Ni fa gashi na ne" Ya mata wani kallo yace "Do i look like i am joking with you?" Bai jira me zata ce ba ya kai hannu kan gashin yana taɓa soft scalp dinta, kauda kanta tayi da sauri tana komawa baya daga kusa da shi ta hade rai tana masa wani kallo tace "Meye haka? Saboda zan yi karyan gashina?" She could see the startle in his eyes yana kallon gashin, sai kuma ya sauke idonsa bai sake cewa komai ba kawai ya mike ya dau wayarsa ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, ta tura baki ta dau hularta ta mayar sannan ta kashe wutan bedside lamp da ya kunna har sannan tana jin kirjinta bai dawo dai dai ba. Washegari Lahadi Khaleesat ta gama duk abinda zata yi ta shirya, tun karfe takwas ta tura ma driver din da ke kai ta school text message tace masa karfe sha daya zata fita, tana rike da handbag dinta ta sauko downstairs tana ma Ajay kallon gefen ido, yayi ending call din da yake ya juya ya kalleta babu yabo babu fallasa yace "Ina zaki?" Ba tare da ta kallesa ba tana ci gaba da tafiyarta zuwa kofar fita daga parlon tace "School" Ya mata wani kallo yace "School on a Sunday? Are you sick in the head?" Ta hade rai ta tsaya sannan ta juya ta kallesa tace "Reading material dina da na manta ranan Friday zan dauko sbda gobe muna da Course din and I need to study before the lectures" Ajay ya mike yace "Mu je school din since you are a liar" Wani kallo ta dinga masa don gidansu Safiyyah take son zuwa, ya hade rai yace "Baki ji me nace bane?" A takaice tace "Bazan je ba kuma, na fasa" Tana fadin haka ta juya zata koma sama ya mata wani tsawa yace "Keee na fara wasa da ke ne? Zo ki fita kafin ki sha mari" Tsayawa tayi sai kuma ta juyo, kamar zata fashe da kuka ta nufi kofa ta fice daga parlon ya bi bayanta, makullin motar ya amsa hannun driver dake jiranta, fuskarta a daure ta shiga motar, har suka bar gidan bata kalli direction dinsa ba, bayan sun isa school yayi parking yace "Go and get the material ki dawo" Rungume hannunta tayi without looking at him taki cewa komai, Yace "Are you daft?" A takaice tace "Ba wani material, kuma ni ba school zan zo ba gidansu Sophie zan je za mu yi karatu tare a can" Kallonta ya dinga yi, ita kuwa taki kallonsa, kamar zata yi kuka tace "Bayan kace kar ta zo inda nake ni kuma sai ka dinga hanani zuwa wajenta bayan tare mu ke karatun mu during the weekends" Kuka ta fara yi ta rufe fuskarta da gyalen jikinta, shi dai har sannan Kallonta yake, can ya tada motarsa duk tunaninta zai yi considering kukanta ya kai ta gidansu su Safiyyah amma taga ya dau hanyar gida direct, wani mugun haushinsa ne ya cika ranta tuni ta dena kukan da take ta daure fuska, har suka isa gida yayi parking bai kalleta ba, ta bude motar ta fice daga cikin motar ta nufi cikin gidan kamar zata tashi sama, har dare bata sauko downstairs ba ranan balle ta nemi abinda zata ci, shi ma ya kyaleta tunda ba cikinsa bane yayi ma Driver order din abinci, shi kuma ya hada salad for himself for dinner. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* ur evidence via 07087865788 HALYSAAH PAGE 111 Ajay na kallon football wajen karfe sha dayan dare kiran Mai martaba ya shigo wayarsa ya rage volume din TV din ya sauke kafafuwansa kasa daga kan kujera sannan yayi picking call din, cikin ladabi ya gaida Sarki, bayan sun gaisa sarki ya tambayesa Khaleesat, yace "Tayi bacci ranka shi dade" Sarki yace "Ohk, goben za ku tafi UK for Hadiyah's Convocation which is on Tuesday?" Ajay yayi shiru, can yace "I thought Wednesday ne ranka shi dade...." Mai martaba yace "A'a, Jawwad din bai tura maka Invitation din bane?" Duk da bai tura masa ba Ajay yace "Ya tura, ban kula bane da date din" Mai martaba yace "It's Tuesday not Wednesday" Ajay yace "Toh Allah ya kai mu lafiya ranka shi dade, nasan ba lallai ka samu daman karasowa ba ko?" Mai martaba yace "Za a wakilce ni, beside Hajja ma gobe za su tashi zuwa England din in sha Allah, Kai ma ya kamata kai da matar ka should leave tomorrow ba sai ranan talatar ba" Ajay yayi shiru at first, sai kuma a hankali yace "Abba i think ba sai na je da ita ba, she will stay with her friend kafin in dawo" Mai martaba yace "Ko saboda me?" Shiru Ajay yayi, Mai martaba yace "To ku je tare, she will get to meet most of ur relatives da basu san ta ba, there is no point leaving her behind shi yasa nasa ayi mata Visa" Ajay ya sauke idonsa yace "Toh Abba, we will go together in sha Allah" Mai martaba yace "Good, Walid ma tun shekaranjiya ya tafi England din" Ajay yace "Ehh he was here yesterday, amma ya tafi yau" Mai martaba yace "Really, America ya tafi dama?' Ajay yace "Eh nan ya zo" Mai martaba yace "Wani irin tafiya ne wannan yayi? Shi da zai tafi England that is just 7 hours from Nigeria me ya kai sa America tafiyar kusan awa sha shidda?" Ajay yace "May be he have something to accomplish here, but ya tafi England din daxu da safe" Mai martaba yace "Ohk then, take care" Ajay yayi masa sallama sannan Mai martaba ya katse wayar, ajiye wayar yayi ya jinginar da kansa jikin kujera yana nazarin ta yanda zai fara tafiya England da Khaleesat, shi ma ba da son ransa zai je ba balle ya wani je da ita, mikewa yayi kawai ya kashe kayan kallon ya wuce sama. Safiyyah da ta rike haɓa tana kallon Khaleesat da mamaki tace "To hakan yana nufin kishi yake da ni kenan ko me? Banda haka me yasa zai hanaki zuwa wajena bayan tare ya gan mu? Ji min mutum, Ko don saboda yasan ni Team Housemate ce? To dole ne sai na goyi bayan cin amanar da yayi yake nufi ko me? Ni dama tun asali kowa yasan Housemate nake yi shine nawa, kuma bazan taɓa canza ra'ayina ba, har gobe bazan dena cewa ba a kyauta ma Housemate ba an ci amanarsa an cucesa, shekaranjiya ma naga ya saka status wai amaryarsa zata yi convocation a Oxford, caption dinsa ne yasa jikina kuma yayi sanyi qlau" Khaleesat ta daga ido tana kallonta, Safiyyah ta taɓe baki tace "Ko meye na wani sa wife dinsa a caption bayan kowa yasan wife dinsa ce ba sai ya gaya mana ba, ni dai kaddai fa ace har yayi move on ya bar ni nan da jiye masa takaici kullum ina babatu, su fa maza ba tabbas gare su ba, zuciyarsu ba shi da tabbas yanxun nan sai su canza in suka samu wata daban, tun da naga ya sa kalmar wife din nan a status jikina yayi sanyiiii, kinga alamar ya dirji amarcinsa yanda ya kamata kenan har da referring dinta to as his wife a status dinsa, to ai shikenan" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba tana jin zuciyarta na mata zafi, Safiyyah ta taɓe baki tace "Duk da dai shi ma Ajay din ba mutumin banza bane mutum ne me shegen class da personalities masu kyau, kuma dama can yana burgeni yanda baya daukan wargi yanxun nan kana raina masa hankali zai kai maka naushi ya hada maka jini da majina, ba irin mijin Surayyah da Housemate ba masu ba namiji ɗan uwansu hakuri, tun daga nan suka sire min wallahi naga inaaa ba gwarzaye bane" Khaleesat ta kalli wayarta jin shigowar sako, sai kuma ta kalli Safiyyah a hankali tace "My driver is around Sophie, sai gobe" Safiyyah tace "Ni dai ki kwantar da hankalinki ki dena damun kanki wallahi, tun da Allah yayi Housemate ba mijinki bane don gashi can har ya rungume er matarsa to kema a gaskiya zan baki shawara kiyi hakuri ki fara kula mijinki duk da ɗan rainin hankali ne shi amma to ya za ki yi? Nasan shi ma wallahi daurewa kawai yake yana pretending amma ya gama macewa a kanki, yana zaune gida daya dake yana kallon ki matsayin halaliyarsa da wannan shape din naki da glowing skin har ya isa yace baya jin komai a ransa? Ai sai dai ya yaudari kansa wallahi, kawai daurewa za ku yi ku sauke hakkin juna a wuce wajen" Mikewa Khaleesat tayi without answering her fuskarta daure ta dau jakarta tace "Bani textbook dina zan tafi gida" Safiyyah tayi er dariya tace "Ranan da zai nuna maki ke halaliyarsa ce may be you will come back to ur senses that day, bar ganin yana kyaleki, ba dai namiji bane? wataran ko yace zai kyaleki bazai iya ba a sannan ne zaki dawo hankalin ki" Takaici yasa Khaleesat ta juya kawai tayi tafiyarta ta bar wajen, cikin bacin rai ta nufi inda driver ke parking yana jiranta. Khaleesat na isa gun motar ta bude back seat zata shiga, still tayi tana kallonsa, yana zaune driver seat ya saka Black glasses irin no respect din nan yana kallon gabansa kamar bai san ta bude motar ba, ta ɗan taɓe baki ta rufe back seat din ta bude front seat ta shiga motar, Without looking at him kamar ana tilasta ta tace "Good evening" Bata ji ya amsa ba ya ja motar suka bar wajen, ba hanyar gida taga ga nufa da ita ba, ita dai tana ta kallon hanya wondering where he is taking her to, sai da suka yi tafiyar kusan awa daya sannan yayi parking a wani babban Mall, ya kashe motar ya sauka, ganin bata sauko ba yace "Don't waste my time" Bude motar tayi fuskarta babu walwala ta sauka, yana gaba tana biye da shi suka shiga wajen, Abayoyi masu tsadan gaske da dogayen riguna ta dinga gani, ita dai tana biye da shi a baya, without looking at her yace "Pick the ones u need" Ta daga kai ta kallesa, yana duba agogon wrist dinsa yace "Do not waste my time" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta daga wani Abaya da take ta kallo tun da suka shigo wajen, tana ganin price dinsa bata san sanda ta mayar da sauri ba, taga ya dau Abayan yana dubawa, ita dai kallonsa kawai take, ya duba size din, daga haka bai sake bin ta kanta ba ya ci gaba da duba Abaya da tsadaddun dogayen riguna yana daukan wanda yaga yayi kyau, sai da ya dau riguna biyar duk masu shegun tsada a wajen, don mamaki ma abun ya bata, yayi payment suka fita wajen ya shiga wajen takalma da jakunkuna designers, ta buda ido sosai tana kallonsa, nan ma duk shi ya zabar mata kala uku uku har tayi mamakin ta yaya yasan size din takalminta ga riga ma da ya siya yasan size dinta, sosai jikinta yayi sanyi ganin prices din items din da yake dauka ba na wasa bane, bayan yayi payment suka fita daga wajen takalman kuma duk shi ke rike da kwalayen da aka zuba masu kayan, ta wani zaro ido ganin wajen designers jewelries zai shiga, ita dai a hankali take tafiya tana bin sa a baya, nan ma set din jewelries lafiyayyu uku ya daukar mata ita dai tana ta kallon ikon Allah, taga ya kara mata da zobuna biyu duk designers, sai wristwatch, zoben ne ma ya bata ta gwada without looking at her, daga nan ya biya kudaden suka fita daga wajen, inda ake siyar da hair accessories irin na turawa ya gani ya shiga wajen tana dai biye da shi cikin sanyin jiki, hadaddun ribbons din gashi ya siya mata iri iri bayan ya biya suka bar wajen sannan suka fita babban Mall din gaba daya, she don't even want to start calculating the amount he spent in just this shopping cause the money was huge especially when converted to Naira, millions masu dama kenan fa in anyi lissafi, bayan mota ya bude ya ajiye kwalayen kayan hannunsa sannan ya bude driver seat ya shiga, ita ma ta shiga gaban motar ta kulle, sae da suka kusa gida after almost an hour and 15 mins ride sannan ya tsaya wani eatry ya siya abinci takeaway biyu, daga nan kuma suka wuce gida wajen karfe bakwai na dare.... A nan parlor Ajay ya bar mata kayan a takaice yace "Get ready za mu yi tafiya gobe karfe biyar na asuba, iya wa ennan kayan zaki tafi da" Yana kai wa nan ya wuce sama ta bi sa da kallo, a hankali ta dau package din kayan gaba daya ta wuce sama ta kai daki, kara fitowa da kayan daya bayan daya ta dinga yi tana duba su, ya subhanallah... they were soo beautiful and unique, the designer bags and shoes where more than gorgeous, har cikin ranta suka yi mata kyau sosai, gashi ya iya zabe ya ma fi wata macen iya zaban kaya, ta gwada takalman taga kamar don kafanta aka halitto su, ta zaune gefen gado ta fito da jewelries din su ma tana duba su, they were screaming nothing but luxury, ta gwada 2 rings din dake ta kyalli ta ɗan yi murmushi sai kuma murmushin yayi fading daga fuskarta ta cire su a hankali ta ajiye bayan ta tuna zoben da Housemate dinta ya siya maya, lokaci daya duk mood dinta ya canza, ɗan farin cikin kayayyakin da take yi yayi disappearing at once daga ran ta, tafi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike a hankali ta goge hawayen dake makale idonta ta nufi banɗaki zata yi alwala, sae da tayi sallan magrib sannan ta fita daga dakin, ta jima tsaye corridor as if contemplating on what she is about to do, at the end kawai ta karasa ɓangarensa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta shiga kamar munafuka, yana zaune parlor ta samesa yana duba wayarsa, taki barin su hada ido ta tsaya jikin kujera a hankali tace "Thank you so much for the wears, Allah ya kara budi" Bai daga kai ya kalleta ba, bayan few seconds taji yace "Thank God instead" Still not looking at him tace "Okay" Daga haka ta juya ta fita daga parlon ta kullo masa kofa, sai bayan da ta koma daki ta fara tunanin kaddai fa convocation din Hadiyah za su je gobe, sosai gabanta ya fadi bayan wannan tunanin ya zo mata rai, lokaci daya jikinta yayi mugun sanyi taji ƙafafuwanta sun mata nauyi sun ma kasa ci gaba da daukan ta, anya zata amince ta bi sa kuwa? da kyar ta karasa edge din gadon dakin ta zauna kamar warce ruwa ya cinye tunani iri iri na yawo a ranta, after some minutes ta jawo wayarta cikin sanyin jiki zata kira Safiyyah ta gaya mata. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 112 Karfe hudu dai dai na asuba Ajay ya bude kofar dakin da Khaleesat take ya kunna wutan dakin yana kallonta, bacci take ta rufe har kanta da Duvet, ya karasa kusa da gadon ya sauke duvet din yace "Kee" firgit ta bude ido ta mike zaune da sauri tana komawa baya, sai kuma ta fara duba hulanta a kan gadon zata rufe gashinta, juyawa yayi ya fita daga dakin, ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe hudu da minti biyu, ajiye wayar tayi ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki.... Kafin karfe hudu da minti hamsin Khaleesat har ta gama shiryawa dama tun daren jiya ta hada duk sabbin kayan da ya siya mata a box dinta ta shirya, tana tsaye gaban madubi tayi oiling dogon gashinta tana combing dinsa zata daure da daya daga ribbons din da ya siya mata jiya, sai kallon baƙin gashin nata take ganin kamar ya kara yawa ma, banda sheki babu abinda gashin yake, bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri ta kalli kofar tana daure tulin gashin nata waje daya cikin hanzari, kallo daya yayi ma gashin yace "Ke Malama you are wasting my time, ko bakya duba agogo ne" Ta ɗan turo baki ta dauke kanta tace "Ni sai nayi sallah tukunna" Tana fadin haka ta ci gaba da abinda take, can ta juya ta kalli direction din kofar taga ya bar wajen, biyar da kusan minti goma ta fito daga dakin da box dinta da handbag ta sauka downstairs, high waisted palazzo ta saka with matching top sai karamin veil dinta da handbag tayi kyau sosai ba kadan ba duk da babu abinda ta shafa a fuskarta sai eye pencil da ta sa a idonta, yana zaune parlor alamar ita yake jira, jin footstep dinta ya juya ya kalleta sai kuma ya dauke kai, kara kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma dai ya fasa ya mike ya nufi kofar parlon ta bi bayansa tana jan trolley dinta, driver na tsaye jikin mota yana jiransu, yana hangota ya tafi ya amshi box din hannunta sannan ya bude mata back seat ta shiga bayan sun gaisa da shi, kallon Ajay dake zaune gaban motar tayi, murya can kasa tace "Good morning" Bai ce komai ba, hakan yasa tayi tunanin bai ji ba ta sake gaishesa a takaice yace "Same" Wani kallo tayi masa ta dauke kai, driver ya shigo motar ya tada suka bar gidan.... Karfe biyu saura suka sauka Ingila Ajay yayi masu order din Indrive da zai kai su har gida, sai bin sa da wani kallo take don he is not even helping with her box, iyaka hand luggage dinsa kawai ya dauka, driver din motar ya dau akwatin ya sa a booth ta bude motar ta shiga don tuni Ajay ya shiga kamar ba tare suke ba, Suna isa gida Khaleesat dai ta tsaya bakin apartment din da taga Ajay ya sa driver ya ajiye akwatin ta, ya gama wayar da yake sannan ya danna bell din apartment din, not long after aka bude kofar apartment din, step sis dinsa Baby ce ta bude kofar tana ganinsa ta rungumesa tace "Oyoyo Yaya...." Yace "How are you?" Tace "Am fine, welcome" Juyawa tayi ta kalli Khaleesat, ya dau box dinta ya mika mata yace "Can't you greet?" Baby tace "Ina wuni" Daga haka ta amshi akwatin Khaleesat ta shiga ciki, ya juya ya kalli Khaleesat dake rakube gefe daya bayan ta amsa gaisuwar Baby, ya hade rai yace "Baza ki shiga ba Malama" Shiga parlon tayi sannan ya bi bayanta ta cire takalmanta nan bakin kofa, Aunty ce zaune parlor sai Ummi uwar Hadiyah da Gimbiya Firdausi, Mami ma na zaune parlon da Hajiya Nafisa, Khaleesat sai da gabanta ya fadi sosai ganinsu gaba daya, duk suka daga kai suna kallon ita da Ajay, kasan carpet ta duka a hankali ta gaishesu tana kallonsu gaba daya, Ajay ya zauna kan kujera ba tare da ya yarda ya hada ido da su ba ya gaishesu shi ma, just Hajiya Nafisa da Ummi sai Gimbiya Firdausi ne suka amsa gaisuwansa babu yabo babu fallasa, Mami dai ko kallon inda suke bata yi ba, ita kuwa Khaleesat dama babu wanda ya bi ta kanta suka ci gaba da labarin da suke a parlon, ko ya hanya babu wanda ya tambaye su, jikin Khaleesat yayi sanyi sosai ta daga kai ta kalli Ajay dake danna wayarsa kawai, bude kofar parlon aka yi sai ga Jay ya shigo yana gyara face cap dinsa, Khaleesat dake durkushe kan carpet bata san sanda ta karasa zaunawa a kan Carpet din ba bayan sun hada ido da shi, within few seconds ya dauke idonsa daga nata, ita kuwa bata fasa bin sa da kallo ba ko kiftawar kirki bata yi, Ajay dai bai yarda ya dago kansa ba tunda ya lura Jay ne ya shigo parlon wayarsa kawai yake ta dannawa, a hankali Khaleesat ta gaida Jay har sannan tana kallonsa, Jay ya zauna without looking at her yace "Lafiya lau, sannu da zuwa" Mami na kallonsa tace "Baka zo kayi breakfast ba yau Jawwad and ur phone isn't reachable" Yace "A restaurant nayi" Mami tace "To Lunch fa?" Yace "Sai anjima" Baby ce ta shigo parlon rike da wayar Aunty ta nufeta tace "Momy u have a call" Aunty ta amshi wayar, Jay na kallon Baby ya nuna mata Khaleesat yace "Take her upstairs Baby" Baby ta kalli Khaleesat tace "Ok let go" Khaleesat ta sauke idonta ta mike ta bi bayan Baby da ta kai ta sama zuwa dakin da su Hadiyah suke, Hadiyah na kwance kan gado sai Maryam da Khadijah sisters din Walid, da Shahuda yarinyar Gimbiya firdausi ta biyu, sai Iklima yarinyar Hajiyah A'isha, ga kuma Bilkisu yarinya Hajiya Sumayya gaba dayansu cousins ne a dakin, kuma duk Shahuda ce babba sai Maryam Kanwar Walid, duk suka juya suna kallon Khaleesat kamar sun ga Alien ta shigo, ita kuwa ji tayi kamar an saka mata chain a kafa tsabar yanda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ganin zuka zukan matan dake dakin gashi duk sun zubo mata ido suna kallonta daga sama har kasa, tayi karfin halin karasawa cikin dakin ta zauna kasan carpet ta gaishesu gaba daya, Hadiyah dai sai kallonta take a walakance kamar taga bola, Shahuda na yatsine fuska ta kalli Baby tace "Wacece wannan kuma Baby kika shigo mana da ita?" Baby ta taɓe baki ta karyar da kai tace "I think Ya Ajay's wife, yanxu suka zo" Shahuda ta mike zaune a hankali daga kwancen da take tana kare ma Khaleesat kallo daga sama har kasa, can tace "Dama wannan ce matar tasa? Ikon Allah, ashe zabiya ce" Tsaki Hadiyah ta ja tace "Don Allah mu ci gaba da maganar da muke, what were we even saying before we were interrupted?" Maryam na kallon Baby fuska daure tace "To ke uwar wa yace ki kawo mana ita nan? Duk dakunan dake sama ki rasa inda zaki shigo da ita sai wannan? Ko baki da kai ne? Dama akwatin ta ne wancan kika shigo mana da shi daki?" Baby ta bude ido ta langwabe kai tace "Ya Jawwad ne fa ya ce in kawo ta Aunty" Hadiyah ta mike zaune jin abinda Baby tace, fuska a murtuke tana kallonta tace "Yace ki kawo ta ina? Ina kika gansa yace ki kawo ta nan, yaushe ya zo? Dalla dau akwatin can ki fitar mana da shi daga nan, kinga nan yayi kama da inda za a kawo bare" Ita dai Khaleesat kallon direction daban take babu ko kiftawan kirki tana jin duk abinda suke cewa, Iklima ta juya tana mata wani matsiyacin kallo tace "Keee duk nan da kike gani jinin sarauta ne babu wani bare, babu ordinary blood don haka can you kindly get out of here? They are other rooms ba wannan kadai bane daki a gidan nan, ko kuma ki tafi Garage dama babu komai a ciki...." Khadijah tace "Can you imagine don rainin wayo ma wani wajen daban take kallo ana mata magana ko er uban wacece ita oho, bari ki ji duk nan babu sa'an ki wallahi, mu ba class din ki bane ta ko ina, don haka get out of this room" Baby na kallon Khaleesat tace "Sun ce ki tafi wani dakin you are not welcome in their midst" Mikewa Khaleesat tayi a hankali bata dai ce komai ba, Baby ta kalli yayyin nata tace "Ko in kai ta dakin Granny kawai?" Shahuda ta jefa mata wani harara tace "Are you stupid? What is Granny's relationship with her da zaki kai ta dakinta? Ordinary person kamar ta zaki kai ta dakin Granny ko baki da kai ne, pls take her out before i loose my temper" Baby tace "Oh ohk, bari in kai ta dakin da ku ka ajiye boxes din ku to" Daga haka ta dau akwatin ta nufi kofa Khaleesat na biye da ita, Hadiyah ta bi ta da wani matsiyacin kallo kamar yanda Shahuda ma ta bi ta da kallon tsana don mutuwa ne kawai bata yi akan son Junaid ba amma daga karshe wai Khaleesat ta samesa a sama kusan a banza ba wani wahala tana er matsiyata da ita shine zata zama matar ɗan sarki me jiran Gado, Iklima ta rike haɓa tace "Dama ita ce Ya Jawwad ya so ya aura ya hadata da ke Hadiyah?" Hadiyah ta hade rai sosai tace "Plss bana son wannan maganar Iklima, keep quiet if you have nothing good to say" Shahuda ta koma ta kwanta tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta mara misaltuwa, gani daya da tayi ma Khaleesat taji duk duniya babu wanda ta tsana kamarta, Khadijah tayi dariya tace "Ko yaushe ma aka aurota da zata fara cuso kanta cikin abun da ya shafi gidan sarauta, who is she to intrude in our affairs? Who even invite her to this Convocation? Wallahi sai tayi da ta sanin zuwa taron nan, next time duk abinda ake a familyn gidan sarauta bazata yi marmarin sake zuwa ba balle ta shigo cikinmu, dama ace ba ordinary person bace da sauki, amma ke ba er kowa ba ki wani ce zaki shigo cikinmu ana mamaki magana ma kina kallon wani waje daban, to mun sa kafar wando daya da ita kuwa" Iklima tace "Wallahi she will regret coming to England" Hadiyah dai kokarin kiran Jay kawai take da wayarta fuskarta daure amma baya shiga. Dakin da Baby ta kai Khaleesat babu kowa ciki sai akwatunan wasu daga yan matan, a hankali Khaleesat ta zauna kasan carpet bayan Baby ta fita, lokaci daya hawaye ya fara sauka idonta kamar an bude pampo, daya bayan daya maganganunsu suka dinga dawo mata kai, Baby na sauka downstairs Jay dake zaune parlor har sannan ya kirata sannan ya mike ya fita waje ta bi bayansa, tuni dama Ajay ya bar gidan bayan da Baby ta raka Khaleesat sama, Baby na kallon Jay bayan ta bi sa waje tace "Gani yaya" Yace "Hope you gave her a separate room?" ta gyada masa kai yace "Ohk akwai abinci a gidan ai?" Ta ɗan karyar da kai tace "Akwai, fried rice Ummi suka dafa mana da chicken and Salad, very delicious" Yace "Ok now ki je ki xuba abincin ki kai mata da ruwa" Buga kafa tayi ta rungume hannu kamar zata yi kuka tace "Yaya na gaji da hawa stairs fa, sai ni ce kawai za ayi ta aika a gidan nan" Yace "C'mon Baby, be a good gal and do what I ask you" Ta langwabe kai a hankali tace "Ohk" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma daga nan yayi tafiyarsa gidan da ya sauka which isn't far from this House kuma duk gidajensu ne, Gimbiya Firdausi da Hajiya Sumayya ma can suke kwana da yayar mahaifin Hadiyah, Baby tayi yanda Jay yace mata ta kai ma Khaleesat abinci da ruwa sannan ta koma wajen uwarta ta kwanta jikinta, hira su Aunty suke amma gaba daya hankalin Aunty na kan Khaleesat da aka kai sama, abincin da Baby ta kai sama ma bata san ita zata kai ma ba ta zata yayyinta ne suka sa ta debo masu abinci da baza a kai ba, ita dai Khaleesat ko taɓa abincin da Baby ta kawo mata bata yi ba saboda bakin ciki gashi ta kasa daina kuka, she was so hurt da abinda suka yi mata, daga karshe haka ta tashi ta shiga bandakin da ta gani kusa da dakin ta dauro alwala ta dawo ta bude akwatinta ta dau hijab ta saka ta tada sallah.... Baby ta fito waje saboda kiran da Ajay yayi mata ta nufesa a inda yake tsaye tace "Gani yaya" ya mika mata ledan hannunsa yace "Take this food to her" Baby ta wara ido tace "Sau nawa za a kai mata abinci, Bayan ya Jawwad ya sa na kai mata abinci da ruwa daxu" Ajay yayi shiru jin abinda tace, can yace "Ohk, but still ki kai mata wannan ma" Tace "To ni ina nawa fa?" Ya hade rai yana kallonta yace "Ina wasa da ke ne?" Tayi yake tace "No Yaya" sannan ta amshi ledan ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma yayi tafiyarsa can daya gidan, Baby na shiga parlor da abincin Aunty ta kirata ganin leda a hannunta, ta tafi har kusa da Aunty tace "Ga ni Momy" Aunty tace "Meye wannan a hannun ki?" Baby tace "Ya Ajay ne ya bani abinci in kai ma wife dinsa" Aunty ta karɓe ledan ta ajiye kusa da ita tace "Tafi ki ban waje" Juyawa Baby tayi ta tafi ta zauna ta dau wayarta ta ci gaba da kallon Cartoon din da take. Khaleesat na kwance saman Carpet bayan ta idar da sallah da kusan minti talatin har sannan ta kasa daina hawaye, ko kallon abincin da Baby ta ajiye mata bata yi ba, text message ne ya shigo wayarta ta dau wayar tana dubawa taga Ajay ne ya turo mata message yace "You need anything?" Taji wani sabon hawayen ya zubo idonta, reply ta mayar masa tace "Eh" Sai ga wani message din nasa yace "What?" Ajiye wayar tayi tana goge hawayen dake zuba idonta bata mayar masa reply ba, bayan minti biyar sai ga kiransa ya shigo wayar, Sai da ya kusa katsewa tayi picking ta kai kunne tayi shiru, yace "Ke kika saka min katin zaki yi shiru? What is that you need?" Shesshekan kuka ta fara yi ta kasa ce masa komai, Calmly yace "What happened?" Ta ma rasa me zata ce masa kawai ta fashe da kuka, shiru yayi yana sauraronta for few seconds, can yace "Come outside" Bata ce komai ba, calmly yace "Kin ji me nace maki?" A hankali tace "Uhm" Daga haka ya katse wayar, goge idonta ta dinga yi duk da hawayen yaki tsayawa, after some minutes ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito, tana tafiya a hankali ta sauka downstairs, kanta a kasa ta nufi kofar fita waje ba tare da ta yarda ta kalli inda su Aunty suke ba, su Aunty da Mami da sauran matan dake parlon duk suka bi ta da kallo har ta fita ta kullo kofar, waige waige ta dinga yi a neighbourhood din ganin bata gansa ba, after almost 2 minute ta hangosa walking toward her, ta sunkuyar da kanta har ya iso inda take tsaye sannan ta daga kai tana kallonsa, yana kallon kwayar idonta da yayi ja yace "Me ya faru?" Ta girgiza masa kai sai ga hawaye na silalowa daga idonta, bai sake cewa komai ba yana kallon wani direction din, bayan few seconds ya nuna mata wani roadside chair yace "Zauna can" Ba musu ta tafi ta zauna wajen da yace, ya karasa cikin apartment din, kallo daya yayi ma su Aunty ya wuce sama without saying anything to them, Aunty dake cin abincin da ya ba Baby ta kai ma Khaleesat ta bi sa da wani kallo, haka ma Ummi da Mami, dakin da su Hadiyah ke ciki Ajay ya bude, gaba daya suka juya suna kallon kofar, one by one suka dinga gaishesa ganin shi ya bude kofar, duk yayi masu kallo daya ya fice daga dakin without bordering to answer their greetings, ya bude wani dakin yaga Hajja tana bacci sai Hajiya A'isha dake dakin, gaisheta yayi bayan ta amsa ya kullo dakin, ya bude last room din yaga box din Khaleesat da handbag dinta sai wayarta, shiga ciki yayi ya dau akwatin da handbag din ya saka mata wayar cikin handbag sannan ya fita daga dakin, tun da ya sauko downstairs su Aunty suka bi sa da kallon mamaki har ya fice daga parlon without looking at them, duk suka kalli juna irin kallon mamaki, Ummi ta gyada kai tace "Tabdi, dauketa zai yi a gidan yake nufi ko me?" Gimbiya Firdausi dai tayi shiru tana kada kafa a hankali fuskarta dauke da wani expression ita ma na mamaki, Aunty ta rike haɓa tace "Kun ga wani ikon Allah kuma" Ummi tace "To ku ka san me ta kintsa masa?" Gimbiya Firdausi tace "Ku kyaleni da shi" Ita dai Mami bata tofa nata ba don bai shafeta ba, Ajay na komawa inda Khaleesat take zaune ta bude ido sosai tana kallonsa da mamaki, ya ajiye mata akwatin ta da handbag ya zauna leaving much distance between them, sosai jikinta ya kara sanyi ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, wani bakin jinin yake son kara ja mata gun danginsu, wayarsa ya ciro yana duba hotel din da zai yi reserving, after a while ya gama making reservation din hotel din da yayi selecting ya biya kudi sannan yayi order din Indrive that will take them there, da kyar Khaleesat tace "Amma bai kamata ka dauko akwatina daga cikin gidan ba....." Wani kallo ya jefa mata yace "I will give you a dirty slap" a hankali ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, after waiting for almost 15 mins sai ga Indrive din ya karaso, Mikewa yayi ya dau handbag dinta ya ajiye mata kusa da ita ya dau akwatin ya kai Ride din, ta bi sa da kallo sai kuma ta mike jiki a sanyaye ta nufi motar ita ma, Front seat Ajay ya shiga bayan drivern motar ya saka akwatin a booth din motar, ita kuma ta bude back seat ta shiga, bayan tafiyar kusan minti talatin suka isa hotel din da yayi booking, without much wasting of time in the hotel reception tunda ya riga yayi reservation online suka yi lodging din hotel room din, gefen gado Khaleesat ta zauna a dakin har lokacin jikinta a sanyaye yake bata taɓa tunanin abinda zai yi ba kenan, ya shiga bandakin dake cikin dakin ya dauro alwala ya fito don lokacin la'asar har ya wuce, mikewa tayi ita ma ta tafi ta dauro alwala, ko da ta fito har ya tada sallah, ta dau wani hijab din nata a box ta saka ta tafi bayansa ta tsaya zata bi sa sallan..... *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 112 Karfe hudu dai dai na asuba Ajay ya bude kofar dakin da Khaleesat take ya kunna wutan dakin yana kallonta, bacci take ta rufe har kanta da Duvet, ya karasa kusa da gadon ya sauke duvet din yace "Kee" firgit ta bude ido ta mike zaune da sauri tana komawa baya, sai kuma ta fara duba hulanta a kan gadon zata rufe gashinta, juyawa yayi ya fita daga dakin, ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe hudu da minti biyu, ajiye wayar tayi ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki.... Kafin karfe hudu da minti hamsin Khaleesat har ta gama shiryawa dama tun daren jiya ta hada duk sabbin kayan da ya siya mata a box dinta ta shirya, tana tsaye gaban madubi tayi oiling dogon gashinta tana combing dinsa zata daure da daya daga ribbons din da ya siya mata jiya, sai kallon baƙin gashin nata take ganin kamar ya kara yawa ma, banda sheki babu abinda gashin yake, bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri ta kalli kofar tana daure tulin gashin nata waje daya cikin hanzari, kallo daya yayi ma gashin yace "Ke Malama you are wasting my time, ko bakya duba agogo ne" Ta ɗan turo baki ta dauke kanta tace "Ni sai nayi sallah tukunna" Tana fadin haka ta ci gaba da abinda take, can ta juya ta kalli direction din kofar taga ya bar wajen, biyar da kusan minti goma ta fito daga dakin da box dinta da handbag ta sauka downstairs, high waisted palazzo ta saka with matching top sai karamin veil dinta da handbag tayi kyau sosai ba kadan ba duk da babu abinda ta shafa a fuskarta sai eye pencil da ta sa a idonta, yana zaune parlor alamar ita yake jira, jin footstep dinta ya juya ya kalleta sai kuma ya dauke kai, kara kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma dai ya fasa ya mike ya nufi kofar parlon ta bi bayansa tana jan trolley dinta, driver na tsaye jikin mota yana jiransu, yana hangota ya tafi ya amshi box din hannunta sannan ya bude mata back seat ta shiga bayan sun gaisa da shi, kallon Ajay dake zaune gaban motar tayi, murya can kasa tace "Good morning" Bai ce komai ba, hakan yasa tayi tunanin bai ji ba ta sake gaishesa a takaice yace "Same" Wani kallo tayi masa ta dauke kai, driver ya shigo motar ya tada suka bar gidan.... Karfe biyu saura suka sauka Ingila Ajay yayi masu order din Indrive da zai kai su har gida, sai bin sa da wani kallo take don he is not even helping with her box, iyaka hand luggage dinsa kawai ya dauka, driver din motar ya dau akwatin ya sa a booth ta bude motar ta shiga don tuni Ajay ya shiga kamar ba tare suke ba, Suna isa gida Khaleesat dai ta tsaya bakin apartment din da taga Ajay ya sa driver ya ajiye akwatin ta, ya gama wayar da yake sannan ya danna bell din apartment din, not long after aka bude kofar apartment din, step sis dinsa Baby ce ta bude kofar tana ganinsa ta rungumesa tace "Oyoyo Yaya...." Yace "How are you?" Tace "Am fine, welcome" Juyawa tayi ta kalli Khaleesat, ya dau box dinta ya mika mata yace "Can't you greet?" Baby tace "Ina wuni" Daga haka ta amshi akwatin Khaleesat ta shiga ciki, ya juya ya kalli Khaleesat dake rakube gefe daya bayan ta amsa gaisuwar Baby, ya hade rai yace "Baza ki shiga ba Malama" Shiga parlon tayi sannan ya bi bayanta ta cire takalmanta nan bakin kofa, Aunty ce zaune parlor sai Ummi uwar Hadiyah da Gimbiya Firdausi, Mami ma na zaune parlon da Hajiya Nafisa, Khaleesat sai da gabanta ya fadi sosai ganinsu gaba daya, duk suka daga kai suna kallon ita da Ajay, kasan carpet ta duka a hankali ta gaishesu tana kallonsu gaba daya, Ajay ya zauna kan kujera ba tare da ya yarda ya hada ido da su ba ya gaishesu shi ma, just Hajiya Nafisa da Ummi sai Gimbiya Firdausi ne suka amsa gaisuwansa babu yabo babu fallasa, Mami dai ko kallon inda suke bata yi ba, ita kuwa Khaleesat dama babu wanda ya bi ta kanta suka ci gaba da labarin da suke a parlon, ko ya hanya babu wanda ya tambaye su, jikin Khaleesat yayi sanyi sosai ta daga kai ta kalli Ajay dake danna wayarsa kawai, bude kofar parlon aka yi sai ga Jay ya shigo yana gyara face cap dinsa, Khaleesat dake durkushe kan carpet bata san sanda ta karasa zaunawa a kan Carpet din ba bayan sun hada ido da shi, within few seconds ya dauke idonsa daga nata, ita kuwa bata fasa bin sa da kallo ba ko kiftawar kirki bata yi, Ajay dai bai yarda ya dago kansa ba tunda ya lura Jay ne ya shigo parlon wayarsa kawai yake ta dannawa, a hankali Khaleesat ta gaida Jay har sannan tana kallonsa, Jay ya zauna without looking at her yace "Lafiya lau, sannu da zuwa" Mami na kallonsa tace "Baka zo kayi breakfast ba yau Jawwad and ur phone isn't reachable" Yace "A restaurant nayi" Mami tace "To Lunch fa?" Yace "Sai anjima" Baby ce ta shigo parlon rike da wayar Aunty ta nufeta tace "Momy u have a call" Aunty ta amshi wayar, Jay na kallon Baby ya nuna mata Khaleesat yace "Take her upstairs Baby" Baby ta kalli Khaleesat tace "Ok let go" Khaleesat ta sauke idonta ta mike ta bi bayan Baby da ta kai ta sama zuwa dakin da su Hadiyah suke, Hadiyah na kwance kan gado sai Maryam da Khadijah sisters din Walid, da Shahuda yarinyar Gimbiya firdausi ta biyu, sai Iklima yarinyar Hajiyah A'isha, ga kuma Bilkisu yarinya Hajiya Sumayya gaba dayansu cousins ne a dakin, kuma duk Shahuda ce babba sai Maryam Kanwar Walid, duk suka juya suna kallon Khaleesat kamar sun ga Alien ta shigo, ita kuwa ji tayi kamar an saka mata chain a kafa tsabar yanda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ganin zuka zukan matan dake dakin gashi duk sun zubo mata ido suna kallonta daga sama har kasa, tayi karfin halin karasawa cikin dakin ta zauna kasan carpet ta gaishesu gaba daya, Hadiyah dai sai kallonta take a walakance kamar taga bola, Shahuda na yatsine fuska ta kalli Baby tace "Wacece wannan kuma Baby kika shigo mana da ita?" Baby ta taɓe baki ta karyar da kai tace "I think Ya Ajay's wife, yanxu suka zo" Shahuda ta mike zaune a hankali daga kwancen da take tana kare ma Khaleesat kallo daga sama har kasa, can tace "Dama wannan ce matar tasa? Ikon Allah, ashe zabiya ce" Tsaki Hadiyah ta ja tace "Don Allah mu ci gaba da maganar da muke, what were we even saying before we were interrupted?" Maryam na kallon Baby fuska daure tace "To ke uwar wa yace ki kawo mana ita nan? Duk dakunan dake sama ki rasa inda zaki shigo da ita sai wannan? Ko baki da kai ne? Dama akwatin ta ne wancan kika shigo mana da shi daki?" Baby ta bude ido ta langwabe kai tace "Ya Jawwad ne fa ya ce in kawo ta Aunty" Hadiyah ta mike zaune jin abinda Baby tace, fuska a murtuke tana kallonta tace "Yace ki kawo ta ina? Ina kika gansa yace ki kawo ta nan, yaushe ya zo? Dalla dau akwatin can ki fitar mana da shi daga nan, kinga nan yayi kama da inda za a kawo bare" Ita dai Khaleesat kallon direction daban take babu ko kiftawan kirki tana jin duk abinda suke cewa, Iklima ta juya tana mata wani matsiyacin kallo tace "Keee duk nan da kike gani jinin sarauta ne babu wani bare, babu ordinary blood don haka can you kindly get out of here? They are other rooms ba wannan kadai bane daki a gidan nan, ko kuma ki tafi Garage dama babu komai a ciki...." Khadijah tace "Can you imagine don rainin wayo ma wani wajen daban take kallo ana mata magana ko er uban wacece ita oho, bari ki ji duk nan babu sa'an ki wallahi, mu ba class din ki bane ta ko ina, don haka get out of this room" Baby na kallon Khaleesat tace "Sun ce ki tafi wani dakin you are not welcome in their midst" Mikewa Khaleesat tayi a hankali bata dai ce komai ba, Baby ta kalli yayyin nata tace "Ko in kai ta dakin Granny kawai?" Shahuda ta jefa mata wani harara tace "Are you stupid? What is Granny's relationship with her da zaki kai ta dakinta? Ordinary person kamar ta zaki kai ta dakin Granny ko baki da kai ne, pls take her out before i loose my temper" Baby tace "Oh ohk, bari in kai ta dakin da ku ka ajiye boxes din ku to" Daga haka ta dau akwatin ta nufi kofa Khaleesat na biye da ita, Hadiyah ta bi ta da wani matsiyacin kallo kamar yanda Shahuda ma ta bi ta da kallon tsana don mutuwa ne kawai bata yi akan son Junaid ba amma daga karshe wai Khaleesat ta samesa a sama kusan a banza ba wani wahala tana er matsiyata da ita shine zata zama matar ɗan sarki me jiran Gado, Iklima ta rike haɓa tace "Dama ita ce Ya Jawwad ya so ya aura ya hadata da ke Hadiyah?" Hadiyah ta hade rai sosai tace "Plss bana son wannan maganar Iklima, keep quiet if you have nothing good to say" Shahuda ta koma ta kwanta tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta mara misaltuwa, gani daya da tayi ma Khaleesat taji duk duniya babu wanda ta tsana kamarta, Khadijah tayi dariya tace "Ko yaushe ma aka aurota da zata fara cuso kanta cikin abun da ya shafi gidan sarauta, who is she to intrude in our affairs? Who even invite her to this Convocation? Wallahi sai tayi da ta sanin zuwa taron nan, next time duk abinda ake a familyn gidan sarauta bazata yi marmarin sake zuwa ba balle ta shigo cikinmu, dama ace ba ordinary person bace da sauki, amma ke ba er kowa ba ki wani ce zaki shigo cikinmu ana mamaki magana ma kina kallon wani waje daban, to mun sa kafar wando daya da ita kuwa" Iklima tace "Wallahi she will regret coming to England" Hadiyah dai kokarin kiran Jay kawai take da wayarta fuskarta daure amma baya shiga. Dakin da Baby ta kai Khaleesat babu kowa ciki sai akwatunan wasu daga yan matan, a hankali Khaleesat ta zauna kasan carpet bayan Baby ta fita, lokaci daya hawaye ya fara sauka idonta kamar an bude pampo, daya bayan daya maganganunsu suka dinga dawo mata kai, Baby na sauka downstairs Jay dake zaune parlor har sannan ya kirata sannan ya mike ya fita waje ta bi bayansa, tuni dama Ajay ya bar gidan bayan da Baby ta raka Khaleesat sama, Baby na kallon Jay bayan ta bi sa waje tace "Gani yaya" Yace "Hope you gave her a separate room?" ta gyada masa kai yace "Ohk akwai abinci a gidan ai?" Ta ɗan karyar da kai tace "Akwai, fried rice Ummi suka dafa mana da chicken and Salad, very delicious" Yace "Ok now ki je ki xuba abincin ki kai mata da ruwa" Buga kafa tayi ta rungume hannu kamar zata yi kuka tace "Yaya na gaji da hawa stairs fa, sai ni ce kawai za ayi ta aika a gidan nan" Yace "C'mon Baby, be a good gal and do what I ask you" Ta langwabe kai a hankali tace "Ohk" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma daga nan yayi tafiyarsa gidan da ya sauka which isn't far from this House kuma duk gidajensu ne, Gimbiya Firdausi da Hajiya Sumayya ma can suke kwana da yayar mahaifin Hadiyah, Baby tayi yanda Jay yace mata ta kai ma Khaleesat abinci da ruwa sannan ta koma wajen uwarta ta kwanta jikinta, hira su Aunty suke amma gaba daya hankalin Aunty na kan Khaleesat da aka kai sama, abincin da Baby ta kai sama ma bata san ita zata kai ma ba ta zata yayyinta ne suka sa ta debo masu abinci da baza a kai ba, ita dai Khaleesat ko taɓa abincin da Baby ta kawo mata bata yi ba saboda bakin ciki gashi ta kasa daina kuka, she was so hurt da abinda suka yi mata, daga karshe haka ta tashi ta shiga bandakin da ta gani kusa da dakin ta dauro alwala ta dawo ta bude akwatinta ta dau hijab ta saka ta tada sallah.... Baby ta fito waje saboda kiran da Ajay yayi mata ta nufesa a inda yake tsaye tace "Gani yaya" ya mika mata ledan hannunsa yace "Take this food to her" Baby ta wara ido tace "Sau nawa za a kai mata abinci, Bayan ya Jawwad ya sa na kai mata abinci da ruwa daxu" Ajay yayi shiru jin abinda tace, can yace "Ohk, but still ki kai mata wannan ma" Tace "To ni ina nawa fa?" Ya hade rai yana kallonta yace "Ina wasa da ke ne?" Tayi yake tace "No Yaya" sannan ta amshi ledan ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma yayi tafiyarsa can daya gidan, Baby na shiga parlor da abincin Aunty ta kirata ganin leda a hannunta, ta tafi har kusa da Aunty tace "Ga ni Momy" Aunty tace "Meye wannan a hannun ki?" Baby tace "Ya Ajay ne ya bani abinci in kai ma wife dinsa" Aunty ta karɓe ledan ta ajiye kusa da ita tace "Tafi ki ban waje" Juyawa Baby tayi ta tafi ta zauna ta dau wayarta ta ci gaba da kallon Cartoon din da take. Khaleesat na kwance saman Carpet bayan ta idar da sallah da kusan minti talatin har sannan ta kasa daina hawaye, ko kallon abincin da Baby ta ajiye mata bata yi ba, text message ne ya shigo wayarta ta dau wayar tana dubawa taga Ajay ne ya turo mata message yace "You need anything?" Taji wani sabon hawayen ya zubo idonta, reply ta mayar masa tace "Eh" Sai ga wani message din nasa yace "What?" Ajiye wayar tayi tana goge hawayen dake zuba idonta bata mayar masa reply ba, bayan minti biyar sai ga kiransa ya shigo wayar, Sai da ya kusa katsewa tayi picking ta kai kunne tayi shiru, yace "Ke kika saka min katin zaki yi shiru? What is that you need?" Shesshekan kuka ta fara yi ta kasa ce masa komai, Calmly yace "What happened?" Ta ma rasa me zata ce masa kawai ta fashe da kuka, shiru yayi yana sauraronta for few seconds, can yace "Come outside" Bata ce komai ba, calmly yace "Kin ji me nace maki?" A hankali tace "Uhm" Daga haka ya katse wayar, goge idonta ta dinga yi duk da hawayen yaki tsayawa, after some minutes ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito, tana tafiya a hankali ta sauka downstairs, kanta a kasa ta nufi kofar fita waje ba tare da ta yarda ta kalli inda su Aunty suke ba, su Aunty da Mami da sauran matan dake parlon duk suka bi ta da kallo har ta fita ta kullo kofar, waige waige ta dinga yi a neighbourhood din ganin bata gansa ba, after almost 2 minute ta hangosa walking toward her, ta sunkuyar da kanta har ya iso inda take tsaye sannan ta daga kai tana kallonsa, yana kallon kwayar idonta da yayi ja yace "Me ya faru?" Ta girgiza masa kai sai ga hawaye na silalowa daga idonta, bai sake cewa komai ba yana kallon wani direction din, bayan few seconds ya nuna mata wani roadside chair yace "Zauna can" Ba musu ta tafi ta zauna wajen da yace, ya karasa cikin apartment din, kallo daya yayi ma su Aunty ya wuce sama without saying anything to them, Aunty dake cin abincin da ya ba Baby ta kai ma Khaleesat ta bi sa da wani kallo, haka ma Ummi da Mami, dakin da su Hadiyah ke ciki Ajay ya bude, gaba daya suka juya suna kallon kofar, one by one suka dinga gaishesa ganin shi ya bude kofar, duk yayi masu kallo daya ya fice daga dakin without bordering to answer their greetings, ya bude wani dakin yaga Hajja tana bacci sai Hajiya A'isha dake dakin, gaisheta yayi bayan ta amsa ya kullo dakin, ya bude last room din yaga box din Khaleesat da handbag dinta sai wayarta, shiga ciki yayi ya dau akwatin da handbag din ya saka mata wayar cikin handbag sannan ya fita daga dakin, tun da ya sauko downstairs su Aunty suka bi sa da kallon mamaki har ya fice daga parlon without looking at them, duk suka kalli juna irin kallon mamaki, Ummi ta gyada kai tace "Tabdi, dauketa zai yi a gidan yake nufi ko me?" Gimbiya Firdausi dai tayi shiru tana kada kafa a hankali fuskarta dauke da wani expression ita ma na mamaki, Aunty ta rike haɓa tace "Kun ga wani ikon Allah kuma" Ummi tace "To ku ka san me ta kintsa masa?" Gimbiya Firdausi tace "Ku kyaleni da shi" Ita dai Mami bata tofa nata ba don bai shafeta ba, Ajay na komawa inda Khaleesat take zaune ta bude ido sosai tana kallonsa da mamaki, ya ajiye mata akwatin ta da handbag ya zauna leaving much distance between them, sosai jikinta ya kara sanyi ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, wani bakin jinin yake son kara ja mata gun danginsu, wayarsa ya ciro yana duba hotel din da zai yi reserving, after a while ya gama making reservation din hotel din da yayi selecting ya biya kudi sannan yayi order din Indrive that will take them there, da kyar Khaleesat tace "Amma bai kamata ka dauko akwatina daga cikin gidan ba....." Wani kallo ya jefa mata yace "I will give you a dirty slap" a hankali ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, after waiting for almost 15 mins sai ga Indrive din ya karaso, Mikewa yayi ya dau handbag dinta ya ajiye mata kusa da ita ya dau akwatin ya kai Ride din, ta bi sa da kallo sai kuma ta mike jiki a sanyaye ta nufi motar ita ma, Front seat Ajay ya shiga bayan drivern motar ya saka akwatin a booth din motar, ita kuma ta bude back seat ta shiga, bayan tafiyar kusan minti talatin suka isa hotel din da yayi booking, without much wasting of time in the hotel reception tunda ya riga yayi reservation online suka yi lodging din hotel room din, gefen gado Khaleesat ta zauna a dakin har lokacin jikinta a sanyaye yake bata taɓa tunanin abinda zai yi ba kenan, ya shiga bandakin dake cikin dakin ya dauro alwala ya fito don lokacin la'asar har ya wuce, mikewa tayi ita ma ta tafi ta dauro alwala, ko da ta fito har ya tada sallah, ta dau wani hijab din nata a box ta saka ta tafi bayansa ta tsaya zata bi sa sallan..... *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 113 Da daddare Khaleesat ta fito wanka kenan taji ana knocking kofar dakin hotel din, tun bayan da Ajay ya fita wajen karfe biyar ya kawo mata abinci ya sake tafiya take ta zaune ita kadai a hotel room din har yanxu da karfe tara da rabi yayi, hijab dinta ta saka har kasa don towel kadai ne daure jikinta ta nufi kofar ta bude tana kallonsa, kallo daya yayi mata ya shiga cikin dakin, ta juya ta bi bayansa still looking at him, ya ajiye ledan hannunsa kan Centre table din dakin, da tsadadden darduman da ya dauko daga gida sannan ya cire Jacket din jikinsa, a hankali ta dau doguwar rigar da zata saka na bacci dake gefen gado ta nufi bandaki, bayan few minutes ta fito daga bandakin ta ajiye hijab dinta da ta linke, ta ɗan kallesa ta gefen ido taga duk hankalinsa na kan abinda yake yi a wayarsa yana zaune kan kujeran dakin, gun ledan da ya ajiye ta tafi ta dauka don ledan restaurant ne, bata ci abincin da yawa ba ta sha drink din ta ajiye sauran abincin ta zauna gefen gado ta jingina da furniture din gadon ta fada duniyar tunani, ta kusa 30 mins zaune maganganun su Hadiyah na dawo mata da irin tarban walakancin da su Aunty suka yi mata a parlor, that not being enough Jay ma yaki ko da kallon inda take shi ma da ya ganta, gaisuwanta ma without much concentration ya amsa mata, duk cikin abubuwan da aka yi mata yau wannan ne yafi yi mata ciwo har cikin ranta, she felt really hurt and pained, hannu ta kai ta goge hawayen da taji na silalowa daga idonta a hankali, don kar ma ta fashe da kukan dake cin ta kawai ta jawo wayarta ta kunna data ko zai yi distracting dinta from what is making her wants to cry, bata expecting ko wani important WhatsApp message da ya wuce na Ummanta sai Sophie sai ko Aunty Farida, sosai gabanta ya fadi bayan ta ci karo da message din Jay, babu ko kiftawa ta dinga kallon message din da ya rubuto mata kamar haka "An maki wani abu ne a gidan?" And he is even online at the moment, cikin sanyin jiki ta masa reply tace "A'a" After few minutes sai ga wani message din nasa yace "Then why did you leave the House?" Wasu sabbin hawaye taji na taruwa idonta ta tura masa "Ba komai" Sai ga message dinsa yace "Alright, take care" har cikin ranta take jin kaman kaso tamanin daga cikin abinda ke damunta a ranta ya ragu, baƙin cikin da take ciki yau taji kamar an yaye mata shi lokaci daya, kallon message din nasa na karshe ta dinga yi babu ko kiftawa, cikin sanyin jiki ta sake masa message tace "Plss me yasa idan nayi maka message kake ignoring? I want to speak to you plss" Without waste of time sai ga shi yayi reply kamar haka "Hum! About?" Ta goge hawayen dake zuba idonta tace "Many things" Ya sake cewa "Hmm, Like?" Tace "Plss spare me even if it's just a little of ur time ka saurareni don Allah" Yace "Kina ina yanxu?" Ta dinga kallon tambayar da yayi mata zuciyarta na bugawa, a hankali ta juya suka hada ido da Ajay, ta sauke idonta sai kuma ta dauke kai daga direction dinsa, tana kallon message din da Jay yayi mata ta mayar masa da reply tace "Nima ban san wajen ba" after few seconds Jay yayi mata reply yace "Forward ur location" Khaleesat ta kusa minti daya tana tunanin ta tura din ko kar ta tura, don tana tura masa location din hotel zai gani, a hankali ta juya ta kalli Ajay taga idonsa na kan wayarsa, kawai ta tura ma Jay location din nata ta WhatsApp, ta fi minti talatin zaune tana jiran reply dinsa amma bai yi ba kuma yana online, daga karshe tayi masa message tace "Kayi shiru" Nan ma dai har bayan minti ashirin bai mayar mata reply ba ta ga ya ma sauka, hawaye ya cika idonta ta kashe data dinta ta ajiye wayar ta kwanta ta rufe jikinta da farin duvet din kan gadon, bata san sanda bacci ya dauketa ba wajen karfe sha biyu bayan ta gama zubda hawayenta. Biyu da yan mintuna na dare Khaleesat ta farka ta dalilin mafarkin da tayi about Jay, ta mike zaune ta dinga bin dakin da kallo don wuta ne mara haske a kunne, she was wondering if ita kadai ce a dakin, tafi minti goma zaune bata motsa daga inda take ba, can dai ta koma daya side din gadon tana leka kasa a hankali, Ajay ta gani kwance kan darduman da ya shigo da shi daxu yana sanye da jacket ya saka eye mask for sleep alamar baya son haske, dakin yayi sanyi sosai saboda Ac dake kunne, gashi dama tun da suka zo kasar ta lura yafi America sanyi, duvet din jikinta ta cire ta rufa masa ta koma ta kwanta tayi using second bedsheet din kan gadon ta rufa da shi. Da asuba ko da Khaleesat ta tashi taga duvet din a jikinta, ta mike zaune ta juya tana kallon inda yake tsaye yana sallah, sauka tayi daga saman gadon tana gyara hularta ta shiga bandaki. Khaleesat na idar da sallah bayan ta gama azkar dinta abu na farko da tayi shine kunna data din wayarta ko Jay yayi mata reply din message dinta, amma taga har sannan bai mata reply ba kuma ya hau not long ago, sosai taji zuciyarta ya karaya, ta ajiye wayar cikin sanyin jiki lkci daya idonta ya kada, kamar ance ta daga kai taga Ajay yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, babu yabo babu fallasa taji yace "What is it?" Without looking at him tace "Nothing" Gaishesa tayi ya dauke kai bai amsa ba, ta mike ta tafi edge din gado ta kwanta ba tare da ta cire hijab din jikinta ba, ji take kamar an kwaso mata damuwar da taji ya tafi jiya an maido mata kayanta, lumshe ido tayi after sometime bacci ya dauketa..... Ajay ne ya shigo dakin hotel din fuska daure yace "Baki da hankali ne zaki bar ni zaune a mota tun daxu are you okay?" Khaleesat ta gama daure gashinta da take yi ta juya tana kallonsa bata dai ce komai ba, bai sake ce mata komai ba ya dauke idonsa ya juya ya fita daga dakin, ta dau veil din kayan jikinta tayi rolling dinsa sannan ta dau handbag dinta ta saka takalmi ta nufi kofar dakin hotel din ta fita, walking slowly ta nufi Indrive din dake jiranta outside of the hotel, sau daya Ajay ya kalleta ta madubin motar da yake ciki ya dauke ido kamar bai ganta ba, har ta iso ta bude back seat ta shiga ta kulle. Da gangan Ajay ya bari suka je Venue din convocation din Hadiyah extremely late, don har an gama taron ana ta hotuna ne suka isa wajen, ita dai Khaleesat tana biye da shi a baya gabanta sai faduwa yake, front dinsa ya nuna mata hakan yasa ta shiga gaba yana biye da ita, tun daga nisa take kallon yanda familyn suke ta hotuna cikin farin ciki da annashuwa ba iyayen ba ba 'ya yan su ba, Hajja kuwa na zaune daga gefe cike da izza ga fruits an ajiye mata gabanta, Hadiyah sai makale ma Jay da yayi mata side hug take kamar zata shige jikinsa su zama daya ko kunya babu ana masu hoto, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa, Khaleesat dai ta sauke idonta daga kallonsu tana tafiya a hankali, lokaci daya duk aka yi noticing Ajay da Khaleesat that were walking toward the scene, gaba daya aka maida attention kansu barin ma Khaleesat, Ba iya su Hadiyah da cousins din ta ba, hatta iyayensu kowa kallon Khaleesat yake barin Aunty, cause whatttt?? she look expensively beautiful, gaba daya dressing dinta ya doke duk na yan matan wajen har me convocation, komai na jikinta is screaming nothing but pure luxury gashi tayi wani nutsattsen kyau duk da babu make up fuskarta pink lips dinta kuwa sai sheki yake, tsadadden kayan jikinta ya kara haska farin fatar ta, Walid ya dinga kallonta kamar zai cinyeta, Khaleesat was only feigning smile ganin all eyes were on her hakan yasa beauty point dinta ya dinga lotsawa ciki, amma tsabar yanda duk ta rikice da yanda suke kallonta sai da ta harde kafa wajen tafiya wanda hakan yasa kirkis ya rage ta fadi banda Ajay da yayi saurin tarota, yana facing dinta speaking calmly yace "Are you a bush gal?" Kamar wanda ya tuna abu sai kuma ya saketa within few seconds suka ci gaba da tafiya, this time around he let them walk together ba kamar daxu da take gaba yana bin ta ba, Aunty taji wani abu ya tokareta a kirji ta juya ta kalli Hajiya Nafisah, Hajiya Nafisah tace "Uhum" irin na takaicin nan, Ummi Mahaifiyar Hadiyah kuwa hade rai tayi sosai ta ci gaba da harkar gabanta a wajen, Mami dai ko bin ta kan Khaleesat bata yi ba tana ta kokarin sallamar wasu ɓakin ta da za su tafi, Hadiyah ta dinga kallon designer bag din hannun Khaleesat da rings din fingers dinta sai kuma ta dauke kai tana jawo wasu frnds dinta da suma suka tsaya kallon Khaleesat, ta kira me hoto yayi masu hoto duk don ta kawar da attention dinta daga kan Khaleesat, Tun da Jay ya kalli Khaleesat sau daya ya dauke kai daga direction din, Shahuda kuwa sai kallon doguwar rigar jikin Khaleesat take with sheer jealousy, sauran yan matan ma dai kowacce zaka ga hassadarta kwance fuskarta kiri kiri, duk wani African in ya zo wuce wajen sai ya sake kallon Khaleesat, Ajay ya karasa har inda Hajja ke zaune ya gaisheta, Hajja na kallonsa tace "Junaid sai da aka kare convocation zaka zo saboda Allah? To menene amfanin zuwan ka kenan muna kokarin komawa gida?" Ajay yaki tanka ta ya dau Apple din kusa da ita, ya gaida su Gimbiya Firdausi dake gefenta duk suka amsa masa babu yabo babu fallasa, kallon Mami yayi ita ma ya gaisheta ta amsa, Khaleesat ta duka gaban Hajja ta gaisheta cikin sanyin murya, neutrally Hajja ta amsa tana kiran jikar wata aminyarta da ta hango wai ta zo ba ayi hoto da ita ba, Khaleesat ta kalli su Gimbiya Firdausi su ma ta gaishesu, har sai da Hajja ta kallesu tace "Ana gaishe ku" sannan suka amsa don yi suka yi kamar basu ji ba gaba dayansu kuma, still at that ma Aunty bata amsa gaisuwar ba fuskar nan nata a murtuke kamar bata taɓa ko murmushi ba, Khaleesat ta ɗan kalli Walid da ke gaisheta yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta mayar masa da gaisuwan, A takaice Ajay ya amsa gaisuwan Cousins dinsa, Jay kuwa dama tuni ya bar wajen yana answering phone call, Baby tayi fari da ido tana kallon Khaleesat tace "10/10 kika yi kyau...." Su Iklima duk suka juya suna kallon Baby, ita dai Khaleesat murmushi kawai tayi ta kalli Baby tace "Thank you" Ganin har sannan Khaleesat na durkushe Hajja tace "To ki je ki yi ma Hadiyah Allah sanya alkhairi mana, ga can kannen mijin ki kuma sai ki duka a nan" Mikewa Khaleesat tayi cikin sanyin gwiwa ta ɗan kalli Ajay dake kallonta, sai kuma ta karasa har inda su Hadiyah suke hotunansu tana Kallonta tayi mata congratulations, Hadiyah tayi kamar bata san da ita take ba sai jawo cousins dinta da kawayenta take suna hotuna happily, duk da tun da taga Khaleesat Happiness din nata yayi vanishing kawai pretending ta ci gaba da yi take fara'an da bai kai zuci ba, wata kawar Hadiyah dake ta kallon Khaleesat kamar ta samu TV tace "Hi, I love your dressing, you look beautiful" Khaleesat tayi mata murmushin karfin hali tace "Thank you, and you too" Hadiyah ta kara jin wani kololuwar bakin ciki ya tokareta kawai dai ta ci gaba da sabganta bata nuna ba, Shahuda dama barin wajen ma tayi gaba daya, babu wanda ya bi ta kan Khaleesat dake ta tsaye a wajen da suke hotunan, daga karshe cikin sanyin jiki ta koma gefe ita kadai ta tsaya, ganin Ajay ne ma yasa duk suka kama kansu babu wanda ya tsaya disgata a wajen cause he is looking at each and every one of them, ita kam Khaleesat time to time take satan kallon inda Jay ya koma ya tsaya da Maminsa tana masa magana, ta kalli wajen for the 4th time kawai suka hada ido da shi and he took his eyes off her ya juya baya, a hankali ta sauke idonta, duk Ajay na kallo, bayan Jay ya gama magana da Mami ya tafi gun wani abokinsa ya tsaya, wayarsa ya ciro yana dannawa, Khaleesat ta bude jakar ta jin shigowar message wayarta, ta ciro wayar tana kallon message din babu ko kiftawa, Ajay dai kallonta kawai yake daga inda yake tsaye, can yaga ta juya a hankali ta kalli inda Jay yake, Jay ya ɗan kalleta bayan sun hada ido ya dauke kai ya mayar da wayarsa cikin aljihu, Wani Apple din Ajay ya dauka zai bar vicinity din Hajja ta bi sa da kallo tace "Ahmad Junaid" Juyowa yayi, sai kuma ya dawo ya tsaya kusa da ita yana jiran jin me zata ce, tayi shiru kamar bazata ce komai ba don babu abinda ya tsaya mata a rai irin yanda taga daga shi har Jay babu wanda ya kalli inda wani yake balle yayi ma wani magana, kamar ma basu taɓa sanin juna ba, duk tunaninta ko ba komai suna gaisawa, can ta kallesa, shi dai cin Apple din hannunsa yake with calmness yana kallon Khaleesat dake danna wayarta alamar she is sending a message, sae kuma ta juya ta kalli Jay that is looking at his phone too shi ma ya ɗan juya ya kalleta, Ajay ya dauke kai daga direction dinsu ya kalli Hajja yace "I am listening" Ajiyar zuciya Hajja ta sauke tace "To shi ma hotunan baza kayi da yan uwanka ba kenan kake nufi ko me? Ban ga alamar kayi niyyar zuwa taron nan ba don da kayi niyyar zuwa ba sai da aka watse taro zaka zo ba" Ajay yace "Ni zan je in samesu mu yi hoto?" Hajja ta kalli Baby da ta zo daukan Apple tace "Ke Hauwa kira min Hadiyah" Baby tace to sannan ta tafi, sai ga Hadiyah ta zo fuskarta babu wani fara'a, to cover that up tace "Wallahi na gaji kaina ma ciwo yake min, da ma mu tafi gida kawai" Hajja tace "Hadiyah ba ku yi hoto da yayanki da matarsa ba" Hadiyah ta kauda kai tana ɗan yatsine fuska sai kuma ta juyo tace "Oh haka ne fa" Kiran me yin hoton tayi sannan ta koma gefen Ajay ta tsaya me hoton ya fara daukansu hoto, Hajja ta kara aika baby taje ta kira Khaleesat, after snapping 2 pictures with Ajay Hadiyah ta zaro ido tace "Wayata fa? Waye na ba wayata ko nayi misplacing dinsa ne?" Da sauri ta bar wajen irin zata je tambayo cousins dinta da kawayenta wanda ta ba wayarta a cikin su, nan kuma hoto ne da Khaleesat bazata yi ba, Hajja ta daga kai ta kalli Ajay tace "Kai yanxu abinda kayi jiya ka kyauta Junaid? Ko da yake bari mu karasa gida tukunna ba maganar nan wajen bane" Dai dai nan Khaleesat ta iso gun Hajja bayan Baby taje ta kirata, ta kalli Ajay da ya juya ya bar wajen sannan ta duka gaban Hajja tace "Ga ni Hajja" Gimbiya Firdausi ta karaso kusa da Hajja tace "Hajja ga mota za a fara kai ki gida" Bata rufe baki ba sai ga Jay ya iso gun yana kallon Hajja, calmly yace "Hajja za ayi dropping din ki gida, the driver is around" Hajja tace "Toh" Kallon Khaleesat Jay yayi yace "Are you following Hajja Home?" Gimbiya Firdausi ta kallesa tace "Kamar ya kenan? Manyan ta basu fara tafiya ba sai ita Jawwad, wannan kuma wani lissafi ne, ae su Hadiyah zata bi ba Hajja ba, Hajja da Fulani kawai za aje ayi dropping a dawo a motar" Jay dai bai ce komai ba, Gimbiya Firdausi ta kara da cewa "Tun da ta shigo zuri'a babba haka ai kamata yayi ta dinga sakin jiki tana shiga yan uwan mijinta ba ta dinga rabe rabe ba" Jay ya kalli Khaleesat calmly yace "Go nd meet them, naga baku yi hoto ba" Ita dai Hajja babu abinda tace a wajen, Khaleesat ta mike a hankali ta nufi inda su Hadiyah suka taru, sai da ta isa wajen ta fara waigen inda zata ga Ajay amma bata gansa ba, kamar yanda suka mata daxu yanxu ma babu wanda ya bi ta kanta harkan gabansu kawai suke suna nishadin su, Shahuda ta lura Ajay baya surrounding din alamar ya bar wajen, hakan yasa ta karasa har gaban Khaleesat fuska daure tace "Wai ke halan mayya ce da dole sai kin zo inda muke? Tun daxu muke avoiding dinki amma sae kara cuso kanki kike wajen mu, Waye ajin ki a nan ko kuma uban wa ya gayyace ki?" Su Iklima duk suka juya da sauri don ganin ko Ajay na wajen sai suka ga baya nan, haba nan duk suka kallo Khaleesat, tana ganin haka bata sake tsayawa ta ji abinda za su fada next ba ta juya ta bar wajen ta koma can wani waje daban ta tsaya cikin sanyin jiki tana dube duben inda zata ga Ajay...... *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 114 Khaleesat dai na tsaye tana ta kallon yanda motoci ke ta zuwa daukan masu sarauta zuwa gida kuma babu wanda ya bi ta kanta, Hadiyah sai aikin makale ma Jay dake rike da graduation folder dinta da wayarta take duk inda yayi sai ta bi sa, a hankali Khaleesat ta bude jakarta ta ciro wayarta, call log dinta ta shiga tana ta kallon number Ajay, can dai tayi dialing number ya fara ringing amma har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma no reponse, jira tayi taga ko zai biyo kiran amma still har bayan 15 mins bai kira ba, mayar da wayar tayi cikin jaka cikin sanyin jiki, ta ci gaba da bin kowa na wajen da kallo, duk baƙin da suka zo taya Hadiyah murna sai da aka tabbatar an maida su masaukin su, ya rage iya Cousins dinta kawai da 3 of Her friends ne a wajen sai Jay, Jay na son ce ma Khaleesat ta je ta hau mota ganin she is just standing amma bai san ta ya ba saboda yanda Hadiyah ta makale masa not even giving him a breathing space, Khaleesat na hada ido da Walid da ya dawo wajen ta sauke idonta kasa, ya nufi har inda take tsaye yana kallon fuskarta yace "Hey, mu je inyi dropping din ki a gida ko?" Da kyar ta daga idonta tace "Yace min yana zuwa in jira sa" Yana mata wani kallo yace "A ina ku ka sauka?" Ta girgiza masa kai tace "Nima ban san wajen ba" Wani shegen murmushi yayi mata yace "Za mu hade...." Daga haka ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo zuciyarta na bugawa, har kasan ranta take tsoron Walid da Aunty, Duk Jay na lura da su kuma duk tunaninsa da Walid yaje wajenta zai ce mata su je yayi dropping dinta a gida ne amma sai kuma yaga ya tafi ya bar ta tsaye wajen, a hankali Khaleesat ta sake bude jakarta ta ciro wayarta tayi dialing number Ajay, har ya katse bai ɗaga ba nan ma, ta sake kiransa no response again, jiki a sanyaye ta mayar da wayar cikin jaka gashi ta gaji da tsayuwa, After some more minutes Jay ya juya ya kalleta, sai kuma ya dubi Hadiyah dake making phone call, ya jira har ta gama sannan yace "Hadiyah go and tell her to come over ku tafi gida it's getting late, the second car is back...." Hadiyah na kallonsa tace "Who?" calmly yace "Halysaah" Da wani expression tace "Wacece kuma haka?" Bai sake tanka ta ba, ta juya masa kunnenta tace "Ni dai cire min dankunnen nan Honey, it's very tight...." Yace "Ba gida za mu tafi ba why remove it?" Ta hade rai tace "A'a just take it off pls, I am not comfortable with it" Bai sake ce mata komai ba ya kai hannu ya fara cire mata dankunnen nata, yana cirewa ya daga kai ya kalli Khaleesat da tayi masu kallo daya ta dauke kai, ya gama cire earrings din ya mika ma Hadiyah tayi masa side hug tana kallonsa tace "Thanks love" Khadijah ya kira bayan ta iso wajensu yace "Je ki ce ma Halysaah ga mota yana jira za ku tafi gida" Hadiyah ta wani hade rai tana kallonsa tace "C'mon Honey ba fa tare muka zo nan da ita ba, definitely mijinta ne zai tafi da ita since they came together, jiya ma ai shi yaje ya dauketa daga can gida suka yi tafiyar su" Khadijah tace "Tare fa suke da Ya Junaid and he is somewhere around here, salon mu tafi da ita mu yi masa laifi, balle ma ya nuna baya son ta zauna cikinmu, gwara kawai a bar masa ita kawai Ya Jay ba ruwana da jarabansa" Jay dai bai ce komai ba ya ciro wayarsa dake ringing yaga Mami ke kiransa, picking call din yayi ya koma wani wajen ya tsaya yana answering call din nata, bayan ya gama wayar kawai ya ɗan kalli side din su Hadiyah kafin ya juya ya nufi Khaleesat, har ya isa inda Khaleesat take tsaye bata yarda ta kallesa ba yace "Ga mota can ki tafi ki shiga a maida ke gida, or are you waiting for anyone to pick you up?" Tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma ta daga kai ta kallesa a hankali tace "Nace ina son magana da kai" He was quiet for few seconds bayan ya dauke idonsa daga kallonta, ganin Hadiyah ta nufosu don sai a sannan ta kula ya tafi wajen Khaleesat, yace "Let's chat, ki je ki shiga mota kawai" Nuna mata inda motar yake yayi, ta juya ta nufi wajen tun Hadiyah bata karaso wajensu ba, shi kuma ya ciro wayarsa ya kira driver din ya ce masa ya tafi da ita kadai ba sai ya dauki kowa ba a motar, Hadiyah ta hade rai bayan ta iso gabansa tana kallonsa tace "Dole ne sai kayi magana da ita ne Baby? Shi mijin nata da ya kawota bai san zai maida ta ba? What's ur business with her??" Jay ya kalleta strictly yace "It's my duty to make sure everyone leaves here to their various destination Hadiyah, stop questioning me" Hadiyah ta ɓata fuska tana kallonsa, ya ja hancinta yace "To yi kukan mu ga" juya masa baya tayi, ya kamo hannunta ya juyo ta yace "Zaki fara ko" Ko da wasa Khaleesat bata yarda ta juya ba har ta isa gun motar, tana shiga ciki driver ya ja suka bar wajen, gaba daya jikinta a sanyaye yake, nan ta fara tunanin ko kawai ta gaya masa sunan hotel din da Ajay ya kai ta jiya yayi dropping dinta a can a maimakon gida don ita tsoron zuwa wannan apartment din take bata san me zata je ta tarar ba, gaba daya family din ma tsoro suke bata she is not comfortable staying together with them, tun bata bari sun yi nisa ba kawai ta gaya masa ya kai ta hotel din, haka kuwa aka yi bayan kusan tafiyar minti ashirin da biyar suka isa babban hotel din, ta bude motar ta sauka tayi masa sai anjima sannan ta shiga cikin hotel din ta wuce sama, a hankali ta bude kofar dakin ai kuwa taji sa a bude ta shiga cikin dakin closing the door gently tana kallon Ajay dake kwance kan gado yayi rub da ciki yana bacci ta can ɓangaren gadon ba inda ta kwanta ba daren jiya, haushi ya cikata lokaci daya ta hade rai, shine zai yi tafiyarsa ya bar ta ita kadai a wajen ya dawo nan yana bacci abunsa, shi yasa take ta kiransa no response, tana tafiya a hankali ta karasa cikin dakin ta ajiye handbag dinta ta cire mayafin kanta ta sauke gashinta da ta nannade sannan ta fara cire jewelries din jikinta gaba daya ta ajiye su saman bedside drawer, ta cire rigar jikinta kenan ta ajiye gefen gado zata dau doguwar rigarta dake linke ta ajiye saman akwati taga ya bude idonsa a hankali sae a cikin nata, zaro ido tayi with shock ta durkusa kasan dakin da sauri ta rufe fuskarta da gado taji kamar kasa ya bude ta shige don she is just wearing bra and pant, kauda kansa yayi daga kallonta ya mayar zuwa daya side din dakin ya lumshe idonsa, Khaleesat tafi minti uku bata dago kanta daga boyewar da tayi jikin gado ba tsabar kunya, a hankali ta lalubo rigar da ta cire a gefen gado, tana durkushe a haka ta saka rigar don ta kasa tashi tsaye, bayan ta mayar da rigar ta dago kanta a hankali taga har sannan yana facing daya bangaren dakin, da kyar ta mike kamar munafuka ta shiga banɗaki don bata yi la'asar ba, ta kulle kofar bandakin ta jingina jiki tana turo baki, ta fi minti goma a toilet din ta kasa fitowa duk da ta gama alwala, daga ƙarshe ta dake ta fito sai taga ya ma fita daga dakin, ita dai har lokacin kunya bai saketa ba, da ta sani bandaki ta tafi ta canza kayan, she thought he was sleeping deeply shi yasa har ta cire kaya a dakin. Ajay na zaune dakin da Hajja take wajen karfe bakwai da rabi na dare yana sauraronta, Aunty da Gimbiya Firdausi da Hajiya A'isha duk suna zaune dakin su ma ko wacce ta murtuke fuska, rai bace Hajja taci gaba tace "To ina amfanin tahowa da ita in haka ne? Aikin banza kenan ai in dai zaka kai ta wani waje ka ajiye bayan kasan al'adar mu ba haka take ba, sam baka dau al'adun mu a bakin komai ba Junaid a haka wai kuma kai ne Yarima me jiran gado, ke kuma Fulani wannan maganar ma har sai kin gaya ma Sarki? Akan me zaki gaya masa?" Gimbiya Firdausi tace "To baya ganin kowa da gashi Hajja, baya mutunta kowa, gwara da ta gaya ma sarki don shi kadai yake gani da mutunci kuma bazai ki jin maganar sa ba, banda raini da walakanci yaushe zai dauki yarinya bai ji kunyan idonmu ba ya kai ta wani wajen ya ajiye bayan yasan duk waje daya ake sauka idan sha'ani irin haka ya tashi, ita yarinyar er gidan uban wacece ita da bazata zauna a gidan nan ba? Wani irin fi'ili ne wannan yake son shigo mana da shi family? Ko akan sa aka fara aure? Auren nasa ma auren joni" Hajja ta kalli Junaid tace "Ka je ka maidota gidan nan har zuwa sanda za ku bar kasar nan da daddaren nan ba sai gobe ba, in ka san bamu kai ta zauna gida daya da mu ba da ka bar ta can Amurka kayi tahowar ka kai kadai tunda kai ne dolen Hadiyah ba ita ba" Aunty da Hajiya A'isha suka gyada kai alamar dai dai kenan yaje ya dawo da ita, After few seconds Ajay ya kalli Hajja calmly yace "Why is it a must sai ta zauna gidan nan? What if I have my reasons for taking her away?" Gimbiya Firdausi tace "Kin ji ko Hajja? Ai in bai yi fitsara ya nuna ba a isa da shi ba bazai ji dadi ba, reasons dinsa na banza da hofi, ita din nace er gidan uban wacece da bazata zauna nan ba? Mu da muke jinin sarauta bamu ce baza mu zauna da ita ba sai ita da ba kowan kowa ba kowar wake? Who the hell is she? Wallahi kar ka bari in yi mugun saɓa maka a kasar nan idan kace zaka kawo min iskanci Ahmad, ni ba sauran iyayenka da ka raina bace yanxun nan zan gyara maka zama wallahi, kuma ka sanar mana er gidan uban wacece yarinyar da tafi karfin zama cikin mutane...." Ajay ya kalli Hajja yace "Saboda wata al'ada can idan ina bukatar matata sai in ki tafiya inda zan tafi da ita kenan? Al'adar ce ta haramta in kebe da ita if the need of that arise?" Kallonsa su Aunty suka dinga yi da mugun mamaki jin kalamansa, duk kowa yayi shiru a dakin kamar anyi ruwa an dauke, can Hajja ta gyara zama tace "To kun dai ji bukatar ta yake, yana bukatar matarsa a kusa da shi don haka sai ku hakura da mita kuma haka tun da ya bada uxurin sa, kin ga ba reason din banza da hofi bane kamar yanda kika ce ke Firdausi, yi tafiyar ka sai da safe Junaid, ga abinci nan ba ci zan yi ba sai ka tafi maku da shi, Allah ya tashe mu lafiya" Yace "Ameen, sai da safe" Mikewa yayi without looking at anybody ya dau warmer din abincin ya nufi kofa ya fita daga dakin, Hajja tace "Tun da bukatar ta yake kun ga ko ai baza a tauyesa ba saboda wani dalili mara tushe, ku bar su kawai su yi zaman su a can, yaran yanxu ba kunya gare su ba kun dai ga kansa tsaye ya bada uxurin sa, yana kuma da gaskiya, shi yasa nace da ba a gaya ma Sarki ba, gashi nan dai kun ga yafi mu gaskiya...." Gimbiya Firdausi tace "Da yake shi fitsararre ne mara kunya ba, ya kamata ya kalle mu ya gaya mana wannan magana idan ba raini ba? Idan Jawwad ne yaushe zai yi haka?" Hajiya A'isha tace "Ai Jawwad bazai ma taɓa dauke matarsa idan ana sha'ani ba balle ya kawo mana zancen rashin kunya" Gimbiya Firdausi tace "Da yake shi ya koshi da tarbiyya ba, kin taɓa ganin yana musu da na gaba da shi ko kuma ace yayi abu yace bazai yi ba shi ga yanda zai yi?" Hajja ta hade rai don no matter what ta tsani a dinga maganganu kan Ajay, tace "Don yace yana bukatar matarsa sai kuma ya zama abun magana? Haramun ya aikata? Babu warce tafi sa gaskiya akan wannan batu duk inda za aje kuwa, laifi ne don ya fadi uxurinsa da za ku dinga hadasa da Jawwad? Naga dai halinsu ba daya ba, in Jawwad ne ko uxurin zai kashesa bazai yi magana ba, shi kuma Junaid bai yarda ya cuci kansa ba, he speaks for himself always, don haka bana son in kara jin maganar Yarima ya dauke matarsa a gidan nan" Babu wanda ya sake cewa komai a dakin ko wacce ranta babu dadi tsabar takaici da bakin ciki, can Gimbiya Firdausi ta mike ta fice daga dakin, Aunty dai takaici sai da ya saukar mata da wani mugun migraine headache nan take a wajen, kalmomin Ajay sai yawo suke mata a kai, wai yana bukatar matarsa, abun har ya girmama haka bayan duk shige shigen da take a can Nigeria, sosai hankalinta yayi matukar tashi a wajen... Ajay na sauka downstairs ya tarar babu kowa parlor duk yan matan gidan na Bedroom a sama, kitchen ya nufa zai dau plate da spoon, shi ba cin abincin zai yi ba don ya sha shayi, Khaleesat zai kai ma idan taga zata ci duk da bai ma yi niyyar kai mata ba, yana shiga kitchen din ya tarar da Jay da Hadiyah makale da juna, within seconds suka yi separating, Ajay dai har ya juya ya fita daga kitchen din ya bar warmer din abincin a nan parlon tunda babu plate yayi tafiyarsa... After a while Aunty ta tashi ta fita daga dakin Hajja tana jin ciwon kanta na tsananta, dakin da Gimbiya Firdausi suke ciki ta nufa amma sai taji kamar suna magana da Hajiya Sumayya kasa kasa, har sai da ta kasa kunne jikin kofar dake bude slightly bayan ta tabbatar babu wanda ke tahowa daga downstairs sannan ta iya jin abinda suke cewa, Ta ji Gimbiya Firdausi na cewa "To ai naga alamar wankin hula na neman kai ni dare ne Sumayyah, ina ga a duk masarautar mu babu wanda ya kai ni ƙin auren yarinyar nan da Junaid, yau ace yarinyar nan tayi ciki ta haihu a masarautar nan shikenan magana ta kare kuma, kin ga idan Allah ya bata namiji Yarima ya samu Magaji kenan fa, wanda hakan na nufin wataran dole ɗan nan da zata haifa yayi sarauta, yaron da uwarsa ba kowa bace facce er matsiyata er talakawa mara asali, Sarki yaki fahimtar cewa yanzu ba a auro bare a shigo da ita gidan sarauta, an dena wannan gangancin, ga 'ya yan 'yan uwa kaca kaca da ya kamata ace ya aura ma Junaid daya kamar yanda Jawwad ya auri Hadiyah, sannan yarinyar nan fa Bazawara ce ba budurwa ba babban abun takaicin, Sumayyah har yanxu fa ban hakura batun sai Junaid ya auri Shahuda ba, yau ace Shahuda ta auri Junaid kin ga dai saurauta kara kusanto mu yayi ba nisa yayi mana ba...." Hajiya Sumayyah tace "Kwarai kuwa Gimbiya zancen ki hakkun, yanxu kamata yayi a tado da batun Shahuda gadan gadan idan mun koma gida, kin san dai kina daya daga mutanen da sarki ke jin maganar su, amma ki bari mu koma Nigeria sai mu tsara yanda za mu yi cikin tsanake, nasan kilishi ma baza ta rasa abinda zata ce ba akan lamarin nan don ita ma tana bakin ciki da wannan aure, nasan ita kanta zata kawo solution din matsalar nan" Gimbiya Firdausi tace "Haka ne, Allah ya maida mu gida lafiya" Hajiya Sumayyah tace "Ameen, ana wani cewa ai shi ma Junaid din bai san da auren ba sai bayan da aka daura, a yanxu kam na ƙaryata hakan, bana jin zanyi kaffara idan na rantse cewar Yarima na sane da shirin Sarki, sarai ya san da auren kuma alamu sun nuna yana son yarinyar shi ma, banda haka ki ga fa shigar yarinyar na yau, komai na jikinta designers ne tana er matsiyata da ita, kuma ba wai kayan cikin lefe ba, don kaf lefenta babu irin wannan kaya masu zunzurutun kudi haka, duk designers ne jikinta fa Gimbiya, da nayi estimating kudin shigar nan da tayi yau sai da nayi takaici, wallahi duk yanda za muyi ma dole mu yi a kawo karshenta a gidan nan don bata da ce da zama matar ɗan sarki me jiran Gado ba, Shahuda ce tayi deserving wannan matsayin ba ita ba" Gimbiya firdausi ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace "Allah ya maida mu gida lafiya Sumayyah" Aunty tayi wani makirin murmushi bayan duk ta gama jin conversation dinsu tana gyada kai a hankali, a ranta kuwa tace "Sai dai in ni Hafsah bana numfashi ne za ku aiwatar da wannan nufi naku, amma baku isa ku wargaza min nawa shirin ba wallahi, Shahudar banza, ban gama da dayan nan dake gabana ba ku ke neman karo masa daya, gwara da aka yi akan kunne na, mu zuba da ku..." Juyawa Aunty tayi da sauri jin Footsteps, ta hango Jay yana haurowa sama hakan yasa ta bar bakin kofar da sauri, ta karasa har wajen stairs din kamar sauka zata yi, cikin nutsuwa tace "Jawwad yau ɗan uwanka ya shayar da mu ruwan mamaki" Jay dai kallonta yake yana haurowa don yasan Ajay take nufi, Aunty tace "Muna ta fadan bai kamata ya dauke matarsa ba bayan ba haka al'adar mu yake ba ya kamata ace ita ma tana gidan nan ayi komai da ita, buden bakinsa sai cewa yayi shi yana bukatar kebewa da ita ne shi yasa ya tafi da ita saboda uxurinsa, bai ji kunyan idanuwanmu ba ya fadi haka kansa tsaye, Hajja kuwa ta hadasa da Warmer din abinci tace sae da safe, is this proper Jawwad?" Jay dai bai ce komai ba yana tafiya slowly bayan yaji abinda Aunty tace..... *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence 07087865788* HALYSAAH PAGE 115 Khaleesat na zaune gefen gado Ajay ya shigo dakin Hotel din ta daga kai ta ɗan kallesa sai kuma ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da danna wayarta alamar she is chatting, Ajay ya ajiye ledan abincin hannunsa ya nufi gaban madubin dakin ya tsaya yana cire wrist watch din hannunsa yana kallonta ta madubin, dai dai nan ta daga kai ta kallesa ganin he is backing her, hada ido suka yi ta madubin which she never expect don bata san yana kallonta ba, ta sauke idonta a hankali sai kuma tace "Good evening" Banza yayi mata kamar bai ji ba, ita dai ta ci gaba da danna wayarta bata sake dago kanta ba, ya ajiye agogon ya shiga bandaki, ta taɓe baki ta sauka daga kan gadon ta duba ledan da ya ajiye taga takeaway din abinci ne, dama yunwa take ji rabonta da abinci tun wanda ta ci around 11am na safe, kan kujeran dakin ta zauna tana bude abincin bayan ta ajiye bottle water da Gwangwanin lemon dake cikin ledan akan table, har ya idar da sallah bata gama cin abincin ba cause ta raba hankalinta tana cin abincin tana danna wayarta, daga karshe ta ajiye sauran abincin don ta koshi, ta saci kallon bangaren da yake dai dai sanda ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa a kasa, hararansa ta dinga yi cikin duhun duk da ba ganinsa take ba, kawai zai kashe wuta bayan yaga bata gama abinda take ba, can ta taɓe baki ta hau saman gadon ta kwanta, da second bedsheet din kan gadon ta rufe har kanta ta ci gaba da Chatting dinta, babu haske kwata kwata a dakin sai na screen din wayarta da ta saka cikin bedsheet, bayan kusan awa daya ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta ta lumshe ido.... Can wajen karfe biyun dare ta farka ta fara laluban wayarta a inda ta ajiye kusa da ita zata je bandaki tayi fitsari, amma bata ga wayar ba, ta mike zaune tana laluba beside drawer nan ma bata ji alamar waya ba, sauka tayi daga kan gadon tana tafiya a hankali ta zaga ta inda switch din wutan dakin yake, being careful kar taje ta buge da wani abu, tumble ta kusa yi kansa yana zaune kan darduma ya turata daga gabansa, tana komawa baya a hankali kamar zata yi kuka tace "Ni switch din wuta zan kunna fa" Jin bai tanka ta ba ta mike tsaye, a haka ta laluba ta kunna wutan dakin ta juya ta kallesa, sai kuma ta kalli kan gado, mamakin yanda wayarta ya dawo tsakiyar gado ta fara yi bayan tasan kusa da ita ta ajiye kafin tayi bacci, taga ya mike ya ci gaba da sallan sa, ta fi minti daya tsaye tana kallon wayar, can ta shiga bandaki, tana fitowa ta hau saman gadon ta dau wayar ta bude Password din don akwai password jiki ta duba abinda zata duba sannan tayi kwanciyarta wondering how the phone changed position, juyawa tayi ta kallesa taga he is still praying, idan ma shi ya dauka ba accessing wayar zai iya yi ba because of the password, a haka bacci ya dauketa. Da asuba Khaleesat tayi mika ta bude idonta dai dai lokacin da take tashi yin Sallah, tsaye taga Ajay gaban mirror wearing just short yana goge gashin kansa alamar wanka yayi, hada ido suka yi ta madubin tayi saurin mayar da idonta ta rufe kamar warce taga mugun abu, kamar munafuka ta ja duvet din jikinta ta rufe har kanta da shi ta wani turo baki, she wish she can unsee that muscular body of his, har karfe shidda da yan mintuna bata yarda ta cire duvet din da ta rufe kanta ba gashi tana son tashi tayi sallah don tasan lokaci ya wuce amma ta kasa, ji tayi kamar ya bude kofar dakin hotel din, cikin dubara ta ɗan bude fuskarta tana lekowa ta duvet din taga fita yayi daga dakin, da sauri ta mike zaune ta cire duvet din jikinta ta sauka daga kan gadon ta daure gashinta sannan ta saka hularta ta wuce bandaki, ta idar da sallah tana cikin yin azkar dinta sai gashi ya shigo dakin, ita dai bata yarda ta daga kanta ba har ya wuce ta ya tafi ya zauna kan daya daga kujerun dake dakin ya dau wayarsa yana dubawa, ta idar da azkar dinta ta mike ta linke pray mat din ta ajiye sannan ta zauna gefen gado ba tare da ta cire Hijab din jikinta ba, satan kallonsa tayi tace "Ina kwana" Danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba balle ya amsa, ta turo baki ta kwanta edge din gadon ta juya masa ba, sai a sannan ya kalleta, dai dai nan aka yi knocking kofar dakin ya mike ya nufi kofar ya bude, ya amshi tray din Hot coffee da Croissant daga hannun daya daga ma'aikatan hotel din sannan ya kulle kofar ya koma inda yake zaune ya zauna ya ajiye tray din kan table. Cikin minti ashirin Khaleesat ta gama shirin da take ta dau jakarta bayan ta saka takalmi ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, sai taga kamar kayan ma yafi na jiya kyau, yau ma dai she look expensively beautiful, kamar dai jiya yau din ma designers ne kaf jikinta, kayan yayi mata mugun kyau ba kadan ba, juyawa tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin hotel din, yana tsaye jikin Taxi yana jiranta ta fito, tun da suka hada ido ta sauke nata idon ta bude motar ta shiga, after some seconds ya dauke idonsa daga kanta ya bude gaban motar ya shiga, Drivern taxi din ya ja motar suka bar wajen, tun da Khaleesat ta lura da inda za su je gabanta ke faduwa don sarai ta gane unguwan, Taxi din na parking gaban apartment din Ajay ya bude motar ya sauka, a hankali ita ma ta bude motar ta sauka ta bi bayansa walking slowly, bell ya danna don kofar a kulle yake, Iklima ce ta bude kofar ganinsu ta koma gefe without much attention tace "Sannu da zuwa yaya" Bai ce mata komai ba ya shiga parlon, Khaleesat ta bi bayansa ba tare da ta yarda ta hada ido da Iklima da ta bi ta da ido tana kare ma dressing dinta kallo ba, juyawa yayi yana kallon Iklima fuska daure yace "Ke baki iya gaisuwa bane don uwarki?" Tayi yake tana sosai kai tace "Lahh yaya nace fa sannu da zuwa" Sai kuma ta kalli Khaleesat tace "Ohh sannu da zuwa" Khaleesat dai bata kalleta ba tace "Yauwa nagode" Cire takalmanta tayi ta bi bayan Ajay tana tafiya a hankali har suka karasa cikin parlon, Iklima ta bi ta da wani shegen kallo, Gimbiya Firdausi ce zaune parlon da Yayar mahaifin Hadiyah Hajiya Shema'u sai Hajiya Sumayya, Ajay ya gaishesu gaba daya, Hajiya Shema'u ce kadai ta amsa masa da kyau, Khaleesat ma ta gaishesu nan ma ita kadai ce ta bata attention dinta, Hajiyah Shema'u na kallon Ajay tace "Ita ce matar taka, da yake jiya bana jin dadi da wuri na bar Convocation arena din bamu hadu da ku a can ba" Ajay yace "Ya jikin yanxu?" Tace "Na ji sauki Alhamdulillah" Kallon Khaleesat tayi tace "Maa sha Allah amarya, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya, ki zauna lafiya da mijin ki kin ji, yi kin yi bari kin bari kin ji, kuma ki zama mai hakuri da kauda kai, Allah Ubangiji ya zaunar da ku lafiya ya baku zuri'a dayyaba" Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta without saying a word tana wasa da veil dinta, Hajiya Sumayya kuwa sai kallon kayan jikinta take da jakar hannunta, Ajay ya kalli Hajiya Shema'u yace "Za mu je wajen Hajja a sama" Hajiya Shema'u tace "Toh sai kun sakko" Mikewa yayi ya bar parlon, Khaleesat na ganin haka ita ma ta tashi ta bi bayansa suka nufi stairs, Gimbiya Firdausi ta bi su da kallon gefen ido har suka haura sama, Ajay ya bude kofar dakin da Hajja ke ciki ya shiga Khaleesat na biye da shi, Hajja na zaune dakin tare da Hadiyah da duk yan matan gidan sai Hajiya A'isha, Khaleesat ta zauna kasan carpet kanta a kasa, Ajay ya zauna kan kujera ya gaida Hajja da Hajiya A'isha, sauran yan matan duk suka gaishesa ya amsa masu a takaice, Hajja ce kadai ta amsa gaisuwar Khaleesat a dakin, sannan ta kalli yan matan dakin tace "Ba ku ga matar yayanku bane?" Dukansu suka kalli Khaleesat kamar sun ga bola, shi dai Ajay daya bayan daya yake bin su da kallo, a walakance duk suka gaisheta banda Hadiyah da ta hade rai tun shigowar Khaleesat barin da taga handbag din dake hannunta da rigar jikinta, Shahuda kuwa danna wayarta kawai take kamar bata san Allah yayi ruwan Khaleesat a dakin ba, Khaleesat dai ta amsa gaisuwar su Khadijah tana ɗan murmushi jikinta a sanyaye, ita kanta tasan ba karamin gata Ajay yayi mata ba na dauketa a gidan nan, she felt really grateful da hakan da yayi mata, don kilan da bai dauketa ba tsaf zata samu heart attack kafin su bar kasar, sam bata ga alamar mutunci da daraja a gun yan matan gaba dayansu ba, as if they have grudges against her from anywhere, daga su har iyayensu ita kam bata san me tayi masu ba, hatta Hajja ba wai wani sake mata take ba, kawai babu yabo babu fallasa ce ita, Hajiya A'isha ta mike ta fita daga dakin ta tafi dakin da Mami ke ciki, zaunawa tayi tana kallon Mami tace "Lallai Fulani ba karamin jihadi kika yi ba da kika wargaza auren shegiyar yarinyar can da Jawwad, ke kinga irin kayan da ta ke saka Junaid yake siya mata kuwa? Kaf kayan nan babu su cikin lefenta don ai mun ga lefen kafin a kai mata, designers fa ta saka jiya, yau ma haka" without much attention Mami tace "To ku kuka ma lura da abinda ta saka, ni kam ban gani ba tunda ba abinda ya shafeni bane, i have no business with her as far as burina ya cika na raba ɗa na da ita, yanxu ba gashi ya hakura ya rungumi Hadiyah ba kamar ba ayi komai ba, ai ni ba abinda zan ma Allah sai godiya, dama nasan komai zai wuce, duk phases din tension din nan da ya shiga da damuwa nasan na lokaci ne, to ba gashi ya wuce ba yanxu sai labari, shi Sarki tunda yace yaji ya gani ɗan sa ya zauna da Bazawara buzuwa to ga su ga ita Allah ya bada sa'a, da yake bata gabana wallahi ban ma lura da kayan nata ba...." Hajiya A'isha ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru bata sake cewa komai ba, Allah ya sani duk wata hanyar da zata cusa ma er ta Iklima Junaid babu wanda bata bi amma abun ya ci tura, bata da wani burin da ya wuce a yau taga Iklima na auren Yarima, amma duk da haka ba hakura tayi ba yanxun ma, tasan ta yanda zata billo ma lamarin don bazata zuba ido wata matsiyaciya ta haifar masa Magaji ba, yau Iklima ta zama matar Yarima kuma Allah ya bata ɗa namiji ai mulki ya kara kusanto zuri'arta kenan duk da ita din er sarki ce, da Gimbiya Firdausi da Hajiya Sumayyah sai Kilishi warce ita ce Mahaifiyar Mukhtar cousin din su Junaid uwarsu daya ubansu daya kuma uwarsu ita ce babban matar marigayi sarki Ahmadu wanda shi ne babansu Mai martaba na yanxu, mahaifiyar tasu ta ma riga babansu sarki Ahmadu rasuwa kuma ita Allah bai bata ɗa namiji rayayye ba don sai da ta haifi maza biyu duk suna rasuwa kafin ta haifi Gimbiya Firdausi warce ita ce first born a family din Sarki Ahmadu, daga uwarsu Gimbiya Firdausi sai mahaifiyarsu Hajiya Shafa'atu warce ita ce matar sarki ta biyu, Hajiya Shafa'atu da kanwarta Maryam kadai uwarsu ta haifa ta rasu, sai dai sarki ya rigata rasuwa, Hajja ce ta uku a matan sarki duk da rana daya aka aurosu da Baabarsu Hajiya Shafa'atu kuma Hajja ta ma rigata haihuwa, wanda ita kuma Hajja 'ya yanta uku kadai a duniya, da marigayi Baban Jawwad wanda is almost age mate da Gimbiya Firdausi, sai Mai martaba na yanxu sannan uwar Hadiyah me suna Maimuna da suke ce ma Ummi, bayan Hajja sai uwar Hajiya A'isha warce ita ce matar sarki ta karshe, ita kuma Hajiya A'isha ita kadai ce gun uwarta, kuma uwar tata na nan da ranta har yanxu a gidanta na Bauchi, ajiyar zuciya Hajiya A'isha ta sauke a ranta ta sha alwashin ko ta halin yaya ne sai Junaid ya auri Iklima, suna komawa zata je ta samu Baabarta da wannan batu don su san yanda za ayi. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 116 Khaleesat na shiga apartment din ta samesa tsaye parlor, ta saci kallonsa zata wuce sama cikin tsawa yace "Come back here" Tsayawa tayi sai kuma ta juya ta kallesa ta bata fuska, using a serious tone yace "From henceforth Kika sake ce min zaki je wani waje zaki sha mamakin abinda zan maki i promise you, ba dai baki da kunya ba? Zan yi maganin ki" Kamar zata yi kuka tana turo baki tace "To ko ba karatu muka tsaya yi ba muna da Quiz da za mu yi" Da gudu Khaleesat ta wuce sama ganin ya nufota fuskarsa daure, ta shige dakinta ta kulle, sai da ta zauna gefen gado na kusan minti goma don seriousness dinsa ya tsorata ta, can ta e baki ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito, bayan ta idar da sallah ta karasa bakin kofar a hankali ta bude tana leka downstairs amma bata ganin komai, corridor ta fito ta leka taga baya parlorn, a hankali ta fara sauka stairs har ta shigo parlon taga alamar ya tafi, dakinta ta koma ta dau duk kayan matan da Safiyyah ta kawo mata ta sake sauka kasa ta shiga kitchen tayi disposing dinsu a dust bin sannan ta koma sama, wanka tayi ta canza kaya zuwa na bacci, sannan ta dau wayarta ta bude ta kunna data ta kwanta, ko yunwa bata ji don hankalinta duk na kan abinda zata yi a wayar, hancinta ta kai wayar jin kamar kamshin turarensa a jiki, she was very surprise, ta sake shinshina wavar to be sure of it, taji kamshin turarensa dai wayar yake, can dai ta bude WhatsApp dinta, after waiting for some second for her messages ta fara scrolling tana neman num Jay, duk iya dubawanta bata gani ba, ta shiga WhatsApp call logs dinta nan ma babu numbersa, mikewa zaune tayi with shock tana kallon wayar babu ko kiftawa, nan tayi searching Housemate da sauri taga bai fito ba, ta koma contact dinta nan ma taga babu number, kasa ko kwakkwaran motsi tayi a inda take zaune, cikin mutuwar jiki ta fara kokarin dialing number nasa thinking she still have it off hands kamar kwanakin baya amma duk yanda ta yi kokarin rubuto number sai taga ba haka yake ba, wasu hawaye ne suka cika idonta ta fada kan gado tana shesshekan kuka, ta yaya yasan password dinta har ya dau wayarta, is this even possible, ita bata taba bude wayarta a gabansa ba ai balle yaga password dinta, kuka sosai take ta ma rasa abinda take ji a ranta, me yasa zai dau mata waya bata nan... Washegari Khaleesat taki tafiya school tsabar bacin rai, tana ta kwance har karfe uku na yamma ko wank ta yi ba balle breakfast, idonta duk sun kumbura don kuka, tun safe Safiyyah ke kiranta taki daga wayar daga karshe ma ta kashe wayar, sai kusan Magrib ta sauka kasa ta nemi abinda zata ci saboda yunwan da take ji, ga mamakinta sai taga foodstuffs bakin kofar kitchen din, da Household items for cleaning, ta hade rai ta tsallake kayan tayi wucewarta cikin kitchen din, bayan ta hada shayi ta debi cookies ta wuce sama abun ta.... Washegari ma Khaleesat taki zuwa school tayi ta kwanciya a daki, wajen karfe sha daya ta kunna wayarta kamar Safiyyah jira take sai ga call dinta ya shigo, Khaleesat ta dinga kallon kiran kafin tayi picking tayi shiru, Safiyyah tace "Me yasa kika kashe waya tun jiya Khaleesat? Hope you are okay?" A hankali Khaleesat tace "Lafiya lau" Safiyyah tace "To me yasa kika kashe wayar? Kuma me yasa baki zo school jiy yau ba bayan kin san Friday ne Quiz din mu? Are you sure you are okay?" A hankali Khaleesat tace "Can you come over after school please?" Safiyyah tace "Sure, amma dai inji mijin ki baya nan?" Khaleesat ta hade rai tace "Bana son haka Safiyyah, it's not funny" Safiyyah ta tabe baki tace "Toh naji, bayan azahar zan taho" Khaleesat tace "Apartment dina za ki zo" Safiyyah tace "Apartment din ki? Har yanzu kina apartment din kenan?" Khaleesat tace "Eh" Safiyyah tace "Ohk to i will come in sha Allah after today's class" Daga haka ta katse wayar, a hankali Khaleesat ta ajiye wayar hannunta looking so gloomy, mikewa tayi ta sauka downstairs har sannan foodstuffs din suna nan bakin kofar kitchen kuma bata ga alamar an shigo gidan ba duk yau, ta kwashi kayan abincin ta kai kitchen bayan ta ajiyes inda ya kamata ta hada breakfast ta fita daga kitchen din, sama ta tafi don kar ma ya zo gidan ya ganta a parlorn, bayan ta gama breakfast din tayi wanka ta shirya sannan ta zauna gefen gado har sannan tana jin ranta babu dadi, ko bude WhatsApp din bata sake yi ba duk da tasan Umma ta ajiye mata sako, a haka Safiyyah ta zo gidan ta sameta, Safiyyah na kallonta bayan ta bude mata kofa tace "Ikon Allah, me ya faru? Why are you like this?" Hawaye ya cika idon Khaleesat tace "Kinsan daukar wayata yayi ya goge number Housemate dina?" Safiyyah ta zaro ido irin tayi mugun mamakin nan tace "Ya goge number Housemate din ki kamar yaya? Ya san password din ki ne?" Khaleesat na shesshekan kuka tace "Nima ban sani ba, kawai i can't find the number again, har chat din mu an goge gaba daya" Safiyyah ta zauna gefen kujera still looking surprise tace "Amma ta yaya kika san shi ya goge ne wai?" Khaleesat tace "Ba na zo downstairs debar maki kayan shayi ba, and we left him upstairs? To ni da na koma na dau wayar naji yana kamshin turarensa beside in ba shi ba aljani ne zai dau wayar ya goge min number?" Safiyyah ta gwalo ido tace "Kika sani? Idan aljanin ne fa yaga kina neman kai kanki wuta ya goge lambar?" Wani shegen kallo Khaleesat tayi mata, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "To Allah ya kiyaye amma abu bai yi dadi ba, ta yaya za a goge number a whole Housemate din ki just like that a wayarki?" Khaleesat ta wani harareta, sai kuma tace "Ni dai bani wayar ki in dau number" Safiyyah tace "Wani number?" Khaleesat tace "Na Housemate na" Safiyyah ta gyara zama tace "Tabb, ai tun da naga yanda ya dinga rungume matarsa suna makale juna kamar za su dawo daya na goge lambarsa a wayata don ina taya ki kishi, ta yaya ke kina nan kina gantalar da aurenki saboda shi, shi kuma yana can yana bidirinsa da matarsa? Ke kina ganinsu kinsan an dirji amarci yanda ya kamata, shi yasa naji haushi na goge numbersa" Khaleesat ta hade rai tace "Me yasa za ki goge don Allah? Me yayi maki?" Safiyyah ta mike tace "Kinga yunwa nake ji kamar in ci babu, don Allah ki taimaka min da abinci, in kin dawo sai mu duba call logs nasan zaki gane number ai, ko da na goge yana nan call log" Khaleesat tace "Toh bari in dafa maki Indomie" Tashi tayi ta tafi kitchen feeling so much relieved, Safiyyah ta tabe baki ta fiddo wayarta ta canza saving din number Housemate, can kuma tayi tunanin kar kuma ace Khaleesat ta san farkon numbers din nasa tana dialing ya fito, hakan yasa kawai tayi copying numbersa tayi pasting ta WhatsApp number dinta ta bar shi wajen, sannan ta goge contact din nasa a wayarta, har ma da chat dinsu na WhatsApp sai da tayi deleting ta yanda dai Khaleesat bazata ga number ba ko ta duba.... Khaleesat was so disappointed bayan ta duba wayar Safiyyah gaba daya babu alamar number Housemate dinta, ga dai shi tana ganin number a idonta amma in ta rubuta sai taga ba haka yake ba, ita dai Safiyyah tayi tagumi tana kallonta with serious face, sai kuma tace "Wallahi da na sani da ban goge ba, ni kuma nan taya ki kishi nake tun da naga hotunan Convocation din da suka yi da matarsa, ban san ke ko a jikin ki ba, baki ma ji haushi ba, ai da ban goge ba in nasan haka" Khaleesat tayi mata banza ta kauda kanta trying hard not to cry, Safiyyah ta tabe baki a ranta tana mamakin halin Khaleesat. Khaleesat na zaune department dinsu tare da Safiyyah, fitowar su daga aji kenan sun gama group discussion don exams dinsu is around the corner, Safiyyah ta gama wayar da take ta juya tana kallon Khaleesat ganin fuskarta babu walwala kuma tayi nisa tunanin da take, Safiyyah tace "Me kuma ya faru? Sarkin 'yan damuwa, Why is ur face like this?" Khaleesat ta dan yatsine fuska tace "Nothing, kawai na gaji ne sosai" Safiyyah tace "Kin gaji ranan Monday? Karatu kika yi throughout weekend ne?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Laundry nayi kawai jiya" Safiyyah ta dan kalleta tace "To jiya din ya je apartment din?" Khaleesat ta juya ta kalleta kamar jiran tambayar take ta girgiza mata kai a hankali tace "Bai zo ba" Safiyyah tace "To wai ba nace ki kirasa ba Khaleesat?" Khaleesat tayi shiru don tun last week Safiyyah ke fama da ita ta kira Ajay don rabonsa da gidan tun ranan da ya ajiye mata foodstuffs da Household items, washegarin ranan kuma ya tura mata 5k dollars ta account dinta, and this was almost 2 weeks ago, amma tayi ta nuna ma Safiyyah ita bazata kirasa ba, Safiyyah tace "Ke in an gaya maki magana kwata kwata baki ji, nace ki kirasa don this is so unusual of him ace har sati biyu bai je apartment dinki ba to see if you are alright" Khaleesat kamar bazata tanka Safiyyah ba kuma sai ta bude jakarta ta ciro wayarta ta shiga call logs ta nuna mata, amsan wayar Safiyyah tayi taga ta kirasa har sau hudu a ranaku daban daban last week, amma duk bai daga ba, Safiyyah ta daga kai ta kalleta tace "Are you sure he is okay?" Khaleesat ta bude hannu alamar bata sani ba ita ma, bayan few seconds a hankali tace "Har WhatsApp message fa nayi masa but he didn't reply" Safiyyah tace "To amma dai nace ki je gidan ranan Friday kika ki, kika san ko bashi da lafiya ne all this while? Kema kinsan no matter how annoying you can be haka nan yake maki duk duk abinda ya kamata, meyasa baza ki je gidan ki duba if he is okay ba" Khaleesat ta zaro ido tace "What if stepmom dinsa da aunties suna nan har yanxu? ni dai bazan je ba tsoro nake ji" Safiyyah ta wani kalleta tace "What's ur business with them? Ai dai ko suna nan sun san ba wajen saurayinki kika je ba" Khaleesat ta tabe baki tace "Ba inda zan je ni dai, i am afraid of them" Safiyyah tace "To kin huta" Canza topic din Safiyyah tayi, ita dai Khaleesat tayi shiru bata cewa komai, kana ganinta kasan she is not herself kawai gata nan gata nan dai ne, Safiyyah tace "Yauwa wai har yanxu baki samu number Housemate din naki ba, ina ta son in tambayeki sai inyi ta mantawa" Khaleesat taki tanka ta, Safiyyah ta mata kallon gefen ido, she could see how disturbed she is, a ranta kuwa taji dadin kin picking calls dinta da Ajay yayi gashi ta damu ta rasa sukuni, after half an hour Khaleesat tayi ordering Lyft da zai maida ta gida don gaba daya bata ma san hiran da Safiyyah ke mata ba she is not just assimilating, ta ma rasa me ke damunta this past days don ko abincin kirki bata ci, karatun ma ko ta fara sai taga bata fahimta, haka tayi weekend kamar mara lafiya taji gidan ma duk ya isheta, har ta isa gida bata sani ba cause she was just sitted absently a motar har sai da drivern Uber yayi mata maganar sun isa, bayan ta sauka daga motar ta shiga apartment dinta ta zauna kan kujera ta jingina da kanta, kullum ta dawo gidan keenlv take kallon ko ina na apartment din ko zata ga alamar da zai nuna ya zo amma sai taga babu ko wani alamar da ya nuna hakan, after almost 10 minutes of sitting down at the parlor ta bude jakarta a hankali ta ciro wayarta, numbersa tayi dialing ta tsura ma screen din wayar ido, amma har ya katse bai daga ba, turo baki tayi ta ajiye wayar gefen kujera. Ranan laraba Khaleesat sun fito daga lectures Safiyyah sai bata labarin Get together din da za su hada bayan exams take, don har da ita a masu shirye shiryen get together din, ita dai Khaleesat kawai tana zaune gefenta ne tana kallonta, Safiyyah ta rike haba tace "Ai ko ranan karya zan ma Ya Musty ince zan je apartment din ki baki da lafiya kuma mijinki ya je Nigeria, don kusan till down fa za mu yi a partyn..." Safiyyah ta gaji da surutunta ita kadai ganin Khaleesat ba biyeta zata yi ba tace "Ni dai tunda ba mu da abinda za mu yi gobe a makarantar nan bazan shigo ba gaskiya bacci na zan vi, ko ke za ki shigo?" Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta girgiza kai tace "Ko ran Friday ma ni bazan shigo ba na gaji, zan yi karatu a gida" Safiyya tace "You look pale kamar baki da lafiya" Khaleesat tace "I am having headache" Safiyyah tace "To Allah ya sauwake, in kin koma gida sai ki sha magani" Khaleesat bata ce komai ba tayi order din Lyft da zai maidata gida, Safiyyah tace "Wai kar ki ce min har yanxu Ajay bai je apartment din ki ba?" Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace "Ko ki rakani can gidan nasu yau?" Safiyyah ta rike haba ganin yanda tayi request din da sauri kamar tana jiran tayi mata tambayar, Can Safiyyah tace "Uhm, ni kaza? Salon Yaya Ajay ya kora ni ko ya hadani da karensa in shiga uku" Khaleesat tace "Saboda me zai kore ki? Abinda ke ce ma kika fara assuming ba shi da makarantar nan bazan shigo ba gaskiya bacci na zan vi, ko ke za ki shigo?" Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta girgiza kai tace "Ko ran Friday ma ni bazan shigo ba na gaji, zan yi karatu a gida" Safiyya tace "You look pale kamar baki da lafiya" Khaleesat tace "I am having headache" Safiyyah tace "To Allah ya sauwake, in kin koma gida sai ki sha magani" Khaleesat bata ce komai ba tayi order din Lyft da zai maidata gida, Safiyyah tace "Wai kar ki ce min har yanxu Ajay bai je apartment din ki ba?" Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace "Ko ki rakani can gidan nasu yau?" Safiyyah ta rike haba ganin yanda tayi request din da sauri kamar tana jiran tayi mata tambayar, Can Safiyyah tace "Uhm, ni kaza? Salon Yaya Ajay ya kora ni ko ya hadani da karensa in shiga uku" Khaleesat tace "Saboda me zai kore ki? Abinda ke ce ma kika fara assuming ba shi da ba shi da lafiya? Kilan kuma hakan ne, don ni ban taba kiransa bai daga ba ko bai bi kirana ba, even the messages i sent him on Whatsapp tick just once, he is not online for more than a week, kuma karen baya gidan yanxu ai"Safiyyah tayi shiru tana kallonta ganin damuwar dake fuskarta, can tayi wani murmushi tace "Toh amma duk kinsan this is unusual of him amma kika ki zuwa gidan ki dubasa yau kusan sati uku?" A hankali Khaleesat tace "Allah tsoro nake kar inje su Aunty suna gidan har yanxu, ni tsoronsu nake da gaske" Safiyyah tace "To bari in baki shawara, bakin ki alekum ki shirya ki je da daddare, kinsan dai da daddare definitely suna daki balle wannan katon gidan ma har ki shiga ki fita babu wanda zai sani" Khaleesat tace "Tabdi, da daddare fa,Aa ni bazan iya zuwa da daddare ba" Safiyyah tac shikenan ke kika sani, tunda baki jin magana, kar ya sa ki je" A haka suka rabu Khaleesat ta koma gida gaba daya bata da walala, tana komawa nan parlor ta kwanta kan 3 seater saboda azababben ciwon da kanta ke mata, sai take jin kamar zazzabi ne ma zai rutera gashi ruwan shayi kawai ta sha kafin ta fita daxu, don ko girkin ma bata yi yanxu. HALYSAAH PAGE 117 Sai kusan karfe hudu Khaleesat ta iya mikewa ta bar parlor tana tafiya da kyar ta wuce sama zuwa dakinta tana rike da wayarta a hannu, ta zauna gefen gado ta sake dialing number Ajay tana kallon screen din wayar babu ko kiftawa, yanxu ma dai har ya gama ringing ba ayi picking ba, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gadon tana jin kamar tayi kuka, bata san sanda kukan ya taho mata ba, ita kanta bata san dalilin kukan ba, tayi me isarta ta gaji sannan ta tashi tayi karfin halin shiga bandaki ta dauro alwala ta fito zata yi sallan la'asar, sai karfe bakwai da rabi na dare Khaleesat ta iya sauka downstairs daga kwancen da take zata je kitchen ta dafa taliya, rabonta da abinci har ta mance sai dai ta sha shayi da cookies, ko kuma ta sha lemo da snacks, bata iya ta ci taliyar da ta dafa ba kawai ta rufe don baya mata dadi ma a baki, ta shiga bandaki ta wanke bakinta tayi wanka sannan ta dauro alwala ta fito, ta kwanta kenan wajen karfe takwas da minti sha biyar tana replying message din Ummanta da tayi mata tun da safe sai ga kiran Safiyyah ya shigo wayarta, picking call din tayi ta kai kunne, Safiyyah tace "Ya ciwon kan yayi sauki?" A hankali Khaleesat tace "Alhamdulillah..." Duk da har sannan tana jin ciwon kan ga sanyin da take ta ji tun da ta fito wanka, Safiyyah tace "Ajay din ya kira ki ne?" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "Hello" a hankali Khaleesat tace "Bai kira ba" Safiyyah tace "Sai yanxu na sake tabbatar da mafarki na" Khaleesat tace "Na me?" Safiyyah tace "Na ce maki da nayi bashi da lafiya mana, kinsan ba sallah nake ba, ai ko tun karfe shidda bacci ya daukeni farkawata kenan, to mafarki nayi da gaske ba shi da lafiya wannan driver din nan me kai ki school ne ke kula da shi don su Stepmom dinsa ma sun tafi da dadewa, daga shi sai Dreba ne a gidan in gaya maki, kinsan ni bana mafarkin banza ko tatsuniya, don haka wallahi idan har abu ya samesa hatta Mai martaba bazai taɓa yafe maki ba don kece ya kamata idan kika ga jikinsa yaki dadi ki kira gida ki sanar masu, yanda aka basa amanarki ku ka taho kasar nan haka Mai martaba ya damka maki amanar magajinsa ko da bai bude baki ya furta ba, amma yau sati biyu da kwanaki baki san halin da bawan Allah yake ciki ba gashi ya dena hawa WhatsApp kwata kwata sannan baya iya daga kira, amma kina apartment din ki hankalin ki kwance tun da ya cika maki gidan da Foodstuffs sannan ya tura maki isassun daloli a account din ki, wallahi ki ji tsoron Allah Khaleesat" Khaleesat da ke ta sauraronta ta ɓata fuska tace "To wai ni ya zan yi ne bayan nace ki rakani gidan kin ki, ko daxu fa sai da na sake kiransa bai daga ba, to ya zan yi?" Safiyyah tace "Aikin banza kenan ai, baki san inda gidansu yake bane da za ki yi ta doka masa kira ki damesa, kila ma bai san inda wayar yake ba yana fama da kansa" Khaleesat ta mike zaune ta jingina da gado looking so disgruntled, Safiyyah tace "Wallahi ki ajiye batun wasa mafarkin da nayi kenan da magariban nan, don haka ki dau wayarki yanxu kiyi order din Lyft ki tafi gidan ki dubo halin da yake ciki, kina ta wani tambayar ya za ki yi sai kace baki san hanyar gidan ba" Khaleesat ta wani bude ido tace "Da daddaren nan?" Safiyyah tace "Kakan dare, karfe takwas da rabi ne dare? As far as zaki samu Uber ina ruwanki da lokaci?" Khaleesat tace "Ni bazan iya zuwa da daddaren nan ba sai dai gobe da safe idan Allah ya kai mu" A ɗan fusace Safiyyah tace "Ke kika sani, dama ba a taɓa baki shawara ki dauka, kuma ni dai babu shegen da zai ce kawarki bata gaya maki gaskiya, i know i am trying my best, rashin lafiya ai ya take komai ko da kuwa mutum enemy dinka ne, amma ke duk yanda za a sa ki a hanya sai kin nuna taurin kai kin maida mutum ɗan banza, ke na gaji da halin ki wallahi, haba na kiraki ina kona ɗan katina amma sai jan magana kike yayi tsayi, idan abu ya samesa nasan hankalin ki zai fi na kowa kwanciya tunda dama mijin wata kika dauka kika makala a ranki" Daga haka Safiyyah ta katse wayar, Khaleesat ta ajiye wayarta a hankali ta koma tayi kwanciyarta, she made up her mind to go to the house tomorrow morning, ta yaya za ta ce mata taje da daddaren nan, after some minutes ta jawo wayar a hankali ta shiga WhatsApp, dubawa tayi ko Umma ta mata reply amma taga bata hau ba, instead sai message din Aunty Farida ta gani tana tambayarta Junaid, ajiye wayar tayi, tayi lamo kan pillow kamar me tunanin, bayan kusan minti goma kawai ta sauka daga kan gadon ta bude press din dakin ta dau hijab dinta har kasa ta dora kan red color Chemise dake jikinta, ta dau wayarta ta fita daga dakin ta sauka downstairs, zaunawa tayi parlor tana danne dannen wayarta, after almost 15 mins ta mike ta kashe wutan parlon ta kunna Flash din wayarta ta nufi kofa ta bude da makulli ta fita daga parlon sannan ta kulle kofar da key din, tana rike da makullin a hannu ta nufi Lyft dake jiranta, ta bude bayan motar ta shiga, wajen karfe tara da minti ashirin suka iso gidan, gabanta sai faduwa yake bayan ta sauka Lyft din ta shiga cikin gidan tana tafiya a hankali har ta isa entrance din parlon, bude babban kofar tayi ta shiga ciki sannan ta tura a hankali ta rufe tana kalle kallen cikin parlon, Laptop dinsa dake parlor a bude take kallo, kamar ance ta juya tayi ido hudu da Legend da yayi saurin shigowa parlorn alamar yaji motsin an shigo, tun bai fara haushi ba ta zaro ido tana kokarin bude kofar da sauri zata fita amma tsabar rudewa yasa ta kasa, da gudu karen ya nufota yana haushi, ta fasa ihu tayi wurgi da takalman ƙafafuwanta har da makullin hannunta da waya ta tattare hijab dinta tun bai karaso kusa da ita ba ta nufi up stairs da gudu yana ganin haka ya bi ta, bata san sanda ta isa part din Ajay ba kawai ganinta tayi a cikin parlonsa ta nufi Bedroom dinsa a guje ta bude kofar jikinta na rawa, Ya fito wanka kenan ko gama goge jiki bai yi ba ya dau rigar pajamas dinsa dake ajiye gefen gado zai saka akan short din jikinsa ya fita saboda haushin da yaji Legend ke yi kawai ta afko cikin dakin ta tafi da gudu ta kankamesa ta baya jikinta na rawa tana cewa "Na shiga uku, wallahi cizo na zai yi, don Allah ka taimake ni ka koresa" Ajay bai gama recovering daga rikon da tayi masa ba bayan ya sake pajamas din hannunsa yana kokarin regaining posture dinsa a kusa da gadon da suke tsaye sai ga Legend har cikin dakin yana haushi, ai kuwa karen na ganin yanda ta rike Ajay ta baya yayi tunanin attacking dinsa ta shigo yi, ya doka wani uban tsalle ya nufi har inda suke tsaye ya cafko dogon hijab dinta, ihu ta dinga kurmawa tana kara makale Ajay at the same time ta tube hijab din jikinta ta cillar, Ajay da duk tayi confusing dinsa yayi saurin juyo da ita suna facing juna ya rufe bakinta da hannunsa cause she is disturbing the peace of the neighborhood with her shout gashi dare ne, ai ko ta kara kankamesa as if that's the only way she will be saved from the barking dog, loosing stamina dinsa yayi all of a sudden sai ga su tim sun fada saman gado, lokaci daya ya fara kokarin banbareta daga jikinsa yana komawa baya ta yanda she won't cross boundary ita kuwa sai sake kankamesa take, kasa kora Legend dake ci gaba da haushi yayi don ji yake kamar an zare masa strength din yin komai, amma yana ganin shi ma karen hayowa saman gadon yake kokarin yi still wanting to attack her kawai yayi karfin halin sa kafa ya hauresa sannan ya jawo duvet dinsa dake saman gadon ya rufeta da shi yana rungume da ita jikinsa duk da yayi using arm dinsa as a barrier between them, tsit Legend yayi ya fasa hawa gadon ya fara komawa baya yana kallonsu, Ajay yayi masa alamar ya fita with his other hand, juyawa karen yayi ya fice daga dakin da gudu yana waigosu, everywhere became absolutely silent banda breathing dinsa that was rapid, ita kuwa sai ajiyar zuciya take saukewa jikinta na rawa, rufe idonsa yayi jin rate din heartbeat dinsa na increasing, after few seconds Khaleesat ta bude ido a hankali jin shiru karen bai kara haushi ba, shesshekan kuka ta fara yi, ya fara rabata da jikinsa zai tashi amma ta rikesa gam cikin kuka tace "Nooo plsss" sai kuma ta leko daga cikin duvet din tana zare ido hawaye caɓa caɓa a fuskarta, ganin karen baya dakin ta daga kai ta kalli Ajay with fears written all over her face, sae a sannan taga she was clinging onto his bare body all this while, komawa gefe tayi da sauri ta jawo duvet din ta rufe har kanta da shi ta takure waje daya, har sannan zuciyarta bai dena bugawa da sauri ba, Ajay ya kasa mikewa daga kan gadon, can ya juya ya ɗan kalleta ta gefen ido yaga she is still covering her head with the duvet, komawa karshen gadon yayi, yayi using switch din wajen ya kashe wutan dakin gaba daya, sai a sannan ya mike ya shiga bandaki, bai fito bandakin ba sai bayan minti arba'in, cikin duhun ya samu ya fita zuwa parlor ya kwanta kan carpet ba tare da ya shimfida wani abu a kai ba ya rufe idanuwansa don kansa yayi masa nauyi sosai. Karfe biyu Ajay ya mike zaune daga kwancen da yake duk da ba bacci yake ba, ya tashi walking slowly ya shiga Bedroom dinsa zai dau Jallabiyansa ko sallah ne ya samu yayi, wutan dakin mara haske ya kunna ya ɗan kalli saman gadon ya ganta same exact position din da take kwance tun daxu gashi ta takure waje daya kuma har sannan tana rufe da duvet, ya gama saka jallabiyansa ya karasa saman gadon ya bude duvet din jikinta yana kallonta, hannu ya kai forehead dinta jin yanda duvet din ya dau hucin zafi, bai san sanda ya zauna kusa da ita ba ya dagota yace "Are you alright?" Sosai ya ji jikinta yayi zafi, ta bude ido da kyar zata koma ta kwanta yaki saketa yana kallonta yace "Me yake damun ki?" Bai jira amsarta ba ya fara tattara mata tulin gashinta that was scattered all over don babu hula a kanta, ya jawo pillow ya dora kanta a kai sannan ya cire duvet din jikinta ya mayar gefe, kamar zata yi kuka tace "Sanyi nake ji" Ya mike ya dau remote ya kashe AC din dakin, ya dawo kusa da ita ya zauna yana kallonta yace "What's wrong with you?" Ita dai bata ce komai ba don duk jikinta ke mata ciwo, tashi yayi ya tafi banɗaki ya jiko karamin towel ya fito ya dawo kusa da ita ya dora mata a forehead dinta don ko pain reliever babu a gidan, ta matsa daga kusa da shi da sauri bayan ta cire towel din daga goshinta, sai kuma ta juya masa baya a hankali tace "Bana so, ni bacci nake ji" Kallonta ya dinga yi, after some seconds ya mike ya mayar da towel din bandaki ya fito, jin saukan numfashinta alamar ta koma bacci ya kashe wutan dakin ya fita ya koma parlor ya kwanta saman kujera ya lumshe idanuwansa. Da Asuba Ajay ya sake komawa dakin, ya kunna wuta ya koma kusa da ita yana kallonta, baccinta take comfortably ga dogon gashinta duk yayi scatterring all over the pillow, ya duka ya kai hannu kusa da forehead dinta yaji temperature dinta is normal babu zafin jiki, bin ta da kallo ya dinga yi don red Chemise din jikinta is just above her knees, dai dai sanda ta bude idonta a hankali suka hada ido, ta wani ɓata fuska tayi stretching din hannunta tana miƙa kamar mage, ya dauke idonsa a kanta sai kuma kawai ya fita daga dakin, zaro ido;;tayi ta jawo duvet ta rufe jikinta da shi ganin kayan bacci ne kawai jikinta HALYSAAH PAGE 118 Bayan fitar Ajay da minti goma Khaleesat ta daure gashinta ta sauka daga saman gadon ta shiga bandaki, kallon set din tsadaddun oral hygiene products dinsa dake bandakin ta dinga yi, duk sai da tayi using mouthwash din da ta gani a wajen ta kuskure bakinta sannan tayi wanka da daya daga set din Body wash din da ta gani, bayan ta gama ta bude inda yake ajiye set of towels dinsa tana ta kallo kamar ta dauka kamar kuma kar ta dauka, can dai ta tura baki ta dau daya ta goge jikinta sannan ta shanya a bandakin, ta mayar da kayan baccinta ta dauro alwala ta fita daga bandakin, tana ta zaune gefen gado don babu hijab din da zata yi sallah bayan abinda kare yayi mata da hijab dinta jiya, bata ma ga hijab din a dakin ba, gaba daya incident din jiya ya dinga dawo mata lokaci daya jikinta yayi sanyi zuciyarta ya dinga bugawa, to me tayi ma karen nan ne haka da ya tsaneta baya son ganinta, hawaye taji ya kawo idonta ta fara gogewa a hankali, ganin lokaci na ta wucewa bata yi sallah ba ta dau duvet dinsa ta lulluba da shi saboda kayan baccin jikinta that is very light and translucent, ta nufi kofa tana leka parlon kamar munafuka, zaune ta samesa kan kujera ya jinginar da kansa jikin kujeran hannunsa rike da Glass din soft drink ya lumshe idonsa, ta jingina da kofar Bedroom dinsa a hankali tace "Ina son zan yi sallah, ka dauko min wani hijab a can dakin pls" Sai a sannan ya bude idonsa jin muryarta amma bai kalli direction dinta ba, har yaji kamshin Body wash dinsa, wato wanka ma tayi masa a bandaki, after almost 30 seconds ya juya ya kalli inda take tsaye, marairaicewa tayi tana kallonsa, shi kam ya dinga kallon farin duvet dinsa da ta lullube da shi har yana jan kasa, can ya kalleta yace "Kee, wai uban me ya kawo ki gidan nan?" Ta turo baki taki cewa komai, ya ajiye Glass cup din hannunsa ya mike yace "Koma ciki ki dauko duk wani property dinki ki zo ki koma inda kika fito" Ta hade rai kamar zata yi kuka tace "Ni wallahi bana son apartment din, bazan iya zama a can ba ni kadai" Ajay ya mata wani kallo yace "Dole kuwa za ki zauna tunda dama can ke kadai kike zama, fito ki tafi" Kamar zata fashe da kuka ta juya ta koma dakin tana cewa "Ni wallahi babu inda zan je, bana son apartment din kuma, kawai ni kadai a katon gidan nan" Tana fadin haka ta tura kofar Bedroom din ta rufe, Ajay ya shafa kansa yana kallon kofar dakin, sai kuma ya koma ya zauna ya tallabi chin dinsa, after almost 10 mins sai gata ta sake lekowa daga cikin dakin ta marairaice tace "Don Allah ka dauko min wani Hijab a daki na, kaga har gari ya fara wayewa ban yi sallah ba fa" Ya wani kalleta yace "Ni zan dauko maki hijab saboda baki da hankali ko?" Tace "To ae saboda karen ne" Yace "Kin taɓa ganin karen a sama?" Shiru tayi tana kallonsa, zata fito ya wani hade rai yace "Idan baki koma kin ajiye min duvet ba zaki sha mamaki yanxu" ta tura baki ta juya ta koma dakin ta ajiye masa duvet dinsa da take lullube jikinta da shi saboda kayan baccinta, bandakinsa ta shiga tana kallon farin towel dinsa da ta shanya, can ta dauka ta fito, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta dora towel din a kirjinta tana tafiya kamar mara gaskiya ta fita parlor, da mamaki Ajay ya bi ta da kallo babu ko kiftawa ganin yanda ta maida masa daki public room, ita kuwa taki yarda ta kallesa ta nufi kofar fita daga parlon da sauri gabanta na faduwa, a haka har ta fice daga parlon, tana isa corridor ta hango legend downstairs yana zarya a parlor, duk da bai ganta ba haka ta kwasa a dari da sittin kamar mahaukaciya ta koma part din Ajay tana shiga parlon ta nufesa da gudu ta zauna kusa da shi cikin gigicewa tace "Wallahi i saw it" Sai kuma ta fashe da kuka kamar er yarinya tana kallonsa, shi dai kallo daya yayi mata ya dauke kai don ba tare da towel din ta dawo parlon ba, ita kanta bata san ta gantalar da towel din a wajen gudu ba, ganin yaki kulata ta mike zata wuce dakinsa ya bi ta da kallo, within few seconds ya dauke idonsa ya maida wani direction daban after seeing what he wasn't prepared to see, Sai da Khaleesat ta koma cikin dakinsa ta hango kanta ta madubi ta zaro ido with shock ganin babu towel a jikinta, ta tafi edge din gado ta zauna da sauri tana zumburo baki, after 10 mins ya bude kofar dakin ya jefa mata hijab din hannunsa without looking at her ya juya ya bar wajen.... Bayan ta idar da sallah ta gama azkar dinta sannan ta kalli wayarsa dake ajiye kan bedside drawer, mikewa tayi ta tafi ta dau wayar da sauri ta duba taga babu Password jiki ta koma kan darduma ta zauna ta bude wayar ta shiga call logs dinsa, kallon yanda yayi saving numberta ta dinga yi babu ko kiftawa, can ta wani tura baki ta fara scrolling taga uban miss calls din da tayi masa and it is not as if baya picking sauran calls dinsa, nata ne kawai baya picking, ta hade rai ta shiga WhatsApp dinsa, taga last messages da aka turo masa was from yesterday night alamar rabonsa da bude data tun jiya da daddare, tayi searching contact dinta sai gashi ya fito, ta shiga ciki, babu ko kiftawa ta dinga kallon screen din wayar ganin blocking dinta yayi ta WhatsApp din ashe, after some seconds ta kunna data dinsa messages dinsa duk suka shigo, wani number da taga anyi saving da Pinky ta bude message din da aka turo tun karfe biyun dare taga an rubuto "Good Morning Aristocrat, hope u slept well, jiya nayi bacci sanda ka kira, idan na dawo school zan kira direct call, have a nice day, bye" Khaleesat ta maimaita message din a zuciyarta yayi sau uku, ta kalli WhatsApp call da yayi ma number wajen karfe takwas na daren jiya, scrolling chat dinsu ta dinga yi tana karantawa, har sai da ta kai dai dai inda aka turo masa hotunan Birthday tana duba hoton taga Inteesar ce, ta dinga kallon hoton for almost a minute, sai kuma ta ci gaba da scrolling chat din nasu, bude kofar dakin aka yi tayi saurin cusa wayar cikin hijab dinta tayi keeping straight face tana kallon wani wajen daban, ko kallonta bai yi ba ya tafi zai dau wayarsa inda ya ajiye amma yaga babu wayar a nan, tana ganin haka tayi dubara ta cusa wayar a kirjinta don rigar baccin jikinta na da tight-fitting daga chest dinta, Yana ta tsaye for like 15 seconds yana kallon wajen da yasan ya ajiye wayarsa, can ya kalli other side din nan ma bai ga wayar ba, ita dai Khaleesat taki yarda ta kallesa fuskarta a daure, ya juya ya fita daga dakin zai duba parlor duk da shi dai yasan wayar a bedroom dinsa ya bar sa, amma ya gama duba parlon gaba daya bai ga wayar ba, har kasa sai da ya sauka yana duba wayar, can dai ya dau other phone dinsa yayi dialing number wayar, Khaleesat na jin vibration din wayar a kirjinta don ma it's very low amma bata fito da wayar ba, bayan minti goma sai gashi ya dawo dakin yana mata wani kallo yace "Bani wayata kar in sa ki kuka yanxun nan" Tayi kamar bata san da ita yake ba don ko kallon inda yake tsaye taki yi, bude kofar dakin yayi sosai yana kallon parlor ya ɗaga murya yace "Hey Legend" Wani uban tsalle ta doka sai ga ta kusa da shi tana zaro ido a tsorace tace "Don girman Allah kayi hakuri, wallahi zan baka" Ya daure fuska yace "Bani" Sai ga Legend ya shigo parlon da gudu wai har yaji kiran da yayi masa, Khaleesat ta kurma ihu ta makale gefen Ajay tana rirrikesa cikin rawan jiki tace "Don girman Allah kace ya tafi wallahi zan baka, send it away plsss" Ajay ya tura kofar dakin slightly, ya juya yana kallonta yace "Where is it?" Ɗaga hijab dinta tayi da sauri tana zaro ido zata ciro wayar ya dinga kallon kirjin nata, tana ganin haka ta hade rai ta sake hijab din ta juya masa baya taki ciro wayar, bata ankara ba sai ji tayi ya fara fixge hijab din ta bayanta, ta rike da sauri tana zaro ido taki bari ya cire tana cewa "Nooo, don Allah ka tsaya zan baka wallahi" Kokuwa ta fara yi da shi taki yarda ya cire mata hijab din ganin da gaske cirewa zai yi, Legend ya ɗan leko dakin saboda noise din da yake ji, Khaleesat na ganinsa da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ajay ya ɗagata sama da hannu daya ya tafi yayi dumbing dinta kan gado ta kwanta tana jawo duvet dinsa da sauri zata rufa da shi, kwace duvet din yayi sannan ya fixge hijab din gaba daya daga jikinta yana kallon chest dinta da ta cusa wayarsa, dama tana ganin Legend a bakin kofa ko yunkurin hanasa cire hijab din bata sake yi ba sai ma jawosa da take yi cikin tsoro tana son ya boye ta tana cewa "Plss send it away, shigowa zai yi, don Allah ka koresa" tsit tayi ganin ya fado kanta kawai daga jawosa, ta kasa kwakkwaran motsi don ji tayi kamar duk weight dinsa ya sakar mata, nan ta fara turasa da kyar tana zaro ido don ko magana ta kasa, amma kamar tana tura Rock don ko gezau, da wata irin muryar da bata san sa da shi ba yana kallonta directly in the eyes yace "Me kika yi da wayata?" Tana numfashi da kyar tace "Wallahi ba komai, ka duba ka gani" kawai ji tayi ya zura hannunsa ta kasan rigar jikinta a hankali, ta zaro ido cikin gigicewa bata san sanda ta kankamesa ba don sai taji kamar an hadata da naked electric wire cikin rawan murya tace "Na shiga uku, ba ta nan yake ba wallahi yaya, ka tsaya in ciro da kaina plss" ashe all this while ba duk weight dinsa ya sakar mata ba don tana kankamesa yayi collapsing gaba daya a kanta, hakan kuma bai hanasa kutsa hannunsa dake cikin rigarta har zuwa saman kirjinta ba, she couldn't even react any more tsabar wani irin shock da taji a ko wani gaɓa na jikinta jin hannunsa a plain chest dinta yana fondling dinsa gently, tuni salon numfashinsa ya canza taji lips dinsa na bin wuyanta yana sauke wani ajiyar zuciya, bakinta; na rawa ta hade laps dinta tace "Plsss i want to use the restroom, ga wayarka na cire maka wallahi, i want to pee plsss" abubuwa da yawa suka yi mugun tsorata Khaleesat a wannan lokacin don ko Abdul bata ji masa irin wannan tsoron ba, cikin rikicewa take ta ce masa zata je tayi fitsari duk tunaninta baya jin ta ne, cikin wata muryar da bata san sa da shi ba me kama da rada taji yace "Yi a nan" HALYSAAH PAGE 119 Mikewa Hadiyah tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin Hajja fuskarta babu walwala kwata kwata, Ajay ya bi ta da kallon gefen ido, dakin da Umminta take ta tafi, ta sameta ita kadai tana waya da Abbanta, zaunawa tayi har Ummi ta gama wayar tana kallonta da damuwa tace "Ya aka yi daughter? An maki wani abu ne?" Hadiyah ta kalleta fuskarta a daure tace "Ummi ta yaya wannan er iskar zata zo Convocation dina ta dinga yawo da designers? Jakan hannunta na yau ma fa designer ne haka ma na jiya, sai da na gaya ma Ya Jawwad shekaranjiya mu je inyi shopping jaka da takalmi for my Convocation kamar nasan abinda zai faru kenan amma yace min wai ya gaji i should use the one of my lefe bayan an gama Convocation din sai mu je ya siya mun wanda nake so, yanxu gashi wannan matsiyaciyar ta zo sai flaunting designers take making me look miserable ni da occasion dina, 3 of my friends fa sai da suka kirani daxu da safe wai they wants to be friends with her don Allah in hadasu da ita, basu san er talakawa bace matsiyaciya luck ne kawai ya kawota gidan sarauta, ni ko nace masu nima ban san daga inda take ba, uninvited guess ce" Ummi dake ta kallon Hadiyah cikin bacin rai tace "To ke da yace ya gaji baza ki takura masa ba, banda iskanci ma me yayi na gajiya sai kace wanda yayi dako? Baki ji nima yanda raina ya ɓaci ba jiya da na ga yarinyar, dama ashe ita Jawwad din yace sai ya aura?" Hadiyah ta hade rai tace "Don Allah ki dena cewa haka Ummi, wannan ai ya zama past tense, bana ma son Ina tunawa, my problem now is the type of bags and shoes and even clothe she is wearing, hatta jewelries dinta fa me tsada ne sosai Ummi, me yasa shigarta zai fi nawa?" Ummi ta daure fuska tace "Ki kirasa yanxu kice masa ke lallai lallai yau kike son ku je ku yi shopping din nan, go and dress up and call him immediately, tana matsiyaciyarta uban me zata nuna maki? abinda ma gidan da uwarta da Ubanta ke ciki Jawwad din ne ya siya, daga baya bayan nan kuma muke samun labarin hatta kudin makarantar ta da kudin hayan gidan da take a Amurka Jawwad ke biya ashe" Hadiyah ta bude baki tana kallon uwarta with shock tace "Don Allah da gaske Ummi? Is this how poor and wretched they are?" Ummi tace "Ba shi yasa Mami ta gigice ba ta fita hayyacinta sai da tasan yanda ta bi ta rusa auren sannan hankalinta ya kwanta, nima kuma daga bangarena ban zauna ba ina ta yin nawa abun na ganin auren bai yiwu ba, shi ne don tsiya shi kuma Mai martaba ya maida aure kan Junaid, Oho dai shi ya sani, amma Allah ya sani ni har yau da Junaid na so ki ba Jawwad ba cause Junaid is the Heir to the throne not Jawwad, I want nothing but the best for you, kema ki gaji kakarki ki zama Sarauniya watarana, amma hakan bai yiwu ba" Hadiyah ta wani kalli Ummi tace "To ni me zan yi da wanda yace baya so na Ummi, beside i love Ya Jawwad soo Much, ni shi nake so ba Junaid ba" Ummi ta taɓe baki tace "Amma dai ai ba haka aka so ba wai kanin miji yafi miji, Gobe za mu je Sheffield tare da Hajiya Shema'u wajen yarinyar ta Basira kinsan bata da lafiya, yanxu yaushe Jawwad din yace za ku koma Nigeria?" Hadiyah ta girgiza kai tace "Bai gaya min sanda za mu koma ba" Ummi tayi kasa da murya tace "Toh ban san kwana nawa za mu yi a can Sheffield din ba, ita kuma Fulani Hafsat naji tana cewa za su je America ban san me zata yi a can ba, kinga kenan duk watsewa za mu yi, to yanxu zan baki sakon da nace zan baki in case bamu hadu ba kun tafi Nigeria" Mikewa Ummi tayi ta kulle kofar dakin da makulli ta tafi gun akwatinta ta bude ta fito da kayanta daya bayan daya daga cikin akwatin sannan ta ciro wani zani da ta nannade wata leda a ciki, sai kuma wani babban ledan daban shi ma ta ciro a akwatin ta dawo kusa da Hadiyah ta zauna ta bude ledan farko ta fara ciro kullin magunguna da wasu kwalabe kanana, sai kuma tayi kasa da murya tace "Da kin san uban kudaden da na kashe kan su wallahi baza ki yi wasa wajen yin amfani da su ba Hadiyah, and it's for ur own good not mine, idan kika yi shashanci wajen amfani da su wallahi kanki za ki yi ma, jajircewa za ki yi kiyi duk yanda aka ce...." Hadiyah tace "Me zai hana ni amfani da su Ummi" Ummi tace "Ko wanne da takarda a ciki na rubuta yanda zaki yi amfani da shi" Hadiyah tace "To, kin ma san me Ummi komai sai ya ce Maminsa abun nan ya fara bani haushi wallahi, why always her? gashi ita ma bini bini ta kirasa a waya ko muna tare, she always have one or two things to speak to him about ni kuma na tsani haka, ko kuma idan yaje bangarenta sai ya dade bai fito ba wani lokacin har minti ashirin yana yi wallahi, kafin fa mu zo convocation din nan har na dena zuwa bangarenta in gaisheta nayi pretending bani da lafiya don haushi take bani wallahi yanxu, ko wani abun dadi ya siyo min ita ma sai ya siyo mata ya kai mata fa kamar wata kishiyata" Ummi ta hade rai tace "To ke uban me yasa zaki dora ma kanki dinga zuwa bangarenta gaisheta? Wa yace maki ana wannan haukan? To kuna komawa gida kiyi cutting din zuwa wannan gaisuwan in kun hadu cikin gida ki gaisheta amma kar ki sake zuwa part dinta, ita sanda aka aurota ko da yaushe take zuwa gaida Hajja ba sai ta ga dama ba?? sannan ki kwantar da hankalin ki wataran in ance yace Mamin ma haushi zai ji, kar ki wani damu, yanxu dai ki bi wannan magungunan step by step babu mistake, shi yasa ma duk na rubuta maki a takarda kuma wallahi ba karamin kudi na kashe ba use them wisely" Hadiyah na murmushi tace "In sha Allahu zan yi using dinsu yanda aka ce Ummi" Ummi tace "Kwanaki kika ce ma yarinyar kanwar babanki you are in pain always during intimacy, har yanxu hakan ne?" Shiru Hadiyah tayi, sai kuma ta sauke kanta, Ummi ta hade rai tace "In zaki bude baki ki min magana ki bude baki, kunyar me zaki ji, ko kina da wata uwar bayan ni ne? Duk wani abu da ya dameki talk to me, ba sai ma kin je kina magana da kowa ba kina tona asirin kanki, I know you are confuse shi yasa kika ma Marwana magana, but I am always there for you my sweetheart, Kar ki ji komai koma menene ki dinga gaya min, I am ur mother and also ur best friend, isn't this how I brought u up?" Hadiyah da ke ta tunanin irin azaban da ta sha during those period duk da ita ce tayi ta shige masa lokacin har komai ya faru, after that kuma yaki daga mata kafa, ta girgiza kai a hankali tace "A'a na dena ji yanxu Ummi" Ummi tace "Good, dama it's just for a while, it's always like that for every woman" Daya ledan Ummi ta jawo wanda ke dauke da authentic magungunan mata masu kudin gaske, nan ta dinga nuna mata su da yanda zata yi using dinsu daya bayan daya, bayan ta gama nuna mata ta ajiye ledan tace "To ita Mamin na zuwa bangaren ki ne?" Hadiyah ta taɓe baki tace "A'a, kawai sanda na dena zuwa gaisheta ne da yace mata bani da lafiya shine ta ke shigowa ta dubani kuma pretending kawai nake yi don lafiyata qlau, ko fita zata yi fa wani lokacin sai tace ya kai ta sai kace wani driver dinta, so annoying, wani lokacin sai ki ga ta sa shi yayi transferring huge amount of money for her businesses, kuma ko musu baya yi mata" Ummi tace "Don't worry, all that nonsense will come to and end soon, yayi resuming aiki asibiti ne?" Hadiyah tace "A'a sai mun koma zai yi resuming fully" Ummi tace "To yanxu ina zaki boye kayan nan kar wani ya gani?" Hadiyah tace "Cikin kayana mana Ummi" Ummi tace "Bazai ce zai bude maki akwatin ba?" Hadiyah tace "A'a, can kasan akwatin zan ajiyesa babu wanda zai gani" Ummi ta sake nannade mata ledan da zaninta, kayan matan ma ta kulle ledansa da kyau ta nannadesa da wani zanin sannan tace "A haka za ki saka su a karkashin akwatin, sannan ki kirasa kice ke shopping kawai zai kai ki, and you make sure duk abinda zaki dauka ya zamto designer ne a wajen" Hadiyah tace "Toh Ummi" Ummi tace "Amma dai je ki dauko akwatin naki, kar kije can dakin gantalallun ya matan can su saka maki ido" Hadiyah tace "Eh haka ma zai fi" Mikewa tayi ta nufi kofa ta bude ta tafi dakin da suke ita da cousins dinta ta dau akwatin ta zata fita, Iklima na kallonta tace "Can apartment din zaki koma ne Hadiyah?" Hadiyah ta yatsine fuska tace "A'a gyara kayan zan yi kawai" Daga haka ta fita ta koma dakin da uwarta take da akwatin nata. Khaleesat ta ɗaga kai ta kalli Baby da ta shigo dakin Hajja, Baby ta wara ido ta nufeta tace "Waow, kin yi kyau yau ma Aunty, I love your handbag, it's soo cute" Tana fadin haka ta dauki jakar tana jujjuyawa with admiration, Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace "Kina so ne?" Baby tace "Sure ina son irin sa" Khaleesat ta amshi jakar daga hannunta ta bude ta ciro wayarta dake ciki sannan ta mayar mata tana murmushi tace "To na baki" Ajay ya daga kai ya kalleta, ita dai taki yarda ta kalli inda yake zaune, Shahuda da Maryam dake dakin su ma sai da suka daga kai suna kallon Khaleesat, Baby kuwa har da tsallenta bayan ta amshi jakar tayi ma Khaleesat side hug tace "Thank you so much" Sai kuma ta nufi Ajay ta zauna gefensa tana nuna masa jakar tace "Yaya look, she just dashed me the bag" Ajay yace "Kin gode" Hajja tace "Ke haka ake yi Baby? Baki ga wayarta bane a cikin jakar?" Baby ta tura baki tana kallon Hajja tace "Ai dai tace ta bani kuma kin ji" Daga haka ta mike ta fita daga dakin looking so happy, Shahuda ta mike ta fice daga dakin, Hajja ta kalli Khaleesat tace "Ke kuma ai ba haka ake ba Jiddah ya za ki zo da abu tace tana so ke kuma ki dauka ki bata bayan kema amfani da shi kike, kamata yayi in ma zaki bata sai ko a gida amma ba a nan ba, kar ki sake yin haka" Khaleesat dai murmushi kawai tayi bata ce komai ba tana wasa da fingers dinta, Maryam ta tashi ita ma ta fita daga dakin cike da mamakin Khaleesat, wato ita ga ta isassa saboda ta nuna masu designers ba komai bane a wajenta idan tana son wani ma Ajay zai siya mata shi yasa ta kyautar da jakar a gabansu su gani, a stairs Baby ta hadu da Jay cikin farin ciki tana nuna masa jakar tace "Ya Jawwad look, matar ya Ajay ta bani jakar nan kyauta" Jay ya kalli jakar yace "Ohk... kin gode, is Hajja sleeping?" Ta girgiza kai tace "A'a tana zaune" Dakin ya nufa ita kuma ta sauka downstairs zata je nuna ma uwarta, Jay na shiga dakin suka hada ido da Ajay, shi ya fara dauke kansa ya karasa cikin dakin ya zauna, Khaleesat dai sai kallonsa take, Jay ya gaida Hajja, Hajja ta amsa tace "Duk yau baka shigo ba Jawwad ko kana can kana sana'ar" Calmly Jay yace "Eh bacci nayi" Hajja tace "Dama na fada, tunda naga baka shigo ba nace kana can kana ba bacci hakkinsa, to ka dai ci abinci ko?" Yace "Na ci" Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa ya fita daga dakin, Hajja ta bi sa da kallo. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 120... Wajen karfe shidda da yan mintuna na yamma Ajay ya shigo dakin Hajja, har sannan Khaleesat na zaune dakin tana danna wayarta ko nan da can bata fita ba, inda Allah ya taimaketa Hajja na dakin all through ita ma ba fita take ba, wannan yasa Hadiyah da cousins dinta sai dai su shigo su harareta su fita babu me ce mata uffan sai kallon banza, Walid ma yayi shigowa yafi goma zuwa dakin amma duk ya shigo zai tarar da Hajja zaune sai dai yayi ma Khaleesat kallon kasa kasa ya fita daga dakin, su Aunty da Gimbiya Firdausi kuwa sun ma ki shigowa dakin tun zuwan Khaleesat gidan, duk da ba hira Khaleesat suke da Hajja ba amma she prefer it that way akan a bar ta da su Hadiyah ko su Aunty ko Walid don kam ba karamin taimako rashin fitan Hajja daga dakin yayi mata ba, a yanda ta lura duk yan matan gidan cike suke da ita kuma akwai magana a bakinsu amma ba dama saboda Hajja, jifa jifa Baby ke shigowa dakin da duk wani abu na dadi in dai ta ci to sai ta kawo ma Khaleesat tunda ta bata kyautan Handbag, in kuma ta shigo dakin sai ta cikata da surutu kafin ta fita, tun da Ajay ya shigo dakin Hajja ke bin sa da kallo tana jin ranta babu dadi, gashi sam baka gane inda ya dosa da mood dinsa, kullum a haka yake baza kace yau yana cikin farin ciki ba ko kuma akasin haka, baka gane walwalarsa da rashin walwalarsa, baka gane damuwarsa da akasin hakan, if you are lucky to see him laughing or vibing probably you met him sitted together with Jay back then, Khaleesat dai taki kallon inda yake sai danna wayarta take, yana kallon Hajja daga inda yake tsaye yace "Sai da safe Hajja, I am leaving" Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "A tsaye zaka min sallaman kuma Ahmad?" Bai dai ce mata komai ba, after some seconds ya karasa cikin parlon ya zauna, tace "To abinci fa Junaid? Me zaka ci?" Yace "Ke komai abinci, to na koshi" Hajja tace "To ai shikenan, Allah ya tashe mu lafiya" Yace "Probably zan koma Maryland gobe in sha Allah" Hajja tace "Gobe kuma? Ai nayi tunanin kuna nan har weekend" Ajay yace "In zauna inyi me a England har weekend" Hajja tace "Daxu naji Hafsat na cewa za su je can Maryland din ita da Gimbiya Firdausi, ban san me za su je yi can din ba" Ajay dai kallon Hajja kawai yake jin abinda tace, Can ya mike yace "Alright, Good night" Hajja tace "To Allah ya tashe mu lafiya, amma dai ba sallaman kenan ba ko, ya kamata goben ku zo ku yi ma iyayenka sallama tunda basu san za ku tafi ba" Ajay yace "Ohk" Hajja ta kalli Khaleesat tace "Toh sai da safe Jiddah, a baki abincin ki tafi da shi ne?" Duk da yunwa Khaleesat ke ji don bata wani ci abincin daxu da Hajja ta zuba mata ba amma ta girgiza kai kawai tana ɗan murmushi tace "A'a na koshi Hajja, Nagode" Hajja tace "To Allah ya tashe mu" Tuni Ajay ya fita daga dakin Hajja, Khaleesat tayi ma Hajja sallama sannan ta bi bayansa tana tafiya a hankali cikin sanyin jiki, Hajja ta bi ta da kallo har ta fita, babu abinda Hajja tace mata akan yanda suka samesu ita da Jawwad daxu don tasan shi ya kamata tayi ma magana tunda ya fita hankali not her, sam bata ji Khaleesat ta kwanta mata a rai ba har yanxu amma kuma bazata iya walakanta ta ba... Tun da Khaleesat taji Hajja tace su Aunty za su je Maryland jikinta yayi sanyi sosai ba kadan ba, har cikin ranta tsoron Aunty take ita kam, ga ita ma Gimbiya Firdausin taga idan ta gaisheta bata amsa mata gaisuwarta, infact tsoron duk family din ma take ita, da kyar take jan kafa tana biye da Ajay har suka isa parlor, babu kowa a parlon har ma da gidan baki daya don Hajiya A'isha da Ummi da Mami sun tafi daya apartment din wajen Hajiya Shema'u Yayar Baban Hadiyah, Gimbiya Firdausi da Aunty kuwa sun fita zuwa gidan wata kawar Gimbiya Firdausi dake England ita ma, Hajiya Nafisah a safiyar yau ta koma Nigeria saboda wani uxurin ta, ita dai Khaleesat na biye da Ajay suka fita daga apartment din, ko juyawa bai yi ba balle yasan tana biye da shi ko akasin haka, ya bude gaban taxi din dake gaban apartment din ya shiga, a hankali ta bude back seat din motar ta shiga ita ma, driver ya ja motar suka bar wajen. Tun da suka shigo hotel room din Khaleesat ke zaune gefen gado tana danna wayarta, tana kallo ya shiga banɗaki ya dauro alwala ya fito don lokacin Magrib yayi, hakan yasa ta ajiye wayarta taje tayi alwalan ita ma ta fito, kamar yasan abinda zata yi bai tada sallah ba har ta fito, tana dauko pray mat zata shimfida a bayansa ya juya ya kalleta fuska daure yace "Fita a bayana" Kallonsa ta tsaya yi, cikin tawa yace "Ko baki ji abinda nace ba?" Juyawa tayi ta bar wajen, ya tada sallahn sa, ta turo baki ta tafi ta zauna gefen gado tana hararansa, yana idar da sallahn bayan kusan minti goma ya mike daga saman darduman alamar ya gama azkar ya fice daga dakin, sai a sannan ta mike ta tada nata sallan, ko da ta idar kayan baccinta ta dauka ta shiga bandaki tayi wanka ta canza kayan a ciki sannan ta fito taga bai dawo dakin ba har lkcn, a haka lokacin sallan isha'i yayi ta mike don yin sallan, har karfe goma Ajay bai shigo dakin ba gashi yunwa take ji, tana kwance edge din gado suna chatting da Sophie da yarinyar Hajiya Zaliha ya shigo dakin, ita dai bata daga kai ta kallesa ba har sai da ya wuce ta sannan ta bi sa da kallo taga ya canza kaya, which shows daga gida yake kenan, kashe wutan dakin taga yayi sannan yayi kwanciyarsa a inda yake kwantawa, ta kalli direction dinsa cikin duhun duk da ba ganinsa take yi ba, tura baki tayi tace "To ni bazan ci abinci ba?" Taji yayi mata banza, after some minutes kamar zata yi kuka tace "Ka ji...." Nan ma bai kulata ba, kawai ta ci gaba da danna wayarta, bayan kusan minti sha biyar ta kashe data din ta ajiye wayar ta hau kan gadon ta rarrafa can daya side dinsa tana kallon ƙasa duk da ba wani ganinsa take sosai ba, kamar zata yi kuka a hankali tace "Ni fa yunwa nake ji wallahi" Still dai bai kulata ba, ta ɗan duka closer to him tana kallonsa cikin duhun tace "Ka ji mana" Cikin kakkausar murya yace "I will give you a dirty slap idan ba ki dena damuna zan yi bacci ba, uban me ya hanaki amsan abincin a can gida" Shiru tayi don sai da ya bata tsoro da intonation din da yayi using, bata ma san sa da irin tone din ba, after a while ta koma inda take kwanciya a hankali ta kwanta ta rufe kanta da duvet tana goge hawayen da ya kawo idonta, after almost 30 mins ta gama juye juyenta bacci ya dauketa. Cikin bacci Khaleesat taji an sauke duvet din da ta rufe kanta da shi, firgita tayi sosai ba kadan ba ta fara kokarin mikewa zaune tana komawa baya tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." Tun da Walid yayi mata haka to tana jin an taɓa duvet dinta komin nauyin baccin da take sai ta firgita don scenario din ne ke dawo mata, kunna wutan dakin yayi yana kallonta, ta sunkuyar da kanta kamar zata yi kuka ta dau hularta tana cusa gashinta ciki a hankali tace "Tsoro na ji" Ya mata wani kallo yace "Tunda baki da gaskiya dama me yasa baza ki ji tsoro ba" Yana fadin haka ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo, Sleeping mask dinsa taga ya dauka, ta juya tana kallon paper bag dake ajiye bedside drawer kusa da ita saboda aroma din abinci da taji, wayarta ta jawo ta duba agogo taga karfe sha biyu saura few minutes, ta ajiye wayar ta bude paper bag din taga takeaway din abinci ne ya siyo mata da ruwa, turo baki tayi ta juya ta kalli direction dinsa taga har ya kwanta, sai kuma a hankali tace "Thank you" Dama bata sa ran zai amsa ba don kuwa banza yayi mata, ta dau abincinta ta fara ci, tana gama ci ta shiga bandaki don wanke bakinta, bayan ta fito ta tafi ta kashe wutan dakin sannan ta koma saman gado ta kwanta ta rufa da duvet. Washegari da safe Khaleesat ta gama rufe akwatinta ta mike tana kallon Ajay dake zaune dakin yana danna wayarsa fuskarsa daure, tashi yayi ya nufi kofa ya fita daga dakin, ta turo baki sannan ta dau handbag dinta ta bi bayansa, can gida suka tafi zai je yi ma wa enda Hajja tace sai yayi ma sallama kafin su tafi, ya sami Aunty da Gimbiya Firdausi da Hajiya A'isha zaune parlor, ya zauna kan kujera ya gaishesu gaba daya, Khaleesat ma ta zauna kasan Carpet ta gaishesu cikin sanyin murya, Ajay bai jira sae sun amsa gaisuwar ba yace "Za mu koma America yau" Gimbiya Firdausi da Hajiya A'isha ne kawai suka ce "Allah ya tsare" without giving much attention, Aunty kuwa kara wayarta tayi a kunne tana answering call, Ajay ya mike ya nufi sama, tuni Khaleesat ta tashi ta bi bayansa da sauri gashi taki yarda ta hada ido da su, duk suka bi ta da kallo don yau ma tsadadden Black Abaya ne jikinta da yayi mugun amsan fatar jikinta, tayi kyau sosai ba kadan ba kamar balarabiya, dakin Hajja Ajay ya tafi ita ma zai yi mata sallama, Hajja na kallonsu bayan sun gaisa tace "Flight din karfe nawa ne?" Ajay yace "Karfe daya in sha Allah" Hajja ta dau wayarta tana duba agogo taga karfe sha daya da rabi, tace "Lokacin ma ai ya kusa, toh Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, amma kaje can apartment din kayi ma Hajiya Shema'u sallama, ita ma Asiya da Ummi suna can, duk ku sallame su" Ajay dai bai ce komai ba, Hajja ta juya tana kallon Khaleesat, ita kanta a ranta sai da tayi admitting kyan Halysaah, amma damuwarta jikokinta da suka samu matsala ta dalilinta shi yasa ma bata jin ta kwata kwata a ranta, Khaleesat ta sauke kanta kasa ganin kallonta Hajja take, Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Kun karya ne Jiddah?" Gyada mata kai Khaleesat tayi tace "Eh Hajja" Ajay ya mike, Hajja na kallonsa tace "To Allah ya kai ku lafiya Ahmad, we will speak on phone idan kun isa" Ajay yace "In sha Allah" Khaleesat ta yi mata sallama ita ma sannan ta mike ta bi bayan Ajay da har ya fita daga dakin, ji yake kamar ya gansa a Maryland yanxu. Apartment din da su Mami suke Ajay ya karasa don it's just few houses away, Khaleesat dae na biye da shi har suka isa gidan, Hadiyah ce ta bude masu kofa bayan Ajay ya danna bell, daga sama har kasa take kallon Khaleesat tana kare ma kayan jikinta da jakar hannunta kallo, can ta koma gefe fuskarta babu walwala, kamar warce ake tilasta ma tace "Ina kwana Yaya" Ba tare da Ajay ya kalleta ba yace "Lafiya" Tuni ta juya ta bar bakin kofar ta koma cikin parlon tana cika tana batsewa, a karo na farko tun fitowarsu Ajay ya juya ya ɗan kalli Khaleesat da ta rakube jikin kofa kamar munafuka, juyawa yayi zai karasa parlon suka hada ido da Jay dake saukowa stairs dake opposite din kofar parlon, Ajay ya dauke idonsa ya karasa cikin parlon ya zauna ya gaida su Mami da Hajiya Shema'u, duk suka amsa masa, da fara'a Hajiya Shema'u tace "Fatan kun tashi lafiya?" Yace "Alhamdulillah" Khaleesat ta karaso ta zauna kan Carpet jikinta a sanyaye bayan da ta hada ido da Jay zai sauka downstairs amma ganinsu ya juya ya koma sama, cikin sanyin murya ta gaida Hajiya Shema'u da su Mami da Ummi, duk suka amsa a takaice, Hajiya Shema'u kadai ce ta bata attention, Hadiyah dai na zaune parlon fuskarta daure tana danna wayarta, Ummi kuwa sai satan kallon kayan jikin Khaleesat take, Ajay yace "Za mu koma America ne dama" Hajiya Shema'u tace "Allah sarki, nima gobe in sha Allahu zan koma Nigeria, kace sallama ku ka zo yi mana kenan" Ajay yace "Ehh haka ne" Hajiya Shema'u tace "To Allah ya kai ku lafiya" A takaice Ummi da Hajiya A'isha suka ce "Allah ya tsare" Ajay yace "Ameen" Khaleesat ta ɗan daga kanta ta kalli sama ko zata kara ganin Jay amma taga ba kowa wajen, Ajay ya mike yace "Jirgin nan da awa daya ne, za mu tafi airport..." Hajiya Shema'u tace "To Ahmad din ne zai kai ku Airport din? Ni duk yau ma ban gansa ba" Ajay yace "A'a nayi booking ride" Hajiya Shema'u ta kalli Hadiyah tace "Ke Hadiyah ina mijin naki?" Hadiyah na danna wayarta tace "Ya fita baya nan" Khaleesat ta daga kai a karo na farko ta kalli Hadiyah suka hada ido, wani matsiyacin kallo Hadiyah ta watsa mata akan idon Ajay, Khaleesat ta sake kallon sama sannan ta sunkuyar da kanta, Hajiya Shema'u na kallon Ajay tace "Ko kun yi sallama ne da ɗan uwan naka?" Ajay yace "Eh mun yi sallama" Hajiya Shema'u tace "Toh Allah Ubangiji ya sauke ku lafiya, Allah ya kara ɗankon zumunci" Ajay yace "Ameen mun gode" Ajay ya mike ya sake yi ma Mami sallama tace "Allah ya tsare" Sannan ya juya ya nufi kofa Ummi ta bi sa da harara ta taɓe baki, Khaleesat ma tayi masu sallama sannan ta mike ta bi bayan Ajay tana tafiya a sanyaye, Hajiya Shema'u ta bi su da fatan alkhairi tana sa masu albarka, sai kuma ta kalli Hadiyah tace "Ji shashashar yarinya, baza ki tashi ki raka su ba" Hadiyah ta kara hade rai sai kuma ta mike ta bi bayan Khaleesat, Khaleesat na isa kofa bayan ta saka takalminta sai da ta kara kallon upstairs tana jin hawaye na taruwa idonta kawai ta juya ta fita daga parlon, Hadiyah dake mata wani tsinannen harara ta kulle kofar parlon da karfi..... Har suka koma hotel Khaleesat taki yarda ta kalli inda Ajay yake, sai daure fuska take tana cika tana batsewa kamar warce ke jiran kiris ta fashe da kuka, bata san shi ma bata ishesa kallo ba don ko bin ta kanta bai yi ba balle ya kalli inda take yasan halin da take ciki, ya dau Charger dinsa da Hand luggage ya fice ya bar ta a dakin don Taxi din da zai kai su Airport din har ya iso, ta bi sa da wani harara sai kuma ta goge hawayen da ya fara taruwa idonta, daga karshe ta dau akwatinta da Handbag after making sure she is forgetting nothing in the hotel room sannan ita ma ta fita daga dakin.... Da daddare karfe takwas da rabi suka sauka Baltimore, nan ma dai ya bar ta da akwatin ta yayi gaba, bayan sun shiga mota she was expecting zai sa driver ya tsaya a restaurant ya siya mata abinci don babu abinda ta ci a jirgi saboda she was moody all through amma sai taga kawai sun wuce gida, shi ya rigata sauka motar ya dau jakarsa ya wuce cikin gida, nan ma ta bi sa da harara, driver ya dau trolley dinta ya kai mata parlor tana biye da shi, daukan akwatin tayi bayan ya ajiye mata ya fita ta wuce sama ta shiga dakin da take, bayan tayi wanka tayi sallah ta gama shafe shafenta ta saka kayan bacci ta daure gashinta ta saka hula tayi kwanciyarta tunani iri iri na yawo a ranta, a hankali ta goge hawayen da ya fara sauka idonta ta jawo wayarta ta kunna data, DM din Jay ta shiga tayi tagumi, it took her almost 2 minutes hawaye na zuba idonta kafin ta tura masa message, ganin baya online yasa ta kashe data ta ajiye wayar ta kwanta tana shesshekan kuka, har karfe daya saura Khaleesat bata yi bacci ba, ta mike zaune jin she needs to eat something, after a while ta sauka daga kan gadon tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta bude ta fita ta sauka downstairs, wuta mara haske ne kunne a parlon, walking slowly ta nufi hanyar kitchen zata shiga ta ci karo da Ajay ya fito hannunsa rike da mug din tea, saurin komawa baya yayi amma sai da shayin yayi splashing har a hannunsa, ta fasa masa ihu don ita ma ya ɗan fallasan mata ta durkusa a wajen, he literally became confused and out of his mind at once, ko bin ta kan hannunsa bai yi ba ba yayi saurin ajiye cup din sauran shayin ya duka gabanta ya dago kanta yana kallonta yace "Are you okay?" Kuka ta fara yi tana yarfe hannu tace "Wayyo Allah" Ya dagota da sauri ya karasa cikin parlor da ita ya zaunar da ita saman kujera ya zauna dab da ita yana facing dinta har tana jiyo breathing dinsa yace "Did it spill on you?" Bai jira cewarta ba yayi saurin ciro wayarsa dake aljihun pajamas dinsa ya kunna flash yana haska kirjinta ganin nan take shafawa, rigar bacci ne dai dai gwiwa jikinta da yayi revealing almost half part of her chest, cire hannunta yayi daga saman kirjinta yana haskawa sosai yace "Where did it spill?" Yana tambayar ne at the same time yana kai yatsan sa saman boobs dinta da ya ga ya ɗan yi ja saboda farin fatar ta, ya shafa gun a hankali da thumb dinsa yana kallonta, lokaci daya ta zaro ido ta duka da sauri cikin rikicewa tace "A'ahh...." Sai a sannan yayi realizing what he just did after coming back to his sense, shi ma da sauri ya koma baya in a state of confusion har sai da wayarsa ya fadi a hannunsa, sai kuma ya mike daga kusa da ita duk ya daburce yace "Ke makauniya ce, why don't you watch where you were going" Khaleesat dai taki dago kanta daga dukawan da tayi saboda shock din abinda yayi mata, within seconds ya juya ya bar wajen kawai ya wuce sama, sau biyu yana missing step a benen har dai ya haura sama, tafi minti biyar bata dago kanta ba duk da taji sa ya wuce sama, daga karshe ta dago a hankali tana kallon stairs din, har sannan she could feel his thumb gently rubbing the upper part of her boobs kamar lokacin yake yin hakan, hade rai tayi ta mike ta wuce sama ta shige daki, direct gaban madubi ta tafi ta tsaya, sai a sannan ma taji kunyar rigar jikin nata duk da ya wuce gwiwa amma saman rigar is too revealing, tana tafiya a hankali ta karasa gefen gado ta zauna ta kai hannunta dai dai inda shayin ya fallasar mata tana shafawa still feeling his finger there, gaba daya ji tayi ta dena jin yunwan saboda incident din nan, turo baki tayi ta kashe wutan dakin tayi kwanciyarta.... *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 121... Har karfe biyu da rabi na dare Ajay na parlonsa, duk da ba kallo yake ba amma haka nan ya kunna TV din parlon, ya canza position from sitting to lying down yafi a kirga a parlon, kuma ko minti biyar bai iya yi a each position din, da ya kwanta zai mike zaune, after some minutes kuma ya sake komawa ya kwanta haka yake ta yi tun daxu, mikewa zaune yayi ya dau sauran coke din gwangwani da ya ajiye kan Centre table ya shanye making it the second Canned coke he is drinking, sake bude wani coke din dake kan table din yayi ya ci gaba da sipping a hankali, after a while ya dau remote din AC ya kunna Ac din parlon jin ya daina jin sanyin da yake ji duk da Jacket ne a jikinsa, karfe uku saura minti goma ya ajiye Gwangwanin coke din hannunsa bayan ya shanye, ya mike tsaye ya saka hulan Jacket din jikinsa trudging towards the door kamar ana tilasta sa, tun daxu yake son zuwa dakin Khaleesat just to check on her after what happened amma bai je ba, yana isa kofar dakin ya bude gently sannan ya kai hannu ya kunna wuta yana kallon saman gadon, baccinta take sai dai bata rufa da duvet ba don AC din dakin a kashe yake, ya kusa minti daya tsaye bakin kofar kafin ya karasa ciki har zuwa kusa da gadon, kallo daya yayi ma laps dinta dake bude gaba daya ya dauke kai kamar bai gani ba, can kuma dai ya juya ya fita daga dakin kawai bayan ya kashe wutan ba tare da ya duba abinda ya kawo sa ba. Tun da gari ya waye Khaleesat ta kasa sauka downstairs gashi she is very hungry don karfe goma sha daya yayi, duk da ranan asabar ce taso zuwa school amma da ta kira Sophie sai tace mata cramps take bazata je school din ba ita, wannan ne yasa ta fasa tafiya makarantar amma da tun da sassafe zata bar gidan, ganin zaman dakin bazai fissheta ba yasa ta sauka daga saman gado a hankali ta dau Hijab dinta ta saka, slowly ta tura kofa ta fita daga dakin, tana sauka downstairs ta gansa zaune study area dake parlon yana danna laptop dinsa, suna hada ido duk suka dauke kai lokaci daya kamar hadin baki, tana tafiya a hankali ta nufi kitchen ta shiga ta kulle kofar, Noodles ta dafa bayan ta gama ta dau ruwan gora a fridge ta fito daga kitchen din, ko by mistake bata yarda ta kalli direction dinsa ba ta wuce sama, sai a sannan ya bi ta da kallo. Ajay ya ajiye wayarsa bayan sun gama magana da Mai martaba ya kalli agogon wrist dinsa dake nuni da karfe bakwai dai dai, yasan definitely jirginsu ya kusa sauka yanxu tunda da rana suka taso, duk da baya jin dadi tun safe ga ciwon kai da yake yi haka nan ya mike daga zaunen da yake ya dau sauran coke dake kan table ya sha ya tafi kitchen yayi disposing gwangwanin sannan ya wuce sama, ɓangarensa ya nufa ya dau over coat dinsa ya saka sannan ya fito, ya bude kofar dakin da Khaleesat take ciki, tana zaune saman darduma ta idar da sallah hannunta rike da wayarta tana karatun Alqur'ani a zuciyarta, tun da ta daga kai suka hada ido ta mayar da kanta kasa still looking at her phone screen, a takaice yace "Take all what you will need and put them inside that box...." Khaleesat ta sake daga kai ta kallesa, ganin ya juya zai fita tace "Kamar yaya?" Ya juyo ya kalleta fuska daure yace "Kamar yanda nace, and I am giving you just 10 mins, idan kin gama ki sauko downstairs with the box, do not waste my time" Yana fadin haka ya bar bakin kofar dakin, Khaleesat tayi shiru tana nazarin abinda yace, to ina kuma za su je da daddaren nan da zai ce ta hada kaya? Can dai ta taɓe baki ta mike ta fara yin abinda yace tayi, tana gama hada abinda tasan zata bukata ta dau akwatin ta sauka downstairs ta ajiye tana kallonsa a parlon, without looking at her yace "Ki je mota ki jirani" Tace "Ina zamu je?" Still not looking at her, calmly yace "Ban sani ba" Hade rai tayi ta dau akwatin ta fita zuwa parking space ta rungume hannu ta jingina jikin motarsa, after some minutes sai gashi rike da makullin mota coming towards the parking lot, bude motar yayi ya shiga yayi igniting motar, ta bude back seat ta ajiye box dinta don bazata iya kai wa booth ba, can tace "To ni ban dauko wayata ba ai" Yace "Kin ga idan kika bari na koma cikin gidan nan you will have to carry ur cross all alone" Bata ce masa komai ba ta juya ta koma cikin gidan tana cika tana batsewa, sama ta tafi ta shiga cikin daki ta dau wayarta da Charger har da laptop dinta da Chargern sa, sannan ta dau handbag ta fita, tana komawa parking space ta bude back seat duk ta ajiye kayan hannunta sannan ta rufe ta shiga gaban motar, tun da suka fita daga gidan take zuba ido taga inda zai kai ta da daddaren nan, after almost a 35 minutes ride ta ga apartment dinta ya kawota, juyawa tayi ta kallesa, bayan yayi parking a garage ya bude motar ya sauka stretching himself, ita dai kallonsa kawai take don he doesn't look alright, lokaci daya ta tuna Hajja tace su Aunty za su zo Maryland, to ko suna hanya ne, bata san sanda ta sauke wani ajiyar relieve ba, and she felt really grateful, bude motar tayi ta sauka still looking at him ganin ya nufi kofar apartment din ta bude back seat ta fiddo akwatinta tabi bayansa zuwa gidan, ita duk tunaninta an saki gidan ne da yake tambayarta ko tana da kudin haya kwanaki da tace ya maidota apartment dinta, yana dusting kujera ta samesa a parlon, ta koma ta dauko sauran kayanta a motar bayan ta ajiye kan Centre table din da yayi dusting tace "Na gama dauko kayan" Don ya kulle motarsa ne yasa ta gaya masa amma bai tanka ta ba, ta dau akwatinta ta wuce sama tana tafiya a hankali zuwa dakinta. Bayan ta yi gyare gyare a dakin ta shimfida bedsheet ta fito tana leka downstairs taga baya nan, sauka tayi ta dau laptop dinta da handbag ta koma sama, ta bude bandakin dake Bedroom din ta shiga ta wanke tas sannan tayi wanka ta dauro alwala ta fito, a ranta ta dinga fatan Allah ya sa ta dawo apartment din nata kenan, don ta tsani zaman gidan nan nasu tafi samun freedom dinta ita kadai bama sai ta zauna da kowa ba, bayan ta idar da sallah ta yi shafe shafenta ta saka kayan bacci sannan ta dora Hijab a kai, tana zaune gefen gadon tana danna wayarta har kusan karfe tara, daga karshe ta mike ta bude kofar dakin, sai da ta leka downstairs taga ba kowa sai ledoji dake ajiye sannan ta sauka, bude ledan tayi taga shopping din kayan shayi ne da bread with butter, ta bude wani ledan taga cookies iri iri da biscuits sai Chocolate, wani ledan kuma taga fresh fruits, sai ledan takeaway din abinci kusan hudu da ta gani, ga kuma pack din bottle water, daya bayan daya take bude takeaway din abincin taga Jollof rice and peppered turkey, white rice and stew with chicken, sai fried rice shi ma da peppered turkey, takeaway din karshe taga shi ma white rice and stew din da beef, tana ta kallon abincin kafin daga karshe ta dau takeaway uku ta kai freezer a kitchen ta ajiye su, nan taga har ya gyara kitchen din ko ina fes kamar yanda yayi ma parlor, ta koma parlor sauran kayan da ya siyo duk suma ta kai kitchen ta ajiye su sannan ta dawo parlon ta zauna ta dau rice and stew din ta fara ci, tana zaune parlon har karfe goma sha daya, can dai ta kalli kofar parlon, mikewa tayi ta tafi ta murda taji a kulle, ta window ta leka garage taga motarsa na nan, ta dawo parlon sai a sannan ta lura da spare key da ya ajiye mata kan kujera, kawai ta juya tayi wucewarta daki. Ajay na ƙishingiɗe parlor a gida yana shan grapes yana kallon football, bacci yake ji sosai amma still yana zaune parlon, yasan baccin da bai yi jiya bane ke damunsa, Walid ma na zaune parlorn har ya gaji da wara ido yana jiran yaga ta ina Khaleesat zata fito amma bai ga haka ba, don har cikin dakinta sai da yasan yanda yayi ya shiga amma bai ganta ciki ba har da duba bandaki, Gimbiya Firdausi ce ta sauko downstairs tana kallon Ajay tace "Kai Junaid ita matar taka isasshiyar wace gari ce da har yanxu bata shigo inda muke ta gaishe mu ba kusan awan mu biyu da sauka gidan nan kenan? Ko dai bata da hankali ne??" Ajay ya daga kai ya kalleta, bayan ya gyara zamansa cikin nutsuwa yace "Ai bata gidan, they are having exams on Monday so bata yi karatu ba saboda tafiyar da muka yi, shi ne ta tafi hostel wajen kawarta za su yi group reading da Coursemates dinta, so she is in school, shi yasa ma na yi maku takeaway din abinci ai" Yana gama fadin haka ya ci gaba da shan grapes dinsa, Walid dai ya juya yana kallon Ajay kamar wanda ya ji mummunan labari, Gimbiya Firdausi ma ta dinga kallon sa for almost 30 seconds sannan ta juya ta koma sama, Ajay ya bi ta da kallon gefen ido yana shan grapes dinsa a hankali, Gimbiya Firdausi na shiga dakin da suka sauka ta kalli Aunty tace "Wai kinji tana makaranta Fulani...." Aunty tace "Karya yake munafuki, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba tana ɓangarensa, ai ya riga ya nuna mata bamu da daraja kar ta mutunta mu, kin ga yanda ya raina mu baya ganin mu da daraja to bari ita ma ya dorata akan wannan layin, amma tana gidan nan babu inda taje, ai ɗan iska ne, ba dai wata biyu ya rage mata ta gama karatun ba kuma dole masarauta zata dawo mu zauna don ubanta, to ina nan ina jiran wannan lokacin...." Shahuda dake zaune dakin tace "Wallahi Aunty sai kin ga irin kallon rainin da ta dinga yi ma mutane a England yanda kika san Ubanta wani ne a kasar nan, sai daddaga kai take tana flaunting designers a gabanmu" Gimbiya Firdausi na kallon Aunty tace "Ina bangaren nasa yake Fulani?" Mikewa Aunty tayi suka fita tare Shahuda na biye da su, Aunty tayi leading dinsu har zuwa part din Ajay, suka wuce parlor suka karasa har Bedroom dinsa Aunty ta bude kofa, babu kowa dakin that was very neat and cool, Shahuda sai bin dakin take kallo, su Aunty da Gimbiya Firdausi suka fito, sai da Gimbiya Firdausi ta bari suka koma daki ta kulle kofa ta zauna gefen gado tana kallon Aunty tace "Fulani meye shawarar ki akan wannan shegiyar buzuwar da Sarki ya aura ma Yarima?" Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya tace "To ni kuwa me zan ce Gimbiya, ai ni i am not against aurensu tunda kinga ba don dubaran nan da sarki yayi ya maida auren kan Yarima ba Fulani Aseeyah so tayi tayi ruining reputation dinsa a idon jama'a, duk abinda zai taɓa reputation din sarki kuwa ai kinga baza mu so ba, don haka i am not against the marriage, kawai babban damuwata yanda ya raina ni haka yake son daura yarinyar akan layi, don har suka yi kwanakin da suka yi a masarauta suka taho Amurka wallahi bata taɓa zuwa ta gaisheni ba a gidan nan, to ni shi ne haushi na, amma bayan nan babu komai a raina sai fatan alkhairi" Gimbiya Firdausi bata sake cewa komai ba jin abinda Aunty tace, don taga bai ma kamata ta sake wani magana da Aunty akan Khaleesat ba, Aunty dai sai kallonta take ta gefen ido, Gimbiya Firdausi tace "Allah ya sa mu dace" Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ameen Gimbiyah" Da asuba bayan Khaleesat tayi sallah ta sauko downstairs taga still parlon babu kowa, ta leka garage taga his car is still there, nan ta gane cewar a can gida ya kwana, bayan ta gyara ko ina na gidan ta goge ta koma sama ta kwanta, wajen karfe tara ta tashi bacci tayi wanka ta shirya sannan ta sauko downstairs ta hada breakfast, tana gamawa ta dau wayarta.... text ta tura ma Ajay cewar zata je gidansu Safiyyah bata da lafiya har da Please dinta a karshe, ta ajiye wayarta hoping he will let her go, after some minutes sai ga text dinsa ya shigo, turo baki tayi tana hararan wayar don ta ma san cewa zai yi a'a, tana duba reply dinsa taga yasa "Ok" sosai taji dadi ta tashi ta tafi sama ta shirya sannan tayi order din Lyft, ko gaya ma Safiyyah tana zuwa bata yi ba ta kama hanyar gidansu. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence 07087865788* HALYSAAH PAGE 122... Khaleesat na isa gidansu Safiyyah ta danna bell ta koma gefe ta tsaya, with the hope that ba Surayyah bace zata bude kofar don ko kadan bata son tashin hankali ita dai, after almost a minute aka bude kofar suka yi ido hudu da Surayyah, Khaleesat ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Ina kwana Maman Aslam" Surayyah ta juya ta bar bakin kofar tace "Sannu da zuwa, shigo mana" Khaleesat ta shiga parlon still not comfortable ta cire takalmanta a bakin kofar, tana tafiya a hankali ta karasa cikin parlon ta zauna edge din kujera, Surayyah ma ta zauna tace "Ya gida, fatan an dawo lafiya?" Khaleesat da mamaki ya cikata tace "Lafiya lau, ina Aslam?" Surayyah tace "Aslam yana bacci, naji kinyi aure, to Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya, congratulations" Khaleesat ta sauke idonta tace "Ameen, Nagode" Surayyah tace "Kawar taki tana daki" Khaleesat tace "Ohk to, nagode" Mikewa tayi ta bar parlon ta nufi dakin Safiyyah har sannan mamaki ya kasa barin ta, wai Surayyah ce ke mata magana faram faram har da mata fatan alkhairi tayi aure, nan taga Safiyyah na lekosu ta kofar dakin nata baki sake kamar taga wawan zama, Khaleesat ta karasa ta shiga cikin dakin tana mata murmushi tace "Yanxu kika tashi ko" Safiyyah ta kulle kofar har sannan bata rufe baki ba alamar shock, can tace "Tun da uwata ta haifeni ban taɓa ganin makira irin matar Ya Musty ba, wato yanxu kinyi aure kin fita daga kasuwa tasan ko kallon ki Ya Musty bazai sake yi ba da wata manufa shine har da zaunawa parlor ku gaisa cikin mutunci da mutuntawa, kiji mata, daxu fa da ace na kulata da mun yi batattciya a gidan nan, duk wani abu da tasan ina ci sai ta dauke a kitchen ta boye a dakinta, gashi tayi ta saka min wakokin habaici tun da sassafe, dama yaronta ta dena barin ya zo kusa da ni yanxu" Khaleesat dai murmushi kawai tayi tace "Kema ai kina da naki" Nan da nan Safiyyah ta hade rai tana kallonta, Khaleesat ta kauda zancen tace "Yaushe aka saka date din Quiz dinmu?" Safiyyah tace "Sai ranan Alhamis, we still have time, yau sunday fa, ina mijin naki? Did you sneak out ko kuma shi ya bar ki kika zo?" Khaleesat ta hade rai tace "Ni ki dena ce masa mijina bana so, mijina kamar yaya?" Safiyyah tace "Au to, ina Guard man din ki?" Hararanta Khaleesat tayi taki cewa komai ta tafi ta zauna gefen gadonta, Safiyyah tace "Bani labarin Convocation da kuka je kawata" A hankali Khaleesat tace "Ba wani labari fa" Safiyyah tace "Uhum, kun yi hotuna a can?" Khaleesat tace "A'a ba hoton da muka yi" Safiyyah tace "Masu convocation din dai sun sha hoto kam su" Khaleesat dai bata ce komai ba, Safiyyah ta ɗan yi murmushi hade da taɓe baki, can ta mike tace "Ni ko breakfast fa ban yi ba, ban dade da tashi ba, ke kin yi?" Khaleesat tace "Na yi" Safiyyah tace "To bara in je in dafa ko Indomie" Daga haka ta fita daga dakin, Khaleesat ta jawo handbag dinta a hankali ta ciro wayarta ta bude data ta hau WhatsApp tana jiran messages dinta, message din Jay ta dinga kallo wanda ya shigo a karshe, tun ranan da za su bar England da tayi masa message sai yau yayi reply kuma ko minti goma bai yi da replying message din ba and he is even online, a hankali ta kai hannu ta danna masa WhatsApp call, amma har ya gama ringing bai ɗaga ba kuma yana online, ta sake kiransa nan ma bai yi picking ba, wani message din taga yayi mata yace "Hm" ta tura masa Sad emoji, yace "Later...." Daga haka taga ya sauka online, dai dai nan Safiyyah ta shigo dakin rike da plate din abinci tace "Ina shiga na tarar ashe tayi girki, ko babu ration dina ni dai na debo ba ruwana" Ita dai Khaleesat bata ce mata komai ba, Safiyyah ta zauna tana kallonta ganin yanda mood dinta ya canza tace "Me ya faru Coursemate?" Khaleesat dai taki ce mata komai, Safiyyah ta kalli wayar hannunta, hannu ta kai zata amsa wayar Khaleesat taki bata, ta mayar da wayar gefenta, Safiyyah bata sake kulata ba ta fara cin abincinta, Khaleesat ta kwanta gefen gadon Safiyyah a hankali, Safiyyah dai sai kallonta take da gefen ido tana cin abincinta. Sai kusan karfe biyu da rabi Khaleesat ta tashi daga baccin da ya dauketa a kan gadon Safiyyah, bayan tayi sallan azahar tana zaune kan darduma Safiyyah tace "Me zan dafa mana, ko za ki ci Indomie? Or should I make us Couscous?" Khaleesat dai tayi shiru don gaba daya taji bata da appetite har sannan she was moody, Safiyyah ta mike ta fita daga dakin ganin ba tanka mata zata yi ba, a hankali Khaleesat ta jawo wayarta wanda tun da ta ajiye daxu bata sake dauka ba sai yanzu, message din Ajay ta gani, ta wani hade rai ta bude message din taga yace "Start coming back home now" Few minutes ago ya tura mata text din, ta wani hade rai zata mayar da wayar ta ajiye sai kuma ta bude data ta hau WhatsApp dinta, zaro ido tayi ganin miss call din Jay ya mata WhatsApp call, she couldn't believe her eyes ta dinga kallon call din babu ko kiftawa, duk da he is not online haka nan tayi returning masa call din, har sai da ya katse sannan ta ajiye wayar, ko da Safiyyah ta dawo dakin bayan minti talatin tayi mamakin ganin Khaleesat ta sauko kamar ba ita ba daxu har da hiranta, Safiyyah ta ajiye masu Indomie din suka ci, duk tana kula da yanda Khaleesat ta sake kamar ba ita ba, Safiyyah tace "Kin ki bani labarin Convocation din da kika je ko" Khaleesat ta ɗan bude ido tace "Da gaske fa ba wani labari, I met Jay's Cousin sisters a wajen kuma gaba dayansu basu yi welcoming dina ba, even his Aunties ni ban san me nayi masu ba" Safiyyah dake ta kallonta tace "Ohk ba cousin sisters din Ajay bane kenan sai dai Jay?" Khaleesat tace "Oho, duk daya ne ai" Safiyyah tace "To baki hadu da matar Jay ba" Shiru Khaleesat tayi taki ce mata komai tana cin Indomien gabanta, Safiyyah tace "Na zata ita ke convocation din ai" Khaleesat tace "Ni ban sani ba kam" Daga haka Khaleesat ta canza labarin zuwa na Practical din da za su yi gobe a schl, bayan sun gama cin abincin Safiyyah ta kai plate din kitchen ta dawo, Khaleesat ta dauko laptop din Safiyyah tace "Let's study a little about the practical before tomorrow" Duk da collective reading da suke yi lokaci lokaci Khaleesat ke jawo wayarta ta duba, Safiyyah duk tunaninta agogo take dubawa, can dai tace "Ya baki lokacin da zaki koma gida ne halan?" Sai a sannan Khaleesat ta tuna text din da Ajay yayi mata daxu, ta turo baki tace "Toh ba karatu muke ba, ban gaya maki ba ina apartment dina fa" Safiyyah tace "Ban gane ba" Khaleesat tayi murmushi don har cikin ranta dadi take ji apartment dinta da ya maida ta, tace "Jiya ya kai ni Apartment din, I think his stepmom and Aunty sun zo Maryland ne, kuma kinsan basa so na...." Safiyyah tace "Ashe gata yayi maki, to ke kadai ce a apartment din?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Eh, kawai ya bar motarsa a Garage ne, amma ni kadai na kwana gidan" Safiyyah tace "Ikon Allah, duk abun sa kuma yana da kirki da hangen nesa fa, gashi baya son a tsangwame ki ya maida ke apartment dinki kilan har zuwa lokacin da za su tafi" Khaleesat bata ce komai ba ta ci gaba da karatun da take, daga karshe ta tashi zata shiga bandaki tayi alwala tayi sallah ta tafi gida kafin ya turo mata wani text din, Safiyyah ta bi ta da kallo har ta shiga bandakin sannan ta jawo wayarta da sauri ta bude don ta san password dinta, WhatsApp ta bude bayan ta kunna data, DM din Jay ta shiga ta fara cin karo da WhatsApp calls din da suka ma juna, can ta fara scrolling chat din nasu tun daga farko making sure she is fast kafin Khaleesat ta fito, ita dariya da mamaki ma abun ya bata ta dinga kallon ikon Allah tana karanta chat, jin alamar Khaleesat zata fito ta maza ta fita daga WhatsApp din ta kashe data tayi saurin mayar mata da wayar ta ajiye ta ci gaba da danne danne a laptop dinta, bayan Khaleesat ta fito ta tada sallah Safiyyah ta mike ta shiga bandakin tayi alwala ita ma. Karfe hudu da rabi Khaleesat ta gama shirinta zata tafi, Safiyyah tace "Bari in shirya in raka ki apartment din naki tunda ke kadai ce" Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace "Da gaske?" Safiyyah tace "Eh mana, in na raka ki ba sai in dawo gida ba" Khaleesat ta ji dadi har cikin ranta, tace "To kiyi sauri ki shirya, tun karfe biyu da wani abu fa ya turo min text in koma gida" Safiyyah ta bude baki tace "Tun karfe biyu shi ne kika yi ignoring text din??" Khaleesat ta hade rai tace "To ba karatu muke yi ba? Ai ba wasa muke ba" Safiyyah tayi er dariya bata ce mata komai ba ta mike ta fara shiri, bayan ta gama tace "Ina zuwa" Fita tayi daga dakin, Khaleesat na ta zaune bayan tayi order din masu Lyft da zai kai su gida, har minti goma ya shude Safiyyah bata dawo dakin ba, zuwa yanxu kam hankalinta yayi gida don karfe biyar ya gota, ganin Lyft din ya iso ta mike ta dau handbag dinta bayan ta saka wayarta a ciki ta nufi kofa ta fita daga dakin, Safiyyah ta fito kitchen rike da leda ganin Khaleesat ta fito tace "Yauwa fito mu tafi" Za su fita daga parlon Safiyyah tayi kasa da murya tace "Tana kitchen leka kiyi mata godiya ki ce kin tafi, har da tsaraba ta baki" Khaleesat ta ɗan bude ido da mamaki, can ta leka kitchen din tayi ma Surayyah sallama, Surayyah tace "Yauwa sai anjima ki gaida gida" Da haka suka fita daga parlon, sai kusan karfe shidda suka isa gida, bayan sun sauka Lyft Safiyyah ta kalli Garage tace "Ke ya dawo" Khaleesat tace "Ai bai tafi da motar jiya ba dama" Safiyyah tace "Au to, don da na juya na yi komawata bana son jaraba" Suka karasa bakin apartment din Khaleesat ta bude kofa ta shiga Safiyyah na biye da ita a baya, kamshin turarensa taji a parlon, can ta juya da sauri ta kalli bakin kofa bata ga takalminsa ba, tayi ma Safiyyah alamar da tayi shiru ta tsaya, tana tafiya a hankali ta haura sama ta bude duk dakunan bata gansa ba, ta sake dawowa kasa ta shiga kitchen nan ma baya nan, turo baki tayi tace "Kilan ya zo ne yaga ban dawo ba shi ne ya tafi" Whereas bata san yana nan neighborhood din ba kuma yaga sanda suka shiga apartment din, Safiyyah ta rike haɓa tace "Naga wani sabon raini kike ma Ajay din nan, ko da yake shi ne bai yi maganin ki ba har yanxu" Khaleesat ta wani kalleta tace "Ni dai mu je sama" Sama suka tafi zuwa dakinta, Safiyyah tace "Ni ba ma dadewa zan yi ba kinga yamma yayi" Zaunawa gefen gadon tayi ta fara bude ledan dake hannunta, Khaleesat dai sai kallonta take, Safiyyah ta tsuke fuska ta ciro magungunan mata dake cikin ledan tace "Ga su nan saboda Allah ta baki kuma wai kin yi aure bata baki komai ba, wallahi ba kowa ma take ba ma ba wannan kayan ba, baki ga jikinta luwai luwai ba da kika zo, duk kayan gyaran jiki ne, ance in mutum na da kyau ya kara da wanka, fatar ki zai kara fresh fiye da yanda kike yanxu, kinga wannan da madara ake sha ko zuma, nasan ba lallai ki samu zuman ba so kiyi using madara, wannan kuma saboda raman nan da naga kinyi ne zai sa ki murmure nima shi nake sha nake cikowa idan naga na rame, shi ma da madara zaki sha, wannan kuma riga-kafin infection ne kinsan mu mata, to shi ne ta baki ki dinga using nima kwanaki ta tsam min....." Khaleesat ta dinga kallon Safiyyah da ta dinga zayyano mata amfanin magunguna kusan shidda dake cikin ledan da kuma yanda zata sha su, har sai da ta gama tace "Kin gane ko in dawo farko? Naji kinyi shiru" Khaleesat ta mata wani shegen kallo daga sama har kasa tace "Sai dai ki raina ma kanki hankali, ke kije ki gyara jikin ki da su mana, zaki wani kawo min maganin mata ki ce min na gyaran jiki, nace maki I have anything to do with them ne??" Safiyyah tayi dariya don ita mance cewar Khaleesat ta taɓa aure ma take, ashe fa tasan duk magungunan nan, can dai Safiyyah ta mayar da magungunan gefe ta hade rai on a serious note tace "Bari ki ji Malama idan zaki kama mijinki ki rike hannu bibbiyu ki dena hauka kan Housemate din ki to ina baki shawaran kiyi hakan tun wuri, don Housemate dai na can yana shagalinsa da matarsa sai abinda suka manta, da koro koro eyes dina naga zafafan hotunan da yayi updating a status dinsa na shi da matarsa kamar zasu hade su zama daya ga wani kallon soyayya da yake mata, ke kina ganinsu kinsan ba karamin amarci aka ci ba, see the way they were looking at each other a pics din ai duk nayi screenshot, tsabar shock sai da na farka cikin dare na sake kallon hotunan na koma na kwanta, sabili da haka yasa na sa Surayyah ta debar maki kayan gyaran nan kema ki ji da mijinki ki samu lada, ke idan ma kina da isasshen hankali har sai wani ya baki shawaran abinda ya kamata bayan dawowarku daga England? Na zata you will be motivated ai ki dawo senses din ki, wai ko ba gabanki suka dinga hotunan bane?" A takaice Khaleesat tace "Ban san maki ba, ba cewa kika yi ba dadewa zaki yi ba idan mun zo, beside it's almost dusk ya kamata ki zo ki tafi" Safiyyah tayi shiru tana kallonta, can tayi kasa da murya tace "Naji amma kina da kayan shayi a gidan nan ki dibar min, Surayya dai ta boye nasu" Har sannan fuskar Khaleesat a daure yake ta nufi kofa zata je ta dibar mata kayan shayin da Ajay ya kawo mata jiya, tana fitowa daga dakin ta gansa tsaye a corridor ya rungume hannu, she was very shock taji kamar ta juya ta koma cikin dakin tace ma Safiyyah ya zo, can kuma ta turo baki ta ki yarda ta kara kallonsa, kamar munafuka ta fara sauka downstairs, ya bi ta da wani kallo, Safiyyah na ganin Khaleesat ta fita ta mike da sauri ta dauko handbag dinta ta bude ta ciro wayarta tayi unlocking sannan ta shiga WhatsApp, blocking number Jay tayi bayan tayi deleting duk chat dinsu, ta tafi call logs dinta na WhatsApp da phone call ma duk ta goge numbersa, ta shiga text message shi ma kafin tayi deleting sai da tayi blocking number ta yanda phone call ma bazai shigo ba sannan ta mayar mata wayar cikin jaka ta ajiye da sauri, waige waige ta fara yi jin kamar kamshin turare alamar dai wani ya shigo, ta mike kamar munafuka tana rike da handbag dinta ta nufi kofar dakin da Khaleesat ta bari slightly open, ido hudu suka yi da Ajay that is looking at the room, Safiyyah ta ɗan yi yake tana sosa keya tace "Good evening" Bata jira sai ya amsa ba ta sauka downstairs da sauri, Kitchen ta samu Khaleesat ta tula mata Milo da Madara a ziplock bag, Safiyyah ta zaro ido tace "Ke kika siya?? Ji min mata" Khaleesat tayi kasa da murya tace "Ya dawo fa" Safiyyah ta rike haɓa tace "Baki ga na lallaba na sauko downstairs ba babu shiri" Khaleesat tace "Is he still upstairs?" Safiyyah tace "Eh mana, kawai kamshin turare naji na leko na gansa, ai ko sum sum na sakko kar ya koreni" Khaleesat tace "To me yake a wajen har yanzu?" Safiyyah tace "Oho" Ni dai nayi ordering Uber, sai mun hadu school gobe, tare suka fito daga kitchen din bayan ta ba Safiyyah ledan kayan shayin da ta dibar mata, a nan kan kujera a parlor Safiyyah ta ajiye mata ledan cikin dubara don ita ba abinda zata yi da kayan shayi, ko damunta bai yi ba ma kawai tana son using privilege din ne tayi abinda zata yi a wayar Khaleesat, Khaleesat ta rakata har wajen apartment din sannan ta koma ciki, amma fa duk ta tsargu kar ace Ajay yaji conversation dinsu da Safiyyah. *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 123 .... Ajay na kallon football wajen karfe sha dayan dare kiran Mai martaba ya shigo wayarsa ya rage volume din TV din ya sauke kafafuwansa kasa daga kan kujera sannan yayi picking call din, cikin ladabi ya gaida Sarki, bayan sun gaisa sarki ya tambayesa Khaleesat, yace "Tayi bacci ranka shi dade" Sarki yace "Ohk, goben za ku tafi UK for Hadiyah's Convocation which is on Tuesday?" Ajay yayi shiru, can yace "I thought Wednesday ne ranka shi dade...." Mai martaba yace "A'a, Jawwad din bai tura maka Invitation din bane?" Duk da bai tura masa ba Ajay yace "Ya tura, ban kula bane da date din" Mai martaba yace "It's Tuesday not Wednesday" Ajay yace "Toh Allah ya kai mu lafiya ranka shi dade, nasan ba lallai ka samu daman karasowa ba ko?" Mai martaba yace "Za a wakilce ni, beside Hajja ma gobe za su tashi zuwa England din in sha Allah, Kai ma ya kamata kai da matar ka should leave tomorrow ba sai ranan talatar ba" Ajay yayi shiru at first, sai kuma a hankali yace "Abba i think ba sai na je da ita ba, she will stay with her friend kafin in dawo" Mai martaba yace "Ko saboda me?" Shiru Ajay yayi, Mai martaba yace "To ku je tare, she will get to meet most of ur relatives da basu san ta ba, there is no point leaving her behind shi yasa nasa ayi mata Visa" Ajay ya sauke idonsa yace "Toh Abba, we will go together in sha Allah" Mai martaba yace "Good, Walid ma tun shekaranjiya ya tafi England din" Ajay yace "Ehh he was here yesterday, amma ya tafi yau" Mai martaba yace "Really, America ya tafi dama?' Ajay yace "Eh nan ya zo" Mai martaba yace "Wani irin tafiya ne wannan yayi? Shi da zai tafi England that is just 7 hours from Nigeria me ya kai sa America tafiyar kusan awa sha shidda?" Ajay yace "May be he have something to accomplish here, but ya tafi England din daxu da safe" Mai martaba yace "Ohk then, take care" Ajay yayi masa sallama sannan Mai martaba ya katse wayar, ajiye wayar yayi ya jinginar da kansa jikin kujera yana nazarin ta yanda zai fara tafiya England da Khaleesat, shi ma ba da son ransa zai je ba balle ya wani je da ita, mikewa yayi kawai ya kashe kayan kallon ya wuce sama. Safiyyah da ta rike haɓa tana kallon Khaleesat da mamaki tace "To hakan yana nufin kishi yake da ni kenan ko me? Banda haka me yasa zai hanaki zuwa wajena bayan tare ya gan mu? Ji min mutum, Ko don saboda yasan ni Team Housemate ce? To dole ne sai na goyi bayan cin amanar da yayi yake nufi ko me? Ni dama tun asali kowa yasan Housemate nake yi shine nawa, kuma bazan taɓa canza ra'ayina ba, har gobe bazan dena cewa ba a kyauta ma Housemate ba an ci amanarsa an cucesa, shekaranjiya ma naga ya saka status wai amaryarsa zata yi convocation a Oxford, caption dinsa ne yasa jikina kuma yayi sanyi qlau" Khaleesat ta daga ido tana kallonta, Safiyyah ta taɓe baki tace "Ko meye na wani sa wife dinsa a caption bayan kowa yasan wife dinsa ce ba sai ya gaya mana ba, ni dai kaddai fa ace har yayi move on ya bar ni nan da jiye masa takaici kullum ina babatu, su fa maza ba tabbas gare su ba, zuciyarsu ba shi da tabbas yanxun nan sai su canza in suka samu wata daban, tun da naga ya sa kalmar wife din nan a status jikina yayi sanyiiii, kinga alamar ya dirji amarcinsa yanda ya kamata kenan har da referring dinta to as his wife a status dinsa, to ai shikenan" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba tana jin zuciyarta na mata zafi, Safiyyah ta taɓe baki tace "Duk da dai shi ma Ajay din ba mutumin banza bane mutum ne me shegen class da personalities masu kyau, kuma dama can yana burgeni yanda baya daukan wargi yanxun nan kana raina masa hankali zai kai maka naushi ya hada maka jini da majina, ba irin mijin Surayyah da Housemate ba masu ba namiji ɗan uwansu hakuri, tun daga nan suka sire min wallahi naga inaaa ba gwarzaye bane" Khaleesat ta kalli wayarta jin shigowar sako, sai kuma ta kalli Safiyyah a hankali tace "My driver is around Sophie, sai gobe" Safiyyah tace "Ni dai ki kwantar da hankalinki ki dena damun kanki wallahi, tun da Allah yayi Housemate ba mijinki bane don gashi can har ya rungume er matarsa to kema a gaskiya zan baki shawara kiyi hakuri ki fara kula mijinki duk da ɗan rainin hankali ne shi amma to ya za ki yi? Nasan shi ma wallahi daurewa kawai yake yana pretending amma ya gama macewa a kanki, yana zaune gida daya dake yana kallon ki matsayin halaliyarsa da wannan shape din naki da glowing skin har ya isa yace baya jin komai a ransa? Ai sai dai ya yaudari kansa wallahi, kawai daurewa za ku yi ku sauke hakkin juna a wuce wajen" Mikewa Khaleesat tayi without answering her fuskarta daure ta dau jakarta tace "Bani textbook dina zan tafi gida" Safiyyah tayi er dariya tace "Ranan da zai nuna maki ke halaliyarsa ce may be you will come back to ur senses that day, bar ganin yana kyaleki, ba dai namiji bane? wataran ko yace zai kyaleki bazai iya ba a sannan ne zaki dawo hankalin ki" Takaici yasa Khaleesat ta juya kawai tayi tafiyarta ta bar wajen, cikin bacin rai ta nufi inda driver ke parking yana jiranta. Khaleesat na isa gun motar ta bude back seat zata shiga, still tayi tana kallonsa, yana zaune driver seat ya saka Black glasses irin no respect din nan yana kallon gabansa kamar bai san ta bude motar ba, ta ɗan taɓe baki ta rufe back seat din ta bude front seat ta shiga motar, Without looking at him kamar ana tilasta ta tace "Good evening" Bata ji ya amsa ba ya ja motar suka bar wajen, ba hanyar gida taga ga nufa da ita ba, ita dai tana ta kallon hanya wondering where he is taking her to, sai da suka yi tafiyar kusan awa daya sannan yayi parking a wani babban Mall, ya kashe motar ya sauka, ganin bata sauko ba yace "Don't waste my time" Bude motar tayi fuskarta babu walwala ta sauka, yana gaba tana biye da shi suka shiga wajen, Abayoyi masu tsadan gaske da dogayen riguna ta dinga gani, ita dai tana biye da shi a baya, without looking at her yace "Pick the ones u need" Ta daga kai ta kallesa, yana duba agogon wrist dinsa yace "Do not waste my time" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta daga wani Abaya da take ta kallo tun da suka shigo wajen, tana ganin price dinsa bata san sanda ta mayar da sauri ba, taga ya dau Abayan yana dubawa, ita dai kallonsa kawai take, ya duba size din, daga haka bai sake bin ta kanta ba ya ci gaba da duba Abaya da tsadaddun dogayen riguna yana daukan wanda yaga yayi kyau, sai da ya dau riguna biyar duk masu shegun tsada a wajen, don mamaki ma abun ya bata, yayi payment suka fita wajen ya shiga wajen takalma da jakunkuna designers, ta buda ido sosai tana kallonsa, nan ma duk shi ya zabar mata kala uku uku har tayi mamakin ta yaya yasan size din takalminta ga riga ma da ya siya yasan size dinta, sosai jikinta yayi sanyi ganin prices din items din da yake dauka ba na wasa bane, bayan yayi payment suka fita daga wajen takalman kuma duk shi ke rike da kwalayen da aka zuba masu kayan, ta wani zaro ido ganin wajen designers jewelries zai shiga, ita dai a hankali take tafiya tana bin sa a baya, nan ma set din jewelries lafiyayyu uku ya daukar mata ita dai tana ta kallon ikon Allah, taga ya kara mata da zobuna biyu duk designers, sai wristwatch, zoben ne ma ya bata ta gwada without looking at her, daga nan ya biya kudaden suka fita daga wajen, inda ake siyar da hair accessories irin na turawa ya gani ya shiga wajen tana dai biye da shi cikin sanyin jiki, hadaddun ribbons din gashi ya siya mata iri iri bayan ya biya suka bar wajen sannan suka fita babban Mall din gaba daya, she don't even want to start calculating the amount he spent in just this shopping cause the money was huge especially when converted to Naira, millions masu dama kenan fa in anyi lissafi, bayan mota ya bude ya ajiye kwalayen kayan hannunsa sannan ya bude driver seat ya shiga, ita ma ta shiga gaban motar ta kulle, sae da suka kusa gida after almost an hour and 15 mins ride sannan ya tsaya wani eatry ya siya abinci takeaway biyu, daga nan kuma suka wuce gida wajen karfe bakwai na dare.... A nan parlor Ajay ya bar mata kayan a takaice yace "Get ready za mu yi tafiya gobe karfe biyar na asuba, iya wa ennan kayan zaki tafi da" Yana kai wa nan ya wuce sama ta bi sa da kallo, a hankali ta dau package din kayan gaba daya ta wuce sama ta kai daki, kara fitowa da kayan daya bayan daya ta dinga yi tana duba su, ya subhanallah... they were soo beautiful and unique, the designer bags and shoes where more than gorgeous, har cikin ranta suka yi mata kyau sosai, gashi ya iya zabe ya ma fi wata macen iya zaban kaya, ta gwada takalman taga kamar don kafanta aka halitto su, ta zaune gefen gado ta fito da jewelries din su ma tana duba su, they were screaming nothing but luxury, ta gwada 2 rings din dake ta kyalli ta ɗan yi murmushi sai kuma murmushin yayi fading daga fuskarta ta cire su a hankali ta ajiye bayan ta tuna zoben da Housemate dinta ya siya maya, lokaci daya duk mood dinta ya canza, ɗan farin cikin kayayyakin da take yi yayi disappearing at once daga ran ta, tafi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike a hankali ta goge hawayen dake makale idonta ta nufi banɗaki zata yi alwala, sae da tayi sallan magrib sannan ta fita daga dakin, ta jima tsaye corridor as if contemplating on what she is about to do, at the end kawai ta karasa ɓangarensa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta shiga kamar munafuka, yana zaune parlor ta samesa yana duba wayarsa, taki barin su hada ido ta tsaya jikin kujera a hankali tace "Thank you so much for the wears, Allah ya kara budi" Bai daga kai ya kalleta ba, bayan few seconds taji yace "Thank God instead" Still not looking at him tace "Okay" Daga haka ta juya ta fita daga parlon ta kullo masa kofa, sai bayan da ta koma daki ta fara tunanin kaddai fa convocation din Hadiyah za su je gobe, sosai gabanta ya fadi bayan wannan tunanin ya zo mata rai, lokaci daya jikinta yayi mugun sanyi taji ƙafafuwanta sun mata nauyi sun ma kasa ci gaba da daukan ta, anya zata amince ta bi sa kuwa? da kyar ta karasa edge din gadon dakin ta zauna kamar warce ruwa ya cinye tunani iri iri na yawo a ranta, after some minutes ta jawo wayarta cikin sanyin jiki zata kira Safiyyah ta gaya mata. Karfe hudu dai dai na asuba Ajay ya bude kofar dakin da Khaleesat take ya kunna wutan dakin yana kallonta, bacci take ta rufe har kanta da Duvet, ya karasa kusa da gadon ya sauke duvet din yace "Kee" firgit ta bude ido ta mike zaune da sauri tana komawa baya, sai kuma ta fara duba hulanta a kan gadon zata rufe gashinta, juyawa yayi ya fita daga dakin, ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe hudu da minti biyu, ajiye wayar tayi ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki.... Kafin karfe hudu da minti hamsin Khaleesat har ta gama shiryawa dama tun daren jiya ta hada duk sabbin kayan da ya siya mata a box dinta ta shirya, tana tsaye gaban madubi tayi oiling dogon gashinta tana combing dinsa zata daure da daya daga ribbons din da ya siya mata jiya, sai kallon baƙin gashin nata take ganin kamar ya kara yawa ma, banda sheki babu abinda gashin yake, bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri ta kalli kofar tana daure tulin gashin nata waje daya cikin hanzari, kallo daya yayi ma gashin yace "Ke Malama you are wasting my time, ko bakya duba agogo ne" Ta ɗan turo baki ta dauke kanta tace "Ni sai nayi sallah tukunna" Tana fadin haka ta ci gaba da abinda take, can ta juya ta kalli direction din kofar taga ya bar wajen, biyar da kusan minti goma ta fito daga dakin da box dinta da handbag ta sauka downstairs, high waisted palazzo ta saka with matching top sai karamin veil dinta da handbag tayi kyau sosai ba kadan ba duk da babu abinda ta shafa a fuskarta sai eye pencil da ta sa a idonta, yana zaune parlor alamar ita yake jira, jin footstep dinta ya juya ya kalleta sai kuma ya dauke kai, kara kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma dai ya fasa ya mike ya nufi kofar parlon ta bi bayansa tana jan trolley dinta, driver na tsaye jikin mota yana jiransu, yana hangota ya tafi ya amshi box din hannunta sannan ya bude mata back seat ta shiga bayan sun gaisa da shi, kallon Ajay dake zaune gaban motar tayi, murya can kasa tace "Good morning" Bai ce komai ba, hakan yasa tayi tunanin bai ji ba ta sake gaishesa a takaice yace "Same" Wani kallo tayi masa ta dauke kai, driver ya shigo motar ya tada suka bar gidan.... Karfe biyu saura suka sauka Ingila Ajay yayi masu order din Indrive da zai kai su har gida, sai bin sa da wani kallo take don he is not even helping with her box, iyaka hand luggage dinsa kawai ya dauka, driver din motar ya dau akwatin ya sa a booth ta bude motar ta shiga don tuni Ajay ya shiga kamar ba tare suke ba, Suna isa gida Khaleesat dai ta tsaya bakin apartment din da taga Ajay ya sa driver ya ajiye akwatin ta, ya gama wayar da yake sannan ya danna bell din apartment din, not long after aka bude kofar apartment din, step sis dinsa Baby ce ta bude kofar tana ganinsa ta rungumesa tace "Oyoyo Yaya...." Yace "How are you?" Tace "Am fine, welcome" Juyawa tayi ta kalli Khaleesat, ya dau box dinta ya mika mata yace "Can't you greet?" Baby tace "Ina wuni" Daga haka ta amshi akwatin Khaleesat ta shiga ciki, ya juya ya kalli Khaleesat dake rakube gefe daya bayan ta amsa gaisuwar Baby, ya hade rai yace "Baza ki shiga ba Malama" Shiga parlon tayi sannan ya bi bayanta ta cire takalmanta nan bakin kofa, Aunty ce zaune parlor sai Ummi uwar Hadiyah da Gimbiya Firdausi, Mami ma na zaune parlon da Hajiya Nafisa, Khaleesat sai da gabanta ya fadi sosai ganinsu gaba daya, duk suka daga kai suna kallon ita da Ajay, kasan carpet ta duka a hankali ta gaishesu tana kallonsu gaba daya, Ajay ya zauna kan kujera ba tare da ya yarda ya hada ido da su ba ya gaishesu shi ma, just Hajiya Nafisa da Ummi sai Gimbiya Firdausi ne suka amsa gaisuwansa babu yabo babu fallasa, Mami dai ko kallon inda suke bata yi ba, ita kuwa Khaleesat dama babu wanda ya bi ta kanta suka ci gaba da labarin da suke a parlon, ko ya hanya babu wanda ya tambaye su, jikin Khaleesat yayi sanyi sosai ta daga kai ta kalli Ajay dake danna wayarsa kawai, bude kofar parlon aka yi sai ga Jay ya shigo yana gyara face cap dinsa, Khaleesat dake durkushe kan carpet bata san sanda ta karasa zaunawa a kan Carpet din ba bayan sun hada ido da shi, within few seconds ya dauke idonsa daga nata, ita kuwa bata fasa bin sa da kallo ba ko kiftawar kirki bata yi, Ajay dai bai yarda ya dago kansa ba tunda ya lura Jay ne ya shigo parlon wayarsa kawai yake ta dannawa, a hankali Khaleesat ta gaida Jay har sannan tana kallonsa, Jay ya zauna without looking at her yace "Lafiya lau, sannu da zuwa" Mami na kallonsa tace "Baka zo kayi breakfast ba yau Jawwad and ur phone isn't reachable" Yace "A restaurant nayi" Mami tace "To Lunch fa?" Yace "Sai anjima" Baby ce ta shigo parlon rike da wayar Aunty ta nufeta tace "Momy u have a call" Aunty ta amshi wayar, Jay na kallon Baby ya nuna mata Khaleesat yace "Take her upstairs Baby" Baby ta kalli Khaleesat tace "Ok let go" Khaleesat ta sauke idonta ta mike ta bi bayan Baby da ta kai ta sama zuwa dakin da su Hadiyah suke, Hadiyah na kwance kan gado sai Maryam da Khadijah sisters din Walid, da Shahuda yarinyar Gimbiya firdausi ta biyu, sai Iklima yarinyar Hajiyah A'isha, ga kuma Bilkisu yarinya Hajiya Sumayya gaba dayansu cousins ne a dakin, kuma duk Shahuda ce babba sai Maryam Kanwar Walid, duk suka juya suna kallon Khaleesat kamar sun ga Alien ta shigo, ita kuwa ji tayi kamar an saka mata chain a kafa tsabar yanda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ganin zuka zukan matan dake dakin gashi duk sun zubo mata ido suna kallonta daga sama har kasa, tayi karfin halin karasawa cikin dakin ta zauna kasan carpet ta gaishesu gaba daya, Hadiyah dai sai kallonta take a walakance kamar taga bola, Shahuda na yatsine fuska ta kalli Baby tace "Wacece wannan kuma Baby kika shigo mana da ita?" Baby ta taɓe baki ta karyar da kai tace "I think Ya Ajay's wife, yanxu suka zo" Shahuda ta mike zaune a hankali daga kwancen da take tana kare ma Khaleesat kallo daga sama har kasa, can tace "Dama wannan ce matar tasa? Ikon Allah, ashe zabiya ce" Tsaki Hadiyah ta ja tace "Don Allah mu ci gaba da maganar da muke, what were we even saying before we were interrupted?" Maryam na kallon Baby fuska daure tace "To ke uwar wa yace ki kawo mana ita nan? Duk dakunan dake sama ki rasa inda zaki shigo da ita sai wannan? Ko baki da kai ne? Dama akwatin ta ne wancan kika shigo mana da shi daki?" Baby ta bude ido ta langwabe kai tace "Ya Jawwad ne fa ya ce in kawo ta Aunty" Hadiyah ta mike zaune jin abinda Baby tace, fuska a murtuke tana kallonta tace "Yace ki kawo ta ina? Ina kika gansa yace ki kawo ta nan, yaushe ya zo? Dalla dau akwatin can ki fitar mana da shi daga nan, kinga nan yayi kama da inda za a kawo bare" Ita dai Khaleesat kallon direction daban take babu ko kiftawan kirki tana jin duk abinda suke cewa, Iklima ta juya tana mata wani matsiyacin kallo tace "Keee duk nan da kike gani jinin sarauta ne babu wani bare, babu ordinary blood don haka can you kindly get out of here? They are other rooms ba wannan kadai bane daki a gidan nan, ko kuma ki tafi Garage dama babu komai a ciki...." Khadijah tace "Can you imagine don rainin wayo ma wani wajen daban take kallo ana mata magana ko er uban wacece ita oho, bari ki ji duk nan babu sa'an ki wallahi, mu ba class din ki bane ta ko ina, don haka get out of this room" Baby na kallon Khaleesat tace "Sun ce ki tafi wani dakin you are not welcome in their midst" Mikewa Khaleesat tayi a hankali bata dai ce komai ba, Baby ta kalli yayyin nata tace "Ko in kai ta dakin Granny kawai?" Shahuda ta jefa mata wani harara tace "Are you stupid? What is Granny's relationship with her da zaki kai ta dakinta? Ordinary person kamar ta zaki kai ta dakin Granny ko baki da kai ne, pls take her out before i loose my temper" Baby tace "Oh ohk, bari in kai ta dakin da ku ka ajiye boxes din ku to" Daga haka ta dau akwatin ta nufi kofa Khaleesat na biye da ita, Hadiyah ta bi ta da wani matsiyacin kallo kamar yanda Shahuda ma ta bi ta da kallon tsana don mutuwa ne kawai bata yi akan son Junaid ba amma daga karshe wai Khaleesat ta samesa a sama kusan a banza ba wani wahala tana er matsiyata da ita shine zata zama matar ɗan sarki me jiran Gado, Iklima ta rike haɓa tace "Dama ita ce Ya Jawwad ya so ya aura ya hadata da ke Hadiyah?" Hadiyah ta hade rai sosai tace "Plss bana son wannan maganar Iklima, keep quiet if you have nothing good to say" Shahuda ta koma ta kwanta tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta mara misaltuwa, gani daya da tayi ma Khaleesat taji duk duniya babu wanda ta tsana kamarta, Khadijah tayi dariya tace "Ko yaushe ma aka aurota da zata fara cuso kanta cikin abun da ya shafi gidan sarauta, who is she to intrude in our affairs? Who even invite her to this Convocation? Wallahi sai tayi da ta sanin zuwa taron nan, next time duk abinda ake a familyn gidan sarauta bazata yi marmarin sake zuwa ba balle ta shigo cikinmu, dama ace ba ordinary person bace da sauki, amma ke ba er kowa ba ki wani ce zaki shigo cikinmu ana mamaki magana ma kina kallon wani waje daban, to mun sa kafar wando daya da ita kuwa" Iklima tace "Wallahi she will regret coming to England" Hadiyah dai kokarin kiran Jay kawai take da wayarta fuskarta daure amma baya shiga. Dakin da Baby ta kai Khaleesat babu kowa ciki sai akwatunan wasu daga yan matan, a hankali Khaleesat ta zauna kasan carpet bayan Baby ta fita, lokaci daya hawaye ya fara sauka idonta kamar an bude pampo, daya bayan daya maganganunsu suka dinga dawo mata kai, Baby na sauka downstairs Jay dake zaune parlor har sannan ya kirata sannan ya mike ya fita waje ta bi bayansa, tuni dama Ajay ya bar gidan bayan da Baby ta raka Khaleesat sama, Baby na kallon Jay bayan ta bi sa waje tace "Gani yaya" Yace "Hope you gave her a separate room?" ta gyada masa kai yace "Ohk akwai abinci a gidan ai?" Ta ɗan karyar da kai tace "Akwai, fried rice Ummi suka dafa mana da chicken and Salad, very delicious" Yace "Ok now ki je ki xuba abincin ki kai mata da ruwa" Buga kafa tayi ta rungume hannu kamar zata yi kuka tace "Yaya na gaji da hawa stairs fa, sai ni ce kawai za ayi ta aika a gidan nan" Yace "C'mon Baby, be a good gal and do what I ask you" Ta langwabe kai a hankali tace "Ohk" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma daga nan yayi tafiyarsa gidan da ya sauka which isn't far from this House kuma duk gidajensu ne, Gimbiya Firdausi da Hajiya Sumayya ma can suke kwana da yayar mahaifin Hadiyah, Baby tayi yanda Jay yace mata ta kai ma Khaleesat abinci da ruwa sannan ta koma wajen uwarta ta kwanta jikinta, hira su Aunty suke amma gaba daya hankalin Aunty na kan Khaleesat da aka kai sama, abincin da Baby ta kai sama ma bata san ita zata kai ma ba ta zata yayyinta ne suka sa ta debo masu abinci da baza a kai ba, ita dai Khaleesat ko taɓa abincin da Baby ta kawo mata bata yi ba saboda bakin ciki gashi ta kasa daina kuka, she was so hurt da abinda suka yi mata, daga karshe haka ta tashi ta shiga bandakin da ta gani kusa da dakin ta dauro alwala ta dawo ta bude akwatinta ta dau hijab ta saka ta tada sallah.... Baby ta fito waje saboda kiran da Ajay yayi mata ta nufesa a inda yake tsaye tace "Gani yaya" ya mika mata ledan hannunsa yace "Take this food to her" Baby ta wara ido tace "Sau nawa za a kai mata abinci, Bayan ya Jawwad ya sa na kai mata abinci da ruwa daxu" Ajay yayi shiru jin abinda tace, can yace "Ohk, but still ki kai mata wannan ma" Tace "To ni ina nawa fa?" Ya hade rai yana kallonta yace "Ina wasa da ke ne?" Tayi yake tace "No Yaya" sannan ta amshi ledan ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma yayi tafiyarsa can daya gidan, Baby na shiga parlor da abincin Aunty ta kirata ganin leda a hannunta, ta tafi har kusa da Aunty tace "Ga ni Momy" Aunty tace "Meye wannan a hannun ki?" Baby tace "Ya Ajay ne ya bani abinci in kai ma wife dinsa" Aunty ta karɓe ledan ta ajiye kusa da ita tace "Tafi ki ban waje" Juyawa Baby tayi ta tafi ta zauna ta dau wayarta ta ci gaba da kallon Cartoon din da take. Khaleesat na kwance saman Carpet bayan ta idar da sallah da kusan minti talatin har sannan ta kasa daina hawaye, ko kallon abincin da Baby ta ajiye mata bata yi ba, text message ne ya shigo wayarta ta dau wayar tana dubawa taga Ajay ne ya turo mata message yace "You need anything?" Taji wani sabon hawayen ya zubo idonta, reply ta mayar masa tace "Eh" Sai ga wani message din nasa yace "What?" Ajiye wayar tayi tana goge hawayen dake zuba idonta bata mayar masa reply ba, bayan minti biyar sai ga kiransa ya shigo wayar, Sai da ya kusa katsewa tayi picking ta kai kunne tayi shiru, yace "Ke kika saka min katin zaki yi shiru? What is that you need?" Shesshekan kuka ta fara yi ta kasa ce masa komai, Calmly yace "What happened?" Ta ma rasa me zata ce masa kawai ta fashe da kuka, shiru yayi yana sauraronta for few seconds, can yace "Come outside" Bata ce komai ba, calmly yace "Kin ji me nace maki?" A hankali tace "Uhm" Daga haka ya katse wayar, goge idonta ta dinga yi duk da hawayen yaki tsayawa, after some minutes ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito, tana tafiya a hankali ta sauka downstairs, kanta a kasa ta nufi kofar fita waje ba tare da ta yarda ta kalli inda su Aunty suke ba, su Aunty da Mami da sauran matan dake parlon duk suka bi ta da kallo har ta fita ta kullo kofar, waige waige ta dinga yi a neighbourhood din ganin bata gansa ba, after almost 2 minute ta hangosa walking toward her, ta sunkuyar da kanta har ya iso inda take tsaye sannan ta daga kai tana kallonsa, yana kallon kwayar idonta da yayi ja yace "Me ya faru?" Ta girgiza masa kai sai ga hawaye na silalowa daga idonta, bai sake cewa komai ba yana kallon wani direction din, bayan few seconds ya nuna mata wani roadside chair yace "Zauna can" Ba musu ta tafi ta zauna wajen da yace, ya karasa cikin apartment din, kallo daya yayi ma su Aunty ya wuce sama without saying anything to them, Aunty dake cin abincin da ya ba Baby ta kai ma Khaleesat ta bi sa da wani kallo, haka ma Ummi da Mami, dakin da su Hadiyah ke ciki Ajay ya bude, gaba daya suka juya suna kallon kofar, one by one suka dinga gaishesa ganin shi ya bude kofar, duk yayi masu kallo daya ya fice daga dakin without bordering to answer their greetings, ya bude wani dakin yaga Hajja tana bacci sai Hajiya A'isha dake dakin, gaisheta yayi bayan ta amsa ya kullo dakin, ya bude last room din yaga box din Khaleesat da handbag dinta sai wayarta, shiga ciki yayi ya dau akwatin da handbag din ya saka mata wayar cikin handbag sannan ya fita daga dakin, tun da ya sauko downstairs su Aunty suka bi sa da kallon mamaki har ya fice daga parlon without looking at them, duk suka kalli juna irin kallon mamaki, Ummi ta gyada kai tace "Tabdi, dauketa zai yi a gidan yake nufi ko me?" Gimbiya Firdausi dai tayi shiru tana kada kafa a hankali fuskarta dauke da wani expression ita ma na mamaki, Aunty ta rike haɓa tace "Kun ga wani ikon Allah kuma" Ummi tace "To ku ka san me ta kintsa masa?" Gimbiya Firdausi tace "Ku kyaleni da shi" Ita dai Mami bata tofa nata ba don bai shafeta ba, Ajay na komawa inda Khaleesat take zaune ta bude ido sosai tana kallonsa da mamaki, ya ajiye mata akwatin ta da handbag ya zauna leaving much distance between them, sosai jikinta ya kara sanyi ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, wani bakin jinin yake son kara ja mata gun danginsu, wayarsa ya ciro yana duba hotel din da zai yi reserving, after a while ya gama making reservation din hotel din da yayi selecting ya biya kudi sannan yayi order din Indrive that will take them there, da kyar Khaleesat tace "Amma bai kamata ka dauko akwatina daga cikin gidan ba....." Wani kallo ya jefa mata yace "I will give you a dirty slap" a hankali ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, after waiting for almost 15 mins sai ga Indrive din ya karaso, Mikewa yayi ya dau handbag dinta ya ajiye mata kusa da ita ya dau akwatin ya kai Ride din, ta bi sa da kallo sai kuma ta mike jiki a sanyaye ta nufi motar ita ma, Front seat Ajay ya shiga bayan drivern motar ya saka akwatin a booth din motar, ita kuma ta bude back seat ta shiga, bayan tafiyar kusan minti talatin suka isa hotel din da yayi booking, without much wasting of time in the hotel reception tunda ya riga yayi reservation online suka yi lodging din hotel room din, gefen gado Khaleesat ta zauna a dakin har lokacin jikinta a sanyaye yake bata taɓa tunanin abinda zai yi ba kenan, ya shiga bandakin dake cikin dakin ya dauro alwala ya fito don lokacin la'asar har ya wuce, mikewa tayi ita ma ta tafi ta dauro alwala, ko da ta fito har ya tada sallah, ta dau wani hijab din nata a box ta saka ta tafi bayansa ta tsaya zata bi sa sallan..... HALYSAAH PAGE 126.... Khaleesat bata fasa rokon Ajay cikin rikicewa ba muryarta na rawa tana cewa don Allah ya barta ta tafi bandaki amma yaki ɗaga ta, da kyar take numfashi saboda weight dinsa da ya sakar mata amma ko lura da situation din da take ciki bai yi ba he was just smooching her tenderly all over her neck kuma iya abinda yake yi mata kenan sai hannunsa da yaki cirewa a kirjinta stroking it back and forth, kana ganinsa kasan he was so lost in the moment don tuni idanuwansa suka sauya launi suka dawo kamar na me jin bacci, Khaleesat ta dade bata shiga irin shock din nan da ta shiga ba don yayi mugun tsoratata, ganin abun ta dinga yi kamar a mafarki don in ance mata Ajay will do this bazata taɓa yarda ba, this was the least thing she expected from him, bai ma yi kama da wanda zai iya yi mata haka ba, kokarin sauke hannun rigar baccin jikinta yake yi cikin zafin nama, nan taji wani sabon strength ya zo mata ta fara kokuwa da shi trying so hard to push him off her cikin tashin hankali tana rokonsa amma sai da ya sauke rigar kasa gaba daya giving him full access to her radiant chest, nan ya kara birkicewa gaba daya, and it seems he was just after the chest a duk jikinta, bata san sanda ta dinga matse laps dinta ba tana cewa zata je restroom amma bai ma san tana yi ba, kawai vibration din wayarsa dake kusa da su ne ya dawo da shi duniyar da ya tafi, lokaci daya ya fada gefenta da sauri yana sauke numfashi looking so disoriented after realizing what he was doing, cikin few seconds ya sauka ƙasan carpet din dakin, tuni Khaleesat tayi using wannan opportunity din ita ma ta koma can daya side din gadon ta sauka kasa da sauri ko ina na jikinta na rawa tana kare kirjinta da hannunta, Ajay ya mike kamar ana hankadasa ya nufi kofar fita daga dakin almost stumbling over his feet, bai tsaya bangaren nasa ba kawai ya nufi part din Jay ya bude kofar ya shiga ya wuce bathroom dinsa, Khaleesat na ganin Ajay ya fita ta mance da wani Legend ta tashi ita ma ta maida rigarta ta fice daga part din cikin firgici ta koma dakin da take zama da gudunta, har sannan jikinta bai daina rawa ba, gaba daya ya tsorata ta, this was something she never saw coming saboda trust din da tayi masa, ta shiga bandaki da sauri tana duba laps dinta jin kamar period dinta ne ke zuba, after almost 15 mins ta fito daga bandakin duk jikinta a sanyaye ta jingina da bango tana shesshekan kuka, gaba daya ji tayi bata da sauran kuzari, she was so weak, har lokacin kuma ta kasa yarda da abinda ya faru don gani take kamar mafarki ne, after a while ta bude press din dakin ta ciro kayanta tana goge hawayen da yaki tsaya mata, cikin few minutes ta gama shiryawa har sannan bugun zuciyarta bai dawo dai dai ba ta nufi kofa da sauri ta bude ta fita, tsabar yanda take a rikice ta ma mance da wani kare a gidan, burinta kawai ta ganta out of the House, a haka ta sauka downstairs, luckily karen ma baya parlon ta nufi kofa ta fita kamar warce ake kora daga gidan ko waigawa bata yi ba. Wajen karfe tara Safiyyah ta bude kofar apartment dinsu jin ana danna bell, pajamas ne jikinta alamar she was still on bed, da mamaki ta dinga kallon Khaleesat daga sama har kasa tace "Ke kuma daga ina haka da sassafen nan?" Khaleesat taki yarda su hada ido kawai ta shiga cikin parlon tana kokarin hadiye kukan da ke neman kubuce mata, Safiyyah ta bi ta da kallo don ko jaka babu a hannunta balle waya gashi gaba daya ta ganta a firgice, can dai ta kulle kofar ta bi bayanta don dakinta ta nufa, zaune ta sameta kan kujera ga tsoro bayyane a fuskarta, Safiyyah tace "Wai me ya faru ne? Ko jikin Ajayn ne?" Kamar jira Khaleesat take ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "I regret listening to you Safiyyah, kin cuce ni wallahi, nayi dana sanin sauraronki, dama kin saba fadin abinda ba shi ba, kin saba zama ki kirkiro karyarki ko kunya baki ji" Safiyyah dake ta kallonta kamar me son gano wani abu ta zauna gefen gado tace "Ikon Allah ni Safiyyah, Wani abu ne ya faru kike kirana da makaryaciya da sassafen nan ko gama bacci banyi ba karar bell da kika danna ya tasheni" Khaleesat ta fashe da matsanancin kukan da yafi na farko ta rufe fuskarta da tafin hannunta cikin rawan murya tace "Don me zaki ce min kinyi mafarkin bashi da lafiya kika sa na shirya da daddare naje gidan alhalin lafiyarsa kalau? Ai ni ban san haka halinsa yake ba wallahi, and i trusted him with all my heart ban taɓa expecting haka daga garesa ba, a duk duniya he is among the people I trust with all my soul cause I feel secure with him, amma ni ban san haka yake ba, kuma har naji na tsanesa, I hate him because of this, he betrayed my trust for him" Safiyyah ta saki baki tana kallonta, can ta ɗan yi murmushi tace "To da kika je wani abu ya faru ne a gidan da kike irin wannan maganganun? Yau naga karfin hali, In ma wani abu ne ya faru naga dai mijinki ne, ko dai mantawa kike ku ma'aurata ne?? meye abun tashin hankali in ma nuna maki yayi shi mijinki ne?" Khaleesat ta wani kalleta da sauri, cikin few seconds tayi maza ta gyara zancenta tace "Ban gane abinda kike nufi ba, karen nan ne fa ya sake bi na ba wani abu ba, what are you talking about" Tana fadin haka ta mike ta tafi ta kwanta gefen gadon Safiyyah alamar bata son conversation din kuma, Safiyyah dai sai kallonta take tana murmushi don bata ga alamar gaskiya take fadi ba, can tace "Gaskiya karen nan bai kyauta ba gashi ya kora ki da sassafe, a can gidan kika kwana kenan?" Khaleesat taki ce mata komai ta hade rai, mikewa Safiyyah tayi ta fita daga dakin zata je kitchen, ita dai tasan ba haka nan Khaleesat ta taho gidansu da sassafe ba kamar warce aka koro, ina ma ace abinda take zargi ne ya faru kuma ace har ciki ya shiga da sai taga karyan iskanci wajen Khaleesat, bayan ta koma dakin tace "To ko dai in hada maki ruwan dumi a bandaki ne? You look stressed" Mikewa Khaleesat tayi ta zauna tana mata wani kallo tace "What are you talking about, wai kina tunanin ni zan taɓa yarda da shi ne no matter what Safiyyah? You think i will accept him as a husband bayan kin san abinda ya faru? Ai ni ba er cin amana bace kuma nasan halacci, don haka kar ma kiyi tunanin ko wani abu ne ya faru don nasan ki da banzan tunani, to babu abinda ya faru wallahi, kuma babu abinda zai taɓa faruwa cause we are not meant for each other, in ma zaki dena tunanin dake ranki ki dena, banda ma karen yasa na yar da makullin apartment dina a parlorn gidan kin zata zaki gan ni gidan nan ne, ba sai ma ya sake ganina a gidan zai yi attempting komai ba...." Safiyyah dai kawai tayi murmushi don tasan duk wannan nonsense din nata ya kusa zuwa karshe yau ko gobe, Ita dariya ma take bata, wai ba er cin amana bace ita, to amanar wa za a ci? Da ba don tasan Khaleesat na da ilimin addininta dai dai gwargwado ba da babu abinda zai sa bata yi tunanin ko dai islamiyya ne bata taɓa zuwa ba duk tsawon rayuwarta, wani lokacin in Khaleesat ta yi wata maganar sai tayi ta mamaki kamar warce ake controlling da battery don ko nazarin abinda zata furta bata yi, kanta tsaye take fadin duk abinda ya zo bakinta, wai ita ba er cin amana bace, Safiyyah ta taɓe baki tace "Samu kika yi, me yasa bakin ki wasn't this sharp for Abdul?? I wish zaki san value din da mijinki yake da shi wajen yan mata da yanda suke rubibinsa da burin mallakansa a matsayin miji da baki dinga shirmen nan ba, all because of Jawwad that is there enjoying his marriage...." Mikewa Khaleesat tayi ta shige bandaki ba tare da ta tsaya ta ci gaba da sauraronta ba. Har bayan la'asar Khaleesat na kwance dakin Safiyyah gaba daya mood dinta a dagule throughout, sai juye juye take yin kan gado, gashi har sannan her body was still weak from what happened in the morning, duk yanda ta so distracting brain dinta daga incident din hakan ya ci tura, don duk bayan mintuna kadan abinda ya faru sai ya fado mata a rai taji kamar it's happening at the moment, she still feels his hand gently moving round her chest, she still feels his rapid breathing on her chest, wani lokaci kuma taji kamar bakinsa na wuyanta don har sai ta kai hannu ta shafa wuyar jifa jifa, Safiyyah ta idar da sallah ta juya tana kallonta tace "Lokacin sallah fa ya wuce Madam" Khaleesat dai tayi shiru don ko magana taki yi da Safiyyah all through, a hankali ta sauka daga saman gadon ta nufi bandaki zata yi alwala Safiyyah ta bi ta da kallo, ta girgiza kai tana ɗan murmushi, dai dai nan wayarta ya fara ring, ta dau wayar ganin Ajay ne ta mike ta fita daga dakin, a parlor tayi picking call din nasa, maganar few seconds suka yi sannan ta fita can waje, gaban apartment dinsu ta gansa yayi parking yana jiranta, ta karasa har kusa da motar ya mika mata makullin hannunsa ta amsa sannan ya ja motarsa ya wuce. Sosai Khaleesat ta ji dadi bayan da Safiyyah ke sanar mata ai kamar akwai spare key din apartment dinta da Housemate ya taɓa bata da dadewa ta ajiye, Khaleesat tace "Don Allah kawo in ga ko shi ne, ko dai key din old apartment din mu ne" Safiyyah ta mike ta bude wani jakanta ta ciro makullin da Ajay ya kawo ta nuna ma Khaleesat tace "Duba ki ga, ban san ko na tsohon apartment din bane" Khaleesat ta wara ido ta amshi makullin tace "Ai kuwa na new apartment din ne wallahi, amma naji dadi sosai, let me just be going to my apartment dama na gaji" Safiyyah tace "To wayarki da kika baro can gidan fa?" Khaleesat ta hade rai tace "I don't want to talk about that" Safiyyah tace "To amma ki jira mu ci abinci don nasan ko kin koma ba abincin zaki ci ba" Daga haka Safiyyah ta fita daga dakin, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo da plate din shinkafa sai robobin drinks biyu, na zobo da wani me kamar kunun Aya, Safiyyah tace "Zan sha Zobon ke ki sha wannan" Khaleesat bata ce mata komai ba ta fara cin abincin a hankali duk da bata da appetite kwata kwata, kadan ta ci ta ajiye cokalin, zata dau ruwa ta sha Safiyyah tayi saurin cewa "To baki sha drink din ba ai" Khaleesat ta kalli robon drink din tace "Maman Aslam ce tayi?" Safiyyah tace "Eh mana, kin san lokacin tana Nigeria shi take siyarwa online, manyan mutane ke siyan natural drinks dinta, a nan ma ana saka order" Khaleesat ta bude ta sha kadan to feel the taste, can ta kalli Safiyyah tace "Kamar ba kunun Aya ba ai" Safiyyah tace "Mix nutritious kunun Aya ake ce masa, sai kin ci gaba da sha zaki ga ya ma fi kunun Aya dadi da gardi, shegen tsada fa garesa shi yasa na dauko daya kawai kar gobe ta kulle fridge dinta" Khaleesat ta ci gaba da sha don yana da zaƙi sosai, bayan ta sha ya wuce rabi ta ajiye sauran Safiyyah ta hade rai tace "To waye zai shanye wannan din da kika rage, salon ta kullaceni in taga na dau mata abu kuma bamu shanye ba" Khaleesat ta dau sauran ta shanye don bata son jaraban Sophie, bayan ta ajiye empty goran ta mike ta fara shirin tafiya Apartment dinta.... Tun da Khaleesat ta isa gida take kwance kan 3 seater a parlor tana jin jikinta duk a mace, weakness din da take ji har yafi wanda ta yini take ji yau, ta ma rasa gane yanayin da take ji a jikinta, kan kace me ta dawo kamar mara lafiya, wajen karfe bakwai da rabi ta mike zaune da kyar a ranta tana addu'an Allah ya sa akwai pad a gidan cause she is expecting her period is here, tashi tayi tana tafiya a hankali ta wuce sama zuwa dakinta, ta ciro pack din pad a cikin kayanta ta dau daya ta shiga bandaki, after taking her bath ta dauro alwala ta fito ta saka doguwar riga ta dau Hijab dinta a cikin press sannan ta shimfida darduma ta tada sallah, tana idarwa ta kwanta kan darduman ta lumshe ido. Washegari haka Khaleesat ta yini a sama tana bacci don daren jiya bata wani yi bacci isasshe ba, da yamma bayan tayi wanka tayi sallan La'asar tana kitchen tana dafa tea taji kamar an bude kofar apartment dinta, sosai gabanta ya fadi ta juya da sauri tana kallon kofar kitchen din duk da ba ganin wanda ya shigo parlon zata yi ba, a hankali ta kashe gas ta koma gefe ta tsaya taki fita daga kitchen din duk da hijab din da tayi sallah ne jikinta har sannan, tana ta tsaye har na minti goma daga karshe ta dake ta leka parlon, yana zaune kan kujera ya saka face cap idonsa sanye da Black glasses yayi keeping serious face, sosai taji gabanta ya fadi ta koma kitchen din da sauri ta jingina da cabinet kamar zata yi kuka, har cikin ranta taji tana tsoronsa kuma yanxu, ta kara tsayuwan wani minti biyar a kitchen din kafin tayi karfin halin fitowa ko ta kan shayinta bata bi ba don har taji shayin ya fita ranta, ko da wasa bata yarda ta kalli inda yake zaune ba kanta a kasa ta nufi stairs tana tafiya a hankali zuciyarta na bugawa, ya bi ta da kallon gefen ido ta cikin Glasses dinsa ba tare da ya juya kansa ba, sai da yaga zata haura stairs yace "Kee" Cak ta tsaya jin serious tone din da yayi using, sai kuma ta juya kamar munafuka ta ɗan kallesa, lokaci daya tayi saurin sunkuyar da kanta tana wasa da hijab din jikinta, duk da ba ganin idonsa take ba amma wani irin kunya taji take ji, after some seconds ya mike ya nuna mata kofar fita apartment din calmly yace "Mu je" Bata san sanda ta sake kallonsa da sauri ba gabanta na faduwa, sai kuma ta marairaice kamar zata yi kuka tace "Ni dai wallahi nafi son apartment din nan don Allah kayi hakuri ka bar ni pls, we are starting exams upper week ina son in dinga karatuna quietly a nan, nafi gane karatun a gidan nan" Ya hade rai yace "Fita mu je na ce" Hawayen dake makale idonta suka zubo, cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri ka bar ni...." Tsorata tayi saboda tsawan da ya daka mata ya nuna mata kofar fita daga apartment din, bata sake masa musu ba tana goge hawayen idonta jikinta na rawa ta nufi kofar fita daga apartment din ya bi bayanta, har suka koma can gidan hawaye take, sosai hankalinta ke a tashe and she felt just like she is with a total stranger, a hankali take haurawa sama tana goge hawayen da yaki tsaya mata bayan sun shiga gidan, tana jin yana biye da ita a baya amma taki yarda ta juya saboda tsoro, zata shiga dakin da take zama taji muryarsa yace "Walk straight" Sai a sannan ta juya ta kallesa, har lokacin yaki cire glasses din idonsa da face cap kuma kallonta yake directly in the eyes baya ko kiftawa, kamar ta sani ta sunkuyar da kanta, Calmly yace "Ba ki jin turanci ne?" Juyawa tayi ta ci gaba da tafiya a hankali walking down the corridor kamar yanda yace, kawai taga ya wuce ta, sannan yayi knocking kofar wani daki yayi sallama, after few seconds ya cire face cap dinsa da glasses din idonsa ba tare da ya bari su hada ido da Khaleesat ba ya bude kofar ya shiga ciki leaving the door open, Khaleesat: da gabanta ke ta faduwa wondering who was inside the room ta ɗan leka cikin dakin before going in, wani ƙara tayi tana zaro ido with surprise ganin Aunty Farida zaune cikin dakin, bata san sanda ta nufeta da gudu ba ta tafi ta fada kanta ta kankameta. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** HALYSAAH PAGE 127 Tsabar farin ciki Khaleesat kawai fashewa tayi da kuka don bata taɓa zaton ganin Aunty Farida a Maryland ba, she thought she was dreaming, ta kara rungumeta muryarta na rawa tace "Wayyo Aunty baki gaya min zaki zo ba ai" Aunty Farida ta ɗan yi murmushi tace "Ai na zata Junaid ya gaya maki" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana hawayen farin cikin ganin kanwar Ummanta, tuni Ajay ya fita ya bar dakin, Aunty Farida na kallonta tace "Ya karatun?" A hankali Khaleesat tace "Alhamdulillah, za mu fara jarabawa sati na sama in sha Allah Aunty" Aunty Farida tace "Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya baku nasara" Cike da shagwaba Khaleesat tace "Aunty ina Ummata da Baba har da Nenne?" Aunty Farida tace "Duk suna gaishe ki" Khaleesat ta gyara zama tace "Amma yaushe kika zo? Yau ko jiya? Kuma naga you look dull, ko dai gajiyan hanya ne?" Aunty Farida tace "Daxu da rana ya dauko ni Airport, dama dolw akwai gajiya mana...." Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace "Aunty naji dadin ganin ki sosai" Aunty Farida na kallonta tace "Bakya cin abinci ne kika rame" Khaleesat ta marairaice tace "Karatun final exams fa muke yi" Aunty Farida tace "Haka ne, Allah ya baku Sa'a" Sosai taga Khaleesat ta kara kyau, fatar ta sai wani sheki yake amma kuma ta rame, abincin da Ajay ya siyo ma Aunty Farida ta dau daya a ciki ta fara ci, don abinci kala hudu yayi ordering mata daban daban, Aunty Farida dai sai bin ta da kallo take, har aka yi magrib Khaleesat taki barin dakin sai labari take yi ma Aunty Farida, she look so excited don ma dai taga Aunty Farida kamar bata son magana don sama sama take amsa ta, kawai tayi tunanin saboda gajiyan hanya ne, dakinta ta tafi zata dauko extra darduma ta kai dakin da Aunty Farida ta sauka, tana shiga dakin taga wayarta saman gado a ajiye, daukar wayar tayi tana turo baki ta duba ko ya fashe taga ba abinda yayi, number Safiyyah tayi dialing babu bata lokaci ta ɗaga, cike da murna Khaleesat ke sanar mata da zuwan Aunty Farida, duk da Safiyyah ta san Aunty Farida na hanya dama amma tayi pretending tace "Ke haba dai? Da gaske Aunty Farida ta zo??" cike da murna Khaleesat tace "Wallahi in gaya maki" Safiyyah tace "Ai ko gobe da safe ina nan zuwa gidan, Aunty Farida a Maryland?? Lallai mun yi babban bakuwa, zan mata girki kuwa in taho mata da shi gobe" Khaleesat na murmushi tace "To sai kin zo goben, ki zo da wuri plss" Safiyyah tace "In sha Allahu kuwa" A haka Khaleesat ta katse wayar ta fita daga dakin tana rike da darduma, ido hudu suka yi da Ajay ya taho daga part dinsa, ta hade rai ta wani cinno baki kamar ba ita ke murmushi ba ta juya tayi tafiyarta dakin da Aunty Farida take, ya bi ta da kallo. Karfe tara da rabi na dare Aunty Farida ta kalli Khaleesat dake zaune kusa da ita tana danna wayarta tace "Ki tashi ki tafi sai da safe, ni kwanciya zan yi" Khaleesat ta ajiye wayar hannunta tana kallonta da mamaki tace "Aunty in tafi kuma, nan zan kwana ai muyi hira" Aunty Farida ta hade rai tace "Hiran uban me za ki min?" Ganin babu wasa tattare da ita yasa Khaleesat ta mike a sanyaye tayi mata sai da safe tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta fita daga dakin, hawaye taji ya cika idonta, tun zuwan Aunty Farida taga ta ki sake mata fuska har tana tunanin ko duk gajiyar hanya ce, magana ma sama sama kawai take yi mata, haka nan Khaleesat ta koma dakinta cikin sanyin jiki ta kwanta tayi lamo kan pillow. Washegari da asuba Khaleesat ta shiga gaida Aunty Farida, Aunty Farida ta amsa gaisuwarta, Khaleesat na wasa da hijab din jikinta tace "Ya gajiyan hanya Aunty?" Aunty Farida tace "Lafiya lau" Kwanciya Aunty Farida tayi don dama zaune take saman darduma tana azkar, after some minutes Khaleesat ta mike a hankali ta fita daga dakin ta koma dakinta, zaunawa tayi gefen gado ta fara tunanin to ko dai Ajay yace mata tayi masa wani abu ne bayan babu abinda ta taɓa masa tunda take, hawaye ya cika idonta ta kwanta gefen gado tana goge hawayen, bata koma bacci ba har karfe takwas sannan ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya ta dau hularta ta saka sannan ta sauka downstairs zata shiga kitchen ta dora breakfast, zaune ta tarar da Ajay da Aunty Farida a parlor suna hira, tana hada ido da shi ta wani hararesa fuska daure ta wuce kitchen, shi dai ya ci gaba da maganar da yake yi da Aunty Farida, har aka yi azahar Aunty Farida bata yi wani hira da Khaleesat ba sai ma voice note da take tayi da Umma suna hira, duk jikin Khaleesat yayi sanyi don har ta gama concluding akwai abinda Ajay ya gaya mata, wani azababben haushinsa ta dinga ji a ranta, tana kitchen tana duba abincin da ta dora wajen karfe biyu Safiyyah ta shigo kitchen din da warmers din abinci a hannunta tana washe baki tace "Su Khaleesat yau a kitchen ga kamshi duk ya cika gidan nan, sai fa Aunty Farida tayi zaton cikin lumana ku ke zaune gidan nan ke da Ajay, sai kace girki kika saba yi a gidan" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba ta amshi warmer din hannunta daya ta ajiye, Safiyyah na kallonta ganin mood dinta tace "Lafiya? Ya na gan ki haka? Me ya faru" Cikin rawan murya Khaleesat tace "Wallahi ban taɓa ganin devil kamar mutumin nan ba Sophie, gashi nan ban san me da me yaje ya gaya ma Aunty Farida ba don tun da ta zo taki sake min fuska alhalin shi tana ta hira da shi, ni kuwa da kyar take amsa min magana idan nayi mata, shi bayan iskanci har da gulma dama ya iya ban sani ba" Safiyyah ta bude baki tace "Kai haba? To ke baki tambayeta me yasa take amsa ki haka ba?" Khaleesat ta fashe da kuka tace "Wallahi taki kula ni mu yi hira tun jiya, alhalin shi sosai take magana da shi har da dariya, wallahi nasan sharri kawai ya laka min a wajenta, dama manipulator ne shi ban sani ba ashe" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Amma anya kuwa Ajay na da wannan lokacin Khaleesat, yaushe zai je yace masu ai kin hanasa hakkinsa?" Khaleesat ta mata wani kallo ta tsuke fuska, Safiyyah ta rufe bakinta da hannunta da sauri tace "Au, to... cewa zan yi yaushe zai ce masu baku zaune lafiya bayan magana ma sai ya ga dama yake ma mutum, kema kin san ba shi da wannan lokacin sai dai ki masa sharri, mutumin da ko magana ma sai ya so yake yi, ni dai bari in je in sameta, Allah ya sa kar laifin ki ya shafeni, bari in tafi mata da shinkafar sai ki taho da miyan" Daga haka Safiyyah ta fita daga kitchen din sai kuma ta dawo da sauri tace "Dakin ki ta sauka?" Khaleesat ta goge hawayen dake makale idonta ta girgiza mata kai sannan ta mata describing dakin da Aunty Farida ta sauka, Safiyyah ta fita daga kitchen din ta wuce sama, a stairs suka hadu da Ajay ta gaishesa ya amsa sannan ta wuce sama, da fara'a Aunty Farida tayi welcoming din Safiyyah, Safiyyah na murmushi tace "Kin sha hanya Aunty, ya gajiya?" Aunty Farida tace "Alhamdulillah, ya mutanen gidan naku?" Safiyyah tace "Lafiya lau wallahi, ya su Umma da Nenne?" Aunty Farida tace "Umma suna gaishe ku gaba daya" Safiyyah tace "Ai mun kusa gamawa da Maryland in sha Allah mu koma gida" Aunty Farida tace "Allah ya baku sa'a Safiyyah" Safiyyah tace "Ameen Aunty" Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta tace "Tun da mu ka yi chatting dake few weeks ago Safiyyah hankalina yaki kwanciya har yanxu, dama kuma Junaid yana ta insisting in zo Maryland tun bayan sun dawo babu dadewa amma naki saboda naga kamar yayi wuri ace na zo, wannan abun da kika gaya min yasa nayi accepting na taho yanxu, ashe dama abinda Khaleesat take yi kenan Safiyyah? Me yasa tun da kika yi noticing hakan baki gaya min da wuri ba?" Safiyyah ta ɗan yi murmushi tace "Aunty ai ina ta kallon ko zata canza ne amma sai naga abun nata gaba yake yi, ga kuma chatting da naga tana yi da Jawwad, i tried my best in sa ta a hanya taki, kuma kin san ta da taurin kai" Cike da takaici Aunty Farida tace "Don bata da kunya har fa message ta min bayan mun yi magana dake da kwana daya wai in tura mata number Jawwad zata gaisa da shi ta WhatsApp tayi misplacing number sa, da baki min magana ba bazan kawo komai a rai ba zan tura mata, kuma ko da baki riga kin min magana ba nima zan ga ai Junaid ya kamata ta tambayi number Jawwad ba ni ba, yanxu abun kunya Khaleesat ke son ja mana a idon duniya kamar bamu bata ilimin addini ba? Allah ya rufa mana asiri tana neman tona mana??" Safiyyah tace "Amma dai baki gaya ma Umma wannan maganar ba ko Aunty?" Aunty Farida tace "Ban gaya mata ba, don zata shiga damuwa ne sosai" Safiyyah tace "To Allah ya sa komai ya canza a dalilin zuwan ki, amma kam Khaleesat tayi nisa bata jin kira, kuma fa duk da haka Ajay bai fasa yi mata duk abinda ya kamata ba just to make her comfortable in this country" Aunty Farida tace "Tsinuwar Allah take ta kwasar ma kanta kuma idan bata yi hankali ba tun ba aje ko ina ba zata gane kurenta, duka duka shekarunta nawa da ta san salon shaidanci haka? Wato rayuwar da tayi da Abdul bata dau darasin komai ba sai ma dodewa da kwakwalwarta ya kara yi" Safiyyah tace "Yanxu da na shiga kitchen take min kuka wai duk yanda aka yi Ajay ya laka mata sharri a wajenki, wai tun da kika zo kin ki kulata in ta maki magana da kyar kike amsata, ni dai Aunty kawai ki nuna mata kamar ba komai sai ki sa ta a hanya kawai idan ba haka ba zata sake kullatar Ajay ne" Shigowar Khaleesat dakin yasa Safiyyah ta gyara zama tana murmushi tace "Allah sarki, amma dai kina nan har mu gama exams ko Aunty? Nan da kwanaki kadan za mu fara jarabawan" Aunty Farida tace "A'a gaskiya, ina ni ina zama har ku gama exams, few days zan yi in koma in sha Allah" Khaleesat ta ajiye warmer din miya dake hannunta sannan ta juya ta fita daga dakin fuskarta babu walwala, parlor ta sauka suka sake hada ido da Ajay dake zaune parlon yana shan fruit, ta zabga masa wata uwar harara kamar yanda tayi sanda zata wuce sama ta kai coolern miya, mikewa yayi fuskarsa a murtuke tana ganin haka ta juya da gudu ta koma sama. Bayan tafiyar Safiyyah da yamma Aunty Farida ta sa Khaleesat ta dauko mata madara da cup a kitchen, tun da Safiyyah ta bar gidan sai sannan Aunty Farida tayi mata magana, ta tafi kitchen ta dauko mata madaran da Cup ta kawo mata tana kallonta cikin sanyin murya tace "Aunty shayi zaki sha in dauko maki Milo?" ba tare da Aunty Farida ta kalleta ba tace "Haka nace maki" Khaleesat dai na zaune tana kallon abubuwan da Aunty Farida ke cirowa can kasan akwatinta har ta gama fiddo su, kauda kai Khaleesat tayi, can ta mike zata fita daga dakin Aunty Farida tace "Ina za ki?" A hankali Khaleesat tace "A'a dama gyara kaya nake a dakina" Aunty Farida tace "Dawo ki zauna" Ba musu ta dawo ta zauna, daya bayan daya Aunty Farida ke mixing mata magungunan da ta ciro akwatinta tana bata, ita dai sai dai ta amsa ta sha don bata ga alamar wasa fuskar Aunty Farida ba balle har tace A'a, amma a ranta takaici take me yasa ba a ga kayan a Airport ba sanda ta shigo kasar, a haka har ta gama shan magungunan matan fuskarta babu walwala ta mike ta fice daga dakin ta koma nata dakin. Khaleesat na ta kwance dakinta har kusan karfe bakwai tun bayan da ta ga Aunty Farida zaune downstairs da Ajay suna hira wajen karfe biyar, beside that gaba daya yanayinta ya canza kamar dai yanda taji shekaranjiya, she was just restless from what she is feeling, har fruits salad tayi niyyar hada ma Aunty Farida amma taji bata da strength din zuwa tayi mata, bayan ta idar da magrib tana sanye da hijab dinta har kasa tana tafiya a hankali ta tafi dakin da Aunty Farida take, zaune ta sameta kan darduma ta idar da sallah ita ma, taga har Ajay ya mata order din abinci, gefen kujeran dakin ta zauna a hankali tace "Aunty a kawo maki fruit ne?" Aunty Farida tace "A'a, Cup zaki dauko min kitchen" Khaleesat ta mike ta fita daga dakin ta sauka downstairs, tana shiga kitchen din taga Ajay a tsaye yana making cup of coffee, ko kallonsa bata yi ba ta dau cup din da zata dauka ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido, tun da Khaleesat taga Aunty Farida wani maganin matan zata bata ta hade rai, sai kuma ta juya zata fita Aunty Farida tace "Gidan uwar wa za ki?" Ta juyo kamar zata yi kuka tace "Ni fa Aunty zuciyata tashi yake yi tun daxu" Aunty Farida tace "Yayi fiffike zuciyar, dalla zo ki amsa gantalalliya kawai" Khaleesat ta tafi ta zauna ta amshi cup din hawaye har ya cika idonta, bayan na cup din Aunty Farida sai da ta kara mata wani daban, tun a nan ta fara jin wani iri jikinta... HALYSAAH PAGE 128... Karfe tara da rabi Khaleesat ta shigo wajen Aunty Farida tana sanye da hijab har kasa zata yi mata sai da safe, kana kallonta zaka yi tunanin she is sleepy by mere looking at her eyes, nan kuwa ba baccin take ji ba, Aunty Farida tace "Kin ci abinci ne?" A hankali Khaleesat ta gyada kai tace "Na ci" Aunty Farida tace "To ga fruits" Ta girgiza kai tace "Na koshi" Aunty Farida ta nuna mata ledan dake kusa da akwatinta tace "Hajiya Zaliha ta bada a kawo maki sakon can" Khaleesat ta karasa wajen ta duka zata dau ledan taji sallaman Ajay baki kofar dakin, kawai ji tayi gabanta ya fadi ga wani tashi da tsikar jikinta yake, ya karaso cikin dakin bayan Aunty Farida ta amsa sallaman sa, yace "Sai da safe Aunty, hope baki bukatar komai?" Aunty Farida tace "A'a ba abinda nake bukata Junaid, Allah ya tashe mu lafiya" Yace "Ameen" Juyawa yayi ya fita daga dakin, sai a sannan Khaleesat ta dago ta koma ta zauna inda take zaune, a hankali take bude ledan taga hadaddun turarruka ne na humra da oil perf, tun bata bude su ba kamshin ya gama gauraye ko ina na dakin, dama tun safe take ta jin wani kamshin a dakin ashe wa ennan turaren ne suka cika ko ina, ta ɗan yi murmushi tace "Nagode sosai, zan mata godiya ta WhatsApp, muna chatting once a while da ita" Mayar da turarurrukan tayi cikin leda zata mike Aunty Farida dake kallonta tace "Ba bangaren mijinki za ki ba, sai ki shafa turaren ai" Nan da nan ɗan fara'an dake fuskar Khaleesat yayi escaping, ta ɗan kalli Aunty Farida dake ta kallonta, hakan yasa ta bude turaren ta shafa kadan a hannu ta goga a hijab dinta, Aunty Farida tace "Dama ance maki na kaya ne ko baki da hankali ne?" Khaleesat dai bata ce komai ba, Aunty Farida tace "Cire Hijab din" Ba musu ta cire hijab din, doguwar rigan bacci ne jikinta da ya wuce gwiwa, sanin babu inda zata je sai dakinta ta shafa turarurrukan sosai a jikinta sannan ta maida Hijab dinta, bata kara minti biyar a dakin ba tayi ma Aunty Farida sai da safe ta koma dakin da take ta cire Hijab dinta ta kwanta bayan ta kara AC din dakin don ita kadai tasan abinda take ji a jikinta kuma har yafi yanda take ji daxu. Khaleesat na kwance wajen karfe sha daya taji an bude kofar dakinta, sosai taji gabanta ya fadi, amma taki juyawa taga wanda ya bude kofar cause she is backing the door, gabanta ya dinga faduwa after imagining Ajay ne, jin an kulle kofar yasa ta juya da sauri, Aunty Farida ta gani hakan yasa ta mike zaune tana gyara hulan kanta ta sunkuyar da kai, Aunty Farida ta nufeta tana kallonta cikin nutsuwa ta kwantar da murya tace "Khaleesat ki gaya min menene matsalar ki da Junaid? Kar ki boye min komai ki gaya min gaskiya" Khaleesat dai ta ki dago kanta tayi shiru, Aunty Farida tace "Ina sauraron ki dota, ko kina da wanda zaki gaya ma matsalar ki da ya wuce Umma ko ni?" Hawaye ya cika idon Khaleesat, cikin sanyin murya tace "To Aunty ai ni ban ce ina son sa ba aka aura min shi fa" Calmly Aunty Farida tace "To shi cewa yayi yana sonki da aka aura masa ke Khaleesat? Shi ma ae bai ce yana so ba" Khaleesat na goge idonta tace "To tunda ba ma son juna ba sai ya rabu da ni ba, ni kallon yaya da kuma Friend dina kawai nake masa" Still speaking calmly Aunty Farida tace "Idan ya rabu da ke kuma sai ayi yaya kenan Khaleesat?" A hankali tace "Sai in auri wanda nake so" Aunty Farida ta gyada kai ta kara kwantar da murya tace "To wanene wanda kike son?" Hawaye sosai ke sauka idon Khaleesat taki cewa komai, Aunty Farida tace "Jawwad ko?" Khaleesat ta fashe da kuka a hankali tana gyada mata kai, kawai jin saukan wani wawan mari tayi a fuskarta, bata gama recovering ba Aunty Farida ta kara mata wani lafiyayyen marin, gigicewa tayi ta dafe duk kuncinta ta fashe da kuka sosai zata sauka daga kan gadon ta daya side din Aunty Farida ta fincikota ta gwabje bakinta tana huci tace "Mahaukaciyar banza kawai shashasha gantalalliya warce bata san ciwon kanta ba, dama jira nake mu kai karshen zancen kafin in ci ubanki, mu za ki kunyata ki tozarta? Tarbiyyar da aka maki kenan a gida? To je ki auri Jawwad din don ubanki tunda ke karya ce mara zuciya warce bata san darajan iyayenta ba balle nata, banda kaddara ke har kin kai class din Junaid kike tunani da har zaki ce baki son sa? Uban me zai yi da ke banda shi din me biyayya ne ga ubansa? Wallahi yafi karfin ki ta ko ina, kuma aurenki da Junaid yayi babban taimako ne gare ki da rufin asirin ki, amma har kike da shegen bakin da zaki bude kice baki son aurensa, ko Jawwad din ne mijinki bazai taɓa iyawa da mugayen halayyarki ba yanda yake da zuciya haka, ni yanxu na ma dena ganin laifin azabtar da ke da Abdul yayi a gidansa, don Allah kadai yasan abinda kike masa lokacin, to bari ki ji in gaya maki takanas na shirya na taho America don in lallasa ki, kafin ki tona mana asiri gwara in karya ki, Muna zaune wata mata ta zo gida ta tada mana iska ta zayyano mana duk zaman da kike da mijinki nace zan kuwa zo in gyara maki zama tunda shi Junaid din yaki fada mana cin mutuncin da kike masa, kuma in baki yi hankali ba kan in bar kasar nan sai na maki shegen duka wallahi" Kuka kawai Khaleesat take kamar an aikota tana bubbuga kafa kamar wata er yarinya, a fusace Aunty Farida tace "Ohh daman kuka kika samu??" Gun Charger din laptop dinta ta nufa da sauri, Khaleesat na ganin haka ta fice daga dakin da gudu bata tsaya ko ina ba sai bangaren Ajay, yana zaune kan kujera a Bedroom dinsa yana kallon wani Movie a Plasma dake dakin, hannunsa rike da cup din Coffee da yayi making a nan dakin da kettle, sai gata ta shigo har cikin dakin ganin baya parlor, ta zube masa kasan carpet ta rushe da wani matsanancin kuka, ajiye cup din hannunsa yayi ya mike da sauri ya nufeta ya duka gabanta holding on to her shoulder yace "Kee, What happened? Me ya faru?" Jinin da ya gani kwance gefen lips dinta da fuskarta da yayi ja saboda marin da Aunty Farida ta lallafta mata yasa yayi shiru yana kallonta baya ko kiftawa, babu abinda ya fado ransa sai ranan da ta kirasa a waya tana kuka yaje kofar gidan Maman Fu'ad a Hotoro ya sameta ta fito fuskarta da shatin marin da Abdul yayi mata sannan jini ya kwanta idonta.... Sauke idonsa yayi bai ce komai ba don ya riga ya gane ita da Aunty Farida ce, baƙin ciki da takaici ya sa Khaleesat ta kara sautin kukan da take yi ganin yaki ce mata komai, bata san sanda ta tura hannunsa daga shoulder dinta ba a fusace tace "Idan baza ka ce min komai ba ka dena kallona" Tana fadin haka ta mike tana kara sautin kukanta zata tafi kan kujera tayi ball da cup din tea da ya ajiye bata sani ba, wani ƙara tayi ta zaro ido tana yarfe hannu tace "Wayyo kafana, na shiga uku...." Lokaci daya ya mike ya tafi kusa da ita da sauri yana kallon kafar yaga coffee din ya zubar mata a kafar, ya ja ta zuwa bandaki ya kunna pampo ya tara kafar a bakin tap din, gaba daya ta cika masa kunne da kuka kamar wata yarinya, kawai gani tayi ya dauketa bayan ya gama wanke kafar suka fita daga bandakin, nan da nan ta dena kukan da take ta turo baki tace "Ni ka saukeni" Bai ajiyeta ko ina ba sai saman gadonsa ya hade rai yace "Zaki sha mari" Gaban mirror dinsa ya tafi ya dauko ointment ya dawo ya duka gabanta sannan ya bude ointment din yana kallon kafarta, gently ya fara shafa mata salve din in a circular motion a dai dai inda ruwan shayin ya zuba, tayi saurin janye kafarta jin kamar an hadata da electric tsabar wani irin shock da taji, ta fara komawa baya a hankali tace "A'a ni bana soo" Ya wani hade rai yace "Ina wasa da ke ne?" Hawa saman gadon yayi ya fixgo kafarta, tayi saurin hade laps dinta waje daya kar taje ya ga inner wear dinta, bai ma san tana yi ba don idonsa na kan kafarta da yake shafa ma ointment din, a hankali ta koma ta rufe fuskarta da pillow still joining her laps tightly together, har sannan kuma bata dena jin shock da take ji ba, can ya ɗaga kai ya kalleta ganin yanda take yi da laps dinta, ya dinga kallon laps din.... Wani ƙara Khaleesat tayi ta bude ido da sauri jin hannunsa a lap dinta, ya daure fuska yace "Har nan shayin ya zuba ne?" Bata tsaya basa amsa ba ta fara kokarin sauka daga kan gadon da sauri don ta tsorata, yayi hanzarin fixgota ya mayar da ita ya kwantar yana kallon kwayar idanuwanta, nan da nan ta gigice masa ganin wai lap din zai yi separating tace "Nooo, don Allah ka bari mana, wallahi ba abinda ya zuba a nan, don Allah stop it, ta ya shayi zai zuba nan??" Yana kallonta da idanuwansa da suka koma lumsassu cikin husky voice yace "Ta sama" kunya yasa taki yarda su hada ido ta fara masa magiyan ita ba komai a laps dinta amma duk magiyanta bai sa ya fasa abinda yayi niyya ba don sai da yayi, ai ko tayi saurin rungumosa jikinta taki basa access din ganin abinda yake son gani, hakan da tayi yasa kirjinta yayi distracting dinsa daga can, cikin zafin nama ya sauke rigar kasa, jikinta ya dau rawa ta fara rokonsa wai zata je bandaki, amma ko sanin abinda take cewa bai yi ba, outburst dinta ma sai yafi nasa a wajen..... *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 129... A hankali Khaleesat ta bude idonta wajen karfe shidda da rabi na asuba cause she slept like a baby, ta mike zaune da sauri don gari har ya ɗan fara washewa bata yi sallah ba, duvet ta jawo tana kara rufe jikinta da shi cause she is wearing nothing, abubuwan da suka faru jiya da daddare suka fara dawo mata daya bayan daya a kai, ta turo baki tayi saurin komawa ta kwanta ta rufe har kanta da duvet ta ji ina ma kawai tayi disappearing daga dakin ta ganta a dakinta saboda kunya, a hankali ta sauke duvet din tana jin wani sabon kunyan, sai kuma ta mike zaune tana dube duben inda zata ga towel da tayi wanka da daddare amma bata gansa a dakin ba, cikin rashin kuzari ta sauka daga saman gadon still covering her self with the duvet ta nufi bandaki, daya daga towels dinsa ta kara dauka sannan ta maida duvet din cikin daki ta koma bathroom din tana kallon sleeping dress dinta da inner wear da ya wanke ya shanya, wanka ta sake yi cause she felt the need of doing so, ta kuma yin alwala ta fito bandakin tana goge dogon gashinta da wani towel din daban, har lokacin ita dai a kunyace take sosai har bata son tuno abinda ya faru, nan ta fara tunanin yanda zata yi sallah saboda babu hijab a dakin, a hankali ta nufi wajen press din kayansa ta bude duk da bata ma san me take nema a ciki ba, ta ɗan bude ido ganin uban kayan da yake da shi kamar wani karamin boutique, haka ta dinga bude buden ko ina tana kallon kayansa, and the press was well organized, komai da inda yake ajiyewa, da mamaki take kallon well ironed hijab dinta dake ajiye cikin press din, nan ta tuna hijab din da ta saka ranan da Legend ya biyota har dakin ne, daukan hijab din tayi ta ajiye kan kujera ta tafi gaban madubi tana ci gaba da goge gashinta don bai bushe ba hair dryer dinta kuma na daki, ribbon dinta har biyu dake gaban madubin take kallo, sai kuma ta dauka ta daure gashinta da shi, kilan wa enda ta bari ne sanda ta kwana dakin, ta saka hijab dinta ta nufi kofa ta bude a hankali tana leka cikin parlon don so take ta koma dakinta, kwance ta gansa kan kujera yana bacci kuma bata ga alamar shi ma yayi sallah ba, ta fito daga dakin tana tiptoeing yanda bazata yi making ko wani sound ba ta fice daga parlon da sauri, tana shiga dakinta ta kulle ta jingina da kofa tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe idonta... Wajen karfe bakwai da rabi Khaleesat ta fita daga dakinta zuwa wanda Aunty Farida take, hijab ne har kasa sanye jikinta, a hankali ta bude kofar ta shiga ciki, ta tarar da Aunty Farida zaune dakin da littafin addu'o'i a hannunta, Khaleesat bata yarda ta hada ido da ita ba ta zauna kan Carpet ta gaidata a hankali, Aunty Farida ta kalleta ta amsa gaisuwarta dai dai sanda Ajay yayi sallama bakin kofar, Aunty Farida ta amsa ya shigo dakin, sosai gaban Khaleesat ya fadi jin muryarsa, yana shigowa suka hada ido daga ita har shi suka sunkuyar da kai kamar hadin baki, ya karaso dakin ya zauna suka gaisa da Aunty Farida, kamar munafuka Khaleesat ta mike har sannan taki daga kanta ta nufi kofa ta fita daga dakin. Throughout ranan Khaleesat bata sake haduwa da Ajay ba don kamar ma fita yayi tun safe, ba laifi yau Aunty Farida ta ɗan sake mata har suka ɗan yi hira kamar ba ita ta gaggaura mata mari ba jiya da daddare, wai sai yanxu ne take mata nasiha take nutsar da ita tana nuna mata Allah na fushi da ita idan ta ci gaba a haka tana matar aure amma tunanin wani na ranta tana shiga hakkin mijinta, ita dai Khaleesat na zaune ta sunkuyar da kanta amma ba wai hankalinta na kan maganganun da Aunty Farida ke yi mata bane, don babu abinda ya makale mata a rai ya hanata sukuni tun daxu sai incident din daren jiya, it's making her to be so ashamed, duk yanda ta so kauda tunanin abun a ranta hakan ya faskara, gashi the thought of the incident alone send quivers all over her body, wani lokacin she will just be carried away with the thought har sai tayi firgit ta dawo reality, karfe shidda saura na yamma Ajay yayi sallama kofar dakin da Aunty Farida take, sosai Khaleesat taji gabanta ya fadi don har sai da ta jingina da gadon dakin to calm her self down, ya shigo dakin ya zauna suka gaisa da Aunty Farida, kana ganinsa kasan he is not himself, Aunty Farida tace "Kamar kana bukatar kaje ka huta, you look stressed Junaid" Ya ɗan yi murmushi yace "Sure Aunty" Mikewa yayi ya fita daga dakin, sai da ya kullo kofar dakin ya jingina jiki for almost 10 seconds, haka ya wuni yau feeling so restless cause he realized he was actually double crossing a vow, and that is the work of the devil, yana tafiya a hankali ya nufi part dinsa.... Aunty Farida ta juya ta kalli Khaleesat ta hade rai tace "Sai ki tashi ki je ki kai masa abinci, ko abincin ma bakya basa?" Khaleesat tayi shiru tana kallonta, sai kuma ta marairaice a hankali tace "Aunty ai shi ba abincin kowa yake ci ba, shi yasa ni ban taɓa basa ba" Bude baki Aunty Farida tayi tana kallonta da mamaki, Khaleesat na ganin haka ta mike da sauri har tana tuntube ta nufi kofa, Aunty Farida tace "Ban taɓa ganin mahaukaciyar yarinya gantalalliya kamar ki ba, wato baki ma taɓa attempting basa abincin ba kenan, sai dai kiyi ki ci tunda ke kika ajiye kayan abincin, tir da halin ki wallahi, ina ga wannan dole sai na gaya ma Umma abinda ke faruwa ba wani batun boye boye kuma" Tuni Khaleesat ta fice daga dakin ta sauka downstairs, ta rasa yanda zata yi gashi tana tsoron kar Aunty Farida ta taho kasa ta sameta, can dai ta tafi Laundry room ta kulle kofar ta nemi waje ta zauna don ita wallahi kunyan zuwa bangaren nasa ma take ji balle har ta kai masa abincin da ba lallai ya kalla ba ma. Sai da gari yayi duhu Khaleesat ta koma sama ta shiga dakinta tayi sallahn magrib, ta jira har lokacin isha'i shima tayi sannan tayi wanka ta dau doguwar riga ta saka ta koma dakin da Aunty Farida take. Karfe goma saura Aunty Farida tace mata sai da safe ta tashi ta tafi, ba musu ta mike tayi mata sai da safe sannan ta fita daga dakin, kamar munafuka tana waige waige ta sauka downstairs ta sake komawa Laundry room ta shiga ta kulle kofar.... Haka Khaleesat ta dinga yi a gidan duk idan dare yayi sai ta tafi Laundry room ta makale, ba ma da daddare kadai ba even during the day sai taje tayi zamanta a can ta yanda idan Aunty Farida ta duba dakinta taga bata nan zata yi zaton tana bangaren Ajay ne, yanda take avoiding Ajay shi ma dai kamar haka yake avoiding dinta a gidan kamar bai son su hadu, ko haduwa suka yi a dakin da Aunty farida ta sauka baya kallon inda take har ya fita daga dakin, a haka Aunty Farida ta gama kwanakinta a Maryland ta fara shirye shiryen komawa Nigeria with the hope that Khaleesat ta canza kenan for good don kusan kullum kafin ta kwanta da daddare sai taje dakinta ta duba sai taga bata ciki duk zaton ta tana bangaren Junaid, nan ko bata san tarewa tayi a Laundry room ba har da shimfida tayi ma kanta a can, ana washegari Khaleesat za su fara final exams dinsu suka kai Aunty Farida airport da daddare, tun basu isa airport din ba take ta matsar kwalla a gaban mota don tasan dole zata yi missing din Aunty Farida duk da zaman takuran da tayi a Laundry room all through her stay, but she is definitely going to miss her, bayan sun sauka Khaleesat ta jingina da motar tana share hawayen dake zuba idonta, Aunty Farida dai tayi kamar bata san me take yi ba balle ta fara lallashinta, tana kallon Ajay ta kara masa sallama tare da godiyar hidiman da yayi da ita, shi dai kawai yayi murmushi leading her inside the airport, Khaleesat ta fashe da kuka a hankali ganin Aunty Farida tayi tafiyarta without even saying a goodbye to her, tana ta tsaye jikin motar har Ajay ya dawo bayan wani lokaci, ba tare da ya kalleta ba ya zaga zai shiga motarsa ya ji ance "Yarima" Juyawa yayi yaga wani colleague dinsa da suka yi PHd tare, ya dawo yana murmushi ya basa hannu suka gaisa yace "Longest time Usman" Usman yace "Wallahi kun buya kai da Jawwad, ba a jin motsin ku" Ajay yace "Kai ma ai ka buya, me kake yi a Maryland?" Usman yace "Na samu aiki a nan" Ajay yace "Maa sha Allah, Congratulations Usman, ka dawo da family din ka nan kenan?" Usman yace "A'a tukunna dai in sha Allah, ina processing din hakan very soon" Sai kuma Usman ya kalli Khaleesat da ta kauda kai tun zuwansa wajen tana kallon wani direction daban, Usman ya bude baki da mamaki yana kallon Ajay yace "Kar dai kayi aure babu labari ko a social media Yarima?" Ajay ya ɗan bude ido yace "Aure kuma? Haba dai, kanwata ce wannan, me zai hana a gaya maku idan aurena ya tashi, but na kusa soon in sha Allah, za a gayyace ku" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalli Ajay jin abinda yace, Usman yace "Ohh maa sha Allah, karatu kanwar taka take a nan ne?" Ajay yace "Yeah, final exams zata zana a John Hopkins" Usman na kallon Khaleesat calmly yace "To Allah ya bada sa'a yan mata, or should i say Gimbiya, don kanwar yarima ai princess ce" Khaleesat ta ɗan kallesa kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "Ina wuni" Bude front seat Ajay yayi ganin yanda Usman ke kallonta maimakon ma ya amsa gaisuwar da tayi masa, Ajay ya kalleta for the first time in many days yace "Get in" Sauke idonta tayi don suna hada ido sai da gabanta ya fadi, tana tafiya a hankali ta shiga motar ya kulle, Usman yace "Ai kuna nan gidan nan naku har yanzu, in sha Allah ko zuwa gobe idan na gama abinda nake yi zan zo" Bai rufe baki ba Ajay yace "A'a bana gidan yanxu, i got a new apartment" Usman yace "Haba, to za dai mu yi waya, sai ka bani address din apartment din" Ajay bai kallesa ba yace "Ohk" Sama sama yayi masa sallama ya zaga ya shiga motarsa ya ja motar ya bar wajen, sai da suka yi nisa sosai Khaleesat taji yace "Ana maki magana ki dinga wani yauki kamar kubewa, to wa za ki burge? Did you know him from anywhere ne yana maki magana kina jujjuya ido kamar owl" Khaleesat taki ce masa komai kamar bata ma san da ita yake ba, bai sake cewa komai ba a motar har suka isa gida, yana parking ta sauka a motar tayi wucewarta cikin gida ta shiga dakinta ta rufe, ta gama shirin kwanciya ta dau wayarta taga miss calls din Safiyyah, zaunawa tayi gefen gado ta kirata, Safiyyah ta ɗaga tace "Ina kika shiga ina ta kiran ki?" A hankali Khaleesat tace "Mun je kai Aunty Farida Airport" Safiyyah tace "Ayya shi yasa nake ta kira inji ko she is still leaving today, nasan kina nan kina kuka ko" Khaleesat taki cewa komai wasu hawayen na taruwa idonta, Safiyyah tace "In gaya maki daxu sai ga kiran Ajay a wayana..." Khaleesat tayi shiru na kusan 5 seconds kafin tace "Kiran me? Kuma ina ya samu number ki?" Safiyyah tace "Tab, ai ina da numbersa shi ma yana da nawa da dadewa, kin tuna shi ya turo min receipt din 10M da aka tura account din ki bayan Maman Abdul sun je sun amshi kudin Abdul dake account din ki? Ai tun sannan ni dai nayi saving number sa" Khaleesat tace "Ohk, kiran me yayi maki?" Safiyyah tace "He requested for Ya Musty's number, wai yana son yayi masa magana ko zai amince mu zauna dake a apartment din ki har mu gama Exams don zai ɗan yi tafiya" Khaleesat bata ce komai ba bayan taji abinda Safiyyah tace, can tace "Zai yi tafiya zuwa ina?" Safiyyah tace "Ikon Allah, ke kina matarsa baki san inda zai je ba sai ni?" A fusace Khaleesat tace "Ta yaya zai tafi ya bar ni ina final exams?" Dariya sosai ta ba Safiyyah, can Safiyyah tace "To ni dai kar yace na kwaso gulma na gaya maki, kar ki sa sauran mutuncina ya zube a idonsa, ki bari idan ya maki magana da kansa sai kice ta yaya zai tafi ya bar ki, ke baza ki iya zama babu shi ba gaskiya, kuma baza kiyi concentrating a exams din ba idan ba so yake ki fadi jarabawan ba" Khaleesat tace "Ni dai sai da safe" Daga haka ta katse wayar. Kamar yanda Safiyyah ta gaya ma Khaleesat hakan ne ya faru don tare suka zauna su biyu a apartment dinta for their final exams with the permission of Ya Mustapha, babu abinda Ajay bai siya ya ajiye masu a apartment din ba, sannan ga isasshen kudi da ya tura ma Khaleesat sai dai ita bata yarda baya kasar ba jikinta na bata yana nan, duk da gata ga Sophie amma duk zaman apartment din baya mata dadi, she was so bored ta rasa dalili, kullum babu wani walwala zaka sameta don ma dai karatu suke ba dare ba rana da Safiyyah, a haka har suka kare jarabawarsu ta final. Washegarin ranan da suka gama exams da yamma Safiyyah ta shirya zata tafi African Store wai tuwo da miyar vegetables zata dafa ita ta gaji da cin junk food, ita dai Khaleesat na kwance gefen gado tana danna wayarta kamar bata ma ji abinda take cewa ba, a haka Safiyyah ta bar gidan da shopping bag dinta, bayan tafiyarta da kusan minti sha biyar Khaleesat ta mike tana tafiya a hankali taje jikin window ta tsaya tana kallon neighborhood din unguwan, babu abinda ya tsaya mata a rai irin yanda ko sau daya Ajay bai taɓa kiranta yaji ya exams ba har suka kare exams din sai dai ya kira Safiyyah, har daga karshe tace ma Safiyyah kar ta sake gaya mata idan ya kira bata son sani, bude kofar dakin aka yi ita dai tana kallon waje don duk tunaninta Safiyyah ce ta fasa zuwa shopping din ta dawo, amma jin Safiyyah bata fara jero excuses din dawowarta ba ga kuma kamshin turaren da ya cika dakin yasa ta juya da sauri, tsaye ta gansa ya jingina jikin side din kofar dakin ya rungume hannu, idonsa sanye da glasses baƙi irin no respect, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, a takaice yace "Congratulations" Ta wani hararesa tace "Ka ce min Allah ya bada sa'a sanda zan fara ne balle kace min congratulations yanxu, bana bukata" Tana fadin haka ta juya kamar zata yi kuka, shi dai kallonta kawai yake, can ya karasa cikin dakin cike da kasaita ya tafi har inda take tsaye, tana jin alamarsa a bayanta ta juyo da sauri ta manne da jikin window din ta kasa kallonsa, yana kallonta ta cikin Glasses dinsa yace "Rashin kunya za ki yi min?" She couldn't say anything because he was very close to her ga kamshin turarensa da ya cika mata hanci, and her heart was racing very fast amma ba na tsoro ba, calmly yace "Ni kin ce min Allah ya kiyaye hanya da zan yi tafiya?" Ta wani kallesa ta turo baki sai kuma ta kauda kai tace "Ai ni nayi zaton auren ka tafi kayi" Ajay dake ta kallonta yace "Ohk, kawarki bata gaya maki ba kenan?" Khaleesat ta maido kanta tana kallonsa, Yace "Ur Aunt, ur Mom, the Jawwad you are chatting with, duk basu gaya maki ba?" Yanda take kallonsa haka shi ma yake kallonta directly in the eyes, speaking calmly yace "To aure naje nayi, so now ki hada kayan ki, you will be leaving for Nigeria tomorrow at noon, I will send you ur flight ticket via Whatsapp" Yana fadin haka ya juya ya nufi kofa ya fita daga dakin ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, har Safiyyah ta dawo gidan Khaleesat na tsaye inda Ajay ya bar ta ko motsawa bata yi ba daga wajen, Safiyyah tayi cilli da mayafin jikinta tana cewa "Tirr sai kin ga ganyen duk ya langwabe kamar na yan iska, in ba dole ba me zan yi da wannan ganyen, ni da nake son fresh vegetable soup" Jin Khaleesat tayi shiru, Safiyyah ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "Me kike yi jikin window ke kuma?" Khaleesat tayi shiru taki ce mata komai tana tafiya a hankali ta karasa gefen gado ta zauna, Safiyyah dai bata sake bin ta kanta ba ta fita daga dakin zata je tayi girki don dama duk kwanan nan Khaleesat ba wani kulata take ba tun da Ajay ya fara kiran wayarta, ita dariya ma abun ke bata sosai ba kadan ba, wani lokacin da gangan take ce mata Ajay ya kira ko da kuwa bai kira din ba. Karfe shidda saura na yamma Khaleesat ta sauko downstairs, Safiyyah dake zaune parlor tana jiran miyanta ya karasa tace "Ina za ki?" Without looking at her tace "Zan ciro kudi ne" Daga haka ta nufi kofa ta fita daga parlon ta nufi Lyft dake jiranta. Domin karanta page 130 sai ku danna bulun rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kasa HALYSAAH PAGE 130... Tun da Mami ta bar parlon Khaleesat ke zaune kan kujera lokaci lokaci take satan kallon Ajay da yaki kallon inda take, daga karshe tayi breaking silence din parlon a hankali tace "Dama fa warmer din da Mami ta baka zogale jiya naje in maida mata...." Mikewa yayi ya dakatar da ita without looking at her fuska daure yace "Ban tambaye ki ba" Daga haka yayi shigewarsa daki, ita dai ta bi sa da kallo, lokaci daya jikinta yayi sanyi, bayan kusan minti ashirin ta mike tana tafiya a hankali ta nufi cikin dakin, zaune ta samesa gefen gado ya dafe kansa, ta sauke idonta ta karasa cikin dakin ta tsaya kusa da gadon cikin sanyin murya tace "In kawo maka breakfast din nan?" Bai tanka ta ba, tana ta tsaye for almost 5 minutes, ganin yaki cewa komai ta juya walking slowly ta fita daga dakin, fita tayi daga parlonsa ta koma can babban parlon dake part din, ta karasa ta kulle kofar parlon don in aka zo wucewa ta corridor din dole sai an kallo cikin babban parlon in dai kofar a bude yake, ta tafi kan kujera ta zauna ta fara goge hawayen da ya taru idonta, sai yanxu ne ma ta fara jin zafin abinda Hadiyah tayi mata, hade kai tayi da jikin kujeran tana shesshekan kuka a hankali... Wajen karfe biyu sai ga Mami ta bude kofa ta shigo parlon Khaleesat dake zaune kan darduma tun da tayi sallah ta gaishe da ita cikin sanyin murya, Mami ta zauna kan kujera ta amsa gaisuwarta, bayan few seconds cikin karfin hali Mami tace "Halysaah ki gaya min gaskiya, kar ki boye min komai, kin tabbata duk abinda kika gaya min daxu da safe haka ya faru ko kin boye min wani abu?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Wallahi abinda ya faru kenan Mami ban maki karya ba" Mami bata sake cewa komai ba, can ta mike ta fita don akwai abinda take son dubawa ne kar kuma ta duba taga ba haka ba don hakan zai kara destabilizing dinta. Karfe hudu saura na yamma Ummi ta diro masarauta, direct bangaren Aunty ta fara nufa, nan ta tarar da ita da su Gimbiya Firdausi da Hajiya A'isha sai Kilishi, nan Hajiya A'isha da Kilishi suka rako Ummi har bangaren Mami, Mami na can bedroom dinta bakin ciki yasa ko zaman parlor ta kasa yau, ko breakfast bata yi ba ga lunch shi ma bata ji zata iya ci ba, tun da Jay ya bar part din Ajay da safe har zuwa yanxu bata gansa ba don bai zo part din nata ba, Ummi na tsaye tsakiyar parlon Mami ta dinga rafka sallama, Hajiya A'isha da Kilishi duk suka nemi kujera suka zauna, Mami na fitowa ta dinga kallonsu daya bayan daya a parlon, Ummi na huci tace "Wallahi kin ban mamaki Fulani, ban zaci haka daga gare ki ba, har wai zaki goyi bayan wata er iskar bare akan Hadiyah?? Me Hadiyah ta maki kika tsaneta haka ne? Kawai don tana auren ɗan ki kuma kina baƙin cikin soyayya da kulawan da yake nuna mata tunda ke ba haka kika so ba shi yasa kike tsangwamarta kike kyararta a gidan nan? ko dai kin mance matsayin Hadiyah ne a gidan nan?" Da mamaki Mami tace "Rashin kunya kika taso tun daga Lagos ki min Maimuna? Ni kike gaya ma maganganun nan?" Hajiya A'isha tace "A'a Fulani mu kan mu mun yi mamakin ki, kuma duk jikinmu yayi sanyi don bamu zaci haka daga gare ki ba, ta yaya kiri kiri zaki hau Hadiyah da zagi akan wata er iska can da bamu san ma cikakken asalinta ba? Meye hadinmu da ita da zaki goyi bayanta akan Hadiyah warce take jininmu? Har kina kallon Junaid ya ɗaga hannu ya gaggaura mata mari ki ki cewa komai, instead ki ja matsiyaciyar yarinyar ki fita da ita ki bar Hadiyah? To in kin mance wacece Hadiyah bari mu tuna maki Fulani, da uwar Hadiyah da Mahaifin Jawwad Allah yayi masa rahama, uwa daya uba daya suke" Cike da rashin mutunci Ummi tace "Ku kyaleta ai amanar marigayi Yaya Ahmad ta ci ba namu ba, dama tun ba yau ba nasan babu alkhairi a zuciyarta, to in haka ne me yasa bata saka ɗan nata a gaba tana kallo ba tunda bata son yayi aure ya nuna ma matarsa kulawa, ko kunya babu ki dinga kishi da matar ɗan ki, matar ma jinin marigayin mijin ki" A hankali Mami tace "Maimuna ni kike ma rashin kirki yau?" Cikin i don't care attitude Ummi tace "koma yaya zaki sa shi ni bai shafeni ba wallahi, akan 'ya ta babu abinda bazan yi ba sai dai ayi hakuri, kuma babu shegen da zai taɓa Hadiyah ya kwana lafiya a gidan nan, zan zuba ido in ga hukuncin da sarki zai dauka wallahi sai dai ayi abun kunya a masarautar nan in dai ba a bi ma 'ya ta hakkin marin da aka yi mata ba" Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Mami ta bi ta da kallo baki bude, su Hajiya A'isha duk suka mike suka bi bayan Ummi, bayan sun fita Kilishi tace "Ai baki san wani abu ba Maimuna kafin sarki ya dau wani mataki ya kamata Hadiyah ta rama marukan da ɗan iskan nan Junaid yayi mata akan matsiyaciyar yarinyar, bayan ta rama marin akan yarinyar sai kuma a jira hukuncin da sarki zai dauka...." Hajiya A'isha tace "Kwarai kuwa, gwara ta fara rama marin kan shegiyar yarinyar kafin ma a zauna da Mai martaba" Khaleesat na zaune babban parlor ita kadai abun duniya ya taru ya dameta, ko Lunch da Yakumbo suka kawo daxu suka ajiye a babban parlon bata ko bude ba balle ta san me aka kawo, bude kofar parlon aka yi ta daga kai duk tunaninta ko Mami ce ta sake dawowa, Ummi ta shigo fuska murtuke tana rike da hannun Hadiyah dake biye da ita, ga Hajiya A'isha da Kilishi na biye da su a baya su ma, ai ko gama shigowa parlon basu yi ba Khaleesat ta mike kan kace me sai gata a parlon Ajay a tsorace, ita kanta bata san ko gudu tayi ba ta dai ganta parlon jiki na rawa, fitowar Ajay daga bedroom dinsa kenan zai je Masallaci, da gudu ta tafi bayansa zuciyarta na bugawa ta fara masa kuka, sai ga su Ummi sun shigo parlon fuskarsu duk babu alamar rahama, Ummi ta sake hannun Hadiyah cikin tsawa tace "Ta fi ki rama marin da yayi maki akan ta" Hadiyah ta kalli Ajay dake kallonta, Kilishi ta mata wani tsawan tace "Baza ki tafi kiyi abinda aka sa ki ba, ko ubanki ne shi Junaid din da kike kallonsa?" Ita dai Hadiyah ta kasa karasawa ganin kallon da Ajay yake mata, Juyawa yayi ya kama hannun Khaleesat ya shige Bedroom dinsa ya bar su wajen a tsaye yayi banging kofar sa. Ajay bai fita zuwa masallacin da yayi niyya ba yayi sallan a dakinsa, ita dai Khaleesat na zaune gefen gado sai goge hawayen da yaki tsaya mata take tana shesshekan kuka, sosai ta kara tsorata da gidan, ji take kamar ta gudu ta bar gidan, banda bugawa babu abinda zuciyarta yake, bayan Ajay ya idar da sallah ya mike ya nufi kofa don ma ya dena jin kukanta dake kara bata masa rai, tana ganin haka ta tashi da sauri ta nufesa muryarta na rawa tace "Don Allah kar ka tafi ka bar ni wallahi tsoro nake ji" Ya mata wani kallo yace "Na aike ki kije ki dauko ma kanki magana?" Ta fashe da kuka moving closer to him tana girgiza masa kai tace "Wallahi kawai naje kai ma Mami cooler ne sai in gaisheta daga nan...." Cikin tsawa yace "Did you know the Mami from anywhere??" Girgiza masa kai tayi tana goge hawayen dake zuba idonta ta rasa abinda zata ce, ya kara daure fuska yace "You went to her part with the intention of meeting with Jawwad, you went there purposely because of him, probably ma shi yace ki je can don haka bear the consequences now kar in gaggaura maki mari...." Kasa cewa komai Khaleesat tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, bata taɓa ganinsa cikin yanayin nan ba, ya bude kofar yayi ficewarsa daga dakin kamar zai tashi sama. Har kusan Magrib Khaleesat na zaune kasan carpet a dakinsa, tun da ya fita ko digon hawaye bai kara zuba idonta ba saboda abubuwan da ya gaya mata, she was just sitting like a statue in the room tana jin zuciyarta babu dadi kwata kwata, daga karshe jin ana kiraye kirayen magrib ta mike a hankali walking slowly ta fita daga dakin, bata gansa parlornsa ba ta bude kofa ta fita, daya daga dakunan dake part din ta bude kofa ta shiga ta kulle da makulli..... Ajay na zaune parlon Mai martaba kansa a kasa, Jay ma na zaune opposite to him sai dai babu wanda ya kalli wani cikinsu, Mukhtar was also in the parlor kusa da Jay, kusan gaba daya familyn masarautan ne zaune a parlon har da Gimbiya Firdausi da Hajiya Habibah, duk ana sauraron jawabin Sarki wanda ko minti biyar bai yi da fara magana ba cikin nutsuwa, duk an kagu yaje main point din da yasa duk aka tara su a parlon, Ummi dai fuskarta a daure yake ta ma fi kowa ƙaguwan sarki ya gama jawabinsa taji hukuncin da zai yanke akan marin Hadiyah da Ajay yayi, sannan kuma su ji makomar Khaleesat a gidan kamar yanda su Hajiya A'isha su ma duk suka baza kunne su ji hukuncin da sarki zai dauka akan abinda aka ce Khaleesat tayi, babu wanda ya wani damu da reputation din Jay a cikinsu su dai kawai a shafa ma Khaleesat baƙin penti da bazai taɓa gogewa ba yanda zamanta zai zo karshe a masarautan don cewa suka dinga yi abomination ta tafka, gashi ba karamin tsari Aunty tayi ma Mai martaba ba akan abinda ya faru and she made it look so bad wajen narrating ma Sarki, bayaninta yayi muni sosai, wanda har shi ma Mai martaba sai da jikinsa yayi sanyi daga sanda ya samu labarin nan ya dawo gashi nan gashi nan ne dai kawai amma bai nuna hakan a fuska ba cause he was very calm, but ko abinci ya kasa ci, Hadiyah dai na zaune kusa da uwarta tana jiran sarki ya tambayeta abinda ya faru dama su Hajiya A'isha sun kara yi mata tsarin abinda zata fada don zancen ya kara girgiza sarki, tun da abun ya faru da safe take bangaren Aunty sun ki barin ko Jay ya ganta don kar ma ya canza mata ra'ayin fadan abinda suka kitsa mata, Jay dai sai kallonta yake a parlon ita kuwa taki yarda ta kallesa cause she is ready to say all what she was instructed to say that will paint Khaleesat black, yayi mata kira yafi ashirin ranan da text messages amma duk su Kilishi suka hanata picking kiran balle tayi replying messages dinsa kawai jiran lkcn da za a zauna da sarki suke, Mami dai na zaune parlon kanta a kasa duk da sai da Mai martaba ya aika ayi kiranta sannan ta taho wajen zaman, Mai martaba na kallonta calmly yace "Fulani...." Mami bata ɗaga kai ba tace "Allah ya taimake ka" Mai martaba ya nisa yace "Me zaki ce game da wannan lamari da ya faru yau? Ina nufin menene ya faru yau a sashin ki Fulani?" Mami ta ɗan yi shiru, after some seconds tace "Ranka shi dade ni babban parlor na akwai Cctv Camera tun bayan abinda ya faru shekarun baya da aka kwashe min gwala-gwalai na" Walid dake parlon shima ya ɗan kalli Mami sai kuma ya dauke kai, Mami ta ci gaba da maganarta cikin nutsuwa tace "Ina jin babu wanda yasan da Cctv din sai yanxu da nake magana, don haka ina ga wannan kadai ya isa bada labarin abinda ya faru ba sai na tofa komai ba, don na sa Mukhtar ya taho da Cctv DVR ayi connecting da TV kowa ya gane ma idonsa, a nan kuma zaka san ba komai suka ma yarinyar nan ba illa kazafi da sharri wanda su masu zuga Hadiyar suna da yaran nan mata kuma basu san abinda gobe zai haifar ba, ba komai ya kawo yarinyar parlor na ba sai alkhairi amma suka mayar sharri" Tun da Mami ta fara magana Ummi da su Hajiya A'isha da Aunty suka daga kai suna kallonta babu ko kiftawa, Mai martaba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yayi shiru na wani lokaci don he felt relieved immediately, can yace "Amma ke kin kalli clip din Fulani?" Mami tace "Kwarai na kalla a laptop tare da Mukhtar ranka shi dade" Mai martaba ya kalli Mukhtar yayi instructing dinsa yayi playing dinsa a TV, ba komai yasa Sarki yace a kunna ma kowa clip din ba kawai yasan hakan ne kadai zai kashe zancen nan, sanin halinsu Kilishi yasan tsaf za su ce gyara zancen Mami tayi saboda reputation din ɗan ta, Mukhtar ya mike da hanzari yayi yanda Sarki yace yayi, aka jona Cctv din da TV, yana fara playing Hadiyah ta sunkuyar da kanta, Ajay dai ya ɗaga kai yana kallon TV din kamar yafi kowa son ganin clip din, kowa a parlon yaga exactly abinda ya faru a parlon Mami tun daga shigowar Jay da Khaleesat da ya tarar zaune a parlon, bayan yayi hanyar dakin Maminsa ya dawo ya zauna parlon and they were not close to each other ko kadan, yana kan kujera tana zaune kasa kuma ba kallonsa ma take ba, bai fi sau daya zuwa biyu ta daga kai ta kalli inda yake ba, sai kuma wayarsa da ya mika mata daga karshe sai shigowar Hadiyah parlon da yanda ta taho ta cakume Khaleesat sai ga yan gidan duk sun shigo parlon su ma, amma Aunty har da ce ma sarki rungume da juna Hadiyah ta kama su, Mai martaba ya ɗaga kai yana kallon Aunty da taki kallonsa, kowa na parlon sai cika yake yana batsewa irin ba haka aka so, daga karshe Mukhtar ya kashe TV din, shiru ne ya biyo baya na kusan minti uku a parlon, Sarki ya kalli Hadiyah da taki dago kanta yace "Ashe ke mutuniyar banza ce Hadiyah? Me yarinyar nan ta maki kike kokarin tarnishing Image dinta a gidan nan? Not only her, har reputation din mijin ki da na gidan nan as a whole kika so kiyi tarnishing, kin san ma'anar wannan abu da kika yi kuwa? To ina me umartar ki da ki tafi har bangaren matar Junaid ki bata hakuri akan abinda kika yi mata, umarni kuma nake baki, and I am highly disappointed in you" Duk aka daga kai ana kallon Sarki jin yace taje ta ba Khaleesat hakuri, Hadiyah dai taki ɗago kanta hawaye cike idonta, Ummi sai wani kumbura take a inda take zaune kamar zata fashe, Cikin kakkausan murya Mai martaba yace "Sannan daga wannan very moment din na kashe wannan maganar a gidan nan, bana son sake jin wani ya tadasa har abada, idan kuwa ba haka ba zan dau mummunan mataki akan koma waye...." Babu wanda ya iya daga kai balle yace wani abu a parlon, bayan minti daya kilishi ta kwantar da murya tace "Ina son er wata magana idan an bani dama ranka shi dade" Sarki yace "Go ahead" Cike da takaici tace "Allah ya taimake ka, sau biyu Junaid ya ɗaga hannu ya mari Hadiyah fa tana matar wan sa ko kunyan wan nasa bai ji ba, gashi nan har sai da fuskarta ya kumbura akan marin da yayi mata, yanxu haka cewa take hakoranta na ciwo sai an je wajen Dentist, shi mijinta bai ɗaga hannu ya mareta ba sai shi saboda yafi kowa son matarsa?? Yanxu da Jawwad bai kai zuciyarsa nesa ba ai batattciya za ayi a masarautar nan tunda shi ma yana son matarsa" Mai martaba ya juya ya kalli Ajay da ya sauke kansa kasa yace "Ahmad" Still Ajay kansa na kasa yace "Ur highness" Strictly Sarki yace "This should be the first and last time da zaka ɗaga hannu ka taɓa ko wani yaro a gidan nan da sunan duka, ina me tabbatar maka idan hakan ya sake faruwa zaka ga ɓacin raina Ahmad, a baya na sha maka warning akan hakan to wannan shi ne na karshe da zan maka" Mami ta daga kai tana kallon Mai martaba tace "Ranka shi dade ka mance matsayin Hadiyah ne a wajensa? Laifi ne don ya hukunta kanwarsa?" Tun shigowar Jay parlon sai a sannan ya daga kai ya kalli Maminsa jin abinda tace, Ummi ma wani tsinannen kallo take ma Mami haka Kilishi, Mai martaba yace "Babu wannan zancen Fulani, Hadiyah matar aure ce yanxu don haka ba shi da right din daga hannu ya mareta, ba ma ita ba idan ya kuskura ya sake daga hannu akan ko wani yaro cikin gidan nan zan dau mataki akan hakan tunda aikinsa kenan shi, na sallami kowa..." Mikewa Sarki yayi ya bar parlon ya shiga second parlor dinsa, Mami ta mike ta fita duk da tana da maganganun da take son yi da Sarki amma ta bari sai gobe da sassafe zata zo ta samesa. Ajay ya mike shi ma ya fice daga parlon su Kilishi da Ummi suka bi sa da wani irin kallo, yana komawa part dinsa yayi using makulli ya bude kofar babban parlon don sai da ya kulle before leaving, bai ga Khaleesat a parlonsa ba har ma a bedroom, and he began wondering inda ta tafi duk da yasan ya kulle kofar part din kafin ya fita, can ya fita ya bude all the 3 rooms in the part, yaji daya a kulle ya gane she is inside kenan, murda kofar yayi ya kwankwasa yace "Ke, bude kofar nan" Duk da Khaleesat na jin sa taki cewa komai tana kwance kan gado, daki ne babba that is well furnished babu abinda babu a ciki, sai bayan da ta shigo dakin taga ashe duk akwatunan ta ma suna dakin, sau uku yana knocking kofar taki tankawa, ya juya kawai ya tafi kitchen din dake part din ya ciro fruits a cikin fridge ya wanke su ya zuba a bowl ya koma parlornsa, yana ta zaune har lokacin isha'i yayi, yayi sallah sannan yayi wanka ya saka pajamas dinsa ya kunna TV a bedroom dinsa yana kallon football amma ya kasa concentrating duk sonsa da Ball, kawai ya kashe TVn wajen karfe goma da rabi ya kwanta kan gadonsa ya lumshe ido, ya dade abu bai dakesa ba kamar yau don ko abinci bai iya yaci ba yau, rabonsa da shiga irin wannan damuwan kilan tun bayan da Mai martaba ya sanar masa auren da ya daura masa da Khaleesat sai kuma incident din daxu da safe, but he felt relieved bayan clarification din da Mami tayi with evidence, mikewa yayi ya fita xuwa kitchen ya duba dinner din da aka kawo masu yaga Khaleesat bata taɓa komai ba a ciki, da rana ma yana lura bata ci abinci ba, ya juya ya fita :,daga kitchen din ya tafi kofar dakin da take ciki yayi knocking calmly yace "Jeeddah, open the door,..." *Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788* HALYSAAH PAGE 131... Da yamma Khaleesat suka sauka Airport din garin Abuja, Driver din da ya zo daukansu ya saka duk akwatunan ta a booth sannan ya bude mata back seat ta shiga ya kulle motar ya koma gefe yana jiran Ajay dake waya ya shiga motar kafin shi ma ya shiga, ita dai Khaleesat kallon Ajay take don duk da he is not too far from the car amma baka ma jin me yake cewa a wayar, few seconds later ya saka wayar a aljihunsa sannan ya juya, driver ya bude masa bayan motar da sauri, Ajay yace "I will take the front seat...." Yana fadin haka ya bude gaban motar ya shiga, drivern ya zaga ya koma driver seat, suna fita daga Airport din Khaleesat ta dinga baza ido taga inda za su a Abuja, bayan tafiyar minti arba'in da biyar suka iso gidan, tun da suka shiga compound din gidan take kallon gidan, driver yayi parking a lot din dake compound, Ajay ya bude motar ya sauka, ita dai Khaleesat sai bin sa take da ido don tun da suka baro Airport ko kallon bayan motar bai yi ba, driver ya bude mata back seat, sai a sannan ta lura she was still sitted inside the car ashe, ta sauko daga motar a hankali tace ma drivern "Thank you" Ajay ya fara tafiya toward building din gidan don dama jira yake ta gama zaman da take a motar ta sauko, hararansa tayi tana bin sa a baya kamar bata son tafiyar, yana danna bell mai aikin gidan ta bude kofar ta koma gefe tana gaishesa da fara'a fuskarta, yace "Ya kike Aisha" Tace "Lafiya lau Yaya Prince, sannu da zuwa, ya hanya?" Cikin few seconds Khaleesat tayi ma mai aikin kallon sama har kasa sannan ta amsa gaisuwar da take mata ta bi bayan Ajay da ya karasa can cikin parlon, ya nemi kujera ya zauna yana gaida Ammi da ta tashi daga zaunen da take tana welcoming dinsu da fara'a sosai, Khaleesat zata zauna kasan carpet Ammi ta dagota ta zaunar da ita kan kujera tace "A'a yi zaman ki kan kujera daughter, sannun ku da zuwa, kun sha tafiya" Khaleesat ta gaisheta da ladabi, Ammi ta amsa tana murmushi tace "Lafiya lau my dear, ya gajiyan hanya?" Inteesar ce ta fito daga kitchen tana ganin Ajay ta taho da gudu ta zauna gefensa tayi masa side hug cike da farin cikin ganinsa tace "Yaya Prince amma fa kace min sai anjima da daddare za ku sauka, dama wasa kake min?" Ya ɗan yi murmushi yana kallonta yace "Ohh... na zata ai daren yayi yanxu, ashe da saura ko" Inteesar tayi dariya sosai tace "Kai Yaya, even for once ka zama serious mana, yanxu da ban yi girkin da nace zan yi ba fa?" Yace "Sai Ammi tayi min" Khaleesat dai kallo daya tayi ma Inteesar ta sunkuyar da kanta tana wasa da veil dinta, Inteesar na lura da ita lokaci daya ta sake Ajay, ta mike da sauri ta koma kusa da ita ta zauna ta rungumeta cike da fara'a tace "Khaleesat sannu da zuwa, yau dai Allah yayi kin sake dawowa gidanmu, ya hanya?" Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace "Alhamdulillah" Inteesar bata sake bin ta kan Ajay ba ta kama hannun Khaleesat tana murmushi tace "Mu je sama ki huta" Ammi tace "Yauwa ki kai ta tayi wanka tayi sallah sai ta huta kafin ayi dishing abinci, she look so tired" Khaleesat dai ta bi Inteesar dake rike da hannunta suka haura sama, Ajay ya bi ta da kallo, Inteesar na haurawa sama da ita ta kai ta har Bedroom dinta tace "Yaya Prince ce min yayi fa sai can da daddare za ku sauka ashe dai wasa yake min, Allah ya so har na gama girkin da nake, let me get you towel ki shiga kiyi wanka, before I dish the food...." Khaleesat tayi murmushi kawai, Inteesar ta dauko mata new towel a wardrobe dinta ta mika mata sannan ta amshi handbag din hannunta ta ajiye kan bedside drawer ta nuna mata bathroom dinta tace "Ki shiga kiyi wanka Khaleesat, i will get ur box now kafin ki fito sai ki canza kaya" Khaleesat tace "Toh nagode" Juyawa Inteesar tayi ta fita daga dakin ta kullo kofar, Khaleesat ta fi minti biyar tsaye inda take, can ta fara unrolling din veil dinta a hankali sannan ta shiga bandakin, ko da ta fito ta tarar Inteesar har ta kawo mata akwatinta ta ajiye a dakin, bayan ta ɗan yi shafe shafenta ta bude akwatin ta cire doguwar riga da hijab dinta ta saka, tana idar da sallah ko tashi bata yi saman darduman ba sai ga Inteesar ta shigo dakin tana kallonta tace "Yauwa taso mu je parlor, anyi dishing abinci a dinning ke ake jira" Khaleesat ta kalleta tace "Bana jin yunwa yanxu" Inteesar ta hade rai tace "Don Allah ki taso, in ma baza ki ci a dinning ba sai kiyi zaman ki a parlor ki ci abincin" Bata jira cewar Khaleesat ba ta tafi ta kamo hannunta tace "Mu je plss" Ba yanda Khaleesat ta iya haka ta mike ta bi ta suka fita daga dakin suka sauka downstairs, Ajay na zaune dinning area yana cin white rice and stew din gabansa, sai Umar yayan Inteesar dake cin tuwo da miyar vegetable yana zaune daga kusa da Ajay, Ammi ma na dining din zaune da nata abincin a gabanta, Inteesar ta ja Khaleesat har zuwa gun dining din sannan ta ja mata kujeran dake kallon inda Ajay ke zaune, gaida Umar Khaleesat tayi ganin yana kama da Ammi sosai, ya amsa da fara'a yana tambayarta ya hanya, tace "Alhamdulillah" zaunawa tayi ta ɗan kalli Ajay dake cin abincinsa without looking at her, Ammi tace "Tuwon za ki ci ko shinkafa daughter?" Khaleesat ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Shinkafa" Ammi tayi dishing mata shinkafa da miya da nama sai coslow a wani bowl ta ajiye mata abincin a gabanta tace "Ga shi daughter, ki saki jiki ki ci abinci kin ji" a hankali Khaleesat tace "Toh Nagode Ammi" Inteesar da ta fara cin nata abincin ta kalli Ajay tace "Yaya abincin yayi dadi?" Ajay ya ɗan kalleta yace "I am still trying to figure out" Dariya tayi sosai tace "Ai na san abinda zaka ce kenan, da na sani da ban dafa shinkafar ba in ga yanda zaka yi da tuwo" Ita dai Khaleesat juya abincin gabanta kawai take a hankali kanta a kasa, Umar yayi ma Inteesar wani kallo yace "Ke wai bakin ki bazai iya shiru for good 10 mins bane, kin cika mutane da surutu wajen cin abinci" Inteesar bata ce komai ba ta ci gaba da cin abincinta, Ajay ne ya fara tashi daga dinning din bayan ya gama cin abincinsa don dama ba da yawa yasa Inteesar tayi masa dishing ba, Ammi na kallonsa tace "Wai har ka koshi?" Yace "Na koshi" Tace "Ko dai shayi zaka sha?" Yace "A'a, sai anjima" Khaleesat ta daga kai ta kallesa suka hada ido a karo na farko, barin dinning area din yayi ya tafi sama.... Ajay na zaune Bedroom din da yake sauka always a duk sanda ya zo gidan Ammi, wanda wannan daki ya fi zame masa comfort zone akan masarautarsu, he is more comfortable and have rest of mind a gidan nan akan Bauchi, don in dai ya dawo daga Amurka ya kan yi kwanaki biyar wani lokacin har sati a gidan Ammi kafin ya tafi Kano, a Kano kuma yayi kwana uku ko hudu before leaving for Bauchi, kuma yana haka ne duk don ya ja lokacin da ya zo yi a Nigeria ta yanda few days zai yi a Bauchi ya koma Amurka, Umar da ya shigo dakin not long ago ya gama wayar da yake sannan ya kalli Ajay yace "Hope an samu canji tsakanin ka da Jay zuwa yanxu?" Ajay ya dauke idonsa daga football da yake kallo a dakin ya kalli Umar yace "Not when i am still together with the girl he has in mind as a wife" Umar yayi shiru na wasu sakwanni yana kallonsa, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace "Ajay nasan ka a mutumin da baya keeping malice no matter what, bar ka dai da saurin hawa wani lokacin amma fa baka da wuyan saukowa, to don me zaka biye ma Jawwad har zuwa wannan lokacin baku magana duba da irin closeness dinku kai da shi?" Ajay yace "I am not keeping Malice with him, jira yake in sakar masa yarinyar before we get back together and I understand that, but he is only not being patient...." Umar ya katse sa da sauri yace "I don't understand he is not being patient? What are you insinuating?" Ajay yace "Eh mana, ba shi da hakuri, da yayi hakuri yayi calm down we will get there in sha Allah" Umar yayi masa wani kallo yace "Are you kidding me? Kana nufin sakar masa yarinyar zaka yi ya aura??" Ajay yace "Idan zai iya ba, balle na ma san zai iya, kuma abinda yake jira kenan, so hakan ne zai faru i told him to calm down" Umar ya girgiza kai yace "This is abhorrent, very disgusting, kuna nufin da ran Mai martaban za ku yi wannan rashin hankalin ko kun mance wani irin gida ku ka fito ne? Kuma ka ban mamaki Ajay don ko ba da consent dinka aka aura maka yarinyar nan ba a sunan matarka take a yanxu dai kuma duk cikakken namiji dole zai yi kishin matarsa ko da kuwa baya sonta aka aura masa ita, balle you can't just tell me you have no feelings for ur wife Ajay, I am not surprise at Jay's action don ba a yi masa komai ba ma ya share mutum yayi ignoring calls dinsa yaki replying Whatsapp messenges balle yana tunanin an masa laifi, shi kaga halinsa ne shariya da banzatar da mutum amma kai ba halin ka bane, kuma bana son ka koyi sabon halin da ba naka ba idan har ba hali ne me kyau ba, i know Jay is hurt but he took the issue to another level, yaki yi maka uxuri, ni kaina nayi kokarin fahimtar da shi daga karshe he stopped replying my chat, I called him once bai daga ba, so nima sai ban sake masa magana ba har yau" Ajay dai bai sake cewa komai ba ya maida idonsa kan football da yake kallo, Umar yace "Ni sai yanxu ma na sake tabbatar da cewar shakkan Jay din nan kake, dama na taɓa gaya maka haka da dadewa, banda kana shakkarsa shi har ya isa yasa ka bijire ma hukuncin da Mai martaba ya zartar a kanka? So kana nufin gwara kayi pleasing Jay kayi displeasing Mai martaba, tunda gashi har kana da burin sakin yarinyar da aka aura maka saboda Jay, to sai kace ma Mai martaba me idan ka saki yarinyar?? I promise you he is going to disown you wallahi, shi Jay yayi ma mahaifiyarsa biyayya kai kuma bari ka bijire ma naka mahaifin saboda ka faranta masa, to ko sakin yarinyar nan kayi sorry to say ai ba masarautar taɓaɓɓu bane masarautar taku da za su amince Jay ya sake aurenta tunda shi Jay din ba shi da tunani" Ajay ya ɗan yi murmushi yace "Ba lallai ka fahimta ba, but i know how to go about everything, just watch and see" Yana kai wa nan yayi concentrating akan football din da yake kallo, Umar dai yayi shiru yana kallonsa, can ya mike ya nufi kofa zai fita dai dai sanda aka yi knocking kofar dakin, bude kofar yayi yaga Inteesar tsaye bakin kofar, ya hade rai yace "Me ya faru? Ko dai baki da hankali ne? kina ganin matarsa a gidan kike shisshige masa, ko kina hauka ne?" Inteesar ta koma baya tana kallon yayan nata, Ajay ya daga kai ya kalli Umar yace "I don't understand Umar?" Umar yace "To ai kasan mata da kishi, is better ku ajiye wani brother and sister things dinku aside don ita matarka ba fahimtar closeness dinku zata yi ba cikin kankanin lokaci" Juyawa Inteesar tayi ta bar bakin kofar bayan ta hade rai ta koma dakinta, tana shiga dakin ta samu Khaleesat zaune kan darduma ta idar da sallah, Inteesar tace "In kawo maki fruit din ne Khaleesat? Or should I make fruit salad for you" Khaleesat bata kalleta ba ta girgiza kai tace "A'a Nagode" Inteesar ta tafi gefen gado ta zauna ta kunna laptop dinta, knocking din kofar dakin aka yi, ta kalli kofar sai kuma ta mike ta tafi ta bude, Ajay ta gani tsaye bakin kofar, yana kallonta yace "Fushi kika yi kika tafi?" Khaleesat ta daga kai tana kallonsu, Inteesar ta jingina da kofar tace "Not at all, just that he reads meaning into nothing" Yace "To mu je" Ta langwabe kai Tace "Ohk" Juyawa yayi ya bar bakin kofar, Inteesar ta koma ta zauna gefen gado tana kallon Khaleesat da murmushi fuskarta tace "Taso mu je dakinsa Khaleesat, tsaraban da ya kawo min zai bani...." Khaleesat ta ɗaga kai ta kalleta tace "Ki je ki dawo, zan fara azkar ne yanxu" Inteesar tace "Ohk" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, nan kan darduma Khaleesat tayi kwanciyarta, har karfe goma Inteesar bata dawo dakin ba, sai da goma da rabi yayi ta shigo rike da ledan kayayyakin da Ajay ya bata, Khaleesat ta rufe ido kamar me bacci, bayan Inteesar ta ajiye ledan hannunta ta tafi kusa da ita ta durkusa tana tashinta tace "Khaleesat me yasa baki kwanta kan gado ba, why will you lie down here" Juya mata baya Khaleesat tayi tace "Zan hau anjima" Inteesar tace "To baza ki kara abinci ba?" Khaleesat ta girgiza mata kai kawai, mikewa Inteesar tayi ta bar wajen ta tafi ta bude press ta ciro kayan baccin ta zata shiga wanka.... A haka Khaleesat suka yi kwanaki hudu a gidan Ammi, wanda a kwanaki hudun nan jin ta take kamar a ƙaya, bata taɓa jin ta matsu ta bar waje kamar wannan gidan ba, infact bata taɓa zama guri da ta zama uncomfortable kamar zaman da tayi a gidan ba, ko magana bata fiye yi ba sai dai idan yi mata aka yi, she is always pressing her phone, hakan kuma bai sa ta canza ma kowa fuska ba ko ta nuna da wani abu a ranta, cikin dare kuma ta sha kukan da bata san dalilinsa ba, gaba daya ta ma rasa me ke damunta, throughout this 4 days ko kallon inda Ajay yake bata yi a gidan, idan abinci ne ya kai ta downstairs iyaka ta cakalkali abinda zata cakalkala ta wuce sama don appetite din cin abincin ma bata da shi, sanda Inteesar ta shigo wajen karfe biyar da rabi ta sanar mata Ajay yace ta shirya they are leaving, cikin minti goma Khaleesat ta gama shiryawa kamar dama jira take, a haka suka bar gidan bayan Ammi ta hada mata sha tara ta arziki, Inteesar ma ta bata wasu tsadaddun turarruka, har suka yi nisa bayan sun baro gidan Ammi Khaleesat taki kallon Ajay dake zaune gaban mota, shi kuwa lokaci lokaci yake kallonta ta madubi, ita dai idonta na outside of the car, suna isa airport ta sauka daga motar, shi ma ya sauka yana kallonta, still dai taki kallonsa tayi tafiyarta cikin airport din, bin bayanta yayi bayan an shiga da luggages dinta ciki. Karfe bakwai da rabi suka sauka garin kano kuma all through the flight to Kano taki yarda ta kalli Ajay duk da waje daya suka zauna, motar da zai daukesu har ya iso airport yana jiransu a wajen parking, Khaleesat ta ɗan ji dama daman abinda take ji a zuciyarta for 4 days ganinsu a cikin garin kano, yau dai tasan gidansu zata kwana zata ga Ummanta da Babanta da twin sibling dinta da step sibling, tunanin hakan yasa ta farin ciki sosai a ranta, taji har ta kagu su isa Tudun Yola, amma bayan tafiyar minti talatin da biyar a mota ta ga sun iso wani babban hotel, ta dinga kallon drivern motar babu ko kiftawa, shi dai driver yayi parking cikin hotel din, sai a sannan ta juya ta kalli Ajay da ya bude motar ya sauka, nan da nan farin cikin zuciyarta ya gushe ta ji kamar ta rushe da kukan takaici, still dai babu abinda tace ta bude motar ta sauka fuskarta babu yabo babu fallasa ta bi bayan Ajay zuwa cikin hotel din. Bayan sun yi lodging hotel din Khaleesat dai ta zauna gefen gado ta ciro wayarta tana dannawa fuskarta a daure, yana kallonta ta madubi ya gama cire wristwatch din hannunsa ya ajiye gaban madubin sannan ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya ya dau wayarsa ya nufi kofa zai fita daga dakin zuwa masallacin hotel din yayi sallah, ko da wasa Khaleesat taki yarda su yi eye contact da shi har yanxu, after 20 mins sai gashi ya dawo dakin ya ajiye ledan abincin da ya siyo mata yana kallonta, sai a sannan ta ajiye wayar hannunta still not looking at his direction fuskarta a daure ta mike ta ciro kayan da zata canza ta shiga bandaki, bayan 30 mins ta fito daga bathroom din taga baya dakin, sallolinta tayi sannan ta tashi ta cire hijab dinta tana linkewa ya shigo dakin, ta gama linkin hijab din ta juya zata koma daya side din gadon taga ya kashe wutan dakin ya fixgota, a fusace ta buge hannunsa zata kwace kanta tace "Meye haka??Ni ka kyaleni kar in maka ihu wallahi..." HALYSAAH PAGE 133... Khaleesat na fita compound taga Ajay zaune a daya daga chairs din dake compound din kusa da flowers yana danna wayarsa, ta sunkuyar da kai ta tafi har inda yake zaune sannan ta daga kai ta kallesa, sai a sannan shi ma ya kalleta, tana da fingers dinta wasa ..... tada maka haka ne don ka kawo ni, ka zata da gaske nake? Ai na dawo gidanmu kenan" Tana kai wa na ta juya ta fara tafiya, ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, after a while ya mike ya bi bayanta, Aunty Farida na zaune parlor bayan taje kitchen tayi ma Nenne magana cewar Junaid zai shigo, Nenne aka bude akwati da sauri aka ciro tsadadden gyale ta fesa turare ta yafa ta fito ta zauna parlor ta kora su Mama Zubaida da Mama Shatu wai baza su zauna parlon da yakunannen hijabin jikinsu ba, haka nan duk suka shiga dakin Mama Shatu don da gaske hijab din nasu duk a yakune yake kamar an kwato bakin kura, Khaleesat na shigowa Nenne tayi kasa da murya tace "Ke dai anyi gantalalliyar yarinya mara seti, dama a waje kika bar Yarima guda tun daxu baki gaya mana ba? Babban mutum haka don kin samesa a banza zaki gantalar a kofar gida?" Khaleesat ta hade rai tace "To ai nace masa ya shigo yanxu" Tagumi Aunty ..... Farida tayi, banda ma dai ta ga Junaid din mingnikal almost 40 mins, da sallama Ajay ya shigo parlon kansa a kasa, Nenne ta amsa cikin nutsuwa tace "Sannu da zuwa Yarima, sannu da zuwa, Bisimillah ga kujera zauna, sannu da zuwa" Bai zauna kan kujeran ba ya zauna kan Carpet din parlon kawai, Nenne tace "A'a Ahmadi kayi zamanka saman kujera kar ka bata farin rigar ka, dama ga yara na ta taka cafet din" Ajay dai ya gaishesu yana dan murmushi, Nenne ta amsa da fara'a, Aunty Farida tace "Fatan kun sauka lafiya Junaid?" Yace "Alhamdulillan Aunty, ya muka same ku" Aunty Farida tace "Lafiya lau Junaid" Nenne tace "Ai duk bamu san kana waje ba wallahi, yarinyar nan Khaleesat bata gaya mana ba, duk farin cikin ganin yan uwanta yasa ta rude ta manta bata ce mana tare ku ke ba, sai daga baya ta farga duk hankalinta ya tashi wai ta bar ka a waje, mu ma duk bamu ji dadi ba wallahi" Ajay kawai yayı murmushi still not raising his head, Umma ta shigo parlon suka gaisa sannan ta koma dakinta, Aunty Farida ta tafi kitchen ta dauko masa ruwa da drinks da aka tanadar ta kawo masa parlor, Ajay bai ..... koma kenan Ahmad?" Khaleesat ta wani kalli Nenne, Ajay yace "A'a anjima zan dawo" Nenne tace o ba laifi, Allah ya kai mu anjiman" Kofa ya nufa bayan ya fita Aunty Farida ta daure fuska tace "Shashasha baza ki tashi ki raka sa ba" Khaleesat ta mike ta bi bayansa fuskarta babu walwala, nan Balcony ta makale har taga ya fita daga gate din gidan, bayan minti biyar ta juya ta koma parlor yanda Aunty Farida bazata gane bata rakasa ba. Da yammacin ranan Khaleesat na parlor tare da Nenne da Aunty Farida, su Mama Zubaida da Mama Shatu ma duk suna zaune parlorn, sai Harira da ta sake dawowa gidan, almajirai ne suka yi sallama bakin kofar parlon, Nenne tace "Lafiya?? ba nace maku ba sadaka yau ba sai gobe?" Almajiri daya ya shigo da babban Gallon din Man gyada cikin parlon yace "A'a kaya ne aka ce mu shigo da su wai" Nenne tace "Kaya? In ji wa?" Yaron yace "A mota aka sauke kayan abincin yanxu aka ce mu shigo da su" Saig wani almajirin ..... taliya carton din wasu cous cous, Indomie, Maggie har da carton din satchet Tomatoe paste, Khaleest dai sai kallon kayan abincin take, Nenne ta gyara zama tace "Ikon Allah, wannan dai aikin Yarima ne" buhunhunan shinkafa uku almajiran suka shigo da su parlon, su Mama Zubaida da Mama Shatu suka kalli juna, Nenne ta mike tace "Ai ciccibosu za ku yi mu kai store, komai na son sirri" Almajiran suka bi bayanta da kayan abincin zuwa kitchen. Kwanakin Khaleesat uku a gidansu suka bar garin Kano, kuka sosai tayi don bata yi tunanin just 3 days za ta yi a gidan nasu ba ga kuma damuwar Bauchi da za su je, ko sunan garin ma bata son ji saboda fargaba, a kwanaki ukun da tayi gidansu kusan yini biyu tayi a gidan Neighbor dinsu Hajiya Zaliha da ta tabbatar duk wani salon gyaran jiki babu wanda bata yi mata ba in and out, a nan unguwan nasu aka yi mata gyaran gashi a saloon, sannan Hajiya Zaliha ta hada mata abubuwan gyara da zata tafi Bauchi da su, Umma raba dare take da ...... Khaleesat tana mata nasiha da bata aniki tana using kanta as reference, ita dai Khaleesat bata cewa komai wani lokacin haka bacci zai daukata Umma bata gama magana ba. Karfe uku da rabi na yamma Khaleesat suka isa gidan Sarki, kasancewar Mai martaha na da baki yasa Ajay ya nufi part dinsa directly, Khaleesat dai na biye da shi cikin sanyin jiki har suka shiga parlon sa, everywhere was sparkling clean kamar akwai mutum a bangaren, ga wani daddaden kamshi in each and every angle, a hankali Khaleesat ta zauna gefen kujera tana kallon Ajay da ya dau remote zai rage AC din parlon don ko ina yayi sanyi sosai, Bedroom dinsa ya shiga ta bi sa da kallo, wani sai yayi tunanin prison aka kawo Khaleesat don from her facial expression zaka gane she is really disturbed, not long after Ajay ya fito daga dakinsa ya fita daga parlon ya kulle kofa, Khaleesat tayi tagumi tunani iri iri na yawo a ...... dawowa uakın wajen kane piyar da rapi ya wuce Bedroom dinsa, ita dai har sannan tana zaune parlor ge abinci iri iri da Yakumbo ta kawo masu parlon, ana kiraye kirayen sallan Magrib Khaleesat ta mike a hankali ta nufi Bedroom dinsa ganin bai fito ba tunda ya shiga, slowly ta tura kofar tana kallon cikin dakin, kwance ta gansa kan gadonsa idonsa a lumshe, ta juya ta koma parlor. Sai bayan isha'i suka tafi babban parlon sarki don gaishesa, bayan sun gaisa Mai martaba na kallon Ajay cikin nutsuwa yace "Amma ka kai ta sun gaisa da mutanen gidan gaba daya kuwa?" Sarki yayi wannan tambayar ne sanin halin Ajay, Ajay ya sauke kansa yace "I will do that in sha Allah ranka shi dade" Ita dai Khaleesat kanta na sunkuye a parlon, Mai martaba yace "Ok do so today" Ajay yace "In sha Allah" Mai martaba na kallonsa yace "Baka jin dadi ne? You don't look okay?" Daga kai Khaleesat tayi tana kallon Ajay, ya girgiza ma Mai martaba kai yace "A'a i am fine, stress din driving da nayi ne from Kano" .... anik bangaren Aunty Ajay ya fara nufa ba don ransa ya so ba, ita kanta Khaleesat faduwa gabanta yake amma da ta tuna abinda Umma tace mata da ta gaya mata tana faduwar gaba idan ta ga Aunty kawai ta fara addu'o'i kamar yanda Umma tace ta dinga yi, suna ta zaune parlon Aunty for almost 15 minutes, kuma tun shigowarsu Jakadiyarta ta tafi ta sanar mata, lokaci lokaci Khaleesat ke daga kai ta kalli Ajay da ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa a lumshe, Walid ne ya shigo parlon, budewar kofar parlon yasa Ajay ya bude ido, Walid ya karaso cikin parion ya zauna kan kujera yana kallonsu yace "Sannun ku da zuwa, ashe kun dawo" Ajay dai kallonsa kawai yake wondering if da su yake cause it's strange and unusual, after some seconds Ajay yace "Mun dawo" Walid ya kalli Khaleesat dake gaishesa ya gaisheta shi ma yana mata kallon cikin ido, sai kuma ya mike yace "Bari in ma Mama magana ai tana ciki" ..... zaman minti asnırın a parion Ajay ya mтіке, Khaleesat na ganin haka ita ma ta tashi da sauri, ya nufi leía ta bi bayansa a ranta har dadi taji da Aunty taki fitowa, bangaren da Hajiya A'isha take Ajay ya nufa, nan ya tarar kilishi ma na parlon, tun da suka shiga parlon Hajiya Misha da Kilishi ke kallonsu, ya zauna ya gaishe su, Khaleesat ma ta zauna kan kujera ta gaishe su, a dakile suka amsa ma Ajay gaisuwansa iya shi kawai, kilishi ta dinga kallon Khaleesat ta gefen ido, wato suna kan kujera ita ma ta zauna kan kujera tsabar raini, ko ya hanya basu masu ba balle su ji sanda suka dawo, after some minutes Ajay ya mike yayi masu sallama, Khaleesat ta tashi ta masu sallama ita ma sannan ta bi bayansa, suka bi ta da wani kallo, cousin sister din Mai martaba Hajiya Habiba dake gidan ita ma Ajay ya karasa dakin da take don gaisheta, tana kallon Khaleesat dake zaune kasan carpet ganin she is elderly tace "Wannan ce matar taka kenan?" Ajay yayi shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "Eh" Hajiya Habibah tace "Ba shakka" Khaleesat dai ta hakka .... anik suka fita daga parlon Khaleesat da kallo, can ta gyada kai a hankali parlon tana biye da shi, ta bi tace "Sai yanxu na kara fahimtar A'isha" Ajay yaki shiga wajen sauran mutanen dake gidan kawai ya tafi part din Mami.... Tun da suka shigo parlon jikin Khaleesat yayi sanyi sosai jin karisnin turaren Jay, ta nemi kujera ta zauna tana wasa da yatsun ta kanta a kasa, mintin su biyar zaune parlon Mami ta fito daga dakinta, Khaleesat ta zamo kasa a hankali ta zauna kan Carpet, bayan Mami ta zauna Ajay ya gaisheta tace "Lafiya lau, ya hanya" Yace "Alhamdulillah" Khaleesat bata dago kanta ba ta gaida Mami ita ma, yanda Mami ta amsa ma Ajay ita ma haka ta amsa mata, daga haka babu wanda ya sake cewa komai a parlon, after a while Ajay ya mike yayi mata sallama, Mami tace "Allah huce gajiya" Khaleesat ta tashi ita ma ta mata sallama, yanda Mami tace ma Ajay ita ma haka ta ce mata, Khaleesat na biye da Ajay kafin ya bude kofar fita daga parlon Jay ya rigasa budewa, Ajay ya koma gefe ya basa hanya bayan sun hada ido, Jay ya shigo parlon, tun su .... yace "Evening Halysaah" Kasa amsa gaisuwan nasa tayi har ya karasa cikin parlon, Mami dai dukana kallonsu, tuni Ajay ya fita daga parlon, Khaleesat na tafiya a hankali ta bi bayansa. Har karfe goma sha daya na dare Khaleesat na zaune parlor ita kadai, don tun bayan üa suka dawo Ajay ya shiga dakinsa bai fito ba har zuwa yanxu, mikewa tayi ta nufi dakin ta dan bude kofar a hankali tana leka ciki ta gansa kwance kan gado ya rufe har kansa, tafi minti biyu tana kallonsa kafin ta shiga cikin dakin ta karasa kan gadon ta zauna gefe, kawai ta kai hannu ta sauke duvet din tana kallonsa, sosai ta ji jikinsa da zafi duk da ba wai taba sa tayi ba but she could feel how high his temperature is don duvet din ma was hot, lokaci daya ya bude ido, kawai taga ya koma dayaangaren gadon ya sauka kasa ya kwanta leaving the bed for her don yayi tunanin kwanciya zata yi, ita dai tana ta zaune gefen gadon sai kuma ta tashi ta zaga ta inda ya kwanta ta duka kusa .... kusa da shi tace "Are you sick?" One could sense the disturbance in her voice, ya mayar da idonsa ya ufe sai kuma ya juya mata baya, ita dai tana ta zaune wajen, after a while taga ya sake tashi ya koma kan gadon alamar he is not comfortable on the Carpet, ya kara rufe har kansa da Duvet, ita dai kallonsa kawai take, can ta tashi ta sake komawa gefensa ta zauna ta sauke bargon tace "In kawo maka shayi?" Bai bude ido ba a hankali yace "You are disturbing me" Tayi shiru bata sake cewa komai batashi tayi daga karshe ta fita daga dakin ta tafi parlor ta bude flask din da aka kawo na ruwan zafi ta hada masa shayi, ta sake komawa dakin, ta tarar har ya kara rufe kansa da bargo, ta zauna kusa da shi ta bude bargon tana .... felt how hot his hand was, yayi sip daya kawai ya ajiye kan bedside drawer ya koma ya kwanta, ta sak dauko shayin tana kallonsa tace "To ai baka sha ba" Bai ce mata komai ba kuma bai bude idonsa ba, tace "Ka ji?" A takaice yace "Na sha" Sai kuma ya juya mata baya, tayi shiru tana kallonsa kafin ta ajiye shayin kan bedside drawer, tana ta zaune kusa da shi har karfe daya na dare ko baccin ma bata ji tana ji ba, sai juye juye yake and his body was getting hotter minute by minute, da ya fara baccin yake farkawa cause he was jolting now and then, sauka tayi daga kan gadon ta fita daga dakin, tana tafiya a hankali ta bar parlonsa, ta kusa minti diyu tsaye dogon corridor din da zai yi leading dinka away from his part kamar me tunani, can dai ta ci gaba da tafiya, after walking for 5 minutes ta iso bakin kofar ta bude a hankali ...... ta ji a bude, shiga cikin parlon tayi tana bin ko aniki halin cewa "Ni ce" Mami ta fito daga dakinta don dama tana zaune ne kan darduma da carbi a hannunta, ta karaso cikin parlon tana kallon Khaleesat da mamaki fuskarta tace "Lafiya?" Khaleesat na wasa da yatsunta tace "Dama bashi da lafiya ne" Mami tace "Junaid din?" Kinaleesat ta gyada mata kai, Mami tace "Me ya samesa?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Tun dai da muka dawo ne" Mami bata sake cewa komai ba ta tafi ta dau wayarta ta zauna kan kujera sannan tayi dialing number Jay. HALYSAAH PAGE 134... Sau hudu Mami na kiran Jay no answer, kuma tasan baya saka wayarsa a total silent sai dai vibration, ita dai Khaleesat na tsaye parlon kanta a kasa tana wasa da fingers dinta, Mami tace "Ki koma can bangaren ina zuwa" Khaleesat tace "To" Juyawa tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon, Mami ta mike ta fita zuwa part din Jay tayi knocking, ta kusa minti biyar bakin kofar tana knocking daga karshe Jay ya bude yana gyara jallabiyan da ya saka, yana kallon Mami da mamaki yace "Mami hope all is well?" Hadiyah na tsaye daga bakin kofar Bedroom dinsu sanye da wasu shegun kayan bacci fuskarta daure, ko kunyar Mami ta ganta bata yi ba, don sarai tasan Mami ke knocking din kofa don ko da ta kira wayar Jay dama wayar na kusa da ita vibration din ya tasheta bacci, tana dubawa taga Mami ke kiran ta saka wayar a total silent ta kife a bedside drawer, duk da Mami ta hango Hadiyah amma sai tayi kamar bata ganta ba tana kallon Jay tace "Ka je bangaren Junaid ba shi da lafiya...." Jay ya sauke idonsa yayi shiru jin abinda Mami tace, can ya daga kai ya kalleta yace "How did you know?" Mami tace "Matarsa ce ta zo bangarena yanxu take gaya min" Jay yace "Sai dai a bada pain reliever a kai masa cause iya shine abinda ke available da daddaren nan, zuwa gobe da safe sai likita ya duba sa yayi masa proper treatment" Mami tace "Sai ka kai masa pain reliever din ai" Tana kai wa nan ta juya ta bar bakin kofar, Hadiyah ta murguda baki ta juya ta koma cikin daki. Khaleesat na komawa bangaren Ajay ta shiga dakin ta zauna gefensa tana kallonsa ta kai hannu goshinsa that is so hot, cire hannunta tayi a hankali still looking at him, can ta mike ta shiga bandaki ta debo ruwa a karamin abu ta saka towel ta dawo dakin ta ajiye bowl din gefen gado, cire duvet din jikinsa tayi, ya bude idonsa da har sun kada yana kallonta murya can kasa yace "Ke" Bata ce masa komai ba ta sauke idonta daga nasa ta fara unbuttoning din masa shirt din jikinsa ya rage singlet sannan ta dau towel din ta matse ruwan jiki ta fara goge masa jikinsa da shi a hankali, he didn't resist cause he was weak, kofar parlor da taji alamar an bude yasa ta ajiye towel din hannunta, sai kuma taji sallaman Mami a parlon, rufa masa duvet tayi jikinsa ta sauka daga kan gadon ta tafi ta bude kofar dakin tana amsa sallaman, Mami tace "Yana ciki?" Khaleesat tace "Eh yana ciki" Mami ta shiga dakin da sallama ta karasa inda Ajay ke kwance tana kallonsa, hannu ta kai forehead dinsa, shi dai idonsa na lumshe, after some seconds tace "Allah ya sauwake, za a kawo masa magani yanxu" Khaleesat tace "To" Mami tace "Sai ki dinga tofa masa addu'o'i kuma" Khaleesat ta gyada kai tace "To in sha Allah" Juyawa Mami tayi ta fita daga dakin, Khaleesat ta koma ta zauna kusa da Ajay tana kallonsa ta ci gaba da goge masa jikinsa da towel, bayan fitar Mami da minti biyar taji ana knocking kofar parlor, sauka tayi daga kan gadon bayan ta ajiye karamin towel din hannunta ta ja masa bargon a jikinsa ta fita zuwa parlon, tana bude kofar suka hada ido da Jay dake tsaye, sauke idonta tayi ya mika mata magunguna biyu yace "Two each...." Amsan maganin tayi without raising her head, ya juya ya bar bakin kofar, ta bi sa da kallo sannan ta kulle kofar parlon, wani tea ta sake hada ma Ajay kadan a cup ta dau bottle water sannan ta koma cikin dakin, ta cire duvet din jikinsa tace "Ga maganin" Ya bude ido, iya maganin ya sha kawai yaki shan shayin ya koma ya kwanta, har karfe uku Khaleesat ko gyangyadi bata yi ba a kusa da shi, addu'o'in da Mami tace ta dinga tofa masa kawai take ta yi, in ta gaji ta huta sannan ta ci gaba, da ya bude ido zai ganta kusa da shi a zaune, duk motsin sa idonta na kai, zuwa sannan temperature dinsa ya dan sauka ba kamar daxu ba, kuma ya dena jolting da yake, and he was just sleeping. Khaleesat bata san sanda bacci barawo ya dauketa ba ta kwantar da kanta a gefensa lying down horizontally shi kuma yana kwance straight, a firgice ta farka wajen karfe biyar ta juya kanta a hankali jin something is holding back her hair, ganinsa tayi ya bar position din da kansa yake ya dawo kusa da ita ya cusa kansa cikin dogon gashinta bayan hularta ya fita, hada ido suka yi don ba bacci yake ba a lokacin, ya mirgina ya koma position dinsa, ta mike zaune tana packing gashin nata da ribbon dinta da ya zame, sauka taga yayi daga kan gadon ya shiga bandaki. Bayan sallan asuba ko azkar Ajay bai yi ba ya koma ya kwanta cause he was very weak, ta idar da nata azkar din ta koma kusa da shi ta zauna tana kallonsa tace "Ya jikin?" Ya dan kalleta yace "Waye bai da lafıya wai?" Ita dai kallonsa kawai take, can tace "Ni" Taga ya lumshe ido bai sake cewa komai ba, bacci ne ya kuma daukesa a haka, ita dai tana ta zaune taji ana knocking, ta mike ta fita, tana bude kofar taga Jay a tsaye, ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ina kwana" yace "Lafıya lau, how is his body?" Ta gyada kai still not looking at him tace "Da sauki" Sai kuma ta koma gefe don bata san ko shigowa zai yi ba, shiga parlon yayi ganin ya tsaya tace "Yana daki" Jay bai ce komai ba ya karasa Bedroom din, tsaye yayi kawai kusa da gadon ganin bacci Ajay yake, after some minutes ya juya ya fita daga dakin, Khaleesat na tsaye inda ya bar ta har sannan, ba tare da ya kalleta ba yace "Likita na hanya zai zo dubasa" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba har ya fita, a hankali ta zauna gefen kujera, tana ta zaune har likitan da Jay yace yana hanya ya iso, bayan tafiyar likitan Khaleesat na zaune kusa da Ajay don drip Dr din ya sa masa yayi masa allurai, Sallaman Mami da taji a parlor yasa ta tashi daga kusa da shi ta tafi ta bude kofar dakin tana amsa sallamarta, Mami na tsaye parlor tace "Ya jikin nasa?" Khaleesat ta duka nan kasan carpet ta gaisheta sannan tace "Da sauki" Mami tace "Har yanxu baccin yake?" Girgiza kai Khaleesat tayi tace "A'a ya tashi" Mami tace "Ok" Ta karasa cikin Bedroom din, ita dai Khaleesat bata mike daga inda take durkushe ba, Mami ta karasa har kusa da gadon dakin tana kallon Ajay da ya mike zaune ganinta, tace "Ya jikin?" Ya gaisheta sannan yace "Da sauki" Mami tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen" After some minutes ta Juya ta fita daga dakin ta koma parlor tana kallon Khaleesat tace "Yaushe Jawwad ya sa masa drip din?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a ba shi yasa masa ba, wani Drine" Mami tayi shiru bata ce komai ba, can ta nufi kofa, Khaleesat ta bi ta da kallo har ta fita daga parlon sannan ta mike a hankali ta koma cikin Bedroom din, jingina tayi jikin gadon tana ta zaune har bacci ya dauketa a haka, Ajay ya juya yana kallonta, sai kuma ya mike zaune yayi disconnecting din drip din hannunsa ya dau pillow ya ajiye kusa da ita, da hannu daya yayi using yayi laying dinta down the bed, ta bude ido da sauri, sai kuma tayi lamo kan pillown tana kallonsa, ya maida drip din hannunsa, lumshe ido tayi bacci ya kara dauketa. Sai kusan karfe tara Khaleesat ta farka taji yana wanka a bandaki, ya cire drip din da ko rabi bai kusa ba, ta cire duvet din da ya rufa mata ta sauka daga kan gadon ta fara gyaran babban dakin, Ajay na fitowa bathroom ko goge jikinsa bai yi ba taga ya kwanta kan gadon da ta gama gyarawa covering himself with duvet, ta ajiye turaren wutan hannunta da ta saka a burner ta koma kusa da shi tana kallonsa tace "Me yasa zaka yi wanka yanxu..." Juyawa tayi jin sallama a parlor sai kuma ta kalli Ajay that was shivering, ta tashi da sauri ta tafi ta bude press din kayansa, ta dauko masa one among the many jallabiyas she saw in one part of the press, ta dawo kusa da shi ta cire duvet din jikinsa ta mika masa jallabiyansa sannan ta fita daga dakin jin wani sallaman, Walid ta gani tsaye parlor taji gabanta ya fadi sosai, ta dan koma baya ta sauke kanta kasa cike da karfın hali tace "Ina kwana" Shi dai kallonta kawai yake daga sama har kasa da idanuwansa kamar wanda ya sha wani abu, sai kuma taji yace "Tare mu ke da Mai martaba, he is here to check on ur so called Husband...." Ta gyada kai without saying anything, Walid ya dan yi murmushi still looking at her ya juya ya fita daga parlon, ita kuma ta koma daki tana kallon Ajay da ya daure ya saka jallabiyansa tace "Mai martaba ne zai shigo Daga haka ta koma parlor ta tsaya gefe tana jiran shigowan Sarki, after almost 3 minutes suka shigo parlon, da Mai martaba da Walid sai Jay da Mukhtar, ta duka har kasa tana gaida Mai martaba ya amsa yana tambayarta me jiki, kanta a kasa tace "Da sauki ranka shi dade" ita dai tana durkushe inda take har suka karasa cikin Bedroom din. Throughout ranan haka Khaleesat ke zaune gefen gado kusa da Ajay Wanda baccinsa yafi rashin baccin nasa yawa, abinci kusan kala uku ta dibar masa a wanda aka kawo masu part din amma bai ci ko daya ba sai fruits kawai da ya sha, da rana Mami ta sake shigowa dubasa bata yi minti uku ba ta fita, sai Mukhtar da shi ma ya shigo bayan la'asar, amma bata ga Jay ya dawo bangaren ba tun bayan da suka zo tare da Mai martaba wajen karfe tara, Yakumbo ma na ta shigowa bangaren ta tambayi Khaleesat ya jikinsa, Khaleesat sai tace mata da sauki, wajen karfe shidda ta sake shigowa Khaleesat ta fito parlor tana kallonta don wannan shi ne shigowarta na kusan goma kenan ranan, Yakumbo ta zauna kasa ta sinne kai da ladabi tace "Allah ya taimake ki, har yanxu Yariman bacci yake?" Khaleesat tace "Ehh bacci yake" Yakumbo na dan kame kame tace "Dama idan ba damuwa ina son wata er magana dake ne, Allah ya sa bazai bata maki rai ba kuma Allah sa ki fahimce ni ranki shi dade" Khaleesat tace "To ina ji, ki zauna kan kujera mana Mama Yakumbo ta girgiza kai da sauri tace "A'a nan ma ya isa ranki shi dade, ni dai fatana Allah sa ki fahimce ni don a dar dar nake son maki wannan maganar, kuma ki dubi Allah maganar nan ya zama tsakaninmu ki gafarceni ranki shi dade ban san ko maganata ta karshe tayi tsauri ba, Allah ya taimake ki" Khaleesat ta zauna gefen kujera tana kallonta tace "To ina ji Mama" Yakumbo tayi kasa da murya tace "To Nagode Gimbiya, ni dai kamar yanda na gaya maki kwanaki kwarai a gidan nan na taso tun ina karamata, a lokacin mahaifiyata na da rai tana matsayin jakadiyar marigayiya mahaifiyar Yarima, don haka hatta ni mahaifiyarsa ta nuna min soyayya sosai, a magana ta gaskiya ranki shi dade duk abinda ke faruwa gidan nan kusan babu wanda ban sani ba, na dade ina son sanar maki cewar ciwon nan da Yarima yake da zarar ya shigo gidan nan a gaskiya har da sa hannu ba ciwon tsakani da Allah bane, jifa ne, tun wancan lokacin da aka kawo ki nake son inyi maki maganar nan amma ina tsoron yanda zaki dau maganata, to a takaice abinda nake son ce maki yanxu shi ne a duk sanda ya dawo masarautar nan idan baya da lafıya kai koma da lafıyarsa ni ke kawo masa abinci ko kuma na kawo masa kayan shayi da ruwan zafı kuma akasari ni ke hada masa abun shan sa saboda yarda da yayi da ni, ki gafarceni ranki shi dade ni dai a duk sanda bai da lafiya nakan zuba masa wannan a shayinsa..... Yakumbo na magana ta fito da kullin maganin tana nuna ma Khaleesat, amma fa duk a tsorace take tana kallon Khaleesat dake ta kallon kullin maganin, sai kuma tayi kasa da murya ga tsoro kwance fuskarta karara tace "Wallahi ranki shi dade ba komai bane illa itatuwa na kaikayi koma kan mashekiya, kuma hadi ne na musamman wallahi, duk naje garinmu nake amso masa wajen kanina don lakani ne da kakanmu ya bar mana, to in sha Allahu Yarima na shan shayin nan kafın kwana biyu zaki ga ya mike kamar ba shi ba, wani lokacin a ranan ma zaki ga alamar samun sauki tattare da shi, bai taba sanin wannan abu da nake yi ba kinsan dan boko ne ina fargaban yanda zai dau lamarin duk sanda ya sani shi yasa nake kaffa kaffa ban taba gaya ma kowa wannan sirrin ba, to yanxu tunda kece matarsa kinga ke ce ke hada masa shayi ko wani abu da zai sha don ba hurumina bane hakan yanxu, idan ma baki yarda ba yanxun nan sai in zuba a ruwa in sha, wallahi bana nufinsa da komai sai alkhairi, da mugun abu ne kin san bazan zo in gaya maki ba kuma duk hanyar da zan bi in zuba masa a abinci to zan bi in zuba babu kuma wanda zai sani" Khaleesat dai sai kallon kullin maganin take yi babu ko kiftawa, har cikin ranta kawai taji ta yarda da Yakumbo, can ta amsa maganin tace "To shikenan zan hada masa shayin da shi in sha Allah Mama" Sosai farin cikin fuskar Yakumbo ya kasa boyuwa tace "To Allah ya kara girma ranki shi dade tun jiya nake son maki magana amma ina tsoron yanda zaki dau maganar, na fi shekara uku ina ma Yarima haka, duk ranan da na tabbatar zan zuba masa maganin sai in dafa shayin da kayan kamshi sosai ta yanda bazai ji kamshin maganin ba, Yarima zagaye yake cikin makiya da mahassada bai da wani masoyi da ya wuce Mai martaba sai Jawwad a gidan nan, rayuwarsa na cikin mugun hatsari a gidan nan, ba sai na bude baki na gaya maki wasu abubuwan ba da kanki duk zaki fahimta daya bayan daya" Khaleesat dai ta sauke idonta bata ce komai ba, sallama aka yi kofar Parlon, Khaleesat ta maida maganin bayanta da sauri ta boye ganin har za a bude kofar parlon, Yakumbo kuwa sai zare ido take a dan tsorace, Hajiya A'isha da Kilishi ne suka shigo parlon sai Hajiya Habiba, suka dinga bin parlon da kallo a walakance, Yakumbo kuwa ta daga hannu daya sai jero masu kirarin ban girma take daga inda take zaune kanta a kasa, Khaleesat ta gaishesu babu wanda ya amsa mata cikinsu suna tafiya cike da kasaita da gadara suka nufi dakin Yarima suka shiga suka kullo kofar, Yakumbo ta kalli Khaleesat da sauri tayi kasa da murya tace "Ranki shi dade ki dinga kulle kofar da makulli sai ki ce masu shi ya kulle kayansa daga ciki in dai ba idonsa biyu ba, shigar wasun su cikin dakin nan ba alkhairi bane wallahi, babu abinda baza su iya yi ba, yanxu da kiyi dubara ki bi su ciki Khaleesat dai tayi shiru, sai kuma ta gyada kai tace "To Mama" Yakumbo ta mike still murya can kasa tace "Kiyi kokarin hada masa shayin yau da maganin don Allah, shi yasa ma na taho da matacin da zaki ta ce shayin da shi in kin zuba Daga haka tayi ma Khaleesat sallama cikin girmamawa ta fice daga parlon, Khaleesat sai kallon kofar dakin take ganin har yanxu basu fito ba, kasa daurewa tayi ta mike ta nufi cikin dakin ta bude ta shiga, duk ta samesu tsaye sun zagaye gadon suna kallonsa, shi ko yaki bude ido duk da shigowarsu dakin sai da ya tashesa daga baccin da yake amma he still pretends he is sleeping, duk suka juya suna kallon Khaleesat da ta shigo, da wani expression Kilishi tace "Ko baki da hankali ne yarinyar nan, muna ciki zaki shigo saboda rashin kunya? Ba a koya maki ladabi bane a gidan ku? Ko mu din sa'an iyayenki ne?" Khaleesat ta sunkuyar da kanta, Ajay ya bude idonsa ya mike zaune fuskarsa daure to stop them from saying more to her, Kilishi bata sake cewa komai ba ganin ya tashi zaune, Khaleesat dai ta juya a hankali ta fita daga dakin, Hajiya Habiba na kallon Ajay tace "Sannu ya jikin?" A takaice yace "Na ji sauki, Alhamdulillah" Hajiya A'isha tace "Allah ya sauwake" Daga haka ta juya ta fice daga dakin, Hajiya Habibah ta bi bayanta, Kilishi ma tayi haka, duk suka koma parlorn, Hajiya A'isha na kallon Khaleesat strictly tace "Idan kika ce a haka zaki zauna cikinmu wallahi sai zaman gidan nan ya gagare ki, this house will be nothing but a living hell for you tunda naga alamar ke din mara tarbiyya ce mara kunya er kananun mutane baki san na gaba da ke ba, ke har er gidan uban wacece ma tukun kike neman goga kafada da mu, ko 'ya yanmu har ki mutu baki isa goga kafada da su ba balle mu, amma mu zuba da ke a gidan nan" Hajiya Habibah tace "Gaskiya sai an gyara mata zama yarinyar nan naga tana da rawan kai, kin san dan talaka sannan gata bazawara, don sabuwar amarya bazata taba wannan rashin da'an ba" Daga haka duk suka fita daga parlon, Khaleesat dai bata dago kanta ba, can ta mike a hankali zata hada masa shayin da Yakumbo tace ta hada masa. HALYSAAH PAGE 135... Khaleesat na shiga dakin rike da cup din shayin da ta hada ta tarar da Ajay zaune drip na biyu dake hannunsa ya kusa karewa, ta zauna gefen gadon tana kallonsa tace "I made this tea for you" jin yayi shiru tasan next reply dinsa cewa zai yi bazai sha ba, hakan yasa ta hau saman gadon ta zauna dab da shi ta debi shayin a spoon ta hade rai ta kai masa baki tana kallonsa tace "Sai ka sha fa tunda na hado" Dariva ma..... sai ka sha ni bazan zubar ba" Ya dan kalleta yace "To ke ki sha mana" Tura masa spoon din tayi a baki har shayin spoon din ya zuba kan farin rigar jikinsa, ya jawo tissue dake bedside drawer da sauri yana goge gaban rigar yace "Ke" Ko sauraronsa bata yi ba ta sake diban wani zata kai masa baki, dariya ta basa sosai, ganin kar taje ta kwara masu shayin dake tiriri a cup yasa ya amshi cup din ya fara shan shayin, ita dai tana zaune kusa da shi tana kallonsa, har ya sha rabi ya ajiye sauran ta girgiza kai tace "Ai shanyewa zaka yi wallahi" knocking da taji yasa ta sauka daga kan gadon ta fita, Jay ta gani da Hadiyah a parlon, tun dawowarsu sai yanxu taga Hadiyah, suna hada ido Hadiyah ta wani hade rai ta kauda kai tana taunar chewing gum, Jay yace "Is he sleeping?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a" dakin ya nufa Hadiyah ta wani harari Khaleesat ta bi bayansa tana makale da shi, tunda Ajay ya hada ido da Jay ya dau sauran shayin da ya ajiye yana sipping, Jay dai ya tsaya few steps away from the bed bai dai ce komai ba, sai Hadiyah ce tace "Sannu yaya, ya jiki?" Ajay na shan shayin hannunsa without raising his head yace "Alhamdulillah" Tace "To Allah ya sauwake, ya sa kaffara ne" Yace "Ameen" Bayan minti uku Jay ya juya ya nufi kofa ya fita daga dakin, Hadiyah tayi ma Ajay sallama sannan ta bi bayansa, Ajay ya ajiye cup din hannunsa don har ya shanye shayin bai ma sani ba. Bayan isha'i Ajay ya shiga wanka, Khaleesat ta fara tidying dakin zata kunna turaren wuta duk da it's very....... yana kallonta ya nufi Bedroom din Ajay yana leka ciki a hankali, ganin babu kowa a dakin sai ma da yaji kamar Ajay yana cikin bandaki sai ya dawo cikin parlon ya nufeta yana kallonta yace "Ina mijin naki?" Komawa baya ta fara yi taki cewa komai gabanta na faduwa ganin irin kallon da yake mata, kawai taga ya mika hannu zai rikota, tsabar tsoro and her mind was already in a state of readiness da abinda zai iya faruwa kawai ta wani turasa da karfi, sai gashi rigijib kan kujera, shi kansa he was very shock cause he didn't see that coming, bai taba tunanin zata turasa ba har yayi loosing balance ya fadi, tuni Khaleesat ta fice daga parlon da sauri, Walid ya bi ta da kallo baki bude ko motsawa bai yi ba a inda ya fadi, tana waige waige ta nufi part din Mami da saurin ta, Mami na zaune parlor tare da mai taya ta aiki dake mata kwadon zogale a gabanta don tafi son a hada mata shi tana kallo, ga zogalen yaji uban tsire da kayan hadi, kana gani kaga rich zogale, parlon duk ya gauraye da kamshi, da ido Mami ta bi Khaleesat da ta sunkuyar da kanta ta karaso cikin parlon ta zauna kasa tana gaida Mamin, Mami ta amsa tace "Jikin nasa ne har yanxu?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a da sauki, kawai zuwa nayi" Mami bata sake ce mata komai ba ta maida attention dinta kan abinda ake hada mata har mai aikin ta gama sannan Mami ta dau plate ta dibi zogalen ta dora fork a gefen plate din tace ma mai aikin "Mika mata" Mai aikin ta amsa ta miks ma Khaleeest plate din zonalen da ladshi...... началаты NIGHT πατίαι τα αργά και και το είναι ma mai aikin nata, Hadiyah ce ta shigo parlon, tun da ta shigo take kallon Khaleesat daga sama har kasa, sai kuma ta nufi dakin Mami without saying anything to anyone, Mami ta bi ta da kallo kamar bazata ce komai ba sai kuma dai tace "Me zaki dauka?" Ko juyowa Hadiyah bata yi ba tace "Sako aka aiko ni in dauka" Daga haka tayi shigewarta dakin Mami, Mami tayi shiru har sannan bata dauke idonta daga kan kofar dakin ba, can sai ga Hadiyah ta fito rike da wayar Jay dake dakin, Mami tace "Saboda zaki dau masa waya shi ne zaki wuce min daki babu magana babu komai Hadiyah, duk yau mun hadu dake ne halan?" Hadiyah taki juyowa tace "To ai shine dai ya aikeni ba wai kawai na shiga dakin bane naka lana fadin haka ta fita daga parlon, Mami dai bata ce komai ba, ta maida zogalenta da zata ci gefe, ta sallami Mai aikinta, Mai aikin ta mike ta fita daga parlon, Khaleesat ta fara cin zogalenta tana kallon Film din da ake yi a TV dake parlon, after almost 10 mins Mami ta dau wayarta ta fara dialing number Jay, amma da ya shiga sai a danna mata busy, ta kira ya kusa sau biyar ana danna mata busy daga karshe ta ajiye wayar kawai a gefenta, bayan Khaleesat ta gama cin zogalen ta kalli Mami dake zaune ita dai ba kallo take ba amma idonta na kan TV, Khaleesat ta mike ta dau wani plate da aka yi using a wajen da babban cokali da bowl din da aka hada zogalen tana kallon Mami tace "Ina kitchen din Mami" Mami ta nuna mata hanvar kitchen dinta, ta mike ta tafi da kavan kitchen..... ajiyesu sannan ta goge inda tayi wanke wanken ta dau wani plate ta fita zuwa parlor, zogalen da Mami ta fasa ci ta ajiye Khaleesat ta duka kusa da zogalen tace "In rufe wannan?" Mami tace "Ohk" Kulle zogalen tayi da plate din hannunta sannan ta koma ta zauna ta ci gaba da kallon TV da take, Khaleesat na parlon Mami har kusan karfe goma tana kallo har sai da Mami ta kalleta tace "Baza ki tafi wajen mijin ki ba kin san ba shi da lafiya" Khaleesat ta sauke kanta sai kuma ta mike a hankali tace "To sai da safe" Mami ta dau karamin warmer din da ta ajiye ma Jay zogale ta mika ma Khaleesat tace "Ki kai masa ko zai iya ci...." Khaleesat ta amsa warmer din ta mata godiya sannan tace "Sai da safe" Kofa ta nufa ta fita daga parlon, nan gabanta ya fara faduwa ta dinga zazzare ido kar ta hadu da Walid, a dar dar ta isa bangaren Ajay tana waige waige ta shiga parlon da sauri ta kulle kofar da makulli, Bedroom dinsa ta nufa ta gansa kwance idonsa a lumshe, ta ajiye zogalen hannunta a dakin ta tafi ta ciro kayan baccinta ta dau turarurrukanta ta fita parlor ta ajiye kan kujera, bathroom din parlon ta shiga ta wanke baki sannan tayi wanka ta fito, ta bata kusan 20 mins kafin ta gama ma saka kayan baccinta..... kashe wutan dakın ya bar mara haske ya rufe har kansa da duvet har zata kunna sai kuma bata kunna ba ta karasa har kan gadon ta duka kusa da shi tana kallonsa don har sai da gabanta ya fadi thinking zazzabin ne ya dawo, ta cire duvet din tana kallonsa amma taji temperature dinsa was very much normal kamar bai yi zazzabi ba jiya, kawai gani tayi ya jawota ta fado kansa yayi wrapping hannunsa a bayanta muryar can kasa yace "What?" Ta wani kallesa ta fara kiciniyar sauka daga jikinsa taga ya maidata kasa shi yana sama, kamar zata yi kuka tace "Ko ba dubawa zanyi ba if you are okay, ni ka daga ni, ka danne ni fa" Tana fadin haka ya karasa kwanciya kanta ya lumshe ido yana zame hular gashinta murya can kasa yace "Ina kika je tun daxu?" HALYSAAH PAGE 136... Khaleesat ta marairaice masa kamar zata yi kuka gabanta na faduwa ganin yanda yanayınsa gaba daya suka canza yana kallonta, cikin rawan murya tace "Piss i can't breathe, don Allah kayi hakuri ka daga ni wajen Mami fa naje shi ne ta bani zogale in kawo maka Kallonta kawal yake cikin duhun jin abinda tace, kuma sai ma da ta fada haka ne ya fara jin kamshin turaren Jay from nowhere, nan bugun zuciyarsa ya kara tsananta yana kallonta, sosai tagi mugun....... side din dakin, jikinta na rawa ta sauka daga kan gadon da sauri tana waigasa ta fita parlor tana daure gashin kanta, nan pärion tayi kwanciyarta amma tana ta tsoron kar ya fito, har dal bacci ya dauketa bai fito ba, can wajen karfe biyun dare ta farka ta mike zaune tana kallon hanyar dakin, tana son shiga ta dubasa amma kuma tana tsoro, daga karshe dai ta mike tana tafiya a hankall ta tali ta tura kofar dakin slowly tana leka ciki, har sannan bedside lamp na kunne a dakin, kuma bata gansa saman gado ba, kunna fitilar dakin tayi nan ta hangosa tsaye kan darduma yana sallah, ta kashe wutan dakin ta koma parlor ta kwanta ta ci gaba da baccin ta. Washegari da sassafe bayan Khaleesat tayi wanka ta gama shiryawa taji ana knocking kofar parior, kailon kofar tayl don tun da taga Ajay bai dawo ba bayan an idar da sallan asuba ta sa ma kobar parlon makulli, ta mike ta tafi kusa de kofar tace "Waye?" Muryar Yakumbo taji, hakan yasa ta bude kotar, Yakumbo ce da wasu ma'aikatan gidan dauke da breakfast, bayan duk an shigo da breakfast din ma'aikatan suka gaida Khaleesat da ladabi suka fita, Yakuinbo ta zauna kasan carpet tana gaidata ita ma cikin girmamawa, Khaleesat ta mayar mata da gaisuwan kawal mamakon ta amsa, Yakumbo tace "Ya jikın Yariman? da fatan dar da sauki you?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Da sauki sosai, bai dawo ba tun da ya fita Masallaci daxu Yakumbo tace "To Alhamdulillah lafiya ta samu, dama baya dawowa da wuri in aka yi sallah, sai kusan karfe bakwai da rabi zaki ganša, don su kan yi karatu da Mai martaba bayan sallah. Ita dai Khaleesat tayl shiru bata ce komal ba Yakumbo tace "To ranki shi dade idan ba damuwa zan dan gyara maki nan bangaren, na hana sauran ma'aikatan nace ni zan dinga gyara maki cikin nan dan ba kowa kake yarda ........ "Ai har na gama gyaran Mama, ina son in dinga yin alkin gyaran da kaina tunda ba yawa ne da shi ba" Yakumbo tace To shikenan in kin zabi haka Gimbiya, su kuma ma'aikatan sal su gyara can parlon da dakuna, zan koma bakin aikina yanxu in kın mın izini Gimbiya Khaleesat ta gyada mata kai tace "To Mama, sannan babu kitchen a nan sal na can inda ku ke aiki? Yakumbo ta bude baki tace "In ji wa ranki shi dade? in ba takura ki taso yanxu in nuna maki kitchen din bangaren nan. Mikewa Khaleesat tayi, Yakumbo ma ta mike suka fita daga parion, nan Yakumbo ta nuna mata extra 3 rooms dake part din tace "Duk na bangaren Yarima ne nan Sai kuma ta tafi ta bude wani kofa nan Khaleesat taga katon kitchen that is well equipped and neat, Yakumbo tace "To kin ga kitchen din Bangaren nan kenan, babu abinda babu a ciki, idan Yarıma na bukatar wani abu da daddare kuma bai son takura kowa to nan yake yin abin sa Suka fito daga kitchen din Yakumbo ta kai ta parlon da za a fara shigowa a part din, Yakumbo tace "Wannan parlon ma duk na bangaren ne, amma shi yarıma yafi son yayi duk abinda zai yi a parlonsa dake dauke da dakinsa a ciki, a duk sanda kika gajl da zama a parlonsa ga wannan parion ma zaki iya fitowa kiyi zaman ki duk naki ne, in ma rufe kofar parton zaki yi kar a hango ki zakı iya rufe abun ki tunda na bangaren ku ne... Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, A haka suka koma parion Ajay bayan Yakumbo ta gama nuna mata ko iha na babban part din har da wata kofar da zaka bude ka fita yayi leading dinka zuwa wani garden me dauke da shuke shuke, ita Khaleesat ta zata just iya big parlor da Bedroom din ne na Ajay ashe he can use all, bata yi tunanin iya su kadai ne bangaren ba, Yakumbo tace, To bari in koma bakin aikina gimbiya idan kin ban izini Khaleesat tace "To sai anjima, Nagode sosai" Tana fita daga parion Ajay Khaleesat ta sake kulle kofar da makulli ........ Lipton me kamshi. Kamar yenda Yakumbo ta fadi karfe bakwai da minti talatin da biyar Khaleesat taji anyi knocking kotar parlor, ta mike ta tafi bakin kofar ta tsaya tace "Waye?" A takace taji yace "Bude min kofa" Bude kofar tayi ta masa kallo daya ta koma parlon ta zauna, yana shigowa ta dan kallesa duk da yanda taga ya hade rai tace "Ina kwana?" Banza taji ya mata yayi shigewarsa daki, ta tabe baki wato ya samu lafiya shine zai ci gabia da attitude dinsa, ko damunta abinda yayi bai yi ba tunda ta saba, ta dau warmer din Mami ta nufi koła zata je kitchen da Yakumbo ta nuna mata ta warike, few minutes later ta dawo parlon bayan ta warike warmer din da nufin gaya masa zata je ta kai ma Mami warmer dinta, amma ganin he is still inside his bedroom kawal ta juya ta nufi kofa ta fita zuwa part din Mami, Kamar mara gaskiya Khaleesat ke tafe tana dube duben hanya har ta isa bangaren Mami, tana sallama ta bude kofar taga babu kowa cikin parlon ta karasa ciki tana sallama a hankali ko Mami zata ji daga cikin dakin ta, jin ba a amsa ba ta zauna kan Carpet ta ajiye warmer din hannunta, the parlor was very neat and cool ga daddaden kamshin turaren wuta dake tashi, juyawa tayi jin an bude kofar parlon suka hada ido da Jay, ta sauke idonta kamar munafuka, ya kulle kofar ya karaso cikin parlon ya zauna kan kujera yace "Good morning Halysaah Without raising her head tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau" Mikewa yayi ya karasa Bedroom din Maminsa yaga bata ciki, ya sake dawowa parion ya zauna yace "Ina Mamin fa" Khaleesat ta girgiza kai tace "Nima ban sameta ba Yace "Ohk, ya jikin mijin ko?" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai suka hada ido da shi, shi ya fara dauke idonsa, ita ma ta sauke idonta tayl shiru bata ce komal ba tana wasa da fingers dinta, after some seconds tayi karfin halin cewa "I lost ur number Caimly Jay yece ......... "A'a ni ba ayi blocking dinka ba.... When last did you chat me up on WhatsApp da zaka san anyi blocking din ka?" Ya ciro wayarsa a aljihunsa ya bude WhatsApp ya shiga chat din su sannan ya mika mata wayar yana kallonta, ta daga kai ta kallesa, sal kuma ta dan matsa ta kai hannu zata amshi wayar da yake mika mata sai ga Hadiyah ta bude kofa ta shigo parion bayan ta kyallara ido bata ga Jay ba tasan bangaren Maminsa ya taho shine tayi maza ta biyo sa kar ma Mami ta basa breakfast yace zai ci, duk suka juya suna kallonta, still tayi bakın kofar parton tana kallonsu with shock bak bude, wani azababben ihu ta kurma kamar warce taga wani abun razana, da karfi ta dinga cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, innalillahi wa Inna ilaihi rajilun, me zan gani haka? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Jay ya mike da sauri ya nufeta ganin ihun da take yi da abinda take cewa yace "Ke Hadiyah? Meye haka kike yi? Are you on ur right senses?" Ita dai bata fasa thun da take ba, wanda tuni ta ja attention din wasu yan gidan sai ga iklima da uwarta da sauri, Hajiya Habibah ma ta taho bangaren Mami da gudu Aunty ma da su Maryam da Khadijah duk suka taho cikin hanzari cause it was still morning kowa na gidan, ita kanta Mami dake bandaki cikin Bedroom dinta tana wanka a nkice ta fito ta saka doguwar riga da hijab har kasa ta taho parlon cikin gigicewa, Su Hanya Alisha da Aunty suka dinga tambayar Hadiyah me ya faru, bata tanka kowa ba kamar mahaukaciya tayı kan Khaleesat da ta mike tsaye with shock tana kallonta, cikin zatin nama Hadiyah ta fincikota ta shaketa tana huci tace "Don uwarki da mijin nawa za ki yi kwartanci? Uban me ku ke yi kusa da juna kamar zaki shige jikinsa? Ashe dama ke kwartuwa ce?" Su Hajiya A'isha da Hajiya Habibah duk suka saki salati suna tafe hannu suna kallon Khaleesat, Jay ya nufi Hadiyah da καισί καπς ποιεις "Sion thie nie liselivsh mama haka bike ....... karasowa cikin parlen hata yi ha ta daka ma Hadiyah tsawa tana isowa ta fara kokarin kwace Khaleesat a hannunta tana cewa "Dama ashe ke mahaukacıya ce Hadiyah?? to saketa kar inyl mugun saba maki, mutuniyar barıza kawal mutuniyar hofi" Da karfi Hadiyah tace "Wallahi bazan saketa ba sai dai a kasheni, da mijina fa na kamata, babu wanda ya isa ya rufe wannan abu da na gani yau, da idona na kamasu, don haka kawai ki kyaleni Mami" Kilishi da a lokacin ta shigo parlon jin abubuwan da Hadiyah ke cewa ta rushe da kuka babu hawaye tace "Mun shiga uku mun lalace, meye wannan nake ji da kunne na haka? abinda bai taba faruwa ba iya tarihin masarautar nan, me zan ji yau ni kilishi, Innalillahi wa Inna llaihi raj'un Jay tsabar yanda ya zama confuse ya ma kasa cewa komal kuma bai sake matsawa ba tunda Hadiyah ta hanasa matsowe, ja Mami sai kokain kwace Khaleesat take hannun Hadiyah amma irin nikon da Hadiyah ta ma Khaleesat ba na Wesa bane, Mami tace "Ni za ki ma rashin kunya ina cewa ki sake ta kina ce min baza ki saketa ha Hadiyah, niza lo ma rashin kunya dan uwark??" Hadiyah ne huci tace "Wallahi bazan salketa ba nace Mami, sai ta fada min uban me ya kawota kusa da mijina, tun ba yau ba nasan dama tana masa messages din soyayya tana kiransa" Jay yo dake yayi karfın halin karasawa kusa da su yace "Hadiyah am talking to you, listen to me please, what is this u are doing for God's sake??" Wani tsawa Hadiyah ta kuma yi masa tace "Wallahi wallahi idan ka kuskura ka matso kusa da ni you will be shock at my next action, sai dai a dauren kuma ubana ya fito da ni, gwara kar ma ka fara matsoWB kusa da nan na gaya maka Hadiyah na fadin haka Jay ya ja ya tsaya, Mami ta juya tana kallonsa da mugun mamaki, Ita dai Aunty na tsaye tana ta observing babu abinda face a ...... faruwa Jawwad? Ka janyeta mana ka wani ja ka tsaya a wajen kana kallonsu, what is the meaning of this?? Da dai nan Ajay ya karaso balun kofar parion ya saya yana kallon Scene din babu ko kiftawa, duk yanda Mami ke kokarin kwace Khaleesat Hadiyan taki yarda don da duk karfin da Allah ya halitto ta da shi ta cakumeta, Mukhtar zal fixge Hadiyah ta massa shegen kallo tace "Kana taba ni wallahi zan Rasheta in kashe barıza ba abinda zai faru Su Hajiya Aisha da Hajiya Habiban da Kilishi babu wanda yayi attempting matsawa kusa da su balle a janye Hadiyah suka bar Mami ita kadai, su dai sai salati kawal su ke suna kara jinjina lamarin adding more salt to injury Ajay ya karasa cikin parlon ya isa nar inda suke tsaye ya sauke ma Hadiyah wasu lafiyayyun tagwayen man, tsabar yanda marin ya gigitata bata san sanda ta sake Khaleesat babu shin ba ta kwala wani kara tana rike fuskarta, Jay ya juya yana kallonsa babu ko kiftawa, Mami ta ja Khaleesat dake kuka sosai suka fita daga parion zuwa can hangaren Ajay, Ajay ya juya without looking at anybody in the parlor yayi ficewarsa shi ma, hannun Kilishi na rawa ta fara dialing number. Ummi uwar Hadiyah a wayarta, Jay da ya daure fuska sosal ya kama hannun Hadiyah dake rusa kuka kamar zata tsaga parlon suka fice daga parion. Kuka kawal Khaleesat take sosai, Mami na tsaye kanta a parlon Ajay tana tamibayarta atinda ya faru, shi dai Ajay na zaune parlon yaki cewa komai, Khaleesat na girgiza kai muryarta na rawa tace "Wallahi ba abinda nay mata Mami, kawal naje kai cooler ne, shine ban gan ki ba na zauna a parlor ina jiran ki, sai Ya jawwad ya shigo parlon ya tambayeni kina ina, nace ban same ki ba nima, shi ne ya zauna ya tambayeni jikin Ya Junaid, sal kuma yace ai nayi blocking dinsa.... Kasa ci gaba tayı tana kuka sosai, shi dai ....... Suyuwa vin, maris is juye la naнтов, а jery wa wani expression yace "Hey Junaid, ina son ka gaya min where you got the guts to slap my wife, uban me tayi maka zaka daga hannu ka mareta???" Khaleesat ta daga kai tana Kallon Jay babu ko kiftawa, Mami ma ta dinga kallonsa looking so shock, shi kam Ajay yaki ma juyawa ya kalli inda Jay ke tsaye, cikin bacın rai Mami tace "Ya mareta din, nace ya mareta din, kayi uban da zaka yi Jawwad, kuma tun raina bai gama baci ba ka bar bakin kofar nan kar ka bari inyi kalamal cikin bacin rai, daga kai har ita Hadiyar bana son sake ganin kafafuwan ku a bhangarena, ka tafi ka ban waje Juyawa yayı kamar zaitashi sama ya bar masu kofar a bude yayi tafiyarsa, Mami ta nemi kujera ta zauna saboda bacin rai ta rike kanta, sai ga hawaye na zuba idonta, mikewa Khaleesat tayi duk jikinta yayi sanyi ta durkusa gabanta a hankali tace "Mami don Allah kiyı hakuri, da na sani da ban je ba, kilan da hakan bai faru ba" HALYSAAH PAGE 137... Tun da Mami ta bar parlon Khaleesat ke zaune kan kujera lokaci lokaci take satan kallon Ajay da yaki kallon inda take, daga karshe tayi breaking silence din parlon a hankall tace "Dama fa warmer din da Mami ta baka zogale jiya naje in malda mata...." Mikewa yayi ya dakatar da ita without looking at her fuska daure yace "Ban tambaye ki ba" Daga haka yayi shigewarsa daki, ita dai ta bi sa da kallo, lokaci daya jikinta yayi sanyi, bayan kusan minti ashirin ta mike tana tafiya a hankali ta nufi cikin dakin, zaune ta samesa gefen gado ya dafe kansa, ta sauke idonta ta karasa cikin dakin ta tsaya kusa da gadon cikin sanyin murya tace "In kawo maka breakfast din nan?" Bai tanka ta ba, tana ta tsaye for almost 5 minutes, ganin yaki cewa komal ta juya walking slowly ta fita daga dakin, fita tayi daga parlonsa ta koma can babban parlon dake part din, ta karasa ta kulle kofar parlon don in aka zo wucewa ta corridor din dole sai an kallo cikin babban parlon in dai kofar a bude yake, ta tafi kan kujera ta zauna ta fara goge hawayen da ya taru idonta, sai yanxu ne ma ta fara jin zafin abinda Hadiyah tayi mata, hade kai tayi da jikin kujeran tana shesshekan kuka a hankali... Wajen karfe bivu sai ga Mami ta bude kofa ta shigo p Khaleesat dake zaune kan darduma tun da tayi sallah ta gaishe da ita cikin sanyin murya, Mami ta zauna kan kujera ta amsa gaisuwarta, bayan few seconds cikin karfin hali Mami tace "Halysaah ki gaya min gaskiya, kar ki boye min komai, kin tabbata duk abinda kika gaya min daxu da safe haka ya faru ko kin boye min wani abu?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Wallahi abinda ya faru kenan Mami ban maki karya ba" Mami bata sake cewa komai ba, can ta mike ta fita don akwai abinda take son dubawa ne kar kuma ta duba ba taga ba haka ba don hakan zai kara destabilizing dinta. Karfe hudu saura na yamma Ummi ta diro masarauta, direct bangaren Aunty ta fara nufa, nan ta tarar da ita da su Gimbiya Firdausi da Hajiya A'isha sai Kilishi, nan Hajiya A'isha da Kilishi suka rako Ummi har bangaren Mami, Mami na can bedroom dinta bakin ciki yasa ko zaman parlor ta kasa yau, ko breakfast bata yi ba ga lunch shi ma bata ji zata iya ci ba, tun da Jay ya bar part din Ajay da safe har zuwa yanxu bata gansa ba don bai zo part din nata ba, Ummi na tsaye tsakiyar parlon Mami ta dinga rafka sallama, Hajiya A'isha da Kilishi duk suka nemi kujera suka zauna, Mami na fitowa ta dinga kallonsu daya bayan daya a parlon, Ummi na huci tace "Wallahi kin ban mamaki Fulani, ban zaci haka daga gare ki ba, har wai zaki bayan wata er iskar bare akan Hadiyah?? Me Hadiyah ta maki kika tsaneta haka ne? Kawal don tana auren dan ki kuma kina bakin cikin soyayya da kulawan da yake nuna mata tunda ke ba haka kika so ba shi yasa kike tsangwamarta kike kyararta a gidan nan? ko dai kin mance matsayin Hadiyah ne a gidan nan?" Da mamaki Mami tace "Rashin kunya kika taso tun daga Lagos ki min Maimuna? Ni kike gaya ma maganganun nan?" Hajiya A'isha tace "A'a Fulani mu kan mu mun yi mamakin ki, kuma duk jikinmu yayi sanyi don bamu zaci haka daga gare ki ba, ta yaya kiri kiri zaki hau Hadiyah da zagi akan wata er iska can da bamu san ma cikakken asalinta ba? Meye hadinmu da ita da zaki goyi bayanta akan Hadiyah warce take jininmu? Har kina kallon Junaid ya daga hannu ya gaggaura mata mari ki ki cewa komal, instead ki ja matsiyaciyar yarinyar ki fita da ita ki bar Hadiyah? To in kin mance wacece Hadiyah bari mu tuna maki Fulani, d da uwar Hadiyah da Mahaifin Jawwad Allah yayi masa rahama, uwa daya uba daya suke" Cike da rashin mutunci Ummi tace "Ku kyaleta ai amanar marigayi Yaya Ahmad ta ci ba namu ba, dama tun ba yau ba nasan babu alkhairi a zuciyarta, to in haka ne me yasa bata saka dan nata a gaba tana kallo ba tunda bata son yayi aure ya nuna ma matarsa kulawa, ko babu ki dinga kishi da matar dan ki, matar ma jinin marigayin mijin ki" A hankali Mami tace "Maimuna ni kike ma rashin kirki yau?" Cikin i don't care attitude Ummi tace "koma yaya zaki sa shi ni bal shafeni ba wallahi, akan 'ya ta babu abinda bazan yi ba sai dai ayi hakuri, kuma babu shegen da zai taba Hadiyah ya kwana lafiya a gidan nan, zan zuba ido in ga hukuncin da sarki zai dauka wallahi sai dai ayi abun kunya a masarautar nan in dai ba a bi ma 'ya ta hakkin marin da aka yi mata ba" Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Mami ta bi ta da kallo baki bude, su Hajiya A'isha duk suka mike suka bi bayan Ummi, bayan sun fita Kilishi tace "Ai baki san wani abu ba Maimuna kafin sarki ya dau wani mataki ya kamata Hadiyah ta rama marukan da dan iskan nan Junaid yayi mata akan matsiyaciyar yarinyar, bayan ta rama marin akan yarinyar sai kuma a jira hukuncin da sarki zai dauka...." Hajiya A'isha tace "Kwarai kuwa, gwara ta fara rama marin kan shegiyar yarinyar kafin ma a zauna da Mai martaba" Khaleesat na zaune babban parlor ita kadai abun duniya ya taru ya dameta, ko Lunch da Yakumbo suka kawo daxu suka ajiye a babban parlon bata ko bude ba balle ta san me aka kawo, bude kofar parlon aka yi ta daga kai duk tunaninta ko Mami ce ta sake dawowa, Ummi ta shigo fuska murtuke tana rike da hannun Hadiyah dake biye da ita, ga Hajiya A'isl Kilishi na biye da su a baya su ma, ai ko gama shigowa parlon basu yi ba Khaleesat ta mike kan kace me sai gata a parlon Ajay a tsorace, Ita kanta bata san ko gudu tayi ba ta dai ganta parlon jiki na rawa, fitowar Ajay daga bedroom dinsa kenan zai je Masallaci, da gudu ta tafi bayansa zuclyarta na bugawa ta fara masa kuka, sai ga su Ummi sun shigo parlon fuskarsu duk babu alamar rahama, Ummi ta sake hannun Hadiyah cikin tsawa tace "Ta fi ki rama marin da yayi maki akan ta" Hadiyah ta kalli Ajay dake kallonta, Kilishi ta mata wani tsawan tace "Baza ki tafi kiyi abinda aka sa ki ba, ko ubanki ne shi Junaid din da kike kallonsa?" Ita dai Hadiyah ta kasa karasawa ganin kallon da Ajay yake mata, Juyawa yayi ya kama hannun Khaleesat ya shige Bedroom dinsa ya bar su wajen a tsaye yayi banging kofar sa. Ajay bal fita zuwa masallacin da yayi niyya ba yayı sallan a dakinsa, ita dai Khaleesat na zaune gefen gado sai goge hawayen da yaki tsaya mata take tana shesshekan kuka, sosal ta kara tsorata da gidan, ji take kamar ta gudu ta bar gidan, banda bugawa babu abinda zuciyarta yake, bayan Ajay ya idar da sallah ya mike ya nufi kofa don ma ya dena jin kukanta dake kara bata masa rai, tana ganin haka ta tashi da sauri ta nufesa muryarta na rawa tace "Don Allah kar ka tafika bar ni wallahi tsoro nake ji" Ya mata wani yace "Na aike ki kije ki dauko ma kanki magana?" Ta fashe da kuka moving closer to him tana girgiza masa kai tace "Wallahi kawai naje kai ma Mami cooler ne sai in gaisheta daga nan...." Cikin tsawa yace "Did you know the Mami from anywhere??" Girgiza masa kai tayi tana goge hawayen dake zuba idonta ta rasa abinda zata ce, ya kara daure fuska yace "You went to her part with the intention of meeting with Jawwad, you went there purposely because of him, probably ma shi yace ki je can don haka bear the consequences now kar in gaggaura maki mari.... Kasa cewa komal Khaleesat tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, bata taba ganinsa cikin yanayin nan ba, ya bude kofar yayi ficewarsa daga dakin kamar zai tashi sama. Har kusan Magrib Khaleesat na zaune kasan carpet a dakinsa, tun da ya fita ko digon hawaye bai kara zuba idonta ba saboda abubuwan da ya gaya mata, she was just sitting like a statue in the room tana jin zuciyarta babu dadi kwata kwata, daga karshe jin ana kiraye kirayen magrib ta mike a hankali walking slowly ta fita daga dakin, bata gansa parlornsa ba ta bude kofa ta fita, daya daga dakunan dake part din ta bude kofa ta shiga ta kulle da makulli..... Ajay na zaune parlon Mai martaba kansa a kasa, Jay ma na zaun opposite to him sai dai babu wanda ya wani cikinsu, Mukhtar was also in the parior kusa da Jay, kusan gaba daya familyn masarautan ne zaune a parlon har da Gimbiya, Firdausi da Hajiya Habibah, duk ana sauraron jawabin Sarki wanda ko minti biyar bai yi da fara magana ba cikin nutsuwa, duk an kagu yaje main point din da yasa duk aka tara su a parion, Ummi dal fuskarta a daure yake ta ma fi kowa kaguwan sarki ya gama jawabinsa taji hukuncin da zai yanke akan marin Hadiyah da Ajay yayi, sannan kuma su ji makomar Khaleesat a gidan kamar yanda su Hajiya A'isha su ma duk suka baza kunne su ji hukuncin da sarki zai dauka akan abinda aka ce Khaleesat tayi, babu wanda ya wani damu da reputation din Jay a cikinsu su dai kawai a shafa ma Khaleesat bakin periti da bazai taba gogewa ba yanda zamanta zai zo karshe a masarautan don cewa suka dinga yi abomination ta tafka, gashi ba karamin tsari Aunty tayi ma Mai martaba ba akan abinda ya faru and she made it look so bad wajen narrating ma Sarki, bayaninta yayi muni sosal, wanda har shi ma Mai martaba sai da jikinsa yayi sanyi daga sanda ya samu labarin nan ya dawo gashi nan gashi nan ne dai kawai amma bai nuna hakan a fuska ba cause he was very calm, but ko abinci ya kasa ci, Hadiyah dai na zaune kusa da uwarta tana jiran sarki ya tambayeta abinda ya faru dama Hajiya A'isha sun kara yi mata tsarin al zata fada don zancen ya kara girgiza sarki, tun da abun ya faru da safe take bangaren Aunty sun ki barin ko Jay ya ganta don kar ma ya canza mata ra'ayin fadan abinda suka kitsa mata, Jay dal sal kallonta yake a parlon ita kuwa taki yarda ta kallesa cause she is ready to say all what she was instructed to say that will paint Khaleesat black, yayi mata kira yafi ashirin ranan da text messages amma duk su Kilishi suka hanata picking kiran balle tayi replying messages dinsa kawai jiran Iken da za a zauna da sarki suke, Mami dai na zaune parlon kanta a kasa duk da sai da Mai martaba ya aika ayi kiranta sannan ta taho wajen zaman, Mai martaba na kallonta calmly yace "Fulani...." Mami bata daga kal ba tace "Allah ya taimake ka Mai martaba ya nisa yace "Me zaki ce game da wannan lamari da ya faru yau? Ina nufin menene ya faru yau a sashin ki Fulani?" Mami ta dan yi shiru, after some seconds tace "Ranka shi dade ni babban parlor na akwai Cctv Camera tun bayan abinda ya faru shekarun baya da aka kwashe min gwala-gwalai na Walid dake parion shima ya dan kalli Mami sai kuma ya dauke kai, Mami ta ci gaba da maganarta cikin nutsuwa tace "Ina jin babu wanda yasan da Cctv din sai yanxu da nake magana, don haka ina ga wannan kadai ya isa bada labarin abinda ya faru ba sal na komal ba, don na sa Mukhtar ya taho da Cotv DVR ayi connecting da TV kowa ya gane ma idonsa, a nan kuma zaka san ba komai suka ma yarinyar nan ba illa kazafi da sharri wanda su masu zuga Hadiyar suna da yaran nan mata kuma basu san abinda gobe zal haifar ba, ba komai ya kawo yarinyar parlor na ba sai alkhairi amma suka mayar sharri" Tun da Mami ta fara magana Ummi da su Hajlya A'isha da Aunty suka daga kal suna kallonta babu ko kiftawa, Mai martaba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yayi shiru na wani lokaci don he felt relieved immediately, can yace "Amma ke kin kalli clip din Fulani?" Mami tace "Kwarai na kalla a laptop tare da Mukhtar ranka shi dade" Mai martaba ya kalli Mukhtar yayi instructing dinsa yayi playing dinsa a TV, ba komai yasa Sarki yace a kunna ma kowa clip din ba kawai yasan hakan ne kadai zai kashe zancen nan, sanin halinsu Kilishi yasan tsaf za su ce gyara zancen Mami tayi saboda reputation din dan ta, Mukhtar ya mike da harizari yayi yanda Sarki yace yayi, aka jona Cctv din da TV, yana fara. playing Hadiyah ta sunkuyar da kanta, Ajay dai ya daga kai yana kallon TV din kamar yafi kowa son ganin clip din, kowa a parlon yaga exactly abinda ya faru a parlon Mami tun daga shigowar Jay da Khaleesat da ya tarar zaune a parion, bayan yayi hanyar dakin Mamin dawo ya zauna parion and they were not clase to each other ko kadan, yana kan kujera tana zaune kasa kuma ba kallonsa ma take ba, bai fi sau daya zuwa biyu ta daga kai ta kalli inda yake ba, sai kuma wayarsa da ya mika mata daga karshe sai shigowar Hadiyah parion da yanda ta taho ta cakume Khaleesat sai ga yan gidan duk sun shigo parlon su ma, amma Aunty har da ce ma sarki rungume da juna Hadiyah ta kama su, Mal martaba ya daga kai yana kallon Aunty da taki kallonsa, kowa na parion sal cika yake yana batsewa Irin ba haka aka so, daga karshe Mukhtar ya kashe TV din, shiru ne ya biyo baya na kusan minti uku a parlon, Sarki ya kalli Hadiyah da taki dago kanta yace "Ashe ke mutuniyar banza ce Hadiyah? Me yarinyar nan ta maki kike kokarin tarnishing Image dinta a gidan nan? Not only her, har reputation din mijin ki da na gidan nan as a whole kika so kiyi tarnishing, kin san ma'anar wannan abu da kika yi kuwa? To ina me umartar ki da ki tafi har bangaren matar Junaid ki bata hakuri akan abinda kika yi mata, umarni kuma nake baki, and I am highly disappointed in you" Duk aka daga kai ana kallon Sarki jin yace taje ta ba Khaleesat hakuri, Hadiyah dai taki dago kanta hawaye cike idonta, Ummi sai wani kumbura take a inda take zaune kamar zata fashe, Cikin kakkausan murya Mai martaba yace "Sannan daga wannan very moment din na wannan maganar a gidan nan, bana son sake Jin wani ya tadasa har abada, Idan kuwa hakan ya faru zan dau mummunan mataki akan koma waye...." Babu wanda ya iya daga kai balle yace wani abu a parlon, bayan minti daya kilishi ta kwantar da murya tace "Ina son er wata magana idan an bani dama ranka shi dade" Sarki yace "Go ahead" Cike da takaici tace "Allah ya taimake ka, sau biyu Junaid ya daga hannu ya mari Hadiyah fa tana matar wan sa ko kunyan wan nasa bai ji ba, gashi nan har sai da fuskarta ya kumbura akan marin da yayi mata, yanxu haka cewa take hakoranta na ciwo sai an je wajen Dentist, shi mijinta bai daga hannu ya mareta ba sal shi saboda yafi kowa son matarsa?? Yanxu da Jawwad bai kai zuciyarsa nesa ba ai batattciya za ayi a masarautar nan tunda-shi ma yana son matarsa" Mai martaba ya juya ya kalli Ajay da ya sauke kansa kasa yace "Ahmad" Still Ajay kansa na kasa yace "Ur highness" Strictly Sarki yace "This should be the first and last time da zaka daga hannu ka taba ko wani yaro a gidan nan da sunan duka, ina me tabbatar maka idan hakan ya sake faruwa zaka ga bacin raina Ahmad, a baya na sha maka warning akan hakan to wannan shi ne na karshe da zan maka" Mami ta daga kai tana kallon Mai martaba tace "Ranka shi dade ka mance matsayin Hadiyah ne a wajensa ne don ya hukunta kanwarsa?" Tun shigowar Jay parlon sai a sannan ya daga kai ya kalli Maminsa jin abinda tace, Ummi ma wani tsinannen kallo take ma Mami haka Kilishi, Mal martaba yace "Babu wannan zancen Fulani, Hadiyah matar aure ce yanxu don haka ba shi da right din daga hannu ya mareta, ba ma ita ba idan ya kuskura ya sake daga hannu akan ko wani yaro cikin gidan nan zan dau mataki akan hakan tunda aikinsa kenan shi, na sallami kowa..." Mikewa Sarki yayi ya bar parlon ya shiga second parlor dinsa, Mami ta mike ta fita duk da tana da maganganun da take son yi da Sarki amma ta bari sai gobe da sassafe zała 20 ta samesa. Ajay ya mike shi ma ya fice daga parion su Kilishi da Ummi suka bi sa da wani Irin kallo, yana komawa part dinsa yayi using makulli ya bude kofar babban parlon don sai da ya kulle before leaving, bai ga Khaleesat a parlonsa ba har ma a bedroom, and he began wondering inda ta tafi duk da yasan ya kulle kofar part din kafin ya fita, can ya fita ya bude all the 3 rooms in the part, yaji daya a kulle ya gane she is inside kenan, murda kofar yayi ya kwankwasa yace "Ke, bude kofar nan" Duk da Khaleesat na jin sa taki cewa komai tana kwance kan gado, daki ne babba that is well furnished babu abinda babu a ciki, sai bayan da ta shigo dakin taga ashe duk akwatunan ta ma suna dakin, sau uku yana knocking kofar taki tankawa, ya juya kawai ya tafi kitchen din dake part din ya ciro fruits a cikin fridge ya wanke su ya zuba a bowl ya koma parlonsa, yana ta zaune har lokacin isha'i yayi, yayi sallah sannan yayi wanka ya saka pajamas dinsa ya kunna TV a bedroom dinsa yana kallon football amma ya kasa concentrating duk sonsa da Ball, kawai ya kashe TVn wajen karfe goma da rabi ya kwanta kan gadonsa ya lumshe ido, ya dade abu bal dakesa ba kamar yau don ko abinci bai iya yaci ba yau, rabonsa da shiga irin wannan damuwan kilan tun bayan da Mai martaba ya sanar masa auren da ya daura masa da Khaleesat sai kuma incident din daxu da safe, but he felt relieved bayan clarification din da Mami tayi with evidence, mikewa yayi ya fita xuwa kitchen ya duba dinner din da aka kawo masu yaga Khaleesat bata taba komai ba a ciki, da rana ma yana lura bata ci abinci ba, ya juya ya fita daga kitchen din ya tafi kofar dakin da take ciki yayi knocking calmly yace "Jeeddah, oper door" HALYSAAH PAGE 138... Ajay na ta tsaye bakin kofar jin bata yi responding ba, ya sake knocking yace "Jeeddah" Still bata amsa ba, bayan kusan 3 minutes ya juya a hankali ya bar wajen ya koma parlonsa, wayarsa ya dauka ya zauna kan kujera yana dialing number.... Khaleesat ta fito daga bathroom tana kallon kofar dakin don tana wanka taji kamar anyi knocking, fuskarta babu walwala ta kauda ko kuka ta kasa yi balle ta dan ji saukin abinda take ji a ranta, nan ta dinga duba boxes din lefenta daya bayan daya har ta bude wanda kayan bacci ke ciki, ta dau doguwar rigar bacci da inner wear ta ajiye gefen gado, sannan ta bude box din cosmetics ta dau tsadaddun turarurrukan da aka zuba mata, ta dau cream din shafa da hair oil sai sabon comb ta tafi gaban mirror ta zauna, ta gama shafe shafenta ta daure gashinta kenan taji ana knocking kofar dakin, ta juya tana kallon kofar sai kuma taji sallaman Yakumbo, sau uku Yakumbo tayi sallama kafin ta mike a hankali ta tafi ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta sa Hijab ta nufi kofar ta bude, Yakumbo ta yi kasa da kai cikin girmamawa tace "Barka da dare ranki shi dade, Allah ya sa baki fara bacci ba na tashe ki" Khaleesat na kallonta tace "Ban fara ba" ido hudú tayi da Ajay dake tahowa daga babban parlor bayan ya ta bude kofar, ta dauke idonta ta maida kan Yakumbo babu yabo babu fallasa tace "Ina jin ki Mama" Yakumbo na dan kame kame tace "A'a dama ba wani abu bane, zan tambaya ne ko da abinda kike bukata ranki shi dade?" Khaleesat na ganin Ajay ya iso wajen tace "Bana bukatar komai, sai da safe" Daga haka ta juya zata koma cikin dakin da nufin kulle kofar amma taga har ya shigo ciki, tana ganin haka ta nufi hanyar bandaki ya kulle kofar dakin sannan yayi saurin rikota, Yakumbo dai tuni ta juya ta bar bakin kofar sum sum ta fita daga part din, Khaleesat ta ki yarda ta kallesa duk da yana rike da hijab dinta, cikin sanyin murya barin su hada ido, manneta yayi da bango yana kallonta murya can kasa yace "Da aka kawo ki gidan nan dama an shigo dake dakin nan ne?" Kin cewa komai tayi, ya dago kanta yana kallonta babu ko kiftawa, ta fara kokarin barin wajen amma yaki saketa, kamar zata yi kuka ta kallesa tace "Don Allah ka kyaleni pls sallah zan yi fa" yayi kasa da murya yace "Why didn't you open the door when I was knocking?" Da sauri ta girgiza kai tace "Wallahi ina bandaki ban sani ba" Shi dai kallonta kawai yake, ta sauke idonta a hankali, can ya saketa har sannan bai cire idonsa a kanta ba, ta bar jikin bangon ta tafi ta tsaya kan darduma zata tada sallah, makullin kofar dakin ya cire da na bandaki sannan ya fita, tana sallah ya kawo mata abinci da cup din tea ya ajiye mata, sannan ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa yana duba mai kiransa, kofa ya nufa ya fita daga dakin, ko da Khaleesat ta idar da sallah gaba daya taji ko appetite din cin abincin ma bata da shi, amma dai taji abinda take ji a zuciyarta ya ragu da almost 80 per cent, ta dan sha shayin kadan ta kwantar da kanta jikin gado a hankali ta lumshe idonta, a haka bacci ya dauketa, wajen karfe sha biyu taji an kwantar da ita sanan gadon dakin ta bude ido ta kallesa, sai kuma ta juya ya rufa mata duvet din da ya dauko daga dakinsa ta ci gaba da baccinta, ya kwashe abincin da bata ci ba da cup din tea ya kashe wutan dakin ya fita, dawowarsa part din kenan daga bangaren Mami. Da asuba Khaleesat na zaune kan darduma bavan ta yayi mata sallama akan zai fita Masallaci,daga can ta tashi tana tana murda handle din taji a bude ta kulle da makulli sannan ta juya ta tafi parlonsa, daga bedroom dinsa har zuwa parlon ta gyara ko ina sannan ta sa turaren wuta ta kunna AC, ta koma dakin da ta kwana ta shiga wanka, karfe bakwai saura ta gama shiryawa ta tafi main parlor ta kwanta don kar ya dawo yana knocking bata ji ba, har bacci ya dauketa taji knocking dinsa, ta mike ta bude kofar, yana kallonta yace "Why did you lock the door?" Girgiza masa kai kawai tayi, ya tafi parlonsa, after some seconds ta bi bayansa, zaune ta samesa parion yana duba wayarsa, ta zauna ta gaishesa without looking at him, jin bai amsa ba ta daga kai ta dan kallesa taga Kallonta yake, sosal taji gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta, ya mike yace "Mu je kina Mami bata da lafiya" Khaleesat ta daga kai ta kalles Jin abinda yace, a hankali tace "Ni dai bazan je ba, in kaje sai kace ina gaisheta...." Kallonta yake jin abinda tace, can kawai ya nufi kofa ta bi sa da kallo, sae kuma ta tashi ta bi bayansa tana tafiya a hankali, tare suka isa bangaren Mami tana biye da shi, ta zauna parlon Mami incident din jiya na dawo mata kamar lokacin aka yi, sunkuyar da kanta tayi shi kuma ya karasa Bedroom din Mami yayi sallama ya shiga, bayan few minutes ya fito ya zauna kan kujera without looking at her yace "Go inside" A hankali ta mike ta nufi Bedroom din ya bi ta da kallo har ta shiga da callama daki na nari murds that is wall furnished nan suka gaisuwarta cikin sanyin murya, Khaleesat tace "Ya jikin Mami?" Mami tace "Alhamdulillah da sauki" Khaleesat bata sake cewa komai ba tayi shiru tana ta zaune kasan carpet din dakin, after some minutes ta kalli kayan gugan Mami masu yawa dake ajiye kan kujera a ledojin su, tace "Mami a sa maki kayan a press ne?" Mami ta dan yi shiru don ba kowa take yarda ya gyara mata sip dinta ba, sai kuma tace "In zaki iya ki sa to" Mikewa Khaleesat tayi ta nufi gun kayan, Ajay na ta zaune parlor yana jiran fitowar Khaleesat, ganin bata fito ba har bayan minti sha biyar ya mike ya fita daga parlon kawai, har bayan minti talatin Khaleesat bata gama jera kayan ba don cikin nutsuwa take yi kamar yanda taga aka jera wer enda ke cikin press din, ko wanne da wajensa, Aunty ce ta shigo parlon da sallama cikin shiga ta allarma, da mamki ta dinga kallon Khaleesat da ta sunkuya da kai ganinta, Aunty ta karasa gun gadon Mami tace "Barkanmu da safiya Fulani, ya jikin?" Mami tace "Jik Alhamdulillah, ya kwanan su Maryam" Aunty tace "Lafiya lau" Dukawa Khaleesat tayi har kasa tana gaida Aunty, Aunty tayi kamar bata san da ita take ba tana dai tsaye fuskarta a murtuke, bayan few seconds Khaleesat ta mike ta ci gaba da abinda take, babu wanda ya sake cewa komai a dakin tsakanin Mami da Aunty, Aunty kuwa mamaki ne ya kasa barin zuciyarta, Mami da duk yanda take da mutum bata taba barin va shigar mata daki wai sai ga Khaleesat a dakin itama tana mai fadin ne na shigo in maki sannu ban san har da karin ruwa ba ma" Mami tace "Na ma ji sauki yanxu, ruwan ma ai ya kare kadan yayi saura" a takaice Aunty tace "Allah ya sauwake" Daga haka ta nufi kofa ta fice daga dakin, Khaleesat ta gama jera kayan gaba daya, sannan ta fara tidying din dakin duk da ko ina a gyara yake, ta kunna burner da ta gani ta saka turaren wuta, taji Mami tace "Kira Junaid ya zo ya cire min ruwan ya kare" Khaleesat ta mike ta karasa gun Mami tana kallon drip din tace "Zan iya cirewa" Mami na kallonta tace "Ke ma likitancin kika karanta" Murmushi Khaleesat tayi tana cire drip din tace "A'a Pharmacy nayi Mami bata ce komai ba, Khaleesat ta kalli flask din ruwan zafi da kayan shayi dake dako Daven ta gama cire drip din tace "Mami a hada maki shayin be ko kin sha?" Mami ta mike zaune tace "Ki dauko cup a kitchen" Mikewa tayi ta nufi kofa zata fita sai ga Jay zai shigo dakin, hade rai tayi without looking at him ta koma gefe ta basa hanya bayan ya wuceta tayi ficewarta daga dakin ta tafi kitchen din Marni, ba a dau lokaci ba ta dawo dakin ta tafi ta duka gun flask ta bude tana zuba ruwan zafin a Mug, shi dai Jay na zaune dakin Mami taki ma kallon inda yake tun daga gaisuwarsa da ta amsa shima kuma bai sake cewa komai ba a dakin, Khaleesat ta gama hada shayin ta mika ma Mami ta amsa tace "Nagode" Khaleesat na durkushe har sannan tace "Zan tafi sai anjima Mami" Mami tace "To bi tum min lunaid Khaleecat taco "To mua jay yang wala yi wa, ya wa la wa nanun yeICH INU har ta fita. Khaleesat na fita parlon Marni ta hadu da Walid da Mukhtar sun zo duba Mami su ma, sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido da Walid, Mukhtar ya gaisheta, ta mayar masa gaisuwan kanta a kasa, Walid kuwa sai kallonta yake kasa kasa suka shiga parlon da Mukhtar, tana tafiya da sauri ta koma bangaren Ajay, tsabar yanda zuciyarta ya tsinke sai da ta zauna babban parlor to calm her self down, ko dai Mami zata yi ma maganar Walid don ita tsoronsa take ji sosai, tana ta zaune a parlon har bayan minti goma sannan ta mike tana tafiya a hankali ta nufi parlon Ajay, baya parlon hakan yasa ta karasa bedroom dinsa ta gansa kwance yana bacci, juyawa tayi a hankali ta koma parlor ta kwanta. Yakumbo ce ta shigo bangaren wajen karfe sha biyu da rabi, Khaleesat ta fita babban parlor ta zauna tana gaidata, Yakumbo tace "Allah ya taimake ki, nace bari in zo in ji ko kina da bukatar wani abu dai" Khaleesat tace "A'a ba komai Mama" Yakumbo tace "To amma ranki shi dade in dai da wani abu da kike son ci a ranki ki dinga sanar min ko a kitchen dinki ne sal in maki, naga bakya wani cin abincin da ake kawo wa, ko kumallon dazu ma naga tabawa kawai kika yi, haka ma dinner din jiya, shi dama Yarima nasan bai wani damu ya ci abinci da yawa ba, amma ke sai nake ga kamar cimar da ake kawo maku ne baki so" Khaleesat tace "A'a duk ina cin komai indan ina hukatar wani ahu ma zan yi magana. Kina nufin zaki kiyi da kanki" Ita dai Khaleesat tayi shiru, Yakumbo ta karasa kusa da ita tana mika mata wani package da hannu biyu tace "Yanxu na shiga duba Mami da jiki ta bada wannan a kawo maki" Khaleesat na kallon package din ta amsa hannun Yakumbo tace "To" ajiyewa tayi kusa da ita don bata san ko menene ba shi yasa bata bude gaban Yakumbo ba, Yakumbo ta koma ta zauna tana kara sauke kai kasa tace "Sannan idan babu damuwa ina son wata er magana da ke Gimbiya amma sai kin ban dama...." Khaleesat na kallonta tace "ina jin ki" Yakumbo tayi kasa da murya tace "Ki gafarceni ranki shi dade, amma a matsayina na me shekaru kuma duba da yanda kike mutunita ni da girmama ni ba tare da kin duba naki matsayın ba yasa har na samu kwarin gwiwan yi maki wannan maganar, Allah ya taimake ki ina son baki shawara ba don na isa ba amma don Allah duk abun da zai hadaki da Yarima kiyi hakuri kar ki sake cewa za ki rufe masa kofa, ba a yi ma miji haka balle ma miji irin Yarima...." Fitowar Ajay zai je masallaci yasa Yakumbo tayi shiru kanta a kasa tana qaishesa da ladabi, Ya amsa va nufi wajen motarsa "A'a, hasali ma ni ban kulle masa kofa ba" Yakumbo tace "To Allah ya huci zuciyarki Gimbiya, na maki mummunan fahimta a gafarce ni" Khaleesat tace "Ina son dama in tambayeki, don Allah bazai yiwu ki dawo nan ki dinga zama ba har dare?" Ba komai yasa Khaleesat tace haka ba sai don kawai tana son mutum ya kasance da ita a part din, don tun daxu ta kasa samun sukuni bayan haduwarta da Walid a part din Mami, Yakumbo tace "Sai abinda Yarima yace Gimbiya, ke zaki sanar masa da abinda kike so kiji abinda zai ce, amma don ta ni banda matsala na ma fi son kasancewa tare dake ina maki duk abinda kike so, balle naga har yanxu baki gama sakin jiki da gidan ba" Khaleesat tace "To zan masa magana....." HALYSAAH PAGE 139... Har Ajay ya dawo part din wajen karfe uku Yakumbo na nan tana ta yi ma Khaleesat labarai iri iri, wani na ban dariya, wani ban haushi, wani tausayi, Khaleesat really enjoyed her company and she wish Ajay zai yarda ta dawo part din nasa gaba daya, Yakumbo na ganin Ajay ya dawo ta bar bangaren bayan ta sallami Khaleesat, Sai a sannan Khaleesat ta bude package din da Yakumbo ta kawo mata inji Mami, tana budewa taga tsadadden Waist bead ne sai Musk shi ma mai kyau da tsada..... taken Hadiyah ga shi ko zuwa bangarenta ta gaisheta ta dena yi komai a walakance take mata yasa ta ajiye kawai bata bata ba, Khaleesat ta maida waist bead din cikin package dinsa sai ga Ajay ya fito alamar fita zai sake yi tana ganin haka ta marairaice tace "To ni sai a barni ni kadai?" Ya dan kalleta yace "Kin koma kin duba Mami?" Ta girgiza masa kai, zai fita ta bi sa da sauri tace "To ka rakani pls" Yace "Kin mance hanyar?" Ta gyada masa kai, dariya ma ta basa bai dai ce komai ba ya fita parlon tana biye da shi har suka isa part din Mami, tun da garin Allah ya waye sai sannan Hadiyah ta zo bangaren Mami dubata da jiki shi ma Jay ne ya tilasta ta, kuma da ta zo part din sai tayi zamanta a parlor bata shiga dakin ba, da safe dama Aunty ta sanar ma Ummi da su Hajiya A'isha cewar taga Khaleesat dakin Mami har tana mata gyaran kaya shi ne har yanxu babu wanda yago part din duba Mami cikinsu, shi kansa Jay da ya zo da safe bai dawo ba sai da azahar ya sake shigowa dubata, Ajay na shiga parlon Mami da Khaleesat Hadiyah ta dauke kai taki gaida shi, ya nufi dakin Mami Khaleesat na biye da shi, Hadiyah ta bi ta da wani matsiyacin kallo, exactly irin kallon Khaleesat ma ta mayar mata ta dauke kai, Hadiyah ta bude baki da mamaki ganin hararanta fa Khaleesat tayi, Mami na zaune ita kadai a dakin ko TV bata kunna ba, ta juya tana amsa sallaman su, Ajay ya zauna kan kujera Khaleesat ta karasa kusa da gadon ta zauna kan Carpet ta gaisheta sannan tayi mata ya jiki, Mami na kallonta tace "Jiki Alhamdulillah" Ajay ma yayi mata ya jiki tace "Da sauki" Mami tace "Ki duba kitchen ki dauko min bowl da cokali" Mikewa Khaleesat tayi ta nufi kofa ta fita zuwa kitchen din Mami, Hadiyah na aonin habe es mile to hi to tans bursi toon be don gaba da tafiya tayi banza da ita, Fixgota Hadiyah tayi tace "Magana nake maki don ubanki idan ba tsoro ba ki tanka min mana" Khaleesat ta fincikota a fusace tace "Sai dai ubanki amma ba nawa ba wallahi, kuma kece matsiyaciya mara tarbiyya not me" Ajay ne ya fito daga daki tare da Mami dake biye da shi jin hayaniyar su, Hadiyah na ganin Ajay ta sake Khaleesat bayan Khaleesat ta cikata ita ma, Mami ta hade rai sosai tana nuna ma Hadiyah kofa tace "Fita ki ban waje, kuma kada in sake ganin kafarki a sashin nan...." Hadiyah ta wani harareta ta juya fuuuu ta nufi kofar fita daga parlon sannan ta juya ta kalli Khaleesat tana nunata da yatsa tace "Zaki san kin zagi ubana kin kirani mara tarbiyya wallahi" Daga haka ta fice daga parlon, Mami na kallon Khaleesat tace "Tafi aiken da nayi maki" Khaleesat ta juya ta wucu kitchen din, bayan ta dauko bowl din ta koma dakin Mami, Mami ta nuna mata food warmer dauke da pepper soup da mai aikinta tayi tace "Dibar min kadan a ciki" Khaleesat ta zuba mata pepper soup din sannan ta mika mata bowl din, Mami ta amsa tace "Kar ki sake kulata a gidan nan" A hankali Khaleesat tace "To in sha Allah" Ajay ya mike ya fita daga dakin don dama pharmacy zai je siyo mata magani, sai bayan fitarsa Khaleesat tayi ma Mami godiyar sakon da ta ba Yakumbo ta kai mata, har kusan Magrib Khaleesat na bangaren Mami a zaune, tana son komawa part din Ajay amma tsoron haduwa da Walid ko a hanya ya hanata tafiya, Har sai da Ajay ya shigo da Drugs da ya siyo tun da rana, ta sauke ajiyar zuciya ganinsa, bayan ya nuna ma Mami prescription din drugs din yayi mata sai da safe, Mami ta kalli Khaleesat tace "Ki tashi ku je sai da safe, Nagode" A haka suka bar parlon Mai martaba kansa a kasa, Sarki dai sai kallonsa yake tun bayan da yaji abinda ya kawosa, after almost a minute sarki ya numfasa yace "Ka koma zuwa ina kenan?" Ajay bai dago kansa ba yace "Ko a nan garin ne ranka shi dade...." Sarki yace "Ohk, kawai dai ya zamto baka cikin Emirate kake nufi ko?" Ajay yayi shiru bai ce komai ba, Mai martaba yace "Isn't it?" Ajay ya gyada kai a hankali yace "Haka ne ur highness" Sarki yace "Ohk, amma meye dalilin ka? Ko don saboda abinda ya faru recently?" Ajay yace "A'a dama ina da wannan intention din in har zaka amince min zan koma daya daga gidajenka na cikin garin nan in zauna" Calmly Sarki yace "To ban amince ba Ahmad, don bana son kayi nisa da ni, kafin ka zo da wannan batu Jawwad ne ya fara zuwa min da shi kuma na hanasa, ina son ku duka biyu a kusa da ni, and i will make sure ur wife lives comfortably in this Emirate if that's ur fear Ahmad" Ajay ya girgiza kai da sauri yace "A'a ranka shi dade ba don abinda ya faru bane, dama tun asali kasan i prefer staying outside of the Emirate" Mai martaba yace "Learn to love staying inside of the Emirate Ahmad, babu zancen barin ka cikin gidan nan, i won't be king forever, I won't rule forever, wataran dole ka gaje ni, and you will rule this great Emirate in sha Allah" a hankali Ajay yace "Allah ya huci zuciyarka, ur wish is my command in sha Allah, a gafarce ni idan na bata maka rai da batun nan" Sarki bai kara cewa komai ba, bayan minti daya yace "Kuma yaushe zaka koma bakin aikin ka?" Ajay yayi shiru don babu inda tunaninsa ya tafi sai kan Khaleesat and how she will Cope in the palace idan ya koma aiki, A hankali yace zan zauna a gida. I know that, ko ka zauna gida naga ba shigowa fada kake yi ba ake yin komai da kai, baka involving kanka a abubuwa da yawa da suka shafi masarautar nan, it is as if you are not even in the House, to me yasa sai kayi shawara kafin komawa bakin aikin ka?" Ajay ya sauke idonsa yace "Ranan Litinin in sha Allah zan koma" Sarki yace "Allah ya taimaka" Ajay na ta zaune parlon har bayan wani dan lokaci Sarki dai sai kallonsa kawai yake, dai dai sanda Walid ya bude kofar parlon ya shigo, yana ganin Ajay a ciki har ya fara komawa baya zai fita sai kuma yaji yana ma Mai martaba sai da safe, hakan yasa ya tsaya, ai bai san yana ciki ba tun daxu da tuni ya tafi bangaren sa wajen Khaleesat, Ajay ya mike ya nufi kofa ya fita Walid ya bi sa da kallon gefen ido sannan ya karasa cikin parlon. Ko da ya koma part dinsa ya tarar da Khaleesat har tayi bacci a bedroom dinsa, yala kan kujera ya jinginar da kansa jikin kujeran ya lumshe ido, bai yi tunanin Sarki zai yi turning down request dinsa na barin Palace ba and he really felt bad about it, yayi tunanin sarki zai yi considering abubuwan dake faruwa ya basa go ahead din barin gidan even if it's just for a while, ga kuma maganar aiki da zai koma ranan litinin and today is Thursday, ji yayi kansa ya kulle gaba daya, bayan abubuwan dake faruwa gidan babban dalilinsa na jin bai son zaman masarautar saboda Jay ne don bai son suna haduwa in anyway ta haka kadai ne zai iya concentrating.... Washegari da asuba Ajay na tafiya masallaci Khaleesat ta je ta kulle kofar babban parlon ta ciki kamar yanda ta saba, tana idar da sallah ko azkar bata gama ba taji ana knocking kofar parlon, mamaki tayi don in ya tafi sallah sai karfe bakwai da rabi wani lokacin har da minti arha'in yake dawowa nart din ranta va hata hra all to open the door tace "Waye?" Yace "Bude min kofa" A hankali ta murda kofar ta bude tana kallonsa ya shigo parlon ya wuce parlonsa, ta kulle kofar ta juya ta bi bayansa har zuwa parlon, kafin ta shiga har ya shige Bedroom still ta bi sa, ta gansa tsaye yana kokarin cire jallabiyarsa alamar kwanciya zai yi, tun bai gama cirewa ba ta koma other bedroom din zata karasa azkar dinta sannan ta shiga wanka, Ajay ya fasa cire jallabiyan bayan ya tuna zai duba jikin Mami ya juya ya sake fita daga dakin zuwa part din Mami, Khaleesat ta daga kai jin kamar fita ya sake yi, after few minutes ta mike ta fita daga dakin, sai da ta kara shiga bangarensa ta duba don tabbatar da fitan yayi sannan ta fito ta nufi babban parlor da nufin kulle kofar da makulli taga an bude, tsabar shock kasa kwakkwaran motsi tayi a wajen ganin Walid, can ta juya da gudu ta koma daki da nufin saka makulli amma taga Ajay ya cire makullin, cikin rikicewa tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Tuni ya shigo har cikin dakin yayi kasa da murya yana bin ta tana komawa baya yace "Babu wani Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, duk ke kika jawo, da kin bani hadin kai tun a America da duk ba a zo nan ba amma ke me taurin kai kika ki bani co-operation, to yanxu dai mijinki na can masallaci suna karatu da sarki da wasu fadawa kuma shi da fitowa daga masallacin nan dai sai kusan karfe takwas, don haka kawai ki sallameni in kama gabana, kin ga kafin nan ma har mun mance mun yi wani abu, idan kuma kika ce yau ma taurin kai za ki min ko kuma ki min ihu wallahil azeem sai in kashe ki in kashe banza, bar ganin an samu CCTV camera part din Mami, nan babu ko normal camera ki ji in gaya maki halle cctv" Randa rawa hahu ahinda iikin Khaleesat ya hau rawa kamar mai jin sanyi, shi ko fisge hijab din jikinta ya fara yi kamar yasan ihu take da niyyar kurmawa ya shake wuyarta da hijab din yanda zata san da gaske fa yake sai ya iya kasheta idan bata basa hadin kai ba, hakan bai sa ta fasa kururuwa ba tana basa hakuri duk da muryarta bai fita sosai saboda shakar da yayi mata, a haka ya yage hijab din jikinta da karfi tun daga wajen wuya har kasa sannan ya jefata saman gado, da sauri ya fara cire belt dinsa jikinsa na rawa ganin alamar kayan bacci ne ma a jikinta, dai dai sanda aka bude kofar dakin, da mugun shock ya juya suka yi ido hudu da Ajay dake tsaye bakin kofar, nan ya fara mayar da belt dinsa da sauri yana zare ido, Khaleesat kuwa kuka ta dinga yi tana rufe jikinta da hijab dinta da ya yage ta sauka daga kan gadon ta tafi gun Ajay jikinta na rawa tana kuka sosai, Walid sai gwalo ido yake bayan ya gama saka belt dinsa yana kallon window din dakin ko zai samu hanya, a nan kasan dakin Ajay ya jefar da wayar hannunsa ya karasa ciki ya fincikosa yana kallonsa da idanuwansa da suka yi ja, ya fito da shi har zuwa Main parlor, ya fara masa wasu mugayen kulli a ciki, Khaleesat na ganin haka ta saka wani hijab ta taho parlon da sauri ta riko Ajay tana girgiza kai tace "Noo plsss, don girman Allah kawai kayi reporting dinsa...." Hankadata Ajay yayi sai ga ta kan kujera ta fadi, Yana jan Walid ya bude kofar parlon suka fita daga part dinsa gaba daya har suka yi nisa da bangaren nasa, Walid na kokarin guduwa Ajay yasa kafa ya kwashesa kasa sannan ya lankwashe hannunsa daya ya take da karfi, Walid ya kurma wani wagegen ihun azaba don sai da hannunsa yayi wani kara bayan Ajay ya take hannun, Ajay ya dagosa ya hau sauke masa wasu arnayen kiss ta ko ina yana yana jin wani irin yanayi ya dena ganin fuskarsa sam ya dena ganin fuskarsa saboda jinin da ke zuba a goshinsa, tuni mutanen gidan suka fara fitowa jin ihun Walid, hakan kuma bai sa Ajay ya fasa dukansa ba yana bugasa da bango yana punching dinsa, Cikin tashin hankali su Hajiya A'isha da Kilishi da Ummi suka dinga cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, mun shiga uku mun lalace, kashe sa zaka yi? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, jama'a ku kawo agaji zai yi kisan kai" Daga nesa Aunty ta tsaya with shock tana kallon dukan da Ajay ke ma Walid jikinta na rawa, ta fashe da kuka ta taho da sauri ta cakumo Ajay tana jijjigasa tace "Kashe min dan nawa zaka yi Junaid? Kashe min Walid din zaka yi?" Ko kallonta Ajay bai yi ba bai kuma fasa dukan da yake ba, su Maryam da Khadijah sai rusa kuka suke, da sauri Ummi ta tafi ta saka ayi kiran Mai martaba dake Masallaci, Dogar Dogarai biyu suka zo kwace Walid hannun nun Ajay bayan Kilishi ta tafi ta kirasu.... aika anyı kıransu also stood in shock yana kallon scene din, ya karasa wajen cikin sauri ya finciko Ajay da karfi yace "Are you out of ur senses? What is this u are doing? shaye shaye ka fara??" Mukhtar da shi ma shigowarsa kenan yayi saurin Janye Walid shi da wani Dogari bayan Jay ya finciko Ajay ya hadesa da bango, Ajay ya fixge hannun Jay daga rikon da yayi masa yana huci kamar zaki, dai dai sanda Mai martaba ya karaso wajen yana kallon Ajay babu ko kiftawa, Ajay yaki yarda ya kallesa ya kauda kai yana sauke numfashi, can kuma ya juya ya bar wajen kamar zai tashi sama ya tafi part dinsa, Sarki ya bi sa da kallo, duk sauran mutanen wajen ma haka suka bi sa da kallo, Aunty na koke koke ta bi bayan wa enda suka fita da Walid su Ummi duk suka bi bayanta da sauri, Mami dai na tsaye bakin kofar part dinta ta kasa cewa komai. HALYSAAH PAGE 140... Ajay na shiga part dinsa ya sa ma kofar key, tsabar yanda Khaleesat ta girgiza har Ikcn bata tashi a inda yayi dumping dinta ba a babban parlon, ko Kallonta bai yi ba ya nufi parlonsa kamar zai tashi sama, ta bi sa da kallo babu ko kiftawa zuciyarta na wani irin bugawa, kawai taga ya juyo ya dawo parlon yana kallonta Strictly yace "Do not say anything to anyone duk tambayar da za a maki Yana kai wa nan yayi wucewarsa parlonsa taji yayi banging kofar, Khaleesat ta fashe da kukan tashin hankali ta zamo abar tausayi, kuka kawai take a parion kamar ranta zai tita, daga karsne ta mike tana tafiya a hankali ta tafi parlonsa bugun zuciyarta na tsananta, ganin yana Bedroom ta karasa ta murda kofar taji ya sa makulli, ta juya hawaye na sauka idonta ta koma parlor ta zauna tayi tagumi, knocking din kofar parlon taji ana yi ta mike a tsorace duk da kofar a kulle yake, muryar Mami taji a bakin kofar, hakan yasa ta karasa zuciyarta na bugawa ta bude kofar, Mami ta shigo tana kallonta tace "Ina Junaid din?" A hankali Khaleesat tace "Yana daki" Mami ta nufi cikin parlonsa Khaleesat ta bi bayanta bayan ta kulle kofar parlon, knocking kofar dakinsa Mami tayi tana kiransa, After a while ya bude kofar, ya ki kallon Mami, Mami ta shiga dakin tana kallonsa tace "What happened Junaid? Me ya hadaka da shi haka??" Ajay yayi shiru bai ce komai ba kuma bai daga kansa ba, a fusace Mami tace "Magana nake maka ko baka ji na ne" Ya dago idonsa a hankali yace "He is just daring me in this house, dama kuma tara sa nake, ko shekaranjiya a gaban Mai martaba ya gaya min maganar banza" Mami tace "Shi ne zaka masa irin wannan duka Junaid? Ko dai baka da hankali ne?" Ajay ya ki cewa komai, Mami tayi shiru tana ta kallonsa, daga karshe ta juya kawai ta fita daga dakin Ajay ya mayar da kofarsa ya sa makulli, Mami na kallon Khaleesat tace "Me ya masa yau din yayi masa wannan duka haka?" Hawaye na sauka idon Khaleesat ta girgiza ma Mami kai kawai alamar bata sani ba tunda ya mata warning kar ta fadi komai, Mami ta nufi kofa ta fita daga bangaren, Khaleesat ta tafi ta kulle kofar ta fashe da sabon kuka ta sulale wajen, Walid dai tuni aka yi asibiti da shi hannu a karye. Tun bayan da Mami ta tafi Ajay bai sake fitowa daga dakinsa ba, Khaleesat dai na ta zaune parlor tana tunanin wannan wane irin bala'i haka, sai lokacin sallan juma'a Ajay ya fito daga bangarensa sanye da fararen kaya kamar ba abinda ya faru zai tafi masallaci, sau daya ta kallesa ta sunkuyar da kanta, yana kallonta yace "Have you eaten?" Duk da bata ci ba kawai ta gyada masa kai, ina taga nutsuwar cin abinci ita kam, yana fita parlon taji ya kulle daga waje, bai je masallacin da ya san Mai martaba da mutanen gidan ke zuwa ba, yayi tafiyarsa masallaci me nisa. Bayan isha'i Ajay ya nufi fadan Mai martaba tare da Khaleesat dake biye da shi a baya zuciyarta na bugawa, tun safe Mai martaba ya sanar da zaman, Ajay ne karshen shigowa ya tarar da kusan duk familyn gidan zazzaune a babban parlon, hatta wa enda ke nesa duk sai da suka amsa kiran Sarki suka zo, tun daga iyaye har 'ya ya da jikoki, Walid ma na zaune parlon da katon bandage an nann kansa ga hannunsa da aka daure saboda karyewan a da yayi, fuskarsa duk a kumbure, ga targade kashi kashi a kafafuwansa, bakinsa ma yayi suntum, Aunty dai na zaune idonta duk sun kumbura don kuka jira kawai take taga hukuncin da Mai martaba zai dauka kan Ajay kafin ma ta ce komai don tun safe taki magana a gidan, Ajay bai yarda ya kalli kowa a parlon ba ya zauna kusa da Mukhtar ya sauke kansa kasa, kowa na parlon kallonsa yake banda Sarki, Khaleesat jiki a sanyaye ta tafi ta zauna kusa da Mami, ita ma aka bi ta da hararan tsana, for 5 mins babu abinda Sarki yace a parlon, ko ina was absolutely silent, in da sabo duk sun saba don sarki sai ya iya bata kusan minti goma bai yi magana ba kamar dai yana nazarin abubuwan da zai furta before saying anything, daga karshe Sarki ya sauke ajiyar zuciya dama an riga an bude waien da addu'a tun Ajav basu karaso ba tunda haka ne sai mai martaba ya fara magana cike da nutsuwa da kuma dattako... ina da labarin abinda ya faru a gidan nan yau da safe, which is so unfortunate, bana kuma tunanin akwai wani abu da Ahmad zai fada da zai yi justifying abinda yayi ma dan uwansa ignoring my few days ago warning akan duka a cikin gidan nan, don haka Ahmad is not and will never be capable of ruling this Emirate one day one time, babu ta yanda za ayi a ba madambaci mulkin masarautar nan, shi ne naga yana da kyau in tara ku nan in fara sanarwa tun daga cikin gida cewar Ahmad Junaid Yusuf is hereby dethroned as the prince of this great Emirate, daga rana irin ta yau na sauke sa a matsayin Yariman wannan masarauta...." Ajay ya daga kai a hankali yana kallon Mai martaba babu ko kiftawa kamar yanda kowa na parlon ke kallon Sarki with utmost shock, Khaleesat ta daga kai hawaye cike idonta tana kallon Ajay, Aunty sai gyara Alkyabbar jikinta take tana kara kallon sarki da idanuwanta kamar za su fito don sai taga kamar mafarki take ba daga bakin Mai martaba hakan ya fito ba ko kuma ita ce bata ji da kyau ba, Jay ma sai kallon Mai martaba yake babu ko kiftawa, Mami ta sauke idanuwanta a hankali, the announcement came as a shock to everyone in the parlor babu wanda ya kawo wannan hukuncin sarki zai yanke kan Ajay, Sai da sarki ya bari kowa ya gama processing abinda ya fada sannan ya ci gaba cikin nutsuwa yace "And from tomorrow in sha Allah Ahmad Jawwad will be crowned the Prince of this great Emirate through all proper rite" Sai da numfashin Aunty ya dauke na yan dakiku, ta dinga kallon sarki babu ko kiftawa, duk tunaninta Walid zai nada sabon Yarima tunda Walid ne second blood son dinsa, kowa na parlon was in a shock da jin wannan hukuncin na mai martaba. Daga can Fulani Aseeyah ta bude baki ta fara magana "Amma Allah ya taimake ka...." Dakatar da ita Sarki yayi yace "Ban bukaci Opinion din kowa ba, and this is disrespect to the king Fulani Aseeyah" Mami tayi shiru, Hadiyah ta kalli Ummi da farin cikinta ya kasa boyuwa sai kallon Mai martaba take unbelievable, hawayen farin ciki ne ya hau sintiri fuskar Hadiyah ta dinga ganin abun kamar a mafarki wai mijinta ne Yariman Masarautar nan yanxu, Mai martaba ya ci gaba yace "Na saka Makama ya sanar ma masu sarautu, tun daga Hakimai, dagatai da sauransu duk su hallara a fada gobe su shaida wannan sauyi da aka samu sannan a nada sabon Yarima, and mind you all... no one is in the rightful place or position to question the decision of the King in anyway, and as for you Ahmad Junaid bana son ganin ka a duk inda kasan za mu hadu a gidan nan, keep a reasonable distance from me, idan ba haka ba you will be surprise at my next action toward you...." cikin kakkausar murya Mai martaba ya kare maganar sannan ya mike ya bar parlon, Ummi ta daga hannu sama da karfi tace "Alhamdulillah Ya Allah Nagode maka, Alhamdulillah" Jay ya daga kai yana kallon Mami da ta kasa ma dago kanta, su Gimbiya Firdausi da Kilishi sai kallon Aunty da hawaye ya cika idonta suke, can Aunty ta mike ta fice daga parlon don kar ma ta fashe da kukan takaici a parlon, Ajay ya mike fice cikin wani irin yanayi na gushewar tunani... bude pampo, she felt guilty don komai ya taru ne saboda ita, Mikewa tayi ta bi bayansa da sauri hawaye na zuba idonta, Mami dai ta bi ta da kallo, Khaleesat na shiga Bedroom dinsa taji yana bathroom ya bude shower, komawa parlor tayi ta cire hijab din jikinta ta hade kanta da kujera tana kuka sosai, she is feeling really bad, she cried for 20 minutes a parlon, daga karshe ta mike ta goge hawayen idonta ta shiga cikin dakinsa, zaune ta gansa gefen gado ya dafe kansa bayan ya fito wankan ko goge jiki bai yi ba, wasu hawayen suka taru idonta ta karasa har gabansa ta tsaya, ya dago kansa a hankali yana kallonta, bata san sanda ta rungumesa ba ta dora kansa a kirjinta tana shafa wet hair dinsa hawaye na zuba idonta, lamo yayi a kirjin nata yana sauke numfashi a hankali, sai kuma taji saukan hawayensa a kirjin nata, daura lips dinta tayi a gashin kansa giving him kisses. HALYSAAH PAGE 141... A hankali Ajay yayi wrapping hannunsa round her waist ya lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya, har sannan kansa na kwance saman kirjinta tana shafa gashinsa hawaye na sauka idonta, they were like that for many minutes har sai da numfashinsa ya dawo dai dai, ta sauke kanta a hankali tana kallonsa taga idanuwansa a lumshe suke, karamin towel din da ya ajiye ta hau goge masa jikinsa... kofar parlor, ta dai ci gaba da abında take har ta gama ta ajiye towel din tana kallonsa, slowly taga ya janye jikinsa daga nata ya kwanta kan gado ya lumshe ido, jin an sake kwankwasa kofa ta dau towel din ta shiga bandaki ta shanya sannan ta fito ta nufi kofar dakin ta fita zuwa parlor ta dau hijab dinta dake kan kujera ta saka ta tafi kusa da kofar parlon ta bude, ido hudu suka yi da Jay dake tsaye bakin kofar, ta dauke idonta ta koma gefe ta tsaya, yana kallonta calmly yace "Where is he?" Still not looking at him a takaice tace "Yayi bacci" Jay bai ce komai ba, after some seconds ya juya ya bar bakin kofar ta kulle kofar, ta tafi ta zauna kan kujera wasu hawayen na taruwa idonta ta rufe fuskarta da hijab tana kuka a hankali, tavi kukanta me isarta sannan ta mike tana share conta ta bude kofar parlon ta fita zuwa dakin dake kallon entrance din parlon, wanka tayi bayan ta gama shafe shafenta ta shirya zuwa nighty sannan ta fito daga dakin ta shiga kitchen ta bude fridge ta fiddo fresh berries tasa a bowl ta ajiye a sink ta zuba gishiri ta wankesu sosai, ta zuba su a wani bowl ta fita daga kitchen din ta koma parlornsa sannan ta nufi Bedroom, har sannan tana rike da bowl din berries din a hankali tace "I brought you some fruits" ya mike zaune ya jingina da gadon ya kai hannu ya dau daya ya fara sha slowly yana kallon press din dakin babu ko kiftawa, ita dai kallonsa kawai take don kana ganinsa kasan tunani yake, can ta sauke idonta ta dau berry daya ita ma tana sha taji bai mata dadi a baki ba saboda how hurt she is, and she assume that is how he is also feeling the taste, bai wani sha sosai ba taga bai kara dauka ba, tana kallonsa a hankali tace "Ya ishe ka?" Ya gyada kai not looking at her, ta ajiye bowl din kan bedside drawer sannan ta sauka daga kan gadon ya bi ta da kallo, Press din kayansa ta bude ta dauko masa pajamas ta dawo kusa da gadon ta zauna suka hada ido, sauke idonta tayi cikin sanyin murya tace "Wa an yayi ko in canzo wani?" Jin bai ce komai ba ta koma kusa da shi sosai ta zauna tana kokarin ganin hawayen da ya fara taruwa idonta bai zubo ba tana kallonsa cikin sanyin murya tace "I'm... I'm sorry, i am sorry it's all because of me, I am sorry you have to go through all this for me...." Muryarta na rawa ta karasa, hawaye na zuba idonta tana va sauka kanca kaca as if he don't abinda take fada masa, gabadaya ta kasa cewa komai hawaye na zuba idonta sosai, sai kuma ta lumshe idonta, sun kusa minti biyar a haka taji hannunsa a kan shoulder dinta ya sauke hannun rigar baccin jikinta a hankali, ita dai tana rungume da shi har sannan idonta a lumshe tana sauke ajiyar zuciya, yayi ma daya hannun rigar ma haka sannan ya sauke rigar gently zuwa waist dinta, ta bude ido suka hada ido da shi a nan taga ya maida wutan dakin zuwa mara haske through switch din dake jikin gadon, da sauri ta mayar da idonta ta rufe ya mannata jikinsa, sai da taji kamar an hadata da electric shock saboda skin to skin contact don shi ma babu komai jikinsa sai short, ya lumshe ido yana shafa lallausan bayar yana kara kankameta zuwa jikinsa breathing dinsa ya fara canzawa, kawai jin lips dinsa tayi a wuyanta giving her kisses all over at the same time yana cuddling chest dinta a nasa kirjin, narkewa ne kawai Khaleesat bata yi a wajen ba, cause the sensation was something else, kawai ya hade goshinsa da nata yana kallon dogon hancinta, a hankali ya lumshe ido ya daura bakinsa kan soft line dinta kiris va rane numfachinta hai dauka nn nanyny yana uuuuillily viico hannunsa, lokaci daya ya sauko da fuskarsa kan chest din nata ta rungumosa da sauri don har sai da suka fada kwance saman gadon, her outburst was something else at that moment don kara rikitasa tayi gaba daya, ya dinga snuggling dinta romantically tana kara rungumosa, gaba daya ta sakar masa jikinta yayi yanda ya so a wannan lokacin, sai da taga ya fara wuce gona da iri yaje har inda bai taba attempting ba yasa ta dan fara dawowa senses dinta amma duk da haka bata yi stopping dinsa ba sai dan nonnokewa da take yi a tsorace tana turjewa, shi kuma bai fasa abinda yake ba duk da yanda take turje masa, it's just like his life depends on that area, duk ya karasa birkice mata don nan kuma gaba daya tention dinsa ya tafi sabanin inda yake concentrating a baya, cikin kankanin lokaci ya sake lulawa da ita cloud 9 ta mance da wani tsoro don deeply yake romancing dinta duk ta sakankance, lokaci daya Khaleesat ta sake dawowa hankalinta jin wani sharp piercing pain, nan ta fara turasa da sauri at the same time hindering him from doing what he was about doing, cikin tsoro muryarta na "No plssss, don Allah ka tsaya" Riketa yayi cikin wata irin murya yace "Plss... Don't say no plss Jeeddah...." Fashewa tayi sosai da kuka tana turasa da duk karfinta ganin ba daina abinda yake zai yi ba ga wani irin azaba dake tsirgan mata tun daga tsakiy kai har toes dinta, cikin tashin hankali tace "Na shiga ukuuu, don girman Allah ka tsaya, don Allah ka tsaya, wallahi bazan iya ba...." Ya dakata yayi kasa da murya ya marairaice mata don kawai consent dinta yake so yace "Why pls Jeeddah?" Bata fasa turasa ba tana kuka tace "Wallahi bazan iya ba, Allah bazan iya ba, it's soo painful, don Allah kayi hakuri" Muryarsa na rawa yace "But the pain is experienced just once in a lifetime, you will fool nothing again beside you will feel nothing again Jeeddan, you will teel no pain now i assure you" Duk yanda ya so daurewa sai da amincewarta kawai ya kasa don har wani bari jikinsa yake duk ya fice hayyacinsa jin abinda bai taba sanin da shi ba, yayi ignoring duk wani rokonta da magiya ya kara attempting for the second time ta kwala masa wani azababben kara da ya ji har tsakiyar kansa, duk tunaninsa kawai don ta dade without intimacy ne and this made her tight from the outside har yasa take raki, yayi saurin rufe bakinta da nasa don kar ma ta samu daman kara wani ihun and he kept going further.... HALYSAAH PAGE 142... Khaleesat ta kwace bakinta cikin gigicewa, letting out another loud scream of pain tana turasa da duk karfinta cikin kuka take cewa "Plsss it's hurtful, nace maka bazan iya ba wallahi, don Allah kayi hakuri" Da kyar ya fada gefenta yayi rub da ciki yana maida numfashi, ita dai kuka kawai take tana jan duvet tana rufe jikinta da ke rawa tana kallonsa, taga kawai ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, duk da azaban da take ji har a lokacin but she felt bad she couldn't bear the pain for him, tana jin sa yayi wanka a bandakin sannan ya fito ya fita parlor, ta hade kanta da gwiwa tana kuka a hankali, bayan kusan minti sha biyar ta jawo rigarta a hankali ta saka sannan ta sauka daga kan gadon tana tafiya da kyar ta shiga bandaki, ruwan zafi ta bude a pampo ta tara sannan ta sirka zata yi amfani da shi, after some minutes ta fito daga bandakin har sannan a hankali take tafiya ta zauna gefen gado hawaye na taruwa idonta, can dai ta mike ta daure ta fita zuwa parlon kwance ta samesa kan kujera, wutan parlon ma dim one ne a kunne don haka bata san ko idonsa biyu ba, walking slowly ta karasa har inda yake kwance ta durkusa tana kallonsa hawaye na sauka idonta, cikin sanyin murya tace "Don Allah kayi hakuri" Idonsa na lumshe calmly yace "Da me?" Ta kasa cewa komai tana shesshekan kuka, taji ya jawota jikinsa a hankali, ta kwanta saman faffadan kirjinsa tana jin bugun zuciyarsa, shi dai bai ce komai ba but deep down yana tunanin kawai taki sake jiki ne for reasons known to her, she didn't let him pass through even a bit duk ta takure jikinta, but even at that he is still a bit confuse at her tightness considering the fact that she is not a virgin, duk da ba wai ya sa mata force bane he was being very gentle with her, but as a Gynaecologist he knows of Vaginismus and with what just happened har ya fara diagnosing hakan as Secondary Vaginismus if at all she have no other plans kenan, secondary Vaginismus wani medical condition ne wanda an sadu da mace a baya but due to Abuse from partner or Sexual Trauma or even emotional factors shi ne take acquiring Matsalan where by vaginal muscles dinta will involuntarily or persistently contract, balle in her own case da bata son auren da aka mata, although sai in bata da wani nufin a ranta shine diagnoses dinsa zai yi count ya zama gaskiya.... murya can kasa taji yace "You have other plans right?" Ta daga kai da sauri ta kallesa, sai kuma ta girgiza masa kai hawaye na zuba idonta tace "Wallahi a'a" Bai sake cewa komai ba, taga ya tashi ya koma cikin dakin ita dai ta bi sa da kallo, babu abinda ya fado mata a rai sai zaman da tayi gidan Abdul da kalubalen da suka dinga samu exactly yanda wannan ya faru yanxu, nan kuma taji hankalinta ya tashi sosai, could it be that something is wrong with her ko kuma kawai tsoro ne ya shigeta da yawa, tafi minti ashirin tana duke a parlon cıkın tashin hankali, ta ma rasa wani tunanin zata yi, daga karshe ta dake ta tashi ta bi bayansa zuwa cikin dakin, ta gansa kwance kan gado ya juya baya, tana tafiya a hankali ta karasa ta hau kan gadon ta zauna kusa da shi amma ta rasa abinda zata ce, after a while ta juya a hankali ta tafi edge din gadon ta kwanta, tana goge hawayen idonta she is feeling bad har cikin ranta, ji tayi ya dawo bayanta ya jawota jikinsa ya rungumeta ta baya yana cusa fuskarsa cikin lallausan gashinta at the same time yana shafa cikinta, ta juya a hankali ta kwanta kan kirjinsa ta lumshe ido tana kara shigewa jikinsa, a haka ta fara bacci tana jin warmth din jikinsa, shi kam ya kasa bacci saboda arousal da yake ji da yafi na ko yaushe, ya saka hannu cikin rigar baccinta yana caressing dinta, a hankali ta bude ido, ya hade forehead dinta da nasa murya can kasa yace "Il... i can't sleep" ta lumshe ido ta daura lips dinta kan nasa tana shafa kirjinsa a hankali, kissing dinta ya fara yi passionately, she tried her best to give him satisfaction by flowing with him duk da bai kara attempting kusantar ta ba, but they romanced each other intensely.... Da asuba Khaleesat ce ta fara farkawa daga bacci, har sannan kuma tana jikinsa yaki saketa, they slept all through the night clinging to each other, ta zame jikinta a hankali sannan ta kunna wutan dakin ta jawo duvet tana rufe jikinta ta juya tana kallonsa, tun daga thick eyebrow dinsa zuwa dogon hancinsa down to his lips that got all the qualities, kallonsa kawai take ko kiftawa babu, a hankali taga ya bude idonsa suka yi ido hudu, da sauri ta boye fuskarta a Pillow tana murmushin kunya, tun bata kai ga boye fuskar ba ya rigata juya kansa, bai ma san dalilin da yasa shi saurin juya kai ba bayan sun hada ido da ita, can ya mike zaune, still not looking at her yana shafa kansa a hankali, bayan ya gama addu'an tashi daga bacci ya mike ya nufi bandaki, a nan bedroom din yayi sallah tana bin sa jam'i a baya, bayan sun idar shi dai bai iya ya kalleta ba, ya koma jikin gado yana addu'o'in sa, ita ma dai kanta na kasa taki dagowa tana supplications dinta a zuciya, after almost 10 mins ta dan daga kai a hankali ta saci kallonsa dai dai sanda shi ma ya dan kalleta suka hada ido, tayi saurin rufe fuskarta da gado a hankali tace "Ina kwana" shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, ta samu ta tashi daga wajen ba tare da ta yarda ta kallesa ba ta tafi karshen gado ta kwanta ta lumshe idonta ta juya masa baya, sauke idonsa yayi kasa a hankali, bai taba tunanin zai iya bacci daren jiya bayan abinda ya faru ba, baccin ma wai me nauyi kuma babu ko wani tunani a ransa, bai yi zaton zai tashi looking hale and hearty like nothing happened ba, for the first time a rayuwarsa gashi an masa abu da ya taba sa sosai har cikin ransa wanda ya kamata yayi weighing dinsa down but he slept over it and woke up feeling strengthen and lively like nothing, it look like magic to him don haka bai taba faruwa ba duk iya tsawon rayuwarsa, ya dan daga kai ya kalli Khaleesat da har bacci ya fara dauketa don daren jiya bai bar ta tayi bacci da wuri ba, they spent hours cuddling and snuggling each other don sai da suka yi wanka before sleeping, wurin baccin ma duk ya makalkaleta kamar zai bude ido ya ga babu ita.... Knocking kofar parlor aka yi, Khaleesat ta bude ido a hankali don baccinta bai yi nisa ba, sake knocking aka yi ta mike zaune, yace "I will check" Tace "A'a let me check" Sauka tayi daga kan gadon ta nufi kofa don hijab dinta yana jikinta, ya bi ta da kallo har ta fita, karasawa kofar parlon tayi tace "Waye?" Muryar Jay taji yace "Good morning" Ta bude kofar ta koma gefe without looking at him tace "Ina kwana" Yana kallonta yace "Lafiya lau, where is he?" Still not looking at him tace "Ya koma bacci bai tashi ba" Shi dai kallonta kawai yake ganin yanda take maganar kamar dole, dai dai sanda Ajay ya fito parlorn, ta daga kai ta wani kallesa, can ta tura baki ta jira Jay ya karasa shiga cikin parlon yana sake kallonta kawai tayi ficewarta zuwa kitchen, ita tsakaninta da Allah bata son ya hadu da kowa na cikin gidan a wannan moment din banda Mami sai ko Mai martaba, tun da Jay suka hada ido da Ajay ya sauke idonsa ya karasa kan kujera ya zauna yana juya wayarsa dake hannunsa, sosai yayi mamakin ganinsa kamar babu abinda ya faru sabanin yanda ya sansa, he was looking like nothing ever happened, Ajay ya zauna kan kujera yana kallonsa Calmly yace "Congratulations on ur new title, Allah ya taya riko" Jay bai kallesa ba for few seconds, sai kuma ya daga kai ya kallesa yace "That is ur title, and it still remains urs, na zo ne ka gaya min abinda ya hadaka da Walid kayi masa abinda kayi?" Ajay ya jingina da kujera yace "Nothing serious, na kuma amshi hukuncin Mai martaba wholeheartedly, so there is no need for any questioning Jay na kallonsa yace "You are not mad to beat Walid that way, sai dai ko shaye shaye ka fara, me yayi maka that warrant such merciless beating?" Kin cewa komai Ajay yayi kuma yaki kallonsa yana jin tambayar ma na sa xuciyarsa ya fara tafarfasa, ganin yaki cewa komai kuma babu alamar zai ce komai yasa Jay bai sake cewa komai a parlon ba, suna ta zaune har na fin minti biyar, Jay ya mike without looking at him ya fita daga parlon, duk da ya ga Khaleesat that is almost near the door zata shiga parlon hannunta rike da tray din Hot chocolate da cookies a gefe amma haka ya ja kofar ya kulle yana kallonta yace "Wato ke me miji sau biyu kina ce min yana bacci whereas idonsa biyu ko?" Bata san sanda tace "Ehh, since he is always made to look like the black sheep and unwanted person of the family, no one is even willing to consider or reason with him, no one is giving him a listening ears, no one cares about his feelings, ban san offense dinsa ba, thank God title dinsa kawai aka rabasa da shi not his life, Kilan he will now be free from everyone's hate henceforth...." Muryarta na rawa ta kare maganar cikin zafi, Kallonta kawai Jay yake babu ko kiftawa, can ya juya ya bar wajen, ta bude kofa tayi shigewarta parlor ta kulle, Bata ga Ajay a parking ba ta karasa bedroom ta gansa zaune gefen gado gaba daya mood dinsa ya canza, tana tafiya slowly ta karasa har kusa da shi ta ajiye tray din kan beside drawer tana kallonsa tace "Baka ci abinci Jiya da daddare ba, i made you some Hot chocolate" Ya kalli tray din shayin da cookies sai kuma ya daga idanuwansa ya kalleta sosai taji gabanta ya fadi kuma bata cire idonta a nasa ba sai shi ne ya sauke idonsa a hankali, ya kai hannu ya dau cup din shayin yace "Ba kazanta ciki dai" Murmushi tayi tace "Ba dai yawa ne... Ya dan bude ido yace "What?" Ta langwabe kai tace "To cup din ne kawai ban wanke ba ai, kuma bayan na hada shayin i wanted to taste if the sugar is okay, ban san da zafi ba shi ne ya kona min bakina, ni kuma na juye na bakin a ciki da sauri, that is just it" Bai san sanda yayi murmushi ba don ba karamin dariya ta basa ba, ita dai kallonsa kawai take don murmushin look cute on his face, iya dariya kawai ta taba ganin yayi sau biyu kuma irin dariyar mugunta na Boss, ranan da ta yanke hannunta a kitchen suna Maryland Ikcin tana apartment dinta together with him, sai kuma a hotel room da zata cijesa, tace "Ko a zubar kawai?" Ya ajiye cup din kan tray din yace "Zai fi dai" Ta mike zata kai hannu ta dauka tray din ya jawota ta fado jikinsa ta sakar masa kukan shagwaba.... Wajen karfe bakwai da rabi Mami ta zo bangaren, Ajay ya fita zuwa parlor ya zauna ya gaisheta don tana zaune parlon, Khaleesat kuma na zaune kan Carpet bayan ta gaisheta tun shigowarta, Mami na kallonsa ta amsa gaisuwarsa tace "How was ur night?" Yace "Alhamdulillah" Sosai tayi mamakin ganinsa kamar babu abinda ya faru sabanin yanda tayi tunanin zata samesa sanin hali, he looks bright, shiru Mami tayi, bayan dan lokaci tace "Junaid, ka gaya min me ya hadaka da Walid?" Ya sauke idonsa a hankali don har ransa baya son ana masa maganar Walid don hakan kara saka masa wani radadi yake a zuciya barin idan ya tuna yanda ya zo ya samesa har ya gama cire belt, ya girgiza kai calmly yace "Mami abinda ya faru kenan na gaya maki jiya, we had issues in the mosque a sanda mu ke karatu" Ita dai Khaleesat kanta na kasa, Mami sai kallon Ajay take kafin tace "To amma menene yasa kai baka iya kai zuciyarka nesa ba? Yanzu meye amfanin irin haka?" Ajay dai yayi shiru, Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya kiyaye, kun gaisa da Mai martaban ne?" Ajay ya girgiza kai kawai, Mami tace "Ka tafi ka gaishesa" A hankali Ajay yace "A'a zan bari har sanda zai huce, zai ga na kara disobeying din abinda yace idan na je wajensa yanxu, and I know he won't take it likely Mami tayi shiru don tasan gaskiya ya fada, tasan yanxu dai kawai sai dai ayi jiran zuwan Hajja ranan talata don tun jiya da daddare ta kirata bayan ta bar fadan sarki, Mikewa Mami tayi tana kallon Khaleesat tace "Kin basa breakfast ne?" Khaleesat tace "Shayi ya sha kawai Mami tace "To ki zo ki amsar masa abinci na girka yanxu saboda shi.... Khaleesat tace "To Mami" Kofa Mami ta nufa ta fita daga parlon. Aunty na zaune dakinta idonta ya kumbura don kuka, Hajiya Nafisah dake zaune dakin bayan Aunty ta kirata ta taho tun daga Kano tace "Don girman Allah ki dena wannan kukan fulani kar ki tado Migraine headache din ki kinsan baya maki da sauki sai anje asibiti" Cikin kuka Aunty tace "Ta yaya zan daina kuka Nafisah ace duk effort dina ya tashi a banza kenan ya tafi in vain, mulkin ma sai kara nisanta zuri'ata yake fisabilillahi, wai Jawwad sabon Yarima? Me yasa Sarki zai min haka duk baya son jinina, wallahi ban taba kawowa zai ba Jawwad Yarima ba bayan ga dan sa na cikinsa, kawai ya maida min Walid dan banza kamar ba dan gidan nan ba ya maida shi kamar ba shi ya haifesa ba rikonsa ake a gidan, dama ba Allah ke shirya yaro wanda ya so ba? Ai bamu fidda rana Walid zai nutsu ba wataran, duka duka nawa yake da har baza ayi masa uxuri ba? Kowa fa da irin yarintarsa, ni dama can wallahi Jawwad din nan a tsane yake a raina ganin yanda Sarki ke fifita shi kamar shi ne dan cikin nasa na asali, ko Junaid baya sawa a lamarinsa yanda yake sa Jawwad, to gashi yayi me gaba dayan yanxu wai ya ba Jawwad Yarima, ba gwara ma Junaid din ba sau dubu tunda ina jin kamshin sarautan kusa da mu Nafisah? Wallahi gwara Junaid yayi ta zama a Yariman da dai wannan abinda Sarki ya min, na ma fi tsanar Jawwad din akan Junaid duba da yanda Sarki yafi fifitasa, kawai saboda Yarimancin ne yasa na sa Junaid a gaba maimakon shi" Nafisah tace "Fulani ki tsaya ki saurareni, ba fa wani abu bane na tashin hankali, aiki ne kawai zai dawo mana sabo ba wani abu ba, amma yanda Sarki ke passing passing title din Yariman nan haka nan zai passo shi ya dawo kan Walid ki sha kurumin ki, me yasa har yau ba a ci galaba kan Junaid dari bisa dari ba?? Ba don ance yana da ibada cikin dare ba, to kawar da Jawwad har wani wahala zai mana mutumin da sai in yanxu ya hakura da bacci?? Balle ma da bakin ki kike gaya min uwar tasa ma ya juya mata baya sai yanda matarsa tayi da shi, kuma kika sa aka maki bincike kika ga ba banza ba ashe Maimuna aiki take ta zabgawa akan er ta ta mallakesa tunda an ga irin shegun dukiyoyin da Marigayi Sarki Ahmadu ya bar masa, ai sai dai in ke kika ce kar a kawar da shi ne baza ayi irin aikin ba Fulani" Aunty na huci tace "A kawar da shi kawai ko nawa zan bayar wallahi, yau in babu shi ai dole Walid za a ba Title din tunda babu ta yanda za ayi Dethroning Junaid sannan a sake cewa za a mayar da shi kamar wasan yara... Walid din dai za a nada daga karshe" Nafisah tayi wani dariya tace "To an gama hasken idaniyan sarki, in sha Allah ina komawa za a fara aiki, sai dai don Allah ki saki ranki ki nuna kin yi murna sosai, ki nuna gwara da aka kwace hannun Junaid dama Jawwad ne yafi cancanta ta yanda babu shegen da zai zarge ki a Masarautar nan" Aunty da har taji wani irin sanyi a ranta tace "In Allah ya yarda Nafisah, zuwa anjima zan je in ma uwarsa Allah ya sanya alkhairi faram faram, sannan in nuna mata takaicin da nake ta yi dukan da Junaid yayi ma Walid duk tunanina sarki zai sa Dogarai su rama masa amma sai naga akasin haka shi yasa raina ya sosu sosai wato ya doki banza kenan, ga karaya biyu a hannu, ga hakorinsa daya na girgidi ya kusa faduwa, ga targade kusan biyar a kafa, hatta kwankwasonsa yau da ya tashi ya kasa zama wallahi yana can a kwance, jikin duk yayi masa tsami baya iya motsin kirki" Nafisah tace "Yauwa, haka za ki yi mata kawai, su ma tsinannun yan uban dake gidan nan ki nuna masu kinyi farin cikin dethroning din Junaid ko ba komai Jawwad yafi cancanta don ya fi sa hankali, ko kuma duk sun watse?" Aunty tace "Ina fa har yanxu suna nan, duk ana jiran Hajja wai tana hanya ranan Talata, baki ji yanda take ta fada ba ita ma tayi bakin ciki da wannan abu da sarki yayi ma Junaid, sai ta zo mu ga me zata yi" Nafisah tace "To ita Maimuna ya tayi?" Cike da takaici Aunty tace "Tana ta murna ita ga er iska har da hamdala da karfı a parlon Sarki wato sarauta nasu ne yanxu..." Nafisah tace "Ki Kyaleta, za ta dawo su yi bakin ciki, ke dai kawai yanxu kiyi abinda nace yanda babu wanda zai zarge ki" Wani makirin murmushi kawai Aunty take tana goge hawayen idonta. HALYSAAH PAGE 142... Khaleesat ta kwace bakinta cikin gigicewa, letting out another loud scream of pain tana turasa da duk karfinta cikin kuka take cewa "Plsss it's hurtful, nace maka bazan iya ba wallahi, don Allah kayi hakuri" Da kyar ya fada gefenta yayi rub da ciki yana maida numfashi, ita dai kuka kawai take tana jan duvet tana rufe jikinta da ke rawa tana kallonsa, taga kawai ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, duk da azaban da take ji har a lokacin but she felt bad she couldn't bear the pain for him, tana jin sa yayi wanka a bandakin sannan ya fito ya fita parlor, ta hade kanta da gwiwa tana kuka a hankali, bayan kusan minti sha biyar ta jawo rigarta a hankali ta saka sannan ta sauka daga kan gadon tana tafiya da kyar ta shiga bandaki, ruwan zafi ta bude a pampo ta tara sannan ta sirka zata yi amfani da shi, after some minutes ta fito daga bandakin har sannan a hankali take tafiya ta zauna gefen gado hawaye na taruwa idonta, can dai ta mike ta daure ta fita zuwa parlon kwance ta samesa kan kujera, wutan parlon ma dim one ne a kunne don haka bata san ko idonsa biyu ba, walking slowly ta karasa har inda yake kwance ta durkusa tana kallonsa hawaye na sauka idonta, cikin sanyin murya tace "Don Allah kayi hakuri" Idonsa na lumshe calmly yace "Da me?" Ta kasa cewa komai tana shesshekan kuka, taji ya jawota jikinsa a hankali, ta kwanta saman faffadan kirjinsa tana jin bugun zuciyarsa, shi dai bai ce komai ba but deep down yana tunanin kawai taki sake jiki ne for reasons known to her, she didn't let him pass through even a bit duk ta takure jikinta, but even at that he is still a bit confuse at her tightness considering the fact that she is not a virgin, duk da ba wai ya sa mata force bane he was being very gentle with her, but as a Gynaecologist he knows of Vaginismus and with what just happened har ya fara diagnosing hakan as Secondary Vaginismus if at all she have no other plans kenan, secondary Vaginismus wani medical condition ne wanda an sadu da mace a baya but due to Abuse from partner or Sexual Trauma or even emotional factors shi ne take acquiring Matsalan where by vaginal muscles dinta will involuntarily or persistently contract, balle in her own case da bata son auren da aka mata, although sai in bata da wani nufin a ranta shine diagnoses dinsa zai yi count ya zama gaskiya.... murya can kasa taji yace "You have other plans right?" Ta daga kai da sauri ta kallesa, sai kuma ta girgiza masa kai hawaye na zuba idonta tace "Wallahi a'a" Bai sake cewa komai ba, taga ya tashi ya koma cikin dakin ita dai ta bi sa da kallo, babu abinda ya fado mata a rai sai zaman da tayi gidan Abdul da kalubalen da suka dinga samu exactly yanda wannan ya faru yanxu, nan kuma taji hankalinta ya tashi sosai, could it be that something is wrong with her ko kuma kawai tsoro ne ya shigeta da yawa, tafi minti ashirin tana duke a parlon cıkın tashin hankali, ta ma rasa wani tunanin zata yi, daga karshe ta dake ta tashi ta bi bayansa zuwa cikin dakin, ta gansa kwance kan gado ya juya baya, tana tafiya a hankali ta karasa ta hau kan gadon ta zauna kusa da shi amma ta rasa abinda zata ce, after a while ta juya a hankali ta tafi edge din gadon ta kwanta, tana goge hawayen idonta she is feeling bad har cikin ranta, ji tayi ya dawo bayanta ya jawota jikinsa ya rungumeta ta baya yana cusa fuskarsa cikin lallausan gashinta at the same time yana shafa cikinta, ta juya a hankali ta kwanta kan kirjinsa ta lumshe ido tana kara shigewa jikinsa, a haka ta fara bacci tana jin warmth din jikinsa, shi kam ya kasa bacci saboda arousal da yake ji da yafi na ko yaushe, ya saka hannu cikin rigar baccinta yana caressing dinta, a hankali ta bude ido, ya hade forehead dinta da nasa murya can kasa yace "Il... i can't sleep" ta lumshe ido ta daura lips dinta kan nasa tana shafa kirjinsa a hankali, kissing dinta ya fara yi passionately, she tried her best to give him satisfaction by flowing with him duk da bai kara attempting kusantar ta ba, but they romanced each other intensely.... Da asuba Khaleesat ce ta fara farkawa daga bacci, har sannan kuma tana jikinsa yaki saketa, they slept all through the night clinging to each other, ta zame jikinta a hankali sannan ta kunna wutan dakin ta jawo duvet tana rufe jikinta ta juya tana kallonsa, tun daga thick eyebrow dinsa zuwa dogon hancinsa down to his lips that got all the qualities, kallonsa kawai take ko kiftawa babu, a hankali taga ya bude idonsa suka yi ido hudu, da sauri ta boye fuskarta a Pillow tana murmushin kunya, tun bata kai ga boye fuskar ba ya rigata juya kansa, bai ma san dalilin da yasa shi saurin juya kai ba bayan sun hada ido da ita, can ya mike zaune, still not looking at her yana shafa kansa a hankali, bayan ya gama addu'an tashi daga bacci ya mike ya nufi bandaki, a nan bedroom din yayi sallah tana bin sa jam'i a baya, bayan sun idar shi dai bai iya ya kalleta ba, ya koma jikin gado yana addu'o'in sa, ita ma dai kanta na kasa taki dagowa tana supplications dinta a zuciya, after almost 10 mins ta dan daga kai a hankali ta saci kallonsa dai dai sanda shi ma ya dan kalleta suka hada ido, tayi saurin rufe fuskarta da gado a hankali tace "Ina kwana" shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, ta samu ta tashi daga wajen ba tare da ta yarda ta kallesa ba ta tafi karshen gado ta kwanta ta lumshe idonta ta juya masa baya, sauke idonsa yayi kasa a hankali, bai taba tunanin zai iya bacci daren jiya bayan abinda ya faru ba, baccin ma wai me nauyi kuma babu ko wani tunani a ransa, bai yi zaton zai tashi looking hale and hearty like nothing happened ba, for the first time a rayuwarsa gashi an masa abu da ya taba sa sosai har cikin ransa wanda ya kamata yayi weighing dinsa down but he slept over it and woke up feeling strengthen and lively like nothing, it look like magic to him don haka bai taba faruwa ba duk iya tsawon rayuwarsa, ya dan daga kai ya kalli Khaleesat da har bacci ya fara dauketa don daren jiya bai bar ta tayi bacci da wuri ba, they spent hours cuddling and snuggling each other don sai da suka yi wanka before sleeping, wurin baccin ma duk ya makalkaleta kamar zai bude ido ya ga babu ita.... Knocking kofar parlor aka yi, Khaleesat ta bude ido a hankali don baccinta bai yi nisa ba, sake knocking aka yi ta mike zaune, yace "I will check" Tace "A'a let me check" Sauka tayi daga kan gadon ta nufi kofa don hijab dinta yana jikinta, ya bi ta da kallo har ta fita, karasawa kofar parlon tayi tace "Waye?" Muryar Jay taji yace "Good morning" Ta bude kofar ta koma gefe without looking at him tace "Ina kwana" Yana kallonta yace "Lafiya lau, where is he?" Still not looking at him tace "Ya koma bacci bai tashi ba" Shi dai kallonta kawai yake ganin yanda take maganar kamar dole, dai dai sanda Ajay ya fito parlorn, ta daga kai ta wani kallesa, can ta tura baki ta jira Jay ya karasa shiga cikin parlon yana sake kallonta kawai tayi ficewarta zuwa kitchen, ita tsakaninta da Allah bata son ya hadu da kowa na cikin gidan a wannan moment din banda Mami sai ko Mai martaba, tun da Jay suka hada ido da Ajay ya sauke idonsa ya karasa kan kujera ya zauna yana juya wayarsa dake hannunsa, sosai yayi mamakin ganinsa kamar babu abinda ya faru sabanin yanda ya sansa, he was looking like nothing ever happened, Ajay ya zauna kan kujera yana kallonsa Calmly yace "Congratulations on ur new title, Allah ya taya riko" Jay bai kallesa ba for few seconds, sai kuma ya daga kai ya kallesa yace "That is ur title, and it still remains urs, na zo ne ka gaya min abinda ya hadaka da Walid kayi masa abinda kayi?" Ajay ya jingina da kujera yace "Nothing serious, na kuma amshi hukuncin Mai martaba wholeheartedly, so there is no need for any questioning Jay na kallonsa yace "You are not mad to beat Walid that way, sai dai ko shaye shaye ka fara, me yayi maka that warrant such merciless beating?" Kin cewa komai Ajay yayi kuma yaki kallonsa yana jin tambayar ma na sa xuciyarsa ya fara tafarfasa, ganin yaki cewa komai kuma babu alamar zai ce komai yasa Jay bai sake cewa komai a parlon ba, suna ta zaune har na fin minti biyar, Jay ya mike without looking at him ya fita daga parlon, duk da ya ga Khaleesat that is almost near the door zata shiga parlon hannunta rike da tray din Hot chocolate da cookies a gefe amma haka ya ja kofar ya kulle yana kallonta yace "Wato ke me miji sau biyu kina ce min yana bacci whereas idonsa biyu ko?" Bata san sanda tace "Ehh, since he is always made to look like the black sheep and unwanted person of the family, no one is even willing to consider or reason with him, no one is giving him a listening ears, no one cares about his feelings, ban san offense dinsa ba, thank God title dinsa kawai aka rabasa da shi not his life, Kilan he will now be free from everyone's hate henceforth...." Muryarta na rawa ta kare maganar cikin zafi, Kallonta kawai Jay yake babu ko kiftawa, can ya juya ya bar wajen, ta bude kofa tayi shigewarta parlor ta kulle, Bata ga Ajay a parking ba ta karasa bedroom ta gansa zaune gefen gado gaba daya mood dinsa ya canza, tana tafiya slowly ta karasa har kusa da shi ta ajiye tray din kan beside drawer tana kallonsa tace "Baka ci abinci Jiya da daddare ba, i made you some Hot chocolate" Ya kalli tray din shayin da cookies sai kuma ya daga idanuwansa ya kalleta sosai taji gabanta ya fadi kuma bata cire idonta a nasa ba sai shi ne ya sauke idonsa a hankali, ya kai hannu ya dau cup din shayin yace "Ba kazanta ciki dai" Murmushi tayi tace "Ba dai yawa ne... Ya dan bude ido yace "What?" Ta langwabe kai tace "To cup din ne kawai ban wanke ba ai, kuma bayan na hada shayin i wanted to taste if the sugar is okay, ban san da zafi ba shi ne ya kona min bakina, ni kuma na juye na bakin a ciki da sauri, that is just it" Bai san sanda yayi murmushi ba don ba karamin dariya ta basa ba, ita dai kallonsa kawai take don murmushin look cute on his face, iya dariya kawai ta taba ganin yayi sau biyu kuma irin dariyar mugunta na Boss, ranan da ta yanke hannunta a kitchen suna Maryland Ikcin tana apartment dinta together with him, sai kuma a hotel room da zata cijesa, tace "Ko a zubar kawai?" Ya ajiye cup din kan tray din yace "Zai fi dai" Ta mike zata kai hannu ta dauka tray din ya jawota ta fado jikinsa ta sakar masa kukan shagwaba.... Wajen karfe bakwai da rabi Mami ta zo bangaren, Ajay ya fita zuwa parlor ya zauna ya gaisheta don tana zaune parlon, Khaleesat kuma na zaune kan Carpet bayan ta gaisheta tun shigowarta, Mami na kallonsa ta amsa gaisuwarsa tace "How was ur night?" Yace "Alhamdulillah" Sosai tayi mamakin ganinsa kamar babu abinda ya faru sabanin yanda tayi tunanin zata samesa sanin hali, he looks bright, shiru Mami tayi, bayan dan lokaci tace "Junaid, ka gaya min me ya hadaka da Walid?" Ya sauke idonsa a hankali don har ransa baya son ana masa maganar Walid don hakan kara saka masa wani radadi yake a zuciya barin idan ya tuna yanda ya zo ya samesa har ya gama cire belt, ya girgiza kai calmly yace "Mami abinda ya faru kenan na gaya maki jiya, we had issues in the mosque a sanda mu ke karatu" Ita dai Khaleesat kanta na kasa, Mami sai kallon Ajay take kafin tace "To amma menene yasa kai baka iya kai zuciyarka nesa ba? Yanzu meye amfanin irin haka?" Ajay dai yayi shiru, Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya kiyaye, kun gaisa da Mai martaban ne?" Ajay ya girgiza kai kawai, Mami tace "Ka tafi ka gaishesa" A hankali Ajay yace "A'a zan bari har sanda zai huce, zai ga na kara disobeying din abinda yace idan na je wajensa yanxu, and I know he won't take it likely Mami tayi shiru don tasan gaskiya ya fada, tasan yanxu dai kawai sai dai ayi jiran zuwan Hajja ranan talata don tun jiya da daddare ta kirata bayan ta bar fadan sarki, Mikewa Mami tayi tana kallon Khaleesat tace "Kin basa breakfast ne?" Khaleesat tace "Shayi ya sha kawai Mami tace "To ki zo ki amsar masa abinci na girka yanxu saboda shi.... Khaleesat tace "To Mami" Kofa Mami ta nufa ta fita daga parlon. Aunty na zaune dakinta idonta ya kumbura don kuka, Hajiya Nafisah dake zaune dakin bayan Aunty ta kirata ta taho tun daga Kano tace "Don girman Allah ki dena wannan kukan fulani kar ki tado Migraine headache din ki kinsan baya maki da sauki sai anje asibiti" Cikin kuka Aunty tace "Ta yaya zan daina kuka Nafisah ace duk effort dina ya tashi a banza kenan ya tafi in vain, mulkin ma sai kara nisanta zuri'ata yake fisabilillahi, wai Jawwad sabon Yarima? Me yasa Sarki zai min haka duk baya son jinina, wallahi ban taba kawowa zai ba Jawwad Yarima ba bayan ga dan sa na cikinsa, kawai ya maida min Walid dan banza kamar ba dan gidan nan ba ya maida shi kamar ba shi ya haifesa ba rikonsa ake a gidan, dama ba Allah ke shirya yaro wanda ya so ba? Ai bamu fidda rana Walid zai nutsu ba wataran, duka duka nawa yake da har baza ayi masa uxuri ba? Kowa fa da irin yarintarsa, ni dama can wallahi Jawwad din nan a tsane yake a raina ganin yanda Sarki ke fifita shi kamar shi ne dan cikin nasa na asali, ko Junaid baya sawa a lamarinsa yanda yake sa Jawwad, to gashi yayi me gaba dayan yanxu wai ya ba Jawwad Yarima, ba gwara ma Junaid din ba sau dubu tunda ina jin kamshin sarautan kusa da mu Nafisah? Wallahi gwara Junaid yayi ta zama a Yariman da dai wannan abinda Sarki ya min, na ma fi tsanar Jawwad din akan Junaid duba da yanda Sarki yafi fifitasa, kawai saboda Yarimancin ne yasa na sa Junaid a gaba maimakon shi" Nafisah tace "Fulani ki tsaya ki saurareni, ba fa wani abu bane na tashin hankali, aiki ne kawai zai dawo mana sabo ba wani abu ba, amma yanda Sarki ke passing passing title din Yariman nan haka nan zai passo shi ya dawo kan Walid ki sha kurumin ki, me yasa har yau ba a ci galaba kan Junaid dari bisa dari ba?? Ba don ance yana da ibada cikin dare ba, to kawar da Jawwad har wani wahala zai mana mutumin da sai in yanxu ya hakura da bacci?? Balle ma da bakin ki kike gaya min uwar tasa ma ya juya mata baya sai yanda matarsa tayi da shi, kuma kika sa aka maki bincike kika ga ba banza ba ashe Maimuna aiki take ta zabgawa akan er ta ta mallakesa tunda an ga irin shegun dukiyoyin da Marigayi Sarki Ahmadu ya bar masa, ai sai dai in ke kika ce kar a kawar da shi ne baza ayi irin aikin ba Fulani" Aunty na huci tace "A kawar da shi kawai ko nawa zan bayar wallahi, yau in babu shi ai dole Walid za a ba Title din tunda babu ta yanda za ayi Dethroning Junaid sannan a sake cewa za a mayar da shi kamar wasan yara... Walid din dai za a nada daga karshe" Nafisah tayi wani dariya tace "To an gama hasken idaniyan sarki, in sha Allah ina komawa za a fara aiki, sai dai don Allah ki saki ranki ki nuna kin yi murna sosai, ki nuna gwara da aka kwace hannun Junaid dama Jawwad ne yafi cancanta ta yanda babu shegen da zai zarge ki a Masarautar nan" Aunty da har taji wani irin sanyi a ranta tace "In Allah ya yarda Nafisah, zuwa anjima zan je in ma uwarsa Allah ya sanya alkhairi faram faram, sannan in nuna mata takaicin da nake ta yi dukan da Junaid yayi ma Walid duk tunanina sarki zai sa Dogarai su rama masa amma sai naga akasin haka shi yasa raina ya sosu sosai wato ya doki banza kenan, ga karaya biyu a hannu, ga hakorinsa daya na girgidi ya kusa faduwa, ga targade kusan biyar a kafa, hatta kwankwasonsa yau da ya tashi ya kasa zama wallahi yana can a kwance, jikin duk yayi masa tsami baya iya motsin kirki" Nafisah tace "Yauwa, haka za ki yi mata kawai, su ma tsinannun yan uban dake gidan nan ki nuna masu kinyi farin cikin dethroning din Junaid ko ba komai Jawwad yafi cancanta don ya fi sa hankali, ko kuma duk sun watse?" Aunty tace "Ina fa har yanxu suna nan, duk ana jiran Hajja wai tana hanya ranan Talata, baki ji yanda take ta fada ba ita ma tayi bakin ciki da wannan abu da sarki yayi ma Junaid, sai ta zo mu ga me zata yi" Nafisah tace "To ita Maimuna ya tayi?" Cike da takaici Aunty tace "Tana ta murna ita ga er iska har da hamdala da karfı a parlon Sarki wato sarauta nasu ne yanxu..." Nafisah tace "Ki Kyaleta, za ta dawo su yi bakin ciki, ke dai kawai yanxu kiyi abinda nace yanda babu wanda zai zarge ki" Wani makirin murmushi kawai Aunty take tana goge hawayen idonta. HALYSAAH PAGE 143... Khaleesat na kitchen da yamma tana dafa Jollof rice ganin kamar shi ne favourite din Ajay ko bazai ci ba dai at least she cooked don tun daxu ya fita, Yakumbo babu yanda bata yi da ita ta kama mata girkin ba amma taki yarda, hakan yasa take ta tsaye kitchen din take mika mata duk abinda taga zata dauka, tun karfe uku Aiav va bar gidan bayan........ da hukuncin da Sarki ya dauka kan Junaid, don ita ma kana ganinta kasan tana cikin damuwa jikinta yayi sanyi tun da abun ya faru, duk sonta da bada labari yau dai ba um ba um um, sai khaleesat ce ma ke mata magana jifa jifa, wajen karfe biyar da rabi Khaleesat ta gama girkin da take yi Yakumbo ta fara goge goge kitchen din tana tidying ko ina, Khaleesat ta gama wanke hannunta da wash a sink jin kamar an bude kofar parlor ta goge hannunta da towel ta fito zuwa babban parlon, tsaye tayi with shock tana kallonsu, bata san sanda ta tafi da sauri ta rungumeta ba cike da mamaki tace "Sophiee" Safiyyah sai washe baki take har kunne, Ajay dai ya wuce ciki ya bar su a parlon, Khaleesat ta koma baya tana kare mata kallo as if still wanting to pure Safiyyah ce, cike da farin ciki tace "Baki ce zaki zo ba ai, baki ma ce min kin dawo Nigeria ba Sophie" Safiyyah ta rike haba tayi kasa da murya tace "Yau sai gani a Great Emirate din Bauchi na zo wajen kawata, abun kamar al'mara, duk wannan parlon gari guda naki ne ke kadai kawata??" Khaleesat tace "Ni dai me yasa baki ce min zaki zo ba" Safiyyah tace "Tun yaushe nake maki magana baki online na kira wayar ma a kashe" Sai a sannan Khaleesat ta tuna da wayarta, ita in ta shiga damuwa mance da wani abu take wai shi waya, kama hannun Safiyyah tayi...... panom Ajay, uama uaxu ta yyara uakin na ud turaren wuta ta kunna a ciki, Safiyyah ta dinga bin dakin da kallo tace "Maa sha Allah matar Yarim-" Khaleesat ta sauke kanta bata dai ce komai L bayan ta ajiye akwatin hannunta tace "Ya Mama da Baba fa?" Safiyyah tace "Da kyar in gay maki aka bar ni, a haka ma sai da na lallaba Y. musty ya saka baki, kin san har da shi da matars muka dawo, to shi ne fa aka bani kwana biyl kacal, kaya kala uku ma na dauko, na hau wata rubabbiyar mota sau uku tana lalacewa a hanya ke kya ce Lorry na hau, muna kusa shigowa Bauchi ta karasa macewa taki tashi kwata kwata in gaya, da mijin ki ya kira ya tambayi ko mun karaso nace masa ai motar ma tayi condemn gaba daya, in gaya maki shi ne fa ya taho a babban motarsa ya daukeni amma fa na sha jira, ashe ashe tafiyar kusan awa daya da wani abu yayi kafin ya iso inda motar ta mutu, sai da muka dau hanya naga daga uwa duniya shi ma ya taho daukata" Khaleesat dai sai murmushi take amma fa hankalinta yayi kan ta tafi ta duba Ajay da ya shiga daki, ta sauke ajiyar zuciya tace "To sannu da zuwa kawata, i am soo happy to see you wallahi, yanxu ki shiga kiyi wanka, idan ma zaki yi sallah duk kiyi, bari in je in hada maki abinci a kitchen" Safiyyah ta cire mayafin jikinta tace "Ohh shkkn duk sanda nake son ganinki sai dai in taho Bauchi kawata??" .......ta gansa ya kunna laptop dinsa yana operating, ta zauna gefen kujera tana kallonsa ta marair ice tace "Shi ne baka ce min Sophie na hanya ba: Ya dan kalleta yace "Au, wai ita ce dama" Ta hara sa duk da dariyan da ya bata, yana ci gaba da abi, la yake yace "Ni ma a bakin kofa muka hadu ai z shigo" Ta sauke idonta a hankali tace "I made some food...." Ya daga kai ya kalleta calmly yace "Yau kika koyi girkin?" Er dariya tayi tace "To ai a America ma nayi ka ci baka sani ba" Yana kallon dimples dinta a hankali yace "In ur dream" Ta zaro ido tace "Wallahi da gaske" Kallonta kawai yake, tace "Ranan da ni da Safiyyah muke PS5 game a apartment dina before our exams ai mun cinye maka abincin da ka dafa shi ne nayi sauri na dafa wani kafin ka dawo" He was just staring at her, can kawai ya dan yi murmushi bai ce komai ba ya ci gaba da abinda yake yayi a laptop dinsa, mikewa tayi ta fita zuwa kitchen taje ta zubo masa abincin ta kawo masa tana ajiyewa yace "Later" Shiru tayi tana Kallonsa, can ta sauke idonta tace "Ohk" Mikewa tayi ta dau tray din ta fita.... Wajen karfe takwas da rabi Khaleesat na tare da Safiyyah da ke shan fresh fruits ga tulin tsire a gefenta ta....... Kalonta tace to da kin tsaya kina wanı yanga wal baza ki daura ba, ba gashi nan waist din ki har ya cicciko ba, ai shi jigida amfaninsa kawai ya ciko da kai idan ka saka kaya ya zauna maka das das, baki ga yanda ya kara maki shape ba" Khaleesat kamar zata shareta sai kuma tace "To ni ai noise din da yake making ne bana so, ko titi mutum ya fit-mutum yasan ka sa jigida?" Safiyyah tace "Haba dai me zai kai ki titi kuma kamar gantalalliya kina matar manya, titi ai sai mu, kuma ni yanxu waye yasan da jigida a jikina tunda ba tsalle tsalle nake a titin ba" Khaleesat bata sake tankata ba ta ci gaba da gyaran kayanta, Safiyyah dake ta kula da cewar Khaleesat na cikin damuwa amma tana ta bovewa tace "Ni fa duk yanda za kiin pretending as if everything is okay ba yarda za ba don nasan halin ki Khaleesat" Khaleesat ayi murmushi kawai don dama jira take ta gama ciye ciyenta tayi mata maganganun dake cinta a rai, Khaleesat ta dawo kusa da ita ta zauna, a han' tace "Sophie tun da muka dawo gidan nan issues upon issues, kuma issues ba kananu ba" Safiyyah ta matsar da tsiren kusa da ita tace "What issue kawata?" Khaleesat ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Different type of issues, daya daga issues din yasa har aka sauke sa Yarima jiya da ..... Baam aaya tajı nawaye ya cıka idonta, satıyyan da hankalinta ya tashi tace "Na shiga uku ki gaya min don Allah, kar dai Ajay kike nufi?" Khaleesat ta gyada mata kai hawaye na sauka idonta, Safiyyah was shock and speechless ta dinga kallon Khaleesat babu ko kiftawa, a hankali ta dinga maimaita "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Bata sake cewa komai ba har na minti biyu a dakin don sosai labarin ya daketa, after a while tace "Khaleesat me ya faru haka? Kuma waye ya saukesa? Me yayi?" Khaleesat na goge idonta tace "It's not even worth speaking about it Sophie, Allah yasa hakan shi yafi masa alkhairi kawai" Sosai jikin Safiyyah yayi sanyi ba kadan ba and deep down her she felt happy ta yanda taga Khaleesat tayi showing genuine concern wato ta damu ba kadan ba da abinda aka yi ma mijinta, cike da takaici Safiyyah tace "Sai aka bama wa Yariman??" Khaleesat bata dago kanta ba tace "Ya Jawwad" Da wani expression Safiyyah tace "Ya Jawwad??? Kuma ya yarda ya amsa? Amma ci amana wallahi, ba gwara ya gudu a nemesa a rasa ba da dai ya yarda a nadasa yarima, title din cousin dinsa fa?? ai ana barin halal ko don kunya, da wani idon yake kallon Ajay yanxu a gidan nan? Gaskiya ban ji dadin wannan han abun ba har cikin Safiyyah tayi jimaminta sosai, bayan kusan minti biyar Safiyyah tace "Har naman ya fice min a rai wallahi, haba ta yaya za a cire Ajay Yarima it doesn't even make sense, wannan kuma rashin son zaman lafiya ne, bari ma in kwanta kawai da wannan takaicin dama na gaji ga kuma wannan labari mara dadi, duk yan gidanmu da yan unguwanmu na gama shelanta masu Kawata na auren Yarima me jiran Gado a Bauchi ana ta min murna wataran ni ce ta daman Sarauniyar Emirate din nan, title din ma ai yafi fitting Ajay" Khaleesat ta dan yi murmushi kawai bata ce komai ba, ganin da gaske Safiyyah kwanciya zata yi Khaleesat tace "And one more thing Safiyyah" Safiyyah tace "Meye kuma? Ai ni wannan bakin labarin ma kadai ya isheni ba sai kin kara min da wani ba kar ki sa in kasa bacci kuma, wallahi na dade ban ji abinda ya sosa min rai kamar wannan ba" Khaleesat tace "This is about me" a takaice Safiyyah tace "What about you?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "I am still a virgin Sophie" Safiyyah ta dinga kallonta kamar taga Alien, can ta koma ta zauna, ta kusa minti daya tana kallonta ita dai Khaleesat tayi shiru tana jiran Safiyyah ta gama processing, Safiyyah tayi karfin halin cewa "Ban gane ba Khaleesat?" Cikin natsuwa Khaleesat ta fara bata labarin da ta boye mata a rayuwar aurenta na abinda ya faru tsakaninta da Ajay daren jiya, duk bata yarda ta kalli cikin idon Safiyyah ba take bata wannan labarin, Safiyyah sai da taji tana jin zufa duk da AC dake kunne dakin, wayarta ta jawo tace "Umma zan ce ta turo min lambar Nenne ko Aunty Farida?" Khaleesat ta karbi wayar tace "A'a tukunna dai Sophie, mu bi komai a sannu tukun...." A fusace Safiyyah tace "Ban gane abi komai a sannu ba, kika sani ko wani abu uwarsa ta maki tunda ba son ki take ba? Ai wannan kawai Nenne zan kira ba maganar nuku nuku bane, kuma ba karamar magana bace" Khaleesat tace "Na sani amma dai hold on first zuwa gobe mu dan yi shawara cause I am still confuse....." Na manta ai kuma an wuce wajen babu wani maganar wait kilan ma a daren nan zata kira Nenne in ta samo number ta, wayar Safiyyah ya fara ringing Khaleesat ta mika mata ganin Ya Musty ke kiranta, Safiyyah na picking call din Khaleesat ta mike cikin dubara ta bude press din dakin ta dau kayan baccinta da hijab sannan ta tafi gaban madubi ta dau turarurrukan da zata dauka ta fita daga dakin, parlon Ajay ta shiga taga yana can cikin daki, ta ajiye kayan hannunta kan kujera sannan ta shiga bandakin dake parlon, bayan tayi wanka ta fito ta gama shafe shafenta har da Musk din da Mami ta bata tayi using sannan ta saka kayan baccinta ta dora hijab dinta har kasa a kai ta fita ta koma dakin... ido tace "Don Allah ki bar ni da abubuwan bakin cikin da suka dameni ki je sai da safe kawai" Khaleesat ta dan yi murmushi tace "Shikenan tunda baki son in kwanta a nan let me go to the next room" Safiyyah tace "Eh tafi next room" Khaleesat na fita wayar Safiyyah ya fara ringing ta dauka tana dubawa taga Aunty Farida ke kiranta alamar har ta kai ma Nenne wayar, mikewa tayi zaune ta daga kiran ta kai kunne tana amsa Sallaman da Nenne ta rafko. Khaleesat na komawa part din Ajay ta cire hijab dinta ta linke ta barsa kan kujera sannan ta shiga dakinsa ta samesa zaune gefen gado ya fito wanka yana goge sumarsa a hankali, ganin haka ta bude press dinsa ta dauko masa pajamas dinsa ta ajiye masa, sannan ta kalleshi tace da cewa na kawo maka fruits? Ya girgiza kai ba tare da yace komai ba, doka zata dauka towel din da ya ajiye ya kalli kugunta, ya dan daga rigar jikinta yana kallon waist dinta yace "Meye wannan?" Ta turo baki tace "Mami ce ta bani" Ya dawo da ita gabansa har sannan idonsa na kan jigidan ya fara sauke wandon baccin jikinta ta rike da sauri tace "Jigida ne faaa, baka san shi ba?" Ya daga ido ya kalleta, saurin rufe idonta tayi tana murmushi, taji ya kai lips dinsa kan waist din nata dai dai kasan cikinta, sai da ta koma baya da sauri don his lips were cold, kawai taga ya dauketa holding her by the waist ya kwantar da ita kan gado ya kashe wutan dakin yana kara laluban jigidan tana nokewa. ........ HALYSAAH PAGE 144... As usual haka Khaleesat ta sakankance Ajay ya dinga sarrafata da sabbin salon da ya rikitata saboda irin abubuwan da yake mata, shi kuwa jigidan jikinta ne ke kara birkita masa lissafi ya fice hayyacinsa gaba daya, sun dau lokaci me tsawo yana mata hot romance, lokaci daya ta dawo hankalinta after she felt a very intense pain, nan ta fara turasa a tsorace tana kwace kanta amma ya danneta da ka, bata san sanda ta kwala gigitattcen ba ga weight dinsa da ya sakar mata ya azaban da take ji na abinda yake yi bai fasa ba, ai ko yayi saurin rufe bakinta still struggling to get his way, sosai Khaleesat ta jigata da azaba kafin Ajay ya kyaleta amma fa sai bayan da ya samu relieve ya iya kyaleta, duk da yau din ma bai samu wuce hanyar ba but ya lura da improvement akan ranan farko da ya fara attempting da yaji kamar ma babu alamar hanyar, but yau sai yaji akasin haka don kuwa duk rokon da ta dinga yi masa tsabar baya ma hayyacinsa bai san tana yi ba sai da yaji alamar hanyar har ya samu nutsuwa a haka, kuka kawai take jikinta na rawa tana kokarin sauka daga kan gadon tana jin wani irin azaba down there ga wani mugun tsoronsa da ya shigeta, ya jaw jikinsa ya rungumeta ya lumshe ido y sauke numfashi, ta dinga turasa a tso tana cewa "Don Allah kayi hakuri, i w use the restroom please" shi dai bai saketa ba kuma bai ce mata komai ba sai sauke numfashi yake, haka ta dinga rera masa kuka jikinta na rawa cause she was still in pain don ji take kamar bai daina abinda yake ba saboda zafin da take ji, shi dai idonsa a lumshe suke yana jin kukan nata, after many minutes ta dena kukan tana sauke ajiyar zuciya, and he could feel how fast her heart was beating, bayan lokaci me tsawo yaji alamar ta fara bacci, ya daura lips dinsa kan gashinta yana kissing a hankali, and a wish immediately struck his heart, wish of virginity.... bude idonsa yayi jin wani abu ya tokari kirjinsa ba ya tuna wanda ya fara saninta a mace, and his mood immediately switched, daya kawai ya kauda tunanin a ransa gaba daya, after a while ya jawo wayarsa ya kunna Flash din ya koma yana parting legs dinta zai duba where exactly the issue is from, da sauri ta bude ido a tsorace tace "Na shiga uku..." Ganin abinda yake kokarin yi wato zai haska between her laps ta hade kafafuwanta da sauri cikin rikicewa ta dinga jawo duvet din kan gadon zata rufe jikinta muryarta na rawa tace "Don girman Allah kayi hakuri plsss" Ya kalleta calmly yace "Dubawa zan yi kawai, nothing more" Ita dai sai kokarin rufe duk jikinta take da duvet, ga kunyan kar ya ga tsaraicinta cikin haske ga tsoro don har sannan jikinta bai daina rawa ha, tana girgiza kai tace "Ni bana so plsss kashe fitilar ya ajiye wayar, ta koma tavi lamo kan gado zuciyarta na bugawa, some minutes taga ya shiga bandaki har lokacin mood dinsa babu kyau kawai daga tunanin da yayi na wanda ya fara saninta, ta mike zaune ta jawo kayanta dake gefe ta fara sakawa da sauri zata fita daga dakin, amma tana sauka daga kan gadon ta taka kafarta taji zafi har laps dinta, haka nan tana tafiya a hankali ta fice daga dakin ta shiga bathroom din dake parlonsa tana duba jikinta, ta ma yi zaton jini zata gani sai kuma taga ba shi bane, ta yagi tissue tana goge jikinta, ta tara ruwan zafi hawaye cike idonta, a fusace ta cire jigidan waist dinta ta jefar a sink din bandakin, bayan Ajay ya fito wanka ya kunna wutan da yaga bata kan gadon, shiryawa yayi lokacin bai da walwala ya saka paja dinsa sannan ya cire bedsheet din Ra gadon ya canza wani, duvet ma ya dauko sabo, ya fita parlor bai ganta parlor din ba, zuwa parlor tana duba Breakfast din da aka kawo, ba a dau lokaci ba sai ga ta da Irish da kwai da plantain da cup din shayi da farfesu duk a tray, daga gefe kuma ga bread da ta kinkimo, sai wainar shinkafa da miya, bayan ta ajiye ta zauna ta fara ci ta kalli Khaleesat dake saka kaya tace "Ke banda abun ki maimakon ki zauna can bangaren mijinki yayi petting dinki yanda ya kamata shi ne zaki wani zo min nan, to in maki me?" Khaleesat tayi kamar bata san da ita take ba, amma fa duk ta tsargu kar dai Safiyyah ta gane wajen Ajay ta tafi daren jiya, tana gama shiryawa Ajay yayi sallama yayi knocking kofar dak da sauri Safiyyah ta boye uban break din da ta jido sannan ta dawo ta zar tana amsa sallaman sa, bude kofar da yayi Safiyyah na dan sunkuyar da kai tana washe baki tace "Ina kwana Yaya". Ajay" Yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Zata kai ki wajen Mom din Jawwad ku gaisheta...." Safiyyah tace "Toh yanxu zan shirya" Juyawa yayi ya bar bakin kofar bayan ya dan kalli Khaleesat da taki kallonsa, Safiyyah tsabar zumudin taje taga uwar Jay ko breakfast din bata yi ba ta tafi tayi wanka da sauri ta fito ta saka kaya ta feshe turare ta yafa mayafi tana kallon Khaleesat tace "Mu je, na shirya" Khaleesat tace "To breakfast din fa?" Safiyyah tace "Mu je dai in na dawo zan yi" A tare suka fita daga parlon Safiyyah na kallon Khaleesat ganin yanda tayi kyau don dama kawartata in ta so dai iya dressing ba kamar ba a Mari taso ba, suna fita Main parlor Khaler tace ma Safiyyah tana zuwa ta da abu, parlon Ajay ta bude slowly tana leka ciki taga bai taba breakfast din da ta ajiye a ba, shiga parlon tayi tana tafi kali ta bude kofar bedroom dinsa ta shiga ta kulle, bacci ta tarar da Safiyyah take yi saman gado, ta karasa cikin dakin ta kwanta kan darduman dake shimfide, a haka bacci ya dauketa... Sai ji tayi Safiyyah na tashin ta wajen karfe bakwai da rabi, ta mike zaune tana murza ido, Safiyyah tace "Meye na kwanciya a kasa kuma? Yaushe kika shigo nan?" Khaleesat ta mike tsaye jin Sallaman Yakumbo, kofa ta nufa har ta mance ciwon da take ji in tana tafiya, sai da ta dan yi jim sai kuma ta ci gaba da tafiya slowly, Safiyyah dai ta bi ta da kallo, a ranta kuwa ta fara addu'an Allah ya sa abinda take tunani ne ya faru cause sarai taji ihun da Khaleesat ta kwala jiya don bat bacci ba lokacin, to in abinda take tunam ne ya za ayi da Nenne da tace zata k hanyar Bauchi ana idar da sallan asusa, Safiyyah ta jawo wayarta da sauri ta kira Layin Nenne, yana fara ringing ta daga tace "Salamu alekum" Safiyyah ta gaida Nenne, Nenne tace "Safiyah ce?" Safiyyah tace "Eh ni ce Nenne" Nenne tace "Ai gamu nan dab da shigowa Bauchin yanxu haka" Safiyyah tace "Ikon Allah ke da wa Nenne?" Nenne tace "Ni da Noor, na sa an kira Murja tayi maza ta tsaftace mana dakinta kafin mu karasa, kuma ta mana girki" Safiyyah tace "To shikenan Nenne, zan kira idan kun karaso" Nenne tace "To Allah ya maki albarka er nan, ina naga ta zama, kuma kar ki kuskura ki ce masu na shigo garin sai na gama abinda ya kawo ni zuwa gobe" Safiyyah tace "In sha A Nenne" A haka Safiyyah ta katse wa ta ajiye, bayan Khaleesat ta gaisa Yakumbo da ta shigo da ma'aikatan suka kawo masu breakfast ta dibar ma Ajay duk da haushinsa da take ji ta dora masa kan tray zata je ta ajiye masa a parlor in ya gani ya dauka, tana bude kofar dai dai sanda yake fitowa daga dakinsa, taki yarda ta kallesa ta ajiye tray din hannunta da sauri zata fita yayi hanzarin rikota, ta samu ta kwace kanta ta gudu ta fita daga parlon ta shige dakin da Safiyyah take tana turo baki, zaunawa tayi gefen gado tayi shiru don har ta tsorata, Safiyyah dai sai kallonta take, ganin kallon da Safiyyah take mata tace "Ga breakfast can parlor ki je ki dau abinda kike so ki ci don varieties ne..." Safiyyah tace "Ohh da kaina ma zanyi serving abinda zan ci babu ko k Khaleesat ta tabe baki tace "Ai ke bakuwa bace" Mikewa tayi ta bude p ta ciro kayan da zata sa don wanka take son shiga tayi, har Khaleesat ta fito wanka Safiyyah bata je ta debi breakfast din ba, cikin shiryawa Safiyyah ta saki "Ina jigidar?" Khaleesat dake shafa mai tace "Wani shegen Jigida" Sosai ta ba Safiyyah dariya amma ta hadiye tace "Ban gane shegen Jigida ba?" Khaleesat tace "Ke ban so... na cire, in kina so sai in baki ki tafi da shi" Safiyyah tace "Tabdi, ko dai tsinkewa yayi dai?" Khaleesat ta wani kalleta tace "Ban gane tsinkewa yayi ba" Dariya Safiyyah tayi tace "Atohh na sani? Daga tambaya, ai yakan tsinke at night" Banza Khaleesat tayi mata ta ci gaba da shafa cream dinta, nan Safiyyah taji zuciyarta ya raya mata cewar abu ya kankama tsakanin kawarta da Ajay, to yanxu ya zata yi da Nenne da tak hanya tun da asubar fari, kar fa Nenne ta tsigaleta a garin mutane gashi Ner tace mata kar ma ta gaya ma Khaleesat din tana zuwa, mikewa Safiyyah tayi ta fita zuwa parlor tana duba Breakfast din da kawo, ciki taga bai taba breakfast din da ta ajiye masa ba, shiga parlon tayi tana tafiya a hankali ta bude kofar bedroom dinsa tana leka ciki ta gansa zaune kan kujeran dakin yana danna wayarsa, kin shiga dakin tayi ta sauke kanta a hankali tace "Baka yi breakfast din ba" Without looking at her yace "An bani ne?" Ta wani kallesa tace "To ba gashi a parlor ba" Still not looking at her yace "Ban gani ba" Bude kofar tayi tana nuna masa inda Tray din ke ajiye, yace "I can't see it" Ta tura baki ta juya ta bar bakin kofar, fita zata yi daga parlon amma ta kasa, after some seconds ta juya ta dau tray din ta nufi Bedroom din n da shi, tana shiga ta dan saci Kallonsa karasa can ciki ta ajiye tray din kan Ca kafin ta dago taga ya mike, hayewa saman king size bed din nasa tayi da sauri ta koma can daya bangaren ta sauka kamar zata yi kuka tace "Ni wallahi bana son irin haka" Duk da dariyar da ta basa yaki yi kawai ya dau laptop dinsa kamar dama shi ya mike ya dauka, ganin bai sake kallon inda take ba sai ma bude laptop dinsa da yayi, ta fara tafiya a hankali zata gudu daga dakin, still yayi kamar bai san abinda take ba, sai da yaga ta kusa kofa bayan ta wucesa a guje sannan yayi hanzarin cafkota, ta durkusa da sauri ta marairaice tace "Wayyo na shiga uku, meyasa kake haka" Dagota yayi duk da she is backing him don ta baya ya kamota ya jawota jikinsa ya rungume, murya can kasa yace "Bed dina kika taka kinga new bedsheet a kai?" Kamar zat kuka tace "Plsss kayi hakuri" ta zaro jin inda yake kai hannunsa cikin rax murya tace "Don Allah ka kyaleni Sop na jirana a parlor za mu je wajen Mami faa" Juyowa da ita yayi yana kallonta, tayi in rufe fuskarta saman kirjinsa tace jin hannunsa saman waist dinta bayan ya dage doguwar rigar jikinta, ya dago kanta murya can kasa yace "Why did you remove the bead?" Kamar zata yi kuka taki yarda su hada ido tace "Tsinkewa yayi" a hankali yace "A ina ake siyarwa?" Ta turo baki tace "Nima ban sani ba" Kallon bakin kawai yake, can yace "In kin je yanxu ki ce Mami ta baki wani" yana fadin haka ya hade bakinsa da nata ya fara kissing dinta passionately hannunsa a waist dinta yana caressing, nan da nan taji kafafuwanta sun kasa ci gaba da daukarta kuma ta kasa hanasa, lokaci daya taji yayi unzipping din gown din jikinta letting the gown fall do barrier din da ya rufe chest dinta ma ciresa, kawai sai jin su tayi samang yana smooching dinta, ya dau lokaci yana kissing dinta before slowly coming down her chest yana kallo, gaba daya Khaleesat ta mance da wani tsoro haka nan ta bari ya lulata zuwa wani world din yayi yanda ya so da ita cause he romanced her deeply daga karshe ya kankameta jikinsa yana shafa gashinta da ya cire ribbon dinsa tuntuni, that was when she realized he off his wears too jinta a bare body dinsa, rufe fuskarta tayi kan chest dinta tana kara shiga jikinsa, a haka bacci ya dauketa.... A hankali Khaleesat ta bude idonta after almost an hour, ta gansa tsaye gaban mirror din dakin ya gama shiryawa yana sa wrist watch dinsa, gaba daya kamshin turarensa ya cika dakin, suna hada ta madubin ta rufe fuskarta da saun duvet tana jin wani irin kunyansa, ba ya gama abinda yake without looking her yace "I am resuming work today...." Ta kara bude ido a hankali tana kallonsa, ya dau wayarsa da makullin mota ya fita daga dakin, a hankali ta sauka daga kan gadon ta shiga bandakinsa babu komai jikinta, sai bayan da ta fito wanka ta tuna Safiyyah da ta bari a parlor, zaro ido tayi tana kallon agogo da sauri taga karfe goma, cikin hanzari ta maida kayanta da ya ajiye mata kan kujera ta dau veil dinta ta fita daga dakin da sauri, tana fita Main parlor ta tarar da Safiyyah zaune ta rafka uban tagumi har sannan Mayafin data yafa a jikinta bata cire ba. HALYSAAH PAGE 145... Khaleesat ta sauke idonta ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, ji take kamar kasa ya bude ta shige kawai, kwata kwata taki yarda su hada ide da Safiyyah, nan ta fara tunanin abinda zata ce mata, sai kuma tace "Maimakon ki kira ni Sophie, i slept off in his parlor ina jira ya bude kofar dakinsa in dau abinda zan dauka, kuma da na tashi yanxu sai naga kofar dakin a bude... Ko dai ya fita ne??" Bata jira cewar Safiyyah ba ta nufi kofar fita daga parlon tace "Ki taso mu je wajen Mamin mu gaisheta" Safiyyah ta cire mayafin jikinta a takaice tace "Ban zuwa, tafi ki ci gaba da baccin ki, nima baccin zan yi kawai" Sai a sannan Khaleesat ta juya ta kalleta suka hada ido, taga yanda Safiyyah ta cika saura kiris ta fashe, Khaleesat bata san sanda ta kwashe da dariya ba ta dawo parlon tace "Ke bacci fa nayi da gaske, baki ga idona ba, wallahi Allah bacci nayi" Safiyyah tace "Eh ai dole kiyi bacci kin je kin amshi sleeping pills a inda ya kamata, ai in kika kara ganin shegun kafafuwana a inda kike kiyi min fiye da haka, ni zaki walakanta ki shige dakin miji ki shanya ni parior for almost 2 hours kamar gantalalliya ina raba ido, ina lefin ki leko kice min ba yanxu zaki fito ba, mijin da ake ta mana iyayin ba a so ana koke koke ana an tsanesa har ba a son zama gida day shi...." Khaleesat ta wani harareta da sauri tace "Ji sharri yaushe nayi haka? Ni dai ban taba cewa haka ba, ai kema kinsan muna shiri da shi right from time he is not my enemy, kilan dai lokacin Abdul kike nufi, ni dai ki taso mu tafi" Tana fadin haka ta kara nufar kofa ta fita, Safiyyah ta bude baki ta bi ta da kallon mamaki, dariya sosai Khaleesat ta bata, wato har ta mance iskancin da ta dinga laftawa a Maryland akan bata son Ajay, eh lallai Ajay ya cika aiki dole Khaleesat ta mance duk cika bakin da ta dinga yi a America, Safiyyah ta girgiza kai tana murmushi, but deep down she is happy yanda taga kawarta ta folla ma Ajay lokaci daya kamar ba ita ba, even daga labarin da ta bata jiya na abinda aka yi masa a masarautar she could see the pain she was wearing on her face and even the pain in her voice gashi har da hawayenta, dama can tana sonsa ita ce bata gano hakan ba saboda taki kwantar da hankalinta tana ta hauka, amma fa ba don wajen Uwar Yaya Housemate za aje ba da babu abinda z Safiyyah ta bita don babu wanda ya taba wannan azababben walakancin da Khaleesat tayi mata sai Surayyah, ita ma haka take ta janye miji su shige daki a bar ta a gantale, barin in ta ganta zaune parlor da Ya Mustyn suna hira, abinda ya kara shock din Safiyyah yanda gogan ya zo wucewa yayi pretending bai ma san tana parlon ba cause he wasn't expecting to see her there, har ya fita ya kulle kofa kamar bai ganta ba, ai ko gobe da sassafe zata tattara dan akwatinta ta karasa Gombe wajen Cousin sister dinta duk da ba shiri suke ba, don in ta ci gaba da zama a gidan nan bata san wani walakancin zata kara fuskanta ba tunda yanzu suke honeymoon dinsu, kwafa tayi ta yafa mayafinta ta mike ta bi bayan Khaleesat, tsabar Khaleesat ta raina mata hankalli haka ta dinga jan ta da hira kamar babu abinda ya faru har suka isa part din Mami, Khaleesat ta bude kofar a hankali ta shiga cikin parlon da sallama Safiyyah na biye da ita, Jay na zaune parlon ya jinginar da kansa da kujera idonsa a lumshe, Khaleesat tayi masa kallo daya ta karasa ta zauna kan. kujera, Safiyyah saura kadan ta tuntsire da darlya ganin ashe har yanxu yana bacci a duk inda ya samu, ita ma ta zauna kan kujera, after some seconds Khaleesat ta mike ta tafi hanyar dakin Mami, tsaye tayi bakin kofa tayi sallama, Mami ta daga ciki, bata shiga ba har sai da Mami tas shigo sannan ta shiga dakin, ta karasa har gun Mami da ta mike zaune daga kwancen da take, ta duka kasa ta gaisheta Mami ta amsa tace "Kun tashi lafiya?" Khaleesat tace "Alhamdulillah, ya karfin jiki Mami?" Mami tace "Na ji sauki" Shiru Khaleesat tayi, Mami tace "Junaid ya tafi aiki ko?" Khaleesat ta gyada kai tace "Eh ya tafi daxu" Mami tace "To in dai baya nan ki dena zama can bangaren ke kadai, ki dinga dawowa nan, ko kuma Yakumbo ta koma can bangaren naki ta zauna da ke har sanda zai dawo" Khaleesat ta sauke kanta kasa a hankall tace "To in sha Allah Mami, dama tare muke da kawata ta zo zata gaisheki...." Mami tace "Kawarki daga Kano?" Khaleesat tace "Eh, tare muka yi karatu a Baltimore da ita, Coursemate dita ce" Mami tace "To maa sha Allah, bari in fito" Khaleesat tace "Toh Mami" Daga haka ta mike ta fita daga dakin ta koma parlor, dai dai sanda Jay ya bude idonsa a hankali, yana ganin Khaleesat ya gyara zamansa ita kuwa taki kallon inda yake ya bi ta da kallon gefen ido, ta tafi ta zauna kan kujera abun ta still not looking at his direction, Safiyyah dake washe baki ganin ya tashi tace "Ina kwana Yaya Housemate" Juyawa yayi da sauri zuwa side din kujeran dake gefen wanda yake zaune, ya dan bude ido yace "Ohh Safiyyah" Tana murmushi tace "Ai mun kana ta bacci abun ka" Da sauri yace "Ala bacci nake ba, i was just meditating" Dariya Safiyyah tayi tace "Saura kadan fa kayi minshari" Murmushi yayi yace "Na ji shigowar ku fa Safiyyah, kawai dai ban gama abinda nake yi bane shi yasa ban bude ido ba, zuwa Bauchi babu announcement?" Safiyyah tace "A'a ni da kayi blocking ta WhatsApp ta ina zan gaya maka, na dena ganin status dinka kwata kwata dama in an maka magana ba reply kake ba in ma an kiraka baka picking, nace to kilan ka goge number ta ne" Yayi er dariya yace "C'mon Safiyyah ta yaya zan goge numberki, i have ur number mana...." Wayarsa ya dauka ya bude ya shiga contact ya nemo number ta yana nuna mata screen din wayar yace "Isn't it?" Ta mike ta tafi zata amshi wayar aka bude kofar parlon sai ga Hadiyah ta shigo cikin shiga ta alfarma ta sha gwala-gwalai, tun da aka ce title din Yarima ya zama na Jay yanxu ta fara ire iren shigar nan ita matar Yarima me jiran Gado, kallo daya Khaleesat tayi mata ta dauke kai, Safiyyah ma ta kalleta sannan ta maida dubanta kan Jay ta amshi wayar hannunsa tace "Ai kuwa ga number na nan, kilan network ne Jay dai yayi shiru bai ce komal ba may be because of Hadiyah, Hadiyah dake ta kallon Safiyyah babu ko kiftawa tana karasowa cikin parlon cikin wani expression tace "Ke wacece?" Safiyyah ta juva ta kalleta, Mami ce ta fito daga parlon, wa yasa Hadiyah ta fasa sauran maganganun Care makale bakinta ta fixge wayar Jay dake hannun Safiyyah, tana kallon Jay fuska daura tace "Ка tashi mu je, Ummi na son zata yi maka magana tun daxu" Jay ya sauke idonsa sai kuma ya mike, Mami dai kallonsu kawai take, Hadiyah ta tasa keyarsa fuska murtuke suka fita daga parion, rabonta da parlon Mami tun ranan da Mami ta koreta da ta nemi Khaleesat da fada, kuma tun ranan rabon da ta gaida Mami a gidan, yanxun ma taki yarda ta kalli inda Mamin ke tsaye ta tisa keyar Jay suka bar parlon, Mami ta karaso ta zauna kan kujera, saboda bakin ciki yasa tayi tafiyarta daki ta kwanta don tana parlon Jay ya shigo ya sameta tun dagal gaisuwar da yayi mata ta amsa a takaice bai sake ce mata komai ba sai ma ya bige da bacci abun sa a parlon, shine ta tafi dakinta cike da damuwa, Safiyyah ta zauna kan Carpet tana kallon Mami ta gaidata da fara'a, Mami ta amsa da murmushi tace "Sannu da zuwa yan mata" Safiyyah tace "Fatan mun same ku lafiya Mami" Mami tace "Alhamdulillah, ya hanya?" Safiyyah tace "Alhamdulillah Nan Safiyyah ta fara wondering ba ance Mami bata da kirki ba gashi kuma faram faram ta ganta, Mami ta kalli Khaleesat tace "Ki shiga kitchen Halysaah zaki ga cin cin da aka kawo min daxu da dublan ki debo mata da drinks" Khaleesat tace "To Mami" Mikewa tayi ta tafi kitchen din, after a wh fito da duk abubuwan da Mami tace ta ajiye Safiyyah, Mami ta mike ta bar masu parlon ta koma daki, Khaleesat tabi Mami dakı taji ko da wani aikin da za ayi mata duk da ko ina na part din fess fess ga kamshi dake tashi ta ko wani angle, Khaleesat sun fi minti arba'in bangaren Mami sannan tayi ma Mami sallama suka koma part dinta da Safiyyah, Safiyyah ta zauna kan kujera a Main parlor tana kallon Khaleesat tayi kasa da murya tace "In ji babu CCTV camera a parlon nan naki, gudun ko akwai a parlon Mami yasa na ja bakina na kume...." Khaleesat ta dan yi murmushi don tayi mamakin da Safiyyah bata ce komai ba duk zaman da suka yi a bangaren Mami, dama da tayi wata maganar ma zata yi maza ta kwabeta amma sai taga bata yi ba, Zaunawa Khaleesat tayi tace "Babu komai a nan Safiyyah tayi mitsi mitsi da ido tace "shanye Housemate din matar tasa tayi ko me???" A takaice Khaleesat tace "Ohon masu" Safiyyah tace Ji min er iskar yarinya, wallahi da Mami bata fito ba da taji ko ni wacece kamar yanda ta tambaya, kaina ya fi nata hayaki wallahi, ki ji fa har da fixge wayarsa a hannuna, kan bala'i bata fa san wacece ni ba yarinyar nan" Khaleesat tace "To ranan fa shakeni tayi kawai daga ta samu ni da mijinta a parlorn Mami Safiyyah ta hangame baki tace "Ta shake ki? Sai aka yi yaya?" Khaleesat ta tabe baki bata ce komai ba don wani bakin ciki tokareta tuno hakan da tayi, dai dal sanda bude kofar parlon sai ga Hadiyah da Iklima sun shigo parlon, daga Khaleesat har Safiyyah suka dinga kallonsu, Hadiyah na ma Khaleesat wani matsiyacin kallo har ta karaso tsakiyar parlon tace "Wato tun da na bi na toshe duk wata hanyar da zaki dinga bibiyan mijina da iskanci a gidan nan shi ne bari ki gayyato kawarki kwartuwa kamarki ta zo ta dora daga inda kika tsaya...." Safiyyah ta mike ta cillar da gyalenta ta nufi Hadiyah tana huci tace "Don ubanki ni kike ce ma kwartuwa? A gidan uwarki kika san ni zaki ce min kwartuwa? So kike in maki duka blue black a nan yanda ko mijin naki bazai gane ki ba??" Iklima na ganin haka tace "Kee hattara yarinya, kar ki ji ma kanki bala'in da baza ki iya fidda kanki ba, kin san wacece ita? So kike ki kare shegen rayuwarki a prison??" Tuni Khaleesat ta shiga tsakaninsu kafin a fara dambe ganin yanda Safiyyah ta hada Hadiyah da Iklima ta dinga kunduma masu zagi ba ji ba gani tana neman cakumosu, Khaleesat na jawo Safiyyah tace "Piss stop this Safiyyah, don Allah ki kyalesu mu shiga daki...." Hadiyah ta juya ta zabga ma Khaleesat wani wawan mari tace "Ke ce dai dai yina ba er tashar kawarki ba...." Khaleesát ta saki baki with shock ta dafe kuncinta tana kallon Hadiyah, bata san sanda ta gaura mata nata marin ba ta fincikota a fusace, nan dambe ya kacame tsakaninsu, Iklima t da gudu zata je kiran yan gidan yanda za ay Khaleesat da Safiyyah taron dangi ayi masu duka, dama duk yan matan gidan da iyayensu suna nan don Hajja na hanya yau, Safiyyah bata taba sanin Khaleesat na da karfi haka ba sai yau, don tuni ta kai Hadiyah kasa ta dinga lakada mata duka ba ji ba gani kamar an aikota tana gaggaura mata maruka Hadiyah na ihu tana kiran Ummi, Safiyyah taki rabasu ta koma gefe tana wani tsumuwa tana kara gingering Khaleesat, sai da taga Khaleesat ta shake Hadiyah da gaske har idanuwanta sun fito, kuma exactly yanda Hadiyah tayi mata a parlon Mami sannan Safiyyah tayi saurin janyeta daga kan Hadiyah tace "Bar shegiya haka, bar ta haka nan kar ta suma a hannunki, gobe ko burkutun arna ta kwankwada bazata sake shigo maki bangarenki ba, er iska mara tarbiyya kawai" Ihu kawai Hadiyah take tana birgima a parlon tana kiran Ummi, Khaleesat na huci tace "Don uwarki gobe ki sake wanke shegun kafufuwanki ki zo bangarena ki gani, wallahi sai na maki fiye da haka don jina jina zan maki, mijin ki din banza naga sanda yake tare dake tani yake ba take ba, kuma da bakinsa ya gaya min ke din zabin Maminsa ce ba zabinsa ba kawai ya rasa yanda zai yi ne da aurenki da aka kakaba maki, abinda Mijina aka so makala maki yaki shi ne aka makala ma Jawwad din, to burgar uwar me zaki ma mutane bayan mun san komai, yaush ya fara baki attention dinsa? Ina ce a rashine ya hakura yayi accepting dinki har yake maki kallon mace? Ke da kike matar chushe har kina da bakin magana mara kunya kawai" Hadiyah was more than shock, kukan ma ta kasa tana kallon Khaleesat jin abubuwan da take cewa, Hayaniyar matan gidan da 'ya yansu Khaleesat ta fara jiyo alamar sun iso bangaren nata, ai ko ta ja hannun Safiyyah da sauri suka shige parlon Ajay tun da akwai key a jikin kofar, suna shiga ta kulle kofar da makulli, Safiyyah na zare ido jin hayaniya sosai a Main parlor tace "To kira mana Ajay ya zo ya kai ni tasha" Khaleesat ta zauna kan kujera tana huci tace "Wallahi kadan nayi mata, ni ma ai haka ta min ranan a parlon Mami ta shakeni, babu wanda yayi kokarin stopping dinta sai Mami da Ya Junaid da ya mareta, but at the end Jawwad was questioning Ya Junaid akan me zai marar masa mata, bayan yana tsaye komai ya faru he couldn't even save me" Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallon Khaleesat tace "Shi Housemate din??" Khaleesat tace "Kuma babu wanda yace inyi hakuri a gidan nan sai Mami, don haka nima yau na rama sai in ga me za a ce" Safiyyah tace "Har Mai martaban?" Khaleesat taki ce mata komai døn ita Mami ce kawai bata jin haushi a fadin gidan nan, mikewa tayi ta tafi dakin Ajay ta dau wayarta ta kunna sannan tayi dialing numbersa, yana fara ringing ya daga amm ce komai ba, ta turo baki tace "Kana gan zaman zamana zaman zamana Hadiyah ta biyoni har part din nan ta mareni ko?" Shiru yayi for some seconds, har tayi tunanin baya kan layin, ta kalli screen din wayar taga yana kai har sannan, sai kuma taji yace "Ta mare ki? Ke kuma sai kika zauna ta mareki ko?" Khaleesat tace "A'a na rama, sannan nayi mata duka" Yace "Kika mata duka?" Khaleesat ta kara turo baki tace "Enh mana...." Yace "Good, hope kin shiga ciki kin kulle kofa?" Tace "En" Yace "Kuma Kawarki bata yi involving kanta ba?" Khaleesat tace "A'a ni kadai na doketa, ita ce ma ta raba mu" Yace "Good, duk me za su ce kar ku bude kofar" Katse wayar yayi daga haka, Khaleesat ta koma parlor, Safiyyah sai zare ido take jin uban zage zagen da mata ke laftawa a parlor kamar maguzawa suna cewa sal sun yi ma ita da Khaleesat lahani, kai baka ce sun hada komai da Sarauta ba yanda suka dinga maganganu kamar yan tasha, gashi sal Bazawara suke kiranta da shi wai aurota masarautar ma Taboo ne at the first place shi yasa daga shigowarta komai ya rikice a masarautar, maganganu marasu dadi sai wanda suka manta ne basu ma Khaleesat da iyayenta ba, Khaleesat ta kunna TV din parion Ajay ta kure volume yanda ma bazata dinga jin su ba, kuma zuciyarta ko dar, as far as Aj yi blaming dinta kan abinda tayi ba. HALYSAAH PAGE 146... Ajay dai ya kasa ce ma Mami komai gashi yaki daga kansa, gaba daya he look very worried and confuse, tsawa Mami tayi masa tace "Baka ji na ne wai Junaid? What is wrong with her?" Ya girgiza kai ba tare da ya yarda su hada ido ba, muryarsa dauke da tsantsan damuwa yace "Bata da lafiya ne" kafin Mami tace komai kawai ya koma cikin dakin don duk hankalinsa na can gaba daya, yana shiga dakin yayi saurin covering zanin gadon that was stained with blood da duvet, yanda Mami ta gansa a birkice yasa ta kasa hakuri kawai ta bi bayansa da sauri zata shiga dakin taji muryar Kilishi da ta taho daga side din Hajja tace "Lafiya me ke faruwa Aunty Aseeyah? Ko iska ta tayar? Mu mun zata ma Hadiyah ce wallahi" Mami ta juya tana kallon Kilishi don sai a sannan ita ma tunanin hakan ya zo mata bayan Kilishi ta fada, ko dai tana da iskokai ne, Mami bata ce ma Kilishi komai ba ta shiga cikin Bedroom din kawai, har kusa da gadon ta karasa da sauri ganin yanda Ajay ke rike da ita with confusion yana kiran sunanta worriedly amma ko motsi bata yi, sai ga Kilishi ta biyo bayan Mami har cikin dakin ita ma, Mami ta zauna edge din gadon tana kallon Khaleesat that was still unconscious ta fara tofa mata addu'a, Kilishi ta wani kalli Ajay tace "Amma kai dai sauna ne Ahmad, idan iskoki gareta dama sunanta zaka zauna kana faman kira kana jij ko ko addu'a ya kamata ka dinga tofa mata?" Sal a sannan Ajay yayi realizing abinda ya kamata yayi in the first place da yaga she is unconscious, da sauri ya sakar ma Mami Khaleesat ya shiga bandaki immediately zai debo ruwa, Kilishi ta bi sa da wani kallo baki bude ganin yanda duk yake a rikice ya daburce kamar ba shi da ta sani ba, dama akwai abinda ke rikitasa har gigice ya kasa boye hakan, haba ta rike tana kallon Khaleesat a ranta kuwa tana cewa har sun fara mallakesa kenan irin wannan gigicewa da rawan jiki kamar zai masu kuka, Mami dai sai gyara ma Khaleesat duvet din jikinta take bayan ta lura babu riga jikinta at the same time tana tofa mata addu'o'i, Kilishi ta tabe baki ta fara komawa baya a ranta tana addu'an Allah ya sa iskan su kara tashi ta shake Mami, ita banda Hajja da ta tasheta ta taho taga abinda ke faruwa da yake a bangarenta ta kwanta yau ai da baza ma tasan wani abu na faruwa ba a gidan, Hajjan ma tayi tunanin Hadiyah ce, Ajay ya fito bandaki da ruwa ya karasa kusa da gadon da sauri har ruwan na zubewa a hannunsa, duk tunanin Mami addu'a zai yi a ruwan ko wani abu, sai kuma taga ya zauna daya side din yana shafa mata a fuska, Mami zata yi magana Khaleesat ta fara juya kai a hankali, da sauri Kilishi ta koma can bakin kofa ta tsaya tana fatan ta makuro Mami a rasa me kwatanta, a hankali Khaleesat ta bude idonta da suka rine, Mami ta dafa goshinta cikin kwantar da murya tace "Sap Halysaah, sannu kin ji" Khaleesat ta kasa komai tana kallon Mami Kamar tana son tabbatar da ita din ce ko kuma idonta ne suke mata gizo, nan ta fara kokarin mikewa zaune amma ta kasa daga ko hannunta, gashi duk jikinta sai rawa yake, Mami zata gyara mata kwanciya tayi saurin kamo hannunta tana girgiza kai muryarta ko fita baya yi sai ga hawaye masu zafi na sauka gefen idonta a wahale tace "Don Allah ki tafi da ni Mami, don Allah ki tafi da ni" a nan ne idon Mami ya sauka kan bedsheet din kan gadon don a sanda Khaleesat take kokarin tashi ta janye duvet din da ya rufe wajen jini, shi dai Ajay ya mike a hankali ya koma daya bangaren dakin ya tsaya looking guilty, Mami tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, meye wannan?" Kilishi ma sai kallon kan gadon take da mamaki, Mami ta kalli Ajay da ya sauke idonsa kasa, sai kuma ta kara kallon Khaleesat that was still struggling to get up tana rike da hannun Mami muryarta na rawa tana cewa Mami ta tafi da ita don Allah, Mami dai sai rufa mata duvet din jikinta take ganin cirewa ma take kokarin yi gaba daya not minding she is naked, mamakin jinin meye a kan gadon Mami ke yi with confusion, gashi sai bin dakin take da kallo ko zata ga wani makami or anything sharp, Kilishi kuwa ta kasa daurewa ta kalli Ajay tace "Wannan kuma wai jinin meye haka kwance a kan gadon Junaid? Fada ku ka yi da matar taka ko me?" Ajay dai bai daga kansa ba, kawai suka ga ya nufi kofa walking slowly ya fita daga dakin don ji yayi kafafuwansa sun ka gaba da daukansa ga wani sanyi da yake shigarsa sosai, Mami ta bi sa da kallo cikin rudani, Khaleesat na kuka da kyar har Ikcn muryarta bai fitowa sosai tace "Don Allah ki tafi da ni Mami, pls take me away, wallahi mutuwa zan yi...." A hankali Mami tace "Ina hijab din ki?" Da sauri ta yunkura zata mike ta nemo hijab amma tayi wani kara me karfi ta rike Mami idonta kamar za su fito ta fashe da wani kukan tace "Bazan iya tashi ba wallahi...." Kilishi ta bude baki tace "Baza ki iya tashi ba? Yanka ki yayi da makami a kafar ko me?" Mami ta cire duvet din jikinta a hankali tana dubata, mamaki tayi sosai and she was shock at the same time amma fa ta rasa gane ma'anar hakan, after a while ta mike ta fice daga dakin ta fita har parlor, kofar dakin da ta gani a bude ta shiga ta gansa zaune gefen gado ya dafe kansa da hannu biyu, Mami na masa wani kallo tace "Meye haka kayi ma yarinyar mutane Junaid?" A hankali Ajay ya daga kansa yana kallonta da idanuwansa da suka kada sosai, sai kuma ya sunkuyar da kai yayi shiru, Mami ta daka masa tsawa tace "Ba magana nake maka ba, me kayi mata haka?" Dakewa yayi murya can kasa yace "Mami ba da gangan bane..." Mami tace "Ban gane ba da gangan ba, meye kayi mata ba da gangan ba?" Cikin sanyin murya ya daure yace "Ni ban san she is a virgin ba" Mami ta dinga kallonsa babu ko kiftawa da wani expression tace "Virgin? Kamar yaya Vy Ajay ya kasa cewa komai kawai sai ga hawa idonsa, Mami tayi still a tsaye kamar an dasa ta a dakin tana kallonsa babu ko kiftawa virgin din da yace na mata yawo a kal, ta dade bata shiga shock irin na moment din ba, a hankali ta juya cikin rashin kuzari ta fita daga dakin, but how is she a virgin yarinyar da aka ce ta taba aure?? A corridor ta hadu da Jay da Hajja sun zo part din, Hajja tace "Aseeyah ke ma zuwanki kenan ko? ni wallahi na zata Hadiyah ce tun da ta saba ta kurma ihu ba gaira ba dalili saboda tabara" Hajja ta shiga parlon tana cewa "Ko dai iskokai gareta ne Jiddan? ina Ahmad din?" Jay bai shiga parlon Junaid ba yana kallon Mami yace "Me ya sameta Mami? Hope she is okay?" Mikewa Ajay yayi jin muryar Jay ya shige bandaki, Mami bata yarda ta kalli Jay ba tace "She is fine, I think she had a nightmare" Tana fadin haka ta shiga parlon ba tare da ta jira me zai ce ba, shi dai bai bi ta zuwa cikin parlon ba ya tsaya bakin kofar, Kilishi dake tsaye bakin kofar dakin Ajay taki zuwa kusa da Khaleesat ta fita parlor da sauri jin muryar Hajja a parlon, Mami dai ta wuce Bedroom ta bar su a parlon, Hajja ta kalli Kilishi tace "Na ji shiru shiru baki dawo ba, lafiya dai ko? Me ya sameta? Kuma ina Ahmad din? Halan tana da mutanen boye ne?" Kilishi tace "A'a ba lafiya ba Hajja, ina ganin Junaid dai fada yayi da ita, gashi can ya yanyanke ta wallahi, don saman gadon kaca kaca da jini, mun tambayesa me ya faru yaki bamu amsa ficewarsa, ita kuwa tana can kan gado" tashin hankali sosai Hajja ta dafa kujera tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ta mutu??" Kilishi tace "Ga ta can dai a dakin, amma kam ta zubar da jini sosai, zanin gadon ya jike jagab da jini" Hajja tayi karfin halin karasawa cikin dakin jikinta na bari tana salati a zuciyarta, tana shiga ita ma idonta ya sauka kan zanin gadon tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Kallon Mami da ta fito daga bandaki bayan ta tara ruwan zafi a bath tub tayi tace "Aseeyah me ya faru?" Mami bata kalli Hajja ba, tana magana da kyar tace "Ta samu rauni ne Hajja" Hajja tace "Rauni? Wani irin rauni?" Karasawa tayi kusa da Khaleesat hankali tashe, Mami dai ta fita daga dakin zata tafi kitchen ta dauko gishiri hawayen dake makale idonta ya fara zuba, Hajja tayi shiru tana ta kallon stain din zanin gadon kamar warce ta fahimci wani abu, sai kuma ta kalli Khaleesat da ta rasa inda zata sa kanta cause she was soo weak and in pain, ta kasa kwanciyar haka zaman ma ta kasa sai Umminta take kira, a hankali Hajja ta rufe dai dai inda yayi staining a zanin gadon sannan ta kalli Khaleesat tace "Sannu Jiddah, Allah ya maki albarka....." Sai kuma ta juya ta kalli Kilishi tace "Idan Aseeyah ta kintsa ta a kawota sashi na komin dare" Hajja na kai wa nan ta fita daga dakin, Kilishi ta bi bayanta zuwa parlor with confusion, ba tare da Hajja ta kalleta ba tace "Wannan ai jinin budurci ne a saman gadon Kilishi" Kilishi ta wani gwale ido "Hajja ai ba budurwa bace wallahi" Hajja tace ко ma dai menene ga dai jinin budurci na gani akan gado, a linke zanin gadon a ajiye tukun" Hajja na kai wa nan ta fita daga parlon, Kilishi ta kasa barin inda take tsaye baki bude abinda Hajja tace na mata yawo a kai, jinin budurci kuma yarinyar da kowa yasan Bazawara ce, Mami ce ta shigo parlon bayan ta dauko gishiri a kitchen, da wani expression Kilishi tace "Aunty Aseeyah ki ji Hajja da wani zance wai jinin budurci ta gani a kan gado, wai dama boye ma Hajja aka yi bata san Bazawara bace yarinyar nan ashe?" Cike da karfin hali Mami tace "Abinda Hajja ta fada haka ne Kilishi, budurwa ce Halysaah.... Ga kuma shaida nan kan gado" Mami ta shiga daki ta bar Kilishi da sakakken baki a wajen, da sauri ta bi Mami zuwa dakin with shock tana kara kallon zanin gadon, ganin irin dagan da Mami suka yi da Khaleesat Kafin su je bandaki don ta kasa tashi tsaya wannan ya kara tabbatar ma da Kilishi gaskiya Hajja ta fada, Kilishi na jan kafa da kyar ta fita daga bangaren gaba daya, to amma ta yaya za ta zama budurwa bayan hatta iyayenta basu boye cewar Bazawara bace da aka je neman aurenta, ko dai wani salon yaudara ne wannan don su dena ce mata bazawara a gidan? Kai inaa yaudaran nan bai yaudaru ba don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata yarda ba, ta yaya warce kowa ya sani a Bazawara overnight ace ta zama budurwa kamar wani wasan kwaikwayo, wato su Junaid zai ma hankali tunda yaji yanda ake kiranta Bazawara now and then shine bari ya zo da plan, Jay was still standing outside of the main parlor don kawai ya kasa tafiya so yake Mami ta fito tace masa she is fine duk da Hajja da ta fito yanxu tace masa kawai iskokinta ne ya tashi ba komai ba ya tafi yayi kwanciyarsa she is fine now, shi kuma fin shekara daya da yayi da Khaleesat bai taba ganin alamar iskokai a tare da ita ba, don ko yaya ne ai da wataran za su tashi ko kuma su dan tabata barin lokacin da take cikin tension din Abdul, take cikin bacin rai kullum, why all of a sudden za ace tana da iska dare daya, bacci yake amma farat daya ihun da tayi ya tashe sa daga baccin kuma yasan sarai muryarta ne, kuma duk yanda ya so kin zuwa yaga if everything was alright ya kasa daure zuciyarsa, yana fitowa Parlonsa sai ga Hajja that was thinking Hadiyah ce don ita bata ma san Khaleesat bace, nan yace mata ba Hadiyah bace, shi ne suka taho part din Ajay tare, Kilishi ta fito daga babban parlon tana kallon Jay da ya juya yana kallonta ta karasa har inda yake babu kunya babu tsoron Allah tace "Jawwad wai don Allah wannan yarinya Halysaah take ko waye sunanta? Budurwa ce ko Bazawara? Ina ga duk wanda zai san matsayinta to a bayanka yake don da kai aka fara sanin yarinyar kafin Junaid Jay ya dinga kallon Kilishi still trying to process what she is saying, Kilishi tace "Dole ka kalleni haka Jawwad, mu dai mun san tun farkon neman auren yarinyar nan da kayi iyayenta basu boye matsayinta na bazawara warce ta taba aure ba, to wai kwatsam dare daya mijinta ya maidata budurwa zai raina ma kansa hankali ba mu ba, sannan ace duk tsawon watannin da suka yi tare sai yau ya fara saninta idan ba raina ma mutane hankali zai yi ba, to kansu suka yi deceiving da wannan jinin saman gadon da Hajja ta lakaba masa suna jinin budurci, na fi karfin yaron da aka haifa a gabana ya yaudare ni" Jay dai ya sauke Idonsa bayan ya gama jin duk abinda Kilishi ta fada, ta juya tayi wucewarta zuwa bangaren su Gimbiya Firdausi ta kai masu labari, Jay stood there for almost 20 mins sai ga Mami ta fito zata je kiran Yakumbo ganin ita kadai bazata iya da Khaleesat da taki bata hadin kai ba kwata kwata, Jay ya daga kai yana kallon Mami da ta sauke idonta bayan sun hada ido, tace "Baka tafi ka kwanta ba?" Bai ce mata komai ba, tace "Ka je sai da safe, sun lafa mata ai tuntuni" Daga haka ta bar wajen ba ta ta kallesa ba..... HALYSAAH PAGE 147... Da asuba Khaleesat na dakin Mami a kwance tana bacci, wanda sai kusan karfe hudu da rabi na asuba baccin ya dauketa bayan Mami ta bata pain reliever har sau biyu a daren, kana ganinta kasan ba bacci me dadi take ba cause she is restless gashi sai firgita take ita kadai, Ita kanta Mami bata yi bacci ba daren don da ta so ma su je asibiti amma tayi considering ko waje bazata iya fita ba sai dai a zo gida a dubata kuma har Dr dinta sai da ta kira a daren bata sameta a waya ba, duk da tasan Gimbiya Firdausi babban likita ce ita dai bata je ta masu magana ba tunda babu wanda ya zo da sunan duba Khaleesat banda Hajiya Habibah ita ma tasan zuwan kwakwaf ne ba wai don Allah ta zo ba don tana zuwa tambayar da ta fara yi shine wai taji gida ya dauka Halysaah budurwa ce, kuma daga bakin Hajja aka fara jin wannan labarin, sannan banda shiri aka yi ta yaya ihunta zai karade gidan duk girmansa in dai ba waje ta fito tayi ihun ba sannan ta koma ciki, har da cewa su basu ma ji wani ihu ba kuma idonsu biyu a lokacin, Mami dai bata kulata ba, ta karaci maganganunta dake nuni da cewa babu wanda ya yarda da batun a gidan sannan ta fita... Mami na ta zaune kan darduma tayi nisa tunanin da take hannunta rike da carbi Hajja ta shigo dakin da sallama, Mami ta gaidata da ladabi, Hajja tace "Ya ba a kai ta can bangaren nawa ba bayan nace ayi Aseeyah?" Mami tace "Ai ko banda labari Hajja" Hajja tace "Kilishi na gaya ma haka ai, bata gaya maki bane?" Mami tace "Wallahi bata sanar min ba, da yake da wuri ta bar bangaren Junaid din ta bar ni a can, to amma bari in tashi mu je can din Hajja" Mami ta fada haka ne ba wai don Khaleesat zata iya tashi ba, da yaya ma suka zo part din nata don sai da Mami ta tausaya mata sosai, kuma da taimakon Yakumbo suka dawo part din nata, ta rasa wani irin zuwa Junaid yayi mata anya ma yana cikin hankalinsa kuwa yaje mata, kuma tasan dai babu abinda yake sha balle tace, Hajja tayi shiru bata ce komai ba don tunaninta kawai Mami bata yi niyyar kai Khaleesat can bangaren nata bane, dama ga maganganun da ta zo ta tarar kwando kwando a gidan akan irin yanda Mami ta dau karan tsana da tsangwama ta dora ma Hadiyah bata amsa ko gaisuwarta a gidan sannan ta hanata zuwa sashinta, wanda jira take yau ayi zama da Sarki ta ji dalili sai ga kuma issue din Junaid da Khaleesat, dama abu biyu ya kawota masarautar, Dethroning din Ajay da aka yi sai kuma tsangwamar da aka ce mata Mami ta dauka ta dora ma Hadiyah, a takaice Hajja tace "A'a ki bar ta a nan din tunda haka kika so, ya jikin nata?" Mami tace "Hajja Kilishi bata sanar min kince a kai ta can sashin ki ba, kuma ki kirata ki tambayeta ki ji...." Hajja ta dakatar da ita tace "Cewa nayi ya jikin nata?" Mami ta sauke kai tace "Bata samu bacci ba, kuma jikinta yayi zafi sosai yanxu haka duk da nayi ta bata pain reliever so nake idan gari ya waye na kira likita ta dubata ko ba wata matsala, ko kuma mu tati asibitin" Hajja dai tayi shiru don alamu sun nuna ba da hankali Ajay ya je ma yarinyar ba, ko kuma gardama tayi masa, ta juya ta kalli Khaleesat warce kana kallonta zaka san she is in pain duk da bacci take, Hajja ta karasa har kusa da gadon Mami tana kallonta ta kai hannu goshinta taji kamar wuta, numfashi ma da kyar take saukewa, duk da bacci take kana iya ganin yanda idanuwanta suka kumbura saboda kuka and she look pale, lebbenta suka dawo pure pink gaba daya, Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Allah ya bata lafiya, amma naga ai Firdausi na gidan nan, me yasa baki mata magana ta shigo ta dubata ba?" Mami tayi shiru jin abinda Hajja tace, can kuma tace "To Hajja, bari ayi mata magana...." Mikewa tayi ta fita daga dakin, Hajja dai sai kallon Khaleesat take, can ta juya ta fita, bangaren Ajay ta tafi ta samesa kwance a parlonsa, ta karasa ciki tace "Kayi sallah kuwa Ahmad?" Sai da tayi tambayar taga darduma shimfide a parlon alamar yayi sallan, ganin yanayinsa ta cire abinda ya rufa da shi duk da bacci yake bai san ta shigo ba, nan ya fara sambatun da bata ma san me yake cewa ba idonsa a rufe yana kokarin juyawa tayi saurin cewa "Ahmad kar fa ka fado kasa, baka da lafiya ne?" Sai a sannan ya bude ido da kyar amma ya kasa barin idon a bude ya mayar kawai ya rufe, ta kai hannu forehead dinsa taji wani irin zafi don har yafi na Khaleesat zafi, she was quiet for some seconds tana ta kallonsa don ya bata tay sosai, sai kuma a hankali tace "Tashi ka shiga Ahmad, me yasa baka kira kace baka da lafiya ba? Haka ka kwana da zazzabin nan me zafi?" Shi dai bai iya ya sake bude idonsa ba yana sauke numfashi a hankali, Hajja ta juya ta fita daga dakin ta tafi part din Jay, kwance ta samesa kan 3 seater shi kadai a parlon, ya juya jin an bude kofa, ganin ita ce ya dauke kansa, ta karaso ciki tace "Nayi tunanin ma ka koma bacci, Sarkin 'yan bacci" Ya sauke idonsa a hankali ya gaisheta, ta amsa tace "Hadiyar bata tashi ba" Bai ce komai ba, Calmly tace "Jawwad ka tafi ka duba dan uwanka ba shi da lafiya sosai, daga can wajensa nake yanxu" Dai dai nan Hadiyah ta fito daga kitchen rike da cup din tea tana sanye da Kayan bacci, ganin Hajja cike da damuwa tace "Yauwa Hajja gwara kiyi masa magana kilan yaji naki a kira masa Doctor, bai fa yi bacci jiya ba bashi da lafiya kuma yaki barin in kira likita" Hajja tace "Subhanallahi, me ya samesa?" Hadiyah tace "To nima dai ban sani ba, he was running temperature and throwing up all through the night, ko masallaci bai iya yaje ba da aka yi sallah yanxu, he is just lying down here" Hajja dai tayi shiru tana ta kallon Jay, can ta karasa har inda yake kwance ta kai hannu goshinsa taji zafi kamar wuta, shi dai kallonta kawai yake, a hankali Hajja ta zauna kan kujera bata sake cewa komai ba. Da gayya Gimbiya Firdausi ta zo bangaren Mami tare da su Ummi, Hajiya A'isha har da Hajiya Sumayya wajen karfe bakwal da rabi na safe duk a sunan ta zo duba condition din Khaleesat bayan Mami ta a waya don Mami kin zuwa sashin da take tayi, dama tun jiya su Hajiya A'isha ke cewa Gimbiya Firdausi taje kawai tace zata duba Khaleesat don ita kadai ce zata tona asirin Junaid har ma da komai ba sai plan da aka shirya na rainin wayo a masarautar, don kaf dinsu babu wanda yaji wani ihu, ita tasan inda ta tafi ta tsaya tayi ihun har Mami da Hajja suka jiyota tunda su ne Main target dinta dama, sai da suka jira ranan da Hajja ta sauka masarautar sannan za su aiwatar da shirinsu, Su Hajiya A'isha duk suka zauna parlon Mami ko dakin basu karasa ba, Aunty dake zaune kan kujera a parlon ta amsa gaisuwansu cike da kasaita, ita din ma kiri kiri daxu ta bi Mami har kitchen ta nuna mata wannan abun shiri ne kawai don babu bazawarar da ta taba komawa budurwa in ba raina ma mutane hankali Junaid zai yi ba, Mami dai bata tanka ta ba ta ci gaba da abinda take a lokacin, Gimbiya Firdausi kadai ta karasa har Bedroom din Mami ta shiga da sallama, Khaleesat na kwance don ko zama ta kasa yi, Mami dake zaune dakin tayi nisa tunanin da take, ga breakfast a gabanta ta kasa ci, ita ma duk ta dawo wani iri kamar tare suke jinyar da Khaleesat, Gimbiya Firdausi ta zauna kan kujera bayan sun gaisa da Mami tace "Sai fa an samo hand gloves, in kuma akwai to a bani...." Mami dai bata ce komai ba, don banda Hajja ce tace ayi ma Gimbiya Firdausin magana ita da kawai likitar dake dubata zata kira ta zo ta duba Khaleesat, can Mami tace "Sai a siyo, don bani da Hand gloves tunda ba aikin lafiya nake ba" Gimbiya Firdausi tace "Da aka san babu ai tanadinsa ya kamata ayi kaf a kirani, tunda dubata aka ce za ayi, hakan kuma ba mai yiwuwa bane babu gloves" Mami bata sake tankata ba, after a while ta dau wayarta ta fara kiran Mukhtar yaje ya siyo Hand gloves din.... Bayan Gimbiya Firdausi ta gama duba Khaleesat a dakin Mami ta fita ta koma can sashinta dake cikin gidan, nan ta tarar da su Hajiya A'isha zazzaune a parlor suna jiran dawowarta don tuntuni suka baro part din Mami bayan da Hajja ta shigo, tun da Gimbiya Firdausi ta shigo parlon su Ummi ke ta kallonta suna jiran jin Feedback, Kilishi ta kasa daurewa tace "Duk plan ne ko Aunty Gimbiyah? Naga duk ranki a bace da alama bata maki lokaci kawai aka yi gashi ko Breakfast baki yi ba" Gimbiya Firdausi ta zauna kan/kujera ta sauke wani ajiyar zuciyar takaici tace "To amma menene fa'idar cewa da aka yi yarinyar ta taba aure? Kuma naji an ce daga bakin iyayenta hakan ya fito, to guduwa tayi bayan an daura mata auren amma dai ko?" Duk su Ummi da Hajiya A'isha suka dinga kallon Gimbiya Firdausi babu wanda yace komai, Can Hajiya Habibah tace "Ikon Allah, a takaice dai yarinyar budurwar ce kenan dai Yaya Gimbiyah?" Gimbiya Firdausi tace "To sai ma an hada mata da dinki, yanda ku ka san mara hankali haka yaje mata...." Takaici yasa Kilishi ta kasa cewa komai ta wani rungume hannuwanta tana zaune ta cika one sitter sal sauke numfashi take da kyar tsabar kibarta, da wani expression Ummi tace "Budurwa ce dai kenan?" Hajiya Habibah tace "Kin ji wani zance Maimuna, abu kina ji ance sai an oa mata da stitches, duk yanda aka yi auren farko da aka yi mata shegiyar kin zama tayi ta gudu saboda ta kwallafa rai kan Jawwad, kilan ma shi zal ce ta tace Junaid take so, sai gashi ma za a amshe title din a hannun Jawwad din yau, kowa fa yana son mulkin nan ace ya dawo gidansa ko ta yaya, ita ma A'isha ina lura da take takenta so take ta cuso Iklima, Ita kanta shegiya Maimuna ji murnan da take da aka kwace ma Junaid Yarima aka ba mijin er ta, don haka gaskiya gwara mu canza tsari Aunty Gimbiya, in har Hajja ta birkice ma Sarki fa to dole zai maida ma Junaid Title dinsa" Gimbiyah Firdausi tayi kasa da murya tace "Ke yanxu ya kike ganin za ayi Kilishi?" Kilishi ta dawo kusa da ita cikin rada tace "Ba kince tana can ya farketa ba har dole sai anyi dinki?" Gimbiya tace "Dole kuwa sai anyi dinki" Kilishi tace "To yanxu an tafi siyo maki kayan aikin da zaki dinka ta din ne? Abinda zai faru kawai cusa scissors zaki yi a mahaifar ki katse sa in zai yiwu, wato dai kiyi damage din mahaifarta kawai Aunty Gimbiya yanda da bazai iya zama ciki ba, ko bazai yiwu ayi hakan ba?" Gimbiyah Firdausi ta zaro ido tace "In ma zai yiwu Kilishi a dakin Mamin zan yi wannan aika aikan matar da saboda bata yarda da kanta ba ko ina na bangarenta Cctv ne" Kilishi ta wani kalleta tace "Kai kin ji ki, wallahi ba wani Cctv a dakinta, Parlon ma saboda satan da Walid yayi mata kwanaki na gwala-gwalanta yasa ta saka Cctv din, amma ba komai dakinta, wallahi in wannan damar ta wuce mu shikenan mun shiga uku mun lalace, kinga in aka ga bata haihuy karin aure ya kama Junaid, to a nan za mu Shahuda ko Humaira" Gimbiyah Firdausi tace "To har Aseeyan ta kira likitan da za tayi aikin, yanxu haka can na barosu tare da likitan, balle ni ba mahaukaciya bace da zanyi wannan aika aikan a bangaren Aseeyah" Kilishi ta ciji yatsa tace "Kashhhh" shigowar Hajiya A'isha ne ya sa duk suka yi shiru, Kilishi tayi maza ta canza zancen. Wajen karfe uku na yamma Khaleesat na bangaren Hajja a dakin da Hajjan ta sa aka gyara mata aka shimfida mata lallausan zanin gado tun bayan da likitan Mami ta gama abinda zata yi mata ta tafi da safe, she felt a lot better akan yanda take ji daga daren jiya zuwa safiyan yau, duk da she is still in pain amma tana jin dama dama yanxu, kula na musamman Hajja ke bata making sure she is alright and needs nothing, haka ma Mami da every now and then take zuwa bangaren dubata, sai a yanxu Khaleesat ta fara jin kunyan da bata ji ba daren jiya, don ta kasa dinga hada ido da Mami ko Hajja, sai tayi ta sunkuyar da kai, kaf gidan babu wanda ya shigo side din Hajja da sunan ya zo dubata sai dai in tasa ta shigo da shi sai Hajja tace ya shiga yayi mata sannu a daki, Hajja na parlor Jay ya shigo kansa a kasa, Hajja dai sai kallonsa take ganin har ya fada zazzabin da yayi, ya zauna kusa da ita tayi kasa da murya tace "Ya jikin Jawwad?" Yace "Naji sauki" Tace "Amma ka kara shan magungunan da likitan ya baka kuwa?" Yace "Na sha" Hajja tace "To ka ci abincin da na aika maka?" Yace "Na ci" Hajja sake cewa komai ba tayi shiru tana kallonsa, tun daxu take son zuwa dubasa a side din nasa amma saboda bata son barin Khaleesat ita kadai gashi Mami ta fita vasa bata le bandaren nasa ba. hatta... dazu baki ta tabe as far as ta taba aure har ta fito kafin ta shigo gidan nan babu abinda zal goge wannan tag din Bazawarar a rayuwarta, ko mijinta na farko ya sadu da ita ko akasin haka to bazawara ce dai tunda ya saketa ta fito ta sake wani auren...." a fusace Kilishi tace "Atohh dai Momy, kema dai kya fada, tunda har tayi aure ta fito mu dai har abada a Bazawara za mu dinga kallonta babu ruwan mu da cewar ta zo gidan nan da budurcinta, da bakin iyayenta suka furta cewar Bazawara ce er su tunda su ma sun san gaskiya, in dai kayi aure ka fito to babu zancen wani Budurci ko da mijin bai sanka ba ka fito gidan" Hajiya Habibah ta wani tabe baki tace "Ga dai Hajja sai nanata cewa take jinin budurci ne kan gadon da yake dama babu wanda take so a gidan nan irin Junaid in ma ba gaskiya bane ita tuni ta nemi rufa ma shi da matar tasa asiri tun a daren jiya, sai wani farin ciki take uwa an mata albishir da aljanna, tayi sintiri bangaren Aseeyah yafi a kirga da safen nan, me yasa bata ma Hadiyah haka ba tunda dai ita ma a matsayin budurwa aka aurar da ita, anya kuwa??? ko da yake mu ma mun fi sati a gidan nan bayan tarewar Hadiyan amma bamu ga alamar komai ba wallahi, ko canjin taku..." Hajiya A'isha ta dinga ma Hajiya Habibah alamar tayi shiru ga Ummi zaune a wajen, tuni Hajiya Habibah ta ankare tayi maza ta canza zancen don shafff ta mance Ummi na parlon, Ummi na mata wani kallo tace "Anya me Yaya Habibah? Me kike nufi?" Hajiya Habibah ta buda hannuwa biyu uwa almajira ta langwabe kai tace "Anya kuwa ta dau Hadiyah da Jawwad yanda ta dau Junaid? Jawwad din da ta rasa mahaifinsa tun yana karami wallahi bata nuna masa soyayya yanda take ma Junaid dake da gatansa ba tunda ga Mai martaba a raye, ko zuwan nan da tayi ma na samu labari daga tushe me karfi ta zo ne don ta umarci Sarki da ya mayar ma Junaid Title dinsa na Yarima kar rai ya baci" Ummi dake ta kallon Hajiya Habibah babu ko kiftawa tace "A ina kika ji wannan magana Yaya Habibah?" Hajiya Habibah ta gyara zama tace "Kema dai Maimuna, kin fa san maganar cikin gidan nan bai boyuwa gaba daya barin ni da na jiyo hakan daga majiya me tushe, muna nan dake ba dai anjima ne zaman Meeting ba zaki ce Habibah ta fada, Hajja bata duba cewar idan aka bar ma Jawwad title din nan ba sarauta bazai taba barin lineage dinmu ba tunda Hadiyah dai dole ita zata haifi future king din Emirate din nan, kuma ita din jikar sarki ce uwarta er sarki, amma take so ta karfi da yaji ta mayar ma Junaid ta yanda buzaye za su amshe mana sarauta wataran muna ji muna gani, kan kace me gaba daya masarautar sai dai a ga jajayen buzaye na yawo maimakon Hausa Fulani" Mikewa Kilishi tayi fuuu ta wuce dakin Gimbiyah Firdausi, ta z kan kujera tana kallonta don shayi take bukata zata sha, Gimbiya Firdausi tace "Amma nayi mamaki ainun kasantuwar yarinyar nan budurwa Kilishi" Cikin bacin rai Kilishi tace "Yanxu Aunty..... tace kakar Khaleesat ce... Dai dai nan Nenne ta shigo parlon da sallama tana rataye da jakarta ta sha tsadadden lace da mayafi shi ma me tsada, kai baza kace ita ta haifi Malam Ali ba, bayanta kuma Aunty Murja ce ita ma ta yafa gyalen da Nenne ta ara mata me tsada akan sabuwar atamfar jikinta, Sai Noor da Aunty Murja ke rike da hannunta, da fara'a Hajja ta dinga masu sannu da zuwa tana kallonsu, Nenne ta tafi har gabanta ta zauna sannan ta mika mata hannu biyu cikin ladabi suka gaisa da Fara'a, Aunty Murja da ta zauna kasan carpet ta gaida Hajja cikin ladabi ita ma, Hajja na mata sannu da zuwa, Mami na kallon Noor da ta rakube jikin kujera tana wasa da kujeran bata zauna ba tayi mata murmushi tace "To zauna kan kujeran mana yan mata" Noor ta sunkuyar da kanta ta zauna kasan carpet, Hajja ta mika mata hannu tace "Taho nan ki zauna yarinya, ya sunanki?" Noor ta mike ta tafi kusa da Hajja tace "Ina yini" Hajja ta rungumota tana Kallonta da fara'a tace "Lafiya lau Baby girl, amma ke kanwar Jiddah ce ko, ga kama nan Maa sha Allah, ya sunanki?" Noor na wasa da fingers dinta tace "Sunana Noor" Nenne na murmushi tace "Fatima ce Ranki shi dade, shi ne ake kiranta Noor, tagwaye ne, dayar me suna Islam tana can ita bata iya nisa da uwar, duk kannen Khaleesat ne uwarsu daya ubansu daya" Hajja ta bude ido sosai tana kara kallon Noor da kamar an tsaga kara it Khaleesat tace "Maa sha Allah, takwarata c ashe, sannu da zuwa Noor, Allah Ubangiji ya maki albarka" Sai a sannan Jay ya gaida su Nenne, Nenne ta rike baki tace "Au, ai ban lura kai bane Ahamad, dama kai ne zaune?" Ya dan yi murmushi a hankali yace "Ya hanya Kaka?" Nenne tace "Ai kwananmu uku kenan a Bauchi amma sai yau Allah ya bani ikon zuwa, na zo duba mara lafiya shi ne nace bara dai in zo mu gaggaisa a gurguje in koma, ashe da rabon zan hadu da Hajiya ne tana gari" Tuni masu aikin dake part din Hajja suka taho da ruwa da lemo sai fresh masu yawa aka ajiye ma su Nenne. HALYSAAH PAGE 148... Khaleesat na kishingide tama repiving message din da Safiyyah tayi mata tun safe, nwa take i sosal amma duk abinda ta kal bakinta sai taji sa kamar magani, ga dal abinci iri ini da aka cika mata amma duk basu da dadi a bakinta sai watermelon kawai take ta sha, ta daga kai a hankali jin an bude kofar dakin, ajiye wayar hannunta tayi da mamaki tana kallon Noor babu ko kiftawa, Noor ta tafi da sauri ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Aunty" Khaleesat na gyars kwanciyarta har sannan mamaki kwance fuskarta tace "Ke da wa ku ka zo Noor?" Noor na murmushi ta zauna gefenta lace "Ni da Nenne da Aunty Murja" Khaleesat ta zaro ido tace "Yau ku ka zo ko yaushe?" Noor tace "A'a 3 days ago muka zo, muna gidan Aunty Murja all this while" Khaleesat felt so happy seeing her sister, amma kuma deep down bata so zuwan su tana cikin halin da take ciki ba, gashi ko zama sai ta daure take iya yi, a hankali ta kamo hannun tace "Umman mu fa?" Noor tace "L tana gida Khaleesat tace "Baba yace a gaisneni?" Noor na murmushi ta gyada máta kai, Khaleesat tace "Islam kuma taki ta biyo ku ko?" Noor tayi dariya tace "Tace ita bazata je ba" Khaleesat ta jawota jikinta tace "How about Aunty Farida?" Noor tace "She is at home too" Nenne ce ta shigo dakin da Aunty Murja, Khaleesat tayi murmushi tana kallon Nenne tace "Shi ne baku ce min za ku zo ba Nenne" Nenne ta zauna kan Carpet tace "Meye hadin biri da gada Khaleesah, ni wajen Murja na zo duba mara lafiya, tana ta yawo gwanin sha'awa a keker guragu da Mijinki ya siya mata me tsada irin na kasar waje wallahi, kamar ma keken da kansa yake tafiya fa" Khaleesat ta sauke kai bata ce komai ba, nan da nan mood dinta ya canza bayan Nenne ta ambato mata Ajay, Nenne dai ta ci gaba da bada labarin keken yarinyar Aunty Murja da kuma uwar kudin da Ajay ya bada a dinga kula da lafiyan yarinyar, gashi yarinyar ta dawo fes da ita kamar ba me lalura ba, To cut the conversation Khaleesat ta kalli Aunty Murja dake ta murmushi tace "Aunty ya Aunty Murja tace "Alhamdulillah Khale Ina ta son zuwa amma ban san ko kun dawo daga Amurkan ba, sai da Nenne ta zo take gaya min ai kun dawo tuntuni..." Khaleesat ta dan yi murmushi tana wasa da duvet din jikinta, Nenne tace "Ni banda ma Murja ta hadani da Allah mu taho mu duba ki ai baza ki gan mu a gidan nan ba Khaleesat, mun ma yi ta kiran mijinki daxu bamu samesa a waya ba, ashe ma baki ji dadi ba yanxu Hajiya ke gaya mana ai baki da lafiya" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Nenne tayi kasa da murya tace "To me yake damunki? Na ma ga kin yi kyau kin kara haske, idanuwanki ne dai suka fada" Sai kuma ta kalli Noor tace "Ke Noor tafi parlor tunda kun gaisa mu ma yanxu za mu fito" Mikewa Noor tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kulle kofar, Nenne ta kara yin kasa da murya tace "Ko ciki ne da ke?" Khaleesat ta hade rai taki bata amsa, Nenne tace "Ba hade rai ba ki bude baki ki min magana don duk nasan halin da kike ciki tunda ke munafuka ce algunguma warce bata san ciwon kanta ba, yanxu idan baki gaya ma İyayen da suka haife ki matsalarki ba uban wa gare ki a duniya da zaki gaya ma? To da yake wannan kawar taki er albarka c ta gaya min halin da kike ciki tun aurki na farko ashe dalilin mutuwan auren kenan ma, mu zaki tona ma asiri wancan kin yi shiru an sako ki duk da gantalallen aure ne kuma sakin shi ne mafi alheri, wannan kuma auren da kowa ke alfahari da shi shima so kike ki kashesa? Ina batun aure babu kwanciya? Aure tsawon wata shidda amma haka Yariman ke kallonki shi bai gaya mana matsalar ki ba don shi din yaro ne me kunya da nutsuwa, ke kuma mahaukaciya kin ki magana mu san na yi? to bamu haifi er da zata tona mana asiri a duniya ba, don haka ga nan magunguna a jakana babu inda ban shiga ba da taimakon uban kishiyar Murja mun nemo maki taimako, an kuma tabbatar mana asiri ne a jikin ki shi yasa hakan ke faruwa, duk ma wanda yayi maki wannan asiri kina fara maganin zai koma kansa, tun da na shigo garin nan ban zauna ba sai fafutukan nema maki mafita nake duk ranan garin ya babbake min fuska, yanxu dakin naki ne nan? Sai ki samu akwati ki saka magungunan a ciki kar ayi tunanin wani mugun abu na kawo maki masarauta?" Khaleesat da har sannan fuskarta ke daure tace "Ni ba dakina bane nan" Hajja tace "Dakin waye nan din?" Khaleesat ta kai tace "Bangaren Hajja ne gaba daya Nenne ta ja bakinta ta tsuke tana rarraba Ido jin abinda Khaleesat tace, can dai kuma ta kara cewa "To babu wannan kamaran da masu kudi ke sakawa ya nannade maganar mutane?" Khaleesat ta girgiza mata kal, Nenne tace "Ba kuma abun in ce ki tashi mu je bangarenki ba ayi tunanin wani abu na kawo maki, ae da sai mu koma sashin ki tunda mun gaisheta" Khaleesat tace "Bani da lafiya ai shi yasa nake nan" Nenne tayi kasa da murya sosai tace "To ni dai ban san yanda zanyi da itatuwan nan ba, ban san yanda zan damka maki a hannu ba ki fara amfani da su cikin gaggawa, ba aburi in bude jakar ba ma yanxu aji kamshinsu a zata wani asiri ne" a hankali Khaleesat tace "Duk ranan da za ku koma Kano ai sai inje gidan Aunty Murja in maku sallama sai ki bani a can" Nenne ta hade girar sama da ta kasa tace "Ni da nake son in ga aikin maganin kafin in tafi? Ai sai naga kamun ludayin lamarin zan bar garin nan, Sai dai in kin zo da sunan yi mana sallama sai in baki sannan in zauna har sai naji yaya ake ciki idan kika yi amfani da su, don gaskiya wannan babban magana ce ba karam wallahi ko bacci ban yi ba ranan da Safiym ta gaya min, ana idar da sallah na sa Malarn Ali ya goyani a machine sai tasha, kin san ya siya machine sabuwa dal Khaleesat ta dan yi murmashi tace "Da gaske Nenne?" Nenne tace "Al Malam Ali Alhamdulillahi yanxu, kasuwancinsa na ta bunkasa a sannu sannu" Khaleesat tayi shiru, nan ta fara tunanin ba ma Abban nata miliyan goma daga cikin account dinta ya kara jari, don kudaden ciki yanxu sun yi 16M, a hankali tace "Nima in sha Allah zan zo Kano, ko kuma in bi ki mu koma tare" Nenne ta hade rai tace "Ki zo ki mana uban me, in ba jinyan laulayin ciki zai kawo ki ba babu shegen dake bukatar ki a Kano a yanxu dai" Khaleesat ta dinga kallon Nenne, Nenne tace "To shikenan tunda mun gaisa kuma kince zaki je can gidan bari mu tashi kawai mu tafi, kar a ga mun dade cikin dakin" Daga haka ta mike tana gyara yafin gyalenta tace "To tashi ki mana rakiya ko?" Khaleesat tayi shiru, Aunty Murja tace "Nenne a kwance fa muka sameta ba lafiya, mu yi tafiyarmu kawai in ta samu sauki sai taje can gidan namu" Nenne ta tabe baki ta nufi kofa, Aunty Murja tayi ma Khaleesat sallama sa murmushi ta bi bayan Nenne, Khai ta sauke idonta jin hawaye ya fara taruwa idon, a nake su zsunty murje suka lite uaja dakin, Hajja na parlor har sannan da Noor a gefenta tana cin Apple din da Hajja ta sa ta dauka, tana ganin sun fito ta mike ta koma wajen yayarta a daki, Hajja na kallonsu Wenne tace "Madallah har kun fito" Nenne tace "Mun fito ranki shi dade, unguwanmu da nisa shi ne nace gwara mu kama hanya da wuri kar yamma yayi mana a hanya" Hajja tace "A'a ba kwana biyu ku ka zo yi mana ba dama" Nenne na murmushi tace "Daga mu sai kayan jikinmu fa ranki shi dade, dama ziyara ce kawai ba wani abu ba" Hajja tace "Ikon Allah, duk tunanina za ku mana kwana biyu, amma ya kamata gaskiya ku dawo da shirin kwana" Nenne tace "Gaskiya ne Ranki shi dade" Daga part din Hajja masu aiki suka yi ma Nenne da Aunty Murja rakiya zuwa bangaren Mami don can aka kai masu abinci, nan din ma Nenne tace a koshe suke iya fruits kawai suka sha sai su alkaki da dublan da suka ci, ba yanda Mami bata yi dasu su ci abinci ba suka ki. Bayan sun yi sallan la'asar Mami tace "Ai Yariman ma ba shi da lafiya Hajiya, shi yasa ma zo gaishe ku ba yana can kwance sh Nenne tace "Subhanallahi, ai kuwa daxu nasa Murja ta kirasa ta sanar masa za mu shigo Gidan Sarki don hatta ita Khaleesat din bata san da zuwan mu ba wallahi, to Murja bata samesa a waya ba ashe bai da Isfiya bawan Allah" Mami tace "Wallahi kam bal ji dadi ba" Nenne tace "To Allah (Ubangiji ya basa lafiya, Allah ya sa kaffara ne" Marni tace "Ameen, bari in raka ku can bangaren nasa sai kuyi masa sannu" Nenne tace "Eh gaskiya kam ya kamata" Mami ta rakasu har part din Ajay suka zauna babban parlor, ita kuma ta karasa cikin Parlonsa, zaune ta samesa yana shan fruit ga darduma a shimfide parlon alamar sallah ya idar, he looks much better akan few hours ago, tace "Ka tashi baccin Junaid?" Ya sauke idonsa yace "Na tashi" Tace "Ya jikin fa?" Yace "Da sauki" Mami tace "Kakar Halysaah ce suka zo, ka fito ku gaisa za su koma ne yanxu" Ajay ya daga kai da sauri ya kalli Mami, ko me ya tuna sai kuma yayi maza ya sauke kai bayan sun hada ido, Mami na kula da tun safe yaki yarda ya hada ido da ita yanxun ma by mistake hakan ya faru, yayi kasa da murya yace "Mami ko dai ka kice ina bacci" Mami ta kallesa daga har kasa tace "Ko ba bacci ba, dalia tashi mu fita Malam, gida za su koma, Drivern da zai maida su ma na jira a waje" Ajay bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba, Mami ta juya ta fita ta koma can wajensu Nenne, da kyar Ajay ya mike ya fita daga Parlonsa, yana shiga Main parlor ya zauna kan Carpet yana gaida Nenne da Aunty Murja kansa a kasa, Nenne ta amsa cike da damuwa tace "Sannu Ahmad, ashe baka ji dadi ba, Allah Ubangiji ya baka lafiya ya sa kaffara ne" Bai dago kansa ba yace "Ameen Kaka" Aunty Murja ma tayi masa fatan samun sauki, yace "Ameen, ya Jeeddah fa" Aunty Murja na murmushi tace "Tana nan lafiya wallahi Yarima" Basu fi minti biyar a part din Ajay ba Mami ta mayar da su bangaren Hajja za su mata sallama, tsadaddun atamfofi biyar Hajja ta sa aka debo ma su, sai turarurruka kusan kala goma, sannan ta hada da dubu dari a kan kayan, ta kuma dage in dai za su bar Bauchi su zo ayi sallama, Nenne dai sai godiya take mata haka ma Aunty Murja, Mami na kallon Nenne tace "Tunda za ku kara kwanaki a Bauchi ai da kun bar takwaran Hajja wajen yayarta tayi mata kwana biyu" Hajja tace "Gaskiya kam, ma naga ai duk anyi hutun makaranta Baby ma yau aka je daukota daga makarantar su, kilan ma sun kusa yanzu haka" Nenne tace "To shikenan ranki shi dade sai ta zauna din har zuwa sanda za mu koma in sha Allahu" A haka Mami tayi ma su Nenne rakiya zuwa gun mota..... Maganganu ne fal cikin Nenne amma ba daman yi, har sai da suka bar gidan a motar da zai maida su gidan Aunty Murja sannan ta kalli Aunty Murja tayi kasa da murya tace "Ke Murja wannan matar da ta mana rakiya fa kamar Uwar Jawwad ce in dal ba idona ke yaudarata ba, har gida fa tayi gayya suka je suka ci mana mutunci babu abinda suka mance basu gaya mana ba daga karshe tace dan ta bazai auri Bazawara ba, muka ci kukan mu muka gode Allah, to sai kuma gashi naga mun zo....." Da sauri Aunty Murja tayi ma Nenne alamar tayi shiru ga dreba, Nenne tayi maza ta rufe bakinta tana zare ido, bata sake cewa komai ba a motar, amma fa kanta ya gama kullewa ganin irin tarban da Mami tayi masu, duk da a farko ta ma kasa hada ido da su, to ko dai kawai kamanni ne. Bayan tafiyarsu Nenne Dr din dake duba Khaleesat ta zo ta d tayi mata injections dinta sannan ta wajen karfe biyar Hajja ta mike tana kallon Noor dake zaune parlon don Khaleesat tayi bacci tun da aka mata allura, Hajja ta sa daya daga masu aikin dake Part din nata su kai Noor wajen Mami don ita part din Jay take son tafiya don yanayin da ta gansa daxu taga alamar magana ya shigo yi mata sai kuma ga kakar Khaleesat, Yana zaune Parionsa ta samesa yana kallo, ta zauna kan kujera tace "Ina Hadiyah?" Ya jinginar da kansa da kujera bayan ya rage volume din TV din without looking at her yace "I don't know, kilan tana can cikin gida" Hajja tace "Maimakon ta zauna ta kula da kai baka da lafiya sai ta tafi gantali cikin gida?" Shi dai bai ce komai ba don shi rabonsa ma da ganinta tun wajen 12 na rana da ta shirya ta ci kwalliya ta tafi can wajen uwarta da yan gidan, Hajja tace "Amma jikin da sauki?" Yace "Na ji sauki" Tace "To an kawo maka abinci kuwa tunda ita gantalalliyar bata nan?" Duk da bai ci ba yace "Na ci" Hajja ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma tace "Daxu ka shigo kamar zaka min magana sai ga baki sun shigo" Ya girgiza kal yace "A'a, naje daukan abinci ne" Hajja tayi shiru kallonsa, ya gyara zama yace "Na ji za ayi meeting bayan Magrib, don Allah Hajja ina son ki nema min alfarma gun Mai martaba Ina son zan koma UK in nemi aiki a can" a hankali Hajja tace "UK kuma Jawwad?" Mace "In sha Allah" Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Kasan bazai amince da haka ba Jawwad" Jay yace "In ke kika yi masa maganan nasan zai amince" Hajja bata sake cewa komai ba a Parlon, after a while ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Ka je can bangarena ka sameni nan da minti sha biyar" Daga haka ta mike ta fita daga parlonsa, bangaren Ajay ta nufa zata dubasa, ya fito daga kitchen kenan rike da cup din Coffee Hajja ta iso corridor din, ta bude kofar Parlonsa ta shiga ya bi bayanta, ta zauna kan kujera tace "Kajl dama dama kenan" Bai ce komai ba ya zauna sannan ya gaisheta ba tare da ya kalleta ba, tana kallonsa tace "How are you feeling now?" Shi dai bai dago kansa ba a hankali yace "Alhamdulillah" Hajja tace "Tunda jikin ka da sauki kaje ka duba matar ka" Sai da gaban Ajay ya fadi jin abinda Hajja tace, yayi yana juya Coffee din hannunsa da s a hankall, Hajja tace "Ko kuma ka tashi mu tafi, tana can bangarena..." Da sauri Ajay yace 'A'a sal anjima Karfe shidda saura Jay ya shigo parion Mami ta dalilin kiransa da tayi a waya, zaunawa yayi kan kujera donsa a kan TV yace "Gani Mami" Mami dai ta ci gaba da dama fura da take, Noor na zaune kasan carpet tana kallon Tv, tun daxu take son komawa part din Hajja taje gun Khaleesat amma ta kasa gaya ma Mami, Noor ta gaishesa, jin bai amsa ba Mami tace "Ana gaishe ka" Bai cire idonsa akan TV ba Without interest ya amsa a takaice, Mami dai ta ci gaba da abinda take, ya kara kallon Mami don barin parlon yake son yi yace "Mami kin yi kirana" Mami tace "Fura da nono ne gashi nan ban gama damawa ba" Yace "A'a bazan sha ba, na koshi" Yana fadin haka zai tashi Mami tace "Ka jira in gama ka tafi da shi, duk sanda ka so sha sai ka sha" Shiru yayi bai ce komai ba amma ransa bal so ya tsaya din ba, after some minutes Mami ta kalli Noor tace "Je kitchen ki dauko cup in zuba maki Noor" Noor ta dan yi murmushi tana girgiza kal tace "Na koshi" hatta muryarta Mami jin sa kamar ne Khaleesat, Jay ya mike à Laka yace "Mami idan anyi sallah zan dawo Dai dai nan aka bude kofar parlon sai ga Hadiyah ta shigo, kallo daya tayi ma Mani sai kuma ta kalli Jay ta hade rai tace "Sni ne tun daxu nake neman ka ashe nan ka zo ka zauna.... Mami ta daga kai ta kalli Jay tace "Je ka, zan bada furan ma...." Hadiyan ta wani kalleta, sal kuma ta tabe baki ts juya ta fice daga parlon without noticing Noor, Jay ya nufi kofa ya fice daga parlon. Bayan Magrib Ajay ya dake ya fita daga part dinsa zai je bangaren Hajja, kansa a kasa yake tafiya slowly yana sanye da thick Jacket dinsa ya saka har hulan Jacket din da ya rufe har kusan goshinsa kamar wani Villain, hannunsa duk biyu na cikin aljihun jacket din, har lokacin jikinsa a sanyaye yake sannan ba wal wani karfi yaji ba sai karfin hali, duk baccin da ya dinga yi yau Khaleesat kawai yake gani a baccin nasa, condition din da take ciki ya tsaya masa sosai a rai duk da halin da shi ma yake ciki but gaba daya hankalinsa na kanta, he couldn't sleep all through yesterday a haka ya isa part din Hajja kansa a ka bude kofar parlorn a hankall ya shiga cikl ya daga kai, ido hudu suka yi da Jay dake zaune parlon tare da Hajja. HALYSAAH PAGE 149... Ajay ya sauke idonsa kamar zai juya ya koma, sai kuma bai yi hakan ba ya karasa cikin parlon ya zauna kan kujera ya gaida Hajja ba tare da ya hada ido da ita ba, Hajja dake kallonsa tace "Lafiya lau Ahmad, ya jikin?" Ajay yace "Alhamdulillah" Jay dai danna wayarsa kawai yake kansa a kasa, after some seconds ya mike yana kallon Hajja yace "Zan je in ci abinci...." Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "To shikenan" Kofa ya nufa ya fice daga parlon, Hajja ta kalli Ajay tace "Ka shiga ka duba matar ka tana wancan dakin....." Ajay dai bai ce komai ba, Hajja tace "Sarki na parlonsa warhaka ko?" Ajay yayi shiru, sai kuma yace "Ko suna masallaci, sai anyi isha'i yake dawowa cikin gida...." Tashi Hajja tayi ta fita daga parlonta, Ajay ya bi ta da kallo, sai kuma ya mike walking slowly ya nufi Bedroom din da Khaleesat take, he was so tensed amma haka ya dake yana tafiya toward the room.... Khaleesat na zaune daki tare da Yakumbo dake mata magana cikin ladabi da kwantar da murya, ita dai juya pepper soup din bowl din hannunta kawai take a hankali idonta a kasa, Yakumbo ta kara yin kasa da murya tace "Don haka ki saka a ranki wannan lamari da ya faru daga darajanki yayi a wannan masarauta me albarka, duk masu danganta ki da bazawara sun ji kunya ainun, na dade banga Hajja cikin wannan farin cikin da take ciki daga jiya zuwa yau ba a gidan nan, nasan har sarki sai da ya samu wannan labari me dadi, kuma babu inda labari bai je ba lungu da sakon masarautar nan na cewa ke Budurwa ce, to wannan ma kadai ya isa yasa ki yi farin ciki a ranki ki kwantar da hankalin ki, abinda zamanin kakanninmu har shela ake yi sannan sai an ajiye wannan zanin gado kowa ya shaida saboda tarihi, don haka nake rokanki ki dubi Allah ranki shi dade a matsayina na warce tayi uwa dake nake cewa kiyi hakuri kar ki kullace mijinki, in ma zaki nuna masa fushinki kar ya wuce na yan mintoci, shi ma ya shiga damuwa sosai baki ga yanda ya koma ba daga jiya zuwa yau duk ya fita hayyacinsa, ko abinci baya iya ci ga zazzabi me zafi da yake yi har sai da likita ya zo dubasa daxu da safe, amma hakan bai hanasa dinga tambayata halin da kike ciki ba, duk shiga idan nayi bangarensa wallahi sai ya tambayeki, ranki shi dade kin san yanda damuwa ke wahal da shi kuma bashi da me kwantar masa da hankali a yanxu sai ke a gidan nan, kema kar ki ce zaki juya masa baya don Allah" Khaleesat ta daga ido tana kallon Yakumbo, da sauri Yakumbo tace "Allah ya huci zuciyarki idan maganganu na sun bata maki rai Gimbiya, Allah ya baki hakuri, ayi min afuwa, a gafarce ni don Allah ba da wata manufa nayi ba wallahi" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, dai dai sanda aka bude kofar dakin, sosai gabanta ya fadi jin kamshin turarensa amma taki kallon hanyar kofar, Yakumbo na ganinsa ta hau jera masa gaisuwa cikin girmamawa har ya karaso cikin dakin, Khaleesat ta ajiye bowl din pepper soup din hannunta a hankali ba tare da ta yarda ta kalli direction dinsa ba ta kwanta ta juya ma kofar dakin baya tana jin hawaye masu zafi na sauka idonta, tuni Yakumbo ta mike ta fita ta bar masu dakin ta kullo kofa, Ajay na ta tsaya yana kallonta saboda rashin courage din karasawa kusa da ita, he is feeling so bad and guilty at the same time, bai ma san ta inda zai fara ba, bayan few minutes ya dake ya fara tafiya a hankali har ya isa kusa da gadon ya duka on his knee yana kallonta, bai samu kwarin gwiwan tabata ba don bai san yanda zata yi reacting ba, ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Jeeddah.... i am truly sorry! i am sorry I made you pass through all this, don Allah kiyi hakuri" Kasa ci gaba yayi har sannan idonsa a lumshe yana jin wani abu game da ita a ransa wanda yake ta dannewa yana ignoring for a year now, ita dai shesshekan kuka take hawaye na zuba idonta ta ki cewa komai don wani haushinsa ne cike zuciyarta at the same time maganganun da Yakumbo ta dinga yi mata for more than 15 minutes a dakin na mata yawo a kai, bude idonsa yayi a hankali moment din da ya amshi pride dinta na dawo masa kai and how he felt at that moment, har yanxu ganin abun yake kamar a mafarki it was something he never saw coming, tambayoyi ne iri iri a ransa suka samu waje suka zauna da yake bukatar amsar su, bai taba jin ya kagu ya samu amsan wani abu da ya sha masa kai ba kamar tambayoyin nan da suka yi occupying every part of his heart, he was so desperate about getting the answers, kuma ba a kasar nan yake son jin amsoshin ba, may be Maldives amma kuma visa din kasar might take a long process, Sai kuma Zanzibar ya zo masa rai, within 48 to 72 hours za a iya samun Visa din Tanzania, bai san sanda ya zauna gefen gadon ba ya dagota not minding how she will react kawai ya rungumeta sosai jikinsa ya daura lips dinsa kan gashinta ya lumshe ido cikin breaking voice yace "I'm..... I am sorry Jeeddah, I am very much sorry, it wasn't intentional" Knocking din kofar dakin aka yi, hakan yasa Ajay ya kwantar da ita ya mike daga kusa da ita ya koma baya yana kallon kofar, ta kara juya masa baya har sannan hawaye bai daina zuba idonta ba. Mai martaba na zaune Parlonsa yayi shiru yana kallon Hajja at the same time yana sauraronta with full attention, Hajja tace "Don haka wannan magana da na kawo maka yafi zaman meeting din da aka tara yan gidan nan za ayi, akan me zaka zuba ido zumunci ya dauko hanyar lalacewa haka a gidan nan babu wani effort din gyarasa? Kai ya ma lalace, a halin da ake ciki yanxu dai komai ya tabarbare mana a masarautar nan, Farko ka dau budurwar wannan ka aura ma wannan saboda wasu dalilai naka, yanxu kuma ka dau title din wannan ka mayar ma wannan, who does that pls? me yasa baka tsayawa kayi tunanin abinda zai je ya dawo Yusuf?" Cikin nutsuwa Mai martaba yace "Duk abinda nayi Hajja idan aka tsaya aka duba daga karshe sai aga hakan shi ne mafi alkhairi for everyone, take for example title din da na kwace hannun Junaid, Ahmad Junaid is never fit to be a king in the future, ba shi da criteria din zama sarki wataran a masarautar nan, he is tough and aggressive most time, worst of all baya behaving irin na 'ya yan sarakuna, wani dan sarki ne kika taba jin bashi da aiki sai dambe da mutane tun daga cikin gida har zuwa mutanen gari? Always throwing fist now and then, beside na lura title din ma baya gabansa, baya ba title din value kamar dai tilasta shi aka yi yake rike da shi, misali na gaba.... wannan yarinya da na aura ma Ahmad Junaid, with the way things are going now in this house da ace Jawwad aka aura ma yarinyar nan zata yi rayuwa ne cikin matsi da takura a gidan nan baza kuma ta taba jin dadin zaman aure ba, and Jawwad can not prevent that duba da mutanen dake zagaye da shi, Hadiyah ma kadai bazata bari yarinyar ta zauna lafiya ba, ko yanxu da ba mijinta take aure ba ki duba abubuwan da suka faru of recent, sannan Fulani Aseeyah ta kawo min wasu complain marasu dadi akan Hadiyah, wanda har da shi za a kawo a zaman meeting da za ayi...." Hajja ta katse Mai martaba tace "A'a kar wanda ya sa min jikata a bakin duniya Yusufa, kar ma a fara sako zancen Hadiyah a meeting din nan, duk ina da labarin mugayen abubuwan da Aseeyah ke yi mata a gidan nan, in taje bangarenta ta koreta, har da shi yasa na taho Bauchi bayan Dethroning din Junaid da kai da kinsmen dinka ku ka yi without even letting me know, idan Aseeyah ta mance wacece Hadiyah gwara a ankarar da ita tun wuri, tunda ita bata da mutunci bata da tsoron Allah" Sarki ya girgiza kai cikin nutsuwa yace "Amma Hajja baza a zuba ma Hadiyah ido a gidan nan tana abinda taga dama marasu kyau ba, nima ta min laifi biyu a yan kwanakin nan, na farko tayi ma matar Junaid sharri wanda hakan da ba karamin tarnishing din Image din masarautar nan zai yi ba banda Allah ya taimaka akwai shaida da yayi disclaiming allegations dinta, na biyu kuma ta min karya, ni kuma kinsan babu abinda na tsana irin a min karya, amma duk nayi overlooking hakan, Hadiyah 'ya ce a wajena nima, bazan zuba ido tana wasu abubuwan da bai dace ba in ki daukan mataki akan haka, duk korafin da Aseeyah ta kawo a kanta abu ne da zata iya aikatawa Hajja...." Hajja ta tabe baki tace "To kuma in zaka mata gyara ko zaka mata fada lallai ne sai an tara duk yan gidan nan da kullum burinsu su ga wani abu mara dadi ya taso ta yanda za su yi barbadi da shi su koma gefe suna mana dariya? Ina laifin in ma zama za ayi akan Hadiyah ayi sa just between us cikin rufin asiri?" Mai martaba ya gyada kai yace "To in sha Allah Hajja" Hajja tace "Meeting din ma gaba daya a soke shi kowa ta koma gidanta, dama ai akan Dethroning din Ahmad Junaid ne za ayi meeting din kuma nice na bukaci ayi zaman, don haka kowa tayi tafiyarta zuwa gobe anyi canceling meeting din kawai, matar Junaid na kwance ba lafiya kuma duk sun san musabbabin rashin lafiyar nata amma babu er iskar da ta shigo takanas da sunan dubata saboda bakin ciki da hassada, hatta Gimbiya Firdausi bata shigo dubata ba amma suna zaune suna jiran ayi meeting su nadi abinda za su nada su tafi da shi, to daga yau duk wata magana da bata shafi Welfare din Masarautar nan ba gwara mu yi iya mu kawai" Sarki dai yayi shiru bai ce komai ba, Hajja ta gyara zama tace "Sannan shin Yusufa ina son sanin ko yanda Jawwad da Junaid basa ga maciji a gidan nan abun farin ciki ne a wajenka da ka kasa daukan mataki a kan haka ka zuba masu ido?" Sarki ya daga kai ya kalli Hajja, sai kuma calmly yace "I know nothing about that Hajja, considering the fact that Junaid basu dade da dawowa kasar ba, kuma normally muke karatu tare da su duk bayan sallahn asuba i didn't notice that, sam ban kula da haka ba tunda shi dama Junaid ba shigowa fada yake ba unlike Jawwad that is together with me mostly" Hajja tace "To yau watanni kusan shidda kenan daga Junaid din har Jawwad babu me cewa dan uwansa ci kanka, duk kuma akan wannan abun da kayi, ni na zata komai ya wuce a wajensu sai da na zo jiya naga ana nan jiya e yau...." Mai martaba ya duba agogo jin an fara kiran sallan isha'i, Hajja tace "Idan ka dawo masallaci zan dawo mu ci gaba da magana, before then ka gaya ma Fulani ta sanar ma Gimbiya Firdausi ita kuma ta gaya ma kowa babu wannan meeting din da suke zaman jira" Mai martaba dai bai ce komai ba har Hajja ta fita daga parlon, jinginar da kansa yayi da kujera abinda Hajja ta fada masa ya tsaya masa a rai sosai, bai taba noticing Jawwad da Junaid basa magana ba, don after every subhi prayer as usual yanda aka saba duk ana gaisawa kafin a fara karatu kuma suna yin hakan a gabansa, kila kawai hadasu zai yi tare su tafi Ethiopia zuwa wajen dangin Mahaifiyar Junaid, it's been 3 years now rabon Junaid da zuwa can din dama (To Alhamdulillahi za aje Ethiopia wajensu Rukky bjw, Moon, Mom twins, parrot, Jiddah, Summy, Yuguda, Aunty Zahrah, da dai sauran dangin uwar Ajay da suka yi bake bake a Halysaah conversation...)" Tun da Mai martaba ya sanar ma Aunty batun janye meeting tasan kawai yayi convincing din Hajja ta hakura an bar ma Jay title din Yariman kenan, ita sai a yanxu ne ma ta fahimci ashe tafi tsanar Jay akan Ajay ganewa ne kawai bata yi ba, ta yaya Sarki zai dinga fifitasa akan ko wani yaro a masarautar nan, bakin ciki take ji kamar ya kasheta duk da assurance din da Hajiya Nafisa ta gama bata ta waya yanxu akan ta zuba ido taga abinda zai faru next, ta sauke wani ajiyar zuciya ta mike ta tafi bangaren Walid taga ko ya ci abincin da ta kai masa daxu don kullum sai ta lallabasa yake cin abinci, kamar kullum yana zaune a yanda yake a dakinsa tun bayan da incident din nan ya faru tsakaninsa da Ajay, ga abincin a ajiye dakin ya ki ci, Aunty tace "Hannun bai dena zugin bane Walid?" Yaki ce mata komai, fuskar nan nasa a murtuke kamar kullum, Aunty tace "Wai Walid ta yaya zaka samu lafiya kana kin cin abinci? maganin ma sai an tilasta ka kullum sai nayi fama akan ka ci abinci ka sha magani, da wanne kake son inji? Da bakin cikin abinda ya dameni a gidan nan ko kuma da bakin cikin halin da kake ciki?" Ya fara huci yana daga kirji yace "Yanxu shikenan kema kin zuba ido a gidan nan an maida ni dan iska mara galihu, dubi abinda Junaid yayi min amma har yau ba a dau wani kwakkwaran mataki a kansa ba sai sauke sa a Yarima, title din da bai damu da shi da rashinsa ba, is that enough punishment for him bayan nakasa ni da ya so yi, ga hannuna ya karya min, kuguna ko zama bana iyawa sosai har yanxu, To duk ba ma wannan ba Momy, maimakon da aka saukesa a nada ni Title dinsa in compensation sai a wani ba Jawwad sai kace ni din agola ne a gidan nan? Ko dai da ni kika zo gidan nan ne Momy? Jawwad fa aka ba matsayin Yarima maimakon ni da nake dan sarki na biyu, To wallahil azeem bazan kyale Junaid ba, wallahi sai na dau fansa tunda anki bi min hakkin abinda yayi min a gidan nan daga karshe agola ma aka mayar da ni, to ina me tabbatar maki Junaid bai doki banza ba don Allah sai na dau mummunan fansa akan sa Momy" Cike da takaici Aunty tace "Daukar fansa ya wuce ka dauka akan Jawwad da ya zame maka barrier din da yayi maka cikas na samun title din Yarima a masarautar nan? Ai Jawwad shi ne babban wanda zaka dau fansa a kansa ba Junaid ba, don mahaifinku ya fifitasa ya kuma fi daukansa da muhimmanci akan kai da Junaid din, kana gani fa duk wani abu shi sarki ke dorawa a kai a maimakon ku da ku ke 'ya yan cikinsa, duk Jawwad yayi bake bake ya kwace matsayin ku kuna ji kuna gani a gidan nan, yanxu haka idan bamu yi hankali ba shkkn sarauta tayi nisa da mu har abada sai dai labari, gwara a sanda Junaid ke rike da title din kai kanka kana jiyo kamshin sa a kusa da kai, amma a yanxu kam kwata kwata ya mana nisa Walid, Hadiyah na haihuwan da namiji shikenan kuma, don haka ka dau duk fansan da zaka dauka kan Jawwad, in kana da halin kashesa ma ni ban ki ka kashesa ba zan baka goyon baya dari bisa dari, kawai dai ka bi a sannu ta yanda babu wanda Zai zarge ka, balle ma babu me zarginka tunda an san da Junaid Kake da matsala ba Jawwad ba" Walid dai sai kallon uwar tasa wake yana huci yana nazarin abinda ta fada. Gimbiyah Firdausi ma kallon Hajiya Habibah tace "To ke amma Habibah a ina kika icewar Hajja zata umarci Sarki ya mayar ma Junaid title dinsa har kike gaya mana jiya?" Hajiya Habibah tace "Wallahi daga majiya me karfi naji wannan batu Gimbiya, abun da mamaki cancelling meeting din da Sarki yayi at die minute, kuma Sarki bai taba canceling meeting ba barin yanda kowa ke zaune gidan nan bai koma ba saboda meeting din" Kilishi tace "Tunda muka ga haka kilan Hajja bata yi convincing dinsa na mayar ma Junaid title dinsa ba kenan, ko kuma ya kawo mata wasu hujjoji da suka gamsar da ita ya bar ma Jawwad din, ni hakan ma ya min wallahi dama kuma fatanmu kenan dai dai mu wayi gari wataran mu ga buzu a matsayin Yarima karami" Hajiya A'isha dai taki tofa nata duk da deep down she is very happy da aka bar ma Jawwad don inda taje a mata aiki an nuna mata probability din auren Junaid da Iklima is very low, amma na Jawwad is very high, ita ma Kilishi dadi ne ya kusa kasheta don plan dinsu zai fi tafiya dai dai akan Jawwad instead of Junaid, in sha Allahu sai sun kawo karshen Ummi da Mami a gidan nan. Ummi ce ta shigo parlon Hajja ta zauna tana kallonta tace "Hajja yanxu nake samun labari wai anyi canceling din meeting din da za ayi bayan isha'i?" Hajja tace "Eh ni nace ayi haka, don duk abinda za a fada a meeting din abu ne da ya shafemu ba wasu ba Ummi, na kuma gamsu da hujjojin da kika kawo da wanda Sarki ma ya kawo min na kan cewar a bar ma Jawwad crowned prince din, kuma abinda yayi Junaid shi yayi Jawwad, dalilin da yasa naki a ba Jawwad Yarima tun farko dama saboda uwarsa ce ba wani abu ba, ni kaina sai bayan da kika yi magana naga rashin dacewar a sake cewa za a amshi title din a mayar ma Junaid din kuma, Allah ya sa hakan da Sarki yayi shi ne mafi alkhairi garemu baki daya, shi kuma Junaid zai iya basa wani title din daban" Ummi ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ranta fari kal don tun jiya take kokarin gamsar da uwar tata akan cewar a bar ma Jawwad title din kar abun ya dawo kamar wasan yara nan kuma for her selfish interest ta dinga yin hakan, amma jiya kwata kwata Hajja taki daukan hujjojinta ta dage lallai sai an maida ma Junaid title dinsa, daxu da safe kuma da Hajja suka zauna da sarki shi ma dai yayi convincing dinta da maganganun da yayi, shi ne har ta saduda da batun mayar ma Junaid title dinsa. Jay na zaune parlon Mai martaba kansa a kasa ta dalilin kiran da yayi masa, after some minutes Mai martaba yace "Jeka ka kira min Junaid ku dawo tare" Jay ya daga kai ya kalli Sarki, sai kuma ya sauke idonsa kasa, a hankali yace "To ranka shi dade" Mikewa yayi ya nufi kofa, Mai martaba ya bi sa da kallo har ya fita, Jay ya koma part dinsa ya zauna kan kujera ya dau waya yayi dialing number Hadiyah don bata bangaren, sai da ya katse ya sake kira sannan ta daga tace "I am coming" Daga haka ta katse wayar ba tare da ta jira taji me zai ce ba, bayan dan lokaci sai gata ta shigo parlon tana yatsine fuska tace "Abincin fa yana ajiye a kitchen kake kirana bayan kasan ina wajen Ummi ne, kuma har yanxu baka tura min kudin ba gashi gobe Shahuda zata zo ta rakani siyayyan tunda ita ta san designers Abaya" Without looking at her yace "Ki tafi ki gaya ma Junaid Mai martaba na kiransa" Hadiyah ta wani kallesa tace "Tabdi, wallahi bazan je ba, what is my business with him da zan je part dinsa, mutumin da ya gaggaura min mari kaki yi masa komai a kai, wallahi bazan je ba meye hadina da wani Junaid" Tana kai wa nan tayi tafiyarta dakinta, Jay ya bi ta da kallo, yana ta zaune bayan ya tuna Sarki na jiransa ya mike ya nufi kofa ya fita daga parlon. HALYSAAH PAGE 150... Bangaren Mami Jay ya nufa yana tafiya kamar wanda bai son tafiyar, ya bude kofar parlon yana kallon ciki, Mami dake zaune cikin parlon ta daga kai tana kallonsa, ya karasa ciki ya zauna kan kujera kansa a kasa, Mami dai sai kallonsa take cause he doesn't look okay, A hankali ya gaisheta, Mami ta sauke idonta daga kallonsa tace "Lafiya lau, ya jikin nakw?" Yare "Na ji sauki" Mami tace "Ina son zan je wajen Mai martaba na jirana yanxu, sai dai zuwa anjima idan na dawo" Noor ce ta shigo Parlon da sallama tana rike da warmer din zogale da Mami ta bata ta kai ma Hajja, warmer biyu Mami ta bata daya na Hajja, daya na Khaleesat sai gashi ta dawo da na Hajja, ta duka kusa da Mami tace "Wai Hajja tace ita ta koshi bazata ci ba" Mami tayi shiru tana kallon warmer din, don tasan Zogale is among Hajja's favourite, bata taba yi mata tace bazata ci ba sai yau, Mami tace "To shikenan, ki kai kitchen ki ajiye" Noor ta daga kai ta gaida Jay da ya maida dubansa kan TV, har ta mike ta tafi zata kai Warmer din kitchen bai amsa gaisuwar ba kamar dai bai ji ba, sai da ta shiga kitchen Mami tace "Jawwad gaisheka fa tayi?" Bai kalli Mami ba a takaice yace "Ban ji ba" Mami dai kallonsa kawal take babu ko kiftawa, after few seconds yace "Mai aikin ki ta tafi ne?" Mami tace "Me zata maka?" Yace "Mai martaba ke kiran Junaid, in tana nan ki aiketa ta sanar masa" Mami tace "Ita Mai martaba ya aika kenan?" Jay yayi shiru bai ce komal ba, a hankali Mami tace "Yaushe ka zama haka Jawwad?" Jay ya kalli Mami jin abinda tace, Mami tace "Sarki ya aike ka shine zaka zo aikan wani? is this proper?" Jay dai bai ce komal ba ya sauke idonsa kasa, Mami bata sake ce masa komal ba saboda Noor da ta fito daga kitchen, Noor tace "Mami zan koma can" Mami tace "Baza ki kwana nan ba Noor?" Dan murmushi tayi tana wasa da hijab dinta tayi shiru, Mami dake ta Kallonta tace "To shikenan, ki tafi sal da safe" Noor ta gyada mata kal tara "Nanorda" Mana haka ta luva ta fita lana........kofar parlonsa bayan tafiyar Yakumbo da ta zo sanar masa sakon da Jay ya bata na cewar Mai martaba na kiransa, mamakin dalilin kiran ya dinga yi, haka dai ya juya ya koma cikin parlonsa still pondering on why the king sent for him, after some minutes ya fito ya nufi sashin sarki cikin rashin kuzari, rabon shi da zuwa side din sarki tun ranan da yayi prohibiting dinsa from doing so, yana kusa da part din Sarki ya ga Jay tsaye ya jingina da bango yana danna wayarsa, Ajay ya dauke idonsa har ya wucesa, sal da ya dan yi nisa yayi noticing Jay na biye da shi a baya from a reasonable distance. Ajay ya shiga parlon Mai martaba kansa a kasa, walking slowly ya tafi ya zauna favourite position dinsa a Parlon ya kasa hada ido da Sarki, sal ga Jay ma ya shigo shi ma ya tafi ya zauna inda ya saba zama, Cikin ladabi Ajay ya gaida Mai martaba har sannan bal dago kansa ba... Mai martaba yayi shiru na wani dan lokaci yana kallonsu kafin yace "Ina son kowannen ku ya fada min dalilin gaban da yake yi da dan uwansa, starting from you Junaid" Ajay was quiet bayan yaji abinda Mai martaba yace, bai taba zaton maganar da Mai martaba zai ush bai yi zaton dalilin kiran Mai martaba kenan ba, Sarki dai kallonsu kawal yake patiently yana jiran amsan tambayar da yayi masu, Bayan few seconds Ajay ya dago da kyar ya kalli Mai martaba cikin calm voice yace "Allah ya kara maka lafiya, ni ba gaba nake yi da shi ba" Sarki ya gyada kai sannan ya kalli Jay yace "Kai kuma fa Jawwad?" Jay ya girgiza kai yace "Ba gaba nake yi da shi ba ranka shi dade" Sarki yace "Ohk, space ku ka ba juna kenan?" Kusan a tare suka gyada masa kai, Mai martaba yace "Good, starting from you Junaid, Ina sauraron dalilin space din da ka basa" Ajay ya kasa cewa komal at first, ganin kallonsa sarki yake yana jiran amsa, yayi kasa da murya yace "Naga yana ignoring dina ne shi yasa i decided give him space Sarki yace "How did you understand he is ignoring you?" Ajay ya sauke idonsa a hankali yace "He doesn't want to speak to me tun bayan da ka daura mana aure da Jeeddah, May be he is thinking ni ne na bukaci a daura mana aure da ita, fun daga wannan lokacin yake avoiding dina, I tried speaking to him twice yana ignoring dina" Mai martaba yayi shiru bayan yaji abinda Ajay yace, can ya kalli Jay yace "Jawwad meye dalilin ka na ignoring dinsa, or let me put it this way, why are giving him space?" Jay ya kasa cewa komal kansa a kasa, hawaye ya ji ya kawo idonsa ya kai hannu yana share hawayen, Ajay dake kallonsa ya sauke idanuwansa a hankali, Mai martaba dai sai kallon Jay yake babu ko kiftawa, Jay ya girgiza masa kai kawai don ya kasa..............hankali yace "Jawwad..." Jay ya daura goshinsa a kan Knee din sarki wasu hawayen na sauka idonsa, sosai jikin Mai martaba yayi sanyi, and he became speechless, ya dinga kallonsa, after almost a minute a hankali Mai martaba ya dafa shoulder dinsa yace "Nayi hurting dinka ko Jawwad?" Jay ya girgiza masa kal har sannan bai cire kansa a Knee dinsa ba, Mai martaba ya daga kai ya kalli Ajay, hawaye ya gani a nasa idon shi ma alamar he couldn't stand seeing his brother crying, Ajay ya sauke idonsa a hankali, Mai martaba bal taba tunanin things will turn out this way ba, bai taba zaton things will get to this extent ba, abinda ya kara masa kwarin gwiwan aura ma Ajay Khaleesat bayan abubuwan da Mami ta dinga yi duk a zatonsa Jay was only covering for Ajay at the beginning don ya saba ya dauki laifin Ajay ya dora ma kansa komin girman laifin, tun suna yara haka suke, ya kuma yi la'akari da cewar duk zuwan da yayi America bai taba ganin Jay tare da Khaleesat ba sai dai Ajay, har cikin dakinsa da baya barin kowa ya shigar masa ya ga Khaleesat a kwance, Mai martaba ya sauke ido yana kallon Jay calmly yace "Gaya min yanda kake son ayi Jawwad..... Feel free and tell me what you want, ka gaya min abinda ke zuciyar ka, I ask for it" Jay ya girgiza masa kai har sannan bai dago kansa ba cikin breaking voice yace "Ina neman alfarman ka bari in koma UK in samu aiki a can ranka shi dade, i will prefer staying there, bana son zaman gidan nan kuma" Sarki ya dinga kallonsa jin abinda.........gathering muen courage ya kaili Mai martaba yace "in ka yarje min ranka shi dade ni zan İya sakin Jeeddah, i know it's taking him long to heal saboda ganinmu da yake yi tare, ni kuma i will never chose her over Jawwad, na kuma san ko na saketa ba lallai ya aureta ba, but if she is far away from us duk za mu mance komai, ta haka ne komai zai wuce kamar ba ayi ba" Jay ya daga kal yana kallon Ajay jin abinda yace, Sarki ma kallonsa kawal yake babu ko kiftawa, Mukhtar ne ya shigo parlon da sallama Sarki ya daga kai yana kallonsa ya amsa sallamansa, zaunawa yayi kan Carpet yace "Allah ya taimake ka, tun daxu kayi wasu baki biyu sun ce ka san da zuwan su, suna kuma kiran wayarka basu same ka ba" Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace "Ehh nasan da zuwansu Mukhtar, wayar tana wancan parion ne..." Mal martaba ya kalli Jay da Ajay a hankali yace "Za mu yi magana da asuba in sha Allah...." Daga haka ya mike ya nufi second parlor dinsa duk jikinsa a sanyaye, sal yanxu ya fahimci kalman da Hajja tayi masa 6 months ago da tace ya bar baya da kura, bal taba yin abu ya dawo yaji da bai yi abun ba sal wannan lokaci, he just realized the harm is more than the good. Har Ajay ya isa part dinsa bai san ya isa ba duk da dishi dishin da ya dinga gani a hanya, ya zauna kan kujera a parlornsa ya dau remote din AC ya kunna don wani irin zafi yake ji a jikinsa, ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi sosal, yafi minti goma a haka yana sauke numfashi a hankali kafin ya a mike mike ya shiga bandakiya...........Mamınsa, Mami na zaune kasan carpet kanta a kasa hawaye na zuba idonta, Hajja kuma na zaune kan kujera a parlon ta inda take shiga ba ta nan take fita ba kamar zata ari baki, Ummi dai na can zaune gefe ta daure fuska sal jefa ma Mami harara take, ga Hadiyah zaune kusa da ita tana matsar kwalla har da shessheka, Hajja na kallon Mami a fusace ta ci gaba da magana don kukan da Hadiyah take kara tafarfasa mata zuciya yake, tace "Ke haka na maki a sanda kike auren da na? Ko kin taba ganin na sa ido a sabgarki da Ahmadu Allah ya kai haske kabarinsa, wani irin mulki ne baki zuba ba a gidan nan Aseeyah na taba ce maki don me? Sai jikata ce zaki sako gaba da tsana da tsangwama ki hanata zaman lafiya ki hanata walwala tare da mijinta? Ko kin mance ni na haifi uwarta? A kanki kadai aka fara haihuwar da dava a......... duniya da zaki ce lallai lallai sai kin saka masa ido kin hanasa rawan gaban hantsi da matarsa? To wallahi tun wuri ki shiga hankalinki, banda akwal abinda kika kulla a ranki sau da nawa sau da nawa kike zaman gidan sarki? Ke da sai kiyi wata da watanni baki zauna a gidan nan ba amma saboda mugun nufin ki na saka jikata a gaba shi ne kika tattaro kika dawo masarauta kika tare gaba daya, to kuwa za su bar maki gidan ko kuma su bar maki kasar ma gaba dayan ta" Mami taji wani abu ya tokareta a zuciya banda hawayen bakin ciki babu abinda take yi, wai Hajja ta rasa gaban warce zata mata wannan cin mutuncin sai gaban Hadiyah, bata taba da ta sani irin wannan da take yi ba a kaf rayuwarta, tayi da ta sani babu lyaka, ina ma zata iya maida hannun agogo baya, ina ma ta varda sha............Da, date kanta tayı nawaye masu zati na zuba iconta, ko ba komal in bata ji dadi ta wajen Hadiyah ba zata ji ta wajen Khaleesat, sosai tayi nadama tayi regretting action dinta gashi ta jefa kanta a damuwa sannan ta jefa dan ta ma a damuwar da ya kasa healing har yanxu, banda ita me zai yi da wata Hadiyah?? babban bakin cikinta yanda Hajja ta sakata gaban Hadiyar da uwarta tana gaggaya mata maganganu marasu dadi wanda duk ba haka bane sharri kawal Hadiyah tayi mata, tun da Hadiyah ta tare a masarautar nan zata iya kirga sau nawa taje bangaren Jay balle ace ta takura su ta hanasu rawan gaban hantsi, bata taba hanasa yi ma Hadiyah komai ba na kyautatawa, wani lokacin ma idan taga wani abu ita ke nuna masa ya siya mata, ita kanta ta sha siya mata duk wani abu da tasan na gyaran mace ne, bata taba yi ma Hadiyah ko da kallon banza ba tun da ta tare a bangaren Jay, kwatsam rana daya Hadiyah ta dena gaisheta a gidan ko kuma in ta ganta sai tayi maza ta canza hanya, sai dai ta tafi can wajensu Hajiya A'isha ko ta tafi bangaren Aunty, idan kuwa ta kira Jay ko tana bukatar yayi mata wani abu sai Hadiyah ta daga tace yana bacci ko kuma tayi ta saka mata kiran a busy,............sakayyan, Jay da yayi tsaye bakin kofa duk yana jin abinda Hajja ke cewa Mami ya karasa cikin parlon yace "Hajja akan Hadiyah zaki sa Mamina a gaba kina duk wa ennan maganganun?" Hajja tace "An sa ta gaban, ita haka nayi mata? Da haka nayi mata ai da bata kai war haka a gidan nan ba, ita ba abun kunya bane ace ta hana er kanwar marigayi zaman lafiya a gidan mijinta?" Mami ta daga kai da kyar tana kallon Jay hawaye na zuba idonta tace "Kayi tafiyarka kawai Jawwad" Juyawa Jay yayi ya fice daga parlon, Ummi tace "To ai ba iya wannan ba Hajja, ta yaya zata dinga fifita bare akan Hadiyah a gidan nan? Kullum bata da aiki sai dora ma Hadiyah laifi duk ta bata ta wajen Mai martaba" Hajja tace "Wacece bare?" A fusace Ummi tace "Matar Junaid mana...." Hajja tace "A'a ba bare bace, kar ki sake ce mata bare a gidan nan, tunda har jikana ke aurenta to babu ta yanda ta zama bare Maimuna, kawai dai don ta cusa ma Hadiyah bakin ciki take yin haka, whereas ita bakin cikin zai kashe don babu yanda zata yi da auren Hadiyah da Jawwad...." Hajja na kai wa nan ta mike tana cewa "Ke ba a tsangwame ki ba duk mulki da isan da kika zuba a gidan nan shi ne zaki takura jikata, akan wani dalili? To wannan na daga cikin dalilin zuwana garin nan, babu wanda zai taba min jikoki in kyale" Tana kai wa nan ta nufi kofa Hadiyah ta mike ta bi bayanta da sauri suka fita tare, Ummi ta tabe baki ko kallon Mami bata yi ba ta mike ta bi bayan uwarta da er ta, Mami ta hi to do ballo bouque Juho idants hoto toho.............sillyu wa zuill Sund bangarenta ta shiga dakin da Khaleesat take tare da Noor, zuwa yanxu kam Khaleesat is getting much better, don kula sosai take samu wajen Hajja da Likitan dake dubata sai Mami, Hajja ta zauna kan kujera tana kallon Khaleesat tace "Zuwa gobe sai ki koma can bangaren mijinki ya ci gaba da kula dake ko Jeeddah?" Khaleesat ta sunkuyar da kanta don sai da gabanta ya fadi jin abinda Hajja tace, Hajja ta kalli Noor tace "Kin ci abincin kuwa takwara?" Noor ta gyada mata kai tace "Na ci" Bude kofar dakin aka yi duk suka juya, Hajja taga Hadiyah ce tsaye bakin kofar, ta wani daure fuska bayan ta jefa ma Khaleesat harara tace "Wajen ki na zo Hajja" Mikewa Hajja tayi tace "To mu je" Fita tayi daga dakin bayan sun dawo parlor Hajja ta kalli Hadiyah tace "Ya aka yi?" Kamar zata yi kuka tace "Kina ganin ya kulle kofar part dinsa ina ta kwankwasawa yaki budewa ko Hajja" Da mamaki Hajja tace "Shi Jawwad din?" Hadiyah tace "Wallahi, har kiran wayarsa nayi yaki dagawa" Hajja tayi shiru, can dai ta zauna kan kujera ta dau wayarta tayi dialing number Jay, sal da ya kusa katsewa sannan ya daga, Hajja tace "Jawwad akan wani dalili ka kulle ma Hadiyah kofa?" A takaice yace "Ta bi Baabarta kawal su koma Lagos, sai na neme ta" Hajja ta bude baki jin abinda yace, without waiting for her yace "Sal da safe" Daga haka ya katse wayar davon ya saka sa gaba......matsanancin ciwon kal throughout night din sallah yayi tayi, bal taba jin bai son asuba yayi ba a rayuwarsa kamar yau, gaba daya damuwansa na baya suka dawo masa fresh, he was so restless, ya canza position a dakin yafi a kirga, he needs to speak to anybody that will calm him down amma ya rasa wa, a hankali ya jawo wayarsa yayi dialing number Ammi yana fara ringing ta daga, daga daya bangaren tace "Ahmad...." Sauke idonsa yayi a hankali yace "Ammi" Ammi tace "Hope all is well dear?" Ya kasa ce mata komal, tace "Ahmad" Ya gyada kai da kyar yace "Ina ji Ammi" Tace "Tell me, me ya faru?" Ya rasa ta inda zal fara, har sai da ta kara kiran sunansa, cike da karfin hali ya fara gaya ma Ammi duk abinda ya faru a parlon Sarki jiya da daddare, Ammi was speechless jin maganar kamar ta wasan yara, Ya girgiza kai muryarsa na rawa yace "Amma ina jin kamar bazan iya sakinta ba Ammi, saboda... saboda ina sonta" Yana fadin haka yaji hawaye sun kawo idonsa, da kyar ya ci gaba cikin sanyin murya yace "Wallahi ina sonta Ammi, bazan İya sakinta ba, I don't know what will become of me idan nace zan rabu da ita, ban san yanda zan yi ba Ammi..." Kasa ci gaba yayi ya hade kansa da gadu, cikin kwantar da murya Ammi tace "Baza ka saketa ba Ahmad, ai ba garin gaba gaba ake ba da za ace ka saketa saboda Jawwad, shi ma Mai martaba nasan bazai bari hakan ta faru ba don wannan babban slap ne to the Emirate as a whole babu inda ake haka to calm tunda ba wasan yara bane abun, i want you to Cam down son, ka kwantar da hankalin ka, Khaleesat will remain ur wife for ever, babu ta yanda za ayi Dethroning dinka a basa title din sannan kuma ace ka saki matarka saboda shi, ko da kuwa bazai aureta ba wannan ba abu bane da hankali zai dauka...." Da sauri Ajay ya daga kansa jin anyi knocking kofar parlonsa, sosai gabansa ya fadi, don yasan kilan Mai martaba ne ya aiko ayi kiransa, da kyar yace "Someone is at the door Ammi, I will call you back" Ammi tace "Ohk I am waiting Dear" katse wayar yayi ya mike cike da karfin hali ya nufi kofar dakinsa ya fita, tsaye yayi bakin kofar yana kallon Jay dake zaune parlon nasa ya tallabi chin dinsa da hannu biyu, Ajay ya sauke idonsa ya karasa cikin parlon cikin sanyi jiki, sai a sannan Jay ya daga kai a hankali ya kallesa, Ajay bai yarda su hada ido ba ya zauna kan kujeran dake facing din Jay dake ta kallonsa. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************