*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* To my big sis, Hajiya Habiba Muhammad, words are not enough to express your worth and my love for you. I pray that Allah grants you the highest place in Paradise, fulfills your desires, and answers your prayers. I'm speechless You're even more than I imagine Wallahi. I dedicate this book to you, Hajiya Habiba Muhammad. You mean more than words can express you are everything I could ever ask for in a big sister. You treat me like your own little sister —I LOVE YOU deeply 🤍❤️ I couldn't introduce myself without mentioning you, Salma Ahmad Isah 🥰 I cherish you Salma, nasan ke ma kin san haka. If anyone is looking for another version of me, they’ll find it in you. NOTE... Labarin nan ya zo da sabon salo akwai abubuwa da yawa a ciki, sai mun taru mun yi hakuri sannan zamu iya isa gurin da nake son muje. Na san halinku abu kadan ku fara attacking mutum. Na fara rubuta labarin tun kamin na rubuta Hurriya, wani gari, da kuma taki zaman aure, amman Allah be ba ni ikon kammalawa shi ba sai yanzu, Allah ya ba mu ikon amfana da darasin da ke ciki.. *©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠* Page - 1️⃣ Bismillahir Rahmanir Raheem. Kai na daga sama ina kallon bakin hadarin da ya fara saukar da ruwa, iska mai karfi na kadawa kamar zata tashi gari. “Mamy.. Mamy... Ahhhh ahhhh ahhhh” Kasa na dawo da kaina na kalli saitin da dana yake, wanda ya kasance autism, sai ihu yake yana murza ido da nake kyautata zaton kasa ce ta shigar masa. Hawaye ne suka sauko min tare gumi, duk kuwa da kasancewar iska ne yake kadawa ko'ina, amman zafin nakudar yar da zan haifa ya tare duk wani jindadi da zai rabeni a lokacin. A hankali na dafa kangon dake gabana na jingina sai kuma na sulale kasa na zauna, sai ruwan sama ya fara saukowa, ďana ya fara ihu na fitar hankali, nakuda ta sallamomin da gaggawa, gani ya fara min nisa, numfashina ya fara yin sama... Babu kowa a tare da ni, babu wanda yace Emily, ki yunkura zaki iya, babu mai fada min haka ake yi ba haka ake yi ba, ba ni da gatan da wani zai damu da ni balle ya kai ni asibiti, zan iya haihuwa da kaina ko sai an sake fasa ni CS kamar wacan karon? A haihuwar ďana London haihuwata ta fari. Jin wani azababben zafi ya ratsa marata zuwa cinyata ya sakani ihu da dukanin karfina, a gurin da babu mai cetona. “Sannu miya same ki? Ko haihuwa ce? Me kike yi a nan? Wacece ke?” Na ji wata sabuwar murya, idanuwana suka yi arba da wata bakuwar fuska dake duke a gabana yana leken tawa fuskar, saukar ruwan sama da kuma zafin nakuda, ba su ba ni damar tantance waye tsugune a gabana ba. Na mika hannayena duka biyu na riko hannayensa ina numfashi daker, azabar nakuda ta hana ni magana. “Subhanallahi... Christen ce ke?” A kokarinsa na zare hannunsa daga nawa agogon hannunsa ya zame ya tsaya a hannuna sai na jimke agogon da karfi ina nishi mai karfi. “Am... Akwai wanda kika sani nan kusa?” Na girgiza kai alamar aa, to ni a kaf duniyar ma wa na sani balle kuma a kusa da ni. “Okay zan kai ki asibiti yanzu nan... Danki ne wacan...” Kai kawai nake iya daga masa, ni dai burina a taimake ni a raba ni da abun da nake ji a yanzu. Da alama maji karfi ne, domin cak na ji ya daga ni yana istigifari. “Astagafullah Allah ka yafe min ba da niya na taba ta ba” Ya saka ni a motarsa, be damu da lalacewar da jikina yayi ba, be damu da ihun da ďana yake kamar zai fasa kunne ba, be damu da banbancin addininmu ba, be duba talaucina da arzikinsa ba, haka ya ja motar da karfi yana tukin yana min sannu, yi hakuri mun kusa karasawa asibitin, kai kace ni din yar'uwarsa... ***  ***   *** Karar bude kofar dakin da take ciki ne ya dawo da ita duniyar tunaninta. A hankali take shafa tsadaden agogon dake hannunta mai ruwan zinari, hawaye masu zafi na sauko mata. “Emily...” Ta daga kai ta kalli mai kiran sunan nata ta cikin madubin dake gabanta. Da sauri ya karaso kusa da ita ya tsaya yana kallonta, a cikin kallonsa akwai tashin hankali, akwai kauna, akwai tsoro, akwai fargaba da suka rufe shi lokaci daya saboda ganin hawayenta. Risinawa yayi kasa a yayinta take zaune agaban madubi mai cike da kayan kwalliya. Fari ne, mai yalwatacciyar bakar fuska mai kama da bakin hadari, kallo daya zaka masa ka fahimci annuri da far'a ba su da muhalli a fuskarsa, sai dai kuma shi din kyakkyawa ne, namiji ne mai kirar mazaje. Sarkar Cross ce a wuyansa irin wadda ke wuyanta, banbancin tashi da nata tata karama ce tashi kuma babba ce wanda ta cika kirjinsa dake dauke da zanen tattoo. Dubansa ya kai kan agogon dake hannunta a take ya kara hade rai. “Har zuwa yaushe zaki daina dauko agogon nan dake tuna miki rayuwar baya?” Ta kalleshi da idanuwanta masu matukar kyau da daukar hankali, da bakin da yayi daidai da tsarin fuskarta ta furta. “Har zuwa lokacin da zan iya manta alheri” Ta maida dubanta a gurin agogon da take jin kamar shi din ya taimaki rayuwarta, a lokacin da mutuwa ta so ta kusantota. “Ko waye mai wannan agogon, yana da kirki, yana da tausayi, yana da kyakkyawar zuciya, shi din ya banbanta da sauran musulmi” Zabura yayi kamar zai dake ta cikin ihu ya rufe ta fada. “Babu banbanci tsakaninsu, babu banbanci tsakanin ko wane musulmi, kin gwada daya kin gwada biyu kin gani, baki bukatar wani ya baki labari, miye a cikin kanki? Meyasa kika kasa manta rayuwarki ta baya? Kina da komai yanzu, baki bukatar kowa I'm here for you and I Love you” Ya rumgumeta daga tsayen da yake sai ta fashe da kuka ta rikeshi sosai. Bayanta ya shafa yana maida numfashi a hankali tare da rarrashinta. “Kina da duk wani abun da kike mafarkin samu a yanzu Babe, kina da Luxury Home and Cars, kina da komai Babe” Dagowa ta yi daga jikinsa ta share hawayenta ta bude aljihun madubin ta saka sarkar ta mike tsaye ta shiga bandanki ta wanke fuskarta, ta cikin madubin dake bandakin take kallon kanta. Ta canja, hallitarta ta sauya, halinta ya sake, kyauta ya ninku, kyaun jikinta ya bayyana. “You can do this Emily, you have to do this, ke din a yanzu Emily ce ba wacan Emilyn ba, ke din a yanzu Emily ce, ba Aysha ba, jaruma ce baki bukatar kowa a kusa da ke” Ta fadawa kanta domin karfafawa kanta guiwa, daman waye zai karfafa mata? Idan ba ita din kanta ba, turawa suka ce when you have no one to push you push yourself. Takawa ta yi baya tana cigaba da kallon kanta sannan ta dauke idonta ta kalli kofar bandakin, ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kofar ta bude ta fita. Gaban madubin ta sake zaunawa ta fara shirya kanta, har ta yi kwalliyar ta gama Vito be ce mata komai ba yana zaune ya dora kafa daya saman daya, wayarsa a hannunsa sai dai duk abun da take jajayen idanuwansa suka kanta. Gurin da ta ware tufafin da zata saka ta nufa ta dauka ta nufi wani karamin daki ta canja tufafin sannan ta fito tana gyara gashinta dake hade da gashin doki attachment. “Kin yi kyau” Ya fada yana nufar gurin da take tsaye, ta yi kyau kam iyakar kyau, kyaun da ya wuce ayi mata kallo daya a dauke ido, yadda aka tsara hallitar fuskarta da kirar jikinta, kai kace ma ita ta yi kanta. “Ban san miyasa kika dage sai kin yi aiki ba, ban san manufar da kike son cin ma ba, na wadata ki da kudi, ban san miya hana zuciyarki natsuwa da hakan ba, arzikin da zaki je nema a wani gurin be taka kara ya karya na arzikin da na aje miki a nan ba, amman dai ko miye, zan goya miki baya saboda ina sonki ina son farincikinki sosai” Magana yake yana zagayeta kamar mai tantance komai na jikinta. “Ba arziki nake nema ba, so nake kawai na yi rayuwa irin na sauran mutane, ka canja ni kuma na canju, na watsar da komai ina rayuwa ne irin na mutane, karka ji tsoro” Ya tsaya daidai fuskarta har numfashinsa yana gauraya da nata. “Vito be san tsoro ba, amman shi tsoro ya san Vito shiyasa idan ya gan ni yake boya, you belong to me karki manta wannan” Ya sumbance ta. “Wish you all the best, fatar ki fara aiki a sa'a i love you, good luck on your new Job” Ya mata murmushi kadan ya shafa fuskarta sannan ya dauke hannunsa ya fice. Tsaye ta yi a gurin na wasu dakiku, sannan ta busar da iskar bakinta ta nufi wayarta da jakarta ta dauka ta fice daga dakin zuwa bangaren da ďanta yake. TURHAN POV. “Baka tafi ba har yanzu?” Ya mike tsaye yana kallonta idanuwa a raunace fuska dauke da damuwa. “Ammy...” Sai kuma ya kasa furta komai saboda yadda ta tsare shi da wani kallo irin na horo daga uwa zuwa ga danta. “Zamanka ba shi da amfani a nan, kasan ba zan taba barinka ka kwana a gidana ba, toh ba amfanin bata wuni” Ya bude baki sai kuma ya maida ya rufe a hankali ya taka zuwa kusa da mahaifiyarsa. “Ammy I'm sorry, na yi nadama kin sani, na tuba ki yi hakuri ki yafe min” Ya durkusa kasa ya rike hannayenta. “Me zan yi ki yafe min Ammy? Me zan yi ki yarda na yi nadama?” “Nadamar ka ba zata gyara abun da ka bata ba, ni ban kullace da komai ba, kawai alaka ce irin ta da na yanke” “Ammy mi zan yi ki fahimci na yi nadama? Mi zan yi ki yafe min? Ina cikin damuwa ina cikin matsala” “Na yafe maka Turhan na dade da fada maka haka” “Ba irin wannan yafiyar nake so ba, irin wanda idan zan bar kasar nan kike kewata, idan na zo kina murna da zuwana, mu zauna mu yi hira mu yi wasa da dariya, Ammy me zan ki min irin wannan yafiyar” Ya tambaya yana shirin fashe mata da kuka. “Zan maka irin wacan yafiyar da kake tsammani ne, only if Aysha ta yafe maka...” Ya girgiza kai. “Ammy karki yi haka, idan kika alakanta yafiyarki da Aysha to ba zaki taba yafe min ba, domin ban san ina Aysha take a yanzu ba, ban san inda zan ganta ba, Ammy idan kika yi haka ba ki min adalci ba...” A take ta daka masa tsawa. “Kai ka yi min adalci kenan? Saboda kai yarinyar nan ta bar addinin musulunci, duk wani gata da na so na yi mata na addinin musulunci ka ture, duk wata shimfida da na yi na yaye mata damuwar da wani ya saka ta ka nade shimfidar ka jefar, na shirya zama mata uwa saboda bata san wannan gatan ba, duk wani buri da nake da shi akanta da akanka ka ruguza shi, aikinka da yadda ka riketa yadda ka wulakantata ya goge duk wani karatu da na shimfida a cikin kanta cewar mu musulmai halinmu ba daya ba ne, a ranar da ka sauke ta garin nan da idona na ganta a gaban coci tana rokon su taimaketa, saboda tana ganin mu musulmai mun gaza. Turhan ka saka Aysha ta ji cewar mu musulmai ba ma iya kaunar wanda ya shigo musulunci, ka saka ta ji cewar ba mu da kirki, da karfi da yaji kun cire mata son addinin musulunci, da karfi da yaji kun nuna mata tubabe ba shi da gata a addinin Musulunci, duk wani buri da nake da shi akanka da ita ka rusa shi... Ka zabi Masarautarku, ka bi mahaifinka, to ka dawo na yi maka?” “Ammy kamar kin fi son Ay...” Be karasa ta wanka masa mari. “Na fi son Aysha da kai Turhan, haka ne baka yi karya ba hashenka a daidai yake, da ka rike ta a yadda na so wata kila da rikon zai iya zame min silar shiga aljanna, duk wani hali da ta shiga ko zata shiga kai ne sila...” “Ba ni ne sila ba... Ammy ba ni ne mijinta na farko ba, kuma ban mata wulakancin da kike tunani ba, yadda kike daukar abun be kai haka ba” Ya fada yana hawaye shi dai kokari kawai yake ya fahimtar da ita kuma ya wanke kansa. Sai ta nuna masa kofar fita falon. “Tashi ka fice min daga falo, ai kasar nan bata cikin rikon ubanka ko? Iyakar mulkin sarautarku da ikonku ya tsaya a Sudan ne, to tashi ka koma can ka rike sarautarka da matarka da yan'uwanka da mahaifinka, ka bar ni da nawa” Ya mike tsaye kai a kasa ya fice daga falon. Ammy ta bishi da kallo har ya fice sannan ta juya ta kalli Amal dake tsaye stairs tana kallon abun da ke faruwa. “Ammy dai kin yi hakuri na ga...” Ammy ta kalleta fuska babu alamar wasa. “Idan kika furta wani abu akan matsalar nan, to zaki hada kayanki ne ki bar min gidana” Ta rufe bakinta da sauri ta juya ta koma sama. A mota Turhan ya samu kansa ya jingina da sitiyarin gaba daya ya rasa me ke masa dadi. Wayarsa ya dauka ya amsa kiran dake shigowa yana gyaran murya domin damuwa ta gama cinye karfinsa. “Ihm ihm Hello” Sai aka amsa masa daga dayan bangaren. “Hello Turhan ya gidan?” “Lafiya Kalau” “Ashe ka shigo kasar, dazun nake ji a gurin Uzee” “Haka ne amman dai yau zan koma” “Why?” “Ba dadi, Aliyu har yanzu babu wani abu sabo, Ammy ta ki karbata, ga damuwar abubuwa da yawa suna rufe ni, na rasa me ke min dadi” “Har yanzu babu labarin Aysha?” “Babu, kuma yau Ammy ya tabbatar min ba zata yafe min ba, sai Aysha ta yafe min, ban san inda zan ga Aysha ba” “Bana jin fa tana raye, domin da tana raye neman da ka yi mata da yadda aka zuba kudi da yanzu an gane ta, ni ma ta gurina ba wani labari gaskiya, ina ganin abun da zai fi, ka koma nan da kwana biyu idan na duba time da ya fi sai ka dawo muje tare mu samu Ammy mu rarrasheta wata kila zata yafe maka” “Abu ne da kamar wuya, ta hau sosai ta yi fushi Aliyu” “Karka karaya, za mu samu kanta In Sha Allahu, ba wai mu kadai zamu tafi ba sai mun gayyaci mutane, ka yi magana da amininka ku tattauna idan kun yi shawara da kuke ganin ya kamata mu shigo ciki sai mu shiga” “Toh Allah yasa ta yafe min, ko da ya yafe min dole zan cigaba da neman Aysha, ina da bukatar ganinta ina son ganin...” Yayi shiru be karasa ba. “I will call you Back” “Okay” ALIYU POV. Ya sauke wayar tare da bude bakinsa ya karbi plantain din da Sultana take kai masa baki. “Uhmm so kike cikina ya fashe ko?” Ta yi dariya tana jan hancinsa. “Eh so nake cikinka yayi kato kamar nawa” Ya saka wayar aljihu ya kai hannunsa ya shafa cikin nata. “Ai da ba zaki zauna da ni ba, amman yanzu saboda kin ga saurayi kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa shiyasa kike zaune da ni” Ta bude baki. “Sai kace ba ni na saka ka yi kyaun ba, kamin na aure ka ai baka da kiba amman ina aurenka ka yi kiba ka kara kyau” Ya zagaye cikinta da hannayensa. “Ke ma dai kin ce na kara kyau, that's mean ina da kyau tun farko shiyasa kika rude kika ce ke sai ni” Ta kai masa yatsina a fuska har sai da ya matsa baya yana dariya. “See this girl” “Zaka yi latti fa, ka tafi ko na kira Momy na fada mata” “Sai nace mata ke kika rike ni kika hana ni tafiya aikin, kin ga idan ta min fada sai na rama akanki” Juyar da shi ta yi ta fara turashi har sai da ya fita daga falon dan dolensa. “Ni da gidana a rika korata” “Ka dame ni ne, and Point of correction gidana ne ba naka ba” Dawowa yayi kusa da ita ya sumbance ta ya shafa cikinta. “I Love you, sai na dawo ayi min addu'a mai ciki” A take ta kai masa rankwashi akai sai ya zuba da gudu gurin motarsa yana dariya “Allah ya kiyaye ya tsare min kai, dan kyakkyawana” “Amin yar kyakkyawata” Ya dago mata hannu ta daga masa sannan ya shiga motar yayi addu'a yayi mata key yayi horn mai gadin da ya kasance inyamuri ya bude masa gate ya fice, zuciyarsa cike da so da kaunar matarsa. ____________________ Share fagen sabuwar tafiyar kenan. Da fatar zaku karbe shi da hannu biyu. Khadeeja Candy... ✍️ +2348036126660 A hankali ta tura kofar dakin da danta yake ta shiga sautin dariyarsa ya saka ta farinciki tun kamin da karasa gurin da yake zaune. Vito ya juyo ya kalleta ko kadan babu murmushi a fuskarsa sai ka rantse da Allah ba shi ne yake yi ma London din wasa ba yana dariya. Kallonta yake har ta karaso kusa da shi gurin da danta yake zaune, ta rage tsaye ta kai hannu ta shafa fuskar danta, shi kuma ya kai hannu zai shafa fuskarta sai ta kauce ta yi saurin mikewa tsaye, a nan ma da kallo ya bi ta, wani irin so yake mata wanda ba zai iya dorashi a mizanin awo ba. “Karfe nawa zaki dawo?” Ta kalli agogon hannuna. “Ban sani ba, sai idan na tafi” “Karki zauna da yunwa idan babu abinci a can ki fada min zan aiko a kawo miki” Ta kalleshi kawai ta dauke kai sannan ta sakarwa danta murmushi, ta sake rage tsayinta tana kallon danta. “London zan fara fita aiki yau, zan wuni ba a gida ba, kai kuma zaka wuni da Chidimma your Nanny...” Bata rufe baki ba ya girgiza mata kai ya bata fuska zai yi kuka. “Ni bana son zama a tare da Chidimma ina son zama tare da Uncle Vito” Ta saka hannayenta biyu ta rike fuskarsa tana masa magana a hankali, domin karami abu ne ya birkice mata a take. “Uncle Vito zai fita yana da aiki, amman idan na dawo....” “Zan zauna tare da shi” Vito ya amsa mata yana kallon gefen fuskarta. Ba tare da ta kalleshi ba ta ce. “Amman kana da gurin zuwa” “Ba karamin abu ba ne London ya sake jiki da mutum, ya fara cewar baya son zama gurin Nannynsa so let him be with me, ko kuma ke ki fasa tafiya aikin ki kula da shi” Ta cire hannunta daga jikin danta ta mike tsaye “Ka zauna da shi ni zan tafi” Ta juya ta nufi kofar dakin ta bude ta fice, da kuzari ta fito cikin gidan ta nufi gate mai gadi ya bude mata ta fice. Tafiya sosai ta yi sannan ta samu taxi ta shiga sai da ta zauna sannan ta fada masa gurin da zai kaita. Direban ya saka sauti mai dadi yayi kasa da volume din yana tukin a hankali. Idanuwanta ta maida gefen titin tana kallon hanya da ababen hawa da kuma shagunan suka yi ma hanyar ado, sai dai gaba daya hankalinta yana wata duniyar da ta kasa mantawa da mutanen cikin da kuma rayuwar da ta yi a ciki. “Idan baki iya larabci ba karki gwada, ba a nigeria kike ba, al'adunmu sun shan banban, saboda haka bana son ki yi magana har zuwa lokacin da zaki koma gida, zan sanarwa kowa cewar ke kurma ce” “Saboda me?” “Saboda bana son kowa ya san wani abu a tsakaninmu, addininmu da na ki ya shabanban, ina da daraja mai girma a nan, ni dan sarauta ne jinin sarauta, ina da iyali da rayuwa a nan” “Ni ma musulma ce ai a yanzu” “Kowa ya ganki ya ji muryarki ya san tuba kika yi, ba wai an haife ki a ciki ba ne, sanin cewar na auri tubabbiya zai zubar min da kima, kuma babu wanda ya san maganar auren nan daga ni sai ke sai Ammy, Ammy kuma bata nan daga ni sai ke ne a nan” “Allah yana nan, be kamata ka yi min haka ba, be kamata ka wulakanta ni ba, wannan zalinci ne kuma Allah baya son haka” Ya dalla min harara. “Ke Allah kika sani? Kin san Allah kika tashi cikin kafirci? Karki kuskura ki ce zaki fadi wani abu akan hakan, domin ke baki san komai ba, sallah ki ma ba a fara karba ba, domin ba mai kyau kike yi ba” “Amman Turhan...” “Kul... Karki kuskura kiran sunana a nan, karki kuskura nunawa kowa cewar kin san ni, ni ba mijinki ba ne a yanzu, na aureki ne a inda aurenki ya zame min dole, a nan kuma ina da wasu iyalin...” ***   ***   *** “Madan a nan zan tsaya ko ciki za mu shiga” Tambayar da direban Taxi din yayi mata ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, hannunta ta saka ta share siraren hawayen da suka zubo mata. “Shiga ciki” Ya kunna kai kamar yadda ta masa umarni har sai da ya isa gurin da aka tanada domin aje motoci, ta bude motar a hankali ta fita ta dauko kudinsa ta mika masa sannan ta nufi babbar kofar ma'aikatar da mutane suke hada hadar shiga da fita, sosai gabanta ya tsananta faduwa domin abu ne da bata taba yi ba zata fara a yanzu, wato aiki, a yanzu zata yi mu'alama da mutane bayan ta yankewa kanta mu'amala da kowa sai mutumen da shi ne silar dalilinsa take tsaye a yanzu wato Vito. Bata bukatar wani yayi mata iso domin wannan ne karo na uku da ta zo ma'aikatar bayan zuwanta na farko da ta kawo CV ta, sai kuma zuwan da ta yi interview.  Third floor ta nufa bayan ta shiga elevator and she pressed the buttom. Kanta ta daga sama  tana kallon gurin tare da aje numfashi a hankali, feeling awkward and excited as the same time. Elevator ya rabe biyu ta fita tana kara gyara gashinta, kai tsaye ta nufi office din da aka musu interview ta yi knocking sannan ta tura ta shiga. Wani saurayi ne a ciki da ba zai wuce sa'arta ba, ta dan yi mamaki domin wacan zuwan nata na farko ba shi ta tarar ba, ta gaisa da shi cikin mutunci ta gabatar masa da kanta. “Nice to meet you Aisha, a nan an muku interview ne kawai, a hawa na hudu dama dake akwai wani office na farko shi zaki shiga, ki gabatar masa da kanki zai fada miki gurin da office dinki yake” “Okay na gode” Ta juya ta fita har lokacin bata jin sakewa domin yau ne ranarta ta farko kuma abu ne da bata saba ba. A tsanake ta nufi gurin da Elevator ke daf da rufewa mutumen dake ciki yana tsaye yana kallonta ita ma kallonsa take bata dauke ido ba har sai da elevator ta rufe. Tsaye ta yi a gurin tana kallon floor din da kowane office yake rufe. Babu tsammani elevator ta sake budewa mutumen da ta hango dazun a ciki shi ne har yanzu, matsawa ta yi gefe domin ba shi hanya a zatonta fita zai yi, sai ta ga tsabanin haka, be ce ta shigo ba kuma shi ma be fita ba, ganin kofar na kokarin rufewa a karo na biyu ya saka ta yi hanzarin shiga sai ta matsa daga gefe. Kamata yayi ta gode masa? Saboda ita ya sake pressing floor din da take ko kuma dai wani abu zai yi, ya fasa. Ta dan dago ta kalleshi kadan sai ta ga idonsa yana kanta ta yi hanzari dauke kai. “Okay Momy zan yi, i love you” Ta ji ya fada sannan ya kai hannu ya taba black iPod din dake kunnensa. Da sauri ta dube shi jin ya ambaci uwa, a duk gurin da mutun yake tare da mahaifiyarsa ko ta ji ya ambace ta, ko kuma ta yi arba da alakar uwa da da, sai hankalinta ya tashi, sai ta ji wani abu ya tsaya a zuciyarta, domin ita bata san wannan gatan ba, bata san mutum daya a duniyar da zata nuna a matsayin dan'uwanta na jini ba balle kuma uwa. Ita din wane laifi ta yi ma iyayenta suka jefar da ita a gidan marayu? Su waye iyayenta? Wane addini suke yi? Wane yare suke ji? Ita ce tambayar da take yawan yi ma kanta. “Excuse me, can i help you?” Ashe kallonsa take da kyakkyawan blue eyes dinta masu matukar daukar hankalin mai kallonsu. Blue eyes din ne suka karafafa masa guiwar kallonsa har yake jin kamar ta taba wanzuwa a wani bangare na rayuwarta ta baya, wata kila kuma kyauta ne yake masa gizo har yake ganin haka, but this is the second time da yayi arba da mace mai blue eyes a Africa. “No, I'm sorry” Be sake ce mata komai ba, sai dai har lokacin kallonta yake ta gafen ido, ita din ai ta kai ayi mata kallo fiye da goma ma, ba daya ko biyu ba, but wait ina ilminsa da tarbiyarsa da koyarwar addininsa suka tafi? A take yayi hanzarin dauke idonsa gaba daya daga barin kallon abun da ba halalinsa ba. ‘Astagafullah’ Ya furta a ransa a daidai lokacin da elevator ya bude a hawa na hudu, ta dan kalleshi tana jiran ya fara fita sai ta ga be fita ba sai danna Apple watch dinsa yake, hakan ya saka ta fita cikin rashin sakewa ta fara tafiya. Sai a lokacin ya dago mistakenly idanuwansa suka sauka bayanta, sai ya rufe ido da sauri ya taba numbers din da suke jikin Elevator a take ya rufe yayi sama da shi to 5 floor. Office din farko ta fara murdawa kamar yadda aka fada mata ta tura ta shiga. Ya san ko dai ta tsaya a 4 flour ko kuma kasa zata koma, domin ma'aikatan kamfaninsa basa wuce 4 Flour the 5th floor is his and his entire team, and be taba ganin fuskarta a kamfanin ba, maybe she's among the new employees ko kuma ta zo gurin wani ne, ko dai minene she should be tsakanin fourth to first floor. Sai ta samu kanta a babban guri da wasu dakunan a rufe, da dan tsoro irin na rashin sabo ta tura kofar Office din da shi ne farko ta shiga ba tare da ta yi knocking ba. Matar dake sanye da abaya da karamin hijab half sunna, tana amsa wayar telephone ta dago tana kallonta fuska babu annuri. Emily ta tsaya a gurin gabanta na faduwa zuciyarta na tsanar matar da ko sunanta bata sani ba a yanzu, ba dan komai ba sai dan shigar ta wato suturar jikinta ta isar da sakon addininta ga duk wanda yayi ko zai yi arba da ita. Ta tsaya a gurin har sai da ta gama amsa wayar, sannan ta karasa kusa da ita. “Am... Sunana Aisha Muhammad ina daya daga cikin sabin ma'aikatan da aka dauka, kuma yau ne zuwana na farko, a office din da aka mana interview yace na shigo nan” Ta fada cikin sakin fuska da murmushi, sai matar ta kara hade rai ta jefa mata wani kallo. “Amman dai baki manners, ta ya zaki shigo cikin office ba tare da knocking ba? Kuma a farkon Shigowarki ai ya kamata ki tsaya sai an miki izini tukuna” Emily ta sassauta murmushinta tana dan ji babu dadi, matar dake gabanta ba san yadda Vito ya jikata da gata ba, wata kila da bata fada mata magana irin wannan ba. “Ki yi hakuri, mantawa na yi” “Koma ki yi knocking idan na miki izini sannan ki shigo” Ta fada kai tsaye tana bude wasu files dake gabanta, Emily ta tsaya kallonta like are you serious right now? Ganin hakan ya saka matar ta sake duban Emily. “Kurma ce ke?” “Aa” Ta amsa sannan ta juya jiki ba kwari ta fice daga office din. Taja tsaki after Emily ta fice. “Mtswwww, na ga Aisha Muhammad na dauka ke kadai ce Musulma a cikin sabin da aka dauka, ina cewa zan samu yar'uwa ashe kafirar ce, irinsu ne ke batawa musulmi suna, suna aikata abu ace musulmai ne, sunan mahaifinta da nata na musulmai amman fuskar kafirai da sarkar Cross a wuya, na tsani kafiran nan Wallahi” Sai fada take kamar zata yi duka, abu ne da ta boye a zuciyarta saboda mu'amalarta da mutanen da suke garin Port Harcourt da kuma kamfanin mafiyawancinsu kistoci ne, amman bata kaunarsu ko kadan. “Na riga na zabe ki, na dauka Musulma ce Wallahi, amman zaki ci ubanki” Ta fada tana dora hannunta a laptop din dake gabanta. Emily na fita kai tsaye ta nufi gurin Elevator yake a fusace domin ta manta when last a wulakanta, kusan wani be taba gwada yi ma makamancin wannan wulakancin ba a sabuwar rayuwarta ta yanzu. Kamin ta karasa wayarta ta yi kara sai ta saka hannu a jaka ta ciro wayar, ganin sunan dake jikin screen din ya saka ta tsaya ta daidai numfashinta, ta sani idan har ta amsa wayar a cikin yanayin da take a yanzu na bacin rai zai ji haka a muryarta zai iya tashin building din ba tare da tsayawa ya ji dalilin bacin ran ba. “Hello” “Emily miyasa baki fita da motarki ba?” “V, idan na dawo za mu yi magana” Ta fada a daidai lokacin da ta dora hannunta Elevator zata danna. “Answer me...!!!” Ya daka mata tsawa har sai da zuciyarta ta yi rawa, and yes this is not the first time da yake tsawa, ya saba dukanta ko ya takata ko ya yi mata fada ko raunatata but shi kadai zai iya mata haka, idan wanin da ba shi ba yayi mata kallon banza sai ya saka an cire masa ido. Ta kashe wayar da sauri tana maida numfashi da karfi, rauni da damuwa irin na wanda ya rasa madafa suka bayyana a fuskarta. Dauke hannunta ta yi ba tare da ta taba ba, ta juyo ta nufi office din da ta fito. Vito na daga cikin dalilinta na son ta inganta rayuwarta ita kadai a yanzu ba tare da taimakonsa ba, duk kuwa da kasancewar shi ne silar komai nata a yanzu. But tana son ta samu freedom so take ta samu yancin rayuwa ita da yayanta kamar sauran mata, ta jika a kangin bauta har yanzu so take ta yi rayuwa ita kadai ta tsayu da kafafuwanta, ta zama Independent woman. Sai da ta daidai tsayuwarta ta nemi kwarin guiwa da confidence ta lullube zuciyarta da shi sannan ta kai hannu ta yi knocking Office din. Shiru ba ta ji ance ta shigo ba, hakan ya saka ta sake kwankwasawa a karo na biyu, ta sani a yanzu kam ba zai yi ace bata ji ba, sai dai dan wulakanci zata aje ta a gurin, kuma ba ta yi mamakin wulakancinta ba, saboda ga dukan alamu macen musulma ce, a iya kar ilimin Emily kuma musulmai ba su da kirki. Ta kusa minti biyar a tsaye sannan ta yi mata izinin shiga. Emily ta tura office din ta shiga sai dai wannan karon babu irin murmushi dake fuskarta a wacan karon. A nan din ma sai da ta sake gabatar mata da kanta, matar ta dan kalleta ta dauke kai, after like 10 seconds, ta dubi Emily tace. “Aisha sunanki ko what so ever, za ki yi aiki da ni a matsayin Assistant dita, aikinki shi ne kullum zaki shigo 6:30am  7am ta yi miki a nan, zaki yi mopping office din nan ki gyara komai, kamin na shigo, zaki hada min abun karyawa kamar tea ko coffee duk abun da yake available dai ko kuma nake ra'ayi, and duk abun da nake bukata na aika ko yi ke zaki min, and lastly Office dinki yana next to mine” Ta mike tsaye cikin izza ta isa gurin wata karamar durowa ta bude ta dauko file da keys ta dawo ta mika mata. “Akwai ID na aikinki a kamfanin mai dauke da sunanki da hotonki, zaki saka a wuya ne kullum idan zaki shigo kamfanin nan, a cikin file din akwai rules and regulations na kamfani ki yi saka hannu ki dawo da shi gobe” Ta dora mata keys din a saman file. “Wannan key din office dinki ne, hadi da nawa saboda ki samu damar gyara min nawa ko daukar wani abun idan bana kusa” “Okay, Ma'am Thank you” Emily ta furta sannan ta juya. “And... Sunana Amal not Ma'am, ba dole sai kin yi aiki ba, idan kin duba office din ki yi tafiyarki, gobe ki shigo da wuri” “Okay” Ta amsa ba tare da ta juyo ba, Amal ta bita da kallo tana yatsina fuska har ta fice sannan ta nufi kujerar. “Da wasu idanuwa blue kamar na aljannu, ko mage, waya sani ma ko mayyace, ko wace yare ne ma oho” Sai kuma ta bawa kanta amsa. “Zata wuce Igbo dama sune kafirai ai” emily na fita office din ta nufi office din dake kusa dana Amal, sai da ta karewa kofar kallo sannan ta saka key din ta bude ta shiga. Komai fes ga computer da karamin tebur daidai ita, ita ma tana da karamin dorowa kamar Amal. Window ta kuma yana facing din gari da makwantan gine gine da suke wajen kamfanin sai titi da zata iya hango hada hadar mutane, ta dan samu sakewar zuciya wanda har ta kaita ga murmushin jindadi. TURHAN POV. Bude motar yayi ya fito yana shafa fuskarsa ya kalli kofar falon bayan ya rufe motar, sai da sauke ajiyar zuciya irin ta manyan mazaje yayan sarauta sannan ya sake komawa falon mahaifiyarsa. Yana turo kofar falon Ammy ta juyo ta kalli kofar, ba yi mamakin sake ganinsa ba, domin haka yake mata naci a duk lokacin da ya zo gidan. “Jajirtacen namiji, gwani na gwanaye, mai isa da tinkaho da burinkasa da sarautar gidansu, mai son farinciki ubansa fiye da na uwarsa, mai martaba auren ubansa ya watsar da na uwarsa” Ya zube kasa yana taba kafarta damuwar dake fuskarsa kadan ya rage ta saka shi birgima, domin ya san ma'anar kirarin da Ammy take masa. Ammy ta matsar da kafarta daga hannayensa. “Da haka kake da na ci da jajircewa a baya, da yanzu Aisha tana nan tare da mu, bata gudu ba” Kansa a kasa ya soma magana cikin magiya tare da fatan zata amsa rokonsa. “Ammy na dawo nan ne saboda na tambaya, a dan zaman da Aisha ta yi a gidan nan ta taba fada miki suna da kuma unguwar da gidan marayun da ta zauna a Lagos yake? Zan tafi Lagos din na bincika ko Allah zai saka a dace” Har Ammy ta yi shiru sai kuma ta kalleshi. “Eh ina zuwa” Ta mike tsaye ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta, wani sanyi ya ji ya sauka a zuciya jin cewar kamar ya kusan samun hanyar da zata sadashi da Aisha. Babu jimawa Ammy ta sauko tana kallonsa idauwanta a kankance irin bacin rai, sai da ta zauna sannan ta mika masa takardar dake hannunta. “A lokacin da ta shigo ta dauki danta ba tare da na sani ba, ta bar min wannan akwai address dinta a ciki” Turhan ya karba da sauri ya warware takardar da kana ganinta kasan ta jima a ajeye. _Kin ce danki ya sha babban da sauran, wata kila dai baki fahimci danki ba ne, wata kila kin hada aurena da shi ne saboda kina neman mafitar yadda zai dawo gareki, amman duk halinsu daya, shi ma be san daraja ta ba, na fada miki musulmai ba su da kirki kika karyata ni, akan abun da yake zahirinsa, musulmai basa kaunar tubabben basa son kowa sai wanda ya tashi dan asalin dan musulmi, ba su da mu'alama mai kyau, basu san darajar kowa ba sai junansu, abun da kuke aikatawa dabam karantarwarku dabam, shi ma ďan da kike cika baki da shi ya wulakanta ni kamar wancan, duk akan me? Addininku? To na bar muku, zan koma a gurin da nake da daraja” Tun gabani ya gama karanta wasikar zuciyarsa ta tsinke hawaye suka taru a idanuwansa har suka sauko a fuskarsa. “Saboda kai Aisha ta ji cewar bata da gata a gurin Musulmi, ka karyata duk wani abu da na yi amfani da shi na karfafa guiwar yarinyar nan, kuma ka saka ta ji cewar na yaudareta, ba ni da wani addireshinta bayan wannan” Turhan ya daga kansa ya kalli Ammy, ganin hawaye a fuskarta, ya saka shi cikin tashi. “Zan nemo ta Ammy, zan nemo ta ko da hakan yana nufin na yawace duniyar nan, zan samo ta ko da hakan yana nufin rasa rayuwata ne, zan kawo miki Ammy wannan alkawarina ne” Ya mike tsaye ya share nasa hawayen ya fice daga dakin rike da takardar. _________________________ Wai me Turhan ya aikatawa Aisha ne? Me yasa Ammy ta gagara shiryawa da shi? Anya kuna ganin Emily zata jure aiki a karkashin Amal kuwa? Bayan kuma Amal bata son kafirai, Emily kuma bata kaunar musulmai? [4/20, 9:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* 3️⃣ Teburin dake office din ta nufa ta dora file din da Amal ta bata, tana karewa karamin office din da be karasa girman na amal ba kallo. Sannan ta nufi windows ta bude tana kallon kasa, iska mai dadi na shigowa office din. Ta dade tsaye a haka sannan ta matsa baya ta rufe, ta nufi gurin da durowar office din take ta fara budewa tana dubawa, kusurwar farko an rabata biyu ne da wani katako tsakiya, daga sama an dor Kur'ane daga kasan kuma Bible, doka ce ta sabon CEO na yanzu, aje Qur'ane mai fassarar turancin, da Bible a kowane office a kokarinsa na son tallata addininsa, ta dayan bangaren kuma gudun complain ya saka yake aje Bible din domin baya kowa hakkinsa, sai idan baka bujata sai ka yi magana a dauke. Risinawa ta yi ta rage tsawonta ta taba Bible din da hannunta na dama. Wani bangare na maganar da Momy ta yi mata ya dawo mata sabo a yanzu. _Emily karki bari yaron nan ya yaudareki, kar kyaunsa ya ja ki ga halaka, domin bayan kyaun ban ga wani abu da yake da shi ba, mun fi shi arziki a gidan nan, zaki samu miji mai kudi mai komai ba, zan inganta rayuwarki ni da mijina, please karki kunyata mu, abun kunya ne ace kina gidan Pastor kin bar mu kin bi musulmi, karki lalata rayuwarki da kananan shekarunki please Emily, ki rike wannan Bible din ki yi karatu bana son na sake jin maganar yaron nan, kin ji my beautiful Diamond Girl_ Ta dauke hannunta da sauri tana hawaye, ta rufe durowar ta juya ta zauna a gurin ta jingina da ita sai kuma ta fashe da kuka, jikinta na karma kamar wanda ta firgita. “Hamza ka cuce ni... Ka cuce ni... Ka raba ni da matar da ta rike a matsayin ƴa, kasa na butulcewa macen da suka rike ni da amana” Ta girgiza kai.. Ta dayan bangaren ba laifinsa take gani ba, laifin zuciyarta ne data  barta ta fada soyayya da mutumen da be san darajar addininsa ba balle ita. Wani irin duka ta kai kirjinta tana jin kamar ace zata iya ganin zuciyarta a fili ta yi mata duka. Tuna cewar ba a gida take ba ya saka ta natsu ta sassauta kukan da be gama fita ba, ta hade kanta da guiwa. Ta dauki lokaci tana rarrashin kanta sannan ta mike tsaye ta dauki file din ba tare da sake taba komai ba ta fice daga office din ta rufe kofar da key ta nufi hanyar da zata sadata da elevator.  Babu abun da take a cikin elevator sai tunanin yadda rayuwa tayi da ita. Har ta isa first floor bata hankara ba sai da kofar ta rabe biyu, ta fita ba tare da ta lura da mutanen da suke tsaye suna kokarin shiga elevator ba. Daya daga cikinsu ya biyo bayanta a sirance har sai da ta yi rabin gate din dake da tsayi sosai. “Excuse me Miss” Ta juyo ta yi sai ta yi arba sa wani bakin mutum bayanta yana sanye da yellow t-shirt da black jean. “Can i help you?” “Yes” Ya matsa kusa da ita. “Kin shigo neman wani abu ne? Ko kina daya daga cikin team din Resrezor?” “No na fara aiki a nan ne” “Yaushe?” “Yau” “A ina? Wane guri office dinki yake?” “Four floor hannun hagu office na biyu” “Nice to meet you, I'm William, ina 5 floor office na hudu” Ta mika masa hannunta kamar yadda ya mika mata nasa. “Emily” “Nice to meet you Emily, kin samu aboki yanzu” Ta yi murmushi tana kallon sarkar Cross din dake wuyansa hakan sai ya saka ta ji dadi ganin kirista ne dan'uwanta. “Har kin tashi ne?” “Eh” “Okay Bye” Ta yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiyarta. Shi kuma ya tsaya a gurin yana kallon yadda wandon jikinta ya dame jikinta yayi mata kyau. “Wow...” Ya shafa kansa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Ta isa gida da wuri saboda ta samu abun hawa da wuri, sai da ta sallame shi sannan ta kwankwasa kofar gate din. Mai gadin ya bude mata ta shiga tana amsa gaisuwarsa. Tura kofar falon ta yi ta shiga sannan ta rufe ta cire talkamin kafarta ta saka na falon sannan ta karasa ciki. Ganin kwalbar giya aje a tsakiyar center Table din dake falon ya karantar da ita V ya bar gidan cikin bacin rai, domin abu ne da ta sani, idan ransa ya bace giya yake sha ko marijuana. Da sauri ta jefar da Jakarta da file din hannunta ta nufi dakin da London yake ta bude gabanta na faduwa, ta duba dakin har bandakin baya ciki, hakan ya saka hankalinta ya kwanta domin shan abun maye ko drugs abu ne da bata son yana yi a gaban yaranta, wannan yana daya daga cikin dalilin da ya saka ta zabi raba gida da shi, ta zabi rayuwa ita kadai sai yaranta. Fitowa ta yi ta dawo falon ta dauke kwalbar ta shiga Kitchen ta tsiyaye ragowar barasar dake ciki ta fasa kwalba ta zuba a dustbin sannan ta wanke hannunta ta fito. A gurin da ta jefar da jakarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, tare da daga kanta tana kallon rufin falon zuwa gurin da katon plasma ta yake. Ta sani ahalin yanzu bata rasa komai ba sai kwanciyar hankali, Vito ya jika da kudin da bata jin akwai wata mace mai tarin dukiya irinta, ita kanta bata san adadin abun da ke account dinta ba, domin kowane sati sai ya saka mata kudi ita da yaranta London da Fadima duk kuwa da kasancewar karamar yarsa Fadima bata son shi, amman be taba kula haka ba saboda yana matukar kaunar mahaufiyarta. A cikin gidan da take rayuwa gidane da ko wucewa kawai ka yi a gaban gate din sai hankalinka ya tashi saboda kyaunsa, shi kansa nasa gidan be kai nata kyau ba, ya zuba mata kayan more rayuwa daga sutura har abubuwan ado na kawata falo ko daki, ga mayan motoci da ya zuba mata a cikin gidan, ga Nannyn da ya dauka mata mai kula da yaronta, ya saka yarta a makarantar kudi ta yayan manya, London kuma da ya kasance Autism ya biya ake karantar da shi a gida. Bayan kudin da ya biya aka yi mata aiki, ya kaita waje ta yi karatu. Amman duk da haka tana jin ta rasa wani abu a tare da ita, she felt something is missing inside her. Ji take bata cika ba har yanzu, tana jin akwai abun da ta rasa kuma bata san miye wannan ba, sai dai ta san dalili daya da ya saka take son tsayawa sa kafafuwanta, wannan sirri ne da ba zata iya budewa kowa shi ba. “Good Afternoon Ma” Cewar Chidimma bayan ta shigo falon. Emily ta kalleta da irin fuskar nan na wanda tunani be gama sakin kansa ba. “Chidimma, a gaban London V ya sha alcohol dazun?” “Aa bayan na shiga dakin Landon ne na canja masa tufafi saboda za su fita tare” Ta sauke numfashi a hankali. “Okay please duk yadda za'ayi karki bari yarana su ga lokacin da Vito yake shan giya, balle har hannunta ya kai gurin” “Okay Ma zan kiyaye” “Ki shirya musu wani abu ni zan yi bachi” Tana fadar hakan ta mike tsaye ta dauki jakarta da file din ta haura sama ta shiga dakinta ta aje jakar da file din a kusa da gadonta ta kwanta, tunani ya fara kawo mata ziyara kamin bachi yayi gaba da ita. ALIYU POV. Dagowa yayi a hankali ya kalli kofar office din da aka turo. Mutumen ya karaso gaban teburin cike da girmamawa ya bude masa daya daga cikin files din da suke hannunsa. “Nan zaka saka hannu” Sai da Aliyu ya gama abun da yake a computersa sannan ya kalli file din ya saka hannu. “Ranka ya dade cikin sabin ma'aikatan da aka dauka har da turawa?” Cewar mutumen dake tsaye gabansa, shi dai be ce komai ba, har sai da ya gama saka hannu a duka files din. “Na ganta zata fita dazun” Aliyu ya sake dubansa ba dan ya fahimci inda zancensa ya dosa ba. “Baka ga sabin ma'aikatan na mu ba” “Ba ni nake da hakkin ganinsu ba, ban san suwaye aka dauka ba” “Wata baturiya ce fara kyakkyawa har ta fika haske ga blue eyes” Aliyu ya dan yi jimmm alamar nazari can kuma sai yayi murmushin da ya kara masa kyau. “Ka ganta kenan?” “William, na ganta and what?” “Tana da kyau, ga fari duk yadda aka yi wannan yarinyar baturiya ce ko half cast, na gode da ka dauketa, and finally kirista ce yar'uwata” “Ka godewa Amal aikinta ne not mine, ni ban san su waye aka dauka aiki ba ma” Ya aje zaren zancen a daidai lokacin da wayarsa ta ringing. Kallon wayar yayi yana murmushi. “Shiyasa ake daudararku koda yaushe kyaun kuke bi ba hali ba” Ya amsa kiran ya kara wayar a kunnensa, at the same time da William yake fadar. “Ka rantse da Allah ka na musulunci cewar ka taba ganin yarinyar da ta fita kyau? Ni fa rudewa na yi na kasa rike kaina sai da na yi mata magana” Da sauri Aliyu yayi saurin yi masa alama da hannu na yayi shiru ya yi tafiyarsa. William zip up his mouth yayi ta tafiyarsa. “Hello yar kyakkyawata” “Na'am ya aikin?” “Alhamdullahi ya cikin?” “Ban sani ba” Ya saka dariya daman da neman magana ya saka shi tambayarta. “Miye laifina dan na tambaya?” “Ni dai ban sani ba, kawai dai na kira na fada maka Gwaggo ta kira tace Anty Sa'ade ta haihu” “Maa shaa Allahu, me muka samu?” “Irina ce aka samu” “Ki ce irinki marar jin magana ko?” Ya fada yana wani abu da ido kamar tana gabansa. “Ba zaka daina ba ko?” “Na daina yar shawalwalar yarinyar yar dirarar yar black beauty na kyakkyawata” Ta yi dariya. “Bye sai ka dawo” “Okay mai ciki” Yana fada ya kashe wayar da sauri yana dariya, sannan ya aje wayar ya maida hankalinsa gurin aikinsa. TURHAN POV. Ya aje mug din tea dake hannunsa. “Yadda kasan yarinyar nan ta yi ma Ammy magani haka ta juya min baya, gaba daya na kasa gane kan mahaifiyata” Mannir dake kallonsa ya ce “Amman dai ka san abun da ka yi mata baka kyauta ba? Baka ji haka ba?” “Na san ban kyauta ba Manir kuma na ji babu dadi, ina kan jin babu dadin ma a duk lokacin da na tuna, amman yadda Ammy ta hau karamin abu ta maida shi babba shi ke daga min hankali kuma ya ba ni mamaki” “Iyaye sai hakuri, kuma kasan Ammy ta dora hope sosai akanka game da yarinyar nan, sai kuma gashi ka bata kunya, waya sani ma da ace ita kake aure har yanzu wata kila da yanzu kun haihu, gashi nan wannan yarinyar da ka fifita akanta har yanzu baka baka ďa ko ya ba” A take yanayin Turhan ya canja duk kuwa da ya san gaskiya aminin nasa yake fada, kuma samu ďa ko ya wani abu da yake fata kuma ya dade yana mafarki. “Mace bata bawa kanta haihu, duk wanda ka ga ya samu haihuwa hukuncin Allah ba yin kansa ba” “Haka ne, sai dai kuma wata kila yana cikin dalilin Ammy na yin fushi da kai, kuma yarinyar nan fa abar tausayi ce” “Na sani, amman Manir ana samun sabani sosai akan abubuwa kuma sai ka samu iyaye sun yafe sun duba dansu, amman ni Ammy ta kawar da idonta a kaina gaba daya” Manir ya sauke ajiyar zuciya. “Yanzu ka aje duk wani hange hange da tunanin banza, ta ina zamu fara?” “Nemanta, zan shirya duk abun da zan yi a yau, gobe zan sauka Lagos zan fara nemanta” “Wane tabbaci kake da shi cewar tana Lagos?” “A can aka haife, acan ta taso kuma bata san kowa a nan arewa ba, kamin ta bar nan Ammy ta fada ta ganta a coci, bana tunanin zata iya zama garin nan ma gaba daya, idan har zata zabi zama cikin kista yan'uwanta ba ta da wani gida da ya wuce Lagos, matsalar kawai a Lagos din ban san wane gida take ba” “Shi ne Matsalar, kuma Ammy bata ffada maka wane gidan Marayu ta zauna ba?” “Bata fada min ba, amman dai zan yi ta bincike har na gane” “Baka san kowa a Lagos ba, nemanta ba zai maka sauki ba, gaskiya Ammy ta dauki abun nan da zafi” Turhan ya busar da iskar bakinsa. “Zan tuntubi Aliyu yayi zama Lagos kamin ya koma Port Harcourt, maybe zai iya hada ni da wani da zai iya taimaka min mu yi neman tare” “Oh na manta ma da shi Wallahi, ka yi masa magana mu ji ba zai rasa wanda zai taimaka maka gurin nemanta ba, ni kuma zan yi ta lallaba Ammy a nan ko zamu samu wani abu daga gurinta” Turhan ya sake daukar Mug din ya sha tea. “Ta fa yafe min, kawai dai ita wai yadda muke a da ne, ta ki ta dawo min a haka” “Irin wannan ai sai ya saka ka ji ka tsani yarinyar, ko da yake..” Manir yayi shiru ba tare da ya karasa ba. Turhan ma be sake ce masa komai ba ya maida dubansa wani gurin sai tunani yake. EMILY POV. Jin an taba fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali tana kallon Vito dake zaune gefen gadon kusa da ita. Tashi ta yi zaune tana kallonsa, kallonta yake shi ma irin kallon nan mai cike da kauna, sai dai girman kai da jin isa ya hana shi sakin fuska balle har ta ga murmushinsa. “Ina London?” “Yana dakinsa, me yasa baki fita da mota ba?” “Bana son kowa ya san wani abu akaina, na fada maka wata sabuwar rayuwa nake son yi” Ta yaye blanket din dake jikinta ta matsa ta saka kan gadon ta dayan gefen, sai yayi hanzarin rikota ya juyo da ita da karfi. “Fita mota zai hana wani abu daga canjin rayuwar da kike so ne? Mi kike shiryawa ne Emily?” “Me kake tunanin ina shiryawa? Na sha fada maka ina son na yi rayuwa kamar kowa, ina son rayuwata ta zama daidai, dole ne sai na shiga mota? Bana ra'ayin haka? Me yasa kake cilasta ni yin abubuwan da bana ra'ayi? Why?” Ya matsa kusa da ita sosai yana kallon cikin idonta. “Saboda ni kadai na isa na cilasta ki, kuma idan tunaninki ko shirinki na rabuwa da ni ne, to kina shiryawa kanki wani rame ne na halaka, domin ban gane duk wannan abun da kike ba? Me ye ban aje miki ba? Amman tunaninki yana wani gurin dabam, ke tawa ce har abada ba zaki iya guje min ba ki saka wannan a ranki, you're forever mine” Ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata amman ta kasa. “You're hurting me...” Ta yi magana cikin yanayin dake nuna tana daf da fashewa da kuka. “Mami” Jin muryar Fadima ya saka shi saurin sakin hannunta domin ko kadan baya cin zafinta a gaban yaranta ko da kuwa me ta yi masa. Emily ta nufi kofar da sauri tana budewa murmushin dole ya ci karfinta a yayinda take kallon Fadime dake kokarin sauke school bag dinta. “My Baby kin dawo” Ta karasa kusa da ita ta rika mata jakar, Vito ya fito daga dakin ya karaso kusa da su. “Lisa” Ya kai hannu zai shafa kanta, haka yake kiransa saboda ya tsani sunan da Emily ta saka mata na musulmai. Sai ta kauce daga taba kanta da zai yi tana hade rai. “I'm not Lisa I'm Fadima” Hakan kuma be hana shi yin gutun murmushin da yayi niya ba, domin idan da sabo ya saba da halin yar Emily na nuna masa kiyayya a fili wani sa'in har ta kan fada masa bata son shi, duk kuwa da irin hidimar da yake da su. Ta kaunce daga gurin gaba daya ta nufi dakin dan'uwanta, daga Emily har Vito binta suka yi da kallo. “I don't know why, Lisa hate me so much” “Yarinya ce zata daina nan gaba” Emily ta amsa masa tana kokarin kare yarta, ta san shi ma be cancanci irin wannan kiyayyar daga gurin yarta ba. “I hope so, i can't ki haifo min babyn da zata kira ni da babanta” Ya fada yana kallonta tare da karantar reaction dinta. “I thought i told you ni na gama haihuwa” “Nope... Baki gama ba sai kin haifo na wa” Kallonsa kawai ta yi ta dauke kai ta nufi hanyar kitchen, binta yayi da ido har sai da ta shige sannan ta juya yayi ficewarsa. [4/20, 9:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Barka da warhaka mutanen arziki😍 Shim kun san cewa Khadeeja Candy komai da komai? Amman banda ɗan mutum da mutum😃 Ina masu neman kayan Kitchen masu kyau masu inganci, Luxury Warmers manya da kanana, ina masu neman Bedsheet kings and Queens manya da kanana, ina masu neman Akwaitunan lefe da na tafiya. Khadeeja Candy na da Boxes kala kala, ina masu neman tufafi, kama daga Atamfa, Laces, Shadda Lace, Veils, shoes and Bags, Materials. Akwai freezer, Gas cooker and water dispenser. Duka zaku samu a gurin Khadeeja Candy Store, Khadeeja Candy dai taku ta makaranta, da fatan za ku yi patronizing ɗina. Za ku iya join group dina domin bawa idanuwanku abinci https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Kuma zaku iya saka order ta wannan number 08036126660 WhatsApp. KHADEEJA CANDY STORE expect more, and pay less...😊 Page 4️⃣ Ragowar cake din dake fridge ta dumama musu, ta dumama madara a microwave sannan ta zuba a plate biyu kowa da cups dinsa sannan ta fito kai tsaye ta nufi dakin London ta shiga da murmushinta sai ta same shi zaune Nannynsa na karanta masa story book. Gefen gadon ta aje masa cup din da cake sannan ta shafa kansa ta sumbance shi. “How are you My love” Murmushi kawai yayi mata daman be cika magana ba, sai idan ta dauro. Emily ta kalli Nannynsa Chidimma. “Ina fatima?” “Ta shigo amman ganina a dakin ya saka ta fita ina tunanin tana dakinta” “Okay” Ficewa ta yi daga dakin ta tura kofar dakin Fadima sai ta ji ta a rufe, cup din da plate din cake ta hade guri daya ta yi knocking da dayan hannunta. “Baby, bude kofar mana” “I won't” “Na kawo miki cake da madara” “Bana so” “Na fada miki babu kyau bachi da fushi, me yasa kike da kafiya ne?” “Ki fadawa Vito ya daina zuwa nan i hate him” Emily ta daki kofar dakin da karfi. “Ki bude kofar nan Fatima and kar na sake jin kin fadi wata kalma marar dadi akan V idan ba haka ba zan bata miki rai” “Ba zan bude ba!!” Fatima ta amsa mata a tsawace kai kace Fatimar ce uwa Emily ƴa, runtse ido ta yi tana maida numfashi a hankali, sanin halin yarta da kafiya da rashin kunya ya saka bata sake bata second a gurin ba ta juya ta sauka kasa, tana saukowa kwakwalwarta na tuna mata da wasu kalamai na bakin littafin da zuciyarta ta aje. _Ka yi hakuri karka rabu da ni, ban san kowa anan ba, ba ni da kowa a nan_ Ina rike da kafarsa nake fadin haka sai ya fisge kafarsa ya matsa baya. _Ina da kafiya akan abun da nake so, da kuma wanda bana so, karki sake nuna kin san ni_ Ina da akan center table ta aje cake da milk din cikin bacin rai, ta zauna a kujera zuciyarta na yi mata babu dadi. _Ina da mata ina da iyali, kin zo ne kawai ki ruguza rayuwata Aisha_ Jefe jefa kanana da manyan abubuwan da suke faru a rayuwarta ta baya suke dawo mata a duk lokacin da take zaune ita kadai ko kuma rai ya bace. A fusace ta mike tsayeta ture madarar da cake din har sai da suka zube kasa. “Daman idan baki yi kafiya ba ai ke ba yarsa bace...!!” Ta karasa da kara sosai kamar mai shirin yin duka sai haki take, windows falon ta nufa da curtain dinsa suke a bude ta tsaya sai ta hango Sarkin nata zauna kishingiden a cikin motarsa gilashin motar yana kasa gaba daya, yana kallon windows din da take tsaye, rufe curtain din ta yi ta nufi kofar falon ta bude ta fita. Hango fitowarta ya saka shi fitowa daga cikin motarsa yana jiran tsorowarta. Tsayawa ta yi a gabansa hasken kwayayen dake cike a gidan suna haska fatarta mai tsananin fari. “Akwai abun da kake bukata ne?” Ta ido yana amsa tambayarta, a sa'ilin da bakinsa yayi nauyi furta mata kalamansa. “You...” Ya furta bayan ya kwaci kansa. Babu bata lokaci ta rumgume shi, ta lumshe idonta dake kwance da ruwan hawaye. Da ace tana da wani abun da zata aikata ta biya V da tuni ta aikata, domin shi ne mutumen da ya mayar da ita yadda take a yanzu, shi ne mutumen da be nuna mata kyama ba, ko da yake shi din kistane dan'uwanta da musulmi ne babu tantama da yanzu ya rabu da ita ko ya ci amanarta, amman shi yana nan tare da ita duk kuwa da irin kyamar da yarta take nuna masa. Slowly ya zagaye bayanta da hannayensa ya rumgume ta comfortably, idonsa a sama yana kallon window Fatima dake rufe cike da bacin rai, domin ya tsani duk wani abu da zai batawa Emily rai idan aka cire shi kansa, a iyakar gidan yasan babu mai yi mata rashin kunya da rashin magana da kokarin bata mata rai ko tuna mata da rayuwar da ta jefar sai Fatima, domin London ba shi da lafiyar damuwa rayuwar kowa sai idan ciwonsa ya tashi. Ta dago daga cikinsa a hankali ba tare da ta kalleshi ba, sai ya kai hannunsa ya rika pink lips dinta ya dan dagota kadan. “Karfe nawa zaki tafi aiki gobe?” “6:30am” Ya sake kallonta da kyau yana matsawa kusa da ita. “Wane irin aiki ne ake tafiya karfe 6:30am na safe?” “Haka matar ta fada min karfe 7 ta yi min a can” Ta amsa har lokacin bata kalleshi ba. Ya kankance ido kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya kai hannunsa yana shafa gefen fuskarta. “Shiga ki kwanta, ki samu bachi da wuri” Ta kalleshi kadan. “Good night” “I love you” Ya furta ba tare da jiran ta mayar masa ba, domin be taba furta yana kaunarta ta amsa masa ba, tun farkon haduwarsu har zuwa yanzu da take kokarin samun kanta, ya mata uzuri domin ya nutsa a labarinta, yayi rayuwa da ita ya san zahiri da badininta, yana iya jin yadda abun ke tsikarta duk kuwa da kasancewar be wanzu cikin wancan rayuwarta ta ba, sai dai a yanzu ya jiku da kaunarta sonta na hana shi ganin abubuwa da yawa a na laifi akanta. Tana tafiya rumgume da hannayenta har ta shiga falon ta rufe sannan ta shiga wani bangare na falon ta dauko mopper ta gyara gurin, a falon ta zauna na tsawon lokaci, ba kallo take ba, ba tunani take ba, ba bachi taka ba, wani yanayi take ji wanda rabinsa babu bakinciki, kuma babu kishiyarsa, wani yanayi taka ji na dabam. Motsin saukowar Chidimma ya saka ta juyo tana kallon stairs din har Nannyn ta sauko. “London yayi bachi, Fatima kuma dakinta a rufe yake, na murda bata bude ba, wata kila ita ma ta yi bachin ne” Nannyn ta fada cike da ladabi, Emily ta dago daga kishingiden da take a jikin kujerar tana cigaba da kallon Chidimma. “Kina kokarin da yarana, musamman Fatima, halayenta ba masu kyau ba ne na sani, amman ina fatan zata sauya nan gaba” Chidimma ta yi murmushi tana jindadin yadda Emily ke karfafa nata guiwa tana appreciating duk wani abu da take yi ma yaranta. “Zata canja ranki ya dade, a yanzu tana da kurciya ne, she's just 6” Emily ta daga gira. “I hope so, Good night Chidimma” “Good Night Ma'am” Ta amsa mata da kai sannan ta fice daga katon falon, Emily ta mike tsaye ta rufe kofar falon sannan ta kashe komai na kallo da kuma na'urar sanyaya falo ta haura sama, dakinta ta shiga ta dauke wani makullin ta nufi dakin Fatima ta saka key din ta bude dakin. Turawa ta yi ta shiga sai ta same ta kwance a kasa rumgume da teddy dinta, sanin yarta sikila ce ya saka ta fara kashe ac dakin dake kunne domin akwai sanyi a garin, karamin abu ne ta tashi da ciwo washe gari. Gefen gadon ta zauna tana kallon Fatima da kamanin mahaifinta suke zube a fuskarta kamar an tsaga kara, ta kai hannunta ta shafa fuskar yarta. “Ina da tsada a gareki Fatima, amman baki sani ba, saboda kina karama, kina fada min magana son ranki, kina wasu halaye da bana so, ina jin cewar kamar ke ma kin tsane ne kamar mahaifinki” Ta share hawayen da suka zubo mata. “Kin yi sa'a kina da ni a raye, a lokacin da nake sa'arki, ina a wani gidan marayu tare da yaran da suka rasa iyaye ko aka tsinta, macen dake kula da ni ta fada min ina jaririya ba a yanke min cibiya ba aka aje ni a gidan, har yau ban san dalilin da zai saka uwa ta aikatawa yarta haka ba” Ta shafa fuskar Fatima a karo na biyu, sai kuma ta yi murmushi. “Na san zafin rashi, na san zafin yaudara, na san zafin kiyayya, ba zan yarda ku fuskanci ko daya ba, zan jure zan mutu saboda ku yara, ku ne kawai iyalina” Ta sumbanci kumatun Fatima ta ďaga daga kan gadon ta gyara mata lullubinta sannan ta fice daga dakin, ta nufi dakin ďanta na fari. Tana kallon fuskarta sai ta yi murmushi ta gyara masa kwancinsa tana zancen zuci. ‘Wata kila ni tawa uwar ta mutu, shiyasa aka kawo ni a nan, amman me yasa yan'uwanta ko yan'uwan mahaifina ba su iya rike ni ba? Haihu ba tare da aure ba a addinin kirista ba abu ne na kunya ba, kamar wasu addinan ba, balle nace ko tana kunyar haihuwata ne’ Ta sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ta fito daga dakin ta koma dakinta, gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, sam ba zaka santa a da ka ganta a yanzu kace ita ce ba, sai idan ka yi mata farin sani, domin jikin da take da shi a can da, yanzu babu, ta zama fit da ita like a model, farin fatarta a yanzu ya sauya ya ninku da kaso mafi daraja domin a yanzu ta samu kwanciyar hankali da abinci mai kyau da lafiyayyen gurin bachi, da kwanciyar hankali, abubuwan da ta rasa a baya. Ta fara tsege kanta tana tuna wani lokaci da Khalifa yake yanke mata gashin kai saboda kawai wulakanci da tozarci, har ta gama tsife kan ta cire gashin dokin dake tsarkafe cikin nata red hair din bata daina hawaye ba. Kwashe gashin dokin ta yi ta zuba a dusbin sannan ta gyara kanta, idan ba ka taba ba, ko kuma an fada maka ko ka sani babu wanda zai yarda gashinta ne domin jan gashi take dashi ba kamar sauran mata da suke da jan gashi ba, ko da yake blue eyes dinta da farin fatarta ya isa ya fahimtar da duk wani mai kallonta cewar ita ruwa biyu ce ba tare da tantama ba. Ta canja tufafin jikinta zuwa na bachi, ta gadonta ta jingina, ta dade a haka sannan ta mika hannu ta dauko file din da Amal ta bata a gurin aiki ta bude tana duba dokoki da ka'idodin kamfanin, bayan ta gama ta saka hannu a duk gurin da aka bukata, sannan ta aje ta kwanta ba tare da ta kashe wutar dakin ba, domin bata bachi da wuta a kashe. Kasancewar a cikin duhu yana firgita kwakwalwarta, ta kan kasa sakewa da rasa natsuwa sa sukuni, sanin hakan da Vito yayi ya saka shi tanadar mata duk wani abu da zai bata haske idan babu wutar nepa. Bata kwanta da wuri ba, hakan ya saka bachin yayi mata nauyi bata tashi a lokacin da ta so tashi ba wato 4am. Karfe biyar da yan mintuna ta farka tana murza ido, alarm din dake gefen gadon mai hade da agogo ta dauka ta duba. 5:14am ya saka ta zabura da kuzari ta sauka saman gadon ta saka bedroom slipper ta fice da sauri. Tun kamin ta sauko kasa ta soma jin kamshin yana dukan hancinta, tsayawa ta yi ba tare da ta karasa saukowa daga kam stairs din ba tana kallon hanyar Kitchen din da dan tsoro, a iyakar saninta Chidimma ba ko da yaushe take shiryawa yaranta abun karyawa ba, sai idan bata gidan ko kuma ta bukaci ta shirya musu din, and babu wanda ya san kudurinta na son shirya abun karyawa da wuri saboda fita aiki, ita kanta bata shirya musu abun karyawa sai 6am. To waye a kitchen din. Ta fara bin falon da kallo, har idonta ya sauka akan rigar Vito dake aje a kan kujera, siririyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin kamar hankalinta ya kwanta, daman idan wani abun cutarwa ne ai zata ji hayani ko a tashe ta, tun da akwai mai gadi a gidan. Saukowa ta yi a hankali kamin ta karasa Kitchen sai gashi ya fito rike da plate, dinning ya nufa ya aje plate din sannan ya nufo gurin da rigarsa take ya dauka ta nufota ta rufe mata jiki da rigar ya kai bakinsa saitin bakinsa zai sumbance ta. “You already know how much i hate physical touch, i hate anything related to love” Ta fada bayan ta kawar da kanta, sai ya juyo da fuskarta yana kallon cikin idonta zuwa gashin kanta dake red, irin na jajayen turawan nan da ake haihuwa da jan gashi. “Good Morning” Ya fada ba tare da murmushi ko sakin fuska ba, daman murmushi da far'a abu ne da suka yi ma fuskarsa tazara, abu ne mai wahala yayi murmushi idan ma yayi kadan ne ko na gefen fuska balle kuma dariya da yake jin bata zame masa dole ba. Hannayenta ta saka ta sauke nasa hannayen dake rike da fuskarta, ta nufi kitchen tana fadin. “Me kake dafawa? Me yasa ka zo nan da wuri haka?” Juyawa yayi yana kallonta madadin ya amsa mata sai ya jefo mata wata maganar da ya saba fada mata a duk lokacin da take kokarin kaucewa kaunarsa. “Da ace zan yi arba da mutanen biyu da suka saka kika tsani soyayya, suka rikita miki lissafi, da na saka sun tsani kansu, da na rikita kwakwalwarsu” “Sun dade da mutuwa a gurina, rayuwa ta baya ma na jafar da ita, Emily din da ba ita ce yanzu ba, wacan ta mutu wannan kuma yanzu take rayuwa” Ya taka ta bi bayanta har cikin kitchen din ya tsaya daga gafe yana kallonta, ita kuma sai duba abincin take, farfesun naman kaza, sai dankali da plantain, dayan cooler kuma samosa ne da zafinsa. Ta daga ta kalleshi da blue eyes dinta masu matukar daukar hankali. “Meyasa ka shirya duk wannan” Ya matsa kusa da ita sosai. “Kin fada min 6:30am zaki tafi aiki, bana son ki tafi da yunwa, kuma na san idan kin farka zaki iya cewa sai kin shiryawa Fadima da Londom abinci zaki tafi, shiyasa na zo tun 4am, na shigo kina bachi” Kallonsa take cike da tausayawa domin hidimar da yake ta yi da ita, bata san wata hanya da zata saka masa ba. “Me yasa kake takurawa kanka da yawa saboda ni? A irin wannan lokacin kamata yayi ace kana kwance kana bachi ne, V baka bukatar hidima irin wannan saboda ni” Hannunsa daya ya kai ya rika fuskarta, kaunarta yake karanta a fuskarta da idonta, da ta san yadda yake jinta a ruhinsa wata kila da bata fada masa magana makamanciyar wannan ba. Be ce da ita komai ba ya saki fuskarta ya gyara mata jacket dinsa dake jikinta ya rumgume ta, ya lumshe ido. Ta jure iya juriyar da zata iya na bashi damar rabar jikinta na second goma ne kawai bayan wannan sai ta fara kokari raba jikinta da nashi. A tare suka karasa dan abun da ba za a rasa ba, sannan ta shiga ciki ta wanke bakinta ta fito ta yi breakfast din yana zaune yana kallon yadda take jindadin abinci, ba lokacin cin abincinsa ba ne, baya karyawa dai 10am, a yau kuma kallonta kadai da jindadin yadda take cin abincinsa ya wadatar da shi, farincikin fada masa abincinsa yayi dadi da ta yi ya kosar da duk wata yunwa da zai ji a wunin ranar. Ya daga mata kai yana murmushi kadan, yana jin kamar ace su daure a haka, su yi zama irin na masoya ko ma'aurata, sai dai ya san samun haka a gurin Emily a yanzu ba abu ne mai sauki ba. Kallon agogon falon da ta yi ya saka ta yi hanzarin karasa cin abincin ta mike tsaye. “Bana son na yi latti, karfe 6:30am zan tafi aiki” “Wane irin aiki ne za'a tafi karfe 6am? Me yasa kike son takurawa kanki a yanzu Emily kina da komai a nan” Bata ce masa komai ba, ta cire jacket dinsa ta aje a jikin dayar kujerar, ta kwashe kayan da ta bata ta kai kitchen sannan ta wuce ta haura sama. Mikewa yayi tsaye ya nufi jacket din ya dauka yana kallon stairs din kamar mai jiran fitowarta. TURHAN POV. “Baka amsa ni ba” Ta maimaita da yaren da ita da shi suka fi fahimta, wato Larabci. Lemun dake gefen Laptop din ya dauka ya sha ya aje sannan ya kalleta ta cikin Systems din dake gabansa. “Ba yanzu ba, akwai wani aiki da ya taso min, ina son sai na karasa shi tukuna?” “ما طبيعة عملك يا حياتي؟” “Wane irin aiki ne Hayatie?” Ya kawar da fuska kaminnya juyo ya kalleta yana shafa kansa, bata jira amsarsa ba ta sake aika masa da wani zancen. “لا أستطيع تحمل غيابك عني.” “Ba zan iya jure rashinka a kusa da ni ba” “Abu mai muhimmanci baki bukatar sani, idan na kammala zan dawo” “Ka canja min a yanzu” Ya shafa kansa yana jin wani sabon fushi na kokarin rufe shi. “Saboda bana haihuwa ne, ko kuma dai ka gaji da zama da ni ne?” “Zaki iya ba ni ďa? Zaki iya haifa min jinina Jalila?” Ta yi shiru tana kallonsa kamar yadda shi ma yake kallonta, kamin ya kai hannu ya rufe Laptop din ya kwanta jikin kujerar yana maida numfashi, me yasa ya fada mata haka? Al'adunsu da dokokin sa ake cilasta masa bi ba daga ita ba ne daga masarautarsu ne da kuma mahaifinsa. Ya tashi zaune yana jin fushinsa yana karuwa tunawa da yayi da yadda Ammy ta yi fushi da shi, saboda yarinyar da bata da ala komai da ita. Gaba daya an hada masa zafi ta ko'ina, babu wani daki daya da zai laba yaji sanyi. Wayarsa ya dauka ya kira abokinsa har lokacin be sauka daga fushi da bacin rai da yake ji ba. ALIYU POV. Yana zaune a kan gado, matarsa na kwance kanta na cinyarsa, ita da shi sun sakarwa plasma dake dakin idonsu, gadon da suke kai kuma ya karbi amanarsu, domin kana kallonsu zaka san hankalinsu a kwance yake basu da wata damuwa ko kadan. Wayarsa dake can kan karamin tebur ajeye ce ta yi ringing, a take ya ja tsaki domin ya ji dadin zaman baya son motsawa. Gashi be saba zama kusa da wayarsa ko yawo da ita idan yana tare da matarsa ba. Abu ne da ya sabawa kansa da shi aje wayarsa a nesa da matarsa a duk lokacin da yake tare da ita, doka ce ya sakawa kansa matukar yana gida tare da iyalinsa to lokacinsa na matarsa zai bata kulawa iyakar kokarinsa. Gwanar na jin haka sai ta tashi zaune tana kallonsa. “Na dauko maka ka ba ni dubu biyu?” A take murmushi ya subuce masa. “Wai ke ina zaki kai kudi da son kudin nan?” Ta saka dariya. “Zaka biya na dauko?” “Aa ni ma fa na san zafin kudi Hajiya, zan dauko kayata” Sai ta maida kanta a cinyarsa. “Ni gaskiya na jidadin kwanciyar nan ba zaka tashi ba” “Okay saboda ni zan dauko ko?” “Idan ni zan dauko zaka biya, idan ba haka ba gaskiya ba zan daga a cinyar nan ba, ai kasan idan kana gida kai nawa ne ni kadai” “Ko ma bana gida ni naki ne har abada, yanzu daga ni na dauko sai na biya 2k din, kin ga wannan tsohon cikin naki ba zan so kina wahala ba” Ta daga masa saboda ta ji yace zai bata kudin kuma zai dauko wayar da kansa. “Hmmm ku dai maza idan kuna tare da mu ku namu ne idan kun fita kuma na wasu dai” Ya mike tsaye ya isa ya dauko wayar yana murmushi already kiran ya yanke. “Ke dai kishi zai miki illa, me ya kawo wannan maganar kuma?” “Ai na san halin maza” “Bayan wa kika aura? Da zaki ce kin san halin maza?” “Kai kadai na aura amman ai ana fadar halinku” “Ni dai na banbanta da sauran, yanzu wanda yake da mace yar dumaduma irinki har wata zata burge shi?” Ya fada bayana bin bayan kiran da aka masa. “Hello Allah ya taimaki Yarima” Daga dayan gefen Turhan yayi murmushin karfin hali. “Tsokanar ta tashi kenan, ya gida?” “Lafiya kalau” “Sorry na kira late na san kana tare da Madan ko?” Aliyu ya kalli uwargidansa yana murmushi “Kamar ka sani kuwa, daker ta bar ni na amsa wayar ma” “To a bata hakuri, wani uzurin ne ya taso min...” Turhan ya shimfida masa kudurinsa sannan ya bijiro masa da bukatarsa. Aliyu ya dan sosa kansa. “Akwai wandanda zan hada ka da su ba ma daya ba, amman Turhan kana ganin nemanta abu ne mai sauki? Ni ma fa na saka anbincika maka lokacin da na yi zama a Lagos din nan amman ba a dace ba” “Wannan karon ina son na bi gidajen marayun da yake cikin garin Lagos ne, na bincika ko zan dace” “Eh toh kuma ka kawo shawara, amman duk da haka ina ganin zai yi wahala saboda an kwana biyu, kuma ka fada min tun tana karama aka yi rikonta a can, kuma ba lallai ne ka sami ma'aikatan gurin na da ace su ne har yanzu?” “Yeah amman ina zaton indai sun santa sosai da sosai za su gane ta idan na bada misalinta wata kila za a dace” “Dama dai kana da hotonta abun zai fi sauki” “Haka din ma zan gwada wata kila a dace, ina tunanin duk wanda na fadawa sifofinta blue eyes red hair, fara mai kiba sosai zai gane ta matukar ya santa” “Allah yasa a dace, zan yi magana da wani yarona da yake can da safe sai na hada ku” “Okay thank you” Ya aje wayar ya sake zaunawa kusa da matarsa, wannan karon sai ta tashi zaune tana kallonsa. “Kyakkyawana” “Hmmm” Ya amsata yana wani tunanin na dabam, har idonsa suna motsawa, sai kuma ya tabe baki zuciyarsa na raya masa abun da be isa ya fada a gaban matarsa mai tsananin kishi ba. “Kana ji na” Ya aje wayar ya mika mata hankalinsa gaba daya. “Ina jinki Sarauniyata” “So nake ka yi min wani alkawari” “Na me?” Ta yi shiru na wani lokaci kamar mai nauyi fada sai kallonsa take tana nokewa kamar marar gaskiya. “Na miki alkawari cewar ba zan kara aure ba bayan ke?” Ta daga masa kai tana mamakin yadda yayi saurin lagonta. “Eh ya aka yi ka gane me nake son fada?” “Na sanki da kishi ne ai, zuciyarki zata raya miki idan na fita waje mata nake kulawa ko?” “Na san ba halinka ba ne, ba zaka kula mata ba, amman su matan za su iya kawo maka hari kuma zuciya bata da kashi, kuma ni gaskiya ba zan iya sharing dinka da kowa ba” Yayi murmushi ya shafa fuskarta. “Saka ranki a inuwa, Aliyu na ki ne ke kadai daga ke babu kari babu wanda zata kawo hari na rufe kofa, na miki alkawari ba zan taba miki kishiya ba” Ta bude ido tana mamakin yadda yayi hanzarin bata hadin kai da wuri haka, ko da yake ta san waye mijinta ba mutum ne mai son mata ba, kuma ya sha fada mata tun kamin ya aureta cewar shi ba shi da ra'ayin aure mace sama da daya. ______________ Anya Aliyu zai rike alkawarin nan kuwa? Turhan zai samu ganin Aisha kuwa? Wane irin so Vito yake yi ma Emily? Meyasa Emily ta dage sai ta yi aiki? Bayan duk gatan da ta samu a gurin Vito? [4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Barka da warhaka mutanen arziki😍 Shim kun san cewa Khadeeja Candy komai da komai? Amman banda ɗan mutum da mutum😃 Ina masu neman kayan Kitchen masu kyau masu inganci, Luxury Warmers manya da kanana, ina masu neman Bedsheet kings and Queens manya da kanana, ina masu neman Akwaitunan lefe da na tafiya. Khadeeja Candy na da Boxes kala kala, ina masu neman tufafi, kama daga Atamfa, Laces, Shadda Lace, Veils, shoes and Bags, Materials. Akwai freezer, Gas cooker and water dispenser. Duka zaku samu a gurin Khadeeja Candy Store, Khadeeja Candy dai taku ta makaranta, da fatan za ku yi patronizing ɗina. Za ku iya join group dina domin bawa idanuwanku abinci https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Kuma zaku iya saka order ta wannan number 08036126660 WhatsApp. KHADEEJA CANDY STORE expect more, and pay less...😊 Page 5️⃣ Bata sauko ba sai da ta tabbatar ya fice daga gidan, sannan ta sauko ta sakawa Fatima lunch dinta a lunch box ta shirya mata komai kamar yadda ta saba, Londom kuma da ake masa darasi a gida sai ta zuba masa a nasa na nasa kayan cin abincin, sannan ta haura saman ta shiryawa cikin shiga ta riga da wando ta saka turare ta maida sarkar Cross dinta a gaban rigarta yadda zata fito da kyau. Red hair dinta ma ya faku da kyau ta yi kyau ta fito tsab, kana ganinta ka ga kyakkyawar mace mai aji, da matukar daukar hankali. Id card dinta na aikin ta fara dauka ta saka sannan ta dauki jacket ta saka saboda yanayin garin akwai sanyin sai dai ba sosai ba. File din jiya ta dauka tare da jakarta ta wayarta ta fice daga dakin, sai da ta shiga dakin Londom ta duba shi ta sunbance shi sannan ta fito ta leka dakin Fatima, sai ta same ta zaune da alama farkawarta daga bachi kenan. Da murmushi Emily ta karasa kusa da ita ta aje kayan dake hannunta ta shafa kanta. “Good Morning Princess” Fatima ta kalleta ba tare da tace komai ba. “Okay jiya na san mun yi fada kamin ki kwanta kin kwanta da fushina I'm sorry” Ta bata fuska. “I just hate Vito Mom, ke kuma kullum kina shigar masa baki ganin laifinsa” “Princess V be mana komai na ganin laifi ba, yana kula da ku yana kula da ni, gidan nan da duk abun da yake ciki nasa ne, be taba mana komai ba” “I just hate him, bana son ki aure shi Momy” Ta fada cikin kuka, Emily ta juyo ta fuskance da kyau damuwar ganin hawayen yarta na bayyana a fuskarta. “Ba aurensa zan yi ba, ni na gama aure a rayuwata, amman baki da dalilin tsanarsa, shi yake kula da mu, shi kadai ne mutumen da ya rike ni ba tare da kyama ba, shi kadai ne ya kaunace ni a yadda nake yake kokarin kyautata min, shi ya maida ni yadda nake a yanzu” “Ya fada min aurenki zai yi ko da bana so, yace min na fara kaunarsa tun a yanzu saboda shi zai zama step father dina” “No no... Princess ba zan auri kowa ba, ba zan aure shi ba, ba zai zama stepfather dinki ba, but ya kamata ki girmamashi” “No... To mu bar masa gidansa Momy” Emily ta shafa fuskarta. “Shi ne kudirina, amman ba zan iya haka ba sai na tsaya da kafafuwana, shiyasa na dage nake son fara aikin nan, zan rika saving kudi idan na tara zan koma wani gurin za mu bar masa gidansa da komai nasa, na miki wannan alkawari Fatima” Fatima na jin haka sai ta rumgume ta da sauri tana murna. “Promise Mom” “I promise” Ta fada yana shafa bayan yarta, Fatima ta dago daga jikinta ta rike fuskarta. “Momy a ina kika samu aiki” “Wani babban kamfani ne dake hakar ma'adanai da bincike akan albarkatun kasa, babba guri mai girma kuma mai hawa har biyar” “Ke a hawa na nawa kike?” “Na hudu, ina aikin da wata mace mai mumman hali, sunanta Amal kin san musulmai ba su da kirki ko? Ita ma bata da kirki ko kadan” Fatima ta wara ido kamar ba ita ce ta gama fushi dazun ba. “But I'm Muslim Mom you know” Emily ta ja kumatunta. "You're different because you were raised by a Christian mother" Ta yi dariya ta sauka daga kan gadon, Emily ta bita da kallo tana jin kaunarta sosai, haka take son yaranta fiye da kanta, tana son farincikinki yaranta fiye da nata, bana son su rasa komai domin ta san yadda ake ji idan ka rasa wani abu, domin ta tashi ita kadai ba tare da yan'uwa ko iyaye ba. Ta sani ta rasa farinciki, sai dai ta daukarwa kanta alkawarin ba zata yarda yaranta su rasa farinciki ko su shiga makamanciyar kazantacciyar rayuwar da ta shiga ba. Tana zaune gurin har Fatima ta fito daga bandaki ta shimfida karamin sallayarta ta dauki hijab, kallonta kawai take cike da burgewa tana jin dadi tana jin farinciki a duk lokacin da ta ga yarta tana ibadar da ta zabarwa kanta, bata son tauye mata hakki ko kadan hakan ya saka ta barinta ta aiwatar da addinin da ta dorata akanshi da farko kamin ta yi kokarin canja mata ra'ayi hakan kuma ya gagara saboda abun da shiga zuciyar Fatima sosai. Even though ba ko da yaushe take sallah ba, amman duk inda zata shiga ko a tambaye zata fadi cewar ita musulma ce, hakan kuma ya kan bawa duk wanda ya san mahaifiyarta mamaki, domin mutanen da suka san Emily a yanzu sun santa a Christian, kamar yadda sarkar Cross din dake wuyanta take nunawa a kullum. “Okay Princess zan tafi aiki, na san yanzu Chidimma zata shigo ta shirya miki zaki tafi makaranta, i love you” Ta fada sannan ta mike tsaye ta dauki kayanta ta fice daga dakin. Ta yi tafiya sosai kamin ta samu abun hawa kasancewar safiya ce ba kasafai ake samun ababen hawa a unguwar da safe irin lokacin da ta fita ba, gashi bana da ra'ayin amfani da motar da V ya siya mata tana son nesanta kanta da wasu abubuwan ne tun a yanzu. Karfe bakwai daidai mai texi din ya shiga da ita cikin kamfanin, sai da ta sallame shi sannan ta fita tana kallon yadda a yanzu ake bude wasu bangaren ma, masu shara da mopping na yi. Tsirararun mutane ne kawai suke shigowa a kamfanin. Kai tsaye ta shiga ciki ta hau Elevator zuwa 4 floor din da take, a nan din ma ta samu masu mopping suna gyara floor din. Da Keys din hannuna ta yi amfani ta bude kofar Office dinta ta shiga sai ta shiga ga mamakinta sai ta samu an goge ko'ina. Da mamaki ta aje file da jakar hannunta ta fito ta tambaye wani namijin dake mopping a gurin. “Dan Allah ka ga wanda ya shiga office din nan?” “Gaskiya bayan ni babu wanda ya shiga” “Kai ka gyara office din?” “Eh ni na gyara ni nake gyara ko'ina ai” “Kana da key din dakunan kenan?” “Eh ni nake kula da ni ni aka hannatawa komai” “Okay sannu da kokari” Ta koma ciki, har ta zauna sai ta tuna da Office din Amal a take ta yi hanzarin tashi ta fito ta nufi office din ta bude sai ta juyo ta kalleshi. “Me yasa baka gyara nan ba?” “Tace ke zaki rika gyara mata” “Okay...” Ta furta with little bit of confused, why her? Bayan ya fada mata shi yake gyara ko'ina, ko da yake Amal din ta fada mata da kanta tun a ranar farko. “Idan ka gama ka ara min mopper zan gyara gurin” A madadin ya bata sai yayi mata jagoranci zuwa gurin da ake aje moppers din ta dauko daya da tsintsiya ta gyara office din tsab sannan ta mayar ta aje. Komawa ta yi office dinta ta zauna bata san me zata yi ba dan haka ta bude data ta ta shiga social media sai misalin tara ma'aikatan kamfanin suka fara shigowa. Misalin 9:15am telephone dinta ta yi ringing, a gurinta abu ne sabo a kirata da telephone in her own office, sai da ta yi murmushi sannan ta amsa kiran “Hello” “Ki same ni a office” “Oka...” Kamin ta karasa wayarta furta okay din Amal ta aje telphone din. Emily ta mike tsaye ta fice daga office din zuwa office din Boss dinta. Tsayawa ta yi tana knocking domin bata manta gargadin da tayi mata ba a jiya. “Yes” Ta mata izinin shiga bayan ta bata lokaci tsaye a gurin. “Good Morning Maa” “Na fada miki sunana Amal ki daina kirana Maa kamar wata tsohuwar” “I'm sorry” “Waya gyara dakin nan yau?” “Ni na gyara” “Good, sauraka kasa ki samo min snacks zan yi breakfast da ki siyo min bubble tea” Ta jafa mata Atm dinta, tana duba wasu takardu. “Ina file din da na baki jiya” Emily ta kalli Atm din dake kasa, me yasa ba zata iya bata da hannunta ba ko ta dora a tebur ta dauka? Me yasa take son wulakantata? Ko da yake ba abun mamaki ba ne ita din ai musulmace, ta duka ta dauki Atm din tana amsa mata. “Yana office dina” “Idan kin ga dama ki kawo nan” Kallonta kawai Emily ta yi ta juya ta fice daga office din, nata office ta koma ta dauko file din ta sake knock ta tsaya har sai da ta yi mata izinin shiga sannan ta shiga ta aje mata ta fito. A nan kuma ta fara tunanin ina zata samo mata snacks da bubble tea a yanzu, ita ba sanin kamfanin ko unguwar ta yi sosai ba. Haka dai ta nufi elevator ta danna botton din dake jiki ta bude mata, ta shiga sannan ta taba number 1, a take ta fara yin kasa har ta isa first floor ta fita, wata zuciyar na fada mata ta tambaye mutane wata zuciyar kuma na hana ta, ita wa ta sani ma balle ta tambaya. Haka ta mike ta fita daga roof din kamfanin ta mike doguwar hanyar har ta isa gate. Ta kalli dama ta kalli hagu kaminnta yanke shawarar nufar left side tana tafiya tana dubawa ko zata samu mai siyar da wani abu amman bata samu ba sai da ta bar unguwar gaba daya ta shiga wata karamar unguwa dake kusa da su, sannan ta fara ganin masu siyar da abubuwa wasu ma yanzu suke fitowa domin goma ta dan gota. Abubuwan da ta fada su ta siya mota ta biya da Atm din sannan ta sake juyowa tana takowa a kafa, tun tana tafiyar tana jurewa har ta fara gajiya ranta ya fara baci, tana daf da isa kamfanin ta ji an yi mata magana da shigar da Vito ne kadai yake mata haka. “My Beautiful Babe” Ta kalli gefen da titi yake sai a lokacin ta lura da motar dake binta, yadda fuskarsa take hade kai kace ba shi ne yayi mata furucin mai dadin sauraro ba, dan murmushi ta yi ta tsaya har ta bude motar ya fito, tana mamakin ganinsa. Ko da yake ba abun mamaki ba ne domin ya san kamfanin take aiki kuma kamfanin ba boyayyen kamfani ba ne. “Waya aike ki siyen abu?” Ta kalli robobin dake hannunta da bubble tea. “Uhmm...” Ta yi shiru kamar mai tunanin abun da zata fada. “Ba ki sha Bubble tea na sani, kuma na shirya miki breakfast kamin ki fito, so don't lie to me” “My Boss” Ya gyara tsayuwarsa yana jin ba dadi. “Are you a maid hare? A aike ki ki siyo abinci shi ne aikin nan Babe?” “No ita kadai ce ta aike ni, saboda a karkashinta nake aiki, kuma ta zo bata karya ba” Ya kalli kayan dake hannunta da kyau sannan ya sake kallon fuskarta. “Ba ki rasa komai a gida ba, ban san miyasa kika zabi wannan rayuwar ba” A kokarinta na kawar da zancen ta ce. “Me ya kawo ka nan?” Ya sauke numfashi a hankali ya matsa kusa da ita sosai. “Na zo ne na yi miki bankwana zan tafi Lagos yanzu, akwai kayana da aka rike dole sai na tafi za a sake su” “Drugs...?” Ta tambaya kai tsaye, be amsa mata ba sai kawai ya kai middle finger dinsa yana shafa soft kuncinta na dama up and down, idanuwanta cikin nasa ita tana jira amsar tambayarta shi kuma kaunarta kawai ke kara zafafa daga idonta zuwa nasa idon then straight to his heart. Dauke yatsansa yayi ganin tana kokarin kawar da fuskarta ya juyo ba tare da yace da ita komai ba ya bude bakar motarsa mai bakin gilashi ya shiga ya ja ya barta tsaye a gurinta yana kallon sawunsa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta karasa cikin kamfani, a nan ma sai da ranta ya kara baci saboda tafiya ce mai tsayi daga gate din zuwa cikin kamfanin, haka dai ta daure saboda tana son aikin, daman hausawa sun ce daukarwa ya fi bauta ciwo. ALIYU POV. Yana daura necktie dinsa ta aje masa littafi a gaban madubin da yake shiryawa ta zauna gefen gado tana kallonsa. Kallon littafin yayi sannan ya kalleta “List din yaudara za a fara min? So kike duk sai kin karar da abun da na tara kin maida ni talaka ko?” Ta saka dariya tana kai apple din dake hannunta a baki. “Aa Wallahi kasan jiya ka yi min alkawari, to ni dai ban gamsu ba so nake ka rubuta, domin a doka ya fi ka'ida” Ya zauna kusa da ita yana murmushi mai sauti. “Rantsuwa fa na yi miki jiya baki yarda ba?” “Na yarda amman dai kara ayi a rubuce ko da ka manta na rika tuna maka, ni fa a rayuwata babu abun da na tsana irin kishiya, ni bana sonta ko kadan, ko wata macen ka kalla a tv bakinciki nake ji, kuma mata a yanzu sun yi yawa da kansu ma suke kawowa mazan mutane hari, idan na mutu dai sai ka yi aure amman idan ina raye ban yarda ka yi aure gaskiya” Ya girgiza kai, ya dauki littafin yayi rubutu a kai. “Ni Aliyu Mudallab na yi alkawari ba zan yi ma Matata Aisha kishiya ba, har abada zata zauna ita kadai a gidana sai yayanta” Yana rubutawa yana fadar alkawarin har ya gama yayi saka hannu, ba tare da tunanin komai ba, domin har ga Allah ba shi da ra'ayin kara aure. “Hakan yayi miki?” Ta daga mishi kai tana murmushi sonsa na karuwa a ranta. Bakinta ya sumbanta kadan sannan ya mike tsaye “Sarkin kishi, anya zaki bar ni a aljanna na more hurul'aini kuwa?” “Wallahi ba zan bari ba” Ta fada da karfinta, kyalkyalewa yayi da dariya sosai ya dauki abubuwansa ya fice tana masa addu'a tare da rakiya har kofar falo. Sai da yayi addu'ar fita daga gida sannan ya fice ya shiga motarsa yana dago mata hannu da blowing mata kiss sannan ya fice. Karatun Qur'ane ya kunna a motar kamar yadda ya saba, domin baya sauraren waka idan ma yana son rage kadaice ne sai dai ya saurari karatun ko ya karanta ko ya rera kirar da kansa. Kamar kullum baya shigowa sai 11am ko fiye da hakan ma, idan yayi sakammako shi ne zai shigo 10am, kasancewar CEO na kamfanin, sai dai kuma baya barin kamfanin sai 3pm ko 4 sometimes har 5pm ya kan kai idan aiki yayi yawa, ko wani Meeting. Ya faka motarsa a gurin da aka tanadar masa sannan ya bude motar ya fito, iPod dinsa ya saka a kunne ya cigaba da sauraren karatun Qur'ane a kunnensa na hagu, ta ko'ina ya wuce gaishe shi ake har nufi elevator, matar dake cikin yake kallon irin kallon nan da ya kasa kyabta ido ma balle ya dauki, kallonta yake da kyau yana tantancewa, tunaninsa kuma yana tafiya wani gefen. Yana shiga ciki sai ya taba 5, a take Emily ta taba 4 ba tare da ta kalleshi ba. “Ni na fara zuwa” Be ce mata komai ba bayan karkatowa da yayi ya kalleta ya kalli ID din dake kirjinsa, ita kuma sai ta yi zaton kirjin nata yake kallo, hakan ya saka ta kokarin gyara rigarta da maballi sama yake bude ya bayyana wani bangare na kirjinta sai dai be fito da dukiyar fulaninta ba. A kokarinta na yin hakan Bubble tea din dake hannunta ya fadi ya zube. Bakinciki ya saka bata san lokacin da ta fara yi masa ihu ba. “Kallo har na bala'i har na masifa, ka kura min ido har na zubar da abun da na yi wahalar tafiya can wata unguwa nesa na siyo” Nan din ma dai be jin magana ta zame masa dole dan haka ya adana kalamansa ya kalli gurin da ya bace kawai ya dauke kansa, his mind is somewhere else shi dai jin yake kamar ya taba ganinta, and he won't lie tana da masifar kyau, ta ko'ina ta kai mace, shiyasa William ya rikice jiya yana ta masa santinta. Suna isa four floor ta Elevator ya bude sai ta fita suna hada ido ta watsa masa masa wani kallo na jin haushi wanda ya fi kama da harara. Ya dauke idonsa da sauri ta har Elevator ya rufe, number 5 ya taba, ya ciro wayarsa ya kira Turhan. “Hello Aleeyou” Turhan ya fada da dan sautin labarancinsa kadan. “Turhan, yarinyar nan da kake nema fara ce sosai?” “Eh fara ce, tana da jan gashi, da blue eyes and tana kiba” Kibar da Turhan ya fada ya saka Aliyu kwankwanto, domin ita dai wannan da ya hadu da ita daga jiya zuwa yau siririya ce. “Tana da masifa?” “No bata da fada ko kadan, tana da tsoro idan ma aka mata fada sai dai ta yi kuka ba zata iya maida magana ba” “Okay, sunanta Aisha ko?” “Eh bata da wani suna bayan wannan?” “Ba zata rasa ba, amman na manta sai na bincika Ammy ko zata fada min” “Ta yi dogon boko ne?” “No bana jin ma ta gama Secondary School, ba wai na san komai ne akanta ba, amman dai zan bincika, me ya faru?” Aliyu ya amsa masa yana ficewa daga Elevator. “No na tambaya ne kawai saboda na taya ka nema” “Na gode sosai Aleeyou, yau zan tafi Lagos din In Shaa Allahu, ka taya ni addu'ar Allah yasa na dace, ga matsalar masarautarmu, ga matsalar Matata ga matsalar neman yarinyar nan” “Karka damu komai zai wuce, ita haihuwa ai lokaci ne, ita kuma za a same ta In Sha Allahu” “Ina fatan haka” “Okay bye Allah bada sa'a” Ya sauke wayar yayinda yake tura office din farko ya shiga. “Good Morning Sir” “Morning Nick. Please inform Michael to notify our new staff members that buying food during working hours within the company premises is not allowed. They can only do so either before work begins or after closing hours, as it seems they are not familiar with our rules. Also, remind them to sign in when they arrive and sign out when they leave” “Okay Sir” Ya amsa yana dan sirinawa alamar girmamawa, sai da Aliyu ya shiga office dinsa sannan Nick ya zauna ya fara cika umarnin boss dinsa da System kamar yadda aka saba, duk wani abu da za'ayi a cikin kamfanin sai dai a tura ta email, sai idan uzuri ne ko kuma wani abu ne da ya shafi mutum personally sannan ake amfani da Telphone din da aka tanadar a kowane Office. _______ Allah yasa Aliyu ya cika alkawarin da ya dauka, domin maza sai Allah. Anya idan Vito ya san kudurin Emily na guje duk wani abu nasa zai barta kuwa? Kuna ganin Emily zata iya jure aiki a karkashin Amal kuwa? Shin Turhan zai yi nasara idan ya tafi Lagos neman Aisha? [4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 6️⃣ Sai da ta sauke numfashi sannan ta tura kofar office din ta shiga, ta manta da dokar Amal na neman izini kamin shiga. A gaban teburinta ta dora mata abun da ta siyo sannan taja ta tsaya tana jiran Amal ta gama wayar da ta shigo ta same tana yi.    Sai da Amal ta gama wayar sannan ta kalleta a fusace. “Wai ke kam baki da tunani ne ko kuma dai rainin wayo ne yayi miki yawa? Zuwanki na farko na miki gargadin shigo min office ba tare da neman izini ba amman baki ji ba ko? Ke ba yarinya ba balle ace za'ayi ta maimaita magana” Emily ta kalleta da kyau tana jin babu dadi domin matar dake zaune a gabanta tana mata fada bata wuce sa'arta ba, amman take kokarin wulakantata saboda kawai tana aiki a karkashinta. “I'm sorry na manta ne, zan kiyaye next time” “Better” Cewar Amal tana daga bubble tea din da ya zube. “Shayewa kika yi?” “No zubewa yayi by mistake” “To zan fada a cire min a cikin albashinki, yanzu kuma je ki siyo min wani” “Okay” Emily ta amsa mata sannan ta juya ta fice jiki a sanyaye, cikin rashin jindadi da kasala ta sauka kasa ta sake komawa gurin dazun ta siyo mata wani bubble tea din ta dawo ta hauro sama ta yi knocking ta jira har sai da ta yi mata izini sannan ta tura ta shiga. Saman teburinta ta dora mata tare da atm dinta sannan ta juyo ba tare da tace mata komai ba zata fice sai Amal ta kirata. “Hey” Emily ta juyo ba tare da tace komai ba, Amal ta nuna mata tulun takardun da suke zube kasa a gafen teburin. “Ki dauki wannan ki je ki yi typing dinsu, a yadda kika gansu a papers idan kin gama ki turo min ta email dina” “Okay” In short sannan ta nufi tulun takardun ta dauka ta fice daga office din zuwa nata Office din, Widows din office din ta bude tana kallon titi da kasan building din, hutun minti goma ta yi sannan ta juyo ta zauna a kujerarta ta bude system din ta fara typing tana murmushi kamar ba ita ce ta gama bacin rai a dazun ba. Sai dai abun da baka saba ba, yana da wuyar aiwatarwa musamman a karon farko, bata jima tana yi ba ta fara gajiya, haka dai ta daure ta cigaba da typing har azahar. Bata bar office dinta ba sai 4pm domin bata yarda ta fito ba sai da ta tabbatar ta gama komai, ko da ta fito kusan wasu sun dade ta tafiya gida, few mutane ne suka rage irinta sai kuma ma'aikatan dake gyara kamfanin. Bata samu Taxi ba dan haka ta hau okada ya kaita gida, bayan ta biya shi ta kwankwasa gate din mai gadin ya bude mata ta shiga ciki cike da gajiya, jakarta kawai ta jefar ta shiga kitchen, lunch da Chidimma ta aje mata ta dauka ta fito falo ta fara ci da sauri saboda yunwa. “Anya zan iya aikin nan? Haka aikin yake ko kuma dai...” Sai kuma ta yi shiru ba tare da ta karasa ba ta cigaba da cin abinci, a gurin da ta ci abincin a gurin ta kwanta ta fara bachin wahala da gajiya bata farka ba sai Magariba. “Momy...” Ta bude idonta daker domin bachin be isheta ba, ta kalli yarta. “Fatima” “Momy yau kin kwanta da wuri” Ta tashi zaune tana murmushi sai a lokacin ta tuna da yaran domin gajiya ta saka ta manta da su. “Ina kuka tafi?” Chimdimma ta tafi da mu park daga can muka je gidansu. Emily ta kalli Chidimma dake tsaye. “Baki fada min ba” “Yes saboda Oga ya zo bayan kin fita yace na rika fita da su, saboda baki da lokacinsu yanzu kar ya zama suna kadaici a gida, musamman Londom da yake ba lafiyayyen ba” “Okay amman daga yanzu, karki sake fita da yarana ba tare da kin fada min ba” “I'm sorry Maa” Emily ta mike tsaye ta nufi gurin da danta yake tsaye kusa da Chidimma ta risina tana shafa fuskarsa. “My Baby how is your day” Ya mata murmushi kawai ya cire hannunta a fuskarshi. Chidimma ta saki hannunsa “Sai da safe ranki ya dade” Emily ta fahimci Chidimma fushi ta yi dan haka ba ta dakatar da ita daga tafiya ba. “Ba zaki karanta mana story book ba?” Fadima ta tambaya. Sai mahaifiyarta ta amsa mata. “Zan karanta muku, ina da labari mai dadi da zan baku, and zan girka muku dinner mai dadi” Tana maganar tana rawa da kai tana murmushi, a take farinciki ya cika fuskarsu, yadda ta fada haka ta aiwatar, tana girka musu abinci tana fada musu yadda ta sha wahalar aiki yau. “Ma'aikatar ana aiki da yawa ne Momy?” Fatima ta tambaya tana cin abinc. “Ina tunanin haka, amman akwai wahala wata zan saba zuwa gaba” Ta busar da iskar bakinta, tana shafa kanta. “Momy can i ask you something?” “Yes My Love” “Me yasa ake sunana ya kasance Fadima Aisha Emily, not Fadima Hamza like London” A take Emily ta ji wani kunci da bacin rai ya tunkarota da kamar fada ta ce. “Again? Ina tunanin mun gama wannan maganar tuntuni?” “Momy kowa yana using sunan babanshi, amman ni sai dai na yi using sunanki? Why? Even London ana kiransa London Hamza, why not London Aisha Emily?” Emily ta aje spoon din dake hannunta ta mike tsaye. “Time to bed” “I need to know Mom kullum yan makarantarmu sai sun min dariya, Yau ma da nafi gidansu Chidimma an tambaye ni sunana na ce Fadima Aisha Emily sun min dariya” “Ba na sha fada miki ba ki da Baba ba?” “London me yasa yake da Baba, Me yasa ake ce masa London Hamza?” “How many time do i have to told you Babansa ya mutu, ke kuma ban haife ki da ubana ba, haka nan na haife ki” “But-” “But, if you ask me one more Question zan doke ki da daren nan” Ta fada mata a tsawace. “But kin taba cewa Babana musulmi ne, amman ban taba jin sunansa ba” Da sauri Emily ta bar dinning din domin ta san idan ta kara minti daya a gurin zata doki Fatima ne, gidan ya rikice mata domin tun a yanzu London ya fara rikicewa yana kuka. Dakinta ta shiga ta zauna bakin gado ta rike kanta tana shafa goshinta a hankali idonta a rufe sai numfashi take maidawa da karfi. Ta kwashe minti talatin a haka sannan ta mike tsaye ta cire rigar jikinta ta shiga bathroom ta yi wanka ta fito ta saka fajamas sannan ta sake dawowa falon ta nufi London da har lokacin kuka yake ta rumgume shi. “Ya isa haka ya isa haka gani a nan” Jikinsa yayi zafi sosai alamar fever, rage tsayi ta yi ta dago shi daga jikinta ta kalleshi. “London saurareni, kukan ya isa haka kaga jikinka ya fara zafi, Fatima London yayi wasa da ruwa?” Fatima ta juyar da kai ta rumgume hannayenta ta turo baki gaba tana cigaba da kallon tv ta ba tare da ta amsa mata ba, ita ala dole fushi take. “Fatima I'm talking to you...!” Emily ta daka mata tsawa har sai da London din ya zabura ya kara fashewa da kuka. “Yayi wasa da ruwa” Ta amsa mata a dikile sannan ta mike tsaye ta haura sama tana wani halba kafa kamar wata babba. Emily ta rumgume London tana jin kamar ta fashe da kuka, domin babu abun da yake firgitata a yanzu kamar rashin danta, He's not just an autisms yana fama da sickle tana yawan tashin masa lokaci zuwa lokaci, abu kadan yana iya saka ciwon nasa tashi, kusan ta fi wahalar da shi fiye da Autisms domin yana a cikin jikinsa ya zama rayuwarsa da hallintarsa ce a haka, wannan kuma a cikin jininsa take. Daukarsa ta yi ta koma saman cushion ta zauna tana rumgume da shi tana juyawa a hankali, kamin ta aje shi ta tashi ta haura sama ta shiga dakinsa, maganin ta dauko ta sauko ta bude ta bashi sannan ta tallaba shi daker ta haura sama, suna shiga dakinta ya fara kwara amai a jikin sai ta sauke shi da sauri ta rike shi. A nan fa hankalinta ya tashi da sauri ta sake shi ta nufi gurin da ta adana keys din motarta ta dauka da nufo shi ta dauke shi saman duk wani nauyinsa sai ta daina jinsa a lokacin. Kamar ba ita ba haka ta saukowa downstairs din da sauri ta nufi kofar falon ta bude ta shimfidashi a balcony ta nufi gurin da jerin motocin uku na gidan suke ta matsa remote din hannunta domin gane keys din wace motar ce ta dauko. Sai da ta fito da motar sannan ta nufo shi ta dauke shi har lokacin amai yake ta saka shi motar, gaba daya ta gama fita hayyacinta, ko kadan bata son wani abu ya sami yaranta sai take ganin zata ragu ne, domin a halin yanzu bata da wasu family bayan Fatima sa London, kuma ta tabbatar ba zata sami wasu ba, domin alkawarin da ta daukarwa kanta abu ne da take jin babu wani abu da ya isa ya saka zuciyarta kusantar kofar da zata karyashi. Yadda ta ja motar ta fice daga gidan kai kace koyon tuki take bata kware ba, domin jikinta rawa yake ta ko'ina irin rawar nan na wanda ke tsoron faruwar wani abu, each and every second sai ta juya ta kalli danta dake gidan baya tana kiran sunansa, kamin ta isa asibitin gaba daya ta fita hayyacinta, domin bata taba ganin danta yayi amai mai yawa haka kamar yau ba. Babbar asibitin kudi ce da aka saba kwantar da London a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ba London kadai ba har Fatima da ita kanta Vito ya dauki nauyin a duba su asibitin ta kudi. Ta karbi kati shiga asibitin suka duba bayan motarta sannan ta tuka da karfi ta isa Emergency ta fito a firgice ta tare da ta kashe motar ba haka kuma tashin hankali be barta ta rufe motar ba, ta bude back seat da sauri ta fara janyo danta sai ta ji karfinta ya kare ta gagara fitowa da shi, sai kawai ta fashe da kuka ta saka ihu, securities din da suke tsaye a emergency din suka nufota da sauri suka fito da London da har lokacin amai yake ta shekawa. Nurse suka fito da gado aka dora shi. “Dan Allah ku taimaka min kar ya mutu, ku taimaka kar ya mutu” Shi ne abun da take ta fada da halshe Ibo tana kuka ta bi bayansu, daya daga cikin security ne ya shiga motarsa ya faka a gurin da aka tana domin aje motoci, ya shiga mata da key din. Tana ta zarya ta kasa tsaye ta kasa zaune, kafarta babu talkami kanta a yamutsa fajamas din dake jikinta ma kadan wandon ya wuce mazaunanta be gama sauka a cinyarta ba, rigar kuma bata da kauri sosai. Kusan kowace fatar jikinta a bude take, ban da kirjinta zuwa kasan cibiyarta. “Ga keys din motarki” Ta kalli key din sannan ta karba ta rike ta cigaba da zirya kafarta babu talkami, kana kallonta kasan a firgice take, hankalinta kuma be kwanta ba sai da London ya samu saukin aman da yake yayi bachi a dakin da aka sauke shi, Likitan da ya karbe shi ya kalleta yana murmushi. “Da sauki ma fa sosai kawai ke ce kika daga hankalinki” “Be saka yin amai irin wannan mai yawa ba, kuma zafin jikinsa ya wuce kima” Ta fada hawaye na sauko mata. “Eh amman da sauki sosai, kuma ina son na baki shawara ya kamata ace kuna da likitan dake zuwa yana duba shi akai akai, kin ga kamar irin yanzu, da ace akwai likitan dake duba shi ba sai kin yi wahalar zuwa ba, sai idan abun ya gagara, yana da ki samu likitan da zai duba shi koda yaushe, yadda kike daga hankalinki wata rana ba zaki iya kawoshi asibiti ba” Ta daga masa kai, sai ya daga kafadarta alamar karfafa guiwa ya wuce, ita kanta zata so ace akwai likitan dake duba danta duk lokaci, sai dai tasan Vito ba zai yarda ba, domin baya yarda da kowa ya shiga gidanta balle kuma rayuwarta ko ta yaranta, ta yi ta kokarin yin haka yin haka ba sau daya ba amman be amince mata ba. Ta shiga dakin ta rufe kofar a hankali ta karasa kusa da shi tana kallon fuskarsa. Rayuwarta take tunawa a wani dare makamancin wannan da rashin lafiya ta kamata, ita kan ta fishi wahala kwananta uku tana ciwon ciki kamin akaita asibitin, sai kuma aka rasa mai jinyarta domin bata da kowa sai gamon tsintsiya da ragga wato mutanen da aka raine ta a tare da su a gidan marayu. Ta zauna a kujerar dake kusa da gadonta ta kama hannunsa ta rike, jininta ne wannan shi ne kadai zata iya shaidawa duniya cewar ita din daga gareta yake, kuma shi din nata ne, bayan wannan da kanwarsa bata da wani abun tunkaho, da ace ta rasa shi a yau da daren yau ya fi kowane dare muni a gareta. Hannu ta saka ta share hawayen idonta tana tunanin Fatima ta san zata ji tsoron zama ita kadai a gidan gashi bata fito da waya ba balle ta kira Chidimma tace ta shiga ta kwana tare da ita, haka kuma ba zata iya barin ďanta shi kadai a irin wannan lokacin da bata san karfe nawa ba ta tafi gida. Bachi rabi da rabi ta yi saboda tunanin Fatima, da kuma danta dake tsare da shi, sanyin asuba na fara saukowa ta mike tsaye daga kan kujerar yana mika, kamin ta sirina ta sumbanci danta dake bachi ta shafa kansa zuwa fuskarsa, tana matukar tausayin rayuwarsa saboda yadda tasa kaddarar ta zo, shi din ba kamar sauran yara ba ne, gashi kuma ciwon sickle be barshi yayi walwala ba. Ta dago ta nufi kofar ta bude a hankali ta fice ta rufe, haka ta taka har gurin motarta babu talkamin domin bata zo da su ba, sai da ta yi ta dubawa sannan ta gane gurin da aka aje mata motar. Ta tuka motar cikin natsuwa ta isa gida, sai dai ta yi horn ya kai goma kamin mai gadin ya taso ya bude mata, ta faka a gurin da ta dauki motar ta bude ta fito tana amsa tambayar jikin London da mai gadin yake domin ya ga yadda aka fita da shi. “Ya ji sauki” Ta amsa a gajiye sannan ta nufi cikin gidan ta bude ta shiga, sama ta haura da sauri ta shiga dakin Fatima, ba karamin dadi ta ji ba ganin Chidimma na rumgume da ita suna bachi, ta yi murmushi kadan sannan ta juya ta fice daga dakin ta shiga nata dakin, tufafin jikinta ta cire ta shiga bandaki ta yi wanka ta fito daure da bathrobe ta daure kanta da tawul. Kitchen ta nufa tana hamma ta kunna gas ta shirya abun karyawa, sannan ta fito a daidai lokacin da Chidimma ta sauko kasa. “Good Morning Maa” “Morning Chi” “I'm sorry na kwana a nan ne saboda Fatima ta same ni tana ta kuka wai ba zata iya kwana ita kadai ba” “Kin kyauta na jidadin haka, ga abun karyawa nan na shirya ki shirya yanzu ki tafi asibiti gurin London, saboda zan tafi gurin aiki yanzu, ki fadawa direban Fatima idan ya daukota daga school ya kirani zan fada masa inda nake aiki sai ya kaita saboda kar dawainiyar ta miki yawa, idan na tashi zan biyo asibitin idan sun ba mu sallama sai mu dawo tare” “Okay Maa” Emily ta ratsa gafenta ta haura sama, cikin kankanen lokaci ta shirya ta fito dakinta ta leka dakin Fatima sai ta same ta a bandaki tana wanke bakinta “Good Morning My Love” Fatima ta juyar da fuska, cikin rashin jindadin abun da ta yi Emily tace “Idan kin tashi daga School ki fadawa direbanki ya kira ni, zai kawo ki gurin da nake aiki idan ban tashi ba a lokacin, saboda Chidimma zata tafi asibiti gurin London, ni kuma zan tafi aiki” Tana fadar hakan ta ja mata kofar bandakin ta rufe ta fito daga dakin ta sauko kasa tana jin zuciyarta na mata babu dadi, ta karasa dinning wayarta na ringing a karo na uku, tea ta zuba ta daga cup din ta sha rabi sannan ta nufi kofar falon ta bude ta fice.    A road din unguwarsu ta amsa kiran Vito dake ta shigowa wayarta, ta sani ba dan baya garin ba da yanzu ya karaso gidanta, domin a ka'ida idan yayi mata kira uku bata daga ba to ba zai yi na hudu ba, zata ganshi gidan ne. “Hello” “Are you okay? Lafiya kike?” Ta ji kamar ta ce masa aa ina cikin damuwa kuma ta fada masa London yana asibiti amman bata son daga masa hankali, haka kuma bata son yana shiga al'amurranta kokarin jenye shi take daga jikinta. “Yeah I'm fine” Dakikun da ta dauka bata ba shi amsa ba ya saka shi fahimtar tana cikin damuwa, daman kuma ya karanci muryarta. “Don't lie to me, me ya faru bayan bana nan?” “Fatima ce kawai bata jin magana” Yayi shiru ba tare da ya ce komai ba, sannan ya kashe wayar, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya ta tari okada ta hau ta, be sauketa ko'ina ba sai gurin aikinta. ALIYU POV. 8:36pm... Gaba daya yanayinsa ya canja zuciyarta ta sosu kuma ransa ya bace sosai saboda abun da yayi arba da shi a wayar matarsa. Sai dai a cikin sharudansa akwai kokarin kwantar da hankali da kuma yin uzuri a duk lokacin da wani abun bacin rai ko tashin hankali ya same shi, ya sani ya dara matarsa Aisha Ilmi da goge, kamar yadda ya fita shekaru haka ya fita hankali da zurfin tunani domin hankalin namiji ba daya yake da na mace ba. Ba da'asar bace bincikar wayar matarsa domin ya yarda da ita 100% ko da yake ita bata yi masa irin wannan yarda ba saboda kishi, a duk lokacin da ta samu dama sai ta bincike wayarsa, sai dai tana daga masa kafa domin bata taba daukar wayarsa ta bincika ta same shi yana chatting da mata ba, ko wani abu makamancin wannan, abu ne da ya daukarwa kanta nisanta wayarsa da duk wani abu da zai dauki hankalinsa daga matarsa a lokacin da tafi bukatarsa a kusa da ita. Ya haddace password din wayarta, ita ma ta haddace masa saboda yarda da suka yi da junansu. Ya aje wayar yana kokarin saita kansa, domin be kamata ya nuna mata bacin ransa a yanzu ba, ko ba komai tana dauke da juna biyu zata iya damuwa, haka kuma ba zama lallai abun da yayi arba da shi a wayarta ya zama wata illa ko laifi a idonta ba. Ta kalleshi bayan ta sallame sallar Isha'i tana murmushi. “Ki yi min addu'a” “Ai kullum ina maka addu'a amman cewa nake Allah yasa daga ni babu kari” Ya daga kafadunsa yana murmushi mai sauti. “Daman ai daga ke babu kari, wai baki yarda da alkawarin da na yi miki ba?” “Na yarda mana, amman matan yanzu fa shaidanu ne, kai dai Allah dai ya tsare kawai kuma ya kawar da idonka” “Ameen” Ya girgiza kai ya kai hannu ya dauki dabinon ajwa ya kai bakinsa, sai da ta kammala addu'ar sannan ta dawo kusa da shi ta zauna ta cire hijab din. Janta yayi a hankali ya kwantar jikinsa. “My one and only ina bukatar tuna miki wani abu, kuma ina son ki dauke shi serious” Ta dago kadan ta kalleshi. “Minene?” “Sirrinmu sirrinmu ne, be kamata wani ya ji ba, musamman na auratayya, yadda muke mu'amala da duk wani abu da ya shafi gonarmu be kamata wani ya sani ba” Gabanta ya fadi, domin ta fahimci kalamansa sai dai kunya irin na wanda aka tsinkawa zane a kasuwa ba zai barta ta nuna masa ta fahimci nufinsa ba. “Ni bana gane yarenka ka fito fili ka fada min abun da kake nufi” Ya tashi zaune da kyau ya fuskanceta. “I'm sorry na shi whatsapp dinki na san be kamata na shiga ba wata kila akwai sirrinki da yan'uwanki da be kamata na ji ba ko na sani, akan hakan ina baki hakuri, wani sako ya shigo ta sama kuma na bude na gani, wata kila saboda na samu damar tunatarki me Allah ya nuna min sakon” “Kana ta jan sakon da tsaye please minene?” Ya aje numfashi a hankali. “Na ga wani chat da kike da kawarki Huda, ban san iya aminci ko yardar dake tsakaninku ba, amman Aisha ban jidadin yadda kike fada mata sirrin shimfidarmu ba, ko a musulunci babu kyau, kuma maganganun ne da basu dace ba” Ta dan wara ido tana murmushin da ya kusa zame mata dariya. “Haba dai, wannan fa duk zancenmu ne na mata, kuma ita da ba ganinka take ba ma” “Ko dai minene tun da kika ga musulunci ya hana be kamata ki aikata ba, akwai illa ciki? Fadin amfanin me zai mata? Shikenan kin bude mata cikinki ta san sirrinki ta san sirrin mijinki, yadda muke mu'alama da komai ta sani, ban jidadi ba kuma in miki daukar mace mai hankali ne mai sani ya kamata, ban yi tsammanin zan ga haka ba, kuma ban jidadi ba” Ya karasa da dan fada domin ya fahimci kamar bata dauki abun a wani abun ba, ganin haka ya saka jikinta yayi sanyi, shi kuma be sake ce mata komai ba ya tashi ya fice daga dakin. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta dauki wayar felling guilty ta bude chat din tana dubawa tare da mayar da amsar tambayar da Huda take mata, kamin da kara da. “Ke yau ya duba wayata ya ga chat dinmu” Sannan ta kashe data ta gyara kwanciyarta da kyau, domin abu ne da ta sani idan suka samu tsabani shi yake bata hakuri, shi yake nemanta. Ba dabi'arsa bace bawa miji hakuri idan ta yi laifi, haka kuma ba mace ce mai saurin karbar laifinta ba, idan ma har ta aminta tana da laifin kenan. And to her hira da kawa ko a group chat da mata yan'uwa Normal ne domun suna suna fadar yadda suke tasu mu'alamar kuma dukansu mata ne babu maza, bugu da kari tana ganin aminci da jindadi ke saka irin wannan chat din. Bayan duk wannan ma why zai dauki wayarta ya shiga chat dinta da kawarta ko kawayenta har ya ga abun da suke tattaunawa, a ganinta a nan kam shi yake da laifi, kuma dai chat irin wannan tsakanin mata ai ba wani abu ba ne, dan haka bata shirya ba shi hakuri a yanzu ba. Yadda ta ayyana haka ne ya faru domin bayan ta yi bachi ya dawo dakin ta kwanta a kusa da ita, daman can no matter how suka samu tsabani baya taba raba gado da matarsa balle kuma har ta kai ga ya raba daki. Yayi bachi not like usual yadda ya saba, domin yana son ya nuna mata illar abun da ta yi, dan haka be shirya abun karyawa ko ya jira ta shirya masa ba yayi wanka ya yi shirin office ya fice daga gidan at early morning. [4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 7️⃣ TURHAN POV. “Shikenan zan jiraka a waje” Ya aje wayar ya nufi gurin da suitcase dinsa yake ya bude ya ciro wani karamin roll on ya murza a wuyan hannunsa sannan ya aje a mirror dake dakin ya sake nufar wayarsa ya dauka ya saka aljihu ya dauki key din dakin ya fice ya rufe dakin. Stairs ya bi har ya sauko daga hawa na uku zuwa na daya, kamin ya karaso kasa ransa ya gama baci domin Turhan ba mutum ne mai son motsa jiki ba sai dole, ko kadan baya son aikin wahala balle kuma wahalar ita kanta da baya hada hanya da ita. Harabar hotel din ya fito yana kallon yadda tsari da kawar babbar hotel din take daga kasa, domin sun sauka sa dare ne a jiya, gajiya bata bashi dama kamar yadda hutu ya bashi a yau da safe ya kalli ko'ina ba. Kusa da wata flower ya tsaya yana kallon ko'ina da kyau, kyam idonsa suka sauka akan wata hallita mai ban tsoro, mutum ne irinsa namiji mai kirar mazaje da jarumtaka, Turhan ya dauke idonsa daga kallon mutumen da shi ma kallonsa yake babu kyabta ido. Ganin sarkar Cross a wuyan mutumen da murdaddiya fuska irin na wanda baya sha'awar dariya, ya saka shi fahimtar addininshi da nasa akwai banbanci, tattoo jikinsa ma ya sanar da hakan. Feeling awkward ya saka shi ciro wayar dake aljihunsa ya fara dannawa, ya dauki lokaci a haka kamin ya sake dagowa ya kalli harabar, a karo na biyu ya sake kallon gurin da mutumen dazun yake tsaye yana kallonsa and wannan karon ma yana tsaye and still kallonsa yake har yanzu, irin kallon nan mai daure kai ga wanda ake yi ma shi, da mace ce take kallonsa sai yace ko tana sonsa ne, amman namiji kamar wannan da zai yi wahala su hada hanya da imani abun tambaya ne a kallon da yake masa, zuciyarsa ta raya masa wata kila yayi masa kama da wani ne da ya sani ne, idan ba haka ba kallon da yake masa yayi yawa, and babu wani dalili da zai saka yayi ta kallonsa haka. Kallo ne mai rikitarwa da mamaki ga wanda ake yi ma shi, hakan ya saka Turhan jin babu dadi kuma ya dan tsorata, ganin ba garinsu ba ne, haka kuma ba gurin da ya saba mutanen ba ne, ko be taba zuwa ba, ya kan ji ana fadar bad side na Lagos, dan haka dole ne yayi taka tsantsan. Takawa ya fara yi cike da izza da takamar da suke zame masa jini ya isa gate din hotel din hannayensa rumgume a bayansa sai kamshi yake zubawa tafiyarma ita kanta ta karbe shi kana ganinsa kasan babban mutum ne kuma dan babban gida. Sai da ya fice daga katon gate din dake bude sannan ya juyo kadan ya kalli mutumen dazun domin jikinsa ya ba shi har lokacin yana kallonsa, ga mamakinsa sai ya ga mutunen yana kallonsa har yanxu, kusan kallon yanxu yafi muni fiye da na dazun, domin a yanzu yana iya hango tsana da harzuka a idanuwan mutumen da be san waye ba, be kuma san dalilin haka ba. Wannan karon Turhan be tsaya shawarta zuciyarsa ya daga wayarsa ya kira Faruk. “Wai baka karaso ba har yanzu? I'm not safe here fa, ina jin tsoron irin mutanen da suke a nan gaskiya” “Gani isowa ranka ya dade, na kusa karasowa, ka kwanta da hankalinka babu komai In Shaa Allahu, Hotel din da ka sauka hotel ce mai tsaro sosai, ba wani matsala In Shaa Allahu, da akwai matsala ai oga Aliyu ba zai bari na sauke ka a wannan hotel din ba” “Ina fatan haka” Ya fada sannan ya sauke wayar tare da jan dogon numfashi, wannan karon be yarda ya sake juyawa ya kalli bayansa ba, balle ya san da wanzuwar mutunen dazun ko akasin haka, sai ya cigaba da tafiyarsa. Kamin ya sake daga wayar ya kira farar uwar data kawo shi duniya. Ringing daya biyu ta daga, daman bata ignoring call dinsa idan tana kusa da waya, tun a lokacin da suke shiri da juna da kuma yanzu da ta sauya mu'amala da shi, banbancin wacan kiran da kuma yanzu, idan ya kira bata kusa bata mayar masa da kiran, kamar yadda ba zata amsa kira da saukin kiransa ba, ba kamar can farko ba da take daukin kiransa da far'a da na jindadi kuma yake kiransa idan ta samu miss calls dinsa, a yanzu sai dai ta amsa masa duk abun da zai fada ne ba a cikin dadin rai ba. “Ammy ina kwana?” “Lafiya Kalau” “Ammy na sauka Lagos jiya da dare sosai, na yi tsammanin ganin kiranki ki tambaya ko na iso lafiya” “Gashi ai mun yi magana yanzu, kuma da ba lafiya kake ba dole za a kira a sanar min” Wani abu na rashin jindadi ya ji ya ratsa zuciyarsa, jiki a sanyaye ya furta. “Haka ne, Ammy na zo nan ne neman Aisha kuma duk saboda ke ne, ba dan ke ba ba zan yi haka ba, ina fatan dacewa ki taya ni da” Kalmar duk saboda ke ne, ya tsayawa Ammy a rai lallai ne ta sani danta yana son farincikinta da albarkarta haka kuma yana nuna cewar har a yanzu bana son zabin nata kawai dai zai nemi Aisha ne saboda gyara laifina ba dan tsantsar nadama da kaunarta ba. “Fatan nasara Turhan Mohamed Abdo” Tana fadar hakan ya aje wayar. Ta lumshe ido ta hade bakinta guri daya ta gumɗe tana maida numfashi a hankali. Jawahir ta rufe magazine din dake hannunta tana kallon Ammy cikin yanayi na damuwa. “Ammy kina daukar abun nan da zafi ne sosai, ni da Maama dukanmu yayane a gurinki, be kamata ki yanke shawara ko ki yi wani hukunci mu saka baki ba, amman bahaushe yace mai shawara aikinsa baya baci, sai dai ba shi da sirri, kuma mai shawara ba ya nadama, amman na san ranki ya bace sosai akan Yaya Turhan amman ya kamata ki yi hakuri...” Bata karasa ba Ammy ta bude idonta ta kalleta, tsoron furuci ko fadan da zai fito a bakin Ammy ya saka ta yanke maganar da bata karasa ba. Ammy ya gyara zamanta da kyau tana kallon Jawahir. “Jawahir mahaifinki ya taba baki labarin cewar bayan haihuwar Turhan ban sake haihuwar kowa ba?” It take her 5 seconds to answer. “Ammy abu ne da kowa ya sani a familynmu bayan Turhan baki sake haihuwa ba” “Amman ya taba fada dalilin da ya saka bayan Turhan ban sake haibuwar kowa ba?” “Aa be taba fada mana ba, Abba baya zama yayi hira da mu yadda kike yi Ammy” Ammy ta yi shiru tare da dora hannunta daya akan daya. “Dauke breakfast din nan” “Baki ci komai ba Ammy” Ammy ta daga mata kai, Jawahir ya tashi tsaye da dauke breakfast din ya fice, Ammy ta mike tsaye ta nufi karfen dake balcony din ta tsaya yana kallon harabar gidan. Ammy na jin lokacin da Jawahir ta bude kofar falon ta fito balcony din da Ammy ta fi yawan zama musamman da safe idan zata karya ko kuma da yamma. “Mahaifinku ya taba fada muku cewar na zauna a gidan kaso?” Mamaki ya cika fuskar Jawahir. “Gidan kaso kuma? Yari fa kenan Ammy” Ammy ta daga mata kai ba tare da ta juyo ba. “A zamanin da na yi yan matancin, a cikin yayan sarakuna musamman na yankin arewa bana jin anyi wata yar sarki mai farinjini irina, ba nufin sarautar gidanmu ko kudin mahaifina ba, ina maganin farin jini ne wata baiwa da Allah ke hallita bawa da ita” Ammy ta juyo tana murmushi ta kalli Jawahir dake tsaye. “Ba ni da kyau sosai, haka kuma ni dan ba za a kalleni ace min mummuna ba, kamar yadda ni ba fara ba amman ba fi fararen matan kyau da shiga zuciyar maza, bana zama a guri na tashi wani be so ni ba, na yi farinjini sosai, yayan manyan mutane da manyan mutane sa kansu sun nuna sha'awar kulla danganta da mahaifina ta hanyar aurena, a lokacin da ace za a titsi ni na fitar da wanda nake so ba zan iya ba, domin hankalina ba a kan soyayya yake ba, kuma dukan masu neman aurena suna kyautata min yadda ya kamata na so su, mahaifina kuma yana alfahari hakan” Ta nufi kujerar data tashi ta zauna Jawahir ma ta zauna a kujerarta tana kallon Ammy fuskarta fal da mamaki. “Wata rana mahaifina ya karbi babban abokinsa kuma babban sarki garin Khartoum, masarautarmu ta san da zuwan sarkin kusan kasar ma ta san da haka, domin ya gana da shugaban kasar wacan lokaci kamin ya iso masarautarmu, bayan tafiyarsa mahaifina ya shigo cikin masarauta ya saka aka kira ni, na zauna a gabansa kaina na kasa ya sanarmin cewar ya kyautar da ni aure a gurin dan Sarkin Khartoum, a wacan zamanin idan iyaye suka yanke shawara ba a musawa ko da a gurin bayi ne balle kuma yayan sarakuna, wacan lokacin yayan sarakuna basa aure sai yayan sarakuna yan'uwansu, na amsa masa babu musu, a lokacin ba zan iya amsa cewar ina son kyautar da mahaifina yayi min ko akasin haka ba, iyakar abun da zan iya shaida an aurar da ni ga mutanen da ba su san darajar dan'adan ba, mahaifina ya kulla alakar ne saboda ya karfafa zumuncinsu, kuma yayi bugun kirji cewar Balarabe ya auri yarsa Maryam ta yi farinjini, sai dai mahaifina ya manta cewar balaraben Asali baya son kowa sai balarabe dan'uwa, kadan ne suke son wani yaren, sai dai ko kadan basan son bakar fata, kuma basa son girmama ra'ayinsa, basa kallonsa da kima, balaraben mutum baya son bakar fata ko kadan, da fari sun nuna kamar za su janye, domin mijin da aka ba shi kyautata be shirya karin wani auren ba bayan wanda yake da shi da farko, ban san miya ja ra'ayinsa ba, sai kuma ya amince” Ammy ta share hawayen da ya sauko mata. “Daga lokacin da aka daura min aure, aka dauke ni akai kai a masarautar, sai na fara fuskantar kalubale, tun da na shiga masarautar ban saka mijina a idona ba sai da aka yi sati biyu, idan na fito cikin masarautar sai na fuskanci wulakanci, ba irin wulakanci na bawa da sarki ne, wulakanci irin na banbancin launin fata, wulakanci irin na wanda aka kyauta a gurin da ba a da bukatarsa, na fuskanci tsangwaba domin yarenmu da na su ba daya ba, kusan babu wanda ya san an auro a wajen masarautar domin ba a fita da ni, ba a nuna ni a matsayin surukar gidan, sai matar da na tarar wato uwargidana Maimunatu, surukarna suna wulakanta ni mijina da abokiyar zamana ma haka, ko da rana daya ban taba fadawa mahaifinta halin da nake ciki ba saboda bana son ya ji cewar ya zaba min abun da be dace ba” Ta rufe ido hawaye na sauko mata. “Shiyasa nake matukar tausayin Aysha, ni kadai na san irin tsangwamar da ta fuskanta a masarautar, domin na san yadda abun yake, gashi kuma Turhan ya watsa min kasa a ido ya tsaba alkawarin da ya daukar min” Ta bude ido har lokacin hawaye ke saukowa daga idonta, ta mike tsaye ta nufi kofar falon ta bude ta shiga, kai tsaye ta nufi stairs ta shiga dakinta. EMILY POV. Ta kara minti talatin akan lokacin da Amal ta fada mata na shigowa office, domin ta shigo kamfanin karfe bakwai saura mintuna na safe, a tare suka nufi elevator ita da mutumen da suka shiga wacan karon, wannan karon ma a tare suka shiga, ta rasa dalilin kaddara na hadata da wannan mutumen, ko da yake a kamfanin yake aiki kamar ita, dole za su rika haduwa ko da bata so, kamar yadda za ta yi ta haduwa da mabanbanta mutane a gurin. A yau din bata cikin walwala da zumudi kamar jiya, saboda danta dake can kwance a asibiti, gashi kuma yarta Fatima na fushi da ita, thirdly kuma bata samu wadataccen bachi ba, ga gajiyar aikin jiya tattara a jikinkinta, sai ya zama mood dinta ya canja gaba daya, ta sama silent ba kuzari. “Good Morning” Ta gaishe shi saboda tana son ta yi masa tambayar da ba lallai ne idan ta yi ma Boss dinta Amal ta amsa mata ba. Aliyu ya kalleta kawai ya dauke ido ba tare da ya amsa mata ba, hakan kuma ya harzukata. “Daman fa tambaya ce kawai zan yi, karka yi zaton ko ina son kullum alaka da kai ne ko wani abu makamanci haka, haduwar da mu ke kaddara ce ke hada mu, ba wai dan ina son haka ba, ni maza ba burge ni suke ba, so ka sauke girman kan please” Ya juyo ya kalleta a nan din ma ba zai iya karyata kyaunta ba, amman ba zallar kyaun yake kallo ba yadda take bulbule shi da masifa a duk lokacin da kaddara ta hada su ne yake mamaki. “Daman zan tambaye ka ne, ko bakon zuwa ma'ana new comer zai iya daukar hutu saboda wani uzuri na rashin lafiya” Nan din ma be jin zai iya amsa mata, sai kallonta da yake kamin ya dauke kansa. Da yaren turanci take masa magana, sai dai ganin be amsa ta ba ya saka ta wani furuncin da Hausa. “Wato dai ma'aikatar nan kowa dan iskan kansa ne, kowa jin kansa yake, na tambaya wata kila shi ma sabon dauka ne kamar ni, sai kallona yake babu amsa kamar kurma, idan na sake magana kace min aku” Wannan karon be kalleta ba, be kuma bar murmushin zuciyarsa ya fito a fuskarsa ba har suka tsaya a 4 -floor. Ta saka kafa zata fice “Tambaya kawai mutum yayi maka shiru kamar kurma” Ta fada da Hausa. “Aku” Ya furta a daidai lokacin da Elevator ya zo rufewa, ya furta mata hakan ne saboda ta san yana jin yaren da ta yi magana da shi. Sai ta juyo da sauri ta kalli elevator da already ya rufe, zuciyarta na bugawa da karfi, sai a lokacin tunani ya zo mata, what if shi babban ta ne a gurin aikin? Wata kila yana a hawa na 5 ne ma ko kuma sako yake kaina, amman be yi kama da karamin mutum ba. Bata dauka yana jin hausa ba, a tunaninta Igbo ne ko yorba, shiyasa bata yi magana da duka yarukan ba sai hausa, bata yi tsammanin a kusa zata samu mai jin hausa ba kamar ita ba, ko da yake ita ma zama a arewa ne ya saka ta kware a hausar ba mamaki shi ma ya zauna a can din ne. Idan ba haka ba Parthcourt da Zamfara ai akwai nisa sosai, a take ta tunatarta kanta abun da ta manta, kamfani ya kan hada mutane kala kala wasu ma daga wata kasar wasu kuma daga wasu yarukan. Fargabar rasa aikinta ko janyowa kanta wata sabuwar matsalar ya hanata ta sukuni har ta gyara office din Boss dinta ta gama, duk kuwa da wani bangare na zuciyarta yana raya ba wani babba ne a kamfanin ba, domin bata taba ganin wani ya rako shi ba, haka kuma zuwan da yayi da safen nan ya fahimtar da ita haka, domin da babba ne a kamfanin ba zai shigo a irin wannan lokacin ba sai 10 ko 9am kamar yadda Amal take shigowa, wannan tunanin ya yaudari zuciyarta har ta samu sukuni. ALIYU POV. Kusan duk wanda ya san shi fari sani a kamfani ya ga shigowarsa a irin wannan lokacin zai yi mamakin haka domin be saba shigowa a irin wannan lokacin ba. Ya wuni da tunanin matar nan da sake gani a yau, yadda halshenta yake iya furta hausa da kyau haka ya nuna alamar ta taba zama arewa ko kuma daga arewar take ma, sai dai abun da ya daure masa kai siffarta gashin kanta ba sun sanar da duk wani mai kallonta cewar ita din baturiyace, haskenta yayi yawa blue eyes dinta da jan gashinta ya fahimtar da shi haka. Sai dai ya kasa tantancewa shin ita din ce matar da abokinsa yake nema ko mai kama da ita? Idan har kama ce ta ina taya sunan zai zama daya Aisha? Ta ya idon da gashin zai zama hali da jikin ne kawai zai banbanta? Sau hudu yana daga waya zai kira Turhan sai kuma ya fasa domin ba shi da wata kwakkwaran hujjar da zai rike cewar matar da yake gani a kamfaninsu ita din ce matar da Turhan yake nema, idan tsabanin haka ne zai wahalar da abokinsa ne, saboda haka yana bukatar hujja, domin Turhan ya fada masa cewar ita wacan tana da jiki kuma bata da masifa gashi bata yi boko ba, ba kamar wannan ba. Ko dai yan biyu ne, ya tambayi kansa sai kuma ya rasa wa zai bashi amsar. Misalin karfe daya ya shiga bandakin office din yayi alwala ya fito ya kashe Bluetooth din dake kunne yana fitar da kirar'ar Qu'ane ya shimfida carpet yayi Sallah, sannan ya mike tsaye ya fito daga office dinsa. “Nick, if there are any newly recruited employees named Aysha, please bring their files to my office” “Okay Sir” Ya bada umarnin sannan ya fice ya sauka kasa gaba daya, Elevator na budewa yayi arba da mutane biyar masu jiran budewarta ciki har da kyakkyawar karamar yarinya mai goye da jakar makaranta, tana sanye da uniform pink short skirt and White shirt, an yi mata parking din bakin gashinta a baya, tana ta kallonsa da blue eyes dinta kamar yadda yake kallonta babu kyabta ido. Zanen halittar fuskar yarinyar ya saka shi manta mutanen dake mika masa gaisuwa kuma suke jiran fitowarsa domin su shiga Elevator. [4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 8️⃣ “Hi” Ya furtawa yarinyar yana faɗaɗa fuskarsa da murmushi, matsawa ta yi baya ta ta kauce daga mutanen da duke tsaye jiran fitowarsa, hakan ya bashi damar fitowa har ya amsa gaisuwar da ake mika masa, sannan ya kalli yarinyar data matse jikin ginin dake bayanta kamar zata shige ciki, gashi ta hade rai irin na yaron da yayi arba da bakuwar fuskar da be sani ba. Tsayawa yayi a gurin har sai da kowa ya shige cikin Elevator sannan matsa kusa da ita yana murmushi ya mika mata hannunsa. “Hi” Ta hade hannayenta ta kawar da fuska. “Momy na tace na daina magana da wanda ban sani ba, za a iya sace ni” Murmushin fuskarsa ne ya fadada ya gingina kai. “Gaskiya ne, ni ma ta fada min haka ta fada miki shiyasa ba zaki amsa ni ba idan na miki magana, amman na san ki mahaifiyarki ta nuna min hotonki a wayarta tun da dadewa shiyasa yanzu ma ina ganinki na gane ki” Ta juyo ta kalleshi. “Da gaske” Ya daga mata kai. “Uhm-” “To waye kai?” “Ni...” Ya nuna kansa yana tunanin me zai fada mata, sai ta ce. “Are you her new boyfriend?” Ya wara ido. “Boyfriend? No... Karki ji haushi ki yi kishin Babanki” “Ni ba ni da Baba ai, Momy na tace bata haife ni da Baba ba, tsaya ma ka ji sunana Fatima Aysha Emily, amman yayana yana da Baba shi sunanshi Londom Hamza, amman shi babansa ya mutu kamar yadda Momy ta fada, amman ni ba ni da Baba, amman ka ga kowa yana sa baba ko a makarantarmu kowa yana da baba ban da ni, shiyasa na matsu Momy na ta yi new boyfriend so that na samu Baba, saboda na tsani Vito bana son shi shi kuma wai yana son Momy ne, amman ni bana son shi....” Sai da ta kai ayar zancen sannan ta numfasa, mamaki da burgewa ya saka Aliyu jan numfashi. “Hmmmmm wannan yarinyar ya a je da ke Hi-five” Ya mika mata hannu ta mika masa nata suka taba, shi kam abun nema ya samu daman bincikarta yake son yin, sai kuma yayi sa'ar ita din ku ace gurin magana, ya kama hannunta yana murmushi tunawa da yayi da matar dazun wanda tace idan ta sake masa magana ya kirata da aku and he did. “Ciki zaki shiga?” “Eh Momy na tace na zo na same ta a nan saboda yau nannynmu tana gurin London ba shi da lafiya yana asibiti shi sickle ne kuma Autisms, baya yarda da mutane sosai daga Vito sai Nanny Chidimma sai Momy sai ni” Ya nufi elevator ya danna ta bude. Sai da suka shiga sannan ya sake tambayarta. “Shi Victor shi ne Babanki? Ko saurayin Momy kika ce ko?” Ta tofar da yawu. “Allah ya kiyaye bana son shi, sunan shi Vito not Victor Vito sunan yan Italian ne da aka samo daga latin word “Vita” Vito yana nufin rayuwa, sunansa ke nan?” “Amman miyasa kika tsane shi? Ba shi da kyau ne” “Yana da kyau, amman baya yin dariya, and wata rana idan Momy ta bata masa rai sosai yana dukanta, i just hate him, kawai ina zama da shi ne dan dole, amman Momy tace da sabon aikin da ta samu yanzu zata siya gida zamu koma can Vito ba zai sake zuwa gurinta ba” Aliyu ya daga girarsa sama ya sauke yana tan tabe baki kadan. “Wow, okay” “Ina son haka, and na san idan Momy ta bar gidan Vito zata samu Boyfriend sai ya zama Daddyna, ni ina son Daddy” Aliyu ya rage tsayinsa ya kama fuskarta ya rike cike da tausayi, ko bata fada masa uwarta ba ya fahimci akan waye take magana, secondly fuskar abokinsa dake shimfide a yarinyar yake kallo. “Amman kai kana da girlfriend?” Yayi murmushi kawai ya mike tsaye ba tare da ya amsa mata ba. Ita ma bata sake cewa komai ba har suka sauka a 5floor. “Momy na tace a 4 Floor zan sauka office na biyu hannu dama shi ne nata” “Na sani, ina son na kai ki office dina ne mu gaisa” Ya shiga office din yana rike da hannunta, ta bude ido tana ta kallon office din. “Amman kai ya sunanka?” “Aliyu” “Okay Mr Aliyu are you Muslim or Christen?” “Muslim amman Momy na Christen ce, but her name is the Aysha” Ya bude fridge dinsa ya dauko mata lemu ya bata. “Taya kika zama musulma mamarki ba musulma ba?” Ta nufi kujera ta zauna ba tare da ta jira ya mata izini ba. “Okay, Momy na tace babana musulmi ne shiyasa ta saka min suna Fatima kuma na tashi ta ga ina son musulunci shi ne take barina ina yi, ta koya min sallah, ta fada min ita ma ta taba yin musulunci, amman yanzu ta daina” Ya zauna a kujerar dake facing din wanda take zaune. “Kin fada min baki da baba? Taya kuma zaki ce babanki musulmi ne?” “Ni ma haka Momy na ta fada min, shiyasa nake son ta samu new boyfriend ya zama daddy na, amman kai kana da mata?” “huh-?” Ya bude baki not knowing what to say. Ta yatsina fuska. “Kana da ita?” “Uhhhh No” Ya amsa mata saboda ta saki jiki da shi ya samu abun da yake so. “Okay Good” Ta masa thumb up ta fara shan lemun da ya karba ya bude mata ya bata, ya ciro wayarsa ya dauketa hoto. “Hoto kake daukata?” Ya juyar da wayarsa ya kalli wayar ya manta flashlight din wayarsa a kunne yake. “Kin min kyau ne shiyasa nake daukarki hoto, kina da kyau, zan so haihuwar kyakkyawar yarinya irinki, so ina son na dauko hotonki ne na aje ina kallo a wayana, saboda mamanki tana min rowarki ba zata tura min hotonki ba” Ya fada mata haka ne saboda ya wanke kansa. “Why? Ko zaka sace ni ne?” “Nooooo ta fada min akwai hotunanki masu yawa a wayarta, nace ta tura min tace aa ba zata tura ba” “Idan kana so zan tura maka” “Taya?” “Zan karbo wayar Momy na tura maka” “Aa ai ba zata yarda ba, amman ina son ki yi a boye, zan rubuta miki number na sai ki saka a wayar Momynki ki duba whatsapp dinta ki tura min hotunan ta can idan kika tura sai ki goge karki bari ta sani, kin iya turawa ai ko?” Ta daga mishi kai. “Na iya, amman ban iya gogewa ba” Ya bude whatsapp din wayarsa ya nuna mata yadda zata goge. “Kin gane?” “Yes” Ya tashi ya bude karamar durowa ya dauko katinsa ya bata. “Idan kika gama sai ki jefar da katin a inda ba za a gani ba” “Okay” Samun hotonta da hoton mahaifiyarta zai taimaka masa sosai gurin samawa abokinsa mafita cikin sauki. Ya matsa kusa da ita ya rumgume ya sumbanci kanta, sai ta lafe a jikinsa ta yi shiruuuuu kamin ta dago ta kalleshi ta yi murmushi. “Muje gurin Momy ki kar ta nemi ki bata ganki ba, amman wannan sirrinmu ne ba zaki fadawa kowa ba haka ne” “Yes” ‘Yanzu na san dalilin Mamankin na cewa kar ki yi magana da wanda baki sani ba, you're talkative’ Ya fada a ransa domin samu abun da yake so cikin sauki, ya kama hannunta. “Mu tafi” Ya rike hannunta suka fita office tana kara masa wasu labarunka da be sani ba, amman hankali ya tafi wani guri he just can't wait ya nunawa abokinsa hoton yarinyar nan da kuma mahaifiyarta, ya san ba karamin dadi Turhan zai ji ba na samun Aysha kawai balle kuma ace ya ga yar nan mai kama da shi. EMILY POV. Ta kalli wayarta dake ringing ganin sunan driver Fatima ya saka ta mika hannunta da yayi tsami saboda typing din da take tun safe ta dauki wayar cike da gajiya. “Hello” “Ranki ya dade gani na iso gurin tare da Fatima” “Bata wayar” Ya mika mata kamar yadda ta umarce shi. “Hi Momy” “Hi Baby ki shigo ciki zaki ga Elevator irin wanda muke hawa a New York da Abuja kin tuna? Sai ki taba number 4 idan ya iso office na biyu hannun dama shi ne nawa” “Okay Momy” Ya aje wayar yana mika ji take kamar ta gudu saboda wahalar typing din da take amman babu saboda muradun dake zuciyarta. Kamin ta kalli kofar office din wata matashiyar yarinya ta turo ta shigo. “Hi” “Hi how can i help you?” Matashiyar ta karaso kusa da ita. “Sunana Raheenatu, ni ce sabuwar Assistant ta Miss Amal da aka dauka” Emily ta gyara zama tana kallonta with little bit of confused. “O... Ka..y.... Congratulations” “Thank you, am an fada min nan ne office dina, na yi tafiya ne yau na dawo shiyasa ban samu shigowa da wuri ba sai yanzu” “No wata kila sun yi kuskure ko kuma ke din baki gane wane office ba, domin ni ce a wannan office din kuma ni ma Assistant din Amal ce” “I don't think so, but bari na tambaya” “Okay” Ta juya ta fice, Emily ta bita da kallo har lokacin mamaki take, ana daukar masu taimakar har biyu ne ko kuma dai kuskuren ta yi kamar yadda take zargi? Can kuma wani tunanin ya zo mata, kar dai ace mutumen da ta yi ma magana dazun babba ne a gurin ya saka aka koreta, bata gama raba dayan biyu ba Amal ta turo kofar ta shigo. “Emily kika ce ba a nan office din ba ne?” Emily ta mike tsaye da sauri domin girmamawa ga Amal. “Yes saboda Ni nake nan, sai dan za a kara wata ne, amman na fi tunanin ko ta yi kuskure ne shiyasa nace ba a nan ba ne, maybe office din gaba ne” Amal ta yi murmushin rainon wayo. “Nan ne, ita sabuwar Assistant dinta” Emily ta wara ido irin na mai mamaki “Ni kuma fa?” “Ke ai da ke da babu duk daya, kamfanin nan be san da zamanki ba?” “Kamar?” “Kamar yadda na fada miki, tun da aka dauke ki aiki baki sign idan zaki fita ko kuma idan kika shigo, saboda haka ke da babu duk daya a kamfanin nan, shiyasa aka daukar min sabuwar ma'aikaciya, dan haka ki hannata mata komai ki bata office” Wani abu da bata yi tsammani ba ne ya zo mata a zuciya ya raunatata yayi nasarar saka ta tara ruwan gishi idonta wato hawaye. Emily ta bude baki ta fara magana a daidai lokacin da Aliyu ya shigo office din da Amal ta bari bude yana rike da hannun Fatima. “Ban san ana sign in and out idan za a fita ba?” “Ni zan fada miki? Ban baki dokokin kamfani kika karanta ba?” Kamin Emily ta amsa Amal ta kalli Aliyu cikin girmamawa ta gaisheshi. “Good Afternoon Sir?” Ya kalleta ya kalli Emily dake hawaye ya kalli matashiyar yarinyar sannan ya kalli Amal with seriousness. “Me ke faruwa a nan?” “Ranka ya dade tana cikin sabin ma'aikatan da aka dauka ne, amman bata zuwa tun da aka dauke ta yau kwana uku, shiyasa kamfani ya dauki wata” “What-... Wallahi ba gaskiya ba ne, ina zuwa tun da aka dauke ni, kawai bana sign in and out ne shi ma ban sani ba, bata fada min ba” “Ba a baki file mai dauki da dokokin kamfanin nan ba? Baki karanta ba?” “An bani amman Wallahi babu gurin a ciki, ban ganshi ba ban sani ba, kuma bata fada min ba, abun da kawai ta fada min idan na shigo na goge mata office dinta na gyara, kuma na rika shigowa karfe 6:30am na safe, jiya ma na yi typing har na 4pm sai da na gama na tafi, gashi a Systems dita, and yau ma gashi ka ga ina yi” Cikin kuka Emily take maganar ta juyar masa da system din. Aliyu ya kalli Amal. “Cire takardar kika yi a dokokin kamfani?” “Aa Sir karya take min sheri ne kawai” “Amman a dokarmu babu aikin saka ma'aikanmu aiki, idan za'ayi gyara ko wani abun akwai masu yi, har sai idan mutum yafi sha'awar aikatawa da kansa zai aikata, muna da masu aika da zasu siya muna abu, muna da clearness masu gyara guri kullum da safe, and time din shigowa kamfanin nan ga ma'aikanta mu is 8am, masu shara ne suke shigowa 6:30am haka ne?” Jikinta ya fara rawa. “Haka amman karya take min, daman tun da aka dauke ta na lura haushina take ji so take kawai ta kulla min sheri” Emily ta share hawayenta. “Na kulla miki sheri? Saboda me? Ina da wata alaka da ke ni bayan ta aikin da ya hada mu kwana biyu zuwa uku? Aikin ne baki son na yi shiyasa kika ce na rika shigowa karfe 6 na safe? Kika sakawa ina goge miki office alhalin ba haka dokar take ba? Kika sakawa ina tafiya mai nisa na siyo miki abun da zaki ci? Kuma baki taba fada min ana sign ba? Aikin ne baki son na yi? To na bari daga yau, ni ban shirya tarwatsa rayuwar kowa ba, daman tun da na ganki na san ba za mu jitu da juna ba, saboda ke musulma ce, musulmai ba su da halin kirki sai karya alkawari sai wulakanci sai kyama da nuna banbanci, daman ai ba zaki taba abun kirki ba saboda ke musulma ce, musulmi be taba min abun kirki ba, sai zalinci shiyasa na tsane ku na tsani addininku” Ta karasa cikin kuka da tsawa sannan ta cire id din da yake wuyanta ta jefar kasa ta dauki jakarta ta nufi yarta da Aliyu ke rike da hannunta ta fisge ta fice daga office din. Aliyu ya kalli Amal a tsanake ya fara mata magana. “Ba iya suturarmu ce take walkiltar addininmu ba, har da mu'alama da kalamai da dabi'u, kasancewarmu musulmai kawai ta hanyar shigarmu ko sunanmu ba zai wadatar ba, har sai dabi'unmu da mu'amalarmu ta banbanta da ta kowa, ta hanyar kyautata, tausayawa, adalci da kuma bawa kowa hakkinsa, ni musulmi ne ke ma haka, addini ya koyar da mu yadda zamu zauna da wanda ba musulmai ba mu ba su hakkinsu, idan musulmi yayi mummunan aiki, to yana wakiltar duka musulman duniya ne a idon wanda ba musulmai ba, su basa banbance akwai na gari akwai bata gari a cikin addininmu, haka kuma idan musulmi daya yayi abun kirki to a idonsu duk musulmi na gari ne, sai su ji suna sha'awar koyarwar addininmu da dabi'unmu, ban jidadin abun da kika yi ba, ya kamata mu zama jekadu na gari ko'ina” “I'm sorry Sir, amman sheri take min ba gaskiya ta fada ba” Be sake ce mata komai ba ya fice daga office din, office dinsa ya nufa kalaman Emily na masa yawo, ya tsinci na tsinta ya watsar da wasu, abun da ya fi tsaya masa a rai kuma ya sosa masa zuciya furucinta na cewar musulmi ba su taba yi mata abun kirki ba, musulmi ba su da tausayi, kuma ta tsani musulunci. Ya yarda da kalamanta ne sama da na Amal saboda ya ganta sau biyu a kamfani ta siyo abu kuma ya ga shigowarta a yau da sassafen nan kamar yadda ta fada. Ya zauna a kujerarsa yana mamakin wani abu. ‘Anya wanda ya tsani musulunci zai iya bari yarsa ta yi addinin musuluncin har ta koya mata sallah? Kuma ta sakawa yarta sunan Fatima? Ita ya aka yi ta samu suna Aysha? Ta tsani musulunci ta tsani musulmai ko kuma dai mu'alamar wasu daga cikin batan garin musulman ne ya saka ta tsani musuluncin?’ Yana ta sake sake a zuciyarsa, for the first time ya ji yana sha'awar jin full dalilin rabuwar Turhan da matar da yake ta nema yanzu, domin ya tabbatar ita ce wannan duk kan wata alama ta bayyana hakan, dole akwai wani babban dalilin da ya saka ta boyewa yarinyar cewar tana da uba, and dole akwai dalilin da ya saka ta tsani musulunci. Har yanzu dai ba zai karyata ba tana da masifar kyau fuskarta ta tsaya masa a ido, and when ever idanuwansa suka sauka a fuskarta sai ya ji kamar ya santa, wadannan blue eyes din nata suna raya masa saninsu but be san a ina ba, maybe kyaunta ne yake rudarsa. Har ya daga wayarsa zai kira Sahibar tasa sai kuma ya tuna horo yake mata saboda ta gane girman laifinta, kuma ya ladaftarta ita da abun da bata saba ba saboda ta kiyaye a gaba. ________________ Masu karatu ya kuke ganin Turhan zai yi idan ya samu Aysha? Kamar dai Aliyu Ni ma ina son sanin dalilin Emily na tsanar musulmai kuma ina son sanin a ina sunan Aishar nan ya samu asali? [4/20, 9:59 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 9️⃣ EMILY POV. Suna isa gate Fatima ta fisge hannunta daga na Emily. “Bana son tafiya gida yanzu” “An koreni a kamfanin ko baki gani ba? Asibiti zamu tafi yanzu” Emily ta sake kama hannunta da karfi ta jata. Sai ta fisge tana daka mata tsawa. “Bana son zuwa” Ta nufi titi da gudu zata tsallaka ba tare da ta tsaya dubawa ba, Emily ta yi hanzarin bin bayanta, motar dake dafe da gudu ta taka burge domin kadan ya rage ta buge Fatima. Emily ta kamo Fatima ta riketa da karfi gabanta na dubawa, gilashin motar aka sauke wata matashiyar yarinya ta leko tana kallon Emily. “Allah yasa ban taba ta ba” “No” Emily ta girgiza mata kai, ta matsa gefe, hakan be gamsar da matar  ba har sai da ta faka motarta kusa da gurin da Emily take tsaye tare da Fatima ta bude motar ta fito. “Kin tabbata bata ji ciwo ba? Ban kula ba ne, ina amsa waya” Cewar matashiyar budurwar dake sanye da gown din atamfa sai fashion cap a kanta, tana jin babu dadi a tunanin kokarin amsa wayar da take a lokacin da take tukin motar ne ya haddasa matsalar. “Ba laifinki ba ne, karki damu ita ta fisge hannunta a nawa zata gudu” Matashiyar ta kalli Fatima dake ta huci kamar wani karamin zaki ta sake kallon Emily. “Amman lafiya” “Haka take min, bata jin magana” Emily na rufe baki Fatima da saka ihu tana son fisge hannunta a na mahaifiyarta. “Ki kyale ni Momy ki sake min hannu, akwai ciwo ina son na tafi gida yanzu” Matashiyar ta dan zaro ido tana kallon Fatima da mamaki, ganinta karamar yarinya amman da take yi ma mahaifiyarta ihu. “Ya sunanta?” “Fatima” Emily ta amsa mata idonta na cika da kwalla. Matashiyar ta rage tsayinta tana kallon Fatima. “Sunana Tasmia, please Fatima ki daina yi ma mahaifiyarki rashin kunya da tsawa kin ji babu kyau, ba ayi ma iyaye tsawa da uwa da uba dukansu abun girmamawa ne” A madadin Fatima ta amsa mata da OK sai ta fada mata abun da ba kowa ya kamata ya sani ba. “Ni ba ni da uba haka nan aka haife ni babu uba, can you imagine?” Matahsiyar ta kalli Emily sannan ta mike tsaye ta yi mata sallama. “Allah ya tsare gaba bye” Ta juya ta fara tafiya Emily ma ta fara takawa tana kokarin ganin hawayen dake idonta basu zubo ba. “Can you take us home?” Cewar Fatima tana kallon Tasmia da already ta bude motarta zata shiga. “Yes darling ku shigo sai na sauke ku” “No mun gode zamu hau okada” “Ni ba zan hau okada ba ni mota nake son ta kai ni gida” Ta fada a tsawa. “Is okay Fatima ba sai kin yi tsawa ba, zan sauke ku, please ki shigo ko dan masalahar yarki” Tasmia ta karasa tana kallon Emily, Emily bata da sauran tace bayan abun da yarta ta take so kuma ta zartar, dan haka ta nufi motar ta bude gidan baya suka shiga ita da Fatima, Tasmia ta shiga mazaunin direba ta ja motar. “Ina zan sauke ku?” Fatima ta fada mata unguwar da Number gidan, Emily kuma ta maida fuskarta gefen titi tana kallon ababen hawa, sai dai a badini, zuciyarta zafi take mata tunanin rayuwarta na baya ya dawo mata, damuwa ta baibaiye mata zuciya. Har suka isa unguwar Emily bata ce komai ba haka ma Tasmia Fatima ce kawai ke nuna inda za'a bi har suka isa kofar gidan. Bata jira komai ba ta bude motar ta fita ta rufe gambun da karfe ta doshi gate din gidan ta fara kwankwasawa. Emily ta bude dayan gefen ta sauke kafafuwanta. “Mun gode, ki yi hakuri da abun da ta yi miki, haka take bata jin magana, yaran yanzu sai a hankali” “Haka ne amman yana da kyau mu rika tsawatar musu, idan har bata tsoronki ko ki hada da wanda take tsoro yayi mata hukunci ko yayi mata fada, kamar yayanki ko kanenki ko mijinki ko saurayinki, su yara wani lokacin sai da mai tsawatawa, amman fa ki yi hakuri na shiga abun da babu ruwana” Tun da Tasmia take magana Emily ke jin wani abu na mata yawo a zuciya, har ya saka ta kasa rike hawayenta sai da suka zubo. “Wata kila ke kina da duk abubuwan da kika lissafa saboda haka ba zaki gane komai ba, na gode sai anjima” Ta share hawayen sannan ta karasa fita ta rufe mata motar a hankali. Tasmia bata wuce ba sai da Emily ta shiga gidan, sannan ta ja motarta. Emily na shiga falon ta jefar da jakarta a saman kujera ta zauna ta dafe kanta sai hawaye. “Duk abun da nake kokarin yi a yanzu, ina yi ne saboda ku da kuma rayuwarku ta gaba, kin ce baki son zama a gidan nan baki son Vito, ina ta kokarin ganin na tsaya da kafafuwana saboda ku, yau kina kallon yadda aka koremu gurin aikin nan kuma mun kama hanyar gida kina min tsawa kina neman ki daga min hankali, dole sai kin fadawa kowa baki da uba?” Fatima dake zaune a kujera rumgume da hannayenta ta kalleta tana turo baki gaba irin na fitsararun yara. “Toh ai bani da uba, ba karya na yi ba” Emily ta dago ta kalleta cikin bacin rai ta daka mata tsawa. “Kar bakinki ya sake furta haka ga kowa, baki san zafina ba ne shiyasa kike fadar hakan, lokacin da nake kamar ke da ace na samu wata macen a matsayin uwa ko yaya take zan rike ta” “Toh miyasa baki da uwa? Ni ina ruwana da hakan?” Ta fada tare da mike tsaye ta dauki remote dake gefenta ta jefar a kasa sannan ta nufi upstairs tana tafiya da karfi kamar wata babbar mace. Emily ta bita da kallo hawaye na sauko mata zuciyata na zafi sosai, ko da damba ne kake wahala da shi kake kokarin ganin ka faranta masa, idan ka fahimci ba kai ne a gabansa ba dole hakan zai maka zafi, balle kuma ace mutum ne, mutum ma yarka jininka. Ta girgiza kai ta share hawayenta ta mike tsaye nufi dakinta, keys din mota ta dauko ta sauko ta sake daukar jakarta ta fice daga falon. Tafi minti goma a motar zaune tana sauke ajiyar zuciya sannan ta murza key ta yi warming dinta ta juyar da ita mai gadin ya bude mata ta fice, restaurant din dake kusa da su ta fara biyawa ta yi takeaway sannan ta karasa asibitin da danta yake, dukanin abun da take tana kokarin ganin ta boye damuwarta ne, so take ta zama jajirtacciya, wannan dalilin ne ya saka take tare hawayenta a duk lokacin da suka so zuba. Ta shiga dakin da danta yake tana murmushi kamar babu damuwa a zuciyarta, Chidimma ta gaisheta ta amsa tana kallon danta daya dauke fuska alamar baya son ganinta. “My Boy how are you” Ya sake juyar da fuskar dayan gafen, bata damu ba ta aje takeaway dake hannunta ta juya gefen da fuskarsa take ta zauna tana masa murmushi sai ya sake juyar da fuska ya matsa gefe. “Tun da ya tashi yake kiran sunanki” Chidimma ta fada mata. “Baki fada masa ina gurin aiki ba?” “Na fada masa, maybe yana son ganinki ne a lokacin be samu damar hakan ba, saboda baki kusa” Emily ta sauke dogon numfashi sannan ta dawo gabansa ta tsuguna ta rike kunnuwanta, tana neman yafiyarsa kamar yadda ta saba yi idan ta bata masa rai. “Okay I'm sorry, Momy ta bata maka rai ka yafe min I'm sorry” “No i hate you” A take yanayinta da fuskarta suka sauya, ta kalli Chidimma ta sake kallonsa, sai dai wannan karon bata sake cewa komai ba ta mike tsaye tana jin zuciyarta kamar zata rufe, domin be taba furta mata kalmar i hate you ba sai a yau, ta fice daga dakin ta sake komawa cikin motarta ta zauna tana ta hade wani abu da ya tsaya mata a zuciya. Bata yarda ta yi kuka ba sai shafa fuskarta take tana kokarin kwantar ma da kanta hankali. Ta sake yi ma motar key ta fice daga asibitin tana tukin motar zuciyarta na kara yin nauyi har ta iso gida, ta faka motar a gun da ta dauke ta, sannan ta bude ta fito tana rike da jakarta har ta isa balcony din kofar falonta ta zauna a gurin ta sauko da kafafuwanta kan interlock tana kallon harabar gidan kamar wata bakuwa. A lokacin da wayarta ta fara ringing sai ta saka hannunta a jakar dake bude ta dauko wayar ta duba, V ne rubuce a jikin screen din. Ta amsa wayar ta kara a kunnenta ba tare da tace komai ba. “How are you?” Kamar jira take sai kawai ta fasa masa da kuka, kuka sosai mai dauke da ihu kai kace yayi mata bushara da mutuwa ne, har sai da mai gadin da mai sharan harabar gidan suka mike tsaye suna kallonta. Be sake furta komai ba ya kashe wayar, ita kuma ta cigaba da kuka da karfi har numfashinta na rawa tana shafa sarkar Cross din dake wuyanta. Da sauri Mai gadin ya karaso kusa da ita yana tambayar lafiya, bata amsa masa ba ta mike tsaye ta shige falonta a kan kujerar falon ta jefar da wayarta da jakar ta haura sama ta shiga dakinta ta kwanta saman gado tare da jan filo ta rumgume tana cigaba da kuka sai dai wannan karon babu kururuwa... VITO POV. Ya aje bottle din Hennessy XO dake hannunsa that's Worth 430k, ya gayen dake kusa da shi. “A siya min ticket din tafiya ina Port Harcourt yanzu nan” “Okay Sir” Ya jingina da kujerar da yake zaune gaba daya ransa ya bace jin kukan Emily da yayi, after like 10m gayen ya dawo ya sanar masa babu flight din da zai tashi daga Lagos to Port Harcourt yanzu sai gobe. Ya dago ya kalleshi. “Ka fadawa manager Happy Home Hotel ya siya min ticket din tafiya Port Harcourt, a siye tickets din duka ina son tafiya yanzu nan” “Okay Sir” Ya sake komawa ya kwanta jikin kujerar da tunani biyu, mutumen da ya gani dazun da kuma kukan da Emily take, kokarin hada biyun yake yaga yadda za su zame masa daya ko zai samu amsar kukanta, sai dai zuciyarsa bata natsu da hakan ba. Yadda ya bukata haka maganer hotel din ya aiwatar aka daukar masa shatar jirgi private jet shi kadai daga Lagos to Port harcourt, tun kamin ya bar Lagos ya turawa direbansa dake port Harcourt sakon lokacin da zai sauka, so that ya zama cikin shiri. In less then awa biyu ya sauka Lagos daman daga Lagos to Port Harcourt 1hr 10m ne to nonstop flight. Yana sauka direbansa ya dauke shi a cikin 2022 -BMW X3 baka mai bakin gilashi. Be sauka ko'ina ba sai gidan Emily, yana fitowa motar be tsaya rufewa ba ya nufi kofar shiga falonta da saurinsa irin saurin dake ake hadawa da guda, a falo ya fara cin karo da Fatima tana zaune a dinning tana shan cornflakes, kallonta kawai yayi ya dauke kai ya kalli wayar Emily dake aje kan kujera da jakarta, be taba komai ba ya haura sama ya tura kofar dakinta a hankali ya shiga. Talkaminsa ya fara cirewa sannan ya taka ya karasa bakin gadon yana kallon fuskarta a take zuciyarsa ta fara rawa ganin yadda fuskarta ta yi ja ta kumbura saboda kukan da ta yi, idanuwanta a lumshe tana bachi sai sauke ajiyar zuciya take irin na yaran da suka gaji da kuka suka yi bachi. Zaunawa ya fara yi a hankali sannan ya kai hannunsa ya dagota ya kwanto da ita a jikinsa a hankali ya kai hannunsa yana shafa fuskarta, jira kawai yake ta farka ta fada masa wanda ya saka kyakkyawar sarauniyarsa kuka. Jin ana shafa fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali ta sauke su akan fuskar mutunen da murmushi ba shi da muhalli a gurin. Ta tashi zaune tana kallonsa sai na juya ta kalli gadon ta kalli agogo ta ga karfe biyar na yamma ta sake kallonsa. “Yaushe ka zo?” Ya ki ya amsa sai kallonta yake. “Kace min zaka tafi Lagos? I thought kana can” Nan ma be ce mata komai ba sai kallonta yake. “Why are you here?” Ya saka yatsansa ya shafe mata gefen bakinta. “Waya taba ki?” Kallon fuskarsa take zuwa kirjinsa da boturan rigar suke bude, sannan ta sake kallon fuskarsa sai ta fashe da wani sabon kuka. “Kowa baya so na, babu mai bukatata a kusa da shi, Fatima tana bata min rai yau sauran kadan mota ta bugeta saboda ta bata min rai, na tafi asibiti London yace baya so na ya tsane ni” Ya matsa kusa da ita ya rumgumeta tare da dora chin dinsa saman kanta. “Sai kuma wa?” So yake ta ambata masa sunan wani dabam ba yayanta ba tace su suka bata mata rai, domin ya san ba zai iya taba yayanta ba, amman zai iya taba kowa bayan jininta. Ita kuma bata yarda sunan kowa ya fito daga bakinta domin ta san waye Vito ta san abun da zai iya, kuma ta san yadda yake sonta. Ya dago ta daga jikinsa ya rike fuskarta da hannunsa biyu yana kallon kyakkyawan idanuwanta. “Akwai wanda ya taba ki bayan Fatima da London? Akwai wanda ya fada miki wata magana?” Ta girgiza kai alamar aa, ya mutsa bakinsa kamar zai yi magana sai kuma ya saketa ya mike tsaye, kasa ya sauka ya shiga kitchen ya dauko mata ruwa ya fito har ya nufi stairs ya fara takawa sai kuma ya juyo ya dawo gurin da fatima take zaune a dinning ya kalleta. “Idan kika sake batawa mahaifiyarki rai har ta yi kuka idonta ya kumbura kamar yau, sai na miki danyen hukunci” Ya fada fuskarsa babu alamar wasa sai ma kara hade mata rai da yayi. “I hate you, kuma Momy ba zata aureka ba” Ta fada masa cikin tsiwa tana murguda baki. Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya dauke kai ya haura sama. Tana ganin haka ta mike tsaye ta nufi wayar mahaifiyarta ta dauka ta haura sama da gudu ta shiga dakinta, jakar makarantarta ta bude ta dauko kati da Aliyu ya bata ta zauna bakin gado tana cire password din wayar. ALIYU POV. Misalin karfe 3pm ya faka motarsa harabar gidan ya bude ya fito yana kallon bakuwar motar dake fake kusa da balcony. Bayan ya rufe motarsa ya nufi entrance din ya fara takawa har ya isa bakin kofar falon ya tura ya shiga. Matarsa ya tarar a tsaye tare da wata bakuwar fuska dake rataye rike da karamin mayafi a hannu dayan hannunta kuma rike da jaka. Aisha na ganin shigowarsa sai hankalinta ya tashi, ta juya ta gefen da bakuwar take tana tarewa dan kar Aliyu ya kalleta da kyau, domin atamfar dake jikinta da matse ta sai dai ba sosai ba, amman ta karbe ta yi mata kyau. Ta inda ta yi sa'a mijinta baya daga cikin irin mazan nan da suke son kallon mata balle kuma ya san halin matarsa da kishi ko a tv ya kurawa mace ido sai ta yi masifa balle kuma a zahiri, tun kallon farko da yayi ma bakuwar a farkon shigowarsa be sake kallonta ba. “Sannu da zuwa” “Sannu Babyna ya gidan?” “Lafiya Kalau” Yayi kamar be san da bakuwar ba ya shafa fuskar matarsa zai wuce sai ta gabatar masa da kawarta tana dan kareta. “Tasmia ce ta zo mana” “Maa Shaa Allah, ina mata barka da zuwa” Ganin alamar be gane ta ba ya saka ta ce. “Tare muka yi Secondary School” “Nice” Ya fada ba tare da ya kalleta sannan ya wuce zuwa dakinsa, tun da ya bada baya Aisha take kallon Tasmia ta ga ko ta kalli mijinta and yes ta kalleshi da kyau har ya shige ciki, Aisha ta dan canja mata fuska tare da jefa mata zagi cikin wasa sai dai har a zuciyarta ta ji zafin kallon da ta yi ma Aliyu. “Yar iska me kike kallo? Da wani billenki a nan” Tasmia ta kalleta ta yi murmushi. “Masu ciki fa zuciyarsu a kusa take, daman gaki ba tsaye kin san ance short people suna da saurin fushi, wai su da fushi 5&6, ni kin ga tafiyata” Ta nufi kofa, Aisha ta tsaya a gurin bakinciki ya hanata raka kawar da suka shafe shekaru ba su ga juna ba, sai ma binta da ta yi da harara. Aliyu na shiga dakinsa wayarsa ya fara cirowa ya aikawa Turhan da sako bayan ya gama karanta wanda ya turo masa. “Yau gidan marayu hudu muka je ba mu dace ba, ko'ina cewa suke ba su santa ba” “Baka amsa ni ba, Turhan me ya rabaka da yarinyar nan? Me yasa ka sake ta?” Ya aika masa sannan ya aje wayar ya fara cire tufafinsa. [4/20, 9:59 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣0️⃣ EMILY POV. Tana shan ruwan tana shan ruwan tana ajiyar zuciya kai kace yar yarinya ce aka saka kuka, hannu ya kai yana shafa saman kanta har ta shanye ruwan, sai ya karbi kofin ya aje. “Ba Fatima ce kawai ta saka ki a cikin damuwa ba, waya taba ki?” “Ita ce kawai” Ya kalleta ba dan ya gamsu ba, ba zai cilasta mata ta fada masa abun da ya haifar mata da damuwa a yanzu ba, amman da sannu zai sani domin ya san yadda take sauyawa idan ta shiga damuwa. Mikewa yayi tsaye rike da cup sai ta rike hannunsa na hagu ta dago tana kallonsa da idanuwanta dake bayyana damuwa sosai. Komawa yayi ya zauna sai ta dora kanta a cinyarsa ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali, ta sani bata da sauran kima a idon kowa sai Vito a yanzu, ita din ba abar tausayin kowa bace sai mutumen da ya ganta a rana ya saka a inuwa kuma ya lullube ta da kulawa da kauna, yake gudun bacin ranta yake kaunarta fiye da kansa, tana jin kamar shi kadai ya rage mata a yanzu. “Mommy ta fada min zata zo satin nan, idan ta sauka a nan na san zata rage miki kewa, ko ba komai zaki samu uwa zata kula dake kamin ta tafi, amman idan baki ra'ayi zata sauka gidana sai idan kin bukaci ganinta” Ya fada yana shafa fuskarta a hankali kaunarta na kara zafafa a zuciyarsa. Bude idon ta yi ta tashi zaune tana kallon wani gafen, ta yi marmarin kasantuwa kusa da wasu iyalin, sai dai kudurin da take da shi ba zai barta ta sake kusantar iyalin Vito ba a yanzu. Ta mike tsaye ta cire ribbons din dake kanta jan gashinta ya sauko har bayanta, sai ta tsaya gaban madubi tana cire dankunenta, shi ma tsayen yayi ya matsa kusa da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta ta madubi, baya bukatar ta bashi amsar tambayarsa, ya zauna da ita na tsawon shekara bakwai ya san me take so da wanda bata so, yana iya karantar yanayinta tun kamin ya san dalilin farinciki ko bakincikinta. Ya dafa kafadarta har lokacin kallon fuskarta yake ta madubin dake tsaye gabansu, ta dago ta kalleshi da blue eyes dinta. “Zata zauna a gurina har sai kin bukaci ganinta” “Ba wai bana son zuwanta a nan ba ne kawai...” Bata karasa ba ya juyo da ita ta fuskance sai ya saka hannunsa biyu ya rike fuskarta yana kallon zanen halintarta hancinta. “Ina sonki Emily, ina sonki, so mai tsanani irin son da alkalin ba zai iya rubuta bawa, irin son da zan karar da kalamai gurin furtawa, ina sonki, irin son da zan iya kashe kowa a duniyar nan na rayu daga ni sai ke, zan iya rabuwa da kowa na rayu da ke, rashin zaman mahaifiyata a kusa da ke ba zai haifar da komai ba sai karin kaunarki, kar hakan ya dame ki, zata a gidana har sai idan ke da kanki kin bukaci ganinta” Ya karasa yana kallon kanta, yana sonta wannan rubuce yake a cikin kaddararsa, shiyasa baya haufin nuna kaunarta a ko'ina haka kuma baya babu wanin abun da zata aikata a duniyar nan da zai saka ya nisance ta. Ya runtse ido yaja dogon numfashi ya sauke ya bude idon ya sauke su a kanta. “Har yanzu baki san miye so ba, har yanzu baki fahimce waye ni ba, har yanzu baki san irin son da nake miki ba, amman ina fatan wata rana zaki san haka” Hawaye ya sauko a idonta sai ya share mata da yatsanta. “Zan tafi gurin London komai zai wuce” Ya saketa ya matsa baya, kallonsa kawai take har ya fice sannan ta lumshe ido hawayen na cigaba da sauko mata, tana tsananin tausayin Vito fiye da yadda take tausayin kanta, ya mata fahimtar baibaine amman ta san son domin ta so mutumen da be dan darajar ta ba, son ne ya janta ga halaka har ta rasa makomarta ta butulcewar mutanen da suke rike a matsayin ďiya. Tana jin tsoron irin son da Vito yake mata, tana tsoron abun da zai haifar tana tsoron yadda makomarsa zata zama idan babu ita a kusa da shi. Tufafin jikinta ta cire ta daura tawul ta shiga bandaki ta kunna shower da nufin wanka sai kuma ta samu kanta da zama a cikin tube din tana nadamar shiga rayuwar Vito da ta yi... Ta dade a haka sannan ta yi wanka ta fito bata shafa komai ba ta saka short gown ta kwanta kwanta saman gadonta, korar da aka yi mata a yau ta dawo mata a rai, a take hawaye ya cika idonta, meyasa bata da sa'a a rayuwa? Meyasa farinciki yake mata nisa? A duk lokacin da ta daura damarar gina ramen farinciki sai bakinciki yayi mata kawanya, idan bata samu damar tsayawa da kafarta a yanzu ba sai yaushe zata yi? Ita kenan ba zata iya bawa kanta farinciki ba sai idan wani ne ya bata, wanin ma Vito mutunen da ya gama mata komai kuma bata da wata sakayya da zata masa, yanzu ko nan gaba. Motsin turo kofar dakin da Fatima ta yi da gudu ta shigo ya saka ta yanke tunanin da take ta tashi zaune, kamin ta yi wani yunkurin goge hawayen da suka bata mata fuska Fatima tace. “Momy ki duba wannan number ki goge ta, amman karki kar duba abun da na tura gashi nan yana kira na san zai ce na goge ne kuma ban iya ba ban gane gurin ba, yace koya min amman na manta ban san ya ake gogewa ba...” Kamar wanda aka ce amsa kiran mana, haka ta taba green botton din sai ga fuskar Aliyu ta bayyana. ALIYU POV. Ya fito wanka rike da karamin tawul yana goge jikinsa sai da ya gama sannan ya zauna gefen gado ya dauki wayarsa yana duba whatsapp dinsa, domin a yanzu ba shi da wani abu mai muhimmancin kamar jiran amsar Turhan, gashi kuma har yanzu Turhan be amsa masa ba bayan kuma ya karanta sakon nasa. Yaje wayar yayi ya mike tsaye ya fara shafa mai ya shirya tsab cikin shigar kanana kaya black T-shirt and White jean, yana tsaka da fesa turare Aisha ta shigo dakin, fuska ba yabo ba fallasa tana kallon bayansa har ta karasa kusa da shi. “Ga abincinka can a falo fa, kai nake jira ka sauko mu ci” “Na ci abincin a waje” Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, sakin baki ta yi tana mamakin furuncin, tasan waye mijinta cin abinci a waje ba dabi'arsa ba ce. “Wai duk fushin ne haka? Fisabilillahi ganin chat kawai ya kai ace ka dauki fushi da ni har haka?” Ya juyo ya kalleta. “A gurinki abun da kika aikata ba laifi ba ne?” “Idan ma laifi ne ai ya kamata kayi min uzuri ko? Har sai idan na sake aikatawa” “Rashin daukarsa laifi shi yake kara bakanta min rai, taya zaki zauna da kawarki ki labarta mata yadda muke rayuwa a shimfidar da ko dan'uwanki ba a yarda ya sani ba, taya zaki ji idan kika kama ni ina fadawa abokina yadda nake da ke a gado?” “Dadi zan ji mana, ai kana fada masa yadda na iya gyara shimfida ne, Aliyu wannan abun fa is normal, yanzu rayuwa ta canja ba yadda muke a baya ba ne, wacan rayuwar da kake tunani ko iyayenmu ba su yi ta balle kuma mu, amman dai shikenan tun da baka so zan daina” “Ina fatan haka” Ya furta yana kokarin danne fushinsa domin kara bata masa rai take da kalamansa na yanzu. Murmushi ya sakar mata ya matsa kusa da ita. “Muje mu ci abincin” “Ba kace ka ci abinci a waje ba?” Ta fada tana masa kallon da yafi kama da harara, ya fadada murmushinsa tare da shafa cikinta. “Wasa nake kawai ina fushi ne amman yanzu na sauko” Ya rike hannunta suka fice daga dakin, falo suka sauka ya ci tuwon shimkafa da favorite miyarsa miyar kuka, sai da ya ci yayi nas sannan ya soma bata labari, da hira ta yi dadi sai ya dauko mata zancen sabuwar ma'aikaciyarsu da kuma fadan da ta yi da Amal a yau. Har a ranta ta ji dadin korar da aka yi mata domin bata son kowace mace a kusa da mijinta, Amal din ma dan ta zama dole ne. “Kasan wasu matan ba ba su da kai, musamman kabilun nan kara ana musu haka, ta nan za su fahimci matsayinsu, kuma wasu ma fa kawai neman maza ke kawo su” Tana maganar tana yatsina fuska. Kallonta yayi yana girgiza kai. “Madam ba fa ni kadai ba ne namiji a kamfanin nan, kawai ke da kin ji maganar mata sai kishi ya tashi” “Matan ne fa yanzu kamar za su auri namiji da karfi, idan mutum be yi taka tsantsan ba sai a aure masa miji” “Ke da kika san waye mijinki ai be kamata ki daga hankalinki akan ko'ina zan shiga ba, kuma karki manta ke kadai zaki rayu a gidan Aliyu daga ke sai yayanki, ko kin manta alkawarin da na yi miki? Ba ke ba kishiya” “Ban manta ba amman ku maza ai wani lokacin zaku iya ganin mace ku bi ku rude kanta duk wani alkawari da kuka yi ku watsar da shi, musamman idan ka ga wata fara kyakkyawa yar doguwa” Yayi murmushi. “Allah ya saukaka miki wannan kishin, ni bana da ra'ayin karin aure” Dadi ya lullubeta ta kwanta jikinta. “To yanzu zaka je ce ta dawo aikin ne ko kyaleta zata ka yi?” “Aa ai ta riga ta rasa kenan, ni ban san a ina take ba balle nace ta dawo, kuma an riga an yi replacing dinta da wata ai” Sanin halin matarsa ya saka shi bata wannan amsar. “Haka ma yafi, waya sani ma ko tana da kyau” Wannan karon dariya yayi, domin ta canja daidai Emily tana da kyau kuma ya san da ta san haka ba zai zauna lafiya ba. “Ai ni kowace mace na kalla ke nake gani a fuskarta” Ta buge masa hanci tana dariya, shi ma dariyar yayi ya dauko mata wata sabuwar hira, sai da aka kira sallah la'asar suka daga falon, a shi ya nufi masallacin dake unguwarsu ita kuma ta gabatar da sallah ta a gida kamar yadda Annabi ya umarta. Misalin karfe biyar da mintuna 58 wayarsa ta yi kara alamar kira, a ka'ida idan yana kusa da matarsa baya taba waya saboda ya bata lokacinsa, sai idan kiran ya tsananta ko kuma ya kasance na gaggawa ne, sai dai jiran amsar Turhan ya saka shi mikewa tsaye ta nufi wayar ta dauka sai ya kira ne ta whatsapp kuma video call da wata bakuwar number da be san waye ba. Rejecting yayi ya bude whatsapp din ya duba bakuwar number sai yayi arba da hotunan Emily sun fi guda hansi, Hello Hi kuma ya fi ashirin, kamin ya samu damar reply wani kiran ya sake shigowa. And this time around baya son rejecting domin ya fahimci mai kira, gashi kuma ba zai iya amsawa a gaban matarsa ba, dan haka ya fice daga falon ya haura sama sai da ya shiga dakinsa sannan ya amsa kiran dake shigowa da zarar wani ya yanke. “Hello...” Fatima ta fada da karfi tana masa waving. “Hi ya kike?” A take murmushin fuskarta ya gushe ta bata fuska ta fara kukan da babu hawaye. “Ba Lafiya ba, Vito yayi min fada sosai har yana cewa sai ya yanka ni, kuma Momy ma fushi take da ni bata so na, saboda na yi mata tsawa lokacin da muke tafiya a hanya dazun kuma, na je gurin titi har mota ta kusan bugeni, muka hadu da wata mata ita ma ta dinga min fada ta kai mu gida, amman ai ina fushi ne na yi, shi ne Vito ya dawo Momy ta fada masa sai yayi min fada, ni kuma na shigo daki na turo maka hotunan Momy ka duba ka gani ko kana sonta” Daga idonsa har girarsa da bakinsa a bude suke, ya rasa ta ina zai kama zaren zancen ma, yadda ta aika masa rahonta ya saka ya manta labarin farko da na tsakiya, na karshen kawai ya rike wanda shi ya fi bashi dariya. Wato ya duba ya gani ko yana sonta, ita a tunaninta son mahaifiyarta yake. “Me ya faru ma?” Ya tambaya domin ya manta labarin nata, yadda ta zayyana masa dazun haka ta sake zayyana masa yanzu. “Okay wait now, yanzu dai me kika yi ma Momy” “Tsawa” “Fada” “Meyasa kika mata tsawa to? Baki san ba ayi ma iyaye tsawa ba? Babu kyau, ko a gurin wanda ba musulmai ba, balle kuma ke da kika fada min ke musulma ce, yana da ace kin fi kowa tarbiya” “Ai musulmai ba su da kirki haka Momy tace” “No ta yi ma musulmai mummunar fahimta ne kawai, amman musulmai sun fi kowa kyan hali da tarbiya” “To miyasa wannan matar girlfriend dinka ta kore Momy? Why?” “She's not my girlfriend, kawai abokiyar aikina ce, abun da ta aikata ba abu ne mai kyau ba, amman musulmai ba haka suke ba, idan kina son na yi shiri dake to karki sake yi ma mahaifiyarki tsawa” “Amman ai bata sona” “Inji wa tana sonki mana, idan kika bata mata rai ni ma raina zai bace, kina son raina ya bace?” “Aa” “Momynki ma ba zata jidadi ba idan kika bata min rai, dan haka ki daina bata mata rai kin ji” “Zan yi tunani akai” Yayi murmushi. “Okay, zan duba hotunan sai mu yi magana” “Okay, zan turo maka wasu ma idan ka gani sai ka goge komai kar Momy ta gani zan aje mata wayarta” “Ba zan iya gogewa ba, ai na nuna miki yadda zaki goge” “Na manta kawai na iya saka number ne, amman zan bawa Momy ta goge min” Tana fadar hakan ta yanke kiran. “Nooo nooo nooo nooo” Ya fada yana girgiza kai, ya sake kiranta videos calls din amman bata daga ba, ya rasa ya zai yi sai ya zauna gefen gadonsa yana dafe goshi. “Oh Allah matsalar yara kenan” Ya hade yawu da karfi yana tunanin abun da zai sake yi ba, can wata zuciyar ta bashi shawarar sake kiranta sai ya sake kiran Number ta whatsapp as videos call kamar yadda suka yi da farko. Boom Emily ta amsa kiran ta bayyana gaban screen din wayarsa tana kallonsa da mamaki fuskarta kuma dauke ta hawaye. Shi ma kallonta yake zuciya na bugawa ciki na kukan rashin gaskiya. TURHAN POV. “Fara ce sosai, tana da jan gashi da blue eyes amman tana da kima” “Gaskiya ba mu santa ba, babu mu da marayu masu wannan bayanin da ka bayyana” “Ba a yanzu ba ne, ta kwana biyu fa, ita kanta yarinyar ta zama babbar mace har da yara” “Gaskiya ba mu santa ba, amman zan bincika maka, idan na ga wani abu makamancin wanda ka fada zan nemeka sai ka bar mana information din” Ya busar da iskar bakinsa ya kai hannunsa a kai, gaba daya ya gama zagaye gidajen marayu dake nan kusa be samu Aisha ba kuma ko'ina yaje cewa ake basu san wata mace mai wannan siffar ba. Kamar yadda suka bukata information din ya bar musu ta yadda idan an samu wani abu game da ita za a iya tuntubarsa. Sannan ya fito jiki a sanyaye ya shiga motar da suka shigo. Ya sauke ajiyar zuciya ya kai sau hudu sannan ya dago hannunsa ya duba wayarsa, babu wani sabon sako bayan wanda matarsa ta aiko masa sai kuma na Aliyu, ya kasa amsa ko daya daga na matar har na Aliyun saboda baya cikin yanayi mai dadi. Faruk ya tashi motar suka fara tafiya, sai a lokacin ya samu sukunin amsawa Aliyu tambayarsa, tare da dora masa da wani bayanin. “Abun da Mommy take kokarin yi a yanzu zai iya haifar da matsalar da tafi ta baya, domin har yanzu bana son yarinyar nan, kawai ina nemanta ne saboda Ammy, wahalar neman nan nata da nake sha ya saka na kara tsanarta Ammy ta kasa gane banbanci...” Be gama amsawa ba ya dago ya kalli Faruk dake kokarin fakawa gefen titi. “Lafiya” “Toh gamu gani, tsohon nan ne yake ta min hannu” “Wane tsoho?” Turhan ya kalli gefensa, mutumen da ya tarbe su ne a gidan marayun har yayi musu iso a gurin shugaban gidan. Faruk ya sauke gilashinsa. “Lafiya?” “Lafiya dai ranka ya dade, kawai dai ina da bayani ne da zai taimaka maka akan neman yarinyar nan” Turhan ya gyara zamansa da sauri yana leken tsohon da yayi jika da shi. “Okay Sir muna jinka” Tsohon ya kalli hanya gefe da gefe sannan ya sauka daga kan okada da yake ya sallami mai okadan sannan ya matsa kusa da su sosai yace. “Ba zai yi na baku bayani akan hanya ba, saboda za a iya ganina a nan, hakan kuma zai iya haifar min da matsala” Turhan ya bude motar ya fita ya bude masa gidan baya ya shiga ya zauna, sannan ya koma ya zauna ya juya yana fuskantarsa. Da yaren turanci tsohon ya fara magana yana hadawa da yarbancin kamar yadda yake da farko, daman kana kallonsa kaga bayarabe tsagen fuskarsa ma ya bayyana haka. “Na ji lokacin da kake bayani akan matar da kake nema, ai ba a neman mutum haka a babban guri irin wannan, saboda ba mu da tabbacin abun da ka fada akanta haka din ko akasin haka” “Haka ne” Turhan ya fada da sauri. “Ba ni da tabbacin neman da kake mata, amman ina fatan ba zaka cutar da ita ba” “Babu cutarwa a ciki dan Allah idan kasan inda take ka fada mana” “Ban san inda take ba a yanzu, amman na san matar da ta dauke ta, akwai information din komai a file din gidan da nake, na san Emily farin sani domin na yi shekaru ina aiki a nan, na gane ta ne ta hanyar kamaninta daka fada amman sunanta Emily ne ba wacan sunan daka fada ba Acha” “Mun gode sosai, yanzu zaka iya kai mu gurin matar da ta dauketa din?” “Aa zan dai iya neman file din da addreshin matar yake sai na nuna muku ku tafi nemanta, amman a bisa sharadin guda uku” Faruk ya kalli Turhan Turhan ma ya kalleshi suka hada ido sannan suka kalli tsohon. “Miye sharadin” “Sai kun yi rantsuwa ba za ku cutar da ita ba, kuma ba za ku bayyana komai akaina ba cewar ni na baku wannan bayanin na yadda za a same ta, na ukun kuma za su biya kudin bayanin da na muku a yanzu, za ku biya kudi idan na kawo file haka ma idan kun tafi gidan matar za ku biya kudi ko da ba ku same ta ba, sannan kuma idan kun ga Emily komai tsawon lokaci za ku biya kudi” Turhan yayi murmushi, kudi daman ba matsalarsa bace, ganin Aisha ne abun da yake buri a yanzu, wai hausawa suka ce bukatar maji hajji Sallah. ___________ Kuna ganin Aliyu zai fadawa Turhan ya san inda matarsa take? Anya da gaske tsohon nan yake ko kuma dai ya shiry cin kudinsu ne.? Ya kuke gane za a kare tsakanin Aliyu da Emily? Ga barawo ga mai kaya...! Kallon kallo akuya kallon kura... 😅 [4/20, 9:59 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣1️⃣ Ta kalli Fatima ta sake kallon Aliyu dake zube a gaban wayarta. Amman ta kasa magana. “My bad” Ya furta sannan ya kashe wayar, hotunan da Fatima ta tura masa ta duba a lokacin ne ta sake kallon Fatima cikin tsawa ta ce. “Me ma'anar hakan? Ina kika san shi? Ina kika samu number shi?” A nan kuma ta kwashe labarin komai ta fadawa mahaifiyarta, babu abun da ta boye ko ta manta tun daga farkon haduwarsu har zuwa yau. “Amman na fada miki ki daina magana da mutanen da baki sani ba, miye amfanin abun da kika yi, baki san manufarsa akanmu ba, bayan ganinsa da nake a kamfanin nan ban san waye shi ba, ban san halinsa ba” “Cewa yayi ya sanki” “Meyasa baki bari na gabatar miki da shi ba? Kin taba ganin na nuna miki shi ko na masa magana? Kin taba ganina tare da shi...” Ta sake daka mata tsawa har tana mikewa tsaye kamar zata dake ta, Fatima ta razana sosai ta matsa baya tana fashewa da kuka. “Sorry Momy” Ta dafa kanta ya juya ta juyo gaba daya ta tsoro kamar wata marar gaskiya, can kuma ta koma ta zauna ta dauki wayarta ta aika masa da sako. “Me kake nufi da abun da ka saka yata ta aikata? Me kake nema a yanzu? Bayan korar da kuka min yanzu kuma wani sherin kuke neman bina da shi?” Ya duba sakon amman be bata amsa ba, kuma da alama be shirya yin hakan ba. “Kana wasa da rayuwarka ne yaro, baka san waye ni ba, kuma bari na fada maka idan wani abu ya same ni ko ya samu yata sai ka yi nadamar zuwanka duniya” “Boy? Huh? Hmm” Ya rubuto mata as reply. Kana ya rubuto mata. “Mutumen da ya fada min halinki ya fada min babu ruwanki da fitina, amman naga akasin haka, bana nufinki cutar da ke, mu musulmai bama cutar da kowa, kawai ina nemi yarinyarki ta turo min hotunanki ne saboda tantance Aisha da Emily, ina son na san banbancin wacan mai kibar da ke, ina son na gane banbancin wacan marar masifa da kuma ke” “Waye kai?” Ta mike tsaye tana kallon wayar gabanta na bugawa da mugun karfi. Hoton Turhan ya turo mata. “Kin san waye wannan?” “Aa” Ta amsa da sauri gumi na karyo mata, sai ta kashe data ta goge chat din ta jefar da wayar akan gado, ta fara safa da marwa cikin dakin kamin hawaye su samu matsugunni a fuskarta. A nan ta fara tambayar kanta? Waye wannan mutumen tun farko? Meyasa yake bibiyar yarta da ita kanta? Yanzu kuma da ya turo mata hoton Turhan me yake nema a gareta? A kokarin samun amsoshinta ta sake daukar wayar ta bude data sai kuwa ta ci karo da sakonsa. “Meyasa kike boya? Meyasa kika boyewa yarki gaskiyar cewar tana da uba? Why?” Ta kasa bashi amsa jikinta rawa yake kamar yadda zuciyarta ma take rawa. “Baki san yarki ta yi farincikin ganin mahaifinta? Baki taba tunanin samarwa yarki iyali ba? Kiran sunanta da ake da Fatima Aisha Emily be taba damunki ba? Idan yarki ta girma ta mallaki hankalin kanta wane irin amsa zaki bata?” Nan ma bata amsa masa ba. “Turhan yana ta nemanki babu dare babu rana, yana ta neman hanyar haduwa dake, wata kila baki san da hakan ba, amman yana da kyau ki hadu da shi ko dan yarki” “Ba kasan komai akan rayuwata ba, baka rayu a cikin duhun da na rayu ba, har yanzu ban gama warkewa daga ciwon da zan bukaci kowane namiji a kusa da ni ba, balle kuma Turhan, ba ni da alaka da shi, alakarsa da yata kuma na yanketa, daman be san da ita, idan ya saka shiga rayuwata da rayuwar yata ne saboda ya san halin da nake ciki, to ka fada masa Aisha da ya sani a da ba ita ce a yanzu ba, kuma kar ya kuskura ya tunkaro gurin da nake” “Ban riga na sanar masa ba, amman zan sanar masa a yau?” “Sanar da shi zai jefa rayuwarka da tawa da tasa a matsala ne kawai, karka aikata hakan, karka jefa ni a matsala, ina da yara har biyu yanzu, kokarin gina rayuwa nake, karka maida ni a kangin da na fito, ina da kudi enough zan biyaka ko nawa kake so, zan nika maka abun da ya baka dan Allah karka sanar masa, ina son yata ina son rayuwata, farincikina kankane karka barar da shi” Tana rubuta masa sakon tana hawaye. “Na miki kama da mutumen da za a biya kudi a aikata wani abu? Ke kina ganina kin na girmi talauci, duk abun da kike takamar kina da shi, ina takama da ninsa sau dari” “Amman kace kai musulmi ne?” “Yes haka ne, babu shakka” “Ina hada da Ubangijinka Ubangijin gaskiya, da Manzon Allah ( S A W) yace ranar tashin alkiyama Allah baya magana da mutum uku har da wanda aka hada shi da Allah be aikata ba, na roke ka dan Allah dan Allah karka fadawa Turhan komai akaina, idan kuma har ka fada masa to ka canja, dan darajar Manzon Allah S A W na san indai kai musulmin kwarai ne ba zaka aikata ba!!!” Bayan wannan sakon bata sake aika masa wani ba, shi ma be sake cewa komai ba, ta aje wayar ta mike tsaye hawaye na cika mata ido har suna zuba ta fice daga dakin ta nufi dakin Fatima da tunin ta fice daga dakin na mahaifiyarta bayan ta fahimci nufinsa abun da ta aikata babban laifi ne. Emily ta tura kofar dakin sai ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Fatima dake kwance akan gadonta tana kuka, ta fara takawa tana tafiya jiki babu karfi, wayen da suke zubo mata a yanzu sun sha banban da na farkon. Jinjirar yarta take jangowa tana tuna lokacin da farinciki da kuma kishiyarsa suka lullube a rana daya, ranar da ta haifi Fatima, ta dauki cikin yarta ta yi rainon cikin ba tare da sanin Turhan ko danginsa ba, ta raini yarta irin rainon da bata fatan ko makiyinta ya fuskanci rayuwar data fuskanta, ta tuna lokacin da Nurses suke fadar a kawo kayan jaririya, kuma aka rasa abun da za a lulluba mata sai da wata ta taimaka mata da zane daya, ta tuna tsawon kwanakin da Fatima ta dauka a hannunta tana lullubeta da zane saboda babu tufafi. Ta tuna yadda ruwan nononta yake kafewa saboda yunwa har sai da ta saci nonon akuya ta shayar da yarta, ta tuna yadda ruwa yake dukanta a rumfar wani bakanike da take fakewa idan dare yayi, ta tuna yadda take bin gidajen masu hali tana neman abun da zata kai a ciki, taya rana tsaka a yanzu Turhan zai bayyana yace nemanta yake me yake nema a gareta? Ya rabata da yarta kamar yadda ya rabata da sauran farincikin da ya rage mata a wacan lokacin? Ya sake dawowa rayuwarta ya haifar mata da matsala? A yanzu ta samu mai bata komai yayi mata ginshiki shi ne yake neman rusawa? Ta kai hannu ta dago yarta, wani mummunan furuci da yayi mata a wani lokaci da farinciki ya juya mata baya ya dawo mata. “Karki sake nuna kin san ni, akwai banbanci tsakanina dake” Ta lumshe ido tana tuna wata rana da matarsa ta saka bayinta suka yi mata bulala yana kallo be yi kokarin hanawa ba har sai da suka bar mata tabo a jiki. Ta rumgume Fatima, wani kalar ruwan hawaye ne yake mata zuba mai zafi da dacin zuciya, ashe duk bayan wannan zai dawo nemanta? “Momy me yasa kike kuka? I'm sorry” Tambayar Fatima ta dawo da ita hanyacinta, sai ta bude idon ta share hawayen tana murmushi. “Ina sonki Fatima, no matter what happen, daga ke sai London ne Iyalina, na wahala na yi sadaukarwa kamin ku kawo inda kuke a yanzu, a yanzu ma ban gama ba dan Allah kar wata rana ta zo ki fifita wani akaina” Ta rumgumeta, sun dade a haka sannan ta sake ta tashi ta fice daga dakin, kasa ta sauka ta zauna a falo zuciyarta cike fal da tunani. Vito be dawo gidan ba sai after 8pm, ya shigo falon tare da Chidimma dake rike da leda tana biye da shi a baya. Emily ta kalleshi ta kalleta. “Ina London?” “Bachi yake, na zo na dauki wasu abubuwan ne na yi wanka” Ta maida dubanta gurin Vito, ya san abun da take bukatar ji tun kamin ta gabatar masa da tambayar ya bata amsa. “Ya sauko ya daina fushi, na yi magana da shi” “Thank you” Ta gyada mata kai kawai, sannan ya kalli Chidimma. “Ki shirya da wuri direba zai maida ke asibitin kar a barshi shi kadai” “Okay Sir” Ta amsa tana wani karairaya daman idan shi ya bada umarni ba ta bata lokaci take aikatawa. Sai da ta fice Emily ta maida dubanta gurin Vito da idanuwansa suka dade a fuskarta. “Zan tafi na kwana can” Ya amsa mata kawai da ido sannan ya nufi kujera ya zauna, ita kuma ta haura sama ta shirya ta fito ta shiga dakin Fatima ta yi mata sallama sannan ta sauko suka fice a tare, ya rigata isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya nufi bangaren da Chidimma take ya fada mata an samu sauyi zata kwana da Fatima saboda Emily zata kwana da London a asibiti, ya dawo motar ya ke kunne tun a lokacin da ya faka a harabar, daman a ka'ida baya kashe mota sai idan ya gama fita gaba daya a wunin ranar. Yana tukin yana karantar yanayinta har suka isa asibitin. “Aikin fa?” “Na aje” Ya kalli irin kallon mai cike da tambaya, sai ta sauke kanta kasa tana taba yatsun hannunta. “Saboda na bawa yarana lokacina” “Ko dai sun koreki?” Ya tambaya ne kawai ba dan hana da tabbacin haka din ba, domin ya san yadda ta kwalla fa rai da son aikin kuma har ta fara zuwa ba karamin abu zai saka ta aje aikin ba. Ta bude motar ta fice ba tare da tace masa komai ba, yana daga cikin motar yana kallonta har ta shige ciki sannan ya ciro wayarsa ya duba time, sai kuma yaja motar ya fice daga asibitin. ALIYU POV. Ya hade yawu a hankali yana mamakin yadda aka yi ta san hadisin da ta kafa masa hujja da shi, ta san addinin musulunci ne har haka? Ta yi nisa a ciki? Me yasa ma ta bar addinin tun farkon fari. Ya sake karanta sakon ta dayan bangaren yana nisa tunanin a wani bangare na labarin da ta gutsura masa, gashi kuma ta daure shi da kalamanta, be rabi Turhan a zamanin da suka yi rayuwa a Emily ne, dan haka ba zai iya shaidar kyautata ko kishiyarsa a tsakaninsu ba, amman a neman da Turhan yake mata a yanzu da kuma gudunsa da take zai iya fahimta daga rayuwarsu. Sama yayi kadan ya sake kallon hotunan da Fatima ta turo masa, Emily ta kai mace har ta wuce, and ya yaba da yadda hotunan duka basu bayyana tsiraicinta ba duk kuwa da kasancewar ba musulma ba. Ya fita daga chat dinsa da ita ya shiga na Turhan, ya sake karanta sakon da ya aiko masa a dazun. “Na aureta ne a bisa cilastawar Ammy ba dan ina sonta ba, she's not my type at all, kuma adadin na ji ina sonta sai ma kiyayya ce ta ginu a tsakaninmu, har dai shedan yafi karfina na rabu da ita, amman ban cutar da ita ba” Kana ta karanta dayan sakon dake biye da shi, a take jikinsa yayi sanyi zuciyarta ta karaya, ya san abokinsa yana neman Emily, and yes ya samu Emily da kuma tabbacin ita din ce, amman yana tsoron kar haifar mata da matsala, ka ya sakata a wani hali kamar yadda ta fada, ta dayan bangaren kuma yana tunanin ya zai yi da abokinsa, idan yayi shiru anya ya kyauta masa kuwa? Ya sani idan Turhan ko mahaifiyarsa suka san da Fatima ba za su bar mata ita ba. “Lafiya kuwa?” Aisha ta tambaya tana aje Bowl ta kunna tap ta wanke hannunta tana kallonsa irin kallon nan na jiransa. “Tun da ka amsa wayar dazun na ga yanayinka gaba daya ya canja” “Ba komai” “Ko dai akan yarinyar da aka kora ne?” Yayi murmushi ya dago daga jikin fridge. “Ba ita ba ne” Ya saka wayar aljihu ya nufeta ta rikata suka fice daga kitchen din tana masa zancen business din da take son ta fara. “Watan cin kudin nawa ya tsaya kenan?” Ta kyalkyale da dariya. “Kasan ai kana cewa na rika sana'a” “Ke da baki san kowa a nan ba, taya zaki fara sana'a, kuma kin san ina binki kudi fa” “Namiji idan namiji ya rantawa matarsa kudi daman ai bata biya, amman shi idan ya ranta sai ya biya” “Saboda shi namiji be san zafin kudinsa ba ko?” Ta saka dariya a tare suka zauna ta kwanta jikinsa tana taba jira kadan bachi yayi gaba da ita, a hankali ya zaro wayarsa wani abun na cizon zuciyarsa ya sake bude sakonta ya karanta a karo na biyar, abu ne da yake bayyana a gurin kowa, zuciyar kowace mace kyakkyawa ce, sai dai wanda ta bar shaidan ya rinjayeta, ko kuma wanda wasu gurbatatun mazan suka yi ma illa. Akwai tambayoyin da yake bukatar amsarsu a gurin Emily, yana son ya ji kadan daga dalilinta na hana yarta da ita kanwata zuwa ga abokinsa dake nemanta kamar zai salwantar da rayuwarsa wata kila hakan ya taimaka masa gurin karfafa rokon da ta yi masa. Sai dai kuma ba lallai ta saurare shi ba, ba lallai ta yarda ta maida shi duniyarta ta baya ba, yana bukatar ganinta face to face domin amsa masa tambayoyin da ita kadai take da amsarsu. Amman kuma? Anya zata yarda su hadu? Zata yarda ta fada masa a inda zai same ta ko ta same shi? Ya shiga contact list dinsa ya tabo William ya aika masa da sako. “Please kana da wani information na gurin da Emily Aisha take zama” William ya masa reply Immediately. “Wace Aisha?” “Yarinyar da ka zo kana ta santi, wata half Cast haka mai jan gashi da blue eyes” “No wani abu ne ya faru?” “Yeah sun yi fada da Amal ne, har ta bar aikin ina bukatar ganinta face to face na bata hakuri kuma na mata bayanin yadda abubuwan suke” “Meyasa ka tambaye ni? Sau daya na ganta ban sake sakata a ido ba” “Saboda baka shigowa Office ne a yanzu, na dauka ko kuna gaisawa da juna ne, na ga ta sace maka zuciya ne” “Ta sace mana zuciya dai” “Nooo sam ba abun da kake tunani ba ne, idan ma kishi kake ka daina, ni ai musulmi ne, kuma ni bata cikin tsarin matan da nake so ma?” “Bata maka kyau ba” “Bana son macen da ta cika kyau sosai, kyaun idan yayi yawa yana zama illa, kuma ni bari da burin kara aure yanzu ko nan gaba” Ya dauki William tsawon mintuna talatin kamin ya aiko masa da address din har da number gidan da take zaune. “Thanks” Aliyu ya rubuta masa a as reply. “Me ya hada ta da Amal?” “Idan mun hadu zaka ji” Ya amsa masa sannan ya saka wayar alijhu cikin jindadi, ya rika matarsa zuwa bedrooms dinsu bayan ya kashe komai na falon. #TeamTurhan #TeamVito A ina kuke? #KhadeejaCandy [4/20, 10:00 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/Dfp3nf5JwbA22eFdvKklyG 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣2️⃣ Assalamu Alaikum. Barka mu da Sallah. Allah ya karbi ibada ya maimaita mana. *** ***. ***. Ta tura kofar dakin ta shiga fuskarta dauke da murmushi. "Hello my beautiful boy" Ya kalleta kawai ya dauke kai ba murmushi babu far'a kuma babu fushi, ta karasa kusa da shi cike da karfin guiwa ta zauna a kan gadon, hannu ta kai zata shafa shi a take ya saka mata ihu. Da sauri ta janye hannun, ta mike tsaye ta matsa gefe. “Ka yi hakuri London I'm sorry” Ta hade yawu tana kallonsa rashin jindadin dake zuciyarta ya bayyana a fuskarta. Hannu ta saka a aljihu jean din dake jikinta ta ciro wayarsta ta yi dialing din number Vito. Ta juyawa London baya hannunta daya a kan lebenta tana cizon akaifarta idonta tab da hawaye. “Na dauka ka yi magana da London kace min ya hakura fa” “Yeah na masa magana kuma ya hakura” “Amman na zo yanzu yana min ihu, baya son na taba shi” Vito yayi shiru for few seconds yana karantar yanayinta "Kuka kike yi?" "To me zan yi" Ta fada a tsawa tana shessheka kuka kai kace shi yayi mata laifin. Daker ta iya hade yawu sannan ta kashe wayar ta juyo tana fuskantar London, rasa makamar yadda zata ba shi hakuri ya sakata ta zauna a gurin tana cigaba da kallonsa har lokacin hawaye sauko mata suke, tunanin rayuwar da ta yi kamin ta haifi London da kuma wanda ta yi bayan haihuwarsa, da yadda rayuwarsa ta zo mata, halin da ta shiga fargabar matsalar saninta da Aliyu yayi a yanzu duk suka taru suka mata tsaye a cikin kai. Sai da ta yi da gaske sannan ta iya runtse ido tana maida numfashi a hankali, sai kuma ta kai hannu ta shafa sarkar cross din dake wuyanta. Wayarta ta fara ringing alamar kira, tana kallon kiran har sai da ya kusa yankewa sannan ta amsa ta kara a kunne ba tare da ta yi magana ba. "I have to take care of something, ba zan iya zuwa ba, amman na yi magana da wani abokina yace akwai wani abokinsa kwararen likitan kwakwalwa, kuma ya shigo garin nan yin wani abu, zai shigo ya duba London kamin ya wuce" “Dana ba mahaukaci ba ne Vito, ciwo ne kawai yake damunsa” Ta rufe da fada zuciyarta na bugawa da karfi tsabar bacin rai, ya san yadda zai tafi da ita dan haka yayi shiru be ce komai ba sai na tsawon lokaci. "Zan aje wayar" Ta fada jin be ce komai ba har na tsawon minti biyar. "Na sani, kawai zai duba shi ne ya bashi ya bamu shawarwari wata kila za su taimaka mana" Tare da ta sake cewa komai ba ta kashe wayar, daga inda take zaune take kallon danta har bachi ya fara daukarta tana angaje har ta kai ta kwanta a gurin, bachi mai nauyi yayi gaba da ita, bata farka ba sai kusan asuba, ta bude idon tana hamma ba tare da ta rufe baki ba, dagowa ta yi kadan ta leki London, ganin yana bachi ya bata karfin guiwar mikewa tsaye ta karasa kusa da gadon da yake kwance ta zauna, ta mika hannunta a hankali ta shafa fuskarsa zuwa kansa, tausayi yake bata sosai saboda lalurar da yake dauke da ita, ba zabin mutun bane ya kasance a yadda yake so, ko kuma waninsa ya kasance a wani hali na dabam marar dadi, abu ne sa yake tsare tun gabanin halittar rayuwa, an rubuta yadda dan'adam da rayuwarsa zata kasance. Knocking aka yi sau biyu da two fingers, da sauri ta dago ta kalli kofar dakin hakan yayi daidai ta turo kofar dakin da aka yi aka shigo. Cak ta tsaya tana kallon mutumen da ya kasance bakuwar fuska a gurinta, kamar yadda shi ma yake tsaye yana kallonta. “Lafiya?” Ta tambaya ganin ya gagara karaso, haka kuma ya gagara cewa komai. Takawa yayi baya ya ja mata kofar ya rufe, bata gama mamakin waye shi da kuma dalilinsa na aikata hakan ba, ya sake turo kofar dakin ya shigo with full confidence... Kallonsa take har ya karaso kusa da ita idonsa cikin na ta. "Sunana Doctor Adam Bello amman an fi sanina da Dr A-B kwararen likitan kwakwalwa, ina aiki a asibitin Special Care Hospital dake Abuja, abokina ya fada min akwai wani yaro da zan duba a dakin nan, wanda nake kyautata zaton kanenki ne..." Ya karasa yana kallon London dake bachi, zuciyarsa na raya masa kanenta, a yanayin halittar jikinta da kuma kurciyar dake fuskarta ba su bar masa alamar da zai aje London a matsayin danta ba. "London ba mahaukaci ba ne" Ya daga girarsa biyu kadan ba tare da ya kalleta ba. “Ni ma ban ce ni likitan mahaukata ba ne, mutane ne suke kuskuren fahimtar ciwon sai suke ganin kamar hauka ce” Ya kai hannu ya kama hannun London yana taba tsatsunsa a hankali. “Fada min idan kanenki ya farka yana farkawa a firgice? Idan babu kowa a kusa da shi?” Ta daga masa kai alamar eh. “Wane kalar turare ya fi so?" Har lokacin be kalleta ba. "Ban taba lura da wannan ba" "Uhm, da wa yake yarda? Bayan mahaifiyarsa da Babansa da kuma ke?” “Dana ne ni na haife shi” Sai a lokacin ya sake kallonta, ya dauke shi tsawon dakika biyar kamin ya iya dauke idonsa daga kyakyawar fuskarta mai matukar daukar hankali. "Ya kamata ki san kalar turaren da yake so, his favorite color, wane kalar cartoon yake so, wane kalar wasa yake so, wane yanayi yake shiga idan yana kuka, su waye mutanen da yake so, ki fahimci idan yayi bachi wane kalar mafarki yake? Ya yanayin sakewarsa da mutane yake?" "Na san wasu daga ciki, amman dai shi ba mahaukaci ba ne” Yayi murmushi ya kalleta. “Da alama zaki sha wahalar rayuwa kamin ki fahimci duniya da mutanen cikinta, ni dai ina baki shawara ne kawai na yadda abubuwa za su miki da sauki tsakanin ke da... Danki...” Ya fada tare da jan zaren furta kalmar danta kamar mai jin nauyin alakantata da jininta. Sannan ya ciro katinsa a aljihunsa ya mika mata. "Bana kallon marar lafiya a free ma, balle kuma magana da shi, sai an yi min biya mai kyau, amman da yake ke tafe kike da sa'a, sai ga shi an lallaba ni na zo har asibitin da kike na duba danki kuma na baki shawarwari a free, so hare is my card idan kina son wanin hakikanin waye danki, taya zaki zauna da shi, wane mataki zaki bi har ki yi nasarar sauya rayuwarsa, da kuma yadda zai samu lafiya, sai ki bi matakin da yake kan card din” Ya aje mata card din ya juya ya fara tafiya. “Bama bukata daman ka zo nan ne dan ka ci kudinmu ko? Toh ni na san waye ďana kuma shi ba mahaukaci ba ne” Juyowa yayi yana murmushi. “Halinku daya sak da matar direban direban Babanmu, amman kuma da ta bi shawarwarin da na dora ta a kai da magani, sai ga shi ta dawo tana min godiya” A kokarinsa na fahimtar da ita kudi ba matsalarsa ba ce kamar yadda take zato ya ambato mata direban direban babansu. Da farko she was confused kamar ya Direban direban babansu kamin ta sake kallonsa cike da mamaki. “Direban Babanku?" "Nope Direban Direban Babanmu" Ya furta yana hade lips dinsa. "Direban Babanku yana da Direba kenan.?" “Uhm” 'Wane irin kudi babanku yake da shi haka ne? Da har direbansa yake da direba?' Kamar ya san tambayar da ta yi ma kanta a zuciyarta sai ya taka ya matsa kusa da ita, yana kallon kwayar idonta. “Babanmu na da kudin sosai, kwatankwacin yadda kike da kyau sosai mai jan hankali” Ya fada cikin wata murya na irin mutumen da kuzari ya bar jikinsa, gaba daya kyauta ya gama rudashi. Ta hade yawu da karfi tana kallonsa. “Akwai wata tambayar ne?” Ta kasa cewa komai, ya kalli agogon hannunsa. “Lokacin sallah yayi, duk lokacin da kika shirya bata kudinki, zaki iya nema till then good bye” Ta matsa baya ya fara tafiya. "To miye amfanin zuwanka? Baka duba yaron ba baka fada min komai ba taya zan tabbatar da kwarewarka ko akasin haka?” Tana maganar tana daga kafadunta. “Ko ba komai ai na auna nauyin kyaunki na fada miki matakinsa, yanzu kin san darajarsa” Ya fada sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ta bi bayansa da kallo har ya fice, sannan ta sauke numfashi ta kalli card din da ya bar mata, ta kalli danta, sai kuma ta dago wayarta ta shiga camera tana kallon fuskarta. Ita kan bata ga wani banbanci a tsakanin kyauta na jiya, shekaran jiya da kuma yau ba. Mai da wayar ta yi ta aje, tana nan tsare da danta har ya farka misalin bakwai da yan mintuna. “Good Morning Sunshine" Suna hada ido sai ya koma ya kwanta ta rufe ya bata fuska sosai kamar zai yi kuka. “Chichi chichi“ "Okay zata zo yanzu" Ta fada ba dan ranta ya so ba sai dan Chidinma ta fi soyuwa a zuciyar danta fiye da ita a yanzu. Ta dauki wayarta ta nufi kofar dakinta ta bude fice tana jin kamar ta fasa kuka. Ta fito asibitin sai ta tsaya a harabar tana kallon mutanen dake hada hada kamar wacce ta rasa abun yi, gaba daya ta rasa me ke mata dadi. Daga inda take tsaye ta dagawa wata matar dake tunkaro inda take hannu matar ma ya dago mata tana murmushi. Emily ta fara takawa ta karasa gurin matar dake tahowa. "Sannu kin gane ni?” Matar ta dan yi jimmm kamin ta amsa. “Eh kamar ke ce na kusan kade yarinyar ki ko?” “Haka ne, kina aiki a nan ne?“ “No na shigo kawo ma wata abincin ne, ke fa?“ “Yarona ne ba shi da lafiya” "Da sauki amman?” "Eh” “Allah ya ba shi lafiya” Tana fadar hakan ta wuce abun ta ta bar Emily tsaye a gurin da mamaki kuma da takaicin yi mata magana da yi. “Okay…“ Ta fada sannan ta juya tana kallonta kamin ta tsuke baki ta cigaba ta tafiyarta, tana fita wajen asibitin ta dauki drop zuwa unguwarsu. Har ta isa gida haushin kanta take ji meyasa ta yi ma Matar nan magana gashi ta wulakantata. “Chere m, a ga m ala n'ulo nweta ego gi ugbua" Ta fada masa da yaren Igbo cewar ya dan jira zata shiga gida ta dauko masa kudinsa. "Okay" Ya amsa mata ta nufi gate din ta buga, mai gadinta ya fara lekowa ya ga ganta madadin ya bude mata sai ya bude ya fito ya nufi motar da ta shigo ya leka mai motar, hakan kuma ba karamin mamaki ya bata ba domin be taba yi mata haka ba. “Me ya faru?” “Babu komai ranki ya dade” Ya amsa sannan ya bude mata ta shiga, kamar zata yi masa magana sai kuma wata zuciyar ta hanata, dan haka ta maida hankalinta gurin manyan bakaken karnukan da suka fara kuka saboda shigowarta, ba karamin tsorata ta yi ba ganin manyan karnukan har biyar daure da sarka a harabar gidanta. Tsayawa ta yi cak tana kallonsu daya bayan daya kamin ta kalli Vito da ya fito daga cikin gidan. “Baka na son kare ka sani” “Na sani ba saboda ke na kawo ba” “Saboda wa?” Ya saka hannu aljihunsa ya ciro kudin da shi kansa be san nawa ba ne ya mika mata. “Je ki sallami mai mota, me yasa kika dawo yanzu? Ina London?” Ta kalli kudin kawai ta dauke kai sannan ta kalli karnukan. “A daure suke ba za su taba ki ba” Tana matukar tsoron kare, amman a haka ta jure ta shiga cikin falonta, Fatima ta zo da gudu ta tarbeta tana sanye da uniform din makaranta. “Momy good morning“ Ta rage tsawo tana shafa kan London “Morning My love” Ta amsa da murmushi kadan a fuskarta sannan ta daga kai ta kalli Chidimma dake jera cups a dinning. “Me yake faruwa a gidan nan“ “Kamar na me ranki ya dade?” “Me yasa Vito ya kawo karnuka a gidan nan? Kuma mai gadina ya leki motar da ta sauke ni yanzu, be saba min haka ba, kuma a yanayin yadda na ga Vito da alama gidan nan ya kwana” “Haka ne, Sir Vito ya kwana a nan a falon nan ma, sauran amsoshinki kuma sai dai ki bincike shi, ban san amsar ko daya ba” Emily ta kalleta daga sama har kasa tana kallon yadda ta saka riga da wando da suka dame mata jiki sosai suka fitar mata da halittar jiki, bata sake furta komai ba ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta, babu jimawa ta sauko rike da kudi a hannunta ta fice daga falon. Har lokacin Vito na tsaye Balcony din yana kallon gate din gidan kamar mai jiran shigowar wani, shi ma kallonsa ta yi daga sama zuwa kasa ta dauke kai ta nufi gate din. Ta bude da kanta, ga mamaki sai ta samu direban ya tafi sai wata farar sabuwar mota ce fake a baya kadan da inda mai taxi din ya faka. Ganin yadda ta tsaya kallon motar ya saka Aliyu ya bude motar ya fito ba tare da ya rufe ba ya doso inda take tsaye tana kallon motarsa, da sauri ta sauke idonta kasa wani irin fargaba da faduwar gaba suka tunkarota da bata san na miye ba, a ka'idar rayuwarta, tana iya kallon kowane kalar namiji ido cikin ido ba tare da tsoro ko jin wani abu ba, sai dai a yau ta samu kanta da kasa motsa ta balle kuma har ta ido da mutumen da yake cikin jerin mutanen da ta tsana. "Ki yi hakuri na sallami mai taxi din da kika hau ba tare da izininki ba” "Me ka zo yi nan?” Ya daga kai yana kallon gidan. “Na zo na bada hakurin abubuwa da suka faru ne, kamar hotunan da Fatima ta tura min ba tare da saninki ba, kokarin shiga rayuwarki son sani wasu abubuwan, aje aikin da kika yi saboda abun da Amal ta yi miki...” “Ka daina kokarin shiga rayuwata, karka janyowa kanka matsalar da ba zaka iya hadewa ba, sanin abubuwan da suka faru ba za su kara maka komai ba face su jefaka a ramen da ba zaka iya cire kanka ba, biya kudin taxi da ka yi kuma ban yafe ba” Ta juya ta fara tafiya. “Ban yi da gode ba, ba jarumi ba ne ni, balle a ba ni kambu ko ayi min jinjina, na zo nan saboda wani dalili, idan ba haka ba ba zaki gan ni kofar gidanki ba” Ta juyo ta tana son ta kalleshi sai kwarjininsa a yau ba zai bar ta ta aikata hakan ba. “Taya aka yi ka san gidan nan” Yayi shiru kamar mai tunanin irin amsar da zai bata. “Baka yi kama da mai boye gaskiya ba, magana biyu bata dace da namiji irinka ba, kuma addininku ya hana karya ko ba haka ba?” "Kokarin sanin gaskiya ko gyara kuskura bai isa ya saka na dora tubalin ginin da karya ba, saboda na faranta miki ko na burge ki ba zai saka na sabawa Ubangiji na ba” Ta yi wani murmushin shedanci tana kallon wani gafe. “Ku dai musulman nan idan kuna magana kamar ace zuciyarku ma haka take, aikinku dabam addininku dabam” “Kar ki yi la'akari da aikinmu ko kalamai, ke dai ki maida hankalinki gurin addini kawai, Williams ne ya bani addreshinki” Ya amsa mata tambayarta bayan ya shimfida mata matashiya akan addininsa. Ta juyo da kyau ta fuskance shi, sai dai har lokacin ta kasa kallon wayar idonta, tana dan mamaki waye ma Williams. Aliyu ya saka hannunsa aljihu ya dauko wayarsa ta kamo hoton Williams ya nuna mata. “Idan ma ya taba fadin sunansa tohm na manta, amman dai shi Williams din be san gidana ba, be san komai a kaina ba” Wani tunanin ne ya zo mata. “Ka yi hanzarin barin gidan nan wata kila saboda kai Vito ya kawo dog's yau, kuma saboda kai ya kwana a nan” Rufe bakinta yayi daidai ta daga kan da Aliyun yayi ya kalli kofar gate din da aka bude gaba daya, Emily ta juya da sauri ta kalli gate din, a take hankalinta ya tashi ganin gogan ne a tsaye fuskarta kamar kullum babu annuri. “Ka yi hanzari bari gurin nan” Ta fada ba tare da ta juyo ba, kana ta saka kai ta nufi gate din da nufin shiga cikin gidan, tana isa a daidai gurin da Vito yake tsaye zata wuce shi, sai ya fisgota da karfi ya dawo da ita. Kamin ta yi wani yunkuri ya dauke fuskarta da mari mai zafi, har sai da dafe kunci hawaye ya cika idonta, sanin karamin aikinsa ne dukanta ya saka ta auna da gudu cikin gidan tana ihu, binta yayi a baya kamin ta haura entrance din ya janyota ta fadi kasa ya fara shurinta yana kai mata duka ta ko'ina. Kan kace me ta cika gidan da ihu tana kuka shi ko dukanta yake kamar an aiko shi. Chidimma da Fatima suka fito da gudu saboda ihun da take, sai dai babu wanda ya iya kawo mata agajiya har sai da ya duketa iya son ransa, sannan Fatima ta zo gurinta ta fada jikinta tana kuka, Chidimma kuma ta juya ta koma cikin gidan ba tare da rika Emily ko bata hakuri ba. Duk abun da ya faru Aliyu yana tsaye yana kallo hannayensa biyu rumgume a baya, sai a lokacin Fatima ta lura da shi, da sauri ta dawo daga jikin Emily tana kuka ta nufi gurin da Aliyun yake tsaye, sai dai kamin ta karasa mai gadin ya hada gate din ya rufe. Aliyu ya sauke numfashi a hankali ya juya ya shiga motarsa dake bude har lokacin, ya dan jima a motar zaune kamar mai tunanin abun yi, kamin ya ja motar ya juya ta hanyar da ya fito. Har ya isa gidansa ransa a jagule yake, damuwar da bata tasa ba na neman mamaye masa zuciya. Be san ya dade a cikin motar zaune ba har sai da Kameela (AISHA) ta fito daga falon ta kwankwasa motarsa sai ya sauke gilashin motar yana kallonta da murmushin da ya fi kama da damuwa a fuskarsa. “Mai ciki?” “Lafiya ka shigo cikin gidan ka zauna a mota, kuma ga damuwa a tare da kai” Ya san daman zata ga damuwar kam domin be iya sauya kansa a duk lokacin da wani abun na damuwa ya same shi, iyakar abun da yake shi ne boye sirrin damuwar tasa har sai ya samu mafita. Sanin halinta na zafin kishi da kuma saurin juyar da abu ya saka be fada mata daga inda yake ba, da kuma dalilin damuwar tasa, haka kuma ba zai iya mata karya ba, domin karya ba dabi'arsa ba ce. Kiran wayarsa ya yanke masa tunanin da yake na yadda zai kawar da maganar a gurin matarsa Kameela, kusan kamar an yi sara akan gaba ne, domin kiran da Turhan yayi masa yayi daidai a yanzu da yake neman amsoshin wadansu tambayoyi. Sanin ba zai iya amsa wayar a gaban matarsa ya saka shi daga gilashin motar ya rufe ruf sannan ya amsa wayar. “Assalamu Alaikum” “Wa'alaikumussalam, Aliyu ya gida” "Alhamdulillah, har yanzu babu wani labari ne?" Aliyu ya shiga shi tambayar ne a kokarinsa na gujewa tasa tambayar. "Babu, na yi yawo duk inda ake saka ran za a samu yarinyar nan ba a same ta, da har nace yau zan dawo gida, sai kuma mutumen da ka hada ni da shi yace na yi hakuri mu sake bincikawa daga yau zuwa gobe, idan ban same ta ba, sai na hakura” "Toh ya zaka yi da Ammy?” “Ba dan Ammy ba, taya zan bata lokacina ina nemanta, kawai dai ina hakuri ne saboda Ammy mahaifiyata ce ba yadda zan yi, amman su ma iyayen suna shiga hakki yaya wani lokacin Wallahi” “Wata kila Ammy ta ji ko ta gani ko tana tunanin ka munana mata a zamanku ne, shiyasa ta gagara shiryawa da kai” “Kaddara ma ace hakan ta faru, amman ai ni danta ne, be kamata ta juya min baya ba a kowane condition, taya zaka fifita wani fiye da naka? Kuma tun farko ita ta cilasta min auren yarinyar nan ni gaba daya bana sonta” “Amman ka cutar da ita?” "Sau nawa zan amsa maka tambayar nan ne Aliyu? Shi daman zaman aure sai an yi hakuri, saboda zo mu zauna zo mu tsaba ne, kuma al'adarmu da addininmu ba daya ba, kuma yarinyar nan bata da asali” “Ban fahimta ba” “Ba a san su waye iyayenta ba, kuma ko da na zauna da ita zuwa can gaba idan an yi zuri'a baka tunanin zata iya juyar da hankalin yaran zuwa addininta?” "Ita miye laifinta dan an haife ta a inda be dace ba, ba a shawara da mu kamin a zaba mana iyaye ko irin rayuwar da za mu yi kai kasan haka” “A haka din kuma addinin musulunci ya hore mu da auren mai asali, abubuwan da suka faru dai sun faru shikenan, sun wuce yanzu kuma nemanta nake na shirya tsakanina da mahaifiyata” “Allah yasa a dace” Ya fada sannan ya aje wayar ya kalli Kameela dake ta leken motar tana dora kunnenta a jikin gilashin ita ala dole sai ta ji da wa mijinta yake magana. Murmushi yayi ya bude motar ya fito. “Wannan ba halinki ba ne” "Kai ma ai ba halinka ba ne idan kana waya ka boye min, me yasa baka son na ji” “Dole ai kin san akwai sirrin da zan yi da yan'uwa ko abokai ba zai yayu kiji ba ko? Kamar yadda ke ma na san akwai abun da ba zaki fada min ba” “Ni ai bana boye maka komai?” “Uhmmm” Ya sumbance ta sannan ya kama hannunta suka shiga cikin gidan. “Baka yi breakfast ba ka fita, kuma gashi ka dawo da damuwa, yanzu kuma ka yi waya ban san da waye ba ka rufe ban ji komai ba” “Be shafe ki ba ne ai” "Abun da ya shafe ka ai ya shafe ni, ka fada min minene dan Allah dan Allah" Allah da ta hada shi da shi sai ya ji ba zai iya boye mata ba, kamar yadda ba zai iya fito mata da komai a zahiri ba. Yaja mata kujera ta zauna ya fara zuba musu abun karyawa sannan shi ma ya zauna. Cin abinci kawai yake baya jindadinsa ba dan matarsa bata iya girkin ba sai dan bacin rai da ya fi kama da damuwa dake tare da shi. “Dan Allah ka fada min” Ya kalleta yana murmushi. "Kina da son gulma, toh akan Yarinyar da Turhan yake nema ne” “An same ta ne?” “Be same ta ba har yanzu, yana cikin damuwar rashin samun nata, hakan kuma ya shafe ni” “Toh ai be kamata hakan ya shafe ka ba, damuwar wani be kamata ace ta zama damuwarka ba” Ya aje fork din hannunsa ya kama hannunta “Ki daina wannan tunanin, indan akwai tausayi a tare da mutum dole ko da ba musulmi ba ne ya shiga wani hali marar dadi zaka ji babu dadi balle kuma musulmi dan'uwanka” “To wai shi ba zai je ya nemi yarinyar da kansa ba sai ya rika dora maka lalura waya sani ma ko yarinyar kyakyawa ce?” Ta fada tana turo baki, hakan ya saka shi yin murmushi. “Idan kyakyawa ce fa?” "Idan kyakyawa ce ko ka ganta ai ba zaka fada masa ba" “Baki yarda da mijinki ba?” "Tohm zuciya ita kuma ai bata da kashi" “Wai ke da na yi ma alkawari na yi ma rantsuwa aka yi abun har a rubuce cewar ba zan kara aure ba, ina ruwanki da duk inda zan shiga" "Shedan fa yana nan kusa zai iya sakawa ka karya alkawarin nan, kuma yadda kake da kyaun nan kake wanka idan zaka fita, ai dole hankalina ya tashi” "Wallahi Kameela ba zan miki kishiya ba, ba zaki taba sharing dina da wata da sunan kara aure ko akasin haka ba, shikenan?“ Ya sumbance ta sai ta yi murmushi ta kwanto jikinsa. [4/20, 10:01 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣3️⃣ Masu tambaya daga farko zaku iya duba channel dina https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 Ko kuma wattpad @KhadeejaCandy Masu tambayar free ne ko na kudi, toh Free ne, yan bati sun hada kai da Iya sun min kiranye ya kamani tare da hadin kan Ummu Faisak yayar Wasim 😜 Asha karatu Lafiya 🥰 ***.    ***.    *** VITO POV. Falon ya shiga ya zauna, can kasan zuciyarsa ya ji babu dadi na dukan da yayi ma Emily, ya saba samun kansa a irin wannan yanayin a duk lokacin da ya duke ta, sai dai kuma dukanta a gaban ko ma waye abu ne da ba zai iya hana kansa ba, ba zai iya rike hannunsa daga taba jikinta da sunan duka a duk lokacin da laifi ya fito ta tsagenta ba. Kamar yadda ba zai iya fin karfin zuciyarsa a duk lokacin da wani yayi mata kallon banza ko na soyayya ba, yana sonta ya sani, yana tsananin kishinta irin kishin da shi kansa yana tsoron kar yayi masa illa wata rana. “Ban san ko kana bukatar ruwa ba” Chidimma ta miko masa cup da gorar ruwa a tray cike da ladabi da kuma gudun bata masa rai. Ya kalleta kawai ya kalli gurin da zata aje ruwan, sai ta risina ta aje a kasa ta daga gorar ruwan ta bude ta zuba masa a cups sannan ta dora ruwan a kan side table. Ruwan ya fi da kallo yana mamakin yadda ya kasa yi ma Aliyu komai a dazun har ya tafi, me yasa ma ya daki Emily bayan kuma Aliyun ya kamata ace ta hukunta domin shi ya nemi addireshinta ya biyo sawunta har gida? Ya kawo karnukansa da nufin idan Aliyu ya shigo gidan ya rufe gate din ya sakar masa su, amman duk be samu nasarar yin hakan ba. A zahirin gaskiya Vito wani kalar mutum ne sa kallonsa kawai zaka yi ka firgita, saboda rashin annurin dake fuskarsa da kuma shigar da yake ta tufafi, amman sam be ga alamar hakan a tattare da Aliyu ba, toh miyasa ma ya biyo ta har gida? Me yake nema a gurinta? Ya kai hannu ya dauki ruwan da Chidimma ta zuba masa ya kai baki yana sha sai wani sanyi ya sauka a zuciyarsa wanda ya kara taimaka masa gurin hararo dalilin Aliyu na bibiyar macen da ba ma addininsu daya ba. 'Tana da kyaun da kowane kalar namiji zai iya cewa yana sonta ko son mu' alama da ita` Zuciyarsa ta bashi amsar da yake bukata, mikewa yayi tsaye ya nufi kitchen din da Chidimma take, tana ganinsa ta juyo da sauri. “Kana bukatar wani abu ne ranka ya dade?” “Me kika shiryawa London na karyawa?” “Gashi nan” Ta dauko big basket ta risina kasa ta aje masa, zai kai hannu ya dauka sai ta riga shi. “Bari na kai maka mota ranka ya dade” Be ce mata komai ba, ya juya ta bi bayansa har gurin motarsa sai da ta saka masa mota sannan ya yi mata key ya fice daga gidan. Sai a lokacin Chidimma ta nufo Emily dake kwance a gurin rumgume da Fatima ta tsaya kanta. “Bana son na batawa daya daga cikinku rai ne, bana son daukar bangaren Sir Vito na bar naki, abu kadan zai iya sakawa ya koreni ko ya hukanta ni, shiyasa bana iya tarewa idan yana dukanki, ki yi hakuri” Uffan Emily bata ce mata ba, ita ma kuma bata jira cewarta ba ta juya ta koma ciki ta cigaba da aikin da take. Yana faka motarsa harabar asibitin wayarsa ta yi ringing, ya amsa kiran har lokacin ransa babu dadi saboda dukan da yayi ma Emily, mahaifiyarsa ce take sanar masa jirginsu zai taso yanzu daga Murtala Muhammed International Airport (MMIA) dake Lagos zuwa Port Harcourt International Airport. Daman ta sanar masa da zuwanta tun kwanan baya. “Safe journey" Ya fada as Answer sannan ya cire wayar daga kunnensa ya bude dayan side din ya dauko basket din da Chidimma ta saka masa ya nufi cikin Asibitin. Ko da ya shiga ya samu Nurse nata lallaba London ya fito daga kasan gadon majiyanta da ya boya amman yaki sai ihu yake mata. “Heyyy my boy” Vito ya fada cikin muryarsa ta manyan mazaje, London na jin muryarsa sai ya leko suna yi arba ya fito da sauri yaje gurinsa ya rumgume shi. Murmushi ko nuna farinciki ba al'adarsa bace balle kuma a yau da yake cikin damuwa, kan London kawai ya iya shafawa ya daga shi zuwa kan gadon Asibitin suka zauna. “Tun dazun yake labe a gurin baya yarda da kowa, idan ka matsa kusa da shi sai yayi maka ihu” Ta fada tana kallon London din da murmushi a fuskarta, Vito be ce mata komai ba, ya kai hannu ya dauko abinci ya bude ya fara ba shi da kansa, tana ganin haka sai ta fita ta bar musu dakin. Sai da London ya ci abinci ya koshi sannan Vito ya fara masa maganar Emily. “Meyasa ka yi ma Momy Ihu jiya?” “Ina fushi da ita” “Na fada maka Momy tana sonka ba zata aikata abun da zai bata maka rai ba, duk laifinta akan kuskure ne, ka yafe mata ka ji?” Ya daga kai, sai ya shafa kan yaron... “Ina son mahaifiyarka, duk kuwa da kasancewar ta haife ku, na kula da ku na nuna mata soyayya da gata, amman ta kasa ganin hakan” Yayi shiru yana kallon London. “Wata kila kuma ta gani, kawai dai bata shirya karbata ba ne” Ya ja numfashin da ya gagara saukewa. “Uhmmm zan mata uzuri har zuwa lokacin da ta dibarwa kanta, sai dai ina da tabbacin abu daya, idan ban samu mahaifiyarku ba, wani ba zai same ta ba, idan ban mallake ta wani ba zai ci galaba a kaina ba” London yayi murmushi domin be fahimci yaren ba. A hankali idonsa ya kai a kan card da Emily ta jefar a dakin. Mikewa yayi tsaye ya nufi card din ya dauka Dr A-B ne rubuce a jikin katin da kuma address din gurin aikinsa sai Email da number wayarsa. A take ya fara jin zuciyarsa ya tafasa, jimke katin yayi ya juyo ya kalli London. “Chi chi zata zo ta kula da Kai bari na je na dawo ka ji?” London ya daga masa kai alamar amsuwa, be bar dakin ba sai da ya kira Chidimma a waya ya fada mata ta bar duk abun da take ta zo yanzu asibitin gurin London, bayan ya shafa kansa ya sumbance ya fice. Kamin ya isa gida ya kira daya daga cikin yaransa ya fada masa ya tafi gidan ya dauke dog's da aka kai, yanayin yadda ya faka motar a harabar ya fito kadai ya isa ya sanar da bacin ransa balle kuma yadda ya turo kofar falon ya shigo, sai da Fatima dake zaune tana zane ta firgita. Yana kallonta ya dauke kai ya nufi upstairs. “Dukanta zaka sake yi?” Ya juyo ya kalli makiyiyarsa Fatima, domin ya fi tsanar ta fiye da kowa a gidan, sai dai duk da haka be taba unkurin kai hannu ya doketa ba, no matter what ta yi masa sai dai ya mata fada ko ya wani hukuncin na dabam amman ban da duka. “Momi zata yi kudi, tana aiki zata samu kudi mai yawa zata gina gida zata maida mu can mu rayu a can ba tare da kai ba, ba zaka sake ganinmu ba balle ka dake ta, i hate you” Ta fada cike da fitsara da tsageranci irin yadda ta saba yi masa, jimmm yayi yana kallonta kamar mai nazari ba tare da ya ce mata komai ba, kamin ya juya ya haura saura zuwa dakin da Emily take... EMILY POV. “Meyasa kake son saka kanka a hatsari? Baka san wacece ni ba, kuma baka san da wa nake tare ba, kuma ya kamata kasan ni ba musulma bace, babu abun da Zai hada ni da kai, domin mutanen da na tsana irin musulmai, karka sake bibiyata karka sake shiga rayuwata, idan ba haka ba zaka jefa kanka a bala'i” Ya mayar mata da amsa a take. “I'm sorry for what happened earlier, bana nufin jefa ki a matsala, akwai wani tsauni ne da na hau ba kuma zan iya sauka ba har sai da gamsantsun amsasoshinki, shin zan iya sanin wani abu akanki? Wata kila hakan zai taimaka ya gina wata katangar da zata katange ni daga fadawa mai nemanki gaskiyar a inda kike” “Ni uwa ce da bata da aure mai zama a karkashin inuwar wani mai karfin kudi da iko, uwa ce da ta haifi yaranta ta raine su ba tare da taimakon kowa ba, ni din na tashi a gidan marayun ne ban san uwa ko ubana ba, balle ayi zancen yan'uwa, bana da kawaye bana da kowa sai Vito da yarana, ni din wata ce da wani musulmi ya yaudara, mummunar kaddara ta yi min dabaibai hada ni da mutanen da bana kirki ba, a yanzu kuma ni christen ce mai alfahari da jindadin addininta, mai kokarin gina kanta da rayuwar yaranta, bayan wannan sai me kake son ka sani?” “Ina son na san a lokacin da kika wanzu tsakanin rayuwa da mutuwa ne, ina son na san komai akanki, ta ina lamarin ya fara? Taya kika kawo har yanzu? Su waye suka munana rayuwarki, miye dalilin komawarki addinin Christianity? Su waye suka saka kika tsani musulmi da addinin musulunci? Miyasa baki son Fatima ta san tana da mahaifi? Wacece ke Emily? Na damu na na sani, kuma na damu da ke” Taja numfashi tana karanta sakon hawaye na cika idonta, kai ta daga sama ta lumshe ido ta bude sannan ta maida idonta a kan wayar, tana kokarin rubuta masa amsa ta WhatsApp din Vito ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta yi saurin saka wayar a lock ta dora ta a kan madubi. “Miye hadinki da likitan da zo duba London da har zai baki card dinsa? Idan wani abun da ya shafi rashin lafiyarsa ne ai da ni zai yi magana” Ta juyo idonta a kumbura ta kalleshi hawaye na sauko mata. “Waya kalleki? Waya miki magana? Gurin wa kika je? Da wa kika waya? Me ye hadinki da wannan? Ina zaki je? Shi ne kawai abun da ka iya” Ta matsa kusa da shi cikin ihu ta fara fashe mata kurcin dake mata ciwo a zuciya. “Ni ba ni da ikon kaina, da wa zan yi mu'amala, su waye masu aikina da masu gadina, su waye makota na, a ina zan zauna, duk kai kake zaba min, ka hana in yi abota da kowa, ka hana na yi mu'alama da mutane kamar kowa, takamarka saboda ina zama a karkashinka ne, takamarka saboda ka tsamo ni daga rana zuwa inuwa ne, idan na yi magana sai kace kana so na ne? Taya ina aka soyayya da son kai? Miye banbancinka da sauran ne? Miye banbancinka da Khaleefa sa ya cusa yarda da soyayya a zuciyata ya aureni saboda kawai ya yaudare ni? Banbanta min banbancinka da Turhan mutumen da ya aureni saboda cika umarnin mahaifiyarsa ya maida ni kaskantacciya a cikin bayinsa, sai yaushe ni zan samu yancin kaina? Sai yaushe zan yi farinciki na har abada?” Yin sa'insa da ita ba abu ne da ya saba yi ba, musamman idan ta ci galaba akansa da hawayenta, saboda haka ya zubar da makaman yakin da ya zo da su ya karasa gurin da take tsaye ya rumgume ta. Sai ta cigaba da zubar da hawayen da take. “Ina tsananin sonki Emily, ban taba son wata mace ba sai ke, kina da kyaun da maza ba za su iya dauke miki ido ba, shiyasa zuciyata ta kasa natsuwa da wasu abubuwan, ina kokarin baki kariya ne, saboda ina jin cewar ke kadai ce mace a duniyar nan, bayan ke babu wata” Ta daga kai tana kallonsa ta san yadda yake ji domin ta taba tsintar kanta a makamancin halin da yake ciki a yanzu, a lokacin da ta yi soyayya da Khaleefa bata ji bata ganin kowa sai shi. Ya sumbancin tsakanin girarta guda biyu sai ta lumshe ido tana tausayinsa da kuma kanta. ALIYU POV. Da abincin dake gabansa yayi feeding dinta daman ba wani son cin abincin yake ba a safiyar nan. Sai da suka gama sannan ya hada kayan ya dauka ya kai kitchen, kamar jira ake ya aje plates din sako ya shigo wayarsa kasancewar data sa kullum a bude take. Ciro wayar yai daga aljihunsa ya duba sakon da ya shigo yanzu. Sakon Emily ne da take gargadinsa tare da shimfida masa dokokinta. Bayan ya gama karantawa ya bata amsa, ta sake rubuto masa wani ya aika mata da tambayar abun da ya fi damunta, ta zayyana masa kadan daga sanin wacece ita, sai ya yi mata matashi da dalilinsa da kuma damuwarsa akanta. Ya dauki dakiku yana jiran amsarta amman be samu hakan ba, maybe mata shiryawa hakan ba, ya raya a zuciyarsa, kamin ya ji takun tafiyar Kameela a bayansa, da sauri ya juyo sai yayi hanzarin saka wayar aljihunsa yana mata murmushi. “Me kike bukata” “Na ga ka dade a kitchen din ne, na dauka ko wanke wanke kake ma” Ta fada da dan mamakinta na rashin yarda, mo matter how Aliyu zai mata rantsuwa, zuciyarta bata natsuwa saboda tsananin kishinta. Ya juya ya kalli kayan da ya aje sannan ya juyo ya kalleta. “No, bari na je na yi wanka yau da wuri nake son tafiya aiki” Kamin tace komai ya fice daga kitchen, ba dan komai ba sai dan gudun ta zargi wani abu, duk da haka kuma be tsira ba, domin hankalin matarsa be kwanta da yadda yayi sammakon fita dazun ba, da kuma yadda yake chat a kitchen dinta ba, ita dai ganin take sheidan zai iya zuga shi ya karya alkawarin da ya daukar mata. A take ta ji ta kwadaitu da son ganin chat dinsa, ta san mijinta ba zai mata karya ba, amman dai yadda mata suke ta zillo akan maza kamar za su aurar da kansu, ai wata zata iya tankwasashi ya fara halayen da ba nasa ba. Ita kam dai ba zata yarda mijinta ya lalace da kara aure ba, kara ta duba chat din ta ga koma miye ko hankalinta zai kwanta. Falo ta dawo ta zauna tana ta sake sake kamin zuciyarta ta fi karfinta har ta tashi ta nufi dakinsa ta tura kofar dakin ta shiga, ko da ta shiga ta samu yana bandaki yana wanka, farkon abun da ta fara neman shi ne wayarsa ta wurga idonta a ko'ina na dakin bata ga wayar ba har sai da ta daga fillon da suke kwanciya. Sai ta samu wayarsa a kasan fillon ya kifeta hakan kuma ba karamin mamaki ya bata ba domin ba halinsa ba ne boye waya, wannan ya saka ta san password dinsa kuma take shiga ko'ina a cikin wayarsa tana masa bincika son ranta. Zaunawa ta yi gefen gadon rike da wayar da bude password dinta ba zai mata wahala ba domin ta saba budewa, kai tsaye ta tafi messenges dinsa wato sakon kar ta kwana ta duba bata ga wani abun ba, ta fito ta shiga WhatsApp dinsa, bayan chat biyu da aka masa dayan na group dinsu na makaranta dayan kuma na abokinsa na ukun ne na Emily mai dauke da kyakkyawan hotonta. Kai tsaye ta tafi kan dp Emily tana kallon yadda Allah ya tsara kyakkyawar halittar kyaun a fuskarta, a take hankalinta ya tashi. Sabon chat ne da aka yi shi da number ta da be yi saving ba, sai da ta karanta sakon da ta turo masa ta karanta wanda ya aika mata sannan ta sauko daga kan gadon ta zauna a kasa hannunta daya a kanta. Miyesa mijinta zai shimfidawa wata mace kalaman ya damu da ita yana son sanin rayuwarta har haka? Watan ma kuma kyakkyawar kamar Emily. Bata san lokacin da ta jefar da wayar ba ta kwala wani uban ihu zuciyarta da mararta suka hau murdawa lokaci daya. ”Wayyo Wayyo...wayyo... Zuciyata... Marata... Bayana... Na shiga uku zan mutu” Aliyu be gama daure bathrobe din jikinsa ya fito da sauri daga bandakin cikin tashin hankali ya rikata. “Meya faru?” Ta rike mararta tana kallonsa son take ta yi kuka ko ta yi masa magana amman azabar ciwon marar da take ji ta hanata aikata hakan. Jini ya fara yi mata zuba da sauri Aliyu ya saketa ya saka tufafi ya saka mata hijab ya dauketa ya fice da ita daga dakin. TURHAN POV. Ya dora hannunsa yana karon addireshi da kuma sunan mutanen da suka karbi Emily a wacan lokacin. “Amman kana da tabbacin idan muka je zamu same su a gurin” Turhan ya tambaya da hausa sai Faruk ya fadawa mutanen da yaren Yarba. "Ban sani ba, amman tun da har sun taba zama a gurin ko da baka same su ba zaka samu wani bayani a kan inda suka koma da zama ai, ni na gama aikina sai ka salleme ni yanzu” "Emi ko mọ, ṣugbọn niwon igba ti wọn ti gbe ni aaye tẹlẹ, paapaa ti o ko ba ri wọn, iwọ kii yoo ni alaye eyikeyi lori ibi ti wọn gbe lọ ati gbe. Mo ti pari iṣẹ mi, nitorina o le fi mi silẹ ni bayi." Yadda ya bukata haka aka yi, Turhan ya biya shi 20k yayi copy din files din ya maida masa da original. Turhan be yarda sun kara minti talatin a gidan ba ganin sun samu abun da suke nema suka kama hanyar address din da ya ba su, sai kuma suka yi rashin sa'a mutanen sun tashi daga gidan sai yan'uwansu suka tarar, a nan ma addireshin sabon gidan da masu gidan suka koma Turhan ya karba, sannan suka kama hanyar Ikorodu daya daga cikin unguwanin da suke da nisa sosai a birnin Lagos. Sun isa da yamma sosai, suka buga kofar gidan mai gadin ya leko ya tambaya su waye su. "A wa lati okere lati ri oluwa ile." Faruk ya fada musu da Yoruba cewar mun zo ne daga nesa muna son gani mai gidan. "Ya sunan mai gidan?” Mai gadin ya tambaya, Faruk ya duba takardar copy dake hannunsu. “Mr Chibuike Adanna” “okay ku jira ina zuwa” Ya shiga cikin gidan babu jimawa ya fito yana tambayar daga ina suke. “Arewa“ Faruk ya amsa masa, babu jimawa aka musu izinin shiga cikin gidan aka kaisu falon matar gidan kasancewar mai gidan baya kusa a lokacin. ________________ Maganar gaskiya Kameela fa tana da gaskiya akan mijinta 🤭 Me kuke hangowa idan Turnan ya samu haduwa da Emily? [4/20, 10:01 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣4️⃣ Dogon numfashi taja ta sauke ta matsa baya ta nufi kujerar dake dakin ta zauna. Ya bita da kallo for few seconds. “Kina bukatar wani abu a yanzu?” Ta girgiza kai alamar aa. Ya gyara tsayuwarsa. “Baki bukatar yin aiki saboda ki gina kanki, baki bukatar tara kudi saboda ki gudu ki rayuwa a wani gurin dabam, daga lokacin da na baki gata ba zaki guje min ba, duk inda zaki je, duk iya gudun da zaki yi kina a cikin duniyata ne, ya kamata ki natsu karki jawa mutanen da suke kusantar kusa da ke mutuwa, bana sharing what ever is mine nawa ne har abada so you're mine” Yana maganar zuciyarta na bugawa da karfi, hausawa suka ce idan babu rame me ya kawo maganar rame, ta san Vito yana kishinta, amman zancen ta daina kokarin gina kanta a ina ya ji wannan? Har ya juyo sai kuma ya juyo ya kalleta. “Wannan mutumen da ya zo yau kin san cewa musulmi ne?” “Na sani” Ta amsa tana hade yawu. “Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da musulmi, kuma baki da alaka da kowa” Ya juya ya fice ba tare da ya jiran amsarta ba, is like umarni yake bata, ya saba hanata hukda da kowa ciki har da kawaye be yarda da kusanci kowa haka ma baya yarda wasu su kusance ta. Ya mike tsaye ta nufi windows din dakinta tana kallon waje ta saka hannunta a baki tana cizon akaifarta, ita kam haka zata yi ta zama karkashin kulawar mazan dake da son zuciya? Kowane burinsa ta rayu a yadda shi yake so ba yadda ita take so, sai yaushe zata samu yancin kanta. Ficewa ta yi daga dakin ta sauko falo sai ta samu Fatima zaune tana zane. “Kin yi magana da Uncle Vito” “Ba Uncle dina ba ne, bana son shi” "Kin yi magana da shi?” " Eh na fada masa, zaki yi aiki ki samu kudi zaki gina mana gida zamu koma can mu bar masa komai nasa” Emily ta rufa ta fada. “Wannan ai sirrinmu ne miyasa zaki fada masa?” “Saboda na tsane shi” “Toh miye amfanin abun da kika yi yanzu? Ya ssn manufata kina tunanin zai zuba min ido ne? Fatima me yasa kike da surutu ne? Kin lalata komai” Emily ta zauna dafe da kai tana nadamar fadawa Fatima da ta yi tun farko. “I hateeeeeee youuuuu” Fatima ta fada cikin tsiwa da fusata. Emily ta dago ta kalleta cike da takaici. “Idan baki tsane ni ba ai baki cika jinin Turhan ba” Ta mike tsaye a fusace ta fice daga falon, dakinta ta sake komawa ta shiga bandaki da nufin wanka amman ta kasa aiwatar da komai sai kuka. Kuka ta yi sosai mai isarta sannan ta fito ta shirya cikin wasu riga da wando ta dauki wayarta da keys ta fice daga dakin. Ta kai hannu zata bude kofar falon Fatima ta yi mata tambayar da bata yi zaton ta tsinci wani abu a maganar dazun ba. “Waye Turhan Momy?” “Abokina ne“ Ta amsa mata kai sannan ta bude kofar ta fice daga falon. A mota ma sai da ta yi da gaske sannan ta iya hana kanta kuka, bata tafi asibitin kai tsaye ba sai da ta fara shiga super market ta yi ma London siyayya abubuwan kwadayi da na wasa ta musu transfer sannan ta nufi asibitin. Sanin waye danta da kuma halinsa ya saka ta guzarin da ya rage mata ya tafi. Ta samu minti talatin zaune a motar sannan ta bude ta fito ta dauki kayan da ta siyo masa ta rufe motar ta nufi cikin asibitin. Kamin ta karasa ta inda zata karya kwanar da ward din London yake ta hango Aliyu tsaye yana waya, tun da ta sauke idonta kasa bata sake kallonsa ba har ta isa gurin da yake tsaye, ya sauke wayar dake kunnensa ya kalleta kadan ya dauke ido domin tsare mace da ido wanda ba muharamararsa ba halinsa ba ne. “Me kake so? Miyasa kake bibiyata? Baka lura da irin mutumen da nake tare da shi ba?” “Be tsorata ni ba, be kuma burge ni ba” “Yana isa sanin komai nake aikawata, kuma ko'ina akwai mutanensa, shin baka yi mamakin yadda Williams ya baka address dina ba? Bayan kuma be taba zuwa gidan ba? Ki ba musulma bace bani da wata alaka da kai” Be sake magana ba yayi gaba ya barta a gurin tsaye juyawa ta yi ta bi bayansa da kallo har ta daina hango shi, sai kuma ta ji babu dadi, a zatonta ta tsorata shi ne. Dip sakon kar ta kwana ya shigo wayarta. “Ba halina bane tsayuwa da mata, balle kuma wanda addininmu ba daya ba, a duk lokacin da kika shirya zaki iya dawowa aiki zamu yi magana a can” Ta maida wayar aljihu sannan ta shiga ward din, tsayawa ta yi jikin kofar ta daidaita fuskarta ta cusawa kanta murmushi da farincikin dole sannan ta tura kofar da shiga. “Hello Big Guy” "Dariya yake amman yana ganinta sai ya hade rai ya juya baya daga kan gadon da yake zaune” “Har yanzu fushi kake da ni London?” “Sannu da zuwa” Chidimma ta fada, ta mike tsaye London ya rike hannunta alamar baya son ta tashi. A haka dai Emily ta danne zuciyarta ta karasa kusa da shi ta gefen da fuskarta take ta leke shi da murmushi a fuskarta. “My Handsome Guy...” Aiko yace me zai mata ba ihu ba, yana ihu yana matsawa nesa da ita kai kace be santa ba ne, ko ayi zaton sace shi zata yi. A gurin ta watsar da kayan dake hannunta cikin tsawa da fara magana. “Kullum damuwata akan yarana ne, tun ina karami ban san wani wanda ya damu da matsalata ba, ban san wani wanda ya damu da farincikina ba, kowa da na gama masa amfabi jefar da ni yake, guduna yake yanzu kuma ta kai har ga Yayana? To ka zauna da wanda kake so” Ta fice daga dakin a fusace. Chidimma taja shi jikinta ta rumgume jikinsa sai rawa yake domin ba kasafai take masa fada ko tsawa ba. “Momy bata son London, Momy ta yi fushi ta tafi ta gurin Fatima, Fatima kawai Momy take so, bata son London, ta gaji da London ta tsane shi” Tana masa maganar tana shafa bayansa. “Bata son yayi wasa da kowa, amman Chidimma tana son London tana barinsa yayi wasa da ruwa tana fita da shi yawa” London ya bata rai sosai ya labe a jikinta kamar zai yi kuka, sauka ta yi daga kan gadon ta duka kasa. “Hau bayana zamu yi doki” Da sauri ya hau yana dariya domin yana son kalar wasar da take masa. TURHAN POV. Sai da Faruk ya gama yi mata bayanin dalilinsu na zuwa gidan da turanci, domin Turhan baya jin turanci sai larabcin Sudan sai kuma hausar da ta kasance yaren mahaifiyarsa. Matar ta yi murmushi ya gyara zaman kujerar da ta yi mata kadan kasancewar kujerar one seater, ita kuma mace ce mai jiki sosai ba kadan ba. “Bani da wata alaka da Emily a yanzu, tana raye ko a mace ba matsala ta bace, ban kuma damu na san kowane irin hali take ciki ba, mu dai mun daukota daga gidan marayu ne da nufin bata kyakkyawar rayuwa da gata, sai gashi ta watsa mana kasa a ido ta gudu ta bi saurayinta, idan ma wani laifin ta yi muku ko to ku tafi can wani gurin ku nemata, bana da alaka da ita a yanzu” “Amman baki san wata hanyar da zamu iya ganinta ba? Ko jin labarinta? A lokacin da ta bar nan kina da labarin inda ta koma da zama” “Ban sani ba” Ta mike tsaye ta fice ta bar musu falon, Faruk ya fadawa Turhan abun da ta fada, sai ya tabe baki yana magana da kakkausar murya. “Butulu ce ma shiyasa ba zata ga daidai ba a rayuwarta, gashi nan ta zo ta shiga tsakanina da mahaifiyata, an kai karshen ba zan sake nemanta a ko'ina ba yanzu” A tare suka fito da Faruk suka shiga mota, kamin su isa masaukinsu Turhan ya kira mahaifiyarsa a waya, sai da yayi mata kira biyu sannan ta daga wayar. “Hello Ammy” “Kuna lafiya?” “Lafiya kalau, Ammy na yi iya yadda zan iya, na yi neman yarinyar nan har na gaji ban samu inda take ba, macen da ta rike ta ma tace bata da labarin inda take a yanzu, ban san ya zan yi ba Ammy” “Ban cilasta maka nemanta ba Turhan kai ka cilastawa kanka” “Amman Ammy fushi kike yi da ni fa, idan ban samu yarinyar nan ba ba zan samu yadda nake so a gurinki ba” “Na dade da yafe maka, kuma bana fushi da kai, iyakar abun da na sani shi ne, Aisha ta tafi da farinciki, ta tafi ta bar min wani tabo da na kasa kankare shi a zuciyata, a duk lokacin da na kalleka sai na ga wannan abun a tare da kai, a dawo lafiya Allah ya tsare hanya” Ta aje wayar. Turhan ya ji kamar ya buga kansa da motar. “Allah ya kara tsine miki albarka Emily mushirikar banza, yadda kika jefa rayuwata a matsala kika raba ni da mahaifiyata Allah ya hana farinciki kusantarki” Ya dafe kansa ya rufe ido, a yanzu kam ba shi wata babbar makiyiya irin Emily. Macijiyace yarinyar nan kawai rabar mutane take tana cutarsu haka zuciyarsa take raya masa. The fallowing day yayi sallama da Faruk yayi masa alheri sannan ya kamo hanyar dawowa Kaduna. Yana sauka Airport ya sanarwa mahaifiyarsa babu bata lokaci da aika masa da direba ya dauko shi zuwa gida. Ko da ya iso ya samu an shirya masa abinci mai kyau a dinning, amman be kula komai ba saboda hankalinsa yana gurin mahaifiyarsa, dakinta ya shiga sai ya zame ta zaune tare da Jawahir suna dariya da alama hira suke, sai dai shigowarsa ya saka Ammy sauya dariyarta zuwa murmushin da ba kasafai take masa ba. “Sannu da zuwa” Jawahir ta fada sannan ta tashi ta fice daga dakin. Cikin wata irin tafiya ta kaisaita daya saba yi ya karasa gaban mahaifiyarsa ya zube kasa ya zauna. “Barka da yamma Ammy” “Barka Labarabe” Ya dan dago Kadan ya kalleta ya maida kansa kasa. “Ammy ki yi hakuri da abubuwa da suka faru, na yi ina yina a yanzu amman ban samu ganin Aysha ba” “Allah yasa hakan shi ya fi alheri” “Ameen” Ammy ta mike tsaye da nufin bar masa dakin sai ya sha gabanta da fadin. “Na yi zaton komai zai wuce idan na dawo, Allah dai ya gani na iya yadda zan iya akan yarinyar nan abu ya gagara, Ammy ki daina bari ana zuga ki kina juya min baya” Jin haka ya saka Ammy ta dawo ta zauna. “Su waye suke zuga ni?” “Jawahir mana Ammy, ita take tare da ke kullum wasu abubuwan ita zata saka ki yi min, saboda bata san zafinki ba, ba ke kika haifeta ba” “Kai da kasan zafina ai gashi nan na aura maka yar mutane ka watsa min kasa a ido” “Dan kuskure kadan ne na aikata Ammy, dan haka” Ya nuna kan akaifarsa. “Amman gaba daya kin canja min, kuma iyakar biyayya ni na san na miki, bana son yarinyar nan kika ce na aureta na daure a haka na aureta, addininmu ba daya ba, na san a lokacin da na aureta ta musulunta amman yawanci ai musuluntar karya suke yi saboda su yi makirci, kaskanci ne a gurin namiji irina, jinin sarauta kuma jinin larabawa ya auri mace irin Emily, sam bata cikin irin matan da nake so, ya kamata ki duba min Ammy” Fuskar tausayi ta bayyana a fuskar Ammy. “Baka fada min baka sonta ba a lokacin da na hada aurenku ba ba zan cilasta maka ba, Allah kadai ya san kalar azabar data sha a hannunka da masarautarku, baiwar Allah” Ya dago yana kallon Ammy cike da mamaki, shi a tunaninsa idan na fada mata duk wannan zata tausaya masa ne, madadin haka sai ta kara jin tausayin Emily din ma. “Haka ne, kaskanci ne auren wanda ba bata tashi a addinin musulunci ba, kuma wanda ba yarenka ba, ba yar sarauta ba ina mai baka hakuri akan hakan Dan sarauta” Ta mike tsaye ta fice daga dakin. “Da ace zan samu damar yin ido biyu da Emily a yanzu, tabbas zan bata hakurin saboda Ammy, amman bayan kwana biyu sai na hada ita da bokanta na kashesu, yarinya kamar mayya gaba daya ta tafi da zuciyar Ammy, ita wacan katuwar kafirar maganin be kamata ba sai Ammy, ni kadai ta haifa a duniya amman yanzu ta tsane ni saboda wata shegiyar yarinya.. عار عليك يا إميلي, ”عار عليك Yama fadar yana wargar da hannu, be san kaskanci da wulakanci ba sai da Emily ta duro gidansu, tashi yayi ya fice daga dakin ya shiga dayan dakin yayi waya da matarsa da mahaifinsa sannan yayi wanka ya fito falon. “Tun kamin na yi aure, ina addu'ar idan na yi aure Allah ya bani ya mace, sai gashi kuma da na yi auren na haifi namiji, sai ya zama ba zan sake haihuwa ba, a lokacin da Aysha ta zo gidan nan sai na ji kamar addu'ar da nake yi ce a can baya Allah ya karba min ya ba ni ya mace ta wani bangaren da ban yi zato ba, yarinyar nan ta tsaya min a rai” Labarin da ya sauko ya samu Ammy na bawa Jawahir kenan, Jawahir din kawai ya kalla yana ayyana munafurcinta a zuciyarsa ya fice ba tare da ya taba abincin da aka jera masa a dinning ba. Bayan fitarsa Jawahir ta kalle Ammy. “Dan Allah Ammy ki yi hakuri ki cire Aysha a zuciyarki, ki kaddara ta mutu, ki shirya da Ya Turhan ku dawo kamar yadda kuka a da, Wallahi tausayi yake ba ni” Ammy ta kalleta tana murmushi. “Baki san waye mahaifin Turhan ba shiyasa yake baki tausayi, larabawa suna da zuciya mai tauri, shi kuma ai jinin mahaifinsa, nonon ma na larabawa ya sha ba nawa ba, kar yi mamaki idan aka ce miki ya sake aikata kuskure bayan wannan” Jawahir ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai cike da tausayi. ALIYU POV. “Tun jiya da aka kawo ki asibitin nan kike fushi da ni, ko dan rantsuwa da alkawarin da na daukar miki ai ya kamata ace kin yarda da ni” “Cikin alkawarin da rantsuwar ai na ga chat dinku” “Ke yanzu ko a mafarki aka ce miki ina son Emily zaki yarda” Ta dube shi kamar zata yi kuka. “Har ka rike sunanta ma” “Turhan fa ya auri yarinyar nan kuma har sun haihu da ita, Turhan kuma abokina ne mahaifiyarsa kamar uwa take a gareni, taya zan iya soyayya da ita ma balle har nace zan aureta? Kuma addininmu ba daya ba, ba abun da kike tunani ba ne” “Yanzu dai gashi nan ai ka janyo min nakuda Edd na be cika ba amman gashi nan nakuda ta same ni, kuma gashi sun ce idan ban haihu da kaina ba za su min CS” Ya rumgumeta. “Zaki haihu da kanki lafiya In Shaa Allahu” “Me yasa ba zaka fadawa Turhan gaskiya ba, bayan kasan nemanta yake idan har baka da wata manufa akanta? Ka san yadda Turhan yake son haihuwa amman baka fada masa yana da ya ba, idan baka da wata mummunar manufa akansa miyasa ka yi haka?” Tana maganar tana cige baki tana numfashi da karfi. “Idan Allah yasa kin haihu lafiya wan warware miki komai” “Allah dai yasa na haihu lafiya, Allah yasa na tashi Wallahi babu wanda zata aurar min miji Wallahi Allah kuwa na rantse” Shi dai kallonta kawai yake be yi zaton tsananin kishinta ya kai haka ba sai yau. “Ummi bata iso ba har yanzu?” “Ta iso kin san ai ta fi kusa, ta sauka gida ne sai ta yi wanka zata zo, su Hajiya ma suna hanya” “Ka min addu'a Aliyu” “Ina ta yi” Ya shafa kanta yana ta karanta mata addu'o'i. Misalin karfe goma sha daya na safe iyayen Kameela suka iso asibitin, a lokacin nakudar ta taso mata gadangadan ya fito waje sai addu'a yake yana kai da kawo. Da waya ya kwatanta musu gurin da yake har suka iso, kana kallon mahaifiyarta zaka fahimci tana cikin tashin hankali haka ma yayarta. Cikin ladani ya gaishe su kamar yadda ya saba mahaifiyar ta amsa rai a hade domin Kameela ta labarta mata komai ta waya. “Hajiya ai da kun wuce can gidan kun dan huta tun da ni ina nan” “Aa kara dai zamana kusa da yata, tsayuwarka a nan wani amfani yayi mata, ba kai ne sanadin duk wannan ba” A take Anty Shafa wacce ta kasance yayar Kameela ta karbe zancen Hajiya ta dora da nata. “Gaskiya Aliyu baka kyauta ba, kasan matarka tana da ciki be kamata kana yin wasu abubuwan ba” Aliyu ya kalli Anty Shafa da duba na tsanaki. “Me tace na yi.?” Ta yi shiru bata ce komai ba, sai dauke kai da tayi. Ya ciro wayarsa yana amsa kiran mahaifiyarsa. “Okay Ummi bari na zo na dauke ki” Ya sauke wayar, ya kalli sarakuwarsa. “Zan je na dauko Ummi daga gida yanzu” “Toh” Ta amsa masa a takaice cikin bacin rai. Aliyu ya saka kai ya fice cikin rashin jindadi, daman ya san za a rina domin Kameela bata da sirri ko kadan mu'amalar auratayya ma sai ta fadawa kawaye ta, be yi mamakin dan ta fadawa iyayenta sanadin nakudarta ba, wannan halin nata na rashin sirri yana bata masa rai sosai. Ko da ya isa ya samu Ummi a harabar tana jiran isowarsa. “Ummi madadin ki zauna a ciki kika fito waje” “Idan ka iso ai zaka iya dadewa shiyasa na tsaya jiranka a nan, mu tafi” Kamin ta shiga motar ya fito da sauri ya zagayo ya rumgume ta. “I miss you Ummiiiiii” “Kai wai baka san ka girma ba, baka jin kunyata” “You're my best friend my first love” Ya je zai sumbance ya ta tureshi ta bude motar ta shiga, dariya yayi ya koma motar yaja suka fice daga gidan, suna tafi suna hira har suka isa asibitin ya zagaya ya bude mata ta fito ya suka jera zuwa gurin da ya bar su Hajiya dazun. Ummi na hango Hajiya da Anty Shafa ta kalli Aliyu. "Kasan ka fadawa iyayenta sun zo to ni miye na fada min na zo?” “Ke ma ai mahaifiyarta ce” “Idan ba mahaifiyarta a kusa ba” Ummi ta dan sham kamshi domin ko kadan bata son raini. Anty Shafa ce ta fara gaishe da Ummi sannan Hajiya ma ta miko mata gaisuwa. “Lafiya kalau” Daga Hajiya har Ummi babu wanda yacewa wani an iso lafiya. "Allah dai yasa ta haihu da kanta, idan ba ita ba haushe zaka dauki halin da namiji ka saka a zuciya” Cewar Anty Shafa. Ummi ta yi kasa da ido tana saurarenta, kamin ta dago ta kalleta tana murmushi. “Shafa ya yaran? Ya Step Mom dinku? Har yanzu dai shiru kin ki kawo mana kati?” “Ina nan ina lalabe Ummi kin san mazan sai a hankali, yara suna lafiya” Ta amsa cike da gatse. “Haka ne Allah ya kawo na gari” “Ameen” Ta amsa. Aliyu ya ciro wayarsa dake ringing ya fice daga gurin, Ummi kuma ta nemi guri ta zauna Hajiya nata safa da marwa tana daga hannu tare da rokon Allah ya saukar da Kameela lafiya. “Ameen ya rabbi, idan ba sakarci irin na Kameela ba, yaushe namiji zai maka alkawarin ba zai kara aure ba ka yarda, gashi nan ta jawa kanta nakudar dole” Hajiya ta juyo ta kalleta. “To miye laifinta? Allah dai ya bude mana idonta lafiya?” “Ameen” Ummi dai bata ce komai ba sai saurarensu take, ta san kuma saboda ita ake yi dan ta ji. After like one hour Kameela ta sauka lafiya sai dai abun da ta haifa be zo da rai ba. Hakan kuma be hana iyayenta mijinta da surukar murna ba domin ita dai ta haihu lafiya bayan ta sha wahalar nakuda. Sai da Aliyu ya rada ma yaron suna sannan aka yi masa sallah aka binne shi a makabarta musulmi dake garin Part-harcour. Ko kadan Aliyu be jidadin yadda yaron ya zo babu rai ba, sai dai babu yadda xa'ayi da hukuncin Allah sai hakuri, ganin yanayinsa ya saka Ummi ta hade maganganunbda take da su a zuciyarta ta daga masa kafa. [4/22, 9:24 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣5️⃣ Ta hado tea ya kawo ma Ummi. “Ni ba irinka bace, me zan yi da tea yanzu da yamma" Murmushi yayi ya zauna yana updating status dinsa domin sanar da duniya matarsa ta haihu amman dan be zo da rai ba. Bayan ya gama ya aje wayar ya kai hannu zai dauki tea kiran Kameela ya shigo wayarsa, fasa shan tea yayi ya dauki wayar. “Hello...” "Kana ina“ “Ina gida“ “Tare da wa?" Ya kalli Ummi sannan ya amsa mata "Tare da Ummi" "Na ji Hajiya tana maganar wai zata tafi da ni gida gobe idan an sallame ni” “Kamar al'ada ce ko mace ta koma gida idan ta yi haihuwar fari” "Bana son na barka, ni bana son tafiya, za a iya min komai a nan mana" "Haka ne amman idan ta nuna tana son tafiya dake ba zamu iya hanawa ba” “Ina son idan ta maka maganar tafiyata kace mata aa kana son na zauna a nan din" Yayi shiru be ce mata komai ba jin hakan ya saka ta kashe wayarta, domin ita ma ta san mijinta ba kasafai take saka shi abun da be yi niya ba. "Kameela ce?“ “Bata son tafiya gida, ni kuma ba zan iya jayayya da iyayenta ba, bana son abun da zai kawo mana rashin jituwa musamman da Hajiya“ "Rashin jituwa na nawa kuma? Bayan wanda aka sha kamin auren?” “wacan ai ya wuce Ummi, kuma tun daga lokacin sun san ni ba kanwar lasa ba ne, Aliyu kike ji fa Ummi” Ya fada yana murmushi, Ummi ta tabe baki. “Aliyu soyayya? Romeo baban kauna, sharukan din masoya? Mai alkawarin da ba zai iya cikawa ba” Ya kalleta da dan mamaki still yana murmushi. “Ummi ina kika samo duk wannan kuma?” “Baka yi alkawarin cewar ba zaka kara ma Kameela abokiyar zama ba?” Ya rausayar da kai. “Ta fada miki ne?" “Aa ai kasan iyayenta ba yan dattako ba ne, sun fada dan na ji kuma na ji" Ya shafa kansa. "Idan baka yi hankali ba, kishin Kameela sai ya halakata ya jefaka a matsala, domin zafin kishin yayi yawa, madadin kai kuma ka nuna mata abun da take yi kuskure ne sai kawai ka shimfida mata tabarma ta hau, akan wane dalili zaka mata alkawarin ka haramtawa kanka abun da Allah da kansa ya hallata maka? Kai da malami ne Aliyu, ban yi tsammanin wannan daga gareka ba” “Ummi baki fahimta ba ne” Ummi ta hade rai. “Toh fahimtar da ni“ Ya gyara zamansa ya aje wayarsa gafe. “Ummi ke kika haife ni, kin san halina ciki da waje, tun kamin na yi aure ke kin sani, bana da ra'ayin auren mace sama da daya, Allah ya hallata mana auren mace mace sama da daya ne idan zamu iya adalci, shi kuma adalci wani abu ne mai nauyi sai dai mu kwatanta, ni kuma bana son na aikata wani abun da zan tashi a gaban Allah wani dan'adam ya tuhume ni da shi, kuma Ummi kin san iya gwagwar mayar da muka sha kamin iyayenta su yarda su ba ni aurenta” “Saboda an yi fadi tashi sai ya saka ka zo ka yi mata alkawarin da ni na san wata rana sai ka karya shi, mata na mahaifinta yake aure bayan Hajiya? Ina ce matansa uku, ai ta tashi ta ga ubanta da mata biyu ko bayan mahaifiyarta, sai kai dan ta raina ka zata saka ka yi mata alkawarin ba zaka kara aure ba, yan'uwanta ma saboda basu da kunya za su nemi fada min magana” "Wata kila yanayin abubuwan da suke faruwa gidan su na kishin ne ya saka take tsoron kishiya, amman me Hajiya ta fada miki? Sun miki wata maganar marar dadi ne?" Ya tambaya yana jiran amsarta, karamin aikinsa ne ya daga waya ya kira Anty Shafa da take yayarta ya ci mata mutunci akan Ummi, bayan kuma abun be kai ya kawo ba. “Wannan maganar suka fada mana, ni ba zance ka kara aure ba, domin Kameela bata min komai ba ta rike ni kamar uwa, family ta ne dai ba su da mutunci shiyasa ake son idan za'ayi aure a nemo yar gidan mutunci, ka karanta ka gani amman duk ka tsallake wannan ka aurota” “Kameela tana da tarbiya Ummi, tana da biyayya daliba tace fa, tana da ilmi daidai gwargwado, ita dai bar ta ga rashin sirrin sai kuma zafin kishi, kuma duk mace ba zata rasa wannan ba, kuma ni ba cilasta ni  na yi mata alkawari ba, na mata alkawarin ne da yakinin zan cika kuma zan iya, saboda ina son kwanciyar hankalinta da farincikinta, kamar yadda Daddy na yake son matarsa” Ummi ta watsa masa harara. “Dan iskan yaro, ai ni ban hana Daddynku aure ba, kuma ban ce yayi min alkawarin ba zai kara aure ba, kawai be yi niya ba ne, waya isa ya hana Daddynku abun da yayi niya?” “Tohm Daddyna zan gado“ “gamu gani ai, farin tuwon nan dai cikin bakar tukuyar can ya fito, muna nan da kai wata rana sai ka zo min jikinka na rawa kace zaka kara aure, saboda iyayenta ba yan mutunci ba ne, kuma ba su so aurenka da ita tun farko ba, na lura matukar ba kashe auren nan suka yi ba hankalinsu ba zai kwanta ba” “Haba Ummi ke ma kin san idan na auri mace ta auru Wallahi, aje dai sama a dawo a shiga wuta da ruwa a mutu ayi rai amman ba zan sake mace ba, noooo saki be ma cikin abun da nake magana, ni dai ina son matata, matata kuma tana so na to duk abin da zai biyo baya daman dole mu yi hakuri da shi” Ummi ta tabe baki. "Allah ya baku zaman lafiya" "Ameen, Ummi ke ma yanzu dai kamar Kameela ta fita ranki" "Aa ina sonta, ai tana mutunta yan'uwanka kuma tana sonka tana girmamani, ni kawai familynta ne bana so, abubuwan da suka yi ta yi kamin aurenku har yanzu ban manta ba“ Yayi murmushi kawai be sake cewa komai ba, Ummi ta dauki wayarta tana amsa kira, shi kuma ya shiga amsa sakwannin dake shigo masa. Sai dare Ummi ta koma asibitin tare da Aliyu, Kameela ta tarbe ta da hannu biyu Ummi ta zauna kusa da ita tana mata sannu. Sai kusan goma Ummi ta yi mata sallama ta fita Aliyu ya mike tsaye. "Zan je na kaita gida na dawo, gobe zata wuce jirgin Safe zata bi" "Okay sai ka dawo" Ya matsa kusa da ita ya sumbance. "Sai wani shinning kike kamar ba haihuwa kika yi ba, kumburin nan ma ya miki kyau" Ta yi murmushi. "Ba zaka yi ma Hajiya magana ba? Ina jin tana maganar tafiyar fa, gashi sunce gobe za su sallame ni“ "Idan an tafi dake zan zo na same ki" Murda kofar dakin da aka yi ne ya saka shi aurin janye hannunsa a jikinta ya matsa baya. Anty Shafa ce ta shigo tana hamma. “Yauwa Aliyu Hajiya tace ka hadowa Kameela kayanta a zo da su nan gobe za su wuce idan Allah ya kaimu" Ya kalli Anty Shafa fuska ba yabo ba fallasa, kamin ya juya ya kalli matarsa. "Me da me zan dauko miki my love" Ta dan bata fuska kamar zata yi kuka, ita ganin take idan bata kusa da shi zai kalli wasu matan ne, kuma kamar ta bashi damar magana da Emily ne. "Ba sai ka dauko komai ba, zan siya a can” Yayi murmushi kawai ya fice. Sai da ya fita sannan Anty Shafa ta zauna tana fadin. “Abun dai be yi ba, kin haihu ace uwarsa wai zata koma gobe gobe kuma jirgin safe zata bi, kamar dai bata sonki, shi kansa ban ga yana wani daukinki ba” Kameela ta hade rai tana magana a shagwabe. “Kin ga Anty Shafa ki daina zarga min uwar miji, kuma ni mijina yana so na na sani” “Gaki ga shi ai indai namiji ne, har zai miki alkawari ki yarda, ba gashi kin janyowa kanki ba har kin rasa danki? Farawa da iyawa kenan daga chat da mata sai zancen kara aure, muna nan dake sai Aliyu ya saka ki kuka da bakinciki, ba namiji ba, can talkaminmu suka tsinke" Kameela dai ta yi shiru bata ce komai ba, sai dai ranta babu dadin tafiyar da zata yi da kuma kalaman da Anty Shafa take fada akan mijinta. Aliyu be dawo dakin hannu sake ba sai da kayan kwalama da kuma akwati daya babba ya saka mata abubuwan da ya san za su mata amfani, ko ba su fada masa ba ya fahimci ba su son tafiya gidansa ne shiyasa suka ce ya hado mata kayan, madadin ita yayarta ta tafi ta hado mata kayan, shiyasa Hajiya take son da am sallameta ta wuce da ita daga nan ba tare da sun tafi gidan ba. Shi kuma be shirya wulakanta kansa ba, ko neman rigima da su ba shiyasa, be musa musu ba ko ya nuna musu damuwarsa akan yunkurinsu. Da kansa ya hada nata wani tea mai kauri ya bude naman da ya zo mata da shi har tiriri yake yana saka mata a baki. “Yanzu ya aka yi da Emily din? Kuma taya aka yi ma ka gane ta?” Anya zai iya fada mata a gurin da yake aiki take aiki? No.. Ya tambayi kansa sai kuma ya bawa kansa amsa. “Hotonta ai ya bada yanayi da kamaninta, kuma kana ganin yarta zaka san yar Turhan ce domin fuskarsa ce” “Meyasa ba zaka fada masa ba, bayan kasan yadda yake ta nemanta” Ya kai mata tea a baki. "Ita ta bukaci kar na yi haka“ “Saboda me?” “Wata kila tana da dalinlinta“ “Dan Allah ka fita sabgarta ka cire kanka a tsakaninsu, ba a shiga tsakanin mata da miji ni dama ace be saketa ba abun zai fi min sauki" "Saboda ke zaki hada aurensu? Dan Allah masoyiyata ki bari mu rabu tafiya, karki saka kanki a wata damuwa dan Allah, ke kin san wanene, kuma yaushe na ce miki ya sake ta." "Au be sake ta ba? Au to da sauki ai" Yayi murmushi yana kara jinjina lamarin Kameela, shi dai ya fadi haka ne saboda hankalinta ya kwanta. A asibitin ya kwana tare da matarsa ya kwantar mata da hankali kuma ya lalabata akam tafiyar da Hajiya za ta yi da ita. EMILY POV. Driving kawai yake tana kalle kalle bata shirya komawa gida, kuma bata san gurin da zata je ba, haka ta yi ta yawo kamar zata zagaye garin kamin ta faka motarta kusa da wasu dakuna da suke kamar quarters. Bude gambun motar tayi ta fito daga cikin motar ta nufi wani katon dutse da yake gurin ta zauna. Kallo daya zaka yi mata ka fahimci bata cikin farinciki, domin fuskarta a fili take nuna damuwar dake zuciyarta. Rabo ido take amman zuciyarta da hankalinta suna wani gurin na dabam. “Me kike a nan?” Maganar ta ji ne daga gefenta ya saka ta juyo gaba daya sai ta yi arba da matar da ya kusan kade Fatima, kuma ita dai matar da ta gani asibiti ta yi mata magana. “idan kina son na tashi na baki guri, zaki iya cewa na tashi na bar unguwar ko gurin, ba sai kin tambayi mai nake ba, ai zaune kike same ni, zama nake yi” Ta dan yi murmushi ta zauna kusa da Emily. “Baki yi kama da masu zafin rai ba, daga ganin yanayinki na san ranki ne a bace, na hango ki tun daga dakina, karki manta jiya ne ko shekaran jiya ke kika min magana kamin na miki” “Da na yi miki magana yi kika yi kamar baki san ni ba” “Ni ma ranar raina yana bace ne ki yi hakuri, Sunana Tasmia" Ta mika mata hannu, Emily ta kalleta kamin ta mika mata nata hannun. “Aysha Emily” "Nice to meet you Aysha, me kika zo yi unguwar mu?" “A nan kika" "huh" Emily ta daga kafadunta. “Kawai dai ina yawo ne ban san inda zan je ba" "Zaki iya shigowa ciki ki sha ruwa?" Emily ta kalleta for few seconds... "Be kamata na yarda da kowa ba" "Haka aka fada miki?" Cewar Tasmia tana murmushi. "Haka duniya ta koya min" "Da alama duniya ta rike ki a makarantarta ta yi ta zuba miki darussa a ajinta" "Haka ne, na zuba min ilmi kuma na karantu, yanzu yayewarta kawai nake jira“ Emily ta karasa zance idonta na cika da hawaye. “Matsalar miji ce? Ko ta yaya? Ko ta family?” “Ya kamata na yi wata maganar dake?” Emily ta yi maganar a siga tambayar. “Zaki iya yarda da ni, baki ga yadda kaddara take ta hada mu ba? Wata kila tana nufin mu zama kawaye, ko kuma abokan shawara ta wani bangaren, karki damu da banbanci addininmu ba, ko launin fatarmu dukanmu mata ne, da suke dauke da matsala in one way or the other” "Zan fada miki damuwata ne kawai saboda ina bukatar fashe kurjin dake min ciwo, kamar yadda na so na yi a wacan ranar da na yi miki magana, saboda bani da kawar da zan tattauna damuwata da ita, ba ni da uwar da zata ba ni shawara, bani da dan'uwa da zai share hawaye, ba ni da kowa sai ni kadai” Tasmia ta zauna a kusa da ita tana kallonta cike da tausayin ganin yadda hawaye suke kwaranya a idonta. “Kin rasa iyayenki ne?“ "Kin rasa iyayenki ne?“ “Ni ma dai ban sani ba, mutuwa suka yi aka rasa inda za a aje ni sai gidan marayu? Ko kuma dai haihuwata aka yi ta gurbatacciyar hanya aka jefar da ni, su waye iyayena miyasa suka bar ni? Shi ya fi tsaya min a rai, ki kalli fatar jikina haskena yayi yawa, ina da blue eyes, gashin kaina ja, waya biyo mahaifina ko mahaifiyata, ban sani ba” “A ina kika samu kanki bayan kin girma? Su wa suka rike ki?" "Mutanen da ban sani ba, labari ne mai tsawo“ "Toh yanzu wa kike aure? Baki jin dadin zaman gidan mijin ne ko me da har kika tunawa da baya tunatar da ba zata miki amfani ba” Ta share hawayen da suka ki tsaya mata. “Wasu sun yi dacen rayuwa Tasmia, sun san su waye iyayensu, wasu sun yi rayuwa da su, wasu sun san a ina familynsu suke, wasu suna da kawaye, suna da masu kula da su, ni ba ni da kowa yarana ma basa bukata ta a yanzu" Jimmm Tasmia ta yi kamin ta ce. “Yaranki suna bukatar tsawatarwa, gaskiya na lura da tarbiyar yarki sai a hankali, me zai saka ba za ku tattauna da mahaifinta...” Bata karasa ba Emily ta tari numfashinta. “Bana tare da mahaifinta, a yanzu ina zama a karkashin kulawa da ikon wani ne, da baya bari ma rabi kowa, baya barin na yi kawa, banbancin rayuwar baya da ta yanzu kadan ne, har yanzu a cikin kangi nake" Tasmia ta dafa ta. "Miyasa ba zaki yi nesa da shi ba?” "Ba zai bari ba, saboda shi yake ciyar da mu shi yake mana komai ko da kuma na yi kokarin gina kaina ba zai bari ba" Tasmia ta juyo da ita suka fuskanci juna. "Ban san iya hidimar da yake miki ba, amman da alama akwai tsoro da fargaba a zuciyarki, irin tsoron da fargabar da yake samu kowane dan'adan mai rauni har yayi nasarar sauya tunaninsa ya saka shi a cikin wani kogo ya hana shi walwala, daga lokacin da tunaninki yake hango miki rauni a tafiyarki, zuciyarki take raya miki ba zaki iya ba, to ba zaki iya ba ne har abada, a yadda na fahimce ki kin sha wahalar rayuwa kamin yau, idan kuwa haka ne be kamata ace wani ne yake fada miki yadda zaki tafiyar da ita ba, ai babu wanda ya san kalar talkamin da suka dace da kafarki, ina nufin babu wanda yayi tafiyar da kika yi a hanyar rayuwar ki saboda kaddarar kowa dabam, idan babu mai sonki shin ke ba zaki so kanki ba? Kar tsoron sherin wani ya hana ki gina rayuwarki, ki tsaya da kafarki irin tsayin da ba za a iya kallon idonki a fada miki wata maganar ba, ki sakawa ranki zaki iya, ki yarda da kanki Emily, idan baki da kowa to ke ki zamewa kanki kowa mana, ki gina labarinki, ki yi taki duniyar ki cikata da zuri'arki" Tasmia ta karfafa mata guiwa ta zuba mata kalaman da wani be taba tsaya ya tsara mata su a cikin kanta ba, hakan ya tsayar da zubar hawayenta a yanzu tunaninta ya karkata ta inda bata yi zato ba. Karar shigowar sako ne ya sauka a wayarta sai ta sauke kanta kasa tana duba wayar. “Kina ina?” Ta karanta sakon na Vito. Kamin ta dago ta kalli Tasmia dake zuba mata kalamai. “Ki fara mafarkinki daga yanzu, kar kowa ya sake baki tsoro, karki yarda zuciyarki ta fada miki ba zaki iya ba, tsoron cutarwa wasu ta hana ki cika burinki, ita rayuwar duniya ciki take da kalubale babu mai kaiwa karshenta sai wanda ya barta, ke kadai kika girma babu kowa a kusa da ke! To taya zaki bari wani ya milke ke a yanzu? Wani be kamata ya rubuta labarinki ba, ke ya kamata ki aje alkamin da kanki... Ki rufe tawadar sai ki bada damar a karanta...” Ta karasa tana share mata hawayenta tare da yi mata murmushin karfafa guiwa. Emily ta yi murmushi still hawaye a idonta. “Ke ce mutum ta biyu da na gani musulma mai zuciya mai kyau, daga wacan mutumen da ya taimaka min lokacin da zan haifi Fatima sai kuma ke, amman duk sauran daga masu gorin addini sai masu cin amana“ “Haka muke mu musulmai cikin akwai na gari akwai bata gari, kamar dai kowane addini, idan kina son zaman lafiya da kowa da kuma fahimtar rayuwa, ki kalli addinin da mutane suke yi, da kuma abun da ya koyar, ba wai rayuwarsu ba" "Haka ne" Ta amsa tana share hawayenta. "Toh yanzu zaki iya shigowa ki sha ruwa?" Emily ta yi murmushi. “Wata kila wani lokacin" "Shikenan tun da haka kika zaba, amman yanzu zaki saka min number ki zan saka miki tawa, ni da ke mun zama yan'uwa daman ni bani da kawa a nan kawata daya ce kuma sarkin kishi ce saboda mijinta bana son zuwa gidanta, ina zaune a gurin wata yayata, ke kuma daman na taba sauke ki a gidanki, amman asali ni yar Kaduna ce" "Amman ke me ya kawo ki nan" "Bautar kasa" Emily ta daga mata kai alamar gamsuwa, sannan ta saka mata numberta ta karbi nata number. Ta mike tsaye “Zan tafi wata kila yarana suna bukatar gani izuwa yanzu" "Hakan yana da kyau, muje na rakaki" Tamia ta rakata har gurin motarta sannan ta yi mata sallama tana daga mata hannu har ta yi nisa. [4/26, 5:40 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣6️⃣ Yadda ta bar gidan haka ta same shi domin kusan lokaci daya Emily ta shigo gidan tare da Chidimma da London. "Ina kokarin gyara falon ne da gidan ne yanzu sai na dora abinci" Ta fada ganin yadda Emily take kallonta. "Ina London" "Tare muka dawo an sallame shi" Har Emily ta juya sai kuma ta juyo ta kalli Chidimma. "Baki kira ni na daukoku ba?” "Na ga kin fita a cikin fushi ne, shi ma kuma fushi yake da ke, ina gudun bacin ransa ne, shiyasa sai na kira Sir Vito ya kawo mu gida" Emily ta juya ba tare da ya sake cewa komai ba. “Ki yi hakuri da abun da London yake miki, kin san yana dauke ta lalura ne, amman a hankali zai fahimta ya daina kamar yadda yake yi abaya" Har ta ci ta cinye Emily bata sake juyowa ba haka kuma bata sake cewa komai ba ta haura sama ta shiga dakinta sai ta samu Vito zaune a ciki yana kallon kofar data shigo. "Ina kika je?" "Inda nake ra'ayin tafiya" Ta amsa masa rudely, kallonta kawai yake har ta nufi closet dinta ta cire talkamin kafarta. Ta saba fada masa bakar magana but like ya tambaye ta wani abu ta amsa masa da wata maganar dabam. Wayar dake aljihunta ta yi ringing ta ciro wayar ta amsa ba tare da fargabar komai ba. "Kin isa gida lafiya?" "Lafiya kalau, na gode da kulawa" Ta aje wayar a gefen closet din bayan ta amsa. “Da wa kike waya?" "Will you excuse me? Ina son na huta ne" Ya sake dubanta a tsanake kamin ya mike tsaye ya fice daga dakin. Yana fita ta sauke numfashi da karfi ta lumshe ido tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa da karfi. Vito ya sauko yana kallon Fatima dake gabansa kadan tana saukowa, juyowa ta yi tana kallonsa har ya kawo daidai inda take tsaye. “Vito... Kasan waye babana" "Emily bata fada miki baki da mahaifi ba?" "Meyasa ni kadai ce a makarantar mu ba ni da Baba? Kowa a duniyar nan yana da Baba amman ban da ni why? Meyasa sunana yake Fatima Aysha Emily?" Ya rage tsawo ya risina daidai ita. “Saboda ke kadai aka haife ki, you're special girl with bad attitudes" Ya barta a gurin tana binsa da kallo cike da tsana, fasa sauka ta yi ta koma sama ta shiga dakin dan'uwanta. Wanka Emily ta yi ta fito ta shirya cikin short gown ta atamfa ta zauna gaban madubi tana kallon kanta. Maganganun Tasmia suna ta yi mata yawo akai, sai ta ji ina ma ace wani ya fada mata haka tun a baya, ko da yake a yanzu din ma lokaci be kure ba. Ta yi murmushi. "Ina fatan yadda kalamanki da fuskarki suke, haka zuciyarki ma take" Ta fada sai ta bude aljihun madubin dake gabanta ta dauko wani karamin box ta ciro agogon mutumen da ta kasa manta yadda ya taimaki rayuwarta har ta rayu. Ta shafa agogon tana rausayar da kanta. "Ku biyu ne kawai musulmai masu halin kirki, kai ka bar min shigo Tasmia kuma ta bar min kalamai" Ta karasa tana murmushi, sai kuma ta mike tsaye ta nufi jakarta ta saka agogon ciki ta nufi wayarta da sako ya shigo ta duba. "Zaki iya zuwa office a duk lokacin da kika shirya, Office dinki yana nan yana jiranki" "Why? Saboda kai ma ka yi amfani da wannan damar ka shimfida min dokoki ka mulke ni a yadda kake so?" Ta yi jira har ta gaji be dawo mata da amsa ko wani sakon ba. Aje wayar ta yi ta fice daga dakin zuwa dakin da danta yake, wasa ta samu yana yi da Fatima har da dariya sai dai shigowarta ya saka dukansu su biyu yanayinsu ya sauya, Fatima ta dan hade rai, shi kuma ya juya mata baya gaba daya irin yadda yake idan yana fushi baya son kallon fuskar mutane. Ta zauna akan gadon ta kai hannu ta shafa bayansa. "My babu, har yanzu fushi kake da Momy? Why saboda Momy ta jima bata zo ba? Me Momy ta yi ne London har kaka juya mata baya? Momy da take kaunarka? Taka siya maka abun dadi...? Ina kake son mu tafi? Kana son mu yi wasan ruwa?" Duk rarrashin da ta yi masa da kalamai be juyo ba kuma be sauka daga fushin ba, da ta yi kokarin juyo da shi ma sai ya saka mata ihu ya ruda dakin har sai da Chidimma ta bar abun da take ta shigo ta rumgume shi. Tashi ta yi ta fice daga dakin ta sake komawa dakinta, ta kwana da tunani kala kala a ranta ta kulla wannan ta kwance wacan, daga karshe ta bi tsarin da zuciyarta ta dorata ta hau ta hakikance cewar ba zata koma aiki ba, amman zata nemi wani aikin domin cika burin da take da shi. Washe gari ita da kanta ta shiryawa yaranta abun karyawa, ta zubawa Fatima nata a lunch box na London kuma ta bawa Chidimma ta ba shi, ita kuma ta koma ciki ta saka kanana kaya da sneakers ta fito ta shiga kitchen ta dauki water bottle ta zuba swan water sannan ta fito. “Zaki tafi wani gurin ne Ma'am?” "Yes zan je motsa jiki ne" Chidimma ta dan tabe baki kadan domin ba abun da Emily ta saba yi ba, Emily ta nufi London da Chidimma ke feeding dinsa ta sumbance shi ta shafa kansa sannan ta fice tana fadawa Fatima ta yi hanzari direban dake kaita school yana jiranta. "Yau ba zan je School ba" "Saboda me?" "Saboda kowa yana tsokana ta a makaranta, idan aka kira sunana" Ta fada tana huci, Emily ta aje gorar ruwan dakin hannunta ta nufi Fatima ta kama hannunta nufi sama da ita. Ta zaunar da ita kan gado. “Cikin masu miki dariya akwai wanda ta fiki gata? Ko ta fiki kashe kudin da kike kashewa?" Ta girgiza kai kamar zata yi kuka. “Toh karki sake bata ranki idan sun fada miki haka, ai su iyaye maza suke da, ke kuma kina da uwa mace jajirttaciyya mai kokarin sama miki rayuwa mai kyau, mai son abun da kika so, ba kin ce kina son mu bar gidan nan ba.?” Ta daga mata kai. “Duk abun da nake kokarin aikatawa a yanzu na yadda zan bar gidan nan ne, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa da abun da suke fada miki, kuma ki daina fadawa kowa labarin ki Fatima ke ma kina da surutu, idan suka miki dariya kice haka kike so, kuma ke baya damunki, ki min alkawari ba zaki sake damuwa da maganaer su ba, ni kuma zan miki alkawarin barin gidan nan cikin kankanen lokaci kuma na siya miki duk abun da kike so, tashin hankalinki tashin hankalina ne Fatima, karki sake min magana makamanciyar wannan“ Ta daga mata kai sannan ta kai mata yatsa. “I promise" "Good yanzu shiga ki wanke fuskarki idan kika yi haka kin wanke bakin ciki babu sauran damuwa sai ki fito da murmushi muje na rakaki mota" Ta tashi da saurinta ta shiga bandaki ta wanke fuskar ta fito da murmushi Emily ta kama hannunta suka fita tana far'a kamar na ita ba. Chidimma na kallonsu har Emily ta dauki lunch Box dinsu suka fice, sannan ta kalli London da fuskar tausayi tace “Ka gani Momy bata son London sai fatima, idan London yayi fushi Momy bata tsayawa ta rarrasheshi amman tana tsayawa ta rarrashi Fatima” Ya bata fuska sosai yana ta yawo da idonta ta saki baki yawu na sauko masa, ta cire tissue ta goge masa bakin. “Amman Chidimma tana son London sosai bata masa fada, Sir Vito ma yana son London amman Momy bata son London" Ta matsar da kujerar ta kusa da tashi ta rumfume shi tana murmushi tare da shafa bayansa alamar rarrashi. Sai da Emily ta ga wucewar motar da aka dauki Fatima zuwa makaranta sannan ta fara tafiya da sassafar, tafiya ta yi mai nisa har ta fita daga unguwar daga daya, daman manufar fitar ba domin motsa jikin ba ne kawai. Unguwar dake kusa da ta su ta shiga tana kallon shagunan da suka gurin wanda ta ga alamar babban shago ne ko super market sai ta dauki hoton gurin saboda kar ta manta. Kusan duk inda ta bi kallonta ake saboda yanayinta, kusan kowa kallon baturiya yake mata saboda yanayin shigarta idonta da kuma gashin kanta dake bude. Taxi ta hau a lokacin da zata dawo gida saboda gajiya da ta yi, cikin gidan ta shiga ta dauko masa kudinsa ta ba shi sannan ta koma ciki ta yi wanka ta karya ta haura sama domin bawa gado hakkinsa. KAMEELA POV. "Na jidadi sosai ko da na iso na tarar an kawo min komai na gode Honey" "You deserve it, Allah ya kara miki lafiya" "Ameen, yaushe zaka zo?" "Soon dear" "Ka kula min da kanka" "I will" Ta sauke wayar tana kallon kanwarta dake tabe baki, Anty Shafa data doro alwala ta tana yarfar da ruwa ta ce. “Kina godiya akan abun da kin fi karfinsa, dole ne daman yayi miki hidima tun da haihuwa kika yi kuma dansa kika haifa ba dan wani ba" "Hmmm Anty Kameela da yanzu ke matar Governor ce, da yanzu ke ce first lady, amman kika ki yarda kika watsa mana kasa a ido kika zabi dan makiyinmu" Ta sauke numfashi. “Siyasa ce fa, saboda Baba ya rasa kujerar Senator mahaifinsa ya samu ba wani abun ba ne, kowa rabonsa yake ci, kuma zamansu yar jam'iyar hamayya wannan siyace, daman ta gaji haka, ni ba zan iya zaman kishi da sa'anin mahaifiyata ba akan zama first Lady, kuma yadda nake da kishin nan ba zan iya raba kwana da wata mace ba, kuma ba zan iya auren dan siyasa, dan haka ku bar ki na zauna da mijina muna son junanmu" "Ga ki gashi ai idan namiji ne, har da wani yarda da alkawarin da yayi miki saboda baki da tunani, mahaifiyarsa har magana ta fada min wai ban yi aure ba" Cewar Anty Shafa again tana kokarin saka hijab. "Aliyu ya san ni ya san halina kuma ya san suwaye iyayena ba zai taba yarda ya karya alkawarin da ya daukar min ba, domin ya san yadda zan hana shi zaman lafiya" Anty Shafa ta tabe baki ta kabbatar sallah, Farida kuma ta yi dan tsaki. “Har abada dai Wallahi bana son Aliyu bana son iyayensa, domin shi ne silar bakincikin mahaifinmu" "Sai ki kashe shi idan baki son shi" Kameela na rufe baki aka turo kofar dakin, Mama Barakat ce ta shigo dakin da far'arta. “Maa Shaa Allah, Kameela jiki yayi kyau" Kameela ta wani hade rai ta juyar da fuska kamar ba ita ake yi ma maganar ba. Farida ta amsa. “Eh jiki yayi kyau sosai Mama Barakat" "Sannu Kameela ashe kuma dan be zo da rai Allah ya baki lafiya ya bada na aikawa yace shi din kuma mai ceto ne" "Ameen" Ta amsa daker kamar an mata dole. "Ayi ma Aliyu gaisuwa" "In shaa Allahu zai ji Mama Barakat an gode" Farida ce kawai take amsa mata Kameela kam ko gafen da da take bata kalla ba kai kace ba ita ta shigo ta yi ma sannu ba, Mama Barakat na fita Kameela ta ja tsaki. "Ni ban san abun da Abbah ya gani a jikin matar ba ya aurota, gashi nan ta zo ta tsika mana zuri'a da yarbawa, sai bakin munafurci da iyayi, Wallahi na tsaneta kamar mutuwa" "Saboda me?“ Farida ta tambaya. Kameela ta watsa mata harara. “Ke har sai an fada miki? Wake son kishiya sai kin yi aure zaki gane kan gari, duk wani abu mai alaka da kishi ko kishiya ni bana ciki, gashi nan ta zo ta tsirka mana da nata jinin a gida" Anty Shafa da ta sallame sallah ta jefa nata baki. "Ai ba laifinta ba ne Wallahi laifin Abbah ne duk matan duniyar nan ya rasa wa zai aura sai bayarabiya" "Wallahi na rantse da nice Hajiyarmu ba zan yarda mijina ya kara aure ba, bayan duk wahalar da aka Sha an samu kudi yanzu sai kawai ya karo aure, tab ai sai dai a mutu" Kameela ta fada. Farida ta kallesu da mamaki. "Yanzu fa ana maganar shekara goma sha biyar da auren nan, toh miye amfanin yin maganar yanzu, tun da har yara ta haifa da ai sai hakuri" "Ke dalla gafara can baki san ma duniya ba" Anty shafa ta karasa tare da jan taja tsaki ta fice daga dakin. EMILY POV. Bata farka ba sai karfe biyu da rabi na rana wani wanka ta sake yi ta yi kwalliya cikin wata shigar ta kananan kaya ta canjan sarkar cross din dake wuyanta zuwa dabam wanda ita ta siya da kanta ba wanda Vito ya siya mata ba, even though da kudinsa ta siya but not t like wanda ya bata da hannunsa, jakarta ta nufa ya dauko agogon mutumen nan ta saka a hannunta sai dai yayi mata yawa yana zubo mata a hannu. Ta zabi haka ne domin ta shiryawa amsawa Vito ko wace kalar tambaya da zai mata a duk lokacin da yayi arba da sarkar wuyanta ko kuma agogon mutumen da baya fatan ta hadu da shi yanzu ko nan gaba. Ta saka turare sosai sannan ta fito daga dakinta tana sanye da fararen flat shoes. Babu karya duk wanda ya kalleta zai san ta yi kyau domin red dress din yayi mata kyau ya karbi farin fatarta, ga gashinta data sako a gaba ta kulle sauran a bayan kanta. Chidimma ma da take mace kallonta take ta ko'ina Emily ta hadu kuma ta kai mace, wata kila shiyasa Vito yake sonta baya sauraren ko wace mata sai ita, sam baya kallon yaranta data haifa ma da kuma yadda yarta take yarfashi a gaban kowa, haka ma yake ta wahala da danta marar lafiya amman ita ma bata gani, idan ba shi ba wake wannan wahalar yanzu... "Are you okay" Emily ta tambaye ganin yadda take kallonta har ta sauko bata san ta iso kusa da ita. Da sauri Chidimma ta sauke kai kasa jikinta ya dan yi rawa. “Ina tunani ne" "Kina cikin wata matsala ne?" "Aa babu komai Ma'am karki damu" Emily ta daga kafadunta ta duba agogon da yayi mata yawo. "Yanzu na san Fatima tana kusan da dawowa, idan zata je makaranta islamiya fine idan kuma ba zata je ba, kar a barta taje ko'ina, zan fita maybe sai dare zan dawo, ki shafa min kan London kuma ki fada masa ina kaunarsa" "Tohm ranki ya dade" Ta amsa Emily ta kalli dinning ta dauke idonta ta nufi kofar fita falon ta fice. Gudun abun da zai je ya dawo ya hanata fita da motarta sai ta zabi tafiya a kafa, haka ta bi shagunan da ta gani dazun da safe ta gabatar musu da kanta ta kuma tallata kanta a matsayin ma'aikaciya idan suna bukata, sai dai ta manta bata dauko cv dinta ba sai a waya take nuna musu ko ta karbi number mai gurin ta tura masa. Kusan kowane shago kallonta ake domin bata yi kama da wanda zata iya aikin siyar abu a duka shaguna nan ba, dan haka wasu a take suke fada mata basa bukata, wasu kuma su yi tunani ko dai an turo ta ne, ko kuma an shirya yi musu wani zagon kasa ne, kadan ne suke bata tabbaci za su tuntube ta idan bukatar hakan ta taso. Ita kam a bakin gaskiyarta take neman gurin da zata iya tallafawa kanta, domin samun aiki na gobnati ko kamfani ba karamin abu ba ne ta san irin gwagwarmayar da ta yi kamin ta samu aikin da Amal ta yi mata sanadin barinsa yanzu kuma Aliyu yake son ta dawo saboda ya mulketa. Wani babban shago siyar da talkamin maza dake cikin quarters din dake kusa da unguwarsu ta shiga, sai suka yi mata maraba bayan security ya bude mata kofar shop din, kai tsaye ta tambaye manajan gurin sai da ta basu tabbacin babu wata matsala kawai tana son ganinsa ne sannan aka nuna mata shi. Ta doshi gurin da yake zaune tare da wani. "Ssnnu kai ne manaja a nan?" Ta tambaya mutumen ya kalleta Aliyu ma dake zaune ana sanya masa talkami a kafa ya juyo ya kalleta daga sama har kasa. "Eh sannu da zuwa fatan dai babu wata matsala ko?" Arba da ta yi da Aliyu ya saka duk wani hanzari da confidence nata yankewa, wani abu mai kamar fargaba kamar tsoro ya lullubeta, har take ji da ace ta san shi ne yake zaune a gurin ba zata karaso ba, gashi ta kasa sake hada ido ta shi kuma ta kasa cewa komai, ta jimke agogon hannunta dake kokarin zubewa dayan hannunta kuma ta rike jakarta. "Lafiya dai?" Mutumen ya tambaya, Aliyu ya sake juyowa a kallo na biyu sai dai wannan karon ya sauke idonsa ne akan agogon dake hannunta, fuska ba yabo ba fallasa ya mike tsaye. "Kala hudu nan sun isa for now" Ya saka talkamin da ya zo da su, ya ciro katinsa ya aje akan babban table din dake gabansa. "A kai min a wannan addireshin" Manajan ya kalleshi da mamaki domin be taba siye abu yace a kai masa gida ba sai dai a saka masa mota ya tafi da shi. "Okay ranka ya dade" Ya nufi gurin biyan kudi ya biya da amt dinsa har kudin kaiwar sannan ya nufi kofar fita, sai a lokaci Emily ta jiya juyawa tana kallon bayansa har ya fice. Sai kuma ta ji haushi kanta meyasa be mata magana ba ko ya nuna ya santa, and why ita ta kasa yin magana a gabansa. "Akwai abun da zan iya taimaka miki da shi" Ta karkarto hankalinta gurin manajan. "Eh, ina neman aiki ne a nan idan da hali" Manajan ya kalleta saka da sama domin bata yi masa kama da mai neman aiki ba. Ta gabatar masa da kanta kamar yadda take a sauran guraren ta karbi number wayarsa ta tura masa cv ta sannan ta fita jikinta na raya mata abu ne mai wahala ta samu aiki a gurin duba da wanda ta tarar da kuma irin kallon da mutumen yake mata kamar be yarda da ita ba. [4/27, 4:43 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣7️⃣ Yadda ta tafi a kafa haka ta dawo a haka feeling so lonely and hopeless. Ta kwankwasa gate din aka bude mata ta shiga, ganin bakuwar mota ya saka ta juyo ta kalli mai gadinta kamar zata tambaya waye sai kuma ta fasa, ta nufi main door din da sauri zuciyarta na raya mata wata kila Aliyu ne ya rigata iso gidan, sai dai hango direban Vito da ta yi a gaban motar ya sauya tunani, ta tura kofar falon ta shiga, sai ta samu babu kowa a falon sai wata bakuwar fuska da ta yi arba da ita a zahiri, a badini kuma mace ce da ta sha ganin hotonta a wayar Vito da kuma gidansa. "Da alama ke ce Emily" Matar dake tsaye a dinning din falon ta fada tana kallon Emily da murmushi a fuskarta. "Barka da sauka Mrs Gloria" Cewar Emily tana kallomta fuska babu yabo ba fallasa. "Vito ya fada miki wacece ni a gurinsa kenan" "Na sha ganin hotunanki a wayarsa da gidansa" "Kamar yadda ya cika ni da labarinki" Tana maganar tana nufo gurin da Emily take tsaye, ta kama hannunta suka zauna. "Fatan na same ki lafiya, ya yaranki" "Duk muna lafiya" Ta kai hannu ta rike fuskar Emily. "Ke kyakkyawa ce, kina da aji amman ba irin kyaun da za'a ce babu wata macen bayan ke ba, ďana yana kaunarki sosai kin jama lu'u-lu'u a zuciyarsa, a duniyarsa kuma kin zama numfashinsa wanda yake jin kamar idan ya rasa ki ya rasa rayuwarsa gaba daya" Ta shafa fuskar Emily. "Kin canja rayuwar ďana, a da babu ruwansa da mace ko wace kala ce, be taba min zancen budurwa ba, ban taba ganinsa da wata ba, idan ma na yi masa ransa baci yake, be taba soyayya sai akanki, ada baya tsoron aikata kowane kalar aiki ko jefe kansa a hatsari, amman sanadin ki a yanzu yana tsoron shiga matsala, ya kan ce min idan wani abu ya faru da shi ya zaki yi? Wa zai kula da ke da yayanki?" Emily ta sauke kanta kasa tana hade yawu. "Amman kin san danki yana siyar da kwayoyi? Drugs" Mrs Gloria ta yi murmushi. "Na sani, wannan sana'ace da ya gada tun daga gurin mahaifinsa, kamin a kashe shi, kar hakan ya dame ki, amman ki yi taka tsantsan da zuciyarsa, ba saboda ke ba saboda wadanda suke tare da ke" Ta mike tsaye. "Be san na zo nan ba, karki sanar masa. Na barki lafiya" Emily ta bita da kallo har ta fice, ta sauke ajiyar zuciya ta jingina da kujerar, ta daga hannunta tana kallon agogon dake hannunta ta lumshe ido ta bude ta maida dubanta gurin Jakarta da wayarta dake ciki ke sanar da ita isowar sako. Ta ciro wayar ta duba sakon da shigo daga number Aliyu even though bata yi saving number ba, amman ta gane number shi ce domin sakon yana a saman wacan sakon da ya turo mata a ranar da suka hadu asibiti. "Mahaifina dan siyasa ne, sau hudu yana tsaya takarar dan sanata amman be taba yin nasarar ba sai bana" Ta karanta sakon ta sake karanta sai ta aika masa da quation marks, like why are you telling me this? Ta tashi ta nufi dakin da danta yake tana ta mamakin dalikinsa na bata tarihim mahaifinsa ba ma nata ba, tana tura kofar dakin sai ta same shi tare da Fatima da Chidimma suna ta wasan doki cikin far'a da sakewa, sai da ta fara kawata fuskarta da murmushi sannan ta karasa cikin dakin ta shafa kan London a take ya hade rai ya matsa gefe, bata damu ba ta shafa na Fatima sannan ta karasa kusa da shi ta zauna a kasa. "My handsome Man" Kamar jira yake ta rufe baki sai ya saka mata ihu da sauri ta tashi daga gurin ta matsa. "Baya bukatar ganinki ne a yanzu, da dai zaki yi hakuri ki fita saboda muna wasa a yanzu kar a bata masa rai, mu wuni a damuwa" Ta daga ma Chidimma kai cikin rashin jindadi ta fice daga dakin, ta shiga nata dakin ta aje jakarta da duk wani abu da yake hannunta ban da wayarta da yake karanta sakon Aliyu da ya shigo mata yanzu. "Wata rana a Kaduna ranar 20 ga watan march 2020 aka ina tare da friends dina a inda muka saba haduwa mu yi shawara ko wani abu mai amfani, a ranar muna kallon tv ne a lokacin ake sanar da sakamakon zabe wanda mahaifina ya tsaya a karo na hudun kuma karo na karshe a rashin nasararsa, aka sanar cewar ya fadi kamar kowace shekara abokin hamayyarsa yayi nasara a karo na hudu, daman shi ya saba yi nasara a duk zabe" "Miye alakata da zaben mahaifinka?" Ta aika masa da tambayar domin har yanzu bata fahimci inda ya dosa ba, ya aiko mata da murmushi sai kuma wani sakon. "Na ji babu dadi sosai, abokaina suka karfafa min guiwa, muna haka sai ga mahaifiyata ta kira ni cewar mahaifina yana ciki wani hali na damuwa saboda faduwa zaben da yayi, na yi hanzarin barin abokaina na shiga motata domin tafiya karfafawa mahaifina guiwa kasancewata namiji daya tilo da ya haifa a cikin yayansa mata, a hanyata ya tafiya aka fara ruwa daman hadari ya gama rufe garin kaduna a wacan lokacin... A hanyata ta tafiya na hango wata mata tare da danta sun fake a wata kazantaciyar tumfa, yana daya daga cikin halina taimakon mai rauni a duk lokacin da na samu hali, and it does not matter if musulmi ne ko ahalul kibat, a nan na gagara wucewa na matsa kusa da inda matar take na faka motata na fita sai na same ta tana ihu da dukannin karfinta, ashe nakuda take a gurin tana dauke da tsohon ciki ne, ga kuma danta da ya kasance marar lafiya, "Sannu miya same ki? Ko haihuwa ce? Me kike yi a nan? Wacece ke?" Haka na jera mata tambaya ina leken fuskarta, sai ta kalleni amman bata iya magana ba sai dai ta kalleni a lokacin ta mika hannayenta ta riko hannuna. "Subhanallahi... Christen ce ke?" Na tambaya domin na lura da sarkar cross din dake wuyanta, sai na yi cire hannuna hannayenta, a kokarin yin haka agogon hannuna silver color ya zame ya tsaya a hannunta, sai ta jimke agogon tana cizon baki tana nishi mai karfi alamar tana jin zafin ciwo, hakan ya saka ban yi yunkurin karbarsa ba. "Am... Akwai wanda kika sani nan kusa?" Na sake tambayarta sai ta girgiza min kai alamar aa, "Okay zan kai ki asibiti yanzu nan... Danki ne wacan..." Na tambaye ta, kamin na dagata na sakata a motata ina istigifari. "Allah ka yafe min wannan ba da niya na aikata ba" Na saka danta na tuka motar ina tafe ina mata sannu har muka isa asibiti, na bada damar ayi mata komai a cikin aljihun familynsu domin asibitin da na kaita kamar ta gidanmu ce, a nan na barta na tafi gurin mahaifina, bayan na dawo sai a aka samu bata dakin da aka aje ta ta gudu ita da yar da ta haifa da danta kamar yadda suka fada min, tun daga ranar ban sake ganinta ba, abun da kawai zan iya tunawa a game da ita ita wacan tana da jiki fara ce sol kamar baturiya, tana jan gashin kai da blue eyes. Fatan kin isa gida lafiya... Ta lumshe ido hawaye na cika fuskarta, jikinta kuma yana ta bari mazari, abun da ya rubuto mata a yanzu shi ne abun da ya faru a wacan lokacin da ta rike a zuciyarta saboda taimakon da yayi mata har ta rayu ta kawo labari yanzu... ALIYU POV. Ya dago daga jikin karfen dage gabansa yana slipped tea dake hannunsa. Mamaki yake yadda time yake gudu kamar jiya komai ya faru amman gashi yanzu lokaci yaja. Yayi murmushi at least ya ceci rayuwa har biyu, ta Emily da kuma Fatima, sai a yanzu yake mamakin kansa na rashin ganeta da be yi ba tun farkon ganinta, ko da yake kamaninta sun sauya yanzu, a baya tana da jiki yanzu kuma babu yanzu ta zama yar kwalliya ba kamar so acan karon da ya ganta ba. Sai dai ko a lokacin da yake ganinta a gurin aikinsa yana ji a jikinsa kamar ya santa ko ya taba ganin wata mai kama da ita, ashe ma matar abokinsa ce ya taimaka a wacan karon kuma yar abokinsa ce ta ceto... "Subhanallahi" Ya fitar tare da iskar bakinsa, amman taya Turhan ya bar har ta fada a wannan halin dauke da cikinsa? Lallai akwai alamar ta tayu da kalubale a zamansu, shiyasa ta yi ma yarta karyar cewa bata da mahaifin, kuma take gudun ya dawo rayuwarta a yanzu. Ya dago wayarsa ya fita daga sashen sakon ya shiga sashen kiran waya ya kira matarsa yana jin cewar shi kam sam ba zai taba iya wulakanta matarsa ba kamar yadda Turhan yayi. Wayar na daf da tsinkewa ta amsa cikin wata murya dake bayyana damuwarta. "Salam..." "Hello Dear, yanzu nake son na kiraka na san ranka ya bace dan Allah ka yi hakuri da abun da ya faru" Yayi jimmm domin be san da faruwar komai ba. "Me ya faru?" "Kayan da aka kawo ne Hajiya ta sa aka maida wai yayi kadan" A take fuskarsa da zuciyarsa suka rikedewa zuwa bacin rai. "Kameela ya kamata ace muna lurar da iyayenmu inda ya kamata su kyautata ko su daga kafa, Ina sonki kin sani amman duk wani abu da zai munanawa iyayena ko ya zama cin mutunci a garesu ba zan jure ba, ban san Ummi ta aika miki da kaya ba sai da kika kirani dazun kika fada min, na kira na yi mata godiya, ban san komai akan al'adar haihuwar mace idan ďa ya zo ba rai ba, duk abun da kika gani kokarin Ummi ne, ina son wannan abun ya zama na karshe" "Yadda kake son iyayenka kake gudun bacin ransu haka nake gudun nawa, ai kasan dai ba zan taba bada go ahead akan amai da kayan da har kiranka na yi ina maka godiya ba, iyayen ba yadda zamu yi da su sai hakuri, mu dai mun san muna son junanmu that's all, wacan a tsakaninsu ne, be kamata ya shafe mu ko ya shiga abun magana a tsakaninmu ba" Be sake ce mata komai ba ya kashe wayar, domin shi ba gwanin sa'in sa ba ne. Dawowa yayi cikin falon ya aje cup din hannunsa sannan ya kira Ummi ringing daya ta daga tana ta masifa. "Anya za a jure a auren nan na ku Aliyu? Har yaushe zaka je ka dauko mata a gidan kananan mutane da ba su san mutunci ba, a nemi wulakanta mu, kayan barkar da aka kai mata ne Hajiya Ramatu ta kira ni wai sun dawo da su, sun raina kenan ko? A gidan su waye za a kai kayan barka na mai jego kadai akwaiti goma ace an raina, alhalin ma ďa be zo da rai ba" Ya sauke ajiyar zuciya. "Ki yi hakuri Ummi yanzu na kirata take fada min, kin yi kokari sosai, ita da kanta ta yaba shiyasa dazun na kira na miki godiya da abun da kika yi" "Akan su aka fara faduwa zabe ne? Kujerar sanata tuwon gidansu ne da za ace dole ko wane zabe sai sun ci? Yanzu saboda sun fadi Allah yace mahaifinka ne zai ďana sai abu ya zama dan zane? Har yana neman zama cin mutunci?" "Ayi hakuri Ummi In Shaa Allahu hakan ba zai sake faruwa ba" "A'uzubillahi wannan hassada ta yi yawa, idan son suke su kashe auren su aura mata Governor su sani dai yarsu ba daraja zata yi a idonsa yanzu ba, kuma wahala kawai zata je ta sha da wannan bakin kishin nata, kuma ya ma yi aurensa me zai yi da ita yanzu" "Ummi kin hau da yawa, Allah ya huci zuciyarki amman dai idan tunaninsu kenan sun yi kuskure domin babu saki tsakanina da Kameela, ko ba ita ba daman na kudurta a raina duk abun da zai faru ba zan taba iya sakin matata ba, kuma na mata magana In Shaa Allahu irin wannan ba zai sake faruwa ba" "It better, domin na fara gajiya sai kace kansu aka fara siyasa, shekara nawa Engr yana hakurin faduwa zabe sai bana dan Allah ya ba shi sai kuma su juyar da siyasa kiyayya" "Ummi ayi hakuri" Ta masa kwatankwacin abun da yayi ma Kameela, ita ta kashe wayar a cikin fushi. Ya sauke ajiyar zuciya. "Daddy ma lalabawa yake da Ummi, balle ni da nake ďa, iyayen Kameela suna neman kunno min wuta" Ya fada cikin yanayin damuwa. Sai bayan bayan sallah magariba Kameela ta kira shi tana bashi hakuri suka jima suna waya, yawanci abun da take bincikarsa na ina yake cin abinci ne sai kuma inda yake zuwa yanzu da bata gidan. "Ina zan je? Ina gida mana" "Yaushe zaka zo" “Soon" "So soon" "Not so soon" "Okay, ka kula min da kanka, kuma dan Allah kar ganin bana nan ya saka ka rika kula mata ko kallonsu" Yayi murmushi kawai ya girgiza kai. "Toh ranki ya dade" Ta yi dariya, ya mata kiss a wayar sannan suka yi sallama. KAMEELA POV. Tana sauke wayar Farida ta shigo kiranta wai Abbansu yana son ganinsu gaba daya a bangarensa, haka suka dunguma gaba daya suka tafi bangarensa suka zauna har Mama Barakat da Kameela ke ta harara. Alhaji Tukur Nazifi Ataka ya fara kallon Hajiya Asma'u ya ce. "Waya ce a mai da kayan barkar da aka kawo?" "Alhaji ba fa wani kayan kirki bane, kamar gidan nan za a kawo kayan barka akwaiti 10, ko ya muke riko a gidan nan ai ta fi karfin haka balle kuma jininka, da gangan suka yi saboda su walakanta mu" A take Alhaji Tukur tsohon sanata ya rufe ta fada. "A wane dalili za a maida? Idan ma sun yi ne saboda abun da kike tunani miyasa za ki fiye masu? Wannan ai rashin dattako ne, kuma ba kowa ya janyo ba sai Kameela, su basa tunanin komai sai soyayya, gashi nan tun ba aje ko'ina ba sai abubuwa ake samu na rashin jindadi, toh daga yau sai yau kar a sake aiko wani abu daga gidan Bappa Mudallab a maida shi, ko ba can ko daga ina ne kar hakan ya sake faruwa" Ya kalli yaransa daga mazan har mata a fusace ya ce. "Ku kuma a cikinku kar wanda ya sake dauko ya ko dan makiyinmu yace sai zai aureshi last warning, shiyasa na tara ku a nan" Mama Barakat ta ce. "Alhaji ayi hakuri, kar a bari siyasa ta yi tasiri akan rayuwar yau da kullum, na san faduwar nan bata yi ma kowa dadi ba, amman kar a hana yara abun da suke so" Hajiya Asma'u taja tsaki. "To ke me kika sani a siyasa Barakat? Da har zaki fadi haka? Siyasa ai mu muka santa ciki da waje, domin Alhaji tun yana ba shi ba nake fadi tashi da shi akan siyasa har ya zama wani abu a yanzu" Alhaji Tukur ya kalli Hajiya Asma'u domin ya san da biyu ta fadi maganar. "Me ya kawo wannan maganar yanzu? Ku tashi na sallami kowa" Mama Barakat ta yi murmushi ta mike tsaye ta fice daga dakin, Hajiya Asma'u ta watsawa bayan Mama Barakat harara ta jin haushin yadda take karkada mazaunai kai kace da gayya take yi. (Mtssss kayan kashi) ta fada a ranta sannan ta mike tsaye suka fice ita da yaranta. ALIYU POV. A yau ya shigo aiki da wuri domin gidan yayi masa ba dadi, saboda hatsaniyar da aka samu tsakanin iyayensa da na Kameela gashi kuma Kameela bata gidan baya jin motsin kowa sai hakan ya saka shi jim gidan yayi masa girma. A nan yayi breastfeed yana gamawa ya kira Kameela suka gaisa ya ji tashinta, a nan ta saka masa kukan yaron da ta haifa ya koma, wai sai a yanzu take jin babu dadi abun yana damunta har mafarki take. Rarrashinta yayi ta yi sannan suka yi sallama, ya dauko qur'anensa dake office din yayi karatu daidai gwargwadon yadda zai iya sannan ya aje bayan yayi addu'a ya amsa kiran Turhan dake shigowa wayarsa ta WhatsApp video call. "Salam.." "Hey Aliyu ya gidan ya aiki?" "Lafiya kalau, ya Ammy?" Aliyu ya tambaya yana karantar ramar da abokinsa yayi. "Tana kaduna" Yanayin yadda ya amsa masa ne ya bashi tabbaci ya bar kasar. "Ka koma Sudan ne" "Eh jiya, abun da naje nema ban samu ba, still Ammy bata duba hakan ba, anyway na kira ne na maka barka matar ta haihu ashe?" "Eh amman yaron be zo da rai ba" "Eh Allah ya baku hakuri, kara kai ai kana haihuwar ba kamar ni ba, ban ma san ya ake ji ba idan aka rumgumi yaro" Tausayinsa kadan ya fada zuciyar Aliyu. "Kai ma wata rana zaka rumgumi yayanka In Shaa Allahu" "Ina fatan haka, agaishe da Madam" "Zata ji" Daga haka suka yi sallama, Aliyu yana jin kansa kamar wani mai laifi, meyasa Emily zata daure shi har haka? Ya kasa fadawa abokinsa a inda take tare da yarsa. Ya dago yana kallon kofar dakin da aka kwankwaso. "Yes" Nick ya shigo ya sanar masa Emily tana son ganinsa, Aliyu yayi shiruuuu yana kallon wani gurin kamin ya bash izinin shigowa da ita. Ya mike tsaye ya nufi windows din office din ya bude ya tsaya a gurin yana kallon kasan benen. Emily ta turo kofar office din ta shigo tana sanye da short gown black color gaba daya ta daure gashin kanta a baya tana rike da makulli mota da wayarta, sai kuma agogonsa a dayan hannunta. Ta dade tana kallon bayansa sannan ta matsa kusa da teburinsa ta dora agogon. "Zumudin zuwa ganin mutumen da ya taimake ni a yau, be bar ni na runtsa ba, da na zo ban san office din ba da tambaya na kawo kaina a nan. Kullum mafarki da buri na yadda zan maida alherin da aka yi min ne da alheri, na kasa manta yadda ka ceto rayuwata, a lokacin da ba ni da kowa babu mai taimako na, Vito yana yawan cewa na jefar da agogon nan ko na manta da shi, sai na fada masa indai har zan iya manta alheri to zan iya mantawa da agogon, manufar ba ta agogon ba ce kawai, ta mamallakinsa ce, ashe kuma na aje kwarya a gurbinta ne, ashe dai ka cancanci ko kasa ka taka na jimke na aje" Ta share hawayen idonta. "Ka taimake ni a lokacin da iyalinka da kai kanka kuke neman taimakon juna na karfafa guiwa, baka damu da addinina ko kazantar da take jikina ko ciwon yarona na ba ka taimake ni, hakika Aliyu kai mutumen kirki ne, kuma na yarda a ciki musulmai akwai na gari" Sai a lokacin ya juyo ya kalleta kallo daya ya dauke idonsa. "Duk abun da na yi na yi ne saboda Allah" "Fada min me zan yi na rama daya bisa ukun abun alheri da ka yi min?" Ya nuna mata kujera sannan shi ma ya zauna. "Wacece ke? Tun farkonki har zuwa yau, yadda kika hadu da Turhan har zuwa rayuwarki ta yanzu, shi kawai nake da bukata a gurinki yanzu" Ta nuna kanta tana hadiye bakin cikin daya tsaya mata. "Ni... Ńi ni ce kawai, ni ce wata yarinya data tashi a gidan marayu bata san kowa ba sai kanta da mafarkinta..." Taja numfashi ta lumshe ido, Aliyu ya kalleta a karo na biyu kwarjin farar fata a cikin bakin tufafi ya cijeshi, ya dauke idonsa da hanzari ya maida akan agogon da ta aje masa. [4/28, 6:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣8️⃣ *June 4 2014* *Lagos State Nigeria.* *Little Saints Orphanage (ABULE EGBA HOUSE) 149, Carpentar B/stop, Ekoro Road.* *MAFARI...* Tafiya na ke a hankali ina kallon sababin talkamin da suke kafata wadanda wata kungiyar taimakon kai da kai ta kawo mana tun satin daya gabata. Talkamin sun min kyau sosai a kafa kamar daman dan ni akai su. "Emily.." Ina jin muryar mai kiran na juyo fuskata ba yabo ba fallasa na kalleta. "Ibo lo lo?" Ta tambayi gurin da zanje da yaren da mafi yawan marayun da suke zaune a wannan gidan na marayu suka fi ji, wato yarbanci. "Mo n lọ si ọja lati ni awọn eso diẹ. kilo de ti o bere?" "Ohunkohun. irin ajo ailewu" "O dara emi yoo pada wa ni titọ" Na karasa amsa mata tare ta mikawa mai gadin gate din gaisuwa "E kaaro arabinrin" Sai ya amsa min da murmushi. "O dara, Ọlọrun yoo bukun fun ọ" "Amen" Da kansa ya bude min gate din duk kuwa da kasancesarsa dattijo, amman yana ganin girma da kuma mutunci. Wani dogon numfashi na ja na sauke sakamakon iska mai dadi da take kadawa, daga kaina nai sama ina kallon hadarin da ke haduwa a tsararin samaniya rana tana ta lumshi tana budewa gwanin sha'awa. Babu mutane sosai daman unguwar ekero road, kamar gra take abu ne mai wahala ka ci karo da hayaniya ko kaikawo na jama'a kamar cikin tsakiyar lagos. Mini skirt ne a jikina mai aljihu sai wata farar vest mai kama da ta kwana wuyana na sanye da sarkar cross hannuna ma yana rataye da warwaron wanda akai da farin dutse. Kitso ne jan gashin dake kaina, na yi parking dinsa da ribbon tsorayen sun sauko har bayana. Tafiya nake cikin natsuwa da aminci, zuciyata kuma nata rara min wakar da muke a coci duk da kasancewar bana jin natsuwa da da wakar amman sabo yasa ni yake jin dadinta. Sai da na fito daga unguwar gaba daya na nufi hanyar da zata sadani da wata karamar kasuwa da take layin. A bakin titi na tsaya sai da motocin suka gama wucewa sannan na tsallaka zuwa gaban teburin wani mai siyar da kayan marmari. Na tarar da mutum biyu a gurin so hakan na nufin dole nai hakuri na jira har ya sallamesu. Da yaren igbo suka yi magana dayan ya siyar masa da abaya da kankana dayan kuma mai zubin hausawa sai ya mika masa dubu biya yace ya hada masa kayan marmarin da turanci. Na saba siyayya gurinsa magidanci ne mai jin yaren igbo domin shi baya jin turanci balle kuma yarbanci, rike kudin da mutumen ya mika masa dan be san abunda zai bashi ba, shi ko kyakkyawan saurayin mai kama da mazan novel ya dage sai bayani yake masa da turanci. "Kaji matsalar rashin jin yaren mutane" Ya fada cike da jin haushi. "Kuma ba zaka nemi taimakon kowa ba?" Da mamaki ya kalleni jin na masa hausa. "What did you just said?" Murmushi nai ban bashi amsa ba, na kalli mai siyardar kayan marmarin na fada masa cewar ya hada masa na dubu daya da dari biyar kamar yadda ya fada masa da yalshen turanci da farko ni kuma na fada masa da yaren da yake ji wato yaren igbo. "Nye ya puku akwukwo nri" Sai ya amsa da okay ya shiga hada masa. Mutumen ya matsa kusa da ni. "Kina jin yarena?" "Duk mutumen daya zauna lagos dole ne yaji yare kala biyu, ko dai ya iya turanci ko kuma yarbanci, har da igbo ma idan ta kama, domin shi wannan mutumen baya jin yarbacin igbo yake ji, ya kamata ka koya" Na fada masa ba tare dana kalli inda yake tsaye ba. Murmushin kasaita ne ya bayyana a fuskarsa da alama na burgeshi jin ina hausa kamar jakin kano. "Amman ina kika koyi yare nan har hudu turanci, hausa, yarbancin, igbo wace yare ce ke?" Kallonsa nai muna hada sai yayi saurin kawar da nasa, ba mamaki blue eyes dina ne suka firgita shi. "Ban san yarena ba" "Why?" "Because ni marainiya ce" Fuskar tausayi yai ya zuba hannayensa a aljihu. "Ayyah I'm sorry" "You shouldn't, it's not your fault" "Yeah i know, mi zaki siya a nan" "Ayaba ina son ayaba" "Owk you look cute" Ya fada yana kallona. "Thanks handsome" Na fada still ban kalleshi ba. Sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro dubu uku ya mika min. "Gashi ki siya" "No na gode" Na fada ba tare da na kalli kudin ba. "Wow ba kasafai zaka bawa yarinya kamarki a lagos kudi ba ta ki karba" "Likewise, ba kowa zai iya kyautar kudi a take ba a Lagos sai bahaushe" "Yeah musulumci ya koyar da mu rika kyauta saboda halin Annabin mu ne, by the way sunana Hamza Ali ana kirana Khaleefa" Cike da burgewa na ke kallonsa, ban san abunda yasa na ke son naji ana maganar abunda ya shafi musulumci ba Hannu na mika masa "Ni kuma sunana Emily Emmanuel" Kin karbar hannun yai. "Mu musulmai bama gaisawa da mace musulumci ya hana mu sorry" "Never mind" Sai da mutumen ya mika masa ledar kayan marmarin sai ya karba yana kallon. "Fada masa ya rike canjin" Da yaren Igbo na fada masa cewar ya ce ya bar canjin, sai ya mikawa mutumen dubu ukun. "Ki fada masa abunda kike so ya hada miki, nice to meet you young lady" Ya fada yana kallona kasa da sama, kamin ya buga babur dinsa ya daga min hannu yana murmushi ya wuce. Murmushi nai na rashin dalili na bishi da kallo har na daina hangoshi. *** *** *** Godiya mutumen igbo yai min sannan na fada masa abunda zai bani ya hada min da sauran canjina na kamo hanya cike da farincikin da ban san dalilinsa ba, kawai dai ina jin nishadi ya cika min zuciya da ruhi. Ina tafe ina wasa da dayan hannuna mai nade da sarkar cross sai aka fara yayyafi, kowa ya fara gudu an fakewa a wani gurin domin ruwan ya sauka da karfi, ni kam tafiyata na ke da dai daya ina daga kaina sama ruwan yana saukarka min a fuska da kai. Hango bakin shagon wani mutume dake road din mu babu kowa a gurin yasa naje gurin a guje na aje ledar hannuna na fito tsakiyar titi da babu motoci na tsaya ina waka da ruwan saman ina juyawa ina rawata domin babu abunda ya dame ni. Shakaf ka jike a guri a gurin idan na hango mota tafe sai na koma gurin shagon a guje na fake dugun kar a min daukar mahaukaciya sai motar ta wuce sannan na fito na cigaba haka nai ta yi har aka gama ruwan a kaina. Sannan naje na zauna bakin teburin mutumen na saka hannuna a aljihu na ciro yar karamar wukar da babu wanda yasan ina yawo da ita na dauki lemu daya na yanka na sha. Sai da naji na koshi da kayan marmarin sannan na faki idon mutane na maida wukar ajihuna, na dauki ragowar kayan marmarin na kamo hanyar gidan marayu wanda zan iya kiransa da gidanmu ko kuma na ce gidana. Kamar dai dazun yanzu ma sai da muka gaisa da mai gadin gurin har yake min sannu da jikewar da yai sannan na wuce sashenmu wato block C. Rossy na ganina ta rugo da gudu ta tare ni, daman ta saba min haka ita ba ma ita kadai ba har da sauran an block din, domin ni mutuniyar kowa ce komai nawa na kowa ne, idan na samu bana iya ci nidai ko da basu san da shi ba. "Ku aabọ pada. arabinrin mi" Ta min sannu da zuwa da yaren yarbancin tana kokarin karbar ledar hannuna. Sakar mata ledar nai ina murmushi na ce. "Kije ku raba tare da du Elina" "Wow wato oga shakur yayi miki sallama ta kwarai kenan nan yau" Da yaren yarbancin muka yi maganar ni dai murmushi kawai nai na kama hanyar dakinmu, daman na san kowa zai dauka cewar kyautar oga Abdulshakur ce, domin ya saba min irin wannan sallamar idan rana tai hi kyau. Oga Abdulshakur wani oganane a gurin aikin gyara mota, shi yake da gurin a gurinsa nake zuwa ina koya duk kuwa da kasancewarsa musulmi, na fara aikin ne a lokacin dana kare makarantan kuma ban samu damar shiga babba ba, an rubuta takarda zuwa ga gabnatin Lagos domin daukar nauyin karatun mu zuwa mataki na gaba mu yan wannan shakarar da muka gama, amman har yanzu babu wani abu da ya fito daga can, wata kila dan aikin har yanzu be kai ba, ko kuma ta manta da sha'aninmu ne. Ni kuma bana son zaman banza ba aiki, bayan kuma shugaban gidan marayu ya bawa kowa damar mai son aiki ko sana'a yayi domin tallafawa kansa. Ko da na shiga dakinmu babu kowa sai Nine ackor ita kadai a gafenta tana bachi, dakinmu babban daki ne mai daukar mutum takwas kamar sauran dakunan, an kawata dakin da kananan gadaje na kwanan mutum daya da yar karamar waduruf ta saka tufafi. Gadona kusa da window yake hakan kuma na min dadi duk kuwa da kasancewar wani lokacin ina jin tsoro. Tufafin jikina na fara cirewa na canja zuwa wata yar karamar gown, sannan na dauki wukata na saka a cikin jakata inda na saba ajeta, gado na hau na kwanta fuskata da murmushi mutum dazun ne har yanzu na kasa daina ganinsa a idona, yana da kyau sosai kamar wani aljani gashi fari ni kuma ina son fararen mutune duk kuwa da kasancewata fara. 'Musulmi ne fa!' Zuciyata ta fada min, miyasa zan yi tunanin musulmi bayan a coci ana yawan fada mana cewar musulmi yan ta'adda ne kuma basa son kistoti irina, a take gabana ya fadi sai na ji kamar nayi wani sabo, take nai saurin praising Jesus na roki gafarsa, nai saurin tasowa na baro dakin gudun kar tunanin ya sake dawo min na samu zunubi. Haka muka raya yammacin ranar da laraba tare da yan'uwana marayu, sai da dare yai sai na nufi gurin dana saba zama na zauna karkashin wata bushiyar lemu na jingina jikina ina kallon sama, yadda taurarin suka jera abun ya burgeni sosai, sun yi ma sama ado sai sheki suke, kirgasu na fara yi da yatsana duk kuwa da kasancewar na san ba zan taba iya kirgesu su duka ba, wata maganar taurari ce dake cikin Bible ta fada min a rai. "Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel" Murmushi nai ina mamakin yadda wani zai iya kona taurarin nan na samaniya har ya kwashe tokarsu. Wani lokacin bana son zufafa bincike akan addini na amman ina ganin kamar akwai gyara a litattafin bible domin kuwa wasu kalaman ko nace surorin da suke ciki sai kaji kamar abun ba zai yiyu ba wani abun ma nakanji kamar labari ne irin na shaci fadi. "Kina nan kina aikin kallon taurari ko?" Maganar marry ce tasa na dawo da dubana izuwa gareta, kokarin zama take kusa da ni. "Wata rana za ki zauna tare da mijinki ku kirga taurari" Na kalleta "Marry kina da ban dariya" "Miyasa na ke baki dariya idan nai maganar miji? Baki taba daukar hakan da gaske ba" Shiru nai kamin na ce mata. "Ina ganin wani abun kamar ba zai faru ba, akwai wadanda suka girmemu a nan gidan kuma suna nan basu yi aure ba balle kuma ni da ke, balle ma ba zamu auri mutumen da zai ga girman mu saboda ba mu da iyaye" "Wata kila ke din kina da iyaye Emily, ina ji a raina kamar muna da iyaye yawancin mu da muke gidan marayu muna rayuwa kawai a matsayin marayu, amman wasu iyayensu sun yi cikinsu ne sun jefar da su" "Indai har haka iyayena suka min bana kaunar ganinsu, domin sune silar shigata wannan hali" "Idan kuma iyayenki suna tsoron ki wahala ne suka kawo ki nan fa? Ko kuma wani ne ya sace ki ya kawo ki nan?" "Zan iya yafe musu idan wani ne ya kawo ni nan, zan yafe musu amman talauci ba hujja bace komai talaucinsu kara su yi hakuri da ni a haka mu zauna a haka, tun da suka kasa hakurin zama da ni ba zan yafe musu ba" Na fada idanuwa na cika da kwalla, sai ta saka hannunta ta lakamoni. "Zaki yafe mata Emily, lokacin da mijinki zai risina a gabanki ya roka mata yafiyarki ba kisan lokacin da za ki yafe ba" "Ba zan iya yafewa ba marry, i just can't" Dariya tai jin yadda nai maganar ina son yin kuka. Mun dade zaune a gurin sannan muka tashi muka shiga block din mu ta nufi dakinta ni ma na nufi namu. Babu wuta a dakin amman an kunna hitila kamar yadda aka saba idan ba wutar, ban kula kowa ba dukuwa da irin wasan da abokina na dakin ke jana da ita, ganin bana cikin yanayin wasan yasa suka kyaleni na hau gado na kwanta wata kofar tunanin ta bude min. 'Suwaye iyayena? Yarbawa ne, igbo ne ko ibra ko hausawa? Ban sani ba, wane addini suke? Miyasa suka jefar da ni? Basa sona ko wani dalilin ne na dabam?' Da wannan tunanin nai bachi kuma har gari ya waye ban samu amsar tambayoyina ba. Ban farka da wuri ba kasancewar ban yi bachi da wuri ba, shiga nai bandakin mu dake can kusa da kofar shigowa dakin nai fitsari ba tare da tsarki ba na wanke bakina kuma nai wanka sannan na fito. Mai kawai na shafa, ni ma ina da kyau kamar mutumen jiya duk kuwa da kasancewarsa namiji. Karamin wandon jean na saka wanda iyakar tsayinsa guiwa na saka wata t-shirt black na dauko kofina na jika gari na sha domin an san by this time an gama raba abincin safe kuma wanda be je ya karbo ba ba za a aje masa ba indai ba wani ne ya karbo masa ba. Bayan na gama sha na rufe waduruf din na saka wukata a aljihu tare da makullin lokar na dauki jacket dita na daura a kwankwaso na sannan na fito zuwa gurin gyaran mota wato gurin aikina. Nayi ta sauri a hanya ganin na yi latti ba kasafai nake son oga na rigana zuwa gurin ba, naje latti sai dai duk da haka oga Abdulshakur be fito ba wata kila wani abun ya tsayar da shi a gida ko wani gurin, rigar aikin na dauka na dora saman tufafina na soma gyara gurin sannan fito da kayan aikin a waje, na kusan awa biyu a gurin sannan ya iso. Cikin girmamawa na gaishe shi ya amsa min da far'a kamar kullum, sannan ya shiga aikin gyara motocin da ke gurin a lokacin ne mutane suka fara zuwa ciki kuwa har da yaran da muke aikin tare da su yan gareji. Ni nake tsaye kusa da shi ina aikin miko masa abubuwan bukata kamin ya bani list din abubuwan da zan je na siyo a kasuwar da ake siyar da jarafuna a unguwar Orile Iganmu a nan lagos. Zuwa nai dakin dake garejen na cire rigar aikin na dawo ya bani kudi na saka a aljihu sannan na kama hanya. Ba mu da nisa sosai da unguwar dan tafiyar bata wuce ta awa daya da rabi ba, so i decided naje a kafa na rike kudin babur din ko wani abu zan iya siya da su. Na tafiyar minti arba'in kamin na kama hanyar da ke kusa da kasuwar, hanyar kamar unguwarmu take babu mutane sosai duk kuwa da kasancewar da rana ne. Gungun wasu mutane na hango za su kai mutum hudu zuwa biyar a tsaye gefen titin, ban ji tsoron ganin mutanen masu kama da yan ta'adda ba domin na saba ganin irinsu da ma wadanda suk fisu a lagos. Ban lura da abunda suke da niyar aikatawa ba har sai da na isa kusa da su, mutumem jiya ne suke kokarin karbewa mashin suna masa barazana da katuwar wukar da ke hannunsa. "Bamu makulli" Dayan ya fada da yaren turanci ni kuma na katsa masa tsawa da yaren yarbancin ganin zagen fuskarsa da yana nuna cewar shi bayarabe ne. "Ba zai bayar ba, ku kananen yan iskane da kuke yawo da wuka, kuma duk wanda ya kuskura ya taba shi ai cikinku sai nasa an kasheshi ba kune yan apapa ba?" Duk tsayawa sukai cirkocirko suna kallona yadda nai musu barazanar yasa sun dan tsorota, ban san su ban san yan ina ba ne amman yawacin yan iskan lagos apapa suke, sun dauka a yadda nai musu kamar na sansu ne ko kuma ina da wani mai tsaya min ne. "Wacece ke?" Dayan ya tambaya da yaren yarbancin kamar yadda nai masa magana dazu. "Idan kun taba ni zaku san ko wacece ni" Na fada ina zaro wukar dake cikin aljihuna na nuna musu ina yatsine fuska kamar yar ta'addar gaske. "Ku wuce daga nan" Kamar umarnina suke jira suka kama hanya suka kyaleshi suna ta waigena. Sai da suka wuce sannan ya kalleshi na ce "Kai sakarene zaka tsaya haka a kwace maka babur?" "Kamar ke ce yarinyar da kika taimake ni jiya" Ya fada cike da mamaki yana nuna ni. "Yes kuma yau ma na taimakeka ba, dan ka zama dolo" Murmushi yai. "No ina tsorone amman kin san su ne?" "Ai a lagos ba dole sai ka san kowa ba, as long as kasan sana'ar mutun barazana kawai zaka masa, idan har kace kyalewa zaka yi kowa zai cuce ka ne, shiyasa na ke yawo da wukata" Na fada ina maida wukar aljihuna sannan na kama hanya tafiya kasuwa ta ba tare da na jira abunda zai ce min ba. "Na gode Emily" Ya fada sai na juyo na kalleshi ina murmushi. "Baka manta sunana ba?" "Taya zan manta sunan Jaruma" Ya fada da dariya nima dariyar nai na cigaba da tafiyata. _________________________ Want more? *Comment* *Share* *Follow* my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 [4/29, 6:17 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣9️⃣ Tun daga wacan ranar ban saka ganinsa ba, amman ban manta sunanansa ba, ban manta kyaun fuskarta domin Khaleefa yana da kyau sosai kwatankwacin yadda mutane suke baya kyauna. Kusan zan iya cewa kyaun ne abun da ya ja hankalina izuwa gareshi. Na cigaba da rayuwata ta yau da kullum kamar yadda na saba a gidanmu na marayu, da safe zan tafi makaranta da yamma kuma na leka gurin aikina na gyaran mota wato garejen oga Shakur, idan aka samu aiki yayi kyau ko kuma muka samu customers da yawa a ranar yana min alheri kamar yadda ya saba. Kasancewar yau assabar na tafi aikin tun safe ban tashi ba sai yamma, da zai sallame ni yayi min sallama mai kyau, ba karamin faranta min rai yayi ba hakan ya kara min karfin guiwar tafiya gida, na yi wanka na shirya na fito domin kashe kudin da aka bani, domin abu ne da kowa ya shaideni da shi alheri hali na, idan na samu kudin na kan sawo abubuwan dadi na kawo, kowa ya saka hannu ya ci, ban san na ci ni kadai ba. Na isa gurin na gaisa da shi da yaren igbo na ba shi kudi nace ya hada min kayan marmari, a nan yake fadan min domin da na taimakawa yayi siyayya ranar nan kullum sai ya zo nemana. Da mamaki na tambaye shi. "Nema na? Me zan masa?" Yayi murmushi ya koma cikin karamin shagonsa ya dauko farar takardar ya miko min. "Number ce ya rubuta yace idan kika zo a baki, duk da haka kuma yana zuwa kullum da zaki iya jiran shi anjima kadan zaki ga ya zo" "Amman yace na yi masa laifi?" "Alamu be nuna hakan ba" Ya miko min ladar na karba, har zan tafi sai kuma wata zuciyar ta ba ni shawarar na tsaya na jira shi mana idan ma wani abun ne ai zan ji. Haka kuwa na aikata na zauna a gurin muna ta hira da Mutumen sai ga shi ya iso da babur dinsa kamar wacan karon. Tun kan ya sauko daga kan babur din fuskarsa ta washe da murmushi, ya karaso kusa da inda muke zaune yayi min sallama, na amsa masa kamar musulmai, sai ya washe hakora. "Garkiwata kamar dai kin fini iya hausa" Na yi murmushi zuciyata na bugawa da wani irin karfi, irin bugun da bata saba yi ba. "Kana ta nemana aka ce, amman dai ba laifi na yi ba ko?" "Laifi kika yi babba kuwa" Ya fada yana dagawa igbon hannu tare da mika masa 2k. "Laifin me" "Kin san kin taimake ni a nan haduwar farko, haduwa ta biyu kuma kin ceto rayuwata kin ceto abun hawana kuma abun sanata, tun daga lokacin zuciyata bata barni na zauna laifi ba, na yi bata hakuri har na gaji amman bata bar ni ba, wata kila saboda ba ni da kowa a garin lagos ne, wata kila kuma saboda taimakon da kika yi min ne, ko kuma dai saboda kina marainiya ne amman dai kin tsaya min a rai kuma kin ba ni tausayi sosai" "Baka da kowa a nan" Na tambaya da mamaki fuskarsa na cika ni da kwarjini, ba dai kyaun ba kam Khaleepa akwai kyau kamar dan indiawa. "Ba ni da kowa, kawai na biyo abokina ne da yake achaba a Lagos saboda ance yafi arewa samun kudi, sai na zo ni ma nake yin achaba, ban san kowa ba sai ke sai abokin nan nawa, sai kuma mutumen igbo" "Interesting" Na furta not knowing what to say next, yayi tagumi yana kallona. "Ashe dai zan sake ganinki, na ji kamar na yi hauka, kullum sai na zo nan neman kyakkyawar fuskar nan" "Amman ya kan yi ka iya magana da igbo nan bayan baka jin yarensa" "Wani na samu yake rubuta min duk abun da nake so na tambaye shi idan na zo, sai shi ma ya rubuta min idan na tafi gurin wacan sai a fassara min" Na yi murmushi ina yaba karfin halinsa, amman fa ya burge ni, neman ganina kawai zai saka shi wannan hidimar. "Ni zan tafi" "Haba ban gama kallonki ba fa, kuma kin san yaushe nake bata lokaci ina zuwa nan nemanki" "Idan na dade ban dawo ba kawaye za su neme ni, kuma ba a son muna fita muna dadewa a waje ba tare da wani dalili ba" "Shikenan muje na rakanki, akwai abubuwa da yawa da nake son sani akanki, kamar yadda aka yi kike jin hausa, kuma kike da kirki da kulawa, kuma gashi kina da kamun kai, dan na yi mamakin yadda na baki kudi baki karba ba, kuma gaki kyakkyawa" Duk yadda na so na tafi ni kadai be yarda ba sai da ya goyani da babur dinsa ya kai ni kusa da gidanmu na marayu, a boye na sauka domin bana son kowa ya gan ni, idan aka gani ma za'ayi min fada. Ya sake rubuta number shi ya ba ni ya bani kudi a nan din ma ban karba ba, be tafi ba sai da na masa alkawarin zan kira shi mu gaisa da wata wayar. A ranar kasa cin abincin dare na yi, na gagara cin kayan marmarin da na siyo sai tunaninsa nake, a wacan lokacin akwai kurciya sosai a tare da ni, domin ina da shekara goma sha biyar ne, a lokacin ina sss1, gashi kuma wani be taba nuna min kulawa kamar yadda shi ya nuna min ba, ina da kyau wannan abu ne da ni kaina na sani, amman kyaun nawa be taba sakawa wani be taba nuna min kulawa mai kama da soyayya kamar shi ba, sai dai mutane su na haba haba da ni, wata kila suna gani ko tunanin ni na yi karama ne. Abu kamar wasa muka fara shakuwa da juna, da wayar mai dafa mana abinci a gidan nake amfani ina kiransa mu gaisa, wani lokacin har cin hanci nake bata, shi kuma da zarar ya ga flashing dina zai kira mu dade muna yawa, idan yana son ganina kuma zan boya na tafi nesa da gidanmu na hadu da shi mu ga juna, a gaskiya na so Khaleepa a wacan lokacin irin son da idan ina tunaninsa bana iya bacci, idan ban yi waya da shi sai na wuni cikin wani yanayi na rashin dadi, a makaranta gurin aiki bana da komai sai tunaninsa. Wani lokacin zai yi min siyayya sai na boya na shigo da ita ba zan fadawa kowa ba, ranar da Marry wacce take kasan gadona ta gane ina soyayya ta tsare ni da tambaya har sai da na fada mata shi ne mutumen da muka hadu kuma na fada mata shi musulmi ni, sai ta fusata kuma ta tsorata ni cewar ai su musulmai basa auren kafirai, kuma a arewa ba a son wanda ba bahaushe ba, arna suke kiranmu, a madadin na yi nazarin kalamanta sai soyayya ta rufe min ido na fara gaba da ita. Na same shi da maganar tabbas a lokacin, sai ya karyata abun da ta fada, a nan yake fada min asalinsa da gidansu da garinsu da yake kauyen Kaduna. Ya nuna min fargabarsa ta daga gurin inda nake zaune ne, yana ganin kamar ba za a yarda a aura masada ni ba, a lokacin ni ma hankalina ya tashi domin na san ba za su yarda ba. Haka dai muka cigaba da soyayya, yana fada min idan ya aure ni, zamu yi rayuwar aure mai kyau, zai nuna min soyayya zamu rika cin abinci a tare wanka kwana komai kamar na masoya, ashe karya yake amman ni ban gane ba, kawai abun da ke daukar hankali kyaunsa da kuma yadda be taba yarda ko da wasa ya taba nuna son taba jikina ba, har ta kai yana kiran mahaifiyarsa ya ba ni mu gaisa, be min karya ba ya fada min sana'arsa kuma ya fada min shi dan kaduna ne, amman a kauye suke zaune tare da iyayensa. Soyayya da muka fara da Khaleepa kusan kamar ta budewa maza kofa ne, domin babu ranar da zan fita wani be nuna yana so na ba, amman bana sauraren kowa sai shi, idan naje church kullum addu'ata na yadda kowa zai amince na aureshi ne. Ana haka wata rana aka shigo kirana tare da sauran yan mata sa'anin na, muka tafi sai muka samu wasu manyan mutane ne suka zo neman ya da zasu rike kamar su suka haifeta. Daman akan yi hakan wasu jarirai suke so, wasu kuma wadanda suka dan tasa, amman ita tace tana son matashiyar buduwarwa, domin ta taba daukar jaririya kuma ta reneta tana can hannunta a gurinta ta girma. Matar tana yin arba da ni, sai ta zabe ni, suka ba ni damar tafiya na shirya domin a ranar zan tafi bayan ta yi duk abun da ya kamata, a ranar na sha kuka sosai a gurin abokan zamana na gidan, domin tun muna yara muka taso tare, har na ji kamar kar na bita, sai dai kuma ina son tafiya ni na shiga family na samu wanda zata rike ni a matsayin ina son na rumgumeta na ji yadda ake ji. Gidanta babba gida ne a lagos tana da masu kyau, ga manyan motoci da ac abinci sai wanda na zaba nake ci, tun a ranar da aka kawo ni ta fada min ita bata taba haihuwa ba, tana da jiki sosai likitoci sun ce kitse yayi mata yawa ba zai barta ta haihu ba, hakan ya saka take son rike yara kamar yaranta. Ta nuna min kauna tace zata rike ni kamar yarta, ban maida sati a gidan ba aka canja min makarantar da nake zuwa makarantar masu kudi makaranta mai kyau. Mukan zauna musha hira da ita idan na dora kaina a jikinta sai na yi ta kuka, ashe dai ni ma wata rana zan samu masu sona. Ta tambaye ni a ina na iya duka yaruka hudu da nake ji, na fada mata yaren Igbo da yarbanci daman kowa ya iya a Lagos domin mun tashi mun ga su ake amfani da su, turanci kuma ba iya a makaranta, hausa kuma na koya a gurin Oga Shakur da yaronsa da ya kasance bahaushe. Kwakwalwata tana da saurin fahimtar abu, kusan duk abun da na sakawa raina zan iya na kan iya cikin kankanen lokaci, haka ya saka tun ina primary har secondary school ni nake dauko ta daya aji. Sai da na yi wata biyu a gidan sannan na samu damar aron wayar mai aikin Momy kamar yadda muke kiranta na kira number Khaleepa da tuni na haddaceta, da na kira shi kamar zai yi karamar hauka saboda yadda nake ta jiran kirana a koda yaushe, ni kaina sai da na yi kuka, daman dauriya kawai nake amman duk tsawon kwananki da na yi a gidan da jindadin da nake samu bana jin farinciki saboda bana jin muryar Khaleefa. A ranar be iya bachi ba sai da na fita na tambayi mai gadin gidan ya fada min yadda zan masa kwatance ya zo ya same ni a gidan muka gaisa, a nan kam ban da fargaba duk kuwa da kasancewar ban gama sanin halin matar ba, amman dai da alama tana da fahimta kuma tana da kirki ina ganin kamar da alama zata bar ni na auri Khaleepa, ya kawo min waya a ranar keypad da sabon layi saboda ba zai iya jure rashin jina ba, ba tare da fargabar komai ba na karba na shiga da ita gida, ban boye mata ba na nuna mata wayar na fada manta wanda ya kawo min. "Saurayinki ne" Na daga mata kai ina murmushi ita ma ta yi murmushi. "Ashe na kai ga buduwar, bari na fara shirin aure" Na rufe ido ina dariya, ta tambaye ni sunansa da kuma inda muka hadu na fada mata komai, a take yanayinta ya sauya, sai ta karbi wayar hannuna tace zata aje sai idan mai gidanta ya dawo kasancewarsa matafiyi, idan sun tattauna abun da ya dace zata ba ni wayar, ban jidadi ba amman haka na daure na cigaba da waya da Khaleepa da wayar mai aikinta. Wata rana sai ta kira ni tare da mijinta suka zauna da ni suka fada min ilolin da suke cikin auren musulmi, ta yi ta fada min kalamai marasa dadi akan musulmai da kuma yan arewa, ita da mijinta burinta su cusa min kyamar musulmi kamar yadda ake yi sauran yara, ta fada min na yi kankanta da fara soyayya a yanzu, kuma Khaleepa ba ajina ba ne domin shi achaba yake yi, ni kuma a yanzu na kalli irin gidan da nake rayuwa. Soyayya bata da hankali bata ji bata gani, duk ban ji abun da suka fada min ba, a haka na nuna musu ni dai ina son Khaleepa ba zan rabu da shi ba, sai suka saka min dokar ba zai sake zuwa na fita ba, kuma ba zan sake waya da shi ba, haka kuma ba zan ma taba aurensa ba, idan ma ina wannan tunanin na aje. Suka saka min kulli mai tsanani bana zuwa koma'ina daga gida sai makaranta sai kuma idan mun fita siyaya, ko kuma ranar Sunday muna fita zuwa church. Sun min gata sun nuna min soyayya suna kashe min kudi amman duk bana gani saboda Khaleefa ne a rayuwata, kullum cikin kuka da damuwar rashinsa nake, ban sani ba a lokacin ashe hawaye ba su cancanci zuba saboda shi ba. Wata rana mun je Church, na sulale na ari wayar wata mata na kira shi na fada masa dokokin da Momy ta saka min ita da mijinta kuma sun ce ba zan aure shi ba, a wayar ya rika kuka yana fadin Innalillahi idan na rabu da shi zai halaka zai mutu, ni ma na rika kuka ina jin kamar ma na kashe kaina domin ban taba soyayya da kowa ba sai da shi. "Emily zaki iya aurena a kowane hali?" Na rasa taya zan amsa masa. "Amman ba addininmu daya ba Khaleepa" "Karki damu da wannan addinin musulunci ya yarda mu auri wanda ba addininmu daya ba, kuma na san idan kina so na zaki musulunta domin ki aure ni" "Zan iya ina kaunarka sosai Khaleepa" "Emily zaki iya bina mu gudu? Idan ba haka ba ban san wata mafita da nake da ita ba, daga wannan wayar ma ban san ta ina zan sake jin muryarki ba, kuma muna nan ba za su bari mu kasance da juna ba" "Idan mun guda ina zamu je" "zan gudu dake mu koma kaduna gurin iyayena, zaki zauna a can a daura mana aure mu zauna a can" "Ina tsoro ba zan iya ba Khaleepa" Duk wata kalma da zata raunata ni ta sanyaya min guiwa da zuciya sai da ya nemo ta ya fada, amman ban yarda be shi ba. Na koma gida ina ta tunanin mafita amman ban samu ba sai wanda ya kawo, gashi kaunarsa sai kara ruruwa take a zuciyata, da kaina na samu Momy a dakinta ina kuka na fada mata ina son Khaleepa ta bar ni na aureshi, madadin ta tausaya min sai tace idan na sake mata maganarsa sai ta min duka kuma ko zan mutu ba zata taba bari na auri musulmi ba. Ranar mutuwa ce kawai ban yi ba tsabar bakinciki da nadamar kin bin shawarar Khaleepa na bishi mu gudu. Da sati ya zagayo muka je church Momy ta saka pastor ya dafa kaina ya rufe ido yayi min addu'a, bayan an zauna zaman church ana tsaka da wakar church na saci kafa na fice daga cikin church din daman Momy tana zama a gaba ne mu muna zama baya. Na fito na ari wayar mai gadin church din na kira Khaleefa na fada masa yanzu na amince zan bishi mu gudu. Sai ya fada min inda zan je na jira shi, haka kuwa aka yi ba bawa mutumen wayarsa na fice daga church din na tari okada na fada masa inda zai kai ni, ko da na isa na samu Khaleepa a gurin tsabtsab da shi kamar kullum, yana jirana. Ya sallami mai okadan ya goya ni ya tafi da ni wani kangon gidan ya aje ni a nan, be dawo ba sai dare ya dawo da kudi mai yawa ya fada min ya siyar da babur dinsa kudin ne zamu hada da wanda ke gareshi mu tafi garinsu. A gurin ya bar na kauna ni kadai shi kuma ya kwana a inda ya saba washe gari da asuba dai gashi tare da kayansa, ba bishi muka isa tasha ni da shi muka kama hanyar Kaduna. Shi a tsorace ni, a tsoroce hankali be kwanta ba sai da muka isa cikin garin kaduna. Garin da ban taba zuwa ba kuma ban taba saka ran zuwa ba ko a mafarki sai ranar. A cikin tashar ya saka ni saka hijabi, kusan ko'ina muka bi kallona ake saboda farin fatana ba fari ba ne na sauran mutane, fari ne mai haske sosai da ya fi kama da na turawa ga kuma idanuwa blue. Tashar muka bari muka isa wata dabam muka hau motar garinsu Khaleepa, garin da basa son tubaben, basa marasa ba ni, bana tausayin kaddara da kuma kuskure da na aikata, garin da suka koya min hankali da sabon karatu, suka maida ni wulakantacciya. _________________________ A jiya na yi mistake a page 17, na yi page din ne kamin na canja akalar labarin, bayan na canja kuma sai ya zama na manta ban yi editing ba, wadanda suka karanta wanda na yi ba edited one ba, za su ga Nace Emily baka ce, ku manta wannan kuskuren ku shafe shi a Kwakwalwarku, ni yar adamce ina kuskure dole na. Emily fara ce kamar yadda aka fada tun a farkon labarin. Shin zaku iya fada min abu daya zuwa biyu da kuka fahimta a page din yau kawai? Kuna son a karo? Zo na gani a kasa, ance da kare ana biki a gidanku yace mu gani a kasa😁 Ma'ana ku suburbudo comments na suburbudo muku pages🤙 Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Karku manta ku yi Sharing* [5/1, 8:59 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 2️⃣0️⃣ Mun sauka garin Rizaga (Sunan garin kirkiren ne) Da dare sosai kusan sawun mutane da yawa ya dauke. Daga tashar garin ya dora ni a babur shi ma ya hau daya muka kama hanyar gidansu, tafiya muka yi mai nisa sannan muka isa. Da duk inda muka bi muna ganin mazan garin kwance wasu a bakin kofafin gidajensu wasu kuma a fili. Bayan mun sauka ya biya mai achaban su biyu sannan ya nufi kofar gidan data kasance katuwa da aka yi da gambun kwano. "Su waye a nan?" Na ji an tambaya, sai Khaleefa ya nufi daya daga cikin maxan da suke kwance a wajen yace ni ne baba, mutumen ya dauko fitilarsa ya haska fuskar Khaleefa duk kuwa da kasancewar akwai hasken wutar nepa. "Lafiya? Hamza kai ne a dare haka?" "Lafiya kalau Kawu, bari na shiga ciki" Sauran mazan duk suka tashi zaune suna gaisawa da shi suna tambayar lafiya ya ce musu lafiya kalau. "Da muka a kuke tare?" Ya tamabaya bayan ya haska fuskarta. "Zuwa da safe za ku ji komai ba Kawu" Ya nufo ni muka doshi cikin gidan, Tun kamin mu shiga gidan na gama fahimtar gidansu family house ne, ashe kuwa na canka daidai da muka shiga ciki sai na bangare bangare na gidan, yana gaba ina biya har muka isa bangare da mahaifiyarsa take, tana cikin bachi ya tasheta ta zabura tana daura dankwali. "Hamza lafiya? Saukar dare? Kuma baka fada mana zaka zo ba?" "Lafiya kalau Inna, ga dai bakuwa na zo da ita a bata gurin ta kwanta, kuma idan akwai abinci a bata ta ci zuwa sa safe za mu yi magana" Ta kalleta daga sama har kasa a lokacin ina sanye da jean sai hijab din da Khaleepa ya siya min "Sannu da zuwa zo nan ki zauna" Na gaisheta ta amsa min, na karasa na zauna a inda ta nuna min zuciyata cike da tsoron abun da na aikata da kuma wanda zan tarar. Tuwon gero aka kawo min da miyar kuka, luma daya na yi na gagara ci domin ban san miye tuwon gero ba a lokacin, miyar kukar ma ban taba jin sunanta ba sai a ranar. Haka na kwana da yunwa, washe gari tun da asuba na ji garin ya karade da kiran sallah, Wallahi idan na ce ban jidadin sautin da na ji ba na yi karya, natsuwa ta sauko min, sai na ji kamar ina cikin wata duniyar ta dabam... A daki aka maida min shimfidar su kuma suka yi sallah a ciki, tun da na shiga bachi mai nauyi yayi gaba da ni, ban farka ba sai karfe tara na safe, ban sani ba ashe Khaleefa yana nan yana rigima da iyayensa akan cewar ba zai maida ni domin shi a yanzu tsoron komawa garin Lagos yake, kuma ni na yarda na biyo shi ba cilasta ni yayi ba. Suka kira ni aka tsare ni a gaban manyansa suka tambaye ni, da amincewata ya taho da ni na fada musu cewar eh ni na mince masa na ce masa mu gudu domin iyayen dake rikona ba za su bar ni na aure shi ba, kasancewar shi musulmi ne, suka sake tambayata shin zaki musulunta ki auri danmu? Na amsa musu a take cewar eh zan musulunta. Sai suka yi farinciki suka nuna jindadinsu musamman mazan, amman mahaifiyarsa kamar bata yaba da hakan ba. Da yamma aka aiko mai gari yana neman yarinyar da aka zo da ita da kuma Khaleefa. Muka tafi har da iyayensa irin bayani na yi a nan shi na yi a can shi kuma haka, mai garin ya gamsu yace gobe idan Allah ya kaimu za a kai ni gurin limamin garin na musulunta kuma a daura mana aure, suna tambaye ni wane suna kike so nace musu Aisha Muhammad, haka nake son sunana ya zama. A lokacin farinciki ne kamar ragagge ne, sai ya zama ban ji wani dauki na auren ba sosai ba, wata kila kuma ishara ake min cewar babu alheri a ciki. Yadda mai garin ya fada haka aka aiwatar washe gari aka kai ni gurin wani limani na musulunta kuma suka daura mana aure, kusan kowa zuwa yake kallona har sai an boye ni, abubuwa biyu ke kawo su, jin cewar ni ba musulma bace da kuma yanayin hallitata. A dakin mahaifiyarsa na fara zama kamin ya gina mana karamin dakin da zamu zauna a tare a bangaren mahaifiyarsa, ya siya mana katifa da zanen gado da dan abubuwan bukata na aikin gida domin ni ba ni da kowa kuma bani da kudin siya. Sannnu sannu ya fara koya min sallah karatun sallah da wasu gajerun addu'o'i kasancewata mai saurin gane abu sai na fara fahimtar yadda zan yi ibada ta. Kusan a lokacin bani da wata matsala kamar yadda idan na gaishe da mahaifiyarsa take amsa min kamar dole, ga kuma rashin iya girki, ya siya min gawayi da murhun gawayi ina girki da shi, akan girka shimkafa ko taliya, ko indomie na girka chabewa take saboda ban taba girki ba, shi kuma yana da saurin fushi, ko kirana yayi na dade ban amsa ba ko ban zo ba sai ya fusata, ya fara fushi da ni, ko gaba, idan ya fara gaba da ni sai ga na zama kamar marainiya yake kula ni, domin ba ni da kowa a garin, gashi mutanen gidan sun ki su saba da ni, ni ma naki sakewa da su, kullum ina ciki daki. Abun da na fahimta bayan aurenmu shi ne Khaleefa yana da farin jinin yan matan garin, shi ka kansa ya fada min kuma kanwarsa da ke dan leko ni muna taba hira wani sa'in ta fada min. Ban kuma yi mamaki ba domin yana da kyau ni kaina kyaun ne ya dauki hankalina a lokacin, gashi ya iya wanka idan ya shirya ba zaka taba yarda a kauye yake zaune ba, su kan shigo gani na wasu wasu kuma idan na fita tsakar gidan nake ganinsu ko su gan ni. Akwana a tashi dan abun da Khaleepa yake da shi ya kare domin ciki muke ci, ga mahaifiyarsa ko gishiri ya siyo min sai ta karba ta raba biyu ta bani rabi, taliya ma idan daya ce to rabi zamu aje mu bata rabi. Da kudinsa suka kare sai ya rika karbo mana abincin da suke, da safe kunu ko dumame, da rana kuma sai dai ayi kwado ko kuma asiyo abunci na siyarwa a ciki da dare kuma tuwon gero. Bana iya cin tuwon kunun ma kadan nake sha domin babu suga, da rana kuma sai na wuni da yunwa, na ga alamar yunwa zata halaka ni idan aka ba ni tuwon geron sai na dukula na hada da ruwa na rika hadewa ba sai na saka miya ba. Washe garin ranar Inna da kanta ta sallama min na fito ta ba ni tabarya wai ai da ni ake cin abinci yanzu, ta saka ni turfe ban iya ba amman haka na rika yi ba, daker na samu yayi na kwashe mata, na dawo daki ina duba hannayena da suka yi kwancin jini suna ciwo. Sai yace "Da sannu zaki saba, mu a nan garin yawanci duk gidan da ake cin tuwon gari a gidan ake surfe, Inna ma bata yi, amman da kin lura dayan bangaren ai har na siyarwa suna yi" Ban ce masa komai ba, gudun kar na yi wata maganar ya fusata. Wasa wasa matar nan ta fara sani surfen siyarwa idan aka kawo kudin kuma sai ta karba tace za a hada a kudin cefane. Gashi haka nan nake wuni da rana babu komai a ciki, domin Khaleefa be da kudin siya min abinci yanzu, sai can wata rana idan an yi kwado ta aiko min idan na ci cikina yayi ta ciwo, da dare kuma abinci kadan nake ci haka da safe. Kan kace me na rame na lalace ba kadan ba, idanuwana suka cicciko suka fito fuskar ta koma karama, kassana suka bayyana. A lokacin ne Khaleefa ya dauki katifar dakin ya siyar mahaifiyarsa ta hada masa da wasu kudi yayi kudin mota ya tafi Nijar gurin nema, ya bar ni babu komai sai damuwa, kullum da fargabar daka nake kwana nake tashi, ga abinci bana iya cin na kirki. Sai aka fara rade raden wai ina da kanjamau shiyasa na yarda na biyo shi. Wata rana ina cikin surfe matar da muke zaune da ita gida daya wadda take kamar matar kawunsa ce ta dube ni tace. "Aisha amman kamin Khaleefa kina da wasu samari ko?" Na yi murmushi ina gyara rigar atamfar da ta yi min yawa, daman tufafina gaba daya kala shida ne a gidan. "AA ban taba yin saurayi ba sai Khaleefa" "Ban yarda ba gaskiya yadda kike da kyaun nan haka ai sai maza sun yi ta kawo miki hari, ko da yake ance ku baku dauki wannan komai ba, ance dan miji ya yayi mu'alama da ku ba komai ba ni shiyasa sai an gwada mace ake aurenta" "Ba kowa ba, wasu dai suke yin haka" "Toh Allah yasa wannan rama taki dai ta yi yawa" Ban fahimci inda ta dosa ba dan haka ban maida hankali akan zancenta ba, na gama surfen na dauka na wanke na kawo na aje na nufi dakina. Na shimda tabarma na dora zane na kwanta, nan da nan sai bachi yayi gaba da ni, can cikin bachin na ji ana tashina kanwarsa ce wai na tashi na yi sallah, na tashi ina jin kamar na yi kuka, domin sallah na daga cikin abubuwan da suke wahalar da ni a lokacin saboda rashin sabo haka dai nake daurewa na yi.   Bayan ta fice na dauki buta na zagaya bandakin, kamar ance saurara ki ji sai na ji muryar mahaifiyarsa kasancewar bandakin yana like da dakinta ne ta gafe. "Badan halin Hamza na son karya, shi gaba daya rayuwarsa ta karya ce ta son burge mutanen, ka tsallake garinku jiharku ka tsallaka har kudu kudun ma Lagos ka dauko mata, Allah kadai ya san dalilinta na biyosa, wannan ramar da take yanzu na fara tsorata da ita" Na kai hannu ma dafe zuciyata idona ya cika da hawaye, can na ji wata kanwarsa mai da da zo ta karba mata. "Yawanci fa yan kudun nan ance idan suna da hiv suke bin yan arewa saboda su lika musu, gashi nan a gari sai rade rade ake wai Ya Khaleefa ya dauko mai ciwo, wasu har da cewa wai ciki yayi mata aka korosu" "Ai yaje dai ya dawo, aure zan saka ya kara yaushe zai zauna da zabiya kalli idonta ma kamar matsafiya, ance a can fa kowa da kalar tsafinsu na gado, kuma nan gaba idan suka haihu ai zata iya kwashe yaranta ta koma can" Kasa fitsarin na yi na fito na dawo dakina na zauna na ci kuka na har na koshi. Sannan na fito na yi sallah, kalaman da na ji ya saka na ja jikina daga mutanen gidan domin idan wani abu ya faru za su iya cewa ni ce. A lokacin damuwa ta kara yi min yawa gashi tun da ya tafi be taba kiran waya yace a ba ni mu gaisa ba sai dai ya yi waya da mahaifiyarsa. A haka ya shafe shekara daya be waiwaye mu ba, sai dai yayi mana aike idan kuma ya aiko komai yana hannun mahaifiyarsa babu wani canji. Yanayin yadda ya turo kudi aka siya masa fili a kusa da gidan aka fara masa gina na fahimci ko wane kalar kasuwanci ko aiki yake can toh ya karbe shi, ina ta jindadin ina murna mijina zai gina gida mu koma a can mu tare, ashe ba ni yake yi ma ginin ba. Ranar da na yi ma mahaifiyarsa maganar ina son ta rika ba ni kudin surfen da nake na rika siyen abinci ranar ta yi min tatas wai duk abun da take min bana gani, ba zata sake min komai ba daman hakkin ciyarwarta ba a hannunta yake ba, har tana fadar musuluntar kawai na yi amman zuciyar kafirarce a kirjina. Da mutanen gidan suka taso madadin su shiga tsakani su bawa mai gaskiya gaskiyarsa sai duk suka goya mata baya, wasu suka dauki gaba da ni ciki har da kanwarsa da nake shiri da ita. Tun daga ranar ba a sake bani abinci ba, sai dai idan na yi surfe dan abun da na samu sai na siya abinci da shi, bayan surfe sai na rika hadawa da wanki domin na samu kudin su min auki, wahala sai ta taru ta yi min yawa har wasu kujera suka fito min kamar na sauyin ruwa kamar na wahala. Idan na samu matsala kadan da mutanen garin sai min gori akan kudin surfe na ko wanki, ko aika ko kuma wani abun dabam, sai min gori, wasu su zage ni ni da iyayen da ban san a ina suke ba, wasu suce min zuciyar kafirar ce tana cikin kirjina, wasu suce min tsintacciyar mage. Gashi idan ina son abu sai dai na fita na yi da kaina, babu mai bari na aiki danta, idan na fita mutanen su yi ta kallona. Ana sauran wata uku ya dawo wata rana ya kira waya sai aka kawo min na karba da murna ina kai masa gaisuwa sai ya rufe ni da fada. Wai an fada masa na yi fada da mahaifiyarsa na ci mata mutunci, kuma ina fita yawon gantali a cikin unguwa, shi ba zai dauki wannan ba. "Ba zan iya daukar wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar kafiran lagos ba, yadda kike tubababiya dole ki dauki halinmu da al'adarmu wannan kiristancin da bakin hali ki aje shi a gafe, ba ni da kamar mahaifiyarsa" "Baka saurara ka ji bangarena ba, yadda kake da addini Khaleefa be kamata ka yanke hukunci ba tare da jin dayan bangaren ba" "Bana son jin bangarenki marar kunya, rashin tarbiyace zaki nuna min ko? Da an yi magana kice baki da kowa sai ni baki da kowa amman baki kokarin rike mahaifiyata? An fada min kuma gaba kika da kowa a gidan, ki gyara halinki Wallahi kamin na dawo Aisha" Ban iya cewa komai ba na fashe da kuka domin shi dai ba zai saurareni ba yan'uwansa kuma ba za su fada masa gaskiya ba. Madadin ya rarrashe ni sai ya kashe wayarsa na mikawa kanwarsa wayar ina kuka. "Baki san dadin yan'uwan ba, saboda baki tashi da kowa ba, kuma baki samu zuciyar kwarai ba shiyasa kike son idan ya dawo ya bata da kowa saboda gaki yar gwal ko?" Ban rama kalma daya daga maganarta ba domin a lokacin ban iya maida marta ni ba, kallonta kawai har ta fita. Haka na cigaba da rayuwa ta bakin ciki a gidan suka gade min kai bana jindadin zama da kowa, idan suna surfe su ta yi min haibaici tun bana fahimtar habaicin na su har abun ya fara damuna. Ina kofar dakina ina wanki mahaifiyarsa na madafa tana girka shimkafa da miya, sai gashi ya shigo dauke da kaya yayi burun burun gashi duk ya tarar masa kai yayi jiki sosai sai dai kuma yayi duhu a lokacin. Da gudu na je na rumgume shi ina murna, a take mahaifiyarsa ta daka min tsawa. "Ke ba mu san wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar ta mutanen Lagos ba karki bata mana tarbiyar gida" Na sake shi ina murmushin karfin hali, domin idan na ce ban ji zafin maganarta ba na yi karya, ta taso ta sauri ta karbe kayan da ya zo da su ta kai dakinta kanwarsa ta kai masa ruwa yayi wanka, ya shiga dakin mahaifiyarsa ya canja kaya ya gaisa da mahaifinsa da yake kamar fanko a gidan, sannan ya shigo dakina ina ganin haka na tattara wankin na aje na bi bayansa wai ni mai miji. Abun da ban sani ba ashe shigarsa dakin ta shirya masa karya da gaskiyar abun da ban yi ba, sai ganin na yi yana ta hade min fuska. "Sannu da zuwa tun da ka tafi ko waya babu Khaleefa" "Tafiyata ai ta miki rana domin gashi nan kin samu sana'a kina yi, kin fallasani a gari kowa ya san bana iyar da ke" "Ko kawa ba ni da a garin nan balle na fada sirrina, ban taba fadawa kowa baka ciyar da ni ba, ban taba ba khaleefa" "wannan wanki da kike ai da shi da fadar duk daya ne" "ina yi saboda na samu abun da zan ci" "Matsalar auren yare kenan baku da tarbiya baku da rufin asiri ga rashin yarda da kaddara" Na nuna kaina ina kallonsa zuciyata na raya min kamar na Khaleefa da na sani ba ne. "Khaleefa ni kake fadawa wadannan maganganun? Ka chanja min ba, yanzu duk ka manta irin sadaukarwa da na yi? Ka yi tafiya shekara daya da wata uku amman daga dawowarka sai ka rufe ni da fada kana ta bani rashin gaskiya?" "Okay mahaifiyata zan bawa rashin gaskiya ke kuma na baki gaskiya kenan? Da kika zancen sadaukarwa sadaukarwar me kika yi? Ai ni na sadaukarwa ni da na dauko ki na kawo ki cikin yan'uwana, na musulumtar da ke, ba dan haka ba ai da yanxu ko mutuwa kika yi wuta zaki tafi" Kalleshi kawai na sauke kaina kasa kuka, daman idan ba kukan ba to me zan yi. "Tun da kin zabi haka, ki ta zaman wankewa jama'ar ga tufafi, sai ki ciyar da kanki" Ya fada, ashe kuma zai iya, sai gashi babu abun da ya sauya bayan dawowarsa, sai ya zama kamar yana kyamata saboda kurajen dake jikina na sauyin ruwa da kuma wahala, mu'amalar aure ma dan kawai ta zame masa kamar dole ne da ko kallona ba zai yi ba. Idan yana son abinci mai kyau zai fita waje ya siya ya ci ko ya siyo mahaifiyarsa ta girka masa... Wata rana na kebe kaina a daki ni kadai ina ta kuka, da nadamar da somin tabi ne a lokacin." ***. ***. *** Emily ta mike tsaye hawaye shar a fuskarta ta nufi dayar kujerar dake office din ta zauna jiki ba kwari ta kalli Aliyu dake kallonta cike da tausayi marar misaltuwa ta ce. "Akwai matukar zafi, da bacin rai a auren mutumen da baka so, akwai da ci a auren mutumen da aka cilasta masa aurenka, akwai tsananin bakinciki da nadama a auren mutumen da baya sonka, ba ka son shi...! Yawancin irin waɗannan aurarraki sakamakonsu nadama ne, da dana sani, wanda kan iya haddasa ciwon zuciya da kan iya silar ajali mai shi. Amman ina makomar auren da aka gina akan soyayya? Miye tukuicin kyakkyawar alaka da kaunar da aka gina aure da ita? Shin minene ribarta?' Soyayyah ruwan zuma! Haka na ke jin sunanta a bakinsu, haka na ke kallonta. Hakan yasa ni shiga dakinta. Da fari tai min marhabun tare da yi min shimfida mai laushi, sai da na mika duka karfina na kwanta a ciki sai ta shammace ni, ban sani ba ashe a saman k'aya da k'usoshi tawa soyayyar tai min shimfidar, tai min matashin kai a saman narkaken garwashin wuta, daga lokacin sai na soma kiranta da dayan sunanta, wato soyayya ruwan guba! Ruwan daya fi ko wane ruwa haɗari a duniya, ruwan da kan aika mai yinta a lahira nan take ta, ruwan da wanda ya dandana ta zai gwammace mutuwa da rayuwa...' Na yi zaton idan na samu matsala da Khaleefa mutanen garin ko na gidan za su rike ni kamar dai yarsu ko yar uwa domin sun san ba ni da kowa, ban sani ba ashe ni shashasha ce, idan na samu matsala da Khaleefa har ta kai ga duka Wallahi babu mai raba mu sai mazan garin idan suna cikin gida, ta zama na yayi masa dadi sai ta kai ko numfashi na yi da karfi sai ya rufe ni da duka, idan na yi magana yace na kai karar duk inda zan iya, ko yace na fadawa duk wanda nake ganin zai zame min gata, wai takamarsa kawai a lokacin ba ni da kowa kuma ba ni da gurin zuwa. Tun kamin ya dawo ake gina, zuwansa karasa kawai yayi, aka yi fanti aka saka wuta, sati daya da gyaran na ga ana ta hada hadar biki a gidan, ashe aure Khaleefa zai kara aure be fada min ba sai ranar da aka daura masa aure, ina zaune a dakina na ga an shigo da katifa sabuwa ya siyo min, na karba na yi godiya na shimfida zanen gado sai ya jefo min turmin atamfa guda daya, a nan na san hausawa suna da wata al'ada wai idan namiji zai kara aure yana yi ma matarsa ta gida kayan fadar kishiya. Na karbi atamfar na masa godiya sai yace. "An daura aurena yau, wannan atamfar fadar kishiya ce, a kuma ga katifa nan na siyo miki a al'adar garin nan ko kuma mu arewa idan aka yi aure ana kawo yarinya da komai, ke kuma na ga ba wasu kayan kike da su ba, dan haka ki zauna a nan tare da su Inna, anjima za a kawo amarya a sabon gidan da na gina, bana son tashin hankali kun zauna lafiya, ki bita sau da kafa kin ga dai baki da kowa a garin nan ita kuma yar gari ce" Ina daga zaune na daga kai na kalleshi. "Ba zaki ce komai ba" Bance masa komai ba bayan kallonsa da nake har ya gaji ya kada kai ya fice. A lokacin na sauko daga kan katifar na ji ba zan iya kwanciya akanta ba, na fara yi ma kaina wadansu tambayiyin da ba ni da amsarsu. "To wai ni mi na yi ma iyayena suka jefar da ni? Miyasa na gujewa matar data rike ni kamar yarta? A wane dalili na tsallake shawararta da dokokinta? Na yi sadaukarwa ga wanda be san darajata ba, na bar ki na zabi iyalin da ba su san kimata ba" Na kwanta a gurin ina wani irin kuka mai karfi ina jin kamar zuciyata zata fashe... Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 Kuma karku manta ku yi sharing [5/4, 6:26 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 2️⃣1️⃣ Ban san a addinin musulunci idan namiji yayi aure yana sati a gurin amaryarsa ba idan budurwa ce, idan kuma bazawara ce kwana uku, dan haka da aka kwana biyu ban ga mijina ya shigo dakina ba sai na sami wata makociyarmu da nake siyen kayan girki gurinta wato Malika ita ma dai yarinya ce sai dai ba kamar ni ba domin tana da yara har uku. Na fada mata cewar ina son ta rakani gurin mai gari saboda ina son na kai karar Khaleefa, ita kam bata yarda taje ba wai gudun kar ace ita take zuga ni nake abun da nake, amman ta kwatanta min gidan kuma ta dorani akan tsarin yadda zan yi magana da shi idan na tafi. Ina fita gidanta ban zame ko'ina ba sai kofar gidan mai gari na aika a sallamo min shi sai iyalinsa suka ce na shigo ciki, na shiga na yi musu sallama suka amsa muka gaisa na gabatar musu da kaina sai dayar tace. "Oh ke ce wadda aka ce an musuluntar ko?" "Eh" Na amsa ina maida kaina kasa, babu jimawa Mai garin ya fito muka gaisa na gabatar masa da korafina cewar Khaleefa ya aje ni a daki daya ita kuma matarsa ya kaita gidansa kuma ya siya mata abinci mai kyau ni kuma ya daina ba ni, gashi kuma kusan kwana biyu be shigo dakina ba, ko da ya shigo gaishe da iyayensa babu ruwansa da dakina, ga kuma duka da yake yawan yi min. A take Mai garin ya aika aka kirashi tare da iyayensa na zayya abun da na fada da farko, sai ya tambayi ba'asi, Khaleefa yace karya nake yana bani abinci kuma baya shigo bangarena ne saboda ai kwana bakwai ake idan aka aure budurwa, ban san mace na zuwa da abinci ba idan aka aureta sai ranar. Yace da abincinta ta zo da komai nata, kuma wai bana masa biyayya abu kadan zan fara cewa ba shi da adalci ina masa ihu da Allah ya isa. Iyayensa ma suka goya masa baya mai garin ya rufe ni da fada. "Ke mu fa irin tarbiyar da kuke a can ta arna ba ita muke a nan ba, tun da har kin yi aure kuma kin musulunta ya kamata ki watsar da wannan dabi'ar" Mahaifiyarsa tace "Ai matsalar auren tun farko bata san musulunci ba ko kuma bata tashi a cikinsa kenan, su fa tarbiyar su da auratayyarsu dabam take, musulunci ma ai suna yi ne kawai a baki" Mai gari ya fadi nasa iyayensa da shi kansa su fadi na su, na rasa ya zan yi sai kuka nake ina bashi hakuri. Da muka dawo gida sai ya fara dukana irin dukam da be taba min ba, dukan da zaka rantse dansa na kashi ko na aikata wani criminal abu, ina bashi hakuri yana duka wai abun nawa ya wuce ina fada a makota cewar yana bari na yunwa da sirrin gidansa ya kai har na dauki kararsa na kai gurin mai gari a nemi tozartashi. Duka yayi min ba na wasa ba, yana dukan yana min gorin wai daga ya taimaka ya tsamoni daga wuta da yanzu idan na mutu wuta zan tafi. "Iyayenki ma suna can cikin azaba, saboda sun yi shirka da Allah, kuma Allah kadai ya san ta hanyar da aka same ki, shiyasa kike butulu, matar ma data rike ki yanzu ai gudowa kika yi kika barta, ni kuma na dauko ki na musuluntar da ke na aureki amman kina min butulci, idan ba ni ba wane namiji ne zai auri arniya ya kuma ba a kawo ta da komai ba, marar asali ma irinki" A lokacin ne kalamansa suka fi yi min zafi da daci fiye da dukan da yayi min, na ji kamar ace ina da ikon da zan zare numfashi daga jikina na manta da kowa da komai. A daren na sha kuka washe gari na dora haka na kwashe kwana uku bana iya komai sai kuka. Abun da ban sani ba be sani ba shi ne, ashe lokacin da ya doke ni ina dauke da cikin dansa, shi be sani ba saboda ba nice a gabansa ba, ni kuma tunani da tashin hankali da nake ciki be bar ni na ankara ba, daukewar da al'ada ta yi min na tsawon wata hudu ban gane ba saboda hankalin ba nan yake ba, gashi kuma cikin fari ne ban san komai akan ciki ko haihuwa ba, domin a gidan marayun da muke zaune ban da karatu da sana'a ban maida hankali gurin koyon komai ba ko kuma sanin wani abu wai shi ciki da haihuwa. Sai da ciki ya kai wata biyar sannan na gane cewar ina da ciki shi ma Malika ce ta fada min. "Wata nawa ne Aisha" "Ni ban sani ba, ni na dauka ko yunwar da nake fama da shi ne ya janyo cikina yayi girma" Ta yi dariya. "Kai Aisha kina da wauta, ga abu har ya fito yaushe rabon da ganin al'adarki?" Na tsaya tunani ni kam bana ma iya tunawa. Ta bani shawarwarin yadda zan yi kuma ta fada min na tafi asibiti. Na dawo gida ina ta murna da dare da Khaleefa ya shigo na masa maganar sai yace min ai ya sani, shi mahaukaci ne da ba zai gane ba. Na yi mamaki ya gane amman be taba min maganar ba kuma be nuna min komai ba? Da na masa maganar zuwa asibiti sai yace shi ba shi da kudi yanzu na bari sai gaba idan ya samu kudi. Ma zan yi a lokacin idan ba hakuri ba, na san ba dan ba shi da kudin ba, domin yana cikin shirye shiryen bude shago a kusa da gida ne, idan kuwa ba shi da kudi ba zai bude ba, nice ba ya son kashewa kudin, sai na bawa zuciyata hakuri na saka masa ido, na jidadi samun ciki domin ya dauke min damuwa sosai ban sani ba ko dan saboda ina da son yara ne ko kuwa dai saboda ina kurciya ne, wata kila kuma saboda ina jin cewa zan samu iyali ne, ma'ana dai zan samu dan'uwa na jini daga gareni. Kusan sai ya dauke min rabin damuwa da tunanin da nake idan na ji motsinsa sai farinciki ya baibaiye ni. Ina cikin wata na shida ne da ciki, na ji yan'uwansa suna shelar Amaryarsa Hindu tana da ciki, shi kansa na lura da farincikin da yake da cikin, amman a nawa shi da yan'uwansa ba su nuna min jindadinsu ba kamar wanda zata haihuwa ba da igiyar aure ba, ashe wai kallon suke wata rana zan iya komawa kafira saboda iyayena da asalina ba na musulunci ba ne tun farko, kuma zan iya komawa da rayana, kusan a lokacin zamana a gidan da kuma aurena kamar ya zamewa Khaleefa dole ne. Wallahi akwai zafi akwai ciwo, ka ga mijinka yana zumudin zuwan wasu yara amman ban da naka, bayan wankin da nake na siyarwa da ya dauke me sakamakon abincin da Mahaifiyarsa ta dawo tana ba ni a kullum babu wani abu da Khaleefa yake min, ko dan siya min wani abun kwadayi babu ruwansa. Ashi ma kwadayi mace mai ciki guri yake samu, domin ba kasafai nake jinsa ba, idan ma naji sai dai na yi hakuri ko kuma na tafi makota gurin Malika na samu idan tana ta ba ni. Amaryarsa ita take girkinta a ranar girkinta ni kuma aka fashe da cewar ban iya girki ba sai idan mahaifiyarsa ta girka ta ba ni. Da cikina ya shiga wata na bakwai sai na fara rashin lafiya da amai domin ban yi laulayi a farkon cikin ba, da na masa maganar tafiya asibiti sai yace min na bari sai wani sati. Haka kuwa na hakura na zubawa sarautar Allah ido. Wata ranar jumma'ah gidan babu kowa sun tafi bikin yan'uwa mazan musu wasu sun fita wasu kuma sun tafi masallaci, ina zaune cikin dakina bayan sallah la'asar daya daga cikin matan gidan da bana magana da ita saboda yadda suka hade min kai. Sai gata a dakina da sallamarta na amsa ina kallonta sai ya duka ta ce. "Aisha, na zauna na yi nazari abun da ake miki a gidan nan an zalince ki, ki yi hakuri ki yafe min, ban gane ba sai da kika samu cikin nan, kalli yadda ake farinciki da cikin Hindu amman ke kamar kin kumsa cikin shege, kuma Hindu tana zuwa asibiti amman ke baki zuwa" Ta kowance gefen zagenta ya ciro kudi yan dari biyu da naira dari ta miko min. "Ungo wannan duku uku ne, ki shirya ki tafi asibiti a duba lafiyarki da abun da yake cikin ki" Na saka hannu biyu na karba na mata godiya sai ta gargade ni akan kar na fada ma kowa, ta miko min takardar da number waya a rubuce. "Kin ga number wayata, idan kina son magana da ni ki tafi wani guri ko makota sai ki kira ni ki tambaya, kin ga ba zai yiyu mu yi magana da juna idan Inna na nan ba, sai mijinki da ita kanta Inna da sauran jama'ar gida su ce na yi munafurci, amman idan kika fita makota kika ari waya sai ki kira mu yi magana ba san mun yi ba, amman ba karki bari a gane da ni kike waya" "Toh na gode" "ba komai Allah ya saukeki lafiya" "Ameen" Ta fita ni kuma na boye kudin, washe gari ban ma fada masa zan tafi asibiti ba saboda gudun kar ya hanani ko yace na bari sai lokaci kaza, domin ina jin rashin lafiya a lokacin, sai na shirya na fita ba tare da na fadawa kowa inda zan je ba, a tunaninsu na shiga makota ne. Kuma tabbas na shiga amman gidansu Malika na tambaye ta wace asibiti ce mai saukin kudi domin dubu uku ne da ni ina son na je, sai ta fada min na kama hanya na tari achaba na tafi, duk abubuwan da ake bukata na yi da na shiga ganin likita sai ta yi ta fada wai miyasa ban zo awo da wuri ba gani yarinya kuma haihuwar fari, ai yanzu an daina wannan dabi'ar ta kauye, sai na fada mata mijina ne be aminta ba yanzu ma ba da saninsa na zo ba. Ta auna ni bayan na fada mata abun da nake ji tace naje na yi hoto a yau din na kawo mata, na je na yi hoton wa inda aka fada min na biya 1200 a lokacin na dawo Allah yasa na same ta da ta duba sai ta fada min abun da ke ciki jirkice yake madadin kan yaro ya juyo ta gurin marata sai ya zama kafafuwansa ne a nan. "Hakan yana da wata matsala ne?" Na tambaya domin ban san kan abun ba. "Sosai kuwa mace zata iya mutuwa ko ta kasa haihuwa sai an fasa ta, ko kuma ta samu matsala ko danta ya samu, za a iya rasata ko a rasa dan, gashi kuma baki da jini sosai ba ki da ruwan jiki da yawa baki cin abinci mai kyau" A take hankalina ya tashi, zancen abinci mai kyau kam bata taso ba domin abinci ma bana iya ci na koshi balle wani mai kyau ko mai gina jiki. "Za mu dora ki akan magani, kuma kije ki shirya ki dawo gobe, akwai abun da zamu fara miki da juyo da kan yaronki kamin ki cika wata tara, dan yanzu cikinki yana da wata bakwai da kwana sha takwas" Na mata godiya na fito jikin a sanyaye domin na san babu wani kudi da zan samu a gurin Khaleefa, ashe ma abun da ban sani ba gidan yana nan ya kusa kamawa da wuta saboda na fita tun safe ban dawo ba har la'asar. Dan canjin da na rage min ne na hau achaba da shi na iso gida sai da na fara biyawa na fadawa Malika halin da nake ciki ina kuka sannan na shigo gidan. "Idan uban wa kika fito?" Ita ce madadin amsa sallamata da yayi kasancewar yana cikin dakin na yi sallama. "Asibiti" Na amsa jiki ba kwari murya na fita daker. "Ina kika samu kudin zuwa asibiti? Da izinin wa kika fita" "Idan na tambaya ba zaka bar ni ba, kudin kuma daman ina da shi" "Karya kike sai dai idan satar min kika yi ko kuma kin fara bakin halinku na kafirai, wato yanzu ya kai ki fara fita baki fada min ba" Na kalleshi cike da takaici da nadama da bakinciki na ce. "Wai kai Hamza wane irin zuciya ce a kirjinka? A matsayinka na musulmi mai addini be kamata na same ka haka ba, dabi'unka da ka nuna min ba su na tarar ba, ka zalince ni kai da iyayenka kunci amanata" Ban gama rufe baki ba ya rufe ni da duka. "Me kika sani akan addini da zaki tsoma baki a ciki? Kafira diyar kafirai? Bubabbiya marar alkibila, rashin kunyarki ya kai ki kira da Hamza gatsatsa ko? Irinki ma son haihuwa ake da ke? Mugun iri irin kafirci wadanda basa tuban Allah da ma'aiki, na haihu da ke kije gaba ki maida yarana kafirai" Ban taba sanin rashin imanin Khaleefa ya kai haka ba sai ranar, baya ji baya gani duka yake ina tare cikina yana kai masa halbi da kafarsa, Matar nan da ta taimaka min da kudin tafiya asibiti Maman Luratu ita ce ta shigo tana ba shi hakuri tana jansa sannan fa sauran suka shigo suna jansa suna fadin ban kyauta ba amman dai yayi hakuri ko dan cikin dake jikina. "Na gaji da ke na gaji da halinki kowa ya san ba haka na tsara rayuwar aureba amman ji yadda kika maida gidana, Aisha na sake" Maman Luratu ta yi hanzarin rike shi. "Abun he kai can ba Hamza ka yi hakuri ga ciki kuma ta tafi ina?" "Ta tafi duk inda zata tafi, ba gaji da halinta bata da tarbiya" Nasan ma'anar saki a musulunci kamar yadda na san ma'anar aure, wato ya barranta kansa daga gareni, ni din nan na haramta a garesa, sanin ba ni da gurin zuwa ba ni da kowa ya saka ni ba shi hakuri ina rokon mutanen gidan su ba shi hakuri na zauna. Sai suka ce na bari sai ya huce na zauna a gidan idan ya huce zai maida ni. Na san yadda suke kina sai zuciyata ta raya min kamar abu ne mai wahala su saka ya maida aurena. Dan haka na tashi cikin daren nan na tafi gidan mai gari na fada masa halin da ake ciki, ashe fita ma matsala domin har an kira an fada masa, mai garin ya aiko kiransa ya zo take a gurin kamin a mana umarni da komai ya ce. "Da zu na sake ki ne da nufin saki daya, toh yanzu na kara miki na sake ki saki uku babu aure tsakanina da ke har abada" Na rude na kama kafafuwansa na rike ina kuka ina rokon gafara, ban wayi addinin sosai ba saboda haka ban san idan an yi saki uku aure ya kare ba kenan. "Khaleefa ka san ba ni da kowa ba ni da komai dan Allah karka min haka, Alkawari be ce haka ba, ka yafe min Wallahi ba zan sake ba" Ni kam rokonsa kawai nake ina son ya maida sai da matar mai garin tace min ai auren ya kare kanan babu zancen gyara. Na yi tunanin ko mai garin zai ce na zauna a gidansa har sai na haihu, daman iyayensa kam ban saka ran za su ba ni gurin zama ba. Ina dawowa gidan na ji na zaba bukatar kowa a tare da ni sai na shiga dakin na dauki can chanjina da fitila da number da Maman Luratu ta ba ni na fice ba tare na dauki komai daga suturar da na samu a gidan ba. Na karasa inda yake zaune a kofar dakin mahaifiyarsa sai duk idon yan gidan ya koma kaina wata kila suna tunanin ko zan rokeshi gafara ne ko kuma ya bar ni na zauna a gidan ne, na tsaya a tsaya ina kallonsa ido cikin ido na ce. "Ka ci amanata Khaleefa, ka yaudare ni, ba ni da kowa ba ni da komai wannan tabbas haka ne, saboda kai na zo gidan nan kuma yanzu aure ya kare zan tafi, ka sani na rayu kamin na hadu da ni, na rayu babu uwa babu uba, babu daya daga cikin danging uwa ko uba, yanzu ma zan rayu domin mai rayawa ya kashe be manta da ni ba, Hamza na barka da Ubangijin da ya aiko Annabinsa da Addinin Musulunci, na barka da Ubangijin da be kwana be haifa ba ba a haife shi ba, Hamza na barka da ALLAH... " Mikewa yayi tsaye yana kallona baki a sake, matan gidan kuma kowa yayi tsit kamar babu abu mai rai a gidan. Bayan wannan wata kalar bata sake fitowa daga baki ba har na doshi kofar fita gidan na fice, ban yi nisa ba na ji ana kirana Maman Luratu ce ya biyo ni tana kuka. "Aisha ina zaki" "Koma ina ne zan tafi Wallahi yau ba zan kwana a gidan nan ba" "Toh Allah ya miki mafita, dan Allah idan kin samu waya ki kira ni, Allah ya sauke ki lafiya, ungo ga dubu biyar ki rike" Ina karba kudin na fashe da kuka sai ta rumgume ni tana kuka, na dago godiya ma kasa yi mata na yi na kama hanya, achaba na fara hawa ya kai ni tashar garin, ina zuwa kuwa na samu mota sanin kudin ba zai ishe ni na je Lagos ba na hau motar Kaduna, idan ma naje Lagos din gurin waje zan je? Matar da na yi butulci? Ko gidan marayun da ba lallai su karbe ni ba zan koma? Lokacin da na hau motar ba zai wuce karfe goma ba kasancewar garin da kowane lokaci ka je ana samu direba saboda akwai masu cin kasuwa, kuma ranar da abun ya faru ranar kasuwa ce. A ranar ban kwana a garin ba da cikina da ciwon da nake ji da kuma bakincikin dake kumshe a zuciyata na kwana a tashar Kaduna... Follow my channel domin samun update https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 And don't forget to SHARE [5/6, 8:51 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 2️⃣2️⃣ Da gari ya waye sai na yi ta raba ido a cikin tashar ina kallon mutane, daman na kwana a kusa da massalaci ne a wani guri da ake aje sako tare da wasu matafiya da dare yayi musu. Na zauna a gurin har zuwa karfe daya na rana saboda ban san a inda zan je ba, ba zan iya komawa lagos ba idan ma nace zan koma ba ni da kudin motar idan kuma na koma ba ni da tabbacin a karbe ni. Jama'ar gurin da suka lura ina zaune a gurin har ana daf da ayin la'asar sai suka same ni suna tambayar na san a inda nake kuma wana sani a garin Kaduna? Nace musu na sani kuma bani da kowa a garin kaduna. Sai suka tambaye ni ni matar aurece? Nace musu aa domin a halin da nake ciki babu aure a tare da ni, idan ma akwai vana bukata domin na gama kakkabe Khaleefa a rayuwata yanzu, sai kuma suka sake min wata tambayar da na rasa amsar da zan ba su. "Toh cikin dake jikinki fa?" Na shafa cikin ina hade wani abu mai daci, dole kowa zai yi zaton cikin shege ne, wata kila su yi tunanin ko na gudo daga gidanmu ne. "Dan Allah inda ake bada taimaka idan mutum yana cikin matsala?" "Kamar wani irin taimako?" Dayan ya tambaya. "Kamar wata kungiya ta musulmai da take bada taimako haka ko masallaci" "Toh sai zakka da wakafi" Dayan kuma yace na tafi massallaci, wani kuma ya tambaya wani irin taimako nake nema, na ce na wanda zai rike ni har na haihu. "Wannan cikin ba shi da uba ne?" "Yana da uba, ni ba ni kowa marainiyace ni, kuma mijina ya sake ni, kuma musulunta na yi ban san kowa a nan ba" Ina rufe baki daya daga cikin dattijan dake tsaye a gurin ya rufe da fada kamar zai dake ni. Wai na tashi na bar gurin haka muke muna zuwa muna cikin shege mu zo tasha mu tare muna haifa musu yara yan iska muna bata musu tasha. "Idan baki da kowa ki koma garinku mana, karya ce suke saboda kawai a tausaya musu, cikin shege suke yi" Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, daman wai waye zai yarda da ni, suna da gaskiya suna bukatar tabtace tashar su. Haka na tattara na bar tashar na fito na kama hanya ina tafiya ban san inda zan je ba, can na samu guri kusa da wata mai wara na zauna na siya wara na ci saboda ban saka komai a cikina ba tun safe. "Dan Allah ina ne? Zakka da wakafi?" Ba tambaye ta, sai ta kwatantamin na bata kudin wararta na siye ruwan leda na sha, na tari mai achaba na hau na fada masa inda zai kaini ban tambaya nawa ba sai da muka isa yace min 500 zan bashi a lokacin 2300 ne suka rage min, na ba shi 500 na doshi gurin gabana na faduwa, domin maraicina be taba saka ni rokon kowa ba. Mai gadin gurin ya fara tambayar ina zanje na fada masa taimako nake nema a take na bayyana masa abun da ke tafe da ni da kuma taimako da nake bukata. "Kin tabbatar cikin nan baki ba na shege ba ne? Domin suna yin bincike idan za a bada taimako" "Wallahi gaskiya ne, ba karya nake ba" Sai yace na jira a nan ya shiga ciki ya fito da wani mutum mutumen yayi min tambayoyi ya yi rubutu akai sannan yace min yanzu kowa ya tashi aiki saboda yamma ta yi, amman na tafi zai saka sunana a cikin mabukata na dawo wani sati, sannan ya tabbatar min kamin su bada taimako suna yin bincike saboda akwai bata gari da suke zuwa suna karya nace masa na yarda su yi duk abun da ya kamata. "Amman yanzu idan na tafi ba ni da gurin zama ban san a inda zan zauna ba" "Ki yi hakuri dai wani satin ki dawo da wuri kamin rana ta yi" "tohm" Na amsa ina kuka, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi naira budu daya ya ba ni wai na hau abun hawa. Na karba na juya na kama hanya daman kam wa zai karbe ni a haka dole kowa zai yi zaton karya nake saboda cikin dake tare da ni ga shi kuma ina fadar ba ni da kowa kuma nace ban san kowa a garin Kaduna ba, ga ina cewa musulunta na yi wasu ma sai su dauka karyar ma ta yi yawa. Daga gurin na kama hanya ina ta tafiya a kafa ba dan na san inda zanje ba, har dare ya fara yi na siye ruwan leda na yi alwala na raba gefen wani icce dake kan hanya na yi sallah, ina addu'a ina kuka ina rokon Allah ya kawo min mafita. A gurin na yi ta zama har aka yi isha'i a nan ma na yi sallah. Da yake akwai mai shayi nesa da inda nake zaune kadan da na yi yunwa ta matsa min sai na tafi na siya birede da ruwan lipton na koma gefe daya na sha, sai wani azababben ciwo ya taso min, da na kawo masa kofin kowa kallon wulakantacciya yake min domin mace mai daraja ba zata saya tea ta raba gefe ta sha ba, gashi na zama kamar mahaukaciya duk na firgice ga rama cikin ma yayi min nauyi haka dai nake ta fama. Da na bashi kayan sai na raba ta wata hanya dake kusa da shagon na bi na lulla da wasu kananan gidaje, a gurin na samu inda na raba. Na wahala a gurin domin ciwon ba kadan nake jinsa ba, sai da na bari sawu ya dauke na tabbatar da dare yayi sosai sannan na tashi na koma inda na fito yadda na ayyana haka na samu. Mai shayin nan ya tashi ya kwashe kayansa a gurin na kwana, washe gari tun da asuba na yi sauri na tashi na koma gurin hanyar na zauna, da haske ya fito sai na shiga wani gida dake kusa na roki ruwa dattijiwar ta ba ni na yi alwala na fito nan na yi sallah. Rayuwa ta zama min haka, da dare sai na kwana a shagon mai shayi da rana kuma na shiga gari Bara da neman taimako. Ta inda Allah ya taimake ni babu wanda ya taba cewa me nake a gurin ko ya kure ni, ko da yake bana dawowa gurin sai dare yayi, idan kuma sawu ya dauke sai na kwana a shagon mai shayin da be san ina yi ba. Ranar da na kwana uku a gurin ciwon ya matsa min sosai har na tafi yawon bara na dawo na shiga gidan matar dake bani sadakar ruwa ina ta gumi na roki ta ara min wayarta na kira wata number. Har tace min bata da waya na juya sai kuma ta kira ni ta ba ni amman tace na zauna a kusa da ita na yi wayar bata yarda na fita ba kuma ta saka wayar a speaker saboda bata yarda da ni ba. Na warware zanena na dauko number Maman Luratu na saka a number na kirata, babu jimawa tana ringing ta daga wayar da sallama “Maman Luratu nice Aisha ce" "Aisha Allahu akbar sannu Aisha ya kike ina kike yanzu" "Ina wani guri, maman luratu dan Allah ko kin san abun da zan yi na daina jin ciwon cikin da baya? Wallahi ciwon nan ya tsananta min yanzu sosai yau ma kamar bana iya tafiya" Ina fada ina kuka. "Toh ko haihuwarce? Amman cikin ai be isa haihuwa ba ko?" "Eh wata bakwai ne, amman ina jin wahala sosai" "Ko nakuda kike yi? Oh Allah gashi bana kusa, amman dai ki daina yawo nesa" "Idan haihuwar ce me zan yi?" "Kina tare da wa ne?" "Babu kowa ni kadai ce" "Ki nemi reza ki aje kusa saboda yanke ciki, kuma idan da hali ki tafi asibiti Aisha kin san baki da lafiya tun a nan ma" "Tohm" Na amsa sannan na kashe wayar na mikawa matar ina godiya, sai matar ta tambaye daga ina nake. "Labarin mai tsayi ne ko na fada miki ba zaki yarda ba, na gode" Na fice daga gidan ina ta sharar kwallah. A rabar ne zuciyata ta debeni na yanke shawarar ziyartar coci ba dan komai ba sai dan na samu kudin da zan tafi asibiti kuma na samu kulawa. Dan canjin da ya rage min na hau abun hawa bayan na tambaye shi wace coci ce a kusa na fada min, da muka isa na bashi kudinsa na doshi gurin gabana na faduwa a zuciyata ina jin kamar hakan ba daidai ba ne amman ya zan yi? Dole ce ta saka. Na isa gurin na yi magana da mai gadin coci na fada masa damuwata da abun da ke tafe da ni, sai yace na jira a gurin ya shigo ciki ya fito da wata Sister tace ba shigo ciki na shiga nayi mata bayanin damuwata sai ta kira wani pastor shi ma ya kira wani muka shiga wani office na sake karanta musu damuwata, da na yi hakan ne saboda kawai su taimaka min. Sai dayan yace za su taimaka min da gurin zama da abinci amman sai idan zan yarda na koma gidan jiya, ma'ana na zama christen kamar baya, har ita macen take ce min ko da ace ban taba yin addinin a baya ba zan shiga a yanzu su kuma za su bani duk abun da nake bukata kuma za su shirya ni da mai rikona ma dake Lagos." ***. ****. *****. Ta daga kanta sama, Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zaro tissue ya mika mata, ta karba ta share hawayen da suka ki tsaya mata. Ta kalleshi da fuskarta da ta yi ja tsabar kukan da take. "Ni na sani a yanzu ba akan shiriya nake ba, na sani ba akan daidai nake ba, na san addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, a wacan lokacin ban yarda da tayinsu ba duk kuwa da kasancewar ina cikin tsananin bukatar taimako a lokacin, amman akwai wani abu da Allah yake sakawa a zuciyar wanda ya so da shirya, na musulumta saboda Khaleefa da aurensa ban san cewar ina son addinin ba sai a lokacin, sai kawai na ji raina ya bace akan me za su ce na koma addinin da bana samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali irin na ruhu sai da na bar shi, ni dai a lokacin na san ina son musulunci dan haka sai na ki yarda, na fada musu ni taimako kawai nake nema ba wai ina nufin barin addinin ba ne, su kuma suka ce ba za su taimaka min ba haka na taso na fito" Ina jin kamar shi kadai ne wani hukunci da na taba yankewa kuma ban yi nadama ba, da kafa na dawo saboda ba ni da kudin da zan hau abun hawa na dawo, sai kuma na sha wahala a hanya saboda ni ba har gari bace hanya da mai achaba ya bi da ni na bi ina tafiya, idan na rikice sai na tambaya mutane da sannu har na kawo kaina unguwar da nake zaune. Na iso ban isha'i sai na samu guri na zauna ina ta jin ciwon cikin da ban gane nakuda ce ba, daker na iya roko ruwa na yi rama sallolin da ban samu yi ba, na kwanta a gurin azabar ciwo cikin bata karu ba sai da dare ya raba. Na koma gurin da nake kwana na kwanta da ji abun ba zai daina ba na taso na fito na dawo gidan matar nan na kwankwasa mata gida sai jikanta ya bude yana haska ni da fitila. "Dan Allah matar gidan nan nake nema" "Lafiya wacece" "Ni ce" Na leka sai ta ga fuskata. "Dan Allah ki taimaka min da ruwa na sha, kuma idan kina sa wani magani dan Allah ki taimaka min na sha, kar na mutu ciwon ciki nake da na mara" "Ba ni da magani amman dai zan baki ruwa ki sha" Ta shiga ta dauko min ruwa na karba da hannu biyu na sha na juya na koma shagon na zauna ina ta kuka domin ciwon ya matsa min ga kuma abu ina ji a kasana kamar zai fito, ban san lokacin da na fara ihu ina rike teburin mai shayin dake gurin ba, sai matse kafa nake ina juyawa, tsabar bala'i da azabar da ciwo har wani juri nake ji ina jin kamar ba a duniya nake ba, ashe haihuwa tana da zafi ban sani ba sai a ranar, gashi babu kowa a kusa da ni, duk zafin nan na haihuwa a haka iyayena suka wofintar da ni? Ina cikin tsananin nakudar dana na farko dan wata bakwai matar da ta taimaka min da ruwa ta iso gurin ta dafa ni, ta haska ni da fitila ina jin jikanta na fadar Gwaggo kika sani ko jikin shege ne. Sai tace. "Ko cikin shege ne ai ba za a kyaleta ba Kabiru rayuwa ce" Ta bude kadata ta haska sai ta saka salati. "Haihuwa ce zaki yi kuma kafa nake gani ba kai ba subhanallahi" Ta rika ni, da taimakon danta suka kai ni gidanta, ita tayi ta fada min yadda zan yi tana taimaka min tana danna min ciki har na haihu, amman na ji azabar da ban taba ji ba, har na ji kamar babu kasana gaba daya a lokacin. Da zanenta ta lullube dana ta yanke min cibi na sake wata nakudar sannan wani abu ya fado wai shi uwa, ta saka a leda ta kulle. Ta dauko wani zane ta lullube ni ta dora min dana a kusa da ni, ni dai ina kwance a gurin bana bachi bana farin ciki haka kuma bana kishiyarsa, hawayena kawai masu zafi suke sulalowa a idona, har ta yi zaton ko na mutu ta girgiza ni sai na kalleta. "Sannu" Na daga mata kai, da safe sai jikina yayi tsami sosai, ta taimaka min da tsumma na tare jini ta gyara dakinta tace na wanke kayan jinina haka na daure da ciwon jiki na da kasa na wanke kayana da kaina na zauna ina jin kamar fata ce kawai ta rage min a jiki, ta kawo min dumame na ci na sha ruwa sannan ta tambayi labari. Na fada mata komai sai ta tausaya min amman ta fada min ba zata iya ba ni gurin zama ba saboda zargi. Kuma ban ga laifinta ba tana da gaskiya ba kowa zai iya rike ni ba, dawainiyar ma ai sai ta yi masa yawa. Ta fada min idan mace ta haihu a musulunci akan yanka mata rago idan yayi kwana bakwai, kuma uba yana yi ma dansa huduba a kunne, amman ni daya be samu ko daya ba, hakan ya saka ni kuka sosai. A lokacin na saka masa suna Ibraheem ba dan na san ma'anar sunan ba, kawai dai na saka masa haka ne. Da dare yayi matar bata bari na kwana a nan ba saboda kukan da London yake ba ji rarrashi ga shi kuma nono na babu komai a ciki, na kwana a ashagon mai shayi kamin lokacin tashina yayi sai ga mutane na gani har hudu ciki har da mai shagon da abun dukansu, suka ce an fada musu a nan nake kwana kar na sake kwana a gurin su yanka ni, dayan ya so ya mare ni wai dan na raina musu wayo wato har haihuwa na yi a gurin. A daren suka kore ni na goya daya da zanen matar na kama hanya ina ta tafiya har gari ya fara haske gashi ko'ina na bi sai an kalleni saboda kukan da London yake domin ba lafiyayyen ďana na haifa ba, gashi dan tsito ba shi da girma, ni kaina tafiyar ma daker nake yi ina ta raba kafa saboda zabar da nake ji a kasana. A haka na rika raba manyan gidaje ina yin Bara wani gidan masu gadi basa bari na karasa ba suke korata wasu kuma basa ma bude gate din. Har na fada gidan wata mata mai farar zuciya mai tausayi mai jinkai, da alama da saba taimakon domin na tarar da gate din gidan a bude kuma da na fadawa mai gadin taimako nake nema sai yace min na wuce ciki. Na shiga sai na zauna daga bakin kofar falon ina jiran fitowarta, na dade a gurin sannan aka bude kofar falon, wata matashiyar yarinya ce ta bude kofar ganina kamar tana mamaki ta tambaye ni lafiya. Nace mata taimako nake nema sai ta tambaye ni wane iri na furta abinci domin shi na fi bukata a lokaci, yarinyar ta juya ta shiga ciki bata jima ba ta fito da plate din shimkafa irin wanda aka ci aka rage tace ba a gama shirya mana abun karyawa ba amman ga ragowar shimkafar jiya idan zaki iya ce. Na karba jiki na rawa na fara ci hannu baka hannu kwarya kamin na kwance dana dake ta ihu ga wani zafi da jikinsa yayi na rumgume shi na gyara zama na fara saka masa shimkafar a baki tana kaiwa makoshinsa sai ya dauke numfashi... ***. ***. ***. ***. Ta aje zaren zancen tana neman nata numfashin dake kokarin daukewa saboda kuka na tuna rayuwar da ta dade da rufe shafinta. Aliyu ya matsa baya yana kallonta cikin tashin hankali, a lokacin ne ta fara zaga office din tana neman numfashinta kamar zata mutu, da sauri ya fita Office din ya fadawa Nick ya nema masa wata mace da take kusa ya dawo ya nufi fridge dinsa ta dauko ruwa ya nufeta hankali a tashe, wata mace ce ta shigo dakin tana sanye da suit. "Rikata dan Allah zaunar da ita ki rumgume ta" Ya nuna mata Emily a take ta nufi Emily ta aikata abun da ya fada sai ya miko mata ruwa yace ta bata. Matar ta karba ta kai mata ruwan a baki Emily na shan ruwan ta fara amai babu kakkautawa bata tsaya ba sai da ta amayar da komai na cikinta, matar na rike da ita har ta fara dawowa hayyacinta sai dai kuma jiki babu kwari. "Shiga da ita ciki ki wanke mata baki" "Okay Sir" Matar ta rika Emily suka shiga bathroom dinsa dake office din ta taimaka mata ta wanke baki da fuskarta sannan suka fito, Aliyu ya mikawa Emily Tissue da hannunsa. "I'm sorry" Ta karba kawai tana kallonsa da idonta da suka kumbura fuskarta da hancinta suka yi ja. "Anna ki rikota ku fito ku same ni gurin mota" Ya fice yana fadawa Nick ya sa a gyara masa office dinsa. Anna din ta taimaka mata suka sauka kasa suka isa har gurin motar da Aliyu take ya bude backseat Anna ta shigar da Emily ta rufe sannan ya shiga gaba yaja motar suka fice. Madubin gaban motar ya saita saitin da Emily take jingine da motar tana hawaye kana ganinta kasan tana cikin bakin ciki da rashin kuzari. "Kina da likitan da yake dubaku?" Bata amsa masa ba tana ta kallon gefen titi ta yi samo kamar ba ita ba. Shi kuma be fasa kallonta ba har ya isa bakin gate din gidan yayi horn mai gadin ya leko ya kalleshi... Sai ya sauke gilashin ta gefen da Emily take. "Ba sai ka shiga ciki ba" Ta bude motar ta fito da kafafuwanta ta yi tsaye kamar zata fadi, Aliyu ma ya bude ya fito ya zagayo inda take. Tasmia dake zaune a can gefe cikin mota ta bude motar ta fito da mamakinta tana kallonsu, tun kamin ta kawo Emily ta mika mata hannu domin jin take kamar zata fadi, Tasmia ta karaso da sauri ta rikata, ta kalli Aliyu. "Me ya same ta? Wani abun ka yi mata" "Eh fyade na yi mata" Ta amsa mata da gatse, sannan ya rufe gefen da Emily take tsaye ya zagaya ya shiga motarsa yayi reverse. Tasmia ta bishi da kallo mamaki domin ta gane waye shi. Emily ta dafata suka shiga cikin gidan ta zaunar da ita falonta. "Emily kin san wannan mutumen da ya kawo ki ne?" Emily ta kalleta hawaye na sauko mata. "Dan Allah karki tambaye ni komai a yanzu, ki tafi gida ki bari sai gobe zamu yi magana" "Shikenan amman ki yi ma maigadinki magana domin yanzu da na zo hana ni shiga yayi wai babu kowa a gidan alhalin na san a nan na taba sauke ki" Emily ta daga mata kai domin shi ne kawai abun da take iya yi. Tasmia ta tashi ta fice har lokacin mamakin mijin kawarta take tana jinjina halin maza duk kuwa da kasancewar bata san me yake faruwa ba. Bayan Tasmia ta fice Emily ta rumgume kanta ta fashe da wani irin kuka mai karfi sosai daker ta iya rarrashi kanta ta mike tsaye ta haura staircase din ta doshi dakin da London yake a hankali ta tura ta shiga ciki, bashi a dakin ta nufi bandaki slowly ta bude nan ma be ciki, ta fito ta janyo kofar dakin ta shiga dakinta ta zauna kan tool tana kallon kanta. Ji tana bukatar ganin danta ya saka ta nufi gurin da dayar wayarta take ta dauka ta kira Chidimma a zatonta London yana tare da ita ne. "Kina ina" Ta tambaya bayan Chidimma ta dauka. "Ina gurin kawata" "Ina London?" "Ba da shi na fita ba, na bar shi a gurin Sir Vito kamin na fita" Emily ta kashe wayar ta kira wayar Vito ringing daya ya daga. "Ina London?" "Na bar shi a dakinsa yana bachi, Ina kika je?" Bata amsa tambayarsa ba ta kashe wayar ta fito ta sake komawa dakin London din ta duba ko'ina har kasan gado bata ganshi ba, ta fito falo tana dubawa nan ma baya nan, ta fara duba lungu da sako na falon wai ko ya boya domin dabi'arsa boya a wani gurin musamman idan yana fushi, a nan ma bata ganshi ba. [5/8, 8:18 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣3️⃣ Ta dauki wayarta da sauri ta kira Vito. "Ban ga London ba ko'ina na duba baya nan, kuma na yi waya da Chidimma tace ta bar shi gurinka ta fita" "Ina Lisa?" Fatima yake nufi domin haka yake kiranta wani sa'in saboda ya tsani sunan hausawa da aka saka mata. "Tana.... Fatima tana...." Ta juya ta kalli agogon falonta lokacin dawowarta daga makaranta har ya gota. "Ina kika je? Jiya ma kin fita ina kika je?" Ta kashe wayar ba tare da ta ba shi amsa ba. Vito ya kalli wayar har ya aje sai kuma ya dauka ya kira Chidimma. "Hello ranka ya dade" Ta amsa da nishadi da girmamawa. "London yana gurinki?" "Aa ai tare na barku da shi da zan fita" "Baki koma gidan ba? An duba ba a ganshi ba" "Wata kila ko yaji muryar mahaifiyarsa ne ya boya, dan yanzu rashin kulawar da take ba shi ya saka baya son zama kusa da ita, madam bata kula da shi yadda ya kamata" "Chidimma ki yi hankali da bakinki, ki daina fada min laifin Emily, idan ma wani abu take marar kyau ki bari na gani da kaina, karki sake fada min tana gida ko bata nan sai idan na tambaye ki, madadin na ga laifinta ke zan tsane ki ne" Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya dauki rigarsa dake aje kan gadon ya saka ya fito dakinsa sai ya samu mahaifiyarsa a falo tana hira da mai dafa masa abinci. "Fita zaka yi" "Eh" Ya amsa a takaice sannan ya dauki daya daga cikin keys din da suke lake a kofar fita falon ya fice. Ta dayam bangaren kuma Emily na aje wayar ta nufi harabar gidan tana tambayar mai gadi ko Fatima ta dawo? Sai ya fada mata bata dawo ba amman direban dake daukota daga school ya fita da mota tun dazun. "Amman ka ga London ya fita?" "Aa be fita ba indai ba Oga ne ya fita da shi ba a mota a kafa kam be fita ba wani kuma be fita da shi ba" "Ya bata ban ganshi ba" "Kin duba ko'ina?" "Eh" Ta amsa masa sai ta nufi kofar gate din ta bude ta sauri ta fita tana ta kalle kalle bata yarda yana cikin gidan ba domin ta duba ko'ina bata ganshi ba, haka ta fi hanya ko talkami babu a kafarta tana tafiya tana kalle kalle idan ta ga mutane sai ta tambaya ko sun ga wani yaro, kowa yace mata a'a. "Yaro ne sosai fari yana ihu idan ya ga mutane wani lokacin yana da jin tsoro kuma yana yin abu kamar marar hankali amman ba mahaukaci ba ne Autism ne, yana da matsalar data shafi kwakwalwa" "Ba mu ganshi ba" Gungun mashayan sun fada suna kallon cinyoyinta dake waje. Ta dora hannu akai har zata fasa kuka sai kuma ta karfafawa kanta guiwa ta kara gaba tana nemansa. Sai da ta kusa kai karshen unguwar tana duba kwararo ko lungu bata ganshi ba kuma kowa ta tambaya sai yace be ganshi ba. Can wata zuciyar ta raya mata ko ya bi direban da zai dauko Fatima makaranta gashi bata fito da waya ba balle ta kira, ta juya ta koma da sauri duk nisan hanyar bata gani ba cikin mintuna ta dawo gidan ta buga gate din da karfi mai gadin ya bude yana kallonta sai dai be ce komai ba ita ma bata bi ta kansa ba ta nufi cikin gidan da gudu sai ta samu kofar falon a bude Fatima na zaune rike da jakarta ta makaranta tana kallon mahaifiyarta a tsorace. Da sauri ta nufeta ta dafa ta. "Fatima kin dawo? Da direba zai je daukarki a school tare da London aka je? Ya bata ban ganshi ba" "Be bata ba, ruwa ya fada Vito ya zo nan ya tsamo London a swimming pool ya tafi ya kai shi asibiti" Emily ta fadi zaune idonta na cika da hawaye wata sabuwar fargaba na tunkarota, tunaninta be bata zai tafi can ba even though ta leka bata ganshi ba amman bata saka ran zai fada ruwa ba. Ta saki Fatima ta nufi staircase ta haura sama zuwa dakinta ta dauko wani makullin motar domin wacan motar data fita da ita da safe tana can gurin aikin su Aliyu ta baro. Ta sauko da sauri tana jin numfashi na sama kamar zai dauke gudu take amman kamar ana daure mata kafafuwa haka take ji, rashin kuzarin nan da ya same ta a office din Aliyu a dazun bayan ta gama gutsura masa labarinta ya dawo mata a yanzu. Gurin shiga motar ma sai da ta yi da gaske sannan ta iya bude motar ta shiga, cikin karfin hali ta yi ma Motar key ta yi reverse, a hanya ma tana jan motar motar na janta sai ta taka burki ta tafi sai kuma ta tsaya ko ta yi baya kamar wanda ta sha wani abu haka ta samu kanta duk wanda ya ganta sai yayi zaton ko ta sha wani abu ne, fakawa ta yi gefen hanya ta dora kanta a sitiyarin motar tana ta sauke ajiyar zuciya ta rufe ido tana maida numfashi, ta yi hakan ya fi a kirga sannan ta samu kuzari ya dan zo mata, ta sake tuka motar ta nufi asibitin da aka saba kai shi a duk lokacin da bashi da lafiya. Ta faka motarta a emergency ta fito ta rufe motar, ta nufi entrance din Emergency din tana kokarin daga kafarta ta taka gurin gabanta ya fada ras ras ras dudududummmm har sau uku, kamar wadda ta tuna wani abu sai ta fasa bata dora kafar, ta ja baya ta tsaya tana kallon Kofar Emergency din dake can ciki wato second door da mutane suke fitowa, ta kasa shiga ta gagara komawa ta tsaya a gurin har na tsawon minti 5. Tana tsaye a gurin sai ga Vito ya fito tare da wani yana hangota sai ya tsaya da sauri kamar mai jin tsoro, sai kuma ya taka ya karasa inda take tsaye. "Mu tafi gida" "Dana ya mutu ko? London ya mutu?" Vito ya dafata kamin ya sake cewa komai ta ce "Na jiya a jikina, an sanar min saboda ni ma uwace, ban taba samu kaina a irin yanayin da na samu kaina a yau ba, ban taba jin abu makamancin wannan ba, saboda ban taba rasa makusanci na jini ba sai yau, na ji abun da ake ji, na ragu yau na koma daga ni sai Fatima" Tana maganar wasu masu tsananin zafi suna sauko mata. "I'm sorry, zan kasance a tare da ke a cikin kowane irin hali Emily" Ta fasa wani irin ihu kamar mahaukaciya Vito ya rike kamin ta kai kasa, wani irin kuka take daya saka hankalin kowa dawowa gareta, bata san yadda ake ji idan an rasa wani ba sai a ranar domin bata taba rasa kowa ba sai yau. Shi ya saka ta mota ya tuko zuwa gida wanda suke tare kuma ya taho da gawar London, ta shiga falonta tana kuka Fatima ta tarbeta ita ma tana Kukan domin tun a dazun jikin yayi sanyi saboda yanayin yadda ta ga an ciro dan'uwanta a ruwan kamar tsumma. "Ya mutu Momi" Emily ta kasa magana ta rumgumeta tana ta kuka. Vito ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa ya runfe ido, domin ba kadan yake son London ba, dama Fatima ce wata kila ba zai ji damuwa da bakinciki kamar haka ba, amman London yana son yaron yaron ma yana sonsa, shi ya canja masa suna Ibraheem zuwa London ya canja masa addinin kuma ya yarda, ba kamar Fatima ba dake nuna masa kiyaya da rashin kunya, kuma ta ki yarda da sunan Lisa da ya saka mata, haka kuma har gobe idan ibadar ta tsikareta sai ta yi sallah ko taje Islamiyar da mahaifiyarta ta sakata. Chidimma na shigowa falon ita ma ta fashe da kuka, kusan idan aka cire Vito London ya fi sabo da ita fiye da mahaifiyarsa musamman a yan kwanakin nan da baya yarda da Emily. KAMEELA POV. "Hhmmm sai yau kika tuna da ni?" "Ke tunawa kike, ke da ba kira kike ba sai dai a kira ki?" "Baki san na haihu ba halam?" "Tohm yaushe?" "Yau kwana takwas, amman abun da na haifa be zo da rai ba, ina gida" "Allah sarki Allah ya bada rayayye" "Ameen kina PH har yanzu" "Eh mana kin san sai na yi shekara a nan ai" "Okay Allah ya taimaka" "Ameen, shi mijinki yana nan kenan?" "Tasmia ina ruwanki da mijina da har zaki tambayi mijina bana fa son haka" Tasmia ta kalkale da dariya "Kameela kina bani mamaki, wai ke lafiya kike kar kishi ya haukata ki fa" "Ke ya haukata ni din ina ruwanki? Toh miye na tambayar mijina" "To ai na ga yadda kike da kishi ne na yi zaton ko ba zaki iya barinsa a can ba tare kuka zo wanka gidan" "Mtssschesssss" Ta yanke kiran. Tasmia ta kyalkyale da dariyar mugunta. "Yau da kin san abun da mijinki yayi da sai kin kusa kashe kanki dan kishi, gashi nan daga tafiyarki ya tsallaka gurin wata da ba addinmu daya ba" Ta sake fashewa da dariya. "Ko da yake gayen ya hadu dole ki yi kishi ki yi taka tsantsan ai" Ta fada tana murmushi kamin ta tashi daga kwancen da take ruf da ciki ta yango Food flask dinta mai two set da ya siya gurin Khadeeja Candy ta bude ta zubawa kanta tsemo da miyar agutsi. Ta sake daukar wayarta ta kira layin Emily sau biyu tana maka miss calls sai a uku aka daga. "Hello..." "Wacece wannan" "Kawar tace" Dip ta ji an kashe wayar ta duba wayar tana mamakin waya daga? Ta sake jira sai ta ji wayar kashe. Ta tabe baki ta aje wayar kusa da ita ta cigaba da cin abincinta. ALIYU POV. Ya kalli harabar gidan da iska mai dadi ke kadawa sannan ya amsa. "Ina gida" "Gida a ina?" "Compound" "Me kake yi a nan toh?" Yayi murmushi. "Wai ke me kika dauke ni ne? A harabar gida gidan dai ba aljannu ne za su tsallako su shigo nan ba ina zan ga mata?" "Baka kallon mata amman ai akwai social media kuma wasu ma za su iya samun numberka su kiraka" "Saboda ni kadai ne namiji a duniyar nan? Kameela wai wane irin kishi ne yake damunki? Ke har alkawarin da na yi miki ba ki yarda da ni ba" Ta yi shiru. "Na san kowa da yadda Allah ya halicce shi, amman ya kamata ace muna damuwa da wasu abubuwan ba wai kishi ba a koda yaushe, already kin aure ni, ina sonki kina sona kina da kishi wannan abu ne da na sani tun kamin na aure ki kuma na aureki na miki alkawari ba zan miki kishiya ba, toh miye kuma abun daga hankali da bin diddigina?" " Mata shedanu ne wata zata iya sakawa ka karya alkawarin da ka yi min" "Akwai abubuwan da ya kamata ace mun damu da su, wata ma kokarin ganin ta samu kwanciyar hankali take, wata bata da iyaye bata da yan'uwa bata da kowa, damuwarta na samun canjin rayuwa ne, bata ta kishi take ba, be kamata muna damuwa da wasu abubuwan Kameela" "Damuwar wasu ba tamu bace, kowa ai da kalar kaddararsa, ni tawa kaddarar kishi ne da kaunarka yaushe zaka zo?" "Sai idan zaki koma zan zo na tafi da ke" "Saboda me? Yanzu baka yi marmari na ba?" "na yi idan na zo mi zan yi? Aiki nake a nan fa Kin sani, zan zo amman dole sai na dauki hutu" "Toh ka dauki hutu mana" "Okay, zan dauka shikenan" "Eh i love you" "I love you more, ki kula min da kanki" "I will sai da safe" "Okay" Ya aje wayar yana daga kansa ya kalli sama, labarin Emily halin da ta shiga kawai yake hangowa, ya kan ji labari kala kala na ban tausayi amman be taba jin kalar nata ba, be taba arba ido da ido da wata mata da ta sha wahalar rayuwa kamar ita ba. Duk kuma labarin da ta bashi na rabin wahalar da ta sha ne na rayuwar da Khaleepa, be san wane irin zama suka yi da abokinsa ba, be san ya ya riketa ba, da alama shi ma bata sha da dadi ba shiyasa har take guje masa kuma ta biyowa yarsa cewar tana da uba a raye. Ya sauka daga bayan boot din motar da yake zaune yana mamakin yadda zuciyar wasu mazan take bushewa su saka rashin tausayi a ciki har su cutar da abokiyar zamansu, ba su yarda ana hisabi ba ne ko kuma dai gani suke kamar matan ba su da hakki su kadai ne suke da hakki akan matansu? Abun takaici ne kuma abun haushi ace Khaleefa ya juya mata baya ya san wacece ita kuma ya amince ya aureta. A yadda taba shi labarinsa mutum mai addini amman ya take saninsa ya rufe ido ya zalinci wanda bata da kowa sai shi. Bata da uwa ba uba sai shi ko da yake har a yanzu a cikin wahala take a ganinsa saboda Vito ya mata duka a gabansa ranar da yaje gidan, shi ma yayi mata hakan ne saboda ya san bata da kowa. Ya tabbatar da ace tana da iyaye a raye wannan kangi da wahalar rayuwar da cin zafin ba za a yi mata shi ba. "Rashin iyaye masifa ne" Yana maganar yana danna kiran mahaifinsa bayan sun gaisa ya nemi ya ba shi Ummi ita ma suka gaisa sannan yayi musu sallama ya kashe wayar. Ya gwada kiran number Emily har sau biyu ya ji ta a kashe sai ya ji duk ya damu ya san halin da take ciki domin ya aje ta gidanta a dazu a wani yanayi marar dadi, yanzu kuma ya ji wayarta a kashe, waya sani ko mutumen dake nuna mata fin karfi ya ga lokacin da aja aje ta a dazun ko kuma wani ya fada masa, waya sani ko ma ya mata duka akan haka saboda kowa ya maida ita baiwa saboda bata da gata. Gashi ya tuna mata da baya ya san yanzu damuwar zata mata yawa, a yanzu ya gamsu da hujjarta na son gina rayuwarta ita kadai da take ba tare da neman taimakon kowa ba. "Idan kin ga wannan sakon ki kira ni, ina son na san halin da kike ciki" Ya aika mata sakon yana jin zafin yadda suka cutar da ita har cutarwa ta yi nasarar sauya tunaninta akan musulunci da musulmai. Ya dan jima a tsaye a waje, labarin da ta ba shi kawai yake ta hararowa yadda ta yi zaman. Sai kuma ya ji ya kagu ya ji irin zaman da ta yi da Turhan yadda ta hadu da Vito kuma taya halittar jikinta ta canja zuwa siririya bayan Turhan ya fada masa tana da jiki sosai a labarin da ta bashi a yanzu kuma ta fada masa ta yi rama sosai a gidan Khaleefa saboda wahalar data sha. Ya bude motarsa ya zauna a ciki yana kai dubansa gurin agogon da ta aje masa dazun a office. Ya kai hannu ya dauko agogon yana ta juya shi a hannunsa. "Kai wasu mazan akwai bakar zuciya" Ya fada yana mamakin yadda wani zai aikata abun da shi ba zai iya kusantar makamancinsa ba me balle ya aikata. "Waya sani shi ma ko yana can yana nemanta" Ya ayyana da nufin Khaleefa a ransa kuma yana jin haushin Turhan tun gabanin ya san wane irin zama suka yi. EMILY POV. Ya aje wayar a hankali kusa da ita bayan ya kashe wayar gaba daya. Ya zauna kusa da Emily da bata iya daga ido saboda kukan da ta sha idon ya rufe mata sai ciwo yake. "Za a maida shi mutuware su aje shi a can kamin ki samu salama a shirya bikin mutuwarsa" "London Musulmi ne, musulmi na haife shi please ka bari a birne shi a makamartar Musulmi, ina jin kamar ban masa adalci ba idan na masa haka, ban bashi kulawa data dace ba, da ace na san zai mutu da na zauna da shi a kowane second da minute" Vito ya rumgume ta. "Ai kin bashi kulawa, shi ne yake kyamarki ba laifinki ba ne" "Amman ai shi ba shi da lafiya ya kamata na masa uzuri" "Baki da laifi a gurin kowa Emily, lokaci yayi da ya kamata ke ma ki so kanki ki dagawa kanki kafa ki yi ma kanki uzuri, kin bashi rayuwa mai kyau ki tuna shi ya rayu da uwa da yar'uwa hakan ma abun farinciki ne a gareki" Ta daga kanta daga jikinsa ta kalleshi duk da kasancewar bata iya bude kwayar idon. "Na gode Vito na gode daka taimaka min gurin bashi gata da rayuwa mai kyau, na gode da baka taba gajiyawa da shi ko maganinsa ba, baka taba kyamarsa ba" Ya maida ita kirjinsa. "Ba zan taba kyamar abun da ya fito daga jikinki ba" Ya shafa bayanta a hankali alamar rarrashi. _______________________ Slowly slowly🥺 VITO is my favorite 🤭 Team VITO iya wuya🫶 [5/10, 7:12 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣4️⃣ "Har yanzu zuciyarki tana sha'awar musulunci ko Emily? Har yanzu baki dauki darasi daga azabar da muslmai suka koya miki ba? Da biyu kike zaune a cikin addinin kiristiyaniti ko?" Ta dago ta kalleta inda take kyautata zaton fuskarsa take domin bata iya gani da kyau. "A yanzu kake son mu yi wannan maganar?" "idan har babu wata manufa a zuciyarki a wane dalili zaki ce a kai shi makabartar musulmai? Ina ruwanki da kasancewarsa a baya musulmi? Ai kin canja masa addini ko? Ubansa da yake a cikin addinin be damu ba sai ke da kika haura kika leka ciki?" Ta rasa abun cewa, domin ta san ya fita gaskiya, Ubansa be damu ya san halin da take ciki ba balle abun da ta haifa gashi har London ya bar duniya be taba ganin ubansa ba. "Ba ni da alaka da musulmi ta kusa ko ta nesa, ba zan iya tafiya makabarta na tambayi wani yadda za a binne London ba, ina son kin Emily ina son yaranki, amman hakan ba zai saka na kusanci addinin da ba ni da makiyi irinsa ba" Ya mike tsaye ya dauki wayarta ya saka aljibu, ba tare da ta gani ba domin idonta a rufe suke. "Ka bar min dana bana son ka masa biki" Be juyo ba kuma be ce mata komai ba ya fice daga dakin, ko da ya sauko ya samu Chidimma zaune a falon har lokacin tana kuka sosai ita ma idonta ya kumbura domin mutuwar London ta zo mata a bazata. Wayar Emily ya ciro ya mika mata. "Ki aje wannan a gurinki karki bata har sai idan na bukata" "Okay Sir" Ta fada cikin kuka sannan ta karbi wayar ta tashi ta fice daga falon zuwa bangaren da dakinta yake ta boye wayar sannan ta dawo ta shiga dakin da Fatima take. Cikin karfin hali Emily ta tashi tana lalabe har ta isa bandaki ta kunna fanfo ta jika kanta da jikinta ta dauki karamin tawul ta zuba ruwan zafi ta gasa idonta, sannan tana iya daga su ta kalli abu but still tana jin ciwo. Ta fito bandakin ta nufi wardrobe dinta ta sauko short gown ta saka ta nufi gurin da makullin motar yake ta ga baya gurin, sai ta tuna yana cikin aljihun gown din data cire motar kuma tana can asibiti, gashi dare ne yanzu idan ta fita ba lallai ta samu abun hawa in time ba, haka kuma ba lallai ne ta tafi inda take nufin tafiya ta samu mutane a gurin ba. A nan ta fara neman wayarta ita ta rasa ina ta aje wayar, ta dafe kanta ta busar da numfashi sannan ta bude gurin da Vito yake aje mata kudi ta dauka ta fito daga dakin ta sauka kasa. Har ta nufi kofar fita sai kuma ta dawo ta sake haurawa sama zuwa dakin Fatima ta tura kofar a hankali ta leka sai ta hango Fatima kwance a jikin Chidimma, jan kofar ta yi ta rufe ta sauko ta fice daga gidan gaba daya. Ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa, ta kwatanta masa inda zai kaita wato gidan Tasmia, domin bata manta inda suka hadu ba har ta yi mata tayin shiga gidanta bata yarda ta shiga ba a wacan karon, da suka isa ta sauka ta bashi kudin da bata san nawa ba ne ta doshi gurin da kofar gidan mai kama da BQ yake ta kwankwasa, babu jimawa aka bude mata bayan Tasmia ta tambayi waye tace mata ita ce. Da maimaki take kallonta. "Lafiya? Me ya same ki?" "Zan iya shigowa?" Emily ta furta muryarta na rawa. Tasmia ta matsa jikin kofar ta bata hanya kana ra leka waje ta ga ko tana tare da wani ne. Ta shiga ta zauna sai wani sabon kuka ya zo mata. "Lafiya?" Tasmia ta tambaya tana dafata cikin tashin hankali. "I lost my Son" "Subhanallahi yaushe? Me ya faru?" Cikin kuka Emily ta fada mata yadda London ya mutu. "Na fi son yaron nan fiye da komai na duniya, saboda lalurar da take tare da shi, ina matukar tausayinsa" Tasmia ta kwantar da Emily jikinta tana hawaye. "Ki yi hakuri Emily amman na tausaya miki" Sai da ta yi kukanta ta koshi sannan ta fada mata dalilinta na zuwa gidan a cikin daren. "Gaskiya ban san wani makabarta ta musulmai ba, ban san inda za a iya binne shi ba, kin ga ni ma bakuwa ce a garin, ban da gidan yar'uwa da kuma wata kawata ban san kowa a nan ba sai ke, ita kuma kawar tawa bata nan ma kuma ba zata yarda ba, yar'uwa ta ma bana saka ran haka, saboda ba jini daya muke ba, cousin dita ce, kuma kin ga a yanayinki nan ba kowa zai yarda danki musulmi ba ne" "Ni ina jin kamar be dace a rufe shi a makabarta da ba ta musulmi ba, domin na san ni kaina ba a daidai nake ba" "Toh yanzu ya zamu yi?" Emily ta share hawayenta. "Akwai wanda nake saka ran zai iya taimaka min amman yanzu ban san inda zan same shi ba, saboda dare ne ya bar gurin aikinsa kuma ban san gidansa ba" "Wanene?" "Mutumen da ya kawo ni dazun ogana ne a gurin aiki, kuma mun taba haduwa da shi tun da dadewa, yana da kirki da zuciya mai kyau wata kila zai iya taimaka min" "Aliyu..?" Emily ta kalleta "kin san shi?" "Ba wanda na tambayi me yayi miki ya min bakar magana ba?" "Eh" "Mijin kawata ne, na san gidansa amman da gaske ba wani abun yayi miki ba?" "Be min komai ba, tuna rayuwarta ta baya ne da kuma mutuwar da London zai yi, ya taba ni yasa na zama yadda kika gan ni, kina da number wayarsa?" "Aa ke baki da ita?" "Ban san inda wayata taka ba, ina zan same shi yanzu" "Muje na kai ki gidansa, daman kuma matarsa bata nan" Sai da ta mike tsaye sai kuma ta fara tunanin inda za su samu abun hawa. "Amman anya zamu samu abun hawa yanzu?" "Ina motarki?" "Ba motata bace ta yar'uwa tace nake karbowa ina zuba mai sai na yi yawo da ita, amman muje wata kila ba zamu rasa samun abun hawa ba" A tare suka fito Tasmia na sanye da abaya da mayafi Emily kuma da tufafin jiki, sun yi tafiya mai nisa sannan suka samu texi suka shiga, Tasmia ce ta yi jagora har suka isa kofar gidan. Emily zata bawa mai motar kudi Tasmia ta hana ta biya kudin motar sannan suka fara kwankwasa gate din gida. Mai gadin ya bude yana musu kallon rashin sani. "Mai gidan yana ciki?" Tasmia ta tambaya da turanci be amsa mata ba sai ya tambayi lafiya. "Ka fada masa Emily tana nan waje tana son magana da shi" Ya juya ya koma ciki, babu jimawa ya dawo ya bude musu gate din suka shiga, Tamia ta wuce gaba domin ita ta taba zuwa gidan sai da suka isa gurin kofar shiga sannan ta koma baya ta bar Emily a gaba, Emily ta tura kofar falon ta shiga Aliyu na tsaye sanye da jallabiya yana raga volume din wa'azin da African Tv suka saka, sannan ya juyo ya kalli kofar yana amsa sallamar da Tasmia ta yi domin Emily bata yi sallama ba ta shiga. Be gama mamakin zuwansu gidan cikin dare nan ba, yayi arba da Fuskar Emily da idonta da suka kumbura. A take zuciyarsa ta raya masa mutumen nan ne yayi mata duka wata kila saboda ya kaita gida. "Me ya same ki? Ko dukanki yayi?" "Danta ne ya mutu" Tasmia ta amsa masa sai yayi kalmar shahada ya zauna ya dafe kansa cike da tausayinta, yaron data gama bashi labarin wahalar da ta sha akansa shi ne kuma ya mutu a yanzu. "Mun zo nan ne saboda tana son ayi masa jina'iza irin ta musulunci, ni ma kuma bakuwa ce a garin nan ban san kowa ba amman ita tace...." Tasmia ta fada masa abun da yake tafe da su domin Emily bata komai sai hawaye. Aliyu ya sauke ajiyar zuciya. "Yaron yana ina yanzu?" Sai a nan Emily ta iya amsawa muryarta na rawa. "Yana can dakinsa yana gida" Aliyu ya dubeta duban da ya dauke shi tsawon dakika 120 yana kallonta. "Emily" Ta dago ta kalleshi ba tareda ta amsa ba, a zatonta zai ce mata ba zai samu damar aiwatar da kudirinta ba ne. "Mu a musulunci akwai shika shikan imani da akan gindawa kowane musulmi, ina kyautata zaton lokacin da kika musulunta an fada miki su? A ciki akwai imani da kaddara mai kyau da marar kyau, na san kin tsani musulmi kin tsani musulunci amman ni ina ji a jikina wannan imanin da kika yi da Allah har yanzu yana nan cikin zuciyarki, kuma ban kara tabbatar da hakan ba sai a yanzu, dan haka ki yi hakuri da wannan rashin Emily, kuma na jidadin shawarar da kika yanke na yi masa sutura irin ta musulunci, shi kanshi da ace zai dawo yanzu zai miki godiya na abun da kika yi masa, kuma ina tabbatar miki zan yi masa duk wani abu da ake yi ma musulmi In Shaa Allahu" Ta amsa masa da kai tana matse jikinta wani yanayi take ji marar dadi. Aliyu ya shiga dakinsa sai gashi ya sauko sanye da kananan kaya. "Zan tafi da mai gadi na mu dauko gawarsa, zan masa wanka a yau da duk abun da ya dace In Shaa Allahu, da safe sai ayi masa sallah a kai shi makwancinsa" Ta mike tsaye. "Idan ba mu je tare ba, ban san iya abun da zai faru tsakaninka da Vito ba idan ka tarar da shi a gidan ba" "Karki damu ina addu'a aljani ma be isa ya cutar sa ni ba sai da izinin Allah balle Vito" "Baka sanshi ba ne, baka san irin hadarin da yake da shi ba" Ta fada tana kuka. "Idan na je na tarar yana gidan ba zan dauko ba zan dawo sai mu tafi da ke" Sam bata yarda ba, saboda ta san Aliyu be san aikin Vito ba, kuma be san hatsarinsa ba. "Zamu tafi tare, mai gadin ma ba zai bari ka shiga ba" Aliyu ya kalli Tasmia. "Kin iya mota? Ko?" Ta daga mishi kai, sai ya shiga ya dauko makullin wata motar ya bata, shi kuma ya shiga motarsa tare da mai gadinsa, ya rigasu isa gidan amman ya tsaya har sai da Emily ta shiga ciki ta yi ma mai gadin magana sannan Aliyu ya shiga har dakin da London yake ya cire shi a cikin coffin ya saka bedsheet ya lullube shi ya fito da shi Chidimma na ta kallonsa Fatima kam ta dade da yin bachi a lokacin. A gidan suka dawo ya fada a musulumci idan mutum ya rasu ana masa wanka sannan ayi masa sutura ayi masa sallah. Tun a cikin daren Aliyu yayi masa wanka na aje gawarsa a wani dakin na dabam. Tasmia na zaune falo tare da Emily, Tamia ce kawai ta iya angaje Emily kam idonta biyu har safe. Misalin karfe shida da rabi Aliyu yayi waya da wani daga cikin yaran da yake sakawa aiki idan yana bukatar wani abu, suka kawo masa likkafani ya shirya London a ciki sannan ya sauko falon Emily na ta kallonsa ya ce. "Kina son ki ganshi?" Ta daga mishi kai. Sai Tasmia ta hana. "Ba lallai ne ta iya rike kanta ba" Aliyu ya kalli Emily. "Ba zaki ihu ba? Kin yi alkawari?" Ta daga mishi kai. "Shiga ki ganshi, kina da hakkin ganinsa ko a musulunci ana son iyalin mamaci su yi bankwana da shi" Tasmia ta ki shiga Emily kam ta taka ta isa har kofar dakin ta tura ta shiga. Ta hango shi kan tabarma an nade shi da zane ta cikin zanen kuma an masa sutura da farin kyalle wato likkafani. Ta karasa ta zauna kasa inda yake ta bude zagen ta bude likkafani har ta kai ga fuskarsa, tana ta kallonsa. "Mun wahala ni da kai, amman kai ka fini wahala saboda kai baka gane komai a cikin duniya, na dauki cikinka da yunwa da wahala na haife ka daker, kuma sai ka zo ba a lafiyayye ba, ammam a yau komai ya zama labari, rashin farinciki da samuwarka da mahaifinka be yi ba, rashin son sanin kana raye ko a mace yau duk ya zama tarihi, yau an rufe babin rayuwarka Ibraheem, ka tafi kana fushi da ni saboda cutar dake damunka bata barka ka fahimci ina kaunarka ba, kuma zan yi ta kewarka har karshen rayuwata" Ta kai bakinta ta sumbanci goshinsa hawayenta na sauka a fuskarsa. Sannan ta rufe masa fuska ta gyara komai kamar yadda ta tararda shi. Ta taso ya fito daga dakin Aliyu yana ta kallonta har ta iso gurin da yake tsaye, sai ya ji ta burgeshi, a iya saninsa wadanda ba musulmai ba idan aka musu mutuwa ihu suke suna faduwa suna tashi suna burgina da tambayar ubangijinsu Meyasa ya aikata hakan? Amman a gurinta ya ga banbancin haka. Misalin karfe tara yayi waya a gurin aikinsa duk wanda yake musulmi ya saka aka dauko shi aka kawo shi gidansa wasu suka suka zo da kansu, Emily tana tsaye jikin window falon Kameela tana kallo suka yi sahu Aliyu yayi jagoranci yi masa sallah sannan suka dauki gawar yaron suka fita da shi. Ta zauna a falon shiruuuuu tana ta tunani kala kala, Tasmia ta kwantar da ita a kafadarta. Suna haka Aliyu ya dawo tare da mai gadinsa domin sauran mutane daga makabarta suka wuce gurin aiki. Da ya shigo sai ta tambaye shi nawa aka kashe mutanen da ya kira suka yi masa sallah da kuma tafiya kai gawar makabarta ma nawa aka kashe. Yayi murmushi yana kallonta. "Mu a musulunci idan aka yi ma gawa sallah kana da lada mai yawa balle kuma ace ka raka gawa zuwa gidanta na gaskiya, ladar suke kwadayi ba biya ake ba, abubuwan da aka siya kuma ni na dauke ladar" "Na yi zatona akan daidai, kai kadai ne namiji mutumen kirki musulmi, na gade Aliyu" "Ina rokon Allah yasa ki samu musulmai fiye da yadda kike kyautata min zato, Allah ya sanyaya zuciyarki Aisha" Tasmia ta amsa da Ameen tana jin dadin abun da Aliyu yayi har cikin ranta ta ji ya burgeta. Emily ta kalleta. "Ban takura ki ba idan na biki zuwa gidanki?" "Aa babu takura haba Emily ni da ke ai mun zama kawaye" Tasmia ta kama hannun Emily suka fice daga falon, kamin su isa gate Aliyu ya iso gurinsu da mota suka shiga ya kai su unguwarsu Tasmia, sannan ya juya ya koma, suna shiga ciki Tasmia ta hada ma Emily ruwan tea Emily ta sha kadan ta kwanta akan gadon Tasmia, tana ta kallon sama hawaye na mata zuba. Misalin karfe biyu na rana Aliyu ya dawo gidan domin babu wayar da zai iya jin Emily kuma yana son ya san halin da take ciki, ya kwankwasa kofar dakin Tasmia ta bude be shigo ba ya tsaya daga bakin kofa. "Na zo na duba Emily" A lokacin Emily ta samu yin bachi dan haka Tasmia ta amsa masa da. "Bachi take, ka shigo ciki" Ya girgiza mata kai ya juya zai wuce Tasmia ta ce. "Karka damu ba zan fadawa Kameela komai ba, ban san a ina kuka hadu ba, ban gama saninta ba, amman alamu na nuna ta sha wahalar rayuwa ina tausayinta sosai" "Wata kila da zaki saurari labarinta da zaki fi tausaya mata sosai, dan Allah ki zama jekadiyar musulunci ki canja rayuwar yarinyar nan tun da har ta yarda da ke" "In Shaa Allah" Ta juya yayi tafiyarsa ta bishi da kallo tana murmushi sai da ta ga zai shiga mota sannan ta rufe kofar gudun kar ya ga tana kallonsa ta koma tana lekensa ta windows. Bayan ya tafi ta dawo falon ta zauna after like 5 minutes ta ji an kwankwasa kofar ta tashi tana mamaki Aliyun ne ya dawo ko kuma wanene. Ta fara lekawa ta hango mutumen da annuri be samu gurin zama a fuskarsa ba, gabanta ya fadi ta matsa baya. "Waye wannan?" Bata samu amsar tambayarta ta aka sake buga kofar dakin. "Waye" Yaki magana sai kwankwasawa yake, sai a lokacin take dana sanin yin magana da tayi domin bata san waye ba gashi ta yi magana ya ji cewar akwai mutum a ciki. "Bude..." Ta juyo ta kalli Emily dake tsaye bakin kofar bedroom dinta. "Wani ne mai kama da marasa imani" "Na san waye bude" Ta bude ta yi baya tana kallon kofar Vito ya turo kofar ya shigo hannunsa daya a aljihu. "Ina tunanin mun kai karshe da ke cewar babu ke babu alaka da kowa? Amman gashi kin tafi gurin wani kato ya rufe danki yanzu kuma kin zo nan, Emily kina manta waye ni ko? Duk wani motsi naki akan idona yake" "Bayan wannan bana da wata kawa ko yar'uwa da nake alaka da ita, dan Allah ka bar min wannan ita kadai" Ta fada ta sigar magiya, ya kalli Tasmia da tuni mararta ta cika da fitsari ya ciro hannunsa ya nuna mata wata yar mitsitsiyar bindiga dake aljihu mai kama da ta wasan yara. "Ki yi taka tsantsan" Tasmia ta zube kasa "Wallahi har taka tsaki da tsakuwa ma sai na yi idan baka son alaka da ita ba zan sake ba, kai ni ban ma santa ba" Ta juya gurin Emily. "Ke na sanki? Kin san ni, ka gani ba mu san juna ba" Sai kuma ta fashe da kuka. "Wallahi ba ni da kowa a garin nan dan Allah ka rufe min asiri, bautar kasa na zo amman idan kace yau na kama hanyar garinmu Wallahi zan tafi..." Vito ya mikawa Hannu. Emily taka ta isa gurin da yake ta rika hannunsa tana kallon Tasmia ya jata suka fice daga falon. Motarsa ya bude mata ta shiga sannan ya shiga yaja motar be zame da ita ko'ina ba sai gidansa. Yana yin fakin ta kalleshi. "Me zamu yi a nan?" "A nan zaki zauna for now" Ya fita ya zaya ya bude mata, fitowarsa ta yi daidai ta fitowar mahaifiyarsa ta nufo inda take. _____________________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/17, 1:00 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣5️⃣ After like 2 hours da tafiyar Emily Aliyu ya dawo gidan Tasmia ya kwankwasa ta bude masa a tsorace. "Ta farka?" Shi ya fara tambayarta domin damuwarsa a yanzu bata wuce ya san halin da take ciki ba. "Ai kana tafiya ina jin ko minti talatin ba ayi ba, wani mutum mai ban tsoro ya zo ya tafi da ita, har da yi min gargadi wai na yi hankali, ka ga kayana can duk na hada gobe ni barin garin ma zan yi" Tana maganar jikinta na rawa. "Saboda me?" "Da bindiga fa ya zo nan kuma daga ganinsa ba shi da imani kafiri ne ga Cross a wuyansa fuska babu annuri, ita kanta daga gani tsoronsa take" "Shi ya kawo ki da zai ce ki bar gari? A wane dalili? Ku daina sakawa kanku tsoro da yawa shi yake bawa mai cuta damar cutar da ku, karki je ko ina ki yi zamanki babu abun da zai same ki sai abun da aka rubuta ya kasance gareki" "Wato ba ka ga bindiga ba ne shiyasa kake fadin haka kuma baka ga fuskarsa ba" "Zaman a nan ra'ayinki ne, tafiyar ma ra'ayinki ce idan kin so" Ya fada mata sannan ya juya ya shiga motarsa ya bar gurin. A wunin ranar da darenta Aliyu ya wuni ya kwana da tunanin halin da Emily take a zuciyarsa, wata kila mutumen yana can yana dukanta saboda ta yi ma danta abun da take jin ya fi zama kwanciyar hankali da natsuwa a gurinta, zuciyarsa na raya masa wata kila yanzu ya canja mata kamanin fuska saboda duka, bakinciki zai zame mata biyu ga rashin danta ga duka. Ya busar da iskar bakinsa ya shafa kansa hannunta rike da mug yana sanye da kayan bachi. Sai da ya kira sahibarsa suka gaisa ya ji tashinta ya kira mahaifiyarsa, sannan ya sake gwada number Emily da har cikin dare yayi ta kira saboda ya ji halin da take ciki sai ya ji wayar a kashe. "Ki kirani idan kin riski sakona, ina son na san halin da kike ciki" Ya aika mata sako sannan ya zauna ya aje Mug din yana kallon harabar gidansa kamar wani bako. Can zuciyarsa ta raya masa zai iya zuwa ba tare da ta kira shi kamar yadda ta yi a wacan karon, waya sani ma ko Viton ya karbe mata waya ya hanata kiran kowa. Ya tashi ya koma ciki yayi wanka yayi shirin office na kananan kaya ya fito yana ta kamshi ya shiga motarsa ya dauki hanyar office dinsa, yadda yayi zato ba haka ya samu ba, domin be samu Emily na jiransa a office ba, har tambaya yayi ko akwai wanda ta zo nemansa aka ce aa. Ya wuni a office da damuwa kamar wanda shi ne yayi silar shigarta a wani hali, nishadin aikin ma ya nemeshi ya rasa, bayan ko wace awa sai ya gwada kiran number ta sai ta ji a kashe. Be tashi aikin da wuri ba sai 4pm duk kuwa da kasancewar da wuri ya shigo office saboda son sanin halin da Emily take ciki. Daga Office dinsa kai tsaye  ya wuce gidan Tasmia ya dade yana knocking sannan ta bude, be shiga ba ya tsaya daga bakin kofar ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ko kin ji daga gurin Emily?" "Aa" "Kin gwada kiranta?" Ta kalleshi tana magana a hankali. "Eh amman ban same ta ba" Ya juya ba tare da yace komai ba, Tasmia ya rufe kofar ta koma ta gurin windows tana lakensa har ya wuce. Haka yayi ta jera mata ranaku kusan kullum idan ya taso daga office sai ya biyo ya tambaya ko ta ji daga gurin Emily, sai ta amsa masa da aa, ko yayi kamar ba zai je ba, sai wata zuciyar ta raya masa wata kila yau ta je ko kuma ita Tasmia ta samu waya da ita. A wani zuwa da yayi neman Emily Tasmia ta bukaci ya bata number shi so that idan ta zo ko ta ji daga gareta sai ta kira shi, be bata ba kawai yayi tafiyarsa. Sai da ya kwana biyu be sake zuwa ba, sai kuma gashi ya dawo neman Emily da har mafarkinta yake saboda ya damu da halin da take ciki, a zuwan da yayi ya tambayi Tasmia ko ta ji wani abu daga gurin Emily ta fada masa har lokacin babu labari, a ranar ya zabi ba zai sake zuwa ba saboda ya hutar da kansa zuwa neman Emily domin ba mutuncinsa bane zuwa gurinta, duk da yake dai be taba tarar da namiji ko wata macen da bata dace ba a gurin, dan haka ya yaba da hankalin Tasmia, domin har zuwa lokacin matarsa bata san wainar da ake toyawa ba. Da Aliyu ya ga an doshi sati na hudu babu Emily babu labarinta sai ya zabi tafiya gidanta kai tsaye, faka motarsa a waje ya bude ya fita ya doshi gate din gidan yana isa ya kwankwasa, mai gadin ya bude yana tambayar abun da yake bukata, sai ya fada masa yana son ganin Emily ne, ya fada mashi bata gidan ya koma ciki ya rufe Aliyu ya busar da iskar bakinsa ya koma motarsa, ya dade a haka kamin ya ja motar ya koma gida. Immediately after gama sallah isha'i ya tuko motarsa ya shiga unguwar Emily ya faka nesa da gidan ta Inda ba za a ganshi ba ya kashe hasken fitilar motarsa yana kallon gate din gidan, so yake ya gane idan da gaske bata gidan ko kuma tana ciki. Be bar gurin ba sai 11pm na dare, ya isa gida tare da yanke shawarar zai dagawa kansa kafa daga neman Emily duk kuwa da ya san zuciyarsa ba zata bar shi ya samu sukuni ba domin be san halin da take ciki. A tunaninsa ya iya abun da zai iya a yanzu, idan ma tana bukatar taimakonsa zata iya nemansa ko mayar masa da amsar sakonnin daya tura mata. Sai da ya fito wanka sannan ya kira Kameela a waya, sun dade suna waya har yake fada mata a satin nan zai shigo domin yayi missing dinta kuma ta yi arba ta kusa dawowa. Suna yin sallama sai ga kiran Ummi ya shigo wayarsa ya amsa yana murmushi. "Hajiyata barka da dare baku kwanta ba" "Yanzu dai nake ta shirye shiryen kwantawar, mahaifinka kuma be ma shigo ba, yana can falonsa da baki" "Oh Ummi siyasa sai ku, karfe kusan sha biyu dare zan tsaya da baki? Kai ni bana iya wannan" "Bata kama ka ba ne kawai malam idan ta kama ai dole ayi" "Haka ne kuma, amman dai Allah ya bar ni a haka bana iya wannan" "Ameen idan shi ne alheri, ya matarka kasan ta gama wanka ko? Ta yi arba'in fa ko da yake ka ma fini sani ai" Yayi murmushi mai sauti. "Eh ba mu dade da gama waya da ita ba, kika kira ina tunanin weekend din nan zan shiga In Shaa Allahu" "Toh Allah ya taimaka, zamu aika ayi bikonta" "Idan mace zata dawo har bikonta ake?" "Eh amana" "lallai mata yan gata, okay zan fada mata" "Aa ba kai zaka fada mata ba, kai dai na fada maka ne saboda na baka naka hakki wannan aikin nawa ne ka bar ni na yi" "Na bari Ummi, akwai abun da ake bukata" "Eh kamar dala dari biyar haka" Ya kyalyale da dariya har yana shafa kansa. "Ummi kun shiga cikin kasar nan har da ni za a daki hancina?" Ta yi murmushi mai sauti. "idan ba iskaci ba duk abun da ake akwai wanda ka taba bada sisinka? Zaka ce akwai abun da ake bukata ko kudin ne suke maka kaikayi?" "Allah ya huci zuciyarki matar dan majalisa ni dai yanzu sai yadda aka yi da ni" Ta girgiza kai tana hamma. Haka suke wani lokacin ita da shi kamar yaya da kanenta ba uwa da ɗa ba. "Mu kwana lafiya ranka ya dade dan masu govnati" "Good Night Ummi Allah ya kara miki lafiya" "Ameen Ya Rabbi" Ya aje wayar yana murmushi. Satin da Emily ta cika sati biyar be ji daga gareta ba ya shirya ya tafi Kaduna gurin masoyiyarta sai dai ko a ranar kamin ya wuce sai da tafi gidan Emily ya tambayi mai gadinta ko tana nan yace masa a a. Shi dai kawai ya damu ya san halin da take ciki ne, wata kila zai iya taimaka mata ko cetota daga wani abun. Ya san ba lafiya ba domin har yanzu bata kira shi ba bata mayar masa da amsar sakon da daya tura mata ba, kuma bata zo ko ta aiko an dauki motarta dake gurin aikinsu ba. EMILY POV. 5 Weeks Later.... Hannayensa ya saka ya rufe windows din da iska ki shigowa da karfi ya ja curtains din, sai ta juyo ta kalleshi. "Kin ci abincin dare?" Ta daga mishi kai, sai ya riko hannunta ya nufi suka zauna kan kujerar dake dakin. "Emily zamanki a nan takura ne? Kina jin kamar na takura miki ne?" Ta girgiza kai alamar aa. "Tun da kika zo kin kasa sakewa, not even me or my mother" Ta sauke kanta kasa. "Zuciyata ta kasa sakewa, yanzu kuma bayan London wa zan sake rasawa? Fatima? Ko kuma Fatima zata rasa ni ta rayu ita kadai, tunani da hankali ya tattara ya koma a kan gobena" Ya shafa kanta. "Ba zaki sake rasa kowa ba, zamu rayu tare zaki samu soyayya da kulawa zaki samu wani iyalin" Ya kwantar da ita jikinsa. "Bani da wani buri a duniyar sai naki, bana jin akwai wanda ya zame min wajibi na kula da shi sai ke, ina son ki Emily ko a ina nake tunaninki nake, duk wani abu da nake kauna a duniya bayanki yake" Ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. "Baki tunanin lokaci yayi da ya kamata mu bawa junanmu farin ciki? Ya kamata ki bude zuciyarki ki manta da baya da rayuwar baya, a ganina lokaci yayi da ya kamata ace jira ya kare tsakanina da ke" Ta dago daga jikinsa ta kalleshi. "Emily lokaci yayi da ya kamata mu yi aure" Ta ji gabanta ya fadi ba tare da dalili ba. "Kin san ni kin san waye ni, na san ki kuma na so ki, kuma kin san cewa har kasa ta nade wani be isa ya so ki ba sai ni, toh bata lokaci na miye? Har zuwa yaushe zan yi ta jiranki?" Ya kama hannunta. "Na lura baki son na taba ki a yanzu, shiyasa nake daga miki kafa, a yadda nake sonki na fi son mu yi komai cikin farin ciki, kuma auren ki kadai ne zai tabbatar da hakan" Ta zare hannunta daga rikon da yayi mata ta mike tsaya ba tare da ta ce komai ba. "Kina jiran mutanen da suka wulakantaki ne su dawo miki? Ko kuma wani kike dako a gaba? Mutanen da suka rasa ki sun rasa ki kenan har abada, wanda kuma yake zuwa nemanki idan wani abu ne a zuciyar sa toh yana wahalar da kansa ne kawai domin ke mallakina ce kamar dai haka" Ya cire zobe hannunsa ya nuna mata sannan ya maida zoben a dan yatsansa. Ya mike tsaye ya fice daga dakin ya barta tsaya tana mamaki da tambayar kanta wa ke zuwa nemanta? Wata kila Tasmia ce, amman namiji yace, bayan Aliyu bata san wani namiji da zai zo nemanta ba, ko kuma Turhan ne? Ta tambayi kanta, for the first time bayan dawowarta gidan ta ji tana bukatar wayarta, wayar da tun a ranar da London ya mutu bata sake bi ta kan wayar ba, a zamanta nan kuma tunaninta ya tafi a gurin danta da ta rasa bata damu ta nemi wayar ba. Tun da ya dawo da ita gidansa bata fita ko'ina daga cikin gidan sai harabar gida, ya dauko Chidimma da Fatima ya dawo da su gidan a tare da ita ga kuma mahaifiyarsa. Sai dai ko kadan Fatima bata son zaman gidan saboda mahaifiyar Vito da take ganin ta takura mata, kuma ga shi bata so bata masa biyayya Vito. Emily ta nufi kofar dakin ta fito ta sauko hawa na biyu a zatonta Vito yana gurin domin ya fi yawan zaman a falon dake hawa na biyu, a gurin ta zauna tana tunanin ko dai Aliyu ya bawa Turhan addireshinta ne ya zo nemanta? Ko kuma Aliyun ne da kansan yake nemanta.? Kamar an tsikare ta mike tsaye ta sauka falon na farko bata karasa sauka ba ta ji muryar Fatima tana ihu da fadin "I hate you... I hate you" Ta sauka da sauri ta nufi gurin da Fatima take tsaye Chidimma na gefenta tana rike da cups din da aka fasa, Vito na zaune kan kujera ya dora kafa daya kan daya yana kallon Fatima fuska babu annuri. "Me ya faru?" "Me yake sabu a ciki? Rashin kunyar da yarki take yi ko kuma fadar bata son Vito a gaban kowa? Gaba daya yarinyarki bata da tarbiya, taya zata kalli idon mutumen da akarkashinsa kuke tana zaginsa?" "Ki yi hakuri Momy ina iyakar kokari gurin ganin na gyara halayyar Fatima na san abun da take ba shi da kyau amman ita yarinya ce" "Ina kokarin da kike yi nuna min na gani. yara nawa ne sa'ainta basa abun da take? Yarinya karama amman ta iya shiga idon manya? Idan ba Vito ba wa zai iya zama dake ko yarki?" Sai a lokacin Vito ya mike tsaye domin ya ji mahaifiyarsa ta fara saka Emily. "Okay that's enough" Yaja Emily ya maida ita bayansa. "Ba laifinta ba ne, wannan yarinyar da kika gani ga dukan alamu bakin halin mahaifinta ta dauko shiyasa bata kama da Emily ko kadan, saboda babu halin ta ko daya a tare da ita" Fatima ta sake kallonsa "I hate you i hatee youuuuuuuuu" Ta kalli mahaifiyarta. "Momi na ce miki bana son nan gida nake son tafiya bana son nan" "Okay zamu je" Emily ta amsa da sauri kana ta kalli Vito. "Ina son zan koma gida" Momin ta Vito ta yi dariya. "Baki da ra'ayin kanki kenan sai na yarki? Karamar yarinya zata juyaki tana fada miki yadda zaki yi? Shiyasa kike kyale ta tana abun da ta ga dama?" Emily ta daka mata tsawa. "Yata ita kadai ta rage min a yanzu ba ni da wata bayan ita, abun da take so shi nake so, ki cire idonki akan yarinyata, tun da muka zo gidan nan kullum sai kin ce ga laifinta" Momynta ta mike tsaye tana kallon Vito. "Kajinta ko?" Vito ya kalli Emily calmly yace "Je ki jirani gurin mota, Chidimma zata hado kayanku yanzu zan kaiki gida" Emily ta kama hannun Fatima suka fice daga falon, Chidimma ta sauke numfashi ta nufi Kitchen ta zuba cups din hannunta a shara sannan ta fito ta haura sama inda dakin Fatima da Emily yake. "Kana ji tana fadar abun da yarta take so shi take so? Daman ina tunanin bata lokacinka kake yi a kan yarinyar nan baka yarda ba" "Bana bukatar Emily ta so ni, tun da ni ina sonta hakan ya wadatar, na sani tuntuni ban gama shiga zuciyarta ba, amman da sannu zata gane kuma zata gode min ta kaunace ni, zuwa lokacin da ta rasa Lisa (Fatima) za ta gane bata da kowa sai ni" "Idan kuma hakan bata faru ba fa?" "Abun da yake nawa nawa ne har abada ke kin sani, dole zan yi ma Emily uzuri saboda ta sha wahalar rayuwa, kuma ta tashi bata da kowa bata yan 'uwan bata san kowa a jininta ba sai yaran da ta haifa, daya ya mutu sauran daya to me zai saka ba zata ki abun da yarta take ki ba?" "Wai miye a wannan yarinyar da lekewa haka ne? Kana da kudi zaka iya samun kowace mace kake so a duniyar nan, idan ma fari ne akwai fararen mata, idan kana ganin kamar ita baturiya ce zaka iya tsallakawa ka auro wanda kake so wanda ta fita kyau da komai, ita wannan fa har ta haihu kana ta wahala da yaran da ba naka ba" Ta nufi windows din falon ya daga curtains din yana kallon Emily dake tsaye jikin motarsa tana cizon hannunta. "Abun ba daga kyau ba ne kawai, wani abu ne ya hada zuciyata da kaunarta ya daure, kamin ita ai na ga mata da yawa ban so kowa ba sai ita, bayan ita ban ga wata wanda zan iya so ba, yarinyar da dukiyata bata dame ta, sanin tana da damar da zata iya sakawa na wulakanta kowa akanta be taba burgeta ba, ita kadai ce macen da ta saka na ji ina sha'awar tara iyali, mutuwar danta nan tana da damar ta tuhume ni saboda ni na barshi na fita alhalin ba a barinsa shi kadai, amman bata tana ce min komai akan haka ba bata taba nuna min bacin ranta ba, a yanzu zuciyarta a bushe take, nakasassun mazan da suka rayu da ita basu gwada mata komai ba sai azaba shiyasa har yanzu bata san yadda zata so kowa ba" Ya juyo ya kalli Mahaifiyarta. "Akwai mata da yawa, amman masu irin halinta kadan ne, a idona kuma ita kadai ce, kuma baki fahimce ta, karki sake fadin wata magana marar dadi akan Emily indai kina so, ki so Emily...!" Yana kawai nan ya nufi kofar falon ya bude ya fita, Emily na hango shi yana saukowa ta nufo shi da sauri tana hawaye. "Vito I'm sorry kasan be kamata na yi magana da mahaifiyarka haka ba, raina ne ya bace kuma..." Be bari ta karasa ba ya rumgume. "Na fahimta" "Zaka iya bata hakuri?" "Eh, shiga mota muje" Ya sake ta sai ta zagaya ta shiga motar Fatima daman ta dade a ciki zaune sai cika take tana batsewa kamar wata babba. Be jira Chidimma ta zo ba yayi ma motar key. "Chidimma bata zo ba" Be ce mata komai ba yaja motar suka fita daga gidan. Har suka isa gidan da ya tanadar ma be ce mata komai ba ita ma bata ce masa ba, amman hannunsa na rike da nata yana tuki da dayan hannun. Be gama farkin ba Fatima ta bude motar ta fita ta bar masa gambun a bude, fita yayi ya zagaya ya rufe motar ya budewa Emily ta fito tana kallonsa, ta kai hannu ta taba fuskarsa sai ya matsa baya ya bata hanya ta ratsa shi ta nufi cikin gidan shi kuma ya koma motar yaja ya fice gidan. Ta samu gidan yayi kura yayi gummm irin na gidan da aka dade ba a shiga ba, guri ta samu kusa da Fatima ta zauna tana jin kewar danta London yana dawo mata. "Kin ce zaki nemi kudi zaki yi gida mu bar karkashin Vito amman har yanzu ba ki yi ba" Emily ta dube ta. "Zan yi Fatima zan nema har ma dace zan zama miki irin rayuwar da kike so, ba ni da wani nauyi da ya rataya a wuyana yanzu sai na ki, amman ki daina abun da kike yi, ba haka yara suke ba, meyasa ke kika fita dabam?" Ta yi shiru tana turo baki, Emily ta ja jikinta ta rumgume tana jin rashindadin fadan da ta yi mata a yanzu. "Momy, yanzu tun da London ya mutu zan iya amfani da sunan mahaifinta a makaranta? So that yan ajinmu su daina min dariya?" Ta tambaya murya kasa kasa, Emily ta hade wani abu daya tsaya mata a makoshi ta lumshe ido. "I miss him" Cewar Fatima cikin sautin kuka. Emily ma kukan take. "I miss him too" Ta kara kankame yarta hawaye masu zafi na sauko mata. A haka Chidimma ta zo ta same su bayan direban dake gidan Vito ya kawo ta. "Zan yi kokari na baki rayuwa mai kyau Fatima, ni kam ba zan miki abun da iyayena suka min ba, ba zan taba bari ki ji cewar baki da kowa ba, ba zan taba wulakanta ki kamar yadda mahaifin London da naki suka yi ba, ina son jini ko yaya yake" "Momy waye babana? Baki san bani da baba ba? To waye kuma baba na?" Fatima ta tambaya tana lafe a jikinta. Emily ta share hawayenta da sauri. "Idan kina son uba to ki rike Vito a matsayin Ubanki" "Bana son shi" Emily ta dago ta. "Baki da hujjar tsanarsa, kalli gidan da kike zaune, makaranta mai kyau ya saka ki, ya dauki mai girka muku abinci, tufafi sai wanda kika zaba kike sakawa, a ciki wadanda na aura akwai wanda ya bani rabin rayuwar da kike ciki yanzu?" Ta dauke da mari tana daka mata tsawa. "Karki sake min maganar abun da ya shafi ubanki" Fatima ta saka wani irin ihu ta dafe kunci, Emily ta tashi ta bar mata falon. Sai dai bata iya fushi ba dan haka ta dawo ta rarrashi yarta saboda tana jin babu mai rarrashinta sai ita ta rumgumeta, a tare suka kwana kamar yadda ta saba mata a yanzu tun bayan mutuwar London kullum a gado daya take kwana da Fatima. Washe garin ranar bayan Fatima ta tafi makaranta Chidimma tana ta aikin gyara gida Emily ta shirya ta fita saboda tana jin gidan ya mata babu dadi. Taxi ta shiga ta tafi gurin sabuwar kawarta Tasmia daman bayan can ai bata da wani gurin zuwa. Bata same a apartment din nata ba dan haka ta zauna a gurin har sai da Tasmia ta dawo. Da gangan ta yi kamar bata gane Emily ba. "Malama lafiya?" "Lafiya kalau" "Toh na ga kin zauna a nan ne" "Ina jiranki ne" "Kina jirana? Kin san ni ne? Wani abun zan miki ne?" "Haba Tasmia" "Malama ni fa ban san ki ba ban taba ganinki ba" Emily ta mike tsaye. "Karki fara wannan wasa" "Fine na gane ki, amman fa gaskiya ba zaki zo ki janyo min matsala ba" "Bana fatan janyowa kowa matsala, kin tsorata ne?" "Yanzu dai ba wannan ba me kika zo yi nan" Ta yi shiru na mintuna. "Bana da gurin zuwa ne kawai na zabi na zo nan, kuma na ji anje nemana gida na yi zaton ko kece ko Aliyu" "Ba ni ba ce, ni ba zan tafi gidanki ba yanzu kam, Aliyu ma ba shi ba ne domin be taba zuwa nemanki ba" "Okay zan tafi, duk lokacin da kika ji zuciyarki ta natsu da ni, kin san gidana kuma kina da number da wayata, sai anjima" Emily ta tafi ta barta tsaye a gurinta tana binta da kallo. A taxi ta dawo kamar yadda ta tafi a taxi ta shigo gidanta tana share hawaye. A falo ta samu Vito zaune Chidimma na zuba masa ruwa a cups. "Do you take my phone?" Ta tambayi abun da yafi zame mata wajibi a yanzu, domin jiya ta duba ko'ina bata ga wayarta ba. Vito ya kalli Chidimma yayi mata alama da kai sai ta tafi dakinta ta dauko wayar ta mikawa Vito da hannu biyu be karba ya aje cups din dake da sauran ruwa ya kalli Emily, sai ta juya da wayar bangaren Emily da hannu daya ta mika mata. "Akwai wata number data turo miki sako har sau hudu wai ki kirashi ya damu da ke" Emily ta karbi wayar da hannu daya sannan ta ware dayan hannunta ta wanke fuskar Chidimma da mari. "How dare you take my phone? Har ki karanta min sako?" "Ta saman screen na karanta sakon ni ban san password din ba ma, shi ma na kunna wayar ne kawai saboda na tabbatar tana yi saboda faduwar da ta yi a hannuna, bayan haka kuma na kashe ta kamar yadda take" Cewar Chidimma cikin kuka. "Waya aikeki daukar min waya? Tsawon kwanakin nan da na yi ban damu da wayata ba ashe tana gurinki?" "Ba ita ta dauki wayar ba, ni na bata ta aje, amman me zai saka wani ya turo miki sako? Miyasa zai damu da ke?" Vito ya bata amsa sannan ya dora mata da tambaya, Chidimma kuma ta fashe da kuka har da zubewa kasa. "Burinka kai ka raba ni da kowa, so kake ka ga ina rayuwa cikin kunci, matar da na samu mai kyakkyawar zuciya ta rike ni a matsayin kawa yau naje ta nuna bata san ni ba, saboda ka lalata tsakaninmu ka firgitata" Ta dauki ragowar ruwan da ya sha ta watsa masa a fuska. "Ni na saka ya damu, zo ka kashe ni ka huta" Ta wuce fuuuu ta haura sama, binta yayi da kallo sai kuma yayi murmushi ya kalli Chidimma dake ba shi hakurin ruwan da Emily ta watsa masa, ya rikota ya mikar da ita tsaye. "Karki damu" Ya fice ya bar falon. Emily ta shiga dakinta ta zauna tana ta haki kamar wanda ta yi yaƙi, ta kunna wayar ta cire Password ta shiga messages box dinta na sms sakon Aliyu ne kadai sakon da ya banbanta da sauran sakwanin dake wayarta na Mtn. Ta karanta duka sakwanin sannan ta gwada kiran numbersa. ALIYU POV. "Wato baki ma wani damu da ni ba kalli yadda kika yi kiba kika yi fari" Yana maganar yana kai mata abincin da ta shirya masa a karamin falon mahaifinsu. Ita kuma tana rike da wayarsa tana abun da ta saba yi masa a waya, wato bincike amman har ta yi ta gama bata ga wani abun da zata zarge shi da shi ba. "In ji wa? Wannan kibar fa ta haihuwa ce kowace mace tana yi da muke Video call baka gani ba" "Aa waya ai rage miki kyau take rabin raina" Ya sake kai mata wani spoon din. "Kina nan kina cinyewa Alhaji abinci ko?" Ta yi dariya tana kallon wayar da kira ke shigowa da number da babu suna a jiki, a take ta amsa kiran ta kara a kunne. "Hello... Aliyu..." Ta ji muryar mace tana ambaton sunan mijinta. "Wacece wannan?" "Emily ce" Mai kiran ta amsa mata kai tsaye. "Emily....?" Ta furta da mamaki, Aliyu ya aje Spoon din hannunsa ya mika mata hannu. "Ba ni wayar" Ta mika masa kamar ba ita ba. Aliyu ya dora wayar a kunnensa. "Emily kina lafiya?" "Ina lafiya" "Babu abun da ya same ki?" Kameela ta zaro ido tana sakin baki. "Aa na kira ne saboda na riski sakonka a wayata" "Okay, ina tare da Matata yanzu" Gudun kar zuciyar Kameela ta sosu ko ta yi zargin wani abu ya saka be ce mata zai kirata ba sai kawai ya kashe wayar. Tsabar mamaki Kameela bata san lokacin da ta mike tsaye tana kallon Aliyu ba. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/18, 7:55 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣6️⃣ Ya daga kansa kadan ya kalleta irin duban na lafiya? "a gaban idona Aliyu?" "Zauna" Ya mata umarni. "Wacece wannan miye tsakaninka da ita?" "Zauna" Ya sake fada peaceful. "Na ban zauna ba, wacece wannan matar?" "Emily ce, tsohuwar matar Turhan ina tunanin min mun taba magana da ke akanta" "Toh ya aka yi kake Communicating da ita? Taya number wayarka ta shiga hannunta? Har ta kiraka har ka damu da lafiyarta? Na shiga uku kirjina" Ta dafe kirjin tana numfashi da karfi daman tuni ta fara daga masa murya irin dagawar da kowa zai iya ji. Kansa ya sauke kasa be sake ce mata komai ba, domin ya san halin matarsa da kishi karamin abu ne ya fita hayyacinta a yanzu nan ta fara masa hauka. "Ni ban ma yarda ba, mu ga wayar mu gani waya sani ko soyayya kuke ka boye wani guri da ba zan gani ba" Ya mika mata wayar ta karba ta sake shiga chat dinsa ta duba ta fito ta sake duba inbox dinsa, kamin ta shiga longcalls dinsa ta yi forwarding number Emily zuwa number ta. "Wai ke da na yi ma alkawarin ba zan miki kishiya ba, miye abun tashin hankali idan kin ga ina magana da wata? Har yanzu hankalinki be kwanta da ni ba? Kuma ko aure zan yi ta ina zan aure matar da abokina ya aura?" "Aliyu ka ci amanata Wallahi da kake waya da matar nan, ashe ina nan ina wankan jego kana can kana soyayya da wata, jira kawai kake na daga kafa" Ta fada cikin kuka da hargowa, sai ya mike tsaye ya karbi wayarsa. "Idan kin huce kin sauko zan dawo mu yi magana" Ya juya ya fice ya barta a gurin tana gurnanin kuka, wani irin ihu ta saka tana shure shure duk ta watse abincin da suka ci da wanda ya rage a warmers ta watse kayan gaba daya a kasa kamar mai aljannu, da sauri Anty Shafa da Farida suka shigo suna tambayar lafiya sai kuma ta kasa fadar komai saboda bata son su ji abun da Aliyu ya aikata kar su mata dariya ko su ce Allah ya kara. "Ba komai" Ta tashi tana cigaba da kukan ta fice daga falon suka bita da kallo. "Ba komai take wannan kukan" Farida ta fada sai Anty Shafa ta kyalkyale da dariya. "Ya gumama ai kadan kika gani daga halin maza, yarinyar da kin yi auren kudi ma da kin more, amman yanzu ai sai bakincikin ya miki yawa ko rabuwa kuka yi ga kiyayyar aure ga ta siyasa" "Ai dai tun da ta nace sai shi sai ta ga babu dadi kuwa" Cewar Farida Anty Shafa ta fice domin labartawa Hajiya Asma'u wato Mahaifiyarsu abun da ke faruwa, Farida kuma ta fita kiran mai aikinsu domin gyara gurin da Kameela ta bata. Kameela na shiga dakinta ta fada kan gado ta fashe da wani sabon kuka tana jin kamar ta shake wuyan Emilyn da bata taba gani ido da ido ba. Ta dago ta nufi wayarta ta dauka ta duba number Emily din ta kira number, sai kuma ta kashe gudun ajin abun da take fada ko halin da take ciki ya saka ta fito dakin ta sauka kasa ta fice daga bangarensu zuwa bangaren Mama Barakat, ta bangaren ma ba shiga ta yi ba waje ta samu inda babu wanda zai jita ta sake kiran number Emily ringing biyu Emily ta amsa kiran da tsoro domin bata tsammani shigowar kira daga bakuwar number. "Hello" "Sannu karuwa, yar iska marar aji mai bibiyar mazan mutane, me kokarin raba aure fasika yar titi, kafirar banza yar wuta, saboda ke baki tsaya kin yi zaman aure ba shiyasa kika kokarin ruguza nawa auren ko? Toh Allah ya fiki, Wallahi ki fita sabgar mijina ko na kashe ki, Aliyu ya fi karfinki ba zai taba sonki ba ba zai taba auren mace irinki ba, karki sake kiran mijina a waya karki sake magana da shi idan ba haka ba Wallahi sai na lahira ya fiki jindadi, akan mijina zan iya komai, shegiya marar tarbiya haihuwar hasara, ke je gurin mijinki mana, wato so kika ki kashe min aure kamar yadda ke naki yake kashe ko? Me yasa dole sai Aliyu? To mijina musulmi mai addini babu abun da zai yi da fasika irinki, wato so kike ki lalata masa tarbiyar ko? Ki shige jikinsa da sunan matar abokina ki gwada masa duniya" Uffan Emily bata ce mata ba har ta yi maganganun da zata yi ta gama. "kina jina dam ubanki ko na sake maimaitawa? Ko da yake ke ai baki da uba ma, baki san zafin hakan ba ko da an zage ki, shiyasa yanzu kike son ki rusa gida ko? Toh ki shiga hayyacinki ni bakar macijiya ce" Ta kashe wayar tana huci, kamin kuma ta saka ihu ta fashe da kuka, ta dawo main door ta shiga bangare Mama Barakat ta zauna a falonta tana ta rusar kuka, Mama Barakat ta fito Kitchen da saurinta tana tambayar lafiya. Da yake Kameela ba mace ce mai rufin asiri da iya rike cikinta ba sai ta fara fadin. "Aliyu ya cuce ni, ya ci amanata mutuwa zan yi zuciyata" Mama Barakat ta yi mata tambayar duniya bayan wannan Kameela bata sake cewa komai ba, ganin haka ya saka Mama Barakat barin bangarenta ta tafi bangaren uwargidanta tana tambayar me ya samu Kameela take kuka da kiran Aliyu ya cuceta. Hajiya Asma'u dake zaune gefen gado tana kwance sarkar zinari ta girgiza kai cikin saurin maganarta ta ce. "Mu ba mu san me ke faruwa ba, bata ma fada min ba, amman yara sun shigo suna fadin sun ganta tana kuka ta watse kaya, yanzu kuma kuka yake can?" "Wai ko dai ce mata yayi zai yi aure? Kin san fa yayi mata alkawarin ba zai mata kishiya ba, kuma yadda Anty Kameela take da shegen kishin nan zancen kishiya ne kawai zai daga mata hankali haka" Farida dake kwance gefen da Hajiya Asma'u take zaune ta fada. "Aiko da na ci mutuncinsa Wallahi, dan ubanshi har cikin gidan Ubanta zai tarar da ita kuma ya fada mata zai mata kishiya? Kuma fa karamin aikin uwarshi ne ta saka shi kara aure a yanzu, ko dan abun da aka yi a gurin haihuwar nan" Cewar Hajiya Asma'u, Mama Barakat tace. "Wata kila dai wani abun ne, amman ga alamu Aliyu yana da hankali ba zai fada mata zai kara aure a gidansu ba, ya kamata dai a bincika" "Baki gama sanin duniya ba Baraka karki ce zaki fada min mutanen cikinta, ke lokacin da aka rufe idon Alhaji aka aura masa ke ba ido da ido ya kalleni yace zai aure ki ba?" Ta karasa da hararar Mama Barakat, Mama Barakat ta yi murmushi kawai ta juya ta fice. Hajiya Asma'u ta kalli Farida. "Miko min wayata na kira shi, ya zo na ji abun da yake faruwa, idan ma wai auren ne burinsa to ko sai dai ya rabu da Kameela dan yadda take da kishi ba zan bari ya halaka min zuciyar yarinya ba shi ya je ya more rayuwa ya bar ni da jinya, ko kuma ya fasa auren domin babu wanda ya masa cilas din yi mata alkwarin ba zai kara aure ba, kuma dan ya kai dan iska ya zo har cikin gidan nan ya fada mata zai kara aure? Aiko yau sai na ci mutuncinsa, yaushe ma aka yi auren da za'ace ya kara aure, duk makircin uwarsa ce na sani saboda ba son Kameela take ba" Farida ta mika mata wayar, Hajiya Asma'u ta kamo number Aliyu ta aika masa kira. ALIYU POV A gidansa dake Kaduna ya koma daman a can yake sauka a duk lokacin da ya zo ko suka zo tare da Kameela, a gidan aka fara kaita lokacin da take Amarya anan aka mata jere da komai, akwai mai gadin gidan da mai share harabar sai kuma mace daya dake zuwa every Friday ta yi mopping din gidan ta saka turare ta gyara ko'ina. Bayan ya faka motarsa ya bude ya fito ya shiga cikin gidan kana ganinsa kasan baya cikin jidadin, ba komai ya janyo masa haka ba sai rashin uzuri da kuma fahimtarsa da matarsa bata yi, yadda take da zafin kishi kuma hankalinta yake gushewa yana damunsa, ga kuma rashin rufin asiri idan ba haka ba miye na daga murya tana ihu da kuka akan abun da be taka kara ba balle ya karya. Shi dai kam ya so ya samu mata mai fahimta da uzuri, ba laillai sai aure ko soyayya kadai ke shiga tsakanin namiji da mace ba, akwai wanin abun da zai iya hadawa aiki ko taimako ko kasuwanci ko kuma wani abun na dabam kamar dai shi da ya shiga tsakanin Emily da Turhan. Wayarsa ya ciro daga aljihunsa ya gwada kiran Kameela domin ya ji babu dadi a halin da ya barta, sai ya ji line busy ya kashe kiran ya sauke numfashi a hankali ya tashi ya shiga Bedroom dinsa ya zauna sannan ya kira Emily. Kiran farko bata daga ba na biyu ma haka, a ka'idarsa baya yi ma mutum kira fiye da biyu amman saboda yana son magana da ita ta son sanin halin da take ciki sai ya sake kiranta a karo na uku. Ta daga amman ta yi shiru bata ce komai ba. "Emily?" Bata amsa ba, shi kuma be damu da hakan ba ya cigaba. "Daman na aika miki sako ne saboda na damu na san halin da kika ciki, ban sani ba ko Vito yayi miki duka saboda abun da na aikata ko kuma ya kore ko wani abun, shiyasa na aika miki da sakon kuma ina yawan kiran wayarki a kashe, na je gurin Tasmia nemanki ita ma bata samu labari daga gareki ba, amman dai kina lafiya ko? Ba wata matsala?" Ta yi shiru tana hawaye, kukanta ba shi da sauti amman jikinsa ya raya masa kuka take. "Emily akwai wata matsala ne?" "Aa zan yi farinciki idan ka aiko min da motata ba tare da na zo dauka ba ko kuma kai ka zo gidana ba, kuma zan fi kowa farinciki idan baka sake kirana ba, ko neman ji daga gareni, na gode da duk wani taimako da ka yi min tun daga ceto rayuwata da ka yi har zuwa taimaka min gurin rufe London na gode, alakarmu ta tsaya nan" Ta kashe wayar, mamaki fal a fuskarsa gaba daya ma ta taushe kusurwar tunaninsa, me ya faru? Vito ne na cilasta mata yanke alaka da shi tun a yanzu ko kuma tana cikin wata matsala ne da bata son ya sani? Ko kuma barazana yayi mata da rayuwarsa ko ta yarinyarta? Sai ya ji ya gagara natsuwa da hakan a take ya sake kiransa sai ta ki ta daga. "Ba kince kina neman hanyar da zaki saka min da abun da na yi miki ba? To yanzu ina son ki saka min ta hanyar fada min me yasa kika yanke alakata da ke? Kina cikin wata matsala ne?" Ya aika mata da sako, sms din ya fita wayarsa kiran surukarsa Hajiya Asma'u na shigowa wayarsa. Sai ya daga da sallama "Assalamu Alaikum" "Aliyu ka zo yanzun nan ina nemanka" "Hajiya Lafiya?" "Idan ka zo zaka ji" Ta kashe wayar, a yanayin yadda ta ji muryarta ta gautsi ya san ba lafiya ba. Ya mike tsaye kenan sakon Emily ya shigo wayarsa. "Matarka ta yi min iyaka da kai a yanzu, ta kira ki kafira yar wuta, da fasika karuwa, na ji ni ba musulma bace amman ni ban taba yin fasikanci ba, tace ban san zafin uba ba, ban zauna gidan aure ba shiyasa nake son ruguza nata ka yi hakuri ba hakan nake nufi ba, bana nufin lalata rayuwar kowa, bata fahimta ba tace ina son na lalata rayuwar aurenta, to me zai saka na yi hakan? Miye ribata idan na yi hakan? Bana bukatar wani tashin hankali a yanzu, ban san kana da mata ba, amman zuciyata ta raya min at age dinka daman ba zai yiyu ace baka da aure ba, ka yi hakuri dan Allah kuma ka bata hakuri" Yana gama karanta sakon ya koma ya zauna yana cire hullar kansa, domin yau shigar manyan kaya yayi. Abun da ya fara zuwa zuciyarsa shi ne a ina Kameela ta samu number Emily ma? Ya fito daga sakon Emily sai ya ci karo da na Kameela dake kasan na Emily a nan ya duba akwai sakwanin da suke turawa juna amman last sakon da ya tura daga wayarsa zuwa nata layi number Emily ce aka yi forwarding, sai ya fahimci dalilin karbar wayarsa da ta yi dazun da sunan bata yarda ba bari ta duba a nan ta tura number Emily. Sosai ya kai makura gurin bacin rai, kuma ya fahimci idan be yi ma tunkar hanci ba abun zai iya fin haka, domin Kameela bata tsaya ta yi tunanin abun da ya dace da kuma wanda be dace ba, karamin aikinta ne ace ta sanar da iyayenta abun nan da ta faru wata kila ma shiyasa mahaifiyarta take nemansa. Ya dauki hularsa ya saka ya fito harabar gidansa ya shiga motarsa cikin bacin rai ya dauki hanyar gidansu Kameela, yana isa ya faka a inda ya faka dazun ya fito ya nufi kofar falon, sai da ya boye bacin ran dake zuciyarsa sannan ya shiga falon gudun kar surukansa su zargi wani abu domin be san dalilin kiran da Hajiya Asma'u take masa. Yan matan da suke falon suka amsa masa suka gaishe shi, sannan ya nemi guri ya zauna yana baza kamshi turare, daman Aliyu akwai kwarjini da cika ido sai idan ba a hadu da shi ba. Hajiya Asma'u ta sauko fuska a daure tana sanye da Australian Lace mayafinta a kafada ta zauna a kujerar dake facing din ta Aliyu. Anty Shafa ma ta sauko ta sai ta yi ma kanenta umarnin su fita falon, duk suka watse aka bar Hajiya Asma'u kawai sai Aliyu da Anty Shafa. Aliyu ya gaishe ta cikin ladabi, sannan ya gaishe da Anty Shafa. "Aliyu me ke faruwa tsakaninka da Kameela?" Aliyu ya kalleta da mamaki. "Ina Kameela take?" "Tana bangaren Mama Barakat. Anty Shafa ta amsa masa. "Me ya faru Hajiya?" Ya tambaya. "Shi nake son na sani, saboda ta shigo tana kuka yan'uwanta kuma sun ce ta fasa kayan abinci a falon babansu, kuma Baraka ta shiga tace Kameela sai kuka take tana fadin ka cuceta" Aliyu yayi shiru yana danne abun da ke masa zillo a zuciya. "Daman dai na kiraka ne na ji ko abun da zamu iya shiga ne a matsayinmu na iyayenta, kuma ba ina maganar saki ba ne, bana tunanin saki zai daga hankalinmu ko na Kameela, tsoron mu kar a karya alkawarin da aka yi mata ne, domin babu wanda ya san kun yi, dan haka be kamata a karya ba, kowace mace da yanayin yadda Allah yake halittarta yara ne ga su nan na haifa amman kowa da halinsa da kuma yanayinsa, ina tunanin ba cilas aka maka ka yi mata alkawarin ba zaka mata kishiya ba, kai ka sakata a daki ka yi mata alkawarin, mace mai irin zuciyar Kameela ni dai a matsayina na uwa da na san darajarta ba zan iya kallonta ta shiga wani hali ba ba zura ido" Cikin natsuwa Aliyu ya kalli Hajiya Asma'u. "Hajiya maganganun da kike min kamar kina nufin by fire by force ban isa na yi ma Kameela kishiya ba?" "Ba zan ba ka isa ka yi mata kishiya ba, ko kuma na hana abun da ka yi nufi ko aka saka ka abun da ka yi niya ba, Ummi take da wannan ikon ba ni ba, amman dai ni a matsayina na mahaifiyar Kameela ina mai tabbatar maka Kameela ba zata zauna da kishiya ba, a yanayin zuciyar Kameela ba zan bari a kashe min ya ba" Aliyu yayi murmushi a bayaninta na yanzu ya fahimci har yanzu bata dauke shi a matsayin danta ba, if not ba zata fada masa magana haka ba, calmly ya fara magana. "Na gode da wannan bayanin da kika min a yanzu Hajiya, kuma na gode da kika fahimci Ummi ce kadai ta isa ta saka ni abun da ban yi niya ba, ko kuma ta hana ni abun da na yi kuduri, wannan sharadin kuma tun farko ya kamata a fada min kamin na auri Kameela ba yanzu ba, amman duk da haka na gode zan kiyaye a huta lafiya" Ya mike tsaye ya ciro 500k aljihunsa ya dora akan center table din dake falon. "Anty Shafa a siyawa yaran wani abu" Daga Hajiya har Anty Shafa babu wanda ya sake cewa wani abu binsa suka yi da kallo har ya fice. Yana sauka entrance din Hajiya Asma'u ya nufi bangaren Mama Barakat sai da yayi knocking sannan ya tura ya shiga, ta amsa masa da far'a tana masa maraba har da dauko masa ruwa. "Mama Kameela tana nan ko?" "Eh tana dakina na ce ta shiga ta kwanta na ganta sai a hankali, Allah yasa dai lafiya" "Lafiya kalau Mama" "Maa Shaa Allah haka muke son ji, Dan Allah Aliyu ayi hakuri, shi zaman aure dole sai da hakuri, ba zaman aure kadai ba gaba daya rayuwar duniyar ma sai anyi hakuri, kuma kowa da inda Allah yake masa jarrabawa wani ta bangaren aure, wani ta iyaye, wani ta yaya, wani ta abokiyar zama, wani ta surukai, dan'adam baya taba zama hakan nan dole sai da jarrabawa, kaf duniya babu wanda zai zauna 💯 percent babu damuwa, dan haka ka yi hakuri kuma ka danne zuciya" "In Shaa Allahu, Mama na gode sosai" "Ba komai, kai ai ko da yaushe ɗana a gurinmu, dole idan muka ga za'a kuskure sai mu lurar, tun da ku yara ne mu kuma manya, bari na kira maka ita" Ta mike tsaye ta nufi staircase, shi kuma ya sauke kansa kasa, be dago ba sai da Kameela ta sauko, sannan ya kalleta fuska a hade. "Zauna" "Ba zan zauna ba" Ta daka masa tsawa tana hararasa idonta har sun kumbura tsabar fitinar kuka. "Ba ni mamaki Aliyu ashe jira kawai kake na daga ka fara soyayya da wata, har kana tambayar lafiya, ita kuma ta samu Audacity kiran ka kai tsaye" "Ban taba sanin baki da hankali sai yau, ban san rashin tunaninki ya kai haka ba sai yau" Ta nuna kanta. "Ni kake kira mahaukaciya?" "Idan ba rashin tunani ba yaushe wannan maganar ta kai ki kaita a gaban iyayenki? Idan ba hauka ba yaushe zaki kira matar da baki san me take Going through ba ki zageta ki kirata da karuwa?" Ya mike tsaye rai a bace. "Miye a cikin kanki Kameela? Wannan ba kishi ba ne hauka ne, matar da kika zaga bata miki komai ba, baki san komai akanta ba, matar dake kokarin picking kanta Piece by piece, abun da kika yi kin nuna baki ma yarda da ni ba kenan, idan wani ya zo ya fada miki wata magana akaina zaki yarda. Ba tsoron ki nake ba duk abun da nake miki ina biyewa miki ina daga miki kafa ina yi ne saboda mu zamu zaman lafiya, na miki alkawarin ba zan kara aure ba saboda ba ni da ra'ayin auren mace fiye da daya, kuma saboda hankalinki ya kwanta, not because of kin fi karfina ko ina tsoronki, ke kin san waye ni kamin ki aure ni bana daukar rainin wayo bana daukar wulakanci, saka miki idon da na yi yana kokarin saka ki raina ni? Idan ba raini ba yaushe zaki zafi matar da ni na fara neman number ta kamin ta nemi number ba, kin yi min magana be isa ba? Duk wata number mace dake cikin wayata ta yan'uwan da kika san akwai aure tsakaninmu ko abokan aiki kin bi kin goge kin yi blocking, kullum cikin bincike wayata kike, mazinaci ne ni? Ni ya kamata na bincike numberki saboda ni ne mijinki, a cikin cousins dina baki shiri da kowa saboda tunanin wata zata aure. Abun da kike kina nuna ban isa da gidana ba kenan ko kuma kin fi karfi. Toh wannan ya zama na farko kuma ya zama na karshe idan Emily tace kin sake kiranta kin ci mutuncin kin kaɗe....!" Tun da ya fara fadan bata komai sai kuka, Mama Barakat data sauko tana kallonsu saboda daga muryar da Aliyu yake ta matsa ta rike Kameela. "Lafiya Aliyu?" "Karamin abu ne da ya faru da be ma kamata ka ji ba, amman yarinyar ta bi ta lalata komai" "Meyasa ba zaka fada mata saboda wata karuwa kake ci min mutunci ba, wata banza yau kake min abun da baka taba yi ba, saboda kana ganin ita fara ce mai kyau baturiya saboda kana ganin kamar ta fini kyaun? Abun kunya ma matar abokinka, yarinyar da ba a san su waye iyayenta ba, yarinyar da tsintarta akayi a Lagos, yarinyar da ba ma musulma bace, ai ko aure zaka yi ko soyayya zaka yi ka yi da mai ma'ana mana" Aliyu ya dube ya sake dubanta ya kuma ya dubeta sannan ya dauke kai ya fice daga falon. Da wani irin kufura da fushi ya isa motarsa, da ace halinsa ne saki ko dukan mata a yau ba zai ragawa Kameela da ko daya ba, domin kalamanta na yanzu sun fi abun da ta aikata zafi, yana barin gidan ya daga waya ya kira Umminsa tana dagawa be tsaya gaisuwa ba ya ce. "Ummi karki aika bikon Kameela a yanzu" "Me ya faru?" "Yar hatsaniya muka samu, kuma na san Hajiya Asma'u zata iya yin wani abun da zai bata miki rai ko ni, ni kuwa a yadda nake jin kaina a yanzu idan ta kuskura ta furta wata kalma marar dadi a gareki ko Daddy, na rantse da Allah sai na nuna mata ta fi kowa rashin sa'ar suruki a duk fadin garin Kaduna...!" "Toh Allah ya kyauta, shiyasa ake son idan mutum zai yi aure ya auro yar gidan mutumci, ba tarbiyar yarinyar kadai ba ta iyayenta ma ya kamata a duba, Hajiya Asma'u fa hankalinta ba zai kwanta ba sai taga Kameela bata gidanka, saboda ta dauke mu makiyansu. Ko da yake ma komai ya faru ai kai ka janyo, babu yadda ba mu yi ba ka nace sai ita, abun da duk iyaye suka ce a bari barin shi yafi alheri ko da babu dadi, idan riba ce yanzu ai ka fara ci" Tana fadar hakan ta kashe wayar. Aliyu ya cigaba da tukin motar sai huci yake har ya isa gidansa. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/20, 10:17 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣7️⃣ The following day ya shirya ya wuce Abuja gurin mahaifiyarsa daman zuwansa kaduna saboda Kameela ne, ya fara sauka a nan idan ya ganta suka gaisa aka masa binkonta zuwa gidansu dake Kaduna sai ya dauke ta su tafi Abuja gurin Ummi su mata kwana biyu sannan su sannu dawo garin da yake aiki a yanzu wato Part hartcour, sai dai a yanzu ta yi nasarar ɓata masa rai yayi tafiyar da be shirya ba. Ya sauka Abuja around 12pm Ummi ta aiko sabon direbansu ya dauki Aliyu daga Airport zuwa gidansu dake Wuse II, kamin su karasa gidan Kiran Kameela ya shigo wayarsa a karo na 32 bayan sako goma sha daya da ta aiko masa, be amsa kiranta ko daya ba haka kuma be mayar mata da amsar sakonta na Sms ko WhatsApp ba, har Instagram dinsa sai da ta bishi tana masa be amsa ba, domin a duka sakwaninta babu wanda ya nuna ta yi nadamar abun da ta yi sai dai ta bashi hakurin bata masa rai da tayi wani gurin kuma tace wai yanzu saboda wata banza yake mata wulakanci, wani sakon kuma tace ya bata mamaki, a na karshen kuma nanatawa take wai zai jawa Emily bala'i idan be rabu da ita ba. A katafaren gidan Direban ya faka ya fito ya budewa Aliyu mota, Aliyu ya fito yana kallon yadda aka kara gidan na mahaifinsa kamar ba za a mutu ba. Sannan ya wuce ciki, falo biyu ya wuce sannan ya isa wani madaidacin falo wanda be kai na farkon sa na biyun girma ba, kanwarshi ta zo da gudu ta tarbe shi ita da wata cousin dinsa, Aqeel kuma ya mika masa hannu suka yi chop knuckle, Ummi ta dan tabe baki kadan tana kallonsa. "Yaushe rabonka da gidan nan?" Ya nufeta ta zauna kusa da ita yana dariya. "Irin Welcome din nan ma na uwa da ɗa ba zan samu ba? Ina shigowa sai a fara min da tambayoyi" Ummi ta yi murmushi kadan, tayi ma direban da ya shigo da akwatin Aliyu sannu. "Hajiya ga wannan ina za a aje?" "Bar shi a nan Khaleepa Ladi zata shigar masa da shi ciki" "Toh Hajiya" Ya amsa sannan ya juya ya fice. "Ummi haka aka kara gyara gidan nan, wato ku babu ruwanku duniya ta muku dadi ko?" Ummi ta watsa masa wani kallo har tana karkatawa dan ta samu ganinsa da kyau. "Ahhh Toh so kake ta yi mana zafi? Ɗan hamayya! Ko ka bi jam'iyar matarka? Kasan fa kai yanzu ruwa biyu ne, kana nan kana can ba gane kanka ake ba, karka mana zagon kasa" Duk suka fashe da dariya har Aliyun, daman haka yake da mahaifiyarsa idan suka hadu ita da shi kamar abokan wasa ko yaya da kanenta, sam ba zaka ce ɗa da uwa ba ne. Sai da suka gama wasa da dariya da Ummi sannan ya shiga ciki yayi wanka ya fito ya dawo dakin Ummi, already ya samu Ramla ya kawo masa abinci a dakin Ummi, abu ne da suka sani idan zai ci abinci duk inda Ummi take zaune a nan yake ci, a daki ne ko falo ko bangaren mahaifinsa, shi dai burinsa ya ci abinci kusa da mahaifiyarsa yana ci yana hira da ita. "Sai yaushe Daddy zai dawo?" Ya tambaya bayan ya kai spoon biyu bakinsa. "Daddynka yanzu ganinsa sai da ticket, ko ya shigo ba samun ganinsa zaka yi ba" Yayi murmushi "Ummi wai ni korata kika yi a gidan nan ko sadakata aka ba da, na ga tun da na so kike min wulakanci" "Daman kai dan gidan nan ne? Ai mun yafe ka tun da muka aurawa Kameela, yaushe rabonka da gidan nan, babu ruwanka da labarin mu komai ake kai baka ma sani ba, yanzu ma ba dan ka samu matsala da Kameela ba ba zaka zo ba" "Yanayin aikin ne ai Ummi kin san ba mu da hutu kullum, kuma daman na yi nufin daga Kd na dauko Kameela mu zo nan mu kwana biyu wannan mu koma, sai gashi notin kanta daya ya cire" Ummi ta tabe baki. "Allah dai ya kyauta, dazun ma ta kira ni tana fadin wai ka mata fada kamar zaka daketa, saboda wata matar abokinka Turhan kuma matar ma kafira ce miye miye... Ni ban ma gane kan zancen ba, wai yanzu kuma fushi kake da ita" "Shareta kawai Ummi ba zaki ganin kan zancen ba" "Kishin yarinyar nan yayi yawa, kuma ba komai ya sa yayi yawa ba sai damar da ka bata, akwai abubuwan da ake takawa mace burki a kansu, amman kai komai ta yi sai ka biye mata saboda kana sonta, wannan ba so ba ne, abun da kake mata yanzu tana wuce gona da iri shi iyayenta suke mata da sunan so alhalin ba soyayya bace lalata mata tarbiya ne suke yi" "Ummi da kin tashi magana sai ki ce Kameela bata da tarbiya, Kameela tana da tarbiya kawai dai zafin kishi ne yake damunta" "Na ji tana da tarbiya, iyayenta fa? Ai komai kyaun farin tuwo a ɓakar tukunya ya fito, kuma kamar kumbo ne kamar korensa duk yadda za'ayi dole Kameela sai ta samu matsala domin barewa bata gudu danta yayi rarrafe, idan bata maka abun haushi ba iyayenta za su maka, kuma duk yadda aka yi sai ta dauki hudubarsu, uwa ba wasa ba ce Aliyu, idan za'ayi aure ba tarbiyar yarinya kawai ake dubawa ba har da iyayenta ana son a duba su waye iyayenta" Be sake cewa komai ba har ya gama cin abinci, domin abun da be yarda da shi ba shi ne mahaifiyarsa ta zauna tana zagin matarsa, hakan zai dasa kiyayyarta a zuciyar mahaifiyarsa, wanda ba zai so haka ba, even though dai Ummi ba wani yin Kameela take cancan ba, amman ya san bata tsaneta ba, haka kuma ko da wasa ba zai yarda ya budewa matarsa damar maganar mahaifiyarsa ba, kowa matsayinsa dabam. Ya gama cin abinci a daidai lokacin da motar Daddynsa ta faka harabar gidan, sai dai be san shigowarsa ba domin gidan ba irin gidan da ake jin fita ko shigowarsa mota ba ne, musamman dakin Ummi da baka sanin wainar da ake toyawa idan kana ciki sai ka fito. Aliyu ya aje spoon din da ya gama cin abinci da shi kenan, kiran Daddy ya shigo masa ya sanar masa ya dawo. "OK Daddy gani nan zuwa" Ummi ta kalleshi. "Wato na yan siyasa mahaifinka yayi min ko? Daga ganin sabuwar jam'iya sai ya tsalleke ya koma can ko? Ai tafiya zaka yi a bar ni da shi" Aliyu ya kai tsaye yana dariya. "Allah ya bar mana ke Ummi, yanzu miye laifin Daddy dan ya nemi ganin dansa?" Ummi ta yi murmushi. Aliyu ya fice shi ma yana murmushin. Wani abun da ya kara bata masa rai a game da Kameela shi ne sanar da Daddy da ta yi bayan Ummi, kuma ko kadan hakan be masa dadi ba, domin a ganinsa abun be kai ace iyaye sun ji ba, ta sanar da iyayenta hakan be mata ba sai ta sanar da na shi. Nasiha Daddy yayi masa akan zamankewar aure ya fada masa wai sai yayi hakuri da matarsa kowa hakuri yake. A tare suka yi Sallah Isha'i a harabar katon gidan dake da matsakaicin masallaci a ciki, Aliyu ya jagoranci Sallah daya daga cikin jami'an tsaron da suke gadin gidan yayi masa ladanci, Daddy da sauran ma'aikatan gidan kuma suka shiga sahun mamu, bayan an gama sallah ne Aliyu ya juyo yana gaisawa da kowa yana musu alherin da abun da ke aljihunsa, har ya kai gurin sabon direban da aka dauka domin shi dai be taba ganinsa cikin ma'aikatan gidan ba, ko da yake gidansu kullum cikin canje canjen ma'aikata yake ba shi kadai ya gani bakuwar fuska ba, amman rabin fuskarsa ta fi tsaya masa a rai, domin rabin kawai ake iya gani dayan gefen a kone yake har zuwa hannunsa na hagu, yayi baki sosai ya alamar wuta ko mai ta kone jikinsa domin fatar kafadarsa ra hagu zuwa wuyansa a hade take, jikinsa ya zama two color. Kwanan Aliyu biyu a gidan kullum suna haduwa gurin sallah gidan, kuma a kullum sai yayi musu alheri, daman duk lokacin da ya zo a gidan ko gidansu na Kd haka yake da kowa har ya koma, a ranar da zai koma Ramla ta fito masa da akwatinsa falonsa dai daga cikin masu aikin gidan ta dauki akwatin ta fitar da shi waje sai direban ya karba ya saka mota. Aliyu na zaune falonsa yana duba agogo hannunsa Ummi ta sauko rike da cup tana sanye da Filafil Swiss Lace dan 530,000 da ta siya gurin Khadeeja Candy. Cup din hannunta ta mika masa ya dago daga kishimgiden da yake ya karbi kofin ya leka ciki sai ya ga ruwa kadan, be tsaya komai ba ya kai kofin baki ya shanye addu'ar dake ciki. "Ita wannan addu'ar idan an sha ana shafawa ko sha kawai ake? Na shanye duka da" Ummi ta yi murmushi irin na su na manya hakwaranta biyu na makka na bayyana. "Baka tsaya ka ji yadda ake shan ba ka shanye" "Ai na san ba saki ba ni abun da zai cutar da ni ba, kuma kin saba min Ummi tun ina yaro kullum sai kin tofa min addu'a a ruwa kin ba ni, kamar dan siyasa" "Ba sai dan siyasa yake da makiya ba, wani baka sanin makiyinka sai ranar da girkin yaƙi dadi, wani ma sai an hadu gaban Allah gurin rabawa kowa abun da ya aikata zaka ga wani ashe ya ci da guminka ko ya cutar da kai kai baka ma sani ba, dan haka ka rike addu'a da addu'a zaka fi karfin komai, kullum idan zaka iya kamin ka ci komai ka karanta fatiha da ayatul kursiyu ka tofa a ruwa ka sha, Allah ya tsare min kai ɗana, ko baka siyasa ai kai dan masu siyasa ne" Ya kwanta jikin mahaifiyarsa yana jin tsananin kaunarta. "Sai ni Aliyu dan Ummi nan gani nan bari adashe manya" Ummi ta shafa kansa ta saka masa albarka sannan ta kai masa rankwashi. "Dan Allah daga min katon banza da kai ka zo ka haye min a jiki" Ya tashi yana dariya. Ramla tana ta daukarsu hoto har da short video. Aliyu ya fito tare da rankiyar mahaifiyarsa har gurin motar da Direban ya bude masa. Aliyu yana ta kallon direban da biyu domin zuciyarsa na raya masa kamar wani abu kamar ba haka ba. "Ya sunanka?" "Khaleepa ranka ya dade" Ya juyo ya kalli Ummi. "Kun canja direba ne?" "aa dayan dai yaje ganin gida, dayan kuma shi yake kai yara Ramla school kasan tsoro ya hana ta iya mota har yanzu, Daddynku yace a karo daya saboda zirga zirga ya zama idan biyun basa nan daya yana nan, shi Daddy kasan ai yana da nasa na musamman ko da wasa baya ara mana shi" "Okay" Ya shiga motar suka yi sallama da Ummi Ramla na daga masa hannu da Aziza, sai da suka yi nisa sannan Aliyu ya ce. "Khaleefa ai ba suna ba ne ko?" "Eh ranka ya dade sunana na ainihi shi ne Hamza" Aliyu ya sake dubansa ta madubin motar, har ya bude baki zai sake wata magana sai kuma ya fasa ya sauke numfashi. Da suka isa Airport din direban ya fito da akwatin Aliyu bayan ya bude masa, sai Aliyu ya sake masa duba na tsanaki ya ce. "Kai dan wane gari ne?" "Kaduna, ranka ya dade" Daga haka Aliyu be sake cewa komai ba Direban ya ja masa akwaitin Aliyu yana gaba yana biye. EMILY POV. A ranar da Kameela ta kirata ta yi mata cin mutunci ta kira da suna kala kala marasa dadi Emily ta kwana da bakinciki da damuwa. Washe gari da ta tashi sai ta tashi jiki babu kwari mood dinta kuma ya canja domin ta kwana da tunani kalakala a ranta. Ko da ta sauko already Chidimma ta gama shirya komai, Fatima har ta wuce school, Vito kuma yana zaune a dinning din falon tare da Chidimma suna karyawa at the same time the same table. To her it's a new thing domin Vito be taba hada table da wata mace ba a gaban idonta balle har ya ci abinci a tare da ita. Kallonsa kawai ta yi ta kalli Chidimma ta dauke kai ta nufi kitchen ta shirya nata breakfast din dabam ta dauko ta fito, a lokacin ne Vito ya mike tsaye. "Good Morning Bae" Bata amsa ba kuma bata kalleshi ba ta haura sama zuciyarta tana mata babu dadi, domin bata gane ma'anar abun da yayi ba a yanzu. Saboda ta yi fushi ne jiya har ta watsa masa ruwa ta mari Chidimma? Ko kuma saboda bata nuna interest dinta akan aurensa ba ne? Ko kuma dai saboda ta yi fada da mahaifiyarsa ne.? Ba zata ce tana kishin karyarwa da yayi a tare da Chidimma ma, amman aikata hakan kamar ya budewa Chidimma din kofar raina ta ne domin a kasan ta take zaune. Ta kasa kai komai bakinta ta mike tsaye ta nufi backyard ta tsaya a gurin tana kallon itacen da suke nan, duk wani abu da yake samuwarta ko kuma ya sameta yana faruwa da ita ne saboda bata da ikon kanta kuma bata da gata, da ace kaddararta bata zo a haka ba, wata kila da salon labarinta ba a haka zai kasance ba. Sai da ta shaki iskar da take jin ta wadatar da ita sannan ta koma ciki ta zauna a one seater ta kai hannunta ta dauki wayarta, sai ta ci karo da sakon Kameela daga wata number dabam ba wacan da ta yi blocking ba saboda yawan sakon da take turo mata da kira. "Idan baki rabu da mijina ba sai na kashe ki, akan mijina bana ji bana gani kuma ban ragawa kowa" "Uhffff" Ta busar da iskar bakinta ta daga kanta sama ta sauke ta shafa kanta ta shafa jikinta gaba daya ta rasa me ke mata dadi. Kamar wasa Vito ya fara shareta kuma ya maida rabin al'amurransa a cikin gidan idan zai ci abinci zai ci tare da Chidimma on the same table, ko da kuwa Emily tana zaune a falon ne, da zarar ya nufi dinning ya zauna sai Chidimma ta tashi ta yi Serving dinsa, idan ta gama sai ya ce ta zauna a nan ta ci abinci ita ma, ya kan tambayi Emily ko zata ci sai ta amsa masa da aa, idan ya shigo ma yana tambayar lafiyarta ko ya rika hannunta, amman ba kamar da ba, hakan kuma yana kona mata rai kuma ya jefata a tunani, a yanzu bata san matsayinta ba, replacing dinta zai yi da Chidimma ko kuma dai yana yi ne saboda ya bata haushi. Da zarar sun fara cin abinci zata tashi ta ba su guri domin bata ita zama tana kallon bakinciki ba, ga Chidimma din sai daukar wanka take tana ta nishadi a yan kwana biyun nan. Ranar Laraba tana zaune a dakinta Fatima ta shigo sanye da uniform ta jefar da Jakarta a gurin haka ma lunch box dinta. "Yunwa naka ji" Emily ta dago ta dube ta kamin ta sake maida dubanta gurin wayarta dake hannunta tana karanta sakon da ya shigo mata. "Kina da Sako a wajen gate ki fito kamin mai gadinki ya hana shiga da sakon" Ta karanta sakon da aka turo da wata bakuwar number. "Momy I'm starving Chidimma bata nan ki zuba min abinci" Fatima ta fada a tsawace kamar yadda ta saba yi mata magana cike da rashin tarbiya. Sai dai ko kadan hankalin Emily baya gurinta tana gurin sakon da ta karanta, bata san waye ba, bata san sakon miye take da shi a waje ba. Kamar ya san tsoro take ji sai ya sake aiko mata da sakon sunansa. "Aliyu ne, sakonki yana waje" When she read the name sai ta ji she's safe ko da yake bata da tabbacin shi din ne ko Vito yake shirya mata wani abu? Ko kuma matar Aliyu dake neman rayuwarta. Ta sauka daga kan gadon da kafafuwanta dake sanye da safe ta fito dakin Fatima ta biyota bayanta. Ta isa gate din ta bude da kanta ta fita sai ta ga motar Aliyu fake nesa da gidan amman tana facing din gidan. Fatima ta janyota da karfi cikin ihu tace. "Na ce miki yunwa nake ji yunwa nake ji baki ji ne? I hate you" Emily ta kalleta kamar mai tsoronta. "Okay" Ta juya zata koma Aliyu ya bude motar ya fito ya doso inda suke tsaye, Fatima na ganinsa a take fuskarta ta cika da murmushi sai ya ware mata hannayensa ta je ta gudu ta rumgume shi ya daga ta sama. "I miss you" "I miss you too, ina ka tafi kwana da yawa?" Ya sauketa kasa yana kallon Emily da ta yi rama sosai "Ina nan, aiki ne yayi mana yawa, shiyasa na zo nace mamanki ta shirya ta koma aiki, kin ga da tana zuwa aiki ai kullum za mu rika haduwa ina siya miki chocolate da ice cream ina kaiki yawo" "Mi kake yi a nan?" "Na zo na fada miki ki shirya gobe ki koma aiki, office dinki yana nan yana jiranki, amman ba a karkashin Amal zaki yi aiki ba a yanzu, idan kuma baki ra'ayin aikin motarki tana nan kije gobe da kanki ki dauka karki aika kowa" Ya rage tsawonsa ya mikawa Fatima key din motar. "Ki bawa Momy" Fatima ta karba ta mika mata. "Good girl, ga ki kyakkyawa ga ki da jin magana to miyasa kike yi ma momy tsawa?" "Na ce ta zuba min abinci bata zuba min ba" "Okay amman ba a yi ma uwa tsawa, saboda ni da ke ai musulmai ne ko?" Ta daga kai. "Yauwa shiyasa kike burge ni, kina da saurin fahimta da ganewa, ga wayo" Ta kyalkyale da dariya. "Mu musulmai bama ma yima iyaye tsawa, muma musu ladabi da biyayya ne, idan kina son mu zama friends ni da ke toh karki sake yi ma Momy tsawa, baki ganin ke kadai kika rage mata ma? Tun da London be nan? Ki daina cewa i hate you idan wani yace miki haka zaki ji dadi?" Ta girgiza kai ta turo baki. "Ita ma bata sona bata min abun da nake so? Ko London ya mutu yanzu amman bata ba ni sunan Babanshi ba, yan makarantar mu suna min dariyar sunana na mata ne duka uku, ka gani Fatima Emily Aisha" "Sunana ne kawai matsala? Idan Momynki ta dawo aiki zan dauke ki mu tafi makaranta a canja miki suna daga Fatima Emily Aisha zuwa Fatima Aliyu" Farinciki ya cika fuskar Fatima. "Da gaske? Ka yi alkawari" Ya mika mata karamin yatsansa. "Na yi ke ma ki min alkawarin ba zaki yi ma Momy tsawa ba daga yanzu, idan ma kin manta kin yi za ki bata hakuri" Ta daga mishi kai sannan suka kulla Pinky promise. "Okay now say sorry to your momy, ask for her forgiveness" Fatima ta kalleta a shagwabe ta ce "I'm sorry Momy please forgive me" Aliyu ya kama kunnunsa yana daga kansa ya kalli Emily. "Kin yafe mana ko Momy?" Ya mike tsaye still yana kallonta. "Please Unblock me, ina tunanin ban cancanci haka daga gurinki ba" Ya shafa kan Fatima sannan ya nufi motarsa yana daga mata hannu, har ya wuce Emily bata motsawa daga inda take tsaye ba balle ta ce wani abu. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/21, 9:26 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣8️⃣ Sai da ta daina hango shi sannan ta juyo ta dawo cikin gidan rike da hannun Fatima dake ta tsalle da murna saboda Aliyu yace zai canja mata suna. Emily ta shiga falon ta nufi dining ta fara aje wayarta sannan ta zubawa Fatima abinci, ta ja kujera ta zauna ta dauki wayar ta duba number Aliyu ta yi unblocking dinsa. "Momy ya sunan wannan oganki ma?" Emily ta kalleta a hankali. "Aliyu...." Fatima ta yi dariya cikin farin cikin. "Fatima Aliyu" Emily ta aje wayar hannunta tana kallon Fatima, tausayinta ne ya fara zuwa a ranta ganin yadda take ta daukin samun sunan uwa ma kawai ba uban ba, to ina ga ace ubanta yana sonta yana ji da ita? "Fatima ba zai yi ki karbi sunan wani ba" "Saboda me?" "Saboda baki da alaka da shi, he's just a stranger" "He's not a stranger he's your friend, Momy ni ina son sunan" "Na ce aa" Fatima ta wulgar da plate din abinci kasa ta kalli mahaifiyarsa cikin kufula tana son ta yi mata tsawa tana tuna alkawarin da ta yi ma Aliyu, gashi tana tsoron kar Emily ta fada masa domin gani take kamar zata iya fada masa cewar ta yi mata tsawa, sai kawai ta fashe da kuka ta nufi dakinta, Emily ta bita da kallo kamin ta maida dubanta gurin wayarta kiran Tasmia ne ke shigowa, ta amsa kiran ta saka a Speaker. "Hello" "Emily ya kike?" "Ina lafiya, kin tuna da ni yau" "Daman kullum ina tunawa da ke, kawai ina jin tsoro ne, ina fatan kina lafiya" "Ina lafiya Tasmia" "Zaki iya shigowa yau mu gaisa?" Emily ta yi shiru domin akwai abun abubuwa da yawa da take bukatar abokin tattaunawarsu. "Eh gani zuwa" "Amman karki bari ya san kin zo nan dan Allah" "Okay matsoraciya" Ta fada da murmushi sannan ta aje wayar ta mike tsaye, dakin Fatima ta fara shiga ta dagota daga kefen da take tana kuka. "Zan fita yanzu zaki je?" "Ba zan je ba" "Ba zan barki ke kadai ba" "Ni ba zan je ba" Emily ta daga wayar kira Chidimma two miss calls bata daga ba, sai ta kira Tasmia. "Zaki iya zuwa Tasmia ina tsoron tafiya na bar Fatima ita kadai, mai kula da ita bata nan kuma tace ba zata bi ni ba" "Ina tsoron zuwa gidanki Emily" "Ba abun da zai faru na miki alkawari" Tasmia taja dogon numfashi ta sauke. "Kin san fa har gargadi yayi min" "Baya ma garin nan ya tafi gurin kasuwancinsa" "Shi kenan, amman idan wani abu ya same ni, ke ce da alhaki" "Na yarda" "Idan na iso zan kira ki kin san mai gadinki be bari a shiga ciki" "Okay" Emily ta tashi ta koma falo ta zauna, after like 40min Tasmia ta kira wayarta ta sanar mata tana waje, Emily da kanta ta fita ta shigo da Tasmia suka shigo har cikin falon ta dauko mata ruwa da drinks. "Kin yi rama sosai" "Ba ni da kwanciyar hankali a yanzu ko kadan" "Rasuwar danki, da kuma wannan mai gidan naki ko?" Emily ta zauna kusa da ita. "Kullum ina tuna London, ga kuma damuwar yadda gobe na zata kasance" Tasmia ta dauke idonta. "Aliyu yayi magana da ke kuwa?" "Eh, na tarar da sakonsa na kira shi ban san wayar tana gurin matarsa ba, abubuwa sun faru" Tasmia ta yi fuskar mamaki ta gyara zama. "Ban fahimta ba, kamar ya?" Emily ta fada mata abubuwan da faru daga lokacin da ta kira Aliyu zuwa yau da ya zo gidan. "Amman ke yanzu kina ganin zaki koma aikin ne?" "Ina da bukatar aikin Tasmia amman ina tsoron yadda zai kasance min domin a can din na akwai wanda ta tsane ni" "Mu ga sakon da ta turo miki" Emily ta cire password din wayarta ta mikawa Tasmia wayar. "Ni dai a tawa shawarar karki koma aiki a gurin nan, saboda zaki haifar masa da matsala tsakaninsa da Matarsa, kuma tun da kika ji tana barazana zata iya miki komai ko ta yi ma yarki, idan ma aiki kike so ki nema a wani gurin kawai zai fi, tsakani da Allah ke kanki ba zaki so wata ta zo ta ruguza farincikinki da mijinki ba" "Baki fahimta ba, ni fa ba soyayya ce tsakanina da Aliyu ba, ko ranar da kika ji yace miki rape dina yayi yana miki bakar magana ne kawai" Tasmia ta dauki ruwan ta sha ta aje. "Na sani, ai a yadda na san Aliyu ba zai taba iya auren..." Sai kuma ta yi shiru. "Mutum ne mai addini sosai, kuma kin ga ke a yanzu baki san ma halinsa ba, be kamata ki sake da shi ba, be kamata ki ba shi fuska ba, ni musulma ce amman ina miki tsoron wasu daga cikinmu, ke kina ganin haka nan kawai wani zan ganki da rana tsaka yace zai dauki sunansa ya lakawa yarki daga baya kuma ya zo ya miki gori ko wani abun ya biyo baya? Emily kina da kyau fa, kyaun ki nan yana jan hankalin maza akanki, ba zaki iya gane mai kaunarki da gaskiya ba sai wanda ya so ki ko ya taimakeki a lokacin da kike tsananin bukatar taimako" Emily ta sauke ajiyar zuciya. "Bana nufin kulla alakar komai da Aliyu, ni a yanzu ba ta wannan nake ba, ina girmamashi ne saboda abun da yayi min ba zan manta ba, kuma a yanzu ma ya taimake ni gurin rufe London, na lura yana da kirki kawai" "Yanzu ke micece babbar matsalarki?" "Vito, kuma ina son na dogara da kaina" "Da alama baya son ki rabi kowa ko kuma kowa ya rabe ki?" "Haka ne" "Me zai saka ba zaki yi masa abun da yake so ba" Kallon rashin fahimta. "Ba sonki yake ba?" "Eh" "Toh me zai saka ba zaki aure shi ba?" Emily ta sakar mata ido tana kallonta. "A duk duniyar nan ban san wani mutum mai sonki ba kamar Vito, ban san yadda ya hadu da ke ba, amman alamu ya nuna yana kaunarki sosai, yana kaunar yayanki, idan ma kina son sauyawa yarki suna ki bata sunan Vito mana, kuma gashi yana da kudi yanzu an daina auren kyau ko wani abu auren kudi ake, gashi kuma addininku daya" "Amman Fatima bata son shi" "Fatima bata son shi ko kuma dai ke din ce baki gama gamsuwa da shi ba? Ai Fatima yarki ce zaki iya cusa mata abun da bata yi niya ba, haka kuma zaki iya nuna mata alfanun da yake cikin auren Vito, kuma idan kika aure shi hankalinki zai kwanta na shi ma zai kwanta duk wannan takurar da yake miki zai daina yinta" Emily ta hade yawun bakinta ta wani bangaren Tasmia tana da gaskiya, sai dai kuma ta wani bangaren bata ra'ayin auren Vito saboda yarta Fatima da kuma halinsa da sana'arsa sai dai ba zata iya fadawa Tasmia bata son sana'arsa ba gudun kar ta bukaci jin wace sana'a yake yi. "Idan har kika koma karkashin Aliyu kika yi aiki shi ma juyaki zai yi kamar yadda Vito ma yake yi a yanzu, kuma kin ga yana da iyali be kamata ki shiga tsakaninsa da matarsa ba, ko wace mace zata yi kishin ace namiji yana hulda da wata mace ko da ta gaisuwa ce, na san kin san yadda farinciki yake da tsada ba zaki so rusa na wasu ba" Emily ta sauke ajiyar zuciya a karo na uku, tana jin gamsuwa da kalaman sabuwar kawarta Tasmia. "Ki yi blocking dinsa, idan har ya damu yayi magana dake to ki ba shi number, yayi magana da ke ta hanyata, saboda gujewa wata rana kar Vito ya dauki wayarki ya gani, ko kuma shi Aliyun yayi miki abun da ba ki yi tsammani ba" Emily ta dubeta. "Miye banbanci magana da shi a wayarki da kuma tawa? Ina da iko da wayata, Vito be san password dina ba, kuma ke kika fada min idan ina son na canja dole sai na yi pushing idan na nuna masa har a waya ina tsoron ya ga wani abu ai zai zama abun kamar yayi min yawa" "Eh toh haka ne, amman dai karki zake, kuma karki kuskura ki karbi aikin nan, karki sake bawa wani namiji damar da zai juyaki yadda yake so" "Aikin aiki akwai abun da ya saka na ke sauraren Aliyu, shi ma akwai dalilin da ya saka yake neman sanin abubuwa akaina, baki san miye ba wata kila sai nan gaba?" Tasmia ta dan yi jimm tana kallon Emily. "Minene? Soyayya?" "Aa..." Turo kofar falon ya saka daga Tasmia har Emily suka juya sai suka yi arba da Chidimma. "Sannu Ma'am, Oga Vito ne yace na dawo na shirya masa wani abu baya son abincin da aka girka yau" Emily bata ce komai ba ta dauke ido, Chidimma ta wuce Kitchen Tasmia ta kalli Emily. "Ba ke kike masa girki ba?" "Da can na kan yi dan kaina ko yarana, amman yanzu ita take yin komai har abinci a guri daya yake ci da ita a yanzu, ina jin kamar yana son yayi replace dina ne da Ita ko kuma me ban gani ba" "No ba zai taba son yar aikinki ba, bayan ma kin fita komai, kuma ai ta yi masa kaskanci ace ya so ta" "Ni kin san yadda na ganki? Kin san yadda ya dauko ni? Shi ya mayar da ni yadda nake a yanzu har ake gani a yaba kyauna, shi ne kadai mutumen da ya so ni ba tare da duba asalina ko halitta ba, kuma har yanzu be taba nuna min jikina yake so ba, be taba min gorin komai ba, be taba nuna min gajiya akan kula da ni ba" Tasmia ta dafa kafadarta. "Irin wannan ne kike neman rabuwa da shi? Ai shi ya fi kowa cancantarki Emily, babu wani sakamako da zaki masa sai na aurensa, akasin hakan kamar kin butulce masa ne, kuma ina tabbacin amana ba zata barki ba, ki yi tunani akai" Emily ta daga mata kai tana hade abun da ya tsaya mata a makoshi. "Amman dawowa zai yi ne da ya ce ta zo ta girka masa abinci?" "Yana nan daman, na boye miki ne saboda ki zo" Tasmia ta ji yan hanjinta sun kaɗa ta mike tsaye da sauri gumi na karto mata, bata ko tsaya yi ma Emily sallama ba ta rumgumi jakarta ta nufi kofar falon ta bude Emily na mata magana bata kulata ba, da sassarfa ta isa gate tana samun ficewa sai ta ranta a na kare ta aina da gudu tana yi tana waiwaye har sai da ta yi nisa da gidan sannan hankalinta ya kwanta. Emily ta dauki shawarar Tasmia na cewar kar ra koma aiki, duk kuwa da irin kyautatawa Aliyu zato da take, amman zai iya amfani da damar ya dawo da Turhan a rayuwarta ita kuwa a yanzu bata bukatar kowa, sai dai ta dayan bangaren ta san taba bukatar aikin haka ta kwana da tunanin yi ko bari har garin Allah ya waye bata samu matsaya ba. Bayan Fatima ta wuce school, Emily ta shirya ta sauko rike da jakarta da wayarta, kallo daya ta yi ma Vito dake zaune yana karyawa ta dauke ido ta nufi kofa. "Zaki je neman aiki ne? Har shaguna nawa zaki rika bi kina neman su dauke ki aikin da ke kanki zaki iya daukarsu? Idan har baki son kudi da nake aje miki ne toh a shagon siyar da talkami da kika nemi aiki ne, shi ma nawa ne, kudin dai still daga karkashina za su fito" Ta juyo ta kalleshi ta dauke ido ta yi ficewarta. Da gaske gurin nasa ne ko kuma dai ya san mai gurin wata kila kuma yana mata barazana ne kawai saboda ya daureta a guri daya, har ta isa gurin aikin na su Aliyu bata daina tunanin maganar Vito da kuma Tasmia ba, ta duk inda zata auna Vito ya cancanci zama da ita, kuma sakamakon da zata masa na mallaka masa zuciyarta ne da yake bukata kamar yadda Tasmia ta fada, wata kila zata iya shawo kan Fatima ta amince da shi. Ta shiga gurin da ake aje motocin kamfanin tana duba motarta domin ta manta gurin da ta faka ta a wacan karon. Sai da ta yi rabin gurin sannan ta ga motarta ta matsa key din hannunta ta bude motar a gurin da zata zauna ta yi arba da wata farar takardar dauke ta rubutu, hannu ta kai ta dauki takardar sannan ta shiga ta zauna. "Idan kin riske sakon nan, ki shiga office dinki ki yi signing cewar kin bar aikin a hukumance kamar yadda kika karba a hukunce" Ta daga kai ta kalli harabar sannan ta aje takardar ta fito motar ta rufe ta nufi cikin ma'aikatar, bata sha wahala gurin haura sama ba domin ba wannan ne zuwanta na farko ba, ta shiga Elevator har hawa na 4 ta fita ta doshi hanyar da office dinta yake, kallo daya ta yi ma kofar office din Amal ta dauke kai ta murda office din da yake zaman nata a da ta shiga. Ga mamakinta sai ta sami Aliyu tsaye a gaban teburinta yana saka two cube of sugar a tea dake kan teburinta. "Babu gaisuwa?" Ya fada ba tare da ya kalleta ba. "Ina kwana" "Lafiya kalau" Ya saka Tea spoon ya motsa tea. "Zauna" Babu musu ta nufi kujera dake facing din gefen teburin ta zauna, ya dauki tea din ya aje a gabanta. "Na san baki karya ba, dauki ki sha" Nan ma kasa musa masa ta yi, sai ta saka hannu biyu ta dauki cup din ta kai baki ta fara sha. "Sai kawai kika ji kira daga sama ko? Ana zaginki?" Ta sauke tea din ta rike a hannunta. "Ki yi hakuri laifina ne, ya kamata na fada miki waye ni tun farko, ko da yake baki bukaci jin haka ba" Ta dora idonta akan ragowar tea din dake hannunta. "Amman kamin wannan fada min miye aikin Vito?" Ta kalleshi da kyawawan idanuwanta ta sauke kai kasa, ba tare da ta amsa masa ba, domin ba zata iya tonawa Vito asiri agurin kowa ba. "Dialer ne na Drugs?" Ta sake dubansa. "Ba fashi yake ba, da boyo zai rika yi ke ma ya boye ki, ba zai iya shiga ciki mutane kamar yadda yake yi a yanzu ba, kuma ba matsafi ba ne da yanzu ya bada ke ko kuma ya mallake ki sai yadda yayi da ke, idan kuwa baya duka biyun nan to yana siyar da kwaya, shiyasa yake samun mahaukanta kudi ko? Kuma shiyasa ya mallaki bindiga ta hanyar da be dace ba, saboda shirin ko ta kwana, domin ya san a tsakaninsu ma suna iya samun matsala da junansu, kin san sana'ar da yake ba sana'a ce mai kyau ba, shiyasa kike kokarin gina kanki kina son ki bar karkashinsa? Siyar da kwana ya kara masa karfi sosai da mutane ko? Da kuma jami'an tsaro shiyasa yake yadda ya ga gama? Kuma yana sha shiyasa bakinsa yake baki idonsa yake da ja kuma yake saurin fusata idan kika masa laifi sai kwakwalwarsa ta nuna masa dukanki ne kawai mafita" Kallonsa kawai Emily take tana mamakin yadda yake cankar abubuwa line by line a daidai. "Na zo nan ne saboda mu yi maganar Vito?" "Aa kin zo nan ne saboda mu yi maganar ki da kuma tawa" Ya zauna. "Mutane za su yi mamaki idan suka tarar da ni a office dinki, na sakan shiga office kowa na so karbar abu ko hannatawa da kaina idan bana bukatar wani ya shiga tsakani, amman ban taba zama office din kowa ba sai Emily" Ya duba agogo hannunsa. "Da farko zan fara da baki hakurin abubuwan da suka faru, matata bata fahimce ki kuma tana da zafin kishi" Yayi shiru na wasu dakiku sannan ya cigaba. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/22, 7:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣9️⃣ "Sunana Aliyu Aliyu AA Bappa Mudallab, sunan mahaifina Aliyu Mudallab amman ana kiransa da Bappa Mudallab kasancewarsa da na farko a gurin mahaifinsa, mahaifina dan siyasa amman a baya yayi aikin gobnati kamin ya sinci kansa a siyasa, ya fara da commissioner kamin yayi dan majalisar hijar kaduna har sau uku daga baya ya tsallaka zuwa tarayya neman sanata, mahaifina manomi ne sosai, kusan siyasar ta karbe shi ne kawai har yayi suna a ciki, amman abun da ya dogara da shi muma muka jingina, ni kaina na kam taba noman a lokacin damina, mahaifina kuma yana nema a rana da damina da baraza, yana da gonaki da gidajen shanu da ake saffara Madara da Fresh kirdirmo, da manshanu, haka kuma mahaifina yana kiwon fili da kaji. Mahaifiyata kuma mace ce da bata komai sai rainon yayanta uku da Allah ya bata, Ummi bata sana'ar fari balle na baki, mu uku kawai ta haifa Yayana Yusuf, sai kuma ni Aliyu sai kanwarmu da ta zo bayan an fidda rai da samuwarta wato Ramla. Ummi ita kadai ce a gurin Mahaifinmu bayan ita be sake auren wata matarba, kuma har yanzu ba mu taba jin wani abu tsakaninsu ba, ko da yake ita da shi yayan wa da yayan kanwa ne, wato su kansu abokan wasan junansu ne. Yayana samanin tattalin arziki ne, gwararre ne sosai a bangaren Economics shiyasa mahaifinmu ya dauke shi ya damka masa rabin ragamar kasuwanci a yanzu shi yake tafiyar da komai, Mahaifina kuma ya maida hankali gurin Siyasa, ni kuma na karanta Engineering ne wannan ya saka ake yawo da ni gari gari gurin aiki, na zauna a sokoto na yi zama a Kano na zauna a Lagos daga baya aka dawo da ni part hart-cour, tarbiyar gidanmi Alhamdulillah Ummi ta yi kokari da jajircewar Daddynmu, ta bangaren karatun addini duk gidanmu babu rago, ba dan karki ce na yi son kai ba da sai na je na fi kowa kokari ta bangaren Karatu, domin na yi karantar wa a islamiya har uku ba dan a biya ni ba, sai dan na samu ladar kawai, hasali ma ni nake musu ihisani a duk wata, da dare kuma sai na je wata islamiyar maza da ta zama majalisi na karo karatu, a islamiyar ne ma na hadu da matata wadda nake aure a yanzu, Kameela. Dalibata ce mai kokari sosai tana da kaifin basira tana yawan zuwa makaranta even though dai takan taba rashin jin magana sosai a makaranta domin ana yawan kawo min kararta, amman ni ban duba wannan ba, na duba karatunta ne domin ni ina son mace mai addini saboda yayana su samu uwa ta gari, sai dai kamin mu auri junanmu mun sha gwagwarmaya saboda iyayenta bata so na, ni ma kuma Ummi na ba wani gamsuwa ta yi da auren ba kawai dai ta mara min baya ne saboda tana son abun da yayanta suke so, banbanci jam'iya da kuma yin nasara da faduwa ya yi tasiri sosai a gurin iyayenta har ta kai suna kallonmu a matsayin makiyansu, ada abun ya fi haka tsami ma, amman dai auren mu ya saka an yafe wasu abubuwa wasu abubuwan kuma an ba shi baya, a lokacin akwai masu son Kameela ita kuma ni take so, iyayenta kuma Governor da yake Mulkin garin Kaduna a yanzu His Excellency Rilwan Mu'azu Mai Nasara shi suka so ta aura, domin abokin mahaifina ne kuma gashi yana Governor, da ta aure shi ita ce zata zama first Lady domin matarsa bata yi karatu mai surfi da zata iya tsayawa a gaban mutane ta yi turanci ba, amman kishi be bar Kameela ta amince da zabin iyayenta ba, kuma kishi be bari kudi ya rufe mata ido ba. Kameela mace ce mai kishi sosai gaskiya, daga lokacin da na fara soyayya da ita na gano haka, bata bari kowace daliba ta kalle a inda nake karantarwa, tun ina boye alakarmu ina jin kunya sai ga shi ta bayyanawa duniya, yadda take yawan fada da dalibai a makarantar a kaina sai ki dauka ni kadai ne namiji, kuma wasu da yawa ba so na suke ba kawai gaisuwar mutunci ce da girmamawa a matsayina na Malaminsu amman duk bata duba wannan ba, an kai ruwa rana tsakanina da iyayenta da kuma iyayena har ta kai na ce ni na janye daga auren saboda ba zan dauki wulakanci ko raini ba, sai dai damuwar da Kameela ta shiga a lokaci saboda tana tsananin so na ya saka na dawo na yarda zan aureta, amman duk wani hidima da ake ta biki like event ban yi ba sai ta Walima ita ta maza kawai ban da mata, ita ma ta yi nata dabam, amman wani shagalin biki da zai janyo shidai a lamarinmu ban aikata ba, kasancewar ni ba mutum ne mai son bidi'a ba, shekara daya da aurenmu Allah ya ba mu karuwa, amman abun be zo da rai ba, yanzu haka Kameela tana gida gurin wankan amman ta gama tana shirye shiryen dawowa ne, lokacin da kika kira ni naje ganinta ne wayar tana hannunta, kin san mace mai kishi bata iya rike kanta idan ta ji muryar wata macen a wayar mijinta, amman dai na ja mata kunne, wannan shi ne takaitaccen labarina, ina fatar a yanzu hankalinki zai kwanta da Aliyu" Ta yi murmushi sosai ta ji dadin yadda yake tsara mata labarinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali muryar ma kasa kasa kamar mai magana da karamar yarinya. "Ba ki tambayi ya aka yi na san Turhan ba, ko ya aka yi ni da shi muka zama abokan juna" A take murmushin dake fuskarta ya gushe, Aliyu ya saci kallonta kadan. "Kamar na taba fada miki mahaifina yayi rashin nasara har sau uku ko? Sai a na hudu ya samu nasara? Toh a rashin nasararsa ta farko gurin takarar sanata bayan ya fadi zabe sai Shugaban kasa na wacan lokacin ya nada shi ambassador Nigeria to Sudan, a lokacin ne ya tafi har da ni domin Ummi bata yarda yaranta su yi nesa da ita, kusan da mu take shawarar komai da mu take hira kuma Allah ya dora mata son yaya kamar dai yadda kike ji Fatima a yanzu, da muka koma can sai kyakkyawar alaka ta shiga tsakanin Sarkin Sudan na yanzu da kuma mahaifina" Ya mike tsaye ya nufi windows din office din ya bude. "Na manta ban fada miki ba, ni mutum ne mai son wasan tseren doki, wani da wata wasa sai ita a koda yaushe idan na samu free time haka zan hau doki na yi ta zaga gari, idan kuma akwai gurin wasan zan tafi na yi, a Khartoum muke zaune babban birnin kasar sunan a birnin akwai wani babban filin wasa na wasa da dawaki, na kam tafi yin wasa duk Weekend, duk yadda nake da son wasan dokin nan Turhan ya fi ni, kuma ya fini gwanewa domin shi dan sarauta ne ni kuma haye na yi, a duk lokacin da muke je wasa akan shirya tsare tsakanin yayan manya ko yan sarauta, wata rana sai aka hada mu na nuna gwanewa shi kuma ya nuna min ya fi kwarewa akai, da haka dai muka sabu ya zama mun san junanmu idan an shigo za a gaisa, har kai idan na shigo be shigo ba wasan baya dadi ni ma bana shi dadi haka shi ma ta bangarensa. Muka fara following juna da a social media, har ta kai muna gaisawa a waya ko chat, har mukan hadu mu yi hira ko mu tafi wani gurin shakatawa da dawaki. A lokacin Turhan ba shi da ikon shiga Nigeria ba Nigeria kadai ba mahaifinsa be yarda ya bar kasar ba, har ya kan bukaci na ba shi tarihin Nigeria da yadda kasar take, da ya ji cewar daga kaduna na fito sai yake ba ni labarin mahaifiyarsa yar kaduna ce amman baya zuwa gurinta mahaifinsa ya hana shi fita Kasar saboda kar ya tsallaka ya tafi gurinta, amman ita an mata lamuni tana zuwa ganinsa, kuma suna magana da waya, wata rana tsaman sai gashi ta shigo da kokon bararta gurin Mahaifina ta hanyar Ummi, tana son Daddy yayi mata tsaye a bawa Turhan damar ziyararta a duk lokacin da ta so, mahaifina ya sha wahala sai da ya jajirce sannan sarkin ya yarda domin ganin yake kamar Ammy zata karbe masa Turhan ne, kuma su a gurinsu bakar fata ba shi da wata kima, like kamar mahaifin Turhan be so mahaifiyar Turhan ta zama bahaushiya har Nigeria ba, mu kan mu saboda muna yayan manya ne a lokacin ya saka ake daga mana kafa a dole, mahaifina yayi nasarar karya dokar sarkin aka bawa Turhan damar ziyararta kasar a duk lokacin da ya so, saman kuma bayan ni yana da wani amini Munir dan Nigeria ne sosai shi kuma a can yayi karatu a can yayi rayuwa daga baya ya dawo gida, Ummi ta san Turhan, Ammy ma ta san ni ta dalilin abota da kuma abubuwan da suka faru, sai ya zama abotarmu ta kara kwari sosai, kusan rabin hausar da ya iya gurina da Ummi da yaran da Ummi take riko a lokacin ya koya, daman kuma na tarar da shi mahaifiyarsa ta shimfida masa kaunarta da yarenta da rabin al'adarta a zuciyarsa da kansa, amman ma kaunarta Turhan yana son Ammy sosai, daga haka abotarmu ta daure har yau" Ya sauke numfashi a hankali. "Na yi mamaki da na ji kin tsani Turhan har kina gudun ganinsa, domin ban san wani hali mummuna na Turhan ba, shiyasa na kagu na ji wane irin zama kuka yi da shi, taya rayuwarsa ta sauya har ya munana miki haka?" Emily ta kalli hannun Aliyu dake sanye da agogon data dawo masa da shi. "Baka yi tunani ba? Da ace ni yar sarki ce ko kuma balaraba kamar shi ba zai wulakanta ni ba? Farkon abun da Turhan ya fara kushewa a tattare da ni shi ne halittata, kamin ya muzanta tubana, sannan ya kaskanta asalina" Ta yi shiru idonta na cika da hawaye. Ya dauki takardar a gabanta ta ciro pen a aljihunsa ya dora a kai. "Idan ina son na canjawa Fatima suna daga Fatima Aisha Emily zuwa Fatima Aliyu Mudallab ya kike ganin zai kasance rubuta min" "Canja sunan Fatima yana nufin daukar ragamarta ne, tsaya mata a matsayin uba ne a kowa guri a kuma ko wane irin hali" "Abu ne kamar ruwan Sha a gurina ko ban yi dan tana yar abokina ba da zan yi dan ke Emily, ki barta ta dandani dadin da yake karkashin inuwar uba" "Na gode da kokarin da kake ta yi Aliyu, amman wannan karon ya zama dole na yi rejecting wannan offer din" "Idan baki ra'ayin sunana ai zaki iya so na Vito ko? Shi zaki iya rubuta min yadda sunan zai kasance saboda gudun kuskure" "Fatima bata karbi Vito a matsayin Uba ba, ba zata yi farin ciki da hakan ba" "Ban taba tambayarta da kaina ba, ban ji amsar daga bakinta ba, dan haka karki yanke hukunci, idan tana ra'ayi ba sai na saka kin rubuta ba, idan kuma bata ra'ayi kin ga shikenan mun huta" Ta rubuta masa full name din Vito da na mahaifinsa ajikin takardar, sunan da babu wanda ya sani sai ita sai mahaifiyarsa sai kuma amininsa na kud da kud sai kuma daidaikun mutanen da aka haifeshi a gaban idonsu Aliyu ya karbi takardar ya karanta. "Toh ina Vito ya samo asali?" After Aliyu yayi mata tambayar ne ta fahimci babu amfanin using wacan sunan a yanzu tun da ya zabi canjawa. "Shi ya canjawa kansa suna saboda sana'ar da yake a yanzu kowa Vito yake kiransa amman ya fada min ba asali sunansa ba ne" Aliyu ya dan yi murmushi kadan yana kara karanta sunan. "Za a iya kiranta Fatima Vito" "Mun gama da yau zaki iya tafiyarki a yanzu, gobe zaki zo aiki karfe 9am haka zaki rika zuwa kullum, Good Luck" Yana fadar hakan ya fice ba tare da ya tsaya jin ra'ayinta ba, is like kamar ya mata umarni ne, yana son ta bishi ta fada masa ba zata iya aikin ba amman ta kasa, lokuta da dama kimarsa bata bari ta musa masa wani abu. ALIYU POV. Office dinsa ya dawo the first time da ya fara yi after zamansa shi ne ya dauki wayarsa dake kan teburin ya duba miss calls din Kameela da kuma sakonta wai ya dauki wayarta ta ji sanyi. Yayi murmushi ya girgiza kai bayan ya gama karanta sakon, sannan ya kirata. Tana daga wayar ya ce. "Idan kin san zaki min maganar Emily ne ko wasu mata ko maganar kishi to ki bari na aje wayata ba sai mun sake kai ruwa rana ba" Sai kawai ta fashe masa da kuka. "Yanzu kuma mi na yi? Waya taba min mata yar jaririya ta yar amanata rabin rayuwata?" "Amman idan ni ce wani yayi min magana ai zaka ji haushi ko?" "Ke ai mace ce a karkashina kike kin san hukuncinki, ni kuma namiji ne, kuma ba lallai sai aure ko soyayya zata hada ni da mata ba, kuma karamar magana sai ki dauketa ki kai a gaban iyaye, na ja miki kunnen Kameela akan kame baki da rike sirri amman babu abun da ya canja" "Ka yi hakuri" Ta fada cikin kuka. Sai ya fadada murmushinsa. "Komai ya wuce yanzu ai, sai ki kiyaye domin ba zan daukar miki wannan ba, yanzu yaushe zaki dawo?" "Ka wuce ko?" "Eh mana, naje gurin Ummi har na dawo gida...." Daga haka ya dauko mata hirar yadda ya so su tafi gurin Ummi su kwana biyu amman ta ruguza komai, sun dade suna magana a waya har ya katse kiran ya kirata Video Call suka ga juna sannan ya fada mata Ummi zata aiko ayi bikonta. Yana gama wayar da ita ya taba chat kadan ya kira mahaifinsa shi kam sun dauki kusan awa daya suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Sai da ya tashi daga aikin gaba daya ya dawo gida sannan ya kira Ummi suna gaisawa ta yi masa maganar Kameela daman ya san zata masa shiyasa ya kira kawai ya gaisheta, daga karshe ta hanye shawarar aikawa ayi masa bikonta daga Kaduna kai tsaye a kawo masa ita har PH. KAMEELA POV. Bayan ta gama wayar da Aliyu a falon Mama Barakat ta mike tsaye zata fice ranta fess kamar ba ita ba, daman a duk lokacin da zata kira shi bangaren step Mom din tasu take zuwa saboda gudun kar ya amsa su samu matsala ko kuma yayi mata wata maganar marar dadi yan'uwanta su ji, gashi kuma Mama Barakat tana yabon Aliyu yana dan mata nasiha yadda zata bullowa lamarin ko ta zauna da shi, ba kamar uwarta da yan'uwanta da suke zugata ba suna zagin Aliyu, shiyasa ko kadan bata son su san tana kiransa ma, haka idan ya tura masa sako sai ta goge saboda kar a dauki wayarta a duba ace naci take masa da magiya. "Haka ya fi, ki daina bari shedan da zuciya na shiga tsakaninki da mijinki" Cewar Mama Barakat tana kokarin zama, ba dan ta ji tattaunawarsu ba sai dan ta ga alamar komai ya wuce a fuskar Kameela da Kuma muryarta. "Ke yanzu ko kishiya za a miki ai be kamata ki tada hankalinki ba Kameela kina da kyaunki daidai gwargado, mace bata gwada miki komai" Ta tabe baki. "Mama Barakat baki ganta bane, kyakkyawa ce kuma yarinya, ina tunanin ma duk yadda aka yi baturiya ce tun a gidan marayu ta tashi wata kila jefar da ita aka yi ko tsintarka, domin gashin kanta ja ne irin na turawa idanuwanta blue ga farinta ma ba fari ne irin na mu ba fari ne irin na turawa" Mama Barakat ta natsu sai kuma ta yi jimmm kamin ta ce. "A a ina take?" "Lagos wai" "Miye sunanta?" "Aisha amman Emily ake ce mata" "Tana da yara? Kina da hotonta?" "Ni mi zan yi da hotonta? Ko kishiyata ce ai ba zan aje hotonta ba balle wata banzar alaka can gamon tsintsiya da ragga, tana da yara, baban yarinyar ma nemanta yake ruwa a jallo wannan matar criminal ce, kin san daman yan Lagos da wadanda ba hausawa ba ba su da tarbiya ita kanta nemanta yake amman kin ga ta mallakewa mijina, ai Wallahi ina komawa ko dai Aliyu ya zare hannunsa daga gareta ko kuma duk yadda za'ayi ayi, haka kawai wata katuwar banza ta lakewa mijina" Tana sane take fadar yan Lagos ba su da tarbiya da kuma yare saboda Step Mom din ta ji haushi, ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya domin ta ciki na ciki ba son Mama Barakat take ba ko da kuwa zata bata duniyar nan, ta mike tsaye ta fice rike da wayar zuciyata cike fal da kiyayyar Emily. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/25, 9:50 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3️⃣0️⃣ ONE WEEK LATER... Ba zata iya musa masa ba, dan haka ta amsa bukatarta ta dora tata bukatar akai. Tun a washe garin wacan ranar ta cigaba da zuwa aikin, sai dai a tsawon zuwan da take bata fada ma Tasmia cewar ta koma aikin ba duk kuwa da irin dukan ruwan cikinta da Tasmia take na son ta ji labarin Aliyu ta, tana yawan tambayarta ya kira ki? Kun yi waya? Emily ta ce mata aa saboda gudun kar Tasmia tace bata dauki shawararta ba, ba kuma dan bata gamsu da shawarar ba, sai dan Tasmia ta bata ba sai dan bata son musawa Aliyu ne. Kusan tun da ta koma aikin bata hadu da Aliyu ba, ko a hanyar shiga Office dinta ko nashi, hakan kuma sai ya kara mata kwarin guiwa da natsuwa, da fari ta yi tunanin ko zai takura mata ne ko dan neman jin karashen labarinta da Turhan, ko kuma ya nemi wani abu a gurinta ko da yake Tasmia ta fada mata bata gama karantarta namiji ba ne, wata kila haka ne wata kila kuma ita din wawuyace shiyasa ta kasa son mai sonta tsakani da Allah, amman kuma idan bata so Vito ba wa zata so? Ai bata isa ta bude zuciyarta ga wani ba. Ta gama saka dankunnenta ta dauki jakarta ta fito tana tafiya a hankali, tun da ta fito Chidimma ta hade rai saboda yadda Vito yake kallonta har ta iso gurin dinning din ta dora jakarta ta fara zubawa kanta abinci. "Good Morning Beautiful" Ta juya ta kalli Chidimma dake kujera biyu kamin tata. Hakan kuma ba karamin bakantawa Vito rai yayi. "Why would I called Chidimma Beautiful?" Chidimma ta ji kamar an tsomata a ruwa tsabar muzantata da yayi agaban Emily, ba kuma dan bata da kyaun ba, sai dan a gurinshi babu wata mace mai kyau sai Emily. Emily ta kalleshi. "Because she is pretty, isn't she?" Ta fada tana kai abinci a bakinta, da ido Vito yayi ma Chidimma magana sai ta tashi ta dauke abincinta ta bar dinning din. Ya dora hannayensa kan dinning din "Miyasa kike tunanin zan ga kyaun wata mace idan kina nan?" "Da bata da kyau ai ba zaka sakata a matsayina har ka ci abinci a teburi daya da ita ba, har ka nemi ta dafa maka abinci, ko ba haka ba VITO" Ta ambaci sunansa da babban baki, madadin yaji haushi sai yayi murmushi, bukatarsa ta biya daman makasudin yin hakan saboda ya gani idan zata ji kishi ne, idan har ta ji kishin hakan ya nuna tana son shi kenan. Ya jimgina da kujerar dinning din yana cigaba da kallonta, kamin ya ciro wayarwa dake vibration ya duba sannan ya amsa kiran. Yayi shiru na dakiku yanayin fuskarsa ya sauya zuwa bacin rai. "Ganin nan zuwa" Ya mike tsaye sai ta kalleshi tana kai lemu a bakinta. "An sake kama kayanka ne?" Har yayi gaba sai kuma ya juya ya kalleta. "Nope wani ne yake wasa da rayuwarsa, someone set me up" Ta aje glass cup din. "Me kake nufi?" "NDLEA aka turo su bincike gidana daga Abuja" Ta mike tsaya da sauri ta karasa inda yake tsaye. "Kuma zaka tafi" "Yes ina bukatar na tafi" "Aa karka je dan Allah bamu san manufarsu ba, gashi kana da saurin fushi ba mu san abun da zai faru ba" Ya shafa fuskarta. "Babu abun da zai faru" Ta rike hannunsa tana girgiza masa kai idonta har ya fara tara hawaye. "Ya kamata na tafi ko dan na nunawa wanda ya turo su wanene ni" "Be zama lallai turowasu aka yi ba, sana'ar da kake yi ba mai kyau bace kana jefa rayuwarka be kawai cikin hadari, daman dole wata rana za a iya bincike za a iya ganeka" Tana maganar tana kuka jikinta na rawa gaba daya ta tsorata. "Set up ne, NDLEA da suke da nan ko jami'an tsoron duk mutanenmu ne, shiyasa ba ayi amfani da su ba aka turo baki daga Abuja, amman ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru" Ta girgiza kai. "Aa karka je" "Dole sai na tafi ai, suna bukatar ganina" "Kace musu baka nan" "Ina nan" Ya amsa mata yana kai hannanyensa ya rika fuskarta. "Toh ka aje bindigarka karka je da ita" "Zata min amfani" "Idan zaka je da bindiga ba zan bari ka tafi ba" Ta rumgume shi tana kuka, sai yayi murmushi ya dago ta daga jikinsa. "Ba zan je da ita ba" Ta fara lalaben aljihunsa. "No idan kika taba zata samu shatin hannunki, idan na aikata wani laifi da ita aka yi bincike za a samu shattin hannunki kai, ba ni bukatar haka" Ya cire bindigar da kansa ya nufi Kitchen ya dauko wata madaidaiciyar cooler ya saka bindigar ciki sannan ya fito rike da wuka ya nufi gurin da Swimming pool dinta yake yayi gina a inda kasa take ya saka cooler ya rufe sannan ya janyo daya daga cikin kujerar da suke aje a gurin ya dora a sama, sannan ya kalleta ya ce. "Ko da bincike ya biyo ta nan baki da matsala babu wanda zai san da wannan you're safe" Ya rika hannunta ya jimke ya saki sannan ya fice daga gurin zuwa gurin motarsa. Biyo shi ta yi ta tsaya tana kallonsa cikin tsoro da tashin hankali, shikam damuwa data nuna masa a yanzu ta gusar masa da duk wani bacin rai da ya ji a lokacin da aka sanar da shi abun da yake faruwa a gidansa. Dawowa ta yi falon ta doshi gurin da jakarta take ta bude ta dauko wayarta, number Aliyu ta fara kira domin shi zuciyarta ta raya mata, wayar ta yi ringing har ta katse be daga ba, ta sake kiransa be daga ba ta sake kira be daga ba, sai da ta jera masa miss calls kusan tara sannan ta maida wayar ta dauki jakarta ta fice daga gidan zuwa gurin aikinta cause she want to see him badly... ALIYU POV. Tana kallon yadda ya saka wayar da ake ta kira tun dazun a aljihu ya ki ya amsa kiran sai ma saka wayar da yayi a silent kuma ya ki ya aje a inda zata ga sunan mai kiran zuciyarta ta raya mata ba kalau ba, amman bata nuna masa ba da ya gama saka turare ta mika masa agogon da ke aje, ya karba ya fara sakawa. "Yaushe ka siya agogon nan Honey?" "Wannan agogon ina da shi, bata yayi sai yanzu na ganshi" "Da alama yana da muhimmanci a gareka kusan tun da na dawo kullum shi kake sakawa idan zaka je aiki" Ya kalleta da dan mamakinsa domin be yi zaton ta maida hankali a gurin ba. "Toh har kin saka min ido kenan, yana da tsada ne shiyasa duk wanda zai gan ni da shi zai san babban agogo ne" "Hmmm" Ta furta sannan ta mike tsaye ya kama hannunta suka fito seating room, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna ya ciro wayarsa gudun ya zaune ta domin ya sakata aljihun bayan wandonsa ne, sai ya ci karo da sakon Emily. "Na zo baka shigo ba, ka yi sauri ka shigo akwai matsala" A take ya mike tsaye ya fasa cin abincin Kameela ta daga kai tana kallonsa. "Lafiya" "Lafiya kalau, wani uzuri ne ya taso zan tafi Office yanzu" "Abincin fa" "Ki ci zan samu wani abu a can na ci" Ya sumbance ya sannan ya fice da sauri tana kallonsa. Ya shiga motar sa yana karanto addu'o'i yana tukin har ya isa gurin aikin, kusan al'adarsa karanta addu'a idan ya shiga motar da safe, ya faka a inda ya saba fakawa ya fito ya nufi cikin ma'aikatar, sai da yayi kamar ya fara shiga office din Emily saboda ta fada masa akwai matsala sai kuma ya yanke shawarar fara tafiya Office dinsa albashi ita sai ta same shi a can. Ya shiga office dinsa bayan ya gaisa da sakaterinsa Nick ya shiga cikin Office din ya zauna, sannan ya kira wayar Emily bata daga ba, ya sake kira bata daga ba, sai ya aje wayar yana mamakin matsalar me aka samu? Tana office dinta ko kuma ta wuce gida? Ya sake daukar wayar ya sake kiranta bata daga ba, ya sake kira sai ya ji user busy alamar tana waya, wannan karon be aje wayar ba sai da ya tura mata sako cewar ya shigo ta same shi a office dinsa sannan ya aje wayar ya nufi fridge dinsa ya bude ya dauko gorar ruwa ya rufe, ya murda murfin ya bude ya kai gorar bakinsa, juyowar da zai yi sai aka turo kofar Office din aka shigo ya cika bakinsa da ruwa yana kallon Kameela dake sanye da green Hijab har kasa hannunta rike da bracket. Ya hade ruwan yana kallonta da mamaki. "Me kike yi a nan?" "Kana ta sauri ka fita baka yi breakfast, ni kuma hankalina ba zai kwanta ba idan ka wuni da yunwa shiyasa na biyoka da abun karyawa a nan" Ta karasa kusa da shi ta dora bracket din kan teburinsa tana kallonsa da murmushi a fuskarta. "Okay Thank You Dear, amman Baki fada min zaki zo ba, kin san bana son ana fita ba da izinina ba ko?" "Haka ne am sorry" "Me kike hau kika zo nan" "Taxi" Ya dauki wayarsa da nufin turawa Emily sako sai ga Emily ta turo kofar office din ta shigo, daga Aliyu har Kameela juyowa suka yi suna kallon Emily da ta yi tsaye ta kasa karasa inda suke tsaye, Aliyu ya dauke idonsa daga kallon Emily ya kalli Kameela, to his greatest surprise ever sai ganin yayi Kameela na murmushi kamar babu komai. "Karaso mana Emily shigo" Ta fada sannan ta juyo ta kalli Aliyu. "Ashe nan take aiki? Maa Shaa Allah tana da kyau gaskiya" Ta sake duban Emily tana danne wani turnukun fadan ibilisan dake kirjinta. "Toh bari na tafi na barku ku yi aikinku, daman na kawo masa abun karyawa ne, idan ke ma baki karya ba sai ya sam miki ki karya" "Kawai na zo nan ne na.... Na..." Emily ta makale a maganar ta ki ta fita, Kameela ta karasa kusa da ita tana murmushi ta dafata. "Karki damu, ba sai kin min bayanin komai ba, ki gaishe min da yarki Fatima" Ta nufi kofar fita ta bude office din ta fice, Aliyu yayi saurin bin bayanta, sai suka sauka kasa tare. "Muje na sauke ki gida" Ya fada yana kallon yanayinta har lokacin bata nuna masa komai ba. "Okay" Ta bi bayansa suka isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya zagaya ya shiga yaja motar, bata ce masa komai ba har suka isa gida shi kuma sai sake saken yadda zai bullo mata yake ba dan yana tsoron ta ba sai dan yana gudun bacin ranta, kuma ya san ko da ace bata da wannan zafin kishin idan ta ganshi da wata dole zata yi kishi balle tana da shi. Sai da ya faka harabar gidan sannan ya ce. "Da zaka min uzuri ki fahimce ni Kameela..." Bata bari ya karasa ba ta tari numfashi. "Dan Allah kar mu yi wannan maganar da kai, ka kaddara ban ga komai ni fa yanzu na yarda da kai, ba ni da matsala ko cikin mata dubu zaka shiga na san zaka fita, hakan be daga min hankali ba ko kadan" Ta bude motar ta fita tana murmushi. "Allah ya tsare me zan dafa maka?" "Anything" "Okay I Love you" Shi dai mamaki ya hana shi amsa mata da I love you too sai kallonta yake kamin yaja motar ya fice. Ya faka a inda ya gurin da aka tanadarsa domin aje motarsa sannan ya fito ya shiga cikin ma'aikatar ya shiga Elevator ya sauka hawa na biyar ya shiga office side dinsa, fada Sosai yayima Nick. "This isn’t professional behavior, why would you allow anyone into my office without notifying me first?" "Apologies, sir. I allowed her in because I recognized her as your wife. As for Emily, she's one of our staff, and you had previously instructed that any staff member who needs to see you should be allowed in. That’s why I let her through" "That policy is now revoked" Aliyu ya fada a fusace. Nick ya amsa masa cikin ladabi da girmamawa. "Understood, sir. I apologize and will be more careful going forward" Ya wuce ya shiga office dinsa. Zaune ya samu Emily ta hade kanta da guiwa. "Miya faru minene matsalar?" Kamar jiransa take ta dago. "Miye ma be faru ba? A wane dalili zaka aikawa Vito da jami'an bincike masu tu'ammali da miyagun kwayoyi? Me ya maka" Aliyu ya dan yin kamar mai tunanin waye kuma Vito. "Vito.. Vito... Oh Vito? Me zai saka na yi haka toh? Miye alaka ta da shi?" "Ni dai na fada maka, idan wani abu ya same shi kamar ni ya sama, domin shi yake dauke da ni, kuma shi ne mutumen da ya taimake ni a lokacin da babu mai taimakona, shi ya maida ni a yadda nake a yau, ko farcensa bana son wani abu ya sama" "Ahh ahhh ni kika gani kofar gidansa ne? In banda dai kina son ki dora min laifi?" "Indai kana son na cigaba da aiki a nan na cigaba da mu'alama da kai, to ka cire Vito a idonka" Ta fada masa har tana nuna shi da yatsa. Ya kalli yatsanta ya kalleta be ce komai ba ya nufi kujerarsa ya zauna ita kuma ta juya ta fice daga office din. Sai da ta koma office dinta sai ya fara jin haushin abun da ta yi ma Aliyu bata san lokacin data fashe da kuka ba, ya wuce makadi da rawa amman bata da zabin da ya wuce haka, saboda gudun jefa Aliyu a matsala, ta san watan wata rana Vito zai iya ganowa kuma komai zai iya faruwa idan ya sani, haka kuma ba ta so wani abu ya samu mutumen da ya tallafawa rayuwarta ta sanadinta ba, ko da yake bata da tabbacin Aliyun ne, wata kila Vito ba zai rasa makiya ta wani bangaren ba tunanin haka ya kara jefa ta a damuwa. Kasa aikin komai ta yi duk kuwa da kasancewar ta yi waya da Vito ya fada mata babu wata matsala har sun tafi, amman kunya da nauyin abun da ta yi ma Aliyu be bari ta iya komai ba a ranar. ALIYU POV. Sai da lokacin tashi aikinsa yayi sannan ya sauko compound din ma'aikatar ya nufi motarsa ya shiga ya saka basket din da Kameela ta kawo masa dazun be taba komai ba, yana shiga motar ya amsa wayar mahaifinsa, ya fara tukin da hannu daya dayan hannun kuma manna da waya a kunnensa domin fitar da yayi ta dazun da gaggauwa be bar shi ya fita da Bluetooth dinsa ba. "Shikenan Daddy na gode sai mun yi magana" Ya fada sannan yayi ma mahaifinsa sallama ya aje wayar a cinyarsa ya cigaba da tukin har ya isa gida ya faka ya kashe motar sannan ya dauki wayarsa ya bude motar ya fita ya dauki kwando. Taku goma sha daya ya kai shi entrance din shiga cikin gidan, ya tura kofar falon ya shiga da sallama kamar yadda ya saba duk kuwa da ya san ba lallai yau a tarbe shi a yadda aka saba ba domin yau ya bata ran uwargidan ba kadan ba ko da yake bata nuna masa ba. "Sannu da zuwa" Ta fada a yanayin da ba na fushi ba kuma ba far'a sosai ba, sai dai kuma ba ta tarbe shi kamar yadda ta saba ba. Hakan be hana shi isa inda take zaune ya sumbance ta ba sannan ya aje basket din a gurin. "Sannu da gida Gimbiya wannan ado haka?" "Duk na ka ne kai kadai, je ka yi wanka ka zo ka ci abinci" "Okay" Ya haura sama ya shiga dakinsa, tufafinsa ya fara cirewa ya aje wayarsa ya shiga bandakin yayi wanka ya fito ya saka tufafi marasa nauyi ya fito falon domin bawa cikinsa abun da yake wajibun, yunwa yake ji sosai saboda be yi karin safe ba, dan haka ya zauna a seating room din ya nade kafafuwansa Kameela ta zera masa tuwon da miyar taushe ta kawo masa ruwan wanke hannu da kuma na sha da lemun kwakwa, sannan ta zauna gabansa tana game da wayarta. Da ya kalli yanayinta sai ya ji babu dadi, saboda ya san akwai damuwa a tare da ita, amman ta nuna masa kamar babu komai, sai ya ji kamar be kyauta ba. "Kameela da zaki fahimce ni ki yi min uzuri, da rayuwa bata wahalar da ke ba, na san kina jin babu dadi a zuciyar kuma kin biye ko kin aje a ido kuma kina min kallon rashin fahimta, Wallahi Wallahi Wallahi babu soyayya tsakanin da Emily, abun da zuciyarta ta raya miki ko zata raya miki ko idonki ya gani Wallahi ba soyayya ba ce, kuma na miki rantsuwa na fada miki ne a yanzu ba dan ina tsoronki ba sai dan ina son farincikinki, kuma ina sonki, tsabani ko kadan bana son yana shiga tsakaninmu, farko cikinki a koda yaushe shi ne burina, idan kin yarda da ni shikenan idan kuma baki yarda da abun da na fada miki ba a yanzu shi ma duk daya" Ya karasa tare da bude Warmers din zai fara zuba abinci, sai Kameela ta yi karaf ta dauke miyar fuskarta dauke da damuwa. "Karki ci wannan bari na zuba maka wata" A matukar kidime Aliyu ya kalleta ya samu kansa cikin wani kalar firgice da be taba samun kansa a zamansa da Kameela, ta nufi kitchen da sauri sai yayi hanzari tashi ya bi bayanta ko da ya shiga ya samu tana juye miyar a sink. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/28, 9:27 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HQSJMqxBuI985hZVzy0S03 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 3️⃣1️⃣ "Me kika saka a miyar Kameela?" Ta juyo a firgice tana kokarin dakewa domin bata yi zaton ya biyo bayanta ba. "Me zan saka a miyar Aliyu?" "Miyasa kika zubar?" "Saboda ta yi sanyi" "Wannan cooler ba yau na fara cin abinci da ita ba, kuma yanayin miyar be nuna yayi sanyi ba, kuma tun da nake dake ai baki taba sauya min miya ba, dan haka ki amsa min tambaya ne kika saka a ciki Kameela?" Ya daka mata tsawa yana hade fuska kamar be taba dariya ba. "Me zan saka a ciki? Ni ban saka komai ba" "Guba kika saka a ciki? so kika yi na ci na mutu? Da kika ga na miki rantsuwa ina baki hakuri sai tunaninki ya sauya ko?" Ta dafe kirjinta ta zaro ido. "Guba kuma? Me zai saka na saka maka guba a cikin abincinka Aliyu?" "Saboda rashin hankalinki da bakin kishinki, shiyasa na yi mamaki da baki yi hauka kin nuna halinki a lokacin da kika ga Emily ba, saboda kin san abun da kika shirya?" Ta fara hawaye jikinta na rawa "Ka zarge ni da kowane irin abu saboda kishina Aliyu amman ban da kisan kai, kuma a kisan ma na rasa wa zan kashe sai kai da nake kauna?" "Abun da kike yi bana masu hankali ba ne, kwakwalwarki ta samu matsala ki shirya gobe zaki koma Kaduna idan kin je can zan samu likitan kwakwalwa ya duba ki" Yana kaiwa nan ya juya ya fice daga Kitchen din, ta bishi da kallo kamin ta jefar da kular hannunta kasa da karfi ta fara bin kayan Kitchen din tana watsewa tana kuka, sai kuma ta bi bayansa tana kuka ta shiga dakinsa. "Ni babu inda zanje, lafiyata kalau ba ni da hauka Aliyu, idan ma wani abun kake zargin na aikata saboda wa na aikata ba kai ba? Yaushe muka yi aure da zaka fara barin wata ta shiga rayuwarka? Idan kuma na yi fada ka buga min warning ko ka dauke kafa kana nuna wata banza ta fi ni?" Ya katse wayar da yake ya matsa kusa da tsinka mata mari. "Karamin yaro kika dauka ko marar wayo? Yaushe zan zauna na miki rantsuwa na miki alkawari kuma ki rika dawo da magana baya? Okay saboda ina fada sai kika zabi ki yi poising dina? A tunaninki idan na mutu ke zaki huta ne? Hakki rai ai ba zai barki ki samu salama ba" Ta zube a kasa gabansa dafe da kunci tana kuka. "Wannan ba kishi ba ne Kameela, hauka ne kina bukatar likita ya duba kwakwalwarki, wato ki kashe ni kije ki auri wani?" "Ko mutuwa ka yi Aliyu ba zan iya auren wani ba, ina sonka ka sani ko wata mace ka kalla Aliyu jin nake kamar zuciyata zata fito, idan har ba son yarinyar nan kake ba me yasa baka hadata da Turhan din ba? Me kake jira?" "Yanzu duk wannan ya wuce na fada miki ki shirya gobe zaki koma Kaduna" "Ni babu inda zan je, na koma na cewa Hajiya Me?" "Ki fada musu guba kika zuba min a abinci, kina kokarin kashe ni, dan haka ni kuma yanzu ba zan yarda dake ba, ba zan iya kwana gado daya dake ba, ba zan iya sake cin abincinki ba, zamanki a gidan nan ba zai taba bani kwanciyar hankali ba, tafiyarki gida shi zai fi a gareki da kuma ni" "Ni ban saka maka guba ba, sai idan daman kana neman dalilin rabuwa da ni ne kawai saboda ka kawo wata, Wallahi Aliyu ba zan taba kyaleka ba, Wallahi ko mutuwa na yi ba zan barka ba, sai fatalwata ta addabi rayuwarka, saboda kai ka daukar min alkawarin da ba zaka iya cikawa ba, Aliyu ko rabuwa ka yi da ni ba zan iya kallon ka yi rayuwa da wata macen ba" Aliyu ya saki baki yana kallonta. "Ah lallai baki da hankali, ashe abun na ki ma ba kishi ba ne, hauka ce, ilminki be miki amfanin ba tun da har kika iya bari zuciya da shedan suka rinjayeki, abun da kike yi a yanzu Kameela yana nuna min zaki iya kauce hanya kam kishi, zaki iya komai ido rufe" Ta lumshe ido tana sassauta kukanta ita kadai take iya fahimtar kanta ita kadai tasan halin da take ciki, wata kila ita kam tata jarabawar kenan so da kuma kishin Aliyu. "Ka yi hakuri Aliyu" "Ba abu ne da za'ayi hakuri ba, maganar rai da mutuwa ake, kin san idan Ummi ta san da maganar nan aurena da ke ya kare? Kuma ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba sai ta kai ki kotu" "So kake na tafi Aliyu? Haihuwa daya ka fara juya min baya? So kake na tafi na barka da wata banza mushirika karuwa macen da akanta babu kalar fadan da baka min ba? Idan na kome me zan fadawa Abbana? Miye ma'anar na koma gida? Ka sake ki ne kenan?" Ya nufi closet dinsa ya canja tufafi jikinsa ya dawo ya dauki keys dinsa da wallet sannan ya ce. "Bana son na dawo na tararda ke a gidan nan gobe da safe" Ya nufi kofa yayi ficewarsa tana kallonsa har ya rufe kofar dakin. Wani bakinciki ta ji ya ratsa zuciyarta, ta raba kafafuwanta tana kuka mai taba zuciya, iyakar karatun data iya na son mijinta ne da kishinta, irin kishin da hankali yake rumgumar tunani su gudu a kwakwalwarta ta aikata abun da bata san inda inda illarsa zai kaita ba, da ace Aliyu be bata hakuri ba a yau da ya ci abunda zai yi sanadin ajalinsa, saboda tana ganin kamar hakan ne mafita a gareta da kuma shi, duk kuwa da ta san ba lallai hakkin rai ya barta ta huta ba. Sai dai sanin bata da wata mafita sai wannan ya saka ta cire batirin agogo falonta ta daka ta saka masa a miya, saboda ta gane hargowa bata canja komai, domin da ta yi haukanta na farko bata samu abun da take so ba. Yau kuma zuciya taso ta kai ta baro, saboda ta biyan mijinta kuma ta tararda abun da take zargi, idan tace bata yarda da shi ba a yanzu bata yi ma kanta adalci ba, amman sanin a guri daya suke aiki da Emily ya fi komai daga mata hankali ko ba komai zai ganta kullum kuma za su yi magana, daga haka bata san iya inda abun zai tsaya ba, musamman data lura kamar Emily tana da muhimmanci a gareshi ko kuma shi din yana da wata manufa akanta, idan ba haka ba miyasa ya sama mata aiki a kusa da shi? Meyasa ba zai hadata da mai nemanta ba? A wane dalili yayi mata tsawa yayi fada da ita saboda kawai ta kira Emily a waya. "Zan iya rayuwa ko babu kai Aliyu, gidanmu kuma ba gidan yari ba ne da zaka ce na tafi na kasa tafiya" Ta fadawa kanta sannan ta mike tsaye ta fice daga dakinsa zuwa nata, tana shiga dakin sai kuma ta nemi courage din ta rasa, kawai sai ta rushe da sabon kuka, tana matukar son mijinta tana matukar kishinsa wannan abu ne da ya ke rubuce a cikin littafin kaddararta, rashin aiki da lissafi zai saka ta kashe aurenta da kanta yan'uwa kuma za su mata dariya su ce daman sun fada, ta tashi ta fita dakin da sauri ta dawo seating room gurin da wayarta take ta dauka ta aikawa Aliyu sakon ban hakuri da rokon kar ya saketa. "Ba zan iya rayuwa babu kai ba Aliyu, ko sakina ka yi ba zan iya rabuwa da kai ba, idan ma har kana tunanin ina kokarin kashe ka ne ka yi hakuri ka yafe min dan Allah" Ta jira be bata amsa ba, hakan ya saka ta kira shi be daga ba kuma be kira ba, ta san halinsa ta san idan yayi fushi yana da wahalar saukowa, ita ma dai jin ta yi bata bukatar zaman gidan dan haka ta sauya tufafin jikinta ta fice duk kuwa da kasancewar ba kowa ta sani a garin PH sai Tasmia. ALIYU POV. Hotel ya kama domin ba zai iya kwana a gidan ba matukar Kameela na ciki hankalinsa be taba tashi ba irin yau, ba dan komai ba sai dan ta fi kowa kusanci da shi ta san lagunsa ta kowane gefe idan har zata iya saka masa guba a abinci to zata iya masa komai ma. A hotel din ya karasa dan yammancin da ya rage masa, kansa a kulle tunanin idan yayi baya tsayawa shi dai gaba daya ya gagara fahimtar kalar kishin Kameela shi ko a tarihi be taba jin irin nata ba, ko da yake a yanzu yana dora abun ne a babin matsalar kwakwalwa. Ya ga kiranta ya kasa amsawa haka ma sakonta be amsa rokonta ba. Ya sani idan be daukar mata mummunan mataki ba abun da zata aikata sai ya fi wannan. Sosai yayi ma matarsa addu'a a sallarsa da Isha'i ya roki Allah ya sassauta mata wannan mugun kishin ya saka mata natsuwa da kwanciyar hankali a zaman aurensu, ya son matarsa kusan son ne dalilin da ya saka yake mata komai kuma yake daga mata kafa har take kokarin wuce gona da iri. Sai da ya hau gadon dake dakin na Hotel ya kwanta sannan ya kira Family Friend dinsa Nura da suka kwana biyu ba su yi waya ba tun bayan da ya kira yayi masa gaisuwa da barkar haihuwar da aka yi masa. Nura ya amsa wayar yana zolayarsa. "Manya masu kasa baku nema sai dai a neme ku" "To yanzu kai ka nemi ki ni na nemeka?" Nura yayi murmushi mai sauki. "Malam har garin Abuja ka shigo fa baka neme ni ba, sai da na hadu da Ummi take fada min ka shigo" "Tafiyar ta kwana biyu ce kuma ban shirya ba tafiyarce kawai ta zo a haka, ka san yanayin aiki ba ko da yaushe muke samun time ba" "Haka ne, aikin ne kusan da yanke mana komai ai, zumuncin ma idan ba mu yi da gaske ba sai mu bar shi saboda neman duniya" "Toh Allah dai ta shirya ka" Nura yayi dariya. "Ya shirya mu dai. Yanzu dai ya gidan ya kowa da kowa" "Lafiya kalau, ya naka iyalin" "Alhamdulillah" "Nura kai ka fi kusa da ni cikin dukan mutanen da na sani masu aikin lafiya, dan Allah wane likita ne ka sani kwarare ta bangaren kwakwalwa da zai iya duba mutum kuma ya fadi gaskiyar komai" "Me yasa kake neman Likitan kwakwalwa? Lafiya?" "Lafiya amman ba kalau ba, Matata nake son a duba" "Subhanallahi Kameela? Meya same ta?" "Wani kalar azababben kishi take fama da shi da ya wuce hankali, shiyasa nake son a duba kwakwalwarta abincika ko akwai wani abu" "Ban katsi hanzarinka ba, domin ni da kai musan duk mata suna da kishi sai dai na wata ya fi na wata, amman miyasa ka ce tana da azababben kishi? Wata kila abu ne da ba saka shi a muhallinsa ba sai ka yi masa fahimta baibai" "Nura, tun da ka ji na ce maka tana da azababben kishi tana da shi ne, ya wuce hankali" "Kamar me take yi" "Kamai ma tana yi har abun da baka tunani, kawai so nake ka bincika min likitan kwakwalwa da zai iya dubata, da ace kai ba likitan kwakwalwa ne ba na yara ba da kai zan nemi ka dubata" Nura yayi shiru na few seconds sannan ya ce. "Aliyu, look idan akwai matsala ne za ka iya fada min, kasan sometimes mu bukatar abokan tattauna sirri, kuma akwai abun da iyaye ba zamu iya barin iyaye su sani ba, kuma da can ni da kai bama boyewa juna sirri sai dan girma da kai muna yanzu da aiki da kuma rashin zama a guri daya, ya saka dukanmu muka maida hankalinmu gurin wasu abubuwan, amman ni har gobe idan ina cikin wata babbar matsala Aliyu kai ne mutum na farko da zan kira na shaidawa, domin bana kallonka a matsayin aboki kawai ko abokin karatu ko abokin gari daya, ina kallonka ne a matsayin dan'uwa na jini, domin sanadinka na zama abun da na zama Aliyu sanadinka na samu komai da na samu a yanzu, idan kana cikin wata damuwa dan Allah ka fada min" Aliyu ya sauki ajiyar zuciya. "Nura ka san Turhan ai?" "Eh na san Turhan" "Amman kamin nan daman Kameela tana da kishi kai ka sani kuma...." Ya fada masa abubuwan da suka faru tsakaninsa da Kameela da kuma Emily ciki har da alkawarin da yayi ma Kameela cewar ba zai mata kishiya ba. "Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, a lallai Kameela bata da hankali, taya zaki yi kokarin kashe mijin da be bijiro miki da maganar aure ba ma? Gaskiya rayuwarka tana cikin hadari, kana iya yanzu?" "Ina hotel na bar gidan" "Ka yi tunani mai kyau, amman ka yi kuskure Aliyu, tun farko be kamata ka mata alkawarin cewar ba zaka mata kishiya ba, be kamata ka haramtawa kanka abun da Allah ya hallata maka ba, ita mace mai kishi daga lokacin da aka fahimci tana da kishi taka mata burki ake, tun tana haukan tana kishin har ta gaji ta hakura idan ta fahimci ba zaka fasa son wata ko auren wata saboda kishinta ba, bayan kuma kishi ka yi hakuri da abun da zan fada da alama Kameela bata da zuciya mai kyau" "Na mata alkawarin ne saboda bana da ra'ayin kara auren, kuma da farko na yi tunanin aikata hakan zai saka hankalinta ya kwanta mu samu zaman lafiya ni da ita, shi aure Allah yace idan baka iyawa adalci karka yi, kuma ba lallai ne na iya adalci a tsakanin mata biyu ba, saboda rayuwa ni ba mutum ne mai son yin nan na yi can ba, ba kuma zan so na tashi gaban Allah da hakkin kowa ba" "Na fahimce ka duk namiji mai son zaman lafiya a gidan sa dole zai bi hanyoyin da yake ganin sun dace domin ya samu salama da matarsa, shawarar da zan baka a yanzu karka sake cin abincinta" "Daman na yanke wannan shawarar, kwana da ita a gida daya ma ba zan iya ba a yanzu sai ta samu lafiya" "Bayan samun lafiyarta ma, Aliyu babban abun da zaka yi shi ne kara aure, ta fahimci ba a ketare iyakokin Allah, kuma hakan zai rage mata kishi wata kila har ta zabi rabuwa da kai, dan na fahimci kana sonta sosai shiyasa ba zan iya baka shawarar cewar ka saketa ba, amman Wallahi zama da ita hadari ne sosai ga rayuwarka" "Zancen aure ko rabuwa da ita be taso ba yanzu Nura, shiyasa ban fadawa Ummi ba, dan na san ba zata bari na zauna da ita ba idan ta ji, kuma komai dan hankali ne, a sannu ake bi ayu bincike, shin yanzu zaka samo min likitan da zai dubata ko kuma na kashe wayata" "Zan samo maka mana dole na, akwai wane babban likitan kwakwalwa sunansa Dr Adam Bello, sai dai yana da wahalar gani gaskiya kamin ka sami ya duba ka ma sai kana da Connection, zan yi kokari na nema maka appointment da shi idan zaka ganshi sai ku zo Abuja" "Shi kenan na gode sai na jika" "Okay" Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Emily ya shigo wayarsa, ya dade yana kallon kiran baya cikin yanayin da yake son magana da ita a yanzu, sai dai kuma ba zai iya ganin kiranta ya kasa dagawa ba, domin be san dalilin kiran ba, sai da ta kusa yankewa sannan ya daga ya kara a kunne, daga ita har shi shiru suka yi babu wanda yace uffan. "Ba zaka yi magana ba?" "Ba ke kika kira ni ba" "Da ka dauka amman kai ya kamata ka fara cewa Hello" Yayi shiru be sake magana ba. A shagwabe Emily ta fara magana. "Daman dai kawai na ji babu dadi abun da na yi maka dazun ne" "Kin san baki kyauta ba miyasa kika kira ni yanzu?" Tana jin hakan ta san ransa a bace yake wata kila har yanzu be sauka daga fushin fadan da ta yi masa ba. Sai kawai ta kashe wayar, tana jin haushi meyasa ma to ta kirashi yanzu. After ta yanke kiran sai kuma ya ji babu dadi na furucin da yayi mata, ko ba komai ta fahimci beta kyauta masa ba ta kira be kamata yayi mata haka ba, a yanzu zata kara jin babu dadin ne. Without second thought ya kira layinta ringing daya ta daga. Ita dai data daga sai ta ari irin halinsa ta yi shiru ba tare da tace komai ba. "Dazun da kika kira cewa kika yi ni ya kamata na farawa cewa Hello" "Na san yanzu ka kira ka yi min bakar magana ne ko fada" "Me kika sani a halina da zaki yanke hukunci?" Ta yi shiru, jin shirun ya saka shi katse kiran, a take ta biyo shi da wani kiran domin bata san dalilinsa na kiranta ba gashi ta yanke masa hukunci kuma ta kara bata masa rai. Da ya amsa kiran ita da shi sai suka yi shiru babu wanda yace uffan har na tsawon lokaci. "Hello..." Suka furta a tare, ita a kokarinta na yanke shirun shi ma kuma a kokarinsa na yin magana kar tace ta kira ya amsa be ce komai ba. Sai kuma shirun ya sake biyo baya. "Zaki ce wani abu ne? Ko wani abu kike bukata?" "Idan baka da abun da zaka ce, ba sai ka sake kirana ba, mu ba yara ba ne be kamata muna haka ba" "Remember I'm your boss, ni da ke waya kira wani yanzu?" Ashe fa ita ta kira shi, bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba, shiru yayi yana sauraren dariyarta a kunnesa tun da yake da ita be taba jin dariyarta ba sai yau, and ya san dariyar zata mata kyau domin farinciki ya dace da ita a yanzu dan haka ya fara imaging yadda take dariyar, kamin ita da shi su sake hada baki gurin cewa. "Okay Bye" Ya mata sallamar ne saboda ya fahimci bayan dariyar bata da wani abun fada, ita kuma ta masa sallamar ne gudun kar ta bata masa rai tun da ba wani abun zai fada ba. Bayan ta katse kira ya bi number ta da kallo sai kuma yayi murmushi. Be dauke idonsa ba wani kiran ya sake shigowa wayarsa da bakuwar number. Wannan karon ya amsa da sallama domin be san waye ba. "Sallamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam barka da dare" An fada cikin wata murya mai sanyi da be fahimci waye ba. "Barka dai" "Na san baka gane ni ba, Tasmia ce kawar Kameela, daman na zo gidan ne ban tarar da ita ba shi ne nace bari na kiraka ko kuna tare dan na kira wayarta ban samu ba" "No ban koma gida ba tukunan" Yana bata amsar ya katse kiran yana mamakin da ya kamata ace tambaya yayi mata cewar ina ta samu numbersa. [6/1, 9:15 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HQSJMqxBuI985hZVzy0S03 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 3️⃣2️⃣ Ta sauke wayar tana murmushi wani irin jindadi da farinciki suka lullube ta na jin muryar Aliyu, daman tana ta tunanin ta ina zata bullo ta fara gaisawa da shi babu dama, domin a yanayin yadda ta fahimce shi ba irin mazan da mata suke saurin burgewa ba ne, kuma ba irin mazan da ake zuwa ma da bukata kai tsaye ne ba, kusan zuwan Kameela gurinta ya taimaka mata sosai gurin samun damar magana da Aliyu tun a bayan da ta sace Numbersa a wayar Emily. Ta dade tana murmushi kamin murmushin dake fuskarta ya gushe kamar mai tunanin wani abu, ta goge number a gurin kira sannan ta fito bandaki da aje wayar a karamin gadonta ta fito falo ta samu Kameela da ta ci kuka har idonta ya canja kala. "Toh ke yanzu miye amfanin kukan da kike yi?" "Ba zaki gane ba, baki san minene soba Tasmia ba" Tasmia ta zauna kusa da ita ta dafa ta With Straight face. "Na san miye so, so yana iya haukata mutum domin yana saka ka ka aikata abun da ba halinka ko kuma baka yi niya ba, so yana maida kai kamar wani wawa ko kuma kakkarfa, shi so wani abu ne da ba a iya cusa shi sau daya yake shiga zuciyar mutum, kuma ya hanaka zaman lafiya har sai ka biya bukatarsa" Ta lumshe ido ta bude. "Amman ke irin son da kike yi ma Aliyu yayi tawa Kameela shi ya kamata ace yana miki irin wannan son, ke fa mace ce, gashi yanzu har yana kokarin wulakantaki akan wata banza da addininmu ma ba daya ba, ba tare da kin masa komai ba" "Ban masa komai ba sai kawai dan na zagi Emily, yanzu haka baya gidan yayi tafiyarsa, kuma yace na bar masa gidansa na koma gida wai zai samu likitan da zai duba ni, mahaukaciya ma ya dauke ni kenan, shiyasa na rasa me ke min dadi naji bana son zaman gidan gashi ba ni da kowa a garin nan" Tasmia ta bude baki. "Ahhh lallai kuwa mahaukaciya ya dauke ki, amman kin yi hakuri nuna masa kishi da kike ai soyayya ce, shi duk be gani ba sai kora da hali? Da ni ce ke ba zan sake kwana a gidansa ba sai na koya masa darasi" Kameela ta kalleta. "Ni ba inda zan je ina son mijina Wallahi, idan na tafi ai na bawa Emily din damar ta rika magana da shi tana samun yadda take so gashi ma gurin aikinsu daya" Tasmia ta girma mata kai. "Kameela ke fa yar manyan mutane ce, kina da gata ina da yan'uwa da kudi, be kamata Aliyu ya wulakanta kuma ki zauna ba, ai tun da har ta kai ya furta ki koma gida idan baki koma ba ai zai cigaba da wulakanta ki ne, ai kawai ki yanki ticket gobe ki kama hanyar gidanku sai ya nemi ki, ai ba ayi ma namiji haka, tun da har ya iya nuna wata ta fiki kara ya san darajarki" "Akwai abun da baki sani ba Tasmia, iyayenmu ba san auren za su iya raba auren idan suka ji cewar Aliyu ya kore ni saboda na kira wata a gurin aikinsu na zageta saboda tana budurwarsa" Tasmia ta daka mata tsawa. "Ke dalla can Aliyu autan maza ne da kike ta wannan rawan jiki da tsoron rasa shi? Haba Kameela sai kace maza sun kare aduniyar nan ne" "Tasmia Aliyu na dabam ne fa, cikin maza dari irinsa daya ake samu, ni na san yana hakuri da ni, yana min komai kuma be taba wulakanta ni irin haka ba sai da bakar Emilyn nan ta zo" Tasmia ta shiru tana kara jin kalamanta cewar Aliyu na dabam. "Toh yanzu ko number shi zaki ba ni na kira na ba shi hakuri? Domin na lura baki shirya tafiya gida ba, kin shirya karbar wulakancinsa ne, daman maza ai idan suna son ka babu abun da ba za su maka ba, idan kuma suka ki ka zaka fara ganin wulakanci kala kala" "Tasmia ko hauka nake dai ai ba zan dauki number wayar mijina da kaina na ba ki ba, tafiya gida dai zan tafi ko dan ya gane ni ba kanwar lasa ba ce" Tasmia ta watsa mata harara. "Kin dauka kowa irin Emily ne? Ko mazan duniya sun kare an fada miki ni zan iya auren mijin da zai nuna ya fi son matar waje da matarsa?" Kameela ta watsa mata wani kallo tana jin zafin kalaminta. "Mijina ba manemin mata ba ne, balle ki ce ya fi son matar waje akan ta gida" "Idan ba haka ba akan me zai fifita Emily take da suna ko Imily akan ki? Ke mai dai ki yi tunani mana" Kameela ta nuna ta da yatsa. "Ke ki iya bakinki, ban zan dan bana son mijina ba, sai dan na rasa gurin da zanje a cikin daren nan, tun da na zo na fada miki damuwata sai wani zuga ni kike kina zagin mijina, an fada miki rabuwa muka yi ne? Ni fa na zo nan ne saboda na samu mafitar yadda zan shirya da mijina, amman sai wani zakewa kike kina ta zaginsa" Tasmia ta yi murmushi. "Matsala ta dake ke zahila ce, idan yabon Aliyu kike son ayi ai nan zaki zo ba, dan ni na san darajar kaina ba zan baki shawarar zama da mutum da har yanzu baki gama sanin ba, Aliyu yana neman hanyar rabuwa da ke ne kawai shiyasa yake wulakantaki domin ba Emily ce kadai budurwarsa ba" Tasmia ta karasa fuskarta babu alamar wasa. "Me kike nufi?" Har Tasmia ta daga wayar sai kuma ta fasa abun da ta yi niya ta dauke kai. "Ki daina yarda da namiji dai kawai" "Ai ke baki yi auren ba balle ki fada min kabli da bad'adin namiji" Fadar bata yi aure Tasmia ta ji abun kamar gorin auren take mata a take zuciyarta ta haye sama san lokacin da ta mayar mata da zazzafar amsa ba. "Kara ni ban yi auren ba, ke da kika yi auren ai ta wuje ta fiki daraja a gurin mijinki, mijin ma da Emily kadai yake nema ba ni kaina da kansa ya saka min Number wayarsa, kuma idan kin koma ki tambaye shi sau nawa ya zo gidan nan gurina" "Karya kike yi Wallahi ai ko Aliyu zai kula mata ba irinki zai kula ba, domin ba ki fini da komai ba, sai idan ke kika nemi shiga gurinsa saboda an yi kwantai babu miji kuma ga bakin jini, ga kuma rashin tarbiya, idan ba rashin tarbiya ba yaushe mace cikakkiya rikakkiya kamar ke zata zo ta kama gidan kanta set-contain da sunan bautar kasa? Duk garin Kaduna be ishe ki zama ba sai kin tsallako kin zo garin da mijina yake saboda shi ne abun farautarki ko?" Ta dago wayar ta kama Number Aliyu ta kira shi na farko be daga ba sai a na biyu. "Assalamu Alaikum" Ya fada Tasmia bata ce komai ba ta katse kiran daman burinta Kameela ta ji muryarsa domin ta gasgata karyarta. "Komai zaki fada ki fada ni dai na riga na gama da ke Wallahi" Kameela ta rufe ta duka Tasmia ta maida himma suka fara dukan dukan gashi babu mai raba su, ta ko'ina Kameela dukan Tasmia take ba kuma dan ta fi Tasmia karfi ko jiki ba halima Tasmia ta fita cika amman ta yi mata kwance galala tana dukanta, da ta gama da ita ta koma gurin kayan falon ta fara watse su. "Wallahi Wallahi akan Mijina sai na kashe ki Tasmia, daga ke har Emily sai na yi maganinku" Ta Dauki Jakarta ta fice daga gidan tana huci. Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa ta hau ta koma gida, tana shiga ta fadi kan kujerarta ta fashe da kuka bakinciki ya mata yawa, yanzu mayakan sun zame mata biyu kuma ba kowa ya janyo ba sai Aliyu, ta san wani abun da Tasmia ta fada gaskiya ne cewar yana neman rabuwa da ita ne shiyasa yanzu yake wulakanta ta, a yanzu ta gano dalilinsa na yi mata alkawarin ba zai kara aure ba ashe saboda yana son ya tara mata awaje ne, gashi daga tafiyarta haihuwa komai ya canja kamar daman dagawarta kawai yake jira, a daren ta siye flight ticket daga PH to Lagos daga Lagos ta hau jirgin Kaduna kwana ta yi tana kuka tana bakincikin da nadamar dama ace ta bar shi ya ci abincin dazun da yanzu duk bata ji wannan ba. EMILY POV. Kanta a sama tana kallon taurarin da suka yi ma samaniya ido, har lokacin hakoranta ba su rufu daga dariyar da take na wayar da ta yi da Aliyu ba, bata sauke kanta kasa ba sai da mai gadin gidanta ya bude gate motar Vito ta kunno kai a harabar gidan, tana kallonsa har yayi farkin sannan ta sauka ta karasa inda motarsa take, ya bude motar ya fito yana mata wani irin kauna da ke kara tabbatarwar kaunarta a zuciyarsa musamman data nuna masa kulawa da tsoronta na gudun kar wani abu ya same shi. "How are you?" "I'm good, ba su maka komai ba" "Ba su yi ba, kuma ba su samu komai ba" "Taya hakan ta faru" "Saboda cikin kasa nake aje abun da yake dole a gidan, kuma ina da yaran da suke hango abun da zai faru idan suka ga bakuwar fuska sai su shirya komai" Ta yi murmushi. "Na jidadi da wani abu be sameka ba" "Daman babu abun da zai same ni ai, sai dai ya samu wanda ya shirya hakan" Ya wuce ya nufi Gardenta gurin da ya binne bindigarsa sai ta bi bayansa da tambaya. "Ka gano ko waye ne" "Ban gano ba amman zan gano, kuma idan na gane kowaye sai ya dandani kudarsa, sai ya raina kansa" Har yayi ginar ya ciro bindigarsa bata sake cewa komai ba, mikewa yayi tsaye ya matsa kusa da ita. "Kin damu da ni Emily ko ba haka ba?" Ta yi shiru bata amsa masa ba. "Miya haka ki aurena? Mi ya rike ki daga nuna min soyayya Emily? Ba ki jin cewar lokaci yayi da ya kamata ace mun kasance karkashin inuwa daya?" Ta sauke idonta kasa tana shafa wuyanta. "Kina da wani buri ne da kike son cin ma kamin ki amince min ne?" "Vito bana son sana'arka" "Bayan shi fa" "Fatima-... La lall" Bata karasa ba ya katsi hanzarinta yayi gaba. "Oh Okay" Ta bi bayansa suka fito daga gurin ya nufi motarsa ya bude ya shiga har yayi mata key sai kuma ya fito ya dawo daidai inda take tsaye ya shafa fuskarta sannan ya koma motar, tana tsaye tana kallonsa har ya fice, abun da ba su sani ba duk abun da suke Chidimma na lekansu. Emily ta shigo falonta kenan wayar hannunta ta yi ringing data duba wayar sai ta ci karo da sunan Tasmia, babu bata lokaci ta amsa. "Hello" Tasmia ta fashe mata da kuka. "Emily dan Allah ki zo ina cikin damuwa ina cikin bakinciki, ki zo yanzu dan Allah ina da bukatar taimakonki" "Okay gani nan zuwa" Ta nufi staircase da sauri ta dauko key din motarta ta fito ta sauri ta nufi gurin da motar take, daga unguwar da take zuwa unguwar da Tasmia take tafiya ce ta mintuna Arbanin amman cikin minti ashirin da biyar ta isa gidan Tasmia hankali a tashe saboda ta ji muryarta tana kuka kuma gashi ta fada mata da bakinta cewar tana cikin tashin hankali. Tana faka motar ta bude ta fita ya fara kwankwasa kofar Tasmia kamin ta tura ta shiga, yanayin yadda ta ga falon a hargice ta san ba lafiya ba, ta zauna kusa da Tasmia dake rusar kuka tana tambayarta abun da ya faru. "Ni ma ban san miya faru ba, matar nan tana shigowa ta rufe ni da duka wai mijinta yana zuwa gidan nan nemanki, gaba daya Kameela bata da hankali, akan Aliyu zata iya komai Wallahi kara ma ki rabu da mijinta, ni din ta yi min haka ina ga ke kuma" "Ba soyayya nake da mijinta ba, kuma waya fada mata yana zuwa nan nemana? Yaushe rabon da na zo gidan nan ma" "Waya sani wata kila bincike tayi har ta gane ko kuma shi ya fada mata ai maza ba su da tabbas, zuwan ba na yanzu take magana ba tun a wacan karon ne, shi ma kuma karya aka shirya mata domin bayan tafiyarki Aliyu be taba zuwa gidan nan nemanki ba" "Toh yanzu me zaki yi? Reporting dinta za ki yi ma police ko kuma yaya? Ko a fadawa Aliyu" "Aa bana son kowa ya sani, so nake ki raka ni asibiti" "Okay tashi mu tafi" Emily ta fada tana kallon fuskarta data dan kumbura kadan. Tasmia ta mike tsaye "Ban san inda wayata take ba, ara min wayarki na kira na sanar da iyayena halin da nake ciki" Ba tare da tunanin komai ba Emily ta mika mata wayar sai ta tashi ta shiga daki da sunan kiran sai dai a badini ba kiran zata yi ba, amfani ta yi da wayarta dake aje a dakin ta saka number Kameela ta aika mata sako sannan ta goge ta duba inbox din Emily ko zata ga sakon Aliyu bata gani ba, ta shiga longcalls a nan ta ci karo da kiransa da kuma wanda Emily ta yi masa ta dago ta kalle kofar cikin wani yanayi sannan ta sake maida idonta gurin wayar ta saka wata fake number ta kira ta yi canceling. "Kin ga na kira wayar Yayana saboda na sanar masa saboda shi namiji ne, kar na fada musu hankalinsu ya tashi su yi zaton ko wani babban abu ne, bari zuwa gobe zan sake kiransa" Ta fada bayan ta mikawa Emily wayarta. "Okay mu tafi asibitin" "Wace asibiti zamu je ni kin san ba wanin garin nan na yi ba" "Muje ni na san asibitin, sun gwarai sosai a can ake duba London ni kaina can nake zuwa idan ba ni da lafiya" "Okay" Ta shiga ta dauko jakarta da wayarta dake boye a jakar ta fito suka shiga motar Emily, da suka isa likitan dake duty dare ya dubata sai ya rubuta mata maganin ganin kamar ciwon be kai a bata gado ba, amman ta ki yarda wai ita ko'ina ciwo take ji ita dai tafi son a bata gadon, ganin tana bukata ya saka likitan bata gado, a dole Emily ta tsaya tare da ita asibitin ganin bata da kowa kuma be kamata ta tafi ta barta ba, domin ita ma ta tsaya mata lokacin da take cikin damuwar rasa danta. ALIYU POV. "Daman abun da kake takama da shi kenan? Shiyasa kace ba zaka min kishiya ba? Sai ta waje? Abun be tsaya iya kan Emily ba? Har da Tasmia kawata Aliyu? Emily ta turo sako ta fada min komai ta fada min ka fi sonta akaina, shiyasa ka zabi korata, ta fada yadda kake ziryar gidan Tasmia gurin nemanta, ka nuna kafira ta yi matarka muhimmanci Aliyu, toh na bar maka gidan sai ka dauko ta ka kawo daman ai ta fada min lokacin da bana cikin gidan har cikin gidan ta kwana ka yi ma danta jana'aiza ka kyauta" Shi ne sakon da ya fara cin karo da shi kenan a wayewar safiyar yau, ya dafe goshinsa yana kallon Number Emily da Kameela ta yi screenshot ta turo masa ta whatsapp tare da sakon data aiko mata, da yayi coping number ya duba sai ya ga number Emily din ce. Amman me zai saka Emily ta yi haka? Be samu amsar tambayarsa sai ga kiran Tasmia ya shigo wayarsa wannan karon be amsa ba, har wayar ta gaji da ringing be kula kiran ba. Sako ne ya biyo bayaj kiran Tasmia tana sanar da shi Kameela ta yi mata duka jiya da dare a asibiti ta kwana. "Ahhh Ahhh" Aliyu ya fada yana zaunawa bakin gadon dake dakin na Hotel. Da kansa ya kirata sai ta daga tana kuka. "Me ya faru?" "Baka ga sakona ba" "Na gani, garin ya ta miki duka?" "Ban san waya fada mata kana zuwa neman Emily a gidana ba, ban san hawa ba ban san sauka ba, sai ganinta na yi a falona babu bayanin komai ta hauni da duka" "Amman jiya ke kika kira ni kika ce kin je gidan nemanta bata nan, ina kika samu number na" "Mai gadinka ne ya bani da na kira ban same ta ba, sai yace ba ri ya ba ni number ka na kira kace baka dawo gida ba, sai na dawo gidana ina zuwa babu jimawa sai gata ta shigo kawai ta hauni da duka har tana fadar sai ta kasheni, ban san hawa ba ban san sauka ba, Aliyu ba ni da kowa garin nan sai Allah, bana son wani tashin hankali duk abun da za ku yi ya tsaya tsakaninku da Emily da Kameela ka jawa Emily kunne dan Allah ta daina saka ki cikin rigimarku, babu ruwana sa soyayyar dake tsakaninku da ni dai ina zaune da kowa da zuciya daya" Bata jira abun da zai fada ba ta kashe wayar tana kuka. Ya mike tsaye yana tunanin damuwar Kameela shi ta saka masa guba ta duki Tasmia bayan ta gama haukata akan Emily. Number Emily ya kira domin ya ji dalilinta na turawa matarsa sakon da yayi sanadin da aka duki Tasmia kuma aka kara kunno masa wata sabuwar wutar. Emily ta amsa wayar ba yabo ba fallasa. "Hello" "Emily" "Na'am" "Kina ina? Me kike yi a yanzu" Ta kalli kitchen din da take zubawa Tasmia abun karyawar da Chidimma ta shirya domin ita ta kwana a asibiti ne sai washe gari ta dawo. "Ina gidana" "Wata magana ta shiga tsakaninki da Kameela?" "Aa" "Tasmia fa?" "Meyasa ka tambaya?" "Meyasa kika turawa Matata sako cewar ina zuwa nemanki a gurin Tasmia?" A take ran Emily ya bace "Matarka bata da hankali, wane irin magana ne wannan? Sai kace akanta aka fara aure? Kwanan baya ta yi min cin mutunci yanzu kuma taje ta daki Kameela hakan be mata ba sai ta hada karyar cewar na aika mata sako?" "Karki sake kiran matata mahaukaciya karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, ban kira ki dan ki zageta ta ba, sai dan tabbatar da abun da na ji ko na gani" "Kasan matarka ai zata iya shirya komai saboda da kanta" "Cikin abun da zata shirya har da tura ma kanta sako da Numberki? Emily karki maida ni dan iska mana, na san matata tana da kishi amman idan an ciza dole za a hura ai" Emily ta yanke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba, hakan kuma ba karamin fusata Aliyu yayi ba. Keys dinsa ya dauka da wallet ya fito daga hotel din ya shiga motarsa a hanyarsa ta tafiya gida Nura ya kira shi ya sanar masa Dr A-B yana cikin PH. "Ka je ka ganshi misalin karfe tara, na yi magana da Dr Osman zai hada ku sai ku yi magana ya baka ranar da ya kamata ku hadu, idan a Abuja zaka same shi sai kaje idan kuma a zai iya dubata idan ya shigo PH duk daya domin yana yawan shigowa nan aka ce" "Okay na gode Nura zan shirya zuwa 9 na tafi gurin ka turo min address da number Dr Osman din" "Okay" Daga haka suka yi sallama, Aliyu ya koma gidan sai ya samu Kameela ta yi masa gyara, wato ta hargitsa gidan gaba daya ta fashe abubuwan da zata iya fasawa ta watse wasu. Zaunawa yayi kan stairs din ya dafe kansa yana ta ambaton Allah, daya daga cikin dalilin daya saka yayi ma kansa kuma yayi ma Kameela alkawarin ba zai kara aure ba har da gudun tashin hankali da kannan maganganun ashe dai ko a yanzu bw tsira ba. EMILY POV. Cikin bacin rai ta fito Kitchen din, Vito dake zaune a dinning yana karyawa ya bita da kallo. "Jiya baki kwana a gida ba" Emily ta kalli Chidimma, domin ta san Vito baya kwana a gidan balle ya san ta kwana ko akasin haka. "Ni ba karamar yarinya bace, ina da damar na kwana a duk inda nake so" "You're just 25yrs old kuma kina karkashin ikona dole ne na san a duk halin da kike ciki" Ta juyo a fusace "Wai duk wannan gatan da wannan kulawar da ka ba ni ka bani ne saboda ka yi iko da ni? Ka juya ni yadda kake so? Da zarar na yi abu sai kace ina karkashin ikonka bauwa ce ni? Nawa ka biya ka siye ni?" "Babu kudin da zai siye ki a duniyar nan Emily, ina kulawa da shiga da fitarki ne saboda ke Matata ce" "I'm not your wife, ni ba matarka bace ba matar kowa ba ce, and i need another maid bana son Chidimma" Chidimma ta kalli Vito tana girgiza masa kai idonta na cika da hawaye. "Dan Allah karku koreni aikin nan da shi kadai na dogara da shi nake komai na rayuwata" Emily ta dauke kai ta fice rike da abincin, motarta ta koma ta shiga ta dauki hanyar asibitin domin kaiwa Tasmia abun karyawa, bayan bacin ran Aliyu na zarfinta da abun da bata aikata ba, yanzu kuma Vito ya kara mata da shi. Ta faka motar a harabar da aka tanada domin aje ababen hawa sannan ta fito rike abincin ta nufi cikin asibitin, tana tafe ranta da fuskarta a bace kamar zata yi kuka. "Da alama kin fini tsada, shiyasa baki nemi ni ba" Ta karkato kadan ta kalli gefenta sai ta yi arba da fuskar likita daya taba bata katinsa saboda rashin lafiyar London, tare da wani likita a gefensa. "Hi" "Hi, ashe kin gane ni" Ta yi murmushi. "Wacan karon na manta ban tambaye ki ba, are you married? Kar mijinki ya fasa min kai" "No" "Cool, ya mai jikin?" "Ai ya rasu" Ta fada cikin wani yanayi marar dadi idonta na son tara hawaye. "Ayyah... I'm sorry" Ya fada cike da tausayawa. Ta sauke kanta kasa ta cigaba da tafiya har suka isa gurin da zai shiga. "This Way Ma'am" Ta kalli hanyar da zai bi. "No ni nan zan bi, akwai wata kawata da bata da lafiya ita na kawoma abinci" "Toh kuma ba zaki so mu gaisa ba" "Mun gaisa a nan ai?" "Asibitin tana da mutane da yawa, ba zai yayu na siyar da ke ba, ni ma akan hanya nake nan da minti arba'in zan bar garinku" Ya fada yana kallon agogo hannunsa. "Da alama baki san waye Dr A-B ba ki zo kawai ku gaisa" Likitan dake tare da shi ya fada, a yanzu kuma Emily bata da wani zabi daya wuce ta yi abun da ya kamata even though bata san makasudinsa na son hakan ba. Da suka jera suna tafiya yake fadar. "Daman alamu sun nuna min baki da aure, amman na yi tunanin mutumen da ya saka aka nemo ni na duba yaronki shi zaki aura" "Aa" "Kin yaudare shi kenan" "Aa ni bana soyayya da kowa, babu zancen aure a gabana ba zan sake yin aure ba balle na yaudari wani" Ya dan tabe baki kadan. "Ihhh da Alama yan'uwa rijalu sun dandana miki gubar soyayya, kin huta ai, ni ma dai ba a dandana min gubar ba amman soyayya bata burge ni, shiyasa mutane har mamaki suke wai ina da shekara 37 na doshi arba'in kuma ban yi aure ba" Ya bude mata kofar Office din da za su shiga sannan ya tsaya. "Ladies First" Sai da ta fara shiga sannan ya shigo, kana ganin Office din ka san ba na shi ba ne, amman a haka yayi mata gurin zama. [6/3, 8:23 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3️⃣3️⃣ Ya duba agogon hannunsa. "Wani kake jira ne?" Ta tambaya tana jin sakewa da shi kamar yadda ta ji a farkon haduwarsa. Sai yayi murmushi "Abun dariya ne, ni bana jiran wani sai dai a jirani, amman ban sani ba ko abubuwa za su canja wata rana na zo ina jiranki" "Miyasa baka jira?" "Wani mataki ne Allah ya kaini, bana jira sai dai a jira ni saboda kullum na tashi aiko aiki har sai na ture idan ina son hutu, saboda haka ya zama mutane sai dai su jira idan na gama wani aikin sai na fara na su" "Toh amman me yasa kake duba agogo" Ya wara ido. "Hmmmmm ashe dai ke ma kin iya sa'ido" Ta rufe idon tana murmushi, likitan dake tare da shi yayi murmushi ya mike tsaye ya fice daga office din. "Ya kamata ki saka min number wayarki, saboda mu rika gaisawa ko? Domin na lura kin fini tsada shiyasa da na baki number wayana baki kira ni ba" Yana maganar yana kallonta har ta bude ido. "Gashi ko sunanki ban sani ba" "Emily, sometimes akan ce min Aisha" "Ehhhh nice name, Allah yasa baki kyamar musulmi" "Kai baka kyamar Cristian?" Ya girgiza kai. "No... Ko kadan Mahaifiyata ahlul-kitab ce ita christen ce kin ga ba ni da hujjar kyamar ki" Ta nuna shi "amman kai..." "Aa ni Musulmi ne mahaifina Musulmi ne, aljanar data aure ni ma ta hana ni aure musulma ce" Emily ta kyalkyale da dariya... "Interesting" Ya fada yana kallonta da murmushinsa mai kyau. "Wa yace aljana ta aureka?" "Haka suke cewa wai saboda kullum cewa nake na ban ga wanda ta yi min ba, amman ina tunanin ta fara gajiya da ni ta kusa sakina" Ta sake kyalkyalewa da dariya. "you're so funny" "Yeah my second job is to make you laugh" Tana kokarin saka hannunta ta rufe bakin daga dariyar da take, Dr da ya fita dazun ya kwankwaso ya turo kofar ya shigo Aliyu na bayansa. A lokacin ne Dr A-B ya mike tsaye "Bakonka ya zo a late jirgina ya kusa tashi" "Hakuri zaka yi Dr ka saurare shi kuma ka ba mu lokaci ba sai mun yi ta daku ba" Cewar Likitan dake tare da Aliyu, Dr A-B ya girgiza kai zai yi magana Emily ta kalli Aliyu da tun da ya shigo ita yake kallo tace. "Da dai ka saurare shi, ba zan jidadi ba idan ka tafi baka ji uzurinsa ba" "Emily ai ba zan ce miki aa ba" Ya koma ya zauna sannan ya nunawa Aliyu kujera. "Malam Bismillahi" Aliyu be zauna ba domin baya son yayi maganar cewar yana son a duba matarsa ne a gaban Emily and the way da ya samu Dr A-B jikinsa ya ba shi kamar ba za su jitu ba saboda alama sun nuna masa Dr A-B is arrogant. "No ka ba mu katinka kawai i will contact you though it" Dr A-B ya dan tabe baki kadan. "Okay Dr Osman zai baka Katina" Ya mike tsaye yana kallon Emily da murmushi a fuskarsa, ita ma ta mike tsaye. "Toh yanzu kuma sai yaushe?" "Sai randa kaddara ta yi nufin sake hada mu sai mu hadu mu gaisa" "Ehmmm hmmm idan kaddara ta sake hada mu, toh na san manufar hakan kuma zan baki mamaki, fatan alheri" Ya risina mata kadan sannan ya wuce ya bude kofar ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice Dr Osman yayi masa rakiya. Sai da suka fice sannan ya maida idonta kan Aliyu sai ya gwatsaleta. "Ashe haka kike da arha?" Ya fada fuska ba yabo ba fallasa. A take ta hade rai ta turo baki. "To miye na min magana ba mun yi fada ba" "Na miki magana zo ki saka wuka ki yanka ni" Ta sauke idonta kasa. "Breakfast kika kawo masa ne?" "Na Tasmia ne" Ta amsa da dan fushi. "Toh ki dauki abincin ki fice ko gadin office din ya barki ki yi?" "Toh ka daina min fada kamar wani ni yarka ce" "I'm your boss tarbiyarki a yanzu karkashina take dole na gyara miki zama" Ta duka ta dauki abincin ta nufi kofa ta bude ta fita sai gashi ya fito. "Tasmia da kika yi sanadin aka yi mata duka yanzu zaki dauki abinci ki kai mata babu ko kunya?" A nan ta zaburo masa ta juyo a tsawace tace. "Ni ban aikawa Matarka sakon komai ba, babu dalilin da zai saka na yi maka karya, babu dalilin da zai saka na turawa matarka wannan sakon, kai ma idan kana neman janye kanka daga jikina ba sai ka yi min shari ba, you can walkway ba tare da ka dasa min bakin ciki ba, ba sai ka zarge ni da abun da ban aikata ba" Ta karasa maganar idonta na cika da hawaye, kallonta kawai yake har hawayen suka zubo mata ta saka hannu ta share. Ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya kama chat din da Kameela ta aika masa daidai gurin da number wayar Emily ta fito ya nuna mata. "To wa aika? Vito?" Emily ta karbi wayar ta duba ganin Number wayarta ya matukar bata mamaki. "Wallahi ban aika ba, ban tura mata wannan sakon ba, kuma Vito baya daukar wayata..." "Toh waya aika?" Ya tambaye sannan ya karbe wayarsa. Ta yi shiru tana nazari babu wanda ta fado mata a rai sai Chidimma da Tasmia domin Chidimma ta taba daukar wayarta, Tasmia kuma ta karbi wayarta a jiya tace zata kira ta sanar da iyayenta, sai dai bata saka ran Tasmia zata shirya mata wannan Chidimma kuma bata iya hausa kamar haka ba, a ina ma number Kameela ta fito bayan ta yi blocking dinta. "Waya karbi wayarki jiya?" "Tasmia tace zata kira iyayenta bayan Kameela ta mata duka, amman Tasmia ba zata yi hakan ba" "Karfe nawa kika je gida?" Ta yi shiru tana nazari "Karfe tara tayi bayan mun gama waya da kai ne" Ya duba time din sakon sai ya ga da safen nan aka turo masa shi, ya duba kiran da Tasmia ta masa jiya sai ya kalli Emily. "Karki yarda na riga ki isa Office" "Kamar ya kuma? Yaushe na kai mata abun karyawa har na koma gida na shirya na tafi office" "Wannan matsalarki ce kamin ki zo nan ya kamata ki yi wannan tunanin ba yanzu ba" Ta kalleshi tana mamakin yadda yake kokarin tsanarta. "Why do you hate me now?" "I didn't hate you" "Zan aje mata abincin sai na tafi" Ya daga mata kafadunsa alamar he don't care. Da sauri ta yi gaba da abinci ya bi bayanta har ta shiga dakin da Tasmia take, tana zaune kan gadon tana waya Emily ta shigo, shigowar Aliyu ya saka ta yanke wayar tana yana jin wani yanayi da dabam tare da mamakin ganinsa a lokaci daya. Emily ba zata iya fadar zata je gurin aiki ba saboda kar Tasmia ta ji kamar ta fifita aikinta akan lafiyarta dan haka tace. "Ga abinci nan ki karya, zan tafi yanzu ina da uzuri" Ta kalli Aliyu sannna ta fice Tasmia na mata godiya murya kasa kasa. "Ina kwana" Tasmia ta fada bayan Emily ta fice ta bar Aliyu. Madadin ya amsa mata sai yace. "Do you plan all this?" Ta sake dubansa kamar da can ba kallonsa take ba. "Ban fahimta ba" "Kin fahimta Tasmia, don't deny it, Emily tace ba ita ta aika sakon nan ba" "Kuma ka yarda da ita?" "💯 percent" Ta nuna kanta gabanta na faduwa sosai. "To miyasa ni ka zarge ni? Me zai saka na aikata hakan? Yaushe ma na dauki wayar Emily?" Ya saka hannayensa duka biyu aljihunsa. "Ban sani ba tukuna, abun da na sani a yanzu shi ne Emily ta yarda dake, ban sani ba ko ta fada miki labarinta, ta sha wahala sosai kamin ta hadu da mu, ta hadu sa musulmai masu gurbatattaccen tunani da son zuciya sun bar mata tabon da take kallon kowane musulmi ma haka yake, sai dai haduwata da ita da kuma ke ya fara sauya tunaninta, toh be kamata ta same mu da wani nakasu ba, ko da musulma ce be kamata mu ci amanar junanmu ba, kuma mu watsar da yardar mutanen da suka minta da mu" Yana kaiwa nan be tsaya jiran abun da zata fada ba ya fice ba tare da ya bata hakurin zubar hawayen da take ba. Sai da ya fice sannan ta share hawayenta. "Shi namiji na gari nemansa ake ba sai ya kawo kansa ba, yadda Kameela tana walawa a gidanka tana watayawa abun so ne a gurin kowace mace, ko da ace baka da kyakkyawar sura kulawarce kawai, dole zata burge duk wata mace mai son auren namiji irinka, ballantaba kuma ka hada duka biyun ko uku ma, ga kyau ga kudi ga bada rayuwa irin wanda mace take so, ku kanku maza wata rana ba kusan wanda ya dace da ku ba, Aliyu kana bukatar mace mai hankali mai wayo ba irin Kameela ba" Ta sauka daga kan gadon "Kowa da kalar kaddararsa wata kila ni tawa a haka ta zo, son mijin kawata ko ba komai matarka ta kira ni da marar tarbiya kuma ta yi min gorin aure, toh sai na nuna mata rashin tarbiyan, kuma sai na koya mata darasin da ace kewa mace bata yi ma yar'uwarta mace gori" Ta zauna a kujera ta bude abinci. "Sai kace ni na fi kowa bakin jini daga fara plan har ya gano ni, wai ni haka rayuwata zata kare ne? Kalar mazan da nake son aure basa zuwa su ce suna so na sai yan wadanda basa cikin tsarina kamar ni na fi kowa bakin jini, gaskiya ba zan bari Aliyu ya subuce min ba, daman tun ganin da na yi masa da farko ya burge ni" Tana cin abincin tana magana da kanta kamar wata tabbabiya. KAMEELA POV. "Ai dama ya samu shiyasa kuma kin ji hausawa sun ce kowa ya ga rana yayi shanya, da bata karya farashinta ba tun farko ta zubar da kimarta Wallahi Aliyu ko marin uwarsa kike yi be isa yace ki dawo gida sai ya neme ki ba? Me yake takama da shi?" Cewar Hajiya Asma'u Anty taba ya tsina fuska. " Wallahi kuwa nan kika watsa mana kasa a ido kika tsaya kai da fata babu mai son auren nan kika ce sai Aliyu, gashi nan tun ba aje da nisa ba ya koraki ya nuna wata banza ta fiki muhimmanci ina alkawarin da yayi miki toh?" "Alkawarin banza, dadin baki ne irin na maza kuma ni daman na san ba da zuciya daya ya aureta ba, ya aureta ne kawai saboda ubanaa ya karbi mukamin ubanki a yanzu, ke kuma ya aure ki ya wulakanta mu, kuma yayi nasara tun da kin ba shi hadin kai" Hajiya ta fada, sai Anty Shafa ta sake karba mata "Ai kara ma auren ya kare kowa ya huta, idan abun be tsaya iya nan ba gaba ba a san ya zai kasance ba, kuma dan Allah Hajiya ki hana D Alhaji kiransa dan jin ba'asi ko kiran iyayensa" Hajiya ta daga hannu. "Ai Alhaji ma ya fini daukar zafi shi da kansa yace tun da ya turo masa ya gida sai ya san yarsa tana da gata" Ganin ba za su barta da damuwar abun da ya isheta ba ya saka ta tashi ta bar musu bangaren gaba daya ta koma part din Mama Barakat ba dan ranta ya so ba, kan kujera ta zauna tana rushe da sabon kuka bayan wanda ta sha har ya kumbura mata ido ya hana ta cin abinci tun da ta dawo gida. Mama Barakat ta aje abincin dake hannunta ta taso da sauri ta dawo kusa da Kameela dake zaune kasa ta zauna kan kujera. "Subhanallahi Kameela lafiya? Yaushe kika zo?" "Aliyu ne yace na tafi gida sai ya neme ni" "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un Me kika masa?" "Ban masa komai ba, saboda wannan bakar kafirar ne, ba ma ita kadai ba har kawata yake bibiya" "Abun be yi dadi ba, amman kin yi bincike? Kar ya zama kin masa mumminar fahimta ne, ko kuma kim yanke hukunci cikin fushi" "Mama Baraka har test fa Emily ta turo min tana fada min magana son ranta" Mama Baraka ta yi shiru na mintuna tana shafa Kameela alamar rarrashi sannan tace. "Kina da hoton Emilyn ne Kameela?" "Ba ni da hotonta" Mama Baraka ta sauke ajiyar zuciya domin tun a fadansu na farko take son ganin hoton Emily saboda yadda Kameela ta siffanta ta. "Ki yi hakuri idan mahaifinki ya dawo zamu yi magana da shi" "Aa ni na hakura ba zan koma ba, kar ma ki masa magana ko Aliyu ne autan maza ni ba zan koma gidansa ba" "Ba'ayi ma aure haka, tun har kuna son junanku baki san abun da Allah ya tsaro a tsakaninku ba, hakuri zaki yi" Kameela ta kara fashewa da kuka tana fadar ita ba zata koma ba ta hakura da Aliyu. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [6/11, 11:51 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 3️⃣4️⃣ Barka da Sallah, Allah ya maimaita mana. EMILY POV. Daga Asibiti kai tsaye gurin aikin ta wuce saboda gargadin da Aliyu yayi mata, duk wanda ya ganta ya san zuwan kawai ta yi ba dan ta shirya ba, domin gashin kanta a yamutse yake tufafin jikinta ma regular one ne irin da wanda ta saba sakawa a gida kafafuwanta sanye da talkamin da ta saba sakawa a gida. A yau din ma data shigo office sai ta rasa me zata yi saboda bata shiryama zuwan ba, dan haka ta zauna a kujerarta taba ta kallo kofa kamar ta san Aliyu zai shigo, after like 30 min ya turo kofar ya shigo fuska ya yabo ba fallasa. "Ai na dauka ba za ki ji magana ta ba" Yana maganar wayar dake hannunsa ta yi ringing da ya duba sai ya ga sunan Abokinsa Turhan kuma direct kira irin wanda ba kadafai yake masa ba, ba ma ta whatsapp ba, Aliyu ya kalli Emily dake cizon akaifa ya kalli kiran what a coincidence. "Sallamu Alaikum" Ya amsar wayar idonsa na kan Emily. "Hello Aliyu, ya kake?" "Ina lafiya ya kwana biyu" "Alhamdulillah" Daga haka Turhan be sake cewa komai ba yayi shiru kamar yana jiran Aliyu ya fara magana, Aliyu ma ya kasa cewa komai feeling so guilty. "Ya Ammy" "Bata jindadi, ina shirye shiryen shigowa na ganta, Aliyu har yanzu babu wani labari ta bangarenka?" Aliyu ya dauke idonsa daga kallon Emily ya juya baya yana shafa kansa. "Ciwon Ammy yana da alaka da hakan ne?" Turhan ya sauke ajiyar zuciya. "No Aliyu i want to make things right, mahaifiyata ta yi going through abubuwa marasa dadi a zamanta da mahaifina, and ni kadai ta haifa ni ne kawai last hope dinta and i failed her, idan na zauna na yi tunanin wasu abubuwan ina jin babu dadi kuma ina son na kyautata mata, ina bukatar Emily a yanzu saboda mahaifiyata if i can turn back the clock, zan gyara abubuwa saboda mahaifiyata, I'm losing my sleep bana cikin kwanciyar hankali a yanzu, Aliyu na shiga na fita na yi iya yadda zan iya just to fix what i broken, amman na gagara samun yarinyar nan, kuma mahaifiyata ta ki ta fahimce ni, rayuwa tana ta tafiya ina tsoron kar ni na mutu ko na rasa mahaifiyata ta tafi da wannan kuncin a ranta" "Hakan yana nufin ka bata abubuwa da yawa Turhan? Akwai abun da baka fada ba?" Emily na jin sunan Turhan sai ta mike tsaye da sauri ta zagayo gaban Aliyu ta tsaya cikin tashin hankali tana girgiza masa kai. "Babu amfanin fada, zamantakewa ce ta aure ka auri wanda ba type dinka ba, ba ka sonta dole za a samu wannan, balantana lokacin tunani be tsaya kamar yanzu ba, and Aliyu you will never know what is arranged marriage saboda kai da Kameela auren soyayya kuka yi, komai zan fada maka ba zaka fahimta ba, yanzu dai Maneer ya ba ni shawarar cewar na saka kudi da tsohon hotonta akan duk wanda ya ganta zan ba shi wannan kudin, ya kake ganin abun?" Aliyu ya ji gabansa ya fadi gumi ya keto masa, be taba aikata wani abu ya ji kansa mai laifi ba irin boyewa Turhan Emily da yayi, anya zai iya bari Abokinsa ya bata kudi akan abun da zai iya masa kai tsaye. "Hello.." Turhan ya fada a dayan bangaren, Aliyu ya amsa a rikice yana dawowa daga duniyar tunanin da yake. "Ehm Hello, Turhan yanzu ina Office bari idan na samu natsuwa na koma gida sai na yi tunanin abun da ya kamata mu yi" "Okay" Ya yanke wayar ya kalli Emily. "Ban san me kuke tattauna ba, amman dai ba zaka fada masa ina nan ba, i trust you" Ta fada idonta tab da hawaye. "Turhan Trust me, ke kin yarda da ni to yardar  wa zan karya? Kun saka ni a tsakiya I'm feeling guilty, wadanda ban sani ba ma suna magana da ke like likitan nan na yau? Shi kuma a ina kika san shi? Kina zaune a tare da shi har kina masa dariya bayan abokina yana can cikin damuwa saboda nemanki? Anya na yi adalci" "Ka riga ka karya nasa tun da har ka kasa fada masa inda nake duk tsawon lokacin ne, hakan yana nufin nawa ya fi karfi a gurinka dan Allah karka karya, idan ya sani ba zai bar ni da yata ba ita kadai ta rage min, kuma baka san iya abun da mutumen yayi min ba i don't need him" Damuwa karara a fuskar Aliyu, ya nufi kujera ya zauna ya dafe kansa. "There is something about you Emily, kin saka na yi abubuwa da ba halina ba, like boyewa abokina gaskiya, kamar saka mahaifina ya saka NDLEA su bincike gidan Vito kai tsaye daga Abuja, so that idan an same shi da laifi a dauke shi ki samu yanci, amman kika ci mutunci akan haka, and na kyale haka be bata min rai ba, like sitting here in your office talking to you?" Ya dago ya kalli Office din sannan ya kalleta. Hawaye ya sauko mata. "I understand, na yi fada da kai ne akan Vito saboda idan wani abu ya same shi ba ni da mai kula da ni, kuma idan ya gane kai ne ba zai kyale ka ba, ba zan so wani abu ya sake ka saboda ni ba. About Turhan kuma idan kana son fada masa gaskiya amman ka sani cikin rai biyu za a rasa daya ne, nawa ko nasa, domin zan yi duk yadda zan iya na saka Vito ya hana shi raba ni da Fatima, idan kuma har yayi nasarar raba ni da ita, to ni tawa rayuwar bata da sauran amfani, babu abun da zan tsaya yi, ko kuma so kake na dauketa mu yi ta gudu muna boya?" Tana maganar tana hawaye sosai. " Daga kai sai Tasmia sai Vito ne abokan rayuwar da nake sa ran idan ina cikin wata damuwa za ku taimaka min" "Ki cire Tasmia, kuma ki aje Vito a gefe" Ya amsa mata yana kallonta ita ma kallonsa take kamin ta nufi kofa zata bude. "Emily dawo ki zauna" Ta tsaya a gurin na tsawon minti uku sannan ta koma ta zauna kamar yadda ya bukata. "Fada min irin zamantakewar da kuka yi da Turhan, wata kila hakan zai kara min kwarin guiwar kara boyeki a gurinsa, i trust you ba zan so wani abu marar kyau ya shafe ki ta dalilina ba" Ya cire agogon hannunsa ya mika mata. "You can keep this" Ba zallar agogon yake bata ba, yana tuna mata da rayuwar baya ne, dan gutun lokacin da yayi sanadiyar agogon ya zauna hannunta, what he need is ta fada masa gaskiya kuma ta tuna yadda ya taimake ta kar ta boye masa komai. Ta tara hannunta ya zuba mata agogon ta jimke...! KAMEELA POV. Mama Baraka ta dafa ta. "Kameela ba ni na haife ki ba abu ne da kika sani na sani, na san kuna kallona a matsayin kishiyar uwa wacce bata son ku alhalin ba haka ba ne, yadda ba zan so wani abu ya samu Aleeya ba haka ba zan so wani abu ya same ki ba, da na kowa ne ba mu san inda na mu yayan za su samu kansu ba, dan haka nake rike yayan wasu da amana" Kameela ta kalleta. "Me ya kawo wannan maganar yanzu?" "Ina son zan baki shawara ne a matsayin na uwa, ina son ki kalle wannan ta fuskar uwa ba kishiyar uwa ko matar uba ba" Kameela ta dan share hawayenta ta natsu. "Da farko na so na ga hoton yadda yarinyar take, na ga shim me ta fiki da shi da har kike tunanin ta dauke hankalin Aliyu akanki, wata kila ke kika ganin haka amman bata fiki komai ba, kin san wani lokacin mu mata mu muke bada kofar da wasu suke gani har su samu damar juya mu, tsakaninki da mijinki kin fi kowa sanin waye shi me ya fi so me ya fi tsana sai ki kiyaye ita kuma wanda ta dauke masa hankali sai ki duba ki ga dame ta dauke hankalin nasa yawan kyalliya ko kalamai, ko biyayya duk yadda take da shi na san kin fita kusanci da mijinki, kuma ke da kanki ke kika kawo Aliyu kika ce kina so, babu wanda ya muku dole, kuma a yadda na fahimta idan har zan fadi tsakani da Allah Kameela na san ke ce mai laifi duk da ban san abun da ya shiga tsakaninku ba, iya wannan ne ko akwai wani, amman a yadda na fahimta Aliyu mutum ne mai hakuri mai juriya" Kameela ta yi shiru tana sauraren maganar hankali da mahaifiyarta bata zaunar da ita ta lurar da ita ba. "Shi zaman aure dan hakuri ne, kuma kowa da kalar jarrabawarsa, wani a gidan mijin ne da wasu abokan zama wasu kuma iyayen miji, wasu mazan ne ba na kwarai ba, wasu iyayensu ne fitina wasu yara, wasu ma shiga gidan miji ko samun mijin aure ya gagara, kaddara rayuwa gata nan birjik an raba an bawa kowa tasa, amman ke baki samu muguwar suruka ba, kuma mijinki yana sonki, toh me zai saka ba zaki yi hakuri da dan abun da aka jarrabe ke da shi ba? Kaddara ma Aliyu neman matan yake ai be yi ba sai da baki kusa ko?" Ta daga kai. "Kin gani, wata kila rashin ki ya saka shi aikata hakan, a yanzu kuma da kika dawo madadin ki gyara sai kika kara lalata lamarin, kin ga kin bude masa kofa kenan kuma ita wacan kin bata galaba, ita na kawarki da kike zance kar yi mamaki ace son take ta cire ki a gidan ta saka kanta ma gaba daya, na san baki rasa komai a gidan nan ba, mahaifina yana da kudi zai iya miki komai, amman karki duba wannan shi aure Rahama ne daraja ce kwanciyar hankali, ki yi hakuri ki jure ki danna komai ki koma dakin mijinki, iya mai turo miki sakon tana yi ne saboda tana son ki bar gidan ita ta shiga" "Mama Baraka shi da kansa fa yace na dawo" "Eh wata kila akwai abun da kika masa ne, ni zan kira shi, zan yi magana da shi duk abun da za ayi karki biye kanenki da yayyenki domin su ba son Aliyu suke ba, ke kuma kina son mijinki, duk yadda za'ayi ki daina bari ana jin kanku, ita mace gona ce ga namiji ka yi gina ka rufe duk abun da kake so babu wanda ya sai idan ta fitar, shi kuma namiji sutura ne ga mace babu mai ganin tsiraicinta sai idan ta bayyana ko ya bayyana, karki nuna masa ma kin fadi abun da ke tsakaninku, kina son komawa dakin mijinki?" Ta daga kai. "Ina son Aliyu sosai Wallahi" "Indai har kina sonshi to ki shirya fuskantar duk wani kalubale akansa, ni zan kira shi da kaina zan yi magana ta fahimta daga ni sai shi, idan ya kama har mahaifiyarsa zan yi magana da ita, amman bana son ki bar Hajiya ta sani" "Ba zan fada mata ba" "Yauwa yanzu na gamsu kina son mijinki, saka min number sa a nan zan kira shi mu yi magana ba zan ma nuna masa kin san na kira ba" Mama Baraka ta mika mata wayarta Kameela ta karba ta saka mata number Aliyu. "Amman fa sai kin taya ni yakin, domin idan ya zo ya nuna yana son ki koma toh ki nuna kina son mijinki kuma kina son komawa idan ba haka ba yan dakinku za su kara bata abun ne kawai" "Na fahimta Mama Baraka" Na fada tana duba dp Emily dake whatsapp ta nunawa Mama Baraka hoton Emily saboda ta ji dadin shawara da karfafa guiwar da ta yi mata. "Kin ga hoton yar iskar yarinyar nan" Mama Baraka ta yi saving number Aliyu sannan ta karbi wayar Kameela tana duba hoton. "Tsohuwar Matar Abokinsa ce fa Turhan har da ya a tsakanin su yanzu haka Turhan din nemanta yake sosai, wai mahaifiyarsa ta yi fushi da shi saboda ita, ni ban gamsu ba wata kila dai ta gudu masa da ya ne, ko da yake Aliyu yace wai be san yana da yar ba, kuma ban san miyasa ya ki ya fada masa ya ganta ba, wata kila saboda sonta yake ko? Idan ba haka ba ai zai fada masa, wata kila kuma ya boye min ne, amman ko minene dai sai na bincika, yanzu ma bake jin karfin guiwar komawa dakin mijina" Duk dogon rattaba zancen da Kameela take Mama Barakat bata ji ko daya ba, gaba daya hankalinta ya tafi gurin kallon hoton Emily kamar mai son tantance wani abu. "Ya sunanta" "Emily amman Aisha ake ce mata" "Tana PH ne tare da shi?" "Eh yanzu tana PH amman yar Lagos ce a wani gidan marayu ta tashi a can ta girma aka ce, kamin ta auri Turhan din ko a ina suka hadu ma Oho" Mama Baraka ta hade abu da karfi yanayinta gaba daya ya canja, ta kurawa hoton ido kai kace ranar ta fara ganin mutane. "Bata fiki da komai ba, hasken fata kawai zata nuna miki, wannan ai bata kai ta kwace miki miji ba, karki daga hankalinki akanta, kuma ita ai ba musulma bace da alama ga Cross a wuyanta" Tana maganar idonta ya cika da kwalla sai dai bata bar Kameela ta gani ba. "Eh kafira ce" "Wata kila ma duk abun da kike zato ba shi ba ne, Aliyu da hankalinsa ai ba zai yarda ya rabi kafira ba, zan yi magana da shi na san zai saurare ki kwantar da hankali" Ta mika mata wayar. "Tashi ki koma bangarenku kar ayi zaton wani abun muka shirya ma" "Tohm" Ta mike tsaye ta fice daga falon tana jin bakinciki dake zuciyarta yana raguwa saboda shawarar da Mama Barakat ta bata da kuma matakin da tace zata dauka, a yanzu kuma tsoron ta daya kar ya fada mata ko mahaifinta cewar ta saka masa guba a abinci, idan kuma har Ummi taji ta san auren ta da Aliyu ya kare har abada, ta san bata kyauta ba, be kamata ta aikata hakan ba kuma ta yi kuskure, da yanzu ta kashe shi wa gari ya waya? Ai ko mahaifiyarsa ba zata fita jin zafin mutuwarsa ba, haka dai ta yi ta sake sakenta har ta shiga bangarensu ta shige dakinta ta kama hoton Aliyu tana kallo da wasu videos da suka yi a tare tana ta jin kewar mijinta da kuma nadamar abun da ta aikata domin ta fi kowa sanin Aliyu yana sonta, ta san ba dan yana sonta ba wata kila da sakinta zai yi gaba daya ba zai tsaya cewa za a duba kwakwalwarta ba ko ya turata gidansu. *** *** *** Mama Barakat ta bi bayan Kameela da kallo har ta fice fuska a raunace, ta yunkura zata tashi kafarta ta hagu ta yi mata nauyi sosai ta gagara daga kafar, zuciyarta ma ta yi nauyi sosai kamar an dora mata dutse. "Aleeya Aleeya Aleeya... Samira Samira..." Ta kwalawa yaranta kira Sameera ta sauko da saurinta tana dariya hannunta rike da waya da alama wani abun take kallo a wayar. "Mama gani zuwa, Aleeya bachi take" Mama Baraka ta daga kai tana kallonta har ta sauko. "Rika ni ina son zan shiga dakina na" Ta fada mata da yaren yarbanci daman da yarenta take magana da yaranta idan su kadai ne a gidan wannan ya saka suke jin yaren sosai. Sameera ta yi hanzarin aje wayarta tana kallon Mama Baraka. "Mama Lafiya?" "Kafata ce ta rike, ina son na tashi na kasa" Sameera ta rika ta cikin karfin hali domin bata iya dagata gaba daya, Mama Baraka mace ce mai jiki, ta mike tsaye daker ta cije baki ta taka dayar kafar dayan kuma ta daga ta, da taimako Sameera suka haura sama suka shiga dakinta Sameera ta dora ta kan gadonta. "Mama ko asibiti za mu je?" "Aa zai saki, ai bata taba min haka ba sai yanzu, tafi dakinku zan kwana na huta" "Okay" Ta fice daga dakin, Mama Baraka ta kwanta saman gadon ta yi ruf da ciki ta danne zuciyarta take mata nauyi ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. [6/16, 2:18 PM] null: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 3️⃣5️⃣ Ta hade yawun bakinta tana kallon agogon da Aliyu ya bata. ***        ***.        ***. "Matar da na faɗa gidanta neman taimako, har aka ba ni abinci ita ce mahaifiyar Turhan, a lokacin da na bashi shinkafa sai ya dauke numfashi, hankalina ya tashi sosai na yi zaton London ya mutu a wacan lokacin a take na fara girgiza shi ina ihu, matashiyar yarinyar da ta kawo min shimkafar ta fito da sauri tana tambayar lafiya, ya mutu shimkafa na ba shi sai ya dauke numfashi, na shiga uku na mutu ba ni da kowa sai shi. Shi ne abun da nake ta fada ina hargowa, sai ga Hajiyar ta fito tana tambayar me ya faru? Bana iya amsawa sai sambatu nake ina ihu, sai tace a kira direba ta shiga da kanta ta dauko mayafinta ta karbi Yaron ta shiga mota na shiga direban yaja mu zuwa wata babbar asibiti, muka zuwa aka karbi Ibrahim suka bude nasa file suka masa duk abun da ya kamata, likitar data karbe shi mace ce a take ta rufe ni da fada a wane dalili zaki ba shi shimkafa jariri kamar wannan, baki da hankali? "Ba ni da ruwan nono ne kuma ba ni da wani abun ba shi" "idan baki da abun bashi sai ki bashi abinci yaushe kika taba ganin an bawa jariri abinci? Haka kika ga ana rainon jarirai" Na girgiza mata kai ina hawaye. "Ban san yadda ake ba, ba a taba haihuwa a gabana ba, ba a taba rainon jariri a gabana ba" Na bata amsa, sai Hajiyar ta dube ni. "Daga wace duniyar kike?" "A gidan marayu na taso, ban san duka wadannan abubuwa ba" Na durkusa kasa ina mata godiya "Na gode Hajiya na gode" Sai ta rika ni ta mikar da ni tsaye. "Sunana Ammy karki damu ki kula dai ko ruwa karki sake ba shi" "Amman idan be ci komai ba ai zai iya mutuwa ko?" "Za a kawo abincin da zakiba shi, yanzu zaki zauna ki yi jinyarsa har zuwa lokacin da za su sallame shi, akwai wanda kika sani nan?" Na girgiza mata kai. "Ban san kowa ba" "Labarin yana da tsaye kuma idan na fada miki ba lallai ki yarda ba" "Zan yarda, saboda na yarda Ubangijina ba zai bari a cutar da ni ba, amman tun da kin ce labarin yana da tsayi ki aje har zuwa lokacin da za mu samu zama" Na amsa mata da tohm sai ta tafi tare da likitar aka bar ni a gurin, can kuma sai ga likitar ta dawo tace na tafi Ammy tana jirana gurin mota wai zan bita mu koma gida saboda jariri zai zauna a hannunsu ne har ya samu sauki, zuciyata bata gamsu da haka ba dan haka na ki yarda saboda ina tunanin kamar sace min yaro suke son yi, ganin haka ya saka dole aka bar ni a asibiti, Ammy tasa aka kawo min abun shimfida da abinci, aka kawo madara ta jarirai ana bawa yaron, kullum za a kawo min abinci, amman bana iya ci saboda hankalina yana gurin yarona, aka kwana biyu sai Ammy ta dawo duba ni a lokacin ne take tambayata ko na san yarona yana da wata rashin lafiya nace aa, sai tace min likitoci sun fada mata yarona yana da sickle, ban ma fahimci ciwon ba sai da ta yi min bayanin cewar jinina da jinin mahaifin yaron ne ya zo daya, tace min kar na damu zata dauki nauyin maganin yaron, haka kuwa aka yi naira biyar ban taba kashewa ba a tsawon zaman da na yi na asibiti na wata daya, a tsawon watan da na yi asibitin nono be kawo ba saboda bana iya cin abincin kirki kullum cikin tunanin butulci da Khaleefa yayi min da kuma makomar yarona, ban san ina da hawan jini ba sai a lokacin kuma  ashe idan mace ta haihu wanka ake mata da ruwan zafi ko kuma a bata magani ban sani ba hakan ya saka na yi ta kumbura, ina jin akwai canji a jikina amman saboda babu mai kula da ni ban damu da lafiyata ba, har sai da Ammy ta same ni ta tambaye ni ina da wani ciwo ne da yake saka ni kumbura haka domin na zama wata babba uwar mata, nace mata aa sai idan abun ya same ni ban sani ba, sai saka aka bude min file aka bincika ni, a nan aka gane hawan jinin da na samu da cikin dana be sauka ba, kuma ba a gasa min jiki ba shiyasa nake ta wannan ciwon. Ni ma gadon suka ba ni ana kula da ni, a tsawon wata daya da na kara a asibitin Ammy ce take kula da ni ni da dana, ta saka mai aikinta tana jinyata har na samu lafiya amman jiki be sauka ba. Da aka sallamo ni sai na amince na dawo na gidanta na bar London a asibitin, ta ba ni daki daya a cikin dakunan da suke cikin gidanta kuma suke kusa da dakinta, daman tun ina asibiti ta kawo min tufafi sai ta kara min wasu tace idan ina son abinci na sauka na ci kuma na sake jiki kamar gidana. Na jidadi ta karammani a lokacin ba tare da sanin wacece ni ko daga ina nake fito ba. Kwana biyu da dawowata aka sallamo London sai aka dawo da shi gida, sai ta siya masa tufafi kusan kala goma sha biyu bayan pampers da madara da ta karo ta siya masa gadon yara da tawul, mai aikinta take masa wanka ta goya shi wani lokacin kuma ita da kanta zata dauke shi ya wuni a hannunta. A haka na kwashe wata uku a gidanta, kuma a tsawon lokacin nan bata taba tambayar labarina ba, bata tana nuna min banbanci ba, idan ta ga ina ja baya gurin shiga lamuran gidan sai ta rufe ni da fada, wai na kasa sakin jiki, ita ta lura da wani bangare na ibada ta daya kamata na gyara sai ta fara koya min a lokacin take tambayar a gidan marayun da nake ba a koya mana ibada ni. A ranar na fayyace mata komai na yadda kaddara ta tsara min rayuwa. Ta yi kuka ta tausaya min kuma ta yi min alkawarin zata zame min uwa, itace ta fara saka ni a makarantar islamiya na fara koyon addini. Sannu a hankali na sake jiki na zama kamar yar gidan, wata rana ina zaune falo ta same ni tace Aisha ina jinki kamar yata daman ina sha'awar ya mace Allah be bani ba, samunki a yanzu ya saka na ji kamar Allah ya maye min gurbinki da wanda ban samu ba ne, fadar hakan da tayi sai ya kara karfafa min guiwa na jidadi, ta fada min yaro daya ta haifa amman baya hannunta matashiyar da na gani a lokacin mai suna Nana rikonta take, yanayin yadda take mu'amalantar danta abun sha'awar ba dan na gani ba sai dan labarin da ta ba ni da kuma yadda take idan ya kirata ko ta kira shi, na fahimci tana matukar kaunarsa ne ta yadda take fada min hallayensa da dabi'unsa, har ta fada min idan ya kan shekara biyu kamin ya zo gurin, amman wnnan karon idan ya zo akwai shirin da ta yi masa, ban fahimci me take nufi ba ashe aurena da shi take son ta hada amman bata fada min ba. Sai dai tana yawan ce min musulmai suna da dadin zama kuma Allah zai min sakamako da miji na gari. A haka har yarona ya shekara daya ina kula da shi, Ammy kuma tana siya masa magani da madara, sai dai ni kam jiki be sauka ba, duk kuwa da kasancewarsa na samu lafiya sosai ga wadata ta abinci, na zama kamar wata babbar mace fari ya fito jan gashina yayi kyau saboda yana samun gyara a yanzu komai a wadace. Wata rana na yi wanka na shirya cikin shudiyar atamfa wanda ta yi mjn kyau sosai, na fito harabar gidan na zauna ina shan iska, da kuma mamakin yadda har zuwa lokacin Khaleefa ba neme ni ba, ba dan ina da bukatarsa ko wani abu daga gareshi ba sai dan cikin da ya sake ni da shi, da kuma irin halin da ya bar ni, amman be biyo sawuna ba. Da ace ban hadu da Ammy ba wata kila da ina nan cikin gararin rayuwa amman be damu ba. Be yi tunanin alhakina ba ko na dansa. Ban san ba, ashe ina tunanin hawaye suna saukowa min amman ban jin ba saboda zuciyar ta yi nisa gurin tunani har sai da Ammy ta fito ta zauna kusa da ni tana fadin. "Me kika tuna? Domin na san kin samu lafiya yanzu ballantana nace ciwo kike ji" "Bana tunanin komai" "Ga hawaye a fuskarki Aisha karki cutar da kanki mana, ki dauke ni a matsayin uwa bana son kina boye min komai" Na kai hannu na taba fuskar sai na ji hawaye. "Kawai ina tunanin yadda Khaleefa ya juya min baya ne, kuma yadda be waiwaye ni ba har yanzu, be damu ta sanin halin da dansa yake ciki ba" Sai ta yi murmushi. "Yarinya ce ke shiyasa baki fahimci rayuwa ba, ai a yanzu ne yake cikin shauki da jindadin yaudara, ba zai neme ki a yanzu ba, sai a lokacin da nemanki ba shi da amfani a gurinsa, kuma ina baki shawarar idan ya dawo miki karki saurareshi ban ce karki yafe masa ba, amman karki yarda ki sake saka kafarki a gurin da aka wulakanta ki aka nuna baki da daraja. Aisha maza na gari suna tsada, ba kowa ne yake iya aure ya rike amana ba, amman ina mai tabbatar miki nan gaba kadan zaki samu samu wanda zai mantar da ke komai zai so ki ke da danki, ni ma na sha wahalar rayuwa a aurena na farko kuma banbanci abun da aka miki da nawa kadan ne, ke kin yi ma arziki an barki da yaron, ni nawa karbe yaron yayi kuma ya hana na shayar da shi, sai da na shekara ashirin kamin na samu ganin dana a ido shi ma kuma sai da na yi fadi tashi shiga nan fita nan, daker na samu haduwa da nada na samu ana barinsa ya zo gurin ko kuma ni na tafi, bayan Turhan ban sake haihuwa ba saboda maganin da aka bani a gidan mahaifinsa, shi ma haihuwarsa ta zo ne kawai saboda Allah ya kaddara akwai da a tsakani, shiyasa a yanzu na maida shi abokin ban kalle ta sigar dan fari ba, komai a gidansu ake masa abinci da nake ci ma daker ya iya koyar cinsa, idan ya zo nan tufafi kalar da nake so yake sakawa, zamu yi wasa da dariya mu yi hira mu yu yawo kamar ni da kane na ba dana ba, matar da ya aura ma daga masarauta aka zaba masa, kuma har yau be taba kawo min ita na ganta ba, sai a waya, shiyasa ni ma na yi masa nawa tanadin na musamman kuma na san zai so ki zaki dace sosai" Na kalleta da kamar mamaki jin ta ambace zan dace, sai na nuna kaina. "Ni" "Eh, ɗana nake yi ma tanadinki, na miki alkawari zai soki zai rike ki amana kuma zai so danki, a yanzu ne zaki san miye aure zaki dace, kuma na san zaki so shi domin shi ma kyakkyawa ne, kusan duk yan mata da nake hada shi da su cemin yake baya sonsu amman ke kam ba zai iya juya miki baya ba, domin kina da kyau kina da haske da gashi kamar matan garinsu, shiyasa nake ta boyonki ina fargabar kar wani yace yana sonki ki karba, kin ga idan ya aure shi zai aje ki a nan dole zai rika zuwa akai akai, kuma ni na zan samu nawa jikokin ta bangarena, idan ba haka ba ina tunani gaban kadan dauke shi zasu yi ba za su bari na zauna da shi ba" Na sauke ajiyar zuciya ina tambayar kaina to idan kuma ya zo ya ga ban masa ba fa. Kamar tasan abun da nake sakawa sai tace. "Karki damu da wai ba zai so ki ba, sai so ki ina mai tabbatar miki zai kaunace ki Aisha kamar zai yi hauka, ke kanki zaki yi mamaki yadda zai kula da ke, saboda ni na zaba masa ke da kaina kuma kin sha wahalar rayuwa Allah zai saka miki ta hanyarsa In Shaa Allahu, abun da na cutar da ni a zaman da muka yi da mahaifinsa shi ne shi baya so na, da ace yana so na da ba zan wahala a yadda na wahala ba, amman ke na san Turhan ba zai bari ko yatsa a nuna miki ba, dana yana da kirki sosai yana da tarbiyar kuma yana da addini daidai gwargwado na miki alkawarin Turhan ba zai taba cutar dake ba ba zai taba cin amanarki ba" Ta yi min campaign ta gyara danta sosai da halin da ta san ba nasa ba ne, ta fada min abun da ba haka yake ba, ta lullube danta da kyawawan halayya alhalin akasin hakan ne a tare da shi. Ni dai ban iya cewa mata komai ba, domin kyautatawa tana biyo kyautatawa ne, ta ina zan iya cewa danta bana kaunarsa macen da bata san ni ba ta rike ni ta kyautata min ni da ɗana, gashi ta yi kuskure bata tambayi ra'ayi akan kudirinta ba, idonta ya rufe akan muradinta da kuma burin da take da shi. Dafa ni ta yi "Aisha karki damu, na lura da kyakyawan halayen dana, kuma ba zan ce ni din mace ce mai nagarta 100 bisa dari ba amman dai na san na kam kamanta na kan kyautata iya yadda zan iya, ba zan yarda a cutar da wani ina gani ba sai inda karfina ya kare, Wallahi ba zan bari Turhan ya cutar da ke ba na miki alkawari, ke din abar tausayi ce Aisha baki da kowa kuma gani ba ki jidadin aure ba, duk wanda ya ji labarin ki dole ya tausaya miki, wata kila ta dalilinki zan samu aljannata gashi ina jinki kamar yata, ba zan taba bari Turhan ya cutar da ke ba" Ba zan iya amsa mata da aa ba amman a lokacin na ji a jikina ban shirya sake wani auren ba, idan kuma nace ba zan auri danta ba a ina zan zauna? Zai kula da ni wa zai rike ni ni da ɗana? Ina cikin wannan tunanin muka ji kyallowar Ibraheem ni da ita muka tashi da sauri muka shiga cikin falon na haura sama na dauko shi ihu kawai yake na yi rarrashi na na ba shi madara be saurara, sai ya yanke shawarar na tafi da shi asibiti haka na saka hijab cikin tashin hankali muka tafi asibitin, su yi iya bincikensu sun ba mu test da hotuna kala kala amman ba a gano asalin damuwarsa ba sai da ya shekara biyu cif, suka ce min ɗana Autism ne, ga shi yana fama da sickle, daga lokacin hallayarsa ta sake yau ciwo gobe lafiya baya yarda da kowa sai ni sai kuma Ammy mai aikin Ammy ma daker yake yarda da ita, ko sallama aka yi da karfi sai ya fasa ihu jiki yayi ta rawa ya cige, tun ina jin tsoro har na saba, ɗana ya sha wahala gashi kuma yanzu be rayu ba, kuma be ji sauki ba har ya bar duniya, kuma be ga ubansa ba" Ya rufe baki tana kuka. Aliyu ya mike tsaye ya nufi windows office din ya tsaya tana kallon harabar ma'aikatar, sai a yanzu na fahimci dalilin Ammy na juyawa Turhan baya, ta ki ta fahimce shi ta saurare shi. Ya sake juyowa ya kalli Emily dake ta kuka, dawowa yayi gurin teburin ya zari tissue ya mika mata ta karba tana shaye hawayenta. "Ba zan ce na fi sauran ba, amman dai na miki alkawari daga yanzu wani ba zai sake cutar da ke ba, sannan ina son na ja kunnenki akan Tasmia karki sake yarda da ita, abu na karshe da zan fada miki shi na har yanzu Ammy tana sonki, mace ce mai kirki kawai danta ne ya tsaba alkawari, saboda wannan ta juyawa Turhan baya, wannan dalilin ya saka yake nemanki, yanzu haka ya fada min bata da lafiya kuma yana tunanin kamar har da tunaninki ya saka ta ciwo" Ta kalle shi tana hawaye. "Asha ma ba nadama yayi ba, ashe ma..." Ta kasa karasa. "Dan Allah Aliyu ka yi min alkawari ba zaka taba fada masa inda nake ba" Ya kalleta sai yayi shiru na dakiku kamin ya amsa mata. "Na yi, ba zan taba bari Turhan ya san inda kike ba ta dalilina sai idan ke kika yi ra'ayi, you have my words" Ta daga masa kai alamar gamsuwa. "Mu je na kai ki gida" "Zan iya tuki na zo da mota" "No i want to take you home safely" "Amman za a iya cewa ranar mun shiga mota daya, kuma yanzu a sake ganin mun shiga" Ya rumgume hannayensa. "A duk lokacin da zan aikata wani abu uku nake dubawa kuma nake jin nauyi, Ubangijina, mahaifaina, matata, Ubangijina ya san ba ni da wata mummunar manufa akanki, sai kyakkyawa, Matata ta san da ke, iyayena ne suka rage su kuma na san ba su da matsala, the rest can go to hell, let's go" Ya fara takawa ya isa kofar ya bude ya juyo ya kalleta sai ya samu shi take kallo. "Aliyu yana da banbanci da sauran ki saka wannan a zuciyarki, you can trust me" Ta mike tsaye ta isa kofar ta fito sai ya janyo kofar a daidai lokacin da Amal ta fito office dinta, dan tsaye ta yi da farko irin na mutum da mamakin ganin sabon abu ya rufe shi, Aliyu yayi kamar be ganta ya jera da Emily suka wuce, a tare suka sauka kasa suka isa har gurin motarsa ta bude ta shiga, shi ma ya shiga. "Amman lokacin tashi aikin be yi ba" Yana yi ma motar key ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. "You need to rest, labarin zaki karasa min wani lokacin, don't stress yourself" Ya tashi motar suka kama hanya, sai ta maida dubanta gurin agogon da ya bata tana ta murza agogo a hankali. Kallo mace ya wuce sau biyu zuwa uku haramun ne a gurinsa amman Emily ya kasa dauke idonsa a kanta, musamman a yau da tausayinta ya zame masa nauyi, tukin kawai yake amman idonsa da hankali yana gurinta har ya isa gidanta, ya faka a wajen gate din gidan yana kallonta. "Aliyu..." Ta kirashi da muryarta kasa kasa. Ya amsa mata yana kallonta zuciyarsa cike da tausayinta. "Ka taba marmarin abun da baka taba samu ba?" Ta tambaya har lokacin bata kalleshi ba. "A'a" Ya amsa mata bayan few seconds. "Me kike marmari?" Ta kalleshi tana kuka. "Iyayena, ni uwa amman ni ma ina neman tawa uwar ina jin kewarta duk da ban taba kasancewa da ita ba, me yasa suka jefar da ni, me na yi musu? Miyasa gashin kaina yake yake da idanuwa na, ni yar asalin wace kabila ce, wa na biyo mahaifina na ko mahaifiya? Minene asalin sunana? Su waye yan'uwana? Duk ba ni da amsar ko daya" Ya busar da iskar bakinsa. "Emily kuka kike son na miki ne?" Ta girgiza kai. "Toh dan Allah ki yi daina kukan nan haka, kin cika zuciyata fal da tausayinki, a yanzu kuma bana son ganin damuwarki, ban wanzu a wacan duniyar da kika sha wahalar rayuwa ba, amman ina ta dorawa kaina laifi miyasa ban san ki tun a farko ba? Wata kila duk wannan wahalar da baki shata ba, iyayenki kuma wata kila ma sace ki aka yi aka kai a gurin ba tare da sanin iyayenki ba, domin alama suna nuna ke ruwa biyu ce, amman ki daina kukan kin ji?" Yana mata maganar cikin sanyin murya da rarrashi. Ta share hawaye. "Good Girl" Ya bude motar ya fita ya zagaya bangarenta ya bude mata ta fito. "Na san Fatima bata nan yanzu, amman anjima idan ta dawo school ta huta ni ma na tashi aiki zan zo na dauke ta mu je yawo" Ta bata fuska kamar zata fashe masa da kuka. "Aliyu dan Allah...." Be bari ta karasa ba ya tare numfashi ta. "No no no noooooo Emily ba abun da kike tunani ba ne, ina son na dandana mata dadin uba ne, tun da kin nuna mata na uwa, kuma kin wahala da yawa ya kamata ki huta, wani ya dauki responsibility, you're not alone we're Family" Kallonsa kawai take. "Kin min izini?" Ta daga mishi kai. "Thank You, ki yi hakuri da fadan da muka yi dazu ki yafe min" Ta yi murmushi, shi ma murmushin yayi tana tsaye yana kallonta har ta shige ciki, sannan ya koma motar ya koma gurin aikinsa. Yana shiga office abu na farko da ya fara yi shi ne kiran Ammy ya gaishe ta kuma yayi mata ya jiki domin tabbatarwa idan da gaske bata da lafiyar ko kuma fadar Turhan ne kawai. "Alhamdulillah" "Ammy me ke damunki?" "Sun ce hawan jini ne da ciwon suga, amman dai Alhamdulillah sauki yana samuwa" "Kina gida ne ko asibiti" "Ina asibiti" "Allah ya kara sauki, In Shaa Allahu zan shigo na dubaki" "Aa karka damu, ba sai ka wahalar da kanka ba ina tunanin da na kara samu sauki kadan za su sallame ni" "Allah ya kara sauki, amman dai zan shigo In Shaa Allahu" Daga haka yayi mata sallama, after like one hour, kira ya shigo wayarsa da bakuwar number sai da ya kai karshen typing din da yake sannan ya amsa wayar. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam, Aliyu kana lafiya?" "Lafiya kalau Alhamdulillah" "Baka gane mai magana ba ko? Mama Baraka ce" Ya dan yi shiru kamin ya amsa. "Maa Shaa Allahu Mama ya gida fatan kowa lafiya" "Alhamdulillah, Aliyu idan ka samu lokaci ina son mu yi magana ka kira ni, nasan yanzu kana kan aiki ne ko?" "Eh gaskiya ina gurin aiki" "Toh idan ka koma gida ko zuwa dare ne sai mu yi magana" "Lafiya dai ko?" "Lafiya amman ba kalau ba, akan matarka ne bata fada mana abun da ya hada ku ba, kai kuma baka biyo sawunta ba, ta zo mana nan duk ta rikice ta zama abar tausayi, sai dai ka samu lokaci za mu yi magana" "Okay Mama" Ya sauke wayar ya cigaba da aikinsa. Sai 4pm ya tashi aikin a hanya yayi sallah la'asar ya isa gida ya dafa ma kansa indomie ya ci sannan yayi wanka ya shirya cikin wani voile lace na maza black color mai kyau, ya saka bakar hulla ya sha turare da bakaken talkama kamar wanda za shi zance, ya cika aljihunsw da sabbin kudi sannan ya fito ya shiga motarsa ya dauki hanya sai gidan Emily, da ya isa unguwar be karasa gidan kai tsaye ba gudun kar ya janyo mata matsala, sai ya faka gida uku kamin nata, sannan ya kirata a waya. "Hello" "Assalamu Alaikum" Ta amsa, sai kuma ta yi shiru. "Gimbiyar tawa ta shirya ne?" "Oh oh oh Fatima?" "Yeah" "Eh ta shirya" "Toh a fito min da ita, ina waje nesa da ku sai kin saka ido sosai zaki iya ganina gida na uku kamin na ku, bana son na zo kusa ne ban san ko Vito yana ciki ba kar yace zai miki fada ko ya dake ki, kin san ni kuwa a yanzu ba zan saka ido ko yatsa wani ya nuna miki ba" Ta yi murmushi mai sauki tana jindadi tare da sauke numfashin da ya ji shi har cikin zuciyarsa. Ya zauna a motar na tsawon mintuna goma sannan ya hango ta ta fito sanye da bakar abaya ta rolling dankwalin abayar ta rufe kanta kai kace musulma ce, ta yi kwalliya sosai har da jan baki, tun daga nesa Aliyu yake kallon fuskarta tafiyarta da yadda bakar abayar ta yi mata shegen kyau ko kyaltawa baya yi gaba daya ta dauke hankalinsa ko Fatima da ya zo domin ita be gani ba sai Emily, da ta iso gurin motar sai ya sauke gilashin ya jingina da kujerar motar yana kallonta kamar wanda ya zauce. "Sannu" Ta fada ta muryar mai dadi idonta suna jan hankalinsa ga wani tsadadden murmushi a fuskarta. Yayi murmushi ya sauke kansa kasa. "Emily ashe kina da kyau, na gode da kika karramani, wannan shigar ta dace da kyau, kin yi ma abayar kyau sosai" Ta yi murmushi ita kanta ta san ta yi kyau. "Wata kila da zaki rika suturta jikinki haka da manyan kaya masu sauko miki su rufe tsiraicinki da zan yi ta kula ina fahimtar kyaunki ne, kuma zan fi sake jiki na jidadi, kin san ban taba kula da kina da kyau ba sai yanzu?" "Saboda na saka abaya?" Ya girgiza yana kallonta da murmushi. "Aa saboda kin rufe jiki, kin dace da sunan Aisha, daga yau ba zan sake kiranki da Emily ba, sai Aisha" A bakin gaskiyarsa yake fada mata tufafin yayi mata kyau domin yayi mata kyau babu karya, sai dai yana karfafa mata guiwa ne saboda ya dawo mata da sha'awar saka tufafin da musulunci ya yarda mace ta saka, so yake ta ji wannan alfarma yaja hankali da abun da yake gani da jin shi ya dace da ita. Fatima ta daga masa hannu tana masa waving domin ta lura be ganta ba, bayan kuma Emily ta fada mata ita ya zo dauka za su tafi yawo. Ku yi hakuri dan ni dan Allah Wallahi uzuri ne yake rike ni. [6/17, 9:33 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 3️⃣6️⃣ "Hey Fatima ya kike?" Ya fada yana kallonta sai ta amsa cike da far'a da zumudi. "Fine" Aliyu ya kalli Emily. "Ni fa ba ke na zo dauka ba, Fatima kawai nace zan dauka" "Ni ma ka ji nace ka tafi da ni ne?" "Ina karantar abun da yake cikin zuciyarki a fuskarki da idonki shiyasa kika yi anko da ni, ni bakin voile ke bakin abaya" "Saboda an rubuta a fuskata ina son ka tafi da ni?" "Bana bukatar a rubuta, saboda ina iya karanta rubutun da alkalin zuciyarki ya ayyana ko babu tawada" Ta bude baki zata yi magana ya tare numfashinta. "Ki cigaba da musawa daman ai kin saba" Sai ta yi murmushi ta sauke kanta kasa, shi ma murmushin yayi ya mika hannu ya bude gaban motar, Fatima bata jira yace ta shiga ba ta shige front seat. Emily ta duba wayarta ganin kiran Vito na shigowa wayarta ya daga mata hankali sai ta yi hanzarin kallon Aliyu. "Ku yi hanzari ku tafi" "Ke fa?" Ta girgiza kai ta rufe motar. "Ba zan je ba" Aliyu ya kalli wayar dake hannunta da yadda hankalinta ya tashi a take sai ya kashe motar. "Dan Allah ka tafi kuma karka dawo da ita sai idan na kiraka" "Idan baki ra'ayin tafiya yawon da ni ba zan cilasta miki ba, amman ke ki fara tafiya gidan tukuna" "Aa sai ka wuce hankali zai fi kwanciya idan ka tafi" "I'm your boss ni zan baki umarni ba ke zaki ba ni ba" Ta kalli titin ta sake kallonsa cikin tashin hankalin da take boyewa. "Amman kace baka son bacin raina, dan Allah ka tafi" Tana fadar hakan ya murzawa motar key cikin wani yanayi na am masa dole ya hau titi, bata bar gurin ba sai da ta daina hango su, sannan ta koma cikin gidan da sauri, ta shiga falon cikin tsoro sannan ta haura sama zuwa dakinta wayarta ta fara kashewa ta boyewa tana dagowa sai ga Vito ya shigo fuska kamar bakin maciji, wani irin cin burki yayi ya tsaya kallonta daga sama zuwa kasa, ganinta da Abaya ya ninka masa bacin rai. "Miye wannan a jikinki?" Ta yi shiru bata amsa masa ba. Sai yayi cikinta mayafin abayar ya fara fisgewa ya jefar ya rike wuyanta da karfi. "Ina Fatima take? Ina kika je? Meyasa kika saka wannan kayan?" Ta ture shi da karfi ta fara magana cikin tsawa. "Saboda ina ra'ayin sakawa, na gaji da abun da kake min Vito komai na rayuwar duniya sai ka zaba min zan yi? Tufafi sai wanda kake so? Bana mu'alama da kowa sai wanda ka yarda da shi? Yar aiki mai gadi duk sai wanda ka zaba?" "No ba zaba miki tufafi ba, ki saka duk wanda kika so, amman ban da wannan! Ke yanzu ba abun kunya ba ne a gurinki ki yi koyi da musulmai? Ina hankalinki ya tafi? Me kike son zama Emily? Zan amince miki ki yi komai zan baki gata amman ban da canja addini Emily ba zan taba yarda da wannan ba" "Bana son zama da kai, ina son na bar gidan nan na yi rayuwata ni kadai" "Baki da wannan ikon, wane yake hure miki kunne ko? Ina kika tafi? Ina Fatima?" "Ba ruwanka da wannan" Ta sake riko wuyanta. "Miye bana miki Emily? Wane irin gata ne ban baki ba? Wane irin jira ne ban yi ba akanki? A duk lokacin da na miki maganar aure hankalinki wani gurin yake tafiya, gaba daya ba nine a gabanki, na gaji yanzu, waya zo gurinki ko kuma gurin wa kika tafi?" Ta ki ta yi magana, a take ya wulgar da ita kasa da dukannin karfinsa, sai kuma ya bita ta kama abayar jikinta daga saman gurin v shafe dake gaban rigar ya yaga daga sama har kasa. "Ba zaki sake saka wannan tufafin ba, ba zaki sake kula kowa ba, you already know yadda raina yake baci idan kika kula wani miyasa kika yi? Me yasa kika kasa karbata har yanzu?" Ta dauke ta da mari, ya kai mata duka a fuska kamin ya mike tsaye ya cire belt din jikinsa ya fara dukanta tana ihu, and he keep questioning her. Sai da yayi mata duka sosai irin dukan da be taba yi mata ba sannan ya jefar da belt din ya zauna kan kujera tana kallon yadda take murza jikinta tana kuka, a yanzu kuma sai ya ji ransa ya fi baci akan duka da yayi mata fiye da laifin da ta aikata. Bedsheet din kan gadon ya yaye ya lulluba mata a jikinta da babu komai sai underwears, ya zauna a gurin ya rike kansa. "I'm sorry" "Ka kashe ni kawai, na gaji" "Ba zan kashe ki ba, amman zan kashe mutumen da yake ziga ki, na san ba zai wuce wannan dan iskan yaron na gurin aikinku, ba mamaki shi ya turo NDELA har gida na" Emily na jin haka ta yi karfin halin tashi zaune. "ba shi ba ne, karka dauki alhakinsa, mutumen da nake aiki a tare da shi shi ne mutumen da ya taimaki ni lokacin da na kusa rasa rayuwata da cikin Fatima, shi ne mutumen da nake ta ajiyar agogonsa, he has nothing to do with this, karka cutar da shi Vito, idan wani abu ya same shi ba zan taba yafe maka ba, kuma ba zan taba yafewa kaina ba" Ta karasa daker tana kuka, ya kalleta ya sake kallonta ya sake kallonta a karo na uku, ya rasa me yasa ta kasa kaunarsa ta kasa bashi hadin kan da yake bukata, bayan duk abun da yayi mata, bayan duk tsawon shekarun nan da suka dauka tare bayan dubun kyautatawa. Mikewa yayi tsaye ya fice daga dakin ya dawo falo ya zauna ya saka hannunsa aljihu ya ciro wani karamin kwalba mai kamar akwati ta zuba wata farar hoda a hannunsa ta shaka da karfi ya rufe ido yana juya kai na dan lokaci, sannan ya tashi ya fice daga gidan gaba daya. ALIYU POV. Da farko yawo ya so yayi da Fatima sosai kuma yayi mata siyayya amman halin da ya bar Emily ya tsaya masa a zuciya, hakan ya saka shi canja kudirinsa na kai Fatima park da guraren shakatawa ya tafi da ita super market kawai ya siya mata kayan wasa da na ciye ciye, tana zabar abun da take so yana tambayarta sallah nawa ake a wuni, me ake karantawa da wane lokaci ake yi, kuma ita tana yi ta bashi amsa daidai ban da yin sallah, tana yi sallah ne a duk lokacin da take sha'awar yin sallah, sai da suka shiga mota ya kama hannunta yana murmushi yace. "Yanzu ki min alkawari kullum zaki yi kowace sallah babu fashi, kuma komai kike zaki aje ki yi sallah" "Wata rana ina gajiya fa" "Eh ko kin gaji ki yi a haka, ai ba zaki so idan kin mutu a kona ki ba ko?" "Eh" "Good kina son idan kin mutum na musance a aljanna ko? Guri mai kyau da ni'ima kuma komai ake so za a samu a ciki" "Har da kayan wasa" "Sosai da kayan dadi kala kala, amman sai idan mutum yana yin sallah, kin ga ina son ki ba zan so ki shiga wuta ba" "Eh ba zan shiga ba wuta ba, Momy ce zata shiga wuta ita ce bata sallah, kuma ita ce kafira" Aliyu yayi murmushi mai sauti. "Toh a duk lokacin da kika yi sallah ki rika rokon Allah yasa Momy ta dawo hanyar musulunci, ai ba zaki so a kone ta ba ko?" "Eh amman wata rana ina son a kone ta sai a cireta" "Aa babu kyau Momyki tana sonki ita ma ba zata so ki kone a wuta ba, duk wanda kake so ba zaka so ya shiga wuta ba" "Sai wanda baka so? Toh Vito ina son ya kone a wuta yayi baki ya soyu" Nan ma Aliyu dariya yayi "Aa shi ma ki masa addu'a Allah ya shirya shi ya dawo musulunci" Ta lake kafada ta turo baki gaba. "No bana son shi ba zan yi ba" "Zan rika biyanki idan kina musu addu'a" "Noooooo bana son shi i hate him ni bana son shi" "Da alama kina da kafiya Fatima ki daina ba shi da kyau kinji don't be a stubborn girl" Ta makale kafada ta juya masa, murmushi kawai yayi ya daga wayarsa ya kira number Emily sai ya ji ta a rufe hakan ya dan kara masa damuwa. "Fatima da kuka fito Vito na cikin gidan?" "Aa Chidimma ce kawai" Ya sake gwada kiran still switch off. A take hankalinsa ya tashi, gashi tace kar ya zo har sai ta kira be san me zai yi ba a yanzu kuma be san a wane hali take ciki ba. Sai da ya fara tuka motar yayi nisa yana ta sake sake kamin ya kama hanyar gidan Tasmia ya faka harabar sannan ya fita ya taka zuwa kofar shiga gurinta ya kwankwasa, shiru ya sake knocking nan ma shiru, wayarsa ya ciro ya shiga WhatsApp ya lalubo chat dinsa da Tasmia ya duba number ta yayi coping ya saka a dial ya kirata, ringing uku ta yi kamin ta yi na hudu ta yi picking. "Hello" Sai yayi mata sallama kamar yadda ya saba yi na kowa, ta amsa masa ta gaishe shi, bayan ya amsa ya dora mata da dalilin kiransa. "Am... Alfarma nake nema" Ta yi jimmmmm kamin ta amsa. "Fadi komai kake so Aliyu, ai ban kai matsayin da zaka nemi alfarma ba, sai dai ka yi min umarni, kuma dole na na bi ko da kuwa wuta ka ce na fada" Ta fada with excitement. "Interesting... Okay.. Anyway na zo gidanki ban same ki ba" "Allah yasa ba laifi aka ce na yi ba ba" "No ina son kije gidan Emily ne ki duba min ita, ina tare da Fatima a yanzu, bana son na je gidan har sai na yi magana da ita, kuma jikina yana ba ni ba lafiya ba" A take yanayin muryarta ya sauya saukin kiran da take ya ragu. "Ni fa bana son jefa kai a matsala, kana son shiga sha'anin Emily Aliyu kamar ka manta waye kai, musulmi kuma mai iyal..." Bata karasa ba ya yake wayar ya koma motarsa sai ga kiranta ya biyo, when he pick ya fada mata. "Kar kiran da na yi miki ya baki damar fada min magana, kuma idan kika dame ni zan bata miki rai ne" "Ka yi hakuri, ina camp ne zaka iya zuwa ka dauke ni, sai mu je na dubata" "Ba kai ki zan yi ba, ke zaki je ki dubata, duk abun da ake ciki sai ki fada min" Yana kaiwa nan ya kashe kansa wayar. "Matarka ce? Daman kana da mata?" Fatima ta tambaya tana shan ice cream. "Aa ba matata ba ce" "Toh kana son mata" Ya kalleta kawai yayi murmushi. "Kana son Momyna?" Ya sake yin murmushi. "Fatima zan tafi dake gidana na zauna a can mu huta kamin Momynki ta kira sai na maida ke" "Tohm" Taja motar suka kama hanya, tana ta masa surutu har suka isa gidan, a lokacin da ta fito motar ta kalli gidan ta ga babba ne sai ta ce. "Da zaka yarda sai mu dawo nan gidan tare da Momy da Chidimma, mu bar gidan Vito, ba za mu maka barna ba" Shi dai be ce mata komai ba ya bude motar ya dauko wasu daga cikin kayan da suka siyo ya wuce cikin gidan tana biye shi tana ta masa surutunta da fluent English dinta pure one domin bata iya hausa ba, duk wata magana da ake da ita da halshen turanci ne, hausa kadan ta iya saboda Emily bata damu ta koya mata ba, kuma bata taso a gurin da ake hausar sosai ba, ba kamar Emily ba. TASMIA POV. Da tufafinta na bautar kasa ta tafi gidan Emily fuskarta sanye da mask, bakin gate din aka ajeta, ta sallami mai okada sannan ta buga gate din mai gadin ya leko, sai ta masa karyar Emily ce ta kira ta da kanta tace tana son ganinta. "Idan ka shiga ka fada mata Tasmia tana waje" Mai gadin ya kira wayar Emily ga ji ta a kashe, sai ya shiga ciki ya kwankwansa Chidimma ta bude ya tambaya ko Emily ta san da zuwan wata kawarta, sai ta amsa masa da eh alhali bata da tabbaci. Mai gadin ya koma ya budewa Tasmia ta shigo, da yaren turanci ta tambaye Emily Chidimma ta nuna mata upstairs, har ta nufi saman sai kuma ta juyo ta saka tambayar Chidimma ko Vito yana nan Chidimma tace mata baya gidan sai ta haura sama da sauri jikinta na rawa, na dan tana son faranta ran Aliyu ba da kuma yi ma kanta yaki, da babu abin da zai saka ta risking rayuwarta a gidan Emily, kiranta kawai da Aliyu yayi a karan kansa ya faranta mata rai balle kuma har ya nemi alfarma a gurinta, a ganinta hakan ma wani matakin nasara ne, domin da sannu bako ke zama dan gida. Tsabar rikicewa ma dakin Fatima ta fara shiga, ta fito da sauri ta tura dayar kofar ta leka sannan ta shiga. Sautin kukan Emily ta fara ji kamin ta hango ta kwance a kasa, ta karasa da sauri. "Lafiya me ya same ki?" Ganin Tasmia ya saka Emily ta dan ji sanyi sanyi har ta dago ta jingina jikin Tasmia tana duka tana fada mata Vito ne ya duke ta. Tasmia ta kalli kofa sannan ta rage murya. "Me kika masa?" Emily ta kasa magana sai kuka take. Tasmia ta kalli yadda fuskarta ta yi ja wani gefen ya kumbura ga kuma shatin belt a saman kafadunta, kana gani ka san dukanta aka yi, kuma ko bata fada mata ba, ta sani ba zai wuce ace saboda Aliyu ba, shiyasa shi ma ya damu ya san halin da take ciki. "Wata kila ya gaji da halinki ne Emily ta ina zaki zauna kina wahalar da shi, bayan duk hallacin da yayi min? Ko da yake ban san me ya faru ba, amman kina cin amanar mutumen nan, yana sonki kin kasa fahimta" Emily ta takaita kukan da take ta share hawayenta. "Ya aka yi kika samu shigowa nan?" "Karya na yi ma mai gadi cewar kin san da zuwa, na ce ya zo ya tambaye ki sai yace na shigo kin san da zuwa" "Be shigo nan ba, ban yi magana da shi ba" Mamaki ya cika fuskar Tasmia. "Toh taya ya bar ni na shigo, ni daman dai na zo ne kawai na duba ki" Emily ta yi shiru alamar tunanin sannan tace. "Tashi ki tafi kar Vito ya tarar da ke a nan, ransa a bace yake" Emily na rufe baki Tasmia ta zabura tsaye ko sau anjima bata cewa Emily ba ta fice gidan fuuuu kamar walkiya. Hankali be kwanta ba sai da ta isa gida, sai kuwa aka yi a daidai tana shiga gidan kiran Aliyu na shigowa wayarta domin hankalinsa ya tafi gurin son sanin halin da Emily take ciki. "Hello" Ta amsa da far'arta kamar gaske. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam" Ta yi shiru tana jiran sai ya tambaye ta. "Lafiya take?" "Lafiya Kalau take na same ta ma girki take yi" "Vito na gidan ko da kika je?" "A A Baya gidan mai aikinta ce kawai shiyasa ban tsaya komai na ina ganin lafiyarta sai na fito, kar ya zo ya tarar da ni a samu matsala, ba dan kai ba a yanzu da babu abun da zai kai ni gidan Emily ko dan gudun fitina" "Me yasa wayarta take a kashe" "Toh ban sani ba, wata kila tana gudun a kira ne yana nan, amman lafiyarta kalau na same ta ma ta sha ado abunta" Idan be ce mata thank you ba ai be kyauta ba ko ba komai ta cancanci godiya domin hankalinsa zai kwnata a yanzu sanin cewar Emily na cikin aminci. "Na gode" "Always Aliyu, ka aje duk wani tunani da kake, ka dauke ni a matsayin kanwarka, bayan shi babu wani ba" Ba tare da ya sake furta komai ba ya kashe wayar. [6/20, 7:25 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3️⃣7️⃣ ALIYU POV. Ya dan ji wani iri shi dai aganinsa babu abun burgewa namiji ya tare da matar da a daura musu aure ba a gida daya da sunan budurwarsa ko wadda zai aura, hakan sai ya saka ya ji addinin musulunci ya kara burge shi domin addinin Musulunci be yarda da wannan ba, a ta dayan bangaren kuma yana tambayar kansa anyaba shi da zunubi na aje mata ya a nan a can kuma ya bata damar shakatawa da yi yadda take so da mutumen da ba muharraminta ba? Ya kalli Fatima dake ta ciye ciyen kayan dadinta hankali kwance. "Fatima mu tafi gida haka nan?" A take ta bata fuska. "No bana so mu tafi yanzu" Ya mike tsaye ya nufi Kitchen, ruwa ya dauko ya sha ya dawo falon ya zauna. "Kai ma baka da kowa kamar Momy na?" Ya dubeta. "Waya ce miki bata da kowa?" "Bata da kowa sai ni kadai" "Sai Vito" Ta girgiza masa kai. "Aa i hate him" "Why do you hate him? Me kake miki ne?" "Baya dariya, kuma yana da fada yana duka, kuma ba ya bari kowa ya zo gurinmu" "Toh mamanki tana da ni yanzu" "Yeehhhhhh" Sai yayi murmushi ya shafa kanta, sai ya ji duk ta burge shi. "Mun zama mu uku ko?" "Yes, zaka zama Babana? Ni kadai ce ba ni da Baba a duniyar nan kowa yana da Baba amman kace zaka maida sunana Fatima Aliyu amman baka yi ba, har yanxu ana kirana Fatima Aisha Emily...." "Ke ma kina da mahaifi Fatima, kuma na san da zai ganki zai kaunace ki sosai zaki ji dadi, da ace mahaifiyarki zata aje abun da ke zuciyarta ta dubi maslaharki da kin yi farinciki sosai, kina da uba sunanshi Turhan"  Ta dafa shi, hakan ya farfado da shi daga guntun tunanin da yake. "Ka ji" Ya lumshe ya bude sannan ya daga taya matsa da ita saman jikinsa ya rumgume ta, ba dan ya ji abun da take tambayarsa ba sai dan tausayinta da ya kama shi. Kiran Emily be shigo wayarsa ba sai kusan Isha'i a lokacin da yayi alwala yana warwarar hannun rigarsa Fatima ta shigo masa da wayar da ya bari a falo, har dakin da yake ta mika masa. Ya karba ya kara a kunne, for the first time sai ya ji nauyi fara yi mata sallama. "Salam alaikum" Ta masa sallamar sai yayi murmushi ba tare da ya amsa ba ya ce. "Yau dai kina da nuna min hallayarki na kwarai ashe kin iya sallama" "Na iya mana, ni da na zauna da musulmai kuma Hausawa" "Kina lafiya Emily?" Ya tambaya, sai ta lumshe ido hawaye na sauko mata, ta girgiza kai kamar yana gabanta tana jin kamar ta fada masa ba lafiya ba, amman tana gudun abun da zai je ya dawo. "Anyways na kira wayarki a kashe, saboda hankali na be kwanta ba da yanayin da na barki, kuma da na ji wayar kashe na damu sai na saka Tasmia ta bincika min ke" Da ya kai iya nan sai ya yanke maganar saboda yana son ya gano idan Tasmia gaskiya ta fada masa ko akasin haka. Emily ta hade kukanta ba tare data bude ido ba ta ce. "Me tace maka?" "Me kika ce tace min?" "Ban fada mata komai ba, bata ma min maganarka ba" "Okay, ta fada min ta same ki kin yi ado kina yi ma Vito girki, nace toh ina nan na damu ita kuma tana can tana girki ma wanda ba mijinta ba, Allah yasa dai kar na samu zunubi" Ta cige baki hawaye na sauko mata kana ta bude ta sauke numfashi a hankali. "Ado tun wanda ka tarar na yi ne, ban sake wani ado ba, ina Fatima tana tare da kai" Ya kalli Fatima dake cin apple. "Yeah, amman Aisha na tambaye ki mana" "Uhmmm, ku haka addininku ya yardar ku zauna da mutane musamman namiji kuna tarayya ko daba muharraminku ba ne...? Mu a gurinmu hakan ba abu ne mai kyau ba" "Ban taba tarayya da Vito ba, wani abu be taba shiga tsakaninmu ba, a tsawon zaman da muka yi, yana jiran sai na aminta da soyayyarsa ne, ni kuma zuciyarta ta kasa fahimtarsa, wannan abun yana wahalar da rayuwata yana jefani a matsala, ni ban taba mu'amala da kowa ba sai Khaleepa da Turhan, shi ma Turhan ya fada min kan kuskure ne, kuma bakar rana ta biyu a gurinsa bayan ranar da aka daura mana aure, yana daga cikin dalilin da ya saka nake son gina rayuwata ni kadai ina son na zama mai ikon kaina" Jin cewar bata taba zina ba ya burge shi, haka kuma jin cewa Turhan ya kira ranar da ya aure da bakar rana a gurinsa ya saka shi kara dora ayar tambaya akan zamantakewar aurensu. "Fahimta, I'm sorry for misunderstanding you" "Dan Allah ka bar Fatima ta kwana a gurinka, gobe sai a kawota" "Okay" Ta bukataci hakan ne gudun kar ya zo kawo Fatima ya hadu da Vito ko kuma ya ga dukan da Vito yayi mata yace zai dauki mataki ya jefa kansa a matsala. Falo Fatima ta koma tana kallo, shi kuma ya tsaya a dakin yayi sallah, be dago daga sujudarsa ta karshe ba sai da yayi ma Emily addu'a, bayan ya gama ya sauko falon ya umarce tayi alwala ta yi sallah, ba musu ta tashi zuwa jnda ta yi alwalar magariba ta yi ta dawo falon ta dauki hijab din Kameela daya dauko mata a dazun ta saka ta fara sallah, shi kuma ya shiga Kitchen ya fara gyara tattasai da attarugu da albarba ya kunna gas ya dora nama akai, ya fara yanka vegetables, sai ga Fatima ta shigo Kitchen tana tambayar me yake yi. "Jallof zan girka kina ci?" "Ka iya girki?" "Sosai ma" Ita ta yi ta taya shi hira yana girkin, duk abun da ya zuba sai ya daga ta ta gani da ya gaji sai ya goyata a bayansa ta leko kanta ta saman wuyansa tana kallon yadda yake girki, idan yayi abun da bata saba gani ba sai tace masa ba a haka ake yi ba, shi dai dariya kawai yake ya cigaba, da ya gama hada komai sai ya koma tare da ita falon suka zauna sai da ya nuna sannan ya koma ya zubo musu a plate daya shi da ita. "Kai kadai zaka ci?" "Aa ni da ke" "A plate daya" "eh ko baki cin abinci a plate daya da wani?" Ta yi dariyar jindadi "A gida raba mana ake kowa plate dinsa dabam, amman ina so" Ya zauna ya sake komawa ya dauko ruwa da lemu, sannan yace ta zo su ci, madadin ta zauna a gefensa ko gabansa sai ta tsallake abinci ta zauna a kan ciyarsa, yana ganin haka sai ya aje Spoon daya ya dauki dayan yana ciyar da ita da shi shi ma sai ya ci, ko loma nawa yayi sai ta kirga tun be hankara ba har ya fara dariya, ita da shi suka ci abinci cikin nishadi, har wayarsa ya dauko yayi mata hoto yayi mata video, kusan a lokacin ne ya ji yana matukar kaunar samun nasa yaran, Fatima kuma ta yi enjoying moment din tana jinsa kamar mahaifinta. Bayan sun gama ya bude quran app din wayarsa ya tana karanta dan abun da ta iya yana mata gyara, har bachi ya dauke ta, daukar ta yayi ya haura da ita sama ya kwantar da ita kan gadonsa ya lullubeta ya zauna gafen gadon ya karanta mata addu'a ya tofa mata sai ta bude ido ta kalleshi. "Meyasa kake watsa min yawu" "Addu'a ce ta tsari idan aka karanta ma yara ko suka karanta babu abun da zai same su har safe, Momy ki bata miki idan zaki kwanga bachi?" "Aa" "Toh ki koya ki rika yi ma kanki kin ji?" Ta taso daga kwance da take ta rumgume shi. "Da nan nake zaune tare da momy da mun rika jindadi, kowa yana son ace yana da ba Baba, momy ta maka girma amman zamu iya zama yayanka mu duka biyu" Yayi murmushi ya shafa bayanta a haka ta sake yin bachi sai ya kwantar da ita ya fito falon, ya dauki wayarsa ya kira Mama Baraka, sai dai bata daga kiran nasa ba har ya yanke, aje wayar yayi a tunaninsa ta yi bachi domin tara da rabi har ta gota, yana dauke hannunsa daga mazaunin wayar sai ga kiranta ya biyo baya, sai ya sake dauka ya amsa, tare da sallama ta amsa masa suka gaisa sannan ta tambaye shi. "Aliyu me yake faruwa tsakaninka da matarka?" "Mama Me ta fada muku" "Bata fada mana komai ba, an yi anyi da ita ta ki ta yi magana ba, sai kuka da damuwa abinci ma bata iya ci, gaba daya ta fita hayyacinta" Yayi shiru na dan lokaci tare da tunanin alfanu da kuma rashin sa da zai haifar idan har ya fadi dalilin da ya saka ya turata gida, ba dan Ummynsa ba da babu abun da zai hana ya fadawa kowa abun da ta yi masa ko dan ta shiga taitaiyinta ta hankalta. "Babu komai Mama" "Aa mu fa iyayene, babu komai zaka turo ta gida ko sakinta ka yi?" "Aa" "Toh me ke faruwa tsakaninku? Aliyu ita rayuwar aure sai da hakuri na san ka yi ne, amman ka kara, na san idan ba kai ba ne ba zaka iya zama da Kameela ba, sai dai bana son kana duba sherinta ka rika duba alherinta ko dan ku bawa marasa da kunya, kaga yanzu dawowar da ta yi nan iyayen sun nuna babu ruwansu da ita yan'uwa kuma sai dariya suke mata, dan Allah ina rokon alfarma Aliyu ba dan na isa ba, sai dan na san ka da biyayya da kawar da ido da kuma hakuri da tunani, dan Allah ka yi hakuri ka zo ko kuma ka aiko daukar maka matarka ka bata hakuri ka bawa iyayenta, ku shirya tsakaninku" Ya sauke ajiyar zuciya. "Shikenan zan yi tunani Mama" "Aa ba tunani nake son ka yi ba, idan ka tsaya tunani ai sai shedan ya samu damar baka wata gugurwar shawara, domin shi kullum burinsa ya lalata rayuwar aure, dan Allah ya shirya cikin weekend din nan ka zo ka dauki matarka, gobe friday zuwa assabar ko lahadi sai ka shigo ka koma, ka turo min number Mahaifiyarka na kira ita ma na bata hakuri" "Aa ba sai kin kira ba, bata ma san abun da ya faru tsakaninmu ba" "Tohm ai haka ake so, ana son ma'aurata su zama masu sirri, Allah ya hada kanku ya baka hakuri da wuyan dauka, kuma maganar nan ta tsaya daga ni sai kai dan Allah, domin Kameela da iyayenta ba su san na kira ba, ni ce kawai na damu da halin data shiga shiyasa na kiraka mu yi magana, number ka ma a boye nasa yara suka dauko min, ba tare da sanin Kameela ko iyayenta ba" "Na gode Mama" "Toh Allah ya maka albarka, kuma ka kara hakuri domin matarka tana kaunarka sosai" "In Shaa Allahu" "Na gode" Ya sauke wayar, ya amsa mata ne kawai saboda yana jin nauyin ce mata aa ba zai iya ba, haka kuma yana tsoron matsalar da fadin gaskiyar abun da Kameela ta yi masa zai janyo, ita yake tausayi ba kansa ba, domin ya san tana son shi, kuma ya san irin gwagwarmayar da suka sha kamin aure, kana ya san idan har aka ji abun da ta yi abu ne mai wahala wani namiji ya sake aurenta, shi kansa ya san auren Kameela jarabawa ne a gurinsa ba dan baya kaunarta ba sai dan zafin kishinta da kuma halin da take kokarin jefashi kuma ta jefa kanta. EMILY POV. Bata farka ba sai karfe takwas na safe, saboda tunani da kuma dukan da Vito yayi mata be barta ta sami bachi da wuri ba, daker ta iya saukowa daga kan gado saboda tsamin da jikinta yayi ko'ina ciwo yake mata. Bathroom ta fara shiga ta wanke bakinta ta yi wanka da ruwa mai zafi sosai saboda ta gasa jikin sannan ta fito daure da tawul, rass gabanta ya yanke ya fadi ganin Vito tsaye a dakin yana jiran fitowarta. Tsayawa ta yi cak a jikin kofar bata karasa fita ba kuma bata koma ciki ba sai kallonsa take. "Good Morning" Ya tako zuwa inda take sai ta yi baya baya zata koma ciki, ta bata fuska sosai alamar zata yi kuka. "Tsorona kike ji? I'm so sorry i didn't mean to hurt you ke kika janyo, jiya ban yi bachi ba saboda tunanin abun da na yi miki" Ya karasa ya rikota ya fito da ita sai ya rumgume ta a kirjinsa. "I'm sorry" Sun dade a haka kamin ta dago daga jikinsa ta nufi kujera ta zauna. "Jikinki da zafi zan kira Likita ya zo ya duba ki" "Bana bukata" "I'm sorry Emily am sorry" Ya karasa kusa da ita sai ya zauna a kasa ya kama hannunta ya rike. "I'm really sorry, zuciya ce ta rufe ni" "Wannan ba shi ne karon farko ba" "Na sani, kuma ba zai zama karon karshe ba matukar baki daina kula wasu mazan ba, kuma baki cire ranki akan addinin nan ba" Ta fisge hannunta daga rikon da yayi mata ta mika tsaye, short gown ta dauko ta saka ta daure kanta da ribbon tana kokarin juyowa ta ji shi bayanta tsaye. "I'm sorry Emily I'm sorry, i didn't mean to hurt you" Ya juyo da ita yana kallon fuskarta dake zubar da hawaye. "But you already hurt me, baka da banbanci da Khaleefa shi ma dukana yake, Turhan ma ya dukene, kowanenku yana juyani ne son ransa, idan kuka gaji da ni sai ku watsar, ina ta fadawa hannun mutanenda babu komai a gabansu sai son zuciya, na tabbatar da ace ni kanwarka ce, ba zaka yarda wani yayi mata wannan dukan ba, jiya ban iya bachi da wuri ba saboda radadin dukan da ka yi min, takamarka kawai saboda ina karkashinka ne, saboda kana ganin ba ni da kowa, da ace ina da gata ba zaka min wannan dukan ba Vito" Ta wuce shi ta fice daga dakin, zaunawa yayi a kujerar data tashi dazun ya dafe kansa, babu abun da ya tsana kamar ganin hawayen Emily, a yau da ace wani ne yayi mata abun da yayi ba zai kwana duniya ba, but still yana jin babu dadi meyasa ba shi da hakuri why yake da saurin hannu? Yana son Emily yana mutuwar sonta yana kishinta wannan ne abun ne ya ci shi da yaki ya gagara fin karfin zuciyarsa har gobe... Tana fita dakin ta nufi downstairs, sai kuma ta fasa sauka ta dawo saman ta nufi dakin London ta shiga, saboda tana bukatar gurin da zata kebe ta tausayawa kanta. Sai dai kuma shiga dakin ya dawo mata da tunanin danta da kewarsa, dakin yana nan yadda ya bar shi babu abun da aka cire ko aka sauya, sai datti da yayi domin Chidimma ta daina share dakin. Kwalliyar dakin ta fara kallo sannan ta sauke idonta gurin hotonsa ta karasa gurin gadon ta zauna a kasa ta dora kanta akan gadon tana hawaye. Can kuma ta dago tana kallon study table dinsa dake gefe daya, ta tashi ta koma kan teburin ta zauna saman kujera tana duba takardun da yake zane da su da rubutu, wani gurin ya zana ta ya zana kansa da Vito da Fatima da Chidimma ya rubuta sunan kowa, ta kai hannu tana shafa zanen, ta bude wasu takardu ta dauko tana dubawa, wani gurin ya rubuta, na yi fushi wani gurin ya rubuta i hate Momy, wani gurin ya rubuta I'm sick har ta kai gurin da ya rubuta. "Chidimma tace Momy bata so na, bata so na bata so na bata so na, tana son Fatima Fatima bata son London, Chidimma tace Momy bata son London, Momy bata son London Momy ta tsani London" Tana karantawa hawaye na sauko mata kamar ruwa, ta girgiza kai da sauri. "Ina son ka dana, ka fi soyuwa a raina fiye da Fatima, baka fahimce ni ba ne" Ta kwala wani uban ihu cikin kuka, ta mike tsaye da fito dakin da gudu kamin ta sauka kasa Vito ya fito dakinta ya biyo bayanta Chidimma dake mopping ma ta tsaya tana kallon Emily dake saukowa tana kuka rike da takardun. "Meyasa kika saka dana ya tsane ne? Me na miki? Me yasa kika tsane ni? Me na miki? Kin sa ɗana ya mutu da tunanin bana son shi, baki kalli lalurar da take tare da shi me yasa kika cusa wannan a kwakwalwarshi? Yanzu ta ina zan fada masa ina kaunarsa? Ta ina zan nuna masa kaunar da nake masa? Why Chidimma why? Shiyasa ya daina son na rabe shi na baya yarda da ni sai ke? Why Chidimma why?" Kalaman Emily ba su daga mata hankali ba kamar kallon da Vito yake mata. " Ki amsa me yasa kika yi?" Ta girgiza kai jikinta na rawa numfashinta na gargada. "Ba haka ba ne, wata kila be fahimta ba shiyasa yake rubuta wannan, amman ban fada masa cewar baki kaunarsa ba, ba gaskiya ba ne" "Meyasa Matata tsone miki ido? Na sha fada miki ki daina fada min idan Emily ta yi wani abu, kamar jiya, ke kika fada min ta shirya ta shirya Fatima cikin abaya sun fita, kika sa na zo na mata duka da ya tsaya min a rai yanzu yana ci na, kuma na gargade ki ba tun yau ba akan ki cire idonki akan Emily, the more kika fada min laifinta the more zan tsane ki, me yasa kika shiga tsakaninta da London why? Answer me....!!!“ Da farko cikin natsuwa ya fara magana da mugun kallo, daga karshe kuma ya karasa da tsawar da ta saka Chidimma sakin fitsari... Hmmmmmm, masu karatu wai ba ku ganin Aliyu yana wuce gona da iri ne? Ina Team Vito? Ni fa iya wuya muna tare🥰🥺 wanda ya so ka taimaka a lokacin da baka da komai ai shi ne naka. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [6/22, 6:33 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3️⃣8️⃣ Cikin karfi hali da kashe murya ta fara magana tana kuka. "Shekara cikin ta shida nake a gidan nan, idan ina nufin cutar da Emily ko yaranta zan yi tun kamin a kawo yanzu, a janye maganar London tun da shi ba shi da lafiya, amman Fatima tana da wayo tana da fitina, da a ce ina musu wani abun cutarwa da yanzu ta fada, ko kuma ta ki ni, bata kila London be fahimce ni ba ne, shiyasa ya rubuta abun da ya rubuta, amman ni miye ribata idan na rabaki da dank? Idan baki gode min a tsawon shekarun nan ba, toh be kamata ki tuhume ni da wani abun ba" Ta juya gurin Vito. "Ka gafarce ni, ina saka kaina aikin da ba nawa ba, amman ni ina tayaka yaki ne kawai, tun da ka kawo ni a gidan matsayin yar aiki, ma lura kuma duk wanda ya kalli yadda kake nunawa Emily gata ya san kana sonta, hakan yana min dadi, ina sha'awar mace ta samu kulawa a gurin wanda take so kamar uba ko miji ko dan'uwa, domin ni nawa uban be dauke ni a matsayin ya ba, na kan fada maka Emily ta kula wani ne saboda taya ka yakin da baka san ranar cin nasararsa ba, na kan zauna na yi tunani yadda ka yi ma Emily gata ita da yaranta ka nuna mata so da kauna fiye da kowa a duniyar nan, amman ko na rana daya bata taba duba wannan ba, har takan bawa wasu mazan damarda za su iya sonta, bayan kuma kai ka cancanci zama a zuciyarta, na kan fada maka ne saboda ayi ma tukkar hanci, amman son da kake yi ma Emily ya hanaka fahimtata, a yanzu kuma kuna zargina da abun da ban aikata ba, kar idonka ya rufe, ka tsaya ka yi tunani gudun yanke hukunci a ciki fushi domin komai daren dadewa sai ka fahimci dalili kuma ka yi nadamar abun da zaka yi min a yanzu, London ba shi da lafiya ba mamaki lokacin da ya rubuta hakan ba a cikin hayyacinsw yake ba" Duk wani yanayi da muryar da Chidimma ta san zata iya amfani da ita ta siye zuciyar Vito daga yi mata hukunci a cikin fushi sai da ta yi, kuma ta yi nasara domin kuzarinsa na son yanke mata hukunci mai tsauri ya karaya, maganganunta suka shige shi. Emily ta turata ta karfi. "Are you saying all this saboda kina son Vito? Ko kuma saboda ki kawar da laifin da kika aikata?" "Ban aikata ba, idan ma na aikata har kake kokarin kawar da laifin shim bancanci ki taya ni ba? Tsawon shekara biyar da na yi ina kula da yaranki ban cancanci godiya ba? Ko kuma dai ke haka halinki yake? Butulu ce ke? Shiyasa shi kansa Oga Vito kika duba halaccinsa ki kaunace shi ko da na kwana daya ne? Ya so ki kamar zai mutu, ya so yayanki kamar nasa, ko matar governor ba zata nuna miki gata ba, amman duk baki gani ba, ni kuma na bauta miki babu dare ba rana, ni nake kula da yaranki, ni nake girka musu abinci na gyara gidan, na karanta musu storybook ko wane dare, idan ba su da Lafiya ni da ke muke jinyarsu, ki kaddara ma na aikata abun da London ya rubuta shin ban cancanci yafiya ba?" Cikin daga muryar da ya fi kama da tsawa take maganar tana nuna kanta sai kuka take sosai. Emily ta kai hannu zata mareta Vito yayi karaf ya rike, Emily ta kalleshi da sauri tana mamaki. "She's right, shekara biyar ba kwana biyar ba ne, ta bauta miki, ni kuma na so ki fiye da komai da kowa a duniyar nan, ita baki gode mata ba, ni kuma baki ba ni abun da nake so ba, akanki na kusa haukacewa, akanki bana ji bana gani na kyautata miki iyakar kyautatawa, na baki gatan da babu wanda ya taba baki, a tsawon lokacin nan bana son bacin ranki, ban taba cilasta miki kwanciya guri daya dake ba jira nake har sai kin amince da kanki, fada min bayan ni ba zai iya miki? Babu mahaifiyata bata fada min ba akanki amman ban saurareta ba, babu iya cin fuskar da yarki Lisa bata min amman na daure saboda ina sonki, na kashe kudi mai yawa akan maganin danki, Emily ni na inganta rayuwar ki kika zama abun da kika zama a yau, a haka duk ban cancanci tukuicin so ba? Amman a kwana daya ko biyu kin hadu da wani a gurin aikinki kin soma ba shi fuska da kofar da zai so ki" "You take her site?" "Yes saboda gaskiya ta fada, abu ne da ya kamata na gane tuntuni, shiyasa yanzu kika tsane ta ai, kike son a kareta what if you make all of this?" Ya fisge takardar hannunta ya yaga. "Enough is Enough Emily, I'm tired, kuma a yanzu na gane duk abun da ya faru da ke, kin cancanci haka, domin ke ma butulu ce, kin butulcewa addininki, kin butulcewa mutanen da suka dauki a matsayin ƴa suka yi nufin baki gata, shiyasa ke ma kika hadu da tasgon rayuwa, yanzu kuma kina son butulce min bayan duk abun da na yi miki" Kallonsa kawai Emily take hawaye na sauko mata. Chidimma ta zube kasan guiwoyinta ta hadu hannayenta. "Ranar yau ta kasance bakar rana a gurina, domin wannan ce rana ta farko da na ga tsakani tsakaninka da Emily, dan Allah ka gafarce ni bana nufin shiga tsakaninku, ni na aje aiki na bar aikin daga yau" Vito ya saka hannayensa ya dago ta tsaye. "Baki yi laifin komai ba, kuma ba zaki bar aiki ba, amman zan kaiki gidanku ki huta har sai ta gane muhimmamcinki" Yana fadar hakan ya kama hannun Chidimma ya nufi kofar fita falo, Emily na tsaye tana kallonsu har suka fice, sai ta lumshe ido tana jin wani abu mai nauyi yana mata yawo a cikin zuciya, duk abun da Vito yayi mata a yanzu, ko wanda zai mata a gaba ta cancanci haka ko fiye da hakan ma, domin ya sama mata komai ya mata gata amnan zuciyarta ta kasa bata hadin kai gurin mallaka masa abun da yake muradi, ta mari kanta ta sake marin kanta ta sake marin kanta har sau uku sannan ta bude ido hawaye na mata zuba ta hada takardar da VITO ya yaga ta kwashe ta juya ta fara haurawa stairs din idonta na rufewa saboda hawayen da take. Dakinta ta shiga ta kwanta kan gadon ta lumshe ido tana miada numfashi. Bata dago ba sai da wayarta ta yi kara alamar shigowar sako, sannan ta bude ido ta daga kan ta kai hannu ta dauko wayarta ta duba sakon da Aliyu ya turo mata. "Barka da safiya, fatar kina lafiya" Ta girgiza kai alamar no bata lafiya, amman bata iya amsa masa kuma ba zata iya fada ba. Ta koma ta kwanta tana aika masa da sako bayan ta yanke shawarar abun da take ganin kamar shi ya fi a gurinta, domin ganin take rayuwata bata da wani sauran amfani a yanzu, ita kanta ta gaji da shiga gararin rayuwa daga wannan sai wacan, idan Vito ya watsar da ita a gurin wa zata koma yanzu kuma? Bayan shi me sake faruwa da ita.. "Na san na hadu da kai akan kaddara like accident, amman zuciyata ta aminta da kai, idan har bayan rayuwa ta ji cewar Turhan zai iya kula da Fatima, kuma zaka rika dubata toh ka ba shi ita" Sakon na shiga wayarsa ya kirata sai ta ki ta daga, hakan ya saka shi aiko mata da sakon karta ya umarce ce data bude whatsapp dinta. Ta bude WhatsApp din ta shiga chat dinta da Aliyu hotunan Fatima ta fara cin karo da su, sai kuma short Video da yayi mata, gaba daya tana cikin farinciki ne da nishadi. "Emily kin yanke shawarar kashe kanki ne? Kin manta da farinciki Fatima? Wannan farinciki kike son ta rasa? Bayan kin san yadda rayuwa take da wahala ga mutunen da ba shi da uwa a kusa? Ashe ke na jaruma ba ce? Kin ce zaki canja ina canjin yake? Ashe ba zaki iya ba? Akwai abun da yake faruwa ne? Ki fada za mu iya maganin abun a tare, Amman dai ki sani Fatima ta yi kankanta da rasa mahaifiya, ya kamata ki girmama farincikinta fiye da naki" Shi ne rubutun da ya biyo bayan sakon. Sai kuma ga Voice din Fatima cikin murna. "Momy ina jindadin zama a nan, Momy ki bar ni na kara kwana, ke ma ki zo kin ji Momy hahaha" Ta shafa screen din wayar tana kallon Fatima da murmushin da ya fi kuka ciwo. Sannan ta rubuta masa amsa. "Bana nufin kashe kaina" "Akwai abun da ya faru ne? Ina son na ganki mu yi magana" Sanin kanta ne idan ya ga duka a jiki zai iya cewa zai shiga fada da Vito, a yadda Vito yake fusace a yanzu komai zai iya faruwa, dan haka ta haramtawa kanta ganinsa har ma ta bukaci kar ya kawo mata Fatima a yanzu sai nan da kwana biyu. "Aa ba yanzu ba, idan babu damuwa babu takura Fatima zata iya kara biyu a gurinka? Ka yi hakuri na saka ka ba tare da neman izini ba, ban san ko zai kawo rashin fahimta a tsakaninka da Matarka ba" "Aa, zata iya zama har na zuwa lokacin da kike so, amman ina jin kamar akwai abun da kike boye min shiyasa baki son na ganki ko?" "Babu, kawai ina son ta yi enjoying zama da kai, wannan farinciki data rasa na uba ta ji shi a tare da kai ko na kwana biyu ne" "Toh zan iya kiranki Video Call?" "Aa Vito yana yawan zama gidana a kwana biyun nan bana son na samu matsala da shi ko da kai, zan jidadi idan baka takura dole sai ka gan ni ba" "Okay na fahimta, zan jira har sai kin samu natsuwa sai na kawo miki Fatima, daga nan ki karasa min labarina" "Zan karasa maka labarinka ta nan, zan bar maka sako a duk lokacin da ka samu dama sai ka saurara" "Idan haka kika zaba ba ni da matsala" ALIYU POV. Ya bata amsa yana mai gamsuwa da cewar data yi Vito yana zama a gidanta, da farko kam yayi tunanin ko Vito ya mata wani abun ne shiyasa take ta boyo bata son ya ganta. Yana dagowa ya kalli Fatima sai ta bata fuska. "Ni ba yanzu zan koma gida ba" Yayi murmushi shi kan shi yana jindadin zama da ita. "Momy tace abarki ki kara kwana biyu" "Yeehhhhhhhh" Ta rumgume shi sai yayi dariya. "Zamu je da ke yau, na siya miki new clothes kina so ko?" "Eh" "Okay, gobe zan yi tafiya zan tafi Kaduna kuma zan tafi da ke, amman ba zamu fadawa Momy ba sai mun dawo, wannan sirrinmu ne kin yarda?" "Yes yes yes yes....." Ta shiga tsalle da murnar zai tafi da ita. Ya yanke shawarar tafiya da ita ne ganin zata yi kwana biyu a gurinsa albashi idan ya dawo sai ya fadawa Emily cewar ya tafi da ita, tafiyar ta kwana biyu ce idan ya isa Assabar da wuri zai tafi gidansu Kameela, idan kuma hakan be samu ba zai bari sai washe gari, on Monday sai ya dawo PH. Yadda ya fada haka ya aiwatar daga Office dinsa ya wuce da Fatima shipping ya siya mata tufafi da wasu abubuwan da ya san zata bukata, kamar Turaren yara shoe's da kuma ribbons. Fatima ta saka jin sha'awar kasancewa uba saboda yadda yake kula da ita a dan zaman da ta yi na kwana biyu shi yake gyara mata gashi da taimaka mata gurin wanke baki. Ta dayan bangaren kuma yana tausayin rayuwarta domin ya fahimci yadda take tsananin bukatar uba a kusa da ita, sannan ya fahimci sakacin mahaifiyarta na bar masa ita a hannunsa ba tare da damuwa da wani abun zai same ta ba, ko da yake Emily ta aminta da shi ne ya saka ta bar masa Fatima hannunsa, sai dai abun da yake ganin ya kamata ta damu da shi, shi ne Fatima mace ce kuma yarinya karama kyakkyawa sosai, zata iya haduwa da wanda zai iya lalata mata rayuwa, shi kanshi Vito ba dan hankalinsa be gurin ba, da tuni yayi mata aika aika sai dai ta koma kuka da bakinciki, ta dayan bangaren kuma yana ganin kamar saboda Fatima bata da uba ne, dawainiyar ta yi ma Emily yawa ita kadai, sai dai duk da haka wannan yana daga cikin abun da yake son tattaunawa da ita akansa idan ya dawo sun hadu. Abu ne da ya sani hatsari ne Sosai tafiya da Fatima ba tare da sanin mahaifiyarta ba, alkawari daya ya daukarwa kansa duk tsanani duk rintsi ba zai taba barin Turhan ya ga Fatima ba, kuma ba zai bari Fatima ta ganshi ba, dan haka zai yi iya kar kokarinsa duk yadda zai iya wajen kare afkuwar hakan. Business class ticket ya siya saboda ya samu yin walwala shi da Fatima, yana gama sallah ya shiga Kitchen ya hada musu light breakfast sannan ya tashi Fatima ta yi sallah ta yi wanka ya ci abinci ya dawo mata rigar da zata saka ya tsaya bayanta ya gyara mata kanta sannan ya fita dakin ya shiga dayan dakin ya shirya ya, ko da ya dawo ya samu ta saka rigar ya saka turare tana gyara masa kayan kwalliyar dake gaban Madubin. "Good Girl" Ya bata hannu suka taba tana dariya sannan ya fito da suitcase karami da babba ya aje direbansa ya dauka ya saka mota. Sai da Aliyu yayi addu'ar fita ya karantawa Fatima ya biya sannan suka fito, a lokacin da suka doshi motar da za su hau yana rike da hannu Fatima sai wata zuciyar ta raya masa ya kira Emily ya fada mata zai yi tafiya na kwana biyu kuma zai tafi da Fatima mana, zai fi zame masa kwanciyar hankali, sai kuma dayar ta hana shi ta hanyar nuna masa Emily ba zata yarda da shi ba, zata yi tunanin ko yana son kai Fatima ne gurin Turhan, shi kuma baya son maida Fatima a yanzu domin yana jindadin zama da ita, ita kanta tana son haka, bayan duk wannan ma ai Emily ce da kanta ta bukaci ya bar Fatima a gurinsa na kwana biyu. Haka dai ya shiga motar yana ta sake sake, can kuma sai ya ji gabansa ya fadi, ba tare da sake wani tunani ba ya ciro wayarsa ya kira Emily 3 missed calls bata daga ba, ya yanke shawarar fada mata idan ma tace bata aminta ba sai ya maida Fatima a gurinta ai ba laifi ba ne. Ta dayan bangaren ma yana jin kamar ba daidai ba ne ace ya tafi da Fatima a garin da Mahaifinta da kakarta suke ba tare da ya barta ta gansu ba. Da be samu magana da ita ta waya ba ya duba agogon hannunsa ya kalli time sai ya juya ya kalli Fatima. "Sweetheart zamu je mu fadawa Momy zan yi tafiya dake, idan ta aminta sai mu tafi, idan kuma tace aa sai na tafi ki ki zauna" A take Fatima ta lake kafada ta fashe da kuka. "Aa ina son na tafi, Momy ba zata bari ba, zan tafi nidai ina son tafiya please" Ta shiga yi masa magiya tana kuka. "Okay zamu tafi ba sai ta sani ba" Ya amsa mata ne kawai saboda ya samu ta yi shuru domin ta fara hargitsa motar da ihunta tana shure shure da kafafuwanta. WhatsApp dinsa ya shiga sai ya tarar Emily ta aje masa voice ne mai yawa and part part, ko be tambaya baya san ba zai wuce labarin da tace zata karasa masa ta nan ba. Sai da ya aje mata nasa sakon ta whatsapp ganin bata online ya saka shi aika mata the same sako ta layin karta kwana sannan ya sake kiranta still bata daga ba kuma bata maido masa da amsa ba. Dan lokacin da ya rage masa a airport din ya karasa shi har zuwa lokacin da suka fara shiga jirgi bata maido masa da amsa ba, suna shiga jirgin ya saka wayarsa Airplane mode. Sai da suka taba hira da Fatima dake dan jin tsoro a lokacin da jirgin ya tashi, ya bata wayarsa tana game sannan ya saka airpods ya yi connecting da wayarsa, ya shiga WhatsApp dinsa ya bude chat din Emily ya fara sauraren Voices din data turo masa..... _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [6/23, 9:05 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3️⃣9️⃣ ALIYU POV. Ya gyara zamansa da kyau sannan ya kunna Voice din ya fara saurare. *** *** *** Tun ana sauran sati daya Turhan ya zo garin Kaduna, mahaifiyarsa ta fara shirye shiryen tarbarsa, duk wani abun da ta san zata girka masa ta tanade shi da wuri, a tsawon satin daya kullum ni take sakawa na gyara masa dakinsa na saka turare. Ana gobe zai iso Ammy tasa na fara shirya masa abincin da ta san ko ya kwana ba zai lalace ba kamar snacks da nama, ranar da zai iso tasa na shirya masa full Medames miyar waken fava daya daga cikin abincin da mutanen sudan suke so sosai, ita ta koya min yadda zan hada har aka yi nasara na gama komai cikin sa'a, ragowar abinci kuma sai ta bukaci na girka miyar waina (masa) bayan na hada na bar miyar a wuta sai kuma ta bukaci na zo na toya Masar, haka dai na daure na karasa aikin, bayan na gama tasa na yanke masa fruit, na hada fruitsalad, kusan komai da Turhan zai ci ko ya sha ko ya taba Ammy ni ta saka na shirya, sannan ta bukaci na shiga ciki na yi wanka na shirya, tufafin da zan saka ma ita ta zaba min. Bayan na yi wanka ina tsaye gaban madubi ina daura lafayar da ya ki dauruwa a jiki Ammy ta shigo fuskarta dauke da murmushi tana kallo. "Maa Shaa Allah kin yi kyau sosai yata, shiyasana zaba miki wannan lafayar ai, nasan bakin abu zai miki kyau sosai, ki yi hakuri yau na saka ki aiki da yau, so nake Turhan ya ci abincin kuma ke ma ki saba da fara yi masa hidima tun yanzu" Ban ce komai ba, kuma ban ji farinciki ko kishiyarsa ba, ita da kanta ta taimaka min na daura lafayar sannan ta fice. Be shigo gidan ba sai da La'asar. Ina daki Ammy ta aiko a kira ni muka dugunzuma gaba dayan gidan har masu aiki zuwa tarbon da ɗaya a gurin Ammy. Sarauta da kudi wani abu ne mai matukar burgewa da daukar hankali, wa can lokacin kamin ranar ban taba ganin irin motar da aka kawo Turhan da ita ba, sai dai na ga tsabanin yadda Ammy ta fada min cewar mutanen kasar Sudan musamman a gidansu Jallabiya suke sakawa, dan haka na tsammaci ganin jallabiyar a jikinsa, sai dai ya zo akasin tunanina domin kananan kaya ne a jikin wando da riga, wani irin kamshi yake mai dadi. Kuma tabbas kyakkyawa ne a zahiri fiye da hoto ma, fari fes kamar dai kai yana da tsaye duk wata siffa da namiji zai cika aso shi ko ya burge Turhan ya cika wannan, Wallahi da na yi arba da shi sai na ji burgeni ba, wata kila saboda kyau ya daina rudata tun daga kan Khaleefa, ba ma akasin kuma ya zama dalili na banbanci al'ada da kalar halshe. Ya shigo da far'asarsa Ammy tana ta guɗa, kowa yana murna da zuwa ni ma sai na yi yake na yi masa sannu da zuwa kamar kowa, sai da ya fara shiga falon sannan kowa ya shiga ya zauna Ammy na watsa masa fulawa tana masa marhabun da zuwa, shi ma dai ba laifi yana da far'a da sakin fuska a farkon ganina da shi, amman yana da jin kai sosai a kallonsa kadai zaka iya fahimtar hakan. Bayan an gama murnar zuwansa na koma dakina shi ma ya shiga dakinsa yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin sannan yayi sallah, sai da kowa ya hallara falon sannan Ammy ta aiko a kira wai na sauko mu ci abinci, daman babu wanda ya ci komai duk shi muke jiran ya iso. Cikin rashin sakewa na sauko na zauna a dinning din na fara zuba nawa abinci ina sauraren yadda yake taba hira da hausarsa mai harshen larabci yana yi yana hadawa da larabci, sai yaba abincin yake. Tun da na zauna be kalli inda nake ba ni ma ban kalleshi ba, haka nan kawai babu dalili nake jin be yi min ba. Sai da yayi rabin plate sannan ya kalleni ya ce. "Ammy ina kuka samo wannan katuwar mace? Mai kama da orange cat" Na ji gabana ya fadi domin ya aybanta hallitatta tun gabanin ya san wacece ni. Ban ce komai ba na cigaba da cin abincina. Sai Ammy tace. "Kasan orange cat fa kyakkyawar mage ce kowa yana sonta, kuma orange cat din ita ta shirya maka komai da yake nan har kake santi, kuma ita ta gyara maka daki ta saka turare" Ya dan tabe baki yayi murmushi. "Yayi kyau" Daga haka be sake cewa komai ba, ni kuma ban sake kallo inda yake ba, ba karya ya fada ba na yi kiba da yawa na wuce kimar shekaruna, domin a lokacin ban kai shekara ashirin ba, amman kumburin da na yi na haihuwar London sai ya shige min a jiki ya zame min kiba, sai dai ban taba jin muzancin kibar ba sai a ranar da Turhan ya kira da big fat, kuma orange cat, a take na ji abincin ya fita raina gudun Ammy ta gane raina ya bace ya saka na yi karya. "Na ji kamar Ibrahim yana kuka bari na duba shi" Ina fadar hakan kan na mike tsaye kan kujera Turhan ya maido da abincin dake bakinsa a plate din dake gabansa. "Haba Ammy kin san tana da yara kika bari ta girka min abinci? Kin san bana son yara kyamarsu nake" Na kalleshi kawai ya dauke kai na nufi hanyar da zata sadani da stairs, kamin na shiga dakin na cika kaina fal da tambayoyi kala kala. Anya abun da Ammy take kokarin aikatawa mai yiyuwa ne kuwa, ni dai tun ganin farko be kwanta min a rana ba, da alama ni ma ban burge shi ba da va zai furta wannan kalamin a yanzu ba, baya ga haka kuma ya fadi cewar baya son yara kazantarsu yake gani, har yana kyamar abincin da na girka masa to ta iya zai iya zama da ni ma? Ko dai minene ni dai na yi alkawarin ba zan taba furtawa Ammy cewar bana son danta ko kuma ba zan amince da kudurinta ba, domin ta yi min hallaci a lokacin kuma idan na ki danta ina zan koma na zauna. Na yi tunanin Ammy zata duba dan abun da ya faru a tsakaninmu gurin cin abincin nan ta tsagaita wasu abubuwa amman babu abun da ta fasa, gaba daya idonta ya rufe saboda tana son danta yayi aure daga bangarenta ya samu nasa iyalin tana son danta ya dawo kusa da ita, bata duba halin da ni zan kasance ba. Tun daga wacan ranar ban sake shiga Kitchen ba ita take girka masa abun da zai ci ko ya sha, sai dai a kullum teburi daya muke zama gaban dayanmu mu ci abinci, na safe ko rana ko dare, idan ya riga ni zama na iso zai daure fuska ya daina dariyar da yake idan na gaishe shi ya amsa min kamar an masa dole. Idan kuma ni na fara zama baya sake fuska yayi hira da Ammy sai idan na bar gurin. Sai da ya kwana bakwai a gidan a gidan sannan ya shigo dakina, bayan Ammy ta shigo ta sanar min zata je dubiya marar lafiya ta dawo. Ina zaune ina yi ma London wasa yana dariya a cikin yanayinsa, kamin ya zabura ya kwalla ihu saboda shigowar da Turhan yayi yanayin bude kofar sai ya firgitashi a take ya saka kwallowa yana wani birkicewa ni kuwa na kama shi na rumgume ina rarrashinsa. "Me ya same shi?" "Shigowarka ce ta firgita shi" "Shigowa ta kuma? Dodo ne ni?" "Aa haka yake idan ya tsoro ta, komai a sannu ake masa saboda autism ne" Ya maida kofar ya rufe. "Kice mahaukaci kika haifa kenan?" Ita ce magana ta biyu da ya furta a gareni mai daci tun bayan zuwansa gidan, abun da ban sani ba ashe shi din gwanin cin fuska da bakar magana ne. "Aa ba mahaukaci ba ne, ba shi da lafiya ne dai" Ya zauna a nesa da ni jikin wata kujera dake kusa da kofar dakin. "Yana daya daga cikin dalilin da ya saka bana son yara, wannan hayaniyar da kazantar ni ba zan iya dauka ba" Yana maganar yana yatsina fuska kamar wanda yayi arba da wani abun kazanta, sai kuma ya bi dakin da kallo. "Ammy ta ba ni labarinki, ta fada min musulunta kika yi ko? Ke tubabbiya ce? Kuma na tausaya miki matuka, amman abun da ban gamsu da shi ba shi ne, miyasa mijinki be tashi wulakantaki ba sai da kika haihu?" "Wata kila ta manta bata fada maka ba, da cikin ya kore ni a hanya na haihu" "Yeah what i mean is, Allah yasa da gaske mijin ne ya koreni ba irin abun nan kika yi ba na yan matan zamani, kin san akwai wadanda kunyar haifar yaron ke saka su barin gari sai su tare a wani gurin su yi karya saboda su samu mafaka" Na yi shiru bance masa komai ba, zuciyata kuma bata fasa sosuwa da kalamansa ba. "Ke ruwa biyu ce? Ko kuma zabaya ce ke? (irin mutanen da ake haihuwa masu fari sosai)" Na fi kyautata zaton ruwa biyu ce ni, domin zabaya ba haka suke ba" "Eh na ga kuna da dan banbanci, maganar gaskiya ba wai na zo ne saboda na muzantaki ba, duk wani abu da zan fada miki gaskiya nake fada miki zahirinta, ban sani ba ko Ammy ta yi miki maganata?" Nan ma ban ce masa uffan ba. "Ke ba wata macen arziki ba sai shegen jinka, baki san waye ni ba? Ko kuma saboda Ammy ta kawo ki a nan gidan kika jin wata ce ke? Har ina tambayarki ki yi min shiru? Kina fama da jiki kamar uwar mata" "Wa can lokacin bana iya maida magana dan haka na danne zuciyata ina jin yana aybanta ni amman bana iya ce masa komai" "Ammy ta so ma yi min maganarki, duk da yake bata fito min a fili ba, amman na san karshen zagayen zai dawo akan ki ne" Ya ciro wayarsa yana tabawa. "Kamin ke Ammy ta hada ni da mata da yawa na fada mata ba su min ba, amman ke na ga alamar da gaske take, dan haka ina son idan ta tunkare ki da maganar ki fada mata na fi karfinki kina tsoron aurena, domin na fi karfinki din ina sa matata kyakkyawa marar jiki, ke kuma kin zama wata uwar mata mace mai kiba bata burge ni, kuma ni sarauta ne idan Ammy bata duba wannan ba ke ya kamata ki duba, kaskanci ne a gurina na auri wacce ba yar sarauta ba balle kuma tubabbiya macen da musulunta ta yi ba wai ta tashi a cikin addinin ba ne, and you're not my type, kuma ga ki da yaron da da Allah kadai ya san gaskiyarsa, and Aisha baki da dangi ba ki da kowa, ni kuma dan dangi ne jinin sarauta mai asali kuma musulmi gaba da baya, irinku sai dai kawai su zo mana a matsayin masu aiki ko kuma bayi, amman ba saɗaka ko matar aure ba, mahaifina ma ba zai aminta ba, ba zan iya tunkararsa da magana irin wannan ba, Ammy ma dai ta kasa ganewa ne shiyasa har take kokarin hada kifi da kaska" Na daga kai na kalleshi. "Dan haka ina son idan ta miki magana karki amince mata, kuma karki ce mata baki so na domin ta san karya ne wata mace ta kalleni tace bata so na, kawai dai ki fada mata na fi karfinki ba zaki iya cusa kanki a rigima ba, kuma kina da ɗa ke kin san ko haihuwa na yi da ke Allah ya kiyayye ba zan taba son abun da na haifa da ke ba balle kuma dan da kika zo da shi, na zo garin nan da niyar na yi wata biyu ko uku gurin Ammy amman saboda ke next week zan koma, i hate your face, idan aka cire Ammy ni bana ganin kimar ko wace mace bakar fata, iyakarmu da su su mana bauta mu ba su kudi" Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya fice daga dakin kofar dakin ma a bude ya bar min ita. Aiko a take hawaye suka ce min Emily yau ma dai zamu ziyarce ki, suka fara sauko min wasu na bin wasu babu tsayawa. Wai fa Turhan yana min haka ne saboda ina zaune a karkashin mahaifiyarsa, kowa yana juya ni ne saboda ina karkashinsa, da ace ina da gurin dazan raba Turhan ko dan Sarkin aljannu ne be isa ya fada min abun da ya fada min a yau ba. A ranar na daukarwa kaina alkawarin ba zan taba yafe musu abun da suka min na wufintar da ni, kuma na dauki alkawarin kasancewa da nawa Yaya a kowane irin hali. Daga ranar sai ya saka min tsoron sa bana ko son fitowa falon saboda kar na ganshi, domin gabana faduwa yake da zarar na ji kamshin turarensa balle kuma ace na yi arba da shi. Da aka kwana biyu Ammy ta ga haka daga gareni sai ta shigo dakina ta same ni tana lallabani wai kar na lalata mata shiri gashi ta fada masa abun da take buri kuma amince sai kuma ni na kirkiro wannan halin a yanzu. "Aisha ko dai baki son shi?" "Sai na kasa amsawa, amsawa bana son sa yana nufin fasa auren da take nufin hadawa amsawar bana son shi yana nufin butulcewa hallacin da ta yi min na tsawon shekaru biyu, yana nufin rusa burinta na son samun danta a kusa da ita, taya ya zan iya mata haka? Wannan dalilin ya saka na boye nawa kunci na so farincikinta fiye da nawa, abun da ban sani ba ashe ina dabawa kaina wuka ne a kahon zuciyata da kaina" "Ki kwantar da hankali, kar wani abu yasa ki fara tunanin Turhan zai zo miki kamar Khaleepa sam ba haka ba ne, yanzu haka na yi magana da shi ya nuna min tausayinki sosai kuma amince zai aureki, kuma zai rike ki amana, amman ya ce na fara tambayarki idan kin amince saboda kar ya zama an cilasta miki, na fada masa tun kamin ya dawo na yi magana da ke amman zan sake samunki da maganar" "Allah ya ba mu zaman lafiya" Shi ne kawai abun da na fada ta amsa da amin ta rumgume tana farinciki da jindadi. "Ya fada min wata biyu yake son yi, amman mahaifinsa ya kira shi akwai wani buki da suke a can duk shekara zai tafi a satin nan albashi idan sun gama sai ya dawo, dan haka nake son a daura aurenku a satin nan, sai ku tafi tare, abar min Ibrahim har sai kun dawo tukuna" "Tohm Ammy" "Allah ya miki albarka" Jindadin da na gani a fuskarta yasa ni jindadi duk da ina fargabar abun da zan tarar. Turhan ya so gyara kansa a gurin mahaifiyarsa ne ta hanyar nuna masa ya amince da kudurinta ni kuma ya buga da kasa ta hanyar amfani da ni na fadawa Ammy ba zan aure shi ba, daga nan zata fahimci na mata butulci wata kila ma ta kore ni ko kuma ya karyata labarina. Washe garin ranar da aka yi haka Ammy ta bukaci dole sai na fito na yi karin kummalo a falon wai saboda ni da Turhan mu kara fahimtar juna. A dole na fito na karya a gurin muna cikin karyawar ne take mana addu'a da fatan alheri tare da nuna jindadinta na yadda muka bata hadin kai. "Allah ya hada kanku ya ba ku zaman lafiya, sa na yi nufin a hade aurenku da na kanwarka (yarinyar da Ammy take riko) amman saboda uzurin da ya same ka yanzu zan tafi family house a yau na yi magana da su na abun da ya kamata, sai a daura auren albashi a bar bikin sai idan kun dawo sai ayi komai cikin natsuwa da kwanciyar hankali" "Eh haka yayi Ammy" Ya amsa mata yana murmushin dole. "Bari na barku ku ci abincinku, zan tafi na shirya na tafi gurinsu Hajiya" Ta mike tsaye ta fice daga dinning din, fitarta ke da wuya Turhan ya kalleni ya ce. "Ba dai kin amince da wannan auren ba? Sai kin ci ubanki" Ya wurgar da spoon dinsa ya fice a fusace, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, domin na shiga tsaka mai wuya idan na fasa auren nan Ammy zata ga laifina, idan kuma na amince ba dadinsa zan ji ba. Ta bangaren iyayen Ammy ma murna suka yi suna nuna farincikinsu, ba a fara shirye shiryen komai ba sai da Turhan ya bukaci ayi min gwaji, aka gwada jinina da na shi dukanmu bama dauke da kowace kalar cuta da zata dakatar da aurenmu. Haka bi dare ina raya shi da kuka da tunani kala kala har zuwa ranar da Ammy ta shigo min da kaya masu dubin yawa akwaiti goma sha biyu a matsayin lefe na, lefen da aka hada gurin Khadeeja Candy Store, sannan ta danka min dubu dari biyar a matsayin sadakina, ko bata fada min ba na san ita ta biya sadakin ko wani nata, domin bani da kima da martabar da Turhan zai siye da ni da sadaki mai tsada haka, a dan kankanen lokacin Ammy ta saka aka fara min gyaran jiki. Ranar Jumma’ah aka daura mana aure bayan saukowa daga Sallah Jumma’ar mai raka'a biyu, ina zaune garden din gidan tare da mai kunshin da Ammy ta kira ta bukaci ta yi min lalle mai kyau. Mai aikin Ammy ta shigo tana rangwada guda da murna ta sanar min an daura aurena da Turhan, a take na ji gabana ya fadi wani abu mai kauri da zugi ya tunkari zuciyata ya tsaya, tun daga wannan ranar har yau wannan abun be sauka ba. Kusan zan iya cewa auren dole Ammy ta yi min da Turhan domin bana son shi tsarin rayuwarsa gaba daya be yi min ba. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 4️⃣0️⃣ Aliyu ya dago yana sauke numfashi ya kalli Fatima dake rike dayar wayarsa tana kallo, ita yake kallo ammam Emily yake tunani wahalar data sha a gidan Khaleefa be gamsar da alkalamin kaddararta ba har sai da ta sake zana mata wani shafin mai daci a tsakaninta da abokinsa. A yanzu ya fahimci duk abun da Ammy ta yi ma Turhan na juya masa baya ta yi daidai, ga kuma rashin samun haihuwa da be yi ba a yanzu sai kuma Allah ya jarrabe shi da son yaran ashe shi ya fara butulcewa tun farko. Ya kai hannunsa ya shafa Fatima sai ta kalleshi ta yi murmushi, shi ma yayi mata murmushi sannan ya maida hankali gurin wayar ya kunna dayan voice note din ya cigaba da saurare. ***. ***. *** A ranar da aka daura mana auren, Turhan be dawo gidan ba sai dare, ina dakina a lokacin da ya shigo tare da Ammy tana ta murmushi sai addu'a take zuba mana, shi ma yana murmushi kamar gaske, ni kuma na kasa ko daya kallonsu ko yin murmushi, London yana hannuna Ammy ta karbe shi ta fice aka bar mana dakin daga ni sai shi, kaina a kasa shi kuma ya nemi guri ya zauna ya dora kafa daya kan daya, sai a lokacin na iya dagowa na kalleshi farar shadda ce a jikinsa sai kamshi yake kamar angon kirki. Mun dauki minti talatin a haka babu wanda yace da wani uffan, sannan ya taso ya karaso kusani da ni. "Wani mummunan abu be taba faruwa da ni ba kamar aurenki" Furucinsa ya tsari kaina, na dago na kalleshi sai ya tofa min yawu da karfi a fuska ya daki kafata dake da lalle da karfi sannan ya sa kai ya fice. A daren ban yi bachi ba, kuma ban yi kuka ba tunani ma na rasa wane zan yi, ina ta sake sake idan na kulla wannan na kulla wacan ta ko'ina zaren warware min yake na rasa gane inda zan raba na fake. A daren Ammy ta kawo min international passport din da ta saka aka yi min saboda barin kasar zamu yi. Washe gari Assabar Ammy ta fara shirya min kayan da zan tafi da su, ita ta hada min komai nawa ido ne kawai sai kuma ɗana sa nake ta rumguma ina jin kewar rabuwa da shi, a daren Ammy ta yi min nasiha sosai kuma ta kara tabbatar min ɗanta ba zai taba cin amanata ba, kana ta yi min godiya na yadda na amince da kudurinta har aka kulla auren, ta ce na toshe kunnuwana daga kananan maganganu ko kuma abun da zan gani da be kai ya dawo ba, na kwantarwa da mijina hankali, ba can zamu zauna ba zamu je ne kawai mu dawo. Ranar Lahadi da safe aka fito mana da akwatinanmu ni ma na fito cikin shirina ina rumgume da ɗana, Turhan ma ya fito cikin nasa shirin yana ta far'a kamar gaske, Ammy ta so ta rakamu Airport amman ya hana wai idan ta bimu har can zan fi kowa kewarta. Kuka be zo min ba sai da Ammy ta kai hannu ta karbi London dake hannuna sai ya fashe da kuka ni ma na fashe da kuka na karbe shi na rumgume, abun mamaki sai ga Turhan ya zo ya karbi yaron ya dankashi hannun Ammy ni kuma ya ciro handkerchief ya share min hawayena. "Ki kwantar da hankalinki mana, ba wani dadewa zamu yi ba, muna gamawa zan dawo tare da ke, kuma a can zamu zauna ba anan kusa da Ammy" Ya kama hannuna ya saka ni mota da kansa Ammy na ta saka masa albarka har sau uku sannan ta yi mana addu'ar Allah ya tsare. Direba ya ja mota muka kama hanya, ba mu zame ko'ina ba sai Airport aka yi mana duk wani check in da ya kamata har muka kai gurin jirgin, sai da muka shiga na gane ba guri daya za mu zauna ba, shi yana Business class ni kuma a economy, na zauna shiru ga damuwa na barin ɗana, ga fargabar abun da zan je na tarar ga kuma tsoron jirgin domin shi ne karona na farko da na hau jirgi. A Lagos muka fara sauka da na fito sai na tsaya sai da ya fito sannan muka kama hanyar Hotel a taxi, a hotel din ma babban daki ya kama ni kuma ya fada min zan zauna a karamin daki daidai ne, haka na karasa dan wunin daya rage na kwana babu wanda ya kwankwaso min yace ga abinci, tun bayan dan abun da na ci a jirgi da be rike cikina ba. Sai 11am ya buga mun dakin hotel din na bude yace na fito zamu kama hanya, na fito da akwatina muka sake shiga taxi ta kai mu air airport aka yi mana screening aka auna kayanmu da duk wani abun da ya kamata sannan muka hau jirgin da zai dauke mu zuwa Sudan, a nan ma business class ya shiga ya bar ni a Economy, dan abun mutsa baki da aka kawo min a jirgin da shi na samu na karya bayan tafiya ta yi nisa suka kawo mana shinkafa na cinye tas da ruwan shayin kai tsabar yunwa ko ruwan sha ban raga ba komai sai da na cinye har ina bukatar kari. Na yi bachi ban farka ba sai da muka jirgin ya fara jijjigar sauka. Yanayin kasar da garin, mutanen da yarensu dabam ne da na kasar mu, tun a Airport din na kara tabbatar dan sarauta ne, saboda motoci da suka zo daukarsa da kuma yanayin mutanen da suke tuka motar. Mota daya muka shiga da shi a motar yayi min gargadin da ban zan taba mantawa ba. "Karki sake ki yi magana, kin ga hausar mutanen nan da na can ba iri daya ba, kuma za ki je ne a matsayin baiwa, zan sanar da kowa cewar ke baiwa da mahaifin Ammy ya bani, kuma zan sanar musu ke kurma ce, dan haka duk tsanani kar ki kuskura ki yi magana, kuma bayan nan karki nuna kin san ni" Bance komai ba, a lokacin ma kuka baya zuwa min wata kila saboda damuwar ta yi min yawa ne ko kuma dai kukan ya gaji da zirarta idanuwana ne. Masarauta ce babba ko da yake ban san komai akan sarauta da fada ba, amman tabbas mahaifin Turhan babban Sarki ne a garin, ayi masa tarba ta girma, ni kuma aka kaini wani daki na daban aka sauya min tufafi zuwa aka ba ni na wasu masu kamar lafaya, wadanda ma'aikatan gidan suka sakawa. Masarauta ce mai matukar fadi da girma, ba Turhan ne kadai dan da Sarkin ya haifa ba amman kowa da bangarensa da kuma nasa bayin. Nidai tun daga ranar ban sake saka Turhan a ido ba sai da na yi sati biyu, a kullum zuciyata tana gurin ɗana, aiki kam babu hutu musamman da ya kasance ni a karkashin matarsa aka barni, domin bangaren mahaifinsa dabam tun da naje ban taba ganin Sarkin ba, bangaren da Turhan yake da matarsa dabam, idan har na huta to dare ne yayi ya shiga turakar mijinta mu kuma sai mu samu hutu, na ga wulakanci na ga kaskanci ga yunwa ba a wani ba mu san adataccen abinci, idan ma aka kawo abinci wadanda suka manya ne suka kwashewa mu kanana a bar mana kadan, gashi ya fadawa kowa ni kurma ce ba damar na yi magana ko na nuna na ji wani abu, haka na yi rayuwa cikin tsananin azaba da azzatarwa, idan aka yi baki ni nake gyara ko'ina na gidan kuma ban isa na ce na gaji ba, gimbiyarsa kuma bayi ba su isa su daga kai su kalleta ba sai hukunci. Wata rana na makara ban tashi ba, domin tun da asuba muke tashi mu fara aiki ga gidan da girma, kananan bayin da muke yin aikin ba mu da yawa, su kuma manyan aikinsu bangaren kula da baki ne ko abinci, sai wata babbar hidima idan ta taso. Ko da na isa na samu wata ta maye gurbina tana aikin mopping din da aka ce na rika yi kullum. Da farko na jidadi na yi zaton ko an dauke min ne na huta na wunin ranar ashe sun shirya kai karata a gurin babbar hadimar matarsa ne. Sai da aka gama komai na fito ina gyara gefen dawaki hadimar ta iso, da wani yare take min magana wanda ban iya ba, ko da ace na iya ban isa na amsata ba, saboda Turhan yace kar na sake na nuna ni ba kurma bace, ina jin tana magana amman ban waigaba, sai da aka tabo ni sai ta yi min alama da bachi da lokaci tana tambayar meyasa, ba ni da amsar bata dan haka na yi shiru sai kallonta nake tun da ban iya maganar kuramen ba balle na fada mata da kurmancin cewar ban san lokaci yayi ba, ashe hakan yayi mata ciwo, a take ta koma ciki babu jimawa wasu mata suka zo suka rika ni suka tafi da ni wani daki, tun daga yanayin dakin na san azabtar da ni za'ayi domin akwai bulala a cikin ga kuma wani namiji tunbuke da da katon rawani yana jiran shigowata. Ba su tirsasani ba gurin shiga da kafafuwa na shiga, mutumen ya fara duka tun ina hawaye kawai ina kukan dole irin na kurame har kai ga ihu ina neman taimako, sai ga mutane an cika gurin kowa yana kallo da mamakin maganar dake fita bakina, sai da na samu sa'ida sannan na fito daga dakin na koma bangarenmu na kwanta ina jin fatata tana min zugi. Can da dare aka aiko daya daga cikin bayin da muke kwana da su ta kama hannuna ta fita da ni ina tafiya daker, daman haka suke min idan ana kirana saboda basu iya kurmanci ba ni kuma ban isa na yi magana ba. Da muka isa bakin fadar gimbiyar Turhan sai babbar hadimarsa ta yi min alama da na wuce ciki na shiga daga baki baki na zube kasa, sai ta yi tafiyarta. Na kusan awa daya a gurin sannan Turhan ya fito cikin shigarsa ta jallabiya da alkibba mai kyau hannayensa a baya ya karasa kusa da ni cikin wata irin tafiya ta kasaita ta ban taba ganin yayi irinta a gidan Ammy ba, fuskarsa babu annuri. "An fada min kin yi magana? Saboda me?" Maganar ma a rarrabe yayi min ita saboda kasaita ta. "Dukan ne yayi min yawa ban san lokacin da na yi ihu ba, ka yi hakuri" Sai a lokacin ya kalleni yana jin kansa. "Wa yasa aka doke ki? Me kika yi?" A tunani da sanin matarsa aka min dukan dan haka da ya tambaye ni sai na ce. "Matarka" Na kama hafafuwansa na rike ina kuka. "Turhan dan Allah ka maida ni gida" Ya ja baya. "Karki sake taba kafata, tashi ki fice, kuma na fada miki ke kurma ce karki sake ki sake yin magana" Na tashi daker na koma bangarenmu, na samu tufafin wata na dora kaina akai domin ni Turhan be bani nawa tufafin da Ammy ta hado ni da su ba, kuma bata kira ta ce a bani ba, kowa yana ta tufafi daga kala biyar zuwa sama ni kuwa kala biyu ne daga tufafin da yake a matsayin uniform dinmu sai tufafin da na cire. Ina dakin aka sake zuwa aka dauke ni hadimar Gimbiyar tana ta masifa sai dai ban san me take fada ba. Wacan dakin aka sake maida ni aka sake zaneni sai dai wannan karon ban yarda na yi uhu ba saboda Turhan ya gargade ni. Dukan ne ya zama silar rashin lafiyata a masarautar har na tsawon sati gashi babu kyakkyawar kulawa babu maganin kirki, rayuwar bauta rayuwa ce ta kaskanci da wulakanci Aliyu, wanda ba zan yi ma kowa fatanta. Da na fara jin sauki sai na koma kan aikina tun daga lokacin bana bari ma asuba ta yi ina bachi, da zarar karfe uku ta yi na dare na farka ba zan sake komawa bachi ba. Zamani ya waye duniya ta canja ban taba tunanin har a lokacin akwai sarakunan da suke mulkin bayin ba sai da na ga masarautarsu Turhan. Gashi basa ganin kimar bakar fata, domin a duka bayin babu larabawa sai yan wasu yarukan ko kabila, ni kaina sai su yi ta kallona wasu har taba gashin kaina suke suna yaren da bana ji, wani lokacin kuma a daga fatar idona a kalli idon. A ranar da Allah ya kaddara za a samu cikin Fatima, da safe ne sosai ina goge fadar Hadimar Gimbiyar ta zo ta kama hannuna ta shiga da ni can ciki sannan ta saki hannuna ta fice, ina tsaye a gurin Turhan ya fito sai na yi hanzarin zubewa kasa na maida idanuwa kasa. "Biyo ni" Ya fada sai na mike tsaye na bi bayansa, da halshen larabci ya sallami masu saka turaren dakin sai daya daya umarci ta ba ni turaren na karba na bi bayansa har muka shiga bangarensa. Muna shiga ya nuna min inda zan aje turaren ya ce. "Shiga wacan dakin akwai bandaki a ciki ki yi wanka, ki cire tufafin ki daura tawul" Yana min maganar yana kallo da kyama da kuma dan bacin rai kamar wanda baya cikin yanayi mai dadi. Na aje turaren na nufi dakin da ya nuna min na shiga, na cire tufafin jikina kenan ban kai ga shiga bandakin na ji shigowarsa. "Dole ce kawai saboda kin min karya kince matata ce ta saka aka duke ki alhalin ba ita ta saka ba, kin saka ta kaurace min na tsawon lokacin nan" Wata kila yana cikin uzurin da ba zai iya jira na yi wankan ba, ko kuma yana tsoron ta shigo ta tarar da mu ne sai ya yi abun da zai yi cikin gaggawa, bayan ya gama yana ta tsaki da tofar da yawu. "Wannan ce bakar rana ta biyu a gurina bayan ranar da na aureki, kuma karki sake na ji maganar nan kin shigo dakina a gurin kowa ko kuma wata alama" "Dan Allah Turhan ka maida ni gida" Na roka ina jin kaina a cikin wani irin kaskanci da ban taba samun kaina a ciki ba. "Idan kika sake fadin sunana ko daga ido ki kalleni sai na saka an miki illar da zai lalata miki idon, ko baki in yaso sai ki zama kurma da gaske, tashi ki bace min da gani" Ya daka min tsawa rai a bace, a cikin rakunan bakincikina, ranar da Khaleefa ya sake ni ba zan manta da ita ba, ba zan manta da furucin da Turhan yayi a gareni ba na kiran ranar aure da kuma ranar da ya tara da ni a matsayin bakar rana ba, haka ba zan manta da ranar da na rasa ɗana ba. Na kimtsa kaina na fito ina jin jikina yana min wani iri domin na dade irin wannan alakar bata hada ni da kowa ba bayan na fito daga gidan Khaleepa. Na cigaba da aikina ina hawaye har na gama, sai rayuwa ta ci gaba tun ina saka ran Ammy zata zo ko kuma ta kira amman babu ko daya, gashi ni kuma ban taba rike waya ba tun bayan dana zauna a gidanta ban san ma ta ina zan same ta ba. A haka na sake shafe wata biyu a gidan, kuncin da na shiga sai yafi na baya saboda matarsa da hadimarsa sun tsane ni a yanzu ba tare da na san laifin da na yi aikata a agaresu ba. Ga kuma lailayin da nake ta yi a boye. Muna cikin wannan halin wata rana sai fadar sarkin ta yi babban bako. Wani babban mai kudi kuma dan kasuwa ya sauka masarautar tare da rakiyar manyan mutane daga Nigeria. Aka saka mu yi wanka muka fito tsaba saboda zamu tarbi bakon tare da tawagarsa. Sai kuma aka yi dace Turhan da matarsa sun tsallaka sun bar kasar zuwa gurin da be fada min ba, na fahimcin hakan ne ta hanyar rufe wani bangare da aka yi a part dinsu aka hanani shiga na gyara kamar yadda nake, kuma aikin da ake yawan sakani ya ragu ba ma ni kadai ba har da sauran bayin. Wasu kuma na daina ganinsu wata kila har da su aka yi tafiyar. Matar Sarkin wanda take zaman step mother din Turhan ta tarbi matar dan kasuwar da ba zan iya fadar dalilinsa na zuwa garin a lokacin ba. Ni da mutum uku aka zaba mu yi Serving din matar dake wanye da abaya kanta da wings ta nada gyalen abayar a wuyanta ga bakin gilashi, da alama dai ba musulma bace shiyasa ta kasa rufe kanta. Kusan shi ne karo na farko da na bar garen Turhan zuwa wani bangare na gidan, wata kila babu wata adatattun bayi ne a lokacin wata kila kuma Allah yayi nufin kubutar da ni ne, shiyasa abun da duk ya faru ya faru. Muna jera abincin a madaidaicin falon da aka ware mata ina satar kallonta zuciya nata yi min sake sake, yadda zan samawa kaina mafita, domin tun da muka shigo naji tana waya da yaren igbo. Sai da muka gama jera abincin tsab sannan na kalli matar cikin karfin hali da nemawa kai masifa na soma mata magana da yaren na Igbo. "Dan Allah ina neman taimakonki, na ga ke ma igbo ce yar'uwata dan Allah ki taimaka min" Sauran bayin da muke tare da su suka kalleni kamar a firgice sai dayar ta fice da sauri. Matar ta kalleni tana mamaki ta ba ni amsa da yaren na Igbo. "Kina jin igbo ne? Daga ina kike?" "Daga Nigeria, ki taimaka ki maida ni gida dan Allah, ni yar kabilar igbo ce, daga Lagos na zo aiki gurin wata mata a kaduna sai ta hada baki da wani suka siyar da ni a matsayin baiwa a gurin dan sarkin garin nan, ina zaune a nan ne a matsayin kurma wahala nake sha sosai a nan, gashi na baro ɗana kuma ba shi da lafiya, yanzu kuma idan baki taimaka min ba kashe ni za su yi saboda sun ji na yi magana ba su taba jin na yi magana ba" Ina maganar da yaren na Igbo ina kuka. "Amman baki yi kama da mutanen Nigeria ba" "Wallahi daga Nijeriya nake, a gidan marayu na tashi ban san kowa na wa ba, idan mum tafi zan kai ki har gurin domin ki tabbatar dan Allah ki ceto rayuwata" Na yi mata karyar an siyar da ni ne domin ba lallai ta yarda ba idan na fada mata dan sarkin garin ne ya auro ni ya mayar da ni haka. Daya daga cikin manyan hidiman bangaren Turhan ne ta shigo ta kama hannuna zata fice sai na cigaba da rokon matar. "Na yi kasada na jefa kaina a matsala na yi magana idan baki taimake ni ba, shi kenan na rasa rayuwata kuma ɗana ya rasa ni, ke fa uwa ce ki taimake ni dan Allah" Bata ce min komai ba, a lokacin ne na gane na yi kuskure na jefa kaina a babbar matsala domin ban samu biyan bukata ba. Waje aka fitar da ni can bangaren Turhan aka bar ni tsaye a rana a lokacin har na sadakar na san hadimar zata min hukuncinta ne kuma idan Turhan ya dawo shi ma yayi min na shi. Tsawon awa uku na yi tsaye a ranar kamin hadimar da kanta ta sake zuwa ta kama hannuna muka koma bangaren na Sarkin da sai a lokacin na taba ganinsa ido da ido a cikin fadarsa. Matar ta nuna ni tana murmushi tana fadar nice da yaren turanci, mai fassarawa sarkin yayi Larabci sai sarki ya daga kai da hannunsa kadan wani na kusa da shi yayi magana sai aka fassara ma matar a nan ni ma na ji yana fadar. "Sarki yace ya baki ita kyauta" Matar ta yi godiya sosai sai aka fitar da ni waje, a nan sai da suka dade cikin sannan suka fito fadawan sarkin suka yi ma mutumen rakiya tare da matarsa ni kuma na shiga a tawagar masu rakiyar dan kasuwar a wata mota ta dabam. Hankali be kwanta ba sai da muka bar fadar da muka isa filin jirgi na yi zaton za'ayi mana irin na farko ne, ashe shi saboda isa da jirginsa yake yawo, sai dai hakan be hana a tantance mutanen da suke tare da shi ba, ni kuma bi ta wata hanyar dabam da ni bata hanyar da kowa yake bi ba, sai da aka isa gurin jirgin aka fito da ni daga motar na shiga aka zaunar da ni can baya nesa da mutane. A lokacin ne abubuwa suka fara yi min gizo ina ganinsu kamar mafarki. Tun da muka tashi ba mu sauka ko'ina ba sai Abuja Nigeria. Da muka sauka jirgin ne matar tasa aka matso da ni kusa da ita ta gargade ni da halshen igbo. "Ina fatan ba karya kike min ba, domin idan ya zama tsabanin abun da kika fada min toh zaki hadu da mummunan hukunci kuma zan saka a nemoki a ko'ina kika a kasar nan" Na ce mata na amince, suka shiga motar alfarma mu kuma aka saka ni a wata motar, ina ta kallon gari da titunan Abuja da tunanin dan yancin da na samu har muka isa gidan mijin matar mai kama da wata babbar fadar Sarki, mutanen da suka tarbeta ita da mijinta ma abun kallo ne, a nan na kara gane kudi suna da muhimmanci sosai a rayuwar dan'adan. Da muka sauka gidan sai ta hannata ni a hannun wata mata yar Kaduna tace mata wai ina da zan je na dauko ɗana tana son kar a barni na tafi ni kadai na tafi tare da rakiyar wasu saboda tana son ta gano gaskiya ta, ni dai an kira ni kawai aka nuna min matar da za mu tafi tare, ta hanyar wayar da matar take da yaren yarbanci, na fahimci kudin wacan matar da ta ceto ni wanda ko sunanta ban sani ba. Komai aka bani kasa ci na yi ina ta zumudin ganin ɗana ga kuma tsoro ya cika zuciya gani nake kamar Turhan zai aiko a tafi da ni ne. Hankali be kwanta ba sai da muka bar garin Abuja tare da matar da mijinta da nake kyautata zaton dan siyasa ne. Guri daya na zauna da matar, da alama ticket din da aka saya min na kusa da ita ne. A nan ta gabatar min da kanta ta fada min sunananta Barakat amman yaranta suna kiranta da Mama Barakat ta fada min ita bayarabiya ce, sannan ta tambayi labarina, ita kan ban boye mata komai ba na fada mata labarina tun daga tashina zuwa auren Khaleepa da kuma Turhan, gaba daya sai ta sauya ta rika kallona har sai da na tsorota, har muka isa Kaduna hawaye ke cika mata ido tana sharewa. Mun sauka Airport din idanuwa a zare kamar wata marar hankali ga rama na yi gaba daya ba ni da natsuwa. Mota daya aka zo daukarmu na shiga gaba ita da mijinta suka shiga baya, duk maganar da mijin yake bata amsawa har ya tambaya lafiya? Tace babu komai. Mun sauka gidanta ba laifi gida ne mai kyau amman ko kadan be kamo gidan wacan matar ta Abuja ba, kuma ita wannan da alama tana da abokiyar zama domin gidan bangare biyu ne, sai da muka fara shiga bangaren na farko ta shiga ita da mijin sai ta fito ita kadai ta shiga motar aka karasa da mu bangarenta. Na sauko motar ina jin kamar na yi tsuntsuwa na gan ni gaban ɗana, haka dai na daure muka shiga ciki, ta nuna min dakin da zan zauna sannan ta haura sama har lokacin hawaye take hawan ma tana yi tana waigena har ta haura stairs din. Ina ganin ta shige na juya ya saci kafa na fice daga bangaren, da kaina na gate din gidan na fice, tafiya kadan na tari abun hawa na hau na fada masa ya kai ni cocin da take kusa a nan garin Kaduna, babu wata daguwar tafiya sai gamu gaban cocin, na gaishe da mai gadin na fada masa ina tafe da matsala ne amman ina son ya bani kudi na sallami mai achaba tukuna babu musu ya biya mai babur din, sannan ya shiga da ni ciki a tunani idan na je ma Ammy kai tsaye ba zata ba ni ɗana ba dan haka na zabi neman taimakon mutanen cocin bayan na fada musu ina ra'ayin komawa alnahin addinina na Christianity. Sai suka ba ni shawara na fara tafiya dauko yaron har sai idan ta hana tukuna za su shigo ciki, na ba su addireshin gidanta sannan na cire takardar na rubutawa Ammy martanin karyar da ta yi min cewar danta na kirki ne ya banbanta da sauran, domin na san ba lallai na samu tsayawa na fada mata baki da baki ba, amman idan na bata wasikar zata karanta. Su suka ba ni kudin abun hawa na hau achaba na isa unguwar a lokacin ne tsoro ya yaye min saboda ina son ganin ɗana ta kowane irin hadi, da Allah yayi nufin ba ni nasara ina buga gate din mai gadi ya bude sai da ya dade yana kallona sannan ya gane ni, ya bar ni na shiga ciki na samu falon babu kowa sai ɗana shi kadai yana kallon Cartoon, na karasa da zafin nama na dauke ɗana na aje mata takarda a gurin da na dauke shi na fito yana ihu domin shi ma be gane ni ba, mai gadin ya tsaya tambayar ina zan je da yaro na kai masa mugun halbi a gurin da ya fi komai muhimmanci a jikinsa, ba shiri yaja baya na bude gate din na fice da gudu kai kace sato yaron na yi. Ina tafe ina waije ko za'a biya ni amman ban ga sawun kowa ba sai da na samu Achaba na hau sannan Ammy ta biyo ni da motarta tana cewa na tsaya na cewa mai Achaba kar ya tsaya, be tsaya ba sai da muka isa cocin na sauka da guduna na tsaya layin mutanen da cocin ke rabawa tallafi. Ammy ta dade tana kallona har sai da mai gadin ya bude min na shige. TIRKASHI....!!! A tunaninku tsakanin Auren Khaleepa da Turhan a ina Emily ta fi shan wahala? Waya ya fi gallaza mata? Team Turhan kuna da katon aiki a gabanku😢 indai kuna son Emily da Turhan sai kun tanadi makaman sallama 🤗 _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [6/26, 9:29 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 4️⃣1️⃣ Sai da ta bar gurin sannan na fito na sallami mai achaba na koma ciki na rika ɗana dake ta ihu, gaba daya ya ki yarda da ni saboda be gane ni ba. Kansa na rike na saita shi ya fuskanci sai na koma kiransa da sunanyen da nake masa ina hadawa da Momy, a take ya tsagaita kukan da yake ya kalleni sai na yi masa dariyar dake tafe da hawaye na rungume shi ina jin kamar za a sake raba ni da shi ne. Kwana na uku a coci, a tsawon kwanakin nan bana sallah bana saka hijab duk wani abun da ya danganci musulunci bana yinsa, saboda na fada musu zan koma addinin Christianity, sai dai a can kasa zuciyata na ni na san ban shirya barin addinin musulunci ba, ba dan mutanen cikinsa sun yi min gata ba sai dan ina jin natsuwa da addinin a cikin zuciyata, domin addinin musulunci addinin mai tsari da tsabta da dokoki, ni kuma mace ce mai son zaman lafiya mai son natsuwa. Sun mutunta ni sosai a cocin domin gidan wani pastor aka kai ni, abinci sai na ture gurin kwanciya mai kyau, matarsa tana ta nanata min halayyen musulmai basa da kyau kuma daman su basa son kafirai, har take cewa na yi kuskure da na bar addinin da ace ban gane gaskiya na dawo ba da Yesu yayi fushi da ni kuma ya kona ni. Kusan duk wa'azinta jinsa kawai nake, amman a zuciya ina kyamar abun, ana gobe Lahadi wanda ta kama ranar coci a ranar za a min wanka da ruwa mai tsarki kuma a maida ni addinin kirista a ba ni bibles kamar yadda na sani yake a hukunce kuma matar ta jaddda min, sai na dauki London na goya ma sanya hijab dina cikin giyon na fito da sunan zagayawa harabar cocin, na nufi gate da yi ma mai gadin karya cewar zan fita naje na dawo kuma sun san da fita ta, domin an fada masa duk wanda ya zo nemana kar ya bar mutum ya shiga sai an sanar saboda ni da su muna tunanin Ammy zata dawo nemana. Salin salin na fice daga gidan, ba kuma dan na san inda zan je ba sai dan ban shirya komawa addinin ba, na hau achaba na tambaye shi dan Allah wace umguwa ce nesa sosai da cikin gari, unguwar da san yi tafiya sosai sannan a isa gurin, ya fada min sai na ce ya kai ni can, mun yi tafiya sosao kamin muka isa unguwar dake kama da sabuwar unguwa ma sauka na ba shi kudinsa na nisa cikin unguwar ina ta kallon yadda tsare tsarenta yake, har na hango wani gida dake da fanfo da kwararo a ciki, na dauki leda na tara ruwan na fara sha sannan na shayar da ɗana na yi alwala sallah na fara yi na rama duka wandada aka biyo ni har na ji na gaji, a lokacin kuma wata zuciyar take ta fadan min na koma dai domin wannan addinin be karbe ni ba, amman dayar data ci karfina ta hana ni komawa na zauna a gurin har dare, a nan yunwa ta fara tunkaro ni ga yarona be san babu ba. Kukansa ya saka mai gadin lekowa ya tambayi tafiya na fada masa yunwa yake ji sai ya shiga ya dauko ragowar abinci ya bani na bawa yaron da muka gama yace dan Allah mu kara gaba kar mai gidansa ya dawo ya same mu a nan zai masa fada. Na yi masa godiya na tashi na kara gaba, haka na yi ta rayuwa a unguwar daga wannan kwararo sai wannan wani gurin a hantare ni wani gurin a bani abinci ko sutura wani gurin kuma a ba ni hakuri, gaba daya na koma wata kazama saboda babu gurin da zan raba na yi wanka, bahaya ma sai na shiga daji, rayuwa ta yi tsanani gareni a lokacin, ga ciki ga yaron da ba lafiyayye ba, idan ciwonsa ya tashi sai dai na yi ta kuka domin ban san wani abu da zan yi ba bayan wannan, ni da shi muka rame muka lalace, nakan shiga gida gida neman aiki ko wanki, idan na samu mai son wanki na yi ta murna na wanke a biyani na ciyar da kaina da ɗana, na samu wani tsohon shagon kwano na laba ciki nake kwana ciki nake wuni idan ina cikin unguwar. Tun mutane ana jin tsorona a unguwar har aka fara sabo da ni wasu ma idan sun raga abinci da kansu suke kawo min saboda suna min kallon mahaukaciya, wani lokacin ba ni sadakar kudi ko abawa ɗana da haka nake ta fadi tashi har cikina ya tsufa, wani sa'in sai na yi tafiya mai nisa zuwa wata unguwa nake samun abun da zan ci, kuma ban sake bawa kowa labarina ba, idan naje gida sai dai na yi bara ko kuma na tambaya idan suna bukatar a musu wanki ko wani aiki. Wasu suka kam tambaye ni waye uban yarona ko kuma cikin da nake dauke da shi sai nace musu ban sani ba ni ma, hakan ya saka suka kara daukata mahaukaciya suna tunanin kamar fyade aka min na samu cikin ko kuma wani ya yaudare ni. Akwai masu fadar wai ko dai kishiya ta yi min asiri saboda ina kyau ta raba ni da mijina? Su tambaya daga ina nake sai na ce Lagos, idan aka ce Lagos a ina? Sai na ce ban sani ba, to gurin wa zan ce daman? Har lokacin ina jin da kamar akwai sauran kurciya a tare da ni, wata kila kuma shiga mawuyacin hali ne yasa ban taba kula da watan cikina nawa ba, ban taba kirgawa na gane ba, ciki dai yana ta girma kuma yana motsi, idan na ji motsin cikin sai na ji zuciyata ta yi fari tas kamar ba ni da damuwa, ni dai burina na haihu lafiya na samu karin wasu iyalin... Ana haka wata rana nakuda ta fara taso min tana kwantawa na kwashe kusan kwana biyu sai ta motsa min sai ta koma, idan ta laba min sai na cigaba da harkokina, wata rana na fita neman abun da zan ci ban karasa inda zan je ba aka sako ruwan sama na kuda ta taso min mai karfi kamar zan fita hayyacina gashi kuma na yi nisa da gida ba zan iya komawa ba, ɗana kuma ya firgice saboda tsoron ruwan da iska sai ihu yake min ni ma kuma ihun nake a gefen hanya babu wanda ya kula ni sai kai Aliyu, shi ne farkon haduwata da kai, na zan iya manta wannan alherin ba, na gode na gode Aliyu, a lokacin ne na rike hannunka har agogon ya cire ya dawo hannu sai na matse shi ina ihu na yi tunanin mutuwa zan yi ma gaba daya, ka taimake ni ka dauke ni ka kai ni Asibiti, duk wani taimako daya kamata likitocin nan sun ba ni na wahala sosai kamin na samu na haihu da kaina, ada har ina tunanin ko dai sai an fasa ni za a iya cire abun da ke cikina saboda na kasa nishi. Da na haihu sai suka bukac a kawo kayan jaririya ba ni da su, zanen da aka hadeta a ciki ma tsohon zanen wata mata ta bada a gurin aka lulkube Fatima, suka ce ina audugar da zan saka ina kaza ina kaza, na ce duk ba ni da, sai suka tambaya wanda ya kawo ni waye shi? Nace ban san shi ba taimakona yayi, a nan wata nurse ta fita ta shigo min da pad ta pant ta kuma ba ni zane na daura sannan suka canja min daki suka kawo ni wani dakin na dabam suna tambayar ina yan'uwana ya kamata na ci abinci na ce musu ba ni da kowa, daya daga cikin wadanda suka karbi haihuwa ta ta kawo min agogonka ta ce ga wannan kin saki a kasa dazun na karba na rike ga. Daker na iya awa hudu a asibitin na kamin na saci kafa na gudu da ɗana da kuma jaririya dana haifa, zanena mai jini da uwar da ke fadowa bayan haihuwa a asibitin na bar musu na gudu. Ban nisa sosai da unguwar da asibitin take ba jiri ya debe ni na fadi ban sake sanin inda kaina yake ba. Sai da na farko naga ana min fifita ga jaririya a kusa da ni ga kuma London yana ta kuka, mutane nata min sannu aka ba ni abinci na ci sannan aka dauke ni zuwa gidan wata mata dake kusa ana tambayar a ina nake daga ina na fito na fada musu a gidan na kwana sai washe gari bayan na karya matar ta siya min wani pad ta bani tsohon wandonta na saka bayan ta dora min ruwan zafi na yi wanka, ta bani wani tufafin na saka da hijab, makota kuma suka kawo min tsofin kayan jarirai na sakawa Fatima, ta kawo min abinci na ci na sha kunu sannan mai gidanta da wasu mutum biyu yan unguwar da kuma ita matar kanta, suka dora ni a napep muka tafi unguwar da nake rayuwa na nuna musu inda nake kwana sai suka fara tambayar wadanda suka san ni a unguwar, kowa sai yace da rana tsaka ya gan ni a gurin kuma ba ni da cikakiyar lafiya, cikin ma suna zargin yi min aka yi ta karfi, wasu kuma su nanata wai asiri aka min. Ni dai jinsu kawai nake idan aka tambaya daga ina nake sai na ce Lagos wane guri a Lagos nace ban sani ba, sai suka yanke shawarar za a kai ni police station ayi report, ina jin haka nace ba zan je ba da suka matsa na saka musu kuka a dole suka koma can gefe suka yi maganarsu sai aka dawo aka fada min wai zan bi matar zuwa gidanta na koma can da zama a nan ma na tirje domin na san akwai abun da suka shirya, ni kuma ina tsoron a yadani Cocin da na gudu su gani ko kuma Ammy. Na dake akan nan gurin zan zauna da kowa ya watse na goya jaririyata na kama hannun dana na bi ta cikin gidanen dan kar ma wani ya gan ni na gudu na bar unguwar. Tafiyar kuma wani sabon labari ne, domin ba san kowa a inda na tafi ba, haka na kwana a jikin wata tsohuwar gina sauro ya cije ni ya cije yarana musamman Fatima dake ta jaririya a lokacin, a daren ne na rana mata suna Fatima sunan da ba a yanka mata rago ba kamar yadda kuke yi a addinin musulunci, a lokacin akwai son addinin a raina shiyasa na zabi sunan da yake min dadi bayan Aisha, da gari ya waye na barka dankwalina na yi amfani da shi domin pad din ya lalace kuma ba ni da wani, na cigaba da tafiya kafafuwana sun gaji haka nake ta mika su ga danyen jego ga yaro karami idan ya fasa min wani ihu sai na rikice, na daukeshi idan na gaje na aje shi haka dai har na isa wata unguwar marowata domin duk gidan da na shiga na yi roko hakuri ake ba ni wasu kuma su koroni. Yunwa ta ci ni sosai ga tafiya na gaji har na fara ganin jiri, tsakaninkanin kafafuwana ma ciwo nake ji sosai domin ban samu hutu da kulawar daya kamata ba bayan haihuwar da na yi kwana biyu da suka wuce. A haka har na isa kofar wani karamin gida irin na mazan nan da ba su da aure a bude na sallama na sallama na ji shiru sai na taka ciki kadan na jiyo kamshin girki, sai na yi sunsun na dawo baya na koma can bayan gidan dake da wata gona na samu wani guri na raba na kwance Fatima dake bachi yarinya kyakkyawa fara sol na kwantar da ita a gurin na zaunar da London dake ta kukan yunwa na fito na koma wacan gidan dake bude na kara sallama ina sallama ina shiga ciki har na kai inda nake jiyo kamshin a wani karamin Kitchen na duba waiga na ga babu mai ganina na nasa kafata a Kitchen din, sai na yi arba da mutum kwance cikin jini farar vest din dake jikinsa duk ta bace da jini, da sauri na dawo baya ina numfashi daker, na ga tashin hankali kala kala amman ban taba ganin gawa ba sai a ranar, na fito da sauri na falfala da gudu na dawo gurin yarana ina dawowa na samu London yana ihu yana yunwa, ni kaina kuma yunwar nake ji, sai hakan ya saka na manta da tunanin abun da zai biyo baya na sake komawa zuciya na zillo kamar zata fado na shiga Kitchen din na duba ko'ina har na hango karamin gas a kusa da kafar mutumen da ban san ko waye ba, da alama dai girki yake aka kashe shi, na fito na sake leka waje na dawo da sauri na nufi girkin na bude indomie ce har ta fara kamawa na tara hijabina na juye na saki tukunyar na fito a guje ga zafin indomie ga tashin hankali na dawo gurin da yarana suke na cire hijab din gaba daya na aje a gurin na bude indomie na saka hannu ina hurawa ina ci ina bawa London. Ban an kara ba ma ga mutum tsaye a gabana dana daga kai na kalleshi sai na ga fuskarsa babu annuri ga katon Cross a wuyansa, ashe ma ba shi kadai yake ba har da wasu mutun uku. "Miye alakanki da Risk Guy" Ya tambaya cikin hausarsa da bata gama zauna wa a bakinsa ba. "Ban san waye shi ba, ni abinci kawai nake nema" Ashe yayi zaton na ga lokacin da ya aikata kisan kan ne, a take ya nuna Fatima da bindiga. "Jaririya ce, bata san komai ba bata maka komai ba karka dauki alhakinta" Ya maida bindigar a gurin London dake ihun ganin bakuwar fuska. "Ba shi da lafiya, Autism ne kuma be maka komai ba" A take ya dawo da bindigar a kaina. "Idan ka kashe ni yarana ba su da wanda zai rike su ba su da kowa sai ni, ni ma ba ni da kowa sai su, Wallahi ban ga abun da ka aikata ba kuma bazan fadawa kowa ba, abinci kawai naje nema tun jiya rabona da abinci ni da yarona yunwa muke ji, dan Allah ka yi tafiyarka ni ban san waye kai ba, kuma daga nan tafiyata zan yi daman a hanya nake, ina neman mafaka ba ma dan yarana da sai nace maka na shirya mutuwa a yanzu" Ina maganar cikina da muryata suna rawa ina kuka sosai a take Fatima ta farka ta fara kuka ga London yanayi. Ya kalli yaran ya sake kallona sannan ya sauke bindigar ya juya ya tafi, ni kuma na dauki yata na rumgume London a dayar cinyata ina hura abinci ina ba shi ina kuka. Kamin na daga kai sama na kwala wani irin ihu iyakar karfina sai kuma na tashi na goya Fatima da sauri na dauki London na dauki agogon ka Aliyu da nake ta yawo da shi na fita gonar domin na fara hango mutane kar ayi zaton ni na kashe shi alhalin ban ma tana ganinsa ba sai ranar. Na yi nisa da gonar na samu wani ice na zauna a gurin na rumgume yarana ina kuka jikina nata rawa ina fargabar me kuma zai sake faruwa da ni. Ashe mutumen daya tashi kashe ni yana biye da ni saboda yana ganin kamar zan iya tona masa asiri ne, a nan kamar daga sama a sake ganinsa gabana sai ya saka hannunsa ya dago fuskata ya kalleni ni ma na kalleshi sai ya hura min abu a fuska mai kamar farar hoda amman yana da karfi sosai da zogi domin ina shakarsa hankalina ya bace... ***. ****. **** Aliyu ya lumshe ido ya jinginar da kansa yana kallon sama, kwallar dake makkale a idonsa suka sauko masa ta gefen idon, Fatima na gani ta fara masa tambaya. "Ba za mu isa Lafiya ba? Mutuwa za mu yi?" Ya bude idon da sauri ya kalli Fatima yana murmushi domin be san ma kwallar ta sauko masa ba. [6/28, 10:18 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 4️⃣2️⃣ Tausayinta da na mahaifiyarta ya ratsanshi ya saka ya tare hawayen yana murmushi sannan ya shafa kanta. "Aa Lafiya za mu isa In Shaa Allahu, kawai wani abu nake saurare na ji tausayinta shi ne" Ta yatsina baki irin na su na yara tana wani iyayi. "Ni bana yin kuka wa mutane, mutum idan yana da matsala ai shi zai yi kukansa ko?" "Eh amman tausayawa yana da kyau, ana son haka" "Okay" Ta amsa ta cigaba da kallon da take. "Mun kusa sauka" "Okay" Ta amsa ba tare da damuwa ba. Aliyu ya sauke numfashi a hankali idonsa basa masa gizon komai sai fuskar Emily, and he remember yadda suka tsabanin kira har ta yi ta masa dariya a waya, sauti dariyar nata dawo masa, ya tuna haduwarsu a office da tsabanin da suka samu na shiga Elevator da lokacin da ta yi masa tambaya har ta so ma magana da yaren da bata yi zaton yana ji ba, tunani na ya jefo masa ganin da yayi mata na karshe da yadda take ta murmushi kuma murmushi yayi mata kyau a cikin bakar abayarta kamin ya ankara sai gashi yana nasa murmushin a take. "You deserve happiness..." Fatima ta amsa masa da sauri tana dagowa ta kalleshi. "Yes i deserve it" Kakkaurar dariya ce ta subuce masa irin mai gunna da kal kal. "Yeah you deserve happiness too baby" A rasa kuma sai ya ce. "And now i know why Vito hate you, idan baki son mutum ya shiga uku wannan baki naki is something else" Ya kunna dayan voice din wanda shi ne na karshe ya cigaba da saurare, wanda a cikin yake son tabbatar da wani aukuwar wani abu ko akasinsa. ***. ****. ****. Daga lokacin da na shaki wannan hodar ban sake sanin inda hankalina yake ba, ban kuma san tsawon awanin dana dauka cikin gushewar hankalin ba, ni dai na farko da karfi ina jan numfashi, numfashi yana janyewa sai dakin da duk abin da yake ciki yana ta juya min ina jin jiri ga jikina a jike da alama ruwa suka zuba min. "Yarana yarana yayana, su kadai gare ni yarana" Yarana kawai nake nema domin su ne a raina, ruwan suka kara watsa min aka kama kaina aka soma a cikin wani bokiti dake cike da ruwa aka cire suka rike gashin suka jijjiga ni da karfi, a take na fara amai domin akwai yunwa a tare da ni ga kuma abin da na shaka warin da nake jinsa wani iri a hancina yana kai min har makoci, ga kuma jijjigar da suke min. Yar indomie da na ci ce na amayar na kwanta a gurin a wahale ina ta kiran sunan yarana. "Fatima ta... Ibraheem.... Yarana..." "Ke musulma ce?" Ita ce tambayar dana fara ji, na dago na kalli mai tambayar daker har lokacin ina dan ganin jiri ga jikin nawa ya kara mutuwa. "Mu kashe ta kawai boss, duk yadda aka yi budurwarsa ce ko kuma ta san wani abu kansa kawai tana wasa da hankalinmu ne" Na ji dayan ya fada da halshen igbo, sai dayan ya ce. "Ko ma ba matarsa bace wannan ai kazama ce daga ganinta, zamu iya kashe ta dai saboda ta san mu muka aikata kar ta kara a gaba ta fada" "Dauko wuka" Wanda yake babbansu ya fada a take na tashi zaune na ce. "Wallahi ban san wanda kuka kashe ba, bani da alaka da shi, ku yarda da ni mana" Na amsa musu da yaren Igbo sai duk suka cika da mamaki, ogan na su ya taso ta zo inda nake ya turani da kafa na koma kwance ya dake wuyana. "Taya kika san me nake fada?" "Ina jin yaren igbo" Na amsa daker har bakina ya fara zubar da jini domin talkamin da ya take ni da su masu zafi da nauyi ne. Ya daga kafarsa "Ya kike jin yaren?" "Saboda na zauna a Lagos" "Wacece ke?" "Labarin yana da tsayi" "i don't care ki fada min yanzu" A dole na takaita labarin na fada masa abubuwa masu muhimmanci har zuwa inda ya gan ni. Kamin yace komai dayan daya dauko wuka yace karya nake na tsara komai ne. "Me zai saka na tsara komai?" ai ba biyana za ku yi ba, ba wani abu nake nema daga gareku ba, me zai saka ba za ku bincika ba?" "ina da mutane a ko'ina har Lagos zan saka a bincika min Idan karya kike zan kashe ki" "Na yarda" Na amsa a take, sai ya saka aka dauko masa takardar na bada address din guraren da komai ya faru ya rubuta sannan ya tashi ya fita ina tambayar ina yarana. Har ya fice be amsa min ba, bayan ya fita wani ya shigo min da yaran London yana ta bachi kai langabe wata kila ya dame su da kuka ne suka shaka masa irin abun da suka shaka min, Fatima kuma tana ta tsosai hannu tana sauke ajiyar zuciya irin na babyn da ta yi kuka ta gaji. "Ba zaki fada mana gaskiya ba ko?" Na kalleshi na rasa me zan sake cewa, shirun da na yi ya saka shi fiddo wata karamar wuka ya yanki kafata da ita sai da na fasa ihu. "Ban san komai ba gaskiya na fada" Na matsar da yarana na rumgumesu domin na lura Fatima yake kallo zai iya cutar da ita. Ya mike tsaye ya fice haka na zauna a dakin har dare jini na zubar min a kafa ga aman da na yi a gurin ga kunzugun da na yi ina son na canja ba ni da wanda zan saka nonona na dauke babu ruwa saboda ban ci komai ba, ga tsoron ban san me zai faru da mu ba, ga kuma ɗana be farka ba har lokacin, abubuwa suka hade min goma da shirin. Ina cikin wannan halin shugan na su ya sake shigowa ya kalleni yana toshe hanci. Ya haska ni da kyau ko'ina na jikina. "Waya yanke ke ni a nan?" "Wannan ne ya yake ni, kuma gaskiya na fada muku ban yi karya ba" "Waye?" "Wanda ya kawo min yarana" Ya juya ya fita be jima ba ya dawo tare da mutumen ya haska min shi. "Wannan ne?" "Eh" Mutumen ya bude baki zai yi magana Shugaban na su ya ciro bindiga ya harbe shi a ramen wuya a take ya fadi kasa yana karkari jini ya samu hanya kamar ruwa, ni kuma na shiga aikin ihu yana daka min tsawa bana ko ji sai ihu nake, jikina na rawa hankalina ya tashi ban tana ganin an kashe wani a gabana ba sai ranar, ban daina ihun ba sai da suka shaka min wani abun a hanci hankalina ya sake bacewa. Da na sake farkowa farkowa sai na gan ni a wani daki na dabam yarana suna kusa da ni sun sai kuka suke, ashe tun da suka shaka min ban farko ba sai safe. Na kama su na rumgume ina jin jikina ba karfi, can anjima sai ga wani ya shigo ya tambaya me nake bukata yanzu? Na fada masa ina son abinci. Sai ya fita ogan da kansa ya shigo min da abinci ya aje min babu ko zancen wanke hannu balle baki a take na bude shinkafar na fara ci, Ibrahim ma ya rika ci da sauri ko minti biyar ba mu yi ba muka cinye abinci har muna neman kari. Shi dai yana tsaye yana ta kallona. "Akwai bandaki a nan ki yi wanka, za a kawo tufafi ki canja tare da yaranki, and why are you bleeding?" "Saboda sabuwar haihuwa ce" Ya juya ya fita. Ya kawo min tufafi dogayen riguna da pad da panties ga kayan yara na maza da na jarirai. Haka na yi rayuwa a dakin na tsawon kwana uku a yan kwanakin nan na samu kulawa da abinci mai kyau wanda rabon da na ci shi tun bayan da na bar gidan Ammy, ko a sudan tura abinci kawai nake ba dan ina iya ci ba kuma ba dan ina jindadinsa ba sai dan babu yadda na iya. A ranar da nake cika kwana hudu ya shigo ya same ni ina zaune a kasa domin a kasa muke kwanciya ni da yarana gashi tiles ne, Fatima har tari take, Ibrahim kuma yana zazzabi har kuma lokacin ban san a wane gari nake ba balle unguwa azo kuma zancen gida. Ya zauna kasa kamar yadda nake zaune yana kallona. "Emily na bincika labarinki a Lagos, here in Kaduna places din da kika zauna da Kaduna, a Sudan ne kawai ban bincika ba, and you're right akan abun da kika fada baki da alaka da mutumen da kika nake zargi, this is the first time da na ji tausayin wani ya kamani sosai wani da ban sani ba, and na ji dadi da ban kashe ki a take ki ba. Emily ina da kyakkyawan sako a gareki" Shirun da yayi ne ya saka na kalleshi sai da ya karanci natsuwata sannan ya ce. "Wannan ne karo na farko da nake son na kyautata rayuwar wani, na yi abun alheri a gareki, Emily ina son ki zauna a karkashina zan baki kulawa zan miki gata ke da yaranki, zaki zama a cikin ikona ni kawai cin amana ne bana so, wanda kika ga na kashe ma amanata ya ci, kina son haka" Na daga masa kai. "Tohm amman fa bisa sharadi daya, zaki bar wannan addinin ki koma addinin ki na asali, domin babu abun da na tsana kamar musulunci da musulmai, kuma kin zauna da su a yanzu kin fahimci yadda suke, idan kin yarda ki fito waje ki same ni, yau zan bar garin nan" Ya tashi yayi tafiyarsa, a lokacin zuciya da tunani suka fara min rawa, har na kasa zaba tsakanin addimai guda biyu, an kai ruwa rana daga zuciyata zuwa tunani kamin na fahimci komawa asalin addinina na shi ne gata ne, kuma shi ne rufin asirina ko da yake ban sani ba a lokacin ko shi ma zai ci amana ta ne, amman ba ni da wani zabi domin na gaji da rayuwar dake. A take na dauki Fatima na saba a kafada na rika hannun Ibrahim muka fita ta kofar dakin da sai a ranar ya bar min ita a bude. Dana fito sai na hango wata kofar a bude na nufi gurin haka na rika bin kofa kofa har na fito harabar gidan dake cike da ciyayi ga kuma wani bangare na gidan da ba a gama ginawa ba. "Zaki bimu ne?" Ya tambaya yana kallona da fuskarsa mai ban tsoro. Sai na daga mishi kai. "Kin yarda da sharadin?" "Nan ma na daga mishi kai" "Miye sunan wannan yaron" "Ibraheem" "Yarinyar fa?" "Fatima" "A cikin sunan mata ina jindadin Lisa, daga yau sunanta Lisa, shi kuma London shi ne sunan da na fi so, ke kuma zaki koma sunanki na asali Emily no more Aisha, that's my number one rule My name is Vito (King)" Ya kada min kai sai yaronsa ya bude min mota na nufi motar na shiga can baya domin mai gida uku ce, shi kuma ya zauna a tsakiya direbansa a gaba. Daga kaduna da direban yaja motar be tsaya ko'ina ba sai Abuja, muna isa ya wuce da mu Airport tun kamin mu bar garin Kaduna ya tambaye full name dina na fada masa ashe zai siya min ticket ne domin muna isa Airport din bamu wani sha wahala ba muka shiga jirgin ya daga zuwa garin da ban taba tunani ko mafarkin zuwa ba wato Part hartcour. A gidansa muka sauka akwai tsoro sosai a gidan domin a kowane lumgu da sako na gidan yaransa ne ga Camera ta ko'ina, a wani bangare na gidan ya aje shi, ya wadata ni da komai ya samo mai aikin da zata kula da yarana ya nemawa London asibiti mai kyau aka fara duba shi ya saya masa kayan wasa. A lokacin ne na ji na tsani musulmai har bana son jin labarinsu ko ganinsu. Ya kan ziyarce mu lokaci zuwa lokaci har na shekara daya a gidan ban san sana'arsa ba, amman ya wadata ni da komai na more rayuwa sai dai baya bari na tafi ko'ina kuma babu wanda yake shigo min. Da jindadin ya samu sai jikina ya dawo, wata rana ya shigo yana kallona yace yanzu me nake bukata, na fada masa da ace zan samu dama zan sha wani abun da zai rage min kiba ne domin ta fara damuna, kuma ina son wani abu da zai iya dauke min hankali domin ina yawan tunanin abubuwan da suka faru har mafarkinsu nake. Tambayar daya fara min ita ce zaki iya karatu? Nace zan iya, sai yace zai sama min duk abun da ake bukata zai fitar da ni waje na yi karatu kuma zai bincika abun da ya kamata akan rage kibata. Kamar wasa sai ga shi ya sama min takardun primary da secondary, ya zaba min London a matsayin kasar da zan tafi na yi diploma in business administration. Ya kuma fada min da yata zan tafi domin akwai gurin da ake bada ajiyar yara a can har sai idan mutum ya dawo daga aiki ko makaranta ya je ya karba. Da na yaye Fatima na bar kasar zuwa London na yi karatu acan na kan kai Fatima day care sai idan na dawo na je na karbota, gida ya kama min apartment daya, kudi kuma har ban sab me zan yi da su ba, sai da na shekara daya a can sannan ya bijiro min da zancen surgery, na ji tsoro amman likitan da zai min aikin ya kwantar min da hankali, ya fada min yadda dokikin abubuwan suke, kuma ya nuna min kudin da za a kashe a rubuce. Aiki aka min aka rage min nama jiki duk inda kitse yake a jikina suka cire min, na yi jinya na wahala ga dokoki da ka'idodin shan magani da abinci, a haka dai har aka yi nasara. Kamin na gama karatun na dawo kasar nan na zama wata kyakkyawa fari ya kara bayyana ni da turawan ba a banbance da wani, musamman idan na shiga cikin masu jan gashi irin nawa. A gida kuma mai aikin da Vito ya dauka Chidimma tana ta kula da London, shi ma kuma yana kula da shi ta wani bangaren, hakan ya saka suka shaku. Na dawo kasar a lokacin da Fatima ta yi wayo, sai ya zamana bata da wani makiyi irin Vito ba kuma dan ya mata komai ba, shi ma kuma baya wani jituwa da ita London ne na shi. A lokacin ne ya fara ba ni yancin fita yawo amman be yarda kowa ya zo gurina ba, sannu a hankali kishi ya fara shiga kamin ya sanar da ni yana so na, sai da ya fara sanar da ni asalinsa sana'arsa da komai. Ya fada min shi be taba son mace ba gaba daya aure ko soyayya basa gabansa sai da na zo rayuwarsa, kuma na yarda domin na lura da zaman dana yi a gidan ban taba ganin mace ko daya ba, kuma be taba nuna min son taba jikina ko yin wata mu'amala da banza da ni ba. Har sai da ya fara nuna min yana kaunata, ya cancanci na ba shi kauna amman zuciyata ta yi firrr ta ki karbarsa, na kan duba alherinsa da kyautatawa amman soyayyarsa ta ki zama a zuciyata wata kila saboda basa jituwa da Fatima ne, wata kila kuma saboda zuciyar tawa ta mutu ne bana jin son namiji a zuciyata. Da fatima ta shekara biyar sai kiyayyarta ga Vito, domin Fatima tana da wani irin hali na kafiya da rashin jin magana,karamar yarinya ce amman ta iya muguyen kalamai. Ko kadan Fatima bata dauko daga hali da kamanin na ba, a duk lokacin da kowa zai kalleta Turhan zai gani kamar an tsaga kara. Gashi da ta yi wayo sai ta tashi da son addinin musulunci ta hanyar CHANNEL din da muke kallo, daga ranar dana fada mata asalin sunanta Fatima ne bata sake amsa sunan Lisa ba, ni kuma bana iya hana ta abun da take so, shiyasa idan Vito ya fita sai na kama mata channel din tana koyon abubuwa na addinin musulunci har ta fara iyawa, domin Fatima tana da wayo sosai da basira ga bakinta a bude yake kamar na babba. Tun tana da shekara daya da wata hudu ta fara kiran Dady ba tare da kowa ya fada mata, sai na hana ta, a lokacin da ta yi wato sai ma fada mata ita bata da mahaifi, shiyasana hade mata suna uku Fatima Emily Aisha. Ko kadan jininta be hadu da na Vito ba har ta kai yayi tsanani har ya kan gwada dukanta ni kuma na nuna masa ba zan lamunta ba, ga shi kuma yana shan kayan maye ni kuma bana son yarana su taso suna sha, ko suna kallon abun, sai na fada masa ina bukatar gurin zama na wa ni kadai, be musa ba ya sama min gida na koma ya cigaba da kula da rayuwata da ta yarana, ni kuma sai na yi amfani da wannan damar na saka Fatima makarantar Islamiya dake garin ta kan je a duk lokacin da ta ji tana bukatar zuwa, a ranar da Vito ya gane dai da yayi min duka, daman ya saba idan na bata masa rai duka yake min tun ban saba ba har na fahimci haka halinsa yake. Vito yayi min komai Aliyu kuma ya cancanci komai daga gareni, a yanzu ma ya fada min ya gaji, kuma na san yayi kokari yana da gaskiya, yana tsananin kishina yana so na kuma ya kyautata min fiye da Turhan fiye da Khaleefa fiye da kowa, kokarinsa da hakurinsa kullum na jiran lokacin da zan amince da kaunarsa ne kuma na aure shi. Wannan ce Emily Aliyu wannan ne tarihin rayuwata, wannan dalilin ne ya saka na tsani musulmai kuma ya saka ba zan taba yarda Turhan ya ga Fatima ba, ba kuma zan taba sha'awar arba da Khaleefa ba, na san idan Turhan ya san da Fatima zai karbe ta ko dan ya kuntata min, ba dan yana sonta ba a yanzu kuma bani da kowa sai ita... Na wahala a lokacin da kowa yake bachi akan tasa rayuwar, na shiga taskun rayuwa a lokacin da babu ni da kowa, na kwankwasa kofofi da yawa ba su bude min ba, a duk inda na saka kafa sai na tarar rame ne na shiga ukuna Aliyu a yanzu ina kokarin gina kaina ne na zama kamar kowa, ni ma na samu yanci ni ma na jidadin da kowa yake ji. Har yanzu abubuwan da suka faru suna ruda kwakwalwata, abu kadan ya kan tuna min da baya, bana nufin cuta ma kowa miyasa ni ake cutar da ni? Shim ko dai ban cancanci farinciki ba? I'm so fighting for peace kwanciyar hankali nake bukata a yanzu, abu kadan zai iya buga kwakwalwata i have done enough i have done everything i can.. I deserve happiness too ko ba haka ba? ****. ****. *** "Kin cancanci, da ace zan iya dawo da lokaci baya Emily da na gyara miki komai, but it's not too late i Will make things right da yardar Allah Emily sai kin yarda musulmai akwai na gari kuma sai kin dauwama a cikin addinin da ke baki natsuwa har abada" Yayi furucin ne a daidai lokacin da jirgin ya sauka garin Kaduna, Fatima kuma take bachi. ______ Toh fa masu karatu kun ji tarihin Emily. [7/1, 9:53 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 4️⃣4️⃣ Aliyu yayi hanzarin saka wayarsa aljihu tun kamin Turhan din ya karaso inda yake, ya zaro handkerchief ya lullubawa fuskar Fatima duk da ya san ba lallai ne a ganin farko Turhan ya gane fatima tana da alaka da shi domin ba zai yi tunanin Emily zata samu ta bangaren Aliyu ba, and he would never think Aliyu zai iya boye masa babban abu kamar wannan. "Abun mamaki, Aliyu kai ne a nan?" Aliyu yayi murmushin karfin hali yana ala ala kar Fatima ta farka, domin ya san karamin aikinta ne ta labarta masa waye ita ko be tambaya ba. "Ni ne, Turhan taya muka hadu?" Turhan yayi murmushin kasaita yaje zai rumgume abokinsa daman al'adar larabawa ce rumgume juna da sumbanta idan suka hadu da wanda suke so, haka Turhan yayi yunkurin aikatawa cikin murna da farincikin ganin abokinsa sai dai babu dama saboda babyn dake hannun Aliyu. "Ohhh Baby waye haka ta hana ni rumgumar abokina, ban jidadi ba" Aliyu ya fadada murmushinsa abubuwa biyu suka zagaye shi, yadda Turhan yake murnar ganinsa ya saka shi jin wani iri na gaskiyar daya boye masa gashi kuma yana fargabar kar Fatima ta farka. "Baka santa ba, daman wai tun da muka yi waya kace min zaka zo baka zo ba?" "Ban samu zuwa ba, daman na so mu zo tare da Reem ne amman haka be samu ba" Ya fada cikin wani yanayi na rashin jindadi. "Toh ya jikin Ammy?" "Da sauki take cewa sai dai naje na gani, muje ma tare ai sai ka duba ta ko? Daman ina neman mai raka ni kasan kullum idan zan je gurin Ammy tsoronta sabo yake zame min, saboda maganganu da kuma fuskar da take karba ta da ita, ta daina murna da zuwa na yanzu" Aliyu can't say no to his friend kuma ya san ba zai yiyu ya tafi tare da Fatima gidan ba hatsari ne ma babba ya tafi da ita gidan. "Yeah amman na yi waya da direba na ce ya zo ya dauki a nan" "Malam ba wani babban abu ba ne direbanka ne fa, karkashinka yake ai zaka iya fada masa ya koma kawai, direban da zai dauke ni yana waje yana jirana mu je kawai kasan dai ba zan barka Airport din nan ba" "Bata zan yi?" "Aa amman dai ba zan barka ba i miss you Aliyu sosai fa" "Okay fine mu jira Direban ya karaso sai ya tafi da wannan yarinyar kar mahaifiyarta ta damu, ni kuma sai na bika mu kaika gida tun da ka zama amarya" Yayi dariya tare da kai hannu ya taba Fatima dake ta bachinta cike da sha'awar yara. "Yar waye wai" Hannunsa na kaiwa a jikin Fatima ta zabura da karfi ta sauke ajiyar zuciya a cikin bachin da take. "Oh Sorry" Turhan ya fada yana dauke hannunsa da sauri gudun kar ya tasheta, Aliyu ya kalleshi jiki a sanyeye ya juya yana fadin. "Mu tafi waje mu jira shi" Turhan ya jera tare da shi suka fito suna dan taba hira, sun tsaya harabar for like 10min direban Aliyu ya kira Aliyu ya kwatanta masa inda yake direban na isowa Aliyu yayi hanzarin nufar motar ya bude baya ya kwantar da Fatima a hankali bachi take sosai kamar wanda ta yi wani katon aiki, Aliyu ya rufe motar a hankali be taba jin ya aikata wani abu na rashin kyautata kamar kin fadawa Turhan Fatima yarsa ce a yanzu ba. Sai yake jin kamar ya ci amanar abokinsa duk da yake yana da laifi. "Ka tafi da ita gida ka shiga da ita ciki ka kwantar da ita" Ya saka hannunsa alijihu ya ciro keys ya mika masa. "Toh ranka ya dade" Ya karbi keys din sannan ya dauki kayan da Aliyu ya zo da su ya saka bayan mota, sai a lokacin Aliyu ya sami relief ya nufi gurin da Turhan yake tsaye jikin motar da za su shiga, yana isowa Turhan ya ware hannu Aliyu ya ware suka rumgume juna. "Na jidadin zuwan nan yaushe rabon da na saka ka ido Aliyu" "Ni ma na yi marmarin ganinka, fatan kana lafiya" "Da sauki dai ina lafiya ga mutumen da uwarsa ke fushi da shi?" Ya bude motar ya shiga baya Aliyu ma ya zagaya ya shiga baya, mutumen da suke tareda Turhan ya shiga front seat direba yaja motar suka fara tafiya, suna taba hira har suka isa gidan. Turhan da Aliyu a tare suka fito motar Aliyu ya wuce gaba ya shiga cikin falon Turhan na bayansa, Mai aikin Ammy ta amsa musu ta gaishesu, Aliyu ya karasa gurin da Ammy take zaune ya zube kasa yana gaisawa da ita Turhan ma ya karasa ya zauna kusa da Aliyu. Cikin murna da farinciki take kallon Aliyu. "Madallah Aliyu ne a gidan na mu yau?" "Ni ne Ammy ya jikin na ki" "Jiki Alhamdulillah Aliyu ina samun sauki, ashe ka samu shigowa" "Eh kin san daman na ce zan shigo na duba ki, sai gashi kuma wani uzurin ya taso aka yi daidai, a airport na hadu da Turhan ai sai muka zo tare" "Maa Shaa Allah, haka fa ka fada min zaka zo ai ka huta baka tsaba alkawari uwarka ta yi farar haihuwa Aliyu" Ammy ta fada har lokacin bata kalli inda Turhan yake ba. Turhan ya sauke kansa kasa yana jin wani iri, Aliyu ma ya ji babu dadi domin Ammy tana kokarin muzanta abokinsa ne a gabansa which it's not fair. "Amman dai jikin da sauki sosai ko Ammy?" "Na samu sauki Alhamdulillah, ai na ma fadawa abokinka ba sai ya zo ba, kawai be ji magana ta ba ne daman be saba ji ba" "Haba Ammy taya baki da lafiya kuma ki ce kar ya zo? Ai ba zai yiyuwa ba, ke fa mahaifiyarsa ce Ammy ki rika duba wannan" "Zuwansa ba zai rage ni da komai ba balle ya kara ni, rabin ciwon nan ba shi ne silarsa ba? idan ya zo ai ba da lafiya zai zo min ba, kuma ina da masu kula da ni nan yayan yan'uwa sun ce wadatar, idan za amin allura kullum sai Nurse ta zo, Likita kuma kullum yana zuwa duba ni, saboda na fada masa ni bana son asibiti ko da mutuwa ce a bar ni na mutu a gida, kaga shi kenan abokinka ya huta ba sai ya sake zuwa kasar nan ba sai yayi zamansa a can daman haka ubansa yake so" Turhan ya kalleta felling hopeless cikin murya mai rauni ya ce. "Wani dan kirki ne zai yi fatan mahaifiyarsa ta mutu ya huta? Ammy ya kike magana haka kamar mai magana da makiyinta? Danki ne fa ni jininki, na rasa ya zan yi na kawar da wannan bakin shatin dake a tsakaninmu, Ammy kina tunanin all this while abun nan dade yake min? Ko tafiya kika yi kika bar ni wannan abun ba zai barni na samu salama ba, Ammy ni ma ina cikin damuwa gaba daya yanzu bana jindadin rayuwar da nake, abun da a aikata kuskure ne kuma ni dan'adam ne aziji" Ammy ta girgiza kai. "Aa abun da ka aikata ganganci ne ba kuskure ba, da gangan ka aikata, saboda baka kallo da daraja irin ta uwa, kuma abun da ka yi min ai ka kyauta tun da ka samu tukuici, Allah ya maka albarka Turhan na gode" Aliyu ya ce. "Ammy ki yi hakuri dan Allah ki yafe masa abun nan ya wuce" "Na yafe masa, amman wucewar wannan abun? Sai na koma ga Ubangijina, ni kadai na san me nake ji, yaron nan shi kadai Allah ya ba ni, idan kai ka manta mahaifiyarka ba zata manta ba Aliyu, irin fadi tashin da na yi akan na samu ganin yaron nan, na wahala a gidan mahaifinsa kuma na wahala kamin a bar shi ya zo gurina, na dauki yar mutane na aura masa da tunanin hakan zai saka na samu dana da zuri'arsa a kusa da ni, amman ya watsar ya karyata duk wata halayya tasa dana fadawa yarinyar nan, marainiya ba uwa ba uba, yanzu Allah kadai ya san halin da take ciki idan ma tana raye, bata da kowa sai Allah bata da wani wanda zai nemi ya san halin da take ciki tun da bata da dangi, yarinyar nan ta yarda da ni amman Turhan ya rusa duk wannan ya nuna ba ni da muhimmanci a garesa kamar yadda ubansa ya nuna min" Ammy tana maganar hawaye ya sauko idonta, Turhan yayi kasa da kansa ya saka hannunsa ya rike goshinsa idonsa suka cika da hawaye, ba na tausayin Emily ba na bakinciki daya saka mahaifiyarsa har ta zubar da hawaye akansa gaban abokinsa. "Wane irin muhimmanci Aisha take da shi a gurinki har haka Ammy? Da har zaki zubar da hawaye akan abun da ya faru?" "Irin muhimmanci da baka da shi" Ta amsa masa kai tsaye da kakkaurar murya. "Indai saboda ni ka zo, toh ka hada kayanka ka koma bana bukata, ka bari idan na mutu sai ka zo jana'iza" "Subhanallahi Subhanallahi" Ya maimaita har sau uku sai Aliyu ya dafa shi. "Turhan fita waje ka jira ni" Ya tashi cikin wani irin yanayi na bakinciki da ya fice falon, sai da ya fita sannan Aliyu ya ce da Ammy. "Ammy bana son na tunatar da ke abun da kika riga kika sani, na san kin so Emily da Turhan kin tsara zamansu, amman haka be samu ba baki tunanin wata su din ba alheri ba ne ga junansu? Kuma haka Allah ya tsara shi da ita babu dogon zama, kuma Ammy karki manta duk yadda zaki so Emily Turhan danki ne, na san be kyauta ba amman fushinki a kanki da damuwarki zai iya janyo masa matsala a rayuwa ko ba yanzu ba a nan gaba, kuma Ammy Turhan yayi nadama sosai yanzu haka zancen da yake min yana son ya saka kudi mai kauri akan nemo Emily, abun ya dame shi ma, ki yi hakuri Ammy" Ammy ta yi murmushi. "Allah ya maka albarka Aliyu, ka san muhimmanci uwa shiyasa ka fadi haka, tafi ka tafi na gode" "Shi kenan Ammy Allah ya kara sauki ya baki lafiya" "Ameen Allah ya maka barka" Ya mata sallama ya fito falon a jikin motar da suka shigo ya samu Turhan ya jingina fuskarsa dauke da damuwa. Aliyu ya saka hannayensa aljihu yana sauke ajiyar zuciya ta dayan bangaren abokinsa ya ba shi tausayi, sai dai kuma idan ya tuna labarin da Emily ta ba shi sai ya ji kamar be tausaya masa ba. "Turhan am sorry iyaye sai lallabawa" "Haka take fada min maganganu marasa dadi a duk lokacin da na zo, kuma ta sani na yi iya kokarina gurin neman yarinyar nan, ban same ta ba toh ya zan yi? Kana jin tana fadin bata san halin da Aisha take ciki ba, ni kuma da nake cikin wannan halin bata jin tausayina na rasa ya zan yi" "Da sannu komai zai zama daidai In Shaa Allah, wai taya ka yi Aisha ta subuce maka.?" Madadin ya amsawa abokinsa sai ya ce "Ita ma fa yarinyar ta jefa ni a matsala, miyasa ta amince da auren nan tun farko fisabilillahi" "Allah ya kawo sauki, ni zan wuce abun da zan fada maka shi ne ka yi hakuri da mahaifiyarka kuma ka yi ta addu'a" "In Shaa Allahu, ma gode Aliyu, bari na yi ma direban magana sai ya kaika gida" Aliyu ya shiga motar Direban yaja shi zuwa gidansa, a mota Aliyu ya gwada kiran Number Emily ya jita a kashe sai ya aika mata sako. "Are you okay?" Domin ya san ya kamata ace ta kira shi bayan riskar sakonsa, and maganar Ammy ta taba shi na cewa bata da wanda zai damu ya san halin da take ciki tun da bata da kowa. Bayan direban ya aje shi ya juya shi kuma ya shiga gidan da yayi datti yana mamakin taya haka ta faru domin yana da mai gyara masa gidan every week. A falo ya samu Fatima na ta bachi har lokaci akan kujera hannu ya kai ya taba jikinta yana mamakin wane irin bachi ne take haka, sai ya ji shi da dan zafi kadan. Mai kula da harabar gidan ya shigo yana masa sannu da zuwa Aliyu ya amsa yana tambayar ina mai gyara gidan. "Tun da ta tafi bata dawo ba, bata fada maka komai ba tace dai zata je ganin gida ta bada keys a aje maka" Ya saka hannunsa aljihu ya ciro keys din ya bawa Aliyu da hannu biyu. Aliyu ya mika masa Atm dinsa ya fada masa code sannan ya fada masa inda zai tafi ya samo musu abinci mai kyau... Sorry ku yi hak'uri gobe zan yi long page in Shaa Allahu. [7/2, 6:50 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 4️⃣5️⃣ Kamin yaron daya aika ya dawo Aliyu ya shiga ciki yayi wanka ya canja tufafi sannan ya dauki wayarsa ya kira Mama Barakat ya tambaya ko tana gida. "Eh ina gida Aliyu ko ka shigo garin ne?" "Eh na shigo kuma yau nake son na shigo gurinki saboda ina son komawa gobe kin san aikin na mu babu daga kafa" "Haka ne to sai ka shigo" Ya sauke kiran sannan ya fito falo yayi sallah yana sallamewa aka yi knocking, knocking din da ya tashi Fatima ta farka idonta har sun yi ja tsabar bachi, Aliyu ya karba ya rufe kofar. "Yaushe muka zo nan?" "Kina bachi little princess" Ta yi mika "Kai ka dauko ni?" Ya risina inda take zaune yana kallonta da murmushi a fuskarsa. "Eh kin tashi lafiya?" Ta kalli falon. "Nan gidanka ne?" Ya daga mata kai. "Ashe kana da wani gida Vito ma gida biyu yake da shi" "Good taso ki wanke baki ki yi wanka sai ki ci abinci ki yi sallah" Ta kalli shaddar dake jikinsa. "Kai ka yi?" "Eh" Ya kama hannunta suka sauka tana fada masa kanta na ciwo, ya shiga da ita dakinsa ya nuna mata bandaki da yadda zata yi komai sannan ya fito ya dawo falon ya zauna yana taba wayarsa, har a lokacin sai da ya gwada kiran Number Emily ya ji ta a kashe. Yana ta nazarin abun da zai saka ta kashe wayarta kuma ta dauki lokaci har haka bata kira ba bayan sakon da ya tura mata, duniyar tunani ta dauko shi daga can bangaren Emily zuwa na Turhan idan ya ce be ji tausayin abokinsa ba yayi karya, ya san da zarar Emily ta bayyana a rayuwarsa komai zai zame masa daidai, sai dai kalamansa na dazun cewar da laifin Emily na amincewa ta aure shi ya sanyaya masa guiwa, jikinsa kuma yana ba shi cewar Emily ta yi gaskiya ko Ammy ta san da Fatima a matsayin jikarta abu ne mai wahala ta bar mata ita balle kuma Turhan, hakan ya saka shi ya ji lallai ya kamata ya bar garin Kaduna gobe gudun kar makamancin abun da ya faru a Airport ya sake faruwa, gashi kuma yana son ya san halin da Emily take ciki domin rashin samun wayarta da kuma maido masa da amsar sakonta ya saka shi a damuwa. A tare suka ci abincin da Fatima tana ta fada masa mafarkin da ta yi, ya rigata koshi a dole ya jira sai da ta koshi ita ma sannan ya kwashe kayan ta bishi Kitchen tana kallo komai ta gani sai ta taba ta tambaya, ko ta fadi Momy na irinsa. "Fatima Zaki iya zama a gidan nan ke kadai naje wani guri na dawo?" Ta lake kafada "Aa ba zan zauna nan ba, sai dai mu tafi tare" "Ba zan dade ba kuma zan iya bar miki wayata ki yi game ki yi kallo" "Duka na kalli komai na cikin wayar ni bana son zama" Ya rasa ta ina zai fara rarrashinta ta zauna domin baya son tafiya da ita gidansu Kameela, na farko dai yana ganin hakan kamar cin fuska ne ga Kameela na biyu kuma iyayenta ma ba lallai su fahimce shi ba domin ko kowa be gane yar waye ba Kameela zata gane kuma karamin aikinta ne ta fallasa shi a gabansu. Ya mika mata dayar wayar da ita ya fi aiki da ita ya dauki wanda ya bata dazun ya saka aljihunsa. "Wannan baki san me ke ciki ba, na kunna data zaki iya duba duk abun da kike so a YouTube ki kalli cartoon kuma ki sauke duk game da kike so, Momy ki na na san zata kira ta wannan wayar idan ta kira sai ku yi magana kamin na dawo?" Ya karba ba dan ranta ya so ba, can ta kalli hotonsa dana Kameela dake makalle a falon. "Waye wannan?" "Matata ce" Aiko take ta hade girar kasa da ta sama ya nukokoce kai. "Ba zan zauna ba, so you have a wife" "Yes Baby" "I hate you" Yayi murmushi "I know I'm sorry, Bari na tafi na siyo miki chocolate da ice cream kinji?" Sam ta ki yarda gaba daya mood dinta ya canja daya fada mata yana da mata, ita a tunaninta idan suka saba da shi zata iya dawowa gidansa ita da Emily su bar gidan Vito, amman tun da har yana da mata ai ba wannan damar. "She's ugly" "No she's not" Ya amsa yana dariya. "I want my momy" "Bari na tafi na dawo sai na kaiki gurinta" Daker ya samu ta yarda ta zauna sannan ya dauki dayan key din motarsa ya fice, daga gidan be zame ko'ina sai family house din su Kameela, a bangaren Mama Barakat ya faka ya fito yana tunanin ya kamata ace ya riko musu wani abu, gashi babu enough cash a aljihunsa, sai dai kuma babu yadda ya iya domin ya riga ya zo dama ace be zo ba ne sai ya tsaya ya nema. Haka dai ya aje komai ya shiga bangaren da sallama, yaranta suka amsa masa suka gaishe shi sannan suka kawo masa drink da abincin, suka fice daga falon cike da tarbiya, babu jimawa Mama Barakat ta sauko sanye da wani lace mai tsada irin na su na yarbawa domin zama a cikin hausawa da kuma auren bahaushe be saka ta jefar da al'adarta ba, yaranta ma yawanci da yaren yarbanci take musu magana shiyasa duk sun iya yaren. "Maraba maraba da Aliyu" Ya sauka daga kan kujera ya zauna kasa saboda ta zauna akan kujerar. "Haba zaunawarka mana" "Aa nan ma ya wadatar, na same ku lafiya" "Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya hanya" "Alhamdulillah" "Maa Shaa Allah baka ci komai ba?" "Already sai da na ci abinci na fito" "Tohm, ina godiya dai Aliyu daka saurare ni kuma ka ni umarnina a matsayina na step mother din Kameela, hakan ya nuna kai yaro ne mai jin magana mai biyayya kuma mai tarbiya, na jidadi sosai Allah ya maka albarka" "Ameen" "ka shiga bangaren na su ne?" "Aa na fara zuwa nan ne tukuna" "To yayi kyau, da har jiya nake cewa ina son na sake kiranka, domin Kameela gaba daya ta fara fita hayyacinta abincin kirki bata iya ci, yarinyar nan tana sonka kai ma kuma na san kana son matarka, ni ban san me yake shiga tsakaninku kuke ta samun matsala ba" "Kameela ta cika kishi ne, da abun da ya kai da wanda be kai ba duk na kishi ne a gurinta, bata tsayawa ta saurara kuma bata amfani da tunani kamin ta aikata abu, amman dai In Shaa Allahu ba za a sake jin kam mu ba" "Hakan yayi kyau domin na tabbatar ita ma kanta a yanzu ta dauki darasi kuma zata gyara" "Allah yasa" "Ameen" Mama Barakat ta ji kamar ta masa maganar Emily sai kuma ta ji rashin dacewar hakan, domin be kamata ta shiga tsabgar rayuwarsa ba, bayan kuma ta fada masa Kameela bata fada musu komai ba, sai kawai ta sauke numfashi ta ce. "Tashi ka tafi, ka yi hakuri da duk abun da zaka ji ko ka gani gurin Hajiya, kasan ita uwa dole ta nuna bacin rai idan aka taba mata ya, balle ma Kameela bata fada mana dalilin dawowarta gida ba, amman dai duk yadda zaka yi ka yi iya kokarinka ka tafi da matarka, Allah ya kawar da fitina a tsakaninku" "Ameen na gode Mama, tafiyar ta zama ta gaggawa ban riko komai ba, sai dai idan na koma In Shaa Allahu" "Haba ina ce ai an zama daya, idan zaka zo gida sai ace dole sai ka riko wani abu? Yanzu ai mun zama iyayenka ba surukai ba, saurarena da kai yi kawai ka bi shawarata Wallahi ya fi duk wani abu da zaka ba ni na gode" Yayi mata sallama ya tashi ya fice ta bishi ta kallon burgewa tana jin ina ma ace daya daga cikin yayanta yake aure yadda yake da biyayya da jin magana haka. Motarsa ya shiga ya yi mata key yayi reverse ya shiga bangaren mahaifiyar Kameela yana faka motarsa tana fitowa tare da kanwar Kameela cikin shirinta da alama fita zata yi, Aliyu ya fito mota ya nufo inda suke sai Hajiya ta yi kamar bata ga Aliyu, sallamar da yayi ma kanwar ce ta amsa masa shi ma cikin rainin wayo domin basa kallonsa da daraja gaba daya, ya mika mata gaisuwa bata amsa ba sai kokarin shiga mota take. "Hajiya Gurinki na zo" Ya dago ta kalleshi a wulakantacce kai kace ba shi da gata ko kuma dan talakawa ne. "Ina jinka?" Ya danna tafarfasar da zuciyarsa ke yi. "Na zo ne akan maganar Kameela" "Ina jinka bani da lokacin batawa fa fita zan yi, kuma saboda kai ka san ba zan fasa fitar da zan yi ba" Ya hade yawu zuciyarsa na bugawa da karfi. "Ina son na dauke ta mu koma ne" "Kam uban nan" Kanwar ta fada Hajiya kuma sai ta fito motar "Ka dauke ta ku koma saboda a titi ka aureta? Ko kuma an fada maka bata da kowa? Ai ko baranta muka yi aka ba mu ita sadaka ba zaka shigo haka nan kawai ka dauke ta ku tafi ba, kuma ta inda aka hau ice ai ta nan ake sauka, kai karan kanka baka isa ka zo na tsaya tattaunawa da kai akan matsalarku ba, idan ma bikonta za zo toh ba kai ya kamata na gani ba, domin kai ka maida auren kamar wasan yara, haka kawai dan ta maka dadi zaka turo yarinya gidansu, yanzu kuma da ta yi maka dadi ka shigo kana fada min zaka dauke ta ku tafi, ai ba ni na baka aurenta ba ubanta ya baka aurenta kuma shi kansa yanzu yadda ransa ya bace ba lallai ne ya yarda yarsa ta koma inda ba a san darajarta ba, daman can abu ne da Allah ya riga ya tsara babu yadda za'ayi, amman da na san idan ka aureta haka zaka wulakantata kai da iyayenka ba zan yarda Kameela ta aureka ba ko zata mutu" "Iyakar abun da zamu tattauna tsakanina da Kameela ne Hajiya ban da iyayena, domin iyayena babu abun da suka mata sai alheri, kuma ina tunanin da ace baki ga alamar za a rike Kameela da daraja ba, da ba za ku ba ni aurenta ba" A take Hajiya ta zaburo masa da fada. "Alherin me suka mata? Me suka kulla mata tun da aka yi auren? Duk tsabanin da kuke samu ummi ta taba tako kafarta gidan nan da sunan danta yayi ba daidai ba zata bada hakuri? Mahaifinka ma harkokin siyasarshi kawai ya saka a agaba, yanzu din ma ai ba kai ya kamata ka zo ba iyayenka tun da ba daga mu sai kai muka baka aure ba, kuma Kameela ba daga sama ta fado ba tana da gata, kar na sake ganin kafarka gidan nan da sunan biko wannan iskanci da tsageranci na surukan zamani ni ba zan dauke shi ba, kana neman bata min lokaci ina da abu mai muhimmamci a gabana" Ya koma cikin motar ta shige direbanta ya rufe sannan ya shiga motar yaja suka bar Aliyu tsaye kunshe da bakinciki kamar ya kashe shi, meya ma ya zo tun farko meyasa ya kawo kansa? Sai a yanzu yake bakincikin neman auren kameela tun farko, domin auren macen da iyayenta ba su dattijai ba ne abu ne mai illa sosai ko da kuwa ita yarinyar tana da tarbiya. Shi aka yi ma laifi ya daure a haka ya zo bikon matarsa amman mahaifiyarta take fada masa magana son ranta. Juyawa yayi ya shiga motarsa ya kama hanya yana yi ma kansa alkawari na damuwa ba ko cewa aka yi Kameela zata mutu akansa ba zai dawo bikonta ba. Yana hawa titin unguwar kiran Emily ya shigo wayarsa. Fakin yayi gefen hanya yana maida numfashi a hankali wani irin tafarfasa zuciyarsa take be san lokacin da ya daki sitiyarin motar da karfi ba tsabar bacin rai. Ya sauke ajiyar zuciya ya fi a kirga sannan ya bi kiran Emily da already ya yanke bayan ta yi ringing be daga ba. KAMEELA POV. Tana can kwance dakinta bata san wainar da ake soyawa ba har sai da Hajiya ta kirata tana mata gargadi wai karta kuskura Aliyu yace ta zo suke ta bishi daga ita sai shi ko saukowa ma kar ta yi ya ganta ko da ya kirata. "Aliyu ya zo ne?" "Eh wai wani ya zo bikonki a nan na bar shi na tafi gurin sabgogina" Kameela ta bude baki kamar ta yi magana babu hali, domin ita kadai ta san yadda suka tsara da Mama Barakat har aka samu kansa ya zo, kuma ta san ita ce mai laifi amman be fada a gidansu ba kuma be fadawa iyayenta ba haka kuma ya danne komai ya zo bikonta meyasa Hajiya zata mata? "Hajiya kuma kika ki saurarensa" "Ke dalla can rufewa mutane baki, shiyasa yake wulakantaki ai, saboda baki san daraja kanki ba kina nuna masa rawar jiki da shegen so shiyasa yake gallaza miki yadda ya ga dama har da wani turo ki gida tsabar rainin wayo da wulakanci, kar na ga kafarki waje dan na san halinki shiyasa na kira na gargade ki" Ka kashe ta tashi ta sauri ta leka windows dakinta bata ganshi ba balle motarsa, saukowa tayi kasa ta shiga bangaren Mama Barakat ta tambaye ta ko Aliyu ya shigo bangarenta. "Ya shigo baki gan shi ba?" "Kai..." Ta juya ta fita da sauri tana kiran layinsa bugu daya aka daga sai ta yi shiru tana jiran ya fara magana. "Hello." Ta ji muryar karamar yarinya. "Wacece wannan?" "Hello can you hear me" Fatima ta sake fada domin bata fahimci yaren Kameela da kyau ba. "Yes who are you?" "Sunana Fatima Aisha Emily" Kameela ta sauke wayar daga kunnenta ta duba layi ta ga na Aliyu ne sannan ta sake maida wayar. "Ina mai wayar?" "Ya fita ya siyo min ice cream" "Ke kina ina?" Ta dayan bangaren Fatima ta kalli inda take. "Ina falo" "Falon wa? A ina?" "A gidan Uncle Aliyu" Da turanci Fatima take amsa mata. Kameela ta kashe wayar tana jin wani jiri yana debanta zuciyarta ma tafasa numfashinta har sama yake yana dawowa. Ta nufo bangarensu tana mamakim abun da ya kai wayar Aliyu hannun yar Emily domin ta san suna da ya kuma gashi yarinyar ma ta ambaci sunan mamanta. "Wato Aliyu ba zai rabu da matar nan ba, kuma be shirya rabuwa da ita ba, wai da ita ya zo ne ko kuma yaya? Ni ban gane ba?" Ta haura sama tana magana da kanta kamar wata mahaukaciya. Sai kuma ta sake kiran Number Fatima ta dauka kamar zata yi kuka. "Kina damuna ina kallon Cartoon ne" "Ke fada min a wane falon? PH ko Kaduna?" "Kaduna jirgi muka shigo muka zo Kaduna ko da muka zo ina bachi ma" Kameela ta kashe wayar tana jin kamar ta haukace tsabar bakinciki wato har Kaduna ya zo dayar Emily saboda ya raina aurenta kuma ya raina mata hankali, hijab dinta ta dauka ta saka ta fita dakin ta shiga dakin Hajiya ta dauki makullin mota ta sauko kasa ta fice falon babu wanda ya sani ta shiga motar Hajiya ta dauki hanyar gidan Aliyu, yau kam ta shirya ayi ta kare domin ba zata juye wannan wulakanci da Aliyu yake mata ba akan wata kafirar banza da ba matarsa ba. EMILY POV. Ta sauka Airport around 5:02 tana fitowa ta kunna wayarta kamin ta kira Aliyu sakonsa ya shigo wayarta, bata wani tsaya duba sakon ba ta danna masa kira ringing daya aka daga. "Aliyu ina yata take?" "Hello" Muryar Fatima na dira kunenta ta tsaya cak ta lumshe ido. "Fatima my beautiful baby girl" "Hi Momy" "Ina kike?" "Ina falo" "Falon waye a ina? Ina Aliyun yake ina ya kaiki" "Gidanshi ya fita ya siyo min ice cream" "Momy ki daina damuna ina kallon cartoon ki kira dayan kira dayan wayarshi" "Okay my Love, i love you okay" Bata tsaya amsawa ta kashe wayar ta cigaba da kallonta, hawaye ya saukowa ma Emily sai kuma ta ji wani iri idan ta yi arba da Aliyu me zata fada masa bata yarda da shi ba? But she has no other choice dole ta sanar masa tana Kaduna kuma hankalinta zai fi kwanciya idan yarta na kusa da ita. Ta gwada kiran dayan layin nasa wayar ta yi ringing har ta katse be daga ba, kanta ta sauke kai ta kalli jacket din Dr A-B dake daure a jikinta sai kamshin turarensa take, kira ne ya shigo wayar ta dago da sauri a zatonta Aliyu ne sai ta ga Vito a nan ma bata daga ba har wayar ta gama ringing sai ga kiran Aliyu ya shigo. "Hello" "Aisha" "Naam" Sai kuma ta yi shiru. "Na gwada kiran wayarki bata shiga kuma na miki text baki maido min da amsa ba, lafiya?" "Lafiya ƙalau, hankalina ne ya tashi da kace min ka tafi da Fatima na kasa natsuwa kuma na kira wayarka ban same ka ba..." Magana take a shagwabe tana yi tana yankewa. "Na zo da ita ne saboda na san kina bukatar space, kuma zuwa da ita ba wani abu zai haifar ba In Shaa Allahu lafiya kalau zan dawo da ita, gobe ma zan dawo, I'm so sorry na tafi da ita ba tare da neman izininki ba" "Aliyu ina Kaduna fa..." "What? Wasa kike yi?" Ta girgiza kai. "No da gaske ina Kaduna ina Airport ma yanzu haka, hankalina ya tashi ne please ka fahimce ni ina son yata ba zan taba samun natsuwa idan bata kusa da ni ba" Mamaki ya hana shi kara tambayarta wani abu. "Kina ina a airport din" Ta fada masa sai ya kashe wayar, guri ta samu ta zauna tana ya kallon mutanen dake kai da kawo feeling so guilty kamar wanda ta aikata wani laifi. Tana zaune a gurin har sai da ya sake kiranta ya fada mata inda ya faka ta daga kai tana kallo har ta hango shi tsaye jikin motar sanye da manyan kaya da hula. "Na ganka gani nan zuwa" Ya rike wayar yana ta kalle kalle har ya hangota tafe sanye da riga da wando sai kuma jacket din dake daure a kugunta, gashin kanta ya rabo gida biyu sai bin iska yake tana tarewa. Idan yace Emily bata da kyau yayi karya ta ko'ina ta kai mace duk wani abu da namiji zai kalla a jikin mace ya sota Emily tana da shi, a kokarinsa na haramtawa kansa kallonta gudun wuce gona da iri ya saka shi kawarda idonsa sai ya lura mutanen dake tsaye kusa shi ma kallonta suke, na nesa da ita ma kallonta suke domin ta ko'ina mace ce mai jan hankali, ko ba dan jikinta da kyauta ba dole a kalleta domin gashinta da idonta da kuma hasken fatarta. Hakan ya saka shi jin babu dadi domin a musulunci mace mai kima ce suturta ake. "Hi" Ta fada tana kallonsa a yayinda take tsaye a gabansa, ya kalleta karab idonsa suka fada cikin nata idanuwan masu matukar daukar hankali, sai ta sakar masa murmushinta mai sanyi da kyau, duk wani bacin rai da damuwa dake tare da shi sai ya ji yayi kasa kamar an jefa dutsen kankara a rijiyar dake cike da ruwa take fitar da kara tit tit tit haka zuciyarsa ke bugawa a hankali ba bugawar tsoro ko fargaba ba. "Wane irin dress ne haka? Kin sake komawa Emily dinki kenan nan?" Ta kalli jikinta sai a lokacin ta saka hannunta kwance jacket din Dr A-B dake daure a jikinta. "Haka na zo, Dr Adam Bello ne ya daura min wannan jacket din tasa" Ta yi zaton yadda ta dauro jacket din ne be masa dadi ba. "Waye Dr Adam kuma?" Ta fada masa shi ne likitan da suka hadu asibiti da Tasmia ta kwanta kuma ta fada masa irin hidimar da yayi mata a yanzu har ta samu sauka a airport din. Aliyu ya dan ji babu dadi kadan ko ba komai uwar yar abokinsa ce be kamata ace tana mu'amala da maza anyhow ba, ya san ta dana kyau karamin aikin yan'uwansa maza ne su kawo mata hari da alheri ko da sheri. "I thought i warning you about this, ko ba komai ke fa mace ce kuma uwa, idan ma baki duba duk wannan ba why not ki girmamani kamar yadda kike yi a wacan karon ki saka tufafi masu kima? And baki fada min matsayin wannan Likitan a gurinki ba har kika karasa labarinki" "Ba shi da wani muhimmanci a gurina wannan ne haduwata da shi ta uku" "Me ya same ki a fuska" Bata amsa masa ba ta ce. "Tafiyar ta gaggawa ce shiyasa ban yi tunanin saka wani kayan ba, ma tsorata ne na yi tunanin... I'm sorry ka fahimce ni please, ka san halin da na shiga ba wai ina nufin ban yarda da kai ba amman hankali zai fi kwanciya idan Fatima tana kusa da ni, na zo na dauke ta ne sai mu koma gobe dan Allah karka min rashin fahimta" Ya motsa bakinsa a hankali har wani iri yake ji saboda yadda ta marairaice murya da fuska tana masa magana sai ya dorawa kansa laifin tayar mata da hankali na tafiya da yarta ba tare da amincewarta ba. "Ma fahimta, shiga mota mu tafi" Ya bude bangaren da yake tsaye ta zagaya ta shiga baya ta zauna gudun kar ayi masa mummunar fahimta domin ta fahimci shi din mutum ne mai mutunci kuma kai addinin. Be ce me yasa kika zauna a baya ba yaja motar suka fara tafiya be yi nisa ba ya samu kansa ta saita madubin gaban motar zuwa saitin da Emily take zaune a baya ba dan komai ba sai dan yana son karantar yanayin da take ciki, jikinsa na bashi wannan kwancin jinin dake fuskarta dukanta Vito yayi ko kuma wani abu ya faru tsakaninta da Dr A-B din ne, waya sani ma ko Vito ne ya cilasta mata zuwa ta tafi da Fatima, sai tausayinta ya kara kamashi, mutanen da babu zumuntar nesa ko ta kusa suna ta juyata yadda suke so saboda rashin dangi da wanda zai tsaya mata. "Shi likitan yayi kokarin taba mutuncinki ne?" "Aa" Ta amsa tana kallon titi. "Ba zaki fada min abun da ya sami fuskarki ba?" "Duka ne" Tun da ta amsa da duka ne ya fahimci wanda yayi mata dukan ba sai ta fada ba. "Saboda na taho da Fatima ne?" "Ba yau ba ne tun wacan ranar ne da na saka Abaya" "Shiyasa kika hana na ganki? Karya Tasmia ta min kenan?" Ta yi shiru idonta na cika da hawaye ta share, be sake cewa komai ba ya cigaba da tukin har ya iso gida yayi horn mai gadin ya bude masa ya shiga ya faka motar harabar gidan ya fito, Emily kuma ta zauna domin bata san su waye a gidan ba kuma be ce ta fito ba. Zagayawa yayi bangaren da take ya bude kofar bayan ya bar kofar a bude ba tare da yace mata komai ba. Tana ganin haka sai ta sako kafafuwanta kasa ta fito tana rike da jacket din. "Na taho?" Ta tambaya kamar mai jin tsoro, Aliyu ya juyo ya kalleta ya girgiza mata kai. "Bari na daukota" Ya shiga ciki ita kuma ta tsaya a gurin ta rumgume hannayenta, ba a dauki lokaci ba ta ga ya fito da sauri ya nufi gurin mai gadi. "Malam Tahir ka ga wata karamar yarinya ta fito nan waje?" "Eh sun fita ita da Hajiya, ba su ma wani jima sosai ba Hajiya ta zo da mota ta dauke ta suka fita" "Hajiya? Wace Hajiya? " Hajiya ta gidan nan" "Kameela" "Eh ranka ya dade" "Me ya faru" Emily ta tambaya tana karasowa inda suke tsaye. Aliyu be ce mata komai ba yayi hanzarin ciro wayarsa aljihu ya kira Kameela kusan 3 missed call bata daga ko daya ba. "Ina Fatima? Ni fa ban gane ba" Ta tambaya hankali a tashe "Kameela ta dauke ta" "Kamar ya Aliyu karka min haka idan ma wasa kake dan Allah ka daina ba haka muka yi da kai ba ina yata take?" Bata tsaya jiran amsarsa ba ta nufi kofar falon ta shiga da gudu. Aliyu kuma ya bude motar sa a fusace ya shiga yana jan numfashi da karfi ya dauki hanyar gidansu Kameela. Emily ta duba duk inda zata iya na falon domin ba wani sanin gidan ta yi ba, ta kalawa Fatima kira shiru ta shiga har dakunan data gani ta duba bata ta ga Fatima ba ta sauko tana kiranta bata ji ta ba. Da wayar dake hannunta ta yi amfani ta kira layin Aliyu na farkon wanda ta kira da shi dazun har Fatima ta daga. Kiran ya shiga yana bugawa tare da bugun zuciyarta. "Hello Fatima my baby girl where are you?" Shiru ba'ace komai ba. "Hello Baby Girl talk to me, ina kike?" Shiru ba'ace komai ba. Ta yi zaton Kameela ce dan haka ta fara magana cikin kaushin halshe. "If you hurt my baby Kameela, sai na kashe ki Wallahi sai na halaka ki" "Your Baby is in safe hands..... Aisha... Emily..." Ta ji an fada cikin wani sauti mai kamar rada kamar rarrashi, da wata murya da bata fatan sake jin irinta, dip bugun zuciyarta ta tsaya wayar ta subuce tsakanin hannunta da kunnenta ta fadi kasa... _________________ Na biya bashin jiya kuma na yi long page Kar inji wani yace Pim.... 😎 [7/4, 5:08 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 4️⃣6️⃣ KAMEELA POV. Tun da ta fara tukin bata tsaya ko'ina ba sai bakin gate din gidanta, ta yi horn mai gadin ya leko ya ga ita ce ya koma ciki ya bude ta shiga ta faka rai a bace bata ko tsaya kashe motar ba ta fita ta banki kofar falon da karfi ta murda ta shiga, Fatima dake zaune kan kujera ta zabura ta mike tsaye tana kallon Kameela. Kameela ta harari Fatima kasa da sama ta tabe baki. "Eh lallai ashe da gaske ne, amman Wallahi Aliyu ya gama cin mutumci na, kuma ya nunawa yarinyar shegiyar matar nan ba ni daraja a gurinsa" Ta yi kwafa ta shiga kitchen din ta duba abincin da suka ci suka rage, ta fito tana tambayar Fatima da turanci. "Ina Emily take?" "Tana can ba da ita muka zo ba" "Ke ma da ganinki zaki yi munarfuci, waya sani ko daukota yayi har uwar suka zo" Ta fada da hausa sannan ta kama hannun Fatima ta karbe wayar hannunta. "Ai yau za'ayi ta ta kare, sai na datse duk wata alaka dake tsakanin matsiyarcin uwarki kwartuwa mai bin mazajen mutane" CONTACT list dinsa ta shiga ta nemo number Ammy ta kirata da layin Aliyu, Ammy ta daga tare da sallama, Kameela ta amsa tana fadar ba Aliyu ba ne. "Ni ce Ammy matarsa Kameela" "Maa Shaa Allahu Kameela kina lafiya ya gidan?" "Ammy ba lokacin gaisuwa kwatancen gidanki zaki min faka faka" "Lafiya?" "idan na zo zaki ji Ammy fada min kawai" Ammy ta kwatanta mata Kameela ta sauke wayar ta kama hannun Fatima sai Fatima ta ficike hannunta. "My Momy warn me not to talk to strangers" "Aliyu ne ya ce na zo na tafi da ke yana can wani gida zai siya miki ice din yace ma kawo ki" Fatima na jin haka sai ta yarda Kameela ta kama hannunta suka fita ta bude mota ta saka ta ta shiga taja motar mai gadin ya sake bude mata ta fita, tana tukin tana bala'i Fatima sai kallonta take domin bata jin yaren da take. "Ki bani wayar zan cigaba da kallona" Kameela ta mika mata wayar ko kira zata yi ai ba shi da amfani yanzu tun da ta riga ta san gidan Ammy, daman sau daya ta taba zuwa shi ma kuma Aliyu ne ya kaita. "Dan ubanki gurin uwar ubankin zan kaiki, ayi ta ta kare, na huta da wannan bibiyar da uwarki take ma mijina, sai kace shi yake nemanta, ga mai nemanta ga wanda take likewa, ina na taba ganin haka dan kawai neman a dora min hawan jini" Bata sha wahala gurin gane gidan ba kasancewar unguwar ba a boye take ba, kuma gidan babban gida ne a layin, tana isa bakin gate din gidan ta gane lallai gidan dai da suka taba zuwa da Aliyu sau daya. Ta yi horn mai gadin ya bude mata ya shiga ciki ta faka ta zagayo ta budewa Fatima ta riko hannunta ta fito da ita. "Ina yake?" "Yana ciki sai mun shiga" Fatima ta bita babu wani rigima suka shiga cikin falon, tsabar neman fitina da tsoron abun da zata aikata da kuma bakin kishi da suka hade mata guri daya Kameela har numfashi take sama sama kamar wanda ta dauko katon dutse. Da sallama ta shiga falon Yan matan nan biyu da Ammy take riko suka amsa mata, Ammy na zaune kan kujera nurse na kusa da ita tana hauna bp dinta, daman ta fi yawan zaman falon gudun wahalar da mazu zuwa ganinta ba sun haura sama inda take ba. "Ina yake?" Fatima ta tambaya da karfi tana fisge hannunta daga rikon da Kameela ta yi mata. A take Kameela ta daka mata tsawa ta watsa mata harara. "Ki zauna" "Ba zan zauna ba, ina Uncle Aliyu? Kina kokarin sace ni ne? Su waye wadannan mutanen mama na tace kar na yi magana da wanda ban sani ba" Ta saka ihu mai karfi babu saurara ahhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh ta cika musu kunne. Ammy ta kalli Kameela tana tambayar tafiya, Kameela ta rasa ta ita zata fara bayani ga Fatima na mata ihu gashi bata san yadda zata fara warware zaren zancen ba. Ihun Fatima ne ya saka Turhan dake dakinsa cikin damuwa ya saukowa kasa domin duba abun da ke faruwa. Saukowa da Turhan yake ne a hankali ya saka Ammy daga kai ta kalleshi daga kansa ta sauke idonta akan Fatima dake ta ihu, sai gata a tsaye kamar ba marar lafiya ba. Ta ko'ina Fatima kama take da Turhan kamar an tsaga kara kamar har ta bace har gashin kanta baki ne kamar na mahaifinta sai ka rantse tsumata aka yi a cikin jikin Turhan aka ciro bata rage komai nasa ba, banbancin kawai ita mace ce shi namiji kuma ita tana karama shi kuma babba. "La'ilaha illallahu, La'ilaha illallahu, La'ilaha illallahu" Kawai Ammy take maimaitawa jikinta na rawa hawaye na sauko mata. "Yauwa kin gane kenan" Kameela ta fada kamin ta juya ta kalli Turhan daya tsaya be karaso ba, bata san yana garin ba sai a lokacin. "Alhamdulillah faduwa ta zo daidai da zama" Ta fada tana kallon Turhan da gabansa ke dukan uku uku ba kuma tare da fahimtar komai ba, shi dai ya san ba lafiya ba, ganin yadda Ammy take ta ambaton Allah ta mike tsaye ga kuma yarinyar dake ihu ga kuma Matar Aliyu. "Ka karaso mana Turhan wannan yarka ce" Turhan ya kalleta ya kalli Ammy. "Ban fahimta ba" "Yarka ce sunanta Fatima, Emily ta haife ta muma jininka ce Aliyu ma da kansa ya fada, tana boye maka ita ne tana boye maka kanta, ni na gaji shiyasa nake son ayi ta ta kare shiyasa na kawo ta, na gaji dan Allah idan ka ga Emily ka rike ta na huta, na samu kwanciyar hankali da mijina, ta kyale min mijina dan Allah duk wani boye boye da ake ban gane kanshi ba, matar nan ta hana ni zaman gidana cikin kwanciyar hankali abun ya wuce PH ya biyo har nan Kaduna na gaji, Aliyu be san na kawo ta nan amman na san dole Emily zata zo" A cikin kalamanta babu wanda Turhan ya ji kuma ya fahimta sai kalmar ƳARKA CE... kalma ta maimaita kanta a kunensa ya fi sau saba'in tun da ya dora idonsa akan Fatima be kyabta ba, sigar jikinsa kawai ke tashi zuciyarsa ta karaya bugun zuciyarsa ya karu fiye da kima, sai a yanzu ya fahimci Ammy na ambatar Allah ba tare da an bata mata ba, kamaninsa ne sak a fuskar Fatima. "Ke dalla dufewa mutane baki kin ga ubanki can" Kameela ta fada ma Fatima da turanci tana nuna mata Turhan. Sai Fatima ta lake kafada ta fara magana cike da tsiwa da iyayi. "Noooo Momy ta fada min ni bani da Baba ni kadai aka haifa haka, kowa yana da Baba amman Momy tace ni ba ni da Baba baki kiji sunana ba Fatima Emily Aisha" Turhan ya zube kasan guiwowinsa ya daga kansa sama ya bude baki yana numfashi da karfi kamar wanda zai mutu. Fatima ta fashe da wani irin kuka mai karfi na gaske domin bata fahimci me suke ba, gashi bata san kowa ba a cikinsu yanzu kam ta fara tsorata. "Take me back to uncle Aliyu or Momy" Kameela ta buge hannu. Ammy ta karasa ta dafa Fatima tana kuka ta kama fuska tana kallo, ta zube a gurin tana ta taba taba jikin Fatima "Allah na gode maka, Allah Aisha kawai nake nema amman ka hado min har da yarta, jikata Allah na gode, Allah ya miki albarka Kameela" Kameela dai bata ce komai ba ta juya ta fice da sauri. "I want my momy" Ammy ta dorata a cinyarta tana kuka ta rumgumeta. Turhan ya ka dagowa daga inda ya fadi durkushe ya kara karasa gurin da Fatima take jikinsa da zuciyarsa sai rawa suke abun ya zo masa kamar mafarki, ya rasa ta yi zai yi ya yarda wannan abun ba mafarki ba ne, shi dai Emily kawai yake nema shi ma kuma saboda Ammy. Da rarrafe ya karasa gurin tana kallon Fatima ya kai hannunsa zai taba ta sai ya kasa ya maida hannu, ya shafe hannunsa jikin rigarsa gaba da baya kamar mai kokarin cire kazanta ya sake mika hannunsa zai taba ba a nan ma ya kasa jikinsa sai rawa yake. "Yarka ce Turhan, jinin ya fi ruwa kauri, jini be karya, yarka ce" Ammy ta kama hannun Turhan ta kai a jikin Fatima, sai ya ji wani abu kamar shokin Fatima kuma ta zabura da karfi, a take ya tuna da abun da ya faru a airport lokacin da suka hadu da Aliyu ya taba babyn da yake dauke da ita tana bachi amman sai da ta zabura. Turhan ya fisge Fatima a jikin Ammy ya rumgumeta da karfi jikinsa ya mike tsaye yana kuka kamar wani karamin yaro, a take kukan Fatima ya yanke ta yi shiru kamar ba ita ba, ita m ta ji wani abu na dabam gashi ta ji yana kuka bata san dalilin ba, daga tsayen kukan ya kasa rike shi ya zube kasa yana rumgume da ita, kusan kowa a falon kuka yake har Nurse din da bata san hawa da sauka ba. Ammy ta daga hannunta tana magana. "Haka na yi nufi, ku zauna tare ku yi zuri'a ta dalilina, Alhamdulillah ko a yau na mutu burina ya cika, na ga jininka Turhan, ashe ba a banza na ke jin bukatar ganin yarinyar nan ba, ashe akwai abun da Allah ya shirya min da ban sani ba Allah na gode" Ta shafa kan Fatima ta shafa kan Turhan hawaye da murmushi, Turhan ya kwanta jikinta yana rumgume da yarsa Fatima. Wayar dake Hannun Fatima ta yi ringing Turhan ya dago da sauri ya karɓi wayar, Emily ya gani rubuce a wayar ya amsa kiran amman ya kasa cewa komai. "Hello Fatima My Baby Girl where are you?" Muryar da ya dade yana nema ta daki kunensa, amman ya kasa amsawa. "Hello baby girl talk to me, ina kike?" Muryar matar daya wulakanta ya nuna mata rashin gata da kiyayya ce take sake magana, ya rasa ta ina sauti zai fito daga bakinsa. "If you hurt my baby Kameela, sai na kashe ki Wallahi sai na halaka ki" Daker ya iya hada kalmomin bakinsa cikin wata iri siga ta kwantar da hankali da rarrashi da be taba sanin yana da ita ba ya furta. "Your Baby is in safe hands....Aisha.... Emily...." Daga nan be sake jin komai ba, aje wayar yayi ya kara rumgume Fatima a kirjinsa yana motsawa a hankali kamar wanda ke rike da sabon kwai. "Momy ta fada min ba ni da mahaifi waye kai?" Fatima ta tambaya tana ta sauke ajiyar zuciya na kukan da ta yi da karfi, Turhan ya girgiza kai ya rufe ido ya kasa cewa komai. KAMEELA POV. Ta kama hanyar komawa gida wata zuciyar na raya mata ta koma ta dauko yar mutane abun da ta aikata zai batawa Aliyu rai, wata zuciyar kuma na raya mata abun da ta aikata daidai ne domin idan ba haka ba Aliyu ba zai fita sabgar Emily ba, gashi abun har ya fara wuce gona da iri, ta san yadda Emily take da kyaun nan komai zai iya faruwa, idan ba haka ba bata ga dalilin Aliyu na boyewa Turhan lamarin ba. Ta isa ta faka motar waje ta fita ta shiga dakinta amman ta kasa natsuwa gabanta sai faduwa yake tana ta jin tsoro da tunanin abun da Aliyu zai fada mata, iyakar abun dai yayi fada yayi fushi, ko kuma yace ba zata koma yanzu ba, idan kuma ya wake ni fa? Ta raya ma kanta. No ba zai ma taba farawa ba da na saka masa guba ma be sani ba balle dan wannan. Kiran wayar Aliyu na shigowa wayarta sai da ta zabura tana kallon wayar har ta gama ringing bata daga ba, ya sake kira baya daga ba har yayi mata kira uku, tasowa ta yi ta fito daga dakinta ta zauna falo tana ta sake sake ta san ko ta koma Turhan ba zai bata yarinyar nan ba, ko da ya bata ai aikin gama ya gama ta fada musu komai, ta saka wannan ta kwance ita kadai ita dai babban hujjarta ita ce Emily tana kokarin anshe mata miji alhalin ga mai nemanta har da ya a tsakaninsu. Tana jin tsayawar mota ta leka Window ta hango motar Aliyu sai ta nufi kofar falon da sauri ta bude kamin ta saka kafarta waje har ya iso bakin kofar falon cikin wani irin yanayi da bata taba ganinsa a ciki ba, kuma bata taba tsorota da bacin ransa kamar na yau ba. Baya baya ta yi hakan ya ba shi damar shigowa falon fuska kamar bakin hadari. "Ina yarinyar da kika dauka take?" "Tana gurin da ya kamata ta kasance, gurin mahaifinta" Aliyu ya dauke ta mari da bayan hannunsa, sautin mari yayi mata chauuuuuuu har cikin kunen, ta dafe kuncinta ta zaro ido kamar za su fado. "Saboda wata banza zaka mare ni a cikin gidan Ubana Aliyu?" Ta daga hannu zata rama ya rike hannu ya jefar ya sake sauketa da mari sai da ta fadi. Mai aikinsu ta fito da sauri, kanwarta Farida ma ta fara saukowa da gudu. Aliyu ya nunata cikin tsananin fushi. "Abun da kika aikata ba kishi ba ne, hauka ne da rashin tunani, kin dauki yarinya kin dankata a gurin mutumen da bata taba sanin waye shi a duniya ba, kin rusa abota da aminci da ke tsakanina da Turhan na shekaru da yawa, kin yi sanadin karya alkawarin da na daukarwa Emily, kin zubar da kimar da Ammy take kallona da ita, wace irin mace ce ke? Alkawarin da na miki be wadatar ba? Bibiyar wayata be gamsar da ke ba? Kokarin kashe ni be saka kin natsu ba? Toh babu abun da zai sauya halinki Kameela, na gaji ko diamond ce ke haihuwar gold na hakura dake Kameela, na dauki abun da zan iya dauka yanzu kam anyi na karshe... NA SAKE KI... Enough is enough" Ya fada kai tsaye sannan ya juya ya fice daga falon ya koma motarsa, yaja ya fice daga gidan rai a bace, gidansa ya sake komawa domin a can ya baro Emily. Ya shiga cikin gidan ya faka ya fita motar ya shiga falon gidan, tsakiyar falon ya samu Emily duke dafe da kanta wayarta kuma a kasa. "Emily..." Be fadi abun da yayi nufi ba ta katse shi. "I want my baby" "Ta... Ta... Tana.... Gurin... Turhan..." "I know ka kawo min yata, ba zan je can ba saboda bana son ganinsa bana son jinsa" "Okay but i want you to know ba ni na shirya wannan ba?" Ta mike tsaye ta daka masa tsawa. "To waya shirya?" "Calm down Emily ki kwantar da hankalinki" Ta zaburo masa ta yi cikinsa da masifa idonta na cika da hawaye. "How dare you told me that? Kana son kwanciyar hankalina ka taho min da ƴa? If you didn't plan all this taya ka san Turhan ya zo? Meya ka zo garin nan just for two days? Ka taho da Fatima ba tare da na sani ba ba, that's means ka san da wani abu Aliyu! Zuwa ba tare da ka sani ba ya rusa yadda ka tsara abubuwa shiyasa ka saka matarka ta dauke ta kamin mu zo ta kaita gurin Turhan right? Saboda ka san ina son yata dole na kai kaina a gurinsa ko? Ka min alkawari Turhan ba zai taba sanina ta hanyar ka sai idan ni na bukata, ina alkawarin yake? Ka ci amanata ba zan sake yarda da kai ba Aliyu, kallon da nake ashe ba haka kake ba, ka dawo min da yata Aliyu" Wani irin ihu take kamar zata tashi gidan sai da Aliyu ya ji wani tsammmmm yayi baya ya runtse ido ya bude saboda tsawar dake saka masa, ya juya da sauri ya fita a rikice. Motarsa ya koma ya koma ya shiga ya dauki hanyar gidansu Ammy. Zuciya a karye jiki a sanyaye kunyar yadda zai yi ido hudu da abokinsa ya rufe shi amman a haka ya daure ya shiga gidan saboda Emily ya san idan be dawo mata da Fatima ba ba zata taba yarda da shi ba, kuma ya san gaskiya idan ba shi ya dawo da Fatima ba Turhan ba zai bata yarinyar nan ba. Be raina kansa ya kara girmama laifin da Kameela ta yi ba sai da ya isa bakin kofar falon Ammy for the first time ya ji kunya da nauyi tura kofar dakin ya shiga, yayi unkurin fasawa ya fi a kirga kamin ya samu kuzarin tura kofar ya shiga da sallama. A tsaye ya riski Turhan yana maida hannayensa duka biyu a baya ya daure fuska yana kallon kofar falon da alama yana jiran shigowar Aliyu ne. Aliyu be taba gani abokinsa a cikin irin wannan yanayin ba sai yau. Aliyu ya gagara furta komai sai kallon Turhan yake babu kowa a falon sai shi kadai. "Fatima ka zo nema ko ka zo ka shirya wata karya ne? Ka ba ni mamaki Aliyu, daman ance acikin abokai da yan'uwa akwai makiyan mutum a yau na yarda, me na maka? Miye manufarka na boye Emily? Matar da ka san nemanta nake ido rufa? Matar da saboda ita mahaifiya ta gagara fahimtata har take ciwo? Abun bakin ciki kuma da kai nake shawarar nemanta? Har a airport na hadu da kai amman ka gagara cewa yata ce? A tsawon lokacin nan a tsawon wahalar nan ka san inda Emily take ka boye min? Da kai muka zo nan kana jin kalaman Ammy akaina amman ka gagara furta cewar ka san inda Emily take? Miye manufar ka? Wallahi kallon mutunen kirki nake maka aboki da ya juye ya zama kamar dan'uwa amman a yau wannan duk ya kau... Ka zama koren maciji a cikin korayen ciyayi, mutum mai fuska biyu! But thanks to your wife daman haka abun yake ka ci amanar wani kai ma aci taka, ta bayyana komai a lokacin da ya dace" Har lokacin Aliyu ya rasa abun cewa tambayar ina Fatima take ma ya gagara yi, Ammy ce ta fito dakin dake kasa a falon, Aliyu ya kalleta cike da kunya da nauyi, ya ambaci sunanta wai ko ita zata fahimce shi. " Ammy..." "Aa Aliyu ban da yau, da ka dauke ni uwa da baka aikata haka ba, na tabbatar da Ummi ce ba zaka aikata mata abun da ka aikata ba, ka ba ni mamaki shiyasa hausawa suka ce halin mutum dabam kalamansa dabam, bana son wani abun bacin rai dan Allah ka tafi" Ya juya ya fice daga falon tsabar kunya da bakinciki yana jin kamar kasa ta bude ya shige ciki ta rufe da shi, yana tafiya yana jin kamar ba kafafuwansa ba, haka dai ya shiga mota ya sak juyawa ya fice gidan sai kuma ya rasa ina zai tafi, ya san be isa ya koma gidansa ba tare da Fatima ba to yace ma Emily me? Haka kuma be isa ya dawo ya ce Turhan ya ba shi Fatima, gaba daya sai ya rasa ina zai saka kansa, gefe hanya ya faka ya bude motarsa ya fito yana sauraren kiran sallah da ake ko zai samu sallama. Shi ma dai yau ya zama marar mafaka be da wani gurin fakewa sai gurin mahaifiyarsa, wayarsa ya ciro ya kira Ummi tana dagawa ya ce. "Ummi ki min addu'a dan Allah" "Lafiya Aliyu" "Ba lafiya ba, kawai ki min addu'a ko zan samu mafita" "Ka daga min hankali wace irin addu'a zan maka? Me yake faruwa?" A takaice ya labarta mata abun da zai iya na haduwarsu da Emily zuwa abun da ya faru yau. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, abu be yi dadi ba Aliyu ka yi sakaci na shiga tsakanin mutane biyu, gashi Allah ya baka mata da bata dace da kai ba ta jefaka a kunya, sannu a hankali idan baka rabu da yarinyar nan ba, nan gaba kadan ma sai ta yi kokarin kashe ka" "Already ta gwada Ummi ta saka min guba a abinci saboda Emily, amman ban ci ba sanadin haka na maida ita gida Mama Barakat ta ba ni shawarar maida ta na dawo ne wannan abun duk ya faru, but i divorced her today" "Guba kuma..... Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un..." Ummi na rufe baki ta ji Aliyu ya amsa yana fadin Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un da karfi sai maimaitawa yake wayar ta fadi yana nishi da karfi sai karar abu take ji kamar ana dukansa. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un.... Aliyu.... Aliyu.... Lafiya? Kana ina?" Baya ina magana sai karar take ji kamin ta soma jiyo hayaniyar mutane sai kuma kiran ya yanke. "Sun kashe min ɗa sun kashe min ɗa, ko dai Turhan ko ita yarinyar ko Kameela sun kashe min ɗa, Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un..." Ta fada da karfi tana fitowa dakinta da gudu har tana zubewa kasa ta tashi tana kuka. TURHAN POV. Bayan Aliyu ya wuce ya ji ba zai iya natsuwa ba ya haura sama ya dauko keys din mota ya sauko keys din a hannunsa. "Ina zaka je?" "Gidan shi zan tafi ba mamaki Aisha tana can, ina bukatar ganinta kuma ba zan sake bari ya keba da ita ba" Ya fice da sauri ya shiga motar da ya dauko key dinta mai gadin gidan ya bude masa ya fice, Ammy fitarsa da mintuna kadan Ammy ta kasa natsuwa da hakan ta dauki wayarta ta kira direban ta ya shirya mota ta saka hijabinta ta bi bayansa. @360 Turhan ya isa kofar gidan Aliyu, yayi horn da karfi babu daga kafa mai gadin ya fito a tsorace ya leka motar. "Me gidan baya nan" "Bude min Malam" Turhan ya fada da karfi mai gadin ya kuma ciki yana fadin "Allah yasa lafiya wannan lamari dake faruwa" Ya bude masa gate din Turhan ya shiga habarta gidan ko fakin din kirki be yi ba ya fita motar ya doshi kofar falon Aliyu ya tura kofar ya shiga Emily na zaune kan kujera ya duba ko'ina a gaggauce ya nufi sama ba dan be ganta ba sai dan tunaninsa da idonsa ba su zayyana masa matar da ya gani zaune a falon a matsayi Emily ba, sai da yayi rabin stairs din idanuwansa suka dawo masa da kamanin jan gashin da ya gani a gurin mace da ya tarar a falon sai ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba, yana kokarin kamanta Emily da wannan matar da ya gani a yanzu. Ya juyo ya kalli Emily da ko kadan bata kalli inda yake ba, sun yi kama ta gashi da hasken fata har ma a fuska amman wannan ta fi Aisha da yake nema kyau da tsari sau miliyan ma, to amman idan ba Aisha bace to wacece? Ya sauko yana kallonta har ya karasa inda take zaune ya tsaya gabanta zuciyarsa kamar zata fado, tsabar kwarjinin da ta cika shi da shi. Sai a lokacin Emily ta mike tsaye ta kalleshi. Cikin tsakanin mamaki da kokarin tantance Emilyn din ce ko mai kama da ita ya furta sunanta a zuciyarsa. "Aisha.... Emily..." Be sani ba ashe tsabar mamakin be iya rike kanshi ba, daga kasa ya kafara kallonta turawa suka ce from toe to head yana kaiwa saitin fuskarta ya ji sauka abu mai sanyi a tsadaddiyar fuskarsa. Touf... Ta watsa masa yawu a fuska. Ya runtse ido da karfi ya jimke hannunsa da mugun karfin numfashinsa na fita da karfi, babban wulakanci a gurin balarabe shi ne ka jefe shi da talkami ko ka tofar masa da yawu. Sai dai a yanzu be isa ya nuna komai ba a hankali ya bude idon, ya sake kallon idanuwanta da be taba ganin tsarinsu da kyau ba sai a yau, tassaa ta wanke masa fuska da mari sannan ta kauce gaba gabansa ta nufi kofar fita falon kamin ta karasa Ammy ta shigo falon da saurinta jikin na rawa na son arba da Emilyn da take ta nema tsawon lokaci. __________________ ABOKIN RAYUWA.... ✍️ [7/6, 9:18 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 4️⃣7️⃣ Ammy ta nufo ta cike da rawa jiki Emily kuma bata fasa dosar kofar ba har sai da ta ita da Ammy suka yi kicibus a falon, Ammy ta kai hannu zata taba Emily sai Emily ta matsa baya. "Yata Aisha muna ta nemanki ina kika shiga? Ke ce haka? Ina Ibraheem?" "Aisha ta dade da mutuwa..." Emily ta fada, Turhan ya juyo da sauri daman zuciyarsa bata gama gamsuwa cewar wannan din Aishar da yake nema ba ce domin ta canja gaba daya. "Aisha ta mutu tun a ranar da kika yi son zuciya kika aurawa mugun danki ita, wannan Emily ce ina yata?" Ammy ta kalli Turhan idonta na cika da hawaye sannan ta kalli Emily tace. "Aisha ki yi hakuri.. Wallahi..." "Ba maganarku na zo ji a nan ba, ina yata take?" "Tana nan lafiya, Aisha dan Allah ki saurare ni mu yi magana, na san kina cikin bakinciki amman yadda zuciyarki take raya ba haka ba ne" "Where is my baby? Bani da wata alaka da ku, and bana cikin bakinciki ni baki gan ni ba? Na wuce yadda kuke tunani, ina yata take?" "Tana gidana dan Allah Aisha ki saurare ni mu yi magana, tsawon shekara shida kenan muma nemanki, ba ni da lafiya amman da na ga sanadin ganinki sai na ji na warke, daman ciwon har da ke ne" Emily ta tabe baki. "A tsawon shekarun nan Ammy kike tunanin zan sake yarda da shirinki ne? Kin yi amfani da kyautatawarki kika cutar da ni yanzu kuma kina tunanin amfani da ciwonki zai saka na yarda ke sake cutar da ni ne?" "Wallahi ban yi dan na cutar da ke ba! Duk wani abu da Turhan yayi miki ban san zai miki ba, ban san haka zai faru ba, ki fahimce ni mana wannan duk ba halinki ba ne waye hore miki kunne haka?" Ammy na maganar cikin kuka domin gaba daya Aisha ta canja mata tun daga shigarta har kalamanta da kamaninta sun sauya. "Ni da na zauna da kazakin mutum kamar wacan har jira nake wani ya hore min kunne" "Kina cikin fushi ne kawai har yanzu, da zaki yi hakuri ki bi ni gida zamu karshe duk wannan" "Har abada ni da gidanki, ba ni ba wata alaka da ke" Turhan ya karaso gurin yana jin ransa na baci saboda kalaman da take furtawa ga Ammy. "Aisha da ni kike da matsala ba da Ammy ba, wannan...." Be karasa ba ta dauke shi mari, Ammy ta rufe baki Turhan kuma ya runtse ido ya bude ya kalleta idonsa har suna canja kala. "Har yanzu haukarka na baka zaka iya kiran sunana? How dare you? How dare you zaka tsaya a gabana har ka ambaci sunana? A tunaninka har yanzu wacan yarinyar ce da ka maida baiwa a bakar masarautarku? Ka fadawa kowa kurma ce? Ka hana ta magana? Hadiman matarka suke dokanta? Matar da aka sadakar a matsayin baiwa ga wasu mutanen? Ai Abun kunya ne aji kana nemanta, ko da yake mutane irinka ba su da kunya" "Aish..." Yana sake bude baki ta sake dauke shi da mari. Sannan ta kalli Ammy ta ce "Ina yata take?" "Tana nan lafiya ki yi hakuri ko dan ita ki saurara ni" "Baki da wannan matsayin Ammy, kin rusa wacan kallon da nake miki, saboda kin nade bakin maciji a farin kyale kika damka min, saboda na yarda da ke kuma ya tsare ni, ban mutu ba sai dai wani abu da ya alakance ki da zuri'arki ya mutu tun a wacan ranar, baki da wannan kimar a ido na yanzu, saboda haka ina Yata take?" "Aish..." Turhan na bude baki zai furta sunanta Emily ta sake juyowa ta dauke shi da wani mahaukacin mari sai da ya nisa "Ahhhh" Ya cije hakora ji yake kamar ya rama amman ya kasa. "Huhmmm Aliyu yana ba ni mamaki, indai Har zai iya boye min inda kike da kuma alakata Fatima to zai iya komai" Yayi furucin da yakinin shirya mata komai aka yi aka hure mata kunne domin sanin da yayi ma Emily ba zata iya tsayawa tana fada masa magana haka ba, amman gashi har da mari, kuma ya san ba kowa zai yi haka ba sai Aliyu mutumen da ya dauka a matsayin aboki ashe makiyinsa ne be sani ba. "Kana nemana saboda ka maida ni masarautarku na cigaba da bautawa matarka? Idan akana akwai wata alaka ta nesa ko ta kusa tsakaninka da Fatima to hauka kake yi" Ta nufi kofa zata fice Ammy ta riko jacket din Dr A-B dake hannun Emily tana rokonta. "Ina zaki je? Aisha dan Allah ki saurare ni ko dan shekaruna?" Emily ta tsaya kamar abun arziki ta juyo. "Danki ya kamata ki fadawa wannan, shi ya kamata ya fi kowa sanin daraja da kimarki ya kyautata miki ya riƙe amanarki, shi be yi ba sai ni da ban hada komai da ke ba?" Ammy ta girgiza kai. "Wannan ba Aisha da na sani ba ce" "Wacan Aishar da kika sani ai ita kika aurawa mutumen da ya tsoratata tun gabanin a daura masa aure da ita, mutumen da ya gargadeta kar ta yarda ta aure shi, ita kuma a kokarinta na maida alheri da alheri ta danna komai ta aureshi, wacan Aisha itace Aishar da ya tofawa yawu a fuska a ranar da aka daura aurensu, ita ce ya kira ranar da aka dauranta da shi a matsayin bakar rana a gurinsa, ita ce macen da ya maida baiwa ya masarautarsu, take bautawa matarsa, ita ce ya gabatar a matsayin kurma a masarautarsu kuma ya cilasta mata amsa haka, wannan kuma Emily ce ta sha banban da wacan" Ta fisge rigar ta fice abunta, Ammy ta kafe idonta akan danta cikin wani kalar yanayi na bakinciki da takaici, matsawa yayi kusa da ita kamar zai mata bayani amman ya kasa cewa komai sai motsa baki yake. "Da gaske ne abun data fada?" Yayi shiru kamar ba zai amsa ba. "Duk abun da ya faru Ammy kuskure ne" Tasssss Ammy ta wanke shi da mari, hawaye na sauko mata. "Allah ya wandaranka, wace irin zuciya ce a kirjinka? Ba ni da Martaba da zaka mutunta ni ashe? Ashe karyar biyayya kake min? Bayan idona ka aikata abun da zai zubar da kimata? Ka rusa duk wani mafarkina da buri da nake da shi, ban taba tambayar wace kalar zamantakewa kuka yi ba amman raina be taba kawo min irin wannan kazamar rayuwar ba, kalli wuyanta ka gani sarkar cross ce a jiki, ka kalli shigarta ta tashi daga musulunci ta koma kafirci, Allah ya biyaka na gode" Gaba daya jikin Turhan yayi sanyi duk neman Emily da yake saboda Ammy ne, ba dan yana jin be kyauta mata ba, amman a yau ya dan ji wani iri. "Zan gyara komai Ammy na miki alkawari, ko dan yar dake tsakaninmu, kuma na faranta miki" Ammy bata ce masa komai ba ta juya ta fice daga falon ta fita ta shiga motar da aka kawo ta, direban ya juya da ita, Turhan na tsaye a entrance yana kallon motar har suka fice sannan ya juya ya kalli kofar falon yana jin kamar ya bankawa gidan wuta domin a yanzu ba shi da babban makiyi kamar Aliyu. "Ina zata je?" Wata zuciyar ta tambaye shi, sai ya sauka entrance din ya bude mota da sauri ya shiga yayi reverse ya fice yana ta kalle kalle zuciyarsa na raya masa wata kila ta tafi ta samu Aliyu wani gurin ne gashi be san inda zai ganshi ko ita ba. Haka ya bi titi yana tafe yana kalle kalle har Napep idan ya gani lekawa yake duk yake dare ne ba lallai ya ganta ba shi dai ya rike kamanin gashinta da hasken fatarta, kamaninta na baya da a yanzu sun hade masa har yanzu ganin yake kamar ba Aisha da yake nema ba ce ya gani. A hankali yake tuka motar yana bin gefen hanya da kallo idan ya ga napep sai ya mika kai ya leka, idan ya ga mota ma sai kallo yana son tantance motar da Aliyu ya zo da ita gidan domin be rike kamanin motar da kyau ba, yayi tafiya mai nisa har yana shirin juyawa ya koma gidan Ammy saboda wata zuciyar na raya masa wata kila Aliyu ya koma gidan ko kuma ita Emily, sai ya hango mai kama da ita an sauke ta a napep ta shiga wani shago da aka kawata shi da haske, da sauri ya faka can gefe yana kallon shagon. EMILY POV. Tana fita gidan ta samu Napep ta hau ba tare da ta fada masa inda zai kaita ba, kawai ta fada masa su yi ta tafiya, tana zaune a Napep din tana jin kamar ta yi kuka amman ta danne zuciyarta da idonta daga zubar da hawaye, tana jin a yanzu jaruma ya kamata ta zama. Ta ina zata samu yarta shi ne abun da yake damunta a yanzu, ta dayan gefen kuma tana jin tsanar Aliyu a ranta domin shi ne silar faruwar komai, meyasa ma ta yarda da shi tun farko? Gashi yanzu saboda abun da ya aikata har Turhan ya samu damar tsayuwa a gabanta da Ammy su yi magana da ita. "Huhmmm Aliyu yana bani mamaki, indai Har zai iya boye min inda kike da kuma alakata Fatima to zai iya komai" Furucin Turhan na dazun ya fado mata a rai, sai kuma ta tuna yadda yake kokarin fahimtar da ita ba shi ya shirya wannan ba, it could be true amman idan ba shi bane miyasa har yanzu be dawo gareta da Fatima ba? Meyasa be kirata ba? Idan ba haka ba meyasa ya zo da Fatima? Wane irin uzuri ne da ba zai fada mata ba? "Ina zan kaiki Hajiya?" Mai Napep din ya tambaya ganin ana ta tafiya bata ce komai ba. "Ka sauke ni gurin da zan samu mai Pos ba ni da cash" Tayi furucin tana gwada kiran number layi da layin yake hannun Fatima sai ta ji layin a akashe, ta gwada dayan layin na Aliyu da wayar take hannunsa nan ma ta ji wayar a kashe, gaba daya sai ta rasa me zata yi, bata gane gidan Ammy a yanzu balle ta je ya dauko yarta idan ma tana ganewa bata son abun da zai maida ita gidan har abada, wannan ya saka no matter how much she try dole ne ta dorawa Aliyu laifi domin shi ne silar faruwar komai. Mai Napep din ya sauke ta gurin wani katon Shagon pos ta fita ta shiga ciki ta yi musu transfer ta waya suka bata cashi ta sallami mai Napep din sannan ta cigaba da tafiya a kasa bata san inda zata je and bata san me zata yi ba babu abin da take bukata sai yarta, wata zuciyar na raya mata taje office station ta fada musu dauke mata yarinya aka aka kaita gidan sai dai kuma ko ta fada bata san yadda zata kwatanta gidan ba. Guri ta samu da babu haske sosai ta zauna, ta sake gwada layin Aliyu shiru be shiga ba, daga baya kuma ya shiga yayi ta ringing ba a daga ba. Duk abun da take Turhan na can gefe a mota yana kallonta bata sani ba, idan ta matsa gaba sai yaja motar ya biyota, ta yi tafiya sosai akafa tana take tana sake sake ta shafa kanta ta daga kai sama ta sauke ta sauke ajiyar zuciya amman ta rasa samu mafita ko daya. Daga karshe wata zuciyar ta raya ta koma gidan Aliyu wata kila zai dawo ko ya dawo, ko be dawo ba komai daren dadewa dole ya dawo ai, shi ya kamata ya dawo mata da yarta. Fitowa ta yi cikin haske ta isa gaban Titin da kyau ta tari Napep ta hau tana kwatanta masa inda zai kaita domin ba sanin sunan unguwar ta yi ba, mai napep yana tafe Turhan na bayansu har suka isa bakin gate din gidan Aliyu, yana ganin haka wani bakinciki ya sake rufe shi, ba mamaki sun shirya da Aliyu ne yace ta dawo gidan domin ya ga tana taba wayarta a dazun. Sai da shiga gidan sannan ya matsa yayi fakin gaban gate din ya fita yayi knocking mai gadin ya bude. "Aliyu ya dawo?" "Aa be dawo ba tun da ya fita, bakuwar da ya zo da ita ce kawai ta dawo" "Okay" Ya saka kafarsa ya shiga cikin gida sai kuma ya juyo ya tambayi mai gadin. "Dan Allah kwanan bakuwar nan nawa a gidan nan?" "Gaskiya yau ta zo" "Amman kamin yau ka taba ganinta a gidan nan?" "Aa Wallahi ban taba ganinta ba sai yau" "Okay" Ya nufi cikin gidan, sanin idan ya shigo da motarsa zai iya janyo hankalin Emily ta san ya dawo gidan, zata iya ficewa ta sake barin gidan ya saka shi barin motar a waje ya tsaya kofar falon cikin rashin natsuwar tsayuwar what if mai gadin karya yake masa Aliyu yana ciki? Ya duba harabat gidan be ga kamanin motar da Aliyu ya tafi da ita gidansu ba. Ya biyo sawunta ne kawai saboda kar ta bace masa domin tsawon lokacin da ya dauka yana nemanta yanzu kuma ya same shi ta ba zai bari ta masa nisa ba saboda Ammy. Yana jin kamar ya bude kofar falon ya shiga be da kuzarin haka, wayarsa ya ciro ya kira layin mahaifiyarsa ya sauka daga gurin ya nufi gate. "Hello Ammy kar fa Aliyu ya dawo ya lallaba ki ki ba shi yarinyar nan" "Ai ko hauka nake ba zan ba shi ita ba, kai dai ka yi kokari ka gyara laifinka, karka damu da wannan ka gyara kuskurenka" Ya kashe wayar, a gurin mai gadin ya karbi ruwa yayi alwala suka ba shi abun sallah yayi sallah Magariba da Isha'i, mai gadi da yaron gidan suna gefe suna ta shawarar me ya kamata su yi domin sun kira kira wayar Aliyu ta shiga tana ringing amman ba daga ba, gashi su ba su gane kan abun da yake faruwa ba. Turhan ya zauna a gurin har karfe goma sha daya na dare, baya son ya tafi ya barta kar tafita be san inda zata je ba, ko kuma kar ya tafi Aliyu ya dawo, ko da yake yarta na gurinsu ya san abu ne mai wahala ta iya yin nisa. Tunawa da Fatima ya jafashi a wata duniyar tunani, ya tashi ya fita wajen gate din inda motarsa take ya bude motar ya shiga ya zauna a ciki yayi mata key ya gyara farkin din ya gitta motar ta gaban gate din ta yadda babu wata mota da zata iya fita ko ta shiga sai ya sani, sannan ya kwantar da kujerar motarsa ya kwanta a ciki yana tuna abun da ya faru a dazun na taba jikin Fatima da yayi, gani yake kamar ba gaske ba ne, ace yana da ya, ba dan be yarda ba yarsa even though dna is the best way da zata tabbatar da haka, amman duk sign ya bayyana dake nuna Fatima jininsa ce, yana mamakin yadda yake ta kwadayi da kewar yara ashe akwai jininsa a doro masa be sani ba, lallai Aliyu ba karamin makiyinsa ba ne, yana daukarsa aboki ashe yana nan yana masa Zagon kasa be sani ba, daman duniya ta gaji haka mutanen da ka aminta da su su suke fara cin amanarka. Ya sake kiran Ammy domin idonsa sun soma kaikayin son sake ganin Fatima, and his mine yana jin kamar za'a iya Ammy wayo a karbi yarinyar ba tare da ya sani ba. "Ammy ina Fatima take?" "Gata nan a cinyata tana bachi, she told me everything Mamanta ta fada mata bata da uba! Haka aka haifeta, kuka take daker ta yi bachi ita ma tana son ganin mahaifiyarta" Ya kashe wayar jiki a amace. Sai kuma ya fita ya shiga cikin gidan ya bude gate din da kansa a hankali saboda kar yayi makin sound din da Emily zata san wani ya shigo gidan, mai gadi ya rika masa dayan gate din ya fita ya shigo da motarsa yayi farkin gurin da babu haske sosai nesa da entrance din gidan, ya kwanta jikim kujerar motar, tambayar farko da ya fara yi ma kansa why Emily zata ce mata bata da uba? Kamin ya tuna ranar da alaka ta kullu tsakaninsa da Emily by mistake, ashe be sani ba Allah yayi nufin ba shi ya ta hanyarta ne, ya busar da iskar bakinsa ya kwanta jikin motar yana kallon gate din gidan yana tuna zaman da suka yi a masarautarsu. Abubuwan da suka faru a baya yake ta tariyowa, yana tuna inda ya kamata ya nemeta kuma ya gwada hakan mutanen da suka karbe mahaifinsa ya tabbatar masa da cewar ta gudu, ba zai iya matsawa mahaifinsa lamba a domin yayi masa karya tun farko, amman zai iya tunawa ransa ya bace sosai ya ji babu dadi a lokacin da ya dawo ya samu mahaifinsa ya bada ita a matsayin kyauta, gurin matar abokinsa data nuna tana shaa'war abata ita, kuma ya nuna mahaifinsa rashin jindadin hakan ya nuna masa baiwar daga bangaren mahaifiyarsa take a gurin tana da daraja fiye da sauran bayin da suke nan. Misalin karfe biyu na dare ya fita motarsa ya bar kofar a bude ya taka har gurin Entrance din ya leka windows din baya iya hango komai dake ciki saboda a rufe suke, amman yana iya jiyo sautin kuka, a gurin ya tsaya kansa a kasa yana saurarenta har sai da ta ji shiru sannan yayi jihadi ya karasa gurin kofar falon ya murda a hankali without making a sound ya tura ya leka ciki, sai ya hangota zauna akan kujera tana bachi, janyo kofar yayi ya rufe ya dawo cikin motarsa ya zauna, a gurin ya kwana har asuba, idan bachi ya debe shi sai yayi maza ya bude idon. EMILY POV. Akan kujera ta kwana zaune bayan ta gama zirga zirgar safa da marwa a falon ta yi ta gwada layin Aliyu ba a daga ba, daga baya ma sai ta ji wayar a kashe, bata san inda zata je ba. No matter how much she try sai da ta kasa rike kanta misalin karfe 2 na dare ta fashe da kuka kuka sosai har sautinsa yana fita, sai da ta yi kukan ta gaji sannan bachi yayi gaba da ita. Bata farka sai 7am shi ma ta ji sanyi ya soma mata yawa ne, sai ta warware rigar Dr AB ta saka a jikinta ta rufe zip din ta saka hannayenta a aljihun jacket din sai tda nufin sararawa sai ta ji abu a ciki, ta lalaba ta ciro arba ta yi da card din Dr A-B mai dauke da email dinsa da number wayarsa da kuma sunansa Business Card mai kyau classic one. Tana rike da card din tana kallo da shafawa kira ya shigo wayarta da sauri ta dauki wayar sai dai ganin number Vito ya katse hanzarinta, bata gama tunanin abun da zata tsara masa ba ta samu kanta ta amsa kiran domin shi ne kadai mutumen da baya betraying dinta. "Hello" "Kina ina?" Ta hade yawu, ta yi shiru. "Kaduna ko?" Ta ji gabanta ya fadi. "Wani abun ne ya taso min da ban yi zato ba shiyasa na tafo" "I can't lie again Emily, wannan ogan na gurin aikin ku kika bi? Butulcin ne kika fara tun yanzu ko?" "No no nooo ba abun da kake tunani ba ne, na san ka yi min gargadi amman kuskure na aikata na bawa Aliyu Fatima ya zo da ita Kaduna va tare da sani na ba, kuma yanzu Turhan ya karbeta ina..." "Good, so me kika son na yi yanzu? Na yi fada da shi? Ko ke na sake yarda da ke? Ko kuma na yarda da duk wannan karyar da kika shirya? Na saka wasu kananan yan iska sun bawa boss dinki warning it's just a warning before i come" "What do you mean?" "Je ki tambaye shi idan rayu" Ya katse wayar. Kirjin Emily ya shiga bugawa da mugun karfi, ta sake gwada number Aliyu a nan ma ta shiga kuma sai ta yi sa'a aka daga kiran. "Hello" "Mai wayar yana asibiti" "Wace Asibiti?" Ta tambaya aka fada mata sai ta nufi kofar falon ta bude ta fitada sauri ta kula da motar Turhan dake can gefe ba domin hankalinta ba a gurin yake ba, ta fita mai gadin na tambayar lafiya bata kula shi ba. "Anya ba guduwa zan yi ba ni ma wannan zirga zirga kar wani abi ya faru ko ya bata a dora min laifi fa" Ya fada yana kallon Turhan daya juyo da mota da nufin bin sawunta. Achaba Emily ta hau ta fada masa inda zai kaita ta hau jikinta nata rawa gaba daya hankalinta ya gama tashi. [7/8, 11:19 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 4️⃣8️⃣ Ta isa asibitin ya sauka kan achaba ta biya shi kudinsa ta Emergency ta shiga tana dubawa yawo ta yi bata gane dakin ba domin asibitin babbar Asibiti ce Emergency ma biyu ce ta shiga dayar ta nan ma ta binciki bata gane ba sai da ta sake kiran wayar aka fada mata, sannan ta gane dakin bayan ta isa aka hana ta shiga domin dakin na tsare da jami'an tsoro. A dole ta dawo waje ta zauna ta dafe kanta, duk abun da take Turhan na biye da ita, shi dai be san me ke faruwa ba, be san wa aka kawo ko ta zo gani asibiti ba, kuma be isa ya tunkarenta ya tambaya ba, dan haka ya zauna nesa da inda ba zata ganshi ba yana kallonta. Can kuma ya ga ta fashe da kuka sosai hakan ya karantar da shi ko ma minene abu ne mai muhimmancin sosai a gurinta, karfin hali yayi ya tashi daga inda yake ya taka cikin takunsa na kasaita kamar wanda baya son taka kasa ya karasa inda take zaune tana kukan ya tsaya daga gefenta ya kalli mutanen da suke gurin yana kirga mutane nawa ne, domin ya san Emily zata iya disgashi ya lura gaba daya an hure mata kunne, har ya kalli inda take zaune kamar ya zauna amman ba dama ya san zata iya tashi ta bar shi a gurin. Ya tsaya a gabanta kamar wani hoto ya kalleta ya kalli harabar ya kasaita ta hana shi bude baki ya tambayi me ya saka ta kuka, baya son ta zubar masa da kimarsa just because yana nemanta kuma yana neman gyara abun da ya bata, sai dai kuma tunawa da Fatima ya saka shi kawar da komai, domin samun Fatima a yanzu yana jin Emily ta gama masa komai, ya hade yawu zauna a gurin, jin alamar mutum ya zauna a kusa da ita ya saka ta mike dago kanta daman tun da ya iso gurin ta ji alamar mutum amman bata dago ba sai da ya zauna kusa da ita. Ganin Turhan ne ya saka ta mike tsaye da sauri sai yayi hanzarin mikewa tsaye ya riko hannunta. Juyowar da zata yi sai ta juyo da shirinta na sauke mata yatsunsa biyar na dayan hannun a fuska, yayi hanzarin saka dayan hannun ma ya rike dayan hannun. "Zaki iya marina ki ci mutuncina yadda kike so idan muna daga ni sai ke a guri a gurin da jama'a suke kai da kawo ba, Aisha kin fa san waye ni na san kina jin haushina amman..." Be kai aya ba ta buga masa kanta a hanci ba shiri ya saki hannayenta. "Ya Rabbi ya Allah..." Ya furta yana jin wani gishirin bala'i a hancinsa yana ratsashi har cikin kai, ya kai hannu ya taba hancin nasa har yana huro iska ya ji ko hancin yayi jini, bata tsaya a gurin ba ta kara gaba, bata wani san asibitin ba da tambaya ta isa gurin da ruwa suke ta tara hannunta ta wanke da kasa sannan ta tara hannunta ta dauraye. Turhan na can daga nesa yana kallonta ganin ta wanke hannun ya saka jin wani iri ya kalli hannayensa even though ya san hannunsa are clean. Karfin hali yayi ya karasa gurin da take duke ya tsaya daga bayanta. Duke take a gurin tana ta kuka, abubuwa sun chabe mata a yanzu, Vito yayi fushi har ya cutar da Aliyu, ga Fatima bata hannunta ga shi ta hadu da daya daga cikin manyan makiyinta wato Turhan, Aliyu yana raye ko ya mutu bata sani ba, but no matter what bata so wani abu marar kyau ya samu Aliyu ba, balle kuma ace sanadinta ne. "Ina son na san dalilin kukan ne wata kila zan iya taimaka miki, ki fada min me ya kawo ki nan kuma me ya faru ba dan ni ba sai dan Fatima" Ta runtse ido cike da bacin rai, yanzu kuma ta rasa dalilin wannan mutumen na bibiyarta, da ace tana da iko da ta toshe kunnuwanta daga sauraren muryarsa. Mikewa ta yi tsaye ta juyo ta kalleshi. "Har abada, har kasa ta rufe idona, har duniya ta nade ba zan taba karbar taimako daga gareka ba, balle kuma har na nema, da zaka iya da ka taimakawa kanka ka nisanta kanka daga ni da duk wani abu da ya shafe ni, idan ka aikata hakan rayuwarka zata tsawaita ka cigaba da zalunci da ka sakawa gaba, kuma saka ceto kanka daga wulakanci, idan akwai muryar da na tsani ji kamar mutuwata to taka ce, idan akwai fuskar da zan iya kwakwale idanuwana na zubar da su saboda kyamar kallonta to taka ce, idan kana kallon Fatima a wani tsanin hawa to ka yi kuskure domin Fatima bata da uba, ko a tsintuwa ta zo ba zata taba zabarka a matsayin uba ba, mutumen da ya kalli uwarta ya aibanta surarta, ya kaskantar da ita a matsayin baiwa a fadar da ya kamata ace an girmamata, ya kira ranar auren uwarta da bakar rana, ya kira ranar da ya kebe da uwarta har aka samu cikinta da bakar rana, ya fadi cewar ba zai taba son abun da ta haifa ba, ya watsa mata yawu a fuska, wai duk saboda kawai ta aure shi dan ta farantawa uwarsa rai, ya kira uwarta da tubabbiya, ya kira dan'uwanta da shege yana musa cewar ta sunna aka same shi, ya bar uwarta ta wahala a titi ta haife ta a titi ta raine ta a titi kuma yana raye yana da hali da Ikon da zai iya kula da yarsa, ya juya mata baya sai a yanzu da yarinya ta yi wayo zai dawo yace shi ne ubanta? Yarinyar da na gina rayuwarta da tsanarka? Yarinyar da bata taba yarda ta zo duniya da uba ba? Kai kan wane irin mahaukaci ne? Har kana da idon da zaka kalli Fatima ka fada mata kai ubanta ne? Allah ya waddaran namiji irinka, Allah ya kwashewa rayuwarka Albarka, ka yi hasara" Kallonta yake kallon da ya hango tsanarsa a cikin idanuwanta ya karantar da shi kiyayyarsa a cikin kalamanta da muryarta, ta tuna masa da abubuwan da ya manta kuma yake ganin kamar ba komai ba ne, ta yi gaskiya shi din be cancani ya kalli Fatima ya fada mata shi din ubanta ne ba, amman hakan ba zai karya guiwarsa ba domin komai ya faru ne saboda rashin sanin inda take da kuma cikin da take dauke shi. Ya bi bayanta da kallo ganin rashin dacewar tufafin dake jikinta. A sanyaye ya juya ya nufi gurin da ya aje motarsa ya shiga ya zauna kalamanta na ta yi masa yawo a cikin kai. Be kyauta ba ya sani, kuma ya zafafa da yawa a yanzu ya gane hakan, kuma ya fahimci kirjinta ya cika da tsanarsa da kiyayyarsa tana ina ma zai fara gyara abun da ya bata, tun da bata ba shi hadin kai, kamata yayi ace Aliyu yayi masa wannan yakin tun kamin ranar yau wata kila da abubuwa sun zo masa da sauki, tun da gashi ya san har da ya a tsakanin su amman be masa ba sai ma kokarin boye masa yake yana munafurtarsa, a yanzu ya kara gane Aliyu ba abokin kwarai ba ne, ta ina ma ya gane ta? Ina ya hadu da ita taya suka kulla alaka abu ne da yake bukatar ya sani.. Ya dauki wayarsa ya kira layi Ammy ta amsa kiran ya gaisheta ta amsa, kasancewarta uwa sai ta fahimcin canjin muryar danta ta yanayin yadda yake amsa mata magana alamar akwai abu a kasan halshensa. "Ammy ina Fatima?" "Tana can falo tana cin abinci, daker ma na samu take cin abincin, babu wanda take kira sai Aliyu da Aisha, gaba daya ta ki yarda da mu, na fada mata ni ina matsayin kakarta ne amman ta ki karbar hakan tace mahaifiyarta bata da kowa, ita kuma bata da uba, ban san yadda zan yi na fada mata kai ubanta ba ne, Turhan ka lalata abubuwa da yawa" Ya sauke ajiyar zuciya yana taba hancinsa da har yanzu yake masa ciwo. "Na sani Ammy zan yi kokarin gyarawa kamar yadda kika ce, ba za su karbe ni da sauki ba amman zan... Zan jure wajen ganin komai ya tafi daidai, wata kila shiyasa Allah ya kawo ciwon nan naki yasa na zo abubuwan nan suke ta faruwa" "Kana ina? Ina Aisha take?" "Ina asibiti, na kwana a gidan Aliyu jiya saboda ina tsoron kar na tafi tayi tafiyarta ban san inda zan same ta ba, kuma yanzu ta zo asibiti ban san wa take nema ba, amman dai kuka kawai take" "Ka tambaye ta mana" "Ba zata min magana ba, na gwada yin hakan ban dace ba, amman dai ko minene yana da muhimmancin sosai a gurinta domin kuka take sosai kuma hankali a tashe ta zo nan" "Duk yadda zaka iya idan ka gano matsalar ka taimaka mata, kuma ka fada min ta hakan za mu yi ta yakin har mu yi nasara In Shaa Allahu" "Okay" Ya sauke wayar, ya sake fita motar jiki a sanyaye ya fara zagayawa ta asibitin har ya samu inda take zaune ya zauna nesa da inda ba zata ganshi ba yana ta kallonta, ta ya ta canja haka? Ina wacan yaron? Yaushe da bar addinin Musulunci ya yi ma kansa tambayoyin a take, tun yana tsayuwa da dadi har kafafuwansa suka yi tsayi domin yayi awa daya da rabi tsaye a gurin yana ganin Emily, a tsawon awa daya da rabin babu abin da Emily take sai kuka domin jikinta na raya mata ko dai Aliyu ya mutu ko kuma yana cikin mummunan hali bata san me zata yi a yanzu ba. Sau goma sha daya yana yunkurin tafiya ya sameta ya sake tambayarta damuwarta sai kalamanta na dazun su rike masa kafa, sai dai kuka yana jin wani iri kamar dai babu dadi tana kukan ko ba komai kukanta na yanzu yana tuna masa da kukanta da ta yi a wacan lokacin har take rokon ya dawo da ita gida ya ki. Ya shafa kansa yana jin babu dadi, lokuta da dama mutum ya kanki abu kuma ya zama shi ne alheri a gurinsa, ko kuma ya so abu ya zama abun sheri ne a gurinsa, a yanzu ya fahimci hakan domin gashi tsananin rabo ya saka ya samu haihuwa da matar da ya tsana yake ganin kamar bata dace da shi ba, ashe uwarsa ta iya zabe kuma ta hango masa abin da shi be hango ba be fahimta ba, kibar ma ashe da ta samu kulawa mai kyau jikinta zai canja ne yayi kyau ita ma ta yi kyau kamar yadda take yanzu, wato sai a yanzu ya fahimci ba karamin aika aika yayi ba, gaba daya ya rasa ta ina zai kama zaren lamarin ma balle ya dinke. Hango waya a kunnenta ya saka shi maida hankali sosai gurin kallonta na son fahimtar abun da yake faruwa, bata ji ma da sauke wayar ba ya hango Ummi ta iso gurin da take zaune sai Emily ta mike tsaye Ummi ta yi mata magana sannan ta rumgumeta, can kuma ta kama hannunta suka shiga cikin asibitin. A nan ne kansa ya kara daurewa zuciyarsa ta hararo masa ko danta din nan ne ba shi da lafiya Aliyu ya turo Ummi ta taimaka mata? Waya sani ko Aliyun ma yana ciki? Amman kuma Ummi ai ba anan take ba Abuja take zama. Motarsa ya koma yana ta tunanin me ya faru me zai faru, be san a inda zai samu labarin komai ba sai da Kameela ta fado masa a rai sai dai kuma ba shi da Number ta. Ya kira Ammy ya bukaci ta kira layin Kameela ta bincika masa abun da yake faruwa, sai Ammy ta fada mata da number Kameela kuma ta labarta masa Aliyu yana asibiti, ta gane hakan ne a lokacin data kunna wayarsa dake hannun Fatima saboda Fatima nata yi mata kuka sai aka yi ta kira ana tambayar abun da sauki. "Ina tunanin ko dai ya samu hatsari ko kuma wani abun ne ya faru da shi" Turhan ya sauke wayar a kunnensa yana wani kashe ido. "Kam uban nan, wato Aliyu take yi ma kukan nan? Lallai ko a cikin munafukai wutarka ta dabam ce Aliyu, har ya aka yi irin wannan shakuwar da ita? " Ta ji kamar ya tafi ya bi bayanta sai kuma wata zuciyar ta hana shi, ya yi ma motarsa key ya dauki hanyar gidan Ammynsa, sai da ya kusa isa ya ji kamar ba zai iya barin abun ya wuce ba yayi reverse ya juya sai kuma wata zuciyar ta tuna masa shi da yake neman mafita a yanzu ai be kamata yayi rigima ma be kamata yayi abun da zai saka Emily ta tsane shi ba, ya sake reverse ya juyo sai kuma zafin abun ya doki zuciyarsa taya wai zata zauna tana kuka hehehe akan wani katon banza munafiki? Alhalin tana matarsa? Da ama ace Aliyun yayi masa abun arziki da sauki ko shi ya bata aurensa ai kukan da take yayi yawa balle kuma yanzu a duk duniya ba shi da makiya kamar Aliyu. Ya juya ya sake daukar hanyar asibitin sai kuma ya sake juyowa haka zuciya ta yi ta juya shi kamin yayi nasara cin galaba akanta ya kawo kansa gida gurin Ammy, ya shigo cikin falon ya zauna takaici ya hana shi magana. Ammy ta dube shi daman ta fahimci damuwa tun a dazun da suka yi waya. "Me ya faru? Ko yunwa kake ji ne? Ko dai minene ka saita kanka be kamata Fatima ta kanka a cikin wannan yanayin ba" Ya kalli Ammy sai a lokacin ya tuna da wani zancen abinci daman rabonsa da abinci tun wanda ya ci a jirgi. "Wato Aliyu munafiki ne Ammy, Wallahi ban tana tsammanin haka daga gareshi ba, wai kin ga yadda yarinyar nan take kuka? Ashe duk shi take yi ma kuka kamar wani ubanta? Shiyasa aka ce makiyinka yana tare da kai Allah kadai ya san abun da ya shuka mata? Shi ko kunya baya ji ma? Ai na yi zaton ko mutuwa na yi Aliyu ba zai min haka ba, har da Ummi ta zo ta rumgume ta yadda kika san wani shirin film wata kila gidansa ko gidan Ummi take zaune, haka yake ta kallonta yana rayuwa da ita kuma ya san ina nemanta, ya boye min komai, ba wai ina kishi ba ne, sam amman dai ni ko dolo ne ai dole na nuna takaici ko?" Yana maganar yana jin abun da be saba ba, daman babu wanda ya kai balarabe mugun kishi na bala'i, Balaraben mutum da muryar matarsa be son aji, ko da yake shi a yanzu ba kishi ba ne haushin Aliyun ne yake ji na abun da yayi masa. "Zaka iya kwantar da hankalinka ka yi min bayani? Ni duk ban gane wannan kewaye kewayen ba" Ammy ta tambaya yana kallonsa domin bata fahimci inda ya dosa ba, sai ya mike tsaye yana huci. "Idan ma na yi kishi ai ina da hujja ko dan Fatima? Emily ko mutuwa ta yi dole na kare martabarta saboda wannan yarinyar, ai ba zan jidadi ace uwar yata ce take wannan shigar ba? Har tana hulda da abokina, lallai Aliyu ya hadiye kashin da zai zame masa masifa a wuya, ba fita ba wucewa, kuma har abada ni da shi Wallahi Tallahi babu wani uzuri, abun da yayi min ya fi ka dauki wuka ka chakawa mutum" Ya koma ya zauna yana cizon hakora. ALIYU POV. Ya bude ido yana jin jikinsa yayi masa nauyi sosai kamar ba na shi ba, kuma yayi matsa tsami, amman karfin hali irin na namiji da juriya yana hada ido da mahaifiyarsa sai ya saka matar murmushi. Yayi yunkurin bude baki yayi mata magana sai ya ji bakin yayi masa nauyi kansa kuma ya fara ciwo daman shi ma kan na shi yayi masa nauyi. Ummi ta yi ma wata yar'uwarta magana ta fita ta kira likita ya shigo da sauri ya duba shi ya cire masa ruwan dake jikinsa ya taimaka masa ya tashi zaune aka kawo roba ya wanka bakinsa Ummi ta hada masa tea ya sha aka ba shi magani ya sha. Ummi na kusa da shi zaune sai matsar kwalla take tana kallonsa. "Ummi da sauki fa kina gani to kuka na me kuma?" Cikin kuka Ummi ta ce. "Allah kadai ya san zafin da kake ji amman ba zaka nuna ba dan kar na damu, kalli yadda suka maka rauni a kafa, jiki ko'ina duka" "Saukin abun ma babu karaya, amman ko suwa gaskiya kashe ka suka so yi" "Ni ban san ko suwaye ba, ni dai ina tsaye ina waya da Ummi kawai na ji duka ta ko'ina da itace da hannu, Allah yasa inda na tsaya kusa da mutane ne kuma ana hada hadar shiga Sallah Magariba domin an yi kira ne lokacin sai mutane suka hankalta da wuri suka kawo dauki, mutanen suka gudu, na ji dai ana ta Innalillahi ni ma kuma ina ta tun da suka hau ni da dukan, a nan jama'a suka taimaka aka dauke ni aka dora ni a babur din wani aka yo asibiti da ni, suka ce ba za su karba ba, saboda kaina da kafata suna zubar da jini lokacin ga hannayenta sun duka bana ma iya daga su, to daga nan dai hankalina ya bace ban san ya aka yi ba sai yanzu da na farko nan" Ummi ta ce. "Muna wayar nan da kai na ji kana ambaton innalillahi sai ina jin karar duka na san ba lafiya ba, ko dai ita yarinyar ko kuma Kameela tun da su ma ba hankali da su ba ko kuma shi Turhan din cikinsu akwai wanda ya saka aka yi maka haka, kiran yankewa yayi na fito na shiga bangaren Daddynka na fada mishi da ya gwada kira sai ta shiga, Allah yasa yana gida a lokacin shi yayi magana da su ya fadi asibitin da za a kaika kuma ya kira CP ya sanar masa maka, yanzu haka kofar nan police ne awaje ba abarin kowa ya shigo, sun ce sai ka farka za su shigo su dauki bayanai" "Ummi ya aka yi kika zo?" "A dare nan ban iya kwana a Abuja ba ai, mota muka biyo da rakiyar jami'an soji sha biyu na dare na sauka garin nan, kowaye ya maka wannan abun ba zai tsira ba In Shaa Allahu" "Allah y sauwake, idan kun dan gana sai a bar shi ya samu hutawa saboda ya ji ciwo a kai yawan magana zai iya haifar masa da matsala" Likitan ya fada sannan ya fice. "Emilyn ma tun dazun take kira ta zo nan ba su barta ta shigo ba" Aliyu ya kalli Ummi. "Taya aka yi ta sani?" "Ban sani ba, amman dazun wayar tana hannun mubarak ya fada min ta kira ya fada mata kana asibiti" Ummi na rufe baki sai ga kiran Emily ya shigowa a wayar Aliyu dake hannun Ummi. "Gata nan ta sake kira" "Ummi abarta ta shigo mana" "Kana ta ciwo wa yake ta wani Emily? Waya sani ko ita ta saka aka yi maka haka saboda yarinyarta" "Ba zata yi haka ba Wallahi na san ranta ya bace amman ba zata saka yi min haka ba, ita ma fa tana cikin matsala, dan Allah Ummi ki barta ta shigo kuma dan Allah Ummi karki nuna mata wani abu ko da ta zo dan ta yi fada da ni ne, Wallahi ta fi ni gaskiya kuma ni ne ban kyauta mata ba, sannan kuma yarinyar ancutar da ita an kuntata mata har tana kallon musulmai a matsayin azzalumai, tana son musulunci na fada miki kafira ce ta musulunta wahala ya saka ta koma ruwa, wannan abun nake son na kankare a ranta kuma na dawo da ita tafarki na kwarai, labarin da na baki jiya ko rabi ban fada miki ba na wahalar da sha a rayuwa, ni kadai ne mutumen da ta yarda da shi, dan Allah karki nuna mata wani abu, idan muka kyautata hali da kuma zamantakewa da ita har ta fahimci musulmai mutanen kirki ne kuma ta dawo addinin ai mun yi jihadi babba ba karami ba" "Ya isa haka, likita yace karka rika yawan magana" Yayi murmushi. "Ummi tana tsoron rasa dan autanta" "Autan da baya jin magana ma? Ashe har guba yarinyar nan ta saka maka amma... Dai bari ka ji sauki tukuna, sai na ci mutuncinka Wallahi Aliyu" Yayi murmushi, ita kuma ta mike tsaye ta mika masa wayar. "Cire min password din" Sai ya fada mata password dinsa sunanta ne tare da numbers, ta yi murmushinn jindadi ta fice daga dakin, sai da ta fita waje sannan ya kira Emily da wayar Aliyu. "Hello... Aliyu" Emily ta amsa da muryar kuka. "Ba shi ba ne mahaifiyarsa ce, kina ina" "Ina wajen asibitin na zo an hana ni shiga, Aliyun yana lafiya" "Daidai ta ina?" Ummi ta tambaye ta tana ina Emily ta fada, sai ta fita da kanta ta isa har gurin da Emily ta fada mata, Emily na hango Ummi ta mike tsaye gabanta na faduwa ta yi tunanin idan Ummi ta karaso gurin zata mata fada ne ko ta tuhumeta, sai da Ummi ta kawo sai ta ce. "Ke ce Emily?" Emily ta amsa ta hanyar daga mata kai a hankali cike da tsoro abubuwa biyu ta ci mutunci ko kuma ta fada mata wani abun ya sami Aliyu wanda ba shi take fata ba. Sai kawai ta ga Ummi ta rumgumeta. "Ki yi hakuri, ba a kyauta miki ba kuma hakika an zalince ke" Emily ta fashe da kuka Ummi ta dagota ta kama hannunta. "Zo muje ki ga Aliyun" Taja hannunta suka koma cikin asibitin Ummi ta shiga da ita har dakin da Aliyu yake. "Gata nan ka yi a hankali ka san dai yanayin da kake ciki da kuma abun da likita ya fada" Cewar Ummi sai kuma ta kalli Emily take share hawaye ta sake kallon Aliyu ta ce. "Kuma ka bi a hankali karka kuskura ka ce zaka fada mata wata magana marar dadi, ka san dai ta fika tarin damuwa, ba zan lamunci hakan ba" Aliyu ya kalli Ummi cikin wani irin jindadi da alfahari na furuncin da ta yi a yanzu, Emily ma ta kalleta tana mamaki da tunani. Ummi ta juya ta fita daga dakin ta rufe musu kofa. Sai shiru ya biyo baya Aliyu ya kasa kallonta ita ma ta kasa kallonsa sai jan majina take tana yawo da ido. A lokacin da ta yi jihadin dagowa ta kalleshi a lokacin ne shi ma sarkin ya fada masa ya kamata yayi nasa jihadin. "How are you Aliyu" "How are you Emily" Suka hada ido da baki gurin tambayar junansu ya kowanensu yake, shi ya damu ya san halin da take ciki a yanzu bayan rabuwa da yarta da kuma abubuwan da suka faru, ita ma kuma ta damu ta san ya yake ji a jikinsa na abun da ya same shi domin ta ga bandage a kansa da kafarsa da jikin ya nuna alamar duka ta ko'ina. Shi ya fara sauke idonsa daga barin kallonta yana jefar da tambayar da amsar ta yi masa nauyi gurin dauka. "Har yanzu akwai igiyar auren Turhan akanki? Da igiyar aurensa kika gudu?" "Ba shi da amfani, na rika na sake shi, ba ni da wata alaka da shi yanzu" Yayi murmushi ya koma ya jingina da ginin dake jikin gadonsa ya rufe ido. Ba shi da dalilin rashin jindadi amsarta, dan haka ba zai ayyana abun da ya ji a yanzu a matsayin rashin jindadi ba, sai dan tausayin rayuwarta da kuma na yarta, ko da yake yadda Turhan yake neman haihuwa yasan ba zai cutar da Fatima ba, ita ma kuma yadda Ammy ta juya masa baya ba zai yarda ya aikata abun da zai saka ya sake rasa Emily ba. "Kin manta baki fada min wannan ba a cikin labarinki" Ya fada bayan ya bude idonsa. "Ba shi da amfani, na riga na sake shi" Yayi murmushi mai nauyi. "A musulunci mace bata sakin kanta, ke matarsa ce har yanzu" "Ni ba musulma bace a yanzu, kuma a addininmu mace sakin namiji idan bata ra'ayi" "Ai amman idan ta yi signing papers ko? Ke baki yi ko daya ba" "Saboda ba a coci aka daura mana aure ba ko kotu" "Shiyasa kike matarsa har yanzu" "Duk tsawon lokacin nan? Duk bayan abun da yayi min?" "It does not matter ke kika gudu ba shi ya barki ba, Emily you're still his wife" Ta matsa kusa da shi ciki bacin rai. "I hate you for telling me that" "I know" Ya amsa mata, ta nuna idanuwanta. "Na yi bakinciki wannan hawayen da na zubar saboda kai, hankali ya tashi saboda abun da ya same ka yanzu ka farka kana fada min I'm still Turhan wife, i hate you Aliyu... I hate you... I hate you... I hate you... So much" Ta furta da karfi ba tare data daga murya ba, sai yayi murmushi mai sauti. "i hate myself more, what else?" "Na tsane ka da ka kasance abokin Turhan" Ta juya zata fice sai ya ce. "Idan kika fita baza su bari ki sake shigowa ba, and we need to talk akan gurin da zaki zauna da kuma Fatima" Sai ta juyo kawai ta fashe masa da kuka ta zube a gurin zaune, komawa yayi ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. [7/10, 1:55 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 4️⃣9️⃣ "Kina son zama da ummi na ko hotel za a kama miki? Ko da yake Hotel ba tsoro, ke ma kuma baki jin magana, dan haka zaki zauna da Ummi" Bata kula shi ba sai kuka take rarewa. "Emily kina son karasa ni ne, hawayen ki nan na san akwai kaso na a cikin zubarsu, ba ni da lafiya ki gani, zubar hawayen nan na ki kuma ya saka zuciyata nauyi, so kike na mutu ne?" "Babu wanda zai fahimce ni, ni kadai na san wahalar da na sha, ni kadai na san damuwar da take cikin kaina, ba ni da kowa wannan ma kawai ya ishe ni bakinciki, yanzu kuma ya karbe min yarinya, be kamata ka kalleni ka fada min wannan maganar ba, Khalifa da Turhan ba ni da makiya irinsu a duniyar nan" "Na fada miki ne, saboda shatawa kaina da ke da duk wanda zai rabe ki layi, abu ne da yake a hukunce ba ni na dora miki ba" Ta kara fashewa da kuka har da buga kafa a kasa kamar yar yarinya, Aliyu ya tashi zaune kenan Ummi ta turo kofar dakin ta shigo, ganin Emily na kuka ya saka ta kalli Aliyu. "Me ka mata?" "Me zan mata Ummi ni da nake haka?" "Toh dadi ya sakata kuka kenan?" "Aa saboda na fada mata har yanzu akwai aure tsakanin ta Turhan ne" Ummi ta dafata ta mikar da ita tsaye. "Taso yata share hawayenki, ki daina bari ana ganin rauninki" "Ummi zaku je da ita gida zata zauna saboda nan bata da kowa sai mu" "Ita kuwa take da kowa tun da take da mu, je waje ki jirani kinji" Emily ta share hawayenta ta fita dakin. "Ka kwanta ka huta, zamu je da ita gida" "Ummi karki bari ta gudu, kuma dan Allah ki kula da ita ki kwantar mata da hankali, Wallahi bana son damuwar Emily ko kadan, kuma ki fada mata da zarar na ji sauki zan dawo mata da yarta, sannu a hankali komai zai zama daidai" "Zan kwantar mata da hankali, amman dai karka manta kai ma fa ka fada akwai igiyar auren Turhan akanta, karka manta da wannan" Aliyu ya kalleta. "Eh kuma hakan ba zai hana na taimaka mata ba, ko kwantar mata da hankali" "Amman dai kar a wuce gona da iri, kar a tsallake iyakokin ubangiji" "Subhanallahi, Wallahi ba abun da kika tunani ba ne Ummi sam sam sam babu wannan ko kadan, kawai dai ina tausayinta ne kuma ina son ta samu farinciki, ta dawo tafarkin musulunci" "Ka san ni uwa ce, na kan iya hango abun da zai taho tun kamin ya taso" "Toh gaskiya a nan baki hango daidai ba" "Toh ga mu zuwa, Allah ya baka lafiya" "Ameen, zan baki mamaki Ummi" "Daman Mamakin nake son ka ba ni ai" Ta shafa kansa ta yi murmushi. "Zan je na girka maka abinci mai kyau, kamin na dawo na san ka samu yin bachi" "Okay, can i have my phone please?" Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya, Ummi ta mika masa wayarsa sannan ta fice dakin taja masa kofa a hankali, a tsaye ta samu Emily ta rika hannunta suka fara tafiya Ummi na kwantar mata da hankali har suka isa gurin motar da aka kawo Ummi ita da Ummi suka shiga baya, daman front seat din akwai dan sanda daya a ciki, direba yaja motar yana tukawa a hankali har suka isa Family house dinsu Aliyu wato gidan da Ummi take zaune a Kaduna tare da Daddy, direban na faka motar harabar katon gidan dake cike da yan'uwa da abokan arziki da suka ji abun da ya faru da Aliyu kuma sun tafi Asibiti ba a barsu sun shiga ba. Ummi ta bude motar ta fita tana amsa wayar Daddy dake sanar mata yanzu jirginsa zai taso daga Abuja zuwa Kaduna, ta doshi Entrance din gidan, Emily ma ta bude ta fito ta bi bayanta sai ta ji an kira sunanta da muryar da bata wayanci ko ta waye ba. "Emily..." Ta juyo domin jin dalilin kiran arba ta yi da direban da ya kawo su a yanzu, sai dai har ga Allah bata wayance shi ba domin rabin fuskarsa a kone take, ta sake juya domin be ce mata komai ba ita ma kuma ba ce masa zata yi ba saboda bata san waye ba. "Emily... Ni ne Khaleefa ne.. Baki gane ni ba? Ni kam ba zan iya mantawa dake ba duk yadda kika chanja, tun da kika shigo motar nan na gane ke ce" Yana magana cikin rawar jiki da rawar murya kamar mai shirin yin kuka. Tun da ya furta cewar Khaleefa ne Emily bata juyo ba ta cigaba da tafiya, a lokacin ne Ummi ta juyo bayan ta kare wayar da take sai ga Emily ta biyo bayanta Khaleepa kuma ya biyo ta yana mata magana. "Dan Allah ki taya dan girman Allah ki saurare ni" "Kin san shi ne?" Ummi ta tambaya. Sai Emily ta tsaya a gabanta "Tsohon mijina ne, shi ne ya fara cutar da ni, shi ya budewa kowa kofa, shi ne mutumen da ya fara raba ni da gata, shi ne ya fara karantar da ni rauta tata, shi ya janyo min duk masifar da nake ciki yanzu, shi ne uban da har ɗana ya mutu ba taba ganinsa ba, shi ne mutumen da ya koreni da tsohon cikin dansa, yan'uwansa suka juyo min baya, su suka fara kirana da tubabbiya" Ummi ta matsa daga gaban Emily fuska a hade ta kalli Khaleefa. "Karka sake ko da wasa ka sake mata magana, taya zan shigo da bakuwa ka tari gabanta ba tare da neman izini ba? Direba ne kai a nan karka manta da wannan" "Tohm Hajiya ayi hakuri" Ya fada yana tare hawayen da suka cika idonsa. Ummi ta kama hannun Emily suka shiga ciki kowa sai kallonta yake saboda dress din dake jikinta ga kuma sarkar cross, Ummi ta shiga da ita ciki ta kaita dakin da Aliyu dake gidan. "Nan dakin ɗana ne Aliyu, ki zauna a ciki ki yi duk yadda kika so, ki sake jikinki kamar kina cikin gidanki" Emily ta kalli dakin. "Idan kin bani dama zan je na dan ji da bakin da suka zo mana jaje" Emily ta saki hannun Ummi ta nufi gadon da Aliyu yake kwana a lokacin da yake gidan ta zauna. Ummi kuma ta juya ta fice, kwantawa Emily ta yi kan gadon ya lumshe ido zuciyarta na mata wani irin zafi. "Wayyo Zuciya" Komai ya taru a zuciyar ya tsaya mata... TURHAN POV. "Kamata yayi kawai na koma na daukota, to miyasa amfanin barinta a can ma? Macen da na shekara nawa ina nema yanzu na ganta na bari wani katon banza yana controlling dinta" "Idan ka je daukar ta zata yarda ta biyoka ne? Tun da fari da baka bata komai ba, ai duk haka ba zai faru ba, ni na ma manta ban tambaye ka ba, sakinta ka yi ko guduwa ta yi?" "Guduwa ta yi ni ban sake ta ba" "Amman ka munana mata a zamantakewarku?" "Ba cancan ba, sai dai wani abun ta dauke shi da zafi saboda bata son zama da ni yanzu, kuma dole za a samu abubuwa da ba za su mata dadi ba, Ammy saboda Al'adar ba daya ba, kuma kin ga ina da mata, ko ma dai minene Ammy abun da ya wuce ai ya wuce yanzu ake fuskanta, tun da gashi har da yarinya a tsakaninmu, kuma matar nan ita muke da ni ma saboda gyara kuskuren da na aikata, ke da kanki fa kin ce na gyara abun da na bata" Ammy ta sauke numfashi. "Tun da har an ganta, to komai ya zo da sauki, balle kuma har ga ya tsakani, ka rika bin abubuwa a hankali, yanzu idan ka ce zaka yi rigima ai zaka karawa kanka bakin jini ne kawai a gurin Emily" "Amman kuma sai na bar wani katon banza yana kallar min mata yana jin sautin muryarta yana karanta mata karya da gasjiya akaina" Ya mike tsaye. "Zan je na yi magana da ita zan bi duk wasu matakai da suka dace ta ruwan sanyi tsakanina da ita, kuma zan jawa Aliyu kunne, shi yana da tasa mata ni kuma yana son ya kashe min aure saboda ya bata tsakanina dake kuma da Fatima, ni na rasa me na tarewa Aliyu ne Wallahi, ashe haka hassada take" "Karka je" "Ammy me yasa kike hana ni abubuwa ne? Miyasa kika kin goya min baya a komai, yau na tabbatar da ace ni na na aikata abin da Aliyu ya aikata Wallahi ba zaki goya min baya ba, amman da idona na ga Ummi ta fito ta rungume Emily sun shiga tare, kin ga ta goyawa danta baya kenan da saninta ake komai waya sani ma ko Emily a gidanta take, shiyasa har Kameela ta san da komai" "Turhan..." Ammy ta kira sunansa, ya kalleta ba tare da amsa ba. "Zauna" Ya koma ya zauna. "Mahaifinka ya fada maka ni na dauki cikinka wata ta haife ka ne?" "Aa" "To taya kake tunanin zan fi son wasu da kai? Duk abubuwa na nake maka ko nake fushi da kai akansu saboda ina kaunarka ne, na aura maka yarinyar nan saboda na samu ka yi kusa da ni, kuma ita ma ina hango mata jindadi a zamantakewarku, saboda ta auri wani bata dace ba, ina ganin idan aka kyautata mata kamar an yi ma musulunci hidima ne, daga lokacin da ta gudu ta bar min bakar wasika na san zamanku be tafi a yadda na yi tsammani ba, shiyasa ban taba tambayar ya kuka yi zaman ba, amman a zuciyata na ji babu dadi kuma na ji idan har baka nemo yarinyar nan ba, ni da kai ba mu gyara abun da ka bata ba, ba zan samu salama ba, na yi fushi da kai ne saboda na auna hakikan abun da yake zuciyarka da gaske zaka iya min biyayya ko aa kuma zaka so abun da nake so ko aa, daga lokacin da ka dage kana neman yarinyar nan zuwa yau data bayyana a garemu, ya tabbatar min da biyayyarka da kuma son farinciki da gujewa bacin raina, gashi kuma ta zo mana da alheri haihuwar da kake ta nema sanadinta ka samu, ko bana raye na san zaka yi alfahari da hakan, kuma na san zaka rike yan'uwa ka rika ziyartarsu, aurenka da Emily zai kara kusancinka da ni, na san yanzu ba zata yarda ta bika ba, amman zata yarda ta zauna a nan, kuma na san a yanzu kam dole zaka bata hakkinta, inda kana son zama da ita kana son yarta dole zaka zo, toh kuma sai ka yi tunanin ba zan taya ka wannan yakin ba?" Kalman Ammy sun kwantar masa da hankali kuma sun saka ya ji sanyi kana sun karfafa nasa guiwa, sai dai hakan be kawar da abun da yake ji na kiyayyar ganin Emily ko magana da ita da Aliyu yake ba, domin baya kusa da ita yanzu. "Tashi ka tafi gurin yarka, ni zan shirya yanzu na tafi gurin Ummi zan yi magana da ita dole ai ayi ma tukar hanci" Turhan ya mike tsaye ya karasa inda Ammy take zaune ya kama hannayenta ya sumbanta sannan ya sumbanci goshinta. "Na gode Ammy" Ya nufi sama, sai ta bi bayansa da kallo tana murmushin jindadi, a yanzu ba ɗa kadai take da shi ba har da jika gashi kuma Emily ta dawo komai zai daidaita ya zama daidai a rayuwarsu. Tashi ta yi ta shiga ciki ta shirya shirin fita kamin ta fito Nurse dake duba jininta ta shigo ta hauro har sama ta auna jinin. "Maa Shaa Allah, Hajiya jiki ya sauka sosai daman Dr yace idan na auna jinin na ga be hau ba, to na fada miki karki sake shan maganinki sai ya shigo anjima zai canja miki da su kuma ya fada miki yadda ya kamata a sha" "Alhamdulillah, hankali na ne ya fara kwanciya yanzu, ciwon sugar ma ina tunanin zai sauka In Shaa Allahu" "Eh shi ma naga jiya ya sauka sosai, Allah ya kara lafiya" "Ameen" Ammy ta janyo jakarta ta ciro kudi mai kauri ta mikawa Nurse din. "Aa Hajiya" "Haba ki karba mana, alheri ne ai ba a maida hannun kyauta baya" Nurse din ta karba tana mata godiya sannan ta fice. Waya Ammy ta janyo ta nemo number Ummi ta kirata sai da wayar ta fara ringing sannan Ammy ta karaa kunne. Ummi ta amsa tare da amsa sallamar da Ammy ta yi, bayan sun gaisa Ammy ta ce. "Ya Aliyu da karfin jikin?" "Alhamdulillah" "Ina son na shigo ne, kina gida ko kina asibiti?" "Ina gida" "Toh gani nan zuwa" Ta aje wayar sannan ta dauki mayafinta ta yafa a jiki ta dauki jakarta ta saka talkaminta ta fice, dakin da Fatima take ta fara turawa a hankali sai ta hangota zaune a kasa Turhan yana zaune gabanta. "Zan tafi" "Okay Allah ya kiyaye Ammy, Wallahi Aliyu yayi min Illa Ammy yarinyar yanzu sunansa kawai take kira sai na mahaifiyarta, tana da hujjar kiran sunan Aisha amman Aliyu fa? Miye hadinta dashi? Yanzu fa ko da na shigo ya kirata a waya magana suke yi" "Ka bi komai a sannu, ai mutum be taba cin amana ya ga nasara a rayuwa ba" "Ni mamana nake so, na tsane ku duka, sace ni kuka yi, Uncle Aliyu zai zo ya dauke ni" Fatima ta fada tana hararar Ammy daman karamin aikinta ne rashin kunya. Ammy ta saki kofar dakin ta shigo ciki ta karaso inda Fatima take zauna ta rikota sai Fatima ta fisge hannunta, Ammy ta sake rikota ta dagota ta nufi gaban madubi da ita ta dorata tsaye akan kujerar madubin, sai Turhan ya taso ya zo ya tsaya kusa da ita yana kallon madubin. Ta cikin madubin Ammy ta nuna mata Turhan tace "Kalli wannan mutunen" Fatima ta kalleshi tana kumbura baki. "Kalli wannan yarinyar" Fatima ta kalli kanta. "Fada min da wa take kama?" Fatima ta kara turo baki ta ki ta yi magana, ba dan kuma bata fahimci me Ammy take fada ba sai dan shakiyancin ba zai barta ta bada amsa ba. "Wannan yarinyar ta yi kama da wannan mutumen ko baki gani ba?" Fatima ta sake kallon Turhan ta cikin madubi ta kalli kanta. "Saboda wacan mutumen shi ne mahaifin wannan yarinyar" "Ba ni da mahaifina Momy ta fada min haka aka haifa ni ba ni da mahaifi, baki ji sunana ba Fatima Emily Aisha" "Aa kina da shi, kowa na duniyar nan yana da uba sai ke kadai ce za ace baki da uba? Kina uba Fatima ni kuma kakarki ce, ke yar dangi ce jinin sarauta daga da baya kuma yar larabawa, kina da uba Fatima kalli ki gani kin taba ganin wani wanda kuka yi kama kamar wannan" Fatima ta juya ta kalleshi. "Meyasa Momy tace bani da Baba? Kuma miyasa be taba zuwa ba?" "Yanzu su ya kamata ki tambaya, kowanensu sai ya baki amsa, amman tabbas wannan mahaifinki ne, daga sunanki ya tashi daga Fatima Emily Aisha, ya kuma Fatima Turhan Muhammed Abdo, idan ba mu da alaka da ke ai ba zai taba yayu mu rike ki mahaifiyarki ta kyale ba" Fatima ta kalleshi da cikin madubi ta ga kamaninsu sosai kuma tana ji ya kwanta mata a rai a matsayin uba tun a ranar daya rungume ta, sai dai kawai bata yarda da su ba ne, domin ba mahaifiyarta ce ta fada mata ba. Fatima ta fashe da kuka "Miyasa Momy tace ba ni da Baba? Idan shi Babana ne miyasa be zo ba shekara da yawa? Yan makarantarmu suna min dariyar sunana, suna cewa ba ni da Baba" "Tsawon lokacin nan, nemanki muke ke da Emily ba mu san inda za mu ganku ba, sai a yanzu da Aliyu ya zo da ke, wata kila shiyasa ya zo dake saboda ya nuna miki mahaifinki ne" "Ina son na yi magana da shi" Ta sauka daga kan kujerar ta nufi inda wayar Aliyu take ta dauka ta mikawa Turhan. "Kira shi" Turhan ya karɓi wayar ya rike, har sai da Ammy ta ce. "Kira mata Aliyun" Kamar zai musa sai kuma ya taba number Aliyu ya saka hands-free, yana jin zuciyarsa kamar zata fashe tsabar bakinciki "Hello My Beautiful Angel" "Uncle Aliyuuuuu wani ne a nan yana cewa shi ne Babana da wata tsohuwa, a nan gidan da wannan matar ta kawo ni gaskiya ne? Tun ranar yake cewa shi ne mahaifina, kuma yana kama da ni" Aliyu yayi shiru na dakiku. "Eh mahaifinki ne" "Miyasa Momy tayi min karya tace ba ni da Baba?" "Saboda.... Ta yi tunanin ya rasu ne... Bata son ta fada miki ki shiga damuwa shiyasa take fada miki haka, amman yanzu mun gane yana da rai shiyasa aka kawo ki nan dan ki san shi kuma ki saba da shi, dan haka ki zama yarinyar kirki yi rika jin magana karki ce zaki yi tsiwa kinji ko?" "Ba zaka zo ka dauke ni ba?" "Zan zo amman sai kin kwana biyu kin saba da shi tukuna, sai na zo na dauke ki, ba na san kina son uba ba? Kina son canja sunanki ki hada da na mahaifi to daga yanzu zai canja" "Ba sunanka kace zaka saka min ba? Ni bana son sunan wannan ni bana son shi ni kai nake so, i don't want this old woman and her Son kai nake so da Momy" Ita kawai bata saba da su ba ne, tana son uba amman ta fi sha'awar ace akwai wani wanda ta wani a kusa. "Okay za mu zo ai, amman sai idan kin yi biyayya kin zama yarinyar kirki, bana son rashin magana da tsiwa, idan kina musu fushi ba zan zo ba, amman idan kika zama yarinyar kirki zan zo" "Okay i will be a good girl" "Yauwa, i love you can you say you love me back?" "I love you ka zo da sauri" "Okay bye" Turhan ya karɓe wayar ya datse kiran ko da be iya mayarda duka yaren turanci ba ai yana jin abun da yake fada kuma ya fahimci komai, kamar zai buga wayar a kasa sai kuma ya daure ya saki murmushi ya mika mata wayar, sai ta kura masa ido tana ta kallonsa ya rage tsawonsq ya duka daidai ita sai ta matsa jikinsa ta kwanta ya rungume suka zauna a gurin Each and every second sai ta daga kai ta kalleshi ya kalleta tana kuka mai karfi ta ce "Zan fadawa yan makarantarmu ina da Baba, zan tafi kai zan nuna musu, i hate Momy i hate her" Hawaye ya cika idon Turhan Ammy daman tuni ta fara zubar da nata. "Ni ma zan fadawa family ina da ya, ina da kaso a jinjina, zan baki duk wani gata da kika rasa Fatima, ki yi hakuri na zo a makare" Ammy ta share hawayenta tana murmushin farinciki. "A yau zaka kara sanin muhimmanci na Turhan, zaka san abun da ake kira da iyaye, zaka san sha'anin yaya" Ta dauki jakarta ta fice daga dakin tana kara shaye hawayenta, sai da ta fito sannan ta sanar da direban ya fito ya same ta ya bude mata mota ta shiga, ta zauna kenan wayarta ta yi ringing sai ta ciro wayar daga jakarta ta duba sai ta ga bakuwar number. "Sallamu Alaikum" Mai kiran ta amsa mata ta dayan bangaren sannan ta gabatar mata da kanta. "Sunana Hajiya Barakat, amman yara suna kirana da Mama Baraka" "Maa Shaa Allahu, sai dai ban gane ki ba" "Eh to ba mu taba magana ba, ba lallai ki yi saurin gane ni ba, ni step mother din Kameela ce matar Aliyu abokin danki" "Okay Tohm Lafiya?" "Ba lafiya ba, ina son mu yi magana da ke ne akan Emily da kuma yarta Fatima da take gurinku" "Ina saurarenki" "Ba maganar waya ba ce ina son ganinki ne" "Zaki iya zuwa gidana zuwa anjima yanzu dai ina hanyar tafiya wani gurin ne, idan zaki taso sai ki sanar da ni na kwatanta miki" "Tohm shi kenan" Ammy ta sauke wayar tana mamakin kiran, zuciyarta na raya mata wata kila Kameela tana son ta karbe Fatima ne ta maidata gurin Emily saboda Aliyu, ko kuma dai wani abun ne tun da Allah kadai ya san me ya faru na kawo yarinyar da Kameela ta yi ba tare da izinin Aliyu ba. Haka dai Ammy ta yi ta sake sake har suka isa gidan Ummi. [7/11, 10:21 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣0️⃣ Ummi na falo tana ta gaisawa da mutane yan'uwa da abokan arziki da suka zo mata jaje sai ga Mama Barakat ta shigo falon da sallamata tare da rakiyar yarinyarta ta biyu. Ummi na ganinta ta dan daure fuska kadan domin ta san zuwanta ba zai wuce saboda Kameela ba, sama sama suka gaisa da Ummi sai Ummi ta maida hankalinta gurin sauran baki bata sake bi ta kan Mama Barakat ba har sai da Mama Barakat ta gaji da zama ta ce. "Hajiya gurinki na zo" Ummi ta maido da hankalinta gurinta sannan ta mike tsaye ta nufi wani dakin baki dake falon ta shiga tana fadin. "Bismillah Hajiya Baraka" Ummi ta fara shiga ta zauna sai ga Mama Baraka ta shigo ta zauna kan kujerar dake dakin. "Na katse ki kina da baki, na tafi asibiti ai aka ce kin zo gida kuma ba su yarda na shiga na duba Aliyun ba" "Eh ana son ya huta ne, kuma saboda abun da ya faru da shi ya saka ake ba shi tsoro dole a san suwa suke shiga da fita" "Allah sarki, Allah ya ba shi lafiya kuma ya tsare gaba, mu ma a gari muka ji abun da yake faruwa" "Ameen Ya Rabbi" Daga haka sai shiru ya biyo baya, Mama Barakat bata sake cewa komai ba hakan ya saka domin ta yi tunanin wata kila ta zo nan ne amadadin mahaifiyar Kameela, dan haka Ummi ta tari hanzarinta tun kamin ta fara magana. "Hajiya Baraka Allah dai ya sa ba kin zo maganar Kameela ba ne, domin dai yanzu Aliyu yana bukatar hutu da kwanciyar hankali, kuma iya hakuri ni dai na yi a matsayi na uwarsa na dauke ido iya yadda zan iya, yanzu kan abun ya wuce duk inda ake tunani ba kuma zan yarda ta kashe min ɗana ba saboda kishinta na banza. Abun ya kai har ta saka masa guba kin ga ai ba so ba ne ba kuma kishi ba hauka ne" "Subhanallahi, guba fa kika ce Hajiya" "Da bakinsa ya fada min, shi ne dalilin turo ta gida da yayi ai, amman be fadawa kowa ba sai a yanzu da ta kai shi makura, kin ga yanzu ko za su zauna da junansu ni ba yarda zan yi ba, ba zai yiyu su da aure ni da zaman zullumi da fargabar me zai faru ba" "Ban taba ji wannan, amman Kameela bata yi ma kanta adalci ba, Subhanallahi, ni ba ma zancen ta ya kawo ni ba, Wallahi ba dan kowa na zo ba sai dan yarinyar da aka ce saboda ita Aliyu ya saki Kameela, shiyasa na tafi asibiti aka ce baki can na tambaya dan Allah ita Emily tana tare da shi ne na kwatanta musu ita suka ce min kun taho tare" "Emily? Toh Allah yasa ba daga mata hankali za'ayi ba, domin yarinyar nan tana cikin damuwa, kuma kamar amana take a gurina" "Haba Hajiya ni ma fa Uwa ce, ta ina zan nemi daga hankalin wata ya? Magana kawai nake son yi da ita, saboda ina tunanin kamar ita ce yarinyar da aka taba hada mu da ita a lokacin da muka je Abuja, na zo da ita har Kaduna sai ta gudu bata tsaya ma na taimaka mata ba" "Allah sarki Ashe kin santa" Nan Hajiya Barakat ta labarta ma Ummi farkon haduwarsu da kuma dalilin haduwa. "Toh ki haura sama, tana nan daki na farko hannun hagu" "Toh na gode Hajiya" Mama Barakat ta tashi tare da Ummi suka fito Ummi ta koma gurin Mutanenta Mama Barakat kuma ta nufi upstairs ta haura sama ta bi hagu da ita kamar yadda Ummi ta fada mata, dakin farko ta fara turawa a hankali ta leka sai ta hango Emily zaune kan gadon Aliyu tana rutsar kuka a hankali marar sauti. A take zuciyar Mama Barakat ta kara karyewa daman ta shigo gidan zuciyarta cike da rauni, ta shiga ciki gaba daya ta maida kofar ta rufe karar rufe kofar ya saka Emily ta kalli kofar sai ta yi hanzarin takaita kukanta ta sauke kanta kasa. Mama Barakat ta karasa cikin dakin ta zauna bakin gadon tana kallon Emily babu shiri hawaye suka zubo mata, yadda Emily ta takure guri daya ya bata tausayi sosai. "Ba lallai ki gane ni ba, sunana Mama Barakat, mun tana haduwa da ke a lokacin da kika bar Sudan Mrs Deborah ta zo da ke, sai tace na zo da ke Kaduna saboda kin fada mata a nan kike, kamin ayi bincike ba ki ma zauna a gidana sai kika gudu ko kin gane ni?" Emily ta kalleta da kyau ta daga mata kai, daman tun farkon shigowarta ta ga alamar kamar ta taba ganinta. Cikin kuka Mama Barakat ta ce. "Meyasa kika gudu? Me yasa baki tsaya ba? Wata kila da yanzu baki shiga cikin wata damuwa ba, baki yarda da ni ba ne a lokacin? Na yi tunanin ke musulma ce a lokacin?" Emily ta kalleta hawaye na sauko mata. "Gaba daya ni a yanzu ban fahimci rayuwa ba, ban gane me take nufi da ni ba, daga wannan sai na fadawa wannan, idan har iyayena ko yan'uwana ba za su iya rike ni tun a lokacin da ban san komai ba, bana tunanin akwai wanda sai rike ni na samu mafita, bayan barin gidanki abubuwa da yawa sun faru, a lokacin na samu gata kuma ina da yarana har biyu, sai ga shi kuma rayuwa ta sake juye min ta kawo ni nan, babu gatan babu uwa ba uba ba babu yaran, dayan ya mutu dayan an karbe, ni yanzu na kasa fahimtar komai" Ta fashe da kuka, Mama Barakat ta matsa kusa da Emily ta rungumota ta kwanto da ita jikinta ita ma ya fashe da kuka mai karfi wanda ya fi na Emily shiga zuciya da sosai rai, ta rumgume Emily sosai tana shafa kanta. Emily ta lafe a jikin Mama Barakat daman tana neman wanda zai rumgume ta kamar haka a yanzu, sai duk ta ji kewa da son kasancewa da tata uwar duk da yake bata taba sanin ya dadinta yake ba, amman ta sani idan har akwai iyaye a tare da ita ko yan'uwa na jini wasu abubuwan za su zo mata da sauki. "I Need my own parents, ni mace ce kawai mai son iyayenta da yan'uwanta a kusa da ita, why all this? Me na yi musu? Me na yi ma rayuwar? Me yasa kaddara take ta juya ni haka? Na gaji na gaji na gaji" Tana maganar tana kuka mai ban tausayi ta takure sosai a jikin Mama Barakat kamar zata shige jikinta, bankarewa Mama Barakat ta yi ta daga kai sama tana ta yaki da numfashi da kuma kukan dake son sakata ihu, hawaye suka rika sauko mata ta gefen ido wasu na bin wasu. Sai da ta kai ruwa rana tsakanin kukanta da numfashinta sannan natsuwarta ta samu daidaituwa, ta maido idonta akan Emily ta shafa kanta. "Na samu labarin abun da ya same ki a yanzu nw ta gurin Kameela saboda sakin da Aliyu yayi mata na abu...." Mama Barakat bata kai aya ba Emily ta daga daga jikinta da sauri ta matsa baya. "Fita dakin nan" Mama Barakat ta girgiza kai da sauri. "Ba ki gane ba ne, bana goyon bayan Kameela ina tare da ke ne..." "Ki fitar min daga nan, bana son Kameela bana son duk wani abin da ya shafe ta, fita yanzu nan" Mama Baraka ta mike tsaye ta dauki jakarta kamar mai tsoro jikinta har rawa yake. "Tohm, zan fita amman idan kina bukatar wani abu ko taimako zaki iya tuntuba ta, kuma zan kasance kusa da ke daga yanzu In Shaa Allahu, idan kina bukatar wani abu ki fadawa Aliyu zai fada min yana da number wayana" Ta nufi kofa tana yi tana juyo ta kalli Emily har ta fice, sai da ta tsaya ta share hawayen ta sannan ta sauko jiki babu karfi murya kuma ta sauya ga ido ma be isa ya karyata cewar ya zubar da hawaye ba. Ta sauko tana ta masa kasa da ido bata son hada ido ta mutane saboda bata son kowa ya gane ta yi kuka, amman hakan be hana Ummi tambayar lafiya ba bayan ta tambaye ta sun gana. "Eh mun yi magana da ita" "Allah yasa dai lafiya, yanayinki kamar ya canja Hajiya Barakat" "Lafiya kalau, dan Allah zan iya samun number mahaifiyar abokin Aliyu nan a gurinki? Domin na kira Aliyu be daga ba, na manta sunan abokin nasa dai amman wanda aka kaiwa yarinyar ta Emily" "Oh Turhan? Eh ina da number mahaifiyarsa" Ummi ta kai hannu ta dauko wayarta ta kamo number ta karanta mata, Mama Barakat ta saka sannan ta yi mata godiya ta yi mata sallama ta fice tare da yarta wacce ta rakota. Fitar Mama Barakat mutane suka ragu har Ummi ta samu damar amsa waya daya daga cikin mutanen da suke kiranta, sannan ta haura sama ta yi wanka ta sauko domin shiryawa Daddy wani abu kamin ya iso, daman bata yarda mijinta ya ci abincin kowa sai ita, sai idan bata gida ko kuma wani babba uzuri ya sha gabanta. Tana Kitchen tana tsaka da girkin ne ta ji sallamar Ammy, sai ta rage wutar gas din ta yi kasa sannan ta fito. "Maraba da Hajiya Maijidda, yau Ammy ce a gidan na mu" "Ni ce Ummi, fatan mun same ku lafiya" "Toh Alhamdulillah, ya gidan ya kwana biyu" "Sai godiya, ya Aliyu da jiki? Ashe haka abu ya faru? Tohm Allah ya saukewa ya tsare gaba" "Ameen Ameen, ashe kun ji" "Eh ai kin san abu irin wannan yana saurin yado, balle kuma wayarsa tana gidanmu gurin Fatima, to yawan kiran da ake ne nake amsawa ta nan na ji" "Oh ashe wayar tana tare da ku, ikon Allah to yarinyar take?" "Tana nan lafiya kalau" "Maa Shaa Allah, tohm bari na duba girkina" "Tsaya dai tukuna Ummi na zo nan saboda mu tattauna abubuwan da suka faru" Ummi ta koma ta zauna. "Toh kamar me kenan?" "Haba ki daina yin kamar baki san komai ba mana, Aliyu be fada miki abun da ya aikata mana ba? Kuma na san Emily ai tana nan ko?" "Eh haka ne, Emily tana nan tare da mu, Aliyu kuma be fada min ya aikata muku wani abu ba" Ammy ta sauke ajiyar zuciya. "Na san kin san yadda muke ta faman neman Emily, shi kansa Aliyun ya fi kowa sani domin Turhan be boye masa komai ba, amman ace Aliyu ya san inda Emily take wai har da ya a tsakaninsu amman ko da wasa be kyankyawasa Turhan ba?" Ummi ta hade yawu. "Ammy a yanzu ba zan iya bawa Aliyu kariya ko wanka ko dora masa laifi ba, Aliyu dai danki ne kamata yayi ace ki same shi ku tattauna" Ammy ta yi murmushi mai sauti. "Emily tana gurinki ne duk tsawon lokaci nan ko kuma dai a yanzu ne ta zo nan" "Aa ni ma a yanzu na san da ita, shi ma saboda abubuwan da suka faru ne na daukar yarta da Kameela ta yi ta kai muku ba tare da izininta ba" "Ai Kameela ta kyauta mana Wallahi, ba dan ita ba wata kila da har yanzu ba mu san komai ba, kuma Aliyu ya san yadda Turhan yake ta neman yaya" "Ta kyauta tun da ta raba uwa da ƴa, kuma ta raba igiyar aurenta kin ga ai ta ci riba, ni kuma sai na yi mamakin da aka ce Fatima tana hannunku kun riketa uwarta tana nan tana fama da kewar da damuwa, kun san yarinyar bata da gata sai Allah, gashi yanzu har ta bar musulunci" "Ummi ya kike magana kamar kina goyon bayan Aliyu? Kina ganin hakan daidai ne kenan?" "Bana goyon bayan Aliyu, amman ni dai na san ban manta lokacin da kike zuwa kamun kafa a gurin Daddyn Aliyu ba saboda kina neman a baki dama ki samu ganin Turhan, daga baya kuma kika koma rokon a bar shi ya rika zuwa inda kike, ke dai uwa ce na san kin san zafin rabuwar da da uwa, ya kike tunanin Emily tana ji a yanzu? Yarinya ta raini yarta shekara da shakaru rana tsaka ku dira a rayuwarta ku karbe mata ya? Anya kun yi adalci kuwa? Abun ma ai da kunya" "Ba karbe muka yi ba, mun rike ta ne ta yadda zata saba da mu, ke kin sani Turhan kadaina haifa, ko kare aka ce nasa ne ya kike tunanin zan so shi balle jika? Ni dai ban aurawa Emily Turhan da nufin cutar da ita ba, idan ma ba su fahimci juna ita da Turhan ba, ni be kamata ta saka ni ciki ba, kuma ko yaya dai za a juya a juyo Emily tana da igiyar auren Turhan a kanta karki manta da wannan" "Ammy idan kin zo saboda Emily ne, tana sama daki na farko hannun hagu, ni dai ba zan fada miki fari da baki akan jikarki da yarki ba, kabli da ba'adin rayuwa kin sani, idan kin yi daidai ko akasin haka a bayyane yake, ni zan shiga na karasa girkina" Ummi ta mike tsaye ta nufi kitchen, Ammy ta bita da kallo mai wuyar fassara sannan ta tashi ta haura sama ta shiga dakin da Ummi ta fada mata Emily tana ciki. Emily ta sauko da kafafuwanta kasa ta kalli kofar tana jin tsanar sunan Kameela ma balle kuma abun da ya alakance ta. Mikewa ta yi tsaye ta nufi inda take kyautata zaton bandaki ta tura ta shiga. Kallon ko'ina ta yi komai yana nan na gyara jiki ko gashi na maza kai kace Aliyu yana rayuwa a gidan har lokacin. Shaving cream ta fara dauka ta duba sannan ta duba shower gel, ta nufo shower ta kunna ta daga kai tana kallo ta tara hannunta ruwan ya zuba a hannunta sai kuma ta juyo gurin madubi ta kalli kanta kamin ta kunna tab ta fara wanke fuskarta, bayan ta gama ta dauki karamin tawul data gani aje a gurin ta dauka ta goge fuskarta ta aje sannan ta fito, tana karewa dakin kallo gaban madubin gadon ta fara nufa tana duba turaruka da suke gurin da mayuka na maza na gyara jiki, daya bayan daya ta dauka tana dubawa sannan ta aje ta nufi closet ta bude tana kallon tufafinsa talkaminsa da kuma hulluna. "Assalamu Alaikum" Sallamar Ammy ce ta saka ta juyowa ta kalli kofar sai ta maida kanta gurin kayan da take kallo ba tare da ya amsa ba. "Kina fushi da ni har yanzu, amman baki fahimce ni ba ne Aisha, bana nufin cutar da ke, daga lokacin da kika bar min wasikar nan kika gudu ba sake walwala ba, Turhan be saka samun damata ba, na yi mamakin da na ganki a cikin wannan shiga da kuma canja addinin da kika yi, wannan duk be dace da ke ba" Emily ta juyo ta kalleta. "Toh me ya dace da ni? Cigaba da zama da mutumen da na fi kaunar mutuwata a kansa? Ko kuma yarda da surukar da ta fifita farincikinta akan nawa? Ke kika fada min danki zai ba ni farinciki zai ba ni gata, sai gashi danki ya maida ni baiwa a masarautar da shi ya kamata ya ba ni gata, ya maida ni kurma alhalin ina ji, ya gabatar da ni masarautar a matsayin baiwa da kika ba shi, ko wace safiya sai na wanke bangaren matarsa, bana iya cin abincinsu a haka nake daurewa, ko da yake laifina ne, ai ya gargade ni tun kamin na aure shi, yace kar na amince, amman saboda ina son na faranta miki rai na miki sakamako da abu mai kyau na amince, ban taba son Turhan ba, kuma ba zan taba son shi ba, na aure shi saboda ke, a daren ranar da aka daura auren ya fada min bakar rana ce a gurinsa, a daren da aka samu cikin Fatima ya fada min bakar rana ce a gurinsa, ya fada min ba zai taba so na ko son abun da zai fito daga gareni ba, na azabtu a masarautar nan kyautar da ni aka yi ga wata mata matsayin baiwa da haka na zamu yanci, na raini cikin yata cikin wahala na haife ta ta girma ba tare da kulawa daga ubanta ba... Ko da yake ba zaki fahimta ba danki ne a gabanki..." Ta karasa tana girgiza ka tana share hawaye. Ammy ta kai zaune tana hawaye. "Na aura miki shi ne da tunanin ke da shi kuna son junanku, ni ma na yi makamanciyar rayuwar da kuka yi, amman ni na cutu ne saboda mahaifinsa baya so na, ban yi tunanin Turhan zai kyamace ki ba, shiyasa sai da na zaba na mika masa, ban ba shi gama garin bakar fata kamar sauran ba, ban yi nufin kulla Sheri ba Emily alheri na yi nufi" Emily ta dauke kai. Ammy ta nuna kusa da ita. "Zauna... Zauna ki fada min wane irin zama kuka yi, kuma me kike bukata a yanzu?" Emily ta kalli Ammy da idonta suke cike da hawaye sannan ta zauna tana aje numfashi mai nauyi a muhallinsa. [7/14, 6:25 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣1️⃣ Cikin kuka da shesshekar kuka Emily ta karasawa Ammy labarin irin zaman da ta yi a Sudan da kuma rayuwar da ta biyo bayan zamanta a can, yadda ta hadu da Vito ta canja addini har zuwa haduwarta da Aliyu da irin rokon da ta yi masa na kar ya sanar da Turhan inda take, Emily bata boye mata ba, ta fada mata har auren nw ta yi ne saboda ita ba dan tana son Turhan ba. Ammy yaja numfashi da nauyi ta sauke hawaye na sauko mata kuka take sosai tata rayuwar take tunawa, yadda abubuwa ta yi zama da mahaifin Turhan. "Zuciyata ta raya min dole akwai abin da yake faruwa da ya saka kika gudu kuma kika bar min wannan sakon, amman ban taba tambayarsa wane irin zama kuka yi da juna ba, ni dai damuwata na yadda za a gano ki ne, wannan dalilin ya saka na daga hankalin Turhan na sauya masa fuska, na yi duk yadda uwa zata yi idan ta rasa yarsa, kin san saboda me? Saboda na gane shim Turhan mai biyayya ne a gareni? Kuma saboda ya nemo ki, ban manta lokacin da kika fada min baki da kowa ba, ina yawan tuna wannan, kuma ina jin wata kila idan na taimake ki zan iya samu aljannata ta nan, ashe ma akwai jinina a tare da ke, na aura miki Turhan ne saboda ni da ke mu samu mafita, ke ki samu miji mai nagarta mai kulawa, ni kuma na samu ɗana da zuri'arsa a kusa da ni, amman na yi kuskure, na jahilci ɗana, na yi zaton zai riritaki ne, ashe yayi miki rikon da kadan ya banbanta da wanda mahaifinsa yayi min" Ammy ta kai hannu zata taba Emily sai Emily ta matsa tana hawaye. "Baki fahimce ni ba ne Aisha, amman har gobe baki da wata uwa sai ni, ban yi nufin cutar da ke ba, na hada aurenki da Turhan ne saboda ina tunanin zai so ki, na duba kyanki a lokaci da yadda siffarki ta banbanta da yayan hausawa, wai ina zaton haka zai daga kimarki a gurinsa, sama da ace bakar fata na aura masa, na so ki kamar yar da na haifa a cikina, har gobe ni uwarki ce" Emily ta kalleta. "Zan tabbatar da hakan ne kadai idan kika saka ɗanki ya sake ni!!! Idan kika yi haka zan tabbatar kin dauke a matsayin Ƴa!" Ammy ta hade yawu da karfi ta yi jimmm na dan lokaci kamin ta sake hade yawun a karo na biyu ta daga kai. "Zan tabbatar miki da haka Aisha, ba zan so yarki ta tashi da iyaye a rabe ba, ke kin san zafin haka, haka kuma na so ki da jinina na yi nufin yanzu mu kyautata gareki, amman zan shure komai saboda farincikinki zan miki yadda kike bukata" Ammy ta mike tsaye ta dauki jakar har ta fara tafiya sai kuma ta juyo. "Zan roki alfarma daya, karki cusa tsanarmu a zuciyar Fatima, haka kuma ba zan iya shiga tsakanin uwa da ƴa ba, ba zan iya yanke hukunci akan Fatima ko Turhan ba, amman dai a tsakaninku ni na hada kuma zan raba, na barki lafiya" Ta juya ta cigaba da tafiyarta har ta isa bakin kofar ta bude ta fice, ta sauko kasa kenan ta hadu da Ummi da zata hauro sama. "Kin fito?" Ammy ta kalli Ummi ido cikin ido. "Eh na fito, Turhan zai saki Aisha zan tabbatar mata da cewar tabbas a ya na dauke ta, idan ya sake ta sai Aliyu ya aureta, na barki cikin amincin Allah" Ammy ta nufi kofa ta bar Ummi tsaye da mamaki tana kallonta har ta fice. Ummi ta haura sama ta tura dakin Aliyu da Emily take ta leka sai ta hangota tana kuka. "Ke haka zaki zauna kullum kuka kuka? Shiga ki wanke fuskarki ki fito muje kitchen" Emily ta mike tsaye ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito Ummi ta rike mata kofa ta fito suka sauka kasa, Kitchen din suka nufa ba dan ran Emily ya so ba sai dan Ummi ta bukata, a tare suka karasa aikin sai da suka jera komai a dinning sannan Ummi ta kalleta ta ce. "Kina fifita farincikin wasu akan naki, kina fargaba tunkarar wasu da abun da yake zuciyarki, shiyasa kika cutar da kanki, ko da yake ta wani bangaren ba laifin ba ne, kin tashi ba tare da kowa ba, duk wanda ya rasa iyaye ko ya tashi a maraya farincikinsa ragagge ne, a kullum yana tsoro ko fargabar rasa farincikin wani fiye da nasa, ko da yaushe kina jin ke baki da amfani wasu ne masu amfani, karki sake tsorata ko cilasta kanki abun da ba shi kike bukata ba, aikim nan da muka yi ranki be so ba ni na sani, amman kin kasa fada saboda kar raina ya bace" Emily bata ce komai ba idonta dai ya cika da hawaye. Ummi ta dauki cup ta zuba ruwa "Shiga dakin ki wanka, Nafisa zata kawo miki wasu tufafin ki saka kamin a siyo miki irin wadanda kika saba sakawa, idan kin ci abinci sai ki kwanta ki huta" Emily ta juyo ta fara tafiya, sai Ummi ta aje cup din hannunta ta fasa shan ruwa ta kira sunan Emily. "Emily" Ta sake juyowa, Ummi ta karasa kusa da ita ta rumgumeta, sai Emily ta rike ta fashe da kuka sosai, Ummi ta rika shafa bayanta tana jin tausayinta sosai karamar uwa ce da takw bukatar uwa a kusa da ita, kuka sosai Emily ta yi har ta karya zuciyar Ummi da tausayinta, Ummi ta zubar da hawaye tana mamakim yadda wasu uwa ko yan'uwan suke juyawa abun da aka haifa baya har ya rasa gata, alhalin ba su san halin da yaran suke samun kansu ba. Sai da Emily ta samu natsuwa a kafadar Ummi sannan Ummi ta share mata hawayenta. "Shiga ki huta, za a kawo miki abinci" Ta daga kai ta fice daga Kitchen din ta haura sama, Ummi ta kalli Nafisa daya daga cikin yan matan da take riko ta ce. "Ki zuba abinci ki kai mata, a fadawa Kulu ta shirya mata wani abu mai ruwa ruwa ko zata iya sha, wacan abincin kuma ki kaiwa Aliyu idan kin je ki fada masa sai Daddynsa ya iso za mu zo" "Tohm Ummi" Daga haka ta haura sama, Nafisa ta debi abincin ta kai dakin Emily sannan ta sauko ta fita harabar gidan neman Kulu, bayan ta sanar mata umarnin Ummi ta sake dawowa falon sai ta samu Ummi na jiranta. "Ungo ga wannan tufafin shigar mata da shi, ki je ki kaiwa Aliyu abinci yanzu nan" "Tohm" Ta karbi tufafin ta shigar da shi dakin Emily sannan ta fito ta saka mayafinta ta dauki abinci ta fice, Direban da ya kawo Ummi ne ya dauke ta zuwa asibitin bayan sun isa ya rika mata kayan har gurin dakin da Aliyu yake ba abar shi ya shiga ba dan haka yace ta fadawa Aliyu yana gaishe shi, ta amsa da Toh ta shiga ciki. Ta shiga ciki sai ta same shi zaune akan kujera yana tasbihi da alama sallah ya gama. "Sannu Yaya Aliyu ya jikin?" Ya daga mata kai sai da ya shafa addu'a sannan ya amsa. "Alhamdulillah" "Ga abincin ka, Ummi tace na kawo" "Ni zan iya cin abinci yanzu na sha tea ma babu jimawa, maybe zuwa anjima zan iya ci" "Tace a fada maka sai Daddy ya iso za su tare" "Okay, Ina Emily?" "Tana can gida tare da ita aka maka girkin ai" Aliyu ya kalli cooler abinci mai kyau da tsada da Ummi ta siya gurin Khadeeja Candy. "Zuba min abinci" Nafisa ta bude Warmers din ta fara zuba masa soyayyar shimkafa da kaza sai kamshi take. "Yauwa Khaleefa yace yana maka sannu da jiki" "Wane Khaleefa?" "Direba?" "Da shi aka zo daga Abuja?" "Eh shi ya kawo ni yanzu" Ya karbi abincin ya fara ci yana taunawa a hankali. "Idan kin tafi ki fadawa Khaleefa nace ya je kauyensu ya huta na kwana biyu har sai an neme shi, ita kuma Ummi ki fada mata na bawa Khaleefa hutu" "Ka kore shi kenan?" "Aa ai ba zan hana shi hanyar cin abincinsa ba, but for now bana son Emily ta ganshi ranta ya bace, yaje ya huta za a rika biyansa har sai idan Ummi ta bukaci a daina tun da Direban ta ne ba nawa ba" "Okay" "Idan kin koma ki shiga gurin Emily make sure ta ci abinci please, kuma ku rika janta da hira kar a wareta, ko nuna mata banbanci ku rika janta a jiki Please" "Okay" Ya kalli wayarsa dake kan gado tana ringing, Nafisa ta dauko ta miko masa ganin sunan Mama Baraka ya saka shi kallon Nafisa ya ce. "Zaki iya tafiya, Muktar yana nan zai min komai idan ina bukata" "Okay Allah ya baka lafiya" "Ameen" Ya amsa ya aje wayar kan cinyarsa ya cigaba da cin abincin a hankali. TURHAN POV Yana harabar gidan yana video call Fatima a hannunsa sai waving take yi ta gaban wayar, ganin direban Ammy ya saka shi sauke wayar ya nufeta Fatima na hannunsa. Ammy ta fito motar cikin wani yanayi da ke bayyana damuwarta amman hakan be hana da ta kalli Fatima ta yi murmushi ba, ta kai hannu ta karbeta daga Turhan kamar wata yar jaririya, Turhan ya karbi jakar Ammy ya bi bayanta suka shiga falon. Sai da ta fara zama sannan ya zauna Ammy ta sumbanci goshin Fatima ta sumbanci hannunta ta shafa kanta tana murmushi. "Tafi can dakina dake sama ko kuma gurin wayar da Aliyu ya baki zan yi magana da Dadynki" Fatima ta juya ta kalli Turhan dake murmushi ita ma ta yi murmushin jindadi ambatar daddynta da Ammy ta yi ta sauka kan cinyar Ammy ta nufi upstairs, daga Ammy har Turhan binta suka yi da kallo sai da ta haura, sannan Ammy ta kalli Turhan. "Kana kama da mahaifinka sosai, ko kadan ba ka yi kamada ni ba, a kamanni da hali duk baka rago shi ba" Turhan ya fadada murmushinsa yana zaton Ammy zata yabi mahaifinsa ne. "Shi ma ya mu'amalance ni kamar yadda ka yi ma Aisha" A take murmushin dake fuskar Turhan ya gushe. "Ta inda ya dara ka, shi be gabatar da ni a matsayin baiwa ba a gidansa, na shiga a matsayin mata, amman boye ni yake bana fita idan yayi baki saboda kar a gan ni, matansa duka biyu basa bukatar ganina dan haka ban isa na chudanya da su ba, shi kansa auren ya zamo masa dole ne kawai a haka yake zaune da ni, da aka samu cikinka sai ya ji tsoro kar na fara yin zuri'a da shi alhalin baya bukatar wani jinsa a cikin familynsa sai nasa, be yarda na shayar da kaiwa, ina haihuwarka aka karbe aka bawa wata balaraba ita take shayar da kai take maka hidima, da ya ga baka yi kama da ni ba har dadi ya ji, shiyasa bayan na haife ka sai aka hada kai da hadimata aka ba ni maganin hana haihuwa na sha ba tare da na sani ba, da maganin ya zauna a cikina sai ya haifar min da rashin lafiya, a dole yake bani kulawa saboda kar na fadawa mahaifin ya wufintar da kyautar da yayi masa, sai da ya ji ya gani da wahala da ni sai wata rana ya saka na shirya masa abinci, ban san ya aka yi ba amman dai bayan ya ci abinci ya kamu da ciwon ciki aka je asibiti suka tabbatar guba ce, abun da har na kasa ganewa shi ne shi ya saka gubar da kansa ko kuma hada baki yayi da likitan saboda ya fadi hakan? Daga gidan sarauta aka wuce da ni gidan yari wai ina son kashe sarki, mahaifina ya shiga ya fita ya samu daker aka fitar da ni, a wacan lokacin sun yi nufin kashe ni saboda su share labarina. Da aka dawo da ni kasar nan sai ya aiko da min da takardar da saki, wannan maganin da aka ba ni ya zama sanadin da ban samu lafiya ba sai da aka yi min aiki aka cire min mahaifa gaba daya" Ammy tana labarin tana zubar da hawaye, ta kalli Turhan. "Kasan me yasa na fada maka duk wannan?" Ya girgiza kai alamar a a jiki a mace ido na zubda hawaye. "Saboda na fahimci na yi kuskure na hada aurenka da Aisha, balaraben asali be son bakar fata, balaraben mutum yana da dagawa, ina tuna yadda na yi ta yaki na yi ta fadi ta shi na ganin hankalin mahaifinka ya dawo gareni amman hakan be samu ba, indai akan auratayya ne balarabe be taba karbar bakar fata. Gaba daya sun ture karantarwa da koyarwa Ma'aiki da yace wani be fi wani ba sai wanda ya fi jin tsoron Allah" Ya share hawayensa. "Ammy me ya kawo wannan maganar?" "A yanzu da na fada maka ka ji dadin abun da mahaifinka yayi min?" Ya girgiza kai. "Taya kake tunanin Fatima zata ji? Ya zaka ji idan wani yayi ma yarka haka? Da ace ba mahaifinka ne ya aikata min haka ba me zaka yi?" "Ba zan bar shi da rai ba?" Ammy ta daka masa tsawa hawaye na sauko mata. "To kai ba zuciya ce a kirjinka ba? Me yasa baka ji haka lokacin da kake cutatawa amanar da na baka ba? Aisha nan uwar wasu ce ai gashi nan ta haifa maka ƴa, yar wasu ce ita ma yar adam ce idan aka munana mata tana jin zafi kamar yadda zaka ji" "Ban san... San... Iya abun da ta fada miki ba, amman Wallahi ban taba dukanta ba, kuma ba a taba dukanta na kyale ba, ban tana hana mata abinci ba, a lokacin da kika aura min ita na yi kuskuren na kin karbarta ne saboda ina tsoron yadda zan gabatar da ita a matsayin mata a masarautar Mahaifina ba lallai ya karbeta ba, matata ma haka kuma wacan lokacin ina jin kamar darajarta bata kai ba, amman yanzu duk na gane kuskuren hakan" "Ta fada min irin zaman da kuka yi, kuma ta fada min a yanzu saki take so" Turhan ya ji zuciyarsa ta buga da karfi ransa ya bace sosai. "Idan tana son saki zata iya fadar tana son saki ba sai ta saka kin tuna da abun da be kamata ki tuna da shi ba" "Ni na hada auren yanzu kuma zan raba, ka rubuta takardarta ka ba ni zan kai mata" "Zan sake ta, amman ba zan bata Fatima ba" "Tsakanin kai da yarka babu ruwana a ciki, amman tsakanin kai da ita ni na hada yanzu kuma zan raba" Ya hade rai sosai ya tashi ya haura sama gurin da yarsa take. Ammy ta dade zaune a gurin zuciyarta na mata turkuki sannan ta tashi ta shiga dakin, a daren kwana ta yi da bakinciki tuna baya da kuma bakinciki abubuwan da suke faruwa a yanzu. Turhan kuma ya kwana tare da yarsa da tunanin abubuwan da yayi Emily, motsi kadan idan Fatima ta yi sai ya farka domin a kirjinsa ta kwana har safe. Washe gari suka hadu gurin karyawa, Ammy ta juye halshe ta gudun kar Fatima ta fahimci me suke magana akai, da yaren Larabcin Sudan ta ce. "Idan ka rubuta takadar ka ba ni da kaina zan tafi na kai mata" Ya tsayar da cin abinci da yake ya kalli Ammy da babu fuskar wasa a maganarta ya ce. "Da gaske kike yi Ammy? Wai da gaske kike na saki AISHA?" "Na taba maka wasa a irin wannan gabar? Alkawari ma daukar mata kuma zan cika" Ya kasa hade abincin dake bakinsa sai dawowa yayi da shi ya zuba a plate din. "So nasty" Fatima ta fada tana daukar plate dinta ta bar dinning din sai yamutsa fuska take saboda ta yi arba da kazanta. Be kula ta ba sai kallon Ammy yake. "Idan har zan sake ta to miye amfanin nemanta da aka yi ta yi? Kin ce na gyara abun da na bata idan na rabu da ita ta ina zan gyara abun da na bata? And Fatima za a raba mata hankali, bana son ta yi irin rayuwar da na yi" "Daman ai ba sonta kake ba ka fada min, nemanta kuma ya maka rana tun da ka samu Fatima, daman ni burina a nemi yafiyarta kuma asan halin da take ciki, ita ma kuma ba sonka take ba" "Na ji ita tana da hujjar da zata ki ni, ban damu ba idan tana sona ko akasin haka, amman ni nace bana sonta wannan a baya ne, kuma na fada ne kawai saboda ta ji haushi ke ma kuma ki kyale ni, amman yanzu ne lokacin da zan gyara komai, taya kuma zaki ce na sake ta? A yanzu babu wanda nake son farantawa rai kamar ita, Fatima da ke" "Idan kana son faranta mata to ka sake ta mana, bata bukatarka a rayuwarta" "Ni ina bukatarta, idan na sake ta ai ban gyara lafina ba, na kara batawa kenan, kawai ranki ne a bace Ammy amman ni ba zan saki Aisha ba noooooo" "Ka sake ta idan kana sonta kuma ka yi nufin gyara laifinka zaka gyara ko baka tare da ita, ka sake ta sai ka sake bibiyarta idan zuciyarta ta natsu ta yafe maka zata iya amincewa ta sake aurenka" "La la la lala lalala idan na saki Aisha ba zata zabe ni, ta sake aurena ba ko da kuwa maza sun kare a duniyar nan, a yanzu ni nake bukatarka ba ita take bukatata ba, la la la Ammy laa ba zan saki Emily ba, ki can ba ni umarni na bi amman ban da wannan la Ammy laaa" Ya mike tsaye. "Kina cikin fushi zan tafi sai kin huce" Ya nufi yarsa dake zaune kasa tana cin abinci tana game sumbance ta ya hada goshinsa da nata ya lumshe ido yana jin wani irin sanyi da be tana ji ba a duniyar, sanyi rahama na arzikin samun haihuwar da yake nema ido rufe. Sai da ya sake sunbantarta sannan ya mike tsaye ya juya ya kalli Ammy. "Zan yi magana da Aisha, zan dawo da ita kusa da ni, a masarautarmu za mu yi rayuwa mai kyau, idan na sake ai wani banza ne zai aureta, idan mahaifina ya jure ni ba zan jure kallonta a gidan wani ba, zamanta da Aliyu ne su suka kitsa mata komai ni kuwa sai na nuna masa ni namiji ne" "Babu wani hucewa da zan yi, wajibi ne ka sake ta wannan dole ne" Ammy ta fada tana dukan dinning din da karfi. Turhan be sake cewa komai ba ya haura sama ya dauki keys dinsa ya sauko ya fice daga gidan gaba daya. [7/16, 10:07 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣2️⃣ Nafisa ta shiga ta sanar da Ummi hukuncin da Aliyu ya yanke akan Khaleefa, Ummi ta dan yi jimmin sannan ta ce. "Shikenan zan yi magana da shi" Ummi ta tashi da kanta ta dauko kudi mai kauri ta sauko kasa sai kyalli take tana zuba kamshi saboda kwalliyar da ta yi ma mijinta kai kace ba ita ya haifi Aliyu da Yayansa Yusuf ba saboda yadda take kula da jiki, kuma bata taba yarda cewar ta tsufa da yi ma mijinta kwalliya ba. Kamin ta karasa fita falon aka turo kofar falon aka shigo daman ta ji tsayarwa mota. Yusuf ne tare da matarsa suka shigo, Ummi ta saki baki "Ah ah ikon Allah yanke tafiyar kuka yi kuka dawo??" Ummi ta rumgume surukarta tana murmushi, Khadija ta yi dariya "Shi yace kar a fada miki, wai zaki ce ba sai mum dawo ba" Ummi ta dago tana kallonsa da harara. "Daman baka yi nufin hutun ba ko?" Yayi dariya. "Ummi ke da kike mahaifiyarsa kika gagara jurewa ki zauna Abuja sai da kika zo nan balle ni da nake yayansa na san zafinsa fa, ita kuma wannan kin santa da lakuwa duk inda ta ji dake a guri sai ta zo" Ya karasa yana nuna matarsa. "Eh mana ai ita ce yata, kai miye hadina da kai" Yayi murmushi ya daga kafadunsa ya nufi cikin falon. "Toh ga ka ga guri nan, barka da zuwa" Ummi ta fada tana murmushi ta kalli Yusuf kadan ta dauke kai domin bata wasa da shi sosai, ba kamar Aliyu ba da ta dauka tamkar kanenta, Yusuf ta aje shi a muhallin ɗan fari ne. Shi ma kuma ya dauke ta uwa ya dauki mahaifinsa aboki shi kansa ya fi sakewa da mahaifinsa kusan duk wani abu da ya shafi kasuwancin mahaifinsa shi yake tafiyar da shi, sukan tattauna abubuwa da dama ba tare da Aliyu ko ita kanta Ummi ta sani ba. "Zauna Khadija bari na sallami wani na dawo" Ummi ta nufi kofa ta fita, sai da ta fita harabar gidan daya daga cikin yaran gidan ya zo da sauri yana tambayar wani abun za'ayi mata. "a Khaleepa nake nema direban da muka zo da shi ina yake?" "Oh Khaleefa" Yaron ya kwala masa kira, sai ga Khaleefa ya fito daga BQ da saurinsa ya karaso gurin Ummi ya gaisheta. Ta amsa sannan ta ce. "Ai kauyenku a Kaduna nan ne kace ko?" "Eh Hajiya" Ta mika masa kudin hannunta. "Ga wannan, ka yi na mota ka tafi gida ka duba su kuma ka tsaya a can ka kwana biyu, har sai ka ji daga gareni" Gabansa ya fadi ya kalli kudin jiki a sanyaye. "Hajiya wani laifin na yi?" "Aa ba laifi kai yi ba, ba korarka aka yi ba, za'aci gaba da biyanka albashi nan da kwana biyu kuma zaka dawo aiki" "Hajiya saboda na yi magana da Emily ne? Wallahi baki san abun da yake tsakanina da ita ba wata kila da ba ki fusata har haka ba" "Ba saboda ka yi magana da ita ba ne" "Ku kuke da komai na ku, duk hukuncin da kuka yanke yayi daidai, amman ina rokon alfarma daya dan Allah a ba ni damar magana da Emily akwai abubuwan da nake son na tambaye da yawa, kuma akwai wadanda nake son fada mata" "Ita ce bata bukatar ganinka shiyasa aka bata hutu" Khaleefa ya zube kasa ya hada hannu biyu. "Hajiya ki dubi girman Allah ki taimaka ki roki Emily ta saurareni, kusan rabin rayuwar nan na karar da ita gurin neman Emily ne, dan Allah Hajiya ki taimaka min na yi magana da ita, akwai zuri'a a tsakaninmu ina son na tambaye ta, kuma Wallahi a musulma na santa ya aka yi ta zama haka? Dan Allah Hajiya ki ba ni dama" "Damar ba daga ni ba ne, daga ita ne bata bukatar magana da kai a yanxu, ka tafi gida idan ta bukaci hakan zan maka waya, yanzu dai ka tafi dan Allah kar na fito na same ka a nan" Ummi ta duka ta aje masa kudin ta juya yana ta mata magiya kamar zai zauce har da kwalla a ido. Ko da Ummi ta shiga falon ta samu Yusuf ya haura stairs, sai Khadija a falon da Nafisa suna hira. "Ke baki kawo mata komai ba? Ke kuma kamar bakuwa ba zaki shiga ki dauko ruwa ki zuba abincin ba" "Ni na ci abinci, Abban Maama ne dai be ci komai ba" Ummi ta zauna tana tambayar jikokinta. "Ni na manta ina kuka bar yaran?" "Suna can gida, tare da nanny" "Wai ku wannan rayuwa da kuka daukarwa kanku anya zata yi? Ku gaba daya rayuwar turawa? Komai dai nanny? Haihuwar ma tun da aka haifi biyun nan shiru ba kari? Kuma kuna kallon yadda muke a gidan nan daga Aliyu sai mijinki sai Ramla da bata yi aure ba, Aliyu kuma shi Allah be ba shi haihuwar ba, ku kuma daga yin yan biyu sai ku tsaya haka? Muna son zuri'a gaskiya" Khadija ta yi murmushi. "Allah ne be kawo ba Ummi" "Ku yaran zamani masu dabi'ar turawa ta ina za a gane ko daga Allah ne ko kuma daga ku ne, mu dai na mu daga Allah ne ai" Ummi ta mike tsaye tana murmushi domin ta ji tsayarwa motar mijinta, da ganganta ta fada ma Khadija haka domin tana son ta ga tarin jikoki saboda Allah be fata yara da yawa ba, ba kuma zata iya zauna da Yusuf ta yi wannan maganar ba amman zata iya da matarsa. A ranar gidan ya cika da jama'a saboda dawowar Daddy masu zuwa gaishe shi da suka zaba suka zo, wasu ba su san ma abun da yake faruwa ba sai da suka zo wasu kuma yan'uwa ne da abokan arziki suka zo masa jaje, da yammancin ranar Yusuf ya tafi asibitin duba dan'uwansa tare da matarsa da wasu daga cikin yan'uwa, Daddy kam sai dare ya samu zuwa tare da Ummi saboda mutane ba su bar shi ba sai bayan sallah isha'i. Aliyu ya gaisa da mutane ciki har da abokai wasu ma ba a bar su sun shigo ba, yayi farinciki sosai da ganin dan'uwansa, Khadija sai zolayarsa take tana tambayar ina Kameela domin bata san wainar da ake toyawa ba, Aliyu dai daya gaji da tambayarta a fada mata sun rabu. Subhanallahi daga haka bata sake cewa komai ba, daga asibitin suka wuce gidansu dake Kaduna daman suna hutun Anniversary ne abun da ya faru da Aliyu ne ya saka suka yi dawowar gaggawa. Da dare Ummi suka zo duba shi tare da Daddy Ummi ta zo masa da wani abincin da ta girka masa, sun sha hira da daddynsa sosai na abun da ya same shi da wanda yake zargi da kuma abun da yake hararowa nan gaba, har statement din da police suka dauka sai da ya fadawa Daddynsa kuma a kaurara lamarin saboda yana son a dauki babban mataki. Daddy ya shaida masa already hukuma sun fara aikinsu, a nan ya kara warwarewa Ummi zare da bawa a game da Emily sannan ya kara fayyace musu abun da ya faru tsakaninsa da Kameela. Aliyu yana son ya tambaya ya Emily take yana gudun Ummi ta masa fahimta ba daidai ba, alhalin shi kuma ya damu ne kawai ya san halin da take ciki. "Idan ba mataki aka dauka ba ita kanta ba zata samu salama ba" "Ai dole ne wannan, indai har aka tabbatar shi ne to ya kai karshe, ni da har na fi zargin Kameela saboda yarinyar bata da hankali, indai har zata iya saka maka guba to zata iya komai" "Abu ne mai wahala Kameela ta yi haka, kuma bana zargin Turhan even though yana cikin bacin rai, amman bana tunanin zai saka ayi min haka, domin na fito gidan kenan ma ba a jima ba, lokacin be isa ace ya je ya samu wasu su yi min wannan dukan ba, na fi zargin Vito ne yake bibita saboda na zo da yarta kuma gashi ta biyo bayana and ita kanta ya saba dukanta balle kuma wani" "Bincike dai zai tabbatar da komai In Shaa Allahu" Ummi ta fada sai Daddy ya ce. "Yanzu ita yarinyar tana Lafiya?" Aliyu ya kalli Ummi da sauri yana jin amsar da zata bada daman tun shigowarsu yake son ya tambaya sai kuma ya danne zuciyarsa saboda Ummi. "Tana lafiya" "Amman ta fito waje?" Aliyu ya tambaya, sai Ummi ta yi kamar bata ji shi ba. Daddy ya ce. "Amman Aliyu kana tunanin Turhan zai fahimce ka kuwa?" "Abu ne mai wahala mahaifiyarsa ma dazun sai da ta fada min magana" Ummi ta fada, Aliyu ya tambaya. "Me ta fada miki?" "Shirmen mata ne, kasan mu sa kananan maganganu" Aliyu yayi shiru slowly slowly ransa ya fara baci amman be ce komai ba. Daddy kawai ya koma gida Ummi a asibitin da kwana tare da dan'uwansu Muktar duk kuwa da irin yadda Aliyu ya so ta tafi ta bar Muktar din ya kula da shi, Daddy har zolayarta yayi wai ta zabi ɗa ta bar miji, ta fada masa ana canja miji ba a canja ɗa ba. EMILY POV. Wannan ne dare na farko da bata ji dadinsa, saboda ta kwana da kewar Fatima sosai, gashi ta yi bakunta a gidan da mutumen data sani baya cikin gidan sai bakin fuska. Abincin ma bata wani ci abun kirki ba abun duniya ya taru yayi mata yawa. Tun gabanin Asuba bachi ya yanke a idonta sai hawaye ne suke ta aikinsu ta yi iya tunanin ta yi iya hangenta amman ta gagara samun mafitar da zata iya amfani da ita yarta ta dawo gareni. Wannan dalilin ya saka duk yadda ta hana zuciyarta daga ganin laifin Aliyu sai ta kasa domin shi ya janyo mata komai. Ba zata hana zuciyarta aminta da shi ba, amman bata da tabbacin abun da yake zuciyarsa da na mahaifiyarsa, domin Ammy da Khaleefa darasi a rayuwarta. Bata sauko kan gadon ba har sai da Ummi ta dawo daga asibiti ta leko dakin daman tun fitar Nafisa a jiya babu wanda ya sake lekota duk wani kai da kawo da ake a gidan bata fito ba. Ummi ta kunna wutar dakin ta kalleta. "Kin tashi lafiya Emily?" Ta tashi zaune. "Good Morning" Ummi ta karasa kusa da ita ta zauna tana kallonta da murmushi. "Kin tashi lafiya?" Ta daga kai kawai tana boye idonta. "Za a kawo miki abun karyawa, asibiti na kwana gurin Aliyu na manta ban fada miki ba, and Aliyu ya bawa Khaleefa hutu saboda ki samu sakewa, zaki iya fitowa harabar gidan ko falo ki shakata, kuma ki saka tufafin da ya miki ki sake jikinki babu wani damuwa" Nan ma ta daga kai. Ummi ta mike tsaye ta fice daga dakin. Sauka ta yi kan gadon ta shiga bandaki ta yi fitsari ta wanke da ruwa domin ta kasa daina wannan dabi'ar ta musulmai wato tsarki da ruwa ko wanke bayan gida da ruwa, ta wanke bakinta ta fito ta tana jin sanyi na abun da Aliyu yayi mata, ya fahimci feeling dinta tun bata fada masa ba, domin babu fuskokin data tsana a duniyar a yanzu kamar ta Turhan da Khaleefa. Ta zauna saman gadon ta kai hannunta ta dauki katin DR A-B data tsinta a jacket dinsa, ta dadde rike da katin tana kallonsa kamin ta dauki wayarta ta saka number shi duka biyun, sannan ta shiga gallery ta kama hotunan Fatima tana kallo sai ga kiran Aliyu ya shigo wayarta. Ta amaa da sauri tana fatan dayan wayarsa ce dakw hannun Fatima aka kira da ita so that ta yi magana da yarta. Tana jin sallama da muryar Aliyu ta san ba yarta ba ce. Bata amsa sallamar ba bata ce masa komai ba kuma bata amsa Good morning da yace mata ba, hakan ya saka shi fahimtar kuka take ko kuma fushi take da shi. "Idan akwai abun da kike son aikawa ki aikata, karki bar tunaninki ya hana zuciyarki abun da take so" "Ina son yarinyarta a kusa da ni, i want my baby" Ta fada tana fashewa da kuka. Aliyu be ce komai ba ya kashe wayar. Kiransa na sauka kiran Vito ya shigo wayarta cikin kuka ta amsa kiran shi ma bata ce masa komai ba sai saurarensa take. "Kalle ki Emily, kin yi yaudara kina tunanin kin yi nasara ko? Saboda zuciyarki na raya miki ba zan iya miki komai ba? Mamana ta yi gaskiya kin din ba abar yarda ba ce, idan kina tunanin kin gudu kin tsira to kin yi kuskure, ba'acin amanata a zauna lafiya, sai na ga bayan wannan dan iskan yaron da kike so, kuma sai na maida rayuwarki labari Emily, ba zan raine ki wani ya ci moriyarki ba, no way! Daman kina nemam damar butulce min ne, shiyasa kika karbar soyayyata bayan duk abin da na yi miki? Ban ga laifin komai da yake faruwa da ke ba, saboda ke yar iska ce fuck you Emily" Maganar yake cikin yanayi na maye. Ta hade kukanta tana jin tausayinsa domin abu ne data sani Vito yana sonta, kuma ya kula da ita irin kulawar da kowa be bata ba, ba al'adarshi ba ce shan kayan maye da safe sai idan yana cikin damuwa, and she knows ita ce silar damuwar tun da har ya kira yana karanta mata wannan bayanan. "Zan dawo Vito, zan karbi yata zan dawo zamu yi aure zamu irin rayuwar da kake son mu yi, kai kadai ne nauyin da ya rage min na sauke, but don't hurt anyone mutumen da kake kokarin ganin bayansa taimako kawai yayi bashi da wata manufa akaina, ba abun da kake tunani ba ne" "I don't need you now, i already have Chidimma na yi replace dinki da ita, daman daga ke sai ita nw kuka san sirrina, dan haka zata kasance da ni har abada ke kuma zan baki mamaki, daman haka kike ko? Su ma butulci kika musu shiyasa suka horar dake, to ni horon da zan miki ya fi na su, a hannuna kike ina kallon duk wani motsi naki" Ya katse wayar sai ta lumshe ido ta cije baki tana jin ba zata iya yafewa kanta ba, domin ta san yadda cutarwa take da ciwo and kasa samun soyayyarta da Vito yayi bayan duk taimakon da yayi mata ya zama kamar cutarwa. Ta kai hannu ta taba zuciyarta tana jin kamar ace zata iya cusawa kanta kaunarsa kai tsaye, tun bayan da Khaleefa ya ci amanar ta bata sake jin tana son wani da namiji ba, Turhan ma ta aure shi ne kawai saboda mahaifiyarsa ba dan tana son shi ba. Sai da ta fara raya ma kanta cewar zata cusa zuciyarta ko bata so ta amince da soyayyar Vito, ko dan rama masa alherin da yayi mata, be zama lallai sai tana son shi ba, zata iya zama da shi su rayu yadda yake so, sai kuma maganar Ummi ta fado mata arai. "Kina fifita farincikin wasu akan naki, kina fargaba tunkarar wasu da abun da yake zuciyarki, shiyasa kika cutar da kanki...karki sake tsorata ko cilasta kanki abun da ba shi kike bukata ba..." Ta bude ido tana ba kanta amsa zuciyarta kuma na raya mata Idan bata amince da soyayyarta ba zai iya cutar da Aliyu. "But i have to Vito ya cancanci komai daga gareni" Ta share hawayenta sakamakon turo kofar dakin da aka yi za'a shigo. Mama Baraka ce da lullubinta dauke da katon kwandon abinci yaranta yan mata biyu ma suna dauke da abinci, ta shigo da far'arta ta aje abincin a kasa suma suka duka suka aje Emily sai kallonsu take su ma suna kallonta, Mama Barakat ta zauna a bakin gadon tana kallon Emily. "Ina kwana, kin tashi lafiya" Emily bata amsa ba, duk kuwa da tana tunanin ko Ummi ce ta ce ta shigo mata da abincin. Mama Barakat bata damu ba ta gabatar mata da yaranta biyu. "Kin ga bakuwar fuska ko? Wannan sunanta Misira, wannan kuma Hakima zaki iya kiransu da kawayenki ko kanenki" Emily ta watsa mata harara. "Bana son ganinki ba na fada miki ba? Duk wani abu mai alaka da Kameela bana bukatarsa" Mama Barakat ta girgiza kai da sauri. "Aa Wallahi zuwana ba shi da alaka da Kameela ba wai ina kokarin gyara abun da Kameela ta bata ba ne, Kameela yar kishiya ta ce kawai bayan wannan babu wata alaka, dan Allah ki yarda da ni" "Ku ba abun yarda ba ne, ku fita daki nan" Mama Barakat ta fara hawaye tana bude abincin da suka zo da shi. "Dan Allah karki tsaurara ganinki da nake ina jin sanyi, kin ga abubuwa na shirya miki na karyawa ban san wanene favorite dinki ba, amman abubuwa sun kai bakwai a nan ki ci duk wanda kike so, jiya kuma na yi waya da ita mahaifiyar yaron da suka rike miki Fatima, da na ce zan je na same ta sai kuma na ga ba zan iya yakin ni kadai ba, dole sai da taimakon mai gidan sai na yanke shawarar na fada masa, kuma na fada masa sai dai ban yi nasara na samun amincewarsa ba, be ma fahimce ni ba, amman... Amman... Dai na san zan samu kansa" Mama Barakat tana maganar jikinta na rawa kamar wanda aka turke, iya kar kokarin na fahimtar da Emily ne bata nufin cutar da ita. Cikin daga murya Emily ta dagawa Mama Barakat tsawa domin ta fahimci so take ta shiga jikinta ta cutar da ita, bata san me suke kullawa ita da Kameela ba. "I don't need your help, bana bukatar abincikin Bana bukatar komai daga gareki, ki fita ki bar nan i don't need you" Babbar yarta ce misira ta kasa jure yadda Emily take magana da mahaifiyarsu ne ta daka ma Emily tsawa. "Ke dan Allah wace irin mace ce, baki san darajar iyaye ba ne da zaki rika cin mutuncin mahaifiyarmu a gaban idonmu? Haba Mama Wacece wannan kika ta rawar jiki da ita ne, duk girkin nan da kika tashi kina yi tun asuba duk saboda wannan banzar ne?" Misira na rufe baki Mama Baraka ta dauke ta da mari ta nuna mata kofa. "Fita fita ki ba ni guri" Misira ta kalli Mama Barakat da mamaki dafe da kumatu. [7/16, 10:07 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣3️⃣ Emily ya hade wani kunci daya tokare zuciyarta. "Kin yi gaskiya, ban san darajar iyaye ba" Ta juya ta kalli Mama Barakat. "Kin gani ko? Yarki tana ganin na zafafa, dan Allah bana son na sake fadar wata magana ina girmama mutuncinki ki fita dan Allah karki sake dawowa" Jikin Mama Barakat ya kara yin sanyi. "Me kika sani game da uwa?" Ta juyar da idonta ta wani bangare na dakin tana sosa wani kurji da ya dade yana mata kaikayi. "Ban san komai ba, saboda tarihin rayuwata be taba wanzuwa da uwa ko uba ba, na tashi ba tare da uwa, uba ko. Yan'uwa ba, dan haka ban san dadin uwa ba sai rashin dadinta, ban san komai game da uwa ba domin tawa uwar bata taba rumguma ta ba, taba nuna min tarbiya ko akasinta ba, bata banbance min yadda zan yi rayuwa da mutane ba, shiyasa ban iya rike halshe ba, ban san zafin da ake ji idan an ci ma uwa mutuncin ba, amman ni ina fatan yata zata sani, domin na tsaya kanta, na iya yadda zan iya na rayu saboda ita, na yi ma kaina alkawari ba zan taba bari ta ji abun da na ji ba, ba zan bari ta yi irin rayuwar da na yi ba, zan hade duk wani bakinciki saboda ta yi farinciki" Ta juyo ta kalli Mama Barakat idonta na zubar da hawaye. "Dan Allah ki tafi bana son na sake fadar wata magana marar dadi a gareki" Mama Barakat ta nufi kofa ta bude ta fice tana zubar da hawayen da suka fi na Emily zafi da kuna a zuci, Hakima na binta a baya. Emily ta daga kanta sama ta shanye hawayenta sannan ta sauke ta shiga bandaki ta yi wanka ta fito ta zauna gaban madubi ta shafa mai ta saka turare kasancewar babu wasu kayan kwaliya ya saka ta lakaci man shafi ta shafa a lebenta ta shace kanta. Wandon balazo da rigarsa da Ummi ta bata ta dauka ta saka blue ne mai wani zane zanen baki sai rigarsa ta yadi baki da karamin dankwali baki, da dankwalin da daure gashinta madadin ribbons sannan ta dauki wayarta ta tsaya gaban madubi ta kalli kanta with full confidence. Ta yi kyau babu karya, tabon dukan da Vito yayi mata ya bace confidence din data sakawa kanta ya kara mata kyau da kwarjini, bakin data shafawa mai sai shinning yake, ta juya ta nufi inda talkaminta suke ta saka ta bude dakin ta fita, ta sauko falon a daidai lokacin da Ummi ta zauna a kujerar dake facing din ta Mama Barakat tana fadin. "Ki yi hakuri fa na barki a nan, na tsaya sallamar mai gida da abun karyawa ne" "Ba komai, wata magana nake son mu yi dake ta fahimta, na kira Aliyu jiya ba daga ba, wata kil yana tunanin ko saboda Kameela ne..." Mama Barakat bata karasa ba saboda saukowa Emily, daga Ummi har ita kallon Emily suke. "Na ce Nafisa ta kawo miki abun karyawa ta kawo?" Kamin Emily ta amsa tambayar Ummi Mama Barakat ta ce. "Na zo mata da abinci amman bata ci ba" Ummi ta kalleta da mamaki. "Abinci kuma? Abinci aka ce mun rasa a gidan ne da har sai an dauko daga gidanki an kawo?" "Aa na yi nufin kyautatawa ne kawai" "Gaskiya karki sake Hajiya Barakat kin ga dai daga bangaren Kameela kike, duk abun da ya faru ya faru saboda Emily kar a zo a cutartar da ita ba tare da mun sani ba" Mama Barakat na yi shiru ta sauke kai kasa, Emily ta kalli Ummi ta ce. "Ina son zan tafi gidansu Turhan ko zaki iya sakawa a kai ni?" Ummi ta kalleta cike da mamaki. "Gidansu Turhan?" Emily ta daga kai, Mama Barakat ta kalleta, Ummi was speechless for a little bit kamin ta ce. "Lafiya?" "Ummi yata tana can, zan je na yi magana da su ne" "Zazzzaki iya?" Ta daga kai with full confidence. "Amman ki bari ki yi breakfast tukuna" "Hankali ba zai kwanta ba har sai na tafi, idan na dawo zan karya" "Okay, bari na yi ma direba kwatacen gurin, ina zuwa" Ummi ta tashi rike da wayarta ta fita. "Zaki iya zuwa ke kadai ko na raka ki? Kuma tafiyarki ba zata zama da matsala ba?" Emily ta kalli Mama Barakat ya wacce ta yi maganar ta gafen ido. "Na saba rayuwa da yin abubuwa ni kadai wannan ma zan iya" Ta nufi kofa ya bude ta fita, a Entrance din ta tsaya tana sauraren Ummi dake fadawa direban inda zai kai Emily. "Number gidan dai na manta, bari na tambayi Aliyu" Ta daga wayarta a gurin ta kira Aliyu ta tambaye shi house number nawa ne gidansu Turhan, sai da ya fada mata sannan ya bukacin jin dalilin tambayar. "Za mu yi magana daga baya" Ummi ta kashe wayar ta kalli direban. "Number 7" "Tohm Hajiya" Ya juya ya sauka ya nufi wata farar mota sai da ya juyo da ita sannan ta sauka ta nufi motar ta bude gidan baya ta shiga ta zauna, direba ya dauki hanya. TURHAN POV. Be yi nisa da gida ba kiran mahaifinsa ya shigo min wayarsa direct international call from Sudan to Nigeria, cikin hanzari yayi fakin yana dan jin faduwar gaba, domin abu ne mai wahala mahaifinsa ya kira shi, idan ma wani abu ne yawanci sai dai ya bar masa sako ta whatsapp ko kuma ya sanar yace a sanar masa. Ya amsa kiran cikin ladabi mahaifin nasa be ko tsaya gaisuwa ba ya gabatar masa da dalilin kiransa. "Wani labari na ji yanzu akanka.... kuma ina fatan ba gaskiya ba ne" Ya fada da yalshen larabci, Turhan ma ya mayar masa da yaren da suka fi fahimta. "Wane labari ne?" Mahaifin yayi shiru ma tsawon lokaci. "Cewar kana da ya da wata mata da ban sani ba?" Turhan ya ji gabansa ya fadi, amman hakan be hana amsawa mahaifinsa ba. "Eh gaskiya ne, amman ni ma ban san da yar ba sai a yanzu, tana tare da ni yanzu haka" "Hmmmmmm... Shiyasa na samu kira cewar mu iyaye ya kamata mu tsawatar saboda a bawa kowa hakkinsa, taya abubuwa suka faru haka ban sani ba?" Cikin isa da isa da kasaita yake maganar kuma cike da zafin ran dake bayyana bacin ransa. Turhan zai yi magana ya kashe wayar sai ya maida masa kira be daga ba. Babu tantama ya san mahaifinsa yayi fushi, sai dai fushinsa ba zai hana shi bayyana gaskiyar komai a yanzu ba, ya san zai fuskanci kalubale daga gurin mahaifinsa da kuma matarsa amman ya shiryawa hakan, kuma ko za aje sama a dawo na zai saki Emily ba saboda yarsa da kuma lokarin gyara abun da ya bata, and of course Emily ta cancanci zama matarsa. Juya motar yayi ya dauki hanyar gida, ya faka harabar gidan ya fito motar zuciyarsa da kansa cike da tarin abubuwa da suke kokarin rinchabe masa, amman dai yana jin zai iya dauka ko dan bawa marasa ɗa kunya.. Ya tura kofar falon ya shiga, sai ya hango Ammy a inda ya barta zaune a dinning tana karyawa. "Ammy Ina Fatima?" Ita ya fara tambaya domin tabbatar tana gidan ko aa what if bayan fitarsa an fita da ita and the way da ya ga Mahaifiyarsa ta dauki zafi akan Emily tsab zata iya damka mata ita ba tare da saninsa ba. Ammy ta kalli Stairs as her response, wani Sighs of relief yayi sannan ya sake kallonta ya ce. "Ammy ke kika kira Mai Martaba kika nemi ya tsawarta saboda bawa kowa hakkinsa?" Ammy ta maa kallon rashin fahimta da kuma mamaki. "Ko da mafarki kar zuciyarka ta raya maka zan iya daga waya na kira mahaifinka balle har na nemi ya shiga cikin wani lamari da ya shafe ni, ka tofar da wannan yawun, bana son shi...!!!" Ya fara takawa zai karasa inda take yana mata bayanin kiran da aka masa, aka turo kofar falon sai ya juya Ammy ma ta kalli kofar dukansu suka yi arba da Emily fuska babu annuri, juyowa Turhan yayi yana kallon Confidence din dake tare da ita wanda ya kara mata kyau da haiba, babu murmushi ko alamarsa a fuskarta amman haka be hana goga fahimtar kyaun surar da Allah ya tsaga a fuskarta da sigar jikinta ba, ga tufafin sun karbe a color kuma sun mata cif in size domin palazon irin wannan ne mai matsewa a sama ya bude a kasa. Emily ta taka ta shiga cikin falon tana wani taku dake nuna ta shiryawa duk wani hargitsu na su. Ba shiri Ammy ta mike tsaye tana kallonta sai kuma murmushi ya cika fuskarta. "Aisha kin zo? Yau kin tuna gida?" "Eh na zo na tabbatar da abun da kika min alkawari, kuma na tafi da yata" Turhan ya maida hannayensa baya ya cira kafa daga ya fara takawa har ya isa inda take tsaye ya tsaya gabanta, yana wani sham kamshi. "Wannan ba Aisha da muka sani ba ce, me yasa kika bari suka cusa miki wannan tunanin da wannan rayuwar a zuciya?" Emily ta kara ta ku biyu forward. "Sautin murya nake ji, amman bana ganin mai magana, saboda mai maganar ba mutum ba ne, kusa ce da fatar akuya" Turhan ya kalli bakinta dake motsi yana kyalli da man data shafa masa, ya hade yawu a hankali, kamin ya kalli kwayar idonta mai matukar daukar hankali. "Na yi kuskure, na bata abubuwa da yawa, amman yanzu lokaci ne da zan gyara, kina da damar ki tsane ni ko ki aiwatar da duk abun da kike so a kaina, amman Please ban da zancen rabuwa" "Kana da karfin hali, har a yanzu umarnin kake ba ni? To wacan Aisha ta mutu, wacan Aisha ita ce kaza, ni kuma Zabuwa ce fira nake, ban zo nan dan na yi musayar kalamai ga wanda be san mutunci kansa da na mahaifiyarsa ba, So...." Ta kauce gabansa ta nufi gurin da Ammy take tsaye tana kallonta rai a bace. "Taya kika sauya Haka Aisha tun daga kan sutura da hali da addini ba wanda muka san ki da shi ba ne" "Danki na daga cikin mutanen da suka sauya ni, ko dai na sake maimaita miki labarin ne?" "Wannan rashin kunyar duk na minene Aisha?" "Na neman rabuwa da mutumen da ya fifita son zuciyarsa ne akan ra'ayin mahaifiyarsa, na yi zaton kin sa ya rubuta takardar ai, kawai zan karba ne ko kuma ki kawo min domin tabbatar da furucinki" "Saki ko? Yanzu nan zai sake ki" Ammy ta nufi stairs, Turhan ya bita da kallo gabansa na faduwa wani hadarin tashin hankali yana haduwa a cikin kansa. Kasaita sarauta da isa duk ciresu yayi ya jingine ya nufi Emily ya sake tsayawa a gabanta, tana daga kai ta watsa masa wani kallo sai da gabansa ya sake bugawa da karfi, ta cika shi da kwarjini. "Dan Allah ki fahimta, na san na bata miki na kuntata na munana miki, abubuwa da yawa sun faru, na rashin jindadi da cutarwa, amman ki yi hakuri, ina son ki fahimci cewar ni dan adam ne, dole mukan yi kuskure... Ko... Ko ganganci, amman mafi girman kuskure shi ne kasa gane cewar kuskure ne, ki yi hak'uri Emily ki yafe min" Emily ta dauke kai zata matsa daga gabansa sai ya kai hannu ya rikota. Hannunsa da gurin da ya rike ta kawai ta kalla ta dago ta watsa masa wani mugun kallo, ba shiri ya dauke hannunsa a jikinta a tsorace. "Please... Kar mu dawo muna nadamar abun nan, ki duba rayuwar ki da ta Fatima, ba zata ji dadi ba bayan tsawon lokacin nan ta tashi ba tare da mu ba, abu ne mai wahala ki iya jure ziyararta a koda yaushe, idan ke baki bukatata a rayuwarki ni ina bukatarki" Emily bata ce masa uffan ba, hankalinsa be kara tashi ba sai da ya hango Ammy na saukowa rike da takardar da biro. "No no nooo Ammy ni fa ba zan sake ta ba, ke kika sa na aureta, na ji na yi kuskure to ku ba ni damar gyarawa mana, duk wata wuta da zata kunna zan iya tarar ta, amman ban da rabuwa, wannan be dace ba, na shirya fuskantar ko wanw kalubale a yanzu, And Emily na shirya gabatar da ke har a gurin mahaifina da kuma ƴar mu Fatima, zan mu na komai a yadda ya dace" Ammy ta karaso gurin ta mika masa da biro. "Rubuta mata saki" Ya matsa baya ya girgiza ma Ammy kai. "Ammy please... Karki cilasta ni wannan, ki kan ba ni umarni na bi dan Allah kar mu samu tsabani a nan, ko sakinta na yi makiya ma dariya za su mana" "Ka dubuta mata saki Turhan" Ammy ta furta cikin kakkausan halshen. Yaja kujerar dinning ya zauna ya rufe ido yana murtuke fuska kamar mai shan wani abu marar dadi. Ya sake bude idon ya mike tsaye. "Bari na yi magana da ita" Ya karasa gaban Emily ya kama hannunta ya rike cikin yanayin dake bayyana tsakanin damuwarsa. "Dan Allah Emily ki yi hakuri ki yafe min, ki ba ni dama na gyara kuskuren da na aikata, ki yi hakuri Emily zan canja, na ma manja ba yadda kike tunani ba ne, zan baki duk wata kulawa da kike bukata" Ko kallonsa bata yi balle ta yi wani reaction da zai nuna ta fahimci kalamansa. "Ka sake ta na ce" Ya kalli Ammy kamar ba shi ba. "Ammy dan Allah karki cilasta ni aikata abun da ban yi niya ba, ba daidai ba ne... I... I... I love her... Ina son... Matata, rabuwarmu zata kara bata abubuwa ne kawai, ya kamata mu fahimce ta zafin zuciya ne yake debanta take kalamai marasa dad..." "Zaka sake ta, ko sai na barranta ka daga gani ni" Ya kalli Ammy babu shiri sai ta sake nanata masa. "Ka sake ta yanzu nan" Kamar wanda aka yi ma shocking haka ya rumgume Emily da sauri ya matse ta a jikinsa ya runtse ido, ya dauki dakiku a haka Emily bata motsa ba sai ya sake ta koma ya zauna ya Ammy ya dora masa takardar a dinning da pen. "Idan baka sake ta ba, ban yafe haihuwar da na yi maka ba Turhan...!!!" Ya kalleta cikin tashin hankali da rashin madafa. "Ammy...." Ya masa cewa komai hannu na rawa ya dauka ya dora a takardar ya kama biron baya ko iya rubutawa har sai da ya saka dayan hannunsa ya rikw hannunsa na dama, ya sake dagowa ya kalli Emily. "Ba zaki ce komai ba Aisha? I'm sorry i Love you, idan ba zaki yi dan ni ba ko dan Fatima" Emily ta ki ta kalle shi. Sai ya kalli Ammy idona na zubar da hawaye ya ce. "A koda yaushe ni mai biyayya ne a gareki, da dadi ko ba dadi, zan saki Aisha, amman ba dan raina na so ba, sai dan ba zan iya jure tsinuwarki ba, amman dai ba haka raina ya so ba" Ya maida hannunsa yayi rubutun da larabci hannunsa na rawa, sannan ya dago takardar ya mikawa Emily, sai a lokacin ta kalle shi tana jin wani sanyi a ranta. "Ashe kana iya kuka Turhan, ko kuma na munafunci ne irin yadda ka yi a lokacin da za mu bar Kasar nan zuwa Sudan" Ta fisgi takardar daga hannunsa, sannan ta juya ta kalli Ammy. "Ina yata?" "An dai baki takardar da kika bukata, kuma na fada miki za a tabbatar miki an kuma yi haka, takardar ita ce wajibi" Emily ta daga kai ta kalli stairs da nufin kiran Fatima sai ta hangota tsaye tana kallonsu tana kuka, bata fahimci me kai da kawo ba ita dai kawai abin da ta gane mahaifinta na kuka Emily ta ki jin tausayinsa. Emily ta mata murmushi ta mika mata hannu. "Fatima zo mu tafi" Fatima ta sauko da gudu Ammy ta juya da nufin idan Emily ta yi yunkurin rikonta ta hana, Turhan kuma hankalinsa ya kara tashi ganin zai yi 2 - 0. Fatima na saukowa ya nufi Turhan ta rumgume shi. "I love you Daddy, stop crying" Emily ta kira sunanta da karfi. "Fatima wannan mutumen da kike gani, ba mutunen kirki ba ne, shi ya bar mu a tsawon shekarun nan, baya son ki ya cutar da ni" "Be cutar da ke ba, na ga yana kuka yana cewa yana sonki, me ya kika min karya Momy miyasa baki son na samu Baba? Kowa yana da baba amman ni ba ni da shi?" Turhan ya dauke ta ya dora a kafada ya rumgume yana jin sanyi a ransa. "Fatima wannan mutunen ya cutar da ni ya wofintar da ke" "Duk abun da ya faru ya faru ne saboda be san an haife ta, kin samu abun da kike so dan Allah ki tafi" Ammy ta fada. "Ba zan tafi ba sai da yata, daman mun saba rayuwarmu ba da ku ba, da Fatima zan tafi" Emily ta fada sai ta nufi Fatima ta riko hannunta zata rabata da jikin Turhan, a take Fatima ta fisge hannunta. "Bana son na tafi tare da ke, ina son babana i hate you" Emily ta fisgota da karfi, sai Fatima ta saka mata ihu tana kuka. "Bana son na tafi da ki, Babana nake so" Emily ta kalli Turhan. "Na rainin cikin yarinyar na haife na raine ta har ta kawo yanzu, ba tare da kai ba, a yau ka bayyana a rayuwarta ka cusa mata kiyayyata alhalin kai ne makiyinta, hakika kai azzalumi Turhan" Turhan ya girgiza mata kai alamar ba shi da laifi, Emily ta juya ta nufi kofar fita, zai yi magana Ammy ta rike hannunsa ta girgiza masa kai. Emily ta fita falon tana zubar da hawaye ta nufi motar da aka kawota ta shiga tana kuka, har direban ya isa gida kuka take, haka ta motar ta nufi entrance din taka ta isa bakin kofar falon, a kokarinta na saita kanta ya jingina da window falon tana maida numfashi. "Ki taimaka min dan Allah, ban san ta ina zan tunkareta ba, ba lallai ta fahimta ba, amman ina son Emily fiye da sauran yayana kuma tsawon lokacin nan Wallahi ban san inda take ba, ban ma san yadda abubuwan nan suka faru ba..." Ta ji muryar Mama Barakat tana maganar cikin kuka, Emily ta dago daga jikin window falon tana jin wani jiri yana debanta, kawai sai ta ji mafarki take ta girgiza kai ta juyo rike da takardar da kuma wayar, ta nufi gate mai gadi ya bude mata ta fice, haka ta kama hanyar titi, ta taba fuskarta sai ta ji kamar ba tata ba, idonta har wani rufewa suke suna budewa hawaye suka fara mata kwarara. Tsayawa ta yi cak ta kalli gabas ta kalli yamma, ta kalli kudu ta kalli arewa, ta kalli sama ta kalli kasa sai ta rasa a ina take. Babu wanda ya fado mata a kwakwalwa sai Dr A-B, ta share hawayen ta dago wayarta ta kalli screen din ta bude ta shiga ciki, one by one ta rika bin number har ta isa gurin number Dr A-B ta danna masa kira. Ta yi ringing uku ya daga. "Hello..." "Emily ce i need your help, ina tunanin kwakwalwata ta samu matsala" "Daman na san zaki kira, a ina kike?" "A inda nake" "Zaune ko a tsaye?" "A tsaye nake" "Samu guri ki zauna ki bawa wani na kusa da ke wayar" Ta mika wayar a iska ta sake ta, sannan ta zauna a kasa, tana bin ko'ina da kallo kawai rayuwar mafarki take ganinta.... [7/19, 5:10 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣4️⃣ Sai da Emily ta fice daga gidan sannan Ammy ta saki hannunsa, ta juya ta nufi stairs ranta a bace zuciya kuma ta yi mata nauyi, bata yi zaton abubuwa za zo a haka, ko ba komai kyautatarwa da ta yi ma Emily bata cancani yi mata hakan ba, and ba ita kadai ce mace da za'ace an fara sakawa a damuwar ɗa namiji ba, balle ace ita ce ta karshe, mata da yawa an yi musu abun da ya fi nata ciwo da kuna wasu ma sukan yafe tun gabannin a nemi yafiyar balle ita da har an jefa kai a kasa saboda ita, ga kuma yarinya me yasa ba zata kalli wannan ba? Ai ta san yadda rashin uba yake da ciwo me zasa ba zata yi ma yarta fatan rayuwa a karkashin inuwar uba ba? Ta zauna bakin gado, wani bangare na zuciyarta yana raya mata wata kila ba laifin Emily ba ne, domin gaba daya wannan ba rayuwarta ba ce, ba mamaki zugata aka yi, indai har zata iya amincewa ta auri Turhan saboda Ammy to taya zata iya kallon idonta ta fada mata magana kuma ta tsaya tsayin daka a cikin gidanta akan lallai sai Turhan ya sake ta, idan an ciza ai hurawa ake, ta san danta be kyauta ba, amman a yanzu yayi nadama, kuma idan danta be yi daidai ba me yasa ita zata saka ta a ciki? "Lallai makashinka yana tare da kai" Ta furta tana jinjina kai, Aliyu da Ummi take hararowa, ba iya alakarta da Ummi ba, daman gaisuwa ai ba sosai suke ba, amman Aliyu da Turhan abokai ne be kamata Aliyu yayi ma Turhan haka ba, ko dan abotarsu da kuma ganin idonta, ta yarda da zancen Emily cewar ta roke shi kar ya fada saboda bata son suna san rana raye, amman bata gamsu wannan ce kadai hujjar da Aliyu zai rike ya ki fadawa Turhan inda Emily take ba bayan kuma ya san har da ya a tsakaninsu, wannan rashin kunyar da da dagiyar ma saka mata su aka yi akai ba nata ba ne. Sai dai dalilin da zai saka Aliyu ya aikata hakan ne bata gano ba har yanzu, sonta yake mana, daman can Emily tana da kyau balle kuma yanzu, amman abun kunya ne ace Ummi ta goya masa baya, idan ba haka ba ai matarsada ba zata yi kishi ba. Ta dago ta kalli kofar dakin Fatima ta turo ta shigo tana rike da teddy. "Dadyna ya ce na shigo zai tafi ya dawo, yace na zo gurinki" Ammy ta yi murmushi ta bude mata hannayenta, Fatima ta tafi ta shiga jikinta, Ammy ta rungume ta sosai tana sauke ajiyar zuciya har tana jin kanta na ciwo, burinta ta yi zuriya ta samu rayuwa mai kyau ta gurin danta domin ita tata rayuwar ta lalace, amman hakan ya gagara. "Ina son ki sosai Fatima, ina son ki saka wannan a ranki, ni da Mahaifin ki muna matukar kaunarki" Fatima ta dago ta kalleta. "Ke ce kika haifi Daddyna?" Ammy ta daga mata kai. "Kin san waya haifi Momy na?" Ammy ta girgiza kai. Sai ta maida kanta ta kwanta jikin Ammy. Ammy ta sauke numfashi a hankali, tana kallon kofar dakin zuciyarta na raya mata Turhan ya bi bayan Emily ne. "Ina son Dadyna, ba zan bi Momy ba ba zan tafi gurin Vito ba, i hate him" Fatima ta fada ta daga kai ta kalli Ammy. "Momy zata zauna a nan ai ko?" "Haka muke fata, abun da ni da Mahaifin ki muke ta kokarin yin kenan" Ammy ta amsa mata yanayin fuskarta na sauyawa, tana mamakin Emily ta dayan bangaren kuma ta yi mamakin Aliyu, ta kara rumgume Fatima... TURHAN POV. Sai da Ammy ta yi minti talatin a dakin sannan Sauke Fatima ya nuna nata teddy dake kan kujera. "Dauki Teddy dinki, ki tafi gurin Ammy ni zan fita na dawo" Ya fada mata da hausa yana mata na kurame domin ita ba fahimtar hausa take ba, shi kuma be gwane a turancin ba, ya sumbance ta ya nuna mata kumatunsa ta sumbance shi tana jin dadi. "I love you" "I love you Too" Ta mayar masa sannan ta yi masa bye bye, tana hawa tana daga masa hannu har sai da ya fice sannan ta haura sama gaba daya rike da Teddy. Motarsa ya nufa ya bude ya shiga yayi mata key, ya bi bayan Emily, shi kansa ya san be kyautu ace ya sake ta ba, amman saboda Ammy ya aikata, sai dai sakin ba yana nufin ya barta ta cigaba da rayuwa a gidansu Aliyu ba, kattan banza suna kallon matarsa ba, gashi ba wani suturta masa jikin take ba, kuma ta tafi da fushisa yana bukatar ya same ta su tattauna mafita, domin shi kam a yanzu be hangowa kansa rayuwa babu ita ba, ko ba komai ta ba bashi abun da kudi ba sai siya ba, ita ce mace ta farko da ta maida shi uba wannan farinciki da jindadin da alfaharin ba zai taba gushewa a gurinsa ba, kuma a yanzu ya shirya gabatar da ita a gaban kowa, gashi ma har mahaifinsa ya sani which be san ta iya ya ji haka ba... He can risk anything to be with Emily yanzu kam, abubuwan daya bata sai ya gyarasu sannan hankalinsa zai kwanta, idan ya gabatar da ita a matsayin baiwa a yanzu yana son ya gabatar da ita masarautar a matsayin mace mai tsada kuma mai cikakke ikon a gurinsa, domin Emily ta gama masa komai a yanzu, ta haifa masa ya, kuma ita ce macen da mahaifiyarsa take so. Farat daya tunanin abubuwan da yayi mata suka fado masa a rai sai ya rasa ina zai saka kansa, yana tunkin yana kawar da da wasu wata zuciyar na ba shi shawarar yadda zai gyara wasu. Ya karasa gidan Aliyu sai da ya tsaya a gurin gate din sannan ya tuna Aliyu ma ai baya nan kuma Ammy ta fada masa a gidansu Aliyu ta samu Emily, a take ya juya Motarsa ya dauki hanyar gidansu Ummi daman babu wani tazara sosai. "Kina takurawa kanki ne kawai Aisha, duk wani abun da za su fada miki ko su nuna miki na karya ne, hakika ba ki dace da kowa sai ni" Ya fada yana tuka motar, ko kadan be so sakinta sai dan babu yadda zai yi ne, wani nauyi yake ji a kansa kamar shi aka saka ba wai shi yayi sakin ba. Daf da zai karasa gidan wayarsa ta yi kara alamar kira, ya duba sai ya sake arba da number mahaifinsa a nan ma sai da ya faka sannan ya amsa wayar ba tare da ya kashe motar ba. "Hello Abie" "Ka bar duk abun da kake ka dawo gobe ina nemanka" Ya fada masa da larabci kamin ya amsa masa ya kashe wayar. Turhan ya kifa kansa da sitarin motar ya cije baki, yana jin bakin cikin yadda aka yi mahaifinsa ya sani ma, waya fada masa me yasa aka fada masa a yanzu, yana da shirin gabatar ma mahaifinsa da komai amman ba a irin wannan yanayin ba, yayi nufin sai idan abubuwa sun gyaru shi da Emily ga kuma yarsa. Yanzu be isa ya ki tafiyar ba, alhalin kuma be shirya mata ba, domin a yanzu baya son abun da zai saka shi yin nisa da Emily. Ya dago cikin damuwa ya cigaba da tukin har ya isa bakin gate din gidan yayi horn mai gadin ya tambaya ya fada masa ciki zai shiga gurin Ummi sai ya bude masa gate, Turhan ya shiga ya faka harabar gidan ya fito yana wani shan kamshi ya doshi Entrance din da Ummi take tsaye tare da wata mata da be san waye ba sai rusar kuka take. Da takunsa na kasaita ya karasa gurin ya tsaya, sallama ce kawai ya gagara yi amman ya gabatar ma da Ummi gaisuwa domin har lokacin safiya ce. "Barka da Safiya" Ya kalli Takardar Hannun Ummi da kallonsa kawai ta yi ta dauke kai zata sauka Entrance din. "Na zo gurin Aisha ne?" "Me kake nema a gurinta? To muma nemanta muke ba mu san inda take ba" Yayi murmushi jin yadda Ummi take son raina masa wayo, calmly ya ce. "Haba Ummi ko na saki Aisha ai har duniya ta nade ita uwar yata ce kuma har yanzu ban gama sauke nauyin hakkin da musulunci ya dora min ba akanta, dan Allah ina son ganinta" Ummi ta juyo ta kalleshi. "Fitsare marar kunya, fita ka bar min gida ko na saka a yi maka wulakanci yanzu nan, an fada maka yarinya ta bata kana fadawa mutane maganar banza" "Taya zata bata bayan daga gidan ta tafi can direban kuma ya dawo da ita..?" Ummi ta sauka Entrance din tana sauraren mai fadin wani yace ya ganta a hanya a kasa dazun amman be san inda take ba a yanzu. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un ina yarinyar ta tafi? Ko dai ta ji maganar da muke ne? Bari na dauko wayata" Ummi ta juya da sauri ta koma ciki, a nan Turhan ya fara fahimtar da gaske Emily bata gidan domin tashin hankalin da ya gani a fuskar Ummi da kuma kukan da matar nan take yayi yawa, ya juya ya nufi motarsa ya bude ya shiga yana mamakin taya zata bata? Ba gidan ta dawo ba ne ko kuma yaya? No ta dawo gidan mana ba gashi har ya ga takardar da ya bata ba a hannun Ummi, hakan yana nufin fita ta yi daga gidan ko kuma me? Yaja motarsa shi ma ya shiga nemanta na dan ya san inda zai ganta ba sai dan ya gwada sa'arsa, ya san abu ne mai wahala ace ta gudu daga garin gaba daya saboda Fatima, amman hakan be hana shi tafiya har tasha nemanta ba, tun yana jin natsuwa da abun har hankalinsq ya fara tashi sosai gashi ba shi da layinta balle ya kira. Amman saboda me zata tafi? Bayan Ummi da Aliyu sun rike ta, ko kuma dai su ma suna cutata mata ne? Ko kuma cilasta mata karbar fatima suka yi da hakan ya gagara ta ji suna maganar wani abun ta gudu? Tun da har ga shi Ummi da kanta fadi cewar ko dai ta ji abin da suke tattaunawa ne? Ko kuma so take ta koma gida ta dauke Fatima what if duk wannan shiri ne? Ya juya motarsa ya kama hanyar gida be samu natsuwa ba sai da ya faka harabar gidan ya fita da hanzari ya shiga falon ya nufi stairs kamin ya karasa ya ji muryar Ammy a kitchen tare da Fatima, ya juyo ya da sauri ya nufi kitchen din sai da yayi arba da sanyin idaniyarsa sannan hankalinsa ya kwanta, ya sauke numfashi a hankali har da shafa kirjinsa, ya kalli Ammy Ammy ta kalleshi tana karantar yanayinsa alamar ba lafiya ba, domin idonsa ma sun sauya. Fatima ta zo da gudu ta rumgume shi tana masa oyoyo, sai ya duka ya dauke ta ya rumgume ya lumshe ido yana jin wani irin kaunarta a ransa, da ace zuwan da yayi yanzu ya tarar bata gidan wata kila da sai yayi karamar hauka, domin ya san idan Emily ta dauke ta abu ne mai wahala kamin ya sake ganinta ko sanin inda take, wata kila ma zata iya barin kasar gaba daya. Ya fito Kitchen din ya dawo falon ya zauna rumgume da yar gudaliyarsa, Ammy ta biyo bayansa ta zauna a dayar kujerar sannan ta tambayeshi. "Me yake faru? Ya ka shigo haka a rikice" "Wai Aisha ta bata" "Ta bata kamar ya?" "Haka suka fada min, daga gidan nake na bi bayanta ne sai na samu Ummi ta fada min wai su ma nemanta suke, hankalinsu a tashe yake kuma har wani na cewa ya ganta a hanya amman be san inda take ba a yanzu, ni kuma na tafi tashar da na sani na bincika sun ce ba su ga wata mace mai kamanin taba, daga baya sai na ji tsoron ko ta zo ta tafi da Fatima ne" "Ai Fatima ta dawo gida kenan Turhan da yardar Allah, ita kanta Emily zata dawo ai uwa bata iya rabo da danta, kawai dai tana son ta tashi hankalin mutane ne gaba daya rayuwar yarinyar nan ya canja" "Wata kila kuma wani abun suka shirya ita da Aliyun, ita kanta Ummi bata sani ba, ko kuma dai ta sani amman..." Ya mike tsaye ya sauke Fatima daga jikinsa. "Ina zaka je? Karka koma gidan nan Turhan karka kuskura ka ce zaka je ka yi ma Ummi rashin mutunci" "Ba gidan zan koma ba, ba da ita zan yi magana ba, ba zai yayu na zauna hakan nan ba tare da ni nemanta ko sanin halin da take ciki ba, What if taje ta shiga wani hali again? Saboda Fatima bata kusa da ita, kuma sun zugata ke kuma kin cilasta min na sake ta, sakin nan fa bata shirya masa ba" "Kai da ba wani sanin gari ka yi sosai ba ina zaka je nemanta?" "Duk inda zan shiga dai ba zan bata ba Ammy, gashi Abie ya kira ni dazun yace na bar duk abin da nake na dawo gobe, ba ni da enough time dole na nemeta a yau, dan Allah ki kula min da Fatima" Ya nufi kofa Ammy ta bishi da kallo for the first time ta ji tausayin danta tausayi na hakika ya kamata, Fatima ta tambaye ta me yake faruwa da halshe turanci, Ammy ta bata amsa da babu komai ta rika hannunta suka koma kitchen din, Fatima na bata labarin makarantar su da zamansu da Vito. Hanyar gidansu Aliyu, Turhan ya sake komawa yana tafiya yana kallon gefe da gefe ko zai ga Emily amman ko mai kama da ita be gani ba, sai zuciyarsa ta raya masa wata kila ba guduwa ta yi ba, ko ta tafi gurin Aliyu ne sai suka yi tunanin ko ta gudu, ba mamaki ta tafi ta fada masa abun da ya faru ne, ya juya kai yana jin kamar ya shafe tarihin Aliyun nan ya huta, Aliyun nan ya masa kaya, a take ya juya motar ya daga wayarsa ya kira Ammy ya tambaya ko a wace asibiti aka kai Aliyu, Ammy ta fada masa kuma ta kwatanta masa yadda zai gane amman duk da haka sai da ya hada da tambaya sannan ya samu isa asibitin ya tambaya aka nuna masa jerin rukunan da dakin Aliyu da ire irensa suka, yayi mamaki na ganin police a bakin kofar ya dan tabe baki wato har wani tsoro ake ba shi kamar wani dan sarki. Da fari hana shi shiga suka yi, sai ya bukaci su fadawa Aliyun cewar Turhan ne da kansa ya zo ganinsa kuma magana yake son yi da shi, bayan mai aikan ya shiga Turhan ya matsa baya yana dan shan kamshi daman kuma daka ganshi kasan ya fi karfin rainin wayo, zuwansa a nan ma ba dan Emily ba, domin Aliyu ne ya kamata ace ya kawo kansa gareshi ya nemi yafiyarsa kuma ya wanke kasa, sai ga shi shi ne ya zo da kansa, but saboda Emily ne if not because of her be jin ko sawunsa zai bari ya biyo bayan Aliyu balle kuma shi da kansa. "Bismillahi ka shiga ciki" Sai da yayi musu wani kallo na rainin wayo sannan ya doshi kofar ya murda ya tura ya shiga ciki. UMMI POV. Ummi ta shiga ciki ta dauki wayarta ta kira Aliyu ba dan ta labarta masa halin da ake ciki ba sai dan ta bukaci number Emily a gurinsa. A ka'ida idan Ummi ta bukaci abu gurin Aliyu baya musa mata baya kuma mata tambaya har sai ya aiwatar, dan haka be tambayi me ya faru ba sai bayan ya tura mata number. "Na turo, amnan me yasa kike neman number ta Ummi ba tana gidan ba?" "Aa ta fita ne tace zata je ta yi magana da Turhan ne, shi ne nake son sani ko ta isa kuma sun yi magana ko kuma yaya?" "Ummi kika barta ta tafi?" "Ita ta bukaci zuwan kaga kuma idan aka hanata sai ta ji ba dadi ai, amman ba ita kadai ta tafi ba na hadata da direban da zai maidota idan ta gama" "Okay" Ya kashe wayar, Ummi ta gwada kiran Number Emily da Aliyu ya turo mata, ta kuma aka yi sa'a wayar da shiga har ta fara ringing, Mama Barakat na jin wayar ta shiga ta mike tsaye kamar zata shige cikin wayar daman ta ci kuka na labarin da ta bawa Ammy ga kuma kukan yadda zata fuskanci Emily, ga na tashin hankalin batan Emily na rashin ganinta ba ba su ba a yanzu, ita kanta bata raba dayan biyu ko dai Emily ta ji abin da suke tattaunawa kai ko kuma sakin ne be mata dadi ba, domin Ummi ta kira direbanta ne ta tambaya halin da ake ciki bayan tafiyarsu gidansu Turhan sai ya fada mata ai har sun ta dawo Emily ta sake fita, a nan suka fito falon a rikice sai suka yi arba da takardar mai dauke da rubutun Larabci, Ummi ta dauka ta karanta bata gane larabci gaba daya ba, amman dai ta karanta sunan Aisha da Turhan dake jiki ga kuma kwanan wata. A nan ta saka masu aikin gidan su fita dubo mata Emily, a wannan halin ne Turhan ya shigo ya same su. [7/19, 5:10 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣5️⃣ Kwantawa ta yi a kasa har gashin ta chudanya da kasa ta lumshe ido kanta na mata nauyi yana juyawa har lokacin bata iya fadin mafarki take ko akasin haka, can ciki kamar daga nesa take jin muryar Dr AB yana magana a wayar data saki ta fadi kasa har ta tsaga. Kamar jira ake ta rufe idon sai wani bachi mai nauyi yayi gaba da ita duk maganar da Dr AB yake a wayar bata amsa ba bata ma sake sanin yana yi ba, shi kuma baya son ya katse kiran be san ko idan ya kira zai samu ta shiga ba kar ya yanke wannan kiran kuma ya zama be sake jinta ba, dan haka ya cigaba da maganar yana fatan wani ya dauki wayar ya amsa masa ko kuma ita da kanta ta amsa. Da ya ga abun ba na yi ba ne sai ya yanke kiran ya sake kiranta shigowar da kiransa yayi a wayarta tare da ringing ya saka Emily ta farka da mugun karfi, idonta ta fara budewa taja numfashi da karfi sai kuma ta yi hanzarin saka hannunta ta tare rana dake hasken fuskarta, ta tashi zaune ta dauki wayar ta duba. Sunan Dr AB ne a jikin screen din wayar data fashe, a take abubuwan da suka faru suka dawo mata, sai ta fahimci ba mafarki take ba kenan duk abun da take gani da ji a dazun matsayin mafarki ba mafarki ba ne zahiri ne. Ranar yau ta kama ta zame mata ranar farinciki amman abun da yarta ta aikata da kuma maganar da ta ji ta rushe duk wannan. Kiran ya katse ya sake kiranta a nan bata daga ba, sai ta mike tsaye ta kama hanya ta cigaba da tafiya, a yanzu kuma ina zata je? Wani guduwar zata sake yi? Haka rayuwa zata kare mata a tsuguno da guduwa, naman gurin zama da mutane? Ta shiga wata kwarkwada tada hango sai ta bulla ta wata hanyar har lokacin Dr AB kiranta yake amman ta ki ta daga. Guri ta samu ta zauna ta cire dankwalin data daure gashinta da shi ta aje gurin ta jingina tana jin ringing din wayarta da ya zame mata kamar wata wakar da zata taimaka mata gurin tausayawa kanta. Wayar ta sake kara wannan karon bakuwar number ce, sai dai ta san ba zata wuce Dr AB yake kira dan ya ji daga gareta ba, ta amsa kiran da nufin fada masa bata bukatar taimakonsa a yanzu, sai ta ji muryar Ummi tana magana cikin rawar murya da hanzari irin na wanda ya zaku ya ji daga wani da aka rasa. "Emily? Kina ina? Direba yace kin dawo amman baki shigo ba kin fita ina kika je? Ga kuma takardar mun gani Turhan ya sake ki ko?" "Eeh ya sake ni" "Kina ina kin daga mana hankali?" Ta kalli gurin da take zaune. "Ummi na shigo na tarar kuna wani zance kuma na ji, matar da na bari a gidanki muryarta na ji kamar tana ikiraran ita ce Mahaifiyata ko kuma ta san inda mahaifiyata take dan Allah ki fada min da gaske ne?" Ummi ta yi shiru ta rasa ta ina zata fara, can kuma sai ta nisa. "Yanzu dai kina ina? Idan wani abu kike son ji ko sani ai gida ya kamata ki taho, ba wai ki tafi wani gurin ba, kin daga mana hankali, ke da ya kamata ki yi farinciki Turhan ya sake ki?" "Dan Allah Ummi ki amsa min, abun da na ji gaskiya ne?" Ummi ta dauke wayar daga kunnenta ta mikawa Mama Barakat. 'Tana son sani idan ke ce mahaifiyarta ko akasin haka, ban san amsar da zan bata ba" Mama Barakat ta karbi wayar ta kara a kunne. "Hello... Emi... Eim...emi...emilllllyyy lyyyyy" Ta amsa murya can kasa. "Na'am" Sai kuma ta yi shiru. "Kina ina dan ki dawo" "Da gaske ke ce mahaifiyata?" Mama Barakat ta fashe da kuka. "Ni na haife ki da cikina... Ni ce uwarki... Mahaifiya..." Emily ta yi murmushi mai hade da hawaye da kuka. "Waya raba ni da ke? Miyasa ban tashi tare da ke ba? Taya zan yarda ke kika haife ni ma?" "Ba magana ce da za'ayi ta ta waya ba, magana ce da ya kamata ace ina kusa da ke kina kusa da ni" "Ki amsa min dan Allah, tsawon rayuwata na karar da ita ne akan nema da son sanin su waye iyayena su waye dangina, dan Allah ki fada min waya raba ni da kowa? Ko kuma dai kina nufin kin san inda iyayena suke?" Mama Barakat ta fashe da wani irin kuka. "Ni ce...." Emily taja numfashi, tana mamakin wace irin uwa ce zata raba yarta da kowa. "Bari na canka, saboda kin haife ni ba ta hanyar aure ba ne ko?....." Mama Barakat ta fashe da sabon kuka mai karfi ta kasa amsawa na tsawon lokaci. "Dan Allah ki yafe min Emily ki zo mu yi magana ki fahimce ni, zan fada miki komai" Emily ta dauke numfashi na wucin gadi, a take duk wani farinciki da ta taba sani ya rushe, ko ba ta amsa mata da eh lallai ba ta hanyar aure ta haife ta, ta fahimci amsar domin shirun da tayi kamin ta amsa da kuma kukan da ya kwace mata sun tabbatar da hakan gashi kuma tana neman gafararta. "Sanin wannan amsar da dade ina tambaya, ya fi duk wani furuci da halin kunci da na taba shiga a rayuwata" Ta katse kiran ta share hawayenta, sauran da suka rage a ramen idonta suka kafe a nan take, kukan ya yanke zuciyarta ta kafe, ashe akwai ranar da bakinciki zai ninku hawaye su tsaya. Wayarta ta sake ruri wannan karon data duba sai ta ga number Aliyu ta daga jiran ta kara a kunne. "Assalamu Alaikum" Ta yi shiru. "Emily" "Aliyu... Ka gafarce ni dan Allah, na shiga rayuwar ka na rusa farinciki da amincin dake tsakaninka da matarka, na yi sanadin kwanciyarka Asibiti" "Me kuma ya kawo wannan maganar? Ni na kira ne saboda Ummi ta fada min kin tafi gidansu Turhan kuma har yanzu baki dawo ba ta ce na turo mata number ki tana son ta ji ko lafiya, Emily me yasa kika tafi? Already mun yi magana da Daddy kuma ya fada min yayi magana da mahafin Turhan komai zai zo karshe cikin lokaci, amman ban so kika tafi gidan ba" "Ba amfani Aliyu... Turhan ya riga ya sake ni, ranar da ya kamata ta zama ta farinciki a gareni wata mata daga dangin Kameela mai ikirarin ita Mahaifiyata ce da kuma yata sun rusa duk wannan, Fatima ta zabi ubanta ta ce ta tsane ni Turhan take so, a yau kuma na gane da wacece ni, tambayar da na dade ina yi a yau na samu amsarta, na gano inda tabarbarewar rayuwar ta samo asali ba ni da sa'a tun gurin haihuwa shiyasa kowa yake taka ni yake guduna, indai har uwa zata haifi ya kuma ta jefar da ita saboda gudun jin kunyar duniya ko shiga wani hali, ta zabi farinciki akan na yarta, ta fifita mutumcin akan na yarta, toh taya kake tunanin wani zai ga yar nan akan hanya kuma ya bata farinciki? Ashe har da uwar data haife ni bata bukata ta" "Ban fahimci me kike magana kai ba Emily amman dai ko minene ni ina da bukatarki, kuma ke ma kina bukatar kanki, karki damu da abunda Fatima ta yi daman na hango from miles away, ita ai yarinya ce wacce ta dade tana mafarkin samun uba, kowa yace zai tsaya a matsayin ubanta karba zata yi balle kuma ta hadu da ubanta na gaskiya, shiyasa data tambaya ni ban musa mata ba, sai na fada mata kin yi zaton baya raye ne shiyasa kika fada mata cewar bata da uba, idan kuma kin hadu da wata tace ita mahaifiyarki ce baki san uzurinta ba" "Wane irin uzuri ne zai saka uwa ta jefar da yarta? Shin bata yi tunanin ya rayuwa zata kasance min ba bayan babu ita babu kowa a kusa da ni? Shim bata damu ta san a wane hannu na fada ba? Saboda ta haife ni bata aure ba ni miye laifina ne? Miyasa bata yi tunani ba kamin ta aikata?, na girma cikin tsangwama da rashin daidai da abokin tafiyarsa, da kowane faruwa tambayar kaina nake ina iyayena suke? Ta san bata bukatata miyasa ta haifo ni? Ashe uwa zata iya jefar da yarta ko danta saboda jin kunyar duniya?" "Ita ta fada miki bata hanyar aure ta haife ki ba Emily ko kuma dai baki saurareta ba na fa san halinki, dan Allah karki jefa kanki a wata matsala, ki daina tunanin babu mai bukatarki ni ina da bukatarki ina son farincikinki" "Ni da kai kamar mafitar rana ne da mafadarta, dukanmu muna fuskantar mabanbanta hanyiyi ne. Baka bukatata a rayuwarka Aliyu, indai har mahaifiyata zata ji cewar ni illa ce a rayuwarta, yar da raina da azaba da damuwa ta zabi mahaifinta sama da ni to babu mai bukatata a rayuwarsa. Ni dai yau gaji na yi yaki har karfina ya kare, na yi iya yadda zan iya na kasa cin ma muraduna, an rusa rayuwata da farinciki tun ina karamata, a yau na haka rame na binne burina zan bar wannan shafi famko ba tare da digon tawada ko zanen alkalami ba, na ga rayuwa rayuwa ta gan ni, na wahala iya wahala daga karshe kuma na hadu da bakin labari, ni dai na fahimce wacece ni yau, tambayar dake yawan yi ma kaina na samu amsarta a yau. Na yi ta kokarin ganin kaiwa ga hasken farin wata, da na isa kusa da shi, sai kuma na fahimci daga nesa ya fi kyaun kallo, duk yakin da nake na samun kwanciyar hankali ne" "Kar idonki ya rufe ki aikata abun da za ki sake dawowa kina nadama, ni dai bana nufin komai a gareki sai alheri, ina son na same miki wani tsanin hawa ne a duk lokacin da kasar da kike taku ta yi miki zafi, ina son na zama wata igiya da zaki rika ki cimma burikanki, na so na zama kamar uba ko dan'uwa a gareki a duk lokacin da ruwan sama ya sauka akanki, na so in kasance wanda zai kawo miki laima, a duk Lokacin da hawaye suka zubo daga idonki, na so in kasance wanda zai share su, a duk Lokacin da kika ji kadaici na so in kasance wanda zai rarrashe ranki kuma ya kwantar da zuciyarki..." "Na gode amman ni a yanzu bana da bukatar ABOKIN RAYUWA, ko wane iri ne na nesa ko na kusa, zan nisanci kowa zan rayu kamar yadda aka bar ni, har zuwa lokacin da da rayuwar ita ma zata gaji da ni ta bar ni.. Sai wata rana Aliyu..." Aliyu ya lumshe idonsa yana jin kamar ya sauka kan gadon, ina ma ace tana kusa da shi a yanzu ya kwantar mata da hankali... "Wata ranar da bata da rana..." Ta sake maimaitawa sannan ta katse kiran ta cire dankunnenta ta juya wayar ta cire layin ta saka a bakinta ta tauna har ta raba shi biyu ta jefar a gurin, sannan ta mike tsaye ta fara tafiya sai da ta fita kwararon sannan ta jefar da wayar. ALIYU POV. "Emily..." Ya furta a hankali idonsa a lumshe, kamin ya bude idon ya sake gwada number wayarta sai ya jita a kashe. Tun da yake a rayuwarsa be taba jin tausayin wani yadda ya ji tausayin Emily a yanzu ba, duk halin da take shiga be taba jin tausayinta irin tausayin da ya rasa ma'aunin dora shi balle ya auna ba irin yau. Emily ta wahala har a yanzu bata samu gatan daya dace ta samu ba, gashi kuma abu ta dade tana nema ya zo mata a ɓaragurbi, da wanne zata ji? Be samu amsar tambayarsa ba, daya daga cikin masu tsoronsa ya kwankwasa ya leko kofar dakin ya sanar masa wai wani Turhan yana son ganinsa. "Ce ya shigo" Aliyu ya fada ba tare da ya kalli kofar ba ma balle kuma mutumen dake tsaye yana sanar masa isowar Turhan. After 3 min Turhan ya turo kofar dakin ya shigo cikin takun sarauta da da martaba. Sai da ya karewa dakin kallo kaf sannan ya kalli Aliyu. "Na biyo sawun Aisha, sai Ummi ta fada min ta bata, wai nemanta suke... Na yi kyautata zaton tana nan ko kusa da nan, zuwan kuma ba na iya nemanta ne kawai ba har da na gargadi" "Da nine kai, ba zan taba bibiyar matar da na nake ganin ba ajina ba ce, ba zan taba bibiyar matar da na rusa mata ragowar farinciki ba, ban ga dalilin da zai saka na yi amai kuma na bibiyi aman na lasa ba, kazanta ai ta kazanta" Aliyu ya fada ba tare da ya kalleshi ba. "Toh ai ba ni ne kai ba Aliyu, ban iya cin amana ba" "Har abada, Turhan ba sai taba zama kamar Aliyu ba, namiji yana cika namiji ne da karfin tunana da hakuri da adalci da kyautata, ba da izza ko nuna isa ba, da kai wani mai wayo ne tun a lokacin da mahaifiyarka ta yi maka kyauta da ka riketa da hakuri wata kila da duk ba mu kawo a wannan ba" "Turhan ya fi karfin Aliyu, shiyasa Aliyu ba zai taba zama kamar Turhan ba, ta ko'ina na damaka na shanye Aliyu" Aliyu ya juya ya kalleshi. "Da ko wace dakika idan na yi maganarka Emily rokon take na boye maka sirrin saninta, saboda tana jin zaka rusa ragowar farincikinta, da ko wane numfashi idan na tuna na boye maka sai na ji cewar ban kyauta ba, daga lokacin da ka gane gaskiya sai na gagara samun salama na abun da nake zaton cin amana ce na aikata, amman a yau na gane abun da na aikata daidaine, na fahimci karatun da Emily take karanta min a yanzu biye da lokacin da take min bitarsa, yanzu a haka sai ka kira kanka namiji? Ka cutar da yarinyar iyakar cutarwa ta raini yarta da dadi babu dadi har ta yi wayo, rana daya ja dira a rayuwarta ka raba ta da yarinyar da ita kadaice ta rage farincikinta? A haka kuma kake neman yafiyarta? Wallahi....! Da ace zan iya sake rubuta farkon faruwar wasu abubuwa da na goge shafinku a tarihin rayuwar Emily...! Zaka gane kana sonta kawai idan ka rasa ta, kuma ka rasata...!" "Ka iya bakinka, karka sake ka sake aikata kuskuren tsoma kanka ko bakinka a tsakanina da Aisha, balle kuma ka sako zancen yata, kuma babu kai babu Aisha babu Fatima daga yau, kallon matata ma karka sake yi, na san inda ka dosa ai, shiyasa kake zugata kake hore mata kunne kuma ka boye gaskiyar komai har sai da matarka ta gaji ta bayyana, ba kai babu Aisha daga yau, kaga dai kamar mutumen kirki mai tarbiya ashe dai kura ce lullube da fatar akuya, tirrr da kai... " Turhan ya juya, sai Aliyu ya gyara zamansa. "La la lala Aliyu. Bari na fada maka wani abun da baka sani ba, a lokacin da Emily zata haifi Fatima ni na dauke ta da hannuna na saka ta a mota na kaita asibiti, gurin aikinmu daya da ita, Fatima ta shaku da ni fiye da kai, na san ciki da wajen na halin Emily fiye da kai, babu abun da bata fada min ba na zamantakewarku, a Part hartcour muke zaune dukanmu, a duk lokacin da na so ganinta ziyara kawai nake kai mata. Yanzu ina son ka je ka mutu..." Turhan ya ji zuciyarsa kamar zata fado tsabar bakin ciki da kishi numfashinsa har daukewa yayi ya dawo. Turhan ya juyo "Kana magana kamar wanda yayi nasara, Jarumi ne kai haka kake son na kira ka? Ko kuma na taba ma? Ka taba ganin wanda yayi cin amana yayi nasara? Ko yanzu kasuwa ta watse dan kwalli ya ci riba, Fatima bata da wani Uba sai Turhan, bata da wasu family sai nawa, har abada kuma alaka ba zata yanke tsakanina da Aisha ba, kuma zaka ga sakamakonka... Ko da yake kq fara gani ai, tun a gurin matarka, yanzu kuma gaka kwance a asibiti waya san mi zai biyo baya kuma..." Ya dauke kai ya juya ya fice yana jin wani irin bakinciki da be taba ji ba irin yau, ba a taba fada masa magana mai daci kamar ta yau ba. KAMEELA POV. "Au baki ci abincin ba?" Hajiya ta tambaya sannan ta zauna bakin gadon da Kameela take kwance jiki ba kwari domin ta kwaracewa komai tun a ranar da Aliyu ya sake ta, bata fahimci girman laifin data aikata ba sai sakin ya shiga tsakaninsu, sai dai kuma sakin ya kara tabbatar mata Aliyu yana son Emily domin ko a lokacin da ta saka masa guba be sake ta ba sai a yanzu dan kawai ta dauki yarta ta kai gurin ubanta, hakan ya kara karantar da ita cewar Aliyu yana son ya auri Emily ne ko kuma shedan ya ci karfinsa yana son ya shirya zaman banza da ita. A duk lokacin da ta yi yunkurin daukar waya ta kira Aliyu da nufin ba shi hakuri sai zuciyar ta ta tuna mata ya fifita wata banza ne akanta fa, bayan marinta da yayi har da saki a cikin gidan iyayenta, gashi kuma ita ma nata iyayen sun dauki zafi sosai kuma sun goyi bayan abun da ta aikata, har suna farincikin mutuwar auren, sai dai ita ta san abu ne mai wahala ta iya cigaba da rayuwa babu Aliyu a tare da ita. Ta yi ta sauraren ko zai gane kuskuren abun da ya kamata mata ya dawo ya bata hakuri kuma ya gyara aurensu, sam a rayuwarta bata taba tunanin Aliyu zai iya furta kalmar saki a gareta ba, kuma abun abun bakincikin ma saboda wata karuwar banza. Bata gane rabuwa da wanda kake kauna bata da dadi ba sai a yanzu da igiyar aure daya ta warware tsakaninta da Aliyu, a yanzu ne ta fahimci ashe duk son da take masa a baya karya ce yanzu ne take ainahin kaunarsa, washe garin ranar da ya sake ta ma sai da ta yi kamar zata yi karamar hauka, kamar wata mai aljannu haka ta zame musu a gidan, ta hanyar ihunta ne Mama Barakat ta san abubuwan da suke faruwa... "Ke kan dai Allah ya wadaran wannan hali na ki, wai anya Aliyun nan ba magani yayi miki ba kamin ya zo neman ki ma? Akanki aka fara saki ne? Ina ce ga yar uwarki nan damuwa kika ga ta yi? Sai ke? Sai kace Aliyu ne autan maza, toh bari kiji na fada miki ko ma dawowa yayi ba zaki taba komawa ba, aure tsakaninki da shi ya kare har abada, da ma ya sani saki uku yayi miki ba daya ba, sai mu san shi dan iska ne" Kameela ta tashi zaune ta sauka daga kan gadon tana share hawayenta ta fice daga dakin kasa ta sauka ta fice daga bangaren na su gaba daya, ta nufi bangaren Mama Barakat domin acan ta san ta saba jin sanyi idan wani abu ya faru tsakaninta da Aliyu, ko ba komai Mama Barakat tana bata shawarar yadda zata bullowa lamarin, ba kamar mahaifiyarta da yar;uwanta dake kara bata abun ba. A lokacin da ta shiga falon Mama Barakat ta samu ita ma shigowarta kenan daga cikin gari idonta ya kumbura yayi ja kamar zai fashe. Mama Barakat na ganinta ta katsi hanzarinta. "Dan Allah indai kin san kin zo ne saboda Aliyu to ki tashi ki koma bangarenku, ni ma ina da nawa tarin matsalolin a gabana, Emily ce kin riga kin yi nasara akanta to me ya rage kuma?" "Wallahi har yanzu ban yi, amman dai zan yi, sai na ga bayan yarinyar nan, kuma na zan sake zuwa neman shawara a gurinki ba" "Karki sake ki sake zagin Emily" Kameela har ta juya ta juyo tabe da baki jin abun da Mama Barakat ta fada. "Tohmmmm ko dai ta miki maganin ne ke ma?" "Emily ƴata ce...!" Kameela ta yi dariyar da bata shirya ba, ta rike kumkuru ta kara matsawa kusa da Mama Barakat. "Eeehhhh? God Forbid Wallahi karya ne, to ta ina? A zaren ma ba kalar yadin ba ne, sai idan dai Lake lake dangin nepa, ko lake laken ne ma Wallahi babu kama, Mama Barakat ki ma daina alakanta kanki da watsan yar iskar yarinyar kafirar ba..." Bata kai karshe ba Mama Barakat ta dauke fuskarta da mari. "Fita daga falon nan" Kameela ta juya da sauri ta fice daga falon babu shiri, domin da take da Mama Barakat bata taba ganin bacin ranta irin yau ba, gashi har ya kai ga ta mareta. "Ahhh Ahhh ni fa duk ban gane wannan ba, anya shekarar nan ba so ake na haukace ba? To ta ina ma zata zama... Oh.... Hadin kai aka yi da Aliyu ko Ummi wai ni ake son durawa bakinciki" Ta shiga bangarensu rike da fuska tana ta mamaki sai tunani take. [7/21, 9:49 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=r_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣6️⃣ Tana jefar da wayar ta cigaba da tafiya, a yanzu ta yi giving up akan rayuwarta da duk wani abun da ya shafe ta, ta sha wahala iya wahala, daga karshe kuma burinta da mafarkin da take da shi ya rushe. Jin tsayawar motar bayanta be saka ta juyo ba har sai da ta ji an fisgota an juyo da ita da karfi. Wani mutum ta gani wanda bata sani ba, ya rike ta gam sai ga wasu maza biyu sun fito daga motar wacce ta kasance ta jigila ma'ana motar haya, dukansu suna sanye da kayan gida ne. "Ke ce Emily?" Dayan dake rike da ita ya tambaya, sai ta daga kai ko kadan babu tsoro ko faduwar gaba a tare da ita, domin a yanzu ta shirya ko da mutuwarce tana ra'ayin a mutuwar. "Kina tare da wani a nan ne?" Ta girgiza kai. Sai ya ciro wayarsa ya kira. "Mun same ta" Yana fadar hakan ya amsa da "Okay Sir" Sai ya kashe wayar. "Su waye ku?" "Jami'an farin kaya ne" "Me aka ce na yi?" Yayi shiru be ce mata uffan ba kuma be sake ta ba duk kuwa da irin kokarin da take na kwatar kanta. Sai da wayarsa ta sake ringing ya daga yayi magana. "Abunda muke gani dai babu wani rauni ko matsala a tare da ita" Ya saka Hands-free ya mika mata. "Emily ki shiga mota za su taho da ke" "Waye wannan?" "Sunana Adam Bello" "Dr A-B, suwaye dan nan me aka ce ana yi?" "Baki yi komai ba, na kira baki daga ba, sai na sake kira na ji kina waya bayan kin fada min kina neman taimakona, shiyasa ni kuma na nemi taimakon Babana aka yi tracing dinki" "Na nemi taimakonka a dazun saboda ina tunanin kamar ƙwaƙwalwata ta tabu, amman yanzu na samu lafiya, bana son taimakon kowa bana son kowa kusa da ni" "Emily ko da tsiya ko da arziki za su zo da ke, dan haka ki bada hadin kai su zo da ke ta arzikin zai fi" Ya katse wayar, mutumen dake rike da ita ya sake ta ya nuna mata motar da suka shigo, ta nufi motar ta dayan ya shiga ta shiga dayan ya shiga aka saka ta tsakiya sannan guda ya shiga front seat direba yaja motar suka yi gaba. Headquartersu suka tafi da ita suka bata guri mai kyau da abinci, bayan sun dauki Information dinta, amman ruwa kawai ta iya sha, shi ma saboda makoshinta yana bushewa ne, daman bata ci komai ba ya tafi gidansu Turhan. Da dare yayi suka dauke ta daga nan suka sakata wata mota mai kyau da ac aka kaita gidan wani babban mutum, suka tarbe ta da hannu biyu a nan ma suka bata masauki mai kyau aka kawo mata abinci, shi ma ta kasa cin komai, bata raina kanta ba sai da dare yayi bachi yaki zuwa mata sai tunani gashi ta gagara kuka, gaba dayan rayuwarta sai da ta tuna shi a dare, yadda Khaleefa ya latsata ya yaudareta, zaman da ta yi gidansu, fitowarta haihuwar London, haduwarta da Ammy aurenta da Turhan zaman da ta yi a masarautarsu, dawowarta wahalar da ta sha da cikin Fatima, haduwarta da Vito yar rayuwar jindadin da ya bata mai hade da duka da kangin na zaba mata abokan mu'alama, haduwarta da Aliyu, mutuwar London, yadda ta rasa Fatima har zuwa yau da Fatima ta zabi ubanta sama da ita, wanda shi ya fi komai yi mata ciwo, da karya zuciyarta. Ba'ayi wani dare da yafi kowane tsayi a idon Emily kamar wannan daren da bachi be rabi idonta ba, tunani be barta ba, kuma hawaye ba su ziyarce ta ba, kamin safe kanta ya cika yayi mata nauyi kamar wanda aka hurawa iska ciki, idonta ma sun yi nauyi sosai kana kallonta kasan bata samu runtsawa a daren ba. Misalin karfe takwas wata yarinya wacce ta fi kama da mai aiki ta shigo gidan ta ce mata ta shirya za a zo a dauke ta karfe 8:30, Emily ta daga mata kai kawai, babu jimawa yarinyar ta dawo ta kawo mata ruwan tea da kayan hada shayi sai bread. "Na a gama hada abun karyawa ba, amman ki ci wannan saboda za ku tafi" Nan ma Emily ta daga kai kawai, saboda bata son yawan magana ko musu, yarinyar ta fita Emily ta kalli kayan da aka kawo ta dauke kai har lokacin bata ji tana sha'awar cin wani abu ba, gaba daya bata jin yunwa cikin ya daure jikinta ne kawai take ji babu karfi sai kuma ciwon da kanta yake. Misalin karfe takwas da rabi yarinyar ta sake shigowa tace ance ta fito. Emily ta mike tsaye ta bi bayan yarinyar suka fita tare, yarinyar ta rakata har harabar gida, har lokacin masu gidan masu farka ba, sai yan aiki ne suke ta kai da kawo. Mutumen da ya kawo ta jiya ne ya dawo ya dauke ta a wata motar ta dabam ba wacan ba, sai da ta shiga cikin motar ta tarar da wani a mazaunin direba, dayan ya shiga front seat suka damka mata duk abun da ya kamata sannan suka nufi airport da ita, suna yin farkin a harabar airport din ta fashe da kuka tunawa da zata tafi ta bar yarta, idan akwai abun da take kauna a duniyar nan be wuce Fatima ba, saboda ita ce kadai sanyin idaniyarta, sai dai tunawa da ita kanta Fatimar bata bukatarta ya saka ta takaita kukanta ta share hawayenta ta duba ticket din hannunta. Da kanta ta bude motar ta fita mutanen suka mata rakiya har ciki, ba su bar gurin ba sai da jirginta ya daga zuwa Abuja, a jikin Window ta zauna ta jingina tana jin kamar jirgin ya juya ta koma ta dauko yarta ko da da karfi ne. ALIYU POV. Duk inda ake saka ran za a samu Emily kamar tasha ko unguwanin dake kusa da su, sai da Ummi ta aika aka bincika mata ana cigiya amman ba a samu ganinta ba, a nan hankalin Mama Barakat ya kara tashi ta sha kuka sosai kamin Ummi ta iya rarrashinta har ta samu karfin guiwar tafiya gidanta, daman yaranta tun gabanin ta yi magana da Ummi ta ce su tafi gida. Ummi bata samu tafiya Asibiti da safe ba sai aikawa ta yi aka kai masa abinci da tufafin da zai canja. Da dare ta dafa masa abun da ya fi so wato sinar da miyar kaza ta tafi masa da shi hadi da watermelon juice. Ko da ta shiga ya same shi zaune yana karatun qur'ane a wayarsa. Direban da suke tare ya aje abincin ya yayi masa ya jiki Aliyu ya amsa masa da kai, bayan ya fice Ummi ta zauna tana murmushi. "Maa Shaa Allah, jiki dai Alhamdulillah alamar sauki yana ta bayyana" Aliyu yayi murmushi ya yi addu'a yayin da ya kai karshen aya ya fita daga app din. "Ummi barka da rana" "Barka dai ya jikin?" "Alhamdulillah" "Haka ake so, wayar nan taka zan karbe ta gaskiya na aje har sai ka samu sauki tukuna" "saboda me?" "Saboda bana son ta dauke maka hankali, zan kawo Kur'ane sai ka rika karatu da shi" Ummi ta bude abinci zata fara zuba masa. "Saboda Emily ne?" Ta kalleshi. "Kamar ya? Ka yi magana da ita ne?" "Na yi magana da ita, ta fada min Turhan ya sake ta, kuma Fatima ta zabi ubanta tace ba zata bita ba, and lastly ta fada min wai wata mata ta bayyana a matsayin mahaifiyarta, kumq ta fada min zata shiga duniya" Ummi ta maida plate din ta aje. "Taya ka samu magana da ita? Mun yi ta kiranta bata daga ba, daga baya kuma muka ji wayar a kashe har yanzu wayar a kashe take" Yanayin fuskarsa ya sauya sosai. "Kamin ta kashe layin na kirata mun yi magana, Ummi me yasa kuka bari ta fita gidan?" "Babu wanda yasanta fita, satar kafa ta yi bayan dawowa daga gidansu Turhan ta gudu saboda ta ji muna magana da Hajiya Barakat, kai ma kasan da sanina dai ba zan bari ta gudu ba, ko dan ma gudun tashin hankalinka, amman ya zan yi tun da haka ta zaba ma kanta?" "Haka dai rayuwa ta zaba mata, ba zata tana zama guri daya ba, sai ranar da wani ya gina gida mai cike da burinkanta da mafarkan da ta dade tana yi, tana guduwa ne saboda tun tashinta bata san wani gida da zata rike a matsayin nata ba, ta kasa aminta da kowa ne saboda duk wanda ta raba sai ya cuceta, ko da kuwa ya taimake ta da farko, shiyasa take kallon kowa haka yake a yanzu, bata da wasu yan'uwa da idan wani ya nunata da yatsa zata juya taje garesu, ita kadai take rayuwarta fadi ta shi duk ita kadai take abun ta, Emily fa ko kawa bata da a yanzu, ni da ke ba za mu gane ba, saboda mun tashi da yan'uwa da iyaye, amman a idon wanda ba shi da kowa yana kallon duniya colorless ne" "Amman yanzu ai ta samu uwa, sai ka ga yadda Hajiya Barakat take ta kuka gwanin ban tausayi" "Daman ta fada min wata daga dangin Kameela ce take ikirarin ta haife ta, amman da gaske ita ce mahaifiyarta?" "A yadda ta fada min dai, ita ta haife ta, amman a zahiri kam ba hadi domin Emily bata kama da ita" Sai a lokacin Aliyu ya cika da mamakin jin cewar Mama Barakat ce mahaifiyar Emily, dazun tunanin tafiyar Emily be bar shi ya sararara ba balle yayi wani tunanin, sai a yanzu ya tuna labarin da ta ba shi cewar matar da ta zo da ita daga Kaduna sunanta Mama Barakat kuma ta tafi da ita gidanta amman bata tsaya ba ta gudu. "Amman da gaske bata hanyar aure aka haifeta ba? Kuma da gaske jefar da ita ta yi?" Ummi ta daga mishin kai cikin yanayin damuwa. Aliyu ya jingina ya rufe ido yana fadin. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un" "Wallahi, ni ma ta ba ni tausayi, wasu iyayen basa da tunani ne kawai, taya zaka jefar da abun da ka haifa bayan duk wahalar daukar ciki da nakuda, saboda kawai ba ta aure aka samu yaro ba sai ka jefar? Ko a ina suke aje tausayi da kaunar da uwa take da shi ga yayanta lokacin da suke aikata haka? Kuma baka san wane hali yaronka zai tashi ba, baka san ya rayuwa zata kasance masa ba, kalli dai wannan yarinyar, yanzu ai ta daukarwa kanta hakkin yarta, wannan kiwon da Allah yake cewa ya bawa iyaye na yayansu ka ga matan da suke jefar da yayansu ba su sauke wannan nauyi ba, kuma sun jefa kansu da yayan a ciki bala'i da bakinciki, Allah dai ya shirya mana zuri'a" Aliyu ya bude ido yana kara jin tausayin Emily ya kama shi. "Amman ta hanyar banza ta same ta ko kuma dai kuskure aka samu?" "Shi ne ban tambaye ta ba" "To miye amfanin bayyana akanta a yanzu? Kuma a irin wannan lokacin da take cikin matsala? Kawai sun kunno mata wuta ta rasa ma ina zata saka kanta? Ban tashi tare da ita ba, amman dan zaman da muka yi ina jin tana yawan maganar iyayenta amman ban yi tunanin haka abun zai zo ba" "Allah dai ya saka idan ta huce ta dawo, idan kuma ta zabi tafiyar ne Allah yasa ta fada hannun kwarai" "Ameen" Ummi ta bude abincin zata fara zuba masa ya dakatar da ita. "Ummi karki zuba abincin nan, ba zan iya cinsa a yanzu ba" Ummi ta yi kamar bata ji ba ta zuba masa ba da yawa ba. "Ka daure da kai ka ci" Ya karba yana kallon mahaifiyarsa, sai kuma ya saki murmushi kadan yana jindadin da shi ta shi uwar ta kasance a tare da tare. Ya fara cin abincin yana tuna wasu kalamai da Emily ta fada masa lokacin da ya kawo ta gida daga gurin aikinsu. "Yarinyar ta yi kokari, ban san irin rayuwar da mahafiyarta ta gani ko ta ji ba daya saka ta jefar da ita, amman dai ita Emily ta tsaya tsayin daka akan yayanta, daga wanda ya mutu har wannan Fatima babu wanda bata sha wahala gurin rainon ciki da haihuwarsa ba, amman bata gudu ta bar ko daya ba, har London da yake da lalura ma, wata kila saboda ta san yadda ake ji ne idan babu kowa na su a kusa da su, saboda ita sa dandana dacin haka, ita kadai sai irin mutanen da suka tashi a irin yanayinta suke iya fahimtar yarenta, amman dai abun da na sani Emily Jaruma ce, ma manta ban fada mata wannan ba" Ya kai abincin a bakinsa ya tauna ya hade amman baya jin dandanonsa ko kadan, kawai dai yana ci ne saboda ya ranta ran Ummi. TURHAN POV. Ammy na tsaye balcony tana kallon Turhan da ya fito motar abokinsa Manir ya doso entrance cikin yanayin damuwa. "Sannu Manir an gode Allah yayi albarka" "Ameen sai da safe Ammy" Yaja motar ya wuce Ammy ta juya ta shiga falon ta zauna kusa da danta. "Ba wani labari ne?" Ya dago jiki a sanyaye, murya kamar ba tasa ba. "Babu, na yi report har gurin police, amman dai har yanzu ba ace an ganta ba, ni da manner mun zagaye rabin garin nan ba mu ganta ba, mun tafi har wata unguwa nemanta, muka kwatanta na nuna hotonta sai suka ce mana ta zo amman da dadewa kusan shekara bakwai da suka wuce, wai mahaukaciya ce sun fada mana irin rayuwar da ta yi a gurin da ciki, ina kyautata zaton bayan ta bar Sudan ne, saboda sunce tana tare da yaro" "Wata kila da cikin Fatima ne, ta fada min ta zauna a unguwanin duk suna mata daukar mahaukaciya" Turhan ya duba agogon falon dake nuna karfe 11pm ya sauke ajiyar zuciya. "Ammy na cutar da yarinyar nan, na gode da baki bar ni sai da na nemo ta, sai dai yanzu ban san wane hali zata fada ba, a ina take?" Ya soke kai kasa ya dafe cike da damuwa. Ammy ta kai hannu ta shafa kan danta. "Alhamdulillah, ka gane gaskiya shi yafi komai kyau ai, na jidadin haka, kuma In Shaa Allahu zata dawo, uwa ai bata iya tafiya ta bar yaranta, komai zai daidaita" "Ina fatan haka" Ammy ta sumbance shi, tana jin kaunar danta sosai ga kuma jikarta dake dakinta tana bachi abun burgewa. "Gobe zan bar garin nan da karfe 10am, saboda kiran da Abie yake min" "Toh Allah ya kaika lafiya ya tsare" "Amman ina son na tafi da Fatima Ammy" Ammy ta janye hannunta a jikinsa. "Aa, ba zan yarda ka sake tafiya da kowa ba, haka ka tafi da uwarta labari ya canja" Ya kalleta. "Wannan baya ne, Wallahi yanzu ba Emily ba ko dankwalinta na tafi da shi ba zan bari ya wulakanta ba, balle kuma Abunda ta haifa min" "Aa ka barta anan dai, kai ma zaka fi jin karfin dawowa" Baya son ya musa mata, dan haka ya amince ba dan ransa ya so ba ya mike tsaye yana sauke ajiyar zuciya ya haura sama, dakin Ammy ya fara shiga ya zauna bakin gadonta yana kallon Fatima dake ta bachi rumgume da teddy, ya matsa kusa da ita ya kai hannu yana shafa fuskarta, matar da ya wulakanta ya kaskantar ita ce yau ta ba shi farincikin da yake nema kuma wanda ba a siyarwa. "Wata mahaukaciya? Mai ciki? Ana tunanin cikin an mata shi ne ko kuma asiri aka mata, wacan shagon ta yi zama lokacin ba ayi gina a gurin ba" Haka yayi ta tuna yadda mutanen suka yi ta labarta masa Emily. Ya kai bakinsa ya sumbanci Fatima hawayensa ya zuba a kan fuskarta. [7/25, 8:28 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 WATTPAD https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy Page 5️⃣7️⃣ Jirginsu na sauka mutumen dake kusa da ita ya kalleta ya ce "Ki biyo ni zan miki ragora, Dr A-B ne yace a kula da ke" Ta kalle shi sai, tun da ta zauna yake a gurin amman be ce mata komai ba sai a yanzu. Yana tashi ita ma ta tashi ta bi bayansa duk inda ya shiga tana biye da shi har suka isa gurin motar da aka kawo, sai ya bude mata baya ta shiga shi kuma ya shiga gaba ya shiga ya rufe aka ja motar, Emily dai na zaune shiru har suka isa unguwar manyan mutane, ba ka ganin komai sai gine gine daga hawa biyu sai uku sai ka tona zaka ga mai hawa daya. Gaban wani katafaren gida direban motar ya tsaya yayi horn security ya bude masa gate, gida ne babba sosai mai dauke da gini mai kyau na burgewa ga shuke shuke ta ko'ina amman ko kadan hankalin Emily be kai can ba saboda tunanin yana wani gurin dabam, direban na fakawa aka bude gefen da take data dago kai sai ta yi arba da Dr AB fuskarta dauke da murmushi ya miko mata hannu. 'Haka rayuwa take tafiya da ni? Daga wannan sai wacan?' Ta tambayi kanta tana kallon hannunsa kamin ta mika masa nata hannun ta rika shi ta fito motar. Tsaya ta yi a gabansa yana ta kallon fuskarta zuwa cikin idonta, kallon karantar damuwarta ne yake, idonta ya nuna alamar bata samu bachi ba, fuskarta kuma na nuna alamar damuwa, sukuku kamar wanda aka yi ma mutuwa. "How are you Emily" Ta daga kafadunta ta tabe baki kadan kamar mai son fashewa da kuka. "Na shiga damuwa, komai ya chabe min" "Is okay" Ya rika hannunta yaja ta tafiya mai nisa sannan suka isa entrance din shiga falon ya taka yana rike da ita ya tura kofar falon ya shiga yana janye da hannunta, falo ne babba mai dauke da kawa da abubuwan burgewa amman Emily bata kula komai ba, ita dai tana biye da shi har suka haura sama hawa na farko ya tura wani daki ya shiga da ita, da kansa ya zaunar da ita kan gadon dake dakin. "Nan ne dakinki, akwai bandaki ki shiga ki yi wanka wardrobe tana cike da tufafi ki saka marar nauyi, za a kawo miki herbal tea ki sha, kamin ki ci abinci, zan tafi asibiti ana jirana daman saboda ke na dawo" Ya mike tsaye ya dauke hannayensa daga kan kafadunsa. "Na gode" Ta furta, sai ya juyo ya kalleta cike da tausayi be ce komai ba ya fice daga dakin. Kwantawa ta yi akan gadon tana tunanin duk wani abu da ya faru da ita na farinciki wata rana da ta yi farinciki sai fa Emily ta tuna ta a ranar sai gata tana murmushi da hawaye, can kuma ta kai hannunta ta murza wuyan hannun tana tuna agogon da Aliyu ya bata ko a ina ta jefar da shi bata sani ba. Ta mike tsaye ta share hawayenta ta shiga bandakin ta tube tufafin jikinta ta kunna shower ta zauna a kasa ruwan yana dukanta ta rufe ido tana maida numfashi a hankali. Ta dade a haka sannan ta yi wanka har kanta sai da ta wanke sosai sannan ta fito daure da tawul ta bude wardrobe din ta cire doguwar riga mai yalwa marar nauyi ta saka. Wata Cristian maid ce ta shigo sanye da short skirt da bakar riga ta kawo mata tea, daga baya kuma ta shigo mata da abinci da ruwa. Emily ta dauki tea ta shanye ta zauna bakin gadon tana jin ina ma bata jefar da wayarta ba da ta kalli hoton yarta ko zata ji sanyi. Bata ankaro ba ta fara jin bachi sai ta kwanta tana lumshe ido da hamma kamin kace me bachi yayi gaba da ita. Bachi ta yi sosai na tsawon awa hudu ko da ta farka yamma ta yi sosai. Tashi ta yi zaune tana murza ido madadin ciwon kan ya sauka sai ta ji ya karu, ta sauko da kafafuwanta kasa kenan AB ya turo kofar dakin ya shigo rike da leda, ya zauna kusa da ita. "How are you feeling now?" "Kaina yana ciwo sosai" "Yeah saboda kin kwanta da tunani ne, kuma bachin be isheki yadda ya kamata ba, amman ga magani zaki ji sauki" Ya bude ya dauki wani sabon Water bottle da aka kawo mata ta bude ta dauki cup din ya zuba ruwa ya balla maganin ya mika mata ta karba ta sha tare da ruwa, sannan ya bude sabon abincin da aka kawo mata tana bachi ya zuba mata kadan ta sauka kasa ta zauna ta ci, bayan ta gama ya sake bata wani maganin. "Ki wake shiga ki yi wanka, amman da ruwan normal ba mai dumi ba kuma ba mai sanyi ba, za a sake kawo tea anjima ki sha, zuwa gobe da safe idan kin huta stressed din ya rage sai ki gaisa da Momy" Ta daga mishi kai, ya mike tsaye ya kunna tv dake dakin ya kama channel din dake nuna abubuwan ban dariya, ya rage sanyin ac sannan ya kalleta ya sakar mata murmushi ya fice, ta bishi da kallo tana mamakin yanzu shi baya cikin wata damuwa shi sam be san wani abu damuwa ko rashi ba, ba kamar ita ba dake da tarin matsaloli. Yadda ya fada mata haka ta yi bayan ta gama ta zauna tana kallon tv sama sama bayan magari aka kawo mata fruit sai madara da ruwa ta ci fruit din rabin plate sannan da shanye madarar da bata da yawa, after like one awa aka shigo mata da tea ta shanye, nan ma babu jimawa ta yi bachi. Sai tara ya shigo dakin ya kashe tv ya lullube ta ya rage hasken dakin sannan ya fita. Washe gari kamin kowa ya shigo dakin shi ya fara shigowa sanye da kayan bachi, shigowar shi ce ta tasheta daga bachi ta farka. "Good Morning" Ya fada da murmushi a fuskarsa sai ta murza idon ta tashi zaune. Ya zauna kusa da ita. "How are you feeling now?" "Much better" "Kan yana ciwo?" Ta girgiza kai. "Good, me kike so for breakfast?" "wannan tea din ina son na yi bachi" "Zaki yi bachi, ana bin ka'ida ne ba a son bachin yayi yawa ne, kina cin kwai? Domin shi ne best abun da nake son ci da safe kwai sai tea" Ta daga kafadunta. "Okay, za akawo miki amman yanzu ki fara shan maganin nan" Ya dauko maganin ya bata kamar dai jiya ta karba ta sha. "idan kin karya ki sha irin wanda na baki jiya, zan fita aiki kin san bama samun zama, ina son ko da zan dawo na same ki kin shirya sai ki haura sama ki gaisa da Momy" Ta daga mishi kai. "Na gode" When ever she says ta gode sai ya ji zuciyarsa ta tsinke. Ita kuma tana jin ita din ba dole ne a kula da ita ba, domin mahaifiyar data haife ta ma ta jefar da ita, duk wanda zai ganta ya taimaka mata ya cancanci godiya a gareta. "Idan na dawo zamu gaishe da Momy karki manta" Ta daga mishi kai, sai ya ja kumatunta yana murmushi ya mike tsaye ya fice. Be dawo ba sai after ta yi lunch sannan ya shigo da ice cream da chocolate ya kawo mata, sai da ta ci sannan ya riko hannunta suka fito, ta yi zaton kasa za su sauka sai ta ga sun haura hawa na biyu a nan ma wata duniyar ce mai zaman kanta, wani apartment ne guda mai dauke da komai daya yafi na kasa kyau da tsari, banbancin falon kasa ya fi fadi da yalwa ma sama kuma ba wani mai girma ne sosai ba, falo ne har biyu ga kuma dakuna da suke cikin falon, ta cikin falon akwai view din falon kasa da kuma gefe dayan gefen kuma harabar gidan ce. Ko'ina na view din glass ne da manyan curtains da aka sako aka bude su da wadi sosai iska na kadawa, dama da falon kuma wani center ce mai dauke da books ga chairs na zama, dayan gefen kuma dinning area ne an yi shi sama kadan sai ka tara stairs biyar sannan ka hau guri. Ga wani katon Tv mai kamar majigi, ta ko'ina sanyi ke bugowa, ya zaunar da ita kan kujera sannan ya shiga one of the bedrooms da suke falon babu jimawa ya fito tare da wata mace da gani daya Emily ta yi mata ta gane wacece. "Barka da zuwa gidanmu" Emily ta mike tsaye, matar ma kallon Emily take har ta zauna tana sanye da short gown da sarkar cross a wuyanta, AB ya zauna kusa da ita. "Zauna mana, ni sai nake ganin kamar na san fuskarki" Emily ta zauna tana rike da hannayenta. "Mun taba haduwa wata rana a Sudan, ke kika zo da ni Nigeria" Da mamaki matar ta sake kallon Emily. "Anyi haka, ke ce? Wannan baiwar da aka ba ni sadaka?" Emily ta daga kai, AB kuma ya shiga rudani. "Kun taba haduwa?" "Yeah, kai ya ka hadu da ita?" Ya fada mata, sai ta kalli Emily tace. "Meyasa kika gudu a gidan matar da na hada ku?" "Saboda na miki karya a wacan lokaci na fada miki an siyar da ni, ba siyar da ni aka yi ba, wani na aura dan sarki garin shi kuma yaje da ni a matsayin baiwa" "Zan iya saninki? I want to know more about you, why do you lie" Emily ta fara hawaye. "Saboda ba zaki yarda da ni ba idan na fada miki dan gidan nake aure, kuma ba zaki yarda ki taimake ni ba" Dr AB ya kalli mahaifiyarsa. "Momy wannan ba lokacin da ya kamata ayi wannan maganar ba ne please" "Why? Ya kamata mu san wacece ita, saboda ita ka yi ma mijina karya ya bada jirgi aka dauke ta, and because of her ka roki mijina ya kula da duk wani responsible nata tun daga kaduna har zuwa nan, ya kamata mu san da wa muke zaune a nan" "Yeah amman ba yanzu ba, she's Cristian" "Matsalar bata addini ba ce, idan kana son mu'amala, kawance ko aure musulma ko wanda ba musulma ba, wannan ba matsala ba ce, matsala shi ne mu san wacece ita" "Zan iya baki labarina idan kina so" Dr A-B ya mike tsaye da sauri ya koma kusa da Emily ya zauna tana hawaye ya rumgume ta. "No ba yanzu ba" Momy ta kalleshi kamar bata jidadin rungumar da yayi ma Emily ba ta mike tsaye. "I'm sorry Son bana nufin bakanta mata, kuma karki dauki hakan a matsayin wani abu, as long as my only son was the one bought you here you're welcome" Dr A-B ya bata rai alamar be jidadin Momy ta yi ba, ita kuma bata sake cewa komai ba ta koma dakinta. Emily ta daga kai ta kalleshi. "Ya zan yi da rayuwa? Ji nake kamar zuciyata zata tsaya" Ya kara rumgume ta. "Ya isa haka" Ta share hawayenta ta raba jikinta da na shi. "Zan iya komawa dakin da ka sauke ni" "Yeah" Ya bita da ido har ta fita falon, sannan ya mike tsaye ya shiga dakin da Momynsa take. Tana fitowa falon ta fara saukowa kasa tana hawaye madadin ta tsaya hawa na biyu inda ya sauke ta sai ta sauka kasa gaba daya tsabar hankalinta baya jikinta, ta shiga wani dakin dake falon na farko tana shiga ta ga ba nan ba ne ta fito ta bude dayan dakin nan ma ba sha ba ne nan ma kuka ya ci karfinta ta durkusa tana kuka, laifi take dorawa kanta domin da ace bata biyewa so ba da yanzu Khaleefa be kaita ya baro ba domin shi ne silar faruwar komai. "Ba haka ake tarbar bako ba, abun da kika yi a yanzu kin kara jefata ne a damuwa kuma baki san iya halin data shiga ba, ba ita ta nemo ni ba ni nake ta kokarin shiga rayuwarta" Ta aje littafin dake hannunta. "I didn't ask her to leave, i didn't say she's not welcome, all what i asked her is who she is, ya kamata musan idan ya cancanci duk abubuwan nan da kake mata, kuma ya kamata mu san da amintacciya muke zaune" "Kina da gaskiya, amman ba a irin wannan lokacin da yanayin ya kamata ki yi wannan maganar ba, kina ganin ganin yarinyar nan kin san akwai damuwa a tare da ita, ni na san yadda damuwa take, ta kan saka mutum ya hauka ko ya fita hayyacinsa, wani ma baya iya bayyana matsalar sa saboda yana jin kamar ba za a fahimce shi ba, tun farkon haduwana da yarinyar nan Allah ya hada wata alaka mai karfi a jinina da nata, na ji ta yi min ta kwanta min a rai, and duk lokacin da zan sake haduwa da ita sai na karanci damuwa a tare da ita, shiyasa nake ta shiga rayuwarta saboda ma taimaka mata" "Aikinka shi ne duba masu damuwa ka ba su magani not to take their responsibility" "I thought you want me to get married? Ko da yaushe kina fadar kina son na canja, why all this now?" Ta yi shiru kawai tana kallonsa. Sai ya juya zai fice. "I'm sorry Son I'm sorry, bari na yi magana da ita a falo" "Already ta sauka, ba sai kin yi ba i will talk to her" "Bari na sauka da kaina na yi magana da ita" Ta mike tsaye ta aje littafin dake hannunta fice daga dakin ta fito falonta, ta sauka hawa na farko Dr A-B yana biye da ita, shi ya fara shiga dakin ya duba ya duba be ganta ba, ya leka bandaki bayan yayi knocking nan ma bata ciki sai ya fito ya duba sauran dakunan da suke jere da nan bata cikin ko daya ya sake sauka kasa gaba daya ya ya bude dakunan dake falon na kasa, yana bude daki na biyu ya same ta kwance a kasa tana hawaye. "Emily" Ta dago da sauri ta kalleshi tana jin zuciyarta na mata wani mugun ciwo. "Na manta dakin ne I'm sorry" Ya karasa inda take ya rikota ya mikar da ita tsaye, sai Momy ta karasa kusa da ita. "I'm sorry, bana nufin bata miki rai, ki yi hakuri na yi kuskure, amman ina fatan zaki fahimce ni bari na rakaki dakinki" Ta kama hannun suka fara tafiya. TURHAN POV. Shiru yake a jirgi har suka sauka, saboda ya bar zuciyarsa a gidan Ammy be tafi da ita ba, wato Fatima ko da ya bar gidan ma tana bachi bata san ya tafi ba, sai sumbantarta yayi ya dauki hotonta ya tafi shi ma baya son ta ga tafiyarsa tace zata bishi Ammy ta hana. Ya sauka airport din yayi waya aka zo aka dauke shi kamar yadda aka saba, sai dai abun da be saba ba shi ne fara ganin mahaifinsa bayan sauka gida, a yadda al'adarsa take idan ya dawo yana shiga bangarensa ya huta ne sannan ya fito gaishe da mahafinsa, amman wannan karon motar na isa masarautarsu ya umarce direban ya faka harabar fadar mahaifinsa, yana jin kamar ba shi da natsuwa idan be ji dalilin kiran da mahaifinsa yake masa ba. Ko da ya shiga fadar ya samu mahaifinsa da baki, haka ya zauna har sai da mahaifinsa ya samu sarari sannan ya doshi can cikin fadar bayan ya saka an sanar masa da bukatarsa ta son ganinsa. Kamin ya karasa Ammy ta kira wayarsa ta fada masa Fatima ta fara kuka saboda be dawo ba, ta mata karya cewar ba nesa ya tafi ba. "Kuka take ne?" "Eh tana tashi bachi dakinka ta fara lekawa ta fito baka ciki sai na fada mata ka tafi ka dawo, tun dazun take tambaya yanzu kuma ta fara kuka" "Bari na kira Video Call sai ki ba ni na yi magana da ita" Ya katse kiran ya kirata FaceTime sai ta kara masa Fatima dake kuka yayi magana da ita yana rarrashinta Ammy na fassara mata har ya samu ta yi shiru. Ya tabbatar mata da gobe zai dawo. "Idan ka dawo ba zaka sake tafiya ba?" "Eh, ba zan sake barinki ba Fatima na yi alkawari, i love you" "I love you too" "Zaka zo tare da momy? Zamu zauna a nan?" "Eh, zamu zauna a tare Fatima zamu zama Family daya" "Okay bye" Ta masa waving shi ma ya daga mata yana jin kamar yayi kuka domin yana matukar son yarinyar nan fiye da komai, sai da ya maida wayar aljihu sannan ya kunna kai a karamar fadar mahaifinsa cike da amsar tambayoyin da ya san mahaifinsa zai masa. _________ Ayi hakuri, muna biki ne. 🙏 _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [7/27, 8:34 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 WATTPAD https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy Page 5️⃣8️⃣ Turhan ya zube a gaban mahaifinsa ya gaishe shi, mahaifinsa yayi kamar be san da shi a gurin ba, bayan mintunan da suka bata a zaune wata kalma bata shiga tsakaninsu ba, Turhan ya yankw shirun ta hanyar sake mika gaisuwarsa ga mahaifinsa a nan ma be tanka shi ba. Bayan tsawon lokaci mahaifin ya mike ya shige wata turakar tashi, Turhan ya tashi ya koma bangarensa ya samu balarabiyar matarsa kyakkyawa kamar shi tana zaune cikin bahon wanka tana shuda jikinta da kumfan shower gel mai kamshi. Ya karasa kusa da ita fuska babu wata walwala ya sumbanci goshinta kamar yadda ya saba, cikin farinciki da zumudi ta mike tsaye ta rumgume shi tana masa barka da zuwa. "Ban yi tsammanin dawowarka yanzu ba, ya Ammyn take?" Ya kalleta kawai yana murmushi a zahiri a badini kuma yana hango dalilin Ammy ne aura masa Aisha, tun da yake da matarsa bata taba sha'awa tafi gaishe da mahaifinyarsaba, ko a waya sai idan shi ya hada su take gaisawa da ita, ya taba mata tayin tafiya Nigeria sai ta nuna bata da bukata be sake maimaita bukatar hakan a gareta ba, kuma a wacan lokacin baya ganin illar hakan sai yanzu da ya fi fahimtar muhimmancin mahaifiyarsa... Ya sake ta juya ya fice hakan sai ya bata mamaki domin be saba ganin jikinta a haka ba ba tare da nuna shaukinsa akai ba, amman yau tambayar ma be amsa ba, a take ta wanke jikinta ta daura tawul ta dayan kuma ta daure kanta ta fito daga Bathroom din ta bullo corridor domin babban bandakin dakinsu ba a daki yake ba a mahadar hanyoyi ne dake tsakanin dakunansu. a ranar dai kam Turhan be samu magana da mahaifinsa domin baya amsa ba. Karamin falon ta fara leka bata ganshi ba sai ta dawo corridor ta shiga dakinsa. "Turwhan... Kana lafiya kuwa?" Ta karasa inda yake tsaye yana cire rigarsa tana kallonsa. "Wata kila gajiya ce, amman idan na huta zan mu wata magana" "Tana da muhimmanci ne har ka bata rai haka?" "Zan ki iya hada min wani abu na ci?" "Shaghala (Mai dafa abincin) zata hada maka" "Shukuran" Ya saka bathrobe ya fice ya barta a dakin, tana mamankin yanayinsa a yau. Da dare ma sai da ya koma bangaren Mahaifinsa nan ma be yi magana da shi ba. Haka ya dawo bangarensa ya zauna a inda suka saba cin abincin shi da matarsa ya samu an jera abinci a kasan wani farin kyalle da aka shimfida ta zauna ya hade kafafuwansa yana kallon kayan marmari da ka'ida ce kullum sai an aje tare da sweet kala kala. Be ankaro ba ya ji an zauna kusa da shi matarsa ce fuskarta dauke da murmushi tana kamshin EOS Khumra Al Dufra Perfume Oil. Ya juyo ya kalleta tana sanye da thobe (or toob / toub / توُب), wata kafaya ce ta al'adar larabawan Sudan, sai ya sakar mata murmushi ya kama hannunta ya rike. "Kana cikin damuwa ina iya ganin haka daga gareka, ina lura da irin wannan yanayin a duk lokacin da ka dawo daga Nigeria, amman na yau na musamman ne" "Na kan dawo da damuwa ne saboda neman mafitarta wata hanya ne, a yanzu kuma na samu karshen ta amman ta kasa bullewa da ni" "Ina gane ko wace kalma da yaren larabci amman ban da tsarke magana a cikin wata magana, fada min Habibi me ya same ka?" Ya juyo ya fuskance ta da kyau. "Ina fatan zaki fahimce ni kuma zaki min uzuri, lokaci yayi da ya kamata ki san komai..." Sannu a hankali Turhan ya yi mata shimfidar da zata mikar da ita zuwa cikin ajinsa har ta dauki karatunsa, tun da ya fara bata ce masa uffan ba har ya kai karshen littafin data kasa fahimtar haruffansa balle ta haddace karatun ciki. Ya fada mata ya aure wata mata matar kuma ita ce wanda ya zo da ita a matsayin baiwa haka kuma ya sake ta a yanzu amman zai dawo da aurensa da ita, haka zalika yana da ya a tsakaninsu, sannan ya fada mata yawan zuwan da yake Nigeria har ya dade yana zuwa nemanta ne. Da farko zancen ya rikice mata ne har ta rasa muhallin dorashi kamin hankalinta ya janyo tunaninta bayan ya nuna mata hoton Fatima. "Mabsoot bikhibalak" Ta furta tana jefar da hannu idonta ya fara tara hawaye. "Ka ci amanata Turwhan, taya zaka yi aure bayan idona? Saboda bana haihuwa? Ko kuma saboda mahaifiyarta bata so?" "Ki zargi komai ban da mahaifiyata, domin bata taba nuna miki kiyayya ba, matar da baki taba sha'awar gani ba?" Ta tsaya cak tana kallonsa kamin ta mike tsaye ta taba masa. "Barakallahu fika Turwhan" Ta juya sai yayi hanzarin mikewa tsaye ya rike ta. "Idan har zaki ji babu dadi wannan abun da na aikata ki yi tunanin yadda matar da na wulakanta zata ji? Kuma na yi ne ba dan kai na kadai ba har da ke?" Ta juyo da karfi. "Idan har baka sonta taya ta haihu da kai? Bayan duk wannan yanzu kuma kana fada min zaka dawo da ita? A tunaninka zan iya zama da kai bayan duk wannan abun da ka yi min? Balle kuma har zaka zauna da matar da bata wuce matsayin mai kula da gidana ba? Aure ya kare tsakanina da kai. "La la la, khalas al-mawdu‘ intiha. Ana ‘ayza talaaq" Furta cewar sai dai ya sake ta ya karya masa guiwa sai dai be karya zuciyarsa ba domin a yanzu Fatima kawai yake hange. Ya kama hannunta ya rike cikin sigar rarrashi ya ce. "Za mu iya fahimtar juna mu gyara komai, ki yi uzuri, ki karbe ni tare da yata" "Ba zan karbi uzurinka ba, kuma har abada ba zan taba son yar wata ba, har karshen rayuwata, Lihaddy akher nafas fi ḥayāti" Ta furta hakan har sau uku tana hade hakora, kalmar ba zata taba son yar wata ba har karshen rayuwarta ya saka Turhan ya saki hannunta domin Fatima yarsa ce, ba yar Aisha kadai ba, be ce ya shirya rabuwa da ita ba, ko rusa aurensa ba, domin ba zai yarda ya maimaita irin wacan kuskuren da ya aikatawa Aisha ba, sai dai kuma hakan ba shi yake nufin ya jure a ciwa yarsa ko mahaifiyarta mutuncin ba. Ta kalli hannunta daya saki ta kalleshi fushi ya dauketa ta fara shure kayan abincin da abinci dake ciki tana ihu tana la'antarsa da kalmomi marasa dadi. Kamin ta fara bin sitting room din ta fara hargitsawa tsabar bala'inta be iya kwana a gidan ba sai fita yayi ya kwana a hotel, washe gari ko da ya dawo be same ta a gidan ba, ya samu ta yi ma gidan barna duk wani abu mai glass sai da ta fasa shi hatta kwalbar turare bata bari ba. Wanka yayi ya canja tufafi sannan yayi ma khadimansa su gyara bangaren, ya fito ya nufi fadar mahaifinsa ko'ina ya bi kallonsa yan'uwansa suke, sauran Khadiman gida kuma sai ya sauke ido ake satar kallonsa, kowa yana mamaki da abun da matarsa ta fada jiya cikin ihu da hayaniya. Yau ma da ya shiga mahaifinsa be tanka masa ba. "A gafarce ni, na san ina da tarin laifuka" Bayan kamar Minti biyu mahaifinsa ya kalleshi. "Na yi zaton ba zaka zo ba ai, saboda ban isa da kai ba" "Ban isa ba, kai kayi kira na kasa amsawa, da baka isa da ni ba da ba za a kawo maka rokon abun da a cikin aikata shi babu adalci ba" "Wata wuta ce aka ce ta kama a wani gida, aka roki na kasheta, da na bincika dalilin tashinta Sai aka fada min har da ɗana a gurin assasata, shin hakan gaskiya?" "An riga ni sanar da kai tashin gobarar data haifar da hayakin sanar da duniya abunda ake ciki ne, amman ina da wannan nufin a yanzu da nake ganin lokaci ne daya dace kowa ya san komai" "Aka ce ka yi aure? Tatsuniya ce ko kuma dai ana kokarin kunna fitina a cikin masarautar ne?" Turhan ya natsu Sosai ya sanar da mahaifinsa yadda auren ya afku da kuma yadda boye lamarin har zuwa yau. Yayi zaton zai fuskanci fushi da natsa daga gurin mahaifinsa ne sai gashi ya tsinkayo mahaifinsa na murmushin kasaita ya kalleshi cike da alfahari. "Wani lokacin akan dora mana nauyin abun da ba za mu iya sauke ba, sai da hikima da yawa, na yaba da kokarinka na boye auren kuma na jidadin da yarka take hannunka, jininmu baya zama a ko'ina sai a kusa da mu" Turhan ya kalli mahaifinsa cike da damuwa. "Be zama lallai Fatima ta zauna kusa da mu ba, idan mahaifiyarta ta zabi, zama a Nigeria ina tunanin ba ni da zabi da ya wuce na bi ra'ayinta domin gyara laifin da na aikata" Mahaifinsa ya sake dubansa. "Baka aikata laifi ba, ko mace bata cancanci auren dole ba balle kuma kai, baka bukatar zama da matar da baka so kuma bata cancanta ba" "Ta cancanta, saboda kyauta ce daga gurin mahaifiyar da bata jidadin zaman gidan miji ba, mahaifiyar da bayan danta da yi ma kyauta bata da wani, mahaifiyar da aka hanata ganin danta na tsawon shekaru, aka hana ta shayar da shi, na wofintar da Aisha ne saboda tsoron kallon da za'ayi min, da kuma tunanin kamar ni laraben mutum na fi wata fatar matsayi, bayan kuma har a gurin Allah ba haka ba ne, ada can bana son Aisha, amman a yanzu ina jin zan iya mutuwa ita ta rayu, ta ba ni sanyin idaniyar da ban samu ba a gurin matar da nake ganin ta fita matsayi, Ya Abiy ina son Aisha so mai tsanani, ina son yarta son da be da misali, ita ce ta maida ni uba, wannan shaukin ba zai taba gushewa ba, na aikata abun da na aikata ne saboda son zuciya, amman da na runtse ido ban ga kyau a makanta ba, anya idan mahaifiyata aka yi ma ko yata, zan iya jurewa? Amsar ita ce aa, ko ban fada ko na nuna ba abun yana a zuciya" Sarkin yayi shiru na tsawon lokaci kamin ya ce "Karka manta da asalinka, kar ka bari mahaifiyarka ta saka maka kalmomi marasa amfani a kanka" "Ba zan taba mantawa da asalina ba, ni dan wata mace bakar fata ne daga arewacin Nigeria, kuma dan Sarkin Sudan balarabe mai asali, Mahaifinta bata saka min kalmomin manta asalina ba, amman ta fada min yadda mahaifina ya mu'amalance ta, wanda ya sha banban da yan'uwana da nake gani a Masarautar, kuma laifinta shi ne ita bakar fata ce kawai. Bana son yata ta tsane ni, ko kuma ta kalleni da laifin dana aikata saboda son zuciya shiyasa ba zan ki mahaifiyarta ba, mahaifiyata ta cancanci girmamawata a kowane irin hali, duk uwar da zata dauki cikin danta ta raine shi ta haife shi ko wace uwa ce ta cancanci biyayya daga gurin ɗanta" Sarki Mohamed Abdou ya dauke kai kamar mai jin kunyar Turhan, kuma ya gagara bayyana bacin ransa. "Mahaifita ta dandani daci mai tsananin kashe halshe daga gurin mahaifina, a yanzu kuma da ɗanta ya kawo sai take ganin ta cancani kauna da biyayya, da kowace dakika tsoron rasani take, ni ma kuma ina fargabar rasata saboda ciwon dake neman rayuwarta, Ya shugaba kuma mahaifina tambaya ce mai nauyi na amsa cewa ina da muhimmanci a gareka ko akasin haka, saboda na zama farin tuwo daga bakar tukunya, be zama lallai ka kaunaci abun da nake kauna ba, saboda ni ba Laraba ce ta haife ni ba, amman dai bakar matar nan daga arewacin Nigeria tana da matukar muhimmanci da kima a idona, ina kyautata zaton ba zaka hana ni yi mata biyayya ba, domin Annabi S. A. W ma ya ambaci uwa sau uku sannan ya ambaci uba, saboda muhimmancinta" Mahaifinsa ya kalleshi, hawaye ne suke saukowa a fuskar Turhan ba na wasa ba. "Idan an yi min izinin ina son na kama hanyar komawa gobe, kuma zan dawo ne kadai idan mahaifiyata ta samu farinciki da ta dade tana nema, kuma na samu matar da ita kadai nake muradi a yanzu" Ya risina cike da biyayya. "A gafarci halshena idan yayi kure, na barka lafiya" Ya mike tsaye ya share hawayensa ya fice daga fadar. Masarautar ya bari gaba daya, ya tafi gurin abokansa da ya nunawa Fatima a waya tun a kamin ya karaso, biyu suka goya masa bayan dawowa da Aisha dayan kuma ya nuna masa ya karbi yarsa kawai ya barta ta yi tafiyarta tun da har ta nuna bata bukatarsa. Ya dawo gidan ya shiga bangarensa sai ya samu an gyara komai an kwashe duk wani abu daya fashe, wasu abubuwan kuma an maida su a muhalinsu. Ya shiga dakin da matarsa ta fi zama ya zauna a kujerarta sai tunani yake kala kala can kuma ya mike tsaye ya fito daga dakin ya shiga dakin da komai nasa yake ciki, yana kokarin cire rawanin kansa ya hango wani karamin kwali a kan gadonsa, ya karasa kusa da gadon ya dauki kwalin ya bude. Sai yayi arba da ticket din first class na jirgin da zai tashi daga Khartoum zuwa Abuja a gobe, ga kuma manyan kudi mai kauri a ciki da wata yar karamar takarda. "Rihla sa‘īda, Allah yisahil tareeqak" (Safe journey, may Allah ease your way) _Ṣāḥib al-Jalāla Mohammed ʿAbdou_ Turhan ya kai zaune da jallabiyar dake jikinsa yana murmushi, ya dade zaune yana sake karanta kalmar da ba zata canja daga haruffa ko ma'anarta ba, sake shiri yayi sannan ya fita zuwa bangaren mahaifinsa sai ya samu an shirya liyafar abincin dare da yaran da suke gidan ya zauna aka ci abincin tare da shi, bayan an gama ya shiga bangaren mahaifinsa duk yadda ya so ya samu wata dama ya yi kibabbantacciyar magana da mahaifinsa be samu dama ba, domin mahaifinsa be ba shi wannan damar ba. Daya fito sai ya dauki motarsa ya tafi gidan iyayen matarsa ita ma dai be samu ganinta ba domin ko kofar gate di gidan ba a bar shi ya shiga ba. Da ya dawo sai ya hada kayansa da abubuwan bukatunsa tsab cikin akwai har biyu sannan ya kwanta, washe gari da wuri Khadima ta kawo masa abun karyawa ya karya yana video call da Fatima saboda ta fitini Ammy da kukan rashin Turhan da Emily a kusa, sannan yayi wanka ya shirya ya sake kiranta video call be kashe kiran sai da suka shiga jirgi aka umarci kowa ya saka maka wayarsa a airplane mode. AMMY POV. "Jirgin nan zai zo?" "Eh" Ammy ta amsa mata tana shafa kanta. "Zai tafi biya ya dauko Momy ne? I miss her so much" "Aa Momy sai idan ta huta zata zo" "When?" "Ban sani ba tukuna, amman a yanzu idan ana son ganin mahaifiyarki ko kuma a daukota a ina kike tunanin za a same ta sanyin idaniyata?" "A waya" "Bayan waya" "Gidan gurin Uncle Aliyu, ko Vito" "Aliyu yana ajeta a gidansa ne? Da kuka zo garin nan a gidansa kuke zaune?" "Aa" "To da kuna PH ma a gidansa kuke zaune?" "Aa a gidan Vito ne, shi yana dukan Momy ne shiyasa bana son shi, kuma baya so na yana hade rai" "Shi Viton Momynki ta aure shi ne?" "Aa ba zata aure shi ba, ba zamu koma gidan ba, za mu zauna a nan da daddyna ko? Da Momy ko?" "Haka muke fata" Fatima ta mika mata wayar da har yanzu bata san yadda zata sarrafata ta kira ba, amman ta iya shiga YouTube da Gallery ko Camera. "Zaki iya kiran Momy? Ita ma zan yi magana da ita" Ammy ta karbi wayar ta shiga gurin kira ta gwada kiran Layin Aisha da sunan da Aliyu ya saka mata a wayar wato Emily, sai ta ji wayar a rufe. "Ba a samu" "Sake kira" Ta sake gwadawa" "It the same thing" "To kira Uncle Aliyu ki ce ya bawa Momy" "Basa tare, kin san a ina za a iya samunta?" Ta yi shiru can kuma ta ce gurin Vito. Ammy ta yi shiru tana nazari. "Amman Momy ma zata dawo? Ina son na ganta?" "Zata dawo Fatima" Ammy ta amsa mata sannan ta sauke ajiyar zuciya. KAMEELA POV. Ta shiga bangarensu da mamaki tun a falo ta labarta musu komai, sai Hajiyarsu taja tsaki. "Aikin kenan, daga Aliyu sai abun da ya shafi Aliyu" Anty Shafa ta kalli Mahaifiyarsu. "Hajiya, abun be baki mamaki ba?" "Miye abun mamaki a ciki? Wata kila ta fadi hakan ne saboda Kameela ta daina zuwa can, daman idan ba neman suna ba yaushe zaka kashi sirrinka ka fadawa kishiyar uwa?" Kameela ta ce. "Ba wai ta fada ne kawai saboda na daina zuwa mata da maganar ba ne, domin na ga tsananin bacin rai a tare da ita, har fa marina ta yi, kuma idon ta ya kumbura kamar ta yi kuka" Can kuma ta juyo har lokacin tana dafe da kuncinta. "To kuma ma idan ba tsananin bala'i ba ta ina Mama Baraka zata zama mahaifiyar tsinaniyar Emily nan? Ta ya ta ina? Kwata kwata ma basa kama fa, kuma ita Emilyn nan ma fa ruwan turawa ne da ita, fara ce sosai mai jan gashi da blue eyes, amman dai ga dukanin alama akwai wata a kasa" Hajiya ta tabe. "Ita fa kishiya ba yar'uwa ba ce, ba mamaki wani abun ta shirya, amman dai anjima idan Alhaji ya dawo, zan kwankwasa kofar na ji ko zata yi kara" Kameela ta haura sama ta shiga dakinta da mamaki da kuma tsananin kishin ace Emily yar Mama Barakat ce, idan har wannan abun da hankali ba zai dauka ba ya tabbata ai ita kam an gama da ita gamawa ta musamman. "Kai ba ma gaskiya ba ne, ai ba hadi hanyar jirgi dabam mota dabam" Ta zauna cike da kewar mijinta da son sanin halin da yake ciki. Wayarta ta dauka zata gwada kiransa sai wani bangare na zuciyarta ya hana ta yi haka sau hudu sai a biyar ta gwada kiransa, wayar na shiga gabanta ya fadi ta mike tsaye tana safa da marwa a dakin, wayar ta katse be daga ba, ta sake gwadawa be daga ba daga karshe sai yayi rejecting kiranta. Ta zauna baki gado tana hawaye domin tana tsananin kaunar mijinta. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [7/29, 10:20 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣9️⃣ BAYAN WATA UKU... ALIYU POV. Ya sauke wayar tare da sauke kafafuwansa dake kan karamin taber. "Tun da aka sallamoka asibitin nan baka zauna ba Aliyu kullum cikin neman yarinyar nan kake" Ya kalli Ummi. "Tun kamin na dawo daga Asibiti abun da nake ta kokarin yi kenan, kuma ai baki yarda na bar asibitin ba sai da na ji sauki radau idan ma akwai abun da ya fi jin garau na ji" "Allah yasa a dace har yanzu babu wanda ya samu labarin Emily" "Ameen, zan tafi gobe, tare da Mama Barakat ki taya mu da addu'a" "Allah ya tsare amman da ka hakura har sai ka samu kwanciyar hankali tukuna, bana son ka jefa kanka a cikin wata matsala" "Babu wata matsala In Shaa Allahu, kwanciyar hankalina yana tare da samun Emily matukar ban san halin da take ciki ba ba zan taba samun kwanciyar hankali ba, wata kila tana cikin mummunan yanayi shiyasa har yanzu bata waiwayi yarta ba, wata kila kuma ta gaji da rayuwar ne ta hakura a haka" "Jikina ya fi ba ni kamar tana tare da yaron nan da ya saka aka doke ka" "Abu ne mai wahala ta koma gurinsa, balle kuma shi da a yanzu yake boya? Daddy ya fada min dan Information kadan ake nema ana samu za a kama shi domin an tara masa duka laifukan da ya aikata kuma yake aikatawa, kin ga abu ne mai wahala ace yana tare da ita" "Haka ya fada min, yanzu haka baya gidansa, babu wanda ya san inda yake, shiyasa nake jin tsoron tafiyarka Aliyu, kar ace shi ma yana nan yana neman hanyar da zai cutar da kai" "In shaa Allahu babu abun da zai iya" "Idan ka je a kwana daya zaka dawo?" "Eh zan dawo a kwana daya saboda ke Ummi saboda ki samu natsuwa" Cikin yanayin damuwa da rashin son tafiyar Ummi ta ce "Tohm Allah ya tsare, ya kaika lafiya amman da jami'an tsoro zaka je?" "Aa zan tafi da addu'a dai" Ummi bata sake cewa komai ba ta mike tsaye ta. "Aliyu kana son yarinyar nan ne?" Ya daga kai ya kalli Ummi sai kuma ya kalli wani gefen alamar nazari. "Aa iyakar abin da na sani shi ne, ina matukar tausayinta, ta shiga mawuyacin hali tun daga haihuwa uzuwa yanzu, kuma ina ganin a yanzu babu wanda ya kamata ya kyautata rayuwarta irin musulmi, ya kamata ta san muma akwai na gari cikinmu, ban ce zan iya ba amman ina son na ga na maye mata gurbin wasu abubuwan da ta rasa ne" Ummi ta sauke numfashi a hankali ya fara takawa cike da girma ta fice daga garden din. Ta yi mamakin ganin bakuwar mota a gidan, duk kuwa da ta san gidansu gidane dake yawan samun baki koda yaushe amman wannan motar ta musamman ce domin sunan mahaifin Kameela ne a jikin number motar, hakan yana nufin motar gidansu ce daman su plate din motarsu ma da sunan familysu ake yi. Ta hau entrance din ta tura kofar falon da ba a gama rufewa ba ta shiga, ta gangan ta yi kamar bata san da kowa a falon ba har sai da Kameela ta mika mata gaisuwa. "Ummi ina wuni?" Ummi ta kalli gefen da Kameela take zaune. "Kameela? Ina ce dai lafiya?" Cikin yanayin damuwa Kameela ta amsa. "Lafiya kalau Ummi, na je asibiti ne gurin Aliyu aka ce an sallamo shi, shiyasa na zo gida" "Okay, akwai wani hakki naki da yake kansa da be sauke ba ne?" Ta girgiza kai kwalla na taruwa a idonta. "Aa na zo na duba lafiyarsa" "Baki bukatar duba lafiyarsa Kameela domin a yanzu babu wani abu a tsakaninku, amman duk da haka mun gode da ziyara zaki iya tafiya" "Sau ba goma ina zuwa ganinsa asibiti ba su bar ni na shiga ba, yanzu kuma na zo gida ba zaki bar ni na ganshi ba Ummi? Wata uku har da sati a sama ban saka Aliyu a ido ba wannan ma azabtarwa ce, saki daya yayi min Ummi ba uku ba akwai sauran gyara" Ta fada cikin kuka. Ummi ta taka zuwa inda take tana kallonta. "Haka ne, akwai sauran gyara a halayyarki Kameela, tun da har son zuciya zai iya daukarki ki yi kokarin kashe mijinki, kuma zuciyarki ta raya miki mahaifiyar mijinki zata yarda ki sake zama da danta saboda hauka ce ta haife ni, kuma zuciyarki ta raya miki wai akwai sauran gyara tsakaninki da mutumen da kika so ki shafe rayuwarsa daga doron kasa, har kika ikirarin an azabtar da ke da rashin ganinsa, ada can kina tunanin idan kika kashe shi gawarsa za a aje miki kina kallo?" Kameela ta kara fashewa da kuka. "Wallahi Ummi ina son Aliyu... Kishi ne Wallahi, kowa zai iya kuskure ki dauke ni kamar..." Ummi ta nuna ta da yatsa da taka mata tsawa "Ke yarinya kama hanya ki fice, idan kishi ne miyasa ita mahaifiyarka bata kashe mahaifinki ko kishiyarta ba? Abunda nake gani a labarai kika so ko wace jarida ta yi ado da fuskar dana a jiki? Lallai har yanzu baki da hankali" Ummi ta nuna mata kofa da yatsa. Kameela ta nufi kofar tana kuka ta fice, Ummi ta tsaya jiki windows har sai da ta ga ficewarta a gidan sannan ta juyo ta nufi stairs. TURHAN POV. Wani irin kuka sosai Fatima take da daukar numfashi tana kiran sunan Momy. "Momy... Momy..." Ammy ta kalli Fatima dake kwance kan godonta tana bachi a motse saboda tunani da rashin cin abinci. Sai kuma ta kalli danta da ya fi Fatima rama da shiga tashin hankali saboda damuwarsa da Fatima take da tambayar ina Momynta, ga kuma rashin sanin halin da Aisha take ciki domin tun da ta tafi har yanzu ba a samu wanda ya ji duriyarta ba, kuma bata dawo gurin yarta ba. "Da ace na san haka rayuwa zata zame maka ta zame mata daban hada auren nan ba" Ammy ta fada cikin tsananin damuwa, abu ne da yake bayyane a gurin kowa babu wanda zai ce ya taba ganin Turhan a cikin wata matsala da ta haifar masa da rashin cin abinci na kwana daya, sai ga shi a yanzu baya iya cin abin kirki bachi ma wani lokacin sai yayi da gaske yake yi, saboda tunanin tambayar da Fatima take masa, da kuma tunanin a wane hali Aisha take ciki, a dayan bangaren kuma yana auna tsakanin tsanar da ta yi masa, saboda kawai yarta ta zaba shi sai ta tafi ta bar shi da ita har na tsawon lokaci babu sako ba aike babu wata hanya da za a iya samunta. "Haba Ammy be kamata wannan kalamin ya fito bakinki ba, ai ke alheri kika yi nufin aikatawa kuma shi kika aikata kuma alheri ya samu tun da gashi ina da Fatima, ni ne na kawo duk wata matsala da muke ciki yanzu, tunani ne sai na rasa wane zan yi, kullum da fargaba nake farkawa a guntun bachin da yake daukata a karshen dare, fargabar tambayar Fatima, ga shi ta dauki damuwa ta saka a ranta yanzu ta daina sakewa da kowa ta daina walwala, kuma ita kanta Aisha yanzu ba mu san wane hali take ciki ba, kuma ina fargabar kar ace ta fada wani hali saboda rashin Fatima idan har haka ya faru laifin a kaina zai sake komawa" Ta kalleshi cike da tausayi. "Ka yi iya kokarinka kuma na baya ba, ka nemeta a lokacin da baka san tana tare da yarka ba, a yanzu kuma da ban saka ka ba, ka saka kanka ka je har garin da ta zauna baka sameta ba, a garin nan bana tunanin akwai inda kafarka be taka ba gurin nemanta, nan ma baka dace ba, tun da ka baro Sudan baka koma ba saboda Aisha, a haka ma ka biya Turhan kuma ina alfahari da kai, jikina yana raya min kamar tana wani guri kusa ta boya ne kawai saboda ta fitine mu, tun da gashi yanzu Fatima kullum sai ta daga mana hankali saboda neman mahaifiyarta" "Amman me yasa bata dawo ba?" "Saboda ta azabtar mu mana, saboda idan ta waige mu sai mu mika mata Fatima jiki na rawa" "Da ma dai ban sake ta ba, zata iya zuwa fa ta dawo da auren wani akanta" "Zuciyar yarinyar nan bata da kyau, duk wata uwar kirki ba zata iya tafiya mai tsayi haka ta bar yarta ba, saboda kawai ubanta yayi mata ba daida ba, ni miyasa ban kyale ka ba? Bayan duk abun da ubanka yayi min? Wani lokacin idan na tsaya ina tunani sai na rika ganin kamar ba Aisha bace ban yi zaton zata iya aikata haka ba" "Na fi tunanin kamar bata lafiya, ko kuma wani abun ya same ta, wata kila da yanzu ta dawo, domin yadda nake jin Fatima ni kam ba zan ma iya sati ban saka ta a ido ba" "To ya sani tun da ta zabarwa kanta guduwa? Wani abun ba kaddara ba ce har da hali" "Kuma ni sai nake ganin kamar Aliyu ya san inda take, kawai dai yana wasa da hankalina ne ko kuma yana jiran na nemi taimakonsa ne wanda abun ne da ba zai taba faruwa ba har abada, gashi ba wani tufafin kirki take sakawa ba yanzu" Yana maganar cike da zafin kishi marar misaltuwa. "Idan har abun da kake zargi ya tabbata to ni ina baka shawarar ka hakura da yarinyar Turhan, shi kuma sai mu ga idan dan halak ne" "Ai be san kunya ba Ammy ina cire kafa tasa zai saka ya taka, da ace ya san kunya ba zai aikata abun da ya aikata min ba, domin no matter what ya fi kusanci da ni fiye da Aisha, amman ya zabi ya ci amanata, na san ban kyautata ba amman dai ai ni abokinsa ne Aisha kuma be da alakar komai da ita" "A wani mutum makiyinka ne Turhan a cikin yan'uwa ma akwai su kuma munafikin mutum yana da wahalar zama da ganewa, amman ba zaka taba sanin sai wani abun ya faru, wani zaka samu yana maka hassada ne domin idan babu wannan ban da dalilin da zai saka mutum ya zabi bare sama da wanda ya sani ba, kuma har ya nuna maka kirkiri ai kiyayya ta kai kiyayya, sai dai ka yi taka tsantsan" Turhan yaja dogon numfashi ya sauke, sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin gaba daya kansa ya kulle ta ina zai samu Aisha? Ina ta shiga? Tana raye ko kuma tana cikin wani hali? Miyasa zata masa irin wannan horon mai azabtarwa haka? Tsanar da take masa ta kai har can? Amman ta saba guduwa halinta ne. Wani bangare na zuciyarsa ya raya masa, sai dai be gamsu da hakan ba domin yana ganin ga rayuwarta a nan wato Fatima. Ya jingina jikin mota yana kallon tausarin da suka yi sararin samaniya ido, ya tsada idonsa gurin wata tauraruwa wacce ta fi sauran haske a dare. "Na zabtu Aisha, na azabtu fiye da yadda kike tunani, na shiga damuwa na rashin sanin halin da kike ciki, fargabar irin tarbar da zan samu a gareki ya hana ni walwala, ban taba sanin muhimmancin wani abu na kimanta shi ba kamar yadda nake jinki a yanzu, na yi iya yadda zan iya na san wane hali kike ciki amman hakan ya gagara, yaushe zaki dawo gareni? Idan kin dawo zaki saurere ni kuma dai yafiyar ba yanzu ba ce? Kin ce baki taba so na ba, kin yi komai saboda mahaifiyata, yanzu miyasa ba zaki yi saboda yarki ba? Ina son ki Aisha ina son kasancewa da ke" A hankali yake lumshe ido yana budewa zuciyarsa cike da kuna, ya hade yawu. "Ni mai tarin laifuna a gurinki na sani, amman ki ba ni damar da zan gyara mana, kina ina Aisha? Na ji fiye da yadda kika ji a lokacin da na barki, saboda ni a yanzu kin tafi ki bar ni da azababben Ciwon Sonki da tsananin kishinki, kin bar ni da tunaninki, ga fargabar abun da zai same ki da yadda zaki karbe ni, a yanzu ke baki jin komai saboda bana kusa da ke, amman ni ina jin duk wata azaba ta duniya saboda rashinki" Ya juya baya. "Ban san dacin rashi ba da kewa ba sai da na rasa ki, amman zan nemo ki, zan jure duk wata tsana ko tsangwama daga gareki har sai kin yarda ni ABOKIN RAYUWARKI ne, a inda na wulakanta zan daukaka darajarki wannan alkawarina ne, ki yafe min Aisha, dan Allah karki bar ni, ina da bukatarki a kusa da ni, ko da ke baki ra'ayi na na san ba zaki so ni ba, amman ni ina Sonki haka ma ya wadatar, abun nan ba shi da sauki ko kadan, ya wuce duk yadda kike tunani" Ta lumshe ido ya cije lebensa na kasa cike da kukan zuci wanda ya fi na hawaye daci. Sai a yanzu yake ta kara dorawa kansa laifin abubuwan da suka faru, yake nadamar abun da yayi mata kuma yake ganin rashin dacewa a hakan, babu komai a tare da shi a yanzu sai tsantsanar kaunar Aisha da kewarta da kuma nadamar da bata da amfani. EMILY POV. Ya aje mata tsarabar da yayi mata a gafen gado sannan ya kai hannunsa ya taba jikinta sai ya jishi da zafi kamar kullum. Taba ta da yayi ya saka ta bude ido daman idonta biyu ba bacchi take ba, ta kalleshi da idanuwanta da bata iya budewa sosai. "Babu ranar da zaki ji sauki idan ba zaki daina tunani ni ba, tunanin nan shi yake haifar miki da damuwa, ita kuma damuwa bata barin kwakwalwa ta huta, kwakwalwa kuma bata mikawa kowa matsalarta sai zuciya da jiki" "Am so fighting for peace, ina ta yin kokarin abun da zan iya, da kowane numfashi ina tunanin yata da rayuwata, na yi marmarin kurciyarta a lokacin da ban san tashin hankali ko bacin rai ba, ban san muhimmanci iyaye ko yan'uwa ba" Ya zauna gefen gadon sai ta tashi zaune ya kalleta gaba daya ta bi ta fita hayyacinta saboda tunani da damuwa, kusan tun da ta zo gidan ta gagara sakewa da kowa abinci sai dai a kawo mata a daki, sai idan yana gidan yake cilasta mata fitowa dinning ta ci abinci tare da kowa, ga ciwo kullum lafiya ta ki sama mata salama. Dr A-B yayi iya kokarinsa gurin dauke mata hankali da wasu abubuwa amman hakan be samu ba, ko Tv aka kukuna mata madadin damuwa ta ragu sai ta karu, idan ta ga yara, idan kuma wani bangare ne da ake kuka haka zata yi ta kuka kamar gaske. Idan ta auna yadda take ji a yanzu da ta san Fatima tana hannu da guri mai kyau, sai ta yi mamakin yadda mahaifiyarta ta iya jefar da ita kuma ta jure rashinta, a nan ta fahimci wasu mutanen an yi su ne kawai saboda su kaunaci mutane ba dan su samu kaunar daga gurin kowa ba. "Da nace zan saka a dauko Fatima ko? Kika ce aa kuma saboda ita kullum kike damuwa?" "Bana son kowa ya san inda nake, ina jin aminci da natsuwa a nan, kawai dai na gafara sabo wa da kowa ne, kuma ina ta guje ni bayan tsawon shekarun da muka dauka a tare, idan har zan kusance ta sai ta bukace ni, ina son na saba da rashin komai kamar yadda kaddara take koya min" Ya kai hannu ya shafa kanta cike da tausayin hawayen da take zubarwa. "Kina horar da kanki ne kawai, Fatima karamar yarinya ce bata iya gane daidai ko kuskure yara suna bin son zuciyarsu ne kawai" "Haka ne, ni ma son zuciyar na bi ya kai ni ya baro" "Wannan tunanin yake haifar miki da damuwa, Momy ta fada min tun da na tafi baki fito ba, da zarar tafiya ta kama ni zuwa wani guri baki sake fitowa, kuma zuwa yanzu ya kamata ace kin sake jiki da kowa Emily" "Ka yi hakuri zan saba, amman ba lokaci daya ba, abun ba shi da sauki ko kadan" "Na sani, yanzu taso muje mu ci abinci a upstairs" Ya share mata hawayenta, ta san duk yadda zata musa masa ba zai taba barinta ta zauna a dakin ta ci abincin ba, dan haka ta sauko da kafafuwanta sai ya yaye mata bargon dake jikinta ya rika hannunta ya nufi kofa ya bude ya rike mata ta fito ta yi rama sosai kurmin idonta har ya fada, kana ganinta ka ga mace mai damuwa. A falon Momynsa yake cin abinci dan haka ya nufi upstairs watching her steps har suka haura ya shiga falon yana rike da hannunta. Tun da suka shigo akan hannunta da Dr A-B ya rike Aliyu ya sauke idonsa, kamin ya isa gurin fuskarta, for the first time ya ji kamar yaje ya da gudu ya rumgumeta ya fada mata komai zai wuce, saboda yadda yayi marmarinta da kuma damuwar da ya gani a tare da ita ga wata rama da ta yi abun tausayi. Tsayawa ta yi cak, Dr A-B ya kalli kafarta kamin ya kalli fuskarta zuwa abun da take kallo, sai ya ga mutanen da ba bakin fuska ba ne a gurinsa musamman Mama Barakat. Ya kalli mahaifiyarsa dake zaune zai yi magana ta riga shi. "Ka same ni ɗaki zamu yi magana" Ya saki hannunta. "Je dakinki" Ta juya tana jin abun some how, taya suka san tana nan? Ko dai shi ya fada musu? Ta sauka kasa tana tafiya hawaye na sauko mata har ta isa kofar dakin ta murda ta shiga ba tare da ta juyo ba balle ta rufe. "Har yaushe zaki yi ta gudu ne ke kam Emily?" Ta juyo ta kalleshi har ga Allah bayan yarta shi ne mutum na biyu da ta yi marmarin gani. "Taya ka gano ni?" Ta taka ya shiga cikin dakin. "Ta yadda mutuwa take neman rai, duk inda kika shiga zan nemo ki Emily, duk inda kika tafi zan biyo sawunki" Hawaye ya sauko mata "I don't need to do this, ban cancanci wannan sadaukarwa ba" "You just don't know what you mean to me, tabbas ban cancanci sadaukarwa daga gareki ba, alfarma nake nema, Emily ina son na maida ke gida" Ta yi baya baya ta zauna tana rumgume da hannayenta tana wasu hawaye masu zafi. Ya karasa cikin dakin yana kallonta cike da tausayi. Ya zauna nesa da ita tana kallonta shiru yatsasu na tsawon lokaci, kamin ya yanke shirun da fada mata abun da ta fi bukatar ji a yanzu. "Fatima tana lafiya, amman ta yi marmarinki sosai" Ta lumshe ido, bata da tabbaci abun da Aliyu ya fada amman dai ta ji sanyi a zuciyarta. "Why are you here?" Ta tambaya ido a lumshe, muryar a dakishe, Aliyu ya amsa mata kamar mai rada. "To take you home" Ta girgiza kai tana maida numfashi sai dai bata ce komai ba, ita a tunaninta rayuwarta ta zo karshe mutuwa kawai ya rage mata. Aliyu ya cigaba da kallonta cike da tsantsar tausayinta dake ta dawainiya da shi. "Duk lokacin da kika ji ba zaki iya ba, ina nan kusa da ke, hankalina zai fi kwanciya ace duk lokacin da kika farka, zan kasance kusa, na ga nauyin da kike ɗauka ke kaɗai yaƙin da kike yi, tabon da kika nuna" Ya hade bacin ran daya tsaya masa a wuya. "Ba sai kin ɓoye shi ba yanzu zan zama ƙarfinki, kuma na yaki baƙin cikinki, idan dare ya yi miki sanyi kuma duniya ta zama maras tausayi a gareki, ki bar ni in zama lafiya da kike nema" Yayi shiru na dan lokaci. "Zan ɗaga darajarki, zan share hawayenki zan tsaya tare da ke cikin kowane hali, farinciki bakinciki ko kuma duka, idan kina buƙatar hannun da zai rika ki ya tsamo ki daga rijiyar da kika fada, zan miƙa nawa, idan kina buƙatar yin ihu, ki yi zan ji kukanki na saurareki Emily" Yayi shiru yana kallom hawayenta, hawaye take sosai har wani kololon kuka ke mata yawo a zuciya. "Duk abin da zan ɗauka don ki samu nutsuwa dauka, zan tsaya tare da ke, hakan zai samu idan kin zauna a kusa, ki bar ni in kiyaye ki lafiyarki cikin guguwar rayuwa, zan zama mafakarki zan ɗauki zuciyarki idan bazaki iya da ita ba, tare zamuyi ƙarfi, za mu fuskanci duhu, ke ce duniyata a yanzu, wata da tauraruwa da ke jagoranta ta" Ta bude ido ta kalleshi, kalamansa na ratsata da tsuma zuciyarta, ashe dai ita ma tana da muhimmamci, a yau Aliyu ya karanta mata abun da ta dade tana musunsa a zuciyarta. "Kowane hawaye da kika zubar, kowa rauni da kika bayyana zan kasance a tare da ke, abun da ke tsakaninmu a yanzu ya wuce tausayi kawai, wata katangar karfe ce da bata rusuwa, wani kololon nauyi ne wanda ni da ke muke dauka da baya zai taba yiyuwa mu aje ba, every time you fall I'm breaking too, amman ina kokarin na ga na tashi saboda ke, so I'm here to take you home karki ce min A A" [8/1, 1:58 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣0️⃣ Dr A-B ya bi bayan Momy ya shiga bedroom dinta, ya zauna cikin rashin natsuwa da kuma bacin rai. "Ya aka yi suka san nan? Kuma suka san Emily tana nan?" Momy ta dube shi. "Samu sakon neman yarinyar nan ta email, waya daga wannan yaron Aliyu, kullum da kalar magiyar da yake min da rokon na ba shi dama ya zo yayi magana da ita, ya fada min Madam Barakat ce mahaifiyarta, ita kanta ta same ni da maganar kuma na fahimce ta na karanci damuwa a tare da ita sosai saboda ni ma uwa ce, and kai kanka mafita kake nemawa yarinyar ai kuma yanzu yan'uwanta sun bayyana me zai saka mu cigaba da boyeta?" "You just don't like her Momy haka ne?" "Me zai saka na tsane ta? Me ta min? Labarinta abun tausayi kamar rayuwarta, amman ba mu da wata hujja na cigaba da rike ta, kasan mahaifiyarta tana da damar ta saka kara ma akan boye mata yarinya? Balle kuma Madam Barakat ta yi min komai? Ba zai yiyu na gagara cireta daga matsala ba" Dr A-B ya mike tsaye ya taka ya juyo. "Amman baki shawarce ni ba, ni na kawo ta gidan nan akalla ta kamata ace ina da labarin abubuwan da suke tafiya akanta" "Ba lallai ita ko kai ku aminta ba, shiyasa ban fada maka ba, kuma ai ba tafiya suka ce za su yi da ita ba, magana kawai za su yi, ni kaina na dauki tsawon lokaci kamin na amince da yaron ma, daga baya Mahaifin yaron ya tuntubi mjjina akan yarinya and i can't said NO" Ya sauke ajiyar zuciya mahaifiyarsa ce ba zai iya daga mata murya ba, sai dai sam abun da ta yi masa be masa dadu ba ko kadan. Ya fito daga dakin yana kokarin boye bacin ransa ya kalli Madam Barakat da bakuwarsa ba. "Barka da zuwa Madam ya hanya?" "Alhamdulillah" Ta amsa tana kallonsa kamin ta kalli Aliyu dake kofar shigowa falon tana takowa a nutse. Dr A-B ya kalleshi shi ma ya kalli Dr A-B kamar ba za su yi magana da juna ba, sai kuma Aliyu ya mika masa hannu. Dr A-B ma ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya nunawa Aliyu kujera shi ma ya zauna. "Yaya Emily take a yanzu?" Aliyu ya tambaya, Dr A-B ya fada masu yanayinta da kuma abunuwan da yake kokarin ganin ya cin ma a game da lafiyarta. "Maa Shaa Allah haka ake so, ka yi kokari mun gode sosai" Mama Barakat ta fada. Dr A-B be ce komai ba ya kalli agogon hannunsa. "Momy tace kun zo nan ku ganta ne, bari na yi magana da ita sai ku shiga ku ganta" "Already na yi magana da ita, kuma mun zo nan ba dan magana da ita kawai ba, maganar gaskiya mun zo nan ne saboda mu tafi da ita gida" Aliyu ya amsa masa, Dr A-B ya kalli Aliyu. "Bana tunanin tana bukatar tafiya wani guri yanzu, domin abun da Emily take bukata a yanzu shi ne kulawa da kwanciyar hankali" "Zamu bata fiye da abun da kake tunani Dr already mun yi booking flight in the next 40 to 1h zamu juya In Shaa Allahu" Dr A-B yayi kokarin mikewa tsaye sai ga Momy ta fito dakin ta dawo falon tana zaunawa Emily ma ta shigo falon tana tafiya a hankali. EMILY POV Mikewa yayi tsaye. "Jirgin da za mu bi zai tashi nan da awa daya, ban sani ba ko rayuwa zata ba ni aron lokaci na dawo gareki, wata kila kuma sa'a ce zata rabe ni ta saki ki bi ni, duk wannan ba ni da ilimi akai, sai abun da zuciyarki ta gamsu da shi" Ya juya ya fice daga dakin. Emily ta bishi da kallo har ya fita yaja mata kofar, sai ta lumshe ido murmushi kadan ya bayyana a fuskarta dake dauke da hawaye. Nemanta kawai da ya bata lokaci yayi abun farinciki ne a gurinta, gashi kuma a yanzu ya daureta da kalaman da wani be taba mata ba, ko da karya Aliyu yayi mata a yau ta jidadi domin ya nuna mata tana da muhimmanci, da ace zata iya da ta zauna Aliyu yayi ta zuwa yana dawowa ba dan komai ba sai dan waken da daya rare mata mai dadi a yau ya karanta mata shi a kullum ya zo neman Alfarma. Ta mike tsaye ta share hawayenta ta nufi kofar dakin ta bude ta fita tana tana takawa a hankali kamar mai tsoron bayyana sautin takun kafarta haka ta haura sama ta shiga falon Momy, sai kuma ta yi tsaye bata karasa kusa da kowa ba. "Emily kin yi magana da wannan" Dr A-B ya nuna mata Aliyu ta kalli Aliyu da be kalli inda take ba tun da ta shigo, ta daga kai. "Ya fada miki sun zo man ne saboda su tafi da ke?" Ta daga kai. "Za ki bisu?" Ta dubi Aliyu har lokacin be kalleta ba idonsa yana kan wayarsa. Ta daga kai "Kin tabbatar kin shirya komawa?" Ta yi shiru na lokaci kamin ta daga kai. Dr A-B ya mike tsaye daman tun dazun yake da shirin tashi ya nufi kofar fita ya raba gefen Emily ya fice ba tare da yace komai ba. Aliyu na ganin haka ya san Emily ta amincewa bukatar da ya zo da ita sai ya hade yawun farinciki ya gyara zamansa ya daga ido kadan ya kalli Emily. Emily ta ji babu dadi ficewar da Dr A-B yayi domin haka ya nuna be yi maraba da tafiyar tata ba. Ta juya ta bi bayansa ko da ta shiga dakinsa Already ya zauna akan kujera and to her wannan ne karo na farko data taba shigowa dakinsa. Ta karasa inda yake zaune ta risina kasa ta dafa hannun kujera. "Ka yi fushi da ni?" Ta tambaya da wata murya gwanin tausayi. "No bani da hujjar yin fushi dake akan abun da ke kika yanka da kanki, kawai dai abun da nake tsoro ya zamana cilasta miki yayi ko kuma yayi miki barazana" "Ba ko daya, kawai ya yi rubutu a kwakwalwata ne, ya karanta min da halshen da da zan fahimta" "Kuma bana fatar ki koma ki sake fuskantar wata matsala" "Ni ma bana fatan haka" "Ko ma dai miya faru ki sani you're always welcome here" Ya mike tsaye ya nufi gurin da yake aje kayansa ya dauko card din ya nufota ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye ya danka mata. "In case of.., kuma ba lallai sai kina cikin matsala ba ya kamata ace ko da yaushe ina jin duriyarki domin sanin halin da kike ciki" "Na gode na jidadin haduwa da kai, ka taimaka min gashi ba ni da wani abu da zan biyaka" "Zaki biya idan lokacin biya yayi" Ta yi murmushi tana hawaye sai ya rumgumeta yana jin babu dadi domin zaman da ta yi a gidan ya saba da ita. "Idan kin tafi karki fasa shan maganinki, kuma ki guje duk wani abu da zai saka miki bacin rai ko damuwa" Ta amsa masa da kai tana kallon katon hoton dake tsaye gefen mirror sa kamar na cikin hoton zai yi magana. Ta dago daga jikinsa tana cigaba da kallon hoton. "Mahaifina ne" Ya amsa mata tun gabanin ta yi masa tambayar. Sai ta juyo ta kalleshi da mamaki ta sake kallon hoton amman bata ce komai ba. "Kina mamaki ne? Ni ma haka nake mamakin jin cewar Madam Barakat ita ce mahaifiyarki" Ta share hawayenta ta yi "Shiyasa nake son tafiya, akwai tambayoyin da ita kadai zata iya amsa min su. "Fatan alheri" Yayi fada da murmushi sai ta saki hannunsa tana jin kewarsa tun kamin ma ta bar gidan. Ta fito dakin sai ta sake dawowa falon Momy ta samu mai aikin gidan ta hado mata kayanta a akwaiti har hudu domin Dr A-B ya wadata da tufafi a gidan daidai gwargwado. A sanyaye ta karasa kusa da Momy ta risina kasa "Na gode da karbata da ka yi, na gode da masauki da hidima da kika yi da ni, na gode Sosai" "You're Welcome, kina jin kina son tafiya Emily?" Ta daga kai. "Okay, ga kayanki an hado, ki shiga ki duba idan baki manta komai ba" Emily ta girgiza kai domin bata son komawa dakin, ji take kamar ta yi kuka ita ma ta saba da su musamman ma DR AB dake shiga mata gaba a komai na gidan. Duk abun da ake Emily bata kalli gefen da Mama Barakat take ba ita ma kuma bata yi saka bakinta ba sai bin Emilyn take da kallo cikin yanayi marar dadi. Mai aikince ta saukar da kayan kasa aka saka a motar da suka zo da ita Aliyu yayi ma Momy godiya sannan ya mike tsaye yana kallon Emily. "Zamu iya tafiya?" Ta kalleshi sannan ta fara takawa ta wuce ya bi bayanta, da suka zo gurin sauka stairs sai ya cira kafa ya rigata sauka just to watching her steps kar ta fadi domin benen mai hawa biyu ne ba daya ba gashi hawaye take ba lallai tana gani da kyau ba. Da suka sauka kasa gaba daya sai ya bude mata kofar falon ta fita Mama Barakat ma ta fita sannan ya fita, sai da Emily ta sauka entrance din sannan ta juyo ta kalli kofar falo, bata sani ba ko zata dawo ko kuma tafiya ce ta har abada, domin kaddara tana hadata da mutane kala kala kuma ta rayu a gida mabanbanta, sai dai a wannan gidan ta hadu da mutane masu karamci da girmamawa. Aliyu ya bude mata back Seat yana tsaye yana kallonta sai ga kira ya shigo wayarsa ya dayan wayarsa, yana ganin haka ya san Fatima ce domin har yanzu wayarsa dayar tana hannun Fatima, kusan kullum sai ta kira shi tace ya bata Momy zata yi magana da ita ko ta ce ya fadawa Momy ta zo, wani lokacin zai ce Momy ta yi bachi, ko kuma yace ta yi tafiya, ta ce ya turo number ya tura mata idan ta kira ta ji kashe. Shi kanshi fargabar kiranta yake domin kuka take masa sosai idan yace Momy bata nan, wani lokacin ta kan ce shi ya zo amman ba zai tafi ba, idan ta bukaci akaita gurinsa Turhan ba zai yarda ba. "Hello" "Bana fadi miki idan kin kira ki rika sallama ba?" Sai ta yi sallamar cikin kuka. "Waya taba ki?" "Momy ce, har yanzu bata zo ba? I miss her i want to see her" "Bari na kira ki FaceTime" Ya yanke wayar ya kirata FaceTime yana kallon fuskarta hawaye shabe shabe sai yayi murmushi ya rage volume din ya juya camera from font to back ya nuna mata Emily dake tsaye tana kallon gidan bata san wainar da ake toyawa ba. Wani irin tsalle Fatima ta yi ta fashe da kuka. "Hi Momy Hi Hi Hi Hi Momy Momy Momy I'm sorry" Aliyu ya juyo da front camera yana murmushi ya kara volume din. "Muna Abuja yanzu tare da Momynki, za mu dawo idan muka dawo zata zo ta ganki" "Okay..." Ta daga mishi kai tana dariya sosai tana daga mishi hannu alamar bye bye, sai duk ta ba shi tausayi, shi ma ya daga mata hannu ta kashe wayar ya kira sunan Emily. "Emily" Ta juyo sai ta kalli motar daya bude ta fara takawa ta nufi motar ta shiga tana ta kallon kofa wai ko Dr A-B zai fito ko Momy sai dai rashin jindadin tafiyarta ya hana Dr A-B fitowa because he don't want to say good bye to her, Momy kuma tana jin kanta ba kasafai take saukowa kasa ba, ba kuma dan wulakanci ba domin bata da wulakanci ko kadan sai dan isa ta naira. Ta shiga ta zauna Aliyu ya rufe motar Mama Barakat ta bude dayan gefen ta shiga ta zauna Aliyu ya shiga front seat sai da suka fice daga gidan sannan Aliyu ya tambaya ko dai su tsaya su kwana Abuja domin to him Abuja gida ce no need to rush, Ummi ma a nan take zauna ba dan abun da ya faru ba da yanzu bata je Kaduna ba. "Aa mu tafi kawai" Mama Barakat ta fada, a nan Emily ta kalleta. "Da gaske ke kika haife ni?" Mama Barakat ta kalleta jiki a sanyeye. "Ni ce?" "Taya? Meyasa kika jefar da ni? Me na yi?" "Baki yi komai ba, na haife kyakkyawa cikin koshin lafiya, na aje ki a inda na bar ki ne saboda na haife ki ba da aure ba, kuma baki yi kala da ni ba, ina jin tsoron irin kallon da duniya zata min a wacan lokaci ne" "Amman kin san ina gurin kuma a gurin na rayu? Kin taba tunanin nemana? Ko sanin halin da nake ciki?" Mama Barakat ta girgiza kai. "Ban taba ba, saboda ina tunanin kamar abun da na aikata shi ne mafita a gareki da ni, ban taba sha'awar na san wane kike ciki ko rayuwa kike yi ba, tun da na aje ki na rufe shafinki, ban sake ganinki ba sai wacan ranar da kika labarta min labarinki, dana kalleki kuma sai na ga siffarki da yanayinki be sauya ba daga na mahaifinki, kuma sai kika gudu saboda neman mafita, sai n aji tsoron nemanki saboda yarana da aurena da kuma ke taya zan fuskance ki?" Emily ta yi juyar da kanta ta jinginar jikin mota tana hawaye, hawayen da ba su tsaya mata ba har suka shiga jirgi. A guri daya suka zauna da Mama Barakat a first class, Aliyu kuma ya zauna wani guri dabam ba kusa da su ba. TURHAN POV "Momy zata dawo na ganta" Turhan yayi mata murmushin zahiri badini kuma wata wuce ta ce take cin ransa. "Wow zata dawo I'm happy, to yanzu sai kije ki ci abinci kar Momy ta ga kin rame ko?" Ammy ta fada, Fatima ta daga kai har ta fara tafiya sai kuma ta juyo. "Idan ta dawo zata zauna a nan? Zamu zauna tare? Bana son wani ya sake tafiya kuma" Ammy ta daga mata kai, sai ta dawo da gudu ta rumgume Turhan. "Ina son haka" Ta fada da hausa domin zamanta gidan ta fara tsintar wasu kalamai na hausa, Ammy ta kan gwada mata magana da hausa ta koya mata wasu abubuwa, idan kuma ta ji ana hira aka fadi wani abu sai ta tambaya me aka ce ko me ake nufi har rubutawa take idan yan kwaran suna bisa kai, idan kuma rigimar neman Momy ya tashi bata kula kowa. Sai da ta fita dakin sannan Ammy ta kalli Turhan ta ce. "Abuja Ummi take zaune, amman a yanzu ance tana gidanta na Kaduna yanzu kuma Aliyu yace suna Abuja za su dawo Kaduna yau, jikina sai yake ba ni kamar aje yarinyar nan suka yi a can na tsawon lokacin nan" "Ni ma jikina ya ba ni haka, wata kila kuma daman ya san inda take ko da shi ya boye ta ba, ko kuma ya nemota ne, tun da ya fi ni sanin mutane a Kasar nan, yanzu kuma ita sai ta yu tunanin ko ban yi kokarin nemanta ba ne, Aliyu be kyauta min ba, na rasa gane me na yi masa, babu yadda za'ayi ta fahimce ni" Ya dafe kanta kansa idonsa na cika da kwalla damuwa ta matsa tsaye a rai. "Ban san dalilin Aliyu na yi min haka ba, amman ni ba zan iya yi ma Aliyu abun da yayi min ba, abota bata ce haka ba, aminci be cancani wannan sakamako ba" Ammy ta tashi ta dawo kusa da shi ta zauna ta dafa kafadarsa. "Haka butulci yake da ciwo, amman ka yi hakuri kuma ka yi addu'a idan kuma ta nuna bata son kasancewa da kai, dan Allah ka saka musu ido, mutum be taba cin amana ya ga daidai ba a rayuwarsa" "Ko ba zata dawo gareni ba, na aminta amman kar ta auri Aliyu, gayen nan ya gama da rayuwata, kuma idan ya sameta hakan ya nuna ya ci ribar abun da ya aikata kenan" "Idan bera da sata daddawa ma tana da wari ai, idan da can kamin ka bayyana a rayuwarta tana kula Aliyu a yanzu be kamata Aisha ta yi haka ba ko dan yarinyar nan, matukar tana da hankali da tunani yadda dai ka dawo mata ka nuna mata kauna be kamata ka saurari kowa ba sai kai, ita uwa koda yaushe tana son abun da danta yake so ne ko dan farincikinsa" "Ammy Aisha bata da laifi, Aliyun nan dai shi ne shege, ita ai daman fansa take son dauka shi ne be dace yayi min haka ba, Ammy ko dai naje na taro ta?" "Ai baka san yaushe zata sauka ba, kuma karamin aikin yarinyar nan ne ta disgaka a gaban mutane, kuma kasan har Aliyu yana gurin sai ya ji dadi ai" Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. "Turhan idan Aisha ta zabi Aliyu ko wani ba kai ba, ka yi hakuri dan Allah ka bi a hankali, kai fa namiji ne kuma kai ka fara wulakanta ta, na san ka yi nadama amman ka kara da hakuri idan ka yi hakuri ita kanta zata dawo maka, ko kuma ja ga Allah ya musanya maka da wanda ta fita alheri, ko kuma Allah ya baka zuri'a da matar da kake aure yanzu, tun da ba cewa aka yi ba zaka haihu ko kuma ita ba zata haihu ba" Ya mike tsaye cikin rashin jindadin maganar. Ammy ta bishi da kallon tausayi har ya fice, saukowa yayi kasa ya nufi dan karamin dinning din daya siyawa yarsa take zama ta ci abinci ya durkusa a gurin ya dauki spoon din da take cin abinci ya cigaba da bata abincin tana ci data gama ya bata ruwa ta sha sannan ya rumgumeta. "Fatima ina sonki, kuma ina son mahaifiyarki Allah shi ne shaidata, yanzu ku ne farincikina" Ta yi murmushi domin ta san ina sonki da hausa Ammy ta koya mata. "Daddy ina sonki" Ta yi kwance jikinsa tana jindadi ga babanta kusa kuma ga mamanta zata dawo. [8/1, 6:32 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣1️⃣ Suna sauka Airport Aliyu ya kira wayar direba ya sanar masa. Kamin ya iso Aliyu ya nuna Emily gurin zama. "Zauna a can yanzu zai zo ya dauke mu" Ta kalli gurin ta fara takawa ta isa ta zauna, sai ya shiga ciki ya siyo mata ruwa ya kawo mata da dan abun tabawa ba, ruwan kawai ta karba ta rike bata kallon sai Mama Barakat data kasa hada ido da Emily. "Daure ki sha ruwa kuma ki share hawayenki" Ta fara share hawayen sai ya karɓi ruwan ya bude mata ya mika mata ta karba ta sha kadan, ta mika masa. "Thank you" Ya fada da murmushi sai ta dube shi, wai shi yake mata godiya saboda ta karbi ruwa ta sha kuma ta share hawayenta. "Ina kike son tafiya? Gurin Ummi ko gurin Mama Barakat? Tana son ki zauna kusa da ita" "Ban taba samun abun da nake so ba, duk abun da kuka zaba min yayi" "Inda ina raye abun da kike so shi zaki samu Emily, dan haka zaki bi mu zuwa gurin Ummi hakan yayi?" Ta daga mishi kai tana ta kallonshi kamar yau ta fara ganinsa. Ya kai goran ruwan dake hannunsa bakinsa ya sha har lokacin kallonsa Emily take bata ko motsa ido, daya sha ya sauke gorar sai ya sska yatsansa cikin ruwan ya cire ya tsarka mata dogon ruwan a fuska yana murmushi, daman shi yana daga tsaye ne tana zaune, sai ta lumshe ido tana murmushi. Hakan ya ba shi damar kallon fuskarta ya koreta ta kallo har ya gano ramar da ta yi ta kara mata kyau ne madadin ragewa. Tana bude idon sai yayi hanzarin dauke kansa ya kawar da fuskarsa, a nan ita ma ta samu damar maida biki wato ta dasa masa nata idon tana kallonsa, sai dai ita ba kyaunsa kawai take kallo ba, duk kuwa da kasancewar yana da siffa mai kyau da kwarjini, sai dai ita a gurinta yanzu kyau bashi da value domin kyaun ta bi Khaleefa ya cutar da ita, haka kuma Turhan ma yana da kyau amman kyaun dan maciji, ita a gurin hali shi ne komai kuma zata iya fahimta a yanzu Aliyu yana da banbanci da sauran, sai dai bata san gaba ba. "Gashi ya zo tashi mu tafi" Ta mike tsaye tana kallonsa kamar babu wani abun kallo a gurin sai shi. Suka jera a tare suna tafiya har suka isa gurin motar ya bude mata baya ta shiga, Direban kuma ya dauki kayan ya saka a bayan mota Mama Barakat ma ta shiga baya Aliyu ya shiga gaba direban yaja motar suka fara tafiya. A harabar gidan direban ya faka Aliyu ya fara fita ta gefen daya fita Mama Barakat take sai ya bude mata kofa sannan ya zagayaya budewa Emily dake zaune tana jiran ya zo ya bude mata, ta kalleshi sannan ta fito ta ya rufe suka jera shi da ita suka shiga cikin falon da Ummi take tsaye tana jiran isowarta. "Maraba Maraba da yata, yar dake guduwa ta bar yarta" Ummi ta rumgume Emily cike da farinciki, sannan ta kama hannunta suka zauna Aliyu ma ya zauna haka Mama Barakat. Direban ya shigo da manyan akwatunan Emily sai Ummi ta kalli mai aikinta ta ce. "Kulu a dauki kayan nan a shigar da su dakina, daga yau dakina Emily zata zauna" "Dakinki kuma Ummi" Aliyu ya tambaya da mamaki. Ummi ta ce "Eh dakin uwa ai na yarta ne, ba zan sake yin wannan saken da na yi ba kika gudu kika barmu, kika daga mana hankali na fi son kina kusa da ni ina jin motsinki, idan muka tashi komawa Abuja ma dake zan tattara mu tafi, idan ma kin zabi sake buguwa ki fada sai na hada kayana mu tafi kin ga neman zai fi dadi" Aliyu yayi murmushi Emily ma ta yi murmushi tana kallon Ummi. "Ba zan sake guduwa ba" "Zamu gani dai, amman ni dai ba zan sake bari ki gudu ba" Ummi ta tabe baki tana yi ma Aliyu kallon zolaya. Emily ta kalli Aliyu suka sakar ma junansu murmushi mai laushi da sanyaya zuciya sannan ta sauke kanta kasa, Aliyu kuma suna hada ido da Ummi ya ga irin kallon da take masa sai ya girgiza mata kai alamar ba abun da take tunani ba ne domin ya san hasashenta, ya mike tsaye yana murmushi mai sauti. "Bari naje na yi sallah" Ya fice daga falon, Ummi ta kalli Mama Barakat. "Ki shigo dakin kasa sai ki yi sallah ko" "Dare yayi Hajiya zan tafi gida dai, gobe sai na dawo" "Toh ba matsala direba yana waje sai ya sauke ki gida" Mama Barakat ta mike tsaye. "Mu kwana lafiya Hajiya na gode" Bayan Ummi ta amsa mata ta juya ta fara tafiya kamar daga sama ta ji muryar Emily. "Sai da safe" Ta juyo jiki a sanyaye ta kalli Emily. "Na yi tunanin ba zaki amsa ni ba ne, shiyasa ban miki sallama ba, ki gafarce ni" "Zuciyata ta saba da karbar ko wane kalar sako na bakinciki, kaddara ta sunnanta min haka, shiyasa na fahimci rayuwar da nake ciki, ni ce nake son mutane ba wai mutane ne suke so na ba, kuma na yarda zan cigaba da rayuwa a haka" Mama Barakat ta fashe da kuka. "Wallahi ba haka ba ne, karki yi zaton bana kaunarki, ina sonki fiye da tunaninki" Ummi ta kwantar da Emily dake kuka a fadarta sai ta yi ma Mama Barakat alama ta tafi da hannu. Mama Barakat ta fice tana kuka. "Toh miye amfanin kuka? Abun da ya wuce ai ya wuce, ni uwa ce a gareki Emily, kuma ki daina wannan tunanin na cewa babu mai sonki, da kin san tashin hankalin da muka shiga ni da Aliyu da mai gidana na rashinki sai kin tausaya mana" Ummi ta dagata daga kan kafadarta. "Muje ciki ki yi wanka ki ci abinci ki huta na baki labarin yadda aka yi muka gano ki, ko Aliyu ya fada miki?" Ta girgiza yau. "Yauwa aikuwa ni zan baki wannan labarin, daman duk ya bi ya ishe ni komai ya tattare baya barin ma wani ya shiga balle ya kyautata miki, shiyasa ma ya fara ba ni haushi sai ka ce shi kadai yake da ke" Cikin yanayin rarrashi da son faranta rai Ummi take maganar da Emily kamar mai magana da yar yarinya karama sa'ar Fatima. Ummi ta rika ta ta kwantaa fadarta ta rike hannayenta suka fara haurawa sama. "Kudi ya zuba can gurin Office din kamfanin sadarwa, bayan mahaifinsa ya saka baki aka duba wayoyin da kika kira, aka ga layina da na Aliyu da kuma na wannan likitan, aka ce wunin ranar da su kawai kika yi waya, Aliyu na jin haka ya ce duk yadda aka yi kina gurin Dr, ya fara bibiyar layin, amman da yake likitan nan baya son mu da alheri da Aliyu ya tura masa sako be ba shi amsa ba, muka rika sama da kasa sai da muka hada da Hajiya Baraka ta sama mana Information din mahaifiyarsa Aliyu ya dage, amman ni nake taya shi da addu'a fa dan kar ki yi zaton kamar ban yi komai ba, ke daga karshe sai da mahaifinsa ya shiga kuma ita ma Hajiya Barakat ta yi magana da roko da komai aka samu ta amsa mana tace su zo wannan satin Aliyu ya saka date suka tafi, kamar a mafarki sai na ga sun dawo min da ke, na ma yi zaton za ku tsaya ku kwana Abuja, ashe ya damu da halin da nake ciki sai ga shi be tsaya kwana ba ya dawo" Emily tana kwance kafadar Ummi tana bata labarin har suka shiga dakin. "Kin ji yadda aka yi, amman fa mum shiga tashin hankali sosai, ba dan ni ba dan Allah Emily karki sake guduwa ko minene kamata yayi ace kin tsaya kin fuskance shi ba wai ki gudu ba" "Na rasa ya zan yi ne, abubuwan suka hade min ko'ina ba dadi" "Har da gidana? Ko kadan ni fa ban bi bayan Hajiya Barakat ba dama ta ba ni labarin abubuwan da suka faru ke na fi tausayawa, to kin ga ni miye nawa da zaki dora min laifi?" Emily ta dago da sauri. "Ban dora miki laifi ba, ko kadan baki min komai ba" "To miye na duguwa ki bar gidan? Na yi tunanin ko ba zaki iya zama ko'ina ba zaki zauna a gurina, har tambayar kaina nake wai ko dai na miki ba daidai ba?" "Baki min komai ba, kuma ba zan sake guduwa ba" "Alhamdulillah Allah yasa haka" Ummi ta rumgume har ga Allah Ummi tana jin tausayin Emily sosai. Bayan Emily ta yi wanka ta canja tufafi sai ta dauki abaya ta dora saman kananan kayan da suke jikinta domin suturta jikinta, na ci abinci ta kwanta kan gado, babu jimawa Nafeesa ta shigo kiranta wai Ummi ta ce ta sauko kasa idan ba bachi take ba. Babu musu ta fito a dakin na Ummi ta sauko kasa tana jin kamar ta samu gata a yanzu ko da yake bata san me gobe zata haifar ba, amman dukanin wani kulawa da uwa zata nunawa yarta Ummi ta nuna mata a yanzu. Ta sauko a hankali ta karaso ganin kowa yana zaune kasa sai ta zauna ita ma, kusa da Aliyu sosai a gurinta ita ba komai ba ne dan jikinta ya taba na wani wanda ba Muharraminta ba, a addinin data samu kanta ciki hakan ba laifi ba ne, kuma ta saba. A kokarin Aliyu na bin umarni Allah sai ya matsa kadan dan kar jikinsa na taba nata, domin ya san ita din ba halalinsa ba ce. "Muna ta fira muna shan tsamiyar dila baki kusa na ce a kira ki sauka mana cikin dangi, amman na fada mata idan bachi kike ta barki ki huta" "Ba bachi nake ba" "To ga abun da muke ci idan zaki iya ci, saka hannunki ki dauka sai an balle ake ci" Ummi ta fada, kamin ta saka hannunta sai Aliyu ya dauki karamin plate ya aje gabata ya zuba mata wanda ya banbanra. "Sha ki ji ko zaki iya ci" Ta dauka ta kai baki sai ta ji abun wani iri domin bata taba ci amman dan tsami tsamin da ta ji ya karbi bakinta dan haka ta cigaba da sha. Kwankwasa kofar falon aka yi kadan kadan kamar bugun yaro, Emily ta kalli kofar da sauri zuciyarta na bugawa da gudu kuma tana raya mata Fatima ce. Aliyu ya mike tsaye ya nufi kofar ya rufe sai ga Fatima ta shigo da gudu. "Uncle..." Har ta rike shi zata rumgume shi sai kuma ta sake shi ta nufo gurin Emily da gudu, Emily ma kasa rike kanta ta yi sai ta zabura da sauri ta rumgume yarta ta fashe da kuka, zata iya yafe komai da kowa amman ban da yarta, ko kadan bata son Fatima ta dandana rashinta domin ta san yadda ta rayu saboda uwarta bata kusa da ita, cikin kuka Fatima ta ce. "Momy ina kika je? Kin dade baki zo ba" "Saboda kin ce baki so na" Sai ta kara rumgume Emily. "Ina sonki ke da daddy ina sonki,. Karki sake tafiya ki bar ni bana son ki tafi" Emily ta rumgume. "Idan baki son na tafi ki daina zabar Mahaifinki kina barina, ko gobe kika ce shi kike so to zan tafi na kyale ki" Sai Fatima ta kara fashewa da kuka. "Amman ina son shi Momy, yana so na" "Who do you love the most? Ni ko Dady?" "You" "Good" Emily ta rumgume ta sosai a kirjinta kamar zata maida ita ciki. Fatima na shiga cikin falon Aliyu ya kalli Turhan dake tsaye bakin balcony din be tako ba, sai ma dukawa da yayi yaje masa wayarsa a kasa. Ya saka hannayensa duka biyu aljihu. Aliyu na ganin hakan ya fita ya karasa gurin da wayar take ya duka zai dauka. "Ka ji kunya Aliyu, ka ci amanata" "Ban ji kunya ba, kuma ban ci amanarka ba, akwai tsarin da na yi sai dai Allah be ba ni ikon cika wannan burin ba har Kameela ta yi abun da ta yi" "Ai baka da bakin kare kanka" "Ba kokarin kare kai nake ba, kuma ba so nake ka fahimta ba, ina fada maka abun da yake gaskiyarsa ne" "Har abada... Ba zan taba barin yata ta kira wani katon banza da sunan Baba ba, yata ba zata yi agolanci ba yana da kyau ka san wannan" "Kai yanzu baka ji kunyar fadar hakan ba? Kai yanzu abun da ya dame ka wa Emily zata aura? Ko wa take so? Baka damu ka san lafiyarta ko samun farincikinta ba? Kana da son kanka Turhan... Kuma har gobe ban yi nadamar taimakin Emily ko kuma boye mata kai ba, saboda ta fada kai ne wanda bata son ganin kuma zaka karbe mata yarta ga shi ka aikata, kai yanzu iyakar burinka Emily ta dawo gareka, idan ta dawo zata dawo ta yi farinciki ko aa ba shi ne a gabanka ba, kaico da zuciyar dake take kirjinka" "Kai kuma Tirrrr da aboki irinki mai fuska biyu, zan baka mamaki Aliyu, kuma ina gargadinka da shiga tsabgar matata da yata, baka da alaka da dukkansu" Aliyu yayi murmushi kawai ya juya ya shiga ciki, Turhan ya tofar da yawu yana jin zuciyarsa tana kuna. Aliyu na shiga falon Fatima ta juya ta kalleshi. "Ka ce Dady ya tafi sai gobe zan koma tare da Momy" "Already ya tafi ai, ni ba zaki min oyoyo ba?" Ya ware hannayensa, sai ta taso tana dariya ta nufe shi da gudu ta rumgume shi ya daga ta sama ya jefa ya chabe yana dariya ita ma sai datiya take tana farinciki domin ta yi marmarinsa da Momynta. Emily tana ta kallonsu tana murmushi. " Kin yi missing din Momy?" "Sosai" Ta fada tana kallon Emily, sai Aliyu ya dauke ta haura sama da ita suna tafe yana mata hira. A ranar Emily ta yi bachin farinciki irin wanda ta kwana biyu bata yi irinsa ba, ta kwanata rumgume da yarta a dayan dakin da Ummi ta bata saboda ta ki yarda ta hau gadon Ummi ta kwanta sai dai kasa, Ummi kuma ba zata iya jurar kallon ta kwana a kasa ba, dan haka ta bata wani dakin ita da yarta. Kamin Fatima ta yi bachi sai da ta yi ta bata labarin abubuwan da Ammy take mata da kuma Dadyta. Washe gari Emily na cikin bachi ta ji an taba ta sai ta bude ido, ta yi zaton Fatima na dakin sai ta yi arba da Mama Barakat ga kayan abinci an jere a gurin kamar dai wacan karon. "Ki yi hakuri na tashe ki kina bachi" Emily ta murza ido ta tashi zaune tana duba gadon har tana kokarin sauka sai ga Aliyu ya kwankwasa kofar dakin, sannan ya turo ya shigo yana dauke da Fatima. "Mama Ummi tace min kin shigo yanzu" Ya fada yana kallon Mama Barakat. "Eh ku yi hakuri na yi muku sammako, bana son Emily ta karya da komai ne sai abun da na dafa" "Wacece wannan?" Fatima ta tambaya tana nuna Mama Barakat. "Kakarki ce, ita ce ta haifi Emily" Fatima ta wara ido kamar wata babba tana mamaki. "Muna da kowa a nan ina farinciki da zama a nan ba za mu koma can ba ko Momy? Ashe ke ma kina da Momy" Emily ta daga mata kai. Aliyu yayi murmushi. "Karki yi zaton ko na shigo na same ki a yanayi marar kyau ne, ita ce ta farka da kanta ta fito tana bin daki har ta same ni, wai ta yi zaton ko na tafi ne" "Momy mun yi sallah mun yi sallah da shi kina bachi" Emily ta yi murmushi tana kallonsu. "Aci dadi lafiya ni zan sauka, Emily idan kin gama da wannan sai ki sauko na mu breakfast din yana jiranki, Ummi ma sai fada take wai Mama Baraka ta dako sakko baki farka ba kuma ta san zata shirya miki abun karyawa" Mama Barakat ta yi murmushi. "Ka bata hakuri, na tashi tun karfe uku na fara shirya komai saboda kar na makara, zan yi farinciki idan ta ci" "Zata ci, ai Emily bata da matsala ko kadan kamar ruwa haka take, kifi ce musulmi nama" Ta fada sannan ya juya ya fita yana dauke da Fatima dake tambayarsa miyasa Emily bata kama da Mama Barakat? Bayan ita tana kama da Turhan. Emily ta shiga bandaki ta wanke bakinta da sabon brush da ta gani ta yi fitsari ta fito ta zauna bakin gado, sai Mama Barakat ta sauka kasa ta bude abincin gaba daya tana tambayar wane zata ci. "Ina son na kira ki da Aisha ban san ko kina son haka ba, Ummi ta fada min ana kira Aisha amman Emily ya fi karfi, amman sunan da na saka miki Aisha ne ba Emily ba, musulma na haife ki ba kirista ba" Emily ta dube ta. "Kina so na haka kika bar ni? Har yanzu na gagara gane wane laifi na aikata miki, na wahala an wulakanta saboda ba ni da kowa, anyi min gori, abubuwa na suka banbanta da na sauran masu iyaye, ban san gata ba ban iya komai sai guduwa daga wannan gurin zuwa wani, fada da kika yi cewar da saninki kika jefar da ni kuma baki taba tunanin ki waiwaye ni ba ya tsaya min a rai, mu ma yaya muna da hakki akan iyaye, baki yi adalci tsakanina da sauran yayanki ba, su kika zabi haifarsu da aure kuma kika zauna tare da su, ni kuma kika watsar da ni, baki yi tunanin waca kalar rayuwa zan yi ba, wane kalubale zan fuskanta ba, kin yi komai saboda gujewa kunyar duniya, shin ba na ji ku musulmai kuna cewa lahira akwai hisabi ba? Saboda kin haife ni ba da aure ba ni miye laifina? Ba shawara aka yi da ni kamin a haife ni ba, ya kamata ki yi tunanin idan kika jefar da ni wace kalar rayuwa zan yi? Zan rayu ko kuma zan mutu ne? Baki tunanin ni ma ina da hakki akanki? Taya kika iya kwantawa ki yi bachi alhalin kin san kina da ya a wani gurin da baki san wane hali take ciki ba? Wace irin uwa ce ke? Taya zaka sha wahalar ciki wata tara da nakuda kuma ka jefar da yaron? Shi ma fa rai ne? Uwa tausayi aka sani da ita ke da iyayen da suke haka ba ku kyauta ba, miye laifin wanda aka haife? Wai illar kawai saboda ba shi da uba, kuma ba da aure aka haife shi ba, miyasa baki yi tunani ba kamin ki haife? Wallahi na Wahala na wahala na wahala, ni kadai na san yadda na yi na Wahala na wahala na wahala na wahala na wahala........... Ahk ahk ahk..." Ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya da ƙoƙon rai. Mama Baraka ta bar inda take ta dawo kusa da Emily ta zauna ta rumgume ta tana kuka. "Ki gafarce ni, ki yafe ni na yi kuskure na sani, ki yi hakuri Emily ki yafe min..." Emily kuka Mama Baraka kuka babu mai iya rarrashin wani... ______________________ Ga iyayen da suke haifar yara ba da aure ba su jefar, shin kun san kuna daukarwa kanku hakki ne? Hakkin zina hakkin haihuwa ba da aure ba hakkin jefar da yaro, ba ku san wane hali zai fada ba wace rayuwa zai yi a wane hali zai girma ko ya samu kansa ya rayuwa zata kasance, wasu yaran ba za su taba haduwa da iyayensu ba sai Alkiyama. Allah ya tsaremu, ka tsarkake zuciyarmu.🤲 [8/4, 9:55 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣2️⃣ Na tashi a wani ƙaramin gida a Beere, cikin unguwar da ruwa ke ta faman gudu daga bututun da babu mai kulawa da shi, cikin amo da hayaniyar kasuwa, da ƙamshin ewedu da ata rodo na mahaifiyata. Baraka suke kirana ɗiya ga wani tsohon malamin addinin. A cikin al'adun Yarbawa, mata suna da 'yancin yin kasuwanci, sana'a ko aiki tun da dadewa. Wannan ya bambanta da wasu al'ummomi da ke takaita mata ga aikin gida kawai. A yawancin biranen Yarbawa, musamman kamar Legas, Ibadan, da Abeokuta, za ki ga mata masu kasuwanci ko aiki a hukumomi. Iyayen Yarbawa suna koyar da 'ya'yansu mace da wuri cewa ta rike kanta Yana daga dabi'unsu su karantar da 'ya mace ta nemi ilimi ko sana'a domin ta rike kanta, ba tare da dogaro da namiji ba. Wannan ya sa da yawa daga cikin matan su ke da ƙwarin gwiwa wajen kokarin ciyar da kansu ko tallafa wa iyalansu. Na koyi juriya daga rayuwa, ba daga littafi ba. Na girma ina kallon mahaifiyata tana dafa abinci a kan itace, tana kula da gida kusan nauyin mu da na mahaifina a wuyanta yake, mahaifina ba shi da wani karfi kuma be damu da nema ba, ta kan ce min: “Baraka, mace na da ƙafa biyu  ɗaya tana goyon gida, ɗaya tana neman arziki.” Na shiga cikin harkar girki wato siyar da abinci, tun ina 15yrs mahaifiyata kuma tana fita shago siyar da kayan masarufi, a lokacin ban fara karatu a kolege ba, na iya hada tuwo da hannu, da kwasar romon miyar ogbono cikin harba guda. Na kammala karatu a wata college Ibadan, amma bayan na gama sai na gane cewa takarda ba ta nufin abinci a kwano. Domin bayan gamawa, ba aikin da ya biyo ba. Na zama kamar mutumin da ya haɗiye ƙashi, ba zai hade wuce ba, kuma ba zai iya fitarwa ba. Na tattara kayan da ba su wuce buhu biyu ba, na tafi Lagos, wurin kanwar mamata, saboda gurin da nake siyar da abinci a da gonati ta kwace, mahaifiyata ta kuma shagonta yayi kasa, ga shi mu bakwai mahaifinmu ya haifa ba daya ko biyu ba, ni ce ta biyu idan ban tallafi mahaifiyar da ta tsaya akan ilimi da abincin na ba me zan yi? Na fara komai daga tushe. Na rika siyar da abinci a Mile 12, da jarin da mahaifiyata ta hada min, wata rana a siyar wata rana ba za a siyar ba, wani sa'in sai na roki kanwar Mamana ta ara min kudi nake samu na kulla wani jarin, gashi mijin aure ya gagareni a lokacin ko da yake ni kaina ban shirya auren ba domin ban tanadi komai na aure ba, haka mahaifiyata ma bata da wani abun aurar da ni a lokacin. Na ci gaba da girki har wani lokaci sai wani NGO  ya fitar da talla, na neman ma'aikata, cika da takarduna na karatuna, ban sani ba ashe aikin ne silar wargewar rayuwarki, bayan wani lokaci. suka sanar min sunana ya fito. Na tafi gurin horarwa suka min interview bayan na yi nasara suka sake sanar min an dauke ni, farincikin be bar ni na kwana ba a ranar. Kusan zan iya cewa addu'ace ta ba ni nasara domin babban guri ne da shugaban gurin ya kasance bature jar fata mai tsakanin fari da jan gashi ga kuma blue eyes, kyakkyawa ne mai far'a da son bakar mace kamar ba jan kunne ba, na fara aikin a gurin a matsayin sakatariya ina kula da komai zuwa kan lokaci girmama kowa bawa komai hakkinsa. Sannu a hankali aka na saba da kowa a gurin ba iya ma'aikan gurin ba har da masu zuwa su fita. Daga gaisuwa da mutunci muka fara sabo da Rowan Alaric MacLeod wato shugaban gurin, a lokacin akan masa lakani da bello, domin farar fata idan suka tsallako kasashenmu sukan nemi suna su sakawa kansu saboda ku saje da mu kuma mu saki jiki da su. Bature ne da ya zo daga Scottish, zan sake maimaita miki wannan, Me kyau ne sosai kamar ke kyaunsa ne abun da ya rude ne, na kasa dauke ido daga gareshi shi kuma ya saka min fuska ya rika ba ni damar matsawa kusa da shi, ba kuma zan miki karya ba ta dayan gefen ina hange kudi da yake da su, kamar idan na same shi a matsayin saurayi na huta, domin ba addininmu daya ba, na san abu ne mai wahala mahaifina ya amince na aureshi, ban sani ba ashe yana da mata, nina fara nuna matsa kauna sai ya sanar min yana da mata yar da yara biyu a tsakaninsu, hakan sai ya saka na yi baya, shi kuma a lokacin ne ya kamu da kauna ta sosai, sai kusancinmu ya fara yawa, har ta kai ya kan bukaci na kawo masa abu a gidansa ko kuma ya saka matarsa da kanta ta kira ni ta sanar min idan wani abun ya taso na aikin ko kuma familynsu kamar taron biki ko birthday ko kuma danta idan ba shi da lafiya ko yarta, ban sani ba ashe ya fada mata cewar nice kadai babu ruwana a cikin matan da yake aiki da su, ni ce kadai ya yarda da ni saboda sauran wasu ba su da amana wasu kuma suna nemansa. Ashe yayi hakan ne saboda matarsa ta aminta da ni da shi, ko da an kawo mata wani zance ko ganin mu wani guri ba za a zargi komai ba, da haka muka fara mu'amala yana sakar min kudi yana nuna min kauna, na sake jiki da shi kuma na zama mai fuska biyu domin matarsa da wacce ta fini komai na mata kuma ta kasance yar kabilar igbo ta aminta da ni, amince da har yau bata daina ba. Ban ankaro ba na samu ciki na tafi asibiti da taimakon likita aka zubar da cikin dan wata biyu, muka sake komawa ruwa. Ina samu kudi na aikawa gidanmu a inda nake kuma ina watayawa yadda nake so, rayuwa ta ci gaba a haka wata rana bayan gama al'ada na tafi aka ba ni maganin hana daukar ciki, aka fada min dokokin yadda zan sha kuma na bi ka'ida da haka ba ni da haufi muka cigaba da shedanci, ban sani ba ashe tun kamin na sha maganin na dauki cikin ki amman babu wata alama a tare da ni dake muna akwai ciki, idan lokacin al'adata yayi zan yi idan na gama na yi tsarki. Wata rana, na tashi daga aiki, ina isa gida ciwon mara mai tsanani ya rufe ni, na sha magani be daina ba kuma be saba min haka ba, kusan ma zan iya cewa ba watan al'adata ba ne, da abun yayi min tsanani kamar ana murza mini ciki da mashin din wuta, sai na yi mamaki "yau kuma al'adar ta zo min a tsakiyar wata da fushi ne? Amma me ya sa take murda ni kamar na yi hauka?” Na sha paracetamol. Na dinga juyawa a gado. Amma ciwon ya ƙi sakina. Na daina numfashi da kwanciyar hankali. Cikin rudani aka kaini asibiti, bayan an ba ni gado na samu kulawar likita sai, Likitan ya dube ni, ya ce cikin natsuwa: “Matar nan, ko kin san kina da ciki ne?” Na ce da shi cikin zafin rai “Dokta kar ka yi wasa da ciwo, al’ada ce kake gani, ba ciki ba ne.” Sai ya ce da ni: “Toh ina jin heartbeat ɗin yaro ma'ana bugun zuciyar jariri yana da rai a cikinki.” Na ce “Jariri kuma? Ciki?? Ai ni bana da ciki! Ba ni da wata alama ta masu ciki ma, Ina nono ya kumbura? Ina tashin zuciya? Al’ada ma tana zuwa kamar yadda ta saba!” Cikin natsuwa ya ce “Wannan ba ciki irin na mutane bane. Wannan cryptic pregnancy ne, ciki mai ɓoye kai. Na ga mata irin ki da yawa da ba su san suna da shi ba sai sun zo asibiti. Cikin na girma ne a ciki, yana ɓoyewa a waje. Kuma Jikinki da kwakwalwarki sun hana ki gane cewa kina ɗauke da rai.” Ya ɗan tsaya, ya ce: “Wasu mata sukan ci gaba da yin jinin da suke ɗauka a matsayin al’ada. Wasu ba sa jin canjin jiki saboda hormones ɗinsu ba su nunawa. Sai dai kawai wata rana a ga ciki ba tare da an shirya ba.” Be gama bayani ba ruwa ya fashe min, a nan na saki hawaye. Ina kallon likitan kamar ace zai iya yin wani abu. Ina tambayar kaina da gaske haihuwa zan yi? Bayan sa’a biyu kacal, na haifi wata yarinya da ta fi hasken idanuwa kyau, fara kyakkyawa mai matukar daukar hankali, ga jan gashi da blue eyes, kikashigo duniya cikin sirri, amma da annuri da kuka kamar kowane jinjiri. Baki rage komai daga kamanin mahaifinkin ba, kuma baki dauko komai daga gareni ba, sam ba za a taba yarda ni na haife ki, saboda gene din farar fata yana da karfi, a duk yadda aka haihuwa ko da yara ba su dauko gaba daya ba, su daukon wani kaso, masu gene mai karfi kuma basa raga komai haka kika zo min, kamar dai na rike ki, amman ina tsoron kallon da duniya zata min da kuma abun da iyayena za su ce, kanwar mamana ta siyo kayan jaririya na saka miki na lullube ki cikin zane, tun a asibitin tayi min fada bayan ni ma na yi ma kaina, ni da ita muka shirya ba za mu bar asibitin ba sai dare saboda mun shirya jefar da ke a inda muke ganin zaki samu masu rika ki. Sai karfe 8pm muka fita asibitin muka tari abun hawa zuwa inda ta bincika tun da rana ta samu, nesa da gurin muka mukaci mai taxi ya aje mu, da kafa muka taka muka isa gurin babban gida ne zagaye kuma inguwa ce da babu mutane sosai, na bude jakar da na zo da ita asibiti kuma wanda nake zuwa da ita aiki na dauko pen da farar takardar na rubuta sunanki "Aisha" domin shi ne sunan da na fi so, na saka a saman jikin ki sannan muka zagaya ta bayan gidan muka aje ki. Ni da ita muka yi ta gudu muka barki kina kuka, ni ma ina kuka. Tun daga ranar mafarkinki be bar ni ba, ban kuma sake zuwa aikin ba, an aiko har inda nake nemana na sanar musu ba ni da lafiya, da kansa ya zo dubani amman ban fada masa ba, matarsa ma ta zo duba ni ita ma bata sani ba. Tsoron yadda duniya zata kalle ya saka ban waiwayeki ba, wata kila sun ga kin yi kama da turawa ne suka saka miki Emily, ko kuma basa bukatar musulmai ne, domin bayan na aje ki na sake bi da gurin sai na ga gidan marayun na Christian ne karkashin kulawar wata coci. Daga lokacin kuma zaman garin be sake min dadi ba, sai na tattara na koma garinmu da zama, dan abun da na tara na cigaba da kasuwancina da shi, ban yi wata uku na miji aure ya fito min daga dangin mahaifiyata na aure shi, ba mu dade ba ya rasu kuma ban haihuwa da shi ba, bayan rasuwarsa rayuwa ta cigaba na kama sana'a duk inda na ji ana neman aiki na kan kusa na nema ni ma, amman ban yi nasara ba sai a wani banki da ke kusa da mu. Sanadin wannan aikin na hadu da mijin da nake aure yanzu, kasancewar dan kasuwa a wacan lokaci ya kan siya abubuwa daga arewa ya shigo da su gurinmu, na gurinmu kuma ya dauka ya shiga da su, wata rana ya samu matsala ya zo bank a nan muka hadu. Har ta kai ya san gidanmu ya fada min labarinsa kuma ya nuna yana son ya aureni, da farko iyayena ba su amince ba, saboda suna ganin bahaushen mutum baya rike aure tun a wacan lokaci sai dai kudin da yake da su sun taka rawa gurin amincewar iyayena, ni kuma ina hangen yadda bahaushe yake wadata matarsa da komai ba sai taje nema ba, a wacan zamanin mazan hausawa suna daukar nauyin dawainiyar iyalansu ne. Da haka aka amince muka yi aure ya dawo da ni gidansa a garinsu, a nan kuma wani tashin hankali ya same ni, domin matarsa fitinanniya ce yayansa kuma fitsararru ne, sai dai yarda da yake da ni da kuma yadda yake kaunata ya taimaka min wajen jure zama da su, sannu a hankali likkafa ta yi gaba arziki ya kara bunkasa har siyasa ta shigo ciki, zuri'a kuma ta samu, ta karkashin kasuwancin ya zama bashi da uban gida sai Alhaji Bello Bulama wani mutumen Maiduguri ne wanda ya shahara ciki da wajen kasar nan ta bangaren kasuwanci. Ba zan yi karya ba, mijin da nake aure a yanzu yana sona sosai domin ba ni da hayani duk kuwa da kasancewa ta bayarabiya wasu sukan ce yarbawa suna da fada, amman ni na sha banban, kuma na rike matarsa da yayansa da amana, sannan ni ce yar boko kusan duk inda zai shiga da ni yake zuwa, idan wani abu ya taso ma kasuwanci na kan ba shi shawara kuma idan ya bi sai ayi nasara, wannan ya saka har maigidansa ya san da ni, da muka tafi gidan muka samu tarba daga matarsa wacce ta kasance mai son mutane kuma ita ma yar kasuwa, muna gaisawa ni da ita muka gane juna, ita ce matar da na yi aiki da mijinta kuma mijinta ya amintar da ita da ni. A nan ta fada min sun rabu da mijinta saboda baya son haihuwa kuma yana da wata mata a can bata sani ba sai da lokacin da zai koma garinsu yayi ya koma da ita, daga baya ta gano yana da wasu iyalan kuma ita baya son ta haihu da shi, ashe a can idan ka saki mace sai ka bata rabin dukiyarka musamman idan akwai yara, ta shigar da kara kotu ta rabu da shi aka danka mata dukiya mai yawa sai ta siyar da komai ta bar kasa ta dawo garinta na Lagos ta fara kasuwanci ta fada min bayan dawowarta yarta ta rasu ya rage yaro ne kadai take da shi. Ta sake wani aure sai ta auri musulmi wanda ya kasance Alhaji Bello Bulama, mai gidan maigidana a bangaren kasuwanci, da haka ni ma na shiga cikin mukarrabanta, ta ja ni a kusa tana saka ni cikin huldodinta. Idan mijinta yayi tafiya ya dawo ko'ina mai gidana yake zai aje abun da yake yaje ya yarboshi, ba shi kadai ba kusan duk yaran da suke karkashinsa haka suke, idan zai tafi daga Kaduna tare muke zuwa saboda yana ganin mun san juna ni da ita kuma muna da kyakkyawar fahimta. A lokacin da suka dawo daga Sudan muka tarbe su har ta hado ni da ke, ina ganinki jikina ya ba ni, ba na gane ki ba, na sanin ni ma ina da ƴa mai kama da turawa a wani gurin da ban sani ba ko tana raye ko a mace, amman daga lokacin da muka shigo jirgi kika ba ni labarinki sai na kasa rike kaina a kamaninki suka bayyanar min fuskar mutumen da na bi son zuciya na biye masa na lalata rayuwata. Na tsorata kuma na yi bakinciki da halin da na ganki kuma kika fada min domin ni ce silar komai na san dole ina da kaso mai tsoka na zunubin abun da na aikata da kuma yadda kika tsinci kanki a matsayin kirista, mun shigo gidana kamin na haura sama na sauko kin gudu, a lokacin na ji babu dadi, amman ban neme ki ba saboda ban san yadda zan fuskance ki ba, kuma ban san kalar amsar tambayoyin da zaki min ba, kuma ban san da wane ido zan kalli yayana da mijina ba, ga ni da kishiya mai zafin kishi da yayanta marasa tarbiya. Amman a yanzu na gane kuskurena na fadawa mijina komai kowa ya san ke yata ce, a daren da na mari Kameela mahaifinta ya same ni da zance tare da neman dalili na fada masa komai ban boye ba, sai ya zabi ya sake ni amman baya son na bar gidan saboda yaransa da kuma gudun makiya kar su masa dariya, yace na yi zaman yayana. Ni kuma na amince na zauna ne kawai saboda baki zo ba, na fadawa yayana daga lokacin da muka gano inda kike kika dawo gareni, zan koma gidana da na siya ne mu zauna ba a gidan da zaki ji wata magana marar dadi ko ayi miki kallon banza ba, idan sun yarda sun ni falillahil Hamdu, idan kuma suka zabi zama gidan ubansu, ni dai ke ce damuwa Aisha... Tun da Mama Baraka take bata labarin Emily ta rufe fuska tana ta sharbar kuka. Mama Baraka ta sauka kwanta a kasa irin na mai neman gafara ta hade hannayenta ta kama kafar Emily tana kuka sosai mai cike da nadama. "Ki yafe min, ki yi hakuri ban kyauta ba na sani, ban sauke nauyin da Allah ya dora min ba na ki, kuma na zalince ki, hakkina yana nan akaina, ku ma yaya kuna da na ku hakki akan iyaye, ki yafe min Emily ki karbe ni, "Ẹ jọ̀wọ́, ẹ dárí jì fún mi. Mo ti dá aiyé mi ru, Ẹ jọ̀wọ́, ẹ dárí jì. Mo ti ṣàìṣe, mo ti wàhálà gan-an" Emily ta kama hannyen mahaifiyata ta rike ta mikar da ita zaune tana kuka. "Idan ban yafe miki ba me zan yi? Zan hukunta ki ne? Zan doke ki ne? Mai faruwa ta faru, komai ya afku rashin yafiyar ba zai dawo da rayuwar baya ba, ba kuma zai cire ni daga kangin da na shiga a baya ba, amman na dauki darasi mai girma kuma na jidadi da ban tafi na bar nawa yaran ba, ina alfahari da haka" Ta sake hannayenta ta mike tsaye ta fice daga dakin ta nufo downstairs. Aliyu Ummi da Fatima Nafeesa suna dinning suna karyawa Emily ta sauko da kuka ta nufi gurin da Fatima take ta dauketa, ta rumgume. "Momy are you okay?" Fatima ta tambaya ganin tana kuka kuma ya rumgume ta sosai. "Karki sake zabar kowa ki bar ni, na wahala na rana da dare na ratsa wuta, amman ban taba sha'awar tafiya na barku ba" Aliyu da tun da Emily ta sauko ya mike tsaye ya kalli Mama Baraka data sauko ita ma tana kuka ta yi zaton ko Emily zata gudu ne, Fatima ta labe jikin uwarta kamar ba ita ba, Emily ta juya ta haura sama tana dauke da yarta sai hawaye take. "Mama lafiya?" Aliyu ya tambaya. "Lafiya kalau ka fada mata komai da take son sani ne" "Okay, amman ki dan bata lokaci yanzu, ki tafi gida na miki alkawari da kaina zan kawo miki Emily idan ta huce" Mama Baraka ta amsa masa da kai sannan ta hade hannayenta zata musu godiya tana bude baki sai ta fashe da kuka ta zube a gurin. Ummi ta taso ta zo tana bata hakuri. TURHAN POV. Da gadon yaki masa dadi gashi bachi yaki ya dauke shi sai fito dakin ya sauko kasa ya zauna falo a nan ma ya ji ba shi da natsuwa saboda Fatima bata gidan yau, haka kuma be samu saka Emily a ido ba, ga bakinciki kallon matarsa da zama gida daya da ita da abokinsa yake babban makiyinsa a yanzu, ba zuciyarsa ba jikinsa ma ya gagara yin dadi komai ya yamutse masa. Ya bude kofar falon ya fita ya zauna a balcony abun da be taba ba, sam be san damuwa na hana bachi ba sai a yanzu da yake kokarin ganin ya gyara tsakaninsa da Emily. Ta ina zai fara.? Gaba daya Aliyu ya bi ya tare masa kofa babu ta inda zai leka balle ta hangeshi, duk wani yunkuri da zai yi da zarar ya tuna cewar Emily tana gidansu Aliyu karkashin kulawarsu sai yaji ya karaya, abu da ya sani idan yayi sanyi Aliyu zai kwace masa mata ne shi kuma ba zai jure hakan ba. Ya mike tsaye ya sauka balcony yana safa da marwa a gidan kar kace ba karfe 3 dare ba ne, ya dade a haka yana ta sake sake sannan ya juya ya koma ciki ya rufe kofar, dakinsa ya shiga yayi alwala ya fito daga bandakin ya nufi corner da yake ibada a dakin ya fara sallah. Daman Larabawa sukan ware wani bangare a dakinsu da suke shimfida Carpet su aje qur'ane ana saka turare domin ibada. Be daga daga carpet din ba har aka yi sallah asuba. Bayan ya gama sallah bachi mai nauyi ya dauke shi, be farka ba sai da ya ji yatsun Ammy cikin kansa, ya bude ido ya kalleta sai ta yi murmushi tana cigaba da shafa kansa. "Ṣabāḥ al-khayr yā Ammy" Ya furta da murmushin karfin hali, ta amsa masa cike da kauna irin ta uwa da ɗa. "ʿĀmil shinu yā waladī? Allāh yiḥfaẓak lī. yā ḥabībī yā waladī? Keif ḥālak?" Ya daga kadan ya kwantar da kansa kan ciyarta. "Babu dadi Ammy" "Ka raya dare da damuwa ko? Ni ma jiya na ji babu dadi saboda Fatima bata gidan, amman dai yau za mu tafi gidan" Ta sauke kansa. "Kwanta ka samu bachi, kana da bukatar kuzari ɗana, Allah ya maka albarka" Ya lumshe ido bayan ya amsa da Ameen, Ammy ta tashi cike da tausayin danta da kuma bacin ran halin da yake ciki ta fice dakin. [8/6, 11:10 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣3️⃣ "Ya kamata na koma haka, ance sun dora wani ma" "Ba fa inda zaka je sai an kama yaron nan, mutumen dake neman ranka zaka koma garinsa ka zauna da sunan aiki, daman can ni bana son aikin da kake a kuda mutanen nan ba su da kyau" "Abun da Allah ya rubutawa bawa baya wuce Ummi, kuma ai yanzu guduwa yake ba zai iya komai ba" "A nan din ma kasan ko yana nan yana haka maka rame? Ba zan barka ka koma ba, idan ma suna son aiki da kai su dawo da kai Abuja ko nan Kaduna" "Idan kuma suka ki fa" "Sai ka bar aikin dole? Ina za a kusa kai da kai a kasar nan baka samu aiki ba? Ga ka da cancanta kuma ga alfarma ta ko'ina, kasan ko bangaren President muna yan gaba gaba" Aliyu yayi murmushi mai sauti. "Ummi wato dai abun da ake fada na yan siyasa da gaske ne, daga kansu sai iyalansu?" Ummi ta yi dariya. "Gurin Surukinka muka koya, kasan ya fi kowa son kai" Aliyu yayi murmushi, shi da Ummi suka juya suka kalli kofar falon da aka turo. Ammy ce ta shigo da sallama fuska ba yabo ba fallasa, Ummi ta amsa mata ita ma tana dan sham kamshi domin abu daya ne Ummi bata yarda da shi ba, shi ne raini wayo ko wulakanci, bata daukar rashin girmamawa daga gurin kowa wannan dalilin ne ya saka suke kara samun rashin jituwa da mahaifiyar Kameela. "Ammy ce a gidan ba mu?" "Ai dole za ku gan ni tun da surukata tana nan, ya muka iya da abun da ya fi karfin wuta, fatan na same ku lafiya" "Lafiya Ƙalau sai Alheri da ke ta shigo mana" Ammy ta yi tsaye bayan Ummi ta amsa mata. "Bismillah Ammy ki zauna" "Aa ba zama ya kawo ni ba, Aisha tana ciki?" Ummi ta yi murmushi. "Tana nan waje, idan kika fita ki zagaya dama kadan gurin Garden tana can ita da jikarki" "Ammy ina wuni" Aliyu ya gaisheta yana sirina. "Lafiya" Ta amsa tare da juya bata ko kalleshi ba. Sai da Ammy ta fice sannan Aliyu ya sauke ajiyar zuciya. "Ammy fushi take da ni, ban jidadin yadda abubuwa suka zo ba, ko kadan Kameela bata kyauta min ba, na so na tsara abun nan cikin hikima ba tare da kowa ya ga laifin kowa ba, Allah ya sani da zuciya daya na yi wannan abun ban yi nufin cutar da Turhan ba, na shiga tsakiya ne kamin na hankara tausayin Emily ya rinjaye ni, sai na fi fifita matsalarta saboda ina ganin ita ce tafi shiga matsala, har gobe idan na tuna abun nan sai na ji zafin abun da Kameela ta aikata" "Ai ni ba karamin taimaka min ta yi ba da ta yi haka, da yanzu ban san miye yake faruwa ba sai idan ka mutu ace ai ka ci guba, ko kuma ka ta daba maka wuka, ka ga masu shegen kishin nan tun wuri ana ganin abun da suke iya aikawa daga musu kafa ake ana ganin kamar ba komai ba ne, da yanzu bata yi wannan shirmen ba ba zaka fada min ta zuba maka guba ba, kuma ai ka kasa sakinta" "A lokacin ina kokarin bata hakkinta ne, hankalin namiji baya taba zama iri daya na mace, ina daga mata kafa da uzurine amman ko a lokacin na yi alkawarin ba zan sake cin abincinta ko kwanciya daki daya da ita ba, and zuwa nan da na yi saboda ita ne Mama Baraka ta kira ni, da na zo kuma mahaifinyarta ta wulakanta, sai kuma ta aikata min abun kawai sai na zabi sauwake mata domin samawa kaina salama" "Aiko gashi yanzu abun yana cinta, babu safiyar bata aiko min sako ban hak'uri, ni kuwa ko ba ni da rai Wallahi ba zaka zauna da Kameela ba, yarinya ta yi yunkurin kasheka kiri kiri sannan ga iyayenta ba son auren suke ba, tun farko ni damam na runtse ido ban ga kyau a makanta ba, domin iyayenta ba masu dattako ba ne, kai kuma ka tsaya kai da fata ai ita tana sonka tana da tarbiya, ga abun da ta haifar maka ai, daman yaushe iyaye za su bada shawara aki bi kuma a ga daidai?" Aliyu yayi dariya. "Yanzu dai ba zan sake zabar mata ba, ke zaki zabar min" "Aa kai da kanka zaka zabo, ni nawa bincika ne da duba dacewa" Ya mike tsaye ya nufi kitchen ya bude firjin ya dauko ruwa ya kafa gorar a baki ya sha, sannan ya fito rike da ita ya dawo falo ya zauna. "Ni yanzu ban san ya zan yi na shirya tsakaninsu ba" Ummi ta dauke kanta daga kan wayarta ta kalleshi. "Ina ruwanka da shirya tsakaninsu? Dan iya? Tun farko daman ai bata son Turhan din, kuma sai ga shi yayi mata abin da yayi ta ji ta tsane shi, kai kasan yadda mutum yake ji idan baya son wani kuma ya zo ya kara zalintarsa? Kai da ka gode Allah auren soyayya kuka yi da Kameela, haka din ma yanzu da ta yi maka ba daidai ba yanzu ya ka ji? Ka ce ta komawa mijinta ta ga kamar kana matsa mata? Yarinya ta sha wahala yanzu har bada son wari maza ai ta ma yi kokari da take kallonka, da ni ce ko hanya ba zan sake hadawa da namiji ba, idan ta ga wanda take so har zuciyarta ita zata yi magana, kuma ni yanzu ko mijina tace tana so ai sai na tattara ni da kai mu bar mata gidan ita ma ta samu jindadin rayuwa" Aliyu ya kyalkyale da dariya. "Ummi Allah ya bar min ke, duk matar da zata yi kishi da Ummi ai sai ta shirya, taya ma Emily zata ce ta so Daddy" Ummi ma ta yi dariya. "Aa wai a misali dan na nuna maka ta cancanci farinciki, kuma kishi da ni wata wahala ce? Ni fa ba zan cutar da kai ba, kuma ba zan zuba ido ka cuce ni ba, magana kuma a fada min daya na rama da goma" "Aa ni ba tsakaninta da Turhan zan shirya ba, tsakaninta da Ammy, tsakanin Emily da Turhan wannan wani abu ne da kowa be kamata ya saka kansa ba" "Yanzu na ji maganar hankali, Allah ya bata wanda zai riketa amana mai sonta tsakani da Allah kuma babu cutarwa" "In Shaa Allahu, daman ai bayan wuya sai dadi, kuma Allah da kansa yace dukkan tsanani yana tare da sauki" Ya sake kurba ruwan ya aje ya mike tsaye ya haura sama. EMILY POV. Tun bayan tafiyar Mama Baraka Emily bata fito ba sai da Ummi ta shiga ta lallasheta, da kalamai na karfafa guiwa ta fada mata yanzu ai komai ya wuce, be kamata ta rika tuna baya ba, kamata yayi ace ta fuskanci gaba. Da lallabawar Ummi Emily ta samu gwarin guiwar cin abinci ita da Fatima ta shiga ta yi wanka ta saka doguwar rigar Atamfa, sai Ummi tace ta fita ita da Fatima waje su bawa itatuwan gardens ruwa, daga bada ruwan ne ta fara jika Fatima tana dariya, sai Fatima ta yi mata gwalo ta boya a bayan itace ita kuma tana binta ta watsa mata ruwan, sai nishadi take kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba. Tana rike da tiyo ta ji kara bude karamin gate din da aka saka a gurin sai ta juya idanuwanta suka yi arba da Ammy. Emily ta dan rage murmushin da take tana kallon Ammy har ta karaso kusa da ita, Fatima ta fito daga inda ta boya da sauri ta rumgume Ammy tana mata oyoyo. "I miss you" Ammy bata damu da tufafin a jike ba ta daga ta sama ta hade da jikinta. "i miss you too, ya kike rabin rai na" "Lafiya lau, ina Dady" "Yana can bakin gate cikin mota gidan kin fita zaki gan shi" Ta sauke ta kasa Fatima ta zura da gudu tana murna ta fita gurin. Emily ta saki Tiyon hannunta. "Ina wuni Ammy?" Ammy ta yi murmushi. "Lafiya kalau yata, ya mai gudun uwarta, kin dawo lafiya?" Emily ta yi murmushi. "Lafiya ƙalau" "Ina kika shiga kika boya? Kin daga mana hankali, kin dagawa Turhan babu inda be shiga nemanki ba har gurin da kika zauna kamin ki haifi Fatima, ita ma Fatima bata bar mu mun huta ba" "Yanzu ai na dawo, komai ya wuce Ammy" "Haka ne sai dai a fuskanci gaba, fatan dai babu wata matsala yanzu ko?" "Babu" "Tohm Alhamdulillah haka nake son ji, yanzu hankalin Turhan zai kwanta na yarki ma ya kwanta ni ma kuma sai na samu farinciki" Emily ta yi shiru bata ce komai ba. "Jiya Turhan be yi bachi ba, gaba daya ya bi ya damu saboda ba shi ya gano inda kika shiga ba, tare da shi muka zo na ce ya jira na fara shigowa na yi magana da ke, kin san saboda Aliyu baya son shigowa gidan nan" "Ammy akwai abun da nake son na fada miki" Emily ta fada, sai Ammy ta kara matsawa kusa da ita. "Ina jinki yata" "Mu zauna a can" Suka nufi gurin da kujerun zama suke suka zauna Ammy ta dora jakarta kan teburin. "Da farko da zan fara da miki godiya, na abun da kika min ni da ɗana a shekarun baya, na rike ni ba tare da kin sani ko kin san inda na fito ba, na gode Sosai, hakan ya saka ni auren Turhan da nufin na rama alheri da kika min, har abubuwan da suka faru suka faru, kowace jarabawa a rayuwa darasi ce ta kan koyar da kai wani darasi ne da baka sani ba, na kara jirmama abun da kika min ne da sanin muhimmanci a yanzu da Mahaifiyata ta bayyana" "Mahaifiyarki?" Ammy ta katse ta sai Emily ta daga mata kai Idonta na cika da hawaye. Ta tsakura mata abubuwan da suka faru. Emily ta rika hannunta. "kin yi kokari da kika rika ni, kika taimaki ɗana, a lokacin da mutunen da ya rabo ni da inda nake samun walwala ya wulakanta ni, danginsa suka ki ni, na rasa inda zan dafa, na gode Ammy na gode" Ammy ta yi murmushin jindadi. "Alhamdulillah da kika fahimci haka, ko kadan bana nufin cutar da ke, hada aurenki da Turhan ma ban yi dan cutar da ke ba, na yi ne da nufin sama miki mafita ta mijin aure ni kuma na samu mafitar ɗana a kusa da ni, idan har ina nufin cutar da ke taya zan aura miki dan da ni na haifa da ciki? Shiyasa da na fahimci akwai matsala na sauya masa na kasa saurarensa a dolensa ya bazama nemanki, gashi yanzu har ya gane kuskurensa yayi nadama babu abun da yake nema sai hada kan iyalinsa guri daya, kuma ina fatan zaki fahimce shi zaki yafe masa, ki yarda da shi ko dan yarki" Emily ta saki hannunta. "Yara ba su kai su hana iyaye farinciki ba Ammy, su yanzu suke tasowa rayuwarsu suke ginawa, shiyasa mahaifiyata bata bar farincikinta saboda ni ba, balle kuma ni da na yi ma Fatima komai da uwa zata yi ma yarta, idan har zan yarda a yanzu farincikin Fatima ya hana nawa hakan na nufin ni ban gina rayuwata ba kenan, abubuwan da suka faru sun faru kuma na ba su baya a yanzu, amman ba zan bar farincikina saboda Fatima ba, ba zan sake kuntata ma kaina sabida kowa ba" "Hakan yana nufin babu wani gyara tsakaninki da Turhan?" "Babu Ammy, ni ban taba son Turhan ba, har yanzu ban ji wani abu akansa ba, kuma bana tunanin nan gaba zan ji, yanzu idan har nace zan sake zama da shi to ni ce zan cutar da shi, kuma na cutar da zuciyata to miye amfanin haka?" "Aisha ni kika kalli kwayar idona kika fada min baki son ɗana?" "Ki yi hakuri Ammy, kin san inda na fito kin rayuwar da ni, ke ma kin yi makamanciyar tafiya irin tawa, miyasa ba za ki fahimce ni ba?" "Saboda mahaifin Turhan be yi nadama ba, har yau be nemi ni ko neman afuwata ta ba, amman ke Turhan ya gane kuskurensa ya tuba kuma ya shirya faranta miki har hawaye ya zubar akanki, ya kauracewa abinci, bachi ma baya wadatarshi, da ace saboda Fatima ne kawai ai ba zai waiwaiyeki ba tun da ya same ta, amman saboda yana son ki yana son farincikinki ya kasa hakura, ki ba shi dama Aisha dan Allah" Emily ta girgiza kai. Sai Ammy ta kama hannunta ta rike. "Haba mana Aisha, ɗana na cikin mawuyacin hali saboda ke, ba shi kadai ba, Khaleefa ma ya munana miki iyayensa ma sun munana amman ni ban miki ba, miyasa ba zaki yafe masa ba, ki ma dakinki ki rumgume yarki da ke son Babanta? Duk wani sharadi da zaki gindaya mana ni na miki alkawarin za mu dauka" Emily ya sake janye hannayenta. "Ba zan iya ba Ammy ki yi hakuri, ba zan iya rayuwa da mutumen da ya shigo dakina a daren aurena ya tofa min yawu a fuska, ya kalli kwayar ido ya kira ranar da aka daura mana auren da bakar rana a gurinsa, ya shiga da ni gidansa a matsayin baiwa, yana kallo nake goge inda matarsa take takawa, yana sane ake dokana, be damu ya ba ni abincin da nake iya ci ba, ban taba dandanar dacin rashin magana ba sai da na auri Turhan, kuma ba dan bana iya maganar ba, sai dan ya gabatar da ni a matsayin kurma kuma ya saka min sharadin kar na kuskura na yi magana, a gidansa ban isa na saka kayan da nake so ba sai uniform din bayi, ban isa na kwanta a inda nake so sai tare da hadiman matarsa, ya kira ranar da ya kusance ni da bakar rana, ya fada min ba zai taba so na ko son abuj da na haifa ba, mutumen da yayi min duk wannan taya zai dauke ni a yanzu ya nunawa duniya yace ina da daraja? Ai ya gama kwance min zane a kasuwa kowa ya ga tsiraicina, Turhan ya haihu da ni kin samu jika har gobe ban isa na goge wannan ba, Ammy haka ma ya wadatar..." Ammy ya mike tsaye ba tare da ta kara cewa komai ba ta fice daga gurin. Emily ma ta mike tsaye ta nufi wani ice ta dafa shi da hannu daya dayan hannun kuma ta dafe kanta tana jin babu dadi na tunawa da rayuwarta ta baya. Tana tsaye a gurin bata motsa ba ta ji an kira sunanta "Aisha?" Ta juya ta kalli Turhan dake doso inda take tsaye hannayensa rumgume a baya yana tafiya daya bayan daya irin ta jinin sarauta. Ya tsaya gabanta yana kallonta daga sama har kasa for the first time ya ga kyauta irin kyaun da be taba ganin ta yi ba sai yau, duk kuwa da babu kwalliya a fuskarta, sai kuma kwarjininta ya kama shi gabansa har faduwa yake da take kallonsa ido cikin ido kallo irin na wanda ya tanadi amsar kowace tambaya. "Za mu iya yin magana da Allah?" "Yau kai ne kake neman izinina akan wani abu?" "Haba ki bar abin da ya wuce ya zama ya wuce mana Aisha! Na yi kuskure na sani kuma na karbi kuskurena, ke ma a yanzu kina cikin kuskure na barin wanda ba muharraminki ba yana kallon surar jikinki da kyaunki yana magana da ke yana jindadin muryarki, be ma kamata ki zauna a nan ba shiyasa duk abun da na fada ba fahimta kike ba, saboda ba zai taba bari ki fahimce ni ba, kuma ba zaki gane hakan ba sai nan gaba." "Na fada maka wani? Aliyu ya fi min kai amfani sau dubu, shi be taba fada min magana marar dadi ba, be muzantani ya fada min magana marar dadi ba, be doke ko ya saka a doke ni ba, be kira ni fasika ba, da na ba shi labarina be musa ba, ban roke shi alfarma ya gagara yi min ba, be yarda an wulakanta ni ba, ne gan ni a cikin damuwa ya bar ni balle har ya jefani a ciki, dan haka ba zan yarda wani ya fadi wata magana marar dadi akansa ba" Turhan ya hade wani abu mai daci da tsayawa rai yayi murmushi. "Ban zo nan saboda wani da be kamata ko sunansa na furta ba, na zo ne nan ne saboda ni da ke" "Babu wani abu tsakanin ni da kai, zama ne dai ada mun yi yanzu kuma ya kare, idan har zaka zo mu tattauna wani abu to ya kasance akan Fatima and Only Fatima" "Aisha miyasa idonki ya rufe har haka ne? Mu fa iyaline be kamata kina haka ba, ki yi hakuri da duk abubuwan da suka faru na san ban kyauta ba ina neman afuwarki ki yafe min dan Allah, Wallahi na yi nadama, kuma na yi bakinciki abubuwa na da na yi miki, ina neman afuwa, kuma na miki alkawari hakan ba zai sake faruwa ba" Ya bata fuska sosai kamar zai mata kuka. "Na yafe Turhan, that's okay zaka iya tafiya ka yi rayuwarka" Ya kalleta da sauri domin be yi tsammanin zata yafe masa haka da sauri ba. "Kin yafe min Emily? Zaki koma zama da ni kenan?" "I forgive, never forget ba za mu sake zaman aure ba Turhan, na kasa manta abubuwan da ka yi min, ka fada min ba zaka taba kaunata ba wannan ya zauna a kaina" "Baki yafe min ba kenan, indai kin yafe min to zaki yarda ki zauna da ni ne Aisha, Fatima ma zata yi farinciki, idan har baki yarda kin aureni ba zan shiga mummuna hali Aisha, Wallahi ba ina fada miki haka saboda kan karya ba ne, har cikin raina ina kaunarki Aisha, kuma ina son zama da ke, idan kika guje min ban san iya halin da zan shiga ba, Wallahi ba dan ke ba, ba zan taba tako kafata a cikin gidan nan ba, ni yanzu damuwata ki amince da ni ban damu ko kina so na ko baki so na ba! Zan iya zama da ke a kowane hali, Aisha karki ba ni kunya a gaban makiya dan Allah, don't break my heart please" "You broke me first.... Shin baka yi tunanin ya abun yake da zafi ba? Ni ma a yanzu ban damu da duk wani zafi da zaka ji ba, ka tafi ni dai na yafe maka amman zama a tsakaninmu ya kare" Ya lumshe ido ya rasa ina zai saka kansa ya zai yi Emily ta fahimceshi. Emily ta wuce shi ta fice daga gurin, tana shiga falon ta samu Ammy zaune ita kadai a falon Fatima na saman jikinta, kallo daya Ammy ta yi mata ta san ɗanta be samu nasara ba. "Momy nace dady ya dawo nan mu zauna tare gaba daya, ya fi dadi kina nan Ammy ma ta zo ga Uncle Aliyu ga Dady ko?" Emily ta girgiza mata kai. "Aa Dady zai zauna gurin Ammy, idan kina so zaki je ki gan shi" Sannan ta kalli Ammy ta ce. "Ammy na gode da ziyara, zan haura sama" Ta nufi stairs, Ammy ta bita da kallo har ta haura sannan ta sauke fatima a jikinta ta kama hannunta. "Fatima muje ko?" "Aa ki tafi sai gobe zan zo" "Baki son gurin Daddynki?" "Ina so gobe zan zo tare da Momy" Ammy ta saki hannunta ta fice rai a bace. [8/6, 11:10 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *©️ Khadeeja Candy* Page 6️⃣4️⃣ Ammy ta same shi zaune a motar cikin wani yanayi marar dadi. Bata ce masa uffan ba shi ma be furta komai ba yaja motar suka kama hanya sai da suka isa gida ta bude motar ta fita sai ya ji shi ya kasa fita, yana mamakin yadda Aliyu ya shige masa hanci, haka zai zura ido wani katon banza yana kallon masa mata? Yana jindadin yayi nasara akansa? Miyasa wai tun farko be yarda girmama zabin mahaifiyarsa da yanzu duk be samu wannan matsalar ba. Ya dade a zaune a cikin motar sannan ya fita ya shiga falon ya zauna, Ammy ta kalleshi cikin tausayi da kuma bacin rai ta ce. "Turhan ka hakura da yarinyar nan, tun da ba mata suka kare duniya ba, ka nemi yafiyarta kuma ka kwatanta kyautata mata Alhamdulillah, a haka ma Allah ya maka albarka, kana da mata ka rike aurenka ka koma a can ka cigaba da harkokinka idan kana bukatar ganin Fatima ka dawo ka ganta" Turhan yayi shiru na lokaci kamin ya ce. "Ammy kin cire rai da dawowar Aisha ne?" "Babu amfanin mu yi ta bibiyarta tana wulakanta mu, sai kace kanta farau wulakancin ɗa namiji na ga mazan da suka fika wulakanta matansu kuma matan ne ma suke neman mazan su zauna da su balle kai da har ka gane kuskurenka kuma ka nemi yafiya? Wai yau ni Aisha zata kalli kwayar idona ta fada min bata sonka. Sai binta muka tana da juya mana baya kamar autar mata" "Aisha fa bata da laifi, laifin Aliyu ne, saboda shi ya fara ganin ta kuma ya shirya mata abun da ba gaskiya ba ya dorata a kai, gashi kuma yanzu tana gidansu su suke kitsa mata komai" "Idan da su har da ita, ai ba jaririya bace balle ace saka mata magana ake a bakinta" "Wallahi Ammy Aisha bata da laifi, laifin duk na shegen katon banzan nan ne Aliyu, kuma da yarda Allah sai na ba shi mamaki" Ammy ta sauke dogon numfashi. "Da zaka hakura da ita da zai fi, tun farko rashin daukar shawara ne ya jefaka a cikin halin da kake ciki ai, da na aura maka ita miyasa baka rike ta ba ka bi son zuciyarka? Da duk haka bata faru ba kuma da yanzu Allah kadai yasan yara nawa ta haifa maka, yanzu kuma idonta ya bushe bata ganin kowa kai kuma ka dage sai ka zauna da ita, ko zaman kuka yi auren ba zai muku dadi ba saboda bata ganin mutuncinka yanzu bata ganin girmanka" "Ni ne mai laifin ai na sani, shiyasa yanzu nake kokarin ganin na gyara laifina, ko na yi kamar zan hakura idan na tuna da Aliyu ba zan iya hakura ba Ammy, hankali ba zai kwanta ba sai idan na ga ta yi aure kuma ba shi ta aura ba, shi ma kuma idan ba zata dawo min ba" "Ai Aliyun ma da wuya ya aureta, kawai dai kai suke son gasawa aya, shi da yake da matarsa ma, dole shiryawa za su yi, idan ka yi hakuri kana nan Aisha zata nemeka, ni na san Ummi ba zata yarda Aliyu ya auri wannan yarinyar ba, ita hauka ce take dibanta" "Ammy saboda kina mace ne, ba zaki gane ba, Aisha ta kai duk inda mace ta kai babu wanda zai ganta be ji yana sonta ba" "Tohm sai ka gwada naka kokari, ni dai daga bakin nan na cire hannuna" Turhan ya ji babu dadi. "Wani abu Aisha ta fada miki ne Ammy? Kamata yayi ki goya min baya, duba yadda Ummi tana bin bayan danta duk kuwa da cin amanar da yayi, na tabbatar da ni ce ba zaki yarda na dauko Kameela matar Aliyu na aje a nan ba" "To me zai saka ka yi haka? Ka nemi wata ka aura idan har kana son auren ne" "Aa Aisha dai, idan ba ita ba..." Yayi shiru takaici ya saka Ammy tashi ta bar masa falon. "Aifa sai dai a mutu, amman ba zan taba yarda Aliyu yayi min wannan cin kashin ba, bayan ya gama da ni ya rabi matata Allah kadai ya san abun da ya faru kuma yanzu yace wai zai aureta saboda kawai bakar kiyayya ba tare da na masa komai ba" Ta juya fuska. "Ita ma dai wani lokacin da matsalarta da gaskiyar Ammy, ni ban ce ta raga min ba, amman ta daina sake jiki mana da wannan katon kwarton, ji yadda ta kyau dan Allah haka zai sakata gaba yayi ta kallo, macuci" Ya hade yawu da karfi, ya saka hannunsa yana karawa rigar wuyansa fadi kokarin yagata take, yana jin kamar numfashinsa na danne, bani irin kishin Emily yake ji har na bala'i EMILY POV. Misalin karfe 9pm tana zaune falo Ummi na kara mata wasu darussan na rayuwa, Aliyu ya sauko Fatima na janye da hannunsa. Da suka kawo kasa sai Fatima ta sake shi ta nufi Emily ta kama gashinta tana yaryadawa a bayanata. "Momy Dady yace in dinga rufe miki jiki" Emily ta juyo ta kalleta, Ummi ta yi murmushi bata ce komai ba, Aliyu kuma ya kalli Emily kadan ya dauke kai. "Uncle Aliyu yace zai koma gidansa gobe, Momy zaki je? Zamu koma can ne kuma? Miyasa ba zamu zauna gidan Dady ba, Ammy tana sonki da Dady sai mu koma can har Uncle Aliyu ko?" Ummi ta kalli Aliyu dake gefenta. "Ina zaka koma" "Gidana dake nan Ummi, zan fi jindadi, kuma yana da kyau mu kiyaye dokokin ubangiji" "Hankalina zai fi kwanciya ka zauna a nan, kwantarka ake ne zaka koma can? Ina jin nan da sati biyu ma za mu koma Abuja gaba daya" "Aa Ummi indai kika ce zaki sama min masu tsoro zan yarda shi ma saboda ki zamu kwanciyar hankali ne, amman Addu'a ta ashe ni, zan koma can In Shaa Allahu" Emily ma ta kalleshi tana jin babu dadi ganin take kamar idan baya cikin gidan ba zata sake sosai ba, yanayin ya sauya har ta kasa boyewa ta cire gashinta dake hannun Fatima ta mike tsaye ta bar falon. ONE WEEK... Ba banza aka bar Aliyu ba, daman fa yarbawa sun iya mugun abu, idan ba haka ba taya Aliyu zai sake ta, daga kawai ta kai yarinya gurin Babanta, gashi har ya fadawa Ummi ta saka guba a abinci, ko Ummi bata nuna mata bata son zuwanta gidan ba ta san ba zata sake aminta da ita ba, gashi yanzu ko zuwa gidan bata son ta yi. "Kai gaskiya ba banza ba, kalli ko Bakar Barakar nan dan ba zan ce Mama ba ni bata haife ni ba, kamata yayi abbah ya koreta gaba daya daga gidan nan kamar kare, amman be yi ba sai saki daya yayi mata har da cewa wani wai baya son kowa ya fitar da maganar ta yi zaman yayanta, yana nufin zai maida ita kenan, shiyasa take ta shige min tana kiran Aliyu tana wani bani shawarar munafukai, ashe ta san Emily yarta ce shi take hangowa" Magana take da kanta tana ta safa da marwa tana dora hannu a kai tana saukewa, ita a yanzu babu tashin hankalinta kamar yadda Aliyu ya juya mata baya, sakonta be reply ya bi yayi blocking din number ta ma, Ummi ma bata amsa mata idan ta kira kuma bata maida mata da amsar sako, gashi yanzu Aliyu gida daya suke rayuwa da Emily. "Wai to shi wannan Turhan din in ban da sakarai ne shi haka zai zuba ido wani ya karbe masa mata? Ayi mutum kamar dusa, wannan bakin ciki ina zan kai shi? Wallahi Aliyu be ma dace da yarinyar nan ba, ga kafirci ga shi bata hanyar aure aka aureta ba" Ta fashe da kuka ta sauke hannu ta sake dorawa, haka take kowace rana ta saka wannan ta kwance waccan ita kadai domin yan'uwanta babu mai tayata gaba daya ma basa son zancen Aliyu, su sun ji dadin haka daman ba sa son aurenta da Aliyu gashi yanzu an rabu kuma sanadin haka Abbah ta saki Mama Baraka, Hajiya sai shiga da ita take na balmar baka tana son mijinta ya kori Mama Baraka daga gidan gaba daya. Kuka Kameela ta ci sosai ta rasa ina zata saka kanta, ko ba Emily ba ba zata so Aliyu ya so wata ba balle kuma Emily, mace da ita kadai ce ta hana ta walwala ta kuma rabata da mijinta, kuma sanadinta ta sakawa mijinta guba gashi yanzu shi ne silar komai, ba dan haka ba da duk abubuwan da suka faru ta san Aliyu zai iya yafe mata su zauna domin tana son mijinta, amman yadda Ummi ta dauki zafi ta san zata sha wahala kamin ta samu kanta. Balle kuma Emily tana gidan ta dauke masa hankali da kyaunta ta san ba zai tsaya tunaninta ba, daman tun farko kyaun ne ya dauki hankalinsa ba komai ba. "Ni ban san ma san miyasa wannan Mama Baraka ta hadu da bature ba har aka haifo wannan yarinyar, kuma abu ya zo ya zama kamar na gida ni na shiga uku, shiyasa na ki ya rabu da ita, ashe ita wannan Mama Barkatar tana nan tana shirya masa soyayyar Emily ni aka maida mahaukaci" Ta kwanta ta tashi ta rasa ma wane irin tunani zata yi, kuma ta san idan ta yi sake bata hankara ba zata ji an daura musu aure domin ba a banza aka bar mijinta ba, kamar yadda aka yi ma Babansu. Ta zauna tana ta cizon baki, babu wanda ta fado mata a rai a yanzu kamar Tasmia zuciyarta ta raya mata babu inda zata samu mafita sai a gurinta. Ta janyo wayarta ta duba sai ta tuna bata da number Tasmia ta goge tun a wacan lokacin da suka samu matsala. Sai dai abu mai sauki ta can gidansu, bata da tabbacin zata iya samunta a gidan amman saboda neman mafita ta dauki key din sabuwar motar da Momynta ta siya mata ya fita ba tare da sanin kowa ba ta dauki kafa zuwa gidansu Tasmia. Ta isa gidan tana ta sake sake kuma tana dan jin kunya da nauyin Tasmia na abun da ya faru tsakaninsu, be ma kamata ace ta je neman taimakon Tasmia ba amman saboda bata da wata mafita sai wannan ya saka ta aje komai a gefe ta faka harabar gidan na masu rufin asibiti bayan mai gadi ya bude mata gate. Ta rufe motarta ta nufi cikin gidan tana rike da key ta a hannu da green din hijab dinta idan ka ganta ba saka yi zaton zata yi fitina ba. Ta shiga da sallama a tsakar gidansu Tasmia jikokin da suka nan suka amsa mata suna wasa da ruwa. Su ta tambaya ko tasmiya na ciki suka ce mata tana cik sai ta nufi kofar falon ta shiga da sallama. Suka amsa mata da mamaki domin Tasmia ta fada musu sun samu matsala da Kameela sai dai bata labarta musu gaskiya maganar ba kawai ta ce saboda Kameela tana da zafin kishi ne. Mamasu ta amsa mata da far'a kanen kam sai kallonta suke. Ta kai har kasa ta gaishe da mamansu sannan ta tambaya Tasmia ko tana ciki, maman ta tambaya ko lafiya ta amsa da babu komai tana dariya. Sai aka nuna mata dakin da Tasmia take, ta nufi dakin ta shiga da sallama tana yaye labule. Ita kanta Tasmia ta yi mamakin ganinta har tana tsoro domin bata san da me ta zo mata ba. "Yan bautar kasa wato kun gama babu ko labari babu ziyara?" "Ke da wacce kika zo? Ni da ke fa kai ta san kar ne" Tasmia ta fada sannan ta tashi zaune da kyau kar a shammace ta. Kameela ta tabe baki. "Ni da alheri na zo miki, ba sheri ba" "Koma da wacce kika zo ni daidai nake da ke" Kameela ta zauna ba tare da an mata tayin zaman ba. "Ke dan Allah ki bar abin da ya wuce ya wuce mana, ni ma yanzu ina cikin tawa matsalar mafita nake nema shiyasa na rugo a guje na zo gurinki" Tasmia dai kallonta kawai take. "Dan Allah ki ba ni aron hankalinki kuma ki natsu sannan kuma ki fahimce ne" "Ina jinki" Kameela ta yi shiru na lokaci can kuma sai ta ce. "Emily ce matsalar, amman ba zan fada miki komai ba sai idan zaki taimaki kanki ki taimake ni" "Zan taimake ki ba tare da sanin me ya kawo ki? Hajiya ki fada min damuwarki kawai ba wani noke noke" Kameela ta rage murya ta marairaice ta fara karanta mata damuwarta sannan ta koro da labarin Emily. Tasmia dai sai saurarenta take har ta kai aya. Kameela ta juya makullin motar dake hannunta tana kallon Tasmiya bayan ta gama bata duk labarin Emily da kuma abun da ya faru. "Tohm yanzu ni miye nawa a ciki? Har kike ba ni wannan labarin?" "Tasmiya aurena fa ya mutu?" "Na san aurenki ya mutu mana, abun duniya ai baya boyuwa na ji tun kamin na dawo garin nan kuma yanzu gashi kin kara fada min, dalilin da zai kawo ni cikin matsalar ne ban sani ba" "So nake ki taimaka min, ni biyanki ne ma zan yi Wallahi, na san da can kina son Aliyu ai ki yi duk yadda zaki iya ki dauke hankalinsa daga gurin kafirar nan, ni da ta aure shi Wallahi gara ke ki aure shi" Tasmia ta yi dariya "Wato Kameela kin dauke ni marar hankali marar wayo ko? Ke ce mai wayo? Bayan duk abubuwan da suka faru yanzu ni kike son na zame miki tsanin hawa? Miyasa ke ba zaki yi yakin da kanki ba?" "ba zaki gane ba ne, gaba daya baya saurare ni yanzu ya juya min baya kamar ba Aliyuna ba, daukar yarinyar da na yi na kaita gurin Turhan har Aliyu ya sake ni ni sai nake ganin kamar ba banza aka bar ni ba, Wallahi idan Aliyu ya auri kafirar nan an gama da ni gaba daya, uwarta ta yi kishi da uwata ni kuma na yi kishi da ita? Da dai ita ta aure shi kara ke" Tasmia ta tabe baki. "Ni yanzu ina da wanda zan aura masa Kameela, kuma mijinki mai wuyar sha'ani da shegen wayon tsiya" "Ai mataki zamu dauka ko ta halin yaya, idan kika ba ni hadin kai ma har acit sai mu watsa mata fuskar ta lalace daman ai kyau ne yake jansa" Tasmia ta yi murmushi a nan ta gane Kameela so take ta jefata a matsala. "Ki yi kishi da ita taya? Ai ke ba Aliyu kike aure ba, kuma tun da kika ga ya sake ki saboda ita ya nuna miki ta fiki muhimmanci kenan, haka ya buga min warning lokacin da muke can fa saboda ita, kin san mijinki dan duniya ne duk inda aka juya sai ya gane mutum, dama kin hakura domin yadda kika cika idda abu ne mai wahala ya maida ke, balle kuma kin ce har mahaifiyarsa bata sonki a yanzu, yo daman Kameela uban waye zai so ki? Kin ga yanzu ni dake ai mun zama daya, wai ke uwar gori kin ce ban da aure ko? To yanzu ni da ke waye shegen? Ni Wallahi Emily ma tausayi ta ba ni da kika ba ni labarinta, daman tun da na ganta ganin farko na fahimci tana cikin damuwa, kuma na kulla abota da ita, sai gashi son zuciya ya dauke ni na so cutar da ita ashe da na shiga uku, ni yanzu na bibiye mijinki kamar wata karuwa? Ko an fada miki karuwanci naje can ba bautar kasa ba? Kuma ni yanzu na samu wanda zan aura, kuma idan ba ki bi a hankali ba duk abun da kika fada min sai na fadawa Emily da Aliyu" Kameela ta fusata. "Tasmia idan ke ba karuwa ba ce wacece ke? Dan ubanki nan kika bar garin nan kika tafi har Ph bautar kasa da kika je kuma kika kama hanyar gida baki zauna inda kowa ke zama ba, kika dinga bibiyar mijina wai saboda kin yi kwantain, yanzu saboda kin samu damata na zo har shegen gidanku neman shawara zaki fada min magana, kutumar ubanki Tasmia, idan kin fasa tausayin Emily ko fada mata abun da na fada Allah ya tsine miki albarka" Tasmia ta yi mata sowa da baki.... "Oohhhhhhhhh an dai ji kunya, ke da kika takama kin fi karfin mijinki yau ke ce namiji ya gagareki, kike raba ni saboda ki samu shiga, ke yanzu dan Allah baki ji haushin kanki ba ma? Kim san kina Aliyun uban waye ya saka ki hauka? Kanki farau kishi mahaukaciya yar marasa tarbiya.." "Ubanki ne shegiya mai warin talauci, kuma muna nan dake zaki gan ni da Aliyu, ni da shi mutu ka raba ne takalmin kaza dan ubaki Zubairu" Tasmia ta rufeta da duka suka fara kaiwa juna naushi sai da kanen Tasmia da mamansu ta shigo aka raba su. "Lafiya" "Mama ki bar ni na ci uban yarinyar can, ganin take saboda suna da kudi zata iya taka kowa? Muma na ao muna da rufin asiri yar iska, daman ina rike da ita a zuciyata, idan ba ke wawuya ba yaushe zaki yi fada ni kuma yanzu ki wanko kafa ki zo wai na taimaka miki ke dakikiya ko.? Kara da Aliyun ya sake ki ai, kuma da yardar Allah sai ya auri Emily ke kishiya uwarki kishiya" "Ke ce yar iska marar tarbiya, mai bibiyar mazajen mutane, ko yanzu wa san mijin wa kika kwato? Muna nan da ke Aliyu ba zai auri Kafira ba, haka kuma ba zai auri yar iska irinki ba" Mama ta rufe baki. "Aa ahhhhh kin ga wannan.... Amm... Kameela kike da suna ko? dan Allah kama hanya ki tafi bana son fitina, ba alfahari ba ni dai yarana ba su da abokin fada, kuma ba zan su ki yi abun da zai saka mu da ke mu yi ta nadama ba, dan Allah yafi kin ga karfi ma ba daya ba, daman tun farko na ganki na san ba lafiya ba" Ta dauki makullin ta dake can karshen kofa ta fice tana ya huci sai zagi take jefowa Tasmia idan ta yi yunkurin ramawa Allah Mamanta ta hana. Kameela ta fito rai a bace ta shiga motarta ta juya kamin mai gadin ya bude mata gate ya daga masa hankali da horn kamar zata tashi gidan. [8/8, 9:58 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣5️⃣ "Idan Hajiya Baraka ta yarda mun tafi dake kuma Ammy ta amince toh wannan makarantar ya kamata a sakata, daman ina jin ana fadar suna karatu sosai" Emily ta yi murmushi kadan. "Na manta ban tambaye ki ba, ko kina zuwa coci a lokacin da kike can? Kar ya zama mun tauye ki a nan ki kasa mana magana" Emily ta kalli Ummi ta mamaki. "Aa bana zuwa coci ko a can" "Okay, tohm yayi kyau, idan kin gama kallon sai ki shiga Kitchen ki wanke kayan da muka ci abinci da su, zan shiga na kwanta" Ummi ta mike tsaye ta nufi hanyar Stairs, Emily ta bita da kallo tana murmushi, sosai take jindadin yadda Ummi take daukarka kamar wata wanda ta dade a gidan ba bakuwa ba, akwai mai aiki da Ummi zata iya sakawa ta yi wanke amman ta zabi ta sakata haka ya faranta mata rai, haka take mata idan za a jera abinci ko a kwashe kayan ita da Nafeesa suke kwashe, su kai Kitchen. Ummi na haurawa sama Emily ta tashi ta shiga kitchen ta fara hada kayan ta daurayewa kamin ta saka kumfa. Tana tsaka da wanke wanken ta ji muryar Aliyu ya shigo falon da sallama, duk yadda take zumudi da marmarin ganinsa bata aje ta fita falon ba, har sai da ya leko Kitchen din yana zaton Ummi ce a ciki, don ya san halin Ummi ba girkin kowa take ci ba, haka kuma bata yarda kowa yayi ma mijinta girki ba sai ita. Ta juyo ta kalleshi suka hada ido, sai suka sakarwar juna silent smile mai laushi. "Barka da zuwa" "Barka da aiki" "Kusan sati baka zo gidan nan ba" "Kirgawa kike yi?" "Har da mintunan da dakikun na sani" Ta amsa a nutse cikin sanyi hali mai shiga rai. Ya fadada Murmushinsa. "Na dan tsaya na huta ne, kusan tun da kika bata ban samu wadataccen huta da bachi ba, shiyasa yanzu nake ranko, kuma akwai guraren da ya kamata na leka sai a yanzu nake samun dama, and you need space too, bana son wani bacin rai ya samu zuciyarki a yanzu" "A space? Space din da zai karantar da ni yadda kewarka take? Ya zabtar da idona da kaikayin ganinka? Nisanta kamar hukunta ni ne Aliyu" "Kina ta siye ni da kalamai, ala dole so kike na ji cewar ban kyauta ba" Ta wanke cup ta dauraye. "Da kalamai suna siye mutum, da ka dade da karbar kudina, ina fada maka abun da yake zahiri ne kuma nake ji, ba wai ina kokarin wuce gona da iri ba ne, ina jinka kamar wani ɗan'uwana na jini" Ya hade yawu yadda take maganar softly and calmly ya saka kara jin tausayinta, a kokarinsa na canja maganar ya dauko wata maganar. "Har yanzu lokaci be yi ba da ya kamata ki fara rufe gashinki Emily? Shi ma fa ba muharramina ba ne" "Gashin?" "Uhmm..." "Ina jin sakewa idan ban saka dankwali ba saboda na saba" "Ni kuma zan fi sakewa idan kika saka" Ya cire black facing cap din dake kansw ya jefa mata ta chabe, ta saka a saka a kanta da ta juyo ta kalleshi sai da gabansa ya fadi saboda yadda ta yi maya kyau ga wani lafiyayyen murmushi dake fuskarta. Fa sauri ya dauke idonsa ya juya zai fita. "Aliyu zan iya samu ayi min welcome back din layina?" Ya juyo. "Yeah amman yanzu? Ba sai gaba ba?" "Saboda Vito ne..." Aliyu ya jingina da kofar dakin ya rungume hannayensa. "Vito... Ba wanda ya san inda yake for now, ya boya inda babu wanda ya sani, saboda an tattara duk wani laifi da ya kamata a tattara a kama shi da shi, tun daga kan abun da muke zaton yayi min da kuma sana'arsa, yanzu haka neman sa ake ruwa a jallo, shi ne dalilin daya saka Ummi bata son na koma aiki har sai an kama shi, kuma Daddy ya fada min ana yin duk abin da ya kamata" Fuskar Emily ta sauya. "Idan aka kamashi kashe shi za'ayi?" "Ko dai ba a kashe shi ba, to za a daure shi a gidan yare ne, ba kuma saboda ni kadai ba har saboda ke" "Idan kuma yace ya tuba fa?" "Irinsu suna da wuyar tuba Emily, kuma suna da wuyar sha'ani mai shaye shaye tunaninsa ba daya yake da na sauran mutane ba, haka kuma zuciyarsa bushewa take shiyasa suke aikata abubuwan da ba'ayi tsammani ba, and ke kika ba ni labarin yadda ya dauki rai ba a bakin komai ba" "Ya taimake ni sosai, shi ne mutumen da ya fara yarda zan iya kamin kowa, mutumen nan ya tsaya a tare da ni lokacin da ba ni da gata, shi ya inganta rayuwata ya ba ni gata, ya kula da yarana, idan ya ji ni a cikin damuwa komai yake zai bari ya zo gurina, ba zan so wani abu ya same shi sanadina ba, a yanzu ne da na samu mahaifiyata nake fahimtar kyautatawar da mutane suke min tana da girma" "Rayuwarsa a fili barazana ce ga rayuwata da kuma ta ki, ban sani ba amman na san ba lallai ya fahimci kyautata muke miki ba, zai iya cewa zai dauki mataki da zai iya illataki, don a yanzu zuciyarsa a rufe take kuma daman ya saba dukanki, sannan shi baya son ki zauna da kowa fa karki manta da wannan, kuma idan ya dawo kusa da ke kin san kudinsa, yana son ya aure ki, ke zaki iya aurensa? Bayan kuma ba son shi kike ba?" Ta girgiza kai. "Bana fatan sake komawa dakin soyayya na rufe wannan kofar, bana marmarin zaman aure da kowa, yadda na sami rayuwa a haka ta wadatar" Aliyu yayi shiru be ce komai komai ba, ita ma ta yi shiru ta cigaba da wanke wanke da take cikin rashin dadin rai har da hawaye. Ya juya ya fita ta nufi inda mahaifiyarsa take, ya kwankwasa kofar dakinta kusan sau uku sannan ya tura ya shiga, kwance ya same ta waya a kunnenta tana ta magana da waya Inlaw dinta gwaggon Aliyu. Sai da ta gama wayar sannan ta kalleshi. "Ai na dauka ka yafe mu" "Na isa ne? Na dan huta ne kuma kuma na ba ku dama ku huta, yanzu ma ba zuwan kaina ne ba, Mama Baraka ce ta ce tana son na taho mata da Emily" Ummi ta tashi zaune. "Nice ko jiya ta zo gidan nan kuma sun yi magana" "Toh wata kila tana son ita Emily din ta tafi gidanta ne" "A yadda na karanci yanayin Emilyn kamar bata marmarin zuwa gidan ne shiyasa ban matsa ba, kuma ni kaina ba son zuwanta nake gidan ba saboda Kameela, kasan yarinyar zafin kishinta ya wuce misali za su iya sanadin da za a karawa uwar sauran igiyar ma, da dai ace bata gidan ne zai fi kyau Emily ta tafi, kuma ko zata tafi ba kai zaka kaita ba, ita zata aiko a dauke ta ko kuma a saka direba ya kaita gidan daga nan" "Ta fada min ta shirya mata wani abun mamaki ne, kuma bata son abun ya wuce yau, ban san miye ba amman ya kamata ta tafi" "Sauka ka fada mata idan ta yarda direba zai kaita, kai kam baka da alaka da gidansu Kameela a yanzu dan haka bana son ganinka a gidan, ka bari sai idan Allah ya kaddara Hajiya Bakara ta zama Inlaw dinka wannan dole ka shiga gidan, amman ba yanzu ba" Aliyu yayi mata kallon rashin fahimta. "Ta ina zata zama Inlaw dita?" "Ta abin da kake karyatawa mana" "Babu abun da make karyatawa, Ummi ba abun da kike tunani ba ne, bayan haka kuma Emily fa tsohuwar matar Turhan ce? Ko mutuwa yayi ai idan nw auri matarsa ban kyauta ba, sai yace daman kudirina kenan shiyasa na aikata abun da yake zargina, alhalin har ga Allah ba dan na aikata hakan ba ne" "Saboda me? Haramun ne? Da ka yarda da abun da yake ranka da karka yarda alaka dai tsakaninka da Turhan da Ammy ta riga ta lalace, kuma ba zata taba gyaruwa ba har abada, ni kawai ina fada maka abun da yake gaskiya ne, ba saka ka zan yi na ba hana ka zan yi ba, ai lokaci alhali ne, kuma komai rufin da aka yi idan ta yi tsami dole sai ya fito, na mu ji ne kawai" Ya mike tsaye ya fice daga dakin yana murmushi don ya san duk yadda zai buga misali ko ya ayyana Ummi ba fahimtarshi zata yi ba, nata tunanin take dabam. Falon ya sake dawowa ya nufi Kitchen kamin ya shiga Emily ta fito tana rike da hullar da ya bata, kamar mai tsoro haka ya waiga ya kalli upstairs sannan ya mika mata hannu. "Zan iya samun hulata yanzu?" Ta karasa ta mika masa sai ya karba ya saka a kansa tana kamshin gashin Emily da ya sha gyara da mayuka da turare. "Mama Baraka ce ta kira waya wai tana son ki zo yau gidanta, kuma yanzu nan ma" Emily ta dan wara ido. "Jiya ai ta zo nan, shekaranjiya ma ta zo kamin shekaranjiya ma ta zo kullum tana zuwa" "Toh yau so take ki tafi, kin san daman na mata alkawarin zan kawo ki, amman dai na zan samu zuwa ba direba zai kaiki, ki shiga ki shirya yanzu?" "Ni bana marmarin tafiya gidan" "Haka zaki daure, umarni ne ai nake baki ba neman ra'ayinki ba I'm your boss" Ta bude ido sosai da mamakinta. "Ai ba a gurin aiki muke ba, a nan gida ne, baka isa kamin dole ba" Ya saka hannayensa alhaji duka biyu. "Really?" "Yeah..... Kuma gwada ka gani" Yayi murmushi kawai. "Kin san daman mun saba fada ko? So kike mu tuna baya kenan? Direba yana jiranki?" Ya fada yana nuna mata kofa da ido, sai ta nufi upstairs ta canja riga da skirt din dake jikinta zuwa gown din atamfa har lokacin kanta babu dankwali bata samu Aliyu a falon ba, kai tsaye ta nufi kofar fita ta bude ta fita sai ta hango shi tsaye jikin wata mota dake kunne, na yi kyau? Ta tambaya da motsin baki ba tare da ta fitar da sautin ba, sai ya girgiza mata kai alamar aa ya dauke idonsa tare da hade rai yadda ake yi ma yara, ta san ba zai wuce saboda bata saka dankwali ba sai ta yi murmushi ta karasa gurin motar daya bude mata ta shiga ta zauna tana ta kallon fuskarsa domin kallonsa na daga cikin abubuwan da take so, shi kuma be yarda ya sake hada ido da ita ba ya rufe motar ya juya ya nufi hanyar shiga Falon. Direban yaja motar suka fice daga gidan, tana zaune cikin motar shiru shiru sai kallon titi take, can kuma sai ta yi murmushi. "Aliyu" ta furta sunansa a hankalita kwanta jikin motar tana juya ido zuciyarta cike da nishadi, sai da direban ya shiga gidan sannan ta saita kanta tana kallon rayuwar baya da ta taba shigowa gidan, ta kai hannu zata bude Direban ya ce. "Hajiya dan jira, Alhaji Aliyu yace kar na bari ki fita motar sai matar ta fito, tun da ban san wane bangare take ba" Ya daga wayarsa ya kira Aliyu ya sanar masa suna cikin gidan. Babu jimawa Mama Baraka ta fito ta dayan bangaren da farinciki ta nufo motar da suke ta budewa Emily. Emily ta fito bata wani dauki sosai Mama Baraka ta rumgume ta tana jindadin zuwanta, sannan ta kama hannunta suka nufi bangaren da ta fito, da suka shiga gate din ta ratsa da ita suka shiga falonta, suna shiga falon Emily ta yi arba da Dr AB zaune sai ta saki hannun Mama Baraka ta nufi shi, shi mike tsaye da sauri yana murmushi suka rumgume juna. "Kina lafiya?" Ya tambaya bayan ya dago ta daga jikinsa, sai ta daga mishi kai. "Ina lafiya, yaushe ka zo ya aka yi ka zo nan?" "Saboda ke" Ya kama fuskarta ya rike. "Madam Baraka ta fada min komai, a washe garin da kuka bar gidan, kuma na jidadi da ya zama ina da alaka da ke" Hawaye ya sauko mata ta runtse ido tana jin wani sanyi na sanin cewar shi dan"uwanta ne kuma ya karbeta. "A yanzu na gane dalilin da yasa nake ta son kasancewa da ke Emily, kowace haduwa kaddara ce take shirya mana ita, amman na kasa cireki a raina na kasa manta duk wani abu daya shafe ki, ada ina tunanin kamar na samu mata ne, ban sani ba ashe ke jinina ce, tun dawowarki gidanku zuciyata ta fara raya min kamar kina da alaka da mahaifina saboda kamar da kike da shi ta yi yawa, amman sai na rika tambayar kaina ta ina? Taya yaya? Da kika ba mu labarin rayuwarki, sai na fara tunanin ko sace ki aka yi aka jefar a can? Ko kuma dai bayan Momy mahaifina ya zauna da wata matar? Ita kanta Momy ta fada min kina kama da Mahaifina" "Ina Momy take?" "Tana gida, ni na saboda ke na zo, kuma yau zan koma" "Ta samu labarin abun da ya faru?" "Eh sai dai bata yi maraba ba, bata shirya karbarki yanzun ba" Emily ta kalli Mama Baraka sannan ta kalli Dr AB "Tana da gaskiya, kuma be zama dole ta karbe ni ba, shi kanshi be zama lallai ya karbe ni ba idan ma yana raya" "Yana raye, na kan je na ganshi a duk lokacinda bukatar hakan ta taso, kuma shi mutum ne mai son yara zai yi farinciki dake na tabbata" Emily ta zauna. "Ina son na ganshi, kamanin da ake cewa ina yi da shi ina son na ga ya fuskata take a jikin wani" Dr A-B ya zauna kusa da ita ya ciro wayarsa ya kama hotonshi ya mika mata wayar. Yaran Mama Baraka duk suka fito suka zauna suna kallon Emily. [8/13, 10:39 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣6️⃣ Mama Baraka ta gabatar mata da yaranta suka gaisa da Emily suka rumgumeta. Emily ta zauna tana hawaye. "A tsawon rayuwata, na yi ta ne ni kadai, idan na hango wani mai dangi ko iyaye sai abun ya burge ni, saboda na yi tunanin ni ba ni da kowa, ba uwa ba uba ba yan'uwa ban san yadda ake ji ba, amman hakika iyali suna da dadi" Dr A-B ya kai hannunsa ya rika nata. "Wani lokacin kaddarori sukan faru da mu, wadanda ba mu isa mu canja komai daga karesu ba, idan ka hango wani yana rayuwa mai kyau sai ka ji ina ma kai ne, idan kuma wani yana rayuwa marar dadi sai ka ji dadi da ya kasance ba kai ba ne, hakan yana nuna mana ba mu da ikon canja komai daga kaddarar mu, domin da za mu iya da mun zama irin wadancan da su ke burge mu, tun da ba za mu iya ba, ai sai mu yi hakuri mu da yadda muka samu kan mu, abun da duk ba zaka iya canja shi daga halitta ko kaddara halayya ba toh be kamata ya zama abun damuwa ba" Emily ta daga mai tare da kai dayan hannunta ta rike hannunsa daya da duka hannayenta, ita kadai ta san me take ji lokacin da bata da kowa, haka kuma a yanzu ita kadai ta san yadda take ji da ta samu yan'uwa. "Na san idan Daddy ya ganki zai yi farinciki domin ko yayansa da suke can ba su yi kama da shi sosai kamar yadda ke kike kama ba, kuma mutum ne mai son yara, na kan ziyarce once in a while" Ta yi murmushi ta sauke kai kasa tare da kai hannunta daya ta share hawayenta, jin an taba kofar falon ya saka ta dago ta kalli kofar sai suka yi ido hudu da Turhan, murmushin dake fuskarta ya gushe ta kalli Mama Baraka dake zaune, sai Mama Baraka ta girgiza mata kai ta juya ta kalli Turhan da ya tunkaro inda Emily take zaune, idonsa a kanta zuciyarsa na bugawa ganin hannun Emily cikin na Dr A-B. "Ban ce ya zo ba, ban san da zuwansa ba, yana zuwa nan mu yi magana amman yau ban fada masa zaki zo ba, kuma ba saboda shi na shirya wannan ba, na shirya miki wannan liyafar ne saboda ina sha'awar ki zo kusa da ni, kuma ina nufin baki mamaki da Dr A-B ne, ba Turhan ba" Mama Baraka ta fada cike da tsoron batawa Emily rai. "Ni na ce ya zo" Emily ta kalli Dr A-B. "Ya kamata mu zama masu yafiya Emily, dukanmu muna laifi wa junanmu, kuma akan daga mana kafa a yafe mana, na san abun da ya aikata be kyauta ba, kin ba mu labari, shi ma kuma ya maimaita min cikin nadama, kusan shi ne dalilin zuwa ba wai domin Madam Baraka kawai ba" Emily ya maida kanta kasa tana jin kamar suna son mata dole ne. Dr A-B ya matsa kusa da ita yana mata magana a hankali yadda zata fahimta. Turhan ya zauna a kujerar dake fuskantarsu yana maida numfashi da karfi, be tana sanin yana kishin Emily har haka ba sai a yau da wani wanda ba Aliyu ba ya zauna kusa da ita kuma ya rike hannunta, saukin abun ma tana da alaka ta jini da shi, da ba haka ba wata kila na zai iya zama ya kalli wani yana kallar masa mata har ya rika hannunta ba. "Ni ma na ba shi rashin gaskiya na abun da yayi, kuma ya karba ya nuna min ya fada min kuma na ga hakan cewar yayi nadama, ban fadawa Madam Baraka ba, amman ya fita matsawa na zo saboda yana ganin ina da alaka da ke kamar idan na saka baki zaki iya yafe masa" "Na yafe masa ai, na fadawa Ammy tun satin da ya wuce, komai ya wuce yanzu gaba nake hari" Dr A-B yayi murmushi. "Haka nake so, daman na san baki da wahalar sha'ani, na gode" Turhan yayi murmushi, Dr A-B ya daga ya kalleshi. "Ka yi farar dabara da ka biyo ta gurina gashi ya yafe maka" "Na jidadin hakan, kuma ina son na kora da bayanin yadda aka yi na san Dr AB dan'uwanki ne, na biyo ta bangaren Mama ne, na fada mata komai kuma na roki yafiyarta na roki ta nema min taki, sai ya zama ita ma tana jin tsoro, hakan ya saka na yi kamun kafa da Dr Adam bayan Mama ta fada min komai na rayuwarki, Congratulations Aisha yanzu komai ya samu, ina miki murna" Emily ta kalleshi kawai ta dauke kai. Emily bata sake sakewa ba a falon saboda Turhan yana ciki, not because of bata yafe masa ba, ta yafe masa har zuciyarta sai dai ta kasa jin walwala saboda yana kusa da ita, idonsa akan duk wani motsi nata. Da suka hadu dinning gurin cin abinci Turhan ya zauna saitin da Emily take, abincin kadan ya ci, Emily ma kadan ta ci tana murmushin dole. "A yanzu nan zaki zauna ne?" Dr A-B ya tambaya. "Aa ina zama gurin Ummi ne" Ya dan tabe baki. "Haka Madam Baraka ta fada min, gidansu wannan yaron ko?" Emily ta kalleshi tana murmushi "Aliyu ba yaro ba ne" "Yayi kamar ni?" "Aa amman dai ba yaro ba ne" "Okay, idan kina zon zama can ba laifi, amman dai ki kula da kanki" "I will" Ta aje spoon ta mike tsaye. "Zan shiga bandaki" "Muje na nuna miki" Daya daga cikin yaran Mama Baraka ta fada, ba musu Emily ta bita zuwa sama ta nuna mata bandakinsu sannan ta fito. Emily na shiga ta maida kofar dakin ta rufe ta jingina ta busar da numfashi. "It's okay Emily, that's how life is komai ya wuce, Turhan shi ne uban yarki, na zaki iya canja wannan ba, dole alaka zata shiga, akan yarsa kawai ba akanki ba, yanzu komai ya wuce" Ta fadawa kanka da nufin karfafawa kanta guiwa, sannan taja numfashi ta sauke har sau uku ta bude kofar ta fito. Ta sauko sai ta zauna a sitting room bata koma dinning din ba, ba su san ta sauko ba sai da suka gama cin abinci suka taso. Sai kuma ga Mahaifin Kameela ya shigo cikin sakin fuska ya mikawa Dr A-B hannu suka gaisa. "Ban san ka zo ba, sai da muka yi waya da Mai gida yake tambayar ya ka sauka kuma an mata tarba mai kyau" "Tafiya ce ta gaggauwa shiyasa ban fadawa kowa ba, shi ma ya sani ne saboda wasu dalilai, na zo ne saboda kanwata Emily fatan na same ku lafiya" "Alhamdulillah, muna maka maraba da zuwa, mu shiga ka gaisa da sauran yan gidan mana" Mahaifin Kameela ya rike hannun Dr A-B suka fita falon suna magana ya shiga da shi bangarensu Kameela ya gaisa da su da sauran yaransa, yayi hakan ne saboda Dr A-B da duk sauran business partners dinsa ba su san Hajiya ba, Mama Baraka aka sani da ita yake yawo, a yanzu kuma basa tare. Da suka fita sai ya zama falon daga Mama Baraka sai Misra second born dinta after Emily, and Turhan. Mama Baraka sai jan Emily take da hira sama sama a kasan zuciyarta kuma bata jidadin abun da mijinta yayi ba, domin da ya shigo be kalleta ba balle yayi ma Emily yayi magana, ko da yake a yanzu ba zata kira shi da mijinta ba sai dai uban yayanta. Turhan kan idonsa na kan Emily wani irin kallo yake mata da ya tafi da hankalinsa ya kusa hango masa yadda jini yake yawo a jikinta. Emily ta mike tsaye. "Bari na jira Dr a waje" Mama Baraka ta kalleta. "Ba a nan zaki kwana ba" "Aa maybe wata rana amman ba yau ba" Turhan ya bita da kallo har ta fice falon sannan ya kalli Misra dake kallonsa ya kalli Mama Baraka ya ciro wayarsa ya shiga tabawa. Da Emily ta gaji da tsayuwa sai ta fita gaban gate din bangaren Mama Baraka tana kallon katon gidan, hakan yayi daidai da fitowar Dr A-B bangarensu Kameela suna tafe Alhaji na masa hira, Kameela da yan'uwata da kuma Hajiya suna tsaye jikin gate din bangarensu. Alhaji be karaso ba ya tsaya nesa da bangaren Mama Baraka, Dr A-B ya karasa shi kadai ya kama hannun Emily da bata san Turhan na tsaye bayanta ba domin nata idanuwan suna gurin Kameela dake aiko mata da wani kallo mai cike da tsana da kiyayya. "Ka dawo" Mama Baraka da fitowarta kenan ta fada. "Eh zan wuce yanzu, mun gaisa da su, ashe kina da co-wife ban taba sani ba sai yau" Mama Baraka ta yi murmushi. "Ka ga zuwan ai yayi amfani, daman ba ni kadai ba ce mu biyu ne ita ce uwargida" "Maa Shaa Allah, Emily a nan zan barki ne ko kuma zaki raka ni Airport?" "Zan raka ka Airport" "Okay" Ya mikawa Mama Baraka hannu. "Thank you so much Madam Baraka i appreciate everything" Mama Baraka ta gaisa da shi, kusan abu nw da ya sana shaking hands da kowa. Sannan ya dafa kafadar Emily to him ita ce kadai yar'uwa ta jini da yake da a kusa a yanzu yana jin muhimamcinta fiye da baya. Tare suka nufi mota ya bude mata gidan baya ta shiga shi ma ya shiga yana dagawa Alhaji hannu. Mama Baraka ta shiga dayar motarta tare da Misra. Kameela ta bisu da kallo har motocin suka fice zuciyarta kamar zata fashe saboda bakinciki. "Hmmm, wai ni aka zo a nuna bakinciki, ga mijinta a gafe ta hada da nawa Aliyu ta zabi wanda take so ko? Ga wani yayanta wai shi mai kudi, ga ubanta bature, ga ta kyakkyawa arziki na daya ma ba da aure aka haife ta ba, da yanzu ina zan kai bakinciki nan? Ga Mama Baraka tana kishi da uwata, diyarta kuma ta karbe min miji, ta hada da nata, wannan bakinciki da me yayi kama? Shekarar nan idan ba so ake na haukace ba me ake so na yi?" Ta fada cikin kuka bayan mahaifinta ya bar gurin. "Ke yanzu miye hadinki da Aliyu? Idan ma dafa shi zata yi ta ci ai sai ta yi" Anty Shafa ta fada, Kameela ta kalleta a fusa. "Aliyu mijjna ne, kina tambayar alaka ta da shi? Duk ba ku kika kashe min auren ba? Kullum mijina yana cikin bakinku cin mutunci babu wanda baku masa, idan ku ba ku san shi ni ina son mijina, yanzu ai gashi nan ya sake ni" "Uban waye ya aikeki saka masa guba a abinci? Ke ba dan ya sake ki ya kyale ki ba ai da yanzu ma gidan yari za a kaiki, karyar banza karyar wofi har ke fada mana wani wai kina son shi, kina son shi kika tashi kasheshi? Ko kina son shi kike daukar sirrinki ki kaiwa Bakar Mama Baraka? Yanzu wa gari ya waya?" Anty Shafa ta maida mata da martani. "Idan ban tafi da damuwata gurin Mama Baraka ba ina zan je? Saurarata kuke yi? Burinku Aliyu ya sake ni kuma ya sake ni, ita kuma zata dauki bakar kafirar yarta ta aura masa ai" Hajiya ta daka musu tsawa. "Miye haka wai? Sai yayanta sun kwashe komai sun fada mata an dawo amana mana dariya? Ke kuma Aliyu autan maza ne da zaki zauna kina fadawa yar'uwa ki magana saboda ya sake ki? Ke daga kin auna arziki ma baki haihu da shi ba? Nan da kwana biyu zaki shige wani gidan, daman can Aliyu ba sa'ar auren ki ba ne, manyan mutane suke sonki kika nace sai shi waya sani ma ko ba banxa ya barki ba? Ɗan makiyinmu kika dage sai kin aura kuma kika aura uwarsa ta mana cin mutunci" Kameela ta fashe da kuka ta juya ta koma ciki a fusace. Turhan da ya shiga motar ya dauki hanyar gida, yana jin farinciki sosai domin Emily bata taba sake masa haka ba and he feel something special about her today. "Ina son Emily ba ki sani ba ne, na yi farin ciki kin samu family a yanzu, kuma na miki alkawari idan kika ba ni dama ta biyu ba zaki yi nadama ba, zan maida ke sarauniya zan baki gatan da ba a taba baki ba, ke kika fara dandanin dadin zama uba, ke kika fara saka ni wannan farinciki, kuma kika yarda kika aure ni saboda Ammy, na yi kuskure na sani, amman yanzu na miki alkawari zan jiyar da ke dadi na wadata ki da komai zan ninka miki farinciki fiye da wanda kika sani, shiyasa na yi alkawarin zan yi hakuri zan jira har ki aminta da ni, kalli yadda kike da kyau da shiga rai, kika ba ni ƴa mai kamanina, to me kuma zan nema a gurinki? Sai dai ni na nemi saka miki, ina son komai naki Emily ina son duk wani abu daya shafe ki, zan kaiki inda ban taba kaiki ba, zan siya miki tufafi mai tsada, zan rumgume ki na nuna miki yadda nake kaunarki na baki kulawa" Yana tuki da hannu daya dayan hannunsa kuma yama shafa kansa yana magana da kansa sai murmushi yake kai kace Emily ce kadai matar da ta rage masa a duniya. Ya isa gidansu tun kamin ya faka motarsa harabar gidan Ammy ya fahimci akwai baki a gidan domin yayi arba da manyan motoci da be tantance na waye ba. Ya faka motar ya fito yana kallon motocin ya tun kari kofar falon, sai kamshin turaren masarautarsu ya tunkari hancinsa. Ya tura kofar da hanzari ya shiga, dogaran da ya fara arba da su suka saka shi fadada murmushinsa, ya kai tsakiyar falon yana jin wata madarar dadi sakamakon arba da yayi da mahaifinsa zaune a falon na Ammy. EMILY POV. "Na ga nadama sosai a gurin mutumen nan, kuma na jidadi da kika yafe masa, kuna da ƴa a tsakaninku ya kamata ace kun fahimci juna" Emily dai ta yi shiru bata ce komai ba sai kallon titi take. "Duk inda namiji ya kai, Mutumen nan ya kai, kuma na tabbatar yayi nadama tun da har yake bibiyarki, wata kila baki san komai akan sarauta ba, amman dai samun dan sarki babban mutum kamarsa yana zubar da kai kasa da neman yafiya abu ne da ba a saba gani ba, shiyasa na yarda da nadamarsa, kuma dukanmu muna kuskure, turawa suka ce the devil you know is better than the angel you don't know, ina son ki san babu mai cilasta ki yi komai, amman dai ki yi a hankali, kar wani ya sake breaking heart dinki" "Turhan ya fada maka wani abu akan abokinsa ne?" Dr A-B yayi murmushi "Ya fada min yadda abokinsa ya ci amanarsa kuma yayi rawa yayi tsaki wajen ganin baki saurare shi ba, bayan wannan be fada min komai ba, ina miki wani furuci ne saboda ina hararo wani abu na dabam, kuma na san yadda halinmu maza yake ai, ki yi taka tsantsan" "Aliyu ba kamar sauran mazan da na hadu da su ba ne, a rayuwa ban taba haduwa da wani mutum mai rikon addini da gujewa tsaba addininsa ba kamar Aliyu, yana da amana, adan karamin lokacin da muka san juna da shi sosai na fahimci mutum ne mai kyaun hali ya nuna min kula, ba tare da duban addinina ba, ko Vito da ya maida ni yadda nake ya maida ni ne saboda na yarda na bar addinin musulunci na dawo nasa, amman Aliyu be taba duba wannan ba, ko a lokacin da ya taimake ni be san wacece ni ba, ya bi ni har a gidanku saboda ya damu ya san halin da nake ciki a lokacin da ban yi tunanin akwai wanda zai da mu da ni ba" "You trust him ko ba haka ba?" Dr A-B ya tambaya da murmushi a fuskarsa. "1,000%" Ta fada ba tare da fargaba ba. "Kin yarda da shi saboda wasu abubuwa da kike jin kin gamsu da su, hakan yana da kyau, amman dai duk da haka ki yi hankali" "Dukanku ba ku fahimce ni ba ne, Aliyu ba so na yake ba, ni ma ba son shi nake ba, ni ban shirya soyayya ba, ba a yanzu ba ko a nan gaba" "Time will tell, amman dai idan lokacin yayi ina fatan wani ne wanda na sani" Ya nuna agogon hannunsa sannan ya bude motar ya fita, ita ma ta fita, ta raka shi har ciki sai da zai shiga jirgin sannan yayi mata side hug. "Ki kula da kanki, a yanzu ina tunanin babu wata damuwa a tare da ke, idan ma akwai wani abun da kike so ko kike neman taimako ki sanar da ni" "Na gode sosai na jidadin da kake nuna min kulawa" "Always, idan komai ya laba abubuwa suka tafi daidai zan gabatar da ke a gurin Daddy, babanki mai kudi ne yarinya zaki shakata... Na gode da kika karbe ni a matsayin dan'uwanki na yi farin ciki da hakan" Ta yi murmushi tana kallonsa "Bye Sis" "Bye Bro" Ya juya zat tafi sai ta rumgume shi tana kuka, ya juyo ya rumgumeta yana murmushi, ta sake shi ya share mata hawayenta, sannan ya daga ma Mama Baraka hannu ya wuce. Emily ta juya ta nufi gurin da su Mama Baraka suke tsaye ta tsaya gaban mahaifiyarta tana kallonta Mama Baraka ta kasa tsayar da idonta guri daya saboda kunyar Emily take ji. Emily ta rumgumeta ta ji sanyi a ranta a yanzu tana da mutanen da zata kira da sunan yan'uwanta na jini. Mama Baraka sai hawaye ya sauko mata ya rumgume Emily kamkam ta lumshe ido. Misra ta kai hannu tana shafa bayan Emily tana murmushi. Motar Mama Baraka Emily ta biyo, Mama Baraka ta tuka ta har gidansu Ummi tana jin kamar ace za ta iya ta roke ta ta kwana a gidanta, amman ta kasa, daman kuma Emily ta fada cewar tafi son zama a gidan Ummi. [8/16, 8:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣7️⃣ Turhan ya kalli Ammy dake sanya da Hijab tana zaune can gefe, ya dube manyan Bakin da mahaifinsa ya zo da su. Sai ya zube gaban mahaifinsa yana jin farincikinsa ya ninku marar misaltuwa. Ya kwashi gaisuwa ya sake kwasa sannan ya hannun mahaifinsa ya sumbanta ya shafa goshinsa a kai. "Ihlan beek ya farḥat ʿomri, sharraftna ya baba w nazalt fi bēt al-mara illi hia ḥayāti.” _Maraba da zuwan mutumen da shi ne farinciki, na jidadi ganinka mahaifina na jidadin da ka sauka a gidan macen da ita ce Rayuwata._ Mahaifinsa ya yi murmushi kadan babban abokinsa da yake tare da shi ya ce. "Mun biyo sawunka na, domin mun lura idan ba mu yi haka ba na zaka gane cewar kana da muhimmanci a gurinmu ba" Ya kalli Mahaifinsa yana murmushi "Na san inda da muhimmanci tun a ranar da ka saka siya ticket aka yi min fatan sauka lafiya, soyayya ce ban tabbatar da ita ba sai a yau, ko a mafarki ban taba saka ran kafarka sata iya taka gidan nan ba, ta ina kuka samu adireshin?" "Ta hanyar Mai Martaba" Ya nuna Ammy da bata ko kallon inda suke zaune. "Gurinsa muka fara sauka, shi ya saka yi mana jagora har zuwa nan" Abokinsa mahaifinsa ne yake amsa masa mahaifinsa be ce komai ba sai hannu da ya kai ya shafa kan Turhan. "Ya labarin mata ta samu?" Sai a lokacin ya tambaya, Turhan ya rage murmushin da yake. "Har yanzu bata saurare ni ba, bata aminta zan iya kula da ita ba, bata yarda zan bata kulawa ba" "Baka fada mata ƴaƴan sarakuna basa karya ba?" "Bata duba komai daga sarautarmu ba, zuciyarta ta bushe da kiyayyata, ko wace gangar na buga bata ƙara" "Ƴar wane Sarkin ce?" "Ita din ba jinin sarauta ba ce" "Tana da tsada ne har haka? A nawa za mu siye ta?" "Kudi ba matsalarta ba ne, ko nawa za a zuba ba zai siyeta ba, amman zan jira zan biyaya har na yi nasara domin na fara ganin alamar hakan a yau" "Kar jiran wasu Iyalin ya saka ka, ɓata wasu Iyalin ko na manta kana da mata a gida?" "Ban manta ba, ba zan yi kuskuren aikata wani kuskuren ba, nakan kirata bata amsawa na aika mata sako babu amsa, ni kuma sai na zabi daga mata kafa har ta huce, na maida hankalina gurin gyara abun da na bata, kuma an samu lokaci da ƴata" "Ina sanyin idanuwan take?" Sarkin ya tambaya da nufin Fatima. "Tana tare da mahaifiyarta, ta kan zo ta kwana biyu ta koma" Ya kama hoton Fatima ya nuna Mai Martaba a wayarsa. "Wata kila har yau baka bata damar sanin ainahin waye kai ba, baka tunanin idan muka saka  baki zata amince?" Turhan yayi shiru yana nazari... "Da ace babu wanda yake zugata, babu mai saka baki, na san zata saurare ni, wani abun ba halin ta ba ne, a gidan da take zaune ne suka tsara mana komai, saboda abokina ne yana neman ya bata ni a gurinta shi kuma ya gyara kansa, wannan dalilin ya saka suka kiraka suka sanar maka saboda su bata ni a gurinka..." Ya labarta masa kadan daga abun da Aliyu yayi masa. "A ina iyayenta suke?" Turhan sai ya ki yarda da fadawa mahaifinsa asalin wacece Emily, saboda kar ya rage mata ƙima a idon mahaifinsa. "Mahaifinta Bature ne, nan yake zaune ba, mahaifiyarta kuma kawar Ummi ce wannan dalilin ya saka Aisha take zaune a gidansu Aliyu karkashin kulawar iyayensa" Shiru ya ratsa falon Mai Martaba be sake cewa komai ba, Turhan ma haka, ganin hakan ya saka Ammy ta mike tsaye, suka bita da kallo har ta haura sama. Mai Martaba ya kai hannunsa da kansa ya dafa kafadar Turhan. "Akwai kyakkyawan mata da yawa a jinsin larabawa, idan har matarka bata maka, akwai daga dangi na nesa da kusa, kai din mutum ne mai kima, ka yi iya yadda zaka iya ta fahimci, idan ta zabi ba zata zauna da kai ba, wannan ma shi ya fi alheri" "Matsalar ba ta neman yafiyarta ba ne kawai, ta neman soyayyarta ne" "Muna bautawa mata muna nuna musu soyayya da girmamamwa, amman balaraben mutum be yarda a wulakanta shi, be yarda mace ta taka shi, suna girmamamu muna ba su hakkinsu, karka manta kai namiji ne, kuma ɗan sarauta, karka bari ta gano rauninta, kuma karka bari makiyinka ya gano inda zame yake a jikinka, tun da har abokinka ya shiga gabanka to ka yi kokarin ganin be illataka" Mai martaba ya mike tsaye baya ya zuba masa wannan karatun a cikin kai. "Za mu tafi, wata kika za mu dawo kamin tafiya, wata kila kuma zan tafe tare da kai ne, ta kan iya yiyuwa na tafe na jira zuwanka, ka mika gaisuwa ga mahaifiyarka" Ya fara takawa cike da kasa mutanen da suke tare da shi suka rufa masa baya, sai da suka fice sannan Turhan ya fita ya tsaya kofar falon yana kallon manyan motocin har aka wuce da su, sannan ya juya ya koma ciki jiki a sanyaye ya shiga gurin Ammy ya sameta tana waya da wata kanwarta, ya zauna har sai da ta gama. "Ban yi saton ganin Sarki a gidan nan ba" "Yana sonka mana, ba abun mamaki ba ne" Ammy ta fada. "Yayi miki wata magana kamin na zo? Ya fada ai zuwan ba nawa ba ne kadai har da duba lafiyarki" Ammy ta dan yi shiru, da halshe larabci ta maimaita masa abun da ya fada mata. "Yace sun kawo jira, kuma sun zo neman afuwa da rokon na bari dansa ya zauna tare da shi wai yana fatan ban rike shi a rai ba" Turhan yayi murmushi. "Wata kila da Mai Martaba ya shige min gaba, da Aisha ta fahimce ni, ko da yake zugata suke ba lallai ta fahimta ba" "Kai kana ganin idan Mahaifinka da kansa ya nema maka aurenta zata ce aa? Ai iyakar kyautatawa fa mun mata, ba zama lallai ta duba wannan ba, amman a matsayinta da kuma indai mutum kamar mahaifinka zai nemi aurenta zata amince mana, be kamata ace ta bar zuciyarta ta kone akan kuskure da kowa yana yi ba, wasu ma mazan sun fi haka munanawa, ni kam dai na sauke zancenta tun da ba yar gwal bace, an san an bata mata amman ba amfanin rike abu kayi ta jayayya ko dan yarinyar nan ba zata duba ba, amman ka tsaya tsayin daka kai dai a yanzu ita kake so wata kila kana tunanin kamar idan ba ita ba ba zaka sake samun haihuwa ba? Toh, Allah yasa ta zama alheri gareka kai ma ka zame mata" "Aa Ammy ba haihuwar ce kawai nake dubawa ba, ina duba rashin kyautar da na yi kuma Allah ya tashi ba ni haihu sai ya ba ni da inda ban yi zato ba, ta cancanci komai a gareni saboda mahaifiyar Fatima ce, kuma...." Yayi shiru ya sauke kansa kasa. "Ammy ina son Aisha.. Ina sonta sosai ina sonta sai a yanzu na gano haka" "Tohm Allah ya baka ita cikin sauƙi, ni ma ina son zamanku tare da farko, bayan abubuwan nan sun faru sai na ji ta fice min arai saboda abubuwan da ta yi kuma ta kalli tsabar idona ta fada min bata sonka, Turhan duk wanda baya sonka bana son shi Wallahi, kuma saboda Aliyu da iyayensa ina son ka maida matarka, na yi kuskure da na cilasta maka sakinta" "Wani lokacin abubuwa sukan subuce a hannunmu, ko a halshe bama iya rike su, sai dai ki taya ni da addu'a" "In Shaa Allahu, amman kasan akwai abubuwan da ya kamata mahaifinka ya sani a game da ita kuma baka fada masa ba" "Bana son na sanyaya kudurinsa ne, inda Emily tana tare da ni duk abun da zai biyo baya mai sauki ne" "Gobe zan je na yi na yi magana da ita, bana sin bata ran Mai Martaba kuma zan koma ko dan na shirya da matata, zan rika zagayowa lokaci zuwa lokaci" Ammy ta sauke numfashi kawai bata ce komai ba. EMILY POV. Bayan Mama Baraka ta wuce, Emily ta haura sama ta shiga dakinta ta zauna bakin gadon dake dakin zata kishingida kenan ta jiyo sauti karatun qur'ane a wajen Window da murya mai dadi. Mikewa ta yi tsaye ta yaye labulen ta bude Windows din sai ta hango Aliyu zaune akan beach chair Fatima na zaune akan cinyoyinta hannunsa rike da waya yana karatun kur'ane. Ba wannan ne karo na farko da ta taba jin karatun kur'ane ba, amman wannan ne karo na farko da taji kira'ar da ta yi mata dadi sosai ta tsuma jikinta ta tsara zuciyarta har ta zubar da hawaye, bata jin komai daga kalman labarancin amman jikinta da zuciyarta suna karbar sakon. Juyawa ta yi ta nufi wardrobe dinta ta dauko karamin mayafi ta rufe kanta fito dakin ta sauko kasa kuma sai ta yi sa'a babu kowa a falo, ta bude kofar ta fita ta zagaye ta kofar garden, cikin sanɗa ta bude kofar saboda kar ta yi kara, ta shiga tana takawa a hankali ta kusa isa inda yake sai ta zauna a kasa tana kallon bayansa domin ya bawa kofar shigowa baya ne. Tagumi ta yi da hannayenta biyu tana kallonsa, hawaye take irin hawayen da suka sha banban da wadanda ta saba yi, wata kila saboda Aliyu ne yake karanta ya saka ta ji dabam, wata kila kuma a yanzu sakon yake son isa ga gabobin jikinta. Sai da ya gama karatun ya kashe wayar sannan ya sauke Fatima daga kan kafafuwansa ya mike tsaye ya rike hannunta. "Muje ciki" Ya juyo tare da ita, arba da Emily zaune a kasa ga fuskarta da hawaye ya daga masa hankali sosai duk kuwa da murmushin da yake gani tare da hawayen. A take ya saki hannun Fatima. "Fatima tafi ciki zan yi magana da Momy" "Miyasa take kuka" "Shi nake son na ji" Fatima ta fice gurin tana yi tana waigen Emily. Sai da ta fice sannan Aliyu ya karasa ya ɗurkusa gaban Emily. "Lafiya? Me ya faru? Mama Baraka ta yi wani abun ne?" "Hawayen ba na tsakanin mutum da mutum ba ne, tsakanin Rai da Mahaliccinta ne, Wallahi na dade da gamsuwa Allah ɗaya ne, wannan dalilin ne ya saka karbar musulunci ya zama abu mai sauki a gurina, ban sani ba ashe ma a musulma aka haife ni. A yau na ji karatun nan dabam, ban taba jin karatun da yayi min dadi ya tsuma jikina irin naka ba" Aliyu ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yi murmushi ya zauna a gurin. "Shi Alkur'ane abinci ne ga ruhi, waraka ce ga ko wace cuta, kuma tsira ce ga kowane rai, ga dadin karantawa, ga dadin sauraro ke ma wata rana zan so na ji yadda ta ki kira'ar take" "Anya zan iya?" "Idan kina tare da ni akwai abun da ba zaki iya ba?" "Ta ko'ina Aliyu kai ZaKi ne, ka tare duk wata kofa da zata nuna gazawata" "Saboda babu gazawa a tare da ke, na yarda da ke fiye da yadda na yarda da kaina, miyasa kike kwankwanto akan abun da ni na hango shi tun kamin ki fada" Ta share hawayenta tana murmushi. "Ta ko'ina fari kake Aliyu, har yanzu na kasa ganin dogon bakin a tare da kai, na kasa ganin abun da ake ta nuna min akanka" "Ke ce mace ta biyu bayan mahaifiyata wanda ta yarda ba ni da aibu kuma bana yin mata laifi, hakika Emily ke ta musammance" "Kai din gwanin magana ne, ka iya kalami, kowane harafi yana ratsa cikin jikina ya fahimtar da ni abun da da ban fahimta ba" "Saboda kin iya saurare ne, kusan ni bawa ne duk wani abun da sarauniya take son ta ji, halshe ne yake sarrafawa ya fada ba tare da neman izinina ba, jindadin yadda kike ba ni lokacinki, alfarma kike min na san ai ban cancanta ba, na gode da karramawa" "Sai ka rika yin abu kamar ni din wata ce Aliyu" Ta fada a shagwabe kamar mai shirin yin kuka. Ya duba ko'ina ya ga babu mai ganinsu. "Ni na taba fada? Sam sam sam ke din ai ba wata ce ba, ke Emily ce mace mai kyakkyawar zuciya, ga hakuri da juriya, macen da data sha wahalar rayuwa kuma ta cancanci girmamawa d soyayya daga gurin kowa, ba zaki taba zama wata ba, wata yana nufin wata wanda ba kowa ba, ke kuwa mutum ce har da rabinsa" Ta yi murmushi ta sauke kanta kasa. "Idan an min izini, ina son zan shiga ciki kin san ke ba muharramata ba ce, kuma a musulunci babu kyau mace da namiji su kebe su kadai" "A har a nan da yake fili kuma da rana?" "Ai bana iya banbance dare ko rana idan kika tsare ni da idonki, kwarjini kike min komai girman guri sai inji kamar muna a cikin karamin daki ne, shiyasa nake ta taka tsantsan kar na bata miki rai, Emily, au Aisha yau kin yi shiga ta mutumci na jidadin laifinsu ne basa fada miki yadda kike musu kyau shiyasa baki damuwa ki rufe kanki da jiki" "Su wa?" "Tufafin mana? Ita mace ai tsada ne da ita, shiyasa idan suka killace a jikinta suke yin kyau, basa son rabo da ita" "Haka suke fada maka?" "Haka na gani rubuce a fuskarki, ki daina musu da abun da baki iya canjawa Aisha kina yi ma tufafi kyau" Ya mike tsaye ya fice gurin ya barta a nan zaune a gurin fuska da murmushi, zuciya da annuri. Tunanin Aliyu ne raya daren Emily, tana ta tunanin da be ma kamata ta fara shi yanzu ba, ba zata iya cewa son Aliyu take ba bata shiryawa ma wannan ba, amman tabbas shi din na musamman ne a gurinta yana da wani mukami mai girma a zuciyarta a idonta kuma yana da nauyin kimar da ba zata iya aunawa ba. Sautin karatun Kur'ane ya tashe ta daga bacci ta bude ido ta juya ta kalli Blue-Tooth din dake aje kusa da kunnenta na dama, sannan ta juyo ta kalli Fatima dake zaune tana kallonta. "Momy kowa ya tashi tun dazun ke ce kawai baki tashi ba, har Uncle Aliyu ya zo ma, shi ne yace na kawo wannan redio mai magana amman kar na tashe ki" Emily ta yi murmushi ta janyo yarta jikinta. "Hmmm ban kwanta da wuri ba shiyasa na ke bachin safe" "Uncle Aliyu yace na rika kunna miki  karatun kina sauraro idan an je na saka carji yace zai rika biyana kudi idan ina haka" Ya shafa fuskar Fatima. "Fatima kina son Aliyu ko?" Ta daga kai. "Yes" "Sosai?" Ta daga kai. "Shi da Dady wa kika fi so?" Sai ta rake murya kamar mai rada tana zare ido. "Dady, amman karki fada masa" Emily ta yi murmushi. "Momy ke har yanzu baki yin sallah? Kowa yayi sallah da safe, ke har yanzu ba zaki yi sallah ba? Gidan Ammy ana sallah nan ana sallah miyasa baki yi? VITO baya nan babu wanda zai dake ki" Tana maganar tana yatsina fuska. Emily ta tashi zaune. "Kin fara dawowa da halinki ne Fatima? Fada min magana any how?" Fatima ta yatsina fuska ta sauka kan gadon ta fice. Emily ta juya rai a ba ce tana sake arba da Blue-Tooth din da Aliyu ya aiko mata sai bacin ran ya gushe murmushi ya cika fuskarka, ya matsa ta kai hannu tana shafa Blue-Tooth din. Sai kuma ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki ta wanke bakinta da fuskarta ta fito, sleeping dress din da suke jikinta masu kama jiki ne, saboda ta girmama Aliyu ta dauko daya daga cikin hijab din da Ummi ta aje mata green ta saka sannan ta fita. Aliyu na tsaye yana magana da Nafisa Fatima na rike da kafarsa tana lilo, Emily ta fara saukowa sai duk suka kalleta. "Wow kin ga yadda kika yi kyau?" Cewar Nafisa, Aliyu ya kalleta daga sama har kasa ya sauke kansa kasa be sake kallonta ba har ta sauko, be kuma fasa murmushin da yake ba annuri ya cika fuskarsa. "Ina kwana Emily" "Lafiya kalau" Ta amsawa Nafisa sannan ta kalli Aliyu da already ya juya. "Ina kwana" "Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah" Ya juyo da sauri ya kalleta murmushin dake fuskarsa ya fadada, sai dai be ce mata komai ba sai da Nafisa ta shiga dakin kasa. "Alhamdulillah.... Baki taba fadin wani abu mai dadi irin wannan ba, musulunci zai miki kyau Emily sosai" Yaja mata kujera. "Bismillah zo ki karya" Ta nufi dinning din ta zauna tana tambayar ina Ummi. "Ta tafi dubiya, tace ba zata dade ba, bari na duba waje" Fatima ta amsa sannan ta fita da gudun wajen. Aliyu ya zuba duk wani abu da yake son karyawa da shi ya dauki plate din. "Zan shiga ciki na karya, ni ma yanzu na shigo" "Har a cin abinci nan din ya mana kadan ne?" Ya kalli gurin kamar wani bakonsa. "Kin manta karatun jiya ne?" "Aa da dare ma da shi na kwanta ina ta bita" "Allah yasa dai kin haddace" "Ido ma suka haddace abun da suka gani, balle abun da kunnen ya ji, ya ratsa kwakwalwa ya zauna a zuciya?" Aliyu ya sake dubanta da kyau ita da shi suka sakarwa juna murmushi. "Da alama dai ba zan sha wahala ba gurin taya hajarna" "Ai tuni aka siyar maka farashi daidai da aljihunka" Ya sauke yin murmushi amman wannan karon mai sauti, ya juya rike da plate dinsa ya haura sama. Sai da ya shiga dakinsa ya zauna sai wani tunanin ya fado masa, a take murmushin dake fuskarsa ya gushe yanayinsa ya sauya, abincin ma kasa ci yayi sai ruwan Tea kawai ya sha. Emily na fara cin abinci sai ga Fatima ta turo kofar falon ta shigo da gudu. "Momy Dady ya zo tun dazun yace na kira ki" Emily ta aje spoon din hannunta, har ta yi kamar ba zata fita ba, sai kuma ta mike tsaye ganin yadda Fatima take ta rawar jiki. Ta nufi kofar da Fatima ta bude ta fita. Turhan na zaune cikin motarsa dake bude kafarsa daya tana waje, fitowa, tun da ta fito ya daga kai yana kallon be sauke ba be kuma kyabta ba har ta iso inda yake, idan yace a cikin hayyacinsa ya fito cikin motar ya tsaya a gabanta yayi karya, domin giyar kaunarta ce ta rinjaye ta hankalinsa. "Abun bakinciki ace idan kika tashi da safe, wani ne zai yi arba da kyakkyawar fuskarki ba ni ba" Fuska babu yabo ba fallasa ta ce. "Na yi tunanin wani abu mai muhimmanci ne ya kawo ka" "Duk wani abu da ya shafe ki mai muhimmanci ne a gurina Aisha" "A yanzu ko?" Ya sauke kansa kasa yana jin nauyinta. "Har yanzu kina kallon abun da ya faru baya, kin kasa fahimtata Aisha, wasu na shirya min gadar zare wasu kuma sun gagara gane lissafina da abun da nake ji a zuciyata, ki yi hakuri dan Allah ki yafe min" "Ina tunanin mun kai karshen wannan tuntuni, na yafe maka Turhan" Ya kalleta. "Zaki yarda ki sake zama da ni?" "Aa" Ya dauke wuta na dakiku. "Na zo ne na jaddada miki cewar ina kaunarki Aisha, kuma zan tafi Sudan na san ba za ki so na tafi da Fatima, zan barta a nan saboda jindadinki, amman na zan dade ba zan dawo, kuma ina son na tafi da Fatima a yau ta ga mahaifina" "Yayi kyau, idan ka dawo idan ba wani abu ne da ya shafi Fatima ba toh ba dole sai ka zo ka gan ni ba" Yayi murmushi yana jin zafi a zuciyarsa ko kadan be yi zaton duniya zata juyo masa dayan shafinta ba, be yi tunanin zai zo yana rokon mace watan ma Aisha, sai kuma rayuwa ta kawo shi nan. A ka'ida be kamata ace yana zuwa gidan makiyinsa ba, mutumen da ya shirya masa zagon kasa kuma yayi masa gadar zare, amman yana zuwa saboda Emily. Ya bita da kallo har ta koma ciki sannan ya kurdusa ya rumgume yarsa, sannan ya kama hannunta ya saka ta mota shi ma ya shiga suka bar gidan. Ta dawo ta zauna tana cin abincin zuciyarta nata tunanin kalaman Aliyu, shi fa ba saurayinta ba ne amman kalamansa sun ratsa ko wane ɓar go na jikinta, ko Khaleefa da ta san asalin soyayayya suka yi kamin aure be zuba mata baiwarsa kamar haka ba. Ta ko'ina Aliyu ya kai namiji, yana da kyau ga siffar irin ta mazan da suka amsa sunan maza ga addini da dabi'a mai kyau, ga tausayi da kulawa, yana taka tsantsan da ita da bacin ranta, yana kokarin ganin ba su wuce gona da iri ba, ba kamar Turhan da yake sonta a yanzu da ta zama mutum ba kuma ta haifa masa yarinya, ba kamar Vito dake kokarin taba jikinta ko dukanta ba kuma ya tsani yarta, ko da yake shi din ma bata gama sanin waye shi ba, kuma be zama lallai yana sonta ba, ta kan iya yiyuwa ita din ma ba tsarinsa ba ce. Kuma anya ta shirya a yanzu? Bata hankara cewar ta yi nisa ba sai da karar aje plate a dinning din ta dawo da ita duniyar hankalinta, ashe Aliyun ne tsaye a gabanta take kallo bata sani ba, zabura ta yi sai ta lumshe ido tana murmushi. "Kina nan kina lissafina a zuciyarki ko? Kaman ni na, dabi'una siffofina, da kuma tunanin ko haka nake ko zan canja a gaba?" Ta bude ido mamaki ya cika ta. "Ta ya ka sani?" Ya dauki plate ya rufe abincin da be ci ba. "Zuciyata bata karya akan duk wani abu da ya shafe ki, ita take ayyana min abubuwa akanki, shiyasa da kika gudu ta hararon inda kike boya, da kika bar min wasiyar rike Fatima ita ta fada min kina kokarin giving up ne, ta haka nake iya hango hasken dake zuciyarki a game da addinin Musulunci tun kamin na ji labarinki, ita ta taimaka min gurin gasgata gaskiyarki tun gabanin tafi da ni a duniyar tarihinki" Ta lankwafar da kai kamar zata yi kuka ido cike da shagwaba. "Wai kai wane irin mutum ne Aliyu?" Ya nuna kansa. "Wai ni? Mutum ne kawai" "Na musamman?" Ta fada a sigar tambaya. Sai ya dan sirinar da kai kadan ya cire facing cap din dake kansa. "Eh, ga ta musamman..." Ta dauke kai tana murmushin da be taba ziyarta ba, shi ma ya dauke kai yana maida hullarsa hakoransa a bude. Bayan sallah azahar tana Kitchen ita da Ummi suna hada lunch ma Aliyu da be iya cin tuwo miyar kubewa da mai aikin Ummi ta girka ba, sakamakon fitar da Ummi ta yi bata dawo da wuri ba sai ta kira waya cewar mai aikin ta girka. Shi kuma ya ji ba zai iya ci ba saboda be ci wani abin kirki ba da safe ba cikin ya zama empty be shirya sabunta shi da tuwo ba. Ummi na mata zancen komawarsu Abuja a satin da zai shigo, da kuma yadda take ganin kamar Ammy ba zata yarda a tafi da Fatima ba. Emily kuma tana wata duniyar bata ma san me Ummi take fada ba bata komai sai murmushi ta kallon wani gurin alamar hankalinta baya jikinta. Ummi ta taba ta. "Ke... Lafiya?" Emily ta zabura sai kuma ta fashe da siririyar dariya. "Ba komai Ummi" Gogan kamar ya san wainar da ake soyawa, sai ga shi ya shigo kitchen din dubawa idan abinci ya dahu cause he's starving, be ma san da Emily ake girkin ba, sai dai ganin bakin Ummi sake da mamaki jin Emily da fitar da sautin dariya. Ya saka shi tambayar mamakin da ke fuskar Ummi. "Lafiya?" "Aa dariya take yi?" Ya kalli Emily? "Are you okay?" Da Emily ta san Ummi ba ita take kallo ba sai ya turo baki gaba tana murmushi mai dauke da shagwaba ta girgiza masa, ya san kan garin ya fahimcin karatun tun ba a biya masa aya ba, yana son yayi murmushi ba dama saboda Ummi tana Kitchen sai kawai ya dauke kansa ya nufi fridge, a yayin da idon Ummi ya dawo kan Emily sai ta yi hanzarin sauke kanta kasa kamar ba komai. Aliyu ya dauki ruwan da ba su ya shigo sha ba ya fice gonar annashuwa ta yaɗu a kirjinsa. Sai da ya fice suka kammala shirya komai sannan Emily ta kalli Ummi ta ce "Ummi yanzu idan ina son, na sake zama musulma zan cigaba da ibada ne kawai? Kuma kina ganin Allah zai karbe ni? Zai yafe min barin addinin da na yi a baya?" Ummi ta aje cup din hannunta tana kallon Emily da mamakin abun da ba su yi zatonsa yanzu ba. "Kina son ki dawo musulunci ne?" Emily ta daga kai with so emotional. Numfashin Ummi ya fara rawa saboda farinciki. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" Ta juya ta fice Kitchen din da sauri jikinta har mazari yake. A falo ta samu Aliyu zaune yana durawa cikin ruwa. "Zan fada maka wata magana amman sai ka ba ni tukuici" Ya kalli Ummi gabansa ya dan fadi ba dan tsoro ba sai dan abun da be san miye ba. "Toh Ummi haka nan zan bada tukuici ban san girman albishir din ba? Idan aka min wayo fa?" "Wannan mai nauyi ne, Emily tana son ta musulunta" Ummi ta fada idonta fal da kwalla, Aliyu ya mike tsaye babu shiri ya leka Emily take tsaye bayan Ummi. "Seee.... Riiii.. Seriously?" Emily ta daga mishi kai, ya juya ya juyo ya daga hannunsa sama ya sauke kasa ya jimke. "Yes.... Yes... ALHAMDULILLAH YA ALLAH" Ya saka hannunsa aljihu ya ciro keys din ya bude hannu Ummi ya saka mata ya ciro Atm dinsa ya danka mata. "Ga tukuicinki nan Ummi" Ya rumgume Ummi cikin farinciki da emotional domim babu halin rumgume Emily dake tsaye hannayenta a baya tana lilo da su hawaye na sauko mata. Ya saki Ummi ya karasa gurin da Emily take tsaye. "Da gaske kin shiryawa wannan?" Ta daga kai. "Ba dan cilastawa ko tsana ba?" Ta daga kai. "Karki yi musulunci saboda farantawa kowa, ki yi musulunci da gaskiya da mana da kaunar Allah ta tsoron azabarsa da kwadayin rahamarsa, saboda mutane suna canjawa suna gushewa, Allah baya taba sauyawa yana tare da bawayinsa na gari a kowane irin hali" "Ina son Allah Aliyu, saboda shi zan yi na san shi ya saka min gamsuwar da nake ji, na shirya ko da zan sake shiga halin da na ninki wanda na shiga a baya, ba zan sake kuskuren barin addinin aminci da salama ba" "Ina son zan musuluntar da ke Emily ki min wannan alfarmar" Ta daga mishi kai. "Zan fadi wasu kalmomi ki maimaita da su ake shiga musulunci, saboda shi addini ne mai tsari da dokoki" Ta daga mishi kai tana hawaye. "Ash-hadu an lā ilāha illallāh, wa ash-hadu anna Muhammadan rasūlullāh" Yana fada tana maimaita da larabci da suka gama ya maimaita mata da hausa. "Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na shaida cewa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne" Ta maimaita kowace kalmar cikin kuka da aminci da rahama da narkewar zuciya. Aliyu ya duka gabanta ya rike kansa, Ummi ta rumgume ta tana kuka kamar yadda Emily ma take kuka. [8/19, 7:16 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣8️⃣ Aliyu da kansa ya daga waya ya kira Mama Baraka ya yi mata albishir da labari mai dadi, sai gata ta dira gidan cikin farinciki ita da duka yaranta suka wuni gidan har dare sannan suka tafi. Washe gari Mama Baraka ta yi waina ta yi sadaka kuma ta aiko musu da ita a nan tace su yi sadaka. Kwanakin da suka rage ma Aliyu na bin Ummi Abuja da su yayi amfani yana ta koyawa Emily addinin musamman karatu da bata iya ba, da kuma wadansu hukunce hukunce wasu baki ne a gurinta wasu kuma ta taba saninsu saboda ta taba kasancewa a cikin addinin a baya. Ana sauran kwana biyu Ummi ta tafi Ummi ta umarce Emily ta tafi gidan Mama Baraka ta fada mata zancen tafiyarsu kuma ta tafi gidan Ammy ma ta sanar saboda Fatima dake can hannun Ammy tsawon lokacin nan da Turhan yayi sati daya da barin garin Kaduna, Emily bata wani damu ba saboda ta yankewa kanta hukuncin zata bi Ummi ba kuma dan komai ba sai dan bata son ta yi nisa da Aliyu, dan haka bata damu ta sanar da Mama Baraka ko Ammy ba a ganinta kamar ita take da ikon kanta, saboda rayuwar ta da saba yi a baya, haka kuma take ganin idan ta tashi tafiyar da Fatima zata tafi ne kawai ta dauko ta a gidan Ammy. Ba Aliyu kadai ba Ummi ma tana taba mata wani bangare na karatun, Nafeesa ma haka Mama Baraka ma ta yi maganar daukar mata malamin islamiya da zai rika zuwa yana koya mata a gida, Emily ta nuna bata so wai ai Aliyu ya ishata, kuma bata yi karya ba, domin karatun da yake koya mata kawai take ganewa saboda yana mata komai daki daki, yana mata bayani ta irin sigar da take so shiyasa idan karatun ya shiga kanta baya fita, amman sauran sai dai ta yi ta tunanin me aka ce a nan ma. Idan Aliyu ne yake koyarda ita tana maida hankali ta iya waninsa kuma karatun wahala yake mata. Shi kanshi da ya fahimci hakan sai ya zama kullum a gidan indai ba wani abun ya fita ba, ko ya bijiro masa, a gidan yake karyawa yayi mata karatu idan ya fita ya dawo da rana su dorada dare ma kamin ya tafi gidansa sai ya fada mata. A yau bayan Aliyu ya gama koya mata karatun Sallah wanda shi yafi kowane muhimmanci yake tambayarta. "Kin yi magana da Mama Baraka? Akan tafiyarki?" Ta fara lilo da kafafuwanta kasancewa tana zaune kan kujera ne can kusa da motocin da suke aje a gidan. "Aa sai idan za mu tafi zan mata bankawana" "Kamar ya? Ta amince ki tafi ne?" "Sai ta amince? Na saba yin komai bana jiran umarnin kowa" Aliyu yayi murmushi ya aje littafin akan teburin dake tsakaninsu. "Da kika ce, yanzu ke ai yar gata ce ba ke zaki yi ma kanki hange ba, yi miki za'ayi, a musulunci mace ita ta ko'ina yar gata ce, idan tana yarinya tana karkashin kulawar iyayenta ne, idan ta girma tana karkashin kulawar mijinta, idan ta tsufa tana karkashin kulawar yayanta, a yanzu ke kina karkashin kulawar iyayenki ne, daga lokacin da kika ce ke zaki yankewa kanki hukuncin ba tare da neman izinin miji ko iyaye ba, to kin jefa kanki a matsala kenan, kuma raina iyaye a zauna lafiya, karki yarda zuciyarki ta raya miki wani abu akan Mama Baraka, ita uwace duk yadda ta zo sai dai ki yi hakuri da ita ki yi mata biyayya ki samu aljanna, ke da yanzu Allah ya cika miki burinki? Ga iyaye ga yan'uwa? To me ya rage? Sai idan miji ko?" Ta yi murmushi tana fahimta ko wane harafi na bayaninsa. "Gwanin Hikima, shiyasa na yi alkawari indai har zan sake aure ba zan auri kowane namiji ba sai mai irin sifofi da halinka" Ya bude ido. "Allah ko?" "Uhmm" "Ki ce kawai idan namiji yana da irin halina ya shigo za a bude masa kofa. "Aa fa, kai tsaye ba sai ya kasance kuma yana da irin sunanka" Ya dauke kai yana murmushin da ya bayyana hakoransa, ita ma ta yi murmushi ta yi kasa da kanta tana wasa da yatsunta can kuma ta dago tana masa wani kallo mai tafiya ta zuciya. "To ni wane hali ne da ni haka? Har Gimbiya da kanta tace ba zata zo kowane Yarima ba sai mai dabi'un wazirinta?" "Ba waziri ba ne, Sarki ne, na birnin wata zuciya da ta dade da jefar da kowa da komai ta shiryawa karbar kowane kalar yaki, ta yarda ta jure ko wane mashi da hakura da tsuka, da Gwarzon ya bayyana a cikin gonarta, sai ya nome duk wata ciyawa dake hana ta sukuni, har ta kai ganin sawun dokinsa kadai ya wadatar da ita da farinciki, da ya yaye komai sai ya maida zuciyar fara da taushi kamar auduga" "Idan kuma Jarumin ya kasance ba shi da sunana fa?" "Sai jarumar ta kasance a raye babu igiyar aure" "Ai mace bata iya rayuwa sai da ABOKIN RAYUWA" Ta yi murmushi kawai ta sauke kanta kasa, shi ma yayi shiru na tsawon lokaci kowane yana nazarin dan'uwansa. "A cikin idonki akwai wani haske dake hana mai kallonsu hango abun da ke ciki, balle ya hango ajiyar da ake, mai tafiyar yana wasiwasi, ya wuce ciki ko ya tsaya a inda aka ba shi masauki?" "Idan idanuwan suna da raunin hango zahiri, to abar zukata su yi aikinsu mana, ba mu isa mu hana su karasa abun da suka fara ba, na gode da karatun yau" Ta mike tsaye ta fara tafiya. "Wai likitan yana tsoron ko zuciyar bata warke ba ne, kar garin dinki liki ya sake sabon tsagi" Ya fada ba tare da ya juya ya kalleta ba domin shi ya bawa kofar shiga falon baya ne. Sai ta juyo ta kalleshi. "Wai sadaukin da furucinsa kadai ya shafe duk wani tabo dake zuciya ta zama sabuwa, shi ne kuma yake tsoron tara hannu ya rike ta daga faduwa? Ko dai shi ma yana raunatata ne?" Ya juyo da sauri. "Waya isa duk duniyar nan ya taba Ayusher, ko da kuwa Aliyun ne da kansa? Humaira sha zamanki ki huta, babu mai tuge shukar da kika yi, zuciya tana son abin da take so" Ta juya murmushi da farinciki sun bayyana a kowane gaba ta jikinta. Ya kwanta jikin kujera yana lilo idonsa a sama ya bude hannayensa sai murmushi yake. Ba zai karyata kansa ba, a da be sani na amman a yanzu karatun a bude yake, zuciyata tana son abun da take so, kuma take ganin ya dace da ita, ba dan kasan kadai ba, sai dan yana jin kamar idan ba shi ne ba, Emily ba zata samu farincikin da ya cancance ta ba ga waninsa, a yanzu kam baya jin saurari shawarar kowa bayan ta iyayensa duk wani abun da zai biyo bayan haka be damu ba, za a iya fadar gaskiya ko abin da ake hangowa amman be damu ba muradinsa ya samawa Emily abun da take so. Daga lokacin da ya fara lura ya fada, sai tunanin Turhan ya bijiro masa, be sani ba ashe wanda yayi nisa baya jin kira, a yanzu baya ganin laifi ko illar hakan, domin be shiga tsakanin Emily da Turhan da nufin bata tsakaninsu ba. Ganimar da ta biyo baya tsakaninsa da Emily kuma wani nauyi ne da ba zai saukewa daga zuciyarsa ba, kamar yadda be isa ya kaucewa kaddara ba, domin haka ya shirya bawa zuciyarsa salama da abun da take laso masa da halshen wuta mai zafin gaske. A tunaninsa kamar Emily ba zata karbe shi ba a yanzu ba ko nan gaba, be sani ba ashe ya gama cinta da yaki, a yanzu ikon garin nasa sai yadda ya juyata. Ya rike wannan a matsayin hujjar da zata hana shi cin amanar ko hana cikar burinta. Bayan La'asar Ummi ta saka direba ya kaita gidansu Mama Baraka. Emily ta shiga tana jin bakonta domin har yanzu bata iya sake jiki kamar gidan Ummi ko gidanta. A falo ta zauna kanenta na fadar ta shiga ciki Mama Baraka tana dakinta, ita kuma ta ki ta zabi zama a falon har sai da dayar ta shiga ta sanar mata, sai gata sun sauko tare da wanda ta shiga kiranta ta karaso inda Emily take zaune tana farincikin ganinta gidan. "Sannu da zuwa? Sun ce ki shigo ciki baki shiga ba why?" "Zan fi jindadi idan ke kika sauko" "Eh amman dai nan ai gidanku ne, ki sake jiki ki yi yadda kike so Aisha" Ta daga kai sannan ta gaishe da mahaifiyarta. Mama Baraka ta rumgume tana amsawa, sannan ta tambaye ta ina su Ummi, Emily ta amsa suna lafiya. "Ita ce mace na zo na nemi izini a gurinki, jibi za su tafi Abuja saboda can suke zama daman, ta ce na tambaya idan za ki aminta za su tafi da ni" Mama Baraka ta kai hannu ta dafa hannun Emily tana murmushi. "Tafiyar ta tashi ne? Ummi ta yi kokari matuka kuma ta kyautata na jidadi, sai dai hankalina zai fi kwanciya idan kina tare da ni, na yi ta son na samu lokaci na kasance da ke ban samu ba, saboda kin fi sha'awar zama a can, idan nace zan amince na barki ki tafi tare da su, na cutar da kaina, kuma babu wani lokaci da za mu samu mu kasance a tare" Emily ta sauke kai kasa alamar bata jidadin maganar Mama Baraka ba. "Ki yi hakuri Aisha, amman ban amince ba ina son na kasance a tare da ke, shiyasa nake shirya komai na barin gidan domin na san ba lallai zaman yayi miki dadi ba, be zama lallai ki sake jiki a nan ba saboda Kameela ko Hajiya, amman za mu koma gidana da na siya ki saba da kanenki su ma su saba da ke, ki yi hakuri dan Allah ki fahimce ni" Emily ta daga mata kai sai ta mike tsaye a take. "Zan koma, daman na zo na ji ta bakinki ne" Mama Baraka ta kalleta cikin rashin jindadi sannan ta mike tsaye. "Yanzu zaki tafi? Na zaki tsaya ko abinci ki ci ba?" "Bana jin yunwa" Mama Baraka ta dan yi shiru. "Toh jira ni ina zuwa" Ta juya ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta. Misra ta taso daga inda take zaune ta tsaya gaban Emily. "Idan baki kasance da Mama ba, baki bata dama ba taya zaki fahimci tana kaunarki? Kuma ita uwace a gareki? A tsawon lokacin kullum maganarki amman saboda bata son bata miki rai ya saka ta hakura ki zauna a can, idan kika tafi Abuja abu zai bata wahala, tana shan gori a gidan nan, ga Mahaifinmu ya juya mata baya, duk abun da muka fada mata bata ji tana cikin damuwa, amman na san idan kina kusa da ita zata samu salama" "Ni kaiwa bana son na yi nisa da Ummi ne?" "Why? Saboda Aliyu? Kar ki yi yaƙi akan namiji, amman ki bar namiji ya yaƙi duniya akanki, ke na ki kawai kyautata ce da biyayya, ta nan ake gane namijin da yake sonka da gaske da kuma wanda a baki ne kawai, indai yana sonki ba zai yi nisa da ke ba, kuma zai fiki shiga damuwa, idan namiji yana son mace duk wani baki da bakibaki nata ba zai gani ba, ke da kika sha wahalar rayuwa, ki bar mai sonki ya nuna miki son gaskiya" Emily ta yi shiruuu tana nazarin kalaman yar'uwarta, Mama Baraka ta sauko ta mikewa Emily waya. "Ga waya na siya miki na zo na baki ne idan naje, amman tun da kin zo duk daya ne" Emily ta karba da hannu daya sai Mama Baraka ta janye wayar bata bata ba. "Saka hannu biyu ki karba shi ne biyayya, musamman ga iyaye" Emily ta saka hannu tana jin wani abu a zuciyarta for the first time uwarta tana koya mata wani abu daga zamantakewar rayuwa. "Allah ya miki albarka" Mama Baraka ta fada. Emily ta mata godiya. "Na gode" Sannan ta juya Mama Baraka ta rakata har gurin motar da ta zo ta shiga. Direban yaja motar suka juya, sun fi to gate din kenan ta hango wata farar mota fara sol fake a can dayan bangaren dauke da bakin gilashi, slowing aka fara sauke gilashin har ta hango mutumen dake ciki, zuciyarta ta buga da karfi hankalinta ya tashi ta fara waige tana kallon motar kamar zata fita ta tafi can. Mutumen da Aliyu yace mata ana nema taya kuma ta ganshi a nan? Hakan yana nufin Vito yana bibiyar rayuwarta kenan? Taya ya san ta zo nan? Ko dai ta cewa direban ya juya ta yi magana da shi? Idan kuma ya sace ta fa? Ya daga hankalin sauran mutane? Domin ta san ba zai iya kasheta ba. Har suka isa gida bata samu amsa ko gamsuwa daga hasashen da take ba. Ta bude motar ta fito tana arba da Aliyu da ke tsaye da Tasmia a harabar gidan, take ta ji numfashinta ya fara gargada, kamar fa wannan tashin hankali da take gani na yanzu ya fi wacan, gaba daya sai ta manta da wacan kuma ta kasa boye hakan a zuciyarta. Tana tahowa Aliyu yana kallonta da murmushi a fuskarsa, hijab a jikin mace ba karamin kyau yake mata ba, sai a yanzu yake gane idan ya samu Emily ba karamar kyauta Allah yayi masa ba. Sai dai ga mamakinsa tana kawowa kusa da su sai ta wuce shi kamar bata gansu ba, Aliyu yayi hanzari shan gabanta. "Ayusher baki ga Tasmia ba?" "Na ganta?" Ta amsa cike da fushin da bata san na miye ba. "Gurinki ta zo fa?" "Kuma take tsaye tana magana da kai?" Ya daga hannayensa sama. "Forgive me my Lady" Ya juya ya nufi entrance yana murmushi, ba karamin dadin ya ji ba ganin yadda Emily ta sauya fuska na ganinsa da Tasmia hakan ya kara fahimtar da shi abin da yake hange a idanuwanta, ya nufi gurin ya tsaya ya juyo tana kallonsu domin zuciyarsa bata natsu ya tafi ya barsu ba. Emily ta juya ta kalli Tasmia with so much confidence. "Ya aka yi?" Tasmia ta yi murmushi ta taka few steps ta isa gabanta ta tsaya. "Bakuwar bata zafi ba ce, na san kina kallona da abubuwan da suka faru a baya, ban kyauta na gano haka daga baya, kuma na zubar da komai saboda ni ma Allah ya ba ni mai kaunata, kwanan baya Kameela ta zo gidanmu ta same ni da labarinki, Wallahi sai tausayinki ya kama ni na hango da ace ni ce a yadda kike ya zan yi? Har na ji kunyar abun da na aikata shiyasa na zabi zuwa na baki hakuri ke da Aliyu kuma na biyo ta gefensa saboda ke ba a samum wayarki ba lallai ma idan na zo kai tsaye ki saurare ni ko ki yarda da ni ba, amman dan Allah ki yi hakuri ki yafe min, ba kuma ina nufin sake alaka dake ba ne aa ina neman yafiyarki ne kawai" Emily ta sauke ajiyar zuciya. "Ba komai na yafe miki" "Na gode, kuma na miki murna Aliyu ya fada min kin musulunta na jidadin haka, sai dai kuma zan baki shawara ki yi taka tsantsan da Kameela, domin tana neman hanyar da zata cutar da ke ne har yanzu, zuwan da ta yi ma ta nemi na bata hadin kai mu yi miki wata illar wai ko acid ne a watsa miki, amman ban bata hadin kai ba daga karshe ma da fada muka rabu" Emily ta matsa baya tana kallon Tasmia da dan tsoro. Sai Tasmia ta yi murmushi. "Ke da kike da Aliyu miye na tsoro, kamin ya yarda ya zo nan sai da na sha wahala kuma ya gargade ni, jakar nan tawa ma sai da bawa wata yarinya a gidan nan ta bincike komai a ciki saboda baya son wani abu ya same ki" Emily ta juya ta kalli Aliyu dake tsaye hannayensa biyu a aljihu yana kallonsu kamar irin kallon nan da motsi kadan yake jira Tasmia ta yi yayi tsalle ya dira gurin. Tasmia ta ciro IV aurenta ta mikawa Emily. "Ba dole sai kin zo ba, tabbaci nake son ki samu babu ni babu cutar da ke har abada" Emily ta karba. "Congratulations" Ta juya, sai Tasmia ta kirata, ta juyo. "Aisha ko? Haka Aliyu yace na kira ki baya son sunan Emily. Ki rike Aliyu shi ne ABOKIN RAYUWARKI, kun dace da juna, ABOKIN RAYUWA ne na gari, ke ma kuma kin dace da shi domin baki da hayaniya" Emily ta juya tana kallon Aliyu. "Na barki lafiya" Har Tasmia ta fice daga gidan Emily bata sani ba domin idonta suna kan Aliyu. Ya sauko a hankali zuwa inda take tsaye. "Wai kokari kike sai kin kure kallona kin hango muni na? Idan ma kin ga haka sai dai ki yi hakuri da ni, domin kaddara ta gina mana gida kuma dole sai mun shiga, idan za a hau sama a fado ni dai ba zan yarda ki bar ni ba, na zama karfen kafa, yanzu akan Ayusher bana jin has, ni kadai nake gane abin da nake ji, idan na mutu ke ce sanadi" Yana maganar cikin sigar kaunar da soyayya. Murmushi ya zama matar wajib zuciyarta na lasuwa da kaunarsa. Ya ciro dayan hannunsa a aljihu tare da wata yar karamar fulawar Rose mai matukar kamshi ya shinshina sannan ya risina ya aje mata kasa a gabanta. "Hankalina yana kwantawa idan na yi arba da murmushinki, idan kika kalleni sai na ji kamar na fi kowa farinciki. Ga tukuicin kallonki Sarauniyar abar da ban fada ba" Ya wuce yayi gaba abunsa kamar ba daga bakinsa kalaman suka fito ba. Emily ta duka ta dauki flower ta kai hancinsa wani kamshi mai sanyi ya ratsa hancinta ya sanarwa kwakwalwarta, kwakwalwar ta sakarwar zuciyarta sakon kai tsaye. A lokacin da ta bude idon sai ta hango shi rike da kofar falon alama ita yake jiran ta fara shiga. Ta mike tsaye ta fara takawa tana kallonsa, shi kuma ya dake ya ki yarda ya hada ido ta ita wannan karon duk kuwa da ya san idanuwanta suna kansa ne. Takunta yake kallo yana kirga tazarar dake tsakaninsu har ta iso kusa da shi ta tsaya. "Na gode da kika karbi kyautata, ina hango rayuwa ta har abada a cikin idanuwanki" Ya kalleta suka sake sakarwa juna murmushi. A cikin wani sabon tattausan halshen ya furta. "Lady's first..." Yana nuna mata cikin falon da dayan hannunta, ta dauke kai ta wata zumar kauna na dibanta ta shiga falon. [8/19, 7:16 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣9️⃣ A lokacin da ta shigo falon bata samu kowa. a cikin ba, hakan ya bata damar nufar dakinta kai tsaye ta shige ta cire hijab ta kwanta kan gado ta aje wayar Mama Baraka ta bata a gafe ta kai flower Aliyu a hanci tana shakar kashin dake jiki sai lumshe ido take fuska dauke da murmushi. A rayuwarta bata taba haduwa da wanda ya iya sarrafa halshe ya karantar da ita sabon karatu ba kamar Aliyu, idan ta ce be tafi da zuciyarta ba ta yi karya. "Ashe kin dawo" Ta bude idon da sauri ta tashi zaune ta boye fulawa a bayanta, tsabar shauki ya mantar da ita yadda ake rufe kofar daki, bata san a sake kofar take na sai da Ummi ta shigo. "Eh na shigo baki falo" "Ina daki ne, toh ya kuka yi?" "Bata amince ba, tace ta fi son na zauna a tare da ita" Ummi ta sauke ajiyar zuciya. "Daman na yi wannan tunanin, ita ma ya kamata ta samu lokaci da ke ai, kuma Abuja babu wani nisa idan kika so ganinmu za ki iya zuwa" Ta yi shiru sai kuma ta mika hannu ta dauko wayar da Mama Baraka ta bata. "Ta ba ni waya" Ummi ta shigo ta zauna ta karba tana murna. "Maa Shaa Allahu" A nan suka bude ashe har da sim ciki ba su sani ba sai lokacin, Emily ta yi kamar ta fadawa Ummi ta ga Vito a yau sai kuma ta yi gudun kar hankalinsu ya tashi musamman idan Aliyu ya sani. "Allah yasa alheri ya tsare, sai kin gama gani sai a saka miki numbobinmu" "Tohm Ummi" "Kin ga Tasmia?" "Eh ta ba ni katin aurenta, a can ma na bar shi waje ina jin" Ta fara duddubawa bata ga Iv ba. "Ai kara da kika jefar babu amfanin tafiya bikin ai, kawai dai saboda ta matsa ne yasa na ce Aliyu ya hakura ya barta ta zo, ai neman yafiya ne ba wani abu ba, amman kin san yaron nan ba shi da ta ido fa ta zo sai da ya saka Nafeesa ya bincike ta? Baiwar Allah har tausayi ta ba ni" Emily ta yi dariya kamar yadda Ummi ma take dariya. "Haka ta fada min" "Kin san Aliyu be son abun da zai same ki, be yarda da ita ba ne gaba daya" Ummi ta sauka kan gadon ta mike tsaye. "Bari na barki ki huta sai kin fito" "Tohm Ummi" Emily ta bita da kallo har ta fice tare da ja mata kofar dakin. Downstairs Ummi ta sauko. "Ta fada maka Hajiya Baraka bata barta tafi tare da mu ba?" Aliyu ya aje red apple din hannunsa. "Ban tambaye ta ba" "Daman na yi wannan tunanin shiyasa ban kwallafa rai akan tafiya da ita ba, idan ma Hajiya Baraka ta yarda ba lallai ne Ammy ta yarda a tafi da Fatima ba? Ka duba ka ga gaba daya ta dauke hankalin yarinyar nan daga gidan nan, ba dan ma Aisha tana da hakuri da kai zuciya nesa ba da Allah kadai ya san damuwar da zata shiga ko matsala" "Ummi ni bana ganin laifin Ammy fa, tsakani da Allah ke kanki kina son jikoki balle ita da Turhan kadai ta haifa, kuma an dade babu abun nan, sannan a inda take ma ita kadai take zaune, taya son abokin hira ai" "Haka ne kuma, Allah ya kyauta" "Ameen, yanzu tafiyar ke kadai zaki yi ta kenan?" Ummi har ta wuce ta juyo. "Ban gane ni kadai zan tafi ba? Ga Nafisa ga ka" "Aa ni ba zan tafi ba, ni da ke koyawa Ayusher karatu? Bata gane karatun kowa sai nawa, idan na tafi wa zai koya mata?" Ummi ta tabe baki tana murmushi. 'Yanzu na yi magana yace ba sonta yake ba, kake koya mata karatu ko dai kake koya mata soyayya' Ta fada a ranta a fili kuma sai ta ce. "Kadai tsoron kake ka tafi wani ya rutsa dan ginin da ka fara ko?" Yayi murmushi "Ai ni idan na yi gini a filin da yake nawa babu mai iya rusa shi Wallahi, bana bada kofa balle ma kuma wannan yarinyar Ummi?" Ummi ta kara tabe baki. "Uhm uhm ɗan duniya hayaƙin taba, Allah ya baka ikon cigaba da tausayinta kamar yadda ka fada" Ta mike tsaye yana dariya ya fice falon. Ummi ta girgiza kai ta nufi Kitchen. "Daman ai na fada idan ta yi tsami ma ji, kullum idan aka yi magana sai kace tausayinta kake, kai ba zaka iya aurenta ba ko Turhan ya mutum yanzu me aka yi? Hmmm yaran zamani ana hango musu abu suna kaucewa, su karyataka" TURHAN POV. Duk wata hanya da zai bi ya fahimtar da mahaifinsa yadda yake son Emily da kuma yadda kasancewa da ita zai kwantar masa da hankali ya hada kan iyalinsa guri daya, ta hanyar auren Emily a karo na biyu ne kawai yake jin zai mallaka masa Fatima a kusa da shi, abu ne mai wahala Ammy ta yarda ya zauna da Fatima a Sudan, amman idan da Emily ba ba shi da haufi, baya ga haka kuma baya ra'ayin wani ya kasance da matarsa sai shi kadai. Da mahaifinsa ya fahimci abun da zuciyarsa take muradi sai ya karbawa bukatarsa. Ya fahimcin hankalin dansa baya a tare da su a yanzu, domin an maido masa matarsa an shirya tsakaninsu ya fahimtar da ita kuma ta yi masa uzuri, amman tunaninsa fa hashensa kullum yana gurin wacan matar ne da be da tabbacin zata dawo gareshi. Ya saka mahaifinsa a gaba ne, da neman yayi masa ruwa da tsaki saboda yana ganin idan mahaifinsa ya wuce masa gaba Emily zata samu, yadda yake gani za a bullo ma lamarin abu ne mai wahala Emily ta tsallake tarkonsa. Kamin su bar kasar Sudan sai da mahaifinsa ya kira Alhaji Bello ya fada masa bukatarsa da kuma rakiyar da yake son yayi masa, Turhan ma da kansa ya sanar da Dr Adam yadda suka shirya komai, ya fada masa yayi hakan ne saboda neman yafiyar Emily wata kila idan yayi wannan zata yafe masa. Dr A-B ya ba shi goyon baya dari bisa dari kuma ya tabbatar masa da cewar tare da shi za'ayi tafiyar. Sosai kaunar Emily ta kama Turhan kusan da ya ji labarin musuluntarta ta gurin Fatima yayi murna yayi farinciki sosai. Sati daya da yayi a garin sai yake jinsa kamar shekara, tunaninsa yana kan Emily ne, har ta kai idan ya kalli matarsa sai ayyana da ma ace Emily ce, ko kuma idan Emily ce ga yarsu ga ta farincikinsa ya cika. Idan kuwa zuciyar ta tuna masa Aliyu yana can yana kalla masa mata sai ya ji kamar ya hade zuciyar ya mutu saboda kishi da bakinciki. Babu daren da baya mafarkin kasancewa da Emily, idan ya zauna shi kadai shiru baya tunanin komai sai nata, idan ya fita aiki tana nan a ransa, wasan dokin da yake idan yana yi sai yayi ta ayyana yadda zai koya mata wasan idan ta kasance matarsa. Be fadawa Mahaifinsa cewar ba da aure aka haifi Emily ba saboda baya son mahaifinsa ya yanke kudurinsa ko ya ki goya masa baya, ya fada masa mahaifinta Bature ne kuma ba a kasar yake ba, mahaifiyarta kuma tana auren wani yaron abokinsa wato Bulama Bello step father din Dr A-B, ya fada masa uba daya suke da Dr A-B, ya kuma fada masa a yanzu tana zaune idansu Aliyu ne, sun yi makirci sun zaunar da ita gidan saboda ya kar ta koma gurinsa. "Za mu nema maka yafiyarta da kuma aurenta gurin Ahji Mudallab, ba zan yi zuwa biyu ba" Da mahaifinsa ya fada masa haka ba karamin dadi ya ji ba, domin hakarsa ta cin ma ruwa daman abun da yake nema kenan Shi ma mahaifinsa ya gama sallamawa da fahimtar irin son da dansa yake yi ma wata mace da ba jintsi da jinin larabawa ba. Turhan kam yana ganin ta ko'ina an daure Aliyu da iyayensa kuma an saka Emily a tsakiya ba zata iya cewa a a ba. Ta waya yake labartawa Ammy komai idan kuma yana video call da yarsa sai ya fada mata yana dawowa zai je ya dauko Emily za su dawo su zauna guri daya. Sarkin Sudan da kansa ya daga waya ya kira Mahaifin Aliyu ya sanar masa za su neman yafiyar Emily a gidansa, a ciki satin nan da zai shigo. Saboda ya kyautata musu ya aje uzurinsa ya sanar da Ummi cewar ta daga zancen komawarta Abuja a satin zuwa Next week saboda zai dawo Kaduna a satin, sai dai be yarda ya fada mata ko Aliyu cewar iyayen Turhan ne za su zo ba, yayi hakan ne saboda gujewa Ummi ko Aliyu su fadawa Emily ko su shirya wani abun da zai zama laifi a gurin Turhan. Dan haka ya zabi shiru da bakinsa ba tare da ya fada musu dalilin dawowarsa ba. Mahaifin Aliyu ya sauka Kaduna on Saturday, Sarkin Sudan ya sauka Abuja on Saturday tare da Turhan da yan rakiyarsa masu fassara masa daga hausa ko turanci zuwa larabci, a gidan abokinsa Bulama, sun samu kyakkyawar tarba a daya daga cikin manyan masaukan baki da Bulama yake da su, abinci aka kawo musu kala kala tun daga kan na Nigeria har zuwa na kasar Sudan. The following day suka suka shiga private jet na Alhaji Bulama zuwa garin kaduna, Dr A-B be fadawa Emily za su zo ba, duk kuwa da kasancewar tana kiransa akai kai da sabon layinta da Mama Baraka ta bata. Sai yayi tunanin ko Mahaifin Aliyu ya sanar musu da zuwan, sai dai duk da haka be yi mata maganar ba saboda yana son ta ganshi as surprise kamar wacan karon. Even Mama Baraka bata san wainar da ake toyawa ba. Domin mijinta baya magana da ita, balle ya labarta mata cewar mai gidansa Alhaji Bulama zai sauka garin a ranar ta Lahadi ba, shi ne mutum na farko da ya fara isa filin jirgin ya tarbe bakin da aka sanar masa da zuwansu amman ba a fada masa dalili ba. Alhaji Bulama ya sanar masa ne saboda shi ne babban yaronsa kuma indai har za su sauka a garin Kaduna babu wanda yake tarbarsa kamar shi, balle kuma wannan da suke ganin ya alakantu da shi. Ya tarbosu tare da yi ma maigidansa tayin sauka a a gidansa ko masaukin baki, amman ba su amsa gayyatar ba domin uzurin da ya kawo su dabam. Hankali be tashi ba sai da ya ji ana zancen makiyinsa kuma surukinsa, suka dunguma gaba daya suka dauki hanyar gidan. Ba zai iya zare kansa yace ba zai je ba, saboda yana tare da mai gidansa, kuma siyasa ta gaji haka idan aka hadu a rumgume juna ana wasa da dariya kamar babu komai. Ba su fada dalilin tafiya gidan ba sai da suka kusa isa, be yi mamaki ba domin ya hararo haka ganin Turhan a karon farko da Alhaji Bulama ya gabatar masa da shi har yana fadar ga surukinka. EMILY POV. Tun a daren Assabar Daddy ya sanar da matarsa cewa yana da baki gobe ta shirya abinci mai kyau da wuri, duk yadda Ummi ta so ta ji ko su waye be bata dama ba sai kawai ya fake da cewar abokan siyasa ne. Sannan ya bukaci ta fadawa Aliyu kar ya shigo gidan gobe sai idan ya kira shi. "Bakin da za su zo suna da alaka da shi ne?" "Aa kin san ita harkar siyasa akan boye wasu abubuwan saboda gaba, shi Aliyu ba mutum ne mai son siyasa ba, to be kamata ace kowa ya san da shi ba, hakan kan iya haifar da matsala wani lokacin a cutar maka da naka" "Haka ne kuma, zan fada masa Allah ya kaimu lafiya." "Ameen Uwargida kuma Amarya" Daddy ya fada yana murmushin manyan mutane. "Ka ji da shi, idan ka tashi auro min yar yarinya dadin bakinka ba zai hana ba ai" "Ni yanzu ke ma ba hakuri kike da ni ba? Ina na ga lokacin kara miki wani aure? Wahalar ma ai sai ta yi min yawa" "Uhmm" Haka dai suka cigaba da hirarsu sama sama har kusan tara na dare, shigowar sirri Daddy yayi amman haka be hana makusantansa da masu saka idon unguwa su fahimci ya sauka garin ba domin dan siyasa ba a boye yake ba, A ranar be kwana ba da ya sallami kowa da abun da ya kamata. Da Aliyu ya zo yi ma Daddy sallama Ummi take fada masa gobe ya zauna ya huta kar ya shigo gidan sai an kira shi domin ba su san saukar yaushe baki za su yi da safe ko rana ko yamma. To him it's awkward and something new, why dan za ayi baki za ace kar ya shigo gidan? Be musa wa Ummi ba domin ta ba shi hujjojinta kamar yadda Daddy ya bata. Shi dai ya amsa musu ne kawai amman ba dan ya gamsu ba, da ya zafafa tunani sai ya fahimci Turhan ne zai ko ko mahaifinsa, a take jikinsa yayi sanyi wani bangare na zuciyarsa ya raya masa titsiye Emily za su yi, su cilasta mata abun da ba shi take da niya ba, wannan bangaren da ya raya masa haka shi ya sake raya masa kowa baya wuce kaddararsa kuma be zama lallai idan ta koma gidan Turhan ya sake cutar da ita ba a yanzu domin ga dukan alama yayi nadama kuma ya fahimci tana da tsada. Haka ya fito bangaren na mahaifinsa yana ta sake sake har ya nufi motarsa sai kuma ya juyo ya sake turo kofar falon ta Ummi ya shiga. Nafeesa da Emily ne zaune a falon sai masu aikin Ummi dake zaune kasa. Tun da ya shigo Emily take kallonsa har ya nufi dinning ya dauki cup ya fara auna madara yana zubawa, ba dan ya sha ba sai dan ya saci kallon Emily din, jin yake yana kewarta fiye da ko yaushe, ya san ba zata iya kaunarta a zuciyarta amman idan aka mata dole ba lallai ta tsallake wannan ba, ya gama satar kallon nata sai ya maida madarar a mazubinta ya fice yana bata wani silent look tana karba cike da kauna. Washe gari da wuri Ummi ta hau aiki tare da masu tayata, innocent her bata fahimci komai ba, har suka kammala hada komai ta shiga ta shirya kowa ya shirya. Emily na ta bude ido ta ga Aliyu ya shigo gidan da safe bata ga ya zo ba, bayan su gama aikin ta ji ba zata iya hakura ba sai ta aika masa da sakon kar ta kwana. "Yau lafiya baka shigo ba?" In few seconds ya maida mata amsa. "Wani uzurin ne ya rike ni?" "Akwai uzurin da ya fi ganina muhimmanci ne? Wuni yau zai min babu dadi" "Ke kenan, balle kuma ni da nake jin awanin da nake a gidan a kullum suna min kadan, Ayusher i miss you more life itself, zan zo soon" Ta aika amsa da sakon Heart emoji ya maido mata smiley face emoji. After like one hours suka ji shigowar motoci a gidan. Emily tana dakinta tana lasa waya, Ummi kuma ta fita tare da Daddy cikin lullubinta domin tarbon bakin da yace mata za su zo. Ganin Turhan da mahaifinsa ya matukar ba ma Ummi mamaki ga kuma Mahaifin kameela a tare da su, sai dai bata yarda ta nuna ba, aka shigo da su babban Falon Daddy ana musu sannu da zuwa. Masu aiki suka shiga jera musu abun da aka shirya musu. Tambayayi suka cika cikin Ummi sai a yanzu ta fahimci dalilin Daddy na hana Aliyu zuwa gidan a yau. Alhaji Bulama da Dr A-B ne kadai sukq sha ruwan da aka jera, Turhan da mahaifinsa ba su taba komai ba daman sarakuna ba ko'ina suke ci ko sha abu ba, balle kuma Mahaifin Kameela, da yaken dole na kawai yake. Turhan na zaune shiru zuciyarsa na raya masa nasara da rashinta. "ina ganin kamata yayi mu yi abun da ya kawo mu? Domin ni yau zan bar garin nan, kasan yadda abubuwan suke ba koda yaushe muke samu lokaci ba, amman abun da yake da muhimmanci kamar na abokina kuma abokin kasuwancina dole na bashi time dina" "Haka ne ranka ya dade, da na so ku fara cin abinci, amman bari a kira yarinyar" Ummi ta yunkura zata tashi Daddy ya hana ta, dugun kar ta tafi ta yi ma ɗanta kamfai, ya daga wayarsa ya kira Nafeesa ya ce ta shigo masa da Emily. Emily na zaune dakinta Nafeesa ta shigo ta ce ta saka Hijab dinta ta fito Daddy yana nemanta. "Lafiya?" Emily ta tambaya domin tun da ya zo ta je ta gaishe shi bata sake shiga bangaren ba. "Wallahi ban sani ba, amman dai na san lafiya kam In Shaa Allahu" Emily ta dauki bakin mayafin abayar dake jikinta ta rufe kanta ta saka talkaminta sannan suka fita tare da Nafeesa, suna tafe gabanta na faduwa musamman da suka doshi falon, tsayawa ta yi cak cike da faragaba kamar tace ba zata shiga ba, ganin haka ya saka Nafeesa ta kama hannunta suka shiga cikin falo, Emily kanta na kasa har ta zauna inda Daddy ya nuna ma Nafeesa. Sannan yayi ma Nafeesa alama da ta tashi ta fita, Emily ta dan dago kai kadan ta kalli mutanen da suka falon gabanta ya buga da karfi, ba dan arba da Turhan kadai ba har dan ganin mahaifinsa da kuma Alhaji Bulama ga kuma mahaifin Kameela a falon. Daddy ya gabatar mata da kowa daya bayan daya, sannan ya fada mata dalilin zuwansu neman gafararta ne na abubuwan da suka faru. "Dukanmu nan har ni mu zauna ne saboda neman yafiyarki ga dan mu, yayi kuskure mun sani kuma yayi nadama shiyasa takanas ta Kano ya dauko mahaifinsa da abokan mahaifansa da ni kaina da yake jin zan iya shige masa gaba mu roka masa yafiyarki, kuma muna fatan za ki dube mu da hurhurar dake kan mu ki yafe masa" Emily ta yi shiru na tsawon lokaci. "Ki bude baki ki yi magana muna saurarenki, kuma ba wai muna cilasta ki ba ne, kuma ba muna son ki ga kamar mun tsareki ba ne, aa yafiyace muke nema ga Turhan kowa yana kuskure abu ne da kika sani, kowa ya sani" Cewar Alhaji Bulama. Emily ta dago kai a hankali ta fara magana ba tare da ta kalli kowa ba. "Na yi tunanin mun wuce wannan gabar, tun kamin na yi magana da shi, na yi da Ammy kuma na fada na yafe masa, gaba daya ni na zubar da abun da ya faru, yanzu ai wata rayuwa muke yi bata baya ba, kuma Turhan uba ne ga Fatima ya cancanci girmamawa ta da yafiya, har a gurin Allah ni na yafe masa" "Maa Shaa Allah" Haka kowa ke fadi fuska a sake cike da far'a. Mai Martaba da kansa ya soma magana ana fassara mata. "Na jidadi da jin wannan maganar, kuma na yaba da hankalin ki da tarbiyarki, a rayuwa ana son mutum ya zama mai yafiya, kuma kin nuna mana ke mai hankali ce ba ki watsa mana kasa a ido ba, mun gode sosai, akwai tsaraba da muka so miki da ita fatan ba zaki raina ba" Mai fassarar na rufe baki aka shigo da manyan akwatuna biyu aka aje a gefen da Emily take zaune. "Sai dai kuma ba yafiya kawai na zo nemawa ɗana ba, ko da yake tafiyar daya ce ai, amman dai haka ba zai hana mu fada ba, Emily muna rokon alfarma, ki duba yadda muka zo nan dukanmu kuma da irin yadda yayi nadama yake ta kai da kawo akanki, kuma ki duba yarki da zuri'ar da za ku samu nan gaba, indai har da gaske kin yafe masa kuma kin manta komai toh ki amince ki koma karkashin kulawarsa da igiyar aurensa, kusan shi ne makasudi zuwanmu a nan" Ummi ta ji abun kamar daga sama, amman babu damar magana saboda Daddy yana gurin zaune, dan haka ta mike tsaye kawai ta fice daga falon. Daddy be wani yi mamaki sosai ba saboda ya hango hakan tun farkon zuwansu gidan. Emily ta kalli Alhaji Bulama wanda shi ne yayi maganar sai ta ji nauyi ba shi amsa. Dr A-B ya ciro daurin dollars a aljihunsa ya aje kasa. "Zan fi kowa farinciki idan ta amince, kuma ace ni na biya sadakin kanwar nan tawa" Emily ta sake daga kai cikin tsananin damuwa. "Dan Allah ku gafarce ni, kuma ku fahimce ni, bana nufin bata ran kowa, bana nufin zubar da kimar kowa, na yafewa Turhan amman hakan baya nufin na yarda na aure shi, Wallahi ba zan iya zaman aure da shi ba, akwai wanda na so" "Wake kike so?" Alhaji Bulama ya tambaya, sai ta yi shiru. "Ki bude baki ki amsa mana, ko a addinin musulunci bazawara amsawarta ake amfani ba shirunta ba, shiru na budurwa ne, haka Annabi S. A. W ya fada" Daddy ya ji kamar yace kar ta fada. "Aliyu..." Ta furta a hankali, falon yayi tsit na tsawon lokaci, kamar babu wani abu mai rai a ciki, tsabar jin nauyi Daddy ya ji kamar kasa ta tsage ya shige ciki. Turhan ya mike tsaye ya fice falon ba tare da ya kalli inda Emily take ba zaune ba. Sarkin Sudan ya tsare ta da ido. "Kin san mutanen da suke zaune a gabanki kuwa yarinya?" Emily ta fashe da kuka ita kanta bata nufin watsa musu kasa a ido. "Ku gafarce ni dan Allah? Ku fahimce ni ku taimaki rayuwata, ku bar ni ni ma na yaki iskar yanci" Sarkin ya mike tsaye bayan an fassara masa abun da ta fada ya fice tare masu rakiyarsa. "Amman baki yi kyauta ba, kuma ba mu tsammaci haka ba" Cewar Alhaji Bulama sannan ya mike tsaye ya fice, tare da rakiyar Mahaifin Kameela. Dr A-B ya kalli Emily dake ta kuka ya sakar mata murmushi. "Aliyu kike so?" Ta daga mishi kai. "Share hawayenki na miki alkawari ba zan bar garin nan ba sai an daura aurenku, ni ma kamar uba ne a gurinki ai zan iya bada aurenki, na nufin biyan sadaki ba zan fasa ba" Ya juya ya kalli Daddy ya tura masa kudin. "A rike wannan a matsayin sadakin Emily, a sanarwa duk wanda ya kamata a sanarwa, zan tafi na dawo daga can zan sanar da Madam Baraka, anjima kadan zan dawo za a daura aurenta da wanda take so, ni dai burina ta kasance cikin farin ciki, amman a tabbatar da shi ma yana sonta gudun abun da zai je ya dawo kar ya cutar mana da ita" Ya tashi shi ma ya fice, Daddy ma mikewa yayi tsaye ba farinciki ba bakinciki domin shi ma be ga dalilin da zai saka ayi ma Emily dole ga abun da bata so ba. Emily kadai aka bari a falon tana rusar kuka, bata sani ba ko shi ma Aliyun ya juya mata bayan ta watsa ma manyan mutane kasa a ido. Ummi ce ta shigo da kanta ta kama Emily ta fita da ita bayan Daddy ya fada mata abun da ya faru. Daddy ya sanar duk wanda ya kamata ya sani cikin kankanen lokaci, Dr A-B ya tafi kai tsaye yayi magana da Madam Baraka ya fada mata abun da ya faru, sai ta daga waya ta kira Emily ta sake tambayarta da gaske Aliyu take so Emily ta amsa mata da eh. Kamin a daura auren sai da Daddy ya jira Aliyu ya tambaye shi ko yana son Emily. "Eh ina sonta Daddy?" Ya amsa kai tsaye babu boye boye babu kwankwanto, gabansa sai faduwa yake ba kamar ya san wainar da ake toyawa. "Tohm za a a daura aurenku, daga baya abubuwa za su biyo baya" "Na gode Daddy Allah ya ba ni ikon sauke nauyin da za a dora min" Daddy ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba. Sannan ya sanar da Ummi yadda suka yi, Ummi ta shigo ta ta sanar da Emily halin da ake ciki yan'uwan Daddy da nata duk sun hallara gidan. "Anjima idan an fito sallah La'asar za a daura aurenku da wanda kike so Aisha" Emily ta kalli Ummi tana kuka. "Allah kasa ya rike ni amana..." Ummi ta kama hannayen Emily tana hawaye. "Wallahi ko ba ni da rai Aliyu ya ci amanarki, ban yafe masa ba..." Emily ta kwantar da kanta jikin Ummi, Ummi ta rungumeta tana amsa sallamar Mama Baraka. [8/21, 10:14 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣0️⃣ 🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟 🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘 Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida. ✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman 📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). 💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau! 📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa! _________ Karfe 4:30pm aka daura auren Aliyu da Aisha, bayan sauke sallah farilla ta La'asar. Daddy da yan'uwansa suna gurin, yan'uwan Ummi ma wasu daga ciki suna gurin. Dr A-B ne ya bada auren Daddy da kansa ya karbawa dansa auren Emily, masu shaidu suka shaida aka yi addu'a sannan masu tafiya suka tafi, Daddy da Dr A-B suka nufo cikin gidan da ragowar goro da dabino. Daddy ya nufi bangarensa Dr A-B kuma ya shiga falon Ummi ya tambaya ina Aliyu yake. "Baya gidan, amman yanzu zan kira shi ya zo" "Emily fa?" "Tana sama, Nafeesa tashi ki kai shi" Ummi ta umarce ta, Nafeesa ta mike tsaye ta wuce gaba Dr A-B na bayanta har suka shiga cikin dakin da Emily take zaune tare da Mama Baraka. Nafeesa ta juya ta fice, Dr A-B ya zauna kusa da Emily sai ta dube shi idonta a kumbure ta yi kuka sosai har ta gode Allah. "An daura aurenki da wanda kike so yau, ina miki addu'ar Allah ya ba ku zaman lafiya, kuma ya saka mutuwa ce za ta raba" Ta kara matsawa kusa da shi ta rumgume shi tana jin sanyi. "Na gode, wannan karo na farko da jinina ya bada aurena..." Ta furta murya na rawa tana kuka, ita kadai ta san me take ji, tana son Aliyu kuma tana tsaron abun da gaba zata haifar, gashi ta watsa kasa a idon manyan mutane babu wanda ya fahimce ta, shi kansa Dr A-B ganin take yayi mata abun da take so ne kawai ba dan ya gamsu da zabinta ba. Ta dago kanta amman ta kasa kallon kowa. "Allah ya ba ku zama lafiya" Cewar Mama Baraka tana share hawayenta. Sun kusa rabin awa a dakin har aka fara kiran Dr A-B saboda Alhaji Bulama zai bar gari kuma tare za su tafi. Ya mike tsaye kenan sai ga Aliyu ya turo kofar dakin ya shigo da sallama duk suka amsa masa ban da Emily da kanta yake kasa, tana ta lissafin rayuwa. Idan Aliyu ya juya mata baya shi kan ita kam ta gama rayuwa kuma makiya za su mata dariya. Dr A-B ya kama hannun Emily ya mikar da ita tsaye ya kama hannunta ya kama hannun Aliyu ya saka hannunta cikin na Aliyu. "Ga amana an baka, ta wahala ka sani, muna fatan daga kanka ta dace, a gaban iyayenmu ta zabe ka ta bar wanda shi ya so ya aureta a yau, dan Allah karka bata kunya. Sannan zan tunatar maka a yanzu Emily tana da uwa, dan'uwa da kuma uban da zata sani nan gaba kadan, karka kuskura ka ce zaka taba ta. Ta fada kai take so kuma na tsaya har yanzu ne saboda na tabbatar da cikar burinta, na sauke nawa nauyin, ni zan tafi ina muku addu'ar Allah ya baku zaman lafiya na bar ku lafiya" Ya dauke hannunsa daga kan na su ya nufi kofa ya fice daga dakin, Mama Baraka ta mike tsaye ta bi bayansa. Aliyu ya kama hannaye Emily duka biyu ya rike yana kallon yadda take hawaye. "Na san nisar tafiyar da kika yi, a hanya kin taka kaya, kin tsallake rame, kin yi dingishi kin karaya, na san zafin wutar data kona ki, na san buri da mafarkinki, ka karanci zuciyarki na san kudurinki, kin yi rayuwar kadaici. A yau ni da ke mun zama iyali, zan zame miki mijin da baki taba tsammanin samu ba, zan cika duniyarki da farinciki har sai kin manta da damuwarki, kuka ya kare hawaye, ba zaki sake zubar da hawaye akan ɗa namiji ba, fargaba ba zata sake kusantarki ba, kin zama jinina, farincikina, kaunarki ce rayuwarta, ina mai tabbatar miki baki yi kuskuren zabe ba" Ya sake hannunta ya matsa baya kadan ya zube kasan guiwoyinsa ya hade hayyansa. "Na gode da kika yarda da cewar zan iya! Na gode da kika ba ni wannan damar, na gode da kika yarda a dora min wannan nauyin na gode da kika yarda na zama silar warakar duk wani ciwo naki, na gode da kika so ni, na gode da kika aminta da ni, na gode da kika aure ni, na gode Saruniyar mata, mace mai hakuri da kyakkyawar zuciya, na gode Ayusher na gode... Na gode... Na gode na gode..." Ta kasa komai wasu hawaye na dabam suna sauko mata, sai ta lumshe ido tana maida numfashi. Aliyu ya mike tsaye ya matsa daf da ita har yana jin fitar numfashinta. "Bude idonki ki kalli mijinki, mijin da be san komai sai ƙaunarki, mijin da samunki ya zama babbar kyauta da rahama a gareshi" Ta bude idon ta kalleshi ido cikin ido daf da daf gab da gab das da das... "Ayusher ina ƙaunarki, ke tawa ce ni ne ABOKIN RAYUWARKI" Ya rada mata cikin wata murya da be san yana da ita ba, furucin yana fitowa ne har can kasan kasan kogon zuciyarsa. Ya kai bakinsa ya sumbanci goshinta. Sannan ya ware hannayenta. "Ina tsarin Allah daga shedan la'ananen, duk wani abun kin, ko na cutarwa da zai shiga tsakanina dake, ina neman tsari Allah daga duk wani abun da zai saka na bata miki rai, kuma ina rokon duk wani alheri da zai kara mana zaman lafiya da kaunarnan junanmu, ina neman rahamar Allah a duk inda za mu saka gaba, ina neman rahama daga Ubangijin da shi ya hada mu, ya kawo mu a nan kuma ya nuna mana wannan ranar mai muhimmanci a rayuwarmu, Allah na gode da wannan kyauta da ka yi mini, da sunan Allah mai rahama mai jinkai" Ya rumgumeta halal hug ya saka a kirjinsa, wani irin rumguma yayi mata sosai kamar za a kwace masa ita, ya yi squeezing dinta har sai da abayar dake jikinta ta dage, yayi sama da ita kafafuwanta suka dage. Emily ta yi shiru..... Hawayen suka yanke mata, numfashinta na fita a hankali yana shiga da kamshin turaren jikin mijinta, ba a taba rumgumarta ta ji damuwarta da fargaba sun gushe mata ba sai a yau. Babu wanda ya taba rumgumarta ta ji hankalinta ya kwanta ya samu sukuni ba irin Aliyu. Yanzu ta san me ta rasa, sai a yanzu ta san what truly halal hug means, ka so a so ka so na hakika dabam yake, auren wanda yake kaunarka kaunar ta gaskiya ta hakika a dabam take, son wanda yake sonka so na hakika dabam yake, lallai akwai wata irin rahama da farinciki, jindadi da cikar buri a auren soyayya. Ranar yau kadai ya nuna mata tana da muhimmanci, wunin yau kadai ya shafe duk wani fargaba da take, ta share duk wata damuwa da ta fuskanta. Lallai macen da miji yake so Sarauniya ce, a yau Aliyu ya furta mata kalaman da babu wanda ya taba yi mata su a ranar aurenta, shi da kanshi yake gode mata, a yau ta shaida soyayyar gaskiya marar algussu. Aliyu be kalleta a matsayin mace da ta taba aure biyu ba, be kalleta a matsayin ta haihuwa biyu ba, ya kalleta a matsayin macen da yake so, lallai mai son be ganin ramarka, a yau ta dandanin miye auren so da masoyin gaskiya. "Meyasa ban hadu da kai ba tuntuni?" Ta tambaya tana murza kanta a kirjinsa kamar zata tsaga kirjinsa ta shige cikin zuciyarsa. Sai ya bata amsa cikin rada shi ma idonsa a lumshe cike da kwalla, auren soyayya suka yi da Kameela amman ko ita bata nuna masa kaunar haka a ranar aurensu ba kamar Emily. "Ita ce tambayar da na dade ina yi ma kaddara, miyasa bata hada ni da ke, tun farkon da ta bude miki shafi" "Aliyu ina ƙaunarka" Ya bude ido ya sauketa ya rika fuskarta yana kallon cikin kwayar idonta. "Duk wata kauna ta furuci ko ta aiki, ko wanda take zaune a zukanta masoya, Ayusher na fi kauna, kaunarki, na fi numfashinki son kasancewa da ke, ni da ke ABOKAN RAYUWA ne, sai da mutuwa" Ta yi sauke wani sanyayen numfashi ya lumshe ido tana murmushi. “Madalla da kasancewarka cikin rayuwata, ka zamo min tauraro mai haske. Madallah da ABOKIN RAYUWA irinka" Ya kai goshinsa ya hade da nata, hancinsa a saman nata, ya saka yatsunsa na dama cikin nata, na hagu ma haka suka tsarkafe yan yatsunsu cikin juna. "Abokiyar tafiyata, har tsawon rayuwa, Madalla da ABOKIYAR RAYUWA irinki" Sun dade a haka sannan ya sake ta ya matsa baya. Ta kalleshi tana murmushi a yau ta san yadda rumgumar masoyi take mantar da damuwa, ya sameta tana kuka ya maye mata gurbin hakan da murmushi. "Idan akwai abun da kike son aikatawa, ni halalinki ne just do it" Ta taka one step forward kamar ya san manufarta sai ya maida hannayensa baya ya duko da fuskansa ta sumbanci gefen fuskansa da sauri, ta juya baya tana jin kunya. Murmushin dake fuskarsa ya fadada har ya bayyana hakoransa. Ya nufi kofar fita har ya kusa isa sai kuma ya yanke tafiyar ya juyo ya dawo gurin masoyiyyarsa ya rumgumeta ta baya, sai kuma ya juyo da ita, da sauri ta saka hannayensa ta rufe fuskarta. Hannayen dake fuskarta ya sumbanta ya goga fuskarsa yana dariya sannan ya saketa ya fice dakin ya rufe mata kofa yana jin kamar kar ya tafi ya barta. TURHAN POV. A lokacin da ya fito daga falon na Daddy waje ya tsaya jikin motar da suka zo, ya ji duniyar kamar tana juya masa, ko da wasa be yi tsammanin Emily zata juya masa baya har haba ba, kuma a gaban iyayensa. Dadin dadawa kuma ta furta sunan wanda take kaunar a gabansa cikin kunnensa. Miya yayi ma Aliyu? Ita ce tambayar data fara zuwa masa a rai. Miyasa ya dauki bata masa ta wannan hanyar? Wace irin kiyayya Emily take masa har haka? Be samu amsoshin tambayayinsa ba Sarkin ya fito, kamin ya shiga motarsa Alhaji Bulama ya fito tare da Mahaifin Kameela, shi dai ya san ya shiga mota, yadda aka yi suka kama hanya har suka isa gidansu Ammy shi ne abun da be san yadda aka yi ba. Ya zauna cikin falon yana sauraren yadda Alhaji Bulama yake labarta mata abubuwan da suka faru, yana jin mahaifinsa yana magana da ita amman be fahimce me suke magana kai ba, a yau ne karo na farko da yaren larabci ya subuce masa a kai. "Aliyu... Aliyu... Aliyu..." Furucin Emily nata dawo masa, be san yaushe aka mahaifinsa ya fita ya dai ji Alhaji Bulama ya dafa shi yana fadar maganar da be gane ba, yana zaune a falon kowa ya fice be san an yi ba sai da Ammy ta girgiza shi. "Turhan nan?" "Ammy me na yi ma Aliyu? Ina ta kokarin tariyo rayuwarmu ta baya zaman da muka yi, me na masa? Ashe ko ba ni da rai bancanci yayi min hallaci ba?" Ammy dake tsaye ta zauna idonta cike da kwalla. "Ka yi hakuri Turhan, ba a taba cin amana aka yi nasara ba, muna nan da kai hakki zai bayyana" "Miyasa ita ma ba zata fahimce ni ba? Ko. Kalaman ne nawa ba su kai ba? Wallahi ina sonta ina kaunarta Ammy, kuma ba zan sake cutar da ita ba, Wallahi na yi alkawari ba zata sake zubar da hawaye akaina ba" Hawaye ya sauko ma Ammy, ko wace uwa bata son ganin danta cikin damuwa balle kuma Ammy da Turhan kadai take da shi, bata tana ganin tsananin damuwa a tsare da shi data gusar masa da hankali ba irin yau. "Tashi ka tafi ka yi sallah" Be haura sama ba sai ya fice falon a masallacin yayi alwala yayi sallah, suna fitowa masallacin mahaifinsa ya kira shi akan ya shirya, jirginsu zai tashi karfe 5pm, daga shi sai DR A-B ake jira saboda Dr A-B yace ba zai bar garin ba sai an daura auren Emily da Aliyu kuma karfe 4:30pm za a daura. A nan ya ji wani labari da yafi furta sunan Aliyu azaba a zuciyarsa. Daker ya iya kawo kansa falon Ammy. Yana shigowa ya nufi agogon dakin ya tsaya yana kallo yadda dakika take juyawa ta zama minti. Jikinsa yayi ma kafafuwansa nauyi yana ta lilo jiri na dibansa kamar zai fadi. Yana ta kallon agogon da second din ke dis da bugawar zuciyarsa yana jin wani dubu na haye masa kai. Har agogon ya nuna karfe 4:30pm. Turhan ya rufe ido, Ammy dake tsaye bayansa tana kallonsa ta karaso ta rike ɗanta tana jansa baya a hankali har ya zauna kan kujerar dinning. "Ammy a yau na san rashi, na san miye kiyayya, na kuma san miye soyayya, da na sani ƙeya, tsanar da Aisha take min ta kai har ta auri abokina ta bar ni? Shin ita bata tafiya ne? Ammy ina son yarinyar nan miyasa kika cilasta na sake ta? Ammy ma rasa Aisha, uwar ƴata na rasa ta, cikon farincikina na rasa shi a yau....!" Hawaye ne masu zafi suke sauko masa, ko Ammy sai da tsoro da tausayin ɗanta suka kamata, domin bata taba ganinsa cikin wannan yanayin na gasawa da rudani irin wannan ba. " Dady?" Ya ji muryar yarsa da sai a yanzu ta filo daga dakinta ta sauko kasa duk abun da ake bata sani ba. Turhan ya saka hannayensa biyu ya dafe kansa baya son yarsa ta ga hawayensa. Fatima ta zo da gudu ta rumgume shi. "I miss you... Dady ka dawo? Ina Momy kace tare za ku zo ba?" "Momy ki ta zabi Aliyu Fatima, ta barki ke da Dady, Momy ki ta auri Aliyu bata auri Dady ki ba, tace Aliyu take so ba Dady ki ba" Ammy ta fada mata tana hawayen tausayin danta gaba daya ta rikice. Cikin tsoro Fatima ta bude hannayen Turhan babu hawaye a fuskarsa amman suna kwance a cikin idonsa, sai kawai ta fashe da kuka sosai ta rumgume. Ya dauke ta ta dora saman jikinsa ya hade duk wani abu da yake ji ya fara rarrashinta. Wayarsa ta yi kara alamar shigowa sako, ya ciro wayar ya duba Dr A-B ne ya aiko masa da sako cewar za su tafi shi ya tsaya sai next week, ya aje wayar ya kalli mahaifiyarsa sai ya sakar mata murmushin karfin hali. [8/25, 8:41 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣1️⃣ KAMEELA POV. Sosai ta natsu tana sauraren labarin da Hajiya take bata kamar yadda Alhajin ya fada mata yadda abubuwan suka faru. "Wai kawai sai ta bude baki tace Aliyu... Na ce daman dai hadin baki aka yi da uwarko?" Kameela ta kai tsaye. "Hajiya dan Allah karku bari a yi auren nan, Wallahi ina son mijina, kuma na san yana so na, kawai makircin yarinyar nan da uwarta" "Zancen banza, aure ai tuni aka daura, babanku yace mai gidansa da dansa ba su bar garin nan ba sai da aka daura auren, wai da la'asar sai kace auren kauye" Anty Shafa ta karba mata. "Auren kauye ai yafi na wannan arniyar daraja, kuma shegiya ce shiyasa suka daura auren kar ya subuce, dadin dadawa kuma Mama Baraka ai zata iya yin komai saboda ace yarta ta auri Aliyu kin ga ai ta yi gasa da ke" Kameela ta dora hannu a kai. "Na shiga uku, Innalillahi... Hajiya ina son mijina ina son Aliyu" Hajiya ta daka mata tsawa. "Ke dalla gafara can mahaukaciya, Aliyu autan maza ne halam? Tun da kika aure shi wani farinciki kika samu? Kuma ke da kike ikirarin ba zaki zauna da mai mata ba? To yanzu ai yayi aure, kuma shi be damu dake ba sai ke? Ko kuma mu mahaukata ne da za mu bar ki yi kishi da marar uba? Yarinyar da bata kai rabin matsayinki ba? Daman can ba son auren nan muke ba, shi kuma be shirya rike amana ba, aure be jimawa daga dawowa haihuwa an fara samun matsala" Ta fashe da kuka tana jin duniyar ta juye mata mijin da take so ya juya mata baya, dakunsa da take kuma ya kare a yau saboda yayi auri abun da bata taba zato ba, gashi iyayenta sun kasa fahimtarta. "Ki duba ba fa Hajiya, ko irin ya dawo yana bada hakuri din nan be yi ba, gaba daya ya nuna shi daman ba sonta yake ba, kawai iyayensa da shi sun shirya wulakanta zuri'armu ne, idan har yana sonki kuma yayi nadama ai kamata yayi ya kawo kansa yana kuka yana faduwa kasa yana tuba, amman ba ko da ya, sai ma tafiya ya auri marar asali ko dai ya manta waye shi ne? Kuma iyayenwai suka bar shi? Tab" Anty Shafa ta fada tana tabe baki da jinjina lamarin. Kameela ta tashi ta bar su a falon, dakinta ta shige ta kwanta kasa tana kuka kamar an yi mata mutuwa, bata taba jin zafin azabar kishi da bakincikinsa ba irin yau. Aliyunta ne dai yayi aure? Ta rarraba ta isa bakin gadonta ta kai hannu zata dauki wayarta kuka ya ci karfinta. " Aliyu ka yi aure? Ina alkawarin da ka yi min Aliyu? Ina soyayyar da na nuna maka?" Ta kai hannu daker ta dauki wayar ta da sabon layin da take aika masa sako ta gwada kiransa tana kuka, ringing daya ya daga, ba dan be san mai kiran ba sai dan ya shiryawa kiran. "Sallamu Alaikum" "Aliyu ina alkawarin da ka yi min? Cewar ba zaka min kishiya ba?" "Na cika miki, tun da ban miki kishiya da igiyar aurena ba" "Ina ladar soyayyar da na nuna maka?" "Na miki sakamako iya yadda zan iya, fadi tashi a tare muka yi har iyaye suka amince muka yi aure, yanayin rayuwar aurenki da zafin kishinki, rashin nazari kamin yanke hukunci sune abubuwan da suka hana zaman aurenmu, kuma ba zan miki Karya ba, kowane namiji yana son kwanciyar hankali da farinciki a gidansa, iyakar hakkinki na baki, har wanda ba naki ba na baki, kin wuce gona da iri Kameela, idan ma na ce zan cigaba da zama dake ba ni da kwanciyar hankali, kuma mahaifiyarta ba zata yarda ba, gashi kuma iyayenki ba so na suke ba" "Munafiki azzalumi maci amana, can da baka ganin komai sai a yanzu da ka auri karuwa? Yar titi marar uba? Yar zina? Matar da aka haifa na da aure ba? Ai baka yi aure ba Aliyu tun da baka auro yar gidan mutumcin ba" "Zaki iya zagina ki ci mutumci, amman ban da matata, dan an haife ta ba da aure ba, miye laifinta? Ko kina tunanin dan'adam yana iya tsallake kaddara ce ne? Ko daga sama ta fado ina sonta a haka, dan haka karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, kamar yadda ban yarda a taba mutumci lokacin da nake aurenki ba, ba zan yarda a taba mutumcinta ba" Ya yanke wayar, Kameela ta ji kamar ta haukace tsabar bakinciki na jin kalaman Aliyu. A daren da bakinciki ta kwana tunani be barta ta runtse ido da sunan bachi ba, ganin abun take kamar mafarki, wai Aliyu yayi aure, a tunanin zai gama kewaye kewayensa ne ya dawo mata. Idan ta tuna yadda take rayuwa da mu'alama da mijinta, ta hango yanzu Emily ce a makwafinta, sai ta ji kamar zata haukace, wani karin bakin cikin ma Emily daga tsatson Mama Baraka take ba, da ace daga wani gurin ne dabam wata kila zata fin saukin kishi. Yanzu kenan Emily ta yi nasa? Bayan ta shiga tsakaninta da mijinta tun a PH gashi kuma ta aureshi, babbar matsalar ta ma babu mai rataya kishin ita kadai take yakin, tun da yan'uwanta sun gagara fahimtarta. Haushinta da Hajiya ta ji ya saka bata damu ta cilasta mata fitowa ta ci abincin ba, a ganinta akwai mazan da suka fi Aliyu komai nesa ba kusa ba, amman tana wahalar da kanta ta wanda tun tashin farko ba su so auren da shi ba, a yanzu ma taki ta bawa wasu kofa ne amman ana nuna mata kauna, gata kyakkyawar bazawara sakin Wawa, babu ɗa balle abu ya dame ta. Sai da ta bari kowa ya gama karyawa sannan ta sauko ta nufi dinning kanta na tsarawa kamar zai fashe, ta zuba madara da suga a cup ta zuba ruwan zafi sai kuma ta ji ba zata iya sha ba. Ta zauna a kujerar tana kallon Anty Shafa dake kwashe kayan wasan yaranta. EMILY POV. Kusan wannan ne karon farko da aka daura aurenta ta kwana da cikakke farinciki. Wacan auren nata na farko anyi shi ne a lokacin da iyayen mijinta basa so, kuma bata da wanda ya tsaya mata, tsabanin yanzu da komai kishiyarsa ne, na biyun kuma an daura da wanda bata so be san darajarta ba... But Aliyu ya zama wani na dabam a gareta, ya nuna mata farinciki da jindadin data kasance matarsa, gashi mahaifiyarsa tana sonta, ga shi yan'uwanta sun shaida. A yau ta kara sanin darajar yan'uwa da dadinsu. Ta farka cike da farinciki, da kuzari tana gama Sallah asuba sakon Aliyu ya shigo wayarta. "Barka da safiya matata mine and mine only, farar mace mai farar zuciya" "Barka da safiya Aliyu?" "Wato Aliyu ko? Idan na zo sai na horar da bakin nan sai na masa hukunci" Ta yi dariya. "I'm sorry" Ta rubuta masa. "I love you" Ta maida masa amsa da heart Emoji guda biyu. Sannan ta dauko karatun da suke fara karantawa, sai ga kiransa ya shigo ta amsa tare da amsa sallamarsa. "Amince ya tabbata ga kyakkyawar yan mata ne mai zazzakar murya, da tattausar zuciya" Ta yi murmushi mai sauki. "Tare da jarumin da ya tare komai ya wanzar da farinciki a zuciyata" "Zai wanzar dai, yanzu ne zai fara aikin, ina nan kwance ina ta tunaninki, kuma na san idan na dako sammako Ummi zata gan ni, dan haka na jira na ji muryarki" "Na gode da ka kira ni" "Aa ranki ya dade na gode da kika amsa, za mu iya karatu ta waya? Ko sai na zo?" "Zaka iya?" "Ta ina zuciyarki ta samu kwarin guiwar tambayar abun da ba zan iya ba saboda ke?" "Ina sonka Aliyu" Ta fada da kwalla a idonta. "Ni kam kaunarki nake Amaryata wacce ta fi ta kowa, bude littafinki ki fada min abun da kika iya" "Ni ba na gane komai idan baka kusa da ni" "Ki sassauta kalamanki, inda ba son kike zuciyata ta fashe da kaunarki ba, da kuma kewarki da na yi a yau fiye da kullum" Ta yi dariya. Sannan ta fara karatun bakin inda ta iya ya dora matada wani. Bayan sun yi sallama ya aiko mata da sakon. "I love you" Ta aika masa da sakon heart. "No ki ko yi fada min I love you, yana kara damkon kauna kuma ni mijinki ne" "Okay" as reply "Okay??" I love you ta tura amsa. "I love you more" Ya maido mata da amsa. Ta kwanta a gurin tana ta kalmomin cike da kaunarsa. Misalin karfe takwas na safe ta fito dakinta ta sauko kasa cike da kunya ta shiga Kitchen domin ta ya Ummi aiki kamar yadda ta saba. "Yanzu nake kokarin cewa a kiraki, ki shigo ko kara koyar abubuwan da mijinki yake so" "Ummi ina kwana" "Lafiya ƙalau, an tashi lafiya?" "Alhamdulillah" Ta amsa tana jin tsananin kunya abun da bata saba ba. Suna tsaka da girkin ne, daya daga cikin ma'aikatan gidan ya kwankwaso kofar ya sanar da Kulu dake mopping din falon cewar ana sallama da Emily. Kulu ta shiga kitchen ta sanar da Ummi. "Wake sallama da ita?" "Ban tambaya ba Hajiya" "To ki tambaya mu ji, yana ina?" Kulu ta juya, bata jima ba ta dawo. "Wai Hajiya Baraka ce" "Ah ah tana ina?" "Can wajen gate" Daga Ummi har Emily fuskar mamaki suka yi. "Bata shigo ba?" Emily ta tambaya. "Eh haka yace tana can waje" Ummi ta dan yi shiru sannan ta amsa. "Toh gata nan zuwa" Sai da Kulu ta fice sannan Ummi ta kalli Emily ta ce. "Wata kila tana son ta yi wata magana da ke bata son mu ji ko mu gani, ki tafi ki same ta" "Okay" Ta amsa sannan ta bude kofar baya ta kitchen din ta fice daman jikinta a lullube yake da Hijab. Ta nufi gate din ta bude a hankali ta fita, ta yi zaton ganin Mama Baraka ne, sai ta yi arba da Turhan tsaye kusa da motarsa. Da ta duba ko'ina bata ga alamar Mama Baraka ba sai ta juya zata koma. "Ba zan samu damar da za ki saurare ni ba Aisha?" "Wata kila zaka fada min magana marar dadi ne" "Aa dan Allah ki saurare ni" Ta juyo ta matsa kadan ta tsaya tana rumgume da hannayenta. Da ya kalleta sai ya ji kamar be san miye so ba sai a ranar. Cikin yanayi na sanyi jiki da damuwa ya soma magana. "Na san idan na ce ni ne, ba za a barki ki fito ba, saboda ke da mutanen gidan kuna kallona a matsayin makiyinku ne, shiyasa na yi amfani da sunan Mama Baraka" Ba ta dai ce masa komai ba har ya dora. "Aisha zan kara da kara baki hakuri na abubuwan da suka faru tsakaninmu, kasancewarki a rayuwata ya koya min darasi mai yawa, na san zafin so, na san zafin rashi, kuma na san zafin da kika ji lokacin da na juya miki baya, saboda a yanxu ina jin fiye da abun da kika ji, ke kin ji zafi ne kawai amman ba dan kina so na ba, ni kuma yanzu ina fama da tsabanin haka ne. Jiya da dare ban yi bachi ba, ina ganin abubuwan da suka faru kamar a mafarki, amman yau da safe sai na fahimci wani abu, idan kana son mutum ai zaka so farincikinsa ko? In har zaki yi samu farinciki da ni na kasa baki a gidan wani ne, me zai saka ba zan so haka a gareki ba? Idan na ce miki ban yi bakinciki ba na yi karya, ban kuma ce zan warke ba, amman sannu a hankali zan samu salama" Ya hade yawu. "Na gode Aisha, da kiyayyata ko tunanin abun da na miki, da wahala bata saka kin zubar da cikina ko jefar da yata ba, na gode da kika kula da Fatima, na gode da kika yi ma Ammy biyayya gurin aurena, a yayin da ni na kasa yi mata biyayya gurin rike amanarki, kuma ina fatar a duk lokacin da wani abu ya taso na Fatima idan na sanar miki za ki shiga ki tsaya mata kamar yadda kika saba, na kawo ne saboda anjima kadan jirgimu zai daga, zata zauna gurinki na dan lokaci, idan na dawo zan dauketa zan tafi Sudan da ita, na yi magana da Ammy ta amince kuma ina fatan ke ma ba za ki, ki yarda ba, ki yi hakuri amman ba zan iya barin yata ta zauna a gidan wani ba" Hankalin Emily ya tashi. "Fatima ta yi kankanta ka tafi da ita masarautarku, har yanzu bata san ta banbance daidai da rashin daidai ba, ta yi kankanta ta fuskanci kalubale" "Kina tunanin zan iya bari a wulakanta ke da kike mahaifiyarta, balle kuma ita? No babu abun da zai faru" Yana rufe baki Aliyu ya iso kusa da gate din gidan da motarsa. Ya bude motarsa ya fito ya tsaya inda suke, yana kallon Emily da karantar yanayinta sai dai be ce komai ba, ba shi da nufin zafafa domin Turhan uban yarta ne matukar ba yayi kokarin wuce gona da iri ba ne, dole zai bar wata karamar kofa a tsakani. Turhan yayi murmushi yana kallon Aliyu. "Ina taya murna, ka yi nasara, amman ka sani, ba a cin amana kuma a zauna cikin salama, kai ma nadama zata tambaye ka kamar yadda ta tambaye ni a yanzu" "Ba zaka fahimce ni ba, amman Wallahi ban tsare wani abu daga gareka ko daga Emily da nufin na raba tsakaninku ba, kuma ban boye komai da nufin na mallaketa ba, ni da kai da ita, muna zagaye ne da kaddara, a jiya da iyayenka suka zo, Wallahi ban tsammaci zan same ta ba, indai har zan iya cutar da kaina to zan iya cutar da kai Turhan" Turhan ya kalleshi sama da kasa kawai yayi murmushi, ya juya ya bude motarsa ya riko hannun Fatima ya fito da ita, yayi mata alama da ta tafi gurin Mamanta, ta kalli Emily da ke miko mata hannu tana mata murmushi. A gurin Fatima ta murje ido ta rike rigar Babanta da hannu biyu ta juyawa Emily baya. "Fatima sweetheart, za ki zauna gurin Momy yanzu kin ji?" Ta girgiza masa kai ya kara rike rigarsa. Ta kalli Aliyu ta shige da fuskarta a jikin mahaifinta. "Wani abun ka fada mata?" Emily ta tambaya tana jin babu dadi. Turhan ya girgiza kai. "Ban fada mata komai da zai saka ta tsane ki ko ta juya miki baya ba, kina kallona a matsayin makiyinki ne kawai, amman abun ba haka yake ba." Emily ta matsa ta kai hannu ta riko sai Fatima ta buga hannun Emily tana hawaye ta kara rike Babanta. "Tun da bata son zama, zan koma da ita idan ta bukaci ganinki direba zai kawota, ina miki fatan alheri ke da sabon ABOKIN RAYUWA" Emily ta kasa cewa komai idonta ya cika da hawaye bata yi zaton haka daga gurin yarta ba. Turhan ya bude mata mota ta koma ciki ta zauna, ya rufe sannan ya zagaya ta shiga yaja motar ya bar su a gurin tsaye, yana jin wani irin bakinciki da be taba ji ba, amman idan ya juya ya kalli yarsa sai ta ji sassauci. Emily ta bi motar da kallo tana hawaye har ta daina hangota. "Kowa na zauna da shi sai ya juya min baya, har da ya..." Aliyu ya rufe mata baki da sauri, ya juyo da ita ya sakata a kirjinsa ya rumgume, yana shafa bayanta a hankali, babu kalma ki yi hakuri rumgumar kadai sai ta ji hawayenta ya yanke, ta haka take iya gane Aliyu ne ABOKIN RAYUWARTA... Ta dago kai ta kalleshi sai ya sake ta ya saka hannayensa biyu ya share hawayenta. "Kuka be miki wahala ko? Zai na zane hawayen nan da suke bata fuskar matata" Ya bude mata gate yana rike da hannunta. "Shiga gida" Ya saki hannunta ta shiga ciki sannan ya koma motarsa ya yi horn aka bude masa ya shiga ciki. Da ya faka harabar gidan sai da ya tsaya ya jira Emily ta iso ta shiga falon sannan ya bi bayanta. A lokacin da ya shiga falon ya ga babu kowa sai ya jidadi yayi hanzarin kamo hannunta ta baya ya juyo da ita. "Hajiya ba ki gaishe ni ba fa" "Mun gaisa dazun" Ta amsa cikin rada kamar yadda yayi mata. Ya rufe baki ya kashe mata ido. "Aw haka na tuna" Ta cire hannunta da sauri ta nufi hanyar kitchen. Shi kuma ya nufi stairs yana murmushi. Dakin mahaifiyarsa ya shiga ya same tana daura dankwali. "Ummi ina kwana" "Lafiya kalau an shigo?" "Eh, Ummi sai na samu Ayusher a waje" "Eh Hajiya Baraka ce ta zo tana sallama da ita" "Waye yace Mama Baraka ce? Ba ita na samu a waje ba Turhan ne" Ummi ta kalleshi da sauri. "Turhan? Wanda aka aiko ce mana yayi Baraka ce" "Ummi baku bincika ba kuka barta ta fita, yanzu da wani ne da zai cutar da ita fa? Da yanzu ni za a bari a matsala" "Na yi zaton ko tana son magana da ita ne Private, ita ma da ta fita ta ga ba ita ba ce ai sai ta dawo" "To ina zata san wannan idan tana son magana da ita ai ga dakuna ko kuma ta aiko a dauketa, amman sai a bari ta fita a bincika ba kuma ba a bi bayanta" "Aisha ce ba zata san ta dawo ba?" "Eh mana, duka duka nawa Ayusher take? Wannan tunanin ba zai zo mata ba, yanzu ne fa kwakwalwata take girma" Ummi ta saki baki tana kallon Aliyu da a bakin gaskiyarsa yake maganar. "Toh za a kula next time, yanzu dai ka dawo da ita ko yaya?" "Ai ba zan bar yarinya karama a waje ba" Ummi ta yi murmushi kawai ta nufi kofa ya biyo bayanta. A falo suka rabu ta nufi bangaren Daddy shi kuma ya nufi dinning din da matarsa take zaune tare da Nafeesa. Nafeesa na gaishe shi ta mike tsaye ta fice dinning din domin ba su damar karyawa su kadai ba tare da takura ba. "Kika yi serving kanki? Baki bari na zuba miki ba?" Ta mike tsaye. "Bari na zuba maka" "No it's my duty to feed you, zauna zan zuba da kaina" Ta koma ta zauna tana murmushi. Ya zuba ma kansa tana cin abincin yana kallonta har ta aje spoon. "Kin koshi?" Ta daga mishi kai. "Ba ki ci da yawa ba, ko wani abun kike so dabam?" "Aa" Ta amsa, ganin Nafeesa ya saka ta jin kunya sai ta mike tsaye. "Bari na dauko wayata" Aliyu ya juya ya kalli Nafeesa. "Idan kika aje plate din ki dauko mata wayarta" Nafeesa ta amsa da tohm. Emily ta koma ta zauna tana dan jin kunya. Nafeesa ta dauko mata wayar ta kawo tana mata wani kallo na zolaya. Emily ta karba ta rike "Thank you" Nafeesa ta yi murmushi kawai ta koma ciki, sai a lokacin Aliyu ya sake kallonta ya ce. "Kamata yayi ta ce you're welcome Mrs Aliyu ko?" "Idan Ummi ta zo ta same ni a nan zata ce ba ni da kunya" "Haka fa, ke ce mai kunya ni ne marar kunya ko?" Ta yi dariyar da bata shirya ba ta sauke kanta kasa tana taba wayar. A nan ta yi arba da sakon da ya sauya murmushin fuskarta zuwa tashin hankali. Tuna Aliyu na gabanta ya saka ta yi kokarin boyewa da murmushin dole. "Miye?" "Ba komai" "Vito ne? Ko Kameela?" "Miyasa ka zarge su?" "Saboda Turhan be jima da barin gidan nan ba, ba zai yiyu ya miki wani sako na tashin hankali da zai bayyana a fuskarki ba, ko mutuwa yayi ba ke za a sanarwa ba, amman Kameela zata iya aiko miki da sako marar kyau, haka ma Vito, cikin biyu dole a samu daya" "Vito ne" Ta fada kamar zata yi kuka. Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zagaya gefenta ya karbi wayar. "Congratulations kin yi aure ko? Kin yi min butulci Emily kuma dole ki dandana dacin hakan, ke da wannan Balaraben da ya aure ki, ke da fitinanniyar yarki" Aliyu ya ciro wayarsa ya kwafi number ya saka a wayarsa bayan ya gama karanta sakon, sannan ya tura masa da sako da wayarsa. "Ba Balarabe ne ya aureta ba, ni ne na aureta mutumen da ya janyo ta daga PH zuwa Kd, mutumen da suka yi aiki tare, wawa ka zo ka tare ni mana, miyasa kake tsoro?" Ya kalleta. "Daman na yi tunanin zai samu number duk da yake sabuwar number ce, amman mai son abun ka ya fika dabara, kuma zuciyata ta raya min yana bibiyar rayuwarki, amman yanzu an zo karshe da yardar Allah, tun da har giyar hauka ta dauke shi ya turo wannan sakon za a gano inda yake" Emily ta mike tsaye. "Kashe shi za'ayi?" A kokarin Aliyu na kwantar mata da hankali ya ce. "Aa za a dai kama shi, sai a gabatar da shi gaban kuliya saboda kar ya cutar da kowa, haka yayi miki?" Ta daga kai. "Zauna kin ji yan matana, bari na nunawa Daddy wannan sakon, kuma zan sanar da Ammy halin da ake ciki, ba lallai idan na yi magana da Turhan ya saurare ni ba, amman na san Ammy zata dauki abun serious" Ta koma ta zauna ya nufi hanyar da zata sadashi da bangaren Daddy, sai kuma ya juyo ba shi da nutsuwar barinta a falon jin yake kamar wani abu zai same ta. "Shiga dakin Nafeesa ki zauna, kuma kar kowa ya sake sallama miki ki fito ko ni ne, mai son ganinki ya zo ya same a nan" Ta sake tashi, zuciyarsa bata bar shi ba sai da ya rakata har bakin kofar dakin Nafeesa ya bude mata ta shiga. "Karki bar yarinyar nan ta fito, idan ta bata ke na sani" Ya bugawa Nafeesa warning, sannan yaja kofar ya rufe ya nufi bangaren Mahaifinsa. TURHAN POV. Ammy bata yi mamakin ganin ya dawo da Fatima ba, daman ta lura tun kamin su tafi bata son tafiyar, tun jiya tana jikin ubanta tana taya shi jimami ko abinci sai da ta ga yana ci sannan ta ci. "Shiga ciki ki yi kallo" "Dady ba zai tafi ba?" Ta tambayi Ammy dake bata umarnin. "Eh" Tohm" Ta amsa sannan ta nufi hanyar dakinta. "Fatima" Turhan ya kirata sai ta juyo, ya tafi inda take ya rumgumeta sosai yayi kissing dinta ita ma ta yi masa kiss. "I love you" "I love you Too Dady" Ya sake ta yana murmushi, ya bita da kallo har ta shige sannan ya dawo kusa da Ammy. "Bata yarda ta zauna can, ko magana bata yi da Emily ba" "Daman na ga alamar ba zata zauna ba" "Ni zan tafi Ammy, anjima kadan jirgimu zai ta shi" "Ba zaka bari sai next week ba" "Garin ne baya min dadi gara dai na tafi kawai, ko zan samu salama" Ammy ta mike tsaye ta bude masa hannayenta sai ta matsa kusa da ita ta rumgume uwarsa. "Jikinka da zafi sosai Turhan, baka da lafiya ne?" "Zazzabi ne kadan na ke ji" Ta sake shi tana taba fuskarsa da jikinsa. "Ba kadan ba ne, ko'ina ya maka zafi fa, gaskiya ba zaka yi tafiyar nan a yau ba" Turhan ya zube kasa ya rike kafafuwan Ammy yana kuka kamar ba shi ba. "Ammy dan Allah ki yafe min, bijirewa umarninki ne ya jefani a halin da nake a yau, da ace na bi yadda kika tsara, da yanzu ban shiga wannan damuwar ba, da yanzu ban shiga wannan bakincikin ba" "Na yafe maka duniya da lahira, kuma damuwa Allah zai maka maganinta, Emily ba ita kadai ce mace a duniya ba" Ta daga shi ya zauna kan kujera ya rike kansa dake tsarawa. "Ba zaka tafi yau ba" Ya sauka kasa ya zauna ya dora kansa akan cinyar Ammy. Sun dade a haka kamin ya ciro wayarsa yayi canceling flight din, ko kadan a yanzu baya son ya sabawa Ammy domin ya ga illar hakan. "Zan bari sai next week" "Allah ya maka albarka, bari na dauko waya na kira Likitana" Ammy ta tashi ta fice daga falon ta shiga dakinta, tana daukar wayarta ta ci karo da sakon Aliyu daga numbersa da tuni ta goge ta a wayarta. [8/27, 11:03 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣2️⃣ 🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟 🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘 Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida. ✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman 📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). 💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau! 📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa! TWO MONTHS LATER... "Ah gaskiya an gyara gidan sosai, Aliyu yayi kokari, iyayenta ma sun yi, ko ku kuka mata kayan daƙin" Ummi ta yi dariya tana kallon kanwarta Hajiya Larai. "Hajiya Larai, ba mu muka mata ba, mahaifiyarta ta karbe ragamar komai daga hannunmu, ita ta yi mata komai, da kam har na yi magana da Khadeeja Candy za mu siya kayan Kitchen ta mana breaking down na komai sai gashi ita mahaifiyar tace dan Allah kar mu yi komai mu bar ta ta yi, sai muka cire hannunmu, lefe kawai ta hada mana, sai na yi ma Hajiya Baraka Recommending dinta, indai ba ta canja ba ina tunanin gurin Khadeeja Candy aka siya komai na kayan Kitchen da bedsheet da curtain har frames ma domin komai saidawa take" "Mhn idan ba ke ba Ummi yaushe za ayi ma yarinya miji kuma ayi mata kayan dakin? Wannan ai shi ke nuna kin an bata sadakar Aliyu kenan, wannan uban lefe da aka zuba ai kam dole uwarta ta dafe ka cire ta a kunya" "Daman shi lefe idan namiji yayi ai kansa yayi ma, tun da shi za'ayi ma kwalliya, ba faduwa ba ce" "Haka ne, ta yi kokari gaskiya, dan kan an zuba kaya komai yayi gwanin sha'awa kam, kai kace ma dauko komai aka yi aka zuba kawai a ciki" "Ai Khadeeja Candy ce ba daga baya ba indai kaya ne, gurinta nake siyan tufafi Laces shadda, Atamfa abaya shoes kai komai fa, har adashe ma na ga tana yi, kuma a kawo maka komai cikin aminci da salama, facebook na fara haduwa da kayanta na gwada saya yanzu kam har mun zama regular customer" "Ikon Allah wasu fa suna da zafin nema, toh ita kuma a facebook take siyar da kayanta ne? Zan so na gwada dan gaskiya kayan nan sun burge ni" "Aa fa kin ji Hajiya Larai da wani zance, a ko'ina kika searching dinta za ki same ta, a TikTok ne, ko Instagram har Snapchat, ko a WhatsApp, amman fa ki tabbatar kin shirya siya" "Hajiya Larai ta yi murmushi, ta dauko wayarta Ummi na karanta mata number Khadeeja Candy wanda take whatsapp chat da ita. "0 8 0 3 6 1 2 6 6 6 0" "Zan dubata ta WhatsApp In Shaa Allahu, auren Maimuna da za'ayi sai mu siya mata komai a can ma, tana dai siyar da manyan kaya ko?" "Sosai, cooler daga 12k har ta dubu tari taskwas za ki samu a gurinta, ya danganta da abun da kike so" "Aiko zan gwada da yardar Allah" "Tohm Allah ya amice, ba da ke za a tafi karbar garar ba ne? Ko da yake kin ga dakin amarya har kin gaji" "Da ni mana, ina za a barku a baya, mun bada sadakar ango kuma ace ba za mu karbo gara ba?" "Wane irin sadaka Hajiya Larai?" "Ah yo sadaka mana mai sunan Mama, ke kin san idan ba Aliyu ba babu wanda zai kwashi wannan yarinyar nan haka, a aje zancen kyau a gafe a kalli asalinta" "Kin gani Hajiya Larai karki bar Aliyu ya ji zancen nan na ki, domin yana son matarsa idan kika fadi wani abu marar dadi akanta karamin abu ne ki ga ya sauya miki fuska, su shegu ba sa da zafi ko gata ne? Miye na su a ciki? Wannan zancen na cikin gidana ne, ni ban san miya ja ni na fada miki ba" "Aiko dai kin san ni bana barin ta kwana, amman ai ba nuna mata zan yi ba, ko shi ta kasa dai tana saka, tun da ke ma kin bi ina ni ina juya baya?" "Kawai ki musu fatan alheri, domin babu abun da zai raba su sai mutuwa da yardar Allah" "Tohm Allah ya sanya alheri, mu din ai sai da hakuri, ko'ina akwai mu, dangin miji ba, mu ga fari mu ga baki, mu koma gefe mu yi magana" Ummi ta tabe baki tana dariya. "Wanda be iya zama da ku ba kuke wahalarwa, wanda kuwa ya san ku ya karanci komai ya huta" "Heeeee Ummi.. Kuma fa haka ne..." Hajiya Larai ta kyalkyale da dariya ta mikawa Ummi hannu suka tabe. Sannan ta sauke kafa daya kan daya ta mike tsaye. "Bari na fita waje mu zauna kamin su iso" "Hajiya Larai jibila da cincin kawai za a kawo mana, kayan masarufi a kai ma angon abun sa" "Toh mu karba ne kawai na mu, ba za a raba ba sai kin ga komai" "Tohm shikenan" Ummi ta amsa tana Hamma, kusan tun da aka daura auren na Aliyu da Aisha Ummi bata huta ba, bata wannan bata wacan har aka yi wunin biki da walimar dare domin ya ki yarda ayi kida, haka yayi ko a aurensa na farko, Ummi ta yi zaton a wacan saboda fadi babu dadin da aka yi ta yi ne da family Kameela ya saka yace ba zai yi biki ba, domin su suka yi komai da ake na hidamar kida da raye raye kuma be halarta ba. A yanzu kuma ta gane haline na gujewa tsabawa Allah, ya fada mata ya sake jadada mata cewar Manzon Allah S. A. W ya ce Allah ya tsinewa duk wata ni'ima da Allah yayi ma bawa aka taru aka yi raye raye aka chakudu maza da mata, auren Emily na daga cikin ni'imomin da Allah ya yi masa dan haka na zai yarda ya rayu da ita a karkashin tsunuwar Allah ba, sai dai ba zai hana ta yi nata taron da mata yan'uwanta ba domin addnin ba haramta ba, matukar maza ba su gani ba kuma ba su chakudu ba. EMILY POV. Bata san miye auren gata ba sai da ta zama karkashin inuwar kulawar Aliyu. Daga ranar da aka saka musu rana tana karbar kyaututukan kauna da soyayya daga mijinta danginsa da kuma danginta. Sabon gidan da ya siya ma sai da ya dauke ta ya tafi ta ita ta duba komai ta fadi inda be mata ba aka canja, komai zai siya mata sai ya nemi zabinta, abun da take so shi za'ayi, bata taba auren wani ya lalaba kamar yadda Aliyu yake mata ba. Ko a lokacin da zai fada mata ba shi da ra'ayin yin biki ta sigar lalama ya biyo mata yana lallabata yadda zata fahimta kar ranta ya bace. Sai kuma aka yi sa'a ita ma bata da bukatar bikin saboda bata da wasu kawaye da zata gayyata idan ma za'ayi sai dai Mama Baraka ta yi na ta gayyatar. Haka kuma aka yi, Mama Baraka ta aikawa kowa katin gayyata da wuri, domin Emily ta dawo a sabon gidanta ne ana sauran wata daya biki. Danginta har wadanda suke nesa sai da suka halarcin biki. Emily ta ji wannan auren a dabam kuma ta kara fahimtar yadda rayuwa take tafiya, a wannan auren ne aka yi mata wankan lalle wanda ake yi ma ko wace budurwa a aurenta na farko, sai dai ita bata samu wannan damar ba sai a yanzu, ba taba shafa mata lalle ba sai a wannan karon, yan'uwanta mata da kawayensu ka shirya henna day wanda Aliyu ya dauki nauyi, domin bikin na duka mata ne babu maza. Anyi Walimar dare walimar data samu halarta manyan mutane daga bangaren Mahaifiyarta da kuma iyayen Aliyu da abokan arzikin Ummi. Ranar wunin biki Mama Baraka ta dauko masu masu kudin kwarya da kuma yarbawa suka kayatar da wunin. A gurin Khadeeja Candy ta siya duka kayan Kitchen din da aka sakawa Emily bayan, Ummi ta hadasu da ta bincika kuma ta ga akwai abubuwan da take bukata sai kawai ta zaba ta tura kudi aka hada komai ta aika da mota aka dauko mata, wasu kuma daga baya ta kara aka aiko mata ta hannun Driver. Mama Baraka ta shiga ta tsayarwa yarta tun daga gyaran jiki karbar lefe da kayan saka rana har kayan daki da gara bata bar kowa yayi mata ba. Dr A-B ma da so ya dauki wani abu bata ba shiyasa dama ba, sai kudi mai kauri ya turawa Emily ta hanyar Mama Baraka yace a aje mata idan bukatar wani abun ya tashi. A auren Aliyu Emily ta san miye gata a aure, ta san dadin yan'uwa da iyaye, ta san wasu abubuwan da suke na daga al'adar hausawa da kuma yarbawa. A wannan auren an yi mata gara an yi mata kayan daki da komai da mace take bukata daga iyaye, ga yan'uwanta a kusa da ita komai zata yi su suke shigewa gaba, su bata shawara ko ma su aiwatar ba tare da jiranta ba, yan'uwan Mama Baraka na nesa da na kusa duk an sadata da su wasu ta waya wasu kuma sun zo bikin. Bata kara gode Allah ba sai a daren da Aliyu ya aiko da manyan motoci zuwa daukarta tare da abokansa da wasu daga gwaggonninsa da iyaye. Mama Baraka da yan'uwanta suka yi mata nasiha suka mata kuduba da uwa ke yi ma kowace ƴa, aka dauke ta tana lullube da zane bayan ta saka tsadadden lace na al'adar yarbawa, Tana sanye da sakarta ta zinari da aka saka mata a lefe, wuyanta da murjani da ya sauko mata har gaban kirjinta, haka ma hannayenta, kafafuwanta da suka sha bakin lallen suna sanye da iborun, tana ta kamshin turare sai guɗa ake masu, suka ta saka mata albarka da yaren na yarbanci. Aka fada mata idan zata shiga gidan ta shiga da kafar dama kuma ta yi addu'a da Bismillah. Tana zaune falon mahaifiyarta Fatima ta shigo ta ratsa mutane ta zauna kusa da ita tana ta kallon mutane, Emily ta miko hannunta a hankali ta kama hannun Fatima ta rike, idan suka yi magana da yarbanci tana jin duk abun da suke fada saboda tana jin yaren yarbanci da igbo tun a zamansu na can. Can kuma ta juya ta daga mayafin mahaifiyarta ta leka fuskarta. "Momy kin yi kyau" Ta fada tana shafa fuskarta tana murmushi, hawayen dake makale a idon Emily ya zubo mata. "Kin fi kowace rana kyau, har da lalle fa da sarka har biyu, da makeup" Emily ta lumshe ido tana murmushi, ko kadan bata yi tsammanin jin haka daga bakin yarta ba, ko da yake tun da Turhan ya saka kafa ya bar garin Fatima ta dawo gurinta daker da sudin goshi sai ta waye cikin mutane, musamman da kannen Emily suke janta a jiki. Da kuma aka fara hidimar auren sai ya zama abun ya burgeta, domin bata taba gani irin wannan auren ba, komai a gurinta sabo ne, duk abun da za'ayi ana yi da ita yana gaba gaba. Aliyu idan ya zo gidan zai zo mata da kayan dadi, ko be zo ba zai aiko a kawo mata, wani lokacin idan ya zo ita yake sakawa a sallamo yayi hira da ita ya bata tsaraba ya tafi. Yana iya kar kokarinsa wajen ganin Fatima ta sake jiki da shi kuma ta kwantar da hankalinta dan kar damuwarta ta jefa Emily a damuwa. Kusan kuma kwalliya ta biya kudin sabulu domin ya samu fiye da rabin abun da yake nema a gurin Fatima. Wadanda suka kasance iyaye ga Emily ne suka bukaci kanen su daukewa Fatima hankali ta yadda za a fita da Emily ba tare da ta sani ba. Domin suna jin lokacin da take tambayar Emily yau sabon gida za su tafi ko? Da wayo aka fitar da ita, sannan aka fita da Emily, a nan ma ta ga wata al'ada da a bata kyauta a karbi Amarya. Emily ta shiga motar tana hawayen da a yau ta tabbatar na farinciki ne. Tana zaune shiru tana saurari tafiyar har suka isa gidan masoyinta kuma Abokin Rayuwarta. An riko hannunta ta sauko motar kanta a kasa aka shiga da ita gidan da duk wanda ya ga tsarinsa da kayan da aka zuba a ciki sai ya yaba da kokari mijinta da kuma iyayenta. Bayan iyaye sun fita aka barta da kanenta da wasu daga familyn Mama Baraka da suka zama kawayenta na short period of time. Abokan Aliyu suka rako shi ya shigo falon da manyan tufafi babbar riga har da hula. Kowane yana rike da babbar leda suka cikin big center table din da kayan taba ka lashe da suka shigo da su. A nan ta san wani abu siyen bakin amarya, abokan Aliyu suka siye bakinta da kudi mai kauri da siyayya da, sun yi farinciki sosai domin ba su bar gurin ba sai da kowa ya ji saukar alert. Sai da kowa ya watse Aliyu ya rufe kofar sannan ya yarda ya bude fuskar matarsa, sannan a hankali ya yaye duk wani abu dake jikinta ya rage daga dankwalinta sai lace ne kadai, har sarkar cire mata yayi saboda yana ganin kamar sun mata nauyi, ya kama hannayenta duka biyu ya sumbanta sannan ya cire abun hannun ya aje, ya sauko kasa ta zauna ya daga kafarta abun adon dake kafarta ya cire bayan ya sumbanci kafar sannan ya aje ta a hankali, ya dago dayar ya cire ya sumbance ta ya aje kasa. Ita kanta ta ji a jikinta jumma'ar da zata yi kyau, tun daga laraba ake ganewa, Aliyu ne kadai Jarumin dake tsoron tana jikinta saboda gujewa tsallake iyakokin da musulunci ya gindaya musu. Har bayan aurensu, be taba kokarin taba jikinta ko wuce gona da iri saboda ta zama mallakinsa ba, kamin ranar yau idan ya rumgume ta ko ya sumbance to ya fahimci tana cikin damuwa ne sai yayi mata haka saboda ya kwantar mata da hankali, shi ma yana kokarin ganin be tsallake iyakoki ba duk kuwa da ya san halalinsa ce tun da an daura musu aure. "Abar kauna? Komai na ki yayi kyau" Ya fada yana kallon kyakkyawar fuskarta, kunyarsa da take ji a yanzu ta fi wanda ta ji a washe garin ranar da aka daura musu aure. Kafarta daya ya daga a hankali yayi mata chakulkuli, ta motsa kafarta murmushi ya cika fuskarta kunya ta saka ta rufe idonta. Yatsansa ya saka yana bin layin lallen da aka zana mata a kafa a hankali kamar mai zanen yana kallon kai kace be taba gani lalle a kafar mace ba. Har sai da ta kasa jurewa ta hanye kafarta. Sai yayi murmushi ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya aje ya zauna kusa da ita, ya juyo da fuskarta ta fuskance shi. "Qalbi, bude idonki ki kalli mijinki, masoyinki, mallakinki abokin rayuwarki na har abada, mijin da yake jin ya fi kowa sa'a da rabo saboda ya same ki" Ya kara matsawa kusa da ita sosai har jikinta yana taba na shi. "Kin san me, uwar ƴaƴa? Tun daga ranar da kika shigo rayuwata, komai ya canja. Na rasa yadda zan bayyana, amma ke ce farin cikin zuciyata. A duk Lokacin da na gaji, sai murmushinki ya bani ƙarfi. A duk lokacin da na shiga damuwa, sai kalamanki su zama shauki da nutsuwa a raina." Ya ɗan janyo hannunta ya riƙe, yana tana saman yatsunya, ya ci gaba da cewa "Kin fi zinari daraja a wurina, kin fi dukiya ƙima. Wallahi idan na dubi idanuwanki, ina jin kamar na mallaki duniya baki ɗaya. Ke ce zuciyata, ke ce abokiyar tafiyata har ƙarshen rayuwata." Emily ta bude ido tana jin daɗin maganganun a zuciya, kowane harafi yana tsarata ya isar mata da sako. Ya saka karamin yatsansa cikin nata irin yadda yara suke yi. "Na yi alkawari ba zan taɓa barin ki, ki ji kaɗaici ba. Zan kasance tare da ke cikin farin ciki da bakin ciki. Domin soyayyarki ita ce hasken zuciyata, kuma ke ce sarauniyar gidana" Hawaye ya sauko mata ya saka yatsansa ya share mata, ya sakar mata murmushi mai taushi ya girgiza mata kai alamar no more tears, ya kwamto da ita kirjinsa yana shinshinar gashin kanta dake kamshi. Slowly and slowly ya dago kanta ta kalli saitin idonsa ya sauko da fuskarsa sai ta lumshe ido tana jin sanyin lips dinsa a saman nata lips din, kamin ya raba lips din gida biyu ya saka nasa a tsakiya. Wani sako mai nauyi da mai wuyar dauka ya aika mata mata ta tsakanin bakinsa da nata, a lokacin da ya cire bakinsa cikin nasa sai ta kalleshi a rikice tana maida numfashi, sai kuma ta lumshe ido ta yi murmushi ta maida kanta kirjinsa tana mai jin kunya. Sun samu lokaci a haka sannan ya tashi dauro alwala ita ma ta yi suka yi sallah, yayi musu addu'a, ya dauko abun tabawa ya ciyar da matarsa, sannan sauya tufafin jikinsa zuwa ma bachi, ita ma ta sauya nata bayan ya bata guri ya fita falo har sai da ta gama sannan ya dawo. Abubuwa da Emily bata saka ran Aliyu ya sani ba, ko ya iya ta gansu, bata yi zaton zai zo mata a haka ba, saboda yadda take ganinsa da kokarin kawarda kai. Kusan duk wani abu mai sunan damuwa sai da Aliyu ya matar da ita a daren, har take jin kamar ita ce ta kwashe kason jarumin namiji, ta rika jin kamar bayan Aliyu babu wani namiji mai halayya da dabi'un da ya rage irin nasa. A kirjinsa ta kwana har safe, ba kuma a daren kadai ba, a kowane dare bayan daren tarewarta tana kwana a kirjinsa ne, idan yana gidan da rana kuma tana sarkafe cikin hannayensa, duk wani abun da zai bada space a tsakaninsu be yarda da shi ba. A nan ta gane kalmar soyayya ba a cikin kalami kadai take ba har a cikin aiki da zamantakewa. Matukar hali da hallayar da Aliyu ya sauke ta da su a gidansa zai daure, to bata jin akwai wata macen da zata fita dace ko jindadin aure a halin yanzu. Idan ya fita har kewa take, shi kan shi kamin ya dawo gareta ya yi missing dinta kamar ba a gida daya suke rayuwa ba. Awa ashirin da hudu yana jin kamar a kara musu wasu awanin domin sun masa kadan. Kusan duk wanda ya shiga gidan sai ya yaba da yadda aka gyara ko'ina kuma aka zuba kaya, sosai Mama Baraka ta yi kokari wajen ganin ta fitar da yarta kunya, kuma ta faranta mata rai, kuma kwaliyya ta biya kudin sabulu domin ta siya komai a gurin Khadeeja Candy ne. [8/31, 11:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣3️⃣ 🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟 🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘 Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida. ✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman 📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). 💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau! 📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa! Jin alamar mutum a bayanta ya saka ta juyo, sai suka hada ido, yana sayen da wando bachi sai farar vest dake jikinsa. Ya daga mata gira like how far, ta aika masa murmushi. "Ina kwana" Ya daga kafadunsa. "Ni ma ban san inda yake ba" "Okay good morning" "it's morning but not Good Morning?" Ta kalleshi with confuse. "Why?" Ya jingina da kofar kitchen din yana bata amsa tare da saka hannayensa aljihu. "Cox i didn't get a kiss from my wife" Ta juya ta aje wukar hannunta tana murmushi, kana ta sake juyawa ta nufi inda yake ta yi dage zata sumbance shi ya yi dage shi ma yana kauce fuskatsa. "Bana so, sai da na yi magana rike abun ki bana so" Ta zagaye hannayenta a wuyansa. "I'm sorry haba autan maza, na tuba handsome na maka kiss ma kamin na fito kitchen fa" "Aa ni ban ji ba, kuma waya ce ki bar ni ki zo kitchen? Ke dai kin dange sai kin wahalar da kanki ko?" "Babu wahalarwa a cikin hidimar miji ko wace kala ce" Ta sake kai bakinta da sauri zata masa kiss ya kauce yana dariya. "Na ce bana so" "Toh ba ni wanda na baka dazun, da kana bachi dawo min da abuna" "Kiss din?" "Eh" Yayi dariya mai sauti. "A ina kika ba ni?" "A nan" Ta tura masa bakinta. "Ni na san ba ta nan aka ba ni ba, amman tun da wayo za'ayi min a yaudarini ba matsala" Yayi mata kiss din. Ta sake shi tana ja baya cikin zolaya da muryar yaudara ta ce. "Ba a nan na yi maka ba, a nan na yi maka" Ta nuna kumatunta. Ya fusgota ya dawo da ita jikinsa. "To dawo min da abuna, na baki na ki" Ta noke kasa tana dariya. Binta yayi kasa yana mata kyaculculi sannan ya sake ta ya nufi plantain din da take yankawa tana soyawa at the same, ya dauki wukar yana yankawa ta karaso ya kwashe sannan ta dauki daya ta hura ta nufin ba shi. "Ki daina hura abun da abun da zaki ci, Annabi ya hana, hura abinci" "Na karu da wannan, amman akwai zafi fa" Ya aje wukar ya dauki daya ya bude yana riritawa a hannunsa har ta sha iska. "Bude bakin" Ta bude ya saka mata. "Kai zan bawa fa" "Kuma kuka ci?" "Kai ka ba ni ai" Ya kai hannunsa ya rikota suka fara kokawa ala dole sai ya cire wanda ya saka mata a baki, ita kuma ta yi hanzarin taunewa ta hade har tana kwarewa sai dariya take. Sai da ya ji tana dari sannan ya sake ta. "Wai Qalbin miyasa baki jin magana?" Ya nufi gurin da ruwa suke ya dauko mata ta bude bottle din ya daga kanta ya saka mata a baki, ta sha kadan tarin ya kwanta. "Kai ka koya min ai" Ya kai ruwan bakinsa ya sha kadan. "Ni din?" "Ko da aka kawo ni gidan nan har kunyarka nake ji, amman ta bi ka bala ni" Tana maganar tana dariya. Sai ya kai bakinsa yana hura amsan kanta. "Haka ake yi ma yarinya idan su ta kware" "Yarinya matar...." Ya zaro ido. "Ni din? Ni za ki duba ki cewa yaro? Gaskiya ne da sauranki" Ya aje ruwan hannunsa kamin ya juyo ta gudu daga Kitchen din, be san lokacin da dariya ta subuce masa ba, sai ya nufi kofar kitchen din ya rufe ta ciki, be bude ba sai da ya karasa aikin da take ya hada komai a ya zuba a mazubinsa sannan ya bude kitchen din ya kawo musu komai a inda suka saba karyawa. Al'ada ce ta ya sabawar kansa tun a lokacin da ya auri Kameela, idan ya rigata tashi shi yake hada musu komai na karyawa, idan kuma ita ta riga sai ta hada, sai dai ya fita kokarin hadawa domin tana yawan bachin safe shi kuma ya kan fita aiki dan haka baya jiranta yake hadawa musamman lokacin da take da ciki, har na rana ma wani lokacin girka musu yake ko yayi musu takeaway. A yanzu kuma ya dora daga inda ya tsaya da Emily, banbancin Emily da Kameela shi ne, Emily tana son girkawa Aliyu abinci saboda tana son yi masa hidima tana son ta yi masa abu na faranta rai, abun da zai yaba mata. Tana gwada new recipe wani yayi dadi Wani kuma yayi ba lada ba la'ada, shi kuma da yake gwanin zama da mace ne, be taba kin yaba mata ba. Ko be yi dadi ba yabawa yake ya gode mata, sai dai ya fara mata inda za ta gyara ko su sake yi tare. Kusan inda ba shi da wani aiki a waje to yana gida kusa da matarsa. Ita vata yarda ta yi nisa da shi, shi ma kuma be koya mata ba. Idan ya fita har kewar dawowarsa take, takan tanadi labarai kala kala da take ba shi, kama daga na littafi zuwa na mutane da take ganina kafafin sada zumunta, wani lokacin har kudi yake sakawa idan labarinta yafi na shi armashi zai biya, idan kuma nata ya fi armashi zata biya, ita ta kan biya ta wata sigar ne, shi kuma ya biya da kudi. Zamantakewa suke kamar daman can ita ce matarsa ta farko, ita ma shi ne mijinta na farko, ko da yake masu iya magana sun ce macen da miji ke so kullum yar gata ce. Tun bikin su da sati biyu Ummi ta bar su a garin Kaduna ta koma Abuja gurin mijinta daman can take zama dawowarsa, abubuwan da suka faru ne suka saka ta dawo Kaduna da zama, a yanzu kuma tun da sun kamalla komai cikin aminci da farinciki sai ta koma gurin tata ibadar ta aure. Kamin ta tafi sai da ta yi musu huduba sosai, musamman Aliyu, saboda tana ganin Emily kamar bata da matsala. Ta gargadi Aliyu ta yi mata uzuri da kuma taka tsantsan akan zamantakewarsu, ya rufe ido kuma ya toshe kunnuwansa daga masu suka ko gulma, ita kuma ta yi biyayya ga mijinta ta gujewa bacin ransa, sannan ta toshe kunnu daga wasu kannan maganganu. Ummi ta roki Emily karta zafafa akan zaman Fatima a hannunta, domin abu ne da dukansu suka sani Turhan ba zai yarda Fatima ta zauna tare da su ba, ko da kuwa tana son haka. "Ki daurewa zuciyarki ko babu dadi ki masa uzuri, saboda ya so ki be samu ba yanzu kuma yana da yarki, to ki masa hakuri ya ji sanyi ko ta nan, kuma karki bude hanyar da zata kawo baraka da mijinki akan yarki, sannan karki yarda mijinki ya raina yarki ko ya kaskantar da ita, kuma ko da tana can ki rika kula da ita akai kai, dan Allah ku bawa marada kunya, kar a ji kanku, idan sulhu ya gafara da mijinki, akwai mahaifiyarki idan abun ya ci tura, ina nan kuma mahaifinsa na nan, ba fata muke ba, amman dai kar aji a waje" Nasihar Ummi ta saka Emily ta dauke kai daga damuwa da rashin Fatima a kusa da ita, domin washe garin ranar da aka daura musu aure Ammy ta aiko aka dauki Fatima, har yau Fatima bata san ya dakin Emily yake ba, saboda ta ki kawota ita kuma bata son ta matsa abun ya zame musu matsala. Dan haka ta saka musu ido, Fatima na garin nan bata nan bata da labarinta almost 3 months da bikin babu amo babu labari. KAMEELA POV. "Ko da mafarki ban dauka Aliyu zai iya juya min baya har haka ba, kusan duka kawayena na bata da kowa saboda da shi, gaba daya rayuwata ta ta'allaka ne akansa" Kanwarta Farida ta dafata. "Kameela ke kika dauki Aliyu wani shege fa, tun farko be dace da ke ba" Kameela ta dube ta. "Zaki iya fada min illar Aliyu daya?" "Zan fada miki da yawa ma, kin ga dai akwai masu sonki masu kudi amman kin nace sai shi, kuma ɗan makiyinmu ne" Ta yi murmushi. "Ba zaki gane ba, wannan ba illa ba ce, kuma na gujewa duk sauran ne saboda suna da aure, Aliyu kuma saurayi ne, Aliyu ba shi da wata illa da za a dube shi da ita a hana shi aure, amman ya ci amanata" "Ko yanzu fa kin ki bawa sauran dama ne, mutane na nuna suna sonki" "Farida ba zan iya zama da mai mata ba" "Ko da Aliyun ne ya dawo?" Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar a yanzu. "Dan Allah karki bari son Aliyu ko abun da yayi miki ya hanaki kula wasu mazan, ki duba fa da zai yi aure ma be zauna a gidan da kuka zauna ba sai ya zabi zama a wani gidan kuma ya kwaso kayanki ya aiko miki, da kin mana yadda muke so ai da yanzu kin riga shi aure" "Ba auren ba ai mazan ne, yanzu duk namijin da zaka ce ya saki matarsa ya aureka ba zai yarda ba, ni kawai sai idan na samu saurayi zan yi aure" Farida ta gwalo ido. "Eyyy sai kice ya saki matarsa ya aure ki? Tsakani da Allah Kameela ki aje wannan tunanin a gafe, yanzu fa gasar kudi ake ba ta kishi ba, kishi da hauka na talaka ne, indai mutum yana da yan kudadensa iya ruwansa da wani kishi, kuma duk manyan mutanan da ke sonki kowa da matarsa da yara ta ina zai saki matarsa ya aureki? Wani ma mata biyu" "Ki daina zancen manyan mutane, na auri wanda ya kusa haihuwa da majina zan ji ko da kishi ko yayansa? Ko kuma so kike na sake auren na fito?" "Aa amman mai kudi wake zancen majinarsa? Murar ma ai sai talaka, da kudinsu wa zai kula wannan kuma mataki suke dauka, ni Wallahi kawai ki yarda hannu ya koma miya bawan Allah nan yana aurenki first lady zai maidaki, daman yana neman yar boko kuma wayayen kyakkyawa ta nuna mai dan jiki fit haka dai kamar ke" Kameela ta ja tsaki ta tashi ta fice ta bar mata dakin. Ta yi ma kanta alkawarin ba zata sake waiwayar Aliyu, ta riga da ta aje shi a gafe yanzu saboda ya yi aure. Abu kamar wasa kamar gaske, Kameela ta kasa kula kowa, idan ta ji labarin kana da aure da iyali sai ta aje ka a lissafi. Mahaifiyarta da iyayenta suna kokari sosai gurin lurar da ita abubuwan da ya kama ta dauka da muhimmanci a aure amman ta kasa domin ba wai iya rabuwa da mata ba, ita ko mai yayan wata bata so. Burinta ace ita kadai ce agidanta sai yayanta. Saurayin da take ta jira ya ki samuwa, akan nuna ana sonta, wasu da yawa da suka nemeta lokacin da tana budurwa ba su samu ba, sun dawo amman ta gagara kula ko daya saboda dukansu suna da aure, jiran take sai ta samu marar mata kuma wanda zai fara gina iyali da ita. Ta kasa karyata zuciyarta ta kasa yarda da kaddararta tana da wasa da lokacinta, zuciyarta na ta yi mata hange hange marasa amfani. Kuma ta kasa cire Aliyu a ranta, kawai ta hakura da shi ne, amman sonsa ya ki barinta, kishinta ya ki ya tafi, kusan kullum idan ta kwanta da tunaninsa ai ta tuna a yanzu wata macen ce a kirjinsa ba ita ba, wata macen ce take kula da shi ba ita ba. Wasa wasa Kameela ta fara nisa cikin burin da zuciyarta ta dora nata, na yaki da umarnin Allah, madadin hakuri da hukuncinsa. Ba iyayenta kadai ba ita kanta abun yana damunta, ta kasa focusing a kan rayuwarta, ta kasa manta Aliyu da zamantakewarsu, ta kasa bawa wasu mazan dama. Tun yan'uwanta suna lallabata mata har lamarin ya fara ba su haushi suna fita sabgarta. Ta kai ita kadai take iya fahimtar kanta, ta kan kebe ta yi ma kanta tambayoyin da ba su da amfani da kuma nadamar da bata haifar mata da komai ba sai bakinciki. A yanzu ta gane ta inda matsalar ta bullo, sanadin zafin kishinta ne, ya kaita ga kokarin halaka mijinta, domin ita ce babbar damuwarta a yanzu, wata kila da bata yi kokarin kashe su ba, da Ummi ba zata hana su zauna ba, duk abubuwan nan da suka faru da yanzu ba su kawo nan ba. Wata kila kuma da ta daure ta hana zuciyarta daukar Fatima ta kai ga Turhan mai yiyuwa da yanzu Aliyu be sake ta ba domin ne mafarin tonon asirinta kuma mafarin rabuwarsu. Idan ta so samawa kanta sassauci kuma sai ta tuna ai Aliyun ne ya fara kula Emily bayan kuma yayi mata alkawarin babu karin aure sai kuma ya zagaya yana bibiyar Emily. Ba ita kadai ba kowace mace ba zata dauka ba balle kuma ita dake da zafin kishi. Wani alkawari da ta daukarwa kanta kuma take da yakinin zata iya cikawa shi ne, hakura da zaman aure da Aliyu, ko da kuwa zai dawo ya ce zai maida ita a yanzu, bibiyar da ta yi masa a baya ma nadama take yanzu, domin ta san ba ajinta ba ne, namiji ya sake ta akan abun da ta fishi gaskiya kuma ta bibiyeshi ya kasa saurarenta. Ita sam bata ma amfanin zama da mutumen da ya nuna wata macen ta matarsa ta gida muhimmanci ba, ba dan haka ba babu abun da zai saka ba zai aje lamarinta a gafe ta kula Emily ba. Idan yan'uwanta suka so kara mata bakinciki sai su ce "Ai daman can Aliyun ba wani sonki yake ba. Ke ce kika makale masa, uwarsa ma ba sonki take ba" Zata iya yarda Ummi bata sonta even though bata mata wani abun dake nuna tsantsar kiyayya ba, sai dai kuma bata taba nuna mata tsantsan soyayya ba, bata yi mata gatan da ta yi ma Emily ba, bata kulata kamar yadda take samun labarin tana kula Emily ba. Kuma a yanzu ma ita ce ta cilastawa Aliyu juya mata baya bayan ta wulakanta a gidanta. Amman zancen Aliyu be sonta, sam hankalinta ba zai dauka ba, ta san mijinta yana sonta, domin mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo, ta san waye Aliyu ta san irin zaman da ta yi da shi, ta san rigimarta da yadda take kureshi kuma duk ya daga mata kafa, ta san yadda yake nuna mata soyayya ciki da waje. Wannan na daya daga cikin dalilin da ya saka take hango yadda zata yi rayuwa da wani wanda ba shi ba. Yan'uwanta a kullum cikin nuna mata yadda zata walwala su ninka arziki da karfi a siyasa suke idan ta yarda ta auri abokin mahaifinsu. "Ni gaskiya ya min tsufa ga mata ga yara, ni ba ta siyasar ko kudinsa nake ba" "Matsalata da ke baki iya daukar shawara ba, ga kuma rashin hangen nesa, ai ko dan ki bawa Aliyun da uwarsa haush da ma matar ya kamata ki aure shi, kullum su yi ta ganinki gaban tv komai za'ayi sai da ke, idan kika yi hakuri ma kina gidan sai ya sake su ki koma ke kadai sai yayan da za ki haifa, ke yanzu ni ban isheki ishara ba? Yau ina Baraka ina Yayanta suke? Sai dai idan ubansu yayi marmarin ganinsu ya je ya gansu ko ya aika musu da sako, ni ko ganinsu ma bana jin yana zuwa yi, domin ko jiya da na masa maganarta cewa yayi na daina tuna masa da ita, na ce ranka ya dade ai dole na tuna maka saboda akwai yaya a tsakanin sai ya ce yara idan suka so ganinsa sun san inda yake ai, shi dai hakkin dake tsakaninsa da su ya kula da cinsu shansu da kuma sauran hidindimun rayuwa, ke har cewa yayi ba dan kar dawowar nan ya zama matsala a gareni da su ba sai ya karbe yaransa sun dawo nan, ni kuwa na yi karaf na ce a'a ya bar mata yaranta ta rike, toh ina zan iya da rikon balagagun yaya?" Tana magana tana tsire baki dadin ya isheta, yanzu Mama Baraka da yayanta basa gidan. Ta shafa kanta yarta. " Shiyasa nake son ki fitar da miji ki yi aurenki ki manta da wani Ali, daman can ba ku dace da juna ba, balle kuma yanzu da ya auri shegiya, kuma yar Baraka, ko dan ke na san dole ta aura masa ita, kuma abun kamar ba na banza ba, kin san lamarin yarbawa fa, in ba shi ba yaushe Aliyu zai auri shegiya? Ko da tana da kyau ai Asali wani abu ne mai girma, ko dan yayan mutum" "Daman ita ta lalata komai gurinta nake tafiya neman shawara lokacin da muna samun tsabani kuma ba ta ba ni shawarar kwarai har cewa take ba laifin yarinyar ba ne, ashe saboda ta san yarta ce" "Eh mana, dan Allah ki bawa maraɗa kunya, ki zabi mijinki ki yi aurenki ga ki tsaye da kyau zaune da kyau son kowa kin wanda ya rasa, idan ma ba ki som shi His Excellency ki zaba cikin masu son ki mana, daman Alhaji yace tun da yayi maganar be sake ba, be zama lallai sai shi ba, ki zaba wanda kike so ki ba shi dama idan vaki bada daman ba baza ki iya kawar da tunani da damuwa a ranki ba, amman fa karki dauko ɗan makiyinmu kuma, karki mana na Aliyu, yanzu kam ba za mu bari ba ma" Ta kwnatar da kanta a cinyar mahaifiyarta. "Ki taya ni da addu'a Hajiya Allah ya sauya abun da nake ji a zuciyata kuma ya zaba min inda zan samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, duk masu mata ne, samarin sun ki zuwa wai ko dai dan na yi aure ne?" "Aa ina ruwan aure da samarin, ke yanzu baki san an fi son zaurawan ba? Kuma saurayin zai iya zuwa, amman dai mun fi son mai kunbar susa, kin san logi be kin dadi, ba mu ki ace surukanmu duk manyan mutane ne ba, su kuma samari nan wasu ba rikon aure ba wasu kansu babu komai ciki sai tunanin abubuwan da ba su za su gina gobensu ba, kadan kake samu na kwarai, yanzu ba ga Aliyu ba? Amman da ace wanda ya san ciwon kansa kika aura inda ba shegen zamani ba ne, babu ruwansa da wani hango wata sai hada hadar kudi, ina za su shigo ina suka fita, daman duk abun da iyaye ba so babu albarka a cikinsa, shiyasa Aliyu ya zama haka" Hausawa suka ce wanda ya cika da yaƙi ya mallakeka har ƴaƴanka, babu yadda Kameela iya bayan bin shawarar mahaifiyarta da yan'uwanta matukar tana son zama lafiya da su, kuma ta shirya samawa zuciyarta salama. Abun babu dadi kam amman dole ta daure a haka ta budewa masu kwankwaso kofarta dama, ko labarin zai sauya. Tun da wadanda take dakon zuwa sun manta hanya, wato marar mata da yaya ko kuma saurayi, har yau bata samu ko daya ba, masu matan ne dai suke ta kawo mata hari, daga mai daya, sai biyu har da mai uku yana nema ta hudu da ita tsabar sun raina mata wayo. [8/31, 11:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣4️⃣ 🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟 🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘 Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida. ✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman 📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). 💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau! 📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa! "Okay bari idan na duba zan miki magana" Ya amsa sannan ya kashe wayar ya aje sannan ya dauki comb din yana gyara mata gashi, suna zaune a falo, shi kan kujera ita kuma tana kan kasa. "Daga gurin aiki ne" Ta dago ta kanta ta kalleshi. "Ban tambaya ba ai, Aliyu i trust you, kullum aka kira idan agabana sai ka ce min ga wanda ya kira, ina son ka san kai ka aje ni ba ni na aje ka, kuma kana aiki dole mu'amala zata hadaka da wasu wani lokacin, dole na yi hakuri, kuma kana da yancin haka, matukar be tsabawa addini ba kamar yadda kake yawan fada, kuma be tsabawa zamantakewarmu ba, ba zai kawo matsala ba, ni na yarda da kai, na san wa na aura" Ya ja hancinsa yana murmushi kadan. "Kin ance hadarin da ya baka kashi, gobe idan ka gan shi gudu kake, na dan shiga damuwa ne, saboda irin haka, kuma ya haifar da matsala kala kala a zamantakewata ta baya, na yi iya yadda zan iya wajen ganin ba a samu matsala ba amman hakan be samu ba, kuma ba a raba mata da kishi dole za ku yi kishi ai, kawai dai ba a son ya wuce gona da iri ne saboda yana haifar da matsala, ko ga matar ko ga miji ko kuma duka" "But don't get mad at me idan na yi kishi" Ta fada a shagwabe tana turo baki. Yayi murmushi ya saka hannayensa ya dagota "Come here" Ta daga ta koma saman jikinsa ya rumgumeta irin yadda ake ma yara har ya dan girgiza ta a hankali. "Thank you for trusting me, i love you Qalbin, ba zan ji haushi ba idan kin yi kishi, ke ma ina hango kishi a idonki, amman ki iya rike shi ki yi controlling dinsa kar ya cutar da ke" Ta lafe a jikinsa tana ta zuba shagwaba. Ya cigaba da shata mata kan a haka tana masa raki har da kuka wai da zafi. "Shiyasa ai nake miki a gida, ba zan yarda kina tafiya shagon gyaran gashi ana kalle min kaya kuma jansa da karfi ana wahalar min da mata ba" Ta kai hannunta tana taba chin dinsa zuwa wuya. "Babe..." "Mhn" "Ina son na yi ma Dr A-B maganar tafiya gurin baban shi ina son na gan shi na ji yayi shiru be sake min maganar ba" "Lallai kuma ya kamata ya hadaku ko a waya, kuma ina son idan kin samu time ki tafi ki gurin Ammy ki bincika Fatima ko lafiya" Ta kara daga kai ta kalleshi. "Ba matsala?" "Bana jin wata matsala to matsalar me? Ni da na rike na mallake ki na malleke zuciyarki, na san kin damu ki san halin da take ciki ai, kina da aurena yanzu idan ma Turhan yana gidan dole ya daga miki kafa, balle na san ba ya nan, kuma ba ni da hujjar hana ki ziyarta su tun da Fatima ta shiga tsakani, kawai dai abun da ba zan yarda ba shi ne ki shiga ki dade ko ki wuni, ni zan kaiki na jira ki gama abun da za ki yi na dawo da ke" "Na damu sosai na san halin da take ciki" "Na sani, ina karantar damuwarki ko ba ki fada min ba, ya kamata ace ko sau daya ne ta zo gidan nan ai" "Za mu iya tafiya gobe?" "Mu tafi anjima da dare" "Da gaske?" Ya kai mata rankwashi a kai. "Ina miki karya ne?" Ta dafe kan "Da zafi fa" Ya kara mata wani, da ta ga zai kara mata na uku sai ta sauka jikinsa da sauri ta dauki fillon kujera ta jefeshi da shi. "Zan kama ki ne ai" Ta masa gwalo ta gudu. Bayan Sallah isha'i ta shirya, Aliyu ya sakata mota suka dauki hanyar gidan Ammy. A waje ya faka ta bude zata fita sai ya sumbanci hannunta dake cikin nasa. "Ko da Ammy ta fada miki wata magana marar dadi karki ce za ki yi fada da ita a gaban Fatima" "Okay" Ya sake mata hannun ta fita ta rufe motar, sannan ta kwankwasa gate din gidan aka bude mata. "Ammy na ciki?" "Eh tana nan" Emily ta shiga tana sayen da hijabinta na islamiya da ya kai mata har kasa, cike da zumudin son ganin Fatima ta kwankwasa kofar falon, aka bude mata ta shiga. Da sallama yan matan da suke nan suka amsa mata bata zauna ba sai da ta tambaya ko Ammy na nan aka ce mata eh tana nan, sannan ta zauna zaman jiran fitowarta. Ammy ta dade sosai kamin ta fito falon ta zauna fuska ba yabo ba fallasa ta zauna tana kallon Emily dake gaisheta. "Lafiya kalau" Emily ta dan yi shiru na lokaci kamin ta ce "Daman kwana biyu ban ga Fatima ba, shi ne na zo na dubata" "Fatima kuma? Ba Turhan ya fada miki zai tafi da ita ba? Ai Fatima bata gidan nan tana gurin Babanta" "Gurin Babanta kuma? Ya fada min amman ban ce masa na amince ba, kuma ko bankwana bata zo yi min ba" "Bankwana me ko? Ba an kai miki ita kun yi biki ba?" Idon Emily ya cika da hawaye. "Amman sai a dauke ta a tafi da ita ba tare da an fada min ba, kamar na ni na haife ta? Wannan wane irin abu ne haka? Yarinya karama a dauke ta a kaita gurin larabawan da basa son kowa idan ba jinsu su ba? Kun zalince ta kun zalince ni" "Kin damu da ita kika bar ubanta kika auri makiyinsa? Ko kuma saboda ke sai ya fasa tafiya da yarsa gidansa? Ita ba jininsu bace? Yadda Turhan yake son Fatima ai ba zai bari a cutar da ita ba, ba fin shi sonta kika yi ba" Emily ta mike tsaye tana hawaye. "Ke ma fa uwa ce, zafin nakuda zafin haihuwa wahalar raino duk kin sani, da aka dauke Turhan daga gurinki ina ne baki shiga kin fita ba saboda ya dawo gareki? Miyasa ni zaku azabtar da ni da wannan?" Ammy ta mike tsaye. "Fita ki bar gidan nan, na girmi na tsaya sa'insa da ke, kuma karki kuskura dora misalinki da nawa, dan muna da banbanci, da kina son Fatima da labarin yanzu ai ba haka yake ba" Emily ta dubeta tana hawaye ta sake dubanta sannan ta fice tana hawaye har ta fita gidan. Ko da ta iso gurin motar Aliyu na tsaye jikin motar yaja jiranta, ya ga hawaye a fuskarta amman be ce mata komai ba ya bude mata motata shiga, ya zagaya ya shiga yaja motar, sannan ya kai hannunsa ya kwanto da kanta jikinsa ya rike hannunta yana tukin da hannu daya. Daman ya raya a ransa Fatima bata gida, ya san da tana gidan ta yanzu ta matsa an kawota gurin Emily ko dan ta ga sabon gidan da Emily take. Aliyu be tambaya me ya faru ba, hawayenta kadai sun sanar masa ba ayi da dadi a gidan ba da suka iso gida ya faka motar sai ya fito ya bude mata ya riko hannunta ta fito yana janye da ita har cikin falonsu. Saman kujera ta zauna shi kuma ya risina gabanta yana kallonta. Kamar jira take kawai ta fashe masa da kuka tana fada masa abun da ya faru. Yanayin fuskarsa ya sauya zuwa damuwa, sai dai be ce mata komai ba ya mike tsaye ya shiga dakinsu ya dauko wayarta data bari a gidan ya dawo falon, da kansa ya saka number Turhan dake wayarsa cikin wayarta yayi dialing sannan ya mika mata. Kallo daya ta yi ma wayar ta gane number Turhan ce saboda number bata Nigeria ba ce kuma akan rigimarsu ake ta san ba zai wuce ya kira mata Turhan din kai tsaye ba. "Are you okay with that?" Ta tambaya cikin kuka ya daga mata kai, sannan ta karba shi kuma ya zauna gefenta ya saka hannunsa daya cikin nata domin karfafa mata guiwa. "Hello..." Ta fada cikin sautin dake nuna ta yi kuka. Turhan yayi shiru be ce komai ba, ba dan kuma be fahimci mai magana sai dan kiran ya zo masa ba a lokacin da yake tsammani ba. "Turhan Aisha ce Emily" "Me ya faru? Me yasa kike kuka?" Ya tambaya daga dayan bangaren. "Na tafi ganin Fatima Ammy tace ka tafi da ni? Meyasa?" Ya lumshe ido ya shafa goshinsa a tunaninsa zata fada masa Aliyu ya mata butulci ne. "Bata min bankwana ba, tun da na yi aure bata zo gidan nan ba, a can bata san kowa sai kai, ta yi kankanta ta fuskanci kalubalen masarautarku a yanzu, kuma ni ina son ƴata, karka raba wannan soyayyar dan Allah, idan ma ba zaka yarda ta zauna a gurina ba, ka barta ta zauna a gurin Ammy mana, idan na so ganinta sai na tafi can na ganta, ka ce ba zaka sake cutar da ni ba miyasa ka yi haka?" Tun da ta fara maganar be ce komai ba sai da ta gama. "Kamin na dauke ta na yi magana ke, kuma alamunki be nuna min kin yarda ba, sannan na fada miki ba zan taba bari a taba ta ba, na zo da ita saboda ina sonta akusa da ni, kuma nan din ma gida ne, ya kamata ta san kowa kowa ya santa, idan tana bukatar zama a can ko nan zata zauna, amman gurin Ammy ba gurinki, Ammy ma da kanta ba zata bar ni na zauna da ita a nan ba, kuma ba zan so karatunta ya kasu guda biyu ba" "Zaka dawo da ita kenan?" "Zan dawo da ita, na yi nufin ta zauna na dan lokaci, amman yanzu tun da hankalinki ya tashi zan dawo da ita satin nan" "Na gode, tana kusa da kai" Yayi shiru na tsawon lokaci kamin ta ji muryar Fatima cikin haki tana fadin "Momy?" Emily ta kara matse wayar a kunnenta. "Fatima, kina lafiya" "Lafiya kalau, Momy i miss you" "I miss you too baby, kina lafiya babu wani damuwa?" "Babu, ina yin wasan doki yanzu, Momy na iya hawan doki, Momy Zaki zo?" "Aa" "I miss you" "I know, babanki ya ce zai dawo da ke gurin Ammy za mu ga juna a can" "Okay Momy i love you, ki rika kirana kinji Momy?" "Tohm, idan wani yayi miki wani abun da baki ji dadi ba ki fadawa Babanki kinji" "Tohm momy gidanki yana da kyau" "Eh" "Mu ma nan yana da kyau" "I know, zan aje waya sai an jima" "Okay bye i love you" "I love you too" Ta kashe kiran sannan ta kalli Aliyu. "Na gode" "Anything for you" Ta kashe wayar. A ranar ta kwana da salama babu tunanin Fatima ko son sanin halin da take ciki. A kokarinsa na faranta mata kuma washe gari ya saka ta shirya da wuri ya sauke ta gidan Mama Baraka shi kuma ya wuce aiki bayan ya gaisa da ita cikin mutunci da girmamawa. After ya fice falon ne Mama Baraka ta kalli Emily tana murmushi ta ce. "Kin yi dace mijin, Aliyu ya dade yana burge ni, wani lokacin har cewa nake be dace da Kameela ba, ashe an kaddara zai rabu da ita ya aure yata ne, ya zama sirikina, ina jindadin yadda yake nuna kulawa da damuwa akanki" Emily ta yi murmushi. "Yana da kirki, ga addini" "Kusan fa duk wasu dabi'u da hallaya da ake so a gurin namiji Aliyu ya hada su, Allah yasa mutuwa ce zata taba, ga Ummi ma tana kaunarki baki da matsala ta ko'ina" "Alhamdulillah" "Allah ya datar da yan'uwanki su ma, su samu mazajen na kaurai" "Ameen, har da ke ai Mama, ko Babansu Kameela zaki komawa?" "Kai anya, ai aurena tsakanina da shi ya kare, kuma ni yanzu ba wani auren zan sake ba, kula da ku ya wadatar, sai idan na ga na aurar da duka yayana" "Allah ya nuna mana" "Ameen Ya Rabbi, kina da labarin Fatima?" "Eh..." Emily ta bata labarin abun da ya faru jiya.. "Daman Aliyu ya fada min yana ganin kamar bata nan" "Ya zo nan ne?" "Eh ya kan biyo, har alheri yake kawo min, da nake tambayarsa ya kike kuna da labarin Fatima yake fada min yana ganin kamar Turhan ya tafi da Fatima" "Be taba min zancen ba" "Ni da har na yi zaton wata kila yana jin tsoron ko kar Rito yake ki bitto? Ya cutar da ita ne da shi shiyasa Turhan din ya dauke ta suka koma can, sai yace aa ba wannan matsalar ba ce, ai Vito ya dade da mutuwa" Wani rudududun Emily ta ji kamar saukar cida, ko a mafarki bata taba mafarkin Vito ya mutu ba, bata ma taba mafarkinsa tun da ta bar gidan? "Ya mutu yaushe? Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un" Ta kai tsaye numfashinta na rawa, jikinta ma haka nan da nan hawaye suka taru a idonta sai kuka. "Miye abun innalillahi a mutuwar kafiri kuma mutumen da ya addabeki? Yake neman rayuwarki data yarki da ta mijinki? Daman baki san ya mutu ba?" "Wallahi ban sani ba, Aliyu be fada min ba, babu wanda ya fada min, yaushe ne?" "Zuwansa na karshe da yayi muke wannan maganar da shi" "Miyasa suka kashe shi? Why not su kama shi su hukunta shi, be cancanci kisa ba" "Mutumen dake kashe mutane? Kuma idan yana raye ke kanki ai rayuwarki na cikin hatsari" "Kawai ya fada ne, amman ba zai iya komai ba, ba mamaki lokacin da ya turo min sakon baya cikin hayyacinsa ma, Vito ne mutumen da ya fara taimakon rayuwata, ya maida ni mutum na zama yadda nake a yau, miyasa za su saka masa ta wannan hayyar? Ban kyauta masa ba, ni ce sanadi be kamata ba" Kuka take sosai kai kace Aliyun ne ya mutu ma, daker ta iya janyo wayarta ta kira Aliyu. Jin muryarta da kuka yayi mugun daga masa hankali. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, me ya faru Qalbina?" "Me... Me... Me... Yasa kuka kashe Vi.. Vito?" "Kun yi magana da Mama ne?" "Mutumen da ya taimaki rayuwata ya so ni shi zaku kashe, ya zama kamar na ci amanar sa kuma sanadina ya rasa ransa, bayan ka yi min alkawarin ba zaka kashe shi ba" Tana kuka tana maganar. Kashe wayar yayi sai ta kara fashewa da kuka sosai tana jin silarta komai ya faru, bata kyautawa Vito ba, be cancanci irin wannan sakamakon daga bangarenta ba. Babu jimawa Aliyu ya faka harabar gidan domin yana jin kamar ba zai iya jure rarrashinta ta waya ba, ba lallai ta fahimce shi ba. Ya shigo falon babu ko sallama a lokacin Emily ta ci kuka sosai har idonta ya kumbura, Aliyu ya zauna kan kujera ita kuma tana zaune kasa rike da dankwali a hannu sai sharbar kuka take. "Na yi rarrashinta har na gaji ta ki ta yi shiru" Mama Baraka ta fada cikin yanayin damuwa. Aliyu ya kai hannu ya karbi dankwali ya rike kanta ya shafe mata hawayen. "Wallahi Wallahi ba mu muka kashe shi ba, ba ta sanadinmu aka kashe shi ba, ko da aka aje an samu police har sun dauke garwarsa da ta matar da yake tare da ita, Chidimma sun kaita gurin aje gawa, lokacin da na nunawa Daddy sakon da ya turo miki, sai Daddy yace na sanar da Turhan saboda kar wani abu ya faru tun da har ya dauka Turhan kika aura ba ni ba, kuma Fatima tana gurinsu saboda kar ayi sake ya cutar da ita, na san Turhan ba zai saurare ni ba, ko ya dauki abun da muhimmanci shiyasa na aikawa Ammy da sakon, kuma na tabbatar mata ana kan nemansa, da sakon da ya turo miki aka yi amfani da Location din sim din aka gano inda yake a Lagos, amman ko da aka tafi sai aka samu gidan a rufe da shairdar police saboda an yi musayar wuta a gidan makota suka kira police amman ko da suka zo aikin gama ya gama sai gawa suka dauka, sun turo mana komai sun mana bayani, kuma da suka zurfafa binciken sai aka gano abokan sana'arsa ne suka masa wannan aikin, ba daga mu ba ne, Ki yarda da ni Aisha Wallahi tallahi a haka muka samu shi, sun turo mana hotuna, ban fada miki ba ne saboda ina jin tsoron kar hankalinki ya tashi" Yana maganar yana share mata hawayenta da dankwalin. Mama Baraka ta ce. "Daman su irin wadannan mutane ai basa tsawon rai, saboda sana'arsu ta shadari ce suna neman rayuwar wasu ana neman ta su" "Haka ne, amman Wallahi ba daga mu ba ne" Ta kwantar da kanta jikin Aliyun da ya sauko kasa yana kokarin fahimtar da ita. Mutuwar Vito wani abu da ya tsaya a zuciyar Emily kuma ya zauna zaman da ba zai taba yiyuwa ta manta ba, daga lokacin da ta ji labarin mutuwarsa sai ya zama bata da walwala saboda tana ganin shi ma ya cancanci farinciki, ta bangaren da take jin sanyi da ya kasance ba Aliyu ne ko ita ba ce siyar mutuwarsa, da ba zata iya yafewa kanta ba. Haka Aliyu yayi ta fama da ita yana nuna mata amfanin mutuwarsa, da kuma tausaya mata har ta fara kwantar da hankalinta. Ba ma kamar ranar da Mama Baraka ta kirata ta sanar mata Ammy ta aiko da Fatima gidan Mama Baraka saboda bata san gidan Emily ba. Ammy ta yi hakan ne saboda bata son aika direbanta kai tsaye gidan Emily din ne, kuma daman bata san gidan ba saboda sanin gidan da Emily take rayuwa da Aliyu baya cikin lissafinta a yanzu. Mama Baraka ta aiko Misira ta kawo mata Fatima a ranar farinciki da far'a kamar su kashe Emily da Fatima. Sosai Emily ta jidadi da yarta bata rame ba, kuma bata labarta mata wani abu marar dadi da aka mata ba, sai ma jindadi da take fada mata da wasu abubuwa da ta iya a zuwanta garin, tana ta bata labarin yadda masarautar take da mutanen cikinta. [9/5, 12:32 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣5️⃣ Kin dade kina sha’awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba? Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na ’yarki? To, ga sauƙi ya iso! ADASHE NE NA GATA! Ki zuba kuɗi, ki ɗauki abin da kike so daga: Sutura da zannuwan gado Kayan kitchen Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu) Talkami da jaka Zanen gado Frames (flowers decoration ko standing ones) Console mirror Boxes na Lefe ko na traveling. Warmers iri-iri Food flask iri daban-daban Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so! Sauƙi ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa. 📌 Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati. 📌 Akwai sharudda da ka’idoji. Domin ƙarin bayani, ki/ka tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660 Ko ta hanyar WhatsApp 👉 Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1 Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Thank you 😍 🙏 Yana warware hannunsa da yayi alwala ya ce. "Ki shirya ina dawowa daga Sallah za mu tafi mu kaita" "Da gaske wai ba zata kwana nan ba? Ni ma fa ina da hakki da ita" Ta fada a shagwabe. "Toh haka Mama Ta fada min, za su aiko a dauke ta da karfe 9pm" "Kai ba zaka saka baki ba? Yaushe rabon da na ga yarinyar nan ta zo kuma sai ace ko kwana ba zata yi ba?" "Yanzu indai ba son kike Turhan ya zo gidan nan da wukarsa ya kwantar da kaina ya yanka ni ba, ina ni ina saka baki a lamarin yarsa? Hakuri za ki yi idan suka ga kamar ba ki damu ba za su daina, damuwar suke so daman ai, ni na tafi masallaci" "Allah ya dawo min da kai lafiya" "Ameen I love you" "I love you" Fadawa junansu kalmar suna son junansu wata sara ce da Aliyu ya koya mata, ba ya fita be ji kamar daga bakin matarsa ba, ita ma bata yarda ya fice be fada mata ba, furta kalmar i love you yana kara danko kauna da soyayya a tsakanin masoya ko da yaushe musamman wadanda suke son junansu. Kamin da dawo ta zubawa Fatima abinci ta kara ci ta shirya ita ma ta shirya. Key ya dauka da wallet ya rike mata kofar falon ta fita sannan ya fita ya rufe, mota ma shi ya bude mata ta shiga ta rumgume Fatima a jikinta. "Ba zaki barta ta zauna baya?" "Aa na fi son ta zauna a jikina" Ya kalli yadda ta lankwashe kai tana ta zuba masa shagwaba. Ba zai iya hanata ba, duk yana ganin kamar zaman zai taba ta, sai kawai ya kai hannunsa ya gyara zaman Fatima daga jikin Emily zuwa kafafuwanta. Sannan ya zagaye ya shiga dayan bangaren ya tashi motar yana tukin yana kai hannunsa ya daga Fatima idan ya ga ta kwanta jikin matarsa. Gaban wani katon shagon kayan alatu ya faka ya shiga yayi manyan ledodi uku ya dawo da su bayan mota ya zuba sannan yaja suka cigaba da tafiya. Harabar gidan Mama Baraka suka faka Aliyu ya fara fita ya zagaya ya bude mata ya riko Fatima ta fito sannan ya riko hannun Emily ta fito ya bude back seat din ya dauko ledodin biyu ya rike. "Ba uku na gani ba?" Ya ja hancinta sannan ya rufe motar. "Daya ta ki ce" Ya dafa kafadarta kamar wata kawarsa. "Uhm Qalbina, dazun Mama ta kira ta ce muna da bako tace na kawo ki bayan na dauki Fatima, sai na ce mata ta mana hakuri har sai idan zan kawo Fatima" "Waye?" "Sai kin shiga zaki gani" "Turha?" "Maybe..." "Ba zan shiga ba, idan ya fada maka wata magana marar dadi fa? Kasan ba zan kyale ba" "Ke yanzu kin shirya fada da kowa akaina kenan?" "Har da kai kanka ba zan bari ba" Ya bude ido. "Eyyyy" "Uhm" "Ba za ayi komai ba, muje ciki dai" Ya sauke hannunsa daga kan kafadarta suka jera suna tafiya, zuciyarta bata hararo mata kowa ba sai Turhan, wata kila zai fada mata wasu dokoki ne ko kuma yace zai sake dauke Fatima gaba daya. Shi ya fara rike mata kofar ta shiga sannan ya shiga, daman Fatima ta dade da shiga ta bar su a waje. Ta shiga da sallama tana ta rabon ido bata ga kowa a falon ba sai Mama Baraka da Fatima ke jingine da ita suna gaisawa. Emily ta kalli Aliyu yayi mata murmushi ta yi zaton karya yake dan kawai ya daga mata hankali ya fada mata haka, saboda haka ta taka masa kafa da kafarta sannan ta wuce kusa da Mama Baraka ta zauna suna gaisawa. "Ya ce mim wai ina da baki, ashe ba gaske ba ne" Mama Baraka ta kalli Aliyu. "Gaskiya ne, Aliyu je ka shigo da su, suna nan BQ da ka zagaya baya ta nan kadan zaka gansu" Sai da ya mike tsaye ya fice sannan Emily ta kalli Mama Baraka ta ce. "Su waye Mama?" "Wai tsohon mijinki ne... Ko Hamza ko Khaleefa, Ummi ta turo su gurina, saboda sun tafi can ita kuma bata nan sai ta kirani tace wai sun zo gidanta ne suna son magana da ke, ita kuma bata ma garin yanzu kuma tana ganin duk wani abun da ya shafe ki mijinki ya kamata a tuntuba ko ni" Fuskar Emily ta sauya sosai zuwa wani yanayi mai kama da fushi da damuwa. Sai dai bata ce komai na har aka turo kofar falon Aliyu ya fara shigo sannan mahaifiyar Khaleefa ta shigo tare da shi da wani kawonsa, duk a kasa suka zauna sai Aliyu ne ya zauna a kujera, Emily ta kalli Khaleefa da rabin fuskarsa take a kone idonta na cika da hawaye rayuwar data manta take tunawa a yanzu. "Toh ga su nan, sun min bayanin komai kuma sun roki alfarmar a kira ki su roki yafiyarki, na yi magana da Aliyu yace yanzu kina murnar zuwan Fatima a bari sai dare idan kun zo kawowata kar a yi ruining din moment dinku" "Ina wuni Aisha" Cewar Mahaifiyar Khaleefa. Emily ta kasa amsawa hawaye na sauko mata, kewar ɗanta ya dawo mata farko. "Wata kila la lallai ki gane mu ba, duk dai Hajiya ta miki bayani kuma ta mana bayanin komai, ashe kin gane mahaifiyarki Aisha, muna miki murna ta fada mana kin yi aure shi ma muna miki fatan alheri, mun zo nan ne saboda neman yafiyarki, abubuwan da suka faru wadanda ba su yi dadi ba, musamman tsakaninki da Hamza, ki yi hakuri ki yafe masa dan Allah, Wallahi abubuwa masara dadi sun faru kuma mun san hakkinki ne, rayuwa ta zama babu dadi, musamman ma yanzu da ya koma gida saboda mai gidansa ya koresa saboda ke, ya fada mana ya ganki amman an hana shi magana da ke, tun da ya koma kullum cikin maganarki yake, daga karshe muka yanke shawarar zuwa kai tsaye mu nemi yafiyarki" Cikin tsoro da fargaba Mahaifiyar Khaleefa take magana. Khaleefa ya dago idonsa da suka zare tsabar yunwa da wahalar ciwo ya kalli Emily da a yanzu ko kafarta be isa ya taba ba ya ce. "Ki yi hakuri Aisha na san ban kyauta ba, na san na zalunce ki na cutar da ke, amman ki yafe min, Wallahi na yi nadama kuma na yi ta nemanki amman ban same ki ba, ban san inda zan ganki ba" "Kowa ya cuceka sai kawai ya zo ya ce ka yi hakuri shikenan aikinka? Ka cutar da ni, ku biyun nan baku ragawa rayuwata ba, kara Ammy ta nuna min soyayya a baya, amman kai mahaifiyarka tana kallo ka tsake ni, na bar gari na kama hanyar da ban san kowa ba, kuka wulakanta ni kuka wofintar da ni saboda kawai ba ni da kowa, kasan ina da cikin ɗanka amman baka damu da halin da zan shiga ba, idan jininku ce za ku yarda ayi mata haka? Na haihu a titi kamar na haifi shege, na dinga wahala da shi kamar ba shi da uba, har ya bar duniya be san ubansa ba, wai saboda kawai ni mushirika ce na musulunta na bar addini na bi na ku, kuka rika kirana tubabbiya kowa ya kasa tsaya min, kuka hade min kai bana jin sanyi kowa, bayan kuma kai ka rabo ni da inda nake da gata, ka yi aure baka fada min ba sai da na ji, kuma haka be maka ba, kuka bini da gori kuka koreni gidan, sanadin wahalar da ma sha na haifi ɗana ba lafiyayye ba" Tana maganar tana kuka sosai kukan dake taba zuciya, Aliyu kallonta kawai yake yana kara jin tausayinta da kaunarta suna shiga ransa. Khaleefa ya girgiza kai yana kuka. "Wallahi hakkinki be barmu ba, bayan kin tafi rayuwa bata mana dadi ba, gidan da kika bar ni ciki ni da matar da na aura gobara yayi komai ya kone, ni kaina daker aka fitar da ni ciki, kalli yadda jikina yayi fuskar babu rabi Aisha, matata bata fita ba, sai yara biyu kawai data haifa min aka samu ceto wa, bangaren mahaifiya aka siyar a gidan aka shiga nema min magani amman har yau ban warke ba, saboda ba ayi treatment din yadda ya dace ba, yanzu haka idan yanayi ya sauya na zafi wutar tana taso min, sun ce akwai cutar har a cikin cikina, Wallahi ba mu da komai a yanzu Aisha, kuma na san hakkinki ne dan Allah ki yi hakuri ki yafe min, aiki ma ya gagara samuwa a gareni sai daker aka dauke ni a gidansu Alhaji Aliyu, ashe shi ma rabon na ganki ne, tun bayan da ya tura ni gida kuma ban sake samu komai ba, ana ba ni da albashin amman kullum gurin magani suke karewa, abun da za'a ci ma wahala yake mana, shin duk ba hakkinki ba ne? Ki yafewa min na zo neman yafiyarki ne da tambayar cikin da na barki da shi" "Na haifi ɗanka da wahala da bakinciki da ciwo, ya rayu da rashin sanin waye ubansa, ciwo ya wahalar da shi, amman abubuwa sun yi sauki da na hadu da Vito, ya taimaki rayuwarmu kamin na rasa shi, ya rasu cikin ruwa ya fada ba tare da mun sani ba, da taimakon mijina an yi masa sutura an masa sallah an kai shi makabartar musulmi. Zancen yafiya kuma ba zan yafe ba, wannan shari'ar sai an yi ta" Hankalin Khaleefa ya tashi jin cewar ɗan da aka haifa ya mutu, sai dai tashin hankalin be kai na jin furucin ba zata yafe masa ba. Shi da mahaifiyarsa da kawunsa da suka zo suka shiga bada hakuri. Aliyu ya mike tsaye "Khaleefa, ina tunanin zai fi kyau ku kuma inda aka ba ku masauki a yanzu, gobe da safe idan kun karya sai ku koma garinku, Ummi na da numberka zan karba, duk lokacin da hankalin Matata ya kwanta ta ji zata iya yafe maka zan kiraka" Khaleefa ya kalli Aliyu... "Ranka ya dade ka fahimce ni, idan na koma ba tare da yafiyar Aisha ba, ban san iya abun da zai faru a gaba ba, wata kila rayuwar ba zata kai lokacin da kake zato ba" "Amman tana cikin damuwa yanzu ba lallai ta yafe maka ba" Mama Baraka ta fada. "Bana cikin damuwa, na samu iyali yan'uwa da uwaye, ma samu miji ina da ya, rayuwa ta sauya na gamsu da abun da aka ba ni a yanzu, na gamsu da wannan sakamakon, kawai dai ba zan iya yafewa ba ne" Aliyu ya nunawa Khaleefa hanya yana jin kamar ya kai masa duka. "Please..." Khaleefa ya kalli Emily yana mamakin yau shi ke zaune a kasa tana kan kujera, yau shi yaje neman yafiyarta tana kin yafe masa, yau ita take da mijin da yake kira da maigidansa, ga duniya ta samu tana gida mai kyau gaba daya ma ta sauya kamar ba ita ba, babu wanda zai fadawa cewar ya taba aureta ya yarda. Baya son jayayya da Aliyu saboda ta bangarensa albashi ke shigo masa duk da baya tuka musu mota a yanzu. "Tohm na barki lafiya Aisha, ina jiran ranar da zaki yafe min, mun gode Hajiya" Ya nufi hanyar fita yana hawaye mahaifiyarsa kuma na kuka wiwiwi kawunsa kam tun da aka shigo ya ma kasa cewa komai. Bayan sun fita Mama Baraka ta kai hannu ta shafa fuskar Emily. "Dan Allah ina sake rokin yafiyarki, ki yafe min, duk ni ce silar shigarki wannan halin" Emily ta kwanta jikinta tana kuka, Mama Baraka ma kuka take tana kara jin tausayin Emily sosai. Aliyu ya sauke kansa kasa. Fatima ta nufi inda Aliyu yake tsaye "Wanene wannan? Ni ban gane abun da ake ba" "Mahaifin London ne" "Amman fuskarsa ta kone fatar wuyansa ta hade, gobara aka yi a fuskarsa?" Aliyu yayi murmushi ya duka ya dauki Fatima ya fice da ita yana mata hira. "Na Wahala, a baya rayuwa bata ɗanɗana min dadi ba, na shiga tasko kala kala, an nuna min ƙyama, babu wanda yake damuwa da matsalata, na zauna a gidan Khaleefa abun da zan ci ma sai ya gagare ni, sai na yi wankakau, ina jin ciwo ya hana ni zuwa asibiti sai a biyo kamar zan haifi shege, amman da amaryarsa ta samu cika suka rika murna, ni gaba daya ban haifi yarana da farinciki ba, mazan nan biyu ba su dandana min komai ba sai azaba da rashin imani, bana kaunar ko ɗayansu har abada... " Emily tana fada tana kuka. Mama Baraka ta kasa cewa komai saboda ta san ita ce silar komai da ace bata jefar da yarta ba da duk ba wannan labarin ake ba. Suna haka yar da Ammy ke riko ta shigo da sallama Mama Baraka ta amsa Emily na share hawaye, har ta gaisa da Mama Baraka ta tambayi Fatima idonta na kan Emily. "Fatima kamar tana waje ko? Tare da Aliyu" "Okay, bari na tafi daman na zo daukar ta ne, babanta yana can yana jira" "Okay tana nan waje" Ta mike tsaye sai Emily ta nuna mata ledodin dake aje gefen kujera. "Ki tafi mata da wannan kayan nata ne" "Tohm" Ta dauka ta fice. Aliyu be dawo falon ba sai da ya tabbatar hankalin matarsa ya ɗan kwanta da ya shigo sai yake ta kallon fuskarta, baya son yayi zancen ta sake tuna damuwar kuma he need to hug her ko zata ji sanyi dan haka ya ce. "Bari mu tafi gida dare yana yi, direban ya dauki Fatima sun yafi" "Eh ta shigo nan ai, yarinyar da ta kawo ta, ban san ko za su sake kawota ko kuma aa" "Yace zai barta a gurin Ammy ai, idan tana nan da sannu zata dawo hannunmu, ita da kanta zata yi hankalin yin haka ai" "Haka ne, haka yayi miki Aisha? Idan ba miki ba ke ma kina da hakki sai a masa magana" Mama Baraka ta tambaya. "Yayi ko ba komai ya kula da yarsa ba kamar Khaleefa ba" Sai da suka kara bata minti talatin sannan suka yi ma Mama Baraka sallama daf da za su fita take tambayar yan'uwanta, Mama Baraka tace mata suna daki ita ta hana su fitowa saboda abubuwan da ta san za su faru. Emily ta shiga ta gaisa da su suna ta murnar ganinta har da rumgume ta sannan suka fito gaba dayansu suka rakota har gurin mota ta shiga. Da suka isa Aliyu ya bude mata mota ta fita ya saka hannayensa ya share mata hawayen dake mata zuba. "Kukan nan ya isa haka Qalbina" "Na tuna ɗana, da Vito ne taimake shi ba da Allah kadai ya san kalar wahalar da zai sake sha" Ta fada jikin mijinta tana kuka, sai ya rumgumeta yana shafa bayanta. "Indai zaki tuna rayuwar baya ne, zaki yi ta kuka da bakinciki ne, ki manta da komai dan Allah, bana son kukanki balle na ganki a damuwa" Ya duka ya saka hannunsa biyu ya dauke taya nufi kofar falon, da zai saka key ya bude kofar falon sai ta raba kafafuwanta biyu ta makale masa yayi sama da ita ya saka key din ya bude sannan ya tura ya shiga da ita, a hankali ya zauna kan kujera tana lake a jikinsa kamar yadda yara suke yana shafa bayanta, hausawa suka ce macen da ake so yar gata ce a gurin mijinta. Haka Aliyu yayi ta rarrashin matarsa kayan dadin daya siya mata ma daya dauko daker ya samu ta sha ice-cream din da ya fara narkewa ya bude biscuit ya bata piece daya ta ci ta kawar da kai. Ta kwana da tunanin abun da Khaleefa yayi mata da kuma London, hakan ya saka ta mafarkin ɗanta, Aliyu na zaune kusa da ita yana lasa waya ya ga hawaye na sauko mata, sai ya kai hannunsa ya share, a firgice ta farka sai da ya rike ta. "Lafiya? I'm here no one can hurt you" Ya dawo da ita jikinsa ya yi mata addu'a ya tofa mata ya shafe mata jikinta, sannan ya bude kur'ane wayarsa ya soma karantawa sautinsa na fita, har sai da bachi ya sake dauketa sannan ya aje ya lullube matarsa ta kashe wutar dakin ya rumgume sosai yadda ba zata ji tsoro ba. Ya san ta kwana da zazzabi saboda a kirjinsa ta kwana jiya, dan haka be bari ta shiga kitchen ba shi ya shirya musu komai na karya, da ya kawo kuma ta gagara cin komai. Ya taba jikinta "Ki daure ki ci wani abu, sai mu tafi asibiti daman ina son muje tun last week, kawai ban miki maganar ba ne" Ya kai kunnensa bakinta. "Daure fada min, me kike so?" Ta kwanto jikinsa. "Kai nake so, Abokin Rayuwata my Soul mate" "Abu mai sauki, a soye kike so na ko gashe?" Dariya ta subuce mata ta daga kanta sama tana jin kaunar Aliyu, sai ya dawo da ita jikinsa yana murmushi. "Fada min mana" "A saka mai da yaji a bani na cinye kayana" "Na nawa kuma? Ai tuni kika cinye kurwar gangan jikince kawai ta rage, na miki na mayu" Ta saka dariya tana shafa fuskarsa, da dabara da waya da hira da janta da nishadi ya samu ta yi breakfast din da bata yi niya ba saboda ta farka jikin nata ma babu dadi bata ra'ayin cin komai. Kamin ya dauke ta zuwa asibiti sai da ya saka ka mata booking komai ta yadda da sun tafi ba sai sun wahala ba, haka kuwa aka yi suna zuwa ta hau layi gaba ta wuce ciki likita ta dubata ta yi mata tambayoyi sannan ta rubuta mata maganin da zata fara sha ta bata test din jini ta bata PT tace taje ta gwada idan sun koma gida, saboda Aliyu ya ki yarda ta yi fitsari a asibitin wai it's public place. Jinin kawai ya yarda aka bada sannan ya sauke ta gida ya tafi gurin aikinsa. The following day shi ya tashe ta bachi kamar yadda ya saba, ya saka ta yi fitsarin ya saka abun awon domin shi ya san yadda ake amfani da shi, ita kam bata sani ba saboda bata taba gwajin ciki ba sai dai kawai ta ganta da shi. A bathroom ya bar abun be sake shiga ba sai da suka gama sallah yayi mata karatu ta koma ta kwanta sannan ya shiga bandakin ya dauki abun gabansa na faduwa ya duba. Ya dube kansa a mirror yayi murmushi mai kyau ya jinjina kai sannan ya fice rike da abun ya isa inda take kwance yayi bedsheet din da aka siya gurin Khadeeja Candy ya kalli fuskar matarsa yana ayyana yadda yaransa za su yi kyau idan suka biyota. "Alhamdulillah... Alhamdulillah..." Ya furta sannan ya sumbance ta, ya shafa fuskarta yana hura mata iska a fuska. "Qalbina... Yi hakuri ki tashi... Ba zan iya barin ki ki yi wannan bachin ba" Ta bude ido daker ta kalleshi sai ya tada ita zaune ya rumgume ta, da ya ji hakan be masa ba ya mike tsaye da ita ya kwantar da kanta a wuyansa kafafuwanta makale a jikinsa. Ita dai ta yi lamo domin bata san wainar da ake soyawa ba. Daga dakin ya fito falo da ita ya zaunar da ita kan kujera ta ya zube gaban guiyoyinsa ya kama hannayenta yana kallonta with so much emotional. "Qalbina, ni zan miki albishir, kuma ni zan baki goro, fada min me kike so? Ko me kike so a duniyar fada min zan miki" Ta zama confused. "Me ya faru?" "Komai ma ya faru, fada min" Ta tsaya tunani mai zurfi. "Ina son ma tafi makka" "An gama, sai kuma me?" "Ina son na tafi Europe" "Bayan shi?" "Ina son ka so ni har abada" Ya matsa da fuskarsa ya hade da tata. "Sonki har abada wajibina ne, kaunarki ciwo da ba zan taba warkewa ba, na gode Ayusher da kika ba ni damar zama mijinki, kin hada duk wani abun da nake so, kuma yanzu ta hanyarki Allah yayi min wata babba kyauta da ba zan taba iya biyanta ba har abada" "Minene?" "Babena you had my baby in your tummy... Daman na san haka zai bayyana tun da kika zo gidan nan ina kirgawa baki yi period ba" Ta bude baki da dan mamaki, daman ita ma ta zargi haka. "Ciki ne kawai, kake ta wannan abun?" Ya zauna kusa da ita ya rike fuskarta kana ganin tasa fuskar kasan yana cikin farinciki marar misaltuwa. "No... Jinina a jikinki Ayusher i got everything i wanted... Kin maida namijin da ya fi kowane gata da farinciki a duniyar nan, to ni yanzu me zan bukata kuma? My dream Girl" Hawaye ya sauko mata. "Wasu mazan ba su min haka ba" "Wasu mazan kika ce, a yanzu kina auren namiji, ina kaunarki Ayusher ina kaunar abun da abun da yake cikinki fiye da tunaninki, hasken da ke haskaka duniyata, ke ce komai nawa, we're family now... Alhamdulillah" Ya kwantar da ita kirjinsa a hankali ya rumgumeta kamkama kamar za a kwance masa, kuka sosai take tana jin wani yanayi da bata saba ba. [9/7, 7:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣6️⃣ Kin dade kina sha’awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba? Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na ’yarki? To, ga sauƙi ya iso! ADASHE NE NA GATA! Ki zuba kuɗi, ki ɗauki abin da kike so daga: Sutura da zannuwan gado Kayan kitchen Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu) Talkami da jaka Zanen gado Frames (flowers decoration ko standing ones) Console mirror Boxes na Lefe ko na traveling. Warmers iri-iri Food flask iri daban-daban Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so! Sauƙi ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa. 📌 Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati. 📌 Akwai sharudda da ka’idoji. Domin ƙarin bayani, ki/ka tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660 Ko ta hanyar WhatsApp 👉 Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1 Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Thank you 😍 🙏 "Kasan jiya da muka je Asibiti" "Uhm" "Likitan tace kowa ta fadawa mijinta idan ta koma gida" "Mee" "Wai akwai wani sabon Technology da ya shigoo" Tana fada tana cin gauta. Shi kuma hankalinsa yana kan system din da yake tabawa. "Tace wai akwai allurar da ake yi ma mace bayan kwana biyu sai ta dawo a debi jininta sai a sakawa mijinta" "Tooo saboda me?" "Wai saboda idan lokacin haihuwa yayi sai shi yayi nakudar ba sai ta yi ba, shi zai ji zafin" Sai a lokacin ya kalleta yana dariya. "Saboda ba ni da gata?" "Aa ita ce tace kowa ya fada idan miji zai iya sai yayi" "Yanzu dai ba dan kin raina capacity na ba ta ina za a saka min nakuda dan Allah? Shi kenan ni ban da gurin kai kara idan an taba ni?" Ta kyalkyale da dariya. "New Technology ne fa" "To ba za a fara da ni ba, ina namiji ina nakuda abun ai ba zai bada kala ba, amman kuma da kin ga jarumta kamin ki motsa ido na haihu" Ya aje system din yana dariya itama dariyar take. Ya nufo inda take zaune ya dauke ragowar gautan da ta ci ya kwashe hancin ya zuba a plate ya kakkabe mata jikinta ya dauke plate din ya sumbanceta. "Allah ya sauke ke ki lafiya" "Ameen" Ya nufi kitchen ya aje plate din ya dauko mata ruwa da cup biyu ya zuba mata daya daya ya zubawa kansa. "Qalbin kin matsawa riguna lamba" Ya fada yana kallom t-shirt dinsa dake jikinta, domin tun da cikinta ya girma kullum kayansa take sakawa. Ta sha ruwan ta mika masa cup. "To ya zaka yi? Laifin waye?" "Na wa" Ya fada yana lankwafe kai kamar wani maraya. Ya aje cup din sannan ya koma ya cigaba da aikin da yake da system dinsa yana mata hira sama sama saboda baya son ta ji kamar ya kyaleta duk kuwa da aikin dake gabansa. Hannu ta kai ta shafa katon cikinta a hankali tana kallonsa, a yanzu kuma me zata roka? Me ye Allah be bata ba? Miye ta raba ba a maye mata gurbinsa da shi ba? Ita ce yau ake yi ma lele ake taraiyarta kamar yar Gold. Wannan ne cikin farko da ta raineshi da soyayya ubansa da kulawa kamar dan da daga shi ba za a sake haihuwa ba a duniya. Aliyu ya bata kulawa, ta soyayya ta kauna, ta tararaiya ta tausayi, ta kyautatawa, ya dauke mata nauyin komai, idan zata yi ma sai ya hana sai idan be gani ba, domin ta saba wahala da ciki sai ya zama aiki be mata illa bata jin nauyin aiki da ciki, amman Aliyu ya sauya kalar jikinta ta zama wata shagwababbiya kamar ba ita ba. Zama da tashi duk rikata yake idan zata yi, motsi kadan sai yace me take ji? Me take so? Bata san ta yi kwadayi da zaben abinci ba sai da ta auri Abokin Rayuwarta. Tun cikin na wata uku Aliyu yake lelenta da abun ciki har cikin ya tsufa, ta bangaren Ummi ma duk bayan kwana biyu sai ta kira, da Emily ta gane amfanin haka sai ta rika rikata da kanta ta gaishe ta. Idan tana kwadayin wani abun na dabam Mama Baraka zata aiko mata. Duk wani motsi nata yana kam idon Aliyu, a yanzu ta san ta yi aure, a yanzu ta san me ake nufi da aka aure mai sonka fiye da wanda kai kake so, a yanzu ta san ribar hak'uri tana da yawa, ta san amfanin wanda yayi hakuri sakamakonsa mai kyau ne. Cikinta na wata takwas aka yi auren Misra da Kameela da mahaifinsu ya hade, banbancin kawai na Event ne, domin Kameela bata yi komai ba bayan henna day, Misra kuma ta yi duk wani event daya kamata budurwa ta yi. Haka Emily ta sake jiki aka rika komai da ita a nan ta kara sanin dadin yan'uwa da kuma muhimmancisu, kusan komai za'ayi sai an nemi shawararta sai an sakata a ciki. Each and every minute sai Aliyu ya kira ya tambayi lafiyarta wanda kusan shi ne abun da ya fi kowane yi mata dadi, tana son kulawa kuma ta samu a gurin Abokin Rayuwa na har abada. Auren Kameela da wata daya Emily ta haifo kyakkyawan yaronta, bayan kwashe awani tana nakuda, ta yi sa'a cikin be so mata da wani laulayi sosai ba, wata kila saboda ta saba da wahala ne, wata kila kuma wannan daga jinin ubansa ne. Amman gurin nakuda bata sha da sauki ba, sai dai daga karshe ta haihu lafiya aka fito da yaron fari kyakkyawa kamar ita. Sau daya Aliyu ya karbi yaron ya duba ya mikawa Mama Baraka ne sake bi ta kansa ba sai da aka fito da Emily daga dakin haihuwa sannan hankalinsa ya kwana. Daki daya aka ware mata saboda ta samu hutu kamin a sallame su. Aliyu ne farkon mutumen da ya shigo dakin ya nufo inda take kwance ya shafa kanta cike da tausayi kamar zai zubar mata da hawaye. "Sannu... Allah ya miki albarka, ya raya abun da ya ba mu, ya ba mu ikon masa tarbiya da daukar nauyinsa, ya baki lafiya i love you so much" Ya sumbance ta sai shafa kanta yake kamar zai cinyeta. Idonta ya cika da hawayen farinciki, ta haihuwa lafiya kuma zagaye da yan'uwa da mijin dake ta daukin zuwan ɗansa duniya. Shi ne namiji na farko da ya nuna mata tsantsar kulawa da soyayya ya tsaya a kanta har ta haihu kuma ya rika yaronsa yayi mata godiya. "Na gode da ka kasance a rayuwata" Ya share mata hawayen sai sake mata kiss Mama Baraka da sisters dinta da yan'uwansa suka turo dakin sai ya daga ya janye hannunsa daga jikinsa. Mama Baraka ta mika masa yaron ya karba ya ciro wayarsa ya kira Ummi video call. Tsabar farinciki Ummi ta ji kamar ta baro Abuja a ranar ta zo Kd dama tana son yara tana son zuri'a balle kuma ta Aliyun da yake kamar abokin shawararta. Rabonta da ganinsu tun cikin Emily na wata shida lokacin da suka zo wani meeting na siyasa ita da mijinta. The following day aka sallami Emily daga asibitin bayan sun yi mata dinki saboda ta samu kari. A gidanta aka dawo da ita, saboda Aliyu yayi yarjejeniya da Mama Baraka tun kamin ta haihuwa cewar a bar masa matarsa a gidansa ba zai yarda akaita gidan Mama Baraka ba. A dole ya amince domin mai son naka shi ma naka ne. Aka dawo da Emily gidan Aliyu, yan'uwansa da suke cikin garin Kaduna na bangaren Daddynsa da na Ummi suka yi ta zuwa barka suna kawo masa alheri daman wacan haihuwa abun be zo da rai ba, ba a yi masa kyauta ko biki ba sai a yanzu. Yayansa kusan kullum sai ya kawo matarsa ta wuni a gidan sai dare ya dauke ta su koma, saboda tana da kyakkyawar fahimta da Emily ba kamar Kameela ba. Abinci mai kyau Emily take babu ruwanta da yaro sai idan za ta ba shi nono, wata yar danginsu Aliyu ce masu karancin rufin asiri aka bar mata tana goyon yaron, mai masa wanka dabam ta shirya shi, ta gasa mata cibiya. A yanzu ne Emily ta san wasu al'adu na jego da haihuwa, domin a baya ita kadai take haihuwarta cikin wahala a yanzu kuma tari da yan'uwa da mijinta a kusa da ita. Ana sauran kwana biyu ayi suna Ummi ta dira a Kaduna a gidanta, abun ka da yan siyasa har abun da be kai ya kawo na yi ake, sai barka ta koma gurin Ummi ana hadawa da abubuwan alheri, daman kuma wani abun biki ne dole ita ma zata rama musu. Kusan ita ta tsara yadda komai zai guna na cikin saboda Emily bata da kawaye, sai sababin makota da kuma yan'uwan miji da yan'uwanta da suka zame mata kawaye. Ranar suna yaro ya ci sunan mahaifin Aliyu Mudallab aka yi masa alkunya da Abulkhary. A ranar Emily ta ga biki ba ji ba, ta san miyen dadin yan'uwa miye yan'uwa da kuma abokan arzikin, ta san dadin haihuwa a cikin dangi ba a gurin bare ba. Ta samu alheri sosai kusan duk abun da aka bawa Ummi na biki tun daga tufafi da kayan jarirai sai da ta kawo mata su, bayan ta yi mata nata kayan barka irin wanda take yi ma matar yayan Aliyu a duk lokacin da ta haihu. Mama Baraka ma ta yi mata nata domin Abulkhary ne jikanta na farko gashi kuma tana kokarin kyautatawa Emily. Dr A-B ma be yarda an barshi a baya ba, duk kuwa da kasancewar be samu zuwa ba saboda shi ma yana ta shirye shiryen nasa auren ne, amman ya saka wata online vendor ta shirya ma Emily kayan barka daga Kano aka aika mata Kada. Uban yaro kam daman tun kamin a haihu yayi booking kayan barka gurin wata cousin dinsa dake siyar da kayan yara, da sharadin idan mace ce ga budget dinsa da zai biya haka ma namiji yayi payment tuntuni ana haihuwarta da kwana uku aka kawo kayan har sai da Emily ta rasa bakin yi ma Aliyu godiya. A haihuwar Abulkhary Emily ta san ta ci naman sunan ɗanta, ta san a aje mata nama mai uban yawa ace nata ne ita kadai bayan an bawa mutane, duk abubuwan da aka yi babu wanda ya fi burge ta kamar taron suna, saboda ta ga mutane sosai wasu ma bata san su ba sai a lokacin, wasu kuma sai a lokacin suka san Aliyu ya sake mata ba Kameela ba, kuma ya sauya gida. Ammy bata zo mata barka ba, amman ta aiko mata da Fatima an yi komai da ita kamar yadda aka yi na aurenta. TURHAN POV. Saboda hankalin Emily dana mahaifiyarsa ya kwanta ya yarda ya bar Fatima a gurin Ammy, ba dan baya son zamanta a kusa da shi ba, ga kuma karatunta da baya son ya rabu biyu idan bata zauna gu daya ba. Yakan ziyarce ta a duk karshen wata, wani lokacin ma ba'ayin wata idan yayi marmarin ganinta zai zo ya ganta. Yana yawan zuwa ne saboda yana tsammanin jin kyakkyawan labari daga rayuwar Aliyu da Emily, tun a wacan ranar da yar'uwar Ammy taje daukar Fatima ta fada masa ta ga Emily na kuka da alama sun samu matsala da Aliyu ne ko sun fara samu. Sai zuciyarsa ta masa dadi yana jin kamar amanar sa da Aliyu ya ci zata fita, yana jiran ranar da Emily zata fito ta dawo masa. Be taba yarda ya tambayi yarsa labarin Emily ba saboda be son ta yi subutar baki ta fadawa Emily cewar Turhan yana tambayarta. Haka kuma yana tsoron ya tambaya ya ji wani labarin da ba haka ba. Be tana tsinkewa ba sai da Fatima take fada masa momynta tana da ciki, a waya suka yi maganar da Fatima amman a ranar be iya kwana ba, sai juyi yake yana tunanin yadda abokinsa zai zauna da matarsa har ta samu ciki. Be kara tsanar Aliyu ba sai da yayi waya da Ammy ta fada masa Fatima na gurin Mamanta saboda ta haihu. A ranar ji yayi kamar ace Aliyu yana kusa da shi ya daba masa wuka ya mutu, domin ya fahimci Aliyu ba shi da niyar sakin Emily ko da yake ai yayi wuri yanzu, ya ba su lokaci zuwa gaba mana idan ta canja. KAMEELA POV. "Kin san fa yau ba girkinki ba ne, ki bari sai girkinki ya juyo sai mu tafi tare, saboda yanzu dare yayi kar mu shiga hakkin madam" Ta dauke hannunta daga jikin angon nata tana murmushin karfin hali. "Shikenan Allah ya tsare" "Ameen" Ya juya ba tare da ya damu da ya sumbance ba kamar yadda Aliyu yake ya shiga motarsa ya daga mata hannu ta daga masa ya fice. Falonta ta dawo ta zauna tana hawaye, wai yau ita ce take son fita wani Namiji ya kalli kwayar idonta ya fada mata yau ba kwananta ba ne, ita take sharing miji da wata a yau, ita take raba girki da kwana da kwana da wata, a yanzu su biyu ne a zuciyar mijinta ba ita kadai ba. Lallai mace yar gaba da baya ce, hakika ta yi aure amman ba ga wadda take so ba, ba ga wanda zuciyarta ta natsu da shi ba, ta yi ne kawai saboda yan'uwanta da kawaye da kuma zuciyata suna zugata ta manta da Aliyu, kuma ta auri wanda ya fishi kudi kamar yadda aka so da farko. Ta yi auren, amman ta rasa soyayya da kulawa da kauna irin wanda Aliyu yake nuna mata, a nan ta san banbancin ba ko wane mai kudi ba ne yake da lokacin iyalinsa lallai irin Aliyu daya ne cikin dari, ya bata dama ta san shi ciki da waje, ta dauki wayarsa ta bincika duk abun da take ra'ayi, wannan kuma ko kusa da wayarsa be yarda taje ba, ga shi yana masifar tsoron uwargidansa fiye da ita. Gaba daya irin zaman da ta yi da Aliyu ya sha banban da wannan da take aure. Sosai da sosai take marmarin mijinta take kewarsa da rayuwarsu, take nadamar abun da ta aika a baya, wata kila ta bata biye zugar zuciya data yan'uwa ba ta tsaya jira wata kila Aliyu zai iya sake zama da ita a matsayin mata ta biyu har ma ya saki Emily tun da ta san yana kaunarta. Ganin kamar zaman ba zai mata dadi ba, tsarin rayuwata be dace da nashi ba ya saka ta fara shirye shiryen barin gidan ko ta halin yaya domin komawa tsohon mijinta, kwatsam sai ga ciki ya bayyana a dole ta zubar da makamanta ta maida hankalin gurin rainon cikinta ta kuma kai zuciya nesa akan kishiryarta if not zata iya mutuwa lokacin be yi ba. Ba laifi da ta haihu ya nuna mata kulawa sosai domin kusan wannan ce haihuwar farko a gurinta saboda wacan ɗan be rayu ba, da yanzu ita ma tana da jini da Aliyu. A yanzu kuma idan ta tuna wata ce ta haihu da shi ba ita ba sai ta ji kamar zata mutu, ga shi ta bangaren mijinta ma ba ita ta fara tara masa yara ba. Tsoron kar ta fita gidan mijin ta sake afkawa wani wanda ya fi shi munin hali, gashi bata da tabbacin ko Aliyu be zai maida ita, ko kuma aa ya saka ta hakura ta zauna gidan sabon mijinta ta rumgume yarta data haifa to her it's not an easy thing ta bar gidan ta bar yarta, bayan kuma bata fuskantar wata matsala a gurin mijinta sai kishiya, sai kuma rashin kulawa kamar Aliyu da yake nuna mata, dadin dadawa kuma tana zargin kamar wani auren yake son karawa su zama su uku, kuma bata isa ta hana ba, domin ba ita ce ta farko ba. Daman hausawa sun ce idan baka yi sharar masallaci ba sai ka yi ta kasuwa ko gidan giya. EMILY POV. "Yace idan an yi hutun karshen shekarar nan zai tafi, daga nan ya nuna masa matarsa" Ta fada tana kwance kan ciyarsa yana wasa da gashin girarta. "Ba za ki bari sai Abulkhary yayi wayo ba?" "Wayo na nawa kuma? Wannan yaron ko kai ya tsofeka" "Eh tun da kakana ya haife shi ba" Ta yi dariya. "Amman za mu je tare da kai ko?" "I don't know kin san yayanki nan ba wani, yi na yake ba, ya kusan sakawa na rasa ki fa, kuma na lura kamar baya son ina shigar masa lamurra tun da yake kira be taba cewa a ba ni mu gaisa ba" Emily ta bude ido. "Kai kasan shi fa rayuwar turawa ce da shi ba wani damuwa yake da mutane ba, shi ne kawai, auren nan ma ban dauka zai yi ba, shi kansa yace be dauka zai yi aure ba sai gashi ya hadu da wanda ta yi masa" "Dan ta kife ne wannan yayan naki, Allah ya so ni aka gano dan'uwanki ne da na sha wuya a hannunsa" Emily ta sake bushewa da dariya har da kyalkyatawa Aliyu sai kallonta yake with affection yana murmushi. "Wallahi ba shi da matsala, ka ga ko bikin nan da aka yi, shi yayi ta gabatar da ni a gurin mutane a komai baya bari a bar ni baya, na jidadin yadda ya nuna min kulawa, shiyasa ban wani damu da yadda mahaifiyarsa ta nuna min bata son ganina ba, saboda naje saboda Dr A-B ne da kuma zaton mahaifinsa zai zo bikin sai gashi be samu zuwa ba" Ya ja mata kunne. "Mahaifinsa ke ba da ke ba?" "I don't know ko ya karbe ni ko be karbe ni ba yet" "Mun gaisa, na gan shi ta system din Dr A-B ya gabatar masa da ni, ya karɓi numberta amman ai har yau be kira ni ba" "Amman da ya ji cewar ke yarsa yayi mamaki?" "Eh Dr A-B yace yayi mamaki sosai, yace shi be yarda ba, da farko har yayi denying cewar ya taba zama da Mama Baraka sai da Dr ya gabatar masa da hujoji sannan ya yarda, amman da muka gaiwa na ga dai kamar damuwa a fuskarsa sosai, amman har yanzu be kira ni wata kila baya so na" "Aa ko dai yana jin kunya ne ba, ko kuma be san yadda zai kalli abun ba, amman yanzu idan muka je zamu gani ai, kawai abun da nake so da ke duk wani abu da zai biyo baya na rashin dadi ba za ki damu ba ki min alkawari" Ta dago ido ta kalleshi a shagwabe. "Ina da kai a yanzu Aliyu me zai saka na damu" Ya kama bakinta ya matse. "Aliyu ko?" "Nooo My Soul Mate" Ya saki bakin ya kai mata rankwashi a kai. Ta da ga jikinsa. "Ka yi na kudinka" Ya san me take nufi dan haka ya kalleta da sauri. "Yi hakuri, zo ki rama" Ya kai hannu zai rikota ta matsa da sauri ta tashi a guje ta bar masa gurin tana dariya. Murmushi ya mike tsaye ya bi bayanta. Before time din da Dr A-B ya tsara yayi, Aliyu yayi nasa tsare tsaren ta yadda zai samu damar raka matarsa, sai kuma aka yi sa'a a lokacin ana hutun karshen sabuwar shekara ne. Ana gobe za su tafi Abuja, Aliyu ya kaita da ɗanta gurin Mama Baraka gurin mata bakwana, ta zaren labari yayi tsawo Emily ta bayyana mata fargabarta na tafiya tana ganin kamar ba zai karbe ta ba. "A gurin Bature haihuwa babu aure ba illa ba ce, kusan ma sun fi yin haka, ina da yakinin zai karbe ki" "Idan ya tambayi labarinki fa?" "Ki fada masa komai, amman ban da mutuwar aurena" "Why? Za ki komawa mahaifinsu Kameela ne?" "Ba lallai ba, na lura kamar ya dauki abun da zafi sosai, ni kuma ban shirya auren kowa a yanzu har sai na aurar da duka yarana, by that time kuma na san aure ya fita kaina" "Amman da yanzu ace Mahaifinsu Kameela zai dawo zaki koma masa" "To me zai hana?" Ta amsa tana murmushi, Emily ta kalleta ta sauke kai ga dukan alamu tana son tsohon mijinta, sai dai kuma zama ya kare a tsakani. Sai dare Aliyu ya zo ya dauke ta bayan ya ajewa Mama Baraka siyaya kamar yadda ya saba. Abuja suka fara tafiya sai da suka kwana a gidan Dr A-B da ya bukaci su kwana a gidan amman Aliyu be yarda ba, sai ya kwana a gidansu gurin Ummi. Emily kuma ta kwana a gidan ɗan'uwanta. Matarsa wayayyiya ce kamar shi, tana da son mutane da nuna kulawa Emily ta yaba da yadda aka tarbe ta. Alhaji Bulama na da na shi uzurin haka ya saka Dr A-B ba samu alfarma tafiya a jirgin mahaifinsa ba sai na kasuwa. Ba a cika samun direct flight daga Nigeria zuwa Scotland kai tsaye ba. Yawanci Ana tashi daga Lagos (Murtala Muhammed International Airport LOS) ko Abuja, kasancewar a Abuja suka kwana a nan jirginsu ya daga sai ya sauka a London Heathrow, sai da suka huta a wani hotel dake kusa da airport din sannan suka dawo suka shiga wani jirgin ya ɗaga zuwa Scotland. Tafiyar daga Abuja zuwa London ta ɗauke su kusan 6–7 hours. [9/7, 7:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣7️⃣ Kin dade kina sha’awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba? Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na ’yarki? To, ga sauƙi ya iso! ADASHE NE NA GATA! Ki zuba kuɗi, ki ɗauki abin da kike so daga: Sutura da zannuwan gado Kayan kitchen Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu) Talkami da jaka Zanen gado Frames (flowers decoration ko standing ones) Console mirror Boxes na Lefe ko na traveling. Warmers iri-iri Food flask iri daban-daban Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so! Sauƙi ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa. 📌 Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati. 📌 Akwai sharudda da ka’idoji. Domin ƙarin bayani, ki/ka tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660 Ko ta hanyar WhatsApp 👉 Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1 Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Thank you 😍 🙏 Daga London zuwa Edinburgh/Glasgow kusan 1 hour flight ne. Jimilla tafiyar ta zame musu ta 10 - 12 hours bisa layin jirgin da suka bi. Scottish, Scotland tana cikin United Kingdom (UK) ne, arewacin Ingila take. Tana da manyan birane kamar Edinburgh (babban birni), Glasgow, Aberdeen, Dundee. Yanayin can yawanci sanyi ne sosai, musamman lokacin hunturu (November–March), akwai ruwan sama da iska mai ƙarfi, balle kuma yanzu da yake January. Shiyasa suna sauka filing jirgin Edinburgh Airport (EDI) dake garin Edinburgh, Aliyu ya rufe matarsa da rigar sanyi da ya riko mata, dan kam tun a jirgi yayi masa tanadi daman shi yake kula da abunsa.. Tun da suka sauka kasar Emily ta tabbatar sun zo garin yan'uwanta domin yawan mutane kasar kowa zaka gani jan gashi ne irin nata, tana ta kallon manyan gine ginen da kawar gari ta zo inda bata sani ba. New Town, wata sabuwar unguwa ce da mai taxi ya kaisu bayan Dr A-B Ya Fada masa domin a unguwar mahaifinsu yake. Aliyu ya fara fita motar yana rike da Abulkhary dake bachi sannan ya bude mata ta fito tana kallon gaban gidan da suka tsaya wanda tsarinsa ya sha banban da na mu na hausawa. Karamin gate ne ba mai tsawo sosai ba an saka flower gefe gefen na gida ga haske normal ba. Gidan sama ne mai fadi amman ba mai ado da lankwashe lankwashe kamar na mu ba. Aliyu ya tsaya a gabanta ya saka hannunsa daya ya gyara mata fuskarta,.ya cire mata hullar kanta gashinta ya bayyana sai ya baza mata gashin ko'ina, sannan ya rika hannunta suka nufi kofar shiga gidan. Dr A-B ne a gaba tare da matarsa Emily tana daga baya tare da Aliyu. Door bell ya taba sannan ya kara fuskar sa gaban ring camera yayi magana kasancewar sun shigo da dare ne a lokacin da sawu ya fara daukewa. Wata kyakkyawar matashiyar yarinya ce ta fara bude kofar tana ganin Dr A-B ta saka ihu ta rumgume shi shi ma ya rumgumeta yana murmushi. Aliyu ya kara matse hannun Emily take hannunsa domin ya lura fargaba ta cikata ta ko'ina. Da suka shiga ciki kowa kallon Emily yake saboda an labarta musu ita tun kamin ta zo, kuma sun ga zahiri domin bata rage komai daga kammanin mutumen dake tsaye gabanta yana kallonta ba. "Dad wannan ce Emily yarka, Emily wannan shi ne mahaifinki" Ya dade yana kallonta kamar ya rasa abun yi, bata bar komai daga kammaninsa ba, shi kasan da ya ganta sai da yayi rabin mutuwar tsaye, domin duk yayansa babu wanda yake kama da shi sosai da sosai kamar yadda ita take yi. ita ma tana ta kallonsa sai hawaye take. "Dare yayi ya kamata kowa ya kwanta gobe za mu yi abun da ya kamata domin tabbatarwa" "Dad baka ga kamammi ba?" "Kammanin kawai ba su isa su wadatar ba ya kamata mu bi ka'idodi" Kamar wanda be san taya zai karbe ta ba, haka ya tarbe ta sai duk kuzarinta ya gushe. Sai dai Aliyu da Dr A-B sun kafarara mata guiwa, a dokar kasar be isa ya amsa cewar shi ne mahaifinta kai tsaye ba ta hanyar kammani ko sheidu sai da takardun shedai gwajin jini kuma sai ya zama tana bin sunansa ne. Emily ta kwana da tunani, washe gari da suka hadu teburin cin abinci sai ta lura babu mahaifinta a gurin sai yan'uwnta maza biyu da mace biyu da kuma matarsa da tun jiya suke rigima saboda abun da ya aikata shekaru da yawa da suka wuce. Kusan kowa be saki jiki da ita a gidan ba, saboda dokar bata tabbatar ba, har sai da suja tafi Asibiti aka yi musu gwajin kwayoyin halitta ita da mutumen da take ikirarin ɗanta ne results din ya fito at 98% sannan mahaifinta ya yarda. Tana zaune wajen asibitin ita da Aliyu dake rike da hannunta ta dora kanta a kafadarsa. Mahaifinta ya fito daga cikin asibitin yana rike da takardun gwajin. Emily na ganinsa ya mike tsaye tana kallonsa ya nufo inda yake with so much emotional tana jiran ya fada mata results din dake hannunsa sai ta ga kawai ya rumgumeta. Aliyu ya sauke sanyayar ajiyar zuciya yana murmushi tare da yi ma Allah godiya. Shi kansa abun da ya faru jiya ya ba shi tsoro. Ya dagota daga jikinsa ya duba fuskarta ya taba ya sake maida ita jikinsa. "Na san kin zo da tari tambayoyi da suka bukatar amsa.." Ya sunbance saman kanta. "No na riga na san amsar komai, na san duk abum da na ke son sani, komai ya faru ne ba da son ran kowa ba" "Yeah ki yafe min, da ace na san tana dauke da cikinki ba zan juya baya ba, dukan mu muna kuskure na yi kuskure na sani I'm sorry" Emily ta rike hannayensa. "Mu daina tuna baya, na zo nan ne saboda samun karin farinciki da kuma sanin asalina, ba amfanin tuna abun da ya wuce" Ta juya ta nuna Aliyu. "Wannan mijina ne, wannan kuma yarona" Ya mikawa Aliyu hannu suka gaisawa, da ya tara hannu zai karbi Abulkhary sai yaki zuwa saboda kewa yake yi baya yarda da kowa sai iyayensa. Duk yadda Dr A-B zai yi ya fahimtar da Step Mom dinsa mahaifinsa ya aikata kuskure kuma yayi nadama sai da yayi, domin a gurinsu kamin abu ne ta maka shi a kotu ta nemi a raba auren, kuma a raba har ma da ganimar daukar dukiyarsa a damka mata kuma a bata ragamar yayanta. Ta inda ta saurara masa be aikata hakan a lokacin da yake aurenta ba. Ya aikata ne kamin ya hadu da ita. Sam ita kam baya yarda ta karbi Emily ba, sai ya zama ma. Kamar tana kishinta saboda Emily ta fi kama da mahaifinta fiye da yayanta, ga shakuwa da ta shiga tsakaninsu na dan zaman da ta yi a gidan, yaran ma sun sake jiki maza da mata amman ita bata yarda da Emily ba. Mahaifinta ya kaita gurare da yawa, ya nuna mata abubuwa wasu daga tarihinsu wasu kuma daga tarihin garin. Mutumen mai kaunar karensa sosai duk inda yaje yana tafiya da su domin rakiya, tun tana tsoro har ta daina. Wata rana da ya tafi da ita gurin da yake kamun kifi ne yake tambaya labarin Mama Baraka, ta fada masa kuma ta labarta masa yadda abubuwa suka faru da ita. Ya tausaya mata matuka, ta nuna masa hoton Fatima a wayarta. Honeymoon din da Aliyu be samu tafiya yayi da matarsa ba lokacin da suka yi aure shi yayi da ita a nan. Ya jata sun shiga gari sun yi yawa har makotan garin sun ziyarci gurare dabam dabam. Sati daya ta yi a gidan ya dauke matarsa suka tafi yawon amarci. Dr A-B daga can wata kasar ya bulla. Mahaifinta ya saka ta gaba suka tafi aka ayi komai a rubuce da ka'ida cewar shi ne mahaifinta a doka. Da za su tafi Emily ta yi kuka sosai tana ta kewar mahaifinta, ta rumgumi yan'uwanta ta yi musu bankwana tare da jaddda musu za ta dawo a duk lokacin da ta bukaci haka. ya rumgume yarsa ya saka mata wata sarka tashi mai tarihi ya dauko kudi mai yawa ya bawa Emily amman bata karba daman bata zo domin kudinsa ba sai dan ta san waye ubanta shi ma kuma ya san wacece ita, amman ta karbi kyautar agogo da hotuna da yayi mata... Karfe bakwai na safe suka bar kasar ita da Aliyu, sai da suka sake daukar awanin da suka dauka da farko sannan jirginsu ya isa Nigeria suka sauka da dare saboda awaninin ba daya ba. Ummi ta aika da mota aka dauko su daga Airport, zuwa gidan inda suka samu tarba ta musamman. Washe gari suka sha hira da Ummi na abubuwan da suka faru da kuma yanayin garin da guraren da suka ziyarta, hotunan da suka dauka da sauransu. Satinsu daya Abuja sannan suka dawo Kaduna, rayuwa ta cigaba kamar yadda aka saba. Da Fatima ta yi arba da hotunan da aka dauka a wayar Emily ta sha kuka sosai ba a tafi da ita, Emily ta mata alkawarin idan zata koma da ita zata tafi. Har a lokacin Ammy bata yarda Fatima ta zauna a hannun Emily sai dai ta rika zuwa tana dawowa, sai kuma idan fitsarar Fatima ya tashi ta nace sai ta kwana a gidan. Emily na yaye Abulkhary Aliyu ya biya mata Ummara ta tafi tare da Fatima da shi, da Abulkhary, a can suka yi sallah karama ba su dawo na sai bayan Sallah. Da lokacin hajji yayi kuma ya cika mata kawarin da ya daukar mata tun tana da cikin ɗansa. Ita kadai ta tafi ta yi hajji ba da shi ba saboda yanayin aikinsa. TURHAN POV. A shekarar da Emily ta tafi hajji a shekarar Turhan ya yafi, shi da matarsa sai dai har kowa yai ibadarsa ya gama be hadu da dan'uwansa ba saboda jirginsa kasar da masaukin kowa dabam. Turhan yana zaune yana waya da Fatima yana fada mata abubuwan da ya tara mata a dakinta dake gidan. Matarsa ta shigo, ta zauna can nesa da shi ta zauna, haka take a duk lokacin da yake magana da yarsa saboda tana kishin Fatima ba yarta ba ce, kuma tana kishin duk wani abu da zai dauke hankalin mijinta daga gareta. Ta jira har sai da ya gama wayar sannan ta koma kusa da shi ta tsaya tana murmushi. "Rufe idonka" Ya kalleta cike da shauki, yayi murmushi ya rufe idon kamar yadda ta bukata. Ta kama hannunsa ta saka masa abu a hannu, ya lakaba abun sannan ya bude idon. Wasu yan mitsitsinan kayan yara ne irin na yar tsana amman na jarirai. "Da leek.. laken testanna tisʿa shuhur." "Wannan domin kai ne, amman ka jira sai nan da wata tara" Turhan ya kalleta ya sake kallon kayan, kamin tunaninsa ya ba shi abun da ya dade yana tsammani daga gareta. Wani irin tsalle Turhan yayi ya dauke matarsa yayi sama da ita yana juyawa. Kamin ya sauke ta tambayeta. "Kina ciki da gaske?" Ta daga mishi kai tana hawaye. Sai ya sake rumgumeta "Wallahi ana baḥibbik shadeed.. Enti addayteeni al-farha al-bat kunt baftaš ʿalaiha, khalleetini mabsoota li-daraja ma baʾat mihtaaja ay farha taanya." "Wallahi ina kaunarki.. Kin ba ni farinciki da nake nema, kin faranta min baya na rasa wani farinciki. Alhamdulillah ya Rabbi, Alhamdulillah Allah” A lokacin ne ya gane rokon da yayi a saudi be tafi a banza ba, rasa Emily ya samu wani farinciki ta inda ya cire rai da samu, ada yayi zaton Fatima ce kadai yarsa, ashe ba iya haka farincikin zai tsaya ba. Da Ammy ta samu labari kamar ta zuba ruwa kasa ta sha tsabar farinciki, kusan duk wanda ke masarautar ya taya Turhan murna da farinciki a lokaci da cikin ya bayyana. Wani irin kula na musamman da tarairaiya kamar kwai Turhan ya shiga yi ma matarsa. Ko da baya son ya shirya kula da abun cikinta balle kuma yana kaunar matarsa tun asali a yanzu ne ma kaunarta take ninkuwa. Ba ma kamar lokacin da ta haifa masa yan biyu mace da namiji, kamar mahaukaci haka ya zama tsabar farinciki macen aka saka mata sunan Ammy namijin kuma ya saka masa sunan da matarsa ta zaba. Sai da suka yi kwari sosai sannan ya cilastawa matarsa shiryawa suka tafi Nigeria a tare aka kaiwa Ammy da Fatima yaran suka gani. Da ya ji labarin Emily na da wani cikin gurin yarsa, sai da zuciyarsa ya sosu, har kullum ba zai cire rai da fatan rabuwar auren Aliyu da Emily ba, yana ji a jikinsa komai daren dadewa Aliyu zai juyawa Emily baya. Ammy ma haka take saka rai saboda tana ganin Emily da Aliyu sun musu butulci. EMILY POV Emily ta saba da ciwon zuciya. Duk wanda ya zo mata a baya sai ya bar ta da hawaye da raunukan da ba sa ganin ido amma zuciya tana ji. Auren farko ta zame mata yaudara, na aure na biyu ya zame mata jinya. Lokacin da ta daina tsammanin farin ciki, sai ta haɗu da Aliyu. A farko ta ɗauke shi ma kamar sauran mutanen me, ya shimfida mata soyayya sai ta hau ya juya baya. Sai dai lokaci ya nuna mata kuskuren tunaninta. Aliyu bai tsorata da raunukan da take ɗauke da su ba. Ya tsaya mata kamar likita ga mara lafiya. Ya saurare ta ba tare da gaggawa ba, ya rungume ta ba tare da sharadi ba, ya nuna mata cewa akwai wanda zai iya sauya ciwon zuciyarta ya mayar da shi farin ciki. A hankali Emily ta fara murmushi inda ta saba zubar da hawaye. Zuciyarta ta buɗe kamar furanni da suka ji ruwan sama bayan dogon fari... *** Tana tsaye a Kitchen tana juya miyar dake kan wuta Aliyu ya shigo, bayanta ya kaiwa duka kadan sannan ya juyo da ita tana dariya ya sumbance ta. "Me kika girkawa haka kamshi har office ya tarar da ni" Ta yi dariya. "Kuma fa yau ba da kai na girka ba" Ya hade rai. "Kai kin ma isa?" "Kai haka kake da kyau daman?" Ya kai mata mitsika a kumatu "Miyasa kika raina ni wai? Kin san fa ni oganki ne" "A baya ba, a yanzu kuma Abokin Rayuwa" Ya rumgume yana murmushi ya shafa katon cikinta. "je ki huta bari na zuba abincin ai yayi ko?" Ta daga mishi kai. "Baka siyo min komai ba?" "Na siyo mana, wani mai nama na gani yana soyawa na cire masa zuciyata na ce ya soya min na kawo miki" Ta chakuli cikinsa tana dariya, shi ma dariyar yayi ya kashe gas din, ya dauki cooler da aka siya mata gurin Khadeeja Candy ya fara zuba miyar. Falo ta dawo ta zauna ta bude ledar kayan cikin dake ta kamshi tana fara ci, tana jin kaunar mijinta, a yanzu ta gane ba dukkan soyayyar gaskiya ake samunta cikin sauƙi ba. Wata soyayyar sai da jinya, sai da yaudara, sannan daga ƙarshe Allah ya kawo maka wanda zai goge komai ya mayar da ke sabuwa. Aliyu ya zama wannan kyauta, Wani lokaci idan ta tsaya gaban madubi, sai ta dubi fuskarta dake cikin madubin tana tambayar kanta “Shin ni ce waccan Emily da ta sha kuka da hawaye a baya? Ni ce waccan yarinyar da ta yi ta fadi-tashi a soyayya, ta rasa uwa, ta rasa gata?” Madubin ya kan nuna mata fuskar mace, amma cikin zuciyarta hotunan rayuwarta take gani, yadda ta yi ta neman wanda zai tsaya mata, yadda ta sha karya da yaudara, yadda ta sha jin kalmar “ki yi hakuri” ba tare da wani ya share mata hawaye ba. Amma yanzu abubuwa sun canza. Wani haske ya bayyana a rayuwarta, hasken da bai zo da wuri ba, sai bayan dogon lokaci. Duk jarabawar da ta sha, duk fuskokin da suka juya mata baya, duk hawayen da ta kwanta da su, sun zame mata darasi guda, hakuri wanda shi ne makullin kowane sauyi mai kyau. Da farko, hakuri ya yi mata nauyi. Amma da ta dage da shi, sai ta ga riba. Ta gane cewa bayan wuya akwai daɗi. Ta dandani zafin lokaci, amma kuma tana kan dandana zaƙin sakamako. A yanzu idan ta kalli kanta a madubi, ba kawai tana ganin mace ba, tana ganin ƙarfi da jarumtarta, tana ganin mace da ta yi tafiya kan wuta ta jure har ta kukanta ya sauya zuwa murmushi. tana kallon wata karamar yarinya da zama uwa, yar'uwa, ƴa kuma mata ga mutumen da ya san darajarta, mutumen daya sauya lafiyar rayuwarta, ya canja tunaninta ya sabunta duniyar da abubuwan da bata sani ba, bata saba ba kuma bata taba tunanin za ta samu ba. Emily ta sha taskon rayuwa, an haifeta ba da aure ba, kuma mutane suka ɗora mata nauyin da ba nata ba. Ta taso cikin hawaye, cikin rashin gata, har sai da zuciyarta ta gushe daga neman farin ciki. A Lokacin da Khaleefa ya yaudareta, ta yi zaton soyayya ba gaskiya bace sai ta karyata gaskiyarta, da Turhan ya juya mata baya, dan zaren farinciki daya rage mata sai ya tsinke, duk da irin hallacin da ta yi wa mahaifiyarsa, ya kasa ganin darajarta. Amman a yau dukansu su biyun sun rasata, bayan doguwar jinyar cin amana da kowanensu yayi a zuciyarsa. Idan cin amana tana da rana Khaleefa ya gani, idan butulci yana da ciwo Turhan ya fi kowa fahimtar haka a yau, yana dauke da ciwon kaunarta gashi ta masa nisa, Khaleefa kuma be isa ko kusa da ita ya tsaya ba. Emily ta samu gata a wajen Aliyu, wanda ya rike ta da gaskiya, wurinsa ta san daɗin addinin Musulunci, a wurinsa ta gane cewa soyayya rahama ce, gata ce. Ta tashi daga matar da ake wulakantawa zuwa wanda ake alfahari da ita. Ta zama uwar ƴaƴa a gidan Aliyu, kuma mata ga mutumen da ya fahimce ta tun farko, ya girmamata, ya so ta, ya bata gata, ya mantar da ita damuwa. Asalinta be hana ta zama abar so a gurinsa ba. Rayuwa ta karantarta ita duk inda aka haife ka da aure ko ba aure ba kai halittar Allah ne mai daraja, kuma ba laifin ka ba ne... Na gyara miki rubutun gaba ɗaya my Lady 🌹, na haɗa da abin da kika buƙata, tare da ƙarin salo mai kyau da ɗan jan hankali ga masu karatu: --- Godiya ga Allah da Ya bani ikon fara wannan littafi har na kammala shi cikin nasara. Alhamdulillah. 🙏✨ Wannan littafi na sadaukar da shi ga Big Sis Habiba Muhammad I love you more than words can ever express. 💖 Masu karatu zan so jin daga gare ku Wane darasi kuka koya daga cikin littafin? Wace ɓangare ya fi burge ku? Kuma da me za ku fi tunawa da littafin Abokin Rayuwa? Kada ku manta, ni ce Khadeeja Candy mai siyar da kaya masu kyau da inganci a farashi mai sauƙi. 🛍️✨ 👉 Khadeeja Candy Store https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Sai mun haɗu a littafi na gaba mai suna GUMBAR DUTSE, in sha Allah. I love you all dearly ina yi muku fatan alheri fiye da yadda kalmomi za su iya bayyana. ❤️🥰 ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************