👑SARAUTAR MATA👑 👑👑👑👑👑 0⃣1⃣ Ya Allahu Arrahamani Rahim,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA Gidane irin ginan wani lokaci da, can baya, wanda yake nuna cewa,a lokacin baya gidan yana a,cikin jerin gidajen da suka dan yi tashe a wancan zamanin, Sai dai a wanan zamani ya zama kamar ginan kauya,a,gare mu, Tsufan gidan ya,sa har shafin da,akaiwa gidan yana dan banbara yana zubewa, don tsufa, Wasu bangare na katangar gidan har sun zube an sa tsufin kwano a,rufe gurin dashi, Tsakiyan gidan akwai iccen durumi, wanda ya baje yana bawa mutanen gidan inuwa da sanyi,,, daga gefen dakin ta waje akwai randan ruwa, suna rufe da,wasu manyan kwanukan lokaci da, can baya, wanda yake nuna cewa,a lokacin baya gidan yana a,cikin jerin gidajen da suka dan yi tashe a wancan zamanin, Sai dai a wanan zamani ya zama kamar ginan kauya,a,gare mu, Tsufan gidan ya,sa har shafin da,akaiwa gidan yana dan banbara yana zubewa, don tsufa, Wasu bangare na katangar gidan har sun zube an sa tsofin kwano a,rufe gurin dashi, Tsakiyan gidan akwai iccen durumi, wanda ya baje yana bawa gidan iska da innuwa mai dadi, daga gefen dakin ta waje akwai randunan ruwa, suna rufe da,wasu manyan kwanukan iri na da,, sai wani rumfan dake ta gaban dakin wanda ke bawa dakin sanyi again,, Wata mata ce mai dan shekaru sai dai ba can ba ta fito daga dakin, tana saye a cikin wani kodadden zani da riga na atamfa, Sai dai zani daban riga daban dankwali ma,daban, Hannunta yana dauke da,wani stohon kwanon silver wanda daga saman shi duk ya dan mokade sosai, Tsakin jan masara ce dauke a,cikin kwanon ba,wani mai yawa ba can, sosai, Wani stohon kujera yar tsugunno irin na mata ta,tsakar gida,shi ta nufa tazauna a kai a hankali, tafara dan gyaran tsakin dake a cikin kwanon, Sallaman da,akayi daga kofan dakin ne yasa ta saurin dago kanta da yake a,duke da farko, bakinta yana karba sallaman a hankali, Dan ta Hamza ne ya shigo gidan hannun shi yana dauke da wata yar bakar leda bag karama wanda zaka iya hango ganyen miyane a cikin ledan, Fuskan shi tar akan mahaifiyan nashi yayin da ya nufi inda take zaune, yana mata sannu da gida Umma, Takara dago kai a cikin fara,a tana cewa Baba na an dawo lafiya ? Kafin ya karba mata sai ya zube a kasa yana cewa, Umma sannu da aiki, an wuni lafiya yana kokarin aje ledar da ya,shigo da ita a hannun shi daga gefen ta, ta ansa mai da fadar Alhamdullahi, Kardai yau ma kana azumin ta fada cikin kashe shi da idanuwan ta tar a kan shi,, Murmushi yayi yana maidan dukar da kai yayin da,ya zauna hannayen shi suna harde da junan su, yake cewa cikin hade wani miyaun bakin ciki, Umma ai gara nayi azumin don koda banyi ba, ba,wani abu zanci ba don kasuwan yanzu sai a hankali wallahi, Allah ya taimaka tace tana mai kokarin mika hannu ta don ta,bude wanan ledan dake a,gefen ta, Gayen miya ne yakuwa da,yar alaiho sai tattasai atta da albasa a cikin ledan, Ta dago kai tana cewa duk wanan haka muka,samu, Baba na, Ubangiji Allah ya ummfana Allah ya sa maku albarka Allah ya tsare muna ku ya shirya muna ku tafarki mai albarka,, Ya amsa da Amin Umma yana saka hannun shi a,cikin aljihun wandon shi inda yafito da,kudi sai dai duk canji ne kudin ba wasu kudi masu girma,daga ciki, Mikawa uwar yayi yana cewa mama ga wanan kasuwan duk ta chushe yau duk naira dari da hamsi na samu sai na,sayo wanan kayan miyan don nasan kina dabukatar su, Wanan kuma nace bari na zo maki dasu kyasai wani abin dashi anan Shiru tayi tana mai kura mai ido a cikin tausayawa, dan nata duk da gashi mai karancin shekaru amma yasan yadda zaiyi ya taimaka masu, Babana kabar wanan kudin ka,samu ka dan sai abin buda baki dashi idan kasha ruwa, don kaga ga tsakin masara nan shi nake gyara muna mu samu na dan tabawa , Kaga wanan ganyen yai daidai da faten da nake son muna,dama,babu ganyen da zan saka muna a cikin sa hakana zanyi yanzu kaga an samu abin hadi Allah yasa,albarka a cikin sa, Kai ya girgiza yana fadin Umma ki karba duk abinda aka dafa a gidan nima shi zanyi buda bakin dashi, Ta ce Babana Allah ya sa wanan wahalan da kake muna yama tushen alherin ka a rayuwan duniya da lahira yace Amiiln cikin jin dadin adduan mahaifitan nashi a kullun tana masu adduan fatan alheri shi da yan uwan, Tausayin sune ya kamashi, don zai iya cewa yau kusan kwana,biyu ke nan yana yan bugabuga amma bai samu wani kudin da zai dan sayo masu abinci ba kamar yadda ya,saba da taimakon mahaifiyan nashi da yan kannen shi dake gidan yanzu,,, Wanda zai ce kusan shekara bakwai tun yana karami shike dauke da nauyin gidan nasu, a komai, Duk da ita,ma mahaifiyan tasu tana nata kokarin gurin dan ciyar da yan marayun yayan nata, Tun bayan rasuwan mijin ta wanda ada can su masu haline da rufin asiri amma mijin ta yana rasuwa yan uwan shi suka wawashe duk wani dan abinda ya,barwa iyalin nashi, Saboda cin amanan maraya,da,sunan wai yaran basu isa rike dukiyan a hannun su ba a lokacin,,, Bayan yan shekaru "yar ta zatai aure babu dukiyan babu labarin su dole hakana akai bukin akai ta,babu komai don dangin mahaifin su sun ciye komai nasu har gona da filayen su duk sun sayar da sunan wai za,a biya mai bashi dasu,,, Yan uwan ta ne suka dan hada mata gudun mawa suka bata shine akadan yi sayayya dasu, Adduan da mahaifiyan nashi ke mai sune suka jawo hankalin shi gare ta daga dan tunanen da yakeyi a lokacin, Cikin dan sauke ajiyan zuciya yake cewa mama yanzu kasuwan baici shi yasa nake son na canza wata sana,a ko zaifi wanan din karbuwa, Tace cikin dago kanta Babana wani SANA,A, zakaiya canzawa yanzu don kaga da wanan din ka,saba nagani, Yace wa mahaifiyar tashi Umma zan duba da zaran naga wanda yake da,daukuwa zan maki magana, Ya mike yana cewa bari ya dan gyara dakin shi kafin magriba ya gabato gare shi, Bayan shi Umma,tabi da kallo a,cikin tausayawa dan nata wanda yataso maraya ga,aikin wahala da yai mashi yawa a,rayuwan shi tun yana yaro karami, *** ********* *** Kiran sallah magrib ne duk ya karade ko ina a cikin garin baka jin komai sai karan speakers dake tashi ladanai na kiran sallah, Daga gurin da yake zaune ya rike da dabino kwara, biyu a hannun shi yana mai tofa addua daga bakin shi, a hankali, Daga gurin da yake zaune, yana alwala malam Ayuba yana kalon shi har zuwa lokacin da ya dauki ruwa yaddan kora, Abinda yasa shi gane cewa azumi yaron yayi a lokacin yana buda baakine, Shidai har kullun wanan yaron yaba,shi sha,awa,sosai a rayuwan shi, ba,yau ba koda yau,she daban yake da,sauran yaran uguwarnan, Bayan an idar da,sallah ake cigiyan duk wanda keda sha,awan zuwa gonan mai uguwa gurin aiki kwadago,, A take Hamza yaba,da sunan shi don yana da bukatan haka ba yau ba, Amma sai mutanen gurin suka,fara sokewa wai bazai iya komai ba kada a,sashi a,cikin su, sai malam Ayuba ne wanda fitowan shi ke nan daga cikin masallaci yake cewa a,yi hakkuri asa sunan shi idan an gwada,anga bazai iya ba,sai a cire shi daga cikin su, Da,sallama dauke a bakin shi ya,shigo gidan inda yake gaida mahaifiyan shi da aikin gida, Tun a tsaye take cewa ,a Baba na barka da shan ruwa Allah ya karba muna bukaun mu na alheri ya amsa dacewa Allahuma Amin Umma daga haka yakai zaune daga gefen ta, a hankali, Bayan yasamu guri ya zauna ne yake fadawa mahaifiyan shi cewa zasu tafi aiki a gonan mai unguwa dasafe indan Allah ya kai mu, Da,sauri Umma dake kokari jawo mai langan abincin shi dake rufe daga gefe,,, Tai wani irin saurin dago kai tana kallon shi a cikin mamaki da tausayawa saboda tana ganin kan,kantar dan nata, Tasan cewa mutuwa ce takai rayuwan su a hakan don da ace mahaifisu yana da rai da duk irin haka bai faru da su ba,,, A cikin wani irin murya yayin da take aje yar langar abincin nashi take cewa anya Baba na zaka iya irin wanan aiki kamar fa kayi karamii da wanan aikin, Murmushi yayi yana kokarin wanke hannun shi da ruwan dake gefe guda, yake cewa Umma adduan ki kawai nake bukata , A sanyaye tace tau Allah ya tsare yasa albarka ga al,amari yace Amin Umma yayin da yake kokarin bude kwanon abincin dake gaban shi, Duk da faten ba,wani kayan hadi taji ba dan tsakine sai attarudu danye, da alaihuu sai gyada kadan da aka watsa a ciki, Amma sai ga kamshi dadi yana tashi daga cikin kwanno tun kafin yaci yar miyaun shi sai ta katse, Muryan shi da Rakiya kaunar shi taji yadan sata fitowa daga daki tana kokarin cire hijab din dake saye a kanta, Sai a lokacin hankalinshi ya kai a kanta yana cewa a,a Rakiya andawo daga makarantar ashe ? Yaya Hamza ina wuni ya kasuwa yace lafiya kalau Alhamdullahi ina, Abdul halan ma, Tace yanzu yafita karbo wa mama kalanzir din fitillah ta, Sallaman da akayi ne daga kofa ya,dakatar dasu daga zancen su inda Ummaa take karbawa da cewa a,a, Kardai nace, Aisha ce tafe a yanzu cikin daren nan ta karba tun daga nesa da cewa, Yarinyar da,akakira da,Aisha take cewa nice maman Abdul, mamace ta aikoni wai na kawo maku wanan abincin don yai muna yawa bazamu iya cinyewa,ba,, Masha Allahu Umma ta ambata yayin da take kokarin karban kwanun daga hannun yar matashiyar budurwan, Sai famqn zabga godiya take da sa albarka ga matar da ta Aiko masu da abincin, Muryan yarinyar ce ta ke cewa Dan wakene mai zafi a a wani roba an rufe shi daban yarinyar ke cewa wanna wanna na marmarine mama tace akawo maki, Dan wake ne yaji mai da yaji sai kamshi ke tashi daga cikin robar, Inda dayan kulan yake shake da farar shikafa da miiya daban miyar busashen kifi, yaji curry,, Sai da Umma ta wanke kwanukan tsab duk da dai, yarinyar tana cewa Umma ta bari ai zasu wanke da safe, ma, Fitar yarinyar gidan wace ke cewa Umma sai da safe yayi daidai da waigowar Umma inda yake zaune tana cewa hamza to kaga ga abin buda baki Allah ya kawo maka sai ka dauka kaci wanda kake so, Sauke ajiyar zuciya yayi tare da,dan kara gyara zaman shi yana cewa Alhamdullahi Umma don wanan da kikayi yai min dadi sosai a raina, Duk yadda uwar taso ya dan ci abinci amma yaki tana lura dashi wanan halin sa ne baya son cin abincin nan da ake kawo masu daga makwabta duk da yasan cewa abincin yana taimaka masu sosai a,fanni da dama, Saukin abin ma, ya yaba kwarai da halaiyar mahaifiyan yarinyar dake kawo masu abincin don bawai sai, wanda ya rage suke kawo masu ba har wanda aka dafa wani lokacin da zafin shi zata debo masu, Baibar gurin ba yana kallon yadda yan kannen shi ke wawason abincin cikin jin dadi da annashuwa, Yayin da,suka,bar na mahafiyar su dan faten da ta hahada tai masu iya karfin ta,, Kwanon dan wake Umma tadangware mai a gaban shi tana cewa kai kaci wanan tunda bazakaci shimkafa ba, Baida yadda zaiyi don kada yai mussu da mahaifiyan nashi dole ya dan jawo kanon yafara kai hannun shi a,hankali, Dan waken yana da zafi inda ya dauki guda yakai bakin shi, Balaifi a hankali yake dan taunawa dan waken yana da,dadi sosai yana tauna yana tunanen Allah ya azurta shi shima ya,dinga taimakawa mahaifiyan shi da yan uwan shi, Ya danci ya kai rabi, sosai ya mikawa uwar duk da yana son karawa amma yabar mata don itama taci, saboda yasan danwake cimar tane sosai, Murmushin jin dadi uwar tayi don ganin cewa yaron nata yaci sosai duk da bawai ya damu da cin abincin makwabta bane kasafai irin hakan nan, ***** ******* ***** Washegari tunda safe, Hamza ya,shirya don zuwa gonan mai uguwan da zasu yi wanda da wanan zancen ya kwana a ranshi, Duk da ba,wani abin karyawa suka kwana dashi ba a gidan dan sauran chanjin da Umma ta bar mai a,daren jiya ya,sayi abin buda baki shine tun daren jiya ya,sayo yar kwaki da,sugar don tafiya zuwa gonan,, Kattan majiya karfine su kayi shirin zuwa gonar maigari gurin aikin gonan daga ciki Hamza ne kawai yaro karami wanda shima da daurin gindin malam mudi makwacin su ya samu shiga wanan aikin ,,, Acikin mota mai budaddan baya akwa kwashe su su ashirin da biyar zuwa gurin aikin, Ba laifi don Hamza ya kwarzanta saboda duk yadda masu karfi sukayi aiki shima bai yarda anbarshi a,baya ba, Don ya turza tukuru anyi komai dashi yadda ya kamata, Duk aikin da akai wa mai, uguwa a tare da Hamza akayi shi har tsawon sati guda, Wanan ne yasa Hamza hada dan kudin masu yawa inda ya dan ware naira dari ya,sayowa malam mudi wanda yai sanadin zuwan shi wanan aiki goro farare masu kyau ya kai mai har kofan gidan shi, Malam Mudi yayi murna sosai da wanan hikimar ta wanan yaron maraya mai albarka, Don sam bai tsanmaci cewa Hamza din zai iya jure irin wanan aikin wahalan ba , Idan anyi la,akari da yadda yaran yanzu suke masu son saukin al,amari ba masu morewa jikin su ba, Abinda Hamza ya samu a aikin gonar mai uguwa dubu daya da dari biyar ya saiwa malam mudi goro ya bawa Umma dari uku "yan kannen sa ya ba su hamsi su sayi silifas a kafan su,, Ya mayar da,sauran kudin cikin leda ya kulle tare da daurewa ya saka a,aljihun sa, Abu na farko da ya fara yi, shine biyan kudin littatafan da,suka,dakatar dashi daga zuwa makaranta,dari biyu da hamsim, Washe gari kwastsam Umma ta ga ya fito da shirin zuwa makaranta abinda yadade baiyi ba tun bayan wata uku da,suka shude,, Tausayin yaron nata ya kama ta don dama tasan cewa karatun yana a,cikin ransa rashin kudi ne kawai ya dakatar dashi,, A makarantar ma sai da kyat ya samu suka karbe shi tare da ja mai kunnen dakatar da zuwa makarantar da yakeyi, Allah mai iko Hamza yana karatu yana dan juya kudin ahi a hankali inda duk ranan kasuwan garin su zai fitar da kudin shi ya dan juya su a,wani fanin , A haka sai Allah ya sa mai albarka kudi dubu daya ya fara zama dubu biyu, uku, hudu,,, Hakan ya bashi sha,awan yin noma a dan gonan da ya rage masu na mahaifisu, Kafin ma yan uwan nasu su yarda da zancen noman nashi sai da suka ja masa rai iya son ransu, Wata gwagon shi ce ta saka baki har suka yarda da zancen noman nashi,, Noma da can baya ba noman kashin kudi bane irin na wanan lokacin yanzu wanda a da can baya sai dai mutum.ya sa karfin shi yayi noma ba wai kudi ba, Inda Allah ya kara sawa abin nasa albarka shine da Umma ta tafi kauyen ganin yan uwan ta tazo masu da iri (Seed) mai kyau irin ta mutanen kasar bauchi, Masara ce ya fara sakawa wanda Allah ya sa wa noman albarka sosai don gonar ta haihu matuka,, Duk wanda yaga gonar sai yayi magana a kan gonar saboda irin yadda masaran ta samu guri ta haihu tai goyo gwanin ban sha,awa da kyau,, Abinda ya haddasa bakin ciki ke nan ga yan uwan mahaifin nashi da suka dauki kyashin da hassada da bakin ciki suka dagwara ga iyalan dan uwan haihuwan su mai tausayin su da tallafa masu a lokacin da yake da rai, Wanda su sam badu kaunar irin wanan rayuwan sun fi son suga cewa suke da irin rufin asirin da yake dashi, a lokacin, Hassadan ganin yadda yai noma kuma noman ta karbe shi yasa su yin dana sanin bashi wanan filin ya noma a cikin sa, Don haka suke cewa wani shekara sai dai ya canza guri ba zai kara noma a,wanan gurin ba, kuma su zasu noma abin su,,, A lokacin da aka cire wanan amfanin gonan ta Hamza kusan kowa ya girgiza ganin yaro karami kamar hamza yai wanan irin noman haka mai albarka, Yan uwa wanan sabon novel din yazo a chanjin yanayi don na,sayarwa ne a kan farashin kudi kalilan naira dari uku kacal, Mai so za ta iya shiga group dina domin register akan shi, Ina fatan zaku fahinceni da kyakyawan fahinta akan wanan sabon yanayin novel din mu mai suna sarautar mata, Inda zamu yadda uwayen gida suke shan kwaram da maigida kishiya uwayen maza, dangin miji makwabta, da sauran su,,,, Allah ya nufe da, yin darasi mai amfani a cikin wanan novel din namu watau sarautar mata labarin Hamza da Aisha,,,, Kubiyoni mu kasance a tare yan uwa kada ai fushi da zee don wanan sauyin yanayi ne yakawo hakan yan uwa don,ci gaba marubuta,,,, ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU👑SARAUTAR MATA👑 0⃣2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA,, SUBBAHANALLAHI WABBI HAMMDI SUBBAHANALLAHI AZEEMUN,,,, Yau kimani sati uku ke nan da fara karatun Hamza inda ya,mayar da hankali sosai ga karatun shi don dama shi mutum ne mai sha,awan karatu, sosai, Idan yadawo da yamma yakan sayar da yan abubuwan da kobo zai shigo mai kamar su, Rake, mazzakwaila, alawa, gyada soyayya da ayya har da madaran gullusuwa,, Da zaran lokacin zuwa daukan darasin addini yayi zai bar gurin zuwa gurin daukan karatu sai dare ya,dawo yakara kasa yan kayan nashi, wanda yaran uguwa har ma da,wasu matasan shiya suke saya, A irin wanan yanayin Allah ya rufawa wanan zuria asiri suke samu suna ci suna sha daga ciki, Abin da yafara jawo hankalin mutane a gare su ke nan ganin yanzu sun rage yawan wahalan da,suke a da can baya, Saboda tasowan wanan yaron da Allah yaba Umma, Rabi mai hazaka da kwazo, Take yan surutu suka fara kewaye shiya cewa yanzu Rabi ta,samu saukin wahala,don danta da ya taso, Wanan dalilin yasa yan uwan mahaifin suka saka idanuwan su a gare su sosai, Wanda hakan yasu hango cewa hakan zai iya sa su cigaba, Don haka babu kunya wan mahaifin nasu yazo har inda Hamza yake sana,ar shi suka ya karbe duk dan kudin da yake a hannun shi yana juyawa da,sunan zai biya tsohon bashin da,aka,saura bin mahaifin su hamza din, Ba musu Hamza wanda dama ya,sayar zai koma zuwa,saro wasu ne ya mika,mai kudin, Baba Ado yana barin gurin, kasuwa ya wuce kai tsaye zuwa gurin yan namq ya sayo kan rago da sauran kayan hadi ya,sayo shinkafa ya nufi gida dasu ran shi fal da wanan ranan, Matar shi kunne har a,baka don ganin yadda yau mijin ta ya kawo masu kayan ciko mai hadi irin hakan, Ba bata lokaci tamike ta shiga gyara ta waka wa sauran matan gida cewa ita mijin ta gwaninne wajan ciyar da gidan shi,, kafin wani lokaci har dahuwa yai nisa sosai gida ya dauki kamshi ko,, ****** ********* ****** Hamza ya shigo gida hankali a tashe saboda ya,rasa inda zai nufa don ya samo dan kudin da,zai ci gaba da sana,ar shi, Wanda haka ne yasa shi samun guri yazauna yai tagumi da hannu biyu ya,shiga tunane mafita, Umma wace ta fito daga bandaki taiwanka don gudun kada magariba ya risketa babu wanka A,a Babana lafiya dai ko nagan ka a nan a,daidai lokacin da ya kamata ace kana lambu gurin sarin rake, Gyara zaman shi yayi yana kokarin ganin cewa ya danne damuwar shi kada mahaifiyar shi ta gane bacin rashi Amma abin da da mahaifi sai Umma ta nufo shi hankali a tashe tana cewa,may akayi may yafaru ne wai, Cikin dan marairaice murya yake cewa ba komai Umma kawai dai dama ina tunanen ida yanzu zan samu kudin sayen wasu kayan ne, Cikin kaguwa taje cewa kudin da kake juyawa din fa, da farko,? Murya kasa kasa duk da baiso fada mata ba yake cewa Baba Ado yazo ya karba dazun nan zai biya wasu bashi da ake bin Abban mu da dadewa, Salati Umma Rabi ta,sa tare da tafa hannayen ta tana mai cewa amma ko yaya Ado baida tausayi a duniyan nan, Yanzu don rashin imani da rashin tausayi yazo saboda mugin hali ya karbe dan kudin dake a hannun ka, Aikuwa yau bazan kyale shi ba don cin fuskan ya isa hakana ban san may suke so damu ba a duniyan nan, Duk dan abinda bawan Allah nan ya bar muna sun kwace sun barmu da wahala da talauci, Yanzu kuma don yaga Allah ya rufa muna asiri shine yazo ya tona muna, Umma da kin kyaleshi don sauke nauyin bashin da ke bin mahaufin mune ai saboda bashi baida amfani ga mamaci,, Daki ta fada tana shiri ta bambami ita kadai yana daga waje a zaune yana bata hakkuri, Cewa take yau hakkurin ya isa don idan har bata je ta tsayar da zancen ba abin zaici gabane ba zai tsaya ba, Hamza sai baki yake bata yana cewa ba komai Umma kada ki bari ku samu sabani dasu wanan ba abin damuwa bane tunda sun muna wanda yafi wanan a baya, Umma Rabi rai a bace tace yau dolene ta tafi gidan idan ma kashe ta zasuyi sai dai suyi, sai da ta daidaici kowani magidanci na gidan ya shigo gida ta shiga gidan Ba bata lokaci ta isa gidan tun a kofa take jin kamshi yana tashi ga katon tabarma an shimfida ansakawa yara abinci suna ta kwasan gara,, Da sallama a dauke ga bakinta tafada part din Baba Ado inda sauran matan gidan sai binta da kallo suke suna kyashin ta da hassadanta duk da mijinta baida rai har yanzu, Sama sama suke gaisawa da matan Baba Ado wanda suke zaune zasu soma cin abinci, Idonta ya sauka a saman abincin dake a gaban su cike cikin wani kwanon tasa mai fadi a kwanon miya ga kashin kan ragon da aka,dafa yana tashi da kamshin kayan yaji, Daidao lokacin Baba Ado ya fito daga dakin amaryan shi yana kokarin zama saman shimfidar da akai mai na cin abinci, Ina wuni tai mashi a,tsatsaye ya amsa mata kamar yadda ya ganta don yasan zancen da ya kawo ta, Zata fara magana yace cikin daga hannuwan shi da muryq da ke dakata don nasan abinda ya kawo ki gidzn nan, To dakata kiji indon kudin da na karba a hannun dn ki ne ina nima dana ne hamza din don karbi kudi a,gurin shi zaki wanko kafan ki ba kunya zaki zo min gida tambayan ba,asi, Shi yaron bai maki bayani bane a kan a binda zanyi da kudin da na karba a gurin shi, Wasu irin hawayen bakin ciki ne suka tokaro mata tace a cikin kuka Yaya Ado aika kashe mu ka huta kawai da wanan irin musugunawan da ku ke muna ni da diyan dan uwaku, Baba Ado yace oho sherin da zaki yi min ke nan lalai ba laifin kowa bane laifina,na ne da,tun farko ban sayar da gidan nan ba kinbar garin nan Hamza din da yan uwan shi su zauna a guri na, Shi yasa har kike ganin yanzu wuyar ki ya isa yanka zaki zo min har gida da cin mutunci haka, To ki jira ki gani abinda zai faru dan yadda kike ganin kina da hakki ga yaran nima ina da hakki a kanku gaba,dayan ku don haka ki jira kigani irin matakin da zan dauka bada dewanan ba, Kin ga sai kiji dadin zuwa min gida da cin mutunci da tushe don samun guri, Aikuwa sai Umma ta fusato tace cikin daga murya wallahi Yaya Ado ta Allah ba taku ba duk abinda kuke nufi damu da dan uwanku da baida rai har yanzu kuna bakin ciki da shi, Duk abinda zakuyi ya tsaya iya ni da abin dan uwan ku, Don kun sayar da komai kun ce zaku biya bashin dan uwan ku dashi, yanzu kuma dan abinda yaron nan yake samu yana dan daukan rayuwan shi dashi ka karbe da,sunan biyan bashin da bai karewa ga dan uwan naku, Cikin harzuka yace mata ke Rabi ki shiga hankaliki da ni don wallahi zanbata maki rai, Yau duk abinda zakai min Yaya,sai dai kaimin don wanan abin ya isa haka, don ban yarda abin har ya kai ga yara ba, Kudi kudi fa kamar naji kina cewa ya karba a hannun dakin ki ? Gaba daya,suka juya daga gurin da suke jin muryan baba Awal daga bayan su wanda shine marigayi mijin ta mahaifin su Hamza ke bi mawa sai mata, Ki fice min daga gida kafin na bata maki rai don baki da kunya zaki zo ki na fada,na karbi kudi hannun dan ki har nawa danki yake dashi, da zaki zo min gida, Malam kudi dai ka karba ko yace eh saboda ya,san halin dan uwan nashi Alwalu wurin rashin mutunci, Umma Rabi tace, ni dai abar cewa wai yaro shi zai biya bashin mahaifinsu wanda ya rasu tun suna kanani sosai, Yanzu kuma dan abinda yake juyawa ka karbe a hannun shi, gaba daya, Na karbe sai kije ke da danki kuyi karata shi nake jira tunda har yai kudi da zaki zo har nan ki yi min cin mutunci a kai, Ba yau ba,duk lokacin da naga wani abu a,gurin shi sai na kwace naga yadda zakiyi, Umma tace ai arziki na Allah ne mutuwa kuma tana a kan kowa, in har Allah ya nufe su da aje abu a hannun su ko kullun kake kwacewa sai sun aje, Inda mahaufinsu kuma ya tafi hanyar kowa ne kulba dade kulba jima kowa zai tafi can din ma, Jinan malam kudi dai anci su don kingan su a telle don haka sai ki koma inda kika,fito don baki da kunya har zaki shigo fadan an karbi kudi a hannun dan ki, Ta share hawaye tace eh dole nazo babu jin kunya tunda tun ranan da mahaufinsu ya kwanta dama har iya babu wanda ya taba tallafa min daga cikin ku, Don haka 'ya'ya na nasani don komai wuya su basu guduna kuko gashi duk.irin halarci da mutunci da dan uwan ku yai maku da yake da,rai duk kun manta, Wahala ai yanzu kika fara don sai kinga na dauki mataki a kanki zaki gane, Ta juya fuuu tabar gidan acikin mita da jinini tana Allah waddai da irin halin su, Tana barin gurin Awal ya juya gurin dan uwan nashi ya na mai mika hannun shi gare shi yake cewa miko min kaso na da ka,karbo a gurin yaron, Wani wawan kallo ya,aika mai yayin da yake kokarin bude kwanon miyan dake a gaban shi wanda kamshi ya daki hancin dan uwan nashi Awal, Sai da ya hade wasu miyau masu zaki yake cewa ai baka isa ka karbo abu ba ka cinye kai kadai dole ne mu rabashi tare, Ganin zai fara kai loma yasa shi azamar dauke kwanon miya anan gaddama ta gaure a tsakanin su suka fara sa,insa akan zance, Haruna wanda shine karamin su yashigo gidan ya shiga tsakanin su inda yake tir da wanan irin halin zaluncin iri nasu,, A,ranan haka Umma ta kwana da bacin rai rayuwan ta,saboda i,yanzu dangin mijin nata sun kai mata ko ina, Don haka hattakai ga fara basu martani akan irin zaluncin da suke masu,,, ****** ********** ****** Zaune take a gaban mirror tana shafe shafe fuskan ta wanda ya zama mata al,ada yin hakan yar karama da ita, Mahaifiyar ta ce ta daga labulen daga kofa tana cewa wanan kwalliya naki Kubura Allah ya,sauka dashi, Yarinya baki da,aiki sai son yin kwaliya a,rayuwan ki irin haka kamar diyar bararo,, Daga kofa taji muryan maigidan nasu yana cewa kibarta tayi ba mace bace, Ai ban hanata ba malam amma dai kwalliyan Kubura ya baci ne malam, Kai Allah yasa ga ki, Kin taba ganin inda gyara ya zama barna a rayuwan dn Adam, Hijabinta ta zura tare da dauko jakar islamiyar ta don zuwa makaranta , Sauri takeyi don gudun kar mahaifiyar nata tace sai ta tafi da wace bata kaunar jerawa da ita akoda yaushe, Daga daya daga cikin dayan dakin gidan taji murya ana cewa ke Nana, ke nana bazaki zo ki shirya zuwa islamiyan ba ko? Gani tafe mama zan kwashe shara ne na zubar da,saura a,waje, Da,sauri Kubura ta fito ddaga dakin mahaifiyanta tana gyara hijab din wuyan ta tazo kusa da yarinyar da uwar ta ta kira da Nana tace cikin kashe murya, Ke yar AGWAI indan kika fara kika bini zuwa makaranta sai nai maki mugun dukan da yafi na jiya zafi yau, Cikin dan tausa murya yarinyar karama tace nima ai bance zan biki ba,sai in mamana tace lalai sai na biki din zan biki mu tafi,, Ta juta taci gaba da kwasan tulin sharan da ke gban ta tana murza idanuwan ta, Mahaifiyar nata wace ta dade tsaye a kofan daki ta,sake labulen dakin nata, ta juya zuwa cikin dakin tana mai jin bacin rai a zuciyar ta, Fitan Kubara sai ta,wuce zuwa gurin Hamza mai rake don ta kashe yar biyar din ta da ake basu idan zasu tafi islamiya, Amma sai yau aka samu akasi babu Hamza babu sanar sa a kofan gidan nasu gurin da ya,saba kasa kayan shi na sayarwa duk yamma, A haka ta yanke shawaran shiga cikin gidan nasu don ta duba ko akwai a cikin gidan, Sallama take tundaga kofa har takai tsakiyan gidan sai dan yatsune yatsune take tana karewa gidan kallo jin motsin fitowan Umma, daga dakinta cikin daga labule yasa ta,saurin juyawa gare ta, Umma ina wuni rake za,a bani ta biyar , Allaj sarki Kubura yau ba rake sai dai zuwa gobe kila Har ta juya,sai kuma tajuya tace to aban mazzakwaila, umma tace ke Kubara kina diya mace zaki saye mazzakwaila kisha , Kul na karajin ki sayi zaki da kudin ki sai na bata maki rai, tai wani iri da fuska har zata juya tace to aban gyada ko ayya ta biyar din, Girgiza kai Umma Rabi tayi a cikin takaicin wanan irin sakaci na iyayye masu bawa diyan su kudi da sunan kashewa wai lalashi basu san cewa,suna bata tarbiyan yaran bane a haka, Daki ta shiga ta dauko mata gyada soyayya ta biyar ta mika mata, tare da mata fatan adawo lafiya don ta lura da cewa islamiya zata tafi a lokacin, Daidai zata fita a gidan ne sukayi kicibis da Hamza wanda yake dawowa daga guri da yake daukan rake , Cikin sakin fuska yake cewa a,a Hadizatul Kubura har anfito dai ke nan zuwa makarantar ko, Ta amsa a tsiwace da cewa yau ba rake ba alawa sai gyada na,samu, A daidai lokacin da ta,facce ledan gyada tafara sawa,a bakin ta tana ci, Murmushi yayi batare da,ya bata amsa ba yadan jaye mata tasa kai ta fice daga gidan, Umma Rabi wace take tsaye daga kofanta tana kallon duk abinda ke gudana a tsakanin su, ta girgiza kai tana cewa Allah ya kyauta a fili, Tun kaan ya karasa karasowa gurin ta takecewa tau ya ina fatan dai da na sara,a tafiyan, Hamza yadan bata fuska alamar ba dadi abin yake cewa Umma na,sayo na daidai dan kudin da suke a hannu naa don na kasa tambayan su cewa su bani bashi, Au dama akwai wasu kudi ke nan a gurin ka baka bawa Baban naka,ba dukka, Yace Umma,wanan din a cikin wanda a kullun nake dan tarawane don zancen karatuna idan ya taso,, Shiru Umma Rabi tayi har zuwa wani dan lokaci daga karshen tunanen ta take cewa Allah Ubangiji yasa masu albarka Allah ya tsare min ku yakare min ku daga duk wani fitinan duniya da lahira, Ameen Umma Hamza ya karba mata da sauri idan akwai abinda yake son ji a rayuwan shi shine jin kalman albarka daga bakin mahaifiyan shi, Izuwa yanzu itace kawai ta rage masu aduniya wace ta san zafin da nuna masu kauna irin ta su ma diyan sone kamar kowani da a duniya, Bazai iya mantawa ba da mutuwar mahaifinsu wanda a lokacin ba wani wayo ne dashi ba amma zai iya kawo zancen a ran shi har kullun na lokacin da mahaifin nasu ke da rayuwa, ****** ********* ****** Alhaji mohammed jega, dan asalin garin jega ne ta cikin jahar Kebbi na kasar Nigeria, Mohammed yataso a cikin gidan su shi kadai ne a gurin uwar shi Allah yai mata rasuwa amma yana da yan uwan haihuwa maza hudu da ba uwar su daya ba har ma da mata hudu, Sannu a hankali ya fara sana,ar sayar da dabbobi sai Allah yasawa abin nashi albarka, kafin wani lokaci sai harkan ta daga shi, sosai, Don haka yaiwa yan uwan shi tazara a rayuwa don shi yana da rufin asiri, yafi sauran, Wanan dalili yasa suka fara dora mai karar tsana a rayuwan shi irin ta yan uba duk da irin taimaka masun da yakeyi, Duk da ya fahince su amma bai sa shi rabuwa da yan uwan nashi ba, don a duk lokacin da yakai dabbobi kurmi yadawo kowa da irin tsaraban da zai sayo mai daga cikin su, Hakan bai hana su kawo mashi yan koken su na bukatoci kuma ya taimaka masu akai, Sun so ya auri wata yar uwar su amma sai yaki yarda da wanan hadin nasu ana cikin haka Allah ya hada shi da Umma Rabi kaunar wani abokin sana,an shi yar jahar bauchi ya aura, Wanan dalilin yasa suka dauki kiyayya suka kara dorawa akan dan uwan nasu, Allah ya azurta mohammed da diya shidda uku maza uku mata, Hamza shine babban dan shi sai zarau da jibrin, da Amina da Raukaiyat sai Aliyu, A ranan wata wata jumma,a sunyi lodin shanaye zasu kai kurmi ne suka samu hatsarin mota a wani kauyen da ake cewa , Rara anan Allah yai mai rasuwa shi da abokan sanaar shi, Gida ya cika da kuka ana ta yan koke koke ne na,wanan rashin da akayi maizafi da cin rai ne yan uwan haihuwan nashi suka fara nuna halaiyar su ta bakin ciki da hassada, a fili, Inda,su kayi tsaye kan cewa sai a fidda duk wani abin mamaci su gani da farko anzaci abin gaskiya zasu suyi sai daga baya aka fahinci zalunci ne a rasu, Don tun wurin rabon kayan suka fara fada a tsakanin su akan hular marigayin wanan yace shi zai dauka wancan yace shi ke so, Yan uwan Rabi suka hanata cewa dangin mijin nata uffan har suka kai ga cewa zasu sayar da,wasu kaddarori nasa su biya bashin da abokan ,sanar shi suke binsa dasu, Wanan aika aikan yajawowa Rabi da diyan ta shiga wani irin mugun hali na talaucin rayuwan su, Ba wanda yake taimakon su sai Allah da sauran na Allah yan gari har diyan nata suka dan tasa sukayi wayo, Da farko daga cikin su an samu wanda ya bijiro mata da zancen aure a tsakanin su amma sam.Rabi taki yarda da wanan hadin auren wahalan da suke son yi da ita, Duk da Hamza yaro ne hakan bai hana sa ya fahinci irin rayuwan ukubar da mahaifiyar ke ciki ba a kan su, Zarau nada shekara sha,uku sukai mata aure don ita ce babba daga cikin diyan gidan, Sun hada ta da,wani tsoho wanda,sukaci kudin sa don abashi ita daga karshe kuma,din suka aura mata,shi don babu yadda Umma zata yi da su, tana ji tana gani aka dauki yarta zuwa gidan wanan tsohon da ko ita bazata iya auren sa ba a matsayin mata, Hakan ne yasa Hanza kara yin zuciya ya dukufa a ranshi don yaga cewa ya shiga yafita ya taimakawa mahaiyar su gurin bukatocin su na yau da kullun , Don babu wanda ke tausaya masu akan rashin mahaifin yadan agaza masu da,wani abin, Wanda yanzu mutane sun shagala basu iya tallafawa maraya ko kadan, Abinda mutane basu sani ba shine taimakon maraya guda daya yafi mutum, ya kai miliyan masalaci yace a rabawa mutane, Haka da zaki rike kan maraya kiyi addua ki roki Allah bukatan ki ki bashi wani alhreri wanda zai sa yaji dadi har a cikin zuciyar shi insha Allahu ke kuma bukatar ki zata biya bi,izzinillahi, Zaki iya daukan sati guda kina ciyar da maraya don samun biyan bukatan ki na duniya da lahira, yar uwa, Don haka mu taimaki maraya duk inda yake mu bar sakaci da falalar da ubangiji yai muna ta hanyayoyi masu saukin aiwatar wa, Marayun wanan zamanin namu suna matukar bukatan taimakon mu ta hanyoyi da dama, Allah ubangiji ya bamu ikon kyautatawa Allahuma Ameen, ****** ********* ****** Kubura tana zaune a tsakiyan sauran yan uwanta dalibai suna daukan darasi, inda sannu a hankali yara ke ta kara taruwa a makarata, A daidai lokacin ne wata yarinya tashigo saye da wani farin hijabi tsoho kudadde yasha gyara, tasamu gefe guda dan nisa kadan da inda kubura take zaune ta zauna, Daga inda take zaune sai kokarin su hada ido da wanan yariyar da tashigo take don ta muzanta mata, amma sam yarinyar taki yarda ko ta juya inda,suke zaune ta kalle su, Sai karatunta take sannu a hankali batare da ta tsaya wasa irin na sauran yaran gurin ba, Wani yaro ne ya jefawa kubura wani abu ga hijab din ta anan fa fitina ya kaure har gurin malam din inda malam yake mata fada akan, cewa ita duk safiya sai anyi fitina da ita,ne wai, Tafe suke kowana yar wasan shi irin ta yara idan an taso daga makaranta amma banda Kubura wace hankalin ta yana gurin Rake da ta hango Hamza ya na sarawa a kofan gidan su, Idan ya,sara ya yarda kasan sai ta dauka tana sha, hakan yasa shi mata fada akan ta,daina ta wuce zuwa gida, Amma fir Kubura taki tafiya dole ya dan datsa masu kasan ya mika mata ita da dayan yarinyar da suke wasoson nakasan a tare, Har zai mayar da kai ga abinda yakeyi sai yahango wanan yariyar a tafe cikin natsuwa ba tare da ta duba inda suke ba hakan ya sashi datsa mata rake azaton shi itama tagani lokacin dayabawa sauran, Yana mika mata amma sai ta girgiza mai kai ta furta a hankali da fadar nagode, tasa kai zuwa hanyar gidan su wanda zan iya cewa ba,wani nisa a tsakani zamu iya kiran su da makwabtan juna,,, Binta yayi da kallon saboda tarbiyan yarinyar tayi mai matsala guda ce bata da gata agidan kullun ka ganta a takure take ba kamar sauran yara ba, Ihu su Kubura ne yadawo da hankalin Hamza gare su inda ya bisu da gudu suka watse kowa ya shige gidan su, Nan yaci gaba da aikin shi tare da kasa yan sauran kayayakin sanar shi wanda Umma ce ke soyawa daga cikin gida, Duk yamma yan matasan shiya da ma wasu manya na aguwa suna saye a gurin shi,, ZAINAB IDRIS MAKAWA YELWA SEENABU👑SARAUTAR MATA👑 0⃣3⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA Godiya gare ku makaranta wana novel din na,sarautar mata tare da fatan kara samun goyon bayan ku gurin bani hadin kai don ci gaban mu Idanuwanta cike da hawaye sai zance zuci takeyi saboda tarin damuwar dake tare da ita, Ganin yamma yayi tasan cewa yanzu yartan gidan zasu shigo gida saboda tasowan su daga islamiya, Fitowan ta tsakar gidan yai daidai da,shigowan yaran gidan, yar tace a gaba, tashigo da sallama dauke a bakinta, Sai kuma Kubura wace ta shigo a guje daga bayanta har tana bangaje yarinyar, Ji kayi tim a kasa tafadi har bakinta ya fashe abinda yasa uwar yin magana ke nan cikin sanyin harshe take cewa haba Kubura baki tafiya a hankali ji yadda kika buge yar uwaki har ta fasa baki, Tana tafiya take cewa nikan ba yar uwata bace wallahi,, Uwarta ce tafito daga dakinta, tana cewa wanan yarinya anyi ar nema yanzu kin ture yar uwar ki shine, baazaki tsaya ki dubata ba, A hankali ta mike yar nata tare da,bata ruwa don ta wanke fuskan ta dashi, Alokacin maigidan ya,shigo dauke da,butan roba a hannun shi yana son diiban ruwan alwala, Ke, ke ke yaya haka kina barnan ruwa haka akan yar ki, kko don baki san yadda zafin sayen ruwan yake bane, Daga kofan ta uwar gidan nashi ke cewa ayya malam wallahi wanan maraa,jin maganaan ce ta ture ta har bakinta ya fashe, Maimakon ya tausaya wa yarinyar sai wani kallon rainin haankali da,ya,watsawa uwar da yar dake tsaye daga gefen shi tana goge mata fuska, Karban mutan uwar tayi tana zuba mai ruwa a cikin buta, A cikin yanayin bacin rai suka fada daki ita da yar nata suna mai kokarin kawar da zancen a,rasan duk da bawai yau bane farkon zancen, irin haka a gidan , Saukin abin shine Allah ya hore mata yarinya mai albarka gata dai karamace amma tana iya shanye duk wani bacin rai na gidan da ake mata, Abinda yaciwa uwasr rai shine har da dan da ta haifa da cikin ta yana nuna ma yar uwan haihuwan shi tsana da kyamar jinsi, a tsakanin su,, kamar yadda sauran yan gidan ke gwada mata, Sallah tayi don gudun kada lokaci ya,shige mata bata bar gurin ba yara maza na gidan suka shigo gida sun dawo cin abincin dare, A lokacin ne ko wani yaro nagidan ya,nufi dakin mahaifiyar shi kamar yadda suka saba yi a kullun , Babban dan nata Abdul shine hankalinshi ya kai ga yar uwar shi wace ke kwance dunkule zazabi ya rufe ta a lokacin,, Ita waccan may ya,samay ta haka take kwance a lokacin nan bazata ci abinci bane yau, Yafada a daidai lokacin da yake kokarin jawo kwanon abincin shi a gaban shi, yana bude, Jin may uwar ke fada ne yasa shi dakatawa daga abinda yakeyi tana cewa Kubura ce tashigo gida a guje ta,ture ta,sai da ta,fadi har hannun taya amsa bakin ta kuma ya fashi, Shine zazabi ya buge ta haka tace bazata ci abinci ba sai anjimaa, Dayan yaro dake daga tsaye a gefen su ne yake cewa ai maganin ta ke nan wallahi , Yarinya hakka kamar yar roka,ba,dadin gani wallahi da za a mayar da ita gidan su da zai mafi min dadi wallahi, A har zuke uwar ke cewa ai, sai ka mayar da ita,din da hannuka tunda baka kaunar ganin ta a nan din, Mama fita zance shi kawai baida hankali shiyasa atake fada kuma ya kaure a tsakanin yaran wasa wasa tun uwar tana fada har abin yafi karfinta, Sai da abokan zamanta suka saka baki a zancen yaran ana cikkin hakane maigidan ya shigo gidan Tun a kofa yake cewa kao kai wai yayane may kke faruwane haka a gidan tun a waje ake jin hayaniyar ku, Nan ake mayar mai da ba,asin zancen komay yakawo hayaniyar haka, Wani irin uban tsuki yaja tare da cewa kai kai gaskiya ni wanan al,amarin ya fara kai min ko ina a gidan nan, Yarinyar nan zaman ta a gidan nan yana dagulamin lissafi a rayuwa na don dai gaskiya dole ne na dauki mataki kafin ta fara hada min kan zuria na anajin su,, Uwar gidan shi Hurera dake tsaye daga kofa take cewa haba dai malam wanan irin maganan bai dace dakai ba a,gidan nan ina,dai yanzu an wuce wanan zance dadewa , Hakan baida dadi wallahi, kadaina don shi da ai na kowane ladan ka yana a gurin Allah fa, Da kuka kamar kullun idan ana irin wanan hatsaniyan ta shige dakin ta tana mai kuka wiwi, Abinda ya sa yarinyar farkawa daga dan barcin wahalan da ya kwashe ta ke nan, a lokacin, Mamana kiyi hakkuri nice dai matsalar taki ko don Allah kiyi hakkuri kinji maman mu, Tausayin yarinyar ne ya kara kama uwar a lokaci guda take ji a rayuwan ta kamar ta mutu ta huta da,wanan irin bakin cikin dake cin ta a rai,, ****** ********* ****** A yanayin shigar ta,duk wanda ya,ganta zaiyi tuunanen cewa tana cikin nagartaccen jin dadi, Sai dai da zaran idanuwan mutum ya yi tozali da fuskanta mutum zai iya gano tarin damuwa a tare da ita , saboda yanayinta da ya dan canza a lokacin, guda, Tafe take tafiya hankalin ta a tashe sai jefi jefi take dan gaisawa da mutanen da suka santa, Wani gida ta shiga da sallama inda kai tsaye ta tun kari wani daki mai labule a,dage zaka iya hango kujerun da ke a cikin dakin daga waje kadan, Tana shiga dakin ta zube a,saman daya daga cikin kushin din dake falon yayin da matan gidan dake waje zaune a tsakar gida suka biyo bayan ta, Ganin irin yanayin da tashigo dashi dakin tasa su gaba daya yin cirko cirko a kanta, Karamar daga ciki wace itace amaryan gidan tai mata gaisuwan karfin hali ta juya inda tafito, A hankali mai dakin ta tako har zuwa saman dayan kujeran ta,zauna idanuwan ta kyam a kan yar uwar ta, Sai da tayi nazarinta na dan tsayin lokaci sannan ta dan nisa tana cewa Yau ma kunyi halin naku ko duk da,bata fada mata dalili ba tasan dai zancen daya,biyu ne, Ta nisa tare da cewa nasan dai ba da abokan zaman naki bane wanan karon ko, ? Kai ta dan girgiza kadan a cikin kukan ta tana cewa a,a sai da taci kukan ta mai isarta batare da yar uwar nata ta dakatar da ita ba, ta yi shiru don kanta Can ta sauke sanyayar ajiyar zuciya tare da dago jajayen idanuwanta tana fuskantar yar uwar haihuwan nata, wace itace silar zuwanta garin, Cikin bacin rai ta soma magana da dakusheshen murya irin ta wanda yasha kuka, gaskiya Anty ni wanan abin ya isheni tun yarinyar nan batai wayo ba har yanzu ta,soma wayo ta soma fahintar tsanar da,ake mata a gidan nan, Dago kai yar uwar nata tayi tana kallonta a cikin damuwa itama sai a cikin dakiyar zuciyar irin wanda zai karama kaunar nata kwarin gwiwa take cewa Ki natsu Fatima kiji abinda zan fada maki kisani cewa yanzu yaran ki girma,sukeyi suna ganin irin halin rayuwar da kuke ciki ke da mahaifin su, Don may bazaki karawa kanki hakkuri ba akan irin al,amarin rayuwan mijin naku, Gashi dai dake da yan uwan zama lafiya lau kuke mutum bazai ce akwai wani abuma kishi ba a tsakanin ku, Don yanzu samun abokan zama irin naki sai an tona amma ke kin kasa hakkuri akan zancen yarinya guda, Iyakar matsalar ki da kowa a gidan akan Aisha ce, Aisha kuma yarinya ce bata san komai ba, Da sauri ta,dago rananun idanuwan ta ta,saukesu ga yar uwar nata, a hankali ta,sauke ajiyan zuciya irin ta,wanda yasha kuka yagaji, Tana cewa wallahi anty yanzu yakai har yarinyar nan ta fahinci irin rayuwan da take a ciki ko, To sai may inji yar uwar nata ai sai ke ki dinga kwantar mata da hankali tare da koya mata hakkuri a cikin al,umma, Baku da rashin ci ba rashin sha balle sutura a gidan naku to may zai sa ki dauki magana guda ki saka,a zuciyar ki har ya batun maki illa a,rayuwa, Don haka ki natsu Fatima ki bawa yar ki kulawa yadda ya dace don kwana biyu diya mace ce girma zatayi idan har ta taso tagan ki a cikin irin wanan yanayin zaki jefata a wani haline,, Ta kara dago idanuwanta,a karo na,barkatai tana cewa, ni dai kawai gara na,tura wanan yarinyar can gida na huta yafi min, Wani irin dan gajeren murmushi yaruwar na ta,ta,sauke a lokaci guda tana cewa ai da kin gwanmace zaman ta a hakan da zuwa ta can din dakike tunane, Ni dai har kullun shawaran da,zanbaki shine kiyi hakkuri don idan da rayuwa,komai na,duniya mai wucewa ne , Sannu a hankali tafara kokarin tsayar da kukan da takeyi tana mai sauraren yar uwar nata Cikin daurewa takara cewa wallahi Anty na,rasa irin wanan mugun kiyayyan da,ake gwada,wa yarinyar nan ace har da diyan cikin ka,suna kyamar yar uwar su, Tau ni dai hakkuri zan baki tun da bai iya bude baki yace yarinyar tabar mashi gida ba iyakar shi dai nuna mata halin ba yar shi bace ita,, Don haka da zaki bi shawarana kawai dashi da yaran duk ki basar da fitinan su gareta, ki koya wa yar ki hakkuri shi ke nan, Kada ki kara,sanya zancen a ranki ki rungumi addua ki tayi Allah zai kawo saukin al,amarin insha Allahu, Daga haka su ka,dan yi shiru na,wani lokaci kowa da irin abjnda yake tunane a ransa, Anty tamike tafita can sai gata dauke da goran kunun ayya sai wani kula mai rikon zafi mai nuna abincine acikin sa, Dago kai Fatima tayi tana cewa da kibar abincin nan don bazan iya cin komai ba, Batace uffan ba ta aje kulan da,goran a gaban ta ta juya zuwa waje ta bar mata dakin, Fitar yar uwar nata a,dakin shi yayi daidai da kwanciyan Fatima saman doguwar kujeran dake dakin, Tana dan sauke ajiyan zuciya a kai akai daga haka barci ya sace ta mai dan nauyi don ta kwana da bacin rai batai barci ba, Zuwa wani lokacin Anty tana daga waje jin shirun Fatima yasa ta fahintar cewa tayi barci ke nan a lokacin, Daga waje abokiyar zaman Anty Saude ke tambayan ta da cewa halan Fatima barci takeyi naji shiru, Anty tace kyale yar rigima ta dauki damuwar duniya ta saka a rayuwanta kan zancen Aisha, Bayan idan tai hakkuri watarana zancen mai wuce wa ne ga rayuwan kowa, gashi mijin ga naki bai kasa da komai naku ba bare kuma kishiyoyin ki da kuke zaman ku na,arziki da su, May zai sa ki kasa hakkuri da abinda ake gwada mata din ai m,sunyi hakkuri da suka rike ta hakan a cikin su, Duk tabi ta ramay tasawa kan ta damuwa da tunanen banza tankar wace bata da ci da sha a tare da ita, Sai wajajen yamma bayan la,asar kadan Anty ta tayar da ita daga barcin da takeyi don ta,taahi tayi sallah, Tana cewa,ki tashi hakana kiyi sallah ki tafi gida don nasan yanzu mijin ki nace yana sintirin tambayan baki dawo ba, Ta mike tare da yar tatausan salati a nakin ta tana mai kallon yar uwar nata, sai a lokacin ta dan saki gajeran murmushi tana cewa, ashe nai barci ne haka ban shina ba, Dan haratan wasa yar ta,jefa mata tana cewa ai duk kika kwaso fitinan ki idan kinyi barcin kina,samun sauki nagani, Ta mike zaune tana murmushi ta nufi bandaki ta gabatar da alwala ta sallaci sallah a take, Bayan idar da,sallah tana zaune tana,addua Anty Saude ta kara shigowa dakin karo na barkatai don daukan abu , Sai tajuya inda Fatima take a zaune ta addua take cewa abinci fa ? Girgiza kai Fatiman tayi alaman ba zata ci ba a koshe take , Fatima ki ci abinci awanki nawa da,shigowa gidan nan zaki ce wai a koshe kike hakan ya kara bata daman samun kujera ta zauna tana cewa Wallahi Fatima ki cire damuwa akan wanan zancen a rayuwan ki ke ko fada bakiyi wa kanki dubi irin yadda uwargidan ku take kokari a kula da zancen Aisha a gidan , Gaba dayan Su sai kiban su suke narkawa hankalinsu a kwance basu saka komai a ran su ba, Dan dariyan yake Fatima ta,sake tare da dan gyara zaman ta tana cewa akwai bambanci sosai Anty tsakanin ni dasu a gidan nan, Cikin mamaki Anty ke kallonta tana cewa may kike ganin sun fiki dashi a gidan Tamike daga inda take zaune tana cewa adai bar zancen kawai don tone tone baida amfani, Lokacin da take kokarin gyara hijjab din take cewa ita yaya watau uwargidan su take nufi ban da ma raina a kan ta don gaskiya duk yadda,babba ke daukan girman shi tana dauka don abinta duk bai wuce mu da yaran mu, Amma ita kan Hannatu na ciki ai yanq ciki ne tsakanin ni da ita kawai ana dai wayyayya ne kawai, Ganin tana shirin tafiya yasa yar uwar nata cewa bari na zuba maki kunun a leda ki kaiwa yara ko tace ai da ki barshi kawai zai fi nake gani, Har kofa fita gidan yar uwar nata tare da,abokiyar zamanta,suka kaita suna kokarin bata baki akan tayi hakkuri ta kawar da idon ta a kan komai tankar bata gani ba ko ji akan duk abinda wani zaiwa Aisha agidan babba ko yaro, Tana dan share kwallah fuskan ta habar hijjab din ta tare da yi masu godiya sosai ta fita zuwa gida,, ****** ********* ****** Alhamdullahi iyanzu Hamza harkan kasuwan shi ya budu mashi don yana yan sana,o,in shi sai sambarka, Yanzu yana dan kimani shekara goma sha tara zuwa da ashirin ne, amma gashi ya iya,sana,oi kala kala, na rufin asiri, Don Allah ya,tarfawa garinsa nono saboda yabzu yana daga cikin matasan da ake kwatance dasu musanman a uguwar nasu, Don indai harka ce ta neman kudi yana daga cikin masu zafin neman tashi suyi aikin karfi don su samu na kan su, Hakan ce tasa iyanzu sun rage yawan talaucin da,sukayi a,baya don yanzu koda yaushe suna dan girka,abinci sabanin da can baya, da zasu kwana su wuni ba,a girka ba, Har takai yanzu yadan kafa yar rumfa mai rufi a kofar gidan su inda yake sana,ar tashi, Matasan Uguwa suna,dan taruw,a,bakin shagon Hamza yaro ga irin sunan da,suke mai lakani dashi, Tsakanin shi da Kubura yanzu soyayya ta kullu inda gidajen biyu zumutar su ya kara kullun duk da dai dama ana hurda a tsakanin su, ****** ********* ****** KUBURA iyanzu ta girma don ta zama babban budurwa kyawon ta yana haskawa a gari ga shi taa iya gyara, da kwalliya irin na yan matan zamani Sai dai duk irin wayewanta bata da lokacin tsayawa ta taimakawa iyayyen ta, Sai dai akwaita,da,kokarin zuwa buki ko yawon gidan abokai da sauran su, Tun mutane basu sani ba har suka fara saka mata idanuwa suna fahintar irin rayuwan ta, dama yanzu haka,duniya take, Kafin jama,an gida,su ganne halin dan yau jama,an unguwa har su gane mai yaro ka ke ciki ko,, Tana zaune kofan mahaifiyar ta tana gyaran kumbar kafanta a hankali daga inda take a zaune, tana iya hango duk wanda ke shige da fice a gidan, A haka ne yaron makwabtan su ya shigo gidan da,sallama yana dauke da wata bakar leda a hannun shi gari yai zafi, Inda Kubura take zaune ya,nufa yana mika maya ledan tare da cewa inji Hamza yaro yace na kawo, A tsiwance ta karbi ledan tana dan wani yatsuni fuskan ta kamar wata babban mace, Beridi ne da,Awara sai karas da lemo daganin tsaraban da alaman cewa ya yadawo daga cin kasuwan wani kauye ne, Yaron ya dan tsaya ta,dago kai a fusace tana cewa to may kuma ka tsaya jira dan gulma ya juya simi simi yafita yana hade yawun abinda ya gani a ledan ana fitar wa, Ke yar AGWAI miko min tasan can na,saka abu a ciki daga inda take tsaye tana yan aikace aikacen ta tajuya inda suke kife kwanonin abincin su ta dauko mata,tasan da take nufi, Tamika mata tawani fisga kamar mai fada ita dai ta juya tana wani ya mutsaa fuska kamar maijin warin ta, Ita dai ta juya zuwa inda take yan tsabgoginta taci gaba da aikin ta hankaali kwance, Tsab taciye abubuwan ta batare da taiwa kowa tayi ba,sai uwarta data danyi wa tayi ta,tura mata dan kadan Ke yar AGWAI zoki dauke kwanon nan daga nan ki mikomin ruwa nasha, Daga daki muryan Fatima ce ke cewa a cikin kakausar murya tana cewa Ke Aisha aje kwanon nan kibar gurin nan, Iyyeh inji Kubura take cewa kuma dai, Aisha ta,aje kwanon tsab tabar gurin kamar yadda mahaifiyar ta umurce ta dayi, Daga daki Fatima taci gaba dacewa ai ba bauta tazo yi a gidan ba, Lalai to ita waye bawan ta kuma dahar za,a nuna min hassada yanzu a fili, Ke Kubura inji Hannatu mahaifiyar ta tace rashi kirkin naki har yakai ga iyayyen ki kuma, Cikin da guna guni take céwa nikan aida uwata ce bazatai ,,,, Pap taji an mangare ta daga bayan ta abinda ya hanata karasa zancen datake son fadi ke nan Nan tafara dan yin zance cikin kuka kuka tana hi a ciki ciki, Kai amma gaskiya Kubura baki kyauta ba don dai yarinyar nan ta na iya kokarin ta a gidan nan, A cikin ku wake irin abinda Aisha take muna a gidan nan, Atika ce dayar kishiyar uwar su Kubura ke wanan zancen daga inda take Tun,daga kofa yake jin muryoyin su abinda ya sashi hanzarin shigowa gidan ke nan don jin ba,asi, Wai mah ke faruwa ne haka inda Kubura tana ganin mahaifin nata takara dan kaimin kukwn nata, Shiru sukayi gaba dayan su babu mai ce mai uffan daga cikin su, Kara tambaya yayi a karo na biyu don son jin ba,asin zancen, Fatima ce daga dakinta inda take zaune tana fama da laulayin sabon shigan cikin dake gare ta wanda yazo mata da futina kalakala Nan ta mayar mai da abin da ya kawo zancen da ya samu anayi, Juyawa yayi a cikin dakiya yake cewa Ohho hakane to mukuma ashe bayin ta, Ashe ko idan kin ce hakan saidai wanan yarinyar tabar min gida don ban yarda akanta ko da yaushe ana, batawa yarana rayuwa haka, Haba malam inji matar tashi wanan zancen bai kamace kaba gaskiya akan wanan magana zakace haka, To ai sai ki koya min yadda zanyi a gidana yace mata a harzuke cikin masifa, Take itama Fatiman tahau zuciya daga daki tana cewa ai sai ta koma din don nima wanan gorin ya,isheni haka kullun zance guda akan yarinya guda nima nagaji wallahi, Amma ta tsaya kowa yadebo sgaran shi yana watsa mata bazan dauka ba yanzu, Acikin kuka irin mai tsima rai take fidda zancen ta tare da tausayi yarinyar nata a ranta, Ganin yadda Fatima yau ta dake ta harzuka akan yarta yashi yin shiru don yasan cewa zata iyayin komai yaudin, Maman Kubura ke cewa Fatima don Allah abar zancen nan haka ya isa don Allah, ban son abin da baikai yakawo ba,adinga ta da jijiyoyin wuya akai, Fita yayi don bai son zance yakara nisa kodon halin da Fatima din ke ciki na wahalar shigan cikin dake gare ta, Gurin da Kubura take tsaye ido mirsisi tana sauraren badakalar da akeyi a gidan a kanta uwar ta juya, Tace yanzu aikinji dadi tunda kin haddasa abinda kike so wallahi Kubura kiwa kanki fada hakana, ****** ********** ****** Ruwan sama yafado don haka duk maza sun koma gona don har da,rago yana dan zuwa gona, Hakan yajawo yanzu Hamza bai zama cikin shagon shi saboda akoda yaushe yana zuwa gona aiki, Kubura wace rashi shagon shi da bai bude kowani lokaci yajawo mata goslow din kwadayin ta, Har yakai sun dan fara samun matsa saboda yawan aikowan da take cewa yabata kudi zata sayi abu kaza , Uwar shi Umma Rabi taimashi fur akancewa duk ta kara jin cewa ya bata kudi rqnan sai ta bata mashi rai, Hakan yasa yazo koda zai aika kirantq sai tace ace mai bata gida ko tana wani abin, Gashi mahaifinta yafi kowa jin dadin wanan hafin nasu don yasan Hamza bazakarin yaro ne zata dan more miji anan saboda yana da sanar yi, Sannu a hankali tafara hira da,wasu samarin tun Hamza yana ji har takai ya fara gani da idanuwan shi, Abinda yai matukar tayar mashi da hankali ke nan don haka ya matsawa mahaifiyan shi a kan ta tafi tayi zancen don ai masu matsaya da ita, Umma Rabi batai kasa a gwiwa ba ta tafi tasamu malam mudi makwacin su wanda shine kuma mahaifin Kubura din akan zancen yaran nasu, Malam mudi yace duk da ba itace ya dace tazo zancen auren yaron nata ba amma ta koma zance yana nan insha Allahu ba zai tayar ba don yayi alkawarin haka, Shi tun farko yana da,sha,awan so hada zuria da Hamza din saboda hazakar shi, Umma tai maganan cewa zata gurin yan ywan mahaifin Hamza din duk da su yarda su amma akan sha,anin aure aidole a tuntube su suji don sune manema auren diyan ta, dole Abinda yasa Hamza yakara mayar da hankali ke nan sisai ga gonar shi don yaga cewa yayi kyau har ya samu abinda koda zancen auren shi ya taso yana da abinshu ga hannun shi, Ita ko Fatima masifan cikin da tasamu yanzu yasa ta koma wata mara lakka don haka a yanzu Aisha ce take mata duk wani laluran gida kamar wata babban ma e don komai ta iya saboda training din data samu ga mahaifiyar ta din, Ba mahaifiyarta ba kawai harma da sauran abokan zamanta Aisha tana kama masu aiyukan su ranan aikin ta da ita za,a gama komai, Wanan yakara,sa ta,samun wani tsana da tsangwama daga mutanen gidan da ake mata, Novel dina a zaman Amana yake a gare ku don haka wace tafitar min tunda kunce banja Allah ya isa ba dole tunda kun saya zaku fitar nabar mutum da Allah, kawai, A hada mutum da darajan Annabin rahama baiyi ba ai sai kabarshi tsakanin shi da Allah duk wace ta,fitar ita da Allah,, ZAINAB MAKAWA YELWA SEENABU,,,👑SARAUTAR MATA👑 0⃣4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA WALLAHU GALIBUN WALLAMM,RIHI,,, Zaune take tana faman shafe shafe a jikin ta saaiu kuma wakan da takeyi a hankali na wata zabaya, Agogon bangon dake dakin mahaifiyar ta ta,daga kai ta dan duba abinda, yasata saurin mikewa ke nan, Wani riga mai ruwan light chuckulet ta jawo yar hannun shi kamar ta shimi , Jikin rigar duk yabi lafiyan jikin ta ya,shafe mata,shi tsab, sai turaren da ta dan kara murzawa a,parts din jikin ta, Wani katon hijjab di ta ta dauko ta,saka daga sama sai ka rantse shigar arzikine a jikin ta, A kitchen ta hango mahaifiyar ta tana kwasan tuwon abincin dare da ta girka, Aisha tana daga tsaye a gefen ta tana kwasa zuwa gurin da,suke aje abinci daga waje, Muryan KUBURA ce ya daki kunnuwan su daga inda take zaune tana cewa mama zan dan fita sai nadawo, Dakatar da kwasan tuwon datakeyi tayi tana mai juyowa inda yar nata take tsaye, Ina zaki da yamman nan haka Kubura don dai yau ba ranan islamiya bace, Cikin dan inda inda take cewa mama ina son nashiga nan gidan su Hamza na gaida Umma Rabi, Dadi mama Saude taji jin cewa yar ta tayi hankalin shiga gaida sarakuwar ta, A cikin washe baki take cewa ki gayar min da ita kice muna gaida yaran gidan, Fat tafice da sauri gudun kada mama tace ga sako takaiwa Umma Rabi din abinda yasa ta cin karo da mahaifinta malam Mudi ke nan wanda ke kokarin shigowa gidan a lokacin, Cikin washe baki yana binta da kallon mamaki don jin yadda ta ke kamshin turare yace Gwagon Baba yau sai ina hakan ga,? A ,a Baba nan zan shiga gaida Umma Rabi na fito yanzu yadan jaye mata daga gefe kadan don ta,samu full hanyar da zata fita daga zauren gidan nashi, Kubura tana fita wajen gidan su tasha wani kwana inda zai sada ta da wani titin mota haka, Tun daga nesa ta hango motan da take tsan manin gani inda ta usa da sauri don gudun kada wani ya ganta ya sheda ta, Tana,bude motan ta shiga taji na cikin motan ya sauke a jiyan zuciya yana cewa ai na zaci bazaki ffito bane don har na debe rai ga fitowan ki yau, Tace cikin dan yin wani har da idanuwanta kaima ai kasan cewa dole ne na fito don alkawari ne, Hijjab din jikin ta yadan duba yana cewa ya haka kuma, ? Yadan nuna hijjab din yana cewa wanan abin nake nufi fa, Sai a lokacin ta sa hannun ta tayene katon hijjab din dake a jikin nata, Woow yace tare da dan fito yana cewa beautiful wanan irin haduwa haka baby, Daga haka ya harba mota suka nausa wani uguwa can mai nisa dda nasu uguwar,, Buki ake a gurin yan mata matasa da samari ne an saka kida sai tashi yake , Shigowan shi da Kubura yasa gurin ya dauki wani irin shewa da sowa a lokaci guda nan aka saka wani sabon kida wanda ya ruda samarin da yan matan dake gurin suka,shiga, wani rausayawa, ****** ********* ****** Gani har magriba ya soma yasa mama saude tura Aisha gidan Umma Rabi don ra kira Aisha, Duk da dadin hakan takeji don yar ta tafara sabawa da matar da zata zama,sarakkuwar ta nan gaba kadan, Aisha tajawo wani tsohon hijjab din ta tasaka a jikin ta zuwa gurin aiken da akai mata, Sam in ba,dole ba bata kaunar fita waje a wanan lokacin don sanin cewa iwar haka kofan gidan nasu aa cike yake fam da matasan shiya,dake zama a kofan shagon Hamza yaro don hira Tafe take a natse kamar kullun yayin da abinda ta sani cewa sai anyi shi ake kan yin shi Don idanuwan matasan gurin duk caa a kanta kowa na kallon ta, Kanta a duke a kasa take tafiya tana zuwa gab dasu duk da matasa ne amma sai da tace masu ina,wunin ku, Wasu suka karba,wasu kuma suka kyale suna ci gaba da hiran su, Tun batai nisa ba taji muryan salisu yana cewa wai ita wanan yarinyar bata da gatane a gidan nan ko,? Naga ko da yaushe kuca kuca zaka ganta gwanin ban tausayi da ita, Sani yace yarinyar dai babu ruwanta wallahi naga ita sam bata damu da kowa ba ashiyan nan, Nafiu yace yar fulanin gidan malam mudi ko ma may suke ce mata farat Audi dake daga gefen su yace Yar AGWAI, Yarinyar kamar a taba takare saboda rama haka aiko taci sunan ta wallahi, Kai na,rabaka irin matan nan masu kama da a kara su sunfi kowa zama manyan mata idan sun girma,don kiba suke sosai, A hakan inji Sani yake nuna inda Aisha tabi da signal don su gane, Sai suka tuntsire da dariya ga baki dayan su sai Hamzane dake ta cikin shagon shi yana mikawa wani abinda yazo saya yake ce masu, Kai haba hakan ba girman ku bane ai ina laifin yarinyar na har fa gaishe ku tayi amma duk bata tsira daga sherin ku ba, sai kun zubar da girman ku da take gani, haba hakan bai yi ba wallahi, Cikin wasa dayan daya fara magana yake cewa ku bari fa kunsan cewa yar gidan su eehhe din shi ce don kada ace a shagon Hamza yaro ake zagin gidan sarakan shi, Bai iya ce masu uffan ba sai dan daga kai da yayi yana kallon yar yalalon yarinyar da,sukewa zari rana shiga gidan su, Nan ya gane cewa a gidan sune ma zata shiga abokan hiran shi suke matc a sheri haka, Allah ya shirya ku yace yaci gaba da aikin shi don yasan ba,bari zasuyi ba, Da,sallama ta shiga gidan Umma Rabi din tare da ganin tana shara duk da saura kadan amma,sai da Aisha ta karba ta kara mata ta kwashe , Ganin ba alamar Kubura a gidan yasa Aisha jan bakinta ta tsuke tai shiru abinta, Tana gama zubar da shara daidai Umma tana fitowa daga daki take cewa Umma ni zan tafi, A,a Aisha har zaki tafi ke nan ai ina ce zaki tsaya ne don yau ba karatu ai, Tace aa Umma dama na shigone na gaida ke da wuni an aikeni ne sayar kalanzir nashigo nan, Kai aiko na gode kwarai Allah yai maki albarka gashi harda shara na,samu anyi min ai nagode sam barka, Shigar Aisha gida takecewa mama saude na fada mata tana tafe na samu tana taya Umma aikine, Dadi sosai ya shiga ran mama saude ganin yar ta yanzu ta fara sanin ya kamata a rayuwa, Sai dai gaban ta,sai faduwa yake don gudu kasa asirin karyan da tayi ya tonu,, ****** ********* ****** Dakin mahaifiyarta ta,shiga tanq kokarin cire hijjab a wuyan ta,sai dai idanuwanta suna a kan mahaifiyar nata, Wace ayanzu tausayi take bata ganin irin yadda take wahala akan cikin dake a jikin ta a lokacin, Sannu Ummi Aisha tacewa uwar tare da dan kashe da idanuwa a cikin tausayawa take cewa Ko na shimfida maki tabarma a,waje zaifi iska acan din, Ki barshi don nan din ma yayi ai inji Fatima dake cije bakinta don wahalan nauyin cikin dake a jikin ta, Tace mama kije asibiti ma ko da sau daya ne don su dan baki magani su duba ki, Aisha ke nan tace a cikin dan sake murmushi danawa zanje asibiti adubani, Kedai bari Aallah da ya bani wanan cikin shi tasan yadda zaiyi dani insha Allah, Gurin dan kantan da kayan ta,suke yarinyar ta nufa ita kam Fatima sai taci gaba da dan fitaran da ttake da mafefecin kaba daje a hannun ta, Muryan uwar taji tana cewa halan baki samu Kubura a gidan Uwar Hamza ba, Tadan juyo daga gurfanen datake tana tonon kayan ta tace a hankali bata gidan, May kika fadawa uwar ta to tace nace tana tafe aiki take taya Umma din a gidan, Yadaifi maki ga sherin Kubura don bake ba har ni uwar ki yau sai tai muna zari ina fama da kaina, Kudine tafito dasu daga cikin kayan ta tazo gaban uwar tana kara gyara shirya su da kyau, Da sauri take cewa ina kika fito da wanan kudi haka Aisha,? Umma wallahi kudina ne danake tarawa dama nace idan kin haihu sai na baki ki yi hidimar suna dasu, Kudin ki a ina kika samau su ka take tambayan diyar nata acikin tashin hankali, Ummi kudin break fast dinane da Baba ke bamu bani kashewa ina tarawa sai kuma kudin da mama Rahana ta bani idan naje gashe ta, Wanan kuma,wasu sabbin kudi masu dan yawa zasuka dari uku tace na barka da sallah nane na boye, Murmushi uwar tasake tace haba Aisha may kike ci a makaranta idan kin tafi, Mama idan munsha koko a gida sai sauran tuwon da ake gyara muna shi nake ci har na dawo gida, Rai uwar ta bata taje cewa gaskiya ban yarda kina zama da yunwa ba haka, Idan wani ciwo ya kamaki fa na yunwa ya kike son nayi gashi ban da kudi ni, Wazai kaiki asibiti kindai san wanan Baban naku bazai damu da ciwon ki ba, Murmushi Aisha tayi tanacewa insha Allahu mama zan dan dinga kashewa tana mikewa tsaye bayan ta hada kudin ta mikawa uwar nata take cewa, Ai Ummi ban iya cin abinci a makaranta sai naga kamar kowa ni yake kallo idan ina ci, Dariya ta sa uwar nata tace kai kedai Aisha bafillatan gaskiya ce wallahi, Juyowa tayi tace wa uwar wai da gaske Ummi ni bafillata ce dama kamar yadda ake ce min din, Take ran uwar ya baci ta tsuke fuska da sauri Aisha ta juya don ita ma zance subul da baka yazo mata, Kiyi hakkuri don Allah Ummi idan na bata maki rai ne bazan sake ba, Yusuf dan Fatima na farko shine ya,shigo dakin da,sallama jikin shi yana saye da kayan aikin kanikawan da yakeyi, Idanuwan shi a kan kudin da suke aje a gaban mahaifiyar tasu yace Ummi wanan kudin fa haka ? Kai ko gaisuwa baka iya ba har yanzu babangida kasancewa sunan mahaifin mijin su ke ga yaron, Ummi ya jiki yace cikin dan zaunawa daga gefen ta yana kokarin ciro dan kunshin naman da ya sayo mata da kudin da,aka,sallamay shi a gurin aiki na yinin ranan, Ta karba tare da,sawa dan nata albarka inda tai masu jam,in gaba dayan su da kuma sauran diyan musulmai baki daya kamar yadda sunna ya koyar akan kyakyawan adduan don ta karbu da sauri a gurin Allah, Tana kokarin bude takardan naman ne take cewa yar uwar kace tabani su yanzu wai naje asibiti gobe a dubani don wahalan yai min yawa, Inda Aisha take tana mayar da kayan ta ga jakar ta, Ina ta samay su haka ita kuma ? Fatima tacee nima ai tambayan da nai mata ke nan yanzu haka, Sai uwar take fada mai bayanin da Aisha din tai mata akan kudin, Kudin yaron ya kara dubawa yake cewa ai wanan basu isheki ba bari na,dauko wanda nake tarawa nasayi keke dashi, A,a Babangida kabar shi kawai naje da,wanan din ai zai isheni sayan kati, dashi, Shima gurin kayan shi ya nufa ya ciro nashi kudin ya kirga ya mika mata ta raba kudin biyu Ta mayar mai da,saura tana mai sawa yaran albarka , Tace wa Aisha ta miko mata plate tasawa kishiyoyin ta dan naman da,yaron ya sayo mata taci, Haba mama dan wanan abin shine zaki raba ke may zakici a ciki abinda baida yawa, Bari dai na basu ai suma suna bamu idan sun samu, Haka al,adan gidan nasu yake duk wanda yadan samu abu komai zaman shi kasan sai yabawa sauran abokan zama sun sa albarka su ma, Hakane yaje dan kara kawo masu zaman lafiya a gidan don suna kokari ganin sun danne kishin su, Daga waje aka daga labulen dakin maigidan ne a tsaye yana,saye da wando sai babban riga da ya aza a sama kawai babu yar ciki, Lokaci daya ya kare masu kallon yana mamakin irin yadda ko yaushe take zama da diyan ta kamar abokan ta , Ya kika kara jin jikin naki ? Ya tambaye ta a cikin yanayin son kulawa gare ta , Ta amsa a cikin dan matse fuska iri yadda mace maiciki idan tana da kishiya take amsawa, Daga gurin da Aisha take, zaune gefen uwar take cewa Baba sannu da,dawowa, A,dakile ya ansa mata batare da,wani sakin fuska ba , Daga gefe Yusuf ke ce mai Baba sannu da,dawowa, A,a Babangida andawo yaya shagon naku ba matsalan komai ko ? Yaron yadan gyara,yana cewa ba komai Baba kuma,muna,samun aiki sosai a gurin, Tau ka,dai mayar da hankali ga,aikin ka,don ka,samu ka iya,abinda ya kai ka, Yana kokarin sake labulen dakin ne Fatima ke cewa malam, Gobe idan Allah ya kaimu ina son zuwa asibiti awo , Awo Fati gaskiya ban da kudin zuwa asibiti don kinga yanzu ba,wani Kasuwa sosai karfin hali kawai nake ina maneji, Kabar kudin ka izzinin ka kawai nake nema ni, Yace Allah ya kaimu gobe lafiya yajuya yafita daga dakin , Summa suka bishi da kallo kowa da irin abinda yake kiyastawa a ran shi daga,cikin su,,, ****** ********* ****** A cikin wata irin kasalaliyar murya mai nuna yanayin shi ya canza yake magana a lookacin, Haba baby ki bari mu dan kara time mana tun yanzu zaki ce zaki wuce gida ni da na zaci cewa zamuyi till down ne a gurin party, Cikin bude baki a cikin sauri take cewa Haba sweetie na baka son na kara fitowa ne yau din ma fa,dabara nayi a gida don ba,ranan zuwa islamiya bane, Badon yaso ba yaja motan zuwa wani shago inda yai mata sayayyan abubuwan tabaa alashe , A hankali yake jan motan kamar wanda nai son yin tuki, Hannun shi guda ya mika zuwa jikin ta inda ya dan fara shafan ta Da sauri ta dago kai tana cewa haba sweetie kabari mana don Allah kaga kana tuki ne fa, Au to na tsayar da tukin ke nan ko ya ce a cikin wata irin murya irin na mayaudaran maza, Ganin yana son yai galaba a kanta yasa Kubura sauri dan ture shi daga jikin ta tana cewa haba dear ban son haka gaskiya kaga wani yana iya ganin mu a hakan a fadawa mahaifana, Fushi yayi yanu baiji dadin hakan ba da tai mashi, Har suka kawo gurin da ya,dauke ta ya tsayar da motar a gurin, Sai a lokacin ya furzar da iskan takaici daga bakin shi yace a kasalance sai yaushe kuma ke nan baby na, ? Tace a lokacin da take kokarin bude motar ta,sako kafan ta daya daga waje, Tace sai wani lokacin tamikaa,hannun ta tajawo hijjab din ta daga bayann motan shi ta zumbula abinta kamar wata ustaziya, Tajuyo inda yake zaune yana akallon ta acikin wani yanayi tace zan tafi sai mun kara haduwa kuma, Nan ta bude motar tafita zuciyar ta fes dashi don ta hada abubuwa da dama, Ta samu saurayi kamar mansur gashi kuma sunje gun fati ,sun cashe kamar yadda take so, gakuma kayan kwadai da,ak,siya mata, A daidai shiga daga cikin gida suka hade da mahaifinta wanda yabita da kallo yana cewa Gwagona sai yanzu akadawo ne ko, Murmushi tayi daga can ta,cikin gida muryan mahaifiyarta ce ke cewa ai na tura Aishi ta,kirata tadawo tana cewa ai tasamu tana that's Uwar Hamza aiki shiyasa bata,dawo ba tun dazun, Sosai yaji dadi hakan inda yake saka mata albarka ta,shige ciki simi simi da ita, Bayan tashiga mahaifiyar ta take tambayan ta mutanen gidaan take cewa duk suna lafiya, Tafaki idon uwar nata ta kwabe kayan jikinta don gudun kada tafahinci irin kaya da ta, fita dasu Shi, Hamza wanda yake zaune daga shagon shi ya hango dawowan Kubura a lokacin, Cikin mamakin inda tafito a wanan lokacin da daren nan haka, Bayan yan mintina ya aika kiranta sai ta aiko mashi da cewa a gajiye take bazata fito ba, Sam ya rasa may yasa Kuburan ta canza mai yanzu don kwata kwata, bata da lokacin shi, Abu gudane idan ya aika mata da abin makulasa zata karba ta lashe ko kuma idan tana son wani abin kwadayi zata iya aiko mashi, da bukatun ta, Abin ya fara damun shi a,rayuwa saboda ya fara dan tuhumar ta,don ganin iri sauyin rayuwan dake tare da ita, Saboda ta waye irin wayen da baza,a ce diyar gidan malam mudi bace ita, Shidai yasan ada can baya bata da wani suturu irin haka amma yanzu ta zama wata yar gayu gaba daya, Gashi ta nuna a fili cewa ita yanzu tafi karffn shi don bata da lokacin shi samm, Ya tunkari Umma Rabi da zancen abinda ke damun shi a rai indz take cewa ita ma ta gane wanan sauyi ga KUBURA din, Uwar shi tafi kowa bukatan akan aiyi wanan hadin tsakanin yan gidan mala. Don haka ta,samu mahaifan Hamza ta turasu zuwa zancen don a,tsayar masu da,matsaya, Kamar yadda malam Mudi yayi alkawari hakan akayi don anyi baiko a tsakkanim su kowa ya sheda cewa Kubura ta a matsayin kamay Hamza ne a garri,, Wanan baikon shi ya tayarwa Kubura da hankali sosai inda har ta kasa boye bacin ranta ta ,soma nunawa a fili wai bata son Hamza yanzu, A gareta abin kunyane a ce kamarr ta wai zata auri Hamza dan gidan tallakawa talas, Marasa galihu agari da gurin dagi tallakawa masu neman abinda zasu ci wa ran su a rana, Ganin tanuna bata so ita kuma mama Saude yanzu irin abin duniya da yar nata ke shigo dasu gida yafara bude mata idanuwan ta, Don haka tafara goyawa yar ta baya akan bata son wanan hadin itama don yanzu Kubura ba matar Hamza bace, Kubar ba matar tallaka bace kalman da mama saude take yawan fada ke nan a tsakar gida a gaban su Fatima da Atika kishiyoyin ta, Shiko malam Mudi ya dage akan cewa sai anyi wanan auren ko basu so Don shi haka kawai Allah ya,dora mai son wanan yaron Hamza a ranshi don irin kwazon shi,,, Don Allah muyi hakkuri da,wanan ba yawa sai mun hadu a na gaba da fatan za,a rike min amanata kamar kullu na gode da taimakon ku a gareni,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU👑SARAUTAR MATA👑 0⃣5⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA RABBIG GAFIRLI WAL WALIDAYYA WAHARHAMHU KAMA RABBA YANIY SAGEERAH 👏👏 Tun daqon Ummin ta daga asibiti hankalin Aisha yake a tashe don jin irin bayanin da Fatima take wa maigidan ta, Akan cewa da likita yayi wai sai tayi scanning a cikin don tantance lafitan baby saboda suna ganin kamar a gilmay cikin yake mata, Don inhar tunanen su gaskiya ne to bazata iya haihuwa da kanta ba kenan sai sun mata aiki, Gaba daya yarinyar duk da karancin shekarunta ta,fahinci may hakan yake nufi ga zancen, Sulale jiki tayi daga gidan zuwa gidan mama Rahana yar maahaifiyar nata, tafiya take a cikin tashin hankali bata ko ganin gaban ta, Ta isa gidan acikin tashin hankali don Mama Rahana tana ganin ta take cewa lafiya dai nagan ki a haka kuka ? Dakin ta tafada tazube a kasa gefen kujera ta fara rusa kuka a hankali, Abinda yai matukar tayarwa mama Rahana da hankali ke nan, Acikin dan daga murya take cewa ki daina wanan kukan ki fada min may ke faruwa ne wai ? Ki natsu kifada min kukan may kike haka wai, Aisha bata boye mata komai ba take fada mata irin abin da taji Ummin ta tana fadawa maigidan ta akan zancen cikin dake a jikin ta,, Shiru Mama Rahana tayi, inda ta dago kai tana kallon Aishan acikin tausayawa,, Tace cikin sanyi murya tauki daina wanan kukan haka don idan har kin tayar da hankalin ki Ummin ki zata kara shiga tashin hankali ne sosai, Don kinga kowa da irin tashi kaddaran rayuwa, wanan ba,wani zancen tayar da hankali bane don su likitocin ai sun san irin dabara da zasuyi mata, Kuma ta haife shi lafiya da yardan Allah don haka maza ki share hawayen ki ki shiga yi mata addua, Allah ya sauke ta lafiya, A hankali taji sanyin maganan da mama Rahana tai mata don haka tafara dan share hawayen dake a fuskan ta da habar hijab din ta, Nan mama Rahana tashiga kwantarwa da Aisha hankali da kawo mata yan musalai daidai fahintar ta, Batai wani dadewa ba tai sallama da mama Rahana inda mama Rahanan take ce mata zata shigo gidan taji yadda za,ayi zancen zuwa asibitin, ****** ********** ****** Daida shiga gidajen su ta hango Hamza dake dawowa daga gona yana dauke da buhu da wasu, yan kayayyaki, Da sauri ta nufi gurinshi ta karbi dan kullin buhun dake a hannun shi, Duk da kokarin hana yarinyar da yayi amma,sai daa ta karba Tana shiga gidan ta samu Umma Rabi tana wanke wanken kwanonin abincin su , Sallaman ta yasa Umma Rabi din saurin dago kanta tana kallon Aisha din, A,a kece ? Karaso mana Kofan dakin Umma Rabi tanufa ta aje buhun dake a hannun nata, Taso ta karbi aikin amma,sai taga cewa har ta karasa din saura kadan shi kuma take daurayewa, Ta gaida Umma din ta juya ta fita a kofan shigowa suka hade da HAMZA yana kokarin aje yar keken shi a gefen ginan daki, Yace tau Ai na gode kin ji da ki tsaya na baki akwai sauran rake yana nan a,daki, Cikin murmushi wanda yadan sa dimple din ta dan lotsawa kadan tace haba kabar shi kawai na gode bata tsaya ba tafita ta nufi gidan su, Shigowan ta gida yai daidai da Uwar nata ta,dan fito waje, tun a kofa ta kafe yarinyar da idanuwa don son fahintar wani abu daga idanuwan ta,, Hawaye ne suka kara ciko mata a idanuwan ta Fatima ta kawar da kanta tankar bata gan ta ba, Ina kika shige ne haka wai Aisha ? Idanun yarinyar taga sunyi dan hulu hulu alamar kuka da tayi sun baiyyana a fuskan ta kadan, ina kika shiga nace hakan, A hankali tace gidan mama Rahana na tafi amma ban dade ba acan, Ki shiga ki dauko abincin ki a daki kici kada yai sanyi da yawa , Har zata shiga dakin take cewa Mama tace tana tafe dan anjima, ****** ********* ****** Yana fitowa daga daki dauke da yar ledar gyada soyayya a hannun shi don ya bata sai yaga bata gurin ta tafi ko, Umma tace ai ta tafi bazata karba ba indai Ai ce narasa gane irin rayuwar yarinyar nan don bata da sabo, Hamza dake kokarin zamma a kasa cikin turbanya yace rayuwan ta daban ne dana,sauran yaran gidan duk da kuwa a cikin su ta tashi amma sam bata irin halaiyan yaran, Dan jingina jikin shi yayi da,bango yayin da,Umma tazo ta shige ta gaban shi zuwa cikin dakin ta, Tafito dauke da kwanon abinci wanda ta dafa masu shimkafa da wake da mai da yaji, acikin sa, Tace a lokacin da take zama, daga kofan ta, ai ni ina,son hali irin na,yaro wandda yasan darajan kashi tun yana katami ammaa kaga ita,ta gurin nan naka sai munyi daga da ita sosai a gidan nan, Murmushi yayi don jin dadin furucin ta a akan cewa KUBURA ta gurin shi ce, Umma ai duk yanzu kurciya ne bari zatayi nan gaba ai, Uhummm Allah dai ya kyauta dan nan amma gaskiya babana yarinyar nan al,amarin ta ya fara bani tsoro, Hamza yadan lumshe idanuwan shi a hankali tare tare da dan tunanen wasu abubuwa a,ranshi, Mama Rahana kamar yadda tai alkawari ta shigon gurin yar uwar nata don ji daga,bakin ta, Cikin daga hankali Fatima take bawa yar uwar ta bayanin da likita yai mata a kan cikin ta da take dauke dashi wanda,ake zargin ya,samu matsala, Mama Rahana tace Allah ya sauwa ka yanzu ki kwantar da hankalinki sai muje wani asibitin muji may zasu ce a akkai,, Don haka ki kwantar da hankali kin ga hankalin Aisha duk a tashe yake tana zaton wani abu, Ta amsa a hanakali da cewa tau, yaya insha Allah zan bar komai a gurin Allah tace dadai yafi maki, ****** ********* ****** Zaune KUBURA take a saman gadon mahaifiyar ta tana karatun wanni littafin hausa mai sunna wayasan gobe wallafan wata shahararra marubuciyar littafin hausa SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA, Yar gurin Atika ce ta shigo dakin tana cewa Kubura Hamza yana waje wai na kiraki, Tadago kai fuska a,yatsune take cewa yana ina ? Yarinyar ta amsa mata da cewa yana daga kofan gidan nan, Jeki ce mai ban samun fitowa tace, cikin jan yar guntuwar tsoki,, Yarinyar ta juya ta,fita jim kadan sai gata ta,dawo tace wai yace nace kizo don Allah sako ne zai baki kawai, Ai sai tai wani hargago yarinyar da wani irin daga murya inda tai wuf ta,fice daga dakin, A zaure suka hadu da malam Mudi yake cewa kin fada mata yaron yana waje, ko, Yarinyar ta take mayar mai da cewa, ai takoreni da ihu wai na bata guri na bace mata da gani, A harzuke ya shiga cikin gidan tare da kwadawa Kubura kira cikin tashin hankkali, Ita ma din dai a gigice ta fito daga dakin tana cewa na,am Baba, Ba,a fada maki cewa yaron nan Hamza yana kofa yana jiran ki ba,, Ciciki ta amsa da an fada min Malam Mudi ya ce to sai kika shanya shiko, Shiru tayi yace zaki wuce ki fata, tun ranki bai baci ba yanzu, Daki ta koma inda ta saka kuka wai ita bazata fita ba gurin Hamza din, Mama Saude wace shigowan ta ke nan daga bandaki, ta soma cewa ke may yafarune wai may akai maki, Tace ba Baba bane yake son takura min cewa wai sai na tafi gurin Hamza a waje, Ni wallahi mama banyin wanan hadin da Baba ke son yi min nidai na fadi wallahi bazan yi ba Bari na fita na gayawa Hamza din daga yau kadda ya kara zuwa gurina da sunan wai yana sona, Haka ta saka hijjab din ta zuwa gurin da Hamza din yake zaune saman dan dakalin da ke kofan gidan, Hamza yana zaune yana dan bubuga kafan shi a kasa a hankali saboda irin yadda yake dan ji a ranshi, Tafito fuuu da ita tana cewa kai wake ne ma Hamza ne ko wa, Da maki yadago kai yana kallon ta don jin abinda tace mai, Yadan murmusa tare da dan dago kan shi ya dan kalleta yace tau fa yau kuma sunana ma baki sani ba Kubura, Hamza din dai nake ba wani ba Ranki shi dade barka da fitowa Tana tsaye kerere a gaban sa tace ai ba fitowan arziki nayi ba tace a zuci, Idan da sabo yaci a ce hamza din ya saba i yanzu don haka din yanzu shine halaiyar ta gare shi, Sam bata kallon shi da dara bata nuna mai wani almar kauna ko kadan, Sam duk wanan abin da takeyi sai ya dan saka Hamza dan murmushi, Don yasan cewa dama can a rashin ji ta tashi daga kurciyar ta, Don haka yasan cewa wanan irin halaiyar nata idan sunyi aure duk daina su zata yi, Don haka hankalin shi a kwance yake don ya riga da ya nasa a ranshi cewa zai mata, tarbiya irin wanda shima mahaifiyar shi tai masu, Fuska a daure tace malam nazone naji lafiyan kirana da kakeyi wai, Yace ba ko gaisuwa Khadija, tace gaisuwa a nawa za,a yita ,? Hmmm Khadija da ki gaishe ni da kada ki gaisheni duk daya a gareni , Don watarana muna tare dake a daki daya don haka kinga bazan damu da gaisuwan a yanzu ba, Ta dago idanuwanta ta re da kara tabe fuskanta ta dube shi tace cikin wata murya , Au dama kazo ne ka karanta min wanan, Idan har wanan ya kawo ka zan koma daga ciki don ina da abinyi aciki, Mikewa yayi daga gurin da yake a zaune da farko yace dama zuwa nayi naga lafiyar amarya ta kawai kuma na gani tunda kina lafiya Alhamdullahi zaki iya shigewa, ai, Ta dan gyara tsayuwar ta tace kana so yin wasa dani Hamza, To tsaya kaji idan ma har mafarki kake to ka farka don ni, Nafi karfin dan talkawa irin ka,wallahi kaje can ka,nemi daidai da kai zaifi maka alheri, Don idan har kai rigimar kai kan ka idan ba kaiba ka zata kwabewa, Don ni KUBURA nafi karfi dan tallaka iri ka don tsayawa dakai a,gareni barnan suna ne sosai, So dan Allah malam daga yau ka da ka kara zuwa kofan gidan nan da sunan wai kazo gurina, Dubeka kalle ni kasan ai sawun rakumi yafi karfin na yaro Gyara tsayuwar shi yayi dakayau ya,dan tako kadan yana cewa Koma dai mai zaki fada don ni nasan cewa duk zaki daina ne wata ran, Dan harara ta,watsa mai tana cewa dubeka ji wai a hakan kake nufin cewa na aure ka din, Kai kan ka,ka,dubeni sama da kasa kasan nafi karfin ka wallahi, Idan zaka tafi naiman daidai dakai tallaka irin ka tun dare bai maka ba zai fi maka alheri,, Tankar a mafarki yau Hamza ke jin irin wanan mugun kalaman daga yarinyar da ya,dade ya reno da dan taro da,sisi shi, Ya murmusa tare da dan tokare habar shi da hannayen shi yace Kubura ki iya bakin ki da zaifi maki alheri ina gani, Ta ja,wani dogon tsuki tare da kara watsa mai harara tana cewa idan ban iya ba ai sai kai ka iya ko, Daga haka ta juya ta,shige warta cikin gida inda ta barshi nan inda yake a tsaye har nawani dan lokaci yana mamakin irin fitsaran Kubura, Wanda bai taba tsanmanin cewa har abin yakai haka ba a rayuwan ta, Mamaki ya hanashi ko da dagawa nan da can wai yau Kuburace take fada mai magana irin haka, Sam ta ma manta da irin mutunci da zumuncin dake tsakanin gidajen su biyun, Sannu a hankali jiki ba karfi ya juya zuwa bakin shagon sa bai wani dadeba a ranan ya kwashe kayan shi zuwa cikin gida, Bai iya,fadawa Umma wanan labarin va don sanin da yayi bazata iya hakkurewa wanan cin mutuncin da Kubura tai mashi yau, ,A dakin shi ma yana kwance muryan ta ne ke mashi yawo a kunnuwan shi yana mamakin yadda ta rufe idanuwanta tai mai wanan cin mutunci, ****** ********** ****** Likita,yayi mata duk wani awo da zaiyi don ya fahinci kan cikin, Bayan ya gwaje gwajen da likita yai matane ya rubuta result din duban ya masu bayani cewa zasu dan bata magani amma sai bayan sati biyu zata dawo yagani, Idan still abinyana on briged dole hakkuri zakiyi muyi mamaki tiyata, mu fitar da dan, Sun dawo gida inda sun samu Aisha ta,gyara ko ina na dakin ta,saka ka kamahi, Ga abincin su data, aje masu ta sai ruwa masu sanyi da ta kawo masu, Ganin Aisha a,daki ya hana su yin zance don kara ta kara tayar da Ahankalinta irin na farko, Ba yawa yau muyi maneji da shi haka please nagode ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑SARAUTAR MATA👑 0⃣6⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA RABBI INNI, LI MA ANZALTA ILAYYA MIN KHAIYRIN FAQIR,,,,👏👏 Asalamu Alaikum yan uwa musulmai, ina son in kara maku tuni akan cewa duk wace bata biya ba don Allah kada ta katanta don gudun shiga hakkin wasu, Wanan littafin Amana ce a tsakani na da wanda ya,biya ya shiga group, Duk wanda ke acikin group na hada shi da darajan Allah da Annabi kada maishi ya fitar min da novel ga out siders, don darajan Annabin rahama, Don haka wace duk tasan darajan Allah da Annabi idan har bata biya ba kada ta karanta wanan novel don Amana ce mai karafi, akai,, karshe dai kenan ba a yafe ma wace tafitar ba haka kuma ba a yafewa wanda ke turawa ba, har yakai ga wanda bai biya hakki ba,,, Tun Faruwan wanan al,amarin Hamza ya dauke kafan shi daga zuwa gurin Kubura da sunan hira, Sai dai hakan bai hana shi aika masu da alherin da ya,saba aika masu a koda yaushe , Yanzu lokacin aikin gona ne hankan yasa shi kara mayar da hankalin shi zuwa gonan shi , Wanda yai sanadiya mutane basu fahinci irin halin da Hamza da Kubura suke ciki ba, Abu guda ne ke ci mashi rayuwa wanda ya kasa fitar da zancen a ranshi, Da Kubura take ce mai wai shi dan matsiyata yan tara tara masu jiran na rabbana su saka a,bakin su,,, Idan ya tuna yakan dan lumshe idanuwan shi yace Allah ka,bamu karka bashe mu ya Allah, Aike sosai Hamza kewa Kubura kuma tana karbe abinta, Idan ma bai kai ba mahaifiyar ta ce ke aikowa da kanta cewa suna bukatan abu kaza, Wasu lokuta Atika ta kan so suyi gulma da Fatima akan abinda ke gudana a gidan, Amma sai Fatima ta jayewa zance badon komai ba sai ganin cewa Uwargidan tasu bata bar su da komai ba a gurin kyautatawan rayuwan zaman takewan su a tare, Shi kan shi mai gidan bai zama a gari anytime yana zuwa gona ko gurin wasu tsabgogin shi hakan yasa bai fahinci da akwai matsala a tsakanin su ba, ****** ********* ****** Alhamdullahi yanzu jikin Ummi yayi kyau sosai ta samu lafiya, don ta,watsake daga irin ramar da tayi a baya, Duk da akwai abinci a gidan malam Mudi din amma tana,bukatan irin wanda zai gina mata jikine sosai, Don haka Yusuf danta ya dage gurin dan sayo mata dan lemo kankana ayaba da,kwai ko ba yawa yakan dan sayo mata,subata a boye taci, Inda ita kuma Aisha take bata kyakyawan kulawa yadda ya dace, Da yake yanzu anyi hutu hakan yasa bata aikin komai sai Aisha din ce mai yin aiyukan uwar tasu, Yau ma kamar kullun daga inda Fatima take zaune take kallon yadda kayan su ya taru suna bukatan wanki, Daga gurin takira,Aisha wace ke waje suna aikin girki da mama Saude, Ta shigo dakin don jin bukatar uwar nata, tace cikin dan murda baki, ki daga pillow din can akwai ashiri a cikin shi ki sayo omo ki dan wanke min wanan tsumakaran da nake daurawa , Aisha ta nufi guri, pillow sai dai ba taga komai ba a gurin duk iya duban ta babu komai a gurin, Ummi ban gashi ba fa Aisha ce ke fadawa uwar tasu haka a lokacin da ta duba ko ina bata gan sh ba a gurin pillow, Ajiyan zuciya uwar tayi tana cewa bari Nasir ya dawo don shi ya,tafi gurin wai yana neman karfen keken shi, Aisha ta juya zuwa waje tabar uwar a zaune a inda ta samay ta da farkon shigowar ta, Hijjab din ta,dake a saman window din dakin su taja zuwa kofar gida, Zuciyar ta fam da tunane yadda zatayi indan ta fita, har ta fara tunanen ta juya kawai don bata ga alaman mutum a,ahagon ba ma, Sai tajiya a yan mata lafita,dai ko ? Kinzo kuma zaki koma mana, Dan murmushi ta kakaro a fuskanta tana cewa a,a dama nazo kuma dai a barshi kawai, May kike so ya tambaya in a serious voice ? Bata san lokacin da tace omo zanyi wanki ne idan Yusuf ya dawo zan karbo kudin na kawo ma tafada idanuwan ta a kasa, Batare da yai magana ba ya juya zuwa cikin shagon omo sabulun wanki sabulun wanka har da man shafi kaman yasa mansu ya kare Baba kuma bai sayo ba tukun, Ya miko mata yana cewa kice wa Ummi abar kudin baku nayi tasaka min albarka, Cikin yar murya tace mun gode yaya Hamza kalman da tai mashi dadi ke nan a,rai don ko kannen shi basu kiran shi da yaya, Ko da ta,shiga gida ta samu Ummi tayi barci a lokacin don haka,sai kawai takwashi kayan wankin zuwa bakin rijiya ta,soma wanki abinta, Sai zuwa gab da ta karasa wankin ne Ummi ta farka daga barcin da ta,samu tayi, Inda ta hagon kayan ta a,shanye ko ina na gidan cikin mamaki take kallon aikin yar nata, Shigowan Aisha dakin don aje wasu kayan da suka fara bushewa take tambayan ta ida ta samo omon da tai wanki dashi, Aisha bata boye mata komai inda a take Ummi tai cikin ta da, fada kancewa ta rufa mata asiri kada Kubura da uwar ta suji suce ai ba yau suka fara zuwa karban abu a gurin shi ba Hakkuri Aishsn tabawa uwar ta akan cewa bazata karaba insha Allahu, ****** ********** ****** KUBURA yanzu sai abinda yai gaba sosai don idanuwan ta ya kara budewa,sosai, Ta murje tayi wani irin kyau da ita,saboda duk masu zuwa gurin ta suna da dan abin hannun su, Kamar yadda take bukatan ganin rayuwan ta zaka ganta tana ciye ciye da taune taunen chewing gun, a bakinta, Yau ma sallama ake da Kubura din a kofan gida inda yaron da yazo yake cewa wani mai mota yace a sallamo mai Kubura, Dama tana daki tana sauraren kida a,dan wani rediyon ta tadan gyara fuskan ta tafito zuwa gun da ake ne manta a,wajen, Munsur ne yadawo daga gurin tafiyan da ya tafi kwatano gurin sayen motoci, Tana fitowa Hamza yana a bakin shagon shi tare da abokan hiran shi, idanuwan su fam a kofan gidan, Zaune mansur din yake kafan shi daya yana daga waje yana duban wasu takardu a cikin motar, Tun daga nesa ta,washe masa baki bata damu da duk wani wanda yake a gurin ba don yanzu ta bushe fitillan ta akan bata son Hamza din, Mansur yafito daga cikin mota shima yana washe baki saboda farin cikin ganin masoyiyar tashi, Yana cewa, Khadijatul Kubura my baby kinko ga yadda nai missing din ki kuwa ? Wani murmushi tayi tana dan gyara gyalen da ta yafa a kanta, Cikin yar siririyar murya take mashi sannu da zuwa tare sa wani yi mai far da idanuwan ta, Yace mata ya take tana lafiya dai ko,? Tace kallau acikin wani tsigar jan hankalin maza cikin kashe murya take cewa ka tafi ka barni zakace wai ina lafiya ? Murmushi Mansur din yayi yana,mai ce mata ashe tare zamu dinga zuwa ke nan next ta wani zaro idanuwan ta tana cewa wace ni Yace oright kina ce ina wasa ne ko, Yanzu dai ga tsaraban ki nan nakawo maki sai ki samu yara su shiga maki dasu gida, Ledoji ne farare manya guda uku abarba lemo Apple da,sauran su irin tsaraban yan kurmi, Daga inda su Hamza suke a tsaye suna kallon su wasun su harda dage sukeyi don su gani da kyau, Hamza dai yana tsaye daga bakin shagin shi a cikin dakiyar zuciya kamar ya kurma ihu don bakin ciki, Yace zai koma ta duka gab dashi sina magana kamar masu yin kiss abinda ya kara tayar wa Hamza da hankali kenan Yaga bazai iya karasa kallon wanan cin fuskan ba ya,shige dan rubaben shagon shi ya zauna, rayuwan shi a bace, Daga haka sukayi bankwana da Mansur bayan sun gama,aje magana akan yadda zasu hadu da dare, Yara ta samu suka kwashe mata kayan zuwa cikin gida su,, Kannin Hamza da akai komai a gaban idanuwan shi da zancen da su abokan Hamza din keyi ya,shige gida kaf ya zaiyana wa mahaifiyar su kamai tiryan tiryan, Rayuwan Umma Rabi yai matukar baci inda ta hau fada da bambamin cewa ana cin amqnan dan ta da son yaudaran shi, Tasha alwashin idan yamma yayi zata ahiga gidan gurin mahaifiyar Kubura ta,fada mata don su tsawata mata, in ma har basu sani bane, ****** ********* ****** Da yamma malam Mudi ya dawo daga kasuwa kauye da ya tafi ci don haka a gajiye yadawo gida, Bai wani tsaya ba don lokacin sallah magriba da ya gaba to yai haraman zuwa sallah, Acan ya samu wani ya fada mai cewa idan fa bai saka ido ga zancen Kubura ba zata saka shi a kunya, Tiryan tiryan mutumin ke fada wa Malam Mudi duk irin abinda ya sani akan kubura din, Umma Rabi tashigo gidan a cikin mutunci inda tai arraba da Kubura a zaune saman kushin din uwarta tana cin apple , Arayuwan Umma Rabi tace tabbass haka zancen yake ashe ba karya bane, Don haka tafara zuwa gurin su Atika da Fatima suka gaisa tadan kara jajantawa ummi din da jikin ta, Acan dakin mahaifitan Kubura wace ta samu zaune a kasa saman salaya ga kanyan marmari nan tana kasawa da alaman abokan zamanta zata aikawa, dashi,, Suna gaisawa mama Saude tai wani hade rai tun anan Umma Rabi ta fahici da akwai magana, Dan shiru ya biyo baya a dakin sai can Umma Rabi tace ummm, dama gurin ki nazo Saude tace to ai gani a gatsale, Umma Rabi tace dama a kan zancen yaran nan ne shine nazo na fada maki cewa ya kamata ace kin tsawata wa Kubura don baidace ace tana kula wasu samarin ba haka, bayan tana da matsaya a kan ta, Jin tai shiru yasa Mama Saude dagowa tana cewa kin gama tace eh, dama abinda ya kawoni ke nan kawai, don Allah ai mata fada Saude, kin san halin kurciya, Ban gane tana kula wasu samarin ba da kikace, ? Ta dan gyara zama tace eh mana bai dace ace kuma tana tsayawa hira da maza a kofan gidan nan da rana tsaka kuma a gaban Hamza din, Shi Hamza din an daura mata aure ne dashi ko kuwa wai ? Dakata Malama bazan tauyewa diyata incin taba na hanata cin kurciyan ta akan wani dan ki can, Yarinyata,Allura cikin ruwa ce mai rabo ka dauka don haka sai kije idan dan ki yana iya shiga cikin takaran mane ma,sai ya,shiga in har rabon shi ce sai ayi dashi O lalai k8ce min duk abinda Kubura takeyi da,sanin ki takeyin shi ashe ? Kwarai kuwa sukaji muryan malam mudi wanda ya shigo gida rai a bace shima yazo da zancen da aka fada mai a,massalaci don yayi bincike sai gashi yaji da kunnuwan shi abinda Mama Saude din take fada, da bakin ta, Nan akafara musayar harshe akan zancen tsakani Baba Mudi da mama Saude mahaifiyar Kubura, Umma Rabi ta bargidan a cikin bacin rai da mamaki uwa kamar Saude ace wai ta zabawa yarta abinda ranta ke so, Har takai kofa take jin malam Mudi yana cewa koda,Kubura zata mutu ne sai ya aura mata Hamza , Ita kuma mama Saude tace wallahi yar ta bazata yi aure gidan wahala,ba, Ita a wahalce yarta a wahalce wazai kama wani a cikin su, Wanan zancen yai matukar tayar wa Umma Rabi da hankali sosai, inda,ta bar gida duk da Atika na mata sai da,safe,, ****** ********* ****** Wanan zancen wasa wasa ya fara karfi a tsakanin mama Saude da baba Mudi, Amma duk wanan fitinan bai sa jikin Kubura rai sanyi ba akan fitinan iyayyen nata, Don ita sam yanzu yadda idon ta ya bude bata jin zata iya auren Hamza, don baiyi mata ba, Bai daga cikin tsarin irin mazajen da take so ko sha,awan mallaka, Don haka ta sha,alwashi a ranta cewa bazata taba yarda da zancen auren Hamzan da mahaifinta ke son ya tursasa mata ba, Wanan fitinan yasa gaba daya gidan ya koma ba,wani armashi don duk mutannen gidan suna a cikin damuwan wanan futinan da,akeyi, Magana wasa wasa har ta kai ga magabantan su sunzo an zauna dasu akan zance baba ya kafe akan sai ya aura mata Hamza,din, Yanzu duk inda Kubura zata fita an kafa mata,dokar cewa dole sai da,daya daga cikin yaran gidan a tare da ita, Sanin da tayi cewa yaran Atika zasu iya fadan duk wani abinda sukaga tayi yasa ta yanke cewa ta dinga fita da Aisha kawai don tasan idan tace kada ta fada bazata fada din ba, Don haka yau taiwa baban karyan cewa suna son zuwa gidan Anty Sadiya babban yarta da suke daki daya, Baba yake tambayan ta ko da,zata fita take cewa da yar AGWAI zata fita, dan shiru yayi sai kuma yace kada su dade a can din yafita, Tunda zasu fita Fatima taiwa yar ta fadan cewa ta iya kanta kuma ta kama bakinta ga duk abinda ta gani don karshen ta akanta laifi zai dawo idan har tazo tafadi wani zance akan Kubura din, Aisha tace wa mahaifiyar ta tau insha Allahu Ummi bazan kasance mai hadin hasumi ba,,, Wasu yan kodadun kayan ta ta,saka ta sukafita duk da ita Kubura bato ace tafita da mai irin wanan shigar ba, Dole ba yadda ta iya,dole suka,fita a hankan don shine rufin asirin ta, Sai da tajata zuwa inda zasu hadu da Mansur din ta inda suna a cikin mota a zaune har suka gama abinda suke tafuto suka nufi gidan Anty Sadiyan su, Ko a gidan yar uwar tasu Aisha bata zauna a daki ba daga waje ta,dawi tadan zauna tana jiran su, Bayan fitowan su zasu tafigidane Anty Sadiya ta rako su take cewa , Shikam baba may yasa wai ya nace a kan zancen wanqn Hamzan da ya matsa haka ne wai, Ai yanzu shi kamshi Hamza din yasan cewa kin wuce ajin sa, Ya dauki yar AGwai ya bashi mana don itace daidai da wanan din, saboda yar talauci ce kamar shi, Sai suka saka dariya har da tafawa a,tsakanin su kamar wasu kawaye can, Daga, can gurin da take tsaye dan nisa kadan dasu tana iya jiyo hiran nasu da irin zagin da,suke wa mahaifin nasu cewa ya tara gida da mata da yara ana ta,wahala, Har suka dawo kan zagin mahaifiyar ta da cewa wai taga guri harda daukan ciki yanzu mai ga cikin nan yana,wahal da ita babu mai taimakon ta, Sai da,sukayi gulman su suka gaji sannan sukayi sallama da ita, Kubura tace ke dallah tashi mu tafi kinji kin zama,wa mutun kamar wata,sojan gona, Aisha da take sauraren su ta,sauke doguwar ajiyar zuciya taiwa sadiya sai anjima suka kama hanya, gida, ****** ********** ****** Hamza kan iyanzu ya kusa kammala karatun shi na diploma da yake yi, inda kuma yake ta har kokin shi, Zance kubura dashi ya lafa don an dakatar da zancen baba ne dai yasha alwashi cewa sai yai mata auren nan komai abinta, Wajen goma sha dayan dare kowa ya,samu mafaka ya kwanta suna barci a dakin Mahaifiyar ta taji kamar ana kiran sunan ta a marki, A hankali ta fara bude idanuwanta inda take jin muryan Ummi a cikin wani irin yanayi tana ce mata ta miko mata kujera daga waje, Ba shiri Aisha tamike ta cire sakatan dakin da,sauri tafita sai gadmta dauke da kauwar kujerar zama, Nan ta dire wa Ummi kujerar a gaban ta, tajuya a cikin kuka,sai da uwar ta daka mata tsawa akan kada ta tara mata mutanr fa, Dole Aisha tai shiru daga karshe dataga bazata iya sauraran halin da Ummi take ciki, don haka tafito zuwa wahe ita kadai a,tsakar gida tadan rakube a gefe guda, Sai zuwa can taji kukan jariri zubur Aisha tamike ta shiga dakin a cikin dan rudewa, Sai sannu takewa mahaifiyar tata dakuma kojatin kallon yaron dake yashe a kasa yana tsala ihu kamar mai shedawa duniya ya iso, Ummi may zan taimaka maki dashi yanzu nune tai mata da hannu data dauko reza da zannuwa a gurin da ta boye su, Da sauri Aisha ta nufi gurin dukawar ta taji uwar na,wani sabon nishi cikin rashi kuzari, Don Allah Ummi kada k8 mutu ki barni Aisha taje fadi daga gurin da take, Yar jaririyar ta guda ce ta karkare fadowa duniya sai wani kuka take tsalawa sosai, Fatima ta umurci Aisha da ta tafi gurin mama saude ta sheda nata ta haihu, Yan mintin suka shigo dakin a tare" da mama Saude da Atika nan aka shigamaram barka da, arziki tare da kammala duk wani abinda haihuwa ta kumsa, Kafin wani lokaci sun yi komai duk sun gyara gidan yadda ya kamat, Ranan Aisha batayi barci ba don farin ciki da takeyi ganin cewa, Allahya sauki mahaifiyar ta lafiya yau, Washegari gida ya tashi da murna da farin cikin ganin sun sami karuwa, Sai yan uwa da,abokan arziki suka fara tururuwan shigowa yin barkan haihuwa, Tun wanan lokacin Aisha tazama wata busy girl bata da lokacin kanta ko kadan, A cikin wanan haline kuma ta fara tsanan tawa Aisha tare da takurawa rayuwanta dana ta urin aikace aikacen don ta koma kamar wata basaraka a gidan , Saboda mahaufiyar ta tana goyon bayan ta akan zancen ta,sosai yanzu haka yasa kowa a gidan bai shiga shirgita, Sai dagwa dagwa suke da ita don a samu a rabu lafiya kawai, Aisha tana,dakin su tana gyara wa uwar ta daki Kubura ta kwada mata kira wai tazo ta kwashi wankin ta,tai mata, Daga inda Ummi take zaune tallabe da yar diyar ta ta cewa Aisha akull nafa k8n tafi gurin wankin nan sai na bata maki rai yau a gidan nan, Shiru shiru Aisha bata futo ba daga dakin yasaka Kubura zuwa ta,wani hankada masu kofan dakin tana cewa Wai Aisha bake ce nake kira ki kwashi wanki ki min ba zaki wani shige daki ki kyale ni, Tau sannu mara kunya diyar sarkin santal bul bazata wanke maki ba ke aiki may kike da bazaki wanke abinki ba, Au tace cikin jefawa Ummi din wani kallon rashin kunya ashe kece kika hanata ke nan fitowa, Ummi tace eh don ko na isa da ita to idan ba,a,son tai wani abu a gidan ta koma gidan ubanta mana, Da,sauri Ummi ta dago kai tana karewa Kubura din kallo acikin mamaki, Juyawa Kubura din tayi tana mai tafita tana sake mugun magana kan cewa aikuwa sun kulla agidan nan da Ummi da yarta don sai tabar mata gudan uban su,,,, 👑SARAUTAR MATA👑 0⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA RABBI LA TADHARNI FARDAN WA ANTA KHAYR AL-WARITHIN,,, YA UBANGINA KADA KA BARNI MAKADAICIN ALHALIN KUWA KAINE MAFI ALHERIN MASU ALHERI,,, Ranan haka muka wuni zugun zugun a gidan ba wani dadi rai alhalin tun bayan daurin aure bamu ga baba a gidan, Ba wani bukin da akeyi kamar yadda mutane sukayi zaton yi don uwar mai buki bata da shirin buki, Sai dai yan uwan baba sun dan taka rawa gurin ganin cewa, sun hada dan kudi sunyiwa mutanen dake nan dahuwar dafa dukar shikafa, Ummi suna daki da yar uwar ta acikin jimamay abinda zai fito daga gurin mutanen da,suka kira da yan uwa na wai iyayyena, Mutanen da,sam basu damu dani ba a matsayin yar su, Don ni da farko ma nayi zaton cewa ko banda ubane don ganin irin yadda ake tsangwama min a,gidan Baba Mudi mijin uwata, Alhalin gashi shine uban yayena da kuma kanne na Ni kadai ce Allah bai nufa nafito daga tsatson shi ba, Sanadiyar fitar da mama tayi a gidan bayan haihuwan yaya Audi, Na fara fahintar hakan ne don ganin irin tarin damuwar da mahaifiyata take shiga a kaina a gidan, Nayi zaton cewa Baba shine mahaifina amma saboda irin bakin cikinnda yake yawan cusa wa mahaifiyata dani agidan yasa na soma fahinta cewa bashine mahaifina ba tun ina karama, Abu na biyu shine irin yadda Baba ya dauki son duniya ya,dora a kan yan dakin su Kubura duk da dai namu diyan daki maza ne, Gashi da azahiri zaka zaci duk diyan gudan bugu daya yake masu a kan so, Amma idan ka tsaya sosai ka natsu sai kagano tarin kin jini da yakewa diyan mahaifiya na, Dan abu kadan zasu yi kaga kyara da hanttara daga gare shi, kodan kuskure kadan ne yanzu za,a jishi dasu har ya hada da uwar mu, Sai da idan ka shiga gidan zaka ga matan gidan suna normal life din su a tare ne tankar babu k8shi a tsakanin su , Hakan ma diyan su komai a tare sukeyi komai babu wari a tsakani nice kawai suke nunawa wari a gidan babu boyo ko shayi, Fitar mahaifiya ta agidan yadda mama Rahana ke fada min tace ya faru ne ga hadin kan ds matan gidan sukai mata wanda matsi yai yawa har takai yan uwan Ummi sun bukaci da yasauwaka mata a lokacin , Bayan komawan Ummi garin su sokoto ne tana cika idda ta,auri wani dan uwansu saidai shi bafillacen daji ne yana zaune a gari yana yar sanaan dabbobi, Sai kuma zaman ba,a kai ko ina ba ya,watse saboda rayuwan ta yana gurin "ya"yan ta da ta bari a gidan Baba Mudi, Wata uku ta kashe auren tafito ashe da akwai rabon ciki a jikinta gashi har ta cika idda ana batun komawa gidan malam Mudi sai ciki ya,baiyyana don haka aka dakata dole sai da ta haihu da yar jaririyar ta ta tare a gidan wanda tun a lokacin take ta samun wani kalubalen rayuwa daga maigidan dama abokan zaman ta dakeyi a boye, Suma abokan zaman sun gwanmace dawowan Fatima gidan ne akan sabon auren da yaso ya kara a lokacin, Don haka zaman nasu ya kara zama na kwarai babu mai tsangwama,wa wani daga cikin su a,fili sai dai kishin boye wanda baa rasa ba can, Wani ikon Allah gaba daya gidan malam mudi babu yaro mai hazaka irin Aisha din, Duk wani karatun da zatayi, zaka,ga tazo na daya a gurin amma duk da hakan babu yabon da take samu, daga gurin maigidan sai ma ya gune cewa andai batane kawai ba,wani ilimi da tafi su dashi, Haka rayuwan Aisha ya kasance a gidan da dadi ba dadi, har zuwa wanan ranan da Aisha ta taimakawa Baba tafitar dashi daga kunya, ****** ********** ****** Gidan su Hamzs babu wani abinda suka gudanar akan zancen don basu ji komai daga gurin Baba ba, Suna sauraren dawowan shi don anzo ance baya gida tun da safe, Ashe shi baba tanufi sokoto ne gidan iyayyen Aisha din ya,sanar dasu irin yadda abu ya kaya,, Da,farko kanin mahaifiyar Aisha ya dauka suka tafi can garin gurin yan uwan mahaifin yariyar don shi uban yanzu bai kusa ya kara gaba ko,, Bayan an fito, daga massalaci suka zauna dasu inda a cikin girmamawa da mutuntawa suka karbe shi don ya rike masu jinin su a gurin shi, Nan Baba ya,fara koro masu da bayani abinda yake tafe dashi tare da sheda masu cewa yazo ya basu hakkuri a bissa kuskuren da yayi na rashi sanar da,su Har ya shige gaba ya,daura wa yarsu aure ba tare da sanin su ba, Sunnuna rashin jin dadin sanar dasu da ba,ayi ba amma kuma sunyi mashi godiya da nuna cewa yana da hakki a kan yarinyar ai tunda shine ya tayar da ita, a gurin shi, Nan suka cecmai idan lokacin da yarinya zata tare a gidan mijin ta yayi ya sanar dasu zasu shigo gurin bukin , tare da abinda Allah ya hore masu, Wani irin sanyi malam Mudi yaji na samu mutane masu saukin kai, ya kara,masu godiya yabar su suna mai godiya, sumq din, akan rikon yar su da yayi har da aurar da ita, Sun hado shi da dan tsaraban kauye cewa yakaiwa iyalin shi agida ai masu godiya, Ba karamin farin ciki Baba ya,dawo dashi da ruggan mu gurin iyayyena, Sai da dare ne ya samu iyayyen Hamza suka dan tattauna dasu yana mai basu hakuri akan sauyin da suka gani , Inda yake cewa yai hakane don ya gwadawa Saude da yar ta cewa idan har bai da iko da isa akan yar cikin shi, To ga diyan bayin Allah sunyi mashi biyayya yadda ya kamata, Sun yake zancen cewa zasu ba uwar Aisha dan lokaci yadda zasu yi dan shiri a tsakanin su, Hamza wanda abin duniya ya kaiwa,ko ina, a rayuwan shi yarasa yadda zai yi da,rashi, Aisha yar karamar yarinya kuma kazama dabata ko san yadda mata,suke gyara,ba,ahine wai yau take a matsayin matar shi, Ya dan gyara juyawa daga saman yar mokaddan katifar da yake a,kwance sama yana mai nazarin siffan Aishan yarinyar da koda yaushe a cikin hijjab take a dunkule baka taba gane kalar surar ta, Washe gari yan abokan shi da suke zama a,shago suka,dasa mashi sheri da,wasa irin ta angwanne, Umma Rabi ce sukai ta tausan shi har ya hakkura da zancen auren Aishan don gudun kada ya budawa malam Mudi kasa a ido, Bayan sati, guda da,daurin auren su ya na zaune a bakin shagon shi suke jin ana yekuwar cewa mai gari yana neman duk wani wanda yasan cewa shi manomi ne don akwai bayani akan gagarumin wasan gwajin amfanin gona da za,ayi, a garin, Wanda manya mayan baki zasu shigo daga sassan kasan nan ta ko ina don kallon wanan amfanin gonan na manoman kasar,, Jin wanan shelan yasa mutane tururuwan zuwa kofan gida sarki don jin karin bayani daga bakin shi, Abinda yai sanadin jefa zukatan mutane da dama a cikin nazarin shiga wanan gasar , Daga ciki harda Hamza cikin masu nazari yadda zasu kokarta,su kawo nasu amfanin gonan a,wajen gwajin mai taken suna AGRIC SHOW, Daga dangin Hatsi, kayan labbu, dabbobi kayan ruwa da,sauran su, A lokaci guda duk gari ya rude kowani gida zance a buguda akeyi kawai, A wanan lokacin kuma uwa da diya a gidan malam Mudi suna a cikin matsi da,tsangwaman matan gidan, Duk da,su suka nuna,basu son auren Hamza din da kansu amma,suna ta,sake magana a tsakar gida, Har da,atika wace take bayan Saude da,yar ta,don muna funci kawai don son halin kishi, Hakan yasa,a koda yaushe mutum ya shigo gidan zai samu Fatima daki da,yaran ta,suna yar hiran su , Aisha wace zuwa yanzu abin duniya ya kaiwa ko ina tana,mamakin irin yadda tai wanan subul da,baka har tace wa Baba ayi wanan hadin auren da ita, Alokacin tausayin Baba ya,raja,a a kan ta har yakaita ga furta,wanan zancen a gaban shi, Umma Rabi ta,umarci Hamza da ya hada yan abubuwan bukatan rayuwa,a,kaiwa, Aisha a gidan su, Hamza wanda har yanzu ganin zancen yake kaman a mafarki don har yanzu ya kasa gaskanta al,amarin cewa wai Aisha a matsayin matar shi take, Sabulun wanka Sabulun wanki omo manshafawa dasauran Sune aka hada a cikin wani leda akabawa Halima sister din Hamza din takaiwa Ummi Fatima, kayan ace inji Hamza din, Tun shigowar yarinya gidan da kaya su Atika da mama Saude suka shiga ya da,magana a tsakar gida, da cewa, Iyakar ke nan tsiya tsiya ankawo wa Amarya kayan tausa, , Wanan gayar tsiyar akai shi can gurin mubukata irin sa,amma ba nan ba dai, Atika tace ai adaiyi mugani uwa,kwance diya zaune, duk a kare a tagumay, Daga cikin daki Kubura ta,dago labule don taga abinda ake zance akai yayin da,tai arba da kaunar Hamza na kokarin shiga,dakin Ummi Fatima da dan leda yellow mai layi layin baki, dan kayan da baikai rabin leda ba a cikin sa, Tace tsiyatsiya ke nan dama a can ya,dace da akai ba nan ba, Ni kan ai nagodewa Allah da ya raba ni da gayar tsiya, Fatima ta tari yarinyar da mutunci tare da godiya,akai akai da haba haba da ganin ta a cikin mutunci inda tabawa yarinyar naira,Ashirin tace tukwaici ne, Kaf zance abin da ya,faru a gidan malam Mudi ba abinda Halima ta rage a bakin ta, Gaba daya ta tsiyayewa Umma Rabi shi a kunnuwan ta kaf, Abinda yai matukar bata mata rai sosai yadda ake cewa wai suna yi, Saukin ta,guda,shine yadda, Ummi Fatima ya karbi yarinyar a,cikin mutuntawa, Hamza yana,tsaye daga bayan Umma har yarinyar ta,gama bada labarin irin cin fuskan da akai masu a gidan,, Muryan shi Umma taji daga bayan ta ya fadin Umma kada ki damu da zancen su don su sai kiji fiye da haka daga gare su, ma, ai, Yafita zuciyar shi na mai kuna yadda yake jin zafin irin wanan gorin da Saude da,yar ta,har ma,da,abokiyar zaman ta dayan, ****** ********** ****** Duk abinda Aisha ke yi hankali ta yanzu ya koma ga zancen Baba, da yake mata a ranan daurin auren ta, Ta dan gyara kwanciyar ta a hankali tare da dan lumshe idanuwan ta tana mai dan hade miyau masu daci, Ta dan kara gyara lumshe idanuwan ta tana mai sauke ajiyar zuciya a hankali, Ki kwantar da hankalinki Aisha wanan aure naki Allah yai mashi albarka Allah yasa muce gwamma da akayi, Saudayawa alheri kancin ma,bawan shi ta hanyar da bai zata ba, arayuwan shi, In har Umma Rabi da danta zasu rike min ke amna Aisha sai ince zaman ki a,gidan su yafi min zama a gidan nan, Zaman da kike a gidan nan a cikin wahala, tsangwama da shagube, Sun manta da cewa Allah ne bai nufi ki fito daga cikin tsatson su ba kika fito a can wani gurin na daban, Wanan hattaran da tsangwaman da suke maki a gidan nan kiris ya rage hawan jini ya kamani a kan hakan, A hankali Aisha tafara dan kuka a hankali don kada mutanen gida suji muryan ta, Washe gari sun tashi da,safe ba fashi daga duk wani aikin da Aisha din ta,saba yi a gidan da,safe, Da ita akai komai amma sai Umma saude taki saka,wa Aisha dan kunun kokon da take saka ma ko wani yaro a gidan da,dan kosai din su kwara biyu a matsayin abin karyawan su, Yau Saude ta hana wa Aisha wanan kosai din haka abincin rana ma again, Malam Ummi ta sama da zancen take tambayan shi ko shine ya hana a sakawa Aisha abin karyawa a gidan shi, Kafin ya ba da amsa buty suka ga mama Saude wace take kamar a jirace a bayan su ta,shigo tana cewa, Nice nan na hana mata ba wai wani yasani yin hakan ba, Ai aure take yanzu don haka sai taje can gidan mijin nata a saka mata shida keda alhakin ciyar da ita yanzu, don duk wani nauyi nata ya rataya a kanshi yanzu, Malam Mudi wanda kr reacting kamar wani shanyaye sai cewa yayi ai zata tafi gidan mijin nata kowa ma ya huta , Ummi bata samu bakin magana ba,sai kallon yadda Mama Saude ke faman budan baki tana vin mutunci wa mijin nasu, Ummi ce ta katse su da cewa Aisha zata koma gurin mamanta Rahana har zuwa lokacin da zata tare a gidan mijin ta tunda abinci da ake bani ni kaina ba isa na yakeyi ba balle nace zan dinga ci da ita, Daga fadar haka tabar daki inda ta samu yar ta Aisha take fada mata cewa ta,shirya zuwa gidan maman ta Rahans, Da sauri Aisha ta dago kai tana kallon mahaifiyar nata don son tagano ko anyi wani abu a tsakani, Amma sai bata iya hango komai ba a fuskan uwar nata,don haka ta dan mike daga zaune ga yunwa,da ya damay ta a,rayuwanta,, Yan tsunmakaranta ta hada a cikin wani bakin leda bag mai giwa, Ta,dawo daga kofan daki ta zauna a rakube tana kallon yadda yau zata tafi tabar Ummin ta, a cikin wanan yanayin zaman hakuri da tsangwama da take gani daga kishiyoyin ta ga,goyon tagwaye a,tare da ita ga,wahalhalun duniya iri iri a gidan, Bayan Ummi ta goya hassan ta umurci Aisha da tagoya hussai din taku ma umurce ta da ta je suyi sallama da su mama saude da,Atika, Ba,wani amsan da ta samu sai dan tabar bakin da,suke suna cewa umma ta gaida Aissha yau kan zamu sha iskan rahama gida ba yar agola a cikin sa, yar gola kiwon Allah ya isa, Sai suka tafa tare da,shewa suna masu rangada guda, Akarata can inda talauci ya yanke cibi mugani, Tafiya suke duk zukatan su a,cakushe saboda bacin rai don har Ummi din, yau ji take tankar tabar gidan malam Mudi din gaba daya, Suna jin shewan mutanen gidan a lokacin da suka fita suba cewa yau yar agwai an tafi, Atika tace yau kin muna maganin wanan shigiyar yarinyan mai kama da mayya kawai, Duk Ummi tana jin su amma ta kyalesu kawai suka,sa kai zuwa gidan Mama Rahana yar uwar ta, ****** ********** ****** Anty Rahaba ta gama komai na yinin ranan ta na,zaune daki ita da,yaran gidan suna kallo Ummi ta,shigo da,sallama, Mamakin ganin ta su keyi a lokacin saboda ba,al,adanta,bane fitowa uguwa da,dare, irin haka, Daya bayan daya yaran suka watse daga don bawa yan uwan guri saboda su sirint a tsakanin su, Bayan gaisuwar da,su kayi a tsakanin sai yar shiru ya biyo baya nan mama Rahana take tambayan ko may kuma ya faru, Ummi Fatima tana kuka tana bawa yar uwar ta labarin abinda ke faruwa a gidan su yadda matan gidan yanzu suka dauki kahon zuka suka saka mata ita,da yar ta,a gidan da kuma hana mata abincin da akeyi a gidan, Ummi ta karasa acikin wani irin kuka mai ban tausayi, atake rayuwan yar uwar nata zuciyar ta ya, baci sosai take, magana a hasale da cewa ni wanan al,amari nagidan ku yana,daure min kai wallahi, Yanzu ace har a hana ma wani abinci a cikin gidan ka kuma shi maigidan bai dauki mataki ba a kai Nan suka yanke shawaran cewa Aisha ta zauna a gurin Rahana har zuwa lokacin da za,a kaita gidan mijin ta, ****** ********** ****** Zancen duniya baya boyuwa don haka,barin gidan Aisha da,kwana biyu labari ya fara kewaye uguwa cewa saboda auren da malam Mudi ya daura da Aisha , Su mama Saude sunyi sanadin da yarinyar tabar gidan da zama zuwa wani gidan irin tsangwaman da ake mata a gidan, Haka zancen yai ta,yawo abinda ba,ayi aka dinga fafin cewa shi akayi a gidan har maganan yazo kunne Umma Rabi, Hakankinta ya tashi don ji irin wullakancin da akaiwa yar mutane saboda dan ta,da ta aura don ba,a bari yai kunya ba, Umma Rabi tasa,a,fara gyara daya daga cikin dakunan gidan inda yaran zasu zauna, Tsohon part din mahaifin Hamza din wanda yake ciki da falo ne sai dai ba masu girma bane sosai haka sune ake tawa dan gyara don su zauna a ciki, Dakin ya tsufa sosai amma dole haka zasu zauna din a ciki ,tunda basu da wani, Yanzu rayuwar Kubura ko ba,a fada wa mutum ba yasan cewa ta zama wata yar birni sosai saboda irin yadda idanuwan ta suka,bude, Shigar ta kawai zai nuna,wa mutum cewa ta sake fiye da tsanmanin mutum, Yau suna da wani dan liyafa da su yi wanda zai hada matasa masu yi da zamani da a gurin, Tayi kitson attachment ya mayar da ita kamar diyar yare, An mata gyara fuska wanda ya,sauya yanayin ta daga na diyan musulmai zuwa na diyan kabilu, Wani dogon riga ta,saka a jikin ta ya dane mata jiki sharp din jikin ta y fito tsab, Sai faman kiran ta ake a,waya cewa tazo an fara taruwa agurin sha,anin nasu, Uwar ta,sai murna,da farin ciki take ganin irin yadda diyar ta yanzu ta koma one in town, Sai washe baki take yayinda,Atika mishon batta da musulmi take faman koda yarinyar agaban uwar ta, Wani daga cikin diyan Atika ne yashigo yake fada masu cewa ga Baba nan zai shigo gida, Da sauri shige daki ta zuro wani katon hijjab a kanta, ta boye takalmanta a cikin jikin ta, A,a yau sai ina haka tace Baba littafin da muke hadda dashine zan karbi a gurin wata yar uwar karatuna tunda Aisha bata,nan, Tasako zance Aisha ne aciki don Baba din ya ya ji dadi ya barta ta fita, zuwa inda zata, Yashige part din shi inda ta,waigo tana,wa uwar ta dan bye bye din samun nasara ta fice abinta, Gurin part din ya hadu sai kida ke tashi samaru da yan mata masu karamin kwakwalwa suna ta sha,anin su gungu gungu a gurin, Kubura tana daga cikin masu gudanar party din haka zirga zirganta yai dan yawa a gurin, Daga inda yake tsaye yana iya hango wanan yawan sintirin da take a guri, Turawa yayi wani dan duniya yakira mashi ita kamar bazata zo ba can ta taso a cikin ragwada tana tako daidai har ta karaso gaban, A dan tsiwace take cewa malam kai ke kirana tana wani taunar chewing gun Yace a cikin kasaita da mu samu dan guri inda babu hayaniya da yawa, Motar big show suka shiga wace ke daga gedaya a Parker wanan shine mafarin haduwan ta da Nura wanda yaxo mata da kudi irin wanda take bukata da mafarkin samu,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA,,, 👑 SARAUTAR MATA 👑 0⃣9⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAHUMA AJINIR MINAL NARRR,,, Wanan novel din kada ku manta amanace tsakani na daku Allah yasa muci gaba da rikewa Allah yasa mu dace yan uwa Hakannan naci gaba da zama a gidan mama Rahana, inda nake zaune ba wani tsangwama komai, Ina gudanar da,al,amurana cikin natsuwa da kwanciyar hankali, Saboda gidan mama Rahana kowa yana nuna min so da kaunz a fili tare da yaba min hankali, Sai nake ji a raina dama ace tun farko a nan din nake zaune ina rayuwana, Matsalata guda shine kewar yan uwana da ke damuna tunda ban taba tafiya na barsu ba, Yanzu duk wani mugun hali a,Ummi suke nuwa shi tare da hattaran ta da yan diyan ta, A wani yanmaci lokacin ina da sati uku a gidan mama Rahana sai ga mahaifiyata tashigo da zancen wai zan tare a gidan mijina, Zance da yadaga min hankali kenan gabadaya wanda itama mahaifiyar tawa hankalin ta duk a tashe yake, ita,ma, Ummi tazowa da yar uwar korafin cewa bata aje komai ba akan zancen aure na yanzu gashi zance ya tashi, Mama Rahana ta kwantar wa da Ummi hankali da cewa shi aure ai alheri ne daga Allah dazaran ka dasashi sai kaga hanyoyin Allah suna budewa ta inda mutum bai tsan mana ba, Da irin maganganun haka har Ummina ta kwantar da hankalinta ta zurawa sarautar Allah ido Yan sayaya akai min duk da bangani ba amma inajin yadda su mama da Ummi ke shawara a,dakin akan zance na, A can gidan baba Mudi matan gida sai gori da habaici suke sakewa wai rana bata karya saidai uwar diya tai kunya, Yau gashi aure ya taso ummi bata aje komai da zatai min aure dashi ba ga shi malam Mudi ba dama ya taimaka min don sun kai karan shi a gurin yan uwan shi cewa yana maida hankalin shi ga yar agolan gidan shi fiye da,diyan su sosai, A tsayar da magana cewa a gidan mama Rahana za a guda nar da duk wani abinda za,ayi sai a kaini daki na, Raban da,za,a kaini a,ranan ne aka,sakani a lalai don ba wasu tarin kawaye ke gareni ba ni, Ranan na yi kuka kuka irin mai tsuma zuciyar mai sauraren ta , Don za,a kaini aure ba gado da shimfida irin ta,al,ada sai tabarmi da yan sauran tarkace kawai, Zokaga murna a gurin masu son gqnin bayan don sai shewa da raha suke suna yadda magana a gaban kowa, Cikin ikon Allah sai ga dangin mahaifina tare da na mahaifiya suka iso tare da mota fam da yan kayan su sai dai irin na kauyawa ne, Isowar su yasa guri yadan rude sai kama baki ake ana mamakin abinda,su kazo dashi, anan sabon gulma ya fara tashi kuma Da yamman fari yan uwa suka tasani a gaba wai naje muyi sallama da mahaifiyata da kishiyoyinta da,suka tayar dani, Mun shiga gidan da,sallama banyi tsanmanin sun karba muna ba,sai dai naji muryan Ummina, Mun shiga dakin ta tana zaune tare da,wasu baki mata mutum biyu yan uguwar mune da,take shiri dasu, Can daga kuryan dakinta kadan na,samu guri na,durkusa a kafana, Kaina ya,sade a kasa yayin da take gaisawa da matan da muka shigo tare, dasu, Daya daga cikin matance take cewa tau fadima ga Aisha nan mun kawo ta tayi maku sallama keda abokan zaman ki, Nan da nan naji idanuwana sun ciko min da hawaye kaina yana sadde a kasa nace cikin kuka Ummi ki yafe min don Allah, Shiru kamar ba zatai magana ba,sai can naji tace nikan Aisha may kikai min a,duniyan nan, Kece dai zance ki yafe min nida a,sanadina rayuwanki ya zamto irin haka, Wani kukane yazo min maiban tausayi da ni da ummi dama sauran wanda ke dakin Dayar matar tace ai shi mutum duk bai wuce kaddaran ubangijin shi don haka sai muyi mata fatan alheri ga sabuwan rayuwan da zata,shiga a yanzu, Ki tashi kije ki roki sauran matan gidan gafaran zama muyi haraman kaiki tun dare baiyi ba,, Dakin mama Saude muka fara shiga kamar bazata amsa muna ba sai can tace ku iso mana, Muka shiga da sallama a,bakunan mu muna gaisheta tare da mata yaya,gida, Daya,daga cikin gwagwanina ta ce mata tau uwargida ga yar ki nan mun kawo maki ita kunyi sallama yau zata tafi dakin ta insha Allahu, Mama Saude tace "Ya ta kikace fa aida yata ce da bazata wanan gidan fakiran ba, To kiyi hakkuri don Allah duk abinda tai maki ki yafe mata akwai kurciya a tare da ita, Mama Saude tace ai mu gamu gani shine namu kawai, To Allah ya kyauta inji gwago na dake kokarin tashi tsaye,, Sai da na dan yi jin nace mama don Allah ki yafe mi duk laifin da naii maki, Allah dai yakai lafiya aini baki min komai ba yar Agwai,, kanki kikaiwa, Mubar dakinta muka nufi dakin Atika amm sai muka samay ta a waje take cewa mu tsaya daga wajen ma yayi ai, Tace yar Agwai sai ayi hakkuri daduk irin yanayin da za,a gani a gidan Hamza don ko sai rarita yasan da zatayi yoyo, An nufi dani gurin malam Mudi wanda shigowan shi gidan ke nan a lokacin, Mun shiga turakar shi yana zaune yana kokarin cin abinci Atika tana tsaye daga kan shi tana kokarin mika mai ruwa, Baba yai muna sannu da zuwa tare da,bamu guri don mu zauna daga dan nesa kadan, Baba yace Aisha yau Allah yayi aure zai raba mu dake, zai rabaki da uwar ki da yan uwan ki ko ? Baba yace aure kenan sha kan yaro duk da,ba nesa zakiyi damu ba amma shi al,amarin aure yana da matukar yawa da a,rayuwa, Baba yace Aisha yau Allah yayi rayuwar ki zata koma a cikin wasu jama,an dabaki saba zama dasu ba, a baya, Aisha kamar yadda na fada maki a baya aure sunna ne maikarfi, Wanda yatara wajibai masu yawa a gare shi sosai , Nan Baba ya kara nanata min yadda mukayi ranan da na umurci yai fitar kunya dani akan Kubura, Baba yace Aisha dake da mijin ki ku kasance masu matsakaiciyar rayuwa kamar yadda nasan halin kowanin ku, Halaiyar ku danasan ku dashi indan har kunci gaba dashi zaku kasance acikin jin dadin rayuwan zaman takewa, Yace yau Aisha abinda kikai min yasa na tuna da wani Hadisi na na mazon Allah inda yake cewa, 1 Mutane zasu so abin halitta su manta da,wanda yayi su, 2 mutane zasu rayuwan su har su manta da makomar su, 3zasu mallakar manya manyan gidaje su mance da kabarin su, 4mutane zasu zabi aikata zunubi su manta da yawan tuba (gafara) 5 mutane zaso dukiya su manta da hissabi,, Baba yace yau Aisha kin gwada min cewa kedin diiyace a duniya kin nuna min cewa mahaifan ki sunyi sa,an haihuwan ki a,duniya, Yadda kika iya fitar da mutumin da kikewa ksllon uba a gare ki alhalin wanan mutumin yai sakaci da damar da Allah ya,bashi na kasancewa uba agare ki tun farko, Sai kawai baba yasa kuka yana cewa Aisha yadda kika fitarni kunyan duniya Ubangiji Allah ya albarkaci auren ki yabaki zuri,aa masu albarka duniiya da lahira, Itama Aishan kukane ya kubce mata inda ,suka bar gidan a cikin hawaye, Yan uwanane kawai suka rakani gidan miji sai yan tsiraru daga matan uguwa masu son ganin kwam, Dakafa muka taka don ba nisa sosai da gidan Mama Rahana da mu, Ina rike da hannub kaunar mahaifna da mahaifiyana, muna kai kofan shiga gidan su Hanza sukace min dakata daga nan sai mukaja mukai tsaye, Yayin da gwago na,tadan rankafo daidai kunnena ta rada min da cewa nac bissimillahi A,uzu bikkalamatillahi tamat min sherin mahallak, 3, Takara cewa kiyi bissimillah kija suratul Iklas kafa uku hagu da daman ki sai ki shiga da kafan dama Allah ya sa albarka a rayuwar auren ki, Kamar yadda gwagona ta umurce ni da nayi hakan nayi don ita din malamar addinice a kauyen mu, Inda ina tafiya bakina yana lailaha,illah hasbunallahi wani,imal wakil,, Kofar shiga dakin da aka gyara a matsayin nawa muka dan ja runga muka tsaya gwagona ta kara furta nin kiyi bissimillah ki kara jan Iklas kafa uku ki shiga da kafar dama, Hakan na kara karantawa tace shiga da kafar dama da,addu,an da duk kika iya domin Allah maji rokon bayin sa ne, Duk abinda yazo min daga fannin addu,a haka nauta jero su har asma,u husna saida na jero su, Nai mamaki kwarai yadda naga an gyara min daki a tallakance dai dan ban zaci haka ba sam, Aka zaunar dani a saman gado shima,da,addua abakina yayin da nadanyi kamar minti goma a zaune sai suke cewa na mike zuwa dakin uwar miji, Mun samu Umma Rabi da dan taron jama,an ta a dakinta tana zaune a saman katifan dake a cikin dakin ta, Duk da bata da miji amma kafanta yasha kumshi yana sheki, ta dan yi kwalliya itama, Yaranta duk suna a cikin dakin azaune suma tare da mahaifiyar su, Daya daga cikin iyayyena take cewa tau yadai ga yar ki mun kawo maki Allah ya baku hakkurin zama a tsakanin ku, Dayar gwagona tace sai anyi hakkuri da yaran yanzu don Allah aita tsawata mata akan abinda tayi ba,daidai ba, Umma Rabi tace ai da na kowa balle Aisha ai dama diyatace, Allah ya bamu hakkurin zama da su, Mijinta yaron kirkine baida matsalar rayuwa duk inda na ajeshi anan yake tsawa inaa fataan zaki bamu hadin kai muyi zaman lafiiya a gidan nan , Kina da kannen miji don haka sai kinyi hakkurin zama dasu don a zaunna lafiya, Bamu jima adakin ba suka ce na taso mukoma dakina, Muna shiga naji kauna mahaifiyana tace tau Aisha tun yanzu na,fara hango hakkuri a gare ki, Din wanan sarrakuwar taki da alamar irin matan nan ne masu goyon bayan diyan su akan komai, Don kiji tun a gaban mu tana yabon danta da kanta bata bari hallinsa ya nuna ba, Don haka nasan kina da kirki kiyi hakkuri kinji gaduk irin abinda kika gani daga gare ta ki kawar da idon ki akan abinda take da diyan ta a gidan nan don ku zauna lafiya kinji, Hawaye ne masu zafi suka zubo min ina kokarin dan share su da habar hijjab din dake a fuska na, Na ji mama Rahana tana cewa nasan tunda baki da nisa da Fatima yan gidan su ma zasu dinga shigowa don yin lecture ki don haka ki zama mai boye sirin ki ga kowa, kadaa naji wani zance a waje akan zaman ki gidan nan, Tsabta, yinayi bari na bari shine zaman aure harki ji daga baya ana fadar ai wance ta samu miji ko ta samu gida, Daga karshe wanan gwagon tawa tace masu salli, allanabiyull karem suka karba da sallallahu alaihim wasallam, Nataita jero adduoin nemamin zaman lafiya da kariya daga duk wani sheri na kalubalin rayuwa, Sukai min sallama sukace su zasu tafi sai da,safe kafin su tafi zasu shigo mu kara sallama, Har,sun tafii mamana,Rahana tadan dawo daga baya tana ce min ki yi duk abubuwan dana koya maki a gida Na,amsa a hankali dacewa tau mama sai na saka kuka haka inaji ina gani suka tafi suka barni a,sabuwar rayuwa a wani gidan, ****** ********** ****** Kubura yanzi ita da,sabon saurayin da tayi mai suna Alhaji Nura dinke suke cif da shi don akan shi duk ta kore mane manta na farko shike masu ruwan kudi suna bushashan su ita da mahaifiyar ta, Yan uguwa suna kallon ikon Allah don har kofan gida zai zo ya,dauketa su fita yakuma dawo da ita, Duk a gaban idon Hamza wanda shagon shi yake kallon kofan gidan nasu, Tsakani Hamza da ita yanzu ko gaisuwa babu sai ma yar harara da take yawan watso mai idan sun hada ido, Malam Mudi tun yana ji har yagani da idon shi ranan yai masu masifa sosai ita da uwar ta Yace yaba sati biyu in har aurenta yake son yi to ta fada mai ya fito ya wanke ta yahuta don shi bazai aje yarinya haka a gida ba,suna gwada sa,a da uwar ta, Hakan yasa ta fadawa Alhaji Nura sakon Baba din da farko yaso ya,doje mata amma kuma ko may ya tuna sai yake ce mata, zai zo yaga mahaifin nata akan zancen, Zuwan Alhaji Nura gurin Baba ya,saka mahaifiyana a,wani sabon kuncin bakin ciki a gidan mu don irin gori da habaicin da suke mata, Amma mama Rahana taba Ummi shawaran cewa tayi tankar bata fahince su ba, Ta zage ta shige cikin su tanuna farin cikin takoda kuwa,suna basar wanne taa nuna tafisu farin ciki da hakan Hakan ko akayi don duk da nuna matan da suke basu ra,ayinta a cikin su tana nuna zakewar ta a zancen Kubura din don dai a zauna lafiya kawai, , Ance idan kana son shanmatar uwa to karike dan ta ganin haka a sannu sannu har mama saude tadan fara rage tsangwamar da takewa Ummi da yarran ta suka dan koma daidai sai dai sama sama don na ciki na ciki, Sai dai su su a ganin cewa ai dai nagaba yai gaba don sun tserewa Ummi din da komai tun da yar ta a gidan wahala take rayuwan ta ai, Su ko zasu tafi inda kowa nasu zai huta har su shafa ma,wani arziki, Arziki kan ana gwadawa kubura din shi don yanzu har takai bata iya cin abincin gidan mahaifin nata sai dai a sayo mata ko ta girka abinda ran ta yake son ci taci, ****** ********** ****** Bayan fitar iyayyena daga dakin ina zaune ni kadai a dakin ba wanda ya leko dakin, Sai dai ina jin hayaniyar mutanen gidan daga dakin su acan naji Zarah tana masu sai da safe inda tadan leko dakin nawa tashigo da yar fara,ar ts tana cewa, Tau amaryan mu ni zan tafi sai da safe nasan cewa ba lalai bane Alhaji ya barii na fito gobe amma insha Allahu idan an kwana biyu zan shigo na duba ku,, Ga amanan yayana nan nabar maki kin san yayana salihin mutun ne idan munga ya canza ke ce, Damm naji don zance mama Hanne ne ya fado min a rai na cewa sai nayi taka tsantsan don su da alamar nasu suka sani, A hankali na dan bude baki nace Anty Zarah sai anjima nagode a gaida gida , Tace ke waya fada maki cewa ni antyn ki ce yanzu ai kin zama matar yayana don haka ni kaunarki ce, Nace cikin dan jin kunya ainima yayanane ko kin mata cewa ni din kaunar ku ce, Tadan dafani tace hakane Aisha Allah yabaku hakkurin zama kinji sai kiyi hakkuri da kowa a gidan nan, Tai min sallah ma ta,tafi na kara komawa ni kadai a cikin dakin, bakowa a tare dani, Sai zuwa dare ina zaune a gefen dan gadon katakona mai cin mutum biyu wanda yasha shimfida da zannuwan gado, Naji Asma,u ta,shigo dakin tana rataye da hijjab din ta da wani zani take cewa Umma tace wai nazo na taya ki kwana, Cikin dan murmushi da,sakin fuska na ke ce mata, to ga wuri ki kwanta don haka na mike tare da jawo kofan dakin nadan rage kayan jikina na,dauki butana wanda yake cike da ruwa nafita zuwa babdakin gidan don nasan dashi, Nai sarki saidai naga an dan gyara bandaki ba kamar yadda na,san shi ba, Ina tsugune na,fara alwala naga shigowan Hamza gidan dauke da,wani bakin leda bag karama a hannun shi, Ganin nice naje alwala a tsanake yadan sashi shan jinin jikin shi kamar zai min magana ssai mukaji muryan Umma Rabi tana cewa kai Hamza zo nan, Ya juya zuwa gurinta nidaii nai alwalana nashige daki na rufo abina inda na tada sallah, Nakai wani lokaci a gurin da nai sallah a zaune ina jero addu,io neman tsari daga Allah ga,wanan sabuwar rayuwan da na,fara fuskan ta a,sabon mazauni na, Na koma can dan nesa kadan da Asmau na kwata inda ina jinta sai nasarin ta take hankali kwance abinta, Washegari asabar na tashi don kiraye kirayen sallah da,akeyi na, dauro alawala , Ana,sallamay sallah nafito na,gyara tsakar gidan nan gaba,dayan shi don dama nasan kan gidan, Har ban daki na tsabtace muna koda gari zai haska ko ina na gidan na gyara tsab har zuwa lokacin banji Umma Rabi tafito daga dakin ta ba, Na nufi gurin da,suke ahe icce na debo na hassa wuta a murfu tare da dora ruwan zafi duk da ban san may za a girka a matsayin abin karya kumallo ba,, Na hada kwanuka zan wanke sai dai babu clean din da zan wake a fili, A lokacin naji motsin Umma ta bude kofan ta abinda yadan sani sauri dan dago kaina ke nan na nufi kofan nata don in gaishe ta, Yayin da take bin gidan da kallon mamakin yadda na gyara shi haka tun da farar safiya, Sai idon ta ya sauka a murhu naji tana cewa ke Aisha wanan irin icce da kika zumbuda a murhu ai yau kawai zaki kashe muna dan jarin namu damuke maneji dashi, Hamza ne yashigo gida a lokacin inaga daga masallaci yake don naga casbaha a hannun shi, Inda murhun yake yake kallon sai naji yace Umma sai naga kamar kwara biyar ne tasa kawai, Kaina na,sada a kasa inda naji Umma tace tau mara kunya zaka hana na nuna mata yadda ake tattali ke nan ko ? Yace a,a wane ni kawai dai na zaci ai baki gani bane dakyau,, Yace mata ina kwana Umma an tashi lafiya ya gajiyan baki, Nima,sai a lokacin na tuna cewa bamu gaisa,ba,shi nazo yi ta tareni da wani magana, Nazube kasa a gaban ta gwiwa bibiyu ina cewa acikin yar murya ta,siririya Umma ina kwana, Tace Lafiya kalau ya kuka kwana nace cikin dan jin kunya Alhamdullahi, Ashe har kun tashi kinyi wanan aikin haka ni barci ya kara kwasana ai ban sani ba, Gefen da yake a tsaye nadan kalla still ina,a,tsugunne nace ina kwana yaya Hamza, Ya amsa min a,wani yanayi da cewa lafiya ya gajiyan jama,a, Idon Umma,Rabi kyam a kan mu kamar wacce ke,son gano wani abu a kan mu, Nace Umma nasa ruwa ban san may za,ayi da safen nan ba, Akwai saura kamun koko yana nan shi zamu dama, aiko, Hamza yace ko na,turo da madara ne ku dan hada tea ko ? A,a kada ka fara min shi ranan da babu tea din fa kariga da ka,saba mata dashi, Na mike a,sanyaye nabar gurin ban tsaya jin may zasu ce ba, Ina bada baya naji tana cewa kawai zaka kwashi dan jarinka a ciye bayan ko yar irin gara,din nan da ake kawo wa Ango banga an kawo muna,ba mu, Hamza wanda ya,danjin gina jikin shi a bayan bangon dakin Umma din ya dan ce a hankali haba Umma wani gara kuma bayan kin san yadda akai wanan auren ba,shiri, Ta,watsa mai harara tana cewa da yake basu san kunya,ba za,sy kawo muna ya hakana , Na dawo nake cewa tabani Omo na wanke kwanoni sai ce min tayi ai kayan basu yi wani dauda,ba na wanke hakanan kawai, Fita naga yayi sai gashi da clean yake cewa idan na gama,saina ahe sauran a gurina lokacin Umma ta daki ita da kanin Hamza din wanda ya,fito yana shirin zuwa makaran tan boko, Kamar yadda Imma tace kunnun na dama inda batazo ta,gani ba amma take ce min wai nadama kunu da,ruwa ruwa kuma,bai dahu ba Yarinyar ce taahigo da robar kosai tana cewa ance a cire na dari wai a raba,abawa kowa nashi, Na karbi ledan na kaiwa Umma kosai din na juya don na bar dakin naji tace min karbi naki kafin ki fita, kosai ne kwara biyu tamiko min na karba gwiwa bibibyu nake mata godiya, . ***** *********** ****** Yan uwa na,suka shigo da kayan garar da Ummi tafa min gori a kanshi , Shikafa garin masara, gero sai kayan miya su mangyda ,albasa, maggi gishiri, kifi da,sauran su,, Sai kuma bahohi dakeda guguru cincin da sauran su,, Haba nan Umma ta,shiga waahe baki tana cewa au a she kuna tafe dama , Nan tafara dan cewa Allah sarki wanan irin dawai niya haka yan uwa, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUN KU 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣0⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA A,kofan dakin Umma Rabi aka jibge kagan gara inda suke ce mata ta karba d hakkuri don bukin yazo ba,shiri, Su ka kaimin wanda zanyi amfani dashi a dakina,, Ina,zaune tare dasu a,daki ne Gwagona take kara min nasiha irin wanda iyayye kewa diyan su, Hawaye ne ki tsiyayo min a idanuwa na, gwago tace, kamar yadda na fada maki jiya yau sji din ne,rayuwa takai a,wani guri kuma na,daban, Yanzu halinki mai kyau ne kadai zai maki jagora a zamantakewar ki da,su, Kada kiyi sakaci da ibadan ki hakkuri da kuma kunya, Idan harkin iya tsare wa yan nan tau kingama tsara rayuwar ki ke nan, Sister din Ummi dake daga gefe tana gyara,min kaya,tace a,kuma hada da tsabta, Don kin san mazan yanzu mai tsabta suke yayi idan mace tace ita yar son jiki ne zaki ga komai nata sai a,slow, Gwago na tace min karbi wanan a cikin dabara na karba kamar mai rada tace wanan farin gorar naso nabaki tunjiya, kisha duk dai ko yanzu bai baci ba, Amma anso kafin miji ya,shigo gurin ka kadan goga kadan a goshin ka zuwa kirjin ki da,marar ki, Abin kurciya sai cewa nayi ai baishigo dakin ba tun jiya, har suna hads baki a tare da mama hanne, Gurin cewa to a ina yakwana shi ? ke nan ke kadai kika kwana, ? Nace tare da Asmau kaunar shi mama tace mu kwana tare Sai naga sun dan kalli junar sai kuma suka,ce lalai da akwai matsala amma Allah ya gyara kawai kiyi ta hakkuri kinji, Tafiyan yan uwa na Umma ta,shiga kasafin kayan cicin da aka kawo mata, Sai muryan ta kake ji yana tashi sama ita da yarsn ta da masu shigowa don ganin amarya, Tun tafiyan yan uwa ina zaune a dakina nayi tagumi sai famsn tuna ne inda matsalar da naji suna kira zai shigo min, Shigowan Hamza sau biyu gida baiga giccin Aisha ba a tsakar gidan, yana son shiga ya duba yana tsoron idon Umman shi, Ganin hankalin Umma yana gurin kayan dake gaban ta ya sashi dan satan shiga gurin da nake, Ina zaune a kasa saman tabar roban da aka shinfida a kasan dakin wanda su Gwago suka tashi a saman shi, Ban san da shigowasar ba sai ganin shi nayi a tsaye yana cewa Aisha ke kadaine a dakin abinda yasani saurin dan dago kaina ke nan sai kuma nai saurin dukar da kaina,a kasa, Ya matso inda nake a zaune ya dan tsuguna gap dani kadan yana cewa kin kuwa karya Aisha, ? A cikin natsuwa da kulawa yake tambayan nawa, ? Na dan dago kaina a hankali nake cewa eh na karya yaya, Hmmm naji yana cewa kiyi duk abinda Umma take so don ku daidaita da ita, Cikin sauri na dago kai na dan kalle shi yayin da idanuwa na,da,basu raina hawaye har sun ciko ko, Yace idan har kin kiyaye abinda take so to zaki ji dadin zama da ita sosai, Don tafi da son duk abinda tacewa mutum to mutum ya to kawai shine zaman lafiya Yace don haka Aisha kamar yadda na,sanki da hali irin na kirki don Allah ki cigaba dz halinki da hakkuri, Duk abinda ta hane ki ko umurce ki dayi ki yishiba lokaci don bata son mussu da tauri kai nace tau a hankali, Nasan baki saba da yadda muke karyawa ba,agidan nan da irin cimar da muke yi amma ina rokon ki daki daure ki ci ko yayane don samun salama kawai, Muna ciki haka mukaji muryan yaro yana cewa wai ana sallama da Hamza a waje, Umma tace ai yana nan shagon ka barshi a ciki yaron ya kara fadi cewa baya shago yashigo ciki yanzu Take naga rudewa a idanun shi kaman wanda yayi wani iri laifi maigirma duk dan rude a hankali yadaga labulen dakin yai waje simi simi dashi yana cewa gani nan ai yanzu nashigo gida, Banga giccin yarinyar nan bane tundazi shine na dubata don naga ko lafiya take, Wani uwar harara Umma ta sakar mai sai ya sadda kan shi kasa da sauri tace baka dai jin magana ke nan ko ? Umma yanzun nashiga don na dubata kawai ba wani abin ba, Har zatai magana ko may ta tuna kuma sai tai shiru kawai ta kuta ya bishi da harara bayan shi inda yafita kofan gida gurin da ake neman shi, Tun daga wanan lokacin ban kara ganin Yaya Hamza a dakina ba sai dai idan ya shigo naji muryan shi a tsakar gida daga nesa, Kwana biyu ke nan ina zaune a gidan duk wani aiki nice ke yin shi batare da najira ko kuma ance ba, Idan na dafa abinci Ummace ke rabawa da kan ta, don sai dai na dauko na kawo mata a gaban ts ta raraba, Umma bata jin kunya ko nauyi gurin cika wa Asmau da dan ta karami Ibrahim tana cewa wai yarane, bari a zuba masu da yawa alhalin sa,ar mu guda da ita Asmau din, Ba ruwan Yaya Hamza da al,amari na nima din haka iyakata dashi idan ya shigo nai mashi ina kwana da safe, ****** ********** ****** Kubura yanzu zancen ta da wanan Hamza din dan uguwar sabon gari ya kan kama don kowa yanzu yasan cewa shine zai aure ta, Take mutane suka,soma magana a kan zance kowa na kawo suka daban daban, Idon mama Saude ya rufe sai cewa take hassada ga mai rabo ai taki ne, Don haka kowa ya cirewa yar ta ido ga,al,amarinta da mai baki da goro da mai baki da taba da mai baki da kuka duk suka kwaso zancen su sai suce wai Kubura to ita hakan ya sheta don haka zata daura kafan wando guda dasu ne, Hakan ne yasa mutane suka ja bakin su sukai shiru suna kallon aikin karya, a cikin uguwa, Ranan da safe babu yaron da zata aika ya sayo mata idomie a shagon hamza, Hakan yasa ta yafa dan yalalon gyalen ta akai na just to cover ta fita zuwa sayowa, Yun bayan cin mutuncin da taiwa Hamza wanan ne karo na farko da zasu gana, Yana daga cikin shago yana mikawa wani yaro kayan da yasaya yaji wani irin kamshi ya daki hancin shi, Da sauri ya juyo don yaga ko waye mai wanan kamshin haka a lokacin yayi zufa zufa dashi, Ba,sallama ba komai tace aban idomie na dari biyu kwai guda shidda, Cikin dan murmusawa yace a, hajiya Kubura ce barka,da,dare ta,wani ya, mutsa fuska tace ka,ban indomie nace, Murmushi kawai yai mata inda a zuciyar shi yake jin ke jin wani radadin abinda take nunawa a kan shi, Abinda tazo saya ya,saka mata a leda ya mika mata ta miko mai naira dubu guda ya cire kudin shi yace jeki kawai kibar shi, Tace look malam wakake ne ma dauki kudin ka kabani canji na don ban son hada abina da abin matsiyata mutum yace ka kashe mai shago kawai, Yai tsaye sororo yana kallon ta a cikin mamaki yace Kubura nine kuma matsiyaci yau don nace ki bar kudin ki, Dakata malam may kake so dani ne bari na fada ma ko wanan ganin da kai min a dalili na,zo inbashi banda lokacin tsayawa harka da yaku bayi irin haka masu zubarwa mutum da daraja, Ta fige ledan ta tawuce tana zuba mai bakaken magan ganu daga bakin ta, Binta HAMZA yayi da kallon mamaki yadda akaiyi idanuwanta suka bude haka aa lokaci guda, Shi bawai da manufar da take nufi yabata wanan alheri ba kawai din mutuncin da ke a,tsakani na,sarrakuta yanzu, Ta shiga gida tana ta masifa Atika ce ke cewa may yafaru ne haka kuma,? Nan tana kokarin cire dan gyalen da ta yafa a kanta take fada mata a cikin daga murya, Wanan matsiyacin mana Hamza ke so ya kawo min rainin wayyo wai na tafi saye indomie yake ce min na bar kudin, Nace mai anfada mai cewa ni matsiyaciya ce ko may yake nufi yatafi can shi da tallakam matar shi ya kara ya,ciyar da ita, Don ni ba,sa,ar yin sa bace ko amfada mai ni matsiyaciya ce da zan buge a dan kayan treder shi, da bai wuce nasha ice cream da shi ba, Ko yana zaton zai iya sayeni da wanan tarkacen banzan nashi ne har yaushe yai kudin da zai bani tsiyatsiya jiya wa yau dashi, Masu kwadan kayan shi dai ai suna can sai suci mu gani in ci banza ne gida ma ba, a koshi ba balle akaiwa bare, Ta shige kitchen din su tana kokari dora girki Atika tace bari na dafa maki ai baida wuya, Daga daki Ummi tana jin su tace a hankali Allah ya kyauta Allah kaga nufin mu, Sai daga baya mama Saude tafito take cewa ke ko hankalin shi yana a kan ki mana tunda dama cushe akai mai bawai da ra,ayin shi ba, yake auren , To wallahi ahir din shi dakr don baiga kin masa kama dayar masiyata ba ****** ********** ****** Rana bata karya sai dai uwar diya tai kunya yau saura Sati guda gasa duk gari inda kabi zancen wanan gwajin amfanin gona ne tako ina, Samarin dake zaune a baki kofan shagon Hamza suna hira yau firan nasu akan zance wasan da za,ayi a garin ne, Hamza ba ma,aboci son surutu bane yana dai sauraren su a hankali duk abinda suke fada a gurin,, Wanan yace shi kaza zai kai wancan yace shi abukaza zasu kai a gidan su, Acikin zuciyar shi yake cewa ni Hamza to may zan kai ? Gashi bamu da kiwo balle nace zan kai gashi bamu da,wani abin azo a gani wanda zan iya kaiwa, Tau Allah dai ya,rufa muna asiri kawai zan dai tafi nai kallon nima kada a bani labari, Daga inda yake zaune Ibrahim kanin shi yafito yana fada mai mama tace yabada dari a,sayo iccen da za,a girka abinci, Ya dan lalaba aljihun rigar sa ya ciro wata tsohuwar naira dari duk ta yage ya mika mai, Sai zuwa wani lokaci ya dan rufe shagon ya,shiga cikin gida don yaci abinci, Ya,samay ni a bakin kwata,ina wanki daga ind nake a duke saye da hijjab dina kamar kullun zan iya jiyo hirar su da Umma , Inda yake fada mata cewa gasar da akai shella a akai lokaci ya gabato don wani satine za a yi, Umma tace Allah ya,ba mai rabo sa,a masu kudi da ma,aikata suke da abinyi , Shikan tallaka ai iyakar shi kallone kawai da ihu ko tafi don farinciki, A daidai lokacin da nake shanyi kayan Umma ne dana Asma,u na wanke, Hamza ya kasa daurewa murya kasa kasa yake cewa amma Umma wanki harda na Asmau kuma, Umma tace tau rasa kunya anya kuwa yaron nan ida ban samaka waigi da bakace kada yarinyar nan ta taimaka min da komai a gidan nan ba, Yace Umma ba hakana bane yariyar nan amana take a gare mu kin ga,wasu abubuwa bai kamata ace tayi ba, Tunda sa,a guda suke da Asmau mai zai hana a raba masu aiyukan nan a tsakanin su su dinga yi tare, Tace amma ita Aisha aure, tazo yi ba zaman gida ba don haka zaka bari tayi bautan aure ko, Watau mama ba hakana bane mutane masu shigowa sune zasu iya fita,da zancen har ya koma a gidan su, Umma tace yanzun dai tunda ban iya,ba shike nan zan baka matarka,sai kayi mata training da kan ka, Umma tace dama ni da akwai dalilin da yasa nake mata hakan don ta saba, Ranan da dare muna daki nida Asmau muna hira sai ga,Umma tazo ta tsaya daga kofa tana cewa Asmau ki dawo daki kibashi guri ya,shiga dakin matar shi, Jin abinda Umma tace yasani jin gabana ya fadi dammm ke nan tana nufin adakina yau Hamza zai kwana, Murya umma ce naji tana cewa Aisha ga amanar dana nan gare ki da fatan zaki kulsmin dashi yadda ya kamata kada ki manta cewa Hamza maraya ne, Don haka ki bi min shi a sannu banda turasasa shi a ksn abinda baida halin yinshi ace sai yayi su,, Ina jin tafiyan ta zance mama Rahana ya fado min a rai cewa kada na taba,bari miji ya,shigo dakina ya,samay shi ba gyarare ba don haka na mike a hankali na fara gyara,daga zanin gado zuwa dan shara da,sauran su duk da kuwa ance sharan dare baida kyau a musulunci, Na,dan fesa kamshi kafin a ce a haka daki ya canza kala kamar bashi ba, ne, Na saci jiki jin umma tana daki tana magana kamar na,siri da diyan ta na,dan kara yin wanka, Tsab na gyara jikina abinda baku fahinta ba,shine duk hakan bada wani manufa nakeyin su ba kawai fadar da,akai min ne nake amfani dashi,bawai don zan kwana da miji bane, Ina gamawa da,sauri na,dauko turare na na mutsuka kamar yadda gwagona tai min bayani, inyi dashi, Kaina wanda aka yarfawa kitso na dunkule shi a cikin yar hulata dana wanke da rana, don yawan gashi da tsawo gareni Nasaka yar rigar barcin da mama hanne tace min indinga sawa idan zamu kwanta,, A,bakin gado na dan kwanta na,dunkule kamar wace ke tsoron wani abu, Sai dare Hamza ya,shigo gida inda Umma tai mashi bayanin cewa ya tafi dakin matan shi yau Asmau a gunta zata kwana, Ya shirya kamar yadda ya saba duk shi dan tallakawane ammw akwaishi da tsabtan jikin shi irin wanka wanke baki da aski, Wankin tufafine dai bai faye samu time din yi ba,saboda ujila, Banji shigowan shi ba saboda barcin da ya fara dibana a lokacin sai dai ji da nayi a hankali kamar ana kiran sunana, Na mike zubur zaune daga kwancen da nake cikin dan rudewa ina fadin yaya Hamza ina wuni, Ya amsa min da cewa tashi zaune muyi magana dake, Ba musssu na zauna dan nesa dashi kadan kamar maijin tsoron wani abu, Tambayqna ya farayi da cewa an yi wani abune a tsakaninki da Asmau, yau ? Cikin sauri na dan girgiza kaina ina cewa a hankali a,a, Shiru naji yayi sai kuma ya furzar da yar iska daga bakin shi yana cewa, Aisha nasan cewa ke yarinyar ce mai hakkuri don haka kiyi hakkuri da irin abinda Umma tai muna, Din ban taba ganin wanda akaiwa irin hukuncin da Umma tai min ba, Duk da ita a ganin ta sone da kauna na ya kaita ga yi min hakan, Ta haramta min zuwa kusa dake don wani akida nata na daban can wanda baida dalili, Don haka nake mai kara,baki hakkuri don dan naman da yake kamar sunna na baki tun rada ya kamata na,sayo na baki Umma ta hana ta karbe, Yanzu tashi mu fita na rakaki kiyo alwala don dare yayi ko, Kamar yadda yace alwalan ne nayi tare da kara dan kimsawa, Sallah ya jagorance mu mukayi nidashi inda daga baya gama adduoin mu yake umurtana da na dawo kusa dashi na zauna, Adan takure na dan matso gab dashi na zauna a cikin jin kunya da fargaban zama a kusa da namiji haka gap da gap, Hannuwana na Hamza ya fara rikewa yana dan wasa dasu a hankali yayin da yake fada min irin dokokin dayake son shimfida min a gidan a matsayin shi na maigidana, Matsar da yakewa hannuwa sun fara canza,sallo don haka na dan fara kokarin bijire mashi a hakan, Yadan jawoni zuwa gare shi inda na, zunbule ina cewa don Allah Yaya Hamza ka daina kaga hakan baida kyau haramu ne,, Murmushi naji yayi inda yake rada,min a kunnuwana cewa ke matatace Aisha zan iya maki duk abinda naga dama, a tsakanina dake, Cikin kokatin fahintar dani da yake ne yaga cewa ba zan tsaya yabini yadda yake so ba, Sai kawai ya yi amfani da karfin shi kuciya ya debe shi ya amfka min yadda yaso, Ganin irin surar dake gareni wanda a kullun yake boye a cikin hijjabin da nake dunkule kaina a cikin shi, Kuka sosai na,dinga yi wanda ban damu da wai wani yajini ba a lokacin, Muryan Ummace mukaji tana cewa ke kada ki hada muna kan makwabta a gida fa a cikin daren nan, May kike nufi dama zaman ciye muna abincine kawai zakiyi ba biyan bukata, Hamza wanda yake kokarin lalashina naga ya dafa kan shi irin idan mutum dinnan ya shiga ukku, Takarashe fadan ta ta tafi tabar mu na inda yai ta bani hakkuri yana min nuni cewa hakan ai shine auren dama, Har saida ya,fahinci barci ya kwashe ni yadan gyara rufe min jikina ya kwanta rigingine ya soma tunane a ranshi, Ashe kallon da yake min da farko abin ba haka yake ba ke nan, Duk wani abinda da namiji zai bukata agurin diya mace Allah ya,hore min shi a jikina, Duk wani tunanen da yake kuma cewa nai karama ga abinda yske bukata sai yake gani ai na kai har na,wuce, Washe gari Ummu ce ta bubuga muna kofa tana cewa yafito ga ruwan wanka can a bayi takai mai, Kunyane sosai ya kama shi inda ya,amsa mata a,dan daddare sai bayan da yafito Umma,ta kai min nawa ruwa, Takara,koya min irin yadda zan gyara jikina,dakuma koya min daurewa,a tare da,miji, Bani ba rana har hamza da,yake danta a kunyace yake a,gidan @ ****** ********* ****** Soi sai nake kunyan hadu da Hamza ita ko Umma sai wani haba haba take da dan ta, Yashigo yana zaune zaici abinci rana Umma ke tambayan shi cewa ashe a cikin karshen sati za ai wana gasar nuna fasahan noma da kiwo, Yace eh Umma insha Allahu ina,son na leka gurin inyi kallo abinda yasa ni sauri dago kaina ke nan, Wanda yai sanadiyar hada idanuwan mi ni dashi amma kuma sai nai saurin mayar da kaina kasa, Zan iya cewa wanan ne karo na,farko dana na saka masu baki a,zance inda,nace Niko sai nake gani kamar mu gyara wanan waken naka da kuma zangamay dawo ai za,a iya zuwa dasu a gurin gwajin , Shiru yayi kamar mai nazari can ya mike tsaye tsamaka min da wanan nan ya gwadan roba y nufi guri da suke aje abincin gida, ZAINAB IDRIS MKAWA SEE,NABUN KU ' 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA RABBI NAJJINI MIN AL-QAWAN AL ZALIMIN 👏👏👏 Abakin murhu nake duke ina,hura wuta don iccen baya ci saboda yana,da sanyi sosai, Sallama naji wanda muryan mai sallaman yasani saurin dagowa daga gurfanen da,nake , Kubura,ce tare da,wata kawar ta wace islamiyan mu guda,da ita, Na dago da fara,a ta ina masu sannu da,zuwa babu kallon arzki daga fusksn Kubura din dan gara ma kawar ta datake cewa a,a amarsu ta ango, Shine akai aure ba,a fada muna ba Aisha balle mu zo walima,, Nai murmushi kawai inda na shiga,gaba da niyar na,fara kai su gurin Umma su gaisa, da ita, Ke dakata ina zaki damu kuma ina nan dakin uwar mijin nakine ? Kubura ce ke tambayana acikin wani murya mai kama da commad, Naja na tsaya ina cewa eh dakin ta ne ina zaku gaisa da itane ai, Bashi muka,shigo yi ba dama bintu ce tace na kawo ta ku gaisa, Din shi kikaga na shigo wanan gidan idan bashi ba ta,wani kada kai alamar a,a , Juyawa nayi don kai su nawa dakin amma,sai naji muryan Umma a bayan mu tana cewa, Au to mara mutunci bazaki gaishe ni ba kenan har kike wani dakawa yarinya tsawa,, Kubura batai magana ba,sai kara shigewa gaba da,tayi zuwa dakin nawa tana wani taunar chewing gun kas kas kas, Ta shige gaba wanda dama nasan cewa tashigone don taga yadda dakin yake, Duk da dakin yana a tsabtace amma Kubura sai wani dan yatsune fuska take tana mayde baki inda na,shimfida masu tabar ma don su zauna , Amma sai sukace a saman gadona wanda yasha gyara zasu zauna, Nafita na dauko wani cup din silver mai hannu na debo masu ruwa a rabdar kasar dake daga gefen dakin Umma Rabi, Na samay su suna dube dube a dakin suna dariya a tsakanin su , Ban damu damay sukewa dariya ba na dire masu ruwan a gaban su ina ce masu bissimillah ga ruwa nan, kusha, Kallon ruwan sukayi shekeke sai Kubura din ce tace haba Yar Agwai aiko a gida kin san ban shan wanan ruwan balle na,wanan gidan naku, Bintu ce tace haba ai kuwa zamu sha,don kada na rantse ban sha ruwan gidan Aisha ba, Ta dauki cup din ta dan kurba kadan ta aje tana cewa ta gode nadan yi murmushi, Suna shirin barin dakin ne sai ga Hamza ya shigo gidan hannu shi dauke da yar ledar da yai cefane a cikin sa, Ganin su Kubura din yasa shi yadan daburcr yana cewa ,a a bakine a gidan haka, Sannun ku da zuwa ince kin basu ruwan sha dai Ausha ? Kaima kasan ai bamu iya shan ruwan wanan gidan naku don haka ruwan ku ya huta kawai, Daga gurin da nake tsaye na dan ji kunyar zancen na ta na zaci maganar zai soki Hamza din, Amma sai naga yana murmushi kawai yana cewa hakane fa nasan da hakan don yar gidan sarkice ta shigo, Tajuyo inda nake ta wani dan wurga min harara tana cewa ke mu mun tafi sai kuma wani jikon, Suka fito sukabar gida batare da ko sun kalli inda Umma take ba a bakin kofar ta tana kawar da kaya, Kunya ne yadan kamani abinda Kubura taiwa Umma din, Mara kunya ai duniyace ita zata sauke ki da kanta daga wahalar daukar ta da kikayi, Cikin dan dari dari na karasa gurin da Umma din take ta dauki tsintsiya za tai shara, Ta wani dan wurga min harara tana cewa bazan yarda wanan fitsaratar yarinyar tana shigo min gida ba, Na kara mika hannu don na karbi tsintsiyar , Tace na barshi zata karasa abinta a hasale take tana son sauke haushi a kaina, Kwanonin da akaci abinci na shiga tattarawa tare da juyawa zuwa inda nake kokarin hasa wutar girkin dare, Hamza yafito bandaki dauke da buta a hannun shi yana kokarin gyara zariyar wandon shi, Idanuwan shi a kan inda nake a gurfane ina kokarin hura wuta, Naji muryan shi yana cewa ai Umma shiyasa nace a sayo wani iccen tunda wanan din yana da sanyi sosai, Tamike daga sharar da takeyi zufa a goshin ta tana cewa, Wai Hamza may ke damin kane naga fa duk ka canza a kwana biyun nan, O saboda bakasan zafin neman kudi ba,shine zaka koma,sayen wani , Abinda Umma tace yasa hamza saurin dagowa ya dan dubeta yai saurin kawar da kanshi bai sake cewa uffan ba yabar gidan, Haka a wahalce taketa faman hura wutan da dan samo wasu yan abubuwan da zasu saka wutar yadan kama da sauri, ****** ********** ****** Bayan dan wayan da tayi da,mai kiranta a lokacin ta aje wayan a saman tsohon mirror din dake dakin mama saude, Ba,wani dogon shiri tayi ba tafito daga dakin cikin doguwar riga baka ta rufe kanta da,wani gyale mai laushi, Ta,dauki wayan dake a saman table din tana cewa Mama zab dan fita nan ba nisa zan tafi ba, Gurin da yai mata kwatancen motar shi ta nufa, inda ta samay shi a tsaye cikin fushi yana dan buga kafan shi guda a kasa, A murde taxo mai tana cewa kace nazo kana da magana dani ? Yanzu Kubura kina ganin cewa auren Nura da zakiyi shine mafita a gare ki, Mutumin da baida mutunci ko kadan bai san darajan kowa,ba a gari zaki sa kanki a tarkon sa, Dakata malam ina mun wuce wanan zancen dadewa ban son mayar da zance baya, Na fada maka gaskiya ba yaudara a cewa shi din na tsayar don a,shirye yake da na aure shi ko da yau ne, Sabanin kai da morewan rayuwa kawai kake bukatan koda yaushr muyi tayi bamu nan bamu can, Ga matsin da muke samu nida mahaifiyata a gurin babana tunda dan matsiyatan nan ya sakani a zancen auren shi, Mansur yadan furzo iska ya shafi fuskan shi yana cewa yanzu daga ke har mahaifiyar naki may na rage ku dashi, Tace komai don yadda Nura yake zuba min kudi ko kwatan shi baka iya min kawai kai a more rayuwane naka, Yace ok naso a ce kin tsaya kin fahinci ko waye Nura ki kawar da zancen auren shi a ranki, Tamike tsaye tana cewa bazai yiyo ba daga yau kuma na fada maka cewa shine zabi na don haka kabar wanan kudirin naka na son yaudara na dawani zance wai Nura ba na kwarai bane, Mune fa yan bariki kar ta san kar a tsakani na dashi, tsuki tayi ta buga marfin motan ta fara tafiya Mansur yana kiran ta amma bata tsaya sauraren shi ba ta wuce abinta, Mansur yaso ta tsaya yadan bata wani labari a gamay da Nura din amma hali irin na Kubura halin tsiwa ya hanata jin komai a kan shi, Ita dai bukatan ta tasamu gidan hutawa ta kuma hango shi a gidan Nura din to may zai fada mata kuma a hakan, Kamshin da tabarshi dashi a,cikin motar shi ce yadan shaka inda yasan cewa yayi missing din Kubura din sosai, Kallon ledojin da yai mata tsaraban irin abubuwan da yasan tana,bukata,ne a,baya yayi inda wani haushi ya dan kama,shi yaja motar shi yabar gurin a fusace , ****** ********* ****** Waken da Hamza ya debo acikin waken da ya noma shi take ta faman gyara kusan kwana biyu ke nan da fara,wanan aikin, Ga girkin gida ga aikin waken da takeyi wanda Hamza din yaso yayi da kan shi amma sai Umma tace yabar wa Aisha don bata komai aikin zai rage mata zaman kadai ci, Da Allah ya azamin dan fasaha,sai na,diga daukan manyan irin ina tara su guri daya wanda hakan yasa waken dana tsince din yazama gwara gwara gwanin ban sha,wa, Irin farar dawa wanda akabawa hamza din ya,shuka sai dai bai samu abin kirki ba don ba kudin gyaran gonan shine yagyara su tsab gwanin sha,awa, Gari ya,cika da jama,a tun ana saura kwana biyu wasan gwajin da za,ayi din, Aikin gyaran waken da nakeyi ne ya,dauke min hankalo inda har rana yayi ban sani ba ina,daga cikin dakina,saboda rana ya fito gashi ba innuwa a,gidan, Umma ce naji tana kwada min kira tun kafin na,amsa take cewa yau baza,a girka muna abinci a gidan bane Aisha, Abinda yasani saurin mikewa ke nan na fito daga dakin da,sauri, inda Umma ta hau yi min fadan cewa zan barsu da yunwa ita da diyan ta na shige daki na kwanta, Shigowan Hamza din ke nan a lokacin yake kokarin gaida Umma din yake cewa batare da ta amsa ba, Yarinya ta shige daki abinta zata barmu mu yini da yunwa don kiyya, irin ta matan yau, Yace ke ina waken da na saki gyara sauran na koma dakin don na dauko wanken inda Umma tabi da fadan tana cewa ai inda sanyi jikine irin na Aisha yanzun haka bata gyara ba, Nafito dauke da waken cike a wani roba nawa mai fadi , Abinda ya san sasauta fadan Umma din ke nan tace kai shi kumq wanan irin a ina aka samo shi haka,? Hamza yace wanan dai namu din ne Aishan take gyara tunda safe dana barta dashi, Hannu Umma din takai cikin waken tana dan juyawa a hankali, Sai ta juyo inda Hamza din yake tana cewa amma Allah yasawa wanan wake ido,da kwari wallahi kamar bashi ba ya samu gyara sosai, To ai saiki ce min ba kwance kike ba aiki kike a dakin amma kuma a zauna ba,aci bane, A lokacin har na share gurin murhu ina kokari tura ittace don tuwon gatin masara ne tace zamuyi da miyar busassan kubewa , Suna hiran su ina,aikina,sai dai kallo guda,mutum zai min ya fahinci cewa na ramay don nadan fada,sosai, Asmau tashigo gidan inda take cewa tun kafin ta kai zaune wallahi yunwa nake ji may kika dafa muna ne, yar Agwai, A cikin wani irin zafin nama Hamza din ya dago kai yace mata cikin dakiya kada na karajin wanan sunan a gidan nan, Tace a cikin yar shagwaba to ai sunar ta ke nan ko, Umma tace tunda yace baya son kina kira mai mata da wanan sunan to ki bari kin dai san halin yayan ki, ba ruwana, Hamza yace Umma bai dace wanan sunar da yan gidan can ke kiranta dashi muma anan mu kirata dashi ba tunda ba,sunan alheri bane, Tau kaji mai mata fa nine zaka fadawa cewa ga,abinda ya dace da matar ka a gidan nan, Yana kokarin daukan roban waken dake a gaban shi ne Umma ke cewa yanzu kana ganin cewa zasu barka kayi wanan gwajin da dan wanan, Yace Umma ki samu na albarka acikin al,amarin don shi muke nema, Umma tace Allah yasa mu dace Allah ya sanya alherin sa ya amsa da amin tare da kokarin wucewa da roban inda na fito dashi, Da,sauri na karaso na karbi robar daga hannun shi ina niyar mayar wa dakina, Umma tace kai shi can dakina ki aje gefen gado kada ya kuma samu matsala, Ba mussu najuya da roban nakai dakin ta kamar yadda ta umurce ni dayi, Na gama abinci da wanan uwar ranan narabawa kowa sai dai da yake garin baida yawa abincin bai kai ba, Gab da Hamza zai shigo gidane yaji Umma tana cewa sai na juyewa Ibrahim nawa abincin nazo ta yanka min nata, Ya karaso cikin gidan yana cewa haba Umma ita da ta dafa ba,a bata taci mai isar taba sai Ibrahim wanda ke waje yana samun abu yana ci za,a ce ta ajewa kason ta, Ya juya inda nake yana cewa na dauki nashi kason zai fita ya samu abin da yaci a waje shi, Umma bataso hakan ba sai cewa tayi na bar ma Ibrahim na Hamza din naci nawa, Ibrahim din ya,shigo gida nan ya zauna zai ci a binci ganin kayan abincin dan uwan shine yake cewa shi Yaya Hamza mai zaici dana ga anbani abincin shi, Nan Umma ke cewa shi yasani don matarshi bata samu rabo ba,shine yai fushin zuciya yace abar mata nashi, Da sauri Ibrahim din ya,dago kai yana cewa amma, gaskiya Umma bai dace ace matar yaya,bata samu abinci ba itace ta girka ba, Kai kama min bakin ka kafin na bata maka rai waya fadama bata,samu ba, Wai don suwa nake zaune a haka da kowan ki zai dinga ganin laifina haka, Ibrahim wanda yakai loma a bakin shi yace Umma ai itace wai naga ya kamata ace taci tunda amana take a gurin ki, Kadan yaci da,alamar a koshe yake nan ya mike ya kwaso kayan abincin yana ce min gashi ki kara kin ji Aisha, Ina zaune inda na idar da,sallah nadago kai acikin murmushi nake cewa dadai kakai wa dan uwanka don shine bai samu abincin ba, ****** ********* ****** Motocine kala kala ke yawo a,cikin garin inda jamian tsaro suka cika ko wani lungu da,sako na garin da tsaro, Wanan dalilin yasa mutane zuwa kama guraren nuna show din nasu da,wuri kafin guri ya cika, Yan kauye dama makwabtan gari duk sun halaro gurin wanan taron mai dibin tarihi a,rayuwa, A gurin zakaga manyan namun daji wanda akadade ba,a gan su ba da kuma dabbobi da ake kiwo a gida sunci sun koshi don samun kiwo na kwarai, Taro yai taro inda har da turawa da, sauran mutanen kasar waje suka shigo don kallon wanan taron, Hamza ma ba,a barshi a baya ba gurin zuwa da nashi kayan show din amma yana ganin irin abubuwan da wasu suka kawo duk sai jikin shi yai sanyi sosai, Yana ji a,rayuwan shi kawai ya koma gida saboda babu wanda zai ko san cewa yana gurin balle ya kalle shi, Zuwan manya naki na kasa yasa gurin ya kara rikicewa gaba daya inda akafara bude taro da,addua tare da fatan samun sa,a gama su nasara, Layin masu gwajin amfanin gona daban inda haka ma layin masu gwajin dabbobin gida dana daji daban su ke, Ga masu wasan gargajiya suna wasa kowani kabila da kalar tasu shigar a gurin, Tafe suke inda duk gurin da wanan shugaban ya tsaya za,a bawa,mai wanan amfanin gonar nomba ta kyauta, Tafe suke tawaga takai tawaga ta manyar ma mutane masu bada zabi ga jami an tsaro nata,bin su bayan su, Gaskiya kaya sunyi kyau sunga abinci masu amfani yadda yakamata don basuyi tsanmanin samun abinci masu inganci irin haka ba a kasar, nan, Wani manomi ne ya baza kayan amfanin gonar shi mutane sun taru sai kallo akeyi yadda,sukayi kyau sosai, Maigirma babban bako ya juya don zuwa kallon wanan shagon na,wanan babban manomin, Abokin tafiyan wanan bakon wanda yazo daga kasar waje don ganin abinda ke guda na, Wani dan saurayi matashi mai karamin shekaru ya hango can nesa kadan da,wanan rufan , Yana tsaye da kayan da yazo gwaji a cikin wasu kananen roba, guda uku, Kawai sai yaga burgewan wanan matashin da kwazon shi har ya kai ga yazo nuna nashi kayan amfanin ba tare da, jin komai ba , A hankali ya tako zuwa gurin wanan saurayin wanda duk yai zufa ga,rana tana kudar shi ga yunwa, A hankali mutmin yaduka ya debo wanan wake dake a cikin roba kursa kursa dasu, yana dan jujuyawa a hankali, Sai daga baya abokan tafiyan shi suka luracewa bai tare dasu don haka suka shiga neman shi inda suka hango shi a tsugune gaban wanan yaron mai kaya, Sauran jama,an suka yo a kansu suna kallon su a cikin mamaki don babu wani abin azo a gani a gaban yaron amma gashi maigirma babban bako ya zo gurin yaron, Shima,shugaban na wanan kasar diban wanke yayi yana dan juyawa yayin da,sauran yan tawagan suka shiga diba suna kallon Kowa sai yabawa da kyau da,girman waken sukeyi gwanin ban sha,awa,,, Nan ya jawo irin dawan da Hamza ya shigo dashi filin shima yana dubawa a hanakali, U Idanuwan jamaa yoyyy a kasu don su azaton su laifi hamza din yayi, Sun dauki lokaci a tare da,Hamza suna,mashi yan tambayoyi ya ba basu amsa sai cewa,suke interested, Daga karshe dai aka,rubuta sunan hamza din daga,cikin wa yan da za,a bawa kyauta a gurin, Nan aka karbi sunan shi aka juye wanan kayan a cikin wasu robobi na gwajin kayan agric din da aka zaba, Hamza ya koma gefe guda ya na sauraren su kamar yadda suka umurce shi da yayi, An dauki lokaci mai tsawo kafina agama wanan gasar gwajin kayan amfanin gonan da,akeyi, Nan aka soma kiran sunayen mutane ana fadin iri abinda mutum ya,burge bakin dashi daga fanin abinci dabbobi da kuma kayan ruwa, Can kamar a mafarki Hamza yaji ana kiran sunan shi inda ya,fara ratsa taro don zuwa inda ake kiran sunan shi, Nan wanan baturen ya daga hannun hamza yana fadin cewa Hamza matashin da yazo na,daya gurin nuna dogaro da kai har ya kawo amfanin gonan shi da,full confidence, Ga kuma waken da yakawo gwaunati tanq bukayar wanqn irin don wani gwaji da zatayi a kan shi don haka gwauti ta,sayi wanan waken akan gudu naira,,,,,,, Haba guri ya rude da,sowa da ihu da kuma tafe daga yan kallon da,sukazo na,sassa daban daban na kashen Africa,, Inda wanan bature ya nemi hamza da ya bashi full address din shi da in da yake da zama, Haba aikuwa hamza yana karba,sai kawai ya,saka kabbaraza fili da cikin zuciyar shi, ****** ********* ****** Ina zaune gurin dana idar da sallah na daga hannaye na biyu sama ina rokan Allahya rufa muna asiri duniya da lahira, Ina gab da zan sauke hannaye na ji murya Umma a cikin murna tana cewa o, o Allah nagode ma,Allah mun godema bisa wanan baiwar da kai muna , Ina kuke yaran nan kufito kuji abin arzikin da ya,samay mu a gidan, Jin abinda ta fada yasani saurin mikewa zuwa kofan daki do ganin may Umma kewa farinci haka, Babu kowa agurin na dai fito sai naji tana cewa yau kan Allah ya nufa Hamza ya samu yar ga Allah yasa shi cikin zabbabu, Yar fara wace ina ga ban taba yinta ba tun zuwa na gidan nasake ina cewa masha Allah ashe yaya Hamza Allah ya karba addun mu,, Uguwa baki daya zance ya karade ko ina kowa da abinda yake fadi a bakin shi, Wasu har dakari sukeyi wai har da mota aka bashi wasu suce ai mashin ne aka,bashi, Ga yan murna sun fara shigo muna gida gashi shi mai abin arzikin bai dawo gida ba har wanan lokacin, Saboda farin ciki Umma taje ta,auno muna shimkafa a,makwabta mudu daya tace nayi tuwo da,miyar sobarodo da busashen kifi, Ina aiki ina Allah Allah kafin na gama kafin yashi nayi wanka na dan kimtsa irin da naga mata sunayiwa maza jen su idan sun fita gurin neman kudi, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU ZAINAB IDRIS MAKAWA👑SARAUTAR MATA👑 0⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA RABBI LA TADHARNI FARDAN WA ANTA KHAYR AL-WARITHIN,,, YA UBANGINA KADA KA BARNI MAKADAICIN ALHALIN KUWA KAINE MAFI ALHERIN MASU ALHERI,,, Ranan haka muka wuni zugun zugun a gidan ba wani dadi rai alhalin tun bayan daurin aure bamu ga baba a gidan, Ba wani bukin da akeyi kamar yadda mutane sukayi zaton yi don uwar mai buki bata da shirin buki, Sai dai yan uwan baba sun dan taka rawa gurin ganin cewa, sun hada dan kudi sunyiwa mutanen dake nan dahuwar dafa dukar shikafa, Ummi suna daki da yar uwar ta acikin jimamay abinda zai fito daga gurin mutanen da,suka kira da yan uwa na wai iyayyena, Mutanen da,sam basu damu dani ba a matsayin yar su, Don ni da farko ma nayi zaton cewa ko banda ubane don ganin irin yadda ake tsangwama min a,gidan Baba Mudi mijin uwata, Alhalin gashi shine uban yayena da kuma kanne na Ni kadai ce Allah bai nufa nafito daga tsatson shi ba, Sanadiyar fitar da mama tayi a gidan bayan haihuwan yaya Audi, Na fara fahintar hakan ne don ganin irin tarin damuwar da mahaifiyata take shiga a kaina a gidan, Nayi zaton cewa Baba shine mahaifina amma saboda irin bakin cikinnda yake yawan cusa wa mahaifiyata dani agidan yasa na soma fahinta cewa bashine mahaifina ba tun ina karama, Abu na biyu shine irin yadda Baba ya dauki son duniya ya,dora a kan yan dakin su Kubura duk da dai namu diyan daki maza ne, Gashi da azahiri zaka zaci duk diyan gudan bugu daya yake masu a kan so, Amma idan ka tsaya sosai ka natsu sai kagano tarin kin jini da yakewa diyan mahaifiya na, Dan abu kadan zasu yi kaga kyara da hanttara daga gare shi, kodan kuskure kadan ne yanzu za,a jishi dasu har ya hada da uwar mu, Sai da idan ka shiga gidan zaka ga matan gidan suna normal life din su a tare ne tankar babu k8shi a tsakanin su , Hakan ma diyan su komai a tare sukeyi komai babu wari a tsakani nice kawai suke nunawa wari a gidan babu boyo ko shayi, Fitar mahaifiya ta agidan yadda mama Rahana ke fada min tace ya faru ne ga hadin kan ds matan gidan sukai mata wanda matsi yai yawa har takai yan uwan Ummi sun bukaci da yasauwaka mata a lokacin , Bayan komawan Ummi garin su sokoto ne tana cika idda ta,auri wani dan uwansu saidai shi bafillacen daji ne yana zaune a gari yana yar sanaan dabbobi, Sai kuma zaman ba,a kai ko ina ba ya,watse saboda rayuwan ta yana gurin "ya"yan ta da ta bari a gidan Baba Mudi, Wata uku ta kashe auren tafito ashe da akwai rabon ciki a jikinta gashi har ta cika idda ana batun komawa gidan malam Mudi sai ciki ya,baiyyana don haka aka dakata dole sai da ta haihu da yar jaririyar ta ta tare a gidan wanda tun a lokacin take ta samun wani kalubalen rayuwa daga maigidan dama abokan zaman ta dakeyi a boye, Suma abokan zaman sun gwanmace dawowan Fatima gidan ne akan sabon auren da yaso ya kara a lokacin, Don haka zaman nasu ya kara zama na kwarai babu mai tsangwama,wa wani daga cikin su a,fili sai dai kishin boye wanda baa rasa ba can, Wani ikon Allah gaba daya gidan malam mudi babu yaro mai hazaka irin Aisha din, Duk wani karatun da zatayi, zaka,ga tazo na daya a gurin amma duk da hakan babu yabon da take samu, daga gurin maigidan sai ma ya gune cewa andai batane kawai ba,wani ilimi da tafi su dashi, Haka rayuwan Aisha ya kasance a gidan da dadi ba dadi, har zuwa wanan ranan da Aisha ta taimakawa Baba tafitar dashi daga kunya, ****** ********** ****** Gidan su Hamzs babu wani abinda suka gudanar akan zancen don basu ji komai daga gurin Baba ba, Suna sauraren dawowan shi don anzo ance baya gida tun da safe, Ashe shi baba tanufi sokoto ne gidan iyayyen Aisha din ya,sanar dasu irin yadda abu ya kaya,, Da,farko kanin mahaifiyar Aisha ya dauka suka tafi can garin gurin yan uwan mahaifin yariyar don shi uban yanzu bai kusa ya kara gaba ko,, Bayan an fito, daga massalaci suka zauna dasu inda a cikin girmamawa da mutuntawa suka karbe shi don ya rike masu jinin su a gurin shi, Nan Baba ya,fara koro masu da bayani abinda yake tafe dashi tare da sheda masu cewa yazo ya basu hakkuri a bissa kuskuren da yayi na rashi sanar da,su Har ya shige gaba ya,daura wa yarsu aure ba tare da sanin su ba, Sunnuna rashin jin dadin sanar dasu da ba,ayi ba amma kuma sunyi mashi godiya da nuna cewa yana da hakki a kan yarinyar ai tunda shine ya tayar da ita, a gurin shi, Nan suka cecmai idan lokacin da yarinya zata tare a gidan mijin ta yayi ya sanar dasu zasu shigo gurin bukin , tare da abinda Allah ya hore masu, Wani irin sanyi malam Mudi yaji na samu mutane masu saukin kai, ya kara,masu godiya yabar su suna mai godiya, sumq din, akan rikon yar su da yayi har da aurar da ita, Sun hado shi da dan tsaraban kauye cewa yakaiwa iyalin shi agida ai masu godiya, Ba karamin farin ciki Baba ya,dawo dashi da ruggan mu gurin iyayyena, Sai da dare ne ya samu iyayyen Hamza suka dan tattauna dasu yana mai basu hakuri akan sauyin da suka gani , Inda yake cewa yai hakane don ya gwadawa Saude da yar ta cewa idan har bai da iko da isa akan yar cikin shi, To ga diyan bayin Allah sunyi mashi biyayya yadda ya kamata, Sun yake zancen cewa zasu ba uwar Aisha dan lokaci yadda zasu yi dan shiri a tsakanin su, Hamza wanda abin duniya ya kaiwa,ko ina, a rayuwan shi yarasa yadda zai yi da,rashi, Aisha yar karamar yarinya kuma kazama dabata ko san yadda mata,suke gyara,ba,ahine wai yau take a matsayin matar shi, Ya dan gyara juyawa daga saman yar mokaddan katifar da yake a,kwance sama yana mai nazarin siffan Aishan yarinyar da koda yaushe a cikin hijjab take a dunkule baka taba gane kalar surar ta, Washe gari yan abokan shi da suke zama a,shago suka,dasa mashi sheri da,wasa irin ta angwanne, Umma Rabi ce sukai ta tausan shi har ya hakkura da zancen auren Aishan don gudun kada ya budawa malam Mudi kasa a ido, Bayan sati, guda da,daurin auren su ya na zaune a bakin shagon shi suke jin ana yekuwar cewa mai gari yana neman duk wani wanda yasan cewa shi manomi ne don akwai bayani akan gagarumin wasan gwajin amfanin gona da za,ayi, a garin, Wanda manya mayan baki zasu shigo daga sassan kasan nan ta ko ina don kallon wanan amfanin gonan na manoman kasar,, Jin wanan shelan yasa mutane tururuwan zuwa kofan gida sarki don jin karin bayani daga bakin shi, Abinda yai sanadin jefa zukatan mutane da dama a cikin nazarin shiga wanan gasar , Daga ciki harda Hamza cikin masu nazari yadda zasu kokarta,su kawo nasu amfanin gonan a,wajen gwajin mai taken suna AGRIC SHOW, Daga dangin Hatsi, kayan labbu, dabbobi kayan ruwa da,sauran su, A lokaci guda duk gari ya rude kowani gida zance a buguda akeyi kawai, A wanan lokacin kuma uwa da diya a gidan malam Mudi suna a cikin matsi da,tsangwaman matan gidan, Duk da,su suka nuna,basu son auren Hamza din da kansu amma,suna ta,sake magana a tsakar gida, Har da,atika wace take bayan Saude da,yar ta,don muna funci kawai don son halin kishi, Hakan yasa,a koda yaushe mutum ya shigo gidan zai samu Fatima daki da,yaran ta,suna yar hiran su , Aisha wace zuwa yanzu abin duniya ya kaiwa ko ina tana,mamakin irin yadda tai wanan subul da,baka har tace wa Baba ayi wanan hadin auren da ita, Alokacin tausayin Baba ya,raja,a a kan ta har yakaita ga furta,wanan zancen a gaban shi, Umma Rabi ta,umarci Hamza da ya hada yan abubuwan bukatan rayuwa,a,kaiwa, Aisha a gidan su, Hamza wanda har yanzu ganin zancen yake kaman a mafarki don har yanzu ya kasa gaskanta al,amarin cewa wai Aisha a matsayin matar shi take, Sabulun wanka Sabulun wanki omo manshafawa dasauran Sune aka hada a cikin wani leda akabawa Halima sister din Hamza din takaiwa Ummi Fatima, kayan ace inji Hamza din, Tun shigowar yarinya gidan da kaya su Atika da mama Saude suka shiga ya da,magana a tsakar gida, da cewa, Iyakar ke nan tsiya tsiya ankawo wa Amarya kayan tausa, , Wanan gayar tsiyar akai shi can gurin mubukata irin sa,amma ba nan ba dai, Atika tace ai adaiyi mugani uwa,kwance diya zaune, duk a kare a tagumay, Daga cikin daki Kubura ta,dago labule don taga abinda ake zance akai yayin da,tai arba da kaunar Hamza na kokarin shiga,dakin Ummi Fatima da dan leda yellow mai layi layin baki, dan kayan da baikai rabin leda ba a cikin sa, Tace tsiyatsiya ke nan dama a can ya,dace da akai ba nan ba, Ni kan ai nagodewa Allah da ya raba ni da gayar tsiya, Fatima ta tari yarinyar da mutunci tare da godiya,akai akai da haba haba da ganin ta a cikin mutunci inda tabawa yarinyar naira,Ashirin tace tukwaici ne, Kaf zance abin da ya,faru a gidan malam Mudi ba abinda Halima ta rage a bakin ta, Gaba daya ta tsiyayewa Umma Rabi shi a kunnuwan ta kaf, Abinda yai matukar bata mata rai sosai yadda ake cewa wai suna yi, Saukin ta,guda,shine yadda, Ummi Fatima ya karbi yarinyar a,cikin mutuntawa, Hamza yana,tsaye daga bayan Umma har yarinyar ta,gama bada labarin irin cin fuskan da akai masu a gidan,, Muryan shi Umma taji daga bayan ta ya fadin Umma kada ki damu da zancen su don su sai kiji fiye da haka daga gare su, ma, ai, Yafita zuciyar shi na mai kuna yadda yake jin zafin irin wanan gorin da Saude da,yar ta,har ma,da,abokiyar zaman ta dayan, ****** ********** ****** Duk abinda Aisha ke yi hankali ta yanzu ya koma ga zancen Baba, da yake mata a ranan daurin auren ta, Ta dan gyara kwanciyar ta a hankali tare da dan lumshe idanuwan ta tana mai dan hade miyau masu daci, Ta dan kara gyara lumshe idanuwan ta tana mai sauke ajiyar zuciya a hankali, Ki kwantar da hankalinki Aisha wanan aure naki Allah yai mashi albarka Allah yasa muce gwamma da akayi, Saudayawa alheri kancin ma,bawan shi ta hanyar da bai zata ba, arayuwan shi, In har Umma Rabi da danta zasu rike min ke amna Aisha sai ince zaman ki a,gidan su yafi min zama a gidan nan, Zaman da kike a gidan nan a cikin wahala, tsangwama da shagube, Sun manta da cewa Allah ne bai nufi ki fito daga cikin tsatson su ba kika fito a can wani gurin na daban, Wanan hattaran da tsangwaman da suke maki a gidan nan kiris ya rage hawan jini ya kamani a kan hakan, A hankali Aisha tafara dan kuka a hankali don kada mutanen gida suji muryan ta, Washe gari sun tashi da,safe ba fashi daga duk wani aikin da Aisha din ta,saba yi a gidan da,safe, Da ita akai komai amma sai Umma saude taki saka,wa Aisha dan kunun kokon da take saka ma ko wani yaro a gidan da,dan kosai din su kwara biyu a matsayin abin karyawan su, Yau Saude ta hana wa Aisha wanan kosai din haka abincin rana ma again, Malam Ummi ta sama da zancen take tambayan shi ko shine ya hana a sakawa Aisha abin karyawa a gidan shi, Kafin ya ba da amsa buty suka ga mama Saude wace take kamar a jirace a bayan su ta,shigo tana cewa, Nice nan na hana mata ba wai wani yasani yin hakan ba, Ai aure take yanzu don haka sai taje can gidan mijin nata a saka mata shida keda alhakin ciyar da ita yanzu, don duk wani nauyi nata ya rataya a kanshi yanzu, Malam Mudi wanda kr reacting kamar wani shanyaye sai cewa yayi ai zata tafi gidan mijin nata kowa ma ya huta , Ummi bata samu bakin magana ba,sai kallon yadda Mama Saude ke faman budan baki tana vin mutunci wa mijin nasu, Ummi ce ta katse su da cewa Aisha zata koma gurin mamanta Rahana har zuwa lokacin da zata tare a gidan mijin ta tunda abinci da ake bani ni kaina ba isa na yakeyi ba balle nace zan dinga ci da ita, Daga fadar haka tabar daki inda ta samu yar ta Aisha take fada mata cewa ta,shirya zuwa gidan maman ta Rahans, Da sauri Aisha ta dago kai tana kallon mahaifiyar nata don son tagano ko anyi wani abu a tsakani, Amma sai bata iya hango komai ba a fuskan uwar nata,don haka ta dan mike daga zaune ga yunwa,da ya damay ta a,rayuwanta,, Yan tsunmakaranta ta hada a cikin wani bakin leda bag mai giwa, Ta,dawo daga kofan daki ta zauna a rakube tana kallon yadda yau zata tafi tabar Ummin ta, a cikin wanan yanayin zaman hakuri da tsangwama da take gani daga kishiyoyin ta ga,goyon tagwaye a,tare da ita ga,wahalhalun duniya iri iri a gidan, Bayan Ummi ta goya hassan ta umurci Aisha da tagoya hussai din taku ma umurce ta da ta je suyi sallama da su mama saude da,Atika, Ba,wani amsan da ta samu sai dan tabar bakin da,suke suna cewa umma ta gaida Aissha yau kan zamu sha iskan rahama gida ba yar agola a cikin sa, yar gola kiwon Allah ya isa, Sai suka tafa tare da,shewa suna masu rangada guda, Akarata can inda talauci ya yanke cibi mugani, Tafiya suke duk zukatan su a,cakushe saboda bacin rai don har Ummi din, yau ji take tankar tabar gidan malam Mudi din gaba daya, Suna jin shewan mutanen gidan a lokacin da suka fita suba cewa yau yar agwai an tafi, Atika tace yau kin muna maganin wanan shigiyar yarinyan mai kama da mayya kawai, Duk Ummi tana jin su amma ta kyalesu kawai suka,sa kai zuwa gidan Mama Rahana yar uwar ta, ****** ********** ****** Anty Rahaba ta gama komai na yinin ranan ta na,zaune daki ita da,yaran gidan suna kallo Ummi ta,shigo da,sallama, Mamakin ganin ta su keyi a lokacin saboda ba,al,adanta,bane fitowa uguwa da,dare, irin haka, Daya bayan daya yaran suka watse daga don bawa yan uwan guri saboda su sirint a tsakanin su, Bayan gaisuwar da,su kayi a tsakanin sai yar shiru ya biyo baya nan mama Rahana take tambayan ko may kuma ya faru, Ummi Fatima tana kuka tana bawa yar uwar ta labarin abinda ke faruwa a gidan su yadda matan gidan yanzu suka dauki kahon zuka suka saka mata ita,da yar ta,a gidan da kuma hana mata abincin da akeyi a gidan, Ummi ta karasa acikin wani irin kuka mai ban tausayi, atake rayuwan yar uwar nata zuciyar ta ya, baci sosai take, magana a hasale da cewa ni wanan al,amari nagidan ku yana,daure min kai wallahi, Yanzu ace har a hana ma wani abinci a cikin gidan ka kuma shi maigidan bai dauki mataki ba a kai Nan suka yanke shawaran cewa Aisha ta zauna a gurin Rahana har zuwa lokacin da za,a kaita gidan mijin ta, ****** ********** ****** Zancen duniya baya boyuwa don haka,barin gidan Aisha da,kwana biyu labari ya fara kewaye uguwa cewa saboda auren da malam Mudi ya daura da Aisha , Su mama Saude sunyi sanadin da yarinyar tabar gidan da zama zuwa wani gidan irin tsangwaman da ake mata a gidan, Haka zancen yai ta,yawo abinda ba,ayi aka dinga fafin cewa shi akayi a gidan har maganan yazo kunne Umma Rabi, Hakankinta ya tashi don ji irin wullakancin da akaiwa yar mutane saboda dan ta,da ta aura don ba,a bari yai kunya ba, Umma Rabi tasa,a,fara gyara daya daga cikin dakunan gidan inda yaran zasu zauna, Tsohon part din mahaifin Hamza din wanda yake ciki da falo ne sai dai ba masu girma bane sosai haka sune ake tawa dan gyara don su zauna a ciki, Dakin ya tsufa sosai amma dole haka zasu zauna din a ciki ,tunda basu da wani, Yanzu rayuwar Kubura ko ba,a fada wa mutum ba yasan cewa ta zama wata yar birni sosai saboda irin yadda idanuwan ta suka,bude, Shigar ta kawai zai nuna,wa mutum cewa ta sake fiye da tsanmanin mutum, Yau suna da wani dan liyafa da su yi wanda zai hada matasa masu yi da zamani da a gurin, Tayi kitson attachment ya mayar da ita kamar diyar yare, An mata gyara fuska wanda ya,sauya yanayin ta daga na diyan musulmai zuwa na diyan kabilu, Wani dogon riga ta,saka a jikin ta ya dane mata jiki sharp din jikin ta y fito tsab, Sai faman kiran ta ake a,waya cewa tazo an fara taruwa agurin sha,anin nasu, Uwar ta,sai murna,da farin ciki take ganin irin yadda diyar ta yanzu ta koma one in town, Sai washe baki take yayinda,Atika mishon batta da musulmi take faman koda yarinyar agaban uwar ta, Wani daga cikin diyan Atika ne yashigo yake fada masu cewa ga Baba nan zai shigo gida, Da sauri shige daki ta zuro wani katon hijjab a kanta, ta boye takalmanta a cikin jikin ta, A,a yau sai ina haka tace Baba littafin da muke hadda dashine zan karbi a gurin wata yar uwar karatuna tunda Aisha bata,nan, Tasako zance Aisha ne aciki don Baba din ya ya ji dadi ya barta ta fita, zuwa inda zata, Yashige part din shi inda ta,waigo tana,wa uwar ta dan bye bye din samun nasara ta fice abinta, Gurin part din ya hadu sai kida ke tashi samaru da yan mata masu karamin kwakwalwa suna ta sha,anin su gungu gungu a gurin, Kubura tana daga cikin masu gudanar party din haka zirga zirganta yai dan yawa a gurin, Daga inda yake tsaye yana iya hango wanan yawan sintirin da take a guri, Turawa yayi wani dan duniya yakira mashi ita kamar bazata zo ba can ta taso a cikin ragwada tana tako daidai har ta karaso gaban, A dan tsiwace take cewa malam kai ke kirana tana wani taunar chewing gun Yace a cikin kasaita da mu samu dan guri inda babu hayaniya da yawa, Motar big show suka shiga wace ke daga gedaya a Parker wanan shine mafarin haduwan ta da Nura wanda yaxo mata da kudi irin wanda take bukata da mafarkin samu,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA,,, 👑 SARAUTAR MATA 👑 0⃣9⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAHUMA AJINIR MINAL NARRR,,, Wanan novel din kada ku manta amanace tsakani na daku Allah yasa muci gaba da rikewa Allah yasa mu dace yan uwa Hakannan naci gaba da zama a gidan mama Rahana, inda nake zaune ba wani tsangwama komai, Ina gudanar da,al,amurana cikin natsuwa da kwanciyar hankali, Saboda gidan mama Rahana kowa yana nuna min so da kaunz a fili tare da yaba min hankali, Sai nake ji a raina dama ace tun farko a nan din nake zaune ina rayuwana, Matsalata guda shine kewar yan uwana da ke damuna tunda ban taba tafiya na barsu ba, Yanzu duk wani mugun hali a,Ummi suke nuwa shi tare da hattaran ta da yan diyan ta, A wani yanmaci lokacin ina da sati uku a gidan mama Rahana sai ga mahaifiyata tashigo da zancen wai zan tare a gidan mijina, Zance da yadaga min hankali kenan gabadaya wanda itama mahaifiyar tawa hankalin ta duk a tashe yake, ita,ma, Ummi tazowa da yar uwar korafin cewa bata aje komai ba akan zancen aure na yanzu gashi zance ya tashi, Mama Rahana ta kwantar wa da Ummi hankali da cewa shi aure ai alheri ne daga Allah dazaran ka dasashi sai kaga hanyoyin Allah suna budewa ta inda mutum bai tsan mana ba, Da irin maganganun haka har Ummina ta kwantar da hankalinta ta zurawa sarautar Allah ido Yan sayaya akai min duk da bangani ba amma inajin yadda su mama da Ummi ke shawara a,dakin akan zance na, A can gidan baba Mudi matan gida sai gori da habaici suke sakewa wai rana bata karya saidai uwar diya tai kunya, Yau gashi aure ya taso ummi bata aje komai da zatai min aure dashi ba ga shi malam Mudi ba dama ya taimaka min don sun kai karan shi a gurin yan uwan shi cewa yana maida hankalin shi ga yar agolan gidan shi fiye da,diyan su sosai, A tsayar da magana cewa a gidan mama Rahana za a guda nar da duk wani abinda za,ayi sai a kaini daki na, Raban da,za,a kaini a,ranan ne aka,sakani a lalai don ba wasu tarin kawaye ke gareni ba ni, Ranan na yi kuka kuka irin mai tsuma zuciyar mai sauraren ta , Don za,a kaini aure ba gado da shimfida irin ta,al,ada sai tabarmi da yan sauran tarkace kawai, Zokaga murna a gurin masu son gqnin bayan don sai shewa da raha suke suna yadda magana a gaban kowa, Cikin ikon Allah sai ga dangin mahaifina tare da na mahaifiya suka iso tare da mota fam da yan kayan su sai dai irin na kauyawa ne, Isowar su yasa guri yadan rude sai kama baki ake ana mamakin abinda,su kazo dashi, anan sabon gulma ya fara tashi kuma Da yamman fari yan uwa suka tasani a gaba wai naje muyi sallama da mahaifiyata da kishiyoyinta da,suka tayar dani, Mun shiga gidan da,sallama banyi tsanmanin sun karba muna ba,sai dai naji muryan Ummina, Mun shiga dakin ta tana zaune tare da,wasu baki mata mutum biyu yan uguwar mune da,take shiri dasu, Can daga kuryan dakinta kadan na,samu guri na,durkusa a kafana, Kaina ya,sade a kasa yayin da take gaisawa da matan da muka shigo tare, dasu, Daya daga cikin matance take cewa tau fadima ga Aisha nan mun kawo ta tayi maku sallama keda abokan zaman ki, Nan da nan naji idanuwana sun ciko min da hawaye kaina yana sadde a kasa nace cikin kuka Ummi ki yafe min don Allah, Shiru kamar ba zatai magana ba,sai can naji tace nikan Aisha may kikai min a,duniyan nan, Kece dai zance ki yafe min nida a,sanadina rayuwanki ya zamto irin haka, Wani kukane yazo min maiban tausayi da ni da ummi dama sauran wanda ke dakin Dayar matar tace ai shi mutum duk bai wuce kaddaran ubangijin shi don haka sai muyi mata fatan alheri ga sabuwan rayuwan da zata,shiga a yanzu, Ki tashi kije ki roki sauran matan gidan gafaran zama muyi haraman kaiki tun dare baiyi ba,, Dakin mama Saude muka fara shiga kamar bazata amsa muna ba sai can tace ku iso mana, Muka shiga da sallama a,bakunan mu muna gaisheta tare da mata yaya,gida, Daya,daga cikin gwagwanina ta ce mata tau uwargida ga yar ki nan mun kawo maki ita kunyi sallama yau zata tafi dakin ta insha Allahu, Mama Saude tace "Ya ta kikace fa aida yata ce da bazata wanan gidan fakiran ba, To kiyi hakkuri don Allah duk abinda tai maki ki yafe mata akwai kurciya a tare da ita, Mama Saude tace ai mu gamu gani shine namu kawai, To Allah ya kyauta inji gwago na dake kokarin tashi tsaye,, Sai da na dan yi jin nace mama don Allah ki yafe mi duk laifin da naii maki, Allah dai yakai lafiya aini baki min komai ba yar Agwai,, kanki kikaiwa, Mubar dakinta muka nufi dakin Atika amm sai muka samay ta a waje take cewa mu tsaya daga wajen ma yayi ai, Tace yar Agwai sai ayi hakkuri daduk irin yanayin da za,a gani a gidan Hamza don ko sai rarita yasan da zatayi yoyo, An nufi dani gurin malam Mudi wanda shigowan shi gidan ke nan a lokacin, Mun shiga turakar shi yana zaune yana kokarin cin abinci Atika tana tsaye daga kan shi tana kokarin mika mai ruwa, Baba yai muna sannu da zuwa tare da,bamu guri don mu zauna daga dan nesa kadan, Baba yace Aisha yau Allah yayi aure zai raba mu dake, zai rabaki da uwar ki da yan uwan ki ko ? Baba yace aure kenan sha kan yaro duk da,ba nesa zakiyi damu ba amma shi al,amarin aure yana da matukar yawa da a,rayuwa, Baba yace Aisha yau Allah yayi rayuwar ki zata koma a cikin wasu jama,an dabaki saba zama dasu ba, a baya, Aisha kamar yadda na fada maki a baya aure sunna ne maikarfi, Wanda yatara wajibai masu yawa a gare shi sosai , Nan Baba ya kara nanata min yadda mukayi ranan da na umurci yai fitar kunya dani akan Kubura, Baba yace Aisha dake da mijin ki ku kasance masu matsakaiciyar rayuwa kamar yadda nasan halin kowanin ku, Halaiyar ku danasan ku dashi indan har kunci gaba dashi zaku kasance acikin jin dadin rayuwan zaman takewa, Yace yau Aisha abinda kikai min yasa na tuna da wani Hadisi na na mazon Allah inda yake cewa, 1 Mutane zasu so abin halitta su manta da,wanda yayi su, 2 mutane zasu rayuwan su har su manta da makomar su, 3zasu mallakar manya manyan gidaje su mance da kabarin su, 4mutane zasu zabi aikata zunubi su manta da yawan tuba (gafara) 5 mutane zaso dukiya su manta da hissabi,, Baba yace yau Aisha kin gwada min cewa kedin diiyace a duniya kin nuna min cewa mahaifan ki sunyi sa,an haihuwan ki a,duniya, Yadda kika iya fitar da mutumin da kikewa ksllon uba a gare ki alhalin wanan mutumin yai sakaci da damar da Allah ya,bashi na kasancewa uba agare ki tun farko, Sai kawai baba yasa kuka yana cewa Aisha yadda kika fitarni kunyan duniya Ubangiji Allah ya albarkaci auren ki yabaki zuri,aa masu albarka duniiya da lahira, Itama Aishan kukane ya kubce mata inda ,suka bar gidan a cikin hawaye, Yan uwanane kawai suka rakani gidan miji sai yan tsiraru daga matan uguwa masu son ganin kwam, Dakafa muka taka don ba nisa sosai da gidan Mama Rahana da mu, Ina rike da hannub kaunar mahaifna da mahaifiyana, muna kai kofan shiga gidan su Hanza sukace min dakata daga nan sai mukaja mukai tsaye, Yayin da gwago na,tadan rankafo daidai kunnena ta rada min da cewa nac bissimillahi A,uzu bikkalamatillahi tamat min sherin mahallak, 3, Takara cewa kiyi bissimillah kija suratul Iklas kafa uku hagu da daman ki sai ki shiga da kafan dama Allah ya sa albarka a rayuwar auren ki, Kamar yadda gwagona ta umurce ni da nayi hakan nayi don ita din malamar addinice a kauyen mu, Inda ina tafiya bakina yana lailaha,illah hasbunallahi wani,imal wakil,, Kofar shiga dakin da aka gyara a matsayin nawa muka dan ja runga muka tsaya gwagona ta kara furta nin kiyi bissimillah ki kara jan Iklas kafa uku ki shiga da kafar dama, Hakan na kara karantawa tace shiga da kafar dama da,addu,an da duk kika iya domin Allah maji rokon bayin sa ne, Duk abinda yazo min daga fannin addu,a haka nauta jero su har asma,u husna saida na jero su, Nai mamaki kwarai yadda naga an gyara min daki a tallakance dai dan ban zaci haka ba sam, Aka zaunar dani a saman gado shima,da,addua abakina yayin da nadanyi kamar minti goma a zaune sai suke cewa na mike zuwa dakin uwar miji, Mun samu Umma Rabi da dan taron jama,an ta a dakinta tana zaune a saman katifan dake a cikin dakin ta, Duk da bata da miji amma kafanta yasha kumshi yana sheki, ta dan yi kwalliya itama, Yaranta duk suna a cikin dakin azaune suma tare da mahaifiyar su, Daya daga cikin iyayyena take cewa tau yadai ga yar ki mun kawo maki Allah ya baku hakkurin zama a tsakanin ku, Dayar gwagona tace sai anyi hakkuri da yaran yanzu don Allah aita tsawata mata akan abinda tayi ba,daidai ba, Umma Rabi tace ai da na kowa balle Aisha ai dama diyatace, Allah ya bamu hakkurin zama da su, Mijinta yaron kirkine baida matsalar rayuwa duk inda na ajeshi anan yake tsawa inaa fataan zaki bamu hadin kai muyi zaman lafiiya a gidan nan , Kina da kannen miji don haka sai kinyi hakkurin zama dasu don a zaunna lafiya, Bamu jima adakin ba suka ce na taso mukoma dakina, Muna shiga naji kauna mahaifiyana tace tau Aisha tun yanzu na,fara hango hakkuri a gare ki, Din wanan sarrakuwar taki da alamar irin matan nan ne masu goyon bayan diyan su akan komai, Don kiji tun a gaban mu tana yabon danta da kanta bata bari hallinsa ya nuna ba, Don haka nasan kina da kirki kiyi hakkuri kinji gaduk irin abinda kika gani daga gare ta ki kawar da idon ki akan abinda take da diyan ta a gidan nan don ku zauna lafiya kinji, Hawaye ne masu zafi suka zubo min ina kokarin dan share su da habar hijjab din dake a fuska na, Na ji mama Rahana tana cewa nasan tunda baki da nisa da Fatima yan gidan su ma zasu dinga shigowa don yin lecture ki don haka ki zama mai boye sirin ki ga kowa, kadaa naji wani zance a waje akan zaman ki gidan nan, Tsabta, yinayi bari na bari shine zaman aure harki ji daga baya ana fadar ai wance ta samu miji ko ta samu gida, Daga karshe wanan gwagon tawa tace masu salli, allanabiyull karem suka karba da sallallahu alaihim wasallam, Nataita jero adduoin nemamin zaman lafiya da kariya daga duk wani sheri na kalubalin rayuwa, Sukai min sallama sukace su zasu tafi sai da,safe kafin su tafi zasu shigo mu kara sallama, Har,sun tafii mamana,Rahana tadan dawo daga baya tana ce min ki yi duk abubuwan dana koya maki a gida Na,amsa a hankali dacewa tau mama sai na saka kuka haka inaji ina gani suka tafi suka barni a,sabuwar rayuwa a wani gidan, ****** ********** ****** Kubura yanzi ita da,sabon saurayin da tayi mai suna Alhaji Nura dinke suke cif da shi don akan shi duk ta kore mane manta na farko shike masu ruwan kudi suna bushashan su ita da mahaifiyar ta, Yan uguwa suna kallon ikon Allah don har kofan gida zai zo ya,dauketa su fita yakuma dawo da ita, Duk a gaban idon Hamza wanda shagon shi yake kallon kofan gidan nasu, Tsakani Hamza da ita yanzu ko gaisuwa babu sai ma yar harara da take yawan watso mai idan sun hada ido, Malam Mudi tun yana ji har yagani da idon shi ranan yai masu masifa sosai ita da uwar ta Yace yaba sati biyu in har aurenta yake son yi to ta fada mai ya fito ya wanke ta yahuta don shi bazai aje yarinya haka a gida ba,suna gwada sa,a da uwar ta, Hakan yasa ta fadawa Alhaji Nura sakon Baba din da farko yaso ya,doje mata amma kuma ko may ya tuna sai yake ce mata, zai zo yaga mahaifin nata akan zancen, Zuwan Alhaji Nura gurin Baba ya,saka mahaifiyana a,wani sabon kuncin bakin ciki a gidan mu don irin gori da habaicin da suke mata, Amma mama Rahana taba Ummi shawaran cewa tayi tankar bata fahince su ba, Ta zage ta shige cikin su tanuna farin cikin takoda kuwa,suna basar wanne taa nuna tafisu farin ciki da hakan Hakan ko akayi don duk da nuna matan da suke basu ra,ayinta a cikin su tana nuna zakewar ta a zancen Kubura din don dai a zauna lafiya kawai, , Ance idan kana son shanmatar uwa to karike dan ta ganin haka a sannu sannu har mama saude tadan fara rage tsangwamar da takewa Ummi da yarran ta suka dan koma daidai sai dai sama sama don na ciki na ciki, Sai dai su su a ganin cewa ai dai nagaba yai gaba don sun tserewa Ummi din da komai tun da yar ta a gidan wahala take rayuwan ta ai, Su ko zasu tafi inda kowa nasu zai huta har su shafa ma,wani arziki, Arziki kan ana gwadawa kubura din shi don yanzu har takai bata iya cin abincin gidan mahaifin nata sai dai a sayo mata ko ta girka abinda ran ta yake son ci taci, ****** ********** ****** Bayan fitar iyayyena daga dakin ina zaune ni kadai a dakin ba wanda ya leko dakin, Sai dai ina jin hayaniyar mutanen gidan daga dakin su acan naji Zarah tana masu sai da safe inda tadan leko dakin nawa tashigo da yar fara,ar ts tana cewa, Tau amaryan mu ni zan tafi sai da safe nasan cewa ba lalai bane Alhaji ya barii na fito gobe amma insha Allahu idan an kwana biyu zan shigo na duba ku,, Ga amanan yayana nan nabar maki kin san yayana salihin mutun ne idan munga ya canza ke ce, Damm naji don zance mama Hanne ne ya fado min a rai na cewa sai nayi taka tsantsan don su da alamar nasu suka sani, A hankali na dan bude baki nace Anty Zarah sai anjima nagode a gaida gida , Tace ke waya fada maki cewa ni antyn ki ce yanzu ai kin zama matar yayana don haka ni kaunarki ce, Nace cikin dan jin kunya ainima yayanane ko kin mata cewa ni din kaunar ku ce, Tadan dafani tace hakane Aisha Allah yabaku hakkurin zama kinji sai kiyi hakkuri da kowa a gidan nan, Tai min sallah ma ta,tafi na kara komawa ni kadai a cikin dakin, bakowa a tare dani, Sai zuwa dare ina zaune a gefen dan gadon katakona mai cin mutum biyu wanda yasha shimfida da zannuwan gado, Naji Asma,u ta,shigo dakin tana rataye da hijjab din ta da wani zani take cewa Umma tace wai nazo na taya ki kwana, Cikin dan murmushi da,sakin fuska na ke ce mata, to ga wuri ki kwanta don haka na mike tare da jawo kofan dakin nadan rage kayan jikina na,dauki butana wanda yake cike da ruwa nafita zuwa babdakin gidan don nasan dashi, Nai sarki saidai naga an dan gyara bandaki ba kamar yadda na,san shi ba, Ina tsugune na,fara alwala naga shigowan Hamza gidan dauke da,wani bakin leda bag karama a hannun shi, Ganin nice naje alwala a tsanake yadan sashi shan jinin jikin shi kamar zai min magana ssai mukaji muryan Umma Rabi tana cewa kai Hamza zo nan, Ya juya zuwa gurinta nidaii nai alwalana nashige daki na rufo abina inda na tada sallah, Nakai wani lokaci a gurin da nai sallah a zaune ina jero addu,io neman tsari daga Allah ga,wanan sabuwar rayuwan da na,fara fuskan ta a,sabon mazauni na, Na koma can dan nesa kadan da Asmau na kwata inda ina jinta sai nasarin ta take hankali kwance abinta, Washegari asabar na tashi don kiraye kirayen sallah da,akeyi na, dauro alawala , Ana,sallamay sallah nafito na,gyara tsakar gidan nan gaba,dayan shi don dama nasan kan gidan, Har ban daki na tsabtace muna koda gari zai haska ko ina na gidan na gyara tsab har zuwa lokacin banji Umma Rabi tafito daga dakin ta ba, Na nufi gurin da,suke ahe icce na debo na hassa wuta a murfu tare da dora ruwan zafi duk da ban san may za a girka a matsayin abin karya kumallo ba,, Na hada kwanuka zan wanke sai dai babu clean din da zan wake a fili, A lokacin naji motsin Umma ta bude kofan ta abinda yadan sani sauri dan dago kaina ke nan na nufi kofan nata don in gaishe ta, Yayin da take bin gidan da kallon mamakin yadda na gyara shi haka tun da farar safiya, Sai idon ta ya sauka a murhu naji tana cewa ke Aisha wanan irin icce da kika zumbuda a murhu ai yau kawai zaki kashe muna dan jarin namu damuke maneji dashi, Hamza ne yashigo gida a lokacin inaga daga masallaci yake don naga casbaha a hannun shi, Inda murhun yake yake kallon sai naji yace Umma sai naga kamar kwara biyar ne tasa kawai, Kaina na,sada a kasa inda naji Umma tace tau mara kunya zaka hana na nuna mata yadda ake tattali ke nan ko ? Yace a,a wane ni kawai dai na zaci ai baki gani bane dakyau,, Yace mata ina kwana Umma an tashi lafiya ya gajiyan baki, Nima,sai a lokacin na tuna cewa bamu gaisa,ba,shi nazo yi ta tareni da wani magana, Nazube kasa a gaban ta gwiwa bibiyu ina cewa acikin yar murya ta,siririya Umma ina kwana, Tace Lafiya kalau ya kuka kwana nace cikin dan jin kunya Alhamdullahi, Ashe har kun tashi kinyi wanan aikin haka ni barci ya kara kwasana ai ban sani ba, Gefen da yake a tsaye nadan kalla still ina,a,tsugunne nace ina kwana yaya Hamza, Ya amsa min a,wani yanayi da cewa lafiya ya gajiyan jama,a, Idon Umma,Rabi kyam a kan mu kamar wacce ke,son gano wani abu a kan mu, Nace Umma nasa ruwa ban san may za,ayi da safen nan ba, Akwai saura kamun koko yana nan shi zamu dama, aiko, Hamza yace ko na,turo da madara ne ku dan hada tea ko ? A,a kada ka fara min shi ranan da babu tea din fa kariga da ka,saba mata dashi, Na mike a,sanyaye nabar gurin ban tsaya jin may zasu ce ba, Ina bada baya naji tana cewa kawai zaka kwashi dan jarinka a ciye bayan ko yar irin gara,din nan da ake kawo wa Ango banga an kawo muna,ba mu, Hamza wanda ya,danjin gina jikin shi a bayan bangon dakin Umma din ya dan ce a hankali haba Umma wani gara kuma bayan kin san yadda akai wanan auren ba,shiri, Ta,watsa mai harara tana cewa da yake basu san kunya,ba za,sy kawo muna ya hakana , Na dawo nake cewa tabani Omo na wanke kwanoni sai ce min tayi ai kayan basu yi wani dauda,ba na wanke hakanan kawai, Fita naga yayi sai gashi da clean yake cewa idan na gama,saina ahe sauran a gurina lokacin Umma ta daki ita da kanin Hamza din wanda ya,fito yana shirin zuwa makaran tan boko, Kamar yadda Imma tace kunnun na dama inda batazo ta,gani ba amma take ce min wai nadama kunu da,ruwa ruwa kuma,bai dahu ba Yarinyar ce taahigo da robar kosai tana cewa ance a cire na dari wai a raba,abawa kowa nashi, Na karbi ledan na kaiwa Umma kosai din na juya don na bar dakin naji tace min karbi naki kafin ki fita, kosai ne kwara biyu tamiko min na karba gwiwa bibibyu nake mata godiya, . ***** *********** ****** Yan uwa na,suka shigo da kayan garar da Ummi tafa min gori a kanshi , Shikafa garin masara, gero sai kayan miya su mangyda ,albasa, maggi gishiri, kifi da,sauran su,, Sai kuma bahohi dakeda guguru cincin da sauran su,, Haba nan Umma ta,shiga waahe baki tana cewa au a she kuna tafe dama , Nan tafara dan cewa Allah sarki wanan irin dawai niya haka yan uwa, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUN KU 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣0⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA A,kofan dakin Umma Rabi aka jibge kagan gara inda suke ce mata ta karba d hakkuri don bukin yazo ba,shiri, Su ka kaimin wanda zanyi amfani dashi a dakina,, Ina,zaune tare dasu a,daki ne Gwagona take kara min nasiha irin wanda iyayye kewa diyan su, Hawaye ne ki tsiyayo min a idanuwa na, gwago tace, kamar yadda na fada maki jiya yau sji din ne,rayuwa takai a,wani guri kuma na,daban, Yanzu halinki mai kyau ne kadai zai maki jagora a zamantakewar ki da,su, Kada kiyi sakaci da ibadan ki hakkuri da kuma kunya, Idan harkin iya tsare wa yan nan tau kingama tsara rayuwar ki ke nan, Sister din Ummi dake daga gefe tana gyara,min kaya,tace a,kuma hada da tsabta, Don kin san mazan yanzu mai tsabta suke yayi idan mace tace ita yar son jiki ne zaki ga komai nata sai a,slow, Gwago na tace min karbi wanan a cikin dabara na karba kamar mai rada tace wanan farin gorar naso nabaki tunjiya, kisha duk dai ko yanzu bai baci ba, Amma anso kafin miji ya,shigo gurin ka kadan goga kadan a goshin ka zuwa kirjin ki da,marar ki, Abin kurciya sai cewa nayi ai baishigo dakin ba tun jiya, har suna hads baki a tare da mama hanne, Gurin cewa to a ina yakwana shi ? ke nan ke kadai kika kwana, ? Nace tare da Asmau kaunar shi mama tace mu kwana tare Sai naga sun dan kalli junar sai kuma suka,ce lalai da akwai matsala amma Allah ya gyara kawai kiyi ta hakkuri kinji, Tafiyan yan uwa na Umma ta,shiga kasafin kayan cicin da aka kawo mata, Sai muryan ta kake ji yana tashi sama ita da yarsn ta da masu shigowa don ganin amarya, Tun tafiyan yan uwa ina zaune a dakina nayi tagumi sai famsn tuna ne inda matsalar da naji suna kira zai shigo min, Shigowan Hamza sau biyu gida baiga giccin Aisha ba a tsakar gidan, yana son shiga ya duba yana tsoron idon Umman shi, Ganin hankalin Umma yana gurin kayan dake gaban ta ya sashi dan satan shiga gurin da nake, Ina zaune a kasa saman tabar roban da aka shinfida a kasan dakin wanda su Gwago suka tashi a saman shi, Ban san da shigowasar ba sai ganin shi nayi a tsaye yana cewa Aisha ke kadaine a dakin abinda yasani saurin dan dago kaina ke nan sai kuma nai saurin dukar da kaina,a kasa, Ya matso inda nake a zaune ya dan tsuguna gap dani kadan yana cewa kin kuwa karya Aisha, ? A cikin natsuwa da kulawa yake tambayan nawa, ? Na dan dago kaina a hankali nake cewa eh na karya yaya, Hmmm naji yana cewa kiyi duk abinda Umma take so don ku daidaita da ita, Cikin sauri na dago kai na dan kalle shi yayin da idanuwa na,da,basu raina hawaye har sun ciko ko, Yace idan har kin kiyaye abinda take so to zaki ji dadin zama da ita sosai, Don tafi da son duk abinda tacewa mutum to mutum ya to kawai shine zaman lafiya Yace don haka Aisha kamar yadda na,sanki da hali irin na kirki don Allah ki cigaba dz halinki da hakkuri, Duk abinda ta hane ki ko umurce ki dayi ki yishiba lokaci don bata son mussu da tauri kai nace tau a hankali, Nasan baki saba da yadda muke karyawa ba,agidan nan da irin cimar da muke yi amma ina rokon ki daki daure ki ci ko yayane don samun salama kawai, Muna ciki haka mukaji muryan yaro yana cewa wai ana sallama da Hamza a waje, Umma tace ai yana nan shagon ka barshi a ciki yaron ya kara fadi cewa baya shago yashigo ciki yanzu Take naga rudewa a idanun shi kaman wanda yayi wani iri laifi maigirma duk dan rude a hankali yadaga labulen dakin yai waje simi simi dashi yana cewa gani nan ai yanzu nashigo gida, Banga giccin yarinyar nan bane tundazi shine na dubata don naga ko lafiya take, Wani uwar harara Umma ta sakar mai sai ya sadda kan shi kasa da sauri tace baka dai jin magana ke nan ko ? Umma yanzun nashiga don na dubata kawai ba wani abin ba, Har zatai magana ko may ta tuna kuma sai tai shiru kawai ta kuta ya bishi da harara bayan shi inda yafita kofan gida gurin da ake neman shi, Tun daga wanan lokacin ban kara ganin Yaya Hamza a dakina ba sai dai idan ya shigo naji muryan shi a tsakar gida daga nesa, Kwana biyu ke nan ina zaune a gidan duk wani aiki nice ke yin shi batare da najira ko kuma ance ba, Idan na dafa abinci Ummace ke rabawa da kan ta, don sai dai na dauko na kawo mata a gaban ts ta raraba, Umma bata jin kunya ko nauyi gurin cika wa Asmau da dan ta karami Ibrahim tana cewa wai yarane, bari a zuba masu da yawa alhalin sa,ar mu guda da ita Asmau din, Ba ruwan Yaya Hamza da al,amari na nima din haka iyakata dashi idan ya shigo nai mashi ina kwana da safe, ****** ********** ****** Kubura yanzu zancen ta da wanan Hamza din dan uguwar sabon gari ya kan kama don kowa yanzu yasan cewa shine zai aure ta, Take mutane suka,soma magana a kan zance kowa na kawo suka daban daban, Idon mama Saude ya rufe sai cewa take hassada ga mai rabo ai taki ne, Don haka kowa ya cirewa yar ta ido ga,al,amarinta da mai baki da goro da mai baki da taba da mai baki da kuka duk suka kwaso zancen su sai suce wai Kubura to ita hakan ya sheta don haka zata daura kafan wando guda dasu ne, Hakan ne yasa mutane suka ja bakin su sukai shiru suna kallon aikin karya, a cikin uguwa, Ranan da safe babu yaron da zata aika ya sayo mata idomie a shagon hamza, Hakan yasa ta yafa dan yalalon gyalen ta akai na just to cover ta fita zuwa sayowa, Yun bayan cin mutuncin da taiwa Hamza wanan ne karo na farko da zasu gana, Yana daga cikin shago yana mikawa wani yaro kayan da yasaya yaji wani irin kamshi ya daki hancin shi, Da sauri ya juyo don yaga ko waye mai wanan kamshin haka a lokacin yayi zufa zufa dashi, Ba,sallama ba komai tace aban idomie na dari biyu kwai guda shidda, Cikin dan murmusawa yace a, hajiya Kubura ce barka,da,dare ta,wani ya, mutsa fuska tace ka,ban indomie nace, Murmushi kawai yai mata inda a zuciyar shi yake jin ke jin wani radadin abinda take nunawa a kan shi, Abinda tazo saya ya,saka mata a leda ya mika mata ta miko mai naira dubu guda ya cire kudin shi yace jeki kawai kibar shi, Tace look malam wakake ne ma dauki kudin ka kabani canji na don ban son hada abina da abin matsiyata mutum yace ka kashe mai shago kawai, Yai tsaye sororo yana kallon ta a cikin mamaki yace Kubura nine kuma matsiyaci yau don nace ki bar kudin ki, Dakata malam may kake so dani ne bari na fada ma ko wanan ganin da kai min a dalili na,zo inbashi banda lokacin tsayawa harka da yaku bayi irin haka masu zubarwa mutum da daraja, Ta fige ledan ta tawuce tana zuba mai bakaken magan ganu daga bakin ta, Binta HAMZA yayi da kallon mamaki yadda akaiyi idanuwanta suka bude haka aa lokaci guda, Shi bawai da manufar da take nufi yabata wanan alheri ba kawai din mutuncin da ke a,tsakani na,sarrakuta yanzu, Ta shiga gida tana ta masifa Atika ce ke cewa may yafaru ne haka kuma,? Nan tana kokarin cire dan gyalen da ta yafa a kanta take fada mata a cikin daga murya, Wanan matsiyacin mana Hamza ke so ya kawo min rainin wayyo wai na tafi saye indomie yake ce min na bar kudin, Nace mai anfada mai cewa ni matsiyaciya ce ko may yake nufi yatafi can shi da tallakam matar shi ya kara ya,ciyar da ita, Don ni ba,sa,ar yin sa bace ko amfada mai ni matsiyaciya ce da zan buge a dan kayan treder shi, da bai wuce nasha ice cream da shi ba, Ko yana zaton zai iya sayeni da wanan tarkacen banzan nashi ne har yaushe yai kudin da zai bani tsiyatsiya jiya wa yau dashi, Masu kwadan kayan shi dai ai suna can sai suci mu gani in ci banza ne gida ma ba, a koshi ba balle akaiwa bare, Ta shige kitchen din su tana kokari dora girki Atika tace bari na dafa maki ai baida wuya, Daga daki Ummi tana jin su tace a hankali Allah ya kyauta Allah kaga nufin mu, Sai daga baya mama Saude tafito take cewa ke ko hankalin shi yana a kan ki mana tunda dama cushe akai mai bawai da ra,ayin shi ba, yake auren , To wallahi ahir din shi dakr don baiga kin masa kama dayar masiyata ba ****** ********** ****** Rana bata karya sai dai uwar diya tai kunya yau saura Sati guda gasa duk gari inda kabi zancen wanan gwajin amfanin gona ne tako ina, Samarin dake zaune a baki kofan shagon Hamza suna hira yau firan nasu akan zance wasan da za,ayi a garin ne, Hamza ba ma,aboci son surutu bane yana dai sauraren su a hankali duk abinda suke fada a gurin,, Wanan yace shi kaza zai kai wancan yace shi abukaza zasu kai a gidan su, Acikin zuciyar shi yake cewa ni Hamza to may zan kai ? Gashi bamu da kiwo balle nace zan kai gashi bamu da,wani abin azo a gani wanda zan iya kaiwa, Tau Allah dai ya,rufa muna asiri kawai zan dai tafi nai kallon nima kada a bani labari, Daga inda yake zaune Ibrahim kanin shi yafito yana fada mai mama tace yabada dari a,sayo iccen da za,a girka abinci, Ya dan lalaba aljihun rigar sa ya ciro wata tsohuwar naira dari duk ta yage ya mika mai, Sai zuwa wani lokaci ya dan rufe shagon ya,shiga cikin gida don yaci abinci, Ya,samay ni a bakin kwata,ina wanki daga ind nake a duke saye da hijjab dina kamar kullun zan iya jiyo hirar su da Umma , Inda yake fada mata cewa gasar da akai shella a akai lokaci ya gabato don wani satine za a yi, Umma tace Allah ya,ba mai rabo sa,a masu kudi da ma,aikata suke da abinyi , Shikan tallaka ai iyakar shi kallone kawai da ihu ko tafi don farinciki, A daidai lokacin da nake shanyi kayan Umma ne dana Asma,u na wanke, Hamza ya kasa daurewa murya kasa kasa yake cewa amma Umma wanki harda na Asmau kuma, Umma tace tau rasa kunya anya kuwa yaron nan ida ban samaka waigi da bakace kada yarinyar nan ta taimaka min da komai a gidan nan ba, Yace Umma ba hakana bane yariyar nan amana take a gare mu kin ga,wasu abubuwa bai kamata ace tayi ba, Tunda sa,a guda suke da Asmau mai zai hana a raba masu aiyukan nan a tsakanin su su dinga yi tare, Tace amma ita Aisha aure, tazo yi ba zaman gida ba don haka zaka bari tayi bautan aure ko, Watau mama ba hakana bane mutane masu shigowa sune zasu iya fita,da zancen har ya koma a gidan su, Umma tace yanzun dai tunda ban iya,ba shike nan zan baka matarka,sai kayi mata training da kan ka, Umma tace dama ni da akwai dalilin da yasa nake mata hakan don ta saba, Ranan da dare muna daki nida Asmau muna hira sai ga,Umma tazo ta tsaya daga kofa tana cewa Asmau ki dawo daki kibashi guri ya,shiga dakin matar shi, Jin abinda Umma tace yasani jin gabana ya fadi dammm ke nan tana nufin adakina yau Hamza zai kwana, Murya umma ce naji tana cewa Aisha ga amanar dana nan gare ki da fatan zaki kulsmin dashi yadda ya kamata kada ki manta cewa Hamza maraya ne, Don haka ki bi min shi a sannu banda turasasa shi a ksn abinda baida halin yinshi ace sai yayi su,, Ina jin tafiyan ta zance mama Rahana ya fado min a rai cewa kada na taba,bari miji ya,shigo dakina ya,samay shi ba gyarare ba don haka na mike a hankali na fara gyara,daga zanin gado zuwa dan shara da,sauran su duk da kuwa ance sharan dare baida kyau a musulunci, Na,dan fesa kamshi kafin a ce a haka daki ya canza kala kamar bashi ba, ne, Na saci jiki jin umma tana daki tana magana kamar na,siri da diyan ta na,dan kara yin wanka, Tsab na gyara jikina abinda baku fahinta ba,shine duk hakan bada wani manufa nakeyin su ba kawai fadar da,akai min ne nake amfani dashi,bawai don zan kwana da miji bane, Ina gamawa da,sauri na,dauko turare na na mutsuka kamar yadda gwagona tai min bayani, inyi dashi, Kaina wanda aka yarfawa kitso na dunkule shi a cikin yar hulata dana wanke da rana, don yawan gashi da tsawo gareni Nasaka yar rigar barcin da mama hanne tace min indinga sawa idan zamu kwanta,, A,bakin gado na dan kwanta na,dunkule kamar wace ke tsoron wani abu, Sai dare Hamza ya,shigo gida inda Umma tai mashi bayanin cewa ya tafi dakin matan shi yau Asmau a gunta zata kwana, Ya shirya kamar yadda ya saba duk shi dan tallakawane ammw akwaishi da tsabtan jikin shi irin wanka wanke baki da aski, Wankin tufafine dai bai faye samu time din yi ba,saboda ujila, Banji shigowan shi ba saboda barcin da ya fara dibana a lokacin sai dai ji da nayi a hankali kamar ana kiran sunana, Na mike zubur zaune daga kwancen da nake cikin dan rudewa ina fadin yaya Hamza ina wuni, Ya amsa min da cewa tashi zaune muyi magana dake, Ba musssu na zauna dan nesa dashi kadan kamar maijin tsoron wani abu, Tambayqna ya farayi da cewa an yi wani abune a tsakaninki da Asmau, yau ? Cikin sauri na dan girgiza kaina ina cewa a hankali a,a, Shiru naji yayi sai kuma ya furzar da yar iska daga bakin shi yana cewa, Aisha nasan cewa ke yarinyar ce mai hakkuri don haka kiyi hakkuri da irin abinda Umma tai muna, Din ban taba ganin wanda akaiwa irin hukuncin da Umma tai min ba, Duk da ita a ganin ta sone da kauna na ya kaita ga yi min hakan, Ta haramta min zuwa kusa dake don wani akida nata na daban can wanda baida dalili, Don haka nake mai kara,baki hakkuri don dan naman da yake kamar sunna na baki tun rada ya kamata na,sayo na baki Umma ta hana ta karbe, Yanzu tashi mu fita na rakaki kiyo alwala don dare yayi ko, Kamar yadda yace alwalan ne nayi tare da kara dan kimsawa, Sallah ya jagorance mu mukayi nidashi inda daga baya gama adduoin mu yake umurtana da na dawo kusa dashi na zauna, Adan takure na dan matso gab dashi na zauna a cikin jin kunya da fargaban zama a kusa da namiji haka gap da gap, Hannuwana na Hamza ya fara rikewa yana dan wasa dasu a hankali yayin da yake fada min irin dokokin dayake son shimfida min a gidan a matsayin shi na maigidana, Matsar da yakewa hannuwa sun fara canza,sallo don haka na dan fara kokarin bijire mashi a hakan, Yadan jawoni zuwa gare shi inda na, zunbule ina cewa don Allah Yaya Hamza ka daina kaga hakan baida kyau haramu ne,, Murmushi naji yayi inda yake rada,min a kunnuwana cewa ke matatace Aisha zan iya maki duk abinda naga dama, a tsakanina dake, Cikin kokatin fahintar dani da yake ne yaga cewa ba zan tsaya yabini yadda yake so ba, Sai kawai ya yi amfani da karfin shi kuciya ya debe shi ya amfka min yadda yaso, Ganin irin surar dake gareni wanda a kullun yake boye a cikin hijjabin da nake dunkule kaina a cikin shi, Kuka sosai na,dinga yi wanda ban damu da wai wani yajini ba a lokacin, Muryan Ummace mukaji tana cewa ke kada ki hada muna kan makwabta a gida fa a cikin daren nan, May kike nufi dama zaman ciye muna abincine kawai zakiyi ba biyan bukata, Hamza wanda yake kokarin lalashina naga ya dafa kan shi irin idan mutum dinnan ya shiga ukku, Takarashe fadan ta ta tafi tabar mu na inda yai ta bani hakkuri yana min nuni cewa hakan ai shine auren dama, Har saida ya,fahinci barci ya kwashe ni yadan gyara rufe min jikina ya kwanta rigingine ya soma tunane a ranshi, Ashe kallon da yake min da farko abin ba haka yake ba ke nan, Duk wani abinda da namiji zai bukata agurin diya mace Allah ya,hore min shi a jikina, Duk wani tunanen da yake kuma cewa nai karama ga abinda yske bukata sai yake gani ai na kai har na,wuce, Washe gari Ummu ce ta bubuga muna kofa tana cewa yafito ga ruwan wanka can a bayi takai mai, Kunyane sosai ya kama shi inda ya,amsa mata a,dan daddare sai bayan da yafito Umma,ta kai min nawa ruwa, Takara,koya min irin yadda zan gyara jikina,dakuma koya min daurewa,a tare da,miji, Bani ba rana har hamza da,yake danta a kunyace yake a,gidan @ ****** ********* ****** Soi sai nake kunyan hadu da Hamza ita ko Umma sai wani haba haba take da dan ta, Yashigo yana zaune zaici abinci rana Umma ke tambayan shi cewa ashe a cikin karshen sati za ai wana gasar nuna fasahan noma da kiwo, Yace eh Umma insha Allahu ina,son na leka gurin inyi kallo abinda yasa ni sauri dago kaina ke nan, Wanda yai sanadiyar hada idanuwan mi ni dashi amma kuma sai nai saurin mayar da kaina kasa, Zan iya cewa wanan ne karo na,farko dana na saka masu baki a,zance inda,nace Niko sai nake gani kamar mu gyara wanan waken naka da kuma zangamay dawo ai za,a iya zuwa dasu a gurin gwajin , Shiru yayi kamar mai nazari can ya mike tsaye tsamaka min da wanan nan ya gwadan roba y nufi guri da suke aje abincin gida, ZAINAB IDRIS MKAWA SEE,NABUN KU ' 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA RABBI NAJJINI MIN AL-QAWAN AL ZALIMIN 👏👏👏 Abakin murhu nake duke ina,hura wuta don iccen baya ci saboda yana,da sanyi sosai, Sallama naji wanda muryan mai sallaman yasani saurin dagowa daga gurfanen da,nake , Kubura,ce tare da,wata kawar ta wace islamiyan mu guda,da ita, Na dago da fara,a ta ina masu sannu da,zuwa babu kallon arzki daga fusksn Kubura din dan gara ma kawar ta datake cewa a,a amarsu ta ango, Shine akai aure ba,a fada muna ba Aisha balle mu zo walima,, Nai murmushi kawai inda na shiga,gaba da niyar na,fara kai su gurin Umma su gaisa, da ita, Ke dakata ina zaki damu kuma ina nan dakin uwar mijin nakine ? Kubura ce ke tambayana acikin wani murya mai kama da commad, Naja na tsaya ina cewa eh dakin ta ne ina zaku gaisa da itane ai, Bashi muka,shigo yi ba dama bintu ce tace na kawo ta ku gaisa, Din shi kikaga na shigo wanan gidan idan bashi ba ta,wani kada kai alamar a,a , Juyawa nayi don kai su nawa dakin amma,sai naji muryan Umma a bayan mu tana cewa, Au to mara mutunci bazaki gaishe ni ba kenan har kike wani dakawa yarinya tsawa,, Kubura batai magana ba,sai kara shigewa gaba da,tayi zuwa dakin nawa tana wani taunar chewing gun kas kas kas, Ta shige gaba wanda dama nasan cewa tashigone don taga yadda dakin yake, Duk da dakin yana a tsabtace amma Kubura sai wani dan yatsune fuska take tana mayde baki inda na,shimfida masu tabar ma don su zauna , Amma sai sukace a saman gadona wanda yasha gyara zasu zauna, Nafita na dauko wani cup din silver mai hannu na debo masu ruwa a rabdar kasar dake daga gefen dakin Umma Rabi, Na samay su suna dube dube a dakin suna dariya a tsakanin su , Ban damu damay sukewa dariya ba na dire masu ruwan a gaban su ina ce masu bissimillah ga ruwa nan, kusha, Kallon ruwan sukayi shekeke sai Kubura din ce tace haba Yar Agwai aiko a gida kin san ban shan wanan ruwan balle na,wanan gidan naku, Bintu ce tace haba ai kuwa zamu sha,don kada na rantse ban sha ruwan gidan Aisha ba, Ta dauki cup din ta dan kurba kadan ta aje tana cewa ta gode nadan yi murmushi, Suna shirin barin dakin ne sai ga Hamza ya shigo gidan hannu shi dauke da yar ledar da yai cefane a cikin sa, Ganin su Kubura din yasa shi yadan daburcr yana cewa ,a a bakine a gidan haka, Sannun ku da zuwa ince kin basu ruwan sha dai Ausha ? Kaima kasan ai bamu iya shan ruwan wanan gidan naku don haka ruwan ku ya huta kawai, Daga gurin da nake tsaye na dan ji kunyar zancen na ta na zaci maganar zai soki Hamza din, Amma sai naga yana murmushi kawai yana cewa hakane fa nasan da hakan don yar gidan sarkice ta shigo, Tajuyo inda nake ta wani dan wurga min harara tana cewa ke mu mun tafi sai kuma wani jikon, Suka fito sukabar gida batare da ko sun kalli inda Umma take ba a bakin kofar ta tana kawar da kaya, Kunya ne yadan kamani abinda Kubura taiwa Umma din, Mara kunya ai duniyace ita zata sauke ki da kanta daga wahalar daukar ta da kikayi, Cikin dan dari dari na karasa gurin da Umma din take ta dauki tsintsiya za tai shara, Ta wani dan wurga min harara tana cewa bazan yarda wanan fitsaratar yarinyar tana shigo min gida ba, Na kara mika hannu don na karbi tsintsiyar , Tace na barshi zata karasa abinta a hasale take tana son sauke haushi a kaina, Kwanonin da akaci abinci na shiga tattarawa tare da juyawa zuwa inda nake kokarin hasa wutar girkin dare, Hamza yafito bandaki dauke da buta a hannun shi yana kokarin gyara zariyar wandon shi, Idanuwan shi a kan inda nake a gurfane ina kokarin hura wuta, Naji muryan shi yana cewa ai Umma shiyasa nace a sayo wani iccen tunda wanan din yana da sanyi sosai, Tamike daga sharar da takeyi zufa a goshin ta tana cewa, Wai Hamza may ke damin kane naga fa duk ka canza a kwana biyun nan, O saboda bakasan zafin neman kudi ba,shine zaka koma,sayen wani , Abinda Umma tace yasa hamza saurin dagowa ya dan dubeta yai saurin kawar da kanshi bai sake cewa uffan ba yabar gidan, Haka a wahalce taketa faman hura wutan da dan samo wasu yan abubuwan da zasu saka wutar yadan kama da sauri, ****** ********** ****** Bayan dan wayan da tayi da,mai kiranta a lokacin ta aje wayan a saman tsohon mirror din dake dakin mama saude, Ba,wani dogon shiri tayi ba tafito daga dakin cikin doguwar riga baka ta rufe kanta da,wani gyale mai laushi, Ta,dauki wayan dake a saman table din tana cewa Mama zab dan fita nan ba nisa zan tafi ba, Gurin da yai mata kwatancen motar shi ta nufa, inda ta samay shi a tsaye cikin fushi yana dan buga kafan shi guda a kasa, A murde taxo mai tana cewa kace nazo kana da magana dani ? Yanzu Kubura kina ganin cewa auren Nura da zakiyi shine mafita a gare ki, Mutumin da baida mutunci ko kadan bai san darajan kowa,ba a gari zaki sa kanki a tarkon sa, Dakata malam ina mun wuce wanan zancen dadewa ban son mayar da zance baya, Na fada maka gaskiya ba yaudara a cewa shi din na tsayar don a,shirye yake da na aure shi ko da yau ne, Sabanin kai da morewan rayuwa kawai kake bukatan koda yaushr muyi tayi bamu nan bamu can, Ga matsin da muke samu nida mahaifiyata a gurin babana tunda dan matsiyatan nan ya sakani a zancen auren shi, Mansur yadan furzo iska ya shafi fuskan shi yana cewa yanzu daga ke har mahaifiyar naki may na rage ku dashi, Tace komai don yadda Nura yake zuba min kudi ko kwatan shi baka iya min kawai kai a more rayuwane naka, Yace ok naso a ce kin tsaya kin fahinci ko waye Nura ki kawar da zancen auren shi a ranki, Tamike tsaye tana cewa bazai yiyo ba daga yau kuma na fada maka cewa shine zabi na don haka kabar wanan kudirin naka na son yaudara na dawani zance wai Nura ba na kwarai bane, Mune fa yan bariki kar ta san kar a tsakani na dashi, tsuki tayi ta buga marfin motan ta fara tafiya Mansur yana kiran ta amma bata tsaya sauraren shi ba ta wuce abinta, Mansur yaso ta tsaya yadan bata wani labari a gamay da Nura din amma hali irin na Kubura halin tsiwa ya hanata jin komai a kan shi, Ita dai bukatan ta tasamu gidan hutawa ta kuma hango shi a gidan Nura din to may zai fada mata kuma a hakan, Kamshin da tabarshi dashi a,cikin motar shi ce yadan shaka inda yasan cewa yayi missing din Kubura din sosai, Kallon ledojin da yai mata tsaraban irin abubuwan da yasan tana,bukata,ne a,baya yayi inda wani haushi ya dan kama,shi yaja motar shi yabar gurin a fusace , ****** ********* ****** Waken da Hamza ya debo acikin waken da ya noma shi take ta faman gyara kusan kwana biyu ke nan da fara,wanan aikin, Ga girkin gida ga aikin waken da takeyi wanda Hamza din yaso yayi da kan shi amma sai Umma tace yabar wa Aisha don bata komai aikin zai rage mata zaman kadai ci, Da Allah ya azamin dan fasaha,sai na,diga daukan manyan irin ina tara su guri daya wanda hakan yasa waken dana tsince din yazama gwara gwara gwanin ban sha,wa, Irin farar dawa wanda akabawa hamza din ya,shuka sai dai bai samu abin kirki ba don ba kudin gyaran gonan shine yagyara su tsab gwanin sha,awa, Gari ya,cika da jama,a tun ana saura kwana biyu wasan gwajin da za,ayi din, Aikin gyaran waken da nakeyi ne ya,dauke min hankalo inda har rana yayi ban sani ba ina,daga cikin dakina,saboda rana ya fito gashi ba innuwa a,gidan, Umma ce naji tana kwada min kira tun kafin na,amsa take cewa yau baza,a girka muna abinci a gidan bane Aisha, Abinda yasani saurin mikewa ke nan na fito daga dakin da,sauri, inda Umma ta hau yi min fadan cewa zan barsu da yunwa ita da diyan ta na shige daki na kwanta, Shigowan Hamza din ke nan a lokacin yake kokarin gaida Umma din yake cewa batare da ta amsa ba, Yarinya ta shige daki abinta zata barmu mu yini da yunwa don kiyya, irin ta matan yau, Yace ke ina waken da na saki gyara sauran na koma dakin don na dauko wanken inda Umma tabi da fadan tana cewa ai inda sanyi jikine irin na Aisha yanzun haka bata gyara ba, Nafito dauke da waken cike a wani roba nawa mai fadi , Abinda ya san sasauta fadan Umma din ke nan tace kai shi kumq wanan irin a ina aka samo shi haka,? Hamza yace wanan dai namu din ne Aishan take gyara tunda safe dana barta dashi, Hannu Umma din takai cikin waken tana dan juyawa a hankali, Sai ta juyo inda Hamza din yake tana cewa amma Allah yasawa wanan wake ido,da kwari wallahi kamar bashi ba ya samu gyara sosai, To ai saiki ce min ba kwance kike ba aiki kike a dakin amma kuma a zauna ba,aci bane, A lokacin har na share gurin murhu ina kokari tura ittace don tuwon gatin masara ne tace zamuyi da miyar busassan kubewa , Suna hiran su ina,aikina,sai dai kallo guda,mutum zai min ya fahinci cewa na ramay don nadan fada,sosai, Asmau tashigo gidan inda take cewa tun kafin ta kai zaune wallahi yunwa nake ji may kika dafa muna ne, yar Agwai, A cikin wani irin zafin nama Hamza din ya dago kai yace mata cikin dakiya kada na karajin wanan sunan a gidan nan, Tace a cikin yar shagwaba to ai sunar ta ke nan ko, Umma tace tunda yace baya son kina kira mai mata da wanan sunan to ki bari kin dai san halin yayan ki, ba ruwana, Hamza yace Umma bai dace wanan sunar da yan gidan can ke kiranta dashi muma anan mu kirata dashi ba tunda ba,sunan alheri bane, Tau kaji mai mata fa nine zaka fadawa cewa ga,abinda ya dace da matar ka a gidan nan, Yana kokarin daukan roban waken dake a gaban shi ne Umma ke cewa yanzu kana ganin cewa zasu barka kayi wanan gwajin da dan wanan, Yace Umma ki samu na albarka acikin al,amarin don shi muke nema, Umma tace Allah yasa mu dace Allah ya sanya alherin sa ya amsa da amin tare da kokarin wucewa da roban inda na fito dashi, Da,sauri na karaso na karbi robar daga hannun shi ina niyar mayar wa dakina, Umma tace kai shi can dakina ki aje gefen gado kada ya kuma samu matsala, Ba mussu najuya da roban nakai dakin ta kamar yadda ta umurce ni dayi, Na gama abinci da wanan uwar ranan narabawa kowa sai dai da yake garin baida yawa abincin bai kai ba, Gab da Hamza zai shigo gidane yaji Umma tana cewa sai na juyewa Ibrahim nawa abincin nazo ta yanka min nata, Ya karaso cikin gidan yana cewa haba Umma ita da ta dafa ba,a bata taci mai isar taba sai Ibrahim wanda ke waje yana samun abu yana ci za,a ce ta ajewa kason ta, Ya juya inda nake yana cewa na dauki nashi kason zai fita ya samu abin da yaci a waje shi, Umma bataso hakan ba sai cewa tayi na bar ma Ibrahim na Hamza din naci nawa, Ibrahim din ya,shigo gida nan ya zauna zai ci a binci ganin kayan abincin dan uwan shine yake cewa shi Yaya Hamza mai zaici dana ga anbani abincin shi, Nan Umma ke cewa shi yasani don matarshi bata samu rabo ba,shine yai fushin zuciya yace abar mata nashi, Da sauri Ibrahim din ya,dago kai yana cewa amma, gaskiya Umma bai dace ace matar yaya,bata samu abinci ba itace ta girka ba, Kai kama min bakin ka kafin na bata maka rai waya fadama bata,samu ba, Wai don suwa nake zaune a haka da kowan ki zai dinga ganin laifina haka, Ibrahim wanda yakai loma a bakin shi yace Umma ai itace wai naga ya kamata ace taci tunda amana take a gurin ki, Kadan yaci da,alamar a koshe yake nan ya mike ya kwaso kayan abincin yana ce min gashi ki kara kin ji Aisha, Ina zaune inda na idar da,sallah nadago kai acikin murmushi nake cewa dadai kakai wa dan uwanka don shine bai samu abincin ba, ****** ********* ****** Motocine kala kala ke yawo a,cikin garin inda jamian tsaro suka cika ko wani lungu da,sako na garin da tsaro, Wanan dalilin yasa mutane zuwa kama guraren nuna show din nasu da,wuri kafin guri ya cika, Yan kauye dama makwabtan gari duk sun halaro gurin wanan taron mai dibin tarihi a,rayuwa, A gurin zakaga manyan namun daji wanda akadade ba,a gan su ba da kuma dabbobi da ake kiwo a gida sunci sun koshi don samun kiwo na kwarai, Taro yai taro inda har da turawa da, sauran mutanen kasar waje suka shigo don kallon wanan taron, Hamza ma ba,a barshi a baya ba gurin zuwa da nashi kayan show din amma yana ganin irin abubuwan da wasu suka kawo duk sai jikin shi yai sanyi sosai, Yana ji a,rayuwan shi kawai ya koma gida saboda babu wanda zai ko san cewa yana gurin balle ya kalle shi, Zuwan manya naki na kasa yasa gurin ya kara rikicewa gaba daya inda akafara bude taro da,addua tare da fatan samun sa,a gama su nasara, Layin masu gwajin amfanin gona daban inda haka ma layin masu gwajin dabbobin gida dana daji daban su ke, Ga masu wasan gargajiya suna wasa kowani kabila da kalar tasu shigar a gurin, Tafe suke inda duk gurin da wanan shugaban ya tsaya za,a bawa,mai wanan amfanin gonar nomba ta kyauta, Tafe suke tawaga takai tawaga ta manyar ma mutane masu bada zabi ga jami an tsaro nata,bin su bayan su, Gaskiya kaya sunyi kyau sunga abinci masu amfani yadda yakamata don basuyi tsanmanin samun abinci masu inganci irin haka ba a kasar, nan, Wani manomi ne ya baza kayan amfanin gonar shi mutane sun taru sai kallo akeyi yadda,sukayi kyau sosai, Maigirma babban bako ya juya don zuwa kallon wanan shagon na,wanan babban manomin, Abokin tafiyan wanan bakon wanda yazo daga kasar waje don ganin abinda ke guda na, Wani dan saurayi matashi mai karamin shekaru ya hango can nesa kadan da,wanan rufan , Yana tsaye da kayan da yazo gwaji a cikin wasu kananen roba, guda uku, Kawai sai yaga burgewan wanan matashin da kwazon shi har ya kai ga yazo nuna nashi kayan amfanin ba tare da, jin komai ba , A hankali ya tako zuwa gurin wanan saurayin wanda duk yai zufa ga,rana tana kudar shi ga yunwa, A hankali mutmin yaduka ya debo wanan wake dake a cikin roba kursa kursa dasu, yana dan jujuyawa a hankali, Sai daga baya abokan tafiyan shi suka luracewa bai tare dasu don haka suka shiga neman shi inda suka hango shi a tsugune gaban wanan yaron mai kaya, Sauran jama,an suka yo a kansu suna kallon su a cikin mamaki don babu wani abin azo a gani a gaban yaron amma gashi maigirma babban bako ya zo gurin yaron, Shima,shugaban na wanan kasar diban wanke yayi yana dan juyawa yayin da,sauran yan tawagan suka shiga diba suna kallon Kowa sai yabawa da kyau da,girman waken sukeyi gwanin ban sha,awa,,, Nan ya jawo irin dawan da Hamza ya shigo dashi filin shima yana dubawa a hanakali, U Idanuwan jamaa yoyyy a kasu don su azaton su laifi hamza din yayi, Sun dauki lokaci a tare da,Hamza suna,mashi yan tambayoyi ya ba basu amsa sai cewa,suke interested, Daga karshe dai aka,rubuta sunan hamza din daga,cikin wa yan da za,a bawa kyauta a gurin, Nan aka karbi sunan shi aka juye wanan kayan a cikin wasu robobi na gwajin kayan agric din da aka zaba, Hamza ya koma gefe guda ya na sauraren su kamar yadda suka umurce shi da yayi, An dauki lokaci mai tsawo kafina agama wanan gasar gwajin kayan amfanin gonan da,akeyi, Nan aka soma kiran sunayen mutane ana fadin iri abinda mutum ya,burge bakin dashi daga fanin abinci dabbobi da kuma kayan ruwa, Can kamar a mafarki Hamza yaji ana kiran sunan shi inda ya,fara ratsa taro don zuwa inda ake kiran sunan shi, Nan wanan baturen ya daga hannun hamza yana fadin cewa Hamza matashin da yazo na,daya gurin nuna dogaro da kai har ya kawo amfanin gonan shi da,full confidence, Ga kuma waken da yakawo gwaunati tanq bukayar wanqn irin don wani gwaji da zatayi a kan shi don haka gwauti ta,sayi wanan waken akan gudu naira,,,,,,, Haba guri ya rude da,sowa da ihu da kuma tafe daga yan kallon da,sukazo na,sassa daban daban na kashen Africa,, Inda wanan bature ya nemi hamza da ya bashi full address din shi da in da yake da zama, Haba aikuwa hamza yana karba,sai kawai ya,saka kabbaraza fili da cikin zuciyar shi, ****** ********* ****** Ina zaune gurin dana idar da sallah na daga hannaye na biyu sama ina rokan Allahya rufa muna asiri duniya da lahira, Ina gab da zan sauke hannaye na ji murya Umma a cikin murna tana cewa o, o Allah nagode ma,Allah mun godema bisa wanan baiwar da kai muna , Ina kuke yaran nan kufito kuji abin arzikin da ya,samay mu a gidan, Jin abinda ta fada yasani saurin mikewa zuwa kofan daki do ganin may Umma kewa farinci haka, Babu kowa agurin na dai fito sai naji tana cewa yau kan Allah ya nufa Hamza ya samu yar ga Allah yasa shi cikin zabbabu, Yar fara wace ina ga ban taba yinta ba tun zuwa na gidan nasake ina cewa masha Allah ashe yaya Hamza Allah ya karba addun mu,, Uguwa baki daya zance ya karade ko ina kowa da abinda yake fadi a bakin shi, Wasu har dakari sukeyi wai har da mota aka bashi wasu suce ai mashin ne aka,bashi, Ga yan murna sun fara shigo muna gida gashi shi mai abin arzikin bai dawo gida ba har wanan lokacin, Saboda farin ciki Umma taje ta,auno muna shimkafa a,makwabta mudu daya tace nayi tuwo da,miyar sobarodo da busashen kifi, Ina aiki ina Allah Allah kafin na gama kafin yashi nayi wanka na dan kimtsa irin da naga mata sunayiwa maza jen su idan sun fita gurin neman kudi, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU👑SARAUTAR MATA👑 1⃣3⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA RABBI HAB LI MIN AL-SALIHIN,,,, YA UBANGIJINA KABANI ABOKAN ZAMA DAGA BAYINKA SALIHAN,,, Washegari Kubura ta farka gari ya waye tangararam haske ko ina, Tamike tanufi bandakin dake a cikin dakin ta tagyara jikin ta tsab ta dauro alwala tafito, Saidai sam zuciyar ta ba dadi har lokacin don na ta gabatar da,sallah asuba tare da jero addu,oi, Kubura ta na zuwa islamiya don haka tasan abinda ya kamata nadaga addini, Matsala guda shine addu,a idan har babu tsabtatacen zuciya ba lalai ne ta karbu ba, ga Allah Domin Allah yana amfani ne da zuciyoyin mu, Yunwa take ji don haka tadan gyara jiki irin na,amare ta nufi cikin gidan don samun abinda zataci, Saboda rabon ta da abinci tun da rana jiya da,mama,saude ta tsare ta dan ci kadan saboda jamma,a Kamshin soye soye ke tashi a gidan ta nufi kitchen inda take jin motsi Yar aiki ce ke ta faman aikin kayan break fast ita kadai a gidan, Motsin yara taji daga bayan ta wanda batai zaton cewa Nura din yana da yara har uku ba haka ? Basu bi ta kanta,suke magana da yar aikin su cewa tayi ta basu abinci kada su makara zuwa islamiya, don yau ba ranan zuwa boko bane, A hankali ta juya don jin abinda yara suke cewa baba oyoyo, Nura ne tsaye daga bayan ta , yana,wa yaran shi murmushi a cikin fara,a, Sai ga Uwargidan mai suna Jamila tafito cikin jefa dan kafa gudan ta take tafiyan ta, tasha kwaliyanta ba laifi don kyauta ya fito sosai, matsalar ta guda shine kafa, Ganin Kubura a tsaye waje yasa ta kago murmushi a fuskan ta tana cewa a,a amarya kece a nan , Yanzu nake cewa na laikoki naga ko kin tashi ai kifito mu karya, Fuska a daure kubura ta amsa mata da cewa eh na tashi, ai, Sai dai idanuwan ta yana a kan Nura din wanda hankalin shi ke gurin yaran shi, Jamila tace Allah sarki to karaso mu isa dinning table sai mu karya gaba daya don ga Angon naki ya iso ai, Kubura wace maganar Jamila din ke bugun ta kamar saukar guduma a kai, Kubura tace ba a nan zanci ba asalima ni ba nawa tsarin ke nan ba ai, To inji Jamila wace amsa yazo wa banbarakwai, don ita a zaton ta tasamu abokiyar zaman kwarai zasu zauna su hade kan su su zauna lafiya, Jamila tace to ai shike nan idan kin tashi ga abin kari a table kya karya ai,, Sai a lokacin Nura ya bar yaran shi ya nufota yana fadin, Kizo a karya gaba daya haka muke karyawa a gidan nan mu a tare, Cikin kwarin gwiwa Kubura tace bata tashi karyawa ba asalima ita ba,a tare da kwamacalan iyalin shi zata karya ba, Wata uwar harara ya jefa mata wanda yasa ta shiga hankalin ta don tun a waje tasan halin Nura bai daukan raini ga mace, Kawai dai kwadayin duniya ce yasa ta yarda ta cusa kanta a gidan shi a matsayin matar auren shi, Juyawa tayi zuwa dakin ta duk da yunwar da take ji amma ta dage sai tajawa kanta aji a gidan , Don ita matar soyayyace ba matar cushe bace wace aka bashi a matsayin kyauta, ****** ********** ****** Ina, zaune a bakin magudanar ruwan gidan ina wankin yan kayan wankin mu don da,safe nake wanki saboda gudun kada rana yai min, Babu kowa a wajen gidan sai ni kadai dake ta faman sintiri a tsakar gidan, Ganin mutum nayi tafado gidan babu ko sallama har saida nadan razana, Zahar ce duk fuskanta a kumbure yake da alamar dai babu lafiya , Nai mata,sannu da,zuwa duk da batai min sallama ba da zata shigo gidan, Ban tsanmaci ta amsa min ba nikan naci gaba da aikina kawai, Daga gurin da nake zaune nake iya jiyo muryan zahar a cikin kuka tana mayar wa mahaifiyar ta,abinda yafaru, Ban damu da wai sai na saurare su ba don ba matsalata bace sai har kokina nakeyi ina jin muryan Umma har kunne, take kwarar makogwaron ta, Sai surfawa kishiyoyin Zahara zagi take tana cewa wallahi basu isa ba, Sai dai maigidan yasan yadda zaiyi da yar nata amma bazata yarda ana cusawa yar ta sunnu ba,agida don an ganta yar karama za,a ce duk wani aiki a gidan itace zatayi shi wai don tana karama, Hamzane ya shigo gidan da,sallama a bakin shi tun daga kofa yakai idon shi a kaina ina kokarin shanya kayan dana wanke a giyar shanyi duk da igiyar yafi karfin tsayi na, Tausayin yadda banda hutu ko kadan agidan yake, wanki, shara, girki, da duk sauran aiyukan gida yanzu nice mai yin su, Kuma babu nuna gajiya ko kadan a tare dani idan ina aikin, sam ban d time din kaina ko kadan, Sanni da zuwa nai mashi yayin da ya karba yana min sannu da,aiki idanuwan shi nabin yawan kayan da,na wanke tun da farar safiyan nan, Dakin Umma y nufa don can ake nemar shi inda tun a kofa yake iya jin muryan Umma din, Yashigo da,sallama idanuwan shi na akan zarah da yaga tana kuka wiwi da hawayenta shabe shabe a fuskan ta, Yana kaiwa a tsugunne yake cewa Zarah lafiya dai ko tun da,safen nan gashi kuma kina kuka haka ? Injin dai lafiya dai ko ? Umma ce ta cabe zancen da,cewa ina fa lafiya munafukqn kishiyoyin ta,sun hana min yarinya zaman lafiya a dakin ta, Umma may yafaru yake tambaya a cikin son kaguwa da jin abinda yasa yar uwar shi take kuka haka da safen nan, Wanan karon ma Umma ce takara magana da cewa wai kamar zarah za,a ce itace zatayi duk wani aiki a gidan su, Yacw Umma ban fahinta ba aiki kamarya za a ce itace zatai komai a gidan ita kadai, Yanzu mai ya kawo matsalane wai take wanan kukan haka ? Hamza ke tambayan uwar cikin dan kaguwar son yaji may faru, A,hasale Umma tace gashi ko na fada maka abinda yafaru , Wai sai tadafa masu abinci tunda safen nan tunda,basu da abin da,zasu dama kunu kowa yasha, Inda Zarah take zaune ya ke duban ta acikin mamaki yace yanzu don dafa abinci kawai ka zo gida da,safen nan zarah, Ina idan mace tai aure duk wani aikin gida ya,wajaba a kanta ke nan, Kamar ya ? Umma ce ta jefo mai wanan tambayan a gagauce, Yace Umma yanzu ina ga Aisha can tun asuban farko take wajen nan bata huta ba, Ita ce komai na gidan nan hatta abinda ya kamata ace Asma,u ko Amina sunyi a gidan dasu jibrin duk itace yanzu maiyi, Waya taba jin tun shigowar ta gidan nan tayi korafi ko wani nata yace wani abu, akai, Umma ta cabe zancen da cewa oho don Aisha tana aiki a gidan nan sai akace Zarah ma taje tayi ko ? To bazan dauka ba gida kamar gidan Bukar za,ace Zarah ce mai girka abinci safiya da marance aci, Hamza ya dan kallo Umma yai murmushi yace Umma wanan abin ina ba bakon abu bane ga diya mace kamar yadda kikace , Duk yarinyar da tai aure tasan cewa akwai irin eanan a gidan aure don haka takoma dakin ta tayi hakkuri kamar yadda kowa ma keyi, Tabari idan wani abin ya hadata da mutanen gidan ko mijinta ba akan girki ko aikin gida da yake bautan aure ba sai tazo ayi magana amma wanan ai kowa yasan dashi a gidan aure, Shiru Umma tayi don bata da bakin cewa wani abin don ita da bakin ta furta mai hakan alokacin da yasamay ta akan zancen cewa, Aiki yai wa Aisha yawa a dan rage mata wasu daga ciki arabawa Asmau da Amina su dinga taya ta, Amma fir umma ta,rufe ido tace ai Aisha zaman aure ne yakawo ta dole tayi don suma idan sunyi aure zasu yi agidajen su, Nan Umma ta shiga fadan karya tana fadin cewa ai ak8n ba,daya bane nan gidan har mutum nawa ne acikin sa da za a hada dana gidan da zarah take, A karshe sai cewa Umma tayi Zarah bazata koma ko ina ba sai maigidan nata yazo sunyi mai iyaka don yarta ba boya bace, ai, ****** ********* ****** Ina zaune daki bayan na fito daga wanka ina shirin zuwa dora girkin rana, Zahar ta,shigo dakin tana ce min bata ganni ba tun dazu gashi ta kasa barci, don ta dan kwanta ta huta amma barcin ya gagare ta, Tace ai ina ce barci kike ke ma nace a,a cikin danbsakin fuska don bawai na saki jiki da ita bane tunda ban saba hakan ba ni, Nake ce mata wankin kayan mu nayi yanzu nake batun fita na dora girkin rana kada na makara, Tace kardai nace kece duk kikai wanan wanki dana gani a igiyar shanya waje, Murmushi nai mata batare da na bata amsa ba ga tambayan ta, Take cewa ina su Asmau ne wai naga basu gidan tun da na,shigo,? Nan ma dai shiru nayi sai ce mata nayi naso nazo gidan ta amma banda time saboda aiki bai bari na fita ko ina, Tace ke dai baki son zuwa ko ina aini nayi fushi wallahi ace wai har yau baki san dakina ba Aisha, Nace ban fita ko ina saudaya na fita ko shi da darene na shiga gidan mu gurin yiwa Kubura murnan aure, Ranan a tare da zarah mukai girki inda sai kallo na take da nazari na kawai, Take ce min a lokavin da muke cin abinci a wani katon ture , Aisha idan yamma yayi Alhaji baizo ba komawa zanyi dakina, Don maganan yayana yasa jikina yin sayi kuma na gane kuskure na, Don dai kinga yanzu bawai muna zaman fitina bane da abokan zamana amma kinga kawai sai shedan ya rudeni nai masu rashin mutinci kan dan abinda baikai yakawo ba, Ita kuma Umma maimakon tai min fada tunda ke ma anan tsaye kike kyam da,aiyukan gida wanda ko kwatan shi banayi amma wai sai ta goyi bayana, Sai a lokacin nai magana nake cewa Anty zarah kiyi hakkuri duk abinda diya mace zata gani a gidan auren ta idan har ba mijintane ya kawo wani abin kaucewa addini ba to muddin tai hakkuri zata ga bayan abin in har akwai rayuwa, Don kin ga ni karama ce amma na,dade da,sanin cewa hakkurine rayuwar aure, Musanman ladabi da biyayya suke kawo zaman lafiya a aure, don wanan kawai ya ishi mutum zama makamin daki, Don haka ki bar sauri zuwa gida kawo karan rayuwan auren ki wa iyayye, Don sai ke kiyi hakkuri amma su gida bazasu matan ba karshe ma,sai su kama ganin bakin mijinki su dauke shi mai rashin adalci, Cikin dan marairaice murya kamar wace zatai kuka taje cewa wallahi nayi nadamar wanan zuwan gida danayi matar yayana, Kuma fa Alhaji baya ko gari yatafi kurmi kai kaya gashi ita uwar gidan mu bata son abinda zai bata rayuwana a gidan nan ko kadan, Nace Gaskiya Anty Zarah kiyi maza ki koma dakin ki kafin Alhajin yadawo kiji kunya tace ai yanzu kuwa don duk abinda Umma zata ce sai dai ta fada, amma ni komawa zanyi dakina tunda ba fada nayi da kowa ba, Tace bari a kira min yayana ya bani kudin mashin yanzu nakoma nace sai kuma kibawa mutanen gidan hakkuri tace bari kedai Aisha, Yaya Hamza ta leka da kanta takirashi dakin mu suka shiga inda ta fada mashi kudirin ta na niyar komawa gidan mijinta, Kirana yayi yana cewa nazo na bashi kudin daya bani ajiya jiya dadaren , Nadauko mai yacire duba daya daga ciki yabata yace taje tayi hakkuri a dakin ta, Anan Allah ke son gani rayuwan ta don haka don Allah ta rika hakkuri don dai taga mijin ta yana sonta sosai kada tabari aji su dashi, Sallama mukaji na wata mace, a tsakar gida Aisha naga tadafe kai tana cewa Lah wallahi yayace tazo da kanta, Sallamar matan biyu ba, amsa mata ba sai nice nafito daga daki ina karba mata cikin sakin fuska nake mata iso da ta shigo zuwa dakin Umma, But Umma din tafito daga waje tana cewa gani ai basai tashiga ba, Murmushi matar tayi a,cikin fara,a take cewa ina dai fatan zarah tana gidan nan a daidai lokacin da nake shimfida mata tabarma don ta zauna, But Zarah ta fito daga dakina tare da yayan ta tana cewa Lah yaya yanzu fa nake batun komawa gida sai kuma gaki, Matar da,aka kira da yaya ta dan kaiwa zarah din harara tace shine kawai kikafito amarya babu sallama ko sai nadawo, Tace ban zaci cewa zai kai har wanan lokacin agida ba shiyasa nafito, Haba Amarya yanzu idan Alhaji yaji cewa kinfito ya kike son ku kwashe dashi, Nima sai da na idar da azzakarah din da nakeyi ne naji shiru shine na tura danki ya,dubo min ke yake cewa,wai bakya nan kuma kin rufe kofa, Shiru shiru zaki dawo bamu ganki ba,shine nake ce masu subari na biyo ki naji injin dai lafiya ko ? Zarah wace ke ta faman shan harara gurin Umma take cew lafiya nazo duban matar yayanane gatanan, Sai a lokacin matar ta kai kallonta gareni tana cewa au itace nan Tubarkkalah masha Allahu, sam barka wallahi, Allah ya bada zaman lafiya yabada kazantar daki da,wuri, Umma kan baki ya mutu don haka taja bakinta tai shiru sai faman cika take tana batsewa don takaici, Tana kallo Zarah da,abokiyar zamanta sukai muna Sallama suka tafi,, Inda nai mats alkawarin cewa zan shigo mata wuni insha Allahu ****** ********* ****** Abin ya,daure wa Kubura kai sosai don tun daren farkon ta,dashi duk abu ya karkare jagule mata a gidan, Gadai komai na arziki kamar yadda take son samu a rayuwanta amma abu yaci tura, Don sam ko kallon arziki bata isheshi ba balle yasan da,wata amarya agidan har yai rawan kafa a kanta, Dakinta yanzu ko kallon part din tanaji ma baiyi,a rayuwan shi kwatakwata, Gashi ita tana bukatar kasancewa a,tare da mijin ta koda yaushe, Irin rayuwan data shirya zasuyi idan sunyi aure dashi ko ita idan tayi aure zatayi da mijinta yanzu duk babu wanan a tare da ita, Saidai ya shigo taji muryan shi yana hira da yaran shi ko kuma magana da yar gurguwar matar shi mai dangisawa, Don haka yau a,shirye take da zaran taji muryan shi zata tunkare shi don taji inda matsalar yake mata, Tana zaune zaman jiran shi don ta san lokacin dawowan shi gida zuwa yanzu, duk da bata samun kyakyawan kulawan shi, Zaune duke falon gidan gaba,dayan su ana hira sai dai ita kubura bawai hiran ne takeyi ba, Ya,shigo da,sallama hannun shi da ledoji guda biyu yau ba karatu duk yaran suna gida a lokacin, Sannu da zuwa suke mai yana ta faman ansawa da fara,ar shi sai da tace mai sannu da zuwa kamar kowa a gurin Sannan yasan da zaman ta a falon itama ledar dake hannun shi ya mikawa yaron shi guda yana cewa karbi wanan naku ne, Dayan kuma ya mika,wa Uwargidan shi yana cewa ga naki ke kuma, Daga haka yai shigewar shi dakin batare da ya amsa mata gaisuwan nata ba abainin iyalin shi, Sai da akai kamar minti biyat zuwa goma hankali yan gidan yana ga tabon tsarabar da ya,shigo masu dashi, Kubura ta mike a hankali tabi bayan shi zuwa dakin nashi sai dai gabanta sai faman faduwa yakeyi, Tai sallama inda ta hango shi yana kokari balle aninin rigar sa baka dake jikin shi, A cikin yar sakin fuska ya karba sallaman nata inda ta tako zuwa gare shi a hankali, Ya zubo mata idanuwan har ta karaso gare shi inda ta zube a gaban shi tana mai marairaice muryan ta, Don girman Allah Alh Nura ka fada min abinda nai maka kake wanan fushin dani haka ? Wata irin tsawa da harara ya,daka mata a lokaci guda Yana cewa amma kin raina min wayo da hankali Kubura, Ni zakizo don baki da kunya kina tambaya na wai may kikai min, Kina nufin ke nan ma baki san abinda kikai min ba, Dake da uwar ki kuna nufin ni shasha nrme ban san may nakeyi ba ne ko ? Oho so kike na zauna nace ke Kubura ga abinda kikai min Kubura tace cikin sanyin murya amma yana dakyau daka fada min don nasan laifin da nai maka kaga sai na gyara ,ko, Tsaki yaja mata tare da kara balla mata wani harara yana cewa look Kubura ki fice min daga daki kafin na kara hasala dake, Rainin hankalinki yana,so yai yawa don har zaki iya,shigowa ki nuna min baki fahinci may nake nufi ba, Bazan taba yarda da ke ba,a,rayuwata don kin bani mamaki sosai wallahi, Kubura ta,dago kai idanuwan ta,da,suka cika da hawaye a lokacin tace a cikin raunin murya, Alhaji shin dama ka,auroni ne don kazi ka,wullakantani kaci min mutunci yadda ranka yaso ko kuwa, Kayiwa Allah Alhaji idan har da,wani manufa ka kawoni gidan nan dama ba,sona kakeyi ba ka sallamay ni na koma gidan mu yafi min wanan zaman a haka, Ya kawo mata wani irin naushi a fuska da,sauri Kubura ta kauce ma naushin, Yana cewa yar iskan banza kawai kin riga da kin gana zubar da mutuncinki duk a,waje shine zaku hada ksi da mahsifan ki ku cuce ni, Don ina Nuran mahaukata zaku yi min rufa rufa ba zurfi azaton ku bazan gane ba ko may ? Da,sauri Kubura ta,dago kai tana mai kallon shi a lokacin duk idanuwanta sun kawo ruwa yai tsuki yanufi hanyar bathroom din shi yana cewa idan nafito ma,samay ki a nan sai na,wullakan taki a gidan nan yau, Kubura taga da gaske yake don haka tafice tabar mashi dakin tafito bata damu da mutanen dake falon ba tana kuka, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑SARAUTAR MATA 👑 1⃣4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA YA ARRAHAMANI RAHIM, YA ZUL,ZALANI WAL, IKRAM,,,, YAN UWA INA MAI MIKA GODIYANA A,GAREKU HAR KULLUN DA IRIN HADIN KAN DA KUKE BANI GURIN GANIN SAKON DA ZAMU ISAR A WANAN DAN LABARI ZAI AMFANE MU A RAYUWAR MU, ALLAHUMA AMEEN ALLAH YA BAMU IKON KARA RIKE AMNA AKAN ADANA MIN WANAN NOVEL DIN ANAN BATARE DA MUN FITAR DASHI WAJE BA,,, NAGODE YAN UWA Zancen karatun Hamza yan zu an kamala komai don haka,sai faman shiri yake na tafiya karatun shi, Inda zai tafi ya barni da Umma Rabi da yan uwan shi a gida, tare zan zauna dasu sai dai yazo indan ya,samu dan chance, Ummu ce mai shiri hatta kayan da zai tafi dasu a dakin Umma jakar tafiyan nashi yake, Ni iyakata ace na dauko abu kaza daga cikin kayana na jeni na dauko, Alokacin Umma tafi nuna matukar damuwar ta ga tafiyan na Hamza sosai, Don har tadawo tana bani tausayi don dan motsi kadan zata daga hannu a sama tana cewa, Ya Allah ga dan marayanka nan Hamza baida kowa a garin mutane Ya Allah ka,zama gatan wanan yaron ka,tsare muna shi, Sai daren tafiyan nashine bayan ya kamala muna komai da ya kamata ace ya bar muna, Kanin Ibrahim dayake shine babban yanzu bayan Hamza din zai zauna a,shagon dan uwar nashi, A wanan daren ne Hamza ke kara jamin kunne akan na kara hakkuri da zama da mahaifiyar shi da yan uwan shi inda yake ce min na kuma dinga kokarin kula,da kaina musan man cin abincin da nake sakaci da ci a cikin lokaci, Lokaci mai tsawo muka dauka dashi a ciki wani yanayi da ban taba sani ba, , Bayan ya samu natsuwar kan shi yake ce min Aisha wanan sauran kudin dake a gurin ki idan wani bukata ya taso zaki iya dan dauka daga ciki kina amfani dashi a,asirce, Sai kuma yai shiru kamar mai nazari can yake cewa naso ace Umma ta barki ke ma kin dan ci gaba da karatun ki don hakan zai kara kawo min kwanciyar hankali a idan nake, Wani irin abune naji a,raina wanda zan iya cewa kolon bakin cikine yadan tokare min a,wuya na, Ya kare zancen shi da cewa ina fatan zan je nadawo batare da na,samu wani matsala daga gare ki ba, Nai maza nace mai cikin dan karayar murya insha Allahu ba zaka,samau ni mai saba maka,ba, Yace madallah Sai naji yana sauke ajiyar zuciya a hankali tare da dan kifa cikin shi ina zaton tunane yakeyi, Gari na,waye gaba dayan mu muna a kofar dakin Umma inda suke daga ciki suna kara kimtsa kayan nashi, Bai dauki dogon lokaci ba ya fito rataye da wata bakar, jakar shi da,ya,sayo na tafiya, Sallama yai damu a cikin wani yanayi, da bana dadin raiba , Umma har kofan gida inda zai hau mashi zuwa tasha ta bi bayan shi a cikin addua, Daki na na juya acikin wani irin dacin rai wanda ban san dalilin shi ba, a lokacin, ****** ********* ******* Iyanzu Kubura abin duniya duk ya taru yai mata yawa a rai don a gurin Jamila matar Nura kawai take dan samun sassauci a gidan, Ko shi ba wani can mai yawa ba saboda ta fahinci a kwai rashin mutunci a tare da Kubura din, Gashi kimanin kwanaki takwas ke nan rabon da taga Nura a idon ta, Kullun bata sani dawowan shi kuma bata sanin fitan shi gidan, Sai da abinda take zato ko tsanmani shine, yana dawowa ne a cikin dare da,asuba yake kuma,barin gidan, Jamila ce ta dan tako a inda take zaune tana cewa kauna ta wallahi yau naso naga mai gidan akan zancen kayan store din mu amma kuma lafins nane daban fada maki tun jiya ba ki fada mai, gashi yafita kuma ina ga mai ma na yau kawai ya rage, Tace a cikin dan sakin fuska aiko da tun jiya naji da na fada mai ,gashi ya fita tun safe kamar yadda ya saba fita, Jamila tace ai nace laifina ne amma kada ki damu zan dan yi dubara don baza rasa abin yi ba ai, Ta mike dingis dingis ta yi hanyar fita waje ta kiran yar aikin su dake daga waje, Kubura tabita da wani wawan kallo tana cewa gurguwar banza kawai sai na ture dan kafa gudan wata rana naga tsiyan botsewa ta bayan nan, Har kwana goma,sha bata sake ganin Nuran ba sai a daren na sha biyar ne tana kwance a cikin dare taji motsin shigowar mutum dakin, Dakyat ta bude nauyayan idanuwan ta dake cike da,barci a cikin su, Ta gefen ta ya kwanta a hankali inda yaja bargo ya dan rufe su aciki a tare, Batai tsanmanin cewa ya kai ga gamsawa da abinda yake so ba taji yaja tsaki, Inda ya mike yakai wani lokaci a gurin window dakin a tsaye can taji yabar dakin a cikin bacin rai, Gaban Kubura ya yanke ya fadi inda take cewa kar,dai ace shiga tsakanin su akayi da angon nata Nura, Haka gari ya waye mata a cikin tunanen abinda ke faruwa a tsakanin su da mijin nata, Sai dai tasha alwashin cewa zata ci gaba da boye sirinta bazata yarda har mazauna gidan su fahinci cewa akwai matsala a tsakani ta mijin nasu ba , Abinda bata sani ba shine Jamila ksllon ta kawai takeyi don ta,fahinci akwai matsala tun farko a tsakanin mijin nasu da amaryan shi Kubura, Don ita fa Uwargida ce duk wani motsi na duk wanda ke acikin gidan yana a idanuwan ta, Sai dai kawai ta nuna rashin ko in kula a fili tunda ba a tambaye ta komai ba a zance, Idan mutum ya ga Kubura zai yi zaton cewa tana a tare da farin ciki saboda akwai ci da sha a gidan ga sutura na alfarma, Abu guda yai mata nisa shine so da kauna mijin da take zaune a gidan shi a matsayin mijin aure, Kubura karo na farko da tazo gida inda take matukar son hanin mahaifitar ta don duk fadin duniyan nan babu wanda zata iya fadawa matsalan ta,sai mahaifiyan nata, Kubura wace ta,shigo gidan su da yar makalalan fara,a a fuskan ta, Amma bai hana su Ummi da Atika su fahinci cewa akwai matsala a tare da ita, Atika ce uwar shishigi take cewa da mai gidan naki kuke be ? Kubura tai wani dan tabe fuska tana cewa yanzu ya ajeni ya tafi bazai samu shigowa ba sai yadawo, Ummi ta dan karaso ida suke tana wa Kubura din yaya, gida da mutanen gidan ba,wai sun damu da sai ta,shigo ta gaida su ba, Badon komai ba,sai don sani halinta da,sukayi na tsageranci tun a gida balle yanzu da take ganin cewa ita ma matar daki ce kamar kowa, Daki mahaifiyan ta ta shiga inda mama Saude wace ke wanki a bakin kwatan gidan ta taso tabi yar nata daki wace ta shigo da,alamar a gajiye take, Mama Saude na,shiga daki ta,samu Kubura kwance saman gado rigingine, Tace a cikin yar fara,ar ta ashe kuna tafe shine bamu sani ba nadan maki tanadin wani abu, Dagowa Kubura tayi daga kwancen da take tace cikin bata fuska mama barshi kawai ba wanan bane matsala, Sai ga hawaye shar daga idanuwan Kubura tana fadin mama wallahi a kwai matsala sosai, Kofa Mama ta,duba da,sauri idan babu mai shigowa dakin a lokacin, Tace wa yar nata share hawayen ki kada wani yazo ya,ganki a haka kina kuna, Juyawa mama tayi zuwa waje don ta dan saka mutana fita daga zargi inda tabar kubura din tana darzan kukan ta ita kadai a daki sai da tai mai isar ta tagaji don kan ta ta share hawayen ta, Mama Saude wace duk abinda take hankalin ta a tashe yake,sai faman tunane take ko daga ina aka samu matsala da yarta, Shin da abokiyar zaman ta ne ko da maigidan nasu ne take da,matsala, Mama Saude ta koma dakin a lokaci yar nata ta dan samu natsuwa daga kukan da takeyi Jin shigowar mahaifiyar ta yasa ta dan dago kai tana sauke sanyayar ajiyar zuciya, Mama Saude ta samu guri ta zauna don ta ji may ke faruwa da yar nata alfaharin ta, Ki natsu Kubura ki min bayanin may ke faruwa,ne wai daga ina kuma matsala ta,fito maki, tafa a cikin dan tausa murya, Cikin dan sauta murya take cewa wallahi mama daga Nura din ne amma don kwata kwata tun ranan da na,shiga gidan ban da wani matsayi mai muhinmanci a gare shi, Sai kiramin yake wai muncuce shi mun zalunce shi mun mai munafunci, Da,sauri mama tace mata a kan may kuma Kubura ? Mama nima ban sani ba wallahi abinda dai yake yawan fadamin ke nan a duk ranan da muka kasance a tare dashi, Kubura ko kin taba sanin wani da namiji ne a,waje kafin kiyi aure, ? Da sauri Kubura ta dago kai a cikin hawaye tace wa uwar nata ,a,a mama, wallahi ban taba kwaci da kowa a waje ba, To idan ko har hakane shiga tsakanin ku akayi ke nan ? Kubura tana kokarin tsayar da hawayen ta take fadin nima wallahi mama tunanen da nakeyi ke nan , Don wallahi matar nan tashi ba karamar munafuka bace don nuna min take wai ita ta Allah ce a fili gata abin tausayi amma,sherin ta yai yawa, In kin ga yadda yake wani nan nan da ita da yaran ta a gidan sai abin ya baki mamaki kamar ba gurguwa bace, Mama Saude tace ai nasan irin su ko bagani dasu ba,a gida badon ina tsaye ba agidan nan da ai yanzu sai tarihi na ko, Don haka ya zama dole mu dauki mataki akan ta zata san da cewa dani take, ai,,, Haka kubura tai yini daga baya tadan sake jiki tafito waje inda suka dan taba hira da matan gidan nasu sama sama, Har take tambayan Ummi labarin Aisha Ummi bata bata amsa ba amma Atika ke fada mata cewa ai Hamza ya koma makaran ta sokoto karo ilimi, Kubura tace wata sabuwa kuma, ****** ********** ****** Abinda ya daure min kai yanzu shine tun tafiyan Hamza makaranta na rage yawan aiyukan da,nake a gidan Umma Rabi, Yanzu a tsakani na da ita sai wani haba haba take min, ba tsangwama ba,takura,, Idan ina daki itace zata kwada min kira tace nazo ko nafito mu sha iska a,waje, Akan shigo da,waya wani lokaci daga waje wurin abokan shi sai mu gaisa da shi, daya bayan dayan , Sai dai hiran da shi da Umma yafi daukan lokaci don bata bari na dauki lokaci muna hira, balle ma ni may zance mai, A wani safiyane muka tashi da labarin cewa motar yan zuwa kasuwar kauye ta,yi accident, Hakan yasa hankalin mu tashi don mun san cewa akwai mutanen uguwar mu masu zuwa don da farko har da Ibrahim za ai wanan tafiyan amma sai daga baya yace bazai samu zuwa ba don rana yayi a lokacin, Amma Baba Mudi yana a cikin motor cewa Ibrahim wanda yazo yana fada muna,wanan labarin na tashin hankali, Hakalin mutane duk a tashe yake a lokacin kafin aji labarin halin da suke ciki, Sai zuwa dan rana akasamun labarin cewa al,amari da sauki sai dai sunji ciwo daga cikin su akwai masu kariya wasu kuma basu ji ciwo ba ma sosai, Shi Baba Mudi yadan samu gwaucewa a kafadar shi hakane yasa bayan an ja mai akadawo dashi gida daga asibiti, Yan uwa da abokan arziki sai shiga suke don zuwa duba lafiyan Baba mudi wanda a zahiri yake jin jiki, Duk yaran shi masu aure a lokacin suna gida gurin ganin jikin mahaifin ns su,, Ganin hakane yasa Ibrahim wanda ke zaune waje yana ganin mutane na ta shiga yashigo gidan , Yana kwada min kira a kwance nake lokacin dakina kadaici yana damuna, Sai nake jin kiran daga sama na taso zuwa waje don naji may yake kirana dashi haka , Ina daga labulen dakin nawa na hango shi a tsaye zai shiga dakin Umma yana fadin ki shirya ki shiga gidan ku ki gaida Baba don naga duk yan uwan ki sun shigo gidan, don duban jikin malam din, Kinga ke gaki a kusa ke ce yadace ace kin fara shiga, amma baki shiga ba har yanzu , Yadda ya fahinci fuskana yasa shi gane cewa umurni nake jira daga gurin Umma, Ibrahim yace kai tsaye jeki shirya ki shiga ki duba lafiyan shi, ki dan zauna har zuwa lokacin da zaku watse, Umma ce tafito daga bandaki hannun ta dauke da tsohuwar butar ta duk ta mokade take cewa, Tau rasa kunya kaine ma mai bata umurnin fita ke nan ko,? To dakata kaji ko mijin da ya ajeta bai isa yace tafitaba kai tsaye ina cikin gidan nan, Ibrahim yace Umma yanzu may ye rashin kunya aciki mahaifin su ne fa ya auna arziki duk yan uwanta dake nesa sun shigo sai ita dake nan manne dasu ne za,a ce har zuwa yanzu bata shiga ba, Umma wanan ai sai ki sa mutane su zarge mu akan yarinyar nan, wallahi dama gashi an fara fadin cewa kece ke takurawa yarinyar nan, Kin ga za,a ce ai fon bashi ya haife ta ba yasa bata shiga gaida,shi ba, Umma ta aje butan dake a hannun ta tana cewa cikin salati tare da tafa hannun ta, Ibrahim bai bari ta furta komai ba yake cewa, yanzu dai Umma,don Allah ki bari ta tafi kawai koma maye daga baya zamuyi maganan, Ya shige dakin ta don ya dauki abincin shi a ciki yayin da yabar Umma a waje tana ta faman sababi dashi, Daki na koma na gyara jikina na canza tufafin jikina tare da sake hijjab dina, Na samu Umma a bakin randar ruwan ta tana zuba ruwa a wani kwano mai fadi, Nake ce mata a,sanyayye Umma zan tafi sai na dawo, ki gayar min dashi don dazun da,aka dawo dashi na,shiga don ina waje suka dawo, ****** ********** ****** Baba yana kwance a saman katuwar tabarman roba a barandar kofan turakan shi Atika tana daga gefe tana mai fitara a hankali, Nashigo gidan da,sallama na idanuwa na akan baba wanda ke cije labben shi ya na gyara kwanciyar shi a hankali, Direct inda yake na nufa ina mai gashe shi tare da mashi sannu da jiki da auna arziki, Daga nan nagaisa da,su mama Saude da Ummi na, dake daga cikin kitchen tana aiki, A hankali na mike inda na kwabe hijjab dina na rataye a saman kofan dakin Ummina na shiga kitchen din muka karasa aikin a tare, Su Kubura suna dakin mama Saude suna tahira a cikin kyalkyala darita kamar ba mahaifin su suka shigo dubiya,ba, A tare Ummi ta,saka muna abinci dasu acikin wani katon ture duk da naci abinci a gida amma Ummi tace naje mu hada hannu dasu, Anty Sa,a ce kece min bayan nadan samu guri a can gefe na zauna, Yar Agwai ke dai ba,ruwan ki da zuwa gurin kowa kin yanke zumunci da kowa ko ? Nai murmushi ina cewa anty ai zan zo sai yadawo gari zan shigo in gaida ku, Kubura ta tabe baki tana cewa idan ma baki shigo ba ba sai ki ta zama cikin wanan rubaben gidan naku ba, Anty Sa,a tace haba Kubura wanan wani irin zance ne kuma haka sai kace ba yar uwar ki ba, Yar Agwai din ? Tawani dan tabe baki can gefe sai uwale ce ta canza topic din hiran a,daidai lokacin da za,a fara cin abincin dana kawo, Wai ya zancen wanan abin da kikace zaki aiko min dashi ne ranan? Nan suka fara hiran irin kayan matan da suke amfani dashi, Da kuma irin yadda abubuwa ke gudana a tsakanin su da mazajen su, Wani irin mamaki ne ya rufe a urin bayanan da,suke tun dai Kubura da yarta, Nan suke musulta abinda ya dace mace ta soma yiwa namiji wanda zai sa macen shiga cikin rayuwan namiji har abada, Tsit nayi zakace ai bani gurin sai sauraren zancen su nake yayin da idan sun fadi wani magana nakan ji shi a matsayin rashin kunya ne, Don tayaya za,a ce mace ta zage tanawa namijin irin bayananan da,suke ta fadi a fili, Ganin hiran nasu bazai kare ba na mike zuwa gurin kara gaida Baba sai a lokacin na shiga daki gurin mahaifiyata, Tana zaune da yaranta suna cin abinci wanda nake gani tashin su ke nan daga barci take basu abinci Bayan na zauna ne Ummi ke ce min to yaya labarin mijin naki ? A kunyace na amsa mata da fadar lafiya kalau , Tau ki daiyi ta hakkuri don duk matar da mijinta yake karatu sai tayi hakkuri, Hakama zama da sararkuwa sai ki yi hakkuri k8n kai zuciya nesa, Don koda yake naga ai zaman naku ba,wani tsangwama sosai, Aiki dai ne kuma kin riga da kin iya su ko tun a nan gida don haka ki ta hakkuri, kin dai san irin halin da nake ciki a gidan nan ni duk abinda muti Um zai yi na kan barshi da,Allah don Allah bai barci , Na amsa a hankali da fadan To Ummi nagode insha Allahu zan kula kamar yadda kike fada min kullun, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣5⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA Na kamla duk wani aikin da zanyi a,wanan safiyan don yanzu ba,wani aiki mai yawa nakeyi ba, Don sau daya,muke dada abinci tinda Yaya Hamza baya gari, Abinci dare kawai nake dafawa inda da rana zamu gyara sauran tuwo ko yan cima muci sai dare kuma za,a ci mai zafi Hakan yasani yau yanke shawaran na tafi vidan zarah nakai mata,ziyara kamar yadda,nai mata alkawari kwanakin baya, Zama babu wani abinyi a gidan zaman haka kawai ya fara isata, banda yadda zanyi don tun tafiyan Hamza sai komai na gidan ya tsaya muna cif, ba wani motsi a gidan kamar baya, Yau dai na yanke shawara a raina zan cewa zan tambayi Umma zance zuwa gurin Anty Zahar kamar yadda nai alkawari zuwa a gaban ta, Da,daddare kuwa suna zaune gaba daya diyan Umma suna a tsakar gida zaune a,saman tabarma suna cin abinci,, A can daga karshen tabarman kadan nazsune sai dai zaman tankar a takure nake a gurin , A hankali na kira sunsn Umma tare da dan sunkuyar da kaina a kasa a hankali, Abinda duk yadawo da hankalin su a gare ni ke nan lokaci guda, A cikin ladabi na fara mata magana da cewa Umma dama ina son na tambaya ne ina son zuwa gidan anty Zahar ne kamar yadda nai mata alkawari ranan , Nakarashe zancen a cikin dan kara dukar da kaina kasa a hankali, Yar nan wai wanan futar da kike yawan yi haka na may nene ? Don kinga mijinki baya gari shike nan wani son fita yawo yazo maki a,rayuwa, To bazaki ba shin gidan Zarah yin ma ma wai kawai don son zuwa ganin may ? Wani iri naji a raina tare da kokarin hade yawun da suka taru min a bakina masu daci, Kafin na karasa hade su sai naji muryan Ibrahim yana cewa Umma yaushe Aisha tafita gidan nan banda labari, Shiru Umma tayi tai banza dashi tankar bata jishi ba yace ko fitan da tayi zuwa gaida baban su shine fita Umma,? Asmau tace ni wallahi Umma, Aisha dai ce amma ina zan iya ta zama gida haka ko da yaushe cabdi gaskiya nikan zanta zuwa gida kuna ganina koda yaushe, Amma gaskiya Umma k8 barta dan Allah dai ta tafi gidan Anty don bata taba fitaba fa, Jibrin yace wanan ai ta zama kifin rijiya bakauya kawai koda yaushe tana gida gurin umma kamar wata tsohuwa can, Umma tace tooo wooo ke nan kuna zugata ta fara kirkiro fita zuwa uguwa nan da can, Umma, kofa kitso da kumshi Aisha bata fita zuwa sai dai kullun itace mai jagwalgwalawa kanta haba don Allah dai Umma a sasauta mata wanan abin haka man, Umma ta juya inda nake zaune a marairaice tana cewa, kinji ai sun yardan maki saiki shirya idan kun tashi zuwa ku tafi, Ni dama bawani abu bane ban son wanan irin yawan fitan na matan zamani yarinya da kurciyar ta kin ganta nan yau gobe ki gan ta can kamar ba aure take ba, Aisha kan ba zatai haka ba Umma wace tun tana gidan su fita bai damay ta ba, ma, Hira,sosai ake a gurin na rayuwan duniya wanda akasarin firan ya koma a can gurin yan uwan su wa yanda zance tun shigowa ni banga suna wani mu,amula dasu yadda ya dace ba, Washe gari tunda safe na shirya don zuwa gidan anty Zahar yini, Na fito a,cikin shirina na nufi kofan dakin Umma don in mata sallama da kuma kiran yar rakiyata Asmau don mu tafi, Nace a sanyaye Umma na, shirya zamu wuce ta miko min wani leda tana cewa gashi ku kaiwa zarah kunce ina gaida ita, Asmau tafito a cikin shirin ta inda na dauki ledan da Umma taba sako mukai mata sai mun dawo muka bar gidan, ****** ********* ****** Karatu sosai yake ba kama hannun yaro don shi dama mutum ne mai kwazo a,rayuwan shi, Dan lokaci kalilan sunan shi yai fice a gurin dalibai da malamai a makaranta inda suka bashi classrep, na su, Mutane suna mashi kallon sauri ne matashin wanda baida ko budurwa balle matar aure a gida, Hakan yasa yan ajin nasu yan mata suke kawo mai hari don son kutsa rayuwan su gare shi, Amma da yake shi mutum ne mai bahagon rayuwa sai ya,nuna masu tankat bai fahince su ba bai gane nufin su ba a kan shi, Wani lokaci zai zauna yana tunanen gida Umma Aisha yan uwan shi, sai kuma shagon shi , Ga damana ta sauko yanzu hankalin shi ya koma ga noma tuburan hakan ne yasa shi yanke shawara cewa karshen wata zai dan je ya ziyarci gida kafin su fara texts da exam yadawo, Sabon Abokin harkokin shi na makarata mai suna Nazifi, shine ya hango shi a zaune daga gurin da yake yana ta faman tunanen gida, Nazifi ya karaso gaban shi inda ya dafa kafadar shi ya zama yake fadin mutumina yaya akayine na hango ka tun can zaune ka,shiga vabration, haka, Hamza ya dan sauke ajiyan zuciya tare da gyara zaman shi yana cewa bari kai dai mutumin Wallahi hankalina ya koma gida ne ina tunanen iyali na ne? Dariya sosai nazifi yayi tare da dan tafa hannayen shi yana fadin wallahi har ka bani dariya sosai, Wai iyalina sai kace wani magidanci wanda yabar mata a gida , Murmushi kawai hamza yaiwa Nazifi tare da mikewa tsaye yana fadin to da kai may kake nufi ne wai, ? Yaro kai ke nan muje hostel mu samu abinda zamuci Nazifi yace da dai yafi maka wanan fargab dajin da kakeyi, Maganar abokiin shi na,gida,ne ya fado mai a,rai inda dazai zo yake ce mai yasamu yar waya yasaya yabar daya koda yar nokia ce a,gida dayan kuma ya rike a hannun shi, Sai yanzu yagane hikimar yin hakan da abokin nashi ya,bashi shawaran yayi kafin ya bar gida, Don gashi yana,son sanin halin da yar mutane take a gida da ya barta tare da,Umma da yan uwan shi, Yana gidan ma yaya,suka kwashe da,Umma, balle yanzu da bai kusa dasu Duk da ga mata,nan wayayyu yan birni yana gani bila,adadi, amna sam hankalin shi bai taba,raya mai ya,shiga cikin so ko kaunar wata har sha,awa,yashiga ba shi kawai idan ma,wani abu yadan bijiro mai yakan dan tuna,da,yar matar shi da yabaro a gida duk da karama,ce amma,tafi mashi wa yanda ba halal din shi bane, ****** ********* ****** Mun shiga gidan sukuburan da,sallama sai yan kalle kalle nake tun a kofar shiga gidan, don wanan ne karo na farko da zan shiga gidan, nasu, Gidane mai tarin iyali mata da yara a cikin sa don tun a kwanan shiga cikin gida zaka fara jin hayaniyar mata da yara yana tashi, Parts, parts na mata biyu biyu suna,fuskantar junan su, Anty Zarah tana tsakar gida tana shanya wankin da tayi mukai sallama inda ta tare mu da murna tana fadin, a,a yau matar yaya ne a gidan namu lalai yau ana ruwa a garin nan, Ina yar dariya yayin da nakewa sauran matan da suka sako muna idanuwa don su kalleni da kyau, Cikin yar siririyar muryata nake masu ina kwana tare da dan karasawa gurin su, Matar da na ke zaton itace uwargidan su na,shedata don kwanaki da ta zo ta biyo bayan Zarah din yasa na gane ta, Mun shiga dakin zarah duk da bawai takai sauran yan uwanta kayan daki bane amma dakin nata fes fes gwanin ban sha,awa, Mun zauna tafita zuwa can sai gata da goran kunun zaki mai sanyi da ruwan leda a cikin wani dan madaidaicin ture, Muna zaune muka fara,gaisawa da ita tana min wasan kaunar miji saidai ban iya mayar mata da,amsa don nauyin ta nake ji sosai, Mun bata sakon Umma inda tabude ledan sai naga tadan tabe baki tana cewa ita mama kullun tana kashe kudin ta,a gurin wanan abin, Ga wanda ta aiko min dashi last banyi komai dashi ba, Aisha ki dauka,mana idan kina so kiyi amfani dashi, Anty na maye fa ? Da sauri ta juyo inda nake tana cewa ke kayan matane fa kuma masu kyau na rasa a ina Umma ke samo su haka masu kyau wallahi, Tace bari wanan tabar nan nai maki bayani a kan su cewar wai Asamau dake dakin tare da,mu, Asmau tace ni yanzu ma gidan su shemau, zan tafi na,dubota nabar ku kuyi ta hiran ku na matan aure, Ta kalli kafata take cewa Aisha, don yayana baigari ki ka bar kafan ki hakan fari ba kumshi, Baki san cewa zai iya fadowa a kowani lokaci ba garin nan Asmau tace wanan aiko yaya yana gari bata gyara don ba ta fita zuwa gurin masuyi su gyara,mata, Zarah tace Aisha kina karamar yarinya ga mijinki yaro baki gyara yana can cikin manya mata yan duniya yana ganin mata kala kala a bariki, Ni,ma matan tsoho amma gani nan kullun dole a cikin gyara nake kin san mazan yanzu sunfi son mace mai gyara, Daki ,jiki abinci da kuma uwa uba can gurin aikin, Murmushi kawai nai mata tare da dan dukar da kai na, Asmau tana gama shanye kunun zakin ta tamike tana cewa zata gidan su Shemau kawar ta, don basu da nisa sosai,, Fitar Asmau dakin yaba anty Zarah damar fara yi min magana acikin sake jiki kamar haka, Yanzu ke Aisha inba abinki ba wake zama wanan zamanin haka dip babu wani motsi, Wallahi mazan yanzu sai a,slowa don basu da tabbas indai maza ne, komai dadin ki da miji sai ya cusa maki irin nashi kalar tsiyan shiya,sa kikaga mata a wanan zamanin a tsaye suke kem akan maza jen su don kada a samu matsala,. Anty Zarah ni to yaya nadsn zanyi tunda ba tare da wata,nake wace zata koya min wanan abubuwan, Don kinga a gidan mu al,amarin sai a,slow amma a kwanaki da baban mu baida lafiya mukaje gaidashi naji su Anty suna hira, Anty zarah tai shiru tana sauraren abinda zan fada mata, amma sai taji shiru, May kikaji suna fadi shiru nayi again ba amsa tace baki fada min sai nake cewa wallahi anty kunya nake ji don akan kwanciyar mace da namiji ne wanda ni Anty Sam ban masan da cewa akwai wanan abin ba ai, Dariya sosai Zarah tayi tana cewa wai yanzu Aisha kina nufin cewa ke haka kike dip dama ? Amma ko abin da mamaki ace wai yar yau wace tadan yi boko bata,san wani abuba akan zancen kwanciya da miji, Sannu a hankali take ce wa saurara kiji abinda zan fada maki kinga,duk da mijina ba yaro bane amma wallahi dole na zage damtse a gurin kyautawa a, makwancin mu, wanda har takai yanzu wallahi shi da bakin shi yakan fada min cewa yana matsuwa ranan girkina yazo ya kwashi garan da,Allah yai min, kinga inda kina tare da mijin ki mussaman ke din ma da kike ke kadaice a gurin mijin ki, Na farko ki tabbatar da cewa kin fara tsabtace jikin ki, Dakin kwanan ku sai uwa uba shimfidar ku wanda duk yadda zakiyi ki dinga kulawa da sake bedshet, Kamshi adakin ki duk lokacin da kikasan cewa mijin ki zai kasance a cikin dakin koda bawai wani abin zakuyi ba, yadai kasance dakin na bada kamshin dadi, Shiru nayi ina,sauraren ta tace, sai kuma nau,in abinci duk wai nasan cewa mu gidan mu ba,wani gidane mai wadatacen abinci ba irin na zamani, To amma kada ya kasance kice kullun sai tuwo zaki dinga bashi nasan cewa idan kin mai magana ya,sayo maku abu kaza a,,asirce zai sawo ki girka batare da,Umma tasan cewa kece kika ce asayo maku ba, Na kara gyara zama tace kinga indan kin hada wanan kin fara hada kanki ke nan, Sai ki koma a gurin nauin kwanciya wanda ko wani lokaci zaki kasance mai zuwa mai da,sabon sallo na dubarun mata, Nan tafara min bayani yadda zan kwanta da miji ba kunya ba wani jin nauyi tun ina dukar da idanuwa har na,sake jikina ina tambayan ta da cewa Anty kina ganin zai yarda kuwa, Ke ai abinda maza ke bukata ke nan mace taita sarrafa,su kamar masa a cikin tanda suya,, Hmmmm Anty ni ai duk na shiga tunane yaya zan iya tunkarar yayana da wanan irin akidar tace to zauna Aisha Idan yazo maki da tsarabar yar jami,a ai zaki gane kuren ki, Nace ai da na,shiga uku anty sai dai na koma gida gurin Ummi na ke nan, Allah ya rabaki inji Zarah abinda na,fada maki su zaki yi kokari ki rike su koda ba dukka, Nace ai anty zance ne fa na kudi kinga ni dake zaune futis saidai an bani ina zan samu kudin yin wasu abubuwa haka, Tace yo ke zaman zakiyi tayi bazaki koyi dan sana,a ko na ciki gida ba yara na shigowa saye, Mijin ta ne ya,shigo dakin wanda ranan ne zance na tantance shi da kyau dan dattijo mai dan farin saje a fuskan shi sai dai ba,wai tsoho bane can don bai kai shekarun mijin su Ummina ba, A,gabana suke dan wasan soyayyan su amma na fatan baki tana wani dan kararaiya a gaban shi take cewa daga dan wani kwanciya datayi tana wani dago gaba, Alhaji dama ina son kiran ka matar Yaya Hamza nane naje son akirawa maikitso mu da kumshi tai mata kudin da,zan sallamau ta nake son kadan bani, Yadan ja mata hanci yana cewa shine kike wani dan marairaicewa Ya saka hannu a cikin aljihun shi ya dauko kudi yana mai mika mata, Kudine wanda bazance ga yawan su ba yake cewa sai ki sallamay ta aciki dayani ai zasu isheki ko,? Tace nagode a cikin wani dan tausa muryan tare da cewa asayo muna dan abin tabawa in an fita, Yadan kara nufota nidai kaina yana kasa sai yar kara naji tayi na,wasa tana cewa wallahi kada matar ka taji kasan ta da kishin tsiya, Yace cikin dan nufar kofar fita daga dakin taji, mana ke dai kinyi arzikin bakuwar ki kawai, Mamaki abin ya bani yadda dattijo kamar wanan yake wasan soyayya irin haka Sabanin ni da ko kadan banga fuska ba daga ni har mijin ba,wanda ya iya wanan abin, Kamar yadda tace din haka akayi mai kitson su da kunshi tazo tai min da yake sana,ar matar ne nan danan aka gama nin duk da kitson sunyi yan yiri,yiri sosai, Asamau koda ta dawo tasamu ana min kwalliya don haka dole ta jirani duk da korafin da take tayi, Ni damuwa na,shine yadda yau zamu sha fada a,gurin Umma agida sai faman dada kitson da kumshi sukeyi, Duk sun kidimay ganin gashina yadda ya,sauko anty tace Aisha ga ki da,gashi kitso mai kyau haka,, Zaki bari ya lalace a banza, Aisha idan kin gyara wallahi nina fada maki sai Yayana yasan cewa yayi dacen mata a duniya, Anty dama da take cewa wai an hada Yaya hamza da yarinya wata kala can, Ai ko ita yanzu inhar tazo zatai mamakin ganiki haka Mai kitson ke cewa inane gidan ta zan diga zuwa intana bukata nai mata, Nadago kai inace mata ai banda kudin biyan irin wanan kitson mijina tallakkane fa, Allah ya kawo yayan mu yaga wanan gyaran irin haka shi da kan shi zai dan dinga bada kudi ai ai maki, Inda Asamau ke cewa ai kafin ya shigo har kitson ya tsufa,ko, kilama har ki canza wani, Tsab na fito a cikin wasu kayan anty Zarah data bani nasaka bayan nai wanka inda takara hada min yan kayan gyaran mata tai min bayanin yadda zan yi amfani dasu, Ni kaina nasan cewa na canza ranan don na dubi madubin dakin nata naga irin yadda na sake lokaci guda,, ****** ********* ****** Kubura inda sabo yanzu ta saba da halin Nuran ta, don haka zaman nasu yake ba dadi ba kuma zafi, Sai dai hakkuri kawai takeyi don yadda Mana tai alkawarin zasu san abinyi akai din tayi, Don yanzu yakan dan shiga bayan dan kwana biyu haka su kasance a tare, Sai dai ta gane cewa aduk lokacin da ya kwana da ita wanan halin na kiyayyan nashi yakan taso mai yai ta tsaki har gari ya,waye su kwana a wahalce, Duk yadda takai korafi a gida mama takan ce Kubura na fada maki kije kiyi zaman hakkuri, Kada kiyi sake ki watsar da daman da Allah ya baki, don kinga duk yan uwanki babu mai aure acikin irin daular dakike, Kubura takance mama daula babu kwanciyar hankali tayaya zan uya kwantar da hankalina har inga wanan daular da kike nufi, Sai ki tatake ki watsar da daman naki tunda baki jin magana, Kubura takan zauna tayi kuka don tasan cewa duk wanda tafadawa damuwar ta shawara daya ce zai bata irin na mahaifiyar ta cewa tayi hakkuri kawai, Mama tace ki tashi ki koma dakin ki tun mutanen gidan nan basu fahinci irin halin da kike ciki ba,suyi muna dariya, Haka uwar kan lalashe ta har tabar kukan ta samu ta koma dakin ta baki alaikum, Ki matsa yadda kikaga abokiyar zaman ki tana tarairayar mijinku kema ki kama Ita ko uwar gidan Jamila da,suke ganin laifin ta a banza tana iya kokarin ta gurin ganin cewa ta sasanta zama a tsakanin mijin nasu da Kubura, Duk da bawai sanin may ya shiga tsakanin su tayi ba amma tana iyakar kokarinta gurin fadakar dashi akan hakkin da ya wajaba akan shi, ****** ********* ****** Wasgegari na tashi da,aikin gyaran daki da,duk wasu yan abubuwa na dake bukatan wankewa, Umma tunda ta kyala ido da,safe taga irin gyaran da yar ta,tasaka akai min sai cewa tayi, Ashe ku dawiniya kuka kai wa yar uwar taku haka wansn irin gyara haka kamar wata yar Arab, Komai sai dana gyara ranan a dakina tare da karawa dakina mazaune na canza kayan daga gurin da sukr zuwa wani position, A take dakin ya koma tsab kamar ba,shi ba har kofan dakin Umma tazo tadaga labulen dakin tana cewa, Ganin gidan su Zarah ne yatayar maki hankali haka aishiyasa ban son ana,shiga gidajen masu kudi kada mutum ya dauko wahala, Acikin dan marairaicewa nake cewa Umma ba hakana bane dakin ne yai min kura shine na ke gyara, Kannen mijina duk wanda ya shigo sai yai min sherin cewa halan yayan mu zai zo ne wanan gyara irin haka, Murmushi nakan yi nace ai ko bai zo ba ku kun isar mashi ai tun da kun gani Haka muka,auni dasu munata barkwance har zuwa yamma inda na gama muna girkin dare wanda ba wani abinci bane mai wuya dan kullun ne nadada mune, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Don girman Allah ku rike min amana novel dina kamar kullun don Allah nagode da hadin kan ku a gareni👏👏👏 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣6⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA Kamar kullun yau ma aikina da na,saba yi shine, nake duk da wani irin kasala da nake ji amma haka,na daure na karasa aiyukan nawa, Sai na koma daga cikin dakina,wanda ni kaina yanzu yana,bani sha,awa, kallo,saboda tsab yake ta ko ina , Umma wace shigowan ta ke nan daga zuwa gurin barka da ta tafi, Jin muryan shigowar umma gidan yasani fitowa ina mata sannu da dawowa, A,a Aisha har kin gama aikin ne naga kin shige daki kin kwanta abinki, Nace acikin sanyin murya Umma na karasa ne yanzun na,shiga daga ciki, Ledan dake hannun ta take kokarin miko min yayin da na karaso gare ta ina mika hannaye na don karban ledan, Umma ke cewa karbi ki dan kwaba min latus ne nagani a hanya na,sayo muna, Na juya zuwa gurin da muke aje kwanonin wanke wanken mu don na dauko kwanon da zan sa a ciki,, Umm take cewa bari ta shiga daga ciki ta duba, guntun man gyadan da ta ajiye, a dakin nata, Sai ganin akuya nayi tafito daga dakin dagudu inda umma ke ta masifa daga ciki tana zage zagen masu kiwon dabbobin da basu iya killance su a guri daya Takara dan fitowa dauke da kwanon da mai ke a ciki tana ce min na karba na,gyara,mata dashi, Ina gyara ganyen Umma,na zaune a saman kujera daga gefe guda tana kallo na, Sai kiyasta yadda nake gyaran ganyen a cikin kwancinyan hankali nake wanda ita Umma din take ganin sanyin jiki ne ke gari ni hakan, Haba Aisha don Allah ki motsar jiki ki gyara min latus din nan yunwa na kwaso ke kuma,, sai sanyi jiki kike simay simay hakan nan, Maganar ta bai sana fasa aikin da nakeyi ba,sai juyawa nake a hankali kamar yadda na saba,, Muryan Umma naji tana cewa waiko ranan kun kai wa Zarah sakon da na baku ku kai mata, Gabana ne ya fadi don tuna cewa,sakon yana a gurina nadawo dashi Zarah ta ce na dauka tabar min, Nace Umma mun bata har tana cewa idan zamu dawo zata bamu sako mu kawo maki sai kuma ta manta, Murmushi tayi har hakoranta suka baiyyanq tana cewa hoo yar nema tasan kan sakon ke nan shiya sa take zance bada abu a kawo min, Jin abinda Umma ta fada yasani sanin cewa abune mai muhinmanci a cikin abin, Don haka,na kudur ta cewa,a,raina da zaran nashiga,daki zan bude ledan don inga abinda ke a cikin sa, Na kamalla na aje gaba daya ganye agaban inda na debo mata ruwa a randa na girke a gaban ta, Daki na,shige inda na jawo ledar tawa gurin da na boye ta na dinga ciro su daya bayan daya ina dan dandanawa, Don ko wani yana da bayani a cikin shi naji dadin wanan abin don zaki gare shi sosai, Na mayar na,boye gurin da nai masu ma,adanan boyewa, Umma ta na a gurin dan barta taci ta koshi sai gyatsa take tana dan sakatan hakorin ta,da tsinken tsintsiya a hankali, Na koma bakin murhu don na tsabtace gurin saboda hakan ka,idatace kafin na dora girkin sai na gyara gurin aikin nawa tsab na tsbtace shi da kyau, . ****** ********* ****** Daga,gurin da nake aikina naji sallama a bayana abinda yasani juyawa baya ke nan don na duba , Muryan Umma ne kafin na katasa juyowa take cewa a,a ikon Allah Hamza kai ne tafe ashe, Sannu da zuwa lalai marhabin da mutanen sokoto ashe kana hanya tafe, Yadan shafa kai tare da dan cewa Umma sannu da gida , Daga guri da nake a tsaye nace sannu da zuwa yaya , Yadago ya duban inda nake tsaye ina kokarin goge hannaye na da ragan dana,tana da don aikin kitchen dashi, Saye yake a cikin wasu kananan kaya suyi matukar mashi kyau kayan sun fitar mai da kurciyan shi na asali, Wata t,shirt ne baka anyi rubutu da jan kala manyan haruffa an rubuta, EASY LIFE, Sai wando irin na,samari velvet, brown color mai laushi takalman kafan shi irin ta maza budadu, Alokaci guda duk na kallace kayan jikin shi tsab, Ya amsa gaisuwa na acikin dan sake fuska yana cewa,, sannu da aiki, Umma tace a, a Hamza wai dama ashe ana,dawowa gida ba,sai hutu ba? Na karaso na karbi yar bakar jakar da ya rataya mai igiya, a kafadar shi, Gurin amsan jakar hannuwan mu suka dan hade idanuwan Umma su na,akan mu, yayin da,kowan mu yadan ji re,action Gaban Umma ya karasa ya durkusa yana gaishe ta tare da tambayan ta bayan rabo, A zuciyan shi sai mamakin ganin yadda a lokaci guda Aisha ta canza mashi, A yadda ya barta a kwanaki yanzu ta,sake mai gaba daya, ta murje tayi wani irin kyau a fuska ga kumshi da yaga anzana mata sai sheki takeyi, Gaban ta sun dan ciciko mata, girma ya kara dan baiyyana mata, Ruwa na dauko a cikin jug duk da basu da sanyi sosai amma yasha ruwan sosai, Najuya zan wuce yake ce min ki taimaka min da,ruwa na watsa nadan ji sanyi, Juyawa nayi zuwa inda nake aje bokitina na,dauka na debi ruwa a randa nakai mai ban daki, soso da sabulu na kara juyawa na kai,, Yamike ya nufi dakin ina a ciki zan fito da zanin da zai daura don kewayawa, dashi, Shigo dakin namu inda yaga wani sabon sauyi danai wa dakin Murya kasa kasa naji yace Aisha na,dan dago ksi muka hada ido dashi sai naga ya kara min wani kwarjini, Sai na,dan sunkuyar da kaina kasa ina cewa yaya hanya yaya,? Yace kina kuwa kewana wanan irin kyau da kika kara haka, Wani irin dadin yabon da yai min naji har cikin raina muryan Umma ne daga waje tana cewa Aisha zuki mai da hankali ki dora girkin nan ya,samu yadan ci wani abu, Yan uwan shi duk wanda ya,shigo da murnan ganin dan uwan su zai shigo suna matukar kaunar junan su sosai, Yafito a cikin wani shiga guntun wandon crazy ce asshr color, wanan karon ya wuce gwiwar shi tare da riga,mai kalar brown, mai zanen layi layi, Kayan zance sufi na farko yi mashi kyau yace wa Umma zai dan fita bakin shago ya gaisa da mutane, Mutum na farko da ya fara gani a,waje shine Baba Mudi, A cikin ladabi ya isa inda baba yake zaune saman tabarman shi da aka shimfida mai, Ladabin yaron yana matukar burge baba akoda yaushe gashi yanzu yafa ya zama mai wani dan birni, sosai, Yai wa Baba jajen accident din da yayi baya gari tare da,adduan Allah ya tsare, Baba yake tambayan shi yaya karatun da jama,an su na can da ya baro, Abokan shi sun ji dadin ganin shi don sunyi kewan abokin nasu sosai, Nan aka zauna ana hiran yaushe rabo don watan shi biyu da kwanaki rabon shi da can, Anan ya,shiga shagon su yana dan bincika abubuwa a yadda ya bar su, Mutane duk wanda ya,wuce zai mashi sannu da zuwa tare da tambaya karatun shi, ****** ********* ****** Dakina kamshi yake na turaren wutan da Anty Zarah ta,bani ranan, Duk bayanin da tai min da wanda naji su Antyna,suyi a,gida yana a raina don yau ina,son na gwada sa,a ta, Tunda yamma nake fakon idon Umma nake kewayawa da ruwan dumi ina tsarki dashi, Kayan hakin da na samu wurin anty Zarah na kara damawa nasha, A dan wasu awani nafara jin wani yanayi a cikin jikina, wanda na kasa fahintar shi, Hira Umma ke jan shi dashi yayin da take sani aiki jefi jefi, a gidan, Sai da hankalin shi yana a,gareni bayan yadan jini shiru gashi yana,son shiga gurina daki ga kuma Umma ta tare shi da firan yan uwan su , Dole yafara mata dan gyangyadin karya kamar maijin barci, Tai magana tai magana taji shiru hakan yasa ta fahintar cewa a gajiye dan nata yake, Hamza ai da ka shiga daga ciki kadan huta zaifi maka don ka kwaso gajiya dayawa, ka kwanta ka huta kaji sai da safe, Hamza yadan mike zaune da kyau yana cewa a cikin muryan yanayin mai barci wallahi duk na gaji barci nake ji, Tashi kaje ka kwanta kaji ka huta hakana gobe ka tashi da,wuri tunda kace zaka,tafi gona ka zagayo, Ya dan mike tare da yin mika ya na hamma take cewa o,o duk ka gaji to ba hutu ana ta karatu koda yaushe, To Umma sai da safe ke nan nashiga nadan samu na huta duk a gajiye nake, Ya,wuce zuwa ciki inda tabi bayan shi da kallon tausayi irin na da da mahaifin shi, Tana cewa a hankali Allah yasa wanan yarinyar dai tayi barci ita ma ko da yake dakariyar bawai wayon wani abu ta iya ba gida humar banza, Bari nima nashige hakana don na tashi da wuri zuwa nemo mashi dan wani abin da za a gyara mai yaci, Tamike tsaye da dan tsuki taso ta kira Aisha don ta kwashe kayan dake waje amms tana gudun ta tayar da ita kuma wani abu yace zai shiga tsakanin ta da dan ta wanda ke bukatar hutu na barci a yanzu,, A da can idan zamu kwanta nakan saka riga da kuma hijjab a jikina, Amma a yau zancen yadan banbanta don hudubar anty zarah zata fara aiwatar wa, Tsab nake don ina jin jikina ni kaina yau din da banbanci sosai a rayuwa na da can baya, Motsin shigowan shi dakin naji wanda hakan yadan sani kara dan lafewa a saman dan gadon mu, Ganina kwance saman gado sabanin da can da nake kwantawa a kasan tabarba da filo sai yai ta faman kirana akan nazo inda yake, Buta naji ya dauka yafita zuwa bandaki don yadan kewaya da alamar kila ruwa zai watsa don naji yana cire rigar shi, Da Umma sukayi kicibis tana kawar da yan sauran kayan da ban kawar ba a tsakar gida don bamu barin komai a wajen gida don gudun shedanun dare dake wa masu sakaci da barin kayan amfani a bude, Too ashe baka kwanta ba Umma take tambayan shi yake ce mata zandan kewaya ne , Koda ya fito bata wajen ya shige dakin tare da rufo kofar mu da addua, Ban san may ya ke a cikin jakar da ya,shigo da ita ba sai daga baya na fahinci turare ne ya fesa don kamshin shi daya zo a hanci na, A hankali naji ya tako bakin gado inda nake a kwance yadan zauna a bakin gado a hankali, Kara lafewa nayi a inda nake tankar mai barci sai naji hannuwan shi a,saman bayana a hankali ya fara dan shafawa, A hankali yake shafa bayan nawa wanda yai sanadiyar sauke numfashina a hankali na bude idanuwana, Na dan juya na gyara kwanciyana wanda hakan ya dan sa kirjina dan fitowa fili, da kyau, Aisha, nayi missing din ki sosai ina fatan yadda naji ke ma hakan kikaji, Banyi magana ba,sai dan kara kwantar da kaina da nayi a,saman filon da nake a kwance, Ya kara kai hannun shi a,saman jikina yana,dan son yi yadda muke a da can baya, A hankali cikin wani kwarin gwiwa na kai nawa hannuwan saman jikin shi a hankali, Take wasan dakin ya canza sallo bisa ga,wanda muka,saba,aiwatarwa da farko, So sai na matse shi a,jikina inda na,shiga shafan shi ta inda ma bai zata ba, Ba fanka ko AC ke gare mu ba, a dakin don haka baka,jin motsin komai sai sautin nishi da gurananin mu ke tashi a,dakin abin kurciya kowan mu ya,shiga,wani sabon yanayi, Irin wanda tun auren mu bamu san cewa akwaishi ba a cikin rayuwar aure da mukayi, Sosai mu ka murji junan mu a,ranan kamar ba gobe gare mu, don da Umma zata ga dan ta da take cewa a gajiye yake da zata sha mamaki ranan, Sai da,muka raba dare a cikin wanan sabom yanayin sanan muka sahirtawa junan muka kwanta ba,don mun so ba, Numfashi muke mayarwa,a hankali daga inda kowar mu yake kwance, Muryan shi data zama mai rauni yake cewa A,isha,,, May ke faruwa ne wai ? Nima a cikin wata sanyayar murya nake cewa a ina Yaya,? Kin canza min Aisha ta ko ina wallahi duk kin rikita min kwakwalwana gaba daya, Waya koya maki wanan abubuaan please ? Wasu abubuwa ke nan yaya ? Hmmmm , Ina kika,fita,zuwa lokacin da ban gida, Gidan mu kawai na shiga lokacin da Baba yasamu accident, Sai kuma , ina yace a gagauce, ? Mun tafi gidan Anty Zarah mu da,su Asmau, shekaran jiya, Ok hmmm, Zarah ce ko ? Tai may yaya ? Tai maki darasi ko ? Nacd cikin murya kamar mai shirin kuka waini shagwaba darasin may kuma yaya, Murmushi naji yayi yayin da hannuwan shi yake a,saman kaina yana wasa da kitson da ke kaina a hankali, ****** ********* ****** Abin duniya yana damuwar ta a rai nafarko mijin da ta aura ba zaman lafiya a tsakanin su, Nabiyu kuma yara fahintar irin sana,ar da Alhaji Nura din ke yi wanda sauda dama tayi tunanen wanqn wani irin sana,a ne zai fitar da mutum gida a cikin dare haka, Sai na uku ta,rasa yadda zata danne zancen Jamila uwar gida a gidan don maigidan shi bai da kamar Jamila dayaran ta,a duniya, Komi ya,samu yace yaran shi idan magana yake yace jamila, dai jamila dai, Jamilan nan kuma aure ne na hadi akai masu a tsakanin su don akwai zumunnci tsakani sosai, Gashi ta dauki watanin tana batun shekarewa amma abubuwa sun ki sauki yadda take so a tsakanin su, Gashi a duk lokacin da tasamu ya shigo dakin ta ya kwana da ita tana dan samun natsuwa amma shi kuma zai ta da tsohuwar gaba a tsakanin su, ya dinga tsuki yana hattaran ta gashi kuma ya kasa sakinta kamar yadda ya kudur ta da farko, Kubura ta kasa hakkurewa wanan karon kamar yadda ta,saba, saboda duk ta bi ta rame ta wani susuce sai kace ba itace Kubura yar kwalisa ba,, Ta,rasa may ke mata dadi a rayuwan ta don kwata kwata tafita cikin hayacin ta, har takai yanzu bata iya boyewa don duk wanda ya santa a baya ya ganta yanzu sai ya tambaye ta may ke damun ta, Gashi tana ganin cewa tayi auren gidan mai kudi yadda zata, huta sai gashi bubu jinbdadi babu kwanciyan hankali ko kadan a,tare da ita, Yar ta anty Rahima ta shigo gidan ganin ta tana kwance tana tunane taji ana,sallama ta, tashi tana karba sallaman Ganin Rahima yasa ta,saurin sake dan ihu cewa wayyo anty kece tafe da ranan nan sannu da zuwa duk ta rasa inda zata aje bakuwar nata, Itako sai faman kallon yadda duk yar uwar nata ta canza kama takeyi , Bayan sun gaisa ne ta gabatar mata da abinsha wanda suke dashi a cikin fridge ko da yaushe, Ta dawo gefen kujera da yar nata take zaune ta zauna tana cewa, Anty kamar kin san cewa dama ina son ganin ki wallahi ido rufe, Lafiya dai ko Kubura ? Anty Rahima ta tambaya da sauri tare da dakatar da cup din lemon da zata kai a bakin ta, Tana mai kurawa yar uwar nata don jin may zata ce inda take kara ganin lalacewa ta a idanuwan ta, Gaban anty ya yanke ya,fadi da,taga Kubura din tana hawaye,tana furta cewa lafiya anty, Anty Rahima tace ina babu lafiya dubi fa yadda duk kika ramae kin wani susuce haka , Kuka Kubura ke ta mata inda ta kasa mata bayanin komai sai she,shekar kuka, Haba Kubura ki daina wanan kukan ki min bayani nasan halin da kike ciki, A cikin kukan Kubura ke cewa, Anty wallahi ina matsala kunci yai min yawa a,rayuwa na, Don tun shigowata gidan nan ni nasan irin halin da nake ciki a gidan nan, Oya yanzun ki natsu ki share hawayen ki kifada min halin da kike ciki don mu san abin yi, a kai, Kubura ta dakatar da kukan ta da kyat bayan dan rarashinta da anty din tayi sanan ta fara bayani haka, Cikin sanyin murya Kubura ta fara magana da yar nata tana cewa, Anty da farko na,dauka cewa aure a gidan mai kudi shine kwanciyan hankalin diya mace, Murmushi yar uwatayi tana cewa idan har an dace haka din ne ai, Kubura tace to ni Anty zan iya ce maki ban dace din ba gaskiya, Subbahanallahi, inji yar uwar nata inda ta kara maida hankalin ta sosai ga kaunar nata, Anty tsakani na da Nura ba zaman lafiya ko kadan asalima sai nake gani yanq,min daukan mazinaciya tun a,wajr, Subbahanallahi shi Nura din kuma ? Sam anty ba ruwan shi da al,amari ina kallon yadda yake tarairayan matar shi da yaran ta amma ni kamar an aje mai ni dole a gida yake kallo na, Kubura ta rushe da wani kuka mai tsuma zuciya tana fadawa yar uwar ta irin mugun tsana da kiyayyan da mijin nasu ke gwada mata wanda bata fahince shiba, Nan Anty Rahima ta samu tai shiru take bata shawaran cewa ta samu lokaci ta tambaye shi, Indan ma har wani abinne to ki bashi hakkuri dan Allah ance dukawa wa wada,ba gazawa bane mijikine zaki iya bashi hakkuri yadda ya dace, In Allah ya karba muna sai kiga ya,sauko yayi hakkuri k7n fahinci junar ku Kubura ta amsa mata da to, anty insha Allahu zanyi yadda kika ce din, idan ya dawo, Taso fadawa anty zance fitan daren da Nura yake sai taga rashin dacewan haka tace a ranta ko banza sirin mijinta ne wanan, Yanzun dai ta samu ta gyara zaman su tukun don shine wajibi, ****** ********** ****** Tun zuwa na gidan Umma Umma bata taba tayar dani sallah asuba ba, Amma sai gashi yau muna cikin wani irin barci mai dadi don rugumay muke da junan mu a lokacin, Karan yadda take bugun kofan tana cewa a cikin daga,murya gari har yai haske haka ace baku bude kofa ba, Dalilin mikewar mu ke nan a cikin sauri ina kokarin zare jikina daga na shi naji ya rike ni gam a jikin shi, A hankali ya rada min cewa, kyale ta har ta tafi sai ki tashi, kara lafewa nayi yayin da nake jin hannayen shi a jikina yana yawo, Muryan Umma daga kofa tana cewa wanan wani irin sabon halin rayuwane, Ace anyi sallah mutum yana kwace like da mace awa chewing gun , Mugun rayuwan nan na diyan fillani daji da nake gudu shine za,a fara kawo min shi a gidana, A hankali na dan rutse idanuwa har takai na dan sauke ajiyan zuciya bashiri, Muryan shi naji kamar mai rada yana ce min kada ki sa zancen Umma aran ki don ba,wurin ramawa bane, Da ace wanine yai wanan maganan ni da kaina yau zan bashi amsa da kaina, Bayan tafiyan Umma da dan mintoci naji ya,sake ni yana kokarin mikewa daga zaune, Inda na dan lumshe idanuwa saboda bazan iya kallon idanuwan shi ba a lokacin, Don abubuwan da yafaru a tsakanin yana dan dawo min a zuciyata a hankali, Umma tana a tsakar gida a bakin murhu tana kokarin kunna wuta a murhun wai zata sa wutan dama koko Taji motsin bude kofar dakin mu a lokacin tadan juyo tare da dan dagowa daga duken da take, Hamza dan tane daure da,wani sabon zani na a jikin shi sai butan da ya rika a dayan hannun shi, Yanzu Hamza wani sabon rayuwa kake son tsiro dashi a gidan nan a ce ana sallah mutum yana kwance har rana haka, Kada ka bari yarinyar nan ta canza maka rayuwan kafa, don ni bani son ganin haka, Bai yi magana ba ya nufi bandaki sai dai bai karasa shiga ba yaji muryan Ibrahim yana cewa wai Umma wani irin haline kumw haka kike so ki tsirowa kanki ne, Gaskiya gaskiyan hakan sam bai dace ba gaskiya ace mutum da matar shi kuma bazasu sake ba a gida, Baki Umma ta bude tana kallon mara kunyan dan ta Ibrahim tace to ubana yi min fada, Ai sai kayi nasan cewa ka isa mara kunya kawai kabari kajira lokacin naka din, Gaskiya dai hakan bai dace ba Umma bakiga laifin danki ba,sai na diyan mutane kawai, Ya fice gidan yana jinini tare da kada kanshi a cikin nuna bacin rai, Cikin daurewa na fito daga dakin tare da dan tafiya kamar mai sanda na,shiga bandakin nai wanka, Ina fitowa tana a bakin randa tana diban ruwa a cikin tukunya na kawar da kaina na,shige, Sai da na shirya tsab nafito don karban aikin a hannun ta ta shige tabarni ba tare da ta tanka min ba, Ina kamalawa nakai mata daki a cikin roban gaba daya don ta raba muna, Sai a lokacin nai mata ina kwana Ummma,? Kamar bazata tanka min ba sai naji ta ansa a kausashe, Zan juya take cewa dauko inda za,a zubawa mijin ki nashi, Cup din silver mai marfi nadauko tare da ludayin shi, Bayan ta zuba ina tsaye sai naga ta ja cup din zuwa wani side din dakin ta mannin bango ta aje haka yasani juyawa fon nasan bazata bani na kai mai a dakin mu ba ke nan,, Sai da ya gama duk wani abinda yake a dakin ina,waje zaune don ina tsoron na,shiga dakin tace min jaraba ya kaini,dakin, Ina a zaune gurin yafito saye a cikin shigar wando da riga na wani farin yadi, ya rikide ya koma saurayin shi tsab, Ganina zaune a kofa cikin yar damuwa ya,sashim dan tsayawa a kaina yana tambayana ko may yafaru, Dariyan yake nayi ina cewa ina son na karasa aikin dake gabanane da,safen nan, Ibrahim ne ya shigo yake cewa Amarya may zamu karya dashi,ne tunda yau muna da bako a gidan, Nace kunu, ne Yaya Ibrahim kuma yana dakin Umma a can zaka karba idan zaka sha, Dakin Umma din ya nufa inda ya samu dan uwanshi a Umma tana miko mai cup din kunnun shi a gaban shi, Yace ba dai a nan zaka zauna karyawan ba matarka tana can a takure waje, Wanan, wanan anyi dakaren da a gidan nan idan ya tsaya yasha anan wani abin ne ko kuwa, ? Ita Aisha din ce takure a waje ina take ta samo kofi na zuba mata nata kokon mana, Baka ji matsala ba yaushe kuma wace tai aikin za,a ce wai za,a, zuba mata wanda zata sha, kuma, Batare da ta kula ibrahim din ba ta fara kwalamin kira nazo da cup dina a zuba min kunu, Simi simi nazo da kofina inda ta zuba min rabin kofi ta ce nadauka na juya nabar dakin , Hamza yana daga gefe cup din shi cike da kunu ga kosai a cikin wani, kwanon silver mai dan fadi, Bina yayi da kallo baiji dadin yadda yaga Umma tai min ba a lokacin, Tsab ya mike tsaye yana daukan kwanon kosai dake a gefen shi, A,a,a ya haka kumar ina kuma zaka ne wai karyawan ka tsaya guri guda kanatsu mana, Yace Umma zan koma daki ne can mu karya don naga bata,samu kosai ba ita, Towoo, To aje min dama kosai dagani sai kai na,sayawa ban saye da kowa,ba don haka idan ya ishe kane sai ka barmin ni na ci, Yace to Umma zanci nabar yar mutane batacu ba ita alhalin tagani, Ibrahim yace koma bata gani ba hakkin cin da kayi batayi ba yana a kan ka ai, Murmushi yayi yabar kwanon kosai a gurin yadauki kunun shi zuwa dakin, Umma tabishi da harara tana cewa to lalai yaron nan kana son zance, Yo ni ina zan iya wanan haka na ciyar da ita wani koko da kosai can, Dakin ya,shigo da sallama ina zaune a saman ledan kasa da kofin koko a hannu sha nake a hankali, Muna hada ido yake cewa ki aje wanan ki sha wanan sai ni kibar min wancan din, Ina dan in, in niya nace a,a kabar shi wanan din ma ya isheni ai, Sautin murmushin sa naji yana cewa Allah ya buda muna watarana sai labari ai, Idan na samu sarari ai sai na dinga sayo abinda zaki girka naki na kanki kici, Nace a cikin sauri kabar shi kawai yaya ai nagidan ma yana isa na, Yace cikin dan lushe idanuwan shi, ke dai Allah yai muna budi kawai, Na karba mai da fadar Ameen ,tare da danci gaba da kurban dan kunun dake a cikin cup din dake rike a hannu na, Wata ajiyar zuciya ya sauke gami da fesar da iska daga bakin shi , Wani irin balain tausayin shi ya kamani a lokaci guda, Don nasan cewa shi mutum ne mai hakkuri da sanin ya kamata ga hangen nesa gare shi, Ranan idanuwar Umma a kaina kamar wace ke son fahintar wani abu a gu na, Na kammala,duk wani aiki dake a gabana kamar yadda Anty Zarah ta,fada min , Wanka nayi nasaka wanan kayan da Anty Zarah ta bani don kayan sun matukar bugeni don ina,son su sosai saboda suna fitar min da sura na waje tsab, Ibrahim ya,fara shigowa sai yake cewa wanan kadafa ki hana mijin naki komawa fa, Hamza ya shigo wanda da alaman dawowan shi ke nan daga uguwa a lokacin, Wani kallon yake min inda nake mai sannu da,zuwa ya dan sake lalausara murmushi alamar a,lama ansawa, Ya is,gurin da,Umma take a kofan dakin ta yana mata,snnnu' da,gida, Inda ya juya take cewa abinci fa yake ce mata shi zan je naci , Ai ga abincin anan bari na,dauko ma kaci ko,? Yace zan turo Aisha ta daukan min acan zanci don akwai abinda zanyi a dakin, Kamar zatai magana amma kuma sai taja bakin ta tai shiru sai dai bataji dadin nisanta ta da danta da akeson yi mata ba, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣7⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA Tun a cikin dare Yaya Hamza yace min washegari na shirya zamu tafi uguwa gidan wani, abokin karatun shi, Naji wani iri a raina don nasan cewa wanan fitan namu zai iya jawo muna matsala ga Umma, Amma banda halin mussawa don haka naja baki na nai shiru inga yadda zamu kwashe da ita, Kamar kullun washegari na kamala yan aiyukan da ya dace nayi duk da Umma ta ban wanki nayi masu, amma sai na kammala da wuri kafin ya shigo gida, Girki ma da, wuri na dora har Umma tana masifa wai don may zan dora girki da,wuri ya huce yai sanyi kafin a ci, Hamza ya,dawo gida da dan saurin shi ya shigo inda ya samu nayi wanka ina shiryawa, Wata farar atamfa mai adon gashin dawisu na saka tare da kara dan gyara fuska na da kyau, Daga daki ina jin muryan Umma tana cewa Hamza wai may kake son komawa ne ne? Yanzu don rashin kunya matar taka zaka dauka darana tsaka kufita kowa na ganin ku kana nunawa mutane ku gaku marasa ta ido ko ? Hamza yace Umma ba hakana bane naga cewa shi wanan abokin nawa matar shi danta baida lafiya shiyasa mukazo tare dashi ya bani lift, Kinga bai dace ace mun koma batare da taje taiwa yaron sannu ba, Too,wooo sai kuma akace kuje da ranan nan kiri kiri kowa na ganin ku haka ko ? Umma ba hakana bane kin san yanayin garin shi yasa zamu tafi yanzu ta dan yini masu, O ashe ma,sai da ka gama ashirin ka shine kazo fada min kai ga mai mata ko ? Umma kiyi hakkuri nayi kuskure bazamu kara ba ko yanzu don na riga na,aro mashin din Hadi ne da mun fasa to har na,zubawa mashin din mai ne, Shiru tayi tana,dan kada kai tana nuna alamar cewa akwai magana gaskiya, To ji nan idan zaku fita ka tabbatar da cewa kun bi ta baya da ita don ban son abin nuna rashi kunya, Tau Umma mun gode sai mun dawo ai gidan ba nisane da namu ba can kasan layin suke gurin sabbin gidajen da akeyi, Kai ka,sani kana,wani rawan kafa wai kai mai mata ko har ina matar take abu haka yar fayau da ita, Wani iri Hamza yaji a rayuwan shi don dai shi a ganin shi wanan yarinyar bataci a dinga mata muzanci haka a gidan nan ba don ta taimaki rayuwan shi sosai yadda ita Umma din bata iya ganewa, sai shi kadai, Daki ya,shigo ya,samay ni zaune, a bakin gado yanayin yadda ya samay yasa shi cewa may kuma ya faru duk da yasan cewa naji abinda Umma ke fadi, Cikin dan marairaice murya nake cewa Yya idan har fitan zai sa ran Umma baci mu fasa mana, Idan kin shirya ki tashi mu tafi kawai amsan da ya bani ke nan a takaice, Namike tare da kokarin jawo dakina don awakin mutane da ke shigo muna, Dakin Umma na nufa tana zaune ta mike kafafuwan ta don zafi ake ranan tana shan iska, Nace a cikin sanyin murya irin nawa Umma zamu tafi a dakile tace min adawo lafiya, Sai da muka fitane naga ashe a saman babur zamu yi tafiyan ya shiga shagon shi yafito da leda baka da abu a cikin shi yana mika min, Ibrahim ya dan leko daga shago a lokacin na hau mashin din yake cewa yau ta daure an samu saki ke nan, adawo lafiya, Nsi dan murmushi kawai don ban iya bashi amsa saboda ina ganin girman shi har yanzu kunyan su nake ji sosai, Daida zamu dan sha kwana fita daga lungun mu mai mashi ya goyo Kubura wace ta bi mu da kallon kamar tana mamaki, ****** ********* ****** A kofan wani gida mai alamar dan hali a gidan dan ginan zamani muka tsaya da matshin din, Yake ce min na,sauko daga bayan shi da nake zaunr ina,sauka ya gyara tsaguwar mashin din nasa da kyau yake min iso da cewa na,shiga nayi sallama na tambaya idan Mansur yana ciki ana mashi sallama , Gaba,na yana faduwa na shiga gidan inda nake jin wani iri a raina don ban saba shiga gida je ba, Sallama nakeyi inda naga daki mai alamar akwai mutane a cikin sa don ga takalma a kofan dakin, Sai dai karan tv yana tashi daga cikin dakin inda na kara dan matsawa ina daga murya na a,sallama, Wata mata fara ce ta leko, daga dakin tana rike da yaro a kafadan ta da gani yar boko ce ta na min kallon mamaki, Nace Ina wuni ta amsa da lafiya nace wai idan maigidan ya ciki ana mai sallama a waje, Juyawa tayi hannunta yana rike da labule tana cewa kai akewa sallama, Inda naji mijin yana tambayan waye ? Tace wata yarinyace ban san ta ba ina gani ba yar shiyan nan bace, Mijin yafito babu riga a jikin shi abinda yasani saurin kawar da kaina gefe ina cewa ina wuni ya amsa da lafiya nace wai ana ma sallama waje, Rigar shi matar ta miko mai yana sawa inda yadan fito ni kuma ina tsaye a inda nake ya dan zo ya wuce ni , Ganin ina tsaye ban bi shi ba ya matar cikin dan kallon kallon da mukewa juna cewa shigo mana daga ciki, Na shiga da sallamana dakine mai adon zamani TV, da DVD sai kayan kida ga kujeru manya set a,falon,, Muka kara gausawa tana ce min ban ko gane ki ba na dan yi murmushi tare da dukar da kaina, Muryan mijin ne ya shigo yana ce mata daga waje ashe matar Hamza ce fa, Tace Hamza wani Hamza ke nan dear ? Hamza course mate dina danake baki labari mun hadu a,school dashi, Tacd OK wanan da kace tare kuka shigo dashi ke nan ? Tambayan ta nayi da cewa Yaya maijikin da sauki ko tace gashi ai ya samu lafiya dama kyandace sai dai bata fito mai sosai ba ya samu lafiya sosai, Na mika hannu na karbi yaron take cewa wanan dan kiwar ai ba zai zo ba don baida yarda, sam, Yaron kuwa ya kara lafewa a jikin uwar shi tare da dan sako min idanuwan shi da yake lumshewa, Hamza da maigidan suka shigo tare inda yai mai iso har cikin falon matar inda matar ta,shiga dakin ta soko riga don dama bata da riga a jikin ta, Dariya suke yana cewa wallahi in ba yau dana gani ba banyarda cewa kana da mata ba, Kai kai kai Hamza wanan ai sai ace kaunar kace ta rako ka, Shima yaima matar ya yaro maijiki tare da mai fatan Allah ya,bashi lafiya ya tsare gaba, Muna daga zaune nake jin magana irin ta manyan mata daga bayan tagar su ana cewa, baki kukayi ne, Matar dakin ce ta bada amsa da cewa eh mama abokin karatun dear ne su kazo gaida Abba, da jiki, shi da matar shi Tace Allah sarki sannun ku da zuwa kunji mun gode ai yaji sauki yanzu bisa ga shekaran jiya Sosai naji mamaki a rai na yadda bata jin kunyan kiran mijin ta da,dear a cikin mutane haka, Matar ce take ce mu na mama ce maman dear take gaishe ku jin haka na Mikewa zuwa waje don in gaida matar da,akace mahaifiyar maigidan ce da muka zo, Ina Fita Mansur ke cewa matarka karamar yarinya mai hankali ba irin yaran yanzu ba, yaushe kukai aure ne wai ? Hanza ya ba da ansa da cewa almost eight months kenan Kai ashe ma baku wani dade da ita ba,sosai, kace dai kai ango ne, Matar,shi tace wallahi ta bani sha,awa sosai tana da kamun kai ba irin yaran yanzuba da sunyi aure sun fara rawan kai ke nan su ga matan aure, Nadawo daki na bar yar dattijuwar a,waje tana ta,saka min albarka tare da muna fatan alheri, Abinda yasani jin dadi dama ace nima haka nake zaune da umma danafi kowa jin dadi wallahi, Yan mintina kadan Hamza ya mike yana cewa tau madam ni zan tafi zan barki da bakuwa sai anjima zan dawo na dauke ta, Tace amma na gode kuwa sai ka dawo din a gaida gida, Ya juya inda yake yana ce min tau zan tafi sai nadawo ke nan Allah ya tsare nai mashi cikin dan sanyi magana Suna fita take ce min wai yaya sunan ki ne ? Nace mata a hankali Aisha, Tace ni kuma suna na Hindatu nake amma anfi kirana da hindu, yara na biyu, ta farkon tana gurin mahaifiyata don ban yaye taba na,samu cikin Abba shine mahaifiyata ta dauke ta, Allah sarki ita kuma mayne sunan ta,? Tace Hadiza take , Tau,fa, sunan Anty nace na bata amsa da fadar hakan, Muna zaune sai dan jana da hira take a hankali ina dan bata amsa a cikin hikima take dan fahinta a hankali duk da wai naga ina boye mata sirina, Haba Abba kabari na dan tashi naje na wanke kanyan ka gasu can a jike tun da safe a ruwa, Sai kuka yaron yake ta faman yi gwanin ban tausayi idan mutum na kallon sa, Tace bari dai na kara ma magani nagani ko zaka samu barci kayi haka ta mike zuwa uwar dakin ta don dauko maganin, Mikewa nayi na fita daga dakin zuwa waje inda famfon su yake ta jika kayan yaron a cikin baho mai dan fadi, Na gyara hijab dina ba tare dana cire ba na,soma wanke kayan yaron da nata a hankali, Har sai da na kusa kamalawa sai ga Hindatu tafito daga dakin goye da goyon yaron ta Abba a bayan shi Lah Aisha yanzun ashe wankin kike yi ni ina ce kina nan zaune a,waje ke da mama, Ashe kina nan kina wanki ne ke haba Aisha idan mijinki yazo ya,samay ki a haka fa, Muryan mama ne daga bayan mu take cewa yar albarka ke nan, Tarbiyan da ta samu daga gidan su ne haka in bashi ba ai da tun shigowar ta zaki gane, Kyakyawan tarbiya wa da,gwada kan shi yake batare da mutum yasan Yana yi ba, Mansur ne ya shigo gidan yake jin Hindatu nace na bari ta kara sauran da kanta, Ikon Allah amaryan kece kuma ke wanki da kanki suke cewa ai shine ake magana a kai, Mama tace ku barta halinta na alheri ne ke nuna kan sa, Ledan kayan cefane ne yashigo dashi a hannun shi wanda inda Hindatu ta karbi ledan tana mashi sannu da zuwa, Suna dan wasa da junan su a gaban mahaifiyar shi itako uwar sai murmushi takeyi tana nuna jin dadin ta a fili, Mansur din ya,shiga daki yake cewa takai mai ruwa yai wanka, Dakin su ta shiga da ruwan ina dan satan kallon su nace a raina kun huta da,sa ido duk da dai uwar mijin ba ruwan ta, Amma ni wani lokacin ma Umma zata zo ta tsaya a bakin bayi da,asuba tace tana son kewayawa ne,, Dole na fito a gagauce na bata guri tashiga tana bina da kallo, Haka aikin girkin kusan nice na karasa wa Hindatun shi saboda yaron yaki yarda sai kuka yake hankalin uwar duk ya tashi, A cikin wani turen silver ta zuba muna abinci a tare inda ta zuba nama da yawa duk ya rufe shikafan take ce min don Allah inci abinci in sake jikina don a gida nake ai, Yaron ta ya samu barci don haka itama ta,samu ta dan shiga wanka ta gyara jikin ta tafito banci abincin ba duk da ina son ci amma kunya bai bari naci don kunya nake ji sosai, ****** ********** ****** Kubura tana ganin Hamza da Aisha taji wani irin haushi da takaici ya tokare mata zuciyan ts, Tana shiga gida ta samu mutanen gidan duk a tsakar gida kowace tana aikin gaban ta, Yanayinta kawai ya isar wa mutanen gidan cewa yau ba dadi sosai, Lafiya ke kuwa Atikace ke wanan tambayan a cikin gwazai irin nata don ita ko yaushe nuna take bata,son Ummi ta rabu da Mama Saude, Don kada a,samu alheri ace su raba tare da ita ko ta shigo tace zatafita iyawa, Kin ganta da wani kamane na alamar rashin lafiya tarr da ita ? Mama Saude ce ke tambayan Atika din cikin hasala, A,a naga kamar baya da dain raine da ta shigo kawai shiyasa na tambaya inji Atika, Daga inda Ummi take tadan murmusa don tasan cewa ramin karya kurara ce, Ita dai badon wani abu take tare dasu ba duk da cewan da,suke diyan su na,aure a gidan wada ta da hutu, To amma ina amfanin dukiya babu kwanciyan hakali a tare da yarinya, Kubura tana zaune a saman kujera kanta sama tana kallon tsohon silin din dakin mahaifiyar na ta, Mama Saude ta shigo dakin tana cewa yau ma kunyi tsiyan naku ko, Wai may yasa baki daukan shawara ne Kubura kowa ya fada maki cewa kije kiyi hakkuri, Kamar jira take uwar ta,shigo da zancen sai kuka ta fara acikin daga sautin maganan ta tana cewa, Mama ni bazan kara komawa gidan wanan macucin mutumin ba, Duk mai ganin laifina sai dai ya gani amma bazan koma gidan Nura ba na barshi har abada, Cikintakaici uwar ke cewa yanzu da kike kukan nan haka so kike ataru muna a kai asan halin da kike ciki a gidan mijin ki har yaushe akai auren nan ne wai Kubura ta kara sautin kukan ta batare da ta tsaya,sauraren uwar ta dake cewa ta tausa muryan ta ba, Abin da yakara jawo hankalin mutanen gidan ke nan suka dan tsaya sauraren may ke faruwa a dakin, Yanzu Kubura wanan abin da kike yi ai baidace ba yaushe akai wanan auren, dazaki zowa mutane da wanan zancen, Atika ce kamar wace take a labe a kofan dakin tun farko ta fado masu daki, Shekaran jiya fa mijinki yazo kofan gidan nan ya aikomuna da abin arzikin Dago kai Kubura tayi tana kallon Atika cikin dakatar da kukan ta, Tace kinji mugu ko azzalumi macuci kawai yana can yana gwada min boni yanzu yazo nan yana gyara kan shi, Duk zancen da sukeyi Kubura bata saurare su sai magan ganu take fadi mara dadi a kan mijin ta, Mama saude da ranta ya baci tafito waje inda ta samu Ummi tana aikin ta a hankali kwance, Kubura na ta kuka tana tujara har lokacin da Ummi ta gama abinci ta zuba mata nata da kanta ta,shiga dakin Mama Saude dauke da abincin don ta kai mata, Ummi tayi wankan ta kafin ya fara rabon abincin don ka,idar tane yin haka bata zama rabon abinci sai ta tsabtace jikin ta tukun na, Kubura na kwance ta kifa ciki a saman gadon mahaifiyar ta inda Ummi ta shiga dakin da sallaman ta, Haba Kubura maynene yai farko baiyo karshe ba yanzu kina ganin kin kyauta ke nan kizo kina tayarwa mahaifiyar ki da hankali haka, Kusa da ita ta zauna tana mai kara dan bata hakuri a cikin tatausan lafazi mai kwantar da hankalin macen da,ranta ya baci Dan tsakaita kukan ta takeyi can ta nisa tana cewa wallahi Ummi abin Nura ya isheni ne duk abinda kike tunanen zanyi mai na ban hakkuri nai mashi amma kamar kara tunzura shi nake yi , Hakuri zaki karayi Kubura kinji kinga ai kowa zaman hakuri yakeyi yanzu idan kince bazaki koma ba sai mutane su fara fadin abinda bashinr ba alhalin ke kikasan abinda ya hada ku dashi, Kiyi hakkuri kiji Kubura mace bata gajiya da hakkuri wata rana shi da kan shi zai gane cewa bai kyauta maki a rayuwa, Kiyi hakkuri kinji Kubura kitashi kici abinci ki watsa dan ruwa ko zaki dan watsake sai kiji zuciyan ki yai sanyi kikai wa Allah kukanki da kan ki Allah maiji rokon bawansa ne musan man ma bawan da ya roka da kan Tashi kinji ki dan watsa ruwa kiji sanyin jikin ki sai kici abinci kinji, muje na zuba maki ruwa kiyi wanka, Ga mamakin Ummi sai taga Kubura din ta mike zaune daga kwancen da take da farko, Kiyi hakkuri kinji Kubura tashi muje kiyi wanka ki karasa hakkuri a zuciyar ki insha Allahu komai zai wuce, Cikin wani sanyin murya kamar ba nata ba tace nagode Ummi nagode insha Allahu zanyi yadda kikace, din, Mama Saude ta shigo dakin taji dadin ganin Ummi ta rarashi diyar nata ta daina kuka, Tace wallahi Fatima yarinyar nan bata daukan shawara na fada mata ba yau ba inda bai son tane ai ba zai zauna da ita ba, Abar zance kawai yaya tashi kijr kiyi wanka kin san mazan nan halin su ne sai hakkuri wallahi kinga kuma ita yarinya ce ba wai komaine yanzu zata iya shayewa ba, Amma idan anbi abin a sannu zakiga komai ya wuce an manta, Kubura ta mike tanufi waje Ummi tabita ta bata ruwan wanka tashiga, A lokacin ne Ummi ke cewa yaya don Allah idan yaro yazo da zancen ce shi acikin taushin lafazi za,a bashi magana yadda zai fahinta tunda hankalin da saura, Mama tace Fatima na gode don wallahi yau badon ke ban san ya zanyi da wanan yarinyar ba a gidan nan, Ummi tace hakkuri za,ayi yayabita a,sannu har gano inda matsalar yake kinga sai a magance mata shi, ****** ********** ****** Kikan yi amfani da kayan mu na mata na baki Aisha,? Muryan Hindatu ce daga uwar dakin take jefo mata tambayan nan, Dan dariya nayi kawai bance komai ba tace to baki so ke nan, Nace ina so mana tace to amma fa bana cusawa zan baki ba don shi yana wa mace illa sosai a jiki, Nai shiru ban bata amsa ba tafito dauke da,wani bukitin roba a hannun ta tana kokarin budewa, Duk wanda ta bude sai ta,lasa ta min bayani ta,daure , Tana dariya tace kin san fa mu mata ne sai da dan gyara dole don dan guntun lokaci gare mu a,rayuwa, Amma fa,sai kin hada da ladabi da biyayya da kwarkwasa , Duk da,a,gida guda kuke da uwar mijin ki rufe idon ki ki kama mijin ki ki mashi abinda ya,dace kafin wata tazo tana mai kina kallo, Don mu matan hausawa kin san bamu da tabbacin cewa ba,ai muna kishiya, Kada ma kiyi mamaki idan anyo wata sai ya nuna,aike baki taba mashi komaiba duk zaman ki dashi, Don kin a wanan zamanin maza suna son suga ana kula,su ana tarairaya idan ba hakaba,sai suje su aro wacce suka ga zata iya kula dasu yadda suke so duk da wahalan da akasha dake a baya sai a fita batun ki ki zama hoto a gefe, Tace Aisha wallahi ai hakan ma yafi faruwa yanzu ka,wahala da namiji idan dadi yazo yace aike baki iya ci ba, Don Allah Aisha ki cire kunya ki kama mijin ki ki kula da abinki kin ji gaki yarinya karama, Wanan abin da zan baki kiyi amfani dasu zasu taimaka maki sosai sai wasu kwalabe da ta bani guda biyu ruwane kamar turare a ciki tafada min yadda,zan yi amfani dadu, Sai a lokacin na nuta da wanda gwagona ta taba bani a baya lokacin ina amarya, Inata mata godiya tana jin dadi yadda nake ta bata girma Ta hada min da bed shet sabo da kuma room fresh masu kamshi da man kitso dana,wanke gashi, Sai yamma lis yazo muka tafi gida da ledana fam shake da kayan tsaraba inda ta,rufewa Umma baki shine sabulai da man shafa babba vasilen tace nabawa umma don yanzu sarakai kyauymta,suke so, Muka,rabu muna ji tankar kada mu rabu da juna don dan sabon da mukayi da ita da,sararkuwar ta mai kirki tabani turaren wuta da yan abubuwan amfani, ****** ********* ****** Tunda muka dawo umma tadan fara shan kamshi amma ina bata tsaraba tare da,fada mata sakon Hindatu cewa zata shigo su gaisa sai ta shiga washe baki, Tana cewa yar albarka ke nan ince yaron dai ya samu sauki, Nace to da dama dai za,ace tace ai zance Hamza ya kaini na dubo shi kafin ya tafi, Na,shiga dakina na,samu guri na boye tsarabata yadda ba mai gani inda,suke, Umma tana min tayin abinci nace mata na koshi munci abinci acan, Tace yar nema anciwo dadi ke nan yau ba,a yayin talen umma ko ? Tun a ranan nafara amfani da abinda anty Hindatu tabani inda take ce min na daina yawan karban abinda Anty Zarah take bani don ko banza matar dan uwanane don duk yadda akayi zatafu son dan uwanta dani, Wata rana ma Uwar ta zata iya bata wani abu a cuta min ta wanan ha yan don haka nai taka tsantsan da dangin miji don ba abin yarda bane sunfi son dan uwan su da matar dan uwan su, Ranan Hamza ya kasa daurewa sai da ya nuna min iya zakuwar shi a kaina sai zance yake sakewa yana tambayana wai may ke faruwa ne haka da yawa yaga fa gaba daya na canza mai sallo da tako wanda bai sanni dasu ada can baya, Kwanan su hudu da mansur suka kwasa suka koma ba tare da ransu yasobba kamar yadda duk wani dan makaranta mai iyali ke komawa yabar matar shi cikin rashi son barin ta ****** ********* ****** Dama ta sauka mai albarka inda mutane sai gona suke kaida kawon zuwa saboda lokaci ne na noma yanzu, Kudin da Hamza ya bani ajiya ya karbi rabin rabi daga ciki ya nufi harka noma dashi, Idan yana makaranta Ibrahim ne mai kula,da harkan noman shi da,sauran abubuwan gida Inda sukan kwashi yan kallo da da Umma su hau sama su fado amma ibrahim yace shi sam bazai yarda ba, Saukin ta sai idan Hamza ya shigo gari takkan dan samu irin yadda take so a gare shi, Shuka sunyi lab lab dasu acikin daji tankar an shimfida Carpet ne a fili, gwanin ban sha,awa dasu, Mutane suka zance a kan noman hamza din inda suke mamakin wanan hikamata karamin yaro kama shi har zai yi irin wana shukan babban gona haka,, Baba Mudi yana daga cikin masu farin ciki da irin wanan ci gaban da karamin yaro kamar hamza ya samu akan amfanin gona, Sun shiga hutun dogon zango inda dalibai su kan dade a gida suna shan hutu kowa da irin abinda yake a wanan lokaci, Wani ranan asabar da hantsi ina sauri na kamala aikin abincin masu zuwa gona, Wanda duk yawan shi babu daya daga cikin yan matan Umma dasuke tayani wanan aikin mai wahala, Ganin yadda nakw ta faman aiki ni daya Ibrahim yake tambayan ina,su Asmau su taya ni, Umma da ke daga daki take cewa to dan na iya bazasu fito ba ina aikin mijinta takeyi ita, Ibrahim yace su kuma aikin yayan su ko do duk abinda aka,samu aidasu ake ci, Hamza din yana daga kofa yana jin zancen da akeyi amma bai ce masu uffan ba don tsakanin Umma da,Ibrahim ba a shiga tsakanin, su, Hakana Umma ta rufe shi da fada ta inda take shiga bata nan take fita take cewa taga kamar ana son a shiga tsakanin ta da diyan ta a raba ta adasu abinda bazata taba yarda da shiba ke nan a rayuwan ta, A karshe Hamza ne ya shiga bata hakkuri inda da kyat ya samu tai shiru a kan zancen, Daga haka Hamza din ya samu ya ja Ibrahim suka fita zuwa gona don gudun kada ya kara jawo wani zance, Suna hanya ne a,saman yar tsohuwar babur din da Hamza ya,saya mazu don rage zirga zirga ata haya, Hamza yake cewa ina son kafin na karasa karatun nan Aisha ta koma makaranta itama ta karasa nata karatu , Sai dai Umma taki yarda da hakan ban san may isa bata son zancen Aisha ba a rayuwan ta, Ibrahim yace idan har kana,ra ayin haka kada ka,fada mata,sai ka kan mala komi yadda ya,dace sai ka sanar da ita zance tafiyan kawai shine fatin ka ka kuma fada mata a lokacin da nake a gurin, Sosai Hamza ya ji dadin wanan zancen na dan uwan shi inda ya,sa aran shi cewa da zaran ya koma zai fara nema min gurbin karatu a inda ya dace, ****** ********* ****** Yanzu ace duk yawan ku yaran nan kun kasa ko da rabin aikin da yaran gi dan Rabi mai gyada suke, Yanzu ku diba kusan mu goma sha amm gona daya karama ta gagare mu nomawa, Audine ke cewa Baba su ba, tun suna yara kanana suke wanan noman a gidan su, Mu tayaya ma,zamu iya wanan aiki da Hamza yake shi da yan uwan shi, su da,suka tashi tun suna yara suke aikin karfi, Rayuwan Baba mudi ya baci inda yai masu kaca kaca akan su dage su tashi tasaye su nemi na kansu don in shine yau gobe ba,shi bane, Ganin yadda rayuwan shi ya baci dasu yasa suka fahinci cewa fada ne yake masu na kwarai a lokacin, Boka ya bata matasa yanzu har takai basu iya,sana,ar hannu ko kadan , Abinda sauran diyan yan kudu sukafi matasan arewa dashi kenan, Don su basu dogara da boko ba kawai ace sai aikin gwaunati, A na son duk uba ko uwar da ya san kan shi yadan koya wa danshi sana,ar hannu ko ta karfi wanda zai iya tallafawa rayunwan shi , Domin mutum in shine yau tau bashine gobe ba saboda mutuwa,a koda yaushe zata iya daukan bawa tabar iyalin shi inda idan ba mataimaka,masu karfi sai zama liability ga,sauran dangi, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA Gurbin karatun da,aka,samo min zanyi heka ka dawo ne ba a,can zan zauna ba, Umma tai masifa tai jidali, tayi jinini amma Ibrahim yace sai ta barni natafi tun da mijina yana,ra,ayi haka, Shekara uku zan dauka ina karatun a makarantar koyon aikin ungwazo ma dake a cikin garin Jega ta jahar kebbi, Wanan karatun da zanyi ya jawo surutu sosai ga mutanen uguwar mu yan daukan wa kai nauyi, Inda duk Umma tafita,a can sukr zugata cewa yanzu ace mutum da auren ta bazata zauna a gida ba,sai tai tafita wai zuwa wani makaran ta can, Da,surutun shiya ya ishi Ummi na,sai ta,bukaci ganina gidan amma bata tsawala,min ba don cewa tayi anytime na,dan samu daman zuwa tana magana dani, Aiken ta,da kwana,biyu ranan Asabar na fadawa Umma cewa ina,son na,shiga gidan mu nagai dasu, Allah ya bani sa,an ta na samu ta barni na tafi don Hamza ya fada mata cewa idan har gidan mu zan shiga ko zan tafi gurin yan uwan shi a barni na tafi koda baya gari Don haka ba bata lokaci na,shirya tsab dani na,shiga gidan na mu, Suna a tsakar gida kamar kullun kowa tana aiyukan gaban ta,nai masu sallama, Inda na bisu daya bayan daya ina gaida su a cikin ladabi kai ba,sai anfada maka cewa irin kallon da mama Saude da Atika suke min na hassada ne ba, A cikin rashi sakin fuska kamar kullun suke amsa min gaisuwan nawa sai dai tankar ban fahince su ba, Atika ce dan ta tsinkani take cewa, ke Aisha kullun da hijjab guda kike fitane, wai ? Nai murmushi tare da dan kara kallon hijjab din nawa nake cewa, ai wanan sabone mama don baki sanni dashi cikin wanda yaya ya,saya min ne da zai tafi din nan don shiga makaranta, Sai na gan shi kamar kullun dashi kike shigowa gidan nan ai idan zaki zo, Dakin mahaifiyata na nufa inda na,samau ta a dakin ta tana jiran karasowa na, Zaune take a bakin gadon ta tana nade kayan wanki da na samu tana kwasa dana shigo, gidan, Har kasa nakai ina cewa Ummi ina wuni a cikin ladabi da girmamawa,, Nace Ummi yaya,su yaya yusuf da su yan biyu take cewa,duk suna lafiya cikin dan ci gaba da abinda takeyi, batare da ta dakatar ba, Na ce Umma an fada min sakon ki shine yau nace bari na, shigo naji, Ta dan dago kanta kadan tare da dan kallo na cikin dan kura min idanuwan ta nadan wani lokaci sai kuma taci gaba da abinda takeyi, Sai take cewa dama kiran ki nayi don naji gaskiyan zancen karatun nan da akace wai kin matsawa yaron nan sai ya mayar dake karatu, Nan da nan naji wani bacin rai idanuwa na suka ciciko da hawaye inda Ummi takecewa Atika tashigo muna da zancen da,bai muna dadi ba,a gidan nan don haka nace kizo naji daga gare ki, Idan har wanan karatun ba,dole bane kiyi hakkuri ki zamn ki a dakin ki shi ya fiye maki, daraja, Don kin ga,surutu yai yawa ga wanan zancen karatun naki Uwar mijin ki tana yada magana wanda ni dai da, wasu ma mun san cewa ba gaskiya bane, Don haka ni dai ba,wai na yarda bane don nasan halinki nasan ko ke wacece, Amma idan ita Umma Rabin yanzu tafadi zance a kanki mutane zasu dauka ne su zaci da gaske ne tunda ita ce ke zama da ke, yanzu, Take naji jikina yai sanyi da jin maganganu Ummina da ake fadi a kaina cikin uguwa, Hawaye yadan fara silalowa,daga idanuwa tace min dakata mana don kuka bazai fishe mu ba ki fada min gaskiya shin ke ce kika matsawa mijinki cewa sai ya mayar dake makaranta ko kuwa ra,ayin shi ne hakan, A hankali na dan girgiza kaina ina ce mata ina wallahi ban san komai a kan zancen karatun nan ba asalima dai ni shine yazo min da zancen, Ummi ki san halina kin san abinda zan iya da,wanda ba,zan iya yin sa ba, Tsawon lokaci Ummi tana min nasiha tare da kara lurar dani zaman duniya da mutanen ta, A karshe take ce min kada ki biyewa halin sararkuwar ki ki ci gaba da hakuri da kowa yadda kika saba yi, Don haka in har kika bi magan ganun da na fada maki zaki samu rayuwa ingan tace a karshen rayuwan ki don zaman lafiya da mutane shine azikin bawa a,duniya, Ganin yadda yau muka samu dan lokaci da mahaifiyata yasa na,dan fada mata kadan daga cikin halin Umma da nake fama dashi har diyan nata ma, Amma,sai Ummi ta katse ni da cewa ko yaya halinta yake mahaifiyar mijiki ce don haka sai ki bita da halinta ku zauna lafiya Hakan kuma zai kara maki daraja da marta a idon mijinki koda taushe don yasan hakkurin da kike yi a gidan ai tunda a gaban shi ake komai, Jeki idan kina,da abinyi a gida don kada, na tsayar dake da surutu kiyi laifi, Zan daga take cewa mijinki ya kawo muna,amfanin gonan da ya,samu a gidan nan duk da dai ance ya rabawa mutanen uguwa da,dama, Sai a lokacin nai dan murmushi ina cewa ai ina ga kamar zakka ne ya rabawa mutane, Muryan mama Saude ce daga kofa take cewa matar sarkin noma sai ga sako daga maigidanki gudan mai yawa haka, Murmushi nayi kawai banyi magana,ba,fon kawaici wa iyayye, Ance kin matsawa mijinki wai sai ya mayar dake makaranta Yar Agwai,? Atika ce ta,dago labulen dakin Ummi na tana tsaye daga bayan mama Saude wace ta rigata shigowa daga ciki kadan, Haba Atika wai may yasa kike magana itin haka ne, Ke yanzu ko wani kikaji yana fadan wanan maganan a gabanki bazaki tare zancen ba akan sanin halin yarinyar nan da kikayi, Ni bani son irin haka gaskiya mama saude ce ke magana a dan hasale ta juya batare da kara fadan wani abuba, Itama Atika ta mara mata baya suka bar kofan dakin ummi din, Shiru mukayi a,dakin Ummi tace min tashi kije rayuwa ce wata rana sai labari ke dai ki ta hakkuri kinji, Har na mike nake cewa Ummi don Allah gobe lahadi ki turo min su yan biyu suyi min yini muyi hira dasu, Ba,wai ban son zuwan su gurin ki bane Uwar mijinki ce nake gudun anyi ance din ta a uguwa, Ummi har da yan uwana sai tace kuma kada su zo gurina haba dai Ummi don Allah ki bari su zo din kinji Ummi, Tace cikin dan guntun murmushi Allah ya kaimu gobe din zasu zo, ****** ********* ****** A makarantar da nake zuwa hijjab nake sakawa har kasa idan zan fita da nikaf, sai zan shiga get din school nake cirewa, Ban yarda nayi kawaye irin na zamani ba kamar yadda Ummi na tai min gargadi ga yin haka, Tace min yin kawayen da,suka fi karfin a jina zai iya jawo min matsalar rayuwa, Mussaman idan ina kallon irin rayuwan da wasu keyi yau da,gobe zance na dauka, Amma idan har naci gaba da normal life dina batare da yawan mu,amula da kawayen zamani ba zanci gaba da,rayuwa a cikin dadin rai babu kunci a cikin sa, Wanan magan na Ummi ne ya tsaya min a,rai nake ta taka tsantsan da komai da nakeyi a makarantan daga gurin lecture sai masallaci sai na,fito zuwa gida, Duk wanda,aka fadawa cewa ni matar aure ce sai kuji mutane suna mussawa cewa wai yar karama dani za,ace nai aure, Da yake Allah ya taimakeni tun ina primary three akai promotion dina zuwa primary five kan wani devet da mukayi da wani makaranta nai sanadiyar cin wanan gasar a makarantar mu, Shine dalilin gama karatuna dawuri ina da karamin shekaru a lokacin Da,nadawo karfe biyar zan dora girkin abincin gida da,nakeyi kullun, Wanda karatu bai kawo sauyi akan duk wani aiki da nake a,gidan ba a baya, Kowa zai kwanta ya barni ina aiki a cikin dare don gudun makara da,safe zuwa makaranta na, Dalilin da yasa Umma ta kasa samun wani dalili ko hujjan da zata kawo suka na akan fita na zuwa makaranta da bata so, Don ina matukar yin taka tsatsan da halin Umma din don gudun abinda za,a jimu da ita, Sai da sati ya,zagayo ne su yan biyu suka zo min wuni kamar yadsa Ummi tai min alkawarin zuwan su din, Don wancan satin basu samu zuwa din ba saboda hassan ya,tashi da gudawa, a ranan, Nai murna kwarai da zuwan yan kannen nawa wanda yar gurin Atika ce yar matashiya takawo min su, Ko da yaran suka zo Umma bata a gida tafita uguwa zuwa buga bugan ta na yau da kullun don yanzu har da dan dillanci take hadawa, Sun samu daman ina girki na gama na zubs a kwano tare da,su muka shiga daga cikin dakina muna ci muna hira ina dariya wanda mutum zai iya cewa tun shigowa na gidan ba,a taba jin dariyana irin haka ba, Umma,wace dawowan ta ke nan daga uguwar da ta tafi, Take jin dariya na da,surutun mu mamaki take yau may ke faruwa yayin da take dan kara karasowa cikin gidan zuwa kofan dakina, Sai da,tazo gab da kofa tai sallama tare da dan tsayawa kamar mai shigowa, Ganin ta yasani cewa,a,aUmma sannu da,dawowa ina,mikewa yayin da nake nufar kofar don karban ledar dake a hannun ta, Idanuwan Umna kyam a,cikin kwanon da nake cin abinci da yan uwa na da,sukajo har yar gurin Atika,din, Au yaran gidan malam Mudine suka, shigo ashe gaske nake jin muryan ki tun a kofan gida, Murmushi nayi tare da karban ledan hanu bibiyu take cewa su yan biyu kyautar Allah, Abinci kowa an zuba mai mai isarsa, ko don kada wani yace min bai koshi ba, daga baya, Nai mamakin jin tambayan da Umma din tai min kan abinci don haka nake cewa, Umma kowa ya,samu, Bude kwanon abincin nata tayi tana dan dubawa komay ta gani sai ta,rufe tana cewa Allah ya kyauta, Na koma gurin yan uwa muna ta shirmay mu a daki sai dai yawan kiran da Umma take min ya,fara isat, aamma haka na daure i ta ta al,amurana, Sai zuwa yamma,nai masu wanka tare da gyara masu jiki don lokaci ankusa shiga islamiya, Cikin irin tsaraban da Hamza ke kawo min na boys nadan basu na ce su gayar min da Ummina, Kafin Umma tafito daga bayi yaran sun tafi batare da taga may na basu ba, Idan Hamza yana gari nakan danji dadin zuwa karatuna,dan yakan rage min hanya akan yar mashin din da ya,siya Wani lokaci kuma Ibrahim ne kan rufe shago ya kaini har bakin get ya juyo abinsa, ****** ********** ****** Ranan ina gida muna hutu ban fita ba ina tsaye a gurin randar ruwan mu ina wankewa naji sallama, Anty Hindatu ce da dan ta Abba sun yi gayen su suyi matukar kyau dasu , Cikin yar fara,ata na nufe ta da murna na abinda ya jawo hankalin mutanen gidan mu ke nan don gani wacece nagani nake wanan murnan haka, Anty Hindatu ta,dan gwauce tana cewa ja can mara,zumunci ai wallahi fushi nake dake, Yar dariya,na kara,yi tare kama bakina ina fadin kiyi hakkuri Anty wallahi karatune ya rike ni, Tana,saye a cikin wasu lace pink color tayi buje da riga hannun rigar ya dan wuce gwiwar hannu, kadan, Ta,yafa farin gyale a iya,wuyan ta tare da jakar hannu fari a gefen kafadar ta, Sai danta Abba shima,ashiga irin ta yara maza na,wando da riga mai dogon hannu da belt, Ganin Umma yasa ta nufi gurin su tana gaida Umma din sai dai ganin Umma din bata gane taba yasani fada ma Umma,cewa, Umma Anty hindatu ce matar abokin karatun Yaya Hamza da,suke tare a can, Au to Allah sarki inji Umma karaso mana ku shigo daga ciki, sai Anty hindatu ta dan zauna daga waje saman wani kujerar yar tsuguno na mata yar karama da ita, Nan suka gaisa umma tana haba haba da ita don jin cewa daga fanin dan ta bakuwar take, Inda na koma dakina kafin ta taso na dan kara gyara dakin yadda ya kamata ai mai, Ta mike zuwa dakina tana tafiya tana fadin wallahi badon ki nazo ba,sai don Hamza bawan Allah na shigo, Umma take cewa ta,sakawa ranta,wahala wai karatu take bata da hutun kanta yanzu, Hindatu tai dan murmushi tana cewa cikin da tsayawa wallahi Umma karatun yana da amfani sosai yinsa don mutun wata rana yana iya cin ribar sa ta inda ba,a zata ba, Mun shiga daki wanda shigar Anty Hindatu na farko daki na ke nan, Duk ganin ta yasa na,dan rude,sai dan kamay kamay nake acikin rudewa, A bakin gado ta zauna,tunda banda kujera a,dak8n nawa na zama sai tabarman dake shimfide a kasa, Na koma na dauko ma su ruwa a,cup dina na,silver na aje a gaban ta , Nai mamaki ganin ta,dauki ruwan ta dan kurba ta aje cup din shima dan ta tadan bashi amma ya kawar da kan shi wai bazai sha ba,, Muka kara gaisawa da ita take ce min anko takawo min na bukin gidan su, Ido waje nace anko Anty ni da,ban sana,a ina zan samu judin anko , Ta saka hannu a hand bag din ta taciro wani turmin zani ta miko min tana cewa ga,ashoben ki nan don har an dika maki buki on 27 ne dis month, Na karba a cikin mama na mike don zuwa nunawa Umma tace umm,umm Ausha dakata, Ba,wai komaine zaki nuna wa Umma,ba ki dan rika boye wani sirin ki ga cikin ki, Don dan shigowan nn nawa na fahinci wani abu a gidan nan naku, ki kula da kanki kiji kaunata, Ta dan daga kai tana karewa dakina kallo a hankali take cewa may yasa kika shimfida wanan bedshet din Aisha ya tsufa da yawa, Murmushi nai mata ba tare da na bata amsa ba sai cewa tayi ai kamata yayi ko mijinki baya gari dakin ki ya dinga zama neat don gudun kar kiyi baki, Don kinsan wani idan ya,shigo gurin ka daga tsakar gidan ka zai fara gane tsabta ka, Sai kuma dakin ki ki da gurin girkin ki don sau dayawa sai kiga mace tsab a waje a waje amma idan kazo gidan ta,sai ka raina mata wayo ga kazan ta, Amma ke ga komai naki neat wallahi kamar ba a gidan yawa kike ba, Asmau ce tashigo dakin da,sallama tana dauke da pure water leda a cikin wani kwano take cewa Umma tace na kawo mata ruwa, Hindatu tace ayya ai munsha ruwa wallahi Aisha ta bamu ruwa mun sha, Sai ta dauki ruwan ta fita dashi zuwa waje inda ta fito murmushi naga hindatun tayi tana cewa wanan ma kaunar Hamza din ne ko,? Nace mata eh uana da kanne yan mata su biyu suna nan gida biyu sunyi aure, Tau kiyi ta hakkuri kinji Aisha zama da yan uwan miji sai an daure idan ba a dace ba, Kafin tai shiru jibrin yashigo daga waje yake cewa Aisha akwai sauran miya ki zuba min da abokina zamuci abinci, Nacd mai wallahi ba miya duk akaraba yace naki fa kin ci ki kara min daga ciki, Nace tau bari na,dauko ma na dauko mai miyan dake cikin wani dan karami kula na bashi gaba daya, Mikewa naga hindatun tayi tana cewa mu zamu tafi har takai kofa taja ta tsaya tasa hannu a jakar ta ta dauko kudi, tamiko min zasu kai dubu biyar sai da na fitar da idanuwana waje tace kiyi kwalliyar buki dasu kitso kunshi da sauran su nai mata godiya sosai tace haba ba godiya a tsakanin mu don ke kaunata ce, yanzu, Amma ki sai wani abu kici don kar ki zauna da yunwa don naga an karbi abincin ki, Nai dan murmushi nace ai da,akwai kunu zan sha shiyasa na baxhi, Tace idan lokaci yayi zandawo nakawo maki kati ko kuma naxo da kaina, A tsakar gida muka samu su Umma ta ba Umma dubu daya zo kiji godiya a gurin Umma din nai mata rakiya tana ce min sai mun hadu akwai maganan da zamuyi insha Allahu nace tau Anty na gode idanuwsn Umma da yaran ta kar a kaina suna son ganin ko za,a bani wani abu, Nake cewa Umma zasuyi buki a gidan su shine tazo fada muna, Umma ta taso tana cewa Allah sarki mu gode kwarai da wanan karancin naki Allah ya nuna muna lokaci lafiya, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 1⃣9⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA FATAN ALHERI DA GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA GARE KU DUKKAN MASOYYANA NA GAISHE KU AKAN KOKARI DA KAUNAR DA KUKE NUNA MIN A KULLUN,,, Rayuwan zamana agidan aure ya kasance na yau dadi gobe daci wanda duk akasarin rayuwa a haka yake yanzu, Yau da gobe yasa na fara fahintar duniya a rayuwa yadda yake, Uwar mijina na dan fahinci kadan daga halaiyar ta wanda shine bata kaunar taga danta ko kadan yana nuna kulawan shi a kaina, Amma ita zata iya gwada min da kanta inda muna mu kadai a gidan, Da,zaran kuma ya,shigo sai zance yadan canza a tsakanin mu, Wanda na,fahinci ba wai kishin shi take ba bata dai kaunan ya nuna min zakewan shine a kaina, Wanda ita a ganin ta idan ya soni zai guje mata tare da yan uwan shi ya koma komai sani kamar yadda matan yanzu sukeyi su raba mijin su da yanuwa har iyayye ma, Su kuma yan uwan shi matsalar mu gudane dasu shine su tambaye abu ban basu ba yanzu zakiji manyan magan ganu suna tashi, a gidan, Hakan ne dana fahinta na dauka ma kaina mataki gare su gaba daya, Ita Umma dai na,sawa raina bazan yarda na nuna afili yadda zamana da mijina yake ba, Duk yadda Hamza yaso ya nuna yadda ko soyayya a,gaban Umma koda a cikin magana ne ban yarda na nuna a fili, Haka su ma yan uwan Hamza din watau dangin miji duk abinda suka bukata a guri na koda shi ke nan a gareni zan basu na huta, Kusan zance rayuwa a yanzu haka yake, yau dadi gobe babu a ko ina mutum yake, Na kasance mai kokarin ganin na hade duk wani bacin rai da zan iya gani daga rayuwan aure na a gidan, Haka Fan,nin ka ratuna yake samun ci gaba acikin nasaran ubangiji na don bawai da Alkah yai min ya taimaka min kwarai da gaske, a school din, Duk da ban shiga har kan mutane amma,su suna kokarin shiga nawa don dai nayi hurda dasu, Yau ma kamar kullun mun fito daga dakin lecture lokacin sallah azahar ya yayi direct massalaci na nufa don sauke farali,, Sam ni ban yarda da zuwa hostel dakunan mutane yin sallah ba,sai dai naje mosque din school nayi, A hankali nake zare sock din dake kafana tare da cire dan agogon da na daura a hannuna, don diban time saboda gujewa fitinar Umma Rabi, Butar dana dauka babu ruwa a cikin sa mai yawa dan waige waige na fara yi inda zan samu ruwan sallah can na hango wata mata baka mai dan kaurin jiki tana cin abinci ga ledan ruwa har guda uku daga gefen ta, Na karasa,gurin da take zaune da sallama a,bakina ina mai gashe da ita da cewa sannu sister, Ta dan dago kai fuskan ta round face ne da dan diple manne gareshi, Don Allah sister ruwa nake son ki dai taimaka min da shi nayi alwala yau ba ruwa a famfo , Ta mike min leda daya na ruwa tana cewa wanan zai ishe ki ko ? Na karba ina godiya na juya zan wuce take cewa bissimillah muci abinci ko,? Alhamdullahi na bata amsa a,takaice na wuce zuwa sallah , Kamshin abinci na tashi gashi ya ji mai dagani miyan tumatir ne zai yi dadin da gardi a,baki don kamshin shi kawai dake tashi ya isar wa mutum da sakon hakan, Gurinbda,na idar da,sallah a nan na zauna ina lazimi kafin time din komawa na lectures yayi, Wanan matar da,ta,bani ruwa itace ta,shigo cikin mosque din da,alwalan ta,zatai sallah, Har ta idar ina zaune a gurin ina,adduoi batare da,na kalle ta,ba, A,kofar fita muka hade ina,saka takalmana ita kuma ta idar zata fito, Gaishe ta nayi irin na,addini a,cikin dan,sakin fuska itama ta karba min, da nata fara,an take ce min amma baki dade da zuwa school din nan ba ko ? Nake ce mata aa mune yan fresh da aka dauka newly, Wani department kike nece mata environmental nake sai take cewa tau ashe kusan department guda muke, ke nan, Mun jero da wanan matar muna hira a hankali take ce min ke a garin nan kike ne ko kinzo ne nai dariya wanda ya dan baiyanar da fararen hakora na a fili, Nakecewa a nan nake nan kuma nake aure, sai naga ta dan juyo tana kara kallona, Ta ce k8na nufin ke matar aure ce na ce mata eh sai take ce min ita daga yauri tazo karatu ne matar aure ce tana da yara biyu, Amma ta barsu a gida tana zaune ne a gidan haya da mijin ta ya kama mata, sunan ta Hadiza , Munkai inda zamu rabu kowa ya,shige department din sa, Sai biyar da rabi nabar makaranta zuwa gida don na samu na karasa aiyukan dake gare ni, ****** ********* ****** Tsaye take rike da filo a hannun ta tana kokarin gyara gadon ta don hakan al,adan tane ta gyara daki tun da safe, Kafin wani lokaci dakin ya,dauki kamshi tare da komawa neat gwanin ban sha,awa, Tashiga,bathroom dinta dake mane da dakin ta, tai wanka, tafito inda ta zauna ta gyara jikin ta tsab a cikn wasu material dake cikin kayan lefen ta, Tun bayan irin lafazin da Ummi tai mata ta daina sa damuwa, a,ranta, kamar farko, Kwata kwata itama ta,daina shiga harkan shi sai harkokinta take a cikin taka tsantsan, Shigowan mutum ta gani dakin ta bai,damu da yai sallama ba tunda gidan sa,ne, Sau guda ta,dan daga idanuwan ta ta kalle shi sai ta,sunkuyar da kan ta kasa taci gaba da mayar da powder ta inda ta,dauko shi saman dressing mirror, Tsayuwar shi ya gyara yana mai kallon yadda ta,ramay tawani koma yar fayau da ita, Ke baki iya gaida mutum ba ke nan har da tarbiyan rashin gaisuwa baki da,, Kubura ta dago kanta da,sauri ta dan kalle shi sai taga yai mata wani kwarjini a fuskan ta, Za,a yi buki a gidan yan uwan mu ina,son kuyi attending din duk event din da zasuyi, Kara kallon shi tayi a cikin mamaki ya fahinci tai mamaki yake cewa Jamila zata karbo maku kayan anko wanda zakuyi amfani da su a,can, don haka ban son naji wani fitina daga iyalina har a,watse daga wanan bukukuwan, A hankali cikin sanyin murya ta amsa da fadar insha Allahu, Sai yaji ta bashi tausayi sosai yaji abinda yake mata bai kyautawa, ko kadan , Hannu ya,saka a,cikin aljihun shi ya ciro kudi da zata iya cewa shima baisan yawan su ba ya mika mata yana cewa wanan ki rike a gurin ki Nagode ta furtaxmai wanda shi kan shi yau yai mamaki da irin lafazin ta a cikin taushi don kuburan da ya sani ba ita bace yanzu, kwata,kwata, Nan ya aje mata k7din yafita,dakin da,saurin shi kamar mai jin tsoron a ganshi dakin nata, Bin shi tayi da kallo cikin wani irin yanayi wanda taji tausayin kanta ya kama ta,a lokaci guda, Tai mamaki kwarai yadda akayi yau shi da kanshi ya,shigo mata daki da maganan lumana, a tausashe, Shawaran Ummi ya fara mata amfani ke nan don ta fahinci yanzu matar gidan kamar hankalinta a tashe yake bata da natsuwa kuma, Kudin daya,bata tafara adanawa sanan tafito don zuwa ta dauko breakfast din ta taci, Sai ji tayi muryan Jamila tana cewa na fada maka matarka yar rashin kunya ce don haka bazan kai muna dinki tare ba tai min rashin mutunci A marairaice taji muryan maigidan yana cewa haba Jamila yanzu duk abinda nake ma yarinyar nan a kan ki bakya gani, Bata ji may Jamilar tace ba tafito daga dakin rai a bace ya fita, Sai ga Jamilar ta fito dingis dingis tabiyo bayan shi, itama, Ganin Kubur din zaune da kayan karin kumallon a,gaban ta yasa su gaba daya dan jin shock don sun san cewa taji zancen su, Daga inda Kubura take zaune ta watsa masu yar karamar harara tace a,zuciyan tace lalai zancen Ummi hakkun gaskiya ne, Tayar da hankali ko wani cin mutunci bazai barni na fahinci inda matsalar take ba, Ta tabe bakin ta ta mike tana fadin kanku dai ake ji don na bar ku ga Allah ni, Dole ne ta shiga gida,gurin Ummi don ta fada masu halin da tafara tsintar kanta a ciki yanzu, ****** ********** ****** Yau da,guri na,dawo daga school inda nai sallah azahar na dan dauko takarduna ina dan dubawa a hankali, A gurin barci mai dan nauyi ya kwashe ni ba tare da na,sani saboda tarin gajiyan dake tare dani,, Ko hijjab din da nai sallah ban cire ba yana,saye a jikina har akai kiran sallah la,asar Ganin ban fito ba,ga yamma yanayi yasa Umma ta, nufi dakin nawa , A cikin barci nake jin kamar muryan ta hakan yasani bude idanuwa na da,sukai nauyi,saboda barci take cewa, Aisha wanan barci fa haka yau ya kamata ki tashi hakana yamma yayi sosai, Nan na mike zubur ina mamaki don ban zaci cewa lokaci ya kai haka ba, Bandaki na nufa inda na yo tsarki nazo saman wani dutse da muke zama a tsar gida don yin alwala a gidan, Umma tafito da mayafinta a kai tana cewa ina son na dan fita na zaga ko zan samu dan kudin da nake bi bashi na sayo muna dan abin minya daga can, Alwalana nakeyi hankalina a kwance ta dan fara tafiya,sai kuma ta,tsaya tana cewa kudin hannuna baida yawa amma ina son mu dan ci dan abin kwarai yau, Nakai ruwa a,bakina tare da karanto adduoin rufe alwala, Namike ina cewa Umma da akwai dan canji a guri na bari na,dauko maki sai ki saya dashi, Kafin nagama fadi Umma tace a,a ayi haka yar nan idan zakiyi wani lalura dashine fa, Na dai shiga daki na zaro dari biyar daga cikin kudin da Anty hindu ta bani nakai mata, Ta karba tana dan juya kudin tana mamaki kamar zatai magana sai kuma ta dake tafita tana cewa sai ta dawo, Taufa ashe na daukowa kaina magana don Umma ta fita tana tuna ne, daga karshe shedan ya ruda tace Hamza ne ke bani kudi nake yadda raina yaso dasu idan zai tafi , Ita ko sai ya bata kalilan yace tayi hakkuri bai da kudi maneji yakeyi shima, Nan ta hau tai fan saigata ta,dawo da nama danye a cikin leda a hannun ta, Wace muka rabu lafiya amma,sai gashi fuskan ta ya canza sai tana,wani matsewa da daurewa, Na fahinci haka don haka naci gaba da,aikina na gida kamar yadda na saba yi, Bayan sallah isha,i ina zaune a dakina still ina,dan karatuna,naji muryan Umma tana cewa Ibrahim din ta, Dan uwanka nake jira yazo garin nan don na,fahinci ya,canza sosai a,rayuwa, Auren nan yasashi kwata kwata yanzu baya jin magana ta a gidan nan, Ibrahim yake cewa may kuma yai maki umma tace ai barni dashi don ba shi da abin cewa sai dai yazo din ai zakaji mu, To koma may yai maki kiyi masa hakkuri don ni kin san halin dan ki fiye da kowa Umma, Yana gudun zuciyar ki fiye da duk wani da naki a gidan nan Umma, Bata tsaya sauraren Ibrahim din ba ta mike ta nufi bayi, Murmushi nayi ina cewa ikon Allah may Umma take nufi danine haka wai ?. Duk al,amari ci gaba yanzu na fara fahintar bata son ganin shi a gare ni tafi da son taganni a,wullakance ke nan, Allah ya kawo dan na ta taji da kunnuwan ta abinda take zargi, Washe gari ma,da,zan tafi school har kofan ta naje sallaman ta amma,sai umma taki amsa min irin yadda ta,saba,ba, Nafito na nufi inda zan hau mashi, don zuwa makaranta, A kullun zanfita zsn saka sock a kafana nasa dogon hijjab har kasa sai na daura nikaf a fuskana tun lokacin da na,fahinci an saka min ido ga fitana, Ina shiga na hagi wata mace tana mun hannu, sai dai ban gane ko wacece ba,sai da na karaso naga,ashe Hadiza ce, Mun gaisa fuskan mu dauke da murmushi don mun sheda junan mu ko, Take ce min tun ranan bamu sake haduwa ba kuma gashi kina a raina, Dan gajeren murmushi nayi tare da cewa Allah ne bai nufi mu hadu ba, Amma ai gashi yau mun sake haduwa dake ,sai take cewa ranan mun rabu bamu karbi nomban juna ba, Na dan girgiza kaina a hankali ina cewa banda waya ni Allah sarki tace min, Yanzu dai idan kin fito ina gurin da muka,hadu ranan zan jiraki muci abinci, Na dan girgiza kaina nake cewa wallahi a koshe nake naci abinci tun a gida ko Hadiza din tace ni naso muyi hurda amma,sai naga kaman ki ja,da baya dani, Murmushi nadan karayi mata inda nake cewa ba hakana bane kin san bamu da time din tsaya irin haka , anan, Kuyi hakkuri dani da,wanan wallahi yau ba yawa da fatan zaku fahince ni, ZAINAB IDRIS MAKAWA👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣0⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA YA ALLAH KA KAREMU DAGA DUK WANI SHERI DAKE CIKIN WANAN ZAFIN, YA ALLAH KASADA MU DA ALHERIN DAKE A CIKIN WANAN LOKACIN, YA ALLAH MUNA ROKON KA DAKA SANYA ALBAKA AGARE MU DA YAN UWAN MU DIYAN MU IYAYYEN DA KAKAN NIN MU, ALLAH KA SADA MU DA RAHAMOMIN KA MASU DARAJA DA DAUKA A DUNIYA DA LAHIRA YA ALLAH KA KARE MU DAGA DUK WANI SHERI NA MUTUM KO ALJAN KO DABBA KO KWARO DAMA,WANDA BA MUGANI DA IDANUWAN MU,,,,,,, Ina duke ina wankin uniform dina,da yan sauran kayana da,sukai dauda , Naji sallama daga bayana, amma Umma ce dake tsaye take karba ma mai sallaman, Sun gaisa naji matar da ta shigo tana cewa don Allah gidan Aisha Mudi muke tambaya, Aisha,Mudi Umma ta maimaita sunan cikin mamaki jin muryan naso na,sheda ga kuma,sunana da,aka fada, Na,mike don inga ko wacece ke min sallama Hadiza yauri ce da wata sai dai ban san sunan dayar ba, Cikin murna da farin ciki na tare su na,dauraye hannaye na na nufo ina masu iso da,su karaso mu shiga daga ciki, Na dauko dan tabarmana na,shimfida masu nafita debo masu ruwan sha, Wanan damar ce yasa su kare ma,dakina kallo da kyau inda,suka fahinci ni din dai tallakace ta gaskiya don ba,wani abin azo a gani a gidan namu da dakina, Nadawo dakin da cup na aje masu ruwan ina masu sannu da zuwa, Hadiza ta,dauki cup din ruwan ta kurba kadan ta mikawa dayar amna,sai ta girgiza kai tace nagode, acikin murya kalar ta yan matan zamani yan gaye Nace Allah sarki kiyi hakkuri ba yaron da zan tura ya,sayo maku ruwan leda ne, Tace cikin daga hannu kada ki damu Iam OK ne aida zan sha wanan din, nace gaskiya nagode da,wanan ziyarar da kukai min , Hadiza tai murmushi ta dan gyara zama tana cewa ai dama zuwan bazata nake son nai maki shiya sa jiya naki fada maki cewa zan zo, Nace to waya gwada maki gidan hankalina a,kwance banji wani kunya ko nauyin yadda suka samay ni ba ba yar kowa ba kuma ba matar kowa ba, Tace wanan mai mashin da ya dauke ki ranan shine na gani da zan tafi BK sai yai min kwatance, da uguwar da gidan ku, Nace ikon Allah to don Allah kuzo muje ku gaisa da sarkuwa ta , Dayar yarinyar da,ban san sunan ta ba take cewa wai da gaske ke matar aure ce, Murmushi nai mata kawai na mike ina masu jagoran zuwa gaida Umma a dakin ta, Abin mamaki a saitin tagan dakina muka samu Umma din cikin dan rashin gaskiya take cewa daga ina muka,samu baki, kuma, Nace Umma abokan karatuna ne suka zo gani na daga makaranta, Wani kallo naga Umma din tai masu wanda hakan ya,dan sani shan jinin jikina kada ta masu halin ta, Sai take cewa wanan ma karatun sukeyi suma tirka sa, Dariya hadiza tayi tana cewa eh mama da yara na kuwa a gida har biyu nabarsu nazo karatu, Ikon Allah inji Umma Allah ya kyata take cewa muka mike zuwa dakina, hira muke dasu zakace mun dade da sanin juna inayi ina duba girki na dake a,wuta, Nayi sa,a shimkafa da wake mukeyi da salad kamar yadda mu kan danyi in muna son cin dan dadi, a gidan, Yaya Ibrahim ya,shigo ya,samay ni ina raba abinci na,da,shake murya kada Umms taji nake cewa don Allah Yaya kadan taimaka min da ruwan leda mai sanyi baki nayi daga makarantar mu suka zo min yini, Yace madallah aiko sun kyauta bari na fita na,sayo maku, Ban zauna ba ina yi ina dan leken kofan shigowa gida, Allah ta taimakeni sai gashi da bakar leda maigiwa ya,sayo min lemon gora masu sanyi har guda biyar da kuma ruwan sanyi, Zan maí godiya ya wuce ciki yana cewa kai haba ai rufin asirin mu ne baki dayan mu, Ina,son na debawa su Umma ruwan sanyi ina jin tsoron fada kartace na,saka dan ta,a lalura na don haka na,ajewa wasu Hadiza gaba daya a,gaban su, Nai mamakin yadda suke cin abincin hakali a kwance muna hira, Ban yarda na ci abincin sosai ba don baida wani yawa sosai ina tsoron Umma tace min na kwashe abunci nabawa kawayena, Naji dadin wanan zuwan da sukai min don ko ba komai sun sake jikin su dani munci mun sha dan abinda Allah ya hore min, batare da kyankyami ba, Wuni sukutun sukai min don sai bayan karfe biyar suka,bar gidan mu sun sake jiki abinsu da kowa, Bayan tafiyan su ne Umma take cewa su kuma haka akeyi kazo gidan mutum ka,wani shagala,har wani lokaci, haka,? Banji dadi ba amma na godewa Allah da,bata fada a gaban su ba,sai bayan sun tafi take zancen ta kamar mai fada, da wani, ****** ********* ****** I yanzu hanakali na ya fara dan kwantawa a gidan don nasan halin kowa a cikin gidan, Sai dai kullun ina cikin taka tsatsan ne da abinda zai ita jawo min fitina daga Umma da kannen mijina Haka zalika ita ma Umma din yanzu ina da dan sasauci daga gurin ta tunda yanzu Hamza din ya dade baizo garin ba, Umma da yayan ta take komai, lokuta da dama koda ina zaune tare dasu ne zata iya kebe ni tai al,amarin ta da yaranta,, Wanda hakan na daga cikin halaiyar ta dake iya kawo matsala a cikin gida, Wata rana bayan an sauko daga sallah jumma sai da na dan kai wani lokaci na mike tare da dan gyara fuskana na leka dakin Umma ina mata ina wuni tare da dan tambayan ta ko may zan dafa,muna a ranan, Don a kullun sai abinda Umma tace min na girka nake girkawa a gidan ko ina ta tafi tane dole sai na jirata duk inda ta,tafi ta dawo zan tambaya na dafa muna, Na,samu Umma da wata bakuwa a dakin suna magana su biyu, Haka,kawai ganin matar ya sanya girjina bugawa don sai naji sam matar batai min ba a raina , Na gaida,su a cikin ladabi inda matar ta dan kalle ni cike da fara,a take cewa ashe kina ciki yar Agwai ai na zata kin futa ne, A takaice nace ina ciki barci ne ya kwshe ni , Na juya har zan fita daga dakin sai na kalli Umma nake cewa Umma may zan dora muna ne, tace ai muna da sauran gari ki girka muna shi mu ci, Na bada baya kadan nake jin bakuwar Umma wace aminiyar tace tana fadin, A,a Rabi wanan yarinyar fa tayi min gwabi a idanuwana, Kardai nace gashin kanta take ci tai wanan kyau haka tabarki a lahaula, Don kin san yaran yanzu sai kin gama wahala da danki sozo suce sun fiki son shi da kaunar shi, Su saka,namiji a gaba suna mai wayyo duk abinda ya samu a hannun su yake, Ke Uwa kina zaune sai dan abin da a ka tsakuro maki zaki gani, Umma tace cabdi ai ban yarda da,wanan sakacin ba shiyasa kikaga na kafa dokan komai a hannu na yake don bazan yarda da rainon inuwar giginya ba, Diyana a tafin hannu na,suke bsn yada sun mami kowa ba gatin nan, Lokacin da nai wahala da abina tana ina da zata zo tai min ikon banza a gida, Wanan ma dabata da,wani galihu ko agidan malam Mudi din yaushe zan tsaya ina kallo taiwa dana yadda suke so, Take naji wani irin zazabi ya,sauka min a jiki da kyat nake aikin danakeyi don irin yadda nake jin zuciyata tana,suya a,ranan, Bayan na kamala aikin da nakeyi na shige dakina ban fito ba, Ina kwance a kan gadona zube kamar wata mara lafiya, nake jin kaina, Idanuwana suna lumshe sai zuciyana dake dan bugawa gap gap gap, May ye laifina a,cikin auren Hamza da nayi da har Umma take min wanan kallon mara galihu, Tambayan da nakewa kaina kenan ni kadai a cikin dakin, Wanda hakan yasa hankalina gushewa daga jin duk wani hayaniya dake a tsakar gidan, Alamar motsin mutum naji a kaina wanda hakan yadan sani bude idanuwa na don ganin waya shigo min daki a lokaci, Hamza na gani tsaye a,saman kaina yana min wani irin kallo a cikin shaukin so da kauna irin na mata da miji, Take na nemi damuwar dake damuna a,rai na,rasa inda na dan yi yunkuri mikewa daga kwanciyar da nake, Cikin wani hanzari ya mayar dani kwancen inda yayo min runfa da kirjin shi ta yadda bazan iya dagowa,ba, Magana kamar mai rada yake min yana tambayana may ke damun ki ne may samay yasa yau na samay ki a kwance, Dan murmushi na kirkiro a fuskana tare da mashi sannu da zuwa a cikin sanyi murya, Dan mikewa yayi yai zaune a,bakin gadon da nake a kwance , Sannu da zuwa na kara,mashi a karo na biyu ya amsa da,mun samay ku lafiya nace lafiya kalau May kike tunane haka nake sallama baki jini ba har nakai ga,shigowa, Murmushi nayi nace barci ne ya,soma dauka ta ba tunane nakeyi ba, Takon shigowa dakin muka ji inda da sauri na karasa kaiwa zaune nima , Daidainan ne kanin shi Jibrin ya,shigo da jakar kayan shi sai naji Hamza yana ce mai ina wanan ledan guda biyu dana zo dasu, Jibrin yadan duka yana aje jakar kayan yake cewa suna,gurin Umma tace na barsu a can gaba daya, Kace nace ka kawo min sakon Aisha ne a cikin su da,sauran kaya na, Jibrin din ya,fita ajima kadan yadawo dakin yana cewa daga kofa, Yaya wai kazo da kanka inji Umma din abinda yasa shi saurin mikewa ke nan daga zaunen da yake, Mikewa nayi don dama kamar a takure nake a inda nake kwance din da nake, Ruwan sha na fita na debo mashi a randa tare da abinci, Muryan shi naji kamar a rai bacd yana fadin mama idan ba aiko ni akayi da su ba kin taba ganin nazo ma Aisha da wani tsaraba wanda ba,gaba daya zan kawo maku shi ba a gidan nan, Tankar banji su ba yafito daga dakin mama da ledan a hannun shi ran shi a bace, ya nufi dakin mu, A tsakiya mukai kicibis dashi ranshi a,bace fuskan shi babu annuri a cikin sa ko kadan, Ina waje ina kokarin hada mai Abinci naji Umma tana cewa wanan ai wani sabon sallon magana ka,dauko min , Gaka da kanne a,gida zakace wai matar ka kawai zakayowa tsaraba to su yan uwanka fa, Na,shigo dakin namu da,sallama yana tsaye yana cire rigar dake jikin shi shirt mai dogon hannu, Abinci na aje daga gefen tabarma inda na ke ce mai ko zaka watsa ruwa ne ko zakaji dan sanyi don ana zafi, juyowa yayi inda nake tsaye yana kallo na jikin shi babu riga sai yar farar singilet, Aisha kwana biyun da nayi banzo yana,da nasaba da irin yadda mama bata son ganini a gida koda yaushe, A hankali ya tako zuwa inda nake tsaye nadan bi lafiyan bango ina sauraren shi, Hannuwan shi ya bude yake ce min nazo a cikin signal , A hankali na taka zuwa inda yake na,shige cikin jikin shi, Gaba dayan mu sauke numfashi muke a cikin ajiyar zuciya gwanin ban tausayi, Kin canza Aisha kin ramay min a idanuwa na kin na cikin damuwar halin Umma ko ? Na,dan dago kaina dake sune a jikin shi ina cewa banda wani damuwa halin Umma kuma ai ba bakona bane, Karatune kawai a,gabana,shine damuwata yanzu, Murmushi yayi yakara mannani a jikin shi yana cewa tare da dan bubuga min baya, Ohoo sorry da ina kusa da baki da matsala yan mata sai dai kashh nesa baya maganin kusa, Amma nasan aike ma baki da sauki gurin kawo wuta ga karatu, Ki dai cire damuwa a,ranki kinga ki kuwa kin wani dan fada haka dake, Bari na baka ruwa sai ka watsa kazo kaci abinci ka huta gajiya, ko Nakai kofan daki yake cewa ga tsaraba nan hajiya, Nurat tace na kawo maki sai dai ina gani Umma ta,debawa yaran nan wai, Kai Allah ya umfana nace acikin dan murmusawa wacece kuma hakana yaya ? Wata course mate dina ce sai da ba yarinya bace shiyasa nake taimaka mata Allah sarki nace sai nafita, daga dakin, Bayan yafito daga wanka ya,zauna yana cin abinci kafin ya fito na canza kayan jikina nai yar kwaliya yadda ya dace nayi, Ina,daga,gefen shi zaune autarsu Sa,ade ta,shigo dakin tana cewa yayan mu, Umma tace wai kazo kaci abinci, Ya dago kai yace a,a autar Umma,ba ko gaisuwa, kin shigo daki kina kumbura haka, Tace a dan shagwabe ba Asamau bane ta kwshd kayan da kazo muna dashi ni ban samu powder ba, Dan jin mu kaji gaba dayan mu amma,sai nake cewa, zo ki bude ledan ki duba idan akwai abinda zaki dauka,saiki hada da,wanda ta bar maki, Ba mussu yarinyar ta nufi inda ledan yake wanda ban ko bude ba tafara dudubawa, a hankali , Naji yana cewa ina turaren dake a cikin ledan suke tace Asmau ta dauka, Jekice wa Umma abincin nake ci Asmau kuma ta baki turaren ki dawo min dashi , Ina dan tsiyaya mai ruwa a,wani dan karmin cup dake a gaban shi naji Umma tana fadin ke Aisha Wani abinci kika bashi bayan ga abinci nan an hada mashi a daki, Da sauri Hamza ya katse uwar da cewa Umma can naga ta debo min mana, O lalai mai mata ko har tasan zafin ka ashe ban sani ba,? To turaren dakace a karbo gurin ma,u na ce tabarshi don matarka batafita ba ai, Mama nawa ne fa bana Aisha bane wanda nake amfani dashi ne a makatanta, Tace nace baza,a bayar ba ko zaka kwatar matane ? Da idanuwa nai mashi nuni da ya kyale don Allah don banson suna jan zance kar yai girma, Haka ya gama cin abincin a dan hasale ran shi a bace amma don na kawar da zance sai nake cewa, Da engineer kukazo neina nufin mansur mijin anty hindatu, Yake cewa, tare muka zo kin san akwai buki a gidan su matar shi a karshen sati mai zuwa, Da sauri na,dago kai nace kenan yaya kana nan har wani sati mai zuwa, Yace insha Allahu haka nake tsamani idai ba wani abin bane ya taso aka kira mu, Allah yasa kada a kiraku baki na ya furta cikin subbucewa ban sani ba, Cikin murmushi kamar mai rada yace baki son na koma ne yanzu, Kunya naji nace cikin dan dafe fuskana ba haka nake nufi ba , Na mike zuwa gefen akwatin kayana da mamana Rahana ta bani lokacin da zantare a gidan, Sunana ya kira inda na tsaya cak na,ansa ciki,ciki gami da juyowa, zoki zauna ba mussu nadawo inda na zauna dafarko na zauna, Yace kiyi min lissafin abinda keke bukata na,saya maki wanda zakiyi fitan bukin su matar Mansur dashi don ina son kije gurin sha,anin bukin ayi shi dake, A sanyaye nace duk abinda ka saya min ina son su yaya basai na fada ma abinda nake so ba, Anty Hindatu din ma tazo gidan nan takawo min anko dina tare da kudin din ki, shine zan dauko maka ka gani, Hindatun ta kawo maki nace eh har da kudi dubu biyar wai nakai dinki, Shiru yayi na mintina sai ya sauke ajiyar zuciya yana cewa Allah sarki , Wa yannan mutanen Allah ya,saka masu da,alheri, Mijin ta haka yake min dawainiya a makaranta wallahi tun ina jin kunya yanzu har na daina jin kunyan shi, Banda abinda zan bashi don shi mai haline tunda yana,aikin gwaunati haka yasa nazama mai kamar yaron shi, shima bai son haka amna dole ya gaji ya kyale ni, Kayan da Hindatu takawo min na,dauko mashi tare da kudin nai mai bayanin naba Umma dari biyar daga ciki, Da,sauri yace dama Umma din tasan cewa ankawo maki kayan ne? Nace a,a don Anty hindatun ta hana na nuna ma kowa wai sai in na,saka a,gani a jikina, Murmushi yayi don yasan ko wacece Hindatun tunda yana da labarin ta,a gurin mijin ta, Nasan da Umma tasan da kudin nan bazata barsu a hannunki ba don haka sai kiyi laluran dakike bukatan yi dasu, Nace cikin kara tausa muryana Ummina nake son nabawa wani abu daga ciki don tun da nai aure ban taba bata alheri ba, Yace kin kyauta kwarai wallahi sai ki bari idan na huta kwana biyu sai mu shirya,mu shiga mu gaidasu, Shigowan Ibrahim ne ya katse muna hiran mu inda na samu daman tashi na dan kimtsa kaina don taron bakona na wanan ranan, Daga cikin tsaraban hindatu da zarah nai amfani na kamala komai ina jin hiran su a tsakar gida har na kai ga kwantawa, ****** ********** ****** Washe gari natashi agajiye saukina guda,shine ranan ban zuwa school, Don na gaji sosai saboda Hamza bai raga min ba,a wanan daren don komawa yai min kamar ya,zautun, Zakace a,wanan ranan ne ya fara kwanciya dani saboda irin yadda ha zarce min, Ni kaina,sai da abin yadan ban tsoro amma haka na,daure na biya mai bukatun shi don Hindatu tace min kada na,yarda na nunawa namiji gazawa koda kuwa bana jin dadi ne na,daure na gamsar dashi ta fannoni da dama, Duk yadda naso na,fito da,safe don yin normal aiyukana hamza din ya hanani yana makale a jikina kamar ba gobe, Sai da ya gaji don kan shi ya,bari muka,fito lokacin gari yai haske sosai inda muka,samu Umma ta cika fam damu, Amma haka na dake nafito nai wankana na koma,daki nai sallah na na gyara jikina inda na,saka,wani dogon riga na material ne don tun a,gida nake dashi, Nafito zuwa gurin da muke girki yau Umma bata dora,wutan girkin ba don haka nice na dora da kaina, Aiki nakeyi amma zullumi nakeyi don zuciyata tana fargaban abin da, Umma zatai muna, ranan, Hamza ya fito daga dakin mu tsab ya shirya acikin wani simple yadi assh, na maza a mai dinki mai dane jiki, Dakin Umma ya nufa inda ya shiga da sallama ya samay ta a,zaune, tare da yaranta sun sayo masa suna ci mai zafi, Nanya,shiga gaisawa da yan uwan shi a cikin jin dadin yan uwan shi, Umma tana daga gefe ko daga,kai ta kalle shi batayi ba sai cin masan ta takeyi hankali kwance, Cikin dan sanyin murya yace wa,Uwar ina kwana Umma,? Lafiya ta amsa mashi dashi a,takaice, Ibrahim ke cewa azubo ma masan ne kaci ko don naga yanzu ka,a shigo, Matar shi ai tana da,abin bashi ya karya a can don haka kudai kuci kuda, kuka,dogara a,kaina,, Wani irin kumci yaji irin yadda Umma tai mai shi haka gaban yan uwar shi, batare da ta bari sai suna su biyu ba, Jibrin wanda bai san dawan gari ba yace ai Aisha akwai kokarin hada abinci wallahi shi yasa nake son ta,don ko yaushe kazo zaka,samu ta gama abinci kaci, Dariya sauran suka saka mai har da Hamza din wanda ran shi yake a bace, Ibrahim yace kaiko don cin abinci kawai kake son ta a gidan nan, Yace a,a komai fa nake so idan tana dashi bani zatayi ai na fada mata,ba kishiya a gidan nan, Kai kai kun isheni da shirmay irin naku inzakuci abinci kuci idan kuma surutu zakuyi min ku cika min kunnuwa da,shirmay ku bani guri don Allah na karya, Mikewa Hamza yayi daniyar barin dakin Asmau ke cewa yaya tsaya mana na,zuba maka masan kaci, Yace No ki barshi Ma,u na gode zan fita na,samu abinda zamu ci, Fushi kayi ne yayan mu inji Ibrahim yake tambayan dan uwan nashi, Yace idan naci wanan ita Aisha fa may zataci daga ciki bari na fita sai na,samo abinda za,a kara dashi, Wanan din ba zai isheku ba ku biyu idan zataci ? A lokaci har ya kai kofa yace abarshi kawai yasa kai yafita yabar su nan, Ina duke a,murhu yake cewa ki sa,ruwan zafi bari na,samo bread asha tea, Na amsa a,sanyaye ya fita daga gidan inda naci gaba da,aiyukana sai dai rayuwana ya,bani cewa,Hamza din ya,fara dan zare wa mahaifiyar tasu, Na hada tea din gaba,daya,wa kowa inda na zuba namu a jug dina nakai daki na dauki bread guda da guntu nakai dakin Umma, Bayan a je zan juyo Umna ke 'cewa kece kika raba da ka ki ke nan Aisha, Cikin dan jin nauyi nai tsaye ina dan dukar da kai murya kasa kasa nake cewa,a yi hakkuri Umma shine yace na hada adebo akawo nan dakin, To aikin san mijinki ne ya,sayo muna shiyasa zaki min gaba gadi, Umma dan Allah kiyi hakkuri nayi kuskure bazan sake ba insha Allahu, Umma a gabana fa ta hada komai kuma,dan kadan ta zuba masu su biyu, Sa,ade ce kaunar shi ke wanan magana, Rufe min bakinki yar nema mai bakin surutun tsiya basu bari mutum yai magana, Haka na,samu dama na koma dakina,sukuku jiki ba kwari na,samu guri na zauna nai shiru a cikin damuwa, Yace may akayi may yafaru kuma ? Ba komai na furta yayin da wani abu ya tokare min zuciya cikin bacin rai nai magana, Shi da kan shi ya zuba min a cup ya miko min agaba tare da turo min ledan bread din a gabana, Dauki ki sha ya furta min tare da kafeni da lausasaun idanuwan shi masu firgita mutum,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, Zaune nake a gaban dan mirron dakina ina kwaliya da kuma kara gyara jikina, Sai dai zuciya ta tana fam da tune da zullumi wanda bai wuce duk sanda Hamza yake gari ina cik8n matsi da tsangwama a gurin Umma, Wanda na rasa gane ko maynene ke jawo min wanan matsalar ba haka a tsakanin mu, Ni dai a iya sanina ina kokarin ganin cewa ina kyautata mata yadda ya kamata, Amma kuma hakan bai sa na samu maslaha daga gare ta ba , Hamza din ne ya,shigo daki da,sallama a,bakin shi, na amsa mai da,wa,a,laikussalam, Sannu da zuwa nai matare da son mikewa tsaye amma,sai ya,mayar dani na zauna ta hanya saka hannayen shi ya,rugumoni ta bayan shi, A hankali ya dan rada min a kune matar Hamza kin yi kyawo Allah ya ba hamzan ki kudi na,di ga saya maki kayan kwaliya masu kyau k8na min kwalliya saboda ina son ganin mace tai kwalliya a,rayuwa na, Ta cikin mirror da nake zaune gaban shi muka hada ido yadan daga mi gira a hankali, sai na sune fuskana cikin kunya ina fadin ameen ya Allah, Mikewa yayi daga dan rankwafo min da yayi yana cewa bari nima na watsa ruwa na zo mu tafi ko, Don har gidan mama Rahana nake son yau mu shiga insha Allahu don ina son matar nan don tana da hali mai kyau wallahi, Duk lokacin da na zo garin nan sai ta aiko danta ya gaidani da sakon gaisuwa, Murmushi nayi mama Rahana ai ba ruwan ta da,sauki ta dauki rayuwa ita, To bari na je na,watsa ruwan nai wanka na,danzo na shirya mutafi, Bari to naje na zuba ma,ruwan wa ka ko kafin ka fito na gama,shirina, Ya ce a,a zauna abinki zan diba a kaina ai watsawa kawai zanyi don naji sanyi, Na koma naci gaba da shirina yafita ina jin shi yana zuba,ruwa a randa, dake daga kofan mu, Lokacin Umma ta fito daga dakin ta ina zaton daga,barci ta tashi, A,a Hamza kai da kan ka ke diban ruwan ne ina matar taka,ne kake diban ruwa da kan ka, Ummz ni nace ta,bari na diba da kaina don ina sauri ne zan fita, To, to, Allah ya kyauta don kana sauri ita kuma shine ta zauna kai mata aiki ko ? Daukan ruwan yayi zuwa banda daki yabarta a wajen tana jinini ita daya, Tsab nafito cikin shirina na,fita zuwa uguwa gaida iyayyena kwaliyar tai min kyau sosai don ni kainaxnasan yanzu na,fara faso gari, Kofan Umna muka nufa gaba dayan mu don muyi mata sallama akan zamu fita, Shi ya fara shiga ina,daga tsaye waje ina,rufe kofan dakina wanda duk masifan Umma banyarda in zan fita na barshi a bude ba, Muryan ta nake ji don dama nasan za,a rina don bata kaunar taga zamu fita a,tare dashi, Hamza duk zuwa kayi wai sai kun fita da Aisha a gidan nan ne don may wai baka da ta ido ne kai, Kana biyewa mace tana sakaka a hanyar shedana don ita tariga ta bushe nata fitilar kunyan bata jin nauyin fita da miji da rana tsaka haka ga, Umma bafa wani guri zamu tafi ba gidan iyayyen tane zata shiga gaidasu kawai, kuma dai kin san ya,kamata taje gaida su, Sallaman Zarah ne ya katse mata fitinar ta tana cewa umma sauri mu keyi nazo ne na,duba lafiyan ki, Ganin yayan ta taja tai turus tana cewa yaushe kashigo gatin nan banda labari ni, In badon na,dan biyo gudu gudu na da har ka koma,ban samun ganin ka, ko, Ya juyo yana kallon ta a,cikin murmushin jin dadin gani yar uwan shi, yake cewa Zarah may kike ci kika koma haka, ne wai, Tace kwanciyan hankali yayana banda matsalar komai a gidan daga mijin har matan shi muna zaman mu na lafiya, To may zai damay ni tunda banda wanda ya sakani a gaba, Sai a lokacin ta hangoni a tsaye ta kofan dakina ina a tsaye ina mai, kallon su a cikin sha,awa, A,a yanzu kina ciki shine kika kyaleni bayan kinji shigowa na , Nace wace ni na kyale ki anty nadai ga kuna magana da yaya ne, Fita zakuyi ne halan ta tambaya acikin kallon kwayan idanuwa na,. Shi ya bata amsa da cewa zata shiga gidan su ne yau ta gaidasu, Zarah tace Allah sarki kasan ita Aisha halinta irin na mutane da ne, Idan da nice ke kusa hakan nan, ai wallahi da kullun sai na,shigo gidan nan, To bake bace inji Umma daga inda take a tsaye take fadawa zarah din haka a cikin fada, Sai lokacin ya,dan dago kai yana duban gurin da nake a tsaye yake cewa to ya muje ko ? Na tako a han zuwa gurin da Umma take a tsaye nace cikin sanyin murya Umma zamu tafi sai mun dawo, Ke nan yau baza a girka muna abinci ba ke nan don ban san dawowar ki gidan nan ba, Zarah tace Umma ita da zata gida dubiya gasu Ma,u nan bazasu girka ba, su, ? Allah kai lafiya don wanan bazata bari na kai ga zance na ba take cabewa, Yana gaba ina bin sa a baya cikin dan takona a nutse, Inda Umma ta raka mu da harara har muka kure ma ganin ta, Take cewa wanan badon ina tsaye ba da yanzu ta dade da mayar da yaron nan susu, a gidan nan, Zarah take cewa Umma ita Aishan har tasan mayar da,wani miji susu yarinyar da wayau ma bai gama isarta ba, Kike gani ko wanan wanan mai suffan muna,fukai din barta nan kawai inda kike ganin ta, don ina maganin ta ne a gidan nan aida kin ga yadda zata mayar da dan uwan ki, To ni bazan yarda ba ace ina kallo wata ta zo ta mayar min da da solobiyo, agidan na , Amma gaskiya Umma kinawa Aisha kallon na,rashin fahinta don dai gaskiya yarinyar nan tana iya kokarin ta ga hakkuri , Ki duba fa Umma ko suturan kwarai fa bata dashi amma bata damu ba sai harkokin ta takeyi kawai, Haba Umma koma irin yadda akai auren nan ai ya kamata ace ta samu karbuwa a gurin ki da gurin mu muma, Amma sai gashi tayi don fitar da mu da kuma uban rikon ta daga kunya kuma,shine za,a mata irin wanan taron a gidan nan, Ikon Allah wai yaran nan may kuke nufi dani ne a gidan nan, Kuna nufin ban san abinda nakeyi ba ne ko ku zaku gwada min yadda zan zauna da ita nifa na haifi mijin ta, Yi hakkuri Umma kawai dai na ga cewa yarinyar babu ruwanta ne inda watace da yanzu anji ku a gidan nan wallahi, ****** ********** ****** Muna fita kofan gida na ga mashin a bakin shagon shi yake ce min najirashi yadan zo, Shagon ya shiga gurin ibrahim wanda na hango yana cin wani abu, Tun da na,shigo gidan su da,sunan aure ban taba shiga shagon nan yin wani abu ba, Hakan ma yau din ina tsaye dafa kofan gidan yazo dauke da leda a hannin shi, Yace oya mu tafi, ko? Ina zaune a bays muka bar uguwar mu, zuwa inda ya tsara zamu fara zuwa, A kofan gidan mamana Rahana muka tsaya da mashin din inda na sauka ya mika min ledan da ya dauko a,shagwan shi, Nice na fara shiga daga ciki inda ya,dan tsaya daga kofa yana,jiran abashi iso ya,shiga daga ciki, Na,samu Mama Rahana a kitchen tana kokari dora girki abincin rana, Daga inda take bayan ta karba sallama,na take cewa a,a a wa nake gani yau a gidan nan kamar Aisha, Murmushi nayi nake cewa cikin dan sone kai nice mama, Kodai yau kin bace hanyane Aisha ? Ni har na,debe tsan manin cewa i a,da,wata ya wai Aisha a,garin nan, Hamza ta hango daga kofan shigowan su tsaye tace kai amma yar nan baki cewa tare kike tafe da maigidan naki, Nai yar murmushi nace mama a tare muke ai, munzo mu gaida ke ne, Aiko na gode take fadi yayin da take dauraye hannun ta,da,ruwa mai tsabta, Kaishi daki mana kin barshi a,tsaye waje, Na fara shiga dakin da yake tana da kujera a,dakin ta ba kamar na Ummina da babu kujera sai siminti dakin hondakwai, Amma sai Hamza din yace bazai zauna a saman kujera ba yana kokarin zama a saman tsohon rough carpet din dake malale a dakin, Mama Rahana akwai tsabta don zan iya cewa da ita da Ummi kamar gadon tsabtan sukayi, don komai nasu tsab zaka ganshi Mama Rahana tana shigowa dakin ta samay shi a kasa tace Subbahanallahi haba tashi ka,hau saman kujerar mana Hamza ka zauna a kasa kuma, Yace cikin yar dukar da kai yana ayar kunya mama nan din ma yayi tace ke dauko mai tabarma ki shimfida mai kada ya bata kayan shi, Na dauko tabarman na,shimfida mai yadan daga kadan yahausama rabin jikin shi a kasa yake, Suka fara gaisawa da mama Rahana acikin girmamawa tana mai mai godiya tare da kara mai bashi hakkuri da azauna lafiya, Yakuma yi hakkuri dani ya rike ni amma kamar yadda yakeyi take cewa yarinyar nan abin tausayi ne hamza idan kai la,akari da yadda rayuwan ta ya taso, Ni abinda yasa kaga hankalina yake a kwance tunfarko wallahi don nasan cewa kai mutumin arzikini yato ne da halin dattako, Yace cikin kwantar da kai mama insha Allahu ba matsalar komai, ku daiyi muna,addu,a shi muke bukata, Addua ai muna maku Hamza sai dai mukara kawai, Yace mungode mama, nace bari wanan shigowan da nayi mu zo mu gaida ku kafin mu koma tace Allah sarki na,gode kwarai wallahi Allah ya,sa maku albarka, Bari na kira,abokiyar zamana ku gaisa ko kafin ku tafi yace zan dan barta na,shiga can cikin kasuwa kafin nadawo kin gaisa da ita,madallah na gode kaji, Sai ta dan mike tafita,da,sauri tana kiran mariya mariya kizo ku gaisa da,surukina, Hamza ya dubeni ya na cewa ki bata wanan ledan tayi hakkuri damu nace angode bai tanka min ba Mariyan ta shigo ashe cikine da,ita tsoho suka,gaisa itama sai godiya take zab ga mai da nasihan a zauna lafiya, Bayan tafiyan ta ya mike yana cewa zai je sai yadawo mukai mai adawo lafiya, Yana fita Umma ta dube ni tana cewa bari na zuba shimkafa nazo nace bari na zuba mama tace zauna abinki Aisha na hutar dake, Tafita taje kitchen din su bayan ta,dawo dakin ne nake mika mata tsaraban inda tafara fitarwa tana cewa kai amma ko angode clean ne da,sabulu da,man shafawa, guda biyu biyu a cikin ledan, Aisha wanda ke karatu kikasa yai muna wanan tsaraba haka mai yawa, Mama wallahi ni ban ma,san da,su basai da muka zo nan, Hira muke da mama acikin sakin jiki tana tambayana ina bata amsa cewa ba matsalar komai lafiya muke a gidan, Tace ita uwar mijin naki tabar mugun halin naya ne ko tana kai don kwanaki Fatima tana fada min abinda ke faruwa tsakanin ku, Tunda Ummi ta fada mata kuma mama Rahana itace yar uwa ta,shakiki da muke da ita a garin yasani fada mata gaskiya, Nace sai abinda ya karu ai amma ni ban damu da abinda takeyi ba tunda ba zaman ta nakeyi ba, Tace aini wanan matar tabani mamaki wallahi da farko kamar ta Allah ashe yar sheri ce bamu sani ba, Nace matsalarta guda shine kada tagan ni tare da,dan ta muna,raha, ko wani jin dadi yanzu zata canza min fuska, Ikon Allah ashe dai da,gaske shan fitsari da yana,saka kishi irin haka tsakanin ka da matar dan ,ka, Nace mama ita,fa Umma idan bai gari kusan lafiya kalau muke sai idan yazo ne matsala ke tasowa a tsakanin mu, Barta Allah ya,fita ke dai kiyi hakkuri kinji ki maida komai ba komai ba,sai a zauna lafiya, Nace a,sanyaye tau mama insha Allahu zan tsare, Nafi, awa biyu a gurin mama Rahana muna hira a tsakanin mu irin na da da mahaifi, Hamza ya dawo ya dauke ni mama Rahana tabashi yaji mai yawa tace yai tsaraban dashi idan zai koma school Har kasa,yakai gwiwa bibiyu yana mata,godiya inda ita ma take mai godiya a kan tsaraban da ya,kawo mata da kuma ziyara, A zatona,gidan mu zamu tafi sai naga munsha gwanan zuwa wani uguwa, Shagon wani tela mai dinki muka tsaya inda muka shiga telan yake cewa ba,sai ya aunani ba yaga size dina, Muka,juyo muna tafe yana,min hiran wani abokin shi da,muka fani a,shagon maidinki, Dadin wanan yanayin na,dinga ji sai nake ji kamar kada mu tsaya mu yi ta tafiya a cikin wanan yanayi Mun iso kofan gidan mu gabanin shabiyu da,rabi na rana yai min umurnin na, tsaya yazo ledoji guda biyu a cike suke ya,dauko muka shiga dasu ciki, Ni na fara sallama tare da danshigewa gaba mun samu baba yana gida a lokacin sai dai kamar yana,shirin fitane daganin yanayin shi Sosai baba ya,nuna jin dadin ganin mu tun kan mu karaso gurin shi yake muna sannun ku da zuwa, Muka,gaishe shi a ciki ladabi da girmawa tare da tambayan shi yaya,kazuwa don a lokacin babu aikin gona,, Baba yake cewa matar noma kune tafe da,ranan nan cikin dan murmushi nake cewa mune Baba, Banga mama Saude ba nake cewa,da,yar fara,ata ina mama take, maman Audi,? Tace ta kewaya ne nake gaishe su yayin da mama,din tafito daga,bayi tana ,cewa,Aisha kune tafe yanzu na amsa da eh mama , Muka gaisa da mama,din tana,min yaya,gida yaya makaranta Ummi tana daki tana shara, muka,shiga gurin ta na bar Hamza da baba suna magana a tsakar gida, Ummi tace kune tafe a she nace na aje lededojin da muka,shigo dasu daga gefe wanda Atika idanuwan ta,suke akai tana kwankwaton taga abinda ke a cikin su, Tabarma na,dauko na,shimfida mu na tare da cire hijjab dina na,dora,saman gadon Ummi, wanda ya,sha gyara da,wani farin zanin gado, tsoho ya,kode amna,da,aka shimfida yasha gyara sai yai kyau, Na zauna ina cewa wasshh duk nagaji kamar nai wani aiki Ummi ina,su yan biyu ? Tace yanzu su kabi Bintu zuwa,sayen icce, nan bayan mu, Lokacin ne Hamza ya,shigo dakin da Sallama a bakin shi Ummi ce ta karba mai, Suka fara gaisawa tana mashi yaya gida ya jama,a ya karatu da sauran su , Ummi take cewa yanzu kuka fito ashe na amsa da cewa daga gidan mama Rahana muke tace ikon Allah, Yau har can kuke tafi kai amma ko naji dafin jin haka wallahi kun kyauta kwarai da gaske, Baba ya dan daga labulr yana cewa matar noma ya ita Umman taku take tana lafiya ko, Na ce lafiya take baba tana,gaida ku , Baba yake cewa tau ni zan fita indan kun koma ku gayar min da yayan taku, Hamza yace a nan ai zata wuni sai yamma zata koma idan Allah yakai mu, Hannu Hamza ya,saka ga aljihu ya,ciro kudi wanda,ni ban san ko nawa bane yana mikowa baba yana cewa ayi hakkuri da wanan ba su da yawa sosai, Abinda ya,dan sa Baba shigowa daga cikin dakin ke nan yana cewa, a,a kai ai ba zancen hakkuri a nan Wanan dawai niya haka Hamza nagode nagode irin kyautan da,aje kiran kyautan yan aljannna ke nan, Lokacin da baka da shi gaba baka dashi baya,sai Allah yai maka budi ta hanyar alheri, Wallahi yau kwana,biyu mudina nake a gidan nan Yanzu sai gashi Allah ya kawo min alheri ta dalilin ka nagode nagode, Aisha kiyi min godiya,a,gurin mijikin kin ji na gode, Murmushi nayi ban iya amsawa ba naiwa baba a,dawo lafiya yafita muna jin shi waje yana nunawa su mama alherin da,akai mai, Godiya Ummi take yi mai yace kai haba Ummi a dai muna addu,a shi muke bukata kawai, Yace min kasakasa da murya wanan ledan kibawa Ummi dayan kuma idan sun dauka su raba a tsakanin su, Ummi na mikewa,ledan nai mata bayani kamar yadda yai min bayani, Ummi tace Hamza kai da ke karatu kai muna,wanan tsarab haka mun gode kwarau da,gaske Allah yasa albarka a rayuwan ku muka,amsa da Ameen , Kadai yi ta,hakkuri da kaunar taka hamzs kasan wayon sai a hankali don Allah kakara hakkuri , Yai muna,sallama ya fita muna ji yana wasu mama Saudde sai anjimsa, Sai lokacin muka, jawo leden muna budewa kayane irin n 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ARRAHAMANIN RAHIM,,, Dinkuna masu kyau a ka dinko min irin na zamani wanda mata ke yayi alokacin daga buje da riga sai wrafer, Kala biyar ne atamfa sai shedda cikon na shidda, takalma gyale da mayafin su da hijjab guda biyu, Maimakon nayi godiya sai hawaye suka dinga silalowa daga idanuwa a hankali, Hamza wanda yake tsaye yana kallona sai faman murmushi yake a fuskan shi, ganin yadda yarinta da kurciya ke aiki a kaina, Ji nayi ya dan rugumoni daga bayana yana cewa haba matar Hamza godiyan ne haka ? Ko kayanne basu yi maki yadda kike so ba ya sakaki kuka,? Da sauri na daga fuskana da,sukr taf da hawaye ina cewa cikin girgiza kai , Ba haka bane ina kuka ne ksn bansan irin kalamin da zanyi maka godiya da su ba, Yaya Hamza wanan kayan masu yawa da kyau da tsada duk ni Aisha ce da su ? Aisha yar agwai ? Rugumani yayi cikin jikin shi yana dan bubuga min baya a hankali alamar ana lalashi yaro, Yace nai maki su ne ki samu na shagalin buki ki samu suturan shiga cikin sa,an ki, Aisha ba yau ba ina da gurin maki sutura idan kinyi la,akari da cewa ban maki laife ba a,baya, Amma kuma sai ban samu goyon baya ba,a,gurin Umma, Wanan din ma Mansur ne yabani shawara na,saya tun a,sokoto batare da kowa ya sani ba, Don haka ki share hawayen ki hakkin ki ne bana,wata ba banga abin kuka aciki ba, Kara shigewa jikin shi nayi ina dan sheshekan kuka a hankali da kyat na iya furta Yaya Hamza na gode Allah ya kara rufa asiri, Jin muryan Umma ta shigo gidan yasani sauri watsakewa na dan goge fuskana don kada ta gane cewa nai kuka, Idanuwan Umma,a kofan dakin mu yadire inda tai ido biyu da takalman danta a kofan dak8n wanda haka ya sanar mata da dan nata yana gida a lokacin, A,a kuna daga cikine Hamza ne ya amsa mata da cewa eh Umma sannu da zuwa, Abinda yasashi mikewa ke nan yayowaje adaidai lokacin da Umma take kokarin zama saman dan kujeran da ke a kofan ta wanda ta aje don zama, Aisha na,amsa da na,am Umma nagyara gurin da na,boye kayana don kada kowa ya gani, sai ranan da zan sa a jikina, Na fito daga dakin ina cewa sannu da zuwa Umma ta karba min da yauwa, yar nan, Zo ga dan zogala na sayo ki gyara min ina fatan kin gama abinci na amsa da eh Umma, Umma ya cire dan kwanli dake kanta tana dan fitaran jikin ta dashi tana fadin yau ana rana a garin nan, Hamza ya amsa da cewa wallahi Umma lokacine ya fara na damana, Gashi bana ina son na kara fadin gonana sosai fiye dana bara,saboda nadan kara samo ilimin akan aikin gona, Umma tace aini nafison kafara yin noma a,gonar ku ta hanyar Kalgo, Umma wanan gonan yai min girma kuma a halin yanzu yai min nisa sosai don haka kinga sai nan zuwa mu dan kara girma idan da rayuwa, takai mu, Nifa hankalina bai kwanta ba ga azzaluman yan uwan mahaifinku, Haba Umma inji Hanza wanda har ga ranshi baijin dadi idan Umma din tana zagin dangin mahaifin su, Cikin dan bacin rai Umma ke fadin nifa inba don ku ba da tuni na koma gida don wanan zaman danake nabar mahaifana da yan uwana ina zaune nan cikin bare, Hamza yace haba Umma yaya zamu kwashi jiki har mu Bakwai mu kai masu lalura su ma,suna fama da kan su, Mai karatu na fada maku cewa Umma yar bauchi ne amma ba bauchi state ba, Wani gari ne da akecewa bauchi har sarautar garin sunan shi sarkin bauchi, Garin yana acikin jahar Niger state, gab da garin Zuru na kebbi state, Garine wanda ya tara alumma kaman Dakkarawa, Dukkawa, Hwakkawa, kabarawa, Aiki nake amma hankalina ya na,akan hiran da sukeyi a lokacin, Na kawo mata ganyen da,na,gyara mata a,gaban ta tace kin saka komai aciki ko nace eh Umma, Najuya na,dauko mata abincin ranan ta wanda tuwone mukayi, shima na girke mata tare da debo mata ruwa, Sai da Umma ta gutsuri towo tare da ganyen ta takai ga bakin ta take cewa, Wai kuwa kana da labarin Baba n ka Madu yana fama da ciwon kafa sosai, Subbahanallahi inji Hamza yace tun yaushe hakan yafaru Umma, Takara kai abincin ga baki tace an kwana biyu fa amma ai ina ganin yaji sauki yanzu tunda ban kara jin komai ba akai, Hamza baiji dadi ba sam a rayuwan shi saboda ya fahinci mama din bata je duba dan uwan mahaifin nasu ba ke nan, Aiki nake amma ban yarda cewa na nuna ina sauren su ba ****** ********** ****** Da yanma Hamza yafita ya,shiga gari ya sayo guro kursa kursa cike a leda, don yasan cewa Baba Madu maciyi goro ne sosai, Ya,samayni ina kwasan abincin dare yake ce min idan kin yi sallah zamu gidan su Baba mu duba jikin nashi, Yadda yace hakan akayi don ina gamawa na shiga wanka tare da daura alwala nai sallah, Najira,akai sallah i,shai, alokacin nashirya a cikin suwa,wax dina mai ruwan yello da green din flowers, Sai ko gashi ya shigo dakin yake ce min idan kin shirya sai mu tafi kada,dare yai muna, Mun futo muna sallaman Umma aiko sai ta fara sababi inda take shiga ba nan take fita ba tana fadin, Na fahinci kacanza rayuwanka kana,son ka,gwada min cewa yanzu ka fi karfina hakan yasa kake kokarin koya wa matar ka tai min rashin tarbiya itama, Amma in bashi ba yaya za,ace tunda kazo garin nan baku da aiki sai fita,kaikenan goya mace a mashin kuna yawo a cikin gari, Ya fahinci manufan Umma so take ta hanashi zuwa sada zumuncin da yai niyya gurin yan uwan mahaifan shi, Don haka cikin girmamawa yake cewa Umma Baba Madu, zamu je dubawa ba dadewa zamuyi ba, Kuma ai kinga itama ya kamata ace na nuna mata yan uwana don tasan su, Wasu yan uwa yan uwan da suka watsar daku lokacin da kuke bukatan kulawan su gare ku, Umma duk abinda,sukai muna sune dai yan uwan mu duk wani da nagari da yan uwan shi yake kadagi, Sai mun dawo, Bata amsa mai ba yasa kai yafara tafiya yana ce min mu tafi ko, Nabi bayan shi simi simi cikin karfin hali nace mata sai mun dawo Umma, A kofan gidan su na gado muka,samu Baba Madu kwance a saman wani tabar roba tsoho da gani a,kwai talauci a tare dashi, Farin gashi ya, rufe mai gemun shi ga,wani tsohon filo a bayan shi,inda yake dan jingina bayan shi, Kafar shi dake ciwo yana a mike tadan hau sosai alamar tana mai ciwo, Inda ya,dan motsa kafar a cikin dan cije bakin shi yana cewa Hamza kune tafe yace eh Baba mune a tafe, Mun dan zauna daga gefen tabarshi kadan muka,fara gaishe shi da jiki yana karbawa da kyat, Baba tun yaushe kafan ke ma ciwo hakane ? Hamza yakewa dan uwan mahaifin nashi wanan tambayan acikin nuna yar damuwa, Dattijon yadan kara cizon baki yace ya kwana,biyu ai sannu sannu ya fara min wanan ciwon har yakai haka, To Baba bakaje asibiti bane a,dubaka? Yai murmushin karfin hali yake cewa, ai sau daya na tafi suka ruboto min magani nasha dana shafawa, Har na,fara,sha shi na,shafawan ne ya gagareni saye har yanzu, Hamza ya dan matsa gap da kafar yana dan dudubawa yana cewa sannu Baba, Nima daga bayan shi inda nake a zaune nake cewa cikin yar muryana sannu Baba, Baba ya juyo yana cewa mai dakin nakane nan ko ? Cikin dan jin kunya yace ita ce Baba , Ikon Allah ai ina ganin baku taba zuwa da ita gidanan ba , Uwar ku ta hana kuyi zumunci da mu Ibrahim ne ma da yakan danzo yanzu ma,sam ya dauke kafan shi, Cikin jin nauyi Hamza yace ba hakana bane Baba don ko yanzu itace ma ta fada min cewa baka jin dadi nazi na,dubaka, Sai naji Baban yace hmmm kawai batare da yai magana ba, Yace ita Zarah ai sun zo da maigidan ta har sau biyu suna dubani, Ledan goron ya,tura a,gaban Baba din yana cewa Baba ga,wanan a yi hakkuri ya dauka yana saka muna,albarka wanda naji dadin hakan, Hamza yace ya bashi takardan magani ya gani yace Hamza maganin yana da tsada dan har gurin dubu ukku akace, Ya,dafa filon shi ya dauko takardan maganin wanda don dadewa ya,tsufa har ya murmurde, MOVE yaga an rubuta muryan babane kecewa ance kala,biyu ne akwai na india yafi kyau da amfani shine dubu uku din, Ya saka takarda a cikin aljihun,shi ya cr zamu shiga mu gaisa da sauran mutanen gida, Sai ga Baban guda tun daga nesa yake kallon mu yana,son ya gane ko su waye, Sai da ya karaso gab damune ya gane Hamza din inda,shima yake gaidashi da cewa sannu Baba, Kai dan gidan Rabi kaine yau an tuna damune aka shigo ko kuma,wani abin ne ya kawo ku, Baba Madu dake zaune yace hmmm yaran nan maye laifinsu su, Mun gaisa dashi ya amsa muna tsatsaye zai shige gida Hamza yace mai baba ga,wanan ba yawa ya dan mike a cikin ladabi yana mika mai takardan dari biyar, Sai a lokacin ya dan tsaya yana cewa duk ni daya ke da wanan din yace eh baba kayi hakkuri, Mun mike zuwa cikin gida lungu lungun gidan munshiga mun gaidasu yabasu dubu daya yace su raba, Muka juyo zuwa gida sai da muka,dan yi nisa nace ashe gidan yana da yawa ne, Ai mu yan yawane Aisha muna da yan uwa da yawa amma bamu zumunta dasu, Nace yaya kakuwa,san irin azaban da aka tanadarwa wanda bai kula da hakkin zumunci ranan gobe kiyama, Yace ai ba,sai gobe kiyama,ba Aisha tun a,nan duniya mutun zasan ya yi kuskure, Don idan abinka ya tashi babu yan uwanka a kusa zaka san kai ba kowa bane, Ban san haka ba,sai a lokacin auren mu don babu yan uwa na,da,suka halarci komai na,sha,anina,saboda suna jin haushin mu tun akan auren Zarah, Shi baba,Madu ne ma na,samu yazo daurin auren namu, Har gobe wanan abin yana ci min rai har gobe a,rayuwana,wallahi, Wanan abin da Ummi taje gani ina yi batasan cewa ina kokarin yiwa yan uwana gata,bane, Don mu samu su sauko kafin bukin auren su Asmau ya tashi su juya muna baya, Allah ya huci zuciyar ku gaba daya na furta a fili tare da,ajiyan zuciya, Ya amsa min da Amin ya Allah, Maimakon mu koma gida sai gidan su Anty Hindatu muka nufa, Munyi hira sosai take ce mi ranan saka lalai zata aiko azo a dauke ni zuwa gurin event din da za,ayi na,saka lalai, Koda muka,dawo gida mun samu Umma ta,shige don haka muma muka,shiga namu dakin,. Duk da nai wanka da zamu fita amma sai da na,dan kara kwara ruwa don naji dadin kwanci da mijina, Shima ruwan ya watsa nasan Umma batai barci ba tana jin mu kyale mu kawai tayi don ran ta ya baci, Yana tsaye a kofa bayan ya,rufe muna kofan dakin ne sai naga yaja ya tsaya,daga kofan daki kamar mai tunane, Mikewa nayi zuwa inda yake a tsaye na,saka hannayenata cikin kunkumin shi kadan, A hankali na kai kaina,a,saman kirjin shi na kwantar da kaina a hankali, abinda yasa shi sauke ajiyan zuciya ke nan, hankali, Nadan dago kaina na kalli fuskan shi sai naga tarin damuwa,a,tare dashi, Cikin baci rai naji ya,dan furza iska yana cewa, Aisha yau ganin yan uwan mahaifina yasa na tuna da mahaifina , A lokacin da mahaifina yake da rai duk jumma,a idan an sauko a babban gidan mu muke zarcewa har sai bayan sallah la,asar zamu dawo gida, Wai kin san may na tuna ne yau wanda ya tsaya min a rai, Nadan girgiza kai nace a,a yace zakiga mutane yan uguwa suna kai da komo zuwa gaida baban mu mai taro mai sisi haka zai tabawa mutane shiya,abinda Allah ya horewa mutum, Amma ki duba yau babu ko kaza a gaban gidan mu balle dan mutum, Allah ka hore mu na Aisha, Na amsa da cewa Ameen yayana, Humaira muje mu kwanta a gajiye nake yau kin san na,shiga gona yau da,safe, Na,dan kalle shi na,sakar mashi lalausar mumushi don in kara,samun damar shige mashi kamar yadda naga anayi a,gidan ma,aurata, Saboda nayi niyar kwatar zuciyar mijina na rike a hannu na duk abinda Umma zatai min bazai girgiza mu ba, Ni yanzu nasihan da Ummi da mama Rahana sukai min ya kara ratsa min zuciyata, Na fahinci Umma dantane bata son taga yana nuna min hakkin na da ya rataya a wuyan shi, ko kadan, Din ita burin ta,shine tagan mu a cikin rashin so da kauna shine zaman lafiyan mu don na fahinci kamar yadda take so shine ko kwana dani zaiyi sai ya nemi izini daga gare ta, Gashi yau Anty hindatu takara min dan hasken rayuwa a fakaice, Nace yayana kada ka damu wata rana sai labari insha Allahu, Ya jani muka,fada saman gado a cikin wani irin yanayi, A take jikin mu ya,dauki wani irin bari inda na,samu damar aiwatar mai da,sabon plan din da na,shirya mai a,daren yau din, Mun dauki lokaci mai tsawo acikin wani yanayi da ni kaina bazan iya cewa ga irin shi ba, Lokaci mai tsawo muka dauka,a,tare bamu san inda muke ba, ****** ********* ****** Washegari na tashi duk jikina yai min tsami amma sai Hamza yake ce min na kwata nai barci na zai sayo muna abin karyawa, Haka yasa wani barci ya,daukeni ban sani ba bani na tashi farkawa ba,sai musalin karfe goma da,wani abu abinda ban ta kawar hakan ina barci ba a gidan, Hayaniyar su Umma yasani saurin bude idanuwa na ita,da yaranta ne suke aikin gida inda nai saurin saukowa daga saman dan gadon katakona mai cin mutum biyu, Na,saka hijjab dina don na kewaya sai naji Asamau na cewa kin tashi Aisha yaya jikin naki,? Da,sauki na bata amsa, Nai saurin fahintar cewa shi yafada masu cewa ban jin dadin jikina , Ina,fitowa daga bayi Umma,na,waje ta tsure autar ta, sai tai wanke wanke, Ita ko sai shagwaba take tana cewa wallahi Umma,sunyi min yawa ni daya,duk zan wanke wanan, Ina fitowa Umma tace a,a,Aisha kan ya lafa ko ashe jiya kin kwana a,wahalce ne kai na ciwo, da mara, Nace a,sanyaye eh Umma amma naji sauki ya lafa min, ai, Ranan a,daki nake abina a kwance nan na,wuni ina,jin yadda Umma ke ta faman sababi da yaranta,sun kada,aikin gida wanda ni kullun nakeyin sa ni kadai, Shi ko dan gogan nawa sai zuwa yake yana,dawowa wai yana dubiyana ya samu daman sayo min yan kayan dadi nasha naci, Nake tambayan shi ko ya samu sayawa Baba Madu maganin yace min ya,samu amma,da kyat sai da ya aika BK aka,sayo mai, Ya ce kin san may Humaira wallahi naji dadinbda Allah ya,bani ikon saya,wa tsohon nan maganin nan bakiji irin albarkan da yau yake saka min ba ne, ****** ********* ****** Alhaji Nura ya shigo dakin da waya a kunnen shi, yana magana a cikin dan fada fada yake magana, Kubura wace take zaune a saman kujera da liitafi a hannun ta ta,dan gyara zaman ta,da kyau don ganin yau ya,shigo dakin ta da rana, Don tasan cewa bai shigowa gurin ta sai da,dare idan yana cikin bukatuwa, Ya kare zancen shi da cewa kaima kasan halina bana,shigowa idan ba wani babban deal bane aka samu, Bata,san may na cikin wayan ya fadi ba,sai dai taji muryan shi yana cewa bana tare da ku idan kun matsa sai anyi wanan gasan da wanan mutumin, Yace look ka fahince ni sosai mana donni bani buga game da kananan yara, Yana gama wayan ne yadan juyo gareta ya na fuskantar ta, Ina kwana tace a cikin sanyin murya tare da dan musgudawa, Lafiya yace cikin dan tsayawa a gaban ta kere tare da dan tsura mata idanuwan shi, Zancen bukin da nai makine nake son na kara tuna maki don jibine za,a fara ina fatan kin ksi dinkunan naki, Kubura ta dukar da kanta bata tanka mai ba,shi kuma bai wuce ba, Yace cikinbson jin amsan ta bakiji bane wai,? Tace ba ka fada min tun ranan ba kuma nasan da date din, Yace OK Jamila zata baki kudin da zaku yi amfani dashi gurin sayen sauran abubuwa, Cikin karfin hali Kubura tace abarshi zanyi amfani da,abinda ke a gareni, Indai har a hannun ta zan karbi kudin da zanyi amfani dasu, Ya kafe ta da idanuwan shi cikin mamakin yadda tai karfin halin bashi wanan amsan, Kina nufin bata isa ta baki abu ki karba ba daga hannun ta, Kubura tace ta isa mana bagashi ka bata ba ta bani, Shine zakice bazaki karba ba ya tura hannu ga,aljihun shi yaciro wasu kudin ya mika mata yace ki karbi wanan ki kara ga,wanda zata baki din, Ta mika hannu tana murguda baki wayar shi tai kara bai samu bata amsa ba ya futa, Haka yasa Kubura yin tsuki tana cewa ji shi dan Allah idan ka ganshi a,waje sai kace wanda yafi karfin matar shi, a gida, Kazo kaga matar kaga gurguwa tana botso a baya kamar zata kife, Jin motsin jamila a falo yasata mikewa zuwa falon don karban kudin ta, Jamila tana jin motsin fitowar ta falon tace yauwa dama yanzu nake son na kiraki don na baki naki sakon, Kubura ta tako har gurin da Jamila take a zaune tana cewa, Yanzu ke baki jinkuyar hanani jin dadi da mijina ba kece wai wace tasan yadda ake juya miji da wani kafar ki shayaye, Am fada maki cewa ni zan yarda da wanan mulkin kamakaryan da kike son yi min a gidan mijina, Hmmm inji Jamila aiko da wanan shayayen kafan yagani har nafiki kadari a gidan nan ba, Don yadda kika shigo da gurin ki mayar da mu yan abi yarima asha kida ya,wuce gare ki, Idan zaki iya zama a haka damu sai ki zau na gurguwa da mijinta aka,samay ta har,da yara uku, Kinga da bai sona da bamu tara wa yan nan yaran dashi ba, Kubura taji wani mugun haushi takaici kishi ya turnuke ta taji kamar ta make Jamila din a,gurin, Ko may ta tuna kuma,sai tace miko min kudina mara mutunci mata zaki san ko ni wacece watarana, Jamila tamika mata kudin tafisga har da hadawa da hannun ta gurin kwace kudin ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣3⃣ MA,LIKK YUM,MIDDIN ZAINAB IDRIS MAKAWA Rana bata karya sai dai uwar diya tai kunya gashi Allah ya kawo mu ranan bukin Sisters din Anty Hindatu da za,ayi, cikin wanan satin, Yau da kaina na,samu Umma akan zancen zuwa wurin rufi da za,ayi a family house din su hindatun, Na,samu Umma a kofan dakin ta tana shan iska ga kayan da taci abinci daga gefen ta, Nakai durkushe ina cewa Umma sannu da hutawa tana dan hitara da wani faifai na,sakan kaba a hannun ta ta karba min, Nace cikin yar murya Umma dama nazo na fada maki cewa yau da yamma ne saka lalai kannen Anyty hindatu, Hindatu hindatu dai cikin kara kwantar da kai nace matar abokin Yaya da tazo kawo muna kati, Au wanan yarinyar yar arziki ko, Na ce eh Umma ita, Yanzu bukin har ya zo ashe akwana a tashi ba,wuya a gurin Allah, Gaskiya Umma na bata amsa,sai na kara cewa Umma anjima in sha Allahu, ina son na halarci gurin taron saka lalai, A fusace ta juyo gare ni cikin fushi take cewa , Eh lalai rainin ashe har ya kawo gareni yanzu fita a gidan nan ya koma ba lasisi , Duk lokacin da kikaga dama fitane gare ki, Amma ba laifin ki bane idan da tun farko naiwa tufkan hauni da ba a kai ga haka ba, Yarinyar mace matar aure ta mayar da fita wani abin ado, da ga mijinki ne wanda ya kawo muna wanan sauyin agida, Yau kinci arzikin yarinyar kirkin nan da,tazo har gidan nan da kanta tafada min da baki fita zuwa ko ina ba koda kuwa ace a gidan ku ne ake bukin, Kiyi hakkuri Umma nace cikin wata irin murya duk da nasan halinta ne masifa dama, Umma kiyi hakkuri nayi kuskure bazan kara ba insha Allahu, Ta wani juyo a yatsine take cewa ai angama kawai don wanan yarinyar da tazo ne ya sani bari a,fita gidan nan yau da babu inda zaki tafi kinji na fada maki Namike ina cewa nagode Umma duk da raina ya baci amma na hadiye komai, Da zan mike na kwashe kayan abincin da taci nakai gurin da nake tara kayan wanke wanke, Sai da azahar Hamza ya,shigo gidan don cin abinci saboda Umma ta hana su cin abinci a kofan gida wai basu koshi abokai ke cinye masu, Murmushi yayi yace ai hindatu din ce maganin Umma don kin san ita ai sai wanda ke mata amshi takewa ragowa, ****** ********** ****** Na kammala duk aiyukana tsab daga yin sallah la,asar na fara shiryawa, Daya daga cikin kayan da Hamza ya dinka min nasa a jikina, Ni kai na dana tsaya gaban mirror sai da naji tsoron kaina don ban taba sanin cewa nakai mace haka ba, Na,daura dankwali na tsab yadda yan matan zamani suke daurawa, zakace budurwa ce yar matashiya, daga Abuja ko kaduna Na dauko kayan kwaliyan da ya sayo min na kara gyara fuskana tsone, Na feshe gyalena da turaren da yazo min dashi kamshi ya fara tashi, Ya shigo dakin don gani ko na shirya ya,samu mashin ya kaini gidan iyayyen hindu din, Murmushi ne ya subbuce mai yace Humaira ce ko idanuwa na ne ? Cikin jin yar kunya nace a shagwabe ita din daice, ba mafarki bane, Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai da ya halicci wanan baiwa tashi, Nai yar murmushi a cikin yanayin jin kuya nace mashi ai saboda kai Allah yai wanan halittan, Masha Allah ya kara furtawa, haka nake son ganin mace akoda yaushe Humaira, Allah ya,samin son mace yar gayu mai tsabta da iya kwaliya, Allah ya hore min kisha sutura a gidan nan Humaira ki tayi min kwalliya ina kallo a raina ina jin dadi, Ya karasa takowa gurin da nake ya dan rugumoni zuwa jikin shi tare da manna goshi na da nashi, Kunya naji inda na,sauke idanuwa a kasa da sauri, kamar mai rada ya fada min a kunnuwa dacewa, Ashe da sauran aiki a gabana tunda,har yanzu ban cire wanan kunyan ba hakana, Yace yau da ina da babbn waya hoto zan maki don na nuwa yan makaranta mu masu cewa banda mata su,gane ki, Da sauri na dago idanuwa ina cewa kai baka kishin matar ka ke nan ko? Ai ba maza zan nunawa ba mata yan uwan ki zan nuwa ke suga basu fiki da komai ba, Dammm naji nace a raina kodai yaya yana hurda da matan makarantar su ne, Sallama mukaji daga kofan shigowa gida ana cewa, Sallamu alaikum kafin mu amsa Umma ce ta amsa ashe hindu ce da wasu mutum biyu, Ta,sha wani irin uban kwaliya kamar itace mai auren , Ta karaso shigowa sai naji ta nufi gurin Umma tana cewa Umma mun samay ku lafiya, Tana mikawa Umma wani leda da ke cike da abinda zasu raba a,gurin saka lalai din, Take cewa Umma wanan abin nace bari na debo maki naku kafin ayi yawa ya kare kayan rabone na gurin saka lalai din, Umma tace ikon Allah harda mu dake gida yar nan muka samu tsaraban, Madallah madallah aiko na gode yar nan Allah yai maki albarka, Lokacin nafito daga daki tare da yaya Hamza muke masu sannu da zuwa, Idanuwan Umma ya sauka a kaina take naga annurin ta ya dan sake a lokaci guda, Ina gaida dasu hindatu take min sheri tana cewa wai wai kaunata (sister na) wanan kyau haka, Shiyasa ashe ogan ya kasa fita waje yau gaskiya Aisha ki godewa Allah wanan irin kyau haka, Kai anty abin kuma yar zolaya ce tsakani na dake tace wallahi babu zolaya, Zo muyi hoto harda Umma don mu dinga tuna,wanan ranan, Umma tace a,a ni a haka ba,shiri za ai hoto dani kuje dai can kuyi abinku, Da yake hindu irin matan nan ne masu halin ko in,kula ga,sauri sake jiki da mutane kamar ta dade da,sabo da su, Ta juyo tana cewa daya daga cikin yaran da ta,shigo dasu daukar mu photo da Umma Ta rungumo Umma akai muna photo tare ita da kanta take nuwa Umma photon, Ta juyo inda nake a tsaye tana cewa da fatan dai kin gama shirya wa,sai mu tafi ko ? A hankali nadan ce Eh tare da kada ks8na kamar wata marainiya, Munyiwa Umma da Hamza sai mun dawo inda shi hamza din yabi bayan muka fita tare, Muna fita naga motar da suka zo da ita a kofan gidan mu sai dai banga driver ba, Anty hindatu ce ta nufi gurin zaman driver ta,bude motar ta shiga, mazaunin driver ta zauna, Hakan yasani gane cewa ita ce ke driving din motar , Ban san may tace wa yan matan ba,sai naga sun shiga baya take ce min in shiga gidan gaba a,tare daita, Hamza yadan dafa motar ya leko ta gefena yana cewa ga amanan madam dina a kanki, Tace cikin murmushi Allah ya bani ikon rikewa kada kaji komai, Nima ai kaunata ce Aishan,,, Munbar uguwar mu mutane sai bina da kallo sukeyi cikin mamaki, Fili wanda yake dagirma amma,sai dai yau duk gitman shi makil yake da mata gungu gungu kala kala nau,i nau,i, Ganin motar hindu ya cin no kai gurin yasa yawancin jama,ar mayar da hankalisu gare mu, Tsayawar ta da motan yasa mutanen gurin suka kara sako muna idanuwan su gare mu, Inda muka fifito daga cikin motan yan uwan hindu suka,saka muna idanuwan su caaa a kan mu, suka nufota kowa da korafinshi gare ta, Daga cikin wanan taron kubura tana zaune tana kallon mutane daya bayan daya, Inda wanda bai san ta ba ake nunwa ga amaryan Nura, nan, Hindu ta riko hannuna tana ce min nazo mu gaisa da yan uwan ta nabi bayan ta zuwa gurin dangin ta, Yannin ta mata suna da kusan kama dasu mukai ta gaisawa da su, acikin mutunci, Jawo hannu tayi zuwa gurin group din wasu mata dake a zaune take cewa wanan matan yayyuna maza ne, Dayar ta juyo muna gaisawa da ita take cewa ina amaryan ki anty Jamila, Tanuna inda take zaune tana cewa gata can kin san amaryace tana jin kamshi har yanzu, Aka taba matar tana juyowa sai mukayi ido biyu da Kubura kallo daya tai min naga tai min kallon up and down, Nace lah Anty Kubura Kin san tane hindu ce ta tambaye ni nace ai gidan mu daya da ita, Kubura tai min wani kallo tana cewa yar Agwai ke ce,? Yar agwai kuma ? Nace a,dan muzance sunan da,suke kirana,dashi ke nan a,gida juyawa tayi tankar bata,sanni ba, Sai dai a cikin zuciyar ta wani irin shock ne taji tana cewa yaushe waban yarinyar idon ta ya bude haka ? Aishan da na,san su tsiya tsiya itace tai clean haka, kamar diyar wata, Ganin bata,son kullani yasa na zauna dan nisa kadan da inda take a zaune ina kalkon yadda event din yake gudana a,gurin, Kadan kadan Hindu taje tadawo gurina tana tambayana ba matsalar komai ko? Aka fitar da amare don saka su a lalai inda guri ya rude da guda da kuma raye raye kida kawai kake jin yana tashi, Yan matan amaren yan gayu ne sai shige da fice suke kowa tana gwada nata kalar fashion din, Hindu tazo taja min hannu wai na shiga fagen rawa nayi rawa nace bazan iya ba,saboda kunya irin namu na fulani, An fara,rabon sabeniyan bukin sai gurin ya kara rudewa, Wasu mata dake daga gefena,suke zance cewa waccan ce dama amaryar Jamila din, Dayar tace itace mana mara mutunci ko gidan ka,shiga bata taba gayar da mutum tana jiran a gaida ita, A lokacin ne naga matar mai dan fingisawa ta nufi Kubura da ledoji a hannun ta tana mika mata, Kamar bazata karba ba sai kuma naga ta karbi ledan a,dan yatsune tana,wani hura hanci, Ta,ratsa,taro a hankali tafita,daga filin wasan gaba,daya ni dai duk movement din ta ina kallo ta,wutsiyar idona, Anan nake dan jin hiran labarin zaman Kubura da Uwar gidan ta jamila dama ance labari yana gurin buki, Hindatu ta dauko ni muka,dawo gida,a cikin farin cikin irin shagalin da muka,gani, agurin sai dai wanan karon bata,samu shiga cikin gidan na mu ba, Nai sallama da ledeji a hannuna niki niki na,shigo inda na,samu Umma ta tayar da,sallah magriba na,bude dakina,na,shiga, Nafito don nima na,samu na gabatar da faralin dake a kaina, a lokacin, Bayan idar da,sallah ne na bude ledojin nadan cire abin da nafi bukata nakaiwa Umma,sauran ina fada mata abinda na samo ne a,gurin, Daidai lokacin ne yaranta suka shigo gidan yaran da Umma ke ji dasu kamar ta hade, Kayan suke ta faman cirewa daya bayan daya kowa na,fadin abinda yake so, Ina tsaye ina kallon abin mamaki don naga basu da niyar bar min komai daga cikin ledan, Umma ta,dago kai tana dariya tana cewa aikinga,wa yanda kika jewa,buki duk sun kwashe, Sai yar dariya take a cikin nuna jin dadin ta tana cewa yaran bazaku bar mata,wani dan abin ba ita ma ta taba, Haka na mike zuwa dakina batare da,sun raga,min komai ba , Raina ya,baci amma sai na na,shanye abin a raina basar kamar bai damay ni ba, Koda Hamza ya dawo ban yarda ya fahinci halin da nake ciki ba sai haba haba na ke dashi kamar ba komai a raina, Washe gari ina zaune ina gyara shimkafan da zan dafa muna a hankali nake ke tsincewa yayinda autar Umma ta,watso ledojin da,sukaci kayan buki a cikin sa a lokacin ne ya shigo yake cewa a,a auta may kika samune haka a leda , Yarinyar tace abin bukin da Aisha ta,samu jiyane mukaci, Umma tafito tana cewa ai yaran nan yan nemane abin bukin da ta,samu shi suka ciye gaba daya wai ai sune ta samowa, Take ya fahinci may ya faru daren jiyan don ya fahinci rashin hadin kai Da sauri Hamza ya dan saci kallon inda nake zaune fuskana ba yabo ba fallasa, Amma kuma a zahiri ba yabo ba fallasa daga fuska na don haka shima ya dake duk da babu dadiba,ran shi, Sai da na shiga daki yana saka tufafi a jikin shi jin motsina yasa shi yake ce min, batare da ya juyo ba, Nasan cewa,ana maki ba daidai ba,a gidan nan don haka ki kara hakkuri ga wanda kike yi a yanzu, Al,amarin Umma nima ina,rokon mata Allah ya,yaye mata wanan halin nata, A lokacin da nake karami akwai abubuwan da,suke faruwa a tsakanin ta da mahaifin mu da ma yan uwan shi amma ban fahinta ba sai yanzu nake fahintar wasu abubuwan, Cikin sakin Fuska nace Umma fa nima uwata ce don haka duk abin da take min tana da dakilin yin haka don haka kada ka,damu da wanan, Abinda na cire daga kedojin niya ne na dan dauko mashi amma,sai yace na barsu nayi amfani dasu kawai, ****** ********** ****** Kubura tun bayan komawan ta gida tunane duk ya damay ta tana matukar mamakin yadda ta ga,Aisha yau din, Aisha yar Agwai da ta,sani ce yau tai wani fresh da ita zaka ce ko wani gidan dadi take aure ga kwanciyan hakali a tare da ita karara, ta hango a danuwa na, Tsuki taja tana cewa kanta to damuwar may zan yi bayan nasan irin gidan da take a zaune ko kwatan irin rayuwan dadin da take ciki babu Kwanciyan hankali da soyayyar mijine bata da shi gaba daya, To amma wanan kaya da Aisha din ta saka a jikin ta ai sai take ganin sunfi karfita , Tajuya kwanciyar ta tana cewa kai akwai dai don gaskiya abin ya daure mata kai, Ita dai tasan cewa Hamza bai taba kama kafan mijin ta don haka sai dai aita karya amma ba aziki ba, Ta ja tsuki tace to wai ma ina ruwana da wata banza can wai yar agwai may zata zama balle don dan wanan shigar da tayi ya razana ta, Har barci ya dauke ta bata daina wanan tunanen ba a ranta, Da,safe ko da ta,tashi bata ji motsin kowa ba a,gidan don haka kawai ta, fito zuwa kitchen don ta,samu abinda zata gyara taci, Jamila tafito daga dakin ta a cikin dan dingisawa inda ta hango Kubura din, Cikin Murmushi tare da,sakin fuska take cewa aa, amarya yanzu nake cewa banji motsin ki ba ko duk ganiyan jiyane, Batare da ta juyo ta kalli Jamilar ba take cewa ai kin san ban taba buki ba dole wanan bukin yasani gajiya, Har may akayi a gurin da zai sani gajiya ko a,zaton ki naga wani abin birgewa ne, Tsaye Jamila din tayi sororo tana kallon ta a cikin mamaki don ita har ga Allah maganan girma da azikine tai mata, Amma sai take mayar mata da irin wanan magana cikin gatse, Cikin dakewa Jamilan ta tsaya yau ta fuskanci Kubura tana cewa wai je wata irin yarinya ce mara kunya da baki san zaman arziki ba, Au ai na ma manta cewa ke yar gidan Sarki ne ba,a gwada maki komai, Kubura ta juyo a hasale abin kaddara tana nufo Jamila din maigidan nasu yana shigowa gidan, Jikin shi a,saye da farar shadda mai maiko an mashi dinkin half gown na maza, Ke ke, may haka may zakiyi mata a hankaki tafara dan ja baya baya kadan da nufin komawa kitchen, Dakata yace mata inda taja guri guda ta tsaya daga inda take, tsaye, Yadan tako zuwa gare ta a hannkali annurin fuskan shi ta canza gaba daya, Sai da yazo gab da ita ya ja ya tsaya yana mata wani irin kallon cikin tsana, Yace ashe abin naki har ya,wuce yadda nake tsan mani a gidan nan, Look ban auro ki na kawo ki gidan nan ba don ban son matata, Kinga ta nan wallahi duk ranan da kikai gigin taba lafiyan jikin ta a gidannan sai ya kada hayen shi suka ba da sauti alamar gwali gwali ke nan (wuya) Yace kingata na idan kince bazaki zauna lafiya da ita ba a,gidan nan kina tare da tarin wahala, Don ban san cewa a haka kike ba koda yake ba abin mamaki bane idan nai la,akari da inda na,fara haduwa dake, Da sauri ta dago kai tana kallon shi don jin mai yace, Yace ina maki kashedi da ki raba kanki da,wahala ki bari ku zauna lafiya shine dan saukin ki a gidan nan, Idan kuwa kiki zaki yi mamaki na sosai a,rayuwan ko dan sai na muzan ta maki, Sam ban san cewa rayuwar rashin tarbiyan naki har yakai haka ba, To amma mu zuba ki gani idan kin ki, Iyalina ba abin wullakan tawa bane a gurinnki don ni banga wanan macen ba tukun, Ganin yadda yake warning din ta da kakausar murya yasa ta natsuwa,don tana ganin kamar zai kai mata bugu ne, Ya juya fuu ya,shige dakin shi bayare da ya tsaya duban wani ba a gurin, Kubura ta dago ksi ta kalli Jamila wace take zaune a lokacin itama din ita take kallo, Wani haushi ya kara kumay ta yau a kan gurguwa ake mata wanan wullakanci haka wani abukuwa,sai aure, ****** ********** ****** Duk sha anin bukin da ake ina zuwa yi wa hindu kara acukin shigana na tufafin da akaimin don shiga mutanen arzikine, Tun Umma tana kyalewa har sai da hakkurin ta ya kure inda ranan da za ai yinin buki na wankin amare shigana yasa Umma yin magana, Cikin fushi Umma ke cewa yanzu Hamza ashe har zaka iya hada baki da matar ka ku yaudare ni a gidan nan, Kamar Aisha ce zaka ce ka fifita akan mu har kai mata wanan irin tufafin don kawai fitan bukin da ba dangin iya bana baba, Hamza cikin dan marairaice murya yace Umma yarinyar nan fa ko laife ba a yi mata ba amma bata taba nuna bacin ran ta ba akai, Wanan kayan ma da kike magana a kan su kusan zance maki bani nai mata ba, Masur ne idan yaje yiwa matar shi sayaya,sai ya dauko da Aisha din, Rufa min baki ka, mara kunya ka mayar da kanka wani solobiyo sai abinda tace kake wa mutane a gida Tausayi shi ya kamani yadda Umma ta tsayar da shi tana mashi masifa a kai, Ranan saboda abunuwa sunyiwa Hindu yawa shi ya kaini gurin bukin da kan shi, Muna tafe kowa rai a bace sai jefi jefi nake sako dan hira don ya,wayance zancen a ran shi, Har Allah ya taimakeni yadan saje ranshi yana min hiran wani babban shago da muka gani a hanya mai suna B,L,K Yana,ajeni ya,juyawashi shi,@³ inda na shiga cikin gidan hankalina duk yana ga tunanen zan can Umma a gare ne, Haka na, shiga mutane duk da bawani sabawa nayi da mutane sosai ba amma haka akai ta,al,amari buki dani, Na lura,da yadsa naga Kubura tana bin abokiyar zaman ta duk da ba a cikin sake jiki take ba amma a tare zaka gan su sabanin ranan farko dana,fara ganin su, Zan iya cewa wanan ne karo na farko dana,fara,shiga mutane akai al,amarin harka buki dani har na,dan san wani abu tare da,samun experience din mata kala kala, An kamala bukin lafiya na,dawo gida a cikin tsarabab buki kala kala,wanda aka raba a gurin buki, Ban shiga gida ba,sai da na samu yaro na,aikawa Ummina da abokiyar zaman ta da,wani abu daga cikin abubuwan da aka bani , Kwanan Hamza biyu suka kwasa,suka koma school inda a,lokacin sun samu lecture yai nisa haka sukai ta kokarin covery din inda aka wuce su, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣4⃣ IYYAKA NA, ABBUD WA,IYYA,KA NAS,TA, INN,,, ZAINB IDRIS MAKAWA Yau gari wani irin zafi ake ga rana, yana kuda wanda hakan ne ya sa mutane shiga wani hali, Rana yana kudan kai da kafafunan mutane sai fama da zufa sukeyi, Cikin nan zafin ranan nake tafe sai kishin ruwa da yuwan dake damuna, Ruwa nake son na isa na dan watsa a jikina ko zan dan ji saida a raina, Gun a kofa kamar yadda na saba idan zan shigo gidan nake ta kwada sallama amma babu wanda ya amsa min sai yar hayaniya su nake ji daga ciki, Na isa har kofar Umma din na kara sallama ina cewa Umma sannu da gida, Dayar mata nace wa ina suni tace cikin yar fara,a lafiya, Ko sarakuwar tawace wanan ? Itace kin san wai karatun boko takeyi don ya mayar da kanshi bai san ciwon kanshi ba, Matar tace haba yaya ai zamani ne mu yanzu fa yaran garin mu har wani gari suke barin mazan su su tafi karatu kuma su dawo lafiya, Allah ya kyauta nikan ai naga abu macen aure ace kullun fita daga dakin ta wai wani karatu, Na juya zan wuce naji Umma na cewa ga kaunata nan tazo daga garin mu ganin mu, Na juya da sauri da dan murmushina ce a, mama sannu da zuwa, Ya mutanen gida,? Itama a cikin fara,a take ce min duk lafiyan su kalau,, Nazo ai ina tambayan ki ake ce min kin fita, bakyanan ashe karatu kike ,na amsa da cewa eh mama, Gurin da muke aje abincin mu na nufan na dan in dauki nawa naci, Muryan Umma ce take cewa, ai ba abincin don shine nabawa hafsi da tazo, Bakuwar tace ai akwai abincin don ban ci ba ma amma sai Umma take cewa a,a barshi kawai ki ci anjima, Fuska a sake na ce tau Umma na juya zuwa dakina, Sai dai a cikin zuciya ta wani iri nake ji ba dadi don haka ina shiga na debi ruwa zuwa bandaki dan na dan watsa naji dadi, Ina watsa ruwan a jikina naji wasu hawaye na biyo min fuska a hankali, ina dan watsa ruwan ina goge hawayen , a hankali tare da tausayin kaina a irin rayuwan da na tsinci kaina a ciki, Ibrahim ne ya,shigo gidan shima murnan ganin mama Hafsi yake cikin jin dadi da farin ciki Daga gurin da,Umna take a zaune take ce ma Ibrahim ga abincin shi ta miko mashi ne, Yace Umma a koshe nake wallahi don yanzu aka kawo wa sule abinci mukaci tare, Sai ta mayar da kwanon inda ta dauko da,farko ta aje tana juyowa, Mama hafsi tace ai sai aba wanan yarinyar da tadawo bata samu abincin ba taci ko, Wata yarinya ke nan Mama hafsi tace matar dan uwanka yanzu ta dawo bata samu abincin ba ance ya kare, Wani irin kallo ne na mamaki Ibrahim din yaiwa Umma yayi wani huci wanda gaba dayan su dakin sunji, Amma,sai Umma tace ai bata rasa abinda zataci a dakin ta, Haba Umma Aisha fa may zataci may ta,aje banda abincin gida wace bata wani sana,a, Kai rufe min bakin ka ban son maganan bazan don kai baka,da kunya kana nufin karya mukayi , Mikewa yayi yabar dakin ya fice gaba daya daga gidan, Mama hafsi ta kalli Umma tace haba yaya wanan abin baidace ba gare ki ace matar da ka kuma ba,a bata abinci taci ba A ina ake son ta samu taci tinda ba shi ke gare ta ba a,dakin, Shi ke hadani dake hafsi son kawo wa mutum Allah kamar kinfi kowa tsoron Allah, Ni wallahi nasan abinda nakeyi don bazan yarda ace nayi sakaci yarinya takawo min wasu akidoji na,daban a,gidan nan bayan na gama gina gidana da tubali irin wanda nake so, Mikewa mama hafsi tayi ta dauki kwanon abincin da Ibrahim yace bazai ci ba ta nufi dakina dashi, Sun hade da Ibrahim wanda ya shigo dauke da bakar leda a hannuwan shi, Lemon kwalbane da breadi acikin ledan sai kosai mai zafi da ya,hado dashi, Ya tsaya daga kofa yana cewa Aisha ga wanan ki dan ci ko, Abinda yasa Umma lekowa daga dakin ta ke nan, Mama Hafsi ce ta karbi ledan daga hannun shi ta karasa shiga dakin dashi, Ina zaunr inda na sallamay sallah anan nake zaunrena dan jingina kaina da gadona kafafuna na,suna a tokare a kasa, sai dan kada su nakeyi, Ganin Mama a dakin da,sallamata ga leda ga kwanon abincin a dayan hannun yasani saurin dagowa ina cewa mama ai da ki, kirani nazo na dauka da kaina, Tai murmushi tamiko min kwanon da nake mika hannu na karba, Tace wanan ledan ibrahima ne ya kawo maki yanzu shine nakarbo na shigo maki dashi, Nakarba nace mama nagode, Daga haka ta fita daga dakin ta koma dakin Umma, Na bude ledan don ganin abinda ke a ciki sai na ga a binda ya sayo min, mai yunwa taga abinci ba bata lokaci na,hauci hannu baka hannu ga leda, Sai da na koshi kat nai gyatsar lemon da nasha nan nai hamdala nagodewa Allah Ubangiji,na, Sai a lokacin na bude kwanon sai naga abincin yai min wani duhu yafita raina,duk dani na dafa shi, duk da,nice na dafa abincin amma sai naga abincin yai min duhu a fuskas, ****** ********** ****** Zan iya cewa zuwan Mama hafsi a gidan mu ya kawo min saukin rayuwa sosai, Don tana kama min aiyuka da dama nagida, duk da Umma ta hana mama hafsi yin aiyuka,amma sai mama hafsi tace mata ai ita idan batai aiki ba jikinta ciwo yake mata, Dole Umna na kallo kusan aiyuka,mama hafsi ce mai yin su tun ranan da tazo washegari da safe zan tafi school taga ina,aiki take cewa ba zaki bokon bane yau, Nace zan tafi mama sai nagama aiki nakan tafi, ai tace haba Yaya ga yaran nan basu komai a gida aikamata yayi su taimaka mata har ta dawo da yamma sai ta dora inda suka tsaya, Umma tace cikin jin haushin zancen yar uwar ta ai ita ta daukawa kanta karatu don haka bazan takura wa yara ba akan nata bukatan, Ganin yadda tabata amsa yasa Umma hafsi sanin irin rayuwan kuncin da nake fuskan ta a gurin Umma,sarakuwata, don haka taja bakin ta tai shiru, Sai dai ita da kanta ta mike tana taimaka min da aiyuka masu dama daga sharan gida wanda takeyi da ta sallamay sallah, Sai kuma wanke wanke, wani lokaci idan nai rana zatace na tafi nabar mata girkin tai min zata karasa da kanta, Umma tun tana jin haushi har takawo ido ta,sa ma mama hafsi din suka zauna lafiya, don mama hafsi macece mai zumunci ita kanta Umma tana jin dadin zama da ita, Hakan ba karamin dadi yai min ba don zan iya cewa tun lokacin da nai aure wanan takin ne na samu kwanyan hankali da ragwamay aiyukan da ke a kaina a gidan, Haka yasa dan haske ya fara,dan dawo min nafara dan yin magurjin jiki, Karatuna yana tafiya a,daidai, don irin baiwar da Allah yai min ta hazaka, Shine sauki na da madogara na gurin rafe expensive din makaranta ba,sai anbi a gwada mi gata,ba da kudi da kwakwalwata nake karatuna, Kawar Umma kum aminiyar ta da basu wanka,su bushe suna tare a kowani lokaci, Watau mama, Sa,a da ta saba zuwa gidan mu wace duk zuwan ta bai zama min alheri a rayuwata, sai sheri,, Yau ma kamar kullun da yake weekend ne ina gida don ban faye shiga school Saturday ba, Naji muryan mama,Sa,a ta bayan na gaishe ta ta karba min a yatsune,ta,wani juya a hautsane tana cewa au kina gida ashe? Nai mata yaya yar ta bintu wace itace auta a,gurin ta, Rabi naga yarinyar nan tai min wani dan fari a idanuwa na har da dan jiki ta kara, nace kodai alheri ya samu ne a gidan, Da sauri Umma Rabi takai idanuwanta gareni tana cewa kin ga alama ne ke ? Mama Sa,a tace cikin wani dan washe baki Aisha Humaira mai babban suna yaki nan, Har nakai kofa najuyo fon kiran da tai min don ni ban fahinci komai a kan zancen su ba Tace cikin washe bakin da goro ya mayar mata da hakora ja Nace kodai kinyi batar wata ne ko don naga dan canji a gare ki, Nace canji mama sai na fara dan dube duben jikina, Tai wani dan shake murya tace nace ko baki ga al,adan ki bane a bin arziki ya samu watau k8n samu ciki, Idanuwan Umma tai saurin kakafe ni dasu don son jin may zan furta, Nai saurin girgiza kai nace mama banda komai fa ni ko sallah banayi ina fashin sallah ne yanzu haka, Kut, inji mama Sa,a tace cikin wani kawar dakai a razane, Umma Rabi tai wani yarfar da hannayen tace ai na sani dama wanan ai kiwon hayan masai ne, Daga taci sai takai masai ta zubar da shi can bata gaji arziki ba balle ta,aje shi, Haba yaya haba, haba, ina wanan zancen yafito daga bakin ki haka sai kace ba musulma ba, Kafira nake ko baki sani bane hafsi,? Nikan jin haka na juya simi simi zuwa dakina jiki ba karfi, don nasan yau kuma mama sa,a ta banbaro min wani sabon fitina a gidan nan, Don ni ban ma taba kawo zancen ciki a raina ba balle ya daga min hakali Tsakanin mama hafsi da Umma sai maganan ta,dan fara tsawo inda mama hafsi ta hada da mama sa,a tai masu tass, Tace ai shawaran alheri ya kamata ki bata akan zurian ta,ba wai kizo ki tayar mata da hankalin gidan ta ba, Ko ita yarinyar ai bataki ace ta,aje ba a yanzu balle, ki ce wai har yanzu, Idan laifine hakan aiki ga laifin dan mu shi da zai saka cikin a jikin ta ko,? Yanzu ina yake ina satina biyu a garin nan amma bai gari ko hakan bai isa kiga hakkuri wanan yarinyar ba karama da ita haka miji ya tafi ya barta sai lokacin da ta,gashi, Haba mutane ku dinga tuna mutuwa fa bafa anan zamu tabbata ba, Mama Sa,a tace nifa bawai da wani manufa nai wanan magana ba gani nayi jikinta ya dan sake min a idanuwana shine na furta hakan, Umma Rabi tace fita zancen Hafsi ita haka take da zaran mutun yai abu a,gaban ta yanzu zata kawo mai Allah da Annabi a gaban shi, Mama hafsi tafito daga dakin tana cewa kudai yiwa kanku fada wallahi don haka yana zubar wa babba da mutunci a idon yaro ne, Ina shiga dakina na nufi saman gadona na zauna a hankali nai tagumi hannu bibiyu ina sauraren su, Cike da takaici nake zaune ina tuna cewar da Umma tayi wai ni bata iri ce sai dai naci nakaiwa masai duk safe, Wasu yan hawaye naji sun silalo min a,raina nace wannan wace irin kaddaran uwar miji na,samu a,rayuwana da mijina lafiya muke amma ga,uwar miji na batun hanani shan ruwa naji sanyi a,raina, Astangafurallah na dinga ambatawa kamar yadda Ummi ta umurce ni dayi a,duk lokacin da naji ba,daidai ba raina, Mama Sa,a tace Rabi bari na tafi don wanan yae uwar taki ina zauna zatai ta ganin laifina ne a banza, Rabu da ita halintane ita idan tana kusa ba,kaiwa yaro fada yanzu zatace bakai daidai ba, Sallama kwarai mama Sa,a bata samu ba a gurin mama hafsi, Bayan tafiyan ta kwada min kira na amsa a cikin dasashen murya nafito take ce min naje na tuka tuwon da na,dora don taji ya fara kauri, ****** ********** ****** Tana zaune a dakin ta yau ta kwashi kwanaki bata saka maigidan nasu ba a idanuwan ta, duk dai tasan cewa yana dawowa gida, Don ta san shine babban dabiar shi rashin shigowa gida da wuri idan dare yayi Wanda haka ya soma damuwar ta a farko amma daga baya da ta fahinci halin shi ita ma Uwargidan haka take zaune dashi sai ta basad kawai, Barci ba wani kwashe ta ba taji motsin shigowan shi ya na,waya acikin daren nan, Gashi shi bai son mace ta,shiga mashi daki idan bashi ya bukaci mace tazo dakin ba, Dabi,ar shi shine ya,samu mace a,dakin ta yai abinda,zaiyi ya fito ya koma nashi dakin, Ya,shiga dakin shi yadan jima a ciki sai taji motsin shi shigowa dakin ta don yau itace da girki a gidan, Shiru tayi yayin da taji ya,shigo dakin dai da taji motsin shi yana kokarin taba tane ta mike zaune, Kallo ya bita dashi, don yasan haka ba halinta bane, sai dai ta barshi yai abinda zaiyi idan ya,shigo yafita, Itama wani kallo take mai ,mai nuna bakinta da magana a cikin sa, Tambayan tayayi da may ya faru kuma don ganin irin kallon da taks masa, Da farko shiru tayi sai da taji ya kara tambayan ta cikin dan tsawa sannan ta,dan bude baki da kyat tana cewa, Ni fa ban fahinci wanan irin zaman ba ace mace da mijin ta bata ganin shi sai dare daren ma sai ya raba fiye da tsakiya zakiga mutum yazo maki daya biya bukatun shi ya barka sai kuma,wani lokaci, Gaskiya nina fara gajiya da wanan irin rayuwan haka ba wani kulawa, A fusace yace wata irin kulawa kike bukatar na baki bayan wanan, May na ragaku dashi a gidan nan daga dangin abinci dasha da sutura, Kubura tace cikin turo baki shi kuma,rashin kulawa fa,? Mace ta zauna ba wani soyayya a tsakanin ta da na miji sai na irin haka , Namiji baya shigowa gida gurin iyalin shi sai tsakiyar dare, Yayi tsaki yace ohh tuhuma ta kike kenan ko may,? Ba kudi kike son samu ba dake da iyayyen ki to kin samu aiko, Wanan madin da kike gani idan bakya so ba,dole bane sai na kwanta dake don ni banda yunwan hakan ? Jikin ta babu kwari tadago kai ta kalle shi, tayi dan dumm sai kuma tace niko nasan da hakan don naga alama,sosai, Kalli fa yadda duk na koma na canza nai wani baki da rama kamar wata mara galihu a duniya,, Amma aikin san ni ba mai zama bane tun farko na fada maki kuma kika amince da hakan ko, Asalima kin san ni banzo maki da zancen aure ba kece kika matsamin ke da iyayyen ki don ni matata ta isheni rufin asiri basai na daukowa kaina wata fitina ba kuma, Kubura wace takaici ya rufe, a lokacin ta rasa may zatace don haushi, Sai kawai tajuya tabashi baya tare da sauke ajiyan zuciya gami da lumshe idanuwan ta, zuciyan ta na mata kuna, Yacd bari kiji daga yau kika kara cewa zaki min fada akan abinda kikasamu a gidan ina yi sunaki sorry, Kubura ta harzuku tana cewa muddin ina gidan nan naga abinda ba daidai ba agidan nan dole ne na yi magana akai, Ganin yadda Kubura ta butse mashi ta bude mai wuta yau din yasa shi shima bude mata sukayi ta musayan zance a tsakanin su, Yake cewa wai an fada maki cewa,saboda wani abu na kawo ki gidan nan ne tausayin mahaifinki yasa na har na amince da zancen auren ki, Amma shigowanki duk kina son ki tada min hankalin gidana, indan ma wa i neya ture ki akan na fada maki inda nake zuwa bazan fada ba, ki kuma kama kan ki, Kubura wace hawaye ya gama wanke ma fuska ta kalle shi ido jajir tace tunda da wani manufa ka ajeni a gidan ka sai ka salamay ni na futa kaima ka huta, Yaja tsuki tare da watsa mata harara yana cewa zaki san ko ni waye, ya fita fuuu, Itama ta rakashi da harara har ya shige wa ganin ta, ta juya ta kwanta gadon tana jan tsuki, duk ranta a bace, Dakin shi ya koma barci ya gagare shi sai tsuki yake yana juya gashi baida enough time din da zai wadace shi haka ya dan taba barci sama sama kafin safe, ****** ********** ****** Tun ranan da mama Sa,a tai man wanan maganan zamana da Umma Rabi ya canza,sallo a gidan, Don yanzu takai har su Asmau ko kadan babu wanda nake jin dadinsa sai hausa suke sake min a gidan da cewa sun matsu wallahi ace an haihu a gidan nan muma ai buki a gidan mu, Jibrin kuma ya kance min idan baki haihu ba Aisha sai na saka yayan mu yai aure ya kawo muna mai haihuwa, ta haihu na dauki dan ina yawo dashi a gari, Murmushi nakan yi nace aiko nima sai na goya shi naita yawo a gida dagari, Ji wayiya maimakon kiyi kishi ko kiyi zuciya ke ma ki haihu, shine zakice wai ki goya dan, Nai murmushi nace to ba dan yaya hamza bane may zai sa nayi kishi a kan dan, Kai amma ko kinban sha,awa Aisha daki ka fadi haka don kin san kan ki ashe, Mama hafsi ce ta fadi haka daga gurin da take zaune, ta gyara min shikafan da ta karba a hannu na, Bayan na wuce zuwa dakina jibrin ya zauna yana cin abinci yana cicika, yana batsewa, Shigowar Umma gidan ke nan daga gidan mama Sa,a ta sha zuga har ta gaji, Tana shigowa idanuwanta a kan dan ta wanda yake a batse cikin fushi, Tace a,a kai kuma may ye haka kana cin abinci kana batsewa,? Yace cikin dan guna guni wallahi Umma mama zata sa Aisha ta raina mutane, a gidan nan dakai magana yanzu mama zata gwale mutum a gaban ta, Daga inda mama hafsi take a zaune tace mara kunya ka fada mata ne ta bugeni ko kuwa, Ita Aisha a,sama ta fado ke nan ko da zaku zauna kuna mata cin fuska yadda ran ku ke so , Umma wace son yar uwar ta dakuma irin halin ta bai bari taga laifin ta yasa tai ajiyan zuciya Tace, kun dai san halin uwar ku don haka indai akan wanan yarinyar ne kama bakin ka kawai , Mama hafsi tace shi dai yafi kan don ni baza a zauna ana wa yar mutane wullakanci don kawai dan uwan ku ya auro ta, Kuba ga na ku yar uwar can tana aure ba ta haihu ne ? Wa ya saka maku ita a gaba? Sai kune da baku san Allah ba zaku saka yar mutane a gaba da zancen banza, Jibrin ya mike ya fice a gidan tare da barin kwanon da yaci abinci mama hafsi tace maza dawo dauke shi waye bawanka da zai dauke ma, Ina daga dakina naji su nai murmushi duk da bacin ran da nake a cikin sa, Umma tayi tsaye daga kofan ta duk da ranta ya baci tana cewa, Jibrin dauke kwanon nan maza , Mama hafsi bata ce komai ba don tai niyar a ranta cewa sai tayi maganin marasa kunyar yaran nan, Yan min tina kadan mama hafsi tace wai niko yaya ina su malam Mudu ne ko zancen su ban jiba dana zo, An,tabowa Umma inda ke mata kyakayi tace hafsi tun yaushe, Aini tunda yaran nan suka kawo girma na fita zancen su na tatara,su gaba daya na,watsar tunda ba, ban saura neman wani a gurin su ba, Dandama dama,shi babana hamza shine ma mai dan sauran zumutun dasu, Mama hafsi tace humm,ummm, amma ko yaya bakiwa yaran nan adalci ba a rayuwa, Ai ance kowa da dangisa yake takama a duniya koda ko a bola suke a zaune, Yanzu yaya ko dan yan matan nan har biyu da suke a gabanki ai zaki bisu, Idan auren su ya tashi yaya wane uban daurin auren nasu, dole fa sune, Ai kamata yayi ace yanzu tunda Allah ya raya maki diyan ki har sun kawo karfi da saiki, nuna masu cewa ke kinfi karfin su ta ko ina, ki dinga zumunta dasu Don kinga hakan da kikayi bakiyiwa marigayi adalci ba, Karki manta yadda yai ta rayuwan shi dasu suna kuntata mashi amma bausa ya daina alaka dasu ba, Shi baba abinda yasa kike ganin kamar yaki jin zancen ki yana hurda su saboda,shi namiji ne, Kai sai ma ince wallahi bai rage halin mahaifin shi ba ta ko ina,, Umma tace ashe kin fahinci haka hafsi tace kwarai kuwa yaya aiduk halin marigayi shiga baba don har ma ince yafi uban saukin kai, Watau hafsi idan na tunairin wullakancin da mutanen nan sukai muna sai naji kwata kwata sun kara fita,raina, Ta yaya yazakiyi tunda zuria ta hadaki dasu sai hakkuri don kan su sukaiwa, Yau bagashi Allah ya,raya maki yaran ba,da,dadi da,wuya dama ance maikarami shike da babba watarana, Allah dai ya,sa masu albarka a,rayuwan su ki more ma abinko tun anan duniya, Ameen hafsi Amin ya Allah, Alokacin nafito dakina hannu dauke da plate din da naci abinci zan kai gurin wanke wanke, Umma tabini da wani irin kallo wanda mutum ba zai iya fassara shi ba, Azuciyar Umma tace wanan yarinyar sai ci kawai agidan nan ba wani karuwa a gurin ta da Hamza wani mai hali sai kawai tace ya kara mata tagani, Muryan mama hafsine ke cewa Aisha ki aje kayan nan idan yaran nan sun dawo sa wanke su, Mama bari na,wanke kada kuda,su hausu da yawa,ai kayan basu da yawa, Tsabtan yarinyar na bata sha,awa sai take cewa a hankali wallahi yaya yarinyar nan babu ruwanta kiyi hakkuri da abarki, Ki godewa Alkah da yar zamani aka kawo maki a gidan nan da yanzu kun fara kai ruwa rana da ita saboda wanan tsangwaman dakike mata har yaran nan sun dauka, Umma taja tsaki tace ba itace ta tsangwami kanta ba yarinyar karama da shigen iyayi Kibari mijinta yazi gatin nan kiga yadda take wani shige mashi tana manne mashi kamar gare ta farau aure, Haba yaya kar ki manta fa zamanki da marigayi shine fa yaja maki tsana ga yan uwan shi har yanzu, Wai hafsi to ni may nake matane bakin halinta ne irin na uwar ta , Ta hana kanta kwanciyan hankali a gidan nan sai wani rama take mutane su gani suce nice umul,abaisin haka, Haba yaya yar nan ko ai duk yadda ake a gidan nan tanayi gwargwadon hali, don Allah ki sarara mata a rayuwa, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣6⃣ SI,RATTAL, LAZINA, AL,ANNTA ALAIHIM,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA Washegari ban fito da wuri ba don ina jin mama tana,aiyukan gida don kuma nasan ba yau ta,fara taimaka min da hakan ba, Don nasan cewa koda na fito zatace na barshi kawai na huta, amma dai sai na dan fito din cewa mama tayi koma ki huta abinki kinji Aisha, Yau dana yana gari yana bukatan ki kusa dashi ki barshi zanyi komai don saura ma kadan na kammala, Barci muka sake koma don dama kowan mu yana da gajiya a jikin sa, Umma da batasan cewa munyi haka da mama sai zaraya take tana duban kofan dakin mu, Don ganin har da Hamza wanda yake fita da wuri yau bai fito ba, A,a su wa yan nan yau lafiya basu fito ba har yanzu? Sai ta nufi kofan mu tana bugawa bugu daya biyu ga na ukku mama dake fitowa daga bayi take cewa, A,a yaya mau zasu yi maki kuma, Kallon yar uwar nata tayi cikin mamaki basu fito ba haka har rana ya hudo suna kwance, Ikon Allah inji mama haba yaya wanan abin naki fa k8na,shiga hakin yaron nan da yawa, Yaro ya dawo gari da gajiya ace bazai huta da matar shi ba ? Yanzu idan sun fito may zasuyi maki ina aiki ne duk na kammala komai da zata fito tayi, Yanzu don bata da kunya shine zata shige daki da miji tabarki kina aikin ke ? Nice nace ta koma daki don mijin ta na bukatar ta a kusa dashi, Watan su nawa basu tare yaya sai yanzu da yazo suna shaukin juna kuma za,a takura masu, Tafe Umma ta fara yi da hannun ta tana cewa lalai hafsi zaki bata yaran nan, May kuma za suyi da ranan nan tsakiya , komay mama ta fada mata sai kawai tai dariya ta juya tana cewa ke kan hafsi sai abarki don zaki sagarta dan nan naki idan anbiye maki, Muna daga daki duk abinda suke fadi a kunnuwar mu, na yunkura don natashi amma sai Hamza din ya mayar dani sai da ya gama abinda yakeyi sannan ya dan sarara min,, Mintina kadan muka fito daga dakin shi ya,fara fitowa don ya kewa ya,wanka, Su Umma suna a waje suna shan tea wanda mama hafsi ta hada da kayan yaji dan citta kadan sai kanumfari da ya tayar da kamshi sa, Fitowan shine Umma tabishi da idanuwa wani abu taji a zuciyar ta wanda ya,sata dan jin wani takaici a ran ta, can kasar zuciyar ta,, Kamar ina tsaye a kofa fitowan shi sai gani na futo a cikin hijjab dina hannu na,dauke da buta, Da kyat nake taka kafana don nauyi da kunyan da nake jin don dai sun san may nayi har zan kewaya, Nagyara jikina nafuto da,daya daga cikin kayan da ya dinka min nai bukin su Hindatu dashi, Nasaka kayan ya kara amsan jikina tsab ni kaina sai da naga sha,awan kaina, Tsab dani nafito sai kamshi nakeyi a lokacin Hamza ya gurin iyayyen sun gaisa yana hira da mama hafsi, Nafito ina tafiya a nutse a hankali nazo inda suke gurin da Umma take a zaune fuskan ta har zuwa wanan lokacin daure tamau, Nace Umma ina kwana cikin sanyin muryan nan nawa mai kama,da ta yanga, ko rowa, Na,samu Umma ta amsa min ciki ciki da kyat da fadan lafiya kalau, Na juya inda su mama,take da dan ta nace mama ina kwana, Aisha kin tashi lafiya ya gajiyan aiki a cikin fara,ar ta da sakin fuska, Inda yake a zaune yana kallon mu yai yar murmushi jin dadin yadda mamatake haba haba dani, A kunyace na amsa da lafiya mama, Zan mike tace maza dauki abin karin kumallon ku ga yacan a flask din can kikai maku daki ku karya ai ina na da,akwai breadi a gurin ku ko na amsa da eh mama, Inda flask din yake na nufa don na dauka sai Umma ke cewa rike min flask da kyau kar ki mayar dani baya tun flask din haihuwan autana nane nake maneji da abina, Sai na mayar da flask din nace bari na dauko cup na juye muna, Mama hafsi tace tafi dashi mana ki rike mata shi da kyau , Hamza yace bari ta juye mama zaifi ta dauki flask din ai, Ni dai ba zan yarda a fasa min abuba don maneji nakeyi dashi gaba dayan wurin shiru mukayi, Don haka sai nabi umurnin hamza na juya na koma na dauko cup na juye ruwan zafi aciki, Banji haushin Umma ba don nasan cewa a gidan mu banzo da wasu kayan amfani ba, ai irin na aiyukan mata, Kwaliya na taiwa Hamza kyau sosai sai bina yake da kallon sha,awa, Suna zaune shi da su Umma inda suke hira da mama hafsi Umma na daga gefe take cewa, Dama ina jiran zuwan kane, don naji shawaran da zaka bayar, Kaga an raba gadon mu gidan da aka bar muna an sayar abawa kowa kudin shi da yan sauran kaddarorin da aka bar muna, baki daya , Shine na hado kudin nazo dasu nan don mu san abinda za,ayi dasu, Banda kowa a duniya yanzu sai ku da yar nan guda da Allah ya bani ita kuma kaga shi Alhaji ba mahaifita bane ga mijinta dan kwaya ne ita kuma ba lafiyayya bace don haka ba dama na,sakar mai kudi su lalace a banza, Shiru sukayi baki dayan su mamata ce yanzu tun da Alkah ya,dawo da kai kaga sai ka ba da,shawaran yadda za,ayi da kudin nan, Zama Hamza ya dan gyara tare da,dan numfasawa yace, Mama kin san shi kudin gado wani abune mai nauyi da karfi, Don haka yanzu abinda za,a yi shine asamu gida ko fili a,saya maku dashi a je a matsayin kaddara wanda ake gani, Don ajiyan su a haka ba zaiyi ba don aje kudi masu yawa kasa dane babba, Mama Hafsi tace a,a Hamza ba zaa sayi gida ko fili ba dasu ni a nawa shawaran may zai hana ka,karbi kudin ka,fara dan juya su kana kasuwanci da su, har zuwa lokacin da zaka samu naka sai ka biya na dai idan kudin suna gurin ka ko ibrahim wallahi hankali na a kwance suke Hamza, Murmushi Hamza din ya,dan sake yace a,gaskiya mama nagode da karamcin da kika nuna min amma gaskiya na Allah bazan karbi ko kwandala daga kudin ki na juyawa ba, Don kin san yadda kudi na amana kuma na gado suke da saurin samu kaddara, don haka shawaran da na bayar shine kawai abin dubuwa da mafita, Amma gaskiya ban so ka musaya min shawarata ba Hamza na sanka tun kana karamin ka na san halin ku zaku iya rike wanan amana, kai da dan uwan ka, Hamza yace mama yanzu abinda za,a yi sai nayi shawara zan san abinda za,a yi da kudin don ci gaban su, Nan suka dauko zancen tsohon mijin nata wanda ya rasu tai mashi wanka da irin taimakon da yai masu a lokacin da suke da bukatan hakan, Har zuwa wani lokaci ya mike zuwa waje don ya gana da mutanen shi , A kofan gida ya hangi Baba Mudi ya karasa su ka gaisa yake tambayan shi cikin murnan yaushe garin yake bashi amsa da cewa jiya da yamma ya shigo, Ya tambaye shi karatun shi da kuma yadda ya samu mutanen gida, ****** ********** ****** Ina dakina zaune bayan na dora muna abincin rana sai nake jin sallaman daga kofa, muryan mamana Rahana nake ji, Nafito daga dakina a cikin murna da yar tsalena na tare ta nai mata sannu da zuwa na karbi abinda ta shigo dashi a cikin wani dan buhu, Sai take ce min ki rike da kyau don akwai abin fashewa a cikin sa, Gurin Umma taje suka gaisa dasu tare da maso godiya da rike mata 'ya da,suke yi, Suna tare na,wani lokaci ta mike tana cewa bari su gaisa da ni a dakina, Mun gaisa da Mamana na,rasa ina zan sakata dan murnan ganin ta yau gida na, Mama ta aika ka,sayo mata ruwan masu sanyi takawo mata har dakina, Nan nake nuna mama ga mama Rahana nace kaunar Umma ce ta dawo zama damu, Ta jajan ta mata akan rasuwan mijin ta da kuma yi mata godiya, Bayan fitan Mamane Mama Rahana take tambayana cewa tana fatan ba wani matsala dai ko, a zaman mu, Nai yar dariya nace babu komai mamana lafiya muke da kowa a gidan, Sai naga tana sance habar zanin ta kudi tafito dasu take cewa na tafi gida Aisha har gurin yan uwan mahaifin ki na tafi, ganin su tinda kin san yan uwan mune, Tsit nayi ina sauraren ta don jin ta ambaci yan uwan mahaifina, da tayi don ni sai nake gani basu kaunana na ko da yake basu da laifi wanda ma ya haifeni bai damu dani ba balle yan uwan shi, Muryan Mama ke cewa sune suka hada wanan kudin suka ce na kawo maki kya,samu ki dan sayi wani abin sana,a kina dan juyawa, Kudin da ta ciro a zanin ta ta miko min a,gaskiya kudin suna da dan yawa don za su kai dubu talati da yan kai, Sunce kudin gadon mahaifinki ne da,aka,sayar da gonan su na gado nashi kason suka dan baki daga ciki, A hankali na,dago idanuwa na,da,sukai ja nace har yanzu Mama ba asan inda Baba yake ba ke nan,? Tace haka,suke fada min amma,wai wani mutum yace ya ga,wani a kasar Niger ko shi ne bai sani ba, Nace cikin murya mai rauni Allah ya baiyanar dashi duk inda yake in har yana raye, Mama tace min Amin nakaiwa mahaifiyar ki kudin shine tace na zo maki dasu nan ki gani, ko akwai abinda zakiyi dasu, Mama ni kan ai banda ta cewa duk yadda kukayi min dasu daidai ne ba matsala shawaran ku itace tawa nima, Mama Rahana tace ni da,shawaran da nayi shine a dan saya maki dan ijimin nika ko dan fridge, kina dan sana,a kudi na shigo maki basai kin dogara ga miji ya baki ba kullun, Tajawo dan buhun da ta shigo dashi tace daga ciki mukai maki wanan sayayyan tun a sokoto, Tafara jawo kayan zanin gadone flask ban san lokacin da nace wayyo Allah na ba mama na gode wallahi, Kinga yau din nan Umma tai min gorin flask a gidan nan sai idanuwa na,suka ciciko da hawaye, Sai kuka nafara yi ina hawaye mama tace ki bar kuka ki fada min may ke faruwa ne ni uwar ki ce baki da wanda zaki fadawa damuwar ki sai ni, Mama abinda Umma take min a gidan nan yai min yawa mama saukina zuwan mama hafsi, Nan nake fada mata zancen haihuwan da ta fara bijiro min dashi da kuma yawan gorin ban da komai a dakina sai tsiya, Hmmm duniya yanzu ita Rabi har ta manta da irin halarcin da,akai masu kika fitar da dan ta daga dariyan shiya, Idan ba aure nufin Allah ba har may zai zaunar da ke a gidan ta ko don basu san asalinki ba , Duk da yan uwan mu a kauye suke zaune ai muna cikin rufin asirin mu gwargwadon hali, Idan ta matsa maki ni zan fito na fada mata,gaskiya wallahi don ba,rasa mai so kikayi ba ko don mun kyale kawai don malam Mudi, Ganin da takewa uwar ki a gidan mijin ta haka ai rayuwan aure ne yakawo hakan, Taci gaba da fitar da kayan ledan kasa sabo spoon, plate sai saitin kula na abinci mijina mai kyau, Mama taso ta lissafa min kudin kayan amma sai nace cikin shagwaba haba mama haba mi zaki lissafa min ni wallahi na gode , Tace akwai bahohi da uan sauran tarkace za,a kawo maki daga gurin Fatima idan an sayo maki nace na gode mama, Muryan Hamza ne ya shigo gidan cikin sallama daga kofan su Umma mukaji muryan shi, Mama hafsi ce ke fada mashi shigowan Mamana Rahana,a zaton shi mamana Fatima, Sai da ya,shigo yaga mama Rahana ce tazo muna, yace, A,a mama sannu da zuwa idanuwan shi a kan kayan dake baje a tsakiyan dakin gaban mu, Nan mama tai mashi bayani, akan komai da tazo dashi sai a lokacin yake cewa mama mahaifin Aisha baya gari ne cikin mamaki yake tambayan, Tace baka sani bane Hamzs nan take dan mashi bayani tare da kara bashi bayani har da wanda ma ni ban sani ba, Yace Allah ubangiji ya baiyanar muna dashi lafiya idan yana raye, Mama hafsi ya fita yana fada mata tare da nuna mata kudin sai gata tashigo dakin tana cewa, Ashe alheri akazo muna dashi haka ? Mun gode Allah ya sa ta amfana da abinta muka ce amin ni da mamana, Umma shiru tayi kamar ruwa ya cita don taga isharan Allah taga rashin amfanin yiwa mutum gori a lokaci guda, Tun mamana tana tsaye mama Hafsi ke cewa sai a sai fridge zaifi samun karbuwa, Don ko samarin nan masu zama kofan shago ai za,a samu ciniki a gurin su, Mamana tai muna sallama inda fitan ta bada dadewa ba sakon sauran kayan suka samay ni nai murna kwarai, ****** ********** ****** Na gyara dakina da sabon ledan kasan da aka sayo mun, tare da yan sauran abubuwan amfanin da mama ta saya min, An samu fridge dan madaidaici da kayan hadin shi sauran kudin da ya rage min yaya, Hamza yace zai cika ya sayo min dan maidaidai cin kujeran zama maicin mutum, biyu, Hakan yasa dakin namu yakara wani kyau, gwanin ban sha,awa na idar da,sallah ina zaune na karewa dakin kallo naji wani dadi ya kumay ni a,raina, Ina kallon dakin yadda ya sake min kamar ba dakina ba ga dan fridge dina,yana aiki sosai don nayi sa,a samun lafiyeyen fridge yana aiki sosai, Ruwan farko da nafara sakawa,har gidan mu na aikawa wasu Ummina da abokan zaman ta dashi su sa min albarka, Hamza da ya dawo yasamu yadda na gyara muna daki ranan bakin shi har kunne yake don dadi, Wata sabowa inji yan caca don Umma ta saka dan ta daki akan cewa bata yarda cewa bashi ya bada kudin da akai min wanan sayayyan ba dasu, Ai ba,a tashi sayo min ba sai da yazo gari kuma sai da tai min maganan flask ai, Wanan sabon maganan da tazo dashi ne daga gidan aminiyan ta, da taje ta fada mata cewa iyayyena,sun kawo min alheri, Sai take mayar mata,da yadda akayi da zancen flask din ranan, Tace amma Rabi gaki kamar mai wayo ashe baki dashi , Yanzu yara kanana ne zasu yi maki wayo mai yasa ba,a tashi saye ba,sai yanzu da yazo gari, Aikuwa take hankalin Umma ya tashi inda tahau zancen mama Sa,a ta zauna a kai, Kamar an ce nazo gurin taga Umma daukan kwano sai naji Umma din nacewa ko sau nawa zaka rantse min cewa,bakai kaba da kudin wannan sayayan ba zan yarda ba, Cikin ladabi naji yana,cewa Umma baki mamakin ina zan samu kudi haka masu yawa nai mata wanan sayayyan, Ai duk inda zaka samo ka,sani tunda kayi niyar gyarawa matar ka,rai don nai mata gori, Innalillahi wallahi Umma ko kur,ani za,a kawo na dafa wallahi na yarda Umma bani na,saya mata ba, Tace tashi ka bari guri tunda ka zama dan bi bawan mata sai yadda karamar yarinya tayi da kai waikai gaka dan soyayya ko ? Da,sauri nabar gurin gudun kada wani ya shigo ya samay ni azaci ko labe nake masu duk da na, yi dan laben, ai Innalillahi nake uya furtawa a zuciya ya ina fadin na shiga uku da Umma a gidan nan, Take zuciyana ya raya,min cewa fitan da tayi zuwa gidan mama, Sa,a ta dawo da wanan sabon zancen, a gidan, Hakalin na yai matukar tashi a gurguje na,samu na karasa aikina ina waje naga fitowan Hamza din dakin mahaifiyan nashi rai a bace kamar zaiyi kuka, Kofan gida ya nufa cikin bacin rai nan ya hadu da mama Sa,a wace dawowanta ke nan ta,shiga cikin gari, Ganin yanayin shi ta matsa mai da tambaya sai da ya fada mata abinda ya faru tsakanin shi da mahaifiyar shi, O Allah jama,a wai ina yaya ta,samo wanan halin daga sama haka ? Don dai a da can baya,ban san ta,da,wanan halin ba sai yanzu, Duk zama da wanan bakar aminiyar nata wace bata kaunar ta da,alheri amma ita,bata gane ba har yanzu, Wannan matar, da tana da hali, ko, ku, diyanta, da tarabaku da ita don kalaman ta babu na alheri daga cikin sa, Nan dai mama tace gabar zance kada ya,sa a ran shi ya,wahala, don Umma yanzu addu a ya kamata muyi mata don Allah ya yaye mata,wanan matsalar, Maganan Mama yasa shi dan jin sasauci ga zuciyan shi har ya dan dawo normal, Ina karasawa na koma dakina ina kwance saman sabon kujera ina,shan iska daga kofan dakina, Yaro ya shigo yana cewa wai a bashi, ruwan sanyi ya saya, amma sai Umma take cewa ba,a sayar da ruwa ya fita ya damay ta, Yaron sukayi kicibis da mama take tambayan shi ko may ke faruwa may yake so ne,? Yaron yace na zo sayan ruwa ne ance wai ba a sayarwa a gidan nan , Zo kawai tace mai suka shigo tare inajin duk abinda ke wakana, Labulen dakina ta daga take cewa tashi kibawa yaro ruwa ya,saya,namike nafara sayar da ruwana sana an da tazo min a cikin sa,a, Umma tana jin mu amma takumay tankar bata jin mau kewa kana a gidan, har ruwan hamsin yaron ya saya ya fita, Mutane suna shigowa saye abamu ruwa a ba mu ruwan sanyi, Ibrahim yace min na dan yi zobo ko za,a saye ya aje min a shagwan shi, Shi da,kan shi ya,sayo min abin hadin zobon da gorunonin da zan zuba a ciki idan nayi, Take na,dan fara tara taro sisi na kaina daga kudin fridge dina da aka,saya min da kudin mahaifina, Kishi karara da kyashi da hassada Umma ta nuna duk da tana wai kokarin taushe zuciyar ta, Hamza ya fara zanceb noman shi duk ya manta da zancen fitinan Umma, Don idan ya fita da safe sai da yamma,zai dawo gidan , Haka yasa fitina yanzu shi da Umma ba lokacin hin hakan saboda bai zauna ba balle suyi, Ina zuwa school ina,sana,ata ga kuma hidimar mutanen gida da ta Hamza, Ina zaune a baki kofana ina kokarin hada zobo ga girki kuma da,nake a dayan bangare, Umma wace shigowan ta ke nan gidan ta,soma cewa aaa wanan wutan fa na may yenewa haka kamar za a dafa Nai saurin daga kai ina kallon gurin da akaice wai ancika wuta a murhun, Tsam namike nabar abinda nakeyi zuwa guri girkina na jaye iccen kamar yadda, tace nabar gurin zan koma, ZAlINAB IDRISMAKAWA SeEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣5⃣ I,HHIDINAS SIRRATAL MUS,TTAQIN,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA Matakin da mama ta daukar min a gidan ya kawo muna sauyi a cikin gidan don, sosai Don a nawa bangare bana yarda abu ya hadani wanda zai kawo cin fuska a tsakanina da kannen mijina duk da sun girmayni sa,adatuce kawai zan iya cewa na girma acikin su, Don haka suma suke taka tsantsan da ni don gudun fadan mama hafsi dake zaune da mu a gidan yanzu, Ba,wai ba a magana ta bace kawai dai an daina min irin yadda ake min a baya can, Don haka samun sasaucin da nayi yasa ni kara kyautatawa uwayen mijina, don kawar da komai, Haka kawai na tashi ina son na gyara dakina don ba,zan shiga school sai Monday, Ganin ina,wanan aiki mama hafsi da,suke zaune da Umma a kofan su suna shan iska sun gama cin dumamay da na kawo masu,, Mama Hafsi tace a,a sarakuwana ko dan nawa zai shigo gari ne naga yau kin tashi da gyaran daki, Daga gurin da,nake tsaye nsi murmushi, kawai, Muryan Umma ce take fadin aikin san dan naki tunda kikaga tana gyara, zai iya fada, maya yana tafe, Haba yaya ko ya,fada mata ai ba laifi bane yanzu bagashi tana gyara ba, Tsab na dan kara,sanfarin dakin nawa washegari kuma nai kitso da kumshi, a gidan inda,na,kira wata,budurwa,mai sana,an kitso da kumshi tazo tai min, Washegari ,ban da aikin komai, kasancewa duk na gama aiyukana da wuri ranan, Don haka na dauko littafaina ina dan dubuwa don kara fahinta, Wani yaron makwabtan mu Aliyu ya shigo gidan da,wasu leda guda biyu a hannun shi bakin shi dauke da,sallama, ya shigo gidan Hamza ne daga bayan yaron shima hannuwan shi dauke da jakar kayan shi da wasu tarkace da yazo dasu, Yaron ya nufi kofan dakina da kayan dake daga hannuwan shi sai daga cikin daki nake cewa ya kai kayan dakin Umma, Shima kanshi Hamza din da kayan dake a hannuwan shi dakin Umma suka nufa, Lalai marhabi inji mama hafsi take cewa cikin jin dadin ganin dan nata ya,shigo gari wanda ta,dade bata saka shi a idanuwan ta ba, Shima Hamza din cikin jin dadin ganin kaunar mahaifiyar tashi a gurin su yayi murmushi yana cewa mama sannu da zuwa, Ita ko mama hafsi duk ta rude cikin jin dadi sai farin ciki take nunawa Umma dake daga gefen ta sai murmushi take na dadi yadda yar uwar ta ke matukar nuna kaunan ta ga 'ya'yan ta, Mama hafsi tace wa yaro kai kai kayan dakin can mana, ka yo nan dasu, Hamza cikin fara,a yace kayan tsaraba ne a ajewa Umma zata raba, Sai fara,ar mama ya dan rage tace kamar ya zata raba ba dakin ka za,a kai kayan ka ba in yaso matar ka ta gama sauke ka sai ta kawo muna abinda muka samu, Umma ma rage faraar fuskan ta tayi don tasan mama bazata yarda da wanan halin ba ke nan tunda tai magana, Aisha fito ga mijin ki yazo ki karbi kayan shi mana, Na,am mama nafito daga daki na yana tsaye daga kofan Umma ya zama dan birni wayayye dashi, Nai mashi sannu da zuwa ida idanuwan shi a kaina Ji yake kamar ya rugumay ni irin yadda yake ji a ran shi, A hankali cikin natsuwa na karaso gare shi na karbi jakar daga hannun shi inda na doshi dakin Umma, Yo ga yar nema kikai mai kaya daki zaki shigo nan dasu kuma nace cikin da sakin fuska, anan ake ajewa, Haba tafi dasu dakin ku mana ban iya mussu da ita sai na juya zuws dakin namu da kayan har na ledan da yaron ya,aje a kofa na shiga dasu, Kai yaka nan inji mama tace karbi nan sheka ka,sayo ruwan leda mai sanyi na,duka kawo muna, Dakin ya fada Umma tana zaune cikin fara,a yake cewa Umma sannun ku da gida, Baba a she kana hanya sannun ku da zuwa, yace yauwa Umma, Ashe mama tazo ne tace ta tuna damu gata nan ai ta kwana biyu ya durkusa har kasa yana gaishe su, Yaron yana kawo ruwan ya mika min na karba na juye a plate na kai mai a lokacin yana zaune saman kujeran dake ta kofan dakin daga ciki, Na ajeruwan a cikin ladabi zan juya mama take cewa dauki saura kikai mashi daki kafin ya,shigo, Har na duka sai Umma ke cewa miko min na dauka na jika raina nima don ita dan ta kawai ta,sani, Nakaiwa Umma ruwan ta dauka har guda biyu nafita da sauran, sai mama ke ce min yanzu Aisha may za a bashi yaci, ne,? Abinda ban taba jin Umma tayi ba ke nan idan ya,shigo gari haka zamu barshi sai ruwan randa kawai zamu bashi, Nace mama abinci ya kare, Tace to ko a,sayo mashi wani abin ne a,waje,? Mama abarshi kawai ai saida mu kaci abinci muka fito , Yanzu haka zaka zauna da yun wa har yamma ? Babu komai mama a koshe nake, Kafin ya,shigo na kara gyara dakin da jikina don taron shi kada yaji ba kamshi, Yai yan mintina yasuna hira ya mike yana cewa bari na dan rage kayan jikina na,watsa ruwa mama, Ya,shigo dakin a lokacin ina tsaye zan dauke jakarshi na kai gurin da nake aje mai, Ta baya naji shi ya,rugumoni yana matse ni da jikin shi cikin yar sauke ajiyan zuciya, Sannu da,zuwa,yaaaa sai naji ya hada bakin shi da nawa abinda yasani dan shiga,yanayi ke nan, Ya furta,min kamar mai rada da cewa miss you my wife, Nai murmushi ina kokarin zullewa sai ya kara riko ni a jikin shi ya matse yana mai kai min kiss har ta wuyana,, Na samu ya,dan sasauta min yake cewa mun samay ku lafiya, nace cikin dan gyara rigana lafiya ya karatu, Ya amsa yana kokarin balle botton din rigar shi yana cewa karatu Alhamdullahi ya,school din naku ? Alhamdullahi yaya mun kusa fara exams, nace na zuba ma ruwa ne ka,watsa, Yace kamar kin san shi nazo yi duk zafi nake ji a jikina, Na fito daki mukai arba da Umma wace fuskan ta yana a kofan mu tana gani na ta,wani kawar da kan ta, Wanka yaya Hamza yayi ya canza tufafin jikin shi sai ya,fita don ya gaisa da mutanen uguwa yana,shiri ne yake tambayana yaya su Ummi da,sauran mutanen gida, Nace a takaice duk suna lafiya, duk da ban shiga ba tun wancan zuwan da mukayi tare da kai, Ya juyo da karfi yana veea har yau baki shiga kin dubo su ba ? Nace ina jin tsoron tambayan Umma tace min na faye yawo, Wa,yai maki kitso da kumshi to nadan daga hannayen nawa nace haulatu ce na aika tazo tai min, jiya, Gaskiya ta iya kwalliya don yayi min kyau sosai wallahi, Nace mama ce ta bata kudin da tai min ai,, Ya ce ashe mama tana garin nan ne ? Nace eh tazo yanzu ai yakai sati uku zuwa hudu Allah sarki tayi kokari wallahi, Mama tana da kirki kwarai yaya don zuwan ta yai min dadi a gidan nan saboda tunda tazo ina jin dadin karatuna wallahi, Don duk wasu aiyuka ita ke yi kuma ta,sa su asmau su tai maka min Ai kadan ne daga,halin ta,don ita,daban take a,cikin su, Ya,fita yana cewa bazai dade ba zai dawo yanzu suma ina jin yai masu sai ya dawo, Futan shi na,dauko ledan da ya,sayo muna breadi da,su lemo kwakwa da Carrots, nakai dakin Umma, Nace Umma ga kayan tsaraban da yaya yazo dasu, Na barsu a dakin na fito waje abina na barsu suna maganan su, Nai mamaki kwarai a irin kason bread din da muka samu a dakin mu,, Ina aikin girkina yaya Hamza ya,shigo gidan da ledojin mayan bakake har guda uku dauke da kayan abinci a ciki, Bayan na karba na gama fitar da komai a inda ya dace, Nashiga aikin girka abincin na Allah ya taimakeni nai girki na tsab sai kamshi ke tashi a gidan, Dama dana a cikkin kayan da ya,shigo dasu a kwai vegetables na gane miyar taushe zan yi ke nan a,daren nan, Tuwon shimkafa nai muna ya tuku ya kwanta gwanin ban sha,awa Na saka a cikin leda na,daure su gaba daya na zuba a cikin babban kulan da muke zuba abinci a ciki, Na,dauka nakai kofan Umma kamar yadda na,saba ajewa idan na gama, Na koma na kwaso kwanonin abincin nazo na girke su a guri guda nabar gurin, Wanka na shiga tunda na gama kafin ayi sallah magriba, Nafito nai alwala na juya zan shiga daki sai naji muryan mama tana cewa, Aisha anan kuma kika girke abincin baki raba kin ba kowa nasa ba, Nadan tsirgar da miyau din dake a bakina , Nace mama ai ba nice mai rabawa ba Umma ce take raba abinci idan nayi, Mama tace ikon Allah ita yaya din ce mai raba abinci a gidan kuma, Na juya zan shiga daki mama tace idan kin idar da sallah kizo ki raba kibawa kowa nashi, Na shiga daki azuciya ta ina nasa cewa bazan raba abinci ba don bani ce na,saba rabawa ba, Ina gama sallah na,zauna a gurin tare da dan kishingidewa, Muryan mama daga waje tana cewa Aisha fito kibawa kowa abinsa mana ko so kike sai dan nawa ya shigo baki aje mai abincin sa ba, Shirun da taji yasa mama daga labulen dakina tana cewa a,a kwanciya kikayi ne baki ji may nake fada bane, Nace mama kaina ke ciwo bari kawai a raba , Murmushi tayi tace hmmm rabon abincin ne yasa ki ciwon kai yan nan, Tajuya tana rayawa a ran ta inko har haka Umma take yi a gidan nan bata kyauta ba, Allah ya hutar da ita ya bata yarinyar arziki a matsayin sarakuwa amma tana wasa da damar ta da,sa,an ta da Allah ya bata, Dakin Umma ta shiga tana cewa sai ki raba abincin tunda kece kika saba robon Umma tace ni dama nasan cewa yarinyar nan bazata raba ba cewa zatayi bata san yadda zata raba ba, Naji Umma ta fito tana raba abinci sai surutu takewa mama hafsi tana amsa wa ciki ciki, Can ta kwada min kira na fito ina saye da farin hijjab dina mai hannun roba, don na dauka, Yaya ki kara masu miya tunda kinga su biyu ne aka sakawa, ta bude tadan kefato miyan ta zuba, muna, Najuya na,shiga dakin mu da abincin Umma tana kallo ba daman tai magana tunda mama ta na a kusa, Don ta hana na,shiga da abincin Hamza daki wai kada aiwa danta barbade magani, a cikin abincin,, ****** ********* ******* Haka nake shiri na irin wanda ya dace mace tayi idan mijin ta zai zo gare ta a cikin natsuwa na dan sha kwaliya na tare da dan kamshe jikina da dakina, Hamza suka shigo gida shi da Ibrahim suna hira da alaman hiran shagwan su sukeyi, don shagon ya fada sosai naji Hamza din ya na fadin cewa zai samu lokaci ya kara dan kayan shagon don gudun kada kudin cefanen su ya kare, Tabarma yace ya shimfida masu na,dauko babban tabar ma na,shimfida masu a tsakar gidan suka zauna Daya bayan daya suke shigowa gidan suna taruwa a gurin inda na gabatar mai da abincin shi , Kowa ma,nashi abincin yana a gaban su suna ci a take yadda na gan su naji sha,awan su ya kamani a zuciyata, Ban kawo komai a,raina ba nima na,samu gefe daya na zauna ina son cin abincin, nawa Umma tace wanan zaman da kukayi abu daya ya rage min jin dadin shi shine rashi jika a cikin ku, Gaskiya na matsu naga an haihu a gidan nan nima nazama kamar ko wace mace mai alfahari da jika da zurian ta, Shiru gurin yayi gaba daya kowa da abinda yake rayawa a ran shi, Asma,u tace wallahi nima Umma ina son naga an haihu ace wai har yanzu ko ciki babu a gidan nan, Muryan mamace ke cewa ai basai a gidan nan ba koke kya iya aure ki haifa aiki kawo mata ko, Mara kunyar yarinya kawai manya suna magana ki wani saka bakin ki a ciki, Ina ita Zarah ma har yanzu Allah bai bata,ba idan da mutum kebawa kan shi da zarah yanzu ta haihu ai, Sai a lokacin kowa ya fahinci zancen da Umma take nufi haka yasa gurin yai shiru na,dan lokaci, Na kasa cin abincin nai shiru sai kallon shi nake a gabana, Hamza ya hankalta dani sai yake jin ba dadi a cikin ran shi don bai dace ace Umma ta fadi haka ba da bakin ta har nawa Aishan take da za ace wai har yanzu, Kuma ai maganar mama gaskiyane ai Zarah ta riga su aure idan ma Yan mintina kadan tsam na mike ban ci abinci ba zan shiga daki, Yabini da kallon tausayi yace Humaira bazaki ci abinci bane,? Nace a hankali ciciki na koshi sai anjima nashige abina daki, Umma tace aikin banza ba dai za,a fadani fadan abin dake damuna a,rai ba, Gaskiya Umma haka bai dace haihuwa ina Allah ne ke badashi ba,wai mutum ba, Ki ka sani ma ko matsalar daga yayan mu yake ba daga gare taba, baga zarah ba mijin ta ai yana da yara amma ita ai bata haihu ba ko, Umma tace Ibrahim ka fita daga idona ina fada maka idan ina zance a gidan na kana cewa zaka tsayar dani zan saba maka fiye da tsan manin ka wallahi, Hamza shiru yayi yana jin daci a cikin zuciyar shi don sam bai taba kawo zancen wani haihuwa ga Aishan ba ma yanzu, Ban shiga daki ba na fara hada kayan dake a,wajen tsakar gida don kada su kwana a wajen, Duk sintirin da nake hankalinshi ya na gareni Sa,a autar Umma tace Aisha kara min miya sai lokacin mama hafsi da take zaune duk ta kai makura tai magana, Tace ungo naki an kafeki ne dabazaki tashi ki kara da kan ki ba, ko boyar gidan ku ce Aishan, Miyan na debo na kara mata yadda ta bukata na juya na,shiga dakina, Kamar jira hawaye suke nashiga,su fara zubo min ina cewa a,raina,wanan kuma wani sabon masifa ce Umma ta ke kokari sakani a cikin sa, Hamza bai jima ba gurin su ya,shigo dakin ya samay ni na kifa kai a filo ban ma san shigowan shi dakin ba, Jin mutum ya zauna daga gefena yasani dan motsawa, a hankali, Muryan shi naji yana cewa kardai nace kuka kike Humaira, Zance Umma zai saki kuka haka ban sanki da,saurin fushi ba Aisha, don haka,share hawayen ki ki saurareni kiji, A,hankali na,dago jajayen idanuwa da,suka kada,sukai ja nace a,cikin da shakaken muryan da yaci kuka yaya yanzu,,,,,, Sai kuka ya hanani karasawa dole na,dakatar da zancen da na,so furtawa na,sake kuka mai ban tausayi, Shiru yayi ya kasa,magana na wani dan lokaci sai naji ya jawoni zuwa jikin shi yana cewa idan kikai min haka Humaira baki kyauta,min ba, Yau ina hakkurin ki ya,shiga Humaira zancen Umma zai tayar maki da hankali har ki na kokari yiwa kanki illa, Maganganu masu sa zuciya taushi, ya dinga min har na fara dan jin taushi a raina, Sai naga ya mike tsaye ya fita, daga dakin gurin su Umma ya nufa inda suke zaune yace, Mama ina abincin Humaira yake, ? Mama hafsi ta mike ta dauko mashi inda t rufe min ya sa hannu ya dauki ledan ruwan mai sanyi guda ya nufi dakin mu dashi, Umma tai wani irin tsuki na takaici batare da tai magana ba sai mama Hafsi ce tace Allah dai ya kyauta, Amana dai guda ce duk wanda yai dakyau don kan shi saboda son kai mutum ya hana diyan shi zaman lafiya, Yanzun dai don na fadi gaskiya kuke jin haushina ko waye bai son yaga karuwa a gidan shi, kuma dole ne nai magana Mama tace, ai, sai ki yi tayi in har yin naki zai sa ta samu Allah bai tashi bayarwa ba, Ganin shi da nayi da kwano tafe ya dan sani mikewa don na karba sai yace zauna abinki, Har gabana yazo da kwanon abincin ya,zauna darsha a kasa yace oya bude bakin,ki na baki, Abin da yasani dan murmusawa ke nan nakarbi kwano ina dan kai abincin a hankali a baki, na, Na danci kadan yana zaune ya kura min ido ya na kallon yadda nake cin abincin Na tura mashi plate din ina batun tashi yake cewa may wai ? Badai wai kin koshi ba ke nan ? Cikin wani murya kamar ta mai shagwaba nace na koshi yaya kamar zanyi kuka, Ki dan kara mana shi, ma ya fadi kamae zaiyi kuka cikin marairaicewa da make murya irin yadda nayi, Nace Allah yaya na koshi amai nakejin kamar zanyi, Yai sauri kawar da kwanon daga gaba yana cewa tashi ki wanke hannuwan ki ko na,debo maki ruwa ne ? Nai saurin girgiza kaina ina cewa zan fita na wanke a waje, Nafito wajen nan na,samu mama da Umma a zaune suna hira na wanke hannuna na,shiga daki Yaya Hamza yafita daga dakin zuwa kofan gidan nikan na,shige daki a abina na fara shirin kwanciya , Tun ina jin hiran su har na fara jin kadan kadan nima barci ya soma dauka na, Motsin shigowan shi naji yana ce min kinyi barci ne Humaira, Tashi ki ci wani abin kada ki kwana da yunwa, a cikin ki ciwo ya kamaki, Kokarin bude kumshin naman da ya shigo dashi tare da gorunan juice drinks, Sosai naci naman tare da kora ruwan lemon sai a lokacin naji duk bakin cikina ya dan gushe min, Yaya Hamza ya samu damar sauke nayin da kishin da ya dawo garin da shi, , Shima,sai zuwa lokacin ya samu, dan sauki a rayuwan shi, Bayan mun dan samu natsuwa,a tsakaninbmu ne naji ya kira sunana a cikin wata irin kasalaliyar murya inda nima na amsa ciki ciki, Yace magana nake son muyi ni dake ta,fahinta jin haka ya sa ni dan gyara,kwanciyana a cikin natsuwa, a hankali, Humaira, don Allah daga yau ina son na baki shawara akan Umma a gidan nan, Duk wani abinda zata fadi ko zata aiwatar maki matukar ba daga gareni kikaji wanan zancen ba, ban son ki kara nuna,bacin ran ki akan komai a,gidan nan, A hankali na furta insha Allahu yaya zan kiyayye hakan daka ce, Ki barta da,mama don nasan zaman su da mama zai kawo mata sauyi a cikin rayuwa sosai, Don haka idan har munyi hakkuri komai zai zo ya,wuce tankar ba,a yi shi ba a gidan nan, Nace a hankali cikin sauke ajiyan zuciya insha Allahu yaya zan yi kamar yadda kace to amma kuma zancen haihuwan da Umma da,su Asmau suke fadi duk har nawa nake da za,a matsa min da zancen haihuwa, Ga su anty kubura nan babu wanda ya ya damu da zancen haihuwan su saini ce kawai xa a sakawa ido don ba,a so na a gidan, Hmmm waya fada maki ba,a sonki a gidan nan Humaira,? Ni dai kin san ina son ki zarah tana sonki haka ma Ibrahim ga kuma mama da tazo, Kai kowa ma kin san yana sonki gidan nan gar Umma din, don haka kar na kara jin ko ganin kin bata ranki a banza, Na kara amsawa da fadar insha Allahu a sanyayaye inda ya sa hannayen shi ya rugumoni a jikin shi tare da matse ni gam cikin jikin shi kamar wani zai kwace ni gare shi,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣7⃣ GAIRUN MAGGALUDBI ALAIHIM WALLAD,DDALI,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA Satin su Hamza biyu yau da dawo daga ma karanta, ke nan, Mukuma sai fama da exam mukeyi inda karatu ya sha min kai don yanzu haka da taimako mama hafsi dake gidan na ke dan samun time din karatun mu, Sai kuma sa,ar dana samu yaya Hamza yana gari yana kara wayar min da kai a inda yai min zafi,, Yau na samu mun gama exam don pepper daya mukayi muka fito tun twelve, Nadawo gida da gajiya a,tare da ni don haka na watsa ruwa don naji sanyi a jikina, Nafito na shirya a cikin wasu kaya nawa masu kalar baki da zanen farin flawer a jikin shi ko ina, Buje da riga ne nai kasan bujen fish tail, ya dan baje daga kasa daga sama na ya tsuke ni, Sai dinki rigar kayan mai umbrella yasha dan tattara yai min kyau sosai, Na dan shafa kamshi na gyara dakina tsab wanda dama a koda yaushe a cikin gyara yake, duk da ba komai a dakin, sai rufin asirin Allah, Ina daura dan kwali naji sallama har ta kofan dakin mu muryan kuma bazan sheda shi ba, Na amsa yayin da naji Mama Hafsi tana kara amsa masu, Mun fito kusan a,tare da Mama Hafsi din a lokaci guda daga dakunan mu, Wasu yan mata ne ko mata zance manya guda biyu farare masu kiba don ko wacen su zata iya goyani bata san cewa ta goyani ba,, Sannun ku da zuwa sai wani shan kamshi suke muna suna karewa gidan mu kallo suna tauna chewing gun kas kas kas, Mama ce tace bayin Allah bamu ko gane ku ba ? Dayar tace O eh gaskiya naku san mu ba don Allah maman Hamze muke ke nema please, Waye kuma Hamze, ina Tau inji mama tana binsu da wani kallo ita ma sai nice nace ku shigo daga ciki, ko, Dakin Umma na nufa dasu tana ciki zaune tana dan gyara wani abu a leda nace cikin yar sanyin murya na Umma ga baki, Gaba dayan su suka bi junar su da kallo cikin jin murya na da kuma yanayin tafiya ta, Suka shiga dakin da,sallaman su tare da dan tsugunawa suna cewa Umma sannu da gida, Cikin mamaki sukewa dakin Umma din kallo suna dan tabe baki dayar tace Umma mu bakine daga Zuru mun zone mu gaida ke dama, Guri guda muke karatu da Hamze na gidan nan shine mukace bari mu shigo mu gaida ku, Lokacin na kawo masu ruwa da zobon gora masu sanyi nace masu ga ruwa kusha, Na dauko tabarma daga can cikin kuryan dakin Umma din na,shimfida masu suka zauna a kai, Mama hafsi tace wanan itace Aisha matar Hamza din da kuka zo gayarwa, Sai duk suka kara dagowa suna kallona nikan na juya nafita sai dai kuma naji wani irin faduwan gaba ya sauka min, Dakina na,shiga na zauna saman kujera na a hankali ina tunanrn cewa su wan yan nan din su waye, Kamar an jefo shi sai gashi ya shigo gidan naji muryan shi yana cewa mama inda mama Hamsi din ta karba tace naam dan mama ka dawo yace eh , Sai ya nufi dakin mu yana,son aje takardan da ya,shigo dasu, a hannun shi, Mama tace idan ka fito kana da baki gasu nan dakin yaya, Baki ya juya yana tambaya da mamaki hannun shi daya rike da labulen mu, Sannu da zuwa nake mai ya kara juyowa gurina yana kallona yace Humaira har kun fito exam din ne nace eh, Dakin ya,shigo yana aje takardan yake tambayana su waye suka zo Humaira, Nace a dakile wasu matane suka shigo su biyu suke neman ka koda yake sun ce Umma,suka zo gayarwa, Yafita zuwa dakin Umma din na mike na dauke takardan na adana mai, a jakar kayan shi, Turus yayi yana kallon su a cikin mamaki,,Halima kune a gidan mu ? Mune inji wace ya kira da Halima din tana wani murmushi tace mun shigo gaida Umma ne ai, Ruwan sanyi da zobon dana aje a gaban su ya,dan kalla yasan bazasu sha ba ya juya yana cewa ina,zuwa , Can yadawo gidan dauke da kwalaben drinks masu sanyi d,biscuits a,cikin wani leda, Ya shigo dakin yana cewa bani cups Humaira nakai masu na mike daga inda nake na,dauko wasu cup din tangaran dina , Yajuyya fuuu ya fita zuwa, dakin Umma din gurin bakin nashi, Ina zaune ina kallon yadda ake dawainiya da bakin sai mama Hafsi ce tafito daga waje ta zauna a saman wani kujera ta mude fuskan ta, Abin fitara Umma ta miko masu tana cewa karba ku dan fita akwai zafi wallahi, Halima din ta daga kai tana kallon tsohon rufin dakin Umma din tana cewa, Umma ya kamata a saka maki fanka a dak8n nan don zafin zai maki yawa, ai, idan ba fanka, Umma tace yar nan mu marayun Allah ta fanka mukeyi muna ta abin da zamu ci, Umma tace aida kun koma daga can dakin Aisha ku zauna zafi nan din dan shan iska ai, Kibarshi kawai Umma ai nan din ma yayi muna zamu zauna a hakana, Dan kadan suka sha drinks din tace Yau gamu a gidan ku yau dai munga Umma, Kullun kana muna hiran Umma Umma dai , Umma taji dadi har a cikin zuciyar ta najin dan ta ya damu da ita a makaranta har zancen ta yake yi, Hamza yace a daidai lokacin da na fito don dauraye plate naji yana cewa, Kun ga wife dina Aisha Humaira ko ? Dayar tace mun ganta da muka,shigo ina itace yar yarinyar da muka gani kamar under ege, ko ? Yai yar dariya yace aiko ta girma yanzu don gashi har tana batun shiga two hundre a health and technology, Ita wanan karamar yarinyar din ? Suna a zaune sai hira suke suna dariya a tsakanin su Umma daga gefen su sai washe baki takeyi, Sallama akai ma Hamza din ya fito daga dakin zuwa gurin da,ake neman shi a waje, Ina duke ina,wanke gorunan zobona yazo ya gitta ta gabana ban ko dago kai na dube shi ba, Sam baiji dadin hakan ba don yasan ban taba mai haka ba a rayuwan zamana a gidan, su, sai yau din nan, Yana magana da bakon shi da ya kawo mai maganin feshi amma zuciyar shi na ga yadda nai mai ko in kula,( kishi) Ledar da suka shigo da shine daya daga cikin su ta aje a gaban Umma tana cewa Umma baida yawa dama mun ce bari dai muzo mu gayar da ke, ne A,a,a duk wanan ni kadai wanan ai yayi yawa ga,zuwan da kukayi ga kuma,dawainiya haka mai yawa, Angode Allah sa albarka nagode nagode kunji sai dayar tace Umma wanan ce Halima itace dama suke tare da Hamza a can makaranta tana yawan taimaka mashi da abubuwa da dama shine tace ya kamata muzo mu gaida ke don ki san da ita, itama, Tau taufa Umma ta dago kai da sauri ta dubi maimaganan tace wani irin magana ne wanan kuma yaran nan,? Tace to may zamu boyewa Umma tunda da aure take son ka ita ? Aure inji Umma ? Gaskiya yarinya kin zo da sabon zance Hamza marayane bamu da kowa sai Allah kinga yar matan shi da muke maneji a gidan tare da ita, Ina muka ga kudin auren irin ki a gidan nan ko ainda zamu aje irinki ai mu bamu dashi, Dariya sukayi Umma wanan ai mai sauki ne a gare mu mu kawai yarda ki muke nema ki bamu baki ya aure ta, Don shi mun rasa gane kan shi bai bata hadin kai yadda muke so, Kuma wallahi a tsakani da Allah take son ta aure shi ita, Kafin Umma tai magana mama Hafsi ta,shigo dakin tana cewa, Ku da kata don Allah wani irin magana kukazo dashi, gidan nan, Yanzu ku don baku da kunya shine zaku shigo muna da wanan zancen haka ba kuyan bajin wani nauyi, a idanuwan ku,, Hafsi ki barsu su fadi abinda ya,kawo su aiji ba aiki bane, dashi dole don haka ki barsu muji shakuwan su ko, Shiru sukayi don jin mai matan gidan suke fadi inda Mama Hafsi tace duk cikin ku wacece sa,ar auren hamza din , Don haka na roke ku da kubar min yaro na ya zauna lafiya da iyalin shi kada ku kawo muna,sabon fitina a,gida, Boyar Alkah dakata ki ji mu bawai munzo ne akan zancen yanzu yanzu ba Mun dai zo ne dan mu nuna kan mu asan da zancen a gida, Hummm,ummm Ikon Allah, Allah ka kawo mu zamani kuma , Ba wai hakana bane mama kawai dai kada ace ana abu baku da labarin komai, Sai zuwa wani dan lokaci a na zaune dasu zugun zugun tsakanin su da su Umma nikan sai sintirina nake ina aiyukana a tsakar gidan, Ya shigo yana cewa sorry Halima na barku a zaune ko, Kuzo ku gaisa da madam dina mana din ta san ku itama, No kabarshi idan mun fita zamuyi sallama da ita ai, Sai ta juya gurin Umma cikin dan kashe murya suna cewa, Umma da,fatan zaki duba zancen mu da idon basira ki fahince manufan mu a gare ku, Wani kallon mamaki yakewa bakin nashi don bai fahinci akan may suke magana ba, Don bai taba tsan manin cewa zasu iya fadawa Umma zance maka man cin haka ba a,gaban ta, Jin ana kiran sallah ko ina yasa su dagawa suna cewa, Yanzu zamu koma sai wani lokaci ta juya inda Hamza yake a tsaye tana cewa dear na zamu, koma amma ga wanan , Tafara kokarin sa hannu a jakkanta tana ciro kudi tace a,sayawa Umma fanka a saka mata a,daki, ko, Ke Halima baki gajiya da yin dawainiya ko yaushe sai kinyi hidima a mutum, Umma itace fa ta aiko da kayan kwaliya kwanaki nakawo wasu Asma,u da sa,a, Yafada cikin yar fara,ar shi batare da fahintar komai ba, a zuciyan shi, Ina a zaune duk zancen da,ake ina jin abinda ake fada dama tun farkon fitowa na mama tai min signal da na kyale na kada kaina kawai ban ce komai ba, Sun futo ana yan dararaku tsakanin su sunayiwa Umma sai watarana,da godiya ita dayar mai suna Bicky tana cewa Umma a diba muna zancen mu dan Allah, Wai wani zance ne wanan kuke ta magana a kan shi Hamza din yake tambayan su don son jin maganan, Babu ruwanka Bicky din ta fada maganar ce da maman mu,ai, Sun mikawa Mama Hafsi kudi tace ku barshi in kunzo ne don ku saye mu ku cuci dan mu toni ba haka nake ba, A,a mama wanan ba haka bane kawai munzo ne don mu gaida da ku kuma ku san mu, Har zasu fita ya sake cewa baku gaida wife dina ba fa tana ciki dakin ta, Dole suka,shigo dakin namu ina zaune na idar da sallah a lokacin na karba masu fuska ba yabo ba fallasa Sun wani zauna suna kallon dakin dawaini irin karkada kafafuwan su, Mikewa sukayi suna cewa zamu tafi sai wani lokaci mun kara haduwa, Nace, sannun ku mun gode da kulawar ku gare mu, Dariyan yake sukeyi suka ce ai ba komai, sai anjima ko, Rakasu na yi zuwa kofa na yadda shari,a tace kaiwa bakon ka,rakiya ladane, Daga nan nai masu Allah ya tsare hanya na koma ciki, Zama nayi zuciya na tana wani harbawa don sai a lokacin nai masu kallon tsab don zan iya cewa sun haife ni dukkan su don ba yara bane gyarane kawai ya rufe shekarun su, Suna ficewa gidan mama hausi tafara fada tana sababin inda take shiga ba nan take fita ba, ba wanda ya tanka mata Abin duniya duk ya,sha min kai ko magana ban samu yi ba, Don ita Umma sai farin ciki take tana cire kayan da,aka,kawo mata,sai faman yabawa take tana sa albarka, Turumin zani ne sabulai, man shafa, turare da takalma silifas mai kyau, Ya kai wani lokaci a,waje bai shigo gidan ba,sai zuwa yamma liss ya shigo ya samay ni a bakin murhu ina kwasan abinci,, Sannu da,zuwan da nai mashi batare da na,dago kaina kona juyo in dubi shigowan shi ba,, Buta,ya,sura zuwa,ban daki yafito ya zauna ya na son daura alwala, Umma ce ta shigo gidan da ledan kayan da ta tafi nuwa,makwabciyar ta, aminiyar ta, Ganin Hamza a gida yasa ta dan tsaya,gurin shi bata karasa isa gareshi ba, Tace ashe ka,dawo sun tafi ko,? Yace ai tun fitar mu suka tafi dama daga Birnin kebbi suka karaso nan, din, Tace kaga,abinda ta zo min dashi ko ? Gasu nan, na tafi nunawa Sa,ade tagani itama ta samasu albarka, Kaya kuma ita Halima,din ta,za maki dasu mama,bafa musulmai bane kin san halin kiristan din nan da son shigewa,mutane, Kirsta,kuma inji Umma ta fada a gagauce cikin mamaki, Umma kina,mamaki ne, kin san su yan zuru ba, a gane musulman su sosai don kirstocin shigar musulmai suke harda hijjab da,gyale suna yafawa, Cudan yan su gida guda da musulmai da kiristocin yasa kowa ya iya aladan wani, Zaki shiga gida guda komai a,tare akeyin sa,amma,kowa da,addininsa uwa daya Uba daya Daga daki mama hafsi take fitowa tace haba biri yai kama da mutum ai, yanzu yaran nan kafirai ne suka zo muna da,wani zancen banza a gida wai yaya ta bada baki ta bari ka auri dayar matar, Mama su suka,fadi hakan da kan su mama tace aiga yaya nan gurin ta,wai, su kazo suna neman hadin kan ta ta,yarda ka,auri mai sonka din, Wallahi mama sam, ni ban san da wanan zancen ba,don wani makamancin irin wanan zancen bai taba,shiga tsakani na dasu ba, Sai dai harka kawai na karatu saboda likewar da tai min yan ajimu ke cewa,wai ni kanin Halima ce, haka yasa muke mutunci da ita amma ba zancen soyayya a,tsakanin mu,, Sai a lokacin ne ya,daga kan shi yana kallon guri da,nake na mike zan kwashe kayan abincin da,na,raba, Yake cewa a,ranshi amma halima,yau ta cutar danin ta,zubar min da mutinci na a,gurin yan uwana, Ya kara dago kan shi kara na,biyu ya,bini sa kallo fuska kawai ya nuna mai canjin yanayi a tare dani, Umma tana kokarin nuna mai kayan ya fara alwala yana cewa, Umma bari kawai zan ciwa wanan matar mutunci ne don kada ta kawo min iskanci har a gida, Ina wanan zancen ya fito haka har take kulla min sheri, haka har a gidan mu zata zo tana irin wanan maganan kamar wace ta samu tabin hankali, Wallahi mama ni a zatona ko zuwa sukayi don zumunci kawai,su san gidan mu, Kayan da bai duba ba ke nan yai, alwala ya fita abinshi kawai ya bar Umma rugumay da kayan a hannuwan ta ****** ********** ****** Duk yadda mutum yai tsan manin rayuwan kubura yan zu abin ya,wuce nan, Gashi mahaifinta ya saka mata dokan cewa duk tafara ta kashe auren ta ba dai gidan shi ba, Don ya fahince ta ita da uwar ta,so suke ta kashe auren ta ta,dawo gida tana mashi iya,shege cikin iyalin shi, Haka yasa dole ta koma dakin ta, tazauna tana hadiyan hakkurin ta ita,daya, Wani iskanci da iya,shegen da tai dammaran yin shi a gidan Alhaji Nura yanzu duk ta sauke wanan mugun hali ta koma bi, da, rarashin kawai, Wani jiji da kai da basarwan da take a gidan duk ta,sauke su don ba wani wanda ya damu da ita kowa ya fahinci halinta tun farko an kama kai da ita, Dole badon taso ba ta sauke fadin rai din yau Jamila tana zaune a falon gidan nasu tana kallon wani Indian film, sai ga Kubura din tafito saye da wani don riga baki ta daura dankwalin shi a,kanta, Jamila tana ganin futowan ta kamar kullun taja mata irin addu,oin da ta,sabayi akan Kubura din kamar haka, La,illah haillah mohammadan rasullillah, sau uku, A,uzu bi kalamatillahi tamatati min sherin min halaq, Muryan Kubura ne ya ratsa kunnuwan ta tana cewa yau India aka i muna, Ta dan dago kanta tankar a lokacin ta ga,fitowan ta daga dakin ta, tace eh wani film nake kallo a tashan, Kubura ta kai zaune tana cewa ni ban faye son tashan irin haka,ba nafi son na kallli hausa ko yaya yake, Don baki saba dasu bane aida bazaki barsu ba don suma,suna fadakarwa a ciki ai, Nura ne ya,shigo gidan wanda dawowan shi ke nan a lokacin don bai kwana a,gida ba, Yana rataye da couth din shi a kafada ya,dan sasauta nicktie din wuyan shi, kadan, Kallon mamaki yake masu gaba dayan su don bai taba tsanmanin ganin su a haka,ba, ya kalli wancan ya juya ya,dubi waccan, Cikin rashi sakin fuska Jamila tace sannu da dawo, Kubura wace take zaune a gefe guda ko kallon shi bata yi ba tace mai ina kwana kawai, Ya dan shiga da yan min tina Jamila wace ita ce da girki a ranan ta dan mike dingis dingis zuwa dakin shi , Idan ba kunnuwan ta ke mata karaya ba zata iya cewa fada tadan ji Jamila din tanawa maigidan nasu, don tafahinci akan dawowan shi lokacin take magana daashi, Mikewa tayi zuwa dakinta don rashin ganin dacewan hakan, don zamata a,gurin tana sauraren sirin su tankar wani abinda bai dace ba take yi, Kwance take tana nazarin abinda taji suna fada wa junan su, Yanzu Nura ya dace ace mutum mai iyali kamar ka dai yanzu zai dawo gida cikin iyalin shi, Yace cikin irin halin shi na,dakawa mace tsawa wani ya turo ki kimin fada ko kuwa, Jamila tace amma kasan hakan baidace ba ace namiji mai iyali baya kwana cikin italin shi yana can yana bariki sai lokacin da yaga dama ya,dawo don kan shi, Tun yaranka basu da,wayo har yanzu sun fara fahintar halinka cewa a can ka kwana ko, Yau Amira dagewa,tayi wai bata zuwa school idan bakai zaka kai su kullun ko wani yaro baban shi ke kai su, Yace look ki fita ki bani guri ina bukatan hutawa kin zo kin cikani da surutun tsiya haka, Sai ka tafi ka,wullakanta kan ka a,duniya ka dawo gida kana wa mutane cika da batsewa, Jin motsin ta yasa Kubura shawaran komawa daga cikin dakin ta Tambayan ta anan shine ina Nura ke zuwa haka wanda duk dare sai ya tafi, Kardai ace neman mata yake haka har yai muni kada fa ya jawo masu matsala ko wani mugun cuta ya saka masu, A hankali ta furta cewa Allah gamu gare ka ka kare mu daga mugun ciwon zamani, a rayuwan mu, Mirginawa tayi tanamai jin haushin kanta akan rashin kwantar da hankalinta tun shigowan ta gidan ta fahinci mai gidan ke ciki, Ta dauki fadin rai ta saka a ranta tana ta wahala tsayin shekara da,watanni, Gashi yau yau da,fara kwantar da kanta tafara fahintar wani abu a gidan, Lalai sai tasan ko may mijin nasu yakeyi wata,sana,a ce yakeyi irin haka har yake hadasu fada da Jamila mata mai hakkuri, kamar ta,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣9⃣ RABBANA, LA TUZIGH QULUBANA, BA,DA, IDDZZI, HADAITANA , WA HAB LANA MIN LADUNKA RAHMATAN INNAKA ANT AL WAHHAB,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA DON ALLAH YAN UWA INA BARAN ADDU,A AGARE KU KU TAIMAKENI KU TAYANI ROKON ALLAH AKAN ABINDA NAKE BUKATA A GURIN UBANGIJIN MU ALLAH SUBBAHANAHU WATA,ALLAH,,,, Wasa wasa yanzu anfi sati Umma tana kwance masasaran yaki tsayawa har ya kaita a kwance, sosai, Yar uwar ta mama hafsi ke faman dawainiya da rashin lafiyan Umma din, sai ni dake faman dafe dafe a gidan Naka shiga dakin fiye da a kirga don na gaida Umma na Kuma duba lafiyan yata, nakuma wanke kayan da tai amfani dasu, Ranan da ta cika sati Daya a ranan na shiga daki na Sami duk yaran Umma suna a kanta, tana cewa sanyi take ji su rufa mata bargo, sai rawan dari take daga kwance, In tsaye daga gurin da nake ina nazarin abinda ke damuwar ta gashi sai faman dirka mata magani akeyi Ina mai kura mata ido, sai naji suna cewa wai, za a Kira Mai chemist yai mata allura, Ni ko na fahinci wani abu a jikin nata sai dai Ina tsoron magana suce ban San komai ba, na jawa uwar su mugun ciwo nake mata fata, Daga inda nake tsaye daga bayan su nace amma yaya da kiran wanan mutumin ai da kawai akai Umma asibiti gurin doctor ya dubata zai fi wanan, kaura da kai din da ake tayi a gida da ita, Duk kan su suka juyo inda nake suna masu sako min idanuwan su, gaba dayan su Kaji malamar asibiti fa aida sai ki dubata idan har kin gane wani abune, jibrin ne yai wanan magana, Mama da Yaya hamza suke cewa tun da kukaji Aisha tai wanan maganan akwai abinda take hasashe ke nan, Ibrahim yake cewa, cikin, tambayana Aisha don Allah kokin fahici wani abin ne suna masu sako idanuwan su a kaina, Cikin harshe turanci wanda zance duk gidan nan ko shi Hamza din bai taba sani na iya turan ci ba haka nake masu bayani, komai, Don ina gudun yi da hausa Umma taji tace ina mata mugun fata ne, Jikin su gaba daya yai la,asar suke cewa gaskiya ya kamata subi shawara na don bai kamata ace sun aje ta a gida ana magani daban ciwo daban, Fita Hamza din yayi zuwa wani dan lokaci sai gashi ya shigo gidan a cikin, saurin shi tun a kofa yake kiran mama, Duk muka yo waje don son jin may zai fada tunda kowa a tashe hankalin mu yake, Ance mai baki bai iya ciwo ba don Umma ta wani koma ragwab da ita duk tafita hayacin ta, sai nishi take daya daya Mama ga mota a,waje mu tafi ko? Ina shiga dakin naga yadda idanuwan ta suka juye sukai, weak a lokaci guda, Da sauri har ina ture Ibrahim na karasa bakin gadon a gaban Umma na kamo hannun ta ina dan massage din hannun nata a hankali har wani dan lokaci, Sai naji tai wani irin ajiyan zuciya a hankali sai da kowa yaji a,dakin, Duk sai suka kara rudewa hankalin su ya tashi, Nace Mama ku kamata a tafi sai dai aiwa driver magana ya tuka ta a hankali don Allah saboda tana bukayar resting sosai,, saboda jikin ta is already been weak, Hankalin su gaba daya ya tashi sai wasu suka fara kuka suna cewa wayyo Umman mu Umma don Allah kada ki mutu ki barmu, Cikin tsawa mama take masu fadan wani mugun fatane haka sukeyi ai ciwo ba mutuwa bane, Ke Humaira dauko hijjab dinki mu tafi asibitin a tare zaifi, Ba musu na shiga daki kamar yadda ya umurce ni na dauko hijjab dina a tare muka tafi, Ni da mama muka zauna a baya tare da Umma ina dan mata masage yadda ya dace ce, Mun shiga inda duk wani abinda ya dace ayi na ganin likita tare da Yaya Hamza mukayi kasancewa akwai yan makarantar mu da su kazo practical a gurin, Sosai zuwana ya taimaka nan da nan muka shiga gurin likita don bada bayani, abinda ke damun ta, Likita ya tambaye, ta ta kasa magana kamar maijin tsoron shi, dole ban san lokacin da na bude baki nafara yiwa likita bayanin yadda Umma din tafara ji har zuwa yanzu da abin ke son zama mata blood pressure, Tambayana yayi wasu irin medication mukai mata a gida nan ma tirya tiryan nai mai bayani har zuwan mu asibiti , Yadan bugi taburin gaba shi yace she is, very luck dat you are around if not she will die or be in critical condition,, Umma tana rike a hannuna sai nishi take guda,guda, tana kara kamay wa,cikin tashin hankali, Are you a student ? Tambayan da yajefo mi ke nan lokacin da nake kokari gyarawa Umma zanin ta daya rankafo, Nabashi amsa cikin gyada kai da cewa yes, Where are you schooling ? Health and technology nabashi amsa a takaice tare da mikewa ina kokarin jan Umma gurin gadon da yace tahau, Sai yace, interested,,, Yakamata ace parents naki nursing suka kaiki ba health ba, Don you are very intelligent gaskiya yakamata ace nursing kika tafi, Maigida na nan yake son nayi karatu shiyasa na tafi can din, Naba shi amsa a daidai lokacin da nake gyarawa Umma kwamciya, Na juya nafita nan na barsu da Yaya Hamza ina fita na samu har su yaya Ibrahim da su Jibrin duk sun shigo asibitin mama tana masu fadan an watse anbar gida babu kowa, su Asmau, su koma gida, Amma sai sukai banza da zancen ta kamar basu ji ta ba, An dan dauki lokaci yaya yafito yana cewa an bamu gado za,a kwantar da ita, Nan muka shiga kuma dawainiyar kwantar da umma wace daga zuwa akai mata allurai masu karfi da kara lafiya sai drips da akai setting za,a kara mata, Ganin komay ya dan kammala nace zan koma gida don nai mu na abinci da za,a kawo asibitin, Tuwon masara,nai masu da miyar kuka,da nama,a cikin sa kamshi kayan yaji da daddawa yana tashi daga cikin miyar,, Ranan ni kadai ce a gida sai ban samu komawa,asibitin ba ina fama da,aikin gida, da yai min yawa, Sai dare sosai ina daki banyi barci ba a lokacin don tsoro nake ji sosai saboda ni kadai ce a gida, duk suna,asibiti gaba dayan su gidan, Ya,shigo gidan inda shima tun a,waje yaga gidan yai mai wani fadi fayau, Ya shigo da yar mashin din shi daga ciki ya kaita kofan mama inda yake ajewa ya kulle, Sannan ya juyo zuwa dakin mu cikin takon shi na, natsuwa, Zaune nake saman kujera na idanuwa na,a kan kofan shigowa, Yana shigowa na gyara zama na mike sosai ina cewa sannu da zuwa Yaya ? Ya dan rugumoni daga gefe tare da shafan dan kumci na yana cewa cikin harshen turanci ni ban son kiran yayan nan da ake min fa,, Murmushi nayi nace anfitar dani a cikin kannen ke nan ko kuwa, Kafin ya kai ga bani amsa sai nace ya kabaro jikin Umma din da sauki yanzu ko? Ya ce da sauki don tana ta barci ne har yanzu sai ruwan ake kara mata nace shine lafiyan ta, Abinci na gabatar mai tare da mikewa nake cewa ga ruwan wanka, zan kai ma bayi, Har na kai ruwan wankan bayi na dawo yana zaune inda na barshi yayi tagumi da hannayen shi, dukka biyu, Lafiya dai yaya ? Natambaya cikin son jin may yasaka shi tagumi haka, Ya sauke yar ajiyar zuciya yace Humaira dole ne ki ganni haka don ban da kudi a hannuna duk na zubasu a gona gashi dan kudin mama da ta ban na saya mata kangon gida dashi, Ga kuma lalurar asibitin nan yataso komai na kudi ne yanzu asibitocin mu ba tausayi a cikin su, Kudin zasu kai nawa, ? Natambaya cikin son jin yawan abinda zai bukata na kudin, Sai daya dan sa hannun shi a bakin shi ya busar da wata iska mai nuna bak8n ciki Yace na, dai rike koda goma ne don test test din da ake yawan yi mata, su ne ke cin kudin, Nace akwai kudin da mama ta bani na bawa Ummi na daga ciki sai na,sana,ata dana tara a asusuna zan fasa naga may ke a ciki, Yace kinga kuma ga abinci don duk da,asibiti gurin jinya ne amma yan sa ido na gurin suna kallon kalar abincin da ake kawo wa mutum daga gidan shi, Wanan matsalar su ce don wani ma idan ka rabu da shi har abada,bazaku kara haduwa dashi ba, Yace hakane Hummaira amma ya kamata na samo dan shinkafa da,sauran abubuwan da,za,ayi amfani da,su, Nace dare yana yi ruwan wankan ka yana a cikin bayi kada yai sanyi ko wani shedani ya taba ma, Yana fita na dauko a susu na nafasa nazauna kasa dirsha nafara kidaya kudin dake ciki na,samu shauku da dari takwas, cif, Yana shigowa da ruwa a jikin shi yana daure da zani na da ya daura da zai shiga wanka, Na ce mai ga kudin na fasa asusu sha uku ne da dari takwas na samu a cikin sa, Yakai zaune bakin gado yana mamaki yace duk da wanan sana,an kika tara wanan kudin haka? Gaskiya sana,a tana da amfani sosai shiyasa akace zaman banza baida amfani a rayuwa, Yanzu gashi zamu ci albarkacin sana,ar cikin gida a gurin ki, Yakarbi kudin yana cewa Allah ya bani ikon biyan ki su a cik8n dadin rai kamar yadda ya dace duk wani wanda ya dauki bashi ya fadi, Ranan ba wani abinda ya shiga tsakani na da Hamza don ya kwana ya na juyi saboda damuwan ciwon mahaifiyar shi,dake a rayuwan shi, Washegari tun da asuba na tashi na,dora ruwan kunu da sauran aiyu ka don nasan bawanda zai taimaka min da aiyukan, tunda mama bata gidan tana asibiti a can ta kwana tana jinyar yar uwar ta, Ranan bani na samu kaina ba sai kusan karfe daya alokacin komai da ya kamata nayi nayi nagama na gyara gidan fes ta ko ina, Nai wanka na sa wasu atamfana wax masu ruwan blue color, Shigowan shi gida don daukan abinci ya samu na shirya nima sai dai ban yarda mun fita ba sai da na zaunar dashi a cikin dubara ya danci wani abin sannan muka rufo kofan gidan zuwa asibiti, Kofan gida zamu hau mashi muka hadu da Baba Mudu wanda ya fito daga cikin gari, Hamza ya sauka ya nufe shi acikin alkunyar sarakuta kamar kullun suke gaisawa, Nan Hamza ke fada mashi Umma ce aka kwantar a sibiti ba lafiya, Ba ya dago kai gurin da nake a tsaye da kullan abincin dana kulle ga wani dan kwalina, yake cewa, Kin aika cikin gida a fadawa iyayyen ki kuwa Aisha ? Nace Baba ban samu yaro ba yau duk su Aina basu shigo guri na ba, Yace kin san yau ana zuwa boko babu kowa duk sun tafi makaranta ku isa insha Allahu yanzu zan karaso nima insha Allahu, Mun samu ba laifi Umma ta samu lafiya don tana zaune saman gadon ta tana magana da kishiyoyin Anty Zarau, Mun gaisa da,su nai masu yaya maijiki suka karba min da,Alhamdullahi, Na aje kwanonin abincin daga can inda naga kayan abin karin safe dana aiko masu dasu, Na lura Umma sai da kyat take amsa min gaisuwa na ina zaune ruwan dake manne a,jikinta ya kare sai ake kira nurse on duty ta cire mata take cewa tana aiki gata tafe, Ganin ruwan ya kare zai iya fara dan sinking din blood din ta yasa na mike daga gurin da nake na nufi inda cotton yake na debo na wuce direct gurin ruwan na cire na mayar da canular din na,rufe mata Ke Aisha kada kije rigima ki ja min matsala a ce sai an sake yi min allura, ko wani abu don walle duk na gaji da soke soken nan, Umma ce ke fadin haka cikin maganan ta na yanayin mara lafiya, take maganan da kyat, Lokacin ne nurse din ta iso gurin don cirewa Umma ruwan bayan mintinoni da na cire mata ganin ancire anyi komai yadda ya dace yasa ta dan fara waige waige tana cewa wacece ta cire maki ruwan, ? Cikin sauri Umma take cewa dama ai na fadi rigimar yarinyar nan kada ya jawo min matsala, Gata nan waje sallonta, ta cire min shi, ina cewa tabari amma sai da tacire, saboda iyayi, To ai tayi daidai don ni ban zaci ruwan ya kare haka ba gaba daya ina ce kadan ya saura suka kirani, kin kuru da yaja jinin ki badon tana gurin ba,,, Inda nake nurse din ta juya tana cewa, amma kina karatune ko,? Nadan bata amsa cikin gyada kai tare da cewa eh , Wani school kike karatu nace mata health, good, good, yana da kyau hakan Muna so mata suyi karatu sosai don taimakawa sauran matan mu nagida da basu son fitowa asibiti, Kamar wanan maman taki sai da jiki ya kashe ta agida akazo muna da ita nan Ai wallahi ta kuru don da sai dai wani ba ita ba a yadda akazo muna da ita , Mama Hafsi daga inda take zaune tace malama ai ita wanan yarinyar taba da shawaran mu wuto da ita asibiti Don duba mai ke damun ta, saboda yadda jikin nata yai tsanani sosai, Tace shine amfani karatun at list a dan samu wanda ya dan san wani abu zai iya taimakawa, ko, yaya ne, yafi a zauna dip gaba daya, a gida, A daidai wanan lokacin da take bayani su Yaya Hamza suka iso gurin sukai tsatsaye cirko cirko suna sauraren bayanin da matar ke yi, Tai setting din wani ruwa bayan taima Umma din allurai sai ta saka mata, Ta juya inda nake tana cewa idan kinga yana rushing zaki iya rage mata don kada ya sakar mata da reaction, Ta juya ta wuce sai mama hafsi tai magana bayan wucewan nurse din take cewa Aikuwa munga alamar hakan don dai yarinyar nan ta taimake mu sosai kan wanan rashin lafiyan na yaya, Ibrahim yake tambaya may yafarune wai, Sai mama take mai bayanin yadda akayi da nurse har cire ruwan da nayi, Ya juya gurin Umma yana cewa wallahi Umma Aisha babbace don dazu na hadu da abokina dake karatu a makarantar su yake cewa tana cikin dal8ban da ake ji dasu a school din nasu don first class ce ita, Umma tai wani mayde baki tana cewa ai sai ka bari har takare karatun sai ka yabeta ko, Hamza daga inda yake sai murmushi yake don yasan Umma bazata taba yabo na ba idai da bakn ta ne, Muna gurin na hangi wasu mata tafe sunyi kwalliya sunyi kyau dasu hannun dayar, matar, dauke da basket din abinci, Dayar kuma tana dauke dayaro karami a kafadar ta sai wani saurayi a bayan su dauke da flask din ruwan zafi da ledojin kayan tea a ciki sai na fruit, Tsayawa sukayi inda gadon farko yake a dakin suna tambaya mutanen dake saman gadon, Sai sukai masu nune da hannu a gurin da muke, direct gurin mu suka nufo, Sai da suka zo gab damune na gane cewa su Hindatu ne ashe, tare da kannen ta suka shigo duba jikin Umma, Nan aka shiga gaisawa da su ana tambayan ya jikin Umma din tare da mata fatan Allah ya bata lafiya, Daga karshe suka gabatar muna da abincin da suka shigo dashi, a matsayin na dubiya, Godiya muke masu tare da fatan Allah bar zumunci, tare, Su waye Zarah take tambaya kasa kasa don son jin kosu waye su Hindatu din, don ganin su yan gayu da tayi, Mama Hafsi ce ta cabe zancen da cewa mutanen arzikin Aisha ne suka zo ai kinga ita suka,sani, Zancen yaiwa Umma zafi tana son cewa mutanen data ne, shi suka sani, bani ba ga kuma alluran da akai mata yana hawa mata kai, Sai kuma ga yar yauri tashigo su ma har su uku suke cewa sunzo gidan mu ake fada mata shine tace bari su wuto direct asibitin, Zarah take cewa yanzu ashe ita Aisha tasan mutanen arzikine haka take hurda dasu, Hira,muke a tsakanin mu na,sake freely zakace bani bace ke yar hira har da dariya na a,cikin friends dina, Bayan tafiyan yan gidan su,Zarah ta bude abincin da Anty Hindatu takawo muna,sai kamshi ke tashi cikin dakin duk ya,bure ko ina, a dakin Mama hafsi ce ganin za ,a cinye abincin ni ina can tare da baki tai min tayi nazo naci abincin Nace Mama sai da naci abinci na,fito daga gida a koshe na ke, Ba wani kunya nan suka bude baki a gaban su hindu suka cinye abincin tas, akarshe ma suka bude wanda nazo dashi suna mai wani kallon wullakanci, Sai mama ce ta shiga rigar arzikin su, take cewa su rufe mana anjima basai ankawo wani ba ai zai masu rana, Ranan mama ta hana ni yin wani girkin dare tace aiki yai min yawa na huta hakanan, Da dare dana dawo gida yaya ibrahim ya sayo kayan shayi yace na hada muna shi mu kasha muka kwanta, ni dasu, Da dare bayan mun kwantane Yaya Hamza yake ce min, Humaira zan so ace idan kin gama wanan karatun kici gaba da yin wani sai dai ina gudun fitanar Umma akan hakan, Don ko wanan din da yaya aka samu ta yarda dashi balle a dauko wani, Allah dai ya hore min nabar gidan nan kin ga alokacin duk abinda muka ga dama sai muyi abin mu a can babu sa idon kowa a kan mu, Nace cikin gyara kwanciya na kadan Yaya aiko wanan din ma na gode don yai min rana, Badon Allah ya hadani da gwarzon namiji irinka ba wanda yasan yakamata a rayuwa aida bankai ga haka ba, ma, Da, har yanzu ina nan zaune ba wani karuwa a rayuwa na irin haka ni gaskiya ko a,wanan din ma nagode gaskiya,, Ya rugumoni zuwa jikin shi yafara dan shafana hakan yasani gane cewa yau da dan karfin shi stress ya rage mai, ****** ********** ****** Kwanan Umma uku a asibiti aka samu sallama suka dawo gida take gida ya rude da yan shigowa gayar da Umma daga makwanta, Yan uwan su baban su hamza maza biyu suka zo suna fadan ba,a fada masu ba, Umma bayan sun wuce tace muna fukai afada maku kuzo kuga yadda nake ku karasa ni, Cikin masu shigowa har da matan gidan mu, watau su Ummina, Umma tana wani cika tana batsarwa wai ita tana da su a,rai tana jin haushin su a zuciyar ta, Suma basu dade ba suka fito zasu tafi Atika tace su shiga mana su gayar da ni a dakina, Duk da sun san cewa gulmace amma sun bi shawarata din sun shigo dakin nawa, Wanda zance wanan ne karo na farko da su mamana suka shigo dakina Don ko sun shigo iyakar su zauna awaje don haka shine karon su nabiyu da suka shigo gidan ina a cikin sa, Sunyi, matukar mamaki kwarai dan ganin dakina a yadda basu zata ba don sun samu dakin acan acan duk da ba, wasu kayan zamani bane a cikin sa Amma yadda yake a gyare yasa yana daukan ido, gwanin sha,awa Don ga gadon yasha gyara ga kujera na tsab ga akwatina daga gefe na aza mai wani dan kyale fari sai fridge dina daga kofan shigowa dakin, Ledan kasan dakin yana kyali sosai a lokaci don yasha guga kuma gashi babu yaran da zasu bata shi da dadti, Mun gaisa dasu sukai min ya maijiki kamshin dakin yai masu dadi sosai, Nace bari na basu sabon zobon danayi da rana yai sanyi sosai mama saude tace nabari idan sun tafi zasu aiko Aina ta karba masu, Mama dai bata ce komai ba tun shigar su don kamar ma a takure take a dakin dole ce ma tasata shigowa dakin, Hamza da yashigo ya tsaya rusunne daga kofa suka gaisa da su cikin girmamawa da mutunci, Abinda yasa Atika cewa a lokacin da suka fito kai jama,a watau dai ana zaton wuta a makera sai a samay shi a masaka, Gidan masu kudi babu tsabta ba tarbiya amma ga gidan tallakawa duk an samu abinda ake zaton samu gidan masu arziki,, Wai ashe sunje gaida Kubura shine suka samu gidan da dakinta kaca kaca kuma mijin da yazo ya samay su shine ya wuce kamar bai gansu ba ita Atikar ce tai mashi magana cewa, baigane su bane yana tafiya yace nagane ku ma,na, Suka fito ran su a bace kan irin yadda yai masu ita mama saude ce ma ta fara magana sai da Ummi tai mata magana cewa ba girman ki bane yaya, Kowa da halinsa ake zama dashi tunda baiwa yar mu wullakanci ba kuma tana zaune lafiya da abinta banga abin bacin rai ga mutumin daba kai ka haife shi kai mai tarbiya ba, Shine sukai shiru ba wanda ya kara tayar da zancen har suka dawo gida, To shine fa ashe maganan na a cikin rayuwan Atika sai yau take sakewa mama saude habaici, akan shi, Mama saude zatai magana Ummi take ce mata ai idan daji bai gama cin wuta ba yaya ba,aiwa kututure barka ko,? Atika tagane inda zancen Ummi ya nufa kuma ita Ummi din tagane cewa badon Allah Atika ta yabi gidana ba don sheri ne kawai da kissa irin na kishiya, Ai itama yaranta zasuyi aure aga inda suka dosa sai sukai shiru gaba daya, Lokacin da Aina ta shigo karban zobon su Hamza na gurin don haka sai yafita waje shagon su ya shiga yadauko omo clean ya saka masu aleda da sabulun wanki, Ranan kan habaici saida a kai fada da Mama Saude da Atika a gidan don ta kaita makura, Da Baba yazo ya samu ana wanan jidalin yake tambayan ba,asi shine Atika tai tsagal tana cewa zance nake ina cewa ashe kwanciyan hankali da samun wadatan zuci yana ga auren tallakan da akai gudu shine yaya tace wai ita nake sakewa habaici, Shi kuma Baba sai yace dama ai hakan gaskiyane ba karya bane, Yau kin fara ganin gaskiyan maganata ke nan Saude, Naso hada zuria da wanan yaron Hamza a rayuwata don gani da sanin halin yaron Amma sai kikai min tutu arai keda yar ki kukayi kokarin watsa min kasa a idon jama,an da na gaiyato a gidan nan, Allah ne ya rufa min asiri wanan yarinyar yar albarka ta share min hawaye na, Yanzu don gaskiya tafara halinta shine zakice wai kada a fadi don may, Ai dama kowa yasai rariya yasan dole zatayi yoyo indon wanan zaben tumun daren da kukayi ke da yar ki babu komai a cikin sa sai tarin bakin ciki da takaici don ko alhakina ya ishe ku, Cikin kuka mama Saude tace lalai duniya malam yau kuma yar Agwaice abin yabo a bakin ka, Ba hakana bane Saude dama ni yar Agwai ban dauketa komai ba sai "ya kamar kowa a gidan nan dama ai can sherin kune kuka,dauki tsana kusawa yar mutane, Ummi dake dakin ta taji abin yaki karewa ta fito tana cewa haba malam haba kubar wanan zancen haka dan Allah, Hakan ba girman ku bane dakai da yaya ko ina duniya ko bana nan Aisha yar kuce don gaba dayan ku bazamu manta da halarcin da kukai mata ba na zaman ta gurin ku, Ta juya gurin mama saude tace Yaya don Allah ki bar maganar nan aishi maso habaici dama maso fada ne, Atika daga kofan kitchen tace nidai na fadi gaskiya don dama daci ne gare shi, Da kyat Ummi ta rarashi mamata shiga dakin ya a cikin bacin rai don zancen atika da mijin su ya bata mata rai sosai, ****** ********** ****** Gidan yai muna tsauri saboda ga,damana tai nisa duk kudin Hamza ya watsa su a gona yana duban abinda zai girba idan lokaci yayi, Don kwanciyar Umma ya jawo masu rashi kudi a hannun su, Mun wayi gari dan kamun da zamu dama kunu a gidan yadan buwaye mu, Gashi babu abincin da zan dafa muna da rana muci, Hamza ya shiga dakin gurin Umma yana tambayar ta ko akwai dan kudi a hannun ta sai ta ara, mashi, har ya,samu ya mayar mata, Amma sai Umma ta kyankyashe kasa tace batada ko kobo a hannun ta ya tafi gurin matar shi ai tana sana,a ta ara mashi, Cikin dan marairaice murya yace Umma bata dashi ne dana karba a gurin ta ai, Wani kallo Umma ta watso mai mai nuna owo kana goyon bayan matar ka ko,? Cikin daga harshe Umma tace duk sana,an da take a gidan nan za,a ce wai bata da kudi a gurin ta, Hamza ya kara cewa bata dashi ne Umma ni na san da hakan, Daidai nan mama tafitowa daga dakinta taji wanan hayaniyan takaraso zuwa gurin, Hamza yace Umma wallahi duk kudin danai ta amfani dasu a,sibitii gurin Humaira na karbe su, Sai duk suka watso mai idanuwan su yace, wallahi mama a,gurin ta nai ta karba don su sauran yan uwana, sun ce min bazan samu ko sisi a gurin su, ba Duk wanda ma na tambaya bana jin mai dadi a,gurin shi, Shiru Umma din tayi don jin dan nata ya rantse cewa a,gurina ya karbi kudaden da ya kashe asibiti, Juyawa tayi sai mama tace duk kudaden da akasamu a asibiti fa yaya ? Bazaki bayar a rufa asiri dashi ba may ye amfanin samu a gida, Daki, tashiga ta dauko dari biyar ta miko mashi a wullakance, Yakarba yana godiya, yace zai je ya samo dan abinda za,a karya dashi, Bai fita ba daki ya shigo ya zauna da dari biyar din a hannun shi yana dan juyawa a hankali, Nafahinci cewa bazasu ishe shiba shiyasa ya rasa yadda zaiyi da daribiyar din, na hannun shi, Dubu dayan da ya rage min a dakin dama kayan zobo zan saya dasu nadauko na mika mai nace ga wanan sai ka kara ko, Yadago idanuwan shi da,su kai ja ya sauke su a kaina yana cewa cikin wani sanyin murya, Wanan kuma fa nace cinikin da nasamu ne jiya da wanda ke a,gurina dama kayan zobo naso saye dasu, Idan kin bani ke damay zaki hada zobon naki dashi ? Tunda ba,wasu kudi a hannun ki, Nace Alkah zai rufa min asiri insha Allahu na samu nayi ko da kadan ne, Ya karbi kudin daga hannuna badon ya so ba ya mike yana ce min bari nadan fita nagani Humaira, Zuwa wani lokaci yadawo da leda ya auno yar shimkafa a ciki da cefane yakawo min yana cewa nayi na rana kafin anjima yagani ko za,a samu na yamma Acikin dabaran mu na mata nai tuwon shikafa na hada da saurwn gari na daure sai yakai muna har da na yamma, Haka rayuwan wanan damanan tazo muna sai na,dan kulla cinikin dan zobon da kakaran nonon da nakeyi mu sai wasu abubuwa don har shagon namu ya kare, Kubura tazo gida yini taba da kudi a,sayo mata idomie ta dafa don wai bazata iya cin abincin da aka,dafa a gida ba,shinkafa da wake, Anya kuwa za,a samu abu a shagwan Hamza din nan don duk kwanakin nan duk abinda aka aika sai suce babu shi ina ga sun lashe, Tawani juywa tana kallon mama din tace wallahi mun ta aikawa hatta maggi cewa suke wai babu shi, Tsiya takai tsiya ke nan tunda har shagon ya kare ai nasan karya ta kare ke nan, Ita yar agwai din fa to mama ? Wanan mai gadon zurfin cikin aibazata taba fadin komai ba ita, Sai dai taita wahala a ciki takare haka na a wahalce, Wai shine da Baba yaso turani cikin wanan wahalan boni yaci har na lalace, Ai har yanzi shi bai san da haka ba don kwanaki yadan bada Omo akawo muna shine munafukar nan kecewa wai suna kina,aure gidan mai kudine amma yar Agwai tafiki sa,an daki da kwanciyan hankali, Halan maman Aina ko ? Ta tambaya cikin canza fuskanta tare kufulowa, Ita mana dawa zaiyi wanan zance in ba itaba mai kwarmaton banza, Wallahi mama sai nayi maganin wanan munufukar matan agidan nan don bazan kara bata fuska ba dani take zancen, Tamike tare da yafa dan yalalon gyalen da ta yafo a kanta tana cewa ina zuwa, Zaune nake ina raba abinci shimkafa da wake da mai da yaji nadafa sai kamshi man dana,soya yake tashi naji sallaman Kubura, A zatona ta shigo gaida Umma ce taji labarin bata da lafiya nai mata iso a cikin washe bakin naga yar uwata, Nace tazo su gaisa da Umma tana kwance daga kofan dakin ta, Cikin wani yatsuna duk da ta ramay ta fada yangan nan da kaudi irin nata yana nan kamar baya, Mun koma dakina da ita,na gabatar mata da abinci na aje mata zobo da ruwan sanyi, Nai mamaki kwarai danaga ta sake jiki ta kwashi abincin dana saka mata din, Tana shan zobo Hamza ya shigo cikin daga labule yana ganin ta ya dan daure yace a kubura kece a gidan namu tace eh, Nashigo ne naga yar Agwai tunda ka hanata zuwa gurina, Ban hanata ba idan tace zata ai zan barta ko na kaita, So kada kiga laifina bani na hana taba, Ta kurbe zobon ta mike tana cewa zata koma tana gida sai da yamma zaya tafi don yini ta,shigo nai mataalkawarin insha Allahi zan shigo gurin ta, Tana shiga gida mama ke cewa ke ina kuma kika,shige tun dazun, Tai gyatsa tace gidan su yar Agwai na shiga naci abinci, Kai amma Kubura baki san kunya ba a rayuwan ki wallahi da hat zaki shiga kici abinci a gidan wanan kaskantatun mutanen,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA JUMMA,AT MUBARAK YA JAMA,ATU MUSULUMINA ,,, FATAN ALHERI GAREKU YAN UWA MUSULMAI,,, FATAN DACEWA DA RAHAMAR UBANGIJIN MU DUNIYA DA LAHIRA,,, Ina zaune inda na idar da,sallah sai addu,oi nake jorowa na neman tsari Ubagina daga sherin mutun, kwaro, dabba ,ko aljan, dama duk wani abin cutarwa gare ni, Ina idar da wanan adduan najini wata wasai kamar har adduan nawa ya karbo ko, Saboda sannu a hankali naji duk wani kunci da na yini acikin sa ya shige min ya tafi, Sannu a hankali na fara jin hayaniyan mutanen gidan yana tashi, alamar sun fara,dawo daga guraren da,suka fita tsabgogin, tunda rana, Allah yai min wani baiwa na yaran Umma duk da bata sha,awan su kyautata min a rayuwan ta, Amma,su Allah ya saka masu damuwa da,al,amarina tare da nuna kulawar su a gareni koda kuwa sun min rashin mutunci ne yanzu yan mintina kadan zakaga sun huce sun biyo ni suna min magana, Hakan yasa nima,duk abinda zasu bukata a gareni muddin ina dashi bazan hana masu ba, Asmau ce tafara tambayan ina Aisha akace mata ina cikin daki na, Can na tsikayo muryan Hamza da Ibrahim sun shigo gida a tare, lokaci guda, Su din ma a,saman tabarman da su mama suka,shimfida a tsakar gida suka yadda zangon, su,,, Bayan sun gaisa da iyayyen nasu ne sai naji hira ta kaure a tsakanin su da mama hafsi wanda hirar ta,su akan yadda yake da gurin yin noma ne a,damanan bana, insha Allahu, Yake cewa mama,din ya kara samu ilimi akan noman zamani sosai yanzu don abin zai zo mai da sauki indan har ya sayar da abinda ke gare shi ya hada Yace kuma ya bada sakon a sayo mashi irin masu kyau da saurin fitowa, Har wani kasar ya tura a,sayo mai irin masara da wake na zamani da,zasu yi kyaun nomawa, Ibrahim ne yake cewa wai ina Uwargidan gidan na ta,shiga ne bangan ta,ba tun da na shigo, Tana dakin ta tana hadiyan rai,,tun shigowar matan nan na dazun, Umma ce take wanan maganar wace tun farko jefi, jefi, take saka masu baki a hirar su,, Wasu mata sun shigo ne gidan nan yau, Ibrahim ya tambaya a cikin mamaki, Mama ta bashi amsa da cewa wasu fitsararun mata yan zamani wai sun zo neman auren dan uwaka Sunzo ne kamun kafa a gurin uwar ku, akan dan uwan ka ya so su da aure, Wai da gaske kike ne mama Ibrahim din yake tambayan ta zancen cikin son jin gaskiya,a gurin ta, Sun zo mana inji Umma ta bashi amsa a takaice cikin gadara abin da yasa shi yarda ke nan, Ibrahim yace ikon Allah bako a,gidan nan ba don da ina gida,sai nai masu tsiya,da cin mutunci wallahi, Don basu da mutunci ku biyo mutun har gida cikin iyalin sa, don rashin ta ido, ga matar mutum agida, Ai dama shi mijin mace hudu ne don haka haka kulba dade kulba jima, sai kishiya ta shigo gidan na watarana Namiji fa mijin mace hudu ne don may zakuyi mamaki don ance ana son sa, Mama ta juya inda Umma take tana cewa da yake ke an maki guda hudun da zaki ce wai mata hudu zasu shigo Ai koda ma sun shigo din sai dai su,bi baya, in ma har sun shigo din, ke nan, Fitowa nayi a lokacin da naji sun kaca may da hira Hamza tankar bai gurin saboda yadda yake jin bacin rai, tare dashi, Fitowa na Idanuwan su a kaina sai a lokaci Asmau tace min a cikin zolaya Uwargida uwargida, Ashe yau amarya tazo ziyara ne gidan nan bama nan, Nai mata yar guntuwar tsuki ina cewa gashi ko bata samay ku ba sai ni aka sama a gidan nai maku kara ai, Tace da kyau uwar gida nan san kinfi da nan ai don haka nake kara sonki sosai Sannun ku da,zuwa nace yayin da na juya inda su yaya suke a zaune, tare da uwayen su Nace cikin kallon fuskan shi yaya, akawo ma abincin ka a nan ne,? Ibrahim yace dakin kyauta sai ma muci a tare ke nan tunda na shigo na juya don na dauko abincin, Asmau takata cewa ashe kwanan nan zamu sha kallo ke nan, gidan nan, Nace gawa kuma ga amaryan taki ko ? Ita da take bakuwar ku Don ni kin saba kallona ai ba yau ba kin sanni tun ina yar karama, Mama tace Ibrahim wasu irin tika tikan matane fa wai su yan mata ba kunya basuji suka,shigo muna, kamar uwayen mata, Amma mama sunyi arziki ban gidan nan wallahi dana ci masu mutunci yau,Ibrahim din ya ce hakana, Sai lokacin Umma tai magana tana cewa kaci masu mutunci a kan may don sunce kawai suna son dan uwan ka, ? May ye a cikin aure in har ya,shirya yin auren, shi,, Wa ? Umma ni ! Hamza ya juyo a gagauce Yana tambayan Umma din,, Aure yanzu haba Umma haba, sai kace wanda bai san ciwon kan shi ba don Allah Umma kibar zancen nan , Wallahi abin yana matukar bata min sosai idan na tuna wai,ni halima zata bude baki tace Tana Sona da aure sosai, Ai, dole kafadi hakan tunda matarka rayuwan ta ya baci, kai ko baka,son bacin ran yar gwal din ka, a gidan nan Ni abin yana bani mamaki don ban san lokacin da yarinyar ga,tai wani wayyon kishi ba haka, har da nuna bacin ran ta tashige daki Tana hadiyan Rai, it's daya, Gurin randar ruwan mu na nufa ina zuba ruwa a butocin mu don safe,Amma Ina jin zancen sure Umma yadda take magana zafi zafi, Kai haba Umma kishi ai dole ne ga mace tayi koda kuwa bata,son mijin ta, Balle auren so irin na yaya da Aisha, Asma,u tai farat tance, wani so kuma, auren hadi har yaushe ne so ya shiga tsakanin su, Ke dai fada min inji Umma tacewa Asmau din da tai magana haka, Ibrahim kasan halin yayana indai taga ci a guri bata da wasa da,wurin, mama hafsi ta fadi hakan was Ibrahim, Duk ina jin su amma,sai harkokina nake cikin kwanciyan hankali batare da nuna,wani damuwa ba,. Sai dai na ciki na ciki don wani irin tukuki nake ji a raina amma,sai na,daure na shanye a fill, Mata haka tirka tirka,don raini hankali kuzowa mutane wai ku aure kuke so a kama,maku, Inji mama hafsi ta Mike Tana fada Tana tafiya ita kadai,,,,,,, ****** ********** ****** Kwance take kanta a sama, Tana kallon silindin dakin da suke a cikin sa, Yanzu kina ganin cewa wanan matar zata yarda ki aure ma,ta,da Bicky kewa Lima wanna tambayan, Nice fa Lima, ta,dan bugi gaban ta kadan da hannayen ta, . Tace na,fada maki sai na,aure yaron nan tunda ina,son shi, Dayar tace ni wallahi kin san matar shi ta ban sha,awa yar yarinya karama kamar da ita kamar yar Fulani, Gaskiya,sun dace da junan su don daidai auren su ke nan , Shi gashi matashi itama yar matashi dagwas da ita abinta, ga tsabta ji dakinta tas dashi har ma tsakar gidan duk a gyare, Bicky idan kina,maganan yarinyar nan kina bata min rai sosai wallahi raina yana matukar baci don ban son na,ma,tuna cewa wai Hamze yana da mata a gida,, Ta wani koma ragwab a saman kujera ta zube ta wani lumshe idanuwan ta a hankali tana sauke numfashin ta,, Can zuwa dan wani lokaci ta,ware idanuwan ta, ta wani sauke ajiyan zuciya Tace wallahi Bicky Hamze irin mazan da nake so ne a,rayuwa na, Don komai nashi yayi min wallahi guy din ya hadu ya hadu, bazaki gane bane, Ko ya hadu yaya zakiyi dashi tunda ba sa,ar yin ki bane shi Ki tunafa irin yadda maza masu kudi ke nuna kwadayin su a kan ki, Amma zaki zo ki wani mutu son yaro karamin wanda ko sa,an kannen ki bai kai ba,a,shekaru ai sai ki saka aimu na dariya wallahi, Bicky ba zaki gane bane bazaki gane ba tunda ba choice din ki bane ke, Bari kiji ko nawane zan iya kashewa akan wanan guy din don kawai na samu na mallake shi ya zama nawa, kuma no kadai, Yaya zakiyi da matar tashi zan barta ta zauna man as pending, su zauna a gidan gado ita da yan uwa,suyi ta,fama ni kuma zan jaye shi mu koma wani guri can daban, Na mantar da Shi kowa nashi da komai nashi Kinga baby masu saka muna ido ke nan Ki dai yi a hankali don kada kwabar ki tai ruwa inji Bicky Don tun farko kin dai ji abinda aka fada muna a kan shi, Ki manta,da,wanan zancen nasan yadda zan bullowa zancen ai, Hmmm ni nasan guy din yana da kyau kuma zai iya wadatar dake don nasan yana daga cikin abinda yasa kike son shi don ganin shi karfafa da kikayi ko ? Tai wani kara lumshe idanuwan ta tana murmushi can ta,ware su tai ajiyan zuciya tace Ashe kin fara fahinta ta ke nan Bicky kin dai san bai da,wani abinda zai bani ,idan ba,wanan harka ba Don haka idan ba zaki tayani faiting ba to ki daina damuna akan zancen kawai, Lima tasake cewa idan ma har baki son zancen to ki yi shiru ki daina,accusing din zance haka da yawa please, Don ni ina,so kuma zanyi don nai niya, hakan, Allah dai ya taimaka inji ita Bicky din ta juya taba Lima din baya wace ta mayar da sunan ta halima tun tana primary, sunan kuma yabita sosai yanzu, Tana mishon bat da musulmi da sunan, ****** ********* ****** Da,farko yasha jinin jikin shi sosai akan abinda yake zato ko tsanmanin zan yi, Amma,ga,mamakin shi duk abinda,na,saba yi mai ban fasa,ba don haka yadan rage damuwar shi, Ya shigo gida a lokacin ni har na kwanta inda ya,samay ni har na kwanta don nagaji sosai a lokacin, Sai dai ina a cikin shirina na kwanciya kamar yadda na saba a kullun, Naji ya,dawo daga,wankan da,ya,tafi duk a lokacin nan,ina lafe ban yarda na motsa ba, Don kada ya gane cewa ai idanuwana biyu banyi barci ba, Bayan ya gama komai na,shirin kwanciya naji ya hawo saman gadon a hankali, Matsowa yayi zuwa jikina naji ya,matsoni gam a jikin shi ya fara sauke dan ajiyan zuciya, Har a lokacin ban bude idanuwa na,ba,da,suke a rintse gam,ba Wani ajiyan zuciyar ya sauke kamar ta mamaki batare da ya,sakeni ba daga jikin shi, Cikin muryan shi mai sanyi naji ya ce min nasan yau ranki a,bace yake a gidan nan Humaira, ? Nasan an maki cin fuska wanda zai sa ki zaci ko ki dauke ni a matsayin wanda ke can wani gari yana barikancin sa, da cin amnan ki, Tare da matan banza kadangarun bariki ina yadda raina ke so, da su tun da har sun Kai ga biyoni gida you, Sai a lokacin na bude idanuwana da sukai min nauyi tare da dan sauke ajiyan zuciya a hankali, A cikin natsuwa na, kalle shi tare da sauke wani lalausar murmushi mai ma,ana, don kawai na gusar mai da zargin shi a kaina,, Na soma magana da cewa nasan da cewa shi aure nufin Allah ne musali, mu diyan hausawa zan iya cewa mun gaji zama da kishiyoyi don duk macen da tai aure tasan cewa mace hudu Allah ya kindanyawa mazan mu musulmai su aura Don haka banga wani abin da zai sani tayar da hankalina ba yadda kuke zato, Kamar yanda Asmau tace auren hadi ne nida kai, ba bu so ko kauna a cikin sa,, Sai dai zaman rufawa juna asiri ina ga ai zaifi kuyi auren ku da wacce ke sonka, don ni kaga auren hadine, aikai mun dakai, Na sani babu abi da zai farantawa Umma rai a gidan nan kamar taga ka yo wata mace mai haihuwa da kuma wayewa yar masu hannu da shuni, ba, irina diyar talkawa ba,, Shiiii naji ya yi min tankar yadda ake tsayar da yaro daga barna ko wani abu, Bana son jin zance auren hadin nan dakike ta nanatawa a tsakanin mu, Idan ma da farko muna zaton aure ne na hadi akai muna ai yanzu ni dake mun san mu wuce zancen wai hada mu akayi, Don ni kinfiye min ko mai yanzu a duniya ina alfahari da kasancewar ki a matsayin mata,ta aduk inda naje duk inda na samu kaina, Humaira ke mace ce da duk wani namiji ke fata da burin mallaka irinki a rayuwan shi, Don may zan tsaya nayi sakaci da baiwa da kyautar da Allah yai min, Hakkuri, tsabta, tattali, ni,ima uwa uba sanin ya kamata duk Allah ya,wadataki dasu, A,rayuwa ke uwace da ko wani namiji zaiyi fatan malakarwa diyan shi irin ta, Zance su Lima, kuma da suka zo wanan ki barni dasu don wallahi idan kin yarda dani rantsuwa musulmi daya ce, Babu wani zance maka mancin abinda tazo muna dashi gidan nan a tsakanin mu, To amma fa nasan cewa ba lalai ne ki yarda da zance na ba don sun riga sun saka muna zargi a tsakanin mu ko, Wani irin sanyi naji a raina don ko ba komai Hamza ya gwada min ya damu da damuwata a fili, Ban san lokacin da na daga hannaye na na makale shi a jikina na ba kamar yadda shima yake rungumay dani, Nace ni matar ka ce yaya ka daina rantse min don ina kasa da kai akoda yaushe, Jikin Hamza naji ya dauki rawa tankar wanda yasha wani irin tsumi ganin haka nai amfani da,damar na kara narke mai a jikin shi, Nafara dan sarafa shi a hankali a nutse kamar yadda nasan yafi bukata,daga gare ni,, Hakan ne ya ban damar mallake abinda dama can mallakata ce, sai yafara sake sambatu yana fadar maganganu akan Lima da Umma, Hannuna na,sa na toshe mai baki daga haka muka nausa wata uwar duniyan baka jin komai a dakin sai gurnanin mu, da ya rude dakin, Yana makale dani a jikin shi bayan komai ya lafa a tsakanin mu, ya samu natsuwa irin wanda nake son gani a gare shi, Gyaran murya naji ya soma yi abinda yasani kara lafewa a saman cheast din shi ke nan, Humaira, zan so ace mun bar gidan nan idan da, da hali mun canza wani guri badon komai ba sai don mu samu kwanciyan hankali daga fitinar Umma, Haba yaya, ni fitinar Umma a gare ni tankara wani karin haske ne a,rayuwata, Don kayi ba daidai ba an maka fada ai ya zama gyara kayan kane, Ka ga ba zai zama lafi ba, Wani irin sanyi Hamza ya kara ji a ranshi, tare da sauke numfashin ajiyar zuciya a hankali, Yace hakane Humaira a hankali to amma kuma gyaran har ta kai ana son yiwa kwanciyan hankali na illi mai yawa, irin haka Ya kamata duk abinda za,ayi ayi adalci a cikin don bawa kowa hakkinsa, Naso ace Umma ta rike ki tankar yar ta data haifa komai za,ayi a gidan nan ai muna adalci akanshi, Don fahintar da tayi cewa ina sonki Humaira kuma ina kaunarki shi yakara saka Umma nuna maki wanan halaiyar, ta tsana da kiyayya, Umma sam, taki la,akarin cewa zamanki tare dani shine kwanciyan hankalina da su ma,Kan su, Don haka na roke ki ina kuma kara jaddada maki cewa ina son ki Humaira kuma ina kaunarki fiye da duk wani abinda na mallaka a duniya, Yanzu ni fatana da buri na shine na samu wani dama wanda zan nuna maki irin halarcin da kike gwada min na tabbatar maki da cewa ni cikakken da namijine , A hankali na kai hannuwana a,saman kirjin shi ina dan shafawa a hankali nace ni ko hakan ma na,gode Don ka gwada min cewa kai dane na halak, don ka fahinci cewa wani irin zama nake a gidan nan wanda a kullun kokari kake koda a,sace ne ka,ga farin cikina, duk da matsin da Umma take muna akai, Sai yai murmushi alamar yaji dadin zance na har a cikin ran shi ,,, ****** ********** ****** Mama hafsi a kullun cikin kwantar min da hankali take a gidan mu, sai rarashina take tana nuna min yadda zan zauna dama ko wacece a duniya, Wanda hakan ba,wani bakon al,amari bane a guri na Don, da shi na bude idanuwana, a gidan baba Mudi, shi, naga mahaifiyata, tana yi watau hakkuri ke nan, Don haka idan ban gaji hakkuri ba ai naiwa Allah buttulci ke nan, Duk wata diya ta gari da irin tarbiyan uwar ta take zuwa gidan mijinta dashi Dashi kuma zata zauna da mutanen da Allah ya hada ta zama dasu, Don haka tankar ban san Umma tana sake habaicin ta ba sai harkokina nake a cikin sakin raina, Nakuma ji dadin shawaran mama hafsi a gare night at Don takara min haske masu yawa a rayuwata, Umma ta matsawa Hamza akan sai ya, saka mata fankan da Lima ta bada kudi a samata a dakin ta, Dole badon yaso ba ya sayo fankan mai hadawa yazo ya saka mata a dakin ta,, Ranan zokiji zance a wurin Umma kamar tsokana, Yi da mai arziki ka,dangwali arziki yafi zama da matsiyaci kullun tsiya, Aini wanan tuntube ne da arziki har a gida,a kofan dakina, Ina zaune a cikin harkan tsiya Allah ya turo min arziki har tsakiyar dakina, Zama da yan arziki irin wanan har za ai min bakin ciki a hanani cin arziki ina kallo, Mama Hafsi ne tagaji da habsicin Umma din, tabata ansa da cewa Shi mutum in yana a,raye ba a debe ran arziki agare shi ,sai randa ya mutu, Hakan yasa Umma yin shiru don tasan idan ta matsa abin ba,zai masu dadi ba, Mama tace kuda dama ai,guri kwadayi yake mutuwa , Wanan dalili yasa Mama Hafsi cewa zata koma garin su yafi mata zaman da Umma Don halin yar uwarta yana matukar bata tsoro yanzu, Kwata kwata Umma ta canza a yadda ta San halin ya da farko, ta rasa gane may be damun rayuwan ta haka, Hankali yaran Umma ya tashi don sun san cewa mama,hafsi tana da,matukar amfani a,gare su, Ranan ba karamin tashin hankali akayi ba a gidan daga karshe yaran maza su suka yanke shawaran cewa zasu gyarawa mama dakin dake a,cikin gidan daga can gefen daki,na ta zauna a ciki Tunda tace Bata shiga inuwar kafira ta sha iskan fan Kan da kafira ta saka masu a daki, Amma said Umma tace ai kyauta tabata ba rokon ta tayi ba itace ta Bata, ganin ta bijere sosai yasa Umma tai nadaman batawa yar uwarta rai da tayi duk da ba da ita, ta ke sake zancen ta ba dani take yi amma sai ta juya zancen cewa ita Umma kewa gori, Ba bata lokaci aka gyarawa mama dakin taba da kudi aka sayo mata katifa dan madaidai ci tasaka tare da wasu yan tarkace, Bayan hankali ya kwanta mama hafsi ta zaunan da yaran yar uwar nata ta maza, ta basu shawara da su fara sana,a don tallafawa rayuwan su, Ta ware masu kudade daga cikin kudin ta taba su tace kuma tabasu ne kyauta Allah yasa wa kowa albarka a nashi, Mata kuma hardani a ciki taba mu kyatan dubu goma goma tace tana son kowa tayi amfani da shi gurin tallafawa rayuwan ta, Wanan abin da Mama hafsi tayi yasa Umma tai sanyi sosai don bata taba tsamani halarci yar uwar na ta ya kai haka ba, Don Bata bakin ciki ga kyautatawa diyan Umma din Tana daukan su tankar itace ta haifi abinta, Ga, Sabbin fankan daki guda biyu na sama, aka sayo mamata saka guda a dakin ta guda a namu dakin, Wanan abin ya kawo muna kwanciyar hankali a gidan don mama ta kashe bakin Umma murus sai gida ya koma kamar farko, Na kaiwa Ummi na dubu uku daga cikin kudina, Nace ta dan juya itama ta dan fara sayar da dan wani abu, a gida Don income yadan din ga shigo mata, Naba su mama Saude dari biyar biyar Atika yar iyawa nan ta fara cewa ikon Allah a she kwanciyan hankali da,sanin ya kamata yana a gidan tallakawa bamu sani ba, Muna can muna na bakar wahalan banza said anmuna wulakanci a bamu, Mama Saude ta fito tana cewa tau kaza aci a goge baki yau kuma dari biyar ya tsone maki ido har kika manta da komai, Fadin gaskiya nayi koda kuwa zaki ji haushina ne dole ce a fadi gaskiya, Ummi na tana dakin ta bata fito ba take sauraren su cewa take a,ran ta kan ku dai ake ji, ku karata can gasu gada, An sayo wa Ummina,su kayan yaji da sugar ta dan kulla ana saye a cikin gida, Wanan ne ya ke yankewa mata zaman banza yin sana,a a gida komai kan kan tar sana,a, zai kawo maki dauki ta hanyoyi da dama,în har kina Dan juya naira, ****** ********** ****** Sosai Hamza ya mayar da hankalin shi akan aikin gonar shi, Wanda zan iya cewa noman zamani, ne yakeyi, Mai amfani da taki irin na zamani da fasaha, Idan ya fits tun safe baya dawowa gidan said da yamma list zai dawo a gajiye , Inda kafin ya dawo ya Sami na Dora Mai ruwan zafi don ya watsa ya watsake, Zai Sami abinci Mai zafi yana jiran shi tare da kunun aya ko zobo Mai sanyi ya Kora, You ma ya dawo kamar kullun a gajiye ya iso gidan duk da gajiyan da yadawo dashi gurin su Umma yake fara zuwa ya gaida su tare da masu Yaya gida jin yan matsalolin su, A kwance ya samu Umma wace take Dan dukule, Yananayi yanuna yau Umma din batajin dadin jikinta, Idanuwan shi kar akan mahaifiyata tashi inda yake tambayan ta cikin nuna damuwar Shi gare ta, Umma lafiya like kwance a cikin wanna yanayin haka,ga yamma tayi, Cikin dan marairaicewa take cewa you Ina dan jin kamar masasara yana son kamani ne, Nai yai mata sannu tare da cewa bari ya dan watsa ruwa yafita ya Sami mata magani chemist, Ruwan Sha na fara gabatar mashi said Kuma ruwan wanka, bayan yafito ya shirts take me min Humaira idan da Dan kudi a gurin ki kibani na Dan sawo was Umma magani tasha wai bata jin dadin jikinta ta you, Da sauri nace subbahanallahi ai ban sani ba don naga Bata Dade da shigowa gidan ba, Inda nake dan tara cinikin fridge Dina na bude na kirgo kudi dubu days na bashi ya fita, Sai da nai sallah Don lokaci yayi na fita zuwa gurin,Umma don na duba jikin nata, Da kyat Umma take karba min amma Sai na sa a raina zafin ciwone yasa ta bata iya ansawa sosai,, Na dan dauki lokaci zaune a dakin daga gefe guda Ina mai mata sannu da jiki, Sai taga dama take karba min sannun da nake mata din, Hamza da Ibrahim suka shigo dakin dauke da ledar magani a hannun su, Ibrahim yana cewa Umma jikin ne Kuma yau yadan tabu Ashe,? Nan sukai mata sannu tare da fatan Allah ya bata lafiya, ta amsa da Amin sai da tasha magani ta Dan Sami sauki masasaran ya dan sauka, Duk muna dakin Mama Hafsi Tana dan mata magana da ta Dan tashi ta zauna ko hankalin yaranta zai kwanta, Da kyat ta dan cewa mama Tana son Dan mikewa ne tane tayi sallah, Nan nafita da sauri na fara aje mata takalman ta daga kofa, na zuba ruwa a but na aje mata daga kofa , Ganin ta kewaya zuwa bayi zatayi alwala idan tafito yasani komawa dakina, Har tafito tashiga daki zata fara sallah ne yaran suka fito shi Hamza sai ya,yo dakin mu, Abinci ya zauna yaci sai Kuma ya buge da waya da abokan karatun shi, ya dauki lokaci Yana kwance rigingine Yana wayan shi hankali a kwance, Ina zaune Nima a kasan daga gurin kanshi idan baka luraba zaka iya, cewa a cinya Kan shi yake Saboda zaman gab gab da mukayi da junan mu a lokacin, Sai ga Sa,a datu, autar Umma ta shigo dakin take cewa yayan mu Umman mu tace na Kira ka,, Yace Sa,a datu har yanzu baki San cewa kin girma bane baki iya sallama ba idan Zaki shigo guri, Tajuya cikin zunburo bakin wai, an mata fada don may zai mata fada haka, Tana shiga daki uwar taga yanayin ta take cewa, May ya faru halqn may akayine wai? Cikin turo baki gaba na shagwaba take cewa wait dan nashiga dakin Yana kwance a jiki Aisha shine ya Koro ni, Bai wani Bata lokaci ba najin Umma tana Kiran shi yamike zuwa gurin karba Kiran nata, Ai yana shiga Umma ta hau a lokacin, jiran shigowa shi kawai take yi, Yashigo da sallama Yana cewa Umma sannu ya jikin naki, ya daina ko ? Kai Mara kunya kamar want wanda ya dami da jin jikin nawa, kakoma can gurin wanna yarinyar da tai gadon iya hilla har tagaji, Itace kawai damuwar ka a yanzu a gidan nan Sam baka san damuwata ba ballet ciwona ya damay ki, Kana can gindin mace Tana Maka kisisina da kutungwila irin wanda ta gada ga uwar ta, Shine har zaka want Koro min yarinyar don ta katse ma jin dadin da kakeyi ko, ? Da sauri ya juya ya dan kalli Sa,adatun cikin mamaki, yace ita sa,a,din want abu tagane Ina yi, Ina ways ta samu munayi da Kabir tashigo dakin ba sallama nai mata fadan takoyi shiga guri da sallama, Ai sai ka koma gurin wace tafini daraja da kima idan ta sallamo ka sai kazo ka gwada min yadda zan kara Shan maganin, Innalillahi wa,inna alaihim raji,unm ya furta yace Umma abinci naci sai ga wani abokina ya bugo min waya,, Nan dai Umma take Mai fada a cikin kakausar murya abinda ya sa duk jikin shi yai sanyi, Daga inda nake tsaye Ina jin may Umma ke fadawa don haka Nasha kwana na juya baya zuwa dakina, Zaune nake a dakin nawa nai tagumi da hannu bibiyu don tuna laifin da naima Umma a rayuwana ko zan gane don abin yai tsauri da yawa tsakani na d ita, Najin an dago labulen dakin nawa abinda ya haddasa min Saurin dago kaina kenan da jajayen idanuwa na da suka rine sukai ja jajirdon bacin Rai,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU SEENABU 👑 SARAUTAR MATA 👑 2⃣9⃣ RABBANA, LA TUZIGH QULUBANA, BA,DA, IDDZZI, HADAITANA , WA HAB LANA MIN LADUNKA RAHMATAN INNAKA ANT AL WAHHAB,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA DON ALLAH YAN UWA INA BARAN ADDU,A AGARE KU KU TAIMAKENI KU TAYANI ROKON ALLAH AKAN ABINDA NAKE BUKATA A GURIN UBANGIJIN MU ALLAH SUBBAHANAHU WATA,ALLAH,,,, Wasa wasa yanzu anfi sati Umma tana kwance masasaran yaki tsayawa har ya kaita a kwance, sosai, Yar uwar ta mama hafsi ke faman dawainiya da rashin lafiyan Umma din, sai ni dake faman dafe dafe a gidan Naka shiga dakin fiye da a kirga don na gaida Umma na Kuma duba lafiyan yata, nakuma wanke kayan da tai amfani dasu, Ranan da ta cika sati Daya a ranan na shiga daki na Sami duk yaran Umma suna a kanta, tana cewa sanyi take ji su rufa mata bargo, sai rawan dari take daga kwance, In tsaye daga gurin da nake ina nazarin abinda ke damuwar ta gashi sai faman dirka mata magani akeyi Ina mai kura mata ido, sai naji suna cewa wai, za a Kira Mai chemist yai mata allura, Ni ko na fahinci wani abu a jikin nata sai dai Ina tsoron magana suce ban San komai ba, na jawa uwar su mugun ciwo nake mata fata, Daga inda nake tsaye daga bayan su nace amma yaya da kiran wanan mutumin ai da kawai akai Umma asibiti gurin doctor ya dubata zai fi wanan, kaura da kai din da ake tayi a gida da ita, Duk kan su suka juyo inda nake suna masu sako min idanuwan su, gaba dayan su Kaji malamar asibiti fa aida sai ki dubata idan har kin gane wani abune, jibrin ne yai wanan magana, Mama da Yaya hamza suke cewa tun da kukaji Aisha tai wanan maganan akwai abinda take hasashe ke nan, Ibrahim yake cewa, cikin, tambayana Aisha don Allah kokin fahici wani abin ne suna masu sako idanuwan su a kaina, Cikin harshe turanci wanda zance duk gidan nan ko shi Hamza din bai taba sani na iya turan ci ba haka nake masu bayani, komai, Don ina gudun yi da hausa Umma taji tace ina mata mugun fata ne, Jikin su gaba daya yai la,asar suke cewa gaskiya ya kamata subi shawara na don bai kamata ace sun aje ta a gida ana magani daban ciwo daban, Fita Hamza din yayi zuwa wani dan lokaci sai gashi ya shigo gidan a cikin, saurin shi tun a kofa yake kiran mama, Duk muka yo waje don son jin may zai fada tunda kowa a tashe hankalin mu yake, Ance mai baki bai iya ciwo ba don Umma ta wani koma ragwab da ita duk tafita hayacin ta, sai nishi take daya daya Mama ga mota a,waje mu tafi ko? Ina shiga dakin naga yadda idanuwan ta suka juye sukai, weak a lokaci guda, Da sauri har ina ture Ibrahim na karasa bakin gadon a gaban Umma na kamo hannun ta ina dan massage din hannun nata a hankali har wani dan lokaci, Sai naji tai wani irin ajiyan zuciya a hankali sai da kowa yaji a,dakin, Duk sai suka kara rudewa hankalin su ya tashi, Nace Mama ku kamata a tafi sai dai aiwa driver magana ya tuka ta a hankali don Allah saboda tana bukayar resting sosai,, saboda jikin ta is already been weak, Hankalin su gaba daya ya tashi sai wasu suka fara kuka suna cewa wayyo Umman mu Umma don Allah kada ki mutu ki barmu, Cikin tsawa mama take masu fadan wani mugun fatane haka sukeyi ai ciwo ba mutuwa bane, Ke Humaira dauko hijjab dinki mu tafi asibitin a tare zaifi, Ba musu na shiga daki kamar yadda ya umurce ni na dauko hijjab dina a tare muka tafi, Ni da mama muka zauna a baya tare da Umma ina dan mata masage yadda ya dace ce, Mun shiga inda duk wani abinda ya dace ayi na ganin likita tare da Yaya Hamza mukayi kasancewa akwai yan makarantar mu da su kazo practical a gurin, Sosai zuwana ya taimaka nan da nan muka shiga gurin likita don bada bayani, abinda ke damun ta, Likita ya tambaye, ta ta kasa magana kamar maijin tsoron shi, dole ban san lokacin da na bude baki nafara yiwa likita bayanin yadda Umma din tafara ji har zuwa yanzu da abin ke son zama mata blood pressure, Tambayana yayi wasu irin medication mukai mata a gida nan ma tirya tiryan nai mai bayani har zuwan mu asibiti , Yadan bugi taburin gaba shi yace she is, very luck dat you are around if not she will die or be in critical condition,, Umma tana rike a hannuna sai nishi take guda,guda, tana kara kamay wa,cikin tashin hankali, Are you a student ? Tambayan da yajefo mi ke nan lokacin da nake kokari gyarawa Umma zanin ta daya rankafo, Nabashi amsa cikin gyada kai da cewa yes, Where are you schooling ? Health and technology nabashi amsa a takaice tare da mikewa ina kokarin jan Umma gurin gadon da yace tahau, Sai yace, interested,,, Yakamata ace parents naki nursing suka kaiki ba health ba, Don you are very intelligent gaskiya yakamata ace nursing kika tafi, Maigida na nan yake son nayi karatu shiyasa na tafi can din, Naba shi amsa a daidai lokacin da nake gyarawa Umma kwamciya, Na juya nafita nan na barsu da Yaya Hamza ina fita na samu har su yaya Ibrahim da su Jibrin duk sun shigo asibitin mama tana masu fadan an watse anbar gida babu kowa, su Asmau, su koma gida, Amma sai sukai banza da zancen ta kamar basu ji ta ba, An dan dauki lokaci yaya yafito yana cewa an bamu gado za,a kwantar da ita, Nan muka shiga kuma dawainiyar kwantar da umma wace daga zuwa akai mata allurai masu karfi da kara lafiya sai drips da akai setting za,a kara mata, Ganin komay ya dan kammala nace zan koma gida don nai mu na abinci da za,a kawo asibitin, Tuwon masara,nai masu da miyar kuka,da nama,a cikin sa kamshi kayan yaji da daddawa yana tashi daga cikin miyar,, Ranan ni kadai ce a gida sai ban samu komawa,asibitin ba ina fama da,aikin gida, da yai min yawa, Sai dare sosai ina daki banyi barci ba a lokacin don tsoro nake ji sosai saboda ni kadai ce a gida, duk suna,asibiti gaba dayan su gidan, Ya,shigo gidan inda shima tun a,waje yaga gidan yai mai wani fadi fayau, Ya shigo da yar mashin din shi daga ciki ya kaita kofan mama inda yake ajewa ya kulle, Sannan ya juyo zuwa dakin mu cikin takon shi na, natsuwa, Zaune nake saman kujera na idanuwa na,a kan kofan shigowa, Yana shigowa na gyara zama na mike sosai ina cewa sannu da zuwa Yaya ? Ya dan rugumoni daga gefe tare da shafan dan kumci na yana cewa cikin harshen turanci ni ban son kiran yayan nan da ake min fa,, Murmushi nayi nace anfitar dani a cikin kannen ke nan ko kuwa, Kafin ya kai ga bani amsa sai nace ya kabaro jikin Umma din da sauki yanzu ko? Ya ce da sauki don tana ta barci ne har yanzu sai ruwan ake kara mata nace shine lafiyan ta, Abinci na gabatar mai tare da mikewa nake cewa ga ruwan wanka, zan kai ma bayi, Har na kai ruwan wankan bayi na dawo yana zaune inda na barshi yayi tagumi da hannayen shi, dukka biyu, Lafiya dai yaya ? Natambaya cikin son jin may yasaka shi tagumi haka, Ya sauke yar ajiyar zuciya yace Humaira dole ne ki ganni haka don ban da kudi a hannuna duk na zubasu a gona gashi dan kudin mama da ta ban na saya mata kangon gida dashi, Ga kuma lalurar asibitin nan yataso komai na kudi ne yanzu asibitocin mu ba tausayi a cikin su, Kudin zasu kai nawa, ? Natambaya cikin son jin yawan abinda zai bukata na kudin, Sai daya dan sa hannun shi a bakin shi ya busar da wata iska mai nuna bak8n ciki Yace na, dai rike koda goma ne don test test din da ake yawan yi mata, su ne ke cin kudin, Nace akwai kudin da mama ta bani na bawa Ummi na daga ciki sai na,sana,ata dana tara a asusuna zan fasa naga may ke a ciki, Yace kinga kuma ga abinci don duk da,asibiti gurin jinya ne amma yan sa ido na gurin suna kallon kalar abincin da ake kawo wa mutum daga gidan shi, Wanan matsalar su ce don wani ma idan ka rabu da shi har abada,bazaku kara haduwa dashi ba, Yace hakane Hummaira amma ya kamata na samo dan shinkafa da,sauran abubuwan da,za,ayi amfani da,su, Nace dare yana yi ruwan wankan ka yana a cikin bayi kada yai sanyi ko wani shedani ya taba ma, Yana fita na dauko a susu na nafasa nazauna kasa dirsha nafara kidaya kudin dake ciki na,samu shauku da dari takwas, cif, Yana shigowa da ruwa a jikin shi yana daure da zani na da ya daura da zai shiga wanka, Na ce mai ga kudin na fasa asusu sha uku ne da dari takwas na samu a cikin sa, Yakai zaune bakin gado yana mamaki yace duk da wanan sana,an kika tara wanan kudin haka? Gaskiya sana,a tana da amfani sosai shiyasa akace zaman banza baida amfani a rayuwa, Yanzu gashi zamu ci albarkacin sana,ar cikin gida a gurin ki, Yakarbi kudin yana cewa Allah ya bani ikon biyan ki su a cik8n dadin rai kamar yadda ya dace duk wani wanda ya dauki bashi ya fadi, Ranan ba wani abinda ya shiga tsakani na da Hamza don ya kwana ya na juyi saboda damuwan ciwon mahaifiyar shi,dake a rayuwan shi, Washegari tun da asuba na tashi na,dora ruwan kunu da sauran aiyu ka don nasan bawanda zai taimaka min da aiyukan, tunda mama bata gidan tana asibiti a can ta kwana tana jinyar yar uwar ta, Ranan bani na samu kaina ba sai kusan karfe daya alokacin komai da ya kamata nayi nayi nagama na gyara gidan fes ta ko ina, Nai wanka na sa wasu atamfana wax masu ruwan blue color, Shigowan shi gida don daukan abinci ya samu na shirya nima sai dai ban yarda mun fita ba sai da na zaunar dashi a cikin dubara ya danci wani abin sannan muka rufo kofan gidan zuwa asibiti, Kofan gida zamu hau mashi muka hadu da Baba Mudu wanda ya fito daga cikin gari, Hamza ya sauka ya nufe shi acikin alkunyar sarakuta kamar kullun suke gaisawa, Nan Hamza ke fada mashi Umma ce aka kwantar a sibiti ba lafiya, Ba ya dago kai gurin da nake a tsaye da kullan abincin dana kulle ga wani dan kwalina, yake cewa, Kin aika cikin gida a fadawa iyayyen ki kuwa Aisha ? Nace Baba ban samu yaro ba yau duk su Aina basu shigo guri na ba, Yace kin san yau ana zuwa boko babu kowa duk sun tafi makaranta ku isa insha Allahu yanzu zan karaso nima insha Allahu, Mun samu ba laifi Umma ta samu lafiya don tana zaune saman gadon ta tana magana da kishiyoyin Anty Zarau, Mun gaisa da,su nai masu yaya maijiki suka karba min da,Alhamdullahi, Na aje kwanonin abincin daga can inda naga kayan abin karin safe dana aiko masu dasu, Na lura Umma sai da kyat take amsa min gaisuwa na ina zaune ruwan dake manne a,jikinta ya kare sai ake kira nurse on duty ta cire mata take cewa tana aiki gata tafe, Ganin ruwan ya kare zai iya fara dan sinking din blood din ta yasa na mike daga gurin da nake na nufi inda cotton yake na debo na wuce direct gurin ruwan na cire na mayar da canular din na,rufe mata Ke Aisha kada kije rigima ki ja min matsala a ce sai an sake yi min allura, ko wani abu don walle duk na gaji da soke soken nan, Umma ce ke fadin haka cikin maganan ta na yanayin mara lafiya, take maganan da kyat, Lokacin ne nurse din ta iso gurin don cirewa Umma ruwan bayan mintinoni da na cire mata ganin ancire anyi komai yadda ya dace yasa ta dan fara waige waige tana cewa wacece ta cire maki ruwan, ? Cikin sauri Umma take cewa dama ai na fadi rigimar yarinyar nan kada ya jawo min matsala, Gata nan waje sallonta, ta cire min shi, ina cewa tabari amma sai da tacire, saboda iyayi, To ai tayi daidai don ni ban zaci ruwan ya kare haka ba gaba daya ina ce kadan ya saura suka kirani, kin kuru da yaja jinin ki badon tana gurin ba,,, Inda nake nurse din ta juya tana cewa, amma kina karatune ko,? Nadan bata amsa cikin gyada kai tare da cewa eh , Wani school kike karatu nace mata health, good, good, yana da kyau hakan Muna so mata suyi karatu sosai don taimakawa sauran matan mu nagida da basu son fitowa asibiti, Kamar wanan maman taki sai da jiki ya kashe ta agida akazo muna da ita nan Ai wallahi ta kuru don da sai dai wani ba ita ba a yadda akazo muna da ita , Mama Hafsi daga inda take zaune tace malama ai ita wanan yarinyar taba da shawaran mu wuto da ita asibiti Don duba mai ke damun ta, saboda yadda jikin nata yai tsanani sosai, Tace shine amfani karatun at list a dan samu wanda ya dan san wani abu zai iya taimakawa, ko, yaya ne, yafi a zauna dip gaba daya, a gida, A daidai wanan lokacin da take bayani su Yaya Hamza suka iso gurin sukai tsatsaye cirko cirko suna sauraren bayanin da matar ke yi, Tai setting din wani ruwa bayan taima Umma din allurai sai ta saka mata, Ta juya inda nake tana cewa idan kinga yana rushing zaki iya rage mata don kada ya sakar mata da reaction, Ta juya ta wuce sai mama hafsi tai magana bayan wucewan nurse din take cewa Aikuwa munga alamar hakan don dai yarinyar nan ta taimake mu sosai kan wanan rashin lafiyan na yaya, Ibrahim yake tambaya may yafarune wai, Sai mama take mai bayanin yadda akayi da nurse har cire ruwan da nayi, Ya juya gurin Umma yana cewa wallahi Umma Aisha babbace don dazu na hadu da abokina dake karatu a makarantar su yake cewa tana cikin dal8ban da ake ji dasu a school din nasu don first class ce ita, Umma tai wani mayde baki tana cewa ai sai ka bari har takare karatun sai ka yabeta ko, Hamza daga inda yake sai murmushi yake don yasan Umma bazata taba yabo na ba idai da bakn ta ne, Muna gurin na hangi wasu mata tafe sunyi kwalliya sunyi kyau dasu hannun dayar, matar, dauke da basket din abinci, Dayar kuma tana dauke dayaro karami a kafadar ta sai wani saurayi a bayan su dauke da flask din ruwan zafi da ledojin kayan tea a ciki sai na fruit, Tsayawa sukayi inda gadon farko yake a dakin suna tambaya mutanen dake saman gadon, Sai sukai masu nune da hannu a gurin da muke, direct gurin mu suka nufo, Sai da suka zo gab damune na gane cewa su Hindatu ne ashe, tare da kannen ta suka shigo duba jikin Umma, Nan aka shiga gaisawa da su ana tambayan ya jikin Umma din tare da mata fatan Allah ya bata lafiya, Daga karshe suka gabatar muna da abincin da suka shigo dashi, a matsayin na dubiya, Godiya muke masu tare da fatan Allah bar zumunci, tare, Su waye Zarah take tambaya kasa kasa don son jin kosu waye su Hindatu din, don ganin su yan gayu da tayi, Mama Hafsi ce ta cabe zancen da cewa mutanen arzikin Aisha ne suka zo ai kinga ita suka,sani, Zancen yaiwa Umma zafi tana son cewa mutanen data ne, shi suka sani, bani ba ga kuma alluran da akai mata yana hawa mata kai, Sai kuma ga yar yauri tashigo su ma har su uku suke cewa sunzo gidan mu ake fada mata shine tace bari su wuto direct asibitin, Zarah take cewa yanzu ashe ita Aisha tasan mutanen arzikine haka take hurda dasu, Hira,muke a tsakanin mu na,sake freely zakace bani bace ke yar hira har da dariya na a,cikin friends dina, Bayan tafiyan yan gidan su,Zarah ta bude abincin da Anty Hindatu takawo muna,sai kamshi ke tashi cikin dakin duk ya,bure ko ina, a dakin Mama hafsi ce ganin za ,a cinye abincin ni ina can tare da baki tai min tayi nazo naci abincin Nace Mama sai da naci abinci na,fito daga gida a koshe na ke, Ba wani kunya nan suka bude baki a gaban su hindu suka cinye abincin tas, akarshe ma suka bude wanda nazo dashi suna mai wani kallon wullakanci, Sai mama ce ta shiga rigar arzikin su, take cewa su rufe mana anjima basai ankawo wani ba ai zai masu rana, Ranan mama ta hana ni yin wani girkin dare tace aiki yai min yawa na huta hakanan, Da dare dana dawo gida yaya ibrahim ya sayo kayan shayi yace na hada muna shi mu kasha muka kwanta, ni dasu, Da dare bayan mun kwantane Yaya Hamza yake ce min, Humaira zan so ace idan kin gama wanan karatun kici gaba da yin wani sai dai ina gudun fitanar Umma akan hakan, Don ko wanan din da yaya aka samu ta yarda dashi balle a dauko wani, Allah dai ya hore min nabar gidan nan kin ga alokacin duk abinda muka ga dama sai muyi abin mu a can babu sa idon kowa a kan mu, Nace cikin gyara kwanciya na kadan Yaya aiko wanan din ma na gode don yai min rana, Badon Allah ya hadani da gwarzon namiji irinka ba wanda yasan yakamata a rayuwa aida bankai ga haka ba, ma, Da, har yanzu ina nan zaune ba wani karuwa a rayuwa na irin haka ni gaskiya ko a,wanan din ma nagode gaskiya,, Ya rugumoni zuwa jikin shi yafara dan shafana hakan yasani gane cewa yau da dan karfin shi stress ya rage mai, ****** ********** ****** Kwanan Umma uku a asibiti aka samu sallama suka dawo gida take gida ya rude da yan shigowa gayar da Umma daga makwanta, Yan uwan su baban su hamza maza biyu suka zo suna fadan ba,a fada masu ba, Umma bayan sun wuce tace muna fukai afada maku kuzo kuga yadda nake ku karasa ni, Cikin masu shigowa har da matan gidan mu, watau su Ummina, Umma tana wani cika tana batsarwa wai ita tana da su a,rai tana jin haushin su a zuciyar ta, Suma basu dade ba suka fito zasu tafi Atika tace su shiga mana su gayar da ni a dakina, Duk da sun san cewa gulmace amma sun bi shawarata din sun shigo dakin nawa, Wanda zance wanan ne karo na farko da su mamana suka shigo dakina Don ko sun shigo iyakar su zauna awaje don haka shine karon su nabiyu da suka shigo gidan ina a cikin sa, Sunyi, matukar mamaki kwarai dan ganin dakina a yadda basu zata ba don sun samu dakin acan acan duk da ba, wasu kayan zamani bane a cikin sa Amma yadda yake a gyare yasa yana daukan ido, gwanin sha,awa Don ga gadon yasha gyara ga kujera na tsab ga akwatina daga gefe na aza mai wani dan kyale fari sai fridge dina daga kofan shigowa dakin, Ledan kasan dakin yana kyali sosai a lokaci don yasha guga kuma gashi babu yaran da zasu bata shi da dadti, Mun gaisa dasu sukai min ya maijiki kamshin dakin yai masu dadi sosai, Nace bari na basu sabon zobon danayi da rana yai sanyi sosai mama saude tace nabari idan sun tafi zasu aiko Aina ta karba masu, Mama dai bata ce komai ba tun shigar su don kamar ma a takure take a dakin dole ce ma tasata shigowa dakin, Hamza da yashigo ya tsaya rusunne daga kofa suka gaisa da su cikin girmamawa da mutunci, Abinda yasa Atika cewa a lokacin da suka fito kai jama,a watau dai ana zaton wuta a makera sai a samay shi a masaka, Gidan masu kudi babu tsabta ba tarbiya amma ga gidan tallakawa duk an samu abinda ake zaton samu gidan masu arziki,, Wai ashe sunje gaida Kubura shine suka samu gidan da dakinta kaca kaca kuma mijin da yazo ya samay su shine ya wuce kamar bai gansu ba ita Atikar ce tai mashi magana cewa, baigane su bane yana tafiya yace nagane ku ma,na, Suka fito ran su a bace kan irin yadda yai masu ita mama saude ce ma ta fara magana sai da Ummi tai mata magana cewa ba girman ki bane yaya, Kowa da halinsa ake zama dashi tunda baiwa yar mu wullakanci ba kuma tana zaune lafiya da abinta banga abin bacin rai ga mutumin daba kai ka haife shi kai mai tarbiya ba, Shine sukai shiru ba wanda ya kara tayar da zancen har suka dawo gida, To shine fa ashe maganan na a cikin rayuwan Atika sai yau take sakewa mama saude habaici, akan shi, Mama saude zatai magana Ummi take ce mata ai idan daji bai gama cin wuta ba yaya ba,aiwa kututure barka ko,? Atika tagane inda zancen Ummi ya nufa kuma ita Ummi din tagane cewa badon Allah Atika ta yabi gidana ba don sheri ne kawai da kissa irin na kishiya, Ai itama yaranta zasuyi aure aga inda suka dosa sai sukai shiru gaba daya, Lokacin da Aina ta shigo karban zobon su Hamza na gurin don haka sai yafita waje shagon su ya shiga yadauko omo clean ya saka masu aleda da sabulun wanki, Ranan kan habaici saida a kai fada da Mama Saude da Atika a gidan don ta kaita makura, Da Baba yazo ya samu ana wanan jidalin yake tambayan ba,asi shine Atika tai tsagal tana cewa zance nake ina cewa ashe kwanciyan hankali da samun wadatan zuci yana ga auren tallakan da akai gudu shine yaya tace wai ita nake sakewa habaici, Shi kuma Baba sai yace dama ai hakan gaskiyane ba karya bane, Yau kin fara ganin gaskiyan maganata ke nan Saude, Naso hada zuria da wanan yaron Hamza a rayuwata don gani da sanin halin yaron Amma sai kikai min tutu arai keda yar ki kukayi kokarin watsa min kasa a idon jama,an da na gaiyato a gidan nan, Allah ne ya rufa min asiri wanan yarinyar yar albarka ta share min hawaye na, Yanzu don gaskiya tafara halinta shine zakice wai kada a fadi don may, Ai dama kowa yasai rariya yasan dole zatayi yoyo indon wanan zaben tumun daren da kukayi ke da yar ki babu komai a cikin sa sai tarin bakin ciki da takaici don ko alhakina ya ishe ku, Cikin kuka mama Saude tace lalai duniya malam yau kuma yar Agwaice abin yabo a bakin ka, Ba hakana bane Saude dama ni yar Agwai ban dauketa komai ba sai "ya kamar kowa a gidan nan dama ai can sherin kune kuka,dauki tsana kusawa yar mutane, Ummi dake dakin ta taji abin yaki karewa ta fito tana cewa haba malam haba kubar wanan zancen haka dan Allah, Hakan ba girman ku bane dakai da yaya ko ina duniya ko bana nan Aisha yar kuce don gaba dayan ku bazamu manta da halarcin da kukai mata ba na zaman ta gurin ku, Ta juya gurin mama saude tace Yaya don Allah ki bar maganar nan aishi maso habaici dama maso fada ne, Atika daga kofan kitchen tace nidai na fadi gaskiya don dama daci ne gare shi, Da kyat Ummi ta rarashi mamata shiga dakin ya a cikin bacin rai don zancen atika da mijin su ya bata mata rai sosai, ****** ********** ****** Gidan yai muna tsauri saboda ga,damana tai nisa duk kudin Hamza ya watsa su a gona yana duban abinda zai girba idan lokaci yayi, Don kwanciyar Umma ya jawo masu rashi kudi a hannun su, Mun wayi gari dan kamun da zamu dama kunu a gidan yadan buwaye mu, Gashi babu abincin da zan dafa muna da rana muci, Hamza ya shiga dakin gurin Umma yana tambayar ta ko akwai dan kudi a hannun ta sai ta ara, mashi, har ya,samu ya mayar mata, Amma sai Umma ta kyankyashe kasa tace batada ko kobo a hannun ta ya tafi gurin matar shi ai tana sana,a ta ara mashi, Cikin dan marairaice murya yace Umma bata dashi ne dana karba a gurin ta ai, Wani kallo Umma ta watso mai mai nuna owo kana goyon bayan matar ka ko,? Cikin daga harshe Umma tace duk sana,an da take a gidan nan za,a ce wai bata da kudi a gurin ta, Hamza ya kara cewa bata dashi ne Umma ni na san da hakan, Daidai nan mama tafitowa daga dakinta taji wanan hayaniyan takaraso zuwa gurin, Hamza yace Umma wallahi duk kudin danai ta amfani dasu a,sibitii gurin Humaira na karbe su, Sai duk suka watso mai idanuwan su yace, wallahi mama a,gurin ta nai ta karba don su sauran yan uwana, sun ce min bazan samu ko sisi a gurin su, ba Duk wanda ma na tambaya bana jin mai dadi a,gurin shi, Shiru Umma din tayi don jin dan nata ya rantse cewa a,gurina ya karbi kudaden da ya kashe asibiti, Juyawa tayi sai mama tace duk kudaden da akasamu a asibiti fa yaya ? Bazaki bayar a rufa asiri dashi ba may ye amfanin samu a gida, Daki, tashiga ta dauko dari biyar ta miko mashi a wullakance, Yakarba yana godiya, yace zai je ya samo dan abinda za,a karya dashi, Bai fita ba daki ya shigo ya zauna da dari biyar din a hannun shi yana dan juyawa a hankali, Nafahinci cewa bazasu ishe shiba shiyasa ya rasa yadda zaiyi da daribiyar din, na hannun shi, Dubu dayan da ya rage min a dakin dama kayan zobo zan saya dasu nadauko na mika mai nace ga wanan sai ka kara ko, Yadago idanuwan shi da,su kai ja ya sauke su a kaina yana cewa cikin wani sanyin murya, Wanan kuma fa nace cinikin da nasamu ne jiya da wanda ke a,gurina dama kayan zobo naso saye dasu, Idan kin bani ke damay zaki hada zobon naki dashi ? Tunda ba,wasu kudi a hannun ki, Nace Alkah zai rufa min asiri insha Allahu na samu nayi ko da kadan ne, Ya karbi kudin daga hannuna badon ya so ba ya mike yana ce min bari nadan fita nagani Humaira, Zuwa wani lokaci yadawo da leda ya auno yar shimkafa a ciki da cefane yakawo min yana cewa nayi na rana kafin anjima yagani ko za,a samu na yamma Acikin dabaran mu na mata nai tuwon shikafa na hada da saurwn gari na daure sai yakai muna har da na yamma, Haka rayuwan wanan damanan tazo muna sai na,dan kulla cinikin dan zobon da kakaran nonon da nakeyi mu sai wasu abubuwa don har shagon namu ya kare, Kubura tazo gida yini taba da kudi a,sayo mata idomie ta dafa don wai bazata iya cin abincin da aka,dafa a gida ba,shinkafa da wake, Anya kuwa za,a samu abu a shagwan Hamza din nan don duk kwanakin nan duk abinda aka aika sai suce babu shi ina ga sun lashe, Tawani juywa tana kallon mama din tace wallahi mun ta aikawa hatta maggi cewa suke wai babu shi, Tsiya takai tsiya ke nan tunda har shagon ya kare ai nasan karya ta kare ke nan, Ita yar agwai din fa to mama ? Wanan mai gadon zurfin cikin aibazata taba fadin komai ba ita, Sai dai taita wahala a ciki takare haka na a wahalce, Wai shine da Baba yaso turani cikin wanan wahalan boni yaci har na lalace, Ai har yanzi shi bai san da haka ba don kwanaki yadan bada Omo akawo muna shine munafukar nan kecewa wai suna kina,aure gidan mai kudine amma yar Agwai tafiki sa,an daki da kwanciyan hankali, Halan maman Aina ko ? Ta tambaya cikin canza fuskanta tare kufulowa, Ita mana dawa zaiyi wanan zance in ba itaba mai kwarmaton banza, Wallahi mama sai nayi maganin wanan munufukar matan agidan nan don bazan kara bata fuska ba dani take zancen, Tamike tare da yafa dan yalalon gyalen da ta yafo a kanta tana cewa ina zuwa, Zaune nake ina raba abinci shimkafa da wake da mai da yaji nadafa sai kamshi man dana,soya yake tashi naji sallaman Kubura, A zatona ta shigo gaida Umma ce taji labarin bata da lafiya nai mata iso a cikin washe bakin naga yar uwata, Nace tazo su gaisa da Umma tana kwance daga kofan dakin ta, Cikin wani yatsuna duk da ta ramay ta fada yangan nan da kaudi irin nata yana nan kamar baya, Mun koma dakina da ita,na gabatar mata da abinci na aje mata zobo da ruwan sanyi, Nai mamaki kwarai danaga ta sake jiki ta kwashi abincin dana saka mata din, Tana shan zobo Hamza ya shigo cikin daga labule yana ganin ta ya dan daure yace a kubura kece a gidan namu tace eh, Nashigo ne naga yar Agwai tunda ka hanata zuwa gurina, Ban hanata ba idan tace zata ai zan barta ko na kaita, So kada kiga laifina bani na hana taba, Ta kurbe zobon ta mike tana cewa zata koma tana gida sai da yamma zaya tafi don yini ta,shigo nai mataalkawarin insha Allahi zan shigo gurin ta, Tana shiga gida mama ke cewa ke ina kuma kika,shige tun dazun, Tai gyatsa tace gidan su yar Agwai na shiga naci abinci, Kai amma Kubura baki san kunya ba a rayuwan ki wallahi da hat zaki shiga kici abinci a gidan wanan kaskantatun mutanen,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU .SARAUTAR MATA THE STORY JUST BEGINNING,, Haka rayuwa tai muna tsauri da wanan damanan ta wanan shekarar, inda mace batakai zuciyan ta nesa ba kullun za,a ji ta da maigida don abin ya kai lahaula tako ina, Duk sai ince da dan sa,na,a ta muke cima a gidan don Umma taja bakin aljihun ta ta tsuke wai bazata bayar ba, Niko abinka mata da miji d zaran na gan shi a cikin damuwa yanzu zan jawo dan asusu na a fasa a debe kudin sai muyi amfani dashi, Gashi Allah ya albarkaci sana,an tawa sosai don mutane suna son zobona da kunun ayya da yar kankarar nonon danake kulawa, Hamza ya koma makaranta sai dai baiwani dade ba ya dawo don cire amfanin gonan daza ai mai, Wani sabon aikine kuma yazo min don nice a tsaye gurin aikin saboda mama Hafsi bata nan tai tafiya duba yar ta da aka aiko bata da lafiya wai mijin ta yasa mata ciwon tari, Ni kadaice atsaye kyam ke faman gyara kayan da duk aka,shigo dasu gidan, Na ramay nai baki na koma wata irin bagidajiya dani, Koda su Asmau suna gida basu iya tayani komai sai suce wai ai kayan mijina ne idan naga dama na tatala ko na barshi ya lalace, Ranan sai akan kunnen Hamza wanda zai shigo ke nan yaji Asmau dake a saman turmi zaune tanw min zari, Yarinya baki isa aure bakin nace ke zakiyi yanzu gashi kullun a cikin aiki kike ba hutu ba tausayawa duk kin kanjamay kin ramay kamar wata tsohuwa, Nace cikin yar dariya Asmau kin taba jin mutum ya wuce kaddaranshi ce ni tawa kaddarance aure da wuri kuma ban raina da hakan saboda Allah yasan dalilin yin aure na, But yashigo gidan kallo guda gaiwa Mau tashige dakin uwar su simi simi don kallon da yai mata kawai yasa ta sanin cewa duk yaji zancen ta, Sai faman bakacen masara nake ina gyara tare da zubawa a buhu, Sannu da zuwa nai mashi tare da mikewa don zuwa dauko mai ruwa yace barshi Humaira na hutar dake Allah yai maki albarka, Wani irin dadi naji ya kumay man zuciyata tare da farin ciki, Yace kiyi hakkuri munyi waya da mama tace min zata dawo zuwa gobe insha Allahu, Kin ga sai ta taimaka maki don aikin nan yai yawa maki, Murmushi nayi na daga fuskana da yai, futufutu da kurar masara nace mashi aiki indai na,samun ladan aure na ne, bazan taba gajiya ko kasawa da,shi ba insha Allahu, Ya dan dauki lokaci tsaye yana kallon yadda nake aiki, Sai kuma naji ya,furza iska sama yana cewa lalai dole na canzawa yaran nan Yanzu nabar gona da bacin ran Jibri na,shigo gida kuma,na,samu na Asmau, Nace hakkuri zakayi don su ai dole da kai suke takama, duk fadin duniyan nan, Bakomai yace a fili dole zanyi maganin iskancin nan nasu in ba haka, ba bazasu gane may ake cikiba, Ya shige daki yana ta mita leda biyu na ruwan sanyi ya zuka yafito don daukan abincin da na gama tun shabiyun rana zai kaiwa yan aiki a gona, Nan kuma ya tsaya yana dan kama,min wasu yan gyare gyaren masaran dake watse a kasa, Tausayi nake matukar bashi don yasan cewa lalai sai aure zai sani hakan duk da auren ma da ganin dama, Don da Kubura ce daga shi har aik8n shi yasan cewa basu isheta kallo ba balle wani zancen gyaran kayan gona, Umma ce ta leko daga dakin ta don zuwa zagayawa ban daki tagan shi tsugune yana tsintar masara a kasa tace, Lah yanzu baba baka tafi kaiwa bayin Allah can dake daji abinci ba katsaya yin shiririta a nan har sai sun tagaiyara, Ya mike zubur da sauri yana fadin Umma yanzu zan tafi naga masara a kasa ne nake tsuncewa, Yamike tare da,wawuran fantekar da abinci yake a cikin sa ya nufi kofan gida, dashi, Mama ta dawo kusan a tare muka kammala aikin da ita, don tana da kuzari sosai, Ikon Allah dama tazowa mutane da haske don duk wanda yai shuka farkon damana ya samu amfanin gona fiye da tsan manin maikaratu, Hamza yana daga cikin irin manoman nan da Allah ya albrkata da yawan amfanin gona a wanan shekaran, Wanan dalilin yasa sunan Hamza ya daga sosai a gari aka fara zancen albarkan gonan da ya samu din, Bai koma ba sai da ya tsaya fitar da zakka kamar yadda sheri,a ta kindaya a kai, Bayan yayi yadda aka sharianta sai kuma yai ta,aikawa a cikin uguwa yana badawa sadaka don asa mashi albarka, Duk gidajen da aka kai Umma batai magana ba,sai da za,a kai na gidan mu sai tace Sa,a datu ta tsaya a rage yawan shi, Cikin dan bacin rai yana daga duke ya dago kai yana cewa haba Umma yawan may kuma a nan Kusan fa tare da yar su muka kayi duk wahalan nan Umma sai naga aiko don Humaira za,a basu wanda yafi nan ma, Cikin daure fuska tace haka naga daman basu ko kana da jane yace a ahankali a,a Umma a rage din, Amma wanda ta,aikawa mama Sa,a aminiyarta yakai biyun na gidan mu kowa yana kallo ba,wanda yace uffan, Har gida Baba Mudi yazo da kan shi yai masu godiya tare da fatan Allah yasa badi afi nan samu, Shine mutum na farko da ya sallama yai godiya haka yasa mama,hafsi cewa kaga wanda ya san darajan alheri gashi ana kaiwa yazo godiya, Umma dake zaune saman kujera yar tsuguno tace ba dole yazo ba kila dama shi ake jira a ci, Innalillahi Umma wa ? Malam Mudi din wallahi karya haramun don ko shekaran jiya buhun dangote naga an shiga mashi dasu, Kai Umma ma dai mutanen da a dacen suke kawo muna abinci duk cikin uguwar nan nifa ban matawa da duk wanda yai min alheri, Ibrahim wanda ya shigo da ledan breadi da kosai yana ci ke wanan maganan, Mama Hafsi tace to itakan yaya ta manta don , har hana akai masu ma wanda babana yazuba akai tayi, Ibrahim yace kai Umma amma wallahi k8na da saurin mantuwa, malam Mudi fa, Tun baba na da rai naga ko tafiya zaiyi yakan ce idan wani abu ya faru a fada wa mudi kafin ya dawo, Ibrahim, Ibrahim shin haihuwana kayi ko ,a,a wallahi kafita idona tun ban bata maka rai ba, To amma Umma yaya za,a ce wai an rage na malam mudi, Ga kawar ki da kika aika mata zan wuce ta gidan su naji tana cewa wai duk amfanin gonan da kuka samu sai dan wanan abin zaki aika mata dashi, Wallahi kamar na,shiga na bata amsa sai nace ai kun fi kusa bari na barku ammq sai na fada maki idan tai musu zan fada mata da wacce naji ta hiran ita da yawale ki hira a soron gidan su, Murmushi naga Hamza yayi yace wai kai baka,barin zancen hakana tunda angama, Wallahi yayan mu matar nan Sa,a munafuka ce Umma dai ne bata gane halinta ba duk zancen gidan mu itace ke yadda shi a gari, Nan Umma ta shiga fadan borin kunya dashi shidai yafita yabar gidan bayan ya shiga dakina ya dauko ledan pure water biyu ya kora, A kofan gida Hamza ya samu dan uwan nashi suka kara tataunawa akan halin Umma din, yace su dai yi hakkuri da ita su samu su rabu lafiya saboda uwace mahaifiya ba abin wasa bace, ****** ********** ****** Duk suna zaune yake lissafo mata yadda zaiyi da hatsin da ya samu din, dakuma wanda zai fitar a gyara na cin gida saboda shi zai koma makaranta ranan lahadi mai zuwa, Yace zanbawa Humaira wake, buhu daya sai shimkafa biyu, Kafin ya karasa Umma tace a bisa wani dalili za,a bata, Umma kada ki manta cewa nakarbi kudin ta tunfarko munyi lalurar asibiti dashi, Sai kuma wanda nake karba muna,,,,, Cewa tayi sai kabiyata ko may don ban fahince kaba yanzu don ka karbi abin matar ka kayi amfani dashi shine za,a ce sai kabiyata da wanan abubuwan haka, To ban yarda ba kaji na fada maka banyarda ba ikon Allah tun ba,aje ko ina ba ina zaune yarinya karama zatai maka wayo ina kallo, May nene abin wayau anan yaya duk abinda yabata ida tasaye da kudin ta daya karba aida yanzu kudin su ya wuce man, Mama hafsi ke bata amsa da fadar haka Nadai ce ban yarda ba kaji na fada maka lalai ashe akwai magana ke nan, Yanzu yaya yaro na son sauke nauyin yarinyar nan dake kan shi amma har kike hanawa , Ina daga dakina duk zancen su ina ji duk da banji dadi a raina ba haka na hade bacin raina nafito don daukan kayan dana wanke nakai daga cikin daki, Ganina bai hana Umma sake maganan da takeyi ba har lokacin da taga dama don kanta ta kyale ita daya, Ya shigo daki ina zaune da hand out dina ina dan dubawa don ina da test, yake cewa, Kada zancen Umma ya tayar maki da hankali Humaira zan san yadda na biyaki kudin ki, Cikin nuna rashin jin dadina nake cewa haba yaya ai Umma tana da gaskiya don ka karbi kudina zaka ce sai ka biyani, Humaira hakkin kine fa dole na baki abinki don ba kyauta kika bani ba nace ni abina nakane ai, Shirin shi yayi tsab na komawa school don ya dan so ya makara ma saboda aikin da ya tsaya yi, na gona, Haka rayuwana yake ci gaba a gidan banda wani freedom din kaina ko ruwan sanyi nasha a gaban Umma yanzu zatace masu abu ku kayin yadda ranku yaso, Ko naji marmarin abu sai dai idan na fadawa mama a boye ta sayo tabani inci a gaban Umma shine samun lafiyana, Don ban isa na dora dan tukunyan idomie ko taliya ba ince zance ranan kila da sai na kwana gidan mu don fitina, Dole abincin da akayi na yawa shi zanci koda kuwa ban son cin sa amma ina kallo su Asmau zasuyi yadda ran su ke so bata cewa uffan har na gaji na saba da hakan, Yaya ibrahim ne kawai ke dan rufe ido yashigo min da abin marmari yace wai ni amana kabar mashi ni, Dole umma tana kallo tayi mai fada hakan amma yaki bari da wuya idan zai shigo bai zo min da irin rake, gyada, karas, mangwaro, lemo ko kankana yace ni ya sayowa shi, Umma da makwabciyan ta aminiyar ta sun kara dinkewa dole yaran tun basu so sun kawo ido sun sa mata, Yanzu ta kirkiro zama gidan su Saan wai yafi gidan mi iska can take wuni sai marance tadawo indan nai girki acan za,a kai mata abincin su ci, a can, Wanan ya dan kawo muna saukin tsangwaman da muke samu a gidan surin Umma don har muyi dan abin marmari nida mama mu cinye bata dawo ba, Gashi gidan da take wunin takai ma matan gidan ko ina don sunce itace ke zuga masu sararkuwar su take matsa masu lamba, ****** ********** ****** Yana zaune a class ya bitar wani takardan da ya daure mai kai tashigo class din, Hamze inata nemaka tun dazun ashe kana nan yadago fuskan shi a daure idanuwan shi a,kanta, Wani irin abu yaji har cikin ranshi bai san lokacin da yar murmushi ta subuce mai ba, Haka kawai yadinga jin gaban shi yana dan faduwa a hankali, Kara matsowa tayi gab dashi ya shaki wani shu,umin kamshin dake tashi a jikin ta, Atake ya rikice ya rude duk ya wani susuce cikin jikin shi wani irin kasala yake jin yana sauka mashi, Kamar wanda ke jin barci saboda weak din da jikin shi yai mashi, Littafin ya rufe tare da dan dukar da kanshi saman tebur din da yake zaune a kai, Hannun ta takai saman wuyan shi don kara aiwatar da aikin ta a kan shi tana dan cewa may ya,samay ka kuma yanzu yanzu, Bayan ta tabbatar da ta shafa mai abinda ke a hannuwan ta , Yadago idanuwan shi da suka canza kala sun rine suyi ja jajir yana cewa ba komai kawai ina son na dan je hostel na huta,, Cikin kara matsowa gab da jikin shi take cewa saboda kaga nazo gurin ka shine zaka gudu ka barni, Yadda yake ji a,rayuwan shi ba zai iya controlling din kan shi ba a kan ya idan har ya kara wasu yan mintina a gurin tare da ita, Don haka ya dai kokarta cikin dan dadin baki yabar guri ya samu ya isa hotel da kyat, Ya,samu mansur mijin Hindatu ya,shigo hostel din na su shima yana neman shi, Ganin Hamza a cikin wa i ir8n yanayi yasa Hankalin mansur din dagawa, Bai boye mai abinda yafaru dashi nan ya,labarta mashi irin yanayin da yake ji a kan Halima din, Innalillahi m Mansur ya ke nanatawa yana cewa munafuska tasan sherin da tai maka,shiya take yawon neman ka tun safe, Tau ta Allah bataya,ba yar iska kawai macuciya sai mun saka wando kafa guda da ita a school din nan, Abu wasa wasa maganin Lima yana shiga jikin hamza bai iya zama idan bai gantaba a yini, Gata irin matan nan ne masu son manna jikin su gana miji abu kadan zata ce ta riko hannayen shi ko ta kai mashi kiss tun yana kunya har ya daina ko a gaban kowa zata iya mashi hakan, Gashi akalla zata bashi kusan shekara goma sha ga haihuwa amma da yake yar wankace sai baza ai saurin fahinta ba, Amma dai dole mutum.ya gane cewa ba,,sa,ar shi bace, ita, Amma tabi ta mutu akan karamin yaro komai zakaji tace my Hamze,, Sai kudi take faman kashe mai gurin sayi banza sayi wofi, Da farko sauran student suna zaton cewa wai don yana da kokari take manne mai sai daga baya suka fahinci zancen ba haka yake ba, Zance ya juye ya koma soyayya mai karfi da tsoron gani, Wanan weekend da zasu shigo ke maymay Hamza yace bazai samu shigowa ba sai wani lokaci, Don ji yake a rayuwan shi bazai iya barin Iima na tsawon lokaci bai ganta don zasu iya kwana hudu ko biyar a gida kafin su dawo, Haka Mansur ya kamo hanya shi daya zuwa Jega ba tare da abokin tafiyan shi ba, Hamza, Gab da magariba kamar kullun ya iso gidan na shi tare da yan tsaraban da ya sayo a sokoto, Ya samu Hindatu kamar kuun ta caba ado tana jiran isowar shi, Ta tare shi acikin so da kauna tare da mai yar irin maraban da ta saba , Tace yau har kakai Hamza din gidane bai zo tanan ya ci abinci ba, Ran shi a bace ya wuce zuwa uwar dakin su yana cewa Hamza ya fada tarko yan zuru sai dai rokon Allah, Da,sauri Hindatu ta bi bayan shi tana cewa ban fahince kaba fa man may kace ne wai, Ina zuwa yace ya shige bandakin su don ya dan zagaya ya,rage cikin shi dan yanajin ya hake mai, Hindatu duk gulma ya ishe ta har ta fara dan jin haushin mansur din da baifito ba da wuri don taji may ke faruwa, Can yafito yai wanka harda alwala ya dauro yadan canza kaya sannan yafito falon nasu ya zauna, yana cewa mama fa? Banji motsinta ba ko ta tafi cikin garine yau ma din, Tace dazun nan aka,aiko wai gwago Amma bata da lafiya shine tace bari ta tafi ta dibo muna yaya jikin nata, Man may kace ne ya samu Hamza, ne wai,? Ya dan furzo iska daga bakin shi muryan shi so angry yace wanan yar iskan yar zurun ta samo kan shi a lokaci guda, Nan ya shiga bata labarin irin halin da Hamza din ke ciki don yana neman taimako gaskiya, Hummm, ummm inji Hindatu ashe Aisha nata ya samau ta wa yan nan da in sun rike namiji kurcewan shi sai Allah, Allah kace ce mu baki dayan mu kai muna tsari da yan barikin kadangaru, Mansur yafita yabar Hindatu ita kadai tana ta saduda a cikin dakin su sai sambatu da zage zage takeyi, ****** ********** ****** Rayuwa yabani cewa zasu shigo wanan satin saboda lokacin zuwansu ne duk karshen wata suzo su kwana muna biyu sai su koma, Duk wani gyara da ya kamata ace nayi nayi shi daga daki gida har jikina nai kitso nai kumshi na tsab, Har dare banga sun shigo ba nasan kuma cewa basu tafiyan dare sai dai su kai gab da magriba iyakar daren su ke nan, Karfe tara da yan mintina sai kawai naji rayuwana yadan soma baci haka kawai naji badadi abinda yasani shigewa dakina ke nan, cikin bakin rai, Ibrahim da ya,shigo shima naji yana tambaya cewa yayan mu bai dawo yau ke nan, Mama tace gaahi bai iso ba har yanzu kuma ai yaune lokalcin zuwan su, Ibtqhim din yace iba ita madam din tana ciki inji mama bata dade da,shiga dakin ba ai, Ya dan daga labulena yana cewa bari na taimaka maki mu kirashi muji ko lafiya, yau bai shigo ba,shi, Wata yar tsohuwar nokia rakani masai mai toci yafito da ita inda yakira nomban dan uwan nashi, Har kiran ya katse ba,a dauka ba ya sake kira a karo na biyu kiran na gab da zai katse ne akadaga wayan , Hello, Ibrahim ya miko min wayan ya juya zuwa gurin da ake aje kwanonin abinci nace Assalamu Alaikum, Wa,alaikis sallam.ya mayar min da martani, Ina cewa yaya ina,wuni sai ce min yayi yaya akayi ne Aisha ? Cikin wani murya muryan da ni kadai nasan irin sirinta a,rayuwan shi, Ras, ras,,ras gaba ya halba har sau uku lokaci guda, Don a take zuciyata raya min wani mumunan abu akan yaya Hamza din, Da sauri nakawar da zargina da fadar Astangafurullah, Nace cikin daurewa yaya lafiya baka samu shigowa ba dis week, Zankiraki anjima yanzu ina wani abune muryan shi so weak tankar wanda yai nisa da yanayin mace tare da shi, Bai jira mai zance ba ya katse wayan da sauri, Innalillahi wainna alaihim raj,un,,, Shi nake iya maimatawa har Ibrahim yakaraso yanace min kin samay shi ko na ce eh cikin wani murya mai ban tausayi, Dariya yake min yana cewa Allah sarki yau wata bataji dadi ba ogan ta bai shigowa , Dariyan yake na samu nai mashi har yafita yana min sheri, Ban san lokacin da na fada saman gado ba na fara kawo wasu musalai barkatai da basu dace ba nayi, Shiko Hamza a lokacin wani irin shafa da baisan anayiwa namiji ba shu,uma Lima ke mashi, duk yadda yaso hanata abin ya faskara, Har yaso biye mata, ga kuma waya munayi da har bai iya boye feeling din dayake jina abinda take mashi din, Da kyat ya samu ya ture ta tafada gefe guda, bayan ya katse wayan yake cewa haba, Halima wanan abinda kike yi baidace ba sam ga addina don koke ga addinin ku hakan bai dace ba, Kefa ba yarinya bace da zakice mudinga watse wa kamar wasu karnuka Mu ga addinin mu haka yana faruwa ne idan anyi aure tsakanin mace dana miji, So daga yau ina warning din ki akan irin haka a tare dani, Ni ban taba zina ba kuma insha Allahu bazan yi ba kan ki, Haba Hamze sonka nakeyi to be sincere zan iya komai a kan ka wallahi, Yans kokarin mikewa yake cewa amma ba irin wanan son nake so ba ki bari har idan wani abu ya shiga a tsakani na dake, Look Hamze wai kana nufin ko dan shan minti baza mu dinga yi a tsakanin mu ba sai lokacin da mukai aure, Daidai ya mike yake fadin eh haka nake nufi mana, Hannuwan shi ta riko tamike tsaye wanda sai da ya kara jin wani shock a jikin shi, Ya daure yana ce mata mu tafi na rakaki dare ya soma kada kiyi dare baki tafi ba kin san yan erea boys yanzu zasu fara fitowa, Tace idan dare yayi ba,sai na kwana nan tare da kai ba, Dakarfi ya juyo yana cewa what tace yes, cikin dan kashe mashi idanuwan ta, alamar eh mana, Wuce mu tafi na,rakaki ki samu mashin ki tafi kada ki manta kince gobe zamuyi karatun safe, Tace a lokacin da tafara takawa nifa indai ina tare da kai bawai karatun ya,damay ni bane kawai dai najini a jikin ka,shine gurina, Waike Lima bakya jin kunyan irin wanan maganan ne dakike yi, Wiwi kunyan may zanji akan abinda nake so a raina, Da haka suna tafiya tana mashi arigizon shedan a zuciyar shi har suka isa bakin titi ya tare mata mashin tahau yajuya zuwa cikin hostel, din su, Sai bayan ta tafi yaji ya koma wani wasai dashi kamar ancire mashi kaya, sai a lokacin ya tuna cewa sunyi waya Ya kira layin Ibrahim din amma,sai yake ce mai shi yanzu bai ma uguwar mu yatafi cikin gari yawo,, Dole badon yaso ba ya hakkura ya kashe wayan yaso yadan bani hakkurin rashin zuwan shi amma sai kuma Ibrahim din yake ce mai ai baya gida, Shiru shiru ban fito ba ga dare ya soma mama hafsi bataga giccina ba yasa ta dago labulen dakin don ganin wutan dakina a kune Hakan yasa ta gane cewa banyi barci ba kila ina wani abin ne, Kwance ta hango ni na kife ciki kamar mai barci sai a lokacin takaraso a hankali gare ni, Dafani tayi ahankali abinda yasani dan dago kaina ke nan don naga kowaye a,dakin nawa, Mama Hafsi ce a cikin dan damuwa tace don mijin ki baizo ba,shine hankalinki ya tashi yau haka , Banaji kunyi waya dashi ba nadan yi kokarin mayar da hawaye na kada mama,ta gane nake cewa mama kaina ne ke ciwo bawai don yaya baizo banr kitson da akai minjiya yaja min ciwon kai, Allah sarki to kisha magani dai ki kwanta ki huta ina akwai maganin a gurin ki ko nafita na,sayo maki a bakin titi ne, Ki barshi mama ina da sauran paracitamol zan sha sai na kwata to maza mike kisha ki kwanta kinji yar albarka kada kuma ki damu tunda kinji lafiya yake nace tau mama nagode, Tana tafiya take cewa may ye na godiya kidai rufe kofanki don dare ya soma yi,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WANI PLEASE,,, Washe gari sunan na tafi makaran ta amma har aka tashi ban fahinci komai ba a lecture ranan, Na hau mashin da nufin na tafi gida amma sai wata zuciya take ce min indan biya gidan Hindatu nagani ko duk kan sune basu zo ba, Tun a kofan gida na ga zahirin cewa Mansur yana gari kamar na juya na koma sai na sallami mai mashin din na shiga don mu gaisa naji may ya faru da nawa maigidan bai zi ba, Suna falo zaune na tsaya daga baya kadan ina kwada sallama, Itace ta leko tana ganina tace man ga Aisha nan tazo jin dalilin rashin zuwa da mijin ta dabakayi ba satin nan, Wani irin kunya ne ya kamani sai da na sone kaina cikin hijjab dina nace haba Anty hindatu najuya ina cewa na koma tunda haka ne abin, Da,sauri tafito waje ta biyo ni tana cewa haba kaunata daga wasa kuma zaki ce k8n juya dawo muji may ya hana ogan ki zuwa satin nan, Nakara cewa wallahi Anty Hindatu cikin yar shagwaba kamar mai kuka, Mun shiga,falon nasu a tare na gaida maigidan ta da ya mike yana son fita yake cewa kinga Hamza bai samu shigowa ba,wanan satin ko, Suna da test ne ranan Monday mai zuwa shine yace na wuto sai wani lokacin mashigo tare, insha Allahu, Har na zauna sai naji muryan mama mahaifiyar Mansur tana cewa, Idon ta tashi go namike zuwa gurin ta cikin girmamawa tana tambayana jama,an gida nace duk suna lafiya Nadawo gurin anty Hindatu ganin mai gidan ta yafita yasani cire hijjab dina nasha iska, Ga abinci nan ki diba don dai nasan daga school kike bakije gida ba balle kice kin koshi, Kulolin abincin ta,turo agaba ba yadda na iya nadan yunkura na fara zubawa acikin plate, Kamar kullum miyan sai kamshi ke tashi ga nama zuku, zuku a ciki kamar basu san ana talauci ba, Na ci cibi yakai biyu Anty hindatu tana daga gefena a zaune, hankalin ta yana ga wayan dake hannun ta, Nace ni kuwa anty wallahi wani abu ke damuna shine kika ganni nazo, maki da ranan tsakiyan nan haka, Abinda take a,wayan tai saurin bari ta dago kan ta tana kallona, May yafaru dake Aisha ? Sosai na natsu na,fara magan tare da,barin abincin danake ci, Anty jiya da dare munyi waya da yayana, Hamza, sai na zamo daga saman kujera da nake zaune a kai na zauna kasa dirsha a gaban plate din abinci na, Ganin yadda nayi yasa gaban tafaduwa tana dubana a cikin natsuwa, a ranta tana cewa kardai yarinyar nan tasan komai, akan mijin ta, Idanuwana a kasa batare da na kalli idanuwanta ba nace, Anty ina zargin Hamza da fara hurda da mata a makaranta saboda jiya jikina ya bani hakan, Wani irin magana,ne wanan Aisha kada ki zargi mijinki ki rayuwan ku a cikin rigima, A hankali na,girgiza kaina tare da cewa ba haka bane Anty Nan na fara fada mata yadda,mukayi dashi a cikin waya tare da fata mata irin yanayin yada yake a ciki, Innalillahi tafara nanatawa tana tafa hannayen ta tana fadin akwi ashe abar namiji kawai ind akagan shi, Nan tafara,bani shawaran a kan wanan irin halin da nake zaton hamza din yana cikin sa tasoma cewa, Aisha ina son ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada maki, Da farko dai ke musulmace kin san abinda shari,a ya yarde wa mazajen mu suyi, Na,daga mata kai alamar eh, Tace da kyau, Don haka ina son ki kwantar da hankalinki ki saurare ni , Babban matsala shine ace yana neman matan banza a,waje, Idan har aure yake son karawa baki da yadda zaki idan har namiji ya tashi aure dole sai hakkuri, Tau kiyi hakkuri don Allah ba don banza ba shine hakurin farko ki share duk wani abinda zai aiwatar yayi, shi k8na kallo tankar abin bai damay ki ba, Aisha al,amarin maza wuya gare shi don a lokaci daya suke birkice wa mutum sai kice basu wanda kuke zaman rufawa juna,asiri ba,a baya, Namiji idan zaiyi aure yaga baki tayar da hankalinki ba,sai ya koma zargin kan sa da kansa yana tunane ko abin banza ya dauko tunda yaga rashin damuwa a kan ki, Abu daya ne shi idan amarya ta shigo kada ki dauki raini run farko daga gurin kishiya, Duk abinda akafara kin san yana da wuyan bari da sauri, Amma idan an shigo gidan ki an samay ki akan kan bun sarautar ki komai naki a daidai yake tafiya kishiya ko da may tazo dole ta barki, A lokscin zaki kara gyara mu,amular ki da maigida dama yan uwan shi, Don zasu shigewa amarya suna ganin cewa ai sabuwace tana saman amarci komai dan uwan su zai iya masu a dalilin ta, Gyara yaranki, gidan ki dake kanki hakan zai kara daga martaban ki uwar gida, Sai kuma kikara kokarin ganin kingyara tallennki, girki ke nan don kar a barki a baya, Idan har zamu rike hakan duk abinda wata zata shigo dashi dole ta barki ke ma, Idanuwa na a,duke suke ina dan juya cibin dake hannuna acikin shikafa ni banci ba ban kuma,bar wasa da cibin ba, Na dago kai sai ga,hawaye duk ya ciko min a fuska wanda na kasa controlling din su Kinga ita Umma yanzu abin zai mata dadi ne idan taji ko taga kin tayar da hankali ga dan ta, Don haka duk abinda zaiyi Aisha don Allah ki daure ke dai ki dage wurin kaiwa Allah kukannki, Kuma ki fadawa mahaifiyar ki itama,ta tayaki addu,a don adduan iyayye a gare mu taki ne, Kiyi hakkuri kiji Aisha gaskiya abinda zafi sosai amma idan kinyi tunane sai kiga mungaji ganin haka,ga iyayyen mu, Don haka,share hawaten ki, tankar ba abinda ya faru ki koma normal, don kinga man ya shedi hamza cewa bai neman mata kuma bai zina, Ai na namijin dake zina yafi tayar da hankali tunda bakasan da,wace irin mace yake taraiya ba, Mai lafiyace ko mara lafiya musulmata ko kafira ce, Nadago da,sauri nace Anty bana fada maki labarin matan da sukazo gidan mu kwanaki gurin shi, Tace cikin girgiza kai baki fada,min ba Aisha, Nan na,bata labarin zuwan su Lima gidan mu da abinda sukacewa Umma ya kawo su, Babban magana ashe makin san da zancen ko har nake maki boye boye da,farko, Gaskiya Aisha sai kin jajirce kin hana idanuwan ki barci gurin neman mafita akan zancen nan, Don jiya Man yana bani labari yace, Hamza ya canza a cikin dan lokaci guda kuma matar ba yarinya bace tsohuwa ce sosai, Innalillahi Anty na,shiga uku, nace cikin dan kuka haba dakata baki shiga uku ba kinji, Allah baibari ki wulakanta Aisha don shi da bakin shi Hamza yazo nan yana,fada muna irin halarcin da kukai mai keda iyayyen ki, Don haka tunda tun yanzu harkin samu sheda a,gur8n shi duk abinda kika,sani wanda kikeyi na kyautata mashi kira saman wanda kike yi ki nuna ta kar baki fahinci may yake ciki ba, Sai inshi yafito maki da zance saiki ce Allah yasa alheri ne hakan ya,raba ku daga haka kada ki kara tayar da zance kuma, Nan taita kawo min musalai masu yawa har na gamsu ban iya cin abincin ba,daurewa nayi namike nace zan tafi, Har kofan gida ta biyo ni tana kara ja min kune akan na,daure na danne fushi na kar na,bari a fahimci halin da nake ciki, Mukai sallama na hau mashin zuwa gida na makara amma,ban samu Umma a gida ba sai mama don har ta kusa kare girki a ranan , Nai mata sannu da gida tace na,dauki abincina na shiga dashi ban mussaba na dauka zuwa dakina duk da nasan ba ci zan yi ba ma, Da magariba naba almajiri sadaka lokacin babu kowa a wajen gidan, ****** ********** ****** Sosai Hamza kan ya kamu da soyayyan lima da,tarkon da take dana mai Abinci lafiyaye zata dafo mai yanzu baida matsalan abinci ko kadan, Ga,drinks kala kala tana kawo mai ga kudin kashi akai akai tana bashi, don ya yiyadda ran shi ke so dasu, Duk inda zaka gansu a tare suke kamar tip da taya, tun mutane basu fahinta har takai yanzu kowa yasan may ye a tsakanin su, Sam Hamza baijin kunya ko nauyin abinda,jama,a suke cewa akan su shi dai ya haukace akan son Lima, Da,farko taso gwada sa,anta akan ya yarde mata sukoma yan addinin ta, Ranan ta gane bata da wayo a rayuwan ta don yai mata cin mutuncin da bata taba tunanen shi ba a,gare ta, Sai da ta dawo tana lalashin shi tare da turo mashi kawayen ta yan duniya suna bashi hakkuri, Sai cika yake yana batsewa yace ai ya zaci kaunar gaskiya take mai da ya yarda da ita ,ashe ita da wani manufa tazo mashi, Sai da kyat ta samu ya,sauka akan daga ranan bazata kara yi mai zance a kan addinin shi ba, Wanan abin ya tayar da hankalin Lima sosai don a gaskiya ita bata jin zata iya musulunta a,rayuwan ta, da tuni ta musuluntar amma ga dan karamin yaro yazo yana son garata saboda Allah ya jarabeta da matukar kaunan Hamza din, Haka tai hakkuri takara kokarin ganin ta kara kaimi wajen kara kamashi da,asirai da kuma abin hannun ta, Sun fara zancen aure wasa wasa dashi, har abin ya fara tasiri a zuciyar hamza inda yake ganin cewa yanzu a shirye yake zai iya auren Lima din don ba wanda ya isa ya hana shi auren ta din, Sai sake sake yake a zuciyan shi na yadda abubuwa zasu kasance masu, Yaya ma za,ayi ya zauna da Lima a cikin gidan su haka, gata ga su Umma, da yan uwan shi, Sam a rayuwan shi ya manta da zancen wai wata Aisha, Yakan dan tuna ta idan asiri yadan fita a kan shi kadan sai kuma yani kai Aishan may ga babban mace ya samu inda zai morewa komai, na rayuwan shi ya huta, Yagama yanke shawaran abinda zaiyi don haka bai tsaya shakka ko shamakin komai ba ya shirya zuwa gida, ****** ********** ****** Na idar da sallah bayan na dawo daga school na zauna a gurin yayin da nadan dage labulen kofan dakina saboda iska ya dan shigo min don ba,wutan an dauke NEPER , Sallama shi mukaji daga sama don ba wanda yai tsanmanin zuwan shi a wanan lokacin Murna sosai naji yan gidan suna yi suna mashi sannu da zuwa, gurin su Umma ya nufa inda suke a zaune, ya zauna, Namike a hankalo baki daukr da addu,a kamar yadda Ummi ta koya min , Kalman shahada na fito dakin dashi inda Allah ya ban sa,a mukai ido biyu dashi a lokacin da nake karatawa, Wani irin yaji a ranshi lokacin da ya ganni, nauyi kunya duk sun tsirga mai a lokaci guda, Nakaraso ina,saye da hijjab din dana kare sallah dashi, Nace Yaya sannu da zuwa ya amsa cikin dan kara dago kai yana kallona da cewa, yauwa sannu Humaira mun samay ku lafiya, Alhamdullahi nace inda na juya zuwa daki don na dauko mai ruwan sha saboda naga shi tare da iyayyen shi, Na tafi ina tunane sam jikin shi ba,alamar wani, wahalan karatu yadda muke zato yayi kiban shi ya haska gwanin ban sha,awa dashi, Nadora ruwa guda biyu tare da goran zobo mai sanyi sama, Har kasa na,durkusa a gaban shi inda yake a zaune yayin da kamshi jikina da ya dade baiji ba ya daki hancin shi, Yadan lumshe idanuwan shi don tuna abubuwa da,dama a hakan, Yasha ruwan sosai tare da,zobon suna hira yana shan a hankali, Umma ce tace yaya akayi ka dade haka baba bayan ba haka kake muna,ba da farko, Gaskiya rashin ziyarar da bakayi muna kaman baya ya saka,mu a cikin damuwa, Yace Umma ai in kaji shiru lafiya ne karatune ya rike ni tare da,wasu yan abubuwan da su ke agabana,, Daki na koma inda na,dan kara kimtsawa kamar yadda mace zata tari maigidan da yai tafiya ya kwana biyu, Ya dauki lokaci a,gurin su Umma da mama suna dan hiran yaushe rabo a tsakanin su, Can ya mike yana cewa,bari yadan watsa ruwa, ko zai danji dadi a jikin shi, Wani balai, sam Lima taki bari yazo da kayan jikin shi koda kwara,dayane ita hikimar ta nayin haka shine kada yazo ya ce zai kwana, biyu tare da ni, Ya,shigo dakin da,sallama a lokacin ina kokarin fitowa don na dauko mar abincin shi, Na,dan kauce mai a hanya yashige a zuwa cikin dakin mu, Sannun na kara mai tare da nuna ba komai a raina akan shi, Sai naji ya jawoni zuwa jikin shi ya wani kankamay ni kamar wace za,a kwace mai yana wani sauke numfashi, Sai kuma naga ya,wani sakeni da sauri kamar andaka mai tsawa ko umurnin ya sake ni, Bakin gado ya zauna ya sauke wani irin numfashi tare da,dan dafe kan shi kamar mai jin ciwon kan, A,uzu,bikallamatil,lahi tammah,, Shi na fadi a zuciya na nabar dakin gaba na,sai faduwa yake nasan da magana ke nan, Ya kai wani lokaci kwance rairai kan shi dafe da dayan hannun shi, Murya na kamar kullun, nake cewa yaya ka tashi lokaci sallah ya kusa yai firgigit ya tashi sai naji banji yai salati irin yadda ya,saba yi ba idan ya farka da barci, Har yamma ta karasa hakane nace eh ga ruwan alwala can a waje, a aje ma, Yana fita na jawo ruwa a leda na tsiyaya ruwan jug din da zan sa a tire din abincin shi,, Nadurkusa gurin sai da na karanta bissimilahi, kafa dari da sha uku a cikin ruwan, Na mayar da marfin na rufe na girke ruwan a ture naci gaba da aiyukana, Duk da tare suka ci abinci da Ibrahim ban yi wa i fargaban shan ruwan da yayi badon dama addu,a ce ta kara asiri kawai, hakan, Daga inda suka ci abinci naji guri yai tsit hakan ya nuna min alamar akwai wani magana mai muhin manci da sukeyi, Sai ko naji murya Umma tana cewa in banda shirmay irin naka don zaka yi jarabawar karshe, shine zaka zo kace zaka kwashe muna abinci mu may zamuci,, badi idan rai ya kai da may zaka noma wani, Gaskiya haka bazaiyuyu ba don bazaka bar mu da yunwa ba ka,arcewar ka, Mama wanan abin fa nawa ne ni ke,da abina ba ina nema shawara ko yadda bane, Haka nake son yi da abina idanuwan shi kawai zaka kalla kasan cewa gaba daya Hamza ya can za, kamar wani zarare, Babana kan ka daya kuwa, yau Mama may kika gani kike cewa hakan kaina daya mana nazo daukan abinane ya zama kudi, Kawai sai naji Umma ta saka kuka tamike ta shiga daki ikon Allah inji Hamza yanzu saboda Allah mama maye abin kuka a nan, Abinane kuma bukata ta taso ina son inyi amfani dashi don na biya wa kaina bukata,, Allah buwayi gagara,mussali mama tace a,fili, Ta gyara zama suna kallon juna da Hamza din tace, amma kamar da alaman wani abu mai muhinmanci zakayi da kudin nan ko,? Shiru yayi yasada kan shi a kasa don kukan da Umma ta shiga dashi dako yasa jikin shi yin la,asar, Ina daga dakina hankalina yai matukar tashi don dai iya sani na da,Hamza tun ina karama ina shigowa gidan ban taba ganin suna sa insa da ,Umma ba sai yau, Mama ta rarasheshi cewa ya bar zancen har da safe sai asan abin yi akai tunda yanzu Umma tayi fushi da yawa haka, Bai fita kofan gida gurin abokan shi ba yadda ya saba sai ya,dawo daki ya zauna a bakin gado yai tagumi da hannu bibiyu, Ban ce mai komai ba ina ,zaune ina gyara ayyan da zanyi kunun zaki dàshi, Ina jin muryan, Umma a dakin ta tana kuka tana magana har dakin mu kana jin muryan ta, Sai da na gama aikina tsab na kwashe kayan zuwa inda nake boyewa nagyara gurin da nai aikin tsab, nafita nadan wanke hannayena da kawar da sauran kayan waje, Wanan karon da na shigo na samay a tsaye ya jingina,jikin shi a,bangon dakin mu, Kafan daya shi na tokare, ta baya a,bangon dakin namu sai hannun shi da ya dan riko habar shi da shi, sai da na shirya tsab na cire hijjab din dake kaina, Matsawa nayi jikin shi a hankali, na jingina kaina a saman kirjin shi, Ajiyan zuciya naji ya sauke mai sanyi, hannaye na,nasa na zagayo tabayan kunkumin shi dasu, Ya dago idanun shi da,suka canza kala ya kalle ni dasu cikin murya mai kaushi yake ce min Humaira ina cikin matsala a rayuwata, Na kara dan matse shi a jikina na dan ce hummm, Yaya Hamza,nace cikin natsuwa, Yaya dakai da,Umma duk zancen ku a kwai gaskiya a cikin sa, Nafarko kai kana da bukata da abinka na biyu kuma ita Umma tana hangen abinda kaje ya dawo a gidan nan, ne Kasan cewa kaine mafi darajan mutum a idon Umma da yan uwanka yau zaka zo masu da zancen sayar da abincin dake gare ku a gida, Kasan dole Umma taji wani iri a,rayuwan ta saboda kune abin alfaharin ta duniya da lahira, Kasameta ku shirya a cikin kwanciyan hankali yadda zata fahince ka sai ku sasanta da ita yafi wanan kai ruwa ranan da kukeyi a tsakanin ku, Zubo idanuwan shi yayi a kan fuskana kamar yana son gano wani abu tsawon dan wani lokaci sai naji ya nisa, Gyara tsayuwar shi yayi yadan rugumoni jikin shi, cikin murya mai sanyi ya soma magana Humaira nasan zaki fahince ni akan irin rayuwan da na tsunci kaina a cikin sa, Da sauri na dago kaina na dan kalle shi ido da ido sai kuma na dukar da kan nawa, Na dan kara shigewa jikin shi a hankali ina cewa idan har aka bi al,amarin a sannu zaku iya fahintar juna da Umma don zancen ai itama ya shafe ta, koma may ye tunda zancen tane, Sai nake ganin zaka iya samun ta ku shirya a cikin sauki tare da fahintar junan ku don wanan abin baikai na har ka bari Umma tana zubar ma da hawayen akan abinda kake son ganin haske a cikin sa,ba, Da sauri naji ya matse ni gam ajikin shi yana wani irin sauke ajiyan zuciya da kyat ya iya bude bakin shi ya na fadin Humaira nagode nagode da irin fahintar halin da nake aciki da kikai min batare da kin kara min pressure ba ke ma, Nan ya jani muka zauna a bakin gado yafara min magana kamar haka, Hummaira ba sai na rantse maki ba ko insa ki yarda dani dole, ba Nidai wallahi ban dan yadda ake zinaba kuma ban taba anyana yinsa a rayuwa na ba, Da sauri nace mai subbahanallahi wanda nai zaton a cikin raina na fada ashe nafada har a fili, A raina nace lalai an samu matsala maigirma a cikin wanan al,amari amma ban yarda na nuna mai damuwa na,a,fili ba sai daurewa nayi nace Allah yai muna abinda yafi zama alheri a rayuwan mu, Ya amsa min da amin Humaira na gode ya mike tsaye naga ya fara cire bottom din rigar shi a hankali, Mai makon inga abinda nai tsanmani kwanciya yayi ya juya min baya fuskan shi a,sama yana tunane, Ban nuna damuwa na ba ko kadan sai karasa aiyuka,na da nayi , Nadawo daga gefen shi cikin kumci na kwanta tankar ba wani abindake damuna, dashi, Kamar yadda na bashi shawara hakan yayi washegari da safe ya shiga gurin Umma ya bata, hakkuri tare da dan mata bayani akan zancen auren da yake son yi, Umma ta kira mama take sheda mata zancen da danta yazo dashi, Cikin taushin murya mama tace Dan nan matarka tai maka wani abune da zaka kara aure yanzu yace babu komai a tsakani da Humaira mama, Auren dai ne yin sa yazo min a yanzu ai ba wani abin damuwa bane don ba,a nan zan zauna da ita ba, Zata zauna a Birnin kebbi ne ko sokoto ita ita kuma Humaira tana nan tare da ku, Umma dake cikin nazari tace sam batayarda da wanan tsarin ba inda har wace zaka aura bazata zo nan inda muke ba ta zauna to sai dai a fasa zancen, Mama take ce mai to matar ka tasan da zancen karin auren naka? Mama Humaira ba matsala bace yanzu yardan ku kawai shine fatana, Sallama akai mashi yafita kafin su kai ga matsaya da su Umma nan zancen ya tsaya har wani lokaci, Umma ta yafa tafita zuwa, gidan mama Sa,a don ta fada mata zancen da ake ciki a lokacin,, Fitan Umma naga mama Hafsi tana min wani kallo a cikin tausayawa, Naga can tafita daga kofan gida ta dan leka sai kuma ta dawo inda nake duke a bakin randan ruwa tace Aisha na, dago daga abinda nakeyi ina cewa na,am mama, Aisha ina sonki bazan iya ganin abinda zai cuta maki na kyale ba agidan nan, Don tun zuwana gidan nan baki taba min wani abinda raina ya baci ba akan, shi sai kyautatawa, Hakan ma mutanen da nasamay ki da su a zaune agidan nan , ba wanda zaice kin mai wani abin assha, sai dai halin rayuwa, Don haka maganan da zan fada maki bani son ki tayar da hankalin ki, akai, Ki natsu ki saurare ni din ki san inda maganata ta dosa,, Na amsa da to Mama a tsanake tare da bata hankalina, Tace wani, sabon rikici mijin ki yazo muna dashi wai aure yake son ya kara Wani irin iri dam dam naci gabana yabada amma sai nadake na nuwa Mama rashin damuwa a fili, muryan mama naji tana ci gaba da fadin Sai dai kuma ba,a nan zai zauna da matar ba hakan ne ya kawo masu matsala yanzu haka da mahaifiyar shi don tace bata yarda ya aje mace wani guri ba na daban, Na kali mama nace mama dama aure yaya zai kara duk yafita daga hankalin sa hakan nan, Mamatace nasan bai fada maki ba shiyasa na ga yadace na fada maki don babu dadin kiji daga sama cewa wai yayi aure, baki da labari, Na rasa may zancewa wa mama din don yadda nake ji a kasan zuciyata, sai kawai hawaye nagani wasu suna bin wasu, Nace cikin murya mai ban tausayi mama sakaiyan da yaya Hamza zai min ke nan duk irin hakkurin da nake a gidan nan, Mamata shiga rarashina tana cewa Aisha kuka a wajenki bashine mafita ba zan fada maki gaskiya mijinki asirine ke aiki a kan shi sosai kuma abin ya kama jikin shi, Bawai don baya sonki bane ko rashin tarbiyan ki zai sashi wanan aure a,a tsabageren asirine aka tafka mashi yake cin shi, Kin san ba wanda asiri yafi saurin kamawa kamar da namiji a duniya, Mu mata kin san saboda jinin hailar da mukeyi bai bari asiri yayi wani tasiri mai tsawo sosai akan mace sai dai idan asirin yayi muni da yawa, Mama tace yanzu ni shawaran da na yanke a raina basai yaya ta sani ba a gidan nan Zan shiga in futa inga nayi wani abu akan zancen nan don ita uwar taku bata da kwanciyan hankalin fahintar halin da yake ciki, Naji dadi sosai ga yadda mama ta nuna min so da kauna kuma tabani shawara kan na dage da,addu,a don mukai karshen matsalan , Nace cikin dan share hawaye, na mama nagode insha Allahu zanyi yadda kikace min, Tace nagode Aisha ki kwantar da hankalinki kinji kada ki tayarda hankalinki ko kadan Naima mama godiya na ci gaba da aiyukana sai dai jikina ba karfi atare dani, Saboda zuciyata tana min tunane kala kala akan ko wacece zai aura din, Sai yama lis yashigo gida tare da wani mutum makulin dakin hatsin shi ya karba a hannun Umma suka shiga tare da mutumin inda sunkai yan mintina acikin dakin tare da mutumin, Sun fito dakin inda suka fita tare da wanan mutumin, jimawa kadan yadawo dauke da wani leda wanda hakan ke nuna kudine a cikin ledan, Sai wasu katai maza su uku suka shigo suka fara jidan buhu hunan abincin zuwa waje suna lodawa a cikin wani mota mai budaden baya, Ban san lokacin dana fada daki ba ina kuka kuka mi tsuma zuciya wanda ni kadai nasan may nakeji araina, Can natuna da wani abu sai nafito waje da sauri gurin masu daukan buhun na nufa nace ku aje min buhun wake biyu ku fada min kudin shi naji, Yadda suka ganni kamar a,hargitse yasa suka dakata dayan su yadaga wayan yakira wani layi yadan fita waje na wasu mintina ya shigo, Ina nan gurin yadawo yake ce min yace nabada dubu hudu hudu nashiga na kirga dubu takwas nakawo masu nace su dauko min zuwa dakina, Sukaci gaba da kwasan abinsu suka fita duk su Umma suna tsaye suna kallo na a cikin yar damuwa, Da dare bayan yashigo sun dauki lokaci da Umma a dakin ta sai daga baya akakira mama hafsi tashiga ta,sasan ta su, A cikin dare maimakon Hamza ya tsaya muyi magana ta fahinta sai wani dan sha min kamshi yakeyi, Ko may ya tuna kuma zuwa can naji ya ce Humaira, jin ya ambaci sunana yasani dago kai na kalle shi, Bana son kiji zancen nan a bakin wani ko wata don haka nake son fada, maki kiji shi a bakina, Aure nake son karawa kuma bawai kin min wani abu bane zan kara aure a,a ra,ayine kawai nayin haka yazo, Tunda ya fra zancen shi kaina yana duke a kasa ban daga na kalle shi ba, Yaci gaba da cewa kuma wanan abin irin yadda nake ji idan har banyi auren nan ba a yanzu zan iya mutuwa Humaira, Da sauri na dago kaina don jin may yafada min don na gaskanta zancen shi, Gaba daya ya canza min ya koma kamar wani tababen ya ramay yayi wani baki, dashi sai dogon wuyan da ya kara, Gabana,ne ya fadi don sai naga,gaba daya ya,canza min kamar ba Hamza na ba, Ya dan sauke ajiyan zuciya tare da,furzu iska yake cewa idan ban yi auren nan ba wani babban matsala zai ita samu na don indan har banga Lima ba acikin yini ji nake tankar zanyi hauka, a rayuwana, Duk abinda na kalla zanga wanan abin ya koma,min tankar fuskan Lima ban ganin komai a duk abinda nake sai ita nake gani , Innalillahi wa,inna alaihim raj,un,,, Ya Allah ka ga bayinka suna,bukatan taimakon aka wanan matsalar da ya bullo muna a gidan Allah kai muna mafita mafi alheri akan wanan al,amari, ya Allah ka tausaya muna ba don halin mu ba,, Shiru mukayi gaba dayan mu ba mai iya yiwa wani magana har tsawon wani lokaci kowa da abinda ke mai yawo a zuciyar sa, Yau ma kamar daren jiya ba,wani abinda ya wakana a tsakani dashi don tankar dutse ce a kusa dashi ba ma mace ba sai dan jayewa yake daga gare ni, Tun da safe bayan ya shiga gurin su mama ya dan dauki dan lokaci tare da su can naga yafito rai a bace ina rakube ajikin bangon dakina daga waje, yafito fuu ya,shiga daki kafin ma nashiga sai gashi har ya fito daga dakin yana ce min yatafi, Dakyat na iya bude bakina ina cewa Allah ya tsare hanya Allah ya rufa muna asiri duniya da lahira,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI KUSAKANI GA ADDU,AN KU,,, IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WANI PLEASE,,,, Ranan haka muka wuni a cikin wani irin yanayi babu mai wani kuzari daga cikin mu, Kowa da irin abinda zuciyar shi yake raya masa dangane da zamcen abinda ya faru a gidan, Wanan abin bai hanani yin aiyukana dana saba yi ba a baya, Umma ma wace tun wucewan dan ta take daki a zaune bata fito ba, Sai zuwa sha biyun rana ta dan fito ta kewaya bayi bayan tafito na ta shirya zuwa gidan mama sa,a gurin hiran ta, Sai gidan ya koma tsit dagani sai mama wace kallo daya zakai mata ka hango tarin bakin ciki a fuskan ta, Bayan nai wanka na shige daki nima ban fito ba har zuwa azahar, nafito nai sallah tare da cin dan abinci wanda sam ban jin test din shi a bakina, Ina zaune a gurin naji muryan Umma wace dawowan ta ke nan daga gidan su mama sa,a, Yan mintina naji tana kwada min kira hakan ya,sani tasowa daga gurin da nake zaune, cikin amsa ma kiran da take min din, Kwanon abincin ranan danta jibrin shine a hannunta tana juyawa a hankali, acikin fada take cewa, Yanzu Aisha wanan abinci ne, za,ace rabon yaron nan a gidan nan, Ko mugun halin ki ya tashi ne zaki sauke a kan shi kuma, Wasu irin yawun takaici na hade a bakina tare da dan karasowa inda take a zaune idanuwa na suna a kan kwanon abincin da take nuna min, A hankali na bude baki da zuman nai magana sai sa,a de autar mama ta leko daga daki tana cewa, Umma wani abinci nice fa na diba na zaci shine nawa ai, shiya sa na diba, Nazaci duk bakin ciki karo kishiyan da za,ayi shine har ya shafi diyana za,ai masu horo da yunwa su ma, Don dai ni bazan hana yaron jin dadin abinda yake so ba a ranshi, Aure ne sai babana ya karashi a gidan nan dama kulba dade kulba jima, Juyawa nayi simi simi zuwa dakina don zancen umma yana min daci a raina, Taci gaba da cewa ban san alherin da ya gano ba don kawai ina Rabin mahaukata zan hana shi abinda yai niyar yi, Idan baki hana shi ba ai, kika zama Rabin mahaukatan, Yanzu danki zai auri kafura, wace bata tsarki bata wankan haila, balle na janaba shine har kike zancen kin ga alheri a ciki yaya, ? Wanan abin bakin ciki da gori da ya samay mu yaya ke har kinga gurin saka yar ki sarakuwar ki karamar yarinya a gaba kina mata fade irin haka,? Shiru Umma tayi don zancen mama yai bala,in shigan ta a rai, Idan baba karami ya tashi karo mace a gidan nan Aisha ta isa hanashi ne ko maye nata aciki ita, Yau yaya mu bakin ciki ya cika damu mu da dan mu zai auri kafira ba Humaura kishiyar kafira ba, Mune duniya zatace dan mu yafi karfin mu ai ko,? Sosai jikin Umma ya kara mutuwa tai wani kai zaune tana cewa, Amma aikowa yasan halin dan yau hafsi sai wanda yaso ya zageni a cikin wanan zancen don ansa dai bazan taba yarda ya surka min zuria da jini kafirai ba a gida, Mama hafsi tace sai ko ki dage da yi mashi addu,a bawai wanan shirmay ba haka, Sosai tai la,asar nan sukai ta zancen da yar uwar ta har ta dauki shawaran mama zata dage da addua kan wanan abin kun ya, Sai dai bayan kwana biyu kuma mama Sa,a ta kara zugata ai ta hau fam sai take gani wai ana mata hassadane don kawai ta hadasu fada da yar uwar ta, Ganin yadda Umma ta sakani gaba ga kuma bakin cikin abida miji ke min yasa mama hafsi zuwa gidan mamana Rahana ta fada mata halin da nake ciki na damuwa akan tazo ta samay ni ta bani magana, Batare da kowa yasan zuwan ta ba, har ta tafi tadawo ba wanda yasan cewa ta tafi, Mama Rahana ta samu Ummi da zancen duk hankalin su ya dan daga amma sai suka yanke shawaran kan su kwantar min da hankali sai su bini da addu,a,, Don namiji idan yai niyar aure ba mahalukin da ya isa ya hana shi yi sai Allah, ****** ********* ****** Yau satin shi daya da tafiya amma ko wayan shi na ya isa lafiya da ya saba bugo muna babu shi, Gashi tun ba,a kai ko ina ba abinci ya fara muna tsaiko a gidan ba irin yadda muka saba sau uku a yini ba, kamar baya, Na rasa may ke min dadi a duniyan nan gashi gurin wanda nake dan jin sanyi a gidan yanzu yafi guba daci, Ina zaune ina tunane hannu yana rike da littafina wanda na dauka don na dan rage tunane dashi, Amma karatun ya gagara sai tunanen da nakeyi ina cewa, ni Aisha, Nagodewa Allah na da can ina cewa na huta da fitinar gidan su Ummina, nai aure na a gidan tallakawa yan uwana, Sai gashi babu jindadin babu kwanciyan hankali a tare dani sai tarin fitina duk safe, Sam ban taba tsan manin irin wanan sakaiyan haka ba daga gurin Hamza, Wanda a dacan nake dauka daga Ummina sai shi gurin masu kaunan farin cikina, Sai gashi ya shigo gari na koma mai kamar wata abin kyama, wanan zuwan, na nisa tare da cewa ina gyara zamana, Ya Allah ka tausayawa boyar nan taka Aisha da hanyoyin alherika ka sauya min wanan rayuwan bakin cikin danake a cikin sa, Ina jin muryoyin su Umma da yaranta daga dakina, mama hafsi ne ma banji ta a,waje ba, Ina a cikin wanan halin ne na tu nane naji murya ana sallama kamar muryan Ummi na, Shiru nayi nakara saurarawa don na fahinci mai sallamar, kara sallama akayi muryan mamana Rahana ne, Da sauri na fito waje daga cikin daki ina mata sannu da zuwa, mama cikin nuna farin ciki na, da ga ganin ta,, Inda Umma take zaune saman tabarma ita da yaran ta mama ta nufa suna gaisawa, saiga mama tafito daga dakin ta hannun ta dauke wani roba cikin fara,a take gaisawa da maman nawa, Niko ina tsaye daga bayan su duk na matsu su gama gaisawa da mutanen gidan, Dan jin mama ta mike tana zuwa dakina ina gaba muka,shige, Umma ta raka mu da harara tana cewa Allah dai ya fiku muna fukai kawai ta Allah ba takuma ba, Mama dake bayan ta daga tsaye take cewa ikon Allah, Shigar mu daki na nuna ma mama kujera ina kara kakabewa duk da babu kuran komai a kai nace zauna mama, Gurin fridge na nufa nadauko ruwa da goran zobo duk da nasan cewa suma sana,an, gidan sune kayan sanyi na gargajiya, Mama ta dauki ledan ruwan dake gaban ta ta dan huda ta ja kadan sai ta mayar a plate din don yai mata sanyi sosai, Ina zaune daga gefen ta tadago kai ta kalleni tace Aisha may yasamay ki haka kin ramay kinyi baki duk kin wani lalace a lokaci guda, haka, Dan dukar da kaina nayi yayin da wani malolon bakin ciki naji ya tokaro min a wuyana, May ke faruwa ne haka wai Aisha idan baki fada min ba wazaki fadawa damuwar ki, Sai naji na kasa magana wasu hawaye ne masu dumi suka silalo min daga kumcina, Ganin na sa kuka irin mai kuna zuciyar mai sauraron ta yasa mama rudewa tana cewa, Haba Aisha nazo naga lafiyan ki na samay ki a hakan ga daga tambaya kuma kin saka min kukan tashin hankali, Baki son ina shigowa gurin ki ke nan ko don ba zan zo gurin ki kina min kuka haka ba Cikin dan sasauta kukana nake cewa, mama ina cikin kunci da bakin ciki ga kuma kuntatawan rayuwa wallahi mama ni kadai nasan halin da nake ciki, a gidan nan, Yanzu ki share hawayen ki ki daina wanan kukan ki fada min abinda yake faruwa, Kamar yadda mama tace hakan nayi na dakatar da kukan tare da,share hawaye na, Cikin kwantar da murya na fara zaiyano wa mama abinda ke faruwa tun farkon zancen da kuma irin yadda yanzu Umma ta sakani a gaba da habaici da gori, Mama tana jin haka tace amma ko anyi dattijiwar kawai matar danka zaka saka a gaba kamar kishiyar ka haka, Mama ma ta rasa may zata ce sai kawai tai tsuki ta ja bakin ta tai shiru nadan wani lokaci,, Can murya a raunane take cewa, Aisha abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalinki ki ki saurari may zan fada maki, Cikin sauri na kara mayar da hankalina a gare ta tafara cewa, Dama shi zaman aure dan hakkuri ne Aisha zo mu zauna zomu sabs haka rayuwan aure yake, Shi namiji tundai namijin bahaushe baki raba shi da bakin aure aure, Walau tun kurciyan sa ko kuma zuwa girman sa wani kuma haka zaitayi a cikin rayuwan shi, Don haka banga dalilin da zai sa ki tayar da hankalinki ba har kina batun illantawa rayuwan ki haka, Ba mace daya, ko uku zai kawo lokaci guda babu abinda ya damay ki, Don nagaba yai gaba nabaya dole sai biya don dai kece uwargida sarautar da sai macen da Allah yazaba ta rike wanan sunan mai daraja zata rike shi, a gida, Don haka maza share hawayen ki ki gyagije kinuna ke yar arzikice bata tsiya ba,, Daga Hamza din har uwar wace bata san mutunci ba ki fita batun kowa ki koma ga Allah, Nuna mata cewa Allah yafisu yafi sherin su kuma, Ke dai ki dage ki dinga kaiwa Allah kukan ki banda rashin kunyawa kowa kiyi masu ladabi da biyayya irin yadda kika saba Allah na tare da masu hakkuri insha Allahu, Cikin murya maiban tausayi tare da gyada kai na ce na gode mama Insha Allahu zanyi yadda kikace mama, Takara dacewa zamu dage da maki addu,a insha Allahu,, Mun dan dauki lokaci da mama mukai sallama da ita ta,sallami su Umma da mama inda na rakata har bakin kofan gida sai da ta fita na juyo zuwa cikin gida, Allah dai ya tsare min wanga yaro daga duk wani kuli da tofe tofe da za ai mai,, Allah ya sauka yaya wanga, bakar dabian bai yi ba,wallahi, Nikan tun zuwan mamana sai naji na koma wata wasai dani ban tare da wani kunci ko kadan kamar yadda nake ji a baya, Sai na koma harkoki na kamar yadda na saba yi a baya can, Sai naga hakan kuma baiyi wa mama dadi ba tafara nuna bacin ranta a ganin ina walwala ba bacin rai a tare da ni yasa Umma kokarin ganin na shiga kuncin ta ko wani hali, amma hakan bayi ba,, Daga gurin practical na wuce zuwa gurin hindatu don bata da lafiya tana fama da lalurar karamin ciki a jikin ta, Irin cikin nan mai wahala take fama dashi ga miyau ga amai komai bata ci sai, dan kafa koshi mai dan zafi wai, Hindatu duk ta bi ta wani ramay ta koma kamar wata yar kauye wai ko wanka bat iya yi da sabulu sai dai ta,watsa ruwa kawai ta tashi, Na tausaya ma yadda na samay ta ga dakin ta duk ya wani yi kura ko ina kaya ne birjik, a dakin, Dole na cire hijjab dina na tsaya na gyara mata dakin ya koma tsab dashi wankin da ta tara nace zan dawo nai mata a cikin weekend insha Allah, Sarakuwar ta mama itace take fama da dawainiyar komai yanzu na gidan su har girki mama din na samu a kitchen tana masu girki, Da sharan gida idan yai datti takumakula da Haidar dan Anty hindatu din, Abin gwanin ban sha,awa, don zakace yarta ce ta cikin ta take a cikin wanan halin , Kadan kadan zata shigo tace sannu hindatu ya jikin naki kina son abu kaza kina son ai maki kaza, Hakane zatai ta shigowa tana duba Anty hindatun wace ke kwance sai faman tsriga miya take a wani roba mai dan girma, Yadda nai Alkawari da aka shiga weekend bamu da wani aiki sosai a asibiti sai na dauki permission na dawo gidan ta nai mata wanki tare da kara gyara mata daki tas,a da gida ranan nai mata girki sai dai ban tsaya na ci ba na wuce zuwa gida, Nabar gidan bada jimawa ba maigidan ta Mansur ya iso gidan tun daga waje yake mamakin irin yadda gidan yasha gyara haka, tas A ranshi yana tunanen ko Hindu din taji sauki ne har ta samu karfin yin wanan aikin haka duk da kuma ai bai fada mata cewa yana hanyaba, Sai gashi ga mamakin shi gida yayi wani tas dashi ga kamshi yana tashi, tun kofan shigowa, Ya,shigo gidan da yar fara,ar shi don rabon da ya ga irin haka kusan wata uku kenan, Sai dai yana shiga yai turus a kofan don ganin hindu din kwance a cikin corido din dakin su, yasa a kasa ko riga babu a jikin ta, Ya karasa gurin ta a cikin nuna damuwar shi a gareta yana tambayan ta, ya jikin nata ya dan zauna daga, gefen ta yana dan taba jikin tayana wani tambayan ta acikin nuna damuwan shi da kulawa a gare ta, A haka mahaifiyar shi tafito ta,samay su tana mashi sannu da zuwa, Sun gaisa da mama, yake ce wa mama ya kokari sannu da aiki amma dai aikin yai maki yawa haka ga girki ga wanki ga kuma gyaran gida, Mama tace wane ni nida lafiya bai isa ba yarinyar ga dai yar albarka tazo tai muna wanan aiki harda girki yau ita ce tai munq kuma bata tsaya taci ba ta tafi yanzun haka ko gida bata isa ba ma kila, Wakenan ya juya yana tambayan Hindatu tace cikin dan bata rai don nuna alamar tana jin ciwo sosai a ranta tace, Aishan Hamza ce tazo tayi aikin nan duka ko shekaran jiya ta,zo ta gyara min daki shine yau ta dawo kuma tai mani wankin ta kara gyara gida da dakin gaba daya har da girki, Wani irin tausayi na yaji ya tsirga a ranshi don tuna irin rayuwan da Hamza yake a school da Lima wanan lokacin Sai da ya natsu yai wanka ya zauna tare da dan shi zasuci abinci, yana ci yake tuna rayuwan Hamza Ita Hindatu take tambayan shi ko ya tare suka shigo da Hamza din weekend, Don yanzu yakai zuwa uku ko hudu tana tambyan shi in tare sukazo da Hamza din gari, Amma sai yace a,a yana can bai samun shigowa shi sai wani jikon, Yau ma amsan da ya bata ke nan cewa sai dai addu,a al,amarin wanan guy din don gaskiya yana bukatan addua, sosai, Tan jin haka tau wani iri da fuska tana cewa wanan mutumin ya na daukan alhakin wanan matar tashi sosai wallahi, Nan suka fara hiran su duk a kan zance mu suke ga kuma, yadda uwar miji ta saka ni a gaba duk da danta yana gasa min kwakwa a hannu, ****** ********* ******* Tun mama tana saka ran dawowan Hamza gida don taji may ake ciki a zancen shi da sai shiru kaka ji, ba wani labari, Abinda ya fara tayar da hankalin umma da yar uwar ta ke nan a gidan, Ita dai mama tana ganin abu yai tsamari ta shirya tafiya zuwa garin su tabar yar uwar ta a cikin wani hali, Duk da bata fada ma ta inda zata tafi ba wanan tafiyan tayi shine don yaron yar nata da,rayuwan shi yake bukatar ceto daga hannun shu,uma, Lima, Mama tashiga nan ta fada can haka taita yi har na,tsawon lokaci tana gida tana iya kokarin ta akan zancen, Koda zata dawo, duk Umma hankalinta yai matukar tashi tashiga mugun damuwa, Har tana shirin abi mata shi a gani ko lafiya yake wanan iri shariyar haka mai yawa, Mama wace ta dawo ke nan washegari ta samu Ibrahim yana shirin zuwa sokoto din don dubu halin da dan uwan shi, yake ciki a can, Bata hana zuwan ba don tasan takaici zasu je su karagani a can din, Tunda safe Ibrahim ya,shirya yafita daga gida ya kama hanya,sai garin sokoto gurin dan uwan shi, Kafin ya fahinci komai yadan sha wahala saida wani guy ya kaishi gurin mansur, Don duk wanda yaiwa magana zai ga maishi yana jijiga kai yana fadin taufa aikuwa sai dai ka binciki wani ko zaka san inda yake yanzu don mu ya dade, bai shigo nan ba, Karshe gurin Mansur akai kai shi yana ganin shi duk ya,shiga guiltyness, ya rude don bai sam mai zai fadawa ibrahim din ba, Karshe dai yace su shigo mota ya kaishi inda yake dashi da wani abokin su, A mota dayan abokin ke cewa gaskiya bawan Allah dan uwan ka yana bukatar naiman taimako don rayuwan shi na a cikin wani hali, Don yanzu haka har wasu suna tunanen ko yayi ridda ne sai da muka tursasa shi yazo ko sau biyu ko uku yai sallah a school mosques kowa ya ganshi asan cewa yana na as musulim din shi, Mansur wansa sai a lokacin yai magana yake cewa mutane suna yawan tambayana ko baida kowane da akabarshi a cikin wanan irin rayuwar haka ba kwabo, Subbahanallahi Ibrahim yace a cikin dacin rai da kunar zuciya, Wani unguwa suka shiga mai dan cunkoson jama,a kowa sai harkan gabn shi yake a uguwar, Wani gida suka nufa sun tsaya a kofan gidan sai mansur ya tura yaro yai masa kiran Hamza din, Sai gashi acikin wani yanayi bottom din shirt din shi duk a bude kwala a tashe baida ko belt a wandon shi idanuwan shi sunyi jajir dasu , Yafito a zaton shi wanda ya aikane ya dawo shi yasa shi fitowa ido biyu sukayi da bakin shi wa yanda sukr tsaye a bayan motan Mansur idanuwan su a kan shi, kar, Yaji nauyi da kunya irin yanayin da aka,riske shi a cikin sa amma ba yadda ya iya sai kawai ya basar da zancen, Ya karaso gurin su, don taron su, duk kan su fuskan ya ya nuna mashi kyama sahihin ta sama sama suke suna gaisawa, Yayi da wata mace mai jiki nono rugun rugun ciki wata yar riga kamar shimi iya cinyar ta , Ta leko daga dakin tana cewa wai waye my baby ? Wanda taki ji da son gani Mansur ta gani tare da wasu mutum biyu ,da bata san su ba , Sun gaisawa da Hamza da ibrahim yana jin muryan ta ya wani firgice, ya rude yana cewa baby ina zuwa brother dina yazo daga gida, Harara Mansur da dayan mitumin suka,watsa mata daga inda take a tsaye tace brother ka fa, Sai kuma ga,wata itama katuwa ta dago labulen falon tana tambayan wai su waye a gurin ne, Duk suka kara saka mata idanuwa ita ma tace cikin yaren zu wanan mutumin mai mugun nacin tsiya ne fa ya kawo dan uwan man nan di , A tsatsaye yake magana yana cewa,ka koma kawai idan na su time zan shigo ai bada dadewan nanba zan zo na gan ku, Yanzu yaya baka tausayi Umma da matar ka yarinyar nan Aisha tana can zaune zaman ka amma kana nan da wayan nan matan banza kana holewan ka haka, Da sauri ya juya baya don kada suji shi ibrahim din sai cewa yayi haba kada ka bari sujika mana dan Allah, Baby kazo mana kada game din ya tsaya muna jiran ka, Innalillahi Ibrahim ya kara furtawa ya juya zuwa shiga mota yana kuka ya na share hawaye daga idanuwan shi, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WANI PLEASE,,, Ganin yanayin da ya,shigo kawai ya ishe mai hankali gane ba lafiya, Duk da shigowan dare yayi don ya dawo ana shirin sallah magarib amma jiki a sanyaye yake karbawa mutane gaisuwan su, ya,suri buta zuwa alawa ba tare da ya wa kowa magana ba, Bayan an dawo daga masallaci ya shigo gida a cikin wani yanayi, Umma wace duk take a,matse don taji abinda ke gudana, a tafiyan nashi, Yana shigowa take cewa ka ganai ? Yace a sanyaye nagan shi Umma yana gaishe ku, ma, Aikina nake sai dai kunnuwa na ya garesu amma mutum bazai iya cewa ina sauraren su ba ma, A irin yadda na lura da yanayin Ibrahim nasan baizo da labari mai dadi ba daga can, Ibrahim ya dan daga kai a lokacin da zai zauna yana kallon sashen da nake tsaye ina zuba goruna a buhu, Sai ya juya inda su Umma suke yana zama dirsha, dashi, Mama tace yaya duk naga ranka a bace ne hakan nan , ko baka gan shi bane wai, Ya dago kai ya dubi Umma tare da dan kashe ta da ido sai kawai ga hawaye suna gangarowa daga idanuwan Ibrahim din nikan ina daga duk naji wani irin gurnanin kuka da Umma ta sake abinda yai saurin dawo min da hankalina garesu ke nan, Naji mama na cewa cikin kunan rai haba yaya yaron ga baiko maki bayani ba,amma kin saka,wa mutane kuka haka, Kada ki tara muna makwabta a cikin gida batare da,ansan may kikewa kuka ba, Ibrahim cikin kuka yake cewa Umma yayan mu yana bukatar taimako sosai don rayuwan shi tana a cikin hadari, Suka kara saka salati nan ya fara basu labarin may ke faruwa a,sokoto da ya je yagani tare da dan uwan shi, Wanda mutane suke wa kallon cewa yayi ridda ma akan wai yana taraiya da yar kiristan, Tankar ban san abinda suke ba,sai aikin hada zobona nake ban nuna komai ba akai, Tunda Umma tace ina bakin ciki don dan ta ya,samu karuwa alheri zaiyi aure na dauki bakin rai na,sakawa raina ina bakin ciki da kowa a gidan, Wanan dalilin yasa koda suke zancen na danne zuciyata ban nuna masu cewa na damu da zancen Ibrahim ba,, Tiryan tiryan Ibrahim ke mayar masu da halin da ya samu dan uwan shi a sokoto cikin wani hali na bukatar taimako, Kuka mai sautin tausayi Umma ta kara sakewa tana cewa Allah ya isar mata ga,wanan bakar mace kafiran banza wace bata sallah, Mama hafsi tace duk wanan yanzu ba,shine abin yi ba yaya mafita ya kamata mu ne ma mashi mu samu a,kwatoshi daga wanan macuciyar matar, Ibrahim yake basu labarin cewa ai, Mansur ya fada mashi duk wani abinda ya,faru, Don kungiyar musulmai na makarantar sun yi iya kokarin su wajen ganin su kwato Hamza a hannun matar amma abin ya,faskara, Don yanzu haka ma har abin yafara shafan karatun shi sosai don yana kokarin samun matsala a karatun shi, Umma tace ita bata karatu take ba kawai dai ta samu dan ta ya,dawo gida shine abin da take bukata yanzu, Yaya ba yau ba ina fada maki cewa wanan zancen ba karamin zance bane, amma sai kika ga kamar ina maki bakin ciki ga samun dan ki to yanzu wa gari ya,waya a cikin wanan magana, Umma shiru tayi don ji take kamar zuciyar ta zai tsage kirjinta ne ya fito saboda zafin da yake mata, Inda suke zaune zugun zugun nazo ina cewa, Mama akwai sauran clean a dakin ki na,wanke kwanukan can, Duk sai suka bini da ido kowa da tashi tunanen sai Umma ce take cewa, cikin hasala ana zancen yaro ya shiga wani rayuwa ke ko ki damu da zancen, Cikin girmamawa nake cewa, Umma ni ban san may kuke magana ba ai da banzo ba zatai magana Mama tace mata haba yaya may ye laifin wanan yarinyar a nan shi kashe ta za,a yi a huta ko may, Yarinya duk tana cikin damuwa mijinta yana cikin wani yanayi kuma zaki aza mata fitina akai, Ai Aisha tayi kokari don duk abin nan bata taba nuna damuwar ta ba sai hakkuri take abinta, Yau azamanin nan haka zai faru bakiji gari ya dauka ba, don Allah mu bita a,sannu, Ansan ke kika haifi yaron nan to ita kuma ai matar shi ce , Lokacin da yazo da zancen ai tai matukar nuna damuwar ta amma kikace wai tana maki hassada ga da, Yanzu kinga ai dole ta kawar da idon ta da kunnuwanta ga zance shi kada kuma kice ga abinda tayi, Ai baki yarda a fadi laifinta don komai tayi daidai ne a gurin ta, Mama tace yanzu ba shiba kamata yayi ki tashi muje mu samu yan uwan mahaifin su mu fada masu, Da sauri mama tace hafsi ko mun fada masu may zasu yau she rabon da naje gurin su, Don nasan yanzu a jirace suke dani suna jiran ranan da zanzo masu da zancen wani daga cikin yaran nan, Mama tace ba na fada maki ba kowani da da yan uwan shi yake alfahari a duniya, Amma hayatan hayatan kin raba yaran nan zumunci da yan uwan su, yanzu dole ne mu tafi don babu yadda zamuyi, Sun tafi gidan su baba madu shine mai dan taushi a ciki dole shi suka sama da zancen, Shima yai fada amma ba wani mai tsawo ba yace yanzu wanan abinda ji bana kai tsaye bane dole ne a tashi tsaye ne man mafita a kai, Yace zai zauna da yan uwan shi suyi magana duk yadda akayi zuwa gobe da yamma zata ji shi, Hanyan su na dawowa ne mama take cewa ya kamata a fadawa malam Mudi don kar yazo yaji bazaiji dadi ba, Amma sai Umma tai fin firin fin cewa, bazata fada mai batayi tallah dan ta, ****** ********* ****** Suna fita na fada daki dama kamar jiran subar gidan nake na fada dakina saman gado sai kuka nan nai kuka mai isata sai da ya isheni babu mai lalashi na a dakin Ina nan kwance, nai shiru sai sake saken zuciya nakeyi wata zuciya tace min tun da hakane na bar gidan kawai, Wata kuma tace min nabi maganan uwayena na,zauna nayi hakkuri komai yazo mai wucewa ne wata rana, Muryan mama naji tana cewa sarakuwata har kin shige ne yau haka da wuri, A firgice na waigo yare da,dagowa daga kwanciyar da nayi ina cewa, mama idona biyu a cikin muryana da ya,dushe don kukan da nayi, Mama ta karaso cikin dakin inda nake zaune tana mai kura min idanuwan take cewa, Aisha kar dai nace kuka kike darza, haka tun fitan mu, ga idanuwan ki duk sunyi sulu,sulu haka dan kuka, Maza wanke idanuwan ki, kafin a farga da cewa kinyi kuka ne haka,, Kamar yadda mama ta umurce ni, hakan nayi na mike kamar mai alawa na wanke fuska na, sa,ilin na tafi gurin Umma ina mata sannu da dawo, Ibrahim da ya shigo gida har kofan dakina ya tafi ya,samay ni a zaune, yake ce min Mansur ya ce ya fada min naje gidan shi gurin matar shi a kwai sakon da zata bani, Nan kuma yake kara min nasihan cewa, na kwantar da hankalina kada na tayar da hankali har na,zo na,shiga wani hali ,dole za,a san yadda akayi akan zance na nan gaba na,dan saurara har aga abinda hali zaiyi, Naji dadi nasihan Ibrahim don tsayawa yayi yai min nasiha tankar wani babban mutum, Tun shigan shi har fitowa shi duk su Umma dasu mama suna zaune a lokacin, Ido tabi shi dashi tana mai jin haushin irin yadda har ya tsaya yana nuna damuwar shi a kaina bayan ga abin damuwar shi a kan dan uwan shi dake a cikin wani hali, Gurin su ya nufo yana kara gaishe su tare da tambayan su halin da ake ciki, Maimakon Umma ta bashi amsa sai take cewa, may kaje fadawa Aisha kuma yanzu, Don naga kamar ita abin ko a jikin ta,don rashin sanin ciwon kan ta har ya kai mijinta na cikin wani hali amma,ba zata iya nunawa ba, Haba yaya inji Mama hafsi ta katse ta tana cewa hakan bagirman ki bane fa iyakar kawaici yarinyar nan tanayin shi a gidan nan, Don Allah yadda yarinyar ta nuna muna kawaici bai, kamata kuma mu saka a gaba ba haka, Wanan dalili ya sa na samu sauki sosai a gurin Umma don ita kanta kamar yadda Umma tace ta gane gaskiyane nima din nafita damuwa kila dan,ne abin kawai nake a raina don kawaici, ****** ********* ****** Tun bayan tafiyan Ibrahim yake jin wani irin dacin rai a ran shi, Sai dai kuma bai iya tabuka komai a,rayuwan shi don yana bala,in tsoron bacin ran Lima, Ranan yini yayi a sanyaye, jiki babu kwari duk yadda,taso ta,sham,mace shi ranan ta,kasa, Yadda ta ta lura da yana yinsa yasa ta gane cewa something is wrong, Don haka ta shiga tai irin abinda takeyi tafito da shirin ta a lokaci Allah ya bashi sa,a yana maimaita kalman La,illaha, illa, anta subbahanaka inni kuntu minal,zalimu, daga can cikin kasan zuciyar shi, A daidai, lokacin tafito daga daki tana wani tako saye take a cikin wani skirt, baki mai tsaga a bayan shi, A hakali takawo gare shi tare da kokarin rugumoshi zuwa jikin ta amma ga mamakin ta yau sai taga ya dan kauce mata kawai, Zauna wa tayi daga gefen shi tana dan kokarin taba jikin shi a hankali nan ma ba,wani abinda tagani, daga gurin shi yadda ya saba, Lafiya kake yau kuwa my dear ? A cikin wani sanyin murya yake ce mata ina tunanen mumm dina ne da yan uwana, Damm taji don rabon da taji haka daga bakin shi kusan tun maganin baiyi tasiri irin haka ba,sai gashi yau taji ya fadi hakan kuma, Ranta ta bata har ta kasa boye fushin ta tace a cikin wani kakausar murya mai daci, May ka,rasa anan da har zakayi tunanen su,? Duk irin hidimar da nake dakai baka gode ba ke nan Ban bukaci komai a gurin ka ba,sai kudin Gulmo da zamu kai gida wanda dole sai a hannun ka zai fito , Bayan shi duk wani abinda muke a nan nice mai yin su amma shine yau zakace kana tunane yan uwanka, da mamanka, Kadai fito fili ka fada min kana kewar matar ka kawai, Da sauri yadago kai don zai iya cewa rabon da ya tuna da wata Aisha har ya manta, Dama a da can baya ko abinci zaici lafiyayye zai tuna da cewa Aisha tana can yanzu a cikin wahala da ukubur Umma, Gashi kuma ya kara bijiro mata da wani sabon masifan rayuwa haka, Fadar Aishan da tayi yasa shi dan lumshe idanuwan shi a hankali, Take fuskan Aisha ya baiyana a idanuwan shi tankar ina tsaye ina murmushi dan dimple dina yana dan lutsawa, Hasbunallahu wani,imal wakeel, ya furta a fili a binda ya bata tsoro ke nan don rabon da taji yai wani abinda ya,shafi adduan addinishi tun ranan da taje kauyen SANCI saboda shi, tun ranan batajin yana addua kamar baya , Don yanzu wani irin kasala yake yawan ji baida aiki sai ci da barci, Amma sai gashi yau kwatsan taji yana karato addu,a a bakin shi, Yinin ranan duk yadda lima taso bata same shi ba don gaba daya ya birkice mata sai nuna kyamar ta da yakeyi, Abinda ya fara tayar mata da hankali ke nan tasan cewa idan tai wasa zata zama abin tausayi sosai nan gaba don yanzu sai da yan uwanta suka, fada mata cewa zai iya komawa normal don asiri aikin sa kwana arba,in ne kawai, dole sai kanayi kana tusa sabo, Hankalinta yai kololuwar tashi don tasan cewa akwai abubuwa da dama a gaban ta wanda dole tai covering din su kada ya dawo a cikin hayacin sa, Saboda bokanta yace yadda yabar nonon uwar sa haka zai manta da kowa nas har uwar sa da matar sa, Da farko taga faruwan haka amma kuma sai gashi yau zancen nason ya zama wani sabon al,amarin da bata zata ba a halin yanzu,,, ****** ********* ****** Zaune suke bayan zuwan su Baba Madu inda shi da wani dan uwan, su suka zo har gida gurin su Umma din akan zancen, Bawani dogon bayani sukayi ba illa cewan da sukayi idan sun samu lokaci zasu aika atura can sokoto don a dubo masu halin da Hamza din yake ciki saboda su san abin yi, Baba Madu yace Rabi ni kin san yanzu ba lafiya gare ni ba, lalabawa nakeyi idan ba haka ba,da ko gobe ne zan iya zuwa na dubo shi gashi kuma banda zarafin zuwa ko nan da tambuwal balle har sokoto, Sai dai Umma tayi hakkuri su dage da addua shima insha Allahu zai dage gurin yin adduan Allah ya kubuto masu da Hamza din daga hannun azzalumar matar mayaudariya, Bayan tafiyan su ne Umma ta sake wani irin kuka cikin tausayi tana cewa yau lalai diyan ta suna cikin maraici, mai tsanani don an nuna masu basu da kowa a duniya sai ita, A sanyaye mama ta kira sunan yar uwar ta cikin yanayi mai ban tausayi take ce mata, Ki bar kuka yaya Allah yana tare da mu insha Allahu koda zan rasa duk abinda na mallaka a duniyan ne, Hamza sai ya dawo gidan nan cikin dan kankanin lokaci insha Allahu, Don haka yanzu zan mike kai Ibrahim yanzu akwai abinda nake son zuwa, muyi da kai taso mu tafi, Can bayan gari suka tafi inda Mama tayi kamar yadda akace mata tayi, Suna dawowa cikin gari ta ce ibrahim ya zagaya gari dasu idan sun samu makaho wanda yar budurwa take masa jagora ya nuna mata, Sun dan sha,wahala sosai yayin da suka hadu da,wani dattijon almajiri shida yar sa suna dawowa daga gurin bara, duk sun gaji, Da,sauri Ibrahim ya,dakatar da mashin din da yake ja suka dakatar da mutumin da yar sa, Baya gaisuwa ne mama ke cewa bawan Allah sadaka muke son baiwa yar ka saboda Allah da Annabi, Dattiijon ya ce madallah mun gode sarkin da,akaiwa ya sani, Taciro farar shadda da farin goro da sugar da kudi dari biyar take cewa, karbi yarinya ki muna fatan alheri a rayuwar mu, Suka wuce dama bukatar mama yarinyar ta karbi kayan daga hannun ta, yayin da ita mama ke mika mata kayan take fadin yadda yarinyar na ta karbi kayan nan ina,son na karbi dan yar uwana Hamza daga hannun azzaluman da yake gurin ta, da gagawa, Shiko makaho da yar sa gaba takaisu sai faman addua suke kwarara,masu, A hanya Ibrahim yake cewa mama naga kamar ya kamata muje gidan liman Audu muyi mashi bayanin irin halin da ake ciki ko da taimakon da zai muna, Don bamu da nisa sosai dashi kuma naga yasan yaya din suna shiri sosai dashi, Mama daga bayan mashi tace kwarai kuwa Ibrahim ka kawo shawara sosai, Gidan liman din suka nufa sun samay shi zaune a zauren gidan shi yana karatu shi kadai, Sauran almajiran shi duk suna daga waje zaune suna karatu, Ibrahim ya saka ai masu iso a gurin Liman din dan jimawa kadan akace su shigo daga cikin zauren Bayan gaisuwa ne sai yake tambayan su ko.may ke tafe dasu ne haka, Ibrahim ya fara bayanin abinda ya kawo su gurin shi inda mama ta cabe zancen tafara mashi bayani tiryan, tiryan, Bayan ta gama malam Audu ya jinjina kan shi gami da gyara zaman shi yana cewa lalai yaro yana cikin tashin hankali , Nan ya fara karanto ayoyin ,alkur,ani maigirma da hadisai yana masu bayani akan sihiri da kuma sherin yahudawa, Suma su mama ya nuna masu nasu kuskuren kwarai da suka tafka wajen kyale shi tun farko da yazo da basu nemi mutanen da sukafi karfin shi su hada shi dasu har su fadakar dashi, Liman yai masu alkawari zaiyi wani abu akai insha Allahu zai yi iya kokarinsa gurin ganin ya taimaka ma wanan bawan Allah ya kubuto daga sherin wanan shu,umar matar, Sosai sukai mashi godiya mama ta ciro kudi daga habar zanin ta tace aiwa yara sadakan alawa dashi, ****** ********* ****** Sun sami su Umma a gida suna dakon zuwan su saboda basu san inda suka tafi ba a lokacin, Tana daga daki ta kunna fankan dakin ta sai iska ke tashi kamar zai fado kasa, Mama taji haushin wanan abin take cewa, kina nan kin kunna fanka kina sha kina jin dadi danki yana can a cikin halin hau,ula,i ke baki ko damu ba, Zaune Umma takai dakyau sai yanzu da mama tai magana taji haushin wanan shegen fanka da aka yaudare ta dashi aka cuta masu ita da dan ta,,, Bayan sun hutane sun kamala komai Ibrahim yake fadawa mahaifiyar su irin kokarin da yar uwar ta take yi akan halin da suke a ciki, Wani irin sanyi da dadi Umma taji a ranta har sai da fuskan ta ya baiyanar da farin cikin ta, Ibrahim yace yanzu Umma dole ne mu dukufa gaba dayan mu gidan mu shiga addua da rokon Allah, Ina daga daki naji yakirani nafito na samay su gaba daya gidan nan suke fada min cewa wai suna son muyi azumi don taimakawa Hamza din, Murmushi nayi nake ce ma Ibrahim din na dade ina azumi akan wanan zance sai dai kawai a kara kaimi, akai, Allah sarki boyar Allah kema kina nan kina faman naki kokarin Alkah dai ya saka maki da alheri kinji kiyi ta,addua Insha Allahu komai zai wuce, Umma tace da yardan Allah sai Hamza ya dawo gidan nan a cikin kwanakin nan Gaba daya muka amsa da Insha Allahu, Allah ya yarda ya amsa muna, Daga gidan mama Sa,a kawar Umma zance yafito yafara yawo a cikin uguwa, Autar Umma,Sa,a datu itace yaran makarantar su, suka fara yiwa gori da kuma fade, kan dan uwan ta saboda mugun halin uwar su ya samu matsala ya auri kafira a birni, Ranan sosai Umma tai fada inda ta tashi suka tafi gidan har da mama , Amma sai mama sa,a din take cewa yanzu ke Rabi maye abin boyewa a cikin zancen nan, Abi duniya ai baya boyuwa ko may ye sai anji shi, , Kuma ai ba karya aka fadi ba don gaskiyane ko nai auri kafira,bane yagudu gida yabar uwar shi da matar shi, Anfada ne don ansan may ya aikata sosai mama ta,zage a gidan ta mayar masu da martani cewa ai babu wanda ya wuce kaddaran Ubangiji a kan shi don wanan jarrabawan rayuwan shi ne daga Allah , Idan ita ta mayar da zancen abin gori sai ta matsa taitayi don su sunyi imani da Allah, ne ya aiko mai da wanan kaddaran a rayuwan shi, Matar gidan wace ta,samu labarin ne a gurin kawar Umma din mama sa,a tace mu dai ku fita mu a gida an fada din ba abin fada yayiba, Wanan dan hasumin da aka samu yakarasa mutane suka,san da zancen a guwa, Taufa abu ya kara rikicewa sosai Don a gidan su Ummina nan aka,shiga yi mata habaici da gori cewa miji ya gudu yabar mata ya dama cusa mashi akayi ba,so yake ba kilama shi yasa ya gudu yabarni yatafi can ya auri wace yake so, Sosai hankalin Ummina ya tashi don haka ta samu yar uwarta da zancen suka ce dole ne suma su taimaka tare da mama suka tafi wurin wani malami yake cewa abawa matar shi abinci takaiwa marayu na,sahihi sadaka har na kwana uku insha Allahu komay ake ciki zuwa kwana ukun zai faru, Haka akayi shimkafa da wake da mai da yaji nake dafawa a cikin wani katon kula sai mu dauka nida mama da Asmau mukai gidan wani makwabcin mu da yarasu yanada yara da mahaifiyar su itama tarasu ta riga mijin rasu yaran mayar nake ba ba,wa yan da mahaifiyar su takr da rai ba, Har tsawon kwana uku muna wanan abin kowa yanata faman kokarinsa akai, Gari ko yadauka kowa da irin abinda yake fadi sai karya ake shararawa don labarin yayi dadi sauraro, Na ramay nayi baki abu yai min yawa ga karatu ga practical ga kuma tashin hankali duk wanda ya ganni sai yaji tausayin irin yadda yagan i na koma a lokacin, Tun ranan yan uwan su ba,wanda yazo sai baba madu ne idan ya samu mai zuwa akan dan kawoshi ya duba lafiyan mu ya ji may ake ciki akan zancen, Sosai yanzu nida Umma mun dan shirya don tabar zuwa gidan Sa,a aminiyar ta, Mamana Rahana tana zuwa tana dawowa don duba halin da nake ciki dakuma jin irin halin da ake a ciki a lokacin, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WANI PLEASE,,,,, Umma ta susuce takoma abin tausayi saboda batan dan ta, da ba,a san inda ya shiga ba, Duk wanda yaga mutanen wanan gidan dole ne ya tausaya masu saboda yadda rayuwa ta koma masu gwanin ban tausayi, Ga yanzu mutane ba tausayi wanda bakai zaton zai maka sheri ba,shine farkon mama sheri, Mutane suna cewa laifin Umma ce don kwadayin ta ne ya ja mata haka din, Sai na Allah ne suke tausayawa suka san cewa abin yazo ne daga Allah suyi mashi adduan Allah ya baiyana shi, Mama Hafsi wace itace tsaye wurin ganin Allah ya dawo masu da dan su gida lafiya, Yau ma bata gajiya da zuwa gidan malam Lima don tana jin dadin kalaman shi a kan dan nasu, Sun gaisa kamar kullun da malam din yake tambayan ta karin hakkuri, Mama ta dan gyara zama tana cewa malam Alhamdullahi sai gaskiya har yanzu ba,wani labari mai dadi, Kai Liman ya kada daga inda yake zaune yana cewa ku kwantar da hankalin ku don dai ni duk inda nai istihara ina ganin wanan yaro yana raye sai dai baida lafiya a jikin shi, Amma zuwa yanzu gaskiya da sauki sosai yadda na gan shi a karshe, Insha Allahu zuwa nan da kwana,biyu zai baiyyana bi izzinillahi, Matar shi ko uwar shi ta kara kai sadaka a gidan marayun nan kamar farko, Kin san duk yadda kikai wa marya alheri a rayuwa tankar wani takine kika zubawa rayuwan ki don insha Allahu ba,a kwana baki fara ganin haske ba a rayuwan ki, Mama zata tashi ta dauko dubu daya taba malam yace cikin kada kai ki barshi kawai don wanan matsalar ta shafi kowan mu a garin nan, Mama tai godiya tadawo gida ta shedawa yar uwar ta duk da ma zarah suka tafi amma saida tayiwa Umma dake cikin damuwa bayani yadda zata gamsu, Mama tace tunda Aisha ce ke wanan sadakar tun farko to abarta tayi abinta, Nai kamar yadda suka umurce da yake labari yabi gari gidan sun san abindake faruwa damu da zan fito yaron yace Allah yasa aga mijiki lafiya cikin murmushi da jin dadin addun ashi na,amsa da amin nagode kaji, ****** ********** ****** Da sallama dattijon ya,shigo dakin inda ya samu Hamza zaune ya rike kafafuwan shi, Malam Hamz zaune kake ashe tsohon ya tambaya tare da kokarin kaiwa zaune, Baba sannu da kokari inji Hamza din yake cew mutumin da ya shigo dakin, Mutumin yace ina fatan yanzu komai kana iya tuno shi a cikin natsuwa ? Hamza ya gyada kai tare da cewa insha Allahu Baba ni yanzu miradina shine naga iyayyena yan uwana da mamatata, Insha Allahu zaka gan su da yardan Allah ka godewa Allah daya kubutar dakai daga hannun wannan shu,umar matar, Yace ire iren wa yan nan matan suna da yawa sai dai kowace da nata sallon yaudara don wata shu,umar mutane bazasuyi sauri gane sherinta ba saboda zaune a ke tare da ita a cikin gida saidai babba da,yaron gidan duk ta sihirce, su suna under control din ta sai yadda tace, Wata kuma iyakarta a mijin don shi take so shi zatayi ta juyawa batare da ya sani ba saboda tsananin sihirin dake kan shi, Sai dai mutane su dinga gani amma shi baya gani a idanuwan shi a rufe suke da sihiri an murdeshi bai iya,wani katabus, arayuwan shi, Wata saboda tsananin sihirin sai tajawa mijin komawa wawa daga karshe ma abin idan yai yawa sai ciwo ya,shige shi ya mutu ko ya koma,mara amfani, Allah kasa mufi karfin zuciyar mu muda zurian mu da sauran yan uwa musulmai, Dattijon yace yanzu abinda nake jira isowar yan uwan ka da suka taimaka maka kafita cikin wanan ukubur wanan bakar kafiran da ta tashi nakasar maka da rayuwa kana dan karamin ka haka, saboda ha,inci da cutarwa wai da sunan so, Idanuwan Hamza ne ya ciko da hawaye yace baban ban san da wani irin ido zan kali iyalina ba dashi, Mahaifiyata yan uwana duk nauyi da kunyan kallon su nake ji kan abinda na aikata don wasu sam bazasu taba yarda cewa wai ba a hayacin kaina na aikata wanan abubuwan ba, a rayuwa na, Kada ka damu tare dani zamu tafi har gida nakaika nakuma yi masu bayani gamsashe yadda zasu fahince ni, Hawaye ne masu zafi da radadi suka malalo mai daga idanuwan shi zuwa idanuwan shi, Acikin zuciyar shi wani zafi yake ji kamar zuciyar shi zai fasa kirjin shi yafito waje, Lima Lima tsakanin shi da,wanan matar Allah ya isa kawai, Ya rintse idanuwan shi daya tuno cewa, ta mayar dashi kamar wani mashi ba dare ba,rana gurin amfani da ita, duk sanda yai mata,dadi haye ta kawai zaiyi yai ta mata abinda take so take bukata shi baida na cewa, Gashi dan kaddaran shi a lokaci guda ta umurce shi da ya,sayar dasu gaba daya yanzu baida komai wanda zai iya nunawa a matsayin nashi koda kuwa kaza ce, Wanan tunane yasa shi fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi yana rausauya wa kan shi yana kuma tausayawa mahaifiyar shi da matar shi, Aisha yarinyar kirki mai hakkuri da sanin ya kamata ko tana cikin wani hali yanzu oho, Allah dai yasa iyayyen ta,da ita basuyi fushi sun dauke yar su ba,daga gidan shi, Don tun auren su bazai iya cewa ga wani abin arzikin daya kara ta dashi ba a rayuwa banda karatun da ya mayar da ita, Yanzu kuma bai san makomar karatun ta,ba tunda ya kaurace masu na tsawon wani lokaci wanene zai tallafa mata a karatun , Ya lumshe idanuwan shi yayin da hawaye suke ci gaba da kwaran yowa daga idon nashi yana dan matse su, Baya kaunar ko a cikin mafarki yaga wanan kafirar mata kuma balle a fili, ****** ********** ****** Kwana biyu sun cika mama ta kasa hakkuri ta koma gurin malam Liman tace malam gashi yau har kwanakin daka,ba,mu sun cika anya kuwa malam yaron nan yana,a,raye kuwa, Malam yai murmushi yace kizama mai tawakkali a,rayuwan ki domin gagawa ba alheri bane, wani lokaci, Tunda nace maki zai zo zai zo din insha Allahu don haka kwantar da hankalin ki kawai, Badon taso ba ta dawo gida jiki babu kwari don sai take gani kawai dubarun liman sun kare ne yasa yace mata haka kawai, don ya kwantar mata da hankali ne yake ta fada masu hakan, Daki mama ta,shige sai kukan ta kawai mukaji abinda yasa gida ya kara rudewa ke nan da wani sabon kuka tashin hankali zalla, Da kyat su Baba Mudi da suka,shigo suna tambayan mu lafiya ko anji labarin shi cewa ya mutu ne da muke wanan kukan haka, Nan mutane suka,taru sukai ta,bamu magana har muka hakkura ranan baba har dakina ya shiga yazauna a saman kujera na yai min nasiha akan hakkuri don ance mai hakkuri baya tabewa duniya da lahira, Haka yasa muka dan kara dada hakkuri a zukatan mu har muka koma dan normal Ganin har karfe uku yau Ibrahim bai kawo abinda zamu ci ba yasani mikewa na hura wuta tare da,tsabatace gurin sanwan nawa dama cikin gidan, Umma tafito daga dakin ta don ji na hura wuta ta tambayeni mai zanyi sai nake ce mata zan gyara muna kanzo dana tara ne aci, Tace tau sauran kayan miya fa nace ma Umma, na aika adan sayo mun tankwa da manja na hamsi da gishiri zan zuba muna, Nagama dama kowa yunwa yake ji agidan na,raraba mu a kuma yai dadi sosai don yana kamshin dadi, Muna zaune a tsakar gida har su Ibrahim mukaji dirin din mota ya tsaya kamar a kofan gida, Ba,wanda ya kawo wani abu a,ranshi sai cin abin mu mukeyi hankali a kwance, Kamar daga waje muke jin hayaniya,amma,sai ba,wanda ya kai hankalinshi don yunwa kowa keji ko karyan wan safe bamuyi ba, ****** ********** ****** Sallaman yara muke ji suna shigowa da ihu ga Hanza yaro ga Hamza yaro abinda ya ja hankalin mu gaba daya ga yaran ke nan, Mikewa Ibrahim yayi zuwa waje don duba gaskiyan maganan yaran, Mutane ne cinjim.a kofan gidan sai rugumay hamza din sukeyi, Daga inda nake tsaye naji abin da yaran ke fadi zancen yazo min kamar a mafarki sai ji nayi, Dif dif dif ban san inda nake ba kuma daga haka sai farkawa nayi naganni tare da,su Ummi su mama saude suna dan mani hitara, da sannu, A hankali na bude bakina da kyat nai magana cewa mama da gaske ne Hamza din yadawo, Mama saude tace da gaske ne Aisha gaya can suna gaisawa da mutane, Na mayar da idanuwana a hankali na lumshe su tare da wasu haye masu dumi da suka biyo fuska na, Gida da uguwa ya cika da masu zuwa muna barka da arziki, Yan uwa duk sun rike shi sai kuka,sukeyi tare godiya ga,Allah da ya,baiyanar dashi, Zarah mijin ta yabugo mata waya cewa tazo gida ance Yayan ta yadawo gari, Ta hawo mashi a,sukwane suka kawo da mai mashin din hankalin ta a tashe tana cewa, wai da gaske ne yayan mu yadawo, Ta na ganin shi tafada mashi tana kuka tana cewa yayan mu munzaci mun rasaka ke nan, Allah mun gode maka da kadawo muna da dan uwan mu gida lafiya,, Sai kuka,suka kara sakewa haka mutane yan uwa da abokan arziki sukai ta kai kawo gurin shigowa har wanda bamu sani ba sunzo, taya mu murnan dawowan shi, Wasu suna cewa wai akaini asibiti amma sai mutumin da suka tare yace a,barni a gida damuwar da na,shiga ne yake sauka, Sai bayan kowa ya rage agidan an watse sai mu yan gida,da,baki koshi sai da aka,rufe kofan gidan, Sai su Baba Madu baba Mudi, da Baba Liman sai mutumin ya fara bayani kamar haka da cewa, Ku godewa Allah daya nufe shi da,dawo cikin ku bai halaka ba ko canza akida, Da,safiya na,samay shi a hanya shine ina ganin yanayin shi nasan ba daidai yake ba sai aka,saka,salati a,dakin baki daya,. Nan dai yai masu bayani akan yadda suka shirya zai fadi shida su Mansur,, Don gudun kada, agane cewa daga gurin su ya,fito shima hamza din yana cikin class akakira shi ana sheda mai baiyyanar Hamza din cikin jin dadi da,sowan su suka,ruda guri da ihu eh anganshi anaganshi,, Abin waya kafin wani lokaci labari yakai wa su Lima cewa anga Hamza dama a under beli take don haka sai tai wani irin ihu da murnan jin dadi sosai, Nan take tafara planning din yadda zata dawo dashi gareta kafin iyayyen shi su dauke mai hankali gare ta, Take ta shiga kullawa da,warwarewan yadda abin zai tafi mata daidai, ****** ********** ****** An natsu kowa yana sauren bayanin mutumin da,sadudan yadda mace shu,uma zataiwa dan adam irin wanan kuli haka, Hamza ya rarafa daga,inda yake zaune zuwa gaban Umma cikin kuka yake cewa, Don Allah Umma da mama ku gafarce ni kuyi hakkuri ku yafe min laifin da nai maku Umma fushin ku a gareni zai iya janyo min fadawa acikin masifan da yafi wanan nan, Umma ta ce cikin kuka yanzu babana abinda kai muna a rayuwar ka ka kyauta ke nan kasayar da abincin mu da duk abinda ka malaka a gidan ka,sayar kabi mace macen ma kafira guzuma ba,sa,ar yin ka,ba, Mama ta cabe zancen da cewa Hamza mu bamu rike ka,da komai ba godiyan mu ga,Allah shine yakwato muna kai daga hannun wanan macuciyar matar kafira mai mugun aniya, Sam baka da laifi garemu tun da mun san cewa bayin kanka bane mun san ka mun san halinka Hamza don may zamu dora maka laifin dabakai kayi shi ba, Kowa gurin ya dauka da cewa wanan gaskiya gaskiya ne kika fada , Suka juya gurin Umma suna cewa boyar Allah don Allah dai kiyi hakkuri kiyafewa wanan yaron kamar yadda yar uwar ki tafadi , Umma ta,share hawaye tace nasan da haka bacin rai ne yai min yawa har na,fadi haka amma nayafe maka Hamza duk abinda kai mun, Sun kai wani lokaci a gurin sai dai duk abinda akeyi hamza hankalin shi ya gur8n yar matarshi don yaganta ko zai ji sanyi a ranshi, irin yadda yake son ganin ta a rayuwan shi, Bayan Anfito daga sallah isha,i aka taru a tsakar gidan mu Liman Baba Madu bakon da yazo da Hamza sai Baba Mudi makwabci su, Liman ya bude taro da,addu,a tare da karayiwa Allah godiya da,sauran mutanen da suka taimaka a kan wanan al,amari,, Yakara yi mai nasiha akan riko mai karfi ga ibada ta yadda zai tsamo kan shi daga fitinar zamani, Nan dai ya nuna mai matukar kuskuren shi dayayi wurin yin sakaci da,addu,oi, saboda neman kariya ga,hadduran zamani, Malam Liman yaci gaba da bayani cewa, yanzu bukatar da muke son ku dashi shine, Har nan da sati uku kada ku bari yayi arba da,wanan matar don kun san bazata barshi ba haka banza don dole ta canza sallon yaudaran ta, Don haka za mu roki Allah duk abinda tazo dashi ya koma mata zamu tafi dashi can guri na mu zauna har wa,adin da aka kidanya na,sati uku cur ya cika kinga alokacin duk wani hari da zata kawo mai, ba zai yi tasiri a kansa ba, Mama ta cabe zancen da cewa insha Allahu, zanyi kokarin ganin haka Anyi sallama da juna inda aka kai bakon masauki ya sauka sai tururuwa mutane keyi shigowa muna barka da arziki har cikin dare, Duk da musan cewa wasu don gulma ke kawo su a lokacin bawai don Allah sukeyi ba, A hankali, ya mike daga cikin taron ya nufi, hanyar shiga dakina , A,lokacin, ina zaune a kasa gefen kujeran dakina, saman salaya na na dan kifa kaina a saman kujera hannu na daya yana rike da tasbaha ina ja a hankali, Sam ban yi tsanmanin shigowan shi dakin ba a lokaci sai ganin shi nayi ya fada min bakin shi dauke da sallama,, A hankali na,dago kai na da dube shi saudaya sai kuma,na,sada kaina tare da amsa sallama shi, Ya samu guri ya zauna, saman kujerar danake zaune ta gefen, guda, Humaira ke ma kina fushi da nine kuma, kamar Umma, Nadan kada kaina a,hankali tare da cewa ,a,a ba hakana bane don dai na ganka da mutane, ne, Huci yayi mai fitar da iskan zafi daga bakin shi, tare da furzo iska yana furta Subbahanallah cikin wani yanayi, na bacin rai, Shiru dakin yayi ba mai magana daga cikin mu sai karan fankan sama dake tashi, Mikewa nayi tsab daga gurin da,nake zaune na dauko mai ruwa nazo gaban shi na durkusa na,aje mai plate din ruwan gaban shi ya,duka,ya,dauka naje na,dago sai muka,shaki, numfashin junan mu a lokaci guda Take, kowan mu ya shiga reacting, don shock din da mujaji a zukatan mu lokaci guda, Da sauri ya dago kai dai dai lokacin dani ma na dago nawa sai muka kara,arba,dashi nasada kaina kasa,a hankali tare da dan kokarin dagawa daga gurin da nake tsugun ne a gaban shi, Rugumoni yayi da hannayen shi bibiyu gaba daya zuwa jikin shi inda ya,dan mike don yaji dadi rugumoni da kayau, Noke kaina nayi ina kuka don wani irin bakin ciki da takaicin dake sukar ziciyana, Kamar mai rada naji muryan shi daidai kunnuwa na yana,magana cewa, Aisha kiyi hakkuri dani ba wai yin kaina,bane don da ban maki haka,ba arayuwan na, Wanan matar ta cuce ni Aisha ta,raunana min rayuwana,sosai a duniyan nan, Tabar min babban tabo wanda bacewar sa sai gyaran Allah, Hawayen, shi naji suna digo min a fuska na a hankali tare da jin yadda sautin kukan shi ke tashi yana kara sakani cikin tashin hankali mara misaltuwa, Nan mukai kukan mu mai isar mu ba wanda ke iya bawa wani hakkuri a cikin mi kowa da abinda ke ci mai ziciya a cikin mu, A hankali muka zauna daga bakin gadon inda yadan dago min haba na yana cewa Nasan duk abinda zan fadi ba zai yi tasiri a gunki ba dan zargi mai girma ya,shiga tsakanin mu dake a yanzu don haka, Dai ina mai kara baki hakuri akan kiyi hakuri ki yafe min don Allah akan yadda wanan matar ta yaudari rayuwana ta,cuta mim ta ida ban taba zato,, Muryan su Baba Liman ce ta,ratsa kunnuwar mu yana cewa,Hamza kazo mu tafi, kada wani ya,san zancen kum, Dole ba don ya so ba ya dan kura min idanuwan zuwa dan lokaci kadan ya mike yana mai sharan hawaye yabar dakin cikin sauri zuciyar shi tana mai tafasa, Ina kwance a kan gadona tun bayan fitan Hamza a,dakin wanda ya fita ya barni a cikin kunar rai, wanda bai missaltuwa, Ina kwance nai kuka nai tunane har baya kirguwa a lokacin, Ina gurin tun ina jin hayani har na daina jiyo motsi wanda hakan na nufin bakin sun fita harda Hamza a cikin su,, Kara lafewa nayi saman dan gadon katakona ina hadiyan rai don abubuwan da sukai min yawa a lokacin, Mama hafsi ce naji muryan ta a kaina tana cewa ki tashi ki kulle kofan ki Aisha don dare yayi sosai kowa zai shige, A zatona ta juya ta tafi ina mikewa don bin umurnin ta naji tana cewa kiyi hakkuri gaduk irin jarabawan da kika gani a rayuwan ki, komai mukkadari ne ga bawa, Inda anyi hakkuri sai a cinye jerabawan abin ya wuce don wanan yana daga cikin kaddarorin ku gaba daya, Adduan, mu yake mubukata don samun kubuta daga sherin shedan,, Kinyi kokari sosai sai dai ki kara don Allah da kikeyi a kansa ya sanar maki, Haka kuma jama,an dake gani Aisha kowa yasan kinyi hakkuri a kan wannan al,amarin, Don har yau baki nuna gazawan ki ba akan zancen, don haka ki kara dagewa,kin ji yar nan Allah ya,baki ikon cinye wanan jerabawan a hankali na amsa da,amin, ya Allah mama, Kullun kalaman su mamana, yana min yawo a zuciya ta tare da kara kwantar min da hankali, ****** ********** ****** Kwana biyu da,dawo wan shi gida, komai yadan fara lafawa don mutane sun dan lafa da shigowa ganin shi, saboda an fada masu cewa ya koma makaranta ko, Ina tsaye gurin igiyar shayin kayan mu ina kokarin shaya tufafina da na wanke naga mata kwatsan a tsakar gidan mu babu ko sallama har su uku, Har sun shigo daidai tsakiyan gida babu ko sallama balle muji shigowar su, Zarah wace tazo tun da safe yini tana tsaye daga kofa tana gyara shikafa a cikin dan wani faranti a a hannun ta, Ganin katan mata tsakar gida kamar kabila ashe su, don sauran biyun ma ba gyale a tare da su, ga,gashin doki sun aza a kan su,, Dayar ce ta dan daura dankawali ta yafa wani dan yalalon gyale iya kafadan ta kawai, Zarah tace a,a kuka wani dabia ne wanan shigowa gida babu sallama hakan nan, don ita a zaton ta masu zuwa ganin Hamza ne, O sorry bami yi maku sallama ba ko sai kowan mu ya kyale su, Nidai na sheda su don na san su saboda zuwanda suka taba yi har sau biyu, take nafara jifan su da abinda yazo min a rai, Addu,a nake daga cikin bakina ina fadar La,illah ha,ilallah mohammadan rasullillah,, Nazo gaban su na gilma ina dauke da bokitina na silver danake wanki a hannu na suna tsaye a tsakar gida cirko cirko, Ina mama suna, tambayan Zarah, wace take masu kallon mamaki, Sam ban kula su ba sai aikina nakeyi hankali a kwance, batare da na kula dasu ba, Sai dai a can kasan zuciyata kamar na sheka da gudu nake jin kaina, Jin suna neman Umma yasa su Asma,u da mama hafsi wace ke dayan dakin fitowa, waje da sauri don ganin ko su waye Sai muryan ta mukaji tana cewa tau munafuka may kuma ya kara kawo ku gidan mu, wani sabon sherin kikazo muna dashi ke nan, kuma, Tau ta,Allah ba taku ba don Allah yafiku yafi sherin ku muguwa muna fukai kawai, Look mama mu ba wanan ne ya kawo mu ba mun zone don naga mijina naga halin da yake ciki, ? Saboda munji labarin cewa angan shi Tashin hankali wai fadawa sarki gaiyya, don kalman mijina da ta ambata bani da nake matar shi ba har Umma da mama, da zarah da yan uwan ta dake gidan a lokacin hankalin kowa ya tashi don kalman ta zama wata mumunar kalla mai lahani a gare mu, baki dayan mu, Zarah ta nuna ta da yatsa tana cewa wallahi a,hir dinki da kiran dan uwana mijinki don Allah ya raba mu da hadawa da mace shu,uma irin ki a rayuwar mu, Ke ki iya bakin ki don ban da time din irin ku saboda ba gurin ki muka zo ba, Wanan zance shiya kara tunzura Umma wace dama take a kule da su, take cewa wallahi ahir dinku da zuria ta don ban haifi dana donku ba wai ku wasu irin mayun mata, ne haka wai da bakin nacin tsiya Murmushi sukayi a tare tare da wani yin har da idanuwan su sai ita Lima ce tace mama kiyi hakkuri son dan ki nakeyi tsakani da Allah Ke rufa muna baki kinji macuciya wazaki yaudara haka ake so ko bala,i inji mama hafsi, Umma tace, Yadda Allah ya kwato min dana,daga,sherin ki da makircinki Allah bai kara baki sa,a a kan sa,insha Allahu, Kiyi hakkuri mama ni mai son dankine ba,wai sheri ba, zakiji dadin zaman mu dashi nan gaba, Abinda su umma basu lura dashi ba shine cewa, Lima daga gurin da take tsaye tana wani saddabaru ne, Nice nafara hango yadda take saka hannu a hand bag take yarfa abu a tsakar gidan mu daidai saman hanya da,zai shiga da mutum gurin da dakunan mu, suke a jere, Ashe mama ta gani daga inda take tsaye zata kara na uku mama hafsi ta nuna ta da hannu tana fadin dakata hakana don idan kika kara wallahi sai kin gane kurenki a gidan nan, Tsintsiya da Parker na dauko batare da nai magana,ba baki ina karanta lai,la ha, illah anta subbahanika in,ni kuntu minal zalimin, Nafara tatara daidai gurin da ta yarfa ruwan magani a gaban mu nai hanyar toilet dashi, suna kallo na, Ibrahim suka,shigo shida abokan shi akai masu tas don kiris ya rage a bugesu a gidan, Sai cewa suke wallahi tunda mijinta ne dole a bari su gan shi saboda itama ai tana da hakki a kan sa, Fitina yai fita ancika sunga rashin mutunci a filin Allah haka ya,saka su barin gidan takalmi a hannu don sunga ruwan bala,i saboda matasan shiya sunce sai sun kashe su sai dai su ma a kashe su tunda sun zo har cikin gida yiwa mutane rainin wayyo, Rikici yafi wani rikicin cikin tashin hankali suka bar uguwan don ganin dandazon jama,a yadda suke karuwa a kan su, Suna barin uguwar Bicky tace wayyo Allah na yau mun ketare rijiya ta baya aida mun fada a jikin mu,, Don wallahi wa yan nan katai indan sun dake mu sun daki banza wallahi, Dayar Mary tace nikan ba zan sake zuwa irin wanan risky din life dina ba,saboda wanan village people, sun fimu hauka, Ke da kikaga kina iyawa zaki iya zuwa for your own, risk ba dai dani ba again, gaskiya,, Sai lokacin Lima tace, hmmm ni duk ba wanan ba wai kun kula da yadda wanan yar ficikan yariyar tawani canza gaba daya kamar bata a cikin wani case haka,, Kina nufin matar Hamza din tace eh ita mana Mary tace wace daga ciki ? Wanan da tazo ta kwashi abu a gaban mu da Parker mana abinda na zuba ne fa wai wanan yarinyar tagani take kwashewa a gabana, Ki duba irin kudin dana kashe kafin na,samu a hada min wanan magani amma duk da haka nasan cewa, dole za,a samu wani da zaiyi amfani a gurin, Muddin Hamza ya bi gurin dole maganin nan yayi aiki a kan shi, Kawai ni bukatana shine yabi gurin kawai koda sau daya ne, Amma ashe matar yarinyace haka karama gata kuma tana da kyau wallahi sosai, Duk lokacin da naga wanan yarinyar nakan ji matukar bala,in kishin ta ya kama min zuciyana sosai, Duk yadda zan raba shi da wanan yarinyar zanyi na shiga tsakanin su muje zuwa suna wasa dani wallahi,, Shiru sauran sukayi don su abin yafara basu haushi sosai don dai sun san suna samun biyan bukatan su ga,alhazawa masu kudi balle wanan yaro karami Da baida ko sisi inba jikin shi da take moraba basuga abinda take mora a gare shi ba, Suna fita mama Hafsi tace a zuba fitsari da ruwan tsami yadda asiri zai kare, a duk gurin da,suka bi suka zuba maganin,, Ina tsaye imani da tsoron duniya duk ya kamani yau naga mai abu ja mara abu ja a filin Allah yadda mace tazo ba kunya tana duban idon mutane tana cewa wanda ba,a,san yadda suka daura aure ba wai mijin ta mijin auren ta, To ni ma,wai yanzu a wani matsayi nake da auren shi da ke a kaina, ne don banga alamar wanan matar zata bar min mijina ba don babu kunya babu tsoron Allah a tare da ita, ko kadan, Ina gurin banyi aune ba sai ji nayi kamar numfashina zai tsaya min don irin bacin ran da nake ji, atare dani, Da kyat na,samu na nemo natsuwana ina fadin innalillahi, wa,inna alaihim rajji,un, Sannan na dan samu natsuwa a tare dani, duk kace nacen da mutane keyi ban iya cewa uffan ba don mamaki, Gaba daya ji na nake kamar ta kwace min miji ko, don may zan gane wa mutumin da ke mu,amula da mace irin wanan matar, Mace ga jiki ga haske ga sutura na alfarma, ga kayan karau ko yaushe da take dazawa,a jikin ta, Nasan kowaye hamza gwarzon namiji a cikin mazaje yabiyo tarihin mai sunan gurin karfi da hazakan nema, Nasan bako wace mace ce zata mallakeshi ta bari ya shige mata kai tsaye ba, batare, da wani jayyaya ba,, Haka naja kafana da kyat zuwa dakina inda na,fada saman gadona na fara wani sabon kukan gwanin ban tausayi dani, Ganin ba sarki sai Allah ni daya a cikin daki sai na,fara jero tasbihi inayi tare da neman sauki a gurin Allah ubangiji subbahanahu wata Allah,, Don wanan masifa yai muni saboda yadda suka shigo muna a cikin fitsara babu burbushin kunya a idanuwan su ko kadan, Wai mijina take kira mijinta a gaban bainan jama,a ina ji ina gani don rainin wayyon da take min, ta daukeni ni da banza duk daya, Haka nake kwance ni kaidai a daki sai juyi danake a saman gado ga tunanen kala, kala da ya addabi zuciya ta, Don sai nake kiyasta irin rayuwan sha, shanci da tambadewan da su kayi tare dashi a idanuwana, Na kara rintse idanuwana raina yana ci gaba da baci don zafin kishin da nake ji ban taba sanin cewa na iya kishi ba sai a wanan ranan da naiwa Lima kallon tsab, Take idanuwana suka kade sukai jawur dasu tankar anyi min duka nake jin yanayin jikina a lokaci guda, Sai ji nake rayuwan gaba daya baida dadi kwata kwata ya fita raina kamar babu wani sauran dadin da ya rage min a duniyar nan kuma, Allah mai rahama maijin kan bayinsa nan cikin wanan halin barci mai nauyi ya,daukeni duk da mafarkine barkatai marasa dadi nake amma na jima ina wanan barcin, Ban farkaba sai gab da la,asar na samu tashi jikina kamar anmin duka, Tabbas naji dadin wanan barcin don dana farka duk wani kunci da nakeji yafita min a raina, Nafito na debi ruwa na watsa don na kara jin dadin jikin nawa, Na samu zarah tai girki don ganin ban cikin dadin rai a ranan, Haka na tutura abinci ba wai don jin cin sa ba ban ci wani mai yawa ba na barshi , ****** ********* ****** Da dare ana zaune bayan duk liman yaji bayanin da su Umma suke mai ya kada kai tare da nisawa Yace lalai wanan matar takai fitsarara don rashin mutunci zata shigo har cikin gidan nan tanawa mutane wanan irin fitsara haka, Dayan mutumin yace ku barmu da ita kwata kwata zata ji ko zancen shi bata kaunan ta ji a,rayuwan ta, Indan ita tsafine nata mu muna karya tsafine da ayar Allah maigirma, a lokaci guda, Mutumin ne yace ni yanzu shawaran da zan bayar shine a yi kokari a auna shi don tabbatar da lafiyan jikin shi, saboda gudun jefa matar shi a cikin halaka ita ma, Umma hankalin ta yai matukar tashi don jin abinda ake zargin hamza dan ta dashi, Sai kawai ta fasa kuka tana cewa Allah ya isar mata ga wanan bakar mace mai muguwar hali da ta jefa mata da a cikin bala,i, Gaskiya idan haka ya kasance sai dai su zauna kotu da Lima don bazata yarda ba ta kashe mata da haka kawai, Hakalin Umma da yai balain tashi tunda safe washe gari sai gata a gidan liman ita da mama, Bayan sun gaisa da mutanen gidan ne sukaiwa malam bayanin suna son ganawa da Hamza din, Malam ya nuna masu masaukin inda Hamza yake zaune,, Sunsamay shi zaune yana karatun kur,ani inda ya yakai aya ya tsaya su gaisa da su, Umma kan tana ganin yadda danta ya koma alokaci guda kamar ba hamzan ta ba, Sai duk ta rude ta,shiga damuwa da kyat mama ta,samu ta,shiga natsuwa, Magana suke dashi kamar baison yin maganan don da kyat yaje bude baki ya basu amsa, Don shi kadai yasan irin halin da yake jin kansa aciki Yajuya inda mama take yana tambayan ta lafiyan matar shi Aisha da sauran yan uwan shi, Umma tace mai kaji zancen gwajin da ake son ai makako don gudun jefa ita Aisha acikin wani hali, Wani irin ba dadi yaji a ranshi take ranshi tmya baci yanajin kowa na mashi kallon mazinaci ke nan a rayuwa, Cikin dakiya yake, cewa indon wanan ne ba matsala Umma Allah zaikare ni daga duk wani sherin wanan matan, Sai dai sun boye mai zancen zuwan su Lima din don kada hankalin shi ya kara tashi, Yai shiru yana jinjina maganan a ranshi wai yau shine za,ai wa gwajin HIV don zargin zina , Ganin ya shiga damuwa ne yasa mama cewa kada kasa damuwa zamu taya ka,rokon Allah insha Allahu hakan bazai faru da kai, ba,,, Sun dan dauki lokaci a tare da su suna dan hira sake wanan kama wancan har sai da suka ga hankalin shi yadan kwanta, Sukai mai sallama tare da mashi alkawari kara,dawowa su ziyarce shi don suga lafiyan shi, zakuma,suci gaba,da taya shi addua insha Allahu, Bayan tafiyan su saiya koma wani iri damuwa da shakku suka saka shi a gaba suna addaban shi, Damuwar shi shine yadda mutane zasu fahince shi a,zarge shi akan abinda bai taba tunanen aikata su ba a rayuwan shi, Tausayin Aisha Humairan shi ce ya kama shi don a gaskiya idan har yakamu da,wani mugun ciwo bazai iya yafe wa kan shi ba don yasan da ya cuta wa wanan yarinyar, mai, Mutunci karamci kamala sanin ya kamata,da,sauran su uwa uba ga hakkuri, Bai san lokacin da hawaye ya fara digo mashi daga idanuwan shi, Yana kokarin sharewa ne sai ga bakon nan da yazo dashi ya shigo dakin idanuwan shi akan Hamza yake tambayan shi ko may yafaru yaga yana kuka, Guri ya,samu ya zauna yana daga gefe shi yana fuskantan Hamza bai boye mai komai ba akan irin zanman da mukeyi tsakanin mu yai ma banin komai, Malam.ya ke cewa sai ka mayar da hankali sosai ga ibadan ka ka kuma daina kwanciya da najasa a jikin ka, Ka dinga addua kafin kafita gida ko ka kwanta, da gurin cin abinci komai kankantan shi ka karata bissimillah kafin ka,saka a bakin ka, Hamza yana saurare inda yasan cewa duk wanan abubuwan yana da matukar sakaci a kan su Amma yanzu insha Allahu zai yi kokari ya gyara wannan kurakuren da ya tafka a baya inda a nan ne shedan da shedanu suke samun shiga jikin bawa da sauri Don Allah kuyi hakkuri da,rashin jina kwana biyu da bakuyi ba, nagode, ZAINAB IDRIS MAKAWA, SEENABU IDAN BAKI BIYA,BA KADA KI KARANTA HAKKIN WANI PLEASE,,,, Kiran sallah da ake a ko ina cikin uguwa ne ya tayar dashi sallah kamar yadda ya saba,a baya kiran farko zai farka ya fara, alwala da nafiloli, Zubur ya mike zaune yana wa kansa tambayoyin yadda akayi ya gan shi a nan haka ya waiga da kyau Lima tana kwace shirif da ita kusan duk rabin jikin ta yana waje, Tambayoyi ya fara jerowa kan shi kafin kiran sallah ya kara tunatar dashi, Zubur ya mike daga kan gadon da sauri sai yake jin shi daga shi sai boxer a jikin shi, Duban ya ayin shi yayi sai yaji wani irin kunya da nauyi sun gama shi, Ji yake tankar duk duniya suna kallin abinda ya aikata, a lokacin, Ruwan da ke a gidan sai yake jin kyamar amfani dasu gurin tsabtace jikin shi, Ruwan ledan pure water da su ke a jingine da yawa gefe daya su ya diba yashiga bayi da su, Wanka yake amma ziciyar shi fam da tunane kala kala a cikin ta, Yafito inda yaga yar bag din shi ya nufa ya dauki wasu kaya nashi daya gani a goge, ya dauko ya,saka ajikin shi don su yake gani suna da tsarki, Har ya bude gida ya fita zuwa inda yake jin ana kiran sallah bata farka ba sai nasari take kwa kwa kwa, duk ta ruda guri da,sautin nasarin, Daga masallaci ya dade zaune yana azzakar har rana ya hudo sosai, ya mike duk zuciyar shi har lokacin a cakushe yake fam, Direct inda zai samu Nape da zata sada shi da inda su Mansur yake ya,shiga watau hostel din su ke nan da suke zama a ciki ko ince inda mansur ne ya kama gurin gida ne babba sai suka dan hada kudi suka biya sai dai share din mansur din yafi yawa a ciki,gidan, ****** ********** ****** Cikin barci taje ta dan rungumo shi amma,sai taji kamar wayau, takara labawa tare da wani mika sai taga baya sama gadon, Bude idanuwan ta tayi cikin sauri sai yaum ta gani a gurin baya kwance a kusa da ita, A zaton ta yana cikin bathroom, don haka takara lumshe idanuwan ta, don a zaton ta yana acikin bayi, Shiru ba shi har takai ga fara, kiran sunan shi tana cewa my my har yanzu kana ciki ne , Jin shiru yasa ta saurin mikewa zaune tayi ta bi dakin da idanuwan ta a hankali sai ta hango wandon boxes din shi daya cire yashe daga kofan fita, bayi, Da sauri ta kai tsaye tana cewa ina kuma ka,shigane wai haka, Bayi ta leka duk da gurin da yai wankan ya,sha iska amma alaman ya nuna yai wanka, Da sauri ta leka falon su baya ciki nan ma kofa a,bude yake ya dai dan saya mata shi, Har wajen gidan ta leka bai gurin sai mutanen shiya dake zirga zirga jefi jefi, a layin, Ta juya zuwa, cikin again nan ta lura cewa, ya yamotse jakar kayan shi dake dakin a jiye, Juses, tace da karfi tare da cewa yau na,shiga uku ina guy din nan ya shiga haka tun da safen nan, Mutumin da bamu tashi barci sai after nine muke tashi amma yau gashi ya tashi as early as possible haka, nan, Takai zaune a saman gado tana dan tunane a hankali can kamar wace a ka tsikara ta mike tsaye da sauri ta nufi wardrobe din ta, Cikin sauri take daga kayan dake a ciki tana binciken wani abu sai dai da gani wani abune mai muhin manci take ne ma acikin wardrobe din nata, Wani leda ta jawo mai kauri baki tana kokarin sance ledan a cikin rawan jiki, Wani kashine, lailaiye da jan kyalle acikin ledan an nade shi kamar gawa,, Tana duban kamshi hankalin ta yai matukar tashi don tasan ba haka ta barshi ba,saboda duk maskin da ke a jikin kamshi wanda har ya fita daga jikin kyalen, Da sauri ta mayar da kashin cikin ledan da ta boye shi sai faduwa gaban ta ke matukar yi, Hankalin ta idan yai dubu ya tashi a lokacin don sam bata taba tsan manin irin haka ba ma da,sauri a rayuwan ta, Kwatakwatama bata taba zaton wanan kashin zai iya bushewa ba irin haka da sauri,, ****** ********* ****** Shirin shiga school yakeyi don suna da test gobe don haka yake son shiga da wuri yadan taba karatu, Jin ana nocking din kofan falon shi a lokacin yasa shi dakatar da abinda yakeyi ya nufi kofan don ya bude Abin mamaki don Hamza ne ya gani a tsaye daga kofan cikin dan yanayin damuwa tare da shi, Hamza ya ambata da karfi a cikin mamaki sai Hamza din ya amsa a cikin wani yanayi na ban tsoro, Ya dan jaye mai ya fada dakin inda ya samu kujeran three seater ya zauna tare da dafe kan shi wanda tun asuba yake mai wani irin ciwo, Fita Mansur yayi zuwa dayan dakunan da yan uwan su suke a ciki suna barci ya kira su yake sheda masu suzo Hamza ne yazo acikin wani irin jalin rayuwa,da ya tayar mai da hankalin sa, Wasu suka ce bazasu zo ba amma sai wasu suka biyo bayan shi mansur din cikin tashin hankali, Sun samu Hamza dafe da kan shi sai wasu hawaye yake fitarwa kamar fanfo, Man may ke faruwa ne haka wai da,safen nan duk ka wani zo ka tayarwa mutane da hankali irin haka,? Maimakon Hamza yayi magana sai kara dafe goshin shi da yakeyi tare da murdewa guri daya tankar zai mutu, Daya daga cikin su dake tsaye daga kofa ya ce kai mu kaishi asibiti fa kada, yazo ya mutu muna a gida haka, Mansur dake duke gap dashi ya dago kai yana sauke numfashi yake cewa, wanan ba zancen zuwa asibiti bane Yusuf akawai wani bakon al,amari da yazo wa guy din nan don haka muyi kokari muga cewa mun taimaka mai kowa ya karato mai abinda ya sauwaka daga cikin alkurani maigirma don ya ida samun sa,id, Sihiri ne da alamar yake fita daga jikin shi a cikin wahala hakan nan, Don rayuwa na ya bani cewa, zuwan da brother din shi yayi ya koma something serious zai faru a kan shi, Nan suka taru kowa da irin ayar da yake ja a bakin shi suna tofawa, cikin tashin hankali suke gaba dayan su don ganin irin yadda yake wahala a lokacin, Cikin ikon Allah bowayi gagara musalin sai suka ga ya fara barci a hankali barci ya soma daukan shi yana rufe idanuwan shi da sukai mai ja jajir kamar garwashin wuta, Gaba dayan su suka fita daga dakin zuwa waje, shawara sukeyi don sun san cewa Allah ne ya kubutar da Hamza daga kaidin shu,uma Lima, Sun yake shawaran daukan shi zuwa wani gida gidan wani dan uwan yusuf malami su gani hakan sukayi suka dauke shi daga gidan zzuwa wani gida na daban inda maigidan yai masu alkawar8n taimakawa Hamza din, Suka dawo gida kowa ya kama shirin shi zakace wani abu bai faru ba da su,, ****** ********** ****** Gap da Mansur zai fita saboda yayi late sai ga,su lima ita da Bicky sun zo rai a bace masu, ko gaisuwa babu suka shigo gidan , Mansur wanda ke waje yana kokarin bude motar shi zai shiga ya,watsa masu harara cikin kawar da kai, Lima ce tace mai cikin dakatar da kai, malam ina mijina yake, Wani kallon banza Mansur ya,watsa mata yace mijin ki ko farkan ki ? Naji koma may yake ina yake don nasan babu inda zai tafi dai nan gurin ka , Dayake nine Uban shi ko uwar shi ba zaki ce baida gurin zuwa, Yadda Mansur yake masu magana cikin tsauri yasa duk wani shirin iskancin da suka zo suyi mai yai sanyi sosai, Gaskiya tunda safe nake neman shi ban san ina ne ya shiga ba ta fada in a angry voice, Bayan kin raba shi da mu kina tsan manin cewa zai shigo wajen mune again, Suka juya cikin sanyi jiki ba wani kwarin gwiwa tare da su, Har sukai kofa zasu fice daga compound din gidan sai taji muryan Mansur din yana cewa, Ke Mansur din ya nuna ta da key din motar dake hannun shi yana cewa, Indan ma har kin san cewa kin mai wani abune kike wani boyewa mutane, To zaki kuka da kan ki wallahi, Wani kallon ta watso mai ita ma cikin kai a suwa kuma tare da jan tsaki tasa kai tafice, Bayan ta tayar da motar ta take cewa, Bicky wallahi iam scared kada fa ace wanan guy din ya salwanta , Dana shiga uku a garin nan da yaya zanyi ga wanan dan rainin wayon har ya fara zargina cewa wai nice nai mai wani abu, Bicky dake zaune daga gefe tace so annoyed dama duk irin abubuwa nan ina maka gudun su Helina, Yanzu gashi wani masifa yana so ya kuno kai sabuwa, Ajiyan zuciya ta sauke a cikin firrigita, take cewa na shiga damuwa sosai Bicky,, Ban tsan mani cewa My zai iya min wanan abin ba haka irin yadda na daure shi sosai Kin manta cewa yana da parents yana kuma da mata a gida ga kuma abokan arziki iri shi wanan guy din, Helina, ban san abinda ya rude ki ba haka da yawa kike ta cewa wai ke sai kinyi zaman aure da guy din na , Bayan kin san cewa ba age mate dinki bane kuma kuma wai wani mai hali bane balle a ce don kudin shi kike son shi, Shiru tayi tana ci gaba da driving idanuwan ta na a gefen titi tana kallo ko zata hango Hamza din, Can tace Bicky bazaki gane ba ke ina fada maki ni na,san dalilin da yasa na ke son guy din nan, Yanzu ma nafara son shi a rayuwa na,saboda ban taba haduwa da namijin dake da skills irin na,wanan guy din ba yana satisfy dina yadda nake so , Baki Bicky ta tabe tace nasgi dai kike ji shiyasa kika ce haka amma ai akwai maza masu abubuwa da dama da zaki bukata, Har cikin school suke suna tambayan ko akwai wanda yaga masu Hamza amma shiru, Sai sun wuce mutane suce killa ya gudu ne ya gaji da,wahala ko wani abu, dai maka mancin hakan, Har yamma ba Hamza ba labarinsa hankalin Lima yai matukar tashi dole aka bata shawara a kan ta fara dubawa a garin su ko ya tafi can ne, Wani iri taji idan ta tafi may zatace wa iyayyen shi bayan sun san cewa ta raba su dashi na tsawon lokaci sai yanzu zata fara cigiyar shi, Gashi saboda kishi ta hana shi amfani da waya, wai don kada ya dinga kiran matar shi dashi, Ga Mansur sun fara mata barazanan zasu karanta sai ta fito masu da dan uwan su don kowa yasan a gurin ta yake, zaune, Wasa wasa sai ga case har a police station an aje cewa za,a tafi gidan su Hamza din a gani ko yana can gida, ****** ********** ****** Barci nake sai dai ba mai dadi ba duk da ban wani nisa da yin barcin nawa ba, amma kuma mafarki yazo min a,wahala lokacin, Sai juye juye nake a fili ashe har da,sambatu nake wanda daga inda Mama Hafsi take zaune tana nafila tajiyo ihu na,. Hamza ne na gani wani naman daji mai mumunar suffa yana na binshi da gudu sai faman gudu yake, dabban tana bin sa baki a bude kamar zata cafke, shi, Saura kiris ya rage ya dabban ta cafke shi ya tuma ya haye wani tsauni da wata mace ke tsaye a kai wanan matar ba kowa bace ashe mama Hafsi ce ta rogumo shi suka gudu, tumar da yayi na,saura kiris dabban ta cafke shi yasani Ihu wanda har na baiyanar a fili su mama sukaji ina cewa Innallilahi da karfi Hamza,,,, Da sauri suka fito daga dakunan su ina kwace a kasa girin dana idar da sallah barci ya kwashe ni naji muryan mama da Umma suna cewa AIsha, Aisha, Aisha da karfi suke kiran sunan nawa abinda yasani farkawa duk nayi zufa ga hawaye yana fita daga idanuwa na, Da sauri na bude kofa na nufi bayan mama hafsi din na boye sai kuma kukan da na,saka a cikin kwanciyan hankali don tunawa da nayi da mafarkin nawa, Sai kuka nake suma hankali a tashe suke tambayana, Nan nake fada masu irin abinda na gani a mafarki abinda yasa Umma ta suri buta zuwa bandaki ke nan, Tsoro ya kama su mama sai nanata kalman innallilahi suke yi, a cikin tashin hankali,. Umma tana fitowa ta jawo kujera takai zaune saboda kafafuwan ta basu daukan ta tana cewa Hafsi akwai matsala ke nan maigirma, Mama Hafsi tace akwai shi mana yaya Allah dai ya kyauta ya kwato muna wanan yaro aduk inda yake, Amma insha Allahu da safe zan koma gurin liman don na fada mai wanan mafarki, Yanzu ke Aisha taso mu shiga daga dakin ki na taya ki kwana da safe sai mu san abinyi, Tare da mama hafsi muka kwana a,ranan tana ta kwantar min da hankali, Har akai kiran sallah farko inda muka,futo muka kara yin alwala da gabatarda nafilfilu,, Ita ma Umma a ranan cikin tashin hankali ta kwana tare da yaranta a daki don sai kiyasta wani irin halin rayuwa dan nata yake a ciki, Nan dai muka karya a tsatsaye ba wai don rai yana so ba, Fitan mama hausi a dakina ya bani damar samun lokaci nai kuka yadda raina ke so, Ban san cewa mama ta tafi gurin mama Rahana ba sai ga ni su mukayi atare sun zo nan suka taru a kaina har Umma suna min nasiha ,, Barcin da ban samu ba da dare bashin shi yake a kaina, shine ya sace ni a bayan mamana nake kwance saman tabarma, Sallama matan da,suka shigo ya,sa su mama mayar da hankalinsu a garesu, Cikin tuna inda suka san su sai mama hafsi ce bayan sun zauna take cewa yau kuma kin biyo mu har gida ne bayan sace hankalin dan mu da kikayi yabar mu har abada, Sai wani nuna,sarakuta sukeyi kan su mama da umma, Murmushi Bicky tayi tana cewa haba mama bashi ya kawo mu ba, Mu alheri ne ya kawo mu gare ku don yanzu mu da ku mun zama daya ko, Zuwa mu kayi mu gaida ku mukuma, ji idan har Hamze ya samu shigowa don muyi zai shigo kafin mu zo, Tau bai shigo ba mama hafsi ta basu amsa a cikin gatse, shiru sukayi suna kallon junan su wanda alamar, ke nuna shock a fuskan su, Gurin yadan yi tsit sai mama ce tace amma boyar Allah kiji tsoron Allah don baki da tsoron Allah shine zaki raba yaro da u Iyayen shi har na tsawon wani lokaci yanzu don baki da kunya zaki shigo muna kice wai kinzo kina zaton ya iso, Mama ki fahince mu mufa bamu son rashin mutunci daku don dan ku amma don may zaki fara gaya muna zance haka, Nan bakaken maganganu ya fara tashi a tsakani su da mama, abinda ya farka dani daga barci ke nan, Sai ganin su nayi suna mikewa zasu tafi cikin wasu dogayen riguna irin ta yan gayu ga manya duwawunan su sun fito daga cikin rigar, Cak ta tsaya tana mai kura min idanuwan ta, duk zancen da Bicky ke yi da mama ita bata samu bakin magana ba sai kafe ni da idanuwan ta da tayi, A take nace mata La,illaha illa anta subbahanaka inni,kuntu minal zalimin, Wallahu galibun Ala,amrihi, Sai naga ta,wani kawar da kai tana cewa mama kuyi hakkuri abin ba haka yake ba zamu tafi sai mun kara shigowa, Waye mamaki sai dai idan ke ce mamata ai don ni kin haifeni ma, Mama hafsi taba ta amsa da hakan tare da tafa hannayen ta tai masu yas suka fita jiki ba kwari don rayukan su a cakushe yake lokacin, You see, what you course for us matan kauye suna zuba muna magana akan jarabar ki, Bicky take fadawa Lima din haja wace sai a lokacin ta sauke ajiyan zuciya tana cewa, Kin faye shirmay Bicky mai zaki tsayawa fada a wayannan yan kauyen dan sune dai na kwace sai dai su haifi wani kuma amma ba Hamze ba, Helin yanzu ke baki hango tarin fitina a idanuwan wanan matar ba ne wai sai fa kin san yarda zakiyi da ita don kin manta ki hada da ita a dafa maki ita, Bicky forget about her, ni ba wanan ba wanan yarinyar nake matukar bakin ciki a rayuwana wallahi dana sani kawai a batar min da ita kwata kwata a,rayuwan mu, Amma bar su kawai zan san yadda zan yi dasu gaba dayan su, Sai ta ce for god sake where this guy hide, Bicky abin ya fara bani tsoro fa wallahi kin ga bai zo gida ba ke nan, Tau shi kuma ina ne ya shige wai haka abu wasa wasa tun jiya,,,, ****** ********** ****** A hankali daga inda yake kwance ya bude idanuwan shi da sukai mashi nauyi, Dakin daya ke kwance a ciki yake bi da kallo sannu a hakali sam bai iya tuna ko ina ne wanan gurin haka, Shigowan mai gidan dauke da wani kwarya dauke a hannun shi sabo ya sashi dan kokarin mikewa zaune, Mutumin yace a bawan Allah ka farka ashe da kai Hamza ya bashi amsa sai ya samu guri daga gurin kafafuwan Hamza din ya zauna a hankali, Kwarya ya mika mai yana cewa karbi wanan ka shaye duk kaji, kayi bissimillah, Ba mussu Hamza din ya mike zaune ya karba inda ya kwan kwade gaba daya ruwan rubutun sai mutumin ke ce mashi karage kadan kashafa a fuskan ka da kafan ka, Yadda aka umurce shi haka din yayi ya shanye ya shafa saura a fuskan shi da kafa, Haka suke ta mashi har hankalin shi ya dawo daidai ya fara tuna wasu abubuwan da zai iya tunawa a baya, Umman shi da matar shi Aisha yake matukar son gani a rayuwan shi tare da yan uwan shi da mama hafsi, Kewan gida yake sosai a ranshi har abin ya fara damuwar shi, Gashi duk wa yan nsn mutanen bai san su ba,sai yusuf ne dakan zo jefi jefi ziyaran shi a kauyen, Nan Yusuf ya ke kwantar mashi da hankali akan ya kara hakkuri har komai ya koma dai, Don an balain saka masu ido ga duk wani movement din su , Yayin da su ma a nasu bangaren su hasawa Lima wutan cewa sai ta fito masu da dan uwan su, Tun Lima na daukan abinda wasa har gashi yau sati daya cif da batan Hamza a gurin ta, Har can garin su ta saka in secret a duba mata ko yana garin amma ba labari, Ranan da Ibrahim yazo muna da labarin batan Hamza da wani abokin karatun su ya fada mashi anga tashin hankali a gidan mu, Tsaye nake ban san lokacin dana fadi ba kasa sai dai bude idanuwana nayi naga matan gidan mu tsaye a kaina, har da Ummina sai mama saude da mama Rahana da suke min hitara, Ranan ne mutune gari suka san irin halin rayuwan da muke ciki wata takwas ke nan rabon Hanza da gida muna ta hadiyan bakin ciki a ran mu, Sosai aka tausaya muna munga yan uwa da abokan arziki masu zuwa muna jaje da Allah ya kawo shi ya baiyanar dashi lafiya, Anty Hindatu tazo da cikin ta wanda ya fito sosai alokacin muna dakina zaune tare da ita mama da Ummi duk muna ciki zaune, Bayan mun gaisa sun gaisa da su Ummi take muna jaje sai ta ke kara bamu labari yadda batan yazo yadda sukaji labari, Wayan ta touching ta ciro daga jakarta takira mijinta mansur take fada mashi cewa, gata a guri na yace ta bani waya, Nakarba da kyat jiki babu kwari, nace cikin muryana da yai sanyi nake cewa,, Hello, yaya ina wuni ya amsa a bangaren shi da lafiyan Aisha sannu ya hakkuri idanuwa na suka kawo hawaye na amsa a muryan kuka da Alhamdullahi, Yace kuna da yawa a gurin ne ina son magana da ke ne nace, ni da mamana ne sai anty yace, good, Kina ji Aisha banson kitayar da hankalinki ki ji ki kwatar da hankalinki lafiya Hamza yake bana,son ko da wasa ki fadawa wani zancen don haka ki kwantar da hankalinki kinji ,, Nace tau yaya na gode hakan kawai daya fadi naji sanyi a raina, tare da tunane barkatai na akwai wani abu a boye ke nan killa, Don haka sai nayi kamar yadda yace din ina daga kai muka hada ido da Anty Hindatu sai ta daga min kai alamar be strong nace mata tau a hankali, Ayarin wasu mata da suka shigo ba wanda yasan su sun dai shigo ne da sunan yi muna jaje, Daya daga cikin su ce ke cewa ina matar tashi aka nuna masu dakina suka shigo muka gaisa dasu sai daya daga cikin su take cewa, Wai yakamata nai shirin takaba kada na zauna ba mayafi a kaina, don killa baida rayuwa gani ban shirya ba, Anty Hindatu tace haba boyar Allah wanan wani irin fatane haka, Daga bayan su suka ji mama na cewa aniya makomiya, bamu cikin takaba yanzu a gidan nan insha Allahu Allah baki hakkuri ni dama naga kamar ya dace tayi hakane, Suka mike suka tafi mamatana masu bakar magana, Nan suka tafi sukka barmu a cikin bacin rai kowa da abinda ke yawo azuciyar shi, Hankalina ya daga da zancen matan nan don sai ina gani zancen su gaskiya ne, Anty hindatu ce ta dan zungure ni da kafa abinda yasani saurin dawowa daga nisan tunanen da na,shiga ke nan, Tace cikin harshen turanci nadaina takurawa kaina dayawa haka nabarwa Allah komai, Nace a hankali da tau Anty insha Allahu zan bari da yardan Allah, Mun kai wani lokaci tare da ita taimuna sai anjima ta tafi taba ni alheri mai yawa wai na sai Omo da sabulu, Bayan fitan ta ta ba su Umma tai masu fatan alheri zan rakasu tace na zauna kawai ta hutar dani, Haka mukai ta zama sai magan ganu muke ji suna zaga gari iri iri wanda ba dadin saurare, Ga abinci yai muna tsaye a gidan wani bi daga gidan mu ake taimaka min da dan abinda zanci a bakina, Wanan maganan yaso ya dan taba karatuna amma da taimakon Mansur na,samu aka gyara komai ya koma normal,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE CIN AMANA NE KARANTAWA BA BIYA PLEASE,,,, Akwana a tashi ba,wuya a wurin Allah don gashi yau har sati ukun da,su baba liman suka kindanya ya cika, Don haka duk wani abinda suka shata cewa ya dace suyi don neman ma Hamza tsari gurin Allah daga sheri shu,um Lima sun yi shi, Nikan ina ganin mutanen gida suna zuwa a,sace gaida Hamza amma,ba wanda ya taba taya min hakan, Ina zaune yau a saman kujera yar tsugunno a tsakar gida, Ina tunane ace mace da mijin ta amma a hanata ganin shi sai dai taga mutane su na zuwa gun shi ita ba,a damu da nata damuwan ba, balle a taya mata zuwa duban shi, Tau sanyin kaina,ne ya kamani don dai zan iya cewa ni dai arayuwa na godewa Allah zance, Wani irin zazzabi naji ya na batun rufe ni saboda bayanin da naji Ibrahim yanawa su Umma din, Wai ni Aisha da mijina amma ace bazan gan shi ba sai lokacin da aka ga daman bari nagan shi ko ya ganni, Na nisa ina fadin Allah na godema kai kadai kasan dalilin jefa rayuwan mu a cikin wanan halin, Ina zaune gurin nai zurfi ga tunanen da nakeyi mama tafito daga dakin don ta karasa aikin da takeyi sai gani na tayi a cikin wani yanayi, Taja tai turus tana kallona a cikin mamaki da tausayawa ta karaso gare,ni tana ,duk ban farga ba sai ji nayi tace, Aisha may kuma kike tunane haka kikayi zurfi a acikin tunane, Jin ta,a kaina batare da na,sani ba yadan sani kaduwa da,dan firgice , Na dago idanuwana cike da firgici mai nuna razana na kalle ta, tana cewa may kike tunane ne haka har baki jin magana, Nace cikin sanyin murya mama babu komai ina,dai zaune ne, kawai, Tace to ki daina ir8n wanan dogon tunanen kada ki jefa kan ki a fitina bayan komai ya kusa kai karshe, Takara matsowa gare ni tare da,dan dafa kafada na tana cewa Aisha kin yi kokari fiye da tsan mani don da watace cewa zatayi fita zatayi bazata daure da,wanan fititinun haka ba, Umma daje fitowa ashe taji mu take cewa wanan ai hakkuri ya zama dole ne don ko an tafi ina,gurin zuwa, Haba mama bata da gurin zuwa kamar wace bata da gida adaji aka tsinto ta, inji Ibrahim wanda ke daga bayan ta, Gaskiya Umma Aisha ta wuce haka garemu don tai muna halarci wanda ba ko wace yarinya mai karamin shekaru irin nata zata iya muna shi ba, Har yau ba mai cewa ga abinda yarinyar ga tace a garin nan tana gida tana kokarin ta duk abinda ta,sabayi da yake nan bata daina ba, don bayanan gashi yadawo acikin wani hali amma duk da haka bata kyamace shi ba , Haba dai Umma wanan abin fa yai ishe mu isharan rayuwa, Jikin Umma yai sanyi ga maganan dan ta don haka,ta juya ta,shige zuciyan ta ba dadi don a gaskiya itama tasan cewa inba Aisha bace da yanzu an kai ruwa rana ga tonon asiri ko kan abincin da basu dashi a gidan, Amma sai gashi wani lokaci da dan sana,an yarinyar suke samun rufin asiri a gidan don komai ya kare masu, Mama tace min ki kara hakkuri kinji Ya ta mahakurci mawadaci a,rayuwa, Na amsa cikin dan sake murmushin yake da cewa tau mama insha Allahu tare da mikewa nabar gurin naci gaba da tsabgogin gabana, ****** ********* ****** Allah maji rokon bawan shi Alhamdullahi an roki Allah kuma ya amsa muna, Don gashi yau su malam Linan sun dawo da Hamza a cikin iyalin shi lafiya ranan bawan Allah nan kuma yai sallama da mutane ya kama hanyan garisu, Anyi gwaji ansamu Hamza lafiyan shi kalau sai dai yar damuwa da take damun shi a zuciya wanda likita ta bashi shawara akan ya daina tunane don gudun kamuwa da wata cuta da ka iya cutar dashi, Ance akwai masana masu hikima da da sani daga cikin alkur,ani maigirma, Wanan zancen haka yake don kuwa sun nuna hikimar da amfani da ayyoyin Allah, Don babu shirka ko wani kaucewa a cikin sa da haka,suka ci galaba akan shu,uma Lima akan Hamza, Kwata kwata yanzu ko kadan baijin komai a gamay da Lima sai jin da yake a shirye yake yai mata cin mutinci idan ta tun kare shi, Damuwar shi yanzu guda da hankalin shi ya dawo shine rashin abin hannu da basu dashi a gida don komai ya kare mashi, Bai aje komai ba ta dalilin yaudaran da Lima sukai mai ta hanya asiri ya,sayar da komai nashi, Suka wullakanta kudin da sunan wai zai ga yan uwanta da aminata dashi, Mama Hafsi itace ta dage gurin bashi shawaran kan ya fitar da komai a ran shi yabarwa Allah Al,amarin yai mashi mafita a kai, Da yamma yai wanka yafita waje don har yanzu majalissan su tana nan a bakin shagon shi duk da shagon a rufe yake, Amma haka bai hana matasa taruwa gurin saboda sabo sukan zauna hira da yamma idan kowa ya dawo daga gurin neman rufin asirin shi sai su zauna hira, Yana fita nan suka shiga nuna farin cikin su suna jajanta mai da fatan Allah ya tsare gaba, Baba mudi ya hango a kofa zaune ya nufi gurin shi suka gaisa yakara dan tsawata mai akan yadda duniya ta koma yanzu ba kowane zakai saurin yadda da shi ba, Sai kuma na yakara dagewa ga ibada don samun kariya daga al,amuran duniya baki daya, Sosai yaji dadin nasihan Baba mudi, dattijon da yake daukan shi a,uguwa tankar mahaifin shi don mutuncin dattijon, Yaran shi dai ne masu rashin jin magana amma bawai maijawo mai futina ba,sai dai rashin kunya da jan magana,ashiya kawai, Nan ya zauna a cikin abokai yana sauraren hiran su abinda ya tuna mai da,baya ke nan lokacin yana Hamza yaron shi da yar tiredan shi yana,samun rufin asirin Allah daga ciki, Amma kuma duk abinda ya samu ya tafi ga banza alokaci daya, Sai imani da tawakkali kawai ya,saura mashi don tuna wani abu fitina ne da tashin hankali, Yana zaune yarinya takawo tallan kayan miya da yake ya saba saye a gurin ta take mai talla, Murmushi kawai yayi cikin zuciyan shi yana jin kunan rai tare da radadi don baida ko kwandala a aljihun shi, Har magariba yana zaune a gurin kamar yadda suka,saba ana ta hiran kamar kullun, ****** ********** ****** Nagama komai na gyara dakina duk da kullun a gyare dakin yake min na dauko sabon kulan abincin da na,saye saboda shi alokacin da zance auren shi yake yawo, Nadan yi saye saye na na,wasu abubuwan bukatun mata don gudun kada a,burgeni ni banda komai, Ba,wanda yasan na,saye su sai yau dana fitar don na sa mai abinci a cikin sa, Na shimfida mai sabon zanin gado wanda nabawa Hindu tasayo min American cotton mai kyau jada fari, kala, Nafshe dakin sai kanshi ke tashi har waje, da turaren da Hindu tabani don wanan ranan wanda tace turaren yana da,siri a cikin sa, Sabon ledan kasana yana sheki da haske a dakin gwanin ban sha,awa, Duk wanan shawaran uwar dakina hinduce ta sakani yin shi da tazo gidan mu last da dan ta datakara haihuwa wanda lokacin muna cikin tashin hankali, Tafada min cewa kada na nuna mai komai koda a fuskane na nuna tankar babu abinda yai min zafi a kan zancen, Kuma tunda Umma tana adawana a zaman gidan haka zai kona mata rai sosai sai dai indan anyi sa,a Allah ya,taro ta ta saduda , Tana zaune kofan ta kamar an kafe ta tana kallon yadda nake harkokina a tsanake ba wani nuna bacin rai a tare dani, Bayan fitowan maza daga gurin sallah ishai shima ya shigo gida kamar yadda suka sabayi a baya can, Nafito masu da babban tabarma na,shimfida kafin su gama gaisawa da,su Umma,sai hadari ya tashi kura ya kora kowa dakin sa saboda iska daya murtuke guri, Badon Umma taso ba ta barshi ya,shigo daki lokacin ina tsaye gurin mirro ina gyara, kayan mirron nawa, Sallama yashigo dashi na karba mai tare da mashi sannu da zuwa ya karba min a cikin shakku ba kamar yadda ya saba ba , Nake cewa na dauko mai abinci ne ko sai an gama iska, zaici yadan furza iska tare da shafan fuskan shi alamar abu yana damuwar shi a ran shi, Yace bari kawai naci yanzu don akwai alamar ruwa tafe ga hadarin baigama rufe baki ba ruwa masu karfi suka,sauko gaba,daya lokaci guda, Kayan abincin na dauko mai na aje mai a gaban shi, tare da girke mai sabon jug din ruwan da na,saye tare da kulolin, Kanshi ya na,sagale a makarin kujeran idanuwan shi a lumshe suke yana dan buga hannayen shi a hannun kujeran, A hankali har nagama shiri na tsab cikin wani dan rigan barcina dark blue mai igiya sirara, iya gwiwa, Saidai na daura zani daga ciki rigar kawai na saka daga sama, Nadawo bakin gadona na zauna duk da banci komai ba ban jin yunwa a lokacin, Jin shirun da yayi na,daina motsi yasa shi dago kan shi ya,sauke idanuwan shi a kaina ina zaune a bakin gado da yar wayata eitel ina dan dakilawa, Sai kuma ya dawo da kallon shi ga kulolin dake a gaban shi suna kyalin sabon taka, Humaira duk da abinda nai maki bakiyi fushi ba dani har da karramani irin haka kikayi, Daga inda nake a zaune nake cewa aini bakai min wani abuba sai dai kawai kanemi gafara ga ubangijin ka shine mafi alheri don Allah gafurun rahimun ne, Sai kawai naji ya,sake wani irin kuka mai karfi wanda ban taba zaton zai iya yin sa ba a,rayuwan shi, Badon karan ruwan saman da akeyi ba,da ba abinda zai hana gaba daya yan gidan mu kowa yazo dakin mu a lokacin, Cikin tashin hankali na mike tsaye ina kallon shi yadda ya ke kuka tare da dafe kan shi, Tsoro ne ya kamani a,zatona ko wani abin ne kuma, ya sake faruwa dashi again, Da sauri zan fita zuwa kiran jama,a sai naji ya riko min hannu tare da kokarin zaunar dani daga gefen shi kadan yake cewa cikin muryan kuka, Humaira ki bari nayi kukan nan ko zan samu relief a mind dina don na dade iba,son nayi shi ban samu halin yi ba, Humaira yau ni Hamza ne nai taraiya da wace ba musulma ba a rayuwa na, wai kuma matsayin matata, Ta yaya bazanyi kukan gamuwana da ubangijina ba ranan gobe kiyama, Jikina yai matukar sanyi don jin kalaman shi yai matukar bani tausayi, sosai tare da jin haushin wanan kafirar matar da ta jefa rayuwan mu a haka, Cikin sanyin murya na bude baki na,da kyat ina cewa, yaya kayi hakkuri komai a,rayuwan bawa mukaddari ne don hakan umurni ne na ubangiji Allah( S.W.A) Yace Humaira kunyar ki nake ji a,rayuwa na,ban san da,wani ido zan kalle kiba yau,don nauyin ki da nake ji,, Humaira kiyi hakkuri ki manta da komai bawai don ban so ki bane nai maki haka, A a wanan kaddararen al,amari ne a kaina an rubuto min cewa sai nayi shi a rayuwa na, Nace a cikin sanyi murya kamar ta mai kuka ni ban kullace ka ba yaya don ni musulma ce yar musulmai, Nasan mata nawa aka kidan yawa namiji ya,aura,a,rayuwan shi duk da,dai kai naka karin auren yazo a,wani bakon al,amari ne, Amma hakan bazai sa nai fushi dakai ta yadda har nima Allah zai iya yin fushi dani ba, Tabbas yaji dan sanyin magana na don yadda naji ya,sauke ajiyan zuciya yai shiru tare da dan kada kan shi, Nace kaci abinci ka cire damuwa a ranka kada ka jawa kan ka matsala fatana shine Allah ya kara nisanta wanan bakar mace nisa damu, Ya,dago idanuwan shi da suka rine sukai ja sun canza kala kamar gauta, abinka ga mai manyan idanuwa, sunyi wani jawur sunfito, Abincin da na dan yunkura na fara zuba mai a cikin plate yabi da kallo har na kara kadan yace min in barshi hakana amma a,tare zamuci don yaga nima banci komai ba, ai, Zan musa yake cewa idan banci ba,shima ba zai iya ci ba dole na zauna muka dan tsankwara kowan mu ya tashi, Sai dai gaskiya mun kasa sake jikin mu da juna kamar baya, can, Nake cewa ga ruwa babu daman yin wanka kuma saboda ruwan saman dake zuba da karfin Allah, Yake cewa ai bai dade da yai wanka ba don haka,ba matsala zai bari har wani lokaci, Munyi shirin kwanciya don kowan mu da zancen dake cin zuciyar shi, kowa da,tashi kuncin Sai neman agaji a,gurin Allah muke don samun saukin yadda,muke ji, a rayukan mu, Addu,a nake abakina don wani irin zafi da bacin rai nake ji nashi sai dai na,dake ina daurewa kamar ba komai, Yadda hindatu tace na zake nima na nuna mai tawa hikimar irin yadda ta koyar dani haka zai sa indan ma wani abu yakoyo daga gurin tsohuwar kilakiyar ya manta dashi, Yana tsaye a bayana,sai kallona yake a cikin tausaya min yana anyanawa a ranshi, Watau ita Humaira komai nata daban yake ke nan ko don komai a tsanake cikin kwanciyan hankali da nuna sanin addini takeyin sa, Har kwanciyar ta daban ne dana,waccan makirar mai kwanciyan kafirai, gashi suranta kamar ita tai kanta, komai dan dagwas ya,daure ya,danne yadda yake ji a,ranshi, Yakai zaune daidai bayana tare da dan tabani a hankali, yana cewa, Humaira ina,sonki ina,son irin haliyar ki, ni kadai nasan irin wahalan da,rashin ki a kusa dani ya janyo min nasha wahala sosai idan na tuna daku sai dai banda halin zuwa gare ku dan irin yadda nake ji idan na kudurta zuwa gare ku, Ina mai rokan Allah da kada ya kara nisantani fa iyalina da iyayyena, Ina mai fatan muyi rayuwa da insha Allahu sai mutuwa zai raba mu,, Jin ya tabani yasani juyowa a,dan tsorace nakalle shi sau guda naga duk yanayin shi ya canza idanuwan shi sai suka fara bani tsoro, saboda na hango wata irin muguwar sha,awa a tare dashi a lokacin, Zancen Hindune ya fado min da taje cewa sai na dage sosai don yanzu zanga matukar canji a,tare dashi don haka naji wani rangwanta ya mamaye zuciyata, Ganin yadda na nuna yadan sashi dan dawowa a cikin dan natsuwa , Yajawoni a hankali zuwa jikin shi tare muke sauke ajiyan zuciya idan kin gan mu a lokacin zaki tausaya muna don zaki fahinci kowa na daukin dan uwa, Sai bayan komai ya kammala,a,tsakanin mu ne yake cewa cikin sauke ajiyan zuciyan shi, Godiya ta tabbata ga sarki Allah wanda ya mallaka min Humaira a matsayin matar aure a gare ni, Humaira har kullun ina mai alfahari da,samun ki a matsayin mata a,gareni wace ta san darajana dana iyayyena, Ina,godewa Allah akan irin wanan baiwar da yai min a,rayuwata, Yana fadar haka ya mike ya,suri buta zuwa ban daki a zatona kewayawa zaiyi yadawo ashe wanka ya tafi yayi a lokaci don jin maganan da yayi nasu liman na cewa kwana da janab a jiki yana saka,sgedanu samun galaba akan dan adam, Yadawo har idona yadan fara nauyi ina son nayi barci ya tadani naje nai wanka haka na,fita nayo wankan nima, Koda nadawo na tadda shi yana sallah nafila a lokacin , Nagaji don haka ban tsayaba na haye gado na kwanta abina kawai ina mai jin wani iri a rayuwa na, Sai tunanen yadda muka kasance da shi yan min tina da,suka shige din duk yadda nai tsan mani abin ya,wuce nan ga Hamza don ya canza min gaba daya, ****** ********* ****** Ance mai hali baya barin halin sa don tunda safe nake jin motsin Umma a tsakar gida wanda ba komai bane don taga may ya,faru a tsakanin mu ni dashi, Sai sabanin zatin ta tagani don alwala yayi yafita zuwa masallaci nima dai shi taga nafito nayi na shige dakina, Don haka ta,shige dakin ta don ta fahinci ba komai a,tsakanin mu ke nan, Tunane da mamakin halin rayuwa irin na umma nake may yasa da yake tare da wata bata samu irin damuwa haka ba,sai da ya dawo gare mu ta fara aikin ta na saka idanuwan ta gare mu, Na gyara kwanciya na tare da lumshe idanuwa na a hankali, sai ji nayi ya dawo yana dan shafa min jiki a hankali wanda ban tsira ba haka ya kara afka min sai da ya samu natsuwa ya barni, Jin mu a,daki shiru yasaka Umma kwada min kira wai na fito na kwashe ruwan saman da ya taru a robobi na juye a randunar ruwan mu na,sha, Dukkanmu mun fahinci manufar umma don haka na yunkura zan mike naji muryan mamatana cewa haba yaya kibar yaran nan mana su futa, Ni zan juye ruwan tunda ba komai nakeyi ba don haka ki barta kawai, Yan kwanakin da Hamza yai muna,a gida kafin ya koma school haka mukai ta fama da Umma aace ta hanamu shakat a gidan gaba daya da,sa idanuwan ta, Sai dai hakan bai hanamu kasancewa tare ba don sai ma,abinda ya karu gurin nuna min so da kaunar da yake min, A haka mansur yazo suka koma school tare yabar mu da kewa a gida, ****** ********* ****** Satin shi daya,da komawa school yana ta kokarin covering din inda aka wuce shi, Bai ko kawo zance wai wata Lima ba aranshi don shi kwata kwata yama fita zancen ta, Tana zaune a class ya nufo hanyan da suke daga inda suke zaune Bicky ce ta fara hango shi a tafe yana rungumay da littatafan shi a hannun shi, Ta zuguri Lima tace ke ashe da gaske guy dinki ya,dawo gayanan tafe da,sauri Lima ta juya don ganin shi, Kallo daya tai mashi taji wani iri gaba,daya taji tsoro ne ko farga ya mamaye mata zuciya a lokaci guda, Har yazo ya,shige daga inda suke zaune ba wanda ya iya daga kai ya kalle shi ko yai mai magana, Sai daya shige take cewa cikin dan dafe kirjinta Vicky kin ji abinda naji danaga wanan guy din kuwa, Har tsawon wani lokaci take jin gabanta yana,faduwa bab bab bab take taji gaba,daya gurin ma ya gundure, Bashiri tabar cikin makarantar zuwa gida hankali a tashe sai dai tana zuwa gida sai a lokacin ta,samu natsuwa a tare da ita, Sai zaraya take a cikin falon su hankali a tashe take ta rasa may ke mata dadi a,rai, Don ganin da tai ma Hamza din yau yasaka zuciyan ta a cikin rudani don taga ya kara zama mata yaro karami yai wani kyau dashi ya,samu natsuwa, Amma kuma tana jin wani tsoro da fargaba yana shiganta akan shi anya kuwa yanzu zata iya kara shawo kan wanan yaron yadda taga yai mata kwarji da kuma jarunta, a idon ta, Lumshe idanuwan ta tayi don abinda takwji yana son fin karfin zuciyar ta ,,,, Ayi hakkuri da wanan baida yawa amna ce gare ku don zalunci ne turawa wani ya karata batare da hakkin mu ba, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE CIN AMANA NE KARANTAWA BA BIYA PLEASE,,,, Akwana a tashi ba,wuya a wurin Allah don gashi yau har sati ukun da,su baba liman suka kindanya ya cika, Don haka duk wani abinda suka shata cewa ya dace suyi don neman ma Hamza tsari gurin Allah daga sheri shu,um Lima sun yi shi, Nikan ina ganin mutanen gida suna zuwa a,sace gaida Hamza amma,ba wanda ya taba taya min hakan, Ina zaune yau a saman kujera yar tsugunno a tsakar gida, Ina tunane ace mace da mijin ta amma a hanata ganin shi sai dai taga mutane su na zuwa gun shi ita ba,a damu da nata damuwan ba, balle a taya mata zuwa duban shi, Tau sanyin kaina,ne ya kamani don dai zan iya cewa ni dai arayuwa na godewa Allah zance, Wani irin zazzabi naji ya na batun rufe ni saboda bayanin da naji Ibrahim yanawa su Umma din, Wai ni Aisha da mijina amma ace bazan gan shi ba sai lokacin da aka ga daman bari nagan shi ko ya ganni, Na nisa ina fadin Allah na godema kai kadai kasan dalilin jefa rayuwan mu a cikin wanan halin, Ina zaune gurin nai zurfi ga tunanen da nakeyi mama tafito daga dakin don ta karasa aikin da takeyi sai gani na tayi a cikin wani yanayi, Taja tai turus tana kallona a cikin mamaki da tausayawa ta karaso gare,ni tana ,duk ban farga ba sai ji nayi tace, Aisha may kuma kike tunane haka kikayi zurfi a acikin tunane, Jin ta,a kaina batare da na,sani ba yadan sani kaduwa da,dan firgice , Na dago idanuwana cike da firgici mai nuna razana na kalle ta, tana cewa may kike tunane ne haka har baki jin magana, Nace cikin sanyin murya mama babu komai ina,dai zaune ne, kawai, Tace to ki daina ir8n wanan dogon tunanen kada ki jefa kan ki a fitina bayan komai ya kusa kai karshe, Takara matsowa gare ni tare da,dan dafa kafada na tana cewa Aisha kin yi kokari fiye da tsan mani don da watace cewa zatayi fita zatayi bazata daure da,wanan fititinun haka ba, Umma daje fitowa ashe taji mu take cewa wanan ai hakkuri ya zama dole ne don ko an tafi ina,gurin zuwa, Haba mama bata da gurin zuwa kamar wace bata da gida adaji aka tsinto ta, inji Ibrahim wanda ke daga bayan ta, Gaskiya Umma Aisha ta wuce haka garemu don tai muna halarci wanda ba ko wace yarinya mai karamin shekaru irin nata zata iya muna shi ba, Har yau ba mai cewa ga abinda yarinyar ga tace a garin nan tana gida tana kokarin ta duk abinda ta,sabayi da yake nan bata daina ba, don bayanan gashi yadawo acikin wani hali amma duk da haka bata kyamace shi ba , Haba dai Umma wanan abin fa yai ishe mu isharan rayuwa, Jikin Umma yai sanyi ga maganan dan ta don haka,ta juya ta,shige zuciyan ta ba dadi don a gaskiya itama tasan cewa inba Aisha bace da yanzu an kai ruwa rana ga tonon asiri ko kan abincin da basu dashi a gidan, Amma sai gashi wani lokaci da dan sana,an yarinyar suke samun rufin asiri a gidan don komai ya kare masu, Mama tace min ki kara hakkuri kinji Ya ta mahakurci mawadaci a,rayuwa, Na amsa cikin dan sake murmushin yake da cewa tau mama insha Allahu tare da mikewa nabar gurin naci gaba da tsabgogin gabana, ****** ********* ****** Allah maji rokon bawan shi Alhamdullahi an roki Allah kuma ya amsa muna, Don gashi yau su malam Linan sun dawo da Hamza a cikin iyalin shi lafiya ranan bawan Allah nan kuma yai sallama da mutane ya kama hanyan garisu, Anyi gwaji ansamu Hamza lafiyan shi kalau sai dai yar damuwa da take damun shi a zuciya wanda likita ta bashi shawara akan ya daina tunane don gudun kamuwa da wata cuta da ka iya cutar dashi, Ance akwai masana masu hikima da da sani daga cikin alkur,ani maigirma, Wanan zancen haka yake don kuwa sun nuna hikimar da amfani da ayyoyin Allah, Don babu shirka ko wani kaucewa a cikin sa da haka,suka ci galaba akan shu,uma Lima akan Hamza, Kwata kwata yanzu ko kadan baijin komai a gamay da Lima sai jin da yake a shirye yake yai mata cin mutinci idan ta tun kare shi, Damuwar shi yanzu guda da hankalin shi ya dawo shine rashin abin hannu da basu dashi a gida don komai ya kare mashi, Bai aje komai ba ta dalilin yaudaran da Lima sukai mai ta hanya asiri ya,sayar da komai nashi, Suka wullakanta kudin da sunan wai zai ga yan uwanta da aminata dashi, Mama Hafsi itace ta dage gurin bashi shawaran kan ya fitar da komai a ran shi yabarwa Allah Al,amarin yai mashi mafita a kai, Da yamma yai wanka yafita waje don har yanzu majalissan su tana nan a bakin shagon shi duk da shagon a rufe yake, Amma haka bai hana matasa taruwa gurin saboda sabo sukan zauna hira da yamma idan kowa ya dawo daga gurin neman rufin asirin shi sai su zauna hira, Yana fita nan suka shiga nuna farin cikin su suna jajanta mai da fatan Allah ya tsare gaba, Baba mudi ya hango a kofa zaune ya nufi gurin shi suka gaisa yakara dan tsawata mai akan yadda duniya ta koma yanzu ba kowane zakai saurin yadda da shi ba, Sai kuma na yakara dagewa ga ibada don samun kariya daga al,amuran duniya baki daya, Sosai yaji dadin nasihan Baba mudi, dattijon da yake daukan shi a,uguwa tankar mahaifin shi don mutuncin dattijon, Yaran shi dai ne masu rashin jin magana amma bawai maijawo mai futina ba,sai dai rashin kunya da jan magana,ashiya kawai, Nan ya zauna a cikin abokai yana sauraren hiran su abinda ya tuna mai da,baya ke nan lokacin yana Hamza yaron shi da yar tiredan shi yana,samun rufin asirin Allah daga ciki, Amma kuma duk abinda ya samu ya tafi ga banza alokaci daya, Sai imani da tawakkali kawai ya,saura mashi don tuna wani abu fitina ne da tashin hankali, Yana zaune yarinya takawo tallan kayan miya da yake ya saba saye a gurin ta take mai talla, Murmushi kawai yayi cikin zuciyan shi yana jin kunan rai tare da radadi don baida ko kwandala a aljihun shi, Har magariba yana zaune a gurin kamar yadda suka,saba ana ta hiran kamar kullun, ****** ********** ****** Nagama komai na gyara dakina duk da kullun a gyare dakin yake min na dauko sabon kulan abincin da na,saye saboda shi alokacin da zance auren shi yake yawo, Nadan yi saye saye na na,wasu abubuwan bukatun mata don gudun kada a,burgeni ni banda komai, Ba,wanda yasan na,saye su sai yau dana fitar don na sa mai abinci a cikin sa, Na shimfida mai sabon zanin gado wanda nabawa Hindu tasayo min American cotton mai kyau jada fari, kala, Nafshe dakin sai kanshi ke tashi har waje, da turaren da Hindu tabani don wanan ranan wanda tace turaren yana da,siri a cikin sa, Sabon ledan kasana yana sheki da haske a dakin gwanin ban sha,awa, Duk wanan shawaran uwar dakina hinduce ta sakani yin shi da tazo gidan mu last da dan ta datakara haihuwa wanda lokacin muna cikin tashin hankali, Tafada min cewa kada na nuna mai komai koda a fuskane na nuna tankar babu abinda yai min zafi a kan zancen, Kuma tunda Umma tana adawana a zaman gidan haka zai kona mata rai sosai sai dai indan anyi sa,a Allah ya,taro ta ta saduda , Tana zaune kofan ta kamar an kafe ta tana kallon yadda nake harkokina a tsanake ba wani nuna bacin rai a tare dani, Bayan fitowan maza daga gurin sallah ishai shima ya shigo gida kamar yadda suka sabayi a baya can, Nafito masu da babban tabarma na,shimfida kafin su gama gaisawa da,su Umma,sai hadari ya tashi kura ya kora kowa dakin sa saboda iska daya murtuke guri, Badon Umma taso ba ta barshi ya,shigo daki lokacin ina tsaye gurin mirro ina gyara, kayan mirron nawa, Sallama yashigo dashi na karba mai tare da mashi sannu da zuwa ya karba min a cikin shakku ba kamar yadda ya saba ba , Nake cewa na dauko mai abinci ne ko sai an gama iska, zaici yadan furza iska tare da shafan fuskan shi alamar abu yana damuwar shi a ran shi, Yace bari kawai naci yanzu don akwai alamar ruwa tafe ga hadarin baigama rufe baki ba ruwa masu karfi suka,sauko gaba,daya lokaci guda, Kayan abincin na dauko mai na aje mai a gaban shi, tare da girke mai sabon jug din ruwan da na,saye tare da kulolin, Kanshi ya na,sagale a makarin kujeran idanuwan shi a lumshe suke yana dan buga hannayen shi a hannun kujeran, A hankali har nagama shiri na tsab cikin wani dan rigan barcina dark blue mai igiya sirara, iya gwiwa, Saidai na daura zani daga ciki rigar kawai na saka daga sama, Nadawo bakin gadona na zauna duk da banci komai ba ban jin yunwa a lokacin, Jin shirun da yayi na,daina motsi yasa shi dago kan shi ya,sauke idanuwan shi a kaina ina zaune a bakin gado da yar wayata eitel ina dan dakilawa, Sai kuma ya dawo da kallon shi ga kulolin dake a gaban shi suna kyalin sabon taka, Humaira duk da abinda nai maki bakiyi fushi ba dani har da karramani irin haka kikayi, Daga inda nake a zaune nake cewa aini bakai min wani abuba sai dai kawai kanemi gafara ga ubangijin ka shine mafi alheri don Allah gafurun rahimun ne, Sai kawai naji ya,sake wani irin kuka mai karfi wanda ban taba zaton zai iya yin sa ba a,rayuwan shi, Badon karan ruwan saman da akeyi ba,da ba abinda zai hana gaba daya yan gidan mu kowa yazo dakin mu a lokacin, Cikin tashin hankali na mike tsaye ina kallon shi yadda ya ke kuka tare da dafe kan shi, Tsoro ne ya kamani a,zatona ko wani abin ne kuma, ya sake faruwa dashi again, Da sauri zan fita zuwa kiran jama,a sai naji ya riko min hannu tare da kokarin zaunar dani daga gefen shi kadan yake cewa cikin muryan kuka, Humaira ki bari nayi kukan nan ko zan samu relief a mind dina don na dade iba,son nayi shi ban samu halin yi ba, Humaira yau ni Hamza ne nai taraiya da wace ba musulma ba a rayuwa na, wai kuma matsayin matata, Ta yaya bazanyi kukan gamuwana da ubangijina ba ranan gobe kiyama, Jikina yai matukar sanyi don jin kalaman shi yai matukar bani tausayi, sosai tare da jin haushin wanan kafirar matar da ta jefa rayuwan mu a haka, Cikin sanyin murya na bude baki na,da kyat ina cewa, yaya kayi hakkuri komai a,rayuwan bawa mukaddari ne don hakan umurni ne na ubangiji Allah( S.W.A) Yace Humaira kunyar ki nake ji a,rayuwa na,ban san da,wani ido zan kalle kiba yau,don nauyin ki da nake ji,, Humaira kiyi hakkuri ki manta da komai bawai don ban so ki bane nai maki haka, A a wanan kaddararen al,amari ne a kaina an rubuto min cewa sai nayi shi a rayuwa na, Nace a cikin sanyi murya kamar ta mai kuka ni ban kullace ka ba yaya don ni musulma ce yar musulmai, Nasan mata nawa aka kidan yawa namiji ya,aura,a,rayuwan shi duk da,dai kai naka karin auren yazo a,wani bakon al,amari ne, Amma hakan bazai sa nai fushi dakai ta yadda har nima Allah zai iya yin fushi dani ba, Tabbas yaji dan sanyin magana na don yadda naji ya,sauke ajiyan zuciya yai shiru tare da dan kada kan shi, Nace kaci abinci ka cire damuwa a ranka kada ka jawa kan ka matsala fatana shine Allah ya kara nisanta wanan bakar mace nisa damu, Ya,dago idanuwan shi da suka rine sukai ja sun canza kala kamar gauta, abinka ga mai manyan idanuwa, sunyi wani jawur sunfito, Abincin da na dan yunkura na fara zuba mai a cikin plate yabi da kallo har na kara kadan yace min in barshi hakana amma a,tare zamuci don yaga nima banci komai ba, ai, Zan musa yake cewa idan banci ba,shima ba zai iya ci ba dole na zauna muka dan tsankwara kowan mu ya tashi, Sai dai gaskiya mun kasa sake jikin mu da juna kamar baya, can, Nake cewa ga ruwa babu daman yin wanka kuma saboda ruwan saman dake zuba da karfin Allah, Yake cewa ai bai dade da yai wanka ba don haka,ba matsala zai bari har wani lokaci, Munyi shirin kwanciya don kowan mu da zancen dake cin zuciyar shi, kowa da,tashi kuncin Sai neman agaji a,gurin Allah muke don samun saukin yadda,muke ji, a rayukan mu, Addu,a nake abakina don wani irin zafi da bacin rai nake ji nashi sai dai na,dake ina daurewa kamar ba komai, Yadda hindatu tace na zake nima na nuna mai tawa hikimar irin yadda ta koyar dani haka zai sa indan ma wani abu yakoyo daga gurin tsohuwar kilakiyar ya manta dashi, Yana tsaye a bayana,sai kallona yake a cikin tausaya min yana anyanawa a ranshi, Watau ita Humaira komai nata daban yake ke nan ko don komai a tsanake cikin kwanciyan hankali da nuna sanin addini takeyin sa, Har kwanciyar ta daban ne dana,waccan makirar mai kwanciyan kafirai, gashi suranta kamar ita tai kanta, komai dan dagwas ya,daure ya,danne yadda yake ji a,ranshi, Yakai zaune daidai bayana tare da dan tabani a hankali, yana cewa, Humaira ina,sonki ina,son irin haliyar ki, ni kadai nasan irin wahalan da,rashin ki a kusa dani ya janyo min nasha wahala sosai idan na tuna daku sai dai banda halin zuwa gare ku dan irin yadda nake ji idan na kudurta zuwa gare ku, Ina mai rokan Allah da kada ya kara nisantani fa iyalina da iyayyena, Ina mai fatan muyi rayuwa da insha Allahu sai mutuwa zai raba mu,, Jin ya tabani yasani juyowa a,dan tsorace nakalle shi sau guda naga duk yanayin shi ya canza idanuwan shi sai suka fara bani tsoro, saboda na hango wata irin muguwar sha,awa a tare dashi a lokacin, Zancen Hindune ya fado min da taje cewa sai na dage sosai don yanzu zanga matukar canji a,tare dashi don haka naji wani rangwanta ya mamaye zuciyata, Ganin yadda na nuna yadan sashi dan dawowa a cikin dan natsuwa , Yajawoni a hankali zuwa jikin shi tare muke sauke ajiyan zuciya idan kin gan mu a lokacin zaki tausaya muna don zaki fahinci kowa na daukin dan uwa, Sai bayan komai ya kammala,a,tsakanin mu ne yake cewa cikin sauke ajiyan zuciyan shi, Godiya ta tabbata ga sarki Allah wanda ya mallaka min Humaira a matsayin matar aure a gare ni, Humaira har kullun ina mai alfahari da,samun ki a matsayin mata a,gareni wace ta san darajana dana iyayyena, Ina,godewa Allah akan irin wanan baiwar da yai min a,rayuwata, Yana fadar haka ya mike ya,suri buta zuwa ban daki a zatona kewayawa zaiyi yadawo ashe wanka ya tafi yayi a lokaci don jin maganan da yayi nasu liman na cewa kwana da janab a jiki yana saka,sgedanu samun galaba akan dan adam, Yadawo har idona yadan fara nauyi ina son nayi barci ya tadani naje nai wanka haka na,fita nayo wankan nima, Koda nadawo na tadda shi yana sallah nafila a lokacin , Nagaji don haka ban tsayaba na haye gado na kwanta abina kawai ina mai jin wani iri a rayuwa na, Sai tunanen yadda muka kasance da shi yan min tina da,suka shige din duk yadda nai tsan mani abin ya,wuce nan ga Hamza don ya canza min gaba daya, ****** ********* ****** Ance mai hali baya barin halin sa don tunda safe nake jin motsin Umma a tsakar gida wanda ba komai bane don taga may ya,faru a tsakanin mu ni dashi, Sai sabanin zatin ta tagani don alwala yayi yafita zuwa masallaci nima dai shi taga nafito nayi na shige dakina, Don haka ta,shige dakin ta don ta fahinci ba komai a,tsakanin mu ke nan, Tunane da mamakin halin rayuwa irin na umma nake may yasa da yake tare da wata bata samu irin damuwa haka ba,sai da ya dawo gare mu ta fara aikin ta na saka idanuwan ta gare mu, Na gyara kwanciya na tare da lumshe idanuwa na a hankali, sai ji nayi ya dawo yana dan shafa min jiki a hankali wanda ban tsira ba haka ya kara afka min sai da ya samu natsuwa ya barni, Jin mu a,daki shiru yasaka Umma kwada min kira wai na fito na kwashe ruwan saman da ya taru a robobi na juye a randunar ruwan mu na,sha, Dukkanmu mun fahinci manufar umma don haka na yunkura zan mike naji muryan mamatana cewa haba yaya kibar yaran nan mana su futa, Ni zan juye ruwan tunda ba komai nakeyi ba don haka ki barta kawai, Yan kwanakin da Hamza yai muna,a gida kafin ya koma school haka mukai ta fama da Umma aace ta hanamu shakat a gidan gaba daya da,sa idanuwan ta, Sai dai hakan bai hanamu kasancewa tare ba don sai ma,abinda ya karu gurin nuna min so da kaunar da yake min, A haka mansur yazo suka koma school tare yabar mu da kewa a gida, ****** ********* ****** Satin shi daya,da komawa school yana ta kokarin covering din inda aka wuce shi, Bai ko kawo zance wai wata Lima ba aranshi don shi kwata kwata yama fita zancen ta, Tana zaune a class ya nufo hanyan da suke daga inda suke zaune Bicky ce ta fara hango shi a tafe yana rungumay da littatafan shi a hannun shi, Ta zuguri Lima tace ke ashe da gaske guy dinki ya,dawo gayanan tafe da,sauri Lima ta juya don ganin shi, Kallo daya tai mashi taji wani iri gaba,daya taji tsoro ne ko farga ya mamaye mata zuciya a lokaci guda, Har yazo ya,shige daga inda suke zaune ba wanda ya iya daga kai ya kalle shi ko yai mai magana, Sai daya shige take cewa cikin dan dafe kirjinta Vicky kin ji abinda naji danaga wanan guy din kuwa, Har tsawon wani lokaci take jin gabanta yana,faduwa bab bab bab take taji gaba,daya gurin ma ya gundure, Bashiri tabar cikin makarantar zuwa gida hankali a tashe sai dai tana zuwa gida sai a lokacin ta,samu natsuwa a tare da ita, Sai zaraya take a cikin falon su hankali a tashe take ta rasa may ke mata dadi a,rai, Don ganin da tai ma Hamza din yau yasaka zuciyan ta a cikin rudani don taga ya kara zama mata yaro karami yai wani kyau dashi ya,samu natsuwa, Amma kuma tana jin wani tsoro da fargaba yana shiganta akan shi anya kuwa yanzu zata iya kara shawo kan wanan yaron yadda taga yai mata kwarji da kuma jarunta, a idon ta, Lumshe idanuwan ta tayi don abinda takwji yana son fin karfin zuciyar ta ,,,, Ayi hakkuri da wanan baida yawa amna ce gare ku don zalunci ne turawa wani ya karata batare da hakkin mu ba, ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Ba karamin farin ciki abokan karatunshi masu kishin addini sukayi ba ganin yanzu ba ruwan shi da,zance wan Lima din da tai mashi yaudara, Duk wani abinda ya wuce a baya an sahilcewa juna andawo daidai kamar farko, Yanzu dashi da Mansur koda yaushe kamar tip da taya,suke don suna gudun shu,umancin Lima, Duk dai itama yanzu bata batun shi don ji take wani irin koda sunan shi aka kira tana,gurin hankalinta duk sai ya,daga, Kwata kwata tafita zancen gaba daya bata batun shi kuma don ya fice mata a rai, Sai dai acan kasan zuciyan ta tana yawan begen kasan cewa da shi, Ga Bicky kuma tana yawan fada,mata cewa ita yanzu ta tsani al,amarin hurda da matasa yara kanana, Don ba karamin zubar masu da mutunci zaman Lima da Hamza yayi ba a idanuwan jama,a, Dalilai da masu dama suka sa zancen yafita a kawunan Jama,a kamar yadda malam Liman yai alkawari zai faru komai ya koma normal, Yau sun dawo daga lectures kasancewa ana mugun zafi ya saka shi dan cire shirt din shi na sama ya zauna daga shi sai singlet a jikin shi, Hannun shi rike da handout din da yake karantawa yana dan fitara, Mansur ya shigo dakin a gajiye ya fada saman kujeran dake a dakin Hamza yake mai sannu da shigowa kamar yadda sukeyiwa ju an su, Yadan juya yana cewa Hamza ance damanan bana ana samun ruwan sama sosai a gida da alamar cewa damana zatai kyau ke nan, Wani irin abu Hamza yaji a zuciyar shi don yasan cewa wanan damanan sai ahankali ke nan do bazai samu noma ba, Saboda bai aje ba bai bawa wani ajiya ba, gashi a baya Allah ya taimake shi ya samu amfani masu yawa da albarka, Sai dai kaddara ya riga fata ga kayan don wanan iftila,in da ya afka mai duk ya ruguzar mashi da plan din shi gaba daya, Duk hiran da mansur yake ta zuba mai hankalin shi ya gurin tunanen abinda zai samu ya taimaki rayuwan shi dashi yadan noma koda kadan ne daga abinda ya samu, Amma kuma baida wani madogara bayan Allah don babu mai baka,aro ko taimako dan katashi kaci gaba a wannan zamanin, Kunci da tashin hankali duk sun mamaye mai zuciyan shi don baida wani madogara sai dai kawai abinda Allah yai mai, ****** ********** ****** Alhamdullahi yanzu komai ya wuce hankali ya kwanta, don kowa hankalin shi a kwance yake, Dama haka rayuwan dan adam ya kunsa a lokacin da ake a cikin fitina zakaga hankalin kowa a tashe amma da zaran an roki Allah ya kawo saukin al,amari sai kaga an dan sha,afa da komai, Duk da hankalina yana a kwance ban daina adduan da na keyi ba na neman samun rinjaye akan kowa ta irin masifa da zata iya kunnu min kai a gaba, Musan man ma ta kishiya don Ummina, takan ce min sai nayi a hankali don mijina mai sha,awan mata ne, Duk da maganan yakan bata min rai don a lokacin sai na dauka baki Ummina take min, Amma kuma da mukai hira da anty hindatu take ce ita fa a tsaye take kyam gurin kokarin ganin ta kare kanta daga matan da ke kawo wa mijin ta hari ko, nuna kauna a fili, Take ce min matan yanzu suke kokarin kamun kafa daga gurin yan uwa miji ko abokan shi har a tursasawa namiji ra,ayin aure, koda baida niyar karawa To balle ni da miji tun farko nasan cewa mutum ne mai sha,awan mace tare da shi kuma macen yar gayu,, Don haka na mike na zama mai yawan rokon Allah akan duk macen da mijina zai aura Allah yai min rinjaye a kan ta ta ko wani hanya Allah ya fifitani, Wanan adduan wasa wasa ya zauna min a bakina don duk abinda nakeyi hankalina yana akan wanan adduan, dauke a bakina, Ance mai hali baya barin halinsa yanzu Umma ta kara dinkewa sosai da, aminiyan ta mama Sa,a, Abu dayane shine ta rage yawan zuwa can ta zauna amma dai suna tare da juna, Don ko unguwa a tare sukan tafi indan haka ya kama masu fitan, Don haka a sannu bakin halin Umma ya fara dawowa tafara sakani gaba da hattara da tsangwama a gidan, Sai dai yanzu abin da dan sauki saboda na rage yawan aiyukan danakeyi a baya,sosai don mama hafsi ta kashe wasu aiyunkan a kaina, Don dole su Asmau da Sa,a sukan fito su kama yi su ma, Idan baki mata ba acikin labarinda nake baki a baya kin san na saye wake buhu biyu da dan kudin dake a hannuna lokacin da Hamza yazo ido rufe zai sayar da kayan amfanin gonan shi, Yanzu gashi lokacin sayar da waban waken yayi don haka na bayar Ibrahim ya sayar min ida na samu riba sosai akan su, Ranan da aka sayar min ranan Hamza ya zo weekend garin yazo da zuman neman kudin da zai dan yi noma dashi koda kadan ne don ya saba da sha anin noma sosai, Ganin ya fada nan ya fada can amma babu inda ya samu ko dubu daya a,ro, kowa sai yakawo uzuri ya kindaya mashi, Ya dawo gida jiki da sanyi baida wani kuzari duk hankalin shi a tashe,ya rasa mafita yadda zaiyi, Mama hafsi tace ya sayar da wanan kangon gidan daya saya mata a,baya ya samu kudi yai abinda zaiyi dasu, Sam bai sha,awan taba hakkin marayu da sunan zai juya su don yasan yakan karye a kan mutum lokaci guda duk su ruguje baki daya, Haka ne ya dan nuna wa mama cewa tabari har a samu mai saye, Sam bai san cewa ina da kudi a hannu na ba sai dai duk maganan da suke ina jin su daga inda nake a zaune, Bayan ya shigo daki yana zaune abin duniya yakai mashi ko ina don ko magana na lura da baya,son yi sosai, Ance tsakanin miji da mata sai Allah tsab na mike na sauke akwatina na inda na boye kudin da aka,sayar min da wake na kirga kudin na miko mashi gurin da yake zaune, Cikin mamaki yake kallo na yana kallon kudin, cikin nuna mamaki yake tambaya na kudin maye wanan Humaira, Nakai zaune a hankali daga inda nake tsaye nace kudi nane wanan yaya, Kudin ki ? Ya tambaya cikin tsureni da idanuwan shi yana son jin amsar tambayan da yai min, Nake ce mai eh na wane kudin da na,sayar da,wanke dana saya a gurin kane, Sai naga ya dukar da kanshi cikin dan jin nauyi da kunya sai kuma ya dan dago kai yana mai kallona a cikin jin nauyi, Nace a hankali idan zasu ishe ka sai ka fara dasu mu gani, Cikin wani murya mai ban tausayi yace Humaira kina ganin ba matsala idan nai haka ban tauye ki ba,ashe,? Nagirgiza kaina nace ba matsalan komai dama fridge naso na canza dashi don wanan da nake amfani dashi ya fara tsufa yana son canzawa, Amma zan ta maneji dashi har zuwa lokacin da Allah zai hore min na,sai, wani kuma, Ajiyan zuciya naji yayi mai karfi tare da fadi a fili Allah nagode maka, Yadda kika taimaka min kema Allah ya taimake ki Humaira nagode, Haba yaya ai abina abinka ne basai kai min godiya ba a kan shi don nima da taimakon ka na samu haka ai, Wasu kudin zasu kai goma sha biyar na kara mika mashi again, Da sauri ya kara tambaya na sukuma wa yan nan na maye kuma nace nakane , Nawa ? Ya tambaya a cikin mamaki yana kallon kudin batare da ya karba ba, Nace eh ka manta kudin da kasamu a gurin gasar amfani gona kace nabar wa yan nan a guri na har ka tambaya, Ido ya zaro yana mamaki tare da nuna kudin yana cewa kina nufin duk tsawonokacin nan kudin nan su a jeye a hannun ki, har yanzu, Nace eh mana ba cewa kayi na aje ma,su ba har ka tambaya, Shiru yayi yana tunane a ranshi cewa wanan yarinyar wata iri ne ita, kudi kusan shekara biyu da rabi zuwa uku tana ta faman boyon su haka ba tare da ta kashe su ba, O ni Hamza Allah nagode maka da,wanan baiwar da, rufin asiri da kai min a cikin dakina, Ya kara juyowa inda nake yana cewa Humaira na gode nagode da wanan rufin asirin da kikai min bazan taba mancewa da irin wanan halarcin da kikai min ba a duniyar nan, Mikewa tsam yayi da kudin zuwa waje gurin iyayyen shi ina jin shi yana masu bayani dalla dalla , Zan iya cewa yaune rana na farko a,rayuwan zamana a gidan su Hamza danaji Umma ta bude baki tana sa min albarka kamar yadda ko wace uwa takewa dan ta, Naji dadin wanan adduan da suke min don har da fatan Allah ya bamu zuria masu albarka tai muna, Sai naji a raina a gaskiya nima yanzu ina bukatan haihuwa a rayuwana Don Hindatu tace min idan har na haihu kila kiyayyana da Umma zai dan rage don albarkacin abinda na haifa, A hankali nakai hannu na a cikina karo na farko ina mai adduan nima Allah ya bani haihuwa hakana, Don ko Kubura da na riga aure duk da tafini cika yanzu tana da tsohon ciki a jikin ta haihuwa ko yau ko gobe, ****** ********** ****** Noma haikan Hamza ya fara da dan kudin daya samu a hannu na,sai dai da yake noman yanzu kudi yake bukata sai gashi tun ba a kai ko ina ba kudin duk sun shige ga a aikin noman, Fada nan fada can haka har Allah ya taimaka gonan ya samu tsayuwa,sosai, komai yai kyau yadda yake bukatan gani sai da muce Allah ya albarkaci gonan ta mu kawai yanzu, Ranan na dawo da gajiya,daga makaranta don yanzu muna rubuta final exam din mu ne a school din, mu, Ban samu abinci ba don yanzu dama ba ko yaushe muke girki ba a gidan kamar baya, can, Ina zaune daga kofana ina dama yar furar da na shigo da ita a cikin jakata don yanzu wani kwazaban shan fura ne yazo min sosai, Ga yunwar da nake ji don haka nake sauri na dama ko zai rage min yuwan da nakeji don ji nake kamar banda hanji a cikina don yunwa, Muryan mama sa,a ce ta,shigo tana sallama daga kofa , Daga inda nake zaune na karba mata tare da gaishe ta a cikin ladabi a matsayinta na,sarakuwana itama, Take tambayana bayan ta karba gaisuwa na da cewa Umma fa tana cikine , Nace eh amma tadan kewaya yanzu zata fito namike nakawo mata kujera don ta zauna, A lokacin itama Umma din tafito daga bandaki hannun ta dauke da butan data kewaya dashi, Daga inda mama Sa,a take a zaune sai bingidan da kallo da dan yatsunan da takeyi, Tun daga nesa Umma ke mata sannu da,shigowa tana cewa ashe har kin karaso yanzu nake cewa kindan taushe hannu kada rana yai muna don da kafa kikace zamu tafi, Tace eh nadan tsaya ne balaraba ce ta shigo shine yasa na dan taushe hannu kin san halin dakaren mijin nata mai hali baya barin halin sa, Ni kashe auren zan yi kowa ya huta don bazan iya ba ace aure ba,wani karuwa sai dan banzan fitina, don iskanci har ya,fara zagin iyayye, Umma tace ai sha anin yaran ne yanzu sai hakkuri Sa,a don abinda kai kake hango masu su basu ganewa sam, Tamike tana cewa ga gidan naku shiru mana kodaya ke dama ku haka gidan yake ba,wani karuwan yara sai dai aci akaiwa masai kawai amma anki aje muna dan kama hannu mu rika mu samu dan rakiya zuwa uguwa, Take Umma ta tabe baki tace bari kedai Sa,a ni wanan abin ya kai min inda yakai wallahi ace gida shiru kamar gidan bariki, Can kuma tace umm bari dai nai shiru duk da yake dai baka ganin naka a cikin cutarwa ka kyale shi dole ne kafada mai gaskiya, Wani irin dimm naji a raina sai da cikina yadan bada kara kulululu don nasan sabon fitina mama sa,a ta jawo min kuma, A cikin karfin hali nai masu adawo lafiya ban tsanmani Umma ta amsa min ba suka fice, Furan da nake dokin sha sai naji duk yafita min a rai annurin fuskana duk ta gushe a lokaci guda, Sai nake tuhumar kaina da kodai ina da matsalanr dasu suke ganin laifin nawa ne ni kadai bada Hamza din ba, Sai nice kawai abin zargi a kullun laifina kawai suke ganin naki daukan wanan cikin, Na mike tare da,daukan furan nakai cikin fridge na je batare da nasha ba, Ina zaune ina hadiyan bakinciki mama hafsi tashigo gidan tun daga karban sallaman da nai mata ta,fahinci ina cikin damuwa, Tun daga tsaye take tambayana may akayi halan Aisha ? Nace cikin kakaro murmushi ba komai mama , inadan dariyan yake, Halan Sa,a ta shigo gidan nan yau ko,? Nabata amsa da eh mama yanzu suka fita zuwa uguwa, Wanan bakar makiran mace yaya taki gane halinta har yanzu duk irin abinda tai mata a gidan nan kan zance yaron nan amma wai shine yanzu suka kara dinkewa kuma,, Haka mama taita mita bata daki bata waje har yamma da,su Umma suka,dawo, Don tasan cewa zataji ko maye a gurin Umma tunda ni naki fada mata komai, Ai ko suna zaune ana hira kowa na gida bayan isha,i yan gidan mu suka shigo suna cewa, Kubura ta haihu da yamman nan su Ummi suna can sun tafi dauko ta wai, Nifa hakkurina akan rashin haihuwan yaran nan yasoma kai karshe ace aure kusan shekara uku har wanda sukayi aure a,bayan su sun haihu suko shiru kakeji haka, To tunda kina da ja da al,amarin ubangiji ai sai kiyi yadda zakiyi su haihu din ko, Mamace ta bata amsa da haka daga inda take zaune tana cin abinci, Tace ni wai har yaushe ne za,a ce yaran nan sun wani jima basu haihu ba har ana batun tayar da jijiya akai Nifa nasan Allah ne mai bayarwa idan lokaci yayi bawai sai mutum yaso ba, Dole na na fadi hafsatu don wanan abin ya fara damuwa na,arai ace gida haka shiru babu hayaniyar yara da mutum zaiji yaji dadi a ran shi, Kin san kowa da irin bayan shi wasu guntun baya garesu wasu dogon baya ne dasu sai andauki lokaci mai tsawo, Don haka kibar wanan zancen haka yaya duk fa yadda akeyi yarinyar nan tana yin shi a gidan nan, Tau ai bance batayi ba,shi maganan haihuwa wani magana ce ta daban don kowa nason yaga nashi a cikin karuwa dashi da ita ai ina son ganin kowa ya samu karuwa, To sai kici gaba dayi tunda ki fi bukatar ganin su a cikin tashin hankali, ko yaushe don zancen ki tayar masu da hankali kawai yake a gidan nan, ****** ********** ****** Da kwana biyu Hamza ya dawo don yanzu bai dadewa bai shigo ba tunda mansur yana da mota kuma ba,wani nisane tsakanin sokoto da mu ba, Wajajen shidda na yamma suka shigo don yin weekend, kamar yadda suka,saba, yi muna, Na tare shi da murna ina fada mashi zancen haihuwan Kubura azatona shima murna zaiyi sosai jin kubura ta haihu don ko banza ai an zama daya yanzu, Sai naji yana cewa aiyya ashe ciki gare ta, Yadda ya amsa min sai banji dadi ba sai dai nabi bayan shi da kallo kawai cikin mamakin irin yadda ya amsa min, Can yadan leko daga waje yana ce min kikai min ruwa na,watsa na cire wanan kayan na jikina, Ban tsaya ba namike zuwa ksi mai ruwan kamar yadda ya umurta nakai masa, Zandawo nake jin Umma na cewa da zuwan ka an tare ka da zancen haihuwan wata can kai ba,a baka labarin maidadi na gidan ka ba, Nikan gaskiya dole asan abinyi don wanan shirun yai yawa haka a gidan nan gida kamar gidan GRA ba wani hayani a cikin sa, Sai lokacin jin yadda Umma ta ke sake zancen ta yasa shi yin yake kadan yace Umma itama idan lokaci yayi ai zata samu din lokacine kawai bai yi ba, Daga haka yai shegewan shi bandaki ya barta tana ci gaba da mita ita sai dai mutum yai taci yana kaiwa masa kullun ba wani karuwa a kai, Ina jin Umma don haka nai shigewa ta dakina ina dan kata kimtsa guri don samun hilin daki, Da dare nace zan shiga gidan mu na gaidasu kafin da safe naje gidan Kubura don ance mijin yaki yarda ta,dawo gida, Kamar ba zai amsa min ba can dai yace min sai kin dawo kawai, Banyi fushi ba jiki ba karfi nai sallama dasu Umma na tafi gidan mu don nai masu barka, Na dan dade gurin mama,saude nafito zuwa gurin Ummina bayan na gaida maman Aina, A dakin mun gaisa da Ummina shine nake fada mata irin sakani gaba da Umma tayi ita da kawar ta, Dariya Ummi tayi tana cewa kai Rabi ho ita yanzu har yaushe kike da zata wani matsa haka wai baki haihu ba har yanzu, Ta manta cewa koda akai auren ki bawai wani shekaru ne masu yawa akanki ba, Nace cikin nunadamuwa nikan Ummi har abin ya fara damuna a rai don yanzu nafara saka abin a raina wallahi, Ji nan Aisha ke dai ba jahila bace don gwargwado kin san addini yanzu, Mutum baiyiwa kanshi abinda Allah bai tashii mashi ba, Ki dinga dogaro da Allah domin shine mai bayarwa kuma,shine mai hanawa, Idan kin biyewa jahilcin Rabi kika cutarwa kanki ke kika,sani don ni ba ruwa na, Ban iya hauka irin na sarakuwar ki ba mutum yana girma yana kara cin kasa saboda jahilci, Shiru nayi ina kallon zanen tabarman da nake zaune akai ina sauraren Ummi din, Tai min nasiha mai kashe jiki nai sallama dasu nafito zuwa gida tare da masu sallama, Washegari da zai fita na roki zuwa gidan Kubura don na dibata da jaririyar ta,, Bai hanani ba sai adawo lafiyan da,yai min inda na,shirya cikin wasu atamfa zani da riga na,sa hijjab dina wanda ya sauka min har kusan kasa, Mashin na hau don gidan yana da nisa da uguwar mu don haka ban dade ba na isa gidan nasu, wanda zuwana nabiyu ke nan, Tundaga wajenake jin hayaniyan mata agidan wanda nakarasa ciki naga gidan dam da mata sai dai zan iya cewa bakin fuskane a gare mu don ba yan uwan mu bane, Na gaishesu na karasa dakin Kubura din tana zaune bakin gado rugumay da yarta wace tai kashi ta rasa yadda zatayi don tace min bata jin dadin jikin ta, Mun gaisa sama sama da ita take ce min cikin dakiya, na samu ruwa na,wankewa yarinyar jiki duk ta bata da kashi, Nafita na samo ruwan na karbi yar na wa ke mata tare da dan dauraye ta tsab nan naga kayan su da,suka bata anjibgesu a gurin famfon gidan, Bayan na mayar da yarinyar nakoma na,wanke kayan tsab inajin matan falon suna gulmana suna cewa wai kila ni yar uwar ta ce, Amma in bashiba ita watake taimakawa da za,a taimake ta idan taje gidan mutane tana masu kalkon raini wayo kamar diyar wani attajiri, Na gyara mata har dakinta nafita na,sayo turaren wuta na,sa a,dakin take dakin yafara kamshi jego kamar na kowa, Ni ce nai ta bata abin sha tana,sha har take ce min tai matukar jin dadin jikin ta ranan, Ina gida har bayan sallah la,asar sannan nai mata sallama na tafi gida, tana tayi min godiya, Ban shiga gida ba sai dana tafi gidan mu nai masu magana akan a samu wanda zai kula da kubura don tana bukatar tai mako, Tun a gurin maman Aina take ce min gaskiya ita bazata ba don da tai ciwo kwanaki ta tafi mijin bai kawo masu shayi sai dai wanda aka hada gaba daya na gida, Ummina ce take cewa idan malam ya dawo zata roke shi ta tafi dama tana gudun taje ne maman Aina tace tai mata cin layi, Nai masu sallama na tafi gida duk da yamma yayi na samu komai ba,ai min ba don mama Hafsi bata nan ta tafi tallan kayan gwanjo da take sarowa kasuwa don samu rufin asirin ta, Tun a,waje na aje hijjab dina na soma tara kayan wanke wanke nakuma yi shara tare da dora girkin dare, Allah ya taimake ni nagama komai da wuri kafin duhu yayi don tuwon masara nayi da miyar kuka, Nabawa kowa nashi na,debi ruwan wanka na watsa don naji sanyi a raina sai dai ziciyata fam take da tunanen halin da na riski Kubura acikin sa, Ina tunanen cewa watau dai haka rayuwan auren yake ko ina ko wani gida da kalar tasu matsalar rayuwa ke nan, Allah dai ya karawa ma,aurata daraja da rufin asiiri juna duniya da lahira, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA YAR UWA DON HAKKIN WASU NE, BA,A YAFE BA ,,, Haka Ummina ta dage taita kokari da Kubura da jaririyar ta wanda a,dan wanan zaman Ummi ta fahinci halin mijin su Kubura din,, Haka yasa ta dinga kwantar mata da hankali tana mata nasiha gwargwadon yadda duk uwa ya dace taiwa yar ta nasiha, akan zaman aure, Dafarkon zuwan Ummi sai ta lura cewa Kubura din tana wa yar ta wulakanci saboda laifin ubanta da ya shafe ta, Ummi ta shigo gidan sun dan gaisa da Kubura din yan min tina kadan sai yar jaririyar ta,soma kuka, Amma,sai Kubura tai biris da ita kamar bata jin may take yi, A,a gyara mana ki bata nono tasha Ummi take cewa Kubura din, Barta, tai tayi kawai Ummi idan ta gaji zatayi shiru ai, Ummi tace auzu billahi may yai zafi kuma haka kubura da zaki horar da yar malaukar Allah da bata san momai ba a,rayuwa,, Juyawa Ummi da yar jaririyar baya tayi yayin da jaririyar ke ta faman tsala ihu,, Jamila ce kishiyar Kubura taji ihun yai yawa ta leko dakin don duba,yarinyar, turus taja ta tsaya, don ganin Ummi a dakin, Gani yarinyar a hannun Ummi yasa ta cewa ai ina ce ba kowa adakin ne ta juya tana kallon Kubura wace ta kwanta ta,bada baya, Ta gaida Ummi wace ke kokarin ba wa yarinya ruwa ta,sha, Jamila take cewa kin gane ta mama bata son bawa yarinyar nan nono ko may zatayi dashi oho, Ummi ta juya gurin da Kubura take kwance ta basu baya take cewa a fusace, Tashi ki bata nono nace kamar ba,zata juyo ba sai can komay ta tuna sai ta dan dago daga kwancen a hankali, Idanuwan ta da,Ummi ta dan kalla taga sunyi wani irin hulu hulu da su alaman tayi kuka,, Mika mata yar Ummi tayi inda ta dan mike ta gyara mata rikon yar sai kawai ta kama zukar nono kamar mayunwaciya, Ganin yarinyar tana shan nono yasa kishiyar tata,juyawa tafita tabar dakin, Tana fita Kubura ta zare nonon daga bakin yarinyar ta kokari azata saman gado, Idanuwa a,waje alamar tsoro Ummi tace lafiyar ki kuwa,Kubura, Ta,dan dago kai ta kalli Ummi kadan ta danyi tsuki tare da juyawa, udanuwan ta sun kada sunyi jawur tace, Ummi ko wanda yai sanadin zuwan ta duniya bai damu da ita ba balle ni, Saboda tsabar kiyayya tun ranan dana haihu ina jinsa a falo yana tambayan may na haifa akace mai mace ce ya juya ya fita yana cewa wai mace a gidan nan kuma, Nan ta dan fara bawa Ummi labarin irin kuncin rayuwan da take a cikin gida Nura, Ummita ce cikin murya mai taushi bayan ta gama sauraren Kubura din, Kubura ke kin san may kika haifa ne da kike taya shi jahilci, Nasan ana zaluntar ki da,yawa Kubura amma kiyiwa Allah kada ki yarda ki fada a tarkon shedan ku aikata babban zunubi dake dashi, Ki rungumi yar ki da Allah ya,baki, ki gode mai da wanan kyautar da Alkah yai maki, Don darajan Annabi kada ki biyewa wanan zance har ki zalunci kanki da yar ki, Kiyi hakkuri kinji ki nuna mashi ke kina da tauhidi kin san Allah a,rayuwan ki don haka kikama yar ki kisota kamar yadda kema iyayyen ki suka so ki, Amma idan kema kina haka tankar kin ba da wani kafane natozarci wa yar ki, A take kubura ta barke da wani irin kuka mai ban tausayi tana cewa, Ummi tunda bai kaunar ta ni may zai sa naso ta ai gara ta mutu kowa ma ya huta, Ummi ta girgiza kan ta tace wa zai huta don ko ta mutu shi baiyi hasara kece kikai hasara, don shi yana da wasu diyan da yake gani, Ke kin taba ganin idan laifin wani ya,shafi wani har aiwa yarinya jaririya irin haka horo da yunwa, Haka zalika wallahi daga ke har shi alhakin wanan yarinyar ya isa Allah yaki saka maki tunda kin dau fan sa da kanki, Don haka ki tashi ki shayar da yarki ki barshi da Allah, Tsayen lokacin da yarinyar ke a jikin mahaifiyar ta tana zukar nono Ummi kuma tana ci gaba da yi mata nasiha, Tana kuma kallon yadda yarinyar ke zukan nono tare da sauke ajiyan zuciya irin ta wanda ya sha kuka,, Da uwar da diyar sai duk suka bata tausayi don haka Ummi ta sha alwashin sai ta gano may ke faruwa ne tsakanin ta da mijin, ****** ********** ****** Muna daki ni da Hamza yayin da,duk sauran yan gidan muna,jin haya niyar su a waje, Mukaji wani yaro yashigo yana sallama, ba,wanda ya karba mai sai mama dake can ta karshen gida, Yaron yagaishe su yake cewa ance idan yaro mai shago yana gida ana sallama dashi, Karasa can kofan ko zai ji yafito don ban sn may yake har wannan lokacin rana ya huduba a cikin daki, Idan kayi sallama basu fito ba sai kayi tafiyan ka ka fadawa wanda ke sallama yana barci, Mama hafsi ce ke cewa haba haba yaya ina fada maki wanan abin ba darajan ki bace wallahi, Lokacin kafin Umma tai magana ya mike daga inda yake kwance dama ni zobo nake kullawa ina zaune, Amma a zaton Umma a kwance muke muna wani abin na mata da miji ne, Fuskan shi alamar barci da gajiya yake tsirga miyau yana cewa yaron wake sallama dani ne, Yaron ya bashi amsa da cewa wani mutum ne a kofan gida, Bayan ya fita dan ajima kadan sai ga shi ya shigo gidan ya samay ni a waje na fito da kayan da nai amfani wanda sai lokacin Umma ta fahinci aikin da nakeyi a cikin dakin namu, Mama ya fuskan ta yake fafin mama yarki ce aka zo kira gidan malam sanusi wai zata duba masu wata mai ciki ce, Murna mamata fara yi tana cewa ikon Allah ashe har lokaci yayi da zamu fara cin amfanin ilimin mu, Maza shirya kije ki gani kin ji idan yafi karfin ki sai su tafi asibiti,, Daga idan Umm take take cewa amma kuwa da an fadi, yanzu tana yarinyar mace za,a shigo sallama mata wai yazo duba mai ciki To may amfani wayar da kan da aketa ma iyayye subar yara mata suyi ilimi, yanzu ba ga amfanin nata ilimin mun fara gani ba, Mata nawa ke wanan uguwar may yasa ba aneme su ba sai ita yar karama da ita, Kinga amfanin ilimin ke nan sai yaro komai kan kantarsa ya,zama babbba cikin manya,, Hand glove na dauka tare da,sauran abinda zan bukata wanda zai taimaka min, Sai faman yatsunan fuska Umma takeyi har ta kasa rufe baki tana cewa, Daukan magana yaron da bai ko san yadda ake daukan ciki ba wai shine zai duba mai haihu kai zamani ina zaka da mu,, Nafito ina saye da hijjab dina har kasa hannu na yana dauke da yar jaka nai masu sai na dawo, Badai girin girin ba tai mai don idan har an dauko da zafi zai kare kan mutum, Murmushi kawai nayi tare da hade zuciya saboda wanan mugun fatan da Umma take min ya kuma sa jikina yai sanyi ban jin courage akan akin da zan tafi yi, Innalillahi wa,inna,alaihim raj,un, Shine abindayazo min a,rai daidai lokacin da zan kada kafana a zauren gidan malam Sanusi tare da furta Allah kataimakeni ka rufa min asiri,, Nashiga gidan da,sallamana yayin da na hango mata a tsatsaye daga kofan wani daki wanda hakane ya tabbatar min da nan ne dakin mai cikin, Ku jaye nan ku bata guri ga malamar asibiti nan ta iso, Na,gaida matan da na samu a gurin cikin mutunci suna karba min ina shiga nake jin ana cewa, Wanan Yarinyan ce mai karban haihuwan wai ikon Allah shi malam karaman yarinya zai kira duba mai tsohon haihuwa, Kiyi nishi da karfi mana ki samu ki rabo dashi lafiya, Cikin murya na mai sanyi nace a,a mama ki barta na duba nagani kada ta yawaita nishin nan da yawa, Saurin juyuwa inda, nake tsaye mata biyun dake dakin sukayi, suna kallo na, Cikin mamaki amma kuma ba wace tai magana kowa a zuciyar ta take magana a rai, Na karasa gaban matan dake zaune duk tai zuba ina mata sannu ya jikin ta ce da sauki na juya gurin matan nace ku dan bamu guri dan Allah, Basu mussa ba, sukai waje kowa tana wani tabe bakin ta, sune ce wa matan waje zamuga ikon Allah, Sannu ya jikin ta amsa min da kyat na kara gab da ita nace kwanta mu gani ba mussu matar zata iya haihuwa na na duba naga haihuwa da saura sosai, Ga kuma zazzabin dayai mata yawa a jikin ta sosai shine suka gani suke cewa wai nakuda ne ya ta so,mata, Nadan leko tare da daga labule ina cewa, don Allah ko maigidan yana kusa ashe bai fita ba yace a razane gani, Nace mai, ya shigo ya,shigo dakin muka tsaya inda take zaune nace mashi ba haihuwa bane zazzabine ke damun ta idan ba an samu ya lafa ba nakudan bazai iya tasowa ba, Amma insha Allahu idan ya kwanta nan da kwana uku mai zuwa ma zata iya haihuwa da yardan Allah, Yace tau bakaji ba ai dama ni naga wanan wahalan yai yawa wallahi, Nan na rubuta mai alluran da zai sayo muna nai mata tare da kwayoyin da zata sha, Naiwa matar allura tare da bata kwayoyi nai mata sannu na fito sai bina da kallo matan gidan ke yi, Na juya gurin ta ina cewa, don Allah kada ki kara irin wanan nishin haka don zai iya jawo maki matsala a rayuwan ki, Nai masu sai anjima suna cewa ikon Allah ga haihuwa muna gani amma karamar yarinya tace muna wai wani zazzabine can, Ta samu barci sosai wanda ya nuna alluran ya karbe ta sosai ga abinci da nace a bata taci sai ta koshi, Tare muka fito da maigidan, yana min godiya tare da kokarin bani wani abu amma sai naki karba nace Allah dai ya bata lafiya, Nakara zuwa duban su Kubura da yar ta na samu tana barci wanda hakan ya nuna min ta samu, lafiya, Sai da,ba magani ko kwalba daya a gurin yarinyar, ba a saya mata komai ba na sa yaro lafiya, Nafita don ina da dan kudin dana hada zan ba uwar buki shina fita wani chemist na kwaso mata kwalabe har guda biyar, Ko da na dawo na samu ta tashi tana zaune tana shayar da yar ta nanuna mata yadda za,a bawa yayinyar magani, Godiya ta fara yi min sai kuma ta kasa saboda idanuwanta da suka ciko da hawaye, Ummi ta dauko abinci ta aje mata agaban ta tace takawo yarinyar ta sauko taci abinci,, Tana cin abincin muna hira da ita ni ranan har ta ban mamaki don ba daukan kai kamar yadda ta saba yi min a baya tana daukan kanta wani abu, can,, Ban jima a gidan ba nai masu sallama na tafi don ina gudun kada ranan suna a hanani fita don karamin aikin Ummane wanan, Aikin gonan shi ya hana Hamza yabi, Mansur su koma don za ai mai aikin karshe a gonan, Don haka yana garin za ai sunan Kubura wanda ban gane mashi ba sam bai kaunan yanzu nai zancen ta sai naga yana wani daure fuskan shi, Yana nuna min bai ra,ayin zancen ta wanda hakan yake matukar bani mamaki sosai, don haka yau ma da nake son tambayan shi cewa gobe suna ina son shiga gidan mu gurin aiki kafin a tafi gurin maihai huwa,, Ai kuwa ina tambayan shi kaman wanda yake jirace dani yai cikina da masifa sai da nai mamakin shi don ban taba zaton haka ba, Har yana cewa may kike a gare su ne wai da kike cewa sai kin shiga harkokin sune wai, Rana na farko dana fara bashi amsan maganan shi don zan iya cewa tun dawowan shi yanzu ya canza min halaiyar shi ba kamar yadda muke ada can baya ba dashi, Aganin ka ne ban komai a gare su amma ni nasan komai nake a gurin su tunda duk abinda ya faru dani gidan nan tare suke zuwa da Ummi, Ni ki ke bawa amsa haka yau Humaira to nace bazaki ba shi ke nan ko? Yama fice yabar min dakin ina zaune cikin bakin rai da mamaki don na,rasa ma, may zanyi,, Ranan haka muka kwana baram baram ba wanda ya kula dan uwan shi saboda kowa ya hau, Da safe na tashi nai aiyukana kamar yadda na saba nai wanka na koma dakina nai kwanciyana, Ina jin yan uwan shi suna tambayana ko har na,wuce ne gurin sunan gidan mu don sunga mutane suna shiga,, Wani irin bakin ciki ne naji ya kumay ni amma sai na dake kawai don ban da yadda zanyi tun da banice keda ikon kaina ba, Zuwa sha daya ya shigo gidan fuskan shi ba wani walwala a tare dashi,, Nasan yai hakane don kada naga daman shi nayi mai maganan fita zuwa gurin sunna, Kawai nima na fulanin ya taso min sai nai zuciya na share shi ban ko kawo zancen ba a raina balle a fili, Sallama mukaji daga kofa na wani mutum abinda yasashi fita don duba mai sallaman ke nan, Zuwa can sai gashi ya,daga labule yana cewa malam Sanusi yake son kije ki duba mar matan sa, Kamar ba zan tashi ba don yana fadi haka ya sake labulen dakin ya koma inda yake zaune yana karyawa, Dan jim nayi zaune wata zuciya na ci na don ji nake kamar nace sukai ta asibiti don rai na duk a bace yake, a lokacin, Sai kuma na tuna cewa ai ceton rai zan tafiyi don ba itace tai min laifi ba da zan ki dubata,, Nashirya tsab nafito zuwa gidan tare da mashi sai nadawo na yiwa su Asmau dake gida sallama su ma, Na samu matan gidan a tsaye cirko cirko don maigidan ya hana kowa shiga gurin matar tashi, Badon komai ba sai don bayanin da nai masu ranan na cewa, Idan mace tayi dan haihuwa da yawa ko ta fara manyan ta idan tazo haihuwa ba ,a,son ta yawaita nishi dayawa saboda yana haifar mata da illoli da yawa arayuwan ta, Zai iya jawo mata yoyon fitsari zai iya jawo mata wani sanadi wanda zai haifar mata da hyniar, da dai sauran abubuwa da dama, Wanan bayani yasa zuciyan malam sanusi a cikin tsoro da fargaba don haka ya hana kowa shiga gurin matar shi, Ina shiga dakin na hango matar can kuryan dakin ta tayi daidai da kafanta tana sauke nishi a hankali ga gumi ta hada sharkaf a fuskan ta saboda zafi ta kunkumay labule babu ko ventolation a dakin, Cikin gagawa na isa gurinta ina mata sannu da ya jikin,, Kanta kawai ta iya gyada min tare da cizon leben ta duk ta hada gumi, Da sauri na nufi gurin window din dakin na dan daga kadan don iska ya samu ya dan shigo muna, Na dan zo gurinta nace mata ko zata yarda na duba stage din da take don mu san abinyi, Na samu ta gyada mun kai da kyata nadan dubata inda naga ai gap take da haihuwa insha Allah don kiris ya saura mata, Nadan fara bata taimakon gagawa gurin tracing din kan yaron daidai,, Sai naga haihuwan yazo daidai lokaci inji Allah, nace mata a hankali ki tayani rokon Allah ya bamu sa,a ki haihu lafiya tace tau Aisha, Da ikon Allah nabata taimako daya dace nasamu Allah ya bamu sa,a ina addu,a tanayi take jikinta ya dauki wani irin bari, nace takara dan nisawa da karfi , Gabaki daya naji taimin wani irin nauyi nace tadai daure takara dan nisawa sai ko ga jariri ta sunbulo shi gabadaya har da uwar tafiyan sun fito tare , Jinayi nima jikina ya dauki bari don shine karo na farko dana karbi haihuwa ni kadai batare da manyan mu a gabana ba , Sai naji yaron ya dauki kuka dole na tsaya nadaure don na taimaka mata, Naji tawani nisa tana fadin alhamdullahi Aisha nagode nagode nace ki godewa Allah, Anty, Sannu sannu kinji Allah ya,raya muna Allah baki lafiya ke da danki tana nishi take cewa Ameen, Idanuwanta a lumshe ta koma daga bakin gado ta dan jingina, Na tambayeta inda reza yake don na taimakawa dan dake kwance saman leda yana ta tsala ihun neman agaji, Tace nakira Suwaiba a waje tazo tabani rezan nan nakwasa da sauri zuwa wajen dakin ina cewa ina suwaiba Nan nasamu matan gidan da suke tsaye cirko cirko sai murna sukeyi, hannuna yana saye da hand glove da dan jinin haihuwa sukabi hannun da kallo, Nace wace suwaiba don Allah ki zo kibani reza, A tare muka dawo dakin da mai sunan Suwaiba ta dauko min duk kayan da suka aje na haihuwan,, Na yanke cibin yaron nai mata komai yadda ya dace namikowa matar mai suna suwaiba, dan bayan na nade yaron a zanin da tabani, Saida naiwa itama uwar yadda ya dace nai mata sannan na tatara komai nafito dashi daga waje ina maigodiya ga Allah ubangiji subbahanahu wata,ala,, Nan nakama tsinkayo muryoyin matan dake waje suna cewa ikon Allah yanzu ashe yarinya karama haka har ta iya karba haihuwa kai amma gaskiya bature mugun mutum ,, Nabasu izinin su shigo su ganta inda na koma daga baya gurin da Suwaiba take rugumay da jariri nadan bude zanin ina kallon dan yaron dake lafe ajikin zani yana ajiyan zuciya idanuwan shi a rufe amma yana dan tsotson baki,, Wani dan abu naji a raina dama ace wanan yaron nawane da yau na,wuce gorin Umma, Nace a raina karo na farko nima Allah yabani haihuwa naga zuria ta, Nace a cikin murmushi tau sai anjiman ku zan tafi Allah ya raya muna, Sai dai a,samu zam, zam da dabino adan bashi, suka ce insha Allahu, Har kofan gida tsohuwar gidan da takaini tana min godiya da fatan gamawa da duniya lafiya, Shiko malam sanusi sai faman washe baki yake saboda farincin don gani suke nice nai dabaran da matarshi ta haihu ba,wani wahala, ****** ********** ****** Wanka nashiga na tsabtace jikina nafito nai alwala don lokacin sallah ya gabato, ko, Mama Hafsi ce da taga takalmana a kofa ta leko tana ce min a,a dama kina gidan nan Aisha nace eh mama sai dai yanzu na shigo don na dan shiga nan gidan malam sanusi karban haihuwa ne, Tau tau madallah ince dai an sauka lafiya ko ? Murmushi nayi nace eh mama ta haihu tunda zu lafiya cikin ikon Allah, Da sauri mama tace kaji ikon Allah ko yanzu kece kikai karban haihuwan da kan ki, Murmushi kawai naiwa mama ba tare da na bata amsa ba umma wace ke fitowa daga bandaki take cewa ikon Allah ashe an sauka din , Cikin zolaya mama tace ance maki sarakuwae tawa ta wasa ce hmmm ai sai ki bari a yabe kuko ? Sai duk aka tuntsire da dariya a tare mama tana ta faman yaba kokarina, Hamza ne yashigo gida hannun shi dauke da leda mai zanen yellow da baki yake cewa su Umma barka da gida, Yana kokarin miko min leda ita ko Umma idanuwan ta kyam a ledan da yake miko min tare da kara miko min wasu kudi zasu kai dubu biyu, Nakarba da mamaki sai yake cewa malam sanusi ne yace nabaki kuma ya hada ni da Allah kada mu mayar mai wai ya baki ne saboda Allah, Wanan kuma wai kayan sayine ki jika makoshin ki dashi kiji sanyi, Wani kunya naji sai nace a hankali nagode juyawa umma tayi zuwa yin alwala tabar gurin, Har ya juya,zai tafi sai kuma ya juyo yana ce min idan baki gajiba kina iya shiga gidan sunan yanzu, Haushi takaici duk ya rufe ni suna a gidan mu ne zan shiga da karfe biyun rana bayan gani nan baki da hanci, Nanu su Umma da ledan ina cewa mama ga kayan nan sai a bawa kowa ya sha ko,? Mama takarba tana cewa Allah dai ya baki naki kema robon mu dauka har mu aika, Na kirga kudin dubu uku nr cif na bude baki don ganin suyi yawa tare da juyawa gurin mama ina cewa mama har fa dubu uku ne kudin, Kodai zan rage na mayar mai da kudin ne don suyi yawa wallahi, An ma kinji abinda mijinki yace yace ya rantse ko kin mayar bazai karba , Nace cikin jin kunya na gode na cire dubu daya nabawa su Umma su raba ita da mama din, Kamar nai fushi naki zuwa gurin sunan sai dai, na daure kawai na tafi don gudun zargin rashin shiga na, Aiko na,samu an kwasa za,a tafi gidan su Kubura a gagauce na shiga gurin Ummina ta hauni da fadan rashin zuwa da,wuri da banyi ba, Naimata bayani yadda duk mukayi tave to al,amarin mazane sai hakkuri don haka idan dai kin san bai barki ba ki koma gida kawai ban son fitina, Nace a maraice da idanuwa da suka kawo kwalla shi ya barni da kan shi ai yanzu din, Jin ana kirana,waje nazo mu dauki kayan da za,a tafi gidan Kubura dasu yasa nabar dakin da sauri na,samu yan uwana muka kwasa sai gidan maijego tare da kayan arziki niki niki, irin su masa, guguru, dibbila, su man gyada shimkafa, maggi kifi albasa, da sauran su,, Mun samu gidan sunan da yan uwan miji Kubura makil sai ita da kawayen ta duk da basu da yawa a dakin ta, Nan ta fara muna korafin rashin zuwan wasun mu mu zauna da ita take cewa tundai ke yar Agwai na zaci ko banga kowa ba ke zanganki kinzo zama dani, Murmushi nayi kawai ina bata hakkuri din banda abincewa saboda nima gaskiya haka na so nai mata nazo na zauna da ita tun safe sai hakan bai samu ba, Nan aka,shiga sha,anin suna yarinya,ansa mata,suna Fatima wai sunan yar maigidan ke nan, Ashe anty Hindatu tana gidan ban sani ba,sai da ta leko dakkin tana nemana nan muka fita muna hiran yaushe rabo da ita, Can take ce min wai yaya alkar mu da Kubura yake sai nake fada mata yadda muke, Tace mijin ta dan iska ne baida mutunci saida iyayyen su sukai mai tas yau da safe wai baiyi murnan da haihuwan ya mace da tayi mashi ba, Kin san ance wanzan bai so a jikin sa yana gudun a rama abinda yakewa diyan mutane a yar shi, Aiko ita yar uwar taki ance cafkeshi tayi don yaso ya yaudare ta ya gudu da farko da yake ita yar duniya ce itama sai ta kamashi, A raina nace ko ina kuma suka samu wanan labarin haka kai mutane a kwai tsegumi, Take ce min ai kila bata,san halin dan iska bane har ta yarda ya aure, ta, Dan cacane fa kuma ga kalwanci da yakewa manyan gari yana daukar masu mata ana,bashi kudi da manyan motoci, Da sauri nace Subbahanallahi shi Alhaji Nura din tace shi mana ai bata rasa sanin halin shi ita, Ko ita uwargidan nashi yar uwar namu ai don tana da dan nakasa aka hada su dashi hakkuri take da dan iska sam baida hali baida mutunci, ko kadan, Itace ma takai karan shi yau da safe wai yaki yiwa maijegon da yarta sayayyan komai na suna, Takr naji tausayin Kubura ya kamani har cikin raina na tausaya mata matuka, Nace mata cikin muryan tausyi kin ko san da itace zata auri yaya Hamza ana gobe a saka ta a lalai taki yarda tasa baba kuka ganin baba yana kuka nace ni a daura dani, Ta tambaya a gagauce da cewa ke ki bari dan Allah dai Aisha ? Nan na dan bata labarin yadda abin ya kaya tace kinga ikon Allah ko, Gashi tayi zaben tumun dare tafada gurin dan caca kuma kalwani,,, Ina muna fatan fara azumi lafiya Allah ya hada mu da rahamomin sa dake cikin wanan wata mai albarka, Sai dai muyi hakkuri da juna don idan azumi ya kama ba kullun ne zaku dinga jina ba sai a hankali, zandinga post idan na samu time insha Allahu, Masu fitar min da novel waje zuwa wani group na bar su da Allah ya isar min da isar sa,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA,, SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE Wanan karban haihuwa danayi a cikin shiyan mu shi ya taimaka min sunana ya samu daukuwa ga mutanen uguwar mu har suka fahinci na yi karatin health nasan wani abu, Yanzu mutane suna dan shigowa guri na don neman taimako, Yaran su dama su kan su matan sai suke ganin sun samu hanyan sauki ba sai sunje asibiti ba, Idan naga abin yafi karfina,saina turasu su tafi asibiti don ban yarda nai kasadan dubu ciwon da,bazan iya treating din sa ba na jawa kaina matsala, Don duk bakin ciki da hassadan su Umma ya kai min ko ina yanzu sosai ban jin dadin irin yadda Umma take yawan, nuna min hassada akan wanan ci gaban da na,samu, Don duk wace tai sallama da zaran Umma ta fahinci cewa mace tazo ne don gani na yanzu zata bata ran ta ta,shiga yadda magana ke nan a tsakar gida kamar yarinya karama, Sannu sanu har ankai ga cire amfanin gona yanzu mutane sai aikin gona ake ko ina ana faman cire amfanin da,aka saka,a gona, duk da dai daman ta bana ta dan zo wa mutane da yar gardama,don duk wanda bai yi shuka,da wuri ba ya samu dan matsalan fari na ruwa da,akayi a karshen damana, Shi ya kawo lalacewan gonakin mutane sai ba a,samu anfanin gona wadattace ba, sosai, Duk da wanan korafin na jama a mu dai zamu iya cewa Alhamdullahi don gaskiya mun samu ci gaba sosai don shi kan Hamza ya samu amfanin gona mazu yawa, a gonan shi har ma yadda bai taba tsan mani ba, Ranan da yazo yana zancen yadda ya samu albarkan gona kowa na murna da farin ciki, a gidan sai mama Hafsi kawai ta kada baki tace, Gaskiya hannun Aisha yana da kyau don a gaskiya da badon taba da bazamu san yadda zamuyi ba har ma da ace a wajen wani aka karbi kudin nan ba lalai bane a samu amfani mai yalwa irin haka don wani hannun ribas gare shi, Koda anyi amfani da abin shi sai kaga komai na mutum ya tafi ya lalace kamar yadda gara take cinye duk abinda yai karo dashi, Azatona Umma zata ji dadin abinda mama ta fadi a kai na , Amma abin mamaki sai naga daga ita har dan ta kamar ba wanda yaji dadin zancen don ita umma cewa tayi Wanan ai ba yin wani bane hannun wanda ya dafa abin ne kawai da albarka, Shi ko Hamza ji nayi yace hmmm mama ke nan ai wanan abin ba haka yake ba, Zataci gaba da magana amma sai Umma ta saka wa mama waigi da cewa don Allah hafsi kibar wanan zance Ina wanan taimako ne tsakanin mata da miji bawai abin wani zance bane, Mikewa Hamza yayi don yasan cewa yanzu uwayen nashi suna iya kaurewa,akan wanan zance,, Duk da banji dadi ba yadda Umma ta zage tana wa yar uwar ta akan dan maganan da baikai ya kawo ba, don kawai ta yaba zance na, ta rufe ido tai mata tas tadai shige daki ta bar ta nan, ****** ********** ****** Alhamdullahi don komai ya kammala ancire albarkan gona gashi kuma Hamza ya kammala karatun shi lafiya yanzu yana zaune a gida suna jiran sakamako, Wanan dalili yasa ya fara sana,a haikan wanda cikin yarda Allah sai abin nasa ya fara bunkasa, mai, Sannu sannu ya fara shiga kauyuka ya na,sayo hatsi yana kawowa birni ya na,sayar wa, Inda ni kuma ina dan buga bugana a gida ina samun dan abin rufin asiri ga yar sana,ata, Dan maganin ciwon kai maleria, ulcer, pain relief da,sauran yan magani duk ana shigowa gurina sayen su, don haka na,rage wasu yan bukatuna, Ganin yana samu akai akai, yasa mutane ganin ai Hamza ya dan samu ci gaba a irin kudin mutanen kauye, Nidai tunda aka cire amfanin, gona bai min zancen kudin da ya karba a guri na ba balle nayi zance canza sabon fridge da nake son yi ba, Haka yasani dan kokarin kukutawa gurin tara dan kudina don na,sai wani sbon fridge din don ina da niyan yin hakan, Da kyat da taimakon Allah da mutanen arzikina na sayo sabon fridge dina LG mai saurin yin sayi da kuma kankara, Aikuwa sayen wanan fridge din ya kara jawo min bakin jina sai umma take gani dan tane ya bani wanan kudin na,sayo fridge din, Ranan da,nake kwana biyar da,sayen fridge din sana,an tawa naji Umma ta tutse dan ta yana ta mata rantsuwar kan cewa wallahi ba shine ya saya min ba asailima bai san da cewa zan sayi fridge shi, Amma ina sam Umma bata yarda ba,sai cewa take gasu da lalurar auren Asmau a gaban su, amma shine zai kwashi kudi don tsoron bacin raina ya sayo min fridge dashi, Idan bashi ya saya min ba wa nake dashi da zai sayo min wanan dalele fridge haka, Ya marairai ce murya yana cewa wallahi Umma bani na saya mata ba ki yarda yadda kika gan shi nima haka nagan shi a gidan nan, Amma sam Umma bata yarda da rantsuwar shi ba sai fada take zazaga mashi tace sai fa ya mayar ko ya,sayowa Asma,u abubuwan da ta bukata ya sayo wa yar ta mai shirin aure, Don haka ita yanzu tunda ta fahinci cewa duk neman kudin shi a kaina yake karewa zata dauki mataki a kai, Daga inda mama take tsaye tai min nuni da na kyale kada na tanka, don haka ma nai shigewa na daki kawai, Can naji yafito yana cewa zata iya bincikawa taji in har shi yasaya min ta dauki matakin da tace din, Nan ya shigo daki rai a bace ban kula shi naji har zai fita ya juyo yana ce min, Humaira kina son ki hadani fada da mahaifiyata a gidan don ta kasa fahintar cewa bani ne nake saya maki wa yan nan abubuwan ba, Duk da nasan cewa kokarin ki kike kina sayan abubuwan ki amma ya kamata ki san yadda kike abubuwan ki don gudun jefa zargi a zuciyar umma, Mamakin zancen shine ya kamani a zuciyana kwarai da gaske, don ban san may ma zan ce mai ba sai binshi da kallon mamaki danayi a lokacin da yake fita daga dakin , Zuwa rana Zarah ta,shigo gidan inda tazo kamar yadda take zuwa kwana bibiyu don duba mahaifiyar ta da yan uwan ta, Nan suka gaisa ina jin su harda mama wace tafito daga dakin ta don ranan bata fita ba tana gida, Don yanzu har da,su turamayn zanuwa take dan daukowa ta sayar wa mata bashi , Nafito muka gaisa da zarah wace ke zaune saman kujera dan tsuguno tana shan raken da ta saya a hanya da zata zo, Na juya zan tafi naji tana cewa Aisha ashe kin samu dauko fridge din dazun Karimay ta shigo take ce muna kin karasa biyan ta kudin har kin dauka, Amma gaskiya kinyi kokari dan nai maki murna kinga shawaran dana baki yayi don ita karimay bata da matsala indai kana bata kudi ko kadan kadan ne sai ta tara ma har lokacinda ka gama, Balle ke ta yaba kwarai da yadda kikai mata biyan kudin tace duk kika dan samu kike kai mata ko baida yawa, Murmushi kawai nayi na wuce zuwa aikina, don nasan zata fadawa mahaifiyarta yadda na samu na sai fridge din da takewa wa bakin ciki duk kwanakin nan, Aiko banko yi nisa ba naji Umma na cewa ta,saye ko aka sai mata ai duk na gane wayon yaran nan don sun mayar dani yar kauye wai nice zasuyiwa wayau ko, Zarah tace haba Umma kamar yaya yanzu fa ta kai wata hudu tana kokarin sayen fridge din nan nice ma nasa yaya taiwa kaunar ta Karimay magana a gurin ta ta,saya, Yanzu ke Umma hakan ba dadin ki bane yau ace sarakuwar ki matar dan ki tasai abin karuwa a gidan ku, Wallahi baki ga yadda ake yabon ku ba kan wanan abin , Baki Umma ta tabe tana cewa, ke dallah matsa min can ke may kika sani ke , Ina zata samu kudin sayen wanan fridge in ba shi yabata ba ta,saye don sun raina wa mutane da hankali, Yanzu in ba itaba ba mai cin abin yaron nan sai dai kagan ta tana yadda take so, Ina duke na fara wanke tukunya,wani yaro ya shigo yana cewa ance a bani maganin ciwon kai dana ulcer, Tace ummu jifa mai sanan chemist za ace wai ina ya samu kudi, haka ga karban haihuwa da take dan yi, don Alkah Umna kibar wanan zargin wallahi ita ce ta,sai abinta da kanta, Umma dai bawai ta yarda da bayanin zarah bane sai ma fita zancen da tayi, Da yamma sai ga mama Sa,a wai tashigo ganin fridge da taji ana na saye yana kankara , Tana gani suka koma daki da Umma sai abinda suka rage a gurin zagina da kuma dan ta Wai inba aure ya kara ba Umma bazata taba gane kan dan taba don nariga na asirce mata shine, sai abinda nace, ****** ********* ****** Wani abokin shi yabashi shawaran yafara sana,an kai hatsin shi kurmi ya gani don akwai ci sosai, Sana,an mahaifin shi ke nan shiga kasan kurmi dama don haka ya shawarci Umma Da farko taso takiya mashi amma daga baya sai ta yarda ta barshi inda ya dan kara kulla jarin shi ya,saro kaya masu yawa ya fara zuwa lagos kai wa, Sannu sannu tafiya tafa kyau dan idan zai dawo sai yadan sayo yan abubuwan da za,a samu karuwa dashi a nan arewa, ga kuma tsaraba da yakan dan sayo muna mu ma, Ai kuwa take abin nashi ya fara bunkasa don ya kara bude idon shi sosai a harkan business din yanzu, Shine Kano shine har kasar Niger yake zuwa dauko kaya yanzu, Ya sai mashin irin na matasa idan yana gari ita yake hawa zuwa yawo ga suturu wanda ke nuna mutum yai lafiya, Nidai saukina dashi shine yabarni ina yan sana,ata bai matsa min akan harkokina kamar yadda Umma takan so yai min, Diyar mama sa,a data fito daga gidan mijinta takan yawan shigowa gidan mu idan Hamza yana gari da,safe ko da yamma, Zatai wanka tashigo takan dan yi wasan kaunar miji dani wai ita kaunar Hamza ce itama, Amna yanzu sai naga idan ta shigo zatai wani fuske min ko ina mata wasa irin yadda muka saba sai naji ta mayar min da mai zafi, Mama Hafsi ce ta jiyo a gurin tallan ta cewa wai Hamza ne yake neman ta yanzu, Ranan da mama take fada min na so na tayar da hankalina amma sau ta kwantar min da hankali da cewa, Akan may zaki daga hankalinki haka Aisha bar su ai yanzu za,aji kan su akan wanan hadin da suke son yi, Don Allah ba azzalumin kowa bane ba sunce wai sakin wawa bane basu san cewa sakin mai wayyo bane, A gaskiya bayanin mama bai kwantar min da hankali ba don sai naga ai cin amana ne wanan, Rasa wace za a aura mashi sai Sadiya wace tasan komai na gidan mu tasan ciki da baidin komai namu, Gidan mamana Rahana naje da rana ina kuka ina fada mata abinda mama ta fada min, Saida na gama fada mata sai naji tanisa tace amma kuwa Rabi ba mutumiyar arziki bace ashe,? Yanzu ita sakaiyan da zata bimu dashi ke nan duk irin wanan halarcin da mukai mata, Nace cikin kuka mama ni inda ma,watace ba wai Sadiya diyar mama Sa,a ba da suke kamar tip da taya da Umma, Shiru mamana tayi tana kada kai tace duk abinda tayi ita da Allah ai don dai in bakici amanan su ba sai Allah ya fitar maki da amanan ki, Don irin wanan aure ba,a kai ko ina yake watsewa saboda badon Allah akayi shi ba, Yanzu abinda nake son ki da shi, shine ki kwantar da hankalin ki Aisha kada ki tayar da hankalinki, Don kinga shi aure nufin Allah ne matar mutum kabarin sa, Idan Allah yayi akwai aure a tsakanin su ba makawa sai sunyi shi don haka kada ki bari aji komai daga gurin ki, Ki koma dakinki ki kwantar da hankalinki kici gaba dayin komai irin yadda kika saba, Yanzu ya kamata ki kara zage damtsenki gurin kokarin kyautata mashi ke har ma da sauran jama,an gidan, Kuma ai shi Hamza din bai nuna maki wani alaman cewa suna tare da ita yarinyar ba ko ya nuna maki hakan ne,? Na hade miyau da kyat tare da girgiza kaina alaman a,a tace to kin gani idan ma hakane aiki barsu kawai mu ga iya gudun su, Nace cikin sanyi murya da to mama insha Allahu zan yi yadda kikace din , Tace madallah yar albarka, hakanake so dake don kinga ba yadda zamuyi saboda shi dama namiji ne mijin mace hudu, Dole ne a matsayinki na matar shi ta farko sai kinyi hakkuri da abubuwan rayuwa da dama don ke ce uwargida duk wani auren da zai kara ko diyar waye kece dai matar shi tafarko da kowa ya sani yakuma sanki dashi,, Na dan kai wani lokaci a tare da mamana har kishiyar mama din ta gama girki takawo min amma sai na kasa cin koda cibi uku saboda damuwan da nake dashi, Naima mamana sallama bayan takara kwantar min da hankali tare da min tuni cewa na dage da yin addu,a tare da sadaka don Allah ya bani rinjaye akan koma wace ce zata shigo min, Tace duk safe na ambaci sunan Hamza da ita nace wallahu galibun Hamza da Sadiya sai na,shafa a fuska na, Na kuma dage da fadan Subbahanallahi wallahamdullahi, Allahu akbar,,, ****** ********* ****** Ina zaune a bakin gado yana tsaye yafito wanka yasa tufafi a jikin shi yana fesa turare, Sai binshi da kallon mamaki nake don yanzu baka raba shi da turare ko yaushe ga kokarin wanke mashin din shi ko yaushe fes zakagan shi tsab dashi , Ya juyo sai muka hada ido dashi tsarguwa yayi saboda irin kallon da nake mai, Sai naga yadan murmusa min yace yaya dai nayi kyau ko, na dan tabe baki tare da kawar da kaina daga kalon shi da nakeyi, Dawowa yayi ya zauna a bakin gadon kusa dani yana cewa naga kamar kina cikin damuwa mana Aisha ban son inganki kina min kallon rashin yardan nan da kike min yanzu, Nace kai dai ke min kallon haka amma ni mai kai min da zan kama maka kallon rashin yadda gani nayi kawai kayi kyau shine nake kallon ka, Murmushi yayi tare da kama min hannuna ya matse a cikin nashi yana cewa aiko na gode tunda na burge ki dama ke nake son na burge ai, Wai ana sallama da Hamza inji wata a waje murya wani almajiri ne mai bara da robar shi mai marfi, Cikin dan kamay kamay ya mike yana cewa kai ji min yaro wai wata kodai wani bari naga ko waye ke min sallama ya mike yafita yana dan gyara hannun rigar sa, Namike muka fito tare nacewa yaron kawo robanka na baka abinci kaji, Bai fitaba don yana gudun kada yaron ya fada min komai sai wani dan kamay kamay yake wai yana duban mashin din shi, Kusan a tare suka fita gidan da yaron da ya,saka a gaba zuwa waje, Bai dawo gidan ba,sai yamma naji karan mashin din shi wanda na haddace sautin karan mashin din a a kunnuwa na kamar yadda haka yake al,adan mata duk inda mace taji karan abin hawan mijin ta zata iya sheda shi, Maimakon naga Hamza ya shigo sai Sadiya ce naga ta shigo gidan hannun ta dauke da leda baki mai giwa, Umma wace take hango shigowan Sadiya tun daga nesa naji tana cewa lale lale sannun ku da zuwa har andawo ashe, sannun ku da hanya, Na juya don naga wace Umma takewa wanan taron cikin raha haka banga kowa ba sai sadiya, Ledan dake hannun ta tanufi Umma dashi tana fadin ga tsaraban mutanen Alairu sun ce a kawo maku, Ina mamaki Alairu kuma Sadiya ta tafi shine Umma take mata wanan sannun da zuwan, Banyi wa Sadiya din magana ba irin yadda na saba yi mata don ganin yadda take min ko yanzu, da ta shigo gidan batai min magana ba don haka nima na,samu corrauge din kyale ta, kawai, Hamza ne yai karshen shigowa gidan naji Umma tana fadin Babana ashe harkun dawo ne sannun ku da hanya ya kuka barsu can, Gurin da nake zaune ina kullah kan karan yara da nake yi yanzu yadan duba don yaga ko ya zanyi amma sai kawai na basar kamar ban fahinci komai ba, Amma kuma sai dai can kasan zuciya ta ji nake gaba daya kamar zuyata zatsage ta fito don wani irin kishine ya turnuke ni lokaci daya, Ban mai sannu da zuwa ba tunda bai fada min zai tafi wani guri ba tun karfe tara da rabi na safe ya fita sai wanan lokacin da ya dawo,, Mutum ya dawo daga unguwa, baki ko tariyan sa da ruwan sha Aisha, don kawai kishin banza da zaki sakawa kan ki, Muryan Umma ce take fadin haka ani, don ganin yadda nayi ko in kula da zancen su, Muryan Sadiya ce karshe take cewa kishi may zataiwa kishi ni da zan shigo naita haiho mata yara tana goyawa, Kishin ta ai ba zai sa a fasa abinda akayi niyar yi ba don haka dama kin sauwaka wa rayuwan ki, Kamar nai shiru amma ina zuciya bazata bari nai shiru ba a yau, Na daga kai ina kallon Sadiya nace amay zanyi kishi anan wani bokon abune ban sani ba akanki ko wata sabuwar Sadiya ce aka canza ba wanan din dai dana sani ba, Na girgiza kaina ina cewa ai da ki mayar da yukanki a kube indon ta Aisha ce mai sauki ne, anan, idan ban goya maki diya ba ai wadda ta kawo ki gidan ta goya maki tunda dama don shi aka shigo dake, gida, Ina kaiwa nan na dauki kayan roban kankarana dana kulla zuwa cikin daki don in saka a fridge, Ina jin yadda Umma ta ayayyako min tana masifa wai ko naki ko naso sai Sadiya yar ta tashigo gidan nan, Simi simi Hamza ya shigo dakin cikin tsarguwa ina duke a bakin fridge yake cewa ke kada naji kin kara tankawa kowa akan zancen nan gidan nan, Ban bashi amsa ba don sai yanzu zai min munafuncin su na maza a daki, Shigowa Mama Hafsi ne ya dakatar da duk wani cin mutunci da rainin wayyon da aka kasa min a tire a na kwasa, da akeyi a gidan, Simi simi Sadiya taiwa Umma sallama tana cewa zata,shiga gida don bata shiga ba da suka dawo, ko kallon inda take mama batayi bq balle ta san Allah yai ruwan ta, Dakin nafito nabarshi ciki, don idan na tsaya a lokacin zan iya fashewa don wani irim haushi da takaicin shi ne ya kamani, Don haka kawai sai naga fita daga dakin a lokacin shi yafi min alheri a raina, Ina fita yafurzo wani iska a abakin shi tare da dan sake fuci mai nuna neman relief of mind daga mai yin sa, Don kada na zauna sai na tsiri yin aiyuka don ya,kawar min da damuwa raina,, Tun wannan lokacin mun dauki lokaci mai dan tsawon kowa tashi ke fisheshi a tsakanin mu don shi yana ganin cewa ya tsaya yai min bayani gazawan maza ne a,gare shi, don haka naje duk abinda zanyi nayi, Wai wai muke ji ga mutane cewa an kusa daurin auren amma su basu fada muna ba, Nima ban shiga shirgin kowa a gidan don ina gudun bakar maganan da suke yaba min wai da sunan wasa, Don haka na kiyayye wa kaina daga haka don wani magana sai yai kokarin hanaka barci, ko walwala,, Ganin yadda na kama kaina ban san may Hamza ya gani ba ranan sai gashi yana min magana da kan shi, Humaira idan kin ce hardani zaki zarga a cikin al,amarin wanan auren da Umma ke son hadawa Humaira baki min aldalciba idan kika ce hardani zaki hada a cikin zancen auren nan, Nidai kin san da hankalina bazan tafi gurin wanan yarinyar wai da,sunan so wanan zancen Ummane kinga kuma ban isa na mussa mata maganan ta ba, Abin mata da miji nan yai ta min dadin baki yana kushe Sadiya a,gabana har naji na yarda dashi hankalina yafan kwanta kadan na daina fushi dashi, Sai kuma Umma ta dawo tana jin haushin ganin mun shirya a tsakanin mudashi, Nan ta fara azalzala kan ya kamata ya fara gyaran daki saboda a samu a daura auren nan kafin lokacin azumi yazo, Ban damu ba don yadda nake samun yana nuna min kulawa yakuma sa wa ita sadiya din waigin shigowa har cikin gidan da take tana muna fitsara nida mama, Don mahaifiyarta ta fada mata mama hafsi bata son ta ko kasheta tana iya yi, Ita kuma sai tasha alwashi sa kafan wando guda ita da mama a gidan nan, Nasan badon komai yakarawa mama bakinjinin hakaba,sai don tana tare dani, Ni tun farko nasan Sadiya don kawar Kubura ce sosai kamar tip da taya suke kuma har sukai auren suna tare suna kawancen su, Don haka duk wani iskancinta a tafin hanni na yake duk da ba wai ina kula su bane, don sun girmay min sosai ina kasa gare su, ga,shekaru, ****** ********** ****** Ranan wata alhamis saiga masu aiki sun shigo wai suna duban dakin dake kusa dana, Umma zasu gyara, shi alaman a nan amarya zata zauna ke nan, Tun ranan suka fara aiki gyara duk da dai kwaskwarimane akaiwa ginan, sai sabon fenti da aka shafa tare da muna dakin girki, agidan, Bayan duk shekaruna a gidan ruwa da iska dama da rani a wajen Allah nake girki na bako dan rufin kwano, Tunda aka fara aikin nan yana can ya tafi Onisha kai kayan masarufi kamar yadda sukeyi , Saida yai kwana tara can yadawo a lokacin angama duk wani aikin gyaran gida baya garin shi,, Zakace ai bashine ya bada kudi ai mai aikin ba irin yadda yai wani fuskewa bai damu da gyaran da akayi ba don ko kallon aikin baiyi ba, Kamar bashi ya,bada kudin da akai komai ba niko ga nawa wautan sai naji dadin haka don ko banza baima dai damu da amaryan ba, Yadda nake mata kallon banza mara tarbiya honko shima sai nake zaton haka yake mata kallon, Kwana biyu da dawowan shi, ranan da safe bayan nakai mai ruwa yai wanaka sai na fito waje don na kwashe kayan abinci zugurin wanke wanke, na hada nai komai na koma daga cikin daki don najira har ya fita,sai na dawo na karasa aiyukana, Ina shiga na samu yayi kwalliya sosai, ya,sa,wasu shaddan shi sabbin dinki dayayi sky color dinkin yai matukar karban jikin shi, Yana tsaye yana gyara hular da zai saka a kanshi,, Na kalle shi sai na ga kwaliyan tashi tai min kyau sosai don shi dama mutum ne mai cikar halitta gashi da tsabta da iya kwalliya mai fitar mai da kwarjinin sa duk dai tallaka ne matashi mai farfadowa a lokacin, A hankali cikin natsuwa nakai zaune daga bakin gadona, Ban san lokacin da bakina ya bude nake tambayan shi, Yaushe ne wai auren naka duk da dai nasan bawai lalaine kafada min ba, Murmushi naji yayi batare daya juyo ya kalleni ba yaci gaba da kokarin saka takalma akafan shi, Sai da ya,sa takalman ya juyo yake ce min may sanin zai kara ki dashi indan an fada maki, ko tsoro kike ji ne ? Na dan murde fuska tare da tabe baki ina cewa ba wai tsoro ko wani abu nake ji ina,dai son sani ne kada ai min girshi, Shiru yayi bai ce min komai ba yake cewa ni zan fita zan aiko da kayan miya don akwai inda nake son zuwa, Daga haka yafita daga dakin inda nabishi da kallo ba tare da na,samu ce mai adawo lafiya ba, Inda ya fita nan ya barni zaune ina tunane ni kadai a dakin ban san yadda,akayi ba,sai ji nayi a zuciya ta tana zargin wanan shigar da naga yayi gurin Sadiya zai tafi, A,take tausayin kaina ya kamani, don sai nake gani kamar duk nice najawa kaina wanan matsalar rayuwa don ni da kaina nace wa Baba Mudi ya,aura min Hamza don kawai na tausayawa halin da Baba yake a ciki a lokacin,,, Yanzu ga irin sakaiyan da nake samu daga gurin mahaifiyar wanda naiwa wanan mutuncin ba ragowa ko sanaiyar halarci a tsakani na da Umma ko kadan, Wanda wanan halin har ya kai ga sanadiyar diyan ta sun fara nuna min tsana da kiyayya akan wai Hamza zai auri diyar kawar mahaifiyar su, Don haka suke nuna min cewa ni barece banda, wani alaka ko farin jini a gurin su, Gurin Mama Hafsi ne kawai nake dan samun sauki sai ko Ibrahim wanda bai yadda, da akidar ace wai a hade min kai wai ni banda kirki, banda mutunci, ina wa uwar su rashin kirki, da rashin mutunci ina,son shiga tsakanin dan uwansu da mahaifiyar su, Wanan dalilan da,kullun Umma take fada masu a kai a yasa suke matukar jin haushina da zamana tare da,dan uwan su, Sai suke ganin idan ya kara aure kuma ya auri Sadiya yar gida Umma zata samu sa,ida a gurin sabuwar matar tashi, Nasa wa kaina damuwa sosai da farko amma daga baya sai kawai na hakkure da duk wani yawan cin fuska da,suke kokarin yi min na bar komai ga Allah, Kamar yadda,basu damu da al,amarina ;a nima yanzu iyakata dasu gaisuwa ce kawai irin ta addinin musulunci, Haka yasa suka kara sa min tsana da kahon zuka sai magana,suke sake min cewa, Yanzu za a auro ta,kwarai wace ta dace da yayan su yar gaye mai mutunci yar gidan mutunci, Su ai sai yanzu suka san cewa dan uwan su zaiyi aure, irin na sa,o,in shi shima zai kece raini a cikin sa,an shi, Asamau kuwa har da karawa da fadan ai arziki zai sauko masu a gida don yayan su zaiyi auren gwadawa duniya don sai yanzu ya dace da mace mai siffan mata ta kwarai, Ba yar raino ba auren wahala shi duk abinda ya samo kokari ake a kwashe a kai gida, gurin iyayye a boye, Kwana biyu a fito dashi ana heleken cewa wai ansaya ne da kudin sana an da ko, tsintsiya ba,a iya saya dashi, Kai Allah sarki naji maganganu na fitsara wanda ma bazan iya fadin su ba , Nakan shiga daki nayi kuka ni kadai sai nagaji babu wanda zai bani hakkuri,, Bayan ya fita daga dakin ne naji motsin shi yana tayar da,mashin din sa zaifita, nadawo da hankalina don tunawan da nayi bai bar min kudin da zan sayo kayan miya ba ga kuma kayan wankin mu da,suka taru ban wanke ba, Da,sauri na mike zuwa kofan fita waje na,samay shi har saura kiris ya fita daga gidan nake cewa yaya Hamza ya ja ya tsaya yana jirana na karaso inda yake tsaye rike da mashin, din sa yana jirana, Nake fada mai bamu da man miya da maggi sun kare, sai sabulun da zanyi wankin kayan mu da,shi, Haba Humaira yanzu mu kwana a guri daya dake bazaki fada min babu kayan miya haka ba,sai yanzun da nake shirin fita zaki zo min da zancen babu babu, Na dan dago kai na kalle shi na furta a hankali da kayi hakkuri yaya mantawa nayi na fada ma tun da zun, Ya saka hannuwan shi a cikin aljihun rigara shi ta gaba yana kokarin ciro kudi don ya bani, Daidai zai mika min Umma ta fito daga dakin ta daga gurin da take a tsaye tana kallon mu take cewa, Ikon Allah shike nan baza,a bar namiji ya zauna da sisi a aljihun sa ba sai ansan yadda akayi aka yaudare shi aka karbe mai canji,, Kai wanan zamanin wai da may yai kama haka ace mata su dai abasu dai abasu, Da kyat na iya hade miyau don bacin rai nace a cikin murmushi, Umma kinsan kayan miya ya kare tun kwana uku da,suka wuce shine nake fada mai babu su, Har nawa zai baki akan wanan sayen kayan miyan don bazan iya sa ido kina kwatar kudi ba kamar kin samu banki, Umma ai dari biyar ne kawai na bata bawasu kudine masu yawa ba hamza ya fada mata hakan, I min shiru kai may ka sani da tace kwana uku babu a haka take miyan ba su, Ai dai gaskiya ta kusa halinta a gidan nan wannan yawan barnan da kuma wullakanta abinci ai yazo karshe dai a gidan nan, Ido muka hada dashi inda na facinci baiji dadin kalaman Umma din ba inda yake min kamar signal da ido na kyale ta kawai, Najuya nafara tafiya nabar gurin Umma tana kara karasowa inda yake tana cewa dama nace ba yaushe zaka tafi gurin shi mahaifin Sadiya din kai kudin da kace sai ka,dawo zaka bayar din,? Wani irin amsawa kirjina yayi wanda hakan ya sakani zaro idanuwa na don mamaki, Shikuma hamza jin furucin Umma ya saka shi saurin dago idanuwan shi yana kallona, Kawar da kaina nayi gefe guda ina mai ci gaba da tafiya na sai dai ina tunanen ko may naiwa,Umma har yai muni irin haka a tsakanin ni na da ita, Har kofan gida suka fita shi da Umma don zancen ba wanda ake bukatan kowa yaji bane, Na shige dakina ina mai tunane tare da kiyasta irin zaman da zamuyi a gidan nan tsakani na da su Umma da kuma ita sadiya har shima kan shi, Hamza din, Kudin abinci ne fa amma saida Umma tai bakin cikin miko min su da yayi inaga wani abin bukatan can na daban, idan ya hada mu, Don haka tunda Umma ta rufe idanuwan ta taimin haka nima na sha alwashin daga yau duk iya inda kudi ko kayan cefanen da suka bani ya tsaya nima a gurin zan tsaya ba zan sake saka naira na a cikin girkin gidan nan ba, ****** ********** ****** Zaune suke dashi da Mansur a kofan gidan su Mansur din zaune saman wasu fararen kujeran roba da Mansur din ya aje don baki, Sai da Mansur ya gama sauraren bayanin Hamza din ya nisa tare da cewa, amma dai ka bani mamaki Hamza yanzu ace duk irin halarcin da kuma hakkurin da yarinyar nan Aisha take maka amma ke mata irin wanan sakaiyan haka, Murmushi Hamza din yayi tare da dan girgiza kan shi yana cewa bazaka gane bane watau, Bawai zanyi wanan auren bane don gazawan ita Aisha din a a zai kara aure ne don daurowan hakan agare mu Saboda ina gani shine mafita da saukin mu baki daya amma ba wai nayi bane don gazawan ita Aisha din ba, wanan auren nawa ra,ayine kawai da kuma nufin Allah, Well, tunda haka kace kuma na fahinci cewa kariga kayi nisa, a kan zancen ba matsala, Allah bada sa,a zan ce ma kawai, mansur yake fadin haka, Idan time yayi sai ka,fada muna mu je gun daurin auren ko, Murmushi yayi Hamza yayi, tare da dago kanshi yana cewa,ai auren coming Friday din nan ne za,a daura, insha Allahu bawai wani tsawon lokacine za,a dauka ba, To Allah ya kaimu inji Mansur ya amsa mai cikin dan jan numfashi yana furza iska daga sautin amsa, shi Sai suka canza hiran nasu ya koma akan harkan kasuwancin dake faruwa a lokacin, bayan sunyi sallama Mansur yana shiga gida ranshi a bace yake fadawa matar shi Hindatu zancen auren da Hamza ke shirin karawa kwanan nan, Sun dauki lokaci maitsawo suna sharhi shida Hindatu suna yaba irin hakkuri da kuma sanin yakamata da nake dashi amma bai hana Hamza yana yawa musguna min ba duk da zamana karamar yarinya, Sosai Hindu ta zage tana fada tare da,sake maganganu tana zagin Hamza da mahaifiyar shi, A Cikin ikon Allah washegari na tashi da zancen zuwa gidan su Hindatu ina cewa ina son zuwa na dubo danta dake rashin lafiya, Kamar bazai barni na fita ba amma kuma komay ya tuna sai yaga ai ya kamata din naje na dubu yaron saboda har asibiti suke alokacin shi baya gari, Sam ya manta da zancen su da Mansur ya fada mai cewa zai yi aure ranan jumma,a mai zuwa Ya manta cewa Mansur zai iya fadawa hindu matar shi komai, Nashirya bayan nagama komai nafita sai dai banyi girkin rana ba saboda ba abubuwa da dama da zan bukata gurin girkin, ranan, Kawai na shirya na rufe kofana na bargidan don ba kowa a lokacin duk sun fita zuwa tsabgogin su, Sallaman da nayi a kofan falon ta yasata saurin lekowa daga inda take tsaye tana cewa maraba da Uwargidan Hamza, Murmushi kawai nayi mata, sai dai ina mamaki a cikin raina ko da yake ba abin mamaki bane don sani yadda mijinta dashi Hamza suke, Mun gaisa tare da tambayan lafiyan yaron yadda ya kara ji take cewa,Alhamdullahi ya,samu sauki, Fita nayi zuwa dakin mama mahaifiyar Mansur nagaida ita sai nadawo gurin Hindatun, Na zauna ina kokarin cire hijjab dina don rana da na biyo a lokacin, akwai zafi, Aisha yanzu abinda Hamza ya ke shirin muna kenan ashe wai kuma wani auren zai karayi, kwanan nan, Murmushi maikama da yake nai mata ina cewa haka dai nima nake ji, Bangane kike ji ba Aisha kina nifin bai fada maki zai kara aure ba da bakin shi ? Na kada mata kai ina cewa hakane gaskiya don tsakanina dashi bai taba fada min ba sai dai alaman da nake gani gurinshi da yan uwan shi, Kutubelesi amma yakai dan rainin wayo yanzu shi fadin ran shi har yakai a haka, To ina ya fada maki ranan jumma,a ne daura aure da tarewa ko ? Da,sauri na dago kai ina kallon ta cikin mamaki nace Jumma,a fa kikace anty hindatu ? Kwarai kuwa wanan Jumma,an mai zuwa za, a daura aure kuma matar ta tare, Take naji idanuwana ya ciko da hawaye amma sai na shayen su basu digo ba, nake cewa Wai Anty Hindatu may Hamza ke nufi da ni ne wanan irin musgunawan yai min yawa a,rayuwa, Tace cikin hasala tsabar rainin hankaline kawai irin na da namiji don sai su dauka ita diya mace bata da wani right a rayuwanta, Nace cikin murya maikama data mai kuka anty ni wanan abubuwan sun fara isata wallahi, Ina karama dani za,a fara cusa min bakin ciki da takaici a,rayuwa irin na da namijin, Hmmm Aisha ke nan ki rabu da namiji kawai don idan auren nan ya motsa masu basu diban gaba balle baya, Yanzu hakkurine kawai ya rage maki ga kowa a gidan, duk abinda kikasan kinayi mashi a baya kada ki fasa yi wai don kinga ya kara aure, Kowa da irin halinta ake zama da it don haka shi da kanshi zai fahinci halaiyar ko wacen ku, Ai dama shi zaman aure dan hakkurine duk inda mace take aure saida hakkuri, Yinayi bari na bari inji manya, shine riban aure duk auren da babu ladabi da biyayya a cikin sa sunan wanan auren lalatace Aisha, Kinga ko ita wanan din da Hamza zai aura kin santa tun farko kin kuma san halaiyar ta, Don haka ni shawaran da zan baki ke nan don nasan akwai zafi ga duk matar da akaiwa irin wanan auren cin fuskan, Ki dage kawai kiyi sunnan auren ki sau da kafa don ku zauna lafiya da kowa , Ki kawar da kanki ga duk wani borin sabon auren da zaki ga sunayi da ita, Badon Allah za ai wani abin ba za,ayi shine don ke uwargida kiji haushi kawai, Kinga idan kin biyewa haukar sai al,amarin ya kwabe gaba daya ke da miji ku koma ba zaman lafiya ko kadan, Amma inadan kin daure kin share kin hadiye abin a ranki sai komai yazo maki a cikin sauki, Ke ce dai uwargida don ba,a taba kai gaba baya dole dai tana bayanki komai shekarunta a duniya, Abinda ta zo takeyi kada kema ya hanaki kokarin tarairayan mijinki, kai mai ruwan wanka idan ya dawo sanu da zuwa , abinci kiyi mai kyau idan kina da girki din kin rigata shiga gidan kin san abinda yake so da bukata, Idan taga kin dage tabuga tabuga bataga daman ki ba sai kiga abin yafara fita a tsakanin su, Don may ? Don bakiba da kafa an wulkantakiba kamar yadda matan yanzu suke shiga da gurin ganin wace akasamu a gida ta nakasa ta koma baya, Sai ta kawai zata dinga yin yadda rantake so indama yara gareki ana kokarin ganin an raba su da mahaifinsu an shiga tsakanin su,dashi saboda kissa da kisisina da akazo dashi, Don haka wallahi kama mijinki ki rike hannu bibiyu Hamza yaro yanzu yake rigimar auren ne kawai Allah ya zo mai a rayuwan shi, Idan kinyi hakkuri bakiyi sake ba duk irin wanan al,amari watarana sai ya zama tarihi, Nasan bawai don kin kasa bane zai sa shi kara aure kawai sha,awan hakan ne dashi, Don Allah Aisha kada kiyi sake tako wani hanya karki yarda ki watsar da daman ki na uwargida da Allah ya baki , Rike auren ki hannu bibiyu, ki kula da duk wani hakkin shi dake a kanki kinji, Insha Allah indai muna tare zan taimaka maki daduk wani abinda ya dace ya taiwa kaunar ta a duniya, muddin kika kwantar da hankalinki,kinji,,, Nace mata na gide anty yayin da idanuwa na suka kara cikowa da hawayen dana kasa mayar dasu, Nace Anty nagode Allah yabar kauna nan naita mata godiya tana cewa babu komai Aisha, aike abin a taimakawa ne, don halinki na alheri, Nan dai ta dinga rarashina tare da kara kwantar min da hankali, Karshe tace min zanji insha Allahu kafin tarewan amaryan zatai min duk wani abindaya dace,, Ta kuma kara jaddada min cewa kada na yarda na nuna damuwa ko kadan kodan Umma da yaranta tunda jira kawai ake aga damata asamu gurin yi min gori ko wulakanci, Nai mata godiya sosai don nai matukar jin dadin wanan shawaran da nasihan da tai min sai nake jin kaina wata wasai dani, duk kuncin danake ji da farko yanzu sai na nemay shi na rasa shi baki daya, Munyi sallama dasu nabar gidan inda ta rakoni take kara jaddada min cewa zan jita kafin ranan Jumma,a insha Allahu, Nadawo gida ina kallon kowa yadda suke kallo a matsayin wace bata san komai ba, Shi kan shi Hamza ina mamaki yadda naga yana shirin shi hankali a kwance baidamu da ya fitar min da hakkina ba na nima ya kamata na sani ai koda akwai shirin da zanyi kafin ranan, Amma ina, sun mayar dani matsiyaciya banda abinda zan gyara dakina dashi, don haka jira kawai suke nasha haushi, Sai shirin su suke tayi iyakata da su idanuwa don babu wanda ya sani a cikin zancen, Zarah ce da farko taso sakani amma sai akai mata waigi dole ta daina komai dani iyakarta gaisuwa a tsakanin mu, Ita ko mama ba,a shawaran komai da ita sai ma yawan wulakancin da take dan fuskan ta daga gurin su yanzu, Da safe zai fita nace ina son shiga gidan mu inga Ummi na, kai tsaye ya ce min bazan shiga ba don kwanan nan nafaye fita zuwa unguwa, Dole na hakura ba don naso ba sai mama ce nadan faki idon mutane na tura ta gurin Ummi don ta fada masu, Zancen tarewan Sadiya da za,ayi ranan jumma a mai zuwa insha Allahu, Saura kwana biyu ke nan da za,a tare din, Ba bata lokaci mama ta shirya ta shiga gidan mu tafada masu komai nan suka,shiga surfawa Mama Sa,a da Umma zagi kan wanan auren da suke son hadawa don cin fuska, Duk na dan shiga damuwa rashi kowa a kusa dani amma kuma ina kokarin yin yadda Anty Hindatu ta koyar dani, Sai Umma da yaranta su shige daki suyi ta gulmana suna dariya kyakyakya har mai shigowa zai iya jin sautin dariyan su, Kitso da kumshi, na tambayi Hamza zuwa amma sai ce min yayi na nemo wace zatai min a gida, Nadago kai a cikin mamaki ina tambayan shi wacece zan kira tazo gida taimin nawa zai bani nabawa mai kitson idan tazo tai min a gida, Look Humaira ban fahince ki ba idan baki fahinci nufina ba sai ki bari, koke ba bahaushiya ba ce baki san hausa ba ko may, Daga haka ya fice daga dakin ya barni raina a bace nace dama ashe zaka kara aure ne don ka zalunceni dama nasan baka sona tunda bakani akayi ba nemana kayi ba, Nidai tunda baka sona ka sallamay ni na koma gidan mu kowa ma ya huta hakana, Har ya kai kofa sai kuma ya dawo har gabana yatako yatsaya muna fuskantar junan mu dashi, Humaira ke da bakin ki kike furta na sallamayki ki koma gida ? Yakai dan tsawon lokaci tsaye a gabana yana mai tsura min idanuwanshi, kamar mai jiran amsa daga gareni, Ya gyada kai tare da juyawa yafita yabar dakin zuwa waje, ran shi a bace sai zuwa sha daya ga wata mao kitso taxo take cewa wai nafuto inji Hamza taimin kitso da siffa, Kamar nace na fasa banyi amma kuma,sai nai gudun sa idon mutane a kan mu, Don haka ba don naso ba nazauna daga kofana muka fara siffan sai kitso daga baya, Ance labari yana gurin masu kitso da siffa da sauran gyaran jikin mata, Saida taga ba kowa, take, ce min kaii namiji ho ko may mijinki yagani gurin wannan matar da zai aura ? Kin fa fita da komai da ake bukata agurin diya mace, sudai maza idan sun tashi aure sai kiga kamar idon su a rufe yake, Murmushi nayi ina ce mata ai kinsan ance matar mutum,kabarin sa Allah ya nufi akwai aure a tsakanin su ne, Tace zan maki kitso da siffa maikyau wanda za ce ko ce amaryan zan kuma dinga zuwa ina maki duk lokacin da kike bukata, ai maki, Zuwa karfe hudu har mun idar naga Zarah tana girji irin na alfarma amma ban damu da nasan may takeyi ba, Zan dora girkin yamma take ce min nabarshi kawai idan ta gama zata zubawa kowa a kwanon sa, Juyawan da zanyi zuwa dakina sai guda naji da dirin mota ana cewa ayyurirrrr Amarya, yar shagali, yar biyan bukata, yar garali, A hayye gamu mu mun iso ko ana so koba,a so yau Allah yayi aure tsakanin Sadiya da Hamza, Ban juya ta kansuba dakina kawai na shiga sai faduwa gabana yake zama zanyi ko kwantawa duk na rude na rasa may zanyi a lokacin, Gani ni kadai a dakin babu kowa nawa a tare dani duk hankalina ya tashi gabana yana ta faman faduwa, Sai addu,a nake ina rakasu da kalman sunan Allah don samun rijaye akan masu sheri daga cikin su, Inajin sai sannunku da zuwa Umma da yaranta suke masu tare da kwasan dariya suna cewa ku iso ga dakin nan, Habaici da gori kawai ke faman tashi a gidan Sadiya da Hamza mutu ka raba ko yan bakin ciki basu so, Wata kuma tace gidan nan sai an cika shi da yara harkofa gida don tsiya da talauci ya kare yau, A hankali na runtse idanuwa yayin da zuciya ta yake min suya kamar zai tsage, Muryan wata mace naji daga cikin su tana cewa haba kubar yin haka mana,arziki fa ya kawo mu ba tsiya ba, Sai kuma naji wani murya a gaisawa da mutanen kofana masu sallaman suka nufo, Ashe, Anty Hindatu ce tare da sisters dinta guda biyu suka shigo da sauri na tashi na rungumay ta sai kuka, Tsawa ta daka min cewa nayi shiru kada na fara na bata tsarina na tashi nayi kwalliya naje nai masu sannu da zuwa, Hakan ne kuwa mukayi nasha kwaliyana acikin dinkin wani atamfa mai ruwan brown color dinki shi yai matukar karban jikina, Na fito zuwa gurin su idanuwan su ccaa akaina nai masu sannu da zuwa tare da gaishesu da aiki najuyo zuwa dakina, Sun bar gida da yamma liss suma hindu sukaimin sallama ina ta masu godiya amma sai tace na bari kawai, Hmmm ikon Allah washegari takwas na safe mukaji durin mota sai kayan gado da su wardrobe mirror mukaga ana,shigowa dasu sun ci uban na Sadiya nisa ba kusa ba, Kowa yafito yana kallo saiga hindu da sisters din ta najiya da ma wasu biyu suka shigo nan suka hau gyara min daki,,, Barkan mu da shan ruwa yan uwa tare da fatan samun rahamomin dake cikin wanan watan mai albarka Kuyi hakkuri dani yan uwa muje zuwa labarin sarautar mata, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Maza ki kwashe duk wani abinda kike bukata daga dakin don yanzu zamu gyara dakin, Tsaye nayi sororo da mamaki ina kallonta ina kallon kayan cikin mamakin inda suka fito dasu, A hankali nace Anty wanan kayan fa cikin fara kware zanin gadon da yake a shimfide take cewa, Idan da kin kwantar da hankalinki dole muyi maki bayanin komai don haka sai banki ba nafara dan daukan abubuwan amfani na da nake so a dakin, Kafin wani lokaci har an gama fita da komai anfara saka sabbin da aka,shigo dasu, ko, Dakin sai ka rantse kace ba dakina wanda nakwana a cikin sa bane, Aikin shape shape akayi shi sai muka bar mutanen gida leke tare da tabe baki, Mama Hafsi wace bata gidan tana shigowata hango kayana,waje a,watse tafara tambaya wai may ye haka taga ko ina kaya a,watse, Dakin ta nufa ta daga labule sai cewa tayi ayyururiii Allah sarkin dadi, Ance mahakurci mawadaci yau Aisha duk wani, sa,an ki bai gwada maki komai sai ma,dai ki gwada mai don ba,a fiki da komi ba na daki, Yanzu zauna kiji bayani abinda ke nan na samu guri daga gefen kujera na zauna ina sauraren ta, Tace da farko dai wanan kayan bana kowa bane nawa ne na dakina da aikai min wasu sai na canza su , Niyyana zan sayar dasu sai ban samu wanda yay min cinikin su yadda ya dace ba, Kayane na kamfani masu kyau sunyi ma dakina kadan ne shiya sa aka canza min aka,sayo min babban seti mai girma, Yanzu tun jiya da muka zo naga yadda dakin ki yake ance idan kana tare da mutum to kaso shi don Allah, kamar yadda zaka so kan ka, Dan haka na yanke shawaran kawo maki wanan kayan a matsayinki na kaunata kamar yadda na dauke ki, duk ranan da,Allah ya hore maki sai kibani dubu, ashirin akan su koda da kadan kadan ne, Da sauri na dago kaina nake cewa dubu ashirin Anty hindatu ina ma laifin kice arbain ko hamasin wanan setin masu girma da kyau da tsada, Tace aiko ashirin din ma akwai dalili da yasa zan karbesu a hannun ki,, Har kasa nakai da gwaiwa na bibiyu ina mata godiya cikin bacin rai take cewa haba Aisha may ye haka dan Allah dai ki bar wanan dabian shi taimako ai takine ga bawa, Anty tace na kwashe tsofin kayana nabawa mahaifiyata su don tana son suyi clearing din kofa na kada a iske komatse a gurin kofan idan an shigo, Mama Hafsi na kira nai mata bayanin komai amma kuma anty tai warning din ta akan ta kama bakin ta kada tafadawa kowa, wanan zancen Ba bata lokaci mamata shiga gidan mu gurin Ummina tafada mata komai takuma je gurin Mamana Rahana ta bata labarin duk tadda abubuwa suke gudana a gidan mu, Guda mama tayi tace Alhamdullahi Allah mun gode maka Allah maji rokon bawan sa, Mama Rahana tazo min da zanin gado maikyau cikin gidan shi sai dinki da taimin na fitan buki shadda da lace sai kulan abinci kala biyu suka saya min,, Na rasa bakin da zanyi godiya dashi sai kawai na,daga hanayena i a godewa Allah tare da jero adduoin, godiya, Wani irin sanyi sosai naji a raina don banjin k8shin komai kuma yanzu abinda nake ji daren jiya da naga an shigo da kayan Sadiya yanzu duk ya gushe a zuciya ta, Don mutum zai iya cewa nice amaryan don yadda na koma wata fresh dani, Umma bata gida har muka gama komai namu ta fita zuwa gurin shirye shiryen ta tunda farar safiya tabar gidan , Sa,adatu auta ce kawai a gidan aka samu sai ni don haka muka gama shagalin mu kafin a karasa komai, Haba bayan sun dawo suka samu dakina ya sake ai fuskan Umma a lokacin kamar an aiko mata da sakon mutuwa take ji, Zarah dai tazo ta daga labulen dakin ta shiga tana fadin kai, kai, kai, azziki, wanan kayan masu tsada irin haka lalai masha Allahu Allah ya kaimu ga danshin ku ke kan kin kece raini Aisha,, Murmushi nai mata kawai sai tajuyo tana fuskanta ta tana cewa kai kunga wanan matar ba,a taba gane gaskiyan ki wallahi, Muryan Umma ta kirata tana fadin ta,zo suyi batun dora girki don masu dawowa daga gurin daurin aure, Ai kafin wani lokaci uguwa anji labarin na gyara dakina wai ya cunawa dakin sadiya goma albarka, Sai misalin karfe biyu da rabi an sauko jumma,a aka daura aure a kauyen da mahaifin Sadiya yake zaune Masu daurin aure suka dawo gida akayi liyafa sukaci suka sha daga abinda Hamza ya tanada domin su, Yan uwana sunzo min zaman tausan gaba daga ciki harda kubura da yar ta tayi wayo sai dai uwar zaka kalla ka fahinci cewa ba dadi zaman, Ba a bani abincin da zanba mutanen dakina ba duk na damu ina cikin bacin rai sai ga kannen Anty hindatu da kula har uku da abin sha sun shigo, Nan suka shiga raba abinci a tsakanin su tare da abinsha sai kuma mutanen su Umma hankalin su yadawo a kan abinvcin dakina don kowa shi yake son ci, Sun dibawa mama Hafsi da kuma, wata matar abikin shi da take zaune a waje saman tabarma, Shinkafa da miya yaji nama sai dafa duka yaji kayan hadi cikin sa, sai kamshi ke tashi ga ruwan masu sanyi, Ranan Umma ta saka sabin tufafi ajikin ta sai faman washe baki take tana murna da farin ciki, wai Dan ta ya samu sakin wawa ko haihuwa bata tabayi ba gidan da ta fito ya aura, Wata abokiyar wasan su ta gurin Uba take cewa, sakin wawa ko dai sakin mai wayo amarya haka tsatsaye da ita shine har za a ce wai sakin wawa,, Sakin mai wayo dai,, Nan dai su kai ta shammatan junan su muna daga dakina muna sauraren su, Sai yamma lis aka watse yan yinin buki sai mu yan gida aka bari,kawai a gidan Rabon Hamza da gidan tun da safe da yai wanka yafita bai shigo ba duk taron nan da akayi a gidan, Idan antambaya ina angon Umma ce mai bada amsa tace yana can tare da abokan shi sun taron buki, Duk taron da ake raina a bace yake watau idan badon Allah ya,rufa min asiri ba da sai dai yau naji kunyan da zanji amma shi babu ruwan shi da damuwa ta, Ina daga kofa naiwa su mama Rahana rakiya saboda tace ba, zata tsaya har a kawo amarya ba, A kofa ya samay mu tsaye da mamana tana kara bani hakkuri tare da kwantar min da hankali, Yashigo gidan da sallaman shi fuskan shi dauke da murmushi a sake ya tsaya yana gaida mamana Rahana, Kai da ganin sa kin sa bai cikin damuwa ko kadan sha sa,wasu sabbin shadda dinkin babban riga a jikin shi mai ruwan milk ban san lokacin daya dinka su ba kuma ban san a ina ya saka su a jikin shi ba, Mama tana ganin sa itama a cikin fara,a ta gaida shi tare da mashi ya taron jama,a take ce mai sai yai ta hakkuri da kuma adalci yake cewa ba matsala insha Allahu, Da kyat na iya bude bakina daga inda nake tsaye nai mashi sannu da zuwa, Ya amsa min da cewa yyawa ya taro sai a lokacin na dan ga kiban da Hamza ya kara , Mama tai min sai anjima alokacin shi har ya fara tafiya zuwa cikin gida, ko, A daidai kofan Umma suke tsaye dashi da Zarah daganin su wani maganan siri suke a tsakanin su, Suna ganin zan shiga dakina sai naga duk sun juyo suna kallo na, Zan shiga daki naji zarah tana cewa Aisha zo nan dan Allah sai da nai dan jimm sai kuma na juyo zuwa inda suke tsaye, Wa8 idan ankawo amarya ba ana bada tukwaici ba tambayan da zarah ta jefoni dashi ke nan ina isa gurin su, Eh kawai na iya ce mata saboda da takaici to ni bazan bayar ba na fada maki zara komai tun da akafara bukin nan cikin kawo dai kawo dai ake min da may zanji ne please, Nikan ina fadin haka naja kafafuna na koma dakina inda na samu wasu abokan karatuna su biyu da sukazo min kara sun zauna har a kawo amarya sai su wuce, Sai dai gaskiya maganan da Zarah ta tambayeni yai min ciwo sosai don rainin hankali nice ma za,a tambaya zancen kawo amarya, Banda yadda zan yi kada kawaye na su gane dole sai hakkuri nayi don haka Allah ya nufe ni da gani,, ****** ********** ****** Maggariban farko muka ji gudan yan kawo amarya, sai yaran unguwa suka dauki ihu da shewa suna fadi ayyuriri amarya kekikace kina so dabakice kina soba da ba,a baki shi ba, Mairabo mairabo , mairabo ya samu mara rabo yana can ya manne da bango, Innalillahi wa inna alaihim raj,un nake fadi a bakina sai kuma, La illah ha illah anta subbahanaka ini kuntun minal zalimin, Wallahu galibun ala amarrihi Hamza, Sadiya Umma Rabi, Sai ga anty Hindatu sun dawo kamar an jefo su daga sama tana shigowa take cewa dama nasan yan iskan nan zasu iyayin haka tunda kamar a gagauce suke da,auren nan, Anna magariba wai ana kawo amarya tace kamar masu uzuri a gaban su basu ko iya tsayawa har zuwa anjima sukawo ta, Muna daga dakina muna jin irin yadda suke ta sake magana dama mutanen mu sun iya irin wanan sakewa uwargida zance, Badi war haka muzo sunan yan uku, Yau sai gado ya kare gobe muzo gyara nai Yau hamza kada karaga ma,shegiya kai mata har dozen, Ku cika buta da ruwan zafi don wagga yar banzan amaryan bata,bari abokai su kawo shi, Haka dai suke ta faman yadda magana a tsakar gida muna jin duk abinda suke fadi, Hindatu ce ta katse shirun da mukayi a dakin kowa da irin yadda rayuwan shi ke suya a lokacin, Yakamata ace kina da kayan kallo a daki Aisha don zai rage maki zafi da kewan idan kina kallo, Sai dayar ke cewa gaskiya nima tundazu nai wanan tunanen nace ga daki ya hadu dama ace tana da kayan kallo ne a,saka da,sai dakin yafi nan kyau, Sallaman su mukaji zasu shigo dakina a lokacin Dangin Sadiya Amarya ne suka kawota daki na kamar yadda akeyi a al,ada, Basu san da gyaran da,Hindatu taimin ba,sai kawai suka fara raraba idanuwan su a cikin mamaki don jiya ba haka dakin nawa yake ba ai, Gurin zama aka basu ina zaune a bakin gadona wanda yasha gyara cikin sabbin zannuwan gado masu kyau da tsada dasu, Daya daga cukin matan tace tau Aisha ga amaryan ki nan yau Allah ya nufa mun kawo ta gidan ku, Don haka ku zauna lafiya a tsakanin ku tunda dama kowa yasan kowa a tsakanin ku don zance kusan a tare aka tashi tunda a unguwa daya aka tashi, Zo mu zauna zo mu saba don haka aita hakkuri da juna ku zauna lafiya, Sai wata tace shi kishi dama ansan dole ayi ahi idan yazo sai hakkuri don mutum bai lokacin shi yayi na,wani, Carraf hindatu ta bata amsa da cewa balle ita mace ance lokacinta kalilan ne kinga tunda amaryan ta girmay ma Aisha dole ai zama na hakkuri saboda shekaru ba daya ba, Haba nan fa guri ya dan so kaurewa da fitina saida manya suka tsawata akai shiru tare da kara rokon a zauna lafiya banda daukan jita jita a tsakani, Suka dauki amaryan su suka tafi suna guna guni wai hindatu ta gasa masu magana, Suna shiga daki Sadiya ta kware munafukin mayafin da ta yafa tana fafin bura uban nan yaushe yarinyar nan ta sake kayan daki haka banda labari, Bar muna fuki, shi yai mata in anyi magana yace wai baida kudi idan bashi da kudi ina ta samu kudin da ta sai wanan kayan haka wanan matsiyaciya may take dashi ita, Daya bayan daya mutane sukai ta,watsewa akabar mu mu yan gida kawai a cikin gidan su Hindatu sukai min sai da safe tare da kara bani shawara, Na koma na dauki buta nai alwala tare da kawar da sauran kayana dake waje na shige tare da kullo kofan dakina kawai, Bayan na idar da sallah na dade a gurin ina,addua na mike na haye sabon gadona don sai nake ganin kamar dakin ba nawa bane yau, Cikin ikon Allah sai ga barci mai dadi ya kwashe ni ban farka ba,sai karfe biyar da rabi na,asubahi, Namike don gudun kada na makara ga,sallah nai suri buta,sai ban daki na fada, nai alawala nakoma dakina, Sau daya na daga idona na kalli kofan Sadiya amarya na kawar da kaina da idona da sauri ban tsaya jiran komai ba shige daki, Ida nai sallah nake zaune ina adduoin safe kamar yadda na,saba yi a baya, nan barci ya,kwasheni ban sani ba,saboda akwai wuta fanka ya na kadawa a hankali, Muryan Umma ne dake kwada min kira cikin tashin hankali ya,sani farkawa daga barcin safen da ya daukeni mai dadi, Naji ta tana cewa Aisha may yai zafi da bazaki fito kiba mijinki da,abokiyar zaman ki abi karyawa ba har rana yayi haka, Nafito tare da kokarin gyara hannun hijjab dina ina cewa wallahi ban ma,san barci ya daukeni ba haka, Ina kwana Umma bata karba min ba,sai cewan da tayi don Allah ji inda rana yakai amma baki sa wuta ba, Hamza ne yafito daga ban daki yana,saye da babban rigar dana gan shi saye da ita jiya ya wani nade jikin shi a cikin ta dakin Sadiya ya nufa a lokacin, Sai ga sadiya din itama tafito ta dauki buta zuwa ban daki har ta danyi nisa naji Umma tana cewa ko ruwan wa ka,bako kaiwa amaryan taki ba saboda kishi ko, Murmushi kawai nayi naje na fara hasa wutan a bin karyan da zan muna, Ina aiki ina tunanen sai yanzu karfe takwas da wani abu suka bude kofa ko may ake nufi ne wai, An dan dauki lokaci naga fitowan Hamza ya fito zuwa kofan gida, Sai gashi dauke da leda breadi ne da kayan shayi a cikin sa ya,sayo a waje, Dakin Sadiya ya nufa dasu a gefen idanuwa na nabishi da kallon mamaki har ya shige ciki, Sai ga Sadiya da Cup inda nake batun yin gudajin kunu a tukunya tabude ta debi ruwan zafi batare da tace min uffan ba, Ta juya ta wuce abinta zuwa dakinta nima ban tanka mata ba duk da dai raina ya baci amma sai kawai na,dake abina, Ina gama kunu nace Sa,an Umma ta karbo min inda zan zuba masu Sadiya da angon ta kunu , Sai ga Sa,a ta dawo tana fadin wai tace nabarshi ita ta karya ko, Na zuba nawa tare da kai sauran gurin Umma don ita mama bata damu da kunu ba,sau sauran tuwo, Na koma na,gyara dakina nafito har wajen dakin, mama hafsi dake makwabtaka dani sai dana,share shi tas sanan na debi ruwa naje na,watsa a jikina, Na dauko dinkin shaddan da mama Rahana tai min na saka a jikina, Na zauna na gyara fuskana yai kyau, sai lokacin na tuna cewa ban karya ba fa, Kayan tea din da Naga Hamza ya shigo dasu dazun suka,fado min a,rai mamaki ne ya kamani yadda Hamza ya iya wuce wa da kayan tea a gaban idona kuma sun hada tea din basu bani ba,, Shida yake cewa ba zai iya cin abinda ba,zaibawa su Umma da yan uwan shi ba, Yau sai gashi an sha tea ba,a bawa kowa ba,sai su kadai suka sha abinsu, Ina nan zaunr na saka kunu a gabana sai binsa nake da kallo ya shigo dakina da sallama a bakin shi, Kunnun dake gabana a cikin cup ban shaba yadan kalla sai ya kawar da kanshi gurin kayan shi ya nufa cikin daurewa nai mashi ina kwana, Ya amsa min da an tashi lafiya ? Alhamdullahi nace a hankali yazo ya wuce ni zuwa waje batare da ya ce min uffan ba again, A hankali na sauke ajiyan zuciya ina mai gyara zamana da cewa Allah ka tai make ni Muryan Sadiya naji daga waje tana cewa Hamza kada ka dade fa dear, A hankali na lumshe idanuwa don wani abu na ji alokacin ya ratsa kunnuwana har cikin zuciyana, Shiko sai naji ya amsa da cewa yanzu zan dawo bazan dade ba, ai Murmushi ne ya,subbuce min daga fuska na ni kadai a cikin daki, Mamaki nake yau yau da farawa na,fara ganin sabbin rayuwa a gurin Hamza, Shiru shiru zata fito dora girki kamar yadda amare zawarawa keyi amma sai mukaji shiru nikan ga kunun dana dama da safe ma na kasa shan shi kuma bana jin yunwa, Aina ce ta tayar dani daga barcin da ya fara dauka take cewa mamanta tace a kawo min dan wake da mai da yaji data dafa masu agida, Naji dadin wanan dan waken dayajin shi yaji tafar nuwa sosai naci nasha Aina tana zaune tana min hiran jiya da dare take cewa wai kin sani ne anty yar agwai, Jiyafa da kyat amarya tayarda zata zo dakin ki wai cewa tayi baki isa taje dakin ki ba,sai dai ke akiraki dakin ta, Murmshi nayi Aina tana tabani labarin abubuwan da mutanen Sadiya sukai ta fadi a kaina, Tace wai Sadiya tace wata biyu tabani a gidan Hamza sai na fita na barya dashi, Wai dama ta dade tana son Hamza a ranta Allah bai nufa ta aure shi ba shine ni na tashi na,aure shi yanzu gashi Allah ya,sa ta aure shi ita wallahi bazata iya zama da dashi da wata mace ba, Murmushi nayi a fili duk da a cikin zuciyata naji wani iri nacewa Aina wace sai yanzu na fahinci kawo dan waken da mamata tabayar takawo mi nagane ma,anan haka, Don naji duk wani labarin daban sani ba agurin yarta tunda su ba halin su shigo gidan mu agansu, Nace wa Aina kyaleta kawai kaunata Allah yafita yafi sherin ta idan ban mata sheri ba tazo tai min Allah bai bata sa,a, Muna ciki ni da Aina har wani lokaci muna hiran mu wanda a gaskiya naji dadin shigowan Aina din don ta debe min kewa sosai a gidan, Sister din Hindatu ce tashigo take ce min hindatu tace takawo min wani ledan vacco da kayan tea da kuma su taliya da miya mai yawa a cikin sa, Nai godiya nai mata raki take ce min ai zata dawo in an kwana biyu, ta dubani, Wai yau gidan nan baza ai muna girki bane ko kuwa yaya akayi ne wai, Muryqn Ummane tsaye a tsakar gida tana tambaya tare da duban kofan dakina, Nikan banda yunwa na ci dan wake nasha zobona mai sanyi na kwanta ina,sauraren wa,azi a cikin wayana bayan fitan Aina, Jin muryan Umma gap da kofana tana maimaita tambayan ta yasani fitowa daga dakin nawa, Umma aikin san yau banice zan muna girki bs shiyasa ban dora muna ba, Wa zai muna take tambayana cikin kafe ni da idanuwan ta, Sadiya ce ai da girki don haka ne ban fita ba kada taga nai mata katsalandan Kwarai kuwa inji zarah daga bayan Umma inda budurwa ce kinga sai a koya mata yadda za,ayi na yau ta gani, Tau bazan yi girki ba sai lokacin da na ga daman karba kokuwa Sadiya ce daga kofan ta ta daga labulen dakin tana kallon mu, Banyi magana ba sai kawai na juya zuwa cikin dakina na kyalesu dole zarah ce tai girkin rana kowa yaci har ita Sadiyan nikan ance wai nakawo guri a,zuba min nace na koshi, Da yamma dole nice nafito na dora girkin dare na kwashe nabawa kowa nashi, Ina ganin yadda ranan Hamza yake shige da fita a gidan amma kamar bai san da zamana ba a lokacin, Bayan na idar da girkin nai wankq na,shige daki ban fito waje ba,sai zuwa dare bayan ishai, ina kwance rigingine a kasan carpet din dakina kafafuwana,a,sama kujerana, Naga shi ya shigo dakin wayana yana a hannu na ina,sauraren kira,a tare da bin kira,an a hankali, Dakin nawa yake bi da kallon sai da ya kewaye ko ina da idanuwan shi kamar bako sai yake cewa kizo ki samay ni a waje yanzu, Namike tare da gyara hijjab din dake a kaina nadan saka silfers dina a kafa na tabarma nagani an shimfida a kofan Umma da mama suna zaune akai sai na nufi gurin nima na zauna suna daki muna jiran fitowan su shiru shiru sai da mama tace kodai yaron nan ya manta da ya,tara mu nan ne, Can sai gasu fitowa dagani sun sha,soyayyan su ne don fuskan su yana dauke da murmushi sake fayau, Kamar zata shige mai a jiki irin yadda suka zauna a tabarman, Shine yafara magana tare da cewa tau da farko dai ina son na godewa Allah daya kawo mu wanan lokacin msi albarka, Yanzu mun kara samun karuwa a gidan don haka nake son na ja maku kunne akan ku zauna lafiya da junan ku , Ban son nani wani hayaniya ko tashin hankali daga dayan ku ko wacece zan batawa maishi rai, Ga iyayyena nan suma ina son a basu girman su don bazan yarda a wullakanta mi uwaye ba ko kadan, Sai zancen girki ku tsara yadda kuke son yi a tsakani ku don na sani saboda ni yanzu kunga matafiyi ne, Shiru ne ya dan fito baya ba,wanda yai magana a cikin mu daga cikin duhu ina iya ganin yadda take wani dan lalaban shi daga bayan shi, Zamuyi kwana daya daya don ni haka naga kamar yafi min sauki, Umma tace girkin kwana daya may zaku gane a cikin sa kwana biyu dai zakuyi shi yafi, Ni kwana daya na tsara zamuyi don haka ne yafi min saukin aiki, Sadiyq ce ta furtawa Umma din haka yayin da gaba daya muke kallon ta da mamaki , Ibrahim wanda tun fara zancen ya shigo gida yana zaune yana cin abinci ya kada bakin shi, Ke mu fa gidan nan duk abinda Umma ta ce shine muke bi don haka ku barshi a kwana bibiyun da tace din, Wanan kuma ai ba hakkin kowa bane hakkin mune mu masu auren shi inji Sadiya tana ba Ibrahim din amsa, Kwana biyun da Umma tace abarshi a haka inji Hamza wanda tun farko bai ce uffan ba a kan zancen, Mikewa Sadiya tayi zuwa dakin ta wanda hakan ke nuna tayi fushi ke nan zuwa dan wani lokaci Hamza ya mike zuwa dakin, Muna gurin a zaune na wasu yan mintina ba wanda yai magana, Allah ya kyauta inji mama hafsi ta mike zuwa dakin ta nima mikewa nayi ina cewa a hankali sai da safen ku nabarsu a gurin inda naji Ibrahim yana cewa yanzu aka fara ai indai wanan fitsararan yarinyace da kuka kwaso wa kan ku, Narufe kofana nai shigewa na daki bankara fitowa ba sai safe yau ma kamar jiya don basu fito ba sai da rana ya take, sosai, Ina daga daki don da,wuri nafito na dama kunu nakoma dakina Har ya gama,shirin shi ban fito ba ina daki yaje ya tayar da mashin din shi, ko may yagani sai kuma ya sauko zuwa dakina , Kwance nake ina barci cikin wasu material mai adon baki da fari, dinkin dogon riga mai dogon hannu, Sai naji yana jamin kafa na a hankali na farka daga barci idanuwa na da suke da nauyin barci ina kallon shi Yana tsaye yau ma,sabbin tufafi ne a jikin shi, sky color, Wanan barci fa haka har rana ya taka haka ? Baki fito ba sai faman barcin da kike yi,, Ina kwana nace mai tare da yin mika ina kokarin dagowa daga kwanciyan danake, Ni zan fita naga banganiki waje ba,shine na shigo na duba ki ko lafiya, Yadda na aje cup din dana,saka kunu na idanuwan shi yakai sama yaga alaman ban karya ba, Ko karyawa bakiyi bakina ta faman barci ko nace sai na tashi zan sha tea Wani kallo yai min a tunanen shi ko shayin da suka,sha da amarya najewa gatse, Nace ina son zuwa gidan musa na duba matar danaiwa karin ruwa yau sati daya ke nan, Rai yabata yana cewa ban faye son yawan fitan nan ba fa kema kin sani ban son yawan shiga mutane sai mutum ya koyo wasu akida na daban, Nidai ban yi magana ba ina sauraren shi kawai muryan Sadiya ce ke fadin ina nan waje fa tsaye but naga ya juya batare da ya tsaya mun karasa maganan mu ba yafita yana cewa sai ya dawo , Sai zuwa wani lokaci naji tayar da mashin din shi alaman sun dan tsaya da ita ne daga kofa, Can na mike nafito don na dauraye cup din da zan sha tea da spoon a hannu na, Wani kallo tai min tare da jan tsuki ta shige dakin ta na zauna ina kada tea Umma ta shigo da kifi danye wai a gyara ayi miyq dashi, Nasan Umma tai hakane don ta burge Sadiya tayi muna miya mai dadi, Umma nikan sai dai a gyara in ma har zanyi miya dashi don ina tsoron kada ya soke min hannu, Murmushi nayi don jin may tace nasan dai baza,a ce nafito na gyara ba don bani ce dagirki ba, Dole Asmau Umma ta,sa ta gyara kifin tana ta faman mita ita haka kawai za,a sakata aiki, Iyye to may kike nufi dama saidai a dafa a baki kici komay kike nufi ni wallahi ba yar Agwai bace da kuka raina, Cafdijam nace ashe akwai magana a gidan nan don Umma bata hada diyan ta da kowa ba, a duniya, Miya kan a fuska ga miya amma gishiri bai bari akai shi a baki don zai iya yanke makoshi, Ranan nan akabar abinci ba wanda ya iya kai ko loma a bakin shi, Miya na wanda nakan dumama abina tunda safe suna daki na diban ma mama hafsi nakai mata a boye mukaci da breadi makasha ruwa muna jin diyan Umma suna jininin yunwa, Washegari karan bugun kofan da Umma keyi na,Sadiya ya ne ya farka dani daga barci naji tana cewa ka tashi kaje ka samu jam,i duk kwanakin nan baka zuwa sallah asuba,, Shiru banji an bude kofan ba sai bayan kamar minti talatin da wani abu aka bude kofan dakin lokacin ma ina ganin an karasa sallah ko, Aiko ya na fitowa Umma tafara magana yanzu kai sallah asuba da ake raba alheri wa bayin Allah shine kake kokarin sakaci dashi har baka iya fitowa kasamu sallah a cikin jam,i, Hmm ikon Allah wai mutum yai lokacin shi kuma ya hana wasu yin nasu sadiya ce ke fadin haka dai lokacin da tazo gap da inda Umma take tsaye, don ta jita, Sakwarkwatai Umma tayi tabi ta da idanu kawai da mamaki abinda ya fito daga bakin ta, ****** ********** ****** Har kwana hudun da ake na bazawara ko uku ya cika banga Hamza yana zancen dawo dakina na nidai ido kawai na sa mai, Har saida Sadiya tai sati daya suna tare da dashi babu wanda ya ce masu uffan a gidan, A bangare na babu wani alaman batarai danayi a fili sai dai a cikin zuciya abin yan bata min rai sosai, Wanda nake zaune gidan don shi bai san daraja na ba don haka nake ganin gara kawai ma nabar gidan Na nufi gurin iyayyena zaifi wanan zaman da yake shirin jefani ciki da kurciyana, Mama Hafsi ne da taga har yau yana shirin kara kwana wurin Sadiya ta samu Ibrahim a,waje take fada mai halin da ake ciki don tana gudun tai magana ya zama fitina, Hamza ya dawo da mashin din shi dauke da dan ledan da yakan riko ya shige da shi dakin Sadiya, Yaya amma dai yau Uwargida ce keda girki ko don dai amarya ta gama kwanakin ta tun kwana uku da suka wuce amma baka koma dakin yar uwar ta ba, Tsayawa Hamza yayi yana kallon Ibrahim din yake cewa dama idan an auri bazawara kwana nawa ake a gurin ta ne, Ibrahim yace kwana uku ko hudu mana akewa bazawara budurwace kwana bakwai, Yakalli dan uwan nashi yace wallahi Ibrahim ban san da haka ba kuma sai na dauka ko ita Humaira ta kyale ne kawai don ita wanan din ta san gidan sosai, Yace to gaskiya yaya baka kyauta ba daga kai har su umma dake cikin gidan nan suna gani ana zaluntar diyan mutane don kawai hakkurin ta, Kaji tsoron Allah wallahi ka kauce wa cin amana don gudun sabawa Allah, Ubangiji zai yi fushi dakai akan wanan abin da kuka aikata Banyi zaton zakayi saurin mantawa da irin halarcin da wanan yarinyar Aisha tai muna ba alokacin da muke bukatan taimako ta fitar da mu a kunya, Ta zauna da mu cikin irin halin rayuwan matsatsin da muke acikin wanan gidan, yanzu don ka auri diyar kawar Umma shine za a hada kai har dakai a cutawa yar mutane Shiru Hamza yayi yana tunane don bai taba tunanen Ibrahim nada kaifin hankalin irin haka ba, Yaji dadin tunasar dashi da dan uwan nashi yayi sosai ya kuma gode mai da ya fitar dashi daga halakan daya tashi fadawa, Yace cikin nuna damuwa a fuskan shi nagode Ibrahim insha Allahu zan kiyaye kamar yadda kace Allah ya bada iko inji Ibrahim din yabashi amsa, Yana shiga cikin gida su Umma suna zaune a,waje da yaranta ga kida da ke tashi na yan wasan hausa daga dakin Sadiya muryan ta tana marming din wankan har waje, Wani haushi ne ya kumay mashi zuciya tana jin muryan shi tai wuf tafito waje sai kawai taga yasha kwana zuwa dakina, Ina duke a gaban fridge dina ina gyaran ruwan dake cikin sa, sai naji ya riko ni ta kunkuru na, Nadago don nasan shine kawai zai iya min ta,sakani yi kwana biyu, Yanzu Humaira kin min adalci ke nan a rayuwan mu saboda Allah ashe kwanan wacan yarinyan ya kare amma,shine ke baki fada min ba kika barni a duhu haka, Kawai sai ma na,rasa may zan ce mai don zancen banza naji yana fadi shi da,yai aure bai san yadda akeyi ba yake nufi ko may Ko kuwa sallon yaudare irin na maz yazo min da shi haka Cikin kuka nace dan Allah ya hamza in har kasan baka bukatanane a gidan nan ka,sallamay ni kawai na koma gidan mu don wullakancin ya isa hakana, Wani tsawa ya daka min tare da nuna ni da yar yatsar shi yana cewa, ina gargadin ki da kada na karajin kin furta kalman rabuwa a tsakanin mu Idan ba haka ba ranki zai baci sosai a gidan nan banyi auren da har kike zaton zan maki wulakanci ba, Don haka ki shiga hankalin ki ledan dake hannun shi na kayan sayi na jika makoshi ya miko min ya juya yana fadin ki karbi girkin ki yau din nan don anan zan kwana, Ya fice yabarni tsaye ina mai binshi da kallon mamaki adake ka,a hanaka kuka ke nan,,, Dakin Sadiya ya shiga inda ta bishi da harara tankar bai fahince ta ba sai ya basar da ita kawai ya fara kwasan kayan bukatan shi, Kasa kannewa tayi tace dear ban fahince kaba namay ke nan shima ya tambaya batare da ya juyo ya kalle ta ba naga kana wani kwasan kaya kaman mai barin gari, Bagari zan bari ba dakin dai zan bari zuwa dayan dakin kuma, Amma dai sai nake gani kamar da sauran time aiko, ko dai har ka gaji dani ne wai, ? Yace ba gajiya nayi dake ba Sadiya bana son na fada cikin sabon Allah ne kwai don itama tana da hakki a kaina kamar yadda kema yanzu kike da hakki a akaina, Tace au kana nufin ke nan daya muke da ita ko da har zaka wani hadani da wanan mara galihun, matar taka, Hamza ya juyo da sauri yana kallon ta yace a idanuwan ki take hakana ni agurina mace mafi daraja gareni, Yanzi musali idan kece nai wa iri haka yaya zakiji a ran ki nasan bazaki ji dadi ba don haka naje son na kwatanta adalci a kan ku baki daya, Hmmm aikama kasan wallahi ba daya muke ba ni da ita don mata suna suka tara aciki dole a kwai zarah, Yace to gaskiya ni har uanzu Humaira ce zarah ta don ban hadata da kowa daga haka yafice daga dakin dauke da wasu kayan bukatoci nashi a hannuwa shi, Hakika maganganun Hamza a kanta sun matukar bata haushi so sai batayi tsanmani duk irin dafuwan da tasha har Hanza zai iya bude baki tun yanzu ya tuna da wata humairacan, Tace wai Humaira kamar wata matar azo agani yarinya karama ta ishi mutane da a guri, Ashe muna fuki duk wanan ihun da satin da yake min duk karya ne nida ina zaton abubuwan dana ci da wanda na sha ne duk suka gigita min shi a she muna fukinkuwan dadi ne kawai yakeyi baifita hankalin shi ba, Hmm,ummm aiki kona gabana ja don wanan yar iskan ni bazan zauna da ita ba ta hanani jim dadi mijina, Yanzu yadda na saba da wanan rugumar nashi kwana biyu ace wai haka zan kwanta babu wani shafa ko tsotso sai ni da pillow kawai, Gaskiya da sake Umma zan fara zuwa na samu kafin na fadawa mamana abinda ake ciki ta tashi min tsaye, Yana fita naga kuka ba zai min ba take zancen Hindatu ya fado min a rai da take ce min duk ranan da mijina yagama kwanakin shi a dakin amarya zai dawo dakina na tabbatar nai mashi tanadi mai kyau, wanda zan tare shi yasan nima mace ce mai daraja da kima, Idanuwana na kai gurin da na boye wasu abubuwan da tai min tanadi tace ance in kana da kyau kara da wanka, Kafin na mike sai gashi dakin dauke kayan aji su boxer din shi touch light, redio da su brush, Ya samu guri ya aje su ya ce min ga kudin cefane na saiyo abinda babu shi a gidan, nayi girkin dare, Ranan Sadiya kamar zatayi hauka don duk tabi ta tayar da hankalin ta sosai agidan don har zuwa tayi cikin dare wurin Umma takai karan Hamza Bayan Umma ta gama sauraren take ce wa yanzu so kike na mara maki baya dana ya kaice duk mu taru mu hallaka gaba,dayan mu, Wata irin zuciya Sadiya tayi tace oho ashe dama muna funtar mu kikayi kina ra,ayin matan shi amma sai kika nina muna ke baruwan ki da ita, Haka tafita daga dakin tana bakar magana ni wallahi idan tsoho baiji kunyan hawan jakiba jaki baijin kunyar yarda tsoho muje zuwa indai nice, Sai kamshi ke tashi daga dakina gado yasha gyara ledan kasa sai kyali yake yi ni kaina dakin ya ban sha,awa irin yadda dakin ya dauki gyara, Bawai ina jin dadi bane acikin raina cewa zai dawo gare ni nai wanan gyaran kwai dai nayi ne don kwato inci na kamr yadda kowa ke min nasihan na zage nayi abinda zan kyautata,mai fiye da da can baya, , Abincin sa yana daki kamar yadda naga Sadiya ta tsiri aje mai adaki ba kamar yadda Umma ta hana ni kai masa dakin mu ba a baya, Bayan yadawo masallaci ya shigo gida sun gaisa da su Umma ya mike zuwa dakin mu nan yasamu abincin saman da center table na aje mai komai a guri daya gwanin ban sha,awan tallaka bawan Allah, Ya,na shiga ya kwabe kayan jikin shi daga,shi sai dogon wandon dake jikin shi, ya zauna don yaci abinci, Gefen shi kadan nadawo na,zauna don ko hakan sai da na tursasa rayuwana yabar min daci, Yana cin abincin kamar mai yunwa abaya sai daya kusa cinyewa saura kadan mukajiyo muryan Sadiya tana fadin, Idan ban iya girki ba ai sai ki fito ke kiyi ko kuma wace ta iya taita maki kullun, Tsuki naji yaja tare da dan girgiza kan shi ni dai tankar ban gan shi ba, Mikewa nayi ina fadin in kaima ruwan wanka ne yanzu cikin kada kai ya bani amsa, da cewa eh, nakai mai ruwan, Ni kaina nasan da cewa akwai canji sosai ga Hamza don ya canza gaba daya ya zama wani dan duniya yanzu, Sai dai duk ta hanyan da ya bullo min yasamu nima nakai gurin don haka bani kadai ce yabar wa mamaki ba harda shi na barshi da mamakina sosai, Washegari da safe tun kan nafito na gyara jikina nafito naiwa mutanen gida ina kwana tare da nifar gurin girkin mu, Na aza girki nadawo na gyara dakina tare da sharo kofana har zuwa na mama hafsi da nake makwabtaka da ita, Sai da na gama komai na koma daki na,shige tare da sake labule don Hamza din yana ciki kwance yana barcin safe abinda bai saba yi min ba yanzu shi yake yi,, Can ina zaune daki ahiko batcin shi yake saman gado yayin da,Sadiya take dakin tatana faman leke ta labule ko ya fito daga dakin nawa saboda takalman shi dake aje a kofan daki zata gane yana nan ko baya nan, Ummata fito tana cewa kai, kai kai wanan mugun sharan kuma fa haka waye yai muna shara a gida tsabbare tsabbare, a kabar min kofa na, Ta daga kai ta kallo kofan dakin mu ni da mama tagan shi a,share tas yana sheki da shi duk na gyara gurin na kawar da duk wasu komatsai a kofan namu, Nice nayishi ba kowa ba ina yatanki da bazasu share maki kofa sai nice boyar su zan fito na share masu guri, Tsaye sororo Umma tayi tana kallon inda Sadiya take tsaye daga kofan dakin ta rike da labulen kofa a hannun ta, Sadiya nice kike kokarin fadawa magana ina fadi kina fadi a tsakar gida haka ? Eyyeh Sadiya ni ce har zakice wai na samo yarana su share min kofan dakina, Sadiya tace Umma ta yaya ma zan maki shara bayan ga yaran zaune tare dake gandan gandan a gaban ki, Muryan Sadiya dayaji yasashi farkawa daga,barci yana fadin subbahanallahi, Mikewa yayi zibur zuwa waje baida ko riga ajikin shi wanda hakan yai matukar batawa Sadiya rai don tana ganin tun safe kilama muna kwance tare makale da junan mu, Wanan wani irin rashin mutunci ne kike sa,in sa da mahaifiyana daga shigowan ki gida zaki fara yiwa mutane rashin mutunci haka, Kai kyaleta nace maka ban son jin wani magana kuma maganan ya isa haka na, Amma Umma ta yaya zan kyaleta tana maki haka a gaban muna gani Mama tace wai batace kawuce ba kada zancen yai tsawo katafi mana kawai zai fi ai, Rai bace yadawo daki bai dadeba nakai mairuwan wanka nafitar mai da sabon man shafi mai kanshi ya shafa bai ma,damu da tambayan ina na,samo shi ba, Yana cikin shiri ya karan redio na tashi daga dakin Sadiya ta kure volume din shi har karshe da alamar rawa takeyi a dakin, Fita yayi daga gidan baidawo ba,sai da lokacin cin abincin rana yayi sanan ya shigo gidan bai dade ba ya kara fita, Hakana nai kwana biyu na kullun da wanda,Sadiya zatai fada dashi ayi cin mutunci ran hamza ya baci kawai, Wai ita niyarta kada yaji dadin zama a dakina ta bata mashi rai kawai, har ya fita ba zan gane ma komai ba daga gare shi ****** ********* ****** A haka muka kai har wata uku da Sadiya a cikin tashin hankali, take da mitanen gidan da suka kawo ta babu sauki ko kadan a tsakanin su,. Shidai Hamza ba mutum bane mai yawan zama a gari, don haka wani abin har aci a sude bai ma san anyi shi ba a gidan Sadiya ta samu uwar ta da karya da gaskiya ta fada mata cewa shi ne abinda Umma ke mata a gidan ita da yaran ta, Uwar ta harzuka sosai inda take shiga ba nan take fita ba wai ita bubu mai wullakan ta mata yar ta kan aure, Da Hamza ya dawo gari ta aika aka kiramata shi tai mashi tas cewa bazata yatda da abinda Umma kewa yarta ba don dama tana da labar8n irin mugun halin da takewa sarakuwar ta shine yanzu take kokarin kawo halin gurrin diyar ta, tau ita baxata dauki wanan ba, Shi taba mata ba Umma Rabi ba don haka ya rike mata diya da kyau in ba haka ba za,a ji su sosai, Saboda kunyan ta da kuma nauyin ta da yake ji ya kasa mayar mata da amsa sai dai yace mata za,a gyara insha Allahu, Wani sabon sallon iskan ci da rainin wayo Sadiya ta dauko a gidan yanzu zata iya shiga girki amma bazata girkawa kowa komai ba, Sai dai kowa ya nemi abinda zaici a cikin sa don yunwa, saboda tace ita ba kuku bace mijinta ne dolen taiwa girki ba wasu kattai ba can, Kuma in baya gari babu wanda zan wa girki ya zauna yaci banza don ni ba yar ga aiki bace, Idan Sadiya batayi girki ba Umma takan so ta sani wai dole sai nayi girkin mama ce ta kashe wanan wutan tace babu hujja don kowa da kudin cefanen shi a hannun shi ai sai suyi hakkuri har lokacin da taga dama tai masu, Hakana muke ta zama ba wani dadi a tsakani da Sadiya wace ta dauki kishin duniya ta dagwara wa zuciyar ta a kaina, Na kai mata ko ina a cikin gidan nan bata kaunan taji wani abu da ya dangance ni ko kadan, Koda baki akayi idan taga bakinane bazata gaisa dasu ba har su bargida nan, Ita kokarinta shine ta daiga na bar mata gida don wullakanci da rainin hankali ba wanda bata gwada yi min koda kuwa yana gidan ne sai yai magana wani lokaci ya tsawata mata,, Ganin da nayi bata da mutunci fiye da yadda nasan ta a baya yasa na dauki mataki a kanta ban yarda wani abu ko kadan ya hadani da ita baruwana da harkanta ko kadan, Duk da rashin mutuncin da takewa Umma da yaranta zaka gan su kan su ahade da ita da zaran sunga ina daga cikin daki ko na fita yanzu za,a dasa gulmata ana zagina,, Lokaci sai na Hamza normal din shi amma kuma wani sain sana ga duk ya canza ya koma min wani zaki sai fada zamuyi tayi har yatafi, Daga baya dai sai na fahinci akwai matsala ta kowani hanya ta gurin Kishiya da kuma gurin ita Umma, Don zai ita zuwa natare shi na,am ,nam amma dazaran ya kebe da Umma ko Sadiya yanzu duk annurin da yashigo daahi zai gushe zai yi kicin kicin da fuska kamar an mai sakon mutuwa Taufa har ya tashi bazan gane mai ba sai dai naga ana ta bushasha da kishiya da kuma mutanen gida tun Ibrahim yana tsawata mashi da hakan har takai baiji dole yakawo ido ya sa mai don yaga yai nisa da yawa sosai uanzi Sadiya ce yar gaban goshi,, Barkan ku da ahan ruwa yan uwa barkan mu da warhaka Allah yasa mu dace da rahamomin sa na wanan watan mai albarka, Allahuma Ameen, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, Ranan da yamma ina zaune daga kofa na iba yan kullin kayan sana a ta, Umma daga inda take a zaune ta kura min ido kallona take a cikin natsuwa, yadda nake aikina a hankali kwance, take kallona cikin tunane, Mamaki take yadda duk irin musgunawan da suke min ban damu ban kuma,sa a,raina komai ba, Sadiya wace fitowan ta ke nan daga dakin ta ta hangoni ina aikina ta tsaya daga kofa daidai lokacin da zan shiga daki da kayan dana kulla din na,saka a cikin fridge di na, Ke yar Agwai ki duba dakin ki ko cup dina yana ciki ki miko min don ban gan shi ba tun jiya, Haushin irin yadda ta kira sunana ne ya kamani don haka naki karba ma kiran da take min, Yar Agwai ko kin zama kurma ne ana magana kin wani kyale mutane haka, Ke dakata taji an fadi daga bayan ta muryan Hamza ne wanda ya shigo gidan ba tare da mashin din shi ba, don haka bata san da zuwan shi ba , Daga yau sai yau ban son naji kin kara kiranta da,wanan sunan banzan a gidan nan, Ta,wani gi mashi wani irin mugun kallo irin na marasa kunyan mata, Tace toh ai sunan ta ne kuma dole akirata dashi ta amsa kai mayye naka na fada, Yace bako a gidan nan ba wallahi idan baki iya kiranta da sunan ta da Allah ya bata akan ki to ki kirata da Aishan ta zaifi, Yanzu akan nakirata da yar agwai kake kokarin yi min cin mutunci irin haka don ka nuna mata kana giyon bayan ta , Yace eh a kan shi kuwa idan kuma kince kartane kikara kiranta dashi kiga yadda zan bata maki rai, Lalai kako nuna min yau kana bayan matar ka may kake kokarin cewa wanan yar sadakan kana nufin tafini daraja a gurin ka ko may, Ya juyo a hasale ya kara cewa da idanuwan shi da suka rine sukai ja kindai ji abinda na fada, Kai kubar wanan zancen ya isa hakana ban son a fara karamin magana ajashi har yai tsawo, Nidai ina dakina lokacin shi kuma dakin Sadiya yake don haka sai ya nufi can, A can din ma ba barin fitinan sukayi haka sukaci gsba da,sa, in sa muna jin su a tsakar gida Sadiya tana fadin wai ua goyi bayana , Yake cewa ba zancen goyon bayan ta bane raini ne da wullakanci ban so tunda kin san sunan ta may zai hanaki kiranta da sunan ta sai wani sunan banza can , Kodan kin ga tana hakkuri da kauda kai ga duk wani al,amari shiyasa har raini zai kai ga haka, A gaskiya cikin ran Sadiya tai matukar jin tsoron yadda Hamza yau ya koma halin mai anihin sunan watau Hamzan gaskiya don babu wargi a idanuwan shi ko kadan, Daurewa dai tayi tana bashi amsa cikin dakewan zuciya don itama ta dan turza mai, kada yaga gazawan ta, Haka suka karaci tsiyan su ba wanda ya basu hakkuri suka gaji sukai shiru, Wanan tsiyan bai hanasu kwana tare ba don da safe sai ga shi dauke da buta yafito wanka, Muna kicibis dashi yai kamar ya dan daburce ni dai na kauce mai na,ci gaba da abinda nakeyi ina fadin jarabbaben banza kawai, Can tafito tana wani kasaita da isa wai ita matar so bayan tafito daga wankan bata shiga daki ba sai ta tsaya daga waje tana wani tsefe ruwa a gahin kanta wai don kowa ya gan ta,tai wankan tsarki, Kwanonin da muka ci abinci nida mama na kwaso zuwa gurin wanke wanke nabi ta gabanta tana gani na, ta wani girgiza kan ta,, Tankar ban fahinci may takeyi ba sai aiyukana nake ta gaji ta dauko buta ta tsuguna wai tana kara alawa, Ana zaton wuta a makera sai gashi a masaka ni ban damu ba amma Umma ta kasa hakkuri tai magana, Wanan ai aikin banza ne mutum ya makara da,sallah har rana ya yi ja da,fitowa shine har zai tsaya wani heleken banza wa mutane,,, Kamar zata bada amsa sai kuma ta ja bakinta tai shiru kawai tare da shigewa dakin ta, Ranan haka Hamza ya yini yana rawan kafa akan Sadiya ita ko sai wani nuna isa da gadara takewa mutanen gida ita a,dole ga matar so a gurin miji, Abin yana matukar bata min rai irin yadda yake nuna mata fifiko a fili a gaban kowan, Washegari kuwa wajajen karfe goma na,safe nafito a cikin shirina na nu fi kofan mama nake ce mata zan tafi uguwa tabar abinda take ta leko tana ce min yau za a uguwa ne nai murmushi nace eh amma ba dadewa zanyi ba, Na nufi kofan dakin Umma yana a rufe har zan fita sai nai shawaran na kulle kofan dakina kawai, Na ja kofan dakin na rufotare da,sa padluck na rufi na fita zuwa gidan mu ina gap da zan shiga gidan namu sai nai wani tunen cewa Ummi tana fama da kan ta zan kai mata wani bakin ciki a cikin kishiyoyi masu jira suji gwam, Take na canza shawara na juya na nufi gidan Anty Hindatu tare da kokarin tare mai yar mashin, A cikin wani irin yanayi na fada gidan saboda irin yadda naita tunane ina saman mashin, kafin na iso, Ko Sallama ba irin wanda na saba yi ba idan na zo mata na yau daban yake da na kullun, Tana zaune a kasan ties din dakin ta ga cup din da ta sha hura mai sanyi da kankara daga gefen ta, sai plate din da taci indomie a dayan gefen nata, Ina shiga dakin sai ta bini da idanuwan mamaki lokaci daya taga duk na canza mata a fuska, Zubewa nayi saman daya daga cikin kushin din dake dakin cikin muryan kuka nake mata ina kwana, Ta dago kan ta tana kara yi ma yanayi na kallon mamaki, tare da saurin gyara zaman ta da kyau, Idanuwan ta kyam a akan fuskana tana kokarin nazarin yanayi na tare da,son tambayana ko lafiya, Kamar jira nake tace Aisha yau kuwa lafiya kike haka sai kawai na barke mata da wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai jinta, Wani irin gululun bakin ciki ne yazo mata a makoshi don ta,san cewa yau da magana ke nan don yadda ta sanni da hakkuri amna yau ta ganni a haka, Wani irin sanyayan ajiyan zuciya ta sauke tare da mikewa zuwa inda nake zaune tazo ga kujeran dake kusa da,wanda nake zaune ta zauna, Cikin sanyi murya ta iya bude baki da kyat don tausayi na tana cewa , Ki natsu Aisha muyi magana don wanan kukan bawai zai maki mafanin abinda ke damun ki bane, Aisha nasan cewa kin yarda danine shiya sa kikazo guri don komay je damun ki nasan ba karamar damuwa bace tafito dake har kika shiga irin wanan yanayin damuwar, haka, Duk maganan da take min acikin nuna damuwar ta gare ni bai sa na dakatar da hawaye da sheshekan kukan danake yi ba mai tsuma zuciya, Dafani ta dan yi kadan tana,fadin Aisha wanan kukan da kike yi ai wani sabon damuwa ne kika korin jawowa kan ki, wanda zai iya maki illa ko jawo maki wani nakasar rayuwa, don haka kibar kukan nan muji mai ke faruwa, Na yi kokarin ganin na,dakatar da,kunkan danake amma,sai dai ina zuciyata ya kasa daina bacin ran da take tare dashi, Tsayin dan lokaci muna zaune a haka ina rera kukana, tana zaune daga gefena tana kallo na acikin tausaya har tsawon wani dan lokaci Kaina yana kife a makarin kujera nadan samu na,sasauta kukan bayan nayi mai issata yadda nake so tana zaune tana kallona don tasan yin kukan shine dan samu sanyin zuciyata, Nadago kai tare da cewa cikin muryan kuka Antu Hamza so yake yakashe ni a gidan nan wallahi, Duk irin hakuri da nake kokari yake suga,karshe na kawai, Anty na,rasa yadda zanyi duk wani shawaran da kuka,bani ke da,su Ummi ina kokarin ganin cewa na yishi don kawai a zauna lafiya, Amma yanzu abubuwan da suke bullo min dashi yafi karfin tunane na wallahi sai a gurin mama nake dan samun sauki a gidan Ita kuma mama bawai wani power ne da ita yanzu ba a gidan don saboda Sadiya Umma bata ragawa yar uwar ta ko kadan, Nace cikin wani sanyin murya yanzu anty don Allah ace kwana kusan tara ina fama da wani irin ciwaon mara mai wahal dani a gidan na fada mashi amma sai yai banza da,al,amarin, Jiya ina jin wai Sadiya tana ciwon kai acikin daren nan yafita zuwa sayo mata magani, Ire iren cin fuskan da suka kamaci wanan agidan su nake yawan fuskan ta a kullun Na koma dani da banza duk daya a gidan gurin shi da yan yan uwan shi har mahaifiyar shi, Don Allah Anty ki fada min may Anty may zanyi wanda zan kwaci kaina daga wanan masifan daya bullo min kuma, Ni da na yanke shawaran cewa nabar mashi gidan shi kawai duk da nasan cewa zama a gurin Ummina wani sabin tashin hankaline a gare ta to amma anty hakan zai fi min sauki gara na koma can sokoto gurin dangin mahaifina zaifi min sauki wallahi, Cikin sauri ina kai nan na ji Anty tace kada kifara zancen barin gida don wata banzan Sadiya Aisha, Duk abubuwan da kikaga yana faruwa a gidan na,dan lokaci ne don ramin karya kurarece wanan abin bazai dore ba, Idan kin kara hakkuri komai zai zo ya,wuce tankar ba a yi shi ba a gidan, Nace cikin sake hawaye anty wallahi, ni banga alamar wanan abin zai kai karshe ba don kullun da,sabon fitinar da suke bullo min da shi a gidan amma ina hakkurewa, Gani ban iya fadawa kowa halin da nake ciki don nasan kishiyoyin Ummi ne zasu fara yi min gwai, don shine ko ita Ummi ban iya fadawa halin da nake ciki a gidan, Girgiza kai Anti tayi tana cewa kada ki fara ki fada mata komai ki kara dai daurewa na dan wani lokaci kiyi hakkuri mugani, Ke dai ki kara rungumar addu,a ki sanyayawa zuciyar ki komai ki kara kawar da kanki a kansu, Insha Allahu addu,a ita makamin muminine, babu abin da yafi karfin Allah, Shawara daya ce da zan iya baki shine ki dan yi tafiya zuwa gurin yan uwan mahaifinki din da kikace don ki dan basu wuri Insha Allahu dagawan ki gidan zai kara saka su kowa ya fahinci halaiyar dan uwa don yanzu ance mugu kariyan na gari,, Don haka ba yanzu ba idan an kwana biyu zaki iya shirya tafiya ki zuwa sokoto din,, Wayan tane akakira don haka sai ta dakatar da maganan da mukeyi take wayan ta, Hakane ban san lokacin da barci yai awon gaba dani ba ganin barci ya daukeni yasa ta mikewa tabarni don ta fahinci barcin ma ban samun yin shi a,wadace, A waje maigidanta ya samay ta zaune fuskanta kawai ya isar mai da sakon bata a,cikin dadin rai tambayan ta yake cikin nuna kulawan shi da,damuwa a gare ta, Nan take mai bayanin abinda nazo dashi tare da sake zance akan dalilin da yasa matan yanzu suke gudun kishiya ke nan, Don a yanzu in ba Allah ya gyaraba duk wace zata shigo ita gurin ta shine ta ture macen da zata samu a gida, Don a,ganin ta tunda kekin yi lokacin ki da,miji ai yanzu turned dinta,dole ke uwar gida ki bar mata miji kwatakwata don ke angama dake take gani tunda har miji ya kara auro to to bai kaunar ki ko ra,ayin ki ne, Tace cikin bacin rai tare da nuna damuwa karara a,fuskan ta ke cewa yanzu don Allah honey har nawa Aisha take da,za,a ce wai hamza yana kokarin jefa rayuwan ta a,cikin wahala irin haka, Yarinyar da ,bata ko kai shekara Shirin da wani abuba akewa,wanan irin rayuwa haka, Ganin yadda ta dage take sababi da abokin shi kuma yaron shi duk da yasan cewa Hamza din baida gaskiya yasa shi cewa yanzu ina Aisha din take ta nuna mai daki su ya dan taka daga tagan su ya hango ni kwance nadan kifa kai a kushin ina barci shima tausayina ne ya kamashi ya dawo inda Hindatun take zaune ya zauna daga gefen ta a hankali yana fadin cewa, Yanzu kinga dole ne mu taimaka mata don ta tafi asibiti a diba lafiyan ta, sai kuma ki tambaye ta idan akwai wani abinda za,a taimaka mata zaki iya dubawa idan muna dashi sai a bata tayi hakkuri, don shi Hamza na,rasa gane may nene matsalarshi da zaidinga gallazawa yarinyar mutane haka, Ai ba a wasa da ciwo balle ciwon maran da tace irin haka, yana yawan damuwan ta, Ya na kokarin tura hannun shi a aljihun rigar shi yake cewa yanzu karbi wanan ki bata tayi hakkuri da shi taje asibiti a fara duba lafiyan jikin ta a gani,, Sun dan dauki lokaci a tare suna hira akan zance rayuwan auren na da Hamza ban ma san sunayi ba don ni barci na kawai nake ta kwasa saboda dama can ina da bashin barci a idanuwana Fitan maigidan nata tai dan guntun tsuki tare da yin tir da halin wasu maza da basu da tausayi a kan mata su sun dauka mace kamar hullace zakayi iya amfani da ita a lokacin da kai ra,ayin ta, Da zaran ka gama da ita,sai abubuwa su dinga tafiya a,slow ta tuna ranan da Hamza ya fara kawoni gidan su gwanin ban sha,awa kamar zai lashe ni, Gashi duk wanda ya gan mu a lokacin yasan cewa mun dace da junan mu sosai dan auren yayi muna matching saboda akwai dan tazara a tsakanin mu ni dashi, Amma ita wanan da yake cewa wai amarya za,a iyacewa sa,an juna suke da junan su a gurin haihuwa amma wai shine har yake rawan kafa a kan ta, Lekawa tayi ta tagan ta inda ta hangoni kwance dunkule a saman kujera na dunkule waje daya ina ta sharban barci a hakanan, Girgiza kanta tayi ta juya zuwa kitchen don duba girkin da ta dora tana cewa haka kawai an dagwara wa yar mutane damuwar da ba nata ba akai, Duk hakkurin irin na yarinyar nan sai da yau aka kai iyakarta wanda dama so ake aga iyarkata a gidan, Yanzu badon Allah yasa tai dabaran zuwa nan gidan ba da Allah kadai yasan abinda zai iya faruwa da ita, Ga yarinya mai hakuri ladabi tsabta addini sanin yakamata, zakace ba karamar yarinya bace da,wanan halin ,duk an kuntata mata tabi ta ramay ta bushe a tsaye kamar wace ake miya da ita, ****** ********** ****** Tafe yake a,saman mashin din shi yana dauke da ledan da,ya,sayo cefanen kayan miya a cikin sa, Yana aje mashin din ya dauki ledan ya karasa dashi cikin gida tun daga nesa ya hango kofan dakin Aisha kamar a rufe yake, Bai kara gaskantawa ba,sai da ya iso gap da kofan ya hango kofan a rufe har da makulli jikinsa, Sadiya wace jin karan mashin din shi yasa ta fitowa dauke da buta don ganin may ya shigo gidan dashi a lokacin, Don idan bata fito ba bazata ga may ya shigo dashi ba don dakin Umma zai shiga dashi, Sai da ya aje kedan kayan cefanen yafito daga dakin tambaya yake yana duban kofan dakin dake a rufe yana fadin , Ita wanan ta fitane kofan ta yake a rufe ko yaya akayi ne wai ? Au kai baka san da fitan ta bane dama nima na shigo gidan na samu kofan dakin a haka nake tambaya ina ta tafi, Wani iri yaji a lokacin don gaskiya ban taba fita gidan ba bada izinin sa ba, Shiru yayi yana,tunane a zuciyar shi to ina Aisha ta, tafi batare da sanin sa ba haka, yau, Muryan Sadiya ce ke cewa nadai ji lokacin da takewa mama Hafsi salama da zata fita, Yanzu ai ta isane don shi har zata fita batare da umurni ba kamar matar bariki, Batare da ya tankawa kowansu ba ya shiga dakin Sadiya yadan, zauna jim na tsawon wani dan lokaci sai gashi yafito, Tana tambayan shi ina zai tafi da wanan ranan haka sai yake ce mata muyi da wani abokina zai zo ya samay ni a wanan lokacin, Amsan da ya bata yadan kwantar mata da hankali don yasan cewa ta tambayane don taji idan ne man Aisha zai tafi, yi, Shiko yana fita ya hango yaran gidan mu a kofan gida suna wasa yake tambayan su da cewa kai Aisha tana cikin gidan nan ne? Yaron yadago kai yace wa anty yar agwai kake tambaya yace eh aciki bata rai, Bata shigo ba don yanzu na shiga gida babu kowa a gidan mu sai su maman mu kawai ne a gidan, Rai a bace yana jin daci a zuciyan shi ya koma cikin gida itako sadiya tana tambayan shi wai har bakon yazo ne yace wai yazo ya,wuce ina cikin gida, Kwance yake amma yana sauraren ko zaiji dawowa na har akai sallah azahar baiji shigowana ba gidan, Sai wajajen karfe biyu Anty ta shigo dakin tana aje kayan abincin da ta sa min a kusa da inda nake kwance, Motsinta danaji yasani farkawa gami da dan bude idanuwa na da su kai min nauyi saboda barcin da nayi, Kin farka injin Anty Hindatu take ce min da taga ina motsawa, na karasa bude ido da salati a bakina ina fadin ashe nayi barci ne dai haka da yawa tace cikin murmushi kin kai kusan awa uku da wani abu kina barci fa, Ki tashi kici abinci kiyi sallah sai ki koma gida har yayan ki ma ya shigo ya,samay ki kina barci, Nace da sauri cikin dago kai ina kallon yaya mansur ya shigo ashe tace eh a daidai lokacin da take kokarin zama saman daya daga cikin kijerun dakin, A gaskiya baiji dafin abinda Hamza yake maki ba sai dai yace kiyi hakkuri zai samu lokaci su zauna dashi, Nace ai da ya bar shi kawai idan an kwana biyu tafiyana zanyi kawai naje na huta anty, Yanzu kici abinci sai ki shirya ki koma dakin,ki ga kudi nan yabar wai abaki kije asibiti don kudin basu da,wani yawa,sosai, Idanuwa ne suka ciciko da hawaye don tausayin kaina nake cewa cikin murya mai rauni, Har da wani dawai niya bayan wanan mutuncin da kukai min kun mayar dani tankar wata yar uwar ku ta jini, haka Hindatu tace kai haba Aisha ake yanzu yar uwar muce ta jiki don Allah yariga da ta hadamu ko da ke, Zan fara sanar tawa kuka tace cikin daure fuska dakata da wanan kukan naki Aisha maye na kuka dubu goma ne fa kawai ya baki don baida kudi yace a hannun shi, Cikin zaro ido tare da tambayan ta da,sauri nace har dubu goma anty shine ba yawa, Wanda ya ajeni ko dari daya ya kasa bani naje a duba lafiyata sai kawai na,sake kuka sai danayi ya isheni, Na mike na shiga bandaki don inyi alwala tace min shiga kiyi wanka dayani sai kiji dadin yin sallah kici abinci, Ban mussa ba don dama ina bukatan jin sanyi a jikina don haka na,watso ruwan koda nafito nasamu wasu sabbin tufafi a saman gadon ya ta aje min na dinkin dogon riga nawasu material masu kyau sabbi wai ta dinka amma sunyi mata kadan, Nasa sai dinkin yai min das a jikina kurciyana yafito tsam a cikin kayan na zauna naci abinci sama sama itako tana akan bakin ta tana bani shawaran cewa, Idan na koma kada na nuna wani bacin rai din idan muyi sa,in sa dashi zai su ji dadi ne don dama ana jiran ajimu ne dashi, Munyi sallama tana nanata min cewa nayi kokari na tafi ganin likita don nasan abinda ke damuna, Ban tafi gida ba,sai da na tsaya wani kayon chemist na BLB nai masu bayanin yadda naje ji suka ban magani na kashe dubu biyu da dari hudu na hau mashi zuwa gida, dauke da leda na dake dauke da tarkacen kayana aciki, Hamza ya fito don fita waje fuskan shi kicin kinci a daure sai mukai kicibis dashi, Ina kika shigane haka tun da safe ba wanda yasan inda kika tafi, Na sunkuyar da kaina kasa nace mashi natafi asibiti ne don marana ya damay ni da ciwo sosai da dare ban samu yin barci ba, Idon shi a kan ledan da ke a hannun inda ya hango maganin da na,sayo Ban ji dadi yadda zaki fita gida batare da sanin kowa ba har tsawon wani lokaci haka, Nace cikin sanyin murya babu kowa ne a kusa lokacin kuma maran ya matsa min da ciwo natafi can kuma sai na samu layi da yawa, Baice min uffan ba,ya dan rabani ya wuce wani haushine ya kumay min zuciyata, Dafa kan da zan yi na hango idanuwan Sadiya da,Asamau a kan mu suna tsaye suna kallon mu, Asmau ce take ce min ina kika shige haka tundazu ba wanda yasan kin fita, Ina kokarin ciro key dina a yar post dina nake ce mata shi ai yasan na fita ya dai mantane kawai, Ai dole ya matan tunda hasken zuciyar shi bata gidan duk yabi yawani damu mutane wai ta fita bai sani ba, Sadiya ce take fadin haka a lokacin da take kokarin juya tashige dakin ta cikin haushi, Allah nagods ma nace tare da fadin wai Anty hindatu Allah ya,saka maki da,alheri dama ance ta yaro kyau yake baya karko, Da nabita nawa shawaran dana yanke da yau anji mu a gidan nan anyi min dariya, Ban bi ta kan abincin su ba don dama ba aimin tayi ba naci gaba da harkokina tare da shan maganin da aka bani a kemis, Alhamdullahi zance don gaskiya naji ciwon yai matukar lafa min don na daina jin shi kamar baya, can, Da dare ya shigo dakina ya bayan yai komai kamar yadda ya,saba yi zai kwanta naji ya ce min Daga yau na fada maki kada ki kara fita gidan nan batare da sani ba don bazan dauki wanan ba a raina, Nace amma na fada maka zancen yadda nake ji a jikina kaki ka,saya min koda dan paracitamal nasha, Amma gabana ka fita zuwa sayawa Sadiya maganin ciwon kai yaya kake son yi da raina so kake na zauna haka ciwo yana cina a gida ba magani, Sai na sa kuka irin mai tayar da hankali ina fadin nidai kagaji dani dama can ba wai ina cikin ranka bane Ni banda kowa a gidan nan sai Allah sai kai sai ko mama hafsi wace ke dan nuna min kulawanta a kaina, Kai din kuma yanzu ka dauko min wullakanci a gaban kowa yadda ranka yaso, idan ban fita na nemo magani ba mutuwa kake son na zauna nayi kuna kallona har kukai ga yadda kuke so, Shiru yayi can yace bana ki kaiki asibiti bane bari nayi nadan samu kudi a hannuna sai muje asibitin,, Ban tanka mashi ba shima bai kara magana ba don ganin yadda nake kuka, Washegari bai fitaba da,wuri don yana son gyara min zuciya, ina jin yadda Sadiya take daga muryan ta don kawai yaji motsinta yafito daga dakin, Duk da ba komai muke adakin ba ina zaune na tsure shi da idanuwa bai fito ba saida yai mashi dadi ya fito daga dakin yai wanka yafita Kwana biyu mun dan sake jiki kamar ba komai a raina wanan sakewan da Sadiya taga tai kaman zata kama da wuta don taga kamar ina a cikin farin ciki ne, a gidan ita, Sannu a hankali nadan hada kudin tafiyana inda na samu zuwa gurin Ummi na fada mata,shirin da nakeyi na tafiya zuwa gurin dangin mahaifina a sokoto, Ummi bataji dadin hakan ba amma kuma sai daga baya take cewa hakan nada kyau tunda suna iya kokarin su a kaina, Itama mama Rahana nasamay ta da zancen inda tai amanna da wanan shirin nawa da yi min fatan alheri a kan hakan da zan yi, Sai bayan kwana biyu ranan da nake da girki nai mashi magana akan ina son zuwa sokoto na duba yan uwana, Yace yana,son sanin dalilin tafiyan da zan yi nake ce mai wan mahaifina da ya rasu nake son naje nai masu gaisuwa sai kuma na gaida sauran dangina na can, Shiru yayi kamar mai nazari azatona zan sha wahala gurin yardan shi sai naji yace kwana nawa zakiyi idan kin tafi, Nace zan yi kwana goma ko sati biyu idan an yardan min da haka din , Ba matsala zaki iya sati biyu sai ki dawo idan kin shirya sai ki fada min lokacin da zaki wuce don na sani, Nace ni ai ko gobe ne kace zan iya tafiya don a shirye nake ko yanzu, Au ashe ma har kin gama shirinki ni ban sani ba nace a,a ni bawai na shirya bane naga ba wani dogon shiri ne zan yi ba ai, Ya zuba min ido yana kallona yake cewa ki bari ranan Jumma,a mai zuwa saiki tafi Allah ya kaimu nace mai, Nan nafara shiri na ba,wanda ya,sani a gidan sai dai kafin na wuce nake jin wai cikine da sadiya ashe sai shafwaba taje wa mutane suko duk sun mutu a kan ta, Duk da naji wani abu a raina lokacin da na samu labatin ciki amma sai na daure naba kaina hakkuri don ban son na zama mai hassada da iyin Allah, Habaici ko da magana na,shagube a bakin Umma,sai abinda ya karu nai kamar ban fahinta,ba, Abakin Hamza sukaji zancen cewa zan je sokoto gurin mahaifana don an min rasuwa, Umma cewa tayi bana an tuna ana da yan uwa ke nan ashe zasu bakuwan yayama ai karo karo a sallamo bakuwa dashi, Nidai ranan Jumma tunda safe na shirya saida na shiga gurin Ummi nai sallama dasu na kuma fadawa baba mudi yana tasamin albarkan cewa na kyauta da zanje na dubosu, Nai sallama da kowa na kama hanyan zuwa sokoto ni kadai a kato na farko da zan tafi gidan iyayyena mahaifana, Barkan mu da shan ruwa yan uwa da fatan samun rahaman ubangiji a tarw da mu, Kutayani addu,a dafatan samun nasara arayuwan mu baki daya,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, Nasamu saura mutum biyu motar sokoto ta cika shi da kan shi ya kai ni tasha a,saman mashin din sa, Don har nafito da kayana inawa mutane sai na dawo sai gashi yafito daga dakin Sadiya yana sa aninaiyar rigan shi tare da, gyara kwalar rigan shi, Inda na aje kumshin kayan da,zanyi tafiya dasu ya nufa ya dauka ya daure su a bayan mashin din shi ya dauko, min yar troler din da kayana,suke a cikin sa ya aza a gaban mashi na hau baya muka fita sadiya ko lekowa batayi ba da zan fita, Amma a lokacin da yake daki na tsaya daga kofa nai masu zan tafi Allah ya,sada mu da alherin sa, Amma hakan nai sa tai min magana ba ta na ciki taki fitowa daga dakin nata muyi sallama, da ita, Ina shiga motan ko minti biyar ba ayiba saiga wata mata da yaran ta ita ma ta zo sai motar tai batun tashi, Ya zaro dubu daya,daga aljihun shi yace nai kufin mota dashi nai mashi godiya na shiga motan baya mu mata biyu da maza biyu muka zauna, a makure, motar ta,daga,,, Tafiya muke yayin da nake tunanen irin yadda zamana da mutanen gidan mijina yake gudana mutanen da zance nake rayuwa da su yanzu, Na gyara zama ina tausayawa kaina irin yadda duk kyautatawan da nake masu agidan basugane min sai ma kara samin kiyayyan da suke a kan samun sadiya wace ke zaman ci masu mutunci amma basu gani, hakan, Mota tana sauka sai na tuna yadda mama Rahana tace min sai nake tambayan ko za,a samu motan zuwa kauyen mu, Aka nuna min gurin da motacin da zasu kaini Illela, ko da mun isa illela kuma sai na samu mashin din da zan hau ya kaini Burkusuma, Ranan haka na yini a hanya sai yamma lissa na isa garin ina ta mamaki kuma banga laifin Ummi ba da taki zama a garin ta kashe auren ta da mahaifina da dan ruwan cikina, Wanda yafito garin jega da sokoto za a dauka akai wanan surkumin kauyen aure ace yai rayuwa acikin jeji irin haka, Na tambayi gidan Liman Lawal tsoho kamar yadda mama Rahana tai min kwatancen idan naje garin, Gidane irin na kauye ginar shigifa na jan laka katangar gidan ma jar lakace akayi da ita duk yaddan darje baida wani tsawo sosai, Har gap da kofan shiga gidan mai mashin din ya,saukeni tare da kayan da nai tsaraba dasu, Ina tsaye sai ga wasu yara sun fito daga cikin gidan dauke da kwano wai suna tallar bakuru, Nace don Allah kuzo ku taimaka min na,shiga da kayan nan ciki ba mussu yaran kauye suka zo da sauri suka kama min muka shiga cikin gidan da kayana Matan gidan suna a guri daya suna aikin girkin dare kamar yadda matan kauye suke yin aikin su a hade guri daya, Nashigo masu da sallama duk idanuwan su ca akaina suna min kallon mamaki gaba dayan su don basu taba sani na ba, Nagaishe su da aiki tare da masu ya gida da kuma lafiyan kowa, Wata baka ta daura dan kwali waware bakinta ja take cewa boyar Allah daga ina haka ? Murmushi na dan sake har sai da dimple dina ya dan lutsa kadan nace don Allah ko gwago Talatu tana nan, Da hannu suka nuna min wani bukka ginan laka mai tabbaibayin haki a saman dakin can na,nufa tare da yaran nan yan albarka biye da kaya a bayana, Gwagona ta fito don yin wani abu dauke da roba a hannun ta sai ganina tayi a gaban ta, cikin mamaki dauke a fuskan ta tace shin Idon ta naka gani ko mafalkina nakai, Cikin murmusawa tare da,sauke kayan dake a kan yaran da muke tare nace nita Gwago, Mun samay ku lafiya tace keta tahe bamu da labari,lale marhabin da zuwan , Yaran zasu tafi nace su dakata, na bude wani leda na dauko sabulu da clean na basu suka tafi suna murna, Daki aka, shiga min da kayana,suna haba haba da zuwana nan matan gidan suka fara shigowa daya bayan daya suna min sannu da zuwa, Gwago Talatu tana fada masu cewa ni diyar Abu ne kanin ta da suka haifa da Ummi na, Sai mamaki suke su na kallona nan naji wata tana fadin ai ni tun shigowar ta naga kama don kamar ta ya baci dana mahaifinta, Kafin wani lokaci an kawo min abinci tuwon dawa surfafe da miyar kuka sai kamshin man shanu ke tashi , Ban tsaya wani tsandaba tunda nima sunan ina birni ne kawai na ci abincina saida na koshi dam, Sai dare iyayyena maza suka dawo daga kasuwan nin da suka tafi ci, tun safe, wasu kuma daji suka tafi aiki, gona,kin su, Suma an gabatar masu dani a matsayin diyar dan uwansu da basu san ni ba, yau gashi nakawo kaina a gurin su, da kaina, An fada min sunayen su an kuma nuna min matan su da ma wasu yaran su, Sai na fahinci a,bayanin gwago mahaifina shine karamin su a,dakin su don su biyar ne dakin su mahaifiyar su ta,bar su a gidan, Sauran mutanen gidan duk yayyensu ne sun takwas sai dayan dakin mai mutum bakwai, Nisawa nayi nace amma gwago ashe yawa ke gareku haka tace ai wasun su sun rasu wasu kuma sun fita daga gidan suna wani guri zaune, Washe gari aka fara kaini gidajen yan uwa muna gaisawa dasu suna nana cewwa ba su sanni ba nima din dai ban san su ba, Tun ranan da nazo nikewa gwagona duk wani hidima dana samu tana wa kanta irin su shara wanki har da, diban ruwa don amfanin mu, Sai dai ban yarda na zauna da kazanta ba don da zaran nagama aiyukana zanyi wanka na gyara jikina tas ba zakace nai wani aikin wahala ba, Wani lokaci nakan fita na taya su aikin girki muyi tare dasu wanan halin nawa ya ja min kwancinyan hankali da,farin jini ga kowa na gidan, Don kin san shi bakauye bai son bakon shi da girman kai ko daukan kai da jin cewa ni wani ne nafiki ko nafika wayewa, yanzu zakiga kun fara kai ruwa rana dasu, Basu girki da rana sai dai asha kunu da masa ko hura sai ganye idan an samu, da yamma ne za,a girka abinci kowa yaci, Ranan da na cika sati daya da zuwa garin su babana suke tambayana yaushe zan koma nake cewa kila zan kai wata daya ko biyu don mijina baya gari ya tafi kurmi gurin sa,na,a, Sunji dadin jin cewa zan kwana biyu a gurin su don haka suka sake jikin su , Da yamma ina taya su inna aikin girki sai naji sunyi cirko cirko suna magana a cikin jimamay cewa wai wata ke fama tun daren jiya take rusunne har ana zancen zuwa da ita asibiti, Kamar na kyalesu sai dai na tambaya ko wacece suke ce min ai matar wani dan babana ne dake can farkon uguwa inda yai ginan shi, A hankali nace da zan ganta aida na duba masu ita nagani sai take cewa Ke har fa Yunusa likita ankira ya dubata yace a kaita asibitin illela a agani don abin yafi karfin shi, bazai iya ba, Nace namiji aka kira ya duba mace mai haihuwa sai suke ce minbai shine likita don shine yaje yai karatu a birni, Tsam na tsamay hannuna daga cikin ruwan da nake tatse masu kamun kokon su, Jakar da,na,zuba magani na aciki da sauran tarkacen aikina danake bukata nace wa wata diyar wani babana da take gida zaune mijinta ya rasu, tana zawarci da ta rakani, gidan naga mara lafiyan, Mutane ne gidan ancika fuskan kowan su babu dadin gani don basu a cikin dadin rai sai faman shawara ake yadda za,a tafi birni da ita, Nake cewa bayan mun gaisa a can na,samu gwagona na ko zan iya ganin mara lafiyan kafin a,wuce da ita, Gwagona tace may zakiyi mata Ido, likita ma yace atai da ita can cikin gari aiki za ai mata, Ganin na dage cewa zan dubata yasa sukace a bari na shiga gurin mara lafiyan na,fara dubata, Tana cikin wani irin condition wanda ba,a,aon mai ciki ta kai a lokacin don bata da jini a jikin ta ga kuma maleria ya kamata, Nadan dubata da kyau naga yan matsalolin da suke damun jikinta don haihuwan ba,zai iya zuwa mata a lokacin ba sai ta dan watsake tukun na, Tausayin mutanen muna kauye naji irin yadda ake ta masu abu a cikin duhu ba tare da sanin gaskiyan al,amari ba, Nakira mijinta da,wasu daga cikin iyayyenta nai masu bayani wasu sun yarda wasu basu yarda ba da zancen gaba daya, Don ba kudi suka yarda dacewa a gwada shawarana a,gani nai mata allura nabata yan kwayoyi na kara duba lafiyan cikin ta, Nace ya samo mata maganin karin jini abata don ta samu karfin a jikin ta amma sai yace min ai baida kudi nafitar da dari biyu nace a,sayo min sprite da tumatir din leda na hada na bata ta shanye su dukka, Sai ga mai na kuda takai kwance sai barci nafito mutane su kabini da idanuwa caaa nakoma gida, nabar su nan, Sai zuwa,magariba na koma gidan nasamay ta ta farka daga barci nace abata wani abu mai dan ruwa tasha koda koko ne ko shayi don tayi losing din afatay din ta bazata iya cin abinci ba mai nauyi sai harshen ta ya,warware tukunna, Tana sha sai wani irin zufa take karyo wa wanda ya nuna ta samu lafiya a jikin ta lokacin nai masu sallama na,dawo gida, Haba zance sai yafara yadawa ai wata,bakuwar likita tazo gidan Liman tsoho tunda safe wata,mata ce ta tayar damu wai na,duba mata lafiyan yaron ta yaki samun karfin jikin shi, Tun wanan lokacin na zama wata mai kula da lafiyan yan uwa da abokan arziki Da yake kauye ne sai gashi wanan Yunusa likita yai karana a gidan mai gari cewa na, zo gari ina son cutawa mutane ban da takardan kare karatu irin nasa, Sai da magana tai magana koda ya fitar da nashi aka,duba nawa sai akaga ai nafishi ilimi sosai shi course kawai ma ya yi ba karatu ba, Nakuma basu hakkuri da cewa ni yan uwana nake dubawa bawai sana,a nazo yiba agatin don bazan dade ba zan koma, Nan ake fadawa maigari koni diyar waye a cikin garin yace Allah sarki yarinya kinyi kokari da kikazo duba yan uwanki Allah kuma ya baiyana muna inda mahaifinki yake idan yana raye, kowa ya,amsa da,Allahuma Ameen, Ranan da na ce matat dan uwana zata haihu sai gashi cikin yardan Allah ta sauka lafiya inda na karbi haihuwan ta, Sai dai na lura da ina,shakan karnin jinin nan duk sai naji jikina ya sake ba shiri nai mata abinda zanyi na koma gida a gagauce na ta shega amai dole na sha magani don ina gani nima maleria ne ya kamani, Da safe a cikin ikon Allah ya tashi wasai dani sai dai ban son shakar karnin haihuwan da a ji wanda acan baya ba haka nakeji ba, idan ina karban haihuwa sai nake cewa watakila ita wanan nata jinin yana da karfine sosai, Alheri sosai nake samu akan wanan harkan hankalina kwance don tun ina tunanen gida hat yanzu na,saba da mutanen garin ban tunanen komai kuma again, ****** ********** ****** Karfe sha biyun rana ko abin karyawa ba,ayi ba agidan tana daki kwance abinta, Mama Hafsi tun da ta gane cewa za,ayi tsiya a gidan sai ta kwashi kayan sayarwan ta zuwa cikin uguwa, Umma wace ta dawo da zuman ta karya tun a gurin wanke wanke ta hango kaya kwanoni kuda nabi yooo, Gurin da na,saba aje mata abin karyawan ta tanufa sai dai babu komai sai sauran tuwon jiya dake acikin wani kwano duk ya bushe yayi bawa ga kuda na bin su yooo, Daga inda take tafara kiran Sadiya Sadiya Sadiya , Sadiya wace take kwance tana ta kwasan barcin ta hankali a kwance taji iri kiran da Umma ke mata ta farka a gigice tana cewa lafiya wai haka, Ta bude labulen dakin ta tana cewa a,a wanan ir8n kira haka kamar wani tashin hankali, Ni wallahi ban son idan ina barci a dinga tayardani ban tashiba sai kaina ya dinga ciwo daga yau kada a kara tayar dani idan ina kwance, Baki a bude Umma tace Sadiya kan ki dayw kuwa ? Ni kike fadawa wanan magana haka ba ko jin kunya , Kunyan may fa don na,fada maki abinda ban so ban kuma ra,ayin ana min shi, Eyy lalai kuwa kin kai ashe baki da kunya ban sani ba haka , Dama shine, dalilin kiran to ban girka ba don bashi nazo yi ba dama ta juya ta,shige daki ta gyara saitin fankan ta na kasa don ya bata iska da kyau, Umma tana tsaye sororo cikin mamaki tace a ranta ashe haka yarinyar nan take batada kunya ko kadan a rayuwan ta, Ga yunwan da,take ji dole ta nufi gurin murhu ta fara hasa,wuta don tasan cewa, har da yaranta dole su ji yinwa don sun saba karyawa duk safe da dumamay tuwo ko koko da kosai, Tana can tana tunane ta tabo wutw da hannunta da,sauri tafara yarfar da hannunwanta don zafi daidai lokacin Ibrahim ya,shigo gidan yana ganin abinda ya faru yake cewa Umma lafiya ? May zakiyi a gaban murhu kuma yanzu da wanan uwar ranan haka ? Rai bace ga,zafin wutan da ta taba yana kona mata rai taceczan nema munw abin karyawa ne, A,a ita Sadiya bazata fito tayi ba,sai ke tace tace batw jin dadi shiyasa nafito ni nayi, Duk wanda ya shigo ya tambaye ta,amsa daya take basu shi dai ibrahim bai yarda ba yasan halin tsiyan sadiya ne ya motsa mata, Sai ma fita da yayi a gidan don bai iya ganin takaici yace a ran shi, Harshi uban tafiyan Hamza yashigo ya,samu ummu tana kashe kunu a gaban murhu tana gamawa ta mayar da,wutan abinci sama, Can sai ga,Sadiya da cup din ta bata jira ma Umma ta zuba mata ba,sai ta,shiga diban kokon da kan ta, Umma tana futowa taganta a duke agaban roban kunu tana diban kokon da kanta, Ikon Allah wai yaya hakane kuma da zakizo kina diban baki ko iya jiran na,zuba maki, Wanda ta diba sai ta mayar ta nufi daki da cup dina hannun ta, Tana,shiga daki Hamza dake kwance yaganta da cup tazo ta zauna a tunzure gaban shi tana huci yake cewa wai may nene kuma, Sai kuka tafara cewa harda abinci kuma za aimin iyaka dashi don kawai anga banda lafiya ban dafa ba, Rai bace yafita yana cewa haba Umma yanzu kuma don bata da lafiya shine kunun mw baza,a bata tasha ba sai a hana ta duk da lalurar dake a jikin ta, kuma, Ikon Allah ita Sadiyan tace ma na hanata kokon ko kuma kai, Yace ai shike nan bari na fita na,samo mata dan abinda zata ci kada ta zauna da yunwa a jikin ta, yai mata illa, Sai kawai yafita yana cewa gaskiya ni ba ai min adalci a gidan nan duk kokarin da nakeyi sai an muguntawa iyalina,, Umma tabi Hamza da kallon mamaki akan Sadiya da itace ta nema mashi auren ta yake mayar mata da magana agaban sauran diyan ta, Jin yafita yasa Sadiya fitowa da buta a hannun ta tana wani fisge fisgen kai, da tafiyan gadara wai ita an cuta mata a gidan mijinta yai cin mutunci, Yadawo dauke da leda mai take away a cikin sa yawuce dashi daki duk suka bishi da idanuwa Can bayan ta gama ci sai ta jefo ledan take away din ta tsakar gida miyar agusi ne da sakwara taci, sai ledan pure water mai sanyi da gwagwanin multina, Ranan Ummatakai matukar hasala,da Hamza duk yadda,taso taboye bacin ran ta abin ya,faskara,dan sai da ta nuna mai hasalan ta a fili, Sai taga dama zatai masu girki ko shi sai idan Hamza ya lalashe ta don ya gaji da,sayo abincin kasuwa kullun, Umma tana ganin ikon Allah ranan Sadiya tsaye tayi tace ita bazata karbi abin girki a gurin Umma ba don ba Umma take aure ba dole kayan girki yadawo gurin ta daga ranan, Umma kamar zatayi hauka don ta hango Sadiya zata raba ta da dan ta gaba daya idan tai sake, Ga aiki yanzu kamar zai kashe ta agidan komai sadiya bata yi wai ita mai ciki ce sai abinda take so zata ci, Shagwaba sai yadda tayi da kowa a gidan shiko gogan baijin kunya gaban kowa,sai faman tarairatan ta yake kamar zai goya ta a bayan shi, Yanzun ma ko fita ya,daina yi sosai koda yaushe suna tare sai bakin jaraba da,sukeyi dare da,rana, a daki, Tafiya ya kamshi dole ya tafi baxon yaso zuwa ba kwanan shi biyar a can yadawo, Yasamu Sadiya tayi kaca kaca da mutanen gidan nan ya hau sababi da yan uwan har yakai ya kira baba Madu kan azauna a sulhunta,su, Bayan amayar da jawabi ir8n rashin mutuncin da Sadiya takewa Umma har yakai yaranta Jibrin da Ibrahim sun ki yarda sunyi niyar lankada mata dan karen duka,sai da ta gudu zuwa gidan su, Shine ita kuma mahaifiyarta ta fito zuwa gidan da nata masifan na aka rikice har mama,Sa,a tana cewa Watau abinda takewa Yar Agwai shine yakawo a kan yar ta to ita gaskiya bazata iya dauka wanan cin fuskan ba wa yar ta, don ita yarta tana da gatan ta, Ibrahim yace oho dama,ashe don bata da gata yasa kika dauko yar iskan yarki kika cinnawa mutane mugun abu , Umma ta hana shi magana ta koreshi daga gidan don kada magan tai nisa sosai, Nan dai tace Sadiya ta koma ta shiga dakinta babu wanda ya isa ya kore ta a gidan tunda ba su ke auren ta ba, Bayan fitan mama sa,a da,tawagarta ne mama hafsi tace ni dama nasan ai za a rina don badon Allah akai wanan hadin ba tun farko, Anyine don aciwa yar mutanr mutunci yanzu kuma sai gashi ganwo ya juye da kaya akai, Aisha dai ta huta ai kwana biyu yanzu za,agani mai mutunci a cikin su Ba wanda ya tanka mata don ran kowa a bace yake a gidan saida yadawo ne su Sadiya da uwarta suka kwashi karya da gaskiya zuka fada mashi shiko ya hau ya zauna yana tawa mutane yankan kauna, Baba Madu yace haba Hamza yau ina hankalin ka yatafi da har kabari mace zata hadaka da mahaifiyar ka haka da yan uwan ka Sai lokacin ya dan sadda kan shi a kasa saboda ya dan dawo hankalin shi, Baba yace Hamza kada ka manta da irin dawainiyar da wanan boyar Allah tayi da ku a baya yanzu lokaci yayi da zata ji dadi a,gare ku, Musan man ma kai da da kowa ke yaba irin hankalin ka da kokarin ka, ga mahaifiyar ka da yan uwanka har da ma mu iyayyen naka, Ga mata yar arziki maikirki da mutunci da Allah ya hada ka da ita tun farko, Sai yanzu ne da rana tsaka zaka bata duk wanan alherin naka akan wata mace bakuwa Baba Sadiya ba bakuwa bace don ita yar gida ce don diyar aminiyar Umma ce, Koma,wacece bata nuna muna cewa ita ta gida ce ba don da batabar mahaifiyar ka tana aiki da kanta ba kuma tana ci mata mutunci, Duk inda yafito don ya kare Sadiya,sai baba Madu ya nuna mai rashin dacewan haka a gare shi har dai baba ya ce kai Hamza barin fada maka ba,a kyauta ba, Kayi gagawan bawa mahaifiyar ka hakkuri akan wanan zancen kuma a gyara, Ke kuma Rabi na dawo a kan ki kin san halin yaran yanzu kokai ka haifi abinka,sai kai hakkuri dasu don haka ki dinga kawar da idon ki akan matan yayan ki don yaran yanzu basu da mutunci, Don kinga a kwai banbancin rayuwa a,tsakani ita waccan ta farkon da,wanan da kika hada da hannun ki don haka sai kinyi hakkuri sosai akan irin zaman takewan gidan na dasu Allah ya kare ku daga duk wani sherin shedan daka iya hada ku fitina agidan nan kowa ya,amsa da,Ameen baba, Ya juya gurin Hamza yace ka,roki mahaifiyar ka gafara don ka ga,haske a rayuwan ka, Ya mike yana cewa ni nabar ku lafiya, Godiya,suka fara mai har ya,fara tafiya,sai ya ja ya dakata yana cewa wai ina ita,wanan yarinyan ban gan ta ba tunda na,shigo, Jibrin ne ya bashi ansa da cewa ta tafi garin su yau sati biyu ke nan da,tafiyan ta, A lokacin Hamza yadago kai ya dubi dakina wanda yake a rufe da padluck yana tunanen yaune fa ya kamata ace nadawo don sati biyu ke nan ashe, Baba yace Allah sarki Allah yadawo muna da ita, lafiya yarinyan tana da hankali sosai wallahi ****** ********** ****** Washegari Sadiya ta,sa habaici a cikin gida cewa oho dai gani nan bari nan tsakanin ta da Hamza dai sai mutuwa, Ko bata da,kirki dai dole a zauna da ita tunda mijinta yana son ya don wasu banza basu son ta ita ko ajikin ta tunda ba zaman su takeyi ba, Ba wanda yabi ta kan ta don duk sunji maganan da Baba yai masu a,daren jiya, Da kwana biyu ciwon baya ya kama Umma gashi dole ta dan gi wasu aiyuka da kanta don ko kallo bata ishi Sadiya ba, Dole zarah ce tazo daga gidan ta taiwa sister dinta,su Asmau fadan cewa gasu a gida har uwar su zata zauna tana ganin bakin ciki irin haka, Shi ke nan don Aisha bata,gida sai su su kasa zama su taimakawa umma sai dai itace zata dafa ta wanke iyakar su ci kawai, Mama Hafsi tace ai basu da laifi don laifin yaya ne da ta koya masu tun farko ai bazataga bacin rai ba, Sai dai ace yar mutane ne zata zauna taita masu komai su suna zaune yanzu ai gashi ankawo wacce ko kallo basu isheta ba, Zarah tacd ai yanzu dai kowa yaga ranan ita Aisha din don wallahi idan tana nan duk wanan abin bazai faru ba, Nan dai tai masu fada dole aka,raba masu aikin da kowa zai yi a gidan, Hamza ya,sayo wa Umma magani din tasha ta dan samu sauki tare da robb ta shafa a,gurin, Aiko take sadiya ta hade rai wai tana son ya,sayo mata fruits ta gyara, bakin ta tun jiya yaki sayowa yana cewa baida kudi, Amma ai gashi ya,sayowa Umma magani yanzu ina ya samu kudin da ya,sayo maganin dashi, Ba,wani ya,fadawa Umma ba ita,da kanta taji zancen da,suke saboda kusa da, dakin su yake, Ikon Allah inji Umma don tasan cewa Allah ya hada ta da mara kirkin yarinya, Gashi tana jin ana mata yaya jiki amma ko tace mata sannu Umma bata,samu ba,daga gare ta, Dole sai da Hamza ya,sayo fruits din sannan aka zauna lafiya a gidan ita dashi, Zarah wace ke kallon ikon Allah tace yanzu kan kin kai ga irin sarakuwar da kike so yar bana tunda kin ce Aish yar kauye ce yar tsiya da,sauran su, Duk da abin yai dan sanyi saboda mama ta je ta samu mama Sa,a akan tajawa yarta kunne don abinda take a gidan yai yawa sosai, Yau gashi sai aci dafa duka da dare don dole saboda tace ita bata iya wahalan tuka wa kowa tuwo da cikin ta, Bayan kwana biyu da Umma ta samu sauki tadan fito waje ta zauna don ta,sha iska, Sadiya tana daki tasa wakan hausa remix sai faman bin wakan take tanayi tana rawan ta, Hamza wanda ya dawo da leda wani yaron makwabta yana bayan shi dauke da leda yaron yakai ledan gurin da Umma take zaune, Sadiya ta dago labule tacewa yaron cikin tsawa kai kawo ledan nan nan, Umma ta dago ksi tace mata ni nada sakon a,sayo min dan ganye ne don na dan gyara bakina dashi, Ai baice min naki bane don haka nace akawo min don ban yarda ni da miji na ai min isa dashi don ni wallahi wanan mulkin ba a kawo min shi, Fitowa yayi daga daki yana cewa ke sadiya ki shiga hankalinki fa don bazan yarda da wanan irin cin fuskan da kike min ba, Mahaifiyata ce zata zama abin wullakantawan ki koda yaushe tace ita ce taba,da sako to maye kuma na jinini haka, Umma tace kyale ta babana akai mata ledan sai ta gyara ta juyo cikin yatsunan fuska take cewa adai bar maki ke k8 gyara , Aiko yai cikin ta kamar zai dake ta,ranan taga masifan shi saida mama tashigo tace ya kyaleta tunda yasan tana da lalura a jikin ta, Kofan gida yya koma ya zauna yai tagumi yana tunanen yaushe wai Aisha zata dawo, Kewan ta ne ya kamashi yarinya mai hakkuri duk abinda akai mata zata iya shanyewa ta hade a ranta batare da wani yasan anyi shi ba a gidan gashi yanzu dan tafiyan ta komai ya kara rikicewa a gidan dama ance mugu kariyan na gari ashe kuwa haka hausan yake, Zan dakata anan sai bayan sallah idan Allah ya kaimu sai muci gaba mu kara jin yadda abubuwan suka kaya tsakanin Hamza da iyalin shi Dafatan zamu sha ruwa lafiya Allah ya sadamu da rahamomin sa Allah yasa muna a cikin yantattatun bayinsa, Ayi sallah lafiya yan uwa musulmai kada ku manta kusani ga,addu,oin ku don Allah,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, Wasa,wasa watana daya da kwanaki a gatin mu sai a lokacin ne iyayyena suka fahinci cewa akwai matsala a tare dani, Dafarko sunji dadin zamana irin yadda nake kula da harkan lafiyan yan garin gida da,waje, Sai daga,baya da,suka,ji ban zancen tafiya ko kadan sai suka,fara tunanen ko akwai matsala a tare da nine, Ban boye masu ba,alokacin da,suka tuntube ni na,fayyace masu komai nan wani wan mahaifina mai saurin fushi yace aikuwa bazan koma ba,muddin bashi ya kawo kafan sho cikin garin nan ba , Sai yasan cewa ke ma ya ce kamar kowa kina da gatan ki, don bai dauke ki a gaban mu ba,shiyasa suke ganin kamar baki da gata ko, Wanan zancen yasa na kara sake jikina acikin yan uwa ina ta harkokin gabana batare da na,sa wani damuwa akan zancen ba a raina, Al,amari na kiwon lafiya take mutum ke samun alheri daga wanan fannin, don haka ba karamin alheri na,samu ba a dan zaman da nayi, Suna jin dadina nima inajin dadin don zaka ce a cikin su na tashi tun farko saboda yadda na sake jikina dasu tundai idan har ance mutum dan uwan haihuwa nane , Ranan da nazo garin idan baki manta na,fada maki akwai wasu yara da,suka daukan min kaya zuwa cikin gidan mu har na basu kyautan clean da,sabulu saboda taimakona da suka yi, Wanan kyautan da nai masu yajawo min hanyan alheri sosai a gurin mahaifiyan yaran, Don ba karamin dadi kyautan yai mata ita,aganin ta na yaba da yaranta da har nai masu alheri,irin haka, Sai ga matar har gida tazo mi godiya nima da aka kwana biyu na tafi har gidan su mun jima da ita duk da ba hira mukeyi ba sai hakan yai mata dadi sosai, daga haka muka saba da Yarbuga, sunan matan ke nan, Sanu sanu har shakuwa mai karfi yashiga tsakanin mu duk da ita ma,a gidan yawa take zaune tare da,sarakanta da matan yannin mijin ta, Duk da ba,a garin mijina nake ba hakan bai hanani kula da duk wani hakkin auren Hamza da ke a kaina ba, Mussan man gurin shiga na da kuma yadda nake mu,amulla da mutane gurin kama mutunci na, Kunsan yan kauye da son ganin bakuwar mace tun dai da suka,ga na kwana biyu a garin sai suke zaton kila dai ni bazawara ce ko kuma budurwa, Sau da yawa akan tuntubi yan gidan mu akan zance na sai suke fada masu cewa da aurena mijina yai tafiyane shine na dawo gida har zuwa lokacin da zai dawo sai na koma, dakina, Yau ma kamar kullun bayan nagama duk wani aikin dana saba yiwa gwago a,shiyan mu da kuma dakin kwanan mu, Sai na shiga wanka nafito na gyara jikina duk da ba wani kwalliya nayi ba ina kokarin saka hijjab a kaina ne gwago ta shigo dakin take kallo na a cikin mamaki, Fita zakiyi ne Indo gwago ce mai tambaya na ganin ina,shirin fita zuwa unguwa, Nace gwago gida malam kabiru zan tafi na duba jikin wanan yaron dana karawa ruwa jiya, Gwago tace hakane amma dai Indo kikara kula da kanki duk da nasan kina yi to amma, kikara akan wanda kikeyi a baya, Don kin san mutane yanzu sai a hankali don ganin da suke maki haka a gida suna daukan cewa ke bazawara ce, Da,sauri na juyo ina fadin nashiga uku gwago kallon da mutane ke min ke nan a she, Tace aikin san maza da zaran sun kyalla idon su ga bakuwar mace zaki ga abin ya,zama masu tankar gasa a gari, Shine dan gidan hakimi ya turo wurin babanki wai suna kamun kafa idan har mijinki ya,sake ki ne, Innalilla wa,inna alaihim rajjiun nasamu furtawa tare da kaiwa zaune, daga tsayen da nake ina cewa na shiga uku gwago kada fa fushin Allah ya hau kaina, Tace ki kwantar da hankalinki Indo don kowa ya,shede ki da kamun kai a garin nan don har ma kin fi matan su tsare dokan aure din ke ga sock ga hijjab gudan babba da kike sakawa a jikin ki, Don haka tashi kije Allab ya tsare ki yakare ki ga,duk wani mugun abinda ka kawo maki illa a rayuwan ki , Na ansa da hankali da fadan Ameen gwago amma gaskiya zan daina fita cikin gari yanzu sai da dare na,dinga fita, Dariya gwago tayi tace ai baki tsira,ba ko a haka din don wani sabon sheri za a dauka a dagwara maki a ka, Don haka fita da rana ya fiye maki fitan daren da kike gani shine saukin ki a,rayuwa, alheri, Badon naso ba haka na daure nafita zuwa duba yaron da nakewa treating don naga yadda lafiyan ta,shi take, Zamu dawo nabiya gurin aminiyata maman saudat muka dan gaisa sama,sama da ita nake fada mata zancen da mukayi da gwagona don haka zata rage gani na gidan ta don tsaron mutuncina,, Take cewa ai haka maza suke ko ita ai akwai wani kanin mijinta baiyi auren fari ba ya matsa mata,wai tai min magana yana sona da,aure, Cikin sauri nace wa iyazu billahi amma dai mutane basu da,akidar arziki saboda son zuciya zasu mayar dani bazawarar karfi da yaji, Tun daga wanan danan na daina fita kamar farko idan ma kazo ne na duba ma mara lafiya zan tsaya a gida sai dai ka kawo yaron na fita na duba shi inga abinda ke damun mutum, iya kofan gidan mu kawai, ban zuwa gidan kowa kuma,, Ganin haka yasa,gwagona kara tausaya min don tasan cewa ba karamin hakkuri da sanin ya kamata nake dashi ba , saboda ganin yadda a lokaci daya na kama kaina, ga komai don gudun zargin mutanen duniya akaina, ****** ********** ****** Tafe yake a,saman mashin din shi amma zuciya shi cike take damuwa dake tare dashi, Saboda duk kwana kin nan ya,rasa abinda ke damun zuciyan shi wanda ba komai bane ya kara haddasa mai wannan yawan damuwa sai rashin kwanciyan hankalin da,bai samu a tsakanin matar shi da yan uwan shi har ma da mahaifiyar shi wani lokaci, Duk itace sillar wanan auren sai kuma ya kasance yanzu abin daga baya babu dadi a tsakanin su, Wanda yake ganin hakan duk laifin Umma ce wacce bata sararawa matar tashi duk da tasan cewa tana dauke da lalura a jikin ta, Amma baisa su daga mata kafa,ba,su barta da halinta duk yasan cewa ita ma Sadiya ba a baya ba gurin takkalar magana, agidan, Don kullun idan zaiji fitina daga itace zancen fitinan zaifara fitowa, amma sai ya take gaskiya wai, don kada ranta ya baci ya shafi dan dake a cikin cikin ta, Tunda shi haihuwa yake so yanzu kamar zai tashi sama ya fadawa Allah, akan yana son ganin gudan jinin shi a duniya shima, Ga Sadiya wacce ta kura mai ido don taga yadda zaiyi da ledan hannun shi, don ganin su Umma a,tsakar gida yayi, Ga kuma su Umma da mama,da,sauran yan uwan shi duk idon su a kan ledan, Cikin dakewan zuciya ya wuce su ya mika mata ledan yayin da yai murya kasa kasa yana cewa ta dan san mai ya ba,su Umma koda kwara biyu ne su ci, Duk suna kallon abinda ke faruwa a gaban su take cewa wanan dan abinda baida yawa zai ce sai yabawa wasu sun ci, Mama Hafsi batasan lokacin da take cewa ba amma dai ke wanan yarinyar baki da mútunci yanzu wanda,zai bawa mahaifiyar tashi kikewa wanan tsiwar ba kunya agaban kowa, Ki dai ji tsoron Allah don kema uwace watarana zaki haifa ne ai maki duk yadda ki kaiwa wata, Haba mama Hamza ya tare zancen da sauri a cikin bata rai yana fadin wanan ai mugun fatane kawai akewa mutum amma don Allah dan wanan zancen ai bakai ace an tsaya wanan zance haka ba, Cikin mamakin shi duk wanda ke gurin yake kallon shi yadda ya murje ido yanawa mama hafsi tsawa akan matar shi, Matar da tun suna kanana take faman dawai niya dasu a duniya ta dauke su tankar diyan da ta haifa da cikin ta, Cikin mamaki shi mama take kallon shi ida ta iya bude baki da kyat tace Hamza kan ka daya kuwa don wanan yarinyar mara mutunci yau har idon ka ya rufe kana fada min magana iya son ranka, Mama idan dai ba wani fitina kike nema ba a gidan nan banga dalilin yin wanan magana ba don dan wanan abin dana kawo mata don tana marmari kawai shine har abinda ya tsone ido, kuma, Mama zatai magana Umma wace take zaune kamar ruwa ya cita tace barshi hafsi , Idon tani ce ya kawo mata abinda ma yafi wanan agidan nan bazan kara mai magana ba, Sadiya ce ta saka wani irin kuka ta mike da ledan a hannun ta zuwa dakin ta tana cewa ita gidan su zata tafi don dai kowa ya tsane ta agidan , Ba yau ba tasan cewa mama hafsi bata kaunar ta akan Aisha take gwada mata kiyayya tau ita zata bar masu gidan bazata zauna da,su ba sai dai idan yana son ta ya nema mata wani gida ta zauna, Ya juya idan iyayyen nashi suke yana fadin kin gani mama yau kun kai ga yadda kuke so Ni ba zan yarda a rabani da mata ta ba muna zaman lafiya kowa a gidan nan ya tsane ta ba mai kaunan ta, Ya bi Sadiya daki wace, take cewa cikin sabo hijjab din ta tana shirin barin gidan cikin kuka, Zan bar gidan sai ku zauna da,wacce kuke kaunan zama da ita kullun Sadiya ce mai laifi, Hamza yana cewa nace ki dawo babu inda zaki tafi don dani kike zama bada wani wani ba agidan, Amma haka bai sa ta tsaya ba fuuu tabar gidan da kukan ta zuwa gidan su cikin kukan kissa da kisisina, Hamza din yabi bayan ta a gigice yana lalashin ta yana bata magana akan ta dawo wai zai dauki mataki, Suna fita mama ta juya inda Umma take tana fadin cewa yaya kinga irin annobar da kika jawo wa kanki a gidan nan, Yarinya karama da irin wannan makircin manyan mata haka kamar wata uwar mata, Umma tace ai da ki kyale su hafsi don duk abinda ake ina gani kyalesu kawai nake yi don ban son yawan fitina, Yaya,bazan kyale ba don kona yaron nan yarinyar nan ke son yi a gidan nan, Yana zaune da matar arzikin shi yar mutunci amma kikai ruwa kikai tsaki akan sai ya kara,aure wai Aisha bata da kirki, Yau ga irin abinda kika daukowa,kanki a,gidan ruwan dafa kanki da kanki wanan makiran yarinyar idan ba,a yi da gaske ba,sai ta rabashi da kowa a gidan nan Yanzu gashi yarinyar nan daga zuwa ganin gida wata biyu da dan kai iyayyen ta sun rike ta a can , Nan kuma babu wanda ya bi bayan ta a ga may ke faruwa da ita da,sunan sati biyu gashi har yau bata dawo garin nan ba, Ibrahim ke tsaye wanda ya,shigo gidan don ganin fitan Sadiya da kuka dan uwan shi yana bin bayan ta a cikin tashi hankali yana son ya tambaya ko may ke faruwa sai kuma ya samu mama hafsi tana mayar da magana, Can Hamza ya shigo gida rai a bace nan yake cewa cikin bacin rai shi gaskiya ba zai yarda a kashe mai aure ba don yana son matar shi, Sai da yamma iyayyen Sadiya,suka kira akan cewa lalai sai ya canzawa Sadiya gurin zama tunda ba,a kaunar ta a gidan,. Nan ya nuna masu cewa gaskiya baida zarahin yin haka yanzu sai dai ayi hakkuri akan zai dauki mataki akan al,amarin za a gyara komai, Amma sai mahaifiyar Sadiya din ta iya nuna cewa sai dai mama hafsi tabar gidan don bazata yarda yar ta,ta zauna da ita gida daya ba bata kaunar ta, Hamza dai hakkuri yake bayarwa cikin kwantar da kai yana cewa ayi hakkuri zai dauki mataki in Allah ya yarda, Andawo mai da,Sadiya a daren don ita kanta ta fadawa mahaifiyarta a mayar da ita saboda,bazata yarda ta kwana gidan su ba kada a juya mata kan shi idan bata kusa, Ba kunya washe gari ya nunawa mama cewa wai zata iya komawa garin su da ta,fito don shi zaman lafiya yake bukata a tare da iyalin shi, Mama Hafsi take ce mai ya kwantar da hankalin shi, don Itama tafi bukatan tabar masu gidan su tunda bai san darajan iyayyen shi ba ita bazata zauna tana kallon yadda yake wullakanta mahaifiyan shi a gaban ta ba, Sai da Ibrahim yafito daga daki yanuna mashi cewa shima fa namijine cikin nuna,shi yake cewa babu inda mama zata indai don wanan munafukar matar takace, wace ta shigo don ta watsa muna gidan mu, Yau gashi matar ka ta kwarai saboda mugun halin da ta sakata, tai tafiyan ta gurin iyayyen ta sun rike abinsu can, Kana nan kana hauka akan wannan mara mutuncin matar taka wacce bata da kirki har kake wani zakewa akanta, But Sadiya tadago labulen dakin ta fara surfawa Ibrahim zagi ta uwa ta uba tana aibanta shi da mugun kalamai, daga baki ta, Umma dake ta hakkuri tana, hadewa don kada a ji muryan ta zancen bata san lokacin da tace ke ar, da halinki sadiya baki da mutunci ko kadan wanan mugun kalami irin haka ga dan uwan mijiki baki ko jin kunya ko nauyi, Haba ai sai ta juya a kan Umma tana fadin dama duk bakin ku a hade yake nasani babu mai kaunata don ba don Allah kika yarda da,zancen auren mu ba,saida mamana tasan yadda ta shiga ta fita tafi karfin ki, Don haka ni bazan kyale kowa ba a cikin ku aure ne da Hamza nayi sai mutuwa, babu yadda zakuyi dani,, Duk wata bakar tsohuwa da bata san kama, mutuncin ta ba nima bazan ji kunyan ta ba daga yau, Baki bude galala Umma take kallon Sadiya tana sauraren ta duk mamakin kalaman ta akanta ya cika ta, Sadiya taci gaba da fadin dama nasan ki gurin son kai da nuna son diyan ki din haka idan kin shigar mashi ne an sayar maki sai mu kara dake, Ni ba yar Agwai bace da kuka raina keda duyan ki kuke takata a duk lokacin da kukaga daman yi mata rashin mutunci, sai kuyi, Sai hamza ne wanda yafito daga bandaki yake cewa ke ke ashe bance kada naji bakin ki a gidan nan ba kuma, Ina bata tsaya sauraren shi ba,sai daga harshe take tana fadawa Umma da danta abinda duk yazo mata a,bakin ta lokacin, Suna shiga daki mama hafsi tanisa tare da cewa, ki ga irin bala,in da kika kwasowa kanki da hannunki, Lokacin da na nuna maki rashin dacewan haka, kikace ina bakin ciki da karuwan danki a fili, yanzu wa gari ya waya ? Washegari da safe Baba Mudi yasa aka sallamawa Hamza inda yafito yana ganin Baba ne duk sai ta dan dabuce dan kunya da nauyin da ya kamashi, Badon komai ba don ya dade suna wasan buya da shi don sam bai yarda su hada hanya da baba din don nauyin shi yake ji sosai, Baya ce mai bayan sun gaisa Hamza idan nauyin iyali ya hau kan mutum sai ya hada da hakkuri don kowa da halinai aka zama dashi, Kaga mu maza idan munkayi sake har mace tayi galaba akan mu ba karamin kona mu sukai ba, akan iyayyen mu, Don haka kayi aniyan gyarawa da mahaifiyan ka kada ka bari shedan ya rude ka akan uwar ka don mace shedaniya ce idan ba,a dace ba, Hamza ya gane nufin Baba ke nan yaji hayaniyar da akai a gidan tun shekaran jiya, Don haka kunya da nauyi suka kamashi don yanzu hankalinshi yadan fara dawowa yasan Sadiya shu,uma ce sai dai babu yadda zai yi saboda gashi aure ya hada kuma har da rabo a tsakani, Shi kuma gaskiya yanzu yana son haihuwa sosai don tun Umma na fadi bai dauka har yanzu abin ya shiga ran shi sosai, Godiya ta sakeyi wa baba yana cewa ya gode insha Allahu za,a gyara da yardan Allah, Sai kuma yaji abinda yake nokewa akan shi Baba ya sako zancen da cewa, Kayi kokari katai ka taho da matanka don nasan cewa akwai dalilin da yasa takai har wanan lokacin a can, Amma in katai koma manene zakaji don nasan iyayyen ta mutanen kirkine sosai, baza su rike ta har zuwa wanan lokacin ba haka kawai, Yace cikin ladabi in Allah yaso Baba zan tafi idan na dawo daga tafiyan da zan yi, Allah yaba da ikon zuwa inji ba yace shike nan ni zan tafi kasuwan Kalgo don yau na taka ci, Yaiwa Baba a dawo lafiya ya juya zuwa gida yana tunanen zancen su da Baba shi dai gaskiya dattijon nan yana ganin mutuncin shi don mutum ne wanda yasan ya kamata, Duk ya ya bashi diya a lokacin da ya ke da bukatan taimako yazo ya kasa rike mai ita yadda ya dace baisa yagan shi zai fada a masifa ba ya ki fada mai gaskiya, Sai kuna zuciyan shi take ce mai itama Aisha may zai sa ta tafi ta wuce lokacin da ya bata ta dawo taje tai zaman ta, har wanan lokaci haka a gurin iyayyen ta, Wanan dalilin da zogin ganin yana da wata mace a tare dashi yasa shi shareta kawai yana gani ai in tagaji zata dawo da kan ta tun da ba fada sukayi ba lafiya kalau suka rabu da ita don shi da kan shi ya kaita har tashan mota da zata wuce, Indan da tana nan yasan duk wanan fitinan daya ki ci yaki karewa tsakani su Umma da Sadiya da baza,ayi shi haka ba, Yawan cin fadan duk akan aikin gida ne don Sadiya raguwace har ta karshe bata son motsa jikin ta ko kadan Sai dai gurin kwanane kawai take da kuzari da lakka bayan haka bata iya komai a gida ba don ko girkin tayi haka zaici shi ba,dadi, tun bai saba ba har yanzu yasaba haka yake hafiyan abin shi, Amma dai koma may ye ya tsayar da ita idan yadawo zaiyi kokari yatafi yagani da kan shi kamar yadda yai wa baba alkawari, Dama can Mansur ya matsama akan cewa ya tafi yadawo da matar shi don wallahi idan ya bari Aisha ta kurce mai sai yayi daya sanin rabuwa da ita daga,baya don wanan da yake gani kamar wata matar arziki babu komai na alheri a tare da uta sai tsiya don tin ba,aje ko ina ba tafara tarwatsa mai kwanciyan hankalin shi, Sai yake ganin don Aisha tana tare da matar mansur ne yake fada mai hakana bai ganin kirkin sadiya din, Haka yasa yanzu bai son ma su zauna dafa shi sai mansur din don kada ya kawo mai zancen Aisha, ****** ********* ****** Rigar da nake sakawa normal a jikina yau shine yaki sizing din jikina dole ina son yin adon jumma,a dashi na cire shi na sakewani, Gwagona dake zaune daga wajen daki idanuwan ta akaina naji tana fadin anya Indo ba zargina ne zai zama gaskiya ba kuwa, Da,sauri na jaye madubin da nake kallon ina mai duban gwagona nace gwago zargin may kike ne kuma, Tace ciki a jikin ki mana don gaskiya idan har ba idona ne ke min gizo ba zan iya cewa ciki ne dake Indo, Cikin dan langabe kaina na marairaice nake cewa haba gwago kada ki sa gaba faduwa mana ki daina wanan zancen kada wasu suji ki a zaci cewa da gaskene zargin ki a kaina Ai, gaskiya take fadi don ba wanda baisan cewa kina da ciki ba,a gidan nan, Cikin sauri muka juya inda Inno take shigowa dauke da kwaryan gari da lariya a cikin sa , Innalillahi na,samu furtawa don jin mugun kazafin da ake shirin min da rana tsaka, Nace haba mama Inna wani irin ciki kuma ni da yau rabona da mijina kusan wata uku ke nan ta yaya zan yi ciki ba miji tare dani, Ciki kan ai da abinki kinka taho, garin ga, Cikin da yanzu yakai wata shidda da yan kai zakice wai wani abu, Shin ko gwagon kina bakin son tasan da zancen cikin wai kika,wani dan boye boye haka, ? Lalaikan Inno walle sai yanzu idon yaggane min zahiri cikina kuwa gashi har ya girma haka, Amma dai yarinyar ga ke, shammace ni wallahi a,a ankayi ban ankara ba da lalura a jikin ki tun wuri, Kesan munafukin ciki na da ita gashi kuma cikin farina shi yassa ba aganewa don har ma sai ta haihu mutane basu sani ba, Amma ko ai jikin ta duk ya nuna,alamar ciki tu dauri naso na hwada maki amma,sai najja bakina nai shiru ka acce min na faye surutun tsiya, Dauri Inno amm, ai da ke sani kifada min wallahi don wanga abu duk ya bashe ni walleh, A hankali nakai zaune daga inda nake tsaye a bakin gadon karan gwagona na dake dakin ina mai fadin, Innalillahi wa,inna alaihin raji,un Shi ciki fa kinkace ajikina mama Inno tace shin wai kina nufin baki san komai ba ko ,a a ? Nace a han kali cikin dago kaina da fuskana daya canza a lokaci daya, Walleh, gwago ban san cewa akwai ciki ajikina ba nidai abinda nissani shina ciwon maran da nai tayi kafin na taho nan niya, kaman zan mutuwa in dare yayi,, Daga haka na fada tunane cewa in ko ciki ne har wata shidda to tun shigowan sadiya gidan ba,a dade ba na samay cikin ke nan, Hawayen bacin rai naji suna silalowa daga idanuwa a hankali, wanda nai bakin ciki dajin wanan mugun labari a wanan ranan, Haihuwa da Hamza mutumin da bai san mutunci naba bai san zafina sai takura da gallazawa kawai, Muryan su gwago naji suna fadin amma ai su iyayyen shi sun san cewa kina da cikin ko ? Sai a lokacin nadan dawo cikin hankali na dan girgiza kai ina cewa ban tsan mani ba gwago don da mama ta fada min ko kowa bai fada min ba,, Ranan haka na,wuni a cikin bacin rai ina da nasanin samun wanan cikin a gidan Hamza da nayi, Mutumin da yanzu nafi tsanar shi da kowa a duniya saboda rashin rike amana da,bai,da shi a,rayuwa, Don idan da da amana da bai wullakantani ba haka a idon duniya, kowa yagani saboda irin halarcin da nai mai a baya, Gwagona bata bari an kwana ba ta samu iyayyena maza da zancen cikin dake gareni don ita tunda nace gidan mijina basu da labari kada su zo su ja zancen suce ba cikin su bane abin ya zama wani sabon tashin hankali kuma, Amma sai dayan Baba na yace ai al,amarin da sauki don kinga watan nin cikin ya zarta na zuwan ta nan gurin mu, Yanzu mu sauri zuwan shi idan har bai zo din ba zywa wani dan lokaci kafin ta haihu sai mu tuntube su da zancen don yasan da ajiyan shi a nan, A haka kabar zancen cewa idan basu zo ba za a samau su da zancen cikin aji daga bakin su, Gashi yanzu Alhamdullahi don na samu alheri fiye da tsanmani maikaratu a kauyen mu don nima ban tsan mani abin har yakai haka ba, Don duk wanda naiwa aiki yaji dadi zakiga sun kawo min hatsi mai tarin yawa sun bani, a madadin kudi, Shine gwagona ta samo daki daba kowa a gidan tana tara min wai idan zan koma sai na koma dashi gida, Masara gyaro da dawa,da maiwa buhu buhu aka dinke min su gaba dayan su, Naso a,sayar dasu a,can amma gwagona tace wai ai idan mutum yazo gida bai koma da amfanin gona ba tankar yan uwan shi matsiyata ne, ni gashi Allah yai min baiwa mai tarin yawa zance wai asayar kada ta,sake jin hakan , Dole naja bakina na tsuke nai shiru gudun kada ran ta ya baci a saboda ni, Hamza ya,shirya kamar kullun yai sallama da mutanen gida ya kama hanya zuwa kurmi kai kaya kamar yadda yasaba yi, Sai dai kafin ya tafi dole yabar dan abin da za,a dinga amfani dashi wadattace kafin ya dawo don gudun fitina, Saboda,wancan tafiyan da yayi na karshe yadawo ya,samu korafin cewa wai Sadiya ta kwashe kayan abinci takai wa mahaifiyarta a gidan su, Da kyat ya,samu ya kashe wanan wutan don Umma ta hau sosai cewa anbarsu da yunwa kuma basu san inda abinci ya shiga ba, Ranan harda yabon Aisha yaji tayi take cewa tunda suke da Aisha ko gishirin su bata taba,dauka ta,bayar a makwabta ba, Da kyat yasamu ya shawo kan zance har aka kashe wutan maganan don Sadiya tace sai dai a raba girki a tsakanin ta,da,su Umma don bazata iya ba ita, Kuyi hakkuri dashi baida yawa insga Allahu zaku dinga jina na gode da kulawan ku a,gare ni tan uwa da fatan anyi sallah lafiya ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU ,IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, Tsatsaye suke saman hanya da bakaken kayan su, don su, satan su na daban ne, Motar kayan abinci suke sata daga motar har abincin da aka dauko su batar dasu zuwa wani kasan na daban, Cikin tashin hankali na cikin motar suka fito don ganin bindigan da aka nuna masu, Nan suka arta cikin daji suka bar kayan nasu da komai aguri kowa yana neman ceton rayuwan shi, Daga ciki harda Hamza cikin masu gudun fanfalakin neman taimakon centon rayukan su sai daji suke ta bazawa dagudu acikin duhun dare, Washegari suka tsinci kawunan su a kauyukan yarbawa da basu ko jin hausa a bakin su, Da taimakon Allah suka samu suka dawo arewa hurjanjan dasu cikin tashin hankali, Kafin wani lokaci labari duk ya karade ko ina kowa da irin yadda yake bada nasa labarin gurin mayarwa, Ranan gidan su Umma Rabi sunga tashin hankali ba kadan ba mutane sai shigowa suke yi yin jaja da Allah ya tsare gaba, Hamza ya shiga tashin hankali mara musali a lokacin haka yasa Umma dan fara shiga da fice gurin nema mashi taimakon don ya dawo a cikin natsuwan shi duk da ya na fada mata cewa normal yake damuwa ce kawai ke damun shi, Tunane ke mai yawa na yaya zai samu wasu kudi nan gaba don yanzu bashi da komai atare da shi, Gashi har da kudin mutane da yadan hada zuwa wanan tafiyan kuma mai kudin ba musulmi bane baida yarda da kaddara, Wanan ne damuwar Hamza har ya shiga wasu hali na tashin hankali, Bayan kaman sati biyu da samun wanan matsalar mutumin dake binsa dubu Hamsi yafara mashi sallama a gida, Hankalin kowa ya tashi don mutumin yana ikirarin cewa, zaiyi karan hamza a gurin hukuma don a karban mai kudin shi, Alkawari yai mai cewa ya dawo bayan kwana biyu zai kokarta ya,sama mai koda kadan ne ya bashi, Hakan yasa mutumin yin hakkuri ya,tafi a cikin fushi da sharadin zaidawo nan da kwana biyu din, Hamza hankalin shi ya kara tashi sosai yarasa ina,zai sa kanshi don tashin hankali, Gashi yanzu ba,wani shiri suke da,mansur ba kamar farko balle ya,tafi neman taimako a gurin shi, Sama sama suke akan yasha mai magana akan ya,dawo da matar shi yana basarwa don shi baiga dalilin da zanje na zauna garin mu ba,wani dalili maikarfi, Kuma iyayyena na can suka kyale ni yaiwa mama Rahana magana tace sunfita iko dani babu inda zata ita, Wanan dalilin yakara sa shi yin fushi tare da kafewa akan bazai tafi ko ina ba ita kuma Sadiya tana kara,zugashi yana hawa dokin karya, Da rarashi da komai Hamza ya,samu Sadiya ta ara mai dubu goma sha biyu wanda take samu daga gare shi a baya take tarawa wai itama zata sai fridge dashi don taga duk da,ban gida mama tana sana,a da fridge dina tana tara min kudin, Yaso ya tambayi mama amma yana tunanen irin rashin mutuncin daya shuka mata na cewa wai ta bar gidan don ba zai zauna da ita tana saka mashi mata a gaba ba, Wanan kunyan da nauyi yanzu yake nadaman da,yasani da baiwa mama wanan aika aikan ba akan Sadiya, Duk abindake gudana mama tankar bata,san abinda ke faruwa ba a gidan share kowa tayi kawai, tana kallon su, Don duk kokarin da tayi dasu a,baya Hamza ya nuna mata bai gode ba saboda mace don tai mashi gyara kayan ka, Ranan da akace mutumi yadawo tunda farar safiya ya,sallama masu da tashin hankali dan kudin da ya,samu a gurin Sadiya ya bawa mutumin amma,sai yace wai sam bazai karba Yana kokarin tara masu mutane a kofan gida sai ga Mama Hafsi ta kasa kyalewa ta fito da kudi a hannun ta ta mika mai, kudin ya kama dubu ashirin da biyar saura rabi ke nan, Mutumin yai hakkuri ya tafi yana dan zage zagen shi don shi yace bai san kaddara ba, Shikuma Hamza kaddarace taja shi don bai taba sana,a da wanan mutumin ba,sai wanan karo da kudin ya hada,su na ledan da ya,saya ya,dura kayan shi a ciki, Yau za,a ji labarin barayi gobe za,aji labarin su sai shiru kake ji babu wanda yaji su don su basu ko kasan sun ketara da kayan kasar Benin republic sun sayar har motar gaba daya a can,,,, ****** ********* ****** Tun ina saka yar damuwa a rai akan cikin dake a jikina har takai na gaji na,bar sa,wani bacin rai a,tare dani, Ga kulawan da nake samu a gurin gwagona wanda yasa nayi kiba nayi wani irin bulbul dani, saboda duk wani abin da ya dace abawa mai ciki shi take kokarin kawo min, Agaskiya banda abinda zan fada akan iyayyena don suna iya kokatin su dani sosai a zaman da nake a gurin su, Zaune muke a dakin mu gwagona tana kada zaren ta irin da mutanen kauye keyi don sana,a sai take ce min , Ikon Allah wai jiya da mahaiginki nai mafarki Indo shine abin ya tsaya min a rai yana matukar damuna wallahi, Din na ganshi a cikin wani yanayi wanda bazan iya gane ko yana mace ba ko a raye, Gurin da na ganshi a tsaye abin ban ko iya musalin shi sai murmushi yake min nace mai ashe kana raye yace min yana nan yadai yi nisa ne damu kawai, Nace gwago aida Sadaka kikayi kafin ki fadi mafarkin na ki don kinga shi sadaka yana mayar da sheri alheri haka kuma,wata katanface babba ga bawa, Mafarki anfiso kayi sadaka kafin ka,fadi don kawar da shedan acikin sa da kwankwanto, Tace aikuwa ina da dan guntun dawa a dakin nan bari na kaiwa Gude makauniya sadakan shi, Gwago sadaka anfison mutum yayi shi da dafafen abin ci ko kosai ko masa ko kulikuli ko ayya ko gyada ko sugar da,dai sauran su, Anfison mutum yai sadaka,da abu dafafe wanda zakawa yana ci yana jin dadi kai kuma Allah yana maka saukin al,amarinka a take, Gwago tace aiko ina da,sauran tuwo a dakin nan da,kulin kuli kuli bari na rabawa yaran shi a waje, Gwagona tana fita daga dakin na nisa tare da cewa ikon Allah ko may ya raba,shi da gida haka ya shiga duniya tsawon lokaci haka, Don dai a gaskiya gidan su a kwai rufin asiri suna noma suna kiwo suna da gonaki da yawa gasu kuma yan kasuwa ne su,, Amma ya tsalake yan uwan shi da kowa nashi ya shiga duniya ba wanda yasan idan yake ko a raye ko a mace,, A gaskiya Ummina ma tayi hakkurin zama a cikin kauye irin wanan gaskiya ba yadda za,ayi ta zauna a haka, Mutum adauko shi daga birni a kawo shi kauye irin haka bawani abinjin dadi ko kadan acikin sa, Kyawo dai ace andauko mutum daga kauye an kawo shi birni zama ba daga birni akai mutum kauye ba, Kauyen da ba ruwa ba wuta, babu wani abinjin dadi a gari ko wani dan abin marmari babu ba abinci mai dadi ko kamshi sam, Gaskiya dolene Ummi ta tayar da hankalinta tabar wanan garin ta koma gurin diyan ta, da tabaro a Jega, su yayana Audi, Muryan gwagona ce tadawo take cewa indo kin kuwa ga kamar kada nai sadakan nan sai naji wani irin sakat a cikin raina duk kuncin da nake ji da farko kamar an zare min shi yanzu, Gwago ai Allah da Annabinsa sunyi gaskiya gurin taimakawa musulmai akan al,amarorin muna yau da kullun, Komai yazo muna a bauyyane sai dai idan mutum bai bi tafarkin Allah ya juya zuwa,shirka shine zai yi wahala, a rayuwan shi, Gwagona tace ai shi nake fadawa wasu yaya akan zancen Halidu don abinda ban mamaki ace daga dan tsantsami mutun ya tafi yabar gida har tsawon wani lokaci irin haka, Ba ma wanda ya sani ko ya mutu ko yana raye don babu wanda zaice ya taba ganin shi, tunda yatafi, Dan tsantsami ne na baki ya hada su da yaya Sale, akan gona shine asuban farko ya sulale yabar garin nan har yau ba mai cewa ga inda yake, Gashi duk cikin mu yafimu zumunci ga kyauta, da son yin alheri har ga,wanda bai sani ba, Matarshi ta farko ta,rasu a,gurin haihuwa ya jima ba aure shine da innar ki tazo ganin gida lokacin tana zawarci sai ya nemay ta bataso ba don zaman nan kauye amma sai iyayye suka fi karfinta aka daura dashi dayake akwai rabonki, Amma auren nasu baiyi wani dadi ba don kokarin bata muna zumunci yayi shine ya zauna ba wani aure har zuwa lokacin da ya bar garin gabadaya, Yanzu gashi kowa nason ganin shi babu dama mugun halin yaya yasa yaiwa dan uwan shi cin fuska a gaban mutane, Shine yaji haushi zuciyar fulanin ta motsa mai yabar gida gaba daya don kunya wai, Cikin zancen gwagona nadan tsunci amsoshin da nadade ina,son sanin su akan mahaifin nawa, Ashe ma ba,dan duniya bane yadda su Ummi ke nufi wai ya tafi yawon duniya ne yabar gida, Dalili ce tasa shi barin gida gaba daya gashi yanzu ba,a san inda yake ba ma gaba daya ko a,raye ko a mace, Idan dai yana rayene Allah kadawi dashi gida cikin yan uwan shi inko yarigamu ne Allah ka,karbi bakuncin shi ka,haskaka mai makwancin sa, Shiru shiru babu labarin zuwan kowa daga jega don haka gwago ta samu maza akan zance, Wan mahaifina yace zuwa wani sati zai shirya ya je yaji may Hamza yake ciki da zancen aurena da shi da kuma cikin dake jikina, ****** ********* ****** Abubuwa duk sun taru sun rukice wa Hamza a lokaci daya gashi baida komai duk an kwashe shi tas, Ga shi ba abinci a gida ga fitinan Sadiya sai abin da ya karu tsakanin shi da ita dama mutanen gida gaba daya, Zancen zuwa ya,dawo da Aisha dake garin su ya tsaya mai a rai don shima a gaskiya yanzu rashinta a tare dashi ya kai mai ko ina, Gashi ko kudin motan da zai je sokoto baida su balle har ya karasa kauyen mu gurin iyayyena, Yanzu kunyan Baba Mudi yake matukar ji don yai mai alkawari bai cika ba hakan yana nufin cewa bai ra,ayin Aisha a ranshi ke nan, Kwana yake da tashi da zancen a,cikin rayuwan shi ya rasa yadda zai yi da kan shi, Ranan da abin ya ishe shi gashi sun kwana suna fitina,da,Sadiya baiyi barci ba ya yanke shawaran cewa ya,samu aminin shi mansur kawai da zancen tunda babu yadda zai yi, Don haka washegari tunda safe ya shirya sai gidan Mansur yai mashi sallaman cewa ace shine ke sallama mashi, Koda hindatu ta fada mai bai gaskanta zancen taba sai da yafito yasamu cewa Hamza din ne dai da kan shi, Yai mashi iso da,su shigo daga cikin gida su zauna a falon shi, Hindatu tana kitchen a lokacin irin yadda ta gaidashi sai baiji dadi a,ran shi ba sam ita ko dama da,gaiyya tai mashi haka din, Cijin dan tsawalla suka kara gaisawa da Mansur din sai Mansur din ne yake tambayan shi cewa lafiya dai ko yafan shi da,safe hakan nan don ya,dade rabon shi da gidan gaba daya, Cikin dan, shakka da kuma kunya yake cewa wallahi zancen Humaira ne gashi ina son zuwa garin su don na,dubata ko lafiya takai har warhakan nan a can, Ga kuma abubuwa duk sun tsaya min a lokaci guda don ko kudin motan zuwa sokoto banda shi Wallahi, Shiru Mansur yayi tare da dan furzar da iska daga bakin shi ya san harka ce ta aure idan bai taimaka mashi ba zancen zai lalace ne gaba daya, Don haka,sai da yadan ja mai gas sannan yake cewa yanzu hankalinka yadawo akan ta ke nan ko da har kake kokarin zuwa dubata, Cikin jin nauyi da kunya yake cewa ba hakana bane, kawai dama ina da niyan idan na,dawo daga tafiyan da nayi na karshe sai na tafi garin shine kuma wanan kaddaran ya,faru dani a hanya, Hmmm kawai mansur ya ce bawai ya yarda da,zancen Hanza din band, Sai cewa Hamza yayi dama ai nabarta ne don kowa a gidan ya gama fahintar gaskiya kafin na,dawo da ita, Yanzu ita wanan da Umma ta ce na,auro ita ce ta gari ai gashi tana,nuna mata halin ta, tunda Humaira bata da amanan su bagashi nan yana fita a tsakanin su ba, Cloud you believe cewa Umma da kan ta shekaran jiya saida tai min zancen cewa wai ya zancen Humaira ne ake ciki, Yace nabata amsa da cewa sai na samu sarari zan tafi garin , Ashe wanan yar arigido din tana,kusa shine tashiga fitina wai in dai Humaira zata dawo ne sai dai na sake ta don ita bazata kara zama da ita ba a matsayin kishiya kuma, Muryan Hindatu sukaji kawai tsagal tana cewa eyyeh yar raini wayyo wallahi saidai ita ta fita tabar gidan amma kamar Aisha ta dawo tagama ko, Ai tsakanin ka da Aisha wallahi sai Allah dama ai munbari ne muga iya gudun ku tunda kunce,wai mu bamu iyaba ga,wacce ta iya ankawo, Banda cikn may zama da Sadiya ya karaka dashi duniyan nan wanan mai farar kafan tsiya haka,? Duk auren ta ya mayar dakai wani iri kakoma kamar wani tsoho ba hamza ba can Dariya kawai hamza keyi ita ko Hindu sai zazaga mai masifa takeyi shiko yana ta faman murmushi kawai, Mansur ne yace mata to ku raga mashi hakana mana tunda yayi saranda ai shike nan ko, Wallahi, abin akwai wulakanci a ciki ace yarinya tana ta hadiyan hakkuri gurin mahaifiyar ka da yan uwanka da gurinka kawai take jin dan sayi shine kai kuma,fon ka auro wanan mai bussashen idon zakawani juya mata baya, Ai haihuwan da kake wa rawan kafan za ai maka a gida na Allah don bai manta da kowa ba ko ita Aishan yaga dama yana iya bata duk sanda yaso, Cikin sanyin murya yake cewa tau yanzu dai don Allah dai ayi hakkuri anyi kuskure insha Allahu za,a gyara, gaba, Oho dai mu wallahi munfi karfi aceza,a wulakanta mu ko a,yarda mu don ko yanzu mun nunawa mutun bafa dole bane zama da mutun don anga muna hakkuri shine ake kokarin takamu yadda aka,so, Kudai yi hakkuri dan Allah insha Allahu bazaa kara ba nan gaba, Da kyat mansur ya,samu ta fita daga falon don ta,barsu su karasa zancen su, Sun aje magana da cewa karshen sati zasu shiga garin mu da yardan Allah dai lokacin da babana yake cewa ranan litani zai shigo jega,don yaji ba,asin zancen mu, Daga haka sukai sallama Hamza yana wa Mansur godiya don yasan duk cikin garin nan shika dai ne mai kaunar shi tsakani da Allah, Sai dai maganganun Hindatu sunyi matukar tsayawa Hamza arai don yasan duk abinda yaji a bakinta akan shi nake zaune nima don bakin mu daya da ita, Hindatu ta san komai akan tafiyana kyale su kawai tayi shida mansur din don a tunanen shi mansur baisan komai ba ke nan, Shi fa ba wai qani fifita Sadiya yake a kaina ba,saboda cikin dake a jikin tane kawai yake dan kokarin shi akanta, Kuma ita,Sadiya mace ce mai masifan son kwana da miji don hakane yake kokarin biye mata,a zauna lafiya kada Umma tace yai laifi, To amma may yarage Aisha din dashi da ake ganin rashin adalcin shi a kan ta hakane wai, Amma yanzu abinda zaiyi shine zai kokarta yaga inda keda matsala sai yagyara don baison a kirashi da,rashi adalci kuma, ****** ******** ****** Ina kwance ina barci a,saman gadon karan gwagona,wanda tunda nazo a,sama nake kwana ita kuma tana kasa saman tabarman roba, A cikin barcin da nakeyi nake jin muryan Inna tana fadin wasu bakine su kazo wai sun na neman ,Indo amma dai ina ganin kamar mijinta ne, Mijin ta,shin daga ina,sunka ce suke ? Wai da Jega suke, inna taba da amsa,, Ke walleh shina duk yadda ankayi suna sunka taho,? A hankali na bude idanuwa na dake lumshe saboda nauyin barcin da nakeyi ina jin zancen su kamar a mafarki, Don gaba daya na,fitar da,rai ga zuwan shi garin mu asalima dai ina ga kamar har mun rabu ko, Saidai, bakin cikina shine wanan cikin nashi dake ajikina shine kawai bacin raina, Don ban son wani alaka ya,shiga tsakani na,dashi gaba daya na,ma manta da cewa na taba auren shi, a rayuwana gaba daya, Sai dai kashh wanan cikin da Allah ya bani a lokacin da zuciya take a cikin kunci bai sani jin dadin sa,ba, Kukai masu tabarma muryan gwagona ne ke tashi da kuma sauran matan uban naina dake sintiri a tsakar gidan mu, A hankali na mike zaune a hankali daga kwanciyar da nake ina mai kura masu idanuwa na don gani yadda duk suka rude da zuwan su , Mutumin da bai rike masu amana diyar su ba kamar yadda,sukai mai halarci da farko, Abinci aka fara gabatar masu dashi tare da fura danono mai kauri sun sha furan sosai fiye da abincin Sannan suka,fara ganin iyayyena maza suka zauna dasu dan su tatauna akan zancen mu, Mansur ne yafara magana yana mai basu hakkurin rashin zuwan su da wuri sai kuma matsalar kaddaran da ya,fadawa shi hamza din wanda ya kara jawo masu delay din zuwa,da,wuri, Nan suka,dauki salati kowa,da irin nashi kabbaran suna mamakin irin yadda za,ace, wai ansace mota har kayan dake cikinsa baki daya kai irin wanan zamani haka babu tausayi ga mutane ko kadan, Dole jin wanan zancen yasa su Baba suka tausaya mashi, suka kasa cewa wani abu akan abinda suka kullayi mashi sa farko, Amma duk da gaka,saida Baba Sale yai mashi nasiha akan jin tsoeon Allah dakuma rike amna da hakkin aure, Inda yake cewa Hamza ya gode wa Allah da ya bashi mata mai mutunci kirki ladabi da,sanin ya kamata, kaman ba karamar yarinya ba a,dan zaman da mukayi da ita mun fahinci halaiyanta tunda tazo garin nan bata,taba ketare maganan mu ko fada dawani ba a gidan nan, Wanan gaskiyane baba halintane wallahi don duk zaman mu da ita wallahi bani mijinta ba har mutanen gida da muke zaune dasu ba may cewa Humaira tai mashi wani abu sai dai kawai zama irin na mata na yau da kullun, To dan Allah a tsare gaba don bawai ba mu son ta bane kaga mun barta can kawai don uwar ta da kuma mijin ta da muka ga ya dauki nauyin yaran mukewa wanan halarci amma a hakikanin gaskiya baso mubaka ita ba takoma gurin ka , Don kagan ni nan wallahi a jibi nake da niyan zuwa mu kashe wanan auren naku, Cikin sauri Hamza yace don Allah Baba kuyi hakkuri insha Allahu ba asakewa, Baba yace ai wanan cikin dake a jikin ta yasa kaga ban dauki wani mataki ba tun zuwan ta, Cikin wani irin mamaki da tsoro Hamza ya ce ciki Baba ? Mansur ma da,sauri yace ikon Allah cikine ga Aisha din ? Ciki har ana batun haihuwan shi kenan kuma baku san da zancen shi ba ke nan ko ? Gyara zama Hamza yayi gumi yana karyo mishi cikin jin nauyi da kunya yake dan cewa Wallahi Baba bamu san tana da ciki ba don ko mahaifiya na ina ganin basu sani ba don banji kowa yana fadi ba, Magana,su Baba keyi da Mansur amma shi hankalinshi yana ga tunanen cewa, Ita Humaira wata irin yarinya ce da zurfin ciki irin haka ciki a jikin ta har ya girma amma ba wanda tafadawa tana ganin irin yadda ake dauki da murnan samun cikin Sadiya a gidan amma tai shiru, Yana son yaga yaya ta koma da ciki ajikin ta yason yaga yadda jikin ta zai koma yadda ciki zai zauna a jikin Humaira, Daga karshe aka basu ison cewa su shiga ciki suga gwagona da nake wurin ta, Daga cikin dakin gwago aka shimfida masu tabarma suka zauna kamar yadda sarakai keyi idan sun zo gaisuwa, Sun gaisa acikin mutunci itama dai hakkuri suka bata sai take dan masu nasiha akan rikon amana da zaman aure, Hamza sai raba ido yake yaga ko ta ina zai ganni na fito don yaga yadda na koma, Matan gidan mu sai tururuwan zuwa suke suna gaishesu da zuwa don kawai su gan shi su san mijina, Dubu biyar mansur ya basu su raba suna ta murna da addua da jin dadi don gani suke kaman an basu dubu dari ne, Ina dakin Inno gwago ta,aika akirani wai nazo mu gaisa da,su, Banji dadi ba naso ace har,su tafi kada su ganni amma ba yadda zan yi dole nabi umurnin iyayyena , Katon hijjab ne ajikina mai ruwan milk color har kasa nashigo dakin acikin sanyin muryana na kamar ta rowa nai masu sannu da zuwa na,samu dan guri can nesa na tsugun na, Mansur nake gayyarwa batare da na dago kaina ba naji muryan Hamza yana cewa, Humaira ya muka samay ku kinzo gida kinga yan uwa kin zauna abinki baki ko tuna mu ko ? Namiji ke nan baida kunya may yake nufi, watau, shi baima san anyi min wani abuba ke nan ko zamana nayi don kaina ko Sun tambaya suna son wucewa dani amma sai su baba suke cewa, sun so ace tunda haihuwan fari zanyi na zauna har sai na haihu amma kuma idan suyi haka,basu kyautawa su Ummi ba,da mijin ta don haka su tafi idan an shirya zamu zo da gwagona da daya,daga cikin matan gidan don suga guri na, Anyi sallama dasu akan cewa zuwa wani sati insha Allahu zamu dawo garin tare da yan uwa na, Sukai muna sallama suka kama hanya bakin su dauke da maganan zancen labarin cikin dake a jikina da basu da labarin shi,,, ****** ********* ****** Ikon Allah inji Umma da mama da suke sauraren bayanin da Hamza din yake masu, Yanzu ita yarinyan ga cikine ajikin ta har tai laulayinta a gidan nan ba wanda ya sani, mama hafsi ce take fadin haka, Yanzu dai cikin watan shi nawa don a,lissafa a gani ita dai yanzu a lissafina watan ta na uku ke nan bata gidan nan, Umma ce mai fadin haka, Wata bakwai da,wani abu, kenan sukace don sun so abarta can harta haihu amma kuma daga baya,sai suka ce idan sunyi haka basu kyautawa Baba Mudi ba, Kaji gaskiya lalai Aisha taci sunan ta na yar Agwai halin irin na fulanin asali, watau ga kunya ga kuma zurfin ciki, Yanzu ita mahaifiyarta ta san zancen cikin ke nan ko sukai muna rufafa akan shi ko yaya Umma ta kara tambaya a cikin son jin yadda abin yake, Hamza yace anya kuwa suna da wanan labarin don dai da Baba ta fadamin gaskiya, Mama hafsi cikin jin dadi take cewa Allah mun gode maka, kai kayin yadda kaso aduk lokacin da kaga dama yau dai dada zancen juya ya kare kuma a gidan nan sai anemi wata, Mama hafsi ne taje gurin mama Rahana da zancen ita kuma ta tafi gurin Ummi duk sunyi mamakin jin wanan labarin su ma, Nan Ummi take fadawa su mama,saude da Atika suma dai sunyi murnan fili tare da fatan Allah ya raba lafiya, Zance ya fara dan yawo a,cikin shiya har maganan yakai ga kunnen, Sadiya da uwarta, Ai kuwa ba karamin tashin hankali, suka shiga ba don duk sun rude, Sadiya ranan bala,i tasa wai bata yarda ba na tafi na dauko ciki a waje an kananadeshi za ace wai nashi, Ranshi ya baci yace wallahi kada tafara ta sheganta mashi cikin shi idan bata da hankali ne shi yana da shi, Nan sukai ta sa in sa da ita take cewa wai ya ce baida kudi a ina ya samu kudin motan zuwa har garin mu guri na, Don haka sai ya biyata kudin ta ko ayi bala,i a gidan don bazata yarda ba ya karbar mata kudi, ya tafi gurin matanshi da su, Yace kudin ki dana karba a gaban ki nai laluran da zanyi dasu ba,wai su nayi amfani dasu zuwa garin su Aisha ba, Tun suna yin fitinan a cikin daki har takai sun futo waje nan Sadiya ta rike mai wuya akan cewa sai ya bata kudin ta, ko ta yi karan shi, Yana cewa sakeni amma ta rike shi gam nan kokuwa ya fara a,tsakanin su sai dambe ya kaure , Abinda yasa su Umma,saurin fitowa daga dakunan su da,sauri kena suna cewa su bari kada yajin mata ciwo, Umma tana zuwa ta na kokarin jaye Sadiya ta sai Sadiya ta Juyo da karfi ta ture Umma da karfi tafadi zaune ta baya a cikin roban kullun (kamu) su saida bayan ta ya amsa, Duk kullun ya zuba mata,ajiki yakuma bata ko ina na gidan gaba daya yai masu fenti, Wani irin kara Umma ta sake da karfi tana fadin wayyo Allah na,zasu karasani sun halakani ni Rabi, yau na shiga uku na lalace, Haka yasa Hanza dake dukan Sadiya ya,daina yayo kan Umma don ya taimaka mata, Ina kasa tashi tayi ai sai yaranta suka,sa ihu suna cewa wayyo ta kashe muna uwar mu, Su kuma Sa,a da Asmau sukai kan Sadiya da duka duk inda suka,samu bugu suke da kyat mutane suka kwace ta a hannun su, Nan ta figi gyalen ta jina jina tai police station kai kara wai aga irin ta,asar da mijinta da kan nen shi sukai mata, Ita kuma Umma aka kwashe zuwa dakin ta ana mata hitara sai nishi takeyi kamar zata mutu, Hamza ya koma daki don ya cire rigar shi da,Sadiya ta yaga mai yai kaca kaca, dashi, Mama tace kada yai saurin cirewa ya tafi dashi police station haka na don aga sheda, Take zance ya gama ruda uguwa mutane suka,shiga zagin Sadiya nan Uwar ta tashigo gidan da nata tawagan, Amma suna ganin irin ta,asan da akaiwa Umma sai jikin su yai sanyi dole akaje daukowa Umma mai duban kariya saboda a duba lafiyan ta, Yan sanda sukazo gida din tafiya da Hamza nan mutanen Uguwa suka mara mashi baya irin su baba Mudi da,sauran dattijan uguwa, An mayar da basain zancen an fahinci matsalace ta maurata don haka akace su tafi gida su sulhunta a tsakanin su, Umma ta samu targade a kwatolon ta don haka dole sai an dan mata dori a kan shi kafanta ma ya,gwauce sai an ja matashi, Anaja tana hawaye sai faman nishi da gumza na,wahala takeyi mutane suna mata sannu dafa wajen kofan ta, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Yana tsaye a bakin bakin gado yana dauko kaya daga cikin ledan shi, da ya,shigo dakina da shi, Yana kokarin ciro kaya daga cikin ledan ban mai magana ba,sai samun guri da nayi na zauna a hannun kujera na, Dan juyowa yayi inda nake zaune don tun da na,dawo a,wanan lokacin ne muka samu kebewa a tsakanin mu sai a wanan lokacin, Sannu da,aiki yace min yana kokarin saka wani wando a jikin shi batare da ya jira na amsa mai ba yake ce min, Kada faki dinga aikin da yafi karfin ki yanzu tunda kina a cikin condition kada kijawa kan ki ciwo, Ban ce uffan ba,sai mikewan da nayi na kwashe kayan daudan da ya kwabe min a tsakar dakina, Nafita da su har lokacin Sadiya tana zaune daga kofan ta tana dan bubuga kafan ta a hankali, Kafin na koma dakin yafito zuwa kofan gidan ni kuma,sai na,wanke kayan daudan don ban son tara kayan wanki a,dakina, Lokacin da nake shanya kayan ne naji muryan Sadiya a kaina tana fadin amma dai kin san cewa nice da hakkin wanke kayan nan bake ba ko, Tankar ban ji ta ba nai banza da ita kamar badani takeyi ba, Takara matsowa kusa da gurin da nake tsaye tana cewa, duk wani rawan kan da akeyi a kan dawowan ki ni bai rudani tunda nasan badon Allah akeyin shi ba, Kafin na bata amsa sai muryan Ibrahim wanda ya shigo gida yayi alwala, muka ji yana cewa ke Sadiya iskan cin naki kuma har ya kawo ga wanan boyar Allah da bata ma,san kina yi ba, Tace au ashe boyar Allah ce niko boyar ka ko ? Gaf da ita ya karaso cikin nuna mata dan yatsa yake cewa wallahi wallahi iskanci kada ya kawo a kaina don zan iya maki mugun bungun da sai kin kwanta asibiti wallahi, Mama tai sauri fitowa daga dakin ta tana cewa kada kafara kyale ta tai tayi tunda ita bata da marmari , Kayi abu ance ka barshi bata san ta barshi ba,sai ankai ga yadda ba,a son kaiwa sannan hankalinta ya kwanta, Barta mama Wallahi ni yanzu sai nayi fata fata da ita Allah ko, Tunda kaine Ubana ai sai ka yi mugani to aida kina da uban ne zakice mu na haka keda kike yar mace, Haba yau ina wuta Sadiya ta saka Ibrahim nan ta hau zagi da ashar da zari sai da Ibrahim yakai ga zuba mata mari biyu masu kyau ta,samu guri ta nade kamar ta somay, Sai can ta yanka wani iri uban ihu ta fadi kasa tana shure shure a cikin kasa, Mama tace taufa ai kinkai ga yadda kike son akai ni wanan yarinyar masifan ki wallahi ya ishe ni a gidan nan haba dai yarinya sai kace iblishiya , Umma tana daki bakin ciki da takaici duk ya kumay ta sai jijiga kai take tana hadiyan zuciya don ta dauko wutan gasa kanta cikin gidan ta, Hamza yana,daga kofan gida zaune a majalissan su duk suna jin irin hayaniyan da akeyi har zuwa fitowan Ibrahim yana huci, Kunya da takaici duk sun rufe shi inda yake zaune cikin takaici da dana sanin auren Sadiya a rayuwan shi, Tir da Allah dai kawai yan majalissan kofan gida suke mata don dama tunda ban gari ko ruwan sha,suka aika bata basu ko na,alwala balle wani abin, ta kai masu ko ina,su ma don ba haka muka saba zama dasu ba, ****** ********* ****** Saboda sanyin da akeyi dole kowa ya shige dakin shi don sanyi yayi yawa a ranan, Daga massalaci Hamza gida yadawo dakin Umma ya fara shiga ya,samu mama tana hada mata maganin ta yai masu sannu da jiki, Sai Mama ce ke cewa fadan ka dai ya koma a kan Ibrahim dashi akai fitinan yau kuma, Tsaki kawai yaja tare da cewa kai Allah dai ya kyauta wanan hali na,Sadiya baiyi ba wallahi, Yana tambayan Umma ko ta ci abinci mama tace ai yau sai kwano duk ta cinye, Murmushi irin na mara lafiya Umma tayi tace badole na ba yau kwanon miyana da nama aciki har tsoka biyar ga mai da kamshi na tashi a miya sabanin karni da zai daki hancin mutum, Sa,a datu tace wallahi ni yau har karawa nayi don dadin abinci bansan yadda akayi na cinye shi ba tas har wanda na karo duk na ciye, Allah ya kyauta yace tare da mikewa ya na shirin barin dakin sai mama take ce mai tau matar kadai ta tafi gidan su tunda magariba, Hmmm, Allah ya kyauta yace, tare da dan guntun murmusawa, kawai, Babu inda zaka in taga dama taita zama can har abada amma babu mai binta, a gidan nan, Umma ce ke wanan magana haka a hasale cikin dan daga muryan ta,alamar ranta ya baci, Zaune nake abinka ga mai tsohon ciki gashi kuma na kwana biyu banyi aiki ba, sai naji duk yar gajiya ta kama min jikina, Da,sallama dauke a bakin shi ya shigo dakin idanuwan shi a kaina inda nake dan gishingide gefen kujera na nai filo da shi, Maimakon nai mashi sannu da zuwa irin yadda na saba yi mashi, da,farko sai kawai na,share shi kamar ban san shigowan shi ba dakin, A, hankali yakai zaune gefe yana cewa Yay Allah tare da zama ya mike kafafunan shi kan shi yana a masangalin kujeran, danake zaune a kai, Shiru ne ya,dan biyo baya dakin dagani har shi ba wanda yai magana sai can cikin wata kasalaliyar murya naji shi yana fadin Hummai, wai fushi kike danine ko kuwa don naga kamar har yanzu baki huce ba still kina jin haushina, haka, Sai naji ya wani furzo iska daga bakin shi tare da dunkule hannayen shi guri daya, Cikin yar muryan da ba zai iya fassarata ba nake cewa akawo maka abinci ne yanzu, Cikin dan marairaicewa yace idan na samu zanci ai, tunda za,a bani ai na gode, Mikewa nayi na jawo dan stol din dakina na aje mai a gaban shi tare da kawo mai ruwan sha mai sanyi, Fita na yi don na kwaso shanyin da na shanya da yamman nan ,sai naji sallaman wasu mata biyu, Na dai karba sallama amma dana fahinci su Sadiya ce sai ban tsaya gaisawa dasu ba na shige ta gaban su kawai, Suka bini da idanuwa caaaa suna kallon irin yadda na mulmule na koma gwanin ban sha,awa dani, Dakin ta suka nufa a lokacin nai alkawarin nuna mata iyakarta nima, don daga kofan daki nake a zaune, Yana daga ciki yana cin abinci hankalin shi kwance sai nake cewa badon naso ba yaya su Anty Hinda da yaranta ? Sai da yai yar ajiyan zuciya yake cewa duk suna lafiya dazun na je na,fada masu cewa kin dawo ai, Yana kai nan sai muryan Sadiya muka ji daga kofa tana cewa wai ana magana da kai, cikin wata murya kamar ta fada, Da sauri naga ya,dago kai ya dan kalle ni tare da tsaki, yana cewa ita,wanan yaushe ta,dawo ne wai,, Kodai yaushe ne sai ta jira idan girki yazo kanta sai bakin su gan ka don yanzu ba lokacin ta bane, Murmushi yayi cikin mamaki yake cewa kema kin koyo naki kalar ke nan, Banyi magana ba sai saya kofan dakin da nayi tare da,sa sakata, ta cikin dakin, Gurin na samu daga gefen shi na zauna ina jin muryan su daga waje mama hafsi nacewa, tunda sun rufe kofa ai sai kuyi hakkuri ku tafi sai da safe ko, Muryan ta,kamar rana,ba,dare ba rara take cewa aiko sai dai mu zuba da mutum a gidan nan don nafi mutum rashi nasiha, Ni za,aiwa iyayyena wullakanci akan watacan wallahi kunyi kadan kuyi min rainin ayyo, Na mika mai abin wanke hannu yawanke tare da ba shi abinda zai zuba ruwa acikin sa, IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Yana tsaye a bakin bakin gado yana dauko kaya daga cikin ledan shi, da ya,shigo dakina da shi, Yana kokarin ciro kaya daga cikin ledan ban mai magana ba,sai samun guri da nayi na zauna a hannun kujera na, Dan juyowa yayi inda nake zaune don tun da na,dawo a,wanan lokacin ne muka samu kebewa a tsakanin mu sai a wanan lokacin, Sannu da,aiki yace min yana kokarin saka wani wando a jikin shi batare da ya jira na amsa mai ba yake ce min, Kada faki dinga aikin da yafi karfin ki yanzu tunda kina a cikin condition kada kijawa kan ki ciwo, Ban ce uffan ba,sai mikewan da nayi na kwashe kayan daudan da ya kwabe min a tsakar dakina, Nafita da su har lokacin Sadiya tana zaune daga kofan ta tana dan bubuga kafan ta a hankali, Kafin na koma dakin yafito zuwa kofan gidan ni kuma,sai na,wanke kayan daudan don ban son tara kayan wanki a,dakina, Lokacin da nake shanya kayan ne naji muryan Sadiya a kaina tana fadin amma dai kin san cewa nice da hakkin wanke kayan nan bake ba ko, Tankar ban ji ta ba nai banza da ita kamar badani takeyi ba, Takara matsowa kusa da gurin da nake tsaye tana cewa, duk wani rawan kan da akeyi a kan dawowan ki ni bai rudani tunda nasan badon Allah akeyin shi ba, Kafin na bata amsa sai muryan Ibrahim wanda ya shigo gida yayi alwala, muka ji yana cewa ke Sadiya iskan cin naki kuma har ya kawo ga wanan boyar Allah da bata ma,san kina yi ba, Tace au ashe boyar Allah ce niko boyar ka ko ? Gaf da ita ya karaso cikin nuna mata dan yatsa yake cewa wallahi wallahi iskanci kada ya kawo a kaina don zan iya maki mugun bungun da sai kin kwanta asibiti wallahi, Mama tai sauri fitowa daga dakin ta tana cewa kada kafara kyale ta tai tayi tunda ita bata da marmari , Kayi abu ance ka barshi bata san ta barshi ba,sai ankai ga yadda ba,a son kaiwa sannan hankalinta ya kwanta, Barta mama Wallahi ni yanzu sai nayi fata fata da ita Allah ko, Tunda kaine Ubana ai sai ka yi mugani to aida kina da uban ne zakice mu na haka keda kike yar mace, Haba yau ina wuta Sadiya ta saka Ibrahim nan ta hau zagi da ashar da zari sai da Ibrahim yakai ga zuba mata mari biyu masu kyau ta,samu guri ta nade kamar ta somay, Sai can ta yanka wani iri uban ihu ta fadi kasa tana shure shure a cikin kasa, Mama tace taufa ai kinkai ga yadda kike son akai ni wanan yarinyar masifan ki wallahi ya ishe ni a gidan nan haba dai yarinya sai kace iblishiya , Umma tana daki bakin ciki da takaici duk ya kumay ta sai jijiga kai take tana hadiyan zuciya don ta dauko wutan gasa kanta cikin gidan ta, Hamza yana,daga kofan gida zaune a majalissan su duk suna jin irin hayaniyan da akeyi har zuwa fitowan Ibrahim yana huci, Kunya da takaici duk sun rufe shi inda yake zaune cikin takaici da dana sanin auren Sadiya a rayuwan shi, Tir da Allah dai kawai yan majalissan kofan gida suke mata don dama tunda ban gari ko ruwan sha,suka aika bata basu ko na,alwala balle wani abin, ta kai masu ko ina,su ma don ba haka muka saba zama dasu ba, ****** ********* ****** Saboda sanyin da akeyi dole kowa ya shige dakin shi don sanyi yayi yawa a ranan, Daga massalaci Hamza gida ya dawo dakin Umma ya fara shiga ya,samu mama tana hada mata maganin ta yai masu sannu da jiki, Sai Mama ce ke cewa fadan ka dai ya koma a kan Ibrahim dashi akai fitinan yau kuma, Tsaki kawai yaja tare da cewa kai Allah dai ya kyauta wanan hali na,Sadiya baiyi ba wallahi, Yace ina can gurin neman kudin da zan kai wa yan sanda gobe ne ranan da suka yanke muna mukawo ko su kaini kotu, Duk na zagaye garin nan ban samu wanda zai ara min koda dubu goma ba , Mansur ne, kuma ina jin nauyin shi sosai don irin halarcin da yake min yaiyawa wallahi, Tafiyan nan da mukayi zuwa garin su Aisha duk da kudin shi mukayi shi babu ko sisina acikin tafiyan, Umma daga inda take zaune take cewa Allah, Allah ka taimake mu ka rufa muna asiri, Amma sai naga ai ga matarka ta dawo da abin arziki daga garin su may zai hana ka tambaye ta tabaka koda buhu hudu ne ka,sayar kabiya kkudin, Da Hamza da maman da ke zaune gefe sukace haba dai ai wanan ya zama rashin hankali, Mama tace ai ita Humaira ta daban ce zata iya bayar da kudin batare da wani ya sani ba, kuma ta basu baya, Amma dai daga dawowanta jiya jiya muce kuma zamu karbe mata,abinda tadawo dashi, Ai sai a raina muna hankalin mu a dauke mu mayaudara muna mata wayyo ne kawai, Ya mike yana cewa Allah dai ya rufa muna asiri kawai don komai akace Allah an kare zance ko, ya mike Yana tambayan Umma ko ta ci abinci mama tace ai yau sai kwano duk ta cinye, Murmushi irin na mara lafiya Umma tayi tace badole na ba yau kwanon miyana da nama aciki har tsoka biyar ga mai da kamshi na tashi a miya sabanin karni da zai daki hancin mutum, Sa,a datu tace wallahi ni yau har karawa nayi don dadin abinci bansan yadda akayi na cinye shi ba tas har wanda na karo duk na ciye, Allah ya kyauta yace tare da mikewa ya na shirin barin dakin sai mama take ce mai tau matar kadai ta tafi gidan su tunda magariba, Hmmm, Allah ya kyauta yace, tare da dan guntun murmusawa, kawai, Babu inda zaka in taga dama taita zama can har abada amma babu mai binta, a gidan nan, Umma ce ke wanan magana haka a hasale cikin dan daga muryan ta,alamar ranta ya baci, Hamza murmushi kawai yayi don takaicin da yake ji a ran shi, Zaune nake abinka ga mai tsohon ciki gashi kuma na kwana biyu banyi aiki ba, sai naji duk yar gajiya ta kama min jikina, Da,sallama dauke a bakin shi ya shigo dakin idanuwan shi a kaina inda nake dan gishingide gefen kujera na nai filo da kujeran,, Maimakon nai mashi sannu da zuwa irin yadda na saba yi mashi, da,farko sai kawai na,share shi kamar ban san shigowan shi ba dakin, A, hankali yakai zaune gefe yana cewa Yay Allah tare da zama ya mike kafafunan shi kan shi yana a masangalin kujeran, danake zaune a kai, Shiru ne ya,dan biyo baya dakin dagani har shi ba wanda yai magana sai can cikin wata kasalaliyar murya naji shi yana fadin Hummai, wai fushi kike danine ko kuwa don naga kamar har yanzu baki huce ba still kina jin haushina, haka, Sai naji ya wani furzo iska daga bakin shi tare da dunkule hannayen shi guri daya, Cikin yar muryan da ba zai iya fassarata ba nake cewa akawo maka abinci ne yanzu, Cikin dan marairaicewa yace idan na samu zanci ai, tunda za,a bani ai na gode, Mikewa nayi na jawo dan stol din dakina na aje mai a gaban shi tare da kawo mai ruwan sha mai sanyi, Fita na yi don na kwaso shanyin da na shanya da yamman nan ,sai naji sallaman wasu mata biyu, sun shigo gidan, Na dai karba masu sallama amma dana fahinci su Sadiya ce sai ban tsaya gaisawa dasu ba na shige ta gaban su kawai, Suka bini da idanuwa caaaa suna kallon irin yadda na mulmule na koma gwanin ban sha,awa dani, Dakin ta suka nufa a lokacin nai alkawarin nuna mata iyakarta nima, don daga kofan daki nake a zaune, Yana daga ciki yana cin abinci hankalin shi kwance sai nake cewa badon naso ba yaya su Anty Hindatu da yaranta ? Sai da yai yar ajiyan zuciya alaman cewa, yaji sanyin magana na, yake cewa, duk suna lafiya dazun na je na,fada masu cewa kin dawo ai,tace tana gaisheki, Yana kai nan sai muryan Sadiya muka ji daga kofa tana cewa wai ana magana da kai, cikin wata murya kamar ta fada, Da sauri naga ya,dago kai ya dan kalle ni tare da tsaki, yana cewa ita,wanan yaushe ta,dawo ne wai,, Kodai yaushe ne sai ta jira idan girki yazo kanta sai bakin su, gan ka don yanzu ba lokacin ta bane, Murmushi yayi cikin mamaki yake cewa kema kin koyo naki kalar ke nan, Banyi magana ba sai saya kofan dakin da nayi tare da,sa sakata, ta cikin dakin, Gurin na samu daga gefen shi na zauna ina jin muryan su daga waje mama hafsi nacewa, tunda sun rufe kofa ai sai kuyi hakkuri ku tafi sai da safe ko, Mikewa naga yayi a zatona fita zaiyi amma,sai naga yana kokarin cire tufafin jikin shi ne, Gurin da,na aje kudin da Mama Rahana ta ware mai na dauko tare da cewa gashi, wai kayi hakkuri dasu, May ye wanan din yana kallon bakar ledan da nake kokarin mika mashi a lokacin, Sai ya karba kafin na bashi amsa komawa yayi ya zauna a saman kujera daga shi sai wando a jikin shi, yana kokarin bude ledan dake hannun shi, Kudin da yagani a ciki sun bashi mamaki don baiga na taba buhuhunan abincin dana zo dasu ba balle ya ce su ne, na,sayar na samu wanan kudin dake hannun shi, Humaira wanan kudin fa haka masu yawa daga ina suka fito haka ? Kudin da nazo da sune su mama suka cire ma wanan, Ikon Allah duk kudi haka masu yawa nawane Humaira,? Ban ce mai uffan ba sai naga ya mayar da kanshi a saman makari kujera yana fadin, Allahu Akbar kabiran Allah na,gode maka da,kai min baiwan wanan matar mai karamci da mutunci da rufin asiri, A hankali yace Humaira cikin wani murya mai rauni, na tabbatar da ke alheri ce a,gareni, Kamar zai kara furta wani kalami sai kuma naji yai shiru yana mai sauke wani irin numfashi, Tsayin yan mintina yashiga kirga kudin a hankali yadago kai bayan yagama yace har dubu ashirin da biyar Humaira ? Idan kika bani wanan kudi masu yawa haka to ke fa ga ki da lalura a gaban ki, Nace batare da nabashi amsa ba don ni baida wani bakin da zai min dadin bakin maza yanzu na yarda, Akwai buhun masara dana dawa sai maiwa wanda za ai amfani dashi agida, Na,shimkafa zan aje a gurina na dinga amfani dashi tunda matar ka bata son zaman lafiya a gidan nan, Ni da ta samu a gidan banyi bakin ciki da,shigowan ta ba amma,sai itace take bakin ciki da zamana dakai, Hmmm kawai yace mubar zancen sadiya kibani amsata kudin nan da,sai ku rage a raba,biyu kibar saura a gurin ki don kinga kina da lalura atare dake gashi yanzu ni banda hali kamar da, Allah zai hore min insha Allahu wanda zanyi fitar kunya dashi, wanan din dai naka,ne, su mama suka cirema, Kan shi, ya,sadda a kasa yai shiru yau kwana kusan shidda yana yawon neman koda dubu goma ne wanda zasu kai police station gobe wa,adi zai cika, Sai gashi Allah ya,rufa mai asiri ta,dalilina a lokaci daya ta hanya alheri da,rufin asiri, Hawaye ne suka digo mai a hankali sai irin cin fuskan da yai min akan sadiya kafin natafi gida ya,fara fado mai arai, Saboda kawai ance tana da ciki yadinga nuna mata fifiko akaina,sai abinda tace a gidan akeyi, Ashe ni ce mai daukr da cikin da ta,dace ace ya taimakaw da kullawa ba,Sadiya ba Matar da ba matar rufin asiri ba gashi dan kudin ta daya karba,duk gari sai da kowa yasan abinda ke a tsakanin su,, Amma acikin dare daya gashi Allah ya rufa mashi asiri ta hanyar wanan baiwar Allah, Dubu bibiyun da mama Rahana ta bayar abawa su Umma da mama hafilsi nakara miko mashi yace wanan kuma fa, Nace su mama za,a bawa, da Umma wai su ma suyi hakkuri daga haka na shiga shirin kwanciya kawai na bar shi nan zaune nan ya zurfafa ga tunane, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,, Ban yarda komai ya,shiga tsakani dashi ba don baima ga fuskan hakan ba, a gurina, Kafin wani lokaci har nagama abin karyawa nabawa kowa nashi masu fita zuwa gurin neman kudi, Na kaiwa su Umma nasu har ita mai jidalin na kai mata,nata a kofan ta ban dai shiga dakin ba, Barcin Hamza ya koma ni kuma wanka nafito ina tsaye nake ina,shiryawa naji a na,wani irin sallama da karfi daga kofan shigowa gida, Nake mamaki a raina waye kuma ke wanan sallaman haka kamar zai shigo, Mama naji tana cewa Innalillahi wanan mutumin baya ko bari gari ya,waye sosai zai wani sallamawa mutane haka, Abinshi yazo amsa don haka ai sai a fito a bashi Sadiya ce ke fadin hakana, Muryan mama hafsi daga kofana take fadin Aisha idan Hamza idon shi biyu ki fada mai ga mutumin nan ya zo, Nan na fahinci wanda ke binsa bashi ne yayo sammako irin haka, A hankali nake tashe shi ya tashi ana mai sallama a waje, Yana bude ido yaji muryan mutumin hamdallah yafara yi sannan ya mike da salati ya fita yana daga labule zai fita na hango Sadiya tsaye a kofan ta ta bishi da harara, Murmushi nayi nace aiki, wai daukan dutse da yatsa mace ki sawa kanki mugun kishi irin haka, Ina fitowa sai naga har Umma dake zaune daki ta dan rarafo zuwa waje duk sunyi zurun zurun gaba dayan su fuskan su na fuskantar kofar gida Sai mamace ta yafa zuwa wajen itama Sadiya ko sai wani zabura take tana yan aikace aikacen karya, Kasa kasa take magana cewa wai wanda yake da matsala shine harda kara shigewa barcin safe kamar wanda baisan mace ba tun farko, Mutumin tare da dan sanda yazo hamza yana fita sai yake ce mashi, may yasa yadawo maigida ai case yana hannun police ne don haka goma akace su hadu police station ko, Mama tace kai kabishi sannu mana a wanye lafiya don haka aiba komai bane, Kaidai kayi hakkuri kawai take cewa mutumi n a cikin yar lalashi irin ta manya, Mama don Allah ki barshi ki koma gida sai goma zamu tafi nida Baba Mudi police station din, Suka tafi suna cewa sai an hadu din a police station din ai yau bazai daga mai kafa ba,sai ya sa,an daure shi, Suna shiga gida mama ke cewa aida kabishi sannu yaron nan don yadan yi hakkuri tunda babu kudin kaga,ai da,sai a bashi hakkuri, ya kara ma,wani dan lokaci a gani, Barshi kawai mama insha Allahu muna rabuwa lafiya dashi bari nai wanka mufita yanzu, Sadiya kamar idanuwan ta zai fito don gulma duk ta matsu taji yaya za,a kwashe dashi da iyamuri mai kudi, Don ita haushinta shine kawai ya shiga gurina ya kwana kuma harda kara kwantawa da,safe, wai barcin safe, da mace, Fitan Hamza da yan mintina sai ga,su Kubura sun shigo tana goye da yarta a,baya yarinyar tayi wayau sosai, Sadiya tana kofan ta tana zuba ruwan jarka a buket tadago kai suka hada ido da,Kubura sai kubura ke cewa, Ke mai kika takane da bazaki gaida mutane ba ki wani ganni kin share kamar ba Sadiya tsami ba, Nan suka tsaya kar ta,sankar suna fadawa juna bakaken maganganu acikin wasa wai, sukr sukar junan su, Na karbi yar ta a bayan ta na,shiga daki itama tashigo take cewa mutanen illela baku so dawowa ba,dai nake gani shiru haka duk wanda na tambaya ace min wai baki dawo ba kina can har yanzu, Mun gaisa tare da dan taba hira akan irin iskancin da,Sadiya take shukawa a,gidan, Take cewa ai gara da,taiwa Umma haka tagani tunda tace bata da mutunci yanzu ta hadu da gamon ta ai, Da,zata tafi har kofan Sadiya ta tafi ta daga labule tana cewa ita ta tafi don taga tana wani shan kamshi bayan tasan cewa, Mijin kaunata ta,aure kuma,shine har zatayiwa mutane rainin senses Ta kuru Aisha ta,samu wallahi da itace koda gigi bata shigowa gidan balle har taiwa mutane iskan ci, Kallin su kawai mukeyi don dama kawaye ne tare suka tashi suna,rashin jin su tare kowa yasan kowa a cikin su sai dai ita,Sadiya tasan Kubura ta fita tsula iskan ci don ko yanzu zasu iya karawa intai wasa, ****** ********* ****** Bayan ya dawo yai masu Umma,bayanin komai ya kuma basu nasu da tsaraban da nace ayi amfani dashi a gida, Sai suka shiga godewa suna sa albarka tundai ma mama Hafsi da ta zake tana ta yabona Umma,sai yar dariyar yake takeyi kawai, kunya da nauyi duk ya rufe ta, Nasha godiya aranan gurin iyayyen shi har ma,da yan uwan shi ,hakan yasa Sadiya kara hakeni a ranta, Nai kwana biyu na nafita batare da,wani abu ya shiga tsakanina da Hamza ba a gidan, Sadiya ranan da ta karbi girki murya har kofan gidan don ta kasa boye zumudin ta a fili, Allah yasa nasan halinta don haka nagama duk wani abinda ya dace nayi da wuri na shige daki abina don dai nasan komai tsiyan ta sai yamma zai bar dakina, Yashigo gidan a gaji yasamu tana bakin gurin da muke girki baiko kai ga karasa shigowa ba take cewa , Yau dama yanzu nake zancen ka don man da zanyi miya baida yawa kadan na samu a roban mai, Yace cikin mamaki tare da kallon ta wani iri haba Sadiya ai dai kya bari na karaso na huta kafin ki min zancen wani abu can, Tace so nake na dora girki da,wuri na kare, shiyasa na tambaya, Tau banda shi sai ki barni na huta ko don agajiye nake, kiyi amfani da kadan din da kika gani, Har ya dan gwauta ta kadan sai take cewa amma da matar ka tai girki naga komai ka sayo mata a gidan nan, Kana ta,wani rawan kafa akan dawowan Aisha don kawai kaga ta dawo da yan tarkace daga kauyen su, Hmmm aikema sai kije kauyen ku ki samo min sai naita rawan kafa akanki, Amma dai kasan muna da kauye zuwa dai ko? Ai dan nasani yasa nake ce maki kema sai ki tafi ki kwaso min, Nan ta,soma tayar da harshe tana son zancen ya koma masu na fitina sai cewa yayi na ban ba Aisha ko kwandala,ba, da,tai girki kuma ban sayo mata komai ba, Ai tamayi kokari da tabar maki guntun man don itace ta,saya abinta,da kudin ta, Bazan saye ba idon na,saya kake cewa hakan baza,a saya din ba, Ina sharan dakina saboda yamma tayi don zuwa biyar na yamma duk na gyara ko ina nawa saboda sharan dare da,baida kyaun yi, Nasharo dakina zuwa kofa har kofan mama hafsi sai ban sharo part din Sadiya da Umma ba, Oho dai dadin abin nima ina d hannun yi basai an min bakin ciki ba don nima zan iya, Murmshi nayi nashiga dakina ina dariyan Sadiyan wacce ke ta zuba hauka akan kishi wai ita kan miji take wanan hauka, Ni batasan cewa akan umurnin iyayyen na dawo gidan shi ba don ni duk al,amarin Hamza yafita min akai, Don nasan kuma na tabbatar kamar sauran maza yake don samun wata,nasa shi shagala da,diyaucin da nake mai a baya, Anyi zamanin Lima yanzu gana Sadiy duk sai da nakai zuciyata nesa akan zaman gidan shi, Ga fitinan mahaifiyar shi wacce take nuna min rashin kaunarta gareni a filin Allah, Sai tsangwama da son jidalin da yan uwan shi ke min akoda yaushe sukaga daman yi min hakan Ga makwabta da Umma take bi tana bata min sunan cewa wai banda kirki ina mata kaza ina mata kaza, Sai dai yanzu wasu sun gane gaskiyan al,amarin don gaskiya tai halin ta, Wanan abubuwan su na rike a raina nake mai kallon mutum mara adalci duk da nasihan da gwana taimin nace nayi hakkuri shi hali da sauyin namiji ba mai dorewa bane, Hakan yasa nake karabawa kaina hakkuri ina shanye duk wani abinda nake ganin a gidan,. Shikan shi na lura da cewan hankalin shi ba a kwance yake ba akan share shin da nakeyi, Abin ya nadan damun shi sai dai dakewa yake baya nunawa kaman yadda nima nake shanyewa, Kwata kwata na fita zancen al,amarin shi ban rawan kan da nake a bayan kamar yadda na saba yi, ****** ********* ****** Na idar da,sallah magriba ina zaune a dakina kamar yadda nake nisanta kaina da kowa a gidan, Mama Hafsi ce tai sallama tashigo dakin ina ganin ta natashi zaune ina cewa mama ina wuni, Guri ta samu ta zauna a saman kujera hakan yasani gane cewa da magana tashigo ke nan, Bayan mun gaisa take ce min Aisha gurin ki nazo, Nace cikin jin nauyi da yar kunya,da tau mama ina mai kara gyara zamana, don sauraren ta, Yanzu Aisha irin rayuwan da kika zaba ki zauna da mijin ki kina gani shine mafi alheri a gare ki, Murmushi nayi tare da,dukar da kaina kasa cikin dan kunya, Mama tace duk irin halin da kike ciki da mijin ki a gidan nan nasani Aiaha, Sai dai banji dadin ganin haka daga,gareki ba don wanan nasan ba tarbiyanki bane, Aisha ko irin halin Sadiya kike kokarin koyo kokuma kin sauya halinki ne wanan tafiyan da kikayi, da sauri na daga kaina na dan kalleta Aisha baki dauko wakanki hanyan alheri ba don har ga,Allah zunubi zaki kwasawa rayuwan ki, Don shi namiji ko ke kadaice a,gurin shi tunkan hauni ne yau dadi gobe madaci, haka zama yake, Balle idan ance ku biyu ne ko fiye da hakana a gurin shi dole ne sai mace tayi tana hadiyan wasu bakin cikin dana mijin tare da kawar da kanta ga,abinda yake tana daurewa , Badon komai ba sai don kada wanda suke tare su fahinci rashin jin dadin ta ga wurin shi, Hakan yasa zakiga mata da yawa idan har suna bukatan dorewa a dakin auren su zasu dinga shanye bacin ran da na miji don komai ba mai dorewa bane zo mu zauna zo mu saba, Don haka kiyi sauri gagauta tsakanin ki da maigidan ki tun mutanen gidan nan basu fahinci irin zaman da kukeyi ba, Don wanan shegiyar kishiryar taki mara mutunci da zaran kin bari tagane tsakanin ki dashi wallahi zakice na fada maki a tsakar gida zata fito tana daga harshe tare da nunawa duniya komai duk da ita ma din ai ba wani zaman lafiya sukeyi ba tsakanin su, Kece dai kike hasashen kan don baki san irin wainar da aka toya ba agidan nan kanki da bakyanan, Ita kanta yaya din datai wanan hadin yanzu abin duniya yakai mata ko ina a tsakanin su don ba dadi daga ita har uwar Sadiya din duk anbata a tsakanin su, Don kowa son danshi ya rufe mai ido suna ciwa juna mutunci da tonon asiri a,tsakanin su, Yau aike Aisha Allah yai maki fada baikamata ba,ace kiyiwa Allah butulci haka, Duba fa ki gani cikine tsoho a jikin wanda Allah ne ya baki kuma ya boyewa kowa ganinsa sai lokacin da yaso , Anyi zaton cewa kina dashi ne da akaita maki giri da cin fuska ana céwa wai baki haihuwa ke juyace aure shekara uku da kai baki taba batar wata ba, Ba abinda ba,ai maki gorinshi ba a gidan nan ke har gorin arziki an maki yau waya fitar dasu daga kankin da ake ciki bakyace Allah yakawo sanadin ki kika biya mai bashin ba duka, To aiko haka ya kamata ki godewa Allah kibar komai ga,Allah don shi yasan abinda ya dace da,bawan sa, Wanan yarinyar Sadiya da kike gani ba yarinyar arziki bace idan kikai hakkuri wanan auren nasu bazai kai ko ina ina ba in fada maki, Kuma kisa ido kiyi kallon dan zakice na fada maki wallahi saboda sam bata da mutnci, Amma idan kin biye mata duk kuka bata kinga ta cuce ki ko ince kin cuci kankan ki, Duk irin rawan kan da amarya tashigo dashi wallahi Aisha idan uwargida ta daure ta,shaye shi watarana, sai ta dara saboda namiji ba dan goyo bane, Ni abinda zan fada maki kenan kada ki bari shedan yai galaba akanki ke ma ki gyara tsakanin ki da mijin ki kafin wani ya fahinci abinda ke a,tsakanin ku dashi, Don wallahi Hamza yana kaunar ki Aisha yakuma san duk irin kyautata mai da kikeyi da biyayya haline dai irin na maza don haka Allah yayi su, Kada ki yarda ki bata aljanar ki don wata wallahi, din kece zaki dawo kina dakin sani daga baya Matan kwarai hakkuri aka sansu dashi don dadin su yana gaba, Shiru tayi wanda haka ya,sani dan dago kaina na dan kalleta cikin natsuwa nace a murya mai sanyi Mama nagode insha Allahu zangyara kamar yadda kikace, Amma mama sai naga duk irin abinda nakeyi agidan sn babu maigani kiduba fa irin abinda yai min akan Lima na,shaye kamar abin baidamay ni ba, Yanzu kuma akan sadiya sai yai ta takani yadda ranshi yaso don yana ganin kamar banda gata ko kuwa ban san abinda nakeyi ba, Hmmm Aisha duk yasani wallahi yafi kowa sanin halinki bashiba ma ai kowa agidan nan yanzu yasan dadin ki, Ko waurin girki ai sun san sunyi rashinki da bakya nan don nan za,a bar abincin da ta girks saboda nai ciwuwa saboda rashin iya aiki ga dan banzan kazanta da rashin mutunci da take wa mutane yadda ranta yaso, Ke dai kawai barsu ai sun gani yanzu don Allah ya nuna masu gaskiya fada ba wanda ba,ayi ba dan dagawanan da kikayi a gidan, Ni zan tafi dama shi yakawo ni don kawai na fada maki gaskiya kin san mu mata bamu da wani power akan maza sai yadda sukayi damu, Kedai yi kokari ki nemi aljanarki kada wata ko shedan su rude ki kifada a halaka, Mama na gode insha Allahu zanyi yadda kikace min Amma ni da gaskiya na jaye komai nawane akan al,amarin shi don naga bai damu da damuwa na ba, Kaiyya inji mama ai abin ba hakana bane kedai kawai komai dan lokaci ne irin hakan da kikayi ne sai a bata goma daya bai gyaru ba wallahi, Ita bata zauna ba kema bata barki kin zauna ba don rashin fahinta irin namu na mata,ai kawai barsu da Allah yai maki yaki, Daga haka mama tafita daga dakin nawa ina mata godiya tana cewa babu komai, Zatafita suka hadu da,Sadiya a kofana sai ta,watsa wa mama harara tafara waka tana cewa munafunci dodo shi kanci mai shi, Mama bata biye mata ba ta dan ci gaba da abinda takeyi a tsakar gida, Sadiya ce da girki don haka ban fito ba ina nan ina nazarin maganan mama sai na fahinci duk zancen mama gaskiyane wallahi, Don yanzu duk amaryan da za,a auro ita gurinta shine tazo ta fitar da,wacce ta sama agidan ko kuma tasa miji yai ta musguna mata har akai ga karshen hakkurin mace itama tafara tsula nata tsiyan duk gidan ataru a rikice ba zaman lafiya, ga kowa, Hakane itama uwar gida idan an shigo mata da,rawan kai taga amarya na son kawo mata ci baya ga miji sai ta fara nata halin duk azauna ba mai dagawa wani kafa a tsakani miji ya koma kamar taya kowa na gara,shi yadda nata ra,ayin yake, A karshe wace tayi galaba da ita za,a zauna takawar da dayan, Amma idan kin zauna da halin ki na gaskiya da kowa yasan ki dashi sai dai tayi tsiyar tabarki nan don gaskiya bata faduwa kasa banza, Don haka zan bi shawaran mama na ci gaba da zama da kowa yadda na saba a baya can ta kare masu a tsakanin su babu ruwa na, Sai dai idan mutum ya shiga gonana a take zan mayar mai da martani baxan bada bashi ba, ****** ********* ****** Zaune yake a saman wani dutse dake daura da tsohon shagon shi yayinbda,abokan hiran shi wasu suke zauns saman benci da kuma tabarman da suke shimfidawa a majalissan tasu, Bakomai ne a ran shi sai irin yadda Aisha ta sauraya mashi dawowan ta daga garin su, Gaba daya ta,sauya mashi a,gidan nan duk wani halaiyan da,yasanta,dashi abaya yanzu babu shi sai guda guda, kawai, Kwata,kwata sai nisanta kanta take da kowa agidan daga shi har mama hafsi da tafi sake jiki da ita da,farko yanzu ya kula cewa,basu wani dasawa a tsakanin su kamar farko, Gashi yanzu dan tafiyan da,tayi na,farko tun bayan auren su ya,fahinci cewa ashe Aisha ta,zama mai wani jigone na,rayuwan shi gaba daya, Don a halin yanzu Allah ya,saka mai wani irin bala,in sonta a rayuwan shi, Abubuwa da dama sun faru wanda yasa ya fahinci ko wacece Aishan yarinya mai karamci da mutunci ga,sanin ya kamata uwa uba ga girmama,na,gaban ta, Bazai iya cewa,zaman shi da ita,ga irin laifin da tai mai ba,wanda,yaji zafin shi har cikin ran shi, Matace Aisha ta,rufin asiri ga,duk namijin da,ya mallaki irin ta a gidan shi, ya huta mai shi, Wanan tafiyan da,tayi garinsu gurin iyayyenta,tadade zai iya cewa wani ishara ne daga ubangiji da ya fitar dashi da ga halaka, Don yaso yayi sake na dafe da daman da Allah ya bashi, Ya biyewa shedan da,shedaniyar matanshi dama mahaifiyar shi wace bai san dalilin daya sa take kin wanan yarinyar ba haka, su taru su kuntatawa yar mutane, Boyar Allah ashe cikine a jikinta take ta faman mukurkusa tana yawan fada,mashi cew bata,da,lafiya maranta yana mata ciwo, Amma,sai yake gani kamar kishine kawai na mata,don taga Sadiya nada ciki yana bata kulawa, Shin wai shima yanzu dawani irin idone zai kalli wanan yarinyar dashi Yarinyan da ta san mutunci shi dana iyayyen sa,da yan uwan shi amma ya wullakantata a kan wata mara mutunci can, Gaskiya a tsakanin Umma da Sadiya ba zainiya cewa ga,wacce ta cuce shi ba, Don dai ita Umma itace silar hadashi da wanan shedaniyar yarinyar da kowa yasan ba,wani tarbiyan kwarai ne da ita ba, Ita ko Sadiya shu,umace ta karshe ba,tarbiya bs kunya a tare da ita ko kadan, Yayi daya,sanin hada ta,dashi da akayi yafi a kirga don ba abokiyar zama bace ita, Ga irin cin fuskan da takewa kowa a gidan yanzu yakai mai ko ina, daga,shi har iyayyen shi babu ragowa akan su, Dafarko tanayi Umma najin dadi ashe abin zai dawo har a kanta itama, Takance ke yar agwai taimakonki nakeyi don kinga yanzu inna haihu sai kawai ki dinga goya min Baby nikuma bada dadewa ba sai na kara sambado maku wani, Darawa sukan yi kawai suna jin dadi wai Sadiya ta samu ciki, duk da bai daukan wanan zancen a lokacin don idan yai magana Umma takance ina ya fito, Yau gashi bata,barkowa ba agidan kowa tanawa shedana son ran ta, Kamar kada Aisha ta dawo da ciki sai bala,in ya karu mata kullun yanzu a cikin tashin hankali take a gidan, Wai shi muna,fuki ne yasan matar shi nada ciki amma yaki fada mata tunfarko ya boye mata zancen, Sulaiman Abokin shi ne da suke hira duk yamma a kofan gidan sune yakecewa, Mijin Aisha angon Sadiya tunanen may kakeyine haka tundazu ana magana bakace uffan ba, Dariyan yake yaiwa Sulaiman din tare da dunkule hannayen shi guri guda a,saman kirjin shi cikin dan murmusawa, Yake cewa ina tunanen wani mutum ne abokin sana,a ta mutumin kirki dashi wallahi, Aiko gaskiya kayi kokari ka jona dashi don mutumin arkizi ba,a sakaci dashi, Zancen sulaiman ya tsaya mashi a rai sosai sai yake tunanen duk yadda zaiyi ya gyara tsakanin shi da Aisha sai yayi kafin abin yafi karfin zaton shi, Nafito daga daki daure da zani agaba na sai dan karamin towel dana dan yafa akaina zuwa kafada na, Ina duke a bakin randa ina zuba ruwa a bucket don na,watsa kafin maggariba yayi, Sai ga Hamza yashigo dauke da buta a hannun shi da alama ruwan alwala zai diban masu a waje, Cikin wata murya mai taushi da laushi nake ce ma Sannu da zuwa tare da karban butar daga hannunwan shi, Ya karba min yana mamaki a cikin rashi don dazun da yashigo ko kallo bai isheni ba amma,yanzu sai gashi cikin mamakin shi na karba mai a mutunce tankar babu komai a tsakanin mu Karban butar nayi na zuba mai ruwan tare da kokari mika mashi , Daidai wanan lokacin ne Sadiya ta fito da, dakinta tana cewa nagan ku muna fukai banza kawai wai kuna ci min amana ku fake ga zuba ruwa a roba kuna cewa wai taimako, Ke dauki bucket din ki ki tafi inda zaki wanan yar fitina tafara jidalinta ke nan, Haka zakace mana munafuki kawai rawa kan da kakeyi dan kaga ta,dawowa da dan abin duniya, Har yafita yayin da take tsaye tana masifa ita kaida,a gurin, Kai ke dai wanan yarinyar wallahi kin faye masifa ace mutum.kullun sai mutum yai masifa a raguwan shi na,safe daban na yama daban, Kibawa kan ki lafiya kawai yafi amma wanan irin rayuwan bai ma ki kyau ba wallahi, Rufe min bakikin ki tsohuwar munafuka kawai ai dakece ake hada bakin duk abinda akeyi a boye, Cikin mamaki Umma ta bude bakin ta tana cewa Sadiya nice kuma mufuka yau gidan nan, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE Duk abinda ke wakana a tsakanin Umma da,Sadiya ko kallon ba su isheni ba, banyi har aci a,sude don kan su, akeji saboda kaikaine ya koma a kan mashekiya Don nice akaso aiwa wanan hadin kan aimin cin fuska yadda rai yaso, Sai Allah ya kareni daga duk wani sheri da kule,kulen da aika yi akaina, Matsala ta tsakani nada maigida na ne ban damu da,zancen su ba ni sam, Don da,zaran na karbi girki mun shiga cikin rikici ke nan da,shi akan wai gudun shi nakeyi, Sam yaki gane kaina tun da na dawo acikin ya,dan samu rangwamay ke nan akan fadar da mama tai min, Yau ma kamar kullun ina zaune a bakin gado na na zuba uban tagumi fuskana babu sasauci a cikin sa, Babu abinda nake tunane sai irin wanan rayuwan da na tsunci kai na a cikin gidan Hamza, Tambayan da a kullun nakeyiwa kaina shine a haka zan zauna naita zama har na haihu abinda zan haifa ya tsunci kan sa cikin irin wanan rayuwan, Jin an taba kofa dakina yasani saurin dago kaina duk da nasan cewa ba kowa bane sai Hamza, Shigowa dakin yayi da,sallaman shi na dan dago kai tare da dan tsura mashi idanu, Gaba daya naga duk ya canza min a fuska ya sauya min duk ya ramay yai baki ga,sutura,duk sun yi wani motsu motsu, Sannu a hankali yakai zaune daga gefena kadan yana mai sauke ajiyar zuciya, Cikin sanyin murya yafara min magana da cewa, Aisha wanan zaman banzan danakeyi a rayuwa ta ya fara isata ace mutum ya zauna ba wani sana,a da yakeyi dan kudi na,shigo mai na rufin asiri Sai da kullun mutum ya yini zaune a lalace ba wani abin yi a gaban shi, Gashi banda wani dan uwa ko jigo da zan iya tunkaran shi don ya taimaka min Cikin dan tausasa murya nace niko a ganina may zai hana kafara dan aikin karfi kana samun dan canji, don kaga girman kai shine ke cutuwar dan arewa, Shiru yayi tare da dan furzar da iska daga bakin shi a hankali, Yace in sha Allahu zan gwada hakan ko zan dan samu nayi nayi,, Can kuma sai yadan tausa muryan shi yana cewa, Ni abin ma duk yai min yawa wallahi a waje ba dadi gida ma ba,dadi mutun da iyalinsa suna gudun shi balle na,waje, Nace cikin daure fuskana saboda na gane may yake nufi, haba, dai yaya ya kamata ace iyanzu ka fahince ni fa, Bafa zan yarda na karya dokan likita ba don idan wahala,ya cika dani babu mai kula da al,amarina balle ya taimaka min, da ko zuwa asibiti ne balle gurin likita, Hmmm Aisha Humaira ya kamata ace yanzu k8n hakkura da,abinda ya faru a baya tsakani da ke bawai ki rike zancen haka ba,a ranki, Wallahi, Kinji na,yi maki rantsuwar muslmi zankiye duk wani hakkin ki da bacin ranki da,ya rataya a kaina da yardan Allah, Cikin dan daga murya da ban tabayi mai ba nake cewa bana bukatar rantsuwar ka don ni lafiyata yafi min ko a yanzu Don ko cikin dagani har kai bawai mun san da zuwan shi bane don da na riga kowa kin yarda da,shigan shi a jikina tunda ba,a kaunar hada zuria dani a gidan nan, Don haka wallahi ba zan saurareka ba don kuwa ni baka da abinda zaka fada min , Duk irin halarcin da nai a gidan nan a,rayuwata rana daya aka nuna min cewa niba yar mutunci bace a gurin ku, Tun dana fara magana kan shi yana kasa sadde bai tankamin ba sai can naji ya sauke ajiyan zuciya tare da shafan kan shi a hankali, Yadago jajayen idanuwan shi yana cewa mai yazafi haka Humaira dakike fadar wanan magana? Na kara cewa a hasale rashin kaunar da ka iya,rufe idanuwan ka,kanuna min a fili shi ya jawo hakan, Yace naji zan dai kyale ki ne don lalurar dake a jikin ki kawai amma in bashi ba,ai bakifi karfina,ba,wallahi, Wani irin azaban radadin soyayyar Humaira yake jin yana taso mashi yana,sukar masa kahon zuciyar shi , Mikewa,yayi rai a bace komai duk ya rikice mashi a lokaci guda sai yake cewa, naji nasan yanzu baki bukata na,a,rayuwan ki ko kadan akan abinda ya faru a baya tsakanin mu Wanda ke kin san cewa hakan bayina bane kawai akasine aka samu a tsakanin mu, Wani irin kallon na,watsa mai mai nuna tsana a fili Murmushi mai nuna takaici yayi cikin kada kan shi, yana tafiya yake cewa watarana zaki fahinci cewa ni ba makiyin ki bane ai, Ya dan kai hannun shi da,wasa yana son ya lakatar min hancina cikin sauri na gwauce ina cewa wallahi kada ka fara na fada maka, Yayi yar dariyar yake tare da cewa Allah ya kyauta yafita yabar dakin ran shi a bace,, Ganin da nayi ya bar min dakin yasani rakashi da hararan takaici nace a fili je ka karata can da matar ka kunfi kusa ai, Muddin ina tuna irin kuntata min da Hamza yayi a gidan banga ranan da zaiyi fari a,gareni ba Da irin wanan tunanen ne har naji an soma kiran sallah magariba haka yasani mikewa zuwa yin alwala, Shiko yana fita kofar gida ya koma ya zauna tare da soma tunanen duniya, Sadiya ta,shigo gidan ahi ta,bata mashi zaman lafiya da matar shi mai kaunar shi a,rayuwa, Alhamdullah don yanzu abubuwa sun dan daidaita a tsakani da maigidan amma babu zancen kasan cewa tare da maigida a tsakanin mu don ban bada fuskan yin haka ba Saboda na fada mai ban daukan wanan akidar a tsakanin mu yanzu, Duk iya irin wayyon su na maza yai min amma bai samu kaina ta wanan harkan ba, Karshe ma,sai cewa yake wai ina gudun shine shiya kawo haka a tsakanin mu sai dai na nuna mai cewa saboda ciwon maran da ke samuna yasa likita ya fada min na,tsare kaina, Hakan yasa ni samun sassauci akan bibiyata da yake yawan yi kan zance guda, ****** ********* ****** Natsuwa ta soma zuwa wa yaya Hamza don shawaran da na bashi na yadan fara buga buga shi yabi, Matsalar sho gudane shine fitinar Sadiya gashi ba dama ya dauki wani mataki a kanta don tana da tsohon ciki a jikin ta, Sai dai yanzu da cikin ta ya girma ta dan rage fitina sai dai sa ido daga zaune take yaba bakar magana ga kowa a gidan , Harkokina nake normal duk da ina cikin lalura amma ina dan sana,ana danakeyi don gujewa zaman banza, Kamar yadda kowa ke fada min cewa naci faba da hakkuri hakan nakeyi, Don al,amarin ubangji haka yake, wani lokacin sai yayi maka abinda zakaita bakin ciki akan shi saboda wauta da rashin hakkuri irin na mu na dan adam don rashin sanin abinda yake boye a,gurin Allah, Sai daga baya sannu a hankali zakagane ai wanan abin shine alheri da a kullun kake roko gare ka , Don haka yanzu da na,samu natsuwar hankali a gida sai na fahinci cewa shigowan Sadiya a cikin mu wani hikima ne na ubangiji rashin ganewa ne yasani tayar da hankalina da farko a kan zaman ta, Don ni kadai nasan irin zaman ukubar danayi tare dasu Umma da yaranta a baya, Rayuwa nayi a gidan irin na bauta banda yancin kaina ko kadan a gurin umma, Nakan ta rokon Allah da yakawo min agajin da zan samu sasauci akan zaman aurena a gidan Hamza na samu saukin al,amari, Batare da wata fitina ko hayaniya tsakani na dasu ba ta jajibo wa kanta auren Sadiya agidan wanda yanzu shine sanadin samun saukin duk wani yawan fitinansu da,sa ido a kaina, Sai gashi da yin auren ba,aje ko ina ba zaman yaki dadi a tsakan su ni kuma na samu nawa yancin ta sanadin hakan Don haka duk halin da bawa ya,samu kanshi da mu tashi muna ta kishi irin na hauka a tsakani gara ki san yadda kika kama kanki ta hanyar hakkuri da dan basarwa har Allah ya kawo adadin abin, ****** ********* ****** Mun wayi gari da labarin haihuwan Zarah wanda kowa a gidan farin ciki yake, Mama bata tsaya ba ta nufi gidan da yan komatsai irin wanda uwa take kaiwa yarta idan ta haihu, Kamar su roban wanka na yaro da uwa sabulu wanda akewa hadin kamshi kala kala, da yan sauran tarkace irin na,al,ada, Zan ita cewa tun bayan dawowana daga gida wanan ne karo na biyu dana fita daga gidan zuwa uguwa, Na,shirya a cikin yar atamfana zani da riga masu ruwan grey color da farin zane, Na kawo hijjab dina na dagwara a saman kayan tare da jawo kofan dakina ina kokarin kulle kofan ne Hamza ya shigo gidan, Ranan yana dakin Sadiya ne don haka ban tsaya ga abinda nakeyi ba sai muryan shi da nakeji daga bayana yana fadin, Zaki fita ke nan na dan juyo ina cewa eh ina son zuwa kafin rana yai min a hanya don da kafa nake son zuwa,saboda na mike kafana, Kada ki rufe idon shi a kan kofana danake kokatin kullewa,yace ina son daukan wani abu a dakin, Hakan yasani bude kofan tare da dan jaye jikina don ya shiga daga ciki, Bayan shigan shi sai na dan bi bayan shi zuwa cikin dakin da ya shiga din, na samay shi a tsaye yana ce min Kinyi matukar kyau Humaira cikin nan ya yi maki matukar kyau sosai a jikin ki, Sai dai kassh ana min rowan na gana da dan tayina saboda wani hujja na likita wanda ba gaskiya bane hakan, Anya Humaira baki tinanen cewa kina shiga hakkina da yawa a gidan nan, Mutum da matarshi amma baida daman ya tabata ace mai zai aikata zunubi ne Cikin natsuwa nace mai wanan ne dama abinda zaka dauka din ko kuwa, Murmushi yayi tare da kokarin jawoni zuwa jikin shi, Da sauri na dan gwauce daga rugumar da yai niyar yimin tare da cewa kada ka manta da cewa banice da hakkin kaba yau, Koma nice din wanan abin bazai yi a tsakanin mu ba don ni lafiyata tafi min komai, Yar murmushi ce ta subuce mai da sauri ya dan jaye min don bani hanya na fice daga dakin, Tsaye na samu Sadiya kamar zakanya tana mai kallona cikin nazarin ko da,akwai abinda ya faru a tsakanin mu dashi, Nakecewa yar wahala sai kitayi don kece da wahala ni wanan bai damayni ba yanzu, Dakin Umma na nufa don nasallamayta cewa zan tafi a daidai lokacin da lokacin da ya fito da wani leda a hannun shi, Kamar bai fahinci mai Sadiya take nufi a ranta ba, ya wani sha toka fuskan shi a daure babu annuri, Ganin ya fita na koma na rufo kofa dakina a cikin zazzakar muryana mai tare da wani sanadarin dake sanya mai sauraron ta rudani, Saina dawo zan tafi barka a gidan Zarah na ce mata batare dana tsaya jin mai zatace min ba Sadiya tana jin abinda na fada ta wani dan tabe bakinta tana cewa wanan matsalar ki ce don baki zama kowa agurin su, Tankar banji taba sai fitan danayi abina sai jin muryan ta nayi tanacewa Hamza dakai nake magana, Nafita ina murmushi don nasan kaidin kishine kawai don kada mu fita tare dashi agidan tai wanan magana, Tafiya nake a hankali har nakai gidan su zarah din dake cike da jama,a yan zuwa barka, Na samu mama hafsi agidan itace mai kula da zarah da yaron ta, Taimin sannu da zuwa tare da bani gurin zamana zauna alokavin zarah wace tafito daga bayi take cewa ,a,a maraba da matar yayana, Cikin murnushi nake cewa matar yayan ku tana can gida zaune, Ni yar uwarkuce don haka ku daina zolayata haka da,wanan sunan, Dariya zarah dake kaiwa zaune takeyi tace rufa muna asiri da wanan bakar anobar matar Ni ai Sadiya takai min ko ina agidan nan Aisha wallahi da ace ina da iko da zan fitar da ita aida yanzu zamanta da ta a cikin gidan mu, ya kare, Ledar dake a hannuna na kayan jariri da zanin daukan yan barka na mika ma mama ina cewa asawa jariri ba yawa Godiya sukeyi tare da kokarin warware ledan don ganin abinda ke a cikin ledan, Nakarbi jariri daga hannun mama ina dan murmushi tare da cewa masha Allahu Allah ya raya muna yasa dadin musulmi ne wanan baby haka maigirma zarah kinyi kokari wallahi, Murmushi tayi tare dan dan zuba ruwan zafi a cijin wani cup ta kawo kunu mai zafi ta zuba kawai ta dan fara kurbawa a hankali, Itace ke sha nice daga gefe nake dan rutse idanuwana a hankali don jjin zafin nakeji kamar nice mai shan ruwan, A take naga ta wani hada gumi a fuskanta zuwa wuya nadan kalleta a cikin murmushi nace sannu, Itama murmushin ta mayar tare da dan share zufan tana cewa aikema kina saman hanya Aisha, Gidan an samu karuwa alokaci daya Umma dake ta cewa wai anki a haihu gashi da,Allah zai bayar sai yakawo muna duk a lokaci guda , Ikon Allah dama ai gajin hakkuri ne irin namu na dan adam ana sa Allah dole ne bai tashi ba Yanzu bagashi gurin neman kiba an samo rama ba may auren Sadiya ya kawo wa yaya a rayuwanta banda zubar da mutunci a idon duniya, Ina dadin ka zauna matar danka tana maka rashin mutinci a bainan jama a harda batin nakasa ta, Lokacin danake fada mata illar abinda take kokarin jawowa kanta zuwa tayi tafadawa Sa,a suka zo gidan sukai min rashin mutunci shine har yau ba mu gaisawa da Sa,a ko mayawa goma zatayi gidan nan ba ruwana da ita, Kin san tashin yarinyar nan kin san kuma halin uwar ta amma har ki yarda ki hada zuria da ita don rashi sanin ciwon kai, Zarah tace ai yanzu yafita a tsakanin su nima kaina saida nai laifi a gurin Umma don nace kada tayi wanan hadin da take sonyi zai iya kawo masu matsalar amintakan su, Amma Umma ta rufe ido tai min tas akan shi harda fushi tayi dani saida Alhaji yakaini na roketa gafara, Yanzu gashi za,a hada zuria dasu kinga ai dole ayi hakkuri da zaman ta tunda ina zata, Zarah ta,amsawa mama dacewa nima zancen da shi yaya Hamza yake min ke nan yace bazai iya rabuwa da mace mai ciki ba haka don shima yana gudun aiwa diyan shi ko kannen shi watarana, Don na kawar da zancen don sam ban ma son naji zancen Sadiya da Hamza din sai cewa nayi amma a,asibiti kika haihu ko tace dolema Aisha ina zan iya haihuwan wanan yaro agida, Nan muka nausa a hiran yadda ta sha wuya wurin haihuwa duk inajin tsoron hiran yafiye min jin zancen Sadiya da sukeyi, Don ni kwata kwata ban son zancen ta a raina saboda irin wanan zancen yana bata min rai sosai, Don gaskiya kishiya koda wace kuke zaman lafiya ce sa ita dole akwai wani abu a kasan ran abokiyar zaman ta,sai dai mutum yai ta kokarin boyewa don kada kafitar a fili sunan ka yafita, Don duk wace nata,yafi zafi har ta baiyyana kishin ta a,fili sunan tane yakan yifice a,duniya koda kuwa itace ake cuta sai kiga gaskiyarta ya dushe an bata mata suna da zafin kishi ke gareta, Allah ubangiji yasa mufi karfin zuciyar mu akan duk kishiyar da zamu zauna da ita aduniyan nan, Ina gidan zarah har zuwa wani lokaci tare da ita da mama sai yan barka dake zuwa yi mata murnan samun karuwa, Ina kallon irin yadda kishiyoyinta suke ta faman yin dawainiya da ita a gidan duk da nasan cewa ta kasa tana kasan zukatan su dannewa kawai sukayi, Zakice ai babu wani zancen kishi a cikin ransu a kanta suna matukar farin ciki ne da haihuwan nata, Wanda a gaskiya zancen ba haka yake ba don ko wacen su sai da ta nuna bacin ran irin yadda Alhaji Bala ke rawan kafan haihuwan zara a fili, Amma a fili suna nuna sunfi kowa farin ciki da,wanan haihuwan kishi ke nan na tsanaki sai kin daure zaki iya hadewa, Na is gida a gajiye saboda tafiyan kafa danayi daga gidan zarah zuwa namu gidan akwai dan tazara amma haka na daure nai wanan tafiyan don na san watsake jikina, Bayan na dan huta sai na kwabe nafito nafara dan aiyukan dake a gabana, Umma da tafito waje don tasha iska take tambayana yaya masu jegon su ke nadan tsaya a cikin fara,a nace, Umma baki ga dan ba gudan babba dashi wallahi zaki ce ba zarah ce ta haifi wanan yaron ba don girma, Tau ijin tana cin abinci tana kula da kanta nace Umma kin manta cewa mama na can ai mama bata yarda komai daya dace mama tanayi a gurin, Allah sarki zarah yau tazama uwa itama kamar kowa yau, Muryan Sadiya ce daga bayan mu take cewa ai dole ta haifi yaro babba tunda mahaifin shi yana kokarin ganin ya bata hakkin ta taci tasha mai kyau yadda ya kamata,,. Azatona zancen arzikine sai najuya a dan murmushi nake cewa ai abin ke dai badaga nan ba baiwane kawai Tace ijiki ba mutum ya kwana ya tashi babu wani cimakar kwarai da,zai sa jikin mutum yaginu, da kyau, Sai anan nafahinci inda zacen ta ya dosa don haka nikan na juya na nufi gurin nawa harkan nabarta nan tana zuba tana cewa, Irin wanan abinda aka dauko ko haihuwa mutum yayi ai saida gaske zai samu abinda zaici wa cikin shi balle wani dan abin maski da zai dora sama, Mama tace tau Allah dai ya sauke kowan ku lafiya yan kuda na kwana mu shine fatan mu yanzu, Umma ta gajar ce zancen Sadiya da fadin haka don tasan inda ta dosa ga maganar ta, Ga haihuwa anyi sai dai babu abin kashin kuyan a hannu don haka duk sun shiga a cikin wani yanayi na damuwa don rashin sanin taka maimai abin yi, Barci na nake irin na masu ciki hankali na,a kwancd saidai zuwa dare nakan dan tashi barci yadan gagareni har zuwa asuba sai kuma shedan yadan rudeni na koma da kyat nakan tashi nai sallah kada asuba ta,wuce ni, A hankali yau ma na bude idanuwa na dake da nauyin barci a cikin su, Muryan Hanza nake ji daga bayana kamar yana magana da wani, naji yana fadin O Allah ga bawankanan Allah kaikasan halin danake ciki a wanan rayuwan Ya Allah kada ka bari muyi kunya akan wanan al,amari Allah kai muna mafita ta hanyar alherin ka, Shiru naji yayi duk d idanuwa biyu ban nu mashi alamar cewa idanuwa na biyu ba a lokacin, Zan iya cewa yai barci amma faskiya a zahiri idanuwan shi biyu ne ba barci yakeyi ba, Don ina jin lokacin da yakai kwance bayan yagama addu,oin shi idanuwan shi suka a kaina gurin da nake kwance yayin da yake karare min kallon cikin mamaki, irin halina don a sanaiyar dayai min ni mutum ce maihakuri da dauri ga kuma uwaba sanin ya kamat, Amma gaba daya duk na canza mai tinanen shi a lokaci daya na,sake gaba daya duk da dai ba,wani rashin mutunci ko jittuwane babu a tsakanin mi ba, Amma kuma bai taba tunanen cewa zan uya bijirewa bukatar shi har na tsawon lokaci irin haka ba batare da na tausaya mai ba, Lalai mata abar su akan kishi don duk danace dokan likita nake bi yasan harda wani dalilina na,daban, Sai faman juyi yake a saman gado shi daya yana jin kansa tankar wani dan maraya mara galihu, Idanuwan shi suna a kaina gurin da nake kwance a kasa saman ledan dakina daya sha guga sai kyali yakeyi don guga, Bina da kallo yayi tun daga kafana har zuwa kai tare da sauke wani irin nufashi yana maigirgiza kai a hankali ya furta why Aisha why doing dis to me ? Mikan da naji yayi da karfi tare da lankwsa hannayen shi saida sukai kara inajin su har inda nake , Cikin dakewa nake sauraren shi daga inda nake a kwance duk tausayin shi ya kamani ji nake kamar na tashi nasamay shi narugumi abina Amma kuma sai na,karasa dauriya da dakewa a,cikin zuciyata batare dana mike na samay shi ba, Har gari ya karasa waye muna a haka kowa da abinda ke acikin ranshi, Ganin irin yadda al,amarin sunan zara yake batun bada ruwa a,gari yasani rufe ido batare dana tuna komaiba nafitar da buhu biyu daga cikin abinda ke aje a gurina na nace suyi sha,anin bukin dashi idan an samu sai abiyani, Ranan nasha godiya a guri Umma fiye da tsanmanina don har dakina take tana min godiya, Bayan an sayar akadan yi yan abubuwan da suka dace na suna dasu anyi buki lafiya an watse lafiya, Yanzu kowa ya zaunu a gida don zarah ma tana gida andawo da ita wai shan ruwan zafi, Duk da mijin baiso ta tafi ko ina ba amma umma ta matsa wai a dawo mata da diyar ta a gaban ta ta duba abinta, Mama Hafsi ta nuna mata cewa zata iya zuwa safe da yamma ta duba lafiyan ta amma fir Umma taki yarda da,zancen ta, Hakan yasa kowa gane cewa wani hikima ce ta son yaudaran mijinnata don akama ce mai kawo kawo, Sam Umma ta manta da,zancen cewa a gidan ta,akwai masu ciki haihuwan fari dake shirin haihuwa, duk da,dai sadiya bana farko bane ta taba haihuwa a baya sai da cikin yakai wata biyar tai barin cikin, sanadiyar faduwar mashin da tayi tasamu miscarriage, Sai kuma yanzu data samu ciki a gidan Hamza shine karo na biyu dayin cikin ta, Dawowan Zarah gida ya kara tayar da,wani fitina don sadiya ta nuna ba yarda da irin yadda akewa Zarah tallen miyan ta daban a,matsayin ta na maijego wai tunda mijin ta ke sayo abin miyan wani lokaci, Ni duk abinda sukeyi ba,bakona bane don haka ban daga kai na kalle su ba,sai dai nai ta abindake a gabana, ****** ********* ****** A cikin dare ina barci na dinga jin hayaniya yana dan tashi a gidan nabude idanuwa na dakyat don barci nake a lokacin mai dadi, Dana,saurara dakyau sai nake jin muryan su mamane harda muryan mahaifiyar Sadiya a cikin su, Da kyat na tashi na bude kofana sai nakejin muryoyinsu zancen na kuda naji sunayi, Ganin na bude kofana shi kuma Hamza a lokacin naga ya shigo gida da saurin shi, yana ce masu ya tafi gurin makwabcin mu don asamu mota amma yace wai motar babu mai acikin ta, Yanzu yaya za,ayi kenan ga yarinya tana ta,wahala haka tun karfe hudu na yamma bata haihu ba, Abinda ba,asani ba na juya na koma dakina don nima dai nayi nauyi sosai a lokacin, Ban kwantaba na zauna a saman kujera na ina iya tsiyakayo maganan su daga inda nake zaune, Yadda nakejin nishinta har dakina sai tabani tausayi sosai, gani da abubuwan da ya kamata nai mata amma kuma kishiya ce ba halin na taimaka mata, Nishin da naji yai yawa uwar na mata,fasa wai ta nisa kwarai tasa nafito nace mama ta daina mugun yunkurin nishi don kada ta samu matsala, Sadiya tanajin muryana ta daga murya tana fadin Aisha don Allah kizo ki taimaka min kada na mutu ba,a,samu motan kaini asibiti ba, Uwar tace baki da hankaline da zakice kishiya ta karban maki haihuwa, Daki na koma abina don jin abinda uwarta tace min sai faman fada take mata wai ashe bata da,wayyo, Sakata nasawa kofana,saidai gaskiya ban samu yin wani barcin kirki ba don tausayin ta, da nake ji, Barci barawo nasamu ya dan daukeni zuwa asuba naji ana ta buga min kofa da karfi da sauri na budd kofa mahaifiyar sadiya ce da mama suke tsaye a kofana, Mama take cewa don Allah nazo na duba,Sadiya tana a cikin wani hali, Na,rasa yadda zan yi do gaskiya nace bazan taba taba don ina gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, Fita nayi zuwa kofan ta,wanda zance na mata yaushe rabon da naje dakin Sadiya koda kuwa kofan tane, Kayane kamar dakin tsohuwa ko ina sai doyin tsamin dauda da dakin keyi, Mama da mahaifiyar ta naiwa kwatancen yadda zasu taimaka mata na fake da cewa ni bazan iya ba don bana jin dadi, Ina daga kofa nake basu directions ba adauki lokaci mai tsawo ba,sai tai wani nishi maikarfi sai ga da yafito, Ikon Allah muna ta,wahala tun dazun ashe ga abu da saukia gida, Gaba dayan su bazu kula da cewa yaron baiyi kukaba,sai faman cewa suke namiji ne gashi gudan babba dashi, Nace mama ku yanke mai cibi don ya samu yadan huta ko, Saboda yasha wuya kuma gashi baiyi kuka ba nan hankalin su gaba daya yadawo ga zance na rezan ma Sadiya bata dashi sai gurin Zarah aka,samu sabon reza, Yaro yaki kuka har tsawon wani lokaci nace gaskiya su kaishi asibiti da sauri don a duba lafiyan shi, Yaron yana hannun Umma, sai numfashi yake sama sama wani iri saboda wahalar da ya sha a ciki, Ruwan wanka na,dora masu sai mamace tazo ta karbe ni tana cewa jeki huta kinji Aisha kema ai ba lafiyane dake ba, Tunda,safe suka tafi asibiti sai gasu sundawo suna cewa wai anbasu gado saboda yaron baida lafiya ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Gaba daya hankalin kowa,a gidan a tashe yakd saboda wanan haihuwan da akayi, Sai dai kuma,gashi an samu karuwa,amma kum,yaron baizo da lafiya ba a jikin shi, Babu wanda ya zauna a gida don hankalin su ya na a gurin yaro mara lafiya, da uwar sa, Ina zaune a kofan dakina na saman tabarman dana shimfida a kofar dakina don daki a kwai zafi sosai a cikin sa, Kafafuwana da suka hau suka kumbura sunyi sutum sutum dasu, Gyara zama nayi cikin kara jingina baya na da bangon da nake zaune a gefen shi, Tausayin kaina ya kamani don ba bu wanda ya,damu da damuwana agidan kowa hankalin shi na kan haihuwan da akai masu sai farin ciki sukeyi, abinsu, Ibrahim wanda tun safe ban gan shi ba,a gida ya,shigo da,alama bai kwana a gida ba dawowan shi ke nan a lokacin, Har zai shiga dakin mahaifiyar su sai kuma yadan dawo baya yana dan kare min kallo ya ke cewa madam yaya akayi ne wai,? Dan murmushi nayi tare da,gyara,zamana nasan har kullun duk cikin diyan Umma babu mai kaunana yadda Ibrahim yake matukar nuna,mi kullawan akoda yai she, Cikin murmushi nake cewa sai yanzu aka,dawo kenan yace wallahi kin san aikin mu sai a cikin dare muke tashi mu fara kwaba flower don kada mu makara, Yana shiga dakin shi sai ga Hamza ya shigo gidan da ganin fuskan shi kasan cewa yana a cikin matukar damuwa Sannu da zuwa nai mashi tare da dan yunkurin mikewa,zaune da kyau nayi don na fuskan ce shi,. Tambayan shi nayi cewa yaya jikin yaron sai yake ce min cikin dan canza fuska mai nuna damuwan mutum da cewan da,sauki a takaice, Murya mai nuna damuwa a fili yadan ce a kasalance magani aka rubuta na,sayo na,samu na,sayo wasu wasu kuma ban samu sayan su ba tukun, Shiru na dan yi zuwa wani dan lokaci ina zancen zuci don nasan yau duk inda zai shiga neman kudi a garin nan ya shiga don yai fari a gurin Sadiya in ba haka ba su sa kafan wando guda dashi da ita, A sake na dan dago kaina nake cewa a zubo ma abinci ne kadan ci ko ? na nuna kamar ba abinda ya damay ni a zuciya na hakana, Idon shibda suka dan kada sukai ja ya dago ya kara kallona yake cewa ashe kin samu girka abincin ne, A,sake batare da na bashi amsa ba nake cewa na,asibiti ga ya can idan ka tashi sai a kai masu nasu don rana ya soma yi ko, Na mike da kyat na zubo mai abinci a plate don nasan ba zama zaiyi ba balle na kawo mai a kulu, Na tafi de bo mai ruwan sha ya kalli abincin ya,wani sauke ajiyan zuciya tare da godiya a ranshi don yasan cewa in badon Allah ya hada shi da nice ba yau da,bai san yadda zai yi ba, Don inda Sadiya ce yadda bai bata, ko kwandala tayi girki ba,sai dai na,asibitin su mutum don baza tayi ba, wani bacin rai da,ahi kadai yasan dalilin shi yazo mai a rai abinda ya haddasa mai, bacin rai ya dan runtse idanuwan shi a hankali, Har zuwa lokacin da nakawo mai ruwan idanuwan shi suna a lumshe bai bude su ba sai da yaji motsina ya dan bude lumsassun idanuwan shi da,suka kada sukai jawur,, Ya sauke su a kaina cikin dan sake ajiyan zuciya, yake cewa wallahi duk abubuwan sun daure min gaba daya duk na zagaye garin nan amma ban samu wanda zai taima min ba da ko kwandala koda da sunan rance ne, Allah ya kyauta nace tare da mikewa nabar gurin cikin dan tafiyana da nake yi da kyat, irin ta masu tsohon ciki, Bin bayana yayi da kallon yadda yaga ina tafiya da kyat kuma a,hakan nayi muna girkin gida, Ya shiga asibiti da kulla Sadiya tana hango shi ta,fara cewa ji shi dan Allah yanzu haka matar shi ce tai girkin don rufin asiri ya wani dauko ya nufo mutane dashi, Tun dazun ance a,kawo magani amma,shiru kake ji ba,wani motsi tun safe sai yanzu ya,shigo wa mutane, da gadara aljihu babu ko kwabo, Wata matar makwabatar su da tazo duba,su take cewa haba Sadiya mijinki ne fa na,sunna kikewa wanan zari haka gaskiya hakan baiyi ba, Daidai lokacin ya iso gare su yana gaida su ya aje kayan abinci daga gefen su kadan Gurin da yaron yake kwance yana mayar da numfashi sama sama ya,dan tsaya har tsowon wani lokaci yana kallon yaron , cikin tausaya mashi, Muryan Sadiya ce tas shi juyowa tana fadin har yanzu ba,a,sayo maganin bane don nurse din ta,zo dazun tana tambayan mu ko an sayo, Ledan da ya,aje gefe tare da,abinci ya,dauko yake cewa ga,wanda aka,samu, Ke nan ba,a samu ba gaba daya ke nan gaakiya ni wanan al,amarin ya fa fara isata ace mutum kamar shi yafi kowa,shiga talauci komai mutim bai iya kata bus akan shi, Tunda,abin ya,ishe ki ai sai kiyi maganin abi ko yafada cikin dan juyawa a,fusace ya fita daga dakin, Yana fita daga,dakin ta jawo kulan abincin da yashigo dashi tana cewa bari naga yar sherin may ta,dafa muna ne wai, Tana bude kulan tayi tozali da tuwon shimkafa da miyan taushe sai kifin da nai amfani da su a ciki, Aka zuba mata tashiga ci tana ta,surutun tsiya kamar ba dantane a cikin wani hali ba na rashin lafiya irin haka, Ban samu shiga gurin su ba,sai da akai sallah azahar na,shirya na tafi dubo su a lokaci Umma ta,dawo gida ita da zarah, Tun daga nesa nake jiyo muryoyin su suna hira cikin dariya ita da matan uguwar su da,sukazo duban ta, Tana hagone ta wani juyawa ta bada baya yayin da na karaso nai ma matan da ke zaune ina,wuni, Sadiya bata juyo inda nake ba nake tambayan matan da na samu a dakin nake ya jikin yaron suka amsa min da,da sauki, Idanuwana akan yaron ina kallon yadda yake mayar da numfashi da,sauri da,sauri, Tausayin yaron ya kamani irin yadda naga yanayin shi nasan yaron yana jin jiki akwai abinda ke damun shi, Tsayin lokaci idanuwa akan yaro ban san lokacin da tausayi yasa cewa ya kuwa samu yin kukan, Har yanzu baiyi ba amma insha Allahu zai yi ai, tunda lafiya tana shigan shi a hankali muryan mama,Sa,a mahaifiyar Sadiya ke fadin haka, Tsayin lokaci suna ta hiran su Sadiya tankar bata,san da tsayina a gurin ba, Ina tsaye ina kallon wasu sun shigo ambasu yaron su dauka ni kuwa an hana min daukan shi don ina kishiya yar a,dawa, Inan tsaye dai ba,a bani ko gurin zama ba, Sai ga,wata nurse tazo tana fadin don Allah su rage yawa a,dakin don sun cika mutane da surutu , da yawa, Zan juya nima na fita Hamza ya shigo yana cewa ashe kin samu fitowa nazaci bazaki iya zuwa ba ai yadda na ganki dazun ai, yana kokarin mika ledan da ya,shigo dashi a hannun shi, Murmushi nayi nake cewa na lalabo nazo na duba su na koma,ai ba,dadewa zanyi ba, Wanan ai basu cika ba abinda aka ce guda shiddane zaka kawo kwali biyu kawai, Su na samu kuma bazanyi sata ba don kiji dadi ko ? Nurse ki duba min wanan maganin da ya,sayo don ba duka ya kawo ba sai nurse din takaraso tana dan duba maganin tace gaskiya sai ka,karo sauran zaifi don wanan kawai ai bazaiyi amfani ba, Caraf nace ai duk antibiotics ne zasu iya amfana da amfara,shan su kafin sauran su zo don su fara yi mai aiki, sai na,fadi sauran maganin da,auka rage bai sayo ba, Daga haka nasa kai zuwa waje nabarsu nan ita,da mahaifiyarta dashi da nurse din suna fafatawa inajin yana fadin shi duk ya buga bai samu kudi ba yaya zaiyi, Ya,fitowa na bude post dina na ciro kudin da ke aciki wanda,suke nan min a,hannuna,danake dan amfani dasu na mika mai, Yakarba tare da dan juyawa yana mamaki a lokacin ne wasu mata masu shiga gurin ta,suka,biyo zasu shiga dakin, Ban so su gan mu ba don nasan zasu iya fada mata tasa wani fitina kuma ba abu mai wuya bane a gurin Sadiya, Nurse din take tambayan Sadiya wanan da tafita wace ce ita Caraf Sadiya tace kishiyata ce , Tace amma dai tayi karatu ko don nnaga ta dan san aikinta gaakiya saboda itace ma kya gwada min inda,zan sa allura na,samu jijiya da sauri, Karatun duba gari tayi a nan makarantar hanyar sokoto takare shine take yar burgar aiki dashi, Nurse tace to ai tafi wanda yake zaune dip kuma wani hanyane na,samun kudi a gare ta, Matan da suka shigo suka katse hiran su da nurse din matan ke cewa ai muga kishiyar ki a kofa tana ba mijin ki kudi, Haba nan ta hau jinini saida uwarta ta kwaba ta tana cewa kada ki bari mutane su fahince ki dan Allah muji da zancen yaron da baida lafiya kawai, ****** ********* ****** Haka akaita faman kashin kudin asibiti yaron kwana biyu da haihuwa amma baiyi kuka ba,sai ma,shiga cikin wani irin yanayi da yayi Wanda duk yaga yaron sai hankalin shi ya tashi don yana jin jiki, Doctor yazo round duba marasa lafiya bayan ya,dan yi yan rubuce rubuce ya ke cewa yaron ku har yanzu bai yi kuka ba, It's means akwai matsala a tare da shi ke nan duk yadda akayi akwai tashin hankali da cikin shi wanda yai ta hadiya bacin rai tun a cikin ciki, Yana da wuya,yaron yayi rai yafadi kai tsaye cikin nuna tausayawa yake cewa don haka,sai dai muyi addu,a kawai, Sai a wanan lokacin hankalin Sadiya ya daga jin abinda doctor ya fada masu akan yaron Kuka Sadiya tafara yi sai kawar uwar ta ke cewa kinga ai irin abin da ake gudu idan kin fara abu akace ki bari baki bari kin fara fitina,sai rayuka sun kaiga baci, Yanzu kinji abinda likita ce yawan bacin rai da ciki ko fitina ya kawo wa yaron dake cikin ciki hawanjini ko wani ciwo na,dabam, Anfi son in mutum yana abu akace mai ya daina yayi hakkuri to kayi kabar wa Allah, Amma ke idan kin fara fitina kin fara ke nan sai kowa ya gama ganin ki ana nunaki don iya masifa, May ke cikin fitina ga diya mace wacce ke karkashin namiji sai yadda akayi da ita, Yanzu ba gashi ba ke aka bari da tashin hankali don kece ke kwana da,yaron a,wahalce, Kuka Sadiya takeyi a cikin tashin hankali don sai lokacin take jin wani iri a,ran ta jin cewa yaron za a iya rasa shi anytime, idan ba ayi da gaske ba,, A lokacin surutai barkatai suka fara yaduwa wasu suce ai anyiwa yaron sammu ne wasu suce manya takama,shi, wasu suce ai bakine yai mai yawa wasu kuma,suce kawai ciwo ne daga Allah, Sai a lokacin na fahinci dalilin hana min daukan yaron da akayi watau nima yar adawa ce ke nan zan iya illanta yaron ke nan, Allahu akbar kishiys kishiya duk da ta,san cewa bazan iya yiwa yaron komai ba amma,shedan ya,shiga ranta ya zugs ta kan cewa zan iya, Tun lokacib ban kara shiga,asibiti ba,sai dai nayi girki na,aika masu dashi ko azo karban ruwan zafi ko da kuwa banji dadi sai na tashi na,dora masu an kai masu shi, Kwanan yaron hudu da haihuwa yace ga garin ku ya tafiyan shi ya koma ga mahaliccin mu sarki Allah, Nagama gajiya da yawan zaryan da nakeyi na,aikin da yai min yawa na gida, ni kadai don yanzu na saba da mu biyu ke bayayyan aiki, Na watsa ruwa na dan zauna da niyar na gyara jikina riga kawai na,saka don na kasa tsaya na dan yi kwalliyan a,fuska na, Kukan mutum da naji shigowa wiwi shine ya sa gabana faduwa lokaci guda da sauri na fito daga dakina sai Sadiya nagani tashigo da kukan ta tana kuka cikin tashin hankali, Innalillahi wa inna alaihim rajjiun, na fadi tare da cewa may yafaru da sauri zarah ma tafito daga dakin su dauke da danta a kafadar ta ce badai yaron ya tafi ba, Daga bayan mu mukaji muryan mama Sa,a tana cewa ya tafiyan shi an huta ai duk wanda yasa hannun shi a ciki sai yayi dariya mu gani shi, Cikin hanzari zarah tace haba mama Sa,a don Allah kubar yaron ga ya huta dan wanan jaririn har wa zai tsonewa ido kuma Alkah ne dai baiyi shi rayayye ba kawai Allah yasa ya huta Na amsa daga inda nake tsaye a sanyayye da amin ya Allah, Nikan ina jin kalaman su kawai sai na juya zuwa dakina don nasan fitina suke ji ke nan, Take barka ya koma gaisuwa sai da kanajin muryan Sadiya sama wai tana mayar da yadda,akayi, Ina jin yadda wata mata take mata magana akan ta tausasa harshen don rashi tayi duk da,cewa yarone yarasu din, Ajiyan zuciya na saukar cikin tausayawa yayin da nake tuna irin halin da naga yaron a,asibiti danaje, Nima dai gani dai, don ban san yaya tawa haihuwan zata zo min ba sai kawai tausayin kaina ya kamani Idanuwa na,suka kada sukai ja saboda tsoro da fargaban abinda kaje yadawo don nima din ai ina acikin damu tun farkon samuwar wanan cikin nawa har zuwa yanzu, Sai wata zuciya take ce min ai lamarin damuwar ku ba,daya,bace don ke ba,wani mugun nufi kike kullawa a ran ki ba damuwa ce kawai irin ta yanayi idan yazo, Allah ya kyauta nace a fili tare da dago jajayen idanuwa ina kallon kofan shigowa dakin nawa, Hamzane ya shigo gidan alamar damuwa a tare dashi karara fuskan shi yanayin shi duk ya sauya cikin yan kwanakin nan, Gurin ya samu daga gefena ya zauna bayan nai mashi sannu da zuwa naja bakina nai shiru tare da dan mayar da baya na akan masangalin kujera, Tsayin lokacin babu wanda yai magana sai shiru da karan fankan sama da ke aiki a dakin A hankali naji yana cewa wanan ban san yadda zamu kwashe da su ba don naji suna cewa wai sai na yanka masu ragon suna duk da yaron baida rai, Cikin boye damuwata nake cewa idan kaga da hali ai sai ka yanka masu a,samu a rabu lafiya dasu, Wakike tsanmanin zamu rabu lafiya dashi wa yan nan mutanen marasa mutunci kike nufi ai ba mutanen arziki bane sai anyi yadda ba,a so dasu, Zarah ce tashigo tana cewa yaya ashe ka shigo yanzu Sa,ade ke fada min shigowan ka, Ya amsa a sanyaye da cewa nashigo yanzu ban dade ba da shigowa ai, Guri ta samu ta zauna tana cewa dama ina son magana da kaine ba,a gaban Umma ba akan zancen wanan maihaihuwar matar taka, Naga sun samu Umma wai dolr ne a yanka masu ragon da kai niyar yankawa yaron tunda da sunan shi ka,saya,ragon, Bazan yanka ba yace da karfi sai dai ayi yadda za,ayi basu da tausayi wallahi jahilan mutane ne na gaske, Zarah tace ai bakama,san wani abin jahilci ba wai cewa,suke kashe yaron akayi wai asiri akai mashi yazo hakana tun yana ciki Mikewa,nayi don nabar masu dakin ganin suna,shawaran su sai cewa sukayi lokaci guda zauna mana abinki aiba,wani magana bane akeyi, Yace zai dai sayo mata nama a kasuwa taci kuma zanuwan da nai niyar bata zan iya bata su bazan fasa ba don akwai bukatan hakan, Mamaki nayi inda ya,samo kudin sayen rago harda zannuwan da yake zance sai dai na hade a raina ina cewa kai namiji namiji kanin ajali, Dubi iri yadda yake zuwa ya marairaice min cewa ya rasa inda zai shiga ya,samu kudi duk dan abin da nake tarawa nayi nawa rufin asirin idan ya tashi duk na kashesu a haihuwan Sadiya gurin girki da,sauran bukatun da,akeyi, Nan dai ina sauraren rabi naji may sukace rabi kuma ina can ina tunane abina har suka,watse suka barni zaune turus gurin da,suka,samay ni, a dakin, Ranan da aka cika sati daya da haihuwa sai ga Hamza da,kumshin nama a cikin takardan Suminti, Dakin Sadiya wace tasha kwaliya da wani atampan da ta dinga don fita suna tasha huni tayi kwalliya tsab, Labule ya,dan daga duk yanajin muryan mata a cikin dakin suna hira da ita a lokacin, Yana magana ta fito daga,dakin sai yake mika mata naman duk da danye ne yasan cewa bazata yarda wani ya gyara mata ba bada yardan ta ba, Yace cikin dakewar fuska don kada taga daman shi karbi wanan ki gyara kici tunda ba yaro, Ya ce Zarah zata kawo maki zannuwan wanda na,samu saya suna gurin ta Cabdijam tace tare da fadin wanan ma ai fadi ba gaskiya bane, Jin abinda ta fadi yasa shi tsayawa ya juya yana kallon ta a cikin mamaki yake cewa may kike nufi da cabdijam, Tace yaya zan haihu bayan yaro ya kai kwana hudu a,duniya zakace bazaka yanka mashi rago ba, To bazan yaka ba ya bata amsa a takaice nan ta hau masifa da zage zage inda take shiga banan take fita ba , Sai da mama hafsi taje ta kira uwar ta,sai gata tundaga kofa take cewa ke tir da wanan hali naki na,fitina, Yau kwanan ki nawa da,dan ki ya,mutu da har zakiyawa mutane wanan daga harshe haka, Sati daya,da haihuwa yarinya har kin manta da abinda likita ya fada maki, Idan kika jawa kanki hawan jini ke kika,sani don ba ruwan kowa da faduwan ki, Maza shige daki ban son ganinki waje kuma tunda ke ba yar ido bace, Mama ki duba,fa ki gani wai naman da,yakawo min a matsayin ragon da yai niyar yankamin, Shige nace maki ban son abin kunya,a tsakar gida kike fadan naman suna irin haka, Daga dakin ta murya sama wai ana,zaman sulhu da iyayyen su amma kamar a tsakar gida,akeyi, Kai o,o Allah na gode ma da bakayi ni da irin wanan murya ba,sai kace mara kimtse nafadi mace matar aure take irin daga harshe haka babu dadin ji, Muryan Hamza naji daga,daki yana fadi wallahi wallahi bazan yanka mata rago ba na rantse iyakar abinda zan iya yi mata ke nan nai mata, Yai wuf yafito daga dakin ina jin sunackirancshi yana fadin nagaji ba zan dawo ba nagaji wallahi, Macuci kawai azzalumi dan cin amana kawai sai kabiyani hakkina ranan lahira tunda hakkinane, Allah ya kyauta na kara fadi naga yafita daga gidan nabi bayan shi da kallon haushi irin na takai, Muna zaman zaman mu ya jawo muna fitinar duniya akan bakar jaraban shi, Muruan Umma naji tana cewa tunda yace ba,ai yankaba baki kyaleshi ai danshine ko ba na,wani ba kwana nawa kin samu wani ba sai ai maki yadda kike so ba din, Fita yayi daga gidan bai dawo ba har yamma ina kallon Sadiya tafito tana gyara naman da kanta tagama,dafa tashige daki da tallenta baki daya muma an sayo nama dashi muka dan watsa a miyan gida kowa ya,dan ci a gidan, Sai dare ya,dawo dakin Umma Rabi ta fara shiga yakai wani lokaci a guri suna dan magana,wanda ba maijin mai suke fadi, Sai washe garine Zarah take min gulma cewa dada mutumiyar ki jiya ko tayi balle dandane bataiwa kowa,ba tashige daki ta cinye abinta tas Murmushi nayi nace ai yafi mata da ta rasa, baki daya fa,gara,data hakkura taci abinta, Magana irin na shirka sadiya ke ta,sakewa akan mutuwan dan jaririn ta wai an kashe mata shi don bakin ciki kada agan shi a gidan , Habaici wanda zai sa mutum ya tanka mata,shi takan tayi kullun har da cewa wallahi mutum ya,bari ya gani yadda ya,sata kuka shima mai shi sai yayi, Wata rana Hamza yana kwance daki tunda safe tafito take cewa wai wa ya,dauke mata, roban wanka inda ta,aje shi wallahi mutum komai tsafin shi sai dai ya barta inda ya ganta kawai Batan fitowan shi daga daki ba sai jin muryan shi tayi yana cewa ke Sadiya jinan wanan zancen wallahi ya,isheni haka don bazan yarda da wanan mugu halin naki ba haka Kullun mutum shi dai ke nan anyi mashi dai anyi tau yau ki fito ki fada muna,wanda yai maki a huta haba keni wallahi wanan halin bai min ba agidan nan ban son nakarajin zancen nan in har kina son mu zauna lafiya wallahi, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Sati biyu da haihuwan Sadiya nawayi gari da na kudu sai dai ban yarda kowa ya,fahinci halin da nake ciki ba a,gidan, Badon komai ba,sai don sani halin yan gidn mu danayi saboda inajin irin yadda sukewa,Sadiya,go wai raki gareta amma yanzu tafi kowa surutu, Yanayin danake ji haka na daure nai masu girki a tsatsaye batare da,sun fahince ni ba, Wata classmate dina da mukai karatun health tare na kira tazo ta dubani batare da kowa ya fahinta ba, Take ce min zuwa azahar zan iya haihuwa insha Allah nan taimin duk abinda ya dace tace idan time din yayi zata dawo ta duba stage din da nake, Saya kofan dakina nayi ina ta faman nukurkusa ni kadai a cikin daki Hamza ya shigo dakin a lokacin na,samu abin ya,dan lafa min sai gumin da na hada abinka,ga wanda bai san kai ba, Kallon mamaki yake min yana cewa wanan zufan fa da kika hada haka kamar wace ke cikin oven, Murmushi nai mashi kawai nace yanayi ne kawai daga barci nake shiyasa nai zufa haka, Fita yayi daga dakin yana cewa bari ya sayo clean ya wanke wasu kaya nashi saboda yaga nagaji da yawa, Barci ya dan dauke ni har ya dawo dakin ya kwashi kayan da zai wanke zuwa waje,ya fara wankin shi, A cikin dan barcin da ya,fisgeni na rika ji sama sama kamar ana yanka min marana da wani irin guduma Da,sauri na bude idanuwana tare da kokarin mikewa,saboda irin yadda nakejin abin yana min ba,sassauci a cikin shi Duk yadda naso na mike na kasa hakan gashi a,kwai fanka,a,dakin amma,sai kice ba,iska cikin dakin gaba daya, Hankalina,gaba,daya ya,daga tausayin kaina ya kamani sai naji kawai a kira min mama hafsi idan tana gida, A raina nace idan hamza ya dawo sayen clean din da ya tafi sai na,fada mai yaiwa mama,magana tashigo guri na, Sai dai kassh i a daga idanuwa na,sai naga har ya kwashi kayan wankin shi ashe ko yafita,dan bar cin da nayi, Tausayin kaina ya kamani na dafe gefen hannun kujerana da karfin Allah, Na fahinci baby na gaf da fitowa don haka,a wahalce nakara rugumar kujerar da karfin Allah, Take duk illahirin jikina naji ya dauki rawa a lokaci guda na,fara dan nisawa,da dan karfi har naji abin ya,zo gap da fitowa, Gabaki daya naji na wani sake kamar rayuwa na zai cire a lokaci daya kamin kiftawa da,bisimillah sai naji gabadaya abinda ke a cikin cikina na sullubo shi waje gaba daya har uwar tafiyan , Take kukan jarirai ya kaure gidan duk inda kake zaka iya jin kukan yar jaririyar dake kwance a kasan daki tana tsala ihu, Idanuwana na lumshe a lokaci guda don ji nake kamar wani abune mai nauyi aka cire daga part din jikina, A guje suka,kwaso zuwa dakina ina zaune gurfane a gefen kushin dina Suna bude labulen dakin sukayi arba da yarinyar tana ta tsala ihu a tsakar daki ni kuma ina daga gefe daya, Baki suka hada xarah da Asmau gurin cewa wallahi Umma Aisha ta haihu, Kafin haka har mama dake dakin ta tafito tafado dakin nawa Hamza ya na daga kofa tsaye ya daga labulen dakin yana mamaki sai da mama tai mashi magana ya sake labulen, Reza inji mama cikin nune na nuna mata inda suke ta dauko sabon reza ta yake cibin jaririyar dashi ta dauko zani dake saman gado ta nade yarinyar a cikin shi, Ni dai ina zaune a gurin da nake tun farko kaina a duke sai murdan baki nake, zufa na dan tsiyayo min, Daga kofa nake jin muryoyin yan gidan mu suna nuna farin cikin su da haihuwa na, Ban san wa yakira mutanen gidan mu sai muryan Atika na tsinkayo daga waje itama tana cewa ikon Allah da zunfa Aina tashigo take ce min nan ta ke gurin Aisha suna kulla kankara, da ita, amma batace muna bata da lafiya ba, Zarah tace itace fa tai muna girkin safe da rana gashi ma bamu ko ci ba tukun, Nan gida ya kaure da,farin cikin samun karuwan da akayi har akaci aka sude aka gyara min daki banga Sadiya ba, Saida Atika da Mama Saude zasu koma gida bayan sun min wanka suke tambayan halan bata nan ne tasan halin mama saude sarai sai ta dan fito daga daki fuskanta ba yabo ba fallasa a cikin shi take cewa, Ina nan mama sannun ku da shigowa dama na bari har a gyara guri ne in ta kimtsa sai na shigo, Haba kubar irin wanan rayuwan mana dan uwanka ya sauka lafiya ai kazo kai mashi barka dai ko, Zarah tace ranan da kika haihu da tsohon cikin ta wallahi duk daren nan da ita ake a kan ki har safe, Babu ruwanki don ni ra,ayinane hakan ko zaki sani dole ne, Don Allah matsa can in kina gyara halin ki ki gyara kinji, zarah ta bata amsa da hakan, In ban gyara ba,ai sai kizo ki gyara min kaji min yar raini senses kawai kidai iya da naki kishiyoyin tukun kafin ki shiga na,wasu, Ke dai kika,sani mutum bai iya boye mugun halinshi ko yaushe sai ya zubar da hali kowa yagani, Ke zarah wallahi kada ki fada min maganan banza wallahi yanzu ajimu a gidan nan Ajimu mana wake tsoron ajiku dashi ko waye bai san halinki ba da zaki wani budawa mutane ido Wai may ye haka kukewa mutane Hamza da yashigo gida dauke da leda da sabulu da Omo da,aka bukaci ya kawo yake magana a cikin daka tsawa, Shiru su kayi suna kallon shi don kowa tana tsoron shi sabboda yafisu zafin rai sun sani yanzu za,ajisu in basuyi shiru ba, ****** ********* ****** Dakina ya dauki kamshin turaren wuta lokaci daya yana bada kamshi da kuma karnin jego irin na,dankin haihuwa, Ina zaune gefe guda can kuryan daki mamana Rahana ta,shirya baby tsab a cikin tufafin yan mata masu kyau da tazo dasu, Mama ta,dago kai tana cewa kin koga yarinyar Aisha wallahi gata kamar hamza yai kaki, Murmushi nayi kawai tare da dan dukar da kaina gefe daya, sai mama ta mike ta nufoni da yarinyar dake nade a cikin showel, Miko min tayi tana cewa karbarta ki gani mana don nasan baki dauketa ba tun dazu, Nace cikin jin kunya mama barta kawai ai zan dauke ta, Miko min tayi batare da nai magana,ba na karbi yarinyar sai mama tafita dakin dauke da,wani robs a hannun ta, A hankali cikin natsuwa nakai dubana ga yar jaririyar dake nade a cikin showel, na,dan bude showel din tare da,sauke ajiyan zuciya nai wa Allah godiya da baiwan wanan yarinyar da yai min, Idanuwan ta,a rufe amma ta dan sanya yatsu a bakin ta tana tsotso na rungumay ta tsam a jikina ina karanto mata adduan neman tsari daga,sherin shedan da shedanu tare da neman tsari daga,zina sata, ko wani mugun abinki, Mama ta dawo dakin tana cewa bari na,shiga gurin Fatima, nafito (Ummi) nace a,sanyaye tau mama, Fitan ta yai daidai da,shigowan Hamza da yar leda a hannun shi yake sallama, Tsayawa yayi yana kare muna kallo ni da yarinyar cikin nuna,so da kauna a tsakanin mu, A hankali ya tako zuwa inda muke zaune yana cewa mama ta tafine nace tashiga gurin Ummi ne, Dan tsugunawa yayi gaban mu yana cewa dabino nake son bata da ruwan zamzam,gashi kuma kamar tana barci ko Nace ai kila zata karba tare da kokarin miko mashi yarinyar yakarbeta tare da mikewa tsaye ya nufi gurin kujera ya zauna, Kiran Sallah yafara mata a kunne sanan ya dauki dan lokaci yana mata addu,a tare da dan daga gefen ta na,dama yai mata adddua yadawo gefen hagu yai mata sai naga ya bude gurin al,auranta yai addua sai ya tauna dabino ya hada bakin shi da nata ya bata tare da,diga mata ruwam zamzam din sai kuwa yarinya ta dan shiga lashe baki cikin yamutse fuska, Ya sauke numfashi tare da dago kanshi yana kallon na yake cewa Allah ya raya muna ita tafarkin addinin musulunci, A sanyaye cikin kunya da murya mai taushi na amsa da amin a hankali batare da,wani yaji may nace ba, Yana mika min ita yake cewa lafiya dai kike ko na amsa still a sanyaye da lafiya ta kalau yace masha Allah, Umma ranan har dakina take tana min barka da,arziki tare da daukan baby zuwa wani dan lokaci tabar dakin, fuskan ta dauke da annuri, Bayan komai ya lafane zuwa dare yan barka,suka,fara shigowa kamar yadda al,ada yake a kasar hausa, Washegari baby ta jawo min yan uwan mahaifinta a dakina don zarah da yan uwanta a dakina suka tare don nuna kaunar su ga diyan dan uwan su, Sai hira ake ana,dariya cikin raha da,daga murya yi suke don su karawa Sadiya da ta kunkumay a daki haushi, Rana yayi amma ba alamar Sadiya gurin dora girki har saida rana yakai take ba tafito ba Hamza ya,shigo gidan gani ba a,dora girki ba sai ya,samay ta a,daki yake cewa, lafiya bazakiwa yar uwar ki dafuwa bane ko yaya, Wani irin kallon ta watso mai daga inda take kwance tace wacece yar uwa na, Wacece abokiyar zaman ki da kika haihu tai maki girki ta dora maki ruwan zafi da sauran su, Ai ban sata ba ba inda zan fita da jegona a jiki na halaka kaina don gudun bacin ran ku kai da ita, Oho ashe hakane ita da tsohon cikin ta take maki aiki har kikai karfe haka yau yazo akanta shine zaki nuna halinku na yan duniya ko,? Cikin wani tsiwa da nuna isa da gadara tace bazan yi banace ko za,a sani yi dole ne, Da kai ya,fara amsa mata yana cewa Ok yayi ba damuwa Ya juya zaibar dakin take cewa haka kawai da jegona zakace wai nawani dafawa wata matar ka can abinci kada taci abinci don Allah, Murmushi yayi gami da cewa Ok yayi hakan ba matsala ai sai ya fita daga dakin a kofa ya tsaya yana kiran Asmau, Asmau tafito tana kokatin daura dankwali a kanta yace mata ku fito kuyi muna girkin da za,aci, Mama dake daga gurin girkin namu tana dora ruwa take cewa kubarshi kawai gashi zan dora ai, Daga ranan mama hafsi ce mai mai muna girki da dora ruwan zafin wankana ni da baby, Sadiya,sai wani isa da toroko takeyi akan bazatai girki ba aci don itama jego takeyi, Da yamma ta shiga gyaran dakin ta tare da yin sauri tai wanka ta saka tufafi masu kyau a jikin ta, ****** ********* ****** Ina zaune da abinci a gabana ina ci duk da bakina bana jin dadin shi don jego yafara aikin shi saboda yadda nake jin jikina gabobina sun fara tsami don wahalar haihuwa da mace keyi, Mama Hafsi tashigo dakin dauke da,wani kwanon silver mai marfi ta girke a gabana tana fadin na bude na diba naci sai na koshi, don ki na girkashi, Ta samu guri a,saman kujera ta zauna tare da daukan baby dake kwance a,saman gado tana dan dubata a hankali, Take ce min sai masu barka sun dauke kafa zan dauraye ta,don rage mata kasala saboda ku samu barci issashe da,dare, Idan ba hakaba sai kafa ya,dauke kiga yaro yaki barci saboda tsamin jiki shiyasa ba,a son yawan daukan nan da,akewa jariri da rana,saboda jikin su ba karfi yana,basu reaction sosai, Kawai daga dakina da muke da mama muna hira mukaji muryan Sadiya tana fadin wallahi baka isa, Sai dai yau ayi duk abinda za,ayi a gidan nan amma dole ne ka kwana a dakina, don nima dana haihu ai a,dakinta kake kwana, Hamza yace kin manta may kikacd ne dazun akan girki cewa fa kikayi jego kikeyi bazaki girkawa kowa abinci ba da jegon ki a jikin ki, Shine nikuma kike son yaudarata na,shiga dakin mai jego na kwana na,sabawa Allah da,al,ada ko, Shiru tayi tare da cewa Owoo tanan kake ganin kafito min ko don nace bazan yiwa matar ka,girki taci ba ko? Macuci aidama,akan wanan figagar matar taka ka saba cin amana ta, Ni zaka gwadawa an haifa ma,diya mace ko kuwa ni ban haifi da namiji a gidan bane kafin mace,? Ya juyo da karfi ranshi a bace idanuwan shi sun kada a lokaci guda sunyi jawur ya nunata da hannu yace ina da namijin naki yake ? Ni a gurina da namiji da mace duk daya suke a gareni fatana Allah yasawa yata albaka yasa rayayyiya ce dazamu more mata, Ni zakaiwa gorin dana yamutu yace anyi maki wayakashe yaron bake ba saboda bakin halin ki, Sai kawai tasa ihu da kuka tana shatar majina tana cewa wai yai mata cin mutunci dagori akan dan ta ya mutu, Umma tafito daga dakinta tana cewa kai haba yaran nan wai may nene haka don Allah, Kullun kuke nan a gidan nan ba,ajin alherin ku sai da sheri ni wanan hali naku ya isheni wallahi, Amma Umma kina jin abinda yake fada min don kawai naki yin girki da jegona a jiki zaizo yana fada min bakar magana da gori akan yaro bai tsaya,ba, Juyawa gurin hamza Umma tayi tana cewa, yanzu kai akan diyar da aka haifa maka har kake gayawa matarka bakar magana da gori, Umma don Allah ki fitar da bakinki akan wanan zancen don wanan karon bazan dauki rainin hankalin da,Sadiya take min ba kina gani kice wai nayi hakkuri da ita , Daga haka yabar gidan fuuu Umma tana kiran shi ya,fice daga gidan, Gurin danake zaune nayi shiru ina,sauraren abindake wakana dagani har ita takece min kada wanan zancen ya bata maki rai kedai rugumi diyar ki da macen da na miji duk Allah ke badasu, a inda yaso kuma shi yasan dalilin baka irin jinsim daya keson ka dashi, Murmushi nai mata, tare da,cewa, mama ni kan Alhamdullahi nagode da baiwar da yai min, Sai da mamata tabbatar da,cewa ban sa, zancen Sadiya araina ba tabar dakin don zuwa ta kimtso dakin ta saboda tare muke kwana da ita a,dakina, Itace ta ce yan uwana su huta don zatai min duk abinda yadace aiwa yaro sai dai kawai azo ai min wanka inda,bukatar hakan, ****** ********* ****** Ga Dare ya raba amma sam na kasa barci don ma babu ko alamar barcin a idona duk da yin barcin ake bukata,agareni don samun hutu, Ajiyan zuciya na,sauke tare da dan lalabo yar diyata da take kwance a kusa dani, Idanuwana na rutse tare da tuno kalaman Sadiya akan yar baby na,dana haifa, Ba,Sadiya ba harda Umma sai yanzu na,fahinci rashin kara shigowar ta,gurin mu don diba lafiyan mu, Ashe wanan dalilin nace na haifi diya mace kecin zuciyar Umma taki kulani da yar dana haifa Maynene illar haihuwar diya,mace da,suke gani da macen da na miji ai duk Allah ke bada su yadda yaso, Shekara kusan hudu da aure ban samu haihuwa, ba,anata min gori da,shagube akan rashi haihuea, Yanzu gashi Allah ya tausaya min ya bani mai makon a tayani farin ciki samun karuwan da nayi Shine kuma don hassada aka kirkiro min wani sabon sheri wai diya mace na,haifa, Nikan gaskiya,alhamdullahi nagodewa,Allah don ina jin so yata har cikin kasan raina, Tsoro na daya shine kada Umma ta cusawa uban ta kin ta a,ranshi don tana diya mace, Idanuwana a runtse suke ina mai sauke numfashi a hankali, na furta,a hankali Allah ka taimake ni, Sai naji muryan mama tana amsa min da cewa Amin Aisha, Tsayin lokaci babu wanda yai magana a cikin ni da ita sai zuwa can take cewa, Kin sa zancen wanan shu,umar yarinyar a ranki ko wanan dakike gani minshon ce bat da musulmi,, Yanayin maganar mama ya,nuna min a cikin bacin rai tai min magana, Tace kada ki fara ta fahinci maganar ta yayi tasiri a ranki don dama haka take son gani duk ta yamutsa maku farincikin ku, Kukan da yar jaririyar ta tsalane yasa mu katse maganar mu inda mama ta mike zaune ta kama yarinyar tabata ruwa take ce min na mike na bata nono a zaune kada na yarda na bata nono a kwance don haka yana da illa wanda iyayye basu ganewa sai yaro ya girma illar yake baiyyana masa, Namike kamar yadda mama ta umurceni nayi din nabawa yarinyar nono sai dai bata iya kamawa ba, tadan ja kadan sai ta sake taci gaba,da barcin ta,, Tsam na kankamay diya na a cikin jikina ina mai kura mata ido yarinyar tana barcin ta hankali a kwance, cikin koshin lafiya, na,sauke ajiyan zuciya ina maijin kunar zuciya da irin halin rayuwar da,ake shirin bullo min dashi a gidan, Jin munyi shiru mama,da dan barci yafara daukata ta farka take cewa idan tayi barcine miko ta nan ki kwanta ki huta kin ji, Naji dadin yadda mama take min kamar uwata da ta,haifeni Bayan na kwanta kafin barci ya daukeni nake cewa a raina may yasa wai Umma take son kuntatamin a,rayuwanta May nai mata har take son kawo kiyayyan da take min ga yar jikanta jinin ta, yarinyar da kwatakwata kwanan ta biyu a duniya, Wanan ai zaluncine kawai irin na Umma data saba yi na ba gaira ba dalilin a cikin iyalin ta,. A hankali naji hawaye ya soma dan zubomin a fuska nasa hannuna na toshe bakina don gudun kada mama taji sheshekar kukana, Washe gari bayan nai wanka na kimtsa cikin dan kwalliya kamar yadda ko wata maijego take dan,dandassa kwaliya saboda ta kara burge mutane, Hindatu ce tazo da yan uwanta tare da manyan ledoji a hannun su, Ba komai acikin sa sai abubuwan amfani irin na maven da ta haihu daga na ci da sha har namfanin jiki nawa dana baby, Nan yan uwanta suka barmu don mu dan tatauna da ita kamar yadda muka saba, Ganin yadda nai shiru cikin damuwa bayan tafiyan yan uwan ta yasa ta dan rage murya tana cewa, Aisha akwai matsala don yanayin fuskanki ya nuna min da,akwai damuwa tare dake, Murmushi na dan kakaro a fuskana don kada ta fahinci komai a,tare dani, Tace look Aisha ban tsanmani zaki iya,boye min sirin ki ba amma tunda bakya,son in sani shike nan, Idanuwana na watso mata sun kara girma saboda hanlin da nake ciki sun koma kamar hasken kwai, saboda basu saba canza launi ba, Nace ni Anty ban san may na kashe wa Umma ba aduniyan nan , Ko auren dan ta danayi ne bata so ba,tun farko bata kauna hada zuria dani, Kuka nafara inda cikin kukan nake labarta mata zancen da Hamza su kayi da Sadiya da kuma amsar da Umma ta bashi, Yadda zancen Umma yake nufin cewa yana kokarin wullakanta matar da take mai haihuwan diya maza akan mai haihuwar diya mata, Shiru tayi har na kare magana ta tana saurare da nazarin abinda nake fada mata, Al,ajabi da mamaki ne suka hanata magana har ta kasa furta komai, Hmm tace tare da jan tsaki tana cewa amma wanan matar babban jahilace wallahi, Yanzu saboda tsabar kiyayya har take son ta saka yar jikan ta a ciki, Wallahi zanga hamza yaudin nan naja masa kunne tare da kara cusa mai son yar shi a rai tun kafin munafukar uwar nan nashi ta umurce shi kan dole sai ya,aiwatar da,abinda ba,daidai ba, Wallahi Aisha,sai yanzu nafara fahintar duk itace mai tillasta shi yin wasu abubuwa yake mata don biyayya, Don ma wanan wagarar kishiyar taki batada kimtsi aida abin yafi nan sai reshe ya juye da mujiya ko ita bata bari ba, Haka kawai mata mara mutunci kiyi kokarin tozarta kyautar Allah kan son zuciya, Wallahi intace tai haka,sai Allah ya tambaye ta don Allah baya jin kan wanda baya jinkan mutane, Shiru nayi ina,saurarenta tana cewa yau din nan da dare zan sa man ya kira hamza muyi mashi bayanin komai yadda zai fahinta wallahi ko, Duk tsiyanta sai ta barshi da yarshi wallahi muguwar mata kawai ni wallahi dama bani son ta don rashin kaunar ki da batayi don banga abinda kika tsare mata ba, In ba,aure ikon Allah ba ai ke ba matar hamza bace wallahi don shima yasan kifi karfin shi sa,a dai Allah ya bashi, Amma mu zuba da ita tagani tasan tayi da maihi wallahi, Da irin wanan maganganun taci gaba da kwantar min da hankali tana bani baki har naji kwarin gwiwa komai ya fita min a zuciya irin kuncin da nake ji da farko, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Alhsmdullahi don yanzu na,warware saboda shawaran hindu yai tasiri a zuciya ta sosai, Na kuma fahinci kamar yadda tace min zasu yiwa hamza nasiha din sunyi don gaba daya,wani irin nuna kulawan shi a,kaina da yar jaririya yake yi, Wanan abin a zahiri ya tayar wa,Sadiya da Umma dake kokarin boye halinta rai, Hindatu da mijin ts duk sune silan dadin ran da nake a ciki don sunyi namijin kokari gurin gurin fahintar da Hamza yadda zai dinga kawar da,kai ga,wasu miyagun shawara da,Umma ke dora,shi akai, Don a yadda ya,fada masu wasu abubuwan dole yake sashi yin su don ya,samu su rabu lafiya da ita, Mansir yake ce mai kada kayi gigin da ka bari yarinyar nan Aisha ta subbuce a hannunka don irin su Aisha abin alfa,arine zama dasu nan gaba kai zaki kowa farinci kansan,cewar ka da ita, Duk shirin da Hamza yakeyi na suna idon Umma da Sadiya yana a kai sai yazama min na samu kishiyoyi guda biyu lokaci daya, agida da guda, Basu fahinci duk wani shirin da yakeyi ba,saboda sabon takon da ya,dauko masu a gidan Mansur ake shirin komai, Saura kwana biyu suna iyayyena suka zo daga burkusuma, da abin arzikin su a gidan mamana Rahana suka sauka su biyar mata maza biyu, Ganin sun shigo inda nake hannu salin alin Umma ta fara sake magana,bayan fitan su wai dama fashi bakauye bai san kunya ba, An kwaso jiki anzo wa mutane haka akara masu nauyi da wahala ita bazata yarda a sa danta cikin wahala,ba don ko abincin da za,a basu ai aikine a gurin su, Mamace ta katse tada cewa sun fada maki anan zasu sauka dakike irin wanan magana haka bakon kafa annabinka, Karuwa kika,samu suka samu suma sunzo taya yar,su farin cikine ne fa saboda nisa kikaga sunzo da guri haka, Don Allah yaya ki kama bakikin don irin wanan magana,bai kamata,ace anajin shi a gurinki ba, Zarah dake zaune gefe tana ba,dan ta nono tace ni wallahi ban san sanda umma ta koma haka ba Haba ace matar danka ta zama abin takaicin ka itace abin yiwa shagube shiyasa mutane suka barki da diyan ki ai kowa yazo neman su sai ace baki da dadi gurin sarakai, Haba aikuwa Umma tai kanta da fitina da zagi wai ta raina ta,shine har take fada mata magana son ran ta, Umma ni gaskiya nake fada maki don haka baidace ba saida ibirahim yashigo yanaji shima yace, Kai haba haba Umma wallahi ni wanan halin yasa sam yanzu ban son zama gida, shiya kashe maganan, Maganan har Hamza saida yaji ta,amma saboda halin shi bai nuna a,fili ranshi ya baci ba yai shiru kawai, Ranan suna yarinya taci suna Hauwa,u sunan gwagon su Hamza wace ta rasu uwar su daya da mahaifin su, Ta rasu bayan rasuwan mahaifin su itama tana da zumunci sosai da hamza yake yaro ance tai kokari dashi sosai, Umma tai masifan saka sunan yar uwar mahaifin shi dayayi take cewa don baisan zafinta ba yasa shi saka,sunan wata ga,ta,a,gida, Yace Umma idan na,saka sunan ki duk wanda ya kirata da,sunan ki zan dinga jin zafi a,raina ne shiya,sa amma kiyi hakkuri ai yanzu akafara, Da,sauri tace may ne akafara yanzu haihuwan diya matan ko may fa ? Yace da macen da namiji duk shiryuwan Allah muke nema a,gare su Shiru tayi cikin jin haushi da takaicin shi don tana ganin bai san ciwon kan shi bane, Da,safe na,saka,wani dinkin atamfa corde voire mai ruwan makuba, a jikina, Ina zaune dakina ni kadai ce a cikin dakin kafin yan uwana,su shigo sai ga mama tashigo daukan kwanonin da nai amfani dasu da dare, Cikin murmushi da nuna jin dadin ta take ce min kai "ya ta,wallahi kinyi kyau don jego ya karbe ki sosai , Ba kamar kishiyar ki da masifa da raki ya hanata tsayawa tasha ruwan zafi yadda ya kamata, Dama ai shi jego na kwana hudune idan ka kuskure wanka kwana hudu zuwa biyar da haihuwa duk sai kika mace ta wani jemay ta yankwamay kamar bata da lafiya, Shi jego dakike gani ba komai bane dama jegon sai kici kisha mai lafiya ko ba,dadi dai cikin ki ya dauki zafi da yaji yanzu zakiga kina sheki saboda irin jinin da mata ke zubarwa yayin haihuwa idan kin ci abinci sosai kinsha ruwa gyambon ciki sai yai saurin warkewa, Shiyasa nai dabaran cewa yabani kudi ni zan dinga maki miyar ki ta musan man yadda ba mai fahintar cewa shine ya bada har akai ga fitina, Nidai ko Sadiya tasha giyar wake bata tambaya don may nake kyautata maki tundani ban samu ragowa ko matsayin uwa a gurin ta ba, Ke kuwa duk inda na tsayar dake anan kike tsayawa kin san kimata,da,darajana Aisha dole duk abinda naga zai cuta maki nayi tsaye a kan shi ba,Sadiya ba har uwar taku nasan ranta yana baci a kaina bata dadai yadda zatayi danine kawai, Murmushi naiwa mama don ni ba ma,abociyar magana bace dama sosai, Haka tafita tana yaba min da bani shawaran na kara dagewa da hakkurin danakeyi don talauci bamai dorewa bane, Duk abinda Allah ya hore maki a gurin mijinki ya baki karba da murna da farin ciki a bainar jama,a kada kiyarda ki nuna bacin ranki don kinfi kowa sanin baidashi yannzu, Nace tau mama insha Allahu bazakiji wani abin assha daga garni ba ko yan uwana, Don kishiyar ki ta hake cewa duk taga yai maki wani abinda bai mata ba,sai ta dauki mata ki sosai bazata yarda ba, Jiya naji tana magana,dadare da matar wanta da,tashigo barka, ****** ********* ****** Karfe goma gida ya fara cika da yan buki yan uwa da abokan arziki nawa dana Hamza, harda ma,wasu makwabta da ake abin arziki dasu, Sau daya nafito tsakar gida na kwashe kayan baby da aka shanya kada aiyawa sufadi a tattaka,su, Sadiya tana kyalla ido ta hangoni a take fuskanta ya,sauya saboda tagane babban zani ne na,daura sai mamaki ya kamata ina na,samo shi , Daki takoma ta,sauya kayan jikin ta itama tare da gyara fuskanta, Yan gidan mu mata dake aure sun min kara don gaba dayan su sunzo gurin sunan nawa kuma ni banyi zaton haka ba daga gare su, Zaune muke sai faman yan gulmace gulmace akeyi ba wani girki mai yawa mutanen gidan mu sukeyi ba don haka,sai suke ga,duk mutanen dake gurin basu iya basu abincin da zasu sai nune da zunde sukeyi, Suna cewa,wai abincin da zasu bayar gaskiya bazai isa ba dafo ba ni basu ga nai wani girki ba wanda zanbawa bakina, Duk zancen su ba,a boye yake ba don haka muna jin su sai Kubura ce ke tambaya na ke Aisha dama bakiyi wani tanadi bane da zakibawa mutane nace akwaishi za,a kawo hakan yasa su kwantar da hankalin su da har suna zancen abinda ya kamata suyi, Don a tsamanin yan dakina,saboda halin talaucin da muke a ciki babu abinda nake dashi da zasu ci, Shigar wani shadda dan senegal nayi mai ruwan dark blue color kalan ya matukar karban jikina,sosai, Daga safe zuwa wanan lokaci shiga kala uku nayi duk acikin yan dabaru irin na Anty Hindatu, Ance zaman lafiya yafi zama dan sarki zuwa sha biyun rana daga gida su Anty Hinda mata suka shigo da manyan kulolin abinci da abin sha kala kala daga zobo kunun ayya, jinger da ruwa masu sanyi, Nan guri ya kicimay da hayani Anty laurat yar kubura tace a,diban wa yan bangaren Hamza su san mu ba marowata bane , Shigana da yanayin abincin da aka,kawo shinkafa da miya da tuwon yarbawa, sai makaroni, dafa duka yaji cabeji da kayan ciki sai kamshi ke tashi, Duk sai yasa jikin Sadiya da yan bangaren dagin miji sanyin jiki dole suka koma kallin mu, Karfe biyu daidai sai ga yan walima da ita kanta gaiyyan aikin Anty hindatu data gaiyyato su nan aka,fara walima, Malaman tai wa,azi ma ratsa jiki yayin da take nasiha akan hakkin a gurin iyayyen shi da kuma hakkin iyayye a gurin diyan su, Sai wata matar da ta mike itama tai wa,azi akan Amana, Wa,azin ya ratsa zukatan mutane sosai duk masu saurara anyi shiru jiki ya mutu nan aka shiga raba take away din da aka shigo dashi a buhu, Sadiya tunda aka fara wa,azi tana daki kamar wacce aka tillastawa zaman daki ita da yan uwan ta,da,suka zo mata zaman daki, Umma suna daga kofanta da farko suna dan hayani sai malaman tai magana akan ai shiru idan ana karanta sakon Allah don bada gagaresu bane sakon , Yar jaririyata tashs addua da fatan samun rayuwa mai albarka har mu iyayyenta an muna addu,an samun abin halak wanda zamu ciyar da ita, Naji dadin wanan waliman don mun samu addu,a gwargwado a gidan mu wanda Allah kadai yasan bakin din amin da zai karba muna, Mutane daya bayan daya aka,shiga watsewa acikin murna da farin ciki kowa kagani da yar ledan shi a hannu, Don kayan snacks da masa wanda iyayyena,suka,sa akayi sune Anty tai take away nasu akabawa yan taron suna suka tafi dashi, Na,yarda cewa duk abinda mutum yabarwa Allah zabin shi zaga abin mamaki don abin da akayi da,abinda na samu ban taba zaton hakan ba,a,rayuwa ta, Nasamu kudi turamay da kayan baby ta inda ma banyi tsanmanin samun su ba, Washegarin yan uwana suka koma gida inda mamana Rahana tazo gidan don nice na aika tazo, Kamar ko yaushe itace na sa agaba da tayi min yadda ya dace tacirewa hindatu abubuwa da kanta takai mata har gida, Bayan tafiyan mama gida na zauna ina ta faman tunane barkatai a,raina, Yanzu yadda mama Rahana tace na fara sanar turamay how comes zan iya sayar da su a gida gaskiya akwai duba a maganan nan, Sai dai kawai na kara dan duba abinda zanyi wanda zai fi karbuwa a gida Maganan mama Rahana gaskiyane cewa haihuwa diyan mata daban yake don tun ranan da aka haifesu har auren su a cikin spending iyayye suke dole na samu dan abinda zan rika yi ina tallafawa rayuna dana diyata, Ganin anyi suna komai ya kammala kuna ina kokari gurin kula da lafiya ns yasa mama hafsi fara fita zuwa harkokinta na neman kudi, kamar yaddacta saba tun da,safe kwarai take barin gida zuwa kai kaya yan kauyukan dake gefen gari, ****** ********* ****** Sabon matsalar da na fara fuskanta a gidan shi ne da,safe ranan da Mama tafara fita gurin sana,ar ta ina daki ina jiran naji Umma tace na kawo maijidda ai mata wanka, Amma sai naji shiru can naji ta tana,wa dan gurin zarah wanka har da dan tawain ta, Shiru shiru har rana sai na fito daga dakin na je har kofan dakin ta nake cewa Umma dama zancen wankan yarinyar nan ne naga har rana yayi, ba ai mata ba gashi mama tafita, Ke bazaki iya mata wanka ba ne ko may shima wanan da kikaga ina mashi don kawai kada nabarta tayi ne ace dan mutane, Zarah tanajin mu tace haba Umma Aisha ce kuma zataiwa yarta wanka gaki a gida, ai idan wani yagani sai ki ja muna abin fade, Abin fade na may fa idan da bani gidan waye zai ma yarinyar wanka ai gara ta,fara koyo tun yanzu ta iya har wankan wanan yarinyar guda nawa yake, Haba Umma gaskiya idan kince haka ko yayan mu bazaiji dadi ba gaskiya Umma tace kada yaji mana ke na,fada maki bazan iya,ba ni wanka yaro wuya yake min, Murmushi nayi na juya dauke da yarinyar a hannuna na kaita daki na shimfide sai na,debo ruwa nadawo daga kofar dakina nafara mata wanka sai dai ban iya ba Ainace tashigo taga ina,wa yarinyar wanka tun kan ta karaso take cewa Lah anty kece ke mata wanka,da kanki kuma yau i a su mama suka tafi, murmushi nayi naje nai magana yarinyar ta tashi sullube min, Salati Aina ta saka daidai shigowan Ibrahim yake cewa kai idan baki iya ba baki ba manya,suyi mata wanan ai rashin hankali ne, Murmushi nayi kawai tare da tsamay yarinyar daga cikin ruwa na,shige da ita cikin daki muna hira da Aina ina,shirya yarinyar, Karban ta Aina tayi ta goya suka fita zuwa uguwa inda aka aike ta, Aina tana zuwa gida ta kwashe tafadawa,su mama cewa ban iya wanka ba dana yar da yarinya a kasa, Wanka kuma ita Aisha da kanta takewa yarta wanka gata da sarakai a cikin gidan, shine sai taimata wanka da kanta , Ranshin kunyafa inba,rashin kunyaba yaya za,ayi ace wai tayiwa yarta wanka ita,da kanta Ummina ce ke fadin haka a cikin zafin rai, Mama Saude tace a,a ku dakata kun san fa Aisha ba mairigima bace ita duk yadda akayi akwai matsala akwai abinda ya faru amma zan shiga na ji koma may nene, Da yamma ranan Aina tazo ta dauki yarinyar sai kawai naga andawo min da ita,an mata wanka, Umma ina ce zancen zarah zaiyi tasiri a ranta amma sai taiwa,dangidan zarah wanka kawai ta kyalemu, Da,dare su mama,Saude da maman Aina,sukazo dakina suka shiga muka gaisa nan suke tambayana dalilin da yasa nakewa yarinya wanka da kaina ga,sarakaina a gida, Ban yi magana ba,sai kukan da na kamayi kawai don yadda nake jin zuciyana yana radadi a lokacin kamar zai tsage yafito don bacin rai, Sun fahinci akwai matsala don haka,sukace natashi mu tafi dakin Umma din , Mun samay su ita da yar uwarta zaune suna hira ganin mu yasa gaba daya hankalin su dawo gare mu, Sun gaisa dasu mama lafiya lafiya sai dan shiru da ya biyo dakin mama Saude ne tace Rabi gurin ki mukazo da Aisha, Don bamu san laifin da tai maki ba,shine malam yace mu kawota ta roke ki gafara indan tai maki wani laifi ne da ba mu sani ba, Sai shiru ya dan kara gauraye dakin a hankali na fara dan sheshekar kuka da na kasa controlling din shi daga idanuwa, Mama Saude ta juya gurin da nake take cewa Aisha ki roki sarakuwar ki gafara indan kin mata laifi ne har ya,shafi yar da kika haifa tare da danta watau jikan ta, A,a ni batai min komai ba,wanka ne dai nace ta koya taiwa yar ta don ban samun lokacin da zance kullun zan diga mata, Assha Rabi wallahi ko kinci kafa bakiyarda ganye ba don yarinyar nan bata ci haka ba a gurin ku, Dakata Saude kada kuzo ku sani gaba har dakina kuna son fada min maganan da,bashi ba Wanan zancen nai maku bayani dalilina amma kuma kuke son juya maganar a,wata,tsiga ta,daban ina dai yarinya jikata ce ba ta,wani ba, Kwarai kuwa jikan ki ce amma kuma baki dauketa a hakana ba nan zancen yaso ya juye masu a fitina, Muryan su Hamzane suke cewa subbahanallahi may yai zafi haka may ke faruwa ne wai, Suka ce min ta shi ki koma dakin ki tunda haka Allah ya nufe ki da,gani a rayuwa, Wanan dai dama kunzo ne don ku fadi abindake a ranku kawai don abinda bai shafe ku bane, Idan kuma ke munafuka kin fada masu cewa nai maki wani abune sai su zo su daukar maki fansa mugani, Rabi kin ga tun farko matsalar da nai hange kenan na jaye halakata dake don na karanci ke ba mutumiyar da za a kama bane Aikuwa nan abu ya kwabe aja mama aja Umma kowa na,fadawa wa dan uwa tsohon famin dake a tsakanin su dadewa, Umma tace da kika hanamashi yar taki ai banga ta,auri wanda ya fishi ba indon wanan tsohon dan cacan da,aura ne har kike gadaran yar ki tayi aure inda yafi gidana, Nan Mama tace macuciya don ban kawo ta kin gasta yadda kike gasa diyan mutane ki hanasu sakata da mijinsu, Kinyi kane kane a tsakanin yara kina masu mulki da izza irin na,zzalumai, Yanzu ai gashi kin daukowa kanki jarabar tsaye har nakasaki sai da akayi kuma kadan kika gani wallahi don wanda za,ai maki nan gaba sai, yafi wanan gurmanta da kike yi, Duk diyan Umma suna tsaye a gaban su suna sauraren tonon asirin da sukeyiwa junan su, Hamza yai ta hada su mama Saude da Allah akan suyi hakkuri su fita, subar zancen hakana, Suna fita mama hafsi take tambayan may yafaru ne bayan fitan ta da,safe, Zarah ce tafada masu duk abinda ya faru da akan Umma taiwa yarinya wanka amma taki, Umma yarinyar nan dai jikanki ce amma,ba laifi wanan ba,Aisha kikai wa bani dai dana ke naki kika yiwa don duk abinda zai sami yarinyar nine dai ubanta , Ina,dashi Aliyun da ita,hauwau, duk jikokin ki daya,suke a gurin ki, sai dai kila,akwai wani abinda bamu sani bane da,yakawo haka, Fita yayi cikin fushi yabar gidan sai su mamane suke ta mata magana,akan yadda tayi bata kyauta ba, ****** ********* ****** Wanan abinda Umma tai min ya,ba,Sadiya wani kafana,ta,raina ni da yar diya ta,sai dadi takeji tana annashuwa Hamza hankalin shi ya,tashi sosai ya kasa fahintar abinda ke tsakanin mu haka ? Yana son sanin ko mai yake kawo wanan matsalolin a tsakanin Aisha da ita, Gaskiya shi yana son matar shi bazai yarda ace sanadiyar fitinar mahaifiyar shi ya rabu da matarshi ba, Kwatakwata gaba daya haduwar Umma da mahifiyar Sadiya duk ta canza gabadaya, Takoma irin su mafadaciya daga dan abu kadan ya hada ta dakai yanzu zata rufe ido tai maka tass, Ina daki mama tashigo dakin ta,samay ni rakube gefe guda duk na,wani ramay lokaci guda, Kallon tausayi taimin tare da kaiwa zaune tana cewa Aisha nasoki gane daga ina duk wanan abin yake fitowa, Kin taba gani ko tunanen cewa Sadiya zata kwanta irin yadda ta lankwasa kanta a gidan nan yanzu, Ko kin taba ganin mai abinkunya irin sadiya da ta buge uwar mijin ta tayi dana sani akan abinda ta,aiwatar a,baya, Sai yanzu da suke da dalilin su shine suka hada kai da ita wai Sadiya ta roketa gafara shine take kokari faranta mata,rai ta hanyar kuntata maki, Naji dadi da yanzu shi Hamza ya fahinci manufarsu yafito daga kaidin mata in ba haka da,har dashi zasu batawa lisafin shi su zugashi yai maki wullakanci ta boka ta malam, Tun haihuwan ki da kwana biyu da,Sa,a ta,shigo barka,aka,fara wanan kule kulen wai ankai Sadiya gurinta ta roketa gafara, Ni ban san irin halin yaya ba,wallahi mutanen nan kin san halinsu ba mutanen arziki bane amma sai ta biye masu, suyi ta tura ta,aikin dana sani, Shi dai mijinki ya,fada mata cewa,wallahi yana,son matan shi in ma,suna ganin zasu tayar maki da hankali ne tau sau dai yabar gidan ya nema maki wani guri ku koma, Shine ya tarya mata da hankali tahau borin kunya tana cewa wai an kwace mata,shi yanzu gaba daya ta,rasa gane kan shi kinje garinku an maki asiri zaki kashe mata da don bai ganin kowa da gashi in ba ke ba, Murmushi nayi na takaici nace ai Allah shine shedu mama idan nai ma Hamza wani abu a garin mu, Ke dai yanzu ki kara,dagewa,da,adduan Allah ya kara doraki a kan su kawai amma wa yan nan mutandn basu da kyau, Magan ganun mama sun kara sani mayar da hankali ga,abinda ke gudana a gidan yanzu, Na,fahinci yanzu tunda na haihu akwai shiri tsakani Sadiya da Umma sai wani, Ladabi takewa Umma, Ita kuma umma duk dan abinda tafita,tasamo yanzu zakaji tace ina ya ta wai ni yar mama hafsi ba yar ta,ba tana take fakewa suna cutana kuma, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,, Alhamdullahi zance don yanzu da hamza yai tsaye abubuwan sun yi dan sauki a kaina, sai dai a rufe akeko mai, Sannu sannu Hamza yadan fara sana,a hankali ba wani sana na,azo a gani ba ko shi sai da ya,ari kudi guri wani dan uwan sana,an shi da can baya, Shine ya dan fara barin gida yana dan shiga garuwa, yana yan kwanaki baya gida, Hakan bai ma Sadiya dadi ba da ya tsiro da wanan tafiye tafiyen don ya hanata ta samu yadda take ita kaidai tunda ni ina jego, Sannu a hankali likkafa ya fara ci gaba ga,sana,ar tashi don yanzu yakai yana dan iya kai kaya kurmi kadan kadan don ya dan kwarai da harkan, Duk yadda akaso ya tsaya iyaka gida yai sanar don gudun abinda yafaru a baya yaki ya dauka cewa wancan kaddara ne haka Allah ya nufa, Wanan zuwan da yayi wake yakai buhu goma sai Allah ya hadashi da,wani iyyamuri matashi shima yana sanar export ne daga kasa zuwa kasa yake kai abinci, Wanan matumin yai matukar yabawa da,wanken da Hamza ya,shiga masu dashi sai yake cewa idan da zai samu wanan wake da yawa yana so ya,saya yakai waje, Nan Hamza ya,dawo gida hankali a tashe don ga alheri ya hango amma ba hali, kamar yadda duk wani dan kasuwa yakan shiga halin yaya nakayi haka wanan bawan Allah shima ya shiga wanan yanayin fada can tashi can yana neman kudin da zai, karfafa kasuwan cin shi, Duk yan uwan shi ya tunkare su akan su dan kara mai kudi ya gwada wanan sana,an amma fir suka ki, Ya,samu Umma da,shawaran cewa ta bashi dama ya,dan sayar da filin su na baya gidan su amma fir umma taki yarda tace abin gado ne bata yarda ba, Jego nakeyi bawai lalaine nasan tsananin halin da yake ciki ba a lokaci, ni dai nasan yana bukatar kudi amma ban sa kaina ba don bazan ma bayar ba, Missali karfe daya da,wani abu na rana na dauraye yarinya kamar yadda na saba yi mata idan rana yayi Powder nake shafa mata,sai watsalniya da kafafuwan ta takeyi irin na jarirai masu lafiya ni ka dai dagani sai ita adaki ina fadin ni dai tsaya na,sa maki leda don fitsari ki yai yawa wallahi, Hamza naga ya shigo dakin mu kaina yana a duke nai mashi sannu da zuwa, Hannun yarinyar ya dan rika a cikin nashi sai ta danke yatsan nashi a hankali yadan lakuci kumatun ta yace gwagona kinyi wayau fa sosai, Zaune yakai da ita,a hannun shi yana mata wasa hakan yasani komawa bakin gado na zauna ina kallon su, Hamza yai matukar ramaywa sosai ya fada sai kasunba da ya aje a fuskan shi, Wasa yakewa Jidda yana hada goshin sa da nata gurin daya yana cewa gwagona Allah ya raya min ke na zama Baba nima azo a rusunna min, Sai nai murmushi kawai,daga inda nake zaune yadago yana ce min duk yarinyar nan ke ta kwaso wallahi, Nace kai yaya abakin ka kawsi naji haka cewa ake wai kamar kayi kakinta ne tafito don komai naka ta kwaso sai fari ne nawa, Murmushi yayi yace ai dole jini yayi aikin shi a kowan mu, Wayan shi tai kara abinda ya dakatar muna da hiran mu ke nan ya dauki wayan sai na fahinci maganace mai muhinmanci yake a,wayan yadda naga action din shi ya nuna, Yana gama wayan sai naga ya dan tugumay yarinyar a jikin shi yana cewa, Allah Allah kadubeni da idon rahamar ka ka bani falalar da zan samu nayi wanan business ne din kada ya,kubce min , Idanuwan shi a lumshe yana bubuga bayan yar baby dake a hannun shi yake cewa ace idan matsala ta sami mutum ya rasa gurin da zai dafa yaji sanyi, Yau kusan sati uku ke nan ina yawon neman taimako aron kudi dazan da,sayi waken da,ake bukata nakai wani company, Amma abu ya,faskara kowa ka tafi sai ya kawo ma lalurar duniya a kindayan maka,sune a,gaban shi, Munan dai zaune muna ta zancen yadda mutane basu iya taimakawa na kasa gare,su, Sai can nake cewa tau yanzu yaya zakayi gashi naji kamar mutumin yana cewa saura, sati biyu idan har ba,a,samu ba zai nemi wani ta,kawo mashi kayan, Yace a,sanyaye haka dai yake ce min dole hakkura zan yi na,bari aba,wani tunda banda shi, Sai dai idan kudin dake a hannuna zan hada na baka kafara saya,mashi dasu, Da,sauri Hamza ya kalleni yana girgiza kan shi yana cewa, haba dai Humaira ai hankali hanjine, Yai murmushi yace sau nawa ina karban kudi a,gurin ki ban taba biyannki su ba har yau ke kuma baki tambayeni su ba, Wallahi har yanzu zancen nan da nakw maki kunya rashi biyan ki kudin ki da banyi nakeyi, Yanzu kuma zaki fito da zancen na karbi wanda suke a,gurin ki kawai gwanda mu hakkura haka Allah ya nufa damu , Na ai bamu san inda alherin mu yake ba da kaita yawo babu mai baka,aro ai gara na mika,ma su ka juya,ko Allah zai sa muna albarka aciki mu gani, Yace to shi ke nan amma,sai k8n shawarci iyayyen ki abinda,duk sukace dashi zamuyi amfani, Na ce tau zan sa,akira min mama ko ummi nai shawara,dasu, Wani irin ajiyan zuciya yayi don bai taba zaton za,a,iya,samun mace mai wanan hali ba azamanin nan da kowace mace idon ta ya bude da,son kudi, Watau ita dai Humaira komai nata a cikin sauki take rayuwan ta bata,saka duniya a gaban ta ba balle ya damay ta kamar Sadiya, Da wuya kaji Aisha tayi wani korafi akan asayo mata abu kaza ko tace kaza nake so bana son kaza, Halin da maza da,yawa yake hada su fada da matayen su don namiji ya,tsani yakawo wa mace abu ta rai ko kuma kullunta kama fadin ba ba ba yana zubar da kimar mace a gurin mijin ta, Gashi yanzu ba matan aure ba harda yan mata sun iya cewa yau kaza nake so gobe ma kaza nake so, Ko kaiwa budurwa kyauta tun ba ai aure ba ta nuna ita kyautar bai mata ba don ba choice din ta bane Iyayyen mu na,da duk abin da namiji yabasu hannu bibiyu mace zata karba tana zabga godiya da farin cikin ta, Amma yanzu gashi duk yadda ya iya fita yai yawo a cikin rana in yadan samo abu ya kawo a,tsiwace Sadiya zata karba tana korafi akan shi, Shiko ba haka Aisha ta,saba yi mashi ba a,baya duk abinda ya kawo sai dai tace mai sannu da dawowa takarba ta,gyara tabawa kowa kuma kowa ya,samu,gwargwado, A haka muka bar zancen kan zan shawarci manya na muji may zasu ce, akai,,, Sai dai shi har kasan zuciyar shi nauyi da kunya yake ji ace ya na karba dukiyar matar shi abu na lalacewa, ****** ********* ****** Bayan nagama fadawa mama da Ummi dana bukaci ganin su suka zo hankali a tashe don a zaton su wani matsalane tunda na bukaci suzo su biyu a lokaci guda, Ummi tace yanzu akan wanan zance kikasamu taso Aisha ni wallahi na zaci wani matsalane keda mutanen gidan ku koda mijin ki, Nace a,a dama ahine yace na,shawarce ku ai muji naku shawaran abinda zakuce, Sai lokacin mama tai magana take cewa tau a gaskiya wani matsala ne kan babba don bai yuyuwa ki dauki abin hannun ki ki bashi ya akoda yaushe don namiji ba dan goyo bane, Sai kin kwashi abin hannun ki kin mika mashi dayazo ya samu ta sanadin ki sai duk yasa kafa yatake komai yace wai ya manta, dake da akai wahalar samu tare da ke, Mace ta zauna da kai da talauci tana hakkuri tana daurewa da,duk halin da kake ciki amma,da,zaran dadi yazo sai duk amanta da hakkuri ki, da dauriyan da kikayi a baya, Sai a tafi zuwa neman matar da za,aci dadi da ita ke baki uya cin dadi ba sai wuya, Ummi dake saurare tace ai shiyasa kkikaga,arzikin sai yazo da miskila,don baikaiwa ko ina,sai a bare, koda kuwa aiki kake yi kace kaidan cin amanane yanzu ko ina ba aikaiwa zaki ga matsaloli sun fara kuno kai iri iri, Mama Rahana tace mijin ki uban yar ki ko ince diyan ki in ya cuce ki wallahi kan shi ya cuta don ke kin mai yadda,Allah yace a rufa dan uwa asiri kamar yadda zaka rufawa kan ka, Imanin dayan ku baya kammala har sai yaso wa dan uwan shi abinda yake so wa kan sa, Don haka ni dai bazan mu ce kada ki baahi ba don mijin ki ne kuma yana neman taimako gashi yayi hankalin cewa kifara,shawartar da magabatan ki tukun,, Hakan yana da kyau don ni indai don shi yaron ne wallahi bazance baza,a bashi ba amma kin ga wanan makiran uwar tashi wallahi ina iya cewa kada a bashi don zata iya cewa nan gaba kada ma ya taimaka maki, inda hali, Ai itama ta haifa ai gasunan a gaban ta sunki aure suna gwada sa,a da juna da ita a cikin gida akwai abinda yafi wanan ciwo ne, Bafa karatu suke ba ba komai ba sai dai kawai ai wanka abi hanya ana laudi kawai,a hanya, Shawara daya da zan kara baki shine ki kasa kudin uku ki bashi kashi biyu kashi daya ki rika,a hannun ki kina dan juyawa a hankali mu gani ai hanyar Allah yawa gare shi, Sun kara jamin kune akan nayi hakuri na kawar da kaina ga,duk irin abubuwan da,ake gwada min agidan suna min ne don sunga cewa nafisu, Inda ace kin zama abin tausayine da yanzu za,akama takaki yadda rai ke so suna cewa kece abin son su, Wallahi ni yanzu na fahinci wanan bakar matar hassada da bakin ciki sune suke cin ta don taga kinfi duk diyan ta kuma baki damuwa da harkan su shine karin bakin cikin su a kan ki, Don haka sai ki dage da,addu,a da kuma,sadaka koda dan kadan don sadaka rigakafin masifu ne ga bawa , A,sanyaye na amsa da,fadin tau mama na gode indan tadawo duk yadda mukayi zanfada maku, Har sun kai kofa fita daga dakin sai mama Rahana ta,dakata take ce min kina nan kina amfani da ruwan dana aiko maki na tantabara ki hada da miski kina tsarki dashi kafin kiyi arba,in, Nace ina yi mama cikin dan jin kunya ki dai tayin duk abubuwan dana fada maki don kinga kin haihu saboda mu mata daran mun fara haihuwa dole mu dan matsa da gyaran jikin mu, Kwalban Alhaji Audun dana kawo maki kada kiyi wasa dashi Aisha don yana,da kyau sosai ga mace, Kanumfari dai nasan cewa kina dashi har yanzu kuma kina amfani dashi, Don ko shi ba baya ba saboda amfanin shi yana da matukar yawa ga dan adam sosai,, Kwara uku ki tsugunna akoda yaushe a kanshi kiyi hayaki kasan ki dashi, Inayi mama na bata amsa a takaice, Bayan fitan su mama na zauna ina tunanen abinda ka je ya dawo akan wanan kasadan da nake son yi naba namiji kudina namijin dabani kadaice mallakin shi ba namijin da,yaje mijin mace hudu uban diya ba iyaka Ke Aisha, rike kudin ki ke da diyan ki, sune naki bana mu duka ba, baban kowa, Har na aje akan haka sai kuma wani tunane yazo min nace to amma kuma, idan ban taimaka mai ba may ye amfanin arzikin da nake fatan ni nayi mijina na,wahala akan son tara abin duniya zan bar mijina a cikin wahala, Abina na shi ne haka abin shi namu ne don haka banji kyashin komai ba sai na yanke kawai na bashi kudin ya gwada sa,an shi ya gani ko za,a dace, Bayan ya,shigo nai mashi bayanin komai sai ya dan yi shiru yana nazarin irin iyayyen da,Allah ya hore min bama su kyashi da,hassada ba, Duk irin abinda yai min a baya basu duba akan shi har sun kara yarda na taimaka shi akaro na barkatai kuma again, ****** ********* ****** Alhamdullahi don dan kufin dana hada mashi wanda babana da sukazo suna suka kawo min kudin gonan su da,suka,sayar suka raba kudin shine aka kawo min na baba, bayan sun cire nasu kason a ciki, Mutumin da Hamza yakaiwa kayan yaji matukar dadi don haka ya saye yadda ya,dace ya bashi kudin shi akan cewa ya dawo ya kara saya ya kai mashi, Da Hamza zai dawo ya dan sayo wa Jidda yan rigunan yara mata kala biyu da permpers da,su man shafi na jarirai, Ranan da ya dawo da yake ban yi arbain ba adakin Sadiya yake har yanzu don haka shigowan dare sukayi bai samu bamu kayan ba don ya samu munyi barci ko, don har na rufe dakina, Ai Sadiya tana ganin kayan tafara mashi masifa kan cewa may yake nufi da zai sayo wa yar shi kaya haka ita kadai ita ko ta dawo hannu rabba bai sayo mata komai sai burodi kawai da manjan miya da,ya,sayo a gida, Tun dare suka fara wanan jidalin saboda yana,da gajiya sai bai biye mata ba ya kwanta yai barci abin shi, Tun da,asuba ya tashi zai tafi sallah ta farka da wanan fitinan nata haka ya tafi rai a bace, Sai lokacin ne nasan cewa ya dawo daga tafiyan shi ashe cikin dare muna barci, Ina jin ta tana fadawa Umma cewa wai tun yanzu zai fara nuna mata banbanci akan yar shi don ita Allah bai bar mata nata ba za, a dinga mata wanan cin fuska haka, Yanzi don Allah ke Sadiya may ye cin fuska a ciki don ya saya wa yar shi kayan sawa shine kuma abin fitina haka, Ina koke mai sayawa yarinyar nan kayan sawa ne in har kina dashi tunda kin a tare da uban ta, Mama ni nafi son mutum ya tsaya yafadi gaskiya ba a goyi bayan karya ba, Ke nan ni ba dolen shi bane da zaiyi tafiya ya,sayowa yar Aisha abu ni ina zaune ko dan kunne, ba zai riko min ba, Tun da ina Sadiyan mahaukata bari abi ta,waban hanyar yarinya a cutata min ni ko sai na kyale shi ko wallahi bazan yarda ba, Sai dai yasan nayi indai haka zai min don wallahi ni ba,wawiya nake ba, Tunda bazaki yarda mama hafsi tace ai sai ki dauki mataki da kanki mu gani, Wallahi dauka zanyi don bazan yarda da alabe a kaba a harbi barewa ba, watau ya,sayowa yar ta kaya don taji dadi niko da ban da da naji haushi, Ina dani da Aisha din duk zaman shi muke a gidan nan ba zaman wani ba, A lokaci ya,dawo daga massalaci yana jin yadda take fadawa iyayyen shi maganan banza, Sadiya,wai may kike so ne da safen nan tun dare kike abu guda,na kyale ki yanzun kuma kin farka dashi zaki ta da makwabta daga barci da masifan ki haba, wallahi kin isheni bazan iya wanan irin rayuwan ba gaskiya, Baki isa ki hanani yiwa gwagona sayyayan abinda rai nake son saya mata,ba don diyata Sai ka dauki mataki tunda bazaka iya ba kamar yadda nima bazan yarda da cin amanan da kake son yi min ba ta hanyar diyar ka, Wai ko Sadiya kina da hankali kuwa ? Kai ka wuce inda zaka ban son wanan fitinan haka maza shige inda zaka, Ya nufi hanyar dakin Sadiya don ya,dauko kayan da take masifa a kan su sai burodi da manjar miyar da ya,sayo kawai ya gani a dakin ta kwashe rigunan ta boye su duka biyu, Daga labulen dakin yayi yana fadin zoki bani rugunan nan kafin ranki ya baci, Yafito da bread din da manja ta,waje ya aje su ya koma cikin dakin nan tabishi da sauri ta samay shi yafara bude akwatin ta yana son ya,duba sai ta rike mai hannnu, Nan su ka,fara kokuwa a tsakanin su karfin ba daya ba ya kwashe ta,sai saman gado tafada kuca ya bude akwatin kayan suna kasa ya kwaso su sai ta rike mai hannu, Ya juyo ya dinga zabga mata mari gana uku da taji uwar bari ta sake kayan tafara kurma ihu yaje fita ta riko shi ta baya ya juyo cikin fushi yai mata dukan tsiya duk muna tsaye waje cirko, cirko muna kallon ikon Allah , Duk dukan da yake mata bakinta yaki mutuwa sai wayyo take fadi shege macuci azzalumi kawai, Wallahi yau sai ka biyani kudina ban yarda duk abinda za,ayi sai ka bani kudina gidan nan macuci kawai azzalumi dan iska, Ya ce kizo ki kwata inna karfine bazan bayar ba tace wallahi sai ka bani kudina yau bazan yarda, Goya Jidda nayi a baya,na don naga masifar da yafi karfin gani na,yau gashi yana dukanta amma bakin Sadiya yaki mutuwa don tsaban bala,i, Kai miko min rigunan nan don saboda,su ake wanan masifan dai ko ta kawo su na raba gardama, A,a Umma ba gaskiya bane kuma Ibrahim wanda ke daga kofa yana kallon duk abinda ke wakana a gaban idon shi yaki rabawa, Ita kanta Umma abinda ya faru a baya take wa tsoron zuwa ya,sake faruwa da ita gashi har yanzu bataji sauki ba tana dan dingisawa ne, Ba hujja bane don wanan matar ace bazai sayawa yar shi komai ba don wai ana gudun zuciyar ta kafin Hamza ya mikowa Umma kaya ibrahim ya karbe su daga hannun dn uwan shi yanufi dakina dashi rai bace, ya aje a saman gado, Wayyo Allah na,wallahi yau sai dai ka kasheni amma,sai ka bani kudina don bazan barka ba,wallahi, Kai Hamza fito gidan nan mana hakana kabarta kada ka bi ta kanta ita mace ce kada ka jin mata ciwo, Muryan Baba Mudi ne mijin Ummina da muke makwabtaka dasu ta gaban gidan mu yake magana cikin bacin rai ya,shigo daga cikin gidan ya tsaya daga kofa, Hamza ya dago idanuwan shi da sukai ja yana mayar da numfashi daidaya yace cikin huci tau Baba , Zai fita Sadiya dake zaune tamike tasha gaban shi tana cewa wallahi yau sai ka bani kudina dubu goma sha biyu zanbarka kafita inba haka ba sai dai mu tafi tare wajen da zaka, Baba ya,sake cewa kiyi hakkuri Sadiya insha Allahu zai baki kudin amma kibi sannu kada yajin maki ciwo a banza, Uwarta ce tashigo gidan rai a bace tundaga nesa take fadin wai may ye haka may ya kawo hakane wai, Tana tambaya cikin bacin rai idanuwan ta,sun nuna mugun bacin rai tace wa Sadiya da ke kuka tashi mu shiga daga ciki, an taru ana kallon zai kashe ki kowa ya kyale ku haka yana dukan ki kamar ya samu jaka, Umma tace haba Sa,a kin san halin Sadiya in tafara abinta bata jin bari wallahi tun abinan baiyi nisa ake mata magana taki bari, Agaban ki fa Rabi danki yai mata wanan itin dukan tsiya na,wullakanci kuna kallo wallahi in "ya ta ta samu matsala bazan kyaleku ba sai nayi karan ku, gaba,daya tun da ba jaka nahaifar maku ba, Yau naga masifa a,filin Allah, uwa jidali diya jidali ga mutane sun cika muna gida, suna kallo da saurare, Daki na koma na gyara goyon yarinta da ke motsiniya a bayana cikin tashin hankali wai ana fada akan yar wanan tatsitsiyar yarinya, Baba ya,samu Hamza yafita gidan cikin takaici da kunar rai ya samay shi a kofan gida yai mashi fada kancewa duk yadda ranshi ya baci ya baci ya bar dukan mace hakana don in ya saba da hakan haka zaici gaba dayiwa matan shi nan gaba, Baba yace kayi kokari kaba yarinyar nan kudin ta don a zauna lafiya kadai ga halin ta ba yar rufin asiri bane,. Baba kudin nan da take zance fa nawane ni nake bata tace zata sai fridge dashi shine Da ta tayar min da hankali shine nace sai dai na bata a hanakali har ya kai rabi sai ta cika ta,sai fridge din dashi, Dana samu matsalar nan shine nace ta aramin din na bawa emeka kudi shi a lokacin, Murmushi Baba yayi kadan yace ai tunda ka bata ya zama nata don haka idan ka samu ka bata abinta a zauna lafiya bashi ke nan ba idan ka biya wani kudi kuma zata kara maka tonon asiri a kan shi haka, Insha Allahu zan bata kudin ta ba kamar yadda kace din, Baba yace abune babu shawara in bashi ba ai wanan zurian ba zurian auren ka bane hamza yarinyar da take tashin mace, Ai babu tarbiya wadattace a gurin irin wa yan nan mata,sai tarin dana,sani kawai dan dadin zama da irin su kadan ne bacin rai yafi yawa, Wallahi hakane Baba duk Umma ce takaini ga,wanan bala,in don ba yadda ban kurce mata akan wanan hadin babamma fir taki yarda tace ala dole sai nai auren nan tama dauki fushi dani dole nayi shi badon naso ba, Yanzu ai gashi harda ita basu raga mata ba suci min mutunci suci mata suci ma yan uwa na ina macen zama haka baba ? Babu komai kadai yi kokari ka biyata kudin a zauna lafiya kawai, Nan ya zauna waje yana tunanen akan dubu goma sha biyu Sadiya take mai wanan balain haka insha Allahu zaiyi kokari ya,biyata sai ya dauki mataki Ashe Aisha ba karamin hakkuri ke gareta ba don da kudin ta dayai sana,a Allah ya albarkaci sanan dasu yai auren Sadiya din, Amma bata taba yi mai magana a kan su duk da ganin yana,wa Sadiya din spending da Umma tace yadinga sawo mata saboda shigan cikin da take dashi a lokacin, Aisha batai magana ba amma karshe Umma din ce kuma abin ya fita a tsakanin su kowa na kallon su, Uwar sadiya da ta fito tana masifa ita bazata yarda akan dan magana kadan aita bugar mata yarinya ba, Har ta,wuce bai ce mata kallal lahu ba don matar duk ta fita mashi a,rai saboda basu da mutunci ita da yar ta, ****** ********* ****** Bayan komai ya lafa ina zaune a,daki ni kadai na kurawa rigunan dake yashe a,saman gadona ido, rigunan da suka hada fada yau a gidan,rigunan da basu kai ko dubu uku ba,don irin masu saukin kudin nan ne, bonanzar hanya ya,sayo, Wai shine a kan su Sadiya ta sha,wanan uban dukan kamar wata jaka can, Yanzu ashe ba,dama ya sayawa Jidda komai a gidan nan kenan sai tare da Sadiya don itace a kuma ta,koma kishiyar ta,. Akan kin rufawa mijinki asiri da,dan magana ya hadaku sai ki shiga mashi gori da tonon asiri har ki tara mashi jama,a wanan wani irin rayuwane haka mai tonon asiri da cin mutunci, Gaskiya halin Sadiya sai ita akan dan abin da baikai ya kawo ba sai kaji muryan ta yana tashi kamar wani babban magana, Ga Umma tsoron cin mutuncin Sadiya take ji kamar zata dake ta,sai kiga tana wani dan sune kai tana tausa murya haba dai Sadiya ki bar yin haka mana da,sauran su, Dan kudin hannu zan zage damtse na fara business na debewa kaina da yar diya,ta takaici tunda na fahinci so ake aga walle na,agidan kawai Kiyayya harda yar yarinyar dake goye abaya,a hada da ita,gurin kishi, Ashe haka kishi yake kowa da irin nata sallon kishi ba,a raina abin yiwa kishi ko kadan, Kai jama,a Allah yasa mufi karfin zuciyar mu jama,a kishi bala,ine akan rigar yarinya tasha dukan banza abanza babu mai rama mata, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,, Duk da,an kashe magana Hamza zai biya Sadiya kudin ta, har zuwa yanzu sama sama suke don yaki sake mata fuska, Zaman yar tsama sukewa junan su duk da ita Sadiyan ta dan sake dama haka halinta yake cin mutunci da zaran tayi shi ke nan zance ya tafi a gurin ta sai wani kuma, Mun cika kwana arba,in cif nasha gyara ta ko ina daga dakina har jikina don a dakina na canza kujeru da ledan kasa, Haka ma jikina yasha,gyara don abubuwa da dama mama Rahana tasa ai min don na kara daraja a gurin miji kamar yadda ko wace mace take kokarin gyara idan zata koma gurin maigida, Nai kitso har da kumshi ba wanda ya fahinci hakan sai mama hafsi ita hankalinta yana a kaina ko yaushe, Duk wanan gyare gyaran da nakeyi Umma da,Sadiya wai basu fahinci cewa na kusa arba in ba a gidan, Sai da safe da suka ga mama hafsi tana aikawa da masan da,Mama Rahana ta,aiko muna dashi, na sadakan arbain, Yan uwa wanan al,adan sadakan arbain bawai jahilci bane don yin haka yana da amfani domin sadaka alheri ga,wanda akaiwa amma gaba daya yanzu mun daina mun marya dashi cikin bidi,a Bidia din ne don annabi bai ce ayi ba amma kuma ance muyi sadaka don haka ya kamata mu dinga yin sadaka wa yayan mu don kariya ce babba akan su Wani leshi nasaka a jikina sabo mai ruwan dark blue,sai farin zare da akai mashi aiki dashi as a flower takalma jakka har hijjab dina duk sabo ne, Na goya Jidda da showel fari a bayana tana barcin ta na jawo kofa na nufi dakin Umma ina mata sallama, Zan fita karo na farko bayan haihuwana kenan don tunda na haihu van fita zuwa ko ina ba ina gida ina jego kamar yadda ya dace mace ta zauna guri daya ta samu hutu ta mayar da jinin ta da ta zubar, a baya gurin haihuwa, Koda ba,hali gariku ba zaman ki guri daya kina ci kina sha kina,samun hutu zai saukar da ni ima a jikin ki, Karar takon takalmana shi yasa hankalin su Umma har da sadiya data dan leko ta kafan labulen dakin ta,din gani ko wacece ke tafiya,da takalma yana kwas,kwas, Daga kofa na tsaya ina fadin Umma zan shiga gida gurin su Ummi na gaishe su, Au injin yau anyi arbain ko ? Muna gayar dasu adawo lafiya nace amin Umma daga bakin kofan Sadiya na tsaya ina cewa Sadiya zamu fita sai mun dawo ke nan Ku dawo lafiya yan arzikin suna kusa an karba min yau ba a kyaleni ba, Ina fita tamike zaune tafara sake sake a ranta sai daga karshe ta samo mafita don haka sai ta kutta kawai, ta,koma ta zauna saman kujeran ta, Nikan farkon fitana gidan mu na fara shiga na samu Baba a gida bai fita,ba muka gaisa dashi cikin jin dadi da farincikin ganin na da yayi, Daki daki na,shiga na gayar da,abokan zaman Ummina, sun nuna jin dadin gani a fili sai da abaya idan na,daga ai muna dariya, wai na nakasa, Atika ce taso zolayana da cewa ina yar fitinan gidan ku kai Sadiya babu dadi wallahi, Murmushi nayi ba tare dana bata amsan komai balle tace taji wani abu a bakina akan Sadiya, A dakin Ummi na nacire hijjab dina already, Jidda na barta a gurin Baba Mudi tun shigowana gidan, Na zauna ina cewa ina su yan biyun Ummi su ke ban gan su ba sai take cewa sun tafi sayo mata kayan miya,yanzu zasu dawo, Gaisawa muka kara yi da Ummina irin na da da mahaifi take tambaya mutanen gida na amsa da lafiya kalau, Ina maman ki nai murmushi nace, ta tafi, cikin gari gurin karban kudin ta don yau bata,samu fita,saboda sadakan da ta,tsaya yi na arbain din mu, Akwai ta dai da kokari wallahi tana kokarin ta da ku a gidan nan amma ita,sarakuwar taki kan halin ta,sai ita, Mijin naku yaba matar tashi kudin ta ko, ? Wallahi Ummi ni ban san tsakanin su ba,saboda ban son saka kaina a cikin zancen su, Ni ko su na abinsu koda ta,sa suban ban biye mata sai dai tayi haukan ta ta,kare shike bata haushi dani wai sai na dinga mayar da ita mahaukaci, Kada kiyarda kuna sa,in sa da ita don yana kawo raini da wullakanci abinda akeson a fada maka na,sheri gurin irin wanan fadan na kishi ake ma mutun kake akan abinda bashi ace shine yayi ko wani mugun tarihi wa iyayyen mutum da,sauran su, Shine dalilin da yasa ba,a son fitinan kishi don babu komai a cikin shi sai sheri da kissa ke ko nasan ko dan kissan matan baki iya ba, tafa cikin zolaya na, Nace a,a Ummi ni wanan ba a gabana yake ba taje taitayi ai sunyi daidai da mijin nata tunda shima yanzu ya iya, ai, Ina dai horon ki kada ki yarda ajiki dashi akan abin duniya don baki san irin ranan da,shima zai maki ba,watarana, Zama dama cudeni na cudeka ne kataimaka lokacin bukata indan kana da hali kaima watarana sai Allah yasa maishi ya taimake ka, Don haka don kin bashi ba,wai ance ki saka mai ido akan duk takon shi ba hakan sai yakai wata rana kin mashi gori baki sani ba, Ummi nifa ban taba bashi abu na sa ido ko na kara waigen abin ba bashi kawai nake don rufin asirin mu, Tace ashe kin gane kin wa kanki kuma dubara duk tsiyan mutum watarana dole yasan kayi mashi rana ta wani gurin, Mun dayi hira nace zan tafi don har gidan Anty Hindatu da Mamana Rahana zan shiga da yan sauran guraren da ya dace, Sai nadawo kafin na,shiga gida zan shigo na kara ganin ku,, Gidan mama na nafara zuwa mun dauki lokaci da ita muna hira ta na bani shawara da,abubuwan da ya dace na rayuwa, Sai gidan Hindatu dana shiga zuwa karfe biyu a can nai azahar har la,asar muna hira da ita, Nafito na,shiga gidan iyayyen ta na gaidasu sai gidan su kibura da yan uwan ta duk sai da na biya a tsatsaye muka gaisa dasu nai masu bangajiyan buki da,suka zo min, Ranan nasha zumunci sosai don nasada zumunci a gurin yan uwa da,abokan arziki, A gurin Ummi na,dawo akaiwa jidda wanka don dare yayi lokacin sai da,akafito sallah magariba nashiga gida a lokacin cikina yai dam da abinci na koshi a gurin Ummina, Nadawo gida na,samu kowa a gida gayar dasu nayi na,bude kofa na nashiga, suna tayi min ba,a wai na samu fita yau sai jnda kafana ya tsinke na tsaya, Sadiya bata samun abinci ba nima haka ban damu da na tambaya ba don a koshe nake, Ganin nadawo ba,a bani abinci ba yasa Mama tambayan ina abincin Aisha , ne ? Ni walle ban sa mata ba don gida naga ta tai, shinas sa ban samata ba, Tsit gurin yayi don jin may Sadiya,ta fada a gadarance kai tsaye, Sai Ibrahim ne yace amma dai ke ina ganin baki da hankali mace da,jego tana shayarwa ki hana mata abinci ke ta taba maki haka ta hana maki abinci a gidan nan, Kai walleh karka damay ni ra,ayinane hakan don may zaka matsa mini ne wai kaji min kai, Umma tace Sadiya wai mi da baki son gaskiya shin ke taba ganin ko dabba anyi horo nai da yunwa, Abinci dai yau gashi an sayo wadatattce kowa yaci ya koshi har abin cikin miyan duk Alhamdullahi, Ai basai ta ci ba dama ai ba don Alkah ya sayo ba don yaga tai arbain azaton shi Aisha ce zatai girki shine ya sayo mai yawa haka, Shiyasa ni kuma na juye duk na rabawa kowa ita da taje gidan su sai taci a can, Yau kan kamar na tanka sai na tuna yanzu fa Ummi ta ga yi min nasiha akan rayuwan Sadiya cewa irin su ba,wai auren ya damay su bane zasu iya cewa namiji goma ba uba goma bane ai Su basu zauna ba kai kuma da aka,sa.u ba,a barka ka zauna dakinka ba su koreka ko su tsaya idan kina da diya,su dinga azabantar da diyanki na wani dan lokaci su gudu, subar yara kamar marayu, Mafiyawan aure yanzu haka yake wallahi, sai kiga an samu mace da mijin ta a,tayar mata da hankali ita da diyan ta karshe ma,akore ta gidan ita kuma amaryan tace bata zama tayi bautan diyan wata, Maza basu da tunane yanzu sai wanda Allah ya sa yagane gaskiya za,a shigo mai gida da iyayi yasa ma,amarya waigi bazai dauki rainin hankali da tazo dashi ba, Amma masu dauka yanzu sunyi yawa don sauyin yanayi zuciyan mazaje yafi karkata ga amarya sai na,Allah ke tsayawa yayi adalci don haka idan kin tsuci kanki a,wanan yanayi kiyi hakkuri ki kawar da idon ki ga irin kaidin da ta,shigo dashi kada kice zaki tsaya wai ku kwata ance mai laya kiyayi mai zamani, A karkashi kasa zaki gasa mata kwakwa a hannu batare da an fahinci naki halin ba, Don haka sai na daure kawai nai shiru batare da na bata amsar duk maganan da takeyi akaina ba cikin gadara wanda duk wanda ke kusa zai dauka cewa tsoron masifan Sadiya nake ji da yawa, hakan, Daya bayan daya suka fara,watsewa,a,gurin Hamza da yafita tun fara zancen sai gashi dauke da leda a hannun shi, Idanuwan su gaba daya yana akan shi dakina ya,shiga da ledan ina tsaye a bakin gado zan yiwa Jidda shimfida, Jin shigowan shi dakin yasani juyowa dan naga may yashigo yi sanin da nayi cewa baya shigowa a wanan lokacin idan har Sadiya ce da girki, Ledan hannun shi yake kokarin miko min yana cewa gashi ki ci kafin ki kwanta kada ki kwana da yunwa, Namika hannu ina cewa nagode amma ban ma da yunwa don naci abinci a gurin Ummina kafin nazo, Ki dai karba kici ko da,zuwa dare don kada ki kwana da yunwa a cikin ki , Sai na mika hannu na karbi ledan yake cewa gwagona tana barci ke nan eh kawai na,bashi amsa a takaice kawai, Har yakai bakin kofa yake ce min ki cire ledan tea a ciki don kada ya yoye maki naga ba ruwan zafi tasa nace a hado maki a can, Nagode na kara furtawa cikin ladabi tare da juyawa inda jug na dauko ledan na fara juye tea, sai wani kumshin da na gani ashe, nama ne gassashe mai yawa,a cikin takarda sai bread longi guda , Ban tsaya ta kan kayan ba na fara zuwa don nayi sallah kafin na kwanta,don na kwaso gajiya a tare dani, Murya kasa kasa naji Sadiya a dakin su tafara halinta ta,na cewa wanan ma zance ne don ba zan yarda,ba ko ka,sayo min nawa ko kuma na,shiga dakin ta na kwaso abin da ka,sayo mata mu raba, Muryan shi naji yace au ashe ba,dadi ke da kika kwashe wanda na,sayo kowa yaci a gida kika hana mata, Aiko yau akwaita, a gidan nan wallahi don bazan yarda da,wanan cin amana ba a filin Allah, Ke jinan yace a cikin wani kakausar murya muddin kikai min balai a cikin daren nan yau wallahi za,ayita a kare don nagaji da fitinar ki wallahi, Daga nan na karasa alwala, na nashige daki abina tare da rufo kofana har na rufe sai na tuna da mama hafsi na diban mata bread da naman nakai mata na,samay ta tana sallah don haka, na aje mata,kawai na tafi, Har na,shige ina jin suna rikicin su yana cewa ai nace idan kin isa, ki je ki dauko, Murmushi kawai nayi, na,shige dakina ina mamakin halin iri na,Sadiya da,son yawan masifa, Ni dai har na idar da sallah na zauna nasha tea tare da cin nama sai da,na koshi na bar saura a plate, ****** ********* ****** Washegari nafito na,sa ruwan wanka don na hutar da mama,saboda mun yi arbain yanzu, Na gyara dakina kafinna,shiga wanka tare da gyara tsakar gida don ko zai shekara a haka ba mai gyara shi daga Sadiya matar gidan har yan matan umma din, Nai wanka na saka tufafi ajikina wani dongon riga body hook mai saukin kudi irin na tallaka na saka ajiki,. Ina zaune ina shayar da Jidda naga wucewar ta ta gefen labule na can ta dawo sai naga ta daga labule tana tsaye daga kofa tace, Ke yar Agwai kada ki ga jiya na kyale ki kinci bulus wallahi ba zan barki ki cuce ni ba don sai na rama abinda kukai min don kunyi da mai yi a gidan nan, Nace cikin bacin rai ke Sadiya dan yatsan rainin da kike kawo min ya isheni, haka, Idan kin isa may yasa bakizo kin dauki abinda na ci bulus din ba, wallahi, duk sallon wullakancin da kika iya na iyashi ina kyalewa ne kawai don a zauna lafiya, ba,wai don tsoro ba, Ta ce haka kikace dama ai hakan nake so mu goga a tsakanin nidake aga wanda zai gaza, Nace to shike yanzun dai ki ske min labule kafin akai ga yadda baki tsanmani ba, Idan ban sake ba may zakiyi min nace to kada ki sake din ki gani don zan iya daukan rainin tsakar gida amma banda na har cikin dakina, Tsam na aje Jidda gefen gado na nufo kofan da take tsaye rike da labulen dakina batai aune ba kawai sai na sakar mata mari kayauuuu, Kafin tace kika mareni Aisha ashe yau akwai balai agidan nan, sai na kara kai mata,wani mari iya karfina daidai tsakiyar fuskan ta iya karfina sai da ta tangada kamar zata fadi, Haba nan muka cakumay junan mu saiga su Umma su Asmau sun fito suna salati, Umma daga nisa kafinta karaso take cewa yau may zan gani haka a gidan nan, Sadiya takkaka kika kai mata har dakin ta su Asmau sukayo kan mu Allah ya kara bani sa,an ta na,shake mata makoshi iya karfina, Sai kokarin kai min nashi take Umma tafita kofar gida gurin maza tana neman agaji cikin su harda Hamza, Innalillahi yake furtawa yana zuwa ja daya yai muna,saida muka watse gaba dayan mu har,su Asma,u dake kokarin raba tsakanin mu, Sadiya har dakin ta kika biyo ta da masifa haka idon ta waje tasha wahalan shakan da nai mata, Tace nabita may zakai min nan yafara kai mata duka sai da aka jashi yace wallahi yau sai tabar min gida, Don ni wanan abin ya isheni wallahi, wallahi ko wa yai mata tsaye sai Sadiya tabar gidan nan, Tace bazan bari ba indon kan wanan figagar matar taka ce sai dai ka kashe ni macuta kawai azzalumai wallahi sai ra fito da abinda ka,sayo mata jiya , Nace baza a fitar ba idan kin isa ki shigo ki dauka ki gani wallahi yau sai na gwada maki figaga nake a gidan nan, Ke wallahi nagaji nagaji Sadiya shiru shiru wallahi ba tsoro bane, Ai wallahi yau sai kin fane kin mare ni don sai na rama kowa yai maki tsaye saina rama marina a gidan nan, Gida ya cika yacika da makwabata masu jira suji sai cewa mutane keyi yau abin ya ishi Aisha ne tunda kukaji tai magana dama mai hakkuri bai iya fada ba ai, Asmau tace wallahi har daki tabita shine ya batawa Aisha din rai, daga gurin da Umma dake tsaye tace ke Asmau waya tambaye ki, Nan mutane suka juya kan Umma wasu nacewa ai gaskiya ne idan bata bitaba may yakawo ta kofanta fada , Shigiya na tafi kofan ta din don wanan shigiyar diyar taki da kika haifa kowa bai so a gidan shine har kikewa mutane daukan kai wake kin haihu, Wake son ta in bashi ba,da yazama, wagili bai san ciwon kan shi ba,diya haka,da,fari kamar zabaya, Nace, koma,wace irice na godewa Allah na daya bani ita Allah yasa mata,albarka, Ke tafi can shegiya yar iska wace saida ta tafi garin su gurin yawon iskan ci tadawo da ciki, anzo an nade shi ance nashine, Kai matar nan ki rage shiri watan tafa uku gida tadawo da,wata daya da rabi ta haihu zaki ce mata haka wallahi kiji tsoron Allah kada Allah ya kamaki da laifin sheri, Wata tsohuwa cikin makwabtan mu da suka shigo suke cewa haka sai gurin yadauka da cewa kai haba dai wanan kan kin yi karya wallahi don Aisha tun tashinta ba,a santa da,abin assha,ba,garin nan kuma da cikin ta tabar gidan nan kowa yasani,sai daiku, Ko zaku shigan matane tajuya gurin matan cikin fitar da idanuwan ta kamar zata hausu da duka, Sai dayan matar tace mi ina zamu shigar mata itama ai ta isheki don kin sha mari ai dama nadan iska ke nan ai sai baki babu karfi, Hamza ya dawo yace wallahi sai tabar gidan kofan dakinta ya nufa da kwado a hannun shi ya kulle dakin, Sai kuma ta juya a kanshi zai kara dukanta aka tare shi nan mutane suka in mata saida Asmau ta bata hijjab suka fitar da ita daga gida sai gidan su, Kowa na tir da,Allah waddai akan ta muna jin muryan ta har waje tana,ashar, A raina nace tir dake Sadiya ashe haka masifaffen mutum yake aduniya kai jama,a halin sadiya baiyi ba,wallahi, Sai daga baya zancen Ummina ya fado min a,rai da tace fadan kishiya dama sheri ne da kake a cikin sa abinda ake son fada maka sai a fade shi acikin fadan kishi, In badon Allah ya wankeni ba da yau ta zarga min masifan daba zan iya wanke kaina akan shi ba wai Jidda ba yar hamza bace yarinyar da take kamar shi yai kaki fari ne kawai ta kwaso nawa, Tsohuwar nan tace amma dai gaskiya wanan yarinyar ba matar zama bace wanan ai masifa ce kuka daukowa kan ku agida ni tun da naji za ai wanan hadin nace may yakai Rabi yain wanan irin gagancin wa dan ta, Dama nasan karshen amintakan ku ne yazo yarinyar da tashi cikin shiya kamar tambadadda shine har zakiyi sha,awan hada zuria da ita, Tun shigowan wanan yarinyar cikin gidan nan babu zaman lafiya dakowa ko ke bata barki ba balle wanda take zaman shi kai may ake da irin wanan mugun auren haka, Umma dai tana shiru daga inda take a zaune sai dayar matar tace yanzu aikin ji sheri inkina kama jiki ki rike sarakuwar ki da mutunci ki rike don kinga har tana batun sheganta maki jikan ki a bainan jamma,a , Badon mun san komai ba,ai sai mu yarda da sherinta, cikin da aka tafi dashi kusan wata bakwai shine take son zarga sheri irin na kishiya, don bakin ciki da takaici, Dakina suka shigo lokacin ina daura zani don nacire kayan da mukai fada dashi dayar matar tace min maza ki fitar da,wanan kayan da kika cire a gidan nan don kada tsiya ya hau mijin ku, Inaji ina gani taba wani yaro tace jeka konashi sai ya zama toka, Kuma daga yau kada ki kara bari ku hada jiki da ita don ba karamin tsiya fadan kishiyoyi yake kawowa ba a gida dama ku kanku, Bamu sanki da wanan hali ba Aisha tun tashinki a uguwar nan babu mai cewa ga abokin fada ki, Don haka mun san kina da gaskiya amma kiyi hakkuri kibar biye mata kikyale ta da halinta Dole ne koma,waye aka bishi har daki ko gidan shi ya ji zafi, a ran shi don hakan ba karamin raini bane, Mama hafsi tana uguwa aka fada mata tadawo rai bace nan itama tashiga na ta fadan cikin bacin rai, Ummina ranan da kanta tashigo gurina taimin fada har saida nai kuka ta kara jamin kunne Akan cewa na fita harkan Sadiya dama namiji yana auro mace ba wai sai dole hali yazo guda ba , Koshi daya dauko ta wani dadi yaji gareta abu kullun masifa ba wani jin dadin zama kawai hakkuri yakeyi, Ni fa ban son ace saboda ke tabar gidan nan gara nasu ya hadasu can tsakanin su da ace don, kuyi fada da itane har ya ce tabar mai gida, Nace cikin share hawaye insha Allahu Ummi bazan kara yin haka ba yauma dai shedan ne ya zugani har nakai ga tanka mata Ummi tace su ai anfada muna duk yadda kukayi su yaya sunce bazasu zo ba don in sunzo ba a mai kyau dasu, Ni wallahi Aisha wanan auren yanzu yakai min ko ina,wallahi badon mijin ki yai min komai ba,sai don kawai irin rayuwan da kika tsuci kanki a ciki da kurciyar ki, Gashi da andayi wani fitina sai munji shi an kafa yi min gori ke nan a gida har sai nagaji na tanka na basu amsa wai dawani mutum zaijine don Allah, Yaya cewa take in dama anyi ne don taji kunya to irin abinda tagani nan ai taki yarda Kubura tashigo, Don ai mata bakin ciki aka dauke ki aka bayar wai don kwadai, Ni may hamza ya taba bani na kwadai da har zai tsone min ido na,daukeki na bayar, In ma cin moriya ne ai sune sukaci moriyan shi a gidan don a lokaci babu abinda bai masu , Ummiinsha Allahu baxan kara yarda ajini da ita ba wanan din ma kaddarace kawai ya kawoshi, Da yamma na,sa girki ranan nice zan yi girki don nayi arbain saboda haka ban tsaya jiran komai ba na dora girki, Ibrahim ne ya,sayo muna kayan cefane ranan yace nai muna amfani dashi, Kafin wani lokaci har na gama komai na,gyara kuma ko ina dazaran mutum zai shigo zaiji kamshin turaren wuta ko ina a gidan, Jidda tana gurin Mama tun da tai mata wanka ta goyata a bayan ta hakanen yabani daman samu na aiwatar da,aiyukana, Ana maggariba aka dawo da,Sadiya,sai dai Hamza din bai gida a lokacin sai suka koma zuwa tara na,dare ya,shigo gida da leda guda biyu a hannun shi dakin Umma ya kai guda dayan kuma ya,shigo dashi gurin mu, Yakecewa yatafi wani kauye ne sayan wake don yana,son ya koma ya kaiwa mutumin dake son waken, Yought, ne mai sanyi da naman kaza gassassa acikin leda yazo dashi sai laccacera,gora, shima mai sanyi, Ruwan wanka nakai mashi kafin yafito daga wanka na dauko kullin kuka da madara na juye su a cup na zuba dan ruwa kadan na juya ban bari ya jika dayawa ba na,shaye da,sauri, Mama Rahana ce tace nai hakan kafin na kwanta yau din tace kuka da madara magani yake sosai a jikin mace kuma yana maganin Ulcer idan kana dashi sai angwada za,a gane amfanin shi yar uwa, Sallaman masu dawo da Sadiya ne mukaji again sunyi dai dai da ya fito daga bayin sun gaisa dashi suke bashi hakkuri anan inda yake tsaye yake cewa wallahi nayi rantsuea yau bata kwana a gidan nan don haka takoma sai ta kwana biyu a gida tukun, Daga haka ya shige daki yabar su a gurin suns kokarin bashi hakkuri, Ina jin matar nacewa ai kin faninidan zama gidan yana da dadi sai ki koma ki zauna aiga gidan nan gaki, Kin samu Allah ya baki gurin zama amma fitinar ki yaki bari ki zauna lafiya dakowa ke bakibar mijinki baki bar mutanen gida ba da wani zaiji yau gashi kin kai ga yadda kikeso in kin fara abu bakijin bari, Abinda yazo dashi na gabatar mai da shi a gaban shi tare da,abincin shi yadago kai yana ce min bazaki ci bane ke nake cewa na koshi,, Don may bazakici ba nace don ina gudun inci yazama min abin fitina da matar ka, Hammm kawai yace tare da dan furza iska daga bakin shi nace yau ace wullakancin Sadiya har yakai ta biyoni har daki da masifa wai don ka,sayo min abu, Tunda bata son gani na da kai ka,sakeni mana ku zauna da matar ka lafiya tunda nice dai ba,a kaunan gani agidan, Ke da bakinki Aisha kike cewa wai na,sake ki na fada maki babu zancen saki a tsakani dake har abada don ni wallahi baki min komai ba, Ban saurari bayanin shiba na fashe da kuka ina cewa Sau nawa kana,sayowa Sadiya abu agidan nan ina gani amma banyi magana ba sai ni da ta raina,zata zo hardakina don wullakanci, Amma dai ai kinga na,dauki mataki akan hakan ko don nasan idan na kyale ta yadda kullun ake cewa nayi hakkuri abin wata rana zafi hakan ne, Yanzu don Allah ace har da yarinyar da bata ko san tana duniya ba za,a yiwa kage don sheri, Ai ba ita taiwa bani taimawa don diya tace kuma,wallahi bazan kyaleta ta ba akan zancen nan sai mun zauna da iyayyen ta Da yaga ban saurare shi ba,sai kuka nake irin mai tsuma zuciya yana ta cin abincin shi hankali a kwance, Sai da yagama sai ya shiga rarashina yana cewa ban son ace a kanki ne mukai fada da sadiya a gidan nan har na saketa Aisha, Nafi son ace koma may zai faru ya faru a tsakanin ni da ita don wallahi Sadiya ta kai min ko ina a halin yanzu sai dai duk abinda Umma zatace tace amma ban iya zama da wanan yar cin mutunci, Amma may zai saki ce wai na,sakeki akan wata,Sadiya can ni in baki sani ba,wallahi yau ki sani nafi kowa farin ciki da irin yadda akika nuna wa Umma da sauran yan uwa na Sadiya bata a gaban ki, Kuma duk abinda take maki baki canza mu,amulan ki da kowa ba a gidan nan, Abokaina awaje wallahi kullun yabon ki sukeyi akan hakkurin ki, Akwai abinda yafi zafi da ciwo ace mahaifiyar ka bata damu da yar da aka haifa maba ta fari a gida, Kawai ki barni akwai abin da nake jira dan lokaci kadan zako gani, Na dago jajjayen idanuwa na kalle shi nace ni bance karabu da matar ka ba kawai dai kai warning din ta a zauna lafiya, Da haka har ya,shawo kaina ranan mukai mu,amula irin na miji da mata sai fama samin albarka yakeyi don yace wai gaba daya yaji duk na canza mashi,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEEENABUIDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON CIN AMANA NE HAKAN,,,, Tafiyan Sadiya gida ya sa gidan mu ya koma shiru don ba kaji yawan sautin kidan da takan kur a MP dakin ta ko waya, Ance mutum ko ya yake rahamace ta wani hanyan yau na fahinci hakan, Don tafiya ya sa gidan mu ya koma tsit lokaci lokaci nakan ji yan gidan na zagin ta suna Allah yasa kada ta,dawo, Har Umma takance wallahi dai badon dubaiyya ba da ba,abinda zai sa nabar wannan yarinyar ta dawo gidan nan wallahi, Amma a gana zakaji Umma tana fadin yaron nan yai kokarin zuwa ya dawo da matar shi dakin ta tun duniya basu zageni ba, Maimakon na daure fuskana yadda Umma take son gani sai nakan ce Sadiya ai tabawa kowa kewa a gidan nan don shi mutum rana gare shi, A da can baya takance min sai Hamza ya kara aure don bazata yarda dan ta ya zauna da mace daya ba kamar laya agida, Don ita tafi don taga gida ya cika da sarakai da kuma jikokin ta ta ko ina ta duba, Idan Umma tafara yin wanan kalaman hankalina yakan yi matukar tashine wani lokaci har nakan shige daki nayi kuka, Amma yanzu da na,zauna da kishiyar kuma masifaffa sai abin ya fice min akai nima na gane wasu abubuwa a cikin zaman duniya har ma da zama da Umma, Tsayin Sati biyu ke nan ana ta kaikawo a tsakanin gidan su Sadiya da gidan Umma cewa a yi hakkuri Sadiya ta dawo dakin ta, hakanan, Sun hana kowa sakat sai mutane suke turo wai aba Umma da Hamza din hakkuri, Hakan yana nuna cewa tayi taushi dayawa yanzu don taga abinda bata taba zato ba, Saboda bata taba tsanmanin zai iya rabuwa da ita ba kamar yadda kullun yake fadi, Sai gashi yau kusan Satin ta biyu ke nan, zaune a gida tare da mahaifiyan ta da kannen ta, Sai dai, har yanzu a ranta tasha alwashin cewa duk randa ta dawo gidan sai Aisha ta dan,dana kudan ta,, Don ba karamin shiri sukeyi ba can acewan su wai zuwan da nayi garin mu naje nai mugun abu na birkita kan Hamza baki daya, Yanzu baijin ko kallon kowa da gashi saini abinda naga dama naka aikatawa a gidan ba wanda ya isa ya hanani, duk nai asiri na shanye mutanen gidan gaba daya, Tun sunayi a can har takai sun idar da,sakon zancen a gurin Umma aiko kamar jira takeyi sai ko ta hau ta zauna wai asiri na bankadowa hamza a garin shine yasa bai zaman lafiya da Sadiya, Ya dawo daga kurmi inda yake kai sanaan shi, Umma ta tare shi da zancen cewa ya dawo da Sadiya hakana dakin shi, Sai yake cewa Umma ko Sadiya zata dawo dakin ta ba yanzu ba don yanzu wallahi kinga hankalina yafi kwantawa sosai, Don ko tafiya nayi banda wani farga ba akan komai hankalina akwance don nasan banu wani fitina a gida, Umma tace ai dama hakana zakace tunda ai maka agumo kasha ka taune ka hade, Bai fahinci may Umma take nufi da zancen ta ba sai yake cewa agumo kuma namay fa wayai min, Tace yar lelen ka mana da,baka son ai zancen ta agidan nan Aisha ni dama wanan yarinyar tun farko ban yarda da ita ba,wallahi don nasan cewa duk irin sherin uwayen ta sai tafisu iya, Dubi gidan malam mudi uwar ta, sai kaga kamar itace ake cuta nan kuwa itace ke cutan sauran, Umma ina kuma wanan zancen yafito haka abakin ki babu ko dadin ji Aisha ce kuma zatai min wani asiri can, Kai may kasani dama banda hauka ga abu afilin Allah ai ni ban damu da yarda ka ba tunda dama ba yardan zakayi ba, Ina dai maka gargadi da kakausar murya kayi mazaka dawo da,Sadiya dakin ta zaman gidan ya isa hakana, Idan kuma kaki wallahi za,ajimu a gidan nan da ksi don zan dauki mataki ta inda bakai tsanmani ba, Cikin mamaki Hamza yace yanzu Umma akan nadawo da Sadiya har kike min wanan kalamin, ? Sadiya fa dakika sani ce ba wata ba agidan nan tace eh ita din kuwa, An susuta ka duk kawani birkice wa mutane, a lokaci guda akan wanan mai fari kamar zabaya din, Wallahi Umma ina mamaki don ni har yanzu nakasa fahintar abinda Aisha take maki a gidan nan , Ai bazaka fahinta ba tunda ka makance a kanta sai kace wata yar gwal can, Umma nifa sani da Aisha a gidan nan ban taba gani kojin cewa tai maki wani abin assha ba, Mutane da yawa suna magana acikin abokaina cewa nai sa,ar mata don suna min korafin yadda matsaloli yake tasowa a tsakanin, gidajen su, Musan man irin rikicin da ake samu tsakanin matan su da iyayyen su a lokacin ni nakan yi mamakin yadda matarka zata ta wa mahaifiyar ka,rashin mutunci, Ashe nima hakan zai faru a kaina sai gashi shigowan Sadiya gidan nan duk abinda suke fadi akan iyalinsu nata yashanye nasu, Koma dai may ye kadawo da ita dakin ta don itama matarka ce tana da hakki a kan ka ta karashe maganar gami da cewa nadai fada maka ranka zai baci idan kaki abinda na fada ma, Maganan Umma bai sa shi dawo da,Sadiya ba a,wanan lokacin, sai da ta,kara kusan wasu sati biyun yai tafiya sau biyu a lokacin, ya dawo, ****** ********* ****** Ana gobe Sadiya zata dawo gidan ya ke ce gobe wanan zata dawo nake gani, Kamar ban san wa yake nufi ba sai nake cewa wake nan fa,? Yace Sadiya nake nufi nace Allah ya kai mu kawai a takaice, Sai dai ina son idan ta,dawo kada ki biye mata kuna fitina duk da dai nasan cewa yanzu tashiga hankalin ta ai dan zaman da tayi a gida, Sai kuma zancen gwagona ban son kina yawan wanan kunyan dakike yi a kan ta ya kamata ki saka ido akan ta ga kowa a gidan nan banda mama, Maganan da ya,daure min kai ke nan don ya tafi ya barni da mamaki da tunane akan zancen, Ke nan har Umma yake nufi na,sa ido akan ta kan jikanta jinin ta lalai akwai wani abu a kasa, Hmmm ikon Allah wai Umma da kanta take zuba,ruwa a randan ruwan Sadiya ta share mata kofa da kayan ta aka,wanke, Ni ko ajikina don duk da raina ya,baci amma ko a jiki ban nuna nawani damu ba don nasan muje zuwa mai hali baya barin halin sa, Ta dawo da wani ladabi da wani dan yin wanka da gaye ni dama wanan bawai sai ranan da nake da girki ba nake abina kullun dagani har diyata tsab zaka samay mu a gidan, Ba wani shiri har yanzu a tsakanin mu don kishiyace balle dani ta dawo a ranta sosai, In har ina da matsala a zamana gidan yanzu to tsakani na da Umma ce da ta sakani a gaba da fada kamar karamar yarinya, Kiri kiri take fitowa fili ta nuna bata so na ko kadan kuma Jidda tankar ba jikan ta ba, Sai yarinyar taita kuka Umma naji ko Sadiya babu mai karban min ita idan ina aiki ga Jidda da,yawan kuka, Umma kance wai yawan tsegumin uwarta ne duk tabiyo yarinya kamar gyare a guri kuwa, Sai in mama Hafsi tana gida ne nakan dan samu sauki a gurinta ta karban min ita nai aiyukana hankali kwance, Sunyi ta kokarin cusawa Hamza ra,ayi musgunawa a kaina amma sam bai taba dauka ba,, An dan samu saukin fitina yanzu saboda irin sharuddan da Hamza din ya kidanya mata kafin ya,yarda ta dawo gidan, Dole badon Allah ba ta sauya halin ta zuwa na zaman lumana da kowa har kusan wata,daya,ba wanda yaji muryan ta da kowa a gidan, Wata rana bayan ya,dawo daga tafiyan shi da kwana biyu nice da girki na idar nai mashi komai yadda na,saba ya shigo don cin abinci yake ce min A Aisha ya kamata na fara rage maki kudin ki tunda yanzu ina dan samun riba sosai a kai, Nace haba dai yaya idan ka bani su yanzu may zanyi dasu tunda ba,wani sana,a nake mai kwari ba duk rushewa kudin zasuyi, Kabarsu kawai a gurin ka kana juyawa zaifi na karbe su su lalace, a hannu ni ban sai komai ba kai baka more ba, Nikan ai Alhamdullahi na more masu sosai wallahi don dasu na samu nawa, nace to Allah ya kara masu albarka yace amin uwar gidan Hamza Dariya kalman ta bani wai uwargidan Hamza nace kalman taimin girma yar karama dani Yace to Allah ya baki ko zaki ki karbane yanzu wata ta karbe ke sai ki koma matar Hamza ko don dai kuma ban yarda ace amaryan Hamza, Abinda yasa mu dariya ke nan har akejin sautin muryan mu daga wajen tsakar gida, Wanan abu ashe ya batawa Sadiya da Ummu dake waje zaune saman tabarma daya rai suka daga ido suka kalli junan su, Umma tace ana can ana mashi karuwanci shiko sai kwasan dariya yakeyi yaga guri, Sadiya ta,wani yamutse fuska tana cewa ai wanan yarinyar Umma ta iya makirci kamar karuwa, Ni maganin su zanyi dukkan su don ban dukan shashanci a mayar min da yaro kamar rakumi da,akala, Sadiya,ta,cije leben ta cikin jin zafi da kunan rai don ita in akwai abinta taki jini aduniya,bayan mutuwan to Aisha ce, Daidai lokacin Hamza yafito dakina da murmushi a fuskan shi yana kokarin sa takalman shi dake kofan daki, Wani wawan harara gaba daya,suka bishi dashi alokacin nima nafito da kayan da yaci abinci don a dauraye, Cikin tsigar son fitina Sadiya tace aikin banza wai cusa kai inda ba,a kaunan ka, Ban bi ta nasu ba nabi bayan shi ina cewa, kada ka manta da zancen sayen permpers din Jidda fa yaya, Yace ai saboda shima zan fita yanzu don kada na manta ban sayo mata ba har dare yayi, Ina wuta su sakani a lokacin kafin nagama wanke wanke ina jin dan kuskus din su koda zan shiga daki har su bar gurin kowa ya shige dakin shi, Nace a raina Umma kan anyi girman atta wallahi da matar danki kuma kike gulman kishiya Allah ya kyauta, Washegari da safe ya shiga dakin don ya gayar da Umma,sai take cewa babana yanzu dai naga kamar gaba daya baka fafin kan ka a gurin Aisha sai abinda tace, Dan abinda zata,sayawa yarta don amfanin kanta shine sai kai za,a matsawa kasayo ita may ye amfanin sana,an nata datakeyi kullun a gidan nan, Cikin mamaki yadago kai ya kallo Uwar yace yanzu Umma kuma banibda halin da zan saiwa "ya ta abu sai najira uwarta ta saya mata, Ai na fahinci Aisha da "yarta kake wa nema duniyan nan don sune kawai a gaban ka bayan su baka damu da damuwar kowa ba, Hmmm Umma ke nan yanzu abin dari da hamsi dana,sayowa Jidda shine kuma abin magana, Hakkin waye sayan kanyan yarinyar banawa ba ko sai na barta Allah ya kamani da,alhakin su a kaina, Aisha abinta bai rufe mata ido ba idan ma ban sayo ba nasan zata sayewa kanta, Jekaita masu facali da kudin idan sun kare ai sai mu zauna mu zurawa kofa ido gaba,dayan mu, Subbahanallahi Umma mai yai zafi haka har da zancen karewan kudi akan abin naira dari da hamsi, Asalima fa kudin yariyar na na,gado na karba nake juyawa a hannuna ba,wanda yaji kuma kin sani amma baki magana ba a hakan sai don nai wa Gwagona lalura dashi don ta fito daga tsatsan Aisha zai zama abin magana, Kai kada ka,fada min maganan banza don kaga wuyanka yai kauri ya isa yanka wallahi yanzu zan bata maka rai a gidan nan, Allah ya huci zuciyar ki Umma amma gaskiya kuma bazan yarda hakkin yarinya ya hau kaina ba, Idan kudin zai zama na gori ne ai sai ka mayar mata da abinta bashi ke nan ba, Bai ce mata uffan ba sai dai ya mike cike da mamakin Umma a ranshi yafito ran shi bace daga dakin, Hamza idan kafita ka,sayo min sabulun wanki da omo don zanyi wanki ne, Ai ba ke ce ke sani saye ba idan na,tashi kuma ma yau kwana nawa da na,sayo maku sabulu ke ina naki suke, Ta amsa a yatsune da cewa nayi wanki dashi mana ya kare inji Sadiya dake tsaye daga kofan ta cikin murde fuska Dama halinta ne duk ranan da yake dakina fuskan ta babu annuri ko kadan kamar zatayi ihu, Yace wanan ba gaskiya bane don kafin nai tafiya na,sayo su agidan nan, Ai kaji irin ta yanzu ka sayo mata abu ka tsaya kana mata tambayoyi kamar tsohon dan sanda, Amma da,wanine yace ka,sayo mai jikin ka har rawa yakeyi gurin sauri kada rai ya baci, Daga inda nake ina jin su murmushi kawai nayi don nasan inda zancen su ya nufa, Nace Allah gani gare ka kai min tsari acikin wanan mutanen daka hadani zama dasu, Fita yayi batare da ya tsaya jin kalaman Umma ba don suna mashi zafi a rai sosai, Har zuwa yamma bai dawo gidan ba sai bayan la,asar lis yashigo da alama ma daga kauye yake gurin sana,anshi, Idan kagan shi bakacewa ma ya taba bako ko yasan biro don yai futu futu dashi already dama ruwan wankan shi yana saman murhu ina jiran yadawo yai wanka, Da,sallaman shi ya shigo a lokacin duk kowa yana waje har da Umma da mama da ta dawo daga gurin neman kudin ta, ta baza kayan da ta sayo tana daurayewa, na gwanjo duk ta sayo sai ta zabawa Jidda masu kyau tace na saka mata, Yana gaisawa da iyayyen nashi yake wasa da Jidda dake hannun mama,daga gefe daya, Hamza ina Sabulun da nace ka sayo man din tun da safe nake jira ka kawo min, Ban sayo ba yace mata a takaice, Oho don ni ba mowar ka bace yasa baka,sayo min ba da,watace da yanzu ka,sawo ko tun dazun, Ai kin gama zance tunda kince da, Kai amma Sadiya baki da dabi a daga dawowan mutum babu ko sannu sai kice wai ya,ina,sakon ki halan kin aike shine, Mama hafsi ke maganan nan cikin bacin rai don Allah ku dinga tausayawa mazajen ku mana ba a rayuwa haka gaskiya, Mama ki kyale ni don ba maganan ki bane wanan , Idan baka,sayo min kabani kudina sai na,saye ko, Ta tsiyan naki yau tashi ke nan dai Allah ya kyauta inji mama tamike tana kokari dauka yarinyar dage gefen ta, Na fito dauke da,jug din ruwa a hannuna ina mika mashi Sadiya taci gaba dacewa sai a dinga yiwa mutum banbanci ana gani baza ai magana ba, Haba ki bi sannu mana ai dole ya,sayo maki inji Umma take lalashinta, Ruwan ya karba yakafa kai yasha sai da yai rabin jug din yamiko min tare da cewa, Kai min ruwa na watsa kafin naci abinci duk a gajiye nake, Har lokacin Sadiya tana bakar magana ya shiga daki zuwa can yafito da kudi a hannun shi yace, Sadiya wai nawa ne kudin naki shin ? Ai kafi kowa sani tace tana kallon hannun shi dake rike da kudi karbi nan gasu, Ta karba tana kirgawa cikin cewa tafi nono fari yau Allah ya kwato min abina, Kuma wallahi idan baka sayo min ba ni ban yafe ba tunda ina da hakki a kan ka , Ya juyo a hasale yace baki yafe may ba hakkin may kike dashi akaina, A,a Sadiya tunda ya baki kudi ki kuma ina zancen baki yafe ba yafito ki daina ja mashi Allah ya isa haka mana, Mijiki ne fa kina ja mashi Allah ya isa haka kuma , Wanda yaji haushi ya rama mashi mana a,a ni din kuma kike nufi na rama mashi ko wa Sadiya, Umma in ma ke din ne ai dake nake tunda in ana magana dashi duk sai ku tare ni mafa ina da iyayyen nan ba shegiya nake ba, Yanzu don nace ki bari shine kike fa damin magana haka nidai yanzu banyi da kowan ku ba magana na ne dashi amma duk kun bi kun shige ciki zance, To ai sai ki tayi tundake in idon ki ya rufe kowa kina takawa ki hau, Ai in hakane kowa ma yana da, dan bana a dakin shi bani kadai bace balle a saka min baki, Ni wallahi ban yarda da wullakanci kowa ya,sa maka baki a hanaka magana kaman kowa ba haihuwan shi akayi ba, Har yafito daga wanka ta,zaune ta zubawa su Umma da mama kwankwami akai Umma duk nauyi da kunya ya rufe, ta, Yanzu dai din nai magana shine ya jawo wanan zancen haka ko tace to anyi dake ne kibar ni dashi muyi mana ai ban ce kowa ya,saka min baki ba, Ke Sadiya yace cikin wani irin murya yafito da rigar da yai niyar sawa a hannun shi, Idanuwar shi sun kada sun yi ja yace ki tafi gidan ku na,sake ki saki daya, Fetur ke nan tace ahayye Umma sai ki zuba ruwa kasa kisha tun da kin kai ga yadda kike so yau zan bar maki gida ga dan naki nan susu sauran mace mijin tace na bar maki sai a daura maki aure dashi dama kishiyar yar agwai kike, Innalillahi Sadiya kina da hankali kuwa kike furta wanan kalamin da bakin ki uwar nashi zai aura, Yace mama ki barta duk abinda tayi ai Umma ce tajawa kanta don ita tasaye, Wanan da ba mutum ba itace Umma ta rike wai mutum don kawai kiyayyan Aisha da take ji, Indon kankane ai da kowa Umma tana fada ba Aisha ba kawai don gashi yau takai ga yadda take so, May nagane dama ga,wanan auren tsiya na gidan ki ba ci ba sha ba sutura sai bakar masifan tsiya da,wahala, Garama da Allah ya kashe dan da nasamu da ku da na hada zuria da irin ku irin tsiya da masifa, Tallakawa karshe masu cin amanan mutane kawai wallahi ni ban dana sani da mutuwar wanan bakin auren wahalan, Macuciya tsohuwa kawai dama don ki cuce ni ki bata mani lokaci kikaje dadin baki wai na,auri danki don na kwato maki dan ki ga halaka , Ashe kece macuciyar ban sani ba,wallahi dake da ummana kuka cuce ni banda bakar kwazaba idan dare yayi babu abin da na karu dashi a gidan ku, Ke kuma Aisha gaki ga gidan in dai wanan gidan ne ina zaune zanji fitowan ki don wanan muguwa bazata barki ba ita da shegun diyan ta matsiyata yan banza kawai, Tajawo kofanta ta rufe tana tafiya tana cewa kada Allah ya,kara hadani daku ko a lahira wallahi macutan banza kawai matsiyata, Ke tafi karyan banza karyan wofi a kwasa akai ma,wani mugun abin kuma yau dai Hamza ya huta kuma, Hamza ne ke fadin haka cikin binta da mugun kallo Ba don komai ya kyaleta ba,sai don yai ma,su Baba alkawarin bai kara taba jikin ta,da sunan duka, Hamza ya juya gurin Umma yace tau Umma kin gani kin ga abinda kika kwaso wa kanki zagi da tonon asiri dai yau munji shi , Mazan dake kofan gida suna ganin tafito suka sa mata dari suna cewa ke nan baki barin mugun halinki Hamza ma yai kokarin zama dake bakar annoba ki zageshi ki zagi uwar shi, Ta juya gurin su tana cewa muna fukan banza muna fukan wofi ai da ku aka hada kai aka cuce ni ban yafe maku ba, Ta samu uwar ta da kuka karya da gaskiya ta kwasa ta fada mata tanaji ance har da,saki ya,shiga tace dawa Allah ya hada ta,bada Umma ba nan suka yo gidan syka,dinga tonon asiri tdakanin su da Umma duniya tana jin su,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,, Alhamdullahi don yanzu abubuwa duk sun daidaita a,gidan mu an yiwa gidan kwasarima sosai ya koma kamar na,zamani, Daga sana,an kai kaya company sai kums ya juya ga harkan noma ya raba hannun don dama shi ma,nomine baida da halin yi ne, A yanzu noma Hamza keyi sosai ba kama hannun yaro dayake Allah ya albarka ci al,amarin shin tun noman farko sai alamarin ya daga sosai, Yana noma masara dawa da,wake sai fadamun noman shimkafa da,su rake daya bude, Nan ya fara,samun yaran aiki masu bin shi su ma su samu daga cikin su har Yahaya dan gidan mama Atika,, Jidda,tana da, shekara daya na samu wani ciki a lokacin wanan cikin yazo min da,banbanci akan na Jidda din,, Don ni kaina ban san dashi ba sai dai ina yawan alolayi kwanakin nan ga yawan tashin zuciyan dake damu na,sosai duk abinda naci sai na amaye shi tas mama ce tace dana ci na,saka dan namijin goro guntu a bakina ko ainihin goro ko dan dabino, Ranan Hamza ya,dawo daga tafiya ya sayo kan sa yace a gyara da taimakon mama na,samu na kamala aikin naman, nai muna tuwon farar shimkafa, yai fari tas ga kamshin kayan yaji dake tashi daga cikin miyan, Kowa yasan idan Hamza yai tafiya yadawo ba karamin dadi muke ci ba a gidan hakan yasa kowa dawowa gida a ranan, Suna zaune kowa na kwasan gara agaban shi har shi uban aikin Hamza ya na gida tare da yan uwan shi ana hira, gwanin ban sha,awa, don Asmau zatayi aure badadewa ba, insha Allahu, Ina tsaye sai aiyuka na nake ta faman yi ni ban zauna cin abincin ba tare dasu, Gurin mama nazo ina cewa mama akwai sauran goron ne a wurin ki don ina son zan danci abinci, Mama tace Eh akwai shi Aisha ai bazan yarda yanzu in rabu dashi ba duk da ni ina kokarin na daina cin shi sai gashi kuma watan cin shi ya kama a gidan mu, Da sauri Umma ta dago kaina tana min kallon tantancewa don ta tabbatar da maganan mama, Sukuma sauran basu fahinci may mama take nufi da zancen ta sai cewa Jibrin yayi a,a mama watan cin goro yakama mu kuma aini ban son goro sam wallahi, Mamatace ai inkai baka son ci dan ka ko yar ka na so don in ba goron taci ba yanzu data sha ko ruwa ne zaka ga, sai ta amaye shi tas, Sai lokacin suka fahinci zancen mama sai sukayo min ido caaa akaina lokacin ina kokari bude ledan goron da mama ta miko min,. Ke madam kice min kin samu kujine har yafara gubda ruwa ban sani ba ni, inji Asmau take zolaya na, Yar sheri kawai nace kema kwana,nawane kin gunda naki mu ga nashi kalan, Hamza don jin dadi sai murmushi kawai yake daga inda yake zaune wani irin dadi ya kumay shi don shi sam bai kawo zazzabin daren da nakeyi wai ciki bane don cewa nake maleria ne ke damuna, Kai wasu matan dai akwai su da bakar jaraban tsiya ace ko yaye yaro baka yi sai ka dauki wani ciki ka halaka dan ka da hannun ka,, Take ran Hamza ya ba ci ya daure fuskan shi da da yake murmushi dashi don sam baiji dadin zancen Umma ba, To ai haraban yana gurin dana shi da ya kasa barin ta ta yaye ya lalabata ya dura mata wani cikin batai yaye ba, Ita Aisha maye nata aciki banda wahalan da take fama da ita ace ko ruwa kasha yana kasa, Inajin haka na juya zuwa kofana don nasan yanzu zancen su zai iya rikidewa don fadin gaskiya, Haba yaya wanan magana aibai dace aji shi a bakinki ba gaskiya abin farin ciki yasamu kuma zaki cewa yarinyar mutane jaraba ne da ita, Da can baya da bata samu cikin da wuru ba ai gaba kuka sata da zuguba a gidan nan bata da shakat taki hauhuwa, Yanzun kuma Allah ya kawo cikin da,wuri zakice wai tafaye jaraba dan adam dai ba,a iyashi wallahi mutum yakama girman shi mana wanan halin gaskiya ki sake fmdin yarinyar nan wallahi bata da makusa a gidan nan duk abinda akai mata komai dacin shi shaye shi takeyi ba acewa ga abokin fadan ta, Hamza da ranshi ya gama baci mikewa yayi bayan ya daurayen hannun shi daruwan wanke hannun dana tanadar masu, yabar gurin ranshi a bace fita yayi yabar gidan zuciyar shi tana mashi kuna, Umma tace taufa ai tunda na taba yar gwal din ku yanzu zanji zance iri iri Ba haka bane wallahi shi babba ya rike girman shi ga yaro don kada yaro ya raina shi, Ida waccan mara kunyar ce Sadiya aida yanzu ta baki amsa daidai dake balle kema bazaki ko fara ba, Da alama duk yaran basuji dadin maganan Umma ba sai shiru sukayi kowa yagama cin abincin shi ya bar gurin Sai mamace ta zo kofana bayan sungama take cewa kin ko iya cin abincin Aisha ? Nace wallahi mama na kasa cin sai dai dan kunu zan dama nasha tace a,a ina Hamza din yake yadan samo maki ko hura ne tunda dazun ma kunun naga kinsha da rana, Muryan shine daga bayan ta yake cewa mama tunda bataci kuma bata da lafiya su Sa,ade su dinga girkawa mana har ta ji sauki gada wahalan yai mata yawa kai aiki a,wahalce kuma ka kare baka lasaba,, Nace ai zan iya cine dai kawai ban iyayi kidai huta kwana biyu inji hamza har kiji sauki, Bari nafita na samo maki furan mai dan sanyi ko zaki iya sha, ****** ********* ****** Cikin dare ne yake ce min Aisha ban son ki saka zancen Umma a ranki don bake take muzantawa ba ni dan ta takewa, Don yau ko dabba na dauko na aje agida a matsayi mata dole ne taso ki don ni balle keda tasan kowa naki take maki haka, Yace yanzu ina dadin wanan maganan da tayi maki a baina kowa ina ko a banza muka samay shi bata halal ba ita mai rikewa ne, Murmushi nayi nace ai fada take min cewa kada mu cutawa Jidda bawai wani abu bane can, Hmmm kawai yace tare da fadin Allah dai ya kyauta wanan abubuwan nadaga cikin abinda yasa nake sin yi gina,mubar gidan nan duk dako muna da filin da,zan iya yin gina acikin gidan mu amma gara na matsa nisa da ita don samun saukin ki, Ban ce uffan ba don nasan bacin raine amma,ai uwa uwa ce duk abinda zatayi dole muyi hakkuri da halin ta don a rabu lafiya da ita, Kamar yadda ya,fada dole na bar wasu aiyukan gida don na,samu dan hutun kwana biyu, Ina zaune a dakina wanda yanzu an mayar min dashi ciki da falo, ina shayar da Jidda mama hafsi ta,shigo dakin ta samay ni, Ina ganin ta zauna nasan cewa tana da magana da ni ke nan don haka na mayar da hankali a gare ta, Mama take cewa Aisha ya kamata a cire wanan yarinyar a,nono hakana don kada ta sha ciki da yawa, dama na bari ne har dan kara sha,sai mu cireta,yanzun kuma nagama duk shirin da nakeyi akan cire ta din, Don kinga tun kwanaki yaya tana ta zancen a cire ta duk wullakancin da take maki akan kina,shayar da yarinya da ciki ina gani, Na dago idanuwa na,da,sukai ja sun dan tara ruwa don gap nake da hawaye su zubo min nace, Ni Umma may ye laifina akancikin nan tunda bani naba kaina ba da Umma take cewa wai samun guri yasani daukan ciki ban yaye yarinya ba don na cika gida da "ya"ya na, Yanzu in kuma na yaye yatinyar nan a lokacin wani abu ya,samayta cewa kuma zatayi da gangan nayi shi don na kashe mata jika, Mama tace bar zancen ai na fada mata cewa nice na ce abarta kada a yayye ta a lokacin, Yanzu dai bar zancen a hannu na zan samu ita yaya nai mata bayanin cewa za a cireta a nono kinga tafiyan da Hamza din zaiyi kafin yadawo tabar nonon , Nace a hankali tau mama, duk yadda kikace haka din za,ayi sai a fada min idan an tashi nacire ta, Mama tafita da ga dakin ta koma dakin ta nadan kallin yarinyar dake manne a,jikina tana zukar nonon ta nace a fili Jidda Allah yaraya ki yasa wanan nonon da kikasha mai amfanine a gare ki, Da daren ranan mama,tanajin shigowan shi tafito ta samay shi a dakin Umma suna gaisawa, dashi sai take cewa cikin kallon Umma Za,a cire Hauwa,u a nono ranan laraba in Allah ya kaimu, Umma tace ai na zaci baza,a yayye taba sai ranan da ta haihu tunda itace sarkin son diya tana son ta tai mata ciki da nonon ta a baki, Haba yaya yarinyar nan fa ta riga da tasha ciki ko to don may za,ai mata saurin yayye a lokacin batayi kwari ba ta tsuge da gudawa da lalururin iri irí Hamza dake zaune yana jin su yace tau mama yanzu da may damay za,a sayo mata na yayyen, Har da,wasu abubuwan can za,a sai wa yarinyar da bata ma damu da abinci ba,. Sai mama take cewa haka za,a barta ko yan kwalaben magani itin na bature ba,a sai mata da,yan sauran abubuwan amfanin ta kuma tunda ba nono take sha ba, Allah yasa a yayye lafiya inji Umma cikin dan kawar da kanta gefe daya, Hamza bai bi ta Umma yayi sayyaya masu yawa ya shigo dasu a ledoji yana fadin ga kayan yayyen gwagona nan Allah yasa a yayye lafiya Allah ya,sa mata albarka duk wanda ke gurin ya amsa da amin, Ranan Laraban kamar yadda mama tace tunda safe tai mata wanka ta goya ta suka fita gidan nabi su da kallo ina tausayawa yarinyar don sai naga maganan Umma gaskiyane mu mu kaiwa yarinyar laifi, Shiko gogan ko a jikin shi sai harkokin shi yakeyi kafin ya wuce tafiyan shi sai dai, ranan da ya wuce da dare da,safe aka cire ta a nono,, Nonuwa na sun hake sun ciko sun fara saka min zazzabi, don haka na shige dakina na kwanta don ji nake ba dadi a jikina, Mama bata gidan sun fita tun safe da Jidda sai na koma ni kadai don dan sabon da nayi da zama da Jidda, Ba,wanda ya damu da ya,duba lafiya sai Jibrin da yashi ina jin muryan shi nasan abinci yake ci har yagama bai ganni ba sai naji da zai fita yana cewa wai yau ina RAN GIDA take ne, Tana ciki kasan tayi yaye yau ba fita tana kewar yar ta, Cikin sauri naji yana ina Jidda din take ya nufo kofan dakina yana tambaya, Yana daga labule yake fadin ran gida ashe yau an wa Jidda laifi ne, na dago ina murmushi tare da cewa, kadawo na,katako ? Irin yadda yadda yaga yanayi yasa cewa bakijin dadi ne halan naganki wata iri haka dan murmushi na kakaro a fuskana cikin sanyin murya nace, Wallahi sanyi nake dan ji da zazzabi shine nadan kwanta ko zai bari, Subbahanallahi, kin sha magani kuwa? Nace zan dai sha yace Allah ya sauwaka ashe yau diya ta tasha yaye tana ina ne wai, Nace sun fita da mama tun safe basu dawo ba har yanzu nasan tana can tana mata rigima yau kam, Yace jiki kina tausayin ta kika cire min ita a nono ai gaskiya yau kin wa baby na laifi sosai, Yafita bai wani dade ba,sai gashi da leda ya sayo min maganunuwa masu yawa a ciki, Na karba nai ta zabbaga mashi godiya yace haba ran gida dole ne fa muyi maki don ke tamuce, Sai dai ni fa har yanzu ina binki bashin ki ce min yaya nace kaji ka dai nikuma wallahi ban yarda tunda ajin mu guda fa da kai, yace kin ji ki,,, Maganin da ya,sayo min na,sha sai naji dan saukin jikina zazzabin ya sake ni, Sai da yamma su mama su ka dawo yarinyar tana a bayan ta, tai barci kuma harda wanka akai mata, A,dakin mama ta kwana sai dai ranan ba suyi barci ba don har da Umma saida tafito daga dakin ta don kukan da takeyi, Duk kwanakin basu zama gida sai dai mama ta goya ta su fita zuwa sha,a nin su da haka har yarinyar ta dan saba tafita zancen nono, Kwanan shidda acan yadawo nima a lokacin nagama dan zazzabin yayena na dan koma normal ko, ****** ********* ****** Cikin yan watan nin da Hamza ya,fara sana,a tuni sunan Hamza ya fara shahara a gari da dan kewaye, Don Hamza ya iya sana,a sosai da kuma tausayi a kan harkokin shi musan man da yan kauyen da yake sayen kayan a gurin su, Daga wanan sana,an sai kuma yafara sana an sayar da kayan maganin amfanin gona na zamani dake sa shuka saurin fitowa da wurin, Ai fa anan kasuwa ta barko mashi balle yan kauyen da yake sana,a dasu don ko basu da kudi zai iya basu idan sun samu su biya shi, Tuni sunan shi ya fara fice a gurin kanan manoma masu karamin karfi dake bukatan taimako Hakan bai hana Hamz zama tare da abokan shi na kuryciya da,suke zaman majalissan su dasu In har tana a gari a tare dasu yake zama suna harkokin su kamar baya ayi raha,ayi zolaya,da,wasa da,dariya, a tare, Yanzu in akwai wani matsala a,tare dani bai wuce irin yadda yan mata da zawarori suke kawo wa Hamza hari ba har gida sukan biyu shi wani lokaci suce ace wani mutum yana mashi sallama sai yafita zaiga mace ce ke mashi sallama ashe, Tun ban sani ba har na fara daukan hannun don zanji yana waya a cikin wani yanayi hakan kan sa na fahinci da mace ne yake waya, Tun ina boye bacin raina har takai na fara nuna mashi a fili cewa nasan may yakeyi, Don daya fara irin wayan nan nakan ja tsaki na tashi nafita daga dakin, Gashi cikin jiki ya tsufa sosai don har yafito daga jikina, Sai dai duk kulawan da ya dace miji yaiwa matar shi ina samu dags gareshi wanan matsalar dai ta neman mata ne ke hada mu fada dashi Ko shi fadan ba,wai can ba nakance ni dai wallahi ina tsoron a kwaso min cuta ina zaman zamana a halakani, Sai dai yayi dariya yace kada Allah ya nufeni da aikata zina, a rayuwana don da ina yi da tun akan Lima zan fara zina, Namiji ai ba abin yarda bane tun da,ba,tare da kai nake yawo ba dariya yakan min yace ki yarda da,mijinki Aisha mijinki ba mazinaci bane, A cikin ikon Allah har cikina yakai watan haihuwan shi a lokacin komai da ya dace asays na haihuwa Hamza ya,saya min, ya aje yakan ce shi ba mazaunin gida bane don haka ya saya kada na haihu baya gida, Jidda tun da mama,ta,yaye ta a gurin ta take har yanzu bata dawo da ita gurina ba acewan mama,wai naji da cikin dake a jikina, Kamar wancan haihuwan wanan ma haka yazo min da sauki duk da na kira wata mai aiki asibiti ta dubani a tare da ita na haihu na,sambado katuwar jaririya,ta, Sai faman ihu take ta,tsalawa don sanar da,mutane cewa ta iso wanan duniyar tamu ta maliki,yumindeen, Mutanen gida suna jin kukan baby suka san cewa an haihu sai murna sukeyi da farin ciki, Sai da nurse din taga,min komai sannan ta bude kofan a lokacin duk kowa na tsaye cirko cirko sun matsu su ji cewa, may na haifa, Nurse tafito tana cire safan hannun ta tanacewa mama barka mama kin samu kishiya katuwa sai fari kamar yar turawa, Daga inda Umma take tace kuma dai Allah ya,sauwaka, Nan su mama,suka hau murna aka shiga aikin jego tare da aikawa mutane cewa na sauka lafiya, Kafin wani lokaci gida ya fara cika da yan uwa da abokan arziki suna zuwa taya mu murnan samun karuwa da akayi, Umma kan kamar ba haihuwa akai mata ba don fuskan ta a daure yake, Ibrahim ya buga ma Hamza waya yake fada mai an haihu ya kara samun baby girl cikin murnan shi da nuna jin dadin shi ga dan uwan shi, Shima hamza yai matukar murna da farinciki nan ya bugowa Umma waya yana fada mata barka, Yace Umma ashe an haihu bayana yanzu ibrahim ya bugo yake fada min Aisha ta sauka lafiya, Umma tace eh takara haiho abinda ta saba haihuwa maka mace kuma, Umma aikin samu takwara ance yariyar babba da ita kuma gata fara itama kamar gwagona, Cikin nuna gundura da zancen shi tace idan kazo ai zaka gan ta ko, Yai murmushi yace to Allah ya dawo dani lafiy ainan da kwana biyu ko uku zan dawo insha Allahu, Allah ya kawoka lafiya tace cikin matsuwa,su gama wayan dashi, Don wani irin haushin shi take jin an haifa mashi mace karo na biyu shine shi harda nuna farincikin shi haka tace sha,sha bai san ciwon kan shiba, Murna,sosai yakeyi sai bugawa mutanen shi waya yakeyi yana,sanar dasu cewa ya samu karuwa an haifa mashi baby girl, Kamar yadda yace kwana biyu haka din da kwana biyu sai gashi ya dawo daga tafiyan cikin murnan shi, Bayan sun gaisa da Umma yai mata barka da samun karuwan da akayi afili ya mikewa zuwa diban baby shi, Ya samay ni a zaune na zuba ruwan zafi a cup sai turiri yake ina son insha Nai mashi sannu dazuwa yayin da shikuma yake min barka da sauka lafiya tare da tambayana ban jin komai da zuwa yanzu a jikina ko, Yarinyar dake kwance saman gado ya dauka tare da dan kura mata ido har wani lokaci nan ya,fara mata adduoi irin yadda addini yace aiwa jaririn da yazo duniya yana cewa mamana Allah ya raya muna ke ta farkin addinin musilunci, Zara da tazo taga yadda Umma take muna take cewa haba dai Umma abinda kikeyi fa gaskiya,bai dace ba idan yar ki ce yaya zakiyi, Bafa Aisha ce kebawa kan ta,wanan haihuwan diya matan da takeyi ba Yanzu dai tunda banda dama na nuna damuwa sai ku sa ta haifi namiji ku gani, Ai da macen da,na mijin duk shiryuwan su yana a gurin Allah mu fatan mu Allah ya,sa masu albarka zarah ta bata amsa da hakan, Ranan suna yarinya taci sunan Umma Rabi, sai umma kecewa nibda,baku saka mata,suna,na ba da sunan hafsi kuka sa mata ai da yafi, Hamza yace sai na kara samun wata in saka,mata sunan mama ai nan gaba, Au ashe kai sakaraine ban sani ba yanzu har kana fatan akara haifo maka macen kuma ? Yace Umma aini dama ina son haihuwan diya mace a,rayuwana Ai ko ka samu don gashi nan ana,ta sambado maka su sai kashi ai maka,su dozin don wanan uwar diya mata din naga tana da niyar yin hakan ai, Murmushi yayi ka wai sai dai zancen yai matukarci mashi zuciya don bai san may Umma take nufi ba da wanan akidar nata, Ni dai kamar yadda kowa yace na share umma da akidar ta hakanne nayi na bar kula da abinda take muna, Hamza iya yakasa yake da yaran shi gasu gwanin ban sha,awa dasu kamar diyan larabawa don kyau, Harkokin shi sai ci gaba sukeyi don yanzu komai ya,kan kama arziki Allah ya,ba,ahi a lokacin kurciyan shi Wata rana suna irin wanan zaman majalissan sai ga wasu yan mata,sun shawo kwaliyan su da alaman wani wuri na muhinmin zasu, Ganin gungun matasa maza yasa su dan canza takon tafiyan su cikin sallo da yanga irin na matasan yan mata, zamani, Har sun dan gwauta su kadan yayin da idanuwan mazan yake a kan yan matan masu tafiya, A,a Habiba yai ko gaisuwa babune daya daga cikin abokan hiran su hamza yake cewa yan matan tajuyo cikin yauki da yanga tana cewa kai, Abdul wallahi na fada maka kabar kirana da habiban nan ko muyi tsiya, Dariya yasa yana cewa ai tunda kinci sunan tsohuwa ni dashi zan dinga kiran ka don ban san wani Biba can, Ashe tobashiyar Abdul ne yarinyar don haka,suke wanan wasan shi da ita idan sun hadu, Hamza ya kura mata ido yana nazarin abubuwa da dama akan yarinyar, Bayan tafiyan su Hamza kece wa Abdul wanan yarinyar fa yar wani gidane Abdul ya dan kalleshi da mamaki yace zi tobashiya tace nan yake fada mashi irin yadda alakar su yake da,yarinyar,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU[6/26, 11:06 PM] اختي خفصة: IDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,, Alhamdullahi don yanzu abubuwa duk sun daidaita a,gidan mu an yiwa gidan kwasarima sosai ya koma kamar na,zamani, Daga sana,an kai kaya company sai kums ya juya ga harkan noma ya raba hannun don dama shi ma,nomine baida da halin yi ne, A yanzu noma Hamza keyi sosai ba kama hannun yaro dayake Allah ya albarka ci al,amarin shin tun noman farko sai alamarin ya daga sosai, Yana noma masara dawa da,wake sai fadamun noman shimkafa da,su rake daya bude, Nan ya fara,samun yaran aiki masu bin shi su ma su samu daga cikin su har Yahaya dan gidan mama Atika,, Jidda,tana da, shekara daya na samu wani ciki a lokacin wanan cikin yazo min da,banbanci akan na Jidda din,, Don ni kaina ban san dashi ba sai dai ina yawan alolayi kwanakin nan ga yawan tashin zuciyan dake damu na,sosai duk abinda naci sai na amaye shi tas mama ce tace dana ci na,saka dan namijin goro guntu a bakina ko ainihin goro ko dan dabino, Ranan Hamza ya,dawo daga tafiya ya sayo kan sa yace a gyara da taimakon mama na,samu na kamala aikin naman, nai muna tuwon farar shimkafa, yai fari tas ga kamshin kayan yaji dake tashi daga cikin miyan, Kowa yasan idan Hamza yai tafiya yadawo ba karamin dadi muke ci ba a gidan hakan yasa kowa dawowa gida a ranan, Suna zaune kowa na kwasan gara agaban shi har shi uban aikin Hamza ya na gida tare da yan uwan shi ana hira, gwanin ban sha,awa, don Asmau zatayi aure badadewa ba, insha Allahu, Ina tsaye sai aiyuka na nake ta faman yi ni ban zauna cin abincin ba tare dasu, Gurin mama nazo ina cewa mama akwai sauran goron ne a wurin ki don ina son zan danci abinci, Mama tace Eh akwai shi Aisha ai bazan yarda yanzu in rabu dashi ba duk da ni ina kokarin na daina cin shi sai gashi kuma watan cin shi ya kama a gidan mu, Da sauri Umma ta dago kaina tana min kallon tantancewa don ta tabbatar da maganan mama, Sukuma sauran basu fahinci may mama take nufi da zancen ta sai cewa Jibrin yayi a,a mama watan cin goro yakama mu kuma aini ban son goro sam wallahi, Mamatace ai inkai baka son ci dan ka ko yar ka na so don in ba goron taci ba yanzu data sha ko ruwa ne zaka ga, sai ta amaye shi tas, Sai lokacin suka fahinci zancen mama sai sukayo min ido caaa akaina lokacin ina kokari bude ledan goron da mama ta miko min,. Ke madam kice min kin samu kujine har yafara gubda ruwa ban sani ba ni, inji Asmau take zolaya na, Yar sheri kawai nace kema kwana,nawane kin gunda naki mu ga nashi kalan, Hamza don jin dadi sai murmushi kawai yake daga inda yake zaune wani irin dadi ya kumay shi don shi sam bai kawo zazzabin daren da nakeyi wai ciki bane don cewa nake maleria ne ke damuna, Kai wasu matan dai akwai su da bakar jaraban tsiya ace ko yaye yaro baka yi sai ka dauki wani ciki ka halaka dan ka da hannun ka,, Take ran Hamza ya ba ci ya daure fuskan shi da da yake murmushi dashi don sam baiji dadin zancen Umma ba, To ai haraban yana gurin dana shi da ya kasa barin ta ta yaye ya lalabata ya dura mata wani cikin batai yaye ba, Ita Aisha maye nata aciki banda wahalan da take fama da ita ace ko ruwa kasha yana kasa, Inajin haka na juya zuwa kofana don nasan yanzu zancen su zai iya rikidewa don fadin gaskiya, Haba yaya wanan magana aibai dace aji shi a bakinki ba gaskiya abin farin ciki yasamu kuma zaki cewa yarinyar mutane jaraba ne da ita, Da can baya da bata samu cikin da wuru ba ai gaba kuka sata da zuguba a gidan nan bata da shakat taki hauhuwa, Yanzun kuma Allah ya kawo cikin da,wuri zakice wai tafaye jaraba dan adam dai ba,a iyashi wallahi mutum yakama girman shi mana wanan halin gaskiya ki sake fmdin yarinyar nan wallahi bata da makusa a gidan nan duk abinda akai mata komai dacin shi shaye shi takeyi ba acewa ga abokin fadan ta, Hamza da ranshi ya gama baci mikewa yayi bayan ya daurayen hannun shi daruwan wanke hannun dana tanadar masu, yabar gurin ranshi a bace fita yayi yabar gidan zuciyar shi tana mashi kuna, Umma tace taufa ai tunda na taba yar gwal din ku yanzu zanji zance iri iri Ba haka bane wallahi shi babba ya rike girman shi ga yaro don kada yaro ya raina shi, Ida waccan mara kunyar ce Sadiya aida yanzu ta baki amsa daidai dake balle kema bazaki ko fara ba, Da alama duk yaran basuji dadin maganan Umma ba sai shiru sukayi kowa yagama cin abincin shi ya bar gurin Sai mamace ta zo kofana bayan sungama take cewa kin ko iya cin abincin Aisha ? Nace wallahi mama na kasa cin sai dai dan kunu zan dama nasha tace a,a ina Hamza din yake yadan samo maki ko hura ne tunda dazun ma kunun naga kinsha da rana, Muryan shine daga bayan ta yake cewa mama tunda bataci kuma bata da lafiya su Sa,ade su dinga girkawa mana har ta ji sauki gada wahalan yai mata yawa kai aiki a,wahalce kuma ka kare baka lasaba,, Nace ai zan iya cine dai kawai ban iyayi kidai huta kwana biyu inji hamza har kiji sauki, Bari nafita na samo maki furan mai dan sanyi ko zaki iya sha, ****** ********* ****** Cikin dare ne yake ce min Aisha ban son ki saka zancen Umma a ranki don bake take muzantawa ba ni dan ta takewa, Don yau ko dabba na dauko na aje agida a matsayi mata dole ne taso ki don ni balle keda tasan kowa naki take maki haka, Yace yanzu ina dadin wanan maganan da tayi maki a baina kowa ina ko a banza muka samay shi bata halal ba ita mai rikewa ne, Murmushi nayi nace ai fada take min cewa kada mu cutawa Jidda bawai wani abu bane can, Hmmm kawai yace tare da fadin Allah dai ya kyauta wanan abubuwan nadaga cikin abinda yasa nake sin yi gina,mubar gidan nan duk dako muna da filin da,zan iya yin gina acikin gidan mu amma gara na matsa nisa da ita don samun saukin ki, Ban ce uffan ba don nasan bacin raine amma,ai uwa uwa ce duk abinda zatayi dole muyi hakkuri da halin ta don a rabu lafiya da ita, Kamar yadda ya,fada dole na bar wasu aiyukan gida don na,samu dan hutun kwana biyu, Ina zaune a dakina wanda yanzu an mayar min dashi ciki da falo, ina shayar da Jidda mama hafsi ta,shigo dakin ta samay ni, Ina ganin ta zauna nasan cewa tana da magana da ni ke nan don haka na mayar da hankali a gare ta, Mama take cewa Aisha ya kamata a cire wanan yarinyar a,nono hakana don kada ta sha ciki da yawa, dama na bari ne har dan kara sha,sai mu cireta,yanzun kuma nagama duk shirin da nakeyi akan cire ta din, Don kinga tun kwanaki yaya tana ta zancen a cire ta duk wullakancin da take maki akan kina,shayar da yarinya da ciki ina gani, Na dago idanuwa na,da,sukai ja sun dan tara ruwa don gap nake da hawaye su zubo min nace, Ni Umma may ye laifina akancikin nan tunda bani naba kaina ba da Umma take cewa wai samun guri yasani daukan ciki ban yaye yarinya ba don na cika gida da "ya"ya na, Yanzu in kuma na yaye yatinyar nan a lokacin wani abu ya,samayta cewa kuma zatayi da gangan nayi shi don na kashe mata jika, Mama tace bar zancen ai na fada mata cewa nice na ce abarta kada a yayye ta a lokacin, Yanzu dai bar zancen a hannu na zan samu ita yaya nai mata bayanin cewa za a cireta a nono kinga tafiyan da Hamza din zaiyi kafin yadawo tabar nonon , Nace a hankali tau mama, duk yadda kikace haka din za,ayi sai a fada min idan an tashi nacire ta, Mama tafita da ga dakin ta koma dakin ta nadan kallin yarinyar dake manne a,jikina tana zukar nonon ta nace a fili Jidda Allah yaraya ki yasa wanan nonon da kikasha mai amfanine a gare ki, Da daren ranan mama,tanajin shigowan shi tafito ta samay shi a dakin Umma suna gaisawa, dashi sai take cewa cikin kallon Umma Za,a cire Hauwa,u a nono ranan laraba in Allah ya kaimu, Umma tace ai na zaci baza,a yayye taba sai ranan da ta haihu tunda itace sarkin son diya tana son ta tai mata ciki da nonon ta a baki, Haba yaya yarinyar nan fa ta riga da tasha ciki ko to don may za,ai mata saurin yayye a lokacin batayi kwari ba ta tsuge da gudawa da lalururin iri irí Hamza dake zaune yana jin su yace tau mama yanzu da may damay za,a sayo mata na yayyen, Har da,wasu abubuwan can za,a sai wa yarinyar da bata ma damu da abinci ba,. Sai mama take cewa haka za,a barta ko yan kwalaben magani itin na bature ba,a sai mata da,yan sauran abubuwan amfanin ta kuma tunda ba nono take sha ba, Allah yasa a yayye lafiya inji Umma cikin dan kawar da kanta gefe daya, Hamza bai bi ta Umma yayi sayyaya masu yawa ya shigo dasu a ledoji yana fadin ga kayan yayyen gwagona nan Allah yasa a yayye lafiya Allah ya,sa mata albarka duk wanda ke gurin ya amsa da amin, Ranan Laraban kamar yadda mama tace tunda safe tai mata wanka ta goya ta suka fita gidan nabi su da kallo ina tausayawa yarinyar don sai naga maganan Umma gaskiyane mu mu kaiwa yarinyar laifi, Shiko gogan ko a jikin shi sai harkokin shi yakeyi kafin ya wuce tafiyan shi sai dai, ranan da ya wuce da dare da,safe aka cire ta a nono,, Nonuwa na sun hake sun ciko sun fara saka min zazzabi, don haka na shige dakina na kwanta don ji nake ba dadi a jikina, Mama bata gidan sun fita tun safe da Jidda sai na koma ni kadai don dan sabon da nayi da zama da Jidda, Ba,wanda ya damu da ya,duba lafiya sai Jibrin da yashi ina jin muryan shi nasan abinci yake ci har yagama bai ganni ba sai naji da zai fita yana cewa wai yau ina RAN GIDA take ne, Tana ciki kasan tayi yaye yau ba fita tana kewar yar ta, Cikin sauri naji yana ina Jidda din take ya nufo kofan dakina yana tambaya, Yana daga labule yake fadin ran gida ashe yau an wa Jidda laifi ne, na dago ina murmushi tare da cewa, kadawo na,katako ? Irin yadda yadda yaga yanayi yasa cewa bakijin dadi ne halan naganki wata iri haka dan murmushi na kakaro a fuskana cikin sanyin murya nace, Wallahi sanyi nake dan ji da zazzabi shine nadan kwanta ko zai bari, Subbahanallahi, kin sha magani kuwa? Nace zan dai sha yace Allah ya sauwaka ashe yau diya ta tasha yaye tana ina ne wai, Nace sun fita da mama tun safe basu dawo ba har yanzu nasan tana can tana mata rigima yau kam, Yace jiki kina tausayin ta kika cire min ita a nono ai gaskiya yau kin wa baby na laifi sosai, Yafita bai wani dade ba,sai gashi da leda ya sayo min maganunuwa masu yawa a ciki, Na karba nai ta zabbaga mashi godiya yace haba ran gida dole ne fa muyi maki don ke tamuce, Sai dai ni fa har yanzu ina binki bashin ki ce min yaya nace kaji ka dai nikuma wallahi ban yarda tunda ajin mu guda fa da kai, yace kin ji ki,,, Maganin da ya,sayo min na,sha sai naji dan saukin jikina zazzabin ya sake ni, Sai da yamma su mama su ka dawo yarinyar tana a bayan ta, tai barci kuma harda wanka akai mata, A,dakin mama ta kwana sai dai ranan ba suyi barci ba don har da Umma saida tafito daga dakin ta don kukan da takeyi, Duk kwanakin basu zama gida sai dai mama ta goya ta su fita zuwa sha,a nin su da haka har yarinyar ta dan saba tafita zancen nono, Kwanan shidda acan yadawo nima a lokacin nagama dan zazzabin yayena na dan koma normal ko, ****** ********* ****** Cikin yan watan nin da Hamza ya,fara sana,a tuni sunan Hamza ya fara shahara a gari da dan kewaye, Don Hamza ya iya sana,a sosai da kuma tausayi a kan harkokin shi musan man da yan kauyen da yake sayen kayan a gurin su, Daga wanan sana,an sai kuma yafara sana an sayar da kayan maganin amfanin gona na zamani dake sa shuka saurin fitowa da wurin, Ai fa anan kasuwa ta barko mashi balle yan kauyen da yake sana,a dasu don ko basu da kudi zai iya basu idan sun samu su biya shi, Tuni sunan shi ya fara fice a gurin kanan manoma masu karamin karfi dake bukatan taimako Hakan bai hana Hamz zama tare da abokan shi na kuryciya da,suke zaman majalissan su dasu In har tana a gari a tare dasu yake zama suna harkokin su kamar baya ayi raha,ayi zolaya,da,wasa da,dariya, a tare, Yanzu in akwai wani matsala a,tare dani bai wuce irin yadda yan mata da zawarori suke kawo wa Hamza hari ba har gida sukan biyu shi wani lokaci suce ace wani mutum yana mashi sallama sai yafita zaiga mace ce ke mashi sallama ashe, Tun ban sani ba har na fara daukan hannun don zanji yana waya a cikin wani yanayi hakan kan sa na fahinci da mace ne yake waya, Tun ina boye bacin raina har takai na fara nuna mashi a fili cewa nasan may yakeyi, Don daya fara irin wayan nan nakan ja tsaki na tashi nafita daga dakin, Gashi cikin jiki ya tsufa sosai don har yafito daga jikina, Sai dai duk kulawan da ya dace miji yaiwa matar shi ina samu dags gareshi wanan matsalar dai ta neman mata ne ke hada mu fada dashi Ko shi fadan ba,wai can ba nakance ni dai wallahi ina tsoron a kwaso min cuta ina zaman zamana a halakani, Sai dai yayi dariya yace kada Allah ya nufeni da aikata zina, a rayuwana don da ina yi da tun akan Lima zan fara zina, Namiji ai ba abin yarda bane tun da,ba,tare da kai nake yawo ba dariya yakan min yace ki yarda da,mijinki Aisha mijinki ba mazinaci bane, A cikin ikon Allah har cikina yakai watan haihuwan shi a lokacin komai da ya dace asays na haihuwa Hamza ya,saya min, ya aje yakan ce shi ba mazaunin gida bane don haka ya saya kada na haihu baya gida, Jidda tun da mama,ta,yaye ta a gurin ta take har yanzu bata dawo da ita gurina ba acewan mama,wai naji da cikin dake a jikina, Kamar wancan haihuwan wanan ma haka yazo min da sauki duk da na kira wata mai aiki asibiti ta dubani a tare da ita na haihu na,sambado katuwar jaririya,ta, Sai faman ihu take ta,tsalawa don sanar da,mutane cewa ta iso wanan duniyar tamu ta maliki,yumindeen, Mutanen gida suna jin kukan baby suka san cewa an haihu sai murna sukeyi da farin ciki, Sai da nurse din taga,min komai sannan ta bude kofan a lokacin duk kowa na tsaye cirko cirko sun matsu su ji cewa, may na haifa, Nurse tafito tana cire safan hannun ta tanacewa mama barka mama kin samu kishiya katuwa sai fari kamar yar turawa, Daga inda Umma take tace kuma dai Allah ya,sauwaka, Nan su mama,suka hau murna aka shiga aikin jego tare da aikawa mutane cewa na sauka lafiya, Kafin wani lokaci gida ya fara cika da yan uwa da abokan arziki suna zuwa taya mu murnan samun karuwa da akayi, Umma kan kamar ba haihuwa akai mata ba don fuskan ta a daure yake, Ibrahim ya buga ma Hamza waya yake fada mai an haihu ya kara samun baby girl cikin murnan shi da nuna jin dadin shi ga dan uwan shi, Shima hamza yai matukar murna da farinciki nan ya bugowa Umma waya yana fada mata barka, Yace Umma ashe an haihu bayana yanzu ibrahim ya bugo yake fada min Aisha ta sauka lafiya, Umma tace eh takara haiho abinda ta saba haihuwa maka mace kuma, Umma aikin samu takwara ance yariyar babba da ita kuma gata fara itama kamar gwagona, Cikin nuna gundura da zancen shi tace idan kazo ai zaka gan ta ko, Yai murmushi yace to Allah ya dawo dani lafiy ainan da kwana biyu ko uku zan dawo insha Allahu, Allah ya kawoka lafiya tace cikin matsuwa,su gama wayan dashi, Don wani irin haushin shi take jin an haifa mashi mace karo na biyu shine shi harda nuna farincikin shi haka tace sha,sha bai san ciwon kan shiba, Murna,sosai yakeyi sai bugawa mutanen shi waya yakeyi yana,sanar dasu cewa ya samu karuwa an haifa mashi baby girl, Kamar yadda yace kwana biyu haka din da kwana biyu sai gashi ya dawo daga tafiyan cikin murnan shi, Bayan sun gaisa da Umma yai mata barka da samun karuwan da akayi afili ya mikewa zuwa diban baby shi, Ya samay ni a zaune na zuba ruwan zafi a cup sai turiri yake ina son insha Nai mashi sannu dazuwa yayin da shikuma yake min barka da sauka lafiya tare da tambayana ban jin komai da zuwa yanzu a jikina ko, Yarinyar dake kwance saman gado ya dauka tare da dan kura mata ido har wani lokaci nan ya,fara mata adduoi irin yadda addini yace aiwa jaririn da yazo duniya yana cewa mamana Allah ya raya muna ke ta farkin addinin musilunci, Zara da tazo taga yadda Umma take muna take cewa haba dai Umma abinda kikeyi fa gaskiya,bai dace ba idan yar ki ce yaya zakiyi, Bafa Aisha ce kebawa kan ta,wanan haihuwan diya matan da takeyi ba Yanzu dai tunda banda dama na nuna damuwa sai ku sa ta haifi namiji ku gani, Ai da macen da,na mijin duk shiryuwan su yana a gurin Allah mu fatan mu Allah ya,sa masu albarka zarah ta bata amsa da hakan, Ranan suna yarinya taci sunan Umma Rabi, sai umma kecewa nibda,baku saka mata,suna,na ba da sunan hafsi kuka sa mata ai da yafi, Hamza yace sai na kara samun wata in saka,mata sunan mama ai nan gaba, Au ashe kai sakaraine ban sani ba yanzu har kana fatan akara haifo maka macen kuma ? Yace Umma aini dama ina son haihuwan diya mace a,rayuwana Ai ko ka samu don gashi nan ana,ta sambado maka su sai kashi ai maka,su dozin don wanan uwar diya mata din naga tana da niyar yin hakan ai, Murmushi yayi ka wai sai dai zancen yai matukarci mashi zuciya don bai san may Umma take nufi ba da wanan akidar nata, Ni dai kamar yadda kowa yace na share umma da akidar ta hakanne nayi na bar kula da abinda take muna, Hamza iya yakasa yake da yaran shi gasu gwanin ban sha,awa dasu kamar diyan larabawa don kyau, Harkokin shi sai ci gaba sukeyi don yanzu komai ya,kan kama arziki Allah ya,ba,ahi a lokacin kurciyan shi Wata rana suna irin wanan zaman majalissan sai ga wasu yan mata,sun shawo kwaliyan su da alaman wani wuri na muhinmin zasu, Ganin gungun matasa maza yasa su dan canza takon tafiyan su cikin sallo da yanga irin na matasan yan mata, zamani, Har sun dan gwauta su kadan yayin da idanuwan mazan yake a kan yan matan masu tafiya, A,a Habiba yai ko gaisuwa babune daya daga cikin abokan hiran su hamza yake cewa yan matan tajuyo cikin yauki da yanga tana cewa kai, Abdul wallahi na fada maka kabar kirana da habiban nan ko muyi tsiya, Dariya yasa yana cewa ai tunda kinci sunan tsohuwa ni dashi zan dinga kiran ka don ban san wani Biba can, Ashe tobashiyar Abdul ne yarinyar don haka,suke wanan wasan shi da ita idan sun hadu, Hamza ya kura mata ido yana nazarin abubuwa da dama akan yarinyar, Bayan tafiyan su Hamza kece wa Abdul wanan yarinyar fa yar wani gidane Abdul ya dan kalleshi da mamaki yace zi tobashiya tace nan yake fada mashi irin yadda alakar su yake da,yarinyar,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [6/28, 4:11 AM] اختي خفصة: IDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON YIN HAKA CIN AMANA NE,,,,, Tun daga wanan ranan alaka ta kullu a tsakanin shi da Biba, soyayya suke mai karfi a tsakanin su, irin ta saurayi da budurwa, Ranan da na fara tsintar maganan ba karamin tashin hankali mukayi da hamza amma si yake gwada min shi ba,wai zancen serious bane kawai dai lokaci ne Don shi, da wasa ya dauki zancen a gurin don haka in zan daina hauka na dai don shi bai ma da lokacin wanan, Ba wai na yarda da zancen shi bane kawai dai na hakkurane don kada wani yaji mu yace ina da matukar kishi, Amma abin yana ci min rai sosai don sai nakan ji su suna hira cikin nuna so da shaukin junan su, Da abin ya damay ni sai na samu anty hindatu da zancen don ta samo min mafita akan matsalar, Tambayoyi tafara yi min akan ko dai ina da matsalane a gurin kwanciya da Hamza, Kunya na kawar nace mata ban tsanmani ba gaskiya don duk yanayin da nake nakan daure da bukatar shi a kaina, Tace kuma duk kin tabbatar da,cewa kina bin duk wani sallo na kwanciya,ki tafiyar dashi don kin san fa,shi namiji yafi son ana juya shi a kan gado, Duk abinda zakiyi in ba kece mai shafar shi sai shi kadaine zakibarwa yana ainkin shi akwai matsala a hakan, Nake cewa,gaskiya ina da dan raganci a wanan fanin don wani lokaci shi kadai ke aiwatar sa kwanciyan mu, Kinga matsalar ki ta,farko ke nan Aisha indon kice daya bukace ki zaki yarda kawai ba tare da kin ba da taki gudun mawar ba ke ma,dole ki dinga samun matsala dashi gaskiya, Don haka ki tabbatar da duk lokacin da zaku kwanta kamar gasar gamsar da junan ku zakuyi bawai ki barshi ya kida yaraya ba shi kadai, don haka nasa wani namijin hangen nesa,duk kowani namiji yana da sha,awar mace tana shafar sa aduk lokacin da,suka kasance tare, Nace a hankali zan gyara hakan Anty tace da kin kyautawa kanki inkinyi hakan, Idan yai tafiya ko ya,shiga gari sau nawa kike kiran shi Aisha ? Nace gaskiya ban faye damuwa dana kirashi ba anty gara mashi yakan kirani kila safe da yamma kafin mu kwanta, Matsala Aisha matsala wallahi, Wa yafada maki mazan yanzu ana masu haka ai in fada maki idan bakira ba a yini tau sau biyar ke nan, Ke ko kazan gidan ku tai koto ce mashi, aikuwa yanzu kazan nan tai min abu kaza na gyara mata kaza, Wayan kiran namiji a waya yana da matukar amfani Aisha shakuwa, so, da kauna yana kara shigane ta haka a tsakanin ku, Ke baki da abin fadi ce mashi kawai yallabai ya rana ya kake, ko kaci abinci kuwa, don hakan zai sa ya san cewa kin damu dashi matuka, Idan yana gari kuma hakan ma ya kasance ki kuma dinga shiga kina fita kina kwalliyan ki, Idan yana gida a tare dake kina kokarin dan manna jikin shi a naki kina dan jan shi da hira koda akan harkan sana,an shi, Sanu sanu sai kiga kin zama abokiyar shawaran shi don ko wani abu zaiyi sai ya kira ki ya nemi shawaran ki, Nasan matsalar ki Aisha shine uwar mijin ki zakice kina jin kunyan idon mutanen gidan ku,. Wallahi ki gyagije ki zama abin, kallo a gurin su don farautawa mijinki rai don samun ci gaban rayuwan ki Hakama fanin girkin ki tunda yanzu kuna da,wadata atare da ku ki dage ki koyi girki masu ma,ana kikuma fahinci wani irin nau,in abinci yafi bukata namu na gargajiya ko na modern one, Gyaran gida dakin ki da kuma yaran ki harshi kanshi maigidan ki tabbatar kina kula da hakan, Nasan kina da biyayya ga iyayyen shi da uan uwan shi to sai ki kara ki gwada mai kin ma fishi kaunan su, Abinda bai so ki ki wanan aban kema har cikin ranki, Haka abinda yake so gwada mashi kinfishi son abin kema don yana so amma banda kishiya, fa sai muka dara duk ni da ita, Tace a in kin gwada kin son kishiya ai sai yakaro maki uku lokaci guda, Balle ma ba kishirya ce ba a so ba yanzu halinta don duk wace zata shigo da gurin take shigowa ko ta fitar dake ko ta nakasa ki dake da babu duk daya a gun miji, Shiyasa kikaga mata yanzu sun jajirce akan kishi don gudun komawa baya a,rayuwa, Hakan ma kawai idan kin gwada zamu iya fahintar wasu abubuwa daga gare shi don a haka zamu gane inda kike da,weakness a,gareshi, Don zaki matukar ganin canji a gareshi a lokaci guda zai sake maki gaba daya, Nan dai taita kawo min musalai irin yadda ya dace mace ta bullowa mijin ta gurin kama kafan shi da daure zuciyar shi baki daya, ****** ********* ****** Abu na farko dana,fara gwadawa shine bugun waya, nakirashi da,safe nai mashi ina kwana bayan mun gaisa sai dan shiru, Sai cewa yayi Humaira lafiya kuwa, Nace may kagani sai yace a,a kawai dai na tambayane ko da wani matsala, Ni kuma na fahinci mamakin kiran da nai mai ne yau muka gaisa bashi ya kirani ba kaman yadda muka saba, Bayan dan wani lokaci kuma sai na kara kiran shi yadauka nake ce mai yakuke can da fatan harkoki suna tafiya daidai, Daga inda nake a cikin waya nadan ji ya,sauke ajiyan zuciya yana cewa, Alhamdullahi Humaira gani nan ma nafito office din director, Zuwa rana bayan munci abinci nake kara bugawa nake ce mai yayana kako ci abinci don mu gamu har mun gama cin namu, A karshe nake cewa ga Jidda wai na gaishe ka yace bata wayan nai magana da ita, Duk da ba magana yarinyar ta iya ba sai na manna mata waya a kunnen ta nace ga Abba yace, sweetie na sai naga yarinyar tai murmushi don jin muryan mahaifin ta, Nan na ji wani irin tausayin kaina da yarinyar ashe na dade ina cutawa rayuwan mu ne ban sani ba, Sai da,dare nakirashi ina ce mai ya gajiya da zirga zirga yace wallahi fa Humaira kamar kin san yau nasha zirga zirga a garin nan don ganin komai ya kammala nake ce mai to a huta lafiya, Yace ina yaran nace ganin dai da Umma na ita ko Jidda tana gurin kakan ta, Yace kai mai raba Jidda da mama ai sai Allah don shakuwar su tai yawa wallahi, Nace cikin dan murmushi mamace ta sai hakan daga gare ta kasan yaro inda yaga fuska can yake,. Yanzu fa zan iyacewa duk neman kudin mama akan Jidda ne tun ina fada har nakawo ido nasa masu, Yace babu ruwan ki shiga tsakanin masoya kibar su suyi abin su don Jidda ta zama yar gidan mama ko nace gaskiya kan, Mun dan yi hira akan Mimi karama dake da,shegen wayo don tasan shi sosai ko nono take sha taji muryan shi sai ta sake dashi da Ibrahim, don shi Jibrin cewa yake wai Jidda ce yar shi, A karshe nake cewa yaya ka kula min da kan kafa kada ka dinga zama da yunwa, Wai madam yau may ke faruwa ne haka,? Nace may kagani yaya ? Yace tau a daibar zancen nace kewan ka da rashin ka a kusa damune yadan fara damuna, Yace taufa ni dan gatan Humaira da Umma ke nan don kune next to me, Munyi sallama acikin dan barkwanci dashi bayan na kashe wayan na nisa a hankali tare da lumshe idanuwa na na ce matsala ashe a gurina take, Allah Allah ka bani ikon gyara duk inda nake da matsala akan hakkin mijina dake kaina, Wallahi kafin ya dawo wani dan shakuwa ne ta musan man ya shiga tsakanin mu ta,waya, Ni kai na ko a haka nasan na samu canji ta musan man daga wani bangare ta rayuwan da nai sakaci dashi a baya amma insha Allahu da sannu zan gyara, komai na,rayuwana ta yadda zai iya jin ba wata sai ni a gaban shi dama kowa a duniyan nan, ****** ********* ****** Ranan da mukai waya yake ce min zai dawo next tomorrow ban zauna ba nai kitso na gyara dakina har wanki sai da nayi ban bar komai a fili ba,sai da na gyara har gidan mu, Na dan zana siffan lale a hannu na da yake na iya zanen dama ban dai son yiwa kowa ne yarana nai masu kitso su ma irin ta yara mai ribbos, Asmau wace dan kwana biyun nan muna da dan shakuwa ta musan man don har hiran saurayin ta dake dan kokarin ja baya da zancen auren su muke yi da ita ina dan bata shawaran da yadace don Umma nacewa wai ta rabu dashi don baida komai, Dama kuma saboda shi taki aure tuntuni don yana karatu ne ita kuma ta nace sai shi zata aura, Hiran shi da shawaran yadda zamu bullo mai da nake mata yasa ta kara manne min don ko yaushe muna dakina anan take cin abinci tayi komai, Sai Umma ke cewa wai bata san ko may mu ke kullawa ba adakin yanzu Asmau ta,wani nace min, Asmau kance mata Umma kin mata cewa dama Aisha kawata ce muna yara kece dai kika rabamu da ta auri yayana wai kada ta raina mu, Sai nace kin taba ganin mata ta raina mijin ta aiku mazana ne dolene na baku girman ku, Tabe baki Umma tayi tace koma may kuke kullawa ai in yai wari muji don mu yan kallo ne, Sai dai muyi dariya kawai muce Umma alheri muke kullawa mu, Shigan dare yai muna musalin sha,dayan dare suka,shigo duk a lokacin ina zaune ina jiran shi don nasan da zuwan shi banyi barci ba yadda na saba, Duk da dare ne ina cikin kwalliya na da makeup a fuskana sai kamshin dake tashi a jikina da dakina mimi tana kwance saman shifidar ta dana tanadar mata a gefe, Ina jin muryan shi ya shigo namike tare da dan gyarawa na fito waje har lokacin su Umma basuyi barci suna zaune suna kallon hausa film da yaran ta, Ban damu da suna gurin ba dana,fito nake ce mai sannu da zuwa yaya tare da dan rugumo shi kadan a jikina na karbi yar jakar dake hannun shi , Kallon juna sukayi kawai kowa da abinda yagani a idin shi Hamza ko sai faman murmushi yake yana cewa Ran gida baki barci ba ashe ke ma, Nace nasan kana hanya ina zanyi barci ban ga isowar ka ba lafiya, Ya tsaya gurinsu sun dan gaisa ya mike don zuwa daki Umma ta bishi da kallo tana cewa har zaka,shige ke nan yace wallahi Umma duk a gajiye nake tun sha daya nake hanya fa, Allah ya bamu alheri tace don nasan ka,shige kenan bazaka fito ba kuma yace gaskiya kan, Yana shigowa daki sai kokarin cire a gogon dake hannun shi yakeyi ta bayan shi na zagayo na dan rugumay shi a hankali tare da sauke ajiyan zuciya a hankali, Nace sannu da zuwa yaya ka tafi kabar mu da kewan ka sai tunanen ka kawai muke yi, Murmushi yayi tare da dan zagoyo ni muna fuskantar juna yake cewa nima ai kun barni can da kewan ku don ban ko gama abinda nakeyi ba nadawo donku, A hankali nace mai ruwan wanka yana a bayi don yanzu da ya gyara muna daki har da bayi akai muna a cikin dakin , Mun huta da wanka ana kirga cewa munyi wanka kazs munyi da,asuba kuma muna yi da rana wani lokaci har da rana inji Umma wai na faye barnan ruwa da yawa, Wani lokaci kuma takance wai mace ke nan kullun bata da,aiki sai wanka buta kamar agwagwa, Yana fitowa nace mai abinci fa yace yana goge ruwa akan shi, Wallahi Humaira ban iya cin abinci yanzu duk a gajiye nake abinci zai min nauyi mun kuma ci a binci a Jaba, Nace cikin marairai cewa aiba mai nauyi na girka ma ba don nasan baka son cin abu mai nauyi da,dare sosai, Ba laifi don ya dan sha perppe soup din kifin da nai mai da yawa ina daga gefen shi zaune ina dan zuba mai ruwa tare da dan jan shi da hira a hankali, Ya, gama na zuba mai ruwa da sabulu ya,wanke hannun shi na kwashi kayan na nufi dashi dakin Umma ko akwai wanda zaici kada ya lalace idan ya kwana, Yana waya ko da na iso dana dan saurara sai naji da wani abokin kasuwan ci shine yake fada mai cewa ya iso lafiya yake tambayan ko an kawo motan maganin shukan da ya bayar a shigo dashi zuwa wani kauye, Kara dan kimtsawa nayi tare da haye saman gadon mu bayan naiwa mimi addu,a, Har ya karaso bakin gadon da waya a hannun shi yana yi inda ya dan zauna a bakin gado, Juyowa nayi don jin shi a kusa dani inda cikin dakiyar zuciya na,dan kai hannu a saman bayan shi nadan fara shafawa a hankali, Ajiyan zuciya naji ya sauke tare da,sallama da mutumin da yake wayan dashi yana cewa sai dai da safe indan mun hadu sai mu karasa maganan, Yana aje wayan yadan juyo gareni tare da sauke ajiyan zuciya yana cewa Hummaira duk kin canz min fa gaba daya, Kafin nai magana kira ya,shigo a,wayan shi kallon wayan yayi yaga mai kiran shi sai naji yadan ja tsaki ya dauki wayan ya kashe gaba daya yana cewa ban son yawan damuwa please, Nan na fara mashi sabon sallon da nazo mashi dashi a ranan duk ya susuce min ya koma min kamar wani karamin yaro sai yadda na yi dashi a ranan, Bayan komai ya dan lafa a tsakanin mu na manne a jikin shi ina cewa yyallabai kafa kwaso gajiya ne nagani, Ya kamata ka huta haka don ka samu dan natsuwa kafin safe don nasan ko goben ma ba hutawa zakayi ba, Yace ban tsanmani gobe zan iya zuwa ko ina don ina son hutawa sai a gida nima cikin iyalina koda sau daya ne a,sati, Washe gari tun da,safe duk da akwai gajiya a jikina ban kwanta ba sai da nafito nai abin karyawa kamar yadda na saba yi a kullun, Nagama nai wanka na tsala kwalliya na cikin wasu English dress da aka sayo min a,sokoto ta gurin hindatu, Ina fesa turare naga yadan juya daga gurin da yake kwance hakan yasani gane cewa ya farka ke nan karasawa nayi bakin gadon ina cewa yayana, A tashi aci abinci ko kada yunwa ya illanta min kai ina gani, Jawoni yayi zuwa jikin shi ni kuma na biye mai tare da haye ruwan cikin shi ina cewa ka tashi kai wanka ka,karya kaje ku gaisa da mutanen gida, Yace ai ban gama gaisawa da iyalina ba ma kafin naje gaida na cikin gida, Nan wani sabon wasa ya fara a,tsakanin mu sai kace kanan yara mun dauki lokaci a hankan cikin wani yanayi na farantawa junan mu rai san,nan yadan sarara min, Ina daga gefen shi a kwance yake cewa bayan ya,sauke numfashi da karfi yace wai Humaira may ke faruwa ne haka please, Kaman ya yaya ? Yace gaba daya naga kin canza min a cikin lokaci guda halin da ban san ki dashi ba sune nake gani a gare ki, Nace ba abin da ke faruwa canjin yanayi ne kawai yanzu kaunan ka ta girama ta kai lokacin ta shine kawai, Yace eyyeh kalai naga alaman haka ashe sai na shirya ke nan don yanzu yarinya ta girma nace lalai kam don kana da,aiki ja a gaban ka, Sauka nayi daga gadon na shiga ban daki ban futo ba,sai da na tsabtace kaina nafito ina cewa ga ruwan wanka can na hada ma kaima, Sai na samu yana waya yana fadin a lokacin da nake hutawa da iyalina ya dace a bugo min waya, Ko sau nawa za a kirani inda i a tare da iyalina bazan dauki waya ba gaskiya don haka a bari kawai, Shan jinin jikina nayi don na fahinci da mace ce yake wayan don haka na wuce gurin mirror ina gyara jikina, Yana kashe wayan ya juyo inda nake a zaune yana cewa azo a taimaka min na tashi tunda duk kin kashe min jiki, Kafin nai magana dama duk a kule nake sai muryan Mama naji a falo tana fadin Aisha yar ki fa nono take so kila don ta ki yarda tun dazu kuma taki yin barci, Don haka na mike zuwa falon don na karbi yarinyar hannun mama kafin na koma ciki har ya,shige bayin don yin wanka, Sai da ya karya yafita zuwa gurin su Umma don su gaisa dasu tun bai zauna ba Umma ke cewa halan yau baka fitane har kakai war haka baka fito ba, Cikin dan yamutse fuska tana kaiwa zaune yake cewa wallahi yau banjin cewa zan fita don hutu nake bukatar yi a gida, Nan ya fara gaishe ta kafin ta furta wani zancen suka shiga hiran yadda al,amari ke tafiya ga,kasuwan cin shi, Ya dan dauki lokaci a gurin ta din har ya bada sakon asayo mai kashin rago da dan naman ragon ai pepper soup din shi da rana a gida, Nai aikina na gaji na koma daki na samay shi zaune a falo yana kallo ga kuma waya a hannun shi yanayi cikin jin dadin yanayi, Nan na zauna gap dashi muna hira nai dan filo da kafadan shi ina kallon TV dake aiki, Sai wasa yake da hannun mimi dake shan nono a jikina tana washe baki irin na yara , A kai, mashi sallama yafita bai shigo ba yana waje da,wani abokin tafiyan shi suna magana, Koda ya shigo nake gabatar mai da abinci don baici ba har zuwa lokacin yake ce min nazo mu zauna muci tare nace mashi dadai yaci don ni nashs furan gora gurin Jibrin, Yace ke da ke shayarwa mai fura zai maki Humaira kawai ki zo ki zauna munci a binci kafin Ummana ta tsotse ki, Nace cikin murmushi wallahi ko bai mata wuya indai mimi ce don tsotso gare ta har na,sayarwa, Munci abincin sosai don ni kaina naji dadin cin da nayi don cikina ya dauka sosai, Umma ranan sai mamaki takeyi don fmganin sauyin danta gashi a cikin gida amma bai fito gurin ta ba kamar yadda ya saba yi in yana gida yana dakin ta suna hira har da,dariyan ta, Niko a lokacin ina daki zaune ina hadiyan zuciya yadda Umma ke bukatan gani na, Amma yanzu ni da kaina sai nake jina wata wasai dani ban tare da wani kunci a raina don yana tare dasu, A haka nake ta takona ina cusa kaina agurin mijina kullun kurciyana yana da da baiyyana a fili, kwaliya na nakeyi ina gyara ko ina na jiki na don kada aga damana, A daidai wanan lokacin ni kaina nasan ban taba samun dama ko freedom din na mallakan mijina ba tun auren mu sai yanzu, Hamza wanda yai tafiya zuwa sokoto don karbo takardun shi da yai karatu amfanin shi sun taso gare shi, Kwaliyan dogon riga nayi tare da dan daura gyalen kayan a kaina na daure gashi na dasu, idan har na tsaya cesa nayi kyau ma bata lokaci ne, Kallona Hamza keyi yana karawa watakila jin yake kamar ya rungumay ni a gaban kowa, ta lashe tun kan lokacin yin hakan yayi muna, Takardun na karba na,shiga daki dasu har na kai kofa cinkin dan ga mutse fuska yake cewa tsaya na dauki wani file a ciki ya tako zuwa dakin mu yabar su Umma a gurin, Ji nayi ya matsoni a jikin shi abinda yasani murmushi ke nan ya kalleni yana cewa Humaira gaskiya wanan shigar taki a cikin gidan nan ya fara sani wani yanayin ki shi kin san fa bani kadai bane namiji a gidan nan, Yana fadi yana dan kara matse ni a jikin shi tare da dan sun sunan wuyana a hankali, Na daga ina cewa haba dai yaya su ina ruwansu dani tunda ba mallakin su nake ba, Kara jawoni a jikin shi yayi yana matsewa da karfi yana cewa, Kina kuwa kallon yadda kika koma kuwa madubi murmushi nayi nace wanda dai nayi don shi in ya kalla zai fada min, ai Kuma in dai kai ka gamsu dashi ai shike nan don badon wani nayi ba don ka kawai nayi, Na gamsu ma ai shi yasa har yau naji kishin yan uwana ya kamani gashi yanzu kurciyar ki sai dada fitowa yake a fili kin koma kamar wata yar sha bakwai fa, Nayi dariya tare da kokarin cire jikina daga rikon da yai min don na,aje takardun dake hannun na ina cewa, Kai yaya yanzu fa ashirin da biyu nake cif, yace Uhmmm humaira wallahi kamar yar sha bakawai yanayin ki yake nunawa a fili, Nace yayin dana duka ai kaima yaya yanzu duk kurciyar ka ya fito ka koma kaman wani mazaunin abuja can don dai kawai ansan cewa a nan kake da zama da babu wanda zai ce ba,a birnin taraiya kake zaune ba, ga wani mutunci da kwar jini da kakeyi wa kowa a fuska, Shiyasa yan mata suke ta faman kawo maka harin don suma,suzo su kwashi nasu garan,sai dai kuma kwalelensu wallahi, Hamza ya kyalkyace da dariya tare da kamoni yana cewa ai kin tare kofa yanzu kan babu guri din duk wace ta kawo kanta gulma tazo, A kusan tare muka fito daga dakin muna dariya Umma tana ganin fitowan mu cikin raha ta,wani bata ran ta a lokaci guda kamar an mata mutuwa, Ni dai nasan ganin da Umma tai muna muna,dariya ne yasata bata ran ta, Gashi yabzh idan yana gida baida lokacin zama a gurin ta kamar yadda yakeyi da can baya, Ganin yanayin fusksn ta a lokaci guda yasa shi dan zuwa gurin ta yana cewa Umma lafiya dai ko cikin son jin may yasamay ta Ta dan girgiza kanta tana cewa ba abin da ya samah kawai dai daurowa ne, Umma idan da,wani abune da ke sakaki damuea ki fada min kawai a san abin yi, Cikin bata rai Umma tavmce niko keda abinda ke damuna Hamza Yanzun ace kana da halinks kana da budi amma zaka zauna haka da mata guda kamar laya sai yadda tayi damu a cikin gida gaba dayan mu ni daku, Kasake nayi ina,wa Umma kallon mamaki tare da sauraren zancen ta tana cewa ni dai a rayuwa nafi bukatar na gan ka da mata biyu a gidan nan don kara samun kwanciyar hankalin ka, da natsuwa, A cikin zuciya ta nake cewa sai dai kuwa ki mutu mama don Hamza mijin humairane kawai, Umma ai komai dan lokaci nd idan anyi hakkuri lokacin hakan yana tafe I, Ka sake nayi ina sauraren su shi da mahaifiyar shi duk jikina,sai ya mutu saboda bacin ran da nake ji a lokacin, Kalaman da Hamza ya mayarwa Umma su wajen bata amsa sun tsaya min a rai sosai Don a,wasu lokuta yakan bata amsa dacewa mama har kin manta da,abinda Sadiya tai maki a gidan nan, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON YIN HAKA CIN AMANA NE,,,,, Ginan gidan Hamza keyi nagani na fada a cikin garin Jega, inda nan surutun jama,an gari ya fara na irin yadda ake zargin duk wani sabon matashi mai kudi, Har dan yan kan kai wasu sunce ma Hamza din duk sun san cewa ya na sana,a neman kudi irin ta zamani kala kala, cikin gari da kewan yan garin har kasan kurmi da kasashen ketare mafi kusa, yana business yanzu duk da karancin shekarun shi, Yan kasu yan uwan shi suka shiga bata mashi suna suna cewa wai karamin yaro da bai gaji arziki ba a ina ya samu kudi irin haka masu yawa, Sai dai ance ba duk aka taru aka zama daya a duniya don mafi yawan mutane sun san irin sana,ar shi yana saurin kawo kudi a duniya in har kana da jari a hannun ka, Ni a bangare na na fitar da zancen wata Biba can don naga basu waya da ita hakan yasa nasan cewa basu tare yanzu duk a kwai yan matan dake kawo mashi hari da zawarori agari har ma da,wani gari, Hankalina yanzu a kwance yake ga,yarana sai girma,suke abin su kuma Uban su da yan uwanshi su na marukar son yaran, Umma ce kawai nake da matsala da ita wanan kuma nasan rashin gamon jini ne tsakani da ita don banga abinda nake mata ba wanda tai hatting dina haka da yawa, Don iyanzu nasan duk abinda zan mata bani fari a gurin ta sai taga laifi na, Don haka ni ban damu da irin kiyayyan da take nuna min ba kan zamana da danta a gidan, Don nasan cewa nakafa sayena a cikin zuciyar shi da gidan ta don duk diyan ta na saye zuciyar su gurin ktautatawan rayuwa, Da taimakon Allah da nawa gashi yanzu har an saka ranan auren Asmau da saurayin ta Abdul, Sai faman shirye shiryen buki mukeyi a gidan inda duk wani shawaran ta bai wuce ni da yar uwarta zarah, Mama hafsi kuma har gobe tana matukar nuna min kaina don ko itace ta haife ni ko Hamza abin ya tsaya a nan, Irin yadda na dage a gurin auren Asmau akan dan uwanta yai mata duk abinda ya dace uba yaiwa yarshi idan zatayi aure yakara sa man farin jini a gidan don ba wani ya fada min banice da kaina naji suna zancen, a daki basu ma san zan ji su ba, Umma take cewa wai ina dafa kifi daruwan shi su basu gane ba szi Zarah take cewa haba Umma bafa wai kanta takewa amfani da abinda take karba Asmau ce fa ake wa sayyan nan, In ba don ita ba kuna ganin cewa yaya zai tsaya ya kashe wanan kudin haka wa Asmau ne kin san halin shi fa gurin makon kudi bai son ace mai akawo akawo ko bani bani, Asma dake makeup daga gefen su take cewa wallahi Anty zarah watarana har fada yakan mata taita kuka akan zance kuma sai tayi hakkuri bata yarda yasan ta yi kuka ko kadan kin san halin yayya da fada dan abu kadan zatayi kaji ya hauta da fada, Ina jin su sai na juya zuwa dakina dama zan shiga gurin su ne sai da aka dan dauki lokaci na fito na shiga dakin nasu, Gurin su sai gaba dayan su sukai shiru suka canza zancen da sukeyi Umma har dace min wai ina mai sunan ta nace tayi barci ita ce, ma tasani kwantawa, Mun gaisa da Zarah a cijin raha take ce min uwar buki yanzu nashigo nake tambayan ki akace min kin kwanta ai, Nake ce mata dama ita nake jiran ta shigo muyi zancen zuwa gurin jeren da za,ayi, Sai take ce min abinda ya kawo ta ke nan don ta kira shi angon yace mata an gama aikin dakin nasu, Nan muka tsayar da ranan da zamu tafi gyara dakin Asmau take cewa na fadawa wanda ya dace ita zata tafi can family house din su tafada masu don kada suce ba,a fada masu ba nace ai dole mu tafi da,wasun su don shine daidai, Wai Aisha kin san ashe mama Sa,a ce ta tafi har gidan su Abdul da,zancen Asmau na banz shine suka so su walwale auren da farko , Murmushi nayi nake cewa ai mun sani, shiyasa muma muka biyo mata tabaya muka gyara zancen yanzu ai ta dai ji kunya mutum idan bai hada aure to kada yayi kokarin bata shi don aure kamar rayuwa yake, Yanzu ba zasu kara ganin ta da mutunci ba ai tun da ba dattijuwar arziki bane, Shiyasa nake son yaya ya kashewa Asmau kunya,wallahi duk mai bakin ciki yaji kunya da haushi, Umma tace cikkin jin dadin zance bari kedai Aisha wallahi naji dadin yadda yaron nan yai wa Asmau kayan mutunci, Nace Umma idan bai ma dan uwanshi haka ba maye amfanin samun mutum ya na dashi bai fitar da dan uwan shi a kunya ba , Shiyasa ma nai ta lurar dashi akan ya taimakawa Abudul ya samu ya karasa ginan shi don asamu ayi bukin a lokacin da aka tsayar don duk abin da zai farautawa yan uwan shi rai shine yanzu ya kamata yayi tunda Allah ya bashi, Shiru Umma tayi don duk wanan zancen bata san dashi ba sai yanzu take jin shi a bakina, Sai da ya dawo take tuntuban shi a kan zancen cikin basarwa yake ce mata eh hakane ai Abdull din ya,zama dan gida a vurin mu don yaron yayi kokari wallahi, Allah ya kyauta kawai Umma tace tare da nisaw tana tunanen gidan da Asmau zata shiga gashi ba,shiri a tsakanin ta da yan uwan shi tun ba,a shiga ba, ****** ********* ****** Sha,anin bukin mu muketayi wanda hakan bai hanani kula da, al,amarin mijina na ina ta faman kafa kafa dashi kamar yadda na saba, Zancen abin da,aka jerawa Asmau yakai ko ina acikin uguwar mu sai yabawa mutane keyi ana ma Hamza adduan fatan alheri wanda Umma take jin dadin haka a ran ta, Wasu yan mata suka shigo sukace a kaisu gurin Umma sunzo harda ledan su dake dauke da cooler a ciki, Sun gaisa da Umma su ke cewa sun zo ne Hamza ya fada masu zancen buki shine suka zo gaida Umma, Nan Umma ta shiga washe baki tana jin dadi da,farin cikin sarakuwar ta tazo, Ina dakina da yan gidan mu da,wasu daga cikin yan uwan su Hamza Umma ta aika akirani, Nashigo dakin cikin kwaliyana na wani rantsatsen lace da na,fara sawa a ranan nayi matukar kyau a cikin shigar sai kamshi nakeyi , Tun shigowa dakin wata tobashiyan su Hamza ta tare ni da ba,a irin na tobasai ke wanan shigar haka zaki bari wanan matsalon mijin naki ya kara aure, Nace may zai hana anty duk wacce zata shigo ta,shigo mana ai ga kofa a bude, Aisha dai ce mutu karaba da shi takalmin kaza, Ai nasani inji matar don duk kin bi kin kalalamay min kani kin hana shi hangen wata kina mashi wanan kwalliyan haka ina zai iya daga ido ya kalli wata, kon koma kamar karamar yarinya dake kullun baki tsufa, Nace bai dai tashi ba anty idan ya tashi ai ko bashiri sai kuzo buki muci yar gwate mu watse, Umma ta,tare zancen mu da cewa kawo wa bakin mijin ki abinci gasu nan, Sai a lokacin na juya inda,suke na san dasu a cikin dakin nai masu wani kallo na son sanin ko su waye su kuma, Ban san su ba don haka gaisawa kawai mukayi najuta zuwa kawo masu abincin, Komai na,aje a gaban su yadda ya,dace na juya nabar dakin sai dai a cikin raina ina tunanen ko su suwaye da suka zo mai buki, Ina shiga dakina na samu Kubura tashigo da yarta wani irin kallo tai min wanda sai da na tsargu don banji dadin kallon ba har cikin raina, Amma sai na,washe ina cewa Anty nayi fushi sai yanzu kika shigo har ana batun watsewa, Tace yanzu nagama abinda nakeyi kuma maigidan bai dawo da guri ba balle ya bani umurnin fitowa, Na kawo mata abinci da kayan shaye shaye na girke a gaban ta sai wani yatsune fuska take tana bina da,satan kallo, Wa wanan ranan nasan na samu canji rayuwa a auren gidan Hamza yadda mutane sai faman bina da kallo sukeyi, Ina ga,su Anty Kubura basu san da ina daga cikin kuryan dakina ba sai naji suna gulmana, Anty Luba ce tafara magana tana fadin ikon Allah ni tun dazun sai mamaki nakeyi wai yar Agwai ce ta samu wanan irin daulan haka ? Ji dan Allah yadda gaba daya ta canza ta koma kamar matar wani minister can tai kyau har da kiban ta, Ba dole ba inji Anty hasiya yar Kubura ta,samu Hamza ya rike mata kan maciji tana wasa da bindi, Ko Uwar ta baki ta canza ba tai kiba ga kuncen kayan da,diyar ke kai mata sai shiga take tana cirewa, Kubura tace aikin banza tunda ba sabo take iya bata ba may tayi ke nan, Yanzu fa da kece nan haka Kubura rabon wanan yarinyar ya kaiki guri wanan dan iskan mijin ki da,baisan mutuncin mutane ba, Kubura tace ai duk wanan uwar tashi ce mai shegen tsegumi tasa mama jin haushin ta raba abin amma nima daga baya ai yadda naga Hamza din yana da kokari da kwazo gashi gaba daya ya canza kamar wani hamshaki Sai nake dana sani dama ahi na aura na huta da wanan auren ukubar ta gidan wanan mara mutucin da nakeyi, In banda wahala da bacin rai mai wanan bakin auren ya tsinana min a,rayuwana, Kawai dai mutum na zama ne dan kar ace ya gaza ko wani abu ni wallahi da tuni nafito daga gidan shi, Yanzu du bi zanin da mutum ya,daura wai yazo buki dashi kamar wata yar aikin gida, Kedai kiyi hakkuri ki zauna dakin ki kowa ma hakkurin yakeyi dama abinda ka raina watarana sai ya baka tsoro shiyasa tun farko ban so ki ki auren hamda ba shi baba yasan abin d,yahango kikaga ya nace a lokacin, Ai kin ga,wanan mai shegen wayau ta bayar da yar ta har muna mata dariya a lokaci ashe mu takewa kallon, wawaye bamu sani ba, Yanzu ga hakkurin su ya haifa masu alheri a rayuwan su don Allah kadai yasan abinda,suke samu a gurin shi, Shigowar wata mata tana nema na yasa su tuhumar ko ina daga ciki ina ji abinda su ke fadi sai da,matar ta,daga labulen dakina take cewa aiko bata ciki, To ina ta shiga ne muna son karban kudi ne a gurin ta da za,a sayo labulen da za,a,sawa dayan dakin Umma tace muzo gurin ta , Daga ciki nai magana zakace fitowa na kenan daga bayi na saka wani dogon rigan shadda mai ruwa maron, Ina kokarin daurin dan kwali gaba daya sun sha jinin jikin su don gani ina daga cikin dakin kila naji su ga kuma wanan rantsatsen shadda da na,saka a jikina sai maiko da,sheki yakeyi yana daukwn ido, Nake cewa wai na dan shiga,ban daki ne na kewaya sai na tsaya na saka kaya a ciki, Sai lokacin suka sauke ajiyan zuciya don sun san banji su ba ke nan tunda ina can bandaki daga ciki, Na juya gurin su ina cewa dan Allah anty kuyi hakkuri na dan kewaya,ne, Ina fitowa tsakar gida idanuwa caaaa a,kaina kowa da abinda yake nasawa a zuciyar shi, Wasu na fadin na samu guri wasu kuma,sai cewa sukr na tare ko ina sai abinda nace wasu kuma suna fadin hakkurina ne yakai ni ga,samun riba, haka , Mutum baka da gadon shi amma,shi yana da gadon maganan ka don bai gani bai nasa ba, a kan ka , Fitana dakin yasa yan gidan mu samu daman ci gaba da zancen su suna mai cigaba da gulmana ni da mijina da uwarshi, da,ta hana rayuwana,shakat, Ina shiga dakin Umma,na,samu wa yan nan yan matan suna shirin fita,daga dakin Umma sai faman godiya,take zabga masu godiya take ta faman yi,, Gani tafe kai tsaye dakin fuska na,sai sheki yaki yi yasa suka, dan kauce min don ba,alamar zan kauce masu, Nake cewa Umma ance wai na bada kudin da,za,a sayo wasu labulaiyya Umma suna jin murya sai suka dan kara tsuke fuskan su, Suna fita daga gidan dayan tace tirka shi ashe akwai aiki a gaban ki ja Biba wanan matar ta Hamza ban taba zaton haka take ba wallahi, Hmm bari kedai Amina wallahi narasa gano wani abin makusa a jikin yar iskan yarinyar nan, Ashe ma karamar yarinya ce haka sharaf wanan ai kin,gimay mata nisa ba kusa ba, Ashe shiyasa yake min wani gani gani yasan abinda ya aje a gidan shi amma dai komai tsiyar ta sai na shiga gidan nan wallahi ko, Zaki ko sha kallo don wanan yarinyar da nake gani akwai shegen wayo gare ta, ba karami ba jifa tun bata masan ko mu suwaye ba irin maganan da takeyi, Ni ko sai nake gani kamar ta gane komu su waye don kin da zamu fita ko kallo bamu ishe ta ba fa, Wanan dole na,sake shiri a kan ta don akwai aiki gaskiya sosai saboda naga kamar ta dan waye, Mu dai yi bincike a kan ta don mu san ko wacece ita , Wai wanan ce ake cewa matar hadi ce ba wai soyayya sukayi da ita ba ya aure ta, Haka dai suna tafiya suna zance a kaina dakuma gidan namu har suka kai gida suke shedawa Uwar su cewa sun ga matar hamza a gidan da suka tafi, Nikan ranan na jigarartu sosai don mun sha fama da jama,a anyi taro lafiya an kuma watse lafiya, Sai dare Hamza ya samu ya shigo gidan don jama,a sun watse sai yan garin su Umma da suka zo mata buki ne a gidan, Tun shigowan shi gidan yake kokarin kallon fuskana sai dai ya kasa fahin ta na , Ban tsaya ta kan shi ba kamar yadda na saba na gama kimtsawa na haye gado abina tare da yar diyata wace tayi wayo ko sosai yanzu, Jin motsin shi danayi a,bayana yasani kara lafewa saman gadon wai make faru dake ne yau nagan ki haka Rangida ? Ran gida ai suna can maka a waje nikan ai yar gadin gida ce ko ince yar aikin gida, Kuma dai duk may yakawo wanan zancen kuma haka yau, Nace matan banzan ka da ka turo buki don ai min dariya mana, Katuro sune dama don su zo su ganin ko kuwa ni fa ban hanaka sha,aninka ba yaya amma cin fuska ne ban so, Su tsaya a matsayin su kada su shiga gonata bazata iya bari idan ka kwaso ta tazo ba, don bata da kunya shine za su muna har gida wai sunzo ma buki, Kuma don a,wullakantani kamar yadda kake son nuna masu shine Umma zatace wai sai ni zanyi services din su, Murmushi naji yayi yace akan zuwan su Biba ne kike wanan cika kina batsewa Humaira, Yaushe kika fara kishi hakane wai ban sani ba nace kasan ni, ba mace bace ko ince ba mutum nake ba, Tau idan kin yarda wallahi ni ban ma,san da zuwan su ba asali ma har sai da sukazo suka koma ne tai min text cewa tazo taga beautiful wife dina da yara na, Nace dama ai shi ya kawo ta kuma tagani tunda wanan ne kawai daman da take dashi na shigowa gidan nan, Ni yanzu wanan zance bai gaba don haka ki sawa ranki sanyi don ni wata Biba can bata a gabana, Daga haka ya mike ya,zagaya ta bayan mu ya kwanta ban bita kanshi don tukaki nake ji a cikin raina a lokacim ina ga ya fahinci hakane ya kyale ni, ****** ********* ****** Ina zaune a falona bayan bukin Asmau da kamar wata daya, Hamza dake fitowa daga kuryan daki a cikin shirin shi nafita, Na,dago idona kalle shi nake cewa yaya dama yau iba son zuwa gidan Antu Hindatu ne na,dubo su, A take ya tsuke fuskan shi yana cewa wai l loop yawan yi zuwa gidan Hindatune, kullun fitan ki ke zuwa gurin hindatu ne, Nace kullun har da,yaushe yaya rabon da nafita fa tun bukin Asmau da akayi a gidan nan, Ko wanan ma ai dalili ne zai kaini don nai mata ban gajiyan zuwa muna bukin da tayi Ni dai ban son kina masu zariya a gida har aga kamar wani abu kike yawan zuwa yi, Nace in ba dalili ba yaya may zai kaini ni gidan wa nake zuwa,a garin nan banda gidan mu sai ko nata, Fusace yace min baki zuwa nace Aisha don ban son yawan fitan nan ni gaskiya, yafita a hasale ya barni nan cikin mamakin shi, Ban daga a gurin ba,sai na fara tuhumar ko dsi da wani abune a kasa yasa ya hanani zuwa gurin ta, Jin ya tayar da motar shi ya tafi baya gidan yasa na dauko wayana na kira Hindatun, Mun gaisa da ita take ce min kwana biyu haka shiru Aisha ba ko waya, Nace wallahi yanzun haka dashirin zuwa gidan ki a jikina amma kuma mai gidan ya hana ni fita ko ina wai ni ke nan kullun zuwa gurin ki, Murmushi naji tayi tana cewa kyaleshi Aisha tsoron kada kizo guri na ki samu labarin shi shine ya hana,shi barin ki kizo, Ashe bai isa ba tunda yana jin tsoron a fada maki abinda yake yi a gari,, Wani irin damm naji kirji yaba da nace ke nan a kwai wata akasa ko anty tace kyaleshi ai nai mashi tas ranan da yazo gidan nan, Anty may ke faruwa ne wai don ni wallahi har hankalina ya tashi sosai wallahi, Tace ke ba wani zance bane zancen yar iskan nan ne da ta lake mashi da kaman sun rabu dashi amma yanzu sai gashi sun dawo sun kara dinkewa kuma har ranan nagashi da ita a mota, Kin san bani bada bashine nadaga waya na kirashi shine yake ce min zai zo gida gurina ya samay ni, Nashiga Ukku anty badai Biban nan ba tace wallahi ita kuwa Aisha Ni banga abinda Hamza yagani ga wanan mace mai tsowa kamar hannun lema ba Magana antu keyi amma ni hankali baya,a,gare ta,ina can ina tunanen cewa wacce nagani baka,doguwa daga cikin su itace ke nan Biba din, Sai ji nayi tana cewa kai kibar namiji kawai Aisha sai kiga sun kwaso abinda ko kwatan na gida bai kama ba, Wanda ke da mace kamar ki a gidan shine wai ya tafi kallon wata Biba can maikama da siffan samudawan dauri, Anty ni na,rasa may wanan mutimin yake tayiwa aure haka don banga abinda na,ragashi dashi ta fannin rayuwa, Amma kuma yake fita waje yana hangen wasu da ba,su kai ko kwatana,ba, Tace ai garama ya,auro maki waccd bata kaiki ba din yafi ace tafiki da,wani abu, ke namiji sai kiga kamar idon shi a,rufe yake neman wata,macen, Ni dai yanzu nasan cewa bawai kina,gazawa da bukatan shi bane kawai dai shi mutum ne mai ra,ayin wanan auren, Wanda idan kin duba,mu diyan hausawa dama mun gaji irin wanan rayuwan tun kakan ni da iyayye, Da,wuya kiga dan bahaushe ya tabbata,da mace daya a,rayuwan sai kin samay su da irin aure auren nan wanda zance maki a jinin mu hausawa abin yake, Don kin ga da,ace ana gadon abin ne da Hamza bai yi ta,wanan halin aure auren ba da kurciyar shi don ance mahaifin shi bai taba auren wata ba bayan Umma, Don haka don Allah dai kiyi hakkuri ki barshi da halin shi yaje yai ta,aure auren shi tunda ke bai rage ki da komai ba na rayuwa, Ba dai komai akewa kishi ba sai jijiyar namiji ko tau ai ajikin shi yake ba,a jikin ki ba shi ya sani da bakin auren don shi zai fadi ai ance jiki magayi, Halin mutum mai kosar dashi, shi da,ya jajibo shi ne zai gasu kina zaune zaki ji shi da ita in har kinyi hakkuri, Ko murai kada ki wahalan tayar da hankalin ki a,banza don ba bari zaiyi ba idan yai niyya, Ke da ki kula da kanki da tarbiyan diyan ki, sa mashi ido kawai don ko shiru magana ne Aisha, A sanyayye nace naji Anty nagode insha Allahu yadda kikace hakan zan yi don baki tabani shawaran da bai min dadi ba a rayuna, Munyi sallama da ita tana ta kwantar min da hankali ina ce mata babu komai insha Allahu, ****** ********* ****** Kamar ban san komai ba haka na daure na dake da zancen a cikin zuciya na sai dan lalaba kaina nakeyi kada na kasa, Ya gama ginan gidan sbi komai ya,saka acikin gidan sai kace wani palace , Sai da wata matsala da,takunno kai a kan zancen komawa gidan shine, Umma tace sai ta koma tare da mu amma kuma shi Hamza din ya ce gaskiya ba zai so takoma can ba abar masu gida ba kowa sai su Ibrahim kawai ta daiyi hakkuri ta zauna dasu idan sunyi aure sai ta,dawo gurin shi din, Da kyat aka samu su liman dasu Baba suka shawo kanta harta yarda amma da sharadin idan taso zata dinga zuwa ta kwana biyu a gurin mú ta dawo, nama dai badon yaso ba yarda,da hakan, Don haka ranan laraba da zamu tare a,gidan tare da ita muka koma sai da tai mu Sati biyu tadawo gida badon ranta yaso ba, Ko shi Ibrahim ne yazo ya,sata gaba sai da ya dauke ta suka tafi tare da shi, Aka barni ni da yarana sai a gidan sai mai gadi don a lokacin shi yana gurin tafiya da kyat Umma tabar mu Sa,ade ta taya ni kwana kafin ya dawo tunda,ban saba da gidan ba, Ranan da ya dawo da dare ya,mayar da,Sa,ade gida akabarmu daga mu sai yan yaran mu biyu a gidan, Bayan ya,dawo daga gurin kai Sa,ade ne ina zaune a falon yaran sun gaji da,wasa,sunyi barci a gefe na ya,shigo gidan cikin shigar kanan kaya, Na kalle shi cikin girmamawa nai mashi sannu da zuwa ledan da ya,shigo dashi nai kokarin tashi na karba sai dai akwai mimi a jikina don haka yske cewa zauna abinki na hutar dake, kada ki tayar min da uwa kin san yazu tana,fara rigiman nan nata ta hana mu shakat, Shi kan shi ya shiga har kitchen ya dauko plate ya ciro kaza guda daga cikin ledan yazo har gabana inda nake zaune ya zauna a kasa gap da kafafuna na yake ce min bisimillah, Naso na,dawo yaran nan basuyi barci ba don su samu suma suci shi da zafin shi amma sai wani ya tsayar dani can, A raina nace wani ko wata kai dai kasani in kaya ne kaji dashi can, Daga inda nake zaune yake dan miko min nama ina ci muna hira, nan yake fada min cewa yana son bana su sauke farali da Umma insha Allahu, Nai matukar farin ciki dajin zancen shi inda yake ce ni kuma badi in Allah ya,kaimu sai na tafi na sauke, nima ban lokacin da na kaiwa kanshi dake daidai cinyata runguma,ba ina matukar farin ciki da jin zancen, Yace min sai dai ina son kija bakinki kiyi shiru kada ki fadawa wa ko sai in har tafiyan ya,tabbata kawai za,aji dan dama ina da pasphot din Umma dashi nake son nai mata amfani na tafiyan, Zaman mu a,sabon gida zan iya cewa wani irin zama ne da muks dade muna mafalkin shi a,ran mu don so ne da kauna tsan tsan ta muke shimfidawa a gidan, Wanan karon nai yaye babu ciki a tare dani don haka ban samu wani tsegumi ba,a gurin Umma don tace ina son na cika maigida da "ya"ya mata ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU,IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE YAR UWA,,, HAMZA ne zaune a falo yana rike da waya a hannun shi magana yake akan wasu kayan da za,a shigo mashi da,su daga kwatano, Nafito daga daki acikin shigar dagon riga ta matan Niger style din rigar yai matukar kabar jikina, tunda na shigo falon gaba daya ya mayar da hankalin shi a kaina, Ya zuba min idanuwan shi sai kace mara gaskiya ya motsa bakin shi don yakirani sai kuma ga waya a kunnen shi da hannun yai min alamar danazo inda yake, Kitchen zan shiga sai na juya zuwa gurin shi alama yai min da na zauna a gefen shi, Ina zama ya dauki hannun shi guda ya rike min hannuwana yana dan murwa a hankali yana wayan shi , Shiru nayi daga gefen shi ina sauraren wayan da yake yi da abokin sana,ar shi, Sai da ya gama wayan yadan sauke numfashi shi ya juyo gareni yana cewa Rangida, ashe aikin nan bai maki yawa ba ke kadai ga gyaran gida ga, luran yara ga kuma girki duk ke kadai, Nace sai kace ba yar Umma nake ba wace tai aikin mutum kusan bakwai a gida daya har tsawon wasu shekaru sai wanan na mu kadai ne zai min yawa, Ya ce Nop ciki daga hannun shi da juya kan shi ina bukatar ki huta yanzu tun da Allah ya hutar damu, Don haka ki samo wata da zata tai maka maki da wanan aiki ko tsohowa ko kuma yarinya, Murmushi nayi tare da dan kwantan da kaina a kafadar shi nace kaidaine kake ganin shi aiki amma ni aguri na wanan ai ba aiki bane, Yace na sani amma ina son ki samo wacce zata taimaka maki da ko da gyaran gida ne ke sai a barki da dawainiya na dana yara, Nace harda girkin ma ni ce zanyi abina da kaina don ban son wata tai maka girki bani ba, Yace cikin lushe idanuwan shi tare da dan sunsunan wuyana nima nafi da son hakan ai amma so nake ki huta ki kula min da wanan jikin naki da kullun yake koma mawa kamar ta under age, Murmushi nayi ina under age inda Jidda da Mimi suka fito yace kece ke ganin haka ni kullun kamar bakece kika haife suba nake gani, Mikewa naso yi don zuwa duba girki da na dora a gas sai yariko min hannu yana cewa ina kuma zaki muna magana nace na,dira abinci a wuta don ka,samu kaci kafin kafita don nasan in kafita sai dare, Ya lumshe idanuwan shi yana cewa kuma gaskiya kika fada don ko nafita din ba wani abu nake ci ba sai fura da dan snacks, A hankali nayi wata yar sanyanyar ajiyar zuciya nace nasan haka wallahi don nakan ga yadda kake cin abinci idan kadawo shiyasa ma yanzu nake kokarin tashi da wuri na girka maka,, Bayan ya kammala cin abincin shi ne ya mike tare da dan shafan gaban rigan shi yana,fadin kin dai kusa sani katon tubi Humaira wanan irin abinci da kike tula min a gaba, Ai nan da yan kwanaki nakara kiba ba kadan ba don dadin dakike bani, Nace cikin murmushi kiba,ai ga,dan Africa kamar ruwa,ne don sai guda,gudane basu kiba idan sun kai age din yin kiba yanzu aikai da,sauran ka sosai, Yace lokacin da mukai aure ana cewa dani dake duk mun yi kanana sosai yanzu gashi har mun kai ga,diya,biyu cikin ma bamu haihu ba da wuri, murmushi kawai nai mashi cikin dan jin kunya Mikewa nayi na bishi har zuwa kofa ina mashi adawo lafiya, ****** ********** ****** Kamar yadda Umma tai alkawarin zuwa ta kwana biyu a gurin mu hakan ne kuwa don wataranan laraba da dare muna zaune a falo muna kallo sai mu kaji ana nocking din kofa, Muryan Umma ce tana fadin ko babu kowa ne a gidan ana,sallama ba,wanda ya karba muna, Jibrin ne yashigo ya kawo ta ya shigo yana,min raha irin yadda muka,saba dashi, Sai Sannu da zuwa nakewa Umma na karbi kayan ta hannun shi ina ta,farin ciki da,ganin ta, Na mata iso da firin zama ta zauna tana bin gidan da kallon yadda yasha gyara ga kamshi ta ko ina a lokacin Hamza yana dagi don bai dade da dawo ba, Na shiga na,sheda mashi zuwan ta, ya juyo yana cewa cikin bata fuska Umma kuma da daren nan haka waya,kawo ta, nace mai Jibrin ne, A tare muka fito dashi lokaci guda yana murmushi yake cewa Umma da daren nan kika taso , Tace tau tun rana nake jiran yaran nan sukawoni suna min yawo da hankali shiyasa da dan neman nan ya,shigo cin abinci yanzu na datse shi, Ai ban ma san kana gari ba da kai zance kazo ka dauko ni, zama yayi suka fara hira da Jibrin yana mashi zancen komawa makarantan da yai mashi, Ina can ina kokarin kawo wa Umma abinci da Jibrin sai da na aje abincin ta bude taga,may na,dafa, Tuwon alkama nayi da miyar kubewa danye sai ta,dan bata fuska tace ki aje min kila anjima naci Jibrin yace anjima kuma umma keda yanzu kikagama cin abinci, Nace wa Jibri kai yaya na zubo maka ne zakaci yace a koshe nake naci tuwon mama na koshi wallahi, Abinci kike dafawa haka da yawa ke kadai a gida Aisha ? Hamza yace ni aikin ne ma yai mata yawa ita daya nake gani shi yasa nace ta samo yar aiki ta taya, Hummm,ummm, inji Umma yar aiki kuma kodai kayi aure ga gida da girma ace wai mace daya ce a cikin shi, Murmushi Hamza din yai mata yace aure ba yanzu Umma don ina da,abubuwa a gaba da zan yi, Ban tsaya jin su ba na dauki kayan abinci na,zan mayar kitchen take cewa nai maganan abinda bata so ai kaga zata gudu, Ko bakiso sai wata tashigo gidan nan don bazaki zauna ke kadai ba , To ai Umma ke kadai kika zauna a gidan Baba don may wai kike son aiwa Aisha kishiyace tana zaman lafiya da mijin ta, Anshi naka taiwa Jibrin dakuwa da hannun ta tace ai da na zauna ni daya ban samu wuri irin haka ba, Kai Umma fadi gaskiya don dai kowa yasan da,baban mu na,da rai yana da,wadatan shi sai dai aga abu a gurin ki, To kai sai ka zauna da mace daya in ka tashi auren amma,shikan sai ya kara wata gidan nan takara daga kai tana bin gidan da kallo, Kaina ya daure da,wanan irin kiyayyan na Umma a kaina ni dai abin wani lokaci yana damuna sosai don ban san, Da dare muna daki dashi ina zaune a bakin mirror ina gyara jikina yake cewa cikin dan jan tsuki,. Wai ni ban san wanan abin na Umma da bazata iya zama da yar uwan ta da yara a gida Nidai ban tanka mashi ba sai yake kwata kwata na fahinci Umma bata son zaman lafiya na wallahi, Don bata fahinci irin yadda rayuwan yanzu yake ba da take wani matsawa wai nai aure aure ba sai mutum ya,shirya yin shi ba zai yi, ya,sake jan wani tsakin yana juyawa, Yace ita gashi taci nata rayuwan ba wanda ya damay su da zaman ta ita daya , Jin nayi shiru yasa shi juyowa inda nake yana cewa yaya ina magana kin kyaleni kin san ban son ina magana ai min shiru ko Niyi dan murmushi tare da,mikewa daga inda nake ina cewa kayi hakkuri ka bar wanan magana yaya, Don kasan ni ban da baki magana akan kan wanan zancen tun da ni ake son kawai kishiya, Saboda zamana a gidan nan ni kadai ya kai wa Umma ko ina shine yasa take son ka kawo wata wace zamu zauna tare muci arziki da ita don ni yai min yawa ni kadai, Yai murmushi don ya fahinci raina yana a bace akan maganan Umma don hakan ne nai shiru, Yace naji amma ai ko na kara auren in da Umma ce bazaman lafiya zasuyi da wata din ba, Kamar nace hakane mana don Umma kishi take da matan ka,, Na hawo gadon tare da dan fara matsa mashi kafan shi a hankali har na,soma yi mashi abubuwan da na san sun fiye mishi wanan magana muhinmanci a yanzu, Tun sanda Mama ta dawo gidan namu da sunan yi muna kwana biyu ban samu wani cikakken natsuwa ba kuma, Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun min karanci saboda a kullun Umma zancen ta shine ita dai ni gida yai muna girma ni da "ya"yana burin ta bai wuce taga raina ya baci ko an dagula min lissafi nayi bakin rai, Gashi duk yadda zata sa yaya ya bata rai a kaina sai Umma ta kirkiro shi, Gashi idan hiranta ya tashi takan ta yaba irin rayuwan da tayi da nata mijin da irin yadda tasha gaban yan uwan shi da kowa da yake tare dashi, Shekarun ta yana karuwa mugun halinta yana kara baiyyana a fili, Shi kuma Hamza sai Umma bata kusa yakan yi korafi akan halinta na takura min yakan yi kokarin kwantar min da hankali akan halin ta, yace wai girma ne ke sata yin hakan, Gashi wanan zuwan taki tafiya gida tace ita bama san ranan tafiyan ta ba, In anyi maganan tabar yara agida sai tace aida uwar su ta barsu har Sa,adatu sai da ta dawo gidan da zama, Wata rana nai muna sakwara da miyar taushe da naman rago sai da taci takoshi tana santi, Zuwa yamma sai cikin ta ya rude tafara haraswa da kewayawa da dan ta yazo yana tambayan abinda taci sai cewa tayi nice naja matashi nasan bata son doya amma nai muna sakwara taci shi ya jawo mata rudewan ciki, Wata kila tafadi hakane don yai cikina da masifa sai yake cewa to ke umma da baki so ai sai kiwa Humaira magana ta sake maki wani abinci, Tace wane ni nasata canza min abinci tace nazo gidan ta na saka tagaba da fitina kadai san halin yaran yanzu, Juyawa yayi inda nake zaune yana ce min may yasa baki girka mata nata daban ba Humaira yanzu gashi kin ja mata matsala irin haka, Raina yai matukar baci ya gama fadan shi ya fita ita kuma ta,shige daki da yar ta ina jin su suna dariya, Daki na,shiga ranan sai da nai kuka mai isata ina hadiyan zuciya ni kadai sai yarana dake kallon yadda nake kuka, Ibrahim ne yashigo gidan yaga bani falo yai ta kwada min kira sai da na fito sama sama nake gaida shi kallo daya yai min yafahinci nayi kuka Yace yau kuwa lafiya Aisha cikin muryan da ya dashe min don kuka na furta mai babu komai yaya Ibrahim, Yace Umma ko nasan dama hakkuri kikeyi da ita har ma,shi mijjn naki nasan baida yadda zaiyi ne amma insha Allahu yau takai karshe don gida zasu kwana wallahi, Fita yayi don ban ma tsan manin ya shiga gurin ta ba inda take, Dan wani lokaci sai gashi ya dawo ya shiga gurin ta yana cewa yazo daukan tane su koma gida don mama bata da lafiya gida ya koma shiru, Kin zuwa tayi sai da Ibrahim din yace mata idan bata bishi sun koma gida ba zai fadawa Baba lawal tasan zafin Baba lawal don haka bashiri suka fito ya kwashe su sai gida, Sai dare ya dawo gidan yake tambayan ina Umma nace sun tafi yaya Ibrahim ya, zo ya dauke ta, yace sai Ibrahim don shi kadai zai iya sata gaba ta koma gida, Wanan dalilai danake lisafawa maki akan umma sai suka sa aurena ya zamo auren da a daidai lokacin da mutane ke ganin ina jin dadi da farin cikin shi sabod nasarorin da zahiri ya nuna ina ciki, Nikuma da nake a cikin matsalolin nasan yanzu nake zaman aure da fuskantar kalubalin rayuwan aure daga uwar mijina, Sai duk da halin da nake ciki ban taba yarda wani ya fahinci ina cikin wani halin rayuwan aure ba, Iyayyena ne idan na,fada masu hakkuri su kan bani suce dama duk wata mace mai aure tana tare da kalubalin aure don haka inyi ta hakkuri kawai don rashi hakuri ga rayuwan aure a yanzu shike kawo yawan mutuwan aure, Dadin abin kawai ina samun sauki a gurin mijina da yan uwan shi, ****** ********* ****** Har lokacin tafiyan su gabas yazo ranan da aka,fada mata tare muka tafi da Hamza don yafads mata zancen tafiyan su din, Tai murna tayi farin ciki sai kuma daga karshe tai mashi adduan tare da,cewa Allah yasa badi kuma ya kai mata zarah da Asmau, Yace Umma bakice Humaira ba sai ki kawo zancen Zarah da,Asmau kuma , Yanzun dai na gane ba zancen yan uwanka kakeyi ba sai na matar ka duk tabi ta shanye ka akowa, Haba Umma kada fa ki manta da hakkurin da humaira tayi a gidan nan shine fa ake gani kamar ta shaye nine, Ni dai shiru kawai nayi ina zaune waje da Mama muna hiran mu muna jin zancen su, Mama tace kada ki damu da zancen ta Aisha ya ci ace yanzu kin saba da halin uwar ku don kishi take da ke haikan, Nace mama ai babu komai halin Umma na hassada a kaina,ba bakona bane, yanzu, Mun kai wani lokaci a gidan muka fito zuwa gida sai da ya,tayar da mota yake cewa, kai ni wallahi idan Umma tai wani abin har mamaki take bani, Na fahinci nine Umma bataso da alheri ba,wani ba taya zatace wai nakai Zarah ko Asmau makka gaki, Idan ma nai haka ai ita mai min fada ne sosai da tana kaunana da alheri da bata sani hanyan da Allah zai tambaye ni, ba kan cin amana, Banyi magana ba sai ma kallon titi da na mayar da hankalina a kai tare da dan wasa da hannun yarinya na da nakeyi ina dan mata wasa, A haka har zancen tafiyan su gabas yataso in da ya sai muna komai da yasan zamu bukata a bayan shi, Sa,adatu zata dawo gidan mu ta zauna wai sabo da tsaro don Umma tace wai mama bata zama a gida da rana, Rashin zaman mama da har take fita zuwa kujiba kujiban ta gurin nema kudi don saboda yawan fitinan Umma na da take mata kamar karamar yarinya, Duk da Hamza ya hana mama yin wanan sana,an amma bata bari ba tafi bukatan ta fita zuwa neman nakan ta gashi kuma abin ya karbe ta sosai, Dawowan Sa,a datu gidan mu ya kawo muna matsloli da dama a zaman ta gurina, Don kullun sai tafita wai tana zuwa gurin yan uwan ta yini, Idan kuma tana gida sai dai ta mike kafa tana kallo ko kwanon da taci abinci bata iya kawarwa sai dai ni mai shi na dauke da kaina, Sai kuma fita hiran da takegi a kofan gida da dare har wani lokaci mai tsawo nai mata magana amma tai banza dani, Gashi yarana duk da kanana ne basu da shakat a gurin ta dan abu kadan ta kai masu duka ko zagi, Wanan bai damay ni ba don nasan diyan tane tana da iko akan su don kaunar mahaifin su ne, Ranan da tana kallo mimi tazo inda remote yake ta dauka tana daddannawa ta juyo ta kwashe ta da mari sai da yarinyar ta gigice da zafin marin, Nace haba Sa,a datu may mimi ta sani da zaki mata wanan irin dukan haka yarinya ce ko anjima karawa zatayi, Tace min ko zaki hana na duke tane zaki gwada min ke ce kika haife ta ko, Ko don nazo gidan ubansu kike son kiyi min wullakanci dama nima wallahi ban so zuwa wanan zaman ba duk yayane yaja min zuwa nan, Don dama nasan bason mu kikeyi da dan uwan mu ba kinfi son abarki ke da diyan ki ku mahe gida ku kadai sai abinda ranki yaso, Nace don nai maki magana akan dukan mimi shine kike kokarin fada min abindake zuciyar ki dani, Sau nawa kike dukan su ban maki magana ba kona yau naga dukan yai tsanani ne bai dace da karamin yaro ba, Tace mai da wukar ki a kube Aisha na daina shiga harkan yaran ki har da naki ma na daina, Nace to dayafi nono fari wallahi Tun daga ranan ta daina shiga harkan mu ta daina yi min magana ko gaisuwa bamuyi da ita, Sai nice ma nake kokari kawar da gaba a tsakanin mu nakan dan yi mata magana ta amsa,min a lalace, Ko shigowa zatayi gidan bata sallama haka ma idan zata fita bata ce min uffan, Naga zata zubar muna da mutunci a guwa yawan fitan ta da zama a kofan gida har wani lokaci yasani daukan mataki a kan ta, Nai mata magana akan ta daina,wuce karfe goman dare bata dawo ba, Sai taso ta zageni don haka na kira Ibrahim nafada mashi irin zaman da mukeyi da ita don ya,tsawata mata, Bayan yai mata fada ya tafi tafito tana,min maganganu, rashin kunya wai dama dan tallaka bai iya samun guri ba na,samu guri shine har dasu kannen miji nake son na mulka to na tsaya iya mijina da na mallake, Zarah nakira tazo gidan nafada mata sai bude baki zarah tayi tanacewa kai Aisha ban son kanan maganganu wanan ai sheri kike son yiwa Sa,a datu, In har tai wani abin da ba daidai ba ki dauki mataki mana da kan ki basai kin fadawa Ibrahim ba, ki kirani mana inzo ki fada min, Nace mata tau babu laifi suyi hakkuri amma zan dauki matakin da tace da kaina, Tun lokacin nafahinci akwai wani sauyi a tsakani na dasu ban sani ba ashe umma ta fada masu wai na hana mijina ya kai su makka don ni ban tafi ba, Ranan da ta fita tun safe ban sani ba,na kira yan uwan ko tana gurin su suka ce batazo ba har dare nakara kiran Zarah da Asmau sukace min bata gurin su, Tana dawowa nai mata magana sai cewa tayi ke kin fa isheni tana magana kamar zata make ni, Sai dai in zaki mutu ne ki mutu yar hassada kawai haka kawai ki sakani gaba da bakin lecture kamar kin aike ni, Kuma duk tsiyar ki ba zan bar gidan ba tun da ba don ki nake a gidan ba don ba gurinki nazo ba, Kince na daina kula diyanki nace har kema bani kulawa bana,shiga tsabgarki dana yayan Gida kuma gidan dan uwanane sai yadda naga dama nayi dole kuma ki dafa ki bani naci koba kyaso, Takarshe zancen ta cikin tsiwa tare dacjan wani irin uban tsaki tace banza kawai, Na kalle ta nai murmushi kawai bayan ta,shige dakin ta, Washegari ma nasan ba fasa fitan zatayi ba don haka na kyale ta,ko shiryo tazo ta,wuce mu zaune a falo tafita abinta, Tana fita nabi bayan ta sai da tafice daga gidan na kalli tsohon bakaben dake muna gadi nace mashi baba cikin girmamawa, Nace daga yau duk wanda ya, zai shigo gidan nan bayan karfe goma kowa ye kada ka bude mashi kofa idan bani nace ka bude ba ya amsa da to cikin girmamawa, Sai sha biyu da yan mintina Sa,adatu ta dawo ta tura kofa get a,rufe yake tai kiran maigadi takafan get din wai ya bude mata gida ta shigo yace mata hajiya ta,ce kadana budewa kowa idan goma ta,wuce na dare, Tai juyin duniya,tsohon ya bude mata amma fir yaki yana,gudun sabawa umurni na yayi laifi, Waya ta,daga cikin daren nan takira layina naki dauka ran ta ya baci ta rasa yadda zatayi Dole takira Zarah ta fada mata karya da,gaskiya wai na hana a bude mata gida, Itama Zarah tai kiran wayana naki dagawa don ai tace na dauki mataki akan sherin da nakewa kaunan ta, Gashi dare ne kuma bata son kishiyoyin ta ko mijin ta suji zancen don mijin ya taba mata magana akan Sa,ade din, Dole badon taso ba takira Ibrahim ta fada mai abin dake faruwa agidan mu sai ko gashi a cikin daren nan yazo yasamay ta tsuru tsuru rakube a kofan get, Kira daya yai min na fito naba maigadi Umurni da ya bude gidan suka shigo tare dashi suna shiga falo yakai mata wawan mari yana tambayan ta inda tafito a wanan lokacin, Yai mata mugun duka ya kuma ce min nai mashi dai dai don ya tambayi maigadi yafada,mai time din da,ta,dawo, Yabani hakuri tare da kara yi min nasiha akan nayi hakkuri kullun zai dinga zuwa safe darana har da,dare ya duba ta, Tun wanan rana Sa,ade bata sake fita ba don tana tsoron Ibrahim yazo bai samay ta a gida ba yaci uban ta, Shima Jibrin dayaji sun zo da mama sun mata tas suka kuma samu zara sukai mata cin mutunci a gidan ta, Duk nasan maganan bai kare ba don in Umma ta dawo akwai magana amma hakan bai damay ni ba saboda nasan haka shine daidai don in wani abu ya samay ta dani za,ai kuka don may ban dauki mataki ba tun farko,, ****** ********* ****** Allah yayi matafiya sun dawo lafiya ana ta murna da farin cikin dawowan su taro na musaman nai masu sai dai shigowan dare sukai muna, Don haka ba,a samu issashen lokacin tsayawa hira ba bamu dade ba muka shige da mijina muka bar Umma da yarta su ma adakin su din duk wanda yazo taron su ya tafi don dare yayi lokacin, Tsab na shiryawa dawowan shi don duk wani abu da mace zatayi don taron mijin ta nasa kudina naiwa shiri wanan ranan, Hamza sai faman santin rashina akusa dashi yakeyi yana cewa Humaira rashin ki a,wanan tafiyan yai min illa da yawa a can na,zabatun da,rashi ki a tare dani Nace ai bautan Allah ka tafi yaya ko da atare muke ba abinda zaifaru a can , Yace amma in ina ganin ki abin zai min sauki sosai kara shigewa yayi a jikina yana fadin kina da,wani siri a jikin ki daba ko wace mace take dashi ba kina,sa nakanji tankar ke din kifi duk saura mata a komai, Murmushi kawai nai mashi batare dana tanka mashi ba nasan kayan maman mujaheed ne ke aiki akan shi lokacin, Washegari tun da,safe nafito nai masu abin karyawa tin da nakaiwa Umma nata dakin da,suke ina gaishe ta naji yadda ta amsa min yasani sanin cewa Sa,ade ta kwashi karya da gaskiya ta fada mata ko, Sai da Hamza yai barcin shi mai isar shi sanan ya tashi yai wanka ya karya yafito don ya gaida Umma don sun dawo tana mura, Bayan ya dawo daga dakin Umma alokacin ina kitchen ina guara gurin na,dora abincin rana don nasan ranan muna dabaki agidan, Ina,shiga dakin na,samay shi ranshi a bace kwarai da gaske da alaman yaji maganganu iri iri a gurin Umma , Wanka nashiga nafito na zauna nagyara jiki shiko sai cika yake yana batsewa ya hau sosai, Ina daura dankwali naji yana cewa, Humaira may ke faruwane bayan tafiyan mu ke da yan uwa na, Najuyo a hankali cikin natsuwa nace mashi kaman yaya kuma ni dasu babu komai, Yace Umma ta tareni da wani labarin da banji dadin shi dana,shiga gurin ta dazun, Ni babu abinda ya faru tsakani dasu in ma akwaishi ka tambayi Ibrahim don shi yasan komai akan idon shi akayi, Yace tau bari Ibrahim din yazo don ai hardashi dama a zancen, Yaya zaki sa yaiwa yarinya mugun duka don kawai wani manufa naki na daban, Da,sauri na dago kai na kalleshi yace idan da wani zai fada min baki son yan uwa na,su mamayni zance karya ne amma sai gashi dan tafiyan da mukayi sa,adatu kawai muka bar maki amma kinyi bakin ciki dazaman ta a gidana , Muryan su mama da mukaji tana cewa ina Alhajin yake ne dan nawa nagan shi Allah mun gode ma da ka dawo muna da,su lafiya, Abinda yasa mikewa ke nan fita zuwa gurin mama yabar ni zaune cikin bacin rai a daki sai daga baya nafito kallo daya mama tai min tafahinci akwai matsala don yadda raina yake hade akan maganan da ya fada min a daki kan yan uwan shi, Sun gaisa,da mama tashiga gurin Umma tabar su da Ibrahim da Jibrin a falon, Suma,zuwa sukayi gaida Umma din yana,shiga umma tace dama kai nake jira yanzu Ibrahim don ban gari kasaman yarinya akan wanan mara mutuncin Aiaha kai mata bugun akawo ruwa, Au haka tace maki Umma ashe ma dana,sani na karya ta kafin ku dawo ki samay ta akare da shegen kafan ta na yawo, Shigowan su Xarah da Asmau danake ganin sun shirya yin tafiyan a,tare ne lokacin, Umma batai shiru ba,sai masifa takeyi sai mama ce tace assha yaya ai kamata yayi ki tambaya mai tayi ya,doketa da,bakinan, May zan tambaya tunda da hadin bakin ki akai mata haka aida bada saninki bane bai kai can yai mata wanan dukan ba hakana, Jibrin ne yatare ta da cewa Umma yaya zakice haka yarinya tana fita tun safe har karfe dayan dare bata,dawo gida ba, Umma tace inji Uban wa wanan yar sherin mai bakin halin tsiua ta hada maku gadar zare kun haye wa Aisha ke son gani gidan nan a cikin ku in ba ita da diyan ta da yan uwan ta ba, Wallahi in tai tsiya sai tabar gidan don ba gidan Uban ta bane itama kuma tabar gidan muga tsiya,, don an bugi diyan ta zata sa yarinya a gaba da tsangwama Ina diyan dan uwantane sai tafita tabar mu da diyan da,take fada a kan su Subbahanallahi inji Mama tace amma,wallahi yaya kin bani kunya wanan yarinyar kokarin da,tayi in ba yaba mata ba kuma ba ace mata Allah waddai, Jibrin yace mama yanzu ya dace ace tun safe Sa,a bata gida kuma ba,wanda yasan in da take zuwa,. Har karfe dayan dare don may Aisha hankakinta,bazai tashi tunda amanan ta aka bar mata , Nan suka kwashe duk irin tsiyan da tai ta tsula min suka fadawa Umma dashi yaya din da yau ya zauna, Yacd ga,zarah nan data fada maki may kika ce bacewa kikayi ta dauki mataki ba, Ta dauki matakin kuma shine za,a ce tai laifi haba Umma ku dinga tsaya ku binciki magana kafin ku dauki mataki, Don kawai kuna kin yar mutane sai kusa mata karan zuka haka, wallahi haka babu kyau gaskiya Kayauuu Hamza ya kwashe Sa,adaru da mari da duka a lokaci guda yace sai ya halakata, Ina jin su wanan yafadi nashi wancan ma yafadi ban shigo gurin su ba na kyale su karshe ma nashige daki don takaici na fara kuka,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA,BA KADA KI KARANTA,HAKKIN WASU PLEASE DON YIN HAKA CIN AMANA,NE,,,,, Ko da ya daina dukan ta ranshi a,bace yayi shiru ns dan lokaci mai tsowo saboda ran shi yai matukar ba ci a lokacin sauraren kalammin kowan su yake a lokacin, Sai can Umma tace naji anyi laifi tana zuwa gidan Audi bata fada mata ba amma kums kuma ku kwantar da hankalin ku kuyi nazari, Kun san fa ita Aisha yanzu baku gane ta,bane ita so take duk wanda zai shigo gidan daga ni uwar ku haku yayana indan zamu mami mijinta sai dai mu yarda ta mayar damu talolo kamar yadda,ta mai da shi mijin nata , Da,sauri suka,daga suna,kallon Umma gaba dayan su don jin may tace, a kaina da dan uwan su, Hamza daga inda yake zaune yana tuku buri da,jin haushi zan tukan su, ya dago kao ya,dubi Umma sai mama hafsi ce tace wai wa kike nufin tamayar solobiyo shi Hamza din ko wa wai, Umma cikin hasala tayi maza tace eh shi din mana kin ko san yadda take wa Su yaran nan Sa,adatu bazata yarda a ce a juyata tun da ita ba sakariya bace, irin su, kuma ba wurin ta tazo ba bakuma don ita ta zauna gidan ba, Don dai gida ba nata bane ita da "ya"yan ta da yan uwan ta da zata kama bakin ciki da hassadan duk wanda yace yazo zama a gidan Gida dai nakane da zata kama bugun kirji tana kafa masu doka yadda ran ta so, Hamza ya katse Umma da cewa nata ne Umma b bugun kirji takeyi ba tun da itace matar gidan,, Amma tunda kince ba wurin Aisha tazo ba ta ba har kin fada da bakin ki yau din nan Sa,adatu ta tattara tabar mata gida tunda ita ba boyar ta bane da tana zaune za,ai mata komai kuma babu ragowa ko mutuci akan ta, Tabar mata gida fakace Hamza ta kira sunan shi abinda ban taba jin tayi ba, Yace da karfi eh Umma kema ai kin fadi da bakin ki ba wurin Aisha Sa,a ta zo ba towurin watazo ni dai ba mazauni gida bane itace ke cikin gidan ta zaune, Yaya za,a zo a zauna a gida ace wai ba wurin matar dake cikin gida akazo ba wurina akazo ni mazauni gidane ko kuwa ? Umma ke kin san Humaira bata ta adawa da yan uwana inda bata damu da halin da zata fada ba sai ta saka mata ido tayi yadda ranta ke so bata damu ba, Kin koga tasan a gurin ta ke take fita yawo dole hankalinta ya tashi ta dauki mataki, Inda haka kawai ta saka ta a gaba ba wani dalili ma kwari kin san nima bazan kyale Humaira ba yau a gidan nan, Ai naga dukkan su gasu nan kin san lokacin da suke turo ta furina neman wani abu kuma ta,dage ta sakani gaba harda kukan ta sai na taimaka masu, Don haka ni Humaira bata da matsala a gurin yan uwana tunda itace mai bani shawara akan na taimaka masu, Sa,ade badon ta na gina gidan nan ba ta kwashe yau din nan ta koma gida don ni banine zaune a gida ba wace ke gida kuma ba,gurin ta tazo ba, Umma tace Uhum zaka kore mu dai ke nan a gidan naka ko? Tun da kasan yin haka shine zai farauta ran Aishan naka , Kuma kasan in ina gidan nan dole ne Sa,a ta zauna cikin shi tunda bazata zauna inda bani ba, in dai kace Sa,a ta kwashe har dani zamu kwashe ke nan, Yace shi ke nan Umma inkin ga hakan yafi maki sai ki bita ni dai nasan bance ke ba amm sa,a kan bata zama min a gida taja min magana a mutanen shiya zaman Sa,a ya isa haka tunda ba biyayya a gurin matan gidan, Daga haka ya mike yabar dakin Umma tana ta faman fada tana fadin dama tasani sherina sai yakai ga narabashi da kowa nashi na zauna ni kadai da yaya na mata da yan uwana, Su ma su Ibrahim fita daga dakin sukayi sukabar su su iya mata, Zarah tace gaskiya Umma abinda Sa,a takeyi babu kyau koni wallahi Alhaji sai da yai min magana akanta yace mu dauki mataki akan sa,a tun bata jawo muna abin kunya ba don inda yake ganin ta a gari bai dace ba, Ke rufe min baki aiduk kune shanyayyu baku son aga laifin yar gwal din ku ko kadan yadai ce mu bar mashi gidan mata shi ko tau yau din nan basai gobe ba zamu bar mai gidan shi, Asamau tace Umma baifa ce da ke ba Sa,a dai da tayi laifi yake nufi kuma in ba ai mata fada ai abin baiyi ba wallahi don ba mai sin yaga nashi ya lalace, A ranan Umma tasa a kwashe su a mayar dasu gida gaba dayan su sai da zata wuce ina tsaye daga gefe ta,waigo tana ce min mun bar maki gidan Aisha gurin ki ya cika, Amma ki sani gidan nan bazaki zauna ke kadai ba sai wata wace zata shigo ta kwato min dana tashigo shi da yardan Allah, Nace Umma Allah ya kawo ta lafiya, ai ba akaina zata zauna ba dai ko,. Duk da,sun koma amma sai nayi girki na aika dashi can kaman kullun sai dai na samu sauki fiye da zaman su a gidan, Tun ranan bai kara min magana akan zancen ba nima haka ban karayi mai wanan zancen ba ko da wasa, Shima ne yai tan dan dari dari sai daga baya da yaga ban dauki maganan araina ba,sai ya,share,, Amma na samu sauki sosai akan tsagwaman da suka dauko yin nacewa,wai na hana akai su makka wannan kuma yafaru ne a,ranan da,suka zo kabar tsaraban su agaban shi nake cewa Allah ya hore mai muma,ya kai mu makka a tare, Suka ce wai da anga yawo a,gari da jibgo kayan gumama, nan mukai ta shamatar junan mu, Suna fita Asamau ke cewa nifa wallahi na,fara zargin maganan nan ba gaskiya bane wai Aisha ta hana akai makka badi, Inda gaskiya may zai satafadi hakan a gaban shi kuma gaban ke nan wallahi duk shirin Ummane fa, Zarah tace ni tun farko na san hakan bai yiyuwa don idan ya tashi bata isa ta hana ya kaimu ba don shi yaya baida gwani gashi ranan da bakin shi ya fadi in muntura ta neman abu avurin shi ta kama binshi ke nan sai yai wa mutum abu,, Ni gaskiya ban kara yadda da maganan da ba,a yi a gaban ido na ba sai nagani ko naji da kaina, Niko a nawa bangaren gaba daya yanzu ban yarda dasu don na fahinci kan su suka sani kawai basu damu da damuwa na ba ko kadan, ****** ********* ****** Tun da ya dawo makka yanzu abin na Hamza kara bunkasa kawai yakeyi don ya,hadu da wani aboki a can wanda ya sashi a harkan sayar da motoci da mashin mashin na zamani, Sosai wanan harkan ta,amshe shi baida issashen lokacin kan shi balle na wani, sai lokacin da na gan shi gida, Hakalina a kwance yake nai kiba farina ya kara fitowa ina samun ci da sha da hutawa, Ba wani zancen wata kishiya da nake ji balle ya tayar min da hankali gashi Umma tun zuwan ta gida dasukayi bada dain rai ba ta daina zuwa gidan mu da niyar kwana,sai dai tazo ta wuni takoma gida da dare ko shi sai tasan dan ta yana gari take zuwa, wai shi take zuwa dubawa bamu ba, Satin shi Ukku baya gari wanan zuwan da yayi ne nake mashi maganan ina son zuwa naga gida, Bai hana ni ba sai shirin tafiyan da yai muna inda yakaini da kanshi nayi tafiyan da mama hafsi da hussaina kaunata zamuyi sati daya acan, Dalilin zuwa mama kuwa tare da mu tana son zuwa taima gwagona gaisuwan dan ta da yarasu ne shine tarakani, Shi da kan shi ya kaimu inda yace idan zamu dawo zai turo wani yazo ya dauke mu, Na samu kowa lafiya nakai masu tsarana masu yawa kwanana biyu da zuwa nashiga zagaya dangi da abokan arzikin da nai zaman lafiya dasu wancan zuwan da nayi, Yan uwa sun tareni fiye da tsamani na don sai dadin ganina suke ji, Yayan babana wanda yanzu shine ke limancin gari wani dare da na shiga gurin shi mu gaisa dashi, Yake ce min wai kuwa Aisha ashe mahaifin ki ba yana da rai ba don inda duk nai istihara nakan ganshi kuma a cikin wadata zan gan shi, Na dan limshe idanuwa na tare da sauke ajiyan zuciya nake cewa baba idan yana raye Allah ya baiyyanar muna dashi, Sai naga yana dan kokarin jawo wani allon karfe daga gefen shi yana cewa bari na dan baki wani abinda zai taimaka maki a rayuwan ki, sai ya jawo tawada yafara rubutu ga allon nan ya wanke allon a gabana ya miko min yace na,shaye da bissimillah, Ya jawo wani dan abu cikin wani takarda yace miko min hannun ki na mika mai sai yafara dan murza abin a hannu a hankali har na daina ganin abin yake ce min tsari ne daga duk wani fitina da za,a iya tura maki diyanki ma zan basu susha don tsari daga bakin mutane saboda kowa yagan su yana kaunan su sosai,baki zai iya kama makisu idan yai yawa, Ki kuma dinga yawaita kama kan su kina masu addu,a safe da yamma ba adduan da ta wuce falaki da nas, da kulhuwallahu ga yaro, Naiwa Baba godiya ina shirin mikewa yake cewa kikara hakkuri kinji Aisha hakkuri bai bar komai ba a duniya, In Allah yaso ya yarda bazaki tabe ba a,duniya kuma duk mai binki da sheri a kan shi zai koma insha Allahu ke di kada kiwa wani mugunta a,rayuwan ki don bamu gaji yin hakana,a gidan m Amma fa mu kuma duk wanda yace zai muna to karshen shi bata kyawo shiyasa kika gani har yau ban yarda wai wani ne yaima mahaifinki asiri ba yabar gari, Kawai dai zuciya ce irin tamu ta fulani ya hau amma duk randa Allah yai dawowan shi gida kwatsam zamu ganshi ya dawo insha Allahu, Jikina yai sanyi akan nasihan da Babana ke min, a lokacin nai mashi sallama na barshi a dakin shi tare da,yiwa matan shi saida safe, Mun yi kwanakin da zamuyi ina ji kamar kada nadawo na bar su don kewan su da nake ji araina, Mun ratse sokoto gurin mahaifan Ummi na suna ta min tsiya wai ni yanzu mahaifa na nasani nabar kowa, Naba su hakkuri tare da aje masu tasu tsaraban danazo masu dashi mukai sallama muka kama hanya sai jega, Jega babban gari garin da babu raggo sai bako, dan jega ba,a gane gidan ku, gida daya kofa goma, Kamar yadda Hamza yace hakan ne yafaru kuwa don ko da muka dawo baya gida, yana kwatona gurin sarin motoci, Na gyara ko ina nagidan ida nazo da,wata kaunata diyan Baba Liman na roka yabani ana cewa yarinyar Madina Yarinyace karama batafi goma ga shekaru amma akwaita da kazar kazar din jiki bata jin nauyin jikin ta ko kadan, Ba sai nace mata tai min abuba sai dai na,samu kawai tai min ita ma yarinyar farace sol kamana irin mu daya da ita don jini yana aikin shi, Duk wanda ya ganta zaice muna kama da ita mun rabawa makwabata tsaraban da muka zo dashi sai suke shigowa yi min sannu da zuwa, A daidai irin wanan lokacin da nake ganin kamar ban taba samun wata dama tajin dadin aurena ba da mallakan mijina na daga ni sai ahi da yan diyan mu agidan sai yadda ran mu yaso ba takura ko tsangwama ga kowa, Hamza ya dawo daga tafiyan da yayi ya,dawo a gajiye cikin dare suka shigo da motocin su don irin yanayi tsaron dake hanya, Da yake dare ne ban tsaya yin kwaliyan atamfa ko lace ba kwalliya ta kayan barci nai mashi, Dan wani mini skirt nayi da,wata yar shirmamiyar shimi don nasan a lokacin su yafi bukata a ran shi, Duk da yana da gajiya bai hana shi bina da wani irin kallo ba yanayi yana dan murmusawa tare da lumshe idanuwan shi, tamfar ya lashe ni tun a,falon, Sai dai a lokaci yaran basuyi barci suna zaune a jikin shi sai shirmay suke zuba mai da jin dadin ganin shi madina tana daga gefe daya zaune a takure don bata saba da shi a lokacin, Ganin suna da mun shi da surutu yafara dan ya mutsan fuska yasani cewa Madina oya Madina kwashe kuje ku kwanta dare yayi hakana, Ta kwashe su zuwa daki ina ce mata gani nan zuwa nai masu addu,a idan sun kwanta, Suna shiga yai murmushi yace kin kora min yara da,wayon manya ko, Nace ai kane naga kamar kafara gajiya da hiran nasu shiyasa nace su barka ka huta yace aiko sun tafi uwar su bata barina na huta, Nayi murmushi nace aidole nabarka ka huta don na hango gajiya a idanuwan ka, Barin tafi na kashe masu wuta don suyi barci don naga yau basu son yin barci a idon su, Na juya zanbi yaran yace look don Allah kada ki dade a gurin su, nace ai bazafi minti talatin ba What ? Gaskiya yai min yawa har minti talatin ina jiranki ki dai rage time din nace yayi na juya naji ya riko ni na fada a jikin shi ya ce Humaira wai ko kinga yadda kika koma zuwa gidan nan da kikayi may nene sirin ne wai haka dayawa, Ko ban gani ba aikai kagani aikin gwagonane da take cikani da kayan dadi danaje, Gaskiya gwago tayi kokari kin zama tamkar wata yar karamar yarinya kamar a shekarun da na aure ki, Nayi dariya kawai ina cewa kai yayana kana dai zugani kawai dayawa naji kamar ba,wata bayan ni, Ya kyalkyale da,dariya yace to ina watan take in bake ba a gidan nan nace agidan kawai ba azuciyar ka ban san iyakar mu ba, Daga haka na wuce ban tsaya jin may zaifada min ba don nasan nabashi mamaki da amsa na, Washe gari yace na,shirya har yaran muje gaida,su Umma yakuma yiwa Mama godiyan rakani gida da tayi, Mun sha kwalliyar mu kamar ran sallah daga ni har sbi da yaran wasu shadda yasa ghalila mai tsada a jikin shi nikuma nasa wasu lace sky color dinkin shi mai dogon hannu, sai yaran da nasawa yan kati, madina tana saye da dinkunan da nai mata da tazo don nata basu fita a gari, dinkin kauyawa ne, sai kamshi ke tashi a jikin mu, Mun shigo gidan suna waje dukkan su suna hira da murna mama ta tare mu tana muna yaya gajiyan tafiya, Umma ko dan ta takecewa andawo lafiya Baba bakadai iya barin tafiyan dare ko ? Ya zauna yana murmushi yana cewa Umma yanayin sana,an na mune hakana sai dai addu,a kawai, Sai Umma ta dan fara kuka take kowa hankalinshi ya tashi a lokaci guda, Kowa na tambayan ta Umma lafiya may kuma ya faru daga shigowan mu yamzu mun samay ku lafiya, Nikan nasan cewa ganin mune ya sata wanan kukan duk wanda ya ganmu a lokacin sai ya yaba muna sai dai makiyin mu, kawai, Hamza ko duk ya rude har da mikewa yayi yana fadin Umma wani abune ke maki ciwo ko may akai makine wai, Mama tace ba abinda ke mata ciwo don tun safe lafiyan mu lau a gidan nan da ita, Kara zama abin tausayi Umma tayi tana marairaice kukan ta duk hankalin su ya daga sai cewa Hamza keyi Umma idan nine nai maki laifi don Allah dai kiyi hakkuri ki yafe min, Ganin da tayi duk ya kidimay har yana rokon ta gafara sai take cewa, cikin kuka, Dole ne nai kuka Baba na ganin burina a kan ka ba zai cika ba har na mutu, Subbahanallahi Umm may akayi kuma wanda ban cika maki burinki ba har zaki mutu baki gani ba,? Duk gaba dayan mu munyi son muna sauraren burin da Umma ke dashi a kan dan nata da zata mutu bai cika mata shi ba, Ina zaune sai shan jinin jikina danayi don ina Allah Allah in ba akaina ne gurin nata zai kare ba, Duk munyi kasake muna kallon Umma wadda harda majina take fecewa don kukan da takeyi gasu Ibrahim duk sun shigo don ganin motanshi a gidan yazo, Wai mama maynene ana tambayan kikin yi shiru sai sa zukatan mu cikin tashi hankali kikeyi, inji Jibrin dan zafi, Hamza yakara tausa murya yana lalashi ta saida ta fece wani maji na tace, cikin sanyin murya irin na wanda ke kuka, In ganka ka,shigo gaidani da matan ka biyu mana Babana kullun bawa idan ya samu ai ya,geadawa Allah yagode ga mata birjit agari kana da wadatan kara aure amma ka zauna da mata guda, Tsaki suka ja banda hamza da ya dukar da kan shi din bai taba zaton wanan ne abinda mama takewa kuka ba haka, Murmushi kawai na ita fuska na kakaro a fuskana nace araina Umma kin kai makira ta nan kuma kika bulo min ana zaune kalau, Kowa na magana shi baiyi magana ba sai can naji ya bude baki cikin sanyin murya yake fadin kiyi hakkuri Umma in har lokacin yin hakan yayi ai zankara mata don ina da gurin yin haka bakiga gidana na mata biyu nayi ba, Insha Allahu bazan barki har ki mutu ban cika maki gurinki ba nan badadewa ba zan kara mata , Kaiyya inji mama wai uwar diya mata ce ke irin wanan maganan haka da baki da diya mace ne sai ace baki san zafin abin ba, Munzo da niyar yini mukazo amma wanan makircin da Umma ta azamin yasa duk jikina yai sanyi lokacin da yagama zai tafi nima namike ina cewa zamu tafi don tun da Umma tai magana sai ban kara magana ba da kowa, saboda wanan gurin na Umma ya sakar min da kasala ajikina Gashi inba gyaran Allah ba kalaman da Hamza yaiwa Umma ya sha banban da wanda yasaba mata idan tai maganan yai min kishiya a baya hakan ya tabbatar min da yana gap dayin yanzu, Ganin nima namike ina cewa yaran suzo mu tafi yasa shi cewa au kun fasa yinin da zakuyi a nan din ne, Ummm kawai nace mashi tare da tattaro natsuwa na ina ce masu zamu tafi, Ke Humaira baki fahince ni bane karin auren da nace yayi aiko ke amfanin ki ne ina kwanan baya ce min yayi aiki yai maki yawa a gidan yanzu idan ku biyu ne ai baxaki wahala haka na ba, Yace hakane fa Umma itama saukin tane idan nakara din ai ba wani abu bane dama,shi aure bana kowa da kowa bane sai wanda yasan zaiyi adalci a kai, Sai dai ina gudun nayi nazo ina zaluntar dayan ko a,taru a zalunce ta najawa kaina fitinan kabari shiyasa ni auren ma yafita min akai, Amma tunda burin kike nan a kaina insha Allahu zan kara auren a zauna lafiya ni dake Umma, Tace yyawa dan albarka haka nake son ka gurin biyayya yanzu da su biyu ne idan dayan bata zauna ba basai dayar ta zauna muna har daren ba, Nai masu sallama naja yarana muka fita mamace kawai tai muna rakiya tana fadin Antina ina nan zuwa nai maku wuni yaya yace ai yanzu gwago gudun ki takeyi, Muna hanya ba,wanda yaiwa wani magana abakin wani shagon sayar da kayan sanyi ya,tsaya yana cewa bari nai maku take away don naga rana yayi baku yi abinci ba, Sai da ya dawo ya zauna amota yafara tuki yake cewa kai Umma akwai rigima daga shigar mu ta tayar wa kowa da hankali nima na dauka ko wani zance ne can nadaban wallahi, Ranan haka na wuni sukuku dani ina kullawa ina kwancewa sai faman tunane nakeyi ni kadai a gida, Sai dare ya dawo cikin anna shuwar shi ban nuna mashi komai ba kuma ban ta da zancen ba don ban mason ayi shi, Dadare bayan mun gama komai sai barcin shi yake hankali kwance niko na kasa runtsawa sai tunanen abinda Umma tai min yau nakeyi, Umma shike nan tai min wanan sanadin ta kishiya a daidai lokacin da muke zaman mu na dadi ni da mijina Amma yanzu zata sa a kawo min wata a cikin gidan nan ta zauna a matsyin kishi a gare ni, Umma bata bukatar zamana a gidan dan ta ko kadan, Yadda na saba zama ni daya yanzu idan ankawo wata na tabbatar da duk farinciki na zai rushe ne kamar yadda Umma take bukatar gani na, A haka muka zauna cikin wani bakon yanayi ina lura da tafiyan shi ko zanji wani abu ya taso akan zancen kishiya sai da har zuwa tsawon lokaci ba abinda ya faru shi kake ji, ****** ********* ****** Watarana ya,shigo gida da takardun shi na karba kamar kullun zan shiga mashi dasu daga ciki sai yake ce no dakata ai takardun nakune na tafiyan ku, saudiya, Ban san lokacin dana juyo ba cikin murna nakai mashi ruguma tare da subantar shi ina cewa kai yayana aiko naji dadi nagode, wallahi, sai faman murmshi yakeyi yana jin dadin yadda nake ta faman yabawa, Nasake shi ina cewa amma ni dawa keda wanan sa,an rana haka yaya ? Keda suwa kike son tafiya dama bada sisters dina ba tare na,samo maku sai mama, Naso ibrahim yabiku kada kuyi tafiya babu namiji a tare daku amma kuma har yanzu ba,a samu kujera ba, Nakara rugumay shi nace wayyao yaya ka gama min komai don kafitar dani daga zargi wallahi, Nace wai ashe saudiya na da kwasan manyan bako bana gaskiya yaya ban san irin godiyan da ma zan maka ba,wallahi, Yace in baki sani ba,aini na sani bari anjima kiga irin godiyan zan gwada maki ai,. Dariya kawai nayi tare da kara kankamay shi ina murna da farin ciki sai sambatu nakeyi ina Allah nagode maka Allah yakara daukaka da budi na alheri yaya, Kafin kwana biyu zancen tafiyan mu kowa yaji sai murna ake muna da fatan aje lafiya a dawo lafiya, Su Zarah har ni saida sukaiwa godiya sina cewa sun san nice silar hakan don basu zaci ma zai kaisu ba,a lokaci daya haka,, Muna ta Allah ,Allah lokacin tafiyan mu yayi don an samo wa yaya Ibrahim nashi, Yai tafiyan shi zuwa lagos ya dawo mun tare shi da murna da farin ciki kamar kullun sbai fita ba sai washe gari ya tafi zuwa gaida Umma, Ban bishi ba dontun lokacin da tai muna kuka nan ban kara zuwa gidan ba har yau din nan, tai korafin hakan ta barni, Yasamu nagama girki ya zauna yaci yana wa madina ba,a wai itace tai girkin shiyasa yaji dadin shi, Ina daga zaune gefen shi sai murmushi nake masu don yana kula min da al,amarin yarinyar sosai kamar shiya haife ta, har makarantan boko ya saka min ita na kudi ita da Jidda suke zuwa, Sai da yakare na kawar da kayan nadawo na zauna daga gefen shi remote din tv dake aiki ya dauka ya rage karan tare da juyowa inda nake, Hakan yasa na fahinci magana ce ta musanman yake son yi dani, Yace cikin kura min ido tun kwanaki naso muyi wata magana dake Humaira sai dai ban samu lokaci bane don tafiyan da nayi, Na zuba mashi ido ina kallon shi tare da sauraren shi, yace nasan zaki dauki maganan tawa da wani manufa ta daban, Amma idan kin fahince ni sai kiga maganan ba,wata abin tayar da hankali bane, Ya dan yi shiru tare da numfasawa yasake kura,min ido cikin natsuwa yace bawani abu bane illa zancen auren da nake son in kara kwanan nan, Abinda naji azuciyata yafi karfi akirashi da faduwar gaba sai dai a fili na dake ina sauraren shi batare da,na nuna damuwaba a fili, Nasan ni dake akwai fahintar juna Humaira kan mi a hade yake bamu da,wata matsala a ko wani bangare, Itama wace zata shigo din ba wai karamar yarinya bace nasan tasan takan duniya sosai, shiyasa na yarda da shigowan ta a cikin mu, Don haka ban son kiyi wani tunanen ko ban son ki ne nace zan kara aure ko kuma ki dauki wani abu da tsanani har ki bata tsakanin mu, Kuma ban son kiyi tunanen ko wanine yasani yin wanan auren ban tashi yi ba, kinnsani tun farko ni mutum ne mai ra,ayin hakan, Banyi bane abaya don ina son in maki adalci sai kin samu natsuwa da kwanciyan hankali, a gidana, Hmmm yaya ke nan adalcin may kai min ko kuma kwanciyar hankalin may nasamu in akwai shi a gare ni nuna min in gani, Shiru yayi tare da,dukar da kan shi kasa sai kuma yadago kai yana kallona kara jin haushin shi naji a raina har ban iya boyewa Namike a zafafe nafara tafiya ina cewa nayi dana sani da auren ka Hamza a rayuwana wallahi, Ya maimaita kslman Hamza da nace yace Hamza yau Humaira, nace eh Hamza ko ba sunan ka ke nan ba, Bukatar Umma ya biya ai ban san ta isa ba da tasaka cika mata,burin da tace sai yau tasa ka sakeni saki uku ta zuba ruwa kasa tasha, Mikewa yayi a lokaci daya ran shi a bace ya nuna ni da yar yatsa yana cewa kada ki fara ki zagar min uwa wallahi yanzu ranki zai baci a gidan nan, Naga kina son kawo maganan da zata lalata tsakanin mu don ba zan kyaleki ba idan kika zagar min uwa Humaira, Ki bari mu fahinci al,amarin yadda muka saba saboda kada mutane suyi maki dariya, Ya kalleshi kasa da sama nace mutane ai sun dade da min dariya tunda ba yau kafara watsa min kasa a ido ba, Yau ne aure ka ake min dariya a gida da,waje tunda kai ba dan goyon baya bane wallahi nayi tir da zama acikin ku mutanen da ba,su san arziki ba, Ai kin san bamu da arziki tun farko kika,aure Aisha ,? Nadauka a lokacin ko ku yan mutnci ne ai sai yanzu na fahinci ko ku suwaye, Na tako har gaban shi nace ka,sake kawai ka huta da,wahalana da,akecewa na shanye ka, Yace baki shaye ni din bane Humaira wana ke gani da mutunci in bake ba yafada cikin murmushin takaici, Ya zo ya gwautani ya wuce nasha gaban shi nace wallahi sai ka,sake ni don ba zan zauna akara kawo wace zata sani agaba da,tashi hankali ba, Hankade ni yayi ya fita daga gidan yabarni nan na tsuguna a gurin tare da rushewa da wani irin kuka bai ban tausayi, Bai, madina tazo ta dafani idon ta taf da hawaye tana cewa kiyi hakkuru Anty ki kyale shi don Allah, Rugumota nayi ajikina muka shiga rusa kukan a tare ba mai ba,wani hakkuri sai nice ma nagaji na kyale gudun karnajawa yar mutane ciwo, Bai kara kula harkata,ba nima ban kara bi takan shi basai zaman doya da,manja muka shiga yi, Bai saba ba don haka yahe ya fadawa mama hafsi a,asirce tazo tai min magana ita da anty hindatu, Lokaci guda sukazo lokacin kwana hudu daya fada min zancen auren nashi, Ina ganin su nasan sun san da zancen zaune nake a,falo dagani sai rigar barcin dake a jikina tun safe da zani, Tun shigowan Hindatu tafara cewa may ye haka Aisha may ye kika mayar da kanki haka kamar wata bakauya can, A take idanuwa suka ciki da hawaye nace muryana na,shirin kuka Anty may naiwa Hamza da Umma,arayuwan su suke min wanan azaban haka may ne masu anty, Dafani tati tace kinga idan kina son muyi magana mai kyau tau share hawayen ki ki saurare ni, Don wannan kishi naki yafi kama da irin kishin jahilan mata ba matan da,sukan kan su da addini ba, Ita fa kaddara ai yarda da ita shine sharadi na cikan imanin bawa don komai da kikaga bawa yayi mukadddarine a gare shi, mai kyau da mara kyau sai ka,rugumay ta idan tazo maka, Aisha mayye acikin wanan zance bafa wanan karon bane farkon kishiyar ki, may zai hana ki natsu ki nazarin wacan artabun da kuka sha wancan karon ki san ta ida zaki bullo mashi, Amma kinzo kina wanan irin ta da hankali haka kamar wace bata da,wayo, Don Allah Aisha ki natsu ki kwantar da hankalinki ki fahinci mijin ki ku zauna lafiya kada wace za,a kawo tazo ta samu kuna fitina har ta samu kafar da zata rainaki, Mamahafsi dake gefen mu ta ce ni Aisha na,rasa ina hankalinki da,wayon ki, ya shiga ne wai,, Da har kika rufe ido kinawa mijin ki wanan tujaran cikin nuna,rashi ladabi da tarbiya, Shiru nayi don zancen su ya fara,ratsa,min zuciya nan suka sani gaba da fada da nasiha har saida nasauko, A,karshe suke ce min na yi hakkuri na kara tausar zuciyata sun san hakan akwai zafi amma idan nai hakkuri komai zai wuce Gashi duk mijin ki ya tayar da hankalin shi don kin ki kwantar da hankalin ki ga buki na karasowa saura Sati daya da yan kwanaki, Da sauri na dago kaina nace satifa kikace mama, mama tace eh sati mana bakin ki kwantar da hankalin ki ku fahinci juna da shi ba, Kin ba yan uwan shi da uwar shi dama sun shige maki gaba tare dasu yake aiwatar da shirye shiryen shi an barkina nan kina ta haukan ki ke kadai, Ni don ansan ina,tare dake komai ba,ayi dani Aisha ina dai jin wanda yazo min a kunne na, Mama yanzu ashe har auren yazo ban sani ba mama wallahi hamza ya cuceni yaci amanata wallahi, Don Allah kibar wanan haukan Aisha ki natsu inji hindatu yanzu ki saurari maganan karshe da zaman maki, Idan yadawo tunda ya nemo mii muzo gareki ki kwantar da hankalinki ki fahinci ina ya dosa ta yadda zaki mayar da komai da yan uwan shi keyi a ba,tare da keba,ki nuna masu ke din kin kai komai yaddawo a hannun ki ki wanke kanki, Nan ta fada min duk yadda zanyi har suka tafi bai dawo gidan ba sai dare yadawo, Lokacin muna zaune falo da yarana ina cikin kwaliyan material pink color da,golding, Yarana,munci kwalliya dasu sai wasan su sukeyi a sanyaye yashigo gidan don yasan ba sannu zai samu ba gare ni dan dama a gurin madina in tana falon Amma ga mamakin shi sai yaji ina mashi sannu da zuwa, hakan yadan bashi mamaki maimakon ya shige yadda ya saba sai yadawo falon ya zauna yana wasa da yaran shi, A sanyaye cikin murya mara sanyi nake cewa abinci fa yaya yace cikin murmushi in Rangida tabani zanci mana tunda kun barnimaraya dake da yaran ki Ban bashi amsa ba na shige kitchen na hado mashi, abinci nakawo mashi yana ci ina zaune daga gefen shi yana satar kallona a hankali, Sai da naga yai rabin abincin nake cewa yaushe ne auren naka za,ayi, Dagatar da cibin da zaikai baki yayi yana cewa kin sauko ke nan daga fushin naki, dan gutun murmushi nayi iya fuska kawai, Yace koke fa Humaira yaushe rabon da nagan ki haka duk kin wani hargitsamu ga baki daya kin hanamu shakat a gida nida yara baki dayan, Yau da kikasake koke bakiga gidan naki ya dawo normal ba kamar baya humaira ban son ki tayar da hankaliki akan wanan zancen kamar yadda kikayi, Kin barni a maraya banda abikin shawara dole naje gurin su zarah na nemi shawaran su, Saida na hade yawun takaici tukun nakakaro murmushi ina cewa ai yanzu komai ya wuce sai muyi yadda kace, Sannu a hankali nake tambayan shi yana fada min abubuwan da akeciki ni kuma ina kafa nawa dokar ina rushe nasu, Washegari da safe zaifita inajin zarah ta bugo mai waya sai ya bata ansa dacewa tazo ta samu humaira asan yadda za,ayi, Komay tace mashi sai naji kawai yai murmushi yace nadai ce kuzo gurin ta bashike nan ba,zata baku komai da za,a bukata, Ya juyo inda nake zaune yake cewa Zarah ce zasu zo su samay ki sai ku tsara yadda za,ayi, Nai mashi adawo lafiya har ya kai kofa sai kuma ya dawo inda nake zaune ya dawo ya tsuguna daidai tsawona yana fadin a dai kara hakkuri please, Ban son naganki a damuwa ko kadan idan har kinga nayi ba daidai ba ki nuna min kuskure na nace naji kawai yamike yafita, ****** ********* ****** Sun shigo gidan suna wani hura hanci sai nafito ina ce masu, a sannun ku da zuwa ashe kuna,tafe, Sai wani bina da kallo sukeyi suna yatsunar fuskan su cikin yan harare harare, Saida suka zauna muka gaisa sama sama dasu zarah tace gamu mun zo ance dole sai mun ganki tunda kece shi, Murmushi nayi nace zarah aiko kin ji dadi tunda,kaunar ki ta zama yadda kike so, Wani harara ta bakado min na wasa tace aini wallahi yanzun kifi karfina Aisha nadan rugomo tanace sai anty na, Nan muka wasance naciki na ciki ga kowan dole ba don sun soba muka tsara yadda za,ai komai, a tare, Sai yamma nya,dawo sai dai naga wasu a bayan shi suna shigowa da akwatina har kala biyu ko wani saiti sai kyali yakeyi yi, Ya,sallami yaran yana mazu godiya tare da basu kudi, ya zauna yana cewa yauwa wallahi tun safe muna,sokoto ni da mansur sai yanzu muka dawo komai banci ba tun safe wallahi ina can ina wahala a kanku, Idona akan akwatinan da ya shigo dasu nace nakawo maka abincine yace eh amma yanzu da zan samu abu mai dan ruwa zaifi min nace na hafo maka tea ke nan ko yacd ok abani, Nakawo mai tea din yasha batare da bread ba sai da ya shanye cup din tas, Wanka yashiga yafito akwatinan suna gurin da aka aje su har yanzu yafito saye da,far jallabiya a jikin shi ina dan lalashi mimi dake kuka wai kafanta yana kaikayi, Daga inda yake tsaye a bayan kujera yake cewa Humaira nadago kai da kafan yarinyar a hannu tare da waigowa inda yake yana cewa, Kalli akwatinan nan ki gani ki zabi guda daga ciki guda kuma gobe su Zarah zasu zo su dauka, su tafi dashi ki dauki naki ki sa a dakin kii yanzu, Kamar banji shiba na dauki yarinyata na goya a bayana ta lafe tai shiru a bayan nawa sai barci sai da na sauke ta na shimfide a kujera, Yace min bakiji may nace maki bane Humaira na dago ido kamar zanyi kuka nace naji mana yace tau kiyi hakkuri ki dauki guda daga ciki, Gaban akwatinan na isa na dan kura masu ido na wani dan lokaci naji muryan shi yana cewa duk abugudane aciki kalar akwatinan ne kawai aka banban ta sai na duka na jawo dan kit din mai ruwan milk din dake a gabana a hankali, Yana tsaye yana kallona nafara jan akwatinan a hankali zuwa dakina daga inda yake a tsaye ya dan girgiza kan shi yabini da murmushi har na shige dakina da akwatin ya sauke ajiyar zuciya a hankali, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,, Sosai akai shagalin buki wanda har lokacin ban ma tsaya tambayan ko wacece Amaryan ba sai daren buki nake jin wai wanan Biban ne da ya nema tun farko, Tayi karatu a college of education na Argungu kuma itace tafarko a gurin uwar ta, amma su goma ne a gurin mahaifinta uwar tace mace ta biyu a gidan su, Yan uwan Hamza sai faman rawan kai sukeyi suna zakewa har da cewa yanzu kan an auro masu wayayya don Biba yar gaye ce, Zancen su yana sani cikin tashin hankali amma sai nake dakewa kawai na basar idan kin gan ni zakice ban damu ba don sai shiga nake ina fita, Duk da sabon kayane a dakina amma sai da mama tasa Hamza ya kara gyara min guri, Sabbin set ya sayo min a sokoto masu ruwan fari da purple, set din suna da matukar kyau sosai wallahi, Abin gaba ya kaini don na kwashi nawa nakaiwa Ummi na sai kuma hakan ya jawo wani fitina Umma take cewa wai don may ita ba,a kawo mata ba zaice na kwashe naba uwana, Yace haba Umma don naba mahaifiyar Aisha abu mai nayi idan har kinyi la,akari da irin halarcin da sukai min su, Kudin sune fa nai amfani dashi na nai jarin da ya kaini haka har yau mutanen nan basu yi zancen kudin su da ke kaina ba, Maganan da ya fadi yasa tai shiru don tasan gaskiya ya fada mata ita kuma Ummi taba mama Rahana tsohon wanda na bata da zan dawo sabon gidan mu, A gidan su Ummi ma sai kananan magana akeyi wai na samu guri na mallake Hamza sai abinda nace in bashi nakaya sabbi haka za,ace wai sai ancanza su don kawai na yaudare shi na kawo wa uwata itama tasa ai yana da uwa shi ma mai yasa bai kai mata ba, Kane, kanen da nayi a harkan ba karamin taimaka min yayi ba don duk wanda ya ganni zai dauka ban kishi komai, sai dai na kasa na kasa, don zuciya ta a,tashe yake, Ko da za,ai auren Sadiya ban ji irin yadda nake ji a yanzu ba ko dan na kara girma ne, duk da maigidan yana iya kokarin shi gurin ganin bai kuntata min ba a harkan auren nashi, Duk abinda nace sai dai yace min tau kawai ya bayar ayi koda baiyi niyayya ba, Hakan yasa kowa na yabawa da hanakalina amma duk da haka ban ganin farin shi kai kishi dai kumallon mata ne kawai, sai hakkuri, Yan kawo amarya suka shigo da gudan su, sai shewa sukeyi Allah yasa ina cikin kawaye da yan uwa da abokan arziki har makwabata dan nayi sabbin abokai matan abokan shi sun cika min daki, Muna zaune tab a dakina ina cikin wani irin rantsatse lace da hindatu ta sa aka kawo min daga lagos, mai ruwan purple da stones farare sai shinning nakeyi zakace ko nice amaryan , Abinda ya daure min kai shine duk wace ta ga amarya sai ta dawo dakina tana fadin kai namiji dai kabarshi kawai wallahi, ni dai ban san abinda suka gani ba, Sai da aka kawo ta dakina wai an kawo ta ai muna fada irin na al,ada da akasaba yi idan an kawo amarya, Matar dake magana tace tau Aisha yau ga Habiba nan mun kawo ta zama a cikin ku, ance zomu zauna zo mu saba sai kuyi hakkuri da junan ku kujewa zagar makiya, Babba ya rike girman shi karami kuma ya tsaya a matsayin shi, sai a zauna lafiya, Sai bin dakina suke da kallo da ajiyan zuciya don sin san na zarce mata matar take cewa ina uwargidan take ne wai Hindatu tace ga tana tare da dan tabani duk sukayo idanuwan su a kaina caaaa, Sai matar tace Ummm lalai to kuyi hakkuri kinji ga amanar ya ta nan mun baki keda mijin ki, A,a mama iniji hindatu idan kunbata amana to ita Aisha a,wa za a bar amanan ta a dai bawa juna amanan su azauna lafiya shike nan, Suka fita zuwa dakin su tun a kofana suke cewa lalai akwai magana wanan ce uwargidan ai kamar ma Biba ta girmay ta nake gani shine akace har diyan ta biyu, Wasu kuma suna cewa wai yar inace halan don basu sanni ba a garin sai akace masu yar sokoto ce o lalai kuwa, A daki na kuma su Hindatu da sauran abokai cewa sukayi kiyi hakkuri Aisha wanan matar da kike gani a tsaye take dubi ko mayafi bata yafa ba a kai kamar amarya, wai ita wayayya ki yi hakkuri ki hidimar ki kawai, , Shi kuma mijinki ki kara mutunta shi fiye da da don ki karawa kan ki girma a idon shi ki kula da yan yaran ki, Muna jin suna cewa Habiba badi war haka muzo bukin yan biyu maza masu kama da uban su, Daya bayan daya mutane suka fara watsewa a gida har aka bar mu saura i mu kadai a gidan amarya tana dakin ta nima ina nawa da yara na da madina, Madina kamar wata babba tun fitar jama,a ta gyara min daki yakara komawa tsab dashi tasa muna kamshi, Sai zuwa sha daya da wani abu ya shigo gidan da alamar gajiya a jikin shi ya na dauke da leda guda biyu a hannun shi muna mashi sannu da zuwa dagani har madina, Madina ya mikawa dayan ledan da ya,shigo dashi, sai ya dan duka ya na taba mimi dake barci ya dago yana ce min ya gajiya Rangida, Lafiya kawai nace mashi tare da dukar da kaina muryan shi naji yana cewa ni zan kwanta sai da safe ke nan Allah bamu Alheri nace mai, Ya juya yana tafiya a hankali yabar dakin nacewa madina rufe muna kofan mu kinji, nace mata bayan ta rufe kofan bude kuci abinda ke ciki sai kun koshi, Tashi nayi na fara cire kayan dake a jikina a zuciya ta ina tunanen yadda zai yi idan ya shiga dakin, Yaran suna hiran su da dariya suna cin naman su da juice niko sai tunane nake yanzun haka kilama Hamza ya gama afkawa amarya ko don nasan shi kamar zaki yake a gurin mace, Har yaran sukai barci ni ina zaune sai faman tunane nake nikadai ina juyi cikin bacin rai sai tsakar dare barci ya dan kwashe ni, Washe gari tun da safe na farka na hada break fast mai lafiya basu fito ba har wani lokaci kofan ta yana a rufe, Har na koma daki na shirya jikina na dan kwanta don nahuta ga kuma bashin barci a kaina, Barci yadan fara daukana naji shigowan shi dakin sai kamshi yake yai kwaliya da shadda mai ruwan makuba, Daga inda nake kwance na dan bude idanuwa na na kalleshi duk da shigar tashi tai min kyau amma sai naga yai min wani baki a idona, Har inda nake kwance ya tako ya dan manna goshin shi da nawa yana cewa antashi lafiya ina dan kaucewa nake cewa Alhamdullahi, Yace abinci fa naga kin aje a dinning kifito muci mana nadan bata fuskana ina cewa ni a koshe nake bazan ci ba, Mikewa yayi yana cewa may kikaci halan ki taso muci ina son muyi magana da ku ne, Shi yafara fita alokacin Biba tana tsaye daga kofa tana kallon kofan dakina don taga ya dade aciki a ran ta, Bai wani jima da fita ba nafito daga dakin ina saye da Arabian gown baki daga gefen kafadun shi an mashi adon light blue color da stones, na daura dan kwalin shi a kaina gashina dana tufke yafito taba da ribon din da na daure kaina, Sun zauna ko da nafito sai dai ina fitowa naji shi yana ce mata zauna daga can ya nuna mata dayan kujeran da ke daga gefen shi, Nima da nazo a dayan dake fuskantar ta na zauna muka sa shi a tsakiya, Banyi nauyi ba gurin fara bude kulan abincin dake a saman tebur din pepper soup ne na kayan cikin rago sai dankalin turawa da kwai sai kayan shayi a tsakiya, Na dan dago ina ce masu bissimillah ko tana duke da kanta tana jagular wayan ta dake hannun ta fuskan ta a,daure yake tamau, Shike fadin a,a zuba min mana tunda ban saba zubawa ksina ba da can, nace cikin murmushi amarya ki fara aikin ki ki zubawa maigida abinci yaci, Ta wani dago kai kamar mai fada tace bake yace ki zuba mai ba, dan kallon shi nayi sai naga yai murmushi yace zuba min kawai Humaira, Umurnin shi nabi na zuba mai abincin ba bata lokaci ya fara cin abincin hankali a kwance har lokacin Biba kanta na akan wayar ta kamar bazataci ba dan kadan na zuba a plate nima na faraci a hankali , Ko may tagani tagani ta jawo plate tazuba itama tafara ci zan iya cew duk tafi mu cin abincin tun a lokaci na fahinci tana da ci sosai tsab nai mata kallon kyau baka ce wuluk da ita,doguwa mai dogon fuska da pinpurs, Duk da tayi makeup a fuskan ta bai hana kurajen fuskan ta fitowa ba a lokacin, Sai da yagama ya goge bakinshi tsab har lokacin Biba cin abinci takeyi ya dan yi gyaran murya abinda yasa kowan mu natsuwa ke nan, Yace am da,farko dai zance na godewa,Allah da,ya hada rayuwan a gurin guda don kasancewan mu a tare, Don haka ina son ku saurare ni da kyau kuji may zan fada maku, Humaira, Sai nadago kai na,kalleshi yace ke ce babba zan ce zamu baki hakkuri akan ku zauna lafiya, a gidan nan da bakuwar ki, Ki sani ke ma,Biba ki sani, cewa bawai ban son mata na bace ko tai min wani laifi ko gazawa na auro ki, A,a ra,ayinane kawai na son zama da mata biyu a gidana don haka ina fatan zan samu zaman lafiya a gurin ku kamar yadda nake fatan samu, Don zaman lafiyan ku a gidan nan shine kwanciyan hankali da cigaban rayuwa ta, Amma in kuna fitina a tsakanin ku gaskiya daukan mataki akan duk wacce takawo min tashi hankali a gida, Don haka ina fatan zaku kasance masu biyayya a junan ku ku kawar da,duk wani kishi ko tsegumi kuyi zaman lafiya don kun sani ni ba mazauni gida,bane, Sai zancen kwana ina son ku raba a tsakanin ku duk yadda kuka raba is ok for me, Dafatan zan samu yadda nake so a gurin ku a zauna lafiya, Gaba dayan mu shiru mukayi ba wacce tace uffan daga cikin mu sai shine yakawar dashirun da cewa umhumm ina sauren ku ne fa don fita zanyi, zuwa kauye yanzu duban wani gona na, Biba ce tace why not muyi kwana bibiyu kamar yadda akeyi juyawa yayi inda nake yana cewa madam hakan yai maki ko ? Nace ba matsala,Allah ya sa mu dace, yace amin sai ga mimi ta shigo tanufi gurin shi nan hankalin shi ya,dauke akan yarinyar, sai biyewa shirmay ta yake suna hira tana dan tataba mashi jiki, Biba tace cikin wata murya shike nan zan iya tafiya, ko? Yace fuska a daure ki tafi mana angama ai da fatan zaku kiyayye dokana , Naji kawai tace tamike zuwa dakin ta nabita da kallo doguwa ce ta sosai bata da baya don zan iya cewa da gaban ta da,baya duk dayane, Ajiyan zuciya na,sauke koda na dago kai yana kallona yace yaya dai na iya zabe ko, Murmushi nayi nace kwarai kuwa yace nasan itace zatai daidai da,ke shiyasa na zabe ta Baki na tabe nace zaku daiyi daidai kai da,take matar ka nikan may ye nawa a,ciki, Yar dariya yayi yace Rangida ke nan bazaki fahince ni ba ke nace kwarai kuwa, Mikewa nayi don na hada kayan dake gabana sai naji kida ya fara tashi a dakin Biba, a,raina nace wata sabuwa kuma sai mimi dake gefen shi tafara rawa nace matsala Allah ya,cece ni da,yara na wanan sabon akidar, Wasu yan matane suka,shigo gida sama sama muka,gai sa dasu suka,shige dakin Biba sai shewa mukaji suna tafawa kitchen na tafi donkai kayan da mukaci abinci dasu, Shima dakin shi da aka,gyara ya shiga ina fitowa muka hade daidai lokacin da sukai wani shewa da,tafawa suna cewa, sai ke ta Hamza yaro, guda daya,ba bari ba aci gaba da gashi kawai muna kallo, Kallon juna mukayi dashi don mun fahinci zance sukai akan kwanan ta,da Hamza, Shigewa,nayi ina cewa sai ka,dawo ban tsanmanin ya,amsa ba don banji ba, Da rana ma nice na girka muna abincin rana ga baki yan ganin amarya suna,tashigowa gidan, Da,dare ma,a gajiye nake don girkin da nai muna na tuwon shinkafa da miyar agushi da naman shanu, Sai farfesun da,na,sake hadawa nai mai hadi sosai don dai amarya da,ango suci Bai dawo da,wuri ba, don haka,na zauna yarana mukaci muka koshi ina dan hira dasu don na,ragewa kaina damuwa, Anan yasamay mu a kasan kafet mun zube muna kwasan girkin mu hankali kwace ina cikin kwalliyan atamfa super, Yazauna gab damu yana cewa wassh Allah na sanu mukai mashi mukaci gaba da cin abincin mu yana bina da kallon shaawa nai kamar ban san yanayi ba, Nawa abincin fa naga kina ci da yanki ke nace bari amaryan ka tafito ta,zuba ma kada,na kara laifi, Sai gata,tafito cikin wani dogon riga baka kamar karan dawa, tsololo da ita a cikin rigar, Tsayawa tayi tana kallon mu kwaliyar da nayi ne ya,tsone mata ido ita da,take amarya ya dace tayi amma sai gani ni na tsala kwalliya na tsab, Hamza ya daga kai ya kalleta yana cewa zubo min abinci naci, Tace mai anan zakaci ko yaya,? Yace a ina zanci dama,? Zuwa,tayi saman table ta,debo mashi ta kawo mai tagirke a gaban shi tajuya ta,debo nata zauna sai da,ta cinye plate din ta sha ferfesup din, tai kat, Na,kwashe kayan da mukaci abinci nashiga dasu nabar su nan falo zuwa wani dan lokaci suka shige daki, Da safe ban fito ba don na,tanadarwa yaran abinda zasu tafi dashi makaran ta dasafe dama, Barci nayi sosai ni da mimi sai wani lokaci na,farka,nai mata wanka nima,nayi na,shirya,na fito waje, don mu samu abinda zamu ci, Samu nayi kayan da akaci abin dare ma ba a,wanke su ba sai da na,dora girkin abinda zamu ci na,wanke kayan, Muna falo mun karyawa nida mimi sai ga Biba tafito tana wani yatsune fuska take cewa Aisha baki girka muna abin kari bane yau har My yafita bai karya, Na dago kaina ce Allah ? Wake da hakkin bashi abinci bake ba don may baki fito kika girka mai ba ? Au kishin naki ashe har yakai ki fara yi min rowan abincin gidan naki dakike cewa gidan ki ne, Murmushi kawai nai mata nace aiko gidanane don gidan mijina ne nan, Jinan bakin ki ya,saba da fadin mijin mu don yanzu ko baki so dole muyi sharing din shi ni dake a gidan nan don haka sunan gidan naki da kike fadi ta,saba da fadin gidan mu, Kuma bari kiji wanan bakin kwalliyan da kikeyi don satan hankalin shi, gara ma ki daina don da yana da amfani a,gare ki da baije gurina ba ya dauko, Murmushi nayi nace ya,dauko ki ko kin matsa mai a,rayuwa ba,dare ba,rana kina rokon shi ya aureki, Kadafa kiga kamar kin shigo kiyi tunanen wai daya,muke dake a gidan nan na girgiza kaina nace har abada,ba daya muke ba biba don sawun giwa yafi gaban na kurawa, Amma,bazaki gane ba sai in mun zuba ni dake a gidan nan zaki fahince ni, don haka,duk abinda kike takamar kin shigo dashi daidai nake dake a,gidan nan don ni kujera ce daidai da na mai hawan shi, Hakakikace tafadi a hasale ke har mace ce Aisha nafasan komai don Umma ta,fadamin ke din bashi akayi , Niko shi yaganni yace yana so na nace a haka,din yace yana,son ki tace a haka din kuwa, Nace to yanzu sai agani da yar sadaka da matar zabe ko wa zataiyi winning a gidan nan, A tunda kin iya bin bokaye da malamai ki raba shi da,uwarshi da yan uwan shi haka zakice to ni nan ban shigo gareki ba,sai dana,shirya maki sosai , Na ce ashe kin san wacce zaki sama din duk da yar sadakace sai anshirya ma,shigan ta, Muzuba dake banza kawai stupid ,,, Nace ashe baturiya,ce aka dauko ban sani ba zamu sha turanci ke nan, Ta kada hannayen ta tace ni ba kamar waccan garar kishiyar taki da kika fitar bane da makircin ki Aisha ki dubeni da,kyau ki gani nafi karfin ki, Nace damay fa da, shigar samudawa ko da,shigar fatalli, Zaki gane kuren ki wallahi don kina ganin Hamza zaki barshi dani a gidan nan nace tau ai saukin abin Allah yafiki, ko, Tashige kitchen don neman abinda zataci tanata jinini da zage zage har tagama tafito, Tun ranan muka,fara zaman kwari a gidan da ita ko sati daya,batayi ba,dashigowa, ****** ********* ****** Tana da kwana hudu da shigowa yace daren yace mu shirya muje gaida Umma gidan ta, Gabadayan mu minyi kwalliya nida yarana,sai kamshi mukeyi koda muka fito ta kalleni sai ta tsargi kan ta, da sauri naga ta fita zuwa, waje yana bayan ta dauke da mimi, Gaban mota tabude tashige nafito ina tako daidaya har na iso gurin motan rike da hannun jidda madina tana bayana, Yana ganin ta a gaban motan yace cikin daure fuskan shi, yace, ke fito ki ba Humaira guri ta zauna nan dago kai tayi tana kallon shi kamar zatai magana sai kuma tai shiru ta bude motar tafita, Maimakon ta,shiga baya sai naga kawai ta juya ta shige gida, shiko hankalin shi naga mimi da yake ajewa a saman sit, Sai da,yajuya,don yaga yadda,suka zauna sai yaga bata cikin motan fita yayi a,fusace ya bi bayan ta, Ya,samu ta cire gyalen ta ta,kwanta yake cewa may kike nufi Biba ? Ta dago fuska a murtuke tana cewa kai dai zance may kake nufi kana nufin zaka fifita matarkane a kaina, Kai har kana da matar da zakace wai na fita a gaban mota na bata guri har i a matar take mace kamar babyn roba, Oh shine kikazo dashi ashe na fifitaki a kan ta kiji dadi don kina yar son kai ko,? To bari kiji kin dai san sharadin da nai maki kafin na,aure ki, wallahi inkizo ne don ki jagula min zaman lafiyan gida na,ashirye nake da na dauki mataki yanzun nan don bazan lamunci rainin hankali a mace ba , Ke yanzu din baki da hankali sai nasa ki a gaban mota Humaira tana baya akan kina yar gwal ko may, Kuma bari kiji wallahi har in baki fito muka tafi ba yanzu sai dai yau ki kwana a gidan ku, Yajuya fita dakin a fusace alokacin har nai shawaran nafito kawai na koma ciki nima don har na hau zuciya, Sai naganshi yafito da saurin shi itama gani nayi ta biyo shi, a baya a raina nace Allah kadai yasan irin lalashi da,yai mata tafito, Har muka kai gidan Umma ba wanda yai magana a cikin mu sai da mukafita muka shiga gidan, Suna dakunan su muka fara shiga gurin Umma tana ganin mu tafara washe baki tana cewa maraba da Biba yar albarka harkin fara fitowa ashe, Hankalin ya gaba daya yana a,gurin biba sai sabari takeyi da farin cikin ganin ta, tana faman gyara mata inda zata zauna, Nice nace Umma ina wuni daga gefen da naiwa kaina mazauni, cikin dan murya ta amsa min, Tajuya gurin shi tana cewa kokai fa Baba na bagashi gida ya cika ba yanzu injin kuna lafiya dai ba wani izza ko ikon da,ake gwada maki, Murmushi tayi tace lafiya muke Umma mun samay ku lafiya cikin murmushi tace lafiya lau yar albarka sanni kinji, Shima maigidan gaisheta yayi tare da tambayan lafiyan su suka dan fara hira a tsakanin su , Mikewa nayi ina cewa bari na,gaida mama dakin ta inda Biba take ya kalla yace tashi kuje mana, Ta mike tabiyo ni simi simi a,takure mun samu mama tana kidayan kudi tana ganin mu taji dadi duk ta rasa inda zata samu, Mun gaida ita ko minti uku Biba batayi ba tafito nikan na zauna saman katifan mama dake yashe a,kasa muka fara hira da ita, Take tambayana babu dai matsalar komai ko nai yar dariya nace babu komai mama tace wajen ita kisharya taki fa,don nagan ta a,tsatsaye, Nace ita tasani na kwshe yadda mukayi da ita da zamu fito na fada mata mamatace, Shiyasa nace ki kwantar da hankaliki kibi mijinki da kina,nan kina bori da yanzu ta samu kafar rainaki yadda taso don wanan da kike gani akwai aki saikin jajirce mata sosai za,a zauna lafiya, Sai da ya dauki lokaci yashigo dakin mama yasamay mu a nan lokacin har yaran sun fara barci, A dakin Umma kuma Umma ke tambayan Biba in ban mata wani abin take cewa ba komai sai dai shi dake nuna fifici a kaina, Umma tace tayi hakkuri zatai mashi magana zai daina kuma kada ki fara ki dagawa Aisha kafa don ba karamar makira bace, Biba tace ai nagani Umma don ko yanzu saida muka kwasa nice da,girki amma wai sai itace zata zauna a gaban mota, tace wanan ma fadine wallahi bari yazo dashi da ita zanci masu mutunci yanzu kuwa, Min fito zamu wuce muka,shiga sallaman Umma sai cewa tayi babana wallahi kaji tsoron Allah kada ka kama cin zalun yar mutane akan wanan makirar matar taka,. Umma may akayi kuma yake tambayan ta tare da duban Biba dake zaune a gefe idon ta da alamar tayi kuka, Ban sani ba tace ban sani ba don may yarinya itace da girki zakace sai wata ta zauna a gaban mota tabarta, Umma wallahi wallahi bazan wa Humaira wulakanci akan wata ba don nayi sabon aure, Idan ma,takawo karanane tasani bazata,sa na,wulakanta matata akan ta ba,dama,dashi tazo Da take son shigowa inane bata tafi ba tana rokon na aure ta kece fa kika,tursasa min nai wanan auren, Kai ya isa haka don naga kazama,wani zarare akan matar ka zamu hadu, Ko banza naji abinda,ban sani ba akan Biba dake cewa ni bashi akayi sadaka ashe itama sai da kamun kafa tashigo gidan, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,,,,, Kamar yadda muka tafi da farko haka muka dawo bai mai magana a motan sai yaran ke dan magana jefi jefi, Yatsaya bakin shago yai muna sayayya muna zaune cikin mota ba wace tai magana daga cikin mu, Wallahi yarinya dani kike wasa in har kince baki bari na more mijina yadda nake so nikuma nai alkawarin hanaku zaman lafiya, Murmushi nayi nace gyara dai kalamin ki kice mijin mu don kin san yana da iyali kika shigo don haka kin makara da kina son more miji sai kije ki auri mara mata ki more ke kadai yadda kike so amma anan ba daman hakan, Kuma,baki so more miji ba don hanyan da kika dauko wa kanki ba mai dorewa bane gareki, Tace cikin kuta haka kikace nace kwarai da gaske kuwa don, bai kaiki ko ko ina a hakan, Shiya shigo motan daidai tana kutawa a she yafada a kunnen shi juyowa yayi da sauri yana kallonta a bayan motan, A hasale ya ganta ya juya inda nake fuskana da mirmushi kawai yadda ya fisgi motan yasani gane a cikin fushi yake, Mun shiga gida Madina ta kwaso ledojin a hannun ta na nufi dakina sai naji yana fadi Madina aje karamin ledan kikaiwa antyn ki babban ledan dakin ku, Da,shiga na dakin nafara cire kwaliya na zuciyata tana tukakin abin da Umma tai muna sai dai yaya zanyi haka Allah ya nufe ni da gani, Muryan Biba na dinga ji gata dai siririyace amma muryan ta tankar na ganga tana cewa wallahi ni bazan yarda ba ko yau she ka dinga fifita matar ka a kaina ni may kake nufi dani ne wai a gidan nan, Kaimin wullakanci da zamu fita yanzu ma kuma bai ishe ka ba sai ka nuna mata fifiko kace wai akai mata,babban leda a,dakin ta, Yace nakai mata daya kuke halan yara nawa ke gareta adakin dazakice dole komai abaku iri guda, Kai dai kawai kace macucine kai baka iya adalci a tsakanin mu sai ka nuna banbanci, Yace wallahi Biba tun ranan da kika shigo nai bakin ciki da,auren ki may nagane akan auren ki banza kawai don kin samu nasawa zuciyata hakkuri a kanki har kinga,wurin zagina a macuci, Akwai macuciyar da ta,wuce ki sai da kika gama watsar da kanki a titi kuka yaudareni ke da dan uwanki na kwaso ki ashe honko kike ban sani ba, Shiru tayi da taji ya fadi hakan yace, wallahi Biba ki shiga hankalinki ki barni da abinda nake ji a,raina, don kika kara kai karana gurin mahaifiyana ko wani zaki barmin gidana, Don dama hakkuri nayi na,taushe zuciya ta akanki matata budurwa na,aure ta kamar ki amma ke ashe bazawarar boye ce ban sani ba, Gidana muna da siri ysakani da matata ba mai sanin may muke ciki amma ke duk kwana hudu da,shigowan ki kin fara tarwatsa min farincikina, Har ya gama zancen shi banji muryan Biba ba kuma sai sbirun da naji yayi bai kara magana ba, Karan rufe kofofin su naji hakan yasani cewa Madina rufe muna kofa kinji kaunata, Washe gari na tashi naiwa yara breakfast na hado nawa dana mimi na shiga dashi daki na saya kofana muka koma muka kwanta abin mu, Cikin barci naji muryan shi yana cewa bakuyi abin karyawa bane agidan nan, Na bude idanuwana da sukai min nauyi dakyat ina cewa, cikin fuska mara walwala, Ina kwana yaya, Yace lafiya kalau ya kwanan yaran nace Alhamdullahi, sun tafi makaranta, Yakara cewa nace babu abin karyawa ne a gidan ina son in fita ne don akwai inda zani, Ka manta cewa matarka ce keda alhakin hakan a kanka bani ba, Ki fito ki bani abin karyawa na fita zani daji ne, maimakon na tashi sai na mike zaune ina cewa haba yaya, yaya kake son nayi ne wai matar nan taka fa,batazo da zanan lafiya a gidan nan ba, Yaya zan fita na girka ma abinci bayan itace da alhakin ba ka na girka kuma ta kirani da azzaluma, Ni wallahi wanan abin ya isheni ya isheni wallahi sai na,sa mashi kuka cikin dan kukan da nakeyi nace ko ina ba dadi ga matsalar Umma ga nata,dawani kake son naji a raina, Kuka nake mai tsanani saboda bakin cikin da ua isheni a,raina yace kiyi hakkuri Humaira nima wanan abin ya koma min ciki yanzu, Biyaygan Ummace da suka sakani a gaba kan sai na kara aure kuma na auri Biba wacce ko yaushe tana gurin Umma ita da yan uwan ta, Yace Humaira ban fayi maki komaiba Humaira ban kuma zalunce ki ba akan auren nan bakuma zan zalunce kiba, Saboda banyi aure don na gundura dake ba ko kin isheni ni ba nayine kawai don ina son hakan da kuma biyayya, don shi yin aure ai ba laifi bane a gurin Allah, Ina da halin da zan kar aure a rayuwana don godewa ni,imar da Allah yai min, Don Allah na roki alfarman ki kada ki biyewa wanan yarinyar kucutar dani a rayuwana, kada kiyi min abinda kika san can da bakiyi min, Karki bi ta nata ki azaban tani ni da diyana akan zancen ta zan hakkura da komai amma banda wanan hanyan hanani samun natsuwa a gurin ki, Ki dan yi hakkuri dani kadan nayi maki alkawarin zanyi mai yawa akan ki, Idan kika dan kawar min da kai kikayi man kawaici na miki alkawarin zanji kunyarki in kuma yita girmamaki a gaban kowa saboda dama ke din maigirma ce da,daraja a gurina, Yace don haka tashi muje ki bani abinci naci na fita kada na makara , Nace idan na baka zai zama matsala a tsakanin mu don bani ce ya dace nabaka ba din, Hummm yanzu kina ganin idan kun azabantar dani da yunwa akwai wani riba a hakan ke nan yadda kika fara bani abin karaya da,farko kici gaba da yi muna har,sati matsayin ina,gidan, Ya kamata ki yarda cewa kin fi Biba daraja a gurina son kin san darajana da zafina fiye da kowa a duniyan nan, Duk da nina ajeku gaba dayan ku nasan halin kowan ku yanzu kuma kin san ina gudun bacin ranki don ina tsoro naga fushiki saboda fushi ki gareni don matsalane fushiki a gareni, Ina yin komai ko barin komai, don neman zaman lafiya dake Humaira don haka na rokeki karkiyi amfani da damar da Allah ya baki a kaina ki kuntatawa rayuwa na, ki hanani more halal di na akan ki, Kalamun shi, sun sani samun natsuwa namike a hankali daga kan gadon na dauki kayan break din dana hadamuna ni da mimi nakai mashi falo na aje na,dawo dakina na kara kwantawa, rai a bace , Sai da ya shirya ya shiga dakin Biba dake kwance tayi dai dai bisa gado kafa a,ware tana kwasan barcin ta hankali a kwance kanta babu komai, gashi jefi jefi tsaki yayi yace ke ni zan fita ta dago tana wani mika Yai tsaki ya juya yafita har ta kai kofa take cewa ina son zuwa gida fa yau don na,dubo su kina ko da hankali Biba ko fa sati bakiyi ba a gidan nan, To shine may ba gidan mu zan tafi ba yace lokacin da ya fara tafiya ban yarda,ba don ni ban son mace mai yawo a rayuwana, Sai zuwa yamma ya,dawo yake fadin shi zaiyi tafiya ne a yaudin ina jin suna fitina akan wai ko sati batayi ba zaice zai tafi tafiya, Yace idan na zauna banyi tafiya ba ke zamuci ko kuwa may kike so nayi tunfarko kin san ni ba mai zama bane a gida don haka yanzun ma baki isa ki hanani ba, don haka kada ko fara,ki fita bada izini na ba agidan nan, kuma har inkin fita zan ji a gurin makwabtana don nasa security akan gida na, idan ban nan ko ban gari nasan shige da ficen kowa a gidan nan, Da zai tafi nake ce mai ina son ranan sati naje gaida su Ummi yace min sai kin dawo amma a kira Ibrahim ya kaiki don ban son hawa masshi kin sani, Yaba ko wacen mu dan abinda zata rika a hannun ta kafin ya dawo ya kuma,bani na zuwa school din yara, ****** ********* ****** Na shirya ranan Sati na tafi gidan mu wanda nakai kusan wata daya rabon da naje na gaishe su da zan tafi kowacen su saida na daukar mata dan tsaraban da zan kai mata da dan kudi a jakata, Nasamay su zaune suna cin dumamayn tuwo a guri daya sun tare ni da fara,an su kamar babu hassada a ran su, Sunyi murna da gani na nashiga dakin Ummi na cire hijjab dina nafito kayan wanke wanken da na samu a gurin wanke wanke nafara tattara na wanke sai albarka suke saka min , Sai da na gama na shiga dakin Ummi na dauko masu tsaraban da nazo masu dashi nakaiwa kowa dakin ta nan suka shiga godiya da samin albarka, Gidan Mama Rahana na,shirya na tafi inda tai min nasiha akan na zauna lafiya da kowa a duniya don duniyan gaba daya ba komai bane a gurin Allah, Da zamu dawone naga Sa,adatu muka gaisa amma ban shiga ba tashiga tana cewa Umma ina nan cikin uguwar taga na shigo, Umma ta zaci zan shigo yadda na saba ta shirya abinda zata fada min sai taji shiru har wani lokaci ban shigo Da yamma nayi sallah la,asar naji muryan Baba ya shigo na tafi na gaida shi yaji dadin ganin mu yake cewa tafiya dai ya kusa ko nace insha Allahu Baba yace ikon Allah, Sai ki kara hakkuri akan wanda kikeyi Aisha don shi rayuwan duniya nan babu komai a cikin shi sai rikici amma idan ka dauke ta da sauki sai abin yazo maka a cikin sauki, Da kin bi ta uwar mijiki da ta sakaki a gaba kinyi fushin zuciya kince ki bar gidan da yanzu kin yi hasaran wanan makkan taki koda yake shi bawa ba,a gama halittanshi ba sai ranan da ya mutu, Kullun shi nake lurar da yaran nan amma sunki fahinta na sai busar duniya suke suna shakar ta, Nan yai min nasiha nai ta godiya da zan bar gurin shi na kawo kudi dubu goma na,bashi sai samun albarka yake yi, Na dawo dakin Ummi na nasamu tagyara daki kai Ummina har yanzu dai wanan tsabtar taki tana nan a she, Tace to haka kawai mutum da lafiyan shi yai ta zama a cikin kazanta hakane kawai zan yi na godewa Allah na, Tace Aisha dama ina son ganin ki sai dai hakan bai samu ba saboda ba halin naje gurin a lokacin da ake shirin maki kishiya, Jikina a sanyaye na dago kai ina kallon ta cikin natsuwa da sauraren ta, Tace ta ya kuke a gidan an kuma,watse lafiya ko ? Nace Alhamdullahi Ummi komai lafiya kalau, kuma duk lafiya,muke tace Allah yai maki Albarka Aisha, Allah ya saka maki da,alherin sa, Ya kuma baki hakkuri da juriya rike girman da ya baki nace amin Ummi tace ina nan ina ta fargaban kada ki kasa dauriya akan zarabawan da Allah yakawo maki, Nace Ummo kamar kin sani don wanan fitinar ta kamar ma zai shaye na sadiya wallahi don tun tana da kwana biyu aka soma, Ummi tace fita ba tun ta,kima harkokin ki kada ma ki sata a ranki mayar da ita,bakima san tana gidan ba ki kawar da idon ki ga duk a kan al,amarin su, Idan kiyi haka,sai kiga kamar yanzu komai ya suce anzama daya a gidan Ke dai kada ki rika kokarin shiga tsakanin su babu ruwan ki da sha,anin su kiyi kokarin kare mutunci ki kawai a,gare su baki daya, Don haka yafi a ce kin damu da matsalar su kedai kawai taki dashi ne kawai zai hada ku, Shiru Ummi tayi sai kuma tanisa tace kishi zafi gare shi Aisha in baka,kai zuciya nisa ba sai ka gudu kabar ladan ka a banza wata ta kwashe, Nace wallahi Ummi hakane don har na fara,biyewa son zuciyana da farko amma da na zauna nai la,akari sai naga kawai naba kaina hakkuri, Tace ki godewa Allah da ya yakince maki shedan a zuciyar ki inkiyi haka ubangiji zai doraki a kan ta , Nan Ummi ta zauna ta dinga bani shawara irin na wanda yafika sanin duniya da mutanen cikin ta Shawaran Ummi sun min dadi a rai don dama har yanzu bakin Hamza nake gani a zuciyata don kwata kwata,yafita min azuciya ta dama dakewa kawai nake dashi a gidan, Ummi tai dariya tace kai Aisha may yai maki haka har ya sure maki baki daya yayan naki keda dan uwan ki don hamza tankar dan uwa yake a gurin ki ba miji kawai ba, Nace ni fa Ummi ko da yake cewa wai harda biyayya yasa shi yin wanan auren ban fa yarda ba don nasan da ra,ayin shi, Shiyasa ma har na yanke shawaran na kama kaina dashi kawai na fita batun shi nabar shi da amaeyan shi sukarata can, Hmmm aiko dakinyi haka da baki mashi adalci ba wallahi har da muma na tare dake nace Ummi harda kefa kikace tace kwarai kuwa, Kina ganin inkiyi haka akwai wani sauran zaman lafiya ke nan a tsakanin ku, kwanciyar hankalin ki fa Aisha shine nawa, da "ya"yan ki, Nina san babu macen da Hamza zai auro a gidan shi yafita batun ki don ko da yanayi da tun akan auren Sadiya yayi maki, Nan taita kawo min irin mutuncin da nace yai min tace kina ganin da,watace zai iya cewa yarinyar tafita a gaban mota tabaki guri ki zauna a gaba tare dashi, Allah kadai yasan namijin kokarin da yayi gurin yi maki wanan yakin ga kuma uwar ku iri n yadda yai mata saboda taso aci maki mutunci tun farko, Mun yini a gida sai da magariba na koma gida nazo wa yara da abinci don nasan ba lalai bane mu samu abinci a gida, Mun shigo muna sallama amma,batafito ba duk da,dazan tafi saida nai mata sallama cewa, mu zamu gida mu, mu gaida su,,, A haka mukai ta zama ni da ita a gida kowa yana sha,anin shi ba ruwan wani da wani kowa harkan gaban shi kawai yake yi, Ya bugo min waya,kaman yadda ya saba cewan yana tafe banda gobe don haka nasan nice zan karbeshi sai na hau shirin tariyar shi, Ban ga tana wani shiri yadda muka saba ba sai al,amarin shirmayn tara kawaye da takeyi ai ta ihu da sowa a dakin, Nai girki na gyara gida tsab don itama irin Sadiyace bata aikin komai a tsakar gida Madina ce mai gyaran main falo din gida duk yamma, da sauran part din gidan, Shigowan dare yai muna ina zaune falo da yara mukaji ana,shigowa da kaya bai samu shigowa,ba yana waje na tura Madina ta fada mata maigidan yadawo, Madina na,shiga dakin tace ke may yakawo ki dakina ko kin zo zuba min barbadin maganin da kuka saba yi ne, Madina tace Antyna tace nazo na fada maki cewa wai baban Jidda ya dawo, Tace yadawo cikin mamaki to tafi naji tace wa yarinyar tafito tana ce min wai taji tace, Ya shigo yana saye da yan kanan kaya ta maza a jikin shi tieshirt fara da bakar wando sai kamshi yakeyi ya koma kaman saurayin da bai taba yin aure ba, Sai faman sannu da zuwa muke mashi tafito daga daki ganin irin kwalliyan da nasha sai faman sheki nakeyi da,annuri, taja tai turus, Wani irin kishina ya,turnuke zuciyan Biba a,sanyaye tace mashi sannu da,dawowa sai na nufi inda yake na karbi jakar dake sabale a kafadan shi, Bina tayi da kallon irin tafiyan da nake kamar wata,tarwada, a kasa, cikin dan rusunnawa nakarbi jakar daga hannun shi, Na nufi dakin shi dashi dakata Aisha inji Biba ta tako inda nake tsaye na juyo ina kallon ta, Amma dai kin san a,dakina yake ko naga kina son shiga hakina ban yi magana ba illa murmushin da nai mata kawai, Yace kamar ya a dakinki nake kwanan na tafi kwana nawa ake a dakin budurwa tace da sauri sati guda nace yau kwanan ki nawa a gidan nan, Tace goma,sha, daya yace tau hakakikayi ne ko may ke damun ki da,zakice wai kece da girki ita Aisha ke nan ba mace bane,. So dai kake ku cuceni kaida ita,amma ya kamata a ce nayi kwanakina a gidan nan na kare satina daya daya dan,na biyyo ka bashin kwana biyu a,baya katafi, You are very stupid Biba are you out of your sense, ? or you have gone crazy ? Ya juyo inda nake yace shige min da kayana,ciki wanan batazo da zaman lafiya a gidan nan ba, Amma zan yi maganin ki very soon tace mu dai yi maganin juna ni da kai don nagane ku macutane dakai har ita, Ya ce tau mu zuba mu gani tunda baki da kunya,wallahi sai na,gwada maki Hamza nake ina fadi kina fadi , Saida na hada mai ruwan wanka nafito daga dakin nazo na,shirya mai kayan abinci, a table, Dakina na,shiga kafin yafito na kara gyara kwalliya na da kyau yafito yana kamshin turaren da ya,sa THE,,, A falo yai sallah duk muna zaune daga ni har ita tana cika tana batsewa, taki shiga ne ina gani don kayan tsaraban dake ajiye tsakar falon a cikin ledoji, Sai da yai sallah ya fara cin abinci ya dan yi nisa yaran na kusa dashi suna mashi hira yace Humaira bude ledan nan ki basu tsaraban su, Haka yake idan yai tafiya da wuya ya,dawo bai sawo wa yaran tsaraban wani abuba wanda haka ke kara jawo mashi kauna ga yaran shi haka kuma in ya,fita komai dare sai ya,sayo masu wani abinda zasu ci, Takalmomi ne na,yara, harda Madina ta samu sai kayan wasa irin su jirgin kasa da mota suka shiga murna da ihu kowa ya dauki nashi abu gudane bai sawo masu shine abu mai siffan halittan abu mairai don Jidda ta damay shi ya,sayo mata babyn roba yace a,a gwagona malaikun rahama basu shiga gidan dake da abu mai siffan gunki don haka kiyi hakkuri, Sauran kayan cine da,sha a cikin shi yace wannan na amfanin gidane kowa ya ci, Biba tai farat tace to a,raba,mana kowa ya,dauki na shi, ba,wanda yai magana, kamar ba,zai tanka mata ba,sai yace Ok, kasa su kashi bakwai kashi kashi daya abawa maigadi kuda yara ku kwashi kashi guda guda sauran kashi daya ku sa min a,dakina, Tace harda yaran da,maigadi za a kasa daidai dasu yace wani yafi wani baki ne a cikin mu, Shiru naga tayi yace taso ki kasa mana kowa ya kwashe nasa rabon bashi ke nan ba, Kamar bazata tashi ba sai ta mike jiki ba kwari ta,shiga rabawa a hankali shiko ya tsure ta da idanuwan shi har ta gama yace ke Madina dauko abu ki kwashewa maigadi kikai mashi a,waje, An fitawa maigadi dashi yace min tashi ki kwashe naki na zabi kashin gabana yace ta dauki nata ta dauka yace Madina kwashinaki dana yaran ki ta hada nata dana yaran nace zoki hada da nawa kikai muna store din mu, Sai gashi nawa yai yawa kamar duk kayan da ya,shigo muna dasu ne gidan murmushi mugunta nayi nace ance in zaka gina ramin mugun ta kagina shi ya zam gajere, Simi simi ta mike tana kwashe nata tana cewa ashe a kwaita kuwa don bazan yarda da haka ba wallahi, yaja tsuki naga ya jawo wayan shi yana magana, Nakai yara daki nace dare yayi duk da goma saura nace kada su makara zuwa school da safe, sai da suka kwanta,naga barci yafara kwasan su na fito, Tunda ya,gyara dakin shi yaune rana na farko da zan kwana a dakin tare dashi, tsab nagyara jikina yadda ya kamata, Babu kowa a falon na kashe duk wasu na,ororin wuta dake falo da tsakar gida, Nashige dakin maigida da sallama na,ashe duk abinda nake tana tsaye bayan labulen ta tana kallo na tace shegiya mai suffan yan ruwa, tasake labulen waya ta,dauka da,daren nan takira uwarta tana kuka tana sheda mata karya da gaskiya, Uwar tace wallahi habiba ki bi a sannu komai asannu ake aiwatar dashi har yaushe kika shiga gidan da zakice dole sai dokanki za,a bi, Wallahi ki rufa min asiri kin dai san irin wahalan da nasha kafin ki shiga gidan nan, Shine yanzu mun samu kike son ki ja min gori a gurin kishiyoyi da makiya nawaje in kin kashe auren ai sai kizo ki zauna ga dakin nan mu dinga gwada tsawo dake a ciki, Tace amma mama ,,,,, rufe min baki wawuya,mara,hankali haka nace maki kiyi idan kin tafi ko kuwa,? Bataji dadi ba ko kadan a,wurin uwarta dake ganin samu da,rashi a lokaci guda yarta na son ta ja mata hasara , ****** ********* ****** Yana zaune a bakin gado da yar computer shi yana duba nashigo dakin ina tafiya,kamar wata queen of ocean, Abinda yakeyi ya bari ya kura min idanuwan shi har na,iso gare shi yace Rangida har kusa binki wallahi na zaci bazaki shigo bane ai, Nace kabini sai kace nice amaryan taka wanan muka min ai sai amare, ke dashi, Tsuki yayi tare da mika min hannun shi alamar inzo gareshi yace nidai zonan ki zauna na shaki kamshiki da nai missing for long, A zuciya na nace wani sabon sallon yaudara ke nan irin ta maza wanda ya kwana nawa da,wata matar daban zai min wanan dadin bakin, Nazauna gab dashi yarufe system din shi yana cewa ai ba,wata amaryan da zata yi irin amarcin da kikayi a guri na Humaira, Kece fa kika fara bude abinki ga leda kika koyar dani duk wani zumar dake cikin diya mace tun kina kuka har kika saba da,kwazabana, Yanzu wace mace zan samu kamar yadda na samay ki Humaira bayan kece matar da tasan dadina da,wuyana, a,duniya Ni har gobe a gurina ina iya nunawa duniya ba wata bayan ke wallahi agaban kowa kuwa, Ki sani Humaira wallahi zan iya barin kowa a saboda ke sai dai kawai kunata tamu irin na mazane zanje vurin wata amma badon na gamsu da abinda kika saba min dashi ba, A ko ina a gaban kowa ina fadin kice farin cikin rayuwana don har yau babu wanda zaice yaji a tsakanin mu, Haka yai min dadin bakin maza har ya kara,karyan min da zuciya na bashi kai bori ya hau yai yadda yake so dani a cikin gidan, Zancen tafiyan mu ya taso sai don haka banda sahran zama a gida sai sintirin shirin tafiya,mukeyi, Umma tazo gidan tana zaune a falo nazo na gaisheta take cewa ashe ina da mutuncin da za,a gaishe ni shine kwanaki kika tafi uguwar mu kika ki shigowa gaida mu ai idan baki shigo ba ki turo min jikokina na gaidasu tunda ba jikokin Fatima bane ita kadai, Murmushi nayi kawai sai Hamza ne ke cewa haka akayi Himaira Umma tace ai gata zan mata karya ne, Nace ba haka bane Umma bance mashi zan shiga gurin ki bane iya gidan mu na roka zan tafi, Eyyeh su biyayya manya ashe zuwa gauda mu din ma sai an bada umurni ake zuwa, Wai ina yar tawa take ne banga giccin ta ba tun da na,shigo gidan ko bata nan ne wai, Nace wa Umma tana ciki bari na fada mata kida na tashi kamar kullun a dakin, na shiga da,sallamana, Nacce amarya Umma ce ke gaishe ki a falo tashigo yanzu, Waye Umma tace cikin yatsune fuskan ta, nace Umman dai da kika sani ta maigida, najuya nakai kofa naji taja tsaki nace a raina kunfi kusa, Bata fito ba yadda nai tsanmani sai zuwa wani lokaci tafito fuska,babu walwala ban san may yasaba duk ranan da tai girki haka take wuni rai a bace a gidan, Nakawo wa Umma ruwa da dan abin tabawa sai ga Biba tafito daga dakinta fuska a daure, cikin malalaciyar murya tace, Umma kece ina wuni a,tsaye kerere, Hakan baisa Umma fushi ba,sai washe baki takeyi tana cewa ,a,a,a Habiba, kuna lafiya yanzu har nake batun na shiga dakin ki ai mu gaisa, Kitchen na,shiga naci gaba da aikina koda nafito Umma ce ita kadai a zaune a falo sai tv dake aiki, Nace sannu da zama Umma, tace yyawa kawai na,shige daki abina don yara suna islamiya a lokacin, Yadda Biba ta shige nima haka na,shige nawa daki muka barta nan zaune a falo, Shiru shiru ba,wanda yafito daga cikin mu sai zuwa ajima kadan nafito tana gyangyadi jin motsina datayi tabude idanuwan ta,da,sauri, Nace a Umma kina nan zaune na ai nazaci kin shiga gurin Biba ne don naji kina cewa zaki shiga, Tace a,a ina nan Habiban ma naga tafito kaman ranta a bace yake bari dai na,shiga naji abinda ya faru, Tamike tashiga dakin Biba da sallaman ta take cewa ashe kin kwanta ne biba tace mata eh batare da ta mike zauna ba Umma tai wa kanta mazauni a dakin tana cewa , An maki wani abin ne Habiba nagan ki wata iri yau, Biba tace may kikagani lafiyata kalau ba komai yasa tace haka ba sai gargadin da Hamza yai mata akan Umma din, Shiru dakin si Umma tace injin wanan makiran batai maki halinta nasu na makiran mata don wanan yarinyar da kike gani sai kinyi da gaske a kanta zaya barki ki zauna gidan nan lafiya da mijin ki, Biba tace wa wai Aisha daga inda take kwance tace ni banda matsala da ita don ba ita ta ajeni ba a gidan, To ai shi nagani haka kuma nake so wayan da aka bugo mata ta dauka ta,share Umma nan a zaune , Ganin bata samu yadda take so ba sai tafito daga dakin ta na kada kai kawai, Nan falo ta,wuni ita kuma Habiban bata fito ba tana ciki abinta yana dawowa take cewa ya,kaita gida,, Daga kofan kitchen na leko ina mata sai anjima a hanya take cewa wai ko Hamza amaryan taka kanta daya kuwa Dariya yayi sosai yace Umma may kika gani ne ko tai maki wani abin ne tace a,a gani nayi dai kamar bata da kunya yarinyar, Murmushi kawai yayi bai mata magana ba har cikin gida ya rakata acikin gida takecewa itama Aishan yau sai naga tana min wani gani gani a idon ta ,, Yace Umma aiko hakan ba halin Aisha bane don kin san halinta ai, Washe gari su Zarah suka shivo gidan tana jin su taki fitowa sai sune suka shiga inda take suka gaisa Asmau ke cewa kinajin mu Biba kin ki fitowa mu gaisa tace yanzu ba gaku kun shigo mun gaisa ba ina kun san dakina, Suna falo muna hira da dariya tafito ta dauki ruwa a fridge Zarah tace ke baki ko zuwa ayi hira, dake, Tace in nazo goya ku zanyi komay banda lokacin fitowa ne shiyasa don ban son damuwa tashige dakin ta Ido suka bita dashi suna mata kallon mamaki sai dai basuyi magana ba, Asmau tace ashe akwai aiki samun gurin har ya fara aiki ashe bamu da labari, Ranan laraba muka kwasa sai hajji cam muyi sallama da kowa a gari yan uwa da abokan arziki Biba taki fitowa sai zuwa can ana ina take ina take sai ta leko tana cewa zaku tafi kenan Allah kai lafiya ta juya ta shige dakin ta, Nikan nasan halin sune dai abin yazama wani banbarakwai don ba haka suka saba gani ba a gidan, Angama komai mun daga zuwa kasa mai tsarki nabar yarana da madina zasu zauna a gurin mama Hafsi da zata dawo gidan gurin su har in dawo, Hamza ya rasa zaune ya rasa tsaye da zamu wuce damuwa karara a fuskan shi, Mun dan kebe yake cewa wallahi sai yanzu nake da na sani na rufe ido mu tafi nace ai babu komai ga yaya Ibrahim dasu zarah yai murmushi yace baki ganewa ne Humaira nace ka kula min da kan ka da yara a gida, ****** ********* ****** Nayi gaskiya gurin zaben mama ta zauna a gida ta kula da yara har in dawo don nasan zasuyi daidai da Biba fiye da kowa, Aiko tafiyan mu da kwana biyu sai tafara batun takurawa Madina wai ta,dora masu girki tayi shara ga aike, Sai mama ranan tace ke bazatayi ba yarinya karama haka duk kin takurawa rayuwan ta keda kike matar gidan idan bazakiyi ba sai ki bari bata kara komai a gidan nan dan dama aike ko shi ba nisa ba, Nan ta zage tana son yiwa mama rashin kunya mama tace ke wallahi nafiki zama yar barki idan ma danbe sai ki fito muyi shi mu cashe yar iska mara kunya ni ban neman komai a gurin ki don ba don ki nake a gidan nan ba, Abincin ma idan bazaki girka damu ba ki barshi zan iya muna nidasu, basai kin bamu ba, Da ya,dawo ta,sashi a gaba wai mama ta sata,agaba ya samu mama yana tambayan ta may yafaru nan mama ta,fada mashi yadda sukayi da kuma yadda tafara hattaran yaran, Yace look Biba gaskiyan mama don koni bazan yarda,da,wanan akidar taki ba,ashe da gurin su nabarki bazaki iya rike min su ba, Tace akan may ma zan rike su tunda suna da kaka kaisu gurin kakar su mana, su zauna, Mama tace ashe baki da kunyane haka ni dama nasan ko yanzu tsugune bata kare ba yadda na gan ki da gani baki samu tarbiya ba tun a gida, Wallahi nikan kada a zagar min iyayye don bazan yarda ba gaskiya tunda iyayye basu fi iyayye ba, Biba ki shiga hankalinki wallahi don zanyi matukar saba maki yanzun nan ranki zai matukar baci, Taje bakin ta tai shiru don ta hango masifa idanuwan shi tasan yanzu da ta muda zai iya bata mata rai yadda yace din Tamike tawuce dakin ta tana guna guni ya juya gurin mama yana cewa mamakin ga kuma abinda na kwaso wanan karo, Mama tai dariya tace duk cikin jarabtan bawane da sannu zata gyaru tunda baka daga mata kafa idan tayi, Matsalar har yanzu a gurin yaya yake don naga har yanzu bata fahinci halin yarinyar ba ina gudun a maimata abinda ya faru a baya, Bayan kwana biyu ya shirya yai tafiya saida yabarwa Umma abida zai ishe su a hannun ta don yasan halin kayan shi, Nan sukai ta gogawa da mama a gidan ba sanya ko kadan a gurin mama tai girkin ta iya cikin ta mama tayi ita da yara tun da madina ta nuna mata yadda ake amfani da gas, Bai dawo ba sai bayan sati biyu yana can ya ketara kasashen ketare yana harkokin shi, Biba tacika tacika ta batse sai waya take mashi nacin mutunci wai don yaga matar shi bata kasan shiyasa ya tafi ya barta ita kadai a gida, Har ya kai ya daina daukan wayan ta,sai in shi yaga damar kiranta don kan shi,ya kirata din, Ranan da ya dawo tai girki ta sawa su mama takira madina wai ta dauka takaiwa mama can sai ga mama tafito da kullan a hannun ta tace bar abinciki Habiba don yau yana gari zaki bamu abinci, Mama kin fara kulla min sherin ki ke nan ko don kinga shi ya dauka da gaske ne, Fayauuuu ya kwashe ta da mari saida ta dafe goshin ta sai kuka tace kin kai ga yadda kike so dama an hada baki dake ne ki zauna don kiga bayan aure na, Nabar maki gidan ki zauna ya aureki idan natafi, Ta shige daki tana dauko gyalen ta tana kuka tabar gidan ko minti arbain batayi ba akadawo da ita uwarta da kanta ta taso tagaba tun kowa bai sani ba ta dawo da ita ta bashi hakkuri, Sai uwar kece wa mama babba dai yasan ya girma tunda yaro zamani sai da hakkuri, Yace mama idan kizo fitinane ki kwashi yarki ku tafi uwar na,fita gurin Umma ta tafi nan Umma ta hau ta zauna tun safe tashigovta samu mama da jidalin masifa Saida mama,ta,gwadawa Umma bata tsoron ta Biba tagane mama,fa,ba kanwar lasa bace bari ta sauko a zauna lafiya tun lokacin ta rage iskancin ta a kan mama, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,, Haka muka zauna da da Asmau da dadi da,wuya duk na hade su na shanye a raina nake nuna ba komai a fili, Sai dai shi ya fahinci ina fama da hakkuri daga Biba har Asmau din daurewa kawai nake ban gwadawa kowa don a zauna lafiya, Biba yanzu tana ganin ta kai ai gidan mijin tane sai abinda taga dama tayi ba takura ankawo tane an kawo ni nima, don haka,ba maima wani ikon don duk bori guda mukewa tsafi ni da ita, Sai ta dauko yi min abu gaba gadi ,gidan komai a,wullakance takeyi shi, Hakama yarn,tasaka,su a gaba,sai zagi da,duka tin ina,sharewa har takai na kasa hakkuri da dukan da,takewa yarna ko agabn uban waye haka,zata,doke,su kota,daka masu tasa sai sun gigice don masifa zafin dukan da take masu, Ranan gaba daya,muna zaune falo sai Jidda ta dauko ruwa a cup taje ta,wuce tafadi ruwan ya zube ji kake tas,da mari takuma kara aza mata rankwashi a ka, Nace haba Amarya wannan dukan aiyai ma Jidda yawa ga mari ga,rankwashi, Ko zaki rama matane don dama ance idan an doke su fada kike yi kamar zaki cinye mutum danye, Nace ai ban san da gaiyya kika,doke taba tun farko tacd da kin rama mata ke nan ko, Sai naga yanzun ma baki makara ba zaki iya rama mata in kina,so, Tausan zuciya na nayi don irin yadda take mi magana a cikin gatse da,rainin hankali, Nace ba wanan karon ba amma tunda na fahinci da,gaiyya kike dukan su muje zuwa gobe ma rana ne, Nan tafara zuba magana yawanci abubuwan da akayi lokacin bata gidan sai nai mamaki ke nan komai an fada mata a kaina harda karya da,gaskiya, Tamike tana cewa inda ma ba diya mata bane har kikewa mutane wanan salon a kan su nace nagodewa Allah daya,bani su ke ai sai kizo ki shiga haifa mashi tagwaye agani ni kuma na rike yan matana, Daidai lokacin Asmau dake barci taji yayan yai yawa tafito taji komai sai take cewa haba Aisha may yakawo hakane wai ki daina shiga harkan wanan matar don ita ba zaman lafiya yakawo taba gidan nn don bata da gwani da kowa yin fadan takeyi, Sai ga Biba ta kara lekowa tana cewa, mace dai ta iya bakinta don in kin isa ki koma gidan mijin ki mana ki samu daidai dake a can, Har ya kai sai da maigidan ya,dawo Asmau ta kwashe komai ta fada mashi ya kira mu gaba dayan mu har Asmau a falon Saye nake cikin wani dogon rigar material green color, na dan yafa dan kwalinshi har wuyana Ita ko Biba wasu atamfane daga cikin kayan auren da yai mun su take sakawa ni ban ko fara dinka nawa ba a lokaci Sai Asmau dake saye da dogon riga baka dake jikinta tun safe dashi ta,wuni a jikin ta Yai gyaran murya yace yana son yaji may ya kawo cacan baki dazun a gidan nan, gaba dayan mu shiru mukayi ba,wace tai magana sai da ya kara nanata tambayan shi shine ita,biba din tace cikin hasala, Wai dan kawai na bugi Jidda shine uwarsu take son gaya min magana akan hakan May tayi kika doke ta ke yatambaya yana kallon ta don son jin amsa daga gare ta, Ruwa ta zubar a nan ta nuna mashi gurin yace da gangan tayi ko kuwa ina son in sani , Shiru tayi don tambayan tashi yafara kureta a lokacin jin tayi shirune yasa shi cewa tambayan ki fa nakeyi Biba, Shiru tayi sai ji mukayi Madina tai farat tace kafan anty Biba ne ya yarda ita, Yadago kai ya kalli biba din itama biba kallon Madina takeyi yace haba Biba sherin makircin kishin ku kuma har da yarana kuke hadawa yanzu, O makirci ne ashe kai ma zaka goyi bayan kada nai wa yaranka fada ke nan ashe, kamar yadd ita uwarsu tayi, Look Biba idan kuna abinku kuyi shi a tsakanin ku amma bazan lamunci duka harda mari ba ga wanan yar karamar yarinyar kamar Jidda, Yanzun dai kawai, kace min bakin ku a hade yake kenan anzuga ka kaci min mutunci, Wai Biba ke wata irin bahaguwar yarinya ce sai ana magana ta gaskiya ki dinga kokari juta mutane, To tsaya kiji wallahi daga yau sai yau zagi ko duka akan yara na nakashe shi a gidan nan, Ga Humaira nan ita tahaife su amma ban daukan mata duksn yarana don tagwada itama batasha da dadi ba, Haihuwace dai ake min gorin shi a gidan nan nima Allah ya bani yace dayafi maki sai ko doka yadda ran shi yaso amma ita kibar dukan mata diya tai magan kuma ki mata cin mutunci, to bazan dauki hakzn ba don duk nakara ji rai zai baci wallahi, Ta mike tana cewa ki sani kuma ki rike duk randa na haihu a gidan nan bake ba,da na wallahi, Nace Allah ya kawo muna su yasa masu albarka ne Asmau tace ba amin ba a ha kali, Nan ta barmu tashige tana zage zage wai duk yadda za,ayi aga tayi fada da mijin ta shi ake kokarin yi itako wallahi zasu zuba ne da kowa a gidan, Asmau ta sauke ajiyan zuciya tace wanan si wani matsalane kuma aka jajibowa mutane don wagga mace ba matar rufin asiri bane wallahi, Shiru yayi bai ce uffan ba sai magana yake da mimi dake a jikin shi tana surutu, ****** ********* ****** Sannu a hankali nake lurar da Asmau akan al,amarin duniy duk da nima ba wani waye wa nayi ba amma nasan nafi Asmau sanin rayuwa, Sai dai kuma wani sabon matsalar da yake kunnu kai shine yawan fitinan da Zarah ke samu da mijin ta don yanzu baida hali irin na da ya samu kariyan arziki sosai, Abinci ma yanzu sai da kyat suke samun shi yadda ya kamata sai tazo gida anbata gashi tana dauke da wani ciki a jikin ta, Wanan dalili yasa Zarah ta tayarda hankalinta wai ita fita zata yi gidan bata iya zama, Mijin yana matukar son ta amma taki kwantar da hankalin ta sai yawan fitina sukeyi dashi, Ranan da yani wanta yana gari yazo ya samu hamz don akirata a tsawata mata, Ranan Umma tai fada sosai tace may yake nufi haka zata zauna da yunwa ga ciki a jikin ta da may zataji, Hamza yace ,a,a Umma mutumin nan fa bai cancanci wanan sakaiyar daga gare ku ba gaskiy don lokacin da yake dashi ya taimaka maku sosai, Umma tace makka ya kaini ko gida ya gina min hamza yace babu ko daya amma dai kunci alherin shi sosai, Yace gaakiya Umna kada kiyi wanan magana a gaban Zarah don kamata yayi ace an tsawata mata tunda yana son ta, Biba dake jin su tace amma Umma gaskiya baki tunane ba kamata yayi faki karfafa mata,gwiwa ta zaun a gidan ta gawata saboda rashin hali tafito shine kuma zaki kara ba,wata damar fitowa, Umma tace Habiba ashe kafarki har ya kama kasa ahaka kike fada min magana yadda,ranki yaso Ke kina da halin ne da ake zaune dake ko don ya zama abinda yazama shi duk yadda kashi yake yana iya shakarshi, Babi da tasan hhalin Umma a kan diyanta da bata,tanka masu ba datai shiru yadda nai shiru ina sauraren su, Umma ni nafi karfin banza a wurin shi tunda nasan nafi diyanki halin kwarai wallahi, Eh lalai ashe kuwa abinda ake fadi gaskiya ne don gashi yau yakawo gareni, Bari kiji duk fa abinda kikeyi nasani ido kawai na,sa maki ba,wai kinfi karfi na bane, Yaran nan ko zuwa sukayi da koken su gurin dan uwan su sai kin san yadda kikayi ki kai suka ya hana masu Biba tace wa wai zancen Jibrin kike yi yanzu kato kamar Jibrin zaice wai sai an bashi kudi shi bai zuwa ya nemo nashi, Indai don nace bazan fadawa yayan shi bane yaje yafada maki to na hana din, Lokacin Hamza yafito daga dakin shi yake cewa ke wai yaya hakane may nene wai haka kuma, Umma tace barta barta kawai ta nuna min ita kyankyasan injin ne, umma ai kyankyasan injin suna da yawa a duniya bani kadai bace, Ke wallahi yanzu tanki zai baci waike mai yasa baki da kunya Umma ce kuma kike ,sa,in sa da ita, Ni ba sa,in sa nayi da itaba ai magana ne kawai tafada min na fada mata sai kuma ace nai sa in sa da ita, Asmau tafito tana fadin wallahi in kika zagar min uwa yanzu sai nai maganin ki Allah, Gurinki tazo ko dake ake magana da zaki sawa mutane baki kin fi Aisha ne da bata tanka bakin ta ba a cikin maganan manya, Ke ki dai ji da haushin mijin ki da ya mayar dake bazawara kawai anzo an cika wa mutane gid da kashi in aure na da dadi jeki zauna dakin ki mana kibar wa mutane gida, Umma ta juya inda Hamza yake tsaye cikin takaici tace kana jin abinda take fadi ko yace naji ta Umma laifin wa kuma, Aina fada maki nayi bincike akan ta tun farko kikace min Umurni kika bani yanzu ni yaya zanyi akan umurnin ki nake ai, Biba tana shiga daki ta kunna gida sauti yana tashi da karfi ta mayar dasu banza, Na,shige dakina na barsu nan suna ta maganganun su nace ai kun fi kusa akan Biba ba irin cin fuskan da Umma batai min a gaban ta saida tai kokarin cusa Biba a zuciyar Hamza tazama wata a ran shi, Yanzun ko gani take daidai take da kow ba yadda za,ayi da ita sai dai kallo kawai don a ganin ta tunda mijinta yana,son ta Umma bata isa ta sa shi yai mata wani abuba, Kun san yanzu mace idan taga,wuri sai taga kamar ba,wanda ya isa da ita a dangi kaf, Umma ta tafi da mamaki a ranta bata taba zaton rashin mutuncin Biba yakai haka ba,sai yau da tai mata shi, Bayan kwana biyu Hamza ya samay ni ina saye da dogon riga na dinkin kasar Dubai mayafin rigar na yafa a kaina , Ganin ya shigo dakin yasani fuskan tan,shi fuskan shi da yanayin shi akwai damuwa sosai a cikin sa, Na tsura mashi ido har ya iso inda nake zaune shima zaman yayi tare da,furzu iskan damuwa daga bakin shi, Yayana may kuka ke faruwa nagan ka a damuwa yace cikin yar murya wallahi Aish al,amarin yaran nan ne duk ya daure min kai, Suna abinda ba daidai ba amma Umma bata bari a fadi sai ta tare da wasu hujjan ta na daban, Yanzu dubi yadd bawan Allah nan duk ya rikice akan yadda Zarah ta tayar mai da hankali lokacin da yake dashi suna ci waji su a gatin nan , Amma yanzu don Allah ya jarabe shi shine zasu juya mashi baya suna batun kashe shi da ran shi, Jiya fada dare yazo min hankali a tashe wai gata can tana fitina da uwargidan shi a kan ruwa, Nai murmushi nace ni wallahi ban san bata da,wayyo ba,sai da haka ta kasance Alhaji Bala bai ci tai mashi wanan sakkaiyan ba gaskiya, Nace kabari gobe insha Allahu zan tafi gidan nai mata magana ko zata ji don abin gaskiya akwai daure kai sosai, Yace gaskiya haka ya kamata ayi don in har ta bari auren nan ya mutu sai na,saba mata fiye da tsanmanin ta, Haka ya tashi gwiwa babu kwari ya bar dakin naw cikin tafiya kamar baida lakka, Dakin Biba ya shiga yana mata sai yadawo tana daga kwance take cewa yaya zancen kudin da ta tambaye shi wanda zata kai gidan su ana buki sunan babban yayan su sati mai zuwa, Yace waike baki da zance ne kullun dai na abaki kudi kudin nan fa idan bidan su na da,dadi a kashe ke ma ki tashi ki nema mana yadda yar uwar ki take yi, Don na tambaye ka kudi shine zaka kawo min gori ita Aisha wa yabata kudin da,take sana,an bakai ba may take dashi ko gidan su may suke dashi da take tunkaho, Don ka,rike mata kan maciji tana wasa da bindin shi ko waye bai san abinda akeyi ba agidan don na barku da Allah kawai yai min sakaiyya, Kallon ta yayi da mamaki yace ashe kina da aiki in zarginki ke nan in ma baki sani ba yau ki sani cikin bata da komai gidan su basu da komai itace sillar samun arzikina, Tace a wulakance ita Aisha din kuma wata sabuwa ke nan inji yan caca, busa ke nan sai a fadawa su kaji, Bakaji zan fadawa ba ke zan fadawa don ko duk kudina naba Aisha taci taci su gaba daya don da kudin ta nai arzikin dakika zo ci, Don nagane ba don Allah kika aureni ba don hangen abin duniya kika aure ni, To ban maki alkawari baki kudin zuwa buki gidan ku ba idan ya taso don itama banine ke bata ba, Bamu iya mu gane wanan kuma sirina ne koke don ki fitar da zargi na fada maki, don ki sani, Yafita don ya san in ya tsaya kara bata mashi rai zata yi a banza kawai, Kamar yadda nai mashi alkawari zuwa gurin zarah haka nayi don washe gari na,shirya ni da mimi sai gidan su zarah din, Na samay ta tana wanki saidai wanan karon ban samu taron arziki yadda aka saba ba a wurin kishiyoyin ta don a tsatsaye muka gaisa dasu, Tace a,Aiaha ce yau gidan ko batar hanya kikayi ne wai nai murmushi nace aiko baki fada min haka Anty Zarah don kin san ina zuwa gidan ki, Tace da ke nan ba yanzu da kika zama matan manya ba kin zama hajiya matar Hamza yaro, Nace haka dai kika ce Anty mun gaisa tare da tambayana mutanen gida nace kowa lafiya Nace ina Alhaji Balan ki sai ta bata rai tace Alhaji balan su dai nace haba anty ke da Alhajinki hakkuri fa zakiyi, da abinki, Tace wallahi Aisha wanan mutumin yafita min arai ace mutum ya zauna gida bai fita ya nemo sai dai a bashi ya,soke kawai, Haba Anty Zarah ki tuna fa da yake dashi ke da bakin ki kike fadin ko baiba kowa abu ba yana baki ,yana fa hakane don yana sonki yaga ke ce karama baki da manyan diya dashi, Tace ai su ma yana basu din don da basu zauna ba ai a lokacin dadin bakin mazane kawai yake min, Tau koma dai may nene kiyi hakkuri don hakan da kikeyi mashi sai kishiyoyin ki suyi maku dariya, Tace suyi mana in naji sai muyi tsiya da mace wallahi, Haba anty zarah in fa kin kwantar da hankalinki ko da kike ganin baida zai baki abinda Allah ya hore mashi, Haka dai kike gani nace haka din ne ma anty don Allah kiyi hakkuri shifa talauci ba mai dorewa bane baki sani ba ko Allah ya kara azurta shi, Aisha ke wa ke iya irin hakkurin kine wai nifa da kika gan ni nan cikin nan ne ya tauye ni wallahi in bashi ba da yanzu nabargidan nan, Nace kije ina Anty ? Hakuri zakiyi ku zauna lafiya dashi da abokan zaman ki don fa shi zaman gida da kike gani ba dadi gareshi ba, Wallahi zama dakinki yafiye maki komai dadi da wuya yanzu su wa yan nan yaran yaya kike son yi dasu inkin fita kibar su kamar marayu acikin wanan gidan yawan, Shiru tayi tana saurare na nace manya kance ayi hakkuri don zuri,a don haka don Allah kiyi hakkuri ki zauna dakin ki, In ma wani abu kike so kiwa dan uwan ki magana yabaki kudi ki fara sana,a kina dan juyawa kina samun dan kudin kashi sai kiga kin rage wani kunci a ran ki, Aisha kwanki fa da baki nan naje gidan ban samay kiba naiwa yaya magana ya taimaka min da kudi nasai koda dan fridge ne ina sa,na,a dashi irin yadda kikai tayi a baya amma sai yaya yace min na tafi zan ji shi, Naiwa Biba magana da zan tafi akan ta taimaka min amma sai ce min tayi wai baida kudi taji yana cewa baida kudi tare dashi, Nace amma shine ni baki fada min ba Anty da kin fada min ai da ansan yadda za,ayi ko, Tace sai daga baya nake ganin wanan shegiyar matar tashi ce ma ta,zuga ki aida nake fadaw Asmau ce min tayi may yasa na fadi a gaban Biba don duk yadda zatayi ta hana shi ya baki sai tayi shi, Yanzu Aiaha in yaya bai taimake mu ba gurin wa zamu je garin nan ya taimake mu Tunda ana ganin dan uwan mu na,dashi amma baya taimaka muna nace kiyi hakkuri zan mashi magana insha Allahu, zai baki, Kinga da,har da engine din nika sai ki hada kina nika don naga uguwan nan naku za,a samu nika sosai tace hakane Aisha amma ai samun kudin ne keda wuya nayin haka, Nace babu wani wuya insha Allahu ke dai ki tayani addu,a kawai Allah yasa mu dace tace Amin Aisha, Nace idan za, saro min kaya,sai ki bada dan kudi a sayo maki koda takalmomine ki sayar da saukin kudi yadda zasu kare da wuri akara saro maki wasu, Murmushi kawai tai min nasan zatace ina kudin suke Aisha, Alhaji Bala ne yashigo sai ko gashi har dakin yana ganina yace a, hajiya Aisha ashe kece a gidan namu nace eh Alhaji nazo ne na gaishe ku kwana biyu ban shigo ba, Yace Allah sarki aiko mun gode da kika tuna da mu yace ko kinga mutumiyar ki yadda ta tsufa tai nauyi da yawa yana yi yana kallin fuskan ta yadda ta wani daure fuska, Mundan gaisa dashi yafita yabar mu nan da ita yana fita nace wallahi Antu kiji tsoron Allah kada ya kamaki da,alhakin wanan mutumin dubi fa yana shigowa dakin ki ya nufo direct, kuma kin bi kin daure fuskan ki, In baiji dadi agurinki ba ina kike son yashiga yaji tai dan murmushi tace baki ganewa ne Aisha iyakan shi fa ke nan dadin bakin nayarda dashi ya,samu biyan bukatan shi, ba komai,da zai iya kara mutum dashi yanzu sai wanan, Nace LOKACI NE,,,, sunan novel dina dake tafe nan da, wasu kwanaki insha Allahu, Da zan tafi dubu goma na bata tai ta mamaki tana godiya suma kishiyoyin ta na basu dubu biyar biyar naba yaran su dubu biyu nace su raba ban rage ko kwandala ba daga cikin abinda yabani da zan zo saima karin danayi don matan suyi matukar bani tausayi duk sun jemay gaba dayan su dagani suna cikin lokaci, Nasha godiya don sun kasa boye farin cikin da,sukayi kan kyautan da nai masu, Nabar gida cikin dadin rai da yarda da shawaran da naiwa zarah din, Daga can na biya gurin Anty hindatu na,samu mijin ta a gida suka kama yi min ba,a wai na koma wata yar birni kamar matan Abuja, Bayan fitar mansur take tambayana inda nafito da rana haka na fada mata halin da zarah take ciki da mijin ta, Tace aidama dole haka ya kasance, ita Umma tana nufin sherin da takewa diyan wasu ba zai tambaye ta bane, Har gobe fa ita gurinta taga kinbar gidan dan ta Allah daine yafita da yanzu taga bayan ki ko, Amma ai kadan tagani don wanan banzan matar da tasa hamza ya aura tana nan tana fadi a gari sai ta rabashi da kow nashi ta mallake shi, Nai murmushi nace ai gata ga gidan muna gani ina ga wanan har yanzu bata san kowaye hamza ba tace barta dai nima da ake fada min cewa nayi itawa din wacce ko ranan da ya,shigo sai da yai ma baban daddu korafi a kanta yace bata da mutunci ko kadan shi ta ishe shi wallahi, Ya barta ne kawai har Umma ta kara koyon darasi a kan ta, Nace nima nafahinci ba banza ya kyale taba yana da,wani manufa akan ta shiyasa nasa masu ido, Tace sai cewa take wai ita maza zatai ta haifo maahi in tafara haihuwa fon takifar maki da gwaunatin ki don diyanki son su yake kamar diyan gwal, Nace tunda itace Allah sai ta zabawa kanta abinda take so mu gani ai nidai nagodewa baiwan da yai min kuma har kullun ina kara gode mai in ma zai kara min mace ne shirye nake dana kara gode mai fiye da kullun, Tace bar jahila ita batasan diya mata yanzu jari bane ga iyayyen su, Mun kai wani lokaci da ita nai mata sallama nadawo gida na samu Asmau tai min aikin komai da nadawo da zumar yi hakan ya tabbatar min da ta canza sosai yanzu,,, ****** ********* ****** Bayan kwana biyu yadawo garin sunyi nasara sosai a,wanan tafiyan da yayi don ya samu riba fiye da tsanmanin shi, Ranan asabar ne don haka yara suna gida muna falo dasu muna hira, sai gashi yafito ciki shigar kananan kaya, yayi matukar kyau da shigan, Fuskan shi dauke da murmushi ya zauna yana cewa mimi tazo sai taki zuwa yace a,a a mamana ba dai fushi kike da dan naki ba ko, Nace cikin murmushi kyale ta fitina takeyi wai sai an bata carprison takara sha bayan tasha biyu dazun, Yace abata mana ba nasu bane zo nan kinji mamana na Madina dauko mata da yawa tasha kinji, Nace haba yaya in mafa tasha,ba bashi yake bata ba don tafara tsuguni ke nan tana damun mutane da kashi kashi, Yace iyakan ku kenan wanke mat kashi kawai ko don Allah kubata,tasha mana, Tana jin haka ta nufi gurin shi ta rugumay shi mu dai kallon su mukeyi madina takawo mashi yafara budewa yana bata a baki, Biba tana jin muryan shi tafito daga dakin ta tana kallon su ba wanda ya damu da fitowan ta don mun san haka takeyi, Shima bai daga kai ya kalle ta ba,sai hira yake da,yar shi sai Asmau ce mai cewa dama ina son tambayan ka ina son zuwa gurin su Umma yau, Batare da ya,dago kaiba yace idan kin shirya sai na tafi dake don dama can zan tafi ko kina zuwa mama muje gaida takwaran ki, Sai yarinyar ta kada kai alaman tana zuwa din yace madina idan ta kare ki shiryata sai mutafi, Muryan Biba ne take fadi ka sauke ni gida ina son zuwa na gaishe su yau, In na yarda ko kuwa ra,ayinki ban san abinda yasa kike min abu haka ba gaba gadi kamar ke kika aje kanki Biba, Gida fa nace zan tafi kaima ba gashi jiya kadawo ba amma kace zaka je gaida uwarka, Yadago kai daga ba mimi lemon da yakeyi yace uwatafa kikace Biba ke ba uwarki bane ke nan ko ? Tace ni bance ba gida kawai na ce ma zan tafi kakawo min wani sabon zance inda watace tace zata wani gurin baka cewa komai sai ni, Amma nan naga an tafi uguwa baka nan kuma bakace komai ba da kadawo , Yace wai fitan da Aisha tayi kikewa wanan magana tau nina aike ta dasani na tafita, Sai lokacin na fahinci zuwa gidan su Zarah danayi take magana kenan wanan matar kishin ta harda na hauka ke nan, Nan take na tuna da,zancen da mu kayi da Zarah nace mai aiko ina da magana dakai ko sai kadawo ne, Yace ko yanzu ma ashirye nake da na,saurare ki nace to muje daki kaji ko may nene zai fi don komai yana son siri ai, Nan muka tafi muka barta tana kunkuni wai ita za,aiwa raini wayyo don an rainata, Muna shiga dakin ya dan matsoni a jikin shi na zille ina cewa bafa nice da hakkin kaba kasani yace and so what sai akace kada na taba kayana don banda hakki a kan shi, ko may, Nace nidai zancen Zarah ne dama yace aikuwa Alhaji bala yafada min kin mashi yaki yace nai mashi godiya kwari da gaske kin zama mai gyaran aure ke nan, Nace ai dole na kada don bazan bari yar uwana tashiga wani hali ba sai yadan murmusa yace da zata biyo halinki ai da ba hakaba Zarah, Nace yanzun dai ba,wanan ba taimako nake son kai muna yace akan may Aisha nace akan Anty Zarah don Allah ka taimaka ka bata jari wanda zai ishe ta ta,tallafawa rayuwan ta dana diyan ta Yai murmushi yace wace bata saba sana,a ba,za,ace ba jari ta kashe su dai a banza ke nan, Nace sai ka kara mata,wani tundaAllah ya hore maka balle ma ba,a banza zata kashe su ba insha Allahu zata fara juyasu ne sanni a hankali, Shine fa samun dan uwa yan uwa,su wadatu da mutum a san nasu ya na dashi ba aga yan uwan mutum cikin matsi ba shikuma yana cikin wadata sai duniya su zagi mutum, Kafara gwada ta ka gani in son samune ma kabasu su duka ita da,Asmau su fara juyawa a hankali, Zaiyi magana nace don Allah ba don halin mu ba don in tana da abinyi ina ganin za,a rage yawan samun matsala tsakanin ta da mijin nata Yace min yaji kawai zai duba yasan abinda za,a ayi amma na sa i idan takashe su ga banza sai sun hadu,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE HAKAN CIN AMANA NE,,,, Alhamdullahi don munyi nasaran samun dubu dari biyu wa kowar su yace su fara sana,a don su tallafawa rayuwan su, Kamar yadda muka tsara nida Zarah hakan mu kayyi, mun sai fridge da injimin nika sauran kudi aka saro mata takalma patis din yara da underwear mata, dasu sarka da dan kunne tai matukar jin dadin sosai, Suka zo gida gurin Umma don su gaid ita sai suka kawo zancen hiran yadda akayi yayan su ya basu kudi kowa tana fadin albarkaci bakin ta, Umma tace ban taba sanin cewa mu wawaye bane sai yau din nan ana,dafa kifi da ruwan shi kuna cewa romo, Tana amfani daku tana karban kudi a furin dan uwan ku tana kara kan ta da yan uwan ta, Da sauri Zarah tace haba Umma wai sai zuwa yaushe zaki jaye akidarki akan wanan yarinyar, Aisha fa bata cancanci wanan irin sakaiyan ba a,gurinki irin yadda ta dauke mu kamar yan uwan ta, na jiki, Baki Umma ta tabe tace kai yaro man kaza ku may kuka sani sai hargowa kawai, Asamu ta tare da fadin nikan wallahi koma yadda Umma ta fadine wallahi ban taba gani bakin Aisha a zuciya ma don ni na zauna dasu nasan halinta, Kina ganin in badon tai muna wanan kokarin ba yaya zai iya bamu kudi haka bayan kullun mutum yai magana ko a kan dubu goma ne fita yazo ke nan, Yanzu gashi da fa kokarinta,da sa hannun ta har muka,samu zaman lafiya,a tare da mu, Dubi yadda taita kori akan taga na koma dakina ke kin san irin yadd sukai ta kwasa da Abdul ne kafin ya amince na koma gidan shi, Bafa karamin yaki tai yi ba,saida tai mashi nasihohin dako ke da kika haife baki iya yi mai, Zarah tace Indon ta Umma ne ai bataki duk mu dawo gida mu zauna mata,ba , Alhaji kullun zancen shi Allah ya karawa Aisha albarka yace iyayyen ta sun dace da haihuwa ya ta gari mijin ta kuma yai sa a da,samay ta matsayin mata a gare shi, Ku kan duk ta,saye ku wallahi saye mu da may Umma da,halinta na alheri ba, dashi kan ta saye mu ke ma inkina ba kan ki hakkuri ki kama,sarakuwar ki ta kwarai kibar yayamay yayamay wallahi Umma ki bari, Ganin yaranta sunyi nisa basu jin kwabo yasa taja bakin ta tai shiru ranta a bace, dasu, Mama hafsi dai tana jin su kyalesu tayi don tasan gaskiyace a makwafin ta tafara baiyyana, ****** ********* ***** Dagani har Biba muna da shigar ciki a lokaci daya kowan mu sai faman lolayi yake, hakan yasa shi fahintar duk mun halbu, Sai dai cikin yasha banban do ita biba nata yazo da,wahala ga amai ga miyau da,sauran kasala, Niko kamar yadda na,saba cikina haka na yazo min sai dai yawan barci da kasala da ya,sakar min,, Dole duk da ina fama da nawa haka nake mikewa nafito nai muna abinda zamuci a gidan shi dai maigidan ba mazauni gari bane don haka yana gurin harkokin shi wimurin ne man kudi, Wata rana tun safe banga tafito koda neman abinda zataci bane, haka yasa na shiga don na duba ta saboda hakkin makwabtaka kawai, Na samayta a kwance duk ta galabaice tanajin motsi shigowa na dakin ta dago kanta da kyat tana fadin, Maman Jidda wallahi banda lafiya tun dare nake fama da zazzabi ajikina ga amai har yanzu yaki ya tsaya min, Nace subbahanallahi sannu amarya, bari na taimaka maki ki shiga k8 dan watsa ruwa sai ki dan ci wani abu tace wallahi bazan iya cin komai ba amai zanyi nace ki dai daure ki dan sha koda tea ne tace bazan iyaba sai ga hawaye shar a idanuwan ta Madina nakira nace ta dora ruwan zafi takawo min da kayan tea, Da taimakona ta shiga taiwanka nasa Madina ta dan gyara mata dakin , Bayin ta,dana shiga saida tsikan jikina ya tashi don kazanta saboda ina ganin an dade ba,a gyara shi ba, shima dakin ko ina kayane ba kyaun gani, Tafito na hada mata tea amma tace kada na sa madara ruwan liptop kawai zata sha, Tana sha sai zufa ya karyo mata cikin muryan tausayi tace nagode maman Jidda nace haba ba komai ai zama tare ne, Tace min har ta danji karfin jikin ta da tasha tea din nace yanzun dai ina wayan ki bari na kira mummy cewa mahaifiyan ta yadda naji tana kiranta dashi, Bugu daya a nabiyu uwar ta dauka tana fadin mama yanzun nake batun kiranki naji yaya jikin naki nace Mummy ba Biba bace nice Aisha don Allah ko za,a samu wanda zaizo daga gida sai mu kaita asibiti a dubata don amman yai mata yawa, Uwar tace ai maman Jidda ce yaya kuke yaya yaran nace duk muna lafiya tace jikin nata ya matsa ke nan nace eh wallahi mummy gara aje asibiti a,dubata kada karfin ta ya kare take ce min gata nan zuwa yanzu insha Allahu, Da mahaifiyar nata zata zo tare da,gwagon Biba din suka zo gidan ganin yadda ta koma hankalin su ya tashi sai faman godiya sukeyi, Nakira yaya ina fada mashi halin da ake ciki da ita yace muje asibiti din aji ko maynene matsalar ta, Ibrahim nakira na fada mashi yake ce min shifa aiki yake a shago kada,na matsa mashi nace yaya Ibrahim kayi hakkuri kazo don Allah, Da zasu tafi ban bi su ba tunda ga yan uwan ta harda mahaifiyan ta nice naba kudi don suje suga likitan, Gado akabata za,a kara mata ruwa, hankalin yan gidan su yai matukar tashi sosai, duk abinda za,a bukata saida na tura Madina takai masu shi, Sai zuwa dare na shirya da yarana muka tafi gaida Biba a asibitin mun samu jikin nata yai sauki tana zaune tana cin alalain da tace nai mata shi take so, Gaba daya dakin ya cika da yan gidan su sai hira sukeyi suna dariya ina shigowa suka sako min na mujiya, Suna kallo na cikin gulma da tsegumi na nagaisa dasu ina masu yaya maijiki wanan gwagon nata ce ta amsa dasauki yaya kokari murmushi kawai nai mata na isa kusa da gadon ina mata sannu yaya jikin ta amsa min da dasauki maman Jidda gashi har ina cin abinci, Dan jin ina tsaye rike da hannun yarana sai take cewa mimi zo kici alale sai yarinyar ta make don bata saba da ita ba, Dan lokaci kadan nace mata,zamu koma don dare yayi ba kowa a gida saida safe sukai muna muka tafi take ce min har nafara tafiya don Allah maman Jidda dasafe ma ki kara min wanan alalen naji dadin cin shi nace Allah ya kaimu, Ina fita daga dakin matar yayan ta tace wanan kan ai ni sai nake gani kamar buzuwa ce ko ? Wata tace bafa wata babba bace ina ga ai Biba ma zata girmay mata ga shekaru, Shegiya sai kyaun tsiya wallahi inbadon biba ma yar iskan kanta bace aida bata kai haka a gidan ba, Gwagon su ce tace haba haba dai ina laifin yarinyar nan itace da takiramu da rana habiba ba lafiya takuma sa akawo ta asibiti aiko kun ga bataci zagi haka ba a gurin ku, Kai dan Allah gwago wallahi duk makirincin kishiya ce ba don Allah tayi ba kawai don a yabetane, Gwagon tace koma don may tayi mu dai mun gode mata da bata kula ba aida ba,a,san yadda za,ayi ba, ita kadai a cikin daki, Biba tace balle wallahi ni yanzu na ma daina damun kaina da al,amarinta don na fahinci haka halinta yake kokai mata abin bacin rai dawuya kaga bacin ranta wallahi ko , Irin masu saukin kannnan ne da basarwa al,amari bata daukan abu da zafi ko kadan, Gwagon yace wallahi in wanan ja,irar ce batai mata ko kwatan kwancin wanan da tai mata, dariya Biba din tayi tace wallahi hakane gwago don balain kishin ta nakeyi don in tana gidan nan ban taba samun kan Hamza a,rayuwana, Gwagon tace to wallahi ki dai rage shifa zama dakike gani na kishi zaman amana ne ita tana kokarin sauke nauyinta a kanki ke ko shedan yana rudinki, Baki rasa ciba baki rasa shaba komai a kwaishi kuma mijinku bai rage ki da komai ba na zamantakewa don may zaki dagwarawa kanki wahala ita bata ko san kina yi ba ma, Biba tace wallahi hakane gwago matsalana yanzu guda ne zuwa biyu uwar shi da yan uwan shi sune matsalata, a gidan, Kinga inda zaki dosa ba inda bai dace dake ba kin kwaso shegen kishin iyayyen ki kin zo dashi har gidan miji, Ko su uwafa uwace akanta wallahi inkin matsa sai ya saba maki, tace shima fa,taishe shi don halin fitinan ta yakai mashi ko ina, Nan dai sukai ta zance akan yadda al,amarin gidanbmu yake dasu, sai da,suka gaji suka tafi don kan su, Tun bayan dawon ta,gida naga ta rage wasu halayanta na sheri sosai don yanzu takan fito in muna falo a zauna adan yi hira da ita, ban damu da rashin girkin da batayi ba don nasan matsala ne na lalurar ciwo, Sai dai ranan da Hamza ya dawo sai gata ta mike tana girki da kan ta da tagama kuma ta nade zazzabi ya tashi, Sai na fahinci bata so idan tana da girki na kama mata don tana zaton zan mata babakere a kan aikin ta, don dan canjin da,ake samu daga gurin maigida, Har wanan lokacin Biba bata fahinci ina da ciki a jikina ba don ban sake yadda ta sake ba, Sai faman rawan kai take mutane na zuga ta suna ce mata wai maman yan biyu, Nan ta dauko sallon da makirici a kan cikin yau tace kaza take so gobe ma tace wancan take so, Tun yana biye mata ranan har yakai gacewa ke nagaji bake kadai bace nafara ganin ciki a gurin ki ba Allah yaba Aisha hakkuri, Aisha kace niba Aish bace Biba ce ni yanayin cikin ta daban nawa daban kasani ko tunda ba haka takeyi ba ko ni cikin nawa namijine shiya sa, Yace look Biba na fada maki ban son wanan rayuwan da kike shirin dauko min a gida ni dana miji da mace duk daya,na,dauke su tace haka dai kace amma ko a gurin Allah ba daya suke ba ai don an fifita su, Rai a bace yafita yana mamakin irin halin rayuwan Biba bata dai bukatan a zauna lafiya, a gida duk abinda zai fitina a kan shi tasan yadda zatai magana sai anyi, Nikaina yanzu har mamakin ir8n saukin kan da Allah yabani nakeyi dafarko na kance kodai nasihan Ummina ne dana hau yai min aiki haka, Sai kuma daga baya nakan yi tuna ne koda sauki na,sama daga gurin Allah don nayi roko sosai dana je makka akan Allah ya yaye min kishi, Allah kuma ya dorani akan duk wata mace da Hamza zai auro yakawo gidan shi daamsunan kishiya ina,rikon Allah ya fifita ta hal8n alheri a kan su, Kan Umma mai nakan tsaya naita add,dua kan Allah ya dorani daga duk wani mugun nufi nata ina mai neman tsari dani da zuri,a na akan ta, Saba,an da zan fara shima saida nai dawafi akan shi tare da yiwa diyana suma dawafin neman shiryuwa a gurin Allah tare da sa masu albarka arayuwan su,, Gashi ko da,alaman Allah ya karbs min addua,a na don duk abinds na roka naga faidan shi a rayuwa na yanzu, Abu daya ne shine baiyyanan mahaifina da har yanzu bai dawo ba kuma ko labarin shi babu, Abin wani lokaci yana matukar damun zuciyana sosai saidai ba yadda zanyi dole nai hakkuri nabarwa Allah, ****** ********* ****** Kamar yadda Bibs ta kwalafa rai ga zancen zuwa makka shekara mai zuwa hakan bai samu ba don cikin dake jikin ta ance gwaunati ta hana mata masu ciki zuwa saudiya bana don matsalolin da ake samu acan da su, Ba yadda batai masifa ba tana cewa ai ance in anbada cin hanci ana bari mace taje yace to shi bazai ba kowa cin hanci ba, Tabari in Allah yasauke ta badi sai ta tafi inda rabon zuwa, case din har gurin mahaifinta takai karan Hamza amma yace wallahi bai biya sai bata da komai Haka ya sata ido ga bado ido ga ruwa ga makka ga ciki tarasa wanda zata zaba daga ciki da kyat uwarta ta,taushe don da tace sai dai ta zubar da cijin taje makkan ta kawai intadawo tayi cikin ai, Ina zaune ranan banjin dadin jikina sai gashi ya,shigo gidan yana,waya duk da,waya yake sai da nai mashi sannu da dawowa yavamsa min cikin lumshe idanuwan shi yazauna gab dani kadan, A yadda na fahinci wayan da wani ma,aikacin hukumar alhazai yake wayan nashi, Sai da ya kare yace wassh tare da shafan kanshi a hankali yace rangida may zan samu naci wallahi duk nagaji nace ga abinci ka can saman table kanakawo ma nan ne, Yace da kin kyauta wallahi don yau duk nagaji gashi gobe kuma tunda safe zan kama hanya don wanan karon wani dajine da ake shigo da motoci ta saukin hanya muka samu can gaba da kwatano garin yake an hada mu da,wani mutum da,zai taimaka muna, Allah ya taimaka nace mashi tare da mikewa zuwa dauko mashi abinci Biba tafito tana wani turo ciki a gaba ta canza tafiyan ta wai ga mai ciki, Yakalle ta yai murmushi yace maiciki ke nan nadauka kina can kina sa,na,anki ai barci tace cikin dan zubar da miyau data tara a bakinta yanzu naji kamshin turaren ka nasan ka,shigo shine nafito ko kadan zo min da wani abin kwadai na dan sa,a bakina , Dariya mukai mata gaba dayan mu nace wanan cikin kan kila dan Baba muka samu tunda har yana jin kamshin turaren mahaifi shi ko a ina ne, Dan Baba ai halinshi sai shi ni duk yabi ya jagwalgwalani wallahi sai faman kwadan dayake sani gashi kuma uban shi da shegen mako, Yace yanzu duk abinda nake sayowa kici bai ishekiba sai kin ce min wai mai mako, Allah yaba Aisha hakkuri da har yau batace min ga abinda cikin ta ke bukata ba tace bata da shine da tace ga abinda take so itama, Murmushi yayi don ya fahinci haukan ta ya hana taga cikina da har yafito a cikin zani na yafan turo don yafi nata girma sosai, Kitchen ta nufa tana fadi bari dai na nemi abinda naci tashige yana cewa sauniya kawai kanta kawai ta sani ita, Yashige ya kwanta nima natafi waje don na wanke kayan yara da suka dawo dashi school, Ibrahim yashigo gidan yana ta,sallama ya kawo mai wasu takardu daya aike shi dasu, Biba tafito daga dakinta zata kitchen suka hade sama sama kamar kullun suka,gaisa dashi, yace ta sallamo mashi Hamza saicewa Biba,, Bazan tashe shi ba don ya samu barci kaje idan ya tashi sai ka dawo anjima mamaki ya kama shi yace kamar ya bazaki fada mai gani nazo ba, yafa san da zuwana , Nace bazan tayar dashi ba ranshi ya baci yaduba dakina bani ciki yafita ranshi a,bace, Sai gurin Umma yaje yana fada mata abinda yafaru tace yaje yai hakkuri , Saida yamma da yadawo yasamu dan uwan shi a falo yake fada mashi ce bata da wayyo nan yabashi hakkuri yace ba komai amma sai tagane kuren ta, Inajin su don ina tsaye ina gyaran falon banyi magana ba don ba abinda ya shafeni bani bane inji yan conversations din sauratan mata sun min fada na rage shishigi kada su yi fushi dani,sunce na faye rawan kai😜 Zan shige naji muryan shi yana fadin zo mana humaira, Juyowa nayi inda suke nazo na zauna a hankali saman daya daga cikin kujerun leather cushion din dake mamaye a,falon bakake, Yace gobe idan Allah ya kaimu kije gurin Ummi kice suyi passport ita da Baba don ina ga tare dasu ne tafiyan bana, Da sauri nadago kai na dube shi yace ko bakiji bane nace yaya makka zasu kake nufi yace shi nake nufi mana, Ban san lokacin da na zube kasaba nace yaya nagode nagode kwarai da ,,,,,, Hannu yadaga min yana cewa may nene haka Humaira don zanbiya wa uwata makka shine zakiyi min godiya may yasa dana biya wa Umma baki min godiya ba sai wanannan, Murmushi nayi cikin murna nacewa Ibrahim yaya katayani godiya don Allah, Saiga Biba bull tafito tace may yafaru ake godiya tana kallona ina rusunne a gaban maigida, da sauri naji Hamza yace ba maganan ki bane wanan, Kallon tuhuma tafara yi muna gaba dayan mu yace wa Ibrahim kajirani mu fita tare akwai inda zamu dama, Yashiga dakin shi yafito tare suka tafi batare da Biba taji abinda take son ji ba sai tuhumar mu takeyi, Suna fita tace dama ai ba yau akafara cin amana ba a gidan nan koma mayye ai ji za a yi, Azuci nace badai yanzu ba kan na kasa fahintar dalilun dayasa yaki fada a,gaban ta da,suka fita yake cewa Ibarahim ko Umm kada ka bari taji zancen nan sai in lokaci yayi, Nima da dare da yashigo yimin saida safe yake ce min kada ki bari kowa yaji zancen nan sai in lokaci yayi, Mun bar zance wa iya mu na tafi gurin Ummina munyi yadda yace muyi itada Baba nakawo mashi daga gidan mama Rahama ya kwashe su zuwa birnin kebbi yin E passport, Salin alin aka gama komai na,tafiyan su batare da surutu yabi gari ba, muna jiran lokaci, Umma ta shigo gidan mu akan zancen auren Sa,a datu sai dai bata san cewa yasamu yin tafiya don dama ya sallamay ta yace ko gobe ko jibi zaiyi tafiyan, Sai gata,tazo bayan ya wuce a lokacin ban gida na shiga makwabtar mu yin barka an haihu kwana hudu yau ban shiga ba, Don haka Biba ce kawai a gida sai Tv dake aiki shikadai a falo yara suna islamiya gaba dayan su, Jin shirun da,tayi tana ta sallama sai ta leka dakina amma a,rufe yake don ban yarda nabar gida dakina a bude kamar yadda nakeyi a can baya, don itama haka naga tazo da sallon yi, Dakin Biba ta nufa ta daga labule tana ciki zaune tana waya ta daga kai ta kalli Umma taci gaba da wayan ta, hankali a kwance,, Habiba bakijin ina sallama ne tun dazun nashigo ba,wanda ya amsa min , Biba tace najiki ina waya ne da uwata sai tai sallama da wayan ta juyo gurin Umma dake cewa, eh lalai ashe kin kai can habiba, Jinan Umma wallahi ni ban yarda ki shigo har dakina ina fama da kaina zaki aza min masifan ki, Ni dai danki nake aure bake ba don haka wallahi ban yarda da zancen ace uwar miji tazo tana ciwa matar dan ta mutunci don ba ita ta haifeni ba, Don Allah ki fita min daga daki kada kuma kice nai maki wani sheri ko, Umma tace har korana kike a dakin ki yau Habiba don wuyanki yai kauri ya isa yanka ko, Nan tafara tafa hannayen ta Umma nace ki fita,ban son fitina haka kawai don tsegumi da bani bani baki iya zama gidan ki kullun mutum yana yawa gidan sarakai babu ko kinya ni wallahi wanan abin ya isheni a gidan nan, Uwarki ce mai yawan gidan sarakai ai nace uwarki ce mai kwadayi nikan wallahi ba uwata ba, sai dai uwar wa ke nan,. Tace ni dai nace ba,uwana ba,wallahi abinda naji ke nan nace subbahanallahi Biba kanki daya kuwa tace da,akayi may fa, Jinan maman Jidda kada kisa bakin ki cikin wanan magana kinji na fada maki, Nace Amarya kibar wanan hakin don ba halin tarbiya bane kema fa watarana haihuwa zakiyi tace na haihu mana Ko na haihu Allah yarabani da halin wanan kullun mutum yawo gidan dan shi yana aikin saka ido haka kawai za,a fado min daki ace wai nabar waya da uwata , Habiba yau ni kika zaga a gidan nan ba laifinki bane don ni najawa kaina hakan, Tace inma kince nazage ki na zaga din don dai ni ba uwata ba, sai kawai umma ta fashe da kuka tana cewa Biba tai mata cin mutinci, Da kyat na samu Biba ta shigd dakin ta tana fada tana cewa wallahi ita batayarda a zage ta ga banza,, Umma tana kuka tana share hawaye da habar jibba din ta tana cewa kaman ni Habiba zata kalla tai min wanan zagin haka, Babu komai bata da laifi nasan inda matsalan nan yafito nace Umma yi hakkuri, tace ai dole Aisha, ina yaron nan yake ne nace Umma bai fada maki cewa yau zai tafi ba tun safe suka bar garin nan, ai, Tace yasamu wuce wa yau din ke nan ko nace eh Umma su tafi ko, Allah ya,dawo muna dasu lafiya nace amin Umma take cewa bari ta koma gida tace dama nazo kan zancen Sa,a datu, Nace Umm idan munyi waya dashi zan fada mashi cewa kinzo baki samay shi ba ai, Tace tau nagode ni zan tafi sai dai in yadawo din zamu ga juna dashi don gidan mazan sunce suna son su san abinda,ake ciki, Nace gaskiyane Umma yakamata su san abinda ake ciki hakana don su san matsayar su, Nace Umma bari a kawo maki abinci tace barshi kawai zan koma ina ni ina zama gidan ku inci abinci ace kuma gotai,gotai dani nazo gidan ku na baje ina cin abinci, Nace haba Umma ke da gidan ki tace gidan ku dai kudai keda gidan ku yanzu tunda har ankai ga korana, Har kofan fita na kaita nai mata sai anjima tafita tana dan maganganun ta, Sun safi matumin da,akatura su gurin shi a can kasar Ivory cost sun kuma gamsu da bayanin shi saidai abinda ya,daure masu kai mutumin ya iya hausan su sosai kamar ba dan kasar ba, Yagane suna mamakin shi sai yace nima mutumin Nigeria ne ai zamane yakawo ni nan na zauna, Amma ni dan kasarku ne sunji dadin zama gidan mutumin kuma sun sha daula a gidan sosai, Yai masu hanya yadda ya dace su samu saukin kaya haka yasa su tunanen in har suka samu shigo da,motocin su ba karamin dagawa zasu yiba wanan karon kafin su dawo sunyi phouna sosai don sunji dadi bakunta a gidan mutumin, Ya fada masu cewa zai shiga saudiya don aikin hajji saboda haka ba lalai ne su dawo su samay shi ba a garin, Sai shima hamza ya ce shima yana ganin in yasamu hali yana son zuwa bana saudiyan don akwai business din da yake son yafara yi a can, Duk process din da mutumin ya tsara,masu haka suka bi cikin ikon Allah sai ga motocin su da masusukan da suka,saro sun shigo Nigeria hankali kwance ba kamar yadd in zasu shigo da kaya suke shan wahala,ba, Yai muna tsaraba masu kyau irin na mutanen kasar yazo muna dashi, kowa har yaran duk mun samu tsaraban shi, Abinda ya,daurewa Biba kai yanzu shine duk kayan da take dasu a cikin kayan lefen ta,sai taga nima ina dasu abin sai ya daure mata kai tare da bata haushin haka, Watau don son da yake min ma harda lefe ya hada min irin nata kenan, ko ranan da yadawo wani lace da take kuri dashi nata blue nawa light pink nasaka ajikina, Ta hadiyi rai har tagaji gashi bata,san hakane ba duk ta mulke nata kayan ita, niko yanzun ne ma nafara,sawa, Sai wanan dawowan Biba taga cikin dake jikina tai matukar yin shock sai dai bata yabbatar da,zargin taba sai lokacin da,taga yadan rugumoni zuwa jikin shi yana cewa ya kuke ya kuma girma, Murmushi nayi kawai tare da karban jakar kayan shi na,shiga dashi daga ciki, Inda take zaune tana dariyan yake ya nufa yana ce mata tare da riko hannun ta wai duk nauyin cikin ne ya hanaki taro na yau, Tace ai kasamu taro gurin dayar mai cikin hmmm lalai ma ashe ko akwaita gidan nan , Daki ta shiga tafara kiran uwar ta hankali a tashe take fadin Mummy yanzin ashe makirar matar nan cikine a jikin ta amma ta boye min, Uwar tace ta boye maki ko suka boye maki don ai mijin yasani amma bai taba fada maki ba, Har da kukan ta,wai wani muna funcine nake shirin kulla mata in bashi ba yaya za,ayi nai ciki amma bata sani ba sai yau da Allah ya nuna mata, Dakyat uwar ta shawo kanta tare da bata hakkuri akan haka din, cewa tafita batuna taji da zancen cikin ta kawai ta,samu Allah ya rabasu lafiya da cikin dakd jikin ta in diya ne bagashi zata,fara haihuwa dash ba to may zai damay ki tun da likita yafada maki namiji zaki haifa,, Kin ga ita ko diya mata take ta zubawa ko yaushe sai fa in kin so ki tayar da hankalin ki, Bayan kwana biyu kuma sai ga zance tafiyan su Ummi na saudiya ya bullo ranan kan hauka tai mashi yana daki kwance ta samay shi da kukan ta,wai yaci amanan ta yaya zaikai iyayyena makka ita yaki koda daukan uwarta yakai, Yace ummmwumm ashe son kaki har ya kai can sadiya to ban biya ba,sai ki kaini kara duk inda zaki kaini, don ni fitinan ki wallahi ya,ishe ni Biba, Tafada tai zage zags takiramu da macuta azzalumai mayaudara da dai sauran su harda fata tayi Allah yasa in su Ummi sun tafi can zu mutu,kada su dawo, Agidan su Ummi ma sai bakin ciki da takaicine ya rufe su mama saude tafara tsegumi wai kilama asiri Ummi tai mata sukaki yarda ya auri kubura don Ummi ta bashi ni Baba yacewa mama yaukuma saude dan maysiyanta da kukace a,wancan lokacin don kinga yanzun Allah yai ikon shi a kanshi shine zaki fadi hakan, Umma kan tayi iya nata jidalin tagaji tai shiru kuma tasa shi sai yaiwa Sa,a duk abind ta lissafa ma shi ba bata lokaci sai da yasayo komai,da,ta,lissafa maShi yasayawa, Sa, datu din,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE HAKAN CIN AMANA NE,,,,, Umma tayi kuka bayan ta koma gida ranan har tagaji tasan cewa itace ta jawa kanta don ba abinda bata fadawa wa Biba a kan al,amarin gidan a lokacin tana ganin Biba zata mara mata,baya ta cin ma manufarta na kawar da ni a gidan, Amma,uwar Biba taiwa yarta kashedin hakan tace duk kika yarda da hakan wallahi ke sai naki yafi muni a,tsakani ku, Na horeki ki kiyayi wanan matar don ba alheri take kokarin shuka maki ba, Shiya ashe Biba ta tsani Umma don uwar ta ta fahintar da ita ko waye Umma din, Koda Hamza yadawo yaje gaida ita sai Umma take fada mai irin cin mutuncin da Biba tai mata, Hamza bayan yagama saurare duk da,ranshi ya baci amma,sai ya daure yace, a,a Umma Biba fa yarinyar ce karama kikace nayi hakkuri da,duk abinda tai min a gidana don haka ke ma Umma don Allah kiyi hakkuri yarintar natane takawo gare ki, Ya mike yana cewa ni zan koma dama,nashigo nan gurin Baba Mudi ne kin san bana ina son su sauke farali insha Allahu, Da sauri ta ce wani Mudi kuma yace Baba Mudi dai mana Baban Aisha, nake nufi dashi da mahaifiyan ta gaba daya zasu tafi tare da mama da Jibrin, Sa,a datu sai in Allah yakai mu sutafi da Biba lokacin ta yi aure, Wai ko yaton nan kasan ciwon kanka haka kawai don kudi suna maka kaikayi zaka kwashi kudi kace kabiyawa Mudi kudin maka shida uwar matarka, Umma kudin nawaye ina kudin yarsu ce yakaini ga haka ko abinda yafi haka zan iya masu muddin ina da halin yin su, Yace ni zan tafi akwai inda nake son zuwa umma sai cewa take ga iyayyenka maza a gari baka kaisu sai wasu don ka,gwadawa mutane kai dan dadin buje ne ko, Yace aiko tellan ya iya dinka bujen ke nan yafadi a zuciyar shi, Nan yafitar yabar ta tana ta faman masifa da jidalin wai an mallake sai yadda aka,ga daman yi dashi baida fadar kan shi, Tai tsuki tace ita wanan banzan Biban da ya dauko bata san ciwon kan ta ba ma balle na wani, Duk da ya hasala da abinda Biba taiwa Umma sai ya ke kokarin share zancen don bai iya daukan mataki a halin da take ciki ga tsohon ciki a jikin ta, Biba sai jira take yai mata magana don tasan cewa Umma ta fada mashi komai yadda,sukayi amma abinda tayanke zata fada mai shine Umma karya take mata da,sheri, Tace Umma ce tazo mata da wani zance da bata yarda dashi ba haka ta kulla a ranta, Sai dai bazaman lafiya don gani take Hamza da Aisha yaudaran ta suke suna cin amanan ta kawai, Abin yakai su har saida iyayyen ta suka zo a wani dare ana sulhunta su a dakin ta ake zance amma zakace a tdakar gidan mu ne saboda yadda Biba ta daga muryan ta tana kuka tana magana, Wallahi gwago bai daukeni a matsayin matar shi nake ba don banbancin da yake muna, Komai yasamu sai Aisha da diyan ta kawai yasani sai yan uwanta gwagon nata tace a dama ke yaya kike so so kike ya,watsar da iyalin shi saboda ke, Kinki kwantar da hankalin ki kina bin rudin shedan yaya kike son gani dama, Kuma mu mun san yana muna duk cikin mazan yan uwan ki bamu da kamar shi wallahi, Idan ke baki ganin abinda yake maki mu muna gani, don mun san yai muna, Kishiyar ki kuma batai muna komai sai alheri don ba mai zuwa gidan ga yace tai mai wani keko fa kinawa nata mutunci yadda take muna, Ni ban ma gan su ba balle inji Biba din sai dayar matar tace kingani basu ma zuwa ke nan, Gwago duk muka tashi magana sai yace min wai shi bai iya yiwa matarshi komai don da ita yake tunkaho, Hamza dake gefe zaune yana wasa da hannun mimi da yashiga da ita dakin yai murmushi zuciyar shi tana mashi soya, Kin dai san yadda gidan ku yake kece uwarki tafara yiwa aure idan baki kwantar da hankalin k8 ba kika bantale auren ki dake da ita sai ai maku dariya, Sai lokacin yai magana yace wallahi gwago tausayin mummy nake ji amma ita batasani ba don koyaushe tana kirana ta bani hakkuri, Amma ita bata san hakan ba burin ta kawai taga tatayar muna da hankali a gida , Itace kullun akewa laifi ita ba taiwa mutane batasan hakkuri kowa keyi ba, Yadda kike nufin na wullakanta mamata saboda ke na fada maki hakan bai yuyuwa don ni batai min komai tsakani da ita sai rufin asiri da zaman lafiya don wallahi tunda na,auri Aisha ba a taba shiga tsakanin mu ba, Gwagon ta tace tau ke kinji ke ko aure ko shekara daya ba a rufe ba kin cika mashi gida da hayaniya, wallahi habiba kiwa kanki fada Allah, Ashiru tayi sukai mata tas akarshe sukace taba mijin ta hakkuri yace ai babu komai ni dai na fada mata komai lokaci ne, idan na samu yadda nake so a gareta komai zai wuce ne, Kwana biyu kamar ta daina a na zaman lafiya da kowa a gidan ba wani matsala kuma sai dai ance mai hali baya barin halin shi don ita kishi halin ta ne karara, take nuna shi ko a bako ne balle mu yan gida, Tafiyan su mama yazo don haka banda zama gida sai faman zirga zirga nake ban gidan mu ban gidan su Umma, don ganin komai ya kammalu, Sun tashi lafiya yabani kudi nakaiwa Baba yabarwa iyalin shi tare da buhuhunan abinci da zasuyi amfani dashi, Tun ban fitaba Atika tace bata yarda ba saidai a raba aba kowa nashi kada diyan mama saude suzo su kwashe , Tana nufin su kubura wace yanzu mijinta komai ya kara dagule mashi tayi yaji tayi fitina ya sake amma yaki sakin ta, Sai bakin wahala da sukeyi don sai sun nemo da kan su sunci har dashi saboda yanzu ba,a harka dashi ga sabbin matasa masu irin harkokin shi sun taso, Dole baba yasa a raba masu kowa ta kwashi nata zuwa dakin ta dashi kudi ma,sun raba ganin haka nacewa Ummi zan tafi dasu yan biyu gidana na zauna dasu harta dawo, tunda abu ya koma haka, Ummi tace nima tunanen da nakeyi ke nan don da gidan Anti naso na kaisu amma kuma itama tana fama da kan ta, Ummo taje tafadawa Baba yadda mukayi yace shima haka yafi mashi kwanciyan hankali Ban dawo gida ba ranan saida yaran da kayan su sai dai ban kwaso duka ba, Ganin yaran ya tayarwa Biba hankali ta samu Hamza a daki tace wai na cika gida da yan uwana da diyana an mayar da ita boya, Ya dago kai ga abinda yakeyi yace haba BIBA Biba ke na gane problem ce, Kin zama Biba PROBLEM wallahi komai kice ke an kun tata maki to naji badai girkin bane matsala tace to kai bakaga yadda nake bane yace angama, Da dare ya hadamu a falon shi yace abinda yasa na taraku shine ina son daga yau ku raba kitchen din ku kowa ta dinga amfani da nata nikuma zan sayo kayan abinci na ajewa kowa nata, Ke Aisha ki girka naki da duk wani wanda yake a karkashiki har ni idan ina dakin ki kiyi dani, Ke kuma Biba daga yau kiyi wanda zaki iyaci iya ke sai ni idan ina gurinki ina shike nan yanzu zance ya kare, Gyaran gida kuma already madina keyi ba,wani kyashi ko jin haushi sai taci gaba dayi yadda ta saba, Ya juya inda nake yace ki min list din komai da ake bukata na amfani gida sai nasa a kawo maku, Biba tace ke nan nima nayo nawa ko yace akan may zakiyi naki daban nata daban kike nufi k8 bari idan an kawo sai ta cire maki naki, ina shike nan an gama zancen ba wano korafi kuma, Najuya na kalli Biba wace ke ta wani kumba tana ya mustan fuskan ta sai na gane cewa itacdme ta samay shi da wani zance ke nan, Kamar yadda yace haka nayi na,saya muna komai yadda ya dace ankawo muna yake cewa shima yana son yai tafiya zuwa saudiya amma ta international yake son zuwa don akwai business din da suke son zuwa can su kullah, Ana saura kwana biyar ya tafi Biba ta tashi da nakuda ba bata lokaci yangidan su suka zo aka kaita asibiti, , Bayan dan lokaci kadan ta haifo yarta,mace bakakirin da ita babu inda yarinyar ta biyo hamza sai uwarta, Tun bata sauke numfashi ba take tambayan nurse din may ta haifa sukace mata baby girl wani irin abu taji ya soki zuciyar ta, Haka ta fito daga dakin haihuwan ranta babu dadi ita yar jaririyar sai faman tsula ihu take tana neman agaji, Babu kowa daga gidan su Hamza kuma kowa yasan cewa za,a zo asibiti da ita a lokacin amma sunki zuwa hakan ya bata ran iyayyenta sai faman masifa sukeyi suna cewa wai lalai akwai kiyayya mai karfi a tsakanin su shi gaiyar aikin shi kadaine yatafi sai abokin shi, Can yabar su yadawo don ance wai a bari ta dan huta saboda jinin da yake dan zuba mata, Biba tana kwance a gadon da aka bata a,sibitin wasu yan siraran hawaye suka zubo mata ba wanda yagani sai gwagon ta ta duka kan ta kamar may rada tace, Amma Allah waddai da halinki Habiba nafahinci hawayen ki na butulcine wa Allah akan yabaki diya mace kike wanan kukan haka, Tace ba hakana bane gwago tace wallahi maza ki share hawayen ki tun duniya batayi dake ba, sakariyar banza kawai su diya matan da aka haifa mashi kinga yakai su jujin da akeyar da su ne, Bashiri tafara dan kakaran dariya a fuskan ta don bata san za,a iya fahintan taba amma ina har sun fara yin rada a kan ta, Saice mata suke dan baba yafito da dabe sai yaya kuma tace wanan ma yar baba ce ai, Ya dawo gida yake sheda muna an haihu lafiya muka hau murna da farinci sai dai ban tambayi mai aka haifa ba, Sai doki da murna kawai mukeyi yakalle ni cikin sha,awa da tausayi yadda nake nuna farin cikina , Dago kai ina cewa yau Amarya ta huta da nauyin ta saura ni kuma Allah ka saukeni lafiya kabani mai albarka, Yace amin su Jidda sun samu kauna ya fadi cikin lumshe idanuwan shi nace a, mace Allah yabamu,? Allah ya raya muna ita yasa mata albarka yace amin Aisha amma ai ita uwar diyar naga batai murna ba sai fushi takeyi, Akan may natambaya yace ba ta haifo maki magajin da tace ba mana ya wuce shi takewa bakin rai, Yanzu suna ina yake ce min tana can ance abari ta dan huta tukunna sai anga yadda ta kasance tadawo, Nan nashiga buga waya ina fadawa mutane Amarya ta haifo ban bari su tambayeni sai na kashe wayana, Umma tanajin an haifu cikin kaguwa tace may aka samu yace mata mace,. Shiru tayi babu ko Allah ya raya, Dariya yayi bayan ya kashe waya yace Umma ke nan haryanzu dai tana ga akidar ta ke nan, Sun dawo gida da yar jaririyar baka batada kama dakowa amma sai naji yan uwa Biba suna fadin wai yarinyar tana da kama da mimina, A zatona yan uwan shi zasu shigo ko don dan uwan su da akaiwa haihuwa amma babu wanda yashigo gidan ranan, Washe garima basu shigo gidan ba sai wajajen karfe biyu sukazo ganin baby nasan daga gidan Umma suke, Matsalar da akasamu shine nadai yi masu abinci dadare na basu amma da rana Anty hindatu ta hana na basu, Shiru shuru suna jiran nakawo masu abinci basu ga na shigo dashi ba ga yarana zaune falo suna cin tuwo shimkafa da miyar agushi yaji manja da nama hudun gudun, Gwagon ce tafito take ce min Aisha sai naga har yanzu ba,a kawo wa maijego abinci ba dai, Nace a gwago ita Amarya bata fada maku cewa girkin mu ba,a hade yake ba don haka ko na jiya dai na taimaka ne nabayar kawai, Subbahanallahi inji gwagon tana cewa ya akai haka kuma, gida daga ki sai diyan ku ace an raba girki nace gwago matsalar yarki ce itace ke da bukatan hakan don ra,ayin ta ne, Gwagon ta juya zuwa dakin dake cike taf da jama,a sai hira akeyi tace Habiba yaya tsarin gidan nan yake maku ne wai don nasamu kishiyar ki da zancen abinci take ce min wai ba hakkin ta bane hakan, Gaba daya dakin tsit akayi ana sauraren zancen gwagon sai yan katsalanda suka fara cewa wai ga zancen banza may take nufi da fadar hakan, Gwagon tace ku dakata koma may ye ai ita habiban tasani don dole akwai matsala ai, Ita ko Biba cewa tayi ga yar iska kawai yar rainin, wayyo bari na fita nai mata magana may take nufi, Wasu suka ce a,a kira mijin ku kawai ki hada yar iska dashi amma ta yaya za,a haihu kice bakiyiwa yar uwar ki girki saboda kishin tsiya, Kiran Hamza tayi yadauko yana fadin salamu Alaikum, tace amin wa,a laikun sallam my kana ina ne, Don Allah kazo gida don akwao magana saboda Aisha ta hana min abinci ni da yan uwana, Yace kamar ya bata baki abinci ba kuma zata fara magana yace ke ganin zuwa ajirani nazo ya kashe wayan kawai, Sai da ya,dan dauki lokaci yashigo gidan da sallama ina dakina kwance don hadarin da akayi ba ai ruwa ba yasa wa garin ni,ima, Hakan yasani jin dadi har barci ya dan kwashe ni ban sani ba duk da yaran suna ciki suna kallo don na hana su zama falo don ina gudun su ja man fitina, Yaran suna gaishe shi amma duk banji sai da ya karaso inda nake kwance yaja min kafa a hankali idona da nauyi barci na bude su kyat yana tsaye a kaina yake ce min, Wai may ke faruwa ne naji wanan ta kirani a waya wai ko zancen abinci,? Dan tsuki nayi ina mikewa nake cewa wai kamar ya abinci cikin matse fuskana yace min zo muje falo muyi magana a can, Da kyat na samu na mike zaune ina daukan dan kwalina da ya zamay a kaina nabi bayan shi nasan yace mu fita dakin ne don yaran dake ciki suna kallo, Dakin Biba ya leka yace su zo ita da gwagon ta suka fito a tare muka shigo falon da su lokaci guda, Yace maynene kike fada min awaya ne wai don ina a cikin mutane banji sosai, Tace wanan yar bakin cikin matar taka mana ta ki dafa muna abinci ga mutane a dakina har ni kaina banci komai ba, Ya juya inda nake yace Aisha yaya akai hakane wai, Nace ban gane yaya akai haka ba ka manta cewa tace bata son hada girki damu ne ko kuwa dan ina Aishan sokaye sai naje mata girki tace wayasani, Ko kuwa don ina neman suna sai naje girka maki abinci ki koro min shi don nasan ba zai maki wuya ba hakan, Munafuka dama,muna funcin da kika hada ke nan ashe ban sani ba ai dana sani da nasan shirin da zan maki nace to ai yanzu kin sani don haka sai ki shirya da kyau,, Badai haka kikace ba akwai zamu zuba cikin gidan nan ni da dake shege ka fasa munafukar banza da wofi kawai, Ke yadaka mata tsawa cikin wani irin murya mai firgitawa, yace da idanuwan shi da suka kada sukai jawur tare da nuna mata dan yatsan shi, Wallahi Biba ki shiga hankalin ki ke wallahi kin isheni kin isheni a,rayuwana wallahi nayi dana sanin auren ki wallahi, Fitinar ki yakai min ko ina wallahi ace mace bata da,aiki sai kirkiro jidali Wallahi bari kiji ban auri macen da zatazo cikin gidana ta,wullakan ta min matana na ba, Wai ashe matace ai ban sani ba take idanuwan shi suka kada sukai ja yace ashe baki sani amma daga yanzu zaki sani ai ban san baki san matana bane tun farko, Ya kada kai yace ba komai zan fahintar dake mutanen dake dakin ta suna jiran aci min mutinci sukai tsit suna sauraren mu, Ita gwagon ta sai fada takewa Biba tana cewa ashe banda mutunci a idon ki habiba, Yace gwago wanan yarinyar bata da mutinci sam bata son a zauna lafiya a gidan nan, Gata a tsaye ita da kanta tai tsaye kan sai na raba girki a tsakanin su don ita bata iya girka abinci Aisha da diyan ta suci, Don gudun fitana badon tafi karfina na yarda aka raba don may kuma yanzu zatace wai Aisha ta girka mata bayan kowa na bashi wanda zaiyi amfani dashi a kitchen din shi, Don may yasa na yarda da hakan badon kawai a zauna lafiya ba ta manta da irin wanan ranan lokaci da take kulla tsiya a ranta ko, To Aisha bazata girka maki abinci baki bari itama in ta haihu kada ki girka mata bashi ke nan, ba, Dama ai ance inzaka gina ramin mugunta gina shi yazam gajere, Ya juya inda nake yana cewa koma dakin ki kawai shike nan zan san abin yi, Nace tare da jefa mata harara nace baki da,wayyo Biba da baki wanan haukan ba sakariya kawai, Nasa cikina gaba na shige abina nabarta nan tana haushi kamar karyan da ta haihu, Nashiga dakina ina mai jin haushin wanan halin na Biba sai dai ba yadda zanyi don zama ya hadamu sai hakkuri kawai namiji mai aure aure tun yana auro na kwarai dama,watarana sai ya,auro manya, da zata cinye shi ta cinye mutanen gida,. Komai na shagalin buki a hannu na yabar shi wanda za,ayi a cikin gidan nace bazan karba ba yace shi tsarinshi ke nan, Don haka duk abinda za a aiwatar nice zan aiwatar dashi ke nan, ya bani wanan damar, Yai muna sallama yatafi sauke farali kasa mai tsarki shida wasu abokan shi, Data kirashi kan yaya za,ayi yace ki tambayi matata na bar komai a gurin ta, Haba ina wuta Biba ta sakani ranan nasha balai da masifan zagi a gurin ta kamar zata cinye ni dan ya,, Sun kira shi akan don may zaiyi masu haka yace don tasan cewa Aisha mata ta ce shiya na lurar da ita cewa a,tare ta samay mu, Doleba yadda za,ayi suna ji suna gani dole suka barni ana karban komai a gurina daga su har yan uwan shi, Anyi suna an watse lafiya yarinya taci sunan mama hafsi bakin ciki a furin Biba bai missaltuwa don har cewa tayi anyi hakane don aci mata fuska an sawa yar ta sunan mama hafsi,, Sai faman nuna ni aje gani da cikina,tsiriri sai bina da idanuwa kawai akeyi kowa da irin abinda ake fadi a kaina, Nikan ina dakina da mutane na abokan arzikina da suke tare dani muna hurdan alheri, Yadda taso ayi shagali na gani na fada hakan bai samu ba don babu halin hakan daure ko ina don ya hana mata kudin komai sai cewa yayi duk abinda za,ayi a tambayi Humaira zata bayar, Ita kuma kishi ya rufe mata ido bata iya tambayan na komai don fadin rai irin nata, Haka akai shagalin ba,wani abin azo a gani na shagali da akayi kamar ba gidan mai hali ba, ****** ********* ****** Asaudiya bayan ya isa ya samu su mama hafsi da su Ummina a masaukin su, yakara masu kudi akan wanda aka basu guzuri na mahajjata, Kamar yadda suka tsara haka akayi don sunyi Meeting kan harkan bunkasa harkokin business din su, Suna gurin Meeting din ne aka bugo mai cewa Baba Mudi baida lafiya don haka ana tashi yace zaizo yaga surukin shi don baijin dadi, Sai suke cewa ya,shigo su rage mashi hanya su sauke shi sun tafi masaukin sai babba daga cikin abokan nashi suke cewa bari su shiga,su gaida mara lafiyan, Gaba,dayan su suka,shiga dakin don ganin jikin Baba dake fama da zazzabi da mura, Mama hafsi da Ummi suna dakin a lokacin sai dai jin mazane suka,shigo dakin yada,su juya bayan su, Suna tsaye mutane suna magana suna gaida baba daya bayan daya sai babban nasu yake fadin, Manene likita yace yake damun shi muryan mutum yasa Ummi saurin dago kanta dake duke don murya ne na mutumin da bazata taba mantawa dashi ba murya ne na mutumin da taki jini a,rayuwan ta da can baya, Sai dai kuma,shi wanan murya hausan ta yasha banban da muryan wanda take tuhuma saboda hausanshi a kwai surki a cikin ta, Saidai ta dan davo kai taga wake da wanan muryan mai balain kama da nashi haka, Fuskan shi ne karara duk da ya kara kiba farin shi ya kara fitowa ya koma wani babban mutum a idanuwan ta, Bata san lokacin da tace, yaya Bello dama kana raye a duniyan nan kabar gida kabar yan uwa ka kabar kowa naka a gida hankali a tashe, Kallonta yake acikin mamaki bashi ba harsu hamza dake dakin kallon mamaki sukewa Ummina, Sai da yai murmushi dama murmushi halin shi ne yake cewa wanake gani kamar Fatima, Sai kallon ya koma akan su cikin mamaki ya nuna ta da yatsa a cikin harshen yaren kasar Ivory cost yake ce masu sister din shi ce kuma matar shi ce ta da har sun haihu da ita, Gurin da Hamza yake tsaye yai mutuwar tsaye a lokacin yace ma hamza din a ina kasan yar uwata wanan yar uwatace kuma matata da muka rabu har na haihu da ita, Yace nafada maka cewa ni dan Nigeria ne tun farkon haduwar mu ni mutumin yankin sokoto ne zamane yakaini kasan da ka ganni, Har Allah yai min arziki haka ina kuma da iyali a can din yanzu haka, Sai kallon mamaki sukewa mutumin harda Baba mudi dake kwance saida ya dan mike zaune yana cewa ikon Allah dama kana raye ake nemanka an rasa inda ka,shiga Alhaji Bello, Ya nuna Hamz yana cewa wanan da kake gani surukin kane mijin yarka Aisha wacce yanzu take da yara biyu na,uku na cikin ciki, Shine kuma yai muna,sanadin zuwa sauke farali ta hanyar arzikin da,Allah yaba shi, Zaune mahaifina ya kai daga tsayen da yake yana cewa ikon Allah Alhaji Hamza dama kai nawane ashe Allah mai iko, Dalilin da yasa ke nan ashe naji ka kwanta min a rai abinda ban taba yi ba aruyuwa na don ban yarda sam da mutanen,Nigeria saboda sun faye yaudara, Hamza yaji a take wani nauyi da kunya ya kamashi na mutumin, da aka kira da sunan surikin shi a gaban shi, Ummina ta kara cewa haba yaya Bello kabar gida da yan uwa a ciki tashi hankali har yau suna a cikin bakin rashin sanin in da kashiga a,duniyan nan, Murmushi kawai yake yana dan buga kafanshi a hankali, tare da tunanen abinda ya faru tsakanin shi da yayan shi shekarun baya da har yai mai gorin arziki akan gona, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,,, ALLAH ya dawo muna da shi lafiya mun tare shi a cikin jin dadi a can yabar su baba sai jirgin mahajjata na hudu zasu dawo, Sai da yai wanka ya huta yaci abinci don lokacin, yamma tayi da ya iso, garin, Daki ya samay ni zaune gurin da na idar da sallah na tasa cikin da yai mai girma a gaba sai damu na da motsi yakeyi, Ya shigo dakin saye da sabon jallabiyar shi, fuskan shi dauke da murmushi yana min kallon kauna a fuskan shi, Yace wanan cikin Humaira nake ganin kamar yafi na su Jidda girma sosai don baki taba ciki haka yai girma ba, Nace cikin ya mutse fuska wallahi nima haka nake ji ga kuma shurina da ake kamar ana kwallo dani kayan ciki na, Dariya yayi yace kila dan kwallo kika samo min wanan karon nace ni uwar diya mata ne fa inji Umma ka manta tace mata zanta haifa ma tunda suna fara dasu, Shirmay ke nan zancen Umma wake shiga daki dashi tunda ba itace Allah ba, Yace ni har ma kin bata min rai wallahi ko diya bata dozen za,a haifa min ni ina maraba dasu Allah yabani abinda zan duba tarbiyan su dashi kawai, Yace ke nazo ne fa in maki wani albishir na gyara zama ina cewa masha Allahu tun ban ji may zaifada min ba, Yace amma sai naji goron da za,a bani tukun don ba karamin albishir nazo maki dashi ba, Nace to may zan baka tunda na fahinci abin babban yadda naga kayi serious akai, Yace cikin shafan fuskan shi kema aikin san abinda zaki bani ya wuce kibani jikin yau namora son rai na, Dariya nayi nace kai wallahi yaya baka gajiya da wannan har kan kai yace ina zan gaji da bautar Allah Humaira, Nace yanzu dai fada min albishiri din yace to kema kin yi alkawari ko nace ai wanan tun ranan daurin aurena nai alkawarin hakan yace good, Tau nafa ga Abba Humaira nace cikin tambaya Abba wani Abba ke nan yaya yace Abba Bello mana mahaifiki, Wani, irin zabura nayi daga zaune na mike tsaye don har na manta da cikin da ke a jikina a lokacin, Nazo gap dashi nace wai da gaski dan Allah dai yaya,? Yace wallahi Allah har Ummi ma da baba sun ganshi don muna tare dashi, Wani irin ihu na tsaga sai kuma ga hawaye shar sun zubo min ban san lokacin da na fada jikin Hamza ba, Ihun danayi ya jawo hankalin kowa a cikin gidan suka yo dakina har Biba da gwagon ta dake zaune damu a gidan suna tambayan ko lafiya, Ganina sukayi rugumay ajikin yaya ina kuka yana dan bubuga min baya a hankali kamar karamar yarinya, Azaton su ko Ummina ce ta mutu a makka don har Biba tafara fadin gwai muga karshen bin bokaye, Gwagon take tambaya sai yadan dago fuska da murmushi yana fada mata cewa mahaifinta da ya bata shekara da,shekaru, tin tana goye ne ya,baiyyana, Allahu akbar inji gwago din tace Allah may iko sai biba ke cewa a,saudiya yana takari ko? Wani kallo yai mata yace ko a inane ai angode Allah tunda ya baiyyana dai, Gwagon ta,shiga fadin wanan abu yai dadi gaakiya,ikon Allah ashe yana kasar Saudiya ke nan duk dadewan nan, Sai Biba tace ai hakana mutanen mu ke yi sai ki ga, don wahala da kwadai mutum yabar gida ya koma can yana watsar da kai don son abin duniya, Abin yai min zafi a,rai amma yanzu ba lokacin mayar da martani bane agareni lokaci ne na farin ciki da godiya ga Allah ubangiji talikai, Shiru yabiyo dakin gaba daya har yara duk suna tsatsaye suna kallon yadda nake kuka yana lalashi na, Yace ai gwago mahaifin Humaira ba saudiya yake ba yana nan kasan Africa zaune, Rashi sani bayau bafa nasan shi don a,gurin shi muke sarin motoci can kasan ketare da muke zuwa , Biba ta wani cewa may ne,? A gurin shi fakace kuna sarin motoci da kuke shigowa dasu yace kwarai kuwa don shi ya na cikin mayan dilolin kasan Africa da aka sani, Shi mahaifin Aisha din Biba ta tambaya yace mata kwarai ban san lokacin da nakai gurfane a kasa ba na fara rusa wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraren ta, Cikin kuka nake cewa Allah na gode maka da ka baiyyana muna da Abba lafiya, Biba bata kara magana ba tun lokacin da taji amsan da ya bata atake, Cewa tayi gwago muje Allah ya kyauta , kawai tafita daga dakin sai gwagonta dake tsaye tanace min kiyi hakkuri haka Aisha ki godewa Allah, Yace mata ai kukan murna takeyi shi yasa nabarta tayi mai isar ta har tagaji, Tace kaiko Hamza ka lalashe tabar kukan haka kaga ba ita kadai bane a jikin ta kada kukan ya taba abin cikin cikin ta, Sai muryan Biba take cewa gwago ki fito mana nace mu koma daki tace ai gani tafe ke dai yar nan a tafi abarta tana kuka, Saida ta dan tsaya tabani magana irin na su na manya sannan tafita daga dakin, Nai shiru kamar yadda tace ita da hamza yajani zuwa bakin gado na zauna yaci gaba da bani labarin yadda suka hadu dashi har da Umma, Nace cikin goge fuskan yanzu Abbana yana raye shine ya bata haka yabar gida yabar kowa nashi ya koma inda baida kowa yace min ya fada min yai aure har da yarinya daya da yaro saidai ba babba ba ce nace Allah mai iko ashe harda kanne, gareni, O, o Allah na Allah na gode ma da wanan ranan dama kullun, Yace yanzu mabar dashi cewa idan ya koma ya huta, zai shigo kasan nan ya gan ku, Ranan barci rabi da rabi nayi don murna bai banni nayi barcin dadi ba ranan duk da gajiyan gurzuwan da nayi a wurin maigidan don sai da ya karbi goron shi, Dasafe tsab na,shirya don zuwa gidan mama Rahana shikuma zai tafi gaida Umma, A kofan gidan su Mama rahana ya sauke mi har yaran gaba daya su biyar nan mukai mashi sai mun dawo yake cewa idan zamun dawo zaizo ya dauke mu, Labarin da na bata yasa ta mamaki tace shin anga Yaya Bello kikace nace wallahi mam a har Ummi ma tagan shi sunyi magana tace shine din ma ba tantama shi din ne tunda har Fatima ta gan,shi, Nan mukaita hiran yadda za ayi dakuma irin yadda ya kwashe shekaru baigida bai kuma waiwayyo gida ba tsawon lokaci yana raye, Mama tace ai mutane da yawa sina wanan hallin su shige cikin duniya,subar iyalin su ba tare da sin dawo gida ba, Tace wani ajaline da kasa kan kirashi nisa da gida wani kuma,arzikin shi ne kan kirashi har inda yake walau na diya ko na kudi, Nace to yanzu mama yaya zamuyi da mutanen gida tace aikiran su zamuyi mu sheda masu don su shirya tunda duk yawancin kaddarorin shi an sayar dasu don su aganin su baya raye ya mutu, Nace yanzu kan yadda yaya yake fada min ai, bai ko kawo zancen wanan a ranshi, tace amma ai hakkin shi ne dole su bashi nace tau sai dai in Allah yakawo muna shi din ko, Sai yamma muka shiga gurin Umma ta,tare mu kadaran kada ham, ba yabo ba fallasa kamar bazatai min murna ba sai take cewa ashe mahaifinki ya baiyyana, Amma ni dai sai nake ganin kamar bashi bane kila kama daine suka gani kawai a take naji wani iri don ta nuna min hassada nasan kuma za,a shiga wani sabon kulli ke nan akan zancen, Ba,a dade ba yaya yazo ya kwashe mu take cewa duk yaran nan ashe kai aka kaiwa dawai niya haka, Allah dai ya kyauta don irin haka nasan watarana har uwar zasu koma gidan ka gaba daya, Umma wai wani irin zance haka saboda Allah to wallahi bari na,fada maki gaskiya mahaifin Aisha duk fadin garin nan yanzu banga wanda ya kaishi hali ba, Ikon Allah Allah yasa yadawo din mugani don wanda ya saba da yawon duniya ai bai tuna gida balle iyalin shi, Mu dai mukai mata sallama muka tafi zuciya na tap da kuncin maganganun Umma sai na,shiga tunane barkatai akan zancen,ta,, Sai washe gari na bugawa gwagona waya ina,sheda mata albishir din ganin dan uwan ta Tace bari takaiwa liman waya don kada tani ita kadai shima na fada mashi yadda yaya yafada min yace masha Allahu Allah mungode ma in har shi baizo ba mu mu shirya mutafi kwanan nan, insha Allahu, ****** ********* ****** Allah yadawo da su Ummina lafiya su yan biyu tunda mukaje taronta sukace basu dawowa, Daga ita har mama sunyi kyaun su saidai sunda fada don aikin hajjin da sukayi amma gaskiya jikin su yayi kyau sosai, Zancen auren Ibrahim akeyi zai auri diyar wani dan kasuwa mutumin Jega amma a kano suke zaune da iyalin shi, Shima Ibrahim ya hadu da itane can wurin business din shi da yake shiga kano saro kaya a nan suka hadu sundan saba da yayanta shine watarana yaje gidan su yaganta sai soyayya ya kullu a tsakanin su, Umma tana ta murna dan ta zai auri diyar mai kudi ba irin mu ba diyan tallakawa, acewan ta Wai harda karyan anga mahaifi gashi har yanzu ba wanda ya gan shi ke nan karya akeyi, Niko da zancen Abbana nake kwana dashi nake tashi a raina ko yaushe, sunyi waya da hamza akan zancen zuwan shi yake cewa akwai abinda yake son yakammala kafin yashigo Nigeria, Yanzu zancen inda Ibrahim zai sa amaryan shi akeyi Umma ta sa hamza gaba sai ya sai masu gurin da zasu zauna, ko yai maigina a gidan su, Ga shini har zuwa lokacin ban haihu ba cikina sai wani girma yake har asibiti sai da hamza ya kaini akace lafiya lau cikin yake har ni, din, lafiya lau nake haka yasa hankalin mu kwantawa, Ban haihu ba sai bayan sati biyu na haihu wanan karon na kasa haihuwa yadda na saba a gida saida aka kaini asibiti, Yara maza biyu ne suka fito daga jikina kusan lokaci guda sukazo duniya batare da nai mugun wahala ba, Mama hafsi da Anty Hindatu suna,waje nurse din take cewa ku bamu zani guda biyu musa yaran aciki, Yara suna hada baki nurse tace eh maza biyu ta haifa ai baku san cikin tagwaye ke gare ta bane, Wani ihu suka sa a lokaci daya suna fadin Allah mun gode ma wana albishir din dole mu baki tukwici inji mama ta bude post din ta ta dauko dubu daya taba nurse din tana godiya, Hindatu ce tafara yiwa hamza albishir shima hamza ya kasa boye farincikin shi a fili, Umma ce mutum na farko daya fara kira ya sheda mata na haifi tagwaye maza, Ta dan nuna farin cikin ta amma ba irin yadda ya zata ba a furin ta, nan yashiga bugawa mutane waya yana,sheda masu zancen haihuwana, Kafin mu dawo gida gida ya cika da yan uwa da abokan arziki sun shigo tayamu murna zance duk yan uwan hamza suna gidan mu har mazan su sai dai banda Sa,adatu amma nasan ko ita laifin Ummane rashin zuwan ta din, Habiba fuskan ta murtuk yake sai magana yan uwan hamza ke sakewa a tsakar gida don ta tanka, Ba bata lokaci akaiwa yaran wanka harni na kimtsa jikina sai zolaya mutane suke suna maman biyu, Ina dan murmusawa cikin jin dadi da farin ciki don nasan gaskiya wanan shekaran shekaran sa,a tace sosai ga mahaifina ya baiyyana ga kuma kyauta diya har biyu lokaci guda daga Allah, Hamza ya dawo gida daga garin dayake cikin murna da farin cikin shi ya nufo dakina direct don duba mu, Ya samu mama tana gyarawa yaro daya kwanciya tana ganin shi tafara murna tana fadin nikan ai Allah ya na sona maza biyu lokaci guda haka, Nan tai mashi murna sosai da kumafatan albarka ga yaran sai murmushi yake yana fadin amin mama,, Fita mama tayi daga dakin tabar ni dagani sai shi da yaran, Daya bayan daya,yake daukan yaran yana rugumay su tare da masu addua, irin na,addinin musulunci ga yaro sabon zuwa duniya, Tun ranan da,na haihu Hamza bai zauna ba sayo wanan sayo wancen akawo gida tun daga dangin abinci da sha da,suturun yara da,sauran abin bukata, Koda yaushe ina daki da mutanen arzikina ban san tsiyan da Biba ke shukawa ba don a,shirye nake kan ta don nasan dama ta kulla abubuwa da yawa a ranta,. Don ta rama abinda ya faru lokacin haihuwan ta amma sai taga duk na shanye manufarta gaba daya, duk yadda taso tarama,babu halin haka, Suna saura kwana biyu Biba ta samu Hamza, da zancen yabata abin suna da za,a aiwatar, ya dubeta a cikin mamaki yace mata akan may zan baki su Zarah fa, , O ashe kasan dasu kaba ba matar ka lokacin haihuwan hausatu, yace na bayar ne don ita ta,tantanci naba don banis gari saboda ita maya tace, Tace niko farkan ka ce ke nan ko ? Yace gaskiya ban sani ba amma abinda kika gani wai may yasa baki son a zauna lafiya ne Biba, Tace nice ban son a zauna lafiya ko kai da kake macuci azzalumi, idon shi suka kada sukai jawur a lokaci guda, ran shi ya baci sosai, Yace naso ace tunda aka fara wanan sha,anin ayin agama shi lafiya dake amma naga alaman baki son hakan ke, Yanzu kije nabaki go ahead kina iya yin duk abinda yadace kamar yadda ita Aisha tayi da kika haihu don ni kinga an min haihuwa yanzu ban son fitina da kowa, Ni may na haifa maka kake nufi wai yace abinda kika haifa mana ko, To wallahi baka son a zauna lafiya ke nan ai naga diya matan da aka fara haifa ma ka na ina akasaka dasu sai wanan guda dayan dana haifa maka kake nuna mata tsana da kiyayya, Yace ciki daka mata tsawa tare da nuna mata dan yatsa,shi yace dakata, Biba kada ki fara ki sawa diya ta tsanata don ina son abina kamar yadda nake son kowani dan da,na haifa, Halinki dai ke uwar tane bai min ba sam wallahi ban son mutun wanda baida mutunci baida tarbiya, Tace nice banda tarbiya ke nan ko may kake nufi yace kina dashi ne dama kike ciwa manya mutunci ido rufe, zatai magana yace ki tafi Ki tafi duk abinda yadace ki yi kiyi ai kema bukin shafe ki tunda mata ta kike, ita Humaira da kika haihu ai tsaye tayi tafitar dani a kunya, Tace in kana son haka kabani kudi yadda ka bata Yace kudi naba yan uwana don sun san zafina kuma zasu fitar dani kunya, Ranta yai matukar bace zatai magana yace for god sake kibarni in huta Biba tun ban bata maki rai ba a gidan nan kinji magana ta Ya duka kan computer shi ya barta nan a,tsaye ta dan dauki lokaci a tsaye sai ta kuta tafita tana yan maganganu, Har akaci aka,sude bata saka kanta cikin duk harkan sunan da akayi ba abinci ma da aka kai dakinta cewa tayi afita dashi bata so, Hamza yai muna kokari sosai sai dai gurin kayan tufafin da ya,samin daidai ne da wanda yasa wa Biba din, don adalci Kayan yara ne dai gaskiya sunsha kaya sosai gurin shi da gurin yan uwa, nan ma saida tai mashi korafi akai, Bai kulata ba don yasan fitina halintane bata raina abin magana ita ita dai ko yaushe ai jidali shine zaman lafiyan ta, Saidai bata da riko da zaran tayi masifan sai kuma ta sake tadawo tana neman shiri kamar ba ita ba hakan yasa sam bai sake mata yadda take so Bayan suna da kamar kwana biyu sukai waya da mahifina yake fada mashi kaya suna hanya ya turo kafin ya shigo amma kuma ance custom sun kama, Bai gama magana da abokin shi dan custom wanda sukai NYSC tare ba, sai ga kiran Umma yana shigowa, Ya dauki wayan bayan yagama magana da mutumin,yakira Umma da daukan shi Umma tafara mashi korafi akan zancen auren Ibrahim Yake cewa Umma na fada maki a nan gida zan mashi gina yanzu kuma ga zancen auren Sa,a ga zancen kayan mu da aka rike muna, duk sune a gabana , ko may tace mashi oho, yadai yi murmushi kawai, Yagama wayan yana cewa komai yazo ana son kwantar da hankali a cikin sa amma Umma bata ganen haka ko dukiyan nawa take son na kwashe lokaci guda nayi lalurar dasu, Ba wanda yai magana a cikin mu don duk muna gurin a lokacin, Hakan baima Umma ba washegari tunda safe sai gata sai dai tai rashin sa a har yafita zuwa Kamba, gurin kayan su, Ni ina dakina kwance don na dan samu barci a lokacin Biba ce a falo tana gyaran gurin ta, Sun gaisa da ita take cewa ina yake ne tace wa , Umma tace maigidan mana don naga yana son raina min wayyo kamar yana bakin ciki da dan uwan shi, Sai Biba tace, kai amma dai Umma wai wanan abin da kukeyi zaku barmu da,arzikin mu kuwa, ? Cikin mamaki Umma ta kalle ta tace, ban gane arzikin ku ba tace ko na kine to kullun ace kawo a kawo kamar an samu saniyar tatsa, Ran Umma yai matukar baci kamar habiba har zata tsaya don rashin ta ido tana fada mata wanan magana haka, Hannu Umma ta daga zata mareta sai Biba ta rike hannun Umma din tace akan may daga fadar gaskiya, Sai ta tura Umma baya iya karfin ta da baya tafadi tafada saman glass din flower dake tsaye gefe, Wani kara Umma tayi tamike tana cewa cikin mamaki ni kika yar a kasa Habiba, Kadan kika gani wallahi, in tsoho baiji kunyan hawa jaki ba jaki bazaiji kunyar kadashi ba,ai, Cikin fushi Umma takara kai mata duka itama rai bace tajuyo takai ma Umma wawan mari kayauuu, Daidai lokacin hayaniyar su da ya tayar dani har yara muka fito da saurin mu, Biba tana huci tace wallahi dadin aure ba zai sa ina tsaya har uwar miji ta doke ni ba, sai faman huci suke yi, gaba dayan su, Madina tace Umma jini yana zuba a jikin ki dubawa mukayi gaba dayan mu, Jini a kafan ta da hannuwan ta duk kwalba ya soke ta ga idon ta da yai kwancin marin da akai mata, Innalillahi nace habiba yaya akai haka dan Allah haba in rai ya baci ai hankali ke nemoshi amma hakan baiyi ba,wallahi, Umma ko take hawayen bakin ciki suka rufe ta sai tafara kuka tana sharan hawaye, Tana cewa yau na,shiga uku Habiba nikika mara tace ni ban mareki ba ki kadai mareni, Da kyat na lalashi Umma nace ta tashi a kaita gida, don kada ta zauna bakin ciki ya kasheta don sai faman ajiyan zuciya takeyi, Tun yana can yan uwanshi suka buga mai waya yadawo ranshi a bace gidan su yafara zuwa yaga Umma wace har ta bayan duwawunta duk kwalba ya soketa, Ya shigo gida rai a bace tun daga kofa yake kiran Biba da karfi idanuwan shi sun kada sunyi jawur, dasu, Biba tafito daga dakinta sabale da yarta a kafa wani wawan mari mai ji da lafiya ya kwashe ta dashi saida ta,wurgada yar ta kasa yarinyar ta tsala wani irin ihu na fito daki da sauri na dauki yarinyar yakara kai mata wani marin, Tace yanzu don naki yarda da shawaran da Umma ta kawo min akan a hada kai dani a cuce ka kake min wanan dukan haka, Tsayawa yayi yana kallon ta yace cikin fushi shawaran may takawo maki da har kika mareta, Tace zuwa tayi fa,wai na bata hadin kai mu kori Aisha takawo min magani wai nasa maka ga abinci kaci sai kaji ranka ya fita ga Aisha da yaran ta baki daya ni sai na zauna ni kadai a gidan, A take naga jikin Hamza yai sanyi ya juyo inda nake tsaye ina lalashi yarinyar dake kuka a hannu na, Yace ita Umma tazo maki da wanan zancen tace harma maganin da ta bani yana a dakina don nan tabar shi ta tafi, Don naki karba shine takai min mari nakuma naje na tare na juyo shine tafa saman glass din flower tafadi kasa,ta buge fuskan ta takara mikewa zata dakeni na rike mata hannu, Kan shi yadafe yana fadin Innalillahi, Umma may nai maki haka kikeson ki kashe ni da raina, Biba tace ta dade tana bani shawara kan nasan yadda nayi na mallake ka ka fita zancen Aisha saini kuma tace ko da ban fita ita zata dinga fita tana samo min magani tana kawo min, Duk wani fitina da kaga inayi a gidan itace ke cewa wai kada na yarda ka maishe ni boran gidan ka, Yace ya ishe ni haka Biba ya isa nace maki tace har yaran nan da aka haifa tace zata bani magani na shafa masu su lalace tun suna yara tunda bani na haife su ba, Ido na ware waje nace su wa yan nan yaran da basu san komai ba za,a hada dasu, Biba tace wallahi ta dade tana bani wai na shafawa Jidda da mimi su lalace, sai hafsat kawai zaka gani, Yace Umma kin kashe ni wallahi Umma mai nai maki zaki min wanan sakaiyan haka Why Umma why me please, Daki yamike yashige gwiwa ba karfi na mika mata yarta na ja yarana zuwa daki ina duban jikin su kamar ina son inga wani abu, Nace Allah ga boyar ka Allah ka kare min yaran nan daga duk wani sheri kamar yadda kullun nake rokon ka, Nidai nasan ban ma dan kowa sheri a duniya nan ba may naiwa Umma take bina da,wanan mugun alkaba,in haka,? Kishi sai hausa kishi harda uwar miji tasaka a gaba kamar kishiyar saure, (fachala),,, Bai fito ba kwantawa yayi abin duniya duk yafamay shi sai tunane yake barkatai kiran Ibrahim ne yashigo ga wayan shi ya kashe wayan gaba daya don yana son samun natsuwa a lokacin, Tunane yake ashe abinda yasa ke nan in Umma tashigo sai ta,shiga dakin Biba tasan abinda take kullawa jinin shi kuma jinin ta, Da akecewa tana fifita diyan Zarah da Asmau akan diyan shi yana take zancen ashe duk hakan gaskiyane bata son diyan shi da gaske, Wata zuciya tace aiba diyan kane bataso ba kaine bata kauna kawai, Yadade a kwance ya kulla wanan ya sance wancan har akai kiran sallah magriba ranan a gida yai sallah bai fitaba, Nima ina dakina kunci da bakin ciki sun isheni a rayuwata sai kawai na yanke shawara nafita nabar mata gidan kawai shi yafi, Tunda har kiyayya na ya shafi yara na za a salwanta min rayuwan su ga banza, Wata zuciya tace min wawiya idan kin fita ma ai kin kara bada kafan ai masu yadda ake so dasu ke nan tunda bada,su zaki fitaba,, Ita ko Biba tana dakin ta sai dariyan mugunta takeyi tana cewa in ke tsohuwar zamani ne nima ai yar zamani ne mu zuba nida ku wallahi, Nagama da wanan saura wanan shegiyar mai zubin bozaye kuma kema ki shirya naki na tafe, Sai bayan sallah ishai Ibrahim ya shigo gidan don yaga wani mataki Hamza ya dauka kan Biba din, Ganin dakin a bude ga wuta yasa shi yin mamakin rashin daukan matakin da Hamza baiyi ba akan ta, Sallama yake da karfi abinda yasa yaran fitowa suna mashi oyoyo Baban mu, Tambayan su yayi ina babanku sukace yana dakin shu tunda ya doki mummy amarya, Dakin ya nufa da,sallama yashiga dakin dan uwan nashi rai a bace sai ya hago shi zaune a saman abin sallah ya hada kai da gwiwan shi wuri guda alaman yana cikin damuwa a lokacin, Da kyat hamza ya dago kai ya kalli Ibrahim din a cikin wani yanayi mai ban tausayi, Yace da kyat ya iya bude bakin shi Ibrahim may naiwa Umma take son kashe ni sai kawai ga hawaye shar a idanuwan shi suna saukowa, sharrrr, Ganin haka yasa jikin Ibrahim yai sanyi yace mai akayi tare da samun guri ya kai zaune, Nan Hamza ya labarta mashi komai yadda,duk sukayi da Biba abinda tafada mashi Innallilahi kawai Ibrahim ke nanatawa yace wanan abin kunya ina zamu kaishi haka yaya may yasamu umamane wai haka, Kai kai Amma Umma ta bamu kunya,wallahi gaskiya ni bazan iya zama a gida daya da Umma ba da matana wallahi gara naje na samu haya yafi mun, Hamza yace shawaran da nakeyi kenan nima na kwashe iyalina daga garin nan nkoma can nesa inda bata ganin mu balle wani abu ya kara shiga tsakanin mu irin haka,. Shiru sukayi kowa da abinda yake tunane a ran shi wanda zai fishe shi, Ibrahim ne ya kawar da shirun da,cewa yanzu Yaya, yaya kake ganin za,ayi magana fa zamuyi wa Umma tasan mun gane abinda take aiwatarwa, Yace Ibrahim may zance wa Umma ni har kunya hada ido da ita nakeyi wallahi ko don ban san may nai mata ba, Kabari gobe zan kira Zarah da Asamau mu hadu a gida sai ai maganan, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON HAKA CIN AMANA NE,,,,, Gaba dayan su suna zaune a kofan dakin umma fuskokin su duk babu walwala a cikin shi, don fuskokin mazan a murtuk suke sunfi na matan daurewa, Shi suke jira, a gurin don haka ne ba wanda yai magana sai shiru a taron Ya shigo gwiwa ba karfi yana gaida Mama hafsi dake zaune daga gefe daya cikin dan damuwa ita ma, A daure ya juya gefen Umma yana cewa ina kwana, bai ce mata yaya jiki ba don ta kwana a,wahalce, saboda sukan kwalabe sun sa jikin ta yin tsami da ciwo, Bayan ya samu guri ya zaune ne mama hafsi ce tafara magana da cewa tau yaya nasan zakiyi mamaki matuka don ganin mu anan baki dayan mu a lokaci guda, Gaskiya mun taru a nan ne a matsayin mu na jininki diyan ki dani yar uwar haihuwan ki damuke muke nan dama a gurin uwar mu, Gaskiya gaskiya yaya abinda kikayi yasa zukatan mu a cikin rudani da tashin hankali don zan iya ce maki kusan duk wanda yaji abinda ya faru daren jiya baiyi barci da dadi ba, Umma tace ina ko zaiyi barcin dadi wanan mara kunyar yarinyar ta hanani lafiya, Mama hafsi tace kika dai hana kanki yaya yanzu don Allah yaya ina ke ina zuwa gurin matar danki da zance ku hada kai kuyi wa dan ki dan cikin ki asiri da wata bare sabba can mara mutunci irin habiba, Umma,bata,fahinci inda maganan mam ya dosa ba sai cewa tayi haba hafsi aini da farko na zaci yar azikine sai daga baya na,fahinci ba yar goyo ba ce ita, Ashe zancen ta gaskiya ne ke nan kin samay akan wasu zantutukan marasa dadin ji ga mai sauraren su,, Kamar yaya basu da dadin ji kuma may tace na fada mata, Zance akan Aisha da,yaran ta harshi dan naki Hamza da kikai mata, Umm tace ai ba wani sabon zance bane in har tace na fada mata wani abu akan Aisha ina dai magan gudane, yadda Aisha ta mayar min da yaro tun shigowar ta cikin mu may na fahinta a kan shi, Innalillahi Hamza ya maimaita tare da rintse idanuwan shi cikin kunan rai, Asmau ta fashe da kuka tace amma Umma wallahi, kin cuce mu kin bata,muna suna ace mahaifiyar ka ce za,a hada kai da ita a cuci iyalinka, Jibrin yace Umma kin gama damu cikin gatin nan yanzu ashe duk abinda Biba tafadi da gaske ne, May yayan mu ya rage ki dashi, har kikai mai wanan irin sakaiyan haka a,rayuwan shi, Umma jikokin ki jinin ki zakice a salwanta masu rayuwan su haba Umma su wa muke gani yanzu muji dadi a rayuwan mu inba diyan da yayan mu ya haifa muna ba Sune kuma ke da kanki kike neman halaka masu rayuwan su, su salwance don kawai kina kin uwar su, Kai banfa fahinci maganan kaba may kake fada min ne haka koda nake adawa da Aisha ai ban hada da diyan taba itace dai bani son irin rayuwan ta a raina, Wani irin rayuwa ne gare ta a duniyan nan wani irin biyayyane Aisha ba tai muna a gidan nan, Mata nawa kika sa shi ya aura amma duk babu na gari yan mata nawa kika sa shi nema amma duk a kareta a tsiyace dake, Yau har takai kece maiba da maganin da za,a yiwa jikokin ki jinin ki Umma Ibrahim ke fadi cikin kunan rai, Tace cikin mamaki magani kuma wani irin magani kake magana wai, Zarah tace wanda kika kaiwa Biba ta ba yayan mu ita kuma taki karba har yakawo maku matsala haka, Magani wani irin magani kuke magana akaine wai ban gane ba fa, Mama tace yaya kin ba habiba magani ta zubawa yaron nan ga abincin shi shine taki karba har ya kawo maku matsala, haka, Innallilahi Umma tace ni magani fa kikace ni zanba wanan mara mutuncin yarinyar magani akan may, In magani ne ai sai dai nayi wa kaina ba na ba,wata tai min ba, Kuka yaran suka fara yi gaba dayan su in ka debe Hamza wanda kan shi yake a dafe don takai, Cikin kuka Zarah tace Umma kin gama damu wallahi kin muna mugun tabo da zamu zama abin kwatance a garin nan, Ace uwar mu don mugun hali har dan ta take son a kashe mata duk da Umma na jin jikin ciwon da ke damun ta bai hana ta kwashe Zarah da mari ba, Mikewa Hamza yayi yana cewa na riga da na gama yanke hukunci zanbar garin nan da iyalina gaba daya, mu koma can nesa da ku don kawaucewa fitina,ya fadin haka ya bar dakin ran shi a bace Gaba daya,sai hankalin su ya tashi suna cewa Umma kinga abin kunyan da kika jawo muna, Ba wani abinda yanzu zamu iya yi don abin yayi muni gaskiya, don hakan da yayi shine daidai tunda baki kaunan shi da iyalin shi, inji Ibrahim shima mikewa yayi yabi bayan dan uwan shi, Umma ta na gani haka sai ta fashe da kuka tana cewa wanan yarinyar ta cuce ni wallahi don bamu taba wanan zancen da ita ba, Tiryan tiryan mama take fada mata,duk yadda Biba ta fada masu kara,sautin kuka Umma takara ta shiga kwashe wa Biba albarka da tsinuwa, ****** ********* ****** Ina zaune a dakina abin duniya yakai min ko ina a,rayuwa na na rasa inda zan sa kaina shawaran karshe dana yanke wa kaina shine na hakkura na bar mata dan ta kawai, Ance in so cutane hakkuri magani ne don haka na shiga hada kaya tun wuri na bar gidan har yaran ita ta dade bata kashe su ba in nafita, Ibrahim ne ya kawo shi gida don ya kasa jan motan da kan shi Madina da yake tana da wayo sai tashiga kuka ganin Madina na kuka yasa itama Jidda yin ku, Sun samu yaran suna kuka ya ke ce mazu cikin kasa laliyar murya may yafaru sai Madina take cewa Antyna tace zamu tafi gida yau tabar su, Jidda har da tagwaye ta dakin ya fada ranshi a bace ya samu ina gyara kayan sawana a cikin akwatina na ya na min kallon mamaki yake cewa, May nene haka wai Aisha ban kale shi ba sai aikin hada kayana nakeyi kawai inda nake ya karaso ya karbi kayan dake a hannu na yake cewa, Nace wai maynene haka Humaira may kike shirin yine wai please ? Na dago idanuwana da sukai ja ina cewa, kabarni kawai yaya in tafi don banga amfanin zamana a gidan nan ba, Tun ina ni daya Umma bata kaunan zamana da kai har yanzu da na tara iyali su ma kiyayyan nawa ya shafe su, Don Allah yaya ka sakeni kowa ya huta in dai na bar gidan ina shike nan zance ya kare ke nan ko sai a,auro masu kirki da mutunci diyan masu arziki ka zauna dasu, Ni kike fadawa haka Aisha nace cikin zafin rai dole na fadi don dai nice ba,a so ko zanbar gidan ka zauna da wa yanda ake son ka zauna din, Ibrahim ya shigo dakin yana kalkon mu yake cewa maman Jidda may nene haka kuma, Nace gidan mu zan tafi yaya Ibrahim don shine kawai mafita a wanan zancen, Bakin jini na har ya shafi diyan da na haifa daku a gidan nan, haka yaran nan may suka sani a duniya da za,ace a illanta man su haka, Yaya Ibrahim may naiwa Umma ne haka a duniya takini taki jini na da ita, Yace yanzun dai ki kwantar da hsnkalin ki don Allah wanan zancen ai baikai haka ba, kuma ma idan kinyi haka bakiyi wa mijin ki adalci ba inda akafito, Ki fa san duk dadewan nan yana bayanki bai yarda ya biyewa Um a ba a cuta maki, Don may ke zaki yanke maku dan yen hukunci haka ne wai, Nace gaskiya ni bazan zauna ba nidaine ba,a so ko tsu zan bar gidan akawo wanda ake so su zauna ba shike nan ba, Ibrahim.ka barta in haka take ganin shine daidai, ban son kuma hukuncin da take so ba bayan wanan nan dana dauka, Barin garin nan ga baki daya daku shi nake ganin mafita a gareni don nima ba zan tsaya nan ba a cuta min haka, Idan aka nakasa min yara aini aka nakasa ba wani ba a duniyan nan, Nace ba sai kabar gari ba a kaina ka bari ni na tafi don ko mun bar gari ai still auren ka na a kaina, Don haka abin ba zai kare ba ke nan amma idan na tafi kaga kowa ya huta shi ke nan, Ba inda zaki inji yaya ibrahim wallahi ke da barin gidan nan Aisha sai mutuwa, Halin Umma ne kuma sabo yau a gareki ko kuwa wani irin fitina ne na Umma baki sani ba Aisha, Nace amma ba irin wanan ba yaya gaskiya don wanan yai muni da yawa sosai, Kafin aiwa yaran illa a kuka dani gara kawai na bar gidan shine mafita, mai sauki, Juyawa Hamza yayi yabar dakin nan ya barni da Ibrahim yana ta faman yi min nasiha dakin shi ya shige ya rufo kofa da karfi yafada,saman gadon shi, Fita yaya Ibrahim yayi sai gidan mama, Rahana ya fada mata ya juya zuwa gurin Ummina yai sa,a Baba Mudi yana gidan shima ya fada mai, Sin samu na gama hada kayana ina zaune a bakin gadona ina ba hussaini nono, don shi sarkin tsotsone, Ganin su kawai nayi don kusan lokaci daya suka iso gidan gaba dayan su, Kalkon bacin rai suke min don ranan harda Baba sai da ya shigo dakina, nan suka fara yi min fada wai banda hankaline nake shirin yankewa kaina danyen hukunci haka, Cikin kuka na zanyana masu duk abinda ya faru gaba dayan su suma hankalin su ta shi yayi Baba Mudi yace eh lalai kina da gaskiyan ki Aisha, Abar mata gidan da diyanta shi yafi sauki don muddin ba,a girgizata ba na gane Rabi bata shiga hankalin ta, Tare da su muka bar gidan sai dai Baba yace dole na tafi da yan jariraina da basu ko kai sati biyu ba da haihuwa, Nan muka bar su Jidda da Mimi yaran na ta wani irin kuka da gurjji, Kukan su ne yafito da Hamza daki yaga dakina a kulle alaman na tafi ke nan, Ya ja yaran zuwa dakin shi yana lalashin su har ya samu sukai shiru, Yakai wani lokaci dasu a dakin shi Biba ko tana dakin ta sai addu,a take Allah yasa na tafi ke nan kar na dawo gidan don duk abin da akeyi tana jin komai, Sai zuwa magariba yafito daga dakin yaga haske a dakin Biba din rai bace ya nufi dakin cikin daga labule yake cewa ke Habiba fito ki tafi gidan ku ke ma sai na nemay ki daga haka yabar dakin, Sai kuma ya juyo yana ce mata,na fada maki ki tafi don in na dawo na samay ki wallahi yau ranki sai ya baci a gidan nan, Ta kalleshi fuska ba tsoro tace akan wani dalili zan bar gidan don matarka ta tafi zakace nima sai na tafi, To bari kaji don wallahi babu inda zan tafi tunda ba laifi nai maka ba daga tai mako sai kari ya koma, ciwo, Yace zaki ko sha mamakina yau wallahi ya juya yafita zuwa sallah don ya dawo kafin yaran su tashi, A gidan Baba Mudi muka sauka ina shiga gida su mama saude suka gan mu harda kaya nanan suka shiga tambayan mayke faruwa ne wai haka don dai ba lafiya ba tunda basu taba ganin haka ba, Baba Mudine yake ce masu garata dawo gida kawai don Rabi dai da kuke gani ba mutumiyar arziki bace wallahi, Mata babu lisafi ko kada a rayuwan ta ta zauna da dan nata tunda haka take so, Daga haka yafita ina shiga dakin Ummina na fada saman gado na kwanta su Mama Rahana da Ummina dasu mama Saude aka,shiga zancen Umma Rabi, Sai dai suna fita suka kama gulma cewa ai ga irin ta dama an samu guri ana wa mutane sallo da daga kai ai gashi yanzu an koro ni hankalin iyayyena ya tashi suga zasu rasa gurin ci, kai kishi bala,i ne wallahi, Mamana Rahana bata bar gidan ba sai da taga na kwantar da hankalina gashi ina jego a jikina ga yan jarirai tare dani, Barcin da ban samu yi ba da daren jiya shi ne ya dauke ni hakan yasa ta sallama ta tafi, Hadari a ka hada duk ina barcin ban fito ba yaran kuma Atika ta goya daya mama saude ta goya gudan, Ummi tai min girki mai lafiya ko dana farka yana gabana take ce min na tashi nai wanka kafin dare yayi sai da nai wanka Ummi ta sani gaba tana kwantar min da hankali har sai da taga na ci abinci sosai tabar dakin, In akwai abinda ya tsaya min a rai shine yarana da na bari gida da Biba ban san cewa itama don dole ranan tabar gidan ba ya rufe kofa daga shi sai su a gida ya cewa maigadi duk wanda yazo yace baya nan kuma ya kulle gidan ya tafi da key, Iyayyen Biba suka dawo da ita amma sai maigadi ya fada masu yadda yace mai din, Haka suka koma da ita gashi ya kulle wayoyin shi duk a rufe suke ba mai samun shi, Sai dare yaiwa Ibrahim waya ya kawo masu take away da zasu ci shi da yaran, Nan maigadi ke fada masu Biba tazo da iyayyen ta amma ya fada masu yadda yace, Ibrahim yake cewa itama bata gidan ne, Ya kalli Ibrahim a sanyaye yace may zata zauna yi itama ai yadda saboda ita har Himaira tabar gidan nan sai ta tafi har nagama yanke hukunci tukun, Ibrahim yakoma gida yake fada ma su mama zancen tafiya na hankakin su ya tashi suke cewa akan may zan yake hukunci tafiya nabar diyana da mijina tunda ba dani akayi ba, Sai Ibrahim ke cewa, ai hankalina yai matukar dagawa jin da nayi ance za a salwanta min da yaran, Tun da daren mama taso zuwa gurin yaran yake ce mata ai Hamza ya rufe gida amma ta bari da safe sai ta tafi yake fada masu ita ma Biba ya turata gidan su, ai Duk da an fara ruwan sama amma saida mama ta shiga gidan mu don gani na, Mama ta samay mu ni da Ummi a daki da sauran yaran bayan an gai sa take cewa may yasa nabar gidana na fito kan zancen da baikai ko ina ba ai wanan ba abinda za,ace nabar gida bane, akai, Duk da halin kawaici irin na Ummina sai da tai magana tace haba Hafsi ai barin gidan ya zama waji bi ga Aisha don in ba gidan tabari ba wanan kiyayyan ba zai kare ba gare ta Gara dai tabata gidan tabar mata dan ta shi yafi don abin har yakai ga shafan diyan ta Rabi ta manta cewa yaran jinin tane na har abada amma idon ta ya rufe saboda kiyayyan da takewa Aisha may yarinyar ga ta kashewa mata a duniya yai zafi haka , Gaskiya anzo karshe don ni inda miyon bakina zata koma badai gidan nan ba, Bafa ban son ta bane na kyale duk wani cin fuska da ake mata ina son abina nima don haks taje ta rike dan ta ita kuma Allah ya bata wani ba shi ke nan ba, amma gaskiya bata komawa gidan nan , Mama taita ba Ummi hakkuri karshe ma dakin ta bar mata alamar bazata ma ji hakkurin ta ba, Haka mama tai muna sallama da fuwan ya dan tsagaita kadan takoma gida dakin Umma take tai mata tas tace yau dai kin kai ga yadda kike son don sun karbi yar su suma kuma sunce badai gidan nan ba, kuma, Magana masu zafi da tsuma zuciya ta fadawa Umma din sai da tai kuka sosai tace ni wanan yarinyar tagama dani hausatu, Wallahi sheri taimin akan may zanki jini na tace ai duniya duk sun san baki kaunan su yaya kin taba jan yaro ko daya a jikin ki harda sanan yarinyar da aka sakawa sunan ki babu duwanki da ala,amarinta, Haba yaya yaran nan ma ai sunyi kokari wallahi in badon iyayyen nata suna da kawaici ba aida tun tuni sun raba wanan auren ko, Hankalin Umma yai matukar tashi sosai wanan ne karo na farko da tai matukar na dama da wanan bakin akidan da take gwadawa a kaina, ****** ********* ****** Waahegari tin da safe ya tashi bayan yai sallah bai kara kwantawa ba yana zaune a falo shi kadai sai faman tunane yake barkatai a ran shi, Duk abin duniya ya damay shi ya kulla wanan ya kwance Jidda ce tafara tashi daga barci, Allah ya taimake shi yaran suna hutu a lokacin, Tana fito ta fada jikin shi tana cewa Daddy ina maman mu ta tafi ne da twins din ta a kaimu gurin maman mu daddy please zan je gurin maman mu ne ni, Bugun kofan da ake da karfi yasa shi tashi a fusace ya fita don a zaton shi su Biba ne yai masu rashin mutunci, Sai ganin mama yayi da Umma da Ibrahim jayewa yayi yabar masu kofan suka shige, Suna zama Jidda takara cewa, daddy please ka kaini gurin mamana sun tafi ita da anty Madina sun bar mu da twins din ta, Gaisawa suka farayi mama na cewa zonan kin ji mutumiya na zan kaiki gurin mamaki anjima kadan, kinji, Nan mama tana rike da hannun Jidd take cewa tau Hamza gamu munzo gare ka da yaya don yaya tace wallahi magana maka mancin wanan bai taba hadata da wanan yarinyar ba, ita, Murmushi yayi yace mama ni mai zance yanzu Umma fa uwatace banda wanda yafi a zuciyana a duniyan nan kuma banga ma wanda zaifita ba a gareni, Amma tunda haka ta zabar ma rayuwa ko yaushe tagani a cikin garari da tashin hankali a tare dani ai shike nan, Yanzun dai Aisha tabar muna gidan sai a auro min wance hankalin ta ya kwanta da ita na zauna da ita, Din iyayyen Aisha hakkurin su ya kare kinga ba abinda ya saura kuma, Sai lokacin Umma tai magana tace zaman ta bai kare ba a gidan nan kuma ba zai kare ba sai ranan da babu dayan ku, In ta tafi ina zata bar yaran ta da gidan ta dole ta dawo dakin ta don yanzu anzama daya, Ita kuma wanan yarinyar na barta ga Allah don shine shedun tsakani na da ita idan na taba mata maka mancin wanan magana a,rayuwana, A hankali Hamza yace ai tunda ta tafi yara zaman su dole ya dawo garesu tunda wa zan kai masu inbaku ba , Biban da kike so ko yarta bata iya rikewa balle na wani don haka bazan bar yarana a gurin ta ba, Mama tace ni yanzu ba wanan ba don Allah a bar zancen muyi magana akan dawowan Aisha kawai don uwarta ta hau fiye da tsanmanin ku don jiya ma dakin ta bar min, Nan sukai ta magana akan irin hakkurina dakuma kyautatawan da nake masu amna duk Umma baki gani gashi yau har su da kan su iyayyen ta sunzo sun dauki yar su wai a kanki haba Umma yaya kike son muyi da rayuwan mu ne wai, Umma dai shiru tayi don zafin da take ji a ran ta Ibrahim yaci gaba dacewa yanzu kai yaya muje mu samu Baba mudi sai mu bashi hakkuri tadawo dakin ta, Yace cikin murmyshin dole Ibrahim da wani ido zan iya kallon wanan bawan Allah, Tun fa muna yara ba mutumin da ya damu da damuwar mu kamar wanan bawan Allah, Umma ke kin sani don halarci ne fa aka bani Aisha ba wai don nakai na aureta ba alokacin amma suka rufa muna asiri suka bani ita don halarci kuma uwarta bata ja da hukuncin shi, Yaya zan iya fuskantashi yau ace wai na kasa rike amanan da ya bani wai ma mahaifiyata ce da matsalar gaskiya ina jin nauyi da kunya wallahi, Ibrahim yace in haka yanzu dole naje na samu su Baba Madu da magana don aje bikon ta tadawo, Umma tace ku dai je ku gwada ku gani ai zai yarda shi mudin ba,sai maganan nan tafita waje ba, Kallon Umma sukayi gaba dayan su da mamaki don sun gane bata son zancen yafita ke nan waje saboda baba Madu zasuyi mata rashin mutunci sosai kan zancen, Tace kai hamza hakkuri zakayi kaje ku gan shi don a sasanta a gida, Baida yadda zaiyi don yana son su rabu lafiya da ita yace tau shike nan zanyi wanka sai mu tafi, Mimi tafito daga daki da gigin barci tana fadin mama mama ta nufi kofan dakina tana bugawa don in bude mata, Mama ce ta jasu zuwa dayan dakin don tai masu wanka nan taga kayan yaran da na aje a saman gado, Tai masu wanka ta shirya su tafito tana cewa, nasan ko abin kari babu ke nan yace Ibrahim yazo ya samo masu abinda zasuci kawai, Mama tace barin shiga na hada don kowa ma,ai bai karya ba nake gani kitchen tafada tafa hada masu breakfast, Sallama akayi daga waje Ibrahim ne yaje don yaga ko wanene mahaifin Biba ne da kan shi yazo gidan, Fita Hamza yayi suka gaisa sai yake cewa jiya nadawo na samu habiba a gida take cewa wai kace tazo gida ,haka kawai ba,wani fitina, Yace hakane Baba ni nace ta tafi don yar uwarta ma tana gidan su kowa yaje gida ya huta, don gaskiya zan iyacewa tun shigowan ta gidan nan ban taba samun kwanciyan hakali a gurin taba, Sai hakkuri nake saboda darajan ku kawai yanzu Baba har yakai Biba ta daga hannu ta mari mahaifiya don rashin tarbiya, Subbahanallahi dattijon yace ita habiban ta mari mahaifiyan ka yace kwari kuwa baba kuma duk ta bata mata jiki da kwalaben da ta rotsa mata a jiki, Nan dai ya fada mashi duk irin abinda takeyi da tashigo gidan yakare da cewa gaskiya bazan iya ba ta kaini karshe wallahi, Dattijon yace lalai kana da gaskiyan ka wallahi aima ka raga mata da shegiya kai mata dukan tsiya don nasan rashin kunyan habiba zata iya fiye da haka wallahi, Amma kayi hakkuri don Allah tunda kace don mu kake hakkuri da ita ni hakkuri zan baka kati hakkuri za,a tsawata mata insha Allahu zata bari, Hamza yai murmushi yace Baba ku barta kawai ai anzo karshe bazan iya daga ido na kalli Biba har na zauna da ita ba kuma a matsayin matana, irin abin da tai min,, Nan dai dattijon ya ci gaba da bashi hakkuri ya tausan zuciyar shi sukai sallama yatafi da bacin rai, Suna shiga gida wanka ya fada, yafito inda ya samu mama ta hada masu abin karyawa ko, Umma sai kamay kamay take tana jan yaran da hira amma sunki sake jiki da ita, sai cewa suke Daddy ka kaimu gurin maman mu please, Umma nacewa kuzo maman ku ta tafi uguwa anjima zata dawo kunji suke sai makewa suke basu yarda da ita, Ibrahim yace Umma ki barsu kawai don basu sba dake ba indai Aliyun zarah ne su kan sun san ko sosai don sune jikokin ki, Kai Ibrahim wallahi ka shiga hankalinka kada na bata maka rai don naga kana son raina min hankali, Kabari in ka haifi naka ka hana su mamayni din tunda naga kana daniyan haka kaji min dan neman yaro mara hankali kawai, Hamza yana gamawa ya mike yana cewa Ibrahim su tafi, din gidan Baba mudi su gan shi, Sun yi sa a sin samay shi a kofan gidan shi zaifita sai dai ganin su ya sa shi tsayawa suka gaisa yace su shigo daga cikin zauren shi, A saman tabarma suka zauna gaba dayan su inda suka kara gaishe shi a cikin ladabi, Sai dan shiru ne ya biyo baya kadan shi Hamza din ne ya kawar da shirun yana cewa Baba dama mun zo ne akan zancen Aisha ayi hakkuri ta koma dakin ta tunda ba fada mu kayi da ita ba, Baba yai dan murmushi yake yace ni Hamza a rayuwana ba kai min komai ba wallahi sai ma ince nagode kwarai da rikon da kaiwa Aisha, Amma matsalar tana ga mahaifiyar ka don bazan yarda ya ta takoma gidan ka ba mahaifiyarta tana gwada mata sanan bakar tsana haka, Yau har abin ya tashi a kan ta ita kadai ya koma ga zurian ta da kai, Don haka don Allah ka koma kaje kayi hakkuri kayi biyayya ga mahaifiyar ka ka zauna da wace uwarka ke son gani a gidan ka, Saboda haka kuyi hakkuri ku koma don yanzun ba abinda zan iyayi don ko uwar yarinyar naga ya hau sosai itma wanan karon don haka ayi hakkuri kawai da wanan zancen in Allah yaraya yaran sun isa yayye sai acire su a nono adawo maka dasu duk ku rike tunda badasu nabaka ita ba, Baba don Allah ayi hakuri hakan ba zai kara faruwa ba insha Allahu inji Hamza wanda ke ji kamar ya fada a wuta don bakin ciki da tashin hankali, Baba yace hamza na fada maka,wallahi kai bakai muna komai ba halin mahaifiyar kane dai bai muna ba gaskiya ayi hakkuri, Shiru zauren yayi kaman babu kowa a cikin zauren saboda kowa da abinda zuciyar shi ke saka mai, Babane ya kawar da shirun da cewa aiko mahaufita yazo ya samay ta a cikin wanan hakin zai ga ban wa yar shi adalci ba na bayar da ita inda ake gallaza mashi ya ne kawai, Nan dai yabasu hakkuri tare da basu magana suka tafi gwiwa ba karci rai a bace, Bai koma gida ba yace Ibrahim ya wuce dashi wani guri don yaga wani abokin shi, Nan yabar shi yadawo gurin su Umma ya fada masu duk yadda sukayi da Baba Mudi din, Wasa wasa karamar magana ta zama babba don Ummi ta kekashe kasa tace bani komawa gidan hamza, Hankalin shi yai matukar tashi sosai don bai zaci abin zai kai haka ba sai ga wankin hula na son kaishi dare, Ana wanan rikici shi kuma yana kokarin samun gida a Kaduna don yace can zai mayar da iyalin shi gaba daya, yafi mai hankali kwance, Ga matsin da yake samu daga gurin iyayyen biba sun sashi gaba da bada hakkuri, Shi kuma ya tsaya a bakan ba zai mayar da ita gidan shi ba yagaji tafita daga ran shi yace masu, Nikan tun zancen yarana yana damuna arai har Ummi tagane wani dare tai min tas don haka na fitar da zancen su a raina na sake jikina, Dafarko sai suka tsiri kawo su wai sunzo ganina amma sai Ummi tai masu kashedin kada,akara kawo su abarsu su saba da Umma, Wanan abin ya taba ran hamza sosai don ranan da yaji har da kuka saida yayi da hawayen shi yabar gidan Umma, ****** ********* ****** Tunda Hamza yai tafiya bai dawo ba yau kusan sati uku baya garin ina gidan mu abina na kwantar da hankalina na fitar da komai a raina, Ranan wata laraba mukaji ance wai ana wa baba sallama Atika tace baba bai nan sai ga yaron yadawo yace wai ance Fatima tana nan, Aka ce yaron yaje yace waye ina jin haka kwance nake ina ba hassan nono, na mike zaune ina mamakin wanda zai ce a sallamo mashi Ummi, Sai muryan yaron naji yana cewa wai ance Bello ne daga Burkusu ma, Zubur na mike, tsaye na zari hijjab dina na zuwa waje da sauri na, wani High lender nagani bak wul a waje gidan mu sai dai ba,a ganin wanda ke cikin motar sai dai na ciki ya gan ka, A hankali akafara bude kofar motar nacikin motar ya sako kafan shi takalman shi kawai mutum zai gani ya fahinci wanda ke cikin motan ba karamin mutum bane, Ina tsaye na zurawa motar ido na kagara na ga ko waye a cikin motar,,,,, ,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,, Fari ne sol ya bude motar a hankali yafito ga ba daya mutanen dake uguwar hankalin su, ya dawo ga motar da mutanen cikin motan, Ina tsaye, kinkyam.na zurawa mai fitowa daga motar ido ina mashi kallon kurullah, Kallo daya zakai mai shi kasan cewa naira ta zaunu daram a gurin daga motar har shi kan shi zuwa suturorin shi baki daya, Daga inda nake a tsaye mutanen shiya sun tsuro min idanuwan su, suna muna kallon mamaki da kyat na iya bude bakina nace Abbana, Cikin murmushi ya ware hannayen shi tare da nuna ni ya cewa Aisha ko ? Haba da sauri na nufe shi cikin wani murya nace Abbana Innalillahi wa,inna alaihim rajjiun wallahi kamar mu daya da Abbana don fari ne sol ga bakin suma a kan shi wululk, kamar bunzun kasar Niger, Kamshin turaren shi duk ya kamsashe uguwa a lokaci guda wata irin shadda ce milk a jikin sai maiko takeyi don buguwa, Rugumay ni Abba yayi tsab a jikin shi yana sauke numfashi a hankali cikin nuna jin dasin shi, Yadan dago ni ya kalle sai kuma ya kara rikeni tsam a jikin shi na dan wani lokaci, Jama,a dake gurin a lokacin sukayo kanmu suna min kallon mamaki don wasun su da yawa basu ma san ina uguwar ba a lokacin, Nan suka fara dan rade radi kodai mahaifinta ne don kaman yai yawa sosai da mahaifina, Kuka nake sosai don na rasa irin farin cikin da zan gwada ina ji a lokacin, Shimmer Abbba kuka yakeyi yadan cire farin madubin idon dake makale a fuskan shi a hankali, ya dan share hawayen shi Jaye jikina nayi daga jijin shi na juya zuwa cikin gida inda na,fito masu, da tabarma, Nai masu iso da su shigo daga cikin zauren Baba Mudi nakawo masu ruwan leda sai bin gidan da kallo yake a tsanake, Waya aka bugawa Baba dake kasuwa sai gashi gida ba bata lokaci, Sun gaisa yake masu sannu da zuwa nan suka shiga hiran rayuwa da shi cikin mutinci ba nuna komai a tsakanin su, Baba ya shiga gida yaiwa Ummi izzini da tafito su gaisa, yaba da kudi a sayo abinda za,a masu girki dashi da abokin tafiyan shi wanda ban tsanmani ya iya hausa ba, Wani yare naji sunayi da French a bakin su hidima sosai aka shiga yi da su bayan sun gaisa da Ummi yake cewa sunyi waya da Hamza yace yana hanyan dawowa ranan, Abbana yake tambayan ina yaran nawa suke akace mai suna gidan su gurin kakan nin su, Duk inda nabi sai ido yake bina dashi yana kallo na don ban kara bi takan shi ba, Sai da su kaci abinci sosai sai Baba yakawo wa Abbana zancen matsalan da nake ciki a gidan mijina, Murmushi Abba din yayi yace hukunci yana a hannun Baba don shi ba zai sa bakin shi ba,, Godiya sosai yaiwa Baba da ya rike mashi ni amana batare da wani matsala ba, Yake cewa Baba ya tayashi rokona nayi hakkuri don yaga kamar ina fushi dashi saboda naki dawowa gurin shi tun dazun, Baba yace ai ko ba halin Aisha bane fushi amma bari na kira maka ita , Nashigo zauren cikin hijjab dina sky color nasamu guri na tsugun nan daga gefen su sai Baba yake cewa, Aisha yau ga mahaifinki Allah ya dawo muna dashi gare mu , Amma kuma sai naga kamar baki wa Allah godiya ba da hakan don naga kamar kina nisanta kanki dashi kuma, Maimakon nai magana sai wasu hawaye na sake masu zafi suka dinga silalin min nan nafara kuka mai tsuma zuciya, Dakyat na bude bakina nace mashi, Baba may zancewa mutumin da yai watsi dani a cikin duniya tun ina yar karama na bai san cina ba bai san shana ba, Baidamu da yana da wata ya a rayuwan shi ba ya watsar dani da dan yan shi, ya manta da kowa nashi sai sabbin abokan rayuwan da ya samu, Haba Aisha inji Baba kowani dan adam da kika gani fa ajizi ne ga Allah don duk kaddaran da zai samu bawa a rubuce yake mai a rayuwan shi, Wanan tafiyan da yayi kaddararen al,amari gare shi ba makawa sai yayi shi don a rubuce yake mai shi cikin littafin shi, Ashe ba godiya ya kamata yau kiwa Allah ba da ya kadara akwai robon kara saduwa a tsakanin ku, Don haka maza ki tarbi mahaifinki kada ki sakawa kanki tsanar shi har ki dawo kina da kin sani daga baya don haka ba halin mumuminai bane, Bai tafi ya barki don bai kaunarki ba Aisha yatafi ne akan kaddaran Ubangijin shi, Kukan da nakeyi harda dayan mutumin yana bani hakkuri cikin harshe da nuna hannun shi, Fita daga zauren baba yayi ya barni zaune da mahaifina shima mutumin sai ya mike yafita zuwa gurin driver su, Inda nake zaune Abba ya taso yazo ya zauna ya dan dafani yana cewa haba Aisha nasan cewa ban kyauta maki ba na tafi na barki a cikin wahalan rayuwa ke da mahaifiyar ki, Sai dai ki sani hakan ba,wai yana nuna na manta da ke bane a,rayuwana ko abinci zanci sai kun fado min arai ina tunanen ko yanzu a wani irin hali kuke ciki a inda kuke ko kuma kina inane yanzu, Sai yai shiru jin da nayi baiyi magana,ba yasani dago kaina hawayene naga suna zubo mashi daga idanuwan shi, Hada ido mukayi yace cikin kuka Aisha ki yafe min don Allah don nasan ban kyauta,wa rayuwan ki ba don nasan kin fuskanci kalubalun rayuwa iri iri a tare dake, Tausayi yabani nace Abba na yafe maka don nice yakamata na,roke ka don sai nake ganin laifin Ummina ne yashafeni a gareka, Yace cikin girgiza kai ko daya ni Uwarki batai min komai ba don yar uwatace halal malal, don may zan kufule ta a raina,. Haka dai Allah ya tsaro muna rayuwan mu, A hankali nafara fada mashi irin abubuwan da na fuskanta da bai nan da kudaden dasu Baba na yan uwan shi suka bani a bayan shi da kuma taimakon da kulawan da nasamu a gurin shi, Yace to Alhamdullahi dama abinda na matsu naji kenan kafin na isa gare su naji wani irin kulawa kika,samu a gudin su, Don nasan yadda zan isa gare su dalilin da yasa banje gurin su ba sai na iso inda kike naji komai daga bakin ki, Yace Aisha na dago kai yanzu mijinki nake son gani amma kafin ya iso ina so ki fada min duk matsalokin sai na san irin taimakon da zan maki ke kuma, Nace Abba ni banda matsalar komai don Hamza yana kokarin shi dani yace nagani kuma nasani don gashi har yakai mahaifiyarki da mijin ta saudiya sun sauke farali hakan ma kawai ya isar min da nasan yana kokari a kanki, To amma yanzu da kika bar gidan ki ka dawo nan kina ganin hakan shine alheri a gareki don ni ban son na saka bakina a wanan zancen don malam Mudi yai min duk yadda akeyi kinga idan nazo nasa baki a matsalarki nai mashi butulci sosai, Ban yi magana ba sai gasu Jidd mama ta kawo su don suka mahaifina suna shigowa sukayo kaina da murnan su suka fada a jikina suna cewa mama, mama mu ba zamu koma gidan batare da ke ba, Ban yi magana ba sai nuna masu Abba da nayi inacewa a gaida babana nima, gashi, Juyawa sukayi sina kallon shi sai Jidda ce tace wanan ai ba babanki bane Baban gona, Yai murmushi yace masu ni ba Baban gona bane baban mama ne ni Jidda tace ba kai bane baban mama ba fa ban gona ne Baban ta, Nan ya dan fara jan ta da dan hira a hankali har suka dan fara sake jiki dashi suna bashi amsa cikin nuna jin dadi Sun gaisa da mama nake fada mashi yadda suke da Hamza ya kaea gaishe ta a cikin mutunci , Sun dan yi hira tana tambayan shi iyalinshi yake fada mata duk suna lafiya suna gaisu ma, Sai an kwana biyune zai zo da su suga gid shi ya fara zuwa ya nemi yafiyan yan uwa tukun,. Mutane sai zuwa suke suna gaida shi yana kuma masu abin arzki take labari ya yadu a uguwa, lokaci guda, Mama Rahana tazo sun dauki lokaci suna hira yaushe rabo a tsakanin su, Sai yamma kis suka bar mu yace a sokoto yake son su kwana da safe zai karasa gida gurin yan uwan shi, Kudi masu yawa ya barmin yana cewa sai ya dawo zai ganni mu karasa maganan mu dashi, Ya tafi cikin farin ciki a ranshi inda suka,gama ganawa da hamza ya kama hanya sai Burkusuma, ****** ********* ****** Da dare ya isa garin don haka ba kowane yasan da shigowan shi garin ba, K9fan gidan su ya tsaya da motan shi inda yafito lokacin Baba Liman yana zaune yana karatu a zauren shi kamar kullun, Sallaman da yaji yasa shi dago kan shi sai ido biyu yayi da dan uwan shi duk da dare ne bai hana shi gane Abban ba a lokacin, yace, BELLO kaine ko mafarki nakeyi haka ne wai, Murmushi Abba yayi yace nine yaya ba mafarki kakeyi ba nine a gaban ka, Rugumay Abba yayi a jikin shi yake cewa Allah na gode maka da ka nuna min wanan ranan dana dade ina jira a rayuwa na, Jan shi yayi zuwa cikin gida yana fadin ina mutanen gidan nan ku fito yau ga BELLO ALLAH ya dawo muna dashi lafiya cikin mu, Babba da yaro na gidan sai faman tururuwan fitowa sukeyi don ganin abinda baba Liman ke fadi in gaskiya ne, Kuka murna da shewa shi kawai ke tashi a gidan don murna da farin ciki a zuka tan su, Duk da dare bai hana mutane na kusa da nisa fitowa daga gida jen su ba don ganin shi duk wanda yazo tun awaje da sunga motocin Abba da security din da yazo dasu sai mamaki ya kama su, su shiga cikin gida don ganin shi ranan zakace ba dare ba ne a lokacin, Sai da mutane suka dan tsagaita shigowa don Baba Liman yace a bari har da,safe kowa ya tafi gidan shi, don dare yayi sosai a lokacin, Kwana raye sukayi da yan uwa yana basu labarin bayan rabuwan su inda yace, lokacin da nabar gida da farko kasar Niger na shiga na kai wata uku a damagaran sai na hadu da wasu turawan faransa da nake wa aikin kula da dawakai da rakuma, Da zasu tafine suka taya min idan zan bisu zusa kasan su banki ba sai nai kasadan bin su can din, Shekara na Ukku a tare dasu sai maigidan nawa ya yarda da zamana dashi, Shike turani fatauci a nan kasa shen Afrika ina mashi business din motoci da sauran abubuwa bayan karatun da yasani na ci gaba na zamani, Sannu Sannu har aka sanni a kasashen da nake zuwa nima idan zamu shigo sai na fara nawa san,an shigo da wayoyi da computers, da sauran kayan naororin wuta, Ganin nawa business din yafara karbuwa sosai yasa shi bani kudi masu yawa wanda ban taba zaton zan taba samun irin su ba a duniya, Ba adade ba Allah yai mai rasuwa shine na kwaso nadawo kasan Ivory cost da zama inda nan ne ake shigo muna da kayan mu daga waje, Sai Allah yasa min albarka shine har ya kaini ga haka na samu nawa nakai wanan matsayin, Nayi aure a can na auri wata yarinya da,namu yazo daya yanzun haka muna da yara biyu da ita matar tawa , Zan kawo su suga gida idan hankali ya kwanta dama nazo ne nafara ganin gida don Fatima da muka hadu a,saudiya ta fada min nabarku har yanzu a cikin damuwan rashin ganina da bakuyi ba, Ina fatan zaku yafe min akan irin halun tashin hankali da damuwar da na barku a cikin shi, Sai da,na,fara zuwa gurin su Fatima din don mijin Aisha cikin rashin sani abokin kasuwanci nane a can, Aishan tafada min irin alherin da kulawan da kuke mata a bayana banda abinda zance sai dai na gode maku da irin wanan kokarin da kukai min a bayana don nasan koda mutuwa nayi ina da yan uwan da nabari masu halarci da alheri a rayuwan su, Sai washe gari kofan gidan ya kara cika da jama,a yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke suna taya shi murna, Sai yamma lis ya koma garin sokoto don ya samu masauki da mutanen shi, Hamza yana zuwa gidan shi yaga duk gidan ya koma mashi bakikirin bai ko jin dadin gidan gabs daya a ranshi, Kofan dakina ya dan tsurawa idanu zuwa wani dan lokaci sai ya nisa da kyat yaja kafan shi zuwa dakin shi, Gado ya fada ko takalman kafan shi bai cire ba sai tunane yake barkatai, Yasan da ina gidan yadawo haka da gajiya da yanzu dani da yara muna nan muna mashi oyoyo da taro mai daraja, Amma yau gashi shi kadai a cikin gidan ba motsin kowa a gidan sai yaji gidan ya koma mai kaman makabarta, A hankali ya bude idanuwan shi da suke a rufe ya furzo iska mai zafi yana fadin haba Umma may nai maki haka kika yanke min farin ciki a rayuwana, Rayuwan mu ya tuna da irin gwagwalmayan da akasha a lokacin da Lima ta daure shi da asirin ta, Duk irin kokari da halarcin da Aisha tayi bata guje mashi ba amma Umma bata gani, Yasan da itace akai wa yar ta haka da tuni ta raba wanan auren ko tuntuni, Sadiya kuma da ta tilasta mashi ya aure ta itama tazo da nata kalan iskancin har tayi tagama ba,a ji shi da Aisha ba sai, Zuwan Biba duk Umma batai saduda ba takara kawo mai wani sabon rikici mai muni, Abin kunya wai ace uwar shi ce tai wanan kalaman haka akan zurian shi shi ko kadan baiga laifin iyayyen Aisha da ita ba gurin dauka mataki haka, Amna gaskiya indai shine zaice ya saki Aisha gaskiya ba,a bakin shi ba kan sai dai in duniya zata hade ne amma bai sakin Aisha gaskiya, Saki saki fa yace ina ai gara na mutu da ace na saki Aisha a rayuwana in na saketa na zauna dawa a gidana, Dunkulewa yayi guri guda kaman mai jin sanyi yana tausayin kan shi da iyalin shi da Umma ta jefa a wani hali, Yasan duk inda Aisha take itama tana can tana zaman hakkuri ne saboda yasan tana son shi da zuciya daya har cikin ran ta,, Amma ga Umma nason ta kawo masu shamaki a tsakanin su ta raba abinda Allah ya hada a halarci, Ya kai wani lokaci a haka kwance cijin matsanacin tunane sai dai ya kasa kai ga mafita har lokacin, Da kyat ya tashi yai sallah shafai da wuturi yana kokarin komawa barci bayan ya dauki lokaci yana addu,a sai kuma yaji cikin shi na son cin dan wani abu, Kitchen din gidan ya shiga komai tsab a kitchen din nawa sai dai yarasa mai zai dafa yaci komawa yayi falo ya dauki wayan shi ya kira Ibrahim din shi , Kira daya gana biyu ya dauki wayan yana cewa ko ka dawo ne yaya ? Murya a kasalance ya amsa mashi da,eh don Allah ka sayo min kaza abincin kowa mai zafi sosai da drinks na kwali mai sanyi, Ba a dauki lokaci ba Ibrahim ya shigo gidan ya samay shi zaune saman kujera yana saye da wani riga mai hannu guntu da wandon rigar tree quarter, Kallo daya yai mashi ya gane cewa yana cikin damuwa tausayin dan uwan shi ne ya kamashi lokaci guda, Gaisawa sukayi ya aje mashi abincin daya kawo mashi yake cewa ashe ka iso ko, Yace eh tun kafin magariba ai ina garin nadan tsaya ne yin wani abu, Ibrahim yace gashi kuma kun sha banban da mahaifin Aisha don yazo yau amma yatafi garin su akace, Yai dan guntun murmushi yace ai muna tare dashi dama na tafi shigo da wasu motocine da ya turo har da na ita Aisha cikin motocin, Ikon Allah Aisha ya sayawa mota ya tambaya cikin fara,ar shi yace don yasai mata mota may akayi bafa karamin mutum bane yadda kake tsanmani ba ita kadai ba inajin harda wasu yan uwan shi don mota biyar ya turo ashigo mai dasu sune costume suka kama su, Sun dauki lokaci suna hira duk Ibrahim yanayi ne don ya kawar mai da damuwan shi, Ibrahim yace amma dai kunyi magana akan zancen Aishan da shi kuwa, Dan tsuki Hanza yaja yace ba abinda zai iya don ba a wurin shi take ba don haka bai sa kan shi a zancen ba, Yaya zancen naka auren Hamza ya tambaye shi sai Ibrahim yace ku ake jira kuje sai a saka rana da lokaci, Ok zanyi kokarin na shirya zuwan su Baba kafin na koma don yanzu zancen gidan da nake son sama muna a kaduna ne yake gabana, Hamza yace amma bazaka zauna gida ba a gurin Umma dai ko don ina gudun abinda ya faru da ni yafaru a kan ka don abin na Umma a jinin ta yake, Don sai nake rasa may Aisha taiwa Umma ne haka a,rayuwa karshe dai ban gano komai ba sai naga kamar bata son taga mace ta rabe ni ne kawai, Don kaga ba wai da Aisha kawai Umma take adawa ba har Sadiya da Biba da na zauna dasu akwai matsala a tsakani, Ibrahim yace ni na dade da sanin haka,wallahi yaya ina dai tsoron nai magana ne inja zagi gurin ta, To mau yakawo wanan hakane wai don gaskiya na rasa may Aisha take mata ta tsaneta haka sai nagane don kawai taki rabuwa dani ne kawai, To Allah ya kyauta don shine matsalar kawai, in bashi ba ni dai banga wani matsala daga gurin Aisha ba wallahi, Sun dauki lokaci suna tataunawa har sai da dare yayi yai mashi sallama yatafi cikin tausaya mashi,, Da labarin zuwan mahaifina ya riski Umma da farko tace karyane sai da su Sa,a suke ce mata kamana da mahaifina har kamar ta baci wallahi, don kamar an tsaga kara ne, Nan suke bata labarin irin shigar sa da kuma motar da yazo da ita, Bata kara gaskan tawa ba sai da taga kudin da Abbana yaba su Jidda a gurin mama yakai dubu dari sabbi dal dasu, Ido ga kudi sai ta rude ta na cewa ikon Allah ashe kuwa ba karamin mutum bane dai don wa zai iya ba mutum kudi haka masu yawa, Nan tafaracyan sake sake a ranta yadda itama zata kwanta a ci arziki da ita batare da wata matsala ba, Ta so mama ta bata kudin amma sai mama tace sai Hamza yazo an gwada mashi kudin tukun , A ran ta tace lalai tayi sakaci sosai don da bata sake ba taja jikokinta a jikin ta da dole kudin nan a hannun ta zasu zo, Tace na samu kudin nan haka ai sai kawai na sayowa autana kayan dakin da bamu saya ba dasu, Amma ai sai na samu ko yayane sai kuma tafara jin haushin mama wai itace ma da shegen shishigi tsiya wallahi duk ta shigewa wanan yar Agwi din mai kama da uban ta, Muna nan da,safe sai ga Sa,a datu wai Umma tace tazo ta dauki tagwaye tana son ganin su, Ummina da su mama saude sukace ace suna barci baza a samu kawo su ba sai dai ayi hakkuri, Maimakon ta fita,sai ta dan tsaya taji Atika tana cewa baza a kaisu ba ta shafa masu mugun abu su ga yara sun gi bulbul a lalata masu rayuwan su, Tana zuwa ta samu Umma da mama sai tace masu Umma sai da nace maki ba zan tafi ba kika matsa min gashi kinji abinda suka ce, Nan Umma ta hau fada tana cewa ko dai anki ko ansi dole ace jikokina ne su don ba,a taba raba anta da jini, Yanzu anga ci yazo shine Atika take nuna ita ta kwarai ne ko ina nan take wanko kafan ta ta,shigo gidan nan da gulma akan Fatima da yar ta, Yanzu tasan tana son su zanje na samay ta a yi tsiyan da take son ayi yau, Mama tace wallahi yaya na raba ki ana kokarin ganin an shirya a tsakani kina son zuwa tayar da wani balli kuma, Dama aikowa yasan akanki Aisha tabar gidan mijin ta bawai basu son junan su bane matsalarki ce kawai tafitar da ita daga gidan ga, Yanzun kuma shine zaki tafi hada wani ki kara lalata zancen gaba daya kowa ya huta ko, Jikin Umma yai sanyi ran ta yai matukar baci take cewa kai wallahi ni dai na shiga uku wallahi, Mama tace ba uku ba yaya har tara ma wallahi kin shiga don kin bada waka an amsa maki, Tun farko sai dana hore ki da hakan don gudu irin haka yanzu gashi an barki a cikin tsaka mai wuya ai don ko gulbi goma kika shiga baki fita sai ace kin yi din ne, Dole ba don taso ba ta kyale zancen fan ta abace don ko magana ta kasa, Mama tace irin ku ne iyayyen mazan da yaran zamani basu son shigowa su samu a gida, inda Aisha yar zamani ne wallahi da yanzu kun raba gari da ita ko duniya taji ku, Ibrahim ya,shigo da murna yana fada masu wai mahaifina ya sayo min motar shiga kawai da mamaki suka ce mota fa yace wallahi har ma motar ta iso ko don jiya yaya yake fada min, Nan su mama suka shiga murna da nuna farin cikin su Umma ko sai dariyan yake takeyi kawai, Sun tafi gidan da Ibrahim ke neman mata,amma abinda sukaji ne ya tayar masu da hankali don iyayyen yarinyar sunce sun fasa, Saboda sunji labarin halin mahaifiyar shi duk macen da dan ta ya,aura sai ta mayar da ita karamar bazawa tafito, don ta, Saboda haka suje suyi hakkuri abar zancen bazasu ba da yar su ba kwana biyu a sako masu ita, Sun dawo da wanan mumunan labarin Umma ta shiga dan koke koke wai mutane suna bin ta dasheri don kawai anki jinin ta, Irahim yana samun labarin haka ya shiga tashin hankali sosai tsaye yai mata ranan yace wallahi shikan bazai yarda ba, Da ya zauna bakin ciki ya kashe shi garin ma zai bari gaba daya ya shiga yawon duniya, Tirkashi ranan Umm taga tashin hankali tai nadama sosai don Jibrin ma yace haka baban yarinyarcda yake bida yai mashi kashedi yabar zuwa gurin diyar shi kada uwar shi ta illanta mashi diyan shi, Lokaci guda ta ramay ta zabge kamar ba ita ba ko abinci bata iyaci sai da ta sha dan hwaro hwaro a cikin ta na kunu, Su Baba Madu da Liman sun zo gurin Baba Mudi amma yace suyi hakkuri abar zance don Aisha ta gama auren gidan Hamza, Sunyi mamakin yadda Baba mudi ya cije akan bakarshi na,rashin yarda na koma haka duk da sunzo da kansu bashi hakkuri, Sun dawo sun fada masu yadda sukayi da Baba mudi da kuma irin cin fuskan da na fuskan ta agidan gurin Umma da yaran ta mata tun shigowa na, Don haka Baba Madu yace wallahi Rabi kin cuci rayuwan yaran nan yaran ga gaba dayan su basu rage ki da komai ba a duniyan nan amma kika jefa rayuwan su cikin wanan garari haka saboda ke, Hamza ko saboda bacin rai baiko tsaya angama maganan ba ya mike yabar gidan rai a bace gashi ko wayana baya samu, Da dare yazo gurin Baba hamza ya kara bashi hakkuri da kan shi sai dai magana guda ne a bakin Baba shine ya kawo min takardana kawai ba zan koma ba, Dukar da kai yayi yana sauraren zancen baba da yake ji kamar ana zuba mashi garwashin wutane a zuciyar shi, Hawaye ne masu dumi suka zubo daga fuskan shi ya bude baki da kyat yai magana yace Baba kodai nima Aishan tace nai mata wani abin ne da za,a yanke min wanan hukunci mai tsauri haka Baba, Baba yace ko daya Hamza in bamu gode maka ba baza mu zage kaba kuma laifin uwar ka dai ne ya,shafe ka don haka aje ayi hakkuri Aisha amana take a gurina idan na yarda ta koma Rabi ba fasa halinta zatayi ba don haka duk abinda ya samu Aisha ni na ja mata shi, Don sabodani ta aure ka don haka yanzu kuma nine zan raba,wanan auren wahala da bautar da yarinyar nan keyi ba a gani ya isa haka a hakkura kawai kowa ua samu nashi rabon, Kuka sosai Hamza yake a gaban Baba yana rokon shi don Allah yayi hakkuri kada ya rabashi da Aisha don itace farin cikin shi baba yace na,sani hamza duk nasan da haka amma ayi hakkuri kawai shi yafi, Yai mashi sallama yace shi zai shiga gida ya tashi ya koma kada dare yai mashi shi yagama yanke hukunci, Har baba ya mike sai ya dan tsaya yana cewa, kayi kokari ka mayar da dayan matar ka,a dakin ta don zaman ka haka ba,alheri bane Mutane kuma zasu iya cewa saboda Ausha ne yasa itama ka sallamay ta kaga zaka,shafa mata bakin jini bataci ba bata sha ba, Nan ya,shige ciki yabar Hamza zaune a guri har tsawon wani lokaci ya tashi, Yana fita yaji bai iya jan mota Ibrahim yakira ya kaishi gida,. A hanya sai kuka yake cikin mota Ibrahim din ya kasa bashi hakkuri shima dai ran shi a bace yake daurewa kawai yayi yake jan motan , Ranan gidan Ibrahinm ya kwana yana ba Hamza magana da kuma yadda zasu bullowa baba mudi,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,, Ya samu gida kamar yadda yake bukatan samu a garin kaduna a wani sabon uguwar da matasa sukafi yawa acikin shi, Sai dai,matsala daya yanzu shine akan zancen dawowana gidan shi don abin yafara wuce tunanen shi sosai don iyayyena sun kafe akan sai dai ya bani takarda kawai a rabu don Umma Rabi, Ya,shiga cikin tashin hankali sosai ga mahaifin Biba yana ta faman bin shi akan yayi hakkuri ya mayar da ita dakin ta amma yaki sauraren shi, Dare daya ya yanke shawara ya tafi can kauye gurin iyayyena na,asali ya fada masu abin da ke wakana a tsakanin mu, Sunyi tafiyan shi da mansur da wani abokin su tun asuban farko suka bar garin zuwa kauyen mu, Sun isa garin musalin karfe dayan rana da wani abu don nisa da ke tsakanin mu da garin Jega, An masu taro yadda ya kamata sosai don yanzu ua zama dan gida sai da aka dama masu fura suka sha,suka koshi ban da hamza da hankalin shi ba a kwance yake ba, Sai Baba Liman yasa ai masu iso da su shigo daga cikin zauren shi don su gana saboda ya fahinci magana ce ke tafe dasu, Hamza bai boyewa su Baba na komai duk abinda yafaru sai da ya fada masu kaf, Baba sahabi dayake shi dan zafin zuciya ne nan take yace shi Mudi ina ruwan shi da,zai kashe wa yarinya aure may nene hujjan shi na yanke wanan hukuncin bada sanin mu ba, Ganin inda yake shiga ba nan yake fita ba yasa Baba Liman yadakatar da shi da cewa haba Sahabi shi fa Mudi bamu da mairaina akan shi kan zancen Aisha, Don duk yadda akeyi yai muna saboda haka wanan zancen sai a tsaya ayi bincike akan shi, don idan baida hujja ba zai yanke danyen hukunci haka ba, Don haka yanzu yadda za,ayi shine kai sahabi da Musa sai ku shirya ku tafi can Jega din ayi ta takare muji maganan dake nan idan kun ga za,a iya sasanta maganan sai ku sasanta ku dawo idan kuma maganan ba mai sasan tuwa bane sai abi shawaran da ya yanke ayi hakkuri, Hamza baiso haka ba amma duk da haka yaji dadin da akace da Baba Sahabi za ai tafiyan, Don yasan in ba wani ikon Allah zai iya yin galaba akan Baba Mudi da Ummi na, Sai cikin dare suka shigo gatin Jega ana sallah magriba, don haka basu tsaya wani magana don gajiyan dake tare da su masaukin BLB guests,in ya sauke su tare da samo masu abinci mai kyau suka ci, Sai washegari suka samu zuwa gidan Baba Mudi wanda yai matukar mamakin ganin su da,safe haka, Su gaisa dashi a mutunce ya rasa inda zai sasu sai farin ciki da ganin su yakeyi, Yace bari ya kawo masu abin karya dakatar dashi sukayi suna cewa a koshe suke sai da suka karya suka fito, Nan Baba Musa ya isar masu da zancen Baba Liman din murmushi Baba Mudi yayi yace haka nake so dama, Kamar yadda Hamza ya fada masu shima haka ya,mayar masu harda ma abinda Hamza ya boye a lamarin mahaifiyar shi bai fada masu ba duk Baba Mudi sai da ya fada masu kaf, Yace bazan taba kashewa Aisha aure da hannuna ba sai dai idan abin yafi karfina to zan iya don ya zama dole amma gaskita shi mijin Aisha sam baida maraina a gare mu, Don yaron kirkine a,gabana aka haifeshi kuma ya taso agabana nasan halin shi fiye da tsanmanin ku don haka ni banga wani aibi a kan yaron Matsala dai itace mahaifiyar shi da tasa yar mutane a gaba har da zancen kissa don kissa mana idan ta halaka yaran wa yai hasara ba Aisha,ba don ita mace ce shiko dan ta namijine zai iya auren wasu mata su kara haifa mai wasu, Ni bukatana da na yanke wanan humuncin mai tsauri haka shine sai sun san daranjan ta da muhin mancin ta a gare su in ba haka,ba da na mayar da ita haka kai tsaye abin ba,za,a samu saukin shi ba, Su baba sukace wanan gaskiya don tunda ba mutunci ke gareta ba zata kara bullowa ta wani hanya ne kuma, So nake sai dan sun kai ruwa rana da ita tazo har gidan nan da kafan ta ta roki Aisha gafara kan abubuwan da take mata, shine kawai zai kawo saukin al,amari amma ai har yanzu indai Rabi ce bata saduda ba gaskiya, Baba Musa yace gaskiya malam Mudi kayi hikima sosai a nan don gaskiya irin wa yan nan Uwayen wuyar sha,ani ne dasu, Yanzu abinda za,ayi shine zamu kira shi yaron nan mu bashi hakkuri yaje su sasanta da,uwar shi, idan har ta yarda ta bari to tazo nan gidan ka da kan ta,taba da hakkuri kaga haka,zai sa mu fahinci ko tayi taushi ga,al,amarin, A haka suka tsayar da zancen suka kira shi ta,waya yazo sun mashi bayani akan duk yadda sukayi da shi, Shiru yayi kan shi a duke can ya dago kan shi da kyat ya iya bude bakin shi yace Baba kuna ganin idan anyi haka ba wani matsala kuma, Sukace haka din shine daidai don su zauna da Umma a fahinci juna ya sauke ajiyan zuciya yace ba matsala Baba zan je nagan ta, Yai masu sallama yafita suka bishi da kallon tausayi kawai a ran su suna cewa baida matsala komai uwarshi ce kawai matsala ga al,amarin, ****** ********* ****** Ya shigo gidan da sallama ya samay a zaune gaba dayan su guri guda, ya gaishe su ya samu guri ya zauna, Kallon shi suke a cikin tausaya don duk ya ramay yai baki ga kasunba a fuskan shi saboda rashin sheven da bai samun yi, Kako ci abinci dana mama take tambayan shi yayin da mimi ta shige mai jiki tana tambayan shi maman ta, Yai murmushi yace mimi maman ki tana na dawowa kinji, kara tambayan shi Umma tayi tace kako ci abinci ana tambayan ka, Yace Umma na karya ai yanzun ma daga gidan Baba Mudi nake don iyayyen Aisha sunzo, Mama tace da kyau sunzo dai ne akan zance ko yace eh shiya kawo su sai kuma yai shiru Umma tace to yaya kukayi dasune wai,? Yai dan ajiyan zuciya yace gaskiya akwai matsala don sunce badani zasuyi magana da Umma suke son yin magana, Shiru ne ya dan biyo baya kowa yai shiru sai mama tace to ai ba matsala sai mu tafi muji shakuwar su ko,? Shiru Umma tayi aran ta tana cewa a gaskiya tana jin nauyi da kunya don bata san da,wani ido zata kalle su ba ma kuma may ma zasu fada mata ne wai da zasu ce sai da ita zasuyi magana, Muryan mamane ya katse mata tunanen ta tana cewa yaya ai sai mu shirya muje muji shakuwar su ko don asamu matar shi ta dawo dakin ta abu kusan fa wata daya da kwanaki ke nan har tayi arbain a gidan su, Ba don Umma taso dole ta tashi suka shirya zuwa gidan Baba mudi din ita da yar uwarta, Sun samay su zaune a zaure suna hiran su da dariya irin ta maza ganin shigowan su mama yasa suka tsagaita dariyan su, An gaisa inda su mama suka samu guri daga gefe suka zauna suna masu sannu da,zuwa da tambayan mutanen gida, Mikewa baba mudi yayi yashiga gida ya kira Ummi da mama saude suka fito, Su ma sun samu guri sun zauna daga gefe suka gaisa da su mama da tambayan su su yan biyu, Sai dan shiru da gyaran muryan da Baba mudi yayi yasa gurin natsuwa kamar yadda ya dace, Baba ya fara da addu,a bayan sun shafa yake cewa, da farko dai ina son muyi magana ta natsuwa da fahintar junan mu, Kowan su yace Allah yasa hakan sai yaci gaba dacewa ba,wani matsala bane don kowa ya san abinda ke faruwa ga a tsakanin "ya"yan mu da Allah ya hada aure har da zuri,a, To ba komaine yasa muka gaiyato kuba ku uwanshi sai don matsalan daga gare ku ne shiyasa yau muke son ayita takare don kowa yasan matsayan shi hakana, Ke Rabi kin dai samu a cikin uguwar nan kamar yadda muma muka sanki don haka mu abin yana daure muna kai don bamu san abinda Aisha take maki wanda yake kawo tsana mai tsanani wanda har yanzu ya shafi zurian da ta samu da dan ki, Shine mukace ya kamata mu gaiyato ki don muji abinda ke kawo matsala a tsakanin ku har ta zama kiyayya irin haka, Shiru Umma tayi sai wani irin zufa da taji yana kokarin karyo mata daga duk sasan jikin ta, Shiru ba wanda yai magana har wani dan lokaci sai Baba Sahabi ne yake cewa ki muna bayani don mu tsawata wa ita Aisha indan da bukatan haka, Da kyat Umma ta iya bude bakin ta tace masu yanzu ni hakkuri kawai zan baku insha Allahu irin abubuwan da suka faru ba zasu sake faruwa ba insha Allahu, Don Allah kuyi hakkuri ku mayar mashi da matar shi dakin ta don samun kwanciyan hankalin su, A,a boyar Allah mu muna son akawo karshen al,amarin ne don baza mu yarda mu mayar maki da yarinyar mu ba dakinta batare da munji hujjanki ba don mu tsawata mata inda bukatan haka, Shiru Umma tayi sai kara dukar da kan ta tayi mamace tace don Allah kuyi hakkuri abar wanan zancen don yawuce babu abinda zai sake faruwa maka mancin haka, Ita ma Umma din sai cewa tayi adaiyi hakkuri don Allah tasan tayi kuskure a baya amma yanzu insha Allahu komai ya,wuce don Allah su mayar da Aisha dakin ta, Baba Sahabi yace munji maganan ki amma gaskiya in hakane sai dai kowa yayi hakkuri don bazamu mayar da ita,ba a dinga cusguna mata ana ganin kamar bata,da gata da,galihu ne, Hawayen nadama yazo ma Umma take cewa cikin kuka gwanin ban tausayi don Allah kuyi hakkuri ku yafe min nasan nayi kuskure sosai a,rayuwana don idan nace maku ga laifi daya da Aisha tai min tun ranan da,ta,shigo gidan da a matsyin sarakuwana, Tausayi sosai Umma ta basu yadda take kuka da kaskantar da kanta a gare su, Baba Sahabi yace to Alhamdullahi tunda munji daga,bakin ki mudai dan ki bai yi muna komai ba arayuwan mu sai sambarka, Matsala dama daga gareki ne don haka ga,sharadin mu kafin muce mun yarda takoma dakin ta da farko dai duk muka kara jin tsana ko tsangwama yafito daga gareki ku dake nan ku sheda ni da kaina wallahi zanzo na fitar da ita a gidan dan ki, Idan kuma wani magana yakara tasowa akan zancen na,sihiri ko wani abu haka shima dai bazamu kyale ba don mu gidan mu gidan malaimaine bamu gaji aiki da sihiri ba ko wani abu na daban, Yara de jikokin kine halal malam don haka ko yankasu zakiyi mu bamu ruwan mu yar mu kawai muka,sani don ba kyale ki zamuyi ba , Hakan ma bazai faru ba insha Allahu inji mama data ari bakin yayan nata nan dai suka kara,bada hakkuri aka sahirtawa juna a tsakanin su, Har zasu tafi mama take cewa yaushene sarakuwar nawa zata dawo dakin ta sai baba yace zata dawo amma sai mun gama magana za,a sa lokaci zakuji a gurin hamza din, in komai ya daidaita, Sukai sallama ana rokon juna gafara a tsakani da yar raha irin ta manya, Sun koma gida suka zauna a,tsakanin su mama take cewa Umma tau yaya kin daiji zancen mutanen nan kuma gaskiya suka fada don babu uban da zaibar yar shi a cikin wanan halin batare da,daukan mataki ba, Yakamata wanan abinda yafaru ya zama maki ishara ki gyara halinki ki taimaki zurian ki daga shaguben yan gari, hakana, Yanzu mutanen da Ibrahim ke neman dutar su daga nan nefa aka kwashi gulma aka kai masu har can kano, Ni yanzu ai sunana ya riga da yayi kauri an azamin sheri da banji ba bangani ba a cikin gari, Sunyi wa Hamza bayani duk yadda sukayi da iyayyena shima rokon Umma yayi da ta yafe mai kuma yana rokon ta da tazama mai kama kan ta ga yaran zamani don abinda Biba tai mata baiji dadin shi ba gaskiya, Ya dai mata dan nasiha yadda ya kamata tsakanin da da mahaifi yai masu sallama yatafi abinshi yana maijin dadi a ran shi, Ya koma gurin su Baba sukai mashi nasiha akan hakin iyayye dana iyalin shi yai masu godiya sukace ranan jumma yazo ya dauke mu mukoma gida tunda komai yawuce sai dai a faki gaba kawai, Yai masi godiya akan kokarin da sukai mai kuma yakara ba Baba Mudi hakkuri kan sakacin da yayi na,rashin rike amanan daya bashi na Aisha dakyau ta sanadiyar mahaifiyar shi, Baba yace mai aikomai ya wuce don haka afaki gaba kawai Allah ya tsare, Mota ya dauka shata hargida tare da,alheri akai su Baba na har garin mu, Mama hafsi ce taje gidan ranan alhamis tagyara ko ina nagidan don rashin mace a gidan yasa gidan yai kura sosai, ****** ********* ****** Washegari jumma,a kamar yadda,akai alkawari su mama na Rahana da mama saude da Atika suka rakani gida inda muka samu angyara ko ina dakunan mu dake rufe ne kawai ba,a gyara ba a gidan, don haka Madina ta shiga gyaran dakin ina falo dasu mama suna kara bani magana da zasu tafi ne Hamza yaba Ibrahim alheri ya basu, Bai shigo gidan ba,sai wajajen tara nagida muna daki dayarana sai faman surutu mimi ke min cikin jin dadi ganin na a gida, Tsaye yake daga kofan shigowa dakin hannayen shi zube cikin aljihun rigar shi yana mai kallon mu cikin murmushi sai dai har lokacin da,akwai alaman damuwa a tare dashi, Sannu da zuwa nai mashi cikin yar siririyar murya da bata da karfin sauti ya amsa yana karasowa gare mu, Zama yayi a bakin gadon hakan yasa madina dake dauke da Hassan mikewa tana cewa su Jidda suzo suje falo tare, Bayan yaran sun fitane nani yai ajiyan zuciya yana cewa Humaira idon ki ke ga, Nadago kai a hankali inace mashi may kuma nayi yai murmurshi yace a,a baki komaiba, May yasa kika azabantar dani haka a,rayuwana Humaira na dauka ko da nine nai maki laifi bazaki iya min wanan horon ba haka , Ashe ban sani ba yadda na daukeki ke baki daukeni haka ba gaba daya kika haramta min koda jin muryan ki ne balle ganin ki why Humaira why zaki min wanan irin hukuncin haka Humaira na, Kin san cewa kinzama pary din rayuwana yanzu sosai fiye da duk wani mahuluki na duniyan nan, Amma sai kika biyewa su Baba aka barni maraya ina gararanba a cikin gari ba mai taimakona sai Allah dana dogara dashi, Murmushi nayi nace kenan yanzu laifina ne zakagani banaka ba ko yace dane maki may Humaira ? Nace yanzun dai ai zancen ya wuce Allah ya,tsare gaba yace amin tare da mikewa tsaye daga zaunen da yake yana cewa ina rokon alfarma azo a hada min ruwan zafi please nai wanka ko zandawo normal Hamza na, Nace da ba normal kake ba kenan yace aikema kin sani don rabin raina bata tare da ni , Yafara tafiya yana cewa zan shiga don duk a gajiye nake wallahi nace gani nan tafe ai, Nasamay shi yana rage kayan jikin shi ina shiga dakin zan shige bathroom ya jawoni zuwa jikin shi ya manne ni sosai da jikin shi a kunne na yake min magana kamar rada yana cewa, I miss you my Humaira miss you alot my dear lovely wife why kika haranta min kaki haka da yawa please, Kokarin kara shige min a jiki yakeyi yana min wasu maganganu a kunuwa na wanda kunne na bazai jure sauraren su ba, Kiss yafara kaimin yana cewa a hauka ce humaira ki taimakeni kada ki kara guje min please humaira ki yarda da ni don Allah humaira, Yaso yaci galabata a lokacin amma sai nai dabara da kyat na zille mashi nabarshi sabale da hannayen shi gurin a tsaye, Sai da muka ci abincin da mama hafsi nasamu ta girka mu na muka koshi yaran suka fara barci daya bayan daya, Sai a lokacin na samu na shige dasu daki nai masu addua nadawo gare shi, Ranan kamar zai lashe ni gaba daya zakace a ranan yafara sani na diya mace a,rayuwan shi don ni kaina saida nai mamakin wanan kaunar da yake min haka, Sai da komai ya lafa a tsakanin mune kowan mu yana mayar da numfashi sai naji yace min Humaira cikin wani murya mai sauya yani na amsa mashi da na,am yayana, Yace don girman Allah daga yau ki rike ni amana a,rayuwan ki kamar yadda zan rike ki kema amana a,rayuwana, Aisha Humaira ki yarda dani don Allah ki amince dani don bazan barki ba komai dadi komai wahala, Nace ni yaya bakai min komai ba halin Umma daine ya bani tsoro har na dauki wanan matakin haka shiru naji yayi maimakon yayi magana sai naji sheshekan kukan shi kawai yana tashi, Rudewa nayi hankalina duk ya tashi don irin kukan da yaya yakeyi bana wasa bane, Nace cijin rudewa don Allah yaya ka daina kukan nan haka please yace cikin kuka Aisha dole ne nai kuka don nasan in har Umma bata daina halinta ba akanki zan iya raski wata rana don irin sharuddan da su Baba suka sa a tsakanin mu, Nace yaya indai nice zan fada masu insha Allahu bazan kara bari su sani ba zan yi kokari na zauna da duk halin Umma nayi hakkuri don kai, Ya jawo ni jikin shi ya manne yana sauke nufashin kukan shi yana cewa tare da matseni a jikin shi nagode Humaira nagode da kika fahinci matsalata har kika amince min da bukatana a gare ki, Don haka na yanke shawaran barin garin nan da ku baki daya don kara gujewa fitinan umma nan gaba, Da sauri nace zamu koma ina kuma yaya yace kaduna nake son komawa mu zauna a can don komai nawa zan mayar dashi can don haka zaifi muna sauki, Nace amma kana ganin Umma zata yarda kayi nisa da ita haka a cikin sauki, Yace cikin dan murmusawa tare shafa min kaina da yaji kitso kanana yace, yarda ya zama dole a gareta tunda haka shine mafita gare mu, Nace to Allah ya kyauta yasa hakan shi yafi zama alheri a gare mu baki daya yace amin tare da sa hannayen shi duka biyu ya rugumoni dasu cikin jikin shi haka barci ya dauke mu sai can cikin dare naji madina tana buga kofa wai Hussaini yana kuka , Zare jikina nayi cikin nashi sai naji yariko ni zuwa jikin shi yana cewa bari na karbo shi kawai, Shi ya tashi yakarbo yaron na fara bashi nono dama shi acicine muna cewa yabiyo baban shi Jibrin, Washe gari na kara tsabtace gidan tako ina muna zaune na kalli kofan Biba sai ta fado min a rai nace ko yaya matsayin auren su yake da ita yanzu oho, Na tuna da fitan nan ta na kadavkaina kawai nace a raina kai Biba Biba problem ce wallahi tazo kawai ta yamutsa muna gida gaba daya don son kai irin nata, Da zata zauna mu fahinci juna muyi zaman lafiyan mu da duk haka bsi taso ba amma ina ita gurin ta kawai ahine ta zauna ita kadai a gidan batare da wata mace ba, Niko nasan haka ba zai samu ba agare ta don na riga na ga yiwa zuciyar hamza barna ko ba yadda zai rabu da ni don ita don hakkuri da kawaici baibar komai ba a duniya, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,,,,,, Iyayen Biba har gida suka tasa keyan ta gurin Umma ta roke ta garafa amma sai shi gogan yakafe ba zai mayar da ita ba duk ta jemay ta shiga tashin hankali lokaci guda ta sauya baki daya, Da kyat da sudin goshi ya yarda ya mayar da ita bayan su Baba Madu sun sa mashi baki dole ya hakkuri ya mayar da ita amma da sharidin bata kara tayar mai da fitina a gidan shi, Haka ta dawo tsamo tsamo da ita daga ita har yar ta suka dawo kamar sunyi jinya, Tunda tadawo ba wani daga kan da takeyi a baya irin na farko sai zaman lafiya da mukeyi da ita yaran mu kuma mun hada su guri guda komai tare ake masu, Mun shirya tafiya gurin mahaifina tare dasu Baba na Sahabi da baba liman da,sauran yan uwa a bisa jagorancin Hamza zai kaimu, Tafiyan kwana da yini muka isa garin da yake don zuwan bazata mukai mashi yai matukar mamaminganin mu, Nan mutanen garin duk da basu jin hausa haka sukai ta zuwa ganin mu natafi duk da yarana hudu harda Madina da mama hafsi, don ta taimaka min da daukan yara, Bani ba har su baba sai da suka tsinke don ganin irin daulan da Abbana yake ciki, Shiko don murna ya rasa inda zai samu fon dafin dayake ji saboda dama mutanen garin suna mashi gori wai baida,asali amma yazo kasan su yafisu kudi, Matar shi fara ce amma ba sol ba doguwa siririya da ita da yaran ta biyu mace da na miji kamar yadda Abba yace muna, Da farko bataso zuwan mu ba amma sai na lura tana tsoron Abba sosai inajin fada yai mata sai ta dan fara sake jikin ta damu kadan, Kwana biyu su Baba sukayi suka barni a can don zan kwana biyu gurin Abba kamar yadda ya roko yai masu goma ta arziki suka dawo, Zaman mu gurin Abba bazan iya cewa ga irin dadin da mukaji ba don ya nuna min so da kauna sosai a fili har matar ta,shiga nuna kishina a fili, Sai dai wani ikon Allah yaranta sun shaku dani sosai ko yaushe suna gurina ba hausa suke jiba amma haka muke zama muna gwalanci da junan mu tunda ba turanci ake a kasan ba, Sannu sannu matar ko may tagani ta dan fara sake jiki dani har muna zama mudan yi hira da ita takaini har gurin yan uwanta suka ganni amma ban yarda naci komai nasu ba don duniya abin tsorone yanzu, Satin mu uku Hamza yazo yadauke mu yai min shatara na,arxiki bani ba harda mama da ta rakani ta samu rabon ta sosai, Dinkunan mutanen kasar da shaddan su sai da Abba yai min akwati biyu na dinkakkakun kayan su na can, Kudi masu yawa yabani idan na dawo nayi sana,a dasu tun acan nasaro zannuwa mutanen kasar na shigo dasu Nigeria, da sauran abubuwan bukata yai muna rakiya har iyakar kasar dashi da mutanen shi, Mun dawo gida lafiya da gajiya a jikin mu mama a gidan mu ta sauka don yanzu na gane dadin ta sosai saboda tsakani da Allah take kula min da yara hakan yasa na roke ta tazauna damu don nadan samu saukin lalurar yarana, agurin ta, Biba bataso zaman mama da mu ba amma ba yadda zatayi dole ta hakkura aka zauna ba mai tsagwaman wani na ciki na ciki, ****** ********* ****** Ya gama duk wani shirin barin garin da yai niya duk da baso ba don ni a gani na ai komai ya wuce ko ga kowa, Ina zaune nadawo daga Birnin kebbi duban wani shago da aka bude min a can na kayan kitchen equipment, na mata sauran abubuwan gida na matan zamani, Yara sun rufe ni suna son nabasu tsaraban da nazo masu dashi daga can, Sallama akayi wasu matane su biyu suka shigo sai da suka zauna na sheda mama Sa,ace kawar Umma dayar na kalla da kyau nagane Sadiya ce da goyon ta, Gaisawa mukayi dasu na katbi goyon nata ina cewa sannun ku da zuwa nace madina takawo masu abinsha, Drinks da ruwa mai sanyi takawo masu Sadiya sai bin gidan da kallo takeyi tana sauke ajiyan zuciya, Mama Sa,a ce tafara magana da cewa Hajiya Aisha gurinki mukazo nace tau mama gani ai ina wasa da hannun yaron da ke kukan kiyyau , Mama Sa,a tace hajiya da farko muna baki hakkuri kan abinda yafaru a baya don Allah kiyi hakuri ki yafe muna, Nace kai haba mama ai rayuwan zamane haka abin yake ni ban rike komai a raina ba tace gaskiya don gashi ai naga kin tare mu da mutunci don bamuyi zaton samun haka ba agurin ki, Ta gyara zama tana cewa dama hajiya munzo don Allah ki taimake mu yadda Allah ya taimake ki ki taimaka muna yau satin Sadiya uku ke nan da zuwa amma mun kasa samun kufin motan da zata koma don wallahi abin duk ya kakare muna baki daya, Nace a ina Sadiyan take ne yanzu tace tana aure ne acan cikin kauyen niger a wani garin nufawa fategi, Gashi kwanakin da mijinta yaba ta shanyesu harda dori shine muka ce bari dai muzo gurinki ko zaki taimaka muna don Allah kiyi hakkuri ki taimake mu na samu takoma dakin ta hakana, Kafin in yi magana sai ga Hamza ya shigo gidan a lokacin Biba da,ta tashi da barci take ce min ashe har kin dawo ne nace mata eh ai na tambayi yara sukace min kin dan kwanta, Sannu da zuw muke mashi inda yake ce min yanzu nake tunanen ko kin dawo sai da nazo naga motar ki a,waje nasan kin dawo, cikin nuna so da kauna yake min magana, Nace ai na samu an hada komai dubawa nayi da dan masu gyara kawai sai na juyo don nabar wa yan nan gida kada su dami mama da kuka nono, Yace ai da gangan kika barsu a gida don kin san halin su da kiuya sosai, yace ai gobe insha Allahu zan shiga naga yadda akayi nima Zai shige nace mashi affa yaya gasu mama fa da Sadiya sai lokacin ya waigo yana cewa wata Sadiya ke nan fa, Cikin mamaki nace mashi Sadiyan mama Sa,a sunzo ne su gaishe mu don Sadiyan zata koma garinsu inda take aure yace mungode, Ya juya inda suke suna gaishe shi ya amsa cikin daure fuskan shi tamau dashi kamar bai dariya a baya, Ya shige dakin shi nan nake nunawa Biba Sadiya nai mata bayani cewa kishiyata dasuka rabu da yaya a baya, Wani kallon raini tai masu tace Umm,wummm, kawai taci gaba da harkokin ta tashi nayi nabi bayanshi dakin shi yana tsaye yana rage kayan jikin shi nashigo dakin nace,mai, Idan kana da wani abu kakawo a basu sai na kara masu wani tsawa yadaka min tun ban karasa zance naba yace wai may yasa Aisha baki san ciwon kanki bane har yanzu, Matar da taita kulla muna sheri da makirci iri iri shine yau zata wanko kafanta tashigo min gida, Wai yaya ma kika bari suka shigo min gidane wai harda zama sukayi fa don sunga ido a gurin ki, Nace haba yaya ai ko don albarkan haihuwan da kukayi tare taci na basu fuska ko, Wani kallo ya,watso min na shekeke yace haihu haihuwa dawa ke kika,san wanan ni hada min ruwa na watsa kinji ban iya ramay ramay ki kinji,. Nace haba yaya taimako ne fa zamuyi amma kace wani abu yace ai ban hanaki ba je ki taimake su ke amma bani hamza ba dan matsiyata, Duk yadda naso ya fahince ni yaki yada shigewa ma yayi bathroom din yabar ni tsaye gurin, Nafito dakin rai a bace sai dai nadan kirkiro dan murmushi a fuskana don kada su gane bacin raina, Idon mama Sa,a a hannu na taga ban fito da komai sai tai murmushi yake nace ina zuwa mama daki na shiga na dauko masu turmi biyu cikin na,sayarwa na da kudi dubu goma nakawo masu nace mama ga wanan kuyi hakkuri kun samu banda kudi a gida yau weekend ne, Su ka karba suna ta min godiya nace babu komai ai nan su kai muna sallama suka mike zasu tafi sai ga mama tafito da hussaini a hannun ta tace a,a yau Sa,a kune agidan dan nawa kuma, Tana murmushin yake suka gaisa ta juya tana cewa zasu tafi don tasan mama zata iya sake mata layi yanzu, Nai masu rakiya har kofan gida ina ma Sadiya Allah ya tsare hanya idon ta ya canza kalla da kyat take amsa min suka,tafi, Suna batin gidan tace cikin muryan kuka mama kinga yadda yar agwai ta canza baki, Abinda naita maki hasashe ke nan a lokacin amma sai kika ki ji giyar shedan ci yana rudin ki yanzu dubi wanan daulan Sadiya da kina cikin shi min huta da wanan bakin talaucin a rayuwan mu, Ban aurar dake gareshi ba Saida nasa akai min duba akaga arzikin shi dake tafe , Yanzu dubi yadda yarinyar nan tabaje take cin arxikin ta kowa na kallo don yanzu ko yan uwan shi da uwar shi biye suke dasu, Shi har yanzu rike yake damu don kiga bai sake fuska ba ai damu, ita ita ko kila ma ya bayar da kudi masu yawa a bamu ta boye ne taba mu kadan, Sadiya tace ,a a mama nasan halin yar Agwai wallahi bata boye wa asalima fa da fushi tafito dakin, nasan ya gasa mata bakar magana ne kila, Ni nasan halin hamza zai iya fiye da haka idon ranshi ya baci da abu aiko yanzu mungode da wanan da muka samu, A gida kuma nan aka zauna a na tuna irin rayuwan da mukayi a zamanin Sadiya Biba tace yanzu shi akan wanan mumunan matar yai ta gasa mutane haka hat may yagani a gurin ta yayi daidai da yana fitowa a lokacin sai ji mukayi yace abinda nagani a gurin ki mana kaddara , Shiru tayi don tasan tund yafadi haka idan takara tankawa zasu kaule da fitina sosai, na kawar da zance da sauri da cewa wai kuwa ka samu zuwa gurin Anty hindatu ka dubota , Don in baka je ba nasan tana jirace da kai duk sanda kuka hadu sai kaji ta, Yace cikin murmushi wani rufa min asiri Humaira kar ta hada dani tace aidani aka kulla mata yin kishiya, Nace haba dai ai tadan kokarin da kayi akan zancen yace haka kike gani ke amma ai ita, cewa tayi nina koya mashi yin mata biyu, Murmushi nayi nace antyna ke nan bata wasa da kishi kamar maman jafar bata san cewa komai mukaddari bane ga bawa duk abinda ke a littafin mutun sai yayi shi a rayuwan shi, Ita dai maman jafar ai arziki tayi don Allah baiyi mijin ta da bakin aure aure ba amma ai mace bata cika baki akan namiji komai tsoron ta in Allah ya kaddara sai anyi, Mutum dai ya zauna da kowa da zuciya daya sai Allah ya kawo mashi agaji ta inda bai zata ba, Biba tace niko ina mamakin wasu mata da wai suce don sun shiga gida su basu yarda wasu su shigo gidan su, Nace ai matsalan kishiyoyin ne na yanzu sai andace don haka kinga tana da gaskiyanta don bakasan wace kala za,a kawo maka mutum kawai ya dage da addua kawai shine mafita ga bawa,a ****** ********* ****** Wata sabu inji yan caca Hamza ne zaune a gaban Umma bayan ta gama sauraren maganan shi tace cikin yake baki, Ashe kace mu shirya tafiya yazo ke nan don ba zan yarda ka barni nan ba gaskiya kafarka kafa na da kayana, Ce haba Umma ina zan tafi dake in mun kwasa mun tafi wa zai zauna da sauran yaran a gida dole sai da babba a kusa dasu ai, Umma tace Allah ko akwai wanda zai basu tsaron da Allah ke basu ne a duniya, Balle ai ga hafsi nan ta zauna dasu mana ai ba komai dani da ita ai duk daya ne gare su, Yace Umma ai ita mama hafsi dama yanzu a gurin mu take don haka kin ga da ita zamu tafi kece dai zaki tsaya dasu balle tafiya na aiba yana nufin na barku ke nan ba anan dole na rika zuwa don ita ma Biba ba ita zan tafi ba a nan zan barta ta zauna kada abar gida ba kowa, Umma tai farat tace Allah baka isa ba hamza don ba,wanda zakaiwa dadin baki kafar ka kafa na don tare zamu, Yace gaskiya Umma ba hakane tsarina ba tsarina ke nan natafi da Humaira can ta zauna da yara don ina son yara na suyi karatu sosai na boko da islamiya, shi yasa na zabi zuwa kaduna na zauna dasu, Kaji na fada maka iya zance na sai dai in fasa yafiyan za,a yi a fasa muddin kace bazakaje dani ba, ehe, Shuru yayi zuciyar shi na tafasa sai dai bai da halin magana don da,wani ne yau da yaji shi , Mikewa yayi yai mata sallama yana tunane a ranshi may yasa Umma tafaye son kan ta haka da yawa ne, wai, Yanzu duk da yafada mata cewa saboda yaran shi zai yi tafiyan amma bata yarda sai ta kanta kawai take yi, Ranan haka ya wuni da bakin ciki da bacin rai a zuciyar baida wallawa don har zazabi yaji yana son kama shi don ya riga yagama shirin tafiyan tsaf komai na bukata ansa agidan a gyara ko ina har kitchen din gidan gaba daya har abincin amfani da drinks ya saya ko, Yana fita Sa,ade tace ba kowa ya shirya haka ba sai wanan makiran matar tashi yar agwai wai ita tana ganin uban ta nada kudi bata son zama da mutane bari taja shi su tafi nisa da kowa, Kuma wallahi Umma duk da mama hafsi aka,shirya wanan makircin sam mama bata kaunarki, Umma tace barta kawai makiran banza da wofi ai nasan duk kule kulen da takeyi akan yaton nan, In haihuwan mai arziki abin yine itama aida ta haifa, yanzu da taga ya zama abin kwarai ai tashige masu itace uwar kwarai, To bazata ba ko ina anan zata zauna dani za,a muga tsiya kuma kema bazan barki a nan ba tunda zancen aurennki ya lalace, Bai fadawa kowa yadda sukayi da Umma ba sai washe gari bayan yakai Biba gidan su vurin suna yar uwarta da,ta haihu ne yadawo yasamay mu a,falo zaune, Ya zauna fuskan shi babu walwala mama ce tafara magana ganin yadda ya zauna a kasalance tace yaya dai dana, Ya wani irin huci tare da shafa fuskan shi yace matsalan Umma daine mama, Mama tace tau anyi wani abin ne kuma ko ka may yafaru haka kuma yace wallahi mama ni ban san may ke damuwan Umma ba, Tasani cewa zan nisantane don yawan matsalata amma wai shine takafe wai dole da ita zamu tafi idan kuma ban yarda sai dai a fasa tafiyan a baki daya, Wani irin son kaine ga Umma sam bata son farin cikin rayuwanane wai, komai fa na riga na shirya mama acan tafiyan mu ne kawai bansa rana ba, Amma gashi yanzu ta bijiro min da fitina kuma zata tayar muna da hankali, Mama tace wanan ma fadi ne bari zan tafi anjima nagane ta muyi shi yace mama dakin barta kawai tunda kikaji tafadi haka gaskiyar ta ke nan tafadi, Don ko kinje ba fasawa zatayi ba tunda kikaji ta fadi haka haka dinne har cikin ran ta, Bari dai naje muji matsalan ta don haka kawai baxai yi ta fito da zance haka ba babu dadin ji tabiku taje tayi may acan, Yace na fada mata itama wanan ba da ita zan tafi anan zata zauna sai dai na rika zuwa don ai sa,ana kusan a nan take gaba daya, Mama tace wa habiba kake nufi bazakada ita ba yace ita din mama don ban zuwa da ita anan zata tsaya ta tsaya a gidan nan kada mubar gida ba kowa acikin sa, Ai kuwa ashe akwai wata fitinan tafe nace masu sai a lokacin nasa masu baki a zancen su nace kaima kasan Biba bazata yarda ba wallahi, Yace idan bazata yarda ba sai tasan yadda zatayi amma ban zuwa da ita gaskiya don ban ma taba shirya hakan ba a raina, Hmm kawai nace tare da ci gaba da abinda nake a,wayana ina sauraren hiran su, Mama kamar yadda tace haka din ta,shirya ita da Jidda suka tafi gurin Umma don su gana da ita, Umma taji zancen mama da tace mata, haba yaya yanzu da girmanki kice sai kinbi yaron nan kaduna may zakije yi, Umma tace, ke mai zai sa ki bisu abinda yasa zaki bisu shi zai sa nabisu nima kafana kafan su na gaya mashi ai, ke ki zauna a gida da yaran, Mama tace aini dama badani za,ai tafiyan ba don bance zanbisu ba ina nan ni, Munafuka kin zaci bai fada min cewa dake zasu yi tafiyan bane shine ni don bakin cikin ni baki son ayi dani ko, Subbahanallahi yaya may yakawo zancen bakin ciki a tsakanin mu kuma akan danki zanyi maki bakin ciki ke da kika haifi abinki da cikin ki aiko danakai annaminiya, Tau ni dai yanzu ai duk ba wanan ba ina fatan kunji shakuwana dai ko dani fa za,a tafi duk inda za,a, Mama tace yaya kardai har kin manta da sharudan da mutanen nan sukayi akan yarsu har kike son ki kawo wani sabon fitina kuma, Wai don sun fadi sharadin su shine har da na, rabani da dana ko suyi min iko dashi komay wai, To tsaya kiji ni dai ni haifi shi da cikina ba wani ya haifa min shi ba balle a juya shi a juyani yadda rai ke so wanan bazai yuyu ba ni iyakar magana ta ke nan ban hana shiba tafiya amma,yasan da sanin kafata kafar shi, Mama tace to shi ke nan idan mutim baiyi sharan massalaci ba ai zaiyi ta kasuwa, Sai mama,takawar da zancen duk da ranta ya baci da kalaman Umma amma take cewa zancen zuwa gurin gaisawa gidan su Asmau fa da sukace zasuyi, Tace a hasale bazaniba kina iya zuwa idan kin tashi ni in na tashi zan tafi , Haka mama tabargidan cikin bacin rai taje gidan sarakan Asmau tai masu gaisuwan tsohon gidan da ya rasu, Tadawo gida tana fada min yadda suka kwashe da Umma nai murmushi nace mama Umma sai hakkuri fa don haka Allah yayi ta ita, Wasa wasa zancen tafiya yana son ya birkice don Umma ta kafe akan bakarta da ita zai tafi, shikuma yace ba haka ya tsara ba, Da abin yakai tura dole yaje yadamu su baban shi yafada masu matsalar da ake ciki sukazo gidan suka samay ta, Nan sukai mata tas suka ce wanan karon har in taki yarda da bukatan su to wallahi zasu cire hannun su ga al,amarin diyan ta baki daya, Ganin da gaske sukeyi zasu iya mata abinda sukace shine tayarda da tafiyan badon taso ba a ranta, Su zarah sun samay ta sun nuna mata bacin ran su yadda take ja masu abin gori a cikin yan uwan su ko yaushe, Tace su suka damu dasu aiko bada su ba,zasu iya rayuwa zarah tace wallahi Umma dole mu damu dasu don kowa da dangin shi yake kuri a duniyan nan ai,, Angama rikicin Umma sai kuma aka shiga na Biba a tsakanin su don tara mu yayi baki daya har mama a falo da dare yake cewa , Ina son kowan ku ta,saurari abinda zan fadi kuma ta fahince ni bawai nai haka,bane da wani manufa nayine kawai don kwanciyan hakalina da wasu dalilai na dani nasan dalilun yain haka, Muna shiru muna sauraren shi yace na samu gida a kaduna don acan nake son nakai wasun ku da zama, don yanzu kun san business dina ba anan kawai ya tsaya ba, Don haka ke Humaira sai ki shirya ke da yara ku koma can da zama ke kuma Biba ki zauna anan har mu ga abinda za a yi gaba, Kafin ma ya kara wani kalma sai cewa tayi tunda gani Biban mahaukata ko, Don ina shatalalagan ka sai na zauna gadin gida ita ka dauke ta ku tafi van kuji dadin ku kubarni nan gadin gida ko, Yace naki tunanen ke nan yanzu kunji magana na don nagama magana ke nan ke Humaira sai ku fara shiri zuwa karshen wata in Allah ya kaimu zamu tafi hardake mama zamu tafi don haka ashirya kafin lokaci, Wallahi ban yarda wa za,a cuta don ka maushini ban son ciwon kaina ba kun gama shirin ku yanzu zaka zo kace wai ni na zaunacmaka gadin gida, Yace to inbaki yarda sai ki san yadda zakiyi ai don baki isa ki sani dole ba, Tace ai in gaskiyane da dani da nake karama zaka tafi ita dake da yara ta zauna gida Yace oho tunda ke ne yar son kai ko toni ba haka nake ba don tare kika ganmu kuma bazaki raba mu,ba Tace to wallahi nima ban zama yace in baki zama,sai ki san yadda zaki yi ai ko don dai ni na tsayar dake inda na tsayar dake, Haka taron ya,watse a hargitse Biba tana ta zage zage wai ita bazata yarda ba dole da ita za a tafi, Ni bata ma san tafiyan ya zama min dole bane bandai son na musa mashine kawai don ban son iyi nisa da Ummina da yan uwa na, Muna shirin mu su ko sai faman fitina suke da Biba kullun cikin jidali suke a tsakanin su kan tafiyan, Da naga fitinan yai yawa nace ni zan zauna ita su tafi yayo cikina da masifa yace ni har na isa yace ga abinda yake so kan wata can nace ban yi, Naje har gidan Hindatu na fada mata abindake faruwa tace, min wai ke Aisha yaushe ne zakiyi wayo mijin ki yana kokarin nema maki sauki kina son jefa kanki ga fitina Wallahi maza ki shirya kibi mijinki bakin ki alaikum in baso kike kijawa kan ki fitina ba kidawo kina dakin sani daga baya, In zuwan ba,sun hango alheri bane aida baki ga harda Umma tsohuwa tana fadan da ita za,a tafi ba, Nan dai ta kara sani a hanya nadawo gida na sa hinma ga shirina itako Biba sai faman masifa suke kwasa dashi tana wallahi bata zama, Komai da muke bukata mun tanada a,tare da mu inda motar kayan mu ce tafara wucewa bayan kwana uku muma muka,shirya mu kaiwa yan uwa da,abokan arziki sallama Umma ma da zamu tafi mun tafi har gidan sallaman ta sai cewa aje lafiya kawai gadai amanan dana nan nabarshi a hannun ki Nace cikin murmushi ni Umma gawa nawa amanan yake da ni zan rike nashi tace wanan kuma ke kika,sani da mama ma basuyi sallaman dadi da ita ba, haka muka kama hanya sai kaduna garin gwauna dani da mama da yarana gaba dayan su har madina nan mukabar biba tana ta kumfar baki da zage zage wai gidan su zata tafi bata zaman yi mashi gadin gida don ita ba sakariya bace ai,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,,, Mun isa garin kaduna misalin karfe hudu da yan mintina na rana gaba dayan mu a gajiye muke sai bin garin muke da kallon mamaki har muka isa masaukin mu watau gidan mu, Wani gida ne mai babban get aka,bude muna motan mu da dayan motan da yake bin mu a baya suka shigo daga bayan mu su ma, Bayan mun fifito ne hankalin mu ya dauke ga kallon gidan cikin mamaki gaba dayan mu, Yafito shima a gajiye yana cewa Bissimillah ku mana ku shigo daga cikin ko, Jidda this is your new home, so feel free, is your home here, enjoy your self,, Gaba daya a falo muka zube saman dima diman kujerun dake mamaye a falon sai raraba idanuwan mu muke yi, Photo na mu ne a ka man na ko wani kusurwan falon cikin dauki yaran ke murna da nuna min photo su a bango tare dani da baban su photo da muka dauka da sallah ke nan, tare da su, shine yasa aka wanke mai manyan glasses din su ya manna a nan,. Sallah na Umurci kowa da su mike muje mu fara sauke farali tukun, Shi da kan shi ya nuna muna yadda gidan yake ko ina kowa ga inda ya kamata ya zauna, Sai muka shiga da kayan mu dakunan da ya gabatar muna din kowa sai da yai mamakin kyau dakin da haduwan shi komai morden one classic, Abinci aka fara gabatar muna wanda aka kawo daga gidan Nasir abokin shi, dake nan garin kaduna din, Abinci ne lafiyayye sai kamshi ke tashi irin girkin zamani na yan birni komai yaji zam,, Sosai muka kwashi girkin mu sai kuma muka,fara hiran mutanen gida, Hamza ne ya shigo falon ya sauya tufafin jikin shi zuwa kananan kaya, Ina matukar son nagan shi a cikin irin kayan nan don yakan fitar mai da kurciyar shi a fili duk da nasan hakan zai iya jawo hankalin wasu mata a kan shi amma ban faye damuwa ba da hakan don wani dare ne jemage bai gani ba, Bayan fitan shi da yan mintina sai namike nafara shiga dakunan gidan daya bayan daya, ni da mama da sauran yaran, Dakina yadda naga an kashe mai kudi sai da abin ya bamu mamaki sosai a hankali na sauke ajiyan zuciya har ana iya jina a fili, Mama dake dauke da hassan a hannun ta tace cikin murmushi Aisha wanan ba komai bane kadan ne daga cikin riban hakkuri , Duk abinda bawa yai hakkuri a kan shi wata rana sai ya girbi alherin shi daga gurin Ubangin mu, ta hanyan da mutum bai tsanmani ba, Yanzu da ace kin biyewa son zuciyar ki akan yawan auren da yayi tayi yana kawo mata kowace da halinta amma kika daure kika sawa ranki hakkuri yau ga riban hakkurinki kin girba , Yara hudu inji Allah a lokaci daya harda kyautan tagwaye akai Hakane koba komai mijin ki ba mai wadata bane, Allah yasan hanyar da zai saka maki da alherin sa, saboda Allah yana alfahari da bayin sa masu hakkuri ga duk yanayin da suka tsunci kan su a ciki, Sai kiga Allah ya,dube su da idon rahama yai masu sakaiyan da,alherorin shi don Allah Aisha ki kara kaimi gurin hakkuri da mijinki ku taru ku rufawa junan ku asiri da diyan ku, Kada zancen auren shi ya taba ruda ki kawai ki dagd da addu,a da hakkurin da kika,saba yi Allah ya,tsaya muna na amsa da amin mama a hankali tare da,fadin nagode mama, Kowan mu ya shiga gyaran guri yadda ya dace don adana yan kayan da mukazo dasu kaduna a,tare damu don ya hana mu kwaso kaya da yawa, Sai dare ya dawo gidan da kaya,niki niki tufafin yara ne da su takalmomi masu kyau kowa kamar debosu yayi, nasan yayi hakane don mun shigo birni yanzu yasa ya sauya masu kaya kalar ta yan birni, Sannu sannu mukafara fara sabawa da garin da rashin yan uwan mu da muka baro a gida, Yasa yaran makaranta mai tsada sosai ta kudi, har da madina dan lokaci kadan sai gashi mun fara sajewa da yan gari saboda yana matukar kashe muna kudi sosai, Tun zuwan mu ban fita ko kofar gida ba amma sai ga yaya ranan yasani gaba wai muje mukai yara makaranta inga hanya don nice zan dinga kwaso su kulun kuma inkai shi don nasan shi ba mai zama bane a gari, Tsoro yakamani yadda zan gane hanya haka a lokaci guda gashi ba tukin mota na iya a birni haka ba iyakata garin Birnin kebbi kawai, nake dan shiga ko shi a,tsorace nake tuki ciki, Da zamu dawo yabani mota wai naja muna tafe yana nuna min hanya har muka kawo gida da za,a dauko yaran ma tare muka tafi ni naja motar har makaranta ina bin kwantancen da yake min sai da mukai kwana uku a haka muna fita tare yana gwada min hanya har ya fahinci na gane don ina amfani da signbod din gurare da muke wucewa, Haka da kwana biyar yai tafiyan shi ya barmu a gatin mutane dole na zage nice mai hidima komai kamar yadda ya koya min yi, Ban samu wani matsala ba don ina amfani da kwakwalwa na gurin fahintar komai wasa wasa sai na fara sabawa, da garin, Batare da naji tsoron komai ba haka yasa watara na,dawo daga kwaso yara mun jero da wata jar mota mai tsada a bayan mu , Sai da nazo na wuce matar dake jan motar naga ta bini da kallo, kusan gidajen mu a jere suke da juna, Nai hon maigadi ya bude muna kofa saida nai parking muna fitowa sai ga wanan matar ta na hon daga kofan get din mu, Dole na tsaya da mamaki nake kallon ta don dai ni ban san kowa ba,a,garin, Ta fito daga motar ta takaraso gare ni fuskan ta da murmushi a makale nima dan murmushin nayi ina karba mata sallaman ta, Tace ashe kece makwabciya ta ina jin yarana suna fada min masu gidan nan sun tare da yaran su farare sosai sai na dauka ku ba hausawa bane kila, Nace cikin murmushi mu ko hausawa ne daga jahar kebbi muke, Tace masha Allahu ni ga gidan mu nan na kusa da ku dinnan sunana Fatima ina da yara biyar, maza uku mata biyu, Masha Allahu na bata amsa nace Aisha nake ina da yara hudu maza biyu mata biyu tace wake da shimkafa ke nan sai nai murmushi, Tace Allah ya bamu hakkurin zaman da junan mu a matsayin mu na makwabta nace amin cikin murmushi, Take ce min ita yar jahar bauchine zamane ya kawo su kaduna su ba yan jahan bane, nace ashe duk mune nima zama ya kawo, Tace ok bari na barki ki shiga don naga daga gurin kwaso yara kike daga makaranta, Sai na shigo taronki don ni yakamata na fara shigo nace nagode tajuya tana mu na sallama tafita, Muna shiga daga ciki mama tana masu oyoyo har ta,fara cire masu kayan makarantar dake jikin su, A,gaskiya ina matukar jin dadin zama da mama don duk wani nauyi tana dauke mana sam bata gajiya da aiki ita, Kasancewa weekend zamu shiga yasa nasa na gyara kayan abinci masu yawa,don nasan yaran zasu wuni damuwar mu agidan, Da,dare unexpected sai ga yaya ya,dawo garin ddaga tafiya yazo muna da kayayakin marmari iri iri na kasar wajen Nigeria, Yara suka hau murna da jin dadin ganin shi bayan kwana goman da yayi baya tare damu a kasan, Bai samu matsalar taro ba don komai a shirye yake yai wanka yafito falo don yaci abinci, sai yaran suka rufe shi, Ina fitowa daga dakin naga yaran suna damuwan shi da,surutu na karasa gurin ina cewa oya kubar gurin kubar daddy ya huta haka baku ga yana cin abinci bane, Sai ya dakatar dani da hannuwan shi yana cewa, bar su kawai Humaira let them enjoy there time with me for a moment please, Tsaye nayi ina kallon yadda suke hira shi da yaran cikin so da kainan junan su freely, Zuwa can ya,dago kai yana ce min sako nan Anty cost, ta bayar nakawo maki wai let's desegn ne na,shaddan mata, Na lumshe idanuwa nace Allah sarki Anty aiko ta kyauta min sai cewa yayi amma Abba yace nace ki bar kudin su shi zai biya kudin, Wani dadi naji har kasan raina nace Allah sarki Abbana na gode Allah yabar kauna da dalili, Da murna nake fadawa mama abinda Abbana yai min sako dasu ta tayani murna,sai kuma tace to amma ai naga garin nan baki san kowa ba,cikin sa nace nima tunanen da nake kenan wallahi, amma dai Allah zai kawo muna mafita, Kirana yayi na kwashe kayan da suka ci abinci still yana gurin da yara yana tambayan su labarin makarantar su, Tambayan su yake a cikin hikima akan makarantar su din, Nan ya,fahinci cewa Jidda tana fuskantar matsala daga wasu daga cikin yan ajin nasu na challenges, Suna ce mata wai bata iya hausa ba kuma suna mata wayo gurin karbe mata abinci breakfast din su, inda taje dashi, Ina jin su sai naji kunya da nauyi abinda ya kamata nayi a matsayina na uwa na fahinci damuwar yara na da kuma wa yanda suke hurda dasu amma ban yi azancin yin hakan ba, Inda nake tsaye ya dan kalle ni cikin lumshe idanuwan shi alaman kin gani ko, Yace wa yarinyar ta bari gobe shi zai kaisu school da kan shi zai yi complain wa malaman su, din,,, Kwance na samay shi a,dakin yai rigingine ya sa hannayen shi daya ya tare goshin shi dashi, jin motsina yasa shi sauke hannun shi ya dan kalli inda nake tsaye ina aje mai dan flask din ruwan zafin shi a gefe, Ina,saye da kayan barci riga da,wando masu shara sharan hannu sai dai babu abin da kayan ya boye daga jikina kamshi kuwa ba,a magana a jikina, Ya saukar da idon shi gaba daya a kaina tare da,sauke numfashi a hankali, Kallo na yayi tare da murmusawa yana jin wani irin sanyi da begena a ran shi yace, Hummaira kayan nan sun maki matukar kyau sosai sai dai mama ta shige ne da kika fito haka, Fuskana dauke da murmushi nace tashige da yara tun shigowan ka ya mika min hannu alaman nazo gare shi, Ina zama yake cewa cikin sauke ajiyar zuciya nai saurin dagowa na kalle shi don yadda naji ya sauke ajiyan zuciya da,alamar damuwa a ranshi, Yace don Allah ina son ki saka idanuwanki sosai akan yaran nan musanman ma matan don yanzu muna a cikin lokaci ne sosai, Yanzu kinga suna cikin damuwa amma baki maida hankali ba balle ki fahince su, Idan da kina bibiyan komai nasu dake dake zama dasu ya kamata ki gano wani abu daga gare,su, Amma dai koma maynene Monday insha Allahu zanga malamin ajin nasu a kan Jidda din, Sai kuma ya dan matseni a jikin shi yake cewa dake dasu duk amana kuke a gareni kinga nan birni ne kai koma kauye ne yanzu dole mutum yada ido akan duk wani movement na yaran shi ko a gida ko a,waje saboda lalacewan zamani, A hankali nace insha Allahi yaya zan mayar da hankaki akan komai nasu baki dayan su, Fara bin jikuna yayi a hankali yana mai fara aiwatar da sunna a kaina ban tsaya wani jikiri ba nashiga mayar mashi da martani yadda ya,dace dashi, Washegari da safe kafin mu tashi har mama ta shirya muna abin karyawa ko yadda ya,dace don koda na,fito nasamu tana wa yaran shirin zuwa islamiya Naji dafin ganin hakan don nasan ko fiye da haka zan samu a gurin mama din, don komai ita da zuciya daya take abinta, Wani lokaci nakan ce a raina dama ace itace mahaifiyar su Hamza da nafi kowa sa,ar uwar miji mai mutunci amma dai ko yanzu ma ba laifi don ta cancanci yabo sosai gaskiya, ko a haka ma din na godewa Allah na, Bayan fitar yaran zuwa islamiya yafito fallon saye da wando tree quarter, sai yar farar tshirt da yake saye dashi, Yana gama breakfast ya koma saman doguwar kujeran falon ya kwata da,waya achannun shi yana yi, Na fito daga daki cikin wasu kananan kaya, wandone da riga sun matseni sun shafe min jikina tsaba, surana yafito tsab a cikin shigar, Tunane naga yanayi ko may yaks tunand oho, na isa gurin shi ina cewa cikin dan durkusowa gare shi, laiya dai maigida, Yai murmushi tare da kamo min hannu na yana cewa Humaira naga fa shigowa kaduna yafara saki bushe fitilar ki ta kunya, Yar dariya nayi nace ai akai kawai nake bushewa ba ga kowa ba yake ce min mama fa dake gidan, Nace ai itama tafi bukatar taga na gyara maka,abinda kake so da kauna a,rayuwan ka, Yai wani galala yana kallona tankar wani wawa can yace eyyeh har fada bagana yanzun kin koya ashe, ya jawoni zuwa jikin shi yana cewa Allah ya barmin matata uwar yayana kuma uwargidana rangidana, Yinin ranan yaya bai fita ko ina ba yana gida a tare damu ya hutawan shi, Tun ina jin nauyin yadda yake min har na bushe fitilar nawa nima nashiga mayar mai da martani ba tare da kunyan idon mama dake cikin mu, Da yamma ni da kaina nashiga kitchen na,shirya muna abincin dare inda na hada muna ferfesun kayan cikin rago dayaji kayan yaji na,gargajiya sai fankasau da miyan naman kaji, Duk wanda yaci sai da ya,yaba da girki sai faman santi sukeyi suna ci da kari, Sai washe gari kayan shi ya iso inda yabani sakona na dibarwa makwaciyana tsaraba mama ta karba da kanta tashiga gidan takai mata don tace tana son fita ta mike kafan ta, Da yamma Fatima tashigo gidan mu tai min godiya sosai ta zauna muka dan taba hira har nake nuna mata kayan da aka kawo min, Tabani shawaran akwai bukin da zata na yar uwar ta da ta haihu a kabala sai muje tare na dan fara nuna,wa mutane take ce min nafara online business ina turawa ana gani mai so zai min magana ta nan ma, Bayan na,raka nadawo na,samu yaya a,falo yake tambayana inda nasan fatima na fada mai yadda muka hadu da ita yake ce min nadai bi sannu don nan birni ne fa, Nace zan kula insha Allahu, nan muka zauna dashi ata hira da dariya yana jin dadi a ran shi, Sai godiya yake ga Allah daya,bashi mata mai kyau hali da iya tattali irin Humaira, Yace a ran shi gaskiya zai ce yafi kowa sa,an mata mai kyau da kyaun hali da kuma hakkuri a duniya don macen da ta tara haka rahama ce ga mijinta ga kuma yara masu kyau da tarbiya da nake haifa mashi, ****** ********* ****** Kamar yadda yai alkawari ya tafi makarantar su Jidda yaga classmaster su yai mashi bayanin komai tare da dan bashi dan ihi sanin wani abu, don yanzu duniya sai da hakan, Munje gidan bukin mata sun rude da gani kayan da naje dasu sai dai ban yarda naba da bashi ba kamar yadda fatima ta gargadeni dayi haka yasa nai ciniki sosai a gurin ban dade ba nadawo gida abina, Wanan fitan ne yai silar fara hurda na da mata da yawa suka fara sanina muna hurdan arziki dasu na,saye da,sayarwa a gida, Alhamdullahi don, gaskiya yanzu, komai ya bude muna arziki sosai Hamza yayi don yanzu fita yake kasa shen duniya yana harkokin sana,ar shi, Duk da yana da arxikin shi hakan bai hanani neman nawa ba ni don business nake sosai ban zauna jiran nashi ba nima da taimakon Allah dana Abban na mike yanzu sosai,inji Allah, Sai dai sam hakan bai hana hamza ya dauke min nauyi duk wani hakkin shi dake akan mu ba, Komai da ya kamata na miji yaiwa iyakin shi muna samu daga gare shi sosai fiye da tsamanin mu, Matsala daya shine kullun fitana suke da Biba idan yaje ko kuma ta waya zagi da tonon asiri yana zuwa yana dawowa ko yaushe sai kira mashi azzalumi macuci takeyi wani zuwan da yayi yasamu ta shirya wai zata biyo shi ita bazata zauna ba, Yakai katanta gurin iyayyen ta suka zo aka zauna suke tambayan ta ko akwai abinda ya rage ta dashi nadaga hakkin aure ne tace da su babu ko daya ita dai kawai bazata zauna ba a jega mu muna can kaduna, Sai da kyat akasamu tayi hakkuri ta zauna sai dai ashe ba har cikin ranta ba, bayan tafiyan shi da kwanaki ta shirya tai shatan mota sai kaduna, Baya gari ni mun dawo daga uguwa ke nan da Fatima naga mota ana masu nune da gidan mu, Mun kurawa motar ido sai ganin Biba mukayi na tare su da murna tare da karban yarta tayi wayo sai dai da,alaman akwai alolayi a tare da ita muka shiga cikin gida sai wani fuskewa take tana shan magani, Bingidan da kallo take tana mamakin irin kyau gidan da muke cikin shi na bata ruwa da abinci amma sai ce min tayi ki barshi kawai nuna min part dina nakai kayana aciki, Nace tau Biba problem anzo ke nan wata sabuwar fitina takawo kai kuma ke nan a gidan, Nace cikin dakewa amma dai ni maigidan bai nuna min part din dake dasu nan ki a gidan nan ba gida dai yace na Aisha ne da yaranta tace wanan kuma fadi ne wallahi kada ki manta cewa gida namune ni dake don gidan mijin mune ba na Ubanki ba, Nace tau harda zagi kuma haka Habiba tace koma may ye dai bakinki ya saba da cewa mijin mu, Ban bi ta kantaba na bata wani daki tagyara shi tsab ta shiga da yar ta, Bayan kwana biyu ina jin kamar na bar gidan yadda Biba ta azazzaleni nida yaran don ma mama tana sa mata waigi ga wani abin, Da dare muna falo ya bugo waya a lokacin yaran sun dauko yarinyar sai kuka take don bata saba dasu ba, Yake tambayan wake kuka haka hussaini ne ko hassan nace a,a mama kara mace ke kukan kiuyya, Yace wacece kuma mama karama din nace a,a mama dai mana mai sunan mama hafsi, yace what , Nace ai suna nan yau kwana biyu ke nan sai naji ya kashe wayan dip ba shiri, Koda na kirashi akece min wai bussy yake bani samun shi don haka na kayale shi sai dai ina mamakin ke nan yana nugin bai san da zuwan su bane ko may wai, ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************