[5/11, 17:15] ~fatieshak🌹: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *Bismillahir Rahmanir Rahim* *Ina farawa da sunan Allah, ina neman tsari da rubuta 'Barna! Ina rokon na yi rubutun da za'a 'karu , ayi amfani da shi.Tsira da aminci ga shugaba Annabi(S.A.W.).* *GARGADI* _A kiyayi taba min labari na ta kowacce siga, Hakkin mallakar tawa ce ni ka'dai, Dole sai da izinina kafin a karanta shi a kowacce irin kafar sadarwa, wadda ya shiga hakkin mallaka kuma ubangiji ya isar mini._ *JAN KUNNE* *Gaba'daya Wannan labarin kirkirarsa aka yi(Fiction)!haka sunaye da garuruwan da ke ciki bana kowa bane, na zabe sune kawai dan 'kawata labarin, dan haka duk wadda yaci karo da abin da ya yi kamacanceceniya da rayuwar sa bada shi ake ba, arashi ne kawai* *JINJINA* _GA MARUBUCIYA_ *FADILA LAMIDO* *SUGARI BA KI YI FARIN BANZA BA*. *SADAUKARWA* _Tun daga farkon labarin har zuwa karshen sa gaba'daya sadaukawa ne ga shugaban kungiyar_ *LAFAZEE WRITERS* *SADIQ ABUBAKAR*. 1-2 Harabar makarantar kwana ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kiyawa (FGC Kiyawa), cike take mak'il da motoci da jama'a kama daga iyayen yara, da su kansu daliban rukuni-rukuni, gungu-gungu, cike da walwala sai ciye-ciye ake yi kasancewar yau ake ziyarar dalibai (visiting day). Daga can gefen lambun makarantar, wata matashiyar uwa ce da a 'kalla ba za ta wuce shekaru talatin da biyu ba. Zaune take kan lallausar darduma wacce da alamu da ita ta zo, gefenta kulolin abinci ne da kuma ledoji masu dauke da tambarin *Sahad Store.* Zaune take tana baza ido ta ga ta ina tilon dan'ta zai bullo, ba ta ankara ba ta ji an rungume ta tare da ambaton "Mamiii!" Cike da dariya ta dago kai. "Jawad wai ba ka san ka girma ba ne? ba don a zaune nake ba ai da ka kayar da ni." Ya sake komawa ya kwanta a jikinta tare da cewa, "Nayi kewarki Mami! Ina Inna?". "Ta ce, a gaishe ka, shekaranjiya ta tafi Gamawa biki" "Ki ce ba ta yi mini girebar ba kenan?" Ya fada cikin turo baki irin na sakalan yara. "Wace ita? Ai ranar Laraba yini ta yi tana hidimar girebarka, bata samu sukuni ba sai da ta kammala." Sai a lokacin ya saki fuskar yana cewa, "Allah Sarki Innata!" Ya tashi a jikinta ya ci gaba da cewa, "Ina yini?" Ta amsa tana bin sa da kallon mamakin irin girman da ya 'kara cikin lokaci 'kalilan da ba ta gan shi ba, tana mamakin inda ya sami girman jiki tun da dai daga ita har mahaifinsa ba wani girma ne da su na a zo a gani ba, hasalima in ba ka sani ba cewa za ka yi 'kaninta ne. "Kai Mami sai kin gano munina!". Ya fada yana rufe idonsa da hannuwansa. Ta yi murmushi, "Girmanka ne yake ba ni mamaki Jawad ka kerewa tsawona fa!" "To, Mami aike tsayinki kadan ne, ni kuma irin tsayin Babana na yi." "A'a, kai kam sai ka fi shi tsayi duka-duka fa watan jiya ka yi sha uku amma ka zan'kale haka!" Cikin shagwaba ya fara fadin "Haba mana Mami ki daina fada, kar ajiyo. I am 15 fa!" Ta kwashe da dariya tare da cewa "Mantawa na yi ashe ka fi ni sanin ranar haihuwarka?". Daidai lokacin ya zuge Jakarta ya dauko tsaleliyar wayarta ya mik'a mata, ''Bude mini na kira malam na ji ko ya dawo." Ba ta ce uffan ba, ta karba ta bude masa kamar yadda ya bukata. Lambobi ya shiga daddanawa har ya jera lambar da ke adane a 'kwa'kwalwarsa a cikin wayar ya danna kira ya kara a kunne, tamkar da ma jiran kiran ya shiga ake yi, ya ji an dauka ba tare da ba ta lokaci ba, sallama ya yi tare da fadin, "Malam!" Daga cikin wayar aka amsa da, "Jawad kana lafiya? Ka gan ni nan ina kan hanyar zuwa wurinka." Cike da murna yace. "Ka dawo daga Bauchin ke nan?" "A'a ban dawo ba yanzu dai nake kan hanyar dawowa na iso Babaldu zan biyo ta Dutse na iso Kiyawa." Dadi ya kama Jawad, ya shiga masa addu'ar isowa lafiya, tare da cewa, "Ina wajen da muka zauna a waccan ziyarar." Ya kashe wayar yana cewa "Oh! Allah ya so ni, jiya fa da na yi masa waya ha'kuri ya ba ni akan ba zai sami zuwa ba sai satin sama, saboda yana Bauchi, ko don bai ji na amsa masa na ha'kura ba ne, shi yasa ya bar komai ya taho?" Ita dai ba ta sa masa baki ba har ya kammala maganarsa. tana nazarin lokaci a agogon hannunta daya nuna 'karfe biyu har da mintuna talatin da biyar. "Ko ina ne Babaldu kuma? Ko har zai iya isowa kafin hukumar makaranta ta rufe shigowa?" Tabe baki ta yi tana ji a ranta to ina ma ruwanta? Amma wani sashi na zuciyarta na fada mata saboda Jawad ne, ina mama ba wadda ya zo mini? Ya katse mata tunani, "Baban Khalifa ne ba lafiya yana asibiti ka ga ai bai kamata na yi maganar mu taho tare da wani cikinsu ba." "Me ya same shi?" Ya tambaye ta cike da nuna damuwa. "Malaria yake ta yi har ta kada shi." "Muma Mami ita ake ta yi anan, Allah ya sauwa'ke ya bashi lafiya, to yanzun a tasha kika sauka?" Ta girgiza kai tana cewa, "Shatar mota muka dauko ni da iyalan gidan Ma'aji. Ka ci abincin sai mu je ku gaisa, suna can gefen mata." Bayan La'asar ba da jimawa ba, ya iso cikin makarantar sanye yake cikin tsadadden yadi fari 'kal! 'Kafar shi dauke da takalmi cover ba'ki, kansa cike da gashi, ya dora hular zanna-bukar wadda ba ta rufe gashin ba, 'kamshin turaren Versace ke tashi a jikinsa. A hankali yake tafiya cikin nutsuwa, matsakaicin jiki ne dashi, amma dogo ne yanayinsa daya da tauraron wasan kwaikwaiyon nan Yakubu Muhd, ba yadda za ka yi ka kalle shi ka ce shi ya haifi Jawad, sai dan tsananin kamar da Jawad ke yi da shi. Tun kafin ya'karaso Jawad ya hango shi, don haka ya kwasa da gudu ya nufe shi. Ga mamakin Sa'adah, sai ta ga ya 'daga Jawad cak ya yi juyi da shi tamkar yadda yake masa yana yaro. Ya dire shi, ya ru'ko shi ta gefen shi suka doso ta, wadda duk ilahirin mutanen dake wajen sai da suka bi su da ido suna sha'awar Jawad da Babansa. Kujera ya samo masa ya zauna daga gefe, amma ba wani tazara da inda Sa'ada ke zaune, ta juya musu baya. Hira suke cike da doki. "Amma anya Jawad kana karatu kuwa? Ina *C.A* Result dinka?" Ya zura hannu a aljihun wandon shi ya zaro takarda ya mika masa ya karba ya bude yana dubawa, fara'arsa na 'kara fadada, ya ninke ya kalli dan nasa ya ce, "That is my boy weldone! Ka ci gaba da dagewa." "Ni da zan zama direban jirgin sama, ai dole sai na yi karatu Malam, ko ka manta?" "Murmushi kawai Malam din ya yi yana satar kallon gefen da Sa'adah ke zaune kamar ko yaushe ta ci kwalliya ta burgewa cikin tsadadden leshi doguwar riga(bubu), hannayen ta sun ci jan lalle da zobunan Dubai Gold, 'kamshinta na dindin na turaran Escada sentiment, turare na mussaman mai sau'kar da nutsuwa ga duk wadda yake shakar shi, sai kai wa hancinsa ziyara yake yi. Ta sake zamowa yar yarinya, ta fi kama da 'yan shekaru ashirin da biyar ba wadda ta ba wa talatin baya ba. Jawad ya mi'ke yana cewa, "Malam Ina zuwa.'' Kai kawai ya kada masa, kai tsaye uwarsa ya nufa, gabanta ya tsugunna ya ru'ko dukkan hannayenta, "Mami ki zo ku gaisa da Malam mana" Kai ta girgiza masa alamun ba za ta ba. "Haba Mami gaisuwa kawai?" Kan ta sake girgizawa a karo na biyu, tana ci gaba da latsa wayarta a cikin manhajar WhatsApp inda abokan tafiyarta suka ce mata ya kamata su ta fi haka nan, kar su yi dare. dan haka ta fara tattare warmers din da ta zo da su, tare da mi'ka masa ledojin siyayyar da ta kawo masa, tana sake jaddada masa ya kula da karatu ya kuma kula da ibada, muryarsa na rawa alamun zai yi kuka ya ce mata, "Ba fa ki gai da Malam ba". A dan tunzure ta ce "Dole ne?" Ganin kwalla a idonsa sai jikinta ya yi sanyi ta dauki handbag din ta tare da basket mai dauke da kulolin ta ce "mu je to." Karbar basket din ya yi suka nufi Malam din da tazarar su bai fi taku biyar ba, don haka a kan kunnen shi duk yake jin tattaunawarsu. Ba ta isa daf da shi kamar yadda Jawad ya yi ba, ta tsaya daga dan nesa ta ce, "Ina yini?" ji ya yi kamar ba zai amsa ba tunda a wulakance ta yi gaisuwar, Irin gaisuwar je ka na yi ka, amma ganin Jawad ya zuba musu ido, sai ya amsa har ya na tambayar Inna, wanda ta ji shi, amma sai ta yi kamar ba da ita yake ba. Hannu ta mikawa Jawad akan ya ba ta basket din, no'ke kafada ya yi tare da cewa! "Mami, Malam fa Kano zai wuce, don Allah ki bari ku wuce tare." Wani malolon ba'kin ciki ya sa ke turnuketa, bayan ya tilasta ta, ta gaishe shi, ya kuma sake baro wata magana. Ba ta ce masa komai ba ta fincike basket din tana cewa, "Na gode ba sai ka kara gani na zo ba bare ka yi mini wannan iya shegen!" Ta juya ta fara tafiyarta mai cike da nutsuwa, da sauri Jawad ya bi bayanta, yana cewa, "Haba mana Mami kar mu yi haka da ke!" Kawai sai ta saki basket din hannunta da jakarta ta riko shi ta ringa zuba masa rankwashi tare da dundu, a sukwane Uban ya taso ya karbe shi yana jin takaicin ta na sake kama shi, wai a makaranta ma cikin jama'a ba za ta fasa halinta ba? Sa'arsa daya ma, wajen ba mutane kusan duk an watse sai tsirarru. Ta sunkuya ta debi kayanta ta tafi tana huci, ganin haka Jawad ya fincike daga hannunsa ya bi ta yana fadin,"Ina zuwa Malam!" Da gudu ya cim mata ta baya ya rungeme ta yana fadin, "Am sorry Mami, very sorry!" "Ai ni kuma ba ruwana da kai Jawad, tun da dai kai ba ka jin magana, na hana ka wannan manyancen naka, na hana ka shiga abin da bai shafe ka ba, amma ka 'ki, to ka je ka yi ta yi." Ya marairaice yana ba ta ha'kuri har dai ya samu ta ha'kura ya ga murmushinta. Malam yana zaune yana kallon su har suka ba ce ma ganinsa, a ransa yana mugun tausaya wa Jawad, tun da shi burinsa a ce Mamansa na tare da su, wadda faruwar hakan sai ikon Allah. Yana zaune, ya dawo ya tarar da shi yana ta tunani, "Ni ma ai zuwa zan yi na tafi. Mu je mota ka kwaso kayanka." Daidai lokacin wayarsa ta dauki ruri, yana dubawa yaga matarsa ce Farida ya amsa, tambayar Jawad ta yi, wayar ya mi'ka ma yaron tare da cewa, "Karbi!" Ba wani karsashi ya karbi wayar har ita ma ta ji babu dadi tana tambayar shi ko lafiya ya ce mata, "Lafiya lau!" Bana son Malam ya tafi ya tafi nee, sannan baku zo ba ke da Hajiyan Bichi". ta shiga bashi hakuri cike da murna ganin ya fara dawo mata tamkar farkon zamansu. Suna tafe yana masa nasiha tare da nuna masa ba ayina uwa ba a yin musu da ita, dole a bi ta yadda take so, sannan ya daina shiga matsalar da ba tashi ba, hawaye yake gogewa tare da cewa, "Ni dai Malam ka dawo da ita gidanmu ni ma in dinga ganin Mamana a gidanmu, kamar yadda nake ganin na friends dina, kowa Mamansa da Babansa tare suke zuwa masa amma banda ni!" Ya 'karasa cikin kuka sosai, janyo shi jikinsa ya yi yana dan bubbuga bayansa alamun rarrashi yana cewa "Ina ce ni ma tare da Antinka nake zuwa maka?" "Amma ai ba da Mamana kuke zuwa ba!" "To ka kwantar da hankalinka, ka dinga mana adddu'a sai ka ga very soon ta dawo har ma ka zama Yaya Jawad kana so?" Ya daga kansa tare da sa hannu yana goge hawayen da ya'ki tsayawa. "To in dai kana son haka, ka daina damuwa ka kuma daina yiwa Mami maganar bare ta dake ka, kawai addu'a za ka na yi, ni kuma ka dinga tuna mini, wataran sai dai ka dawo hutu ka ganta a gidanmu." "Malam da gaske?" ya tambaya cike da zumudi. "E Mana indai ka daina kuka, ka daina damuwa, ka daina damunta, kana addu'a to ina tabbatar maka ba abin da ya fi addu'a juya lamura!" Murmushi ya shiga yi yana goge hawaye da handkerchief din hannunsa yana 'fadin, "Ai ko Malam ban san murnar da zan yi ba,, kuma har da kai zan 'dauka a jirgin nawa". Dariya Mk ya yi tare da cewa "Ai kuwa dai nima naji dadi tunda albakacin Mami zan shiga jirgin Jawad" Kunya ta kama yaron yace "Ai dan ita bata taba shiga bane" Ya sake cewa, "Malam ka gai da Hajiya, kuma ina zuba idon zuwanta, tunda ba ta zo yau ba, ina bin ta bashi!" Alkalamin Surayya Dahiru ✍️ [5/11, 17:15] ~fatieshak🌹: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *Tukuici ga* *FADILA LAMIDO* *BINTA UMAR ABBALE* *ZAINAB MAZAWAJE* *Nagode da Shawarwarinku da 'karfafa guiwa, Allah Ya saka muku da alheri, Ya 'kara daukaka.* *GODIYA GA MAKARANTA* *Na gode da yadda kuka 'karbin wannan labarin, ha'kika jiya na ga ruwan masoya, ban yi zaton a 'kankanin lokaci littafin zai 'karade duniyar karatu haka ba, na gode muku sosai, in sha Allah ba za ku yi NADAMAR bibiyar wannan labarin ba!Heart U all* 3-4 A sanyaye ya fito wa da Jawad kayayyakin provisions din da ya kawo mishi, tamkar wanda zai yi rabin shekara bai je gida ba, yana sake jaddada mishi ya daina damuwa ya kuma ci gaba da karatunshi. Ya shiga mota Jawad na 'daga mishi hannu har ya fice, bai yi nisa sosai ba don kuwa bai gama barin garin Kiyawa ba, ya hango su Sa'adah da wasu matan a waje, gefe kuma an bude motar bakanike sai tabe-tabe yake, ga dukkan alamu motar ce ta lalace musu, kamar ya wuce sai kuma ya kasa. Don haka sai ya tsaya a gabansu, bai fito ba, sai ya lalubo lambar da Jawad ya kira shi da ita dazu, ya san tabbas layinta ne duk kuwa da ba ainihin layin ta ba ne daya santa da shi. Ya danna alamar kira, yana hango ta tana ta kici-kici da jakarta wurin lalubo wayar, amma abin mamaki ya ga ta fito da wayar amma ba ta dauka ba har ta katse, mamaki ya kama shi wai yaushe Sa'adah ta ko yi jarumta akan lamarinsa ne? Ya yi jim yana tunanin rabon da Sa'adah ta shiga harkarsa, ba shakka ba lokaci ne Mai tsayi, ba ta sake neman shi ba, ba ta sake duba dukkan lamarin sa ba, ta yi fatali da shi da dukkan soyayyarshi, abin da ya dade yana mamakinsa. bai daddaraba, ya sake 'kira tana gab da tsinkewa ta daga ba ta yi magana ba, amma dai ta kara a kunnen ta, sanin halinta da ya yi na ba za ta fara magana ba, yasa shi cewa, "Ke na gani a titi a na muku gyaran mota?". Cikin rashin nuna damuwa ta ce "A a ba ni ba ce." Bai yi mamakin amsarta ba ya ce. "Amma ba ke ce nake hangowa a tsaye kina amsa wayar nan daidai jikin Alheri bread🍞 ba?" Shiru ta masa sai ji ya yi ta ma ka'tse wayar gaba'daya. Shiru ya yi ranshi na suya ya na sake jaddada halayyarta a jininta ne ba za ta sauya ba. Har ya ta da motar da niyyar barin wajen ta je ta 'karata, sai kuma ya tuna uwar Jawad ce tilon 'dansa, ya tabbatar da tare yake da Jawad din, ba zai yarda su tafi su bar Maminshi a bayan gari jejin Allah ba, ga yamma ta yi likis sosai, sanyin da ake 'dan busawa ya sake taimaka wa garin ya yi dan duhu, don haka sai ya fito bayan ya kulle motar ya nufe su. Yana zuwa ya ga har da Zainab Ma'aji da wasu mata biyu da bai gane su ba. Ita ko Zainab tana ganin shi ta saki fuska."Lah! Uncle kai ne ashe." Ta gaishe shi irin gaisuwar da dalibi ke yi idan ya ga malamin da ya koyar da shi a baya. Shi ma ya amsa da jin dadin girmama shi da Zainab ke yi tun fil azal. Hannu ya mi'ka ya dauki yaronta Walid ya masa wasa sannan ya ce, "Motar taku lalacewa ta yi ne?". "E wallahi ga mu nan dai ana ta faman gyara". "To ku zo mana mu wuce tun da ba tabbacin za ta gyaru yanzu". Kallo ta kai ga Sa'adah da ta koma baya ta yi kamar ba ta gan shi ba, ta kuma cika ta yi fam kamar kububuwa. Zainab ta ce "To uncle bari na yi wa abokan tafiyar tamu magana." "Okay" Kawai ya ce, yana ci gaba da wasa da Walid dake ta bingila mishi dariya tamkar ya san shi. Bayani Zainab ta musu kamar yadda ya bu'kata, dukkan su sun amince, su bi shi, amma ban da Sa'ada. Don haka Zainab da 'yan uwanta su ma suka janye tun da dai ai sun san saboda ita ya tsaya har ya nemi ya taimake su, to kuwa ta ya ya za su ce za su bi shi alhalin ita ta yi rantsuwar gara ta kwana a nan da ta shiga motarsa! A matu'kar kunyace Zainab take ba shi ha'kuri tare da ba shi uzirin direban ba zai ji dadi ba, ya san sarai Sa'ada ce ta'ki amincewa, amma sai ya ce ai zan sallame shi ku zo mu tafi kawai. Nan ma sai ta sake dora wa 'yan uwanta laifi akan yayarsu tace ba zasu sab'awa direban al'kawari ba. Ya jinjina hankali da Zainab ke da shi, duk da ya san 'kawar ta ce ta'ki amincewa, amma ba ta fadi hakan ba, sai kariya take ta bayarwa, ina ma tun farko Sa'ada ita ta ri'ka a matsayin 'kawa, ba bara gurbi irin su Halima da Safina ba? Wanda 'kawacenta da su bai amfane ta da komi ba sai muguwar asara da nadama, tunda sun mata ingiza mai kantu ta yarda har ta tsinke igiyar aurenta, a yanzu kuma sun bar ta sun koma suna zunden ta. Don haka sai yace "To shi kenan ba damuwa ya matsa ga bakaniken dake ta iyakar kokarin shi don ya ga motar ta tashi. magana suke yi da direba, cikin ikon Allah ba a wani dauki lokaci sosai ba motar ta gyaru, amma har an yi sallar Maghriba, dan haka malam da direban suka yi jam'i suka yi sallarsu, yayin da matan suka shiga wani kewaye su ka yi ta su. Bai yarda ya tafi ba sai da ya ga tashin su sannan ya taka ya isa inda motarsa take shi ma ya bi su a baya. A cikin motar kuwa yayyen Zainab sai caccakar Sa'ada suke da rashin kirkinta, "A haka kike son komawa gidan nasa? Ba kya girmama shi, a gaban kowa za ki iya keta shi?" Cikin turo baki ta ce "Ni fa Anty da ne na yi haukan banza na son sai ya mayar da ni, yanzu kuwa ko ni da shi muka rage ba na sonsa ba zan koma ba" Cikin fushi ita ma Anty Asiya wadda ita Zainab ke bi, kuma da ita duk a ka yi gwagwarmayar su Sa'adah, ta ce, "Ai shima ba son naki yake ba, shashasha da ba ta san me ya kamata ba." Dattijon dake jan motar ya ce, "Um'um fa! Ba'a shiga lamarin mace da namiji, ai koni da yau na fara ganin su na hango soyayyarta mai yawa a idonsa da gangar jikinsa, ita ma kuma duk wannan kumburin da take yi da fiffi'ka duk soyayyar ce, da alama dai kishi ne ke dawainiya da ita a kansa, dan na ga fishi take mai tsanani da shi!" Dukkan motar a kasa dariya a na cewa Baba ashe duk ka gano su? Yace , "Haba yara mu da muka ga jiya muka yau, ku duba fa duk iya shegen da ta yi akan ba za ku bi shi ba, bai fa iya tafiya ba har sai da ya ga tashinmu, wannan kadai ya isa kowa yasa lunzami a bakinshi akan lamarinsu, suna da yara ne?" Zainab ce ta ce "Yaro ne daya har ya fara girma, shi suka jewa visiting" Ya ce, "Ai shike nan magana ta 'kare, ko kowa bai musu sulhu ba, yaron zai zama tsanin afuwa a tsakaninsu, mu yi musu addu'ar fatan alheri, amma soyayya akwai ta" Aka sake sa dariya ban da Sa'ada da ta yi kicin-kicin da fuska. Tsohon ya sake cewa, "Ina cewa da za mu zo ita ce a gaban motar nan haka da za mu dawo,har muka zo inda motar ta lalace ita ce a gaban?amma ina ganinsu da za ta shiga gaba ya galla mata harara sai kawai naga ta shige baya." Gabadaya aka sake dariya har da Sa'ada wadda ita ta karfin halin wannan bawan Allah ne, ita ba ta ga harara ba, ta san kuma tabbas bai yi 'karya ba, kaifin idon Malam ne yasa ta kasa shiga gaban motar wani akan idonsa, sai ta bige da cewa "Lallai Baba ba komi na gode" da haka ta sace ta daina fishi. Shi ko Malam yana tafe yana ayyana abubuwa masu girma game da lamarin ta, komai nata burgeshi yake, bai ta ba ganin halittar da ke daukan hankalinsa irin surar ta ba, kawai wasu daga cikin halayyarta ke 'dimauta tunaninshi su hana shi zaman lafiya amma duk sanda zai dora idonshi a kanta sai ya ji bai ganin komai da kowa sai ita. Har yau har gobe yana son ta, amma ta riga ta shayar da shi bakin cikin da zaman aure zai yi wuya tare da su. Har suka iso Kano tunaninta yake idan ya tuna *happy moments* dinsu yayi murmushi, idan ya tuna *though times* dinsu sai ya ja tsaki ko ya furta ya *Salam* ko *SubhanAllah.* Ba su rabu ba sai da suka zo Gandu ya yi wa direbansu fitila ya wuce, a nan ma sai da Baba ya tsokaneta da cewa "To Sa'adatu wannan fitilar fa da ya yi bata kowa bace, taki ce!" Suka hada baki wurin fadin, "Ai kuwa dai Baba!" suna kuma dariya. ```Alkalamin SURAYYA DAHIRU``` ✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ` https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GABA'DAYA GA* *SADIQ ABUBAKAR* 5-6 Har 'kofar gidan yayarta Sumayya suka kaita dake kan titin Kwankwaso Gandun Albasa, sannan suka juya, Baba direba, nata jaddada mata ta daina saurin fushi mabudin fitina ne, ta yi godiya, tana cewa su Zainab sai nan da kwana uku za ta dawo unguwar tasu lokacin innarta ta dawo daga tafiyar da ta yi. Da sallamarta ta isa cikin katafaren falon Sumayya, ba kowa sai TV da take ta babatu hadi da dan dirin AC da ke tashi a hankali, ga 'kamshin *Air Freshner* dake tashi sannu a hankali, take ta ji duk gajiyar da ta kwaso ta taso mata gabadaya. Dan haka sai kawai ta zube a Kan doguwar kujera ta yi kwanciyar ta ba ta jima da kwanciyar ba, barci mai nauyi ya yi gaba da ita. Sumayya fitowa tayi daga bangaren maigidan, da a yammacin yau aka sallamosu daga asibiti, ta ganta tana ta barci. Murmushi ta yi tare da cewa, "Oh a 'yar wannan tafiyar ne kika gaji har haka?" Ta gyara mata rigarta da ta 'dage, ta shige kicin don hada tea. Hayaniyar yaran gidan ne da suka taso da ga lesson wadda takanas aka dauki malamin da zai zo har gida yana musu bita, yasa ta tashi musamman da 'karamar cikinsu ta fada kanta tana fadin, "Mami yaushe kika dawo?" "Khairat kin san yadda na gaji!" Ta 'daga ta, tana cewa "Ina Yaya Jawad?" "Ya na lafiya, ya ce duk yana gaishe ku" Ta sake cewa, "Mami bai ba da komai ki bani ba?" Daga Sumayya har Sa'adah dariya suka yi yadda Khairat din ta yi. Jakarta ta bude ta dauko wani dan abu a nade da wrapping paper ta ce, "ga shi nan ni kaina sai da ya ro'ke ni kar na bude tunda ban san ma ya saba, ya dai ce mini zan ga abin Khairat don Allah kar na bude." Yayansu Ayman wanda shi ma yana da yayu Abba da Khalifa suna Egypt suna karatu, ta nufa tana cewa, "Bude mini yaya!" Nan da nan ko ya hau warwarewa sai ga Lush Cookies Biscuit har guda biyar sai Teddy Bear 🧸 'yar 'karama mai kyau da yar 'karamar takarda an rubuta little Khairat. Da murna soasai tace "Yaushe to zai dawo Mami?" Anis ne ya ce, "Sai nan da 6 weeks." Ta galla mishi harara, "Na tambaye ka ne?" Da yake sa'kuwar shi ce ba su cika jituwa ba. Ta juya ga yayansu,"Yaya Ayman kwana nawa ne a 6 weeks?" Kai tsaye ya ce mata, "42 days." Da sauri ta ce, "Gobe zan samo stones 42, kullum na dinga minus, ranar da suka 'kare to ranar zai dawo saboda na soya mishi wainar fulawa." Dukkan su dariya ta ba su, amma Sa'adah mamakin wayonta take, tana kallon Anis tana tuna daidai lokacin haihuwar sa ta shiga matsaloli masu yawa da Malam. Shekarunta biyar a duniya amma wayonta da azancinta ya zarce na 'yan shekaru bakwai. mutumiyar Jawad ce sosai ta fi shiri da shi fiye da yayyenta. Shi ma kuma haka yake ji da ita musamman da shi ba shi da 'kani ko 'kanwa sai ya tattara dukkan 'kaunar da yaya yake yi wa 'kanwarshi a kanta. *Bayan kwanaki uku* " Iya Iya dai, na san tabbas daga shigarki ba za ki ce mini wai har kin yi barci mai nauyin da za ki kasa jin kuwwar da wayar ke faman yi ba." Da kanta ta tashi ta leka, ganinta ta yi tana kwance ta 'kudundune ta rufe fuskarta da dukkan hannayenta, "Kin san Allah? Idan kika bari na shigo ba ki tashi ba sai na ci mutuncinki, ai na san sarai kina ji na" Tashin ta yi tana murtsika idanuwanta "Ni fa Inna barci nake yi!" Kafin Innar ta yi magana wayar ta sake daukan ruri a karo na uku dan haka ta kafeta da idanuwa, akan dole Sa'adah ta sa hannu ta amsa wayar. Sannan Inna ta juya ta fita tana fadin, "Shashasha haka ki ke tunanin za mu bar ki ki yi ta zama? Ai tunda kin gama karatun to kuwa wallahi sai dai ki fito da miji cikin jerin wadanda suke son ki dan ba zan yarda da wannan zaman ba. Haka kawai kowa ya zo ki ce bai yi miki ba, kowa bai miki ba, wanda ya yi mikin kuma bai shirya sake zama dake ba. Amma kin kasa gane gaskiya, kin kasa gane ita mace lokacin ta 'kan'kani ne! Bari Baffan naku ya dawo na gaji da halinki!" Sa'adah kuwa da alatilas ta dauki wayar Alh. Mamman wanda dan majalisar tarayya ne mai ci a yanzu, ya so ta tun tana budurwa, a lokacin yana dan majalisar dokoki na jaha, shi ne har yau yake ta bibiya, tun lokacin budurcinta ta san komai game da shi. Mutum ne mai yawan kyauta da kyautatawa, ta tabbatar da hakan, ita kanta ta san ya mata 'barin kudi. Tun a lokacin yana da mata biyu da yara takwas wanda wannan dalilin yana cikin dalilin da ya sa ba tayi marmarin ma auren shi ba, Illa dan ta sami rabonta kawai, to yanzu kuma amaryar ce ta rasu shekaru biyu da suka wuce a wurin haihuwa, shi ne yake ta bin kanta ta maye mishi gurbinta, tunda ya riga ya saba da mace biyu ga kuma tsananin 'kaunarta da yake. A nata bangaren kuwa ba ta fatan 'kaddara ta 'kaddaro ya zamo miji a gareta shi yasa tun watanni shida da suka shude ta yakice shi a dukkan lamarinta, tunda dai kam ai ta riga da samun rabonta🤔. Ta yi amfani da alfarmar shi ta cimma burinta, da kuma mallakar kayan 'kawa na alfarma, idan ko hakane dole ta yi gaggawan wullar da shi tun kafin reshe ya juye da mujiya. Uzirin tana aiki ta ba shi akan za ta 'kira shi anjima, murmushi ya yi ya ce, "Ranar da na ga 'kiran ki a wayata Sa'adah tabbas rana ce mai muhimmanci a raina!" Ya'ke ta yi tare da fadin, "Aiko idan hakane zan baka mamaki, ka saurare ni zuwa anjima".. Ba ta jira cewar shi ba ta daste kiran, ta yi wulli da wayar ta na neman tsari da 'kaddarar da za ta hada su zaman aure da wannan mai tulelen ciki. Kanta ta ji ya cushe musamman yadda Inna ta fara matsa mata a cikin kwanakin nan akan lalle sai ta tsayar da miji cikin manemanta, har zuwa yanzu ba ta jin akwai wani da za ta yi zaman aure da shi kamar Mukhtar Kabir Bichi. Amma ko shi da ta tabbatar da abu 'daya, ta ha'kura da shi ba dan ba ta so ba sai dan ha'kurin shi yafi. Ta kuma gamsu ita ke da laifi da kaso mai yawa na 'kaddarar rabuwar su da Abban Jawad, ta tabbatar ya so ta, son da ba algus amma *HALIN YAU* da rudin 'kawaye ya jefa ta cikin kogin nadama. Irin wanda ake cewa tsalle daya mai jefa mutum rijiya, ya yi dubu bai fito ba! A hankali ta koma ta kwanta tana tariyo rayuwar ta, ta baya, tun kafin haduwarta da Mk Bichi. haduwarsu, aurensu, rabuwarsu, har zuwa yau da take jin duniyar ta yi mata daurin goro. Ashe 'dan Adam baya rabuwa da matsala? Ashe duk matsalar da mace za ta fuskanta indai tana zaune a dakin aurenta matsalar da sauki, akan matsalar rashin auren, da rabuwa da 'ya'yanta? Wanne tabbas mace keda shi a wannan halin na yau, za ta sake samun damar aure a karo na biyu? Idan ta samu din ma ba za ta kauce wa matsalar *HALIN YAU* ba, ko kuma ta tabbata tana aure-aure. Ta nisa ta tuna wata maganar gyara kayanka, da fasihiyar marubuciya, Fadila lamido inda take fadin, *"Uwa da sadaukarwa aka san ta, domin rayuwarta da ta 'ya'yanta, ta inganta.*' To shin ita me ta yi ne dan ganin ta SADAUKAR da komi dan inganta kanta da tilo 'danta? Tabbas ba ta yi ko mai ba, sai rusa farincikin kanta dana 'danta Jawad! Ta yi dalilin da yake rayuwa ba a tsakanin uwa da uba ba, hawaye ya gangaro mata na takaici da kaico iri iri. Ta tuna wani darensu a Abuja, ya dinga rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta su zauna lafiya, komai take so zai dinga yi mata a hankali, a lokacin ita kuma tana ganin tamkar idan ba ita, ba zai iya rayuwa ba, saboda yadda yake tsananin sonta da kulafacin son zama da ita, duk yadda take ganin aibun su Halima, a yanzu da take fuskantar NADAMAR biyewa Halayyar yau, ta fi ganin aibun kanta da kanta, tabbas zuciyarta da tunanin ta basu mata adalci ba, domin tunda ta taso take jin ana azanci da cewa idan mafa'din magana wawane majiyinta ba zai zama wawa ba, amma ita sai ta zama mahaukaciya ma. Zuciyarta ta sake ba'ki wani irin numfarfashi take yi tamkar mai fama da cutar Asma, hakanan hawayen ba'kin ciki ya kwace mata tamkar mai yin Takaba. ```Alkalamin SURAYYA DAHIRU ```✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GA* *SADIQ ABUBAKAR*. 7-8 HAWAYEN nadama marar amfani ya ci gaba da zuba da ga kyawawan idanuwanta ba 'ka'kkautawa, a hankali ta koma ta kwanta, zuciya na suya, rabon da ta shiga irin wannan yanayin tun shekarun baya da suka shude. Shekarun da suka fi kowanne tsauri da tsanani a rayuwarta, a lokacin da ta dinga yun'kurin gyara kuskurenta amma MK bai ba ta wannan damar ba. Duk da ta san ita ke da kaso mai yawa na lalacewar aurensu, tunda ba irin 'kabali da ba'adin da bai mata ba, ba kalar rarrashin da bai yi mata ba. amma tasa hannu har da 'kafafu ta tankwabar da dukkan ha'kurinsa, ta tabbatar akan dole ya rabu da ita, ita kanta ta shaida hakan. Tissue tasa ta goge hawayen da ya 'ki yankewa, take kuma zuciyarta ta yi tsalle ta hasko mata irin kyaun da ya yi cikin tufafin da take matu'kar son ganin sa a ciki wato farin kaya, sam ba ya girma, ba wanda zai kalle shi yace ya kai shekaru arba'in har da biyu. Dan kuwa idan ya ce bai yi auren fari ba, ba wanda zai 'karyata shi, Ubangiji ya mishi kyakkawan jiki matu'ka gaya. Murmushi mai hade da hawaye take yi lokaci guda, saboda yadda ta ji a ranta da zuciyarta domin ita ya yi shigar tare da fatan ko Allah zai sa su hadu, a hankali ta fara jin sau'kin 'kullewar da 'kirjinta ya yi yana raguwa, a dalilin tabbacin da ta sake samu na har yau shi ma yana son ta, dama idan akwai abin data yarda dashi to son da ya ke mata ne. Amma kuma me yasa bai yarda da ita ba? Nan da nan 'kuncin 'kirjinta da ya fara warwarewa ya dawo ya 'kulle fiye da farko idan akwai abin da yake 'daga mata hankali bai wuce rashin amincin daya jefe ta da shi ba, alhalin shine mutum na farko daya kamata ya shede ta, ta kuma zama amintacciya a idonsa, kuka ya 'kwace mata sosai, da sauri tasa hannu ta rufe bakinta dan kar Inna ta jiyo. Haka ta danna kanta a pillow ta yi kuka mai nuna tsantsar bakin ciki da takaicin da mai yinsa ke ciki, duk yadda zuciyarta ta yi zafi, kanta take 'kalubalanta, ta san ko mai Malam ya yi ko ya ce mata, ba shakka ita ce sila, ita ta janyo. Istigifari ta dinga ambato dan ta sami sau'kin zuciyarta, tsawon lokaci kafin ta ji ta fara samun nutsuwa sai ajiyar zuciya take saukewa. Wayarta ta dauko tana nazarin shin a littafi zata rubuta ne ko a waya? A littafin tafi gamusuwa da ta rubuta tarihin rayuwarta dan ya zama izna ga sauran mata. Idan ta sami halin buga shi, za ta buga dan ya zama gargadi ga duk wacce son zuciya da *HALIN YAU* ke dawainiya da ita. Mi'kewa ta yi tana laluben littafi da biro a cikin jakar karatunta, amma cikin rashin sa'a ba ta samu ba, kowanne ta yi rubutu mai yawa a ciki. Tsaki ta ja, ta rike 'kugu kafin ta yi wani yun'kurin abin yi, ta ji sallamar almajirinsu yana fadin na dawo. Da sauri ta iso ga katifarta, ta 'daga pillow ta dauki gudar dari biyar ta fita ta ba shi, ya siyo mata littafi na rubutu mai shafi tamanin (80 leaves). Daga nan ba ta dawo dakin ba, buta ta dauka dan tayi alwalar la'asar tunda yan mintina ka'dan ne su ka rage. ***** Kwance ya ke kan sofa a dakin barcinsa, ya lumshe ido tamkar mai barci amma a zahiri ba barcin yake yi ba. Tun ranar da ya ga Sa'adah nutsuwa ta masa tutsu duk yadda ya kai ga daurewa har abin ya bayyana a fuskarsa da gangar jikinsa gaba'daya. Wata irin nutsuwa ya gani a tare da ita, wadda bai taba gani a tare da ita ba, gaba'daya ta canja, ilimi da hankali sun matu'kar ratsa ta. ba kamar lokacin da suka rayu tare ba. ko dan ya dauki lokaci mai yawa bai ganta ba ne? Farida ce ta shiga dakin, kusa da 'kafafuwansa ta zauna tana mai jan yatsun 'kafarshi, a hankali cikin sanyin murya da halittarta ce, ta 'kira shi "Abban Jawad!" Bai amsa ba, amma ya bude idanuwanshi da suka yi ja alamun ko barci bai ishe su ba ko kuma ana cikin damuwa. Ta sake nazartar shi a hankali ta ce, "Tunda ka dawo na kasa gane maka, na san akwai abin da ke damun ka amma ka'ki fada mini, ni kuma na san matsalar! Idan na yi rantsuwa cewar Sa'adah ke da ala'ka da wannan damuwar da kake ciki ba zan yi kaffara ba, mai yasa ba za ka yafe mata ba, mai yasa ba zaka daina wahalar da zukatanku ba, me yasa kake gudun gaskiya da gangan? Ni dai na san ', kullaci, da rashin yafiya ba halayyarka ba ce! Ban san me yasa ka aro ka yafa akan Sa'adah ba! yau shekaru kusan bakwai kana ta wahalar da zukatanku, sai yaushe za ka hutar da ku? ko makaho ya ji halin da kake ciki yasan kana sonta, balle ni da nake tare da kai, na ro'ke ka ka gaggauta gyara tsakaninku, tun kawaicina bai 'kare ba, tun ban fara kishi da ita kamar yadda take yi dani ba, na tabbatar idan hakan ta faru ba zaka samu nutsuwa ba!" Sai a lokacin ya bu'de baki murya ba amo ya ce, "Kece kike ganin haka duk yadda kike tunanin lamarin ba haka ba ne, kinsan kuma ban taba 'karyar ba zan dawo da ita ba, saboda Ubangiji ne ke jujjuya lamura, idan ya 'kaddara sake zama a tsakaninmu zan dawo da ita." "Zuwa yaushe za ka dawo da ita din? Ka fi shekaru uku kana wannan maganar, ba irin girman kanta da ba ta ajiye ta baka ha'kuri ba, ni kaina na sha ganin ta tsugunne a gabanka. haba Abban Jawad! Wanne irin abu ne haka da ba zai wuce ba?" Ta fada muryar ta na karyewa. Shi kansa bai san mai yasa ya shiga ru'du a dalilin halin ko in kular da Sa'adah ta mishi ba, da kuma yadda ta daki 'dansa a gabansa, alhalin kuma tun tuni ta san baya son ta masa haka a gabansa. Amma saboda da ta nuna masa ba shi da sauran gurbi a zuciyarta, ba shi da mutunci a idonta ta rufe Jawad da duka akan idonsa. Sannan a gaban jama'a ya tsaya dan ya taimake su amma ta wula'kanta shi, ta nuna masa iyakarsa, idan ya tuna wadannan abubuwan sai ya ji har zazzabi ne ke neman kama shi, hakan na nufin Sa'adah ta daina son sa, ta ha'kura da shi ke nan? Zuciyarsa na bugawa idan ta hasaso masa cewar ta samu wanda take so, ko kuma za ta sabunta soyayyarta da Khalil Ibrahim wanda yake jin komai na iya faruwa da shi idan hakan ta faru. Ya nisa ya ce, "Ke fa duk yadda kike tunanin lamarin Sa'adah ya kerewa tunaninki, yanzu bata so na, ba ta da burin sake zama da ni" A yadda ya yi maganar ta san akwai abin da ya gani a tare da ita da ya jefa shi cikin wannan yanayin. Wata'kila ta gaji da bin kansa, ta tattara ta jefa shi a kwandon shara, kamar yadda ya mata, shine kuma dan son kai irin na namiji zai ji an masa rashin kyautatawa, su dai sun fi son mace ta yi ta bin su, suna jan ta a 'kasa. "A hankali cikin son 'karfafa masa guiwa ta ce, "To ina ruwanka da soyayyarta? Ina tabbatar maka son da kake mata ya isa ya ri'ke auranku, muhimmin da za ka damu da shi mutuncinka a idonta, balle ma nasan nan duniya ba namijin da take so sama da kai, ba kuma wanda zai zarce ka a gunta. Wata'kila ta gaji da yadda kake tamaula da ita ne, ko ba ta ci albarkacin so ba, taci albarkacin Jawad! ko ka san Jawad, komai zan yi masa ba zai gamsu ba, matu'kar ba uwarshi ya gani a tare da kai ba" Idonta ya dan ciko, ta dan tsahirta sannan ta ci gaba da magana, "nan gaba Jawad zai tattara dukkan tsana ya dora mini, zai ga saboda ni ka 'ki zama da uwarsa, kai ma kasan tunda muka dawo 'kasar nan ya canja, na ro'keka dear kar ka ruguza farinciki da kwanciyar hankalinka da na 'danka" Janyo ta jikinsa sosai ya yi, ya ri'ke hannunta ya kalleta sosai ya ce ,"Farida ke din mai kirki ce, mai ha'kuri ce, mai sanin ya kamata ce, kina sona kina son kwanciyar hankalina, ina yaba miki, ina kuma fatan Allah ya fi ni yabawa, Allah ya ba mu zuria dayyiba!" Hawayen da take ma'kalewa ya zubo a kan fuskarta ta ce, "Ni da ban da lafiya ne zan haihu?" Cikin kulawa mai yawa ya ce, "To menene ya gagari Ubangiji? Son da nake miki wallahi ko ban taba haihuwa ba, zan zauna dake a haka domin ke nake so ba wani abin da zan samu a gareki ba, sannan rashin haihuwarki kullum ke sa na ji son ki da tausayinki na sake cika mini dukkan zuciyata, ina son ki da ke da dukkan lalurarki Farida!" Sai kawai ta fada jikinsa tasa mishi kuka, shi kuma yana dan bubbuga bayanta, yana jin ina ma zai iya bude mata 'kirjinsa dan taga 'kololuwar matsayinta a zuciyarsa?. Ya tabbatar bata san yadda yake jin ta a Zuciyarsa ba ne. ```Alkalamin SURAYYA DAHIRU```✍🏼✍🏼 [5/14, 11:03] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·• _GAISUWAR GIRMA GA_ *HAJ HAFSAT SODANGI* _(MIJIN TACE)_ 9-10. Tsawon lokaci suna wannan halin har ya samu nasarar dawo mata da walwalarta, "To kawo mini abincin nan mu ci don nasan ke ma ba ki ci ba". Ta yun'kura tana cewa, "Ina zan iya ci alhalin mijina bai ci ba!" Kicin ta nufa ta hada komi a kan faranti ta kinkima ta yi dakin nashi kamar yadda ya ba ta umarni, Sai da ta shimfida ledar cin abinci sannan ta zuba musu abincin a faffadan plate, shinkafa da miyar kifi ne, sai hadin Salad, gefe kuma zobo ne wanda ta sarrafa da tsurar sugar da cocomber sai flavour. Ba ka jin komai sai karo tsakanin cokali da plate kasancewar shi ba ya magana idan yana cin abinci. Suna gamawa ta kwashe komai ta gyara wajen sannan ta hada masa ruwan wanka ya shiga. Ta fice zuwa nata dakin, ta fito falo sukayi kicibus da shi, ya fito cikin lallausan yadi mai kalar sararin samaniya,(Skye blue) bai dora hula ba, amma ya taje sumar nan da ta cika kan fam! Ya dora farin glass a idanuwanshi, sai tsadden kamshin turaren Versace ne ke tashi a jikinsa. Kugu ta rike ta zuba mishi ido tana murmushi ta ce, "Na san mijina gwanin iya wanka ne, amma irin wannan kwalliya haka da La'asariyar nan! Sai ina? ko wurin Iya Basiru za a?" Ya fashe da dariyar tuna baya, sai ya ce, "Kinsan fa har yau fadanta na nan lalle idan ta ji wannan sunan kin san 'yan kallo zaku kwasa." Ita ma cikin dariya sosai ta ce, "Ai na san yanzu ta girma da fada, ka san me?" Ya girgiza kanshi, "Ada idan mun hadu sai na faki idon mutane naga ba kowa, sai na ce mata Sa'ade ko na ce Iya Basiru, sai na ga ta fara sababi, kawai sai na sulale na bar ta a wajen." Ya sake sakin dariya "Ashe ke ce kike tsokanar ta duk mu hadu a ba ta rashin gaskiya?" "E to ai haushi nake a lokacin, ta dauke maka hankali, har sai da ta kwace mini kai!" Ya nuna ta da yatsa, "ke ko! kin san irin su Sa'adah suna dadewa kafin a gane cutar su da ake yi, saboda hayaniyarsu sai sun dade kafin a gane a fahimci gaskiyarsu. yau kwana biyu ban je gidan Hajiya ba can na nufa idan kuma za ki dauko mayafinki, Bismillah". Kai ta girgiza alamar a'a tare da cewa, "Na fi son na je na wuni, ka gaishe ta da kyau!" Ya fice ita kuma ta bi shi da addu'ar dawowa lafiya. Da sallama ya shiga gidan, a tsakar gidan ya same ta zaune kan tabarma tana jin radio, kusa da ita ya zauna. suka gaisa tana tambayar Farida, daga nan kuma tayi shiru da bakinta. "Hajiya wai har yau fishin rashin zuwanki wurin Jawad din ne? Ni ma fa ban ji da wuri ba, ina Bauchi ya yi mini waya daga can na zarce amma ki yi mini uziri, kiyi hakuri." "Ni abin da ya dame ni, ba a kai masa abinci da 'yar miya ba!" Dariya ya yi sannan ya ce, "Ai yanzu ba a barin su su tafi da shi hostel, iya wanda suka ci a wajen shike nan, saboda kwalara sannan kuma a can na tarar da uwarshi ta je masa da abincin". Shiru Hajiyar ta yi tana jin takaici rashin Sa'adah cikin ahalinta, ba karamar asara ba ce. Tunda ita kam a iya zamanta da yarinyar ba za ta ce ga ta'kamaiman laifinta ba, sai yan 'kananun kura-kurai da ko 'danka na cikinka wani lokacin zai yi maka. Duk artabun da ake yi tsakanin uwar miji da surukan zamani ita ba ta san shi a zamanin zaman Sa'adah ba, yarinyar ta iya zama da manya. Komin fa'da da rashin ha'kurinta, ita dai ba ta ganin su, tunda dai mafi yawa akan kishi take fadan. duk mace kuwa ba a raba ta da kishi, sai dai wata ta iya dannewa wata kuma nata mai zafi ne. Sannan abu mafi dadi a halayen Sa'adah yadda ta yarda ta isa da ita, duk yadda ta murde, da zarar tasa baki za ta ha'kura ta bar maganar. Amma ga shi nan, shi da ta haifa ta kasa sarrafa shi, akan komen yarinyar, shi yasa take jin kunyarta, take jin nauyin iyayenta, duk da aure rai ne da shi, Ubangiji idan ya 'karar da zama ba yadda za ayi. Ta kalle shi, "Kuma kun gaisa da ita?" Tausayin uwarsa ya tsirga mishi ya san babban burinta Sa'adah ta sake zama surukarta a karo na biyu, ya yi 'dan murmushi "Hajiya ai da ma muna gaisawa" Harara ta galla mishi tare da cewa, "Ina ce nan da ta zo duba Jawad akan idona ba ku gaisa ba?" "An yi haka Hajiya amma ai ba ni zan gaishe ta ba ko?" "Kai ne namiji, Kai ne zaka fara magana tunda gidanku ta zo, kuma uwar dan ka ce!" "To ni Hajiya ba uban 'dan nata ba ne?" Kwafa ta yi, "Wallahi ba ka ta ba bata mini rai na ji zafinka sosai ba sai akan Sa'adatu." Kai tsaye ya ce, "Na ba ki ha'kuri Hajiya! yanzu ma shi zan ba ki, ki yi ha'kuri ki yi mana adddu'a." "To tun yaushe nake adduar?" Niyya ce dai da ba ka yi ba!" Ya katse mata fadan nata ta hanyar cewa, "Da kyar fa Jawad ya sa ta gaishe ni, kuma na taho a hanya na ga motarsu ta lalace, wai ni da abin arziki, na tsaya na ce su zo mu taho amma yarinyar nan a gaban jama'a ta tsinka ni! Ko kallon tsiya ba ta mini ba, bare na arziki." Ya nisa sannan ya ci gaba da fadin, "Amma kullum sai ki yi ta dora mini laifi, ki yi ta ganin ni ne marar kirki, alhalin tsiyarta tafi ta tsohuwar mota. Inda tana son sake zama da ni ai lallaba ni za ta ci gaba da yi, tunda dai ta san ba na son rashin kunya." Tunda ya fara magana ta zuba masa ido tana nazarta shi, tsawon shekaru bakwai da rabuwarsu, yau ne ya bude baki yake magana mai tsayi a kanta. Ta kuma lura da sassauci da afuwa mai yawa akan lamuranta a yau, ta tuno farkon rabuwarsu da ta nuna iko irin na uwa, akan sai ya mayar da ita tilas, yasa mata kuka riris lamarin da yasa ta janye takunkumin dolen da ta mishi. Yana rufe baki ta ce, "To saboda Allah wanne irin ha'kuri ne bata ba ka ba? So kake ta tabbata tana bin ka kana walagigi da ita? kuma ko don ka nuna na isa da kai, ka ji abin da na ke fada maka, saboda rayuwar 'danku ta inganta, yau yaro ba abu mai dadi a wajensa irin ya bude ido ya gan shi a tsakanin uwa da uba. Amma ku iyayen yanzu ba ku cika duba wannan matsalar ba." Ajiyar zuciya ya saki, "To shike nan Hajiya In sha Allah zan je na yi istikara ba za ta gagara ba!" Nan da nan Hajiya ta hau murna har da hawaye take sharewa tana kuma fadin, "Na gode, Allah ya tabbatar da alheri, da ikon Allah akwai alheri tsakaninku. Duk ba'kin cikin da na kwashe shekarun nan a cikinsa, wannan maganar kadai ta sanyaya min zuciyata, Allah ya yi maka albarka." Ta mi'ka hannu ta dauko wayarta, "Kira mini Yayar ku". Ya karbi wayar yana cewa, "Me za ki ce mata?" "Na shaida mata wannan abin arz'kin mana, duk wannan bacin ran ai da ita muke yinsa!" Ya kalle ta, "Amma Hajiya na ce sai na yi istikara fa, idan kuma ban sami nutsuwa da abin ba, a zo a ce na yi baki biyu? Ni dai na ro'keki, ki yi shiru da bakinki, mu yi addu'a nan da kwana uku muga mai Ubangiji zai rinjayar mana a zuciya." Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Da ikon Allah ma alheri ne, jiya mun gaisa da Ahmad." Ta fada cikin jin dadi,"Ai ni tun ina Bauchi rabon da mu gaisa ya ce mini wai satin sama zai zo." Addu'a ta bi shi da ita kamar kullum, ya mi'ke, "Hajiya bari na tafi Magariba ta kawo kai" "To ka gaida Farida, ya jikin nata dai?" "Da sauki da na ce ta zo mu taho tare, ta ce yini ta ke so ta zo ta yi miki." "Ina zuba ido Allah Ya kawota lafiya." Ya amsa da "Amin!" Ya fice yana fadin, "Allah Ya tashe mu lafiya." Ta bi shi da kallon 'kauna zuciyarta fes! Tamkar wacce aka mayar da aurensa da uwar dansa haka take ji. Ta san shi kansa sai ya fi samun nutsuwa idan yana tare da Sa'adah saboda ita shaida ce na tsananin son da yake mata. ta tuna jinyar da ya yi a dakinta a dalilin rabuwarsu. Abin kuma da ke ba ta mamaki yadda har yau bai ta ba bude baki ya ce ga sanadin rabuwar tasu ba, ita ma Sa'adah ba yadda ba a yi ba ta'ki fada, lamarin da kowa ya kyale su aka bi su da addu'ar alheri. Duk irin sha'kuwa da aminci da ke tsakanin Sa'adah da Baffanta, ko shi ta'ki fada masa dalili. Haka ma Mk duk yadda yake jin nauyin surukin nasa bai iya fada masa dalilin rabuwar tasu ba, illa ya ro'ke shi, akan kar ya yi fushi ko ya ga laifinsa, ko rashin kirkinsa akan sun rabu da Sa'adah. 'Kadarrar su ce haka, shi ma kuma Baffan bai zafafa ba, bai kuma takura sai ya ji dalilin ba, ya yi ammana tunda suke boye sirrinsu da alamun za su iya yi wa junansu afuwa a gaba, duk kuwa da a farkon mutuwar auren hana Sa'adah zaman gidansa yayi. **** Bayan yaron ya kawo mata littafin, ta dauko al'kalami ta fara, ta yi layi kamar uku ta goge tana ganin bai tsaru ba, ta ina za ta fara ne? Daga haihuwarta har zuwa girmanta, ko kuwa daga rayuwar makaranta inda nan ne mafari tsakaninta da MK Bichi, ko kuwa ta rayuwar aurensu za ta fara? Ashe rubuta labari da tsarawa ma iyawa ne? Lalle a gaida marubutanmu. Sau uku tana yi tana sokewa, ta tabbatar dai ba za ta iya ba, tunda ba ta taba ba, ai ko za ta ne mi wata cikin fasihan marubuta, ta bata labarin ita kuma ta fasashi ya zama littafi. Ta tabbatar ba za a rasa darasi da jan kunne cikin rayuwarta ba. Alkalamin SURAYYA DAHIRU ✍️✍️ [5/14, 15:55] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.} https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GA* *SADIQ ABUBAKAR*. 11-12 A cikin wannan yanayin Zainab ta yi sallama a tsakar gidansu, sai da ta fara shiga gurin Inna ta gaishe ta, ta bar mata Khalifa, ta yi dakin Sa'adah. Zaune ta same ta kan katifarta hannunta ri'ke da littafi da biro. Gefenta ta zauna tana fadin "Nazari kike ne haka?" "A sanyaye tace "Wai nan littafi zan rubuta amma na rasa ta inda zan fara." Dariya Zainab ta yi tare da cewa, "Sa'adah manya, to wanne irin labari za ki rubuta?" Kai tsaye ta ce "Akan rayuwata, wata'kila ba za a rasa matan da suke cikin rayuwar da na yi a baya ba!" Ina fatan su ji labarina don su farka daga barcin makantar da suke, kafin su bude ido su gan su a *HALIN YAU* da nake fuskanta! Hawaye ya zubo mata ta sa gefen dan'kwalinta ta dauke a 'ko'karinta na kar Zainab ta gani. Cikin sanyin murya da tausayawa Zainab ta ce, "Amma kuma Sa'adah na dauka zuwa yanzu kin gane rayuwar nan bata da tabbas, bamu muke tsarawa kanmu rayuwa ba, da ace kowa shike sarrafa rayuwarsa da baku rabu da Uncle ba, da baki yi kukan rabuwar ba, Ni kaina ba irin kukan da ban taya ki ba, ba irin walankeluwar da ba mu yi ba a waccan lokacin, amma da yake a lokacin ubangiji bai nufa zamu samu cikar burinmu ba mun hakura kan dole. yanzu kuma Allah ya karkato da hankalinsa, maimakon ki yi wa Allah godiya, ki bishi sannu a hankali,har Allah ya taimake ki, ki koma dakinki, ki ri'ke 'danki, amma sai ki 'bullo da iya shege? Ni sai yanzu na gane ashe duk kuka da damuwar da kika yi ba har zuciya bane! Wallahi Sa'adah iskancinki ya fara damuna yanzu abin da kika mishi, da ya tsaya don ya taimake mu ya yi dai dai?" Sai a lokacin ta bude baki ta ce "Idan dai taimakon daga gareshi ne ba na so, ya je ya rike dukkan taimakonsa, ke duk wani abu da ya shafe shi bana bu'kata. ya yi harkar shi na yi tawa, idan Allah ya so ma ba zan sake kuskuren bari mu hadu ba, ai wannan visiting 'din ma dole ne yasa na je, Inna bata nan, Anty Sumayya kuma tana da uzirin mijinta ba lafiya, dama su ne suke zuwa masa. Jawad ne yace, Malam ya ce masa baya gari ba zai sami zuwa masa ba, kin ji 'karfin zuwana." Ta ja majina ta ci gaba da cewa, "Amma ban da haka ba zan je a ranar ba, balle mu hadu! Zainab da ne na yi haukan banza na son na koma masa, amma a yanzu ko zan mutu ban yi aure ba, zan yi iyakar 'ko'kari na ga ko zaman mota bamu sake yi ba, balle zaman aure" Muryarta ta karye alamun kukan da take ma'kalewa gaf yake da ya kubuce mata, ta ci gaba da cewa, "Ban taba dauka Mukhtar zai jefe ni, da abin da ya jefe ni da shi ba, in da tun farkon rabuwar mu na san kallon da yake mini ke nan da ko zan mutu ba zan bi shi ba, bare na ba shi ha'kuri, tunda na san shi ban huta ba. Ban ga kuma da me na tsira a cikin zamana da shi ba, sai ko rabon Jawad da ya ratsa shi ma Ubangiji ne Ya 'kaddara ni ce uwarshi, amma a zuciyar MK, Farida yaso ta zamo uwarshi" Sai lokacin Zainab ta katse ta da cewa, "Wallahi karya kike yi, ina ce ba dole aka mishi ya zabe ki a farko ya barta ba? kin dai san namiji ba a mishi dole, kuma ke da kanki kin tabbatar ke ce kike da alhakin mutuwar aurenki?" "Tabbas ina da laifi amma ai shi ma ba za a rasa nashi ba, sannan kuma bi-ta-da-'kullin da ya bi ni da shi a idonshi da zuciyarsa ya sa na ji ko son shi ne ajalina sai dai na mutu da na koma masa, balle ma ba abin da hakuri ya bari" "Ko za ki kwana kina rantsuwar ba kya son sa, ko ba kya son ki koma, ba yarda zan yi ba don kuwa 'karya ne tsagwaronta, don kuturun munafunci kun 'ki fa'dan mussababin rabuwar taku ai wannan ka'dai ya isa a san kuna son junanku tunda ba ku yarda aji sirrinku ba. Amma ban sani ba ko kin fa'da wa Halima tunda 'kanwar Inna ce ko kuma madadin Anty Sumayya" 'Kin tanka mata Sa'adah ta yi dan ta san magana ta fada mata a fakaice. Ganin haka yasa Zainab canja magana don tasan idan ta ci gaba da zungurarta yanzun nan Inna za ta shigo ta raba su don ba 'karamin aikin Sa'adah ba ne ta rufe ta da sababin da duk wanda ke gidan sai ya san an ta'ba ta. Sai ta bige da lallashi, "Haba Maman Jawad na san ki da fa'da amma ba ki da ri'ko sam, na ro'keki kar fishi yasa ki yanke hukuncin da za ki yi kukan da ya zarce wanda kika yi a baya". Ta nisa ta kalli Sa'adah, ta sake cewa "Idan ma wani Abu ya ce miki da ya miki ciwo wata'kila ya fada ne a lokacin da yake cikin fishi, ko kuma ya fada ne don ya 'kuntata miki, ki ji yadda shi ma yake ji. Amma shi ba abin a ranshi yanzu, tunda akan kunnenki Baba direba ya tabbatar da shi kanshi ya fahimci irin son da yake miki, ke ma kuma ya lura kina son shi, haba Sa'adah!" Kukan da Sa'adah ke ma'kalewa ya kwace mata sosai, har Zainab ta ji to ko akwai wata magana data fada cikin kuskure wacce tasa ta kuka haka? Amma da ta tuna Sa'adah sarkin kuka ce ko ba dalili, yasa ta samin nutsuwa. Shiru ta yi, ba ta yi yunkurin hana ta kukan ba, ta san ko ba komai dai za ta sami salama a zuciyarta, sai da ta tabbatar ta yi ya ishe ta sannan ta ruko hannunta tana fadin ya isa haka, ki yi hakuri komai zai wuce ya zama tarihi, ki yi addu'ar zabin alheri, bawai zabin ranki ba." Ta mike tana cewa, "Kin ji har ana kiran Maghrib bari na tafi sai na sake shigowa, ko kuma sai na gan ki." Sa'adah ba ta ce mata uffan ba, ita ma Zainab din sanin halin 'kawarta tun fil'azal yasa ba ta damu ba. Ta juya ta fita, a tsakar gida ta tarar da Inna ta goya Khalifa ya nata barci, "Ah goyo ki kayi haka Inna? Ai sai yasa miki ciwon baya." Murmushi Inna ta yi tare da cewa, "Ku dai yaran yau da bakwa son goyo ne kuke kallon zai sa ciwon baya, alhalin shakuwa da tausayi ke 'karawa a tsakanin uwa da danta, amma ku boko da gayu ya hana ku goyo sai dai a hannu" Dariya Zainab ta yi tana fadin "Inna Allah ina 'ko'kartawa." "Allah Ya sa!" Inna ta fada tana kunto shi, yaro yasa kuka, wai shi an saukko da shi, ai ko Inna ta ce, "Juyo na sa miki shi a bayan." Cike da kunya da girmamawa tace, "To" Ta sunkuya ta sa mata shi har zanin Inna ce ta daura mata, sannan ta bar ta ita kuma ta hau kiciniyar gyara goyon. A gurguje suka yi sallama ta tafi ita kuma Inna ta yi bandaki da buta a hannunta. Ta idar da sallar Maghrib tana zaune kan sallayar tana jan carbi, wayarta ta hau 'kuwwa, hannu tasa ta janyo ta ganin sunan Hajiyar Bichi, yasa gabanta ya fadi, duk da suna waya lokaci zuwa lokaci, amma ba tasan dalilin faduwar gaban da ta ji a yau ba. katsewa ta yi sai ta kira ta, Hajiya ta ambata sai kuma tace, "Assalamu alaikum!" Ciki-ciki Hajiyar ta amsa. Sai jikin Sa'adah ya yi sanyi ta ce, "Lafiya kuwa Hajiya?" "Ba lafiya ba Sa'a, yanzu a ce za ki tafi wurin Jawad amma ki kasa fada mini? Na san kuma kinsan ubansa baya nan?" "Hajiya ni ban sani ba". "kin sani mana ai ba zuwa kike ranar da ake taron ba, amma wannan karon kin je saboda wanda kike gujewa haduwar ta ki da shi ba zai jeba, sai kuma Allah ya yi nufin haduwar taku wanda shi kadai ya san manufar hakan. Ban ga kuma laifinki don kin kame kanki ba. Laifinki daya da kika san dukkan ahalinki ba za su sami zuwa ba, sai ki fada mini mu tafi bibbiyu, wannan abu da kika mini sai nake ganin kamar ni ma fushin da kika dauka ya shafe ni ganewa ne ban yi ba sai yanzu." Cikin son kare kai da kuma iyakacin gaskiyarta tace, "Wallahi ko ka'dan Hajiya ba haka ba ne, ba abin da za ki mini nan duniya na yi fishi da ke, har gobe ke uwa ce. Tunani na bai ba ni na yi hakan ba, na ma yi tunanin direba zai kai ku tare da Antinsa, amma ki yi ha'kuri Hajiya" Take ko Hajiyar ta ce, "Na huce dama rashin fahimta ne, ki gaida Innar taki, kuma In sha Allah ina nan tafe cikin satin nan" "Allah ya kawo ki Hajiya!" Ta ajiye wayar tana jin idan akwai asarar da ta yi cikin rabuwa da MK to kuwa rashin nagartatciyar suruka irin Hajiya na kan gaba, jin kanta ya mata nauyi ne yasa ta ci gaba da ambaton Allah. Alkalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍️ [5/15, 19:03] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.} https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GA* *SADIQ ABUBAKAR*. *ALLAH KA JIIKAN* _HAUWA M. HASSAN_ *(FINE GIRL)* _UBANGIJI KA ALBARKACI SU FA'EEZA_. 13-14 Tsawon kwanaki addu'ar za'bin alheri ya dinga yi tsakaninshi da Sa'adah ba 'kak'kautawa, kuma ALHAMDULILLAH, ya ji takurar da yake ji akan zama da ita ta kau, ya sami sau'kin nauyin da zuciyarshi ta yi akan ta. Ranar Juma'a bayan an sau'ko Masallaci kai tsaye gidan su ya zarce kamar yadda ya saba a falo ya tarar da Hajiya zaune kan sallaya, tana lazimi. Ya jima yana zaune kafin ta shafa addu'arta ta juyo ta kalleshi, a nutse ya shiga gaishe ta tare da tambayar jikinta kasancewar kwanaki biyun nan fama take ta yi da zazzabin cizon sauro. "Jiki kam na ji sau'ki sai rashin 'karfin jiki wanda sai a hankali." Ta fada tana daddanna 'kafarta. "Hajiya 'kafar ciwo take miki ne?" Ya fada cike da kulawa. Ta ce, "Ba wani ciwo kawai kasala ce!" "Sannu idan kin gama shan maganin ba ki ji daidai ba, sai na mayar da ke wajen likita." Da sauri ta ce "Kai raba ni da zancen Likitan nan na ji sauki." Dariya ya yi! dama tsokanace wannan zazzabin ma da 'kyar ta yarda ta je asibitin bare ta yarda ta koma. "Har yau ba ka ce mini komai akan maganar Sa'a ba?" Murmushi ya yi "Oh! Hajiya ai na ga ba ki da lafiya ne." "A a na ji sauki " Gyara zama ya yi sosai ya fuskance ta, "Hajiya!" Ya kira sunanta. "Na'am!" Ita ma ta amsa tare da mi'ka dukkan natsuwarta gare shi. "Kamar yadda na ce miki zan yi addu'a, to na yi! kuma na ji tsoro da razanin da nake ji a tattare da zama da yarinyar nan ya gushe daga zuciyata, amma..." Sai kawai jin ta ya yi tana ambaton Alhamdulillah! tausayinta ya kama shi na ganin tsananin murnar da take yi akan abin da ba tabbacin yi yuwar faruwar shi. Ya san Sa'adah, ta kyautata mata matu'ka. Lamarin da Hajiya ta tattara dukkan kaunar da take mishi ta mi'ka mata, duk irin laifin da za ta mishi tofa a idon Hajiya ba laifi ba ne sai ta ce ai yarinya ce, 'kuruciya ce ba kuma hankalinsu 'daya ba. Har ya fara yi wa Sa'adah kallon macijiya ta sare shi, ta kuma koma gefe ta lullube uwarshi da alheri, haka nan hatta 'yan uwansa, mussaman Samira da Hafsatu basu dauki lamarin Sa'adah da wasa ba, saboda yadda ta kyautata musu iyaka, ya san ba ta da rowa, tana da saurin sabo, ba ta kuma sa ido a lamarinsa da 'yan uwanshi, komai zai musu kuwa, wani lokacin ma ita take ankarar da shi. Shi har mamakin ta yake yi yadda duk wani rikicinta, fa'danta, rashin kirkinta, da kuma rashin ha'kuri duk akan shi ya 'kare. Ta 'dago tana kuma ambaton ALHAMDULILLAH. "Hajiya abin da nake so ki gane yarinyar nan fa yanzu gaba'daya ba yadda kike zaton ta ba ne, na tana son dawowa 'dakinta, don haka kar ki sa a ranki cewar za ta dawo, azo kuma abu bai yiwu ba, ki zo ki sake shiga damuwa kinsan dai kullum girma 'kara kama ki yake" Shiru ta yi can ta nisa, "Shin kai a wurinka magana ta wuce ta 'bacin rai ba tashin tashina?" Ya yi jim, yasan dole sai sun sake baje tashin hankalin da ya gitta a tsakaninsu, kafin a manta shi gaba'daya! Amma sai ya amsa mata da cewa "Babu Hajiya! amma wallahi bazan ta bin kanta ta amince ba, don na lura yanzu wani iya shege ta ke ji" Da sauri Hajiya ta 'daga mishi hannu,"Kai da'dina da kai ba ka fahimci yarinyar nan ba, kishi ne ke 'dawainiya da ita, ka duba mana kafin ka yi auren nan wanne irin bibiya ne ba ta maka ba? har kowa ya gane ita ce mai laifi a tsakaninku, duk da ba ku cewa kowa ga yadda abin yake ba". Ta yi 'kasa da murya, "Yanzu fa duk girman laifinta, kama ta hukuncin da yanzu kai ne mai laifi a tsakaninku tunda ka mata kishiya, abin da nake so da kai, kar ka yarda wani borinta yasa ka yi 'kasa a guiwa, ka lallaba ta ka'dan, ni kuma sai na lalla'ba mana ita da yawa" Dariya ya dinga yi,"Oh Hajiya saboda Allah ni da Sa'adah wa kika fi so?" "Ai kai ma kasan ita na fi so! nan kusa za a dade ba'a samu mai girmama uwar miji da 'yan uwanshi irin ta ba. Ina fa ji ina kuma ganin yadda she'danun yaran yau suke wa iyayen mazan su iyashege kala-kala, har sunaye suka la'kaba musu, wai uwar miji ce Ulcer, BP, ciwon kai, da sauran sunaye na tsiya, amma Sa'a bata a cikin wannan layin". Dariyar ya sake yi tare da cewa, "kun yi dace ne kawai ke da ita wasu laifin iyayen mijin ne ai, da basa 'dauke kai ga harkar gidan ya'yan su maza, sannan basa jan surukan nasu a jiki, basa kuma yi musu sassaci da uzziri. Wasu kuma tabbas laifin *Matan Yau* ne da suke ganin uwar miji tamkar wata 'yar katsalandan ga rayuwar su sai afara zaman Allah ya kawo maraba. Allah dai ya rufa asiri kawai, amma Hajiya ita Farida fa?" Da sauri ta ce, "Ita ma ba ta da laifi tana da irin nata alherin, amma..." Ya katse ta da cewa "Ba kamar Sa'a ba ko??" Dariya ta yi tana cewa "Yaushe zaka je gun nata?" "Zan je In sha Allah!" Jin yadda ya sau'ko ya kuma amince da maganar Sa'adah a karon farko tun bayan rabuwarsu, yasa bata matsa mishi da yawa ba, sai ta ce, "To ka mayar da hankali don Allah, a yi a gama komai cikin 'kan'kanin lokaci ku dai yanzu ba yara ba ne" Mi'kewa ya yi yana gyara sakun hularsa tare da cewa, "Ke da kika ce za ki lallaba mana ita, ai ni ba sai na yi komai ba." Cikin sauri ta furta, "Ai ko tilas kai ne mai magana a farko" Murmushi ya saki tare da yi mata sallama ya fita yana fadin, "Sa'a ta same ki sosai Hajiya" Gidansa ya nufa, a falo ya tarar da Farida cikin kwalliya ta burgewa tana zaman jiran shi, ta hau hidimar kawo mishi abinci, da abin sha, sai daya kammala, ta kwashe komai sannan ta dawo ta zauna tana tambayar Hajiya. ya amsa da cewa "Tana lafiya! ta ce a gaishe ki." Murmushi ta yi tare da fadin "Na gode!" Hannunta ya riko ya janyota sosai kusa dashi, "Ina son mu yi magana mai mihimmanci, ki nutsu ki ji me zance miki, ki kuma fahimce ni" Idanuwanta masu sheki ta zuba masa tana jin a jikinta abin da ta dade tana jiran ya tabbata ne yake neman faruwa a wannan karon, kai ta gyada tare da cewa, "Ina jin ka." Sai kuma ya kasa cewa komai tsawon lokaci, ita kuwa da ke ba mai gaggawa ba ce ba ta ce masa uffan ba. Har ya gaji ya nisa don kanshi sannan ya ce, "Ba sabuwar magana ba ce mun sha yin ta, sai dai ta yau 'din ta sha banban!" Nan ma cewa ta yi, "Ina sauraron ka!" Abin mamaki sai ya ji shakkar furta maganar yake. Cikin dauriya ya ce, "Maganar Sa'adah ce zan fara magana da ita, idan Ubangiji bai 'karar da zaman namu baki 'daya ba, zata dawo " Gabanta ya fadi duk da a kullum cikin tsammanin faruwar hakan take, amma sai da ta kadu matu'ka da gaske, amma da yake tana cikin jerin matan da Ubangiji ya ba su ha'kuri mai yawa da sanyin hali, da kuma ha'diye damuwa sai ta ce! "Ai da ma ka sha fada mini a kowanne lokaci idan 'kaddarar zamanku ba ta 'kare ba za ka dawo da matarka, ni kuma na sha fada maka cewa ba zan baka matsala ba hakane?" Ta tambaye shi, kai ya 'daga mata, "To a yau ma ina tabbatar maka baka da matsala da ni. amma zan ro'ke ka abu daya, na san kana son ta sosai, ni kuma ina son ka sosai, don Allah ka yi mini adalci" Wani abu ya ji ya tsirga mishi tun daga kanshi har zuwa 'kafarshi. Gaba'daya ya janyota jikinshi yana jin tausayin ta na tsirga mishi a zuci da gangar jikinsa gabadaya. Cikin murya marar amo ya ce, "Farida a tsayin zamana da ke kin san ina son Sa'adah amma abin mamaki ba ki san ina son ki ba?" Luf ta yi ba ta amsa ba, saboda yadda take kokawa da zuciyarta da numfashin ta. "Kai, kishi, bala'i!" Ta fa'da a zuciyarta, ban da haka abin da take da tabbacin zai faru ne, don yana neman faruwa kuma sai ya dame ta? kamar ba ita ce take ta mishi kau'din ya dawo da matarsa ba? Amma a yau da ya amsa, har ya zauna yana fa'da mata da bakinshi akan zai dawo ita sai ta ji kishin da ba ta yi tunanin zai taso mata ba, ya taso da wani irin 'karfi mai gigitarwa. Jin ta yi shiru yasa shi fadin, "Ban aure ki akan wani dalili ba sai don ina son ki, ina zaune da ke saboda ina son ki, ina kuma jin dadin zama dake, don haka ba wani abin dazai raba ni da ke matu'kar ba ke ce kika bijire mini ba. Ina son ki Farida irin son da zan iya sadaukar miki da komai, ba abu mai da'di a soyayya irin a so ka da kai da dukkan matsalarka, a mutuntunta ka, a kuma yarda ka isa koda kuwa a zahiri baka isan ba. Ba abin da baki mini na kyautatawa ba, ba kuma zan manta ba, kar ki yarda ki sa a ranki wai zan juya miki baya akan Sa'adah, kar ki ji a ranki na fi son ta akan ki, ni ban san wacce na fi so ba, wacce duk ta kiyaye mini 'bacin Raina, ta zauna da ni lafiya cikin aminci, ta yarda bazan musguna mata da gangan ba, ba shakka itace zata jagoranci zuciya ta. Idan kuma kina da matsala akan dawowarta fada mini zan iya fasawa, idan har hakan zai fi zama masalaha." Rungume shi ta yi sosai ta na jin wata irin nutsuwa ta na shigar ta. Ashe har haka matsayinta yake, ashe darajarta ta kai haka? kai ta hau girgizawa, ta ce, "A a ban da matsalar komai wallahi, kawai dai fargaba nake kar ka canja mini kar ka juya mini baya". Murmushi ya yi yasan tana da hujjarta tunda an yi hakan a baya, don haka sai ya ce, "Aure ya wuce wasa ba na fatan kuma na rabu da matar aure na akan wata matar, ki cire wannan tunanin don yanzu ke ce matata, zan iya ha'kura da ita, matu'kar ta ce ba za ta zauna da ke ba, ke ko ba zan iya rabuwa da ke akan ta ba" Sai kawai ta saki kukan da take ta haniniya da shi akan kar ya zubo, ya 'dago ta ya shiga lashe hawayen nata, wanda na tsananin murnar maganganunsa ne ko da ba haka ba ne a zuciyarsa ya nuna mata girmamawa tare da karramawa, ta kuma gamsu yana son ta sosai. "Ubangiji Ya sanya alheri ya zaunar da mu lafiya, Allah ya 'kara maka lafiya, da bu'din arziki ya kuma hore maka ikon yin adalci" Amin ya ke ta fa'di tare da jin ba abu mai dadi a duniya irin mace ta gari, mai fahimta, mai kuma ilimi da aiki da shi, don sau tari shedanun matan masu ilimin ne, kawai aiki da shi ne ba sa yi. A fili ya ce, "Ubangiji Ya miki albarka My Feri-Feri, Allah Ya ba ki rabo mai amfani." Zuciyarta ta yi fes ta na jin dadin wannan addu'ar da yake yawaita yi mata na albarka da samun zuri'a mai albarka. Suna haka har aka kira La'asar sannan suka mike shi ya yi Alwala ya yi masallaci ita kuma ta yi a 'dakinta. Bayan ya dawo Masallaci bai shiga gidan ba a 'kofar gidan ya samu gefe ya zauna ya ciro wayarshi ya fara lalubo lambarta, karon farko bayan shudewar lokaci mai yawa, daf da za ta tsinke ya ji ta dauka, Sallama ta yi, ya amsa, sai kuma ta ja bakinta ta tsuke, shi kansa sai al'amarin ya zo mishi a bai bai, cikin 'karfin halin da aka san namiji da shi ya ce, "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?" Cike da son ta nuna mishi ba shi da sauran matsayi a zuciyarta ta ce, "Waye?" Bai yi mamaki ba, dan haka sai ya nufin 'kunsa mata takaici shima. "Wadda ki ke ta sallar dare ne akansa". Yana rufe baki ta ce, "Babu wannan halittar" tare da kashe wayarta. Zuciyarta na bugawa wai yau mafarki take ne ko kuwa da gaske Malam ne ya kira ta taka nas? Wacce iriin sa'a yau ta tashi da ita? tana tuna kalaminshi na 'karshen maganar su a wani lokaci da ya shu'de, sai ta ji murnarta ta koma ciki, ba za ta saurare shi ba har sai ya janye kalamunshi, da kallon da yake mata, idan ko ba haka ba, to tabbas ba za ta sake mu'amala da shi ba, bare babbar mu'amala irin ta aure, ko da hakan na nufin mutuwarta ne. Al'kalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍🏼✍🏼 [5/16, 13:26] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIQ ABUBAKAR* *Fatan Alheri ga* _DANDALIN MUM KHADY_. 🤝🏽 15-16 Mamakin ta ne ya yi matu'kar kama shi wai yau shi ta kashe ma waya? Anya Sa'adah za ta canja hali kuwa? Sake 'kiran ta ya yi a karo na biyu, amma ga mamakin sa har 'kiran ya katse ba ta 'daga ba. Ya ri'ke wayar ya yi jim cikin sanyin jiki da tunani iri iri. Ya san kirkinta ya fi sharrinta yawa, har yau kuma, shi dai a idanuwanshi bai ga wacce ta iya tsara kwalliya da gayu irin Sa'adah ba, ma'abociyar son 'kyale-'kyale ce, kusan wannan dabi'ar tata na son kayan 'kawa masu tsadar gaske ya taimaka wurin sake jefa aurensu cikin garari. Lambar amininshi ya lalubo Dr. Mahmoud Karfi, ba ta dade tana dokawa ba, ya ji an 'dauka, tare da sallama, kai tsaye MK ya ce, "Kana Ina?" Daga can bangaren ya amsa da cewa, "Ina makaranta, lafiya?" "Lafiya Lau jira ni gani nan zuwa" Ya katse wayar ya mi'ke ya shiga gida, ya dauki mukullin motarshi, tare da yi wa matarshi sallamar ya fita, ta bi shi da addu'ar dawowa lafiya. "Kai tsaye sabuwar Jami'ar Bayaro ya nufa, bai bi takan ofishin saba, ya zarce ofis din Dr. Mahmoud Karfi. Da sallama ya shiga shi ka'dai ya tarar yana dakon isowarsa, musabaha suka yi, Dr. Karfi ya dube shi, "Ka sa ni tunani iri iri fa" Jim MK ya yi tare da cewa, "Wallahi ru'dani na shiga, ka san Hajiya ta matsa akan maganar na dawo da yarinyar nan, to dai yanzu na amsa mata akan na amince bayan na yi addua na kuma ji na aminta da lamarin. Wai yau na 'kira ta a waya da farko ce mini ta yi waye?" Dariya ta so subuce wa Dr. 'Karfi, amma ya kirne, shi kuma ya zarce da cewa, "Karshe kuma sai ta kashe mini waya" "Alhamdulillah!" 'Karfi ya furta a fili tare da cewa "Ni na da'de ina ji a jikina idan dai ba mutuwa ce ta sure dayanku ba, to kuwa za ku sake ha'dewa. Shi yasa na kyale ka ka sami nutsuwa, ka san dai Sa'adah ta bi ka iyakar bi akan ka yafe mata, amma ba ka yi ba, ka zo ka yi aure dole ta gaji ta yi fishi, amma na san fishin ba mai yawa ba ne, tunda tana son ka." A sanyaye ya ce, "Anya kuwa? ba ku san ta ba ne, a makarantar su Jawad fa baka ga iya shegen da ta mini a bainar nasi ba" Dariyar da Dr. 'Karfi ya ke ri'kewa ta subuce, ya hau yi sosai, har ta sha'kar da MK, don haka sai ya mike ya ce, "Na gode" Da sauri 'Karfi ya ruko shi ya na fadin, "Yi hakuri ka zauna ai ba mu gama ba" Cikin fushi ya ce, "Ya zan zo maka da matsalar da ta dame ni, ka sani gaba kana mini dariya ka mayar da ni mahauka ci!" "Wane ni Allah ya huci zuciyarka zauna mu gama" 'Karfi ya fada bayan ya shanye dariyarshi. Komawa ya yi ya zauna amma fuskar nan a ha'de. "Yanzu ka san me? Zan je na same ta mu yi magana, idan ya so sai mu koma tare, daga nan kuma shike nan sanda za ka je ma ba zan sani ba" Cikin cin magani ya ce "Ni wallahi bazan ta zarya a wajenta ta na mini iya shege ba, yanzun ma Hajiya ce ta matsa amma banda haka ta je can ta 'karaci tsiyarta" Mahmoud ya ce, "Yanzu ma damuwar da na gani a fuskarka, akan ta kashe maka waya, Hajiya ce ta matsa ka fada mini?" Tsaki ya ja, ya san sha'kiyanci zai masa, tunda idan akwai wanda ya san yadda yake son Sa'adah to kuwa Mahmoud ne. Sai kawai ya mi'ke ya fice yana fadin, "Sai ka yi kai ka'dai." Shi kuwa ya ci gaba da dariyar shi a sake yadda yake so. Ta idar da sallar Maghrib ke nan tana zaune tana tasbihi, zuciyarta cike da farin cikin fara gyaruwar al'amuranta, wayarta ta hau kuwwa, ganin sunan Baban dady yasa ta jin wani farin ciki ya 'kara kama ta, ba ta yi azarbabin 'dagawa ba har ta katse. Kafin ta yi wani yun'kurin, ya sake 'kira, haka ta gama yau'kinta, ta dauka hadi da yin sallama,"Ranki ya dade ai na zaci ba za ki dauka ba ne" 'Yar dariya ta yi, "Akan me? Sallah na idar." "Ya mutanen gidan to?" Ya tambaya, ta amsa mishi da, "Duka lafiya Lau" "Ina son ganin ki wanne lokaci zan same ki?" sanin mutuncinsa da karamcinsa ya sa ta fadin ko yaushe "Ina gida!" "To ki saurare ni anjima kadan zan iso." "Sai ka zo." Ta fada tana jin wani irin nisha'di na tsirga mata. Wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin lallausan yadi ruwan hoda, mai shegen tsada ba shi da adon komai haka yake plane sai yauki yake da 'daukar ido. Doguwar riga ne aka 'kawata da shudin stones masu sheki matu'ka, don haka ta yane jikinta da matsakaicin mayafi blue, mai da roll on kawai ta shafa, kasancewar turarukanta sun kama kayanta sosai kuma ma'abociyar yin turaren kaya ne irin na barebari (garam). Duk da dare ne, sai da ta shafa powder ta kuma zagaye le'banta da jan baki ruwan hoda. Yanayin jikinta irin tauraruwar wasan kwaikwayon nan ce Hafsat Barauniya, duk da Hafsar ta fi ta shekaru, ta kuma fita hasken fata, kasancewar Sa'adah mai duhu ce, ba kuma ta yarda ta shafa man da zai canja mata launin kalarta ba, illa tana 'batar da kud'a'de masu yawa wurin siyan tsadadden man dake fitowa da ainihin kalarta, ta goge ta yi tas da ita, ta yadda ko mace sai kin yi sha'awar launinta shi yasa idan akwai tambayar da a rana ana mata ya kai sau biyar, ita ce wanne mai ki ke shafawa, wanne mai ki ke amfani da shi? wani lokacin ta fa'da, wani lokacin kuma ta yi murmushi wushiryarta ta sake 'kawata ta tace "Vaseline" Tana tsaye jikin Shoe Rack (ma'adanar takalman)ta ta fito da wani Tom's blue, Innarta ta shigo ta kalle ta ta ce, "To 'dawisu sarkin ado a wannan daren kike wannan kwallliyar anya Iya baza ki rage wannan 'kyale-'kyalen ba? Shi yasa ai da yawa mazan suna son zuwa gunki amma gani suke kin fi 'karfin su" "Inna tunda ba ni na fa'da ba ai shi kenan, idan mutum da gaske son nawa yake ya zo mana idan mun daidaita ai zan aure shi ne" "Yanzun kuma mai za ki yi da takalmi, da na ga kina gogewa? Na san dabi'ar ki ce ca'ba kwalliya ba sai za ki fita ba, amma wannan takalmi ai na fita ne, kuma kin san ba inda za ki a wannan daren" "Kai Inna don Allah!" Ta fa'da cike da shagwaba, "Ni fa ba fita zan yi ba, ba'ko zan yi" "Kin fa'da wa Baffanku za ki yi Ba'ko?" Kai tsaye ta ce, "Na fada masa kafin ya tafi sallar Isha" "Shi kenan amma don Allah Iya ki daina bata wa mutum lokaci kina kuma karbe mishi abin hannunsa alhalin kin san ba auren sa za ki yi ba, yaudara ba kyau. Alhaji Mamman din nan ni ban ga laifinsa ba, mutum mai mutunci mai nagarta ga shi babba ne ya mallaki hankalinsa amma kina tasa 'kafa kina shure shi, kuma kina kar'be mai dukiya" "In sha Allah, Inna ko mai ya kusa zuwa 'karshe, ki 'kara 'kaimi wurin yi mini addua" Dadi ya kama uwar tata kusan yau ne Sa'adah ta bude baki ta yi magana mai kyau akan aure. Nan da nan ta hau fa'din, "Addu'a kam ai kullum yin ta nake, mantawa na ke da ko mai sai ke idan ina addu'a, Allah ya miki zabin alheri" Ta fita tana sake cewa, "Ba abin da ke raina irin in gan ki a 'dakinki kin nutsu wuri daya" Har sai da ta yi sallar Isha sannan ya mata waya ya iso. Fararen kujerun da ta tanada saboda zuwan wanda tabawa izini, ta 'diba ta fita dasu zauren gidan nasu da ke da yalwar fili, tana zuwa shi ma yana 'karasa shigowa, da sauri ya karbe kujerun yana cewa "Ai da kin sani kin jira na zo na 'debo, wannan ba aikin uwargidanmu ba ne" Dariya ta yi, "Za ka fara ko?" Shi ma dariyar ya yi, "Zan fara fa'din gaskiya ba" komawa ta yi ta ha'do mishi ruwa (pure water) da kuma kunun ayan da Inna ke yi akan faranti tare da Tumbler, ta ajiye mishi tare da cewa "Ga ruwa" Ya yi godiya ita kuma ta hau gaishe shi tare da tambayar iyalinshi, ya ba ta amsa da cewa, "Ai ta yi fishi da ke tace rabon da ki taka mata tun barkan haihuwar Kausar, ga Kausar tana gudu ko Ina." Ta ce, "Hidimar makaranta ce ta 'boye ni amma yanzu kam na gama za ta gan ni, a ba ta ha'kuri" Sai da ya bude ruwa ya sha sannan ya yi gyaran murya ya ce, "Zuwan fa na mussaman ne, tare da albishir din abin da muka dade muna nema ya samu, takanas MK ya same ni ya ce mini ya kira ki, amma kin kashe mishi waya haka ne?" Kai tsaye ta ce "E ai ban san shi ba ne" "Ban gane ba ki san shi ba ne"? "To bai gabatar da kansa ba, ya fara maganganun da ban fahimce su ba". Shiru ya yi tare da cewa "Amma ba ki da lambarsa ne?" "Ban da ita" "Ba ki da ita?" Ya tambaye ta cike da mamaki. "E!" Kawai tace ta ja bakinta ta tsuke. Kamar zai bar maganar sai kuma ya ce, "Amma aikin haddace a kanki" Nan ma ta ce, "Na manta" Ya yi dariya, "Sa'adah wai yaushe kika cire mu a ranki har haka ne?" Murmushi ta yi ta ce, "A lokacin da na fahimci ba komai ne idan ka rasa yake dawo maka ba, ba kuma komai ne kake so yake zama alheri ba" Da sauri Dr. 'Karfi ya ce, "To mu dai alheri ne kuma mun dawo mu sake daukar ki a karo na biyu." "Amma bai kama ta, ya manta cewar aure ya 'kare a tsakanin mu ba?" Ta fa'da cikin 'daure fuska. Alkalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·• 17-18. " A a ban sani ba bai kuma fa'da mini ba." 'Karfi ya fa'da cikin yanayi na rashin gamsuwa, tare da zuba mata ido yana ta a uziya saboda yadda shaidan ke 'kawata mishi ita, ya riga ya binne wannan abin a ransa har abada ba zai yi tarayya da MK akan mace ba, macen da ya tabbatar amininshi yana mata son da bai yi wa kansa ba. Ya numfasa ya 'kira sunanta, "Sa'adah karki wahalar da ku, da ke da Mukhtar kuna son junanku, nan duniya ba abin da zai kankare wannan son, dole za a sami matsala a cikin zamantakewar aure, muhimmi shine ayi afuwa, a yafe, a kuma manta, amma ba za a iya kaucewa matsalar ba. ko wani sabon auren kipka yi komai jin da'din da za ki riska sai kin tarar da matsala" Ya nisa sannan ya sake fa'din, "Ina tabbatar miki kuma a yanzu ne ya fi dacewa ki koma dakinki, ba a wancan lokacin da ke kadai kike son komawar ba, yanzu da shi ya bukaci hakan da kansa za ki fi 'kima, ki fi daraja" Sunkuyar da kai 'kasa ta yi hawaye na cika idonta, amma ba ta ce komai ba, ganin yadda jikinta ya yi sanyi, hakan ya 'kwarara guiwar 'Karfi. Ya sake kur'bar ruwa ya ce, "Kar ki bari wannan damar ta kubuce miki, ina tabbatar miki, MK bai so wata mace kamar ki ba, kar ki bari rudin 'kawaye da zuciya su sake rudar ki a karo na biyu, wai ya yi aure, ko kaza da kaza, da duk abin da zai sake dagula miki lissafi. Ki sa a ranki cewar ko kuna tare zai auri Farida! tunda an rubuta a cikin littafin 'kaddararshi cewar matarshi ce, mu gode Allah da ya kasance rabuwa ku ka yi, ba mutuwa kika yi ba, kin san akwai rabon da ke kashe mutum". Hawayen da ta ke tattalawa ya zubo akan lallausar fuskarta, ta ce, "Ai ni sai daga baya na gano dama auren ya 'kallafa rai zai yi shi yasa ya yi ta zungurata, komai 'kankantar laifi sai ya juya shi ya zama garma, ashe dama akwai abin da ya 'kudure, to ya aureta hankalinshi ya kwanta, ni ma kuma ai bai jini a gadon asibitin mahaukata ba, bai kuma ji labarin auren nashi ya zama ajalina ba" Kuka ya so kubuce mata saboda haka ta yi shiru sai rishin kukan kawai. Sai da ta nisa sannan ta sake dorawa da cewa, "Ni kuma nan duniya ban ga mai zai mini na ga farin shi ba" Ta fada cikin dakewa da shanye kukan dake son kunyata ta. Jikin Mahmoud ya sake yin sanyi, ya yi shiru cikin rashin abin cewa. Tsawon mintuna biyar kowa ya yi shiru a tsakaninsu sai fama suke da tunanin zuci. Shudewar yan mintuna kafin ya ce, "Ni fa ba tone-tone za mu yi da ke ba, dukkanku, kowa da irin nashi laifin amma kin sani, laifin ki ya fi yawa" Cikin takaici ta ce, "Baban Dadi tunda laifina yafi yawa, ai ya sake ni ya auro wacce ba za ta yi kuskure ba, wacce son da ake mata zai sa ayi ta mata uzirin ri'ke igiyar aurenta da kyau, sai dai a nuna mata kurenta cikin ladaftarwar da shari'a ta tanadar, shi yasa ni ma da na gane ba son nawa ake ba, kuma duk ni ce mai laifin sai na dau hukuncin da macen da ta san ciwon kanta za ta dauka don ta tsira daga ba'kin cikin namiji". Shiru Mahmoud ya yi mata ya lura kishin Farida ne ya ke cinta shi yasa take ta furzar da magana, don haka ya 'kyale ta, at least dai za ta sami sau'kin ciwon dake addabar zuciyarta. Sai da ta yi shiru don kanta, sannan yace"Ki yi ha'kuri, ki bi komai a sannu, ban hana ki nuna bacin ranki ba, amma kar ki wuce gona da iri, saboda kin san kema kin mishi laifin da sai da ya yi jinya bayan rabuwarku, tunda har ya sau'ko, to fa kar ki wuce makadi, ina fada miki wannan maganar ne a matsayin yayanki" Ya dan numfasa, kana ya zarce da fadin, "Lamarin aure yanzu sai ha'kuri ba Perfect Marriage, kowanne aure da irin nashi 'kalubalen, duk abin da aka ce ibada ne, to fa sai an yi hakuri". Ya mi'ke yana cewa, "Zan wuce, ki saurari zuwanmu!" Hannu yasa a aljihunsa ya fito da yan dari biyar guda ashirin ya zuba kan kujerar daya tashi, da sauri ta ce, "Don Allah ka bar su, kullum a cikin hidima kake " Murmushi ya yi yana cewa, "Wannan kudin zance ne, ina fatan dai za a karbe mu da dukkannin raunin mu, kasancewar mu Malaman makaranta masu sadaukarwa, ba ma su satar kudin jama'a ba" Ta san sarai inda maganar shi ta dosa, da Alhaji Mamman ya ke, tunda ya sha ganin ta da shi, wanda 'karara yake taya amininsa kishi. Dariya ta yi tana kuma godiya amma ta ci alwashin bashi ya ci, dole sai an baje maganar nan ai ya san tun farko ta zabe su tabar Alhaji Mamman din da dukkan abin da yake da shi. Tun a mota yake 'kiran lambar MK amma bai dauka ba, har ya gaji ya mayar da wayarshi caji a jikin motar. Mintuna kusan ashirin har ya shiga layin gidansa yaji 'karan wayar shi, ganin sunan MK yasa shi dauka da sauri, tare da cewa, "Wai ina ka shiga ne?" Daga can ya amsa mishi da cewa, "Wallahi ina tare da Farida ne ba zan so ka yi mini maganar Sa'adah a gabanta ba" Shiru Dr Mahmoud ya yi yana jin shi kam bai san wani namiji da ke gudun 'bata wa matarshi da gangan irin MK ba, ya tuna lokaci da dama da yake zaunar dashi yana caccakar shi akan tsoron Sa'adah ya ke yi, ashe ba tsoro ba ne tunda ga Farida ma hakan ya ke mata. Mutum ne mai martaba abin da yake so, ko wadda yake son sa, ya sake tuna ko a abotarsu, MK ke ha'kuri da shi, shi ke masa hidima ba tare da tunanin ai yasan yawan albashinsu 'daya ba, samun irin Mukhtar Kabir Bichi zai yi wuya a wannan lokacin. Amma duk da hakan sai da ya tsokane shi da cewa, "Dadi na da kai mijin ta ce ne kai, ni ban san me ya sa kake jin tsoron mata ba, ai na 'dauka Sa'adah ce kawai dodon taka, ashe wa lnnan alankosar ma murza ka take yi". Shi ma cikin 'kosawa da shakiyancin da ba ya gajiya da mishi ya ce, "Kai ai ba za ka gane karatun ba ne ni kadai na san mai suke jiyar da ni, ka ga kuwa ai dole na yi tattalin farincikinsu, kar ni ma a hana ni nawa farin cikin" Dariya sosai 'Karfi yake yi yana cewa, "Ashe haka karatun yake ganewa ne ban yi ba? amma da dukkan alamu karatun naka na daban ne" "Idan kagama iya shegen naka, ina sauraranka don waje na fito, idan kuma ba ka gama ba, to zan koma, ma hadu gobe" 'Karfi ya gintse dariyarsa hadi da cewa, "Kai MK wallahi da alama 'yar darun taka, ta shiryawa daru kala-kala, amma dai na san kishi ke 'dawainiya da ita, ka san tunda ka yi auren nan bata bude baki ta ce 'kala ba, yana ta cin ranta, na ga soyayyarka mai yawa a idanuwanta duk da bakinta na 'kirarin rashin son" Shiru MK ya yi har Mahmoud ya yi tsammanin ko wayar ce ta katse. Amma da ya ce, "Kana ji na kuwa?" MK ya amsa da cewa "Ina jin ka. Mamakin ta ne ya ke ta kama ni". "Ai ba mamaki a lamarin mace." A cewar 'Karfi. "Ka shirya gobe muje mu same ta, kada Hajiya ta tambaya ta ji ba ka fara kafa tubalin kome ba ta yi fishi" Ya 'karasa maganar cikin zolaya. "Hmmm!" Kawai MK ya yi tare da cewa "Na gode sosai sai mun hadu gobe idan Allah yaso" * Sa'adah tana shiga a dakin mahaifiyarta ta ci burki, "Inna na dawo" "Zo ki zauna magana zamu yi" Ba ta musa ba ta shiga ta zauna daf da ita,"Waye ya zo?" "Ba wani daban ba ne Baban Dadi ne" Tabe baki ta yi tare da cewa "Waye hakan, kar ki ce mini Mahmoud abokin Muutar? Cikin shagwaba ta rungumo uwar tata ta ce "Shi fa mene ne Inna?" Ture ta ta yi tana cewa "Ashe baki daina bibiyar yaron nan ba ko? 'dazu amsar da ki ka bani na komai ya kusan 'karewa akan maganar aure, ashe kina nan kina zawarcin Muutar ne? Wannan shi ne al'kawarin da ki ka mini? Tunda kin zabi son ranki sama da nawa to ki je ki ta yi, amma ki sani ba da yawuna ba, ba kuma da son raina ba, sai don kin fi 'karfina, don kin san zaki samu goyon bayan mahaifin ki ne" Ta nisa sannan ta ci gaba da cewa, "Tunda na ga kina ta hanzarin shiryawa tare da 'doki na tabbatar ba kowa kike wa wannan rawan jikin ba sai shi" "Inna ba fa yadda kike zaton lamarin ba ne wallahi ban karya al'kawarinmu ba, amma don Allah ki yi hakuri ki gafarce ni ba na son kina damun kan ki akan wannan maganar" "Ai dole na damu tunda na gane ke da Baffanku, ba ku da burin da ya wuce ki koma gidan Muutar, ni kadai na san ba'kin ciki da wahalar da na sha kafin na samo ki a dalilinsa. kuma yanzu da komai ya wuce sai ya lallabo ya sake dama miki lissafi, saboda ya mai da ke marar zuciya, wacce ba ta san ciwon kanta ba" Cike da tausasa murya Sa'adah ta ce, "In sha Allah Inna ba zan sake shiga halin da kike jin tsoro ba, ni ma nasan abin da kike guje mini, tuni na cire shi a raina." "To idan dai haka ne ki ba wa Alh Mamman ko yaron nan Anwar dama wani cikinsu ya fito, ki yi aurenki idan ba haka ba, hankalina ba zai kwanta ba." Ta fada tana goge hawaye da hannun zaninta. Jikin Sa'adah ya yi sanyi ashe dai da gaske Inna take akan ba za ta koma wa Malam ba? Ashe haka ta zafafa lamarin? Wannan wacce irin ba'kar 'kaddara ce ke bibiyar ta ne? Bayan doguwar wahalar da ta sha akan komawarta 'dakinta, sai da abu ya zo a lokacin da ba ta yi tsammanin zuwansa ba, kuma mahaifiyarta ta yi bara'a da lamarin, hankalinta idan ya kai dubu to ya tashi. *_Wai mene ne ke faruwa a tsakanin ma'auran biyu? Mene ne ainihin labarinsu? Mene ne ya raba su duk da matsananciyar soyayyar da ke tsakaninsu? Mu je ga mafari don jin wacce irin waina suka toya?_* Al'kalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 19-20. *MAFARI* Malam Basiru Ado Gogel, haifaffen garin Gogel ne, wani gari a 'karamar hukumar Warawa. Karatun Allo ne ya kawo shi cikin garin Kano, ya sa himma har Allah ya taimake shi, ya haddace al'kur'ani, sannu a hankali kuma ya fara sana'ar tura kura a kasuwar Singa Da damina zai tafi gida yayi aikin gona gadan-gadan kasancewar al'ummar garin Gogel manoma ne, duk da ya ta so ba uba, domin ya na da 'karancin shekaru mahaifinsa ya rasu, dan haka ya yi birgimar ta shi fa'din rayuwa a tsakanin mahaifiyarshi da 'yan uwan mahaifinsa. Da haka ya hada jarin sa ya bude 'yar tireda a cikin unguwar da ya ke hayar 'daki, a unguwa uku, a shekarar kuma aka masa aure da Salamatu 'diyar 'kanin mahaifiyarsa wadda asalin mahaifiyar ta shi 'Yar asalin gamawa ce ta jahar Bauchin Yakubu, aure da rabon haihuwar sa ne ya kawo ta Gogel, kenan Salamatu ma, da ga Gamawa aka ba shi ita. Ya taho da ita cikin kano, suna zaune lafiya, cikin rufin asiri. Yarinyar su ta farko da suka haifa bayan shekaru uku da aure, sunan ta Sumayya, ba sunan kowa taci ba, illa sunan Nana Sumayya, macen farko da ta yi shahada a musulunci. tare da fatan yarinyar ta sami albarkacin mai sunan. Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin rufin asirin Allah, dukkansu sun da ce da juna, masu ha'kuri ne, masu kuma wadatar zuci ne. Sai da Sumayya ta yi shekaru takwas sannan aka haifi Sa'adah wadda sunan mahaifiyarsa ta ci (Sa'adatu). Daga shi har Innar su Salamatu su ke kiran ta Iyah, kamar yadda ake kiran mai sunan nata. A shekarar kuma mahaifiyarshi ta rasu, shi yasa ya tattara ko mai da ya ke dashi a Gogel ya siyar illah gona 'daya da ya bari, wadda zai dinga noma wa, sai kuma 'dakin mahaifiyarsa da yake cikin gidansu ya rufe shi saboda idan ya je Yana da gurin zama. ya zo kano ya si yi madaidai cin gida anan cikin unguwar gidan akan titine a kuma babban layin na Unguwa Uku. Haka rayuwar su ta ci gaba da tafiya cikin ha'kuri da godiyar Allah, har Sumayya ta kammala 'Karamar sakandire manema suka mata ca kasancewar ta doguwar mace fara sol irin fulanin Gamawa. Idris shi yafi kwanciya a ran Malam Basiru dan haka ya ce ya bashi, ba kuma ya bu'katar komai a gunsa sai sadaki da musulunci ya wajabta, komai zai ma ta idan ta je gidan shi sai ya yi. Wannan karamcin da iyayen Idris suka ga ni ya faranta ransu ba ka'dan ba, suka girmama lamarin Sumayya da iyayen ta, kullum cikin jan kunnen shi su ke, akan ya ri'keta cikin aminci. Haka aka yi auranta ba wani hidima, ya 'dauke ta zuwa ogshobo ta jihar osun inda yake aiki da babban bankin Nigeria (CBN) reshen jahar osun. Dan haka Sa'adatu ita kadai ta taso a gidansu domin kuwa, ba ta wuce shekaru takwas ba, aka aurar da yayarta kasancewar mahaifinsu bai wani damu da karatun boko ba, muhimmi dai a gunshi a haddace alkur'ani. Tun kuma akanta basu sake samun haihuwa ba, shi yasa sha'kuwa mai yawa ce tsakanin ta da iyayenta biyu har tana rasa gane waye yafi sonta a cikin su. Yau da gobe aka ce ba ta bar komai ba, Iyah ta kammala 'karamar sakandire, amma ganin yadda ta k'wallafa rai a boko da kuma yadda ba ta sauraren ko wanne saurayi yasa Malam Basiru barin ta ta tafi babbar sakandire, kamar wasa aka zabe su, su biyar a makarantar su, ta GGC U/Uku, su rubuta jarrabawar shiga sakandire ta gwamnatin tarayya ta Kano (FGC KANO). jarrabawar na fitowa kuwa sunanta ya fito cikin mutum uku da suka yi nasara, ita kanta ta yi mamaki tunda duk ragowan da suka fa'di sun fita 'ko'kari. Ganin ku'di tsululu da za'a kashe a hidimar makarantar Malam Basiru ya tabbatar ba makarantar dan talaka ba ne, da bashi da ko mai da kowa sai Allah, shiyasa ya zaunar da ita yace, "Iyah kin san ni ba mai kudi ba ne, bani da halin sa ki a wannan makarantar, ki ci gaba da wadda ki ke yi, kin san dai, ko yanzu idan kin samu mijin da na yarda da nagartar shi auren ki zan yi. Shuru tayi amma a ranta tana jin ba 'karamin abin kunya ba ne ace ta sami damar shiga babbar makaranta irin wannan, amma ace ba ta tafi ba, ba ta san ma da wanne ida za ta kalli 'yan ajin na su ba, mussaman Zainab Salisu Ma'aji da su ke kusan unguwa 'daya, kuma ita ma taci makarantar tana da tabbacin za'a kai ta tunda ta na da yayye ma'aikata. Kasancewar ta mai tsananin tsabta da gayu sai ake mata kallon tamkar ta fito ne a gidan wadata, ita kuma ganin haka yasa ta yin alfahari mussaman da ba ta da makusa a halittar ta. 'Karfe takwas na dare ta dauki wayar innarta, ta shige 'dakin da ya ke mallakin ta ne, Yar uwarta Sumayya da a yanzu suke zaune a Jos babban birnin jahar Plateau da yaran su biyu Abba da Khalifa, ta shiga yi wa flashing, cikin 'kan'kanin lokaci ta biyo baya, tana 'daga kiran, ta sa mata kukan da ta kasa yi a gaban mahaifan nasu, jin kukanta ya matu'kar tada hankalin Sumayya, ta shiga tambayar ta menene, me ya same ki? jin yadda Sumayya ta 'daga murya a gigice ya janyo hankalin mijinta wadda ya ke kur'bar shayin da ta hada masa, cikin kukan ta fa'da mata yadda ta ci makaranta irin FGC KANO, amma kuma Baffan su ya ce ba shi da kudin sa ta a wannan makaran ta. Jim sumayya ta yi kafin ta ce "To ban da abin ki Iyah! Ba sai ki yi ha'kuri ba, kinsan dai nan duniya idan Baffa bai mi ki abu ba, bashi da hali ne, da girman ki da komai ki zauna ki na kuka, akan abin da ki ka san ba da gan gan aka 'ki miki ba?" Shesshkar kukan ta cigaba da yi, Sumayya ta sake cewa "kukan shagwaba ki ke yi Iyah! ni da ba a barni na gama ba fa? Turo baki ta yi kamar ta na ganin ta, tace "To ai ke yanzu maganar ki ta wuce, kuma gaskiya Aunty, ki dena cemin Iyah". da sauri Sumayya ta furta "Yi hakuri Anty Sa'adatu" 'Dan murmushi ta yi hade da jan majina, sannan ta ce"Ina su Abba? Sumayya ta ce "gasu can sun yi barci sun gaji" A haka Sumayya ta lalla'ba 'kanwar ta har sai da ta yi dariya sannan su ka yi sallama, amma Sumayya ta dinga jin jina halin kanwarta na yadda ta ke kai kanta inda Allah bai kai ta ba. Mijin Sumayya da ya fahimci maganar su, sai ya 'kudure abu a ranshi amma bai mata maganar ba, kamar yadda bata sa shi cikin maganar su ba, idan akwai abin da ya ke 'kara mata 'kima to rashin hayaniyar ta da 'karancin buri ne, da wahalar gaske ta bude baki ta ro'ke shi wani abu kai shi zai iya cewa bata ta'ba ba. Abin da ya mata shike nan, sai shi ne da ya fahimci halin ta, sai yake yawan kyautata wa iyayenta, mussaman da ya fahimci suna bu'katar taimakon amma halin su, na wadatar zuci da rik'e girma, basu ta'ba nunawa ba, bare a gane. Kwanaki uku a 'tsakani ya tura ku'di masu yawa ta hannun amintaccen amininshi akan ya je ya kai wa surakin nasa, ayi wa Sa'adatu hidimar makaranta, wadda da 'kyar Malam Basiru ya karba. Ya 'kira Sumayya ya ma ta fa'da akan mai za ta 'dorawa mijin ta nauyin da ba nashi ba? Rantsuwa ta dinga yi akan ita bata fa'da masa ba, sai dai idan ya ji sadda suka yi waya da Iyah ne, sannan kuma bai fa'da mata, zai yi wani abin ba. Yace to " Ki masa godiya kudi masu yawa ya aiko, ki kuma 'kara masa biyayya, ki 'kara ha'kuri dashi" Shikenan sai aka fara shirye shiryen shigar ta makarantar har komai ya kammala. Ana cikin Shirye shiryen sai ga Baffa yazo da dimemiyar katifar yan makaranta har da filo dukkan su(Vitafoam)ne,da kuma bargo duniyar kule amma 'karamin size, sabo dal a cikin jakar shi. Da mamaki Inna ta hau duba katifar ta na fadin "wannan katifar ai ta yan makaranta ce". Sai da ya zauna akan tabarmar da aka shimfida domin shi sannan yace "Wallahi Salamatu wani yaro ne muke gaisawa da shi,tun ba yanzu ba, 'dan gaban tireda ta yake da shago, kullum yazo sai ya gaishe ni, a haka muka yi sabo na gaske. Yau kwanaki uku na fada mishi yarinyar waje na ta ci babbar makarantar gwamnatin tarayya. Bawan Allah sai ya zaci ta kwana ce, ashe wai akwai bangaren ta kwana (boarding), akwai ta je ka ka dawo(day)". Ya numfasa ya dauki kofin ruwan da aka ajiye mishi ya sha, sannan ya 'dora da cewa "Sai ganinsa na yi 'dazu da katifar nan, wai ya kawowa 'yar makaranta, nace kai ma ka na fama da kan ka, ya za ka takura kanka"? Tunda dalibi ne a jami'ar Bayaro, yace min yana shekarar 'karshe, na'ki karba tare da nuna masa ita ba ta kwana ta ci ba, dan haka ya mayar ya amshi kudinsa, nan ya rantse ba zai koma da ita ba, tunda ya riga ya siya, ya kuma yi niyya, abata ta dinga kwana a kai. Kuma abin mamaki har da ku'di wai a siyi littafai" Sai lokacin Inna tace "oh mukam mun gode Allah, Allah ya saka masa da alheri, Allah ya sanya alheri da farin ciki a rayuwarsa". Take kuma ya ce "Iya zo ki dauki katifar nan da bargon nan naki ne, wani yaron arzi'ki ne ya baki, sai ki sa shi cikin adu'oi'n ki". Da murna ta ja katifar tana fadin Nagode Allah ya saka da alheri. "Ya sunansa Baffah?" "Sunansa Muuktar amma ni Mutari na ke ce mishi ya kuma amsa ci ke da girmamawa". Inna ma ta bi sahun Iyah a wurin murna tana sake dauko sabbin addu'a, "Madallah da wannan yaro, Allah ya bashi ilimi mai amfani,ya bashi mace ta gari". Da ga Iyah har Baffan suka hau rige rigen amsawa da Amin. Inna ta sake cewa "sunan shi mai da'di amma ka ke ce masa Mutari? Ni kam Muutar zance" Suka sa mata dariya, Sa'adah na cewa ai ko dai Inna gara ma ki ce Mutarin. A daren ranar ta fito da yar tsohuwar katifar ta, da ta zama tamkar tsumma, ta shimfi'da sabuwa cike da zumudi, a ranta tana ta kwararawa wadda ya siyi katifar fatan alheri. Shigar ta makarantar sai ya 'kara mata girman buri, saboda yadda ta hadu da 'kawaye fe'kak'ku wadda suka fita rawar kai da waye wa. Kusan dukkan daliban makarantar ya'yan masu dashi ne, ko kuma na ma'aikatan gwamnatin da suke daraja ilimi. Arts Class ta zaba a burinta na son zama Barista, ba'a kammala farkon zangon karatu ba (first term) sai da sabo da sha'kuwa ta shiga tsakanin ta da Halima mu'az Matazu, Safina Usman Bunkure, da Humaira Suraj wadda dukkan su iyayen su masu 'kumbar susa ne, itace kadai yar talaka, ko Halima da ba wani kudi ke gare suba, sun wuce matsayin su Sa'adatu, tunda Baban ta ma, aikaci ne a ma'aikatar Revenue yayin da mahaifiyar ta take principal a wata makarantar 'yan mata ta gwamnatin jaha(GGC). Ita Sa'adatu kawai kwalliya da gayu ne ya janyo mata 'kawaye tunda tana samun abubuwa masu tsada daga yar uwar ta Sumayya. Tunda suka hada group basu cika mai da hankali kan karatun su ba, illa kwalliya da kuma soyayya tunda kowa ya san FGC KANO co-education ake yi, ma'ana makarantar maza da mata ne a ha'de. Dukkan su suna da samari a ajin, inka dauke Halima da ta ce ta fi 'karfin soyayya da yara 'kananu, kasancewar tana da saurayi na gaske a gida, wadda ya kasance 'Dan 'kawar maman ta ne. Khalil Ibrahim na cikin wadda su ke son Sa'adatu Bashir, mahaifinsa ne kwamishinan ilimi na Kano a wanccan lokacin, ita ma kuma ya fi kwanta ma ta a rai, dan haka tana kula shi, dukkan kudaden shi na kashewa a makaranta a kanta ya ke 'karewa. Wani lokacin ma har fakar idon mahaifiyar shi ya ke ya debo mata kudi kasancewar ta shahararriyar yar kasuwa domin Dubai take fita ta shigo da kayayyakin mata na alfarma, wani lokacin har da Abaya da lace yake daukowa dan ya bawa Sa'a🤔 Suna da 'kokari amma da yake basu mai da hankali kan karatun ba sai suka sha mugun kaye. Halima da ta kasance ogar su saboda duk tafi su 'kokari ta kuma fi su izza da buri, ita ce kawai ta yi ta shida, amma kowacce a cikinsu ta wuce ta ashirin. Sa'adatu ita ce kashin baya ta kai ta talatin tunda duk sun fita background din makaranta mai kyau. Dukkan su jikin su yayi sanyi da ganin sakamakon su, amma Sa'adatu ba ta wani damu ba, tunda dai ta san daga Inna har Baffa sun san tana da 'ko'kari a makarantar da ta baro. zai yi wahalar gaske ma a wani tuhume ta in dai ba Sumayya ce ta zo garin ba. A cikin wannan yanayin suka kammala SS1, suka shiga aji biyar, budurci sosai, ya bayyana a jikinsu, duk wadda ke FGC KANO ya san da zaman 4stars. Barin Sa'adatu Gogel, ba wai kyau ta fi su ba, a a kawai ita ma'abociyar kwalliya ce kusan kowanne term sai tasan yadda ta yi, tsakanin 'karya da gaskiya an sabun ta mata uniform, sannan ko mai na ta mai tsada ne tunda ga kan sandal, da school bag, Sumayya ta tsaya ma ta a wannan bangaren, duk kuwa da tana mamakin yadda kowanne hutu sai ta canja komai. Hakan yasa ta saje cikin Ya'yan ma su wadata har ma ta fi su daukar ido, mussaman saboda 'kirar jikin ta. Zangon karatu na biyu, a aji biyar din su, a ka turo sabbin 'yan hidimar 'kasa (COPPERS) Cikin su har da Mukhtar Kabir Bichi (MK Bichi). [5/19, 18:52] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 21_22. Ranar da ya fara shiga ajin su a matsayin malamin harshen turanci(English language), ba abin da ya musu illah introduction, wato gabatar da kai, ya sanar musu zai koyar dasu harshen turanci. Bayan sun masa barka da zuwa, sai ya bu'kaci da kowannen su zai tashi ya gabatar da kan shi, as he did. Sa'adatu da hankalin ta ya yi nisa wurin rubutawa Khalil Ibrahim reply din wasi'kar da ya mata na zai je School shop mai ta ke son ci?. Ba ta san har anzo kan ta ba, sai da Halima tace "Gogel"! Sannan ta yi firgit ta mi'ke, ba tare da ta rufe takardar da ta ke rubuta reply din ba, cike da yanga da iyayyi tace ,"I am Sa'adatu Bashir Gogel" daidai lokacin ya 'karaso jikin desk din na ta, Yasa hannu ya na nazarin rubutun da ya 'dauke mata hankali, baice uffan ba ya dauki takarda ya zira a aljihun sa. Wucewa ya yi yana fadin "next" har aka kammala ya cinye period dinshi ya fice tare da takardar. Takaici ya kama ta, ta fara tunanin mai ta rubuta ne? _Nagode da kulawa Khalil komai ka ga ni indai ya burgeka, ni ma zai burgeni, Sa'a luvs you_. Abin da ta rubuta kenan, haka kawai ta ji takaicin wannan Malamin da ya kira kanshi Mukhtar ya kama ta, Ina ruwan shi da ita daga zuwan shi? Washa gari da ya shiga, karatu sosai ya zazzaga musu cikin turancin da ya kama bakin shi tamkar a 'kasar ingila ya girma. Ya yi tambayar an fahimta ko da akwai mai tambaya? Serious student din cikin su ne, su ka shiga tambayar abin da basu fahimta ba, shi kuma ya sake bayani a hankali dalla dalla, har kowa ya ce ya fahimta, sai yace zai yi tambaya. Ba zato yayi pointing Sa'adatu Bashir ta tashi ta yi masa bayanin yadda ta fahimci topic din da ya gama bayanin sa. Nan da nan taji ta muzan ta, saboda ba wani fahimta ta yi sosai ba, ta mi'ke ta na rarraba ido ta kasa furta kalma ko guda cikin tambayoyin da ya ke mata, da 'kyar tace "ban gane explanation din ba dama" Ido ya zuba ma ta yace "We're not talking in Hausa but we're in English" kunya ta kama ta, wato har ya gane ba ta iya mayar da magana da turanci? ya sake cewa "I ask all of you who didn't understand, but you mutter"! Ita dai ba baki, sai ido tana jin wata kunya na kama ta. ya dade yana nazarin ta, sannan yace ta zauna ya sake bayani sosai, a lokacin kuma ta mai da hankali ta na sauraro tunda tana jin maganar, wurin mayar wa ne ke mata tasga'do. Cikin 'kankanin lokaci ya fahimci ita da 'yan group din su, ba abin da suka sa gaba irin kwalliya da soyayya, mussaman idan class ba teacher to hirar kenan. Transfer ta baza ta ce ta sami malaman makarantar, ciki har da class master din B class, na ss2 ajin su Sa'adatu, nan take kuma akasa Mukhtar Kabir Bichi a mastayin Class master din nasu. Wannan damar da yasa mu ne ya 'kudure a ran shi sai ya canja wa'dannan daliban, abu na farko da ya yi musu ya rarraba musu gurin zama ya cillasu ta yadda sai dai hange a tsakanin su. Haka kawai ya ji duk yafi jin haushin Sa'adatu saboda yadda ya lura wadda ta hada kai dasu din sun fita dama, kullum sai ya ga an kawo su a motoci masu kyau, an kuma zo an dauke su, sa'banin ita da ta ke zuwa da kanta cikin adaidaita sahu ko mashin,'kawarta da ya ke ganin suna zuwa tare Zainab Ma'aji sam ba halinsu 'daya ba, ba ta da hayaniya ta na kuma maida hankali wurin karatu duk da ita tana c class, ajin commercial. Amma yayi nazarin sa ya gane buri da ra'ayin Sa'adatu ya kerewa mu'amala da irin su Zainab. Saboda haka sai yafi matsa mata, kullum da kalar tambayar da zai mata, wadda kesa ta muzan ta. Abin da ya lura dashi bawai 'ko'kari ne Sa'adatu ba ta da shi ba, illah mai da hankali ne ba ta yi. sannan kuma tana da (infiority complex). ma'ana rashin 'kwarin guiwa akan kanka, tunda ya gane tsoron kar a mata dariya yasa ba ta son yin magana da turanci. Wannan matsin da ya mata sai ya janyo tsanar shi a ranta, ta shiga fargaban zuwan period 'din shi, a haka har akayi jarrabawar gwaji(Test). ganin a kowanne darasi bata ta'buka ko mai ba sai shiririta, sai ya canja salo ya fara disgata a gaban aji, ta hanyar 'kiran ta da sunaye kala kala, da suke nuni da ba abin da ta sani sai dai ta wanke uniform, ta yi yanga, amma empty brain, har cema ta yake bata dace da wannan makarantar ba. Sannan kullum cikin bada misali da za'kwa'kuran dalibai masu azama yake, takaicin ta 'daya, yadda kullum misalin sa ba ya wuce da Farida Nasir Torodi , tun fil'azal ita jinin ta bai hadu da Farida ba, duk kuwa da ba ajin su 'daya ba, Farida a A, science class kenan, doguwa, siririya sosai, fara 'kal buzaye ne, gashin ta har gadon baya, farkon zuwan ta makaranta har nuna ta ake, na yadda ta ke tuma a cuci a kanta saboda idan ta tufke gashin yake girma, sai a hankali aka gane gashin ta ne. Mai sanyin hali ce ko kadan ba ta da kwarafniya, bata kuma harkar 'kawaye. 'Kawar ta 'daya wadda kullum zaka gansu tare Ru'kayya mustapha. Ga ilimi kamar me, dan kuwa tana cikin 'yan gaba gaba na 'dalibai masu haza'ka a duk fadin makarantar. Sannan iyayen ta ma su wadata ne, domin mahaifin ta ambasadan Niger ne a Nigeria. Wadannan abubuwan da Farida ta hada sai wasu cikin dalibai su ke mata kallon mai girman kai, da 'daukar ita wata ce yasa take ganin ta wuce kula su, shiyasa suma basa wani harka da ita ba ta da farin jini a tsakanin set dinta. barin ma da 4stars da suke ganin sai dai ta nuna musu kyan fuska amma ba dai na jiki ba😀. Yawan misalin da yake yi da Farida ya 'kara tsanar ta a zuciyar Sa'adatu. Cikin abubuwan da ba zata manta suba indan har za ta tuna rayuwar ta a FGC KANO, shine ranar da ya musu dictation wato yana fa'da suna rubutawa, ita kuma slow writer ce, kafin ta kammala rubuta wata kalmar, ya fadi ta gaba, kan dole ta ha'kura da bin, ashe yana lura da ita. Sai da ya gama ta ji ya kira sunanta"Sa'adatu Bashir where's your note?" Cikin daburcewa da tsoron yadda zai kunyata ta, murya na rawa ta tattaro kalaman da zai fahimce ta a gajarce ta ce "My pen stop" kafin ya yi magana anyi attishawa mai 'karfin gaske wadda ta iya shege ce, ba kowa bane illah Fahad Auwal! wadda shima haushin yadda ta za'bi Khalil ta barshi ne yasa yake jin da'din dizgin da ake mata. Hannu ya mi'ka yana cewa "let me see" zuciyarta ta buga amma hakan nan ta mi'ka mishi biron, ya duba ya ga lafiyar biro 'kalau ya watsa mata kallo tare da cewa "out of my class! I am tied of your manners" ta mi'ke sai kuma ta tsaya tace "Am sorry" cikin tsawa yace "don't sorry me, say sorry to ur parents who are keep westing their money". Jin haka yasa ta fita, hawaye ya cika idonta, a baranda ta tsaya amma sai ya le'ka yace mata "on your kneels" kuka sosai ya kwace mata . A ranta ta na tambayar kanta me ta mishi ne ya ke wula'kanta ta? mai yasa ya matsa mata? saboda ba ta da 'kokari ne dalilin? ta ke ta ji in dai 'ko'kari zai sa ta tsira da mutunci a idon wannan mutumin da ya yankewa tozarci cibiya to kuwa za ta nemo shi a ko'ina yake. Sai da ya kammala darasinsa sannan ya fito ya kalleta yace "I want you to borrow your boyfriend's note, and copy what you can't write by urself, if not u will be in.." ya girgiza kan shi ba tare da ya fadi mai zai biyo baya ba . Ya wuce ta yana sa ke fadin "useless girl, you can go back to ur class". Tsawon lokaci ta shafe a gun tana kuka tsabar ba'kin ciki zuciyarta Kamar ta fashe, har sai da ta hango Mr uche's wadda ya ke 'daukan su darasin tsumi da tanadi(economics). sannan ta mik'e ta na kar ka'de jikin ta, ta shige ajin ta na ganin wa'danda dama su na jin haushin su, ita da 'yan group din su, su na bin ta da wani irin kallo, mai kama da madallah. AL'KALAMIN SURAYYA DAHIRU ✍️✍️. [5/20, 16:04] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *Fatan alheri ga marubuciya* *Zainab Ilyas Mazawaje*. 23_24. Tsananin matsin da Uncle Mukhtar ya mata yasa ta zama shiru shiru, ta matu'kar rage kaudi da iyayyi. Kullum tana ri'ke da littafan koyon turanci, ire-iren su Teach ur self. Ta sake mannewa Safina Bunkure. kasancewar Safeena girman Lagos ce, mafi yawan maganarta turanci ne, dan haka ba ta yarda su yi magana da hausa tare da safina, itama kuma Safina ba ta gajiya da gyara mata a inda ta ji ta yi kuskure. Ba'a dauki lokaci mai tsayi ba,ta fara rage tsoron kar ta yi turanci a mata dariya, ganin ta na iya mayar da magana cikin harshen da ke mata nauyi, sai kuma ta mai da hankali akan ragowan darussan gaba 'daya. Ta matu'kar rage shiririta, yanga, da hirar soyayya, da duk wata sharholiyar da su ke, abu 'daya ne ba ta bari ba, kwalliya, wadda wannan kam a jinin ta ne. Su Halima cewa su ke basu ga Malamin da zai uzzura mu su, babu dalili basu yi maganin sa ba. Ita ko tsaki take ja a fili, ta yi shiru. A zuciyarta ko cewa take ai ku ya ga kun iya turanci, kuma yana ganin yadda ake zuwa 'daukan ku a motoci na garari, ni kuwa ya ga ba ko 'daya, ba dole kowacce shara ya debo ya juye a kaina ba. Tabbas tana takaicin yadda ita kadai ya ke gallazawa. Shikuma ganin yadda ta yi laushi ta kuma maida hankali kan karatun ta, sai ya sassauta mata, duk kuwa da zai yi wahalar gaske ya yi darasi bai ce ta tashi tayi bayanin yadda ta fahimci darasin ba, kawai dai kyara da disgin ya rage. A haka har suka yi jarrabawar mock wadda duk 'dalibi ya ke tsoro da fargaban kar ya fa'di. Ana yin hutu da kwana biyu mijin Sumayya ya turo takanas a dauki kannen shi 'yan mata guda biyu da yar autar dakin su, da kuma wadda suka hada uba yar amaryar Baban su, sai ya ro'ki Baffah! akan ya basu Sa'adah ta yi musu hutu tare da 'kannen shi. ba musu ya amince, har gida suka zo suka dauke ta, sannan suka dauki hanyar jos kwata, ta yamma da Bauchi😀. Wannan hutun yana cikin abubuwan da Sa'a bata Mantawa da shi, domin kuwa ta yi matu'kar jin dadin zama da 'kannen Idris yadda suka kasance yara kamammu, marasa hayaniya amma kuma yan kwalliya ne na sosai, shiyasa abotar su ta yi da'di. Sumayya kuwa ba ta matsa musu, hatta abinci wadda suke so shi zata ce su yi, mai gidan kuma kusan kullum sai yasa direbansu ya zaga dasu, sunga gari, da wuraren sha'katawa , sannan kuma duk fita sai ya basu kudin kashewa, wadda ba abin da suke siya sai kayan kwalliya ko dai abin da ya shafi sutura. Ba abin da ya dame su illah tunanin mock exam din da suke fargaban fitowar ta, tunda dukkan su set daya suke Amma makaranta daban daban. Haka suka 'kare hutunsu cikin jin Dadi da mutunta juna, da kanshi Idris ya kawo su har gida tare da kayan tsarabar ni'ki ni'ki, barin ma dankalin turawa da dangin su cabbage da Kara's, harta atile kamar wadda za'a ci a tsawon wata. Baffa da Inna sai godiya suke,tare da sake godiya ga Allah, na yadda Sumayya ta sami mijin daya San alheri yake kuma rama alherin da kyautatawa da mutunci. Barinma idan ta zauna tana bawa Inna labarin daular da Anti Sumayya ke ciki, sai dai ta yi murmushi mai nuna yadda zuciyar ta ke cikin farin ciki. Ba zata yi magana ba sai dai ta bige da cewa kema Allah ya ba ki mijin rufin asiri, yasa ki dace kamar na yar'uwarki. Ita kuwa kai tsaye take cewa "Amma fa Inna gaskiya ni bana son irin tsarinsa, ace mutum duk inda matarka zata fita kace sai ta zumbula hijabi har 'kasa, kuma wai dole sai ansa safa? ko 'dan wanne mazahaba ne?" Cikin mamaki Innar ta zuba mata ido, tare da tafa hannu tana sallallami tace "ke kuwa Iyah wannan tsarin da yake yi na martaba shari'a ne bai Miki ba? Na mijin kwarai shi ke kishin matarsa, ya 'dora ta akan ka'idojin shari'a, wadda zasu gudu tare su kuma tsira tare! "Daular da ya sanyata a ciki ta burge ki, kina kuma fatan ki samu irinta, amma abin mamaki, hijabin da Ubangiji ne yace a saka shine bai miki ba? Anya Iyah, Baffan ku bai yi kuskuren barinki shiga wannan makarantar da ta ke sake girmama burinki ba?" Da sauri tace "Haba mana Inna! ni fa ba cewa nayi kar asa hijabi ba, gani na yi tana da tsala tsala dogayen riguna tunda ga kan yan 'kasashen Oman, Qatar, Saudi, Dubai, masu tsadar gaske masu kauri, amma wai dan 'kauyanci kuma sai akawo hijabi a maka, bayan su karan kansu hijaban ne". Ta fa'da tana fashe wa da dariya. Allah ya shirye ki kawai, Inna ta fada tare da mi'kewa ta yi tsakar gida, tana fadin wannan dogon burin na ki yana ban mamaki Iyah. Ban da 'karya da fariya, da kai kanka inda Allah bai kai ka ba, gidan uban wa kika san 'kasashen da suke sarrafa riguna masu tsada? Naga dai ke kam baki da halin samun su, ban da Allah ya miki gata ya baki yar'uwa mai halin girma tana baki kuncen su, wasu ma ko saka su bata yi, ta ke baki, amma har ki zauna ki karkace baki kina min lissafin inda ake sarrafa su?". Ta cika fam saura 'kiris ta fashe cikin turo baki tace "Amma Inna abin har da gori?" Da sauri tace "Eh dole na goranta miki, dan na ga nema kike ki manta cewa ke'din ba yar kowa bace, face malam Basiru mai 'yar tireda😀wadda ko hanyar inda jirgi ya ke sauka ba ki ta'ba zuwa ba, Amma kina bada labarin 'kasashen duniya, wallahi Iyah ki canja wadannan halayen da nake ganin kina sake arowa kina yafawa". Shiru Sa'a tayi amma takaici ke cin ta shikenan sai mutum ba zai fadi ra'ayin sa ba? Sai a hau mishi gore-gore, har a nemi cewa ya raina shari'a? Hawaye ya siraron mata, ta goge ta tashi ta yi 'dakinta, tana fatan Allah ya bata miji mai kula da iyali kamar Idris, amma ba mai a'kidunsa na asalin bahaushen arewa ba. Kayanta na makaranta ta shiga fitowa dasu tunda ga kan uniform, sandal, school bag dukkan su sabbi ne, ta shiga shirya su ta yadda gobe sai dai ta dauka a kammale. Ba tasan meyasa ta ke 'dokin komawa makarantar ba wannan karon? domin kuwa tunda Mk Bichi yaje makarantar ko hutun weekend ne fargaban zuwan Monday take yi. Wata'kila kuma dan ta sami sau'kin kunyata ta da yake yi ne. Amma Kuma duk da sau'kin da ta Sami a bangaren shi, haushin shi da tsanar shi na nan cike a zuciyar ta. kwanukan abincin su ta wanke su tas kafin ta kammala wanke wanken har gawayin ya fara kamawa, dan haka ta cika tukunya ta dora ruwan wanka, tana gama wanke kwanukan, sai kuma ta hau share tsakar gidan hadi da wanke dan matsakaicin bandankinsu, kafin wannan lokaci kuma ruwanta yayi zafi, ta juye ta shiga wanka! bayan ta maida ruwan kunu da ta jefa mishi tsamiya kan wutar. Tana fitowa a wanka innarta ma ta fito tsakar gida, tana ganin yadda Sa'a ta gyare mata gida tsab. Da'di ya kamata na yadda ko kadan Iyah bata da son jiki. Ba zato ta ji anrungumeta tare da cewa "morning Innah" Ture ta tayi tare da cewa "oh ni kam Ina kallo a gun ki". Dariya tayi tare da fadin "Inna gaisuwar kawai shine abin kallon"? Wuceta ta yi tana bude ruwan dake Kan gawayi, ganin yana shirin tafasa yasa ta fara shirin dama kunun, ita kuma sa'a tayi 'daki tana shiryawa. Cikin 'kankanin lokaci da dama kunun, ta kuma dauko fulawar data kwaba a 'karshen dare dan yin fanke, ganin ta tashi sosai yasa ta maida mai kan wutar tana shirin suya, tana kwashe kaskon farko Sa'adatu na fitowa ta shirya amma bata sanya uniform ba. Ganin yadda innarta ke kwaso fanke yayi brown ya tashi sosai, da'di ya kama Sa'adatu. Sai kawai tafara rawa tana juyi tana wa'kar "Mamana, mamana! mai sona, mai tattalin zuciyata". Kwafa Inna ta yi tana fadin "zanga sadda za ki girma Iya" "Idan Kinga na girma sai kin haifa min 'kani ko 'kanwa". Ta wuce ta dauko, kofi da plate tana fadin "Allah Inna Ina son 'kanne gashi Anti Sumayya tayi min nisa bare na dinga debo su Khalifa". Ta fa'da cikin muryar tausayi tamkar hakan zaisa innar ta haihu yanzu yanzu. Numfasawa Inna ta yi sannan tace "Ai kin kusa samun 'ya'ya ma indai kina da rabo, ba'di iyanzu ai kina dakin ki ". Daure fuska tayi, sannan tace "Nifa sai na fara karatu". Da sauri Inna tace "Inma karatun za ki zama sai dai a dakin ki, tun yanzu kina ruwan ido kowa ya zo kice ba kya sonsa, amma kuma kina son duk wani abu da zai 'kullo ya baki". Mi'kewa ta yi bayan ta debi kunu da fanken tana cewa "To Inna ai ba ro'konsu nake yi ba, Kuma Annabi yace ba kyau mai da hannun kyauta baya" "Wannan maganar dai kin fi ri'keta a duk maganganun Annabi. saboda ta dace da ra'ayin ki, amma saka hijabi da ke yaci karo da tsarin ki, ai jiyan nan a gabana kika ce 'kauyanci ne" Kasa magana tayi kawai ta shige 'dakinta, ta fara cin abincin ta, tana ayyanawa a zuciya duk saurayin da yayi gigin yi mata kyauta, ita ko ba zata 'ki amsa ba, tunda dai ba ro'kon su take yi ba. Tana gama karyawa ta fita da kayan sannan ta sake yin brush wadda sau biyu take yi a kullum safiya tun Inna na mitar barnar makilin har ta gaji, ganin hakan yasa Baffa ya ware mata makilin din ta yana cewa uwar masu gida dole a bata komai, indai ba wadda ya wuce ka'ida bane. Sai da ta shirya tsaf ta fito tana fadin Inna zan tafi, kallo daya ta mata taga yadda ta yi kyau tamkar ba uniform tasa ba, tasan 'yarta mai kyau ce fiye ma da Sumayya dan dai kawai ita duhun fatar mahaifin su ta kwaso amma Ubangiji ya mata cikkaken diri. Ta nisa tace "Iya! wannan turaren na ki bana zuwa makaranta bane,'kamshin sa bana shiga cikin maza bane". "To Inna" ta fada a gajarce ba dan ta gamsu ba. " 'Daga can ki dauki kudin makarantar,yau Baffan ku jana'iza ya tafi tun sallar asuba bai dawo ba". Turus tayi dan kuwa ba yadda za'ayi tasa hannun ta a wurin sana'ar Inna tunda ta riga ta shirya. Ganin yadda taja ta coke tasan ta'bawa ne baza ta yi ba, kwafa tayi sannan ta mi'ke ta 'daga daron kayan, ta 'kirga kudin ta mi'ka mata, maimakon ta karba sai ta mi'ka mata pos din akan ta sa mata a ciki, hakanan tasa mata tana mata adduar shiriya, tun tana yar 'karamarta, bata son daddawa da kuka, da kubewa bushasshiya, da Inna ke 'kullawa tana siyarwa. A bakin titi suka hadu da Zainab kamar kullum,suka rankaya suka tafi. Suna Isa makarantar suka tarar da dodon na ta on duty, yana sizing kayan da makaranta ba ta yarda dasu ba. Kowa yazo sai ya gaishe shi, hatta Zainab Ma'aji sai da ta risina ta gaida shi cike da girmama wa, amma ita banda kirne fuska ba abin da ta yi. kallo ya bi ta dashi yana raya wadda duk ke mata gugar kaya, ya kamata a bashi sarautar shugaban masu guga. Ita ko sanin ba wani abu na karya doka a tare da ita yasa bata ji 'dar ba. Har sun wuce sai yasa baki yace "Gogel" Zuciyarta ta buga tare suka juyo da Zainab, amma sai yace Zainab ta tafi, itakuma ta dawo, tsaye ta yi mishi 'kerere fuskar nan tamkar gobara, ta gefen idonshi ya ke 'kare mata kallo baisan mai yasa kyaun da ta yi cikin sabon uniform 'dinta ya mintsine shi ba. Sassanyan 'kamshin da ke tashi a jikin ta ya matu'kar ta'ba shi, ta na zuwa gaba daya gun ya cika da 'kamshi. ita kanta bata san tsadadden turare bane dan kuwa na Sumayya ne ta dauko mata. Ba tare da ya kalle ta ba yace "On ur kneels" Nan da nan hawaye ya cika idon ta wanne irin mugun mutum ne wannan? mai ta mishi zai wula'kantata daga dawowa? haka ta zube cikin 'kasa da ciyayi bai sallame ta ba, sai da ya tabbatar ta shiga sahun 'yan late comer's(makararru). bayan ya mata bulala biyar a hannu masu zafin gaske, yana ce mata " for ur indispline manners, u are not here only to learn, but da tarbiya in ganeral". Haka nan dai aka sake mata punishment (horo)na latti. a wannan rana haka ta yini da ba'kinciki, murna da ake na shigar su aji shidda ita kuka ne ya maye gurbin, hankalin Khalil dana 'kawayen ta ya yi matu'kar tashi sai lallashinta suke. dukkan su tsanar Mk ta cika 'kalbin su mussaman ma Khalil da ya ke jin tamkar ya yi hayar yara a bishi unguwar su a mishi dukan kawo wu'ka. Alkalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍🏼 `Alkalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍🏼 [5/22, 12:02] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*!🌺 ·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 25_26. Kwanci tashi har jarrabawar mock ta fito cikin ikon Allah Sa'adatu ba ta sami matsalar komai ba tasan kuma MK ya taka muhimmiyar rawa ga samun nasararta, tunda a sanadin matsin da yake mata yasa ta zama cikin jerin daliban da suke nacin karatu. A wannan term din kuma ta tsinci kanta da jin haushi idan ta gan shi da Farida, gashi dai ta tsane shi, amma ko yaya ta gan shi da ita, musamman da ya kasance Farida Prepect ce, kuma mafi yawa idan shi ne Duty Master, to kuwa za ta kasance Duty Prefect, sai ta ji ranta ya mugun 'baci. A yanzu tafi jin takaicin 'kokarin da Farida take da shi fiye da komai cikin FGC. Kasancewar Farida na cikin daliban da suke wakiltar makarantar gaba'daya, dan yanzu ma shirin tafiya Lagos gasar Cowbell Competition suke yi, tunda sun cinye na jahar Kano, yanzu matakin 'kasa zasu tafi, kuma Uncle MK din na cikin tawagar Malaman da za suyi masu rakiya zuwa birnin na Ikko. Wannan dalilin sai ta sake zama so mute, ita kadai ta san mai ta ke going through a zuciyarta. Kullum idan ta zauna ta dinga bincikar kanta, me yasa ilimin Monica Paul bai dame ta ba?me yasa Khalil Ibrahim da yake da 'kokarin shima bai dameta ba, tunda har da shi za'ayi ma tafiyar? Kanta har zafi yake dauka akan wannan tunanin. Kyashi take mata ko kuwa hassada ne?. Kullum kuma indai ta ga Farida, a ranta sai tace, oh ance mutum tara yake bai cika goma ba, komi da ake so Farida ta hadasu, doguwar mace, Fara tas, mai dogon gashi, mai ha'kuri, mai tarin ilimi gashi ta yi sa'ar fitowa a gidan wadata, kawai dai ba ta da dirin jiki, sai tsananin kyaun fuska. siririyace ta sosai, shiyasa komi na jikinta 'karami ne. Sannan kuma ta lura bata da cikakkiyar lafiya wadda takan shafe sati idan ciwon ya tashi ba tazo ba. wannan ciwon da rashin cika irin ta cikkakun mata, shine tawayar da tasa bata cike goma cif cif ba. Tauraron Farida ya sake haskawa ne bayan sun yi nasarar zuwa na 'daya a gasar da suka yi, wadda itace tafi bada amsa a tsakanin Monica da Khalil. Kowa nan nan yake da ita tunda ga kan principal da sauran teachers, dama student gaba daya. Wannan ya sake sa tsanar ta a zuciyar 4stars da suke jin su din isassu ne. A kuma wannan term din Sa'a ta dage, ta 'kure malejin jarumta, ta dau ki 8th position, wadda shine sakamakon farko mafi kyau a tarihin rayuwarta, dan ko a makarantar da ta baro, double lamba take dauka, bare wannan makarantar da ta ha'da za'kwa'kuran 'dalibai. Wannan sakamakon shine mafarin dai na 'yar tsamar su da Uncle Mukhtar, duk 'karshen zangon karatu ya wajabta wa kanshi bawa daliban ajin nasa daga na daya zuwa na uku kyautar 'karfafa guiwa, a matsayin sa na class master dinsu, a A class ya bawa Farida. A wannan karon har Sa'adatu ya bawa kyautar the most hardworking student in the class, Kamar kullum Khalil Ibrahim ke daukan 1st position, shi ya 'Kira a 'karshe bayan ya bawa Sa'a. da monicca as 2nd, da wani Abdulrashid da ya zo na uku.amma da yaje karba sai yasa left hand ya Kuma juya fuskar shi, wannan rashin 'da'a da ya nuna ya hassala Mk ya fasa bashi kyautar ya kuma hukunta shi ta hanyar sa shi, sharar school area. Tunda ga nan aka fara cece kucen son Gogel yake banda haka, ta yaya ga Halima ta zo ta hudu bai bata ba, ga na biyar, duk ya tsallake ya tafi Kan 8? asalima sai da wannan kyautar ya kawo mata matsala tsakanin ta da Khalil da kuma Halima. Na Halima kyashi ne, shikuma Khalil kishi ne, gani ya ke kawai soyayya suke yi amma ai kowa yasan yadda ya takura mata, menene dalilin gift din? alhalin akwai wadda suka fita cancanta amma bai basu ba. Kusan wannan ta'kardamar ne dalilin afkuwar soyayyar ta su dan ta dade tana jin kishinsa akan Farida bata gane kishi bane sai a wannan lokacin daya sake da ita, ya gamsu tana karatu kamar yadda ya kamata. Ranar juma'ar da akayi hutu, tana cikin ranakun da bata Mantawa cikin rayuwar ta a makaranta, a ranar ne ta nutsu ta 'kare mishi kallo na tsanaki, a lokacin da ya shigo dan ya musu bankwana sai kuma bayan hutu. Dogon saurayi mai matsakaicin jiki, ma'ana siriri ne, amma kuma bashi da rama ko kadan kai tsaye za'ace mishi fari, duk da idan irin su Farida na gun, duhunsa za'a gani, doguwar fuska mai dauke da dogon hanci, da madaidaitan idanuwa, farare tas, da zagayayyen 'karamin baki mai dauke da 'kananun ha'kora jerraru, ya kuma zagaye bakin da gemu. yanayin sa tamkar 'kani ne ga tauraron wasan kwaikwaiyon nan Yakubu muhd saboda yadda suke yanayi. sanye yake cikin shadda fara 'kal, ma'abocin tara suma, mai kuma yawan gyarata dan kullum comb din shi na aljihunsa, hular yan bautar 'kasa ya saka, kafar sa dauke da open takalmi ba'ki, hannunsa daure da agogon silver samfurin (D&G). tun kuma a lokacin yake amfani da turaren Versace,'kamshin sa na cikin abubuwan da dalibai ke magana akai. A wannan kallon da ta mishi na 'kurillah ta janyo wa kanta, domin bata dauke idon ta akan shi ba, sai da son shi ya cika zuciyar ta dam, irin son nan da yake shiga ba tare da an ankaraba, lokacin da za'a ankare din ya riga da yayi illar da ba yadda za'ayi dashi. Da kanta ta dinga cewa Madallah da 'ka'idojin musulunci, sai da akace kallon shari'a 'daya ne tak, amma ni na mishi kallon 'kwal uwar 'daka. Nasiha ya musu, akan ko a gida su dinga bitar karatunsu, su kuma zama yara masu tarbiya, ta yadda duk inda aka ga 'dalibin FGC KANO aga ya banbanta da na kowacce makaranta soboda ladabi. 'karshe ya kulle bayanin shi da lallai su kyautata wa iyayen su, su musu biyayya, su kuma taimake su akan sha'anin ayyukan gida. Ya kalli side din maza yace "wadda kuke tu'ki, ku bi a hankali kusa nutsuwa". Banda kallon shi ba abin da Sa'a keyi tana jin turancin sa tamkar Baturen da yanke wa yaren cibiya. Yana kammala wa yayi waving hannun shi alamar bye, ya fice da sauri. Basu bar class din ba sai da Safina ta yi sulhu a tsakanin Halima matazu da Sa'adatu Gogel, dan haka rabuwa suka yi ta salin alin a tsakanin su tare da al'kawarin zasu hadu a gidan su Humaira asabar din sama, bata gobe ba. Tafe suke ita da Zainab da Asiya wadda yayar Zainab din ce. kamar ance ta juya ta hango Uncle Mk da Farida a tsaye jikin wata bishiya da dukkan alamu ba a zo 'daukar ta ba, hira suke hankali kwance. Take ta ji tamkar ta mutu, zuciyarta ta daure,'kirjin ta yayi nauyi ainun, tafiya kawai take amma bata sanin inda take jefa 'kafarta. Suna tsaye a bakin gate din makarantar suna jiran abin hawa ta ga yazo ya wuce su akan mashin 'dinsa da a wancan lokacin ake mishi la'kabi da tsuntsun soyayya. Hannu ya daga musu amma sai ta juyar da fuskar ta, tayi kamar bata ganshi ba, Zainab ce kawai tayi waving 'din shi. Tana isa gida 'dakin ta, ta wuce ta fa'da kan katifarta wani kuka ya kwace mata, tayi abinta ta 'koshi kasan cewar Innar ta na wanka, daga kukan barci yayi gaba da ita, sanin da mahaifiyar ta yi na fashin salla take yasa bata tashe ta ba. Haka ta yi hutun nan su ku ku, ciwon so na wahalar da ita, a tunaninta tasan so akan khalil, Ashe ba son sa take ba, kawai shakuwa ne da kuma yadda yake mata hidima, a yanzu ne take dandana azabar soyayya, yanzu ne take jin so tun daga zuciyarta, idanuwanta, da gangar jikinta gaba'daya. Idan ta tuna Farida yake so, sai taji tamkar za ta sume. A yadda ta ji ciwon ganinsa da Farida a tsaye yana mata magana cikin walwala komi yana iya faruwa da ita idan ya kasance kullum zata na ganinsa tare da ita. Zaune ta ke tana fargaban komawar ta makaranta wani satin, a da ta dauka zullimin zuwa makaranta ya 'kare tunda yanzu ta tsira daga tozarcin Uncle Mk! ashe tsugunne bata 'kare mata ba?. Agogon bango ta kalla taga 2:30pm da sauri ta 'mike ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin lallausar atamfar quali-wax mai kalar samaniya(Skye blue)da ratsin ja, Riga da skirt ne, dinkin yayi matuqar zama a jikinta,'katon jan 'dan kunne mai round tasa, a lokacin yayin kwalliya irin ta wannan zamanin ba tazo ba, amma duk da hakan ta she'kawa fuskar ta kwallliyar da ta dace da ita. Mayafi jah ta ya fa, sumfurin(internet). ta sanya takalmi half-cover amma hills. da yar mitsitsiyar jakarsa wadda zuwanta jos ta siyo su masu Jan duhu. ta fesa turare ta fita zuwa 'dakin Inna. Inna na shirya, mi'ke wa tayi daga kishingidar da ta yi, hannun ta ri'ke da carbi tunda ta idar da sallar azahar bata tashi ba. "Yanzu Iyah ba za ki daina zabga turaren nan idan zaki fita ba? Ba kyau fa, ki kiyayi taba shari'a wallahi" A hankali tace "Allah Inna 'dan ka'dan ne, kawai 'kamshi ne dashi". "To tunda kin san yadda yake dole ne, idan zaki fita sai kin saka? Ki fa dinga jin tsoron ubangijin ki, kina kiyaaye ka'idojin shari'a". Kafin tayi magana, ta sake cewa "A gabana kika ce da Baffan ku, bayan la'asar za ku dawo, ki sani idan kika wuce wannan lokacin ba zan 'ki fada mishi ba" "In sha Allah bazan kai maghrib ba Innah" "Sannan kuma kiji tsoron Allah idan mu bama kallon ki, shi yana kallon ki. inda kika tambaya nan kawai aka lamince miki zuwa. Sai kin martaba kanki, kafin wani ya martaba ki, sannan kuma duk saurayin da ya tsayar da ke kice mishi yazo gidan ku, ya nemi izinin magana dake a wurin mahaifin ki." A sanyaya ta amsa da "Zan kiyaye Inna" Sannan ta juya ta tafi, tana rayawa ko sai yaushe Inna za ta dena mata bitar wannan nasihar a duk sadda zata fita? Jikin ta yayi sanyi, nasihar ta matu'kar ratsata. take ta ji ta fasa zuwa inda ta yi niyya, tunda gidan su Halima zata je su hadu da Khalil dake duk kusan unguwar su daya. Tunda akayi hutu basu hadu ba, a dalilin fushin da yake yi da ita, yana zargin soyayya suke ita da Uncle Mukhtar. Baisan gidan su ba, kullum cewa take ba a barinta yin zance, sannan indai aka ganshi yaje gun ta za ta Sami matsala babba, nan kuwa gani ta ke da kunya yazo ya ga gidansu. Nasihar Inna tasa ta canja shawara gara kawai yau ta kaiwa Zainab Ma'aji ziyara ta huta da gorin da ta ke mata na ba ta zuwa gidansu, tunda dama nan ta cewa iyayen ta za ta. Tana fita yar tafiya tayi 'kadan, tana jiran ta tsallaka, kamar ance 'daga kanki kawai sai idanuwan ta ya fada cikin na shi yana fitowa daga wani shagon aski da ke gaban gidansu kadan. Mamaki ne ya kamashi ya tsallako ya same ta, tuna nasihar da ya musu na nuna ladabi yasa ta risina tare da fadin "Barka da rana" Maimakon ya amsa da hausa sai ya juya harshe, yace "Sa'adah how are you"? how ur parents and everything?" A hankali tace"very fine" Ya sake fadin "are you living here?" Kai kawai ta 'daga tare da nuna mishi gidansu "this is our house" bata san mai yasa shi bata ji, kunyar nuna masa gidan nasu ba, kamar yadda ta ke jin kunyar su Halima da Khalil su ga gidan. duk kuwa da bashi da makusa tunda ginin bulon siminti ne, a shafe yake da filasta, 'kyauren 'kofar shiga lafiyeyye ne mai aminci, sabanin gidajen su 'kawayen nata manyan gates ne dasu, masu zubin mahadi ka ture mussaman gidan su Safina da Humaira Suraj, nasu Halima ne dai ba wani shararren gida bane amma darajar unguwar ma kadai ta kerewa tasu unguwar. Yayi murmushi tare da fadin "wonderful I know ur father since" Da mamaki ta kalle shi tace 'Realy"? "Sosai kuwa for over 5 years, is he around?" "No yaje Gogel 'dazu" "Said it in English" Ta tura baki alamun ya fara son 'kureta wadda shikuma hakan da tayi drives him crazy. Tace, "He went to our Home town" ta tsuke bakinta ta yi shiru in ma bata yi dai dai ba 'karshen dagewar ta kenan. Murmushi yayi ya sake cewa "oh rude Sa'adah!" Har cikin ranta take jin dadin yadda ya yanke sunan yake fadin Sa'adah! Bashine farkon fa'da mata hakan ba, amma shine farkon wadda ya iya fadin sunan, shinea farkon wadda yasa mata son sunan. Ba zato ta ji yace "where's is ur loverboy"? Kunyar duniya ta kamata ta yi 'kasa da kai tana jin kamar 'kasa ta tsage ta shige, Ganin yadda ya kunyata ta, yasa shi tambayar inda zata, Kai tsaye tace "Gidan su Zainab Ma'aji". Sai ya mata sallama, ya tsallaka ya hau mashin dinsa. ganin haka yasa ta wuce ta nufi gidan su Zainab. Cike da shauki ta isa gidan su Zainab din, a dakin dake mallakin tane da yayarta Asiya suka zauna, suna hira, tare da Anty Asiya gaba'daya, cike da farinciki take basu labarin haduwarsu da Uncle Mk yanzun nan. Asiya ta ri'ke baki tana kallon yadda Sa'adatu ke bada labarin shi cike da 'doki da farin ciki, kasa 'boye mamakinta ta tayi, tace "Sa'adatu da wuri haka?" Cike da rashin fahimta tace Kamar "Yaya da wuri haka, ban fahimce ki ba?" Cike da iya shege Asiya tace "Ato na ga a duniya kin washi ayi maganar bawan Allah nan, abin mamakin kuma sai gashi yau da kanki kina hirar shi cike da shauki da jin dadi, shine nace da wuri haka har 'kiyayyar ta 'kare?" Kunya ta kamata sai cewa tayi "Ni fa ba gun ki nazo ba, kuma bada ke nake zance na ba". Dariya suka sa mata daga Zainab har yayar tata, take kuwa takaicin su ya kamata sai kawai ta fashe musu da kuka. Nan da nan kuma jikin su yayi sanyi, suka gintse dariyar, suka hau bata ha'kuri, barin ma Asiya da ta ke ta fadin "daga wasa, nifa tsokanar ki nake, to yi ha'kuri ba zan sake ba" da ga haka ta mi'ke ta bar musu dakin cike da mamakin shagwaba irin ta Sa'adah. Da 'kyar Zainab ta shawo kanta ta huce, ta shiga bata labarin tunda akayi hutu basu hadu da Khalil ba, saboda yana fushi da ita akan Mk. Tabe baki Zainab ta yi tana fadin jimin yaro da 'karfin hali, to shi da nufin sa baza ki kula wani ba? bama shi da hankali. Sanin da Sa'a ta yi Zainab ba ta yin Khalil, ya sata tsuke bakin ta, har sai da ta gama caccakar shi ta 'kosa dan kanta, ta bar maganar. Wai a Ina kika ga Uncle Mk din? Zainab ta tambaya cike da son jin 'karshen maganar da Asiya ta so watsawa. Bata rai ta yi tace inace dariya ku ke min?" "Ni ba ke na yiwa dariya ba, Yaya Asiya ce ta bani dariya da ta shiga zancen da ba na ta ba". Numfasawa ta yi tace "A 'kofar gidan mu ya fito a wannan shagon na The Boss barbing shop". Amma dai kin gaishe shi, Zainab ta tambaya da sauri. "Ah sosai ma har hira mun yi" Murmushi Zainab tayi tare da fadin "In sha Allah wannan ne mafarin hirar taku, ba 'karshe ba" Da sauri Sa'adah ta dube ta, tace "saboda me kika ce haka?" Kai tsaye ta bata amsa da cewa "saboda kuna son junan ku" Sunkuyar da kai Sa'adah ta yi tana mamakin yadda ta hasko tana son Mk, sanin Zainab akwai ta da sa ido sai ba tayi mamakin gano ta da ta yi ba. Kamar zata yi shiru sai ta kasa tace "Zainab shi ba ya sona, Farida ya ke so", ta fada cikin muryar kuka. Hannunta Zainab ta ru'ko cikin lallashi tace "Wallahi yana son ki, ke duk wannan takurar daya miki a banza ce? kin ta'ba tunanin mai yasa ke kadai ya damu ki maida hankali a kan karatun ki? Ni na dade da gane yana sonki amma irin mutanan ne masu kiyaye doka da oda. kinga ai bai dace ya nuna miki soyayya alhalin aikata hakan laifi ne babba da hukumar makaranta ba za ta amince da shi ba, Sannan Farida 'daliba ce mai haza'ka irin su farin jini ne da su a gun dukkan malami ba wai Uncle Mk ba kawai. gaskiya ba sonta ya ke, so irin na soyayyar saurayi da budurwa ba, illa 'kaunar da malami yake yiwa dalibarsa mai ladabi da haza'ka". Cike da gamsuwa Sa'adah ta sake cewa "Ba kya ganin 'kaunar da ya ke mata zai iya juyewa zuwa irin son dana ke jin tsoro?" Shiru ta yi na 'dan lokaci,sannan ta nisa tace "Sa'adah gaskiya zai iya juyewa amma idan kin cigaba da bada 'kofar faruwar hakan". *Alkalamin Surayya Dee* ✍🏼✍🏼 [5/22, 12:02] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 ·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *Gaisuwar fatan alheri ga Zauren Fadila lamido!* *BA LABARI FANS 2* _MK DA SA'ADAH NA GAISUWA_🥰. 27_28. Cike da fargaba ta zuba wa Zainab ido, zuciyarta na bugawa ta ce, "Ban gane ba?" Muskutawa Zainab din ta yi sannan ta ce "Ina nufin ki toshe dukkan 'kofofin da kika bude na rashin 'da'a a gabanshi, kinga yanzu ya gamsu kin canja, kin shiga sahun 'dalibai masu dagewa, to ki tattaro dukkan ladabi da nutsuwa ki sanya su a fuskarki da dukkan ayyukanki, ba iya haka ba har a zuciya, ina tabbatar miki idan kika yi haka kin rufe 'kofar da zai dinga miki ganin mai 'karancin tarbiya. Sannan ki yi addu'a, ki bar wa Allah za'bi, idan alheri ne kuma an 'kaddara mijin ki ne, kina zaune Allah zai turo miki shi". Shiru ta yi tana nazarin maganganun Zainab, wanda ta tabbatar iyakar gaskiya ta fa'da mata. Ta nisa sannan ta 'dago ta ri'ke hannun Zainab ta ce Na fahimce ki, na kuma gode da shawarar ki, amma don Allah ki ri'ke mini sirrina." Murmushi Zainab ta yi tare da cewa, "Ki sa a ranki amana mu ka yi wannan maganganun, kuma mutum amintacce ne mai 'rike amana. Ina tabbatar miki da ikon Allah baki da matsala da ni" Haka suka ci gaba da hirarsu, bayan sun yi sallar La'asar ba da jimawa ba, ta musu sallama ta tafi, Zainab ta raka ta har kusan gidansu. Tunda suka koma makaranta gaba'daya ta mayar da hankali kan karatu, sannan ta bi shawarar Zainab, don haka gaisuwar girmamawa tare da mutuntawa take wa Uncle MK, har ya ji cewa lallai wannan ita ce Sa'adah 'diyar Malam Basiru, waccan da ta gabata ta aro ce. don haka ya daina duk wani gallazawa da yake mata, sai ma wani shiri da yake da ita. Wanda hakan ya janyo hankalin 'dalibai aka fara gaskata ra'de radin da ake yi cewar son ta yake yi. Wani abin mamakin kuma ita ma Farida sai ta fara jin haushin Sa'adah, tana ganin ta tamkar wata 'yar fashi a soyayya ko mai barazana a rayuwarta. ta san duk yadda take da 'kyaun da ya kai ya kawo, ba ta yaudari kanta ba, ta tabbatar ba za ta nuna wa Sa'adah komai ba, sai fari da gashi da kuma tsayi. Amma batun cikar halitta da kuma boyeyyen kyau da sai an nutsu ake gane shi ta sani Sa'a ta kere mata. Wata rana sun hadu a Biology Lab, kawai Sa'adah sai ji ta yi Farida ta ce "Iyah Basiru" Ranta ya yi mugun 'baci, tunda da izgilanci ta fada mata, take ko ta 'daga murya ta fara mata sababi, saboda Sa'adah mafadaciya ce ta gaske, sai dai kuma ita wacce ta yi tsokanar ta si'dade ta barta a gun. Wanda hakan da ta yi har ya fi wa Sa'a ciwo fiye da tsokanar da ta mata. Shike nan sai Farida ta mayar da tsokanar ta zame mata 'ka'ida sai dai idan ba su hadu guri 'daya ba, ranar kuma a shop suka hadu ta faki ido ta galla mata harara tace, "Sa'ade gwalli" Abinka da wanda aka dade ana tsokana kuma mai 'karancin ha'kuri sai kawai ta zabura ta kai mata wawura, ta sha'ke ta da 'karfin gaske, nan da nan hankalin mutanan gun ya kai kansu, aka taru aka karbe Farida a hannunta, tana mayar da numfashin wahala dan ba 'karamin sha'ka ta sha ba, musamman da ke ba ta da da kuzari saboda rashin cikakkiyar lafiya. Aunty Ngozi malamar (Mathematics) ce ta zo wucewa ta tsaya tana tambayar ba'asi, bayani aka mata wanda kusan duk gurin shaida aka wa Farida cewa tana tsaye kawai aka ga Sa'adatu ta kama ta da kokawa. Saboda haka sai ta tattara su ta tafi da su Staffroom wanda a can aka yi shari'a. Kusan dukkan staff din bayan Farida suka bi, saboda rashin hayaniyarta, ga ta kuma hazi'ka ce, haka aka yi punished din Sa'adah ta hanyar sa ta shara da kuma gargadi mai tsanani, akan komai za a mata ba ta da ikon daukar doka a hannunta. Hatta Uncle MK, Sa'adah ya jawa kunne akan zai yi wahalar gaske Farida ta tsokane ta wanda hakan da yayi yasa ta jin wani takaici ya kama ta fiye da yadda aka ba ta horo bayan kuma ita ce da gaskiya. Wannan abin ya yi matu'kar tsaya wa Sa'adah a ranta, shi yasa ta ji gaba'daya makarantar ta fita akanta musamman ko yaya idan ta ga gilmawarshi da Farida sai ta ji dukkan walwalarta ta kau, duk da dai ba ta da tabbacin abin da take zargi a tsakanin su. Tunda ga nan kuma Farida ba ta sake marmarin tsokanar Gogel ba dan kuwa ta ji 'kamshin mutuwa a hannunta🤩. Ana cikin haka aka fara register din JAMB, tana fada wa Baffan su maganar kai tsaye ya ce mata ba wata jarrabawar shiga Jami'ar da za ta yi don kuwa aure zai mata idan mijin ya yarda sai ya siya mata ta yi a 'dakinta. Wannan ma na cikin damuwar da ta sake sa mata tsanar FGC KANO. Dukkan 'yan ajinsu za su yi wannan jarrabawar sai ita kadai ce a ajin za a ce ba za ta yi ba. Wanne irin koma baya ne wannan? Wannan ba da kai har ina? Kamarta ace ita ce koma baya a komai?🤔 Sa'adah ke nan! Wadannan damuwowin sai suka sa ta ji gara ta koma asalin makarantar da ta bari a baya ta zana jarrabawar kammala sakandire, nan ma da ta gabatar da maganar gaban Baffa tare da ba shi uzirin ai ba sosai ake cin jarrabawa a wannan makarantar ba, kai tsaye ya ce mata bazai yiwu ba, tunda anriga an biya mata kudin jarrabawar ba, ba za a yi asarar su ba, wannan shi ne karon farko da Baffan bai goya mata baya akan wani abu ba. Ganin ba ta sami goyon baya ba, ga kuma ba'kin cikin da za ta kwasa a FGC KANO, sai kawai ta daina zuwa makarantar gaba'daya, wanda hakan bai damu Baffanta ba, sai cewa ya yi to ta fito da miji, ai Sumayya ma ba ta sami hakan ba ya aurar da ita ga shi nan kuma tana zaune lafiya cikin rufin asiri mai yawa, fiye ma da wanda suka yi karatun. Inna kuwa uffan ba tace mata ba saboda yadda take ganin take-taken Sa'adah nan gaba fin 'karfinsu za ta yi, garama a aurar da ita ya fi mata kwanciyar hankali. Tsawon sati tana gida ba ta je makarantar ba, rannan da yamma tana kwance a dakinta, tunda yanzu Inna fushi take da ita sosai, don haka ba ta jin da'din zaman gidan gaba'daya, ta ji murya Baffa na fadin"Iyah" Da sauri ta amsa ta fita tsakar gida inda yake tsaye, ta tsugunna tare da cewa "Gani Baffa" Ya kalle tay ya ga duk ta lalace tsabar fitinar da ta sawa ranta. ya ce, "Da ma yaron nan Mutari ashe a makarantarku ya ke koyarwa?" Shiru ta yi tana nazarin sunan, kafin ta ce, "Wani abu ya sake cewa?" "Dazu ya same ni a inda nake zama shima nan ne wajen zamansa ya tambaya an tabbatar masa nan ne gidan ku, ya yi mamakin yadda, bai gane ke yarinyar wajena ba ce sai a kwanakin nan, kuma ya ga ba kya zuwa makaranta shine ya tambaya lafiya kuwa?" Ya nisa sannan ya ci gaba da fadin, "Na fada masa kawai makarantar ne ba kya so, ni kuma ban takura miki sai kin ci gaba da zuwa akan dole ba, amma ba zan zauna na zuba miki ido ba, aure zan miki! Ya ro'ke ni alfarmar yana son ya zo ya ganki ya ji dalilinki na gudun makarantar alhalin aski ya zo gaban goshi, na amince masa ya zo ba dan komai ba, sai don mutuntani da yake yi, katifar ma da kike kwana a kai shi ya kawo miki ita, don haka idan an yi sallama da ke bayan La'asar na miki izinin ku tsaya a zaure" Kai ta 'daga tare da cewa "To" ya juya ya fice ita kuma ta koma daki tana jin faduwar gaba. 'Karfe hudu da rabi 4:30pm yaro ya shigo ya ce, "Wai ana sallama da Sa'adatu" Daidai lokacin ta fito a ban'daki dan haka ta ce, "Je kace tana zuwa". A gurguje ta shirya cikin tsadaddiyar doguwar riga Coffee Colour ta yi roling da mayafin rigar, ta fesa turare bayan ta shafa powder da wet lips, ba ta cikin walwala don haka ba ta sami sukunin yin kwalliya sosai ba, duk da hakan rigar ta karbe ta, ta yi mata kyau. Dakin Inna ta le'ka ta ce mata, za ta fita." Kai ta 'daga mata ita kuma ta dauki 'yar 'karamar tabarmar da take jingine a dakin ta fita. A jingine ta same shi, ya yi shigar 'kananun kaya, wandon jeans ne mai kalar ba'ki, sai T-shirt fara 'kal an rubuta *PYRAMID* da manyan ba'ki a gaban rigar, zanen dutsen pyramid 'din kuma ta bayan rigar, 'kafarsa dauke da boot farare sai zabga 'kamshinsa na dindin yake yi, sumarshi tasha gyara sai she'ki take yi, yau har farin glass ya saka wanda ba kasafai yake amfani da shi ba, ba ta yi mamakin shi ne Mutarin da Baffa yake bayanin sa ba, saboda ai ya taba ce mata yasan Baffan shi ma. Ba 'karamin kyau ya mata ba, amma da yake haushin sa take ji sai bai wani burge ta ba, sai da ta shimfida tabarma ta ce "Bismillah!" Ta juya ta dauko ruwa, a zaune ta same shi a farkon tabarma ita kuma ta sai ta zauna a 'karshen tabarmar. Da 'kyar ta bude baki ta gaishe shi, ya amsa yana nazarin yadda ta zabge lokaci guda. Kai tsaye ya ce, "Mai ya hana ki zuwa makaranta tsawon sati guda?" Shiru ta yi amma a zuciyarta fadi take na bar muku makarantar sai ku tabbata kai da Farida da sauran staff masu shaidar zur, har Mahdi ya bayyana. Sau biyu yana tambayar ta, ba ta 'dago kanta ba, bare ta amsa mishi. A karo na uku ya yi magana a kausashe tare da cewa "I will not repeat myself!" Cikin turo baki ta ce "Ni ban son makarantar ne na gaji" Mamaki ya kama shi wacce irin yarinya ce wannan? Ka zo shekarar 'karshe a karatunka kuma rana daya ka ce wai ka gaji? Ya zuba mata ido yana nazarinta matsakaicin tsayi gare ta, ba'ka ce amma ba sosai ba, irin su ake cewa wankan tarwa'da, zagayayyiyar fuska ce da ita, mai dauke da manyan idanuwa dara-dara, gashin girar ta a cike, sannan hancinta ya dace da fuskar sai dan 'karamin baki irin na Baby Girl🤩, mai dauke da wushiryar da take 'kawata murmushinta, ga ta kuma da dimples a dukkan kumatunta ko motsa bakin ta yi sai sun lotsa, ba siririya ce ba amma kuma bata da jiki na sosai, sai dai a cike take, 'kasanta ne mai fadi, amma ta sama a tsuke take musamman da ta yi sa'a ba ta da tumbi sai hakan ya taimaka wurin fito da cikakkiyar sura mai birgewa. Shi yasa uniform ke mata kyau tunda sai sun mishi shape sannan kuma hijabin su 'dan mitsil ne. Ya nisa yana kokawa da zuciyarshi, ya ce, "Ban gane kin gaji ba"? Shiru ta yi ba ta ce 'kala ba. Ganin yadda ta rame ya san dole akwai wani abu daya sata wannan borin sai ya tausasa murya ya ce, "Sa'adah what's your problem, mai yasa haka? Ba za ki ji tausayin iyayenki ba, duk wahalar da suka yi sai da abu ya zo gaf, kice ke ba za ki yi ba, ko auran kike so wata nawa ya rage ki kammala sai a miki" Wani malolon ba'kin ciki ya tokare mata wuya, tasan Baffa ne ya ce mishi haka, ta kasa magana amma ranta in ya kai dubu to ya baci. Sai shi ne ya gaji da shirun ya ce, "Tunda gajiya ce kawai dalilinki ai yanzu kin huta tunda kin fi sati kina hutawa, kuma gobe Monday lallai ki shirya ki zo makaranta. Kai tsaye ta ce, "Idan har FGC ne sai dai a kai gawata!" Ta fada kuka na kwace mata, ta sunkuyar da kai tana danne kukan. Shiru ya yi tare da tunanin dalilin 'kin makarantar haka farat 'daya, murya ba amo ya ce "Listen, idan aka canja miki wata makarantar za ki je"? Kai ta 'daga mishi. Ya ce "it's ok but let's talk the reality. Fada mini dalilinki na son barin makarantar ni kuma idan na ji kina da hujja da kaina zan nemo miki wata makarantar na kawo wa Baffa" Ta yi shiru sai shesshe'kar kuka take yi, jikinsa ya yi sanyi zuciyarsa sai kisima mishi abubuwa take yi. Ya dade yana lallashinta da kalmomi masu dad'i har ya samu ta bude baki ta ce, "Akan me zata dinga tsokana ta sannan duk a hadu a ba ni rashin gaskiya? Saboda ita Babanta mai kudi ne, ni kuma nawa talaka? Saboda ita mai haza'ka ce, ni kuma ba ita ba ce? Duk staff kowa ita ya gasgata! amma ni da nake yar class 'dinka, ka kasa kare mini hakkina, saboda ita Bebinka ce, ni kuma ka tsane ni? To na bar mata makarantar ta tabbata a ciki kar ta fita" Mamaki ya yi matu'kar kama shi amma ganin ta hau dokin fushi mai yawa, sai ya tattaro dukkan alhini ya ya'ba a fuska da gangar jikinsa. Ya kira ta, ta amsa ba tare da ta 'dago kanta ba, cikin muryar lallashi ya ce, " Have I ever said I hated you?" Ta girgiza kai alamun a'a sai kuma ta ce. "No, but actions speak louder than words!" A thick silence sweeps the atmosphere! Ya zama speechless, bai yi tunanin irin kallon da take masa ba kenan. Cike da ta'ajibi ya ce, "Kar fa ki zama cikin jerin mutanen da idan an musu gyara yake zama gaba, tunda haka ne na miki al'kawarin ba zan sake shiga cikin case 'dinki ba, wannan bai kai dalilin da za ki bar karatu ba, sai dai idan da gaske auran kike so, ko kuma ba gaskiyar maganar kika fada mini ba." Ta yi shiru ya ce, "Yanzu kin ha'kura za ki koma?" "Amma ai cewa ka yi idan na fada maka dalilina za ka samo mini wata makarantar." "E na fadi hakan! €amma nima sai da nace idan na ji kina da dalili, to ban gamsu da wannan dalilin ba." Ta yi 'kasa da kanta,"Ai dama na san ba zaka mini adalci ba, tunda abin ya shafe ta." Ido ya zuba matat kamar kishi take da Farida, amma kuma ai shi ba wacce ya ce yana so a cikinsu, daga Ubangiji sai shi sai zuciyarshi su kasan me yake ciki. "Wai ta ina ta zama Bebina?" Da sauri ta ce, "Saboda kullum bakinka baya gajiya da ambaton ta, duk fadin makarantar nan da ita kake misali, alhalin ba ita ce kawai daliba mai 'kwazo ba, sannan za ta tsokane ni, amma har da kai a masu gaskata ta, ni kuma a 'karyata ni" Ta fada cike da takaici kwarai da gaske. Ya nisa, "To ai nace ba zan sake shiga case din ki ba" Ya sake sassauta murya ya ce "Sa'adah!" Har cikin jikinta sai da 'kiran ya ratsa, jikinta ya yi sanyi, ya sake kiran a karo na biyu. "Sa'adah!" Ba ta amsa ba amma ta dago ta zuba mishi manyan idanuwanta da sukayi ja saboda kuka. "Idan na ce ke ce Bebin nawa fa?" Da sauri ta yi 'kasa da kanta saboda yadda maganar ta dirar mata a ba zata! kuma yanayin sa ya matu'kar sa kunya ta kama ta. "Ki dago ki amsa mini." Ya fada murya ba amo. Ganin ta kasa magana, ya fara gaskata zarginsa na ita ma tana son sa, ya nisa tare da cewa. "Ban so na fada miki sirrin zuciyata yanzu ba, na so sai kin kammala karatunki, sai na zo na nemi aurenki a gidanku, amma ke na lura gaba'daya kallon wani 'dan ta'adda kike mini, idan za ki yarda da ni, ni ba son Farida nake yi ba, amma na san ina tausayin ta, sannan idan ke ba ki amince mini ba, to tabbas zan iya maye gurbinki da ita" Wani takaicin ya sake kama ta akwai alamun tausayin nan zai iya rikidewa zuwa soyayya kamar yadda Zainab Ma'aji ta hasaso, abin da take ayyanawa a ranta ke nan. Ya gaji da jiran amsarta ya ce, "Kin yi shiru?" 'Kasa ta sake yi da kanta cikin fushi ta amsa, "Tunda har za ka iya maye gurbina da ita, kawai ka ri'ke ta tun yanzu ai dama ita ce a ranka." Ta fada murya na rawa. "Wai ke kam wacce irin yarinya ce mai 'karyata na gaba da ita? Kin sa na fada miki sirrin zuciya ta, amma kina 'karyata ni. zan maimata miki a karon 'karshe, ke ce Bebina ba Farida ba, da gaske auren ki nake son yi, don nan ba gidan da zan yi wasa ba ne". Ya mi'ke yana sa takalmi, yana ci gaba da fadin, "Idan kin amince kin kuma gaskata ni, to lallai gobe na gan ki a makaranta, zan kuma fada miki wata magana. Rashin zuwan ki amsa ne na baki amince da soyayya ta ba, ba kuma ki gaskata ni ba, kin ga ba zancen ki ji ma maganar da zamu yi, zan tafi sai yadda hali ya yi ki gaida Inna!" Ya juya ya fice. Alkalamin SURAYYA DAHIRU. ✍🏼✍🏼 [5/26, 20:33] Aminan Ibrahim: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Dan Allah masu son Halin Yau! Daga farko, ku dinga tambaya a group, a kullum nakan turawa mutane daban daban sama da sau goma, nasan soyayyar labarin ne ta kawo hakan, amma abin yana mini yawa mussaman da kullum'kara yin nisa muke yi! Idan anturo ku dinga tarawa, idan antambaya ku yi sharing, yanzu aka fara, labari na gaba, JAZAKUMULLAHI KHAIR.* *Comments din ku na sani nisha'di na gode sosai fans Allah ya fini yabawa* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 29. Ta jima zaune a gun, tana jin wani irin nisha'di tare da shauki yana ratsa zuciyarta da gangar jikinta gaba'daya, tana tuno yadda ya lankwashe murya yana fadin, "Ke ce Bebina ba Farida ba" Cike da farin-ciki ta na'de tabarma ta shiga gida, dakin Inna ta fara shiga ta shaida mata ta dawo sannan ta jigine mata tabarma inda ta dauka. 'Dakinta ta shiga, ta fara tattara uniform din da ba ta wanke su ba, ta fita tsakar gida ta hau wanki, hatta sandal sai da ta wanke ta shanya, tana gamawa ana kiran Maghrib. Koda Inna ta fito ta ga shanyar uniform uffan ba ta ce mata ba. Sai da Baffa ya shigo bayan sallar Isha ta je ta durkusa gabansu, ta shaida musu gobe za ta je makaranta, Inna dai ba ta tanka ba, Baffa ne ya ce, "Allah ya kai mu" Ta dade a tsugunne tana jinta wani iri, ta san fushi suke da ita dukkansu musamman Inna. don haka sai ta sanyaya murya ta ce, "Don Allah ku yi ha'kuri na san ban kyautata muku ba, na yi musu da ku, ku yi mini afuwa" Ta fada cikin muryar kuka, kasancewar Baffa ya fi mata sassauci, shi ne ya fara tankawa da cewa, "Ni ban san inda kika samo dabi'ar yin musu da iyaye ba Iyah? Ni da kaina na rarrashe ki akan wannan maganar kika kafe, kika nuna mini ni ne zan bi ki ba ke za ki bi ni ba". Jikinta ya yi mugun sanyi ta shiga kuka na sosai tana jin kunyar maganganunsa na matu'kar ratsata, musamman yadda komai take so yana kokarin yi mata duk kuwa da wani abin don ya faranta mata yake yi, ba don yana so ko yana da karfin yi ba. Cikin kuka sosai ta ce, "Don Allah ka yi ha'kuri Baffa In Sha Allah ba zan sake ba." Ya nisa ya ce, "Shike nan na yafe miki, amma ki kiyaye, wannan ba dabi'ar kwarai bace, musamman kasancewar ki mace, ko wani daban wanda kika san ya girme miki ya ce miki kar ki yi kaza, ai kin mutunta shi ki bar abin kasancewar ya fi ki hangen nesa, bare kuma ni mahaifinki da ba zan cutar da ke ba ta kowacce fuska". A hankali ta ce, "In Sha Allah zan kiyaye, na gode Allah ya kara lafiya da nisan kwana Baffa". Cike da tarin soyayya mai yawa ya amsa mata da, "Amin Mamana!" Sai kuma ta juya ga Inna da ba ta tsoma musu baki ba ta ce, "Don Allah Inna ke ma ki yi ha'kuri da bacin ran da na saku". "Ni ba ki yi mini komai ba Iyah, amma tabbas inda ta ra'ayina za a bi kin gama yin boko tunda ke naki karatun na raini ne, haka siddan ana wahala da ke rana tsaka ki hau iyashegen ke ba kya son makarantar sai an canja miki, alhalin tun farkon samun wannan makarantar kin san ta fi karfinmu, amma kika kafe sai ita, kina kallon yadda yar'uwarki da mijinta suke 'dawainiya da ke, mu ma muna irin namu kokarin tunda wahalhalun makarantar yawa ne da su, sai kuma don kin raina mu ki ce lallai sai kin bar makarantar kin koma wata saboda ki nuna duk wahalar da ake yi akan makarantar ba karatun da'a kike koya ba, na raini ne da iyashege." Jikin Sa'adah ya sake yin tubus ta san Innarsu mai zafi ce amma a yau yadda take furzar da magana ta san ba karamin fishi ta yi da ita ba. don haka sai ta sake yin kasa da kai ta ce, "Ki yi ha'kuri Inna" Ta nisa ta ce, "Ke ce da ha'kuri Iyah, domin ina lura da take-takenki, kwatakwata ba ki ajiye kanki kusa ba, ina jiye miki kar ki jefa kanki a *HALIN YAU* na nadama marar amfani". Sai da Baffa ya sa baki sannan ta ha'kura ta ce ta huce magana ta wuce, Sa'adah da kyar ta mik'e bayan ta musu godiya tare da tabbacin ba za ta sake 'ba ta musu ba. Kasancewar sanyi ake kadawa yasa uniform din, nan da nan suka bushe, kafin ta kwanta barci sai da ta goge su tas! Sai da ta kammala komai ta kwanta ta fara tunanin yadda za ta kaya a tsakaninsu, anya ma ba zai ga rashin ajinta ba? daga magana daya sai ta hau bare-bare, kodai ta ki zuwa makarantar ne a iya gobe ta yadda idan ta koma zai gane ba saboda shi ta koma ba, tunda yanzu kam ta gane, ba karamar wauta ta yi na barin karatunta saboda wani dalili marar kangado ba? Da sassafe ta tashi ta yi ayyukan da ta saba yin su, ta karya sannan ta shirya, ta yi wa iyayenta sallama ta karbi kudin makaranta ta tafi bayan sun bi ta da addu'ar albarka da dacewa. Kai tsaye makarantar ta yi saboda ta san Zainab ta riga ta tafi, tunda ta sha biyo mata, tana cewa ba za ta je ba. Ba irin banbakin da Zainab ba ta mata ba, har ta gaji ta fusata ta daina biyo mata. Tana shiga class dinsu aka hau ihun murna tare da fadin "Gogel is back!". Ba su sarara ba sai da Uncle MK ya shiga don yin attendance, ya shiga rarraba ido, ya hango ta zaune kan desk dinta sanye cikin uniform sai daukar ido take yi, ga mamakin ta sai ta ga ya yi kamar bai gan ta ba, bare ya nuna wata alamar ya ji dadin ganin ta. Ya shiga kiran sunayensu, har aka zo kanta, tana amsawa kuwa ya ba ta umarnin ta mike tsaye, sai da ya kammala gaba'daya sannan ya tambaye ta dalilin rashin zuwanta makaranta tsawon sati biyu, cikin rawar murya ta ce, "Am sick!" Ya daure fuska sosai, cikin harshen turanci ya ce, "Waye ya zo ya fadi cewar ba ki da lafiya? Ina kuma shaida daga asibiti da makaranta za ta gamsu da gaske rashin lafiya kika yi? Ta rasa me za ta ce, sai ta yi shiru tana mamakinsa, ganin haka yasa ya ce ta fito, ta bi shi zuwa Staffroom. Bai dake ta ba amma ya yi punished din ta, ta hanyar sata wankin staff toilet wanda duk dalibi ya tsani a sashi wannan aikin. Tana gamawa ya sake cewa ta wanke window glass din Staffroom wanda duk malamin da ya zo wucewa sai ya gan lta, wani ya tambayi me ta yi, wani kuma ya wuce. Mrs Ngozi, Maths Teacher dinsu kuwa sababi ta yi ta mata, tana cewa, "You again? You're rude student." saboda yadda kwanaki ta musu case da Farida. Zuciyar Sa'adatu kamar ta fashe don bakin ciki, tana aikin tana kuka tana raya ashe da ma so yake ta zo ya ci ubanta shi yasa ya yi tattaki har gidansu ya mata kalamai wanda duk karya ne tsagwaronsu?. Har aka tashi, tana wannan aikin, kuka ta yi shi kamar idanuwanta su fado kasa. Koda aka tashin, da kyar Mr. Charles (Chemistry Teacher) ya ro'ki MK akan ya mata afuwa, ya bar ta haka nan, wanda ita a lokacin ta riga da ta fusata ba ma ta bu'katar ya mata afuwar, ai duk tsananinsa dai ba zai raba ta da numfashi ba, sai da aka gama watsewa sannan ya ce ta tafi. Tana kuka sosai ta wuce shi ya ce, "Sa'adah dawo, ba za ki gode mini ba? Takaicinsa ya sha'ke mata wuya, amma sanin halinsa na zai iya janye afuwar da ya yi mata sai ta ce, "Thank you!" Cikin kuka. Zuciyarsa ta yi rauni amma sai ya dake ya kalle ta tana tsugunne cikin kasa, ya tuna yadda ta zo cikin tsabta tana daukar ido amma yanzu ta yi futu-futu ta fita a hayyacinta. Sai ya ce ta jira shi a gate, wajen makarantar ke nan. Takaicinsa ya sake kamata, amma sai ta amsa da to ba don za ta jira shi 'din ba. Tana tafiya ita ka'dai kasancewar duk 'daliban sun tafi, tana rayawa ita kuwa mai zai ce mata? Ai kuma ba zai sake yaudararta a karo na biyu ba. Makaranta dai za ta ci gaba da zuwan ko don zaman lafiyarta da iyayenta, amma In Sha Allah za ta yi iyakar 'ko'kari ta cire MK a ranta, tana shirin tsayar da abin hawa ya cimma ta kusa da ita ya tsayar da mashin dinsa. Ta dauke kai tamkar ba ta gan shi ba ya ce, "Hau na kai ki". Fur ta 'ki, don haka ya sauko ya kafe mashin din, suka gangara inda ba wucewar ababen hawa sannan ya tsaya ya dube ta ya ga yadda ta hade rai tamkar hadari. Ya nisa ya ce, "Sa'adah are you angry with me?" Hawayen ba'kin ciki ya ziraro ta ce, "A a, Am happy with you". Ya san inda ta dosa, don haka sai ya ce, "Saboda Allah kinga ya kamata, ki yi laifi na kasa hukunta ki alhalin dokar makaranta kika karya? Kin san fa, if you want to show an example, you have to start it from your section for them to know you are not a selfish. Ke yanzu na san dauka zaki yi da gayya na miki hakan, Ni kuma na rantse miki, ba zan yi son zuciya a cikin aikina ba, don haka ki ri'ke, ki kuma kiyaye". Ta tura baki irin na sakarci da nuna takaici ba tare da ta ce uffan ba. Ya nisa ya ce, "Ba za ki daina wannan fishin ba?" Sake daure fuska ta yi tare da 'kin tankawa. "Amma kin san na yi farin cikin zuwan ki makaranta yau?" Sai a lokacin ta fashe, cikin kuka ta ce, "Ni kuma ban yi farin-ciki ko ka'dan ba, sai tarin ba'kin ciki da nadama." Alkalamin *SURAYYA DAHIRU*. ✍🏼✍🏼 [5/26, 20:33] Aminan Ibrahim: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 30-31. Kuka sosai ya kwace mata, wanda ya yi matu'kar taba shi, tun a wannan ranar kuma ta gane rauninsa yana motsawa ne idan ya ga tana kuka. A ki'dime ya shiga tattaro duk wata kalmar sanyaya zuciya, da nuna kololuwar kulawa, duk da ba ha'kuri yake bata ba, tunda shi ya san akan 'ka'idojin makaranta ya hukunta ta, ba ya kuma fatan ya ci amanar aikinsa. Tsawon lokaci tana kuka, ta koma ajiyar zuciya tunda dama tun safe take yinsa. Da kyar ya shawo kanta ta yi shiru, sai da ya ga ta nutsu sosai, sannan ya samu sukuni a zuciyarsa, yana mamakin yadda yake jin matsananciyar soyayyarta na ratsa dukkan jikinsa gaba'daya. Cikin murya marar amo saboda shauki ya ce, "Jiya na ce miki zan zamu yi magana ko?" Bai jira amsarta ba ya ci gaba da fadin, "Ban yarda ki fada wa wani ko wata cikin makarantar nan abin da ke faruwa a tsakaninmu ba, wannan sirrinmu ne ni da ke da ba zan so ya shiga kunnuwan students ba." "Sannan bana bu'katar, ki nuna wata alama da students za su fahimci akwai wani abu a tsakaninmu, lastly ki rabu da fitunannen yaron nan (Khalil), ki fita harkarsa in dai kina bu'katar kwanciyar hankalina". Ta yi shiru tana nazari maimakon ta fahimci inda ya nufa sai ta karkace, zuciyarta ta shiga kissima mata ai saboda Farida ne yasa zai ce bai son aji yana sonta banda haka mene ne na boyewa tunda dai aure za su yi ba wata 'barna ba. Ya gaji da shirunta, ya ce, "Kina tare da ni kuwa?" Nan ma shiru ta yi, bai ji dadin shariyar da ta mishi ba, amma sai ya waske, ya san dama haka take, bare kuma yau ya ta'bo ta. 'Kasa ya yi da murya sosai ya sake cewa, "Magana fa nake miki, amma kin yi mini shiru". Cike da fishi sosai ta ce "To ni me zance?" Zuba mata ido ya yi, yana kallon yadda take ta cika tana batsewa har wani huci take yi, jikinsa ya yi sanyi bai cika son mace mai fusata sosai irin haka ba, sai dai son da yake mata ya riga ya yi bunkasar jurewa duk wani kalubale daga gare ta. Wannan karon ido ya zuba mata, tare da bude murya sosai ya ce, "Ina ta miki magana amma kina jina kin mini shiru, kar ki bari na ji a zuciyata son da na ce ina yi miki shi ne dalilin da za ki fara raina ni". Kawai sai ganin hawaye ya yi yana tsere a kan kuncinta, tana ta yunkurin bude baki don ta yi magana amma ta kasa. A ransa yake fadin akwai aiki a gabana, a kankanin lokaci ya gane shagwababbiya ce ta gaske, banda haka mene ne kuma abin kuka a maganar da ya yi? kan dole ya yi ta rarrashi akan ta fada masa abin da yasa ta kuka cikin maganganun da ya yi. Cike da kukan kuwa ta hau cewa, "Ai an sha fada mini duk saurayin da yake boye kanshi kar a san yana son mace, to ba da gaske yake ba, yaudarar ta zai yi". Ta 'karasa maganar cike da gunjin kuka, mamakin ta ya kama shi sosai ya ce, "Amma na sha fada miki gidanku ba gidan da zan yi wasa ba ne, tunda kina shakku a kaina a satin nan zan gabatar da kaina a gaban Baffa shike nan?" Ta goge Hawayen da ya'ki tsaya mata, a hankali ta ce "To saboda kar Farida ta sani ne kake son a boye?" Takaicinta ya kama shi, amma kuma ya kasa yi mata jan ido, sai ma lallaba ta da ya shiga yi, ta hanyar fadin. "Sa'adah ya kamata ki dinga fahimta ta, inda Farida nake so, nake burin aure ba abin da zai kawo ni gunki tunda ba dole aka mini ba! Ribar me zan ci idan na zo don na miki karyar ina son ki? Mahaifinki mutumin kirki ne, na san shi, tun kafin na san ki, akan me zan yaudari yarsa? Ina son ki yarda da ni, yarda ita ce matakin farko a soyayyar gaskiya, abin da yasa nake son mu bar maganar a tsakaninmu ba komai ba ne illa don na kiyaye dokar makaranta! Ba makarantar da ta yarda malami ya yi soyayya da 'daliba, ni kuma zan yi iyakar'ko'kari na kiyaye kowacce irin dokar makaranta, ta kowacce fuska wannan shi ne gaskiyar magana". Ta yi kasa da kanta, tana jin nutsuwa da maganganunsa. Ya nisa ya ce, "Kin yarda da manufata?" Kai kawai ta 'daga mishi alamar eh, sai ya ce "To ba ki ce komai akan wancan yaron ba" Ta sake yin kasa da kanta ta ce, "Ai ni ba saurayina ba ne". Da sauri ya ce "Magana muke ta gaskiya fa Sa'adah! kin san har letter da kika masa wacce na dauka tana nan, kawai idan kin amince kina sona, to ki fita harkarsa, kin san dai yaro ne karami, da ba zan iya hada soyayyarki da shi ba, ga shi dama ba tarbiya ce ta wadace shi ba". Kanta tsaye ta ce " To! na ji zan rabu da shi, kai ma kuma ban yarda na dinga ganinta tare da kai ba, kodayaushe tana hanyar staffroom saboda kai, kai ma da ka motsa sunanta ne a bakinka, to ba ita kadai ba ce mai 'kokari ba, ire irenta suna nan, wasu da yawa ma a cikin makarantar sun fita kokarin, ita zubin Sadakar Yallah da kuke gani a tare da ita yasa kuke ga kamar ta fi kowa". Mamaki da dariya suka kamashi lokaci guda, amma ya dake bai bari dariyar ta fito ba, ya ce, "Amma ai na tabbatar miki ba son ta nake ba, sannan kin san dole wani abin zai hada mu tunda dai ni malaminta ne, abin da za ki yarda da shi shine wallahi ba budurwa ta ba ce, ba ni kuma da niyyar auren ta". "Amma da bakinka kace mini za ka iya maye gurbina da ita". "Tabbas na fadi hakan amma ki sa a ranki sai idan ke ce kika so faruwar hakan, ina nufin kika juya mini baya, sai na yi maleji da ita a rashin ki, kin san Bahaushe ya ce a rashin uwa, akan yi uwar'daki". Da'di ya kamata har murmushi ya subuce mata, shi ma ya taya ta murmushin tare da cewa, "Na rantse miki ban taba ganin wacce ta fi ki kyau a duniyata ba, musamman idan kika murmusa". Kunya ta kamata tasa dukkan hannunwata ta rufe ido tana jin kamar su tabbata a haka. Ganin sun dan fahimci juna ka'dan ya ce "To muje ki tafi gida kar aga kin dade da yawa, tunda ba za ki yarda na kai ki ba". Sai da ya sa ta cikin Adaidaita Sahu ya biya kudin, sai da ya ga sun tafi sannan ya koma ya hau mashin dinsa yana jin shauki na shigarsa, yana kuma jinjina kishin Sa'adah. WAYE MK BICHI? Haifaffen karamar hukumar Bichi ne, a jahar Kano. Mahaifinsa Alhaji Kabiru Wadata, Bafulatanin Bichi ne, mai arziki ne a lokacinsa, don zai shiga cikin jerin attajiran Bichi shi yasa ake masa la'kabi da Wadata. 'Dan kasuwa ne mai sana'ar fata, yana fataucin ta zuwa jahohin Arewa. Mukhtar shi ne babban dansa na namiji, shi ne kuma na biyar a dukka gidan, an haifi mata hudu kafin shi. Matan gidan biyu ne Hajiya Babba (Indo), tana da yara bakwai wadda ukun farko dukkan su mata ne, Zainab, Khadija, Amina, kuma duk sun girmi MK, sannan Abbas, Akil, Sameera, da auta Bilkisu. Sai dakin amaryar gidan wacce ita ce mahaifiyar MK, Hajiya Rabi yaranta uku kacal, Hafsatu ce Babba, sai Mukhtar sannan auta Ahamad, da Mk ya girme masa da shekaru kusan goma Mahaifin MK mutum ne mai sau'kin kai, mai kokarin wadata iyalinsa da komai na bukatar rayuwa, dukkan su, sunyi karatu, matan dai suna kammala sakandire yake aurar da su, yayin da mazan ke zurfafa karatunsu a jami'o'i daban-daban a cikin kasar nan. Gidansu akwai zaman lafiya, duk da ba a rasa yan kananun gutsuri tsoma irin na gidan Polygamy Family, amma dai nasu da sauki ainun kasancewar iyayensu matan ba su cika samun sabani ba. Idan ma sun samu to suna bari a tsakaninsu ba tare da sun bari yaransu sun shiga rigimar da ba tasu ba. Wannan dabi'ar tasu, tasa hankalin mijinsu ya kwanta da su, inda yake musu hidima su da ya'yansu kan jiki kan karfi. Mahaifinsu a tsaye yake kan sha'anin tarbiya, sannan ya dace da mata na-gari da suke taya shi, dora yaran akan kyakkawar turba, domin kuwa duk yadda namiji ya kai da kula da tarbiyar yara in bai yi dace da mace ta-gari ba, to da wahalar gaske yaran su bi tsarinsa. Mukhtar ya fara karatunsa a kwalejin ilimi ta tarayya dake garin Bichi, bayan ya kammala sakandiren hadaka ta gwamnatin jaha (Unity Boys Karaye). Sai da ya kammala NCE, sannan ya yi JAMB ta D.E, ya yi sa'a ya samu level 200 a jami'ar Bayero, inda ya karanta harshen turanci (English Language), yana shekara ta biyu ne Allah Ya yi wa mahaifinsu rasuwa a hadarin mota ya je dauko Bilkisu a makarantar kwana, wacce tare suka rasu da Bilkin. Wannan mutuwa ta matu'kar taba ahalin wannan gidan, dole suka tattara suka ha'kura suka bi su da adduar samun rahamar Ubangiji. Haka iyayensu mata suka ci gaba da zama suna ci gaba da kula da ragowar yaran da ke gabansu wanda Sameera ce kawai ta rage ba a aurar ba sai maza su kuma suna ta karatunsu cikin nutsuwa. Da ma can suna da sana'oinsu, sai suka samu sau'kin tafiyar da gidan da kuma tallafin 'ya'yansu maza da mata, musamman MK da ya kasance shi ne babba, kuma shi ya debo kusan halin mahaifinsu, na hakuri da yawan kula da lamarin gidan. Yana da sau'kin kai ta yadda duk yan'uwanshi suna jin da'din mu'amala da shi, kafin ya fusata yana jimawa, amma fa idan ya yi fishin wuyar sauka ne da shi. Abu mafi kyau cikin halayyar MK Bichi, ma'abocin addini, mai kokarin kiyaye dokoki ne na gaske, sannan duk layin da ba gaskiya, ba za ka same shi a ciki ba. Akidar son bokon da ya taso da ita bai sa ya yi watsi da kyawawan al'adun Malam Bahaushe ba. Sannan MK ma'abocin 'kamshi ne tun yana Secondary, da kamshinsa ake gane ya zo guri, bayan haka kuma He is Frank and friendly to all. Wannan ke nan. Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍🏼✍🏼. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *KAR KU BARI A BARKU A BAYA WURIN KARANTA LABARIN HAZI'KAR MARUBUCIYA*. *⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️* *Jameey yar'mutan kankia*. *Promo* *Promo* *Promo* _Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake_. *#300-sau biyu a rana* *#500 -sau ukku a rana* *#700 -sau hudu a rana* _Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316_. *MASU SON A TALLATAH MUSU HAJARSU 'KOFA A BUDE TAKE* _TUNTUBI_ 08032773332. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 32-33. Tana isa kofar gida ana kiran La'asar, sai da gabanta ya fadi saboda yadda za ta sha tuhumar inda ta tsaya har zuwa wannan lokacin a wurin mahaifiyarta. Ilai kuwa a tsakar gidan ta tarar da ita sai safa da marwa take yi, jin sallamar ta yasa ta tsaya cak, tare da zuba mata ido, amma ganin ta futu-futu kuma idanuwanta a kumbure sai ta sami sau'kin tashin hankalin da ta shiga, don ta tabbatar Iyah ba za ta iya biyawa wani wajen a haka dukun-dukun ba, amma duk da hakan sai da ta ce "A ina kika tsaya har zuwa wannan lokacin?" Fuska daure ta ce "kwanakin da na yi ban je makarantar ba shine suka ci zalina." Ajiyar zuciya Innar ta sauke sai kuma ta ce "Madalla da wannan cin zalin." Sannan ta dauki buta ta zaga ban'daki. Sa'adah daki ta yi tana tube kayanta, zuciyar ta fes ,tana tuno hirar su da MK da ya mantar da ita takaicin da ya kunsa mata a safiyar yau. Tana idar da sallah ta wanke uniform din da ya baci da 'kura sannan ta zuba abinci, kai tsaye falonsu ta shiga wanda ba komai sai leda a shimfide da labulaye, sai yar karamar talabijin kirar (sharp) a kan dan karamin tebur, kusa da mahaifiyarta ta zauna da ta ke kulla bushasshiyar kubewa. Ganin Innar ba ta 'daga kai ta kalle ta ba yasa ta fadin, "Inna ko ki tambaye ni, ko na ji ciwo a cin zalin da aka mini?" Cike da rashin kulawa ta ce "Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, tunda kin yi girman da za ki zabawa kanki abin da ya dace da ke ai magana ta 'kare" Jikinta ya mutu ta ce "Inna kin ce magana ta wuce, amma kina ta share ni kina nuna ko oho da ni" Ta ture abincin tare da fashewa da kuka. Da farko share ta ta yi, amma jin yadda take ta sauke ajiyar zuciya, ga kuma hawaye nata tsere a fuskarta, sai ji ta yi raunin da bata son ta nuna mata ya kubce mata cike da tarin soyayya irin ta uwa ta tausasa murya ta ce "Share hawayen kin san dai ba na son kukan ki ko?" Ta tura baki cike da shagwaba ta ce "Inna ai da ne ba kya son kukan nawa, yanzu sau nawa za ki ga ina kuka amma ko ki nuna kin gani bare ki rarrashe ni?" Murmushi ta yi ta ajiye ledar da take hannunta ta zuba mata ido sannan ta ce "Iya bawai kukan naki bai dame ni ba ne. Ni kadai na san yadda zuciyata ke zafi idan na gan ki cikin rashin sukuni, halayen da nake gani a tare da ke ne ba su mini ba, ina matu'kar kaduwa da yadda kike kokarin jefa kanki a rayuwar da ba za ta bulle da ke ba" Sa'adah da jikinta ya yi laushi amma sai ta yi karfin halin cewa, "Don Allah Inna wai mene ne nake yi wadda bai miki ba?". Muskutawa ta yi sannan ta ce "Iyah kin san dai ke din nan ba 'yar kowa ba ce, mu iyayenki ba wasu ba ne illa masu neman abin da asirinmu zai rufu, amma ke kina daukar ra'ayin ya'yan masu wadata, ba kya duba idan ba yawan gashinku daya ba, yawan kitson ku ba zai daidaita ba! Watanni kadan ya rage ki kammala makarantarki, kin san kuma aure za a miki amma duk saurayin da zai zo gidan nan da maganar aure za ki yi tsalle ki ce bai miki ba, amma kina son abin hannunsu saboda kawai kin 'dorawa kanki sai kin daura abin da kike gani a jikin yaran da 'karfin iyayenku ba 'daya ba" Ta nisa tana jiran ko Sa'adah za ta yi magana sai taji sabanin hakan, duk da dai ta lura jikinta ya sake yin laushi fiye da 'dazu, don haka sai ta sake cewa, "Ki ajiye wannan dabi'ar, sannu a hankali idan kina da rabon yin arzikin za ki yi shi ne. Yanzu dai babban misalin da zan miki da yayarki ne, duk da cewa lokacin da aka aurar da ita ba ki da wayon da za ki gane komai, mijinta ko mashin din da kika raina mai hawansa ba shi da shi, amma a yau mene ne bai mallaka ba? A saninki 'kasashe nawa ya debi iyalinsa suka fita? Wace irin hidima da karamci ne ba ya mana ke ma shaida ce tunda dai ko wannan makarantar da kike yi ba don shi ba, da ba ki yi ta ba, da ace farko ta raina matsayinsa da yanzu ta cim ma wannan jin dadin da kowa ke mata kallon tana ciki? Tsakanin ki da Allah ba don ta sau'ka'ka buri ba ta kai wannan matsayin?" Kai Sa'adah ta girgiza wa mahaifiyarta don kuwa harshenta ya mata nauyi, amma a ranta tana raya in dai akan zaben miji ne an wuce wannan babin, zuciyarta ta riga da ta aminta da MK Bichi kuma shi ma ai talaka ne tunda ko mota ba shi da ita. Jin da'di da son kayan 'kawa kuwa ba mahalukin da ba ya so sai idan bai samu ba, ita a jininta ne son gayu ba wai fariya ko 'karya ta sa a ranta ba. 😀 Don haka ba ta dauki maganar ajiye dogon buri da aka mata nasiha da wani muhimmanci ba. "Kullum addu'a ta Allah ya ba ki miji nagari wanda zai kula da ke da amana, ke ma irin adduar da za ki rike ke nan. Dauki abinci maza ki ci kar ya gama hucewa, Allah ya miki albarka." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Amin na gode?" Sannan ta ja abincin ta hau ci, danwaken fulawa ne da yaji mai da'din gaske, tana ci tana yaba yadda Innarsu ta iya sarrafa abincin gargajiya masu da'di, kawai dai abincin zamani ne ba ta yin su ko kuma don za su ja kudi ne? Sai ta tsinci kanta da cewa "Allah Inna na kusa daina cin abinci mai nauyi." Cike da mamaki ta ce "Me za ki dinga ci to?" Murmushi ta yi, ta ce "Chips, chicken, sai dangin su pizza, da indomie da kwai, sai na bi bayansu da ababen ruwa irin su juices da yougurt ko hadadden shayi hadin kauri." Salatin da Inna ta 'dauka ne ya sa ta dakatawa tare da tunanin ta yi subutar baki. "Ashe duk togaciyar da na gama yi miki bai shiga kunnenki ba? A gidan uwarki kika san wadannan kayan, wadda ba ta alfahari da abin da ta bude ido ta gani a gidansu, sai hangen kayan wani da ba ya rufa maka asiri! Nasan kina nufin idan kin je gidan miji ne kike tunanin wannan rayuwar za ki yi" Ta kafe ta da ido tana mata kallo mai tsanani sannan ta ci gaba da cewa, "To saurare ni da kyau aure ya wuce wasa tun wuri ki cire wannan tunanin a ranki, gabadaya aure ibada ne, duk abin da akace ibada ne, to ba son ranka za ka yi ko zaka gani ba, sannan ba abin da ke ri'ke da aure gabadaya sai ha'kuri don haka ki cire wannan tunanin a ranki. ki yi fatan Allah ya ba ki miji nagari, da hankalinki zai kwanta, domin komai za ki samu idan ba kwanciyar hankali ina tabbatar miki ba za ki ji dadinsa ba Allah ya shirye ki, adduar da zan dinga miki ke nan." Ta fada da iyakacin gaskiyarta, domin ta lura addu'a ce kawai za ta canja mata Iyah ba hantara ko nuna fishi ba. *** MK yana isa gida ya tarar da Hajiyar Bichi ta zo, a falo ya tarar da su ita da Hajiya Babba suna cin makani wanda ba ya tantamar daga Bichi ta taho da shi, da murna ya hau fadin, "Hajiya ashe da gaske kike da wuri za ki dawo?" Dariya ta yi ta ce "Allah Ya yarda ban dade ba". Suka ci gaba da hirarsu har su Abbas da Ahamad suka dawo aka ci gaba da hirar da su, Maghriba ce ta dakatar da su. Bayan sallar Isha MK ya tarar da Hajiya Babba a dakinta, ya gama kame-kame da soshe-soshen 'keya, sannan ya ce "Hajiya so nake aje a tambayar mini izinin magana da wata yarinya a wajen mahaifinta." Dadi ya kama ta, ta shiga fadin "Alhamdulillah! Allah Ya sa abokiyar arziki ce, ina ne gidan nasu?" Sake kasa ya yi da kansa da kyar ya ce "A babban layin Unguwa Uku suke mahaifinta mai karamin karfi ne amma mutumin kirki ne, na san shi tun kafin nasan yarinyar." Farin ciki ya bayyana a fuskar Hajiiya Babba ta ce, "Yanzun nan za mu tattauna da Hajiyar Bichi tunda Allah ya sa ta zo garin, gobe In Sha Allah zan je har gidan Babanku Alhaji Isa (Aminin mahaifinsu ne) na shaida masa. Sai ya je ya tambayar maka, tunda ka kammala karatun kuma ka iya harkar kasuwanci ba za mu ji tsoron aurenka ba, bare da ikon Allah da wuri za ka sami aikin yi ka ci gaba da rike mu gabadaya." Koda ta sami Hajiyar Bichi da maganar fatan alheri kawai ta yi tare da cewa, "Hajiya Babba ai ke ce uwarsa, ni 'yar addua ce!" Wannan biyayyar da tun fil'azal Hajiyar Bichi ke yi wa Hajiya Babba ta taimaka kwarai wurin samun zaman lafiya a tsakaninsu, tare da saukaka kishin junansu matu'ka da gaske. A satin aka tambayo masa izinin magana da Sa'adah, a take kuma Baffa ya ce ya bashi damar ya nemi yardarta ba don yana jin tsoron halin dan yau ba, da a take zai ce ya ba shi ita, to tsoron kar ta ce ba ta sonsa ta kunya ta shi yasa ya ce idan har sun daidai ta kansu to ya ba shi, aka yi murna aka rabu ana addu'ar Allah Ya sa hadin Allah ne. A ranar Baffa ya zaunar da Sa'adah tare da mahaifiyarta ya ce, "Bakin da suka bakunce ni a yammacin yau, zuwan Iyah ne. Yaron nan Mutari ne ya turo a ba shi iznin neman amincewarki, ni kuma na ba shi dama ya nemi yardarki ba don Ina jin tsoron kada ki yi mini *HALIN YAU* ba, da kai tsaye zan ce na ba shi su zo ayi maganar aure. Saboda yaron nutsatstse ne , ya san mutuncin manya mai kokarin neman na kansa ne, kullum ya zo shagon askinsa sai ya zo ya gaishe ni, ban kuma taba jin hayaniyarsa da wani ba, kiga dai yadda shagon yake cika dam da matasa amma ban taba jin an ce ana fada da shi ba. Da shi muke sallar Magariba da Isha kullum yana sahun gaba, ba zan miki dole ba amma da a ce zan miki zabi ki karba, to da ba zan tsallake shi ba. Idan kuma kin kafe shi ma bai miki to lallai ki tsayar da wanda ya miki da zarar kin kammala makaranta zan aurar da ke, ki ri'ke wannan!" Alkalamin SURAYYA GWARAM ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *TALLAH* *TALLAH*! *KAR KU BARI A BARKU A BAYA WURIN KARANTA DADDAN LABARIN NAN* *⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️* _NA_ *Jameey yar'mutan kankia*. *Promo* *Promo* *Promo* _Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake_. *#300-sau biyu a rana* *#500 -sau ukku a rana* *#700 -sau hudu a rana* _Kiyi ma wanann number magana danjin yanda zaki biya 08160508316_. *MASU SON A TALLATAH MUSU HAJARSU KOFA A BUDE TAKE* _TUNTUBI_ 08032773332. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 34-35. Baffa na rufe baki, Inna ta yi caraf ta ce "Gara ka jaddada mata don ni a halin da nake ciki da ita, ban ki ka kawar mini da ita a cikin wannan watan ba." 'Dan murmushi ya yi mai sauti tare da cewa, "Anya Salamatu ba gaskiyar Iyah ba ne da take cewa kin fi nan nan da Sumayya?" Da sauri ta ce "Hmm Ni yaushe ma na ga yayar tata bare har na nuna son kan da take korafi? Mafi yawa ai karamin 'da ya fi shiga rai, sai idan halinsa ne marar kyau ko ba ya jin magana". Ya sake fadada fara'arsa ya ce "Ato ni ma dai na ce ban taba ganin wacce ba ta ririta autarta ba sai ke". Da sauri Sa'adah ta ce, "Ai ni Baffa Inna ba ta dauke ni a auta ba, ALLAH ne ya mayar mata da ni auta akan dole." "To ki dinga jin maganar da ake fada miki, ki rage dogon buri, sannan ina sake jan hankalinki akan yaron nan kar ki bari ya kubuce miki." Ta yi kasa da kanta, nuna alamun kunya, a ranta fadi take "Son sa nake sosai Baffa daina jan hankalina" 😀 Sa'ade ke nan. Daga haka ya sallame ta ta mike tana fadin "Sai da safe." Tana zuwa, ta zube kan katifa tana jin wani irin nisha'di na tsirga mata, idonta a rufe wani irin shauki yana mamayar ta. Can kuma ta fara tunanin maganar Baffa in da ya ce, "Shagon aski! Kar dai The Boss barbing shop?" Duk titin ba katon shago irinsa, shago ne da ya samu karbuwa wurin samari yan kwalisa da kullum suke dafifin zuwa gyaran suma ko yin aski. Ashe shi yasa kwanaki ta gan shi agun? A fili ta ce, "Hadadden guy dan boko da yin aski?" A take wani sashi na zuciyarta ya ce mata ai ya huce takaicin bani-bani a wurin iyaye da dangi, ya kuma kere sa'a a tsakanin abokai masu jiran gwamnati ta ba su abin yi. Maimakon ta ji abin alfahari ya yi, ta yabawa kokarinsa na dogaro da kafafunsa, sai ta ji tana jin kunyar ace saurayinta wanzami ne 😁. Washegari da wurwuri ta shirya ta biya wa Zainab Ma'aji, a hanya ta ba ta labarin yadda ta kaya tsakaninta da MK, murna sosai Zainab ta yi tare da cewa "To ki kiyaye abin da ya ce baya so, sannan ki kama bakinki." Duk sa idon su Halima ba su iya gano soyayyar da ke tsakaninta da Malamin nasu ba, saboda yadda suka rufe kofar da za a gane akwai wata alaka a tsakaninsu da ta wuce Malami da dalibarsa. Khalil ne kawai ya kasa gamsuwa musamman yadda ya lura Sa'adah ta yi matu'kar sauya masa, sannan ta toshe duk kofar da suke samu su yi hira, zai mata letter sau goma bai fi ta ba shi amsa daya ba a dukunle. Wannan sauyin da yake gani a tare da ita yasa ya sake kullatar MK yana ganin tun zuwansa makarantar ya canja masa Sa'arsa. Saboda haka ya sake daukar samfurin nuna rashin da'a a gaban Uncle MK, duk lokacin da ya zo ajin sai Khalil ya yi abin da zai harzuka zuciyarsa, wanda hakan ya janyo kiyayya mai tsananin gaske a tsakaninsu, wata rana an fita break ya samu ya yi magana da ita a dalilin ya sa Halima ta tsayar masa da ita, duk tambayar da ya mata idan laifi ya mata ta yafe masa. Ta ba shi amsa da cewa, "Khalil ba ka mini komai ba, kawai ganin jarrabawarmu ta gabato akwai bukatar mu fuskanci karatunmu ne." Kai tsaye ya ce, "Zan so wannan dalilin ya zama shi ne gaskiyar magana, amma na san idan na rantse ba zan yi kaffara ba, cewar akwai wani dalilin ba wannan ba. Ni koma mene ne zan yi ha'kurinsa amma idan wannan mugun Malamin is behind your changes, to ba zan yafe masa ba!" Ya fada cike da 'bacin rai. A tunanin Sa'adah tunda ya turo a ba shi iznin neman amincewarta, an kuma bashi ai zai dinga zuwa zance, sai ta ga an kwashe kwanaki kusan goma bai zo ba, bai kuma sake waiwayar ta ba ko a makaranta, wannan abu na ci mata tuwo a kwarya musamman da a safiyar yau 'yan ajin nasu suka yi laifin da gaba'daya ya zane su, amma da ya zo kanta sai ta ga ya dage iya karfinsa ya zabga mata bulala har hudu maimakon bibiyu da ya yi wa kowa. Abin ya tsaya mata a rai sosai, sai kawai ta tsiri fishi da shi, ya lura da fishin da take yi amma sai ya share, tun ranar da ya gan ta tana hira da Khalil ya ji gabadaya ya rasa inda zai sa ransa shi yasa da ya samu damar dukan yan class din ya ninka nata dukan! Ranar wata Juma'a da yamma Sa'adah na zaune a tsakar gida tana yanke farce ta yi kwalliya da daguwar riga ta shadda purple (Mai ruwan Shanshanbale) a lokacin surfani aikin sama ake ya yi, dinkin ya yi kyau sosai! Innarta sai mita take yi, akan har yau Muutar bai zo ba, ganin Sa'adah ta yi shiru ba tare da ta ce komai ba, sai ya harzuka ta, ta zuba mata ido ta ce, "Iyah ba magana nake yi ba ne kika mini kunnen uwar shegu?" Tura baki ta yi da ya zame mata jiki cikin yanayin tabara ta ce, "Ayya Inna ni ma ban sani ba fa!" A tunzure ta ce, "Kin sani Iyah kawai dai kin nuna masa halin naki ne" "To ni a ina zan nuna masa halin nawa tunda ko a makaranta ma ba kula ni yake yi ba, ni wallahi na fara tantamar shi ya aiko yana so na? Shekaranjiya ba ki ga dukan da ya mini ba." Jikin Inna ya yi sanyi ta fara wasiwasi tana fatan Allah ya sa lafiya, amma sai ta ce, "Allah ya sa dai ba wani abin ba ne." Tana rufe baki yaro ya yi sallama ya ce, "Wai ana sallama da Sa'adatu" Da sauri Innar ta ce, "Je ka ce Wai waye?" Ba a jima ba ya dawo ya ce, "Wai Mukhtar ne." Dadi ya kamata da sauri ta ce, "Je ka ce ta na zuwa." Ta juya ta ga hakimar ko motsawa ba ta yi ba tana ci gaba da yankan farcenta, kamar za ta yi magana sai kuma ta shanye, tana mai son ganin iya gudun ruwanta. Fiye da shudewar mintina goma tana zaune ta gama yankewar. Amma sai ta tsiri kankarewa, zuciyar Inna ta hau ba tare da Iyah ta ankaraba, kawai ta ji saukar duka da mafici a zabure ta mike tana dire-diren shagwaba tana cewa, "Me na yi kuma na duka Inna?" Dakuwa ta mata da hannunta na dama tare da cewa, "Za ki wuce ki dauko mayafinki ko kuwa?" Ta shige dakinta tana cewa "Daga zuwansa zan debi jiki na fita, ba jan aji ba komai, salon ya ga arhata." Mahaifiyarta bin ta yi da kallo, jiki a sanyaye ta rasa bakin magana, ta shiga dakinta ta fito da lemon kwalba guda biyu, da Swan roba biyu, da tuni Baffa ya tanada saboda zuwansa, ta zuba mata a kan faranti mai kyau ta ajiye. Kan dole ta bi ta dakin a zaune ta same ta ta sake gyara fuskar ta yi kyau sosai ga mayafin da ya dace da zaren surfanin dake jikin rigar, kamshin tsadadden turaren Escada sai tashi yake a dukkan dakin! Sassautawa ta yi ta ce, "Yanzu zama ki ka sake yi Iyah? ko ba komai ai malaminki ne, malami kuwa ai kamar uba ne, ki duba fa tsawon lokacin da kika shanya shi yana faman jiran ki?" Bata ce komai ba ta mi'ke ta fice ta dauki tabarma, ganin ruwa da lemo a kusa da tabarmar yasa ta ganewar iyayenta sun fi ta kambama lamarin MK. Tabarma kawai ta dauka ta nufi zauren, a tsaye ya jigina da bango ta same shi. Sanye yake da farar shadda kal (Bankole style) ya dora hula ba'ka, kafarsa dauke da bakaken cover shoe. Sallama ta yi tare da shimfida tabarma sai da ya zauna sannan ta zauna ta gaishe shi. Ya amsa ba yabo ba fallasa, kamshin turarensa na Versace da wanda ta yi amfani da shi Escada suka cakude suka cika zauren da wani irin lafiyayyen kamshi mai nutsar da zuciya. Tsawon mintina suna zaune shiru, ita kanta a kasa yake tana ta wasa da yatsun hannunta da ta musu kwalliya da zobuna (fashion). Shi kuma kawai kallon ta yake yi, yana nazarin yadda ta iya tsara simple kwalliya ta burgewa tamkar wacce take karantar fashion and design. Gani ya yi ta mik'e tana cewa, Ina zuwa." Ba ta jima ba ta dawo dauke da faranti a hannunta ta ajiye a gabansa. Ta koma in da tashi ta zauna. Can ya nisa ya ce, "Wai fishin ne har yanzu?" Takaicin sa ya makure mata wuya, tunda ya zo ban da kallon ta bai ce komai ba, sai gaisuwar da ya amsa mata ba karsashi, shi ne yanzu zai ce wai fishi take yi, so yake ta saki baki ta masa hira bayan shi ya kame bakinsa ya tsuke, saboda yana jin isa? Don haka sai kawai ta daure fuska sosai, sannan ta juyar da kanta gefe ba tare da ta ce ko mai ba. Dariya ta kamashi ya murmusa, sannan ya ce, "Ke kullum a cikin fishi kike? Da kin san yadda murmushi yake sake kawata miki fuska da kullum kin kasance a cikinsa" Ba ta ce komai ba, ya yi shiru yana nazarin mai zai ce da zai sa ta kula shi. Ya nisa ya ce, "Babana ya yaba da karbar da Baffa ya masa, ya yi murna sosai har cewa ya yi na iya zaben suruki, yana fatan a ce ke ma ki yo halin karamci irin na gidanku " Ba ta ce komai ba amma ta sassauta daurewar fishin, yana kula da ita, don haka sai ya sake cewa, "Kin san kafin na zo raina a bace yake da ke amma kina fitowa na ga wannan kwallliyar da aka cancanda mini sai na ji na manta komai! Ke kawai nake gani kin cika ko ina fiye da duniyar gaba'daya!" Dadi ya kamata ta murmusa kadan, amma ba ta ce uffan ba. Ya dade yana rarrashi kafin ta ware su yi hirarsu, cikin dabara ya tabbatar mata ai ya gan ta da Khalil suna hira a class shi ne kuma dalilin da ya hana shi zuwa, don Allah ta kiyaye. Ba ta musa ba, cike da dariya ta ce, "Shi ne dalilin da ya sa ka ninka dukan da ka mini?" "E, saboda ki ji dan kadan cikin takaicin da nake kwana ina tashi a cikinsa." Bai tafi ba sai da aka fara kiran sallar maghrib, ya mike yana cewa kawo mini buta na yi alwala. Tana tsaye har ya yi alwalarsa ya mayar da agogon da ya cire ya zura hannu ya ciro sabbin yan dari-dari da suka sha turare guda ashirin ya mika mata da 'kyar ta karba wanda sai da ya rantse akan sai ta karba, sannan ta sa hannu biyu ta karba, ita kanta a ranta addu'a take Allah ya sa kar ya mayar da kudinsa! Ta ga samu ta ga rashi 😁 a wancan shekarun dubu biyu tana da daraja ba kamar yanzu ba. Ta kalle shi a kunyace ta ce, "Ka tsaya sai ka rasa sahun gaba, Baffa yana ta cewa kullum a sahun gaba kake sallah." Dadi ya kama shi tare da cewa, "Ashe har kamfen Baffa yake mini a gunki, lallai ki ce na kwantar da hankalina, na same ki na gama! Amma yanzu ba na iya zuwa wurin da yake yin sallah, kunyarsa nake ji." "Ta yi dariya sosai ta ce, "To kuma a ina kake yi?" Ya kalleta yana jin wani irin abu na tsirga masa da sauri ya fice yana cewa, Nan Masallacin bayan layi nake zuwa." Ya tabbatar sai ya sake alwala saboda yadda ya tsinci kansa cikin yanayi na sha'awa sosai. Bata lura da yanayinsa ba ta dauka kawai gaggawa yake yi tunda an tayar da sallah, shi yasa bai bari sun yi sallama ba. Sai da ta yi sallah sannan ta je falo gun Inna ta mika mata kudin da ya ba ta, za ta fita ta ce "Zo ki zauna." Kusa da ita ta zauna, a hankali ta ce, "Ina fatan dai ba shi da matsala ko Iyah!" Dariya ta kama Sa'adah ta cije ba ta yi ba, amma sai ta yi nufin tsokanar Innar, don haka sai ta ce "Ba shi da matsalar komai Inna amma gaskiya ni wanzancin da yake yi ne bai mini ba!" Ta fada a dake tamkar gaske. Salati sosai Inna take yi tana karawa, amma sai ta taushi zuciyarta cikin lallashi ta ce, "Iyah mene ne laifin sana'arsa saboda Allah? Ai abin alfaharinmu ne duka ace matasanmu sun daina zaman banza, sun daina zaman jiran gwamnati ta basu abin yi, ke yanzu raina wanzancin kika yi? To bari ki ji tun a lokacin ma'aiki akwai wanzamai, sannan duk inda wanzamai suke mutane ne masu amana masu kuma tsananin zumunci, bare kawai don yana da shagon aski sai ki mayar da shi wanzami?" Dariyar da take dannewa ta kubuce ganin yadda Inna ta kwantar da murya tana lallaba ta, tana cewa a ranta Inna ta koma lallashi. A fili kuma ta ce "To shikenan ki cigaba da addu'a Allah ya sa na ji ina son sa tunda na lura duk ya kwanta muku a rai" "Ai ni tunda na ji Baffanku ya yabe shi na ji ya kwanta mini a rai, kinsan mijin yayarki ma shi ne ya zaba mata, halayensa da nagartarsa kawai ya auna, shi yasa kema nake so ki masa biyayya kar ki yarda ya kubuce miki". Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *KAR KU BARI A BARKU A BAYA WURIN KARANTA DADDAN LABARIN NAN*! *⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️* NA *Jameey yar'mutan kankia*. *Promo* *Promo* *Promo* _Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake_. *#300-sau biyu a rana* *#500 -sau ukku a rana* *#700 -sau hudu a rana* _Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316_. *MASU SON A TALLATAH MUSU HAJARSU KOFA A BUDE TAKE* _TUNTUBI_ 08032773332. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 36-37. Sannu a hankali cikin nutsuwa MK ke tafiyar da Sa'adah, a sati sau daya yake zuwa zance. Duk da ya karbi lambar wayar Inna tun da yanzu koyaushe wayar na hannunta amma ba kasafai yake kiran ba, duk a kokarinsa na ganin bai raba mata hankali ba, musamman da kullum jarrabawarsu kara kusantowa take yi. A bangarenta kuma sai ta ke ganin kawai rashin daukar ta da muhimmamanci ne yasa yake nuna mata rashin kulawa, musamman yadda Khalil ke kiranta safe da yamma sannan su raba dare ana musayar kalamai, shi yasa ya daina damuwa da rashin saurarar shi da ba ta yi a makaranta. A haka har aka rubuta jarrabawar JAMB, duk kokarin da MK ya yi na ganin Sa'adah ta samu rubuta jarrabawar abin ya ci tura! Saboda yadda Baffa ya ce masa "Ni sakandiren nan ma a dole na bar ta ta kammala ,yar uwarta aji uku kawai ta yi na aurar da ita, don haka ni ba zan barta ta tafi wata babbar makaranta ba, ta zo tafi karfina". Ya dan tsahirta sannan ya rufe maganar da cewa, "Idan Allah ya sa ta zo hannunka komai ma sai ta yi, amma ni a yanzu babban burina shi ne na sauke nauyinta da ya yi saura a kaina, na aurar da ita a hannun da ko ba na numfashi ba za ta koka ba". Kan dole MK ya ha'kura da maganar amma ya kudire a ransa Sa'adah za ta yi karatu har sai ta ce ya ishe ta. Gab da za su fara rubata WAEC wa'adin da MK zai yi a makarantar FGC ya cika, amma saboda yajin aikin da jami'o'i suke yi, yasa hukumar makarantar ta roke shi ya ci gaba da zuwa kafin lokacin da ASUU za ta janye yajin aikin. Kasancewar MK da sakamako mai daraja ta daya (First Class) ya fita, yana cikin wadanda Jami'ar Bayero za ta dauka don yin koyarwa. A haka suka ci gaba da tafiya a baibai tsakanin MK da Sa'adah, shi yana ganin ya ba ta lokacin da za ta yi karatu sosai, ita kuma tana masa kallon wanda bai girmama lamarinta ba, hakan ya sa take saurarar duk wanda ya nuna yana son ta ba tare da tunanin ai tana da wanda take so ba! Musamman da a lokacin damina Baffa ya fi zaman Gogel saboda kula da noman da yake yi, ita kuma Inna zuciyarta daya ta dauka MK ne yake zuwa. A haka har ta kammala makaranta gaba'daya, cikin wannan yanayin ta hadu da Alhaji Mamman! Asibitin (Arewa Surgery) suka je duba Mahaifiyar Safina ita da Halima, sun fito harabar asibitin suka hadu da shi, ya nemi su shigo mota ya kai su, Sa'adah ta'ki amincewa amma da yake tare suke da Halima sai da ta rinjaye ta suka shiga motar, a hanya ya nuna ra'ayinsa akan Sa'adah, wanda sam-sam bai kwanta mata ba, musamman da yake ta gan shi dattijo da alamun yana da iyalai masu yawa a karkashinsa. A lokacin wayar hannun ba ta da yawa sosai kamar yanzu, sannan mai madannai ce komai tsadar wayar. Ya tambayi lambar wayarta, Sa'adah ba ta ce komai ba sai da ya sake tambayar a karo na biyu sannan ta ce "Ba ni da waya." Bai yi mamaki ba tunda a lokacin ba ta zama ruwan dare irin yanzu ba, ko iyayenta ma Sumayya ce ta sayo musu don ta ri'ka gaisawa da su tun da ita ba mazauniyar gari ba ce. Ita kuma ta gaje ta Inna. Halima ta ce "Ba Inna na da waya ba?" Shiru ta yi da alamun dai ba ta son ba da lambar ne, shi kuma sai ya ce "Yawwa 'kawarmu a taimaka a ba ni lambar Innarmu!" Haka Halima ta bude wayarta ta karanto masa lambar Inna saboda ta ga alamun za su sami kudi a tare da mutumin. Duk kokarinsa na son sai ya kai Sa'adah har kofar gidansu, amma hakan bai samu ba, saboda ta kafe akan idan aka gan ta cikin motar da ba a san mutumin ba, za ta fuskanci tashin hankali, wannan kalaman ya sake jin son ta sosai, ya san daga dukkan alamu da ga Babban gida ta fito ma'ana gidan tarbiyya. Kan dole ya kai su gidan su Halima wanda ita ko dar ba ta ji ba, hakan ya sa yake ganin anya iyayen Sa'adah ba tufka suke wannan 'kawar tana musu warwarba? A dan haduwar nan tasu ya lura da kamewar Sa'adah, ya kuma gane rawar kan Halima, a ransa yana rayawa da zarar ya sami Sa'adah zai raba ta da wannan kawar da idan kawancesu ya ci gaba da wanzuwa, zai ta ba tarbiyar Sa'adatu. Halima ta shige gida ta bar su, bai wani jima ba shi ma ya ce zai tafi don ya lura da Sa'adah kamar a tsorace take, kudi ya dauko har kimanin dubu talatin ya ba ta ya ce ta bawa kawarta goma a ciki. Ta tattaro dukkan kunya ta yaba a fuskarta tare da cewa, "Ka bar su ba zan karba ba!" Shi kuma ya na ta fadin "Idan ba ki karba ba, ba zan ji dadi ba Sa'adatu." Da kyar tasa hannu ta karba ta yi godiya bayan ya karbi address din gidansu, wanda kai tsaye address din gidansu Zainab Ma'aji ta bayar. Jiki na rawa ta shige gidan su Halima ta tarar da ita a falo da kaninta suna kallo kasancewar mamansu tana wurin aikinta, haka suka shige dakinta, kudin ta ciro ta nuna mata suka hau ihun murna! Halima na cewa "Ai tunda na gan shi na san akwai rodina tare da shi sannan ba matsolo ba ne." Dariya Sa'adah ta yi tare da cewa, "Kin ga kuwa takanas ya ba da naki sakon." Dadi ya cika zuciyar Halima da ta ji yawan kudaden da ya ba ta, haka ta sake jan Sa'adah zuwa Country Mall wanda a lokacin aka bude shi, suka kashe kudin nan tas a wurin siyan kayan kwalliya, da takalmi da jaka. daga Country Mall suka rabu kowa ya yi gidansu, Sa'adah zuciyarta sai wasiwasi take yi mai za ta cewa Inna akan wadannan kayan? Ta tabbatar uwarta ba sakaryar uwa ba ce! Duk wani motsinta akan idonta ne, wa za ta ce ya ba ta wadannan kayan? A ina ta zubar da nasihar da kullum take yi mata idan za ta fita na kar ta tsaya da saurayi a hanya, ko dazu kafin ta fita sai da ta jaddada mata duk mai son ta ya zo gidansu ya same ta, kar ta yarda a tsayar da ita a hanya. Ta gama tunaninta kaf ba ta sami kalaman da zai shiga zuciyar mahaifiyarta, ta fahimce ta ba, don haka kai tsaye gidan su Zainab ta sauka, ta ba ta ajiyar kayan tare da ce mata khalil ne ya ba ta, ba ta son a gani a gida, don ta san idan ta fada wa Zainab gaskiyar magana sai ta iya zuwa ta fada wa Inna tunda ta tsani abotarsu da Halima, kullum sai tace mata, "Sa'adah ki kiyayi kawance da Halima Mu'az ba wayewarku daya ba, ba kuma irin tarbiyarku daya ba" Da kyar Zainab ta karbi kayan bayan ta gama mata mitar ita a rayuwa ba ta son shiga shirgin rashin gaskiya, ban da rashin gaskiya ina ke ina sauraran wasu mazan tunda dai kin san namiji daya za ki aura! Kuma kin tsayar da wanda kika aminta da shi. Sa'adah da yake mafita ta ke nema sai ta yi mukus ta kasa tanka wa Zainab tamkar ba ita ce mafadaciyar nan ba. Tana isa gida ta tarar da Baffa ya dawo daga Gogel, ta yi farincikin dawowarsa amma a gefe takaicin yadda za a ci gaba da yin tuwo ba kakkautawa take yi. A kwanakin da baya nan hilatar Inna ta ke yi ba sa yin tuwo amma yanzu kam ba hilar da za ta mata ta yarda, tunda tafi girmama ra'ayin Baffa fiye da komai, sannan kuma ba za ta bari ta yi nata girkin ba, ce mata ta ke yi nan ba gidanki ba ne, ki bari idan kin yi naki gidan sai ki yi yadda kike so. Kallo daya Inna ta mata ta gano rashin gaskiya a tare da ita, ba ta mata magana ba, sai da ta gama da hidimar Baffa ya fita waje. Sannan ta iske ta a daki tana game a waya, ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta ta ce, "Iya na ga sauyi a tare da ke mai kike ciki ne da har ban cancanci na sani ba?" Duk da yadda Sa'adah ta maze akan ita ba komai, bai gamsar da Innar ba, amma sai ta ce, shike nan Iyah! Ki sani tun kafin ki san kanki na san ki, tun kafin ki yi dabarar boye mini halin da ki ke ciki nake tattalin ki, don haka komai za ki yi, zan gane. Ki sani idan har mu ba mu san mai kika yi ba, Ubangiji ya sani! Shi ne kuma zai kama ki saboda ha'intar da kike kokarin yi Mana." Ta fada tana kallon ta irin kallon nan mai tsanani. Jikin Sa'adah ya yi sanyi sosai musamman kallon da uwar take mata mai kama da ban yarda da ke ba, sai ta ce, "Ni fa Inna ban je ko ina ba." "Iyah ai ban ce kin je wani gun ba amma fada mini ina kuka biya daga asibitin sannan bayan Zainab da wa ku ka hadu a tafiyar?" "Yan makarantar mu ne kawai Inna" "To wa ye kuma ya ce yana son Zainab?" "Babu!" Ta sake ri'ko hannun ta sosai sannan ta ce "Waye ya tsayar da Iyah?" Kai tsaye ta ce "Kai Inna ni fa ban kula shi ba, wani mutum ne tsoho ne fa!" "To tsohon ba namiji ba ne?" Idan har nagari ne kuma kina son sa ai magana ta kare! Ba za mu miki dole ba, don haka ko waye ya tsayar da ke idan kin ga ya miki ki turo shi wurin mahaifinki, laifin da za ki mana shine ki yaudare mu, ki yi abin da kika san ba za ki iya yi akan idon mu ba, ina abin da ya ba ki?" Dariya ta kwace wa Sa'a ta ce " Ban karba ba Inna" Ita ma Innar dariyar ta yi tare da cewa "Ban yarda ba Iyah! Na san ki da martaba kalmar nan ta ba kyau mayar da hannun kyauta baya, amma na san Iyah ba za ta boye mini duk wata kyauta da za ta samu ba. Don ta san ba zan ki ta da alheri ba, sai dai na kiyaye ta daga fada wa hatsarin MAZAN YAU musamman da ba gidansu aka biyo ta ba." Tana fadin haka sai ta mike ta fice ta bar Sa'adah da sanyin jiki da kunya iri-iri suna saukar mata a lokaci guda. A ranta kuma fadi take, "Ko yara nawa ne irinta suka dace da samun tsayayyiyar uwa mai sa ido akan duk wani motsin 'ya'yanta?" A fili kuma ta furta "Madalla da uwa irin Inna!" Tana Jin komai za ta yi In Sha Allah ba za ta tozarta tarbiyar da Inna ke yi a kanta ba gajiyawa ba, amma kuma ba ta jin, za ta ki karbar duk wata kyauta da za a mata kawai dai boyewa ne ba za ta sake yi ba. don haka da kanta ta fada wa Alhaji Mamman gaskiya cewa gidansu na gaba kadan da wancan da ta fada masa da farko, haka nan hatta Khalil ta ba shi damar zuwa, ta gaji da boye-boye tunda wanda take yi domin sa ba fin su son ta ya yi ba, ita ce dai tafi son sa. Yawan wayar da Alhaji Mamman yake mata ba kakkautawa, sau tari ma gajiya take yi da amsa kiran nasa, ya sake sa ta raina kulawar MK, tunda dai yanzu ai ta gama karatun tunda ada uzurin kar ya raba mata hankali a karatu ya gabatar. Amma har yau ya ki canjawa idan ya kira ta da safe ba zai kara kira ba sai da daddaare shi ma a ya dade su yi maganar mintina uku, sabanin Khalil da Alhaji Mamman sai su shafe fin awa akan waya suna neman saye zuciyarta tamkar ba kati suke sawa ba. Tana yawan tambayar kanta shin Uncle MK soyayya ne bai iya ba, ko kuwa matsayinta ne a zuciyarsa bai kai ya mata yadda su Khalil ke mata ba? Zuwan ma bai canja ba sau daya a sati, duk da kullum sai ya zo unguwar, sannan ba ya mata kyautar bajinta kololuwar kyautar sa dubu biyu, sai dai karshen wata ya kan hado mata shopping din kayan kwalliya masu matsakaicin kudi da tarkacen alawowi masu dadi da biscuit, wanda ba sa dadata da kasa saboda yadda Alhaji Mamman da khalil mai sato kudin iyayensa suke mata barin kudi. Wani zuwa da Alhaji Mamman ya yi ya fa'da mata matansa biyu, da yara bakwai, bai boye mata shi dan majalisar jaha ba ne mai wakiltar karamar hukumar Gezawa, uwargidansa na can Gezawa yayin da amarya ke nan cikin Kano a kwatas din 'Yan Majalisu na Farawa. Da daddare Sa'adah na kwance a daki tana hira da Khalil, cike da nishadi take amsa wayar don kuwa tabbas tana jin son Khalil, kawai sanin ba za a masa aure yanzu da kuma soyayyar MK da ta danne tasa ne! Amma tana son sa yana burge ta ya dace da tsarinta na Luxury Life. Tana ganin kiran MK sai shigowa yake yi amma ba ta katse ba, tunda ta san shi ba wani lokaci mai yawa zai dauka yana lallabar ta ba, sai daga baya ta katse kiran Khalil bayan ta dauki excuse akan ya ba ta mintina biyar tana zuwa. Tana kiran sa ya katse ya kira ta bai mata complain din da wa take waya ba, hakan ma yasa ta sake jin haushinsa, ya tambayi lafiyarta, ya kuma sanar mata cewa gobe zai zo abokinsa na son ganin ta, to kawai ta ce, a ranta kuma tana cewa abokinsa ne yake son ganina ba shi ba. Washegarin kuwa suka zo shi da amininsa Mahmoud Karfi, wani abu mai kama da almara Mahmoud na dora ido a kan Sa'adah ya ji son ta ya cika zuciyarsa, ta zo masa a yadda yake burin samun matar aurensa ta kasance. kwalliyarta, yangarta, shan kamshinta duk sun tafi da shi, amma sai ya yi yaki da zuciyarsa ya danne ta yana nanatawa kansa MK ya wuce ya hada soyayyar mace da shi, ya tabbatar idan MK ya gane yana son ta to tabbas zai bar masa. Idan kuwa haka ne shi ne ya kamata ya haramta wa kansa wannan yarinyar da a yau ya dora ido a kanta, a daddafe aka yi hirar Mahmoud ya ba ta kyautar kudi dubu biyar suka tafi yana ta neman tsarin shaidan da zuciya da suke sake kawata masa Sa'adah. Madalla da aboki irin Mahmoud wanda yake daraja abota da kuma sadaukarwa, ba wanda zai zagaye ya yi wa abokinsa kafar ungulu ba. *BAYAN WATA UKU*. Zuwa wannan lokacin Sa'adah ta canja sosai domin ba karamin kudi Alhaji Mamman ke sakar mata ba, ta mallaki zobunan Dubai Gold a boye har guda biyu. Ta mallaki waya mai kyau Sliding 'kirar Nokia da SIM a ciki, wayar dai Inna ta sani amma zobuna ta kife ta musamman da Innar ba ta san Gold ba. Tun MK bai lura da canjawar Sa'adah ba har ya fara ankara da yadda kwallliyarta ta karu, ta daina dokin amsa masa waya, ta daina mitar rashin zuwansa, sannan dan flashing din da take masa ta daina idan zai kwana ya yini bai kira ta ba, baya taba ganin text ko flashing dinta. Duk da bai san tana da waya ba har zuwa wannan lokacin shi da layin Inna ya ke kiran ta, so yake ya mata bazata jiran fitowar results dinsu yake yi, idan har ya yi kyau, waya zai siya mata, idan ma bai yi ba dai zai siya mata. Ashe shi bai san ta kerewa rike kananun wayoyi irin wanda yake harin siya mata ba. Jikinsa ya fara sanyi don haka ranar wata Laraba ya kasa jiran Juma'a ta zo, ya shirya ya nufi gidansu da yamma. Sai dai yana zuwa ya tarar da Alhaji Mamman zaune a kan tabarma, yana tsayawa a bakin zauren ita kuma ta fito daga cikin gidan ba ta 'karasa isowa zaure ba, amma idanuwansu sun sarke da juna, bai ce kala ba ganin Alhaji Mamman bai ganshi ba sai kawai ya yi murmushin da babu nisha'di a cikinsa ya juya abin sa. Sai ta tsinci kanta da diriricewa, ta ji tamkar ta ruga da gudu ta ce masa ka dawo, kai nake fatan ace kai ne a zaune ba wannan mutumin ba, amma ba damar yin haka, a daddafe ta gaishe shi, ta gabatar masa da uzurin zazzabi take yi don kar ya ji ba dadi ne yasa ta daure ta fito. Ya gamsu a yadda ya ga duk jikinta ya saki ta yi wani iri, tashi guda, don haka ya fita ya je mota ya kwaso mata sayayyar da ya jido mata, bayan ya ajiye mata rafar yan 200 sabbi kal. Tayi godiya ta shiga gidan zuciyarta daya tunda Inna ta je cikin Unguwa yinin biki don haka ta rage wasu kayan ta boye akan sai wani zuwan ta nuna mata. Jikinta na rawa ta shiga lalubo lambar MK, amma har ta katse bai dauka ba, ta sake kira har sau uku nan ma bai dauka ba. Alkalamin *SURAYYA GWARAM* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan, ba tare da iznin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *Fatan alheri ga* *Asma'u Sani* *Aisha Lagos* *(Mrs Dan manya)*. *Shafin na ku ne ku yi yadda kuke so da shi*. 38_39. Haka ta ci gaba da kiran har ta gaji, tana 'kiyasta adadin kiran da ta yi masa ya kai ashirin, jikinta ya mutu tamkar marar laka, zuciyarta ta cunkushe da fargaba, tasan tana son MK sosai amma a yau ta sake sanin son da take masa marar adadi ne, duk da kasancewar ba lokacin zafi ba ne sosai, amma zufa sai karyo mata take yi. Waya kuma na hannunta, tana ci gaba da kiran sa. Tunda ya bar gidansu Sa'adah Masallaci ya nufa da 'kyar ya karasa saboda yadda zuciyarsa ta daure, ba abin da yake bukata sai kadaici. Ya Jima a zaune yana ta ambaton Allah har ya sami sassauci sannan ya dauki Qur'ani ya fara karatu a fili, a hankali, duk kiran da Sa'adah ke yi masa yana gani, duk da a silent ya mayar da wayar. Bai bar massalacin ba sai da aka yi Magariba zuwa wannan lokacin ya samu saukin daurewar da zuciyarsa ta yi a dalilin kishi, ya fito daga Massalacin ke nan kiran ta ya ci gaba da shigowa ba kakkautawa. Gefe sosai ya samu ya zauna ya fito da wayar ya katse kiran nata sannan ya kira ta. Jikinta har rawa yake yi wurin amsa kiran wanda ta dade ba ta ji zakuwa da dokin amsa kiran sa ba kamar a wannan lokaci. Muryarsa ba amo sosai ya mata sallama tare da cewa, " Sorry Sa'adatu! Kin kira na bar wayar a caji ne tun dazu sai yanzu na ga tarin missed calls." Wani nauyin jiki ya kara kama Sa'adah, ta rasa kalmar da za ta furta saboda abubuwa biyu, na farko bai nuna ta masa laifi ba tunda da ban ha'kuri ya bude maganarsa bugu da kari ma katse kiran ta ya yi, ya Kira ta. Na biyu ya ambace ta da Sa'adatu rabon da ya kira ta da hakan tun lokacin suna yar tsama, ita kam ya binneta, ha'kuri za ta ba shi ko kawai sharewa za ta yi kamar yadda ya yi? Da kyar ta bude baki ta ce "Ai na dauka kana sane ka 'ki amsawa." Tana rufe baki ya ce "Ko daya to mai kika mini?" Ta san sarai a cikin fishi yake, don haka sai ta lankwashe harshe ta ce "Ka yi ha'kuri don Allah!" Da sauri ya cafe da cewa "Ni fa ba ki mini komai ba, laifina ne da na zo kai tsaye ban sanar da ke ba, sannan ai yaudarar kai ne na yi tsammanin ni kadai kike kulawa, ke allura ce a cikin ruwa don haka feel free you did nothing." Ta kasa gane inda ya dosa shin gatse ya ke mata ko kuwa da gaske hakan yake nufi a zuciyarsa? Don haka sai ta ce "To ka dawo na ganka dama ai na kwana biyu ban gan ka ba" Kai tsaye ya ce, "Ai ba na zuwa zance da daddaare" Shiru ta yi sannan ta ce "To gobe za ka zo?" Tana rufe baki ya ce "Ina da schedules masu muhimmamanci a gobe." Kawai sai ji ta yi kuka ya zo mata, cikin rawar murya ta ce "Har sun fi ni muhimmamanci?" Cike da rashin kulawa ya furta "Wadancan tabbas ne, ke kuwa gaibu ce." Ta yi shiru amma kuka take yi, yana jin yadda ta ke jan majina da shassheka, amma ya yi burus da ita, yana fatan ta ji a ranta cewar ita ba wata tsiya ba ce a gunsa. Cikin kuka ta ce "Ni ka ke kwatantawa da gaibu?" Ko dar bai ji ba wurin ba ta amsa da cewa, "E!" A gajar ce. Bai sani ba ko kishin dake cin zuciyarsa ne, ya sa bai ji kukanta ya taba shi sosai ba. Yayin da ita kuma bakin cikin yadda yake nuna mata rashin kulawa yake dada addabar ta. Duk da hakan sai ta daure ta ce "Jibi Juma'ar za ka zo?" "Zan zo idan ina cikin masu rai da lafiya idan kuma uzuri ya taso ban sami zuwa ba, to sai satin sama." Ta yi shiru tana jin ta rabu da wannan mutumin da yake nuna mata ita ba komai ba ce a idonsa, sanin ya gan ta da wani ta san dole zai ji ba dadi yasa ta ajiye komai ta neme shi. Har ha'kuri ta ba shi amma shi ya nuna ma ba laifi ba ne bai yi fishi ba, anya kuwa yana son ta, anya ba ita ke bankaura akansa ba? Jin ta yi shiru ya sa ya magantu da cewa, "Sai yadda ta yiwu." Ya katse wayar! Bakin ciki ya kama ta sai kawai ta kife kai a kan filo tana kuka. Shi kuma ya mike ya mayar da wayar aljihunsa, yana sake jin sau'kin radadin da zuciyarsa ke yi masa, tunda dai ya tabbatar ita ma ta shaki takaici. Washegari tun safe Sa'adah ke zuba idon kiran MK har aka yi sallar Isha bai kira ba, a lokacin ha'kurinta ya gaza, ta dauko wayar Inna ta shiga kiran sa, sai da ta gama ringing bai dauka ba, tana shirin sake kira sai ga kiransa ya shigo. Ba ta tsaya jan aji ba ta dauka da sauri sai kuma ta yi shiru ta ki yin magana. Sai da ya yi sallama har sau biyu sannan ta amsa ciki-ciki, mamakin ta ya kama shi amma ya waske ya ce, "Mura ki ke yi ne?" Nan ma ta yi shiru ya nisa ya ce, "Yau yini guda ban zauna ba, ina ta yunkurin kiran ki, sai wani al'amarin ya mantar da ni. Yanzu kuma na dauko wayar da nufin na kira sai kika riga ni, Ina fatan kin yini lafiya?" Haushin sa ya kama ta sosai ta kasa tanka masa, amma tana raya cewa wai ya manta da jin muryarta. Jin ta sake masa shiru sai ya kashe wayarsa. Ita ma ta ajiye wayar daga kunnenta, tana gaskata zarginta na zaton MK da gaske ba son ta yake yi ba. Kafin ta yi yunkurin yin wani abu kiransa ya sake shigowa ta yi kamar ba za ta dauka ba sai kuma zuciyarta ta kasa jarumta. Haka ta sa hannu ta amsa, ba tare da ta yi magana ba. "Kina jina?" Abin da ya furta ke nan, ta sake yin shiru! takaici ya kama shi cikin fa'da fa'da ya ce, "Kin san ba za ki yi magana da ni ba mene ne zai sa ki kira ni?" Sai kawai ta saka masa kuka mai tsananin gaske irin mai cin rai! Ya yi shiru yana jin kukan nata wanda yake rasta dukkan sassan jikinsa musamman yadda take yi tana ajiyar zuciya. Jikinsa ya yi sanyi sosai sannan kuma hankalinsa ya tashi, duk da ya san ma'abociyar kuka ce ita din, amma wannan ba na zallan shagwaba ba ne, da alamun damuwa sosai a cikin kukan. Ya yi kasa da muryarsa sosai ya ce, "Me ya faru, fada mini mene ne yasa ki kuka haka?" Jin ya karya murya yana tambayar ta sai wani kukan ya sake kwace mata sosai wanda ya tayar da hankalin MK sosai. A gigice ya dinga fadin "Don Allah ki yi shiru ki fada mini me ya faru, kin tayar mini da hankali." Ta kasa magana saboda kukan ya ci karfinta ita kanta so take yi ta daina amma ta kasa sai shesshka da ajiyar zuciya ta ke yi. Ya yi shiru yana jinta, yana jin shi ma tamkar ya rushe da kukan ko ya sami sau'kin yadda zuciyarsa ke bugawa. Ya lankwashe murya ya ce, "Sa'adah! so ki ke ni ma na yi kukan ne? Don Allah ki taimake ni ki yi shiru haka nan , ko so ki ke kanki ya yi miki ciwo?" Cikin kukan ta ce, "Ka damu da ni ne da har kake gudar mini jinya?" Ya ce, "Haba Sa'adah wacce irin magana ce wannan! Ai ni gani nake yi Baffa da Inna ne kawai suka fi ni damuwa da ke " Ta yi fit ta ce "A hakan?" Ya nisa sannan ya ce, "Ke matsala ta da ke ba ki fahimce ni ba, har yanzu kin kasa gane manufata. Kowanne Dan adam yana da tsarinsa, don ina sonki ba zan miki karya ba, abin da nasan zan iya shi zan miki, amma tun ba mu je ko'ina ba, na gane kin raina kulawar da nake ba ki gaba'daya" Ya dan yi shiru sannan ya nisa ya ci gaba da fadin, "A farko tsakanina da Allah kamar yadda na fada mikil saboda jarrabawar da za ki yi yasa ban cika yawaita zuwa da kuma kiran ki a waya ba, sai ke kuma hakan ya zama dalilin da kika mini kishiyoyi, alhalin kin san har a gidanku na bayyana kaina ina son auren ki" Ya fada muryarsa da rauni sosai. Yayin da ita kuma kukan ya tsaya mata cak, tana jin wani irin abu na taso mata da ta kasa tantace mene ne shi. Ya sake cewa, "Sa'adah duk motsin ki akan idona kike yin sa, ta ya ya ki ke tsammanin zan saki jiki da ke alhalin na tabbatar zuciyarki tana rawa a kaina! Na dade da gane kin samu mai kudi, na dade da sanin kina tare da Khalil har yanzu, ba don ina son ki sosai ba ai kamata ya yi na janye kaina a cikin 'yan takara amma kullum ina karfafa wa kaina guiwa da cewa idan rabona ce ke zan same ki, duk da haka dole na yi kaffa-kaffa don ba ni da tabbacin kina so na bare nasa rai Sugar Daddy ba zai kada ni ba!" Kunya ta lullube ta, da kyar ta iya cewa "Ba ka da tabbacin Ina son ka fa ka ce?" Da sauri ya amsa da cewa, "E wallahi da kina so na ba za ki saurari kowa ba, kin ga ni namiji ne zan iya hada mata biyu ko sama da hakan a rana na aura, amma tunda ke nake so, ke na aminta ta zamo mini uwar 'ya'yana ban sake kula wata da sunan soyayya ba. da na lura ba ki ba ni irin wannan matsayin ba, shiyasa na ke janye jikina, musamman yadda kika ci gaba da kula fitanannen yaron nan." Kalamansa sun sa mata kasala sosai bayan kunyata ta da suka yi. Da kyar ta bude baki a hankali ta ce, " Na daina!" Ya yi murmushin da ya iso har cikin kunnenta, ya ce, "Mai ki ka daina din?" "Abin da nake yi da ba ka so! Sannan kai ma ka daina mini wulakanci, kana nuna mini ba ni da daraja a gunka" Ya sake murmusawa ya ce, "Akwai darajar da ta wuce na aure ki, na killace ki a gidana?" Kunya ta kama ta, ta yi shiru dadi na cika mata zuciya. Ya lankwashe murya sosai ya ce, "Ke ba ki san idan na tsananta zuwa ina kallon ki, za a samu matsala ba? Ko fa waya mu ka yi mai tsayi sai wanka ya kama ni, ya kike ganin kuma idan kullum zan gan ki a kusa da ni?" Kunya mai tsananin gaske ta kama ta ta kashe wayar tare da rufe idanuwanta tamkar yana tsaye a gabanta. Ya kira tana gani har ta katse amma ta kasa dauka ya ci gaba da kira har sau uku ta kasa dauka saboda yadda ya ba ta kunya. Sai ga text ya shigo ta bude ta karanta kamar haka _"Da gaske nake yi Sa'adah, don haka na roke ki, ki daina kallon rashin zuwana akai-akai da sunan rashin daraja ki, kokari nake yi mu kiyaye dokokin shari'a! zan zo gobe bayan Masallaci amma plz kisa hijabi ki 'boye wadannan abubuwan da suke karya mini alwala. Good night!"_ Ta karanta yafi sau ashirin tana jin shauki mai dadi na fizgar ta, tana jin ta tamkar a gajimare take yawo tsabar dadin soyayya. Ta hakikance MK shi ne mabudin farincikinta, duk wata damuwar zuciyarta ya wanke mata tas. Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 40. Washegari tun safe Inna ta lura da yadda Iyah ta tashi da kuzari da walwala, duk ayyukan gidan cikin kuzari take yin su sabanin kwanakin biyun da suka gabata da ta ke sukuku. Kafin La'asar ta shirya, sai dai ta rasa hijabin da za ta saka. Gabadaya hijaban ta guda uku ne, biyu na Islamiyya ne, dayan kuma sallah take yi da shi, ta yi shiru tana nazari sai ta zabura ta fita. 'Dakin mahaifiyar ta shiga ta lalubo wani hijabinta da ta sayo a Jos amma ba ta taba sawa ba, a tsakar gidan ta ware shi kalar fari da maroon fulawa a jikinsa ya yi kyau sosai, ta saka ta ga ya zarta guiwarta da kadan, ta isa kusa da Inna da take zaune ta na tsinkar zogale ta ce, "Inna na dauko Hijabin nan." "To." Kawai ta ce mata ta bita da ido, tana mamakin yau Iyah ce za ta saka hijabi ba don zuwa makaranta ba? 'Dakinta ta koma ta gama shiri, ta fito sanye cikin riga da siket na wani yadin material mai laushi, maroon colour! Hijabin ya hau sosai, ba karamin karbar ta suka yi ba. Tana fitowa Inna ta juyo ta zuba mata ido tana raya komai Iyah ta saka sai ya mata kyau, ta ce, "Da kin san yadda Hijabin nan ya miki kyau da kin daina saka mayafi kin koma ado da hijabai." Dariya ta yi tare da cewa, "Allah Inna tsokana ta kike yi" "Da gaske nake yi miki, ba ki gan ki ba tamkar bakar Balarabiyar Habasha." Dariya Sa'adah ta dinga yi sosai tana cewa, "Ashe har haka autar ki take da kyau Inna?" Can kuma ta katse dariyar ta ce, "Inna Uncle Mukhtar ne zai zo kuma ya ce zai shigo ya gaishe ki." Dadi ya sake kamata da sauri ta ce, "To! Kamo mini Baffanku a waya na fada masa." "Kai Inna don zai gaishe ki ne za ki ce a fada wa Baffa?" "Dole na fada masa mana tunda dai bai san wani zai shigo masa gida ba, idan bai amince ba ai kin san kuwa ba yarda zan yi ya shigo ba." Sa'adah ta tura baki gaba alamun maganar Inna ba ta mata dadi ba ta ce, "Inna Uncle din ne wani?" "Wani ne mana tunda ba mu da alaka da shi, sai ya aure ki tukun, zai zama cikin ahalinmu, amma a yanzu kam dole yana da iyaka." Hakan kuwa sai da ta sanar da mijin nata, ya ce ya shigo idan ya zo babu damuwa. Ta kalli Iyah ta ce, "Komai aka yi shi akan ka'idojin shari'a ba a nadama, ke ma ki yi koyi da hakan. Kar ki yarda ki yi wasarere da hakkin mijinki, ko da baya gidan ki kiyayi duk abin da kika san ba ya so." Sa'adah ta amsa da "To!" Sannan ta sauya maganar da tambayar, "Inna na dauko juice din?" Da sauri ta amsa mata da cewa "Dauko mana ki hado da ruwa, ai ba sai kin tambaya ba." "To Inna ai shekaranjiya na ga kin hana ni dauka ne!" Tana rufe baki ita ma ta ce "Ai ba don shi aka saya ba, saboda Muutar ya sayo ya ce a ajiye idan ya zo ki dinga ba shi. Kin ga kuwa idan har ba Muutar ba ne ai ni ba zan bayar ba." Wucewa dakin Sa'adah ta yi tana dariya tare da cewa,"Oh Innah maganar Baffa tamkar hadisi take a gunki!" "Aljannata nake nema kin san kuwa aljannar mace ta fi samuwa idan mijinta ya yarda da ita." Cikin dariya sosai Sa'adah ta ce, "Sadaqati Inna! Kin yi gaskiya In Sha Allah har a aljanna ke ce uwargidan Baffah." Dariyar ita ma ta shiga yi tana fadin, "Allah ya shirye ki Iyah" Daidai lokacin kuma waya ta hau kuwwa tana dubawa ta ga MK ne, ta amsa, ya sanar mata ya iso. Ta mikawa Inna wayar tana cewa, "Ya iso." Daki ta koma ta sake gyara fuskarta sannan ta feso turare ta fito, ta dauki tabarma ta na fadin, "Ki tashi Inna ki kintsa, na ajiye miki Hijabin da za ki saka a kan gado." Harara ta galla mata tare da cewa ba zan saka wanda kika ajiye din ba 'yar fariya! Kin yi shigarki ta burgewa, amma kin tashi kin fesa turare." Ta yi kwafa tana ayyana dauke shi za ta yi ta boye. Murmushi ta yi tare da cewa, "Take heart mom!" Sannan ta juya ta tafi. Ta isa da sallama yana tsaye yana amsa waya, ya yi kwalliya da yadin kufta kalar ruwan kasa (brown), ya dora hular da ta dace da kayan. Sosai ya yi kyau, musamman yadda sumarsa da hula ba ta rufe ta gaba'daya ba tana ta sheki alamun ta sha gyara na musamman. Ya katse kiran yana zuba mata ido sosai sai kuma ya hau murza dukkan idanuwansa, ya sake kallon ta soasai, ya bude baki alamun mamaki tsawon sakanni goma sannan ya nisa ya ce, "Sa'adah ce kuwa, ko idona ne ya ke mini gizo?" Ta tura baki tana dan murmushi tare da shagwabe fuska. Hakan da ta yi sai ta sake burge shi ya ce, "Kin canja fa! Ba ki ga yadda kika yi kyau ba, ganin ki na yi tamkar 'yanmatan Ethiopia." Da'di ya kamata musamman yadda bakinsa ya yi daidai da na Innar ta, ya lura da yadda take murmushi, ya fahimci tana son a ce ita mai kyau ce, ko ta yi kyau. Ya ce "Ki fa daina wannan shagwabar ita ma tana sani a wancan yanayin!" Ta rufe fuskarta da gefen Hijabinta, ba tare da ta iya cewa komai ba. Ya sake cewa, "Idan ba so kike na zama agwagwa ba, to ki daina yin ta a yanzu. Ki tara mini ita zuwa lokacin da za mu tsinci kanmu a dakinmu!" Ta sake rufe ido sosai tana ayyana wai shi ba ya jin kunya ne? Ganin yadda ta rufe ido ta makale a bango sai ta ba shi dariya sosai. Ya dan juya dan ganin ba wanda zai ji shi, ya yi kasa da murya ya ce, "Ba ki ji yadda na ji ba, ina ma ni kika makale ba wannan bangon ba! Kunyar nan ma burge ni take yi, komai na ki is special!" Shiru ta yi ta kasa juyowa, bare ta tanka masa, tana ji a jikinta yadda idanuwansa ke yawo a kanta. Da kyar ta bar jikin bangon ta shimfida tabarma tana cewa, "Bismillah!" Ya yi kicin-kicin da fuska tamkar ba shi ne mai walwala yanzun nan ba. Ya ce, "Ba zan zauna ba!" Ta dago ta kalle shi a kunyace ta ga yadda ya hade fuska, gabanta ya fadi, tana tunanin me ya 'bata masa rai kuma? A hankali ta ce," Tafiya za ka yi?" Ya girgiza kai sannan ya ce, "Zaman ne ba zan yi ba, ki dinga shimfida wa Honorable." Ta yi shiru tana jin fargaba na taso mata! Ta nisa ta ce, "Amma dai ai na ba ka ha'kuri, magana sai ta wuce." Da sauri ya ce, "In dai sai na zauna a inda yake zama to kuwa magana ba za ta wuce ba!" Ya juyar da kansa gefe guda, ganin yana Shirin dawo mata da yanayinsa da ba ta so na nuna ko in kula ta kalle shi ta ce "Bari na dauko maka wani abin zaman to." Bai ce komai ba, ta nade tabarmar ta shiga da ita, ta dawo da kiret din lemon kwalba mai kwari, ta ajiye ta dora sallaya a kai, kamar ba zai zauna ba sai kuma ya zauna din. Ita kuma ta zauna a kan wani dutse da ya ke zauren. Ta kalle shi ta ga bai ware ba, ta daure ta ce, "Ba don fishinka na gigita zaman lafiya ta ba, da haka zan so ganin ka kullum. yadda ba yanmatan da za su ga fuskar tunkarar ka, saboda kwarjini da tsare gida." Dariya ta kwace masa, ya nisa ya ce, "Kina da son kai Sa'adah! Ba kya son na kula yanmata amma ke ba ki kiyaye kula wasu mazan ba." Ganin ta yi kasa da kai sai ya canja maganar da cewa, "Mahmoud ya na gaishe ki" A hankali ta ce "Na gode!" Sun jima suna hira bayan ya sha ruwa, suka shiga ya gaida Inna, ya ajiye mata kudi, sannan su ka koma zauren, ba su dade da zama ba Baffa ya dawo, ya tarar da su, a kunyace, MK ya sauko daga inda yake zaune ya tsugunna ya gaishe shi. Baffa ya amsa cike da farinciki, har ya wuce sai ya dan tsaya ya ce, "Da ma kuwa ina son ganin ka, idan ka samu lokaci ka same ni." Da girmamawa MK ya amsa da Fadin, " Koyaushe ina da lokaci." Baffa ya ce "To bayan La'asar gobe idan ranmu ya kai." Sai da ya shige sannan ya koma gun zamansa, Sa'adah na masa dariyar yadda ya takure. Ya kalle ta ya ce, "Idan akwai abin da ya fi haka na kunya zan ji tunda yarsa nake so ya ba ni, ya kuma san abin da zan yi da ita!" Shike nan ya rufe bakinta ruf. Ya zuba mata ido ganin yadda ta turo baki gaba alamun fishi-fishi. Ya waske kamar bai gani ba, ya nisa ya kira ta da alamun seriousness "Sa'adah!" Ta yi shiru, sanin halinta na shariya da sanin ta ji shi ya zarce da fadin, "Magana za mu yi ta gaskiya, ki nutsu ki ban hankalin ki." "A kan kunnenki Baffa ya ce za mu yi magana, ga zatona mafi karfi ina ganin zai yi maganar idan mun shirya kanmu na turo da magabatana." Nan ma ba ta ce kala ba. Ya nisa ya sake cewa, "Kina ji na kuwa?" Kai ta daga masa alamun tana tare da shi. Ya ce, "Tsakaninki da Allah ki fada mini gaskiya don na san yadda zan tunkare shi. Mun kai lokacin da ya kamata a ce mun fahimci juna, maganar aure idan manya suka shiga ta kare fa! Ba maganar canjawa idan dai ba mayar da iyaye abokan wasa za a yi ba. So nake yi, ki fada mini da bakinki idan Baffa ya tambayi mun shirya kanmu, me zan ce masa?" Ta yi kasa da kanta ta kasa cewa komai, tsawon minti guda sannan ya dora da cewa, "Kar ki ji nauyin fadar gaskiya na yi miki al'kawarin zan fahimce ki, zan kuma fahimtar da Baffah yadda ba zai ga laifinki ba." Ta kasa bude baki ta yi magana ita kanta ba ta san me yasa harshenta ya yi mata nauyi ainun ba? Tsawon mintuna yana dakon ta magantu amma shiru. "Ina ta magana kin yi mini shiru kuma kin san ba na son ina magana kina ji amma ki yi kunnen uwar shegu." Ta sake yin kasa da kai, da kyar kuma a hankali ta ce, "Ni to me zan ce?" Bai ji dadin yadda ta ce ba amma sai ya ce, "kinsan me za ki fada mini da zai nuna kin aminta da Ni ko akasin hakan". Ta kasa fadar ko daya, ya gaji da sauraronta ya ce "Shirunki yana nufin na yi hakuri, na sha kaye a hanun abokan takara". Yana gani ta bude wayar dake hannunta wacce ta Inna ce ta fito da ita. Ba zato ya ji wayarsa ta yi kara kadan, alamun shigowar sako (message) bai duba ba ga zaton sa MTN ne. Ganin ta share ta hau daddana waya sai ya sake jin rashin dadi sosai, a tunzure ya ce, "Silent again?" A kunyace ta ce, "Ka duba wayarka!" Bai yi musu ba ya dauko wayar sa ya shiga ma'adanar sakwanni (inbox) ya ga text din da ya shigo ita ta turo shi. Da sauri ya bude, harrufa uku kawai ya gani. "*YES*" Kawai ta rubuta wani irin dadi ya mamaye zuciyarsa da sauri ya ce, "Kin amince mini na turo Sa'adah da gaske?" Kai kawai ta daga masa don ta sake ba shi tabbaci. "Alhamdulillah!" Yake ta fadi tare da cewa "Na gode!" Ya bude murya sosai ya kira ta, bai jira amsawarta ba ya zarce da cewa, "Idan fa kin zabe ni har na turo aka nema mini aurenki, hakan na nufin kin rabu da Honorable, da wannan tabbataccen yaron! Da ma kowa da kowa, sai ni kawai. Kin ga saboda na san kina da damar ki zabi wanda ya miki shi yasa nake danne kishina, amma tsakani da Allah idan har maganar aure ta kullu tsakanin manya dole ki rabu da kowa kin amince?" Ba wani dogon Turanci ta ce, "E!" Farincikinsa ya karu ya hau fadin, "In Sha Allah ba za ki yi nadamar zabe na a matsayin mijin aurenki ba." Shauki ya debe su ba su ankara ba har aka fara kiran sallah sannan ya tafi yana cewa, "Duk yadda muka yi da Baffa za ki ji." Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH*! _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 41-42 A Daren ranar Baffa ya sake zaunar da Sa'adah tare da mahaifiyarta, ya ce "Ina sane na bar ki kina sauraran wasu bayan Mutari. Saboda na ba ki damar da shari'a ta ba ki, na kar na aurar da ke bisa dole, duk da shari'ar tace ni na fi cancanta na zaba miki mijin aure kasancewar ki budurwa. Amma tunda muna wani irin zamani da 'ya'ya suke ganin sun fi iyayensu sanin abin da ya dace da su, ya sa na ba ki damarki, na sha fada miki aure zan miki, ba kuma zan miki auran dole ba, sai dai na dora ki akan shawara mai kyau. Alhamdulillah lokaci ya yi, don haka ki fada mini a cikin masu zuwa wajenki wa kika zaba? Ina son ya turo mini magabatansa a tsayar da magana guda daya." Ta yi shiru kanta na kasa, Inna ce ta tanka , "Ai na ga alamar sun daidaita da Muutar din." Hannu Baffa ya daga mata alamun ta yi shiru, ya bude murya ya ce, "Iyah tsakanin Alhaji Mamman da Mutari wa kike so?" Ta sake yin shiru, ya nisa ya ce, "Dole fa ki yi mini magana saboda duk hukuncin da zan yanke, ya kasance da yardar ki, ba na so daga baya ki ba ni matsala, kwanakin baya da Alhaji Mamman ya same ni ban ba shi amanna ba, amma na ce ya nemi yardar ki, saboda shi ma mutumin kirki ne, ya samu yabo a wurin mutanen da suke kewaye da shi. Yanzu kuma lokaci ya yi da zan sallami daya a cikinsu." Inna da ta ke sauraran su ta ji tamkar ta ce Alh Mamman zai sallama amma ta yi shiru saboda bai ba ta damar yin magana ba. Ya sake kiran ta a karo na biyu, "Iyah!" Ta amsa murya a dakushe. "Wa zan sallama a tsakaninsu? Ko kuma dukkansu ba ku shirya ba?" Ta jima kafin ta bude baki ta ce, "Dazu Inna ta fada ai." Da'di ya kama dukkansu, ya ce, "Kina nufi da Mutari ku ka shirya?" Kai ta sake yin kasa da shi ba tare da ta amsa ba, Inna ce ta yi fit ta ce "Ka san ba za ta iya amsawa ba, amma na lura da Muutar ne za'binta." "ALHAMDULILLAH!" Baffa ya furta a fili. Ya zarce da fadin, "Shike nan da kaina zan ba wa Alhaji Mamman hakuri, Allah Ya sanya alkhairi a tsakaninku, ki yi ko yi da uwarki wurin biyayya, Allah Ya tabbatar da alherin da muke zaton sa tsakaninki da yaron nan." Da haka ya sallame ta wanda da kyar ta iya tashi. Washegari kuwa bayan La'asar MK ya samu Baffa, zatonsa ya tabbata domin kuwa maganar turo magabatansa ya yi bayan ya tabbatar masa ya yi magana da Sa'adah ta ce shi ne zabinta. Godiya sosai MK ya yi tare da cewa, "Za su zo ba da jimawa ba." Baffa ya nisa ya ce, "Ka yi shirinka a hankali sannan zan fada maka ni ba a kawo mini lefe sannan ni ma bana yin kayan daki, don haka ka shirya dakin da za ka ajiye ta da iya abin da za ka iya, ni ma zan hado ta da yan tarkacen da zan iya. Daurin aure kawai za a yi sai kuma uwarta za ta dan yi taron mata a gida, zuwa yammaci da kaina zan kai ta dakinta, Ban yarda da wani taron maza da mata da sunan fati ko wani abu na daban ba! Idan kun tare kuna da ra'ayi, da damar yin walima wannan sunna ce sai ku yi. idan har wannan tsarin ya yi, akan hakan za ka turo mini magabatanka, Saboda idan sun zo, zan sanar da su." Godiya sosai Mk ya sake yi tare da fadin, "In Sha Allah yadda duk ka ce haka zan yi Baffa, na gode sosai da karamci Allah ya saka da alheri." Da haka suka rabu MK na jinjina halin wannan dattijon, ko irin su nawa ne suka yi saura a cikin al'ummar mu? Gefe guda kuma tunanin yadda Sa'adah za ta karbi lamarin yake yi, ko ya ya za ta ji idan aka ce ba za a yi mata lefe ba? Sannan ya za ta yi idan ta gane cewa ita ma haka za a kai ta ba kayan daki, ba biki irin na zamani?😁 Da kansa ya ji dariya ta kufce masa haka ya samu gefe ya yi dariyarsa mai yawa, sai da ya gama a fili ya ce, "Sa'adah big girl ba lefe!" 😁 MK shiru ya yi bai fada wa Sa'adah tsarin Baffa ba, bai san mai yasa yake jin tsoron fada mata ba, ya ja bakinsa ya tsuke, ta ji maganar a bakin wanda ya tsara lamarin. Takanas 'yan uwan mahaifin MK, Baba Umaru, da Baba Idi, suka taho Kano suka hadu da Alhaji Isa, suka rankaya gidan su Sa'adatu nema wa MK auranta. Kai tsaye ya ce ya ba su sannan sadaki kawai za su kawo masa. Bai boye musu tsarinsa na rashin yin hidima ba. Dukkansu, sun yi farinciki, sun kuma yi amanna da tsarinsa, suna fadin ai mu ma da ga yau za mu yi koyi da kai don mu sami sauki a cikin zamantakewarmu, sannan darajar aure za ta karu za a daina fargaban yin sa, saboda an kewaye shi da hidimomi masu wahalarwa. Baffa ya sake cewa "Na baku wuka da nama duk lokacin yaron ya kammala shirinsa kusa ranar aure da kan ku, sai ku sanar da ni, ina kuma rokon ku fada masa iya abin da zai iya shi zai yi, fatana dai Ubangiji ya albarkaci auren." Godiya sosai suka yi suna yaba halin kwarai irin na mahaifin Sa'adah, suka jaddada masa ba da jimawa ba kuwa zai ji ranar da suke ganin ta dace da shirin MK, suka sake yi masa godiyar wannan girman da ya ba su. suka rabu cike da farinciki, a hanyar su ma tattauna karamcin da suka gani suke ta yi. Alh Isa ya ce, "Ai ni tun zuwan da na yi a farko na gane Mukhtar ya nemo aure a gidan mutunci, sai dai mu yi fatan Allah ya zaunar da su lafiya." Dukkan su, suka hada baki wurin fadin, "Ameen." Baba Umaru ya nisa ya ce, "Saboda karamcin wannan Mutumin, bayan sadakin da zan biya wa Mutari har kudin da zai shirya wa yarinyar daki zan ba shi ya kara saboda iyayenta su san muma mun iya karamci." Su Alh Isa su ma suka hau fadin, "Ai kuwa mu ma za mu sake sabon shiri." Sai da suka je gidan su MK suka yi wa Hajiya Babba bayanin halin da ake ciki, sannan suka tafi. Dukkan dangin MK sun karbi tsarin mahaifin Sa'adah, na ba zai yi kayan daki ba, musamman da bai nemi a ba shi wani kudi ba, illa ma lefen da ya ce su ma kar su yi. Da daddare suna falon gidan gaba'dayansu har Hajiyar Bichi, kasancewar duk sun zo gidan saboda haihuwa da Sameera ta yi, yau kuma aka yi suna, shi ne suka zarto gidan su. Hafsatu ce kawai ba ta nan, saboda a Lagos take aure, Hajiya Babba ta sanar musu. Ta kare maganar da cewa "Kayan da na fara tarawa na lefe kuwa tabbas zan ba ta, don da sunanta na ke sayan su." Hayaniya ta cika falon na yadda suka ji dadin tsarin suka hau fadin, "Ai kuwa dai za mu dage mu yi kayan daki masu kyau." Abbas ya dubi MK ya ce, "Amaryar taka tana da 'kanwa ne?" Falo ya sake daukar hayaniya Akil ya ce, "Saboda ka ji ba lefe ba bidi'oi?" Shi dai MK bai sa musu baki ba, suka yi shewarsu, suka gama. Haka ma Hajiyar Bichi uffan ba ta ce ba! Haj Babba ce da ragowan yaran suke ta dabdalarsu. Kwanaki uku tsakanin zuwan iyayen MK, Alhaji Isa ya sake yin tattaki da kansa ya sanar da Baffa suna son a yi auren bayan karamar sallah watanni biyar masu zuwa. Bai musa ba ya ce, "Allah ya sa ranmu zai kai" Baffa bai yi kasa a guiwa ba ya hakurkurtar da Alhaji Mamman, da ke ba yaro ba ne rabuwa aka yi irin ta salin alin, duk da bai so hakan ba, amma ya hakura, ya kuma roki Baffa ya ba shi damar ganinta, a karo na karshe. Baffah bai ki ba ya ce zai iya ganin ta. Maimakon ya jira a turo masa ita sai ya ce bari ya je ya dawo. Ashe sayayya ya tafi lodowa, bayan ya dawo bai jima ba, ya ba wa Sa'adah manyan leda har biyu shake da kayayyaki, yana fadin, "Na gode da mutuntuwa, Ubangiji Ya sanya alheri a tsakanin ki da wanda za ki aura" Ya yi mata sallama ya tafi yana jin ciwon rasa ta don so yake mata na fisabilillahi. Sai a lokacin Sa'adah ta ji sanyin jiki tana jin tausayin sa na ratsa ta. Tana shiga gida, ta zauna kusa da Inna ta fara bude ledar da ya kawo mata. Ta shiga dubawa, manyan leshi masu tsadar gaske guda biyu, da shadda getzna, ita ma biyu, da kuma atamfa Super Wax ita ma biyu, kowanne kuma da mayafinsa sai turaruka. 'Dayar ledar kuma takalmi da jaka ne har set shida masu tsananin kyau da tsada, da envelope wanda da dukkan alamu kudi ne, za ta ya ga ke nan, Inna ta ce, "Kar ki bude ki bari Baffan ku ya gani". Inna tana daga kaya tana fadin, "Wannan ya gane cewa aka yi ya yi ha'kuri? irin wannan kayan sai ka ce mai hada lefe?" Sa'adah dariya ta yi sannan ta ce, "Kai Inna duk da dai kayan masu daraja ne amma ai ko an sayar da su sai dai a hada lefe irin local din nan." Zuba mata ido Innar ta yi, sai kuma ta yi kwafa sannan ta ce, "ko ma yaya ne ai an yi 'ko'kari wata ai ba ma za a mata lefen ba, bare ta ga ya yi ka'dan." Cikin dariya sosai Sa'adah ta ce, "Yo kuwa Inna wacce ba za a mata lefe ba ai sai bazawarar da ta sarayar don tana bu'katar auren, da kuma budurwar da ba ta da daraja ake neman kai da ita." "Dariya ita ma Innar ta yi tana cewa "Ashe yayarki ma ba ta da daraja! don kuwa babu lefe aka aurar da ita, ba kuma neman kai mu ka yi da ita ba." "Auran Anty Sumayya ai irin na zamanin jiya aka mata, kar ki ba da misali da auranta" Ta nisa ta ce, "Iyah ba ki ga kuma saboda mijin natan ya san mutunci ya zame mata irin mijin da ba a cika samun su a Yau ba! Ke da kanki kin san mijinta irin mijin JIYA ne ba na YAU ba, ki yi fatan dacewa kawai, duk auran da aka ƙaranta wahala da bidi'a ya fi karko ya fi albarka". Cike da rashin gamsuwa ta ce, "A'a Inna gara dai a yi maka din, mijin ma ai sai ya raina ka, danginsa su isheka da gorin sadakar ka aka ba shi." Shiru Inna ta yi ta kyale ta, tana tunanin ashe akwai kallo ranar da tasan irin auran da za'a mata. Baffa da ya ga kayan da Alh Mamman ya kawo bai yi fada ba, kamar yadda yake yi a baya, ya farke envelope din sai ga rafar dari biyar wato dubu hamsin wanda ta zarce darajar dubu darin yanzu. Ya ajiye kudin, kayan kuma ya ce su dauka ta yi amfani da su, tunda dai sai da aka fada masa gaskiya sannan ya ba ta. shikenan rabuwar su da Alhaji Mamman. Tunda aka tsayar da maganar aure Sa'adah ba ta sake tsayawa da saurayi a fili ba, sai ta waya wanda suke cika mata waya da kudi, sai kuma Khalil da ta kasa rabuwa da shi duk da ba ta yarda ya zo gidansu sai dai idan ta je gidan su Halima ko kuma idan ta je gidan su Zainab Ma'aji sai ya zo. Soyayyarta da MK a gurinta za ta ce ba laifi, idan ya kira ta a waya yana dan jimawa su yi hira, haka nan yanzu sau biyu ya ke zuwa zance a sati, wani zubin ma har sau uku. Amma dai ita ba sosai ta gamsu da kulawarsa ba, kawai dai tana bin sa da yadda yake yi, da fatan Allah Ya sa ba soyayyar ne bai iya ba ta bakin Halima da Safina, da suke kushe shi duk da sai yanzu da aka tsayar da maganar aure, suka san da gaske soyayya suke yi. Kiri-kiri suka nuna mata me zai sa ta yi gangancin barin Alhaji Mamman inda za ta huta, ta bige da auran mai fama da alli da hidimar gidan su? Ita dai Sa'adah sai dai ta ji su, ta yi shiru. Musamman da ta ta'ba ce musu ba son sa take yi ba Baffa ne ya mata dole, ai nan ma suka mata ca tare da cewa, "A wannan karnin na 21st century za a miki dole?" Ta yi shiru tana jin yadda suke ta sakin maganganun rashin 'da'a tare da ingiza mai kantu, suna jaddada mata da dai ta auri mugun Malamin da ya gama tozarta ta a bainar nasi, gara ma ta auri Khalil Ibrahim sa'anta. Shiru take yi, wani lokacin zuciyarta ta shiga wasiwasi akan MK Bichi, musamman yadda bai kai su Khalil nuna mata soyayya ba. Amma dai ta san ba ta isa ta koma ta ce wa Baffan ta ta fasa ba. Alkalamin *Surayya Dee* ✍🏼✍🏼. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH*. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 43-44 A kwana a tashi ba wuya wurin Ubangiji. Watanni biyu suka zo suka shude tamkar walkiya, mai ya'ki da zuciyarsa kadai ke ribatar lokacin sa a cikin wannan zamanin da ababen shagala suka kewaye shi. A wannan lokacin manhajar 2go ta bullo, matasanmu samari da yanmata suka yi tururuwar karban wannan sabuwar manhajar wanda hakan ya taimaka wurin sake ruguza tarbiya matasa da yawa, saboda yadda ake hira da musayen hotuna na rashin da'a ba tare da jin shakku ko nauyi ba. Sa'adah na cikin jerin yan matan da suka yi tashen 2go da taimakon su Safina da Halima, yini take yi da waya a hannu har sai da Inna ta fahimci sabuwar rayuwar da ta shiga na yadda ta fi bawa waya muhimmanci fiye da komai. Ada kafin Inna ta fito da safe Sa'adah ta kammala komai na gyaran gida, wani lokacin har abin karin kumallo za ta yi, musamman idan Baffa ba ya gari, amma a yanzu sai ta kai rana ba ta share gidan ba, ga wanke-wanke a gefe kudaje na bin su, ko karyawar ma sai Inna ta yi ta faman kiran ta sannan za ta fito, Nan ma tana cin abincin amma wayar na hannunta, tana ta latse-laste tana murmushi. Wannan abin ya yi matu'kar damun Inna musamman yadda ta lura wanka ma Sa'adah sai ta kai la'asar ba ta yi ba, sabanin lokutan baya da sanyin safiya take wankanta da zarar ta kammala ayyukan gida, amma yanzu sai yamma likis ko ma dare. Ranar wata Litinin aka tashi da rashin wuta a unguwar gabadaya, cikin rashin sa'a ta kwana da rashin caji a wayarta, don haka sai ta tashi sukuku da rashin karsashi. Tana kwance lamo a kan katifarta, ta kalli agogon bango dake jikin dakin, ta ga karfe 7 na safiya, sai ta ga lokacin ma baya gudu don haka sai ta yun'kura ta gyara dakinta, ta gangara tsakar gida. Kafin wani lokaci da ba shi da yawa ta gama komai har wanke-wanke, gefe kuma ta dora musu abin da za su ci. Koda Inna ta fito ta gan ta, a tsakar gida sai mamaki ya kamata, musamman yadda ta gan ta ba waya a hannunta, ta gaishe ta ita ma ta amsa da walwala, sai da suka karya, ta yi wanka ta shirya ta yi fes da ita, ta fito tsakar gida ta sa tabarma ta zauna saboda lokacin zafi ne. Sai lokacin Inna ta dube ta ta ce "Wannan ita ce Iyah da na rayu da ita, wannan ita ce Iyarmu, ta jiya da ragowar kwanakin da suka shude ba Iyar mu ba ce ma'abociyar aikin gida da kuma ado"!. Kunya ta kama Sa'adah ta sa hannunwanta biyu ta rufe fuskarta, ita kanta ta san ta shagala, tana son ta tashi ta yi ayyukanta, amma sai ta kasa ajiye wayar tana ganin bari a dan jima, a haka har sai lokaci mai yawa ya tafi ba tare da ta an kara ba. Cikin hikima Inna ta sake fadin, "Ko a mafarki idan aka nuna mini wai zai ki zama yadda kika zama Iyah zan karyata na kuma yi gaggawar neman miki tsari da wannan karko irin na kifi. Ta ya ya za a ce kin rayu kina tafiyar da komai na aikin gida da tsaftar jikinki akan lokaci da kuma kuzari, amma sai da aurenki ya zo gaf kuma sai lalacewa ta zo miki? Wayar nan mai tsada ta zamani hatsarin dake cikinta ya fi alherin da ke tare da shi. Ki rabu da wannan shiriritar tun ba ki fada tarkon da za ki kasa fitowa ba!" Jikin Sa'adah ya yi sanyi sosai tana gaskata mahaifiyarta, yau kadai da wayar take kashe ta samu rarar lokaci har sallar walaha ta yi. Ta kuma samu sukunin tattaunawa da uwarta, ta yi abin da ya dace na ayyukan yau da kullum. Inna ta sake nisawa ta ce, "Ba namijin da za ki je kina masa wannan ba'kin dabi'un da kika fito da su, ku samu zaman lafiya da shi, duk son da yake miki kuwa. Ban hana ki amfani da waya ba, amma ki dinga ajiye ta sai kin kammala komai na aki, nauyi ne zai sake kama ki, shi namiji idan yana da mata komawa yake yi tamkar jariri komai sai an yi masa, ta ya ya za ki iya kula da miji da hidimar gida da wannan danne-dannen wayar da tun ana ganin na 'dokin wayar ne har kuma ya koma na kauyanci da asaranci ya zarce hankali da ka'ida." A hankali Sa'adah ta ce, "Zan gyara Inna." "Na ji za ki gyara, sai mai za ki ce mini kuma"? Inna ta fadi haka tare da zuba mata ido. Cikin kunya "Sa'adah ta ce kai Inna don Allah, to ki yi hakuri." Kai tsaye ta ce, "Tafiya za ki yi ki fara rayuwa da wani mutumin da ba ki saba da shi ba, ba shi kadai zaman zai kasance ba har da dukkan ahalinsa don haka ki koyi ba da hakuri idan kin yi laifi, ki kuma zama mai karbar gyara yayin da aka gyara miki laifinki, wannan shi ne mafi dadin zama a cikin mutane, na lura da ke ba da hakuri na miki nauyi, sai tura ta kai bango kike tuba wanda alamu ne na girman kai. idan mijinki ya gane kina da girman kai kuwa, wahalar ki zai yi don shi ma girman kan zai miki indai ya san ciwon kansa, sai dai idan solobiyo ne." *** Bangaren MK yana ta Shirinsa musamman na gyran gidan da zai zauna, saukin da ya samu gidan mallkinsa ne da ya fado a gadonsa, tun lokacin yan haya suke ciki sai yanzu aka tashe su yake gyara, a unguwar Gadon Kaya gidan yake, ba wani babba ba ne amma tsarin gidan ya yi kyau, falo ne matsakaici mai dauke da manyan dakuna biyu da bandaki a cikin daki daya. Sai tsakar gida mai matsakaicin girma, daga gefe wani dakin ne shi ma da bandakinsa, sai daya gefen kuma kicin ne da wani bandakin karami, daga harabar gate kuma akwai karamin filin da zai dauki mota guda daya, ya shuka flowers sun fara fitowa wanda nan gaba za su 'kawata gurin. Gini ne mai aminci amma ba tayals ba ne siminti ne a dakunan. Shi kuwa a kokarinsa na son dadawa amarya Sa'adah yake son sanya mata tayals a falo da bandaki duk da a lokacin an fi saka carpet irin dan yankan nan. Aka fara aikin gida sai lashe kudi yake yi sosai, wanda hakan ya sake mayar da MK ya zama very busy kullum aka tashi a makaranta yana gidan gurin masu aiki, ko wurin neman ku'dinsa ba shi da lokacin kansa wanda hakan ya sake karfafa zaton Sa'adah na bai iya soyayya ba. Shi yasa take kula Khalil har yanzu! take kuma shan soyayyar 2go, idan MK ya zo shike nan idan bai zo ba, huta roro ba ta kewarsa. Sakamakonsu ya fito wanda WAEC din Sa'adah ta kasance ba yabo ba fallasa, amma NECO ta yi kyau sosai, a lokacin suka shirya bikin kammala makaranta da murnar sakamakonsu, ba laifi a shekarar an ci NECO sosai. A *HANG OUT* suka shirya yin bikin, a lokacin gun ne yake tashe a wurin samari da 'yan-mata, da kyar Inna ta bar Sa'adah ta halarci taron. Shi ma sai da ta yi karyar yayar Zainab ce ta haihu za su je, nan kuwa iya su 4stars ne, sai samarinsu na aji Irin su Khalil da kuma saurayin Halima Sagir. Haka suka yi wannan bidirin. Sa'adah a takure saboda wannan ne karon farko da ta ta'ba zuwa wani guri da sunan party, kuma a cakude da maza sai abin ya zame mata bako, ga dai kayan kwalama cike da teburinta hatta ice ream da ta ke jarabar so bata iya 'dan'danawa a bakinta ba, Khalil sai kaffa-kaffa yake yi da ita don ta sake, ita kuma sai raya ina ma kulawa da iya soyayyar Khalil, MK ne ya iya su. Tana cikin wannan tunanin wayarta, ta shiga ruri, tana dubawa taga MK ne, ta 'ki amsawa, tana tunanin idan ya ji wannan kidan sai ya ishe ta da tuhumar inda take. Bai daina kiran ba har sai da ta yi shahadar amsawa, jin hayaniya da kade kade yasa shi tambayar inda take, ta karkace baki ta shirya karyar ta raka Zainab gidan suna, yayarta ce ta haihu, ya yi shiru ba don ya gamsu ba, saboda ki'dan music yake jiyowa ba dan ka'dan ba. Ya nisa ya ce, "Son ganin ki nake yi, ya za a yi ke nan?" A ki'dime ta ce, "Ai anjima za mu dawo na san dai zuwa magariba mun iso." Da sauri ya ce, "Har Magariba za ki kai a waje? yanzu karfe 4, ki tabbatar biyar da rabi ta miki a gida, ina jiran ki." Ya kashe wayarsa ba tare da ya jira mai za ta ce masa ba, saboda bai gamsu a gidan suna suke ba. Ta yi shiru da waya a hannunta, tana tunanin yadda MK ya mata magana a gadarance tamkar ya zama mijinta, wani sashe na zuciyarta kuma so yake ta isa gida kafin lokacin da ya ce din. Duk kokarin Sa'adah na son ta bar wurin da wuri ya ci tura, su Safina sun hana ta, kan dole ta kashe wayarta don kada MK ya sake samun ta. Sai bayan Maghrib suka kawo ta gida, ita ce a gaban motar su Halima na baya, duk yadda ta so su ajiye ta a hanya Khalil kin yarda ya yi, don so yake mugun malaminsu ya ganta a motarsa tunda a unguwar yake sana'ar sa ta wanzanci, ya san kuma saboda shi take son su ajiye ta daga nesa. Su Halima na sake zuga shi ta hanyar cewa, "Idan ka ajiye ta a hanya wallahi soyayyarka ba ta kai ba!" Dai-dai lokacin MK yana kofar shagon kusa da jikin gidansu ana masa gyaran tayar mashin dinsa da ta yi faci, daf da shi Khalil ya tsaya, tsaleliyar mota(Continue Discussion) a wancan lokacin ita ce motar da take tashe ko'ina ka shiga maganar motar ake yi wanda shi ma ta mahaifiyarsa ce ya dauko, gaban Sa'adah ya sake tsananta bugawa musamman yadda hankalin mutanen wajen ya juyo kan motar, ga ta ita ce a gefen hannunsu, ma'ana tana bude kofa dole kowa ya gan ta. A tsarin mahaifinta ba ma MK kawai ba, bai kamata mutanen gurin su gan ta ta fito a motar saurayi a irin wannan lokacin ba. Ta rasa yadda za ta yi ta fita, musamman yadda kayan jikinta suka kamata sosai duk da mayafin babba ne. Sai dai shara-shara ne, hijabi ta saka da za ta fito, saboda Inna ba za ta barta ta fita da wannan dinkin ba wanda anko ne telan Safina ya dinka musu, da ma nufinta tana isa zaure ta maka Hijabinta baki alaikum. Kunya da tozarci iri-iri suka dinga bin ilahirin jikinta, ganin yadda ta kasa fita a motar ya sanya Khalil fita ya zaga, ido biyu su ka yi da MK ya hura hanci ya dauke kai, ya bude gaban motar yana fadin fito, da kyar ta fito fuskarta a kasa ta kuma ja mayafin har kanta aka bita da ido, mazan da suke gun dukkansu a ransu yaba surarta suke yi har daya a cikin su wanda dan kwaya ne ya kasa hakuri, a fili ya furta "Kai waccan baby an zuba mata halitta Billahillazi da ina da kudi da na yi kerwa da ita." Tun tsayuwar motar MK ya ji zuciyarsa ta tsinke musamman da ya ga mace a gaban motar ta kare fuskarta, haka kawai ya dinga fatan kar ta kasance Sa'adah ce, ya san zai yi wahalar gaske ta zama ita ce, amma sai ya kasa nutsuwa, a lokacin da ya ga Khalil ya fito da gadara sai ya tabbatar Sa'adatu ce, take ya ji wani irin matsanancin kishi ya kama shi, irin kishin da yake danne soyayya. Maganar da wannan saurayin ya yi na yabon surar ta sai ya sake ninka bacin ransa wanda bai taba Jin irin sa a tsawon rayuwarsa ba. Zuciyarsa ta yi zafi, take ya ji yawun bakinsa ya kafe makogaronsa ya bushe, kansa ya sara da wani irin ciwo mai tsananin gaske. Ashe Sa'adah da Khalil ta fita, ashe shi yasa ta kashe wayarta, don ta nuna masa tana tare da wanda ya fi shi, ta kuma yarda ya kawo ta har titin da take da tabbacin zai iya ganin su a tare, karo na farko da ya ji ya yi kuskuren barin Farida saboda Sa'adah. Ya tabbatar ta fi ta son sa kawai dai shi Sa'adah ce ta fi shiga zuciyarsa, kuma ta fi daukar hankalinsa. Ko ta kan gyaran mashin din bai tsaya ba, ya tari abin hawa ya nufi gidansu, kafin ya isa wani irin zazzabi da azababben ciwon kai sun masa mugun kamu. Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH*. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 45-46 Tana shiga zauren gidan ta fito da hijab ta sanya, sukuku ta shiga gidan. A tsakar gidan ta sami iyayenta. Tsoron da ke cikin zuciyarta ya sake bayyana a fuskarta da jikinta. Baffa ne kawai ya amsa sallamar, da 'kyar ta tsugunna ta gaishe shi, ya amsa ba sakin fuska, ya kalle ta fuska ba wasa ya ce, "Daga ina ki ke?" Cikin rawar murya irin ta rashin gaskiya ta ce, "Zainab na raka gidan yayarta kuma sai da na tambayi Inna." A kufule Inna ta ce, "Tabbas kin tambaye ni amma ce mini kika yi ba za ku dade ba, don haka na gode miki da cika al'kawari." Ganin yadda ran Inna ya baci sosai sai shi kuma ya sassauta, ya mata nasiha tare da cewa, "yarinyar kirki in dai ta san kanta, killace kanta take yi a gida, bai kamata dare ya riske ta a waje ba." Har ya sallame ta sai kuma ya ce, "Yawwa dama zan fada miki, aurenki bayan sallah za a yi, nan da wata uku kenan. Bayan haka kuma na sanar da iyayen yaron cewar kar ya yi lefe, ni ma kuma ba zan wahalar da kaina wurin saya masa kayan daki ba, ke zan ba shi ina kuma da yakinin na miki tarbiyar da zai sami nutsuwa da ke. Uwarki kuma ta koya miki yadda zai yi alfahari da ke a matsayin uwar yayansa. Haka na yi wa Sumayya har yau din nan da ta kai shekaru goma a dakinta ban taba jin ance mini ga wani abu na kaico daga gare ta ba, mijinta kullum kara girmama mu yake yi, Ina fatan ki yi koyi da ita, Tashi ki je." Ta mike ta wuce dakinta cikin wani irin yanayi, tana zuwa ta fadi kasa ta fara kuka kasa-kasa, tana jin karshen tozarci an yi mata. Ta ya ya za a dinga hada Sumayya da ita, ai ba lokacin su daya ba, sannan ba iyayen mijinsu daya ba, a wannan zamanin ma an kai yarinya da kayan daki idan ba na alfarma ba ne, dangin miji suna yi wa yarinyar izgili da habaici, to ina kuma ita da za a kai ta tsurarta? Wanne irin raini da kaskanci za a janyo mata? Ba'kin cikinta ya ninku ta rasa inda za ta tsoma ranta. Ashe shi yasa MK yake mata gadara da isa, saboda an nuna masa sadaka za a ba shi an dauke masa lefe? Shima kuma kar ya sa rai za a je a yi masa jere. Ba ta san lokacin da ta bude murya ta dinga zunduma ihu ba. Daga Inna har Baffa a kidime suka mike suna rige-rigen isa dakinta a tuninsu wani abin tsoro ne a dakin, ko maciji ko kunama ta harbeta. Sai dai ganin ta ras illah kukan da ta bare baki tana yin sa tamkar yarinya yar karama yasa suka yi cirko-cirko! Baffa ne ya ce, "Mene ne ya saki wannan ihun sai ka ce wacce ba ta zuwa Islamiyya, ba za ki ambaci Allah ba! Sai ki cika mana kunne da kuka har da ihu?" Cikin kuka sosai ta ce, "Ka taimake ni Baffa! kar ka kai ni ba kayan daki wallahi gori za a yi mini, ko a yi ta zunden sadaka ta ka bayar." Ta karasa cikin gunjin kuka. A zuciye Inna ta ce, "Watau ke ba za ki bi shi ba, sai shi ne zai bi ra'ayinki, ke kullum sai an yi artabu da ke? Kin taba ganin wanda ya bi iyayensa bai ci ribar rayuwarsa ba? Ashe ba za ki koyi da yayar ki ba?" Ta sake kara sautin kukan ta ce, "Ai samun irin mijinta da yan'uwansa sai an tona a wannan lokacin, sannan kuma ni da ita akwai banbanci." Takaicin ta ya kama Inna ta ce, "Banbanci kuwa a bayyane, ita ta yarda duk talaucinmu, mu ne iyayenta, za mu yi iko a kanta ba tare da ta ga gidadancinmu ba, sannan karatu kadan ta yi amma mai cike da ladabi da biyayya, in sha Allah Ubangiji ba zai kunyata ta ba." Tana fadin hakan ta fita ta bar su da Baffa. "Iyah!" Ya kira ta da muryar da bai saba mata irin ta ba, tunda shi kullum a cikin lallashi da tausasawa yake mata magana. "Na riga da na zartar da maganar nan a gaban Mutari da iyayensa, ba zan koma na ce na fasa ba. Ko a fuska kika nunawa yaron nan tsarina bai miki ba, ki tabbatar kin nuna ban isa da ke ba, ba kuma zan sake yin iko akan ki ba." Ya na rufe baki ya juya shi ma ya fice abinsa, sai ji ta yi kukan ya tsaya mata cak! Amma wani irin ba'kin ciki take ji ya shake mata wuya da zuciya. Da 'kyar ta fita ta yi alwala ta yi sallar Maghrib da Isha wanda ba nutsuwa a cikinsu. Da rarrafe ta isa kan shimfidarta, hawaye na bin fuskarta, ta ya ya za a mata irin wannan auren sai ka ce mutanen da? Ai ko shi Baffan da zai auri Innarsu, ya mata hidima, ita ma kuma da kayan dakinta aka kawo masa ita har yanzu gadonta na aure ne a dakin, duk kuwa da auren zumunci aka musu, shekaru kusan talatin. Amma sai ita a wannan lokacin za a mata irin wannan auren, kuka ya sake balle mata.😭 Tsawon lokaci tana kuka har kanta ya fara ciwo, a ranar dai ba ta yi wani cikakken barci ba, ba ta tuna matsalarta da MK ba sai da Asuba. Tana idar da sallah ta ciro wayarta a caji ta lalubo lambar MK ta kira, har ta katse bai dauka ba, ta kira ya fi sau biyar amma bai amsa ba. ta ja wani dogon tsaki tana furta "Sai ka yi ta yi." Ta kwanta ta yi shiru, amma sai ta kasa hakuri, ta sake kiran sa, nan ma bai dauka ba, ta yi ta kira har ta gaji, takaici ya sa ta yi jifa da wayar. Har rana ta fito tana kwance ta ki fita, fishi sosai take yi, ga idanuwanta sun kunbura saboda tsabar kuka. Inna kuwa ko ta kanta ba ta bi ba, ta yi dukkan ayyukanta, ta yi abin karin kumallo suka karya da Baffa amma ba ta nemi Iyah ba bare ta ba ta. Sai da Baffa zai fita ne ya tsaya bakin kofar dakinta ya kira ta. Ta fito sanye da hijabi duk fuskar ta a kumbure, ta tsugunna ta gaishe shi, ya kalle ta cike da kulawa ya ce, "Iyata yau ban ji motsin ki ba ga shi har zan fita, kin san idan ban gan ki ba yini zan yi ba kuzari". Ta sake yin kasa da kanta hawaye na cika mata ido, "maza fito ki yi wanka, ki sami abinci ki ci idan zan dawo zan taho miki da indomie har da Sadine na gwangwani, da ma kwanaki kin ce mini indominki ta 'kare, yau zan sayo miki ki ajiye a dakinki har da madara." Cikin kuka ta ce, "Na gode" Ya tafi yana jin kukan ta har cikin ransa, ya na raya yadda Sumayya ta zarta ta biyayya da gudun zuciya amma Iyah tafi shiga ransa matu'ka da gaske. Ko da ta koma dakin sai ta sake dasa sabon kuka mai cike da kururuwa, yin sa take iya karfinta, fishin da MK ya dauka ya sake dagula mata lissafi. Tun Inna na danne bacin ran ihun da Sa'adah ta cika mata kunne da shi, har ta kasa jurewa. Don haka ta shiga 'daki ta samo wani danko mai kauri ta nada a hannunta, ta nufi dakinta, tana shiga kuwa ba bata lokaci ta shiga zabga matata ko ina, da iyakacin karfinta, da kyar Sa'adah ta kwace ta fice a guje, ta nufi hanyar zaure ta tsaya tana kuka sosai. Ta dade kafin ta dawo gidan, tana rabe-rabe, Inna ta kalle ta rai a bace ta ce, " Idan kin san za ki ta sani a gaba kina mini kukan iyashege ki juya ki tafi duk inda za ki shiga, watau ni kika raina? Kin ga Baffanku ya fita shine za ki 'bude mini wannan ja'irin bakin naki da bai iya komai ba sai 'kulla karya da munafunci kina mini ihu. Wai har kin yi wayon da yafi nawa, ni za ki yiwa karyar Zainab za ki raka unguwa? Ashe da wannan shedanun kawayen naki masu yi wa Babba kallon raini kuka fita, har kin yi lalacewar da za ki shiga gaban motar namiji ya kawo ki har kofar gidanku, ki fito akan idon jama'a, oh ni Salamatu wacce irin yarinya nake tare da ita ne haka?" Ta Fadi hakan tare da tafa hannu tana salati. "Wai kuma don ki bata ni a gunsa shi ne zaki ce nasan zaki fita, to don uwarki daga yau kika kuskura kika ce mini za ki fita da sunan zuwa unguwa wallahi sai jikin ki ya fa'da miki. Na daina raga miki tunda ke rarrashi baya bi da ke, kafin nan kafin ki bar gidan nan sai na miki tabbuna ba ma tabo ba. Tunda nake da Baffanku bai taba ganin kasawa ta ba sai akan ki, jiya da daddare ba abin da bai fada mini ba, bayan an tabbatar masa a mota aka kawo ki." Jikin Sa'adah ya yi sanyi kalau, ta yi shiru amma hawaye bai daina zubo mata ba, tana jin tsanar Khalil sosai a ranta duk shi ya janyo mata wannan tashin hankalin, da ya ajiye ta a hanya ai da ba wanda ya ganta, ga fushin Uncle MK, ga fishin Baffa duk da dai shi mai yawan yi mata afuwa ne. Amma yau har zane ta Inna ta yi, ba za ta iya tuna yaushe rabon da Inna ta dake ta irin haka ba. A darare ta shigo ta shige dakinta, ta fito da shirin wanka, sai da ta fito ta shirya, sannan ta je ta tambayi abincinta, ba tare da ta kalle ta ba ta ce, "Ban yi dake ba tabbatacciya! Kina kwance na tashi na yi komai saboda zuciyarki ba imani balle tausayi, amma har ki iya cewa ina abincinki? Saboda ga baiwa kin ajiye, to ga tuwo can da kika raina sai ki hada wuta ki 'dumama, idan kuma kin fi nan sai ki zo ki dora abincin rana idan kin gama sai ki ci." Tana kaiwa aya ta ja bakinta ta tsuke. Cikin rawar murya ta ce, "Me zan dora?" Kamar ba za ta kula ta ba sai kuma ta ce, " Dambu!" Hawayen da ta ke matsewa ya balle tasa gefen dan'kwalinta ta goge, sannan ta ce, "To!" Haka ta hau aikin sarrafa dambu tana goge hawayen da ya'ki yankewa ta san dan a musguna mata yasa aka 'kir'kiri yin abincin da zata jima bai kammala ba. Ba ta sami kanta a hannun Inna ba sai wajen karfe uku, saboda yadda ta'ki sa mata hannu, ada idan za su yi dambu kusan Inna ke jagorantar yi, kawai sai dai Sa'adah ta sa ido tana lura tare da gyara gyada ko zogale. Amma na yau komai sakar mata ta yi, ta kuma kara yawansa a cewar ta za ta aika wa makwabta, ita dai Sa'a ba bakin musu saboda a tsorace take da ita don ba karamin duka ta mata ba. Faranti guda ta cika da danbun ta debi ruwa a randa mai sanyi ta sami inuwar bishiyar dake tsakar gidan, ta fara ci hannu baka hannu kwarya tamkar ba Sa'adah mai cin abincin a gayance ba.😁 Inna na kallon ta a ranta ta ce, "Ja'ira yau kin gane yunwa ba kanwar uwa ba ce." Sai da ta share abincin nan tas ta yi gyatsa gumi ya karyo mata, ta yi Hamdala. Ta jima a zaune a gun, sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan ta cika bokiti da ruwa, ta jira Inna ta fito a bandakin sannan ta shiga wanka. Sai da ta yi sallah sannan ta shirya, kana kallon ta kasan zuciyarta ba walwala, tana zaune waya a hannu tana ta kiran MK amma ya ki dauka, lamarin da ya sake dugunzuma damuwar da take ciki, a fili ta ce, "Me yasa nake son mutumin nan ne?" Ta sunkuyar da kai tana tunano adadin yadda take shiga damuwa saboda shi. Haka ta ci gaba da kira ba kakkautawa har ta gaji. Sai kuma ta koma tura text din ban hakuri da maganganun soyayya masu taushi. Amma ko sau daya ba ta ga amsa ba duk kuwa da sun nuna mata sun yi delivered, (Watau sun je). Wasa-wasa sai da aka shafe sati biyu ba ta ji daga MK ba idan kuma za ta yini tana kira ba zai dauka ba. Abin ya yi matu'kar tayar mata da hankali tun tana boyewa har abin ya fara fin karfinta, ta zama wata iri, ko abinci ba kasafai take iya ci ba. Ga Inna ba sakar mata fuska take yi ba, abin ya hade mata biyu, ta fara ramewa a tsaye. *** Bangaren Mk kuwa ba karamin zafi ya dauka da Sa'adah ba, kwana biyu ya yi a kwance yana fama da ciwon kai da wani irin zafi a cikin kirjinsa. Idan ya tuna yadda Sa'adah ta fito a gaban motar Khalil jikinta a dame sai ya ji tamkar ya shide, haushin ta yake ji ba ka'dan ba, gara ya gan ta da Alhaji Mamman akan wannan dan iskan yaron, so yake ya hakura da Sa'adah amma kunyar mahaifinta yake ji musamman yadda ya girmama lamarinsa. Sannan ya san ko giyar wake yake sha bai isa ya tunkari iyayensa maza da maganar ya fasa auren ta ba, ya rasa inda zai tsoma ransa. Yana ganin yadda kiran ta yake shigowa wayarsa ba adadi. To me za ta ce masa? Ta je su karata da wanda ta zaba. Kwanaki na ta shudewa, damuwar da Sa'adah ke ciki na sake karfafa, tsawon kwanaki ashirin ke nan MK bai dauki kiranta ba, balle kuma shi ya kira. Ranar wata Laraba da daddare suna zaune da Inna a tsakar gida amma kowa na gefensa, Yan NEPA suka kawo wuta, daidai inda Sa'adah ke zaune hasken ya fi karfi, Inna ta zuba mata ido tana kallon yadda ta lalace ta birkice. Nan da nan tausayin ta ya kama ta, sai dai ba ta nuna mata ba, amma ta kudiri aniyar yi mata sassauci. Washegari kuwa da walwala ta amsa gaisuwar Sa'adah, ta daina daure mata fuska, idan ta mata magana cikin dadin rai take amsa mata, sab'anin lokutan baya da hantara ce a tsakaninsu. Afuwar da Inna ta yi mata yasa ta samu sau'kin halin da take ciki, amma har yanzu ba ta da kuzari da walwala, Inna da kanta ta ce mata, "Idan ban manta ba na kai wata ban ji Muutar ya zo ba." Sunkuyar da kai kawai Sa'adah ta yi ta kasa cewa komai! Amma idanuwan ta sun kawo 'kwalla. Ganin yanayinta ya tabbatar mata akwai matsala a tsakaninsu ta ce, "Hala kin sallame shi saboda ba zai miki lefe ba?" Da sauri ta ce, "Haba Inna! Ni wallahi ban sake tayar da maganar ba." Cikin takaici sosai Inna ta ce, "To labarin abin da kika aikata ya same shi." Ganin hawaye ya kwace ma Sa'adah ya sa ta hadiye fa'dan da za ta fara yi mata, sai ta bige da fadin, "Kadan ke nan a cikin sakamakon da mai yin 'karya ya ke fuskanta." A ranta kuma tana raya dole su yi magana da Baffa akan rashin zuwan MK shirun ya yi yawa. Washegari Zainab ta kawo mata ziyara, suna zaune kan katifarta, "Sa'adah me yake damun ki haka?" Zainab ta fada cike da mamakin ramar da ta ga Sa'adah ta yi. Bata boye mata halin da take ciki ba, ta zayyane mata komai. Cikin takaici Zainab ta ce, "Ai indai kina biye su Safina sai sun kai ki sun baro, ka'dan ke nan." Tana kuka ta ce, "Ni yanzu ki nemo mini mafita don Allah!" "E ai yanzu da yake ta kwabe miki za ki neme ni, amma lokacin da kika bi su ai ban sani ba." Waya ta mi'ka wa Sa'adah tana fadin, "Saka lambar Uncle Mukhtar din mu kira shi da layina." Jikinta na rawa ta karba ta hau jera zababbun lambobinsa, tana fatan Allah ya sa ya dauka tunda har layinta da bai san da shi ba ta sha 'kiran ba ya 'dagawa. Cikin Sa'a kuwa ya dauka! Zainab ta gaishe shi, ya tambayi wacece? Ta amsa da gabatar da kanta, sai ta shiga ba shi ha'kuri a madadin Sa'adah, ya yi shiru har ta gama. Ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce, "Ba dan ina ganin hankalinki ba da ba zan saurare ki ba. Ki yi hakuri, ki cire kanki a cikin wannan maganar, ba zan iya da halin yarinyar nan ba, duk yadda nake zaton ta ta wuce nan". Yana fadin haka ya katse wayarsa. Bugun da zuciyarta take yi ya sake tsananta, a rikice ta ce "Zainab mai yake nufi? Ya fasa yi da ni ke nan?" Cikin son ta kwantar mata da hankali ta ce, "Ba fasawa zai yi da ke ba In Sha Allah! Kawai ya yi fishi ne sosai, ai kema kin san ba ki kyauta masa ba." Ta dade tana kwantar mata da hankali, kafin ta mata sallama ta tafi da al'kawarin za ta sake tuntunbar sa. Kwanaki biyu da zuwan Zainab, Anty Sumayya ta yi waya Sa'adah ta je ta karbo mata sa'ko a karkasara gidan kawarta. Akan dole Inna ta barta ta fita bayan ta sha jan kunne da nasiha iri-iri akan kar ta biya ko ina, har kunya ta kama Sa'adah ta na jin ita ta janyo wa kanta rashin yarda a idon iyayenta. Tana karbo sakon ta juyo, duk da yadda Anty Walida ta yi nacin ta zauna ta karasa yi mata yinin, ita kuma ganin biyu da rabi ta yi yasa ta gaggauta fitowa dan ta zartar da kudirinta na son ganin Mk a yau. Kai tsaye FGC Kano ta sauka, sai dai ba makarantar ta shiga ba, gangare can gefe ta tsaya inda suka ta'ba tsayawa da shi, ta san kullum ta nan ya ke bi. Cikin sa'a kuwa ba ta dade tana jira ba ta hango shi, yana doso inda take, a kafa yake tafiya. Ta ce, "Ko ina ya baro dan mashin 'din?" Sanye ya ke cikin 'kananun kaya yana rataye da jakar da yake zuba takardun shi, ya mata kyau sosai duk da ta ga ya dan zube kadan. Sai da ya wuce ta sannan ta bi bayansa, jin ana ta bin bayansa yasa shi jiyowa, ba zato idanunsu suka sarke, ya hade girar sama da ta kasa tamkar bai ta'ba dariya ba, ya juya ya ci gaba da tafiyarsa tamkar bai gan ta ba. Sai lokacin ta yi magana "Uncle na yi kewar ka, idona sun yi kukan rashin ka!" Ya ji ta sarai, bacin ransa ya dawo sabo, ya rasa wane matakin zai ajiye Sa'adah, duk inda ya ke ajiye ta, yau ya tabbatar masa ta kere gurin!har ta san ta bi saurayi gun aikinsa? Ita kuma ganin bai kula ta ba har sun fara hango titi sai ta fara masa kukan da babu hawaye tana kuma fadin "Zuciyata ba za ta iya daukar fishinka ba, ka kalle ni ka ga yadda fishinka ya ramar da ni, ba na iya barci, ba na iya cin abinci, kamin afuwa, don Allah ba don halina ba!" Ta fada cikin wani irin yanayi mai motsa ZUCIYA. Ya juyo ya zuba mata ido tabbas ta rame, ta birkice amma hakan bai yi tasiri a zuciyarsa ba, musamman da ya tuno kallon rainin da Khalil ya yi masa, ya sake hango yadda ta fito a gaban motarsa, sai kawai ya juya ya ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya ce mata uffan ba. A kidime ta ru'ko hannun jakarsa murya na rawa ta ce, "Na san na yi ba daidai ba, na ba ka ha'kuri, ka yi hakuri mana!" Bacin rai sosai a fuskarsa ya dube ta sannan ya ce, "Ke ba na son ballagazanci, a titi za ki ri'ke ni?" Ba'kin ciki ya kama ta ta fara kukan gaske ta ce, "Ni ka kira da ballagaza?" Kishi ya rufe mai ido sosai, ba wani ja-in-ja ya ce, "E, idan akwai sunan da ya fi haka muni ma ki hada da ballagazar, don kuwa sunayenki ne, dabi'un da kike yi irin nasu ne. Yanzu kuma kin nuna mini kin saba cu'danya sosai da maza, har kike ganin za ki iya cakuma ta a titi." Ba'kin ciki ya turnuke ta, ba a taba yi mata tozarci a rayuwarta irin na yau ba, kuka sosai take yi wanda ya matu'kar taba shi, kawai waskewa ya yi. ba tare da ta sake fadin komai ba, ta yi gaba da sauri ba ta ko sanin inda take jefa kafarta saboda tsananin 'bacin rai. Al'kalamin *Surayya Dee* ✍🏼✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH*. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 47-48 A gigice ya ga ta nufi titi gadan-gadan tamkar zararriya, zuciyarsa ta buga, da azama ya bi ta ganin da gaske tsallakawa za ta yi ba tare da ta duba ba. A ki'dime ya fuzgo ta, ganin mota na shirin yin wasan-kura da ita, amsa-kuwwar motoci sun cika gun, har sai da mai motar ya tsaya ya fito ya dinga zazzaga mata sababi, yayin da ita ko kallo bai ishe ta ba illa fizgewa da ta yi daga ri'kon da MK ya yi mata, ta koma gefe tana hawayen ba'kin cikin maganganun da ya gasa mata. Sai da ya ba wa mai motar hakuri ya tafi sannan ya tsayar mata da Adaidaita Sahu, juyin duniya ta ki hawa, har mai Adaidaitan ya ji haushi ya yi tafiyar sa. Ya kalle ta ya ce, "Watau da ma zuwa kika yi ki sake tayar mini da hankali ko?" Yana rufe baki ta ce "Kadai so hankalin naka ya tashi ne, ha'kuri na zo ba ka, ka ki ha'kura. Ka bi ni da kalaman muzanci, to ai sai ka yi tafiyarka tunda da ma ba kai ka kawo ni ba balle ka ce sai kasa na koma dole." Ya kalle ta ya ga tana cikin fishi irin wanda bai taba ganin ta yi irinsa ba, sai ya sassauta ya ce, "Na ji ba ni na kawo ki ba, amma kin ce gurina kika zo, idan kuwa haka ne to ba na son zuwan. Ki koma gida ni zan zo." Kamar ta ce "Ba na son zuwan naka ni ma!" Sai ta daure ta kalle shi ta ce, "Nasan ba da gaske ka ke ba." "Zan zo mana da gaske nake." Ta yi shiru tana rantsuwa a ranta ba za ta yarda da maganganun da ya yi mata ba. Dolensa sai ya janye ko ya ga tashin hankalin da ya ke kirari. Ya kalle ta ya ga ta turo bakin nan gaba, mamakin yadda ta ke son mayar da laifin da ta masa ya koma kansa ya ke yi. "Kin yarda na tsayar miki da abin hawa?" Shiru ta yi masa alamun ba ta yarda ba. Ya kalle ta ya ce, "Magana nake miki." A gajarce ta ce "Ban yarda ba!Yawon ballagazan ci zan wuce." Ji ya yi kamar ta wasta masa ruwan dalma a zuciyarsa, ya hassalo sosai ya nuna ta da yatsa ya ce, "Ni kike yi wa magana kamar kina yi da sa'anki? Saboda ba kya ganin girma da mutuncina?" Ta yi mai shiru ta kasa cewa komai. Ya sake cewa "Ki dinga sanin abin da za ki na fada mini ba na son kau'din baki." Duk yadda ya so ya tafi ya bar ta a gurin kasawa ya yi, ita kuma ta kafe akan ba za ta tafi ba, shi ya yi tafiyarsa ya 'kyale ta. Da kyar da jubin goshi ta yarda ya tarar mata Adaidaita, bayan ya rantse zai zo gida ya same ta, sannan zai 'dauki kiran ta. Yana tsaye yana kallon su har suka bar wajen. Wata ajiyar zuciya da bai san yana ri'ke da ita ba ta kwace, a fili ya ce "Wacce irin yar daru na kwaso wa kaina ne? Da motar nan ta taka ta, ina take son na sa raina? Me zan ce da iyayenmu idan aka gane muna tare ta sami wannan hadari? Ya dade a tsaye yana mamakin irin son da yake wa Sa'adah. Ya dauka idan ya gan ta ba zai ji komai ba, ya dauka kaifin son ta ya dakushe, ashe ya nan daram. Musamman da ya ga mota na shirin take ta sai ya ji zai iya rasa ransa don ya tserar da ita, ko muzuran da ya mata na karfin hali ne kawai da son kwatar kansa a idonta. Tana isa gida ana sallar La'asar, sai da suka yi sallah sannan ta ba wa Inna sakon da ta karbo, ta koma daki ta hau kiran MK. Sai da ta kira har sau uku bai 'daga ba, shi kuma ya fito a Masallaci ke nan kiran ya shigo, bai daga ba sai da ya koma dakinsa ya kwanta sannan ya 'kira ta. Har ta fara hasashen da ma zai iya rantsuwa akan 'karya? Sai kuma ta ga kiran sa ya shigo, da sauri ta dauka sai kuma ta yi shiru ta tura baki gaba tamkar yana ganin ta. Shiru ya biyo baya tamkar ba kudi ke bin iska ba. A shagwabe ta ce, "Na gode!" Ya ce, "Godiyar me kike yi?" "Ka cika al'kawari, don Allah ka yi ha'kuri wallahi na horu ba zan sake yi maka laifi ba." Ta fa'da da rauni a muryarta. Jikinsa ya mutu, wata irin kasala da ba ta da nasaba da gajiya ko barci ta lullube shi, murya a dakushe ya ce, "Kin bata mini rai, kin tayar mini da hankali, kin jefa ni cikin wasi-wasi mai yawa, kin janyo mini raini." "Ka yi ha'kuri!" Ta fada da sauri. Shiru ya yi ba tare da ya yi magana ba, saboda yadda ya ke fama da kansa, ji yake ina ma ya jita a jikinsa. Murya ba amo sosai ya ce, "zan fada miki, ba na son yaron nan. Ina bakin cikin tarayyarki da shi, wannan ne karon karshe da zan miki afuwa a kansa, ba don girman son da nake miki da kunyar Baffa ba da na ha'kura da ke Sa'adatu. Saboda kina cutar da ni, da ni kika gani da Farida da ban san kalar tashin hankalin da za ki mini ba. Amma saboda yadda nake son ki, na ke gudun bacin ranki haka na rufe ido na rabu da ita da dukkan lamarinta. Ni kuma kin kasa tsayawa gare ni ni ka'dai." Yanayin muryarsa da yadda ya ke maganar cike da rauni sai ita ma ya jefa ta cikin wani irin yanayin da duk mai lafiya ba zai iya kauce masa ba, tsikar jikinta har tashi take yi. "Am sorry!" Ta fada a gajarce tana jin ina ma inama... "Shike nan ya wuce amma kisa a ranki cewar yaune karon karshe da zan saurare ki na miki afuwa akan Khalil". "Na gode my love!" Mamaki ya kama shi, karon farko da ta kira shi da wani suna bayan Uncle. Ya ce, "maimata abin da kika ce?" Dariya ta yi "Thank you na ce!" Sai ya saki maganar ya ce, "Ba ni labari." Haka suka sha hirarsu cike da Begen juna, dukkansu sun tabbatar sun yi missing din juna, sun kuma yarda farincikinsu na hannun junansu. Washagari da yamma ya zo, ba Sa'adah kawai ba, hatta Inna sai da ta yi murnar zuwansa, hira suka yi cikin tattalin juna, har ya ba ta labarin irin gyaran da yake mata a gidan da za su zauna. Tun daga wannan lokacin Sa'adah ta yanke hul'da da Khalil saboda ba karamin tashin hankali ya janyo mata ba. Hankali ya kwanta sun shirya da MK amma ta 'kullaci kalmar ballagazancin da ya jefe ta da ita ba ka'dan ba, ta kuma ci alwashin maganar ba za ta bi iska ba, lokaci ta ke jira. Haka kwanaki suka yi ta zuwa suna wucewa, har watan azumi ya kama al'ummar Musulmai kowa ya koma ga Allah ana fatan dacewa da Rahamar Ubangiji. Zuwa wannan lokacin shirye-shirye ya yi nisa a bangaren MK, an kammala gyaran gida, gyaran da ya dawo da gidan tamkar sabo. Mahmoud ne ya hado wa Sa'adah kayan shan ruwa da kayan sallah masu tsada har set biyar da takalmi da jaka set uku sai tarkacen kayan kwalliya da turaruka. Tare suka kawo mata, da za su tafi kuma ya sake ba da kudin 'dinki wanda ta 'ki karba sai da MK yasa ba ki sannan ta karba. Yawan kayan da kuma tsadarsu ya dan rage mata damuwar rashin lefe musamman idan ta tuna tana da kayan wurin Alh Mamman a ajiye. Ana yin sallah da sati 'daya iyaye da 'yan'uwan MK suka hada kudadensu, aka sayo dukkan abin da za a bukata, tun daga kan gado da kujeru masu kyau da aminci suka sayo aka shirya gida ya fito sosai, labulaye da carpet suka ajiye sai satin biki za a zo a saka. MK da ya je ya ga irin kayan da aka zuba masa sai da ya yi hawayen farinciki, ya duba ya ga an 'kawata dakin Sa'adah da dan'kareren gadon da duk fariyarta ba za ta raina ba, ga kujerun ma masu kyau, ba irin gama gari ba, dayan dakin ne kawai aka malale shi da carpet aka bar shi empty, bai sha mamaki ba sai da ya shiga dakin dake tsakar gida wanda shi ne mallakinsa, an saka masa gado amma bai kai na dakin amarya ba, kowanne gado kuma da dimemiyar katifar Vitafoam a kai. Ya zauna a bakin gadon yana goge idonsa, yana mai yin addu'a ga dukkan ahalinsa, sun masa zumunci ba ka'dan ba. Ya zauna yana ganin TV da Fridge kawai ya rage wanda su kuma yayarsa Hafsatu ta ce ta aiko da su. Isowa ne ba su yi ba tunda a Lagos take. Alhaji Isa shi ya sake komawa wurin Baffa ya ce idan ba damuwa suna son a yi auren a cikin sati biyu masu zuwa. "Yadda ka ce ba ka bu'katar komai a gurinmu sai sadaki, mu ma muna ro'kon ka!Yarinyar kawai muke so don Allah!" Suka rabu cikin walwala, tare da addu'ar albarkar Ubangiji a cikin auren. Duk da Baffa ya ce ba zai mata kayan 'daki ba, kan dole ya karbi tsalelen gadon da mijin Sumayya ya aiko masa. Sumayya na zuwa ta nunawa Inna ku'din da za ta kashewa Iya, ita ma ta fito da nata ajiyar ta hada suka shiga kasuwa tare da Sa'adah, suka zabo kayan kicin na garari duk a 'ko'karinsu na kwantar mata da hankali, tunda sun san halinta na son kayan 'kawa. Hatta kayan fitar biki masu kyau aka tanadar mata shike nan sai hankalinta ya kwanta. musamman da Sumayya ta ha'kur'kurtar da Baffa ya yarda za a kai mata gadonta 'kirar Dubai. Kafin ranar 'daurin aure gidan amarya ya fito fes komai ya ji, Sumayya ta yaba 'kwarai da kokarin MK da iyayensa, saboda haka sai ta sa aka mayar da gadon dake dakin MK zuwa dakin dake cikin falon wanda babu komai a ciki, shi kuma aka saka masa hadadden gadon Dubai. Kicin aka sake 'kawata shi da tsirarrun kayan alfarma, aka rufe gidan ana jiran isowar TV da Fridge da kuma amarya! don Mk tuni ya tare a cewarsa gadi yake yi.😁 *05/06* Ranar aka daura auren Mukhtar Kabir Bichi da Sa'adatu Bashir Gogel, a Masallacin Sahaba dake Kundila, kamar yadda Baffa ya ce ba za a yi party ko ka'de-ka'de ba hakan ce ta kasance. Amma kuma ya tsaya an yi abincin 'daurin aure da yini na fitar kunya, duk wanda ya halarcin auren Sa'adah mace ko namiji ya ci abinci mai rai da lafiya don kuwa Bijimin sa Baffa ya yanka, duk tanadin Baffa a shirya abincin fita kunya ya kare. A lokacin sarkar gold din dubu hamsin babba ce, ita ya siyawa amarya da shawarar Sumayya da take ta 'koda irin kokarin da MK da iyayensa suka yi. Sai kuma 'dinkunan da ya mata na kwalliyar amarci. A Daren da aka daura aure suna zaune a gabansa ita da Sumayya da mahaifiyarsu, bayan ya yi addu'a ya ce, "Duk wani burina a yau ya cika Iyah, ina kyauta zaton na dan'ka ki a hannu na gari don Allah ki bi mijinki, nasan kinsan idan mijinki, ya yarda da ke to Ubangijinki ma ya yarda da ke, idan kika ri'ke wannan kadai za ki gane komai za ki yi a 'dakin mijinki ibada ne. Ibada kuwa sai an daure domin za ka ci karo da abin da kake so da wanda ba ka so. Na ro'ki ki yi koyi da yar uwarki wurin boye sirrin aurenta, har yau din nan Sumayya ba ta taba fa'din ga laifin mijinta ba, mun sani ba fa don ba ya mata laifin ba ne, haka shi ma yana ri'ke da ita cikin ha'kuri da girmamawa. Ina sake miki nasiha ki zama mai ha'kuri, baki da'yan aure wallahi hakuri ne ya fi yawa, ina fatan ki yi ko yi da mahaifiyarki wurin ha'kuri da biyayyar aure!" Ya janyo ledar dake gabansa ya fito da sallaya da kur'ani ya mi'ka mata, ta miko dukkan hannunta biyu da suka sha adon lalle ta kar'ba, yace "Ki rike ibada da kyau ita ce za ta jagorance ki duniya da lahira." Ya kalli Sumayya yana fadin "Ina abin da nace ki ajiye?" Da sauri ta mi'ka masa dama ta shigo da shi ya karba ya sake mika wa Sa'adah yana fadin, "Ki rike tsabta da kwalliya da ma ba na jin ki a wannan bangaren. Inda nake da shakku akan biyu ne. ki 'karanta buri Iyah kin dai san ni ubanki ba kowa ba ne, ki yi alfahari da abin da yake hannunki, ki daina sha'awar wanda suka fi ki ko kuma wanda ba tsarin tarbiyarku daya ba, a yanzu da za ki koma 'karkashin mijinki, ina hada ki da Allah kar ki dinga dora masa hidimar da ba zai iya ba, ko ba ra'ayinsa bane. Da ace za ki rabu da harkar kawaye to ina tabbatar miki za ki 'karantawa kan ki buri saboda ba kya hangensu. A karshen karshe na yafe miki dukkan kurakuran da kika mini, ina fatan Allah Ya lullube rayuwarki da albarkaSa, ya ba ki zuri'a mai albarka, ya kuma hore miki ha'kurin zaman aure." Daki ya yi shiru sai shesshekar kukan Sa'adah, Baffa ya nemi Inna ta ce wani abu, ta girgiza kai tare da cewa, "Duk abin da zan fada na dade ina mata bita indai mai ji ce ai ta haddace su. Fatana Allah Ya albarka ci aurenta." Cikin soyayya mai yawa Baffa ya kalli Sumayya ya ce, "Saura ke babbar yaya uwa ta biyu!" Ta yi murmushi cikin sanyin murya ta ce, "Komai kun fada Baffa, fatana a ce duk ta ji ku da kunnen basira, ta kuma ri'ke 'yan'uwansa da girma, musamman iyayensa. Ki rike su da mutuntawa komai za su miki kar ki nuna kin ji haushi ki yi hakuri, ki sake ninka kulawarki a kansu, duk kuma wanda ya je gidan, ki karbe shi da sakakkiyar fuska su ji tamkar a gidan yar'uwarsu mace su ke saboda sakewa da walwala." Baffah ya nisa yace " idan Kika bi maganganun mu kin tsira! Idan kuwa kika je kika biyewa 'kawayen banza da son zuciya ki tabbatar ke 'kadai za ki dauki 'bacin ran da zai same ki, ki bi mijinki ko zaluntarki yake yi ki bishi da addu'a idan abin ya gagara, sai mu shiga, amma idan ke Kika bijire to fa kisani baki da wurin zama a gidannan". Ya rufe zaman da doguwar addu'a ya kuma rike ta a hannunsa ya tafi kai ta 'dakinta da kansa a motar Alhaji Isa da ya zo daukar Amarya. 'Yan'uwan Baffa da na Inna da suka zo, sai mamakinsa suke yi da ya hana su zuwa kai amarya, ya tafi da kansa ya kai 'yarsa dakinta. A lokacin kam ya zo da sabuwar dabi'ar da ta sha banban da al'ada, ashe shi yasa yasa aka kai su suka ga gidan amarya tun jiya? *SURAYYA DAHIRU*. ✍️✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* *TUKUICI GA* _*AISHA IBRAHIM BAFARAWA*_ (*BEAUTY*) *MK DA SA'ADAH NA GAISUWA* 👍 49-50. *GIDAN AMARYA* A gidan su Baffa suka tarar da su Baba Umaru da Baba Idi da kuma MK. Tunda Baffa ya fa'da musu a wurin 'daurin aure cewar shi zai kai amarya 'dakinta kar a turo mata, sai suka fasa komawa Bichi a yau, suka ce su za su karbi amarya da kansu. Haka Baba Umaru ya tisa MK da jan kunne iri-iri akan ya ji tsoron Allah ya ri'ke matarsa cikin tausayi da adalci, komai za ta yi ya dauke kai ya fahimtar da ita cikin ruwan sanyi. Baba Idi ya nisa ya ce, "Sannan zan fa'da maka gida naka ne, amma kayan ciki na matarka ne, kana dai ganin irin mutunci da karamcin da aka maka, to ina ro'konka! ka nuna kai ma ka san mutunci ta hanyar zama da yarinyar nan da kyautatawa, ba hankalinku 'daya ba, mata lamarinsu yana da gigitarwa. Amma idan aka yi ha'kuri da su, aka musu afuwa sai a ji dadin zama da su, saboda masu rauni ne, kuma masu tausayi ne". Alh Isa kuwa cewa ya yi, "Abin da zan fada muku ni ne uban Mukhtar, ni ne uban Sa'adatu, sannan ni ne alkalinku dukkanku 'daya kuke a gurina. Ba zan saurara wa duk wadda ba shi da gaskiya ba". Ya kalli Sa'adah da take gurfane a lullu'be cikin lafaya, "Sa'adatu duk da ba na fatan matsala, amma duk abin da ya taso na rashin jin dadi, ni ne Babanki, ni za ki fadawa kar ki ji nauyi ko kunya, waya kawai za ki mini, ni kuma zan miki maganin ko mene ne, domin duk girman Mukhtar yaro ne karami a idonmu, na san kuma mun isa da shi". Baffa dai bai ce komai ba, da'di ya cika zuciyarsa, Allah Ya kai Iyarsa cikin ahalin da suka san mutunci suke kuma rama shi da alheri. Bai ce komai ba sai da suka mike, ya kalli Mukhtar ya ce, "Ban baka aure ba sai da na tabbatar kana da nagarta, ina kuma zaton kai din adali ne saboda ka siffantu da kyawawan dabi'u don haka ni ba na shakku a kanka. Sai dai kar ka bari jan kunnen da ake ta faman yi maka na ka kyautata mata, ya yi dalilin da za ka bari ta yi abin da ta ga dama, ka bude kunne ka ji ni sosai. Duk 'kawa ko makwabciyar da ka ga dabi'arta ba ta yi maka ba, ka shata wa matarka layin mu'amala da ita, idan ka bari ta fi karfinka to kai ne za ka sha wahalarta". Su Baba umaru suka hada Baki wurin cewa, "Ba ma za ta bijire masa ba, ai barewa ba za ta yi gudu d'anta ya yi rarrafe ba, In sha Allah, irin halin gidansu na girma za ta yi ba *HALIN YAU* ba". Aka rufe maganar da doguwar addu'ar zaman lafiya da neman tsari daga sharrin shaidan, da shaidanun mutane. Suka tafi MK ya bisu a baya, yana ta musu godiya tare da fadin duk abin da suka fada zai kiyaye, bai juyo ba sai da motarsu ta bace wa ganinsa. Sannan ya bi bayansu zuwa bakin titi ya karbo gasassun kajin da tun yamma Mahmoud ya yi masa booking, ya hado da yougurt din L & Z da kuma lemon 5alive, yana tafe yana ayyana bai taba ganin nisan bakin titi zuwa gidan nasa ba sai yau. yana isa ya rufe gidan. Kamar a guje ya fada falon! ya tarar da ita zaune a inda suka bar ta, tana rufe ruf cikin lafaya. Gefe daya ya ajiye ledojin hannunsa, ya isa kusa da ita ya tsaya, a zuciyarsa yake ta fadin Alhamdulillah! sannan ya sunkuya ya 'dago ta tare da fadin , "Assalamu alaiki! Barka da zuwa gidanki, ina miki murnar wannan rana mai cike da farinciki". Ta yi shiru, ta kasa amsawa saboda yadda zuciyarta, take a cunkushe da alhinin barin gida. Ya ri'ke hannun ta yana janta zuwa cikin 'dakin da shi ne mallakinta, a bakin gadon ya zaunar da ita tare da fadin, "Haka na ga ana yiwa amare." Yana warware mata laffayar zuwa kafadarta, fuskar ta masa kyau duk da ta kode saboda kukan da ta ke yi. Kusa da ita ya zauna sosai har jikinsu na gogayya da juna ya dan ri'ko ta ya ce, "Kukan na mene ne tamkar ba gidanki za a kawo ki ba, ke da kika yi sa'a a gari za ki zauna duk lokacin da kika so zuwa gida, zuwa za ki yi to menene abin kuka sai ka ce ba gidana kika dawo ba". Tissue ya dauko a kan madubi ya shiga goge mata fuska, yana ta fadin maganganu masu taushi. Ya kalli agogo ya ga tara saura,ya mi'ke ya dauko ledar kajin da ya bar su a falo, sai da ya shimfida musu abin zama sannan ya janyo ta ta sau'ko 'kasa, ya bude ledar ya tura mata gabanta yana cewa, "Nasan tun safe ba komai a cikinki. Taimake ni ki ci" Ya zabura ya nufi kicin ya samo 'yar roba ya wanke hannu sannan ya zubo ruwa a ciki ya dawo, da rarrashi da hikima ya sa ta cin kazar nan, har ta manta ita ba'kuwa ce, dama kuma azabar yunwa ce a cikinta. ya sake lallabawa ya tura mata yougurt, sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya kalle ta ya ce, "Ga toilet nan ki shiga ki yo brush ki dauro alwala" Ya mike yana fa'din ni ma bari na yi alwalar. 'Kirjinta ya buga fargaba ta kama ta yau gata a daren farko da ta ke karantawa a cikin littafai ko ya ya nata daren zai kasance? Har ya dawo tana zaune a inda take. "Kin yi alwalar kuwa?" Shiru ta masa ya tabbatar ba ta yi ba sai ya ce, 'Tashi mana!" Ya sa hannu ya 'dago ta, sai da ya raka ta har kofar bayin da ke cikin dakin sannan ya dawo yana tattare kayan da suka yi amfani da su, ya shimfi'da musu sallaya ya koma gefen gadon ya kishingi'da yana jin matsanancin bege na ratsa shi. A bandakin ta tarar da sabon brush da makilin, sai da ta wanke bakin sannan ta 'dora alwalar sai kuma ta tsaya a bakin 'kofar ta kasa fita. Wata irin fargaba ce ke haniniya da ita. MK da ya ga shirun ya yi yawa, sai ya tashi ya tura kofar ganin ta a tsaye, yasa shi yin turus, bai ce komai ba ya ru'ko hannunta yana fadin, "Ba na son ba'kon yanayin nan da nake gani tare da ke a yau". Laffayar ya mi'ka mata ta fara kokarin na'de jikinta, ya kalle ta ya ce, "kin ga ba sai kin yi wannan na'din ba, kawai ninka ki yafa". Ba ta musa ba saboda yadda bakinta da jikinta suka yi mata nauyi ainun. Ya ja su, suka yi sallar da Annabi ya kwa'daitar da sabbin ma'aurata su yi. Bayan sun idar ya ri'ke goshin ya yi addu'a sosai, tana amsawa da amin a cikin zuciyarta. Suna shafa adduar ya mike ya fita! bai jima ba ya dawo bayan ya rufe 'kofar falon tare da kashe fitila da fanka, kasancewar farkon damina ne yanayin zafi ne. Yana shiga ta kalle shi da gefen idonta saboda yadda kamshin sa ya sake cika dakin da hancinta, ta ga ya sauya kayan jikinsa zuwa farar jallabiya sabuwa 'kal. Hannusa ri'ke da wasu kayan, kai tsaye ya isa kusa da ita ya m'ikar da ita ya cire mayafin ya wurgar da shi, ya zame dan'kwalinta!dogon gashinta da ya sha gyara na musamman ya bayyana, ya kasa cigaba da dauriya ya fizgo ta jikinsa ya sa hannunsa biyu ya rungume ta sosai tamkar zai mayar da su halitta guda. Ba ita ba, shi kansa jikinsa 'bari ya ke yi, 'kamshin man gashinta da na jikinta da kuma nasa kamshin suka hadu guri 'daya suka sake rikita shi, hannunsa sai kai komo ya ke yi a bayanta cikin wani irin shau'ki mai rikitarwa. Ta yi luf a 'kirjinsa jikinta sai 'bari ya ke yana sake rikicewa da sa'kon da ya ke kar'ba. A kunne ya ke rada mata "please hold me Sa'adah, sa hannu ki ri'ke ni don Allah!" Cikin wata irin murya da ba ta san shi da ita ba yake ro'kon. Kunya da tsoro suka sa ta kasa koda 'kwak'kwaran motsi balle ta iya masa abin da ya ke ro'ko. Da 'kyar ta samu ta zame daga jikinsa ta koma bakin gado ta zauna kunyar duniya ta rufe ta. Murya a da'kushe sosai yace, "Ga rigar barci tashi ki saka". Kai ta sunkuyar 'kasa tana kallon 'yar guntuwar rigar da ba ta da maraba da abin tatar koko, ta ya ya za ta iya sanya wannan rigar, ko a ina ya samo ta? Ganin ba ta da niyyan tashi ya matsa kusa da ita ya 'dora mata akan cinyarta tare da fadin, "Tashi ki saka don Allah" Ta 'daga taga lalacewar riga ta wuce ma yadda ta ke tunani, da sauri ta ajiye ta tana fadin "Ni ba zan iya sawa ba, ba na son ta". "Ni ina so! kin san tun yaushe na siya miki na ajiye? Kullum addu'a nake Allah ya kawo mini ranar da zan gan ki a cikin ta. Ta shagwabe fuska ta 'daga rigar da sauri ta mayar ta ajiye, ita rigar ma kawai kunyata take yi, balle kuma a ce ta saka, kanta a kasa ta ce "Ka yi hakuri ni ba zan iya sawa ba". Nan da nan ya ci laya, "Wallahi sai kin saka na gani". Ya fada a dake! gabanta ya yanke ya fa'di ta shiga bubbuga 'kafa, tana 'kananun kukan da babu hawaye, hakan da ta yi ya sake 'kawata masa ita, ya sake matsawa kusa da ita sosai, ya yi 'kasa da muryarsa ya ce, "Rufe idon ki ni sai na sa miki da kaina". "Ni dai ka yi hakuri ka bari". "Amma kin ji na rantse, so kike tun yanzu ki fara 'ba ta mini rai, ki fara kwasar zunubi?" Kai ta girgiza, ya ce, "To ki bar ni na yi abin da nake so, tun yaushe nake ha'kurin ki zama halaliya ta". Ya fara zuge zip din rigarta ta ri'ke da sauri, tana fadin "Ka kashe fitila to". "Idan na kashe fitila me zan gani?" Ta yi shiru tana jin tamkar kasa ta tsage ta shige. Ta kasa kallon sa a raunane ta ce, "Ka juya to, ya yi murmushi ya ce, "To" Ya juya mata baya. Kan dole ta sanya rigar amma ta kasa cire kayan ciki! Ta kuma lullube jikin da mayafi. Jin ta daina kiciniyar sanyawa ya sa shi cewa "Na juyo?" Jin ta yi shiru ya sa ya juyo gabadaya, sai dai ganin ta a lullu'be kuma a takure ya sa shi fa'din "mene ne haka kuma?" Ya isa ya mikar da ita tsaye ya fara janye mayafin, ita kuma ta 'kan'kame 'kirjinta da dukka hannun ta biyu. Ya juya ta bayanta ya ga yadda rigar ta kama ta, shape din surarta ya fito sosai. Da 'kadan ta rufe mazaunanta 'yar guntuwa ce sosai, mai kuma kama jiki, rashin kirkin rigar ya kai 'kurewa. Tsayawa kawai ya yi yana kallon ta yana fadin "Ma Sha Allah kin yi mini fiye da yadda nake so". Jin yana 'kokarin 'daga rigar sama sai ta yi maza ta saki 'kirjin ta ruko kasan hakan ya ba shi damar juyo wa ya kalli 'kirjin ta. bai ce komai ba kawai ya ci gaba da tasbihi, ya jawo ta ya rungume ta sosai fiye da rungumar farko. A haka ya dangana su da gado, ya sa hannu ya kashe fitila, hasken bandaki ya ragewa dakin duhu, ya cire rigar da ragowan kayan ya wurgar. Sannu-sannu ya bi da ita, duk wata ga'ba da 'kofa ta jikinta ba inda bai sa baki ya lashe ba, ya rikita mata jiki sosai! nishin da yake yi ya sake jefa ta cikin tsananin shauki da za'kuwa. A ranta kuma ayyana rashin 'kyankyami irin na MK take yi, inda ba ta yi zaton ana sa baki ba, shi yasa harshe yana lasa bai kuma tofar a 'kasa ba. Sai da tafiya ta fara nisa ta gane al'amarin ba mai sauki ba ne, bai 'kyale ta ba sai da ya mayar da ita cikakkiyar mace. Dukkansu sun galaibaita, saboda a tare suka bude junansu a leda. Sai da nutsuwa ta zo wa MK ya rungume ta tare da shafa kanta yana fadin maganganu masu nuna 'kololuwar soyayya da yabawar yadda ta kame kanta, kamar yadda shi ma ya kame. Wani irin son junansu ya cika zuciyarsu da gangar jikin su gaba'daya. A tsakiyar Daren ya fita kicin ya dauko buta ya jona musu ruwa, shi ya fara shiga, kafin ya fito nata ya tafasa, ya kai mata ban'dakin ya taimaka mata ta sauko da ga gadon sai da ya ga ta shiga toilet din sannan ya ye zanin gadon saboda yadda suka bata shi, idan ya bushe jirwaye zai yi, ga kuma jinin budurci. Ya shimfida wani, daga yadda yake aikin ka san a cikin farin ciki ya ke sosai. Ita kuma Sa'adah tana can tana gasa kanta tana fadin ai a littafi daukar amarya ango yake yi, ya gasata ya mata wanka, sannan ya nade ta a towel, ya mayar da ita daki, ya shirya ta a kuma kwantar da ita kamar jaririya, shi komai bai iya ba. Amma tana tuno yadda 'dazu ya sarrafa ta, ya jagwalgwalata son ransa, ya lashe ta tas, sai ta rufe ido da hannunta saboda yadda kunya ta kamata, ba ta taba karanta yadda ya mata din ba, salonsa daban ne. Ta fito tana ra'be-ra'be, ya taro ta yana fa'din, "Sannu My Sa'adah! Allah ya miki albarka, da kansa ya shafa mata mai, da turare, suka kwanta ya dora ta akan cikinsa yana shafa jikinta a ranta fadin take shi baya gajiya ne da wannan shafar? Kafin barci ya dauke su, sai ji suka yi ana kiran sallah. Mamaki ya kama MK yana tunanin ashe ba karamin lokaci suka shafe a tare ba, ba su kwanta ba sai da suka yi sallah. Zuwa masallaci ya gagari MK, ba zai iya tuna ranar da ya yi sallar Asuba ba a jam'i ba, sai yau da suka yi da amarya. 😁 Wayarsa ya kashe ya rungume amaryar sa bayan ya lullube su da duvert, barcin gajiya ya yi awon gaba da su. Alkalamin *SURAYYA DAHRU* ✍🏼. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* *UZZIRI*. *kwanaki biyu baza'a Sami posting ba, Ina cikin hidimar Biki ne, da zarar na Sami nutsuwa, zaku ji ni, na gode sosai da yabawar ku akan Rubutuna*. 51-52. Barci sosai suka yi sai wurin 12:25pm MK ya farka, idonsa ya sauka kan agogon dake makale a bango. Salati ya yi, bai ji mamakin yadda suka shafe lokaci suna barci ba, saboda sun ci bashinsa a jiya. A hankali ya raba jikinsa da Sa'adah, ya zuba mata ido yana ganin yadda take numfashi a hankali gashin kanta ya barbaje ya zubo har kan fuskar ta. Ba karamin kyau ta masa ba, duk kuwa da ba komai na alamun kwalliya, sai ya tsinci kansa da yi mata hotuna a hakan. Da 'kyar ya yunkura ya shige toilet ya watsa ruwa don ya samu sau'kin nauyin da jikinsa ya masa musamman cinyoyinsa da yake jin su a daure suna masa ciwo. Ya fito daure da towel babba, bayan ya dauro alwala. Ya shirya cikin kananun kaya da suka yi masa kyau, sannan ya hau bakin gadon ya fara shafa gashinta da ya tarwatse, yana kiran ta a hankali, kamar a mafarki ta ji shi. Sai dai kunyar sa ta hana ta bude ido bare ya gane ta farka, tana ayyana da wane ido za ta kalle shi da rana? Ya san ta ji shi sarai, don haka ya shammace ta ya zame bargon da ta rufe jikin ta da shi, 'kirjinta ya bayyana, da sauri ta sa dukkan hannun ta, ta kare su, tare da fadin "Na shiga uku!" A shagwabe idonta kuma a rufe. Dariya sosai MK ya yi tare da cewa, "Ashe ban gama cire kunyar gaba'daya ba?" Cikin tsokana ya hau gadon sosai, ya riko ta jikinsa yana fadin "second round ina kallon ki, kina kallo na, sai mu binne kunyar nan kawai". A sukwane ta bude idonta ta ce "Uncle wallahi ban da lafiya, ka yi hakuri". Murmushi ya yi sannan ya ce "Kalle ni to". Idonta a bude amma ta kasa dora su akan fuskarsa, da gaske kunyar sa take ji ba kadan ba. Ganin hakan sai ya 'kyale ta, ya ce ta tashi ta shiga wanka, ya hada mata ruwan wankan. Ba ta yarda ta saki bargon ba, sai da ya ba ta tawul ta daura, nan ma ta kasa tashi sai da ya rike hannunta ya kai ta bakin kofa sannan ta shiga. Kafin ta fito ya gyra gadon ya share dakin da falon har tsakar gidan kasancewar kwana aka yi ana kada iska, kura da ganyayyaki sun ba ta tsakar gidan. Yana gamawa ana kiran sallar azahar dan haka ya le'ka ya gan ta tana shafa mai, daga bakin kofar ya ce "Bari na je Masallaci idan na dawo sai mu karya ko?" "Adawo lafiya." Ta ce ba tare da ta kalle shi ba, ya amsa yana jin dadin addu'arta, shi ma ya zama magidanci. Ana idar da sallah ya juyo, a kicin ya yada zango risho kirar Butterfly ya kunna. Ya shiga fasa kwai yana soyawa bayan ya sa albasa sosai, da atturuhu, da maggie. Yana kammala soya musu ya kashe rishon tunda ya riga ya dafa shayi a kettle kafin ya fita ya juyo a tea flask. A falo ya shirya komai ya leka ya gan ta kishingide a gefen gado da doguwar rigar shadda da aka mata shahararren dinki. Fuskarta ba kwalliya amma ta yi kyau sosai duk da ta yi fayau, ta dan fada kadan. Kamshinta ya cika dakin, da sauri ya isa gareta yana fadin "Woow Amaryata kin kara yin kyau fiye da jiya." Ya sa hannu ya dago ta yana ci gaba da fadin "Anya yarinyar nan za ki dinga barina ina fita kuwa?" Kallon ki kawai, ya fi mini komai". Dadi ya cika mata zuciya, tasirin kalamansa, suka bayyana akan fuskarta, saboda yadda take ta murmushi dimples dinta na lotsawa. A haka suka isa falo yana cewa "Zo ki karya, ni kaina yunwa nake ji bare ke da nayi ta dabdala da ke" Kunya ta kama ta, ta rufe idonta, kunya na burgeshi sosai bai yi zaton kunyarta ta kai haka ba, musamman yadda ya san ta da fitina. Da kyar ya samu ta bude fuskarta, amma fa idonta na kasa tana kallon yadda ya baibaye falon da kayan shayi, dangin su madarab(peak), Ovaltine, sugar mai iyali (cube) da bread din Oasis Bakery, ga kuma soyayyen kwai. Da kansa ya hada mata tea din da ya zama tamkar kunu saboda yadda ya ji kayan hadi ya tura mata gabanta yana cewa "Ki yi ha'kuri da iya wannan Amarya! Gobe In sha Allah, da wuri zan tashi na miki girki na musamman, yau mun makara ne". Ita dai bata ce komai ba illa juya tea din da take ta faman yi ta kasa kaiwa bakinta. Ya sake cewa "Akwai fa cake a fridge, ko na dauko miki?" Kai ta girgiza ta ce, "A'a". Kofi ya dauka ya hada nasa shayin, wanda ba shi da madara sai ganyen shayin (Beyond Comment) na asalin. Sosai suka ci abinci saboda dukkan su yunwa suke ji ba kadan ba, duk da dai Iyah ta kasa sakewa sosai, sai dai shayinta kadai ya isa ya kosar da ita. Ganin sun gama ya sa Sa'adah tattara kayan da suka bata, MK ya karba yana fadin "Yi zamanki ki huta, ke bakuwa ce a gurina don haka ni zan tayin hidimar har sai kin zama yar gari a gidanki". Murmushi ta yi, tana zaune ya kwashe komai yasa tissue ya goge mata hannu da baki, yana yi yana tsokanar ta, sai da ya fita zuwa kicin ita ma ta shiga toilet ta wanke hannun ta da bakinta sosai. Ta fito tana karewa kayan furniture's din dakin ba karamin kyau suka mata ba, ko a ina ya samu kudin siyan wannan gadon?Haka nan tsaruwar falon ma ya burge ta, ta tabbatar ko iyayenta ma ba lallai su shirya mata gida haka ba. Tana tsaye a falon tana jin buruntunsa a kicin da alamu wanke wanke yake yi, sai ta ji babu dadi yadda ta sakar masa yin komai, don haka sai ta saka takalminta da yake gefe wanda ta sako jiya, ta nufi kicin din ta tarar ya kammala, Frying Pan kadai ya rage, da sauri ta ce "Kawo na karasa, dama ka bari zan yi". Ya juyo da dukkan hankalinsa gare ta ya zuba mata ido yana jin sabon son ta na huda zuciyarsa, idanuwansa da gangar jikinsa gaba'daya. Ba ta san dalilin da ya sa ita ma ta zuba masa ido ta kasa daukewa ba, tsawon sakwanni suna kallon juna, Chemistry na aiki a jikin su. Ita ta fara janye fuskarta tana jin kunya na taso mata Murya a dakushe ya ce "Ki koma ki yi hutawar ki, na gama yanzu zan zo". Tana shiga falon NEPA suka dawo da wuta, ta kunna TV, a lokacin DVD ce tafi yawa, fim din sai Wata Rana ya bayyana akan gilashin TVn. Ba ta kai ga zama ba, ya shigo falon, kai tsaye ya isa kusa da ita yasa hannuwa ya janyo ta zuwa jikinsa sosai, bugun zuciyarsu ya karu, har kowa yana jin yadda zuciyar dan'uwansa ke bugawa. A hakan ya zauna a kujera, ya zaunar da ita kan cinyoyinsa, ya zame dan'kwalinta yana shinshinar ta tamkar maye, hannuwansa na ta kai komo a jikinta. Jikinta sai tsuma yake tare da wani irin shauki na ban mamaki. Ya dinga kici-kicin ya zura hannunsa kasan rigarta amma ya kasa kasancewar doguwa ce kuma fitet. Karamin tsaki ya yi, yana rada mata "Ki daina samin doguwar riga irin wannan a yanzu". Ba ta iya cewa komai ba, sosai yake ya mutsata. Ya yi nisa wurin tsotsar harshenta, ya ji wayarsa da ke aljihunsa tana ta kuwwa, da kyar ya hakura ya raba bakinsu ya fito da da wayar, ganin sunan Mahmoud ya sa shi sakin tsaki a fili sannan ya amsa tare da cewa "Saboda Allah mene ne hakan?" Mamaki ya kama Karfi ya ce "Yi ha'kuri leko ina kofar gidan ka karba wa Amarya sako" Daga haka ya katse wayar. Kan dole ya fita yana bude gate din ya ga Mahmoud a cikin adaidaita sahu, ga kuma kaya ya sauke masa a bakin kofar gidan. Ganin ya fito yasa Mahmoud ba wa mai adaidaita sahu umarnin ya ja su tafi ba tare da ya yi wa MK magana ba. Da sauri MK ya bi su yana fadin "Karfi tsaya mana!" Amma fur ya hana direban tsayawa kan dole ya juyo yana mamakin yawan kayan da Mahmoud ya jibge masa. Akwatina masu kyau guda biyu babba da karami, kwalin indomie guda biyu, kiret din kwai biyu, da leda mai dauke da kayan shayi. Gefe madaidaicin botiki ne dauke da soyayyar miyar kaji da katan din ruwa na SWAN da katan din coke da fanta. Daga jikin akwatin ya hango yar takarda da alamun soke ta aka yi, hannu yasa ya ciro ya fara dubaw *Abawa Amarya, miyar kuma In ji Umma*. Murmushi ya yi ya san fushi ya yi, a ransa kuma jinjina yawan alherin Karfi yake yi. Haka ya yi ta kinkima yana shiga da su cikin gidan, sai da ya kammala shigowa da su, sannan ya zauna yana cewa "Duka wannan sakon ki ne in ji Karfi". Da walwala a fuskarta ta ce "waye hakan?" "Mahmoud fa." "Oh shi ne Karfin?" Kai ya daga mata yana kokarin bude akwatin da ya fi girma, kaya ne tamkar na lefe, sai dai dogayen riguna da English wears sun fi yawa. Dayan akwatin kuma shake yake da kayan kwalliya da na gyaran gashi. Sosai ta nuna farincikinta kan kayan tare da yi wa Mahmoud fatan alheri. MK ya yi kasa da muryar sa soasai ya ce, "Mu je daki ki ji wata magana". Nokewa ta yi tare da fadin, "Fada mini a nan". "Maganar ba ta nan ba ce Sa'adah na!" Ya tashi yana jan ta zuwa dakin, ganin da gaske yake yi, ya sa ta cewa "Amma dazun nan ka ce ni bakuwa ce, ba zan yi komai ba sai na zama yar gari?" "E na fadi hakan, amma kuma ban ce har da wannan al'amarin ba". Tabe fuska ta yi hadi da tura baki gaba ta ce "Ban warke ba, zafi zan ji." "I promise you, ba za ki ji ba, I will be soft and gentle". "Ni dai a'a uncle". "Bangane a'a ba?" Ya fada yana mata wani irin kallo. Kan dole ta mi'ka masa kai ya yi yadda ya ke so. Bata fahimci komai a sai zafi da wata irin takura. Bai samu kansa ba sai bayan La'asar, don haka a gurguje suka yi wanka, suka yi jam'i. Kwalliya sosai Sa'adah ta sake yi duk da yadda take jin radadi a kasanta. Kwanciya ta yi a dakin, tana ayyana gaskiya ba wani dadi a wannan lamarin, sai dai a barka da radadi da ciwon jiki. Romance dai, idan za a yini ana yi ba za ta kosa ba. A karo na biyu ya sake shigowa dakin. "Kin san dai barcin bayan La'asar ba kyau ko?" Idonta a rufe ta ce "Ni ba barci zan yi ba". "To fito falo, fita zan yi na dora ruwa akan risho idan ya tafasa ki wanke shinkafa ki zuba". Shiru ta yi tamkar ba ta ji abin da ya ce ba, ya san ba ta gamsu da fitar da zai yi ba ne. "Kin ji". "Ni gaskiya ka kashe rishon". "Ba za ki yi abin da na saki ba ke nan?" Cikin tura baki ta ce "Ni tsoro nake ji kar barci ya dauke ni abincin ya kone". "Ba fa dadewa zan yi ba, salad zan sayo kawai". Da sauri ta ce "shike nan adawo lafiya, amma dai kana sayowa ka dawo gida." "Mai za ki ba ni idan ina gidan?" Kai tsaye ta ce, "Abin dadi mana." Murmushi ya yi tare da fadin, "Kamar gaske, a haka kamar jaruma ana taba ki kadan sai raki". Shiru ta yi tamkar ba ta ji shi ba. Ya juya yana fadin, "Bari ma na zuba shinkafar na san yanzu ruwan ya tafasa". Biyo shi ta yi tana cewa, "Ka je kawai zan zuba, a dawo lafiya" Bai wani jima ba ya dawo, da hanzari ta karbi ledar tana masa barka da dawowa, ya amsa cike da jin dadi. Cikin kankanin lokaci ta yanka salad din ta wanke da gishiri, ta bar shi a kolanda, ta hau yanka cocomber da su tumatur. Ba ta koma falon ba, sai da ta tace shinkafar, ta yi kasa da rishon ta mayar kan wutar don ta silala a hankali. Tana shiga daki ta nufa, ganin hakan yasa MK da ke zaune a kujerar kusa da kofar daki ya fizgo ta ta fado masa. "Kin ce na dawo da wuri na dawo din kuma sai ki shige ki bar ni, ko dai kari kike so?" Zabura ta yi, ta zame tana cewa "Indai ba so kake ka mayar da ni chopping the rice 🍚 ba, ya kamata ka daina wannan maganar haka nan". Dariya sosai ta ba shi, ya dinga kyakyatawa, ita kuma ta shige daki tana cewa, "Dole ka yi dariya mana ka same ni kana yin yadda ka ga dama da ni, ba tausayawa". "Oh haka kika ce? Za ki ga rashin tausayin kuwa". Yanzu ma shi ya shiryo musu abinci, tana zaune tana kallon karamin tray din da ya zubo salad, mamakin yadda ya zauna ya yi garnishing din salad din da waken gwangwani da su cocomber da tumatur take yi, tamkar a restaurant. A plate daya ya zuba musu abincin, suna ci suna yaba dadin miyar Umman Mahmoud. Suna kammalawa Sa'adah ta kwashe kayan ta share gurin. Ya kalle ta ya ce "Sannu da kokari, amma na ce miki sai kin fita daga bakunci kafin ki fara hidima". Ta gefe ta kalle shi, ta juyar da idonta gefe sannan ta ce "Ka bar ni kawai na yi ayyukana tunda hidimar ba duka ka dauke mini ba". Murmushi ya yi tare da cewa "Ashe ban yi gwaninta ba?" Cikin kunkuni irin na shagwaba ta ce "Ba ka yi ba". Karar wayarta ya katse damkar da ya yi niyyar kai mata, daki ta shige don a can wayar take. Da sauri ta amsa kiran "Anty Sumayya kin ce fa za ki zo mu yi sallama kafin ki wuce, ga shi har Maghriba ta kawo kai ban ganki ba". "Kai Iyah! Da gaggawa kike, to muna kofar gidan, zo ki bude mana". Katse wayar ta yi, ta isa gaban madubi ta kalli kanta, riga da siket din atamfa ne jikinta, powder da turare ta sake shafawa sannan ta fito. "Uncle, su Anty Sumayya ne suka zo" Kafin ya yi wata magana har ta fice da sauri. Bin ta ya yi da ido, yana jin wani irin abu a zuciyarsa akan me za ta fita a haka? A hankali ya mike ya fita daga falon ya shige dakinsa da yake tsakar gidan. Ba su jima da shigowa ba, ya fito, suka gaisa da Anty Sumayya da yaranta, ganin Sa'adah ba ta ba su ruwa ba yasa ya shiga kicin ya shirya ruwa da lemo a tray, da tumblers, ya doro cake din da yasa a fridge, yana jin farincikin ruwa da lemon da Mahmoud ya kawo musu na ratsa shi. Da kansa ya dauka ya kai musu, Sumayya sai sannu take masa tare da fadin "Ga yara kuma sai ka dauko da kanka, sannu na gode". Murmushi ya yi tare da cewa, "Ba komai Aunty". Alwala ya yi, ya fito daga waje ya tsaya ya kira Abba ya danka masa sabbin kudi na dubu biyu,"Ku sayi sweet kai da kannenka". Fir Abba kin karba ya yi, tare da cewa "An hana mu karbar kudi Uncle" Dole sai Sa'adah ya kira ya ba ta, ya ce ta ba su. Ta kalle shi bayan Abba ya koma falon ta ce "Fita za ka yi ne? "Masallaci zan je daga nan kuma zan je gida". Bata rai ta yi sosai "Ba dadewa za su yi ba Uncle, so kake na yi ta zama ni kadai? tunda dare ya yi kawai ka bari gobe ka je da wuri". "To" Kawai ya ce ya daga labulen falo ya ce, "Anty Allah ya mayar da ku lafiya, mun gode sosai." Ita ma ta amsa cike da mutuntawa. Daki suka shige, suka bar yaran a falo suna kallo suna fama da cin cake. Jan kunne da nasiha iri-iri Sumayya ta sake yi wa Sa'adah. Ta dauko wata leda a jakarta mai dauke da tambarin Welcare,ta mi'ka mata ta ce ki adana su sosai, likitan ya ce za ki iya shan wannan ba komai. Ganin da Sumayya ta yi Sa'adah ba ta bude ledar ba yasa ta ce "To ki bude mana na nuna miki yadda za ki sha". Kin budewa ta yi, sai Sumayya ce ta bude ta fito da su, daya a cikin wata yar roba yake mai kyau an rubuta Women's Formula. "Kinga wannan na robar Multivitamin ne 100 pieces ne kullum daya za ki sha" Sai wannan ta nuna na kwalin shi ba kullum ba sai ranar da kika so. Ki kula da shi mai tsada ne sosai, daurewa na yi na siyo miki package dinsa, kafin ya kare dai na san za'a dade sosai". Ba tare da ta kalli fuskar Sumayya ba ta ce "Na gane, na gode." Ta mayar da su ledar. ganyin wata takarda a ciki yasa ta janyo ashe recit din kudin ne, ganin yawan kudin da maganin suka lashe musamman na kwalin ya matu'kar ba wa Sa'adah mamaki. Ta fito dana kwalin tana dudduba mene ne special a tare da shi da ya yi wannan darajar haka? "Viagra" Ta furta sunansa a fili, a kunyace ta sake cewa "Na gode sosai Anty". Sumayya ta muskuta ta tsare Sa'adah da kallo mai tsanani sannan ta ce "Ina rokon ki Iyah kar ki jefa kanki a hallakar da MATAN YAU suka jefa kansu na shaye-shayen magunguna barkatai marasa fa'ida da inganci, da sunan mallakar miji. Kar ki yarda da wannan bankaurar wallahi ba a mallakar miji da wannan sai dai ki ta asarar kudaden ki, karshe ki hadu da ciwon da zai raba ki da mijin gaba'daya". Cike da wauta Sa'adah ta ce "Fada mini abin da zan yi na mallake shi kamar yadda kika mallaki mijinki". Dariya sosai Sumayya ta dinga yi har da kwanciya akan gado, lamarin da ya fusata Sa'adah, kawai sai ta fashe da kuka, da kyar Sumayya ta hadiye dariyar ta shiga rarrashinta. "Yanzu mene ne abin kuka Iyah?" "To akan me za ki mini dariya kamar mahaukaciya?". "Tambayar ki ce ta ba ni dariya, amma nutsu ki ji mai zance miki. Mace tana kama mijinta da girki mai da'di, da kuma ba shi kulawa ta musamman a shimfida, da kuma tsaftar jiki da ta muhalli. Amma wadannan kadai, ba zai sa ta mallake shi ba, sai ta yi ha'kuri ta bi ra'ayin sa akan komai, ko da kuwa ita ba hakan take so ba, ya zama ba ta da ra'ayin kanta sai na mijinta, ta iya ladabi da biyayya, ta kiyaye harshenta akansa. Ina tabbatar miki idan kika hada wadannan abubuwan sai kin mallake shi fiye da yadda kike so". Tura baki gaba ta yi tana goge hawayen idonta, ta sake cewa "To idan ina son ya zama mijin ta ce fa?" Mamaki da tsoro ya kama Sumayya, wai wannan yar mitsitsiyar yarinyar auren jiya, ita ce ke son ta mallake miji, bayan mallakar kuma ta mayar da shi mijin ta ce. Wane irin son zuciya ne ya shigo wa matan wannan zamanin haka? Sumayya tsintar kanta ta yi da ri'ko hannun kanwarta ta kalle ta da tarin kauna sannan ta ce, "Abubuwan da na fada su ne za su miki jagora akan komai, sai kuma ki hada da addu'ar Allah ya zaunar da ku lafiya cikin aminci da tausayi. Amma karki yarda da kawayen da za su ba ki maganin mata ko a saki a hanyar zuwa wurin malamai wallahi ba za ki samu yadda kike so ba, ba komai a wannan hanyar sai bata da lalacewa". Ta dan tsahirta kafin ta zarce da fadin "Ki ba shi dama ya zama sarki a gidansa, ke kuma ki zama baiwa kuma bafadiyarsa, duk abin da kika san yana so, ki masa tun kafin ya bu'kata haka nan ki guji abin da baya so kafin ya ankarar da ke, ina tabbatar miki idan kin yin hakan bayan mallakar da za ki masa zai ya zame miki mijin kan ta ce ma, matu'kar yana rayuwa kan tsarin ilimi da shari'a ne. Ga turaren wuta nan Inna ta ce a kawo miki sai dazu suka iso, ni ma na diba na ga masu kyau ne, har da na tsugunno". Ta mike tana fadin, "Kin ga an dade da idar da sallah bari mu tafi". Da za su tafi rungume juna suka yi kuka kowacce ta ke yi tamkar ba za su sake haduwa ba. A dole suka rabu Sumayya na mata fatan zaman lafiya da zuri'a mai albarka. Ba su jima da tafiya ba ta zuba gawayi a kasko ta zuba kalanzir tare da kyasta ashana, ta barshi a tsakar gida, ta share falon inda su Khalifa suka bata. Sannan ta shiga wanka, sai da ta yi sallar Isha, sannan ta duba ta ga wutar ta kama, ta dauko ta zuba turaren. Kan ka ce kwabo gida ya cika da kamshi, sai kallon agogo take yi,har tara na shirin yi bai dawo ba. Daidai lokacin ya dawo, waya ya kira, ta fita ta bude masa, kamar dazu ba mayafi a tare da ita. Suna tafe yana fadin "idan za ki fito ki dinga saka hijab, ban son wani ya hango ki a haka". Ta amsa da tom. Tunda ga tsakar gida yake jin daddadan kamshi, suna shiga falon ya rikota yana cewa "Madalla da Antyn mu, irin wannan kamshi haka". Ita dai ba ta ce komai ba, sai da suka zauna ta ce "Sannu da dawowa" Ya amsa mata cike da walwala. "Shi ne ka tafi ka bar ni ni kadai har tsoro ya fara kamani". Ta fada cike da shagwaba. "Ai kuwa dai gara ki cire tsoro, kin san har sha dayan dare ina kaiwa a shago". Murmushi ta yi kawai ba ta ce komai ba, amma a zuciyarta tana raya ba za ta yarda da wannan dogon zaman a waje ba, tana gida ita kadai. Haka suka ci gaba da cin amarci ba kakkautawa cike da soyayya da kulawa, tun Sa'adah na jin zafi da tsoron haduwarsu har ta saba ta fara fahimtar dadi da nutsuwar dake cikin haduwar. ```Alkalamin *Surayya Dee*. ``✍🏼✍🏼 [6/5, 14:08] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *Fatan alheri ga Amare* *Hafsa Sani Abubakar* *Halima Sani Abubakar* _Ubangiji ya albarkaci auren ku, ya Baku zuri'a mai albarka_. 53-54. *BAYAN SATI SHIDA* Zuwa wannan lokacin, sabo da shakuwa mai karfi sun shiga tsakanin ma'auratan biyu, soyayya da aminci sun sami wajen zama a gidansu, kowa kokarin kyautatawa dan uwansa yake yi. MK ya dauki soyayyar duniya ya dora akan Sa'adah da da hali kirjinsa zai bude ya cusa ta, saboda yadda ya ke jin ta a zuciyarsa, musamman yadda ba ta gajiya da bukatunsa. Duk da dai ya gane ita ma mabukaciyar ce ta gaske ga tsafta ga iya sarrafa girkin gargajiya, saboda ire-iren su aka fi yi a gidansu. Babban abin da ya ke gigita shi a kanta, shagwaba da iya kwalliya, kullum sabuwa take zama a idonsa, kullum da sabon abin da zai gani a tare da ita, babban abin birgewa ta kama dukkan ahalinsa ta ri'ke da hannu biyu, ta zama yar gida a gidansu, akai-akai take kiran Hajiya Babba da Hajiyar Bichi tana gaishe su. Sun zo sau daya sun ga gida, da amarya. Tana kokari sosai wurin yin abinci akai gidan su Mk mussaman masar Bauchi da miyar ganye, da kuma Dambu. Kasancewar mahaifiyar ta daga Bauchin take, sosai ta iya masar Bauchi. Kullum yana gida, hatta FGC Kano ma ya daina zuwa, shago kuma sai Azahar yake fita, da zarar karfe biyar ta yi zai juyo ya bar su Abbas da kula da wurin, Mahmoud ya masa tsiya ya gaji. Shi kansa Mahmoud din tunda ya je ya ci girkin amarya, dambun shinkafa ta yi musu da ferfesun naman rago, sai kunun aya bai sake yi wa MK tsiyar ya zama bita-zai-zai ba, musamman yadda kamshin turaren gafgaf da kajiji ya kama gidan gaba'daya, dole idan mutum ya yi katarin samun irin su Sa'adatu ya manne musu ya kasa fita ko ina. A wannan tsukun ASUU ta janye yajin aikin da ta ke yi, a kuma lokacin aka tabbatar da MK da Mahmoud da sauran da suka yi sa'ar samun koyarwa a Jami'ar Bayero takarda shedar fara aiki. Ranar da ya fara fita aikin dukkansu sun galaibaita, sati shida kullum suna manne da juna, ko fita ya yi Allah-Allah yake ya dawo. Don haka yanzu ma da zarar ya ga yana da tazarar lokaci, sai ya dawo gida ya ci abinci, ya yi abin da zai yi, sai kuma ya yi wanka ya koma, idan kuma ba shi da sauran darasi shike nan sai ya yi zamansa gurin amaryar sa. Watannin su biyu da aure Sa'adah ta tsiri fushin da babu dalili, share shi take yi, ta daina hira da shi daga eh sai um um, ta rage walwala idan yana gidan, idan tana falo ya zauna, sai ta san yadda ta yi ta bar falon, haka nan daki. Ba ta gudunsa, amma shi kadai zai yi kidansa yayi rawarsa, babu gudunmawa daga gare ta. Wannan canjin ya matu'kar 'daga masa hankali ya yi tambayar duniya tace ba komai, kuma lafiyar ta 'kalau. Rannan da daddare ya dawo da ga Masallaci, jikinsa a sanyaye ya zauna kusa da sallayar da ta ke sallah ya jira ta idar. Tana ganinsa ta yi kamar ba ta gan shi ba ta fara kokarin tashi a gurin ya kira sunanta a kaurare. "Sa'adah zauna magana za mu yi". Ba ta 'ki ba, ta koma ta zauna amma fuskar nan a 'daure, sannan ta juyar da kanta gefe, ta ki kallon inda ya ke. "Na tambaye ki mene ne yake faruwa kin ce mini ba komai amma kuma kin canja mini, kin tayar mini da hankali, wallahi da kinsan yadda nake ji a zuciyata da kin tausaya mini cikin kwanakin ukun nan. Shiru ta yi, tamkar ba da ita yake ba, ya matsa ya riko hannunta, ta fizge tare da zura su cikin hijab, wata irin fargaba ta kama shi, bakinsa har rawa yake yi ya ce "Har abin ya kai mu ga haka, laifi na yi ke nan?" Nan ma shiru ta sake yi. "Don Allah Sa'adah me na yi miki? Ki fada mini, ba ni za ki duba ba, Allah na hada ki da shi". Jikinta ya yi sanyi sosai, ta kasa cewa komai sai da ya sake rokon ta sannan ta bude baki ta ce, "Ni gaskiya zaman ne ba zan iya ci gaba da yi ba, na gaji". Gabansa ya yanke ya fa'di. Murya ba amo ya ce "Me na yi miki?" Shiru ta yi, hankalinsa ya yi mugun tashi ya fara fa'din, "Ban miki komai ba fa Sa'adah, don Allah idan wasa kike mini ki bari bana so". Yana rufe baki ta ce " "Wallahi ba wasa na ke yi ba, zaman ya isa haka nan". Ya tsura mata ido tsawon lokaci ba kakkautawa yana nazarinta, ya lura da gaske take yi, bugun kirjinsa ya karu, gumi ya fara karyo masa, jikinsa na bari ya ri'ke kafadunta da karfi, ya ce "Kar ki mini haka Sa'adah don Allah, ina sonki fiye da kaina, fada mini inda na gaza, me na ke yi wanda ba kya so?" Ta yi shiru amma fuskar nan a daure tamkar hadari, hannunta ya ruko da karfi ya dora a kan kirjinsa ta ji yadda zuciyarsa take bugawa da sauri. "Kin ji yadda zuciyata ta ke bugawa, tun daga ranar da kika canja mini Sa'adah har yanzu ban huta daga wannan bugun ba, ya sake matsarta sosai ya ce "Ko aikina ne ba kya so? Idan shi ne sai na je na ajiye musu". "Ni ban ce ba, idan ba ka yi aiki ba 'kasa za ka ci?" "Me yasa kika cire kanki, da gaske za ki iya rabuwa da ni?" "E mana indai zan tsira da mutunci na." Kansa ya kulle ainun ya kasa gane me take nufi. "Ban gane idan za ki tsira da mutunci ba?" Ta zumbura baki ta ce "Kai ba Bahaushe ba ne?" Ransa ya fara 'baci, ya kalle ta cike da bacin rai ya ce "Kar ki fara Sa'adatu, kar ki fara mini rashin kunya ba zan 'dauka ba". Ya mike ya fice da ga falon ya nufi dakinsa. Zuciyarta sai rawa take yi, ita kanta jarumta take yi, ta kuma riga ta kudire sai ya janye waccan kalmar da ya jefe ta da ita, amma ta lura ransa ya baci sosai don ta fahimci indai ya ce mata Sa'adatu to ransa ya baci da ita ne. Da kyar ta tashi ta yi wanka, ta shirya cikin guntuwar rigar barci cotton marar nauyi, ta zauna shan black tea, amma zuciyarta na tunanin ko MK ya yi barci, ko me yake yi, ko shima fishin zai dauka yau ba zai zo 'dakinta ba? Ta dade a falo kafin ta kashe fitila da fanka ta shige daki ta kwanta, adduar barci ta karanta ta shafe jikinta, tana ta tunani, sai ta ji shigowarsa, dadi ya ratsa ta har da sakin ajiyar zuciya. Yana tsaye ya kunna fitila idonsu ya hadu, nan da nan ta dauke idonta, ya kashe fitilar ya nufi gadon yana kwanciya ya janyo ta jikinsa ya saki ajiyar zuciya tare da fadin "Ni ba zan iya fushi mai yawa da ke ba, bacin ran da kika sa ni dazu na yafe miki kin ji My Sa'adah! Ke ma ki yafe mini abin da na miki, ki kuma fada mini din kar na sake maimatawa a gaba". Uffan ba ta ce ba, amma farinciki ke ratsa ta yadda yake ta rawar jiki da neman sulhu. "Kin ji" Bai jira amsarta ba ya sake cewa " Don Allah me na yi haka har zuciyarki ta gaji da zaman mu tare, ban yi zaton akwai abin da zan yi ki daina sona ba". Haka kawai ta ji zuciyarta ta karye, hawaye ya cika mata ido, cikin rawar murya ta ce "Ban daina sonka ba ai, kawai ha'kura zan yi don shi ne ya fi alheri tun ba ka juya mini baya ka fara wulakantani ba". Jikinsa ya yi sanyi kalau, a sanyaye ya ce "Mafarki kika yi akan zan juya miki baya, yanzu a zaman da muka yi ba ki fahimci irin son da nake miki ba? Kin fi karfin ki wulakanta a hannuna." Ta kasa cewa komai saboda tana bude baki kuka za ta yi. Ya sake cewa "Na ji dadi da ba daina sona kika yi ba, ina hada ki da girman Allah ki fitar da ni daga duhu, me na yi miki?" Kukan da ta ke matsewa ya subuce mata, hawaye har a kan kirjinsa, ya rasa abin da ya ke masa dadi, hankalinsa, in sun kai dubu to a tashe suke. Haka ya dinga jijjigata yana shafa gadon bayanta tare da fadin sorry, tamkar mai mata bita. Da kyar ya shawo kanta ta bude baki ta ce "Tun farko na so na hakura da aurenka saboda yadda kake nuna mini am nothing to you, sai dai na san Baffa ba zai fahimce ni ba, tunda sai da ya tambaye ni na ce ina sonka, iyayenka sun zo gunsa to ba ni da sauran dama, ban isa na ce na fasa ya saurare ni ba". Ta sarara, ta ja hanci sannan ta dora da fadin, "Muna cikin wannan yanayin, sai na yi kuskuren shiga motar saurayi, kuskuren da ni kaina na yarda ban kyauta ba, ba irin ha'kurin da ban baka ba amma ka 'ki, karshe na sake yin wani kuskuren na dauki jiki na bi ka har inda kake, don ka gane yadda fushin ka ya hana ni zaman lafiya. Sai ka bi ni da wulakanci kala-kala har ka iya ce mini Ballagaza akan idona!" Kukanta ya dawo sabo, ta shiga yin sa har da rerawa tamkar a cikin nisha'di take, don kawai ta sake tayar masa da hankali, ai kuwa gogan ya kasa cewa komai tsabar yadda komai ya tsaya masa, yana tuno Baba Idi da ya ce lamarin mata yana da gigitarwa, tabbas ya yarda ga shi 'yar yarinya karama tana neman zautar da shi. Cikin kukan ta ce "Tun lokacin na tabbatar barin ka shi ya fi alheri, tunda za ka iya jifa na da wannan mummunar kalmar a ranka, sai kuma na ga gara na nuna maka ni ba ballagaza ba ce, hakan kuma ba zai yiwu ba sai mun yi aure dole, zuwa yanzu na san ka gane in ma ni Ballagazan ce ko a kasin hakan". Tsawon lokaci MK ya kasa bude baki ya yi magana. Ya yi shiru yana jin kukanta har cikin kwakwalwarsa. Da kyar ya bude baki murya ba sauti ya ce, "Ba har zuciyata nake nufi wannan kalmar ba, subul da baka na yi". Da sauri ta ce"Ai sai da na tambaye ka, ni ce ballagaza, ka ce e, idan akwai kalmomin da suka fita muni na hada da su domin na siffantu da hakan". "Billahillazi Baby kishi ne ya rufe mini ido a lokacin, amma ba har zuciyata hakan nake nufi ba, na yarda na yi laifi ki yi ha'kuri na tabbatar ke din katangaggiya ce". Zamewa ta yi a jikinsa ta koma karshen gado tana sake sabunta kukan da take yi tare da fadin, "Ni ba zan hakura ba, kai ne za ka yi ha'kuri kar ka wahalar da ni". Mirginawa ya yi ya tarar da ita a karshen gadon, ya riko ta tana tirjewa, kukan gaske take yi, har da bubbuga kafa tamkar yar karamar yarinya. Kwantar da murya ya yi sosai tare da cewa "Babyna tsaya ki ji, tsakaninki da Allah, tunda muka yi aure wacce kalar soyayya ce ba na yi miki?" Cikin kukan ta ce "Ai don ka ga zargin da kake mini ba gaskiya ba ne, bayan haka kuma kana hutawa da ni". Ya rasa ta inda zai bullo wa wannan yarinyar, ya nisa ya ce "Zaman da muka yi na wata biyu har da doriya, ban yi wani abin da kika gamsu son ki nake yi da iyakacin gaskiyata ba? Ko a lokacin da kike ganin ba na tarairayarki, ai kona mini rai kike yi, na ce ba na son ganin ki da dan iskan yaron nan, amma ba ki ji ba, haka na yi ta ha'kuri ba don ina son ki ba za mu yi auren ne?" Ya sake tausasa murya ya ci gaba da fadin, "Saboda Allah indai dama ba wani abu ne a ranki ba, mene ne na dawo da abin da ya wuce, ba haka kawai na fada miki maganar da kika kullace ni a ranki ba, ke kika janyo, ko ba ni da alaka da ke zan yi kishi yanayin da na gan ki, a matsayinki na mace mai daraja". Ya yi shiru yana jin shesshekar kukanta, tana ta ajiyar zuciya tamkar wadda ya yini yana dukanta. "Na roke ki, ki daina kukan nan haka, na yarda ban kyauta ba ki yi hakuri". Ta yi shiru, kamar yadda ya roka din har da gyara kwanciya, da lulluba alamun barci za ta yi, tana sakin ajiyar zuciya, a ranta kuma tana fadin sai kuma rikicin gobe. Ya so su kasance tare, amma saboda tsoron kar ta ci gaba da masa kuka yasa ya kyale ta, ba a jima ba ya ji saukar numfashinta alamun barci ya yi awon gaba da ita. Ya saki gauron numfashi, ya haska fuskarta, da hasken wayarsa ya ga hawaye duk ya bushe a fuskar, kuma wani abin dariya ita da kanta ta boye fuskarta a jikinsa. Tsintar kansa ya yi da gyara mata kwanciyar yadda za ta ji dadin barcin. Ya dawo Masallaci, ya tarar ta dira sabon kuka ga akwati a kan gado sai zuba kaya take yi tamkar mai shirin yin balaguron wata guda. Zama ya yi gefen gadon yana kallon ikon Allah, da Asubar fari za ta fara masifa tamkar jiya ba ta yi ba, duk irin ha'kurin da ya ba ta ashe bakam ta masa. Yana kallon yadda ta gama shirya akwatin ya kasa cewa komai saboda gaba'daya He is speechless. Wanka ya ga ta shiga yana zaune ta fito, ta shirya cikin riga da skirt na English wears, skirt (purple) iya guiwarta rigar kuma body hug (pink) an rubuta *BABY GIRL* ta kama ta ainun musamman daga kirji, ta gyara zaman ribon dinta a kitsonta na shuku, ta masa kyau ba kadan ba, har ya dinga raya don ta tayar masa da hankali ne yasa ta yin wannan shigar da Asubar nan tunda ta san yau ya kwana bai taba ta ba. Ta shafe jikinta da turararuka kala-kala tun daga na jiki har na kaya, sannan ta dora bakar doguwar riga akan kayan ta yane fuskarta da dan mayafin rigar. Ta dauko takalmi da jaka ta saka sannan ta ja akwatin ta nufi kofar barin dakin. Wata irin fizga ya mata ta dawo da baya kamar za ta fadi sai kuma ta dire kan kafafunta. Kafin ta yi magana ya riga ta da cewa "Me kike shirin yi ne haka, ina ce tun jiya magana ta wuce?" Hawaye yana zubar mata ta ce "Wallahi ba ta wuce ba don kuwa ni ba zan sake zama da kai ba". Dariya ce ta subuce masa wadda babu nisha'di ya ce "Ok tunda haka ki ka zaba shike nan, sai na ga wadda zai raba ki da ni". Ta juya za ta sake fita, wannan karon da karfin gaske ya janyo ta ya jefa ta gado tare da fadin "Wannan shi ne gangan, ba za ki fita ko ina ba, bai wani bata lokaci ba ya bita ya turmushe ya sakar mata dukkan nauyinsa. Ta kasa koda kwakkwaran motsi, sai da ya tabbatar ta yi laushi sannan ya daga ta, sai kuka take masa mai sauti bai kula ba, sarrafa ta yake yi kawai, tun tana tirjewa har abin ya shiga jikinta ta yi lakwas ta sallama. Tsawon lokaci kafin ya samu nutsuwa. Sai da ya huta sannan ya tashi ya fita bayan ya zura jallabiyarsa, a shirye ya fito hannunsa ri'ke da mukallin mashin, tana kwance inda ya barta tana kallon sa, ta tura baki gaba ta dauke kai. Murmushi ya yi ya ce "Kin ga kwana uku ke nan ina fita da yunwa amma yau a koshe zan fita, kullum haka zan dinga miki". Harara ta watsa masa tare da cewa "Idan na zauna ba". Murmushi ya yi tare da fadin "Ba inda za ki iya tafiya ki bar ni, wa zai iya da wannan fitinar ta ki ai sai ni din". Ganin magana yake nema yasa ta daina tankawa. "Zan tafi, ki tashi ki yi wanka ki karya, idan na dawo ban tarar da abinci ba, ki tabbatar ke ce abincin." Ya fita yana fadin "Sai na dawo." A fili sharewa ta yi amma a zuciyarta addu'a take masa. Yana barin tsakar gida ya janyo kofar ya rufe ta da kwado ya saka mukallin a dan jikin flowers, ya fitar da mashin dinsa, ya bar kofar gate din ba tare da ya rufe da jamlock ba. Wanka ta sake yi, tana yi tana tsaki, haka kawai an mayar da mutum kamar agwagwa wanka dai wanka dai ba kakkautawa. Ta mayar da kayan da ya cire mata bayan ta shafa mai, doguwar rigar ta ninke ta mayar durowa, sai da ta gyara gidan fes ta share ta goge ko ina. Ta kunna risho ta dora tukunya don dafa indomie, dogon Hijabi ta dauko ta saka, ta dauki kaskon turaren wuta, lekawa za ta yi ta samu yaron da zai samo mata garwashi a gidan Maman Nana, jan duniya kofa ta'ki budewa ga shi kuma ba da mukulli aka rufe ba, kan dole ta ha'kura bayan ta hango kwado ta yar karamar kofa, murmushi ta yi tana fadin "Ya dauka da gaske tafiyar zan yi". Tana karyawa ta yi wanke-wanke, ta dora abincin rana, farar macaroni ta dafa ta fito da miyar kifi daga fridge ta dumama ta bar ta akan rishon, ta juye macaronin a foodflask ta ajiye, ta tsinci kanta da son hada masa zobo, nan da nan ta dafa ta hada ta saka a fridge. Sai da ta gyara kicin din sannan ta tafi ta kwanta, ba ta jima da kwanciyar ba, barci ya yi awon gaba da ita. Bude ido ta yi ta gan shi tsaye a kanta alamun shi ya tashe ta, mi'ka ta yi ta sake juyawa don ta ci gaba da yin barcin. "Ki tashi ki yi sallah biyu fa ta wuce". Kan dole ta tashi don kuwa ba karamin jin dadin barcin ta yi ba, har ta idar yana kishingide a gefen gadon, ya kalle ta ya ce "Kin yi abincin, ko kuwa ke ce abincin?" "Don Allah ka barni na ji da abin da ya dame ni, ina dai rufe ni ka yi, ba ka tunanin faruwar gobara ko wani abu na ibtila'i, ina kulle ba?". Cike da rashin damuwa ya ce "Na fi ki tattalin lafiyar ki, na riga da na yi riga-kafin komai. Ba ki amsa mini tambayar da na yi ba?" Shiru ta yi ta kyale shi, ganin haka ya mike ya na cire rigar shaddar jikinsa, ya cire wandon, ya yi saura daga shi sai Boxer da singileti. Inda take zaune ya nufa ya mikar da ita yana fadin "Taso". Kwacewa ta yi ta fita falo a guje, tana fadin, "Wallahi ba za ka tsofar da ni ba, ga abincin can a kicin". Yana dariya ya biyo ta ya zauna a kujera ya ce "Zubo mana" "Ni na koshi". "To ni zubo mini". Ta fita tana kunkuni ai tun farko shi ne ya'ke zubo musu abinci, sai yau zai ce ita za ta zubo. Haka ta shiryo masa abincin har da zobo, dadi ya kama shi sosai, ya dinga cin abincin hannu baka hannu kwarya, tabbacin tunda ya fita bai sa komai a cikinsa ba. Yana kallon yadda ta zauna a falo ya san ta ki shiga daki ne don kar ya mata wani abu, abin da ba ta sani ba a falon ma ba abin da zai fasa. "Sa'adah! Don Allah mu shirya haka nan, wallahi na gaji da fushinki, ki yi hakuri kin ji na janye wallahi ke kamila ce, mai kirki ce". Ko kallon sa ba ta yi ba, bare ta amsa masa. "Kin ga siyar mini da fushin to". Ta zumbura baki sosai, ta sake yin shiru. "Ki shirya gobe na kai ki, ki yini a wurin Inna, idan za mu dawo sai mu tsaya a Sahad store mu sayo iron din da ki ka ce na sayo miki" Nan ma shiru ta yi. "Kin ji" "Ni wallahi albarka". "Tom shike nan satin sama makaranta za ta tura mu Jami'ar Jos Seminar, ki shirya mu je, ki gaida Anti Sumayya". Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta. Shi ma murmushin ya yi tare da tambayar "Kin sayar?" Kai ta daga tare da cewa "E amma fa har da fitar goben". "Na sani ai, tunda mun shirya, mu je ki taya ni barci, kin san jiya ban yi wani cikakken barci ba, kuma na yi fitar sassafe." Sai da ya fita ya kewayo sannan ya kwanta, ta bi shi tana masa tausa har ya yi barcin. Shike nan rikici ya kare. Ranar da suka tafi Jos ba su isa ba sai yamma likis, don haka a Hotel suka sauka, duk da Sa'adah so ta yi ta sauka a gidan Sumayya. Washegari da safe da zai fita wurin aikin da ya kawo shi ya ce ta shirya ya raka ta, da yamma zai zo su dawo, nan da nan Sa'adah ta canja fuska, tana fadin "Ni dai ka bar ni na dinga kwana a can tunda dai kwana uku kawai za mu kara yi". Kai tsaye ya ce "Ba zan miki karya ba, ba zan iya ba, zan dinga kai ki da safe, idan yamma ta yi, zuwa Maghrib zan dinga zuwa muna dawowa". "Ni gaskiya kwana nake so na yi" Ido ya zuba mata sosai, ba tare da ya ce mata uffan ba, ta sunkuyar da kai kasa, saboda yadda ta ke jin kallon na ratsata. "Yini za ki yi" Ya sake maimatawa a gajarce. Bata rai ta yi sosai amma ba ta ajiye kayanta da ta dauka ba. Ya kalle ta ya ga ta yi kicin-kicin da fuska, ga kuma kaya a hannun ta, shi ma ya daure tasa fiye da yadda ta yi. "Ni ko kwana daya ka barni na yi". Ransa a bace ya ce "Ke ki yi duka kwanakin ma, mu hadu a tasha ranar tafiya, idan kuma kwanakin ma sun miki kadan, ki yi ta zama har sai kin gaji". Ajiye kayan ta yi, sannan ta bi shi suka tafi. Kowa sai kunci yake yi da dan uwansa. Shatar taxi ya dauka suka nufi unguwar su Sumayya, ba mai cewa kowa uffan. Da murna Sumayya ta karbe su, cikin kankanin lokaci aka cika gabansu da abin karyawa, a gurguje ya ci abincin ya tafi, ciki-ciki Sa'adah ta ce "Sai ka dawo" Ba tare da ta raka shi hanya ba. "A hakan kike so ki mallaki mijin?" Sumayya ta tambayi Sa'adah. "Tunda kuka zo fuskarki a daure, sai da ya tashi, kika ware, tun yanzu za ki koya masa bagarar da lamarinki? Tun yana tsoron ganin fushinki, har ya daina?" "Da bakinsa ya ce mini zai zo Jos, na shirya zai kawo ni na gaishe ki, kuma yanzu ya ce ba a nan zan sauka ba, sai dai na dinga zuwa yini, akan mai zai hana ni kwana?" "Akan ya damu da lamarinki mana, ke yanzu ba ki ga alherin da ya miki ba, idan kuwa haka za ki dinga masa zai daina kokarin kyautata miki. Me ya kai ki yin musu, har da fushi akan abin da ya zartar?" Haka ta dinga mata nasiha cikin rarrashi, har Sa'adah ta ji ba ta kyauta ba. A ranar Sumayya ta fahimci Iyah na da ciki, amma ganin ba ta san tana da shi ba, yasa ita ma ba ta mata maganar ba, kuma lafiyar ta kalau, ba wani tsirin abinci ko laulayi, kawai dai yawan kwanciya take yi. Da kanta ta masa waya, da ta ga an yi Magariba bai zo ba, tana tambayar yaushe zai zo. "Kin fasa kwanan ne?" "Yinin da na yi, ba tare da kai ba, a daddafe na yi, sai yanzu na gane, ko kace na kwanan ma ashe ba zan iya ba." Da'di ya kama shi ya ce "Har na dawo masaukinmu amma bari na zo". Sosai suka huta, zuwan su Jos sai ya zama tamkar Honey Moon a gurinsu. Son juna ya karu a zukatansu. Wani irin so da zazzafan kishin MK, ya cika zuciyar Sa'adah, zuwa yanzu ta tabbatar ya iya soyayya, irin wadda ma ba ta yi zaton akwai irin ta ba. Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍🏼✍🏼. [6/7, 11:54] Aminan Ibrahim: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* 55-56 Kwanan su uku da dawowa, jikin Sa'adah ya rikice da wani irin zazzabi da amai. Ganin kullum ciwon gaba ya ke yi ba baya ba, yasa ya kaita asibiti, test aka ba su, tunda kan Taifod, malaria, da ciki (P.T). Sakamakon na fitowa komai Negative, illa na cikin da ya kasance positive. Maganin tsayar da amai da karin jini aka ba ta. Sai Panadol, tare da fadin sai a hankali za ta sami lafiya tunda jikinta na samun sauyin yanayi. Sosai MK ya ji dadi, sai fadin Alhamdulillah yake yi har suka dawo gida. Sannu kuwa har gajiya da amsawa take yi, motsi kadan zaicce sannu, tamkar mai nakuda. Kwana biyu ta warware ta shiga harkokinta ba wata matsalar komai, lafiyayyen ciki ta samu komai ci take yi, ko sau nawa MK zai neme ta ba ta gajiya, wani lokacin ma ita take yin dalilin da za su hadun. Mamakin yadda ta zama expert a wannan harkar take yi ba gajiya, har Allah-Allah take yi idan ya fita ya dawo, ko kuma dare ya yi. Ta san mabukaciyace ita, amma ko kusa ba kamar yanzu ba. Tunda ta sami ciki, ba ta sake hadiyar Viagra, bare ta ce ko shi ne yake sababa mata yawan son sex. Daga dukkan alama cikin ne ya zo mata da wannan salon, wadda take fatan kar ya zame mata dabi'a ta dindin, MK da'din hakan yake ji ba kadan ba, kullum a cikin fadin "Madalla da Babyn nan yake." Cike da zumudi suke goyon cikin, wani irin kyau Sa'adah ta yi, fatarta ta sake yin laushi, ta goge ta yi tas, MK baya gajiya da kallon ta musamman yadda kirjinta ya cika dam, kugunta ya bude sosai. Shi kansa MK ya murje farinsa ya karu sosai, kallon su kawai za a yi a san suna cikin kwanciyar hankali, da mutunta juna. *BAYAN WATA SHIDA* Zaune take a tsakar gida tana waya da Inna, "Inna har yau ba za ki zo kiga inda nake ba?". Daga can bangaren ta amsa da cewa " To Baffanku ne ya hana ni, wai mai zan zo na yi miki". "Cikin shagwaba ta ce "Na san da kin karfafa Inna da tuni kin zo, haka na sha jinya har na warke ba ki zo ba, da Anty Sumayya ce a garin nan take rashin lafiya da kin je kin ganta, amma ai ni ma Baffa ya zo ya ganni." Ta fada a sanyaye. Dariya ta yi tana cewa "Iyah ashe dai har yanzu da saura, na dauka kin yi hankali sosai, musamman da na ga kina zaune lafiya da mijinki kuma kin tsare kanki ba kya yawo". "To Inna yanzu na kai wata biyar ban zo gidan nan ba, tunda na ji fa'danku, ba na yawo na tsare kafata, ba sai ki dinga zagayowa kina gani na ba". "E gaskiyar ki, to ki kwantar da hankalinki, ina tafe tunda ga Baffanku ma yana jin ki da kunnensa". Da haka suka yi sallama ta kashe wayar, da kyar ta samu ta tashi saboda yadda cikin ya mata nauyi sosai tamkar ba cikin fari ba. Watansa bakwai, amma sai a yi zaton a watan nan za ta haihu, duk da cewar watansu takwas da aure. A fili ta ce "Gara ki zo ki gan ni, ki ga yadda na zama". Washegari kuwa bayan azahar sai ga Inna da yar rakiyarta Zainab Ma'aji. Mamaki ya yi matu'kar kama Inna ko kadan ba ta san cikin har ya tsufa haka ba, ta san dai tana zargin ko da cikin tunda rabon da ta sa Iyah a idonta an kai wata biyar koma ya zarce hakan. Ta zauna tana mamakin yadda ta aune ta zama babbar mace komai nata ya bude, da kyar take zama da tashi. Kallon Zainab Inna ta yi ta ce 'Ashe kin kusa zama uwa amma ba labari?" Dariya sosai Zainab ta yi tare da fadin "Inna Ina zan iya hirar haihuwarmu ta fari". Yayin da Sa'adah ta sunkuyar da kai kasa alamun kunya. Zainab ce ta shiga kicin ta hado ruwa da lemo ta kawowa Inna, ta sake komawa ta dauko tiren da ta gani an shirya kayan abinci a kai. Hira suka yi, cikin walwala har Inna ta fahimci sauyin da Iyah ta yi, ta fara yin hankali. Sai da suka zo tafiya, ta fashe da kuka, kamar wata sokuwa. Cike da tarin kauna Inna ta sata a jikinta, tana fadin "Kukan na menene kuma Iyah? so kike ki tayar mini da hankali bayan cike nake da murnar ganin ki cikin nutsuwa da walwala, ko wani abin na damun ki ne?" Cikin kukan ta ce "Ni so nake ki dinga zuwa". Cikin rarrashi ta ce "Wani satin zan dawo, ai yanzu kam dole Baffanku ya bari na dinga zuwa akai akai". Da haka ta lallaba ta suka rabu lafiya, ta raka su har gate bayan Inna ta shiga dakunan ta gani tare da sanya albarka. Suna tafe Inna ta ce da Zainab "Ina murna Iyah ta yi hankali ashe dai da saura, indai ba so take na zama uwar zamani ba, ina ni ina zarya a gidanta?" Dariya sosai Zainab ta dinga yi tana fadin "Mene ne a ciki Inna? Kin san Baffa ne ya hana mijinta barin ta zuwa gida, ke ba sai ki dinga zuwa ba". "Ba ku da hankali" Har gida Zainab ta raka Inna sannan ta tafi gidansu. Allah- Allah Inna take yi Baffa ya dawo ta ba shi labarin Iyarsa ta kusa zama uwa. Tunda su Inna suka tafi, ta debo kayansu da ya wanke jiya, ta zauna ta fara guga. Ta kammala nasa tsab ta-ci karfin nata, ya dawo. Ta fara kokarin tashi ta karbe shi, ya tsaya daga inda yake ya bude murya ya ce "Yi zamanki ki ji da kanki". Ta koma ta zauna tare da cewa "Sannu da dawowa" Bai amsa ba ya shiga kicin ya ajie ledar hannunsa, ya zubo abinci a plate, tare da cokula biyu. Gefe kuma ya wanko guiba ya zubo a bowl. Yana zama tun kafin ya yi magana ta sa hannu ta dauki gwaibar ta fara ci. Ya kalleta ya ce "Sau nawa zan ce miki ki daina gugar nan idan na sami dama zan yi?" "To ina zaune haka ai bai fi motsa jiki ba, ni fa har wankin ma zan iya mana, kawai dai na bari ne saboda ka ce ba ka so. Ya zuba musu abincin, yana fadin mun yi Ba'ki ne yau, ko kuma wani abin za mu yi da daddare?" Tana murmushi ta ce "Yau babbar bakuwa muka yi baka nan" Ya zuba mata ido cike da neman karin bayani. "Inna yau dai Allah ya nufa ta zo" Da sauri ya ce shine baki fada mini za ta zo ba?" "Ni ma fa ban sani ba kawai ganin su na yi ita da Zainab". "Ba ni labarin yadda ta kaya, kin saka hijabi kin boye cikin?" Tana dariya ta ce "Ban saka ba, amma dai na ji kunya ba kadan ba, ita fa ba ta san ya girma haka ba". Shi ma cikin dariyar ya ce "To me kika ba su da za su tafi?" "Ban basu komai ba". Ya rage fara'a ya ce "Kai Iyah don rowa?" "To ai na ga farkon zuwa na na kai mata atamfa da sabulai, zuwan da na yi na karshe ma ka ba da kayayyaki na kai mata, yanzu ni kuma ba kudi ne da ni ba". "Kudin da yake cikin durowa a dakina fa?" Ya tambayeta yana kallon ta. "Uncle ai ban fada maka zan taba ba, sannan kuma cewa ka yi na sayayyar kayan Baby ne". "Daga yau ban miki iyaka da komai nawa ba, akan su Hajiya da Inna, komai kika ba su ba zance don me ba?". "Tom shike nan na gode zan gyara". "Ina ta cin abinci baki sa hannu ba?". "Ci abinka ni kunu zan sha, dazu Zainab ta taya ni muka yi". "Kwana biyun nan ban san me yasa ba na son shinkafa ba". Sai da ya kammala cin abincin ya tashi ya zubo mata kunun a katon mug, sannan ya jona gugar ya ci gaba da yi. Suna zaune aka fara kiran Magariba, daidai lokacin kuma ya kammala musu gugar gabadaya. Ya yi alwallah ya nufi Masallaci, ita ma ta tashi da kyar ta yi alwalar. Kafin ya dawo ta shirya kayan su cikin durowa, ta tattare falon, ta kunna turaren tsinke na Touch Me. Haka kwanaki suke ta shudewa har watan haihuwa ya kama, komai na Sa'adah ya sake canjawa, fuskarta, ta yi wani iri, hanci ya bude sosai, baki ya zama kato tamkar ba Sa'adah yar kwalisa ba.🤣 Ita da kanta ba ta son ganin fuskarta a madubi, MK idan ya kalle ta dariya take bashi, amma ba ya iya dariyar a gabanta, tun kwanaki da ya kalle ta ya fashe da dariya, ita kuma ta saka masa kuka mai tayar da hankali, da kyar ya shawo kanta, shike nan bai kara ba, sai idan ya fita ko ya shiga dakinsa ya yi mai isarsa. Ranar Alhamis da yamma ya isa gidansu, bayan sun gaisa da Hajiya Babba, ya tambaye ta yadda za a yi akan sayayyar kayan haihuwa. Ta kalle shi da kulawa ta ce "Haihuwar ta matso ne?" Ya ki tankawa. Ta yi murmushi ta ce yanzu fa an daina wannan ala'adar, a yi sayayya amma wai sai ranar suna da a ba da kaya, kawai ku je ku sayo kayanku, ku ajiye Allah ya raba su lafiya". A zuciyarsa kawai ya amsa, ya mata sallama ya yi dakin uwarsa!ya mata bayanin yadda suka yi da Hajiya Babba. Ta ce "Shike nan a yi yadda ta ce din, ko ka hada su da Samira ta raka ta, tunda ku ba ku san mai aka fi bukata ba". A gidan ya ci abinci kasancewar daga makaranta ya zarto, sannan ya musu sallama ya tafi. Haka kuwa aka yi tare da Samira suka je kasuwar kayan jarirai ta asibitin Nassarawa suka zabo kayayyaki daidai misali, wadda za a fi bu'katar su. Ganin kayayyakin nan ya karawa Sa'adah kaguwar ta haihu, da MK ya dawo ya ga yawan kayan da kyaunsu, shi ma ya ji dadi tare da yabawa Samira. Dadi ya kama shi ganin da ya yi Sa'adah tana ta murnar kayan. Ya ce mai ya rage ba a saya ba?" "Uncle komai an siya kawai rigunan ne unisex, sai anyi haihuwar za a sayi na mace ko na namiji, sai durowar Baby kawai". "Tom shike nan su ma zan saya muku, ke ina naki kayan?" Ta fara daddaga kayan gun tana neman ledar da kayan suke ciki, shi ne ya hangota ta fada tsakanin kujeru, da kyar ya janyo ta. Ya bude yana ganin inner wears ne, sai pads, saboda ya tura Lagos Anty Hafsatu ta siyo mata lace da shadda. Ya daga bireziyar da ta masa kyau sosai, har zai mayar, sai ya yi niyyar tsokanar ta, ya ce "Anya wannan za ta miki kuwa?" "Za ta mini mana ba ka ga an kara size din akan wadda na saba sawa ba?" "To abin ne na ga kamar ba za ta rufe su ba". "Kuma haka zan ta zama, ai Inna ta ce zan huce". Ya guntse dariyarsa ya fita yana fadin, yanzu zafi ne da ke?" Sai da ya dawo ya zauna ya ce, "Ki fito da kayan da zan kai miki dinkin". Shiru ta yi masa tana ala'adarta ta zumbura baki. Ya maze ya ce, "Da ke fa nake magana kin san na sha fada miki ba na son na miki magana ki yi kamar ba ki ji ba. Ga mamakinsa sai ya ga hawaye na zuba a idonta, kafin ya tambayi ba'asi ya ji tana cewa, "Da alama idan na yi kiba daina sona za ka yi, kullum sai ka mini dariya, ina kallon ka kawai sharewa nake yi, don ma kai ka mayar da ni hakan din". Ta kare tana kifa kai a hannun kujerar da ta ke zaune, tana masa kukan iyashege. Maimakon ya ji ya damu sai kawai dariyar ta zo masa sosai, ya dinga kyakyatawa. Lamarin da ya harzuka ta, ta tashi ta koma daki tana kuka sosai. Sai ya yi shiru da ya hasaso yadda hanci da bakinta suka zama sai ya sake fashewa da dariyar, ya jima kafin ya samu dariyar ta tsaya masa. Ya shiga mayar da kayan cikin ledoji ya kai su dayan dakin da ba kasafai suke amfani da shi ba, ya bude wardrobe ya zuba su ya rufe. Dakin ya bi ta, ya samu tana ta goge fuskarta da tissue, kusa da ita ya zauna ya rungumo ta ta gefe, so take ta fizge amma ta kasa, ya fara magana a hankali. "Me ya sa kike da saurin kuka ne Iyah? So kike Babyn mu ya zama mai kukan banza? Me yasa ba ki san wasa ba, ko buhu kika zama wallahi ba abin da zai ragu a son da nake miki, ba sha'awar ki nake yi ba, ba jikin ki nake so ba, ke nake so. Tsufa ko tawayar halittar ki ba za su canja soyayyar da nake miki ba, ki ri'ke wannan". Sai ta lafe sosai a jikinsa tana sha'kar kamshinsa, ta sa hannu ta balle links din dake gaban rigar ta zura hannu tana shafo kirjinsa. Cikin lokaci kalilan suka birkice, Sa'adah, ba karamin kidima MK take ba, nauyin cikinta baya tasiri a wannan fagen. Sosai kalamansa suka sata farinciki, shi yasa ita ma take mayar masa da tarin soyayyar da take masa a aikace ba ka jin komai sai numfarfashin MK. Soasai suka sha shagalinsu, katon cikin su ba ya hana su komai, sai dai Mk ya san yadda yake yi ba tare da ya takura ta ba. Yana tsaye gaban madubi, yana daura Agogon hannunsa, ita ma ta fito daga wanka daure da tawul, a bakin gado ta zauna tana ta numfarfashi, shi ya taimaka mata da shafa mai, pant da siket kawai tasa ta zura doguwar riga marar nauyi. Ya dauke tawul din ya shanya a kofar bandakin. Ya dauke bireziyar da ba ta saka ba ya mayar inda take ajiye su. Dake ya saba da tsokanarta ya kalle ta yace, "Iyah na lura idan kina koke-kokenki inviting dina kike yi ashe, daga yau na fahimta. I will be noted". Hararar sa ta yi tare da cewa "Ka daina ce min Iyah, ba na so". "Ni kuma ina so". Duk wani abin da za a bukata lokacin haihuwa MK ya tanadar mata, hatta dinkunan da za ta saka ya karbo, ba abin da suke jira illa zuwam ranar haihuwa. Ranar Talata da ta yi daidai da hudu ga watan Mayu 4/5, tun Asuba take faman murkususu, tun tana daurewa har ta gaza, a sukwane ya samo Adaidaita Sahu suka nufi asibitin Murtala, waya ya yi wa Hajiya Babba, ita ma a gaggauce ta bi su, sai da ta isa, sannan ya koma gida don dauko akwatin da suka shirya kayan zuwa asibiti, da kuma tabarma. Karfe 1:45pm na rana Sa'adah ta haifo sankacecen yaro namiji mai cike da koshin lafiya, kukan da yake canyarawa ne ya tabbatar ma Hajiya Babba, Sa'adah ta sauka. Ana zuwa albishir da karban kayan jariri, MK na isowa, ya tarar da labari mai dadi. A Daren ranar aka sallame su, bayan an tabbatar da lafiyar uwa da jaririnta. ```Alkalamin Surayya Dee``` ✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 57-58 Kafin wayewar garin labarin haihuwa ya isa kunnen Yan uwa da abokan arziki. Umman fanshekara da ta kasance kanwa ga Baffa, Ya'yan Baffani su ke(cousins)! za ta zauna da Sa'adah kasanitacecewar mijin ta ya kwana biyu da rasuwa, kuma ba ita kadai bace tana da abokiyar zama. Sosai Mk yake hidima da mai jego, komai akace ana bu'kata da rawar jiki zai kawo, har wadda ma ba a nema ba. Umma sai yaba kirkin Mk da iyayensa ta ke yi, kullum suka zauna da Sa'adah sai tace "kin yi Sa'a Iyah, kin hadu da miji da ya gaji arziki d mutunci a wurin iyayensa, shi kam bai shure kyawawan dabi'un gidansu ba". Murmushi kawai Sa'adah ta ke yi tana gasgata maganar Umma. Ranar suna yaro ya ci sunan mahaifin Mukhtar, wato Muhd Kabir tun a ranar kuma Samira ta lankaya masa Jawad. A zuciyar Sa'adah ba Jawad ta so ba, amma saboda kara ga kanwar Mk sai bata canja ba. Sosai aka yi shagalin sunan Jawad abinci mai kyau aka yi a gidan su Mk, aka ciko manyan kuloli aka zo da su, jollof din shinkafa, bandashen Gurasa, da Alale. ga kuma dangin kayan sha irin su zobo, ginger, da kunun Aya masu dadi da sanyi. mai daukan hoto da video duk motsin Sa'adah sai dai ta ga hasken camera, tun safe kafin a cika suka sha hotuna da Mk cikin kwalliya ta burgewa. Da azahar sai ga Halima da Safina sun zo kwatsam,sama sama suka gaisa da Zainab Ma'aji ta gabatar musu da abinci da kuma abin sha, yayin da Sa'adah keta rawar jiki akan su, suna ta yatsina, hatta abincin ma ko hannu ba su saka ba bare su ci. Cike da murmushi Sa'adah tace "idon ku kenan, sai yau kuka tuna da Ni, ashe ma kunsan inda na ke! nema na ne baku yi ba?". Halima da tafi Safina ginshira ta ce " Akan mai zamu neme ki, inace kin dauke mu kin watsar a shara, shiyasa muma muka manta da ke, kin ri'ke miji kin manta da kowa! zuwan ma yanzu da muka yi ba naki bane, na 'Dan mu ne ko kin fada mana kin haihu?" Dariya sosai Sa'adah ta yi, tana fadin "shikenan yana godiya" tare da cire nono a bakin sa, a kafada ta saba shi, sai da ya yi gyatsa sannan ta nade shi a shawul da ke canja masa riga aka yi, ta mi'ka ma Safina da tafi makwaftaka da ita. Ido ta zuba tana yaba kyaun jaririn, ta ke ta ji sha'awar ta samu nata, ta jima tana ri'ke da shi, har sai da Halima tace " Ba za ki bani na ganshi bane?" Sannan ta mi'ka mata tana fadin "Babyn ne so mashallah". Halima na zuba ido akansa taga kamannin Uncle Mukhtar sak a fuskar yaron. A fili ta furta "Allah dai yasa kar ka kwaso mana halinsa". Da sauri Sa'adah tace "Uncle din kike cewa kar ayi halinsa? ai kuwa zan fada masa". Ta no'ke kafada, alamun ko ya ji Ina ruwanta. Har kusan maghrib sannan suka tafi, suka ajiye mata leda mai dauke da rigunan yaro masu tsada guda uku da Pampers mai 48, ta musu godiya. Zainab tana daga falo tace ku gaida gida! da kyar ta basu ledar da ta ke rabawa mai dauke da sunan jaririn!cikin kuma memo ne mai hoton Jawad. Kwana uku da suna dan kishiyar Umma ya rasu, daga ciwon ciki kawai sai mutuwa, dole ta tafi, ta taya yar uwarta zama da juyayi! mutuwar matashi akwai gigitarwa. Kwanaki biyu a jere Inna ke zuwa da safe ta mata wanka da sauran hidima, sai ta mata wankan yamma sannan ta tafi. Ganin zirga zirgar zata mata yawa kullum, yasa ta roki Baffa ya bari Sa'adah ta zo gida ko sati biyu ne, ta kula ta ita, ita kadai tasan me ta gani, da dukkan alama daki daya suke kwana da mijin ta, tunda Umma ta bar gidan. Bai tsananta ba, ya amince amma da sharadin idan mijinta bai amince ba, baza'a matsa masa ba. Tace "Ni ai da iyayensa zan yi magana, idan ka bani dama a daren nan zanje gunsu". Bai hana ba, itakuma bata yi sanya ba, tana idar da magariba ta tafi gidansu Mk, a falo duk ta same su har Hajiyan Bichi, bata bata lokaci gurin fayyace bu'katar ta ba. Dukkansu sun yi shiru!sai Hajiya Babba ce ta yi kundunbalar cewa "tunda har kika zo ba za'a hanaki ba, sai dai ki yi hakuri da kaina zan kawo miki ita, idan aka shirya". Godiya sosai Inna ta yi ,har kofar gida suka rakota suna ta yiwa juna godiya. Har ta isa gida tana mamaki! ko kishiyoyi nawa ne suka dace da kyakkawan zama irin na iyayen Mk? ko Ana samun adalar uwargida irin Hajiya Babba, mai hade kan ahalin gida babu banbanci, ko kai sukar wani ga wani, da sauran gutsiritsoma irin na tsofaffin mata masu kitsa munafunci da sunan kishi? Ko Ana samun amare masu kawaici da biyayya da sanin mutunci da alherin uwayen gida irin Hajiyan Bichi? sha'awar zamansu ya kamata tana jin inama, itama tana da abokiyar zama, ba yabon kai ba, da zata yi koyi da Hajiya Babba. Da murna ta bawa Baffa labarin yadda suka yi, shi da kansa sai ya zaku Iyah ta dawo kusa da shi duk da dai bai furta ba. Suna komawa gida, Hajiya Babba ta Kira Mk a waya, ta sanar da shi bu'katar mahaifiyar Sa'adah! ya yi shiru ya rasa mai zaice, jin shirunsa ya tabbatar mata da bai ji dadin maganarta ba, bashi kuma da niyyan amincewa. Dan haka sai ta kwantar da murya cikin hikima tace " Da na yi karambanin amincewa, har naci alwashin da kaina zan kai musu ita, amma ba zai zama komai ba, idan banyi daidai ba, sai na koma na lashe amai na". Cikin takaici iri iri yace "Ni bance ba, tunda kin amsa shikenan! amma dai sati daya za ta yi". "Akan mai zaka 'kayyadewa iyayen ta kwanakin da zata yi a gaban su, ba ka ga mutunci irin nasu ba? neman alfarma suka zo yi gaban iyayenka, saboda girmama hakkin aure. ba dan basa sonta, ko dan sun gaji da ita suka dauketa suka baka ba, yau kusan shekara guda. me zai sa ka shata musu layi dan su nemi su kula da lafiyar yarsu?" Ya yi shiru yana jin maganar na shigarsa sosai, ya nisa yace "Shikenan Hajiya duk yadda kika yi dai-dai ne" Dadi ya kamata! ta shiga jero masa addu'ar albarkar ubangiji a dukkan kasafin sa. "Tunda ka yarda da hukuncin da nayi, duk da ba ka so! Ni kuma zan fada musu sati uku za ta yi maimakon wata guda". Takaici ya sha'ke masa wuya, wai har sati uku, shi ya dauka anyi wuta ta yi sati biyu, to da fiye da wata ake nufi zata yi ko me? Sa'adah na zaune a daki tana shayar da Jawad, shi yana falo yana musu guga, ya tattara kayan ya kulle ya kashe iron din saboda yadda jikinsa ya mutu da 'bacin rai. ' Jiki a mace ya shiga 'dakin bai kalleta ba, ya wuce ya hau gado yana jin zazzabi na namen kama shi. A gigice ta dinga tambayar sa lafiya kuwa, me ya same shi? Jinsa shiru yasa ta shimfi'de Jawad! ta isa kusa da shi tana ta'ba jikinsa ta ji ko zazzabi ne yake san'darsa. Ras ta ji jikinsa, sai rashin kuzari, ta shiga tambayar sa, ya kasa bu'de baki ya mata bayani, amma ganin zata masa kuka, ya fisgota jikinsa ya kankameta, yana sakin ajiyar zuciya. Tsawon lokaci suna haka, cikin rashin kuzari yace "Tun yanzu na fara kewar ku" Gabanta ya fadi ta kalleshi ido a bude "Tafiya zaka yi ka barmu?" Sai kawai ta fara hawaye, ya kalleta yana jin sonta na sake daskarewa a zuciyarsa, shagwabarta, rauninta, soyayyarta na sake gigita shi. Ya sake kankameta sosai yace " Kune dai za ku tafi ku barni, yanzun nan wayar da kika ji inayi!Hajiya Babba ce, wai na shirya miki tafiya gida, ki yi wankan acan". Da'di ya cika 'kalbinta! ta ji tamkar ta tashi ta taka rawa, sai kuma ta ga yadda ya shiga damuwa akan tafiyar ta, idan har ta nuna murna! Tamkar ta baro bacin rai a tsakaninsu, dan haka sai ta hadiye dukkan murnar ta! Ta tattaro dukkan damuwa ta yaba akan fuskarta da jikinta. Cikin shagwabe fuska har da sake matso hawaye ta hau fadin " Ni dai ba zan je ba, ai kaima kana kula da mu sosai". Idan yace bai ji dadin kalamin ta ba yayi karya, ya shiga kissing dinta ba kakkautawa, ganin zai wuce iyaka, yasa ta katse shi, ta lura ya manta da halin da ta ke ciki na rashin tsarki. Idonsa sunyi ja, sun kankance saboda fitina, ya zuba mata su,ya ce "Hajiya Babba da Innah ne suka zartar da hukuncin nan, hakuri zamu yi, mu yi yadda suke so". Wani irin farin ciki ya sake kamata, amma a iya zuciyarta ya tsaya, tana jin zumudin sake zama da mahaifanta na taso mata. Haka suka kwana yana jaddada mata irin kewarta da zai yi, tamkar wadda kasar za ta bari. Kwanaki biyu a tsakani ta koma gida tare da dukkan abin da za'a bukata, Hajiya Babba ce kuma ta kaita kamar yadda ta yi al'kawari. Sosai Inna ta ke kula da Sa'adah, wankan rumfu take mata ba tausayi, ga duren kunu, da tuwo, duk ranar da zata mata gardama kuwa cewa take yi " Na lura dakinki kike son komawa, zan 'kira Hajiya ta zo ta mayar da ke, tunda ina tattalinki, kina 'ki! idan kika kufu'de na ga yadda za kiyi rawar jiki akan mijin, ko shi ya yi rawar kai akan ki". Shiru ta ke yi, kan dole kuma sai ta yi yadda Innar take so. Jawad ya sami kyakkawan kulawa, kullum safe aka masa wanka ya sha nono, Inna take goya shi, haka zai yini a baya sai anyi azahar yake tashi, cikin 'kan'kanin lokaci ya bundume, kammaninsa da Mk suka bayyana 'karara. A yini Mk na kiran Sa'adah kamar sau uku koma fiye, koyaushe cikin tambayar lafiyar su, ko yace Babana na kukan dare har yanzu, ko ya tambayi me take so, menene bata da shi, kar fa tace zata dinga 'dorawa Baffa nauyi. Ire iren tambayar kenan a kullum, itakuma cewa take, komai akwai Uncle. Duka-duka ma yaushe muka zo ne? Ranar da suka yi kwana biyar, ya je musu. Ana idar da sallar la'asar ya Isa gidan, a zaure ya tsaya, yana faman kiran wayarta, tana ta ringing amma ba'a dauka ba, ya jingina da bango, yana ri'ke da wayar. Baffah da yake faman jijjiga Jawad, saboda wankan da Inna ta ke yiwa Sa'adah, kullum ana idar da Sallar la'asar yake dawowa gidan dan ya ri'ke musu shi, su yi wankan, saboda riko da al'adar ba a barin jariri shi ka'dai.😁 Yau sai koke koke yake yi a dalilin cikinsa ya kumburaba a ankara ba, yana sa'be da shi a kafada ya doshi zauren, kwatsam yaga Mukhtar a tsaye. Cike da girmamawa ya tsugunna ya gaida shi, Baffa sai fadin "ya ka tsaya anan? da ga yau ka dinga shiga kanka tsaye". Baffah da kansa ya masa jagora har 'dakin Sa'adah yana cewa "wanka suke yi, zauna ka saurare su kadan". Ya mika masa Jawad tare da fadin "dama so na ke na fita ana jirana za mu je dubiya asibitin Malam". Cike da kunya ya karbe shi, yana masa godiya. Baffah na shirin fita Inna ta fito duk ta hada zufa, ta kalle shi, ta ce "kwantar da abokin naka ka yi?" "A a Babansa ne ya zo, yana gunsa, na shigo da shi, yana dakin Iyah ni fita zanyi, za mu je asibiti mu sake dubo Malam lado". "Adawo lafiya, shikuma Allah ya bashi lafiya". Ya fita, yana fadin "Ameen ameen". Sai da ta sako hijabi sannan ta shiga suka gaisa da Mk, da yake ta fama da Jawad. Ta karbe shi tana fa'din "Bari a masa wanka kar sanyin yamma ya sauka, ko idan ya ji ruwan dumi zai daina wannan koke koken". Murmushi kawai ya yi, kansa a kasa, ya bata shi, a zuciyar sa tana jinjina kunyarsa, ko Idris din Sumayya bai kai shi kunya ba. Yana zaune yana jin kukan wanka da Jawad ya ke tsalawa, jikinsa sai tsuma yake yi, yana jin tamkar ya leko yaronsa ko sabulu ne ya shigar masa ido, amma kawaici ya danne shi. Ana cikin haka Sa'adah ta shigo da daurin kirji, ta yi mayafi da faffadan tawul. Mamakin ganinsa a zaune ya daskarar da ita a tsaye. Da azama tace " Uncle yaushe ka zo?" "Tun dazu, dan Allah hanzarta ki dubo yaron nan , ki ji har shidewa ya ke yi?" Ri'ke baki ta yi tare da cewa"oh oh wato Innah tace mini bani da kunya ko?" "Haka yake da kukan wanka, da angama kuma ya yi ta barci, sai dare zai ishi Inna da kuka". "Oh barinta ki ke da shi?" Eh to, shi sai yace ba zai kwanta ba, sai dai a baya! itace kuma mai jure goyon, tace na kwanta na yi barci na huta". "Amma kuwa dai ba ki da tausayi ko da ya ke, Auta ce ai". Dariya suka yi a tare, ts shirya cikin doguwar rigar atamfa, irin dinkin masu shayarwa. Ta zauna tana shafa mai tare da turare, ta yi cas, ta masa kyau, da gaske ta huce din, duk wani kumburi ya sace, fuskar nan da ta aune, duk ta sabe, ta dawo masa Sa'adatun nan mai burge masu kallon ta. Yace "kin huce din fa Iyah, kin zama so mashallah". Ta tura baki gaba, tace "ai so na yi na zauna kar na huce din, naga yadda zaka yi". "Hmm ke dadina da ke misunderstanding dina kike yi sometimes". "Iyah Iyah" Ta mike da sauri tana amsawa ta fice gurin Innah da take 'Kiran. " Zo ki dauke shi ki bashi ya sha, ashe cikinsa ne ya kumbura shiyasa kukan yau yafi na kullum, yanzu Ina bashi wannan maganin ya hau gyatsa, sai kuma ga tutu, dole sai canja masa Pampers din na yi" Ta karbe shi tana fadin"Ayyah, sannu da kokari Innah". Ta dawo dakin ta zauna ta fara shayar da shi, Mk da ya zuba musu ido yana jin duk wani bugun da zuciyar sa ke yi da kaunar su ta ke bugawa. Sai da ya 'koshi, sannan ta mi'ka masa, ya karba yana mai masa kallon kurillah, yana ganin hoton fuskar sa, akan ta yaron. Ya dago ya kalleta, ya yi kasa da murya sosai, sannan ya furta "Duk yadda kika yi ta makale min, ashe ba wani abin da kike tabukawa? dubi! ba wani abu, na ki a jikinsa". Kunya ta kamata, ta kasa cewa komai sai ta buge da murmushi. Haka suka sha hirarsu, ta na shan yoghurt din L&Z da ya taho mata da shi. Kwana ashirin da haihuwar, Sumayya ta zo ganin Baby, tare da kayan uwa da jariri kala kala,sun zo juma'ah suka juya lahadi saboda makarantar Yara. Ranar da ta cika sati uku ta koma dakinta, rawar jiki ba irin wadda Mk bai mata ba. Sun tabbatar sunyi missing juna, irin wadda ba su taba yi ba! haka suka cigaba da rainon dansu cikin tattali, da kulawa mai yawa. Surayya Dahiru ✍🏼✍🏼✍🏼 19/03. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 59-60 Irin kulawar da MK yake yi wa Sa'adah da danta, yasa take mamakin da ake cewa da zarar mace ta haihu sai namiji ya canja mata, ita kam ba ta ci karo da wannan matsalar ba, ta dinga tunanin ko don ta sami kyakkawan gyara ne a wurin Innarta da Sumayya, ko kuma dabi'ar wasu mazan ce haka? Lafiya Lau suke zaune, har yanzu a cikin marararinta yake tamkar amarya, hakan ba karamin faranta ranta ya ke ba. Ya wadata su da komai daidai gwargwado, sannan da ya fahimci, ta fishi saurin fishi, sai ya ke kaffa-kaffa da abin da zai bakanta ranta, shi yasa zamansu lafiya, sai yan kananun sabani na yau da kullum da ba za a iya kauce masa ba. Kuma ba sa bari fishinsu ya wuce na yini daya. Watan Jawad uku, Sa'adah ta kasa gane kanta, yau zazzabi, gobe mura, jibi jiri, kullum da abin da za ta tashi da shi. Zazzabin hakori da rashin kuzarin Sa'adah, sai suka yi wa Jawad rubdugu, duk sun yi laushi. Ganin yadda suke yamushewa ya sa MK ya kai su asibiti, gwajin farko ya nuna ciki ne a jikinta, na tsawon sati hudu. Dankari! tun a asibitin take kuka, bakin ciki ya turnuke ta, da danyen goyo za ta sami wani cikin? kuka take yi sosai tana fadin sai dai a san yadda za'a yi, amma ita ba ta shirya sake haihuwa yanzu ba. Tun MK na rarrashin ta bari suje gida, har ya gaji ya kama bakinsa ya zuba mata ido. Suna shiga gidan ko zama ba ta bari sun yi ba, ta ce "To mun zo gidan fada mini yadda za'a yi". Ya kalle ta da tausayawa ya ce "Zauna ki nutsu, ki huta sai mu yi maganar, ba inda zani yau, ina tare da ke". Ba tavce komai ba, ta zauna tana huci, tana jin duniyar ta mata kunci. Shi kuma ya shige cikin daki ya shimfide Jawad da ya yi barci. Yana fitowa kicin ya wuce, ya zauna ya dafa musu indomie, ya juye a plate, ya kai gabanta ya ajiye, ya koma ya hado tea Sai da ya zauna sannan ya kalle ta ya ce, "Bismillah sauko mu ci." Hawaye na bin fuskarta ta girgiza kai tare da fadin "Na koshi". Ya kafe ta da ido, ya nisa ya ce "Me kika ci?" Ta kasa ba shi amsa, tunda dai ba su karya ba, suka yi sammakon fita. Ya sake kallon ta, sai goge hawaye take yi, har ransa shi ma bai so samuwar cikin nan a yanzu ba, amma tunda ya riga ya shiga, to ba zai ba ta kofar da za ta yi abin da take so ba. "Idan har na gama cin abincin nan ba ki ci ba, fita zan yi, ba zan yi maganar da zamu yi a yau ba kuma". Kan dole ta wanko hannu, ta fara ci, turawa kawai take yi, saboda gabadaya ba ta jin dadi, ga kuma bakin ciki da ya cika mata zuciya. Sai da ya hada mata tea, ta sha, ya ba ta magani, ya dauke plate da cups din ya kai kicin ya dawo! ya zauna kusa da ita sosai. Ya sassauta murya cikin lallashi ya ce, "Fada mini matsalar ki akan cikin nan, da kike ta wannan koke-koke da bacin rai". Cikin kukan ta ce "Har sai na furta matsala, sannan za ka fahimci matsalolin da suka dabaibaye ni?" "E fada mini mana wata'kila sai na fahimta a yanzu". Ta goge fuskarta da ta yi kozai-kozai, sannan ta ce "Ba ka ga Jawad har yanzu jariri ba ne? sannan wannan cikin ba irin waccan ba ne, yau kusan sati uku ban da cikakkiyar lafiya". Ta yi shiru tana jan hanci. Sai da ya ji shirun ya yi yawa sai ya ce "shike nan matsalolin?" "Ba shike nan ba, yanzu fa wannan lalacewar da Jawad ya fara yi, yana ta tsinkewa, cikin da yake sha ne, kuma bai isa yaye ba". Da azama ya ce "Duk na fahimce ki Sa'adah, har zuciyata kuma tausayinku nake ji musamman Jawad, amma tunda Ubangiji ne ya ba mu ya za mu yi? Sai mu raini abin mu cikin farinciki da godiyar Allah". Kukanta ya dan kara yawa ta ce "Yaye Jawad din za'a yi ke nan?" "Wane irin yaye kuma ba dadin ji? Ai kin ji bayanin likita, ga magunguna nan ya rubuto muku, ba abin da zai same shi". Maganganunsa suka haska mata sai ta haifi cikin nan dole, don haka ta dage ta dinga zunduma masa ihun kuka da ya yi sanadin tashin Jawad a gigice, shi ma ya cika dakin da kuka. MK ya rasa wanda zai lallaba a cikinsu, dole ya wuce daki ya dauko yaron ya fara jijjiga shi. Sai da ya yi shiru sannan ya kalli Sa'adah da take kuka irin na mutuwar Jahiliyya ya ce "Wane irin abu ne haka kike yi?" Ba ta kula shi ba ta ci gaba da yin kukanta hannuwa aka. Kan dole ya zauna kusa da ita yana cewa "Ki ga fa yadda kika sa Jawad kuka, don Allah ki yi hakuri, ke baki san baiwa ce Ubangiji ya yi mana ba?" "Ni ba na so!" Ta fada da karfi. "Shike nan na ji ba kya so, ni Ina so". Ya fada da alamun ya ji haushin maganarta. "Karbe shi, ki ba shi ya sha". Banda kuka ba abin da take yi, ko kallon sa, ba ta yi ba bare ta karbi yaron. "Kin ji". Ta kalle shi cikin ido ta ce "Na yaye shi". Ganin yadda ta rikice neman tashin hankali take yi da gaske, ya ce "To ba shi ya sha yanzu, kafin a jima na siyo masa abin da zai dinga sha". Nan ma a zafafe ta ce "Ba zan bayar ba". Kyale ta ya yi, ya ajiye shi ya hado masa shayi mai dan dumi, ya dauko sabuwar feeder ya wanke ta da ruwan zafi, ya zuba shayin a ciki, sai ya zauna sannan ya dauke shi, ya fara ba shi, cikin ikon Allah ya shanye har da gyatsa. Ya hada ruwa ya masa wanka, ya shirya shi tsaf, yana ta yi masa wasa, shi kuma yana ta dariya har barci ya sake awon gaba da shi, bai kwantar da shi a dakin Sa'adah ba, ya fita ya kai shi dakinsa don kar kukan uwarsa ya sake farkar da shi, ya rage masa karfin fanka sannan ya fita zuwa wurin Sa'adah, da har yanzu take yin kuka. A kasan da take zaune, shi ma ya zauna ya ru'ko hannun ta, ya kira sunanta, ta ki amsawa, ya sake tausasa murya ya ce "Yi hakuri tashi muje na taimaka miki ki yi wanka, ki ji dadin jikin ki. Yi hakuri kin ji my sweetheart". Da kyar ya shawo kanta ta yi wanka, bayan ta ce ba ta son taimakon nasa. Mai kawai ta shafa ta zura doguwar riga cotton marar nauyi, ta kwanta, tana ta ajiyar zuciya ba jimawa barci ya wuce da ita. Kwanaki uku ban da tashin hankali ba abin da Sa'adah take yi gaba'daya ta burkice, ban da kuka ba ta komai, ko wanka ba taki yi, bare aje ga hidimar gida, Jawad kuwa da tashin hankali take bashi nono sau biyu a rana duk kukan da zai yi kuwa. MK ganin ba irin ha'kuri da rarrashi da bai yi mata ba, yasa ya zuba mata ido, shi yake yin komai na gidan har girki, ya ki yarda ya biye mata, ya tabbatar tana cikin halin da za a tausaya mata, duk da abin nata har da rashin mutunci, amma da zarar ya tuna abubuwanta na alheri sai ya mata uziri, babban abin da ya dame shi, rashin shayar da Jawad musamman da yake ana ba shi supplement na yara mai sa su kuzari da saurin girma, akai-akai yake jin yunwa, don ma yana shan madara da fricso cream. Washegari da yamma ya dawo da ga wurin aiki tun daga waje yake jin kukan Jawad, a sukwane ya shigo cikin gidan, ya tarar da ita, tana zaune a falo tana ganin sa, amma ba ta dauke shi ba. Bai taba jin haushin ta irin na yau ba, ya jima yana tsaye ya zuba mata ido, yana kallon ta, yana jin tamkar ya rufe ta da duka. Kwafa ya yi, ya dauki yaron ya hada masa abincinsa, ya ba shi ruwa sannan ya kwantar da shi, yana ta shure-shuren 'kafa, tamkar ba shi ne mai kukan nan ba, da ma shi ba mai fitina ba ne, indai ka ji kukansa to dayan biyu ne, ko yunwa ko rashin lafiya, tunda ya yi kuka kafin su yi arbain shike nan ya daina kukan banza. Wanka ya yi, ya fito ya zauna a falo, ya dube ta ya ce "Na gaji fa da abubuwan da kike mini, na yi iya hakurin da zan iya, na ga abin naki babu mutunci ko kadan". Kai tsaye ta ce "Da ma ai so nake ka gajin, matu'kar kana son zaman lafiya, sai dai ka zabi daya cikin biyu, ko dai a yaye Jawad gaba'daya, ko a cire cikin nan". Ransa ya yi matu'kar baci ya kalle ta ya ce "Ni ban san inda ake cire ciki ba, ke da kika sani sai ki je, ai don kin ga na damu da ke shivyasa kike mini wannan iyashegen, mafi yawa idan mace ta samu ciki da wuri irin haka, daga wurin mijin take fuskantar kalubale, amma ke don samun guri ni kike yiwa wulakanci". Ya nisa sannan ya ce "Ba zan kai kararki ba, amma daga yau ba zan sake rarrashin ki akan wannan matsalar ba, idan kin ga dama ki bar cikin nan, idan kin ga hagu ki zubar a rariya, Jawad kuma In sha Allah yau an yaye shi, Ubangiji zai raya mini shi, ina ce idan mutuwa kika yi ma ba zai fasa rayuwa ba?" Daga haka bai kara cewa komai ba, ya tashi ya shiga kicin ya hada cornflakes ya shige dakinsa, bai dawo falon ba, yana kudire ba zai sake dafa abinci ba. Bai wani jima ba ya shigo, ya tashi Jawad ya canja masa riga, ya samo leda mai kyau ya zuba tarkacen da Jawad zai bu'kata, ya nade shi a shawul, ya saba shi a kafada ya fice, ba tare da ya kalli gefen da takep a zaune ba, bare ya yi mata sallama. Kawai sai ta ji kuka ya zo mata, bakin cikinta daya yadda bai dafa musu abinci ba, kuma yunwa take ji, ta kalli agogo biyar da kwata 5:15pm, kan dole ta shiga kicin din ta hada tea ta dauko biscuit din super2 ta hau ci. Gidan Samira da yake Dan'agundi ya tsaya ya ba wa yaro ya kai mata Jawad, sai da ya kira ta a waya ya tabbatar ta karbe shi, sannan ya tari Adaidaita ya wuce shagon askinsa, yana tafe yana tunani biyu, na yadda zai bullo wa Sa'adah, da na sayan motar da yake shirin yi. Tana zaune har taran dare ba MK ba Jawad, hankalinta ya tashi, ga wata muguwar yunwa na addabar ta, ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji dadi, kewar Jawad ta addabe ta. Sai goma saura ya dawo, a dakinsa ya ci burki, ya kwantar da Jawad da yake ta barci, tunda Samira ta masa wanka ya yi barci. Sai da ya gama komai tunda ga wanka, har shafa'i da wutiri, ya nufi gurin Sa'adah, tana zaune a falo ta rasa me yake damunta. Sallama ya yi bai jira amsawarta ba, ya shige daya dakin inda nan kayan Jawad suke, akwati babba ya dauko, ya hau zuba sabbin rigunansa da ba a kai ga bude su ba, sannan ya zuba na cikin drower kayansa, hatta bargonsa sai da ya saka cikin akwatin, da kyar ya zuge sannan, ya kashe fitilar, ya ja akwatin zuwa dakinsa, da ido ta bi shi, tana sake jin tashin hankali na kamata. Dakin ta shiga, ta hau dubawa, ta tarar ba kayan Jawad sai tsirarru wadda suka fara yi masa kadan, sai dryar shanya. Kuka ya kwace mata, tana raya duk bala'i, ba inda za'a kai mata yaronta. Tana fitowa shi kuma ya shigo, ya zauna a kujera ya ce "Zo ki zauna, magana za mu yi." Ba ta ki ba, ta zauna din, yana kallon yadda ta lalace tsabar fitinar da sanya a ranta. "Gobe zan yi Asubanci zuwa Lagos, jirgin karfe shida zan shiga, kafin sallar Asuba Mahmoud zai zo ya kai ni Airport, zan kai Jawad wurin Anty Hafsa." Kafin ya karasa ta fashe da kuka tamkar yarinya karama tana cewa " Billahillazi ban yarda ba, jaririn yaron za ka kai har Lagos?" Dariya ta so subuce masa, ya cije yavce, "Ba yardaki na nema ba, fada miki na yi, saboda kina da hakkin ki sani". "Idan na yarda Allah ya tsine mini, ai da ma na san yanzu ba ni da wani muhimmanci a gurinka". Ficewa ya yi ya bar ta, ba tare da ya ba ta amsa ba, yana jin farinciki, da dukkan alamu shawarar Mahmoud za ta yi tasiri. Kwanciya ya yi, bayan ya kashe fitila, addu'a ya fara yi, kawai ya ji ta shigo masa ba sallama. Tasa hannu ta kunna fitilar dakin, suka kalli juna, na tsawon sakwanni, wani abu na taso musu a zuciya. Shi ya fara dauke idanuwansa, murya ba amo ya ce, "Kin san dai ba na iya barci da haske a kaina ko? Yanzu kuma na gama fada miki Asubanci zan yi, don Allah ki bar ni na yi barci". "Ka tashi mu yi magana". "Ki adana maganar ki, idan Allah yasa na dawo lafiya, gobe irin wannan lokacin sai mu yi maganar". "Wallahi yanzu za a yi ta". Ta fada cikin rawar murya hadi da kuka. Ta zauna kusa da kafafuwansa, tana cewa " tsanar da ka mini har ta kai ka kaurace mini, sannan ka raba ni da yarona?". "Ni ban kaurace miki ba, ba kuma zan raba ki da danki ba, kin taba jin inda aka raba uwa da danta? ko'ina na kai shi, ina tabbatar miki wataran da kansa zai neme ki. Ke kika ce idan ina son zaman lafiya sai dai a yaye shi, zaman lafiyar nake so". "Wallahi ba zaman lafiya kake so ba Uncle, kawai so kake ka sake jefa ni cikin wani tashin hankalin, ai ba a nan kake kwana ba, sannan mene ne na kai wannan dan kilifin halittar har Lagos?" "Kin ga Sa'adatu ni kwana a nan dakin ba ina nufin wani abin ba ne, kullum ni nake bin ki dakinki for more than a year, ke mai yasa yau ba za ki zo nan ba, ko kin zo na kore ki?" Jikinta ya yi sanyi da jin kalmar Sa'adatu a bakinsa ta san fushi yake da ita. A hankali ta furta, "So nake ka fasa tafiyarku Lagos". "Ba zai yiwu ba, na riga da na fada mata gobe tasa a tare ni a Airport, kuma sai na koma nace na fasa zuwan?". Ta fara kuka tana fadin, "Ba na son tashin hankali Uncle, na roke ka kar ka raba ni da yarona". "Yau kusan sati ina fama da ke, ba irin ha'kuri da rarrashi da ban miki ba, amma kin runtse ido kina mini diban albarka, ko daukar yaron nan sai na miki wuta-wuta kike yi, dazu ga ki, ga shi, amma kika bar shi yana tsala kuka, zan zauna kullum a gida ne? Dole zan fita. Bayan haka kin daina yin komai a gidan nan tun daga kan shara, da girki, duk ban ce komai ba, ina yi, duk da haka ban tsira ba, duk maganar da ta zo bakin ki fada mini kike yi, har ki kalli idona ki sa mini sharadi idan ina son zaman lafiya sai na yi kaza". Jikinta ya sake yin laushi, bai ba ta damar yin magana ba ya zarce da fadin, "Kin yi strike din wanka, da yi mini magana, akan cikin da ba ni kadai na samar da shi ba, ikon Allah ne. Kin san adadin matan da suke jika filon su duk dare a dalilin rashin haihuwa? Kin san adadin matan da suke fuskantar tashin hankali akan rashin haihuwa, ALLAH kadai Ya san adadin ba'kin cikin da irin wadaccan matan da suke cikin jarrabawar rashin haihuwa suke ciki, ke Allah ya ba ki, ba tare da kin sha wahala ba, ya sake kara miki, maimakon ki zama cikin bayi masu godiya, sai kika zama cikin masu butulci". Zuciyarta ta yi sanyi, salama ta shige ta, ta fara fadin, "Astagafirillah!" A zuciya. A fili kuma sai ta tsinci kanta da cewa "Ka yi hakuri". Dadi ya lullube shi, amma bai nuna ba, ya ce "Ya wuce." A gajar ce. Ya zuba mata ido yana ganin yadda idonta suka fada ciki, bayan rashin lafiya ya tabbatar har da yunwa ke sakadar ta. Kafin ya yi magana ya ji tana cewa yunwa na ke ji. Ya basar ya ce, "Babu kayan abinci ne a gidan?" "Kwana biyun nan fa ba ni da lafiya, na san kuma idan ba na jin dadi kai ne kake dafa mana". Ya harareta kadan sannan ya furta, "To na daina yi tunda ba kya gode mini, ba kya ganin kokarina". Ta yi kasa da kai, sai kuma ta mike ta shiga toilet din dakin, ta yi wanka sosai, tana ayyana yau kwananta uku ko hudu ba wanka, ta fito ta tafi dakinta, ta shirya cikin Riga da wando iya guiwa na barci, ta feshe jikinta da turararukanta masu tsuma zuciya, sannan ta koma dakinsa. Inda ta tashi nan ta sake zama, ya dago ya kalle ta, yana jin tamkar ya rungume ta, fiye da sati bai ganta a nutse haka ba, kamshinta, sai ratsa shi yake yi. Ya dan kalle ta kadan sannan ya ce "Ba za ki kashe fitilar ba, na ce miki barci nake son yi kada na makara". Kafin ta yi magana Jawad ya farka, ya fara kukan neman abinci. Da sauri MK ya dauke shi, sannan ya fara hada masa Madararsa da take kan side drower, tun dare ya ajiye komai na bu'katar Jawad kusa da shi, jego ya same shi a kwatsam😃 A kunyace ta matsa kusa da shi sosai, ta mi'ka dukkan hannu ta ce "Kawo shi". Bai musa ba don kuwa, so yake ta ba shi nono, amma ya riga da ya kudire ba zai kuma rokon ta ta shayar da shi ba. Ya mika mata, yana ci gaba da kokarin hada masa madara, rabin hankalinsa kuma na kan Sa'adah da I'm ya ga ta kwantar da Jawad a jikinta ta na kiciniyar shayar da shi. Da'di ya kama shi, amma sai ya waske da cewa "Gaskiya da ba ki ba shi ba, tunda dai ya saba yinin yau bai sha ba, da an bar shi, tunda gobe ai ba sha zai yi ba". Tura baki ta yi, sannan ta ce "Zan ba shi mana". "Lagos din za ki bi shi, ki ba shi?" Cikin shagwabe fuska da kuma hawaye ta ce "Na ba ka hakuri fa, ka ce ka ha'kura, ba sai a fasa tafiyar ba". Ta yi shiru yana kallon ta, yana kuma kallon yadda Jawad ke ta faman shan nono ba kakkautawa. Tsintar kansa ya yi da tambayar ta mai za ki ci?" Kanta a kasa ta ce "Komai na samu zan ci, amma mai zafi" Ya kalli waya ya ga shadayan dare, ya mike ya shiga kicin ya dade a tsaye yana tunanin mai zai mata mai sauki? Ya bude fridge ya ga akwai ragowan ferfesun naman kaza duk da ba shi da wani yawa, ya fito da shi, a tunaninsa ta cinye tunda yasan ta da son kaza, sannan ta ki yin girki. Ya dumama ya juye a bowl, ya hada tea sannan ya dauko bread, duk ya shirya a kan tray, ya dauka ya kai mata dakin. Har a lokacin kuma Jawad sha yake yi. Kusa da ita MK ya zauna, ya ce "Kawo shi ki ci abincin kar ya huce, a hankali ta dago yaron da yake shirin yin barci, ta mi'ka masa, Jawad jin an raba shi da abincin sa, yasa kuka, sai dai da yake ya koshi, dan jijjiga shi kadan Babansa ya yi ya koma barcinsa, yayin da Sa'adah take ta cin abinci tamkar tana ci da wani. Sai da gama ta gane jirin da ta yini da shi na yunwa ne. "Uncle ba ka ba ni ruwa ba, ya sake zuba mata wata irin hararar kauna ya ce, "Kar ki sha ruwan, ke wannan abincin ma dana hado miki biyan ki na yi, kin shayar min da yaro na, saboda adalcina, ni ma na miki ya kamata". Dariya ta kama ta sai ta bige da cewa, "Ke nan dai Jawad ya fi ni a gunka?" Ta fada cike da shagwaba. Shiru ya mata, ga mamakinsa, sai ji ya yi ta kafa masa kuka, ya tashi ya zauna, ya kalle ta sosai ya ce "Kin koshi ba! Shi yasa za ki dora daga inda kika tsaya? To Allah ya baki sa'a". Ta kara karfin kukanta tana fadin, "Ruwa zan sha, wayyo cikina". Kan dole ya tashi ya dauki tray din gabanta, ya fice, ya dawo da ruwan ya dangwarar, yana fadin "Ki ci gaba da yi mini iyashege". Haka ta dauki ruwan ta sha, sannan ta ce, "Thank you dear!" Bai kulata ba, ya ce "Idan kin gama sai ki kashe mana fitilar". Da rarrafe ta isa gefen gadon da yake kwance, a durkushen ta kamo hannuwansa ta ri'ke, cikin rauni ta ce, "Am sorry dear, na gane ban kyauta ba, ka yi mini afuwa, ka manta duk wani inconveniences da ya faru pls". Bai ja ba , ya ce "Shike nan na yafe miki, amma ki dinga sanin abin da za ki dinga fada mini". Da azama ta ce "In sha Allah, sannan don Allah ka hakura da kai Jawad Lagos, idan Allah ya kai mu na haihu sai ka kai shi, sannan ya kara girma". "Wannan ne kuma ba zai yiwu ba, ba kula shi, kike yi ba, idan na fita kullum hankalina, ba a kwance yake ba, Allah-Allah nake na dawo na kula da shi, kin ga aikina yana bu'katar nutsuwata, don haka ki yi hakuri, idan ya isa shiga makaranta zan dauko shi, idan kuma ta nuna sha'awar ci gaba da rike shi, to zan bar mata". Ta sake ri'ke hannun sa sosai, tana fadin, "Wallahi zan kula da shi fiye da yana jariri". "Na ji zan bar shi amma bisa sharadi". Da sauri ta ce, "Ina jin ka ko mene ne zan yi" Ya kalle ta ya ga ta matsu ta ji sharadin. Ya nisa ya ce "Ba za a yaye shi ba har sai na ce". Da sauri ta ce, "Na yarda, har sai na haihu ma". "Ni ba ruwana da haihuwa, ko kin haihu idan da yiyuwar ya ci gaba da sha, za ki dinga shayar da shi, idan lokacin sa ya yi, sai a cire shi! Idan kin amince da haka shike nan, idan bai miki ba, tabbas gobe zai bar gidan nan". Kai tsaye ta ce "shike nan na amince". Ya janyo ta, ya kwantar da ita a saman kirjinsa, yana shafa bayanta, yana fadin, "Allah Ya miki albarka Ya sauke ki lafiya." Yana ta ba ta misalai masu dadi, ba akanta aka fara irin wannan ba, sannan matan so ne su ke yin kwane.🤣 Rawahul Mk. ```Alkalamin *Surayya Dahiru* ✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 61-62. Washegari da karsashi Sa'adah ta tashi, kafin karfe bakwai na safe, ta kammala soya dankalin turawa da sauce, gefe kuma ta dama kunun gyada da ake yi da danyar shinkafa. Sai da ta share falon, sannan ta kai kayan abincin bayan ta shimfida ledar cin abinci. Tana cikin share tsakar gidan ya fito yana sabe da Jawad, ya kalle ta, ya ce, "sannu da aiki." Ba tare da ta dago ba ta amsa da, "yauwa!" Yana tsaye yana kallon ta har ta gama shararta ta kwashe, ta wanke hannuwanta, sannan suka rankaya zuwa falon, shi ya zuba musu, suka karya, Jawad na kwance yana ta shure-shure da furzar da yawu tabbacin yana cikin yanayin masu yin hakori. Suna kammalawa, ya shiga wanka, ya fito a shirye cikin shudin (blue) jeans da fararar shirt, mai yarfin blue, sai tashin kamshinsa yake yi. Har cikin dakinta ya bi ta ya tarar wanka ta yi wa Jawad, tun kafin a gama shirya shi ya yi barci. Cike da farinciki ya mikar da ita tsaye, ya ja ta jikinsa, ya rungume, ya rasa kalmar da zai fada mata, kowacce kalma sai ya ga ta yi kadan ta wakilci yadda yake jin ta a rayuwarsa, a karshe dai cewa ya yi "I really love you Sa'adah. Stay blessed!" Ya sake ta ya juya ya tafi ba tare da ya sake cewa komai ba. Ta dade a tsaye, cikin sanyi jiki, kalaman ba karamin tasiri suka yi a zuciyarta ba, da kyar ta tattara kayan Jawad ta mayar da komai inda yake, ita ma ta yo nata wankan ta shirya, ta kwanta kusa da Jawad, suka sha barci, don sai kusan sha biyun rana suka farka, ta fara kokarin hada abincin rana. Haka rayuwarsu ta ci gaba da gudana, ranar da tashi da karfin jiki, za ta yi komai, ranar da kuma jikin ba dadi zai yi abin da zai iya, kullum cikin tattalin ta yake, ba ya kaunar abin da zai tunzura ta, mai ha'kuri ne, amma a wannan yanayin da gimbiyar take ciki, ya sake ninka hakurinsa akan lamarinta kwarai da gaske yake tausayin ta. Har cikin ya shiga wata shida ba wanda ya sani, saboda kwatakwata ta ki fita, duk son ta da ta fita unguwa musamman gidansu, ko gidan su MK, amma yanzu juyin duniya ya yi da ita, fur ta ki zuwa, sai dai ta gaishe su ta waya. Tun Inna ba ta damuwa da rashin zuwanta har ta fara damuwa, idan lissafin ta daidai ne tunda ta koma gidanta sau daya ta je musu, sannan aka yi wattanni shida da zuwan. Ranar nan suna waya ta ce, "Iyah wato yanzu Jawad da mijinki sun debe miki kewata ko?" Da sauri ta ce, "Haba dai Inna! Kullum fa idan ban ji muryarki ba, kin san ba na jin dadi, har yaushe na same su! da za su dauke mini hankali?" "To ai gani na yi muna gari daya, amma ki iya shafe rabin shekara ba ki zo kin gan mu, mun gan ki ba. Mijin ki duk bayan sati biyu zai zo ya gaishe mu, abin mamaki har ki iya ba shi Jawad ya kawo mana, amma ke shiru! Anya za ki yi imani kuwa?" Jin haka ya sa Sa'adah ta fashe da kuka, tana fadin, "Ban da lafiya fa Inna duk zuwan da Uncle din yake yi bai taba fada muku ba?" A gaggauce ta ce "Me yake damun ki?" Kuka kawai take yi, da kyar ta ce "Ni dai idan na mutu ki yafe mini, ba da gangan na ki zuwa ba". Sai ta katse wayar tana goge hawayen, a fili ta ce, "Na san gobe zan gan ki kin zo, kin ga abin da nake boyewa." Hakan kuwa! Inna kwana ta yi tana zullumin wane ciwo ne ya addabi Iyah haka? Karfe goma na safe ta isa gidan don ma Baffa ne ya hana ta fitowar sassafe, da tuni ta dade da zuwa. Mamakin cikin da ta gani jikin Iyah ya zarta wanda ta yi a lokacin cikin Jawad, ta rasa mai za ta ce musamman da ta ga ya yi kwari, har yana shirin fitowa duniya. Ganin irin kallon mamakin da Innar ta bi ta da shi, yasa ta kifa kai a hannun kujera ta fara sana'ar kuka. Da tausayawa Inna tace, "Ni kin san akan koke-koken nan naki, muke batawa, mene ne kuma na kukan? Mene ne yake damun ki?" Sanin bata da matsalar komai sai na cikin nan da ya mata shigar sauri yasa ta kasa cewa uffan. "Idan na fahimce ki, halin da kike ciki yasa kika mayar da kanki mujiya a cikin jama'a, ke baki san baiwa ce Uabngiji ya miki ba, ai ba kowacce mace ke samun damar samun irin wannan haihuwar ba". Ta ja numfashi ta ci gaba da cewa "jiyan nan aka mana tarihin Nana Fadima a Islamiyyar da na shiga, ashe Sayyadi Hassan da Sayyadi Husain ba tagwaye ba ne? Duk zatona 'yan biyu ne, ashe daban-daban aka haife su amma Malamai sun yi ittikafin wata goma sha daya ne tsakanin su, ashe matar da tayi irin wannan haihuwar abin alfahari ne a gurinta, abin a mata barka ne, don kuwa albarkar diyar Ma'aiki ta samu". Haka ta dinga rarrashin ta har ta sami nutsuwa. Ta kara da cewa "Har addu'a nake miki kar ki yi irin haihuwa ta, ko irin ta uwar mijinki, kin ga dai shi ma su uku ne a dakinsu, da bakin ki kika ce mini sai da ya shekara goma aka haifi Ahmad kaninsa, ni kuwa tun a kanki aka rufe mini kofa, ki kwantar da hankalinki, idan Allah ya sauke ki lafiya, idan mijinki ya yarda zan daukar miki Jawad ke ki ji da jariri ko jaririya". Sai Azahar ta tafi, har girki ta mata, sannan ta tafi ta bar Jawad na kukan zai bi ta ya gan ta da Hijabi. Ba ta da'de da tafiya ba, Sa'adah ta dinga jin kwankwasa kofa, ta san ba Mk ba ne tunda da key a hannun sa budewa kawai yake yi shi yasa ba ta sa sakata. Da Jawad a hannunta, ta fita ta bude kofar, ta yi turus ganin Halima da Safina a tsaye, cikin kwalliya ta burgewa sai kamshi suke yi. Har suka shiga cikin gidan wani irin kallo suke mata, na uku saura kwata, suka zauna, ita kuma ta fice zuwa kicin ta zuba pure water mai sanyi, akan tray, ta kawo musu tana cewa "Sannun ku, daga ina kuke haka?" Safina ce ta ce "Daga makaranta kin san sai yanzu aka fara daukar sababbin dalibai saboda dogon yajin aikin da ASUU ta yi". Sa'adah ta ri'ke baki ta ce "Oh kuce da students nake tare, wane course kuke yi?" Still Safina ce ta sake cewa dukkan mu Diploma in Public Administration muke yi, ba mu samu degree ba, saboda points din mu ba su kai ba, amma a satin nan zamu cike JAMB tunda an fara za mu sake trying". "Ma Sha llah! Congrats, na muku murna, ni ma In sha Allah zan yi JAMB din, gara da na ji da wuri, amma ni Sociology ne zabina ko kuma English Language". Sai lokacin Halima ta ajiye wayarta da take ta latsawa ta dube ta sannan ta ce "A ina za ki yi wannan karatun da kike fa'da? Kai tsaye Sa'adah ta ce " B.U.K mana". Dariya Halima ta yi irin ta iyashege sannan ta kalle ta, ta kalli cikin jikinta, ta sake mahar da kallon ta ga Jawad, ta ce, "Sai dai idan a gaban Uncle za ki yi karatun, tunda shi ma harshen Turanci ya karanta, yake kuma koyarwa". "Ban gane ba?" Sa'adah ta tambaya da alamun karin bayani. Ba kunya ba komai Halima ta kalli cikin idonta ta ce "Na ga ya mayar da ke akuya ne, ke kuma kin biye masa, don Allah dubi yadda kika zama just one year da aure". Kalmar akuyar nan ta bugi Sa'adah, ta kasa hakuri ta ce, ni ce na zama akuya?" "To mene ne banbancin ki da ita? Ki kalli kanki mana, 'da a hannu, 'da a ciki". Idon Sa'adah ya cika da kwalla tabbas da gaskiyar Halima irin haihuwar akuya za ta yi. Kafin ta yi magana, Safina ta tsoma baki ta ce "Ni fa tunda na zauna mamakin Gogel nake yi, ta saki jiki za ta mayar da kanta tamkar irin jakunan matan nan na kauye da ba su san komai ba sai dai su ci, su haihu duk shekara, duk iyashegen da namiji zai musu ba yadda za su yi saboda sun tara garke da shi, yo a wannan karnin wacce macen ce za ta yi irin wannan?" Halima ta cafe da fa'din "Ba ki ga yadda ta susuce ba? tamkar ba Gogel fine girl din nan ba, duk ta tsofe, ta sakar masa jiki, shi ya tsotseta da daddare, dansa ya yini yana tsotsarta, duk kuma abin da zata ci sai anraba musu da unborn, in and out suke lasar ta, ba dole ta fita a hayyacinta ba". "Sai ikon Allah, ke da karatu, sai ya gama tsofar da ke, kin daina burge shi, kiga ya dallo sabuwar yarinya, da ilimi ya gogar da ita, tunda kullum yana ganin yan mata sabbin 'kyan 'kyasa". Hankali Sa'a ba karamin tashi ya yi ba, saboda yadda ta gasgata maganganunsu, mussaman da tasan kullum a cikin ganin tsala tsalan yan matan Jami'a ya ke. A sanyaye tace "ya zanyi ne? ni kaina ban shirya haihuwa yanzu ba, sannan kuma shine yaki yarda! da nace sai dai a cire" Dukkansu dariya suka sa mata, sai da suka tsagaita da dariyar! sannan suka ce, mai yasa da kika yi arbain, ba ki je asibiti an dora ki akan maganin tsarin iyali ba?" Kafin ta amsa, sun zarce da fadin " kar ki sake yin ganganci irin haka, idan kuma kin ki ji, ba Kya ki gani ba". "Tuwo Inna ta yi mana zaku ci ko na dafa muku indomie?" Shiru suka yi tamkar basu ji ba, sai can kuma Safina tace "Ni kam bana cin tuwo". Halima bata dago ba, tace yi Indomie din kawai, amma plz kisa mana pepper sosai". Haka ta dafa musu indomie da ta ji albasa da attaruhu, ta hada musu lemon Tang a jug ta fasa kankara ta jefa a ciki. Sai da suka ci, suka gyatse, suka yi la'asar sannan suka tafi bayan sun jefa mata wasiwasi a zuciyar ta. Daf da maghrib ya dawo gida, a gurguje yayi wanka ya tafi masallaci, sai da ya dawo, ya dauko musu abincin, suna ci, ya lura Sa'adah ba ta da walwala sosai, ya tambayi ko bata jin dadi ne! ta ce kalau take, ta isar da sakon gaisuwar Inna, da fara'a ya ce "Ina amsawa, ta biyo sawunki kenan? Ina fatan dai kin fa'da mata, bani da alhakin rashin ganin ki a gidansu?" Kai tsaye ta ce "ko ban fada ba, ai tasan kaine, tunda ka mayar da Ni Akuya". Maganar ta shige shi, amma sai ya ce ban gane na mayar da ke akuya ba?" "Eh mana wata biyu da haihuwa ka sake dirka mini wani cikin, ai akuya ce mai hakan". Ya kalleta soasai ya tabbatar wannan maganar ba daga zuciya da kwakwalwarta ta fito ba, ya kuma tabbatar ba a bakin mahaifiyarta ta ji ba. Ya numfasa yace " Inna bata yi farincikin ganin ki da cikin ba kenan?" "Hmm ita da take ta murna wai dama har addu'a take yi mana kar na gado rashin yawan haihuwar su ita da Hajiyar Bichi". Ya sauke ajiyar zuciya, hankalinsa ya sake tashi, tabbas akwai wacce ta zo take kokarin birkita masa zaman lafiya a gidansa. A zahiri sai ya murmusa ya ce " Ashe adduar Innace ta sauka akan mu, ba wai akuya na maida ki ba". Ta tura baki gaba, tana jin ba zata sake yarda ta yi irin wannan gangancin ba a gaba. A kicin ya ga tray din da aka ci indomie mai dauke da fork guda biyu. duk yadda akayi wadannan bakin da ta yi ne, suka kitsa mata maganganu, tunda duk boren da ta masa a farko, ai tunanin ta bai bata irin wannan kalamin ba. Bai sake shan mamaki ba, sai da suka kwanta, ya ji ta ce zasu yi magana, ya ce "Ina jinki". "Uncle so nake yi nima na cike jamb foam". Ya ji zuciyar sa ta buga, sai ya danne, cikin dabara dan ya fahimci inda ta dosa. Ya ce " da kam ina da buri ki yi a wannan shekarar, kafin lokacin da komai zai kammala na samun admission kin yaye Jawad sai ki fara karatun ki, ba wata matsala". "Yanzu kuma shikenan sai ba zan yi ba?" Ta fa'da da gatsali. "Ya sake dannar zuciyarsa ya ce " za ki yi mana, amma dai sai next year". Ta tunzuro sosai ta ce "kenan sai nan da shekaru biyu kake nufi zan fara?" Ba ja in ja ya ce " eh". Jin haka ta fara sakin magaganu "Ni wallahi bazan yarda ba, kafin nan da shekaru biyu only God knows mai zaka mayar da Ni". Ya yi shiru yana ta neman tsarin Allah ya kare zuciyar sa daga sharrin shaidan da fishi. Jin ya mata shiru ba'kin cikin ta ya karu,ta fashe masa da kuka mai sauti, tana fadin son kansa ya yi yawa, duk 'kawayenta kowa na karatu sai ita kadaice mai zaman banza da kashe wando. Rukota yayi zuwa jikinsa tana fizgewa, kan dole ya kwantar da ita, yasa hannun sa ya zagayeta. Ya ce "Duk kawayen na ki fa'da mini me kamar Jawad? fa'da mini mai miji irin naki da yake tsananin son ki". Ta yi shiru tana jan hanci, sai kuma ta ce "su ai ba'a tauye su ba, ba a rufe su a gida ana shirin tsofar da su ba". Ya yi shiru, yana nazarin maganganunta, da ya tabbatar kitsa mata aka yi. Ya sake fadin yanzu zaman aure ne ya zama abin kashe wando da tauyewa a gurinki? duk yadda Allah ya miki ni'ima, kin raina?" " Kawai ni son kanka ne ya dame ni" Mai na yi miki na son kai a zamantakewar mu?" "Gasu nan kala kala, ka sani haihuwa dole, sannan ka rufe ni a gida, kai kuma kullum kana ganin yanmata, wataran sai inji zaka w amarce da mai degree". "Su Halima sun zo too nan ko?" Ya fada ba tare da yasan a fili ya fada ba. "Ba su zo ba". "Hmmmm! kawai ya fa'da ya fara lalubarta a kokarinsa na son ya kawar da bacin ran dake neman taso masa. Ai kuwa ta buge hannun sa tana cewa " Dan Allah ka bari, kullum aikin kenan, ka fitine ni da daddare, danka ya tsotse ni da rana, ga kuma wadda yake cikima bai barni ba, so haba da wanne zan ji". Ai kuwa hakurinsa ya 'kwace ya ce "Duk ma wadda suka zo suka miki famfo, ke kuma kika yarda ina tabbatar miki kidahuma suka mayar da ke, sannan maganar karatun da kike ganin sun tsere miki da shi, su a gidajen iyayen su aka basu damar su yi". Maganar ta mata ciwo ainun a harzuke ta ce "wato ni iyayena basu bani dama ba kenan?" "Eh" kawai yace ya tsuke bakin sa, ai kuwa ta kara 'karfin kukanta, tana ta yunkurin tashi amma ya danneta ya'ki bata dama. Sosai suka yi rikici, saboda ya ki amincewa da ra'ayin ta, na ta yi jamb a wannan shekarar. Sai dai kan dole ya ajiye nasa fishin, Yana fadin ta yarda da shi, bazai taba juya mata baya ba, ita kanta yake so ba wani abu na kyan surarta ko zurfin ilimi ba. indai zata biyewa maganganun wasu, ba abin da zata ci ribarsa a rayuwar ta, ko karatun take yi, wasu sai sunce ta 'ki aure da sauran maganganun marasa Da'di. Sannan ba abin da yake ruguza Jin dadin zamantakewar aure irin ka bawa wasu dama su shigo cikin matsalar gidanka. Tun a daren suka shirya, ya saukar da ita, daga famfon su Halima. Haka rayuwar ta cigaba da gungurawa da su,har Allah ya sauki Sa'adah lafiya, ta haifi kyakkawar yarinya mai kama da ita kwabo da kwabo, sai dai yarinyar da lalura ta zo, ko kuka bata yi ba. Aka ri'ke su a asibiti, ko numfashi sai da oxygen take zuka, kwanata biyu tace ga garinku nan. fadin irin tashin hankalin da Sa'adah ta shiga ma, bata lokaci ne, domin tunda ta dora ido akan yarinyar nan, sonta ya shigeta fiye da na Jawad. Ashe mai gajeran kwana ce. Kan dole ta ha'kura, ba kunya ta karbi Jawad a hannun Inna ta cigaba da shayar da shi ba tare da an ro'ke ta ba. Mk ya dinga tarairayarta da lallashi, da nuna soyayya har ta warware ta cigaba da jegonta cikin salama. Da yardarsa da amincewarsa suka je asibiti aka aunata, aka dora ta kan maganin tsarin iyali da ya dace da jininta, duk dan ta samu ta huta ta gyagije, shima ya samu hutawa da ita, da sau'kin gorin da ta ke masa na ya maida ta akuya😃. *SURAYYA DAHIRU*. ✍🏼✍🏼 25/03. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 63/64. *Shekara daya a gaba*. Zuwa lokacin shekarun su uku da aure, a shekarar Allah ya yiwa Hajiya Babba rasuwa, a dalilin ciwon siga da ya kamata, ba'a gane da wuri ba, har ya taba kodarta, kwananta uku a asibiti ta rasu! mutuwar da ta gigita dukkan yan gidan su Mk dama wadda yasan Hajiya, barin Hajiyar Bichi da akayi zaman makoki ita tana gadon asibiti. Kwarai suka shiga alhinin rashinta, sai dai ita mutuwa duk yadda zaka yi, ba zata dawo da mutumin data dauka ba, dole aka ha'kura aka bita da addu'a. Mafarin dawowar Hajiyar Bichi Kano gaba'daya kenan, kullum ta Allah sai ta yi kukan rashin Hajiya, ko na ido, ko na zuci, karshe sai ta musu addu'a tare da mijinsu, tana fatan itama ta riske su cikin aminci. Mutuwar Hajiya Babba yasa Hajiyar Bichi ta gane abubuwan da Hajiyar ta kare , mussaman na rashin tasowar fitina a tsakanin yaran, tunda ta kwanta dama, yaran gidan kansu ya fara rabuwa mussaman manyan yaransu mata na 'dakin Hajiya Babba, da suke ganin dama kamar mallake musu uwa Hajiyar Bichi ta yi, kawai Samira a cikinsu bata biye musu to kuma itace karamar su. Haka Hajiyar Bichi take ta ha'kuri da su tunda dai uwarsu ba abin da bata mata na alheri ba, duk yadda suke 'da'darewa da ita, yi take yi kamar bata gane manufar su ba, Abbas da Akil ne basa bata matsala, ko dan su maza ne? Su Halima sun sami nasarar samun admission, dan haka ba sosai suke zuwa gidan Sa'adah ba, saboda sun koma new side. Amma duk ranar da suka sami sararin zuwa gidanta sai Mk ya gane saboda yadda take daukan sabbin dabi'u. Ranar wata litinin Safina da Halima sunje students affairs na cikin Jami'ar, gun a cike da dalibai kowa na yin abin da yake gabansa. Suna daga can baya, kamar ance da Safina 'daga kai, sai ta hango Farida Torondi, da Uncle Mk na Sa'adah, da wata da bata ganeta ba. A hanzarce ta zunguri Halima da hankalinta ke kan waya ta mata nuni da abin da ta gani. "Munafiki dama ai nasan cin amanar Gogel yake yi, marar mutunci, ba dama aje gidansa ya dinga 'dacin rai da muzurai kenan, banda rashin gaskiya, menene na zargin mutane suna zuga maka matarka, ai dan yasan yana rashin gaskiya a waje ne". Kafin su kammala, har su Farida sun gama sun fice tare da Mk. Halima so take su wuce gidan Sa'adah, yayin da Safina tace ita ba zata iya zuwa ko'ina ba tare da taci abinci ba, dan haka suka zarce capteria. Anan ma suka sake yin tozali da Mk da su Farida suna cin abinci suna hirar su cikin nisha'di. Suka kewaye su, suka tafi can baya suka zauna, ta inda su Farida baza su gansu ba, yayin da sukuma idonsu na kan duk motsin su, suna daukarwa Sa'adah rahoto. Halima fadi take "wannan mutumin mugune, ya rufe yar mutane ya hanata fahimtar komai. ashe shi yana nan yana sheke ayarsa" Safina ta furzar da hucin takaici tace saboda Allah kiga ya hanata karatu, shima daf yake da ya kammala Masters dinsa, (Jami'ar ce ta dauki nauyin karatun nasa). Sannan yana tarayya da mai yin degree a fannin hada magunguna (pharmacy), above all daga rich family ta fito, oh Allah sarki! na tausayawa poor Sa'adah". "Ka'dan kenan a sharrin namiji" inji Halima da take jin tamkar taje ta rufe su da duka. Suna zaune suka ga su Mk sun mike, sun fita, a motarsa ya 'debi su, kuma Farida ce ta shiga gaban motar. Ba'kin ciki ya kamasu da gaske suka ji, suna taya kawarsu kishi, Safina tace "takaici na daya, da bamu samu damar yiwa Gogel bidiyon su ba". Halima ta amsa da cewa "wlh kuwa basirar yin hakan ba ta zo mana ba" Daga capteria, basu zame ko ina ba, sai gidan Sa'adah, suka kwashe komai suka fa'da mata, a kokarinsu na tserar da ita daga cin amanar namiji, ita kuma bata gane duk mai zuwa ya fa'da maka abin da zai ruguza farin cikin ka, ba masoyi na hakika bane, mai sonka idan yaga abin da zai tayar maka da hankali! 'Boye maka yake yi mussaman a fannin auratayya tunda dai kowa yasan namiji is entitled to 4 wives, dan angan shi da budurwa matu'kar ba ba'dala suke yi ba Ina ruwan ki? Kuka ta dinga yi, tana fa'da musu kwanaki biyun nan wulakanci ya ke tata mata, ya tsiri ya yi wanka da magariba ya she'ka kwalliya ya ce mata ya tafi shago, ba zai dawo ba sai after 11. Suka hada baki wurin cewa "karya yake miki ba wani shago, wurin Farida yake zuwa, yau munga zahiri". Safina da ta fi Halima kishi tace duk ranar da ya wuce goma na dare bai shigo ba, ki rufe gidanki, ya koma can su kwana tare, ai dan ya ganki sanyi kalau ne ya samu damar yin wani abin" "Wallahi kisan me kike ciki akan makaranta, baya son ki dinga ganin mai yake yi, shiyasa yake ta miki yawo da hankali akan karatunki, oh mai za'a yi da irin su Mk". Ita dai banda kuka ba abin da take yi, tana jin wani irin kullutu ya tokare mata wuya da zuciyar ta, ya sababa mata nauyin kirji, da kyar take zuko numfashi. Haka suka tafi suka barta da kunan rai, suna jaddada mata tasan matakin dauka akan mijinta🤔 Wawiyar kuma ta cika fam! tana jin yau ko yafi gyatumarsa kokari, ba zai yaudare ta da kalamansa na yaudara ba, ya maida ta wata nympho, da sun fara rigima sai yasan yadda ya yi suka kusanci juna shikenan sai ya kashe fa'dan, da zarar ya hau samanta bata sake tuna komai na bacin rai a tsakaninsu. Ta ci kukanta ta 'koshi bayan tafiyar su, sai ta yi dabarar fara karatun kura'ani dan ta sami sau'kin 'kullutun dake neman fasa mata zuciya da makoshi. A haka ya dawo ya tarar da ita, ta sami sau'kin bacin ran da ta ke ji. Kusa da ita ya zauna yana sauraron kira'arta mai dadi, sai da ta kai Aya. sannan ta ajiye kura'anin ta mike tace "sannu da dawowa". Ya amsa da "yauwa! Na gaji yau dinan sosai, na sha zirga zirga, ba tare da kalle shi ba, tace " wata'kila har wanka ya hau kanka". Zuciyarsa daya ya ce "gaskiya kam idan na yi zanfi wartsake wa", ya kalli agogo ya ce bari na yi sauri na watsa ruwan kafin a kira sallah". Ya mike ya yi dakinsa, ita kuma ta bishi da kallon tuhuma, da takaici mai yawa. Da ya dawo bai nemi abinci ba, ta kara gasgata su Halima, ya taba jikin Jawad da yake kwance yana fama da zazzabin hakorin fi'ka, ya kalleta yace a kwance ya yini ne?" Kai kawai ta daga masa, ya riga da ya saba da halinta na rashin bashi amsa da baki wani lokacin, dan haka bai damu ba. Wani ikon Allah yau da wuri ya dawo, kamar yasan anshirya masa ya kwana a waje, haka suka kwana bai gane kan gimbiyar ba, ya daure, shima ya 'kyale ta. Washagari suka tashi Jawad yana ta suma! ga wasu irin abu sun feso masa kamar borin jini, asibiti suka kai shi, aka bashi magaunguna bayan anmasa allurai, sunje siyan magani, suka tarar da Farida a pharmacy din, da azama ta zo gunsu ta karbi Jawad da yake hannun sa ta dudduba jikinsa tana fadin "Abban Jawad wannan ai 'kyanda ce(measles)". Da kanta ta hado maganin da aka rubuta musu, har ta kara musu da wani sabulu da zai taimaka wurin baje fatar. Lokacin da take yiwa Mk bayanin maganin da yadda za'ayi amfani da su, Allah kadai yasan yadda zuciyar Sa'adah ta ke tafasa, ko da Farida ta karaso fuskar Sa'adah a daure ta gaisa da ita, har Mk yaji kunyar yadda ta mata a gaban jama'a. Ya mika kudin Farida ta ce "A a Uncle ka barshi, da dai na Gogel ne sai na barka ka biya! Amma ai Jawad 'dana ne nima", ta fa'da da sigar tsokana da wasa. Ya yi godiya ta rakasu har mota, ya karbi Jawad a hannun ta, ya mika ma Sa'adah ta hakince a gaban mota, suka tafi. Suna Isa gida bata jira ya gama daidaita parking ba, ta dauki ledar maganin da Jawad ta fice. Tana kwantar da Jawad da yake ta barci tunda aka masa allura, ta samo biro, ta yiwa magaungunan nan shaida ta yadda ita kadai zata gane, ta daure ta ajiye su. Ya shigo ya zauna, yana son yi mata magana amma ganin yadda ta 'daure fuska tamkar wadda ya zagi iyayenta, yasa ya mi'ke yana cewa " na tafi! Dan Allah kar kiyi wasa da bashi magani". Ci kanka ba ta ce ba, ya gaji da tsayuwursa ya fita, yunwar da yake ji dole ya fita da abarsa, dan yasan tunda take wannan fishin ba yi zata yi ba, yasan ganin Farida ne ya sake tunzuro ta, tunda tun jiya take ta faman 'kunci, a ransa yana ayyana da jiya kuma ta ganshi yana taimaka wa kanwarta da ta samu admission zata karanta economics fa? Farida ba tasan komai a new side ba, tunda ita a old side take karatunta, shikuma sai ya rakasu a kokarinsa na kyautata mata kamar yadda take girmama shi a matsayin malamin ta. Shi bai san har anzo anfesa mata ba.😄 Da yamma ya dawo, ya ya tarar da ita goye da Jawad, kayan da ya barta da su ya dawo ya same ta da su. kallo daya ya mata, ya gane bata ci komai ba, sannan bata yi wanka ba. Ya rasa gane wannan masifar da ta 'dorawa ranta, da 'kyar ta bude baki ta ce "Sannu" ya amsa da yauwa ya isa bayanta yana duba Jawad da yake ta Nishi, shi dai ta masa wanka fes yake, sai dai jikinsa kamar wuta. "Kin bashi maganin kuwa? na ga jikin, har yanzu bai sauka ba". Ko kala ba ta ce ba, ya isa inda ledar maganin take ya bude ya ga ba wadda aka taba, bare a sha. Ransa ya baci matu'ka da gaske, ya nunata da yatsa ya ce " Wai ke wacce irin yarinya ce marar mutunci?" Ta yi 'kasa da kanta tamkar wadda ta saduda, yaci gaba da fadin "kin fara kaini bango Sa'adatu, kullum a cikin zullumi nake zaune da ke, masifar yau daban, ta gobe daban, haka ta jibi". "Ai kaci moriyar ganga, sai ka kawo karshen zaman zullumi Mk" ta fada kanta tsaye. A razane ya zuba mata ido, yana kallon ta, itama ta kafe shi da idon da suka cika da 'kwalla ba alamun tsoro ko shakka a cikinsu. Ya kasa cewa komai, dan kuwa a yadda yake jin bacin rai zai iya na'da mata dukan tsiya, abin da baya fatan ya aikata kenan, dukan matar aurensa. Ya mika hannun yana fadin "bani yaron, kai tsaye ta ce "idan kai ka haifar min, ba sai ka 'kwata ba". Ya yi kanta yana fadin "Me kika sha ne? Bari na sauke miki iskancin da kike fama da shi". Ga mamakinsa ko motsi ba ta yi ba, sa'banin da, idan ya mata irin haka take kwasa a guje ta 'buya. Ya isa kusa da ita ya kama kafadunta ya girgiza da karfi har sai da Jawad ya motsa, ya ce " fada min me yake faruwa, me na miki har ya shafi wannan yaron da bai san komai ba?". Tsaki ta ja, tare da fizgewa, ta koma gefe tana sake 'daure goyonta sosai. " What! Ni Kika yiwa tsaki Sa'adatu? abin da kinfi kowa sanin na tsani a mini?" Ai kuwa ta sake jan wani fiye da na farko, sannan tace " ka kashe ni! an maka tsaki Mukhtar". Wani irin shock ya kama shi, a farko da tace Mk gatsal mamaki ta bashi, amma a yanzu da ta ambaci cikakken sunan sai ya gane ashe Mk din a mutunce ta fa'da. " Allah ya tsare ni da kisan kai, duk bala'in da kike nufi na da shi, in sha Allah ba zai same ni ba". "Tunda abin har ya kaimu ga haka, to shikenan! ki yi harkar ki na yi tawa, sauko shi na bashi maganin, sai ki mayar da shi". "Baka ji mai nace tun farko ba? ka 'kwata' a shirye nake da mu karya yaron nan! idan har ni na tsugunna na haife shi wallahi ba zai sha wannan maganin ba". "Ya zuba mata ido, yana jin haushin ta na samu gurin zama a zuciyarsa, ya ce "idan na siyo masa wasu zai Sha?" "Idan na tabbatar da sahihancin su ba". Ya dauki ledar maganin ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba". Bai wani jima ba, ya dawo da su, a wata ledar mai tambarin lamco pharmacy. Ya mika mata, tare da cewa "gashi" ya juya ya fice. Ta dudduba ta tarar da su dinne, illah ledar da ya canja, ta yi 'kwafa ta dankwarar da su. Ana idar da Isha ya dawo, ya tarar da maganinsa akan kujera ita kuma ta shige 'daki ta rufe kofar, Jawad sai kuka yake yi. Ya duba maganin ya tabbatar ba'a bashi ba, ya hau dukan kofar, amma banda kukan yaron ba ya jin komai. Ya kirata ya fi sau hamsin amma tamkar bata gidan. Ya hassalo sosai ya ce "wallahi idan yaron nan ya mutu, ke kika kashe shi, da hannuna zan mika ki wurin hukuma". Sai lokacin ta ce "yi sauri kar 'kuda ya riga ka, wato ka maida ni bagidajiya, ka fita da magani kamar gaske, ka sake dawo min dashi, idona tar yake, bazan bashi ba". A fili ya dinga fadin "Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un". Ya fice zuwa dakinsa, yana karfafawa kansa guiwar ya rabu da ita, ai ta fishi son yaron. Karfe shadayan dare ya dinga jin kukan yaron, da farko ya yi biris, amma da ya dinga jin 'ka'karinsa baisan yadda akayi ba sai ganin kansa ya yi a jikin kofar dakin Sa'adah yana bugawa, yana cewa "ki dubi girman Allah ki bude min kofar nan, komai na yi miki, na yarda kimin komai, amma banda yaron nan, ki ji tausayinsa, ki ji tsoron hakkinsa". Har ya gama bilayinsa bata tanka ba, tana jin ta shirya faruwar komai ciki har da rabuwarsu. Cikin ikon Allah, sai Jawad ya sami barci adalilin ta bashi tea, ta bashi maganin zazzabin sa da yake da shi. Da asuba kukan Jawad ya sake tayar da hankalin Mk, ya rasa inda zai tsoma ransa, a take ya kira Hajiyar Bichi a waya, bai fa'da mata komai ba, ya ce dai kwana suka yi Jawad bai yi barci ba. Ba bata lokaci, ta taho,har da garin kunun ko zai dinga sha, tare suka shiga falon, ya dinga kiran Sa'adah amma ta 'ki budewa, sai da taji muryar Hajiya tana cewa"Sa'a, menene yake faruwa ne?" Da sauri ta bude 'kofar, ta fito idonta, yayi luhu luhu, yayi ja tsabar kuka. Ta mi'ka mata Jawad ta zauna a gefe tana kuka tamkar wadda aka yi wa mutuwa. Hajiya ta kalleta, taga ta fita a hayyacinta, ta rame farat daya, ta maida kallonta ga Mk taga shima a firgice yake. Tace ciwon Jawad ne ya susuta ku haka, ko kuwa wata matsalar ce?" Ya dauko maganin ya mi'ka ma Hajiya ya ce "Dan Allah ki bashi maganin nan", ta karba, ai kuwa Sa'adah ta saka uban kuka tana cewa "Kar ki bashi Hajiya". Hajiya ta rasa maganar wa zata dauka a tsakanin su, ta dubi Sa'adah tace "Yi shirunki bazan ba shi ba, fada min me ya faru?" Ta kasa magana sai kukan da take yi mai dauke da shesshekar ajiyar zuciya. Ganin hakan yasa Hajiya ta rufe Mk da fa'da, ta inda ta shiga, ba tanan take fita ba, tana jaddadawa laifinsa ne, tunda Sa'a ba me fitina bace. Ya yi shiru ya dauki laifin da bai yi ba. da lallashi, Hajiya ta samu Sa'adah ta fada mata dalilin da bata son maganin alhalin ba expired suka yi ba. Da rawar murya ta ce " Budurwarsa ce ta siyi maganin, akan idona suka yi zance ta siya ta bayar". Ta karasa cikin gunjin kuka. Dariya abin ya bawa Hajiya, amma sai ta dake, ta dinga salati tana fadin "kice cin fuska ya miki? banga laifin ki ba, dole ki guji magani, ko nice haka zan yi". Shi dai Mk ya zama tamkar gunki, yana kallon shari'ar son rai a wurin Hajiya. Ba zato Hajiya ta ce yaje ya siyo wasu maganin. Ya ce " Bafa su bane, tunda take wannan bala'in na zubar da su, na siyo masa wasu, amma ta "ki bashi" Da rawar murya ta ce "Billahillazi, baka canjo wasu ba, duk abin da ya fito ta hannunta, na tsane shi, zan kuma gane". Jin haka yasa Hajiya fadin "Bar Wannan gadddamar je ka siyo wasu a bashi ya dan sami sauki" Bai q musa ba, ya mike, ya dauki ledar maganin, ya fita. Sai da ya fita Hajiya ta dinga mata nasiha, tare da cewa "ki rage nuna masa kishinki a fili, sai ya samu dalilin da zai dinga musguna miki". Ta kalleta tace "tunda da wuta jona ruwan zafi kuyi wanka". Ta mike ta cika buta ta jona, mintina kalilan ta kashe kanta, ta juye, ta sake maida wani, kafin ta fito, Hajiya ta wanki Jawad a bandakin tsakar gida. Ta dama musu kunu, ta juye a flask din shayi, ta zubawa Jawad a kofi, ta bashi, ya shanye tas har da kari, ta tabbatar shima har da yunwa ta sake gigita shi. Sa'adah ta fito sanye da riga da zani na atamfa, dinkin ya zauna sosai, mussaman da bata cika daura zani ba. Ta mikawa Hajiya kayansa, sai da ya koshi ta koge masa baki sannan ta saka masa kaya, dai dai lokacin kuma, Mk ya dawo dauke da magungunan, leda biyu, ya mikawa Hajiya, sai da Sa'adah taga na wurin Farida, ga kuma wadda ya sake siyowa, sannan ta saki ranta, a ransa fadi yake masifaffiya kawai. Take Hajiya ta bude ta bashi, ta shafa masa na shafawa, barci ya dauke shi mai nauyi. Sosai Hajiya ta musu fada, kuma duk na Mk yafi yawa, jan kunne 'daya, ta yiwa Sa'adah, kar ta sake saka Jawad a cikin fa'dansu, ta ki cin abinci, shi akan mai zata hana shi? Ta cika kofi, da kunu ta mika wa Sa'adah tace "Shanye ki bani kofin". Ta karba, ta fara sha, ya mata dadi sai kamshin kayan yaji yake yi. Shi dai Mk yana kallon ikon Allah, anbawa Jawad, da Sa'a, shi ko oho. Sai da Sa'adah ta shanye sannan Hajiya ta mike ta ce "zan tafi nasan ki da jin magana, na kashe wannan magana kar a kuma tada ta" Da sauri ta amsa da "in sha Allah ta wuce". "Na gode Miki Sa'a, Allah ya miki albarka". Sa'adah ta amsa da "Ameen Allah ya kara girma" ta tashi tana mata rakiya hanyar waje. Tare suka fita da Mk zai kaita, a hanya tana sake masa fa'dan, lallai ya kiyayi zungurar Sa'a, ta dora da cewa "Kana ganin irin yadda take mutunta ni, tana haba haba da yan'uwanka, iyayenta mutanan kirki, lallai ba zamu shirya da kai ba, idan kace zaka wulakanta ta, mussaman ma akan wacce bata zo hannun ka ba". Har ya kaita gida, kashedi take masa iri iri. Da za ta sauka ya ce "kin basu kunu, amma Ni baki bani ba". "Ina sane, kai Sa'a ce mai ba ka". Murmushi ya yi, tare da cewa "Hajiya kar kisa na fara kishin yarinyar nan, naga tana neman zarta ni a gunki". Ta yi murmushi tace " maza ka juya ka sake rarrashin ta, ka tsaya a hanya ka siya musu dan wani abin, kunu kadai bazai ri'ke ta ba, ta tara yunwa". Haka kuwa, ya biyo ta titin Hausawa bawo road ya siyi wainar shinkafa da ake yi mai dadin gaske, a falo ya tarar da ita, tana zaune tana kallo. Bata dago ta kalle shi ba, ta amsa sallamar sa, daga haka bata kara magana ba. Ya tsaya ya ce "Ba ki mini sannu da zuwa ba fa". Ba tare da ta kalleshi ba, ta ce "inace ka ce kowa ya yi harkarsa?" "Na fa'da! amma dai Hajiya ta kashe maganar, ta ce kar a kuma tada ta". "Ita maganar maganin Jawad ta kashe". Ya zauna, yana cewa "ga waina na siyo miki, tashi ki zubo mana". Kanta a kasa ta ce" ci abinka". Ya kai kicin ya adana, ya zubo wadda zai iya cinyewa, tare da kunu a kofi, yaso ya shiga dakinsa, sai kuma yafi zumudin zama kusa da ita. Ya zauna yana fadin "dan Allah sauko ki taya ni ci". "Ba zan sake cin abinci da kai ba, tunda muka yi aure, baka taba kaini restaurant munci abinci ba, amma ka dauki wacce kake so kun je! ba ruwana da sabgarka". Ta fa'da hawaye na balle mata, ya yi shiru, yana jin sabon tashin hankali, ya rasa da bakin da zai kare kansa. Ya yi shiru, ya kasa cin abinci, ko kaffara ba zai yi ba, su Safina ne suka kawo mata wannan labarin. "Ki yi hakuri kin ji Sa'adan Uncle". Kamar ya watsa mata garwashi, ta zunkudo ta ce " ta Ina ka zama kawuna?" Kai ba 'kanin Baffa bane, bare na Inna, daga jiya ba zaka sake jin bakina ya kiraka da Uncle ba, ita dai da kuka hada dangi, sai tayi ta fa'da na bar mata" "Ashe lokacin da kace min dole kayi kishin mace, idan ka ganta a gaban motar wani da ba Muharraminta ba, 'karya ka fada tsagwaronta? To ita mai kuka hada daka dauketa a gaban motarka?" Kansa ya kulle, ya kalleta ya ce "Na yarda ban kyauta ba, ki yi hakuri, ki bani wata damar, ko banci albarkacin komai a gunki ba, naci albarka cin mahaifiyata da tazo ta baki ha'kuri, ta kashe maganar". Jikinta ya yi sanyi, ta ce shikenan na ha'kura". Da'di ya kama shi, ya matsar da kwanon abincin kusa da ita, ya ce to sauko muci". Ta girgiza kai, "Na hakura, amma ba zanci da kai ba". Ya tura mata, "to ci wannan, bari na zubo wani," ya mike ya fita da sauri. Cikin sa'a ranar bashi da lakca sai 'karfe daya, dan haka, bai fita ko ina ba, yan tare da ita, yana ta kokarin wanke mata zuciya, shi da kansa ya tabbatar a duniya ba abin da yake so sama da Sa'adah da 'danta, idan aka cire Hajiya. Sai dai duk nacinsa bata yarda da shi ba, kan dole ya 'kyale ta. Kwana biyu tana mai yawo da hankali, kafin ta ha'kura ta sallama masa kanta, cikin rawar jiki yake komai, yana ayyana distance fa yana da amfani, domin ji yayi ta dawo masa sabuwa. Yana samun kudi kuwa, ya dauke su ita da Jawad suka je restaurant din Royal Tropicana suka ci abinci, suka yi hotuna, irin wadda ake wankewa a take, take & wash, suka zarce country mall, ta zabi abin da take so. A hanya ya ce "shikenan yanzu na dawo Uncle?" "Hmm! magana ta wuce ka daina dawo mini da ita". Ya shagwabe fuska ya ce " idan har da gaske ta wuce, then called me Uncle". Ta fara dariya, tana cewa "ashe son girma ne da kai ban fahimta ba?" Shima ya taya ta dariyar sannan yace "tsakanin ki da Allah! Idan nace Miki Sa'adatu ba kya jin wani iri? ke da kike kanwata nasan kina jin ba dadi, bare ni ki gatsa sunana gatsal" "Amma ai tun ranar ban sake fada ba". "Eh baki sake ba, sai dai kimin ta kurame, kiyi maganar ki ba tare da kin kama sunana ba". "Nifa Wallahi na tsani, waccan sunan da kake kulafacin sai na cigaba da kiranka da shi". "To shikenan zabo min wani, mai sweet, kika rufe ido kika cemin wai baki hada dangi da Ni ba ko?" Ta ce "eh mana ai ba karya na fada ba". "Ni Malamin ki, Ni Mijin ki,Ni Baban danki, duk wannan ha'din kin raina shi?". Ta tura baki gaba, ta ce "shikenan, ka zabi sunan da zan fada maka a cikin wadannan,Malam, Miji, ko Uban 'da" Dariya ta kwace masa sosai, cikin dariyar ya ce, "ke yanzu sai ki dinga cemin Uban 'da?" *Surayya Dahiru* ✍🏼✍🏼✍🏼 26/03. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *Lafazi writers*. *A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba* *Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*. *GODIYA* *Ina matu'kar godiya ga wadanda suka yi mini addu'o'in samun lafiya ga warwarewar lamura, tunda ga kan masu kira ta waya, da masu text, da masu yi mini ta dandalin WhatsApp, dukkanku na gode madallah, ubangiji ya fini yabawa*. 65-66. Ta yi murmushi ta ce " mai zai hana na fada maka idan kana so?" Ya bugi sitiyari ya ce "my sweet Sa'adah, sometimes you are so funny". Ta yi shiru ta kyale shi, ya sake cewa " ke yanzu ko inkiya da Jawad baza kimin ba, naga yanzu daga mace ta haihu take karawa Mijin ta matsayi ta hanyar yi masa alkunya da sunan yaronsu". Ta tabe Baki, ta yi shiru, sai kuma ta kasa hadiye maganar. "Akan mai zan maka alkunya da Jawad alhalin wadda ta fini cusa kai ta riga ni? Inace Farida Abban Jawad take kiranka? Kasan Ni kuwa har abada bazan bi ra'ayin ta ba, banda azarbabi, ba sai ta bari idan ta haifar maka nata sai ta yi komai ba, amma dan son sai ta nuna ita gwanace akan kayan da ba nata ba yasa ta ke yi mini katsalandan, ai na so ta yi kataborar ce min Iyah Basiru, wallahi da jikinta ya fa'da mata domin kuwa ba abin da zai hana na mata 'kamshin mutuwa". Ganin za ta tunzuro da yawa sai ya share maganar da cewa "Na zabi miji, amma Zauj za ki dinga fad'a maimakon miji". Yana rufe baki ta ce " duhun fata ta kadai, ya isa ka gane ni ba balarabiya bace, dan haka nafi kishin yarena". "Amma duk musulmi dole ya dau larabci yarensa ne, domin yaren kura'ani ne, duk sallar duniya kuma a larabce muke yinta". "Wannan daban" ta bashi amsa a takaice, daidai lokacin kuma suka iso gida. A gidan ma maganar ya yi ta ja, inda ita tace Malam ta zaba, dan haka Malam zata dinga fada. "Na fada miki ban son wani Malam, duk sunayen zamani, da na soyayya ki rasa mai zaki ce mini sai Malam sai kace tsoho ko wani Malamin zaure, duk yadda muke da ke darajata a iya ta Malami take a gurin ki?" Tana dariya tace "kololuwar daraja kenan, Malaminka ai tamkar mahaifi ne, ana canja Miji, amma ba a canja mahaifi da Malami, domin ko ka guje shi, ya dai koyar da kai abin da baka sani ba, sannan ya koya maka tarbiya, a wurina Malam is a jewel. Shikenan mafarin cemasa Malam tun yana ki, har ya fara amsawa, a lokacin da Jawad ya fara iya magana shima ya bi bakin uwarsa wurin kiransa da Malam. Juyin duniya ya yi da Jawad kar yace masa Malam, amma da ya fara cewa Daddy, idan yaji Sa'adah tace Malam shikenan shima zaice Malam. Sai ya fara cemata Daliba, ko abune sai ya bawa Jawad yace humm kaiwa Daliba, a kokarinsa na itama Jawad ya dinga kiranta haka😂 Amma sunan bai bita ba, sabanin shi da Malam ya zauna a bakinsa radam, ita kuwa Mami yake kiranta. Tun lokacin Mk yake yiwa Sa'adah mitar yasan Jawad yafi sonta da shi, itakuma dariya yake bata idan yana wannan rikicin nasa.wataran tayi dariya, wataran tace haba Malami na. Sai ya yi murmushi yace "A da nake Malamin ki". Tace "har yau Malami na ne, tunda har yanzu karatu nake yi a gabanka". "Wanne karatun kike yi yanzu?" Tace " da ka koyar da Ni, ilimi da tarbiya, yanzu kuma kana koya mini karatun kyankyansar jarirai". Tana fadin hakan ta gudu ta barshi, ya bita yana dariyar maganar ta karshe, wai kyankyansar jarirai? ya zauna kusa da ita yana cewa "ai kuwa dai kin yi gaskiya, Ni yanzu ma so nake mu zama mu hudu, ya kamata kije ki cire abinnan, mu fara sabon karatun kyankyansar jariran". Tana dariya tace "ka rufa min asiri kai da kace sai na fara karatu, na yi nisa, da ka sake yi min ciki?". Yana dariya yace "da bakin ki Kika fadi wannan maganar?" Ta rufe ido tana Jin kunya na kamata. Ya zauna kusa da ita yace "kisan dai kin yi jamb, kyau ne bata yi ba, nace ki cike F.C. E. Kin kasa fahimta ta, da yanzu za ki fara N.C.E, kinga yanzu dole ki sake zaman jiran wata shekarar, maimakon haka gara mu sami Baby, ai akwai masu karatun da goyo". Shiru ta yi, itama tana son haihuwar yanzu, mussaman idan ta tuno fuskar baby girl dinta da ta rasu mai kama da ita, sai ta ji ta zaku da ta sake haihuwa, tasan da ta rayu, da ta nan tana tafiyarta ko ina. " Ance mini idan Ina haihuwa rututu ba barina zaka yi na yi karatu ba?" "Ni kuma nace za ki yi, har sai kince ya ishe ki, shin maganar wa za ki dauka, tawa ko ta su?". "Shikenan zan cire, amma yanzu ka manta Jami'an lafiya na yajin aiki?" " Na manta, idan su koma bakin aiki sai muje a cire ko?" Ya fada cike da kulawa da rarrashi. Su Halima na zuwa ta fada musu, Malam yace ko da goyo zata yi makaranta, karatu har sai ya isheta. Safina ta kaikaice tace "wato ya ga kin yi kyau, kin bar Sa'ade kin dawo Sa'adah, shine zai sake dirka miki wani cikin? ke kuma har kin yarda da maganar sa?" Suka kwashe da dariya, Halima tace "na rantse miki da Allah karya yake miki, barinki ne ba zai yi ba, kar ki sake ki cire abin nan sai kin tabbatar kin fara makaranta, tunda shi son haihuwar yake, sai ki yi amfani da hakan ki cimma burin ki". Sa'adah ta yi shiru amma bata fahimci bitar Halima ba. Tace "kamar ya ya na cimma burina?" "Eh tunda so yake ki cika masa gida da Yara, sai ki kafe, ba za ki haihu ba, sai ya nemo miki admission, idan har da gaske zai barki, maki uku ne kacal ya hana points dinki su kai, da ya so, da tuni ya samo miki admission, lakcara ne fa, Yana da alfarma wallahi". Safina tace "Ai ni bansan wadda ya iya rainin wayo irin Man din nan ba, mugun macijin sari ka noke ne, idan kika ga yadda yanmata suke sintiri a gurinsa, sai mamaki ya kamaki, farar fatarsa da tsayinsa ke rudar su". Halima ta cafe da cewa "itama Gogel din ai abin da ya rudeta kenan, banda haka Ina da kamar Alh Mamman da bazan yi kukan rasa komai ba, Ina zan tsaya kula wannan mutumin, kinsan Allah Safina! da Alh Mamman ta aura Ni kaina da tuni na jike da arziki, mu ture ta Alh Mamman, zata iya cewa ya mata tsufa, matashin saurayin nan da kasuwa ta daukaka ke shi chairman din Buji ventures, shima ya sota fa". Safina tace "Ina ruwanta da tsufansa? Lokacin da Dadin mu ya auri mom Dina, ai kamar ita da Alh Mamman ne, gashi nan har yau suna tare, ta yi lub tana cin arziki, har muma muna cikinsa,kawai rashin rabo ne irin na Gogel, ga kuma rabon Jawad da kanwarsa a jikin Uncle" "Ai kuwa rashin rabo ne na yarda da ke, Allah ya rabamu da rabon wahala". Halima ta fada tana Jin takaicin rashin auran Alh Mamman. Duk zuwansu basu da aikin komai sai kushe Mk, alhalin a gidan suke zuwa suci abinci mai rai da motsi, suna ci suna kushensa, barin ranar da babu wuta ko nama a abinci, sun dinga fadin mutum kamar Mk ya kasa kunnawa matarsa da dansa 'daya janareto su ji dadi, dole sai dare, daren ma sai ya fara nisa, Allah muna rokon ka tsari daga auren matsolon namiji. Haka har lokaci ya sake ja, basu fasa zuwa ba, yanzu kuma sun dauki sarar shanye mata kayan tea ta hanyar yin Yar gullisuwa, ko sai sunci abinci, suce za su sha tea, ko cornflakes. Suka sake cusa mata karya a ranta, bada komai take amfani ba, sai kaya masu tsadar gaske, yadda take tafiyar da tsarin rayuwar ta tamkar matar attajiri ba wai 'karamin lakcara ba. Gayun ta ya 'karu, komai nata daukan ido ya ke, saboda sai zababbe, a lokacin Mk ba abin da yake so irin farin cikin ta, shi da kansa har mamakin yadda yake tsoron fishin ta yake yi, komai take so haka yake mata, kusan albashinsa da kyar yake rike su, saboda hidimnar Sa'adah, kowanne wata da Abin da zata ce, tana so, haka zai yi mata jikinsa na rawa, mantawa yake yi da hidimar kansa, daga ya sallami Hajiya shikenan zai sa Sa'adah da Jawad a gabansa. Amma duk da hakan Sa'adah bata fahimci matsanancin sonta da take yi bane, da kuma sa'a da tayi mai son kyautatawa iyali ne, sai ta fara wuce makadi da rawa, bata cika nazari kafin ta aiwatar da komai ba. Suna cikin haka Jami'ar Bayero ta fara yanka fili manya tana rabawa Malaman makarantar, a hankali za'a dinga cira a albashinsu. Mahmoud da sai a wannan shekarar ya yi aure, kai tsaye biyu ya karba, da nufin idan ya tashi ginawa ya yi gini mai yalwa. Mk kuwa fargaban karban 'daya ma ya shiga, saboda a halin yanzu, badan shagon askin sa ba da sai ya hada da bashi a wata. Mahmoud ya yi ya karbi biyu, Mk na bude bakinsa sai cewa ya yi daya zan iya karba, shima sai na yi shawara da Sa'adah, kar nazo ta 'kuntata. Mahmoud ya yi galala yana kallonsa ya kasa hakuri yace " idan nace ka bari tafi karfinka kace ba haka ba, idan nace tsoron ta kake ji ka karyata Ni". Murumushi Mk ya yi tare da caewa "kowanne namiji da yadda yake zaune da matarsa, kowacce mace da irin alherinta, da irin kuskuren ta, Ni sonta nake da dukkan alherin ta, da kuma kuskuren ta, bana jin tsoron ta, amma Ina jin tsoron fushin ta, dan haka duk abin da zan yi ,dan na samu zaman lafiya da ita zan yi". Mahmoud ya tsinci bakinsa da fadin "Hakane". Mussaman da ya tuno, yadda ta iya girki, da kwalliya, gidanta kullum a gyare, hatta Jawad kullum fes za ka ganshi, sannan tana da kyakkawar mu'amala da jama'a, dan kuwa hatta amaryarsa yabon kirkinta da gayunta take yi! iya abin da ya sani na zahiri a kanta kenan, Ina kuma ga mu'amala ta sirri tsakanin ta da Mk, sai ya tsinci kansa da rashin ganin aibun yadda abokinsa ya yi deep a soyayyar ta, ya lalace a kanta, da yadda zai siya mata suturu na makudan kudade, shi ya siyi masu sau'kin kudi ya saka. Bai karbi filin nan ba sai da ya shawarceta, tace "ka karbi biyun mana Malam". "Idan na karbi biyu fa, hakan na nufin sai mun rage wasu abubuwan, tunda za a dinga yanke mini kudi ne". "Tunda dai wataran gini zaka mini mai kyau, gashi kace idan filin biyun ne har garden zaka mini, ai sai a ha'kura da wasu abubuwan har Allah ya sa ka kammala biyansu" Ya ji Dadi har ransa, da yadda ta fahimce shi,ya karbi filaye, Mahmoud na ta masa tsiyar Madam ta bashi go ahead kenan. Shikenan sai suka canja daga rayuwar luxury zuwa tsaka tsaki, sai dai ba a dauki lokaci mai tsayi ba, abubuwa suka fara canjawa saboda yadda su Halima suke mata shaguben yadda Mk ya canja mata, suka dinga fadin ba wani fili da ya karba, yanmatan banza yake kashewa kudin, Raina ki ya yi, shiyasa ya shirya miki wannan karyar, itakuma tana gaskata su, ta kasa gane gadar zare suke yi mata. Sannu a hankali sai suka fara kushe talabijin din falonta, alokacin plasma bata yawaita ba, sai irin ta falon wato LG slim tv. Kullum Suka zo sai sunce wannan tv kamar ba gidan ma'aikacin gwamnati ba, kusan shekaru hudu amma ya kasa canja miki komai, tunda muke zuwa kullum abu daya muke gani. Idan ta kawo musu pure water, sai sunce ruwan warin nama ko karnin kifi yake yi, suna fadin freezer da zai siya ta nama da kayan miyane yake ganin asara, gara yaje ya rabawa yanmata a waje. Tun bata yarda, har maganganun suka shigeta, mussaman da ta ga falon amaryar Mahmoud, sai ta sake rikicewa, ba tare da ta yi nazarin kayan da suke rainawa, ita ba'a Mata kamar su ba. Ta fara rikice masa, ya kasa gane kanta, ya zauna yana rarrashin ta, har ya samu tace ita tibin bango take so ya siya mata. Ya rikota cikin kwantar da murya yace "ki yi hakuri zan siya, amma ba yanzu ba, kinsan dai yanzu ba cikakken kudi nake samu ba, amma da zarar naci karfin biyansu, zan siyo miki, ba sai na kammala biya gaba'daya ba, ya kara da fadin wacce kamfanin kike so?" "Sumsung" "To ki daina bata ranki akan maganar tv, mecece talabijin kuma?" Ya lallaba ta da maganar tv. sai kuma wayar Black berry ta shigo, kullum su Halima hirar BB chart, Safina kam tuni ansiya mata, yayin da Halima take fatan saurayin ta ya siyo mata. A ranar da saurayin Halima ya kawo mata wayar, suka je gidan Sa'adah suka nuna mata, Halima na fadin " kina ganin saurayi ma, da bana daga masa kafafuwa, ya fidda kudi ya siyo mini, bare ke da kullum yake hakar ki". BB chart din nan ya matu'kar gigita Sa'adah mussaman da aka tabbatar mata, sai masu irin wayar ne suke yi. Kullum mitar ya siya mata waya take, rannan da ya gaji, ya zaunar da ita yace "kinsan za ki dame ni mai yasa za ki sani karban filaye biyu? bani da kudin siya miki wayar da kike magana akanta, Ni kaina ban ri'ke ta ba". Ai kuwa zamansu ya dawo wani iri, saboda ta kudire a ranta da gaske yanmatan banzan yake yiwa hidima, ita ya barta ko oho, mussaman da ya ki yarda ya kaita ta ga filayen nasa. Ranar wata juma'ah sai ga shi da sabuwar plasma TV 32 inch, ga mamakinsa ba ta yi wani murna ba, lamarin da ya bata ransa sosai. Haka ya daure, ya kira mai gyara ya hada mata har da satellite. Kallonta kawai yake yi, a zatonsa siyan tv zaisa zamansu ya dawo normal, amma sai ya ga sabanin haka, saboda ta riga ta yi nisa a son Black berry, ta samu shedanun kawaye na mata famfo. Haka suke ta gungurawa, yau fari gobe tsumma, mussaman da ya tsaya akan ra'ayinsa na ba zai siyi waya ta makudan kudade ba. haka jarrabawar jamb ta fito, a lokacin da F.C.E. ta fidda jerin daliban da suka sami gurbin karatu har da ita, inda zata karanta primary care education jiran lokacin fara daukan darasi take yi nan da yan wattanni. Hakan bai sa ta sauko ba, saboda ita B.U.K. take so, Safina sai cewa take "mijinki is very smart Ya rantse ba zai kai ki makarantar da yake ba, dan kar agane yana da mata". Yau da gobe akace ta fi karfin wasa, ya gaji da zaman rashin walwalarsu, ya kukuta ya siyo musu Android shi da ita, a lokacin bata jima da fitowa ba, dan haka itama mai tsada ce, ga mamakinsa ko Na gode ta gagareta fa'da wadda ko kadan ba halayyar ta bace, ko abu bai yi mata ba zata yi godiya ko a gajarce ne. Amma wannan ajiyewa ta yi a inda ya bata ba tare da ta duba ba, ransa ya baci da ita, irin wadda bai taba ji ba. Ganin idan ya cigaba da zama kusa da ita, komai na iya faruwa a tsakaninsu na rashin jin dadi, yasa ya mike ya fita zuwa shagon sa, bai dawo ba, sai shadaya da ashirin da bakwai 11:27pm. Ya sake tarar da wani 'bacin rai fiye da na farko, wato rufe masa gida, bugu ka'dan ya yi, ya hakura dan kar makwabta su fahimci abin da ke faruwa, ya dinga kiran wayarta ba kakkautawa, tana shiga amma taki dauka, karshe ma sai ta kashe wayar gaba'daya. Haka ya kwana a gate a cikin mota, ya yi kwanan zafi, da sauro, barcin kansa rabi rabi ne, wannan daren yana cikin jerin dare masu tsayi da ya fuskanta a rayuwar sa. Duk juyin da zai yi, tunanin irin hukuncin da zai mata yake yi, ya gaji da wannan bala'in, zai nuna mata, neman zaman lafiya ba shine lasisin da zata dinga wulakanta shi ba. Koda asuba kin bude masa ta yi, dan iskanci kuma ta kunna wayar amma taki 'dagawa. Ya Mata text yafi sau goma, har kurarin zai fadawa Baffa ya yi, amma ko gezau. Har taran safiya, yana harabar gidan. Takaicin sa daya, ba ya ajiye kaya a mota. Mahmoud ya kira ya fada masa halin da yake ciki. Da kyar Mahmoud ya shawo kanta ta bude masa, domin kuwa cewa ta yi, ya koma ya dauwama a gurin Farida. Yana jin lokacin da ta zare sakata, amma ba'kin ciki ya hana shi tashi, ya jima yana addu'ar samun sau'kin zuciya kafin ya samu sassauci. ya shiga gidan kai tsaye dakinsa ya shiga, ya yi wanka, ya fito ya shiga kicin, ya hadawa kansa Abu mai sauki, ya koma dakinsa ya rufe, yini guda bai fita ba, domin ramuwar barcin da bai samu ya yi ba. Itakuma tana zaune cikin shirin ko ta kwana, har sun yi waya da Halima ta fada mata abin da ta yi masa jiya, tace mata da kyau, gobe idan ya sake har gate din za ki rufe. Sai azahar ya tashi, ya fito da shirin fita masallaci, Jawad ya biyo shi, ya ri'ke hannun sa, suka tafi bayan ya masa alwala, suna dawowa, Jawad ya dinga Jan hannunsa, Yana cewa" Mami falo". Ya daka masa tsawa ya shige dakinsa ya daga murya yace "je ka wurinta kai, domin ita da babu duk daya ne a gurina" Jawad ya fashe da kuka saboda tsawar da bai saba da ita ba. Abin ya yiwa Sa'adah ciwo, a fili tace "Allah yasa yau ka sake yin dare, zaka san Ni da babu daya muke". Tsawon kwanaki biyu, zaman nasu ya sake yin tsami, domin shima fishi ya dauka sosai, ya dauke sabuwar wayar da ta bar masa a gurin, sannan ya karbe wadda take amfani da ita. Lamarin da yasa rikicin ya sake ta'azzara a tsakanin su. Ta dayan bangaren kuma sai shirin tafiya Abuja yake yi, saboda za su yi wata jarrabawar scholarship da gwamnatin tarayya zata tura malaman jami'oi karo ilimi a kasashen Birtaniya, Canada da kuma Rasha. Bai fada mata zai yi tafiya ba, har sai da ya kammala shirinsa, da zai tafi, ya tsaya daga bakin kofar falon yace " Zan yi tafiya, sai Allah ya dawo da Ni, ya bawa Jawad dubu uku yace "kai mata". Mamaki yasa ta kasa bude baki ta yi magana, ya juya ya tafi, Jawad na kukan zai bishi. A tunanin ta kwana daya zai yi ko biyu, amma sai da ya shafe kwanaki biyar ba shi ba alamun sa, a kwana na shida ne, idonta ya fara raina fata, mussaman da ta tabbatar da Mahmoud suka yi tafiyar, Amma shi ya dawo kwana biyu kawai ya yi. Kuka ta dinga yi, tamkar shine mafita, ga rashin waya dake addabar ta, ga rashin sa. Sai da yayi sati guda ya dawo, kallo daya ya mata yasan ta ji jiki, sakonsa ya daketa sosai, amma saboda Halinta na taurin rai, ko kallo bai isheta ba. Washagari da ya fita, sai da ya kai 11pm kafin ya dawo, domin ya jarrabata ya gani. A bangaren ta tana son rufe masa gida amma ta kasa, kwanakin da ya yi baya gida, sune mafi tsauri a dukkan rayuwar ta, tunda suka yi aure bai ta'ba yin tafiyar da ya kwana ba tare da ita ba. tasan rufe masa gidan da ta yi ne, yasa yayi tafiya mai tsayi ba tare da ita ba, ba magana mai dadi, ko na zai yi missing dinta. Ya dawo ya tarar da gida a bude, ya yi murmushi, yauma 'dakinsa ya zarce, wannan abin ya dameta, amma bata ji zata bashi ha'kuri ba, tunda ai ita ya zalunta. Washagari yana shirin fita, ta fito ta tsaya a tsakar gida, sai da ya fito sannan tace " Ina son zanje gida". Ba tare da ya kalleta ba, yace " Ba za ki je ba". Ya sa kai zai fita, taja tsakin da yasa shi juyowa da sauri, kafin yayi magana tace "dama idan mutum na cin amanar matarsa, sai ya yi ta boyeta a cikin gida, mai za'a yi da auren likitan mata, da mai koyarwa a Jami'a, aiki ne na yan iskan maza, masu juyawa matansu baya idan sun sami biyan bu'katar su" Ya zuba mata ido yana jin wani iri Abu mai kama da tsanar ta na son yiwa zuciyar sa dirar mikiya. Ya nuna kansa da yatsansa, yace "Ni ki ka zaga?" Idonsa ya kada ya yi jawur, ya rasa inda zaisa ransa ya sami sau'kin zafin da zuciyar sa ke yi. Ya girgiza kai yace " Na gode, amma U will pay for it Sa'adatu".ya juya ya fice da sauri. Ganin yanayinsa yasa ta jin nadama na dan shigarta mussaman yadda ya nuna kansa yana tambayar shi ta zaga? tasan bai taba zaton zata iya zaginsa ba, ita kuma ba'kin cikinsa ne yake neman kashe ta a tsaye, sannan ma a ina ta zage shi? Fishi ya dauka sosai, sun kai sati a haka, abin ya fara fin 'karfin ta, rama take yi a tsaye, ko uffan baya cemata, Idan yana gida Jawad na manne da shi yana bashi labarin yaci abu kaza da iri kaza, ko yace su Anty Safina sun kawo masa abu kaza. Hankalin ta bai tashi sosai ba, sai da yayi shopping, taga iya abin da ya zama dole ya siyo, wadda ya saba siya na kyautatawa duk bai siyo ba, duk wani tarkacen kayan kwa'dayi babu a siyayyar nan, hatta kayan miya da yake zuwa janguza ya lodo musu, wannan karan ko guda daya bai siyo ba. Sannan a drower yake ajiye kudinsa baya mata iyaka, ya zara , ta zara, har su 'kare a haka, a wannan lokacin sai ya zauna ya yi 'kiyasin 200 zai isheta kullum da sunan kudin cefane, dan haka sai ya adana kudinsa yake bata wannan darin biyun, Jawad yake bawa ya kai mata. A wannan lokacin da ya rikice mata, ya canja sosai, sai ta gane ashe dai da kirkinsa har yawa ya yi. Ta fara neman hanyan sulhu, amma ta rasa yadda zata yi, yaki ya bata dama ko kadan, ko ta kai masa abinci baya ta'bawa haka take daukan abinta, ta fara daukan wanka da kwalliya, shikuma sai yake runtse idanuwansa daga kallonta. Ta rasa mai kuma zata yi, sai ta dawo da gyara masa dakinsa, kullum idan ya fita, zata shiga ta gyara, gyara na mussaman, ranar da ta fara, da ya dawo ya gani, a ransa yace zaki san ba ke ka'dai kika iya neman masifa da tashin hankali ba. Ganin ta debi kwanaki tana bin hanyoyin neman sulhu, amma ya yi biris da ita, sai ta canja salo. Rannan da daddare ya dawo, ta kai masa abinci da tea din da ya zame masa ka'idar sha duk dare, tana ajiyewa yace " fita da su na gode". Ta yi shiru tana kallon sa shikuma yana zaune, yana nazari a waya, amma yana jin kallon ta a jikinsa. "Dan Allah Malam ka sha shayin nan na roke'ka". Ya girgiza kai yace "Na koshi ne, ki ajiye zan sha da safe". Da murna tace "Na gode". Ta mayar kicin ta adana abincin a fridge, a gurguje ta yi wanka, ta bi dukkan jikinta ta shafa Arabians perfume masu kamshi sosai. Ta dauko rigar barci ruwan madara, mai santsi ce kuma very transparent, ta gyara gashin kanta ta shafe shi da man gashi na Kuza. ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, tabbas ko ita ta burge kanta, ta tsinci bakinta da yin tasbihi da godiya gurin ubangiji,hakika an kyautata halittar ta. Har taje falo kuma sai ta dawo, tana bin cinyoyinta da kallo, iyakacin Rigar rabin cinyarta ne, ko kusa da guiwata bata zo ba, bugu da kari, bata sa komai a kasan rigar ba. Shaidan da zuciya suka fara wasan kura da hankalinta, suna kitsa mata idan taje a haka, ta yarda itace mai laifi, bayan duk irin yadda ya nuna mata ita da babu basu da maraba. Ta tuna yadda ya shafe sama da sati biyu bai nemeta ba, shaidan ya sake tunzuro ta, yana jaddada mata irin zalamarsa akanta, idan ba wata ya samu a waje ba, yaushe zai iya jure tsawon kwanaki bai rabeta ba, tabbas mata yake bi na banza. '' Ta koma ta kwanta a gadonta, tana Jin hawaye na bin fuskarta. Sai juyi take yi, tana kallon yadda Jawad yake barcinsa cikin nutsuwa, tana jin inama itace shi, da bashi da wata matsala a duniyar sa, indai zai ci abinci, a masa wanka, a bashi sweet shikenan baisan komai na bacin Rai ba. Ta kasa barci ta zabura ta sauko daga gadon, tana jin dolensa ya fada mata mai yake nufi da ita, ya kuntata mata, ya kuma fita fishi🤔 Ta kunna fitilar dakin, ta fice ba tare da ta kashe ba, saboda Jawad . A zaune ta same shi, yana marking din exams din 'dalibai. Ya amsa sallamarta, hankalinsa na kan takardar da ke gabansa. Ganin bai 'dago ba, yasa tace "Ina son magana da kai". Yana cigaba da marking yace "Amma dai kinga aikin da ke gabana ko? Sai ki jira na kammala, ko ki tari lokacina na gaba". Hawaye ta ji na neman kwace mata, da ta tuna kafin su fara takun saka, baya iya yin aiki sosai matu'kar suna tare, ya fi kauri wurin tsokanarta, ta hanyar dumbulan kirjinta, ko ya biyeta su yi ta shiririta, tana bashi labarin ai tana yawan mafarki ta zama Hajiya, ta zama big madam, shikuma ya yi kudi, ya zama Alhaji, ya gina musu katon mansion. sai yace Ina fatan dai ba kiga na 'kara aure ba? Wani lokacin tace bata gani ba cikin da'din Rai, wani lokacin tace abin da yake ransa ne, sai ta hau bori, shikuma ya lalace wurin rarrashin ta, a haka har su cinye lokaci mai yawa basu farga ba. Amma a yau, gata a gabansa yana nuna mata bashi da lokacin saurarenta, aikin da yake yi ya fita muhimmanci kenan?. Da gaske ita da Babu 'daya ne a gurinsa? sai kawai ta fashe masa da kuka irin wadda ta tabbatar yana gigita shi. Surayya Dahiru ✍️✍️. 30/03. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *Surayya Dahiru*. Lafazee writers. *Doka mai lamba ta 68 ta nina cewa satar fasaha babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*. *A kiyayi ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* 67-70. Ya yi shiru yana jin kukan da take masa, yana ayyana rashin mutuncin ta kullum kara gaba yake yi. ransa ya baci iyaka, mussaman yadda ta ware murya tana masa kuka tamkar wadda ya ke mata dukan kawo wu'ka. Ya kasa cewa komai, domin zuciyarsa sai fada masa take, ya daketa kawai, ko ya huce kadan cikin takaicin da take guma masa, itama kuma sai ta yi kukan mai dalili. Tsawon lokaci tana kukanta, jikinta ya yi sanyi tubus, a dalilin halin ko in kula daya ya mata, da gaske dai Malam ya gaji da ita, hakan ya sake sa ta fashe da sabon kuka fiye da wadda take yi. A harzuke ya nuna ta da yatsa yana cewa " tashi ki koma dakin ki, kici gaba da kukan a can. Idan kuma ba ki gama min tuya a gurin makwabta ba, sai ki kara himma har su shigo su ceceki." Jin hakan yasa ta rage sautin kukanta, shikuma ya cigaba da aikinsa amma bashi da sukuni ko kadan, ya kuma yi al'kawarin ba zai ce ta daina kukan da take yi ba. Aikuwa kusan raba dare ta yi, tana masa gunjin kukan da babu shagwaba, sai zallar bacin rai, irin kukan da me yinsa yake son a rarrashe shi, lura da hakan da yayi shikuma ya yi biris da ita, dan kuwa bai ga dalilin kukanta ba, shi ta musganawa, ta masa rashin kunya, bata bashi hakuri ba, shine take sa ran shi ya risina mata, lokaci ya yi da zai daina biyewa son zuciyar sa akan lamarin ta. A inda take zaune barci ya sureta, sai sakin ajiyar take yi. Sai da ya gama aikinsa, ya kammala komai, ya dauko Jawad ya kwantar da shi, ya dauko bargo ya lulluba mata, sannan ya kashe fitila ya kwanta bayan ya rungumo Jawad a jikinsa. Da asuba ta tashi ta ganta lullube da bargo, ta ji dadi, sai dai rashin tashinta ta yi sallah ya dakushe waccan jin dadin, ta kalleshi har ya dawo daga masallaci, ta zuba masa idon da ya kumbura saboda kuka, murya a dashe tace "Malam abin har ya gagareka tashina na yi sallah?" Ya yi mata shiru tamkar ba da shi take yi ba. Takaicinsa ya sake kumeta, tace "Ma'aiki dai yace Allah ya jikan mijin da ya tashi cikin dare ya kuma tashi iyalinsa suka yi sallar nafila, to ina kuma ga wadda ya tashi, ya kuma tashi iyalinsa dan sallar Farillah? ka rasa wannan ladan, ba nice da asara ba". Ya zuba mata ido yana kallon ta, Yana jin sabon tashin hankali na shigarsa, tabbas ta kerewa tunaninsa, an mata famfo fiye da duk yadda yake zato. Haka ta gama sakin magaganu sannan ta fita zuwa dakinta, don yin sallah. Kan Mk ya kulle, ya rasa mai zai mata, ya yi fushin, ya bagarar da ita, Amma duk a banza, wai ya zai mata ne? kawai sai ya tsinci kansa da daga hannunsa sama yana cewa "Allah kasan irin son da nake yiwa Sa'adah, Allah ka shirya min ita, ka bude kirjinta ta gane gaskiya, ta fahimci bani da nufin zaluntarta, ka zaunar da mu lafiya, Allah ka kara min ha'kurin zama da ita cikin adalci". Ya kishingida yana tunano kafin shigowar su Halima cikin rayuwar aurensu, ko ya ya taga ya canja mata, ta dinga tambayar me ya same shi, ko itace ta masa laifi? Ta dinga bashi hakuri kenan, ko yace bata masa komai ba, kawai yanayi ne, ko baya jin dadi ne, duk da haka hankalin ta baya kwanciya sai ya dawo da walwalarsa, amma a yanzu kusan sati uku suna dauki ba dadi, amma kullum da abin da zata yi da zai sake bakanta masa Rai, karon farko da ya fara zargin Anya kuwa dama Sa'adah da gaske tana sonsa? Ya dinga hasaso yadda yake gudun zuciyarta, har wasu da yawa suna ganin tsoronta yake ji, alhalin ba haka bane, kawai tsananin sonta da yake yi ne, yasa baya shiri da duk abin da zaisa ta koka, mussaman na rashin wani abu, zai ha'kura da dukkan bukatun kansa, matu'kar ita zata wadatu. Amma duk su Safina sun lalata mata tunani, sun jefa mata shubuha, wai yan mata ne da shi na banza! Tabbas suna neman raba shi da ita ne. A fili ya furta " Allah kana ganin masu son shiga tsakanin aure, Allah ka min maganinsu". Sai da ya isa makaranta! Ya na cikin motarsa ya ciro wayarsa, ya lalubo lambar Anty Sumayya, cike da girmamawa ya gaisheta, sai kuma ya yi shiru ya na jin nauyin zartar da kudiransa. Jin yanayinsa yasa ta tambayarsa ko akwai matsala ne? Cikin jin nauyi ainun yace " So nake ki yiwa Sa'adah magana, mun dade cikin rashin nutsuwa, na yi iyakacin kokarina dan mu fahimci juna abin yaci tura, bana son na tayarwa da su Baffah hankali". Hakuri Sumayya ta dinga bashi, tare da al'kawarin yanzun nan zata kirata. Kai tsaye yace "ba waya a hannun ta". Jikin Sumayya ya sake mutuwa, shiyasa kwana da kwanaki tana gwada layin Iyah baya shiga, ta damu kwarai da rashin jinta, sai da Inna tace mata, lafiya ce take buya, Ni kaina an kwana biyu bamu gaisa ba, da kuma wata matsalar ce ai da mun ji, tunda mijinta kusan kullum sai yazo unguwar, kowacce juma'ah kuma zai shigo ya gaishe ni, ya bar Jawad sai zai tafi ya zo ya dauke shi, na fahimci Iyah! indai naji ta shiru haka, to cikine da ita. "Yanzu kana gida ne?" Ya girgiza kansa tamkar tana ganinsa "Ina makaranta, sai da yamma zan koma". Ai kuwa da yamma yan isa gida ba jimawa, Kiran Sumayya ya fado wayarsa, bai dauka ba, ya bawa Jawad wayar tare da cewa" sauri ka kai mata, Maman Gombe ce" dake tuni sun bar Jos tun shekaru biyu da suka wuce. Da gudu kuwa Jawad ya fita sai dai kafin ya isa inda take ya danna ok, ya fara yiwa Sumayya surutu, ita kuma ta biye shi, duk da ba komai take fahimta a hirar tasa ba. Fada sosai Sumayya ta yiwa Sa'adah, ta yi shiru tamkar tana jinta, sai da ta gama ta saka mata kuka tana fadin "Yana zaune da yan'uwansa kalau, amma ni yana ba'kin ciki da hadin kan dake tsakanina da ke, Ina zaune da shi ne kawai, amma ba irin wulakancin da baya mini, ya fifita farin cikin yan matansa akaina, ya koyo wata dabiar da ba tasa ba, ko kukan jini zai ga inayi ba ruwansa, shine har ya kawo karata?". Mamaki ya kama Sumayya tace "Ni kike fadawa wadannan maganganun? Eh na tabbatar Mijinki ba karamin ha'kuri yake da kaifin harshen ki ba, amma ki saurare ni da kyau, wlh idan baki canja ba, za ki jefa kanki a nadama mai yawa, wato ke har yanzu baza ki yi hankali ba? Kowacce mace da akwai inda take ha'kuri, ance miki auren wasa ne, ke naki ma wallahi ba matsala bace, kawai dorawa kanki kika yi, Ina ruwan ki da yanmatansa, ko aure yace zai kara Ina ruwan ki? Tun zuwan ku Jos na lura sai kin koya masa bagarar da lamarin ki". "Dan ke mijinki ba mai hayaniya bane, ba mai kule kulen mata bane shiyasa kike ganin bani da matsala" Sa'adah ta fada a tunzure. Cikin bacin rai sosai Sumayya ta ce "shikenan ki yi duk abin da kike so, ya dauka ina da wata kima a wurin ki! shiyasa yake ganin zan iya muku sulhu basai iyayen mu ba, amma tunda ban isa ba shikenan! Rayuwarki ce, kina da ikon yin duk yadda kika so, sai dai ki sani wadda bai ji bari ba, ba zai ki ganin hoho ba". daga haka ta kashe wayar ta, ta bar Sa'adah ri'ke da waya tana kunshekin kuka. Jikinta ya yi sanyi, tana Jin Aunty Sumayya uwace ta wuce ta yi misayar yawu da ita! Dan haka sai ta sake kira, Sumayya ta daga tana cewa "menene?" Cikin kuka Sa'adah tace "Na ji! kiyi ha'kuri". Sumayya da bata da zafi, tace "yauwa Iyata, ni nasan indai a cikin Innarmu kika fito ba zaki 'ki jin abin da na fa'da miki ba, saboda kinsan nan duniya bani da kamar ki, mu kenan iyayen mu suka haifa, ki daina duk abubuwan da mijinki baya so, ki kara hakuri, idan ma ke yake zalunta ki yafe masa, ki yawaita addu'a sai kiga Ubangiji ya warware miki komai, fiye da yadda kike zato! Yanzu abin da nake so da ke, ki bashi ha'kuri, kar kuma a sake tada maganar koma wacce iri ce". Sai da Sa'adah ta ja majina murya na rawa tace "Anty shine fa yake fishi da ni, yake ta share ni, ba abin da banyi dan mu shirya ba, ya ki bani fuska, kuma sai ya kawo karata?" Cikin rarrashi Sumayya ta ce "bafa kararki ya kawo mini ba, nasan dai kuna zaune kalau ba zai barki ba waya ba, nice dai na tambaye shi Kuna lafiya kuwa, yace na miki magana baya son ya shigo da Baffa cikin matsalar, iya haka ya fada min wallahi". "To Anti na ji fa'danki, amma shima ki fa'da masa idan ina kuka, ya daina cemin na dame shi da kukan banza, ko na iyashege, ya bar komai ya rarrashe ni". Sumayya ta 'kunshe dariyarta tace "Zan fada masa, amma ki bashi ha'kuri first, nasan kafin ki yi tuba sai tura ta kai bango, kullum ina fada miki hakan sifface ta girman kai. "Anty sanin da, kika mini, wlh na bashi hakuri, ta hanyoyi da dama, ai ba sai na fada da baki ba, shi da kansa yasan na bashi hakuri, kawai dai ya runtse idanuwansa ne". "To yanzu ki fada da bakin ki yasan Ina da mutunci a gurinki, idan na fada miki zaki ji! Idan kuma kin ki, shikenan, kin wula'kanta Ni, kin wula'kanta kanki". Da haka Sumayya ta risinar da Sa'adah, sun dade suna magana har sai da kudin wayoyin ya kare tas, sannan suka ha'kura. Da kanta ta kai masa wayar, duk da Jawad na cewa ta bashi ya kaiwa Malam! ta bashi wayar ta zauna gefen gadon Sannan tace " Malam ka yi hakuri dan Allah". Idonsa a rufe, bai bude su ba yace "Ni dama barcin da kike hanani yi da daddare ne, bana so, hakuri na zai iya :kwacewa, idan zaki yi kukan ki ban hana ki ba, amma pls stay away from me, na riga na gane ban da mutunci ko ka'dan a gurinki, zaki iya zagina kan ki tsaye, zaki iya fada min duk maganar da ta zo bakin ki, na zuba miki ido ki yi duk abin da kika ga dama, amma ki jira sakamakon zagin da kika min, na rantse miki! ba zai tafi a banza ba". Ya karasa da rawar murya saboda 'bacin rai. Hankali Sa'adah ya yi mugun tashi, mussaman yadda ya yi maganar da dukkan zuciyarsa, ta zuba masa ido tana ganin yadda yake numfarfashi tamkar wadda ya yi gudun fanfalaki, dan tsananin bacin rai. Ta zame ta durkusa a jikin gadon ta ru'ko hannunsa "ka yi hakuri, ba zan sake ba". Ya bude ido da suka yi jah yace "wallahi za ki sake, ba dai kin bada kofar da wasu suka shigo cikin rayuwar aurenmu ba? ba kin fi gaskata maganganunsu, sama da nawa ba, nace ban son su zo min gida, kin nuna ban isa ba, saboda kina jin isar gidan na ki ne, na sha jan kunnen ki akan kaifin harshen ki, amma kullum sake koyon dabarun ba'kaken magana kike yi, ki rubuta ki ajiye wañnan *HALIN YAU* din da suke cusa miki, kina dauka babu nazari bare tsinkaye, ba inda zai kai ki sai nadama, na fara gajiya da halin ki, hakuri na ya fara kaiwa geji gaskiya, Menene bana miki da kike wulakanta ni haka?" Jikin Sa'adah ya yi wani irin nauyi, zufa sai karyo mata take yi ta ko Ina, ta kasa bude baki ta yi magana, dan hatta harshen ya mata nauyi ainun, hawaye kuma tamkar an bude famfo, Jawad da yake tsaye yana kallon su, ya karaso ya fara goge mata hawayen, Yana cewa "biskit za ki ci? ko Malam ne ya doke ki?" Ta kasa magana kamar yadda hawayen ya ki yankewa,ya zuba musu ido yana ganin yadda Jawad ke goge mata hawayen,yana kuma fa'din ta yi shiru, zai goyeta a kekensa, wani irin abu mai kama da tausayi ya tsirga masa yana ayyana karfin soyayyar da ke tsakanin uwa da 'da. Murya a dashe Mk yace "ki ci gaba da kukan, so kike ya 'kullace ni, ya zaci kamar Ina gallaza miki ne, idan girma ya cimmmani ya'ki jin 'kaina" Da sauri ta dago manyan idanuwanta ta zuba masa, a fili akan idonsa tace " Malam plz ba kai bane, ka dawo wancan Malamin nawa! mai yawan yi min afuwa, mai tausasa mini". Ya mayar da idonsa ya rufe yace "shikenan ya wuce, dauki "danki ku tafi gurinki barci zan yi". "Ka yafe mini?" "Nace ya wuce" ya fada a gajarce. Taja hannun Jawad! amma yaron ya coge alamun ba zai bita ba, ta tsaya tana kallon sa ya hau gadon ya kwanta jikin Babansa, Mk ya rungume shi yana ji a ransa shima fa Jawad na sonsa sosai😀Mk manya. Kwana biyu, Sa'adah ta sauko, tana komai yadda ya kamata, ta bangaren Mk shima yana iyakar kokarinsa na bai sake yin wata maganar ba, zai ci abincinta, idan ta masa magana, yana amsawa kadaran kadahan, kawai a shimfida ne ba ya kulata, ta gama shure shurenta, ya yi biris, duk da shima fama yake da shan lemon tsami. Tana zaune tana tunanin mai zata masa ya ta'ba ta, hawaye na siraro mata, saboda yadda abin ya dagula mata lissafi, mussaman yadda ta san shi da rashin ha'kuri a wannan harkar, idan ta hasaso ko a waje yake samu sai ta ji tamkar ta sume, ta sake ramewa ta yi zuruzuru, kamar ance kunna radio, aikuwa nan ta ji sanarwa a gobe litinin hukumar zartarwa ta kwalejin tarayya ta kano (F.C.E.) zata rufe yin registration.dan haka duk dalibin da bai yi ba ya hanzarta kafin a rufe. Ta yi shiru, ta tabbatar Malam yasan ranar da aka bude dan farawa, dan kuwa yana da aboki da yake aiki a gurin, duk da ba lakcara bane.(Non academic staff)ne.wani sashi na zuciyar ta yace kika sani ko ya biya miki ne? Da haka ta samu sukuni kadan. A ranar bai dawo da wuri ba, dan haka ta danne komai ta barshi ya gama komai cikin nutsuwa, sai da suka kwanta ta bijiro da maganar da ta ji a radio. Tsawon lokaci ya mata shiru, zuciyarta ta sosu da wulakancin nan da ya tsira, ashe haka yake jin rashin dadi idan ya mata magana ta share? ta daure tace "kana tare da ni kuwa?". "Ina jin ki, na sani, har na biya miki, yasa hannun ya ja drowar gefen gadon ya fiddo da teller ya nuna mata, farin ciki ya mamayeta, kafin ta yi magana sai taji yana maganar da ta kasa gane manufarsa. "Na gama miki komai illah wurin da yake bu'katar signed dinki!amma a yanzu na fasa, matu'kar da aurena akan ki! wallahi ba za kije makarantar nan ba". Cikin rudu tace "Ban gane ba fa?" Ya tashi ya kunna fitila, sannan ya zauna! ya zuba mata ido yace "Ina nufin idan har sai da yardata zaki yi karatu, to baza kiyi ba, idan kuma ya zama dole sai kin yi, sai dai kije a matsayin single amma ba matata ba". Hawaye ya balle mata, ta ru'ko hannuwansa cikin rawar murya tace "Na roke ka kar min haka! dan Allah kar bari na gasgata masu fadin ba zaka taba barina na yi ilimi ba". Ido cikin ido yace "gara ki gasgata su Sa'adatu, ada kam na kudiri aniyar ilimi sai kince ya isheki! amma Billahillazi yanzu na fasa, ba ki fara karatun ba, kina iya zagina, bare kuma na baki damar da kullum sai kin fita, kin yi cudanya da mutane daban daban, tunda na gane kawaye zasu iya rinjayar ki, zasu iya canja miki dabi'a, zasu iya ruguza mana kyakkawan zaman mu, daga lokacin na gane barinki karatu mai zurfi ha'dari ne, ilimin sakandiren da kika samu, yasa kina jin kina da yanci, Ina kuma ga kin shiga babbar makaranta, ki zauna ki yi rainon Jawad kawai, tunda nace ki cire loop din nan, amma sun zuga ki, kar ki bari ki tara yara mu tsufar da ke, to ki zauna ki tabbata da kuruciya". Kuka take yi, tana bashi ha'kuri, yace "na gama maganata, zabi na gareki, dan kuwa wallahi ba za kije ki koyo mini karatun raini da rashin da'a ba, a haka kina iya zagina,nan gaba kuma sai dai na ji mari." Kuka take yi tun daga kasan zuciyar ta, a duk tsayin rayuwarta a duniya a ranar ta fara sanin Ashe kuka ma kala kala ne, duk wadda tayi a baya na nisha'di da shagwaba ne, na yau ne take yin na zunzuruntun bacin rai. Ya kalleta yace "Ba abin damuwa bane Wannan fa, domin na riga da na baki damar ki, dan hakama nake ta dan jah baya, dan mu dan saba da rashin tarayyarmu, Ina tabbatar miki idan kin zabi makaranta akan aure! Wallahi zan dauki nauyin karatunki, kuma zan wanke ki a gun su Baffa, zan dauki laifin rabuwarmu Ni ka'dai." Murya na rawa tsabar kuka tace, "Dan girman Allah yaushe na zage ka?" "Kina nufin na miki sharri ba ki zage ni ba?" Ta sake ru'ko hannuwansa da kyau tana harhado kalmomi tace " Ni bance haka ba Malam! amma dan Allah ka yi hakuri, na canja Wallahi, ba zan sake ba" "A ranar da kika zage ni dama na tabbatar miki u will pay for it! zaki yi karatu da yardata ka'dai, idan na gamsu kin canja din da gaske, idan na tabbatar ba mahalukin da zai canja ni a zuciyar ki". Ya zare hannuwansa daga nata ya mike, itama ta mike ta tsugunna ta ru'ko kafafuwansa, tana fadin "Malam bazan iya barinka ba, dan Allah, ba dan halina ba, ka janye wannan kudirin ina son karatun amma da yardar ka nake so". Yace "idan kuwa kina son karatu da izinina, wallahi ba bana ba, to be frank Sa'adatu! ban san time din ba, har sai na gamsu ba third party a tsakanin mu, sai na gamsu na wuce zagi da diban albarka ta kowacce fuska daga gareki". Ta sake shi! sanin halinsa idan ya rantse shikenan ya gama magana, ta ha'kura tana jin bakin ciki tamkar ta mutu! ta huta. Kuka ba irin wadda ba tayi ba, Mk da kansa mamakin kansa ya ringa ji, bai taba zaton zai iya mata haka ba, sai dai wata'kila yadda take gasa masa duk maganar da ta zo bakinta yasa ya iya jarumta haka. Sa'adah tana ji, tana gani, ya hanata makaranta, duk ta zama wani iri, zaman nasu dai gashi nan, ta koma shiru, ba walwala sosai, kullum cikin kunci take amma bakinta dif, sai kuma yanayin data koma ya dame shi, fata yake su koma kamar da, rayuwar farin ciki, amma abin na neman cin tura, a zahiri dai suna zaune lafiya amma kuma babu nisha'di a cikin zaman. Saboda su Halima da suke fadin "dama ai sun san pooling dinta yake yi, ba wata makarantar da zai barta, duk dan'iskan namiji zai yi iya yinsa ya kulle matarsa a gida saboda sun San Annabi baya tuntuben harshe, duk abin da ka yi da matar wani, sai anyi da taka. Wattanni kusan biyu zamansu ba armashi, bata masa komai na laifi, amma kuma ta dadare ranta, suna cikin haka, aka fara babban zabe na kasa, kowa yasan Malaman jami'oi ne baturen zabe, Dan haka wata guda aka dauka ana yiwa su Mk horo na mussaman kan yadda zasu kare muradan yan kasa, kar su yarda ayi amfani da su, ayi wa dimokaradiya kafar ungulu, Malaman addini suka dinga musu wa'azi na suji tsoron Allah su yi gaskiya a cikin aikin da za su yi, karshe suka rufe bayanin da cewa duk wadda aka bashi kudi dan ya yi magudi, to ya karbe kudin ya adana, sannan ya yi adalci, ma'ana ya fadi sakamako na gaskiya. A yanzu da suke shiga shekaru biyar da aure shi da kansa ya tabbatar tsoron ta yake yi, idan akwai abin da ya tsana to ta share shi, ko ta tsiri fushi, ko ya fita sai ya dawo, yasan yadda ya yi ya shawo kanta, yayin da ita kuma take jin kanta a sama komai take so sai ta same shi, SUMAYYA kanta mamakin yadda Sa'adah ta dawo take yi, kullum cikin tsadaddun sutura take , hatta salooon din da Sa'adah take zuwa one in town ne, kullum suka yi waya sai ta mata nasiha ta saukaka buri, ta rage dorawa mijinta hidimar da bai kai ya yi ba. Itakuwa sai tace da ba zai iya ba, ai da bai yi ba, ya hanani karatu ai kuwa dole yamin yadda nake so, tunda idan ban ci ba ma, na waje ne zasu ci, har Sumayya ta gaji ta zuba mata ido tana mata addu'a. Rannan da yamma Zainab Ma'aji ta ziyarce ta, kasancewar ana daukan lokaci kafin su hadu a dalilin Zainab din tana karatu ne a Jami'ar jahar kaduna(K.a s.u). ba kowanne hutun ma take zuwa Kano ba, sai take barin hoste ta tafi gidan kanwar mahaifiyarta ta yi hutunta indai ba mai tsayi bane. Mamamki ta tsaya yi ganin yadda Sa'adah ta koma, ta goge sosai, fatarta ta yi fresh tabbacin tana samun tsadadden mai, tasan Sa'adah Yar gaye ce, amma ko kusa ba kamar yanzu ba, da ta ke samun dukkan wants dinta. Sauyi sosai ta gani tunda ga jikinta, da abubawan more rayuwa na gidan, da cima ta mussaman, ga wata irin ginshira da ta gani a tare da ita. A sanyaye Zainab tace "Kin zama wata Hajiya ko big madam zance? lallai Uncle a gaishe shi, ina Jawad? hatta maganar Sa'adah ta canja sai anfitar mata da wani salo na daban. lamarin da Zainab ta dinga dariya tana fadin ko za ki yiwa kowa wannan iyashegen ban da ni. Suka yi dariya gaba daya sannan suka shiga hira, a gidan Mk ya tarar da ita, ta gaishe shi da girmamawa, shikuma ya dinga mata barka da zuwa cikin karamci, a dan dawowarsa da ya yi , Zainab ta fahimci abubuwa biyu, Uncle Mk ya gama lalacewa akan soyayyar kawarta, yayin da ita kuma Sa'adah take amfani da hakan take yin duk abin da take so. Zainab ta tsinci kanta da adduar ALLAH yasa su Halima ba su jefa ta cikin HALIN YAU na bin malaman tsubbbu, domin ta tabbatar tun shekarun baya da Halima bata gama sanin kanta ba, take zuwa gidan malamai, ko aiken uwarta ko na kanta. Har ta bar gidan tana jinjina wa Mk tana fatan Allah ya bata miji mai kwatankwacin halayyar sa. Manyan kudade Mk ya samu a zaben da aka gudanar, saboda karamar hukumar da aka kai shi, itace mafi yawan jama'a, ganin gwamnati mai ci zata sha kaye, sai ta hargitsa zaben wannan yankin, tare da kiran Mk har gidan gwamnati a sirrince, aka tura makudan kudade a asusunsa akan ya canja alkulluman zaben, ya karbe kudin kamar yadda aka sanar da su. bai canja alkulluman ba, amma sai sakamakon ya zama inconclusive, ma'ana bai kammala ba. Kwana biyu yana jin farin ciki, yana ayyana indai kayan 'kawa sune muradin Sa'adah zai mata su, zai kashe mata ko nawa ne dan zamansu ya dawo tamkar shekaru biyun farko na aurensu. Ba zato, ta ganshi da deep freezer, hankalinsa ya kwanta da ya ga Sa'adah ta yi murna, rabon da ya ga murmushinta sosai irin haka tun kafin su fara yar tsama. Tare suka fita, suka yi siyayya mai uban yawa da tsada, hatta Sa'adah da kanta sai da ta girgiza da irin manyan laces da atamfofi super, da kuma shadda getzner da Mk ya dinga dibar mata. matu'kar tace abu ya mata kyau zaice ta dauka. Barin takalma kirar itali da dogayen riguna rantsatsu, hatta turaren Escada da yasan tana so amma baya iya siyansa saboda tsadarsa, a wannan lokaci guda biyu ya siya mata, bayan kayan kwalliya na garari, suka zarce bakin asibitin Nasarawa, suka yiwa Jawad siyayyar hadaddun kaya masu yawa, hatta dan gidan Mahmoud da ya kasance jariri(Dady) sai da suka masa siyayya sosai. A hanyar su ta komawa ya bata labarin inda ya samo kudi, ya kara da cewa "Ina son na kewaye mana filinmu, a kuma fara ginin zuwa inda zai samu, a hankali kuma sai na dinga yi, har na kallama". Ya kalleta ya ga farin cikin ta ya kasa boyewa yace "ki nutsu ki fada mini irin tsarin da kike so a miki a ginin, nasan dai kina son garden?" Da azama tace "Da swimming pool, sannan upstairs nake so, irin wadda kafar benen zata kasance a tafken falo, a mini dining area, sannan kicin ya zama a cikin falon yake a fili, Ina fatan ka gane irin wadda nake nufi?" Cike da shauki yace "Na gane duk da bai gama zuwa mana ba, nasan kema a finan finan ketare kike ganin kicin din, ba damuwa za'a miki irinsa Ummu Jawad my dear". Ta rufe ido tana jin duk wani kunci na zuciyarta ya wanke mata tas. Shikuma yana ta barin jiki wirin sake sata walwala. Tafiya ya shirya musu zuwa Abuja, duk a kokarinsa na son dawo da amincin dake tsakanin su. Gidan Mahmoud da yake Goron Dutse, aka kai Jawad saboda makaranta, kuma yafi kusa. Ranar Alhamis suka tafi, sun Isa lafiya, karfe uku suna madaidaicin Hotel din da ya kama musu daki. Sallah suka yi, sai cin abinci ya biyo baya, wadda a hanya suka tsaya ya siyo, sai da suka koshi, suka yi wanka dan warware gajiya, sannan suka dora da sallar la'asar. Barcine ya gwada musu fin karfi, Mk ne yafara yi, Sa'adah ta zuba masa ido tana kallon kyakkawar fuskarsa, da yadda yake sauke numfashi a hankali cikin nutsuwa, wani irin shauki na mamayarta, tana jin sonsa na bin duk wata kafa ta jikinta. A haka itama barci ya wuce da ita ba zato. Sai daf da maghrib suka farka, suna mamakin lokacin da suka shafe suna barci. A gurguje, Mk ya dora alwallah ya fita neman massalaci, ai kuwa cikin sa'a bai yi tafiya mai yawa ba, ya samu. Kafin ya dawo Sa'adah ta ninke shimfidar gadon, ta dauko bedsheet din da ta zo da shi ta shimfida, ta sake dauko burner ta jona ta zuba turaren wuta, nan da nan daki ya dauki daddadan kamshi. Ganin lokaci ya tafi bai dawo ba ta gane sai ya sallaci isha lafin ya shigo. Ya dawo ya sameta cikin kwalliya sosai, ga sanyi ac da kamshin turarenta da kuma na turaren wuta ya cakude, dakin ya zama na mussaman. Da sauri ya yi wurgi da ledojin hannunsa wadda gasasshiyar kazace, sai kuma ruwa da yogurt masu sanyi. ya isa kusa da ita yasa hannun ya rungumeta tsantsan yana ta shin shinarta, ita kuma ta lafe a jikinsa tana jinta in a new world. Sun jima a hakan, kafin ya saketa, ya zauna a kasan kafet, idonsa ya kada, leda ta bude ta dauko plate da ta juye musu kazar, suna ci ta gabatar masa da shayi a dan karamin flask ga kuma cup da spoon a ciki, ya kalleta da murmushi yace "shiri kika yi haka?" Murmushi ta yi kawai. Suna kammalawa Sa'adah ta yo brush, ta hadawa Mk ruwan wanka. Kafin ya fito ta shirya cikin sabbin nighties masu daukan hankali. Ya fito daure da faffadan tawul, ya tarar da jallabiya da gajeran wando akan gado, ga kuma body spray dinsa na Malizia. Turaren kawai ya fesa ya dauke kayan ya dorasu kan side drower. Ya zauna sanyi dakin na ratsa shi, yana ayyana suna komawa zai sanya musu Ac. Tana tsaye tace "ba zaka sanya kayan ba?" Ido ya kanne tare da fadin "Ban bukatar su a yanzu". Kunya ta kamata, ta waske da fadin "Mai ba zaka shafa ba shima?" Maimakon ya amsa mata sai ware ya dukkan hannuwansa biyu alamun ta zo gare shi, ta tsaya tana kallon sa, ta kasa motsawa, yace "plz Dear come to me". Cikin kunya ta isa gare shi, ya zaunar da ita kan cinyoyinsa ya rungume ta tamkar zai hade su. Ta lafe a kirjinsa tamkar wadda zai shayar da ita, ya sunkuyar da fuskarsa daf da tata, numfashin su ya dinga haduwa, tsinin hancinsa akan nata, jikinsu ya dauki wani irin tsimi. Ya raba hancinsu, amma fuskokinsu a hade. Cikin wata murya da Sa'adah bata sanshi da shi ba yace "Ina sonki, ina son na rayu da ke! Dan Allah stay with me". Jikin Sa'adah ya yi la'asar, da murya marar amo tace "kana ganin zan iya barinka ne Malam?" "Matu'kar kina tare da su Halima, kina basu damar da suke cusa miki ra'ayinsu Ina tabbatar miki zasu raba ni da ke" ya fada cikin rawar murya. Kafin ta yi magana ya zarce da fadin "Ina miki son da zan sadaukar miki da komai, idan nace komai, ina nufin har rayuwa ta amma ke baki fahimci hakan ba" Ya sake ri'keta sosai, cikin wata murya irin ta karaya da lamari yace "Bana son kaifin harshe Sa'a, bana miki akan me zaki dinga mini? zan ro'ke ki! dan Allah fada mini inda na kuskure miki da ban cancanci ki zauna da ni lafiya da kyautatawa ba?" Ta yi shiru tana jin hawaye na cika mata idanuwa, haka kawai take jin tamkar wani abu na tashin hankali zai biyo baya. Jin shirunta sai ya zarce da fadin "ki bude baki, ki mini magana, ki fada min inda na gaza sai na gyara tunda ubangiji ya dora mini sonki da son zama da ke". Ta girgiza kai muryar ta na rawa tace "Ba ka gaza ba Malam". Ya nisa yace "Am not good in bed?". Kunya ta kamata, ta cusa fuskar ta a kirjinsa, yace "magana muke yi ta gaskiya". Ta dinga dan dukan kirjinsa tana cewa "Ai kasan dai kure ni ka ke yi anan ma." "Idan kuwa hakane, to mai ya kawo Kika canja, mai yasa kike bijire mini?" "Ka yi hakuri zan canja". Yaushe zaki canja din?". Ta tura mai Baki gaba cikin shagwaba tace "Na canja fah". Da'di ya kamashi ya dinga kai mata kisses ta ko ina tamkar mayunwacin zaki.hannuwansa suna ta kai komo a jikinta. Da kyar ya sarara mata, dukkansu sai numfashi suke mayarwa, daga inda yake ya mika hannu ya janyo ledar yogurt ya bude ya fara bata a baki, Yana cewa "ke Amaryace yau! irin Amaryar da ta kerewa mata hudu" Da'di ya kamata, ta sha iyakar shanta, ya shanye ragowan da ta bari daga nan ya sa harshe yana lashe mata baki, ya janyo harshenta Yana sucking irin deep din nan, daga haka suka fada zazzafar soyayya mai dimautarwa. Haduwar ta zama so ma sha Allah, saboda hadin kai da Sa'adah ta bayar, sabanin kwanakin baya da take zame mishi very doll. *Surayya Dahiru* ✍️✍️ 07/04. 🌺 *HALIN YAU*!🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. lafazee writers. *A guji taba Wañnan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *Doka mi lamba ta 68 ta yi nuna cewa satar fasaha Babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* *Tukuici ga* *HAJIYA RABI SANI* *Bisa yaddda kike son rubutun Halin Yau, Na gode, Allah ya shirya zuri'a* *SA'ADAH NA GAISUWA*. 71-74. Wannan dare ya shiga cikin dararen da ba zai shafe a zukatan su ba, saboda sun jiyar da junansu farin ciki na ban mamaki. Sosai Mk ya bawa Sa'adah soyayya da kulawa mai yawa, kullum suna tare ba inda yake zuwa idan ba masallaci ba, itama kuma bata komai sai gyaran daki, wannan hutun ya sabunta soyayyar su, ya kara musu shakuwa, ya kuma goge dukkan tsattsar dake zukatan su, aminci da Nishadi ya cika 'kalbinsu. Kwanaki biyar suka yi amma fahimtar da suka samu a cikinsu ya zarta na wattanni biyar. Ana gobe za su dawo da daddare, suna kwance ya rungumeta sosai tamkar zai maida su halitta 'daya, hatta bugun zuciyar su suna ji, sai dai bugun da zuciyar Mk yake yi ta zarce ka'ida. A hankali Sa'adah ta ce "Malam baka da lafiya ne?" Murya a dakushe ya ce "me kika gani?" "Bugawar da zuciyarka take yi yanzu ya sha ban ban". Cike da rauni ya ce "fargaba nake yi Sa'adah! bana son mu koma Kano ki canja mini, na fi son wannan rayuwar da muke yi, mai cike da nutsuwa da girmamawa". "Nace komai ya wuce fa, sannan ai na baka ha'kuri, mai yasa ba ka gamsu ba?" Kai tsaye ya ce "ki mini al'kawarin yanke kawancenku da su Halima, Ina rokon ki, ki rabu dasu, sannan ki mini al'kawarin baza ki dinga 'daga mini hankali ba, komai kike so a hankali zan miki kin ji? Ni dai fatana mu zauna lafiya". Haka kawai ta ji hawaye na zubar mata karon farko da ta ji tausayinsa ya cika mata zuciya, sai take jin tamkar mutuwa ce zata sure wani a cikinsu. Jin 'dumin hawayenta na zuba akan kirjinsa, yasa nasa hawayen da tun dazu yake kokawa da su, suka kwace masa! kwatsam Sa'adah sai jin saukar hawayensa ta yi akan goshinta, karon farko da ta ga ko jin hawayensa a cikin shekaru biyar da ta yi tare da shi, hatta mutuwar Hajiya Babba da ta masa mugun bugu, ita dai bata ga hawayensa ba. Kuka sosai Sa'adah ta saka tana cewa "Malam me kake yi haka, me na yi haka? me yasa kake zullumi har haka akaina? Kai baka ganin laifin kanka sai nawa ka'dai?" Da rawar murya ya ce " Nan duniya ba wadda zai cusa mini ra'ayi akan ki na yarda, saboda na fishi sanin ki, hakanan son da nake miki ba za bani kuzarin da zan cutar da ke ba". "Nima ba a cusa mini ra'ayi akan ka ba". Murmushi mai sauti ya yi wadda baya dau'ke da nishadi ko ka'dan. Ya ce "shikenan fatana dai ki kulle kofofin da kika bude wasu suke shigowa cikin matsalar mu, wadda Ni da ke kawai ta shafa". "To Malam ya maganar makaranta ta?" "Da gaske za ki yi, amma sai kin dawo mini Sa'adah ta, kinsan tun farko bana shiri da Gogel badan komai ba, sai dan rudeness dinta, shine yanzu zaki dawo mini a Gogel din?" Ta 'dan dara kadan! kafin ta yi magana, ya rigata da cewa "Ban so na fada miki yanzu ba, amma bari ki ji, kinsan naje Abuja na yi jarrabawar scholarship, idan na Sami nasara, zan yi PhD dina tsawon shekaru hudu a kasar England, so nake idan na tafi, naga da yiwuwar ku bini ke da Jawad sai ku bini, sai kiyi karatun ki acan, amma ba al'kawarin hakan na yi ba, Ina fatan dai hakan ya kasance, muna komawa zaku yi passport, na riga na yi nawa, idan hakan bai samu ba sai kiyi anan, kafin na dawo kinci karfin karatun ki". "Allah ya zaba mafi alheri" Inji Sa'adah. "Ameen ameen" MK ya amsa mata. Da haka ya shiga lasarta cikin wani salo mai gigitarwa, tsawon lokaci yana sarrafata kafin su fada duniyar masoya mai nauyin bayyyanawa. Karo na biyu da Sa'adah ta gasgata ana kwana ido biyu, a ranar basu runtsa ba, dan kuwa a kunnen su aka fara kiran sallar asuba, wanka Mk ya fito ya ganta kwance tamkar matacciya barci na kai mata caffa "Daurewa za ki yi, ki yi wanka ki yi sallah, sai ki yi barcinki". Da kyar ta tashi tana Jin dukkan gabb'anta sun mata nauyi wadda ba komai bane ya sababa hakan ba illah sububurdar da ta sha a hannun Mk hatta farcenta nauyinsu take ji, ya fice masallaci yana jaddada "kar fa ki koma". Ta yunkura ta nufi toilet din tamkar mai koyon tafiya, da ruwan mai zafi ta yi wankan, ta jima zaune cikin ruwan saboda yadda take jinta a bude, tana ayyana me yasa shi baya kaita toilet ya gasa mata jiki, ai yasan yau bai mata da sauki ba. A daddafe ta yi sallah, akan sallayar ta kudundune tana ta fama da kanta tare da fatan ta sami barci ko ta dawo daidai. Koda ya dawo ya iske ta a kasa, murmushi ya yi sannan yace "ga ta da kwadayi ga kuma lalaci". Ya dauke ta cak ya dora a gado, ya cire jallabiyarsa, sannan ya kwanta ya lullube su da bargo, a tsarinsa so ya yi su tafi daidai wannan lokacin, rashin barcin da bai yi ba, yasa ba zai iya tuki cikin nutsuwa ba, dan haka ya kwanta yana raya ko da la'asar zasu iya tafiya kaduna, su kwana acan, jibi da safe sai su wuce Kano, a lokacin hanyar Abuja zuwa kaduna cike take da aminci da tsaro, Allah mun tuba, Allah ka dawo mana da aminci da tsaro a yankin arewa da Nigeria gaba'daya. Lafiya Lau suka dawo kano, a gidan su Mk suka fara tsayawa suka ci abinci, Hajiya sai Ina ka saka ta ke yi da su, mussaman ta dinga murnar yadda ta ga Sa'adah ta yi kiba ta yi kyau alamun ba ta da matsala. A lokacin Sa'adah ta ga freezer Hajiya irin ta su ce, da alamun tare ya siyo musu, sai cinikin kankara da pure water take yi kuwa. Ta gabatar musu da abinci wadda shinkafa da wake ne, da miya sai salad, yayin da Sa'a tace da mai da yaji take sha'awar ci, da hanzari Hajiya tace duk Ina da su, ta fice cikin sauri tana ayyana Allah ya sa ciki ne da ita. Ta dawo ta ajiye mata tana cewa " jiya Mahmoud ya kawo mini Jawad, ku shiryawa darunsa dan yace ba ruwansa sa da ku, tunda kuka gudu kuka barshi shi ka'dai. Suka zube mata doya da dankalin turawa da tuffa, sannan suka tafi, ga mamakin Sa'adah sai ta ga ya sauka kan titi ya fada layin unguwar su, farin cikinta ya kasa boyuwa ta ce "Na gode Malam ". Tare suka shiga gidan suka gaisa da su Baffa da yake yana gida yana fama da mura, sun dan jima tare da Baffa sannan ya fice dan dubo shagonsa. Hira sosai Sa'adah suka sha a lokacin kuma ta ga gyaran da aka yiwa gidan nasu. Baffa ya kalleta yace "Iyah Dan Allah ki dinga yiwa mijinki biyayya, ki kyautata masa, ki zauna da kowa nasa bisa karamci, ki ga yadda Gidan nan ya dawo duk aikinsa ne, Ni kam ba abin da zaki mini ki sanya ni farin ciki irin ki zauna da mijinki lafiya da kyautatawa, mazajenku suna wanke mini takaicin rashin haihuwar Namiji, ba abin da zance musu sai dai Àllah ya yiwa nemansu albarka ya shirya musu zuri'a". Inna ta amsa masa da "Ameen ameen". Suna cikin haka almajirai suka shigo da doya da dankali. Mk da Sa'adah sun sha albarka da nema musu tsarin shaidan da makiya. Da zata tafi Baffa ya ce "kice da mijinki ranar juma'ah ya taho mini da Jawad na kwana biyu ban ganshi ba, kewarsa da ta surutunsa ne suka sukurkutani ba mura ba". Dariyar jin dadi ta yi tare da cewa "Zan fada masa kuwa Baffa". Ranar wata alhamis ta ce ya kaita asibiti ta cire abin tsarin iyalin da ke jikinta, da kansa ya ce ta bari suga ko tafiyar za ta yiwu, sai ta cire a can. Sosai suke zaman lafiya, saboda Sa'adah ta daina zungurar rigima, shi kuma yana kaf kaf da farin cikin ta. A haka har suka kwashi wattanni biyar. Rannann ya dauketa suka je filinsa da ake ta aiki, ya dinga nuna mata yadda fasalin ginin zai kasance, amma bata fahimci komai ba. Sai da suka dawo ya dako littafin zanen gidan ya nuna mata, ta yi muranr ganin katafaren gidan da zai zama mallakinsu, sai dai ta kalubalanci ta yaya kafar bene zata zama biyu?. "Ke kika ce kafar bene a falo kike so? wannan kuma ta baya ne sai kin shiga corridor sai ki ga kafar benen, idan Ina sama, kina da bakin ki, zan fita ta bayan, ko kuma idan Ina tare da bakina baki da matsalar komai, bari a gama, na tabbatar zai burge ki. Ta tura baki gaba ta ce"Na ga sama ma katon falo ne ga dakunan barci tamkar na 'kasa sannan har da kicin, ko dai na Amarya ne?" Ta fada tana matso 'kwalla, ya wurgar da littafin, ya ru'ko ta jikinsa ya ce, "Ke ce uwargida kuma amarya ta, da gaske nake kin cike mini gurbin mata hudu, ki daina wasiwasi akan maganata, ko an kaddara mini zan 'kara aure ina tabbatar miki, ba zan hada ki da kowa a gidan ba, daga ke sai yaranki ki yi yadda kike so". "Ban cike gurbin mata hudun ba kenan?" "Oh Sa'adah! kin zarta mata hudu ma, kawai ban son na miki al'kawarin da za'a jarrabe ni da rashin cikawa ne, kinsan bamu muke tsarawa kanmu rayuwa ba, idan haka ne kuwa bai kamata mu yi katsalandan akan goben mu ba, Ina tabbatar miki a burina ke kadai kin isheni rayuwa, sannan har yau ban taba jin son wata a zuciyata da ya kai matsayin da zan aurota ba". Ta lafe a kirjinsa tana jin dadin yadda ya ke rawar jiki idan za ta botsare masa. Kudin da Mk ya samu sun yi albarka kwarai da gaske, ya fadada shagon askin sa, ya sake budewa Ahamad wani shagon, hatta gidan da suke ciki ya sha gyara na mussaman, ya sakewa falonsu kujeru da sauran abubuwan more rayuwa da ya dace da ra'ayin gimbiya Sa'adah.ya kuma biya kudin aikin Hajj. Sa'a kam ba a maganar yadda take lasar kudi har gold ya sai mata, waya ce dai bai siyi wacce take so ba, amma ya bata waccan da ta raina da kuma ainihin tata da ya karbe. Baba Isa da su Baba umaru duk Sun Sami tagomashin inconclusive, duk da dai dama akai akai yana waiwaryasu da abin da zai iya na Alheri da neman albarkar su. Shigowar what'sapp ya taimaka wurin tabarbarewar tarbiya, a farkon shigowar sa ya rudi mutane da yawa mussaman Mata dan hatta abinci sai andauka an dora a WhatsApp, gida mai kyau kuwa kullum cikin tallansa ake yi. Ya zama ba sirri, mussaman idan mace tana cikin wadata ta hanyar status take bayyana matsayin ta, hakan ya sake jefa Sa'adah cikin buri sosai kullum cikin kara son kayan garari ta ke . Sannu a hankali aka fara bude groups daban daban ciki har da na tsofaffin dalibai, babbar mastalar group din su Sa'adah hade yake da mazan set dinsu tunda makaranta tasu hadaka ce da maza. A haka Khalil ya samu numban ta, suke gaisawa lokaci zuwa lokaci, duk da baya nan yana Egpt yana karantar sociology. Ta hanyar what's app ya mallaki hotunanta dana Jawad, idan ta yi status zai yi saving, ba a karan kanta ta ke tura masa ba. Haka Kuma taron tsofaffin dalibai (reunion) sai ya zama ruwan dare, ko Ina taron tsofaffin dalibai ba 'kak'kautawa. A wannan lokacin FGC Kano ta shirya nata tunda ga kan daliban farko har zuwa daliban da suka kammala a shekarar taron. Taron ya kai taro, mafiya yawa daliban ma'aikatane ko manyan Yan kasuwa' har tsoffin Malaman duk sun halarta, dan haka Mk ma ya je, manyan mata masu aji, wadda suka yi wanka da ilimi da gogewar rayuwa duk sun kewaye harabar makaranta. Sai farin ciki ake yi, mafiya yawa kuma cikin shiga ta alfarma suke, Sa'adah na cikin jerin da basu da makusa tun daga kan suturarta har zuwa fatar jikinta, kawai na'kasun ta 'daya ba a motar kanta ta je gurin ba, bata ji muzanci ba, sai da Mk yace mata zai tafi idan sun kammala ta wuce gidan Inna zai 'dauketa acan. Kusan 'Yan set dinsu kowa da mota ta je har 'yanmatan cikinsu, Halima a motar Safina suka je, motar da Sa'adah taga Farida a ciki ta matu'kar tsaya mata a rai. Hira ake ta yi, ana zuga wadda rayuwar su ta yi nasara ta hanyar kambaba lamarinsu, wasu kuma ana yi musu gadar zare, daga gefen su Sa'adatu, wasu matan ke hirar da ta ja hankalinsu, duk da seniors din sune sosai, 'daya cikin matan ta ce "Ni da aure kuma mun yi hannun Riga, ba komai a cikinsa sai jidali, da hawan jini, baka da ikon yin komai na ra'din kanka, sai ka jira namiji, sannan baka da 'yanci ko kadan a aure". 'Dayar wadda da alamun ra'ayin su daya da wadda ta kammala bayani itama ta cafe da cewa "ai kuwa dai lubna da gaskiyar ki, dare, asuba, tsakar rana kowanne lokaci miji saka'dar ka yake yi tamkar jaka, amma da za ka bijiro da bu'katar ka, ba za'a maka ba, ko za'a maka din kuwa sai ka gama wulakanta". Lubna tace da Asiya "Ashe kin gane karatun! dan haka tsakanin mu da namiji a hadu ayi ar'kallah kowa ya kama gabansa, yanzu kiga da ka ke cin gashin kanka cikin kankanin lokaci ka mallaki abubuwa masu daraja, wadda macen aure sai ta shekara fiye da ashirin ba ta mallake su ba". Wata cikin su, tana bude Baki ta ce "Amma kuma matan aure sun muku zarra da mutunci da kuma 'kima, macen aure tana tsufa tana sake daraja, adalilin gatan da musulunci ya mata". Dukkan su suka sa mata dariya, suna ganin wautarta, Lubna ta ce "kai ku rabu da Hajara kunsan tunda ta gama wannan makarantar ba ta sake shiga aji da nufin zurfafa ilimin ta ba, kenan kanta a duhu yake bata san komai ba, tana cikin jerin matan da maza suka rufe a gidaje suke gallaza musu, suka kuma hana su fahimtar cigaban da duniya ta samu" Su Halima da suke jin tattaunawar suka kwashe da dariya suna fadin "ai yanzu duk wadda ta zauna namiji na mata mulkin kama karya mata ta rako duniya, a wannan karnin da ilimi shine komai yaushe zaka yarda a barka da jahilci, barin ma idan mijin naka mai ilimi ne? Da zarar muguntar namiji ta motsa sai dai ki ji ya amarce da mai ilimi, ko kiga yana jin kunyar ya saka ka a al'amuransa". Jikin Sa'adah ya yi sanyi ganin itama cikin rukuninsu ita kadai ce mai sakandiren, haka akayi ta kutsiri tsoma, ba a gama da wannan maganar ba, a saketa a kamo wata, da za su tafi, a motar Safina suka dunguma har kofar gidansu suka kaita, a hanya suka yi hirar Humaira Suraj da a yanzu take aure a sokoto, dama can ne garinsu aiki ne kawai ya kawo mahaifin ta Kano. Tun wannan lokacin Sa'adah ta fara canjawa, ita da kanta tasan ba abin da ta nema ta rasa illah motar kanta ba wai ta Mijin ta ba, amma zuciyar ta sai tsalle take mata tana ganin kamar ita ta wuce komai sai ta jira iznin miji kafin ta zartar, tana bu'katar ta zama yantacciyar mace mai yin komai babu 'dar balle fargaba. Kullum a WhatsApp su Halima na sake kuranta kyakkawar siffarta, har suna cewa ba wadda zai ganta yace ita ta haifi Jawad, ko su da suke 'Yan mata basu fita komai ba. Suna cikin wannan zaman na ba yabo, ba fallasa, Su Halima suka zo mata da kaya cike da katuwar leda, kana ganin ledar kasan tafiyayyace, sai da aka bude kaya, suka ga kayan Jawad ya kai set biyar, sai agogo na English gold, da kuma waya blackberry bold 4, da tarin alawowi da biscuit duk tsaraba ne inji Khalil abawa Jawad waya da agogo kuma nata ne. A kidime Sa'adah ta ce "Na shiga uku Safina idan Malam ya gani fa, da me zan kare kaina? Gaskiya bazan karba ba tsoro nake ji. Harara Suka galla mata, Halima tace "to kuma barinsa zaki yi ya gane daga inda suka fito, sai an kwana biyu kice Anty Sumayya ce ta aiko muku, waya kuma ki boye abarki sai ba ya gida, ko idan zaki je taron fitar kunya, na gaji da ganin ki da karamar android shiyasa na fa'da masa baki da wayar shiga taro". Safina ta dora da cewa "Da yake ya damu da farin cikin ki kasa da awa ashirin da hudu da fa'da masa ya siyo, ya bayar akawo miki, gaskiya Gogel kin tafka asarar masoya, na tabbatar ko yanzu da kika zama uwa, Khalil zai aure ki a matsayinsa na saurayi". Suka hada baki wurin cewa "duk da ke 'din ma kinfi 'yanmata da yawa nagarta". Tun lokacin hankalin Sa'adah yafi karkata kan wayar nan, kullum Mk ya fita za ta fito da wayar ta, ta yi komai, mussaman take da layi na daban a ciki, amma da layinta ta bude komai. Tun Mk na tambayar ba'asin canjinta har ya gaji, yana ganin ya kyaleta ya huta shima, dan taga yana damuwa ne shiyasa take masa wulakanci, dan haka ya rungumi sabuwar rayuwar da ta bude musu, hatta a shimfida ta canja, ba wai gudunsa take yi ba, kawai zama take yi tamkar gunki, sai dai ya yi kidansa ya yi rawarsa shi ka'dai. Haka nan abu kadan Jawad zai yi ta rufe shi da duka tamkar wadda take dukan babba. Wadannan dabi'u suna matu'kar ciwa Mk tuwo a 'kwarya mussaman dukan yaron da ta tsira, ko abu ne ya hadasu sai ta huce akan 'dansa. Rannan suna kwance sun gama mu'amalar da ba gishiri a cikinta balle Maggie, ran Mk a bace yake sosai, ya rasa mai zai mata kuma, ya riga ya kai gejin rarrashinta, ya gane gaba'daya kwakwalwar kifi ne da ita. Ya yi gyaran murya ya ce "tsakanin ki da Allah ki fada min me kike nufi da ni, rokon ki nake yi, yanzu na tabbatar ba kya sona Sa'adatu". Yana rufe baki ta ce "Kaine dai baka sona, komai zan yi a laifi na ke, 'dazu ba ka ga irin 'barnar da Jawad ya mini ba, dan na dake shi, ka hayayya'ko mini, salon kasa ya raina Ni". "Amma tun ba yau ba ki ke wannan fizgewar, yaushe rabon da ki saurare ni cikin da'din rai, kullum da bacin rai kike yarda da ni, ko kin yarda kai tsaye to sai dai ki zame mini tamkar gawa, anya kuwa dama kina sona? anya kina jin tsoron hakki na akan ki, amma na yafe miki, na kuma dauki laifin ko menene ki yi hakuri ki yafe mini". Ta tura baki ta ce"Tun yaushe nake ce maka zan dubo mahaifiyar Halima da ta yi hatsarin mota, duk yan ajin mu sun je banda ni". Murya ba amo ya ce " Hana ki dubo uwar Halima yasa ki ka na'de kafar wandon yin min wula'kanci haka?" Ta yi shiru ta kasa cewa komai saboda ta ga ya hassalo sosai, ya furzar da iskar bacin rai ya ce "Shikenan ko da wani laifin bayan wannan?" Kamar shasha ta ce "yauwa ni fa yanzu nake son motar nan, na ga kai kuma kana nufin kamar sai anja lokaci, kawai ka dakatar da ginin ka siya mini". Ya kalleta ido cikin ido ya ce "yin hakan shine sharadin samun zaman lafiya a tsakanin mu?" Ta kasa amsawa tsawon lokaci, dan haka ya ce "Ba wadda zan miki ko 'daya, idan ya so zaman namu yafi haka muni". Ta tashi ta fita tana 'kun'kuni, akan sai ta je, ta gaji da 'yadda ya maidata bagidajiya marar yanci, kansa ya sara yana jin ba'kin cikin ta na neman kassara shi. Haka har kwanaki uku suna zaman doya da manja, Rannan cikin dare ta ji hannunsa na lalubarta, ta zabura kuwa ta bige hannun, tare da fadin "Bana so". Bai saurare ta ba ya damko ta, ya fara kokarin gwada mata 'karfi saboda ya gaji da rarrashinta. Ganin da gaske zai cimmata alhalin ta riga ta kudiri aniyar ba za ta saurare shi ba. Dan haka ta fashe da kuka ta ce " raping dina za ka yi? na fahimci bani da mutunci a gurinka indai ba bu'katarka ce ta ciyoka ba, na daina ganin aibun 'yantattatun mata wadda suka juyawa aure baya, saboda sun san ba komai a cikinsa sai ba'kin ciki da takura da kuma 'bacin rai". Jikin Mk ya mutu yana rike da ita, da ta lura, tashin hankalin da ke zane baro baro a fuskarsa ba zai bari ya ci gaba da rarrashinta a YAU kamar yadda ya Saba ba. "Matan da suke zaman kansu, duk abin da suke so, aguje suke samu, amma matan aure sune agaba wurin samun hawan jini saboda tsabar bakin cikin da mazajensu suke 'kulla musu". 'Kololuwar tashin hankali Mk ya shiga, ji yayi jiri ya kwashe shi dan ma a zaune yake, ya tafi luu ya buge 'keyarsa da fuskar gado. Da kyar ya dauki hannunsa ya ri'ke kansa da yake tsananin sarawa, da karfi ya dinga ambaton" innalillahi wa Inna ilaihir raji'un". Ya dade yana nanata kalmar, har ya dan sami nutsuwa kadan, ya mike ya saka rigarsa da wando, ya ware murya sosai ya ce "Ni ki ka fadawa wannan maganar? Ashe kuwa har yau baki gane ni ba, zan nuna miki ba a bariki muke ba, ba kuma auren bariki na ke yi ba, ki ri'ke dukkan abin da ki ke tun'kaho da shi bana so, ki ji'ka ki shanye abin ki, amma ki sani yau da Gobe zasu biyar da ke indai kina sha'kar numfashi". A daren ya dauke dukkan abin da yake nasa ne a cikin dakin Sa'adah, sai Agogon hannunsa da yake cikin wadirof dinta ya manta bai dauka ba. har ya kwanta ya tuna bai dauko tawul dinsa ba, ya koma ya dauko, kafin ya fita ya tsaya ya kalleta tana zaune duk jikinta ya saki da alamun ba tasan girman munin maganar data furta ba, sai bayan ta fada. A kausashe ya ce "Na tsane ki, na tsani na bude ido na ganki, ba dai kin fi sha'awar rayuwar 'kazanta akan ta sunnar Ma'aiki ba? kin raina duk kokari na, kin raina ni'imar da kike ciki, Na rantse miki! ba dan kunyar Baffa ba, da a yau na mayar da ke 'yantacciyar macen da kike fata, ni kaina NADAMAR auren ki na ke yi, amma na gode Allah da nake ganin sakamakon son zuciyata a duniyar nan, ba sai naje lahiraa ba,'kiri 'kiri na nunawa mai sona da gaskiya HALIN YAU, na butulci". Ya juya ya fita ya barta cikin rashin sukuni mai yawa. Tun daga ranar ya bala'in dauke mata wuta, idan ya fita tun safe, sai dare ya fara turawa zai dawo, sannan matu'kar yana gida to kuwa kofar dakinsa a gar'kame ta ke hatta Jawad ba kasafai yake ganinsa ba, kullum cikin tambayar Sa'adah Ina Malam ya tafi?". Wannan ne karon farko da ya yi fishi ba waiwaye, hatta fuskarta baya son gani a yanzu, sabanin da da ganinta shine cikon farin cikinsa, har yau fama yake da ciwon da bakaken maganganun suka sababa masa a zuciya yake yi. Ana haka mijin Sumayyah ya yo waya akan bata da lafiya sosai, haihuwa ne ta zo mata da tangar'da anmata C's an fito da yaro amma kuma bata da lafiya. A ranar Baffa ya sanar da Mk, akan gobe za su yi asubanci zuwa Gombe shi da Inna, idan ba damuwa ko zasu tafi da Iyah ta gano jikin yar'uwarta. Bai yi nauyin baki ko kunya ba, ya ce "Zan zo na kai ku Baffah amma ita daga baya zata je". Godiya sosai Baffa ya masa tare da fadin "ko bata je bama ai kai kaje , ka wakilceta". Haka akayi tafiyar Sa'adah ko labari bata ji ba, a ranar Baffa suka juyo da Mk, da kuma Hajiyar Bichi da ke ta bisu, suka bar Inna dan ta kula da Sumayya, kafin Umma fanshekara ta je sai Innan ta dawo. Ganin da innah ta yi har washagari Iyah bata 'kira ta yi jajen mai jiki ba, sai hankalin Inna ya tashi tana tunanin ko itama ba ta da lafiya ne? Tana Shirin 'kiranta, sai ta 'kira suka gaisa, mamaki ya sake kama Inna ganin ba alamun ta samu labarin halin da 'yar'uwarta take ciki, dan haka sai tace "mijinki bai fada miki Ina Gombe ba?" "Wallahi bai fada mini ba, wani abin ne ya faru?" ta tambaya a kidime. A sanyaye Inna ta ce "yayar taki aka yiwa tiyata ga yaro nan lafiya lau, sai itace bata Jin dadi, amma dai da sauki". Cikin muryar kuka ta ce" shine ba ki fada mini ba Inna?". "Mijinki ne fa ya kawo mu, jiyan suka juyo da Baffanku, Kinga ai bana yi zaton ba ki ji ba, duk yadda akayi ba zaman lafiya kuke yi ba Iyah, tunda da bakinsa yace baza ki zo ba, sai muka dauka ko kema ba Kya jin dadi ne ya rufe mana, har da Hajiyar Bichi muka zo, duk jiyan suka juyo". Kuka kawai Sa'adah ta ke yi, irin kuka na rashin madafa, sosai kukan ya ta'ba Inna, tashin hankalin ta ya 'karu ga na Sumayya da ta ke kwance bata san wadda ke kanta ba, ga na Iyah da ba tasan ha'ki'ka in matsalar ta ba. A sukwane ta kira Baffa tace lalle akwai matsala tsakanin Iyah da Mijinta, cikin rashin daukan maganar da muhimmanci ya ce "Mijin ta bai kawo 'kararta ba, ita ba ta ce ga laifinsa ba, sai kawai naje na hau bincinkarsu, tunda sun iya 'boye sirrinsu, sai a bisu da addu'ar Allah ya daidaita su". "Ka shiga maganar nan, da alamun fa abin babba ne, hatta zuwan nan da ya yi Gombe bata sani ba, kar a zuba musu ido fa". "To" ya ce mata a gajarce ya katse wayarsa! yana cewa lamarin mata yana da ban mamaki, kawai dan kina so a tursashi ya barta taje inda baya so taje sai kice naje na shiga tsakanin su, duk tsawon lokacin da suke tare waya ya san yadda suke zaune? Haka kwanaki suka yi ta shudewa a cikin Wannan hali tsakanin Mk da Sa'adah, kullum 'kara nesanta kansa yake da ita, zuwa yanzu da suka cika sati biyu cikin wannan halin, wadda ko a mafarki bata yi zaton zai iya shareta har haka ba, domin tun ranar da ta yi wannan katobarar bai sake bin takanta ba, asalima ta lura bai son ganinta ne har zuciyar sa, tana ganin idan ya dawo a gaggauce yake shigewa dakinsa ya rufe kofa, hakanan idan zai fita a hanzarce ya ke ficewa, duk yadda bai son ya ji kukan Jawad amma a yanzu duk kukan da zai masa ba ya tsayawa ya bi ta kansa. Ta shiga damuwa da tsoro irin wadda bata taba shiga ba, tsoron ta 'daya idan iyayenta suka ji mai ya jawo wannan tashin hankalin, wanne irin kallo zasu yi mata,? Ta 'kudiri aniyar yau zata bashi, ha'kuri ta kuma nemi ya barta taje ta gaida Aunty Sumayya. Haka akayi, taran dare ta yi wanka, ta shirya cikin kwalliya ta burgewa, tana jin dirin motarsa da kiciniyar bude gate, ta fita a hanzarce ta shiga kicin mai ma'kwabta ka da 'dakinsa ta tsaya. Ai kuwa ya shigo da sauri, ganinsa rungume da kayan wankinsa da ya kai wanki, jikinta ya sake yin sanyi, komai zata yi masa, idan zai kai wanki zai shiga har 'dakinta ya hada kayanta akan nasa ya kai musu wankin amma banda Wannan karon. Kafin ta yi yunkurin shiga dakin nasa sai ta ga ya fito ya fita da alamun ya yi mantuwane, dan haka sai ta yi wuf ta shige 'dakin, yana shigowa kuwa ya rufe 'dakin bayan mukulli har da sakata ya sanya. Yana shigowa ya ganta lafe jikin wadirof, ga mamakinsa sai yaji kwalliyar da ta yi, bai ji komai na burgewa akanta ba, hakanan kamshin ta da ya cika masa hanci bai yi tasiri a jikinsa ba, kyakkawar fuskarta da ke sanya shi nisha'di, a yau ba'kanta masa rai ta yi, hakanan surarta da ke jefa shi cikin shauki, a yau takaici ya ji ya maye gurbi. 'Bacin ransa ya dawo sabo fil tamkar yanzu take gasa masa maganganun da suka zame masa tamkar 'digar dalma a zuciya, suka yi awon gaba da kaso mai yawa na matsananciyar soyayyar da yake mata. Baice mata komai ba, ya shiga rage kayan jikinsa, ya shige wanka, tana tsaye ya fito ya shirya, ya tada sallar shafa'i da wutiri. Sai da ya idar ya zauna bakin gado ya kalleta, ya ga duk ta takura, ta susuce, ta lalace, idonta ya fada alamun dai tare suke 'dan'danar 'bacin rai. Kafin ya yi magana ta rigashi! Ta tsugunna ta ri'ke gadon ta ce "Dan Allah Malam ka yi ha'kuri, ban taba jin nadama irin wadda nake ciki ba". "Ba ki mini komai ba, abin da ke zuciyarki ki ka amayar, sai dai ina so ki sani wallahi ba ki fara nadama ba, ina tabbatar miki za ki shiga NADAMAR da ta zarce wadda kike ciki, da kinsan yadda na tsani ganin ki da hakan ka'dai ya isa ya saki nadama, da kinsan yadda kika wanke kanki a zuciyata da kin gane asarar da kika yi ba ka'dan bace". Kuka ya goce mata, ta rarrafo da nufin ri'ke shi, ya zabura ya mike tsaye cikin bacin rai ya ce "idan kika yi kuskuren sa hannun ki a jikina, na rantse miki sai na miki abin da za ki gamsu ba ki da sauran 'kima a gurina. domin duka zan miki irin yadda ake na'dawa 'yantattatun matan bariki idan angama cin moriyar su". Kukan ya tsaya mata! da gaske ta yi kuskure, irin kuskuren da ake yi sau daya amma sai an nemi hanyoyi gyara dari bai gyaru yadda ake so ba. daga jiyo magana a bakin shedanun mata ta ara ta yafa, har ta zo ta fa'dawa mijin aurenta wadda da gaske samun irinsa zai yi wahala. Ta zauna 'dabas tsakanin gado da wadirof ta dinga kuka, mai cin rai, na tsantsar nadama. Daga inda yake ya ce "Ta shi ki bar mini 'daki ban bukatar ki a cikinsa". Ta kasa koda kwakwkwaran motsi. tace "ka yi hakuri ba dan ni ba, ka dubi girman Allah ka yi hakuri". Jikinsa ya yi sanyi yace "Na ji, amma dai tashi ki fita, ina bukatar ka'daici ne, duk sadda nake da bu'katar ki a dakin I will let you know". "To ka daina rufe 'dakin, na yarda duk sadda na zo ka kore ni, amma ka daina rufewa". Ya zuba mata ido yana jin takaicinta na sake kama shi, amma da yake so yake ta fita ya shaki iska marar takura sai yace mata to a takaice. Ganin ya amsa mata sai ta tashi ta bude 'kofar ta fita tana fadin " ka yi hakuri, ka yi barci mai cike da walwala". Ya bita ya rufe kofar, ya dawo ya karanto adduar barci ya kwanta. Washagari da sassafe ta shirya masa abincin karyawa ta zauna zaman jiran ya bu'de 'kofar, ai kuwa yana budewa ya ganta da tiren abinci, a bakin kofar dakin, yasa kai zai wuce ta ce, " Ina kwana?" Ya amsa a gajarce, "ga abinci na gama". ya girgiza kai ya ce "ki daina wahalar da kanki wurin yin abinci saboda Ni, na riga da na 'yanta ki daga dukkan yi mini hidima kowacce iri ce". "Cikin rawar murya ta ce "kace fa ka yi hakuri?" "Da ban yi hakuri ba, da baki ganni akan 'kafufuna ba, da ina can akan gadon asibiti saboda ba'kin cikin ki, da ban yi ha'kuri ba, da ban tsaya ina miki magana ba". Ta goge hawaye ta ce "ka kara hakuri dan Allah nasan na yi ba dai dai ba". Ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba, ya fara tafiya, da azama tace " Malam! Umman fanshekara gobe zata tafi Gombe, dan Allah ka bar ni mu tafi tare, ni sai na dawo ko jibi ne". Ya juyo a zabure tamkar wadda ta fadi mugun abu ya nunata da yatsa ya ce" dama nasan duk wannan saukar da kan da kika yi, kina da bu'kata ne, ba kya tashi mutunta ni, ko kwantar mini da kai sai kin ganni da kudi, ko kina son na barki kije wani guri". Cikin kuka sosai ta ce "Haka ka dauke Ni?" "Kin wuce hakama ke kam, saboda ke ciki ce mai manta kyautar jiya, mai manta alheri, da kina da hankali, da baki cemin za ki tafi yawo Gombe ba, kawai tafiya za ki yi kanki tsaye". Ta zuba masa ido ta ce "dubo Anty Sumayya ne yawo?" A kausashe ya ce "ke kika san Sumayya, ni mai na hada da ita! ko dole nace?" Tashin hankali 'baro 'baro ya bayyana a jikinta gaba'daya, lalle da gaske Mk ya shiryawa tashin hankali iri iri, wai Anty Sumayya ce yake fadin sunan ta gatsal, duk da ya girmeta da shekaru biyu amma Anty yake cemata, sannan kuma har yana cewa mai ya ha'da da ita?. Ta kalleshi baki na rawa ta ce "Dan Allah Malam ka yafe mini, mu zauna lafiya ba zan iya kar'ban wannan tashin hankalin daga gareka ba, na rantse maka ba zan kuma maka laifi ba, zaman lafiya zamu yi, fiye da yadda ka ke so". Ya yi murmushi ya ce "na la'anci zaman lafiyar da ki ke so mu yi Sa'ade, zuciyarki bata da alheri, kwakwalwarki ba ta da tsinkaye, harshenki yafi na maciji dafi, ba sauran zaman lafiya tsakanin mu, idan har kika zauna lafiya da ni ban yafe miki ba". "Zuwa Gombe, ko yanzu kina iya tafiya, sai dai idan ina da hakki akan ki, ba za ki ga alheri a yayin tafiyar da dawowar ba in sha Allah". Ya ja dogon tsaki yana fadin shashar yarinya da bata san mutunci da kyautatawa ba". Ya sake jan dogon tsaki ya fice, ya barta tana kukan ita yake yi wa baki da mugun fata?. SURAYYA DAHIRU ✍️✍️ 18/04 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKAWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 75_77 Hannu ta 'dora aka ta dinga kuka,tana fadin "Hasbunallahi wa ni'imal wakil". Har akayi azahar tana zaune inda take, ba abin da tasa a bakinta, duk da ga tiren abincin nan a gabanta, ba idonta kawai ba, hatta fuskar ta kumbura ta aune sosai saboda kuka, ta fada ta yi zuru zuru, ta dinga lissafin adadin rikicinsu, aduk fa'dan da zasu yi ita take janyowa, ta sake tuno adadin alherinsa hatta iyayenta bai huta da yi musu alheri ba, tun kafin ma ya aureta. Ta sake tuna duk laifin da take ganin ya mata cikin biyu ne, ko dai kawai zuciyarta ta raya mata ya Mata kaza a matsayin musgunawa, sai wadda 'kawayenta zasu ce ya yi a makaranta, ko ya mayar da ita Bagidajiya, alhalin ita tasan yadda yake girmamata yake girmama dukkan ra'ayin ta, amma sai tunanin ta ya bace ta biye musu. Ta tuna yadda yake tsananin son su zauna lafiya, su rayu cikin walwala da mutuntata juna, sai gashi yau da bakinsa yana la'antar zaman lafiya, yana fa'din bai yafe mata ba, idan ta zauna lafiya da shi. Idan ta yi wadannan tunaninka sai ta rushe da kuka, tana yi tana cewa "wallahi da gaske na gane gaskiya". 'Kiran sallah ya sa ta tashi, ta yi alwallah ta yi sallah, ruwan Lipton kawai ta sha. Tana zaune har dare! sallah ke tayar da ita, gefe kuma tana tunanin Jawad, da ya nan da ya debe mata kewa, yau kwanansa uku a gidan Samira, tunda suna hutu. Akan idonta ya dawo, kusan a guje ta sha gabansa tana kuka, tana cewa "Dan Allah ka yi ha'kuri, ya girgiza da ganin yadda fuskarta ta koma a yini 'daya kacal, ta so bashi tausayi amma da ya tuna haka take idan tana son abu, da zarar ta samu muradinta kuma za ta sake kirkiro wata matsalar. Ya dubeta ya ce "Ba ki fara kuka ba, sai burina na raba Safina da gararanba a titi ya cika" Ta kalleshi a razane, bai damu ba ya ce "babban burina ta zame mini amarya, na tabbatar zan sami nutsuwa da ita, ki adana hawayenki zuwa wannan lokacin". A gurin ta yi fa'duwar yan bori tana kuka tamkar yarinya har da tirza 'kafa irin yadda Jawad ya ke yi. tsaki ya mata yana fadin "Ba kuka ba ko bubburwa za ki yi bai dame ni ba". Ya shige ya rufe kofarsa. Washagari daga sallar asuba bai dawo gidan ba, hankalin ta ya tashi ba ka'dan ba, ta kalli agogo ta ga har karfe uku ta tabbatar yana shago tunda yau lahadi. Abin duniya ya taru, ya mata yawa, idan ta tuna kalamunsa wai son Safina ya ke yi, sai taji tamkar ta shide, ta tuno yanayin halittar su daya, ko a makaranta ana yawan fadin dirin jikin su shigen iri daya ne, da gaske za ta iya daukan hankalinsa kenan? Hawaye ya sake goce mata, karon farko da ta fara jin tsanar Safina a ranta, tana raya ba zata kuma ganin dariyarta ba, bare ta ga fuskar zama a gidanta Maganar ta mata ciwo fiye da zaton mai zato. Tana zaune ta ji wayarta ta hau kuwwa, da hanzari ta dauka, ganin Hajiyar Bichi ce, tun daga muryarta Hajiyar ta gane ba ta cikin sukuni. "A kwance kike ne Sa'a? na ji muryarki ba walwala". Duk yadda ta ke danne kukan sai da ya subuce mata, hankalin Hajiya ya tashi ta dinga tambayar ta dalili amma ta kasa yin magana, sai kukan kawai. Dai dai lokacin kuma Mk na zaune dakin Hajiya yana cin alalan gwangwani da ya ji lafiyayyen manja da yaji. Ta kashe wayarta ta zubawa Mk ido, tana jin takaicinsa na kamata, a kausashe tace "mai ya hada ka da Sa'a?" A nutse ya ajiye cokalin hannunsa, ya kalleta yace "Me tace na yi mata?" Ranta ya sake baci ta ce " Na tambaye ka, ka amsa mini da tambaya! Na lura da kai, ka mayar da ni shashar uwa, duk sadda ka sami matsala da matarka sai ka tattaro ka dawo da kwanon abincinka wurina saboda ka zubar mini da mutunci a idon yarinya, amma zan gyara". Ya yi sukuri dan yasan gaskiya ta fada, yana yin hakan. A raunane yace "Hajiya ni fa ba abin da ya ha'damu, kinsan kuma yadda nake son 'dan'danon girkinki, dan na yi aure shikenan sai bazan ci ba?". Ido kawai ta kafe shi da shi, tun yana murmushi har ya fara shafa 'keyarsa, yana jin kallon na shiga jikinsa, yana tuna lokutan baya na 'kuruciya, idan Hajiya ta musu irin wannan kallon take suke shiga hankalin su, saboda yadda ya 'kunshi abubuwa da yawa ba sai ta yi magana ba . "Tashi ka kaini gidan, na ji ba'asin kukan da take ta faman yi, wa ya sani ma ko dukan ta ka yi". "Haba Hajiya! Kinsan dai ban samu tarbiyar dukan mace ba, ita kukan banza ne da ita, duk sadda zuciyarta ta raya mata, kuka take yi, da dalili ko babu". "Mahaukaciya ce ai". Jin amsar Hajiya yasa shi yin shiru ya lura ranta a bace yake da shi, ya mi'ke ya dauki waya da mukallin motarsa da ke gefensa ya kalleta ya ce "Allah ya huci zuciyar ki Hajiya, ina jiran ki a mota". Kozai kozai suka tarar da ita, cikin kwanaki uku kacal gaba'daya ta lalace, karon farko da Hajiya ta ganta kaca kaca, kullum fes zata tarar da ita, haka muhallinta. Hajiya ta ka'du kwarai da yadda ta ganta, da sauri ta isa kusa da ita, ta ri'ke ta, ita kuma ganin ta sami mai rarrashinta yasa ta kwantar da kanta a jikin Hajiyan ta dinga rera kukan tamkar mai wa'ka. Mamaki ya kama Mk! ya coge a bakin kofa yana kallon kukan shagwaba da iskanci a wurin Sa'adah, ta masa laifi, ta kai 'kararsa. Ya na'de hannunsa a 'kirjinsa, yana sauraren 'korafin da ta ke rattabawa Hajiya! "kuskure na masa cikin rashin sani, na yarda na yi laifi, na bashi hakuri tamkar harsena zai tsinke ya ki ha'kura, yanzu kuma sai ya fara soyayya da kawata dan ya ci mini fuska ya kuma janyo mini raini" Cikin kuka sosai take bayanin. Hajiya ta rasa mai za tace! ta fahimci Sa'a ba 'karamin kishi ne da ita ba, kishin nata kuma ya zarce ka'ida, amma da ta lura har da 'kuruciya a kanta, sannan dabi'a ce ta matan YAU sawa miji ido da kuma 'dorawa kai zazzafan kishi tamkar wadda aka musu busharar an janye ayar da ta bawa maza damar auren abin da ya musu da'di, daga mata biyu, uku ko hudu. A hankali ta ce "akan yana da budurwa ki ka maida kanki haka, Ina ruwan ki? ki daina sa ido ko bibiyarsa, ba ruwan ki da abin da yake yi matu'kar bai tauye miki hakkin ki ba, idan kuma ya na 'ketare dokokin shari'a wannan kuma tsakaninsa da ubangijinsa ne". Kan Sa'adah na 'kasa tana ta kuka, kukan kuma shi yake tayar da hankalin Hajiya. "Wai wannan kukan na menene haka Sa'a? Kin ga kuwa yadda fuskar ki duk ta aune?" Murya a dakushe ta amsa da cewa "ki ce ya daina mini fishi, sannan idan na dafa abincin ya dinga ci". Kafin Hajiya ta yi magana, Mk ya yi fit yace "Ni yaro ne da za ki dinga control 'dina? Na 'ki na ci abincin na ki" "Kin ji da kunnen ki ban isa da shi ba, dan haka ki share hawayen ki, komai da ki kasan hak'kinsa ne ki masa kar ki gaji, ubangiji ne yace ki masa biyayya, idan ya zalunce ki, ba zai barshi ba". Ta mike tana gyara zaman Hijabin ta, ta sake cewa "Ki yi hakuri, kar ki biye masa, kinsan idan tururuwa ta so lalacewa fuffuka take yi, Allah ya miki albarka kin ji! Ki tashi ki yi wanka ki ji da'din jikin ki". Ta juya ta fita ba tare da tabi ta kan Mk ba, da ya bita a baya yana cewa "Hajiya! ko kula shi bata yi ba ta yi ba, a waje juyin duniya akan ta shiga motarsa ya kaita, kamar yadda ya kawota, ta 'ki bude baki ta masa magana bare ta amince, haka ya dinga bin ta har titi, ta tari adaidaita sahu tana shiga, shima ya yi wuf ya fa'da, har suka isa Na'ibawa ba abin da ya ke yi sai tunanin mai zai yiwa Sa'adah ya huce. Ba zai iya tuna lokacin da Hajiya ta masa irin wannan fishin ba. Suna isa ta sau'ko ta wuce gida, ya tsaya ya biya kudin, sannan ya bita cikin gidan Yana isa ya tarar da ita zaune a tsakar gidan, bata shiga dakinta ba tabbacin ba zata saurare shi ba. Ya tsugunna, ya dinga bata ha'kuri, ya dade yana fama, kafin ta ce "Nunawa ka yi fa ban isa na zartar da abu a kanka ba, ganin na isa ne yasa ta ce na yi maka magana, kai kuma ka bata amsa da ta ke nufin ban isa ba, dan haka duk ranar da Sa'a ta fara ganina ba 'kima kar ka ga laifin ta". Ya yi shiru yana ayyana wai su mata haka suke ne? manya da yaransu sun iya kacaccala magana, su juya ta, komin gaskiyar ka sai sun nuna su ka zalinta ko ka ketawa haddi? Kan dole ya ce "Ki yi hakuri Hajiya Dan Allah! sannan ina tabbatar miki da ikon Allah ba macen da zan zauna da ita alhalin bata ganin girman ki". "Fatana ki huce, ki yafe mini bacin ran da na sanya ki". Fuska ba walwala ta ce "idan har kana so na huce, hankalina ya kwanta, to ka zauna lafiya da matarka, na lura itace bata da gaskiya, amma abin da zaka lura ko a lahira wani na cin albarkacin wani, ka manta komai ta yi maka, ka mata afuwa, ba hankalinku daya ba". Ya nisa ya ce "Allah Hajiya ban so ki ka shigar mata ba, so nake kawai ta banbance tsakanin zaman lafiya da kuma zaman tashin hankali, ta fitine ni wallahi". "Kaine Babba hakuri za ka yi! sonka take yi, shiyasa ta ke kishin ka, tunda ka fahimci matsalolinta sai ka kiyaye abin da zai tunzura ta, har hankali ya shigeta, wata rana ko ance ta yi wani abin ba zata yi ba". "Shikenan na ha'kura saboda ke, amma wallahi ki dinga mata fa'da Hajiya! tana sake yin mini yadda ta ga dama ne saboda kina bin bayanta, kwalbar ha'kuri na ta kusa fashewa akan lamarinta". "Kai kuma haka za ka yi? mahaifinka mai ha'kuri ne akan sabgogin mata, kafin muga fishinsa mukan 'dade, duk yadda zan bata masa rai kuwa da zarar nace yi hakuri to maganar ta kare". Shiru ya yi! A ransa kuma sai cewa yake yi ba za ki gane mai yarinyar nan take mini ba ne, inda a iya kishin ne ai da sauki. A fili kuma ya ce "shikenan Hajiya ta ci albarkacin ki magana ta kwanta". " So nake ta mutu murus, ba wai ta kwanta ba". Ya yi dairya ya ce "ki mata fa'da, idan ta kwantar da hankalinta, magana ta wuce, amma idan tana tayar min da hankali ai dole laifin baya ya dinga tasowa, yana zama sabo". "Zan ja kunnenta sosai, amma ka ri'ke a ranka na kashe wannan matsalar, kaima ka kashe ta a ranka, sannan kar ka kuma zuwa cin abinci gurina idan kun yi fa'da, bana so! bana so". Ya amsa da "to sannan ya mata sallama ya tafi, yau har zaure ta taka shi tana cewa "ka zarce gida kai tsaye ka nuna mata na isa da kai." Ya amsa da fadin "To In sha Allah". Madallah da uwar miji irin Hajiyar Bichi, masu maida surukansu tamkar ya'yan su, suke musu adalci irin wadda ko wacce uwa take so ayiwa 'yarta. Gidan kuwa ya zarce, ya sameta a inda suka barta har lokacin kuma kukan ta ke yi, sai dai alamun sun nuna ta yi wankan duk da ba kwalliya ta yi ba. Ya tsaya a bakin 'kofar falon ya zuba mata ido yana jin takaicinta na kama shi sosai. A kausashe ya ce "Rashin mutuncin ki kullum 'kara tunbatsa take yi, ki mini cin mutunci, ki raina arzikina ki nuna mini bariki ya fi aurena, sannan ki zame ki kai 'karata, saboda kin koyi munafunci?" Ta kasa magana sai kukanta da ya 'karu. Shi kuwa ya zarce da fadin "Tunda kin zama macijiya ki sare ni, ki koma ki baibaye uwata da kalolin alherinki na makirci da tuggu, to Ina tabbatar miki nima daga yanzu kome kika mini sai na fadawa Baffa, su dinga raba 'bacin ran tare da Hajiya". Ya ja tsaki ya shige dakinsa. Ta jima tana zaune cikin rashin sanin abin yi, sannan ta tashi ta bi bayansa, cikin sa'a bai rufe 'dakin ba, yana zaune a bakin gado iskar fanka na kada shi. Akan gadon ta zauna kafadunsu na gogaiya da juna, ta ri'ko hannunsa tare da jingina kanta a kafadarsa murya ba amo tace"Am sorry Malam! Wallahi zuciyata ba za ta iya 'daukan fishinka irin haka ba, ka yafe mini' ka manta dan girman Allah". Ta karasa cikin kuka na sosai. "A hankali yace "Na ha'kura, amma mantawa sai a hankali, idan kin kiyaye, kin kuma rufe 'kofofin da zan dinga tunawa din! ki sani ba dan Hajiya ba, da ban san ranar da zan miki afuwa ba, saboda kin riga kin shayar da ni mamaki da ba'kin ciki mai yawa". "Na yarda na yi ba dai dai ba, dan Allah kar ka yanke mini kauna, ka sake bani dama". Ita da kanta ta yi dalilin da sai da suka hadu a lokacin, tun Mk na basarwa, har ya kasa cigaba da jarumtar ya ru'ko ta suka sami nutsuwa, haka nan sai da haduwar ta yi awon gaba da kaso hamsin na bacin ran da ke zuciyarsa. Tun a wannan rikicin Sa'adah ta fahimci ta rasa damammaki a gurin Mk, ya matu'kar rage rawar jiki akanta, ya daina tattauna halin da yake ciki da ita, haka nan baya zama ya shiririce mata da hirarrki kamar da, za su yi hirar amma a gajarce, sannan mafi yawan hirar sai dai ita ta kawo. Haka suke wannan zama har Jawad ya dawo daga gidan Samira, so take ya barta ta je Gombe amma tsoron tambayar ta ke yi, har mamakin kanta take yi, yadda take tsoron su yi rikici yanzu. Washagari alhamis da safe ta tura Jawad ya tambayo musu za su je su gaida Maman Gombe da ganin Baby boy, tunda sai satin sama hutun su zai 'kare. Jawad bai jima da zuwa ba, ta ji Mk na 'kwalla mata 'kira, gabanta ya fadi sosai da hanzari ta shiga dakin tana cewa" Na'am". Kallonta kawai ya yi, ta gane ba zai barta ba, ta tsugunna tana sauraronsa. Sa'a an 'kara kwas na respect 😁 "Kin aiko Jawad za ku Gombe, inace dama ban hana ki ba tun farko?" Ta yi sukuri tana jin fargaba na kamata, da 'kyar ta bude baki ta ce " ai kace ba zan ga alheri ba". "To yanzu na ce ki ga alherin! Aje lafiya, adawo lafiya shikenan?" Ta kalle shi ta ga yana daddana waya hankali kwance. "To kwana nawa zamu yi?" "Sai kin gaji da zama sannan ki dawo". Ya fada hankalinsa na kan wayarsa. Hawaye ya cika idonta tana jin tamkar ta sume. Murya na rawa ta ce "Malam yanzu fa ban yi maka komai ba, Allah shine shaidata, na yadda na ke gudun na 'bata maka, amma kai kwata kwata ka yanke mini kauna, ka ki ka yafe mini, kana zaune da ni akan tilas.." Kuka ya kwace mata sosai, cikin ko in kula ya ce "kin so yin kuka ne, kince za ki je Gombe, nace adawo lafiya, har da abin arzikin ki yi iya adadin kwanakin da kike so, shikenan kuma sai ki bare mini baki, to fada mini me kike so na ce miki?". Ta dago da manyan idanuwanta da suka yi ja ta zuba masa akan fuskar sa, tsawon lokaci idanuwansu a sarke, chemistry na aiki akansu, a sanyaye Mk ya janye fuskar sa gefe daya, yana kokawa da abin da ya taso masa. A hankali ta furta "so nake ka ce kwana kaza za ku yi". "To sati hudu ya yi miki?" Da mamaki ta kalle shi ta ce"ai zuwa wannan lokacin su Jawad sun ' dade da komawa school". Kai tsaye ya ce "Ba da shi za ki tafi ba ai, ke 'kadai za ki yi tafiyar ki, ki je ki yi abin da ki ka ga dama". Jikinta ya yi sanyi ta tabbatar ba barinta zai yi ba, sai kawai ta mike ta ce "Na gode". Ta fita zuwa kicin, ta hau aikin abincin rana, ta na yi tana kuka, bata ta'ba sanin Mk na da ri'ko ba sai a wannan karon. Haka tana ji tana gani har Inna ta dawo ba ta je ta gano su ba. Ko zuwa ta yiwa gidansu dan ta yiwa Inna barka da dawowa, da 'kyar ya barta, shima sai da la'asr lis da zai tafi shago ya tafi da ita, kafin su Isa magariba ta yi, amma dan son ya musguna mata bata fi awa daya ba ya mata waya shi zai tafi, idan kuma bata gama ba, ta taho idan ta kammala, alhalin yana kaiwa fiye da goman dare. Haka ta fito ta bishi yana ta cin magani, har suka iso ko uffan ba suce ba, wannan sabuwar rayuwar ta yiwa Sa'adah tsauri matu'ka da gaske mussaman da bata saba ba, ya riga ya sabar mata da wasa da raha, uwa uba kullum shine cikin rarrashinta da son ganin murmushi a fuskarta, shiyasa yanzu sauyin ya zo mata da tashin hankali. Hatta Inna sai da ta yi 'kwalla da taga irin ramar da ta yi, sai dai fa'da sosai ta mata tana fadin tasan itace duk ta jànyowa kanta komai take ciki. Cikin kuka ta ce "Ni damuwata 'daya yadda Anty zata ga rashin kirkin banje na gaishe ta ba". Da sauri Inna ta ce "ba zata ga laifinki ba ai tasan aure ki ke yi, ba zaman kanki ba, kar ki damu ta warware sosai, Ba ki ga Anis ba ya yi 'bul'bul da shi, ki bi mijinki a hankali kin ji". Haka suke rayuwar yau fari gobe tsumma, shi kansa Mk so yake ya manta komai amma maganganunta sun dasa masa wani irin ciwo a zuciyarsa, sun yi karfin da suka sababa masa hawan jinin da yake shan magani kullu yaumin, idan ya tuna sadda ta ke fada masa matan bariki na da daraja fiye da matan aure sai ya ji tamkar ya sume. Ranan asabar da safe suna karyawa da wainar shinkafa da miyar ganye da ta ji tantakwashi, sammako ta yi ta shirya masa tare da kunun farar shinkafa da danyar gyada, tasan yana son wadannan abincin, sai da ta yi wanka ta ci kwalliya sosai sannan ta gabatar musu. Suka kammala ta kwashe komai, ta zauna kusa da shi sosai, a ladabce ta ce "Malam ina son na je asibiti". Ya kalleta ya ce,"me za ki yi? Ta sunkuyar da kanta 'kasa ta ce " abin nan zan cire ". Ya zuba mata ido yana jin tausayinta na neman kama shi, yasan so take ta yi abin da zai sa shi farin ciki, dan haka sai ya sassauta ya ce "Inace tun a Abuja na ce ki bari mu gani tukun, ko abin da nake fata zai kasance, idan ki ka haihu kun zama ku uku lissafi zai canja". Ta dago idonta cike taf da hawaye ta kalle shi " Na dauka ka fasa tafiyar da ni, tunda yanzu ka canja mini akan komai". Ta fa'da hawaye yana zubo mata. take ya ji sonta ya dawo daga suman da ya yi, Ashe son ba raguwa ya yi ba, comma ya shiga. Ya bude mata dukkan hannuwansa biyu, a yau bata tsaya jan aji ba, da sauri ta fada masa, yasa dukkan hannuwansa ya rungumeta tsantsan ita kuma tana kuka kasa kasa. Baice komai ba, illah shafar bayanta yana jin sau'kin 'daurin da kirjinsa ya yi akanta. Tun daga ranar ya canja, ya daina 'daure fuska, sannan ya bu'de mata kofar nisha'di a tsakanin su, sab'anin satikan da suka shude da ya rufe ta rif. Saukowar Mk ya sa ta fara murmurewa, tashin hankalin da ta shiga yasa ta manta da wayar ta Bb, sai yanzu da ta sami nutsuwa take fitowa da ita, idan ya fita. * Tsautsayi* Ranar da ta zama 'bakar Rana ga rayuwar ma'auratan guda biyu, wadda tarihin rayuwar su ba zai cika ba, sai an sako ranar. Asabar ce cikin watan Augusta da safe bayan sun kammala karyawa cikin walwala, ya shirya ya mata sallama, zai je ta'aziya Baban Abokinsu ya rasu daga nan zai zarce gidan su ba zai dawo ba sai yamma, ta masa addu'ar dawowa lafiya,ya tafi tare da Jawad. Kafin ya fita ta nemi iznin za ta je kitso, bai hana ba, ya amince mata. Sai da ta gama komai na gyaran gida, ta yi wanka, ta tsaya jikin wardrobe tana nazarin rigar da zata sanya. Wata daguwar riga ta janyo data jima bata sa ta ba, garin janyowar ta hado da ledar kayan da su Halima suka kawo mata na tsarabar khalil, wadda ta manta da su, ta leka ta ga rigunan Jawad ne da agogon ta, sai kwalin wayar Blackberry, ta jefa kan gado akan sai ta dawo zata san yadda zata yi ta nunawa Mk rigunan, dan ta fara sakawa Jawad tunda tsadaddu ne. Ta dauko wayar daga inda take boyewa, ta jona a caji, ta shirya ta rufe gidan ta fita, zuwa bayan layinsu inda take kitson. Mk da ya fito daga gidan rasuwar gidan Mahmoud suka zarce adalilin motar Mahmoud din ta lalace, dan haka ya kai shi, ai kuwa Jawad ya ce anan zai zauna wurin Dady. Anan ya 'bata lokaci, ganin hadari ya hadu sai ya yanke hukuncin komawa gida ya huta bayan la'asar sai ya je wurin Hajiya. Ya isa gidan, da mukallin hannun sa ya bude gidan, ya shiga, dakinsa ya kwanta sai ya tuna yana son dauko Agogon sa dake dakin Sa'adah da bai dauko ba, kullum sai ya fita yake tunawa. Ya mike ya doshi dakinta, ya duba ya dauko Agogon, har ya kai bakin kofa sai ledar kan gadon ta ja hankalinsa, mussaman da ta kasance ta waje ce, dan haka sai ya koma ya dauko ya bude, ganin kaya ne, ya zazzage su akan gadon, kayan Jawad basu dauki hankalinsa kamar tsadadden agogo da kuma kwalin wayar ba. Zuciyarsa ta dinga bugawa, wani irin tsoro, da razani suka shige shi, shaidan ya kawowa zuciyar sa caffa! kawai sai ya dinga tuno sadda take cewa matan bariki na mallakar duk abin da suke so cikin gaggawa. Innalillahi wa ilaihir raji'un kawai ya ke ambata, ya kalli socket ya hango wayar da bai san da ita ba, ya karasa gurin ya dauko, yana dubawa, ganin Blackberry ce kuma babbar sai hankalinsa ya sake tashi, ya kasa budewa saboda ta sa mata password. Da yake data a kunnen ta ke Ya dinga ganin sakonni na shigowa ba jinkiri. Ya dinga jin jiri na katantanwa da shi, bai taba jin tashin hankali irin na yau ba,me Sa'adah take yi haka? A ranar ya gane duk yadda yake daukarta ta wuce nan. Kusan mintina talatin yana zaune a dakin nata, cikin tashin hankali iri iri. Daidai lokacin ta shigo gidan a sukwane, tunda ta ga motarsa a waje ta shigo a hanzarce, zuciya na 'bari, ba ta yi zaton zai dawo ba, wacce irin 'kaddara tasa ta bar kayan nan da waya a fili? Kai tsaye 'dakinsa ta shiga dan ganin wanne kallo zai mata? Har 'bandaki baya nan, bugun zuciyar ta ya karu, cikin shahada ta nufi ta nufi falon , bata ganshi ba, fargabar ta ta 'karu ta tabbatar ya ga wayar nan. 'Karfin hali ta lalubo ta dora a fuskarta duk kuwa da zuciya da gangar jikinta sun 'ki karban wannan 'karfin halin. Da sallama a bakinta ta shiga dakin, yanayin da ta iske shi, sai da ya ka'da mata 'ya'yan hanji. Bai 'dago ya kalleta ba, amma ya amsa sallamarta da murya marar amo. Ta aro jarumtar 'boye kaduwar da take ciki, ta matsa kusa da shi tana cewa "Ba ka jin dadi ne, da kace sai yamma za ka dawo, a Ina ka baro Jawad?" Ya dago yana kallon ta, yana jin wata irin tsanar ta na neman Samun muhalli a zuciyar sa. Bai amsa mata ba, ya zuba mata ido yana jin tamkar ya tashi ya yi ta dukanta. marar gaskiya akace ko a ruwa gumi ya ke yi, ta dinga jin 'barin jiki irin na fargaba, ta yi sukuri tamkar ace 'kyat ta fece da gudu. Ya mi'ke ya isa inda take tsaye yace " A Ina kika samo wadannan kayayyaki masu daraja?" Cikin rawar murya tace "Anty Sumayya ta aiko mana, dama na fito da su idan ka dawo, ka gani" Ya zuba mata ido yana kallon yadda ta ke shirya zancen da babu azanci a cikinsa, ledar kayan ta nuna daga Egypt kayan suke, sannan a cikin kwalin wayar akwai risit din siyan wayar a ciki mai dauke da sunanta a takaice( S.B). Kwanan watan ya nuna ta kai wattanni biyu a hannun ta. Ya ce "Sumayya yaushe ta je Egypt ban sani ba? Ta hannun wa sa'kon ya same ki?" Ta muzanta kwarai da gaske, ta kasa bude baki ta yi magana. Ya dauko wayar yana cewa "Wannan wayar da ta lashe manyan ku'da'de Sumayya ta aiko miki? Ko kuma saurayin ki, ki ka fa'dawa mijinki ya gaza?" Ya mi'ka mata ya ce "Bu'de mini! tashin hankalin ta ya ninku, Baki na rawa ta ce "kar ka yi aiki da zato, wayar Halima ce ba tawa ba". Idonsa ya canja zuwa jah, jijiyoyin kansa suka bayyana ru'du ru'du, makoshinsa ya bushe, zuciyarsa ta cushe da tsananin bacin rai, hankalin sa ya kai 'kololuwa wurin tashi. "A zafafe sosai ya ce " wacce maganar zan kama, wayar Halimace ko Sumayya ce ta kawo miki? ki bude min wayar nan tun kafin na tozarta ki, domin sai na dauke ki munje gaban Halima, Ina rantse miki da ubangiji agaban Baffa za'a yi komai". Ta fara kuka tana cewa "Ajiya ta kawo mini itama ba tata bace, dan Allah ka yi hakuri, gaskiya na fada maka". Karon farko da hakurinsa ya kwace ya dauke ta wani irin mari mai katse ji da gani na wucin gadi! ya ce "Da aurena Sa'adatu, da aurena akan ki? Idan wayar Halima ce to wannan Agogon da kayan na uwar waye?" Tsananin zafin marin yasa habo ya goce mata, duk da hakan bata damu ba, asalima kukan tsayawa ya yi cak duk da hakan furucinsa ya fi firgita ta sama da marin A gigice ta ce " gaskiya na fada maka, ka yarda da Ni" Ta riga ta kudiri aniyar komai zai mata ba zata bude ba, domin a jiya ma sun yi chart da Khalil, duk da ba wani dirty abubuwa suka tattauna ba, amma akwai maganganun da ba zata so Mk ya gani ba, mussaman hotunan sa da ya turo mata, ita kuma ta tura masa na Jawad. Hankalin Mk ya kai ma'kura wurin tashi ya matsa kusa da ita sosai yace "ki bude min wayar nan idan ba so kike ki wulakanta kanki ba". ta karba, amma ilahirin jikinta rawa yake yi na tsananin tsoro da firgici. Fiye da mintina goma tana ri'ke da waya amma ta 'ki budeta, lamarin da ya sanya Mk ya ce ta fita suje gidan su Halima, ya tasa ta a gaba har tsakar gida, anan ta coge akan ita ba zata je gidansu wata Halima ba. Ya nuna ta da yatsa ya ce "Billahillazi sai kin je, daukota zamu yi, muje gaban Baffa shine al'kalin wannan jahilcin na ki". Ta rasa inda zata tsoma ranta, ta tabbatar Halima kai tsaye za ta ce ba wayarta bace tunda ba ta 'ki ta kashe auren Mk ba dama. Ya koma 'daki dauko mukallin mota, tashin hankali yasa ya kasa ganin inda ya ajiye, yana cikin dube dube kawai sai jin 'karar fashewar abu ya ji da karfin gaske. Ya fito da sauri, ya ga wayar ta rotsa, ta fashe sosai, ta wargaje yadda ba zata tashi ko ta moru ba. Bai san sadda ya isa gareta ba, ya sha'keta sosai, sai da ya lura tana dab da sumewa ya wancakalar da ita, ya hau dukanta da hannuwansa. Ganin yana dukan amma ba abin da yake ji na sauki sai ma 'karin tafasar zuciya, ya kyaleta ya zauna a kasa dabas ya dinga ambaton innalillahi wa ilaihir raji'un, hawaye bakin ciki na tsere akan fuskar sa. Ta dago da 'kyar ta ga yadda ya ke zubar d hawayea! a fili bai damu da aga yana kukan ba, duk wata dauriyarsa sa ta kwace a YAU. Hankalin ta ya sake ri'banya tashi, ta dinga kuka tana fadin " Ka yafe mini, wallahi ba wayata bace". A tunzure ya antayo ashar irin wadda bata taba jinta ba, ya maka mata, tare da cewa "Idan ki ka kuma bude baki da nufin yi min, magana ko bani ha'kuri Billahillazi sai na miki abin da baza ki manta ba". Wayarsa ya ciro aljihu, da kyar ya iya lalubo sunan Fahad Auwal! Dalibinsa ne tun a FGC yana cikin samarin Sa'a duk da dai bata ta'ba kulashi ba, sannan yanzu ma dalibinsa ne a B.U.K. Da girmamawa ya gaida Mk. Cikin rashin sukuni Mk yace "Fahad cikin class mate din ku na FGC akwai mai karatu a Egypt kuwa?" Dan Jim Fahad ya yi sannan yace"Khalil Ibrahim ne kawai a Egypt". Ko godiya Mk bai tsaya yi ba, ya katse wayar. A fili ya ce "ban da tabbas, amma idan har yanzu kuna tare na tabbatar kun tabbata wakilan manyan shedanu a doron 'kasa". Ta 'kara karfin kukanta ta ce "Mala.. ya katseta ta hanyar jifanta da takalminsa da hagu. Tare da cewa "ki mini shiru, dama ai na fada miki ba zan sake yi miki uzziri akan shedanun yaron nan da baisan kimar da darajar aure ba". Ya jima yana ambaton addu'ar we yayewar ba'kin ciki, *"YA HAYYU, YA QAYYUM BI RAHMATIKA ASTAGIS*. Ya 'dan sami nutsuwa ka'dan ya kalleta ya ce " kin yi wankan ko ba ki yi ba?" Da'di ya kamata mussaman da ta tuna da asuba ya gama mitar hakurinsa ya 'kare, wannan karon period dinta takes too long. ta yi dariya ta ce bai 'karu ba kawai matsuwar da ka yi ne, amma dai nasan ba tantama I will be ready today. Tunaninta nemanta zai yi tunda dabi'arsa ce ya kusanceta a lokacin da ya ga shaidan zai dagula zaman lafiyar su. Da hanzari ta ce "Na yi". Ya zuba mata ido sosai yana so ya ji ko akwai sauran gurbi a zuciyarsa da zai sake yi mata uzziri, sai ya ji babu saura, yana jin idan bai rabu da ita ba, tabbas ba'kin cikinta ne zai zama ajalinsa. Dan haka muryar sa cike da rauni, hawaye na zirarowa ya ce "*Na sake ki, saki daya Sa'adatu*! Na ba ki dama ki zama yantacciyar da ki ke fata". Ta 'kwala uban ihu mai gigitarwa. 30/04. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *Godiya ga makaranta* *Ina matu'kar Jin dadin yabawar ku kan rubutuna, Hakika da kune Halin Yau ya je inda ban yi zaton zai je ba. na gode muku dukkan makaranta littafin HALIN YAU da fatan ana lura da sakon da nake nufin isarwa, ana watsi da shiriritar da yake ciiki, Ubangiji ya bamu damina Mai albarka*. *Bari na sada zumunta da ku masoyan Sa'adah* *Hajiya Rabi Sani* *Aisha(cisse)* *Tababa ta Malam* *Asma'u Umar Ingawa* *Samira Annuri*. *Khadija Sadiq* *Safara'u Niger*. *Zainab Abdallahi* *Aishatu maina* *Khadija Bishir(Dijengala enterprises)*. *Masoyan da yawa mu tara a shafin gaba*. * SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 78. Kuka ta ke yi tamkar ranta zai fita, ta rarrafa ta ri'ke kafarsa ta dama. Cewa ta ke yi " Kar ka mini haka Malam, laifina bai kai ka 'dau wannan hukuncin ba, dan Allah ina sonka, ina son zama da kai". A hanzarce ya fincike kafarsa, ya nunata da yatsa amma ya kasa bude baki ya mata magana saboda yadda yake jin wani irin sanyi na ratsa shi duk kuwa da yanayin garin a daure yake da zafi, saboda hadarin da ya hadu amma ruwa bai sauko ba. Da 'kyar ya mike, ya shiga dakinta, ya dauko mukallin motar wadda yana tsakar dakin a yashe, rashin nutsuwa ya hana shi ya gani. Ya fito, ya tsaya yana kallon yadda take kuka mai tsananin ciwo, irin kukan nan da ba ya sa a ji sau'kin tashin hankalin da aka tsinci kai a ciki. A hankali ya ce "Tashi muje na kai ki gida". "Dan Allah Malam ka yi hakuri Ni bazan tafi ba". Fuskar nan a daure tamkar hadari ya ce " Ba za'bi na baki ba, ki tashi na kai ki cikin mutunci, tun ba ki tafi dutse a hannun riga ba". Hawaye face face a fuskarta, Ta ce "iddah zan yi a dakina kamar yadda shari'a ta tanadar, ka girmama shari'a. A kufule ya ce "wallahi ba anan gidan ba, ki je, ki yi a gidanku duk wata zan aiko miki abin da zai ishe ki! Na 'ki na girmama shari'ar, ke iyakokin ubangiji nawa ki ka take saboda son zuciyar ki, yanzu ne ki kasan ka'idojin shari'ar?" Ta yi 'kasa da kanta dan kaucewa kallon tsanar da yake mata. "Tashi muje" ya fada a kausashe. Ta 'ki koda motsin kirki, sai shesshekar kukanta kawai, wadda ta ke yinsa har cikin 'bargonta. A hasale sosai ya ce " Sa'adatu taurin kai a yau ba zai amfane ki da komai ba, bazan dauke ki da karfi ba, amma ki sani idan har ba ki tashi na mayar da ke cikin mutunci kamar yadda aka bani ke cikin mutunci ba, komai zai iya faruwa a tsakanin mu, na tsani na bude ido na ganki". Nan ma ko uffan ba ta ce ba, sannan kuma ta 'ki tashin. Ai kuwa ya ce "shikenan! Komai ya faru ki kuka da kanki, ya shiga 'dakinsa, mintina biyu ya sake fitowa ya dubeta tana kuka tamkar Baffah da Innah sun mutu rana 'daya, amma ko tausayi ba ta bashi ba. A kausashe ya ce "Zan fita yanzu! kuma wurin Baffan zani na fada masa yau na mayar da ke 'yantacciya, amma ki sani Billahillazi idan har na fita ni ka'dai na haramtawa kaina ke, idan haka ta faru, shari'ar ta ce ba dalilin ki zauna kimin idda a gida ko?". Tamkar tab'ab'biya ya ga ta mike ta fita waje a guje, ya bi bayanta dan ya lura tamkar ta zauce ne. Ba ta tsaya a harabar gate din su ba, waje ta fita kai tsaye, ta yi kicibus da wani tsoho sosai, zai wuce, a gabansa ta zube cikin fitar hayyaci tace "ka taimake ni Baba"! Dai dai lokacin Mk ya fito ya tarar da su a hakan. Da sauri ta dinga cewa "ga shi nan Baba, bashi ha'kuri saki na ya yi, fa'da masa Allah ba ya son saki, yana kuma tare da masu hakuri" Kallonta kawai za ka yi ka gane sakin nan ya susuta ta, ya gigita ta sosai. Tausayinta ya cika zuciyar dattijon, ya kalli Mk ya ga shima a gigicen yake kwarai da gaske. Duk da hakan sai yace "zo kusa da ni 'dana, Mk bai 'ki ba, hakan nan ya matsa kusa da shi ya tsugunna, a tausashe yace "ka yi hakuri ka ji! da gaske Allah na tare da masu ha'kuri, ba a biye sha'anin mata, yanzun nan za su rufe ido su yi abin da za su shekara suna nadama". Mk dai baice masa komai ba, bai ji kuma zai janye sakin nan ba, tabbas sai ta je ta banbance tsakanin zaman gidan miji da rayuwar da take hari wannene 'yanci? A hankali tsohon ya kuma fa'din "na tabbatar ko iya haka ka barta ta gane bakin Rijiya ba wurin wasan makaho bane". Murya ba sauti Mk ya ce "Baba kar ka sa na yi abin da zan zalunci kaina, ina ro'kon ka, ka yi ha'kuri, al'kawari 'daya zan maka, matu'kar zuciyata ta huce da lamarin yarinyar nan, to kana cikin wadda zata ci darajar su na yafe mata, amma a yanzu idan ka tirsasani na mayar da ita, auren namu zai iya lalacewa gaba'daya, ka yi ha'kuri ka fahimce Ni". Kafin Dattijon ya yi magana Sa'adah ta zabura ta sake kwasa a guje ta shige gidan. Tausayinta ya cika zuciyar wannan tsohon, ya riko Mk sosai ya ce " Na fahimce ka 'dana, ba kuma zan maka dole ba, mai 'daki shi yasan inda yake masa yoyo! Amma ina son ka ri'ke a ranka cewar yarinyar nan tana sonka sannan uwar ya'yan ka ce, dan haka kar ka yi amfani da zato wurin hukunta ta, ka boye laifin ta, Allah ya muku albarka gaba'daya, ya kuma huci zuciyarka". Da ga haka ya saki Mk ya juya, ya tafi, ga mamakin Mk sai ya ga cikin sakwanni mutumin nan har ya yi tafiyar da ya bacewa ganin sa, ya dinga wasiwasi anya kuwa wannan mutum ne? a tsufansa ba zai iya irin wannan sauri haka tamkar walkiya ba, ya shiga gida yana ayyana ko dai aljanine cikin aljanun Sa'adah.😂 A bakin motar ya tarar da ita, tana tsaye hawaye ya ki tsaya mata. Ya bude gate din, sannan ya karasa ya bude motar suka shiga, sai da ya rufe gidan sannan suka tafi. Ta by pass hanyar 'Dorayi ya bi dan haka hanyar ba yawan motoci, sun zo daidai Wailari ya ga ta fara wata irin jijjiga tana cewa "Laifina bai kai wannan hukuncin ba, kar kasheni da raina, Baffa ba zai bar Ni na zauna masa a gida ba, ina ka ke son na tafi?" Sai kawai ya ga ta sume. Kan dole ya gangara gefen titi ya bude ruwan roba na Highland da ke gaban motar mai dan sanyi, daga gidan Mahmoud ya taho da shi, ya watsa mata, ajiyar zuciya ta saki tare da rushewa da kuka sosai har muryar ta fara dashewa, fadi take yi "Ka ji tausayina mu koma gidanmu, Jawad zai yi kukan rashi na, komai ka ce na yi bazan kuskure ba, na yarda ka 'Kara aure, ka sake 'karawa, ka sake 'karawa, ya fi mini sau'ki da na rasa ka". Idan ya ce jikinsa bai yi sanyi ba, ya yi 'karya, idan yace maganganun ta basu yi yunkurin karya masa zuciya ba ya yi munafunci. Ya zuba mata ido yana kallon yadda tashin hankalin awa daya rak ya susuta ta, yaci gaba da kallonta yana so ya samu dalili gamsasshe da zai mata afuwa, amma da zuciyarsa ta hararo masa cewa "Hai'ntarsa take yi shiyasa ta 'ki bari ya ga ta'addacin da ta ke yi da aurensa akanta, sai ya ji zuciyar sa tana zafi tamkar ana gasa burodi. Ya zuba mata ido ya ce"Sa'adatu kowanne bawa da irin kaddararsa, Allah ya sani na iya bakin kokarina na mu zauna lafiya, kuma shine shaida akan son da nake miki, matu'kar gaskiya zan fada miki, zuciyata ba za ta nutsu da ke a yanzu ba! Al'kawarin da zan miki daya ne, ba wadda zai ji mai ya ha'damu, Ina tabbatar miki zan dauki laifin a idon kowa, kema kuma kar ki fa'dawa kowa ko da Baffa ne kuwa". Ya yanko tissue yana goge'kwallar da ta cika masa idanuwa. Ta zama very speach less, bugun zuciyar ta ya karu, wani irin zazzabi mai zafi ya fara kokarin kai mata caffa. ta koma ta kwanta a jikin kujerar tana jin duk wani tashin hankalin duniya yau ita aka ha'dawa shi. Tsawon lokaci suna haka, shiru ya ratsa, sai fama suke da radadi a zukatan su. Cikin 'karfin hali ya tayar da motar ya hau titi, karon farko da Sa'adah ta yi fatan inama su yi hatsarin da zai zama ajalinta, ta huta da azabar ciwon da ke damun zuciyar ta. Bai tsaya ba, sai a kofar gidan su, gabanta ya yanke ya fadi, ta tuno maganganun Baffa a ranar da zai kaita dakin aurenta. Ta kalle shi ta ce "Baffa korata zai yi, kar ka barni anan, mu tafi gidanmu Malam, na yi al'kawarin ba zan sake ri'ke kowacce irin waya ba". Ta ru'ko hannunsa ta sake fa'din " Na amince ka yi amarya ka tafi da ita karatun da za ka tafi, Ni ka barni zan jiraka, fatana kar ka barni". Magana ta ke yi ba kuka, sai tsananin bacin rai da tashin hankali. Ya kalleta sosai "a karon farko da ya ganta cikin NADAMAR gaskiya, sai dai nadama marar amfani ta ke yi domin ta riga ta yi a 'kurarren lokaci. Baice komai ba, ya bude motar ya fita, haka ta bude itama ta fita sanin akan titi suke, a zaure ya tsaya ya ciro wayarsa ya 'Kira layin Baffah, ya sanar masa ya zo yana zaure. Cikin rashin sa'a ya ce "dazun nan na tafi Gogel, sai jibi kuwa zan dawo, ko akwai matsala ne?" Kai tsaye Mk ya ce "akwai Baffa Amma zan zo na sameka anan din" "Ba sai ka zo ba Mutari, in sha Allah zan juyo a yau ba sai gobe ba". Ya yi godiya, sannan suka kashe wayar. Sa'adah na rakube a jigin bango, ta matso ta tsugunna guiwa biyu ta ce " Rashin samun sa alamun ubangiji bai son rabuwarmu ne, Dan Nabiyur Rahamati ka dauke ni mu koma gida". Ya kalleta sosai ya furzar da iskar bacin rai ya ce "wa ya siya miki Wannan Agogon da kuma waya?" Hawaye ya balle mata, ta rasa mai za ta ce. Ganin ta yi shiru ya sa shi cewa tashi ki shiga gidan zan je shago na jira dawowarsa. Ya fita da sauri, ya yin da ita kuma ta durkushe a 'kasa tana kuka sosai. Ta jima tana kukan da 'kyar ta tashi ta shiga gidan ta tarar da mahaifiyarta tana zaune tana Jin radio. Tana layi ta 'karasa kan tabarma sabon kuka na kaico iri iri na sake ku'buce mata. Tambayar duniya ba wadda Inna bata mata ba amma ta 'ki tankawa, lamarin da ya dagula hankalin ta. Kan dole ta 'kira wayar Baffah ta sanar da shi ga Iyah ta zo tana ta kuka, kuma ta ce mijinta ne ya kawota da kansa. Ya amsa mata da gashi nan ya juyo. Ta ajiye wayar cikin sanyin jiki ta kalli yadda ta ke kuka jikinta har 'bari yake yi, ga wata irin rama ta yi, har ba'ki ta ga ta sake yi mata sosai. A hankali ta;ce "kin tasa ni a gaba kina irin wannan kukan mai tayar da hankali, amma kin 'ki bu'de baki ki fa'da min mai ya same ki, ba Kya jin tsoron ciwo ya kada ni, kinsan fargaba da zullumin da nake ciki?" **** Mk na zaune a shago, amma jinsa yake tamkar a cikin rijiya saboda tsananin yadda ya takura ga wani irin matsanancin kishi ya matse kofofin numfashinsa, ya sababa masa azabben ciwon kai mai tsananin. Yawun bakinsa ya kafe sai daci yake ji har makoshinsa! ya ciro wayarsa ya kira Mahmoud ya sanar da shi, yana cikin matsala ya zo gidan Hajiyan Bichi ya same shi. Ya fito kai tsaye ya tari mai acaba(A lokacin ba a hana ba) ya kai shi gidansu, dan bashi da sukunin da zai iya tu'ki, domin al'amarin na nisa damuwar sa na 'kara girmama, wani abu ne mai tsananin ciwo ya tokare a 'kahon zuciyarsa mai azabtarwa. Yana isa kai tsaye can cikin dakin Hajiya ya shige ya wuce ta a falo tana yanka kankana. Mamaki ya kamata, ba zata iya tuna yaushe rabon da ya shigo ya ganta a falo amma ya zarce uwar daki ba. Ta yi jim, tana sauraronsa ganin fitowarsa, amma abin mamaki mintina fiye da goma sun shude bai fito ba, dan haka sai ta mike ta bi bayansa dan jin ba'asin wannan sabuwar dabi'a. Yanayin da ta tarar da shi ya tabbatar mata akwai matsala, da azama ta isa gareshi tana cewa lafiyar ka kuwa? A hankali ya ce"kaina tamkar zai fashe Hajiya" Da jimami ta ce "Ai da Abbas ko Akil ka kira wani ya raka ka asibiti, a kwanta da ciwo ne ba a sha magani ba?" Dai dai lokacin Mahmoud ya iso suka gaisa da Hajiya da ta fito falo tana masa iso. "Shiga! yau zuwa ya yi ya mini sake sake a gado da sunan ciwon kai". Mahmoud na dariya ya mike yana cewa " Hajiya ai gara ya kwanta ya more da zarar kunga mun yi aure shikenan sai ku dora mana dukkan girma alhalin matu'kar kuna raye mu yara ne 'kananu". Ya shige cikin dakin. Kallon Aminin nasa ya yi ya tabbatar yana cikin tashin hankali babba. Yasan karfin zuciyar Mk duk abin da ya bayyana a jikinsa tabbas ya yi tsamari ne. Da gaggawa ya shiga ya zauna a gefen gadon, ya na fadin "me ya ke faruwa ne?" Cikin rawar murya Mk ya dinga yunkurin magana amma ya kasa yi, ga mamakin Mahmoud sai ganin kwalla na gangarowa ta gefen idon Mk. Take hankalin Mahmoud ya yi tashin gauron zabi, murya kasa kasa cike da tsantsar aminci da kulawa, ya ru'ko hannuwansa ya ce "Yi hakuri Mukhtar! Fada mini damuwarka in sha Allah I will stand for you". Da rawar murya Mk ya dinga ambaton Sa'adah, Sa'adah". A hanzarce Mahmoud ya ce" me ya same ta, me ta yi?" Da 'kyar ya bude baki ya ce "mun rabu, na saketa Mahmoud"! ya karasa da murya mai cike da tashin hankali. Wani irin zabura Mahmoud ya yi ya mike yana cewa"How comes, akan me? subhanllah!" Shiru ya ratsa dakin! kowa tunani, na katantanwa da shi. A kasan makoshi Mk ya ce " ka fa'dawa Hajiya, tashin hankali na yadda zan fa'da mata, da yadda za ta karbi lamarin". Mahmoud ya zuba masa ido, yana kallon irin yadda Aminin nasa ke zu'ko numfashi da 'kyar tamkar mai fama da cutar asma. A hankali ya koma ya zauna yana jin tashin hankali shima na ziyaryartar sa. Tausayin Mk ya ratsa shi ya sake ru'ko hannuwansa a karo na biyu ya sassauta murya ya ce," Ina fatan sakin sunna ka yi, ina fatan mu gyara wannan matsalar kafin su Hajiya su ji, yanzu ina ita Sa'adah ta ke?" Cike da rashin kuzari ainun ya ce "Na kaita gidansu, saki daya na yi mata, abin da nake so ka fahimta, da abin zai gyaru da ko kai ba zan raba 'bacin ran da kai ba". A hankali Mahmoud ya muskuta ya ce "Kar ka yi haka, ka yi hakuri mana, da wanne irin ido za ka kalli dattijon arziki irin Baffah?" Wannan karon Mk ne ya tamke hannun Mahmoud ya zarce da cewa "shine babban tashin hankali na, fiye ma da yadda nake jin fargabar da Hajiya za ta shiga, amma kuma bana jin zan iya cigaba da zaman mu tare, iya adadin zaman da 'kaddara ta hukunta za mu yi kenan, ka fa'dawa Hajiya sai muje ka raka ni wurin Baffah, duk da bana jin dadin jikina". Ya fada a sanyaye cike da yankewar Buri. "Mukhtar Nima ba zan iya fa'da mata ba, da wanne baki zan fadi wannan 'bakin labarin?" "Cike da rauni ya ce " daurewa za ka yi Mahmoud". Shiru ta ratsa dakin a karo na biyu, nazari soasai Mahmoud ya ke, yana tunanin wacce irin 'kaddara ce mai zafi ta raba Mk da Matar da ya shaida yafi sonta akan kansa? Yana son jin menene ummul aba'isin wannan matsalar, amma kuma tunda Mk bai bu'da masa ba, shikuma ya yi al'kawarin ba zai tambayi komai ba, zai kuma yi dukkan mai yiyuwa dan ya sulhunta tsakanin su. A dabarance Mahmoud ya 'daga murya ya ce "Sam bazan iya fadawa Hajiya wannan tashin hankalin ba, kai da ka yi, kaine mai fa'da ba Ni ba". Ai kuwa wannan kalamin na Mahmoud ya janyo hankali Hajiya, da azama ta fa'da 'dakin tana fadin " menene ba za ka iya fada mini ba Mahmoud! wanne tashin hankalin ya rakito?" Dukkansu suka yi shiru aka rasa mai bakin magana, ta zauna da'bas a 'kasa tana salati, da fatan ba wani rashin gaskiya Mk ya aikata ba. Ganin irin damuwar da ta shiga yasa Mahmoud yin 'kundunbalar fadin "Hajiya ki yafe mu, ina ba'kin cikin sanar da ke yau Allah ya 'karar da zamansa da Sa'adatu". Salati mai 'karfi Hajiya ta rafka, tana cewa "Kar ka jinginawa Allah'karar zamansu, jingina masa, dama ya da'de yana fatan rabuwar, ganin ya kasa samun damar shine yanzu ya murde zaman da 'karfin tsiya." "Oh ni Rabi'atu ina ganin tasku, da wanne 'bakin ciki zan ji? da wadda yan'uwanka suke guma mini, ko da naka? Alhaji da Hajiya Babba sun mutu sun barni da ku, kuna neman kashe ni da ba'kin ciki". Ta fara hawaye, tana gogewa da hannun zaninta . Da ga Mk har Mahmoud sun yi laushi tubus da jin kukan Hajiya, hankalin su kuma ya sake tashi matu'ka, da rawar murya Mk ya ce "Na roke ki, ki daina zubar da hawayen nan dafi ne a rayuwa ta, da kinsan azabar da nake 'dan'dana na tabbatar da sai kin sassauta mini, ki yi hakuri Hajiya ba yadda zan yi ne, abin ne ya fi karfina, ki mana addua ki kuma yafe mini". "Yanzu ina Sa'a din ta ke?" Mahmoud ya ce "tana gidansu, yanzu ma komawa zamu yi dan bamu sami Baffan ba". Hajiya ta sake sa salati tana tafa hannu, tare da cewa "yanzu idon ku, idon tsohon nan ku iya fa'da masa kun mayar masa da 'ya Bazawara? kaico na taya ku jin kunya". "Yanzu ku tashi ku kaini gurin Alh Isa". Sai da Mahmoud ya taimakawa Mk sannan ya mike. Fada sosai Mk ya sha a gurin Alh Isa, sai daga karshe ya sassauta ya ce " Ka yi kyan kai da ka yi saki 'daya tal, fatana ka janye ka mayar da matarka, kowa hakuri ya ke yi da abokin zamansa ,ta ci darajar mahaifinta". Kan Mk na kasa baice komai ba sai da Baban ya kammala sannan cikin ladabi ya ce "A mini afuwa Baba, a yi hakuri, a sani cikin addu'a ina cikin ru'dani mai yawa, ina rantsuwa da ubangiji ina cikin ru'danin da nake jin inama ajalina ya riske ni a yau saboda tsananin asarar da nake jin na tafka, ba yadda zan yi ne, abin ne ya fi 'karfina" Dukkansu jikinsu ya yi sanyi mussaman yadda yake maganar cikin rawar murya tamkar ba Mukhtar ba, namiji mai karfin zuciya. "Allah ya daidaita ya kawo mafita " cewar Alh Isa da ya rasa mai zaice, dan ya lura Mukhtar na cikin rashin nutsuwa da firgici, ya tabbatar kuma yana da gaskiya, sannan mai 'daki shi yasan inda yake masa yoyo. Dukkansu suka amsa da "Ameen, ya yin da Hajiya ba haka ta so ba, so ta yi ya wula'kanta mata shi, ya kuma tirsasa masa ya mayar da matarsa ko ba ya so. Har da Alh Isa suka 'dunguma zuwa gidan su Sa'a, Hajiya ce kawai ta ce ba zata je ba, bata san da idon da za ta kalle su ba. A tsakar gidan Baffa ya jagorancin zaman, Alh Isa ne ya yi karfin halin bayyana mutuwar auren wadda ya matu'kar dukan zuciyar iyayen na Sa'adah, juyin duniya ba wadda ba'a yi musu ba, amma sun 'ki bayyana menene dalilin da ya haifar da wannan tashin hankalin, kukan da Sa'a ke yi tamkar za ta shi'de ya sake 'daga hankalinsu. A hankali Mk ya ce "Baffa Ina rokon ka, kar yanke mini kauna, ka yafe mini, kaddarar muce ta zo da hakan, har wayewar garin YAU bamu san zamu tsinci kanmu a cikin wannan mawuyacin HALIN da muke ciki ba, ina kuma fatan itama ka yafe mata, ba laifinta bane Baffah". Gurin ya yi tsit sai shshshekar kukanta kawai ake ji, Mahmoud ya kamu da ciwon tausayin masoyan biyu, mussaman Sa'a kallo daya za ka mata kasan tana cikin tsaka mai wuya. Baffa ya nisa ya ce "Ba aurenta ne ya hadamu ba Mutari, ba kuma zai zama dalilin rabuwarmu ba, nasan halin girma irin naka, tsiyar a gunta take, yanzu kuma zata gane tsiyar har wasali gareta, domin na tabbatar laifin nata ne, ba zata 'ki zaman aure ta yi tunanin zata zauna a gabana ba". Ga mamakin Mk sai ya ji kalaman Baffa sun sake girgiza masa zuciya. Da sauri ya mi'ke ya koma kusa da shi ya ce "Baffa Dan Allah dan Annabi ka yi ha'kuri, idan ka yi haka bazan yafewa kaina ba, ka yiwa Allah ka barta ta ji da tashin hankalin da na jefata, ba laifin ta bane, nawa ne, Ni za ka hukunta ba ita ba". Ido kawai Baffah ya zubawa Mk da yake gurfane a gabansa yana rokonsa idansa jawur, ga wata irin rama da ya yi ta farat daya. A ransa fadi yake Iyah kin tafka asara, kubucewar miji irin Mutari abin ki shimfi'da tabarma azo a miki jaje ne. Ya tabbatar laifin na Iyah ne, amma ya 'boye laifinta, ya kuma tsaya kai da fata wurin nema mata sassauci da aminci a gurinsu. Baffa ya dafa kan Mk ya ce " Madallah da mutanan kirki irin ka, madallah da mutane masu irin dabi'ar ka, madallah da zuciya mai adalci irin ta ka! Saboda kai zan bar Iyah ta zauna a gidan nan, ban taba jin takaicin rashin ya'ya da yawa ba sai yau, da ace Ina da wata 'yar! da wallahi taron nan bazai watse ba sai na musanya maka da ita". Kwalla ta 'kwacewa Mk ya na jin kunya da tausayin Baffa na sake masa rubdugu, wacce irin kauna ya ke masa haka, anya bai yi rashin kirki da ya kasa yin ha'kuri da 'yarsa ba?" Ba zato suka ji Mk na cewa "Baffa me yasa ba zaka ba ni umarni na mayar da ita ba, sai ka yi fatan ka bani yar'uwarta idan hakan ya yiyu ka haramta mini ita gaba'daya fa?". Ba ki 'daya jikinsu ya dan yi karfi saboda kalaman Mk, wadda suke bushara da zai iya daidaitawa da matarsa, yanzu ko anjima. Inna ta ce "Tunda baka da wata da za ka bashi, ai sai ka mayar masa da wadda ka ke da itan". Cikin kuka sosai Sa'adah ta ce " Na gode Innah". *Surayya Dee* ✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai da satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *Gaisuwa da fatan alheri ga wadannan groups din* *LAFAZEE FANS* *DANDALIN MUM KHADY* *HAFSAT SODANGI fans* *DAGA DAJI 1&2 fans* *PAID GROUP na BINTA ABBALE* *DANDALIN SADA ZUMUNTA NA ANNURI.* *JIDDA REAL FANS* *FADILA LAMIDO FANS* *SADNAF NOVELS GROUP* *TASKAR AISHA MICHIKA* _*Dama sauran wadanda ban ambato ba, mu hadu a shafin gaba, Kuna da yawa Allah ya bar kauna_*. *MK, SA'A DA FARIDA NA GAISUWA* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 79_80. "Ba zan ba ka umarnin da na san kunya da nauyi ne zaisa ka yi shi ba. Ba ni na maka umarni ka auri Iyah ba, ku ka hada kanku, ka aureta bisa ra'din kanka, ka zauna da ita cikin shekaru bakwai, Ni da mahaifiyarta shaida ne akan kyakkawan rikon da ka mata, haka nan, ka na girmama mu da dukkan zuciyarka, kana jin nauyi na tun kafin na baka aurenta, idan har za ka iya sakin Iyah, to ni kuwa bazan yi son zuciya ba, na tabbatar abin ne ya fi 'karfin ka". Ya nisa ya cigaba da cewa "Zan so kwarai ace na mutu na barta a hannun ka, domin Ina da yakinin ba za ta wulakanta ba, amma ya na iya da HALIN 'dan YAU mai yin aiki da son zuciya, daga baya kuma ya jinginawa tsautsayi da 'kaddara". Alh Isa ya muskuta ya ce "Tun kafin mu zo nan, na umarceka da ka janye, ka mini gardama, amma yanzu kana cewa ya baka umarni ka mayar da ita, Ni baka jin nauyi na Mukhtar?" Kunya iri iri ta sake rufarwa tashin hankalin da Mk ya ke ciki, a sanyaye ya ce " A a Baba bayan nauyin ka da nake ji, wallahi kallon uban da ya isa ya zartar da hukunci akai na na ke maka! Abin da yasa ban amsa ba, ina jin tsoron kada na mayar da ita a yanzu auren ya lalace gaba daya, saboda zuciyoyin mu cike suke da bacin rai mai ya.." Cikin dimaucewa Sa'adah ta katse shi da cewa "Ni zuciyata ba komai sai salama da nadamaar *HALIN* da nake ciki, na yi al'kawari zan jure duk wani kalar fishinka, ba zan yi abun da za mu kai ga lalata auren mu ba". Tausayinta ya ratsa su dukkan su, gurin ya dauki shiru, sai fama suke da tausayin su, kowa ya lura laifin Sa'adah ne, amma Mk ya kafe laifin sa ne, su gafarce shi, haka aka tashi ana addu'ar, Allah ya daidaita su. Bayan tafiyar su Mk, kukan Sa'adah ya karu, sosai ta ke rusa kuka, yayin da iyayen ta suke fadin ba ki ma fara kuka ba, domin sai nan gaba za ki gane asarar da ki ka yi ba 'yar 'karama bace. Zazzabi mai zafi ya rufe ta, hakoronta suka dinga karo da juna, jikinta sai rawa yake tamkar mazari. Da farko shareta suka yi, sai da suka ga abin na sake 'kamari sannan Inna ta kai mata 'dauki, tana sa hannu a jikinta ta ji zafi zau. Har dare tana cikin wannan yanayin, kan dole Baffa ya 'kira wani jami'in lafiya, mai chemist a unguwar ya zo ya bata taimakon gaggawa. Haka al'amarin ya kasance da Mk, bayan sunje sun sauke Baba Isa, yace da Mahmoud gidan Hajiyar Bichi zai maida shi, suna shiga falon nata ya yanke jiki ya fadi, alma'arin da ya matu'kar tayar da hankalin su, 'Karfi ya fita a gigice, ya yi sa'a ya tarar da Abbas na gida, ya 'Kira shi suka ciccibi Mk zuwa wani asibiti mai zaman kansa mafi kusa, dole aka kwantar da shi sakamakon jininsa da ya yi mugun hawa, baya ga haka yana cikin damuwa da ya ke bukatar hutu.. Abbas ne ya zauna da shi, sauran yan'uwansu kullum suna zarya a asibitin, haka nan Mahmoud kullum sau biyu yake zuwa duba shi. Har zuwa wannan lokacin Jawad na gidan 'Karfi bai san me yake faruwa ba, takanas Mahmoudya je ya debo masa uniform da kayansa kullum da safe zai kai shi, idan anta shi kuwa mai aikin matar ke hawa adaidaita ta dauko shi, idan ya tambayi Mamin shi ko Malam sai ace sun yi tafiya ne, bai damu ba, tun tafiyarsu Abuja ya saba zama gidan Mahmoud Karfi. Kwanansa uku aka sallame shi, tare da gargadin ya rage damuwa, ya kuma kula da shan maganinsa. Haka ya tattare dakin Hajiya, tun tana ki, har ta ha'kura ta barshi, kan dole ta koma kwana a babban falon su, da suke zama ayi dab dabla lokacin Hajiya Babba. Kwanansa biyu a dakinta yana warware wa, a cikon na uku ne ganin ya dan sami sauki har ya ci abinci, yasa ta bijiro da maganar Sa'adah. "Matu'kar kana son mu shirya to ka dawo da matarka, rashinta ne duk ya susuta ka haka, idan kuwa ka 'ki jin maganata kar kuma takowa inda na ke, ko gaisuwar ka bana so". Hankalin sa ya tashi, ya fara 'ko'karin fahimtar da ita da hujjoji, amma fur ta hau dokin na 'ki. Ganin da gaske ta ke yi, shikuma a yanzu wani irin tsoro da firgicin zama da Sa'adah ne ya ke kama shi, bai ta'ba tunanin za ta yi abin da ta yi ba, mussaman yadda ya ke wadata da komai, uwa uba kuma yadda ya ke tarairayarta da gudun zuciyar ta, idan har hakan bai sa ta kiyaye masa amana ba, bai ga kuma me zai mata ba. Kansa har zafi yake wurin tunanin, me yasa ta yin hakan? Ya tabbatar shi baya ha'intar ta akan me ita zata ha"ince shi? Wani irin tsimin bacin rai ya taso masa, mai hade da kishin da ya haddasa tsanar Sa'adah, ya kasa bu'de baki ya yi magana kawai ya kife kansa akan guiwowinyasa ya fashe mata da kuka tamkar yana cikin shekarun 'kuruciya. Wannan kukan ya matu'kar ta'ba zuciyar Hajiya, ta shiga ru'dani da wasiwasi akan lamarin Sa'adatu, kan dole, ta ha'kur'kurtar da zuciyar ta, ta ce ta janye takunkumin dolen da ta yi masa. Amma a zuciyarta sai hasashen wanne irin abu ta yi mai muni haka?. Sati guda da faruwar wannan lamarin, amma har lokacin Sa'adah na kwance ba lafiya., saboda ta 'kuntata zuciyar ta, ta 'ki cin abinci, kullum cikin kuka ta ke, ta yi wata irin rama mai tayar da hankali, kuka ta yi shi irin wadda ba ta yi tunanin akwai mahalu'kin da ya yi irinsa ba, ko ya ya ta ayyana Mk ya saketa, shikenan sun rabu? sai dai Inna ta jiyo ta 'barke da kuka tana fadin na tafka asara, na yi nadama. Sannu a hankali zance ya shiga kunnuwan dangi, kowa ya ji mutuwar auren sai ya shiga alhini saboda yadda aka shaida soyayyar da Mk ya ke yiwa Sa'adah, mussaman Auntyn Lagos, Maman Gombe da Samira, hankalinsu ba karamin tashi ya yi ba, da kuka Antin Lagos ta 'kira Hajiya tana tambayarta gaskiyar magana, cike da tausayi Hajiya ta tabbatar mata sun rabu tabbas. Da rawar murya take fadin "Hajiya ki matsa masa ya dawo da ita, na tabbatar duk inda ya ke, ba ya cikin nutsuwa, yana sonta". "Hmmm kawai ki musu addu'a amma lamarin na su akwai tashin hankali." Inji Hajiya . Wata guda Mk ya 'dan wartsake, ya koma harkokinsa da 'karfin zuciya irin ta namiji, sai dai abin na nan ma'kale a zuciyar sa yana jin har ya koma ga mahallicinsa ba zai manta ba, idan ya tuna dalilan da zai hana Sa'adah ta bashi wayar nan sai ya ji bugun zuciyar sa ya karu, wani lokacin har jiri ke dibansa. Ga Sa'a kuwa wannan watan ta cinye shi ne a kwance tana 'dan'danar azabar ciwon so da nadama, tunda gyatumarsu ta kawo ta duniya bata taba fuskantar tashin hankali irin wadda ta ke ciki ba, fata take mutuwa ta dauketa ta huta da wannan zugin da zuciyar ta take mata, inama ta bashi wayar nan ya gani? Wata'kila da ba zai zafafa lamarin har haka ba, tun shekaranjiya da ya aiko mata wasu cikin kayanta shake cikin akwati babba, yini ta yi a ranar tana kuka, ba abin da ta ke fata irin ta ji ko da Muryar Mk, amma abin ya faskara, ga tunanin Jawad rabon da ta ganshi tun ranar da suka rabu da Babansa, ta yi dalilin da suke rayuwa a wuri daban daban, wannan kadai ya isheta ladabtarwa. Cikin wannan 'kangin ta sake cinye wani watan har da 'karin kwanaki goma, zullumi ya ishi Sa'a, saboda kwanakin iddarta na gab da kammala, duk wadda ya ganta yanzu, muddin ya santa a wattannin baya, sai ya tausaya mata, gashi dai ba ta rasa komai ba, amma ta rasa kwanciyar hankali, satin ta biyu a gidan Mk ya aiko da kayan abinci kala kala wadda za su kwashe rabin shekara suna ci, sai kuma ya mata siyayyar komai na bukatunta tun daga kan kayan shayi har sabulai, da tarkacen abubuwan da zata bu'kata, amma ko taba su ba ta yi ba, hakanan abinci sai Inna ta tausaya mata, ta zauna kusa da ita, ta matsa mata sannan za ta yafita . A lokacin Sa'adah ta fahimci ba abin da yafi nutsuwar zuciya da'di, addu'a ta ke sosai akan ta sami sau'kin tashin hankalin da take ciki, idan ta ji yo su Baffah na hira har da raha shi da Inna sai ta tambayi kanta yaushe za ta fara dariya ne ita?. Yanayin da ta ke ciki ya fi kama da na mai takabar da mutuwar managarcin miji ya zo mata kwatsam. Daidai wannan lokacin Sumayya ta iso Kano dan jajantawa yar'uwarta halin da tsinci kanta a ciki. Halin da tarar da Iyah a ciki ya bala'in girgiza ta. Cike da tausayawa tace " Na sha fada miki halin da kika jefa kanki ba inda zai kai sai nadama, gashi tun ba a je ko ina ba, kina fuskantar Halin Yau! duk wadannan kawayen na ki da kika mayar allon kwaikwayon ki YAU suna Ina?" Karon farko da Sa'adah ta fara jin sassauci domin sai a ranar ta Sami wadda ya mata fa'da, iyayen ta sun zuba mata ido, ba wadda ya buda baki ya mata fa'da, sun mata dungu suna gasa ta da idanuwan su kawai, hatta Baffah da ta tabbatar ba abin da yake so a duniya irin ta, wannan karon ta na hango ko oho da yake yi da lamuranta. Ta ri'ke hannun Sumayya ta na wani irin kuka, tana fadin "kin fada mini, ba irin gaskiyar da ba ki fada mini ba, sai dai an riga an kadddara mini yanka kazar wahala, dole kuwa sai na figeta tas, Mukhtar mutumin kirki ne, laifin duk nawa ne, sai dai nima kadddara ce da bazan iya kauce mata ba, ki taimake ni Aunti! ki bashi ha'kuri, Tunda Baffa ya barni da kaina". Ta shide tsabar kuka! Hankalin Sumayya ya ru'banya tashi, amma hakan ta daure, ta tausasa murya ta ce " ki daina irin wannan kukan, idan har kin yi amanna kaddara ce ta hau kan ki, to ki yi hakuri ki bita da istigifari, yawan kuka da 'kauracewa abinci da takurawa zuciya ba abin da zai haifar miki sai ciwon da zai kayar da ke, ina tabbatar miki duk wadda zai shiga damuwa a dalilin rashin lafiyar ki, ke ce dai mai jin jiki?" "Na gode sosai Anty dan Allah ki 'kira shi, ko zai ga girmanki". Sumayya ta nisa ta ce "Bana jin girmana zai sa ya janye kudirinsa tunda har bai janye saboda Baffah ba". Hawaye ya kwaranyowa Sa'adah ta ce " Baffa ba ya son na koma ne, a gaban mu Mukhtar ya ce ya bashi umarnin ya mayar da ni, amma 'kememe Baffa ya 'ki, ya barni na ji da dabarata". Sumayya ta yi shiru, tana jin tausayin 'kanwarta na sake kamata, ba ta gane muhimmancin mijinta ba sai da ya kubuce mata, ta tuna wani lokaci da ya shude tana mata fadan ta bi mijinta su zauna lafiya. Ta nisa ta sake tuno amsar da Sa'adah ta bata a waccan lokacin, "Anty ki ta cemin na bishi, na masa biyayya ko da yana cutar da ni, akan me zan yi irin wannan rayuwar auren alhalin ko yau Mukhtar ya barni Ina da yakinin zan samu wadda ya fi shi." Ta dago ta kalle ta, yau Mukhtar ya barta, da ya tashi barin nata ba shi kadai ya tafi ba, sai da ya yi awon gaba da dukkan nutsuwa da walwalarta, bugu da 'kari hatta kyaun da ya sa take ta'kamar zata samu wadda ya fi shi, ya tsiyaye tas, ta kai duba ga kirjinta , ta ga sun yamushe a cikin riga, mamaki ya kama Sumayya bata taba sanin nonon Iyah zai iya zubewa haka ba, domin ko da take shayarwa a tsaye kuma a cike suke, irin wadda suke ma'kale ne a kirjin mace, amma tashin hankalin da take ciki suma ya tabasu, hakanan gashin kanta sai saukewa yake yi, ga uwar rama sai ido gwara gwara tamkar idon agolan Banufe. Ta ke Sumayya ta dinga neman tsari da shiga tashin hankali kwatankwacin irin wadda Iyah ke fuskanta, ta kuma nemawa yar'uwarta samun sassauci da mafita. A hankali ta ce "zan 'kira shi, sai zuwa dare tunda yanzu yana gurin aiki, fatana dai ki kwantar da hankalin ki, ki karbi kaddarar ki da hannu biyu, yanzu a ina Jawad ya ke?" " Ni ma ban sani ba" Sa'adah ta fada a sanyaye. A daren ranar kuwa Sumayya ta 'kira layin Mk, da girmamawa ya amsa wayarta, suka gaisa, ta fara da tambayar Jawad, ya amsa da yana nan lafiya Lau, shima ya tambayi nata iyalan, da 'kyar Sumayya ta iya masa maganar Iyah, ga mamakinta sai taji ba alamun zafafawa, ya ce "Anty ku bimu da addu'a da ga ni har Sa'adatu abin ya zo mana a ba zata, muna bu'katar mu nutsu, zuwa gaba muga me ubangiji zai zartar mana, har yau ina sonta, Ina fatan mu sake zama, sai dai muna bu'katar hutu da nutsuwa, idan dukkan mu mun fahimci manufar auren, zamu dawo mu sake zama abu guda, amma for now, ya kamata mu bar komai a hannun mai juya al'amuransa ya mana zabi". Sumayya ta amsa da "Hakane" tare da yi masa godiyar amsa 'kiranta da ya yi, ta rufe maganar da ro'kon ya kawo mata Jawad yaranta suna ta tambayar shi. Ya amsa da gobe juma'ah zai kawo shi ya yi week end tare da su". Ta ajiye wayar, tana kallon Sa'adah da ta yi mata 'kuri tana son jin abin da ya ce. Kasancewar Sumayya na cikin jerin mutanan da basa yiwa 'karya kwaskwarima dan su da'dawa wani, kai tsaye ta ce "Iyah ki barwa Allah zabi kin ji, idan zaman ku bai 'kare ba, za ki koma dakin ki, idan kuwa iya adadin da aka deba muku za ku yi kenan, ina tabbatar miki ba za ki koma ba, hakan kuma ba shine 'karshen farin ciki ba". Kuka sosai Sa'adah ta yi a wannan daren, kafin ta tashi ta 'doro alwallah ta fara sallar nafila, idan ta na addua a fili take fadin " Allah ka rufa min asiri, ka mayar da ni 'dakina, Allah na tuba". Sumayya kawai kallon ta take tana sake jin tsoron ubangiji na kamata, yau Iyah ke wannan haukan akan Mk, Ashe duk wani kau'di da ginshirar da take yi shine kanta ya dawa? Ko yau Mk ya mayar da ita, ta yi amanna ya karya duk wata fuffukar da take ji da ita, za kuma ta nutsu ta daina fitinarsa, tun lokacin da ta haihu amma ya iya hana ta zuwa ta dubo ta, ta tabbatar Sa'adah ta fara kai shi bango ne, ta kuma koya masa rashin kirki. Washagari kuwa ya kawo Jawad har kofar gidan Baffa da 'yar karamar jakar kayansa da kuma ledar biskit da alawowi ga su Ayman. Da gudu ya shiga cikin gidan! Mk na tsaye yana jin rashin dadi, yana son ya shiga ya gaida Inna, amma kunya ya ke ji, hakanan ya ke ganin rashin kyauta wa idan har bai shigan ba, saboda ya saba duk sadda ya kawo shi zai shiga su gaisa sannan ya tafi, haka idan zai dauke shi. Har ya juya sai kuma ya dawo ya shiga, ya dade a tsaye a zauren, yana tuna moments dinsa da Sa'adah a cikinsa. Dukkansu suna tsakar gidan Suka ga Jawad ya shigo a guje, suka rungume juna da Ayman 'din Sumayya, duk da Ayman din ya bashi shekaru biyu, amma abota suke yi sosai. Inna ta tashi ta dauko hijabin ta da ke rataye a bakin 'kofa ta saka tana tambayar Jawad wa ya kawoka? Yace "Malam ne", ba ta zauna ba ta dauko tabarma ta shimfida a inda ta saba shimfida masa, tana ayyana tasan zai shigo, aikuwa kafin ta dago ta ji sallamarsa. Ganin Sumayya lullube ta ke da mayafi, Sa'adah ce kawai a zaune ba mayafi daga ita sai doguwar rigar atamfa wadda wuyan ya mata yawa tsabar rama, kanta ba dankwali asalima tsifa take yi, ga tulin gashinta a gefen ta wadda ya ke zuba tamkar wutar daji. Inna ta amsa masa tare da bashi iznin shigowa, Sa'adah da tun jin sallamarsa ta daskare a zaune, ta rasa me za ta yi duk kuwa da yadda Jawad ya saki Ayman ya zo ya haye cinyarta yana taba wuyanta, alamun ramar da ta yi shima ta bashi mamaki. A hakan Mk ya shigo, idonsa ya fada cikin na Sa'adah, gabansu ya buga a tare da azama ya dauke idanuwan sa, ya isa ga tabarmar da yasan dan shi aka shimfida, a ransa ya dinga godewa ubangiji da 'kaddare shi ya shigo, da ya kunyata Inna. Suka gaisa cike da kunya da girmamawa tamkar komai bai faru ba, haka suka gaisa da Sumayya. Da Sa'a ta gaishe shi ya amsa mata ba yabo ba fallasa, amma yanayin da ya ganta ya matu'kar bashi mamaki da tausayi, mussaman da ya ga Jawad ya lafe a jikinta. Ba ta ji kunyar Inna ba, bare Sumayya, ta ajiye Jawad ta mike ta dauki hijab ta bi Mk hanyar waje, a zaure suka tsaya, ya zuba mata ido, bai ji so ko tausayin yadda ta lalace ba, domin tare suke shan bakin cikin, kawai dai shi Namiji ne, namiji kuwa da juriya aka san shi. Ya daure ya ce "har yau ba ki fara cin abinci bane? kin ga irin ramar da ki ka yi kuwa?" Hawaye ya 'balle mata ta ce " Ka yi hakuri , na 'kira Jawad ka tafi da mu, ka mayar da ni gidanka, ba sai ka kulani ba, zama tare da kai 'karkashin inuwar aure ya gamsar da Ni". Ya yi murmushin da babu nisha'di ko kadan yace " ba kya yawan addu'a, ki nemi zabin Allah a tsakanin mu, ba son rai ba, sau da yawa mukan so abu 'kololuwar so, sai abin ya zama sharri ne a garemu, hakan nan muna 'kin abu iyakacin 'ki, sai ya zama alheri a garemu". "Kar ka kwatanta ni da sharri Malam, ina hadaka da girman Allah ka yi hakuri ka yafe mini". Ta tsugunna guiwa biyu a 'kasa Ta cigaba da cewa "saura 'kiris na kammala idda, ka taimake ni, ka ji 'kaina." Daidai lokacin Baffa ya shigo zauren ya kewaye su ya wuce ba tare da yace uffan ba. Jikin Mk ya yi mugun sanyi, bai so Baffa ya gansu a haka ba, ya dubeta ya ce " ki koyi karban rayuwa a yadda ta zo miki, ki kuma daina wasa da damar da rayuwar za ta baki, na so ki, iyakacin so, amma menene amfanin son da babu kwanciyar hankali ko aminci a cikinsa?" Da haka ya juya da sauri yana fadin "ki yi murna kin zama 'yantacciyar macen da ki ke fata". Ta jima tana kukan zuci da na fili, sannan ta shiga gidan, ba ta tsaya a tsakar gidan ba ta shige daki ta kwanta tana cigaba da rizgar kukan da ba ya amfana mata komai. Ganin wulgawar Jawad ya dan rage mata kewa, ga Sumayya da take tausarta. Ranar lahadi suna zaune, Sumayya na mata kitso bayan Ahamad 'kanin Mk ya zo ya tafi da Jawad, kawai suka ga ana ta shigo da kaya, kallon su kawai Sa'adah ta yi ta fahimci kayan ta ne Mk ya Aiko musu, tunda ya ga an'ki zuwa a debo. Abin mamaki sai ba ta ji kuka ya zo mata ba, ko dan ta yi kukan har ta gaji ne? Tsakar gidan sai da ya cika da kaya, domin duka gadajen nan uku ya Aiko mata haka nan kujerun falo da tv plasma hatta freezer da bai 'dade da siya ba, ya ha'da ankawo mata. Ga wasu bakko guda uku sha'ke da kaya, Sumayya ta bude biyu duka kayan Sa'adah ne, ya yin da 'dayar labulaye ne da zannuwan gado a wanke a goge, sai lokacin 'kwallah ta zowa Sa'a, wato ya da'de yana shirya mata kaya, tunda ga labulayen da suke dakunanta ma ya cire su anwanke su. Haka akwatunanta duka kayanta ne a ciki, ba kayan da ba' a wanke an goge ba, a cikin fishi ma Mk ya iya alheri, ta ayyana a ranta. Gwala gwalan ta ne kawai ba ta gani ba, indai ba a tsakiyar kayan ya 'boye su ba. Ilai kuwa cikin katon akwatin ta ya saka mat su a tsakanin kaya. Dukkansu jikin su ya yi sanyi da ganin kayan, hatta Baffa da yake nuna mata bai damu ba, ganin wannan kayan ya tayar da hankalinsa, balle Inna da take ta faman goge hawaye a fuskarta. Ganin hakan Sumayya ta roki Baffan su, za ta tafi da Sa'adah Gombe, ta kwana biyu, idan ta 'dan warware sai ta dawo. Ya kalli Sumayya, a sanyaye ya ce "kin manta ba ta kammala iddarta ba? har yanzu a matsayin matar Mutari ta ke, bani da ikon da zan turata wani guri alhalin ba hakki na bane yin hakan". "Baffa dan Allah ka bari mu tafi, mutumin nan, ba mayar da ita zai yi ba, gaba'daya ya fita a kaina wallahi". Murmushi ya yi ya ce " Ban sanki da son zuciya ba, Sumayya! Kar son 'kanwar ki ya mayar da ke mai son kai, kinsan me ta shuka masa ne? Ruwa ba ya tsami banza, har yau ya 'ki fadan me ta yi masa, maimakon haka sai ya 'dorawa kansa laifi, Ina rantse miki da Allah! Iyah ce ta yi wani abu marar 'dadi, ko shekaranjiya na ganta durkushe a gabansa, Ni na fara tsoro da wasiwasi akan lamarin ta, Allah dai ya sa ba wani mugun abu ta yi ba" Sumayya ta kasa magana, tausayin Iyah na ratsa ta. Ko da shiga dakin a zaune ta sameta, ta tsurawa gefe 'daya ido, idonta a soye, sai da Sumayya ta kirata sau uku sannan ta amsa a firgice. "Ki fa rage dogon tunani Iyah Ina jiye miki ciwon farat 'daya. Ta dago ta dubi 'yar'uwarta ta ce "Dama na mutu Aunti". Da sauri Sumayya ta ajiye Anis ta 'karasa kusa da ita ta rungumeta ta ce " idan ki ka mutu, ki barni da wa Iyah? ke ka'dai gare ni bayan Innah, ko da na haifi mace ba zata cike min gurbin ki ba, bare ban haifa ba, me yasa ba za ki duba wadda farin cikinsu na 'damfare da ke ba? Yanzu Mukhtar din da ba ki san shi ba sai da kika mallaki hankalin ki ne, zai sa ki yi fatan mutuwa ki bar Baffah, ki bar Inna, ki bar Jawad, ki bar Ni?" Sai lokacin kuka mai ciwo ya gocewa Sa'a. Sumayya ta cigaba da cewa ki fauwalawa Allah lamarin ki, ina tabbatar miki zai kawo miki mafita, ki ha'kura da Mukhtar yadda ya ha'kura da ke, ba sai da shi za ki rayu ba, ba sai da shi za ki yi farin ciki ba, ki dube mu, ruwa da iska ba zamu canja ki ba, shi kuwa ko gobe kina iya jin ya auri madadin ki, ya shayar da ita soyayya irin ko ma ta zarta wadda ya miki, fatana dai ki 'dauki darasi, kar ki sake maimata irin kuskuren da ki ka yi idan kin samu wata damar". Ganin maganganun na shigar Sa'adah sosai, Sumayya ta zarce da fadin "gaba'daya aure ha'kuri ne da kawar da kai, duk macen duniya da ki ka ga ta tsufa a 'dakinta ta shiga 'kalubale kala kala, amma idan aka yi ha'kuri aka danne sai a cimmma babban matsayi, ki cire buri, da son 'kyale 'kyale ki rabu da 'kawayen banza na tabbatar wadannan abubuwan sun taka muhimmiyar rawa wurin mutuwar aurenki". Sosai ta ke kuka a 'kirjin Sumayya karon farko tun bayan rabuwar su da ta samu ake rarrashinta cikin tausayawa. Haka suka shafa lokaci mai yawa Sumayya na lallashinta, tare da 'karfafa guiwarta. Kwanaki goma Sumayya za ta yi tare da yaranta, adalilin Yaran suna hutun zangon karatu na uku, sannan kuma mijinta na cikin tawagar da aka zaba zuwa New York din 'kasar Amurka akan sanin dabarun inganta bankunan 'kasashen Africa. Zaman Sumayya ya taimaka wa Sa'a sosai, tare suke cin abinci, sannan sai da ta sa Inna ta sauko da ga fushin da take yi da ita, Baffa kuwa cewa ta yi tasan duk dauriya yake yi, amma ai shi da Iyah sai Allah. Ya yi dariya ya ce "wato ta tabbata kema zargina kike akan na fi sonta, kamar yadda itama ta ke 'kalubalantar gyatumarku ta fi son ki". Sumayya ta yi dariya ta ce "Ni bana kalubalantar ka Baffa, ai ita 'karama ce, sannan sunan iyakar ka ce". "Allah ya miki Albarka Sumayya, yau kusan shekaru sha bakwai da auren ki, ba ki taba janyo mini bacin rai ko jin kunya ba, ina fatan ki dore da hakan, ina matu'kar jin dadi, Ina alfahari da kasancewa ta uba a gare ki, Àllah ya miki shirya miki zuri'a, ya faranta miki, ya buda miki kofofin alheri". Cikin kukan farin ciki ta ke fadin "Ameen Baffa!ni ma Ina alfaharin da ka kasance uba mai kare mutunci da martabar yaransa a gidajen aurensu madallah da uba irin Baffah na". Sa'adah da ke 'daki tamkar mujiya ta ji wani 'kullutun ba'kin ciki ya mamayeta tun farko dama tana kishin taga iyayen ta suna nunawa Sumayya soyayya sama da ita, duk da Inna ta fi wannan abin dan ta cusa mata takaici, amma Baffah kowa yasan itace 'Yar gaban goshinsa, amma wai yau ita ya ke yiwa zambo, yana nunawa Sumayya ce mutum, yana ta 'kwararo mata addu'a ita ka'dai. Hawaye na zuba 'kasa 'kasa ta ce "Ni da na yi shekaru bakwai aka sako ni, sai a kore ni ko a tsine mini na bi titi ina tsince tsince". Da sauri ta tura hular kanta a baki tana cewa " Astagafirillah Ubangiji ba da Baffah na ke ba da kaina na ke, Allah na tuba, ka yafe min, ka mini albarka, ka saukaka mini lamarina, ka mayar da ni 'dakina". *SURAYYA DAHIRU* ✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU GWARAM*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A kiyaye ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *Gaisuwa da fatan alheri ga wadannan groups din* *M HAUSA NOVEL* *MAMAN YUSUF FANS*. *ASMA BAFFAH FANS*. *MAMAN MAMAH NOVELS*. *HUGUMA CONVERSATION*. *THE SPARKLE*. *DUNIYAR NOVEL*. *UMMU ILHAM HAUSA NOVEL*. *MARUBUTA* *BENEFICIAL WRITERS* *ZAUREN KARATUN HAUSA*. *FAR JEED-DAH HAUSA NOVEL* *BAKANDAMIYA HIKAYA*. *QIYAS HAYAT HAUSA NOVELS *_Dukkan ku madallah na gode da yabawa*_. *Fatan alheri ga Aminyata* *SHAFA'ATU ALHASSAN BAUCHI* *Na gode sosai da yabawar ki kan rubutuna ubangiji ya dorar da zumuncin mu, Sa'adah ta ce ki rokar mata Mk*😁 *_JAN HANKALI_* *BABU MAHALUKIN DA YAKE SO A TABA MASA ABIN DA YA SHA WAHALA KAFIN YA SAMAR DA SHI BA TARE DA IZININSA BA! SABODA HAKA A CIKIN MAFI YAWAN SHAFUKAN NA KAN YI GARGADI AKAN LAIFI NE TA'BA WANNAN LABARIN TA KOWACCE IRIN SIGA BA TARE DA IZININ MAI HAKKIN MALLAKA BA. A YAU NA CI KARO DA HALIN YAU DOCUMENT WADDA AKA YI BAN SANI BA, NA ROKE KU KAR A KUMA, NASAN SOYAYYAR LABARIN CE TA KAWO HAKAN, AMMA NI KO KUNGIYAR DA NAKE CIKI NE KA'DAI KE DA IKON YIN HAKAN, INA FATAN ZA'A FAHIMCE NI, DOMIN RASHIN KIYAYEWA KA IYA ZAMA DALILIN KATSEWAR LABARIN GABA'DAYA. UBANGIJI YA BAMU DAMINA MAI ALBARKA!_* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 81_82. Zaman Sumayya ya taimaka 'kwarai wurin ragewa Sa'a damuwa, haka nan basu koma Gombe ba sai da suka kwashe kwanaki sha biyar a maimakon goma da za su yi. Ranar da suka tafi ba 'karamin filin'dakin Sa'adah ta gani ba, tana jin tamkar sun tafi da wani sashe na jikinta. *SATI BIYU* Ranar da ta ga period 'dinta na uku, hankalin ta ba 'karamin tashi ya yi ba, damuwarta ta dawo sabuwa fil. Cikin dare ta kasa barci ta rasa inda zata tsoma ranta, ga fanka na ka'dawa a sama, amma zufa ke damunta ji take tamkar ana hura mata wuta, tana zaune banda tunani iri iri ba abin da ta ke yi. Tsawon lokaci tana zaune, kafin ta tashi da 'kyar ta fita zuwa ban'daki, dan watsa ruwa. Ta fito, har za ta shiga 'daki idonta ya hango mata wayar Inna a cikin bahon kayan sana'ar ta, da mugun sauri ta juya ta 'dauko ta shige 'dakinta, dan Inna bata bari ta 'daukar mata waya. Sai da ta kintsa kanta sosai gudun staining. Sannan ta 'dauko wayar ta shiga lalubo lambar Mk! Zuciyarta na bugawa da 'karfi, cikin sa'a kuwa bai kashe wayar ba, abin mamaki kuma bugun farko ya 'dauka, ta daburce ta rasa me za tace, sanin halinta da ya yi wadda masu azancin magana suka ce yafi sanin kama. Yasa yace "me ya hana ki barci?" Cikin rawar murya tace " Malam!" Sai kuma ta kasa magana kawai ta saka masa kuka sosai. Kukanta da yake ji ya taimaka wurin sake jefa shi ru'danin da yake ciki, tun rana yake cikin fargaba da yaga kwanan wata a wayarsa. take ya tuno a irin wannan kwanan watan Sa'adah ke fara ala'adarta kenan tana gaf da fita daga matarsa, tun lokacin, ya rasa kwanciyar hankalinsa. Ya tabbatar itama dalilin da yasa take kokawa kenan. Ya rasa me zai ce mata. Tsawon lokaci suna haka, tana rera masa kuka, shi kuma yana ri'ke da wayar a kunnensa yana sauraronta, sai kuma ya ji 'kiran ya katse. Ya duba sai ya ga ashe ita ta 'kira, wata'kila kudin wayar ne ya 'kare. Bai yi jinkiri ba, ya bi bayanta, ta 'dauka ta na cigaba da kuka tamkar matar sabon mamaci. A hankali ya ce "ki daina irin wannan kukan za fa ki ha'du da ciwon farat 'daya". Cikin kukan sosai ta ce "ina fatan ciwon ya shige ni da 'karfi irin 'karfin guguwar iska, idan na yi sa'a ya dangana ni da kusheweta, wata'kila na huta da azabar da nake 'dan'dana da raina a cikin wannan duniyar". Kuka sosai take yi, wadda ya matu'kar dukan zuciyarsa sosai. Ya nisa ya ce "Zan tambaye ki, kinsan na san ki tamkar tafin hannu na, kar ki mini 'karya dan kuwa zan gane ki". Ta tsagaita da kukan, kafin ta bashi amsa ya ce "wa ya baki waya da agogo da kayayyaki a Jawad?". Zuciyarta ta buga ta 'barke da kuka tana cewa "Dan Allah ka fahimce ni, ba fa yadda ka ke zato bane". Ya busar da iskar 'bacin rai ya ce " ok to fahimtar da Ni! ina sauraron ki, warware mini". Da rawar murya ta ce "Tsakani na da Allah! Saurayin Safina ya siyo mata, ita kuma already tana da ita, shine ta bani, akan na bata rabin ku'din ". Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Ina jin ki! A ina kika samo ku'din?" "Zobena 'daya na gold na bata, a hankali kuma zan cika mata sauran ku'din da suka rage tunda ba yawa". Ya yi shiru yana nazarin anya Sa'a za ta shiryu, yanzun nan ta tsara labari tamkar a wasan kwaikwayo ko a littafi? A kausashe ya ce "kuma ya aka yi naga ba sunanta bane akan rasit din siyan wayar?". "Malam! baka lura bane domin kuwa SB aka saka ma'ana Safina Bunkure". "Hmmmm" ya furta kawai ya yi shiru. "Gaskiya na fa'da maka Malam". Yace " idan kina ganin na gamsu ba Sa'adatu Bashir ake nufi ba. to ki fa'da mini, ta ina kika mallaki agogo mai daraja haka tunda English gold ne". Duka na Safina ne, kayan da ka gani kuma siyawa Jawad ta yi tunda Alheri ta samu ba ka'dan ba". Ya ce "alheri irin na 'yantattun Mata?" Jikinta ya hau ' bari ita kam tam ta shige su, kalma 'daya tak da ta fa'da ta wanke ta a zuciyar Mk! ta janyo Mata tashin hankali mai yawa, ta yi amanna har da wannan kalamin suka 'kara fusata shi, ya yi irin fushin da bata ta'ba hararowa zai yi ba, hakanan kalaman sun janyo ya kasa gasgata ta. A daren ta gane tuntu'ben harshe yafi zafi fiye da wadda za'a yi da 'kafa ta fashe. Jin ta yi shiru ya ce "Sa'adatu har yanzu ba ki shirya fa'da mini gaskiyar magana ba, bare na auna naga zan iya miki afuwa ko bazan iya yafe miki ba! Abin da nake son ki fahimta shine, ki daina yaudarar kanki cewar wannan laifin zai wanku a gurina da kwaskwarimar 'karya. matu'kar kin san ba zaki fa'da mini gaskiyar lamari ba to ki daina tunanin maganar zata bi ruwa da sau'ki." "Gaskiya na fa'da maka Malam! ka zafafa ne, ya kamata ace kasan abin da zan iya da wadda ba zan iya ba! ko ban tsira da komai ba, ka gaskata ni mana". "Ki mini adalci! wacce maganar zan 'dauka na gasgata ki akanta, alhalin tunda abin nan ya faru, kike ta canja magana, kin ce Sumayya ta baki, kin ce ta Halimace, kin ce ta Safinace shin wacce zan 'dauka na gasgata ki akanta?". Shiru ya ratsa amma zukatansu sai bugawa suke yi tamkar ana lugude, ya nisa ya ce "ki kwantar da hankalin ki, duk sadda kika yi nufin fa'da mini gaskiya, Ni kuma na miki al'kawarin zan saurare ki, nasan kuma zan sami nutsuwa a zuciyata tunda gaskiya a bayyane take bata bu'katar ado". "Malam na kusa kammala iddah fa, dan Allah " sai ta fashe da kuka fiye da na farko. Yace "Na sani! yau kika fara period 'din ki na uku, me kike jin tsoro?" Ta kasa yin magana, ya ce "Ni ya kamata na yi fargaba, Ni ya kamata na koka, domin zan rasa damata, sai dai na shiga sahun zawarawa, ke kuwa ai baki da damuwa idan har kina sona ai za'bin a hannun ki aka dam'ka shi". Cikin kukan ta ce "Ban son muje ga haka, Ni ka zo ka dauke ni mu koma gidan mu, na yarda kar ka ci abinci na, kar ka kula ni har sai ka gamsu kamin abin da ka huce". Ya ce "matu'kar muna tare kin san ba zan iya wannan jarumtar ba". Ya sassauta ya ce "ki dinga addu'a sannan ki bar komai a hannun Ubangiji. Abin da nake so ki fahimta, wallahi na fiki shiga damuwa da tasku, kawai ni jarumta na fiki saboda kasancewata Namiji! Sannan ba zan ta'ba sauya hukuncin da na yi mana ba, har sai kin fa'da mini gaskiya koda hakan na nufin rushewar farin-ciki na gaba'daya, duk lokacin da kika shirya fa'da mini gaskiyar magana, ki mini magana". Da haka ya kashe wayar gaba'daya. Ta yi sororo da waya a kunnen ta, tana kallon agogo da ya nuna uku da rabi da minti biyu. ' Har aka fara 'kiraye 'kirayen sallah barci bai iya surarta ba, tana ta tufka da warwara, ta yaya zata iya fa'da masa Khalil ne ya bata wadannan kayan? To akan wanne dalilin zai mata kyautar su ta karba? zuciyarta ta shiga harbawa, bare da ta tuno waccan kato'barar maganar da ta yi. Ta yi amanna har da wancan laifin ya sake girmama wannan laifin a zuciyar Mk, sai ta yi kamar ta fa'da masa gaskiya sai ta tsorata, a yadda tasan ya tsani Khalil zai iya 'kararsa ko dan ya ci mutuncin gidansu tunda mahaifin Khalil fittacen 'dan siyasa ne, ita kuma ta hadu da zubewar mutunci a idon dangi dama duniya gaba'daya tunda tasan suna chatting da shi, ha'kika Sa'a na cikin hali irin na canka ca kare. A fili ta dinga fa'din "Allah na tuba! na cuci kaina, son zuciya ya janyo mini 'bacin rai da damalmalewar lamura! Na keta alfarmar shari'a shiyasa na ke 'dan'danar 'bacin rai mai azabtarwa". Tamkar mahaukaciya take surutai, tana sake cewa "Na yi al'kawari idan har na koma 'dakina bazan sake yin wani abu na rashin gaskiya ta kowacce fuska ba, sai da nace wa su Halima ina jin tsoron abin da zai biyo baya ta mini ingiza mai kantu, na biyewa 'kawar zuciyata na gasgata su, waiyo waiyo! Lah ilah ha illah anta subhanaka inni kuntu minan zalimin". Duk akan kunnen Inna take wannan koke koken, da suratai duk da bata fahimci me take fa'da ba, da farko tsorata ta yi, ta 'dauka gwaiguna ne, sai daga baya ta fahimci daga 'dakin Iyah ne, a hankali ta fito, kasancewar Baffah yana Gogel. Har ta isa bakin 'kofar dakin, sai kuma ta fasa, ta juya a zuciyar ta kuma tausayin'diyarta ya fara kamata, ta dinga mata addu'ar samun sassauci a zuciya. Haka kwanaki suke ta shudewa, fargabar Sa'a na sake girmama, ba ta sake tuntunbar Mk ba, sai ana gobe za ta kammala iddarta, duk yadda ta kada billenta ta dinga ro'kon kar ya bari ta fita a matarsa bai ji ba, ya nan akan bakansa sai ta fadi gaskiyar lamari. Washagari ta tashi da zazzabi ga kuka ya ki yanke mata. Inna ta kasa jurewa yanayin da ta ganta a ciki, har 'dakinta ta shiga ta zauna kusa da ita, ta ta'ba jikinta. Zafi zau ta ji, ruwa ta samo da tawul ta dinga goge mata jiki. ta taimaka mata ta canja Riga, ta zubo mata kunu a kofi ta matsa mata ta shanye, sai dai tana gama shan ta amayar da shi tas. Haka Inna ta sake gyara mata jiki, da kuma wurin, tana fatan inama ace ciki ne da ita wata'kila hakan yasa mijinta ya mayar da ita. Baffah da bai fita ba, shi ya nemo Usaini mai chemist ya duba ta, ya kawo mata magungunan da zata Sha. Tafi kwana uku tana mukurkususu, kafin ta fara warewa, saboda yanzu Inna ta sassauta mata, damuwar ta dan yi sauki. Sati biyu da kammala Iddarta, tana tsakar gida tana wankin kayansu dana Inna sai ganin Jawad suka yi ya shigo a guje kamar yadda ya Saba. Kai tsaye ya nufi uwarsa ya rungume ta, ita kuma idon Inna ya hana ta rungume shi, sai ta bige da fa'din wa ya kawo ka? Yana jikinta yace " Malam ne, kullum sai na yi kukan gurin ki zan zo shine yau Hajiyar Bichi tace sai ya kawo ni, tunda jiya anyi hutun boko". Inna da ta ke zaune tana fere doya tace "wato Jawad ba ka ganni ba ko, Anya kuwa za ka yi al'kawari?" Kafin ya yi magana sallamar Hajiyar Bichi ta cika kunnuwansu tare suka shigo da Baffa, Inna ta mike da azama tana fa'din lale da Hajiyar Jawad, ashe tare ku ke tafe?" Falo suka shiga! Inna ta gabatar mata da ruwa ta zauna Don gaisawa, sai taga Hajiyan na share hawaye Baffa na cewa "to ya za'a yi, sai ha'kuri, komai rubutacce ne, idan rabo bai 'kare ba za su koma, idan kuma ya 'kare sai duk mu yi ha'kuri, mu bisu da addu'ar fatan alheri! fatana dai ki cire damuwa a ranki. Wallahi bamu 'kullace ku ba, Ni ko Mutari har yau ban ga laifinsa ba, Allah shine shaidata, kawai dai zan so ace sun shirya kansu ko dan rayuwar 'dansu ta inganta". Murya a dakushe Hajiyar ta ce " Nima abin da nake ta hango musu kenan ban da dole yaushe za'a raba yaro da uwarsa! kome za'a masa ba zai gamsu ba idan ba uwarsa yake gani ba. Haka nan ba kowacce mace bace zata ri'ke'dan da ba nata cikin adalci da kyautatawa ba, akwai su amma sun yi 'karanci 'kwarai da gaske". "Allah ya musu za'bi mafi alheri" Baffa ya fa'da yana barin falon. Hajiya da Innah suka ha'da baki wurin cewa " AMEEN". sannan suka shiga gaisawa tare da jajanta 'kaddarar da ta fa'dowa yaran su. Jikin Hajiya a sanyaye yake sosai, tunda abin nan ya faru take son zuwa, amma kunya da nauyi sun hanata, sai yau ta yi shahadar zuwa, ha'kuri ta bayar yafi cikin kwando, karbar da ta samu daga iyayen Sa'a yasa ta sake jin nauyinsu ainun, karamci a jininsu yake, tabbas Mukhtar ya yi asarar irin zuri'a me yakana da alheri. Ganin Baffah ya fita ya Sanya Sa'a dauko Hijabinta ta saka ta shiga falo Jawad na binta tamkar jela. Daga gefe ta tsugunna, ta gaida Hajiya kanta a 'kasa. Hajiya ta hau fa'din taho ki zauna kusa da ni Sa'a. Da rarrafe ta karasa kusa da Hajiyan, amma kanta a 'kasa tana Jin kunyar Hajiya na kamata irin wadda bata ta'ba ji ba. Sosai Hajiya ke kallon yadda ta lalace ta yi ba'ki sosai, 'kwalla ta cika idonta a sanyaye ta ru'ko ta jkinta, hawaye ya gocewa Sa'a ba tare da ta shirya ba, tana yiwa kanta jajen rashin suruka irin Hajiya! Ta tabbatar samun uwar miji irinta a Yau zai yi matu'kar wahala. Itama Hajiyar kukan take yi, tausayin Sa'a da Mukhtar da tilon dansu na matu'kar sa ta zubar da hawaye. Wacce irin ba'kar 'kaddara ce ta afka musu haka? Mussaman yanzu da taga irin bibiyar da Jawad ke yi wa uwarsa, duk inda tasa 'kafa nan yake mayarwa, duk irin gatan da take masa, duk yadda ubansa yake masa siye-siyen kayan wasa da na ciye-ciye kala kala, bai hana ya yi kukan neman uwarsa ba, yanzu da ya ganta kuma ita ka'dai yake bibiya duk kuwa da yasan ubansa na 'kofar gida a zaune. Duk dabarar Hajiya dan Sa'a ta fa'di musabbabin rabuwar ta su ta 'ki!kuka kawai ta ke yi mai tada hankali, Jawad kuma na ta goge mata kamar yadda ya saba yi mata idan tana kuka. Tausayinta ya sake cika zuciyar Hajiya, ta dinga rarrashinta da kalmomi masu da'di. Da zasu tafi Hajiya ta kalli Jawad taga ya ri'ke Sa'a sosai, sai ta yi nufin tsokanar sa ta ce "to zo mu tafi Jawad". Ai kuwa nan da nan yasa kuka yana nuna dukkan yatsun hannuwansa yana cewa "Malam fa ya ce kwana haka zan yi?" Hajiya ta yi gaba tana cewa "yi shiru da bakinka wasa nake maka". Har zaure ta yi wa Hajiya rakiya, Mk na bakin kofar gidan a jingine yana waya, take zuciya ta ayyana wa Sa'adah da Farida yake waya a kofar gidansu. Hawaye ya sake kwace mata, Hajiya da ta zaci ganinsa yasa ta kuka ta hauta da fa'da sosai tana cewa "wanne irin sakarci ne wannan Sa'a? Kina bada ni, banda bayar da kai menene ba zaki warware ki saki ranki ba, kina kallon kanki a madubi kina ganin irin lalacewar da kika yi?" Ita dai Sa'a kuka kawai take yi 'kasa 'kasa, Hajiya ta nisa ta cigaba da cewa "ki kwantar da hankalin ki, kin ji!komai zai wuce kamar ba ayi ba, so nake nan da wata daya na ga kin dawo Sa'adatun nan mai birge yara da manya, Allah ya shiga lamarin ki, ya baki miji nagari, da zai wanke miki dukkan ba'kin cikin da kika kwankwa'da". Wani irin kishi da Mk bai yi zaton zai sake ji akan Sa'adah ba, ya kama shi, takaici yasa shi barin bakin 'kofar ya nufi mota ya shiga yana ta a'uziya, saboda yadda ya ji takaicin Hajiya ya kama shi matu'ka da gaske. Yana tuki amma zuciyarsa tamkar ta fashe, a gabansa Hajiya ke wannan fatan. ita kuma da ta lura da yadda yake ta 'dacin rai, tunda ta shigo motar ta gane kishi ne ya turnike shi, dan ayiwa matar da ya saka, ya ki mayar da ita fatan samun wani mijin. Ta dinga kallon yadda ya fusata tamkar kububuwa, Hajiya ta tsinci kanta da mamakin kishin maza, ka saki mace, kace ba za ka dawo da ita ba. Sannan baka son kowa ya aureta alhalin tana cikin shekarun da take bu'katar auren. Itama haushinsa ya kamata da ya kasance cikin masu son kansu, sannan har ita zai yi wa wannan fishin?. Dan haka Yana shan kwanar layin 'Dan Hassan da shine layinsu amma a ciki suke sosai, sai an hau abin hawa. Murya a dake ta ce samu wuri ka tsaya! Bai yi musu ba, ya gangara ya yi parking. Ba jinkiri Hajiya ta fito cikin sa'a kuwa ta tsayar da dan adaidaita da zai shiga ciki, ba 'bata lokaci ta shiga suka tafi. Ba'kin ciki ya sake kama Mk idonsa ya yi jawur, ji yake tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu, Hajiya da Sa'a su huta da ganinsa. Yasan Jawad kawai ke da asarar rashin mahaifi, amma ita Hajiya tana da Ahamad, haka nan Sa'adah zata auri wani ya iya mantar da shi a ranta, amma Jawad fa? Duk yadda yake da tabbacin Abbas da Ahamad har ma da 'Karfi baza su bar tilon 'dansa ya yi kukan maraici ba, ya tabbatar Jawad ba zai rasa uba ba, amma tabbas zai yi asarar rashin mahaifi da ba a samun biyu. A hankali ya ja motar yabi bayan su Hajiya. Tsawon lokaci yana gurfane gabanta, ita kuma ta yi 'diban karan mahaukaciya da shi. "Hajiya Dan Allah ki gafarce ni, ban san me na yi miki ba, fishin ki dafi ne a rayuwata, ki mini ha'kuri dan Allah". Karo na hudu kenan yana maimaita wannnan kalamin, ta kalle shi ta ga duk ya sake firgicewa, da gaske tasan yana tsananin gudun zuciyar ta, amma dole ta nuna masa ita ba UWA bace irin Agwagwa ba, yaranta a gaba ita tana binsu a baya. Ita kaza ce da ta ke gaba 'ya'yanta na bayanta, sannan idan ta ga 'da ya yi rashin 'da'a ta take shi ba dan bata sonsa ba sai dan ya zama nagari abin so da kwatance a ckin alumma. A raunane ta ce "Kai ne da ha'kuri da na yi laifin da zaka iya mini fishi, har yaushe ka yi motar? da zaka dauko ni ka hade mini fuska tamkar wadda ka mini alfarma, ka sani ai ni ba bakuwar mota bace, idan ana sako wadda suka fara mallakar mota a Bichi da kewaye sai ansako gidanmu. sannan tun kafin a haifeka duk inda zani a mota ake kaini, bude ido ka yi ka ga mota a gidannan bare ka mini wani iyashege". A matu'kar gajiye Mk yake fa'din "Na yi kuskure, ki yi hakuri abin ne yafi 'karfi na, ki mini uzziri Hajiya, ki sake dagewa wurin yi mini addu'a". Ya Dora hannunsa daidai setin zuciyar sa ya ce, "zuciyata ciwo take mini sosai, tana mini zafi, wataran har numfashi bana iya yi, dan Allah ki yafe mini kar mutuwa ta zo mini kina fishi da ni, zan roke ki, komai na miki, da wadda zan miki nan gaba ki dubi Allah ki yafe mini, Ina rayuwa ne kawai amma wani lokacin bana sanin me nake ciki". Tausayinsa ya kama Hajiya sosai, ta zuba masa ido tana nazarinsa.ta sassauta murya tace kana son ka warke daga ciwon da keke 'dan'dana, kana son nutsuwa ta zo maka, ka dinga sanin halin da kake ciki, kana son nutsuwar da ta yi maka tutsu ta dawo maka? Ya ri'ke hannun ta muryar sa na rawa ya hau cewa 'ina so Hajiya, bana iya barci fa, ko abinci da na fara ci sai na ji ya tokare mini a wuya shikenan sai na kasa ci, kuma ina jin yunwar". Hajiya tace "fada mini laifin da Sa'a ta maka na san shine yake neman kassara ka, rashinta kusa da kai ne yasa kake rasa gane halin da kake ciki domin kana sonta, farincikinka na 'damfare da ita ne". Bai musawa Hajiya ba domin kuwa yasan gaskiya ta fada, amma sai ya saukar da kansa 'kasa ya ce 'kaddara ce ta rabamu Hajiya". Cikin rarrashi ta ce "Ni uwarka ce, duk wadda zai ri'ke maka sirrinka a bayana yake, me yasa kake gudun abin da ka ke so da gangan?" Sai lokacin bacin rai ya sake taso masa cikin fitar hayyaci ya ke firzar da maganganu " Ina sonta sosai, Ina son na rayu da ita, komai Ina yi mata, har da wadda ya fi 'karfina yi mata nake yi, amma kullum cikin zullumi nake zaune da ita, fa'da mini Hajiya me na gaza da ban cancanci na sami kwanciyar hankali da ita ba?". "Ba ka gaza ta ko Ina ba, itama ai kullum cikin damuwar take tunda kishin rashin hankali ta 'dorawa kanta". "Yanzu fa'da mini abin da ya kawo musabbabin rabuwar dan nasan irin hukuncin da zanyi, na kuma daina zarginka da manta alheri, da kuma rashin ha'kuri". "BA KOMAI QADDARAR MU CE". Ta zuba masa ido ta ce "Ko dai Ni ta zaga ko mahaifinku ko Hajiya Babba?". A hankali ya girgiza kansa ya ce "Haba dai, ai komin tsiyarta ba ta isa ta mini hakan akan idona, na barta haka salin alin ba, sannan fa Hajiya yadda kike sonta haka take son ki, Ina mata shaida ko giyar wake ta sha ba abin da zan yi mata ta zage ku". Ta kalle shi tana tuna fa'dar gaskiyarsa tun yana Yaro yana cikin abin da ya janyo masa soyayya a zuciyar mahaifinsa. "To Ni dai indai ba wannan laifin ba, banga me zata yi ka 'ki yafe mata har haka ba". Zuciyar Hajiya ta kasa daurewa tace "ko dai kama ta ka yi da wani?" A zabure ya mi'ke yana fa'din subhanllah! haba dai Hajiya me yasa za ki yi wannan hasashen, har abada Sa'a ba zata yi hakan ba, in sha Allah ba zata yi hakan ba duk lalacewar *HALIN YAU* SA'ADATU ba zata yi hakan ba". *SURAYYA DEE* ✍🏼✍🏼. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A kiyayi ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *Fatan alheri ga* *UMM ASGHAR NOVELS*. *NOVEL ONLY GROUP*. *Da dukkan grops din da ake tura wannan labarin ake sharhi tare da fatan alheri, ina ji ina kuma godiya da fatan Allah ya bamu damina mai albarka*. *Gaisuwa ga* *Fati Eshaik(Ummu Asghar)* *Zalhatu Umar(Yayar mu)* *Hauwa Umar(Mrs Nasir)* *Zainab Abdullahi(Beneficial group)*. *Fatima (Maman Aslam)* *Aunty Ai'nau* *Hauwa'u Umar Gwaram* *Balki Sani*. *Rahma Shu'aibu Kankara*. *Kulsum Baffah Azare*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 83-84. Sosai Hajiya ke nazarinsa, sannan ta sami nutsuwa da ya kasance ba abin da shaidan ke kissima mata bane. Dan haka sai ta ce "idan kuwa hakane banga menene mai zafi da ba zaka yafe mata ba, wallahi ta gane kuskuren ta, ka bata wata damar Ina tabbatar maka lafiya lau za ku zauna". A hankali ya ce "Dan Allah Hajiya na ro'ke ki, ki bar wannan maganar, ki mini afuwa, ki kuma yi mini alfarmar daina yin wannan maganar, kawai fatana ki mini addua". "To shikenan Allah ya yi zabin alheri". Ta fa'da jikinta a sanyaye. Ta bangaren Sa'a kuwa, har lokacin tana yawan 'kiransa a waya ta bashi ha'kuri, ko ta yi text, har ta kai har makaranta ta bishi, ta tsugunna a gaban sa cikin cire girman kai, tana bashi ha'kuri, a irin haka Farida ta fa'do ofis 'din ta tarar da su a hakan, ta juya da mugun sauri tana fa'din "Sorry excuse me" Ganin da Farida da ta yi mata gurfane a gabansa ya matu'kar dukan zuciyar Sa'a, da muryar kuka ta kalle shi tace "yanzu ita ka ke so shiyasa ka rufe mini 'kofar afuwa ko?" Kai tsaye ya ce "kinsan ba haka bane ,amma idan haka zuciyar ki ta rinjayar miki to bazan 'karyatata ba! Kar ki kuma zuwa mini nan, idan kina son magana da ni ki kira Ni a waya, Ni Kuma zan zo!amma wannan ya zama shine zuwan ki na karshe if not, zan fa'dawa Baffah". Da kuka sosai ta isa gida, ta wuce Inna, ta fa'da dakinta, ta kwanta tana rusar kuka mai tada hankali. Ada Inna ta 'kudiri aniyar duka zata mata, tunda ta fita bata sani ba, to kuwa zata nuna mata dan ta yi aure ta haihu ba ta fi karfin ta ba, bata wuce ta zaneta ba.😀 Amma ganin yadda ta shigo a kidime ga kuka tana yi na fitar hankali sai wanccan alwashin ya bi iska, ta ajiye lagwanin rishon da ta ke gyarawa, ta bita dakin. Ta shiga! ta zauna kusa da ita, ta sassauta murya ta ce "Iyah Ina son ki gane gaskiya, ki gane sunnar rayuwa, ba komai ne kake samunsa a lokacin da kake so ba, mata da yawa basu sami nasarar auren wanda suke so ba, amma sun yi ha'kuri da wanda 'kaddara ta za'ba musu, suna cigaba da rayuwar su tamkar basu da damuwa. Sa'banin ke da kin samu cikar burinki, sai dai *HALIN YAU* yasa kin tankwabar da dukkan daukakar da minjin ki ya miki, Ni na haife ki, ko Baffanki bai fini sonki ba Iyah". Wannan maganganun na Inna ya sake karyar da zuciyar Sa'a, ta kasa daina kuka. Yayin da Inna ta cigaba da cewa "Sai dai duk soyayyar da nake miki ba zan 'ki fadar gaskiya ba! Na tabbatar ke kika 'kullawa kanki wannan salalar tsiyar, ke Kika biyewa'kawar zuciya da shedanun 'kawaye suka jefa ki a kogin nadama, na shaida Muuutar mutum ne har da rabin mutum! Abin da nake so ki fahimta 'daya ne, A yanzu dai bae zai mayar da ke ba, na tabbatar da zai mayar da ke da sauri haka, da ya ha'diye abin da kika shuka masa ko dan mahaifin ki! Ki fuskanci rayuwar ki ta gaba, kin rayu a duniya shekaru goma sha shida zuwa Sha bakwai babu Muutar a cikinta, yanzu ma kuwa dole ki rayu babu shi, idan mutuwa yayi ai dole ki ha'kura bare yana raye, kuna sha'kar numfashi a duniya 'daya". Cikin rarrashi Inna ta sake cewa"Zan fa'da miki wani abu ki ri'ke shi da kyau, Wannan bibiyar da kike masa ita take sake sawa Yana nesanta da ke, kin yi laifi, kin bashi ha'kuri tamkar yawun baki zai 'kafe, kin yi nadama, nadama ta gaskiya, to ki barwa Allah lamarinki ya miki za'bi, zabin Allah kuwa gaba yake da son ranmu, idan Kika ha'kura kika yarda da kaddarar da ta afkoiki, kika gamsu idan kin samu wata damar baza ki sake maimata kuskuren ki na baya ba, kika gane darasin da rayuwa ta koya miki, ina tabbatar miki Allah ba zai barki haka ba, ko dai ya dawo miki da Muutar da kansa ta yadda zaki fi 'kima da daraja, ko kuma ya baki wani mafi alherin". Da sauri ta fada jkin Inna tana cewa "na gode Inna dan Allah ki dinga mini addua, ki mini adduar dangana ji nake zan mutu, Ina cikin kunci da ba'kin ciki mai yawa". A tausashe Inna ta ce kin bar Allah ne, shiyasa ya bar ki, ki yawaita addu'a, ki lazimci istigifari, duk tsaurin damuwa istigifari na wanketa. ki daure zuciyarki,ki daina rokon Muutar akan ya zauna da ke a dole, fadawa Allah damuwar ki yana jin ki". Da kuka sosai ta ce " To Inna". sai kuma ta dinga fadin Astagafirillah da karfin gaske hadi da salatin Annabi. "A hankali za ki yi Iyah, ko a zuci kike yi Ubangijinki ya ji ki" Bata daina ba, haka bata rage ba, ganin da Inna ta yi tamkar ba a cikin hayyacinta take ba yasa ta fita ta 'kyaleta, tun tana jinta har ta daina ji, ta leka ta ga barci ne ya mata shigar sauri, a fili Inna ta ce Allah ka dawo wa da yarinyar nan nutsuwar ta, Allah ka tausaya mata". Kwana biyu kullum Inna ke tausarta, hakan kuma ya taimaka gurin rage kaso mai yawa na damuwar ta, dama kuma ganin da Farida ta mata, tana tsugunne gaban Mk ne ya susuta ta, sannan ta sa a ranta soyayya yake da ita. A 'ko'karin Inna na son ta 'kara nesanta Iyah daga tunanin Mk yasa ta roki Baffa akan ya barta ta tafi Gombe ta yi ko wata 'daya ne, ko hankalin ta ya 'dan kwanta idan tana tare da yar'uwarta. Ai kuwa Baffa na bude baki yace "Eh ita ta'ki zaman aure sai kuma taje ta zauna gidan SUMAYYA, arasa gane wacece matar gidan a tsakanin su, wata'kila kuma idan ba sa'a aka yi ba, ta koyawa Sumayyan iyashege tunda tana ganin ita wayayyiya ce kuma me ilimi ce, sa'banin Sumayya da tasa Allah da Ma'aiki a gabanta! Ba inda za ta je nan ne dolenta, ba gidan Sumayya ba". Da 'kyar Sumayya ta roki Baffah ya amince Iyah ta je Gombe amma da sharadin sati biyu zata yi. Zuwan ta Gombe ya sake sa mata hakurin rashin Jawad da Babansa, duk da dai kullum dare sai ta ji'ka filonta da hawayen takaici da kewa mai yawa. Daga sati biyu sai da ta shafe wata uku a Gombe, wadda yayi dai-dai da wattanni bakwai da mutuwar aurenta. Ranar wata lahadi Mk da Mahmoud suka je wurin Baffa, suka gabatar masa da takardar admission din da Mk ya samowa Sa'adah A Aminu Kano college of legal studies (LEGAL KANO). Inda zata yi diploma a fannin Sharia tsawon shekaru biyu. Kai tsaye Baffah ya ce "Mutari ba zai yiwu ba, ka sani tun tana 'karamarta ban barta ta tafi babbar makaranta ba, aurar da ita na yi, sannan kaima tsawon shekaru bakwai ba ka'dan da ta yi a hannun ka, ba ka sata a makaranta ba sai yanzu?" Ya girgiza kansa alamun bai amince ba. Mk ya yi kasa da kai ya ce "Allah shine shaida tuntuni na so ta fara, to makarantar da take so bata samu ba, sai na mata sha'awar F.C.E KANO. Ashe mun makara sai muka bari sai bana, to ga yadda banan ta zo mana ba yadda muke zato ba. Dan Allah Baffah ka mini wannan alfarmar, ka barta taje ta yi ilimi ai yanzu ta yi hankali ba kamar da bane da kake jin tsoro". "Mutari ka bar wannan maganar dan kuwa bata shiga kunne ba, ba kuma zata shiga ba". Sai lokacin Mahmoud ya ce " Hakuri zaka yi Baffah! Idan ka gamsu da gaske Mukhtar bai rabu da Sa'a da nufin tozarci ba, to ka bashi dama ta shiga makarantar nan, yadda ya dauke ka, wallahi ko aure bai gitta a tsakanin su ba, shi me yin alheri ne ga ahalinka. Sosai su Mk suka matsawa Baffa da roko har suka shawo kansa ya amince, zata yi karatun amma da zarar mijin da ya cacanta ya fito neman aurenta to zai katse karatun, domin kuwa yafi bu'katar auren akan karatun. Jikin Mk ya yi sanyi tubus adalilin kalaman Baffah, na farko da Baffa yace ya fi bu'katar auren sai ya ji tamkar gugar zana ya masa, sai kuma kishin da ya ce idan ta sami miji zai yi aurenta. A satin ta dawo kasancewar har fara karatu a makarantar, ba ta yi wani murna ba, amma dai ta gamsu ta fara karatun shine yafi mata alheri, zuwa wannan lokacin ta fara ha'kura da Mk! duk da zuciyar ta tafi son ta koma masa, ha'kurin na dole ne mussaman yadda Inna da Sumayya suke ta yi mata nasihar hakuri da karbar kaddara. Ana jibi zai tafi Uk, inda ya samu gurbi a Jami'ar Bhirmingham zai yi digirin digir gir (P H.D). duk akan harshen turanci. Baya so ya tafi bai yi sallama da Sa'a ba, haka kawai zuciyar sa ke ta azalzalar sai ya mata sallama, kunyar zuwa gidansu yake yi, ta yaya ya saketa, bai mayar da ita ba kuma ya je nemanta, me iyayenta za su dauke shi?. Dabara ta fa'do masa, dan haka lokacin tashin Jawad a makaranta na yi ya bar koami ya 'dauko shi da kansa bai zame ko Ina ba sai legal. gefe ya samu kusa da masallaci a jikin wata bishiyar darbejiya ya yi fakin. Ya jima a zaune a mota cikin rashin abin yi, tunda yanzu bata da waya, ko ta Inna ma bata sha'awar ri'kewa dama shi take nacin kira, zuwa yanzu kuma ta yi matu'kar rage 'kiran nasa, duk da dai idan abin ya juyo mata tana kiransa ko text me dauke da kalaman fatan alheri, da tuni akan girman ladan da me yin ha'kuri ke samu. Ya yi zurfi, cikin tunani ya ji Jawad na cewa "Mami" da 'karfin gaske. Ya zabura ai kuwa itace ta fito a masallaci sanye take cikin dogon hijab har kasa kalar albasa, ya sha guga, fuskarta dauke da farin glass, ba kwalliya ko ka'dan a fuskarta, sannan zuciyar ta ba sukuni amma sai ta yiwa Mk kyau. Da sauri ta 'karaso yayin da Jawad ya balle motar ya fice ya nufeta da gudu, ta tsugunna ta bu'de masa dukkan hannuwanta ya fa'da, sakwanni goma suna haka sannan ta dago shi, ta ce "Halan biyo Malam ka yi akan dole, Na ganka da uniform?" "A a dauko ni ya yi daga school ko gida bai kai ni ba! Ya zarce da cewa "Mami me yasa ba kya daga Ni sama irin yadda Malam ya ke mini?" Da murmushi a fuskarta ta ce "saboda bani da 'karfi Jawad". Maimakon ya yi shiru sai ya sake cewa "yau kin rungume ni, amma a gidan Inna ba kya yi mini haka". "Oh Jawad! to kunya nake ji kar Inna ta ce ban da kunya". Ya kalleta badan ya gane manufar ta ba. Mk da ke jinsu ya bude motar ya fito, suka kalli juna, a nutse Sa'a ta gaishe shi. Ya amsa yana cewa " ya karatun dai ?" Ta amsa da fa'din Alhamdulillah". Kai tsaye ta ce "wani abu zaka yi ne anan?" kai ya girgiza ya ce "sallama na zo yi miki duk yadda nake cikin bacin rai ba zan iya tafiya ban miki sallama ba, jibi idan ubangiji ya nuna mana zan tafi ingilah, Ina fatan za ki yi karatun ki da kyau, Ina miki fatan dukkan alheri a rayuwar ki" Da ga jin yadda ya ke magana kasan cikin rauni yake yinta. Ita kuma tuni hawaye ya goce mata, ta yi 'kasa da kanta ta kasa furta ko da kalma guda. Takaici ke cinta ta ko'ina, tafiyar da ya dinga cin burin dai ita da Jawad zai tafi, har ta yi karatu ta kuma haihu acan sai gashi tafiya ta zo amma ba ita. Kusan kullum sai ta ci karo da abin da ta rasa a dalilin rashin Mk. Ya nisa ya ce " duk hidimar ki ta makaranta tana hannun Mahmoud, zaki bude account, fatana kar ki tambayi Baffah kome, ke kanwata ce, ko ba ma tare zan miki komai Dan rayuwar ki ta inganta, ina miki fatan alheri a rayuwar ki ta gaba, na yafe miki dukkan kurakuran da kika mini, fatan nima zaki yafe mini inda na musguna miki". Ta 'dago idanuwanta cike taf da 'kwalla ta ce "Baka mini komai ba sai alheri, ban san wani abi da kai mini ba face mutunci da karramawa, nima ina maka fatan alheri, Allah ya bada sa'a ya tsareka a duk inda zaka samu kanka". Sai kuma kuka sosai ya 'kwace mata, bai yi yun'kurin hanata ba, domin shi kansa da yake namiji ji yake tamkar ya yi ta zunduma ihu ko a fahimci Halin da yake ciki. Idanuwansa sun yi jawur tabbacin yana cikin damuwa mai yawa. Tsawon lokaci tana kuka kafin ya ce "it's okay ya isa haka zuwa yanzu ai kin dan samu relief, kukan ya isa haka share fuskar ki Jawad na kallon ki fa". Ta dago ta sake kallonsa ta ce "Da gaske ka yafe mini Malam". Da sauri ya'daga kansa yana fa'din har zuciyata". Murmushi mai ha'de da hawaye ya subuce mata ta ce " zan yarda ka yafe mini ne, idan har ka mayar da Ni, zan gamsu da gaske ni 'kanwarka ce idan ka mini adalci irin yadda yaya zai yiwa 'kanwarsa na duk girman laifinta ba zai janye jinin da ya hada su ba. Ka mayar da ni zan jiraka ko da baza mu bika". Ta yi shiru tana shanye kukan da yake son kwace mata. Ta nisa ta ce "Har gaban abada ba zan ri'ke waya ba, ba zan sake mu'amala da su Halima ba, sai abin da kake da dama shi zaka yi mini Dan Allah kar ka tafi ka barni a haka". Ya nisa yana jin wani irin abu ya shake shi, ya ce "Sa'adatu ki barwa Allah ya mana zabi kin ji, ina son ki har yau, idan 'kaddarar zaman bata 'kare ba ubangiji zai sake hada mu, amma ni yanzu fatana ki cire damuwa a ranki, ki fuskanci karatun ki, shi zai taimake ki a ko ina zaki samu kanki, duk abin da ya taso miki ki fada mini kai tsaye ki ji tamkar Nima Sumayya ne a gurin ki". Ta kasa yin magana sai goge fuskar ta take duk ta bata Hijabin nata, haka ya shiga mota suka tafi Jawad ya yi lakwas, ya zama marar kuzari adalilin Halin da ya ga uwarsa a ciki. A hanya ya dinga fa'din"Malam sai yaushe Mami zata zo ta dauke ni, mu koma gidan mu, me yasa kullum sai ta yi kuka? ko abinci bata ci sai Inna ta zauna kusa da ita, me take yi anan din?" Ya 'kasa bude Baki ya amsa masa, ganin da Jawad ya yi bai kula shi, yasa shima ya yi shiru dan yasan idan ya dame shi zai mammake shi ne. A kofar gidan Hajiya ya ajiye shi, ya juya karban wani sakon, sukuku Hajiya ta ga Jawad ya shigo Mata, ta dinga tambayar me ya same shi a Ina kuma ya Da'de ?. Ai kuwa ya marairaice ya ce "Mami ce take ta kuka". "A ina ka ga Mamin?" "Malam ne ya kai mu, tana wani waje babba har da masallaci, tana ta kuka, tana ce masa ya mayar da mu gidan mu". Jikin Hajiya ya mutu ta ayyana idan Mukhtar bai yi taka tsan tsan ba zai jefa 'kinsa a zuciyar 'dansa. Wacce irin zuciya ne da shi haka mai tauri bata sani ba, kana son mace kana bibiyar ta amma ka kasa yafe mata ko dan kaima hankalin ka ya kwanta?. Haka da ya zo ta dinga masa fa'da akan lalle ya mayar da Sa'a, amma ya kafe akan ta cigaba da addu'a abarwa Allah, ta yi shiru ta fara wasiwasi ko jifansu aka yi, ko aljana ce ta shige shi, tunda matsalar kin auren a gunsa take. Haka ya tafi kasar ingila ya bar Jawad a hannun Hajiya. Kuka ba irin wadda Sa'a bata yi ba dan kuwa tafiyar sai ta sake dagula mata lissafi, sati guda bata zuwa ko makaranta, har ta kai tausayinta sosai Inna ke yi, saboda ta gane sosai Iyah ta yi nadama, amma Mukhtar ya rufe 'kofar sulhu, duk da har a lokacin bata kullace shi ba. Zainab Ma'aji da ta kammala karatunta tana bautar 'kasa ita take ta jelan zuwa tana jinya ha'di da ban baki har ta fara samun sukin jiki da na zuciya. A wannan lokacin Sa'adah ta gane Bata da 'kawa ta amana irin Zainab domin ta nuna mata kauna ta gaskiya, ta tsaya mata a sadda ta shiga taskun rayuwa, yayin da su Halima da Safina har yanzu da ta shafe watanni masu yawa a gida basu waiwaye ta ba. Haka nan ko a group din su na old girls basu ta'ba jajenta ba, dan tana yawan tambayar Zainab ko ta ga sun neme ta, amsar dai itace basu yi ba. Ganin Mk ya bar kasa yasa Baffa amincewa da shawarar Sumayya da ta bayar na asiyar da kayan furniture's din Sa'a, a waccan lokacin kin amincewa ya yi, yana tunanin ko Allah zaisa su daidaita kansu, sannan kuma ai ba su suka yi kayan ba. Tv da freezer kawai suka bari sai set din gado daya da katifarsa, aka hada kan kudi akaje can kauyen Alu gaban unguuwa uku aka sai filaye a jere guda biyu, bayan ta siyar ta zobenta daya aka cika kudin, tunda ba kamar yanzu bane da komai ya yi tsada. *Shekaru uku a gaba* Zuwa wannan lokacin kome ya lafawa Sa'a, sai dai damuwar zuci wadda karfin imani ke sawa ayi harka sosai har aga kamar mutum ba shi da damuwa Sau daya Mk ya zo yayi sati uku ya koma Ta kammala karatunta na diploma, ta yi jarrabawar D.E. don 'dorawa da karatun digiri a Jami'ar Bayero, duk da Baffah bai sani ba jira suke a samu admission din sai asan yadda za'a bullo masa, har yanzu kuma Mk ke dawainiya da ita duk da ba kasafai ma suke waya ba, Dan har yanzu ta'ki rike waya sam, amma duk karshen wata zata ji alart na kudi a wayar Inna tunda da layin ta bude ko mantawa ba ya yi, hakanan duk karshen wata Hajiya ke kawo mata Jawad da kanta yayi kwana biyu, idan kuwa aka yi hutu gaba'daya a gun uwarsa yake yinsa. Ba wata wahala ta sami admission a B u.k kasancewar ta dage ta fito da sakamako me kyau a diplomarta hakanan jamb dinta ta yi kyau. Wannan karon Sam Baffa Bai tirje ba saboda ya yadda iya a nutse take, sannan idan ba makaranta ba ko kofar gida bata fita, haka nan idan antashi bata tsaya ko Ina gida take Yi, hanyar ta daya tamkar tururuwa. Sai dai a ranar da zata fara zuwa Jami'ar Bayero, a tsakar gida a gaban Innah Baffah ya ce "Iyah kina karatun nan ba dan ina so ba, na so ace daga gidan mijin ki, kike wannan karatun amma na yarda ki yi, domin na gamsu alfaninisa yawa ne a rayuwar ki da dukkan wanda ya shafe ki, ina fatan yaddda na barki kike karatun ki ba dan ina so ba, sai dan rayuwar ki ta inganta, Nima wataran zaki mini abin da nake so ko da bakya so, sai dan kin san ba zan miki sanadin shiga wahalar rayuwa ba". Kai tsaye ta ce "In Sha Allah Baffah, bana fatan na fifita son raina akan na ka, bana fatan ranar da zaka ce na yi wani abu na bijire maka". Ya dinga mata addu'ar samun Nasara a dukkan al'amarin ta. Ba abin da ke gabanta sai karatunta, bata saurarar kowa, haka nan bata da kawa saboda ta ga illar kawance, tsakanin ta da abokan karatunta, gaisuwa da tattauna inda ba'a fahimta ba, amma ba kawance ba, ta riga ta fita harkar 'kawance duk da dai tana da kawar arzikin wato Zainab, sai dai bata san wacece zata sake zame mata kamar Zainab din ba,wadda a da raina Zainab din take yi, tana mata kallon bagidajiya, ashe itace Bagidajiyar bata fahimta ba sai da komai ya kubuce mata. Ta fara karatunta daga aji biyu a Jami'ar Bayero duk dai a fannin Sharia, dan haka a old side take lectures din ta. Second semester a year three dinta Mk ya kammala karatunsa, sai dai Jami'ar Bhirmingham din ta ri'ke shi tsawon shekaru biyu inda zai koyarwa masu degree na farko. Ya dawo gida, ya yi hutun wata guda tunda sau 'daya ya zo Nigeria. Zuwa wannan lokacin Mk ya murje, ya goge fatarsa ta goge farinsa ya sake fitowa, gaba'daya ya canja, ilimi da gayu sun sake kama shi, Yan mata sai kai masa caffa suke, tunda ga dalibai har abokan karatunsa, bakake da fararen ingila. Haka anan gida Nigeria ma bai huta da Yan mata masu ui masa kutse cikin shafukan sa na yanar gizo ba. Al'amarin mata ya tsorata shi, wadda ya so, son da baisan iyacinsa ba tasa tsoron mata yake yi, gaba'daya, wahalar da ya sha a soyayya tafi da'din ta yawa shiyasa ya juyawa soyayyar baya, tsawon shekaru hudu haka yake gudanar da rayuwar sa, sai soyayyar Sa'adah da ke makale a kasan ransa. Da Farida kawai yake dan gaisawa sama sama saboda nauyinta da yake yi, wadda yanzu ta kammala karatunta tana aiki da asibitin Nasarawa. Har gida ya zo ya gaida Baffa tare da tsarabar yadi da turare da liptons masu yawa na Ahamad tea. Sosai suka yi hira, haka nan ya shiga ya gaida Inna itama da tata tsarabar. Ta dawo makaranta sanye cikin Hijabinta kamar kullum, suka yi kicibus da shi ya fito a gidansu, Jawad ya kawo, tunda ya zo basu hadu ba adalilin kullum tana makaranta, yana son ganin ta amma ya rasa yadda zai yi tunda har ya zuwa wannan lokacin ta ki ri'ke waya. A zaure suka gaisa ya lura da yadda ta samu cigaba a nutsuwar ta, haka nan da alamun ilimi ya fara bin komai nata, kawai yadda ta kankace ta sake zama Yar karama ne ya bashi mamaki, ba alamun kwalliya a tare da ita amma fes take ba ta da makusa. Ta kalle shi ta ce "Malam ka canja, ka sake girma, idan ka shiga cikin turawan sajewa kuke yi da su ko?" Ya yi dariya baice komai ba, ya sake kallon ta ya ce "ke kuma kin zama Yar karama tamkar ba ke ce uwar Jawad ba". Ta yi kasa da kanta bata ce komai ba, amma a ranta tasan rashin sa shine dalilin tunda kullum zuciyar ta ba Da'di ** "Ba fa za ka koma wannan kasar da sunan aiki ba, ka yi ta zama ba aure kenan, muma nan kasar ai ana bu'katar irin ku" Hajiya keta wannan fa'dan yayin da Mk ya yi shiru, ita kuma so take ya mayar da matarsa ko sati guda suyi tare sai ya yi tafiyar sa tunda ba zai yiwu ta bar karatunta ba. Amma tana fara maganar ya hade fuska iya fuska, jikinta yayi sanyi, daga karshe ma sai ga Alh Isa ya zo mata da maganar ai ya samu yarinyar da zai aura, za'a daura auren kafin ya tafi, daga baya zata bishi idan Jawad ya samu visa. Girman Alh Isa ya hana Hajiya cewa komai saboda kawaicin kar ta nuna masa iyaka akan Dan amininsa, wadda tunda maigidan nasu ya kwanta dama , Alh Isa Bai taba juya musu baya ba, yana tsaye akan almarinsu dana 'yayansu. Ba'kin ciki a zuciyar Hajiya tamkar ta fashe kan dole Alh Isa ya hakurkurtar da ita tare da nuna mata aure kaddara da rabo ne, shi kansa Mukhtar din har ya dira a kasar bai san zai yi aure ba. Al'amarin ya faru ne, da ya samu labarin rashin lafiyar Farida a bakin aminyar ta Rukayya Mustapha. Bai yi kasa a guiwa ba ya je asibitjn data ke kwance da niyyan dubata, ai kuwa mahaifin ta yana asbitin suka gaisa, Farida ta gabatar da shi tare da cewa "Dadi yau ga Uncle Mukhtar a gabanka". Ai kuwa budar bakin Dadi sai cewa yayi "madallah da Mukhtar ganin ka yau na ji ka shiga Raina Kamar yadda ka shiga ka kwanta a zuciyar 'diyata, na gode da alherin ka, ka turo mini waliyyan ka, na baka auren Farida ba tare da neman komai daga gurinka ba". Daga Farida har Mk abin ya zo musu tamkar saukar aradu, barin Mk da yaji tamkar mummunar kaddarace ta kawo shi asibitin, ba dan ba ya son Farida ba, sai don bai shirya aure a yanzu ba, bai shirya aurenta ba, a yanzu da ya gama sanin kansa ya fahimci mata masu duhu sunfi burge shi fiye da farare 'Kal, yana jin tsoron kar ya kasa yi mata adalci, tunda yasan ba karamin so take masa ba. Cikin hikima irin ta manya Alh Nasir ya tisa Mk a gaba ya bashi lambar Alh Isa a matsayin Babansa dan su Baba umaru sama sama suke da shi adalilin sakin da ya yiwa Sa'a sun kuma lashi takobin matu'kar ba Sa'a zai dawo da ita ba, ba za su sake neman masa aure ya kunya ta su ba. Cikin cire girman kai mahaifin Farida ya gaisa da Alh Isa ya zarce da cewa "yaron ka na bawa matar aure amma na ga tsoron tunkarar ku da maganar ya ke yi, shiyasa Ni na gabatar maka da maganar, na fada maka cewar nutsuwar danka ta sa na bashi kyautar 'yata mafi soyuwa da fatan zaka karbar masa". Matu'kar mutum yasan daddako wa za'a yiwa haka ya ce ba zai karba ba? Jikin Alh Isa ya mutu ya ce "kyuatar dan mutum ba mahalu'kin da za'a bawa ya tankwabar mun gode zan zo in sha Allah da kaina zan zo na karbar masa na kuma yi godiya. Washagari Alh Isa da Mk suka tarar da Baffan Sa'a suka masa bayanin Halin da ake ciki, idan ya ce bai ji rashin da'di ba ya yi 'karya, idan ya ce bai so Iyah ce zata koma 'dakinta ba yayi karya, hakan nan idan ya ce mahaifin Farida yasan ciwon kansaa Nan ma bai yi karya ba. Amma ko dan ya ramawa Mk kadan cikin alherin da tunda yasan shi yake masa ba gajiya har yau yasa shi cewa "madallah jibin idan za ku tafi ku biyo ku dauke ni da ni za'a je neman aure tare da godiya ina fatan alheri tare da fatan ta kasance abokiyar arzikin ka ce". Kafin jibin kuwa sai da Baffa ya siyar guda cikin filayen nan wadda kudin daya ya zarta kudin duka biyun sadda aka siya, sosai gurin ya yi daraja adalilin anata gine gine. Dubu 'dari uku da talatin aka siyar. Da daddare ya Kira Mk ya danka masa dubu dari biyu akan ya bawa Alh Isa dan akai gidan su Farida. Kunya ta kama Mk ya ki karba, ai kuwa Baffa ya rantse sai ya karba sai idan ya raina me ko yana ganin bashi da arzikin da zai masa alheri. Da sauri Mk ya sa duka hannunsa ya karba yana cewa "Haba Baffa, mahaifana ne kawai suka mini alheri sama da kai, har yau kuma banga dattijon arziki sama da aki a idona ba gani na yi na doara maka nauyi mai yawa Baffa! Ina rokon na raba biyu na dauki rabi". "Duka na baka Mutari sadaki ne haka nake so ka bayar dan su san iyayen ka sun san alheri, ko da sunce basu bu'katar komai daga garemu dole ka bada sadaki, burina ace na biya maka fiye da haka, ban son Alh Isa ya gane ni na bada kudin shiyasa na baka a hannunka da sai munje zan bayar, sannan shine wakilinka dole shine mai bayarwa". Zuciyar Mk ta karye ya yi kasa da kansa yana jin hawaye na Shirin zubowa. Haka kuwa! Da Baffah aka kai kudin auren Mk akasa 'daurin aure sati mai zuwa, tunda ba tarewa zata yi ba, sai sun dawo, can ingila zasu tafi. Har zuciyar Alh Isa yake jin rashin da'di, har jinyar kwana biyu ya yi adalilin kunyar Malam Basiru da takaicin Mukhtar. Haka kuma Mk da yake jin tamkar 'kasa ta tsage ya shige dan tsananin kunyar Baffah. *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 Na *SURAYYA DAHIRU GWARAM*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *Comments din ku na sani nisha'di kwarai da gaske! Na gode muku ubangiji ya bamu damuna mai albarka*. *Gaisuwa da fatan alheri ga dukkan yan KUNGIYAR LAFAZEE WRITERS*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* 85-86. Murna wurin Farida tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha, ta godewa Allah, ta godewa mahaifinta Ashe da gaske yake da ya ce sai inda karfinsa ya kare wurin nemo mata farin cikinta. Ta tuno sadda Mk ya auri Sa'a irin kukan da ta yi a kirjin mahaifin ta, yana lallashinta da kalmomi masu da'di, tare da al'kawarin matu'kar yana raye sai ta auri wadda ya fi Mukhtar, ko kuma shi Mukhtar din kansa. A wanccan lokacin bata gasgata ba, kawai ta dauka saboda ya kwantar Mata da hankali ne. "Wa yake da uba irin nawa?" ta furta a fili, hawaye na zirarowa wadda ta tabbatar sune na karshe akan rashin Masoyi. Sa'a kuwa ba tasan me yake faruwa ba, har sai da auren ya rage kwanaki uku, Zainab ta gano musu a group, da farko bata gasgata ba, amma da yake Rukayya Mustapha aminyar Faridan suna dan gaisawa da Zainab sama sama tunda duk class mate ne, anan ta tabbatar jibi Uncle Mk Bichi zai angwance da Farida Torondi. Hankalin Zainab ya kasa kwanciya, a gigice ta tafi gidan su Sa'a amma da ta lura Sa'adah bata san mai yake going ba, sai ta fasa fa'da dan kuwa be kamata ace a bakinta aminiyarta zata ji wannan ba'kin labarin ba. Tasan da tana da waya da ta ji. Baffah da kansa ya fa'da wa Innah da Iyah auren Mk, ba Sa'a kawai ba hatta Inna kuka ta fashe da shi mussaman da ya tabbatar musu ya siyar da fili daya cikin filayen Sa'a ya biyawa Mk sadakin auren. Sosai suka tayar masa da hankalin sa domin irin kukan da suke tamkar ance Sumayya ta yi mutuwar fuju'a ne. Har cikin ran Inna take jin wani irin azabben kishi na ratsa ta, bata san kishi ba sai a ranar tunda ta wanzu ita kadai ne a wurin mijinta A kuma ranar ta fara jin tsanar Mk irin wadda bata yi zaton zata yi masa ba. Kuka na fitar hankali Sa'adah take yi 'karshe ta dinga kelaya amai ta hanci da baka. Hankalin Inna da Baffah ya yi tashin gauron zabi. Ranar Inna a wurin Sa'adah ta kwana karon farko da ta bar mijinta shi ka'dai alhalin suna gida 'daya. Sosai Inna ta ke jin takaicin Baffah a ranta, idan ba zai yi kishin 'yarsa ba, menene zai siyar mata da kadararta ya bawa tsohon mijinta kudin dan yayi aure, babbar damuwar ba wai Rashi ne yasa akayi hakan ba, kawai dan ya nunawa duniya har da shi a cikin masu musgunawa farin-cikin Iyah. Washagari da rashin kuzari ainun Iyah ta tashi, babban damuwarta ta ga Mk, ganin Inna ta shiga wanka yasa ta dauko wayarta ta 'kira layinsa, tana ta wasi-wasi ko an rufe layin?. Ai kuwa bugu 'daya ya shiga, da sauri ya 'daga zuciyar sa tana bugawa. "Malam ina son ganinka, ya za'a yi?" Yadda ya ji muryar ta, da yadda ta yi maganar ya san zancen aurensa ya sameta. "Ki saurare ni zan zo nan da awa guda". "Ni dai mu ha'du gidan 'KARFI". "Ok yanzu haka Ina gidan sai kin iso, ina jiran ki". Yana ajiye wayar Mahmoud na fitowa daga kicin 'dauke da ruwan roba da tumblers guda biyu, ya dire wa Mk yana ta faman cin magani, ko abincin da suka gama ci, haka suka ci tamkar kurame adalilin fishin da Mahmoud yake yi da auren da Mk zai yi nan da kwanaki biyu. Mk ya kalli Mahmod ya ce "Karfi ka daina wannan tunbatsar! kwanaki 'kalilan suka rage mini, na bar maka 'kasar ka huta da ganina". Da rauni ya yi maganar hakan yasa Mahmoud sassautawa ya ce "Mk tunda ka amince zaka auri yarinyar nan, to ka hada su da Sa'adah, wallahi kai take jira, ko mai ta yi maka ai ka hukunta ta, shekaru hudu ba wata hudu bane, ba kuma sati hudu bane, Ni kaina na taya ka jin kunyar Baffah, wallahi tallahi karfin hali kawai yake yi akan lamarin ku, shi ya haifi Sa'adah, alkunyar da yake yi fa ta kai geji". Kallo 'daya zaka yi wa Mk ka gane kalamin Mahmod sun sanyaya masa jiki kwarai da gaske, amma baya jin zai iya yin wannan al'amarin, ya kalle shi ya ce. "Mahmoud na 'dade da gane ban da kirki, Ni da kaina zaluntar kaina nake yi, saboda wallahi har ya zuwa yau ban huta da kewarta ba, ban daina jin cewar na tafka asarar rashinta ba, ina son na rayu da ita, amma tsoron ta nake ji, ko ayyanawa na yi a zuciyata ya kamata na bata wata damar, sai na shiga ru'du da tashin hankali". Ya yi shiru yana sakin ajiyar zuciya! Ya 'dora da cewa "wata'kila wannan na cikin 'kaddarata, na rayu a duniya ba da wadda nake so ba, alhalin tana raye". Mahmoud ya rasa abin cewa, tausayin Sa'a yake ji, amma yanzu har Mukhtar 'din tausayi ya bashi, ya tabbatar a matu'kar takure yake da 'kadddarar da ta fado masa na auren Farida ba'katatan Suna cikin haka! Yayan Mahmoud ya kira shi a waya, da sauri ya mi'ke yana cewa " yau tawa ta same ni wurin Auwal, sai da ya yi ta gargadi kar na bar shi yana jirah na. Mukallin mota ya 'dauka da sauri akan center table din da ke tsakiyar falon. Ya kalli Mk da ke kishingide bai da niyyar tashi, ya ce "ko na je na dawo?" Kai kawai Mk ya iya 'dagawa a dalilin mutuwar jiki, saboda yadda al'amarin Sa'adah ke damunsa. A hanzarce Mahmoud ya fita ya na fadin "saboda gidan ba kowa yasa ka yarda ka zauna". Da yake matar Mahmoud din sunje Kaduna bikin cousin sister dinta sai jibi zasu dawo. Mahmoud na fita 'kofar gidan inda ya ajiye motarsa, bai shiga da ita cikin gidan ba, saboda yasan ba wani jimawa zasu yi ba, kawai sai ganin Sa'adatu ya yi tana bawa mai adaidaitanm sahun da ya kawota, ku'dinsa. Da sauri ya karasa kusa da ita yana mata barka da zuwa, yana jin wani irin yanayin da ya ganta a ciki, alamun rashin lafiya da rasnin kwanciyar hankali baro baro a jikinta. Ba dan 'karfin dangantakar sa da Mk ba, da ya aure yarinyar nan ko ya huta da motsawar da zuciyarsa ke yi a duk sadda zai ganta, kai so masifa ne, Madallah da mutanan da suke sadaukar da soyayyar su dan halacci, aminci, ko masalaha. Suka gaisa, ta tambayi iyalinsa, Har zaice matarsa bata gidan, sai kuma ya yi shiru, ya ce "ki shiga, zan je na dawo". Ya dinga addua da fatan sulhu a tsakaninta da Mk. Tana shiga, kai-tsaye bangaren matar gidan ta dosa, ta dinga knocking, jim ka'dan Mk ya leko daga bangaren maigidan yana cewa "iso nan, bata nan matar gidan". Ta shiga falon da sallama, ta gaishe shi, sai kuma ta kasa magana, sun Jima a zaune suna ta sake-sake a zuci. Mk ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "ina jin ki, kin ce zamu yi magana". "Malam da gaske ne wai aure zaka yi?" Zuciyarsa ta buga, mamaki ya kama shi na yadda ya ji fargaba ta kama shi, saboda yadda ta yi tambayar muryarta na rawa. Ya kasa koda motsi, hakan ya tabbatar mata da gaske auren zai yi". Hawaye ya balle mata, ta ce " Na shirya fa'da maka gaskiya". Ya ce "Ina sauraron ki, waya baki kayayyaki nan?" Cikin kuka mai yawa ta ce Khalil ne! ya bani agogo da rigunan Jawad tsarabar Egypt, shine ita kuma Halima ta ce da ya bar agogon ya siya mini waya! sai kuma ya hado har da wayar". Ransa ya matu'kar baci tamkar yanzu abin ya faru, ya fesar da iskar bacin rai, ya ce "Ta hannun wa sa'kon ya same ki?" Da kukan ta ce "wallahi Safina da Halima ne suka kawo mini! wannan itace gaskiyar magana ban munafunce ka ba". Idonsa ya ka'da ya yi jawur dan tsananin kishi, ya ce "Munafunci kuma na nawa Sa'a! Ni dai kafin ki yi hakan wallahi ban ta'ba tunanin zaki mini wannan Munafuncin da aurena akan ki ba". Kukan Sa'adah ya 'karu ta ce "Tsautsayi ne, ban ta'ba yin haka ba, wallahi a lokacin da kayan suka zo sai da na ce tsoron kar gani nake yi ba zan karba ba". Ransa ya sake ri'banya baci a tunzure ya ce "Amma da suka fa'da miki Ni 'din banza! sai kika karba, mussaman da suka nuna miki idan ma na rabu da ke ga wadda ya fini 'kuriciya da kudi yana son ki ko?" Ganin yanayinsa ya sake tada hankalin Iyah, saboda rikici ne zallah cikin idanuwan sa irin wadda bata ta'ba gani a tare da shi ba. Da sauri ta ce "Wallahi Malam.." Ta yi shiru sakamakon harar da ya watsa mata ya ce "Idan kika 'karyata ni wallahi zan miki duka, ki kiyaye ni". Ta yi shiru sai kuka kawai ta ke yi wadda Mk har cikin zuciyar sa yake jin kukan, ya yi shiru yana sauraron kukan, sai ya dinga jin ashe har da kukanta cikin abubuwan da yake kewar su a tare da ita. Tana rerewa yana tuna sadda take tisa shi a gaba tana masa kukan iyashege ko na shagwaba. Tsawon mintina biyar kafin ya yi karfin halin cewa "Kinga idan iyakacin maganar kenan tashi ki tafi tunda kuka kika zo yi mini". Ta shiga goge fuskar ta kafin ta yi 'karfin halin hadiye kukan ta ce "Kai ka ce duk sadda na shirya fa'da maka gaskiya, zaka saurare Ni fa". Ya zakudo yace "eh na fa'di haka, amma ai ke yanzu bansan gaskiyar ki ba, sau nawa kina canja mini baki, da me zan dogara har na gamsu?" Ta zube a gabansa kan guiwowinyata ta ce "Billahillazi iyakar gaskiyar kenan ubangiji shine shaidata". Ya yi shiru! Bai ce komai ba illah fama da yake da zafin zuciya. Cikin rawar murya ta ce "Ina ha'da ka da girman Allah da Ma'aiki ka yafe mini, ka mayar da auren mu, gobe kafin ka 'daura da wata jibi, na yarda na amince, ka yi auren har ma ka tafi da ita, Ni ka barni anan zan jiraka, na cigaba da amsa sunan matarka shine kwanciyar hankali na! Wallahi tunda ga ranar da ka sake ni Malam har yau ban sake barci da Ido biyu ba, me yasa ba zaka gasgata ni ba?". "Sa'a ta ya ya zan gaskata ki alhalin ke baki gaskata kan ki ba? Ke ce kika janyo komai, ke kika cusa mini rashin aminci game da lamarin ki". Murya na rawa ta ce baka aminta da Ni ba fa ka ce?" Kai tsaye ya amsa "kwarai da gaske Sa'adatu, menene alakar ki da Khalil da zai baki Agogon gold? kin tattauna da kawayen ki na kasa siya miki wayar da kike so, ke kika san tsiyar da kuka yi , ya mallaka miki kayayyaki masu daraja tamkar ke din yantacciyar mace ce". Ta rushe masa da kuka tare da ru'ko kafarsa ya kwace da sauri. "Kar ka zarge ni da abin da baka da tabbaci, kar 'bacin rai yasa ka daukarwa kanka zunubin da ba zaka iya daukarsa ba". Ya mike da sauri, a fusace ya nuna ta da dan yatsa ya ce "ke kika haskaa mini kofofin zargin ai, akan wanne dalili zai baki Agogon gold?" Da waya mai tsadar gaske?" Murya a dakushe saboda da kuka ta ce "English gold ne Malam! Bai kai darajar Dubai gold ko Saudi ba" "Amma dai me daraja ne? tunda a lokacin ai ba zan iya siya miki ba. Bayan haka me ya hana ki bu'de mini wayar? Me kuke yi da ba kya so na gani, ha'inta ta kawai kike yi Sa'adatu, dama ance yanzu mata ta waya ma suna tura tsaraicin su ga shedanun mazan da basu san darajar mace da kuma aure ba, bare wannan 'Dan iskan yaron da bani da tabbacin aure ne ya kawo shi duniya". Ya yi shiru saboda yadda kirjinsa ke masa ciwo. Ido Sa'a ta zuba masa, ta jima tana kallon shi, tana jin wata irin jarumta na shigarta, ido cikin ido tace "wannan dalilin ne yasa ka kasa mini afuwa, ka kasa kallon nadamata, ka kasa yi mini alfarmar cigaba da zama matarka da kuma rayuwa tare da Jawad?" Ba ja in ja ya sake cewa "kwarai da gaske ai dama na ta'ba fa'da miki, ba zan sake miki uzziri akan dan'iskan yaron nan ba, ashe a lokacin ma abin na ku da tsabta". Ya zarce da fa'din "dama yanzu ai anfi lalata da matan aure saboda kome aka kwaso kai-tsaye za'a likawa mijinta ya yi ta wahala da abin da ba nasa bane, ko ayi ta masa sharing matarsa hankali kwance, tunda darajar aure ya bata dukkan kariya daga jifan da zai ta'ba mutuncinta dana ahalinta". Wani irin abu mai tsananin nauyi ya tokare a wuya da zuciyar Sa'a, hawaye mai zafi ya balle mata, ta mike tsaye, ta sake zuba masa ido ta ce "Na gode da dukkan dawainiyar da ka yi da ni har ya zuwa yau, ina maka fatan alheri a sabon aurenka, Ina fatan ko wacece ta kasance abokiyar arzikinka ce". Kuka ya nemi subuce mata, amma ta sa dukkan dauriya ta danne shi, ta yi shiru, na dan sakwanni goma, sannan ta dora da cewa "A yau na tabbatar komawa gareka ba alheri bane, domin cikin shekaru hudu ba yan waattani kullum a cikin sallar dare nake, ba abin da nake ro'kar ubangiji sai ya 'kaddara ka mayar da auren mu, duk satin duniya sai na yi azumi biyu, idan na zo buda baki ba abin da nake ro'ka irin na koma dakin ka". Anan kuma sai kukan ya gwada mata fin karfi ya kwace ta sunkuyar da kanta 'kasa tana kukan sosai, a zuciya kuma sai ambaton*Hasbunallahu wa Ni'imal wakil* take yi! Ai kuwa ta sami sau'ki sosai . Yana tsaye yana kallonta yana jin tamkar yasa ruwa da omo ya goge tsatsar da ta yiwa zuciyarsa, Amma ya kasa, ya tabbatar kishi ne ya rufe masa ido, fasa wayar nan da ta yi means a lot to Him. Kanta na kasan ta bude murya ta ce "Na yarda da kalaman ka na cewa mu kan so abu alhalin sharri ne, haka nan muna kin abu alhalin alheri ne, na gamsu sosai tunda har Kai da ka tabbatar kaine mutum na farko da ya fara taka ta, amma ka kasa kubutar da ni daga sake saken zuciya da na shaidan. Idonta a soye ta ce "shin ka gamsu Jawad 'danka ne ko kuwa kana tantamar li'ka maka na yi kake ta wahala da shi alhalin ba jinin ka bane?" Da rawar jiki ya dunfare ta ba zato ta ji ya faskawa bakinta mari mai zafin gaske har sai da jini ya fara fitowa tabbacin ya fasa mata shi. Cikin gajiyawa da neman sulhu ta ce "wannan shine kawaicin da zan maka na karshe akan 'daga mini hannu da kake yi, kuma dole na tambaye ka, idan shima a Ballagazancin da ha'incin na samo shi, sai ka dawo mini da 'dana ni zan cike masa gurbin uba, tunda dama ai mutum baya rasa uwa sai dai uba, to ka bani shi kawai, domin ba 'danka bane! nawa ne". Kallonta kawai ya ke da tsananin mamaki, can ya nisa ya ce " Ashe kaifin harshen ki yana nan, ashe rashin arzikin ki na nan fal a zuciyar ki? No wonder na kasa yarda da gaske kin canja, yanzu na tabbatar da na mayar da ke din ma kina wartsakewa zaki 'dora da dibar albarkar da kika saba". Yana rufe baki ta ce "Ni Iyah Basiru Ado Gogel idan ka mayar da ni ban yafe maka ba, ko da gwal aka yi ka na barka, ai da tun farko nasan kallon fasi'ka kake mini, da ka yi tsararo na bika, wallahi Mukhtar ko zaman mota bana fatan ya sake hadamu balle zaman aure! Idan har ni diyar Malam Basiru da Malama Salamatu ce na barka. Koda kai ne autan maza, idan kuma ban aikiata abin da ka jefe ni da shi ba, to na yafe maka, idan kuma na aikata ubangiji ya bayyana ni, na kunyata na kuma tozarta a idon duniya". Ta juya ta tafi sai da taje ba'kin kofar barin falon ta juyo, suka hada ido tunda kallonta kawai yake yi, ta ce "ka manta ka sanni domin kuwa daga yau nima na rufe shafinka, sannan hidimar da kake yi da ni ta makaranta ka dakatar bana so, ban bu'katar komai daga gareka, idan kuma har na ji alert din kudi zan mayar wa da Mahmoud, turowar kuma na nufin in sha Allah baza ka rabu da Hajiya lafiya ba". Ta juya da saurin gaske ta fita, ta bar shi a tsaye cikin mugun mamakin kalaman da ta jefa masa, mafi tayar da hankalin a ciki shine alakanta Jawad da datti, ko makaho ya shafa ya san Jawad jininsa ne, domin komai na jikin Jawad nasa ne, hatta tawadar Allah da Mk yake da ita akan lebansa Jawad na da ita. Bugu da kari da ta masa fatan mugun alkaba'i na rashin gamawa da duniya lafiya, to ai mahaifiyar ka itace duniyar ka. Da kyar ya ja kafarsa ya isa kan kujera ya fadi yaraf yana jin tamkar kansa ba a jikinsa yake ba tsabar nauyin da ya masa. Zuciyarsa ta kuntata sosai, gumi ya dinga karyo masa, fargabar auren da zai yi gobe ta sake nunkuwa, fishin da ya gani a tare da Sa'adah ya sake kassara shi, Anya haka kawai Sa'a ta bar shi kuwa, wanne irin so yake mata haka? Ya dinga tambayar kansa, a cikin wannan yanayin 'Karfi ya dawo ya tarar da shi. Cike da tausayawa ya ce "Bichi ka dawo da Sa'a itace matsalar ka, Ina jin fargaba kar hawan jininka ya sababa maka ciwon zuciya". A shake sosai Mk ya ce "Dan Allah 'Karfi ya zanyi ne, ban son auren nan da zan yi, ka taimake ni ka 'boye Ni". Ido kawai 'KARRFI ya zuba masa amma zuciyarsa sai harbawa take fiye da 'kima saboda yadda maganar Mk take nuni da rashin nutsuwar da mai yin ta yake ciki. Amma ya san ganin Sa'adatu ne ya gigitashi haka, da kansa Mahmoud ya dinga jinjinawa kansa, ya tabbatar Mk na mutuwar son Sa'a amma ya tabbatar bai fi shi sonta ba, kawai girman aminci ke hakurkurtar da shi, sau tari zuciyarsa da tunaninsa na fa'da masa ba haramun bane, ya gwada Sa'arsa kawai, amma da ya tuna girman Mk da tarin sadaukarwar da ya masa a baya, sai ya ji a ransa ana barin halak dan kunya! A fili Mahmoud ya ce " Ashe dai ni jarumi ne na gaske, Allah ka samu a cikin masu yin soyayya da abota saboda Kai". Mk da yake fama da zafin da Sa'a ta hada masa, bai fahimci 'Karfi ba bare ya nemi fashin ba'ki kan kalamansa. Hannuwan Mk ya ru'ko ya ce "ka yi hakuri nasan yadda kake ji, auren Nan na cikin kaddarar ka, ka karbe shi da zuciya daya, ubangiji zai buda maka kirjinka in sha Allah! Fatana dai ka dawo da Ummu Jawad, ka sau'ka'ka muku wannan dambarwar tura ta fara kaiwa bango, bana son a kai matakin da zata janye nadamarta tunda ka ki bata damar da zata gyara kuskuren ta, wallahi yarinyar nan ta gane kurenta, komin sharrin zuciya da mahassadi ansan dai ta nutsu ta fahimci rayuwa yanzu". Ido jawur Mk ya ce "mumunar karyace baka ga Tijarar da ta mini ba yanzu, sosai ta wulakanta ni tare da yi mini mugun fata, ashe so yana zama tsiya?" Mahmoud ya fahimci Mk yana cikin tension sosai sai ya kyale shi, ya rasa gane wannan masifar ta Mk, Yana son abu yana cutar kansa, yana cutar Yar mutane, haushin yadda Mk yake wulakanta Iyah yana neman samun muhalli a zuciyarsa. **** Ikon Allah kawai ya kaita gida lafiya, domin daga gidan Mahmoud ba tasan ya aka yi ta isa titi ba. Haka nan tunda ta hau abin hawa, bata sake sanin inda take ba, sai da Mai adaidaita ya ce "Malama mun iso fa, ta daga kai ta ganta jikin shagon da suke kwatance da shi, a sukwane ta fice yana ta Kiran ta tsaya ta karbi canjinta amma ina, ba ta tsaya din ba, ta dai samu sukunin daga masa hannu alamun ta bar masa. Tamkar an jefota haka Inna ta ganta ta fa'do, ta shige dakinta ta kwanta ta dinga gunjin kuka mai dafa zuciyar Dan Adam, kuka take yi na kaicon yadda rayuwa bata zuwa mata a yadda ta zace ta, kuka take yi akan kalaman Mk da suke nuni karara kallon mai cin amanar aure yake mata, wanne irin zalunci ne wannan? A hanzarce Inna ta bita dakin ya zauna kusa da ita, ta dauki kanta ta dora a cinyarta, a tausashe ta ce "Iyah ki daina bibiyar Muutar, ba zai mayar da ke ba, ki fita harkar sa idan ba kina son ni na fita a harkar ki bane, ki fuskanci rayuwar ki, ki bawa wasu dama kafin ya dawo kasar kema ki yi aurenki". Kuka kawai Sa'a ta ke yi na fitar hankali har da shidewa, sosai hankalin Inna ya tashi mussaman da taga yadda lebunan bakin yarta suka kubura tabbacin an musu dukan zalunci. Kwalla ta cika idonta ta ce Muutar ne ya dake ki haka? Me kika mayar da kanki ne Iyah? To saurare ni da kyau, kinsan daukan kafafuwan da kike yi kina binsa ba komai bane face Ballagazanci, duk shashancin namiji kuwa bai son Ballagazar mace! Wallahi ba zai saurare ki a cikin wannan halin ba, ki fita a harkar sa, ki manta da shi, ki tattara shi ki watsar, ba shi kadai bane namijin kirki ba, Ina tabbatar miki Sa'adatu akwai wadda suke son ki kwatankwacin son da Muutar ya miki, ki kwantar da hankalin ki, zaki Sha mamaki". Idonta dauke da hawaye ta kalli Inna da mamakin jin ta ambaci zahirin sunanta, Bata taba jin ta fa'di hakan ba, saboda riko da al'adar ba a fadar sunan uwar miji. "So nake na manta shi Inna, amma na kasa! fada min me zanyi na huta da azabar da nake ji ta rashin sa" Ta fa'da cikin rushewa da kuka sosai. "Ki ji a ranki yanzu ba kece a gabansa ba, da yana sonki, da ya hadaku ku biyu ya aura, hakan ma wani nau'i ne na ladabtarwa tunda komai nasa zai raba muku biyu ne maimakon da, da bashi da komai a gabansa sai ke da 'dan ki, na sani ke kika jawowa kanki komai ya miki, amma ai ya ladabtar da ke, sannan kin yi nadama kin sauke girman Kai kin bada ha'kuri, ya kamata ya yi ha'kuri shekaru hudu yana jan ki a kasa, yanzu kuma zai yi aure tabbacin ya riga da ya sallama ki". Zuciyar Sa'adatu ta dinga budewa tana fahimtar maganganun mahaifiyar ta, tana gasgata dukkan kalmomin ta, matsanancin kishi da miyagun kalmomin da Mk ya jefata da su sun taimaka wurin narkar da zazzafar soyayya da take masa, sun dakusar da kulafacin ta na son sake zama da shi by fire by force. Inna ta Kai hannun ta kan leben Sa'a tana jin wani bacin rai na taso mata fiye da kowanne lokaci, akan me zai dukar mata 'ya alhalin ya ce ba ya yi da ita, dan mugunta har ya ya nemi canja mata fasali, sai dai ya makaro domin tana da yakinin ko hakori ya cire mata, ta zama mai wawulo ba zata rasa wadda zasu sota ba, da yawa ma kuwa. Da karfin zuciya ta ce "In sha Allah Inna na miki al'kawarin bazan sake bibiyarsa ba, ba zan sake rokon ya zauna da ni akan dole ba, ba zan sake masa kallon idan ba shi rayuwa ta bata da amfani ba, na jingine shi, ki taga ni da addu'a Allah ya taimake ni" Ta fa'da hawaye na gangarowa, da sauri Inna ta ce "da ikon Allah idan kika yi haka ba zaki wofinta ba". Har dare Mk na murdadawa da bacin ran mugun fatan da Sa'a ta masa, da kyar ya lallaba ya isa gidan su Farida adalilin kiran da mahaifin ta ya masa. A katafaren mahaifin Farida Mk zaune kan lallausan karfet na alfarma, kamshi na mussaman da sanyin AC ya sake maida falon aljannar duniya, duk juyin da Alh Nasir ya yi da Mk ya hau kujera ya 'ki hawa, hakan ya sake karawa Mk kima a idon dattijon. Cikin 'kankanin lokaci aka baibaye gaban Mukhtar da nu'ikan abinci da na sha kala kala. Cikin hikima yake jan Mk da hira har ya zo kan maganar da za su tattauna. "Ka saurare ni da kyau Mukhtar! Na baka auren Farida ba dan ka nuna sha'awar ka ba, sai dan yadda ka ke da matsayi a wurinta, sannan nima da na ganka na gane tabbas kai din mutumin kirki ne! Amma na yi wani kuskure guda daya, da tun farko ban fa'da maka cewa ita din bata da koshin lafiya sosai ba, duk da lalurar bata hanata komai, amma dai tana tashi akai akai sannan hakkin ka ne a fa'da maka tunda dawainiya mai yawa ce zata sake hawa kanka". Ya nisa ya cigaba da cewa "Farida tana fama da ciwon gabbai(Arthritis)! Wanda hakan ke sababa mata kumburar yatsu, da guiwa dama kafafuwanta, daga lokaci zuwa lokaci, an tabbatar mana ba zata warke ba, ma'ana zata dauwama akan shan magani ne, idan har zaka yi shahadar karban aurenta, Ni kuma ba zan gaza da 'dawainiyar maganin ta ba". Ya nisa yana sauraron Mk amma ganin ko kwakkwaran motsi bai yi ba, ya ce "Ka je ka yi nazari idan kaga da damuwa ko zaka takura, ka yiwa Allah da Ma'aiki ka fa'di gaskiyar ka, sai na maida auren kan 'Dan uwanta da ya 'dade yana sonta tana ki! Hakan zai fi mini sau'ki da na baka aurenta ta kasa samun kwanciyar hankali da nutsuwa a tare da kai". Harshen Mk ya yi nauyi ainun, shashen zuciyarsa da ba son auren Farida yake yi ba, ya dinga tsalle yana jin ga dama ta samu, da zai zillema auren cikin kwanciyar hankali. *SURAYYA DEE.* ✍️✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 Na *SURAYYA DAHIRU* •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *Gaisuwa da fatan alheri ga* *kanwata* *Fatima Isiyaku (Baby)* *Mrs* *Nasir Auwal Gwaram* *Na gode da nuna yabar ki kan rubutuna* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 87-88 Mugun fatan da Sa'a ta masa na ba zai gama da Hajiya lafiya ba, ya Fado masa, ya hassalo sosai. Cike da ladabi ya ce "Ciwonta ba matsala ba ce ina sonta a haka, zan kuma kula da ita da iyakacin iyawata". Da'di ya cika zuciyar Alhaji ya ce "Ubangiji ya maka albarka, ya rufa maka asiri duniya da lahira, Allah ya zaunar da ku lafiya" "Iyayenta mata suna son zuwa yin jere na dakatar da su, akan sai mun tattauna, nasan baka shirya komai na auren ba, dan haka na gyara maka wani karamin gidana da ke LAMIDO crescent" Ya ajiye mukulli tare da takardun gidan kusa da Mk. A nutse Mk ya ce " Na gode sosai Alhaji amma ba zan karba ba, domin zan dinga jin tamkar Ina gidan mace ne, ina fatan kalamina ba zai zama laifi ba". Sosai Alh Nasir ke nazarin Mk, yana jinjina masa, domin samun irin su da zuciyar su bata zarme ba, zai yi wahalar gaske, saboda yau muna cikin wani irin zamani da ake auren jari. Da murmushi a fuskarsa ya ce "Mukhtar ina da tabbacin ko a gaban Farida na baka wannan gidan ba zai zame maka na'kasu ba, ba a shaidar 'dan Yau amma na shaidi Farida. Balle ma ni a satin nan na siye shi, ba kuma wadda yasan na siya, da sunanka na siye shi, Dan haka mallaka maka na yi ba aro ba". "Na gode sosai, Allah ya kara arziki, amma ba zan karba ba, abawa masu son zuwa jere ha'kuri, ba zata tare ba, zamu tafi Uk ne, idan ubangiji ya kaddara mun dawo lafiya, Ina da 'karamin gida a gadon kaya sai ayi komai". Ganin da mahaifin Farida ya yi da gaske Mk yake yi ba zai karba ba, sai ya bar maganar gida yana 'kudire dole ya masa wani abu na alheri komin dadewa. Ya ce "idan nace ina son na dauki nauyin tafiyar iyalin naka fa, ko shima baka so?" Kunya ta kama Mk ya sake yin kasa da kansa domin ya gaji da yin musu ya ce "Na gode sosai, Allah ya kara arziki". Alh Nasir ya mike yana ta musu addu'a da fatan alheri, tare da cewa "Bari na turo maka ita". Ba a dauki lokaci ba, ta iso cikin tsadaddiyar abaya baka sai walainiya take yi daga hannun rigar an masa ado da shudin duwatsu, dan haka ta yi anfani da shudin mayafi a maimakon na abayar, ba kwalliya a fuskarta tunda ita ba ma'abociyar adon fuska bace, kawai powder ta shafa sai wet lips sai tsadadden turaren ta na amour amour. Soasai ta masa yi kyau, sai ya dinga tuno sadda yake zuwa zance wurin Iyah yana ce mata ta yi kyau tamkar balabiyar Habasha. Ya zuba mata idon da suka yi jah tamkar mai fama da ciwon afolo, alhalin bacin ran da Sa'a ta jefa shi ne yake neman kassara shi. A hankali cikin sanyin muryar ta gaishe shi ya amsa da karsashi. Ya zuba mata ido sosai, kanta a kasa tana jin yadda kallon ke ratsata. A hankali ya ce "ya jikin ki? Ko da yake kin warware, irin wannan kyau da kika 'kara yi tamkar balabiyar Yemen" Kanta na 'kasan ta murmusa tana jin kunyar sa sosai. Ya dinga janta da hira, har ta dan sake da shi. "Na fadawa Dadi ba zaki tare ba, Ni Kinga nan da kwanaki biyar zan wuce, ke kuma da zarar visar ki ta fito, sai ki bini, abar maganar jere tukun yanzu". "Allah ya nuna mana" Ta fada a hankali. Suka yi shiru. Na dan gajeran lokaci, Farida ce ta katse shirun ta hanyar cewa "Dadi ya baka aure ba tare da ka ce kana so ba anya ba'a takura ka ba?". Tausayinta ya sake shiga jikinsa sosai! a hankali ya kira sunanta ta dago suka zubawa juna ido tsawon sakwanni, Farida ce ta yi karfin halin janye idanuwan ta saboda yadda take jin sonsa na sake dafa duk ilahirin jikinta, yadda idanuwansa suke a jirkice da kuma yadda suka yi ja sun sake jefata cikin matsanancin so. Murya ba amo sosai ya ce "Na yi mamakin da kika yi tunanin aurenki zai zamo mini takura! Tun yaushe muke soyayya da zaki ce na takura?" Ta sunkuyar da kai kasa ta ce "kafin shigowar Gogel cikin rayuwar ka nasan muna soyayya, amma bayan ta shigo sai ta kashe tawa soyayyar". Ta fa'da cike da rauni sosai. Idan gaskiya zai fa'da yasan ba 'karya ta yi ba, amma dan ya faranta mata sai ya ce "Ba mutuwa ta yi ba dogon suma kawai ta yi, saboda ina ganin bani da halin da zan zo neman aure wannan gidan, Amma da yake ubangiji yasan yadda na ke sonki sai ya 'kaddara mini samun ki a lokacin da na cire rai, idan kinsan farin-cikin da nake ciki da baki yi wannan tunanin ba". Ya nisa ya ce "tunda da bakinki kika sako maganar Sa'adah bari na fa'da miki wani Abu, kin san yanzu bama tare, amma idan ubangiji bai karar da zaman mu ba, zan dawo da ita, kar hakan ta faru a gaba ki ji a ranki kin gaza ne, sosai nake sonki Farida, sannan ba zan boye miki ba itama ina sonta, kaddara ce ta rabamu, Ina fatan wannan ya zama na karshe da za ki sako mini maganarta mussaman akan ina sonta ko saboda ita na rabu da ke a farko, an 'kadddara mini sai na fara aurenta ne kawai". Sosai ta fahimice shi ta kuma gasgata shi, duk da ta ji fargabar da ya ce zai dawo da ita, ba dan ba ta so ba, sai dan kishin da kowacce mace ke da shi akan abin da take so, dan ma ta yi sa'ar na ta kishin mai sauki ne saosai. Ta katse maganar da cewa "Ya Hajiya da Jawad?" My 11 amsa mata suna lafiya. Ta sake fa'din"kun je anyi masa passport din?" "Anyi masa sai dai da alamu visar ki zata riga tasa samuwa, kawai idan ta ki ta zaama ready, zaki taho ne, shikuma Mahmoud zai taho da shi nan da wattanni uku". Yana rufewa ta ce "wallahi ba zan iya ba, kafata, kafarsa, sai dai nima na jira shi, ka riga kasa masa rai, sai kuma ya ga shiru, Ni bama zan iya zama da kai babu shi a tsakanin mu ba, ni ka'dai nasan yadda nake jin yaron nan a zuciyata". Dadin kalaman ta suka kama Mk ya ce "wato saboda Jawad sai ki barni ni ka'dai, baki damu da halin da zan shiga adalilin rashin ki kusa ba?" "To idan hakane sai ka yi kokari mu samu visa tare da shi". Sosai suka sha hira mai cike da 'doki. A ranar ta nuna masa yatsun kafarta guda biyu da suke a tankware , dan kar sai daga baya ya gano ya ji an yaudare shi, sosai ya sake jin tausayin ta, bai san me yasa yake jin tausayin ta ba tun fil'azal, ya yi ammana wannan tausayin ba zai barshi ya zalunce ta ba. Har wajen harabar Adana motoci ta rako shi, anan ma sun sake bata lokaci suna hira. Sai da ya koma gida ya kwanta tunanin ciwon Farida ya zo masa menene (Arthritis?). Da tunanin ciwon barci ya yi awon gaba da shi, yana karyawa kuwa bai zame ko ina ba sai asibitin kwararru na Murtala, ya samu Dr Babangida Bojuwa abokin kaninsa ne Akil, suka gaisa sannan ya nemi alfarmar ya masa bayanin menene ainihin ciwon Arthritics da hanyar da za'a bi a kula da mai fama da wannan ciwon. Dr Bojuwa ya yi murmushi sannan ya cire gilashin idonsa wadda yake taimaka masa wurin gani sosai sabanin da mutane suke kallon tamkar na ado ne. Cike da girmama yayan abokinsa Dr Bojuwa ya ce "Zan maka bayanin da harshen Hausa tunda kai Baban turanci ne, gara na adana turancina da bai fi cikin cokali ba". Da murmushi a fuskar Mk ya ce " kowa a fanninsa gwani ne 'kanina, baka ga takakkiya na yi domin ka sanar da ni abin da ban sani ba?" "Hakane yayan mu". Dr Bojuwa ya ce "A likitance an fassara Arthritics (Ga'ba) da mahadar kasusuwa biyu zuwa sama. Ba iya 'Kashi ke bada abin da ake kira ga'ba ba! Muna da ga'bo'bi da yawa a jikin 'Dan Adam amma anraba su zuwa manya biyu mafi shara wato masu motsi da marasa motsi". Dai-dai lokacin Dr ya nisa sannan ya zarce da fadin "(osteoarthritis) wannan nau'in shine yafi yawa yana farawa adalilin kokewar shimfidar kawunan kasusuwan(articular cartilage) wacce take hana kasusuwa gogar juna yayin motsi, daga karshe hakan na janyo sidewar kawunan kasusuwan da kuma curewar su zuwa 'Kashi guda daya. Wannan nau'in na faruwa adalilin jin rauni a ga'ba ko shigar kwayoyin cututtuka". "Na'aam" Mk ya furta cike da gamsuwa. Dr ya cigaba da cewa "sai kuma na biyun (Rhematoid arthritis) mai farawa da kumburin shingen gabobi, wannan nau'in yana farawa da kumburin da ya zagaye gabobi wanda ya ke samar da ruwan gabobi. Daga baya kuma ya cigaba har ga kokewar shimfidar kawunan kasusuwan. Wannan nau'in na faruwa ne sammakon rikicewar Garkuwan jiki har ta kai suna yaki tare da lalata shingen da ya zagaye gabobi wato(synovial membrane). Cikin nutsuwa Mk ya fahimci Farida na fama da ciwon Arthritics nau'i na biyu wato (Rhematoid arthritis). Dan haka ya ce "Na gode sosai Dr! Na gamsu da bayanin ka, amma me yake kawo wannan ciwon?" Cikin rashin gazawa Babangida ya ce "zuwa yanzu dai an tabbatar tasirin wannan ciwon ya hada da GADO- ana iya gadar wannan ciwon idan an samu wani a ciki dangi yana da wannan ciwon ma'ana yana bin jini. SHEKARU- yawan shekaru na tasiri sosai wurin samuwar wannan ciwo. MATA-Jinsin mata sunfi kamuwa da ciwon Rhematoid arthritis yayin da jinsin maza suka fi kamuwa da (Gouty arthritis). NAUYI- nauyi fiye da kima na jagorantar kamuwa da wannan ciwon, da kuma buguwa a gabobi". Kafin Mk ya yi magana Dr Babangida ya sake cewa "kalubalen da masu wannan ciwon suke fuskanta bayana rad'ad'in azabar ciwon, sun hada da Tankwarewar yatsu, hannu ko kafa, ciwo yayin motsa gaba, kumburi sosai a gabobi, dama daina aikin gabobin gaba'daya". Mk ya ce "Madallah da hazikin Dr! shin wanne shawarwari zaka bani don kulawa da mai fama da irin wannan ciwon?". "To shawarar da zan baka kasancewar wannan lalura kusan ta dindince, ma'ana za'a tabbata ne ana s!han magani. Mafi soyuwa a inganta abincin marar lafiya, a yawaita masa cin kifi, a karanta masa cin nama mussaman Jan nama. Da kuma yawan motsa jiki da shan maganin da likita ya 'dora mai lalurar akan ka'ida, sai kuma rage kiba ga masu ita". Mk ya mika masa hannu tare da cewa"likita na gode sosai da lokacin ka da ka bani tare da mini cikakken bayanin da na gamsu, ina rokon ubangiji ya yiwa rayuwar ka albarka, ya kara maka ilimi mai albarka, ya sa sunanka ya yi fice a cikin 'kasa da waje". Babangida ya amsa da cewa "Amin Nima na ji 'Da'din yadda ka nemi bayanin likita, baka tafi kanka tsaye siyan maganin rage rad'ad'in ciwo ko kumburi ba, domin yawan shan irin waddanan magagunan na janyo ciwon ulsa da ma gazawar 'koda bagatatan, ubangiji ya bamu lafiya gaba'daya". Har wajen ofis din Dr Bojuwa ya rako Mk dan karramawa ga yayan abokinsa Akil, Mk yana ta masa fatan alheri da samun mace ta gari, tare da jinjina fasahar Babangida, yana hakaito sadda yake biyowa Akil makaranta, oh rayuwa gaibu ce, ba wadda yasan me gobe zata zo da shi. Yana tafe yana tunin bashi da matsalar gwajin rukunin jini, tunda tuni yasan Farida A.s ce yayin da ya kasance A.A basu da matsala, kawai fargabar sa daya ciwon da ta ke faama da shi ance ana iya gadarsa kenan akwai yiyuwar ta haifa masa mai irin ciwonta. Alatilas zai yi auren nan, ko dan ya nuna mata martanin soyayyar da ta wanzu tana masa ba gajiyawa amma a zahirin gaskiya kaso mai yawa na zuciyar sa da gangar jikinsa gaba'daya Sa'adah suke so, da ita suke son su rayu muddin rai, shi da kansa yasan hukunta kansa yake yi da rashinta. Yana tu'ki yana ayyano cikakken dirin jikinta bata da rama kamar Farida, duk da a yanzu ta tsiyaye, amma ya yi imani da zarar ta dawo hannunsa komai da ta rasa zai dawo mata tunda zata sami nutsuwa, ga iya girkin gargajiya tamkar Innarta, ga ga gayu, kullum tamkar mai Shirin shigaa gasar kyawawa saboda kwalliya. uwa uba ta kasance mace mai lafiya, A.A ce sannan O positive duk wadda ya san darajar lafiya ya san wadda ubangiji ya hada musu wannan nau'ikan ba karamin ni'imomin ubangiji suke ciki ba. Kalamanta na karshe ya fado masa wai idan ya sake tura mata kudi ba zai gama da uwarsa lafiya ba! Bai taba ganin inda abin arziki ya zama sharri ba sai a gurin Sa'adatu. Ba 'karamin bata masa rai wannan kalmar ta yi ba, bayan tasan ita mai laifi ce, ya tsani kaifin harshe, umm Kusan Wannan bacin ran da ta haddasa masa ya rage masa fargabar auren Farida da yake ji. Washagari asabar dai dai da 17/09 aka daura auren Mukhtar Kabir Bichi, da Farida Nasir Torondi. Daurin auren da ya samu halarta manyan mutanen na Nijer da Nigeria. Sosai aka yi hidima ta bangaren amarya, duk yadda Farida ta so ya halarci Dinner da zata yi a harabar gidansu ha'kuri ya bata, bai je ba, yana ji a ransa tunda bai yi irin wannan sha'anin a bikin Iyah ba, to yanzu ma ba zai yi ba da yake da shekaru talatin har da tara. Bangaren Iyah kuwa sai da aka daura auren ta gane Farida ya aura. Duk yadda ta so yin jarumtar boye yadda auren Farida ya bugeta kasawa ta yi, ta fito daga dakinta, daidai lokacin Baffanta ya dawo daga wurin daurin auren ya ci sabon dinki tamkar yarsa yake aurar wa. Tana tsaye tana kallonsa , sai kuma ta fara ganinsa bibbiyu, basu ankaraba suka ji tim ta zube a kasa. Dukkansu suka kai mata dauki, tsawon lokaci ana kanta har sai da aka kira Maman Ema wata kwararriyar nurse ce har ta kai mukamin metron, ita ta dinga dawainiya da ita har ta farfado, tana fa'da musu jininta ne ya yi kasa sosai adalilin rashin samun barci da kuma damuwa da ta sanya a ranta. Kwana biyun da suka biyo baya ba karamin tsauri suka yiwa Sa'adah da iyayenta ba, domin ba karamin wahala ta sha ba, har zabura take ta kwasa da gudu, gaba'daya ta gigice ta fita a hankalin ta, ba kuma komai ke damunta ba illah matsananciyar damuwa wato (Desperation). Yadda take zabura da suratai ya matu'kar tada hankalin ahalinta mussaman Inna da ta ke uwa, ansan kuwa raunin uwa akan danta. Bayan maganin asibiti har rubutu Baffa yake zama da kansa ya ke mata wadda na dangana ne da samun sukunin zuciya. A wannan lokacin Inna ta kudiri aniyar Mukhtar ko shine namiji tilo a duniya da ya hallata Iyah ta yi zaman aure da shi, to kuwa ita ta Haramta mata shi, wannan abin da ya yiwa Iyah ta tabbatar ya yi tsauri da yawa ya wuce laifinta, ta yi imanin 'yarta ba zata yi zina ko sata ko wani mugun kaba'irar da zai kasa yi mata afuwa ba, ta lura so yake ya susuta mata yarinya ya sa zuciyarta ta buga, tunda shi bashi da asara ya angwance da 'diyar masu kambun susa. Asalima Inna sai take ganin tamkar so yake ya shafawa Sa'adah kashin kaji. kuma raina arzikinsu ya yi. Kwanaki biyu suka ragewa Mk ya wuce, ya dauki Farida da hantsi suka je ta gaida Hajiyar Bichi, duk yadda Hajiya take jin dama Sa'a ya dawo da ita, ta karbi Farida da sakakkiyar fuska, yayin da Jawad ya ke ta murnar Malam ya ce zasu bishi Ingila a jirgi da wannan balabiyar Auntin. Dai dai lokacin shekarun Jawad goma. Kunyar Farida da sanyin ta yasa Hajiya ta dan rage 'kin data ke yiwa auren na su. A hanyar su ta komawa gida ta ga ya sauka daga kan titin da zai bi ta unguwar su, ya hau wani daban. Bata ce kala ba, ta zuba masa ido kawai. Bai tsaya ko ina ba sai a harabar hotel din Tahir. Jikin Farida ya yi sanyi sosai, ta shiga cikin rudani da fargaba, amma haka ta bishi, har dakin da ya riga da ya kama a safiyar yau, domin taga a aljihunsa ya fito da mukallin daki mai lamba 008. A dadare ta shiga ta zauna, shikuma ya juya ya fita, ba'a jima ba ya dawo da leda mai dauke da yougurt da gasasshen kifi, sai lemuka masu sanyi hadi da ruwa. Ka'dan ta dan ta'ba adalilin matsawar da ya mata, shi kuwa da dama yunwa yake ji sosai ya ci, sannan ya shiga ya yo wanka, ya fito daure da tawul iya kugunsa. Mk da kansa ya dinga mamakin kansa bai yi zaton zai ji sha'awar wata macen bayan Sa'a ba, bai yi zaton zai yi rawar jiki har ya kasa ha'kuri su isa Uk kafin ya tare da amaryarsa ba, amma abin mamaki jiya kwana ya yi yana juyi, rabon da ya shiga irin wannan yanayin ya manta, bai sani ba ko dan yasan bai da wadda ta halatta a gare shi ne. Ganin abin na neman kassara shi, shiyasa ya murje kunya ya je har gidansu ya daukota da zummar zai kaita ta gaida mahaifiyarsa sannan sisters dinsa na son ganinta sosai. Sanin mijinta ne yasa ba a nemi ba'asi ko fargabar fitar su tare ba, asalima kyakkawan shiri aka mata, domin turaren da mahaifiyarta ta dinga bin duk wata ga'ba tana shafa mata na alfarma ne, takanas ake yiwa manyan matan da suka amsa sunansu a sanin duniyar kamshi. Sannan ta bata wani irin tsumi da tunda aka fara aurenta kullum sai ancika mata ciki da shi, akan Dole Farida ke Sha, saboda kasancewarta masaniyar magaganuwa bata yarda da Shan kowanne irin abu da sunan magani ba. Wannan kamshin ya sake rikita Mk yana jin tamkar wani maganadisu ke jansa ga Farida, shi ka'dai yasan yaddda ya kosa su kadaice. Duk yadda Farida ta ke da kunya ta yi iyakcin bakin kokarinta ta bashi hadin kai, duk da yadda ta ke cin kwakwa a hannunsa kasancewar ita din cikakkiyar budurwa ce ta daure ya samu nutsuwa sosai. Koda ya kammala kifa ta ya yi akan cikinsa fatar jikinsu na manne, yana jin nisha'di sosai ya dinga mata addu'a, yana gode ma ubangiji na yadda duk shine ya fara bude matan da ya aura, ya tsare kansa bai taba Zina ba, ubangijinsa kuma sai ya mutuntata shi ta hanyar bashi katangaggun mata. Zuciyarsa ta buga da ya tuno Sa'a yasan sharrin zuciya ne da yake jin tamkar tana ha'intarsa ne, amma shi da kansa yasan zai yi wahalar gaske ta aikata wannan al'amarin. Jikinsa ya dinga bari har Farida ta dinga jin barin, saboda yadda ya ke jin wani iri abu da baisan dalilinsa ba, yau gashi da Farida a cikin yanayin da Sa'adah kawai ya ta'ba tsintar kansa a ciki, ko ya take ji a dalilin aurensa yasan idan itace ta yi aure tabbas sai ya kwanta a gadon likita. A sanyaye Farida ta ce "baka da lafiya ne? jikinka na rawa fa". Murya a dashe ya ce" farin cikin yadda na same ki ne, duk son ki ne yake kidima Ni" A ransa kuma fa'di yaushe zan iya fa'da miki abin da ya kidima ni ai ya zama tamkar cin fusaka ne, gangar jikinmu a hade amma tunanina da zuciyata na wani waje daban. Ita kuma zuciyarta ta yi fari kal har tana ganin sannu a hankali zata iya mantar da shi Gogel kamar yadda Gogel din tasa ya manta da lamarinta a baya. Yini zur Mk ya yi da Farida bai yarda ya mayar da ita ba sai bayan Isha, wadda sai da ta yi kuka, domin kuwa da murje idonsa zai yi ya kwana da amaryarsa, kafin su tafi ta fahimci mabukaci ne na gaske, domin sai da ya sake yin second round ,sannan yana daukar lokaci yana abu 'daya tabbacin yana da lafiya yana kuma kula da lafiyarsa. A iya wannan awannin da suka yi sai da Farida ta dinga yiwa Iyah jajen rashin mijin da iya sarrafa mace, lalle Gogel jaruma ce da ta iya shafe wannan lokaci babu zumar da ya 'dade yana lasa mata, ita yau kadai da suka kasance da shi addu'a take yi, da neman tsarin abin da zai rabata da Mk. Fata take ta kasance da shi muddin rai, zata yi dukkan ladabi da biyayyar da zata dauwamar da ita a zuciyarsa, zata yi ha'kuri da duk wani abin da baya so koda ita tana so, matu'kar zasu samu zaman lafiya , ta kuma rayu da shi, idan har zai iya rabuwa da Gogel tsawon lokaci bai waiwaye ta ba, to ta tabbatar ita idan ta yi kuskuren da suka rabu shafeta zai yi gaba'daya. Suna tafe yana tuki yana ta mata hira da suke nuni da kololuwar jin dadin yadda ya sameta, ita kuma tana ta murmusawa alamun tana Jin dadin yabawar ta shi, a ranta tana fa'din karatu a Jami'a baya sa mace ta lalace sai idan dama lalatacciya ce. *** Har Mk ya tafi ba su hadu da Sa'adah ba, domin ko da yaje gidan ana gobe zai tafi, ya fadawa Baffah zai tafi amma nan da sati biyu su Jawad za su bishi, cikin karfin hali Baffa ya yi masa addu'a tare da fatan alheri. Inna kuwa ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar sa, tare da yi masa fatan alheri a aurensa. Ya jima a zaune bai ji Inna ta hau Kiran Iyah ba, dama ita ce take yin hakan a kokarinta na su dinga gaisawa har a samu ayi sulhu, amma wannan karon bai ji hakan ba, illah shigewa daki da Inna ta yi ta bar shi da Baffah akan tabarma. Yayin da ita kuma Sa'a tana kwance akan gado tana fama da zugin zuciya duk da dai Alhamdulillah ansamu cigaba kwarai da gaske akan kwanakin ukun da suka shude. Tana jinsa Amma sai ta ji a duniya ba halittar da bata son gani kamar Mk, tabbas ya wulakanta ta, ya tozarta mafi munin tozarci, hawaye ya dinga silalowa ta gefen kunnenta, ta dinga hasashen me ya Mata na alheri ne, me ya mata na kyautatawa wadda bai cancanci ta ji wannan tsanar da take ji akansa ba, ta gama duk lissafinta ta yi alkalanci, ta yarda a zamansu bai zalunce ta ba, ta kuma gamsu ya kyautata mata, ta kuma gasgata itace ta janyo komai. Amma kuma hukuncin da ya dauka akanta ya yi tsauri matu'ka da gaske, zargin da ya jefeta da shi ya ketare iyaka, haka nan kin mayar da ita, kafin ya sake aure tozarci ne Babba ya mata, kishi ya daure mata kirji, duk irin alheri da dawainiyar da ya mata har bayan ya rabu da ita a yanzu duk sai ya tashi a banza a idonta, tana jin ba wani alherinsa data sani da zai lullube cin mutuncin da ya mata, a kuma wannan lokacin ta yanke duk wata mu'amala da shi, tana jin idan har ta sake yiwa Mk kallon masoyi, ko kallon Rahma tabbas ta zama asararriya. Kunya sosai ta hana Mk tambayar Baffah Sa'a! Sai ya buge da sake bawa Baffah hakuri, tare da neman afuwa. Duk da a ran Baffa ba ya jin da'din yadda yake ganin Iyah adalilin Mukhtar, sai ya ce " Ba komai Mutari, har yau kuma ban kullace ka ba, kawai dai ina son ka ka daina mini kallon wannan matsalar zata lalata amincin da ke tsakanina da Kai, kallon uba kake mini, Nima kallon 'da nake yi maka, har abada mun hadu ga Jawad nan a tsakanin mu". Jikin Mk ya sake yin sanyi tunda a da cewa yake yi, idan da saura zama a tsakanin ka da Iyah da kanku zaku shirya kanku, bana ji a jikina an rabu kenaan ba, sai kuma yau ya ce ga Jawad a tsakani, kenan Baffah ya karaya ya daina jin zasu sake zama ma'aurata a tsakaninsa da Iyah. Ya dade zaune Baffa na ta yi masa nasihar ya kula da amanar yarinyar da aka bashi tunda zai dauketa ne ya kaita wata duniyar da ba ta san kowa ba sai shi, sannan ya sa ido sosai akan Jawad kar ya bari ya koyo dabi'un yahudu wal Nasar😀 Da kyar ya mike ya na kallon dakin Sa'adah da fitila a kunne tabbacin idonta biyu, ya tuna idan ya zo gidan ta dinga sintiri tsakanin dakinta da tsakar gida, ta dinga bare bare kenan, ba ita ba hatta mahaifiyarta rawar jiki take yi, ta dinga fa'din Iyah kaza, zo ki kawo masa kaza mana, amma yau duk sun yi likimo tabbacin sun watsa shi a kwandon shara.p A sanyaye sosai ya bar gidan. Washagari kuwa ya bi jirgin Mangal air zuwa Lagos daga can ya shiga jirgin arik air zuwa kasar Birtaniya. Haka Sa'adah ta cigaba da jinyar zuciyarta, tana samun karfin guiwa wurin mahaifanta da Sumayya, domin Baffah da ya ga sun hade masa kai a gidan dole ya ajiye powaer sa ta maigida ya lallashe su da kalmomi masu laushi, da kuma sanin muhimmancin hakuri. Ya sake fa'da musu ba su fi shi takaicin auren Mukhtar ba, amma tunda shari'a bata hana shi ba, akan me shi zai kullace shi? Ya rufe da cewa "kuna ganin laifina dan ban roki Mutari ya zauna da ke akan dole ba, alakawari na yi ba zan bada auren 'yata ba sai a inda nasan za ta yi daraja, a farko da yake so ai na bashi, idan kum zaki fadi gaskiya ai ya ri'ke ki da daraja! a yanzu kuma, da baya so, bashi da abin da zan kalla da zan nemi ya zauna da ke akan tilas, hakuri wuya ne da shi, idan aka daure sannu a hankali za'a cimma buri". Ya nisa ya sake 'daure su da cewa "A zatona Salamatu, da ke da yaran da kika haifa mini da kuma duk abin da kuka mallaka zan yi iko da ku kai tsaye, ba tare da jin shakku ko fargaba ba, amma tunda laifine dan na yi ikon da abin da yake mallakin Iyah ne to ku mini afuwa, Iyah ta bini bashi in sha Allah zan biya a hankali" Kunyar kalamansa suka kama su mussaman Innah da ta bari hankalinta ya kwace akan wannan lamarin. A ranta ta dinga fa'din babbar jarrabawar da aka yiwa mata kishi ne, domin da yawa Mata sun halaka adalilin kishi, da yawa sun rasa Imani, ubangiji ka tsare mu ka sau'ka'ka mana. Hakuri suka bashi, Innah ta ce "Ba siyar da filin bane ya ta'ba ni ba, yadda ka shiga cikin lamarin auren ka yi kane kane ne ya kidima ni, amma ka mini afuwa wallahi ban taba jin bin da ya dama mini lissafi irin halin da na ga Iyah a ciki ba, amma Alhamdulillah komai ai ya wuce ina rokon kar Allah ya sake maimata mana wannan wakiar". Sa'adah ta nisa ta ce " Dayan filin ma na barka maka Baffa tsakani da Allah bana so, tunda na mallakesu ne adalilin Mukhtar. Kawai so nake ka daina nunawa ya fini a gurin ka, sannan ka mini afuwa akan komai ka daina fushi da ni, domin a yanzu Ni Mukhtar ya zalunta". Ya yi murmushi ya ce " ko Sumayya ba ta fiki ba Iyata, amma ina son ki gane gaskiya ko kuna tare da Mutari ba zan 'ki shiga hidimar auren sa ba, domin ya mini alkairori daban daban da bazan mance su ba, duk girman kuskure kuwa bai kamata Dan adam ya shafawa idonsa toka ya mance alheri ba, nasani hukuncin da ya dauka akan ki ya yi tsauri da yawa, adalcin da nake yi masa shine ban san mai kika yi masa ba, sannan auren da yayi ba zaluntarki ya yi ba, domin kuwa ko kuna tare zai yi aure shari'a ta bashi dama, idan yana so kuma zai iya adalci. Fatana ki kwantar da hankalin, ki yi hakuri in sha Allah komai zai daidaita miki, Na da'de da ya yafe miki Iyah, fatana ki bu'de zuciyarki ki fuskanci goben ki, sai kinyi nazari hadi da tsinkaye masu zurfi sannan gobenki zata inganta, na yarda da nutsuwar ki a yanzu, na kuma gamsu a kame kike dan haka bana fargabar zamanki! Amma ba ina nufin kita zama a hakan bane, ki bawa masu sonki kofar da za su tunkare ki, domin a hakan kika samu Mutari, yanzu kuma da kika barwa Allah ya miki zabi, ina da yakinin ba zai barki haka ba". Jikinsu ya sake yin sanyi, suna gasgata maganganunsa, mussaman Sa'adah da take jin karfin zuciya na dirar mata, tana hango ya kamata ta budewa kanta kofofin farin-ciki, zata dawo da kwalliyar da ta da'de da daina yi, sannan zata sake dagewa a makaranta domin a yanzu da Mukhtar ya auri Farida sai take ganin tamkar ya raina arzikinsu ne. *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 16/06. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji ta'ba wannan LABARIN ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *Gaisuwa da fatan alheri ga* *HADIZA TINAU*. *Ki yi yadda kike so da wannan shafin, farar mai farar zuciya, ubangiji ya yi mana abin da bamu yi zati ba na alheri* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 89- 90. Maganganun Baffah sun sake 'karawa Sa'a kwarin guiwar gina sabuwar rayuwar da babu Mk a cikinta. Tana kwance har tsakiyar dare tana nazarin yadda zata koma sabuwar Sa'adah da bata san Mk ba, ta nisa tana hakaito abubawan da zata nema, bata da bu'katar sutura domin tana da su ba adadi tsadaddun gaske, da yawansu ma bata sake waiwaryasu ba. Kayan kwalliya da waya tafi bukata a yanzu, sai hanyar da zata dinga samun ku'di tunda yanzu bata bu'katar na Mukhtar, tasan shima ba zai yi gigin bata ba. Ta sani iyayenta da Sumayya suna iyakar kokarinta amma dai ba zai yiwu ace dukkan lalurarta sai an yi mata ba. Saura kwana uku tafiyar su Jawad, Ahamad ya kawo shi gurin Sa'adah inji Hajiya ya kwana mata biyu, tare da sallama, tunda Mk ya yi aure Hajiya ta shiga cikin wani hali na kunyar Sa'a da iyayen ta, mussaman da Mk ya fada mata Baffan Sa'a ne ya biya masa sadaki, sai ta ji inama ace Hajiya Babbace a raye ita kuma a mace, tasan Hajiyar ta fita juriya da shanye 'bacin rai. Sosai Sa'adah ta samu sau'kin zuciya cikin sati biyu nan, domin ko da ta ji tafiyar da Farida da Jawad za su yi bata wani damu ba, illah ta ji ba da'di, Jawad ne ma ya nemi karya mata zuciya da yawan tambayoyinsa akan me yasa ba zata bisu ba? Da daddare suna kwance kansa na kirjinta yana bata labarin abubuwan da zai siyo mata idan zai dawo. Can ya ce "to kawai Mami mu tafi tare mana, kema ai baki taba hawa jirgi ba". A hankali ta ce "Malam bai ce na je ba, Aunty Amarya ya ce ta je". "Mami idan kin je ai ba zai yi fa'da ba". Cike da soyayyar 'danta ta ce "Ai bai biya mini kudin jirgi ba". Ya yi shiru sai ya ce "Na ji kafin ya tafi ya fa'dawa Hajiya, Baban Antin ya ce shi zai biya kudin tafiyar mu". Zuciyarta'daya ta ce " To ka ga ba ni a tafiya kenan tunda Ni Baffahna bashi da ku'di". Ya yi shiru, can kuma ya kalleta tamkar wadda aka kitsa masa ya nisa! ya ce "Ni zan tara ku'di da yawa na kai ki, har jirgin ma zan siya miki". Hawaye ya cika mata idanuwa, ta yi kokarin gogewa ba tare da ya gani ba. Sai da ta shanye kukan da ya zo mata ta shafa kansa ta ce "Allah ya nufa Jawad, ubangiji ya maka albarka, idan ka je ka dinga sallah da wuri, komai Anti ta ce ka yi, kada ka yi mata musu kawai ka yi, ka dage da karatu sosai banda wasa, domin wadda zai siyi jirgi sai ya zama mai jin maganar iyayensa ya kuma yi karatu tukuru. U.K. A airport suka tarar da Mk yana fama jiran isowar su, da Jawad ya hango shi, da gudu ya nufe shi, da azama Mk ya daga shi sama domin abin da Jawad ya ke so kenan ya ga Babansa ya daga shi sama ya'ki yarda ya girma. Taxi suka hau, zuwa gidan da zasu zauna, a hawa na takwas gidan yake dan haka Suka shiga lifta abin da ya burge Jawad, domin dai shine bai santa ba, tunda Farida ta saba fita kasashen waje. Gajiyar hanyar da suka kwaso bai hana Mk sake dorawa Farida wata gajiyar ba, domin a matu'kar takure yake sai da ya samu ya zubar da abin da ya takura shi sannan ya ji shi daidai. Rayuwa suke cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, Mk ya shayar da Farida mamaki da ya samar mata gurbin karatu a Jami'ar da yake inda zata yi masters dinta duk dai akan sanin magungunan (Pharmacy). Ya ce " wurin aikin ki sun baki damar tafiya ne dan ki zurfafa ilimin ki, gara mu ki kiyaye ka'ida, sannan kema baza ki yi zaman kadaici idan bana nan, kuma Jawad yana school" Cikin gaskiya da amana take ri'ke da Jawad komai yake so yi masa take yi, duk sadda ta je makaranta bata mantawa sai ta siyo masa abinda zai ji da'di, sun shaku sosai, da ke mai son jiki ne indai suna zaune to kuwa rabin jikinsa yana jikinta, sau tari Mk ke cewa "kina fama da kanki, amma sai ki kama katon yaro ki jingina wa kanki". Murmushi take yi ta ce "Duka duka nawa ne adadin nauyinsa?" Sosai ta samu saukin Ciwonta duk tashin da zai yi baya kayar da ita, kamar sadda take Nigeria, domin kwararren likitan ('kashi) take gani a asibitin jamiar, sannan zurfafa ilimin da take a fannin magunguna ya na taimakawa wurin sake sanin maganin da ya kamace ta. Jawad yana ta karatunsa domin haziki ne sosai kamar Babansa bai yiwo shiriritar uwarsa ba, ko acan da suke da tsarin ilimi mai nagarta sosai yake ja, domin parfomance dinsa is very high hakan na farantawa iyayen nasa rai shiyasa komai ya ce yana so suke rige rigen yi masa. Ba abin da yake damunsa sai rashin Jin muryar uwarsa a waya, tunda Mk yana ha'dasu da Hajiyar Bichi, da kuma Baffah, amma ya kasa samun layin Inna da Sa'adah ta ke amfani da shi, ita kuma tunda take ganin missed call din lambar waje ta kuma gane lambar Ingila ce sai ta yi blocking din layin shiyasa basa samun layin. kunyar Baffah take hana Mk tambayarta. Rannan Jawad sun gaisa da Baffa ya ce "Baffah ka bawa Mami wayar zan yi magana da ita". Baffah da bai san Iyah ta rufe musu hanyar samunta ba ya ce "yanzu tana makaranta, Ni kuma bana gida ku nemeta a layinta ko na Innar ta. Domin kuwa basu jima da barin kasar ba ta ce da Sumayya tana son waya, a satin ta turo mata da kudin waya mai tsadar gaske, tunda murna suke yi ta yarda zata ri'ke waya, alamun ta cire komai a ranta akan Mk, zata fuskaanci rayuwarta ta gaba. Tsawon wattanni takwas kenan Jawad bai ji muryar uwarsa ba, a hankali sai abin yake 'dan ta'ba shi har abin ya fara bayyana a komai nasa, ya rage yawan surutu, ya daina walwala a tsakanin su, ya zama shiru shiru, sannan yafi son zaman daki fiye da falo. Abin ya fara damun su mussaman Farida, ta yi tambayar duniya ya ce ba komai, Mk da ya gaji da yadda Farida take yawan damuwa da canjin Jawad ya ce "kifa daina damuwa, tunda dai ba wani abin aka masa ba, miskilin yaro ne na gaske, ni na yi mamakin yadda ya sake da ke tashi guda". A marairaice ta ce "gaskiya akwai abin da yake damunsa domin ai ba haka ya ke ba, kamata yayi mu gano damuwarsa ko da cikin hikima ne". Ranar alhamis da yamma, Mk da Jawad suna gida, yayin da Farida ta ke makaranta adalilin tana da lectures. Cikin hikima ya hilaci Jawad akan ya ji me ya kawo changes din da suke gani a tare da shi, tunda bai fi sati da canjin nasa ba. Cikin muryar kuka Jawad ya ce "Mamina! Na dade ban ganta ba, sannan tunda na zo bamu yi waya ba". ya fada yana rushewa da kukan sosai. Jikin Mk ya yi sanyi yasan Jawad ya yi kokari wattanni takwas da yawa, domin bai taba yin wata daya bai ganta ba, ko da yake hannun Hajiya duk karshen wata sai ya je ya yi kwanaki biyu. Sannan tun farko yafi kulafacin uwarsa fiye da shi. Jikinsa ya janyo shi yana fa'din ka yi shiru yau din nan zaku gaisa, ai da tun farko ka fa'da mini wannan ne damuwarka da tuni na magance maka ita. Da kuka sosai Jawad ya ce "Am scared Malam". Da mamaki sosai ya ce "Mai ya ke firgita ka?" Last week na kalli wani firm a Fox movie (pendamic) yaron ciki ya tafi boarding school, shiru shiru bai ga mamar ta je ba, sannan baya samunta a waya Ashe she was died bai sani ba". Kuka sosai ya sake barkewa da shi, zuciyar Mk ta dinga bugawa tamkar Sa'adatu ta mutu ne da gaske sune basu sani ba, domin yadda ya santa da Jawad bai zaci za'a shafe wannan wattannin bata nemi jin lafiyarsa ba. Anya tunanin Jawad ba gaskiya bane? Ya kasa cewa komai bare ya rarrashe shi wani irin abu ke masa yawo a jikinsa, ga dai sanyi a garin amma wata irin zufa ne ta fara karyo masa. Ya dauko waya ya dinga gwada layin Inna amma sam baya tafiya. Dabara ta fa'dowa Mk ya dinga lalubo lambar Zainab Ma'aji amma bashi da ita. Ya rasa yadda zai yi sosai Jawad ya firgita shi shima. Da kyar ya shawo kan Jawad ya yi shiru bayan ya yi masa al'kawarin idan har ba'a sameta a waya ba, zai shirya musu tafiya Nigeria next week. Duk kokarin Mk ya samu Sa'a a waya ya ci tura. Tunda ko Baffah da ya mata maganar Jawad na ta cikiyarta ta daure ta kira shi su gaisa. Kai tsaye ta ce "idan da rabon zamu gana zai dawo ya tarar da ni, Ni bazan kira shi ba, tunda ba shi da wayar kansa". Daga Baffa har Inna ba wadda ya tilastata. Mk da ya gaji da kiran lambar Baffah yana cewa tana Makaranta ko shi baya gida, sai ya kira layin Sumayya ya bawa Jawad suka yi magana yana ta mata kukan yana expecting Mami has gone. Tausayinsa ya cika zuciyar Sumayya, ta dinga lallashinsa tare da al'kawarin daga yanzu zuwa kowanne lokaci zai ji muryar ta, tana nan cikin koshin lafiya. Suna gama waya kuwa ta tura musu sabuwar lambar Sa'a. Jikin Mk har bari yake wurin kiranta, amma sama da sau goma ta ki picking. Tana kwance a dakinta tana kallon Yadda Kiran ke ta shigowa. A ranta tana fa'din har abada ban son jin ka, Jawad din ma na yafe maka shi". Mintina goma sai ga kiran Sumaayya a layin Inna, ta dinga yi mata fa'da tamkar ta shigo ta wayar ta daketa, saboda itama ta kira layin nata bata dauka ba a tunaninta Mk ne. "Iyah kalaman Jawad sun tayar mini da hankali tunaninsa mutuwa kika yi ake boye masa, idan kina haka har yanzu akwai kullin Mukhtar a ranki. Ki amsa masa waya Jawad ne zai yi magana da ke yafi sati yana cikin damuwar rashin ji daga gareki". "Ni wlh Anty har Jawad din ma bana bu'katar jinsa ina masa addu'a, ina fatan ta zame masa garkuwa a ko ina yake". Sumayya ta ce " To shi laifin me ya miki haba Iyah! Ki ji tausayi mana". Da kyar ta shawo kanta ta yarda zata 'daga wayar. Ba a jima sosai ba kuwa, 'Kiran ya sake fa'dowa wayarta. Ta dauka ta yi shiru, sanin da Mk ya yi dabiarta ce ba zata fara yin magana idan ya 'kira a waya tun fil'azal sai bai wani damu ba, ya dinga yin sallamah, ya koma cewa hello nan ma shiru, ya mayar da wayar hand free, a tunaninsa jiyota ne ba ya yi. Yaayin da Sa'adah tsananin bacin rai ne ya kamata akan me zai mata magana, ya bawa Jawad din wayar mana. Murya a sha'ke ta ce "Jawad!" Ran Mk ya baci wato tana jinsa amsawa ne ba zata yi ba. Amma a zuciyarsa ya samu nutsuwa kwarai da gaske da ya gane tana nan cikin koshin lafiya har ma tana da kwarin guiwar yin wulakanci, dan haka sai ya mi'kawa Jawad wayar a fusace. Ya tsurawa Jawad ido yadda ya ke magana yana wani irin murmushi, ya sake kallonsa sosai yana ganin ba kammanin Sa'a tare da yaron illah wushirya da farcen hannayensa, inka dauke Wannan tamkar Mk aka raba biyu aka yi shi dan tsananin Kamar da suke yi. Ya nisa ya tuno yadda Sa'adah ta tsaya a gabansa tana sheganta masa yaro, banda dai so baya shawara ai da bai kamata ya cigaba da son Sa'adah ba. Ya muskuta yana kasa kunne yana sauraron hirar su inda ya ji Jawad na maganar da ta ja hankalinsa. "Mami na tara ku'din da zai ishe ki zuwa, zan fa'dawa Malam zan zo na taho da ke". Ya juyo murmushin Sa'a da yake kashe masa zuciya ta na cewa " A ina ka samu kudi?" "Idan Malam ya bani bana kashewa, sannan munje gidan freinds dinsa na samo ku'di da yawa, kuma Anty ta je da ni gidan sister dinta nan ma anbani kudi duk na boye miki su". Dariya ta kwacewa Sa'adah ta ce "Ka siyi abin da kake so ka ji Jawad! Kudin ba zai isa na zo ba". Ya fara mata kuka yana cewa "kudin fa da yawa Mami! a school ma da muka yi tseren gudu da quiz na zo na daya an bani kudi da yawa har da chain din gold, na boye miki shima". Kukansa ya ta'ba ta sosai dan haka sai ta ce "To ka ai baka da kudin zuwa da na komawa, iya nawa ka tara ka bari sai ka sake tarawa sai ka zo ka dauke ni". Cikin kuka ya ce "Zan fadawa Malam ya biya mini". "To ka daina kuka, idan kana kuka, bazan yarda na zo ba, sannan ka bari sai anyi hutun school, dan kar a wuceka a karatu, kuma ko ba ka ji ni a waya ba, ka daina damuwa kasan Ni ma ina zuwa school, karatu ne yake boye ni, amma kullum ina yi maka addu'a". Ya goge hawayen ya ce " Na daina kukan, idan zaki mini addu'ar, ki dinga addu'ar kudin nawa ya isa na siyi jirgin kawai. Kinga sai na yi ta yawo da ke har da su Inna da Hajiyar Bichi." Suka dinga hira sosai, suna Shirin yin sallama ya ce na bawa Malam ku yi magana? shima ya damu da ba bamu same ki a waya ba". Mk ya sake kasa kunne dan ya jiyo amsar da zata bayar. "Ai mun gaisa kafin ya baka wayar, stay blessed my Boy". Daga haka ta katse wayar. Da wani irin kuzari Jawad ya mikawa Mk wayar yana fadin "thank you very much Malam". Da zai karbi wayar sai ya hada da hannunsa ya janyo shi ya dora shi akan cinyoyinsa. "Da sakakkiyar fuska ya ce " Me yasa ka damu sai Mami ta zo nan alhalin kasan bata son zuwan?" Da sauri ya ce "Lah tana son zuwa fa, tana son ka mayar da mu gidanmu mu dinga kwana tare, da zamu taho na roketa ta biyo mu na san ba zaka yi fa'dan mai yasa ta zo ba". Mk ya dinga jin wani iri, a karancin shekarun Jawad ya shaide shi ba zai wulakanta uwarsa ba, anya bai kamata ya sasanta da Sa'adah haka nan ba? Tunda ya lura a fili Jawad yafi son uwarsa akan komai. A hankali Mk ya ce "To ya baku taho taren ba?" Ta ce mini "Ba ita ka ce ta zo ba, Anty amarya ka ce ta zo, sannan bata da ku'din zuwa, na ce mata ai Baban Anti ne ya biya mana, shine ta ce ita Baffanta ba shi da kudin da zai biya mata! Sai na ce to ni zan tara kudi na biya mata itama". Jikin ya Mk ya yi wani irin sanyi, ya dinga jin kalaman yaron har cikin zuciyarsa. A shekarunsa na goma sha'daya har yasan kishin uwarsa? ya tuna duk sadda ya samu kudi yake nacin shi zai ajiye abinsa ashe uwarsa yake yiwa tanadi? Ya nisa ya sake tuno lokacin da makarantarsu ta karrama shi da bashi chain din gold, da suka dawo gida ya shige dakinsa ya masa boyo na mussaman duk rarrashin da Mk ya yi masa akan ya kawo a ajiye masa, ya ce shi ya boye da kansa, ashe duk uwarsa yake yiwa? ba abin da ya tsayawa Mk a zuciya irin da Saadah ta ce wai ita Baffanta ba mai kudi bane. Shiyasa 'danta ya kudiri aniyar ya tara mata kudi, dan ya huce mata takaici. A ranar Mk ya ji ya yafe mata kaso sittin cikin kullacin da ya mata, ya samu saukin da zuciyarsa ta yi akan lamarinta, sai dai wannan tsoron nata da ya shige shi, bai ragu ba. Ya lura idan bai bi a hankali ba, nan gaba ba karamin matsala Jawad zai bashi ba, mussaman da yana sane uwarsa tana son ya mayar da su gidansu, amma bai yi hakan ba. *** Tunda suka yi shekara da aure ba labarin samun karuwa! Farida ta fara jelen ganin gynecologist, duk wani gwaje gwaje anyi mata an tabbatar komanta lafiya kawai lokaci ne bai yi ba. Zuwa wannan lokacin Mk ya samu budi sosai adalilin tallafin da gwamnatin tarayyar Nigeria take bashi, ga albashinsa, ga kuma wadda yake karba na gwamnatin kasar ingila. Bugu da kari ya na kasuwanci sosai, ya sake fadada shagunan askinsa, ya bude na shagon saida kayan maza masu daraja da kyau. Dan haka ya kammala katafaren gidansa da yake ginawa akan hanyar zuwa sabuwar Jami'ar Bayero, fenti kawai ya rage da Yan kananun abubuwa da sai a shiga gidan za'a fi bu'katar su. Gida ya yi kyau sosai, ya tuna Sa'a ce ta tsara yadda gidan zai kasance, a ransa ya gamsu Sa'adah tana da baiwar fashion and design hadi da creative. Cikin abubuwan da Mk yake yawan tunawa ya Sha mamaki akan lamarin Jawad shine wani lokaci da yake daf da barin kasar ingila, ya fita da su shopping, shagon kayayyakin Mata da kananun Yara na alfarma suka je, Farida ta zabi dogayen riguna na alfarma da suka amsa sunansu, guda biyar ga turarenta designer na Amour amour, ta hada da wani dan kunne mai kawanya da alamunsa daham ne. Kasancewarta bata amfani da kowanne irin mai sai veseline ta cakude shi da gilasirin, tafi bada karfi a shower gel. Jawad na tsaye yana kallonsu. Mk ya juyo ya ganshi a tsaye bai dauki komai ba, ya kalleshi ya ganshi tsaye ya rungume hannunsa a kirjinsa. "Jawad baka dauki komai ba". Ko sai mun je wani mall din?" Ya girgiza kai ya ce "I thought Anty ce kawai zata yi shopping yau". "Kaima ka duba duk abin da kake so ka dauko" Suna tsaye suka hango shi rungume da dogayen riguna irin na Farida sai banbancin kaloli guda hudu, sai takalma na mata masu tsananin tsada kafa biyu, dukkansu kirar kasar itali, ya ajiye gurin buga kudi, ya wuce ya dauko zobe guda daya da ya kusan ninka Dan kunnen Farida. Mk ya kalle shi ya ce "Me zaka yi da wannan kayan? " Ya shagwabe fuska ya ce "Malam so nake yi ba kai ka ce na dauko komai nake so ba?" "Na fa'da amma ai naka na ce ko?" "Malam ni wannan nake so a maimakon nawa, kaga rigunan Nan tsaraba zan yi da su, daya Antyn Lagos, daya Maman Gombe, daya kuma Anty Samira". Mk da Farida suka zuba masa ido domin kuwa wadda duk ya ambato zai bawa Mk bai isa ya ce komai akan su ba. Ya ce " Amma Jawad wadannan sunyi kudi da yawa". Ya kwakkwabe fuska ya ce Ni dai su nake so Malam" Mk ya ce "To wadannan ragowan rigar da takalman da ka kwaso fa, kasan ku'din takalmi daya ma kuwa?" Kai tsaye Jawad ya ce "Mami zan siyawa a kudina tunda bata zo ba". Mk ya yi shiru ya ce "to ai kudin naka ba zai isa ba, sai ka mayar da zoben". Ya ce "Ka cika mini ko ka ara mini ni dai ina son su". Kan dole Mk ya biya kudin kayayyakin nan, wadda ba karamin jijjiga asusun ajiyar sa yayi ba, hatta Farida sai da abin ya mintsine ta, ta lura kusan kullum idan suka fita siyayya irin haka sai Jawad yasan me ya siyo wa uwarsa, Mk kuma baya iya tsawatar masa, kafin su tafi ta san ba karamin kaya zai tara mata ba. Kawai shanyewa take bata ta'ba bari abin ya bayyana ba, Amma abin na tsaya mata a Rai, sai dai ana jimawa take kokarin mantawa. Mk bai sha mamakin Jawad ba sai da ya bishi dakinsa ya ga ya dauko katuwar ledar da yake tara kayan da yake siyowa da sunan Iyah kayayyaki ne masu tsadar gaske. Ya zauna a bakin gado ya ce "to kawo kudin da kace na ara maka, tunda ai kasan ciko mai yawa na yi maka" Haka kawai Mk ya fada Jawad ya fashe masa da kukan shi kudinsa Mami zai siyawa jirgi tunda antaho anbarta a gida kuma Baffa bashi da kudin da zai biya mata. Jikin Mk ya yi sanyi ainun ya kasa cewa komai, da kyar ya ce "Ai ba a haka Jawad! kenan wayo ka mini? Kullum ka yi ta fa'din jirgi za ka siyawa Mami ko zaka biya mata, amma ni ko keke banji kana cewa zaka siya mini ba, alhalin na fita sonka". Yana goge idonsa da rigarsa ya ce "Zan siya maka Malam amma dai ka yi ha'kuri na fara yiwa Mami, kai kana da ku'di, Baban Anty yana da kudi, ita kuma basu da kudi". Mk ya ji haushin Sa'adah ya cika masa zuciya na yadda ta zauna ta yi maganganu da yaro 'dan karami, gashi maganar ta shiga zuciyarsa ainun, ya tsinci kansa da fadin "me za'a yi da halin wannan yarinya". Jawad ya ce "wacece?" Ga mamakin Mk sai ya kasa cewa Sa'aadah, sai ya buge da fadin "wata fitananiyar student dina ce mai baudadden hali, mai wuyar sha'ani". Haka suka cigaba da rayuwar su har wa'adin da Mk zai yi a kasar ya cika. Ya tattara ya taho ya bar Farida da Jawad tunda ita saura wattani uku suka rage mata, Dan haka ya bar mata Jawad dan shima ya kammala third term dinsa. Duk juyin da Mk ya yi da jawad ya bashi kayan tsarabar sa da ya tara cikin katon akwati, baisa ya bayar ba, ya ce shi da kansa zai taho da kayansa domin ba ya so a kaiwa Sa'adah kafin ya dawo. Har Suka kammala watan ukunsu Jawad ba ya bata matsalar komai, sai duk sadda suke hira Rabin hirarsa kuwa ta uwarsa ne. Da azahar Suka sauka a Kano. Kai tsaye gidan Hajiyar Bichi suka zarce suka samu kyakkawan tarba daga Hajiya ga abinci ta tanadar musu ba karmin mamakin girman Jawad ta yi ba Ta kalle shi ta ce yanzu a shekaru biyun nan ka yi wannan uban girman wa zai ce shekarunka sha biyu?". Yamma na yi Mk ya dauki Farida zuwa gidansa da suka zauna da Sa'adah, bai san me yasa ya kasa shigar da ita wanccan gidan da Sa'adah ta tsara shi ba, sai ya gyara ainihin gidansa. gaba'daya gidan ya sha gyara na mussaman hatta fasalin ginin ancanza shi ya zama mai upstairs (bene) an mayar da shi na zamani kwarai da gaske , haka nan ba karamin jere na garari aka yi wa Farida ba. Duk wadda ya shiga gidan sai ya burge shi sosai saboda tsarin ginin tamkar gidajen turawa. Duk yadda Mk ya so ya tafi da Jawad Hajiya kin yarda ta yi ta ce "Ai dama daga nan gidan ka dauke shi, dan haka dauki matarka kuje ta huta gajiya, sosai Jawad ya yi murna da hakan domin yasan goben nan zata sa Uncle Ahamad ya kai shi wurin Maminsa. Leda guda Jawad ya ajiyewa Hajiya na tsarabar ta ta dinga murna tana fadin "Na san zaka yi Imani Jawad". Washagari kuwa Hajiya tasa Ahamad ya kai shi da katon akwatinsa da sai da ya nunawa Hajiya duka kayan ciki, ko kadan bata yi ba'kin cikin uban kayayyakin da Sa'adah ta samu ba, a ranta kuwa murna take yi tana fa'din "Haihuwa wadar sarari ko kana gudu haifi ka Yar". Murna soasai Sa'a ta yi tana fa'din "ai Ni ka yiwa tafiyar nan Jawad, ubangiji ya raya mini kai, ya maka albarka mai yawa". "Amin Mami" ya fada yana kwanciya a jikinta, tare da sake cewa "kina addu'ar na samu kudin ya kai na siyan jirgin naki kuwa?" Inna da take gurin ta ji Hawaye na neman kwace mata, ta mike ta shige dakinta, tana jin dadi da tausayin yadda Jawad yake girmama lamarin uwarsa. Dawowarsu Nigeria ya sake wayo sosai, aka saka shi a makarantar Intercontinental college tsananin hazakarsa yasa suka dauke shi J s 3, maimakon aji biyu da zai shiga. Iya turanci gangariya da Jawad ya yi ya janyo masa farin jini ainun a gurin malamai hatta student son abota suke da shi. A haka ya Saba da wani dan ajinsu Muhsin Sani Yar-gaya, a hirar su da Muhsin Jawad ya fahimci Malam da Mami sun rabu ne, wato divorce ne a tsakanin su. Kusan Muhsin ne ya cusa masa dabi'ar kin Farida a dalilin shi Muhsin din mahaifiyarsa ta rasu shekaru biyu, sannan amaryar Baban su azabtar da su take yi, shi da yayarsa makaranta nan da suke zuwa ne kawai bata yi nasarar rabasu da ita ba, hatta magana da mahaifinsu sai a sace suke yi da shi domin shima tsoronta yake ji. A hankali Jawad ya fara janyewa Farida idan ana son aga damuwar sa to weekend ne ace zai tafi gadon kaya. Ba irin rarrashin da Farida bata yi masa amma ya kame daga yawan yi mata hira, idan kuwa yaje gidan a takure zai zauna tamkar bai santa ba, abin ya damu Farida sosai hatta Mk ya damu, ya tabbatar kuma ba zaluntarsa take yi ba tsiya ce kawai irin ta 'Dan Yau. Har aka kai jallin da kuka yake zuwa gidan, idan Hajiyar Bichi ta ce da Mk ya barshi tunda baya son zuwa, ya kafe sai yaje. Rannan dai da abin ya ishe Mk a gaban Hajiya ya dinga fa'din "ko zai shide sai ya je gidan, da suka rayu shekaru biyu tana masa wahala bai 'ki ta ba, sai yanzu saboda ya samu shashar uwa tana kitsa masa maganganun iyashege to kanta zata cuta ta kuma cuci 'danta. Ya kalli Jawad da yake bayan Hajiya yana kuka da hawaye ya zare masa ido ya ce "idan na kuma jin kace mini zaka unguwa uku sai jikinka ya fa'da maka ai can ba gidanku bane, kana kin gidan ubanka kana kwadayin gidan wasu, zo ka shige girma da arziki tun ban tashi ba, kuma nan din ma ba zaka dawo ba can din da baka so a can zaka zauna". Jawad ya rushe da kuka yana cewa "Hajiya ki ce ya dawo da Ni dan Allah". Aikuwa haka ya tafi da shi yana kuka , sai dai kaya kala biyu Hajiyan ta bashi tabbacin zai dawo kenan. Shiyasa ya rage sautin kukan nasa. Wannan matsalar gaba'daya Mk Sa'adah ya jinginawa ita ya dinga tunanin hanyar da zai magance ta. Ana haka Jawad ya dinga wani irin zazzabi, karshe farankama(chicken fox) ta feso masa a jiki. Hajiyar Bichi da kanta ta bugawa Inna waya ta sanar musu, Inna bata yi kasa a guiwa ba ta zo ta duba shi har da tsarabar kayan dubiya, ba yadda bata yi da Sa'adah akan su tafi tare su dubo Jawad amma ta ki. Da kyar Inna ta shawo kanta bayan taje da kwana biyu, Suka shirya Suka je da Zainab Ma'aji wacce a lokacin wattannin ta biyar da aure, da kuma cikin wata hudu a jikinta. Ma'aikaciya ce a hukumar kidaya ta kasa reshen jahar Kano. Cikin kwalliya sosai Sa'adah take, ta dawo wata irin mace da gayu da ilimi suka ratsata mussaman da Alhaji Mamman ya sake dawowa cikin rayuwar ta, ba karamin kudi yake sakar Mata ba, ita kuma bata kwangen yin sutura ta daukar hankali. Komai nata daukar ido yake yi, ado take a yanzu irin wadda bata yi zaton zata yi irinsa ba, amma kuma cike da hankali da nutsuwa. A wannan lokacin ta kammala karatunta tana makarantar horar da lauyoyi ta Bagauda(call to Bar). A motar mijin Zainab Suka je bayan sun tsaya a hanya sun masa siyayya ta sosai, kai tsaye suka shiga gidan ba wani nauyi domin dai Sa'a ta kan zo gaida Hajiyar duk da ba kasafai ba. A falon Hajiyar suka tarar da Mk yana shafawa Jawad calamine lotion a jikinsa ko ina jikin Jawad din maganin ne adalilin duka jikinsa ta feso masa har fuska, farin maganin ya maida Jawad wani iri. Suka gaisa da Hajiya cike da girmamawa, suka tambayi mai jiki. Zainab ce ta gaida Mk cikin mutunci, har tana cewa "Uncle rabon da na ganka har na mance". Ya yi murmushi yana cewa "kina cikin daliban da nake cikiyarsu Zainab! Ya mijinki da Yara?" Ta 'kasa kuma kallon Sa'a kawai ya ke yi zuciyarsa na wani irin tsalle, yayin da ita ta yi tamkar bata ganshi ba, ko arzikin gaisuwa bai samu ba, ko Jawad da yake kusa da shi, sau daya ta masa sannu ta maida hankalinta wurin Hajiya. Rashin gaisawar da basu yi ba, ya ta'ba Hajiya kwarai da gaske, yayin da Mk ya dinga fargabar wayewar da cigaban da ya gani a tare da ita, kwarai da gaske ta banbanta da Waccan Sa'adan da ya rayu da ita. Zainab sai zungurar ta take yi akan ta gaishe shi, amma ta yi mirsisi. Suna zaune Ahamad ya shigo ya ganta yana cewa "yau wa nake gani kamar Antina" Da murmushi sosai ta ce "Nice me zan Samu?" Ya mi'ka mata 'datar da yake ci, aikuwa ta karba ta hau ci, hakan kawai sai da Mk ya ji haushi dan me zata ci ragowan yawun Ahamad? Ta mi'ka masa mukallin mota tana cewa "daure ka debowa 'danka kayan dubiya da mamarsa Zainab ta kawo masa". Da azama ya karba, ya dinga shigo da kayayyaki har Hajiya ta ce " wanne irin hidima kuka yi haka Sa'a? Sai kace wadda zai bude shago?". Ran Mk ya baci saboda yadda yaga uban kayayyakin ciye ciye masu tsada sai kawaia zuciyarsa ta kisima masa Bazawarinta ne ya yi wannan siyayyar. Ya dinga huci karshe ya fice bai ko sake kallon kayan ba, da kyar ya ce da Zainab ta gaida gida. Jawad ya warware ya koma zuwa School amma rashin son zuwa gidan Farida na sake ruruwa a ransa kullum da kuka yake isa gidan, sannan har yaje ya dawo sai ta 'kure da ya yi mata magana har zane shi Mk ya yi amma bai canja ba. Kan dole Mk ya samo masa makarantar kwana ba tare da ya yi shawara da kowa ba, da kyar aka samo makarantar saboda anci karfin zangon karatu na biyu. Sai da komai ya kammala na makaranta ya fa'dawa Hajiya dan kar ta hana, Kan dole ya dauki Jawad ya kai shi makarantar gwamnatin tarayya ta Kiyawa, a kokarinsa na nisanta shi da masu hure masa kunne da masu son cusa masa muguwar dabi'a. A dai dai wannan lokacin aka dawo da Mijin Sumayya aiki Kano, da Karin girma sosai. Tuni dama sunyi gininsu a gandun albasa layin kwankwaso, da farin ciki Suka tattaro Suka dawo kano cikin gidansu na alfarma. Zainab ta haihu ta sami Musa sunan uban mijinta ne, Sa'adah ce ta yi masa inkiya da Walid. Farida ce dai shiru har yanzu da suke cikin shekaru uku da aure, Mk na iyakacin kokarinsa wurin kwantar mata da hankali ya na tabbatar mata zai cigaba da sonta ko bata haihu ba. Amma deep inside his heart ba abin da yake so irin yaga an masa haihuwa, ya matsu ya samarwa Jawad gishirin duniya. Watan Mk uku da dawowa Jami'ar ta yi bikin karrama shi, tare da bashi mukamin Dr! Sannan ya zama shine H.O.D na English department. Wanda shine mafi karancin shekarun da ya taba zama Head of Department. A wannan lokacin kuma mahaifin Farida ya bashi dan'kareren guda a Rijiyar Zaki, a matsayin kyautar karramawarsa ya taya shi murnar kammala karatunsa. Gida ne mai kyau, mai dauke da bangare biyu, matu'ka da gaske gidan Flat ne amma ya tsaru kwarai da gaske. Har Jawad ya shekara Sa'adah bata ta'ba zuwa masa ziyara ranar visiting din ba adalilin tana gujewa haduwarta da Mukhtar. Sai dai Sumaayya da Inna su je, haka Farida da Mk da Hajiya duk suna zuwa. Sai visiting din karshe wadda suka hadu da Mk har zuwa ranar da Mahmoud ya je gurinta da neman sulhu da irin bijirewar da Innah ta yi akan maganarta da Mk. *'karshen labarin abin da ya faru a Rayuwar Sa'adah da take fatan matan da suke cikin waccan rayuwar da ta yi a baya su hankalta kafin komai ya kubuce musu*. *Surayya Dee* ✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *Assalama Alaikum*! *Tsokaci* *Ina jinjina da godiya ga dimbin masu bibiyar wannan labari na *HALIN YAU* ina kuma jin dadin yadda kuke sharhi akan labarin, Allah Ya bar zumunci*. *Bayan haka zan so na yi dan tsokaci game da wata sa'dara a cikin labarin, a shafin baya da na saki. Watau daidai wajen da MK ya tare da Farida a hotel din Tahir na yini daya. Wasu daga cikin masu kokarin bibiyar littafin kullum, sun yi sharhi akan cewa don me MK ba zai bari har sai sun tafi UK ba kamar yadda aka tsara? Me yasa bai yi hakurin ya nuna zumudinsa wanda hakan tamkar cin fuska da tozarci ne ga Sa'adah?* *To abin da nake son na ja hankalin masu bibiyar labarin shi ne, a dabi'a ta namiji wannan ba komai ba ne. Idan har namiji na bukatar abu idonsa rufewa yake ya manta da komai, musamman ma bukatar kwanciyar aure. Abin a halittar maza yake, don haka shi MK bai yi haka da nufin muzantawa ga Sa'adah ba ko kuma jin cewa Farida ta fita. Sai dan a fahimci kaso casa'in da tara da digo Tara na mazan Yau haka suke, domin zasu iya kwanciya da macen da bama sonta suke ba, kawai dan su biya bukatar su ne sabanin da yaje wahalar gaske mace ta sallamawa wadda bata so kanta Akan tana so sai alatilas.* *Watakila tsawon lokacin da ya dauka ne yasa shi gaza hakurin jurewa har sai sun tafi UK din*. *Ina fatan masoya Iyah za su fahimci MK kuma su yi masa uzuri.* *Wasalam*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 91-92. *Barkan mu da Dawowa* *Asalin labarin*. Kwana Sa'a ta yi tana juyi, Abu goma da ashirin sun cakude mata, na farko idan ta ce bata son Mk ta yi karya, duk yadda take jin haushin sa, da jin bacin rai akan lamarinsa, bai hana ta ji wani irin murna da farin-cikin dawowarsa ba. na biyu kuma bata jin a karan kanta zata saurare shi har sai ya janye kalamansa, sannan kishin auren Farida da ya yi yana matu'kar kassara tunaninta, yana gushe dukkan farin cikin da take ciki, haka nan yana sanya mata jin haushinsa marar misaltuwa, sannan ya sababa mata jarumtar da zata iya yin fito na fito da shi. Sai kuma fargabar yadda Inna ta zafafa lamarin ta da shi. Haka gari ya waye ta tashi da idanuwanta a kumbure ga ciwon kai tabbacin babu isasshen barci a tare da ita. Tana tsakar gida tana brush ta dinga jiyo sautin wayarta, bata wani damu ba tana raya koma waye ya sake kira. Maimakon ta shiga dakinta, dakin Innarta ta shige ta sameta ta idar da sallar walaha. Ta sake gaisheta tunda sun riga sun gaisa tun asuba. Ta zuba mata ido ta ce "Iyah wani Mafarki na yi da ya tayar mini da hankali, amma zan bishi da sadaka da kuma addu'a domin ba abin da sadaka bata wanke shi, kema ki tsananta addu'a ki kuma fita harkar Muutar tun baku sake jefa mana ba'kin cikin da ya zarta wadda muka shiga a baya ba". A sanyaye Sa'adah ta ce "wani abin kika gani ne marar Da'di Innah?" Da sauri Inna ta ce "ai idan akace marar da'di da sauki, abin da na gani muninsa ya zarce hankali, abin a nemi tsari ne, ba a kanmu kawai ba, akan kowanne musulmi ma, Malamin islamiyarmu ya ce ba kyu fa'dar Mafarki marar kyau domin duk yadda aka fassara maka shi haka zai zo maka, dan haka zan kame bakina , na bishi da istigifari da sadaka, ina sake jan kunnenki ki sake nesanta kan ki da Muutar". A tsorace Sa'a ta ce "To Inna zan kiyaye in sha Allah, ashana zaki bani, ta kicin din na jefata a ruwa ban lura ba". Ta karba ta fita, tana Kissimmee kissimmen mafarkin Inna da dukkan alama ita da Mk ya shafa. Haka ta yini sukuku har yamma, Innar ma haka take ba kuzari adalilin mafarkin da ya mata tsaye a zuci, domin ta san da wahalar gaske ta yi Mafarki amma idan ta yi, ta kuma tashi da abin a kanta ma'ana bata manta ba, to kuwa lah shakka sai abin ya faru ko da ba kwabo da kwabo ba. Amma kaso sittin sai ya zama reality. Mafarki ta yi wai Muutar na ta bin Sa'a da gudu, suna ta tseren, so yake ya kamota amma tana ta zille masa ga wani abu Abu a nade a hannunsa, sun ci gudu, har Sa'a ta gajiya ta zube a kasa tana haki ya karaso, da gudu ya jefa mata abin da yake ta faman kankame shi, tamkar 'kwai. Da kuka Sa'adah ta bude ashe jariri ne, maimakon ta ga Sa'adah ta mayar masa da abinsa, sai kawai ta ga ta hau shayar da shi, cikin zafin nama ta nufi Sa'a, tana zuwa tasa hannu da nufin fisge yaron sai kawai ji ta yi an tureta da wani irin karfin da ya zarta na bil'adama, ta sake yun'kurin sake kwace yaron, aka sake turata cikin wani irin rami. Da wata irin murya ta ji ance "Zaki iya mutuwa akan wannan yaron, domin 'dansu ne, ke ce shamakin zuwansa duniya, to kuwa zai zo, idan baki yi Sa'a bama a dakinki zasu yi cikin su haifar miki shi a matsayin shege". Da kyar Inna ta fito a cikin ramin nan bayan ta kukkuje kafafuwanta, dai dai lokacin Kuma ta farka adalilin Kiran assalatu da ta ji Anayi a masallaci. Ta tashi duk jikinta a jike tsabar fargaba da rudu, ta mike a hankali tana neman tsari da samun shege a cikin zuri'arta. Yammaci sosai kafin Sa'a ta shirya ta fito da Shirin tafiya gidan Sumayya. A tsakar gidan ta sami Inna, ta ce "Inna zan tafi". Ta daga ido ta kalleta ta ce "Ince sai wani satin kike da zama a kotu?" "A a Gobe ne Innah". "To ki gaishe da Yayar ta ki, sannan ki fa'da mata lalle ta sake taya mu da addu'a". Har Sa'adah ta kusa kaiwa zaure Inna ta dawo da ita, ta zaunar da ita ta fa'da mata komai na mafarkin da ta yi, ta rufe da cewa "Dan haka ki nisanci Muutar. Kunya ta kama Sa'adah amma ta daure ta ce "in Sha Allah hakan ba zata faru ba ubangiji ba zai kunyata ku ba Inna". Sa'adah na aiki da (supreme Court) ta court road. Watan jiya Alh Mamman ya kawo mata (upper) takardar samun aiki har gida, wadda wannan na cikin abin da ya sake dagulawa Mk lissafi, domin kuwa a bakin Ahamad yà ji Sa'a ta samu aiki, duk da tafi zaman gidan Sumayya adalilin daga gandu zuwa court road ba nisa. Ya fi mata sau'kin zuwa. A bincikensa ya gano Alh Mamman ne ya samo aikin, ya dinga jin takaici yana kallon Alh Mamman a matsayin a karambana, da ga fitowarta a makaranta sai ka nemo mata aiki? Tamkar ance masa ana bu'katar hakan, kai dattijan mazan nan wuyar sha'anine da su idan suna son Yar yarinya. Ko kunya ba ya ji, zai dage yana son Sa'adah alhalin yana da 'dan da yake sa'anta ne. A fili Mk ya ja tsaki ya ce "zanga yadda za'ayi ka mallaketa shekaru da yawa ka kasa rabuwa da ita, tamkar ita ka'daice yarinyar mace bayan ga yanmata nan masu shekaru irin na ta". Ya sake jan dogon tsaki yana cewa "Halima tana nan har yau a kasa ta ke da gudu zata soka, amma wannan kam a yanzu ma ba samunta zaka yi ba". sai dai a zuciyar sa ya tabbatar son gaskiya Alh Mamman ya ke yi mata, wani irin abu mai nauyi ya danne shi a zuciya, wadda shi ya damalmala masa lissafi har ya ji ba zai sami nutsuwa ba, idan ba shiryawa ya yi da ita ba, ya lura ba zai ta'ba iya jarumtar wani ya aureta alhalin yana da rai ba. A zaure ta tarar da Baffa da Mk da kuma Mahmoud a zaune kan tabarma suna tattaunawa, sai da zuciyarta ta buga tunda ta ganshi da Mahmoud lah shakka maganar kome ya zo yi, a ranta ta dinga jinjina rashin ta ido a gurin namiji, yanzu da yake son komen ya na'de kafar wando zai nemi komenta duk yadda ya jingineta shekaru bakwai, Anya kuwa Mk yana da adalci a yanzu? A ladabce ta ce "Baffa sannu da yammaci, zan tafi, sai wani satin Kuma". Da wani irin farin ciki ya amsa mata da fa'din "To ki gaishe su, ki kula da kanki, Allah ya tsare". Ta amsa da cewa "Ameen". Ta kalli 'Karfi ta ce " Baban Dadi barka da yamma ya iyali?" Ya amsa ta saka kai ta fice bata ko kalli inda Mk yake ba, bare ta gaishe shi ko da gaisuwar da zai raina ne. Ran Baffa ba karamin baci ya yi da abin da ta yi ba, ta ganshi da ba'ki, ta gaishe da 'daya, ta wulakanta 'daya, idan dai da gaske bata son Mutari a yanzu menene zaisa ba zata gaishe shi ba? "Iyah" Baffah yasa baki ya kirata da karfi, ta dawo tana cewa "Ga ni Baffah"! "Me yasa kika gaishe ni, Me yasa baki wuce kanki tsaye ba? Ai na yi zaton ko da rago Ki ka ganni zaki tsaya ki tambayi lafiyarsa saboda ya shiga rigata, akan idona ki yiwa Mutari wannan wulakancin? Amma ba komai ai ni kika yiwa ba shi ba, Na gode miki je ki, yi tafiyar ki". Ta kasa tafiya, ta yi sukuri tana jin takaici na kamata, hawaye ya balle mata, Mk yana kallonta ta gefen ido, yana ganin yadda ta turo baki gaba, sai ya dinga jin wani irin tsumi na tsumashi, abubuwa masu yawa akanta suka dinga bijiro masa, ya dinga jin wani irin abu na taso masa. A hankali, kuma cikin bacin rai ta ce " Mutarin Baffah ina yini?" Dariya ta kwacewa Mahmoud ya dinga kyaykatawa Baffa kuwa ya gintse tasa dariyar ya dubi Mk da ya hade girar sama da ta kasa kuma bai amsa ba, hakan da ya yi ya sake hassalo da Sa'a. Baffah ya cije ya ce "Yanzu kuma laifinka ne ta gaisheka baka amsa ba, tunda hakane sai ka tashi ka kaita, ai bazai yiwu ka sace mata iska a banza ba, dole ka hutar da ita tsayuwar jiran mai adaidaita sahu dama kuma garin hadarine sossai". Mahmoud ya yi maza ya ce "To Baffa bari mu kaita mu dawo, mun gode Allah ya kara girma". Baffah ya shige gida ya barsu a zauren Sa'a ta na jin tamkar ta yi ta zunduma ihu. Hawaye ya dinga tsere a idonta, wannan irin bada ita da Baffa ya yi? Duk wula'kancin da Mk ya mata wato Baffah bai ga laifinsa ba, daga zuwa da magana zaice ta shiga motarsa ya kaita a matsayinsa nawa din ta? Zauciyarta ta kuntata sosai tana jin gara ta tafi da kafa a kan ta shiga motar Mk. Har suka fita kofar gida kuka take marar sauti, Mahmoud ya bude mata gaban motar, ta cije, a hankali ya ce "a titi muke fa, sannan umarnin Baffa zaki bi, ba son ranki ba" . "Akan me za'a tilas ni shiga motarsa,?" Ta fa'da cikin rishin kuka. "Yi ha'kuri ai dukkan mu umarnin Baffa zamu yi wa biyayya akan kunnen ki dai ya hukunta Mk ta hanyar mayar da shi dureban ki, adalilin amsa gaisuwar ki da bai yi ba. Kina kallon bai yi musu ba sai ke?" Hawaye ya zubo mata ta ce "Ni na yafe masa zan tafi da kaina". Mahmoud ya ce "Ai tunda Kika bari Baffa ya shige cikin gida dolen Mukhtar ya miki direba kar ki yadda ki sab'awa mahaifin ki adalilin wani Mukhtar". Take Sa'adah ta gane gaskiyar Mahmoud ne, tunda rashin gaisuwar da bata yi bane ya janyo mata wannan hukuncin mai kama da saukar aradu. Maimakon ta shiga gaba inda Mahmoud ya bude mata sai kawai ta bude baya ta shiga. Da azama Mahmoud ya isa setin direba Mk ya juya musu baya tamkar baya wurin hakan da ya yi ya sake tunzura Sa'a tun fil'azal ta tsani a nuna mata rashin kulawa. Mukullin hannun Mk Mahmoud ya karba, a hankali ya ce "shiga baya mu je". Ba musu Mk ya bude bayan motar ya zauna, Yana rufewa Mahmoud ya ja motar. Zuciyar Iyah tamkar ta fa'do kasa dan tsananin ba'kin ciki mussaman da ta tuno irin addu'ar da dinga yi, tun bayan da ya auri Farida na kar Allah ya sake ha'data ko da zaman mota ne da Mukhtar balle kuma zaman aure, sai gashi karon farko da zaman motar aka sake ha'dasu, zuciyar ta dinga bugawa fiye da kima tana fargabar menene zai biyo bayan wannan zaman? Ta dinga jin takaicin kin shiga gaban motar, da ta shiga ai tasan shine dole zai ja motar, Kuma dolensa ya zauna iya kujerarsa sannan ya kula da tukinsa. Amma yanzu ya babbake har gefen jikinsu na gogar juna, gilashin motar irin na munafunci ne wato tint, ya matseta sosai tamkar su hudu ne a bayan motar. Ba'kin ciki ya isheta sai kawai ta fashe da matsanancin kuka mai sauti sosai, Mk ya yi tamkar bai ji ba, yayin da Mahmoud ya juyo da sauri tunda a tsaye suke traffic ya tsayar da su. "Menene kike yi haka Sa'adatu?" Zuciyarsa ta buga ganin yadda Rabin jikin Mk na jikinta, wani irin abu ya tsayawa Mahmoud da bai yi zaton zai ji ba, ya juya da sauri ya dauke fuskarsa yana ambaton innalillahi. Kukanta ya dinga tsuma Mk ya dinga jin tamkar ya danneta ko ya samu sau'kin halin da yake ciki. Ya lura fishi na fitar hankali take yi da shi, idan ya ce zai lalla'ba ta to ya kai shekara yana fama adalilin taurin kai irin nata. Ba zato Sa'a ta ji Mk ya ja uban tsaki mai tsayi, sai kuma ta ji yana cewa "Mahmoud saka mini wa'kar Auren Dole ta Ali jita". Dariya Mahmoud ya yi ya ce "bansan jita yayi wakar auren dole ba, ta aure mai da'di nasan ya yi" A gajarce Mk ya ce "to lalubo mini wadda zata dace da halin takurar da nake ciki, banda Hajiya da Baffa sun matsa mini, ina zan zo gurin wannan shugabar masu wula'kancin da niyyar wata magana, ai tun wulakantani da ta yi a ziyarar Jawad na gane idan ka shekara dubu baka mutum ba, kar ka tambaye shi komai binciki halinsa". Ya nisa ya sake jan tsaki ya ce " Ta tisa ni tana kukan gulma da iskanci, alhalin kasan ranta murna da farin-ciki ne fal, dan kuwa ban tsammaci zata iya barci ba, mafi yawa butulcin mace ke kaita wuta, abin da aka jima ana rokon ya tabbata ne, ya zo kuma sai a bude shafin iyashege, har da kuka kala kala tamkar wata yar yarinya alhalin gyara da kwalliya ne kawai domin ana kallon Jawad za'a gane ta tsufa". Wani irin daskarewa Sa'adah ta yi, wato Mk da rashin mutunci ya zo, ta tabbatar da hakan tunda a gaban Baffa ma ya yi mata diban karan mahaukaciya, amma ba laifinsa bane, Baffa ne ya bada ita, dama kuma ance naka ne yake bada kai. Duk yadda ta so shanye maganar Mk kasawa ta yi, ta yi jarumtar shanye kukan ta ce "duk tsufana dai ka girme ni, kuma ina rokonka ka koma ka fadawa wadda suka yi maka dolen aurena! na ce bana sonka, bana sha'awar zama da kai, domin wadda ya soni ina budurwa, yanzuma da na tsufa son nawa ya nan a tare da shi saboda ba sha'awata yake yi ba, idan kuma na so ma saurayi zan aura wadda ni zan cire masa samartakarsa fiye da yadda na ta'ba cirewa wasu". Ai bata karasa ba, ya shammaceta ya wawurota ya kama bakinta ya murde da karfin gaske, dan kansa ya saketa bayan ya tabbatar ta ji a jikinta. Jikinsa na rawa ya ce "wallahi idan baki kiyaye harshen ki a gabana ba, zaki sha wahala ai yanzu ke ba yarinya karama bace da zaki dinga mini kaifin harshe". Mahmoud kuwa da ya lura da abin da Mk yake yi ya kasa juyowa balle ya bude baki yayi magana saboda tamkar ya fashe da kuka haka yake ji. Kuka sosai Sa'adah take tana fadin idan yafi karfinta ai bai fi karfin ubangiji ba, ya fa'da mata bakar magana, dan ta rama shine zai mata wannan wulakancin? Har suka iso layin gidan Sumayya kuka sosai take yi, yayin da Mk ya biris tamkar bai ji ta ba, wani wula'kanci da Mahmoud ya yi mata, maimakon ya isa gidan sai ya samu gefe ya yi perking ya kunna musu a.c ya fice ya barsu, a kokarinsa na su dan sami daidaito shima kuma ya fita ya shaki isakar da zai dan samu sukunin zuciyarsa, da gaske da son Iyah zai mutu a ransa, wannan na cikin kaddararsa rashin cikar buri. Tsawon mintina Sa'a na kuka sosai, Mk da ya tabbatar ta yi shi ba ka'dan ba, ya santa da son a rarrasheta. Dan haka ya matsa sosai daga jikinta, ya yi gyaran murya ya ce " kukan ya isa haka My first love". Wani azabben kishi ya duro mata na ba zata, ta sake karfin kukanta tare da cewa "karka kuma cemin first love dinka, domin ni ba ita bace, kaima kasan ba ni bace. First love dinka tana can tana jiranka wacce ba zata tsufa ba tunda bata da kamar Jawad, Ni barni a makiyarka domin bansan komai da ka mini, kuma kake kan yi mini ba Sai kiyayyya da zalunci hadi da wulakanci". Jikin Mk ya yi sanyi ya ce da bakinki kika ce ban miki komai ba sai kiyayya da zalunci?". Da azama ta ce "kwarai kuwa! zan kuma rokeka ka koma ka fa'dawa Hajiya da Baffah su janye dolen da suka yi maka, domin ni ba sonka nake yi ba, ko ina sonka to na ha'kura, domin a yanzu sun nuna mini ka fini a gunsu tunda sai yanzu ne zasu maka dole,to ni kuwa ina tabbatar maka na wuce haka wallahi". Ya ce "Zan so kwarai mu fahimci juna, domin ni ban zo gurinki bisa ra'ayin wani ba, tsokanar ki nake yi, na gane ke ce cikon farin ciki na, ki zo mu rayu tare na sauran shekarun da ubangiji zai ara mana a gaba. kin san ina son ki, kin san ke kika mini laifi, na dauka ko wani kika ji ya ce na zalunce ki, zaki kare ni, amma fa'da mini me nayi miki na zalunci?" Ta yi shiru tana kuka kasa kasa, tana jin tamkar ta tashi ta yi ta rawa dan ta nunawa duniya irin farin cikin da kasan zuciyar ta yake ciki. Ta kasa cewa komai, ya nisa ya ce "Yanzu mu ba yara bane Sa'adah, ya kamata mu bar komai mu manta komai, mu gina sabuwar rayuwar da babu gillin bacin rai a ciki, ubangiji shine shaidata ba komai a zuciyata na yafe miki, na kuma manta komai". "Kema ki daure ki manta duk wani zaluncin da kike ganin na yi miki, ina tsananin son na rayu da ke my Sa'adah". Da kuka sosai ta ce "Ba haka bane a zuciyarka, kaima kasan ba haka bane, akwai dalilin da ya saka ka yafe mini amma ba dan kana sona ko dan kana son ka rayu da ni ba, daga ranar da ka jefe ni da mafi munin al'amari, a ranar na gane baka sona, wata kake so, kake neman hanyar da zaka rayu da ita, tunda ni amfani na ya kare a gurinka, ka riga ka dandana ni, shiyasa ka 'karanta tunaninka, ka kasa shaidata, ka kasa gane abin da zan yi da wadda ba zan yi ba, dama Kuma ai tun bamu yi aure ba, kake jifana da wannan zargin, yanzu kuma idan na koma maka ai cewa zaka yi har dakinka nake iskancin". Ta nisa ta sake cewa "na tabbatar ita baka ta'ba dukanta ba, amma ni saboda rashin gata da 'kin da kake mini kanka tsaye kake duka na" Ta fa'da cikin kuka, maimakon hankalin Mk ya tashi sai ya ji wata irin nutsuwa ta zo masa domin kuwa ya gane da gaske 'Karfi ya ke da ya ce akwai soyayyarsa mai yawa a zuciyarta duk da bakinta na kirarin 'kinsa. Kishin Farida ke ya galgalata wannan kuwa ba yadda zata yi sai hakuri. Domin ya riga ya kudire ba zai ta'ba barin matsanancin son da yake yiwa Sa'a ya sa ya zalunci Farida ba, ba kuma zai yi kuskuren rabuwa da ita dan zai dawo da tsohuwar matarsa ba. Bashi da burin auren mata biyu, amma tunda kaddara ta zaba masa to kuwa zai yi iya kokarinsa bai bari soyayyar daya tasa ya danne daya ba. Cikin lallashi ya ce "sonki ne yake rufe mini ido shiyasa nake dukan ki, Amma ai kinsan iya bakinki nake duka dan shine mai dafi, amma ta yaya zan doki jikin ki alhalin shine abin hutawata. Na rantse miki banda tsoron ubangiji da a motar nan sai na shige, dan ki gane ba karamin kewar ki nake yi ba, har yau din nan 'kwarar Farida nake yi domin idan ina tarawa da ita bana samun nutsuwa, sai na ayyano ke ce a 'kasana amma kina fa'din wai ban miki komai ba sai zalinci". Kuka sosai Sa'adah ta fashe masa maimakon ta ji da'din kalamansa, ai sai ta ji tamkar cin fuskarta yake yi, yanzu ya murde mata baki Dan ta yi jam'u ta ce wasu samarin alhalin yasan shi ka'dai ta cirewa samartaka. Amma shi yana fa'da mata yana tarawa da wata kansa tsaye. A cikin kukan ta ce " in Sha Allah Babu sauran zama a tsakanin mu, zan yi dukkan kokarina naga ban jefa kaina a uku ba, a satin nan zan fitar da wadda zan aura, ba zan iya auren ka ba Mukhtar. Ka yiwa Allah ka rabu da ni bana sonka yanzu". Cikin rashin damuwa ya ce "Ban damu da ki so ni ba, domin son da nake miki ya isa ya ri'ke auren mu, idan kuma kin kafe ba zaki yarda mu yi auren ba, shikenan amma ki sani ban yi al'kawarin zan iya cigaba da jarumtar kawar da ido akan ki ba, kin sanni sarai! Billahillazi ki shirya yin jegon da babu sannu, domin kuwa ciki zan miki, ki haifarwa Innah, kafin a ankara zan sake dirka miki wani sai akaiwa Hajiyar Bichi". Gaban Sa'a ya buga da karfin gaske, mafarkin Innah ya Fa'do mata, amma sai ta waske ta daure fuska ta ce "saboda kana jin isa, ko dan ka raina gidanmu?" Ya make kafada ya ce " whatever". "Dan Allah Mukhtar ka bude min kofa zan fita na gaji da jin Wannan maganganun marasa azanci da kan gado". Ya yi dariya ya ce "inace dan kin san bana son kina gatsa sunana ne yasa kike ta fa'da, to idan kin so kina iya cewa Mukhtar Kabir Bichi. Zan amsa miki amma nan gaba ka'dan Billahillazi idan akace ki fa'da ba zaki iya ba, zan fa'da miki wallahi ba zan ta bin kanki akan ki dawo gareni ba. Kina so, Ina so to karmu wahalar da juna dan wallahi kika ce zaki ja ni a kasa, ba zan yarda ba, ki rabu da Alh Mamman ban son ganin ki da shi". Da guntun hawaye ta ce "sannu ubana, to shi nake so, domin kuwa kullum zai ta ganin yarinta ta ne, dama kuma ai tsofaffin sun fi dadiin harka. Sosai ransa ya baci, a fusace ya dinga kwankwasa gilashin har Mahmoud ya ankra ya iso ya ja motar har kofar gidan Suka kaita, Mahmoud Yana ta faman tsokanarta ya san ai anshirya sai maganar shan biki, duk yadda take jin nauyin 'Karfi yau haushin sa take ji dan haka har ta sauka kala bata ce masa ba. Da shigarta Sumayya ta dinga bin ba'asin kukan da take yi, bata boye mata ba, ta bata laabrin wula'kancin da Baffa ya janyo mata a wurin Mk na sawa ya kawota. Ran Sumayya ya baci sosai ta ce "ai sai dai ki dau dangana domin kuwa Baffah burinsa bai wuce ki komawa uban Jawad ba. Duk irin bacin ran da ya jefa mu, duk irin yadda ya jingine ki shekara da shekaru, yanzu kuma dan gata da rashin kishin naka, Dan ya dawo sai ka sake bashi aure?". Kwalla ta cika idon Sumayya tana ji a ranta Mk bai cancanci auren Iya ba, har ga Allah ta fi sonta da Anwar, amma ko ita ai ba karamin ba'kin cikin Mk ta hadiya ba. Amma sanin maganar mahaifin su gaba take da kowa, yasa ta hadiye maganganun a zuciyarta, sannan kuma tasan komin borin da Iyah zata yi ba wadda take so irin uban na Jawad. **** Sai bayan magariba ya isa gidansa, ya iske Farida cikin cotton din doguwar riga kirar Pakistan, kanta dauke da hular da ta dace da rigar, sai kamshi take yi, ta yi kyau sosai, amma saboda ba ita yake son gani a yanzu ba , sai yaji ba haka yake bu'katar ganin kirjinta ba, so yake ya kamo wadda zasu cika masa hannu kamar yadda dazu ya lalubo na Sa'a da nufin zai kamo bakinta. Ya zauna a kujera ta tashi ta kawo masa ruwa da lemon coke, da cake da ta yi a yammacin yau. Yana zaune ya rike kansa alamun yana cikin rashin sukuni. A hankali ta ce "halan baka jin da'di ne?" Dai-dai lokacin sai ya dinga jin muryar Sa'a na masa kuwwa tana fadin Alh Mamman take so, ai tsofaffi sun fi dadin harka. A fusace ya mike ya ce mata "A a asibiti ne a kaina ban son katsalandan wallahi". Sannan ya wuce ya haye sama. Jikin Farida ya yi mugun sanyi, ta zauna tana ambaton Allah. Ta jima tana nazarin me ya same shi, kaso mafi yawa tafi zaton Sa'adah ce ta zaunguro shi, kishi ya kamata sosai, domin ta lura duk sadda ta ganshi a burkice to ba shakka itace ta birkita mata miji. Haka ta yi ha'kuri ta kwashi abincin ta bishi da shi, abin mamaki kuma sai ya rungumeta yana fa'din ta kara hakuri da shi, Yana cikin wani irin al'amari ne da yake neman fin karfinsa Dan Allah ta kara hakuri, ta kuma yi masa uzziri. Matsananciyar sha'awar Sa'a da ya taho da ita tasa ya kasa fita sallar isha, domin akan Farida ya sauketa, sai da suka samu nutsuwa, suka yi wanka sannan suka yi jam'i tare. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *Wannan shafin Tukuici ne ga* *Amina Mukhtar Nashe* *Bisa yaddda kike kaunar labarin, ki yi yadda so da shafin, Allah ya raya zuri'a* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* 93-95. Ana idar da Sallar isha Baffa bai tsaya a shagonsa ba, saboda yadda ya ke zumudin tattauna al'amarin da Mk ya zo masa da shi a yammacin yau, dan haka kai-tsaye gida ya dawo. Sai da ya kamallah cin abincin da aka gabatar masa ya wanke hannu da baki. Ya kalli Inna ya ganta duk a takure tun safe haka ya ke ganinta sukuku. Cike da kulawa ya ce "me yake damun ki ne Salamatu?" A sanyaye ta ce "Ba komai jikin ne nake jinsa ba tsanani, amma lafiya ta kalau". Nan kuwa mafarkin da ta yi ne ya saukar mata da rashin walwala. "Allah ya rufa asiri" Baffa ya fa'da yana kallonta, ta amsa da "ameen a takaice. "Ina tafe da albishir mai dadi wadda na tabbatar zai tsananta jikin nan naki saboda tsananin karfin farin-cikin da zai saukar Miki a zuciya da ma gangar jikin ki gaba'daya". Ta gyara zama ta ce " Ai kuwa kana da Babban goro fari kal Baffan Iyah". Da murmushi ya ce "Abin da muka Dade muna addu'a da fatan ya kasance ne zai tabbata bayan mun debe kauna da samunsa". Zuciyar Innah ta sake takura amma sai ta shanye ta ce "Al'amarin ubangiji ya wuce hakan, yana zartar da komai a sadda ya nufa". "Baffa ya ce "kwarai kuwa komai nufin Allah ne, bana dai kukanmu ya kare domin ubangiji ya nufa zaman Iyah yana daf da karewa a gabanmu, dazun nan Mutari ya zo mini da wannan albishir din, tun yamman na so na fa'da miki, ganin ki wani iri yasa na ce wannan maganar mai dadice bari na bari sai mun zauna". Yana rufe baki ta fashe masa da kuka sosai fiye da wadda ta yi akan auren da Mk ya yi. Kuka sosai ta dinga yi, tana ambaton raini ne zaisa Mukhtar ya iya zuwa gabansa ya ce zai mayar da Iyah a yanzu, bayan ya gama wulakanta ta, ya gama cusa musu ba'kin ciki. Ba dan karfin imani ba da yanzu barin jikinta ba ya aiki saboda tsananin tozarcin da Muutar ya yiwa Iyah har da su, shine yanzu da aka samota da kyar zai dawo ya ce zai mayar da ita, saboda yana ganin komai ya ce maka haka zaka yi masa?" Baffa ya yi shiru yana sauraronta, wannan ne karon farko tun aurensu da ta zauna take fa'da masa magana cikin kara'di da daga murya, kullum harshenta a kasa yake dan haka ya mata uzziri domin ba dabi'arta ba ce. Ya zuba mata ido yana kallon yadda take kuka sosai tamkar yarinya karama. Ya ce "Yanzu wannan kukan na menene Salamatu?" Kai tsaye ta ce "Na ba'kin ciki ne, saboda wallahi na tsani duk abin da zai hada Iyah da Muutar, Jawad ne a tsakanin su ubangiji ya raya shi, amma ni kam na rufe babin wannan yaron mai kafirin ri'ko, da 'Kullaci da kuma rashin ragayya". "To kuma idan ubangiji bai rufe babinsa da Iyah ba fa? Ya ya zaki yi ne?" Kafin ta yi magana ya sake cewa na bashi dama ya nemi amincewarta, zan kuma ta ya shi neman yardarta". Ta kuwa sake fasa kuka tamkar wata sa'ar Iyah. Ya hassalo ya ce "lallai kin bani Babban goro fari kal Salamatu! na gode miki, amma abin da zan fa'da miki, 'daya ne, Ni ne na haifi Iyah kuma nine wakilinta, ko da shari'a ta bata damar ta zabi wadda ta aminta da shi, a matsayinta na bazawara, Nima kuma shari'ar bata ba ta bata damar yi mini kwangen biyayya ba, dan haka ba zance miki komai a yau ba, sai ta zo gidan nan a gaban ki zan tambayeta ra'ayinta. Da ra'ayin ta zaku ga matsayata". Haka tsofaffin masoyan suka kwana zuciyoyinsu ba da'di amma Inna ta ta nan kan ba'kanta tana fatan ko zaman mota kar Allah ya sake hada su bare zaman aure, shekaru bakwai yarinya na zaune, sai yanzu tana shirin tsayar da miji zai lallabo ya watsa maneman, kai Muutar ya cika tabbataccen marar kunya, kuma marar mutunci, ta tabbatar zai iya aikata abin da ta gani a mafarkinta sai dai da ikon ubangiji ba da Iyanta ba. A bangaren Sa'adah kuwa ta shanye murnar dawowar Mk, domin sai da suka zauna da Suamayyah ta sake gane ba 'karamin wauta ta yi ba da ta bari ta ji da'din dawowarsa cikin rayuwarta, domin washagari da zata fita zuwa kotu hawaye Sumayya ta dinga yi tana cewa "Iyah yanzu dai da kike da shekaru talatin da biyu ai ya kamata ace kin fahimci ba abin da mace zata ri'ke a duniya sama da martabarta da 'kimarta. Domin kyau da arziki duk suna samun tawaya, amma idan mace ta ri'ke darajarta to ko da tsufa ya yi wa kyakkawar surarta tawaye wannan 'kimarta da ta ri'ke zata bata kariya. Kar ki bari matsananciyar soyayyar da kike yiwa Mukhtar tasa ki kasa gane a yanzu kinfi bu'katar ki yi daraja a maimakon samun son zuciyar ki. Sa'adah da take jin magaganun Sumayya har cikin kanta ta dago ta kalleta, sai ta ji a yau tausayin Sumayya ne ya kamata saboda yadda take ganin rauni da wata irin fargaba a kwayar idanuwanta, tana kuma ganin wata irin soyayya da jini kawai ke samar da ita saboda tsananin karfinta da amincinta. Ta matsa ta rungumeta cikin rawar murya ta ce "Na gode Anti! Ko yau Baffah da Inna suka barmu na san Zan yi kukan rashin ganinsu ne, da kuma adduionsu gare ni, Amma ba na rashin gata ko rashin samun wani abu ba, na tabbatar ubangiji ya zaba mini ke ki zame mini Yar uwa kuma garkuwa domin ya san idan ban samu irin wannan katangar ba zuciya ta tana iya tarwatsewa adalilin jarbawar rayuwata mai zafi ce, Ina tabbatar miki Anty ke ka'dai idan na kalle ki na ga tarin kaunar da kike mini fiye da ta ya'yan cikin sai na yi ta godewa ubangiji domin gatan da ya yi mini mai girma ne". Suka dinga kuka tamkar anyi musu Rashi ne. Da kyar suka rabu Sumaayya ta bita har hanyar waje tana fa'din ki rufe dukkan kofofin da kika san Mukhtar zai gan ki, idan kuma kaddara ta sake hada ku, to ki rufe dukkan kofofin da zai ji kayyawan kalmomin bakin ki domin shi din bai cancanta ba, bai dace da ke ba, shekaru bakwai da Kika yi, ba shi kika tsaya jira ya zo ya miki alfarmar mayar da aurenku ba. kin yi wadannan shekarun ne kawai dan gina Goben ki, da samarwa kai nutsuwa. Sa'adah ta kasa bu'de baki ta yi magana domin kuka ne zai kwace mata mai karfi, saboda kalaman Sumayya tausayi su ke baata. Tana tafe tana yiwa Sumayya addu'a da dukkan ahalinta tana fatan shakuwa da soyayyar da Jawad da Khairat suke yiwa juna ta bisu har girmansu dan su sake hada zuri'arsu ta zama dunkulalliya. Tana isa kotun sai ta sake tarar da shari'ar da ta bata mamaki, mahifin Khalil hukumar ya'ki da yiwa kasa zagon kasa da ta'annati wato (E.F.C.C) ta gurfanar domin tuhumarsa da take yi da sama da fa'di da ma'kudan kudaden da ya wawure a lalitar gwamnati a laokcin da yake shugaban maaikatan gwamnati (Head of service). Ido biyu suka yi da Khali cikin jerin mutanan da suke zaune suna dakon yadda shari'ar zata kaya. Rabon da ta su yi ido da ido idan har lissafinta dai dai ne, shekaru kusan goma sha hudu, tun ranar da suka je partin kammala sakandire a Hang out, ta tuno jidalin da Mk ya yi mata a lokacin. sai dai ta ganshi a hoto, sosai ya girma ya zama zabgegen saurayi na kece raini. Wani irin abu ya dinga ta so musu dukkansu. Da sauri Sa'a ta wuce gaba inda tawagar lauyoyi suke zaune. Shi kuma ya bita da kallo yana fata iri iri akanta ya kasa daurewa a fili ya ce "Ba zai zama illah dan na auri age mate dina ba, domin har yau din nan da yake da yanmata daban daban yana jin son Gogel din sa, yana tuno moment dinsu kafin kutsen Mk Bichi cikin soyayyar su mai cike da kuruciya da Sanya nisha'di. Sosai ta yi masa kyau, tafi Halima da ta ke budurwa komai da komai, domin ko a jiya sun hadu tunda basu da nisa . Hula da rigar lauyoyin nan ba karamin kyau da kwarjini suka kara mata ba, ga wani siririn farin glass a Idonta , kamshin ta na turaran Escada sentiment da ya santa da shi tun cikin kuruciya wadda a lokacin na Sumayya take daukowa bata san ma mai daraja bane, yauma kamshin ya shaka, tabbacin har yau da shi take tu'amalli. A yanzu mahaifin Khalil Sanata ne mai ci, Dan haka yan adawa suka dinga rubuce rubuce akansa har sai da suka ja hankalin hukimar E.F.C.C ta damke shi, wata biyu ana ta dauki ba da'di tunda shi ya kafe ya'ki daukar lauya, ya kuma hana a daukar masa, da yake yana da kyakkawan alaka da gwamnatin jahar Kano sai ta bashi lauyoyi har guda biyar dan su tsaya masa, tunda mai girma gwamna da kansa ya gamsu Hon Ibrahim Hassan bai ci wannan kudaden da ake ambatonsu ba. Manyan kwarrarun lauyoyi har guda uku masu mukamin (S.A.N.) sai guda biyu 'kananu amma hazi'kai, Bar Sa'adatu Bashir Gogel da Bar Mustafa Isa Gwaram. Kotu ta 'dage sauraren shari'ar Alh Ibrahim Hassan zuwa 28/6 a shekarar da muke ciki, wattanni biyu masu zuwa. Duk da adalilin Khalil ta rasa aurenta ta kudiri aniyar tsayawa mahaifinsa da dukkan iyawarta ko dan ta nunawa Khalil martanin kaunar da ya da'de yana yi mata da tarin hidimar da ya mata a rayuwa, ta tuno sadda suke FGC Kano ku'din break din Khalil akanta yake karewa, ta sake tuno sadda zai kwaso abaya da lace tsadaddu da mahaifiyarsa take siyarwa ya kawo mata. Har gate ta bisu ta gaisa da iyayensa tana jaddada musu su kwantar da hankalin su zasu yi aiki tukuru har komai ya zama tarihi. Suka yi musayen lamba da Khalil. A gajiye ta isa gidan Sumayya, amma haka ta yi wanka ta Fara shirin tarbar Anwar da zai kawo mata ziyara. Anwar bashi da mace amma ba saurayi bane, ya yi aure wata sha'daya da auren matar ta zo haihuwa ta rasu ta bar yaro yana hannun kakarsa wadda ta haifi marigayiya. Shekaru hudu kenan, tun akanta kuma bai sake kula kowacce mace ba, sai SA'ADAH da yake sonta sosai, duk da dai har yanzu bai samu cikakken hadin kai daga gareta ba, amma dai yana ganin cigaba. Anwar Ma'aikacine a ma'aikatar zabe(INEC). *Bayan wata Daya* Zuwa wannan lokacin Mk ya kasa gane manufar Sa'adah domin tun ranar da Baffah ya sa ya kaita gidan, Sumayya bai sake ganinta ba, a rana yana kiran layinta kamar sau biyar amma bata 'dagawa wani lokacin ma zai kira ya ji tana waya, amma da za'a jima ya sake kiran sai dai ta gama ringing ta katse, tun baya jin damuwa sosai har ya fara ji har cikin ransa. Ranar Talata yana zaune a bakin shagonsa kawai ya hango wata dalleliyar mota ba zato yaga Iyah ta fito sanye cikin shigar lauyoyi, kyau iya kyau ta yi daga nesa ya hangota amma ba karamin kwarjini ta yi masa ba. Bai gama hasashen da wa suke tafe ba, kawai sai ya ganin wani matashin namiji y fito cikin fararen kaya kal, ba shi da gajarta amma sa Mk zai jera da shi sai aga gajartar tasa tunda Mk dogone mai cikakken jiki. Ganin da ya yi matashin yana nuku nukun shiga gidan sai ya gane bazawarinta ne, domin sai da ta Fara shigewa sannan ya bita a baya, Mk bai san ya akayi ba sai ganin sa ya yi, ya tsallako titi yana leka gidan su Iyah, Bai gansu a zaure ba, kenan ciki suka shiga wani irin azabben kishi ya mamaye masa kalbinsa, ya matsa ya zauna a shagon faci na jikin gidansu, jikinsa ya dinga shaking wato har fa'da masa ta yi tana son namiji cikin fararen kaya? Shiyasa ya mata kwalliya da su. Duk addu'ar da ta zo bakinsa sai ya yi amma baya iya yinta cikakkiya, Karin tashin hankalinsa da Baffa ba ya nan yana Gogel, tunda daminace, shiyasa garin yake da dan sanyi, amma Mk sai zufa yake yi. Mintina goma ya ji fitowarsu ya yi maza ya juya gefe daya, yana kallon kyakkawan matashin da ba zai nuna masa komai ba sai tsayi da shekaru, a kiyasin Mk zai iya bawa Anwar shekaru talatin da bakwai, shikuwa shekaransu arbain har da biyu kawai dan yana yawan motsa jiki ne ake ganinsa tamkar Yana cikin early 30th ne. Ba bata lokaci Anwar ya ja motarsa ya tafi, Mk ya na zaune yana jin tamkar ya bi wannan matashi ya masa dukan kawo wuka, Sai ya ga wani saurayi da ba zai wuce sa'an Ahamad ba, ya zo akan mashin. Ya kafe mashin din ya fito da wayarsa Jim kadan ya Kara a kunne, ya ce "na iso". Ba jimawa ya ga Sa'adah ta fito cikin dogon hijab har kasa, ta karbi ledar ta mi'ka masa kudi, kafin ta juyo Mk ya yi wuf ya mi'ke ya isa kofar zauren nasu, tana juyawa ta ganshi, zuciyarta ta buga ta rasa gane wanne irin abu ne duk sadda zata ganshi sai ta ji wannan bugun zuciyar. Kai tsaye zata shige ba tare da ta nuna ta ganshi ba, ya jah Hijabinta tare da cewa " kina nufin Baki ganni bane?" Ranta ya baci sosai ta fincike, cikin gatsali ta ce " Mukhtar bana son wula'kanci ko da nake bin maza nake Ballagazaci, ai ba cikin gidan da ubana ya samar da ni nake yinsa ba, kar kuma ta'ba ni, iskancin da nake yi ba da irin ka bane, da yara ne sa'anina wato matasa irin Ahamad dinka". Ya kai mata wani irin bahagon mari, ta yi maza ta goce ta bar shi da marin iska, a kufule ta daga ido ta zuba masa nata, ta tsorata da yaddda ta ga idonsa ya yi jawur, zuciyarta ta sake bugawa Amma duk da hakan sai da ta yi jarumtar cewa "A da ne ka dake ni ka kwana kalau Mukhtar amma a yau ina rantse maka da Allah da ka mare ni da ka ga 'kwanjina domin kuwa sai na gurfanar da kai gaban Human Right". Ya juya tamkar tafiya zai yi, sai kuwa ya juyo ya kaiwa bakinta damka ya murde da iyakacin karfinsa, yana fa'din ai tunda kin riga kin tsufa ba zai yiwu ki dinga mini kaifin harshe ba, jikin ki ne zai fa'da miki. Cikin kishi mai yawa ya ce "ki je ki kai ni court of appeal, ko kuma ki sakaye ni a gidan gyaran hali na muddin Rai karshe dai na san ba komai ya saki hakan ba sai kishin na auri first love Dina". Hawaye ya goce mata ta ce "Me zan yi wa kishin, ina abin kishin ya ke?" Ya make kafada ya ce "kin fi kowa sanin inda abin kishin ya ke? wato har kin yi ilimin da za ki kai ni Human Right ko? Ina rantse miki da Allah sai na raba ki da wannan damar". Ta yi tsaki ta ce "Bismillah". Gaba'daya ya damkota ya jijigata idonsa ya ka'da da wani irin karfi saboda yadda taga idonsa ya juye nan kuwa wani irin tsumin kishi ke huda masa zuciya. Ya ce " Ni Kika yiwa tsaki? ta yi kasa da kanta ta kasa magana saboda yadda ta razana, ta san baya son tsaki. Ganin da ya yi ta dan risina sai ya saketa ya ce "Wa ye wannan da ya kawo ki a mota? Anya Sa'adatu ba zaki bar zuciyata ta huta ba? Na fa'da miki ban son na gan ki da kowa shine kika dauko wani gajeran yaro kika zo da shi, kuma kin san zan iya ganin ku?" Nan ma shiru ta masa tana jin haushin yadda ta kasa tafiya ta barshi, zuciyarta tana bada ita da yawa. Zuciyarsa ta dinga zogi tamkar ya curo ta, ya daure ya ce "Baffah na dawowa zance a daura auren nan tun ban janye komen da zan yi da ke ba, na san dai sadaki kawai za'a ce na kawo, ko yanzu na ruga shago zan hado dubu ashirin dan baki wuce hakan ba". Hawaye ya balle mata ta ce "Dan Allah ka janye komen dan kuwa ba sonka nake yi ba, maganar ban wuce dubu ashirin ba kuma, idan ka so ka ce sadaka ce ta dace da Ni, ina ce kai kana da wadda ta cancanci kudade masu nauyi?" Ya saki murmushin da Babu nisha'di ya ce "kwarai kuwa, kin san dai fari da tsayin amaryata kadai ya isa namiji ya biya kowanne irin farashi domin irin sune na shiga gaban mota, idan kuma kana gida a maka kwalliya da gashi yala yala kana jin ka tamkar kana tare da balarabiyar Yemen". Hawaye ya balle mata, har da shesshekar kukanta, shi kuma ya dinga jin dadi, domin ya san har abada shi da Sa'a suna son juna dan haka dole su ji kishin junansu, akan dole yake yin hakan dan sai yafi samun lagonta a maimakon ya yi ta rarrashi tunda ya san bata biyuwa ta da'din rai. Kafin ya yi magana ta ce "idan ma Balarabiyar Saudiya ce ina ruwana, sai dai kuma na san banbancin jikinta da zagarniyar dabino kawai numfashi ne, ta fa'da hawaye ya na sake zuba". Jikinsa ya yi sanyi ya ce "very sorry my sweet Sa'adah". Haka kawai ya fa'da kukan ya zo mata gaba'daya ta dinga yinsa saboda yadda ta ji kishin maganganun da ya yaba mata "Yi hakuri mana tunda na bata miki Rai ki yi ha'kuri, shiga ki dauko mani abin zama, zance na zo, ai ba maganar kuka tunda dai kin san nafi son ina kamo halittu suna cika mini hannu, zangarniyar dabino ai kawai ta fashion ce". Ta goge fuskarta ta ce "da wa zaka yi zancen?". Kai tsaye ya ce "Sa'ade". Ta ce "bani da muradin ka, je ka dauwama da ta shiga mota, ni ma ubangiji ya bani rabona". Da sauri ya ce " zuciyata ta gama yarda tunda kika shafe wannan lokacin wani bai yi mini shigar sauri ba, to kuwa tabbas ni ka'dai ne zai mallake ki, ada na kudire idan na dawo na tarar kin yi aure zan nemo Safina na aureta, amma tunda kin cigaba da jirana to na fasa da Safina, dan haka ki ajiye duk wani borin da kike da nufin yi mini yanzu da sunan jana a kasa, ki adana idan an shafa fatiha sai ki ta yin su ni kuma zan ta lallashinki da allurorin kauna kala kala". Kawai sai ganin ta ya yi ta zube a kasa tana kuka sosai tana tirza kafa ya dinga kallon ta yana murmushin ashe dai har yanzu bata girma ba, zai mata komai ta shanye amma idan ya jingina kansa da wasu matan sai yaga gazawarta da rauninta, bata iya jan aji akan kishinsa, ya yi amanna ba macen da take son sa kamar Sa'adah. Da wata irin murya da sai suna cikin mayafi guda daya yake yinta ya ce " Yi shirun ki Ummu Jawad ai na fasa, kuma ma wasa nake miki ai na san karatu kika tsaya yi, ba Mukhtar kike jirah ba". Ya sake cewa duk girman laifin da kika mini ai dai bana kin daukar wayar ki, na ro'ke ki ki dinga amsa kirana, idan kuma kin ki jin rokona Ina tabbatar miki zamu je lokacin da zaki ta kira na cikin tsananin son na dauka ba kuma zan saurare ki ba Nima". Da kuka sosai ta ce ka auro har da Halima Mutari, menene hadina da kai da zan damu ne, kuma Wallahi ba zan yarda da wannan abin da kake mini ba, Baffah na dawowa Zan fada masa ya bawa 'Karfi kyautar aurena shi nake so, dan kuwa birge ni yake saboda sanin ya kamatansa". Jinsa ya yi shiru na dan lokaci ya sa ta dago ta ga idanuwan nan sun sake kadawa tamkar garwashi, wani irin tsoro ya cika zuciyar ta amma bata ce komai ba. Cikin murya ba amo ya ce "sonsa kike yi da gaske ko kuwa ramawa Kika yi dan na ce zan auri Safina? Ai bance ina sonta ba ni, akan me zaki nemi hada ni da aminina, ke dai burin ki a duniya bai wuce ki tayar mini da hankali, ki kassara zaman lafiyar zuciya ta ba ko? to Billahillazi zaki san kin fa'da min wannan mummunar kalmar wai yana birge ki. Na rantse miki U will pay for it" Ganin yadda ya fusata ya sanya ta shamace shi ta mike ta shige cikin gidan da saurin gaske tamkar gudu gudu. Sai da ta tsaya ta gyara fuskarta, tana raya yadda zuciyar ta take fatali da hudubobin Innah da Anti Sumayya akan kar ta bari ta dinga kula Mk, batavsan dalilin ba, bata iya wannan jarumtar. Ya jima a zauren kafin ya tafi, ya roki Akeel ya tuka shi zuwa gidansa domin ba zai iya tuki ba. Kwana ya yi cikin wani irin matsanancin kishi, bai yi barci ba duk juyin da zai yi Sa'a yake gani da wani namijin cikin shigar farin taufafi, sai kuma da ta ce Mahmoud na birgeta. Tabbas idan bai tashi tsaye ba, ba zai samu Sa'adah ba, domin sosai ya hango wani irin fishi mai danne soyayya duk karfinta kuwa a tare da ita. Washagari daga fitowar Mk daga masallaci ya dauki mota bai zame ko ina ba, sai gidan Alh Isa. A falonsa na waje ya tarar da shi bisa al'adar sa na zama ya gana da iyali, baya tashi sai 8 sai ya shiga ya kwanta zuwa goma sai ya tashi ya karya. Ganin da Alh yayi Mk na bu'katar yin magana da shi ya sa ya sallami iyalinshi, ya ce su basu wuri. Bayan sun sake gaisuwa. Mk ya sunkuyar da kansa kasa ya ce "Dama zuwa na yi, na fa'da maka, ina son kaje wurin Baffah ka tambayar mini auren Sa'adatu". Alh Isa ya yi shiru, yana jin wani irin bacin rai na taso masa. Mk ya sake yin kasa da kansa yana sauraronsa, amma tsawon lokaci bai ji Baban ya yi magana ba. Ya dago sai ya ga Alh yana goge hawaye a idonsa. A sanyaye Mk ya ce "lafiya kuwa Baba? Subhanllah! Ban san a cikin damuwa kake ba dana bari har ka samu nutsuwa". Sai lokacin Alh ya nisa cikin rawar murya ya ce "Takaicin yadda wannan ranar ta riske ni ne, Ni ka'dai babu mahaifinka, domin da yana da rai da bulala zansa na zane maka jiki don in tabbatar maka har yau din nan ina maka kallon yaro dan karami da bai kai yaronka Kabiru ba! na kuma ganar da kai irin isar da na yi da kai, don na lura ka manta. Amma tunda bashi da rai ai dole na yi ta ha'kuri da duk cin kashin da kuke mini tunda na san idan shine na mutu na barshi ba zai fita a cikin sha'anin ahalina ba". Hankalin Mk ya tashi, ya rasa inda zai tsoma ransa ya rarrafa jikin dattijon da girma ya sake kama shi ainun. Ya ce " Dan Allah Baba yanzu ma doke ni indai zaka huce! Ai komin girman da zanyi har gobe Ni yaro ne a gabanka dole na jira abin da zaka zartar". Hawaye ya sake zubowa Alh ya ce "Ai yanzu idan na dake ka kana iya daina zuwa wurina dan ka nuna mini abota ce kawai ta hada ni da ubanku ba jini ba, yau shekaru bakwai ina kwankwa'dar bacin ran jingine yarinyar dattijon arziki irin Malam Basiru, Ina fama da kunya da nauyinsa iri iri. Amma saboda Ubangiji ya zuba alheri mai yawa a zuciyarsa tunda nake jinyar nan da bana iya fita sosai duk juma'ah sai ya zo ya gaishe ni, ba tare da tunanin ina da halin da zan mayar masa da yarinyarsa dakin miji amma banyi ba. Ni kuma na san isane kawai ban yi ba, ka zo yin aure ka saka ni a maganar tsundum tare kuma da uban 'yar da ka saketa. Dan ya gane zan iya nemo maka sabon aure, na yarinyarsa ne ba zan gyara ba, Abin da baka sani ba na shiga lamarin aurenka ne dan kar na ji kunyar kushewa ne kawai! Sai yanzu kuma ka zo ka ce wai naje na nemar maka auranta, saboda kawai ka nuna mini amfanina a gurinka sai sadda ka so Abu akaran kanka, idan baka so ba kuwa da ni da wadda baka sani ba duk daya". Maganganun Dattijon ba karamin rikita Mk suka yi ba, ba karamin tayar masa da hankali suka yi ba. Ya kasa bude baki ya masa magana, sai ya hado kalmomi sai ya ga sun yi kadan su wakilci ba da nufin hakan ya yi ba, tsawon lokaci yana gurfane yana ta goge zufar da take yanko masa. Ya ciro wayarsa ya dinga lalubo lambar'karfi amma ya kasa saboda yadda kalaman Baba suka kassara shi, da kyar ya tsaida hankalinsa, ya samo lambar, Mahmoud! Ya na dagawa ya fara masa sababi ya dauka akan Sa'adah ne zai kira shi da sassfe, har yana cewa " Lokacin da ka rabu da ita menene ba'a fa'da maka ba akan ka yi hakuri amma baka ji ba". Murya a dusashe ya ce " Ina cikin masifa 'Karfi taimake ni ka zo ka same ni a gidan Baban Na'ibawa". A sukwane 'Karfi ya ce menene, ko jikinsa ne ya tashi?" A sanyaye sosai Mk ya ce"ka bar komai ka zo yanzu Dan Allah" sannan ya kashe wayar yana ta faman fadin innalillahi. Mintina biyar Mk ya kasa ha'kuri ya ce "Ka dubi girman Allah ka yafe mini Baba wallahi ba haka bane a Raina, amma na gamsu na yi laifi ban kyauta ba! ka mini afuwa fishin ka dafi ne. Baba abota babban al'amarine da ya wuce a kira shi da kawai, domin sai da Annabi ya jaddada mana mu ri'ke Aminan iyayen mu, mu sadar da ZUMUNTA da su domin ya nuna mana suma suna da Hakki akan mu, ina ba'kin cikin cewar da ka yi baka isa da ni ba". Alh baice komai ba, illah ajiyar zuciya alamun ya dade da abin yana cinsa a zuciya. Ya nisa ya ce "Idan ban yi hakuri ba yaya zan yi Muhammadu?" Dai-dai lokacin Mahmoud ya iso cikin tashin hankali, ya gaida Baba cikin girmamawa. Mk ya ce 'karfi laifi na yiwa Baba tsawon shekaru bakwai yake ta kallona da abin, Amma ya ce " takaicinsa daya da Baban Samira baya raye domin da a gabansa zai zane ni tamkar yadda za'a zane Jawad, shine nake so ka kawo masa dorinirka ta cikin motarka ka zane masa ni domin yanzu shi ko ya dake ni ma sai ya ji a jikinsa, tunda lafiyar lallabata ake yi, ka cire tausayi ka zane ni har sai ya ce ya isa haka". Da sauri 'Karfi ya juya mota ya dauko wata irin sharbebiyar dorina ta dukan dokinsa ce da ya mutu, shine yake ta ajiye da dorinar yana yiwa yaransa barazana da ita. Daga shigowarsa, yasa iyakacin karfinsa ya shammaci Alhaji ya zamba'dawa Mk dorinar nan, a kidime Mk ya zabura domin kuwa ba karamin kidima shi bulalar nan ta yi ba Ba dan tsananin jarumtar da ya saka a zuciyar sa ba, ba abin da zai hana ya zunduma ihun neman agaji. Alhaji ya ce "Ashha Mahmuda ai ba umarninsa zaka bi ba, ni zaka jira na baka damar yin hakan, maida bulalar ka dawo ka ji mai zance muku". 'Karfi ya fita, sai da ya ci dariyarsa mai isarsa ko banza ya rage zafin dukan da Mk ya yi wa zuciyar sa tunda amincin da ke tsakanin su ne ya haramta masa samun abin da yake so, da ya zurfafa tunani sai ya gane abotarsu ta yi karfin da zabin zuciyoyinsu ya zama iri daya. Duk da idan anbashi gida da mota akan a bashi Farida ba zai karba ba, kyan fuskarta da farinta bai zama abin burgewa a gunsa ba. Da alhini a fuskar sa ya koma falo ya gurfana a gaban Baba yana cewa "Ina rokawa Abokina afuwarka Baba, ni shaida ne akan yadda Mukhtar ya ke girmama lamarin ka". Dattijon ya miskuta ya ce " aminci na da mahaifin wannan yaron ya zarta karfin naku zumuncin domin ku da hankalin ku, kuka hadu amma ga shi nan kun zama tamkar cikinku guda! Ni kuwa tsakanin mu abota ne tun bamu wuce shekaru bakwai ba, da aka kaimu gabas almajiranci har zuwa yau din nan". Ya yi tari ya cigaba da cewa "saboda giraman abotarmu iyayen mu sai da suka zama tamkar shakikai ne duk da ba garinmu daya ba,shi daga Bichi, Ni kuma daga Wudil. A lokacin da Kabiru zai auro uwarka Rabi, mahaifina ne ya zo ya karbar masa, duk da ga kannen mahaifinsa nan hakan ya faru ne bisa amincewar mahaifin nasa da yan'uwansa. Ka san dai kaine dansa namiji na farko amma baisa sunan mahaifinsa ba, sai ya saka sunan yayana da ya fa'da a ruwa ya rasu a shekarar". Ya yi shiru yana goge hawayen da ya kasa maida su, dukkan jikin Mk da 'Karfi ya yi sanyi, da kyar 'Karfi ya ce "Sannu Baba sai a ha'kuri!" Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi fiye da ta farko ya zarce da cewa "A bayan mun yi aure har mun haife ku na samu matsala da Zuwaira na yi fishin zuciya na saketa, na yi rantsuwar na gama zama da ita. Bana mantawa dawowar mahaifinka daga Bichi ya samu labarin rabuwarmu a bakin yara, da ya juya Ashe Wudil ya tafi a yammacin, wajen karfe takwas na dare sai gashi ya dawo da ita. Washagari na tashi da azumin kaffara domin bazan iya kunyata Kabiru ba, ko na nuna masa bai isa ya yi hukunci a gidana ba. Har yau din nan ban sake tada maganar ba sai yanzu da nake baku labarin, amma kai sai ka nuna mu iyayenka bamu isa ka mana alfarmar cigaba da zaama da matarka bare kuma wannan abokin naka". Ya ja hankici ya goge fuskar sa ya ce "Har Kabiru ya kwanta dama bashi da aljihun kansa, haka nima bani da nawa, koman mu daya ne, Ina da ikon zartar da hukunci a gidansa haka nima yake da cikakken iko, shiyasa na tsorata ainun hankalina yake tashi idan na kalli al'amarin da ka yi mini, na baka umarni, ka kafe ka kasa yi mini alfarma, sai nake ganin da mahaifinka yana da rai da ka ga 'kwanjina. Amma tunda ni ka'dai na saura muku sai na biku da yadda kuke so tunda ubangiji ya nuna mini wannan zamanin da ya zama iyaye sun koma agwagi." Mk ya ce "Ka yi hakuri, ka kara hakuri Baba" Ya nisa ya ce "na ha'kura amma ka sani ni ba zan iya zuwa wajen Malam Basiru ba, bani da wannan kwarin guiwar, domin har yau din nan girmama ni yake tamkar shakikin yayansa ba kuma dan kowa yake mini hakan ba, illah dan kai domin ni ban san shi ba, sai adalilinka" Hankalin Mk ya sake tashi ya ce " Duk cikin Kano bani da wadda ya fika Baba! Idan kuwa ka ha'kura to kaine mai karba mini aure a ko ina". Alhaji ya ce " ka fadi Gaskiya! sai dai na san daddako irin na Malam Basiru da irin yadda ya girmama lamarinka zai iya tirsasa yarinyar nan ko bata so ya dawo maka da ita dan soyayyar da yake yi maka. Ni kuma na ta'ba fa'da muku kai da ita daya kuke a gurina nine alkalinku, alkalanci na gaskiya zanyi a tsakanin ku. Zan je na nemar maka aurenta kadai, idan na ji a bakin yarinyar da amincewarta zan nema maka aurenta". Da sanyin muryar ya ce "fishi take yi da ni Baba! Amma da zarar anyi auren zamu dai-dai ta, tana sona wallahi" "Ashe dai ta san ciwon kanta, domin kuwa ka yi mata laifin da duk wadda ba ya jin tsoron zuciyarka zai fa'da maka cewa "komin girman laifin da ta yi maka, hukuncin da ka dauka akanta ya yi tsauri, ya wuce makadi da rawa, ko kadan babu a ragayya cikinsa". Jikin Mk ya dinga bari sosai, shi da kansa ya san kunyar Baffah ya jita irin wadda bai yi zaton anan kusa akwai wadda ya ta'ba jin irin wannan kunyar ba. Amma ya tabbatar da ya fito ya fa'di laifin da ta yi masa na cigaba da mu'amala da tsohon saurayinta, da ba wadda zai dora masa irin wannan laifin na bai yi adalci ba, domin munin abin ya baci, ba ta da hurumin yin hakan ta kowacce fuska tunda ba muharraminta bane bata da alaka da shi ta kowacce fuska, sai tsohuwar soyayya. Amma son da yake mata ba zai bari ya fadi wannan al'amarin ba, domin da yawa wasu zasu zargeta, zasu kyamaceta, tunda idan ya ce tana tare da wani ne musabbmabbin rabuwar kowa da abin da zai raya a ransa, ba a kuma isa ace sai kowa ya yarda ba barna suke aikatawa ba, shi yasa ya zabi ya boye a ransa shi ka'dai, amma kuma dole su nisanta da juna tunda ba abin da shaidan ba zai dinga raya masa ba, zai dinga zarginta ne ko da kuwa ba hakan bane a zahiri kasancewar sa dan Adam mai rauni ba a ma'asumi ba". *UZZIRI* *Duba da muna cikin kwanakin nan masu tarin falala da albarka, sai nake ganin ya kamata mu jingine Wannan labarin dan samun damar ribatar kwanakin da ubangiji ya rantse da su, ba lallai mu riski na wata shekarar ba*. *Dan haka zamu tafi hutu sai bayan sallah idan muna cikin rayayyu zamu zo mu karasa abin da ya yi saura in sha Allah. Dafatan ubangiji ya karbi ibadunmu ya sa mu yi hidimar sallah lafiya, kar mu manta da yiwa KASARMU addu'a.* *Ubangiji ya bamu damuna mai albarka*. *Na gode muku sosai da yabawar ku kan rubutuna*. *Surayya Dahiru* ✍️✍️ Surayya Dahiru. ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®️_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai dai da satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *Barkan mu da ibada! Barkan mu da bikin farin-ciki. Ina fatan ubangiji ya karba mana kyawawan aiyukanmu, ya shafe mana kurakurai. Ina yi mana Barka da bikin Babbar sallah, ubangiji ya dawo mana da Alhazanmu lafiya, ya kuma zaunar mana da kasar mu lafiya.* *Allah ya maimata mana*. 96-97. A tunaninsa space din da ya bayar a tsakanin su, dan ya samu zuciyar sa ta nutsu ne, ta daina wasiwasi akan ta, ashe laifine tunda ba kowa ne yasan azabar da yake dandana adalilin hakan ba. A sanyaye ya ce "shikenan Baba na yarda da hukuncinka zan kuma yi biyayya akansa in sha Allah". Tari ya sarke shi sai da ya lafa masa, ya ce " duk Ranar da kuka dai-dai ta da ita ka zo ka dauke ni, ka kaini gabanta, tunda nema muke yi". Suka yi godiya sosai suka Mike bayan sun ajiye masa kudi. A mota Mk ya ce "Karfi ka ji dadi da dake Ni, duk yadda aka yi dama kana son ka samu damar da zaka dakenin shine yau da Ubangiji ya ara maka dama, ka cire tausayi ka tafka mini bulalar da sai da na ji tamkar na saki fitsari a wurin". Cikin dariya sosai 'Karfi ya ce "Ashe baka iya tsiya ba, da ka saki fitsarin ai kaga dole na yi bi'kin wurin da ka bata, dole kuma na ruga wajen Farida na karbo maka wasu kayan ai ko banza ka wahalar da ni". Mahmud da ya ga yadda bulalar ta kwanta a kafada zuwa gadon bayan Mk ta tashi sosai wani wuri har ya yi baki tabbacin ya fara fashewa jini ya kume a ciki. Ya tattaro dukkan alhini ya yaba a fuskar sa yana faman fadin "sannu Bichi ashe haka ta shige ka wlh mancewa na yi ta dukan doki ce ba bil'adama ba" Mk ya ce "idan ban yi hakuri ba na Yi Yaya da kai?" Ya nisa ya ce "Ya zan yi ne 'Karfi? da gaske yarinyar nan so take sai dukkan rauni na ya bayyana, ga dai idanuwanta cike suke da soyayyata amma bakinta sai ambaton kiyayya yake, bayan na san abin da nake gani a idonta akwai ninki ba ninki a zuciyarta, Ni kuma ba zan bata damar da zata ja ni a kasa ba, wahalar da na sha akanta bana jin nan kusa akwai namijin da ya shata, ko da na ki dawowa da ita na tabbatar na fita shiga tagayyara akan rabuwarmu! Yanzu kuma naga Shirin shayar da ni wata azabar take yi, bata daukan wayata, jiya kuma 'kaddarar zan yi gamo da ba'kin ciki ta kawo ni shago, kawai sai ganinta na yi da wani dan guntun halitta sun zo tare a motarsa, a gaban motarsa fa ba mayafi sai wannan rigar da hular lauyoyin da basu rufe kwalliyarta ba, gaban rigar bai rufe komai ba". Ya fada yana dukan sitiyari, Mahmud shima ya ji kishin yaron ya kama shi, amma ya daure ya ce "Kai ka bada kofar da zata yi hakan da ka mayar da ita tuntuni da bata zo tana sake shayar da mu wannan ba'kin cikin ba". 'Karfi ya shanye dukkan yadda zuciyarsa take bugawa ya ce "Mk tsakani fa da Allah tsananin rabo ne zaisa yarinyar nan ta saurare ka, ka yi mata zunubin da 'ya'ya mata basa yin sassauci a cikinsa, ka tsaurara kwarai da gaske. Ka yi tsam da ranka wallahi ko Baffah kawai dan zuciyar sa irin ta mutanan da Allah ya zaba ya musu alheri da ha'kuri ne. Banda hakan da tuni gaba ne a tsakanin gidanjenku, amma ko ni din nan Baffah ya na mutuntata ni adalilin ka! Barah gaf da zaka dawo ranar juma'ah ya mini waya akan idan ba damuwa na zo washagari asabar dan Allah. Na taho cikin wasi-wasin menene ya faru, ina zuwa sai ce mini ya yi Daurin aure zamu je Bichi, za'a yi auren cousin dinka, baka nan bai kamata bamu halarta ba, muje mu wakilce ka, a hanyarmu ta dawowa ya ce mini ya ji dadin tafiyar mu domin na debe masa kewar ka kwarai da gaske. Wlh da na dawo gida sai da na yi hawayen tausayin bawan Allahn nan, sonka yake irin son da babu algus, gefe daya kuma na dinga jin kunyar matakin da ka dauka akan jininsa, matu'kar da gaske son Sa'adah kake yi sai ka na'de kafar wandon jure dukkan borenta har mu samu ta zo hannu". 'Karfi ya zarce da fadin "Ka gama da ita, ka sha da ita, ba abin da zata yi maka ta huce tarin takaicin da ka cusa mata". Jikin Mk ya yi sanyi yana ayyana ina ma zai iya fitowa ya fa'di irin abin da ta yi masa da ya tabbatar an gane shi din adali ne na gaske, domin aure ba adadi ya mutu a irin wannan matsalar sannan kuma zubewar mutunci shi ya biyo baya, tunda duk macen da aka saka adalilin tana mu'amala da wani namiji komin kankatar muaamalar kuwa mutane da yawa zasu mata hukuncin babbar mu'amalar take yi. Basu zame ko ina ba sai gaban Hajiyar Bichi suka fa'da mata abin da Alh Isa ya ce. Ta yi jugum ta ce "Ashe kuwa Allah ne ya so ni domin wlh ni kaina kunya ce ta sa nake ta jan kafar zuwa gidansu Sa'a, yanzu kuwa na fasa ba zan iya ba, maganganun Babanku akan turba suke, yanzu ne kake so mu shige maka gaba alhalin a farko ka nuna musu baka da iyaye". Hankalin Mk ya yi tashin gauron zabi. A hankali ya ce " Amma Hajiya da bakin ki kika ce zaki rarrasar mana ita". Ta ce " eh na fa'da amma yanzu na gane bai kamata na shiga ba, domin a lokacin da yarinyar nan take cikin tasku ai baka yarda na yi iko irin na uwa da kai ba, ka ga kuwa bai kamata ace yanzu ita na yi mata karfa-karfa ba, tunda na san da dukkan zuciyarta tana sona tana girmama ni, ku je Mahmoud ya taya ka, zan biku da addu'ar dacewa ubangiji ya huci zuciyarta, amma ni kaina ban jin zan iya yafe irin abin da ka yi mata idan aka yi mini irinsa". Idonsa ya ka'da ya ce "wai har me na yi ne haka Hajiya? Saboda na zabi na bar abin da ta mini a zuciyata shine kuma sai aga ni na zalunceta, na san dai laifin bai wuce kawai dan na yi aure ba". Daga 'Karfi har Hajiya suka hada baki wurin cewa " Ai kuwa ya fi karfin ace kawai, kai yanzu ka barta ta auri wani mana indai kawai ne". "Bana son haka 'Karfi bana son wannan kwatancen" "A a ba da Mahmoud kake ba, da ni kake, ni kuwa ba yadda zaka yi da ni, domin ko yanzu Sa'a za ta yi wani auren da kaina zan jagorancin kaita dakin mijinta". "Dan ka ji irin ciwon da ta ji alokacin da ka tura ubanta ya nemo maka aure". Da rawar murya ya ce "Haba Hajiya! Haba mana! ni ban tura Baffa ba, kawai na fa'da masa zan yi aure, shikuma saboda yana mini kallon Ni 'da ne a gunsa ya shiga cikin harkar tsundum, amma menene laifi na anan?" Hajiya ta ce "Baka da laifi ko kadan, yanzu na gane kawai sanin ya kamatansa ne ya yi yawa. Bai kamata kuma ka ji haushi dan nima zan nuna irin nawa ya kamatan ba". Tashin hankalin da Dr 'Karfi ya lura ya fara bayyana a jikin Mk yasa shi cewa "Ha'kuri dai zaki yi Hajiya, dole a samu Babban da zai taya mu nema da rarrashi" Hajiya ta ce "To sai kuje ku laluba a wani gurin ko za'a dace, sai ku tafi Bichi ko 'Karfi ku samo ai hidimar dan dangi bata lami". Daga haka ta ce "Na sallame ku sallar walaha zan yi". Kwanaki biyar Mk ya na fama da matsanancin kishi da damuwa domin ya kasa ganin Iyah sannan idan zai kwana yana kira ba zata dauka ba, ya lura idan bata ganinsa ta fi jarumta sabanin idan idanuwansu suka sarke da na juna zuciyarta take kasa boye sonsa da yake cikinta. Har gidan Sumayya ya je amma bai Samu ganinta ba adalilin ta cewa mai gadin ya ce bata nan, tunda ta san ba su yi da Alh Mamman ko Anwar wani zai zo ba. Ranar juma'ah bayan masallaci ya samu Baffa a shagonsa a kuma ranar ya dawo daga Gogel. Da sakakkiyar fuska Baffah ya ce "Ina fatan zuwa yanzu ka shawo kan mutumiyar taka ta daina fishin kun shirya kanku?" A raunane Mk ya ce "Ai sam ta'ki saurarona Baffah, jiya har Bichi na je wurin su Baba umaru akan su zo, su bawa Baba Isa hakuri, sai kuma su zo wajenka, amma kowa ya ce shi ba zai zo mini ba, kunyar abin da na yi maka suke ji". A filin gurin Mk ya durkushe kan guiwowinsa ya ce "Ina sake bada ha'kuri Baffa! Ba zan ta'ba gajiya wajen neman afuwa da alfarmar kar ka kullace ni ba, kaddarar mu ce a hakan amma ba da gangan na yi hakan ba". Baffa ya dago ya ce" Tashi ka zauna kada ka 'bata rigar ka" Sai da ya nisa ya ce "kullum ka yi mini irin wannan rokon Mutari ina jaddada maka ba auren Iyah bane ya hadamu, ba kuma zai zama silar rabuwarmu ba! Yanzu kana tunanin har sai ka sake turo mini iyayen ka da na baka aure? Kawai wadda zai karbar maka ne zaisa na jira sai anzo tunda dai dole iyayenka da jini ya hada ku, sune a hakku akan ka, indai ba ina son na shiga al'amarin zumunci ba ne, ka kwantar da hankalinka ni sai na je na same su da kaina, a ko ina ni mai Nemo maka aure ne, ni so nake ka shawo kanta ko yaya ne, kasan tana yarinyarta ma cewa na yi ka nemi yardarta, to yanzu ma nemi yardarta ko ya ya ne idan ya so sai naga ta yadda zan bullo mata". Mk ya dinga godiaya yana cewa "Baffa gaskiya idan ba taya ni ka yi ba, ba saurarona zata yi ba". Farin-cikin Baffa ya kasa 'boyuwa saboda yanzu ya gamsu idan Iyah ta koma hannun Mutari zata yi daraja sabanin shekarun baya da ta koma din sai dai ta yi zaman hakuri da taka tsantsan. "Ya labarin Jawad kuwa?" Baffah ya tambaya. "Rana ita yau ne hutun su in Sha Allah". Murmushi sosai ya bayyana a fuskar Baffah har ransa yake jin kaunar Jawad fiye da ta su Khalifan Sumayya, wata'kila soyayyar uwarsa ce ta shafe shi. Ko da yake ai Mk ma na daban ne a wurinsa. Kamar da rada Baffa ya ce"tana cikin gidan dazun nan ta zo mini barka da zuwa, je ka ku gaisa mana". A kunyace Mk ya ce "Bata daukan 'kirana, har gidan Aunty Sumayya na je amma bata fito ba" Jeka dai yanzun! Ina hango ka shiga zaure zan mata waya ta fito kamar zata karbi sako". Mk ya rasa mai zai ce a duniya idan aka cire iyayensa biyu ba wadda yake sonsa yake karrama shi irin Baffan Sa'adah. A matu'kar kunyace ya ce "Baffah na gode sosai Ubangiji ya fini yabawa, in sha Allah komai Iyah zata mini zan yi ha'kuri da ita muddin rai, ina maka al'kawarin zan ri'ke ta fiye da ri'kon farko, ka bimu da addu'a". Da sakakkiyar murya Baffa ya ce " Bana jinka Mutari! Amma yau zan fa'da maka wani abu da ba wadda ya sani sai ni da ubangijin zuciyata. Iyah itace abu mafi soyuwa a gare ni, ban taba mallakar wani abu da ya fita a gurina ba, ko mutuwa na yi idan kana ayyana ina ma ina nan da ka mini kaza. Na ro'ke ka duk abin da ka raya a zuciyar ka zaka mini na kyautatawa to ka yiwa Iyah shi. Basu da 'dan'uwa namiji ka taimake ni ka zame mata miji kuma 'danuwa, ta wahala akan ka, ta yi kukan rashin ka, na ro'ke ka kar ka bari ta yi kukan ita ubanta talaka ne, amanarta nake baka". Hawayen tausayin Baffah ya kwacewa Mk ba tare da ya shirya ba, amma yasa dukkan karfin zuciya ya ce "Na karbi amana, na karba da dukkan zuciyata, zan taya ka sonta, zan jiyar da ita da'di, sai dai yau da gobe dole za'a samu sabani, mussaman da yake ita din Yar daru ce sosai. Wata'kila sai kana mata rubutun rage daru Baffah". Murmushi sosai ya yi "ya ce zungurar ta kake yi Mutari, amma yanzu ai ta girma ta yi hankali wani abin ba zata yi su ba! Jeka kar lokacin maghrib ya karaso baku gaisa saosai ba". Yana isa bai fi da minti biyu ba, ya fara jiwo takun dogayen takalmanta mai tsinin gaske, kamshin ta ya riga ta isowa. Kwalliyarta na cikin abubuwan da ba zata iya dainawa ba. Ta karaso cikin taku 'dai'dai tamkar wata hamshakiya sanye cikin Riga da skirt na atamfa kalar ruwan hoda da fari. Dinkin ya zauna tamkar a jikinta aka yi su. Farin mayafi ta sanya dan haka takalmin kafarta ma fari ne mai tsananin tsada, da Mk ya lura zai gane wanda Jawad ya sa shi siya dole ne, wadda fa'dan kudinsa a lissafin naira sai aga tamkar fariya ce zata sanya a zuba wannan ma'kudan kudin a siyi takalmi kafa daya. Sosai ta yi kyau domin ta zubawa fuskarta kwalliya, hakanan sabon kitsonta na shuku ya taimaka wurin kawata daurin dan kwalinta. A ransa ya dinga yabon kyaun halittarta. Ya dinga tasbihi da hamdalar yadda aka jefa soyayyarsa a zuciyar wannan halittar da take tsananin daukan hankalinsa, duk tsawon shekarun da ya shafe a duniyarsa bai ga wadda ta zarta Sa'a iya tsara kwalliya ba. Bai ga wadda take zuba ado iya ado ba tare da fita zata yi ba, ya fahimci tana samun farin ciki a cikin kwalliya, bata ta'ba bashi matsalar wai bai yabi kwalliyarta ba, yi take domin ta zame mata jinin jiki. Ta wuce shi tamkar bata ganshi ba, ta fita kofar gidan, ta shafe minti biyu a tsaye, yayin da zuciyar Mk take wani irin bugu, mayafin jikinta iyaka cinsa kafadarta wadda tunda ga kanta ta na'de shi, gata a tsaye skirt dinta ya matu'kar fito da zahirin surarta, ba namijin da zai kalleta ya tsaya a iya kallon sharia guda daya, dole sai ya sake yin kallon bawa ido hakkinsa. Mk ya dinga jin wani irin tashin hankalin yadda take tsaye a tiiti a hakan, anya akwai wadda ya saki matarsa a duniya amma yake dandana kudarsa kamarsa? Can ya juyo ta tana cewa" Baffa na dade da fitowa banga kowa ba" Ta juyo da nufin shigewa ta bar shi fuskar nan daure tamkar hadarin da ya gama tunbatsa. "Zo mana Dawisu sarkin ado, ni ne mai baki sakon ai". Ta yi kamar ba ta ji ba, ta doshi hanyar shigewa da azama ya sha gabanta, ya ce "kwanakin baya fa a gabana Baffa ya ce miki ko rago ya kawo ya kamata ya shiga rigarsa". Ta turo baki ta ce " Ai son rai ne yasa shi fa'din hakan, ya san komai yake so ina taya shi son abin ina kuma girmama shi. Amma kai Baffa ne yake sonka ya daukaka lamarinka ya girmamaka. Yayin da kai baka sonsa kana amfani da shi ne dan cikar burinka da zarar ka samu, zaka iya ture komai ka kunyata shi, ka cusa masa takaicin da yake fakar idon mutane yana goge hawayen ba'kin cikin ka". Idonta ya ciko da hawaye, ta shanye ta zarce da fadin " wannan karon wallahi har Baffan na shirya shayar da shi mamaki tunda baya kishina. Matu'kar Sharia ta damka mini zabin mijin aure a hannuna to ina tabbatar maka zan yi iyakacin yi na na dora hukuncin Sharia akan hukuncin Baffah. Ka rabu da ni, ka daina zuwa wurin ubana, kai ba 'dan-uwanmu bane, bamu da alakar komai da kai, akan me zaka zo ka dinga yi mini katsalandan a tsakanina da ubana, alhalin lokacin da ya kamata na shiga rigar uban nawa nuna mini ka yi bai isa ba, amma yanzu kana mini karfa karfar dole ka shiga rigarsa". Jikin Mk ya yi sanyi kwarai da gaske ya ce "Allah dai ya so ba daga sama na fado ba Sa'adatu, kina yawan yi mini gorin bamu hada komai ba, na yarda bamu hada komai ba, amma Jawad ya hadamu, Baffa ai kakansa ne wannan hadin ai ya wuce ace na zama bare". Ta kufulo ta ce "oh saboda Jawad kake mini wannan bibiyar, kake neman hada ni ya'ki da tsohona, to albishirinka, duk duniya uwace kawai ta san ainihin uban danta". Wannan karon bai kai hannu jikinta da niyyar duka ba, amma ya yi matu'kar kidima, wani irin tashin hankali ya bayyana a fuskarsa da jikinsa, sai ta ganshi tamkar ranar da ya saketa. Ya jingina da bango yana fa'din"Ya Hayyu ya QAYYUM bi Rahamatika astagisu". Abin mamaki tausayinsa ya shigeta soasai, amma ta daure ta hadiye shi. Ido jawur ya kalleta ya ce "Ki yiwa Allah da Ma'aiki ki fa'da mini mai zan yi ki daina jifana da irin wadannan kazaman kalaman da suke nufin tarwatsewata". Yana rufe baki ta ce "ka daina shiga tsakanina da ubana saboda kai Baffa ya mini abin da har na mutu ba zan daina takaici ba, ba zan daina zubar da hawaye ba, ba dan darajar sa ta zarta komai a gurina ba, wallahi da ba zan yafe ba domin iyakacin cin fuska anyi mini, ba kuma dan komai ba sai dan ya faranta maka". Ya tausasa murya ya ce " Fada mini abin da ya miki saboda ni, na miki al'kawarin idan na ji kina da hujja ba zan sake zuwa wajensa akan maganar ki ba, ke kawai zan tunkara, ke kuma ai sai kin amince". Murya na rawa ta ce "kasan dai ai kusan sadakata Baffah ya baka, Nima nasan haka aka kai ni ba wata hidima, amma dai naje da gadona da kayayyakin amafanin da suka fi zama Dole. Na so a mini kayan daki da lefe kamar yadda ake yi a al'ada amma na yi hakuri na bi ra'ayinsa, dan samun albarka. Bayan mun rabu na tattara komai da nake ganin kamaar lefe na ne, har da gold dina sai da ya nutse na sayi filaye da zummar idan hidimar iyayena ko aure ya zo mini a siyar ayi hidima, kawai Baffa ya je ya siyar mini ya baka kudin ka yi aure kana jin dadinka ni kuma ko na mutu ko na yi rai ko oho". Wani irin kuka ya kwace mata, fiye da wadda ta yi a ranar rabuwarsu a mota, sosai take yinsa saboda yadda abin yake dafata. Kukan da take yi ya wanke bacin ran da ta jefa shi a farko. Tausayinta ya maye gurbin takaicin maganar da ta caba masa ya ce "Tabbas ba a miki adalci ba Sa'adatu, amma ki yi hakuri, na yarda kuma Baffah ya na sona, amma ko daya cikin goman son da yake miki ban samu ba. Da ciwo sosai, da gaske kuma na taya ki jin takaici, amma bari na tuna miki wasu abubuwa, Ni dai na da'de ban ga mai sa'a irinki ba, tabbas kin ci sunan ki na Sa'a". Ya nisa ya ce da" kin san irin soyayyar da Baffah yake Miki da kin ji kunyar takaicin ya siyar da abinki ya bani na yi aure." "Da kin san yadda Jawad yake son ki, yake fatana ya girma ya yi ku'di dan ya jiyar da ke da'di, da ba abin da sai sake damun ki na dai wani abu da ku'di zai iya siyansa." "Da kin san yadda nake son ki, nake kwana nake tashi da ke, nake jin kin fi duniya da abin da yake cikinta da baki yi kishin auren Farida ba". "Bari yau na fa'da miki gaskiyar magana ba dan ki yarda ki karbi soyayyata ba, sai dan ki gamsu iyakacin gaskiyar kenan, ina da yakinin ban ta'ba yi miki karyar da ban cancanci ki 'ki gasgata ni ba". "Farida na cikin jerin matan da ubangiji ya kaddara mini zan aura. Rabuwarmu ta zama tilas Sa'adah domin itama kaddarata ce. Kin sani idan ina tare da ke wallahi duk yadda nake zage 'kwanjina akan ki, zai yi wahalar gaske na iya aure, bani da wannan 'kwarin guiwar saboda tsananin son da nake miki. To fa'da mini ta yaya zan auri Farida alhalin hakan ya zama dole, na farko mutuwa na iya kauda ke, na biyu kaddara ta rabamu, kinga da ki mutu ki barmu, ai gwara kadarar rabuwar tunda idan da rai ai da rabo". Sannan Dan Allah bai isheki daraja ba ace ke ce kika biya sadakin kishiyarki, ke kuwa ni zan biya na ki, na tabbatar abin da Jawad yake yi miki a shekarunsa ya isa ki gane ubangiji yana tare da ke". Jikinta ya yi sanyi ta san kalamansa duka ba karya, illah wadda ya ce ta fi duniya, da hakane ai da sai ya bari kaddarar ta kasheta in yaso shima ya zauna jiran wa'adinsa babu aure har ya mutu, su hadu a aljannah su sake rayuwar da babu bacin rai, amma yanzu ya gama curarta ya bari wannan makirar da take boye ainihin kalarta, ta san komai nasa, ta mallake shi, shine zai zo ya mata da'din bakin wai ta zarce duniya? kai namiji Hankaka ne tabbas. Ganin ta yi lakwas sai ya ce "kin gamsu kin yarda?" Ai kuwa tamkar wadda ya mareta har huci take yi ta ce "Wallahi ko shiga kunnuwana wai kana sona fiye da duniya bata yi ba, na dai yarda Baffah da Jawad na zarce komai a gunsu". Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya ya ce "shikenan ba sai kin yarda ba. Ko ba kya sona mu komawa aurenmu, son da nake Miki, da wadda Jawad yake miki ya isa yasa ki rayu cikin farin-ciki". Ta goge kwalla ta ce "har abada ba zan yi farin ciki a hannun ka ba, ka rufe idonka ka ce mini ina ha'intarka, ka rufe ido ka ce mini ana maka sharing dina" Muryarta ta fara rawa tabbacin tsumin bacin rai ya taso, ta nisa ta ce "ka rufe idonka ka barni ka dauki wadda kasan na tsaneta saboda munafuncinta, ta faki idon mutane ta tsokane ni, amma sai ta layance a kuma bata gaskiya. Allah ne ya rufawa al'umma asiri ba karatun lauyanci ta yi ba, dan anga kwarewa wurin bada kariya ga karya". Da 'kyar ya ce na janye kalamina, wallahi tashin hankali ne da kishinki, Amma nasan ha'inta dai babbar ha'inta ba zaki yi ba, na san ni ka'dai ne na muaamalance ki, na tabbatar da hakan har zuciyata". Wani abu mai nauyi da ya danne kirjin Sa'adah shekaru uku ya fa'da mata sai dan saura. Ta ce "to shikenan na yafe maka. Amma ka sani gaskiya ban da buri ko sha'awar auren mai mata kishi kashe ni zai yi, kawai ka barni na auri wadda zan sami nutsuwa, ka bar ni nima na dandana wani namijin kamar yadda ka ke dandana Balarabiyar Yemen". A sanyaye ya ce "Sa'a ina jiye miki tsoron kar ki zama ajalina, domin kuwa banda lafiya, duk sadda na ganki sai kin yi mini fami a akan jinyar da nake yi". Kai tsaye ta ce" Tunda bakin cikin ka bai mayar da ni gawa ba, na tabbatar kaima ba zaka zama ba". Cikin gajiyawa ya ce "Next week Jawad zasu yi hutu, gaba'daya zai yi hutunsa a gurinki". Maimakon ta ji dadi saboda ta san dan ya faranta mata ne yasa ya yanke wannan hukuncin, sai ta yi nufin gwasale shi. Ta ce "bana bu'katar ganinsa ma bare ya mini hutu, inace saboda kar ya zo na zuga shi yasa ka kai shi makarantar kwana? Saboda kana son sai ya so Farida sama da ni yasa ka hana ya kwana a gidan nan sai dai ya zo ya yini? To shima na barka maka shi ban bu'katarsa, Ni kuwa a duniya me zaka mini na huce, ka zalunce ni iyaka". Kafin ya yi magana sai ganin Innah suka yi, a ladabce Mk ya sunkuya ya gaishe ta, ta amsa babu yabo babu fallasa, daga gaisuwar bata ko tambayi Hajiyarsa ba bare matarsa, ta juya tana cewa "kin dora girki kin barshi zai kone, daga cewa zaki karbo sako?". Wannan shagulatin bangaro da Inna ta yi masa ya matu'kar dukan zuciyar sa, yana ganin rashin nasarar sa a fili, Bai ga laifinta ba ko kadan, domin ya fahimci tana kan fahimtar su Baba Isa da Hajiyar Bichi ne. Wato Baffah ne kawai hoope dinsa. Akwai gumurzu kenan dan kuwa sai inda karfinsa ya kare, yanzu ne zai yi dambar jefa alkalamin sa cikin Tawada. Domin ya ga maneman nata dukkansu basu da makusa, shine ma mai tarin kalubalen rashin samun goyan baya a wurin iyaye da Sa'adatu sa'ar Mata. Surayya Dee ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai da satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *GAISUWA GA* *HAUWA BELLO GANDI*. *MUM KHADY*. 98-99. Har sati ya zagayo Mk bai da nutsuwa, Farida kanta bata da sukuni adalilin halin da take ganin Mk a ciki, duk yadda take jin kishin Sa'adah sai take yin jarumtar boyewa. Take ta hadiye sauyin da take gani a tare da shi, gefe daya ma sai take hilatar sa da bashi labarin fa'dansu da Iyah a FGC, idan kuwa ta yi hakan sosai ta ke samun walwalarsa ya yi ta dariya, hirar kuma ta yi tsayi. Ranar dauko Jawad da wurwuri Mk ya tashi yana ta saurin tafiya, wani irin zumudin dawowarsa yake yi domin shine tsani na biyu da zai taimaka wurin shawo kan Sa'adah. Ya tuna yadda Jawad ya matsa mata ta gaishe shi ranar visiting. Ya sake tuna rokon da ya mata akan ta yarda su taho Kano tare, dalilin da ya zama sanadin da ta doke shi. Ya dinga murmushi yana jin kwarin guiwa na shigarsa. Tun jiya kuma Farida take ta faman hada masa snacks din barka da zuwa. Domin a harkar Baking ta yi zarrah, abinci wahalar sarrafawa yake yi mata amma idan ta yi za'a ci cikin dadin rai ba wai iyawa ne ko kadan bata yi ba. Amma harkar cake da su meatpie hadi da su samosa tafi karfi anan. Wannan karon har wani cake ta yi masa na mussaman, tamkar na murnar zagayowar haihuwarsa saboda girmansa da kyaunsa. An rubuta welcome to Home Dear Jawad!. Lamarin da ya farantawa Mk rai ba ka'dan ba, ya dinga gode mata, tare da yabawa. Yana futa ta zube kan kujera, tana son ta ga dame Mk ya rageta? Ta gama tunaninta ta gamsu bai rageta da komai ba, ko a harkar auratayya kuwa, anan bangaren ma ta lura yana daga mata kafa soasai saboda lalurarta, amma bu'katar sa ta zarta yadda yake mu'amalantar ta saboda rauninta da yake gani. Tsananin son Jawad da yake yi ne kawai yake dan mintsinin zuciyarta, domin ta gane son uwarsa ne ya shafe shi. Ta kuma amince ba laifi bane yin hakan, sai dai zuciya da bata da kashi, yasa take jin rashin da'din soyayyar, duk da kuma zata shaidi soyayyar Jawad bata rufewa Mk ido ya kasa tsawatar masa ba, yana iyakar kokarinsa wurin saita yaron, ko akan al'amarinta ma ba ya yi masa ta Da'di. A bangare 'daya ne, take ganin raunin Mk akan 'dan nasa, matu'kar suka fita shopping, indai ya ga ta zabi kaya to kuwa sai ya daukarwa uwarsa irin kayan sai banbancin kala, Mk kuma baya iya hana shi, ko cewa ya yi ya rage, da zarar ya bata rai shikenan zai ce ya dauka. Ta dinga jin sha'awar haihuwa na mamayarta, ta daga hannu ta ce "Na sani sarai baka manta da ni ba ya Allah! Idan ka tashi bani, ka bani mai lafiya, mai jin kai, mai kuma albarka. Ina neman tsari da wadda zai gigita zaman lafiyata da ta mutanan da suke kewaye da shi, Ina neman tsari da marar lafiyar da jinyar sa zata shagalar da ni yin ibada da yawan tuba da godiya bisa ni'imomin da ka mini marasa adadi". Hawaye ya ziraro mata ta sa tissue ta goge idanuwanta, ta sake cewa"Allah kar ka bari na kunyata, kai ka halattawa maza yin mace sama da daya, albarkacin yarda da hakan da na yi Allah kar ka bari na wulakanta akan wata da muka yi tarayya a jinsi guda". Kuka sosai ya kwace mata saboda kishin Sa'adah na neman hanata sukuni a zuciya. Ta Dade kafin ta tashi ta yi wanka, ta doro alwallah ganin takwas har da rabi sai tada sallar walaha, tana ta rokon a sau'ka'ka mata kishi, a kuma karawa Mijinta sonta da tausayinta. Ta rufe addu'ar da yiwa Mk fatan samun cikakkiyar lafiyar da zai gamsar da su, da kuma budin arziki, ta sake rokar masa ikon yin adalci, tana kuka take cewa Allah ka hana shi zaluntata, Allah ka bashi karfin zuciyar da zai yi adalci na gaskiya. *Ko mata nawane masu irin wannan dabi'ar?* *Shin kina sallar Duha kuwa?* *Idan ba kya yi maza ki fara domin Allah ya yi rantsuwa da lokacin, sannan kin yiwa gabbanki sadaka a yinin gaba'daya*. Sun iso Wudil, Mk ya ji bari ya ziyarci tsohon amininsa da suka yi F.C.E. Bichi tare. Ya laluba ba lambar wayarsa, ya dai dinga shiga hanyar ya gano gidan. Ai kuwa a kofar gidan ya tarar da shi yana alwalar sallah juma'ah. Da wata irin murna ya kar'bi Mk! Ganin lokacin sallah ne kawai sai suma suka yi alwalar suka zarce masallaci. Suna dawowa aminin nasa ya baibaye su da abinci tamkar dama yasan da zuwansu, Mk ya dinga tsokanar su da cewa wai har yanzu baka kara aure ba? Kullum uwargida na office?" Dai dai lokacin matar gidan ta dawo sanye cikin uniform tabbacin Ma'aikaciyar lafiya ce. Mk ya tasa ta gaba yana fa'din " bazai yiwu kullum kina barin aminina shi ka'dai a gida ba, dole zamu lalubo wadda zata zauna ta kula da shi. Tababa da ke mai kunyace ta fice ta bar Mk na yi musu sha'kiyancinsa da baya gajiya. Za su tafi ta kawo turare ta bawa Jawad, da wata kullin leda mai dauke da man shafawa da na zafi ta ce na Hajiyar Bichi. Mk ya tsaya cak yana fa'din" Tababa ta Malam ki ji tsoron ubangiji, ita kuma Farida ina nata sakon, gaba'daya kin saka son zuciya a lamuran ki, saboda ba kawar ki ba ce ita" Da sauri ta koma daki ta dauko kyawawan mafitai guda biyu ta ce ga shi nan, ta yi maka fifita ni bana son sarhutunka". Ya karba yana fa'din kin fanshi kanki, yayin da mijinta ya yi gaba yana fa'din ranar da za'a mata amarya ai ban san irin boren da zata yi ba, idan ka ga yadda ta yi kukan aurenka sai ka yi mamaki, ta taya Sa'adah kuka irin wannan ina kuma ace ita za'a yiwa?' Mk ya murmusa ya ce ai kuwa dai Tababa kwantar da hankalin ki, daga yadda na ga kin iya karrama ba'ko , zaki dade kina jan zarenki, muma kaddara ce ta fado mana, Ina fatan idan kuma kaddarar ta fa'do muku ba zaki yi watsi da kyawawan dabi'unki ba". Ya damkawa yarinyarta karama kudi, Yana ta godiya da karamacinsu, ya tafi ya barta da sanyin jiki tana addu'ar kasancewa ita ka'dai. Har la'asar Mk na Wudil domin tare da aminisa suka je ainihin gidan su Baba Isa ya ziyarce su, suka dinga sa masa aalbarka ya ajiye musu buhun shinkafa da katon din taliya, har da ku'di a kanin Baba Isa Wanda shine babba a gidan yanzu. Sai da suka fito ya ajiye Aminin nasa a kwanar gidansa, suka yi sallamah. Sun tsallake gadar Wudil ya samu wuri ya tsaya. Ya ce "Jawad dawo gaba kusa da ni, kana mini hira". Hakanan kuwa aka yi, sun zo dai dai Yar gaya, Jawad ya ce "Allah sarki Muhsin Yargaya! ko yana ina yanzu?" Ya dinga bashi labarin Muhsin da irin halin da yake ciki da matar Babansa. Nan Mk ya fahimci inda Jawad ya samu dalilin juyawa Farida baya, ya dinga jin tausayin yaran da suke fuskantar kalubalen rashin rayuwa tare da uwarsu. Cikin hikima ya ce "Ashe Muhsin ya fa'da maka u have to be careful with Aunty saboda kar ta raba mu?" "Eh mana Malam! Saboda na san kai baka san hakan zai iya faruwa ba". Mk ya yi murmushi ya ce "Jawad kowa da halinsa! Da zata raba mu da tuni ta yi hakan, fa'da mini ta ta'ba dukan ka lokacin da muke Uk?" Ya girgiza kai alamun a a, Mk ya zarce da fadin "abinci ne bata baka ko?" Da sauri Jawad ya ce "Ah Malam tana ba ni, every day sai ta cika mini lunch box dina, abincina ya fi na kowa yawa, kullum sai na dawo da shi". "Ka ga kenan ba halin su daya da Waccan da abokinka yake baka labarinta ba". "Amma Malam ai ita kake so ba Mami ba". Jikin Mk ya yi mugun sanyi a shekaru sha uku Jawad ya yi wannan maganar? Al'amarin yaran yau idan kana daukar maganar su tabbas zasu raba tsakanin ka da jama'a ne, ka yi ta ganin tamkar kitsa musu magana ake yi. Ko kuma ana koya musu iyashege ne alhalin kuma abin a jikinsu yake, sai dai ayi ta nuna musu kyakkawar turba cikin azanci da nasiha. Mk ya nisa ya ce "wa ya fa'da maka bana son Mami? Ita ce fa ta haifa mini kai! Kasan kuma u are my only son, dole kuwa ta zamo very precious to me". Da'di ya kama Jawad ya ce " To yaushe zata dawo gidan mu, tunda we are Muslims, polygamy is allowed, above all ma ka mini al'kawarin zan dawo hutu na ganta a gidanmu ba a gidan Baffah ba". "Eh na yi maka ban kuma manta ba. Amma matsalar itace bata mini magana, bata gaishe ni, har Baffa yana mata fa'da amma still bata ji ba". "Ni zan fa'da mata ta daina yin haka tunda kullum sai ta ce mini arogance ba kyau, ba dabi'ar mutanan kwarai bane". " Yauwa sannan ka fa'da mata, kana son ganinta a gidanmu, if not jirgin nan da zaka siya mata zai zama nawa". Dariya Jawad ya dinga yi yana cewa" Malam ka damu da jirgin nan, amma ai yanzu na ce har da kai zaka shiga. Ni ban san me yasa ta daina son dawowa ba, bana manta sadda take kukan so take ka zo ka dauke ta mu koma gidanmu" Jikin Mk ya yi sanyi ya ce "tafiyar da muka yi, muka barta ne, amma idan zan sake komawa da ita zan tafi, kai kuma ka zauna tare da Anti a anan". "A a Malam gaskiya ba a yin haka, da ni za'a tafi" " To na yarda da kai zamu tafi, yanzu idan ka je gurinta sai ka yi ta bata hakuri ta dawo ta zauna da mu". Murna tamkar Jawad ya zuba ruwa a kasa ya sha, wani irin farin-ciki ya bayyana a dukkan jikinsa Sun iso kano Mk ya kalli Jawad cikin uniform dinsa sai ya dinga tuno shima lokacin da yake makarantar su ta 'Karaye. Haka yake tamkar Jawad, sai dai da alamu Jawad yana iya zarta shi tsayi domin a yanzu ma ya kusa kamo shi. Tsayin Jawad da saurin da karatunsa ya yi sai ake ganin tamkar ya zarce shekarunsa. Da tarin kauna ya ce " A ina kake son yin hutunka?" Kai Jawad ya sunkuyar ya ce "gidan Hajiya". Mk ya ce "Antinka fa tana can ta shirya maka something special". "Zan je amma ni gidan Hajiya zan zauna". "Me yasa to ba zaka je unguwa uku ba?" Ya marairaice tare da cewa " Na san idan na ce can zani ba zaka yarda ba". Da sauri Mk ya ce na yarda Jawad! Ka yi hutunka duka acan idan kana so". Jawad ya kalle shi da mamaki! ya ga seriousness a fuskar Baban nasa ya kasa gasggatawa ya ce " please Malam are you serious, are u sure?" Da sauri Mk ya kada kai ya ce very sure Babana! Yanzu zamu je gida kaa ci abin da Anti ta shirya maka, daga nan sai mu zo ka gaida Hajiya, sai mu koma ka kwana tare da mu, tomorrow morning da kaina zan kaika gidan Baffah ko gidan Anty Sumayya ko ina kake so nan zaka je". Ya dinga murmushi irin murmushin Sa'adah, wurshiryar da ya samu daga gareta ya sake kawata murmushin nasa". Da farin ciki sosai Mk ya ce "kyaun ka na bayyana idan kana smiling my boy". Jawad ya sa hannunsa ya rufe fuskarsa wai shi kunya. Da murna sosai Farida ta karbi Jawad ta dinga ina ka saka da shi, karshe ya shige dakinsa da komai na ciki blue ne, irin kayan alatun da aka shirya masa duk dan a hilace shi ya daina gudun gidan basu yi tasiri ba. Wanka ya yi, ya shirya ya fito ya tarar da kayayyakin da aka tanada dan shi kala kala. Farida ta dinga rawar jikin kyautata masa adalilin taga sassauci a tare da shi fiye da wattannin baya da ko kallon inda take ba kaunar ya yi. Ta ji farin-cikin sauyin da ta gani a tare da yaron. Sai yamma lis suka fice da Babansa. Basu dawo gidan ba sai dare sosai domin har sai da Jawad ya yi barci a dakin Hajiya. Da ya zo yana tashinsa Hajiya ta ce "Barshi mana tunda ya yi barci". Da sauri ya ce " A a Hajiya bari kawai mu tafi lalla'ba shi nake yi ya daina gudun Farida, ta dora hankalinta akansa, amma yana gudunta tamkar kunama, yau dai na ga ya fara saukowa, gobe zan kai shi wurin uwarsa dan hankalinsa ya kwanta". Hajiya ta ce "dan hankalinsa ya kwanta, ko dan ka samu dalilin ganin uwarsa babu hijabi?" Mk ya ce "haba Hajiya" "Haba Hajiya ko dai haba gaskiya?" Washagari kuwa ya kai shi gidan da tarin tsaraba Niki niki tamkar wadda zai shekara, har da cake dinsa na murnar dawowar sa gida, bai ci ba, Mk ya ce ya taho da abinsa. har cikin gidan Mk ya shiga ya tarar da Innah na yin wainar shinkafa irin ta garin su Shafa'atun Bauchi ko da yake itama Innar ai daga Gamawa take kenan Inna Yar Bauchi ce. Sa'a na kicin na hada miyar cin masar. Ya dinga tuno yadda Sa'adah take yi masa waina da miyar ganye da yake santi, haka nan ya yi kewar dambunta, ya yi kewar farfesu mai daddawa, ya yi kewar kunun danyar gyada da shinkafa, da alkubus. Traditional dishes da ya yi kewar su ba za su lissafu ba, hatta shinkafa da wake har yau bai sake cin mai gardin ta Sa'adah ba. Haka nan kwa'don zogale da Rama. Yana matu'kar jinjinawa Inna yadda ta horar da Sa'adah nau'in abinci kala, kala masu dan karen 'dan'dano da kashe kowacce irin yunwa, ga kara lafiya. Sa'a tana jinsu ta rakube, ko kwakkwaran motsi ta ki yi dan kar a hangota. Baffa ya fito yana marabatarsu, yayin da hankalin uba da 'da ya karkata a son ganin Iyah. Lura da hakan da Baffah ya yi yasa ya kirata, ta fito sanye da doguwar riga ta atamfa, dinkin free ne amma ya matu'kar yin kyau. Da sauri Jawad ya ruga ya rungumeta yana fa'din "Daure ki gwada daga ni sama Mami". Baffah ya yi saurin cewa "wannan shine gangan Jawad, a gabana ka ke son ka kayar mini da uwa?" Mk ya murmusa ba tare da ya ce komai ba, bagarar da shi da Inna ta tsiri yi masa na matu'kar damunsa. Duk yadda Inna take jin haushin Mk bai hana ta zuba masa waina ba, ta zuba masa masar a ledar ta sake kara wata ledar, ta mike ta dauko flask ta shiga kicin ta zubo miya, ta kawo ta ajiye masa a gabansa, a hankali ta ce ga waina, ta koma ta cigaba da aikinta. Baffah kuwa fa'di yake "wannan tafiya zai yi da shi zubo masa wadda zai ci yanzu" Da sauri Mk ya ce "Na riga da na karya, na gode, a ransa kuma fa'di yake yaushe zan iya cin abinci a gaban ku?" Idon Baffa ya sa Sa'adah cewa Mk "Ina kwana". Ya amsa da sauri, cike da walwala. Ta shige dakinta Jawad ya bita, ya kwanta a shimfidarta, yana cewa "I miss your scent, I missed everything about you my Iyah". Ta ce "Ashe ban hanaka fa'dar Iyan nan ba?" Ya turo baki irin yadda ta ke yi ya ce "Iyah means mother, means uwa, Mami da Iyah all the same". Ta ce "To dai ban son sunan a bakinka barwa Baffa da Innah kawai". Mk suka fita tare da Baffah! Jawad ya fito da sauri ya bisu, daga kofar gida Baffa ya wuce inda za shi, yayin da su kuma suka tsallaka zuwa shagon Mk . Jawad ya yi mamakin yadda aka sake kawata shagon, komai na wurin na zamani ne, ya zauna yana cewa " Azo a wanke mini kafata". Harara Mk ya galla masa ya ce " Saminu ba ya nan, ina fatan ba Uncle Akil kake nufi ya wanke maka kafar ba?". Jawad ya yi shiru! Yayin da Mk ya zarce da fa'din, kullum ana idar da Sallar la'asar ka tabbatar ka zo nan kana koyon aiki, zan fa'dawa Akil duk ranar da baka zo ba, ya yi dealing dinka well well, kasan dai shi no nonsense ne baya wasa da yara, ba kamar Uncle Abbas bane da yake yi muku yadda kuke so". Jawad ya nisa ya ce"Malam ni bazan iya yiwa mutum aski ko wanke kafa ba, zan bata jikina ne kawai". Mk ya zuba masa ido yana kare masa kallo, a zahiri dai yaron kamarsa ya yi, amma dabi'unsa sak na uwarsa ne, gayu da pride dinsa na Sa'adah ne. Ya daure fuska sosai ya ce "Jawad ai baka kai a baka yin aski ko wankin kafa bama tukun, share wurin zaka dinga yi, kana wanke towels din da aka yi amfani da su, sannan ka dinga ganin yadda ake gudanar da aikin". Ya shagwabe fuska ya ce"Haba mana Malam a shagonka zan dinga irin wannan wahalar?" Mamaki ya kama Mk amma da yake yasan a iya shekarun Jawad da iya tunaninsa shi hakan abin kunya ne, a gurinsa. Sai ya sassauta ya ce, "Jawad Ni dai a tarihin Nigeria ban taba ganin wadda ya yi karatu mai zurfi ya mallaki jirgin sama ba, Amma na san yan kasuwa da suka fara da kananun business, a hankali business din y tunbatsa har suka sayi jirgin sama. Na san kai kuma burinka ka samu damar siyan jirgi, fa'da mini idan ba ka koyi business ba, how ur dreams will be reality one day?" "To zan dinga zuwa, amma plz Malam! tell Uncle Akil to be gentle, I really dislike his hershness" Mk ya sake daure fuska sosai ya kafe shi da Ido, har sai da Jawad ya dinga jin wani irin abu na ratsa shi, ya sunkuyar da idonsa kasa ya ce " very sorry Malam". Mk ya nisa ya ce "Akil din ka ke fa'din haka akansa? Kanina, kanina Jawad? ashe kuwa nima na shirya, domin Ni da shi ai daya ne a gunka! Ko Ahamad da yake karamin mu ban za ci zaka iya fa'dar wani abu da bai maka a tare da shi ba". Ya ru'ko hannun Mk ya ce "ba zan sake ba Malam! Plz forgive and forgot". Ya na fada yana leka waje, yana fatan Akil din bai iso ya ji me ya ce ba". Mk ya ce daina ma wani lekawa dan kuwa zan fada masa. Nan da nan kuwa ya fara kuka yana fa'din sorry Malam, ya tsorata sosai, domin Akil mala'ikan Yara ne, baya musu ta Dadi shine discipline master a family din nasu. "Ok stop crying! Ba zan fa'da ba, amma idan ka sake, ko idan ka zo ka ga baya shago ka ce zaka dinga yiwa su Saminu rudeness to ka tabbatar zai ji komai". Ya goge fuskar sa yana fa'din " Thank you! Komai suka ce na yi, yi kawai zan yi". Mk ya ru'ko shi yana fa'din "good boy! Sannan islamiyar nan ta safe zaka dinga zuwa. 9 ake faraawa, a tashi 1pm. *A samarwa Yara lokacin da zasu dinga zuwa wurin koyon sana'a domin hakan zaisa su taso da burin tsayuwa akan kafafuwansu, zai rage musu burin su kammala digirin farko su zauna zaman jiran gwamnati ta basu abin yi, lokaci ya yi da zamu daina yaudarar kanmu cewa gwamnati zata iya WADATAR da kowa*. Haka kwanaki suka dinga shudewa, har shari'ar mahaifin Khalil ta zagayo, aka yi ta cakudawa bisa taimakon lauyoyinsa mussaman Sa'adah suka samu kotu ta bada belinsa, bayan sun kawo wadda kotu ta bu'kata a matsayin sharudda. Kotu ta sake zabar ranar 28/08 a matsayin ranar yanke hukunci na karshe. Wannan shari'a ta matu'kar Jan hankalin yan siya domin gaba'daya al'amarin siyasa ne, belin da ya samu ya matu'kar daga darajar lauyoyinsa mussaman Sa'adah da ta kasance mace tilo, duka shafin jaridun kasar nan shafin farko sai ka tsinci hoton Sanata Ibrahim Hassan da lauyoyinsa. Mk da ya tsinci hoton Sa'adah a tsakanin manyan lauyoyi gefe kuma ga mahaifin Khalil sai ya ji tamkar ya shide dan tsananin takaici. Ya sani tabbas burinta ne tun tana secondary ta zama lauya, shiyasa a lokacin da zai samo mata gurbin karatu ya yi iyakacin kokarinsa ta samu fannin shari'a, Dan ta sami sau'kin halin da take ciki a wanccan lokacin. Sai gashi duk irin fa'di tashin da yayi akan karatun nata, ashe a mahaifin wannan Dan isakan yaron da ya tsana, zai fara yi wa rana? Ya sake zubawa hoton idon suna kallon juna ita da Bar. Mustapha, da ya kasance saurayi, wani irin al'amari mai nauyi ya danne masa zuciya, idan ba Sa'a ba kishin Sa'adah ne sanadin mutuwar sa domin zuciyar sa zata iya bugawa. A fili ya dinga ambaton "wallahi ba zan iya ba, ba zan jure ba, dole ki ajiye aikin nan, inko ba haka ba rana daya za'a tarar na zama gawa". Karfin addua ne kawai ya daidaita Mk. A yammacin ranar ya shirya ya nufi gidansu yana jin yau kam dole sai ya ganta. Yana zuwa ya tarar da wani bacin ran domin tarar da ita ya yi tana zance da Anwar da ta ganshi kuma ko dar bata ji ba, bare ta sallami bakon ta saurare shi. A sanyaye ya juya ya tafi, cikin sanyin jiki. Hankalin Mk ya yi matu'kar tashi domin ya fara gasgata Sa'a cewa da gaske take zata dora ikon da Sharia ta bata akan ikon Baffa. Ya kasa jurewa, washagari da yamma ya bita gidan Sumayya, da kyar ta saurare shi adalilin Idris din Sumayya na gidan ya masa masauki a katafaren falonsa na kasa. Sumayya tana ta fishin akan me zai saurare shi, bayan ya san duk irin ba'kin cikin da suka sha adalilin sa. Haka dai ya lallaba su tare da fa'din ai mahaifin Jawad ne, dole kuwa ayi taka tsantsan. A rikice Mk yake fa'din "ya kike so na yi miki ne Sa'adatu? Ke fa kika mini laifi, ke kika zalunce ni, yanzu na samu, na farfado daga gashin Kumar da kika mini, shine kike son sai kin Kai ni kasa, wai me na miki ne da ban cancanci na sami nutsuwa da ke ba?". Ya nuna kansa da yatsa ni kike cewa ba Kya so? A akan idona kike hira da wani namijin, kika wulakantani a gabansa? Ashe ba ni da wata alfarma a gurinki komin kankatarta, sai na fa'di na mutu ko sai na hadu da mummunar jinya sannan zaki gane ina son ki?" "Ki na fadawa mutane ba Kya so na ko?" Ya fa'da da wata irin murya mai nuna sarewa kwarai da gaske. Ya mike shikenan Sa'adatu, shikenan, na yafe miki komai, ko na mutu ma, na yafe miki". Ya tafi ko waiwaye bai yi ba. Kwana ta yi tana jin fargabar ko ya tafi kenan? Washagari Jawad ya biyota gidan Sumayya ya tarar da ita a compound din gidan tsaye da Alh Mamman da alamu rako shi ta yi zai tafi. Wani iri Jawad ya ji, ya zo zai wuce su, ba tare da ya musu magana ba. Alh Mamman ya ce" zo mana tare da yafito shi. Jawad akan dole ya karasa ya ce "ina yini a tsaye kerere, sannan fuskar nan a hade tamkar bai san murmushi ba, bare dariya. Alh ya ce " da gani wannan shine 'Dan nawa ga shi nan sak Babansa". Ya zura hannu ya dauko bandir din Yan dari biyu sabbi ya mikawa Jawad yana fa'din ka sha Ice-cream". Jawad ya sake daure fuska fiye da dazu "Ya ce Babana zai mini fa'da ka ajiye' ka bawa masu bara". Ya juya ya bar Alh Mamman da kudi sororo yayin da kunyar duniya ta kama Sa'adah, ta kasa cewa komai, mussaman yadda take bashi labarin hankalin Jawad da yadda yake sonta yake tausayin ta. Haka Suka rabu ita a kunyace, shi Kuma jikinsa a sanyaye na mamakin iskancin karamin yaro irin wannan wato ya san kishin uban sa? Sai da ta bari sun kwanta ta dinga yiwa Jawad nasiha da nuna masa rashin tarbiyar da ya yi ka iya ta'ba cigabaansa. Ya amsa da ya daina. Bayan kwana biyu ta je kotu Anwar ya dawo da ita. Jawad na compound din suna ball da su Ayman da Anis har ma da Khairat, suka ga shigowar motar Su Sa'adah. Dukkansu yaran suka ruga wajen Yi mata oyoyo tare da gaida Uncle Anwar, soasai suke sonsa saboda yadda yake ciko musu leda da kayan ciye ciye. Jawad ne kawai bai doshi inda suke ba sai kawai ya ja ya tsaya ya rungume hannunsa a kirjinsa. Sa'a ta yafito shi da hannu, ya karaso ya tsaya bai ko kalli inda Anwar yake ba. Ta ce Jawad ga Uncle kullum na tambayar ka". Ya sake dauke kai ya ce "na ganshi sannunsa". Ba'kin ciki tamkar ta hadiye zuciya. Ta ce "ba zaka gaishe shi ba?" Ba kunya ko shakka ya ce "Ai ba ubana bane" a hankali, sai dai dukkansu sun ji shi. Ya juya ya barsu. Anwar da ransa ya baci sosai, dole ya mata sallama ya tafi. Ta shiga gidan a fusace tana neman Jawad tana jin tamkar zuciyar ta ta Fado dan tsananin bacin rai. Ta nemi shi ta rasa amma ta kudiri aniyar yau sai ta masa dukan kawo wuka, gobe idan akace ya sake wulakanta ba'kinta zai ji shakka. Ta rasa irin wannan rashin tarbiyar da ya tsira a yan kwanakin nan. Shikuma yana can ya buya a boys quarters. Sai yamma lis ya fito, ai kuwa ta hango shi ta windo ta dauki wayar wuta ta fita domin ta san bata isa dukansa a gaban Sumayya ba, cewa zata yi rainata ta yi shiyasa zata doke shi akan idonta. Cikin Sa'a Jawad ya ankara da yadda ta tunkare shi a fusace, ai kuwa ya kwasa ya yi gate a guje, ba'kin ciki yasa ta bishi itama. Suna fita suka yi kicibus da Mk a waje zuwan sa kenan parking ya gama yi. Ai kuwa ya ruga ya buya bayan Babansa. Mk ya ri'ke shi yana fa'din "menene?" Ya kalli Sa'adah da take hawayen takaici, tana rantsuwar sai ta dake shi. Jawad ya ce " yau zan bika mu tafi Malam kar bar ni anan duka na zata yi" Mk ya daure fuska ya ce " me ka yi mata?" Jawad ya turo baki gaba irin na gado ya ce " wani gajeran mutum ta ce na gaisar shine na ce ai ba uba na bane. Shikenan zata doke ni, Ni kuma bana sonsa ne, haushi yake bani, I hate him so much". Ya fa'da da karfi tare da buga kafa. "Kar ka bari ta doke ni Malam domin ni sonsa ne bana yi, ba laifi na yi mata ba". Surayya Dahiru. ✍️✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai dai da satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 100_101. Cikin mintina kadan Mk ya fahimci dalilin wannan takaddamar tsakanin Jawad da uwar da yake mata wani irin so marar misaltuwa. Kishin Babansa da yake yi ne sanadin da zai iya yin fito na fito da ita. Da'di ya yi matu'kar kama Mk ashe dai soasai Jawad ke sonsa, ba uwarsa yake so ba kawai, ya lura bai son kowa ya ratsa tsakanin su, ya fi son ya gansu a tare muddin rai. Ya ja numfashi ya kalli Sa'adah da idonta ya kuje dan tsananin bacin rai, ya yi jah tabbacin ba yanzu kawai ta yi kukan ba. Cikin rarrashi ya ce "Wai sai yaushe zaki girma ne? Yau kuma a koke koken na ki har Jawad zaki yiwa?" Da kuka sosai ta ce "Ai kaine ka ke hure masa kunne ka ke so ya raina Ni. Dama na san da biyu ka tattaro mini shi, to burinka ya cika. Sai dai duk abin da ya mini har zuciyata ta baci, na yafe masa, in Sha Allah ba abin da zai same shi, amma tabbas sai na zane shi, domin ai wannan ba tarbiyar kwarai ya dauka ba, ya dinga yiwa manya rashin mutunci". Kafin Mk ya yi magana Jawad dake ri'ke da Babansa ya ce "Ni bana raina manya, ba haka kawai na ki gaishe shi ba, sonsa ne bana yi, bakon jiya da na ga mai farin gemu ne ai na gaishe shi saboda ana yawan fa'da mana mu girmama tsofaffi masu farin gashi". Sa'a ta kai masa wawura amma ya zille, da taimkon Mk. Mk ya shanye dukkan dariyarsa ya ce yanzu a gabana sai ki doke shi? Kin san dai bana so ko?". Cike da shagwabar da ba ta yi zaton zata sake yiwa Mk ba ta ce " Billahillazi sai na doke shi, zaman ka lafiya ka miko mini shi". Ta fa'da cikin dire 'kafa da goge hawayen idonta. Ta sake cewa "Baka son na dake shi. Amma ka 'ki yi masa fa'da". Ya ce "cool down Ummu Jawad"! Ta katse shi da cewa "kar ka kuma ambata mini wannan sunan, ka 'Kira wadda take maka alkunya da shi". Ya ce "To Na ji". Amma abin da nake so da ke, ki yi hakuri, yaro ne ai, tunda dai kin rantse, to zan kubutar da ke daga yin kaffara, zaki doke shi, amma ba da wannan wayar ba". "Ni kuwa da ita zan dake shi" ta fada da sauri. Mk Yana so ya ce to shi ta dake shi da ita, Yana jin tsoron kar ta zabga masa ta rashin tausayi tamkar ta 'KARFI. Ya ce "A a Sa'adah kin so ki yi rikici ne kawai, yaushe zaki dake shi da wannan uwar wayar da alamun ta suka nuna ta A.c ce. Zo ki ga yadda za'ayi". Bata san ya akayi ba, shauki ya kwashe ta, ta isa kusa da su, domin ganin da ta yi Jawad na rungume da shi, sai ta ji tamkar ta tabbata tana ganin su a haka, sune cikon farin cikin ta, ta yarda. Mk ya rungume Jawad sosai ya ce "Dan yi masa dundu amma ba wadda ya zarta 'kwarin 'kashinsa ba, duka duka ma yaushe kika haifo mana shine?" Ai kuwa kamar sokuwa ta yar da bulalar ta yi masa dundu har uku, za ta yi na hudu ya ce " oh sorry ya isa haka nan, ni ma zan yi masa fa'da ai". Ta koma gefe tana harara tamkar idon zai fa'do. Mk ya saki Jawad da suka kankame juna tamkar zasu zama halitta guda, ya ce " shiga ciki muna zuwa". Ai kuwa ya tafi da gudu ya na dariya. Abin da ya sake kular da Sa'adah. Ya kalleta ya ce "wannan ka'dai ya isa ki gane shima yana dandanar azabar da nake sha idan na ganki da wani". Ta tabe baki ta ce "Allah ya bawa wadanda aka 'ki su, ake zaune da makiyansu ha'kuri". Ya kasa cewa komai. Ya saki maganar da cewa "ina son azo nema mini auren ki, jiya Baffa ya ce mini wai Gogel za'a je domin Yayansa dan wan Babansa ya ce wannan karon can za'a je". Ta murmusa sosai ta ce "Ashe duk wasa ka dauki maganata? Wallahi bana fatan zaman aure ya sake hadamu, na riga da na yarda kaddarar haihuwar Jawad da kanwarsa ya sanya na yi muku kutse cikin soyayyarka da Yar mutanen Yemen". A sanyaye Mk ya ce"Amma ai na sha fa'da miki sunan kanwar Jawad Aisha ko? Tunda ta zo da ranta, ko bata zo da rai ba matu'kar yaro ya yi motsi a ciki to a sanya musu suna saboda zasu tashi da sunan su ranar Gobe, dan haka sunan Hajiya Babba ta ci, Nana Aisha ce ina fatan ta zame mana sanadin shiga aljannah babu Hisabi". Sa'a ta amsa da Amin a zuciyar ta. Ya nisa ya ce "ke yanzu da gaske kike yi ba kya so na?" Yana rufe baki ta ce "Wallahi ina sonka Mukhtar! amma bana sonka da aure, ina neman tsari da kaddarar da zata sake hadamu. Ka sani sarai, ina da kishi, idan na dawo ma ba abin da zan tarar sai bacin rai, na ro'ke ka mu rufe wannan maganar tun da sauran mutunci a tsakanin mu". Ya matsa sosai kusa da ita murya a dakushe ya ce "Na miki tanadin farin ciki marar yankewa, kin sani Ina son ki, son da ya zarce kwatance, kin sani har zuciyarki ban zalunce ki ba, ke ce kika musguna mini, amma ina tabbatar miki Sa'adah zan sake ninka miki soyayya akan wadda na miki ta baya, zan sake tausaya miki, zan kuma yi iyakacin kokarina ban yi abin da zai yawaita motsa miki kishi ba, na dade ina roka miki sau'kin kishi a wurin ubangijin da yake sarrafa zuciya. Ko baki dawo dan ni ba, ki dawo dan Jawad, ki dawo ko ubangiji zai azurta mu, da sama masa yan'uwa". Jikinta ya yi sanyi sosai da kalamansa, wadanda ta tabbatar babu yaudara ko da'din baki a cikin su. Amma sai ta waske da cewa "Ina yiwa Jawad fatan samun yan'uwa ta bangaren Farida. Domin kuwa ni dai ba da kai zan samar masa ba". Wani irin abu ya soki Mk tunda ga kan kansa har kan yantsunsa . Ya dinga jin kansa na yi masa nauyi, ganinsa ya koma dususu, jiri ya fara katantanwa da shi. Cikin hikimar ubangiji sai kawai ya zauna dabas angurin, farin yadinsa na tissue original din, ya debi 'kura da ciyayi amma baima sani ba. Yana zaune sai zufa ke karyo masa, take kuma hakoransa suka dinga kadawa tabbacin zazzabi ya kawo gudunmawa a tashin hankalin da yake ciki. Da kyar ya ciro wayarsa ya mika mata ya ce "Taimaka ki lalubo mini Abbas". Jikinta a matu'kar sanyaye har bari take yi saboda halin da yau ta ga Mk a ciki ya matu'kar kidima ta. Bugu daya Abbas ya dauka. Cikin karfin hali Mk ya ce taimake ni ka zo ka dauke ni, ina nan gandu gidan nan na layin Madugu, ba zan iya tuki bane". Ya kashe wayar ya kalleta idonsa ya ka'da sosai ya ce "kin manta duk rayuwar da kika yi ta jin da'di a hannuna, kin manta alheri na, kin manta duk kalolin soyayyar da nake gwada miki, kin dora kuskurena akan dukkan wadannan abubuawan". Ta kasa magana, ya sake kallon ta soasai fuskarsa duk gumi tamkar ya yi alwala ya ce "ki manta dukkan dadin da nake raba dare ina jiyar da ke, kin ri'ke sharri na guda daya. Har yau din nan ban ji a jikina na zalunce ki ba, na san dai babban laifi na auren da na yi ne, aure kuwa ko muna tare idan bu'katar yinsa ta zo ba zaluntarki na yi ba. Amma duk da hakan na yi ta baki ha'kuri, na fada miki kaddara ta ce auren nan da na yi. Amma ubangiji shine shaidata akan ba abin da ya ragu na daga son da nake miki, bana jin kuma a cikin wannan duniyar akwai abin da zan so ya zarta ki". Ya nisa ya ce "Amma duk kin yi fatali da komai, kin dage sai kin yi ramuwar gayya. Abin da baki sani ba, shine ba ni da karfin guiwar juriya akan kishin ki, amma tunda kin dage shikenan, kawai ina jiye miki fargar jaji ne, ina jiye miki ki maida 'danki maraya. Shiga gida na gode sosai". Ya yi shiru, zufa na sake karyo masa ta ko ina. Kafin ta yi magana Abbas ya iso a adaidaita sahu. Ya gaisheta, tare da tambayar ahalin gidansu. Mk ya mika masa hannu, shikuma ya mikar da shi. Suka doshi mota ba tare da Mk ya sake cewa komai ba. Abbas ya dinga jin tausayin wadannan masoya, a ransa ya dinga musu addu'ar samun daidaito ko hankalinsu ya kwanta. Kwanan Mk biyu a kwance Farida na jinyarsa domin a wnanan karon har ruwa aka kara masa, a gida. Mahmoud ya damu sosai ya sake komawa wurin Sa'a Amma ta kafe ita fa ta riga ta ha'kura da Mk. Haka da Baffa ya tambayeta ta ce ita kam bata sonsa, abin ya farantawa Inna rai, ba irin kabalin da Baffa bai yi ba ta ce ita kam ta riga da ta shafe babinsa. Lamarin da ya farantawa Inna rai ba ka'dan ba. Da ta ga da gaske Baffa zai mata fin karfi ta shirya suka tafi Gogel ita da Sumayya, ta kai korafi wurin Yayan Baffah da ya ce a Gogel din za'a daura aurenta wannan karon. Baffah bai san da gaske Iyah take ba, sai da ya ji kokenta akan a roke shi ya barta ta auri wadda zata nutsu da shi. Ya dawo gida a sanyaye, ya tarar da su duk suna gidan har Sumayya. Ya zauna a cikinsu, suka gaisa. Ya kasa daurewa ya ce " Iyah na ji sakon ki, na san wannan hukuncin da kika yanke a iya fatar bakin ki ne, amma tunda kin yarda da shawarwarin makusantan ki, kin tauyewa zuciyar ki, da 'danki fari ciki shikenan. Ai dama ke ce kike da hakkin zabawa kanki miji domin kin girma hankali ya ratsa ki". Ya daga kai sama ya ce "Allah ka zame mini shaida, na yi iyakacin kokarina, na mikata inda zata sami nutsuwa amma basu fahimce ni ba, Allah ka sani ban yi fishi ba, Ina dai roka mata sassauci kar abarta da zabinta, a bata mafi alheri." Ya sauake idonsa a akanta da duk jikinta ya mutu, kunyar 'karar da ta kai shi na kamata, ba ita kadai ba har Sumayya, Innace kawai take kan ba'kanta gara da suka yi hakan. Ya nisa ya ce" ki cewa wadda kuka aminta da shi, ya tura iyayensa Gogel wajen Babanku Ayuba, ni ba sai sun zo mini ba". Ya mike ya barsu da sanyin jiki. Yana fita kuwa, ya kira Mahmoud ya zo ya same shi. Ya kalli'Karfi ya ce "Mahmouda Ina ba'kin cikin sanar da kai cewa duk yadda nake ganin Zan shawo kan Iyah akan al'amarin ta da Mutari abin ya ci tura, na rasa inda zansa kaina kunyar yaron nake ji. Yau din nan sun je can gida sun fa'dawa Yayana Akan na matsa sai ta auri Wanda ba shi take so ba, na samu umarnin akan lalle na barta ta tura musu iyayen wanda take so". Takaici ya kama Baffa ya kasa cigabada maganarsa. Sai ya nisa ya ce "Bazan iya fa'dawa Mutari wannan maganar ba, domin ya riga da ya gamsu na isa da ita, to gashi sun hade min kai, sun nuna mini *HALIN YAU* na rashin girmama ra'ayin magabata. Dan haka ka fa'da masa ya yi hakuri dan Allah, yau ma zan sake maimatawa da ina da wata yarinyar da na bashi, in fatan ubangiji ya albarkaci Jawad da ya ratsa a tsakanin mu". Jikin 'Karfi ya mutu kwarai da gaske! Kenan biyu babu zasu yi? Mk ka'dai zai iya sadaukarwa da Sa'adah, amma matu'kar ba Mk ba kuwa zai shiga ya fafata da kowanne mahalu'ki dan ya tabbatar ya hana shi daukarta, a yanzun ma abin da zuciyarsa take kissima masa kenan indai yana raye bai kamata ya bari ta subucewa Mk din ba. Ya riga da ya hakura da ita, badan ya daina sonta ba, sai dan ya san ubangiji ya dubi girman hakurinsa ya bashi mace ta gari, matar da ako ina zai bugi kirji ya ce ta gari ce, matar da take sonsa da dukkan zuciyarta, take mutuntunta shi, take hakuri da dukkan matsalolinsa, ya sani ba iyawarsa ba ce, horewar ubangiji ce. Ya nisa ya ce "Baffah mu bamu sare ba, har sai ranar da muka ga an daura mata aure". Ka cire kanka cikin maganar kawai, ka barmu da ita, yanzu ne zamu kafa alkalamin mu cikin tawada, jikina yana bani bakin alkalamin mu bai bushe ba". Baffah ya nisa ya ce "To Ubangiji ya dafa muku, ya yi zabin alheri". Kwanaki uku kenan 'Karfi ya kasa fa'dawa Mk sakon Baffa adalilin har yanzu jikin nasa ba kwari, jiyama sai Mahmoud din ne ya mayar da Jawad makaranta, da hutun ya kare a jiyan. Sai da aka sake yin kwana biyu'Karfi ya tarar da Mk har gidansa suka tattauna sakon Baffah! A farko maganar gaba'daya rikicewa ya yi, amma 'Karfi ya shawo kansa ta hanyar fa'din ina tare da kai Bichi banji a raina zamu rasata ga'badaya ba, fatana mu yi addu'a, mu bi hankali kar kuma mu sare, mu yi ta binta tunda mu muke nema, sannu a hankali har mu samu mu damketa". Mk ya nisa, ya ce" tunda na rabu da yarinyar nan wani abu mai tsananin nauyi ya tokare ni a kirji da makoshi, har yau din nan bai fada min ba, sai kara girmama da abin ya yi a yanzu da nake ganinta da wasu, wai ya zanyi ne? Wallahi na fara debe kauna da rayuwa domin Ni ka'dai nasan azabar da nake hadiya mussaman ace dare ya yi lokacin da zan samu na huta, a lokacin ne nafi shiga tasku bana iya barci, yanzu kuma abincin ma baya shiga". 'Karfi ya nisa ya ce "ka daina damuwa komai zai wuce, idan ka ga ka rasata, to kawai ka dauka babu alheri ne a kasancewar ku, ubangiji ne ya karar da zaman. Sai ka duba ai ka rayu shekaru bakwai babu ita, kuma baka mutu ba, idan har ita zata iya yin jarumtar hakuri da kai gaba'daya, bayan ta sha dukkan ba'kin ciki da tashin hankalin son komowa gareka, to kuwa kaine ka fi cancanta da irin wannan jarumtar". Mk ya yi shiru yana gasggata Sa'a ta fi shi jarumta, tunda har zuciyarta bata buga adalilin aurensa ba, don kuwa shi yanzu ya gama yin imanin duk ranar da aka daura aurenta da waninsa tabbas a ranar ajalinsa zai sauka adalilin bugawar zuciya, ko hawan jinin da ya zarce kima. A raunane ya kalli 'Karfi ya ce "Ai ita mace ce, ubangiji ya sanya musu wani irin karfin jure dukkan kalubalen tarbiya da kishi, amma mu ba a bamu wannan ba, namiji karfin gwagwarmaya aka bashi, da karfin tsayawa iyalinsa akan dukkan bu'katun yau da kullum". 'Karfi ya nisa ya ce "Hakane! Abin da nake so yanzu da kai shine, ka dora jarumtar gwagwarmaya a zuciyar ka, tunda ka gamsu muna da karfi da juriya anan bangaren, to idan kuwa hakane, zamu yi gwagwarmaya har mu samu mu kwato abin da yake namu ne". Tun daga ranar suka fara yiwa Iyah wani irin naci, mai cin rai. A Rana su kanje sau uku, kowanne lokaci zuwa suke yi, tun Inna tana ganin zasu gaji su daina, har ta fara ganin ba zasu gaji ba, domin kuwa kullum zaryar kara gaba take yi, ba baya ba. Haka gidan Sumayya, hatta Idris a yanzu tausayin Mk yake ji, shiyasa ya fa'dawa mai gadin gidan matu'kar Mk ne suka zo, to ya bude masa gate kai tsaye. Tsawon sati uku ana wannan zaryar bai fi kuma sau biyar suka samu nasarar ganinta ba, a cikin zuwa fiye da arbain. Duk inda hankalin Mk yake a tashe yake, yayin da Mahmoud yake ta karfafa masa guiwa duk da shima bai yi zaton kafiyar Sa'adah ta kai haka ba. Ranar alhamis da hantsi suka isa gidan Sumayya, sun shafe lokaci mai yawa a zaune, sannan ta fito, sanye da hijabi fuskar nan a daure, ta iso, da alamu tilas aka yi mata. Dr Karfi ya mike ya na fa'din barka da fitowa sarauniyar mata. Ta yi shiru tamkar ba da ita yake ba, domin ta lura shine jagoran wannan nacin da suke mata kamar ba'kaken mayu. Ya ce "Allah ya huci zuciyar giwa kuma gimbiyar Mata, ba zamu gaji da bada hakuri ba, ba kuma zamu gajiya ba, har sai kin dawo mana da walwalar da ta yi mana tutsu. Ki yi ha'kuri, ki zo ki haska mana zuciyar aminina da gidansa gaba'daya, Ina rokon ki, badan mu ba, sai dan ubangijin ki, ni shaida ne na irin tsananin son da yake Miki". A tunzure Sa'a ta ce "ka dinga jin tsoron ubangiji Baban Dady! Sai yanzu! Sai yanzu! Sai yanzu zaka tirsasa ni, me yasa a wanccan lokacin baka tirsasa shi ba, me yasa ka bari na wulakanta, na tabbatar ba zaka so ayiwa kanwarka abin da aka yi mini ba. Amma yanzu da yake farin-cikin abokinka kawai ne a gabanka, ka na'de 'kafar wandon yi mini dole, kasan ina jin nauyinka, akan me zaka takura ni irin haka, an ta'ba yin aure dole, to ko Baffah ma na tabbatar masa bana son wannan mutumin, kaima na fa'da maka, ka sakar mini mara, na ro'ke ka". Ta karasa cikin kuka sosai, Dukkan su sun yi laushi, mussaman Mk da yake jin tamkar ya hadiyi zuciya saboda yadda yake jin ciwon yadda take fadin bata sonsa, a gaban kowa. Mahmoud ya kalli Agogon hannun sa, ya ce "hakuri zaki yi, ba yadda zamu yi ne, ki 'kara hakuri, ubangiji zai baki ladan masu hakuri. Ya kalli Mk ya ce " ina da appointment nan da mintina talatin a makaranta, zan wuce, idan ka gama kawai mu hadu a gidanka bayan azahar". Daga haka ya fice da sauri, da mukallin motar Mk a hannunsa. Tana tsaye tamkar soja. A hankali Mk ya ce "zauna mana Dan Allah". Bata yi musu ba, ta zauna. Ya zuba mata ido yana kallon yadda ta ke cika tana batsewa ya saki ajiyar zuciya mai zafi ya ce "A gaban kowa kike fadin ba kya sona, Ni kike wulakantawa haka? Kada kishi yasa ki manta ke ce kika mini laifi?" Da kuka ta ce "Ni na maka laifi tabbas, ka kuma hukutan ni, to menene kuma ba sai a barshi a hakan ba, gaskiya kun matsa mini, tsakani da Allah kun shiga rayuwata, sau nawa zan fa'da maka bana sha'awar sake rayuwa da Kai? Na ha'kura, na bar mata, Ni ma ka bar ni, Dan Allah". Kafin ya yi magana ta sake cewa "kafin ka aure Ni ka kira ni Ballagaza, na yi hakuri saboda ina ta'kama da Budurci, yanzu kuma ka ce ina ha'intarka, fa'da mini dame zan kare kaina, tunda ba ni da Budurci a yanzu?" Da sauri Mk ya karaso kujerar da take zaune, ya zauna a hannun kujerar ya sassauta ya ce " Na da'de ina fada miki, bacin rai ne, ba ina nufin haka har zuciyata ba, ki yi hakuri. Na janye kalamina, wallahi tallahi ke din katangaggiya ce, ki bar wannan maganar, ko tunawa bana so, hankali na tashi yake yi. Na janye! Na janye! Na janye Dan Allah a rufe wannan maganar har abada". Ta dinga kuka sosai mai cin rai, ta kasa cewa komai. Ya nisa ya ce" kukan ya isa haka, ki yi hakuri ina fatan wannan ne kukan ki na karshe akan wannan matsalar". Ta kifa kanta a dayan hannun kujerar tana sake tsananta kukan sosai, Ta ce "indai baka rabu da ni ba, na tabbatar zan dauwama ina kuka ne, domin zan rayu ina raba ka da wata ne, Ni kuwa da haka gara na auri me mata uku na zama ta hudu". Mk ya rasa mai zai yi, ko ya ce, gaba'daya tunaninsa gaba'daya ya kulle. Ya tabbatar auren Farida ne cikas dinsa a gurinta, shine yasa ta kasa amincewa da shi. Ba yadda zai yi akan Farida kuwa domin bai aureta dan ya saketa akan wani 'karamin dalili ba. Ya sassauta ya ce "Yarda da 'kaddara na cikin sharuddan cikar imani, ki ture komai, ki kalle ni har yanzu ba abin da ya canja na soyayyar ki a tare ni, ki bani amanar kan ki wallahi ba zaki yi nadama ba". "Ko yanzu kika amince mini, wallahi na sha wahala, na azabtu, yanzu haka ina daf da kamuwa da ciwon zuciya, ba komai bane ya janyo mini ba, illah ganin ki da wasu mazan". Ya sauko ya dur'kusa a gabanta karon farko ya ce "Ga ni akan guiwata, ki yi hakuri, ki yafe mini, ki sake bani wata damar, ni na san kina so na. Plz Sa'adah let Gone by gone, ba zan iya wannan rikicin ba, na horu hakanan, ki fa'dawa Baffa mun shirya, na kuma kawo miki Baba Isa gaban ki, ki fa'da masa mun shirya, kin yafe mini, Ni kuma na miki al'kawarin zaki rayu cikin soyayya mai wuyar samu a Yau". Ta dago ta kalle shi a durkushe a gabanta, da'di ya kamata, amma sai ta waske ta ce "Ni fa ba zan yafe ba, matu'kar ba wani ne ya aure ni ya ta'ba ni kamar yadda kake ta'ba wata macen ba". Ya mike da sauri ya ce "shikenan, dama ke ai ba'a taba rarrashin ki, kin gamsu cikin da'din rai ba, kaddara ce ta hau kaina ban kuma isa na kauce ba, tunda kin kasa fahimta shikenan, amma ki sani idan fa 'kaddara ta gwada iko akan ki, kika dawo mini, ba zan gamsu kin mini uzziri ba". Ta tura baki gaba sosai ta ce " Da ikon ubangiji ma ba zata faado kaina ba". Ya koma ya zauna a inda yake zaune tun farko yana tunanin mai kuma zai yiwa wannan yar darun ta fahimce shi, shi tashin hankalinsa daya ya ganta da wani, ba dan haka ba, da ya daure ya kyale wannan yarinyar da take neman manna masa ciwon zuciya. Sun Jima a zaune ba um bare um um. Ya mike ya ce "zan tafi ina fatan idan na kira wayar ki, ki dauka. Allah ya huci zuciyarki". **** A cikin wannan yanayin shari'ar Sanata Ibrahim Hassan ta sake zagayowa, bayan doguwar muhawara da tarin hujjojin lauyoyinsa, kotu ta wanke shi daga dukkan tuhumomin da ake yi masa. Sa'aadah ta bukaci a bashi naira miliyan hamsin a matsayin diyyar bata masa suna da lokaci. Jajircewar da Sa'a ta yi a wannan shari'ar yasa sunan ta ya shahara, ta yi farin jini. Har gida Mai girma Sanata ya aiko mata da dankareriyar mota kirar Toyota Camry new modern. Direbansa da wasu yaransa ne suka kawo, suka danka a hannun Baffah. Bayan sun yi godiya a madadin Sanata. Washagari asabar Khalil ya mata wayar zai zo ya mata godiya tare da ban gajiya. Saboda jidalin Mk ta masa kwatancen gidan Sumayya dan kar ya zo shago ya hango ta da Khalil, duk da a gidansu ta kwana. Sai bayan azahar ta tafi gidan Sumayyan tunda ya ce sai bayan la'asar zai zo. Aikuwa ana idar da Sallar la'asar ba jimawa ya iso, sosai suka sha Hira, wani lokacin kuma suyi ta jifan junansu da kallon kauna sai kuma a waske da murmushi, tabbas soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa. Amma Sa'a ta 'kudire ba zata auri Khalil ba, domin ta san komai na iya faruwa da Mk a sanadin hakan. Da zai tafi ya ajie mata envelope mai dauke da dalar amurka, wanda idan a kiyasin naira zasu iya kaiwa dubu dari biyar. Ya yi ta mata godiya tare da cewa "Na so kwarai ace na aure ki, sai dai jiya Mum 'dina ta tabbatar mini Yar kanwarta ta zaba mini, bijirewa ta kuma na nufin lalacewar al'amurana, na sani har na mutu ba zan daina son ki ba, sannan tsayiwar ki, kadai kan mahaifina ya tabbatar mini da cewa tabbas baki manta ba, duk irin kaini 'kasa da Mk yake ko wa, da ya yi" Tana dariyar wai ya manta sunan Mk ta rako shi har wajen da ya ajiye motarsa, Suka sake tsayuwa a wajen adalilin ya ce zai shiga gidan Madugu wurin abokin karatunsa a Egypt. Suna tsaye motar Mahmoud ta tunkaro su, zuciyar Sa'a ta buga, kafafuwanta suka dinga barazanar kada ita. Mk dake gaban motar ya ji tamkar ya sume, mussaman da ya tabbatar Khalil ne wannan zabgegen saurayin ya girma sosai. Suka hada ido amma Khalil sai ya dauke kai bayan ya galla masa kallon raini tamkar shekarun baya. Har zuwa yau bai ji zai iya kallon Mk a matsayin malamin sa ba, sai dai a matsayin dan fashi a soyayya. Wannan kallon ya sake rikita Mk, domin yasan na rainine tsantsa. Yayin da Sa'a bugun zuciyarta ya tsananta, tana raya ina ma motar Mahmoud ce mai tint? Mai gadi ya bude musu gate Mahmoud ya ja suka shiga, ya juya ya ga Mk yana wani irin numfarfashi, tamkar ya samu attack na asthma. A farko 'karfi ya dauka abin Wasa ne sai da ya ga Mk ya sume sai kawai ya ja motar a kidime zuwa asibiti. SURAYYA DAHIRU. ✍️✍️ *HALIN YAU*! *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *Lafazee writers* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* *GAISUWA GA DUKKAN MAMBOBIN* *HALIN YAU FANS* *_Na gode sosai da yabawar ku, comments din ku na matu'kar sa ni Nisha'di, Allah ya bar zumunci_*. 102-103. Suna tsaye suka ga mai gadi ya bude musu kofa, Mahamud ya fito a guje kana ganin tukin da yake yi kasan babu sukuni a tare da shi. Hankalin Sa'a idan ya yi dubu ya tashi, Khalil ya kula da yanayinta ya ce, ina son ki sosai, ke kuma kina son wanccan wicked man din. Ya'ke kawai ta yi, ba tare da ta ce komai ba. Ya juya ya fara tafiya yana cewa" sai wani lokaci, muna godiya, kwarai da gaske". Da azama ta juya itama tana jin tamkar ta yi ta zunduma ihu, ya ya zata yi ne? Ta san ganin Khalil tare da ita means alot a wurin Mk. * ** Suna isa Asibiti aka shiga da shi dakin agajin gaggawa wato (emergency). Likitoci suka rufu akansa ana kokarin shawo kan matsalar, tsawon lokaci kafin a samu numfashin sa ya dawo, sai dai ba dai dai ba, Dan haka dole aka saka masa na'urar sau'ka'ka zukar numfashi (oxygen). Sai dare 'karfi ya sanar da Farida da Abbas halin da ake ciki. Dukkansu sun yi jigum jigum a asibiti suna kallon Mk a kwance bai san wanda yake kansa ba. Farida sai fama take da tissue tana goge hawayen da ya kasa tsayuwa a idonta, ta dade da sanin mijinta bashi da lafiya, ta Dade tana jiye masa shiga irin wannan halin, adalilin kullum yana cikin rashin sukuni, ta dinga jin haushin Sa'adah na kamata, ta tabbatar ita take son kaishi barzaku dan kawai ta musu biyu babu. Hajiya kuwa sai da gari ya waye aka sanar mata, ta isa asibitin cikin tashin hankali, ta kalli yadda ya ke shimfide akan gadon asibiti, ya zabge sosai, dama ya dade a rame Amma yanzu ramar ta bayyana karara. Haka suka tasa shi a gaba masu addu'a na yi, masu share hawaye na yi. Sai da aka kwana biyu Baffa ya samu labarin ciwon Mk adalilin Bai ganshi ba, bai ga Mahmoud ba, haka Abbas, har shagon su ya je, anan ya samu labarin ai yana asibiti an kwantar da shi. Akeel ne ya raka shi asibitin, ba karamin damuwa ya shiga da ganin Halin da Mk ya ke ciki ya yi ba. Ya dinga yi masa addu'a yana tofa masa. Har ya gama zamansa Mk bai farka ba, ya isa gida ya tarar da Innah a tsakar gida tana yanke farce, ta masa sannu, ya amsa, ya samu gefe ya zauna. Ya nisa ya ce "Mutari ne bai da lafiya rabona da shi yau kwanaki uku kenan, dazu na je shagonsa jin ba'asi sai ake fa'da mini bai ji da'di ba, na je na gano shi, Amma ban ji da'din ganin sa ba, domin gaba'daya yana kwance tamkar gawa. A sanyaye Inna ta ce "Assha Ubangiji yasa zakkar jiki ce". "Ameen dai! Amm an tabbatar mini jininsa ne ya hau fiye da 'kima, na san baya rasa nasaba da bijirewar ku, Ayyah Salamatu ba zaku yiwa yaron nan sassauci ba, ko bai ci arzikin kowa ba, ya ci na tilon 'dansa mana". A sanyaye ta ce "Àllah zai bashi lafiya, Iyah har karamin hauka ta yi, amma da aka yi hakuri ai gashi nan ta mike, har ya zama tamkar ba a yi ba, shima zai tashi ne". Ran Baffa ya fara 'baci da lamarin ta sosai, Amma sai ya mike ya fice domin ya san cigaba da zamansa a cikin gidan yana nufin rikici mai tsanani a tsakanin su, abin da ba zai iya tuna ko sau nawa suka yi a tsayin rayuwar aurensu ba. Sa'a da ke daki take jiyo su, hankalin ta yayi tashin gauron zabi, ta da'de tana wasi-wasin fishi su Dr 'Karfi suka yi, ko kuwa jikin Mk ne har yanzu domin yadda ta ganshi kwance a gaban mota da irin gudun da Mahmoud ya yi ta tsorata. Gashi kwana biyu bata sake jin su ko a waya ba. Hawaye ya 'balle mata, ta tuno sadda yake ce mata, yana jiye mata fargar jaji, yana jiye mata kar 'danta ya zama maraya. Ta kasa fitowa waje dan idan Inna ta ga tana kuka akan Mk to kuwa ta kade har ganyen ta. Ta rasa inda zata tsoma ranta. Washagarin ranar sai ga Baba Isa sun zo har da su Baba umaru, daga asibiti suke, ganin Halin da Mk ya ke ciki, yasa suka ji tausayi, suka saka Mahmoud ya kawo su, su zo ko Allah zai sa a samu yarinya ta huce . Amma wani abu da Sa'adah ta kasa gane menene ya daure mata baki da zuciyarta, ba abin da take hange sai Mk da Farida cikin mayafi guda, duk tambayar da suke yi mata ta kasa amsawa sai kuka take yi, tana satar kallon mahaifiyarsu. Hade ran da Inna ta yi, yasa ta ce "Na yafe masa, amma ni bana sonsa da aure". Jikin su Baba Isa ya mutu kwarai da gaske, dan haka suka ha'kura domin dai sun san yarinyar ta hadiyi ba'kin ciki kala kala. Ran Baffah bai ta'ba baci irin na yau ba, gaba'daya ya ji Sa'adah da mahaifiyarta sun kunyata shi, sun tozarta shi. A daddafe ya sallame su, ya dawo gida, ya dinga surfawa Inna sababi, yana fa'din "Ban san ladabin karya kika yi mini ba, a tsawon shekarun da muka kwashe ba sai yanzu". Ya nisa ya ce "wallahi Salamatu kin yi 'karko irin na kifi ace wai ke kika raba mini gida zuwa jami'iya biyu, kin hana yarinya zabin zuciyarta, saboda son rai irin naki. Yanzu haka yaro yana gadon asibiti rai a hannun Allah! Tabbas idan ya mutu, ke ce sila, kin bada muhimmiyar gudunmawa wurin kisan rai" Ta fara kuka ta na cewa "Eh ai da yake shi ka damu da lafiyarsa, shiyasa kake akilon samo masa mafita, amma sadda ta dinga zabura tana surutai ai duk ka manta. Ina nan akan bakana bana son Muutar da Iyah". Ya hassalo ya ce "to kuwa ba zan iya zama da ke da wannan bakar zuciyar ta ki ba, har kina iya buda baki kina ce wa wanii mai ru'ko da 'Kullaci, to ke ai zuciyar ki tafi ta kafiran farko ma tauri". Da kuka sosai ta shige 'daki ta fara tattara kayanta tana fa'din "akan Iyah ta komawa Muutar gara na ha'kura da zaman tunda ka ce ba zaka iya zama da ni ba". Sa'adah da take tsaye tana kukan bacin ran yau akanta iyayenta da bata ta'ba ganin sunyi ko da musu ba, suke wannan tashin hankalin. Ta bi Inna daki tana bata hakuri amma ko kallonta ba ta yi ba, sai hawaye take yi, tana cigaba da hada kayanta. Baffa ya shigo ya ce "daina ha'da kayan ki, yau shekaru arbain har da uku da auren mu, kike tunanin dan na rabu da ke zan tura ki gidanku? Ai ni ba azzalumi bane, ba zan karar miki da karfinki da kuruciyarki sannan na sallama ki ba". Ya nisa sosai ya ce "mahaifiyata ita ta sha nono ta barwa mahaifin ki, kenan a ko ina ni mai tsaya miki ne, ba me tozarta ki ba. Ni ne zan fita na barki miki gida, ki yi yadda kike so da yaranki, tunda ni ban isa na yi iko da su ba, kin riga kin zama 'Yar birni, son ya'ya kawai shine a gabanki ba tare da tunanin abin da zai biyo baya ba". Ya sake cewa "ki yi zamanki, ko ban aure ki ba, aike kanwata ce da zan baki 'daki a gidana, bare kuma nine na karar miki da komai". Ya juya ya fice zuwa dakinsa ya dinga ha'da kayansa. Sa'a ce ta ankara da yadda yake ta fito da kayayyakinsa tsakar gida. Ta fito da sauri, cikin kuka sosai ta zube tana cewa "Na ro'ke ka Baffah ka yi hakuri, kar ka bar mu ina zaka tafi ka barmu? Muryarsa na rawa ya ce "ko ina ma zan shiga menene matsalar ku, ina ce yanzu kun yi wayewar da zaku iya rike kanku, ku zartar da hukuncin da ni ne zan yi muku biyayya, ba kune zaku mini ba, saboda kuna gamsar da kanku da uwarku, kyale-kyalen duniya fiye da yadda zan yi muku. Dan haka gara na nesanta kaina da ku, tunda ban isa na ce ga yadda za'ayi a gidana ace mini to ba". Inna da take bakin kofar daki hawayenta ya kasa tsayawa, da sauri ta tsugunna tana cewa "Ka mini hakuri, na yarda na yi kuskure, na yi laifi, ka gafarce Ni, na amince Muutar kaddarar Iya ne, ina fatan ubangiji ya sa karshen bacin ran mu kenan. Ka yi hakuri na ce to, na amince, ka yi yadda kake so da 'yarka". Dadi ya mamaye zuciyar Baffa ya ce "Na gode miki Salamatu! Ubangiji ya kore shaidanun da suke son tarwatsa mana kyakkawan zaman mu". Ya kalli Iyah ya ce "A lokacin da na barki ki yi karatun ki, na tabbatar miki bana so, amma na amince miki dan na yarda alfanu ne a gare mu baki'daya. A lokacin na ro'ke ki duk sadda nima zan zo miki da wata bukata ki daure ki mini biyayya ko da ba kya so, sai dan kin san ba zan dora ki akan abu marar alfanu ko cutarwa a gare ki ba". Kafin ta amsa masa, ya sake zarcewa da fa'din "To yau ina son na roke ki, ki koma dakin ki, burina a duniya bai wuce ace kina dakin mijinki a zaune kin nutsu ba. Mutari shi nake so ya zame miki miji a karo na biyu". Da rawar murya ta ce "To Baffah! Na ji, na kuma amince zan yi maka biyayya, zan yi ha'kuri na zauna lafiya da shi komai runtsi". Da murna Baffa ya ke cewa "Na gode miki in sha Allah ba zaki yi nadama ba, ubangiji ya miki Albarka, ya zaunar da ku lafiya, ya baku zuri'a mai albarka". Ya nisa ya ce " ku shirya gobe zamu je Gogel ki fa'dawa Yaya Ayuba kin amince ba dole na yi miki ba, Sannan ku samu lokaci ku gano Mutari domin yana jin jiki" Da sauri lya mike yana cewa "Bari na bi su Alhaji na fa'da musu wannan labarin mai da'di". Inna ta bi bayansa da ido har ya fice daga gidan, tana ayyana girman soyayyar da yake yiwa Mukhtar. Kai tsaye gidan Alh Isa ya dosa, a kofar gidan ys tarar da Dr 'Karfi zai shiga mota, ai kuwa ya ce "Mahmouda zo mu shiga, ba tafiya zaka yi ba". Baffa da murna yake fa'da musu "ai yanzun nan yarinya ta tabbatar masa ta amince, dan haka ku zama cikin shirin zuwa Gogel, a satin nan. Domin a son raina ku tafi da sadaki, a ranar da kuka je a daura auren a huta, kafin ta sake botsarewa saboda na lura kishin banza ta bari yake rinjayar ta". Daga Baba umaru har Baba Isa kowa ya yi shiru amma suma jinjina alherin bawan Allahn nan suke yi, da karfin son da yake yiwa 'dansu. Baba Isa ne ya yi karfin halin cewa "Malam Basiru ka dai matsa mata ta amince, gashi muma zamu sake yin son rai, mu amince da abin da ka zartar domin a samu lafiyar yaron nan ta dai-daita, bamu da bakin godiya, abin da zamu ce maka daya ne, da ikon Allah mu kabawa amanar yarinyar nan, mune iyayensa abin da ya faru a farko ba zai sake maimaituwa ba da ikon ubangiji. Kira mini yarinyar a waya" Baffa da ya san bashi da fargaba da azama ya fito da wayarsa. Bugu 'daya ta dauka, ya ce " Baban ku na Na'ibawa ne zai yi magana da ke". Kalaman kwantar da hankali tare da yabo da kuma girman mai hakuri Alh Isa ya dinga yi Mata, ya sake jaddada mata kar ta sake yin shiru har sai abu ya girmama, komai ya taso matu'kar yafi karfinta to ta sanar da shi zai magance mata da ikon Allah. Ya rufe maganar da cewa ko kina da korafi domin mun tsayar da kwanaki biyar masu zuwa na daurin auren ku". Zuciyarta ta buga sosai, cikin rishin kuka ta ce "Ba ni da matsala Baba! Amma zan ro'ke ka dan Allah a bari sai na kintsa sannan ayi tariya". Da sauri ya ce "Na miki Wannan laminin ki shirya a nutse, ai na san tutsiye Malam Basiru ya Miki ko na ce karfa-karfa, dan haka daga wata daya zuwa wattanni shida ki yi shirinki a hankali, bu'katar mu dama a daura auren hankalin kowa ya kwanta". A yammacin ranar suka je asibiti ita da Inna har da Sumayya. Har suka gama zamansu barci yake yi, wannan barcin shike daga hankalin kowa, ya rame kwarai da gaske. Har waje Hajiyar Bichi ta rako su, tana ta faman godiya, yayin da tausayin Hajiya ya lullube Sa'a, kallonta kawai take yi saboda yadda ta zabge ta yi zuru zuru tabbacin tare suke yin jinyar ita da Mk. Cike da rauni ta ce musu "Idan har zuwa gobe bai samu sassauci ba, zan tura Ahamad ya dauko Jawad ya zo ya ga ubansa don".. sai kuka ya kwace ta kasa karasawa. Jikin Inna ya mutu kwarai da gaske, ta dinga bata ha'kuri tare nuna cewa cuta ai ba mutuwa ba ce. Har suka isa gida ba mai cewa komai saboda ba su zaci haka jikin Mk ya yi tsanani ba. Washagari cikin ikon ubangiji jikin Mk ya yi sau'ki domin har cire masa oxygen aka yi, sannan ya yini idonsa biyu. Akan idonsa Inna da Sumayya suka iso, sosai ya ji da'din zuwan su tunda ya lura, sune kanwa uwar gamin wurin tunzura Iyah, sune suka hau dokin na ki, da tallafin su ta sami kwarin guiwar yi masa bore. Amma da ya tuna wai Sa'adah ya gani da Khalil sai ya ji wani irin kunci ya mamaye zuciyarsa! Tabbas ya yarda a duniyarsa bashi da wani kalubale irin Yaron nan, sannan yadda Khalil ya zama tsalelen saurayi na kerewa Sa'a ya sake tayar masa da hankali kwarai da gaske, domin kowacce mace ta ganshi zata so mallakarsa a matsayin miji. Ba komai ke nukurkusar Mk ba irin kishin Khalil, a sanadinsa ya rasa aurensa da matar da yake so fiye da kansa, gashi har yanzu basu rabu ba, ya tabbatar Khalil ne ke da nasara akansa, wani irin karfin zuciya ya shige shi, ya dinga kalubalantar kansa meyasa ya kasa mantar da shi a zuciyar Sa'a tamkar yadda ta mantar da shi soyayyar Farida a lokacin da suke tare. Ya saki ajiyar zuciya yana jin ciwo mai yawa a kirjinsa mafi girma a ciki haushin Sa'adah yake ji kwarai da gaske, a gaban kowa take fa'din bata sonsa, amma dan lalacewa tana soyayya da yaro sa'anta. Su Innah na zaune Farida ta iso dauke da kwandon zuba abinci. Tana kallon Sumayya ta gane sister din Gogel ce, duk kuwa da Sumayya fara ce tas. Har kasa ta tsugunna ta gaishe su. Hajiyar Bichi ta ce mata "Kakar Jawad ce da Yayar Mamansa" Da girmamawa ta sake gaishe su, a ranta sai take ganin Gogel da yayarta dan sun yi kyau ba zai zama abin mamaki ba, domin ko a yanzu da Inna take cikin shekarun tsufa, tana nan da kyaunta, mai kyakkawan jiki ce da yake boye tsufa. Wata'kila haka mahaifin su yake, dan ta lura ba kammanin Inna a tare da Gogel, Sumayya ta fi kama da ita, wanda hakan na alamta cewa mahaifinsu ma ba baya bane. Sumayya ta 'karewa Farida kallo tsab, takaicin Iyah na kamata da ta dinga kukan Mk ya auri Farida dan ta fita kyau ne, a yau da taga zahairin Farida ba hoto iya fuska ba, sai take ganin ba karamin kerewa Iyah ta yi mata ba. Kawai fararen mutane suna da kwarjini ne ta yadda ake ganin kyaunsu ko da kuwa masu 'karancin kyau ne. Farida bata dade da isowa ba, su Inna suka yi sallama suka tafi. Suna isa gida suka tarar da Sa'adah cikin kwalliya ta birgewa, amma tana kwance a falo tana kallo. Inna ko zama ba ta yi ba, ta hau ta da fa'da "Iyah cewa ki ka yi zaku tarad da mu a asibitin tare da Zainab, ashe karya kika yi mini?" Cikin rashin damuwa ta ce "na shirya jiranta nake yi". Kafin Inna ta sake magana Zainab ta kira wayarta, sannan suna jiyo horn dinta tabbacin ta fita, ba shigowa zata yi ba. Ta mike tana fa'din "gata nan ma, sai mun dawo". Sumayya ta ce Yanzu irin wannan kwalliya tamkar kin manta asibiti zaki ba gidan biki ba?". Dake Yan darun akusa suke ta ce "Anty ke kika manta cewa ni wannan ban dauketa kwalliya ba, domin ko a gida haka nake". Da sauri Sumayya ta ce "gaskiya ce sai na fa'da miki, Hajiyar Bichi na gurin, duka danginsa suna gurin, ki je dubiya cikin irin wannan kwalliyar tamkar me shirin shiga gasar miss Beauty. Ba nadama ba komai a al'amuranki". Inna ta ce "ta shi ki wanke fuskarki sai ki dauko Hijabin ki dora, ai kinsan yadda hijabi ma yake karbar ki". Ta mike tana kunkuni wadda yake nuna Sumayya ta fitineta da yawa, dan yanzu ta fi zaman gidanta, to wannan satin ma ba komawa zata yi ba, har sai ta nemeta da kanta. Yayin da Sumayya ta ce "Ai yanzu kin tabbatar zaki samu burin ranki dole ki tattaro dukkan iyashege ki dawo da shi". Ai kuwa Sa'aadah ta fasa uban ihun kuka. dai dai lokacin Baffah ya shigo, ya dinga tambayar ba'asin kukan da take yi mai daukar hankali. Ai kuwa ta fito cikin kuka ta ce "Baffah shata mini layi da Maman Khalifa, ta takura ni, ta matsa mini, saboda ta san duk abin da ta yi mini Inna ba zata ce ta yi laifi ba". Ya murmusa ya ce "Uwata an taba shiga tsakanin hanta da jini ne, inace da dukkan uku hade mini kai kuka yi. Yanzu kuma sai kice na shata miki kayi da ita? Ni bana haka, ya kalli Sumayya ya ce ke kuma ki ri'ke girmanki ai dai yanzu kin wuce kisa ta kuka irin haka". Murmushi sosai Sumayya ta yi, cikin sanyin muryarta ta ce "Baffa daga na ce bai kamata ta je dubiya da kwalliyar da ta yi bane shikenan fa laifin nawa, kuma gani na yi tunda ba zance zata je ba, dubiya ne ai sai ta rage zumudi". Dariya ta kwace wa Baffah ya shige dakinsa. Ba tare da ya yi magana ba. Yayin da Sa'adah ta cigaba da kuka sosai, har Zainab ta gaji ta shigo gidan a fusace. Ganin kukan da take yi, ya tayar mata da hankali ta yi zaton ko Mk ya amsa Kiran mahallicinsa ne. Amma da ta ji ba'asin kukan sai itama ta hau dariya har tana fadin "Yo dama Ni nasan ba wani bata sonsa, idan akwai abin da na gasgata a duniyata, to kuwa son da take yiwa Uncle na cikin su". Ai kuwa ta mi'ke a fusace ta ce "Wallahi Zainab har yau din nan ina jin karfi a tare da ni, ya ishe ki". Zainab ta watsa mata harara ta ce "Da shekarun nan naki, da ilimin lauyancin na ki, da Jawad duk basu sa kin ji cewar kin girma ba? Amma kuwa dai kin ji kunya, kuma na gasgata Anty Sumayya lallai murnar zaki komawa muradin zuciyarki yasa ki wannan fallin, gara ma ki 'dore da kyawawan dabi'un da Kika dauka a shekaru bakwai din nan domin dai kin san yanzu ke Uwargidace kina da amarya mai tsananin wayo da kissa". Ba'kin cikin maganar Zainab ya sake sawa ta fashe da sabon kuka tana fa'din " Asibitin ma ba zani ba". Baffah ya fito ya dubi Zainab ya ce "Ni na fi ku fahimtar Iyah tuni Mutari ya fita a ranta, biyayya kawai zata mini, zuwa duba shi ma ai dole na yi mata, ta kuma yarda zata mini biyayya, dan haka ku daina cewa tana sonsa, ko dan shi ta yi kwalliya domin kuwa dukkan mu shaida ne akan Iyah dangin Dawisu ce". Jin hakan ya sa ta yi shiru. Yayin da Zainab ta ce "To Baffa ka fa'da mata a biyayyar da zata yi maka ta hada har da sanin ta girma, kar ta koma ta zama ta bizaro a gidan Uncle domin yanzu ba ita ka'dai bace, tana da kishiya mai fi'ilin tsiya". Baffah ya murmusa ya ce "ke kam Zainab sai a gaishe ki, dukkan mace ai da inda take da tasiri, Ni kuwa na san ko mata uku ne da Mutari ban jin Iyah zata kasa samun kansa, ai duk wannan shagwabar da take yi na gata ne". Daga haka ya fice ya na fadin "lallai ki fito ku je dubiyar nan Iyah, kinga ba lalle Zainab ta sake samun sukunin fitowa a gobe ba". Ta fito cikin bakar doguwar riga mai kyau. Tana rataye da Yar karamar jaka, kafarta sanye da flat din talkalmi wadda mahadin jakar ne, powder ce kawai a fuskarta. Zainab ta mike ta na cewa "Inna sai mun dawo". Har suka isa asibitin Sa'adah bata ce kala ba, duk da Zainab na janta da hira. A wajen asibitin Zainab ta samu jikin bishiya ta yi fakin. Suka fito suka taka ciki da kafafuwansu. Da Abbas suka fara yin tozali, yana zaman jiran Farida ta fito ya mayar da ita gida, dan haka ya mike ya musu jagora har dakin da Mk yake kwance. A zaune suka taradda shi, Farida tana tsaye a gabansa hanunta na dama ri'ke da hannunsa, yayin da hannun na hagu ri'ke da kwandon zuba abinci, alamun tafiya zata yi. Zuciyar Sa'a ta buga da tsananin gaske, ta zabura, zata koma da baya, Zainab da Abbas kawai suka lura da hakan, Dan haka cikin hikima Zaynab ta ru'ko hannun ta da karfin gaske, kan dole suka karasa shiga sosai. Zainab suka gaisa da Farida ta tambayi mai jiki, sannan ta gaida Mk da ya yi mutuwar zaune, saboda yadda ya ji wani abu da bai san menene ba ya dirar masa, gashi dama fama yake da rashin karfin jiki. Surayya Dee ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* *GAISUWAR GIRMA GA* *HAJ SALIHA A.A. ZARIA.* *MARUBUCIYAR BEGE* *ALLAH YA KARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA MAI ALBARKA*. 104-106. Farida na ri'ke da hannun Mk, ta kalli Sa'a da murmushi ta ce "Maraba da Gogel, karaso kusa mana". Takaici a zuciyar Sa'adah tamkar ta rushe da kuka, ta ki sakar masa hannu dan ta nuna mata itace matarsa. Sannan dan ta tabbatar mata ita bakuwa ce yanzu a wurin Mk, shine take mata iso a gabansa? Ta daure ta hadiye damuwarta ta yi kamar bata ga hannuwansu a sarke ba, ta cewa Farida "Sannun ki". Daga inda take tsaye ta kalli Mk ta ce "ya ya jikin?" Daga haka ta tsuke bakinta, tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta, tabbas Mk ne ya wula'kanta ta saboda ya nunawa Farida ita ba wata tsiyar ba ce. Shiyasa ya ki zame hannunsa da yake cikin nata. Amma ai ya yi da yar halak. A hankali Mk yake kallonta ta kasan ido, yana nazartar yadda take kokawa da fishin da ya ke yun'kuro mata. Cikin hikima ya zare hannunsa a hannun Farida, gumi sai yanko masa yake yi. Da sauri Farida ta 'kara karfin A.C da gudun fanka, saboda zufar da taga na karyo masa wadda kawai ta fargaba ce. A ransa ya dinga nazarin anya zai iya jarumtar ri'ke mata biyu kuwa? Saboda yadda ya dinga zullimin kasancewarsa a gabansu a lokaci 'daya. Mk na wanna tsinkayen ya ga Farida ta ajiye kwandon hannunta tabbacin ta fasa tafiyar kenan. Wato duk ha'kurin mace ta iya shu'umanci indai akan kishi ne? Yau ya gasgata hakan domin ko kaffara ba zai yi ba, idan ya yi rantsuwar saboda Sa'adah ta 'ki tafiyar. Dan haka ya yi kicin kicin da fuska, ita kuma sai kokarin yi masa fifta take yi. Yayin da Sa'adah da Zainab suke ganin ikon ubangiji na yadda Farida ta kankane komai, Zainab da Mk ne suke mamakinta. Yayin da Iyah ta san dama Farida zata yi abin da ya fi haka. Abbas ne ya leko daga bakin kofar ya ce "Farida ina ta faman jiran ki, so nake na yi maza na kai ki na dawo, kafin su tafi kar abar shi ba kowa, Hajiya ta tafi tun dazu, zan biya na dauko su Anty Amina Kuma". Ai kuwa ta ce "je ka dauko su kawai, idan Akil ko Ahamad sun zo, sai je su dauko mini motata, ko kuma na fita na hau adaidaita sahu". Abbas ya yi sakare yana mamakinta a ransa tare da cewa "Ah adole ita ba zata basu damar ganawa ba, duk da dai bata nuna bacin rai ko damuwa ba. Sai a lokacin Mk ya ce" amma kin san ban son Ahamad yana hawa motar ki saboda ba ya tuki da nutsuwa, Akil kuma yana shago sai dare ya fara jah yake zuwa". Ta marairaice ta ce "Ba damuwa sai na hau adaidaita sahu". "A a bana so kin sani, bana so". Ya sake sassautawa "ya ce ki je ya kai ki, ana idar da Sallar isha ki rufe gidan, sannan ki taimake ni ki sha maganin ki please". Ya fa'da cikin sigar rarrashi da kulawa. Amma ta yi mirisisi ta ki tafiya, lamarin da ya sake dagula lissafin Sa'adah, wai yau a gabanta wata macen take nunawa ta fita son Mk, ta fita kusa da shi. A gabanta shima ya ke nunawa wata macen tattali da kulawa? Wannan shine duniya rawar yanmata. Shirun da Farida ta yi ya tabbatarwa da Mk bata amince bane, ya kalleta a tausashe ya ce "Ban son ki wuce lokacin shan maganin ki ne, gobe idan zaki taho, ki taho da shi, sai ki yi ta zamanki, amma yanzu taimake ni ki je ki kular mini da lafiyar ki". Nan ma ta yi shiru, Mk ya ce "shikenan ai, tunda so kike mu kwanta gaba'daya". Dakin ya yi shiru na mintina uku, Zainab na mamakin irin wannan al'amarin, ta kasa cewa komai duk da bakinta cike yake da tarin maganganu, da suke bu'katar fashin ba'ki. Irin kallon da Farida take yiwa Mk da idanuwanta masu maiko ya sa nan da nan zuciyar Sa'a ta hauro, ta kalli Abbas dake bakin kofa yana tsayawur jiran Farida, amma ganin Sa'adah yasa ta fasa tafiyar dan kar ta samu damar 'dagawa mijinta hankali 😀 Ta ce "Uncle Abbas" "Na'am Anty Sa'adahtu". "Tafiya zan yi, kuma akwai sakon da zan fa'da masa, zo ka ri'ke mini shi zuwa waje na mintina kadan". Da sauri Abbas ya shigo yana cewa "daga nan ma na zagaya da shi, dazun nan likita ya gama ce mini kwanciyar ta yi yawa, ya dinga yin atisaye ko a cikin dakin nan ne". Ya isa jikin gadon ya mikawa Mk hannun, ya dago shi. Ya sunkuya ya janyo masa takalma a a kasan gadon ya saka sannan ya mikar da shi, suka fita a hankali. Zainab ta dinga jin wani irin farin-cikin iyakar da Sa'a ta nunawa Farida. Sun Jima da fita sannan Sa'adah ta dauki handbag dinta zata bisu, Farida ta ce "Gogel ko zaki fitar masa da kujera, jikin nasa ba kwari har yanzu". Da sauri Sa'adah ta saki murfin kofar, ta dawo ta zuba mata ido, sai kuma ta sassauta fishinta tace "Da a ce Sa'adatu Kika kira ni da shi, da ko kula ki ba zan yi ba, sai dai na ce miki to, ko da ba zan yi abinda kika ce din ba, sai dan na nuna miki am matured now. Amma tunda Kika 'Kira ni da Gogel zan tabbatar miki har yanzu waccan Gogel din ce dai da kika sani, Billahillazi ki fita a idona, kada ki sake yun'kurin shiga tsakani na da shi, ko ki nuna mini ga yadda zan yi masa, if not kin dai sani. Ba zai zamewa Iyah Basiru komai ba wajen nuna miki har yanzu ina cikin shekarun da ba a mini kan kara ban yi na ice ba". Daga haka ta juya tana cewa "Zainab zo muje, idan na gama sai mu wuce ba sai na dawo nan ba". Suka fita bayan Zainab ta cewa Farida Allah ya Kara lafiya. Sun zo inda su Mk suke zaune, Zainab ta yi masa addu'ar samun lafiya mai dorewa ta yi gaba, haka Abbas ma ya mike suka basu wuri. Sa'a ta zauna tamkar gaske magana zata yi masa, amma ban da cika tana batsewa ba abin da take yi. Ta tabbatar Farida na hango su ta windo, shiyasa ma da ta zata zauna sai ta juya baya ta yadda ba zata ga fuskarta, ba haka ma Mk bayansa zata hango. Banda son ta nunawa Farida dan taki tafiya ba shine dalilin da zata hanata magana da shi ba, da bata tsaya kula Mk ba, tunda agabanta yake nunawa Farida soyayya har ya na lallaba ta. Dukkansu kowa fishi yake da dan'uwansa, domin ganin ta da ya yi da Khalil ba karamin kidima shi yake yi ba, dan haka, ya danne zuciyar sa ya ki mata magana. Amma dai a kasan ransa sun bashi dariya ita da Farida kwarai da gaske. Mintina ashirin na cika ta tashi ga mamakin Mk ya ga ta mi'ke tana murmushi ta fito da wayarta ta Kira Zainab tana fa'din idan Abbas na kusa ki ce masa ya zo mun gama". Aikuwa sai da Abbas ya zo, ta tafi bata ce da shi uffan ba, sai Abbas ta yiwa sallamah da fatan samun lafiya ga marar lafiya. Mk ya bita da ido yana ganin yadda take tafiya, sai ayyanawa yake yi ko sai yaushe zata daina rikicin gan-gan? Ban da karfin halin Sa'a ya zata zo ta tarar da mace da mijinta, sannan ta ce sai ya fito waje sun yi magana alhalin ba maganar zata yi ba, kawai son rikici ne da son nunawa Farida karfin da take da shi a zuciyar sa. A mota Zainab ta ce "Tabdi yau na ga kishi, ashe haka abin yake?" Sa'a da dama kiris take jira sai kawai ta fashe da kuka. Jikin Zainab ya yi sanyi sai kuma ta ce "Menene abin kukan kuma? Duk irin jarumtar da Kika yi". Ta kasa magana illah kukan da ya ki yankewa, tana ta hararo hannun Mk a cikin na wata a gabanta kuma, tabbas har ta mutu ba zata daina kokawa ba. Da kyar Zainab ta shawo kanta, "kin samu labarin auren Halima next week?" Murya a dakushe ta ce " a a" Zainab ta ce "to ai ke ce kinki shiga cikin group din mu na old girls a WhatsApp". A sanyaye sosai ta ce "Bar ni kin ji, inace ga abin da biyewa 'kawayen ya janyo mini, kina kallon yadda wai magana da Malam ya zama sai an mini iyaka. Ta rushe da kukan da ya sanyaya jikin Zainab, itama idonta ya ciko ta kasa ce mata komai, tana tuki tana taya Sa'adah kuka. Da kyar Zainab ta shanye kukan ta ce "Ai Halima tana cikin bala'i ke har Safinan ma, domin dai saurayin Halima ya ki aurenta ne adalilin wastewarsu suke yi. Dake akwai alaka tsakanin su da gidan iyayen saurayin shine aka masta masa amma ko kadan babu kwanciyar hankali a tare da ita. "Ita Kuma Safina har yau dai bata karbi result dinta ba, kiga dai a bayansu da shekaru masu yawa kika shiga makarantar amma kin kammala kin barta". Aure kuwa shiru kake ji sai dai ana nan ana addu'a. Komai lokaci ne. Amma su kam hakkin kashe aure ne ya saka suka kasa samun nasu auren". Cikin kuka sosai Sa'a ta ce "Tabbas su Halima sun yi wa rayuwa ta illah, Amma kuma ai da gudunmawata, yarda na yi da su, sannan nima ina da tawa matsalar, bayan wadda suka cusa min, kawai iza mini wutar suke yi, Amma ni na hura abata. Dan haka na yafe musu, amma bana fatan mua'amala ta sake hadamu, rabona da su tun ina gidan Malam, in sha Allah kuma rabuwarmu kenan domin tarayya da su halaka ce, na rufe babinsu har abada, dan haka kema daina yi mini maganar su". Zainab ta dinga lallashin Sa'adah da maganganu masu taushi, tana nuna mata, ta yawaita addu'ar sau'kin kishi, itama zata taya ta, sannan yadda ta yi maganar a fita mata da shi waje suyi magana a gadarance, amma ya tashi duk da baya jin da'di ya isa ta gane har gobe ita ke jan ragamar zuciyar sa, sai dai dole ya yiwa Farida adalci domin matarsa ce, dole kuma zai sota. Zainab ta nisa ta ce "Dan Allah Sa'adah ki 'dore da kyawawan dabi'un ki, kar ki bari kishi ya mayar da ke 'yar gidan jiya, kin san dai yanzu ba ke ka'dai bace, kuma Wallahi duk son da namiji yake yiwa mace indai ta cika kishi da korafi, fita fit take yi a zuciyarsa. Ke ce uwargida tunda baki yi wani auren ba, dole ki 'dauki hakuri mai yawa. Ki koyi hakuri da juriya, duk yadda kike da mutum kar kiyi zancen abokiyar zamanki da ita mussaman dangin miji, domin duk ranar da abu ya ha'do ku da su, sai sun zayyane mata komai, a hada da sharri ma, daga nan girman ki ya zube a idonta, itama kuma ta sami damar da zata dinga fa'din munanan dabi'un ki". "Na gode miki Zainab! Na sani ke din mai sona ce ubangiji ya sanya mu cikin masu zumunci dominsa". Sa'a ta fa'di hakan a sanyaye. Zainab ta ce "gida zan ajiye ki, ko gidan Anty Sumayya?". A tunzure ta ce "gidan ubana zaki ajiye Ni, ai Ni da gidanta sai ta neme Ni". Zainab ta yi shiru! ta san tana tofawa baza su rabu cikin da'din rai ba. Wasu daga cikin halayyar Sa'a a jinita ne ilimi ko shekaru ba zai sa ta sauya ba, rikici na cikin abin da ba zata daina ba. A Daren ranar Baba Isa ya dawo asibitin ya fa'dawa Mk ranar juma'ah mai zuwa za'a mayar da aurensa da Sa'adatu, amma ta nemi abarta ta kintsa kafin ayi maganar tariya tunda titsiye ubanta ya yi mata, ba dan tana so ba. Ya ce " Na kuma yi mata wannan laminin, dan haka ba zata tare ba, sai ta shirya, wannan umarni na ne". Baban ya nisa ya ce "Soyayya da sanin darajar Dan Adam ne kawai ya sanya Malam Basiru zai sake baka aure a Karo na biyu! Ka sani da ni da mahaifinka ra'ayin mu daya, shawarar mu daya, hakanan neman kudinmu daya, abin da Zan fa'da maka yau, na tabbatar da yana raye a gabansa zan fa'da maka domin ka sani idan ina waje baya ta'ba nuna shine ubanku yana dora ni akan komai nasa matu'kar anan Kano ne, da bashi da dan'uwan jini. To ka saurare ni da kyau ni na karba maka amanar yarinyar nan, idan har ka bari ta wulakanta ina rantse maka da Allah ni ka wulakanta, na kuma tabbatar idan har ka wulakanta ni, zaka wulakanta Kabiru, hakkin abotarmu ba zai bari ka ga haske ba, ko bayan ba raina, ina maka wasiyya akan yarinyar Malam Basiru domin ni dai banga mai arziki a wannan zamanin irinsa ba, Ubangiji ya bashi wadatar zuciya, ya bashi alheri mai yawa, wadannan kuma sune kololuwar arziki". Da tsananin farin ciki Mk ya ce "Na ji Baba, in sha Allah ba zan sake kunyata ku ba, komai zata yi zan yi ta ha'kuri, zan kara hakuri akan ha'kuri. Ya sauko ya durkushe a gaban dattijon ya ru'ko hannun sa ya ce " Baba ina maka shaida baka watsar da iyalin amininka ba, har yau din nan da tsufa ya cimma maka sosai, baka huta da yi mana hidima ba. Ina yi maka fatan samun aljannar da Annabi ya yi bishara ga masu kyautatawa iyalan wadda suka rasu". Jin wannan albishir din ya sake 'karfafawa Mk jiki, domin zuciyarsa ta yi haske. Washagari da safe aka sallame shi. Ya isa gida bisa rakiyar Dr 'Karfi, tarba na mussaman ya samu daga Farida. 'Karfi bai jima sosai ba ya tafi. Mk ya dinga biyewa Farida na yadda take ina ka saka da shi. Ya fito wanka ya tarar da ta ajiye masa kaya a bakin gado, gajeran wando ne tiri kwata kalar ruwan 'kasa, sai farar riga ti.shet ya fesa body spray ya sanya kayan da ta riga ta feshe su da turaransa na Versace. Tawul din da ya dauro, ya dauka ya rataye shi a bandakin, yana fitowa ita kuma ta shigo dauke da tiren kayan abinci. Yana zaune bakin gado yana kallon yadda ta yi masa shimfida, ta fara zuba masa abincin da ya kasance dankalin turawa da miyar albasa sai gashashiyar kaza, gefe yankakkiyar kankana ce jawur da ita, an lullubeta da ledar rufe abinci. Sama sama ya ci abincin, ya mayar da hankalinsa wurin shan kankana, ya kalleta ya ce "zanga ranar da zaki daina bani lemo da safe". Ta mike da sauri tana cewa"wallahi na dafa maka shayin ga su cups nan flask din na manta". Cikin kankanin lokaci ta kawo masa, da kanta ta zuba masa, tunda ba ma'abocin shan shayi da madara bane. Bayan ya kammala ta 'ballo masa magungunansa ya sha. Ya mike ya ce " Bari na sauka na dan kewaya, bana jin ciwo a tare da ni, amma sam jikina babu karfi". Ta ce "hakan ma babu laifi, ko na dauko maka lucozade it will help". Ya kalleta ya ce "Bari na kewayo dai, so nake mu yamutsa shimfidar can." Ya yi nuni da gado. Kunya ta kamata ta yi murmushi, ba tare da ta sake cewa komai ba. Ya juya ya fita. Hakan kuwa aka yi, domin bai wani jima ba ya dawo, hakanan duk yadda yake jin rashin kuzari, sai da ya zartar da kudirinsa. Duk yadda take ro'kon ya bari ya warware sosai, amma bai ji ba. Sai fa'di yake "kewar ki na yi sosai, har addu'a nake na samu sauki na dawo gida, ba dan komaai ba, sai dan na kasance tare da ke". Da'di ya matu'kar kamata, ta tabbatar tana da matsuguni a zuciyar mijinta. duk dai abin da Sa'adah ta yi mata a asibiti, yasa ta gane har gobe tana da karfi a zuciyarsa. Yini guda bai fita ko ina ba, da aka yi azahar ya ci abinci, ya sha magani barci ya yi sosai. Dan haka bai fita ba, sai a washagari, ya fita zuwa gidan Hajiya, fa'da da Jan kunnen da ta yi masa akan ya ri'ke Sa'a da girma ba ka'dan bane. Fa'di take "ubanta mutum ne har da rabi, ka ji tsoron ubangiji ka ri'ke ta da Amana, na sha fa'da maka ba hankalin ku daya ba". Ya amsa da zai kiyaye. Daganan ya leka shagonsa, ya kuma gaida Baffah. Baffah ya ce "wannan karon ma sadaki kawai zaka bata" Da sauri ya ce "A a Baffah bar ni kawai na yi mata komai, gatan zai mini yawa, yanzu Ina da halin yin dukkan abin da ake yi, na gode sosai da karamci, Ina fatan kar Allah ya sa na sake kunyata ka Baffah". "A a ni ba ka kunyata ni, bare ka nemi tsari da sake maimaitawa, ba komai tsakanin mu sai karramawa, domin tunda kaki fa'dar abin da ya hadaku, kuma kowa ya gane itace mai laifin, sai na gane kai din jarumine, adaline, mai kuma kaunata ne, Koda ha'kurin ka ya kwace amma ai hankalinka bai kwace ba, domin baka tozarta mini Iyah ta hanyar fa'din aibunta ba, dan haka Ni baka mini komai ba, sai alheri." Ya zarce da cewa "a farko da zan baka ita, sai da na jaddada maka kar ka bari ta kangare maka, duk kuma wadda ka ga tana mu'amala da su, hankalinka bai kwanta da su ba, ka shata musu layi, Ina jin dai baka dauki wannan shawarar ba shiyasa kuka tsinci kanku a halin da kuke ciki, ba fa zan rufe ka ba, kaima kana bari soyayyarta na rinjayar ka a gurare da dama, a farkon rikicin banyi magana bane saboda yadda ka boye komai ka sata itama ta rufe komai" Mk da ya san Baffah gaskiya ya fa'da sai ya sunkuyar da kansa kasa, ya kasa cewa komai. Tsawon lokaci kafin Baffa ya sake cewa "Na horeka da yin adalci a gidanka, ka yi iyakacin bakin kokarinka, ka yi adalci, sai kuma ka barwa Allah ya taya ka. Domin a yanzu ma ina sake fa'da maka duk abin da bai maka a tare da Iyah ba, tun kafin ku yi nisa ka taka burgi akansa, su mata da ka gansu idan ba a kula da tarbiyar su ba, nan da nan zasu halaka kansu su halaka mazansu". Jikin Mk ya yi sanyi, domin kuwa a kullum dabi'un Baffah na fahimtar da shi bai gama saninsa ba, har yau din nan bai ci karo da mutumin da ya fi mahaifin Sa'a karamci da fadar gaskiya ba, ko da kuwa gaskiyar akan kansa ne. Mk da ya rasa mai zai ce sai kawai ya sunkuyar da kansa kasa ya ce "Madallah da zuciya irin taka, dama ka sha fa'da mini ba Sa'a ce ta hada mu ba, ba kuma zata zama dalilin rabuwarmu ba, tabbas na gasgata hakan". Mk ya zarce da fa'din " Alherinka yawa ne da shi Baffah! A duk lokacin da nake gabanka sai nake jina tamkar ina cikin shekaru irin na Jawad. Saboda zuciyata tana samun nutsuwa, domin tana tare da wadda yake girmamata, yake ganin kimarta. Kai ka'dai ne baka ga laifina akan kaddarar rabuwarmu ba, Kai ka'dai ne ka yi mini shaidar fin 'karfina al'amarin ya yi, haka kai ka'dai ne a duk tsayin wannan tafiyar bai juya mini baya. Haka nan yanzu kowa jan kunne yake mini akan na rike Sa'adah komai zata mini na yi hakuri, kar na ce komai. Kai ka'dai ka ce na yiwa 'daya matar tawa adalci, kai ka'dai ne ka ce kar na yi hakuri da Sa'adah a inda zata kuskure ko ta sab'awa ka'ida. A yau na sake ganewa kai din ba uban Sa'adah bane nawa ne" Ya yi shiru saboda yadda yake jin rauni na shigar sa, ko mutane nawa ne irin Baffaha a Yau? Ya tuna kwanakin baya yadda ya zaunar da shi yana fa'da masa tsananin son da yake yiwa Iyah! Amma a yau ya ture wannan soyayyar ya fa'di gaskiya, ayiwa Farida adalci, kar kuma ya bawa Sa'a damar da zata halaka, ta halaka shi. Ya dago idansa da suka ka'da ya ce "Baffah kwanakin baya ka ce mini baka ta'ba mallakar abin da kake so kamar Iyah ba". "Eh" Baffah ya amsa a taikace . Mk ya ce "Nima yau zan fa'da maka ban ta'ba son wata mace a duniya kamarta ba. Zan yi iyakacin kokarina na dauki shawararka na kar na bari ta halaka mu, Amma fa'da mini maganin rikicinta Baffah! Ita din sarka ce mai rikicin gan-gan". Dariya ya yi ya ce "ai ba zata daina ba, Amma ina tabbatar maka zata rage da yawa daga cikin rikicin nata mussaman na dogon buri da kawaye yan karya domin ka shayar da ita mamaki. Abin da na san ba zata daina ba, shagwaba, saurin kuka, da kishi. Wannan kuma kaine zaka kiyaye motsuwar kishin, shagwaba da kuka kuwa idan ta yi ai sai ka rarrashi abarka". Kunya ta kama Mk ya kasa cewa komai Sosai ya yi godiya sannan ya mike yana cewa "Makaranta zan tafi". Da sigar tsokana Baffa ya ce "Ba zaka leka ku yi tozali ba?" Kunya ya ta sake kama Mk ya ce "Ai mun yi fa'da Baffah, ba zan nemeta ba, sai ta neme Ni". Dariya sosai ya yi tare da cewa "Anya kuwa ka yi gaskiya Mutari? Amma dai ba ruwana". Ko wayar Sa'adah bai nema ba, bare ya je gidan wurinta, ya wuce makaaranta. Sa'adah ganin kwanaki biyu da sallamo Mk amma bai nemeta ba, ya sake hauhawar fishinta, yayin da shima fishin yake yi da ita mai tsanani, kawai ya samu salama ne na tabbacin zata dawo hannunsa, amma ganinta da ya yi da Khalil ba 'karamin haushin ta ya ji ba, kullum da aikinta yake kwana, yake tashi tunda shine sanadin da yasa take mua'amala da ahalin Khalil. Kwanaki uku ya rage daurin aurensu amma babu fahimta a tsakanin su lamarin da yake ciwa Sa'a tuwo a kwarya, wani sashi na zuciyarta ya ce saboda yana da wata matar ne, wani sashen kuma ya kore wannan tunanin tare da tuno mata, tana budurwa ma haka ya dinga Wannan wula'kancin har ta yi zaton soyayyar ne bai iya ba. A daren Mk na zaune a falon sama yayin da Farida ta yi filo da cinyarsa, yana wasa da dogon gashinta tamkar mai yin kitso, sai fama yake da bugun zuciya adalilin yana son fa'da mata, juma'a mai zuwa daurin aurensa da Sa'adatu. Sau uku yana yun'kurin fa'da sai ya kasa, da 'kyar ya yi kundubalar cewa " My ferial tashi ki zauna magana zamu yi da nake bu'katar nutsuwar ki'. Ta tashi da sauri kuwa, ta zauna sosai tana fuskantar sa. Cikin karfin hali ya ce " Ranar juma'ah mai zuwa idan muna cikin rayayyu, za'a mayar da aurenmu da Sa'adah". Wani irin tashin hankali ya ziyarci Farida, irin wadda bata ta'ba hasashen zata ji shiga ba, ta dinga yun'kurin bude baki ta yi magana amma hakan ya gagari Kundila. Ta dinga karanto addu'a, amma duk da hakan sai da hawaye ya goce mata, wani irin tukuki ya mamaye zuciyarta, ta dinga jin tamkar ta mutu ta huta. Da sauri ya janyota jikinsa ya rungume sosai, ya dinga fa'din sorry a hankali, wannan rarrashin ya sanya kukan ya kwace sosai, ta dinga yi, shikuma yana saka tissue yana goge mata. Ta jima a hakan, sannan ya ce "Ya isa haka, Yi shiru ki fada mini menene ya kidima ko haka". Cikin kuka ta ce "Tsoro nake ji kar na rasaka, tsoro nake ji kar juya mini baya, tsoro nake ji kar ka kasa yin adalci ka halaka". Cikin rarrashi sosai ya ce "Na ta'ba fa'da miki ba macen da zata sa na rabu da ke saboda ita, sai idan tamu ce ta hado mu, ba yadda za'ayi na juya miki baya Farida! Ina mamakin har yanzu da muka yi shekaru uku baki fahimci iri son da nake miki ba zai tan'kwabu bisa 'karamin dalili marar tushe ba. Ba zan miki 'karya ba, da gaske an jarrabeni akan Sa'a! Amma ki taimake ni ki fa'da mini shin ina miki wani abu da kika kasa gamsuwa son da nake mata, ba zai hana na so ki ba" Ta yi shiru tana ajiyar zuciya! Ta sani bai ta'ba mata wani abu da zata ce baya sonta, ko ya tauye ta ba, amma da ace zata iya da ta ce so take ya fi sonta akan Gogel, sai dai ba zata iya ba, shima kuma bata jin zai iya hakan, tunda ta san ubangiji ne yake cusa soyayya a zukatan bayi. Ya sake rungumeta tsantsan ya ce "fa'da mini mana ke nake sauraro" Ta girgiza kai ta ce "Babu" Ya ce "Zan fa'da miki gaskiyar magana! Wallahi ina sonki, Ina tsananin sonki, hakuri da kawaicin ki ya 'kara miki 'kima a idona da zuciyata, kar ki bari kishi ya kwace miki wadannan halayyar, domin kina jan hankalina da su, ina jin kunyar bata miki. Sannan zan ro'ke ki arziki! Ki bani hadin kai ta yadda zan yi muku adalcin da zaki gamsu, idan na kuskure dan Allah ki mini uzziri wallahi ba zanyi abin da muzanta ki da gangan ba". Ta saki ajiyar zuciya taare da cewa "To". Ya dinga yi mata maganganu masu da'di, Wanda wasu ta tabbatar ya fa'da ne dan hankalinta ya kwanta amma dai ta ji da'di kwarai da gaske, ta samu sau'kin daurewar da kirjinta ya yi. Ya kalli agogo ya ga har sha'dayan dare ta gota ya mike da ita cak tamkar yar jinjira ya shige daki da ita ya dire kan gado ya ce"Ashe ma fafaloloce ba nauyi" Ta dan murmusa kadan ba tare da ta ce komai ba. A haka ya dinga hilatarta sai da ya raya daren da ita cikin wata irin soyayya mai tsayawa a zuciyar mace. Har ranar daurin aure ta zo ba wani jituwa tsakanin Mk da Sa'adah. Ranar juma'ah 15/7 aka sake daura auren Mukhtar Kabir Bichi da Sa'adatu Bashir Gogel akaro na biyu akan sadaki Mai darajah. Sai yamma suka baro Gogel, duk yadda Mahmoud ya so suje gun amarya Amma Mk ya ce ba inda za shi. Dr 'Karfi ya kalli Dr Mk da ya yi kicin kicin da fuska ya ja tsaki ya ce "aikin kawai duk wani cin magananinka na 'karya ne, wato yanzu ka sami kwanciyar hankali shine zaka hau wani fiffika, to dan ma dai tsiyar Sa'adah ta fi taka, yanzun nan zata sumar da kai, farfadowa sai a gadon asibiti". Fuska a daure Mk ya ce 'Tunda ba a lahira zan ji ni ba, ai da sau'ki, ka takura ni fa ". Da dariya 'Karfi ya ce wallahi ka bini a hankali ka san ina da dorinar da idan na zuba maka sau uku, amarcin da kake rawar jikin zaka sabunta shi ba zai yiwu ba". Dariya ta kwace musu dukkansu Mk ya guntse ya ce "Na rantse kuwa da ba zan yarda ba". Har suka rabu caccaka Mk yake sha a wurin Mahmoud. Washagari da hantsi Mk ya yiwa Sa'adah siyayyar komai na amfani, karon farko da shi a karan kansa ya siya ba wai Jawad ya saka shi akan dole ba, ya tuno sadda take cewa idan ya sake yi mata wani abu na alheri ba zai gama da Hajiya lafiya ba. Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya yana ayyana banda zuciya ba a ganinta bare a hukunta ta ai bai kamata zuciyar tasa ta zarme akan soyayyarta haka ba. Ya nisa a fili ya ce "Albarka cin Baffah na yafe wannan maganar". Amma haushin ganinta da Khalil da kuma tariyar da ta ce ba zata yi yanzu ba, ya matu'kar bata masa rai, shiyasa kullum ya yi sallah sai ya roki ya samu dalilin da itace zata nemi ta tare da bakinta. Ya cika mota da kayayyakin ya nufi gidan su Sa'adah. Domin ya kai mata ,tunda yanzu ta rataya a wuyansa, duk da ita bata da niyyar sauke nasa hakkin da ya rataya a wuyanta. Surayya Dahiru ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *GAISUWA GA*. *Haj Zulaihatu Sani Kagara* *Haj Maimuna Beli*. *Hassana 'Danlarabawa*. *Ku Dade, ku yi 'karko irin na Dabino*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 107-108. Sannu a hankali yake yin tuki, har ya isa gidansu Sa'a. A zauren kofar gidan, ya tsaya, ya fito da wayarsa, ya dinga 'kiran layin Sa'adah amma tana gani ta yi mirisisi, yana tsaye Baffah ya shigo, suka gaisa ya ce "Ya ka tsaya shigo mana". Tare suka shiga cikin gidan, Inna ce a Zaune tana kwadon zogale. Mk ya zauna a gefen tabarmar da Baffah yake kai, ya gaida Inna! ta amsa ba yabo ba fallasa. Cikin nutsuwa Mk ya ce "Inna ina neman afuwarki, na sani ni mai laifi ne, amma tunda ubangiji ya sake hadamu ina rokon ayi mini hakuri, bana jin da'din yadda kuke mini ke da Hajiyar Bichi". Kunya ta matu'kar kamata, ta dinga jin wani iri, da kyar ta yi kundubalar cewa "Ni ba fishi nake yi ba, Allah ya kiyaye gaba, yasa albarka a aurenku". Da'di ya yi matu'kar kama Mk, ya yi ta godiya. Baffah ya ce "Idan ka zo, ka dinga shigowa, ai yanzu ba maganar tsayawa a zaure, Ina fatan ku kammala shirin ku da sauri ta tare hankalin kowa ya kwanta". Innah da ta gama 'kwadon ta zubawa Mk, ta kai na Baffa dakinsa sai ta yi shigewarta daki, yayin da Baffah shima ya fita yana cewa Mk "shiga tana ciki, bakam ta yi". Ya shiga dakin ya sameta a zaune cikin kwalliya tamkar ya yi mata waya zai zo, ta yi masa kwalliyar. Ya zauna yana shakar kamshin turarenta, ya kalleta, ya na tuna sadda ta zo wankan haihuwar Jawad irin soyayyar da suke fakar idon Innah suke yi a dakin, amma yanzu ba wani farin-ciki a tare da ita, asalima tunda ta amsa sallamarsa bata sake yin magana ba. Ya daure ya hadiye komai ya ce "Barka da lokaci" A hankali ta ce "Barkan mu dai". Ya nisa ya ce"Tsakanin ki da Allah ya kamata ace anan kika wayi gari? Komai mutum zai yi ya auna abin nan a mizanin hankali da sharia, saboda kawai ki kuntata mini kika cewa Baban Na'ibawa sai kin shirya zaki tare dan Allah ba ki ji kunya ba?" Ta yi masa banza, abin da ta san ba ya so. Bai yi fishi ba, ya sake cewa wanne shirin zaki yi? Ki tashi kawai mu yi tafiyar mu, ke kanki nake so ba wani shiri ko kwaskwarima ba, har yau ina kallon ki a little Sa'adah dalibar FGC Kano". Ta tura baki gaba amma ba ta tanka ba. Ya sake yin kasa da murya, ya ce " Kin amince na kira Baban Na'ibawa a waya ki fa'da masa kin yarda zaki tare yau? kawai sai mu yi tafiyar mu da waccar katifar da kike ta ajiye da ita. Zan dai siyo miki wata, tunda naga har yau din nan tana cikin abubuwanki masu daraja". Ta hango katifar da take saman wadirof a 'daure wadda ya siyo mata ne tun shigar ta FGC a lokacin ma basu san juna ba, amma ta ki yarda a bayar da ita, ta kafe tana son abarta. Ya taya ta kallon katifar da ba abin da ta yi, tunda ta da ce mai aminci. Ya ce "ya kamata mu tafi da ita, ko akanta ubangiji zai sai a samowa Jawad kani ko kanwa". Ta dauke idonta daga kallon katifar ba tare da ta ce 'kala ba. Ya matsa kusa da ita ya ce "pls Sa'a zuge mini zip din rigar nan, ina son ganin kirjin ki, just gani zan yi, I won't touch it" . Ta mike ta koma kan wata kujera da take dakin, ta juya masa ba, tabbacin ba zata yi ba kenan, zuciyarta sai hango mata take Allah 'dai ya san me ya yi da wata matar kafin ya zo nan, yana mata maganganu na rainin wayo da dasa ciwo a zuciya. Ya nisa ya ce da alama, dukkan hardship din nan da muka yi going through bai zame miki iznah ba. saboda kawai kina da masu daure miki gindi ana dannata, abin da baki sani ba, indai har kika ce zaki cigaba da yi mini taurin kai wallahi zan yi dealing din ki with iron hand". Ta ce "Ai daman na san ba abinda da zan kwasa a hannunka sai ba'kin ciki, na ce bana sonka, bani da burin aurenka amma an matsa mini". Kuka ya kwace sosai. Cikin kuka sosai ta ce"Idan ina sha'awar auren mai mata Allah ya tsine mini. Amma saboda ka fini a wurin Baffah ya mini fin 'karfi, ni an cuce ni, gaskiya angama da ni". Jikinsa ya yi mugun sanyi, amma ya waske da cewa "Da gaske ba kya sona? To Ki yi hakuri son da nake miki ya isa ya ri'ke mana auranmu". Bata tanka ba, haka bata daina kukan da take yi ba. Ya ce zo muje ki raka ni unguwa, daga nan mu biya, mu yi lunch a restaurant din Royal Tropicana, mu tuno moment din mu na baya". Ta 'kara sautin kukanta ta ce "sai dai ka je ka dauki Farida kuje Tahir sai ka fi shaukin tuna bayan. Ni kuwa me zaka yi mini na ga haskenka? ai babu shi, iya tozarci ba wadda ba ka mini ba, ina cikin bala'i amma ka iya daukar wata macen ka tare da ita a hotel, sannan har ka iya ce mini wai sai ka tuno ni kake gamsuwa". Ya matu'kar firgita da kalamanta, ashe. duk motsinsa ta sani? Ya kalleta a kidime ya ce "waya fa'da miki wannan maganar?" A hassale sosai ta ce "wadanda suka ganku, masu son na kalli yadda ka tattara ka yi wurgi da ni da dukkan al'amarina. Masu son na cireka a raina, na daina ganin idan babu kai ba zan iya rayuwa ba, domin kana can kana more rayuwarka da wata macen, ahalin ni ina shirin zaucewa adalilin ka". Ta yi shiru tana shesshekar kuka mai ha'de da gunji mai cin rai. Tausayinta ya maye gurbin takaicinta da yake ji, ya dinga jin komai ya narke na laifukanta a zuciyarsa, ya sani ita din mai tsanani kishi ce akansa, tamkar yadda yake tsananin kishinta. Ya sani kishin Farida ne yake yagalgalata mussaman da bata samu damar amayarwa a lokacin auren ba, ta bar abin a zuciyarta yana cinta. Ya numfasa yana jin sonta da ya makale a kasan zuciyar sa yana ta tunkubowa yana mamaye kowanne gurbi da sako na cikinta, sai shine yake ta kokawa cikin jarumta kar son nata ya mamaye har inda Farida take makale. Ya sassauta ya ce "mu yafewa juna hakanan, zukatan mu sun wahala, gangar jikinmu sun yi kewa ba ka'dan ba, pls My dear Sa'adah let gone be by gone". Har ranta ta ji da'di, dan haka ta sassauta kukan ta sa hannu ta dauko, tissue ta fara goge fuskar ta. Ganin ta rage kukan, ya nisa ya ce "muje ki yi shopping din kayan kwalliya". Ta girgiza kai tare da cewa "ina da su". "To muje ki raka ni, na gaida Aunti Sumayya, na bata ha'kuri ta daina watsi da al'amarina, tunda mun shirya ta yafe mini". "Ba zani gidanta ba, sai ta neme ni". Ya yi shiru, amma jikinsa wani irin bari yake yi, ba abin da yake so irin ya jita a jikinsa, so yake ya samu dalilin da zai rungumeta, ya yi kissing dinta, ya yi sucking harshenta da yake jin zakinsa har cikin kwanyarsa. Sannan yadda ta yi masa magana cikin kwanciyar hankali ya sake sa shi nisha'di ya dinga kallonta yana jin tamkar ya tabbata a hakan. Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "Sa'adah" Bata amsa ba, haka nan bata dago ta kalle shi. "Sa'adah! Sa'adah! Sa'adah! Sa'adah". Haka ya dinga kiran sunan ba adadi, tun bata jin komai, har abin ya dinga ratsa jikinta , ya na saukar mata da dukkan kasala, yana kuma tuno mata al'amura masu yawa da suka shude. Ta sani idan yana mata irin wannan Kiran cikin laushin murya, to ya kai kololuwar gajiya da son ta daina fishi da shi ne, hakanan ya kai ma'kuran wurin son su shirya, sannan a matu'kar matse yake da ita. Ta sake zurfafa tunani, tana tuno idan yana mata irin haka, ita kuma sai ta yi bakam, har sai kiran ya huda dukkan sassan jikinta, ya saukar mata da matsanancin begensa, kawai sai dai ta tsinci kanta da yi masa kukan shagwaba, tana dirza kafafuwanta. Yayin da shi kuma ya ga hakan ya san ya riga da ya gama kunnata shikenan, sai ya sa dukkan karfinsa ya ru'ko ta, ya bita da kisses da maganganu masu nauyi, tun tana zillewa har sai ya gwada mata, bada ha'kurinsa ba dai macen bil'adama ta tankwabar da shi ba, saboda tsananin dadinsa da shauki mai makalewa a kwanya da zuciya. To a yauma hakan ta tsinci kanta, tunda ya 'kira sunan ta ana goma shi takwas, shikenan ta ji wata irin kewarsa na yi wa gangar jikinta wani irin kutse mai karfin gaske, ta fara mutsu mutsu. Yana kallonta, Yana jin da'din yadda ya fara samun lagonta dan haka ya sake lankwashe murya ya cigaba da 'kiran ba kakkautawa. Zuciyarta ta yi laushi tubus, ta sami sau'kin nauyin da ta yi adilin kishi, domin ta gasgata shi da ya ce har yanzu shine bai canja ba, ba kuma abin da ya ragu na soyayyarta a zuciyarsa. Cikin muryar tabarah ta zallan shagwaba ta ce "Haba Mana, Inna ta na cikin gidan nan fa! Ni dai ka daina, na amsa Na'am, Na'am Na'am". Ya zuba mata idanuwansa da suka kada tamkar ya tashi daga barci ne. Murya ba amo ya ce "Ba zan boye miki ba, sha'awar ki nake ji sosai, tunda muka rabu nake fama da matsanancin ciwon kai da mara, sosai na sha wahala a farkon shekaru uku da rabuwarmu, a lokacin da nake Uk, na sha zarya a gaban manyan likitoci, suka tabbatar mini rashin mace a kusa da ni ne dalili. Da na yi aure na samu sassauci, baya tashi sosai, ko ya tashin ma baya takura ni sosai, amma wallahi Sa'adah, tun ranar da muka kai ki gidan Anty Sumayya nake Jin alamun ciwon na neman takura ni, jiya ko runtsawa ban yi ba, adalilin yadda nake jin ciwon da marata take yi, ga gangar jikina taki sarrafuwa domin ba abin da take so ya rabeta sai ke". Ya bu'de dukkan hannuwansa yadda yakee mata tun fil azal, da rawar murya ya ke fadin "come closer to me my dear"! Kishin yadda ya tabbatar mata, bayan ya yi aure ya samu sau'kin ciwonsa, ya sake sawa ta hargitse. A tunzure ta ce "ka gaggauta tafiya ka rungumi wadda ta kwantar maka da ciwon rashin mace da ka yi fama da shi a baya! Wai kwana ka yi baka yi barci ba, kwana ka yi dai kana rarrashinta, kana kasheta da soyayya amma saboda ka mayar da ni bitacan shine ka karkace baki kana fa'din min tatsuniyar da ko Jawad yasan 'karya ne tsagwaronta, 'karya kawai". Jikinsa ya yi sanyi, tabbas gaskiyar Baffah ne akwai abubuwa da yawa da Sa'a ba zata canja ba, domin a jininta ne, gashi dai a zahiri hankali ya shigeta, ilimi ya ratsata, Amma kishi yasa agabansa ta karyata shi, ba shayi ko shakka. Wanda shi kuma ba zai ta'ba yarda ya sake daukan kaifin harshenta ba, a yanzu da take shekaru talatin da biyu. Ya mike ya ce "Ni ne mai fa'dar tatsuniyar karya? Ni Kika karyata, nine makaryaci?" Ta saci kallonsa, ta ga yadda ya bata rai sosai, ta yi shiru tana jin guiltiness na kamata, amma ta kasa bu'de baki ta ce masa sorry. Ya kada kai ya ce "Tabdi jam ashe kuwa da sauran ki". Dai dai lokacin Inna ta fito tsakar gida taga zogalen da ta ajiye wa Mk, yana gurin dan haka ta bude baki ta ce "Iyah zo ki daukar masa zogalen nan mana, nasan shi da son zogale". Farin ciki ya mamaye Mk! Ba dan komai ba, sai dan sassaucin da yake gani tare da Innah. Da azama ta amsa, ta kuma mike ta fita duk a kokarinta na kar Inna ta zargi wani abu. Ta dauko ta ajiye masa a inda yake tsaye, kamshinta ya cika masa hanci, da ta sunkuya ajiye masa zogalen, ya ga yadda siket din jikinta ya matu'kar fito da taswirar mazaunanta, sai ya matu'kar kidima, ya dinga kokawa da zuciyarsa domin kuwa, ba zai sake kulata ba, har sai ta bashi ha'kuri. A kausashe ya ce "juye mini a leda sai naje gida zan ci". Ta sake juyawa ta fita! Tana jin tamkar ta bashi ha'kuri ya fasa tafiyar, ta sani badan maganar da ta fa'da ba, da sai anyi kiran sallar azahar da ya tafi, haka Kuma zai ta zama yana rarrashinta da son ya jagwalgwalata. Amma yanzu zai tafi gurin matarsa, ya barta da kewa da bacin ran zuciya. Ta hango shi ya zaunar da Farida a cinyarsa yana bata zogalen a baki, tunda ta san shi da son dora mace a kan cinyarsa. Tana juye masa a ledar ta ri'ke, ta kasa bashi, kawai ta saka masa kuka. Ya yi sakare yana kallonta, yana ayyana ko sai yaushe zata daina kukan banza marar dalili, ya sani tafiya gida da ya ce zai yi ne ya mata ciwo. Tabbas kishinta ba zai bari su yi amarci mai da'di ba, ba zai bari su rayu cikin farin-ciki ba. Shikuma ya riga ya kudire duk runtsi ba zai rabu da FARIDA ba, zai yi kuma dukkan kokarinsa ya ga bai tashi a sahun masu shanyewar barin jiki ranar gobe ba. Wahala ne dai zasu dandana shi da ita tunda idan ranta ya baci, ko idan ya ganta cikin rashin nutsuwa shima hakan zai zama marar nutsuwar. Domin ya tabbatar itace jagorar farin-cikinsa. Ya daure ya kore raunin da yake neman sawa ya fasa tafiyar, ya kalleta sosai ya ce "Zaki san kin ce mini makaryaci, na rantse miki sai na miki abin da gaba idan zaki mini magana, sai kin tauna harshen ki sosai. Godài godài da ke amma lafazinki na yara 'kananu, ko Farida ai ba ta mini irin wannan iyashegen". Ai kuwa ta fàdi kan shimfidarta ta fashe da kuka, tana cewa "Na gode da cin fuska, kullum sai ka mini gorin na tsufa, saboda kawai na haifar maka Jawad! to wadda kake yiwa kallon 'kuruciya saboda Ubangiji ya jinkirta mata haihuwar ta girme ni da shekara guda, domin ina Sha bakwai na kammala sakandire, ita kuwa Sha takwas cif. Amma saboda son sai ka nuna itace mai daraja shiyasa kake bata kuruciya, ni ka maida ni tsohuwar mace, to koma menene dai, kai ka zuke mini komai, sannan daga kai har ita dukkanku kun girme mini". Ya Galla mata harara tare da cewa "Sokuwa marar wayo kawai, wacce ba abin da ta iya sai kaifin harshe da kukan banza". Ya juya ya fice, bayan ya dauki wayarsa a inda ya tashi, ya barta tana kukan banza nata. Sai da ya yiwa Innah sallamah, sannan ya fita. Ya fito ya bu'de but din, ya samu almajirai biyu, ya dinga basu kayan suna shiga da shi. Sai da suka kammala ya basu dari biyar ya ja motar sa ya yi gidan Hajiyar Bichi. Ya isa ya tarar da Hajiya cikin Shirin fita unguwa, ya zauna ya gaisheta, ta amsa da murmushin da ya jima bai ga ta yi masa irinsa ba. Ya murtsike kunya ya ce "Hajiya ki yiwa 'yarki magana, tana nemana da jidali, ta fa'dawa Baban Na'ibawa ba yanzu, zata tare ba, saboda Allah wanne shiri zata yi? Tunda tana jin maganar ki, ki mata magana, wannan ai tsokanar shari'a ne, an daura aure mace ta cigaba da zaman a gidansu". Hajiya ta daure fuska sosai! Ta zuba masa ido na tsawon lokaci, shikuma ya sunkuyar da kansa kasa, ba dan ya yarda ya yi laifin da take masa kallon tuhuma akansa ba. Ta nisa ta Nuna kanta ta ce " Ni ka zo kana fa'dawa wannan maganar? Shi Babanku kana jin nauyinsa, kana ganin mutuncinsa shiyasa ka kasa cewa komai a gabansa, sai ni da ka raina zaka zo ka yiwa rashin ta ido?" Ya kuwa maze ya ce "To ni ya zanyi ne? ni wallahi ki yi magana, bana so a kaini bango, ban so na fusata, dan kuwa komai yana iya faruwa". Mamaki ya kamata, ko da yake a halittar maza ne, idan suna son abu idonsu rufewa yake, ta yadda zasu iya murje kunya su yi abin da za'a dauki shekaru ana Jin nauyin abin da suka yi din". Ta rasa inda zata sa ranta don kunya, domin kuwa ta gama gane tsananin zakuwar da ya yi ya kebe da Sa'a. Amma sai ta ce "To tashi ka fitar mini, ai kaga fita zan yi". "Kwanciya zan yi, na huta, ki je ki dawo, bana Jin da'di ne da na Kai ki, ko ki zauna na Kira Abbas ya kai ki". "Wallahi ba zaka kwanta mini a gado ka mini sake sake ba, ko kunya ba ka ji, ko Jawad idan yana kwance wataran takura nake yi, bare kai, baka tashi zuwa mini sai ka yiwa yarinyar arziki rashin kyautatawa. Dan kawai kasa na ga bekenta, to nikam har yau banga laifin Sa'a ba, sai nauyinta da nake ji". Ya mata shiru ya dauki ledar zogalensa ya fice, tunda ta riga ta rantse ba zai kwanta ba. Ya fita yana fa'din "Na tafi Hajiya, Sa'a ta ri'ke ki gam, ta tattare komai a gunki, ai shikenan, nima sai na hada kai da Farida baiwar Allah". "Komai zaka fa'da, ka fa'da ni Farida bana ganin laifinta, bata mini komai na laifi ba, Nima kuma na sani bata kuka da Ni, sai dai kuma ko kai wallahi baka fi mini Sa'a ba". Ya fita yana cewa "ai shikenan sai ta zuba ruwa a kasa ta sha, ta nema ta samu fitinanniyar yarinya kawai". **** Sai da ta aka yi sallar la'asar sannan suka bude kayayyakin da Mk ya jido Mata, wadda kayan shayi, da sabualan wanka mai tsananin gyara fata na *OLAY* *(quench)* ya hado mata setin su har da bath gel dinsa, da mayukansu. Sai kayan ciye ciye na gwangwani kala kala tamkar zata bude kanti. Indomie da kwai suma ga su nan birjik. Inna ta yi galala ta ce " ban gane wannan siyayyar ba, kuna nufin haka zaku zauna, ba za ki tare ba? Dan na ga wannan kayayyakin yana nuna cewa ba yanzu zaki tare ba". "Eh Innah ni na ce ba yanzu ba, domin ai ban shirya komai ba". Ta nisa ta ce " Kika yanke hukunci babu shawarata, ko ta Yayarki saboda kawai kin zama uwar kanki! Ki sani to ba dabara kika yi ba, tunda an riga an daura aure, ai ba abin da shari'a bata bashi dmaa ba, bijirewar umarninsa kuwa ai kin san yana nufin tsinuwar mala'iku ne akan ki. Haka kawai sai kin janyowa kanki ya gama zumudin ki, a titi, ke dai naga sadda zaki yi aiki da lura". Kunya ta kama Sa'adah! Amma ta waske da cewa."To yanzu Inna sai a sake kai ni ba kayan d'aki alhalin yanzu Ina da kishiya?" Ta fa'da a shagwabe. Dake Innar mace ce nan da nan ta yarda da ra'ayin Sa'a na bai kamata ta je babu kayan d'aki ba alhalin tana da kishiya diyar masu kambun susa. Ta nisa ta ce " Bari Baffan ku ya zo sai a siyar da dayan filin da ya rage, sai ki hada da albashinki na watan nan tunda ya raba tsakiya, ki yi abida ya sauwaka ayi tariyar nan cikin girma da arziki". Ta turo baki gaba Inna ki bari dai nan da wata uku, kinsan ai na ce na barwa Baffah kyautar filin, yanzu kuwa ai ba zan koma na ce na fasa ba". To kayan Baffanki ai naki ne, Ina jiye miki tsiyar namiji Iyah! Muutar din nan fa na riga da na gane shi bashi da kunya ko ka'dan, ba abu mai wahala bane a gidan nan ma, ya yi abin da ya ga dama tunda Baffanku ya daukake shi ba ka'dan ba". **** Kwanakin mako da zuwan Mk wurin Sa'a har yau bai sake zuwa ba, bai kuna yi mata waya ba, abin da yake ta cin ranta kenan, ya sake tunzurota, idan bata tare ba, ai dai tana da hakkin ya duba lafiyarta, wato ya kawo mata kayan abinci saboda ita ci kawai ta sani da kwalliya. A na cikin haka wata waki'ar ta kunno a jahar Sokoto inda aka samu matasa sun kasa ha'kurin hukuma ta dauki doka, saboda an tabowa musulmi inda basa iya ha'kuri matu'kar aka tabo wannan matsayin. Dukkan hankalin musulmai a tashe yake an zuba ido, an kasa kunne domin aga irin hukuncin da za'a yiwa wadannan matasa. Kungiyoyin musulmai kashi daban daban sai kiraye kiraye ake yi akan akaiwa matasan nan dauki. Kungiyar lauyoyi musulmai reshen jihar Kano ta bawa wadanan matasa lauyoyi hamsin da suje su harci zaman kotun da za'a yi a gata, su kuma basu kariya. Cikin wadanda aka tura har da Sa'adah. Baffah da Innah sai murna suke yau ga yarsu zata je ta kare martabar Ma'aiki, ilimin Iyah bai musu da'di iri a wannan karon ba." Da murna Baffah ya ce " yaushe zaku tafi?". "Jibi zamu tafi, dan mu sami zaman kotun, tunda gata da sassafe za'a fara shari'ar". "To ki 'Kira mijinki, ki sanar da shi, tunda dai ba zaki yi tafiyar bai sani ba". Ta amsa da to badan ta so ba. Tun yamma take kiransa yana gani, amma ya yi biris, bai dauka ba,sai bayan magariba wadda hakan ya sake fusata, Sa'a ta botsara.😄 Ya dauka, amma ta yi shiru, sanin da ya yi dabi'arta ce ba zata fara yi masa magana a waya ba. Sai ya ce "Ina jinki, na ga 'kiranki rututu, kin gama mini shirin ne, na zo na dauke ki.?" Ba'kin ciki ya tokare mata wuya, wato shi a haka ya barta ma? Ta daure ta ce "Dama Sokoto zani". "Sokoto zaki je?" "Eh" ta amsa a ta'kaice. "To ba zaki je ba". Daga haka ya kashe wayar ya barta da waya a kunne. Ba'kin cikin da ya turniketa ba'a magana. Hawaye ya kwace mata. A hakan Baffah ya shigo ya sameta, ta fada masa abin da Mk ya ce. Baice komai ba, ya fita waje. Ya 'Kira Mk a waya, ya ce "lallai ka zo ina nemanka". Mintina ka'dan ya iso tunda dama yana cikin shagonsa. Ko gama gaisawa ba su yi ba. Baffah ya ce "Iyah ta ce wai ba zata je sokoto ba?" Ya sauya fuska ya ce "Eh haka na fa'da mata Baffa?" Ai kuwa Baffah ya dauki salati yana fadin "Lallai kuwa, ka bani mamaki, ana tsayawa garabitin mutane a gaban shari'a, balle a taba janibin Ma'aiki. Ai kuwa shine mafi tsayawa a kare darajarsa." "Da wata irin murya mai nuna mutun na wurin da zai yi shagwaba son ransa. Mk ya ce "Baffah sanar mini fa kawai ta yi, ba wai izini ta nema ba". A wannan karon ko ka'dan Baffa bai karbi uzzirin Mk ba, kawai umarni ya bashi akan lallai ya barta taje ta wakilce su, wurin bawa Ma'aiki kariya. "Shikenan Baffah zata je, amma ban yarda ta yi tafiyar nan cikin kungiya ba, ta jira zan zo na kaita, idan sun kammala na dawo da ita" "Yauwa Ubangiji ya maka albarka, ya kore shaidanun da suke ta tunzuraku, Suka 'ki su barku ku gane kun girma". Mk Yana dariya ya ce "itace ai yar burutsa". Baffah ya taya shi dariya sosai ya ce "Kai kuma baka iya rarrashinta ba". "Hmmm Baffah ai ba zaka gane ba". *** A lokacin da Baffah yake bayanin Mk ne zai kaita, Inna hankalinta bai kwanta ba gaba'daya, amma ba yadda za'ayi ta hana ta zuwa wannan shari'ar domin ba karamin daraja bane ace ka samu damar bawa Annabi kariya. Sannan kuma mijinta ne da shari'a ta bashi damar ya tafi da ita duk inda ya so. Yayin da Sa'a ta ji takaicin wulakancin da Mk yake mata, zata bishi suje, Amma ko shine 'kuda wurin naci sai dai ya kalleta kawai, ba zai yiwu ya shareta na sati guda, sannan yanzu ya ce "tare zasu tafi ba". Haka ce ta kasance lafiya Lau suka isa Sokoto. A hotel ya kama musu daki, ya dinga tuno moment dinsu a tafiyar da suka yi Abuja, a wanccan lokacin ba karamin hutawa da soyayya Suka sha ba, amma wannan karon ta yi kicin kicin da fuska, ko kallonsa bata yi. Haka suka kwana! da wuri suka nufi kotun, ta shige cikin tawagar lauyoyi, shi Kuma ya zauna a sahun masu kallo, duk kuwa da an tsaurara matakan tsaro kwarai da gaske. Da azahar suka bar kotun, saboda yadda aka 'daga Shari'ar zuwa wattanni biyu masu zuwa. A hanyar su ta komawa ya ce "ba wadda zaki kaiwa ziyara ne a Sokoto?". Fuska a daure ta ce idan ina da su kaini zaka yi ne?" Da sauri ya ce "Eh Mana ranki ya Da'de, to menene aikina idana ba direbanki ba?" Ta tura baki ta ce "Humaira Suraj da muka yi F.G.C anan take aure sai dai bani da contact dinta". "Amma bari na kira uwar dakina idan tana nan ta mini kwatance muje mu gaisheta". Da kulawa ya ce "Wacece uwar dakin ki ?" Da murmushi ta ce "uwar marubuta, da makaranta da kuma marubuta masu tasowa, Umman mu Hajiya Saliha A.A Zaria." Dariya sosai Mk ya saka tare da cewa dadina da ke ri'ke alakawari! Na tuno sadda kike karanta mini littafin Yarda da kaddara kina fa'din yadda Abba lawal yake yiwa Asama'u zan dinga yi Miki. Dole kam muje nima zan gaisheta, domin littafanta no yasa na samu tagomashi a wurin Sa'ade nah". Ta yi masa shiru. Ta fido da waya bugun farko Umma ta dauka, tare da cewa "maraba da diyata Sa'adatu". Soasai Sa'a take jin da'din karamci da mutuntata Dan adam da Umman Sokoto take yiwa masoyan litttafanta, komin 'karancin shekarun mutum kuwa. Cikin farin-ciki Sa'a ta ce "Gani a Sokoto, kuma ina kan hanyar zuwa gidanki dan gaisuwar girma. Dadi ya kama Hazi'kar marubuciyar mu ta ce "na gode miki Sa'adah, ubangiji ya kawo ku lafiya. Haka kuwa Mk ya tsaya ya tambayi adireshin da ta turo musu, ba wahala suka isa. Murnar da Haj Saliha ta yi, ba yar kadan bace, a lokacin Sa'a da Mk suka gane ashe alherinta da suke ji a waya ba komai bane, sai ka ga zahirinta zaka san ita din Ummul khairi ce. Ta dinga yi musu nasiha da jan kunne kan hakuri, da kuma gwaggaban ladan da mai yinsa ke rabauta da shi. Da zasu ta fi ta bawa Sa'a abu a leda da ba tasan ko menene ba, ita kanta Sa'a da aka bata, bata kula da sadda ta ru'ko hannuta ta saka mata ba, saboda tsananin yadda Umma ta iya karrama dan Adam. Suka tafi cikin Jin da'di kusan saboda nasihar da Umma ta yiwa Sa'a yasa, ta biyewa Mk a hanya suka yi ta hirar arziki, suna ta yiwa Haj Saliha addu'ar samun lafiya da nisan kwana mai albarka. Hadi da yiwa iyalanta addu'ar shiriya da tsari daga dukkan abin ki. Ya ce sai "Ina kuma". "Sai gidan kawar Anty Sumayya! Anty Zalihatu Umar, da k'awata Hauwa'u Umar matar Nasir, Shinenan". Ya ce "angama Hajiyata". Haka yayi ta kewaye da ita tana samun karamci daga wurin mutanen Sokoto da basu san komai ba sai alheri. Sai maghrib suka isa hotel dinsu. Ya dawo daga sallah isah, ya dinga yi mata rawar da lallashi kala kala, amma ta yi funfurunfus ta 'ki ko da kula shi, balle ta bashi hadin kai. "Ashe duk nasihar Umma ta bayan kunnen ki ta bi? Duk yadda na gama yawo dake a gari, dan ki mini yadda nake so, sakayyar da zaki mini kenan? Wallahi cikina ciwo yake yi, marata a daure take, ki yiwa Allah ki bani dama, ban son na yi miki dole plz my Sa'a". Ko motsi ta ki yi balle ta tanka, ya gaji ya kwanta a gefenta, yana ta murkususu. Can kamar awa daya ya kasa hakuri ya janyota, ya fara shafata, ta yi firgit ta tashi, ta fizge, ya kalleta ya gano har yanzu rarrashi baya tasiri akanta, dan haka ya bita ya danne yana jin komai zai faru a yau kam sai dai ya faru amma ba zai 'kyale ba. Ya fara kici kici da doguwar rigar atamfar da ta sanya, wadda ta kamata soasai, amma dan ta takura shi, yasa da ta yi wanka ta daukota a akawatinta ta sanyata a daren ta kwanta da ita. *Gashi nan har da na gobe* SURAYYA DAHIRU. ✍️. *HALIN YAU*! *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916 *Ga Dukkan daliban UNITY KACHAKO* *Mussaman aji na 2008*. *Fatan alheri a duk inda kuke.* *Sakon taya murna ga dukkan ahalinmu bisa samun karuwar 'Ya mace da muka yi a ranar alhamis 21-7-22.* *Ina addu'ar Ubangiji ya Raya Rabi'atu akan tarfin islama, ya albarkaci rayuwarta. Allah ya bawa mahaifiyarta lafiya, ya bawa Mahaifinta ikon kulawa da su*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 109-110. Duk kokarin Sa'a ta kasa kwatar kanta a hannun Mk! Domin gaba'daya a rikice yake, ba zato ta ji yasa dukkan hannuwansa da 'karfinsa ya keta rigar nan, wadda sabuwace ko ruwa bata shiga ba. Haka ya cire mata tare da yin wurgi da ita. Ya matu'kar jigata kafin ya samu, ya isa inda yake nufin isa, saboda yadda ta ki bashi hadin kai ko kadan. Sai da ya gwada mata karfin kwanji. Ya matu'kar jimawa yana abu guda, ba karamin kidima ya shiga ba, a lokacin da ya zo samun nutsuwa, saboda yadda ya ji wata irin jijjiga tunda kansa har kafarsa. Karshe ya kammala cikin kuka tamkar ba Namiji ba. Dukkansu kuka suke yi, mai tsuma zuciya, na Sa'a mai sauti, na Mk kuma hawaine zallah, na tsananin farin-ciki, ya da'de yana ro'kon ubangiji ya sake nuna masa lokacin da zai kebe da Sa'a a matsayin miji da mata. Gefe kuma takaicinta ne ya kama shi na yadda ta wula'kanta shi, tamkar bata san shi ba, duk irin ro'konta da ya yi. Ya yi shiru yana jin kukan da take tamkar wadda ba aure suka yi ba. Ba'kin cikin ke nukurkusarta, mussaman idan ta hararo haka fa yake yiwa Farida. Ta kasa daina kukanta, shikuma Mk wani irin zazzabi ba zato ya saukar masa, tun yana daurewa har hakoransa suka fara kadawa, jikinsa ya dinga bari. A farko share shi ta yi, sai da ta ga tabbas jikin ne, tasa hannunta, ta ji zafi sosai a jikinsa, ga hawaye sai zubo masa suke yi. Ta yun'kura ta laluba akawatinta ta dauko rigar barcinta ta saka, ta debo ruwa, tare da 'karamin tawul 'dinta, ta dinga goga masa a jiki. Hankalinta ya matu'kar tashi, ba ta san har yanzu haka son Mk yake da karfi a zuciyarta ba, sai da taga yana zazzabi nan, saboda gaba'daya jijjiga yake yi. Damuwarta ta kai kololuwa, ta dinga jin inama ita take wannan ciwon shi kuma yana jinyarta. Ta dauko paracetamol ta bashi da kyar. Tana hawaye, tana tofa masa addu'a. Mk bai samu sassauci ba sai wajen 'karfe biyun dare. Barci ya yi awon gaba da shi. Sai da ya yi barcin sannan itama ta kwanta kusa da shi, hannunta rike da nasa hannun. 'Kiran farko akan kunnensa, ya tashi baya jin ciwon komai sai kasala, ya jima yana zaune yana kallon yadda take barci, tana sauke numfashi a hankali. Gashinta da ya sha gyara, yanzu duk a hargitse. Wula'kancin da ta yi masa na rashin yarda da shi a farko ya matu'kar tayar masa da hànkali, zuciyarsa tana gasgata sonsa ne da gaske ba ta yi a yanzu. Amma damuwar da ya gani a fuskarta a lokacin da bashi da lafiya, ya fahimci sonsa take da dukkan zuciyarta, kishi ne babban matsalar da idan ba'a yi taka tsan tsan ba zai sake ruguza musu rayuwar aurensu a karo na biyu. Ya kudiri aniyar yi mata addu'ar samun sassauci akan kishinsa da take yi da ya wuce ka'idar Sharia da mizanin hankali, tunda ko aka ran kanta ba zata ji dadin rayuwarta ba. Da kyar ya sauka ya shiga bayi, ya yi wanka, ya doro alwallah, sai da ya yi nafila, sannan ya tashe ta, ya fice zuwa masallaci. Ya dawo, ya tarar da ita zaune akan sallayah da hijab a jikinta. Ya cire jallabiyar jikinsa, ya kishingi'da a bakin gado, tana daga zaune a inda take. Ta ce "Ina kwana, Ya jikin?" A hankali ya amsa da cewa ", Lafiya lau Alhamdulillah". Daga nan kowa ya yi shiru, sai tunanin zuci suke yi. Tsawon lokaci kafin ta ji ya yi gyaran murya ya ce "Yau nake son mu tafi, amma jikina babu kwari, ba zan iya tukin nan ba". A hankali ta ce "Ubangiji ya baka lafiya, sai mu jira zuwa gobe, mu ga mai zai zartar." Ya yi shiru! Yana kallonta, yana jin sonta da tausayinta suna neman kassara shi. A hankali ya ce "sanyi nake ji, da sauri ta mike ta fara kokarin ware bargo, Dan ta rufa masa. Ya kalleta ya ce "Ba shi ba". Zuciyarta ta buga, ta sani tun fil'azal idan yana zazzabi, sai dai ta cire kayanta ta mannu da shi, dumin jikinta shine maganin sanyin da zazzabi ke sababa masa ji. Ta yi sororo bata san me yasa a duk sadda ya nemi ta'ba ta ba, sai ta ji wani irin bacin rai ya taso mata ba. Tsayuwar da ta yi, yasa shi fahimtar abin da yake son ta yi masa ne, ya sake sanyaya jikinta. Ya waske kamar bai gane halin da take ciki ba, ya sake cewa "Dan Allah". A sanyaye ta cire rigar jikinta, ta bar pant dinta, ta isa gare shi, ta kwanta, ya yi mata wata irin runguma mai tsananin gaske. Suka dinga sakin ajiyar zuciya! Ya dinga rada mata "Hold me tied please". Amma Sa'a ta kasa yin komai, saboda rashin sukunin zuciya. Tana jin yadda ya gyra kwanciyarsa ya fara laluben kirjinta da bakinsa, kan dole ta kyale shi ya zama tamkar sabon jariri saboda yadda yake tsotsar su. Jikinta gaba'daya ya amsa, sai tsuma take yi, shi kuma rashin 'karfin jikinsa ya masa cikas din tafiya second round ko da ta 'karfi ne kuwa irin na daren jiya. A hakan da suke barci ya yi awon gaba da su. 9:18am dai dai Sa'a ta bude idonta, har lokacin kuma Mk barcinsa yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Fuskarsa na manne da kirjinta sai ka rantse baya samun iskar zukar numfashi. A hankali ta zare jikinta, ta mayar masa da filo gurbinta, kamar yadda take yi masa a baya. Bata tsaya a ko'ina ba sai a bayi, kai-tsaye ruwa mai zafi ta ha'da, ta yi wanka sosai, ta fito, ta shirya cikin matsakaiciyar kwalliya, ta zauna akan stool ta kasa daura dankwali saboda yadda take jin tsananin yunwa. Bata son tashinsa, gashi kuma ji take tamkar ta ci babu saboda tsananin yadda cikinta yake yi mata karta. Ta dauko hijabinta ta saka, ta dauko jakarta, ta nufi kofa da nufin fita ta nemi abinci. Ta bude kofar kenan ya tashi, da azama ya ce "Ina zaki?" Ta dawo da sauri ta ce "yunwa nake ji, tamkar an mini yasa a ciki". Ya bata rai sosai ya ce "shine dalilin da zaki dauki hijab ki fita babu izni, alhalin kina kallona, Wai ke wanni irin raini kika mini ne? Ke ce zaki fita siyan abinci? Karatun naki abinda ya koya miki kenan?" Ta yi shiru, ta kasa cewa komai. Idonta ya ciko da kwalla. Ya ja tsaki ya mike ya shige bayi. Bai wani jima ba ya fito, amma ita sai ta ga tamkar ya kusan awa guda. Jallabiya ya zura ya dauko wallet din sa ya fice. Mintina Kamar biyar, ya dawo dauke da ledoji a hannunsa. Ya tarar da ita tana kan stool din mirror tana faman goge hawaye da tissue. Ya ajiye ledar a gabanta ya ce "gashi sauko ki ci". Ta yi tamkar ba ta ji shi ba, shikuma ya shige bayi, ya fara wanka. Amma da yake yunwa ba kanwar uwa ba ce, sai ta sauko, ta hau duba ledar. Leda daya dankalin turawa da kwai ne, 'dayar kuma doyace da aka soyata cikin kwai. Sai kuma leda mai dauke da daurin kunu biyu, na gyada da na tsamiya. Doyar ta hau ci a yunwace, kafin ya fito ta cinye tass, sai ragowan kunun tsamiya a hannunta da take shirin zuke shi. Sai da ya shirya, sannan ya zauna yana cewa "yanzu duk doyar nan kin cinye ke ka'dai, yaushe kika zama mai cin abinci haka? " Takaici yasa ta cigaba da matso kwalla ta na gogewa, shikuma ya hau cin abincinsa hankali kwance, yana jin wani irin shau'ki. Bai san me yasa iskancin Sa'a ke tafiya da shi ba, ya lura a yanzu bata da burin kayayyakin 'kawa, ba ta harkar kawaye, cikin dabi'unta masu Muni kaifin harshe ne ya rage mata, shima kuma dole ta rage indai tana gabansa. Amma sakalci, sai ya ga tamkar tana girma, yana sake bin jikinta ne. Ya tabbatar har kukanta yana jerin abubawan da yake kewarsu. Sai da ya kammala ya dubeta ya ce " ke kam kin ji kunya wallahi! Ai bai kamata ki tisa ni gaba kina mini kukan shagwaba ba, tunda dai jiya ba irin ro'kon da ban miki akan ki taimake ni ki mini abin da zan samu nutsuwa, amma ki kika shafawa idonki toka. Sai dai kuma na nuna miki ba zanci gaba da zuba miki ido kina mini iyashege ba. Da ace kin ji rarrashin da na miki, da kin ga yadda zan tarairaye ki, na lallashe ki, amma yanzu ko bubburwa zaki yi ba ruwana da ke, bare na san kina sakalcin banza". Da rawar murya irin tana gaf da fashewa da kuka ta ce "kin yarda da na yi da kai ya isa ka gane sonka ne ba na yi, haka karfin da ka gwada mini, da har yanzu nake Jin ciwo a inda ka bubbbga mini guiwar hannunka ya almata mini kaima sha'awa ta kawai kake yi, amma ba so ba". "Eh bana son ki". Ya bata amsa a ta'kaice. Ba'kin ciki ya turniketa ta ce "Allah ya kawo zazzabi anjima zaka gane lalle nima bana sonka". Ya ma'ke kafada ya ce "Ameen! Ciwo na kan kowa, nawa ya yi kyau ai. Kema kuma na ki na tafe, domin ciwo ai ba a fatansa, idan yau kaine, gobe na ga waninka. Idan ubangiji ya juya abin ya dawo kanki, a lokacin zaki gane tsiyar ki ka'dan ce". Ya mike ya na cewa "To ni kam dama kwanaki uku iyalina ta san zan yi. Yau kam ko hayar direban da zai tuka ni zuwa Kano, zan yi, bare kuma Ina fatan ubangiji ya bani ikon tukin da kaina. Don bana cikin mutane masu yiwa masoyansu 'karya ko butulci, ko danne musu hakkin su". Zuciyarta ta buga da tsananin gaske, ta san shagube ya yi mata, sannan kai tsaye yake nuna mata yau gurin Farida zai kwana, domin kwana ukun da ta bashi ya cika. Haka suka dawo Kano, ba wani jituwa a tsakanin su. Ya sauketa a kofar gidansu ya ja motarsa ya yi gaba. Tunda ya ajiyeta yake jin tamkar ya rusa ihu, shi dai ko zasu kwana suna Yar tsama yafi son ya ganta a kusa da shi, ko da ba zata kula shi ba, haka nan shima ko ba zai mata maganar ba, amma dai ya ganta kusa da shi shine samun nutsuwarsa, ko shareta da yake yi, Karfin hali kawai yake yi da son kwatar kansa a hannunta, tunda ya san halin iyashegenta. *Bayan sati biyu* Tunda Suka dawo kullum Mk sai ya Kira Sa'a a waya, sau tari bata dauka, ranar da ta yi niyya ta dauka, to kuwa zai ta yi mata magana ne, sai ta yi kamar bata ji shi ba. Bai yi fishi ba, a hakan dai yake 'kiranta, zuwa ne dai ba ya yi. Wani lokacin ma zai je shagon Baffah su sha hirarsu, amma ba ya neman Sa'a. Suna cikin haka tafiya ta same shi zuwa jahar Akwa-ibom. Zasu yi wani bincike a Jami'ar jahar na tsawon wata 'daya. Ya gama lissafinsa ba zai yiwu ta tafi da Farida ba, domin aikinta ba irin wadda za'a yi masa shan ruwan tsuntsaye bane. A zuciyarsa yafi dokin tafiya da Sa'a tunda dai har yau bata bashi dama ba, ko waccan ma, da tsiya tsiya aka yi, shikuma so yake, ayi da yardarta da amincewarta, ta yadda zata shayar da shi kalololin soyayyarta masu gigita shi. Saura kwanaki biyu ya yi tafiyar ya iske Sa'adah a gidan Sumayya. Suna zaune a falon mai gidan. Ya sassauta murya ya ce "Tafiya ce ta same ni, zuwa south, shine nake son ki yi mini rakiya, zan jima domin zan shafe akallah wata guda". Ta girgiza kai ta re da cewa "ba inda zani". "Umarni fa na baki". "Gaskiya ba zanje ba, tunda dai ban tare ba, umarninka baya kaina, ka je ka tafi da wadda idan ka yi tafiya baka wuce adadin kwanakin daka fa'da mata zaka yi, saboda sonta da isar da ta yi. Ya numfasa tare da mikewa yana cewa "na gode sosai da wannan shawarar, ya ajiye mata kudi masu auki, ga su nan ko wani uzzirin zai taso miki, sai na dawo". Har ya kai bakin kofa, sai kuma ya juyo, ya kalleta ya ce "zuwa yaushe kika shirya tarewar?" Kai tsaye ta ce "idan abin da nake so ya samu nan da wattanni hudu". Ba'kin ciki ya kama shi, amma sai ya yi nufin su raba bacin ran tare ya ce "To kawai a barshi a rabin shekara mana, wattanni shida kenan"! "To kawai mu bar shi a shekarar kawai". Ta fa'da a kufule sosai. Ya yi tafiyarsa ba tare da ya sake cewa uffan ba". Sai itace tana ganin fitarsa ta fashe da kuka sosai, tana gasgata da gaske ne yafi son Farida akanta. Mk yana tuki amma a fili yake cewa " Ubangi ka mallaka mini zuciyar Sa'adatu da tunaninta, Allah ba zan iya ba, kaine mai sarrafa zukatan bayinka, Allah ka hore mini wannan yarinyar da take neman manna mini hauka, bayan hawan jinin da nake fama da shi adalilinta! Kai ka jarrabi zuciyata akanta, ubangiji kar ka jarrabe ni a cikin hankalina da tunanina akan sha'aninta". Haka ya tafi Uyo shi ka'dai tamkar ba mai mata biyu ba, amma a kullum yana ro'kon ubangiji akan a mallaka masa tunaninta tamkar yadda aka mallaka masa zuciyarta, hakanan duk sallar duniya sai ya roki Ubangiji akan a sassautawa Sa'adah kishin dake neman jefasu yanayin da yake tunanin sun yi bankwana da shi. Satinsa biyu da tafiya Wanda ya yi dai dai da watansu daya da dawowa daga Sokoto. Sa'a ta kasa gane kanta, bata ciwon komai, amma yini take tana zubar da miyau, da ta gaji sai take fama da alawowi ko cingum, ko kuma kaninfari. Matu'kar kuwa ba komai a bakinta to kuwa miyau zai cika mata shi. Ga 'dan karen barci. Da kanta ta yiwa kanta alkalanci tabbas ciki ne da ita, domin tana iya hakaito haka cikin Jawad ya yi mata. Duk da yadda ta gamsu tana da ciki sai da ta yiwa kanta gwaji da P.T strip, sakamakon kuwa ya kasance positive. Wani irin tashin hankali ya dinga ziyaryarta, ita kuwa da wanne ido zata kalli Innah da kuma Anty Sumayya?. Da wanne irin harshen zata musu bayanin da zasu gamsu, sau 'daya tak wani abu ya gitta a tsakanin ta da Mk, shima kuma ba da sonta da yardarta ba, fin karfi ya gwada mata. Mk ya shammaceta kwarai da gaske, gashi yanzu ya dawo da asalin halayyarsa ta bagarar da ita da lamarinta. Ta nisa tana tunanin hanyar da zata bi ta boyewa Innah halin da take ciki. Ta shafa cikin tana Jin wata irin zazzafar soyyaarsa na huda dukkan sassan jikinta. Cikin Jawad ta same shi cikin kuruciya, da kuma sa Rai za'a samu tunda tana ganin da anyi aure ake samun ciki a haihu. Cikin kanwarsa kuma bai zo mata a sadda take so ba, asalima unwanted pregnancy ne, sai dai bayan ta haifeta ta dora ido akanta aka dora mata sonta fiye da tsammani, a yanzu da hankali ya shigeta ta tabbata tana jin son cikin jikinta kwatankwacin yadda take jin son Jawad. Shine kuma cikin da ta yi 'mararin samuwarsa duk da bai zo a lokacin da ya kamata ba. Washagari ta nufi asibiti, aka yi mata gwaji na sosai, sakamakon dai 'dayane da wadda ta yi da kanta. Ta dawo gida tana ayyana lissafin zuwanta Sokoto, lissafin cikinta wanda yana shirin shiga sati na biyar. A yanzu ba abin da take so irin ta tare tun kafin a ankara da halin da take ciki. Ta dinga tunanin yadda zata sanarwa Mk tana son tariya da wuri, ta tuna ranar da ya sameta gidan Sumayya kafin ya yi tafiyar, da muradinsa na son su tafi tare, Amma ta kekasa kasa ta 'ki. Ta nisa tana sake tuno sadda suke yiwa juna gatse, inda ita ta ce a bari sai nan da shekara guda. Zuciyarta ta harba idan kuwa hakane har sai ta haihu, da kusan wata hudu. "Tirkashi" ta furta a fili, tun yanzu kunyar Innah take ji, gashi dai a gabansu ta yi ciki, sa'ar da aka yi, ba cikin gaba da fatiha bane kamar yadda Inna ta gani a mafarkinta. Kwanaki uku da zuwan Sa'a asibiti ta kasa daurewa saboda yadda kullum take Samun sababbin alamomin da Za'a fahimci halin da take ciki. Da daddare tana kwance a dakinta, ta kalli agogo, ta ga lokaci ya fara ja, amma hakan ta kasa hakuri ta 'kira layin Mk. Ringing biyu ya dauka, Yana ayyana zuciyarsa da ta Sa'aadah tare suke bugawa, domin kwnaciyar da ya yi ba abin da yake tunani sai ita, yana mamaki yadda bata neme shi ba, gashi har ya doshi kwanaki ashirin, amma ko ta 'Kira ta ji ko ya Isa lafiya. Ya dauka! Amma ta yi shiru, ya nisa tare da cewa "Ina Jin ki, ta jima tana zumbure zumburen baki tamkar Yana gabanta. Da kyar ta ce "Ina yini?" Ya amsa da cewa "lafiya kuwa?" Ta 'kulu amma ta daure ta ce "sai ba lafiya zan neme ka?" "To na ga tunda na yi tafiyar nan ko Kirana ki ji yana isa baki yi ba. Ni kuma na kira ki ba adadi kin ki picking, saboda kawai ki nuna mini da gaske kike ba kya sona, ba kuma wani abu na alheri a tsakaninmu da cin arzikinsa" Ya fa'da a dan tunzure ka'dan. Ta yi shiru tsananin sonsa na ratsata mussaman cikin jikinta idan ta tuna bai yi gaggawar kaita auren wani ba, sai ta tsatson Mk ya fito sai ta ji kawai tana ambaton Alhamdulillah! Babbar matsalarta kishin auren Farida , ta tabbatar da wata ya aura ma zata ji kishin amma ba kamar na Farida ba, domin shi ka'dai me dalilin da yake sawa ta ji tsanarsa da tsanar cigaba da kasancewar a doron 'kasa. Hawaye ya cika idonta sosai, ta daure ta kuma cije bata bari kukan ya kwace ba, da rawar murya ta ce "yaushe zaka dawo?" "Inace na fa'da miki sai na cinye kwanakin wata?" Ta yi shiru! Ya nisa ya ce "fa'da mini menene tunda na san haka kawai ba zaki nemi ni ba tunda kin ringa kin jefa ni sahun Marasa adalci da daraja a duniyar ki". "Ni ni bani da lafiya ne". Ta fa'da a rarrabe kuma a shagwabe. "Me ya same ki?" Ta yi shiru, ta kasa cewa komai. "Na san dai ba kewata kike yi ba, tunda tuni kin cire ni a masoyinki". "Dama zan fa'da maka ne, Anty Sumayya da Umman Fanshekara suna son zuwa su ga gidan da zan zauna". Ya murmusa ya ce "Na san ki tamkar tafin hannuna, fa'da mini dai gaskiyar magana. Kawai ki ce kin fasa yin rabin shekarar kina son tarewa dan kar abin da kike boyewa ya bayyana a gaban su Baffah". Zuciyarta ta tsinke, da sauri ta ce "me nake boyewa?" Ya waske da cewa "Tarin Sona mana na zuciyar ki, bayan bakinki yana ta jifana da kiyayya". Ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. Ni ai dama ban ta'ba cewa bana sonka ba, sai dai na ce da aure ne bana yi, saboda kaima ai ba ni kake so ba". "Fahimtar ki ce hakan, kuma Wallahi ina taya ki jin kunyar ace kin rayu da ni shekaru bakwai, amma baki ki san wannene Mukhtar ba". Ta katse shi ta hanyar cewa "Ni yanzu me zance wa masu son zuwa ganin gidan?" Kai-tsaye ya ce "ki ce ban kammala gyran gidan ba, sai nan da wattanni shida lokacin ya yi dai dai da kammaluwar na ki Shirin". A mugun shagwabe ta ce "Bana son haka, bana so, ka daina daukar hakkina haka Nan". Wani irin farin-ciki ya mamaye Mk ya ce "fa'da mini me na yi miki na daukar hakki?" "Ni kawai ka fa'da mini gaskiyar abin da zan fa'da musu". "Ki fa'da musu saboda kin ce sai kin gama shiryawa, ya sanya nima na shiririce. Da gaske ban tanadi inda zaki zauna ba". Hakan da ya fa'da ya sa ta fashe masa da kuka sosai. Ya matse dariyar da ta so subuce masa ya ce "Share hawayen ki kin ji my dear, ki bari idan na dawo sai mu yi maganar a nutse, ki fa'da musu bana gari, Amma da zarar na dawo, zamu tattauna". Da yake son tariyar take yi a kwanakin nan yasa ta biye masa, suka rabu kalau. Yana ajiye wayar ya dinga dariya yana fa'din Ubangiji ka kaddara addu'ar da nake yi ne ka karba, ubangiji ka kaddara hasashena ya zama gaskiya. Ya yi shiru yana murmushi a zuciyarsa sai fa'dawa Ubangijinsa yake yi idan har ya tabbata ciki ne da ita azumi uku zai yi na godiya ga Allah, abin da ya da'de yana son ayi masa kenan haihuwa! yana son ya ga Jawad ya na da mahadi, yana son 'kananun yara. Ya tuna lokacin da ya matsu Sa'a ta sake haihuwa amma kawayenta suka zugata wai zata tsufa da wuri. Ya fesar da zazzafar iskar bacin rai, a fili Kuma sai ya ce "Na yafe komai, na manta komai". Sati biyu Mk ya dawo, zuwa wannan lokacin cikin yana shiga sati na bakwai, ta fara wani irin fari, sai kuma ya canja salon ba komai zata ci ba, asalima bata isa ta sha tsurar ruwa ba. Sai dai ta sirka ya dai canja launi. Ga miyau bai tafi ba. Kullum cikin Hijabi take da safa, saboda yadda kafafuwanta suka yi fari, suka yi fresh, da zarar Baffah ya tafi Gogel zata tafi gidan Sumayya, saboda kada Innnah ta ganota. Washagarin dawowar Mk ya iso wajen Sa'a da tarin tsarabar manja da kuma kwakar manja. Da rawar jiki ta kai ta zubo a bowl ta dawo ta hau ci tamkar nama. Ya zuba mata ido yana ganin sauyuka a tare da ita karara. Zuciyarsa ya gama gasgata zatonsa. Ya dinga Hamdala a ransa. Lafiya Lau suka gaisa, ba bacin rai. Ganin Bai sako maganar da ya ce sai ya zo ba, ya sa ta kawar da fuskarta gede ta ce " Ya maganar da na yi maka?" "Wacce?". Ta tura baki gaba ta ce "su Anty sun matsa mini akan zasu je su ga yanayin windows da kofofi saboda maganar labule". Ya cije ya ce "idan dan wannan ne ba matsala na riga na tanade su". "Kar ku damu". Ta juyo ta ce "Na damu ni na gama shiryawa ranar juma'ah zan tare". Dariya ta kwace masa sosai, yayin da itakuma ta hau kuka marar sauti. Ya kalleta sosai sai fahimci kuka take tunda ga zuciyarta ba wai na shagwaba bane. Ya hadiye dariyarsa ya ce "menene kuma amma dai kinsan ban son irin wannan kukan ko?" Ta kasa magana. Sai da ya dinga rarrashinta ya samu ta daina kukan. A hankali ta ce "Akan me zaka mini dariya bayan abin da ka janyo mini?" Da sauri ya ce "me na yi miki? "Abin da ka yi mini a Sokoto mana". "Oh sorry Sa'adah! na dauka abin ya wuce ai". "Ina ya wuce tunda kullum yini nake da yawu a bakina, ga idan Innah na girki sai dai na rufe daki, na yi ta amai ban son ta gane mai nake ciki." "Ya waske, da cewa to ana boye ciwo ne? Tashi muje ki ga likita". Ya kalleta gaba'daya ta yi laushi, ya san laushin da ta yi dan ta samu yadda take so ne. "Ni ba inda zani". Ya kuwa mike da sauri ya ce "shikenan na fita hakkin ki, mu yini lafiya". Tana daga zaune tasa hannu ta ru'ko rigar farar shaddar jikinsa. Ya juyo suka ha'da ido suka dinga kallon juna, suna jin wani irin tsumin soyayya yana tsuma su. Sa'adah ce ta yi saurin dauke kai. A hankali ta ce "da gaske na gama". Ya juyo ga'ba daya ya ce " Sa'a ba zai yiwu na tare da ke a hakan ba, kina musguna mini, ban isa ki mini yadda nake so ba, ban isa na ce ga yaddda zaki yi, ki ce to ba, haka kawai fa kika ce ba zaki tare ba, sanin kanki maganar ba a hannuna take ba, tunda Baba Kika fadawa, shine kuma ya bani umarnin na lamince miki ki kammala shirin ki, yanzu kuma cewa zai yi na nuna bai isa da ni a karo na biyu ba". Ta tura baki gaba ta ce "Amma ai da ka ro'ke ni akan ka kira shi , na fa'da masa zan tare da bakina". "Eh na fa'da amma sai na ga bai kamata na matsa miki ba, shekaru bakwai na yi ina kuakan rashin ki, Kinga kuwa duk dadewar da zaki yi kina shirin ba zaki kai irin wannan lokacin ba. Ki Bari ko wata uku ne, nan gaba sai mu san yadda za'a tunkare shi. Kuka ta fara tana cewa" ba wannan maganar, wallahi ba zan yarda Innah ta fahimci Ina da ciki ba, tunda ba za su gane da bada son raina hakan ya faru ba". Ya zauana ya fuskanceta sosai, sai kuma ya tafi ya yi sujjud shukur, ya dago yana cewa "Alhamdulillah, ubangiji ya raba ku lafiya, na dade ban ji farin-ciki irin na yau ba". "Tashi muje ki siyi abin da kike so a matsayin tukuici". "Ni ba inda zani". Ido kawai ya zuba mata, jikinta ya yi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa. Ta mi'ke tsaye, tana tura baki gaba, irin wadda take yi masa a shekarun baya, mai ha'de da wani irin ta'bara da shi kawai take yiwa irinsa. Nan da nan jikinsa ya hau tsuma da sauri, ya matsa kusa da ita, ya rungumeta sosai, dukkansu sun shiga wani irin yanayi mai tsuma jiki da gangar jiki gaba'daya. A kidime Mk ya saketa ya shiga waiwayen inda zai ga hijabinta, can ya hango wani a ninke akan akwati. Da kansa ya ware ya fara kicinyar saka Mata. Tmda taimkonta hijabin ya daidaita. Ya kalleta sosai ya ce "Bari na fita, sai ki fito muje asibitin a duba ki, daga Nan sai ki raka ni unguwa". Ta kasa yi masa musu, tana tsaye tana jin yana yiwa Inna sallama, ya fice ya barta tana faman tauna maganar da zata fa'dawa Innah. Haka ta fito rataye da yar 'karamar Jakarta, ta kalli Inna da take kofar kicin a tsaye, ta ce "Inna zanje asibiti, daga nan kuma zan wuce gidan Maman Khalifa". Ido Innah ta bita da shi tabbas tana ganin kasala a tare da ita, kuma ba kasafai take cin abinci ba. Ta ce "wanne asibitin zaki je?" "Ban san wadda zai kai ni ba, Ni ba dan ya dage bama, da ba wani asibitin da zani, na san zazzabin cizon sauro ne". "To sai kin dawo, amma kar ki kwana gidan su Khalifa, Baffan ku baya gari, gara ki dawo mu kwana tare". Sa'adah ta amsa da cewa "To Innah". Innah ta sake cewa "ki kula da kanki, ki lalla'ba shi, kar ki yi abin da zai ja hankalinsa akan ki, har sai anyi tariya. Ni ba gaskiya ba zaki mini wata uku a gidan nan da auren ki ba, wanan watan da wani watan ya isa, koma kudin bai isa ba, kina dakinki sai ki dinga siyan abin da kike so, tunda dai ai ansan mu masu karamin karfi ne". A sanyaye Sa'a ta ce "Hakane Innah! Ni idan kin ce ma a wannan watan na tare zan yi biyayya ba dan Ina so ba, sai dan na nuna miki na fi girmama ra'ayin ki akan nawa". Sosai Innah ta zuba mata ido tana son ta gasgata maganar Iyah, amma bata san meyasa take ganin tamkar akwai wani abu da yasa ta sauko haka da wuri akan tariyar ba. Ta tafi, Inna ta bita da addu'ar dawowa lafiya. Suna tafe yana ta yawo da su akan titi, shi kansa tunanin inda zai kaita yake yi. Can ya kalleta ya ce "wanne asibitin kike zuwa yanzu?" A hankali ta ce "Ni fa na je asibitin an duba ni, ta butde jakarta ta fito da magungunan da aka bata tana nuna masa. Ya ce "To sannu My Sa'adah". "Yanzu bari ki raka ni unguwa" Basu zame ko ina ba sai gidansa na rijiyar zaki. *Ina ta shan korafi daga makaranta cewar yanzu yanga nake yi, ko kadan ba wannan maganar, a farkon fara posting Ina da pages masu yawa a 'kasa, a yanzu kuma babu, sai na yi typing kafin na turo, kowa ya san akwai hidimomi irin na yau da gobe akan kowanne bawa.* *Ni Kuma har da ciwon idon da yake sani rauni a typing din, Ina fatan za'a yi hakuri, saura kiris ma mu kammala, ban yi tsammani labarin zai yi tsayi haka ba* *Zan sanar da cewa ba kullum zaku ga update ba, amma ba zai dinga daukan lokaci ba* *Na gode sosai da yabawar ku kan rubutuna*. Surayya Dahiru ✍️✍️. *HALIN YAU*! *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *TAIMIYYAH*❤️ Ina kuke ne masoya kuma makaranta littafan Hausa,me kuke jira baku afka cikin wannan tafiya ba? ko kuna da labarin cewa shahararriyar marubuciyan wato Ayshat Ɗansabo Lemu,marubuciyan👇🏻 *LAIFIN ƁOYE* *HAMAL* *HURAYYAH* *BURIN ZUCIYA* *ƘALUBALE* *NAILAH* *INA DA HUJJA* ta sake yinƙurawa domin tazo muku da zazzafan labarin ta me suna asama,domin faɗakar da ku da kuma nishaɗantar da ku,haɗi da koyar da ku dibarun girkunan zamani da gwangwaje ku da salon soyayya me tsayawa a zuci,duk acikin wannan shahararran labarin nata me suna *TAIMIYYAH!* Labarin da yazo da wani irin salo me cike da ban tausayi do motsa zuciyan me karatu,duka wannan zai zo muku akan farashi me sauƙi,da kuɗin ki 500 kacal zaki mallaki naki don gujewa shiga hakkin marubuciyan,zaku biya kuɗinku ta wannan asusun kamar haka👇🏻 *0504192664 Aisha Ibrahim Dansabo GTbank.Sai ku aiko da shaidan biyanku ta wannan layin 08167768704.* *Masu turo katin waya zaku turo katin MTN ta wannan line ɗin 08167768704.* Kada ku bari abaku labari domin wannan karan salon na daban ne,tuna da sunan *TAIMIYYAH!* sai ku garzayo don ji wacece TAIMIYYAN ya rayuwanta zai kasance alhali ta kasance gurguwa! Masu buƙatan a tallata muku jahar ku a wannan daddaɗan labari zaku tuntuɓi marubuciyan ta wannan layin 08167768704. Share it ga wanda taci karo da wannan tallan,tayi sharing ɗinsa fisabilillah! 👏🏻 THANK U ❤️ *GAISUWAR GIRMA GA* *IYAYENA! KUMA MANYA MATA!* *HAJ HAMZIYA ALI(MRS BELLO BAFFAH MAITAMA)* *AUNTY ZAHRAH IBRAHIM* *AUNTY KHADIJA ABDULLAHI(MRS IBRAHIM BABA)* *HAJIYA MAIJIDDA TA GWARAM(MRS ALI BUKAR MAKO'DA)* *AUNTY AISHA HAMISU KANO(MRS ABDULAZIZ SHEHU)* *AUNTY AISHA SANI GWARAM* *AUNTY SA'ADATU SANI GWARAM* *AUNTY SHEMA'U SANI GWARAM* *AUNTY AMINA SANI GWARAM* *AUNTY ZARA'U BILYAMINU USMAN HADEJIA* *AUNTY A'I GARBA* *AUNTY SHAMSIYYA USAINI* *AUNTY ZAINAB SIBA* *AUNTY FIDDAUSI 'DAYYABU TAURA* *AUNTY WASILA MUHAMMAD* *(AMINYAR AUNTINA TA KAINA RABI SANI)* *FATAN ALHERI ALLAH YA KARA MUKU LAFIYA DA NISAN KWANA MAI ALBARKA*. *FATAN ALHERI GA AISHA JOS MARUBUCIYAR TA CUCE NI*. *ALLAH YA 'KARA BASIRA* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* 111-112. Katon gida ne mai dauke da babbar haraba, ga wasu irin gini flat guda biyu, a tsakiyar filin. Sai daga can kusa da karshe kuma wani flat din mai kama da boys quarters. Shuke shuken fulawowiyi sun 'kawata harabar, sosai gidan ya burgeta, saboda tsarin gini ne na kasashen ketare inda zaka samu yalwar iska(ventilation). A jere suke da juna, sai dai akwai Yar tazara a tsakanin gidajen. Kai tsaye ya nufi wadda yafi kusa da 'bangaren dama. Ya fito da mukalli a aljihunsa ya bu'de babbar kofar, tunda akwai karamar kofa wadda 'karamin falo ne da toilet a ciki saboda zama da abokansa ko ba'kinsa maza. katon falo ne a farko mai dauke da wurin cin abinci da kicin sito, akwai kofar a kicin din da zaka iya shigowa daga waje. Sai ta gefe kuma dakunan barci ne suma manya guda biyu kowanne da bandakinsa a ciki. Har ilah yau daga can karshe akwai wata kofa idan ka bu'de dogon corridor zaka ga ni mai dauke da wasu 'dakuna guda biyu, da bandakinsu. Ta jikin wannan koridon akawai kofar da zaka iya fita waje ba sai ka shigo falon ba. Sosai tsarin ya burge Sa'a marbles din da aka shimfida a ko ina, da kuma girman falon da dakunan ya sake sawa ginin ya zama na mussaman. Sannan ko ina ansaka labule masu tsadar gaske. Cikin dakin guda da suka yada zango har da madaidaicin karfet a shimfide. Suka a zuana akan karfet din. Ya ce" ina fatan ya yi miki?" A hankali ta ce "ko gidan da muka fara rayuwa ka kai ni, ya yi mini sosai, bare wannan". Ya tsura mata ido yana gasgata ta domin yanzu babu dogon buri a tare da ita, amma da yake tana samun hanyoyin samun ku'di bata yiwa kanta kwangen sutura da kayan kwalliya na alfarma. Son ta yi gayu a jininta ne ba wai 'karya ko fariya ba ne. Ya matsa sosai kusa da ita, yana shakar 'kamshinta, ya na kuma yi mata wani irin kallo mai tsanani. Ta sunkuyar da kanta 'kasa tana Jin kallon har a zuciyarta. Ya nisa ya ce "yunwa kike ji ko?" Da sauri ta 'daga masa kai. "Shine kuma ba zaki fa'da mini ba? Ai da na tsaya a hanya na siyo miki". Bata ce komai ba. "To me zaki ci?". A hankali ta ce gasheshshen nama da yourgt mai sanyi". A zuciyarsa sai ayyana irin haka ta yi a cikin Jawad, ba rashin lafiya, sai kasala da rashin cin abinci sai kayan kwadayi, da barci. Ya mike da sauri ya ce "zamu je mu siyo, ko na je na dawo?" "Je ka dawo! na gaji". Bai 'dauki lokaci mai yawa ba, ya dawo da dukkan abin da take bu'kata, ya tarar da ita, tana sharar barci hankali kwance. Bai tashe ta ba, ya ajiye ledojin ya shiga bayi ya 'doro alwallah ganin 12:45 pm ta yi, yanzu za'a fara 'kiran sallah. Ai kuwa yana fitowa ya jiyo Kiran sallah, sai da ya yi nafila, sannan ya fice zuwa masallaci. 'Karar rufe kofar ya tasheta, a hankali ta yun'kura ta zauna da salati a bakinta. Kamshin nama ya bugeta, da sauri ta mike ta wanko bakinta ta dawo ta fara cin naman nan a hanzarce saboda yadda ta tara yunwa. Bata son cin abinci, sannan bata iya siyan abin da take so dan kar ta janyo hankalin Innah. Ko a gidan Sumayya bata iya cewa ga abin da take sha'awa shiyasa take zaman yunwa, sai ta ga zata galabaita ne take zuwa gidan Zainab, ko ta siya ta samu inda zata buya ta ci. Duk yawan nama da gurasar da suke na'de a poil paper 'dan ka'dan ta rage, ta bude dadda'dan yougurt ta fara sha tana jin sanyinsa har cikinta. Sai da ta huta, sannan ta yi gyatsa ta mike ta 'doro alwallah. Ta kusa idarwa ya shigo. Ya zauna yana jan ledar gabansa dan shima ya ci, mamaki ya matu'kar kama shi, saboda ganin wanda ta rage. Ya karasa cinyewa ya bude yoghurt ya sha. Bata yi masa magana ba, ta sa hannu ta dauko robar ruwa ta bude ta kai bakinta. Sai da ya kammala ya matsa kusa da ita sosai, ya ru'ko ta. Yana cewa "zo ki ji wata magana, na sani ba iya yunwar nama kike ji ba". Ta fara ture shi tana cewa "Ni wallahi iyakacin yunwar kenan, kuma na koshi sosai". "To ai ni ban koshi ba, tunda dai baki rage mini na kirki ba". Ta 'ki tsayawa, shi kuma ya'ki sakinta, ganin da ya yi da gaske ba amincewar zata yi da shi cikin kwanciyar hankali ba, sai ya saketa. Ya koma gefe ya na jin bacin rai sosai. Jikinta ya yi sanyi, amma bata san me yasa take jin tsananin bacin rai idan ya nemi kusantarta ba. Tsawon lokaci suna zaune ba um, ba um um, a tsakanin su. Ta saci kallonsa ta ga yadda yake cikin fishi sosai, ta hadiye maganar da take son amayarwa. Ya mike yana cewa "Tashi mu tafi"! Ta 'ki yin ko da motsi, balle ta tashi. Dan jim ka'dan! Ya nufi hanyar barin dakin yana cewa "ki same ni a mota". Ta daga murya ta ce "Ba ka ce mini komai ba akan maganar da na yi maka 'dazu, kuma ka ce mu tafi?" Ya dawo ya tsaya akanta fuska ba walwala ya ce "wacce magana ce? Tuna mini, dan ni na manta". Takaici ya shaketa, amma hakanan sai ta daure ta ce "Tariyar Mana". Kai-tsaye ya ce "Ban kammala shiri na ba, ba kuma ku'di a hannu na". Ta fara kuka tana cewa "Ni ko ba ku'din zan tare, kar ka mini haka, so kake na kunyata?" "To ki ta kunyata mana! Ina ruwana? idan kuma kina da yadda zaki yi da cikin dan ki tsallake kunyatar sai ki yi". Ta dago a razane dan ta ga shine yake wannan maganar ko kuwa?. Ai kuwa suka ha'da ido, fuskarsa a matu'kar 'daure. Ta Sanyaya murya, hawaye na zubo mata, ta ce "Haka ka ce mini?" Take ya ji tausayinta! Ya zauna ya ce "Haka na fa'da miki Sa'adatu. Hakan kuma shine gaskiyar magana, ba zai yiwu kina wulakanta ni tun yanzu ba, sannan ki yi tunanin zan miki abin da kike so, bakya yarda da ni, na sani ko tariyar aka yi haka zaki cigaba da yi mini, dan haka ki zauna ki haihu a gida. Zuwa lokacin idan kin ji a ranki, kin shirya zama da ni bisa tsarin sharia sai na saka ranar tariyar". Hawaye ya dinga zubo mata ba kakkautawa, a hankali ta ce "kar ka mini haka dan Allah". Nan da nan ko ya ci laya da cewa "Wallahi ba zan yi abin da kike so alhalin har yau din nan bani da mutunci a idonki ba, inace dai jikina ne ba kya so ya rabe ki? To ba zan sake ba, zan ta siyo miki nama da yogurt da duk abin da kike son ci, nima kuma in sha Allah ba zaki ji, ko ki ga na mutu ba adalilin ba kya yarda da ni". Ta dinga kuka sosai, ya dinga jin wani iri, ya sassauta ya ce "daina kukan haka! Ta shi mu tafi" "Ni ba inda zani sai an tsayar da maganar nan". "To ai na gama, sai dai tunda ni zan biki dole, sai ki tsara na ki, ki kuma sa ni biyayyar dole". Ta goge hawayen ta ce "Na yarda ni zan bika". Ya mi'ke ya ce "To tashi mu tafi, tunda Ni na zartar da nawa hukuncin, ba kuma zan canja ba, sai na tabbatar da gaske kin daina mini wulakanci". Da rawar murya ta ce "Ai yanzu ma na yarda! Ba zan sake tureka ba". Da'di ya yi matu'kar kamashi, dama abin da yake so kenan. Da rawar jiki ya isa ya rungumeta. Ya dinga jifa da Hijabinta da komai ma, haka ya dauki lokaci yana abin da ya ga dama da ita. Yayin da itakuma ta ke share hawaye. Har ya yi wanka ya fito bata bar kuka irin na sharbe ba. Ya waske ya yi kamar bai gani ba. Suna tafe a mota da rawar murya ta ce "Yanzu yaushe ne tariyar?" A gajarce ya ce "sai kin daina mini kukan da babu dalili, sai na gamsu da gaske idan kin tare din zaki barni na dinga samu nutsuwa da ke". Da kuka ta ce "kawai na gane yawo kake mini da hankali! Dan kasan ka gama da ni, inace yanzun ba abin da baka yi da ni ba, amma yanzu kana wata magana". "Tabbas na yi, amma mai na tsinta ban da bacin rai, dame kika taimake ni? inace zama kika yi tamkar ruwa, sannan kina ta Kuka". A matu'kar gajiye ta ce "To ai ba zan sake yi maka kukan ba". "To zame mini tamkar gawa fa?" Da sauri ta ce "Na daina". "To ki bari sai na tabbatar da gaske kin daina din har zuciyarki". Cikin kwantar da murya ta ce "yaushe to zaka tabbatar din?" Ya dauke kai ya ce mu barshi nan da wata daya, idan yanayin biyayyar da kike mini ya gamsar da ni, shikenan sai ki tare abin ki". Da rawar murya ta ce "idan na kara wata Innah zata gane halin da nake ciki". "To wai ke wannan boye boyen da kike yi na menene? Abin kunya ne, Inace an daura auren?" "Ni dai bana so a sani ne kawai". Ya murmusa ya ce "ai dole ki ji kunya, kin gama fadin ba kya sona a gabansu, sai gashi daga dan ta'ba ki ka'dan, kin yi ciki, ai dole ki ji kunya, ina kika kai 'kiyayyar?" Ta kasa bashi amsa. To mu barshi sati biyu nan gaba, amma sai na tabbatar fah". Tunda ga wannan ranar Mk ya mayar da Sa'a tamkar ya tare da ita ne, domin kullum sai ya fita da ita, ya yi abin da zai yi sannan su dawo. Har satin biyun ta cika amma baice komai ba, a lokacin cikinta yana shirin shiga wata na uku. Rannan suna gidan da suke yini, zuwansu kenan, ta kalle shi, ta ce na gane so kake dai sai na kunyata dole. Banda haka menene bana yi maka Kullum sai ka fita da ni, amma ka dage akan bana yi maka yadda kake so? Fa'da mini me zan yi maka kuma?" Cikin rashin damuwa ya ce "ba Kya mayar mini da martani kamar da can, sannan kullum na kusance ki da kuka ake karewa, ke yarinyace? Sannan ba har zuciyarki kike amincewa ba, kina yarda ne akan dole, sai dan kina son ki tare kar agane kina da ciki. Abin da baki gane ba, ni ba abin kunya na yi ba, tunda na yi hakuri sai da aka 'daura aure, ke kika ce ba zaki tare ba da bakin ki. Babana ya goya miki baya, yanzu kuma sai ki dame ni da maganar tariya alhalin kin san inda zaki fa'di kin matsu ki tare, asa ni dole, ko bana so". Ya nisa ya ce "ki kira Baba da bakinki kice zaki tare". Idonta ya ciko da kwalla ta ce "Kaine zaka kira ka ce ka shawo kaina na amince, idan ya nemi jin ta bakina sai na yi shiru alamun kunya, shikenan sai ya gane ina bu'katar tarewar da gaske". Ya tsura mata ido ya murmusa ya ce "Sannu Sa'adah! Ke idan kina son abu, kin iya shirya zance". Daga haka ya janyota jikinsa yana kissing dinta. Sai dai yau yana kammalawa ta dinga kelaya amai tana kuka. Sosai ta yi, sai da ta kammala ta koma gefe ta cigaba da kukanta. Haka Mk ya kwashe Aman nan, ya sa tissue ya goge. Ya kalleta ya ce "je ki yi wanka". Bata Musa ba ta mike ta shiga toilet. Ta fito ta same shi ya yi tagumi da hannuwa biyu. Ta zauna a sanyaye. Ya kalleta ya ce "Anya kuwa Sa'adatu kina jin tsoron ubangiji? Anya kuwa baki kafirta ba?" Da saurinta ta dago ya ce "kwarai kuwa! Na sani kishi ne yake son halaka ki! Amma ki sani ubangiji ne ya halasta, sannan shine ya bada umarnin a auri bibbiyu ko uku ko hudu. Aaya ce sukutum cikin al'kura'ani mai girma. 'Kin amincewa da hukuncin Allah kuwa tamkar ka kafirta ne". Ya yi shiru yana nazarinta. Ya nisa ya cigaba da cewa "ina jiye miki kada ki halaka kanki, ki halaka ni, Ina jiye miki tsoron kada na samu aljannah adalilin ba'kin cikin da kike ta 'kunsa mini, ke kuma ki tsince kanki a wuta. Annabi ya ce akwai mazan da suke rabauta da aljannah adalilin hakuri da taurin kan matayensu da kaifin harshensu. Ina jiye miki na shiga aljannah, na hadu da Farida ba da ke ba". Dai-dai nan ta rushe da wani irin kuka, fiye da kukan da ta yi ranar da ya saketa. Da sauri ya matso ya rungumeta, domin ya tabbatar wannan kukan ba na shagwaba ko iyashege bane, na tsantsar damuwa ne. Bai hanata ba, ya barta ta yi, iya yinta, ganin yana neman wuce ka'ida ya sanya ya fara lallashinta da gwalagwalan kalmomin da suke nuna kololuwar matsayinta a zuciyarsa. Cikin kukan ta ce "Me yasa sai ita zaka aura? Me yasa na shafe shekaru hudu, Ina binka ka mini afuwa ka 'ki, karshe sai ka hukunta ni da auren wadda na tsana, Dan Allah baka ji a zuciyarka ka tozartani ba?" Da sauri ya ce " Ni ban tozarta ki ba, domin 'auren da na yi 'kaddarata ne, wadda ko muna tare ba zan iya tsallakewa ba. Ta ture shi ta ce "Ai kuwa zamu rayu a haka cikin damuwa, domin zuciyata ba zata huce ba, har sai ka yarda ka wulakantani, ka mini hukuncin da ya wuce laifina". Ya sake rungumeta tsantsan tamkar zai mayar da ita cikinsa ya ce "Anya mutum yana tozarta zuciyarsa da rayuwarsa? Amma tunda shine abin da zaisa ki yafe mini, shine abinda zanyi ki dawo mini da nutsuwata, to na yarda na wulakanta ki, amma wallahi ba intentionally na yi hakan ba, ki yafewa masoyinki, kamar yadda na yafe miki, ko na tuna abubuwan da kika yi mini, a take nake jaddada cewar Ubangiji ya zama shaidar na yafe miki, ya kuma hane ni tunowa". Da rawar murya ta ce "Ai ni ko ina son na manta din ba zai yiwu ba, a da kai din nawane ni ka'dai, kome zan yi maka na san ba inda zaka je ka kwana zaka dawo gare ni ne, amma yanzu fa? Zan dinga rabaka ne da wata muddin rai". Ta karasa cikin kuka na sosai. Shi kansa da ya tuna bala'in da ya shiga da ya ganta da Khalil ya gamsu ita din jarumace, domin shi akanta ba zai iya shanye abin da ita ta shanye ba, ya dinga ji har zuciyarsa yana taya ta Jin ciwon kaddarar nan da ta kutso musu. Ya Dora bakinsa daidai kunnenta ya ce "Daga yau din nan ba zan sake maimata miki wannan kalmar ba! Ki ri'keta ta zame miki jagora a zaman da ubangiji ya kaddara zamu yi". Ya nisa ya ce "Wallahi ban taba son wata halitta a doron 'kasa irin ki ba, Hajiya ce kawai ta fiki darajah a duniyata. Ke nake yiwa so na 'kauna, so na sha'awa, so na burgewa, wani irin so nake miki da a kullum ina tuna ki sama da sau sabain a rana, ke kadaice nake tuna abin takaicin ki, amma sai na tsinci kaina da yin murmushi. Ke kadaice kike mini iyashege ya burge ni. Ke kadaice macen da idan na kalla sai na tsinci kaina da yawan ambaton Alhamdulillah! Ke ka'daice macen da idan na ta'ba ki, ba ki mayar mini da marta ni ba, nake Jin bacin rai da tashin hankali. Haka nan ke ce macen da nake fatan idan na tsinci kaina a aljannah na fara tozali da ita cikin jerin matayen da ubangiji zai bani. Wallahi idan kika cire Hajiya ba wadda nake jin sonsu a raina da zuciyata irin ke da d'anki." Ya nisa ya cigaba da cewa "Ba zan miki karyar bana son Farida ba, ba zan miki karyar bata da wata daraja a idona ba, hakanan ba zance miki bana jin da'din zama da ita ba. Sai dai idan har gaskiya zan fa'da miki! Ina jiye miki a wayi gari Farida ta yi kunnen doki da ke a zuciyata, koma ta zarta ki, domin ita din mai hakuri ce, mai kawaici ce, ta sani na fi sonki, amma bata ta'ba tayar mini da hankali akan hakan ba. Zuciya a kirjina take kawai, amma bani nake sarrafa ta ba, ubangiji ne, Annabi kuma ya ce an gina zuciya da kaunar wadda yake kyautata masa". Jikinta ya laushi irin tubus din nan, tana gasgata dukkan furucinsa, ta kuma gasgata tana da kafiya da kaifin harshe. Tun ranar da ya auri Farida bata sake jin nutsuwa a zuciyarta akansa ba, sai yanzu. Ta nisa ta ce "Shikenan! Ka yi ha'kuri zan gyara, zan kuma kiyaye, amma dai ka dinga mini uzziri, ni akan ka, bana iya sarrafa kishina, ka taya ni addu'a, ka kuma kara ha'kuri da ni, kar kuma ka bu'de kofar da wata macen zata kamo ni a zuciyarka". Ta fa'da hawaye na zubowa. Da sauri ya matsa ya rungumeta, yana jin tamkar an yaye masa wata katuwar masifa a rayuwarsa, yana jin wata irin salama tana mamaye dukkan zuciyarsa. Ashe wannan 'daaurin da 'kirjinsa ya yi, ashe wannan fargabar da yake tsintar kansa a ciki, duk saboda rashin samun aminci ne daga wajen Sa'a? A yanzu da ta yarda zasu zauna lafiya sai ya ji tamkar anyi masa bushara da gidan aljannah ne. A fili ya dinga fa'din "Alhamdulillah! Allah kasa karshen tashin hankalin da zamu fuskanta kenan, Allah ka sanya wannan shine karshen jarrabawar mu". Sau uku tana yun'kurin yin magana sai ta kasa, da ya lura da hakan sai ya ce "fill free, fa'da mini abin da ke ranki". Ta tura baki gaba ta ce "Amma dai ka yi mini al'kawarin ba zaka ha'da ni zama da wata matarka ba, kuma yanzu na tabbatar waccan part din na Amaryarka ne". Ya sake ru'ko ta sosai ya ce "Ban manta al'kawarin ba, amma sai nake ganin a waccan gidan da kika tsara yadda za'a gina shi, na miki wannan al'kawarin, yanzu kuma ai bashi bane". Da rawar murya ta ce"kar ka hadani zama da ita, kar ka bari na dinga ganin mua'amalarku, zaka iya rasa ni a dalilin ciwon zuciya ko hawan jinin farat 'daya". "Ina son ki koyi jarumta Sa'adah! Ina son hankali na ya tsaya a wuri daya, a yanzu da nake matu'kar mararinki, idan na rabaku zan halaka ne, Ina tabbatar miki zan tare ne a inda zuciyata tafi so, shi kuma adalci wajibi ne ka yiwa kowa. Addinin musulunci! Addinin adalci ne, ubangiji ya sani namiji ba zai iya raba soyayyar matansa ta zama daidai a zuciyarsa ba, sai akace an masa uzziri anan, ma'ana bai yi laifi ba dan ya so wata sama da wata ba. Har ilah yau Sharia bata ce dole abin da ka yi da wannan, idan ka koma wajen wannan ma sai ka yi mata irin wannan ba, domin ansan ba zamu iya ba. Amma duk da hakan sai da Annabi ya yi ta wasiyyar kar mu jingine mace, mu ratayeta ita ba sakakkiyar mace ba, ita ba matar aure ba, dole a rabon kwana, muhalli, abinci da sutura ya zama daidai (eqaul). Shari'ar musulunci ta yiwa mata gata da adalci, ta yadda ko ba ke aka fi so ba, to kuwa indai ana kan tsarin sharia din ba za'a ki wulakanta ba". Ya numfasa sannan ya ce "ki min hakuri zaki koma wanccan gidan amma ba yanzu ba, ki bari nima na koyi jarumtar da zan kiyaye ka'idojin shari'a". A hankali ta ce"To" ba dan tana so ba, sai dan kar ta cigaba da yi masa gardama yana ganin Farida ce mai biyayya kawai. Ya tsura mata ido yana kallonta, sonta sai huda dukkan sassan jikinsa yake yi, cikin kasalalliyar murya ya ce "har yanzu baki huce da ni ba, har yau baki yafe mini ba?" Murya ba amo ta ce "me yasa ka ce haka?" "Har yanzu ban ji kin kira suna na ba, Na sani kuwa idan kina fishi ne kike gatsa sunana dan ki nuna mini iyakata. Idan kuma ba kya son shiga shirgina sai ki yi maganar ki ba tare da kin kama sunan ba" Ta zuba masa wani irin kallon da yake kidima shi, tana murmushin da wurshiryarta ta bayyana, hawaye kuma ya zubo mata Ta ce "Malam". Farin-ciki ya dirar masa fiye da wadda yake ciki, rabon da ya ji ta ambaci Malam a bakinta, tun ranar da suka hadu a gidan 'Karfi kafin komai ya tabarbare musu. Ya sa baki yana lashe dukkan hawayenta da yake zubowa. Ya yi gyaran murya ya ce "nan da kwanaki shida zaki tare, Ranar juma'ah mai zuwa. Yanzu mu je ki za'bi funtures din da kike so, masu harkar 'kawata gida, za su zo su shirya miki". A hankali ta ce "Na gode sosai! Amma ka barsu, domin yanzu ina da kishiya idan ta gane haka na zo, zata samu dama akaina". Ya kalleta ido cikin ido tsawon lokaci sannan ya ce "Na ta'ba rokon ki a shekarun baya ina so ki ji a ranki nima tamkar Sumayya nake a wurin ki, ashe baki dauke ni hakan ba?" Ta kasa bashi amsa. Ya ce "Wallahi Sa'adah ko wani kika aura ni zan miki komai da uba yake yiwa yarsa domin Baffah zan yiwa, lokaci ya yi da zai huta, a yanzu abin da nake ji game da shi ba wai kallon mahaifinki nake masa ba, kallon nawa uban nake masa, domin ya mini abin da na tabbatar uba ne kawai zai yi wa 'dansa. Na yarda da maganar da ake cewa ko baka haihu ba, idan ka yi alheri ga marayu da masu rauni, ka zauna da mutane lafiya, ka yi hakuri da cutarwarsu, to ubangiji sai ya turo maka wadda zai yi maka abin da ko 'danka ba zai maka ba, haka nan idan kana da zuri'a ubangiji zai baka wadda zai jibanci lamarinsu ko da baka numfashi". Baffah uba na ne, da ubangiji ya bashi, komai zan yiwa jinisa a duniya ban biya shi ba, dan haka ki yarda da ni, ko ba aure a tsakaninmu Ni din mai yi miki komai ne, mai kuma tsaya miki ne a ko Ina". Ya yi shiru! Sai kuma ya cigaba da cewa "wanccan gidan da kike magana akai tun ranar da kika ce mini filin ki Baffah ya siyar ya bani ku'di, zuciyata take ta bugu akan na baki shi kyauta, sai dai bani da halin bawa Farida irinsa, dan haka na bawa Jawad shi, na je an canja takardun, sunan Jawad ne akai. Idan na gamsu sosai zan iya ware miki gida, shikenan sai ki koma gidan d'anki kafin na samu damar da zan sake yi muku wasu gidajen a jere amma ko haraba ba zan ha'da ku ba". Karon farko da tasa hannu da kanta ta rungume shi tana kuka 'kasa-'kasa. Ta tabbatar da gaske Malam din nata ne har yau. Ta ce" na gode sosai ubangiji ya fini yabawa. Zan iya kokarina ban tayar da hankalinka ba, ba zan cuci matarka ta hanyar asiri, ko sharri ko zagon kasa ba, lafiyarta da mutuncinta har ma da dukiyarta amanace a gare ni, na yi maka al'kawarin ba zan tsokaneta ba, ba zan taba mutuncinta ba, ba zan yi shirka dan na farraqa tsakaninku ba, na yarda 'kaddararka ce itama. Amma abin da nake so ka yi mini dalci a ciki shine ni ban iya munafunci ba, am straight forward, ka ja mata kunne akan tsokanar da take fakar idon mutane tana yi mini, ba zan yi gaba da ita ba, amma kuma babu aminci a tsakaninmu da zamu zama so close, kowa ta yi harkar gabanta". Jiki na rawa ya dinga fa'din"thank you! Thank you so much my love". Saboda ba 'karamin nutsuwa ya samu na saukowar ta botsarar tasa ba,😅 ya dinga neman tsari da abin da zaisa ta sake mur'dewa. Ya tabbatar har zuciyarsa tsoron fishinta yake yi, tsoron ta birkice yake yi, 'karfin hali kawai yake gwada mata, idan yana bagarar da ita ko yana nuna mata iyakarta. Bai nemi ya sake ta'ba ta ba, duk da yana bu'katar hakan. A waya ta zabi furniture's din da take so, amma Mk ya canja mata da masu tsadar gaske, ta dinga jin tausayinsa, shikuma so yake ya wanke mata zuciya, ya sani dan ta kwantar masa da hankali ne, da kuma son ya fahimci ita yanzu ba luxury life a gabanta yasa ta zabi masu sau'kin kudi, shikuma sai ya daure ya siya mata masu daraja sosai tunda ya yi 'karfi yanzu, business dinsa yana garawa 'kwarai da gaske. Ya mayar da ita gida, suka rabu cikin shau'ki tamkar wani abin bai ta'ba gittawa a tsakaninsu ba. Kai-tsaye gida ya wuce tunda biyar ta yi, ya samu Farida a falo ta yi kwalliya ta sha kyau, ga abinci a dining, yana jiransa, ya dinga jin kunyar me zai ce mata kuma yau? Tunda yake fita da Sa'a baya cin abincin rana a gida, saboda tare yake ci da Sa'adah. Ya daure ya bita zuwa dinning din, ta zuba masa brown sphagetti da ta ji kayan lambu, sai papper fish a gefe. Ya dan ci ka'dan ya ture domin ya riga ya shafa'a ya ci a waje. Takaici ya 'kume Farida, idonta ya ciko da 'kwalla. Ya kalleta ya ce "menene yake damunki?" Da rawar murya ta ce "yau kusan kwanaki goma baka cin abinci na, jiyan nan ka gama yi mini al'kawarin yau zaka dawo mu yini tare, kai ka ce na yi maka wannan nau'in abincin, na yi kuma ka bar mini abina". "Yi ha'kuri my ferial! ba haka bane, ai dai kinsan duk safiyar duniya da abincin ki nake karin kumallo, idan na yi aiki na gaji ne, yunwa ta kamani sai na kasa daurewa na je capteria na ci, amma yi hakuri zan dinga jurewa". Yana rufe baki ta ce duk zamana da kai ban san kana zuwa capetaria kullum ba, sai yanzu dai da ka yi Kome! Na san abin da nake yi, Ina sawa abin da nake so ido fiye da kaina, kullum ka cire kayanka scent din Gogel nake ji, ban yi magana bane saboda na sani matarkace kuma cike kake da 'dokin sake dawowar ku abu guda, amma kuma shikenan sai abin ya zama ba waiwaye tun yanzu kake son sai dukkan rauni na ya bayyana? Ka yini a wajenta, ka dawo mini gida a gajiye da ka kwanta sai barci". Ta fa'da muryar ta na rawa. Sanin da ya yi ita din ba mai 'korafi ba ce, sai ya gano lallai bango ya nemi kaita, ya sani kuma da gaske ne ya watsar da ita a wannan tsukun. Dan haka ya sassauta murya ya ce "very sorry my dear! Ko ka'dan ba abin da kike nufi bane, amma tunda na bata miki, ki yi hakuri ki sake yi mini afuwa da uzziri. Ubangiji ya miki albarka, ke mai hakuri ce, mai kuma fahimta ce." Da haka ya lallaba ya jata bedroom, second round din da bai yi da Sa'a ba, ita ya yi da ita. Sai daf da magariba suka samu kansu, a gurguje ya yi wanka ya wuce masallaci, yana jinjinawa duk Namiji da yake da mace sama da guda, yake kuma tsaye dan ya yi adalci. Sai da ya dawo ya fa'da mata Sa'adah zata tare ranar juma'ah mai zuwa, ita kuma zata tare juma'a ta sama. A ranta ta ji ita ya kamata ta fara tarewa, tunda itace suke tare, bai kamata ace ita zata je ta tarar da Sa'adah ba, shikuma ya yi hakan ne dan ya tabbatar da Sa'a ce uwargida ba dan wani abin ba. Amma sai ta ce "Allah ya Sanya alkhairi". Ranar laraba aka gama shirya komai na bangaren Sa'adah! duk inda tsari da haduwa wurinta ya kai, a ko ina kuwa, ba kananun kuda'de aka fitar ba. A ranar dai ta laraba Sa'a na zaune a tsakar gidansu ba hijabi a jikinta adalilin Inna ta je unguwa, ba zato ta ji sallamar Innar a tsakar gidan. Gabanta ya yanke ya fa'di, ta hau dube duben Hijabinta ashe a 'daki ta barshi. Zabura da waige-waigen da take yi ne ya ja hankalin Innah ta tsura mata ido, take ta gano abubuwa masu yawa da suka sauya a tare da Iyah. Kirjinta ya matu'kar cika, sannan ta yi fari ta 'dashe tamkar mai shafa man bleaching, sanin da Innah ta yi duk kwalliyar Sa'a bata yarda ta canja launin fatarta ba. Ta kalli fuskarta tana ganin yadda ta 'danyace, alamun dai mai shigar ciki 'karara. Dabas Innah ta zauna tana hirji. Ta jima tana kokawa da numfashi, sannan ta ce "mafarkina ne zai tabbata Iyah, ko kuwa yanzun ma mafarkin nake yi?" SURAYYA DAHIRU ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ 113-114. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *PROLOGUE*. *Masoyan FARIDA*! *Team FARIDA na so na ambato sunanku, sai na gane yawanku ba zai bari ba, Farida tana sonku, tana yaba muku, Ta ce na ce muku son so Fisabidillahi*.🥰 *MARUBUTA* *Hajiya Saliha A.A Zaria* *Hajiya Hafsat Sodangi*. *Hajiya Maimuna Beli* *Aunty Sumayya Takori*. *Hajiya Zulaihatu Sani Kagara* *SADIK ABUBAKAR*. *Fadila lami'do*. *Binta Abbale*. *Hassana 'Danlarabawa* *Maman Mama*. *Ayusha Muhd* *Kulsum Baffah Azare* *Umm Azghar*. *Gidan Iko* *Asiyah(asi beauty)* *Aisha jos* *Hafsat Bature* *Rabi'atu Shitu* *Aysha Dansabo*. *Da dukkan yan kungiyar lafazi writers da ma sauran marubuta gaba'daya* *Ina godiya sosai tare da fatan alheri.* *Allah ya 'kara Basira.* *Da* matu'kar kunya Sa'a ta ce "wanne irin mafarki kike magana Innah?" "Kul kika yi mini iya-shege Iyah! Ai kin san dai mai nake nufi, mike tsaye na ganki soasai". Ta 'ki mikewa sai 'boye jikinta da take yi. Salati sosai Inna take tana cewa Ni dama na da'de ina mamakin yadda aka yi kika sauko har kina nuna zakuwar ki akan ki tare, dan munafunci har kina cemin wai saboda ra'ayina zaki ha'kura ki tare ko ba kayan daki, ashe ke kin tare ma kawai ankara ne ban yi ba. To yanzu sai ki fa'da mini lokacin da kuka kunsa cikin dan asan ko auren na ku bai yiwu ba." Da rawar murya Sa'a ta ce haba Innah yanzu sai ki yi tunanin zan iya yin wannan ta'asar?". "To ina zan sani tunda daga ke har Muutar din ba mutunci ne da ku ba , bare kunya. Wato shiyasa kullum sai kin san yadda Kika 'kirkiro fita, ko dai da sunan zuwa gurin aiki, ko wani uzzirin da ba za'a hana ki fita ba? Oh ina zaune anmayar da ni garmaho, ko a dakin nan kuka yi abin da kuka yi?" Kuka Sa'adah ta saka, tana jin wata irin kunya tamkar ta tsaga kasa ta shige. Ta kasa magana, tana jin haushin Mk da ya janyo mata wannan muzantar a idon uwarta. Ana cikin hakan Baffah ya shigo ya ce "me ya samu uwata take kuka har da hawaye ne?" "Kukan iskanci take yi, ba dama ta yi ba dai-dai ba, ayi magana sai ta bare ja'irin bakinta ta yi kuka tamkar yarinya kankanuwa." "Me ta yi da ba zaki iya hakuri zuwa jibi ta tafi dakinta, itama hankalinta ya kwanta ba?" "Hmmm! ciki ne da ita, daga na tambayeta yaushe suka yi cikin dan asan matsayin aurensu shine take wannan gunshekin kukan tamkar na daketa ne, ke kam wallahi kin ji kunya, ba dan ni na haife ki ba, da tuni ki ba'kanta ni a idon duniya". Kunyar da Sa'a take ciki ta sake nunkuwa, dan haka ta sake 'kara sautin kukanta dan ta kawar da su daga sake kunyata ta. Aikuwa dai Baffah ya ce "To ai a hankali zaki bita, ni na gasgata Iyah ba zata kunyatamu ba, ba ta yi shashanci a 'karancin shekarunta ba bare a yanzu da ta yi hankali, na kuma shaida Mutari ba zai ha'ince ni ba". Wani irin farin-ciki ya kama Sa'adah tana gasgata Mk da ya ce Baffah Babansa ne ba nata ba. Innah bata gasgata ta ba, amma Baffah ya shaideta ba zata yi Zina ba, haka ya shaidi Mukhtar ba zai lalata masa 'yah ba. Kuma hasashen Baffah shine gaskiya. Kawai Innah mafarkin da ta yi ne, yake sata wasiwasi. Ya sassauta murya ya ce "Yi shiru ki mini bayani" Ta kasa cewa komai saboda tsananin kunyar da ta tsinci kanta a ciki. Ya juya ya fita yana cewa yanzu nan na hango shi ya zo unguwar bari na ji daga bakinsa. Ganin Baffah ya fita! Ya saka Inna cigaba da sababinta, "munafukar banza, kika dinga cika bakin ba kya sonsa, kika yaudarar da ni da cewa ba zaki tare babu kayan daki ba, ashe kina zagayewa kuna abin da ranku ya so, saboda tsananin fitina da rashin kunya" Daga ganin yadda kika aune, ansan ciki ya kwana biyu a jikinki, yo ina ganin HALIN YAU ni Salamatu!". Sa'a ba baki sai kuka. Baffah kuwa shagonsa ya 'kira Mk. Cikin nutsuwa sosai ya ce "Mutari ka ce mini jibi juma'a Iya zata tare?" Kai tsaye ya ce "Eh Baffah". Ya numfasa ya ce "yanzu na shiga gidan na ji wani irin al'amari da ban fahimice shi ba, na tarar da Iyah da gyatumarsu a halin 'bacin rai saboda ta fahimci tana da juna biyu". Mk ya mi'ke da sauri , zuciyar Baffa ta buga a tunaninsa kaduwa ya yi da jin maganar saboda ba shi da alaka da cikin. Da azama Baffah ya ce "Ina zaka? Nutsu ka saurare ni, baka da alaka da cikin da yake jikinta ne?" Ya koma ya zauna ba kunya ya ce"Haba Baffah! Ni fa zaburar da na yi, zuwa zan yi na fahimtar da Innah ta daina yi mata fa'da, Ni zata yiwa, tunda nine Babba! Domin na san kai zaka shedi ne ba zan yi lalata da jininka ba! Amma sai na ji kana tambayar ko bani da alaqa da al'amarin. Kawai ayi ha'kuri Baffah! Abin da za a kallah a samu nutsuwa matatace, na kuma shaida akan ka'ida komai ya faru". Hankali Baffah ya kwanta sosai ya ce "To Allah ya rufa asiri". Mk ya mi'ke yana cewa "Yau ba doguwar hira Baffah na ji kunya ba ka'dan ba". Murmushi Baffah ya yi tare da cewa "ja'iri da kana jin kunya da baka yi abin da ka yi ba". Ya rufe shago ya koma gidan ya tarar har lokacin Innah na zubawa Sa'a sababi da gorin ta ji kunya, ta yi ciki a gida. Ita kuma sai kuka take yi tana jin takaicin abin da Mk ya janyo mata. Baffah ya ce "Mayar da wukar ki Salamatu! Bata hanyar banza suka same shi ba, ni dama ina da kyakkawan Ya'kini a ziciyata baza suyi hakan ba". Takaici ya kama Inna ta shige daki ta barshi da Iyah, tana Jin irin rarrashinta da yake yi, tamkar ba abin ayi mata kashedi ta yi ba. Ranar juma'ah Mk da kansa ya zo ya dauki Sa'adah! A mota sai kuka take yi. Sai da suka zo kofar famfo ya ce "Fisabidillahi kukan nan na menene? Na ro'ki karki bata mini Rai". Tara saura suka isa, taga irin daular da aka shirya mata, ta rungumo shi tana ta fa'din thank you Malam"!. Ya ce "ki yi hakuri ban samu damar yi miki lefe ba wannan karon ma, ki bini bashi, idan komai ya dai-daita zan yi Miki" Kwana suka yi cikin farin-ciki mai yawa ha'din kai da soyayyar da Sa'a ta nunawa Mk yasa ya dinga hawaye ba tare da ya san yana yi ba. Da sassafe ta tashi ta shirya masa irin kunun gyadan da tasan yana so tare da wainar rogo mai dadin gaske. Ya tashi ya ganta ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar shaddar da ta karbeta, cikin jikinta ya' kara mata kyau da yarinta. Ya dinga kallonta, a zuciyarsa sai faman godiya ga ubangiji yake yi. Ta ce "wannan kallon fa? Ka tashi ka yi wanka ka zo mu karya ni wallahi yunwa nake ji". Ya diro daga gadon yana cewa "zo muje ki tayani wankan". "Ni na riga dana shirya dan Allah ka yi sauri ka fito". Ya wuce toilet din yana cewa to 'Ranki ya da'de". Cikin kwanaki ukun da ya yi a gidanta wadda shari'a ta bashi, ba karamin soyayya ya nuna mata ba, ba irin rawar jikin da bai mata, shekarun bakwai din da suka shafe cikin tashin hankali da ba'kin ciki sai da ya wanke musu a cikin kwanakin, har Sa'adah take mamakin maganar Innah da tace idan ta yarda da shi kafin ta tare, ba zai yi 'dokinta ba. Ga mamakin Mk ranar da zai koma wurin Farida yini ya yi cikin zullumin kada Sa'a ta botsare, amma har 'karfe shida na yammaci ta biye shi suna ta harkar arziki. Da zai tafi, ya rungumeta ya ce" idan na yi sallah zan wuce gidan Hajiya, zan kaita unguwa wata'kila kafin na dawo kin yi barci". Ta ce "ba damuwa ma hadu da safe". Da'di ya kama shi, ya dinga kissing 'dinta. Suka rabu 'kalau, yana murnar addu'ar da yake yi mata na samun sau'kin kishi ya fara ganin tasirinta. Yayin da ita kuma tana sallah tana kuka, tana ro'kon ubangiji ya sassauta mata kishi, ya bata jarumta da ha'kurin danne shi. Kwananta hudu wata babbar motar daukan kaya ta zo shake da kayyaki, yini guda aka yi a bagaren Farida har washagari suna fama. Ranar da juma'a kuwa wadda yayi dai-dai da satin Sa'a daya a gidan Mk ya dauko Farida da kansa. Kai tsaye bangaren Sa'adah suka yada zango, cikin 'karfin hali ta karbe su, ta gabatar musu da ruwa da lemo har da abinci. Cikin son K'ulla alaka a tsakanin su, Mk ya ce " kin zuba mana abinci tare, ke kuma kin koma gefe, dauko cokali kawai muci tare". Ta daure ta ce "Na riga da na ci tun 'dazu". Kallonta kawaya yi ya gane bata ci ba, sannan kokawa kawai take yi da zuciyarta. Dan haka sai ya mike ya dauko mata spoon din da kansa. Ta karba suka ci dukkansu uku a plate 'daya. Ba magana sai karo a tsakanin cokula da plate. Sai da suka kammala ya yi musu addu'a! Sannan ya roke su arzikin su zauna lafiya da juna, bayan ya tabbatar musu zai yi iyayinsa ya yi adalci a tsakaninsu, ya tabbatar musu dukkansu yana sonsu dan haka ba wadda zai musgunawa da gangan, ranar da aka samu akasi ya 'batawa wata, to ta yi masa uzziri yau da gobe ne, sannan dole idan ana tare dole a fuskanci matsaloli, sai dai kar a bari matsalar ta yi girman da ba zata gyaru ba. Ya nisa ya kalli Sa'adah da kanta yake 'kasa ya sassauta murya ya ce" Sa'adah ta dago ta kalle shi sannan ta ce "Na'am"! "Ku fa'da mini tsarin da ya muku wurin rabon kwana" A sanyaye ta ce "Farida fa'di yadda zai yi". Cikin nutsuwa Farida ta ce "Majority anfi yin kwana biyu, mu barshi a hakan mu ma". Ya sake kallon Sa'a ya ce "Hakan ya yi miki?" Ta amsa da "eh" a hankali. Ya sake yi musu nasiha tare da shawartarsu su sanyawa ransu zaman ibada zasu yi, yin ibada tsabtatacciya kuwa sai mai hakuri mai kuma Imani na gaske. Ya mi'ke yana cewa Sa'aadah "muje ki yi mata rakiya". Ta bisu ba dan tana so ba, sai dan kar ya ga gardarmarta. Da gaske ta dauki aniyar canji. Suka isa bangaren Farida da ya 'kawatu da kaya na garari. Duk yadda Sa'adah ta yaba haduwar bangarenta, da ta ga yadda aka narka dukiya a wurin Farida sai da ta girgiza matu'ka da gaske. Jikinta ya sake mutuwa, bata fi mintina biyar ba ta mike tare da cewa"Allah ya sanya alkhairi". Itama Faridan ta mike tana cewa "zo mu shiga mu ga gidan sosai mana". Akan dole Sa'a ta bita, ta ga 'dakunan da suke falon wanda 'daya tsarinsa ya tabbatar mata Jawad aka shiryawa dakin. Akwatuna da ta gani guda uku set, masu tsadar gaske, ya tabbatar mata kayan fa'dar kishiya Mk ya yi mata, Amma ita ko akwati 'daya bata samu ba. Sai dai take ta tuno milyoyin da ya kashe mata, sai ta yarda ta kuma gane ba laifi ya yi ba. Ta riga ta gamsu Mk bai kai 'karfin da zai zuba irin wannan kayan ba, ta kuma yarda idan har yana da ku'din yin hakan to ita zai fara siyawa. Suka gama da dakunan suka yi kicin da yake shake da na'urorin zamanin da ba zasu lissafu ba. Sa'a taki yarda da shiga dakunan su na cikin corridor wadda ta tabbatar sai ya ninka na falon 'kawatuwa. Tunda dakunan Farida da Mk ne. Har bakin kofar Farida ta rakota sannan ta juya ganin Mk na waje, ta sani rakiya zai yi mata, tunda wurinta yake ma'ana Faridan ce mai girki. Sa'adah tana ganin Mk ta wuce shi fuu tamkar bata ganshi ba, ganin haka ya bita yana 'kiranta amma bata tsaya ba. Har suka isa bangarenta, ta zauna a falo ta fashe da kuka, jikinsa na rawa ya ru'kota, ai kuwa ta dinga dukansa ta ko ina, ganin dukan ba mai illah bane, sai ya sunkuya mata sosai ta yadda zata ji da'din dukan nasa. Sai data gaji dan kanta sannan ta barshi, shikuma ya janyota ya rungume. Ya dinga karfafa mata guiwa, tare da zugata, har ya samu ya zagwanyar da rikicin da ya taso mata. Sai da ya kaita har 'dakin barcinta, ya jira ta yi wanka, ta kwanta ya lulluba mata bargo. Sai a lokacin ta ce "Malam" ! Ya amsa Mata da cewa "Na'am my dear Iyah"! Cikin rauni ta ce "Amana dai itace amana! Haka cika alakawari sai mai Amana, kar ka bari a kwace mini kai, kar kuma ka saba al'kawarin ni zan jagoranci zuciyarka". Ya kamu da tausayinta! Ya sani irin kayan alatun data gani an zubawa Farida shi ya sanya ta karaya. Ya matsa jikin gadon ya ru'ko hannuta ya ce "shekaru uku na yi da aure amma ba a kwace miki ni ba, sai yanzu da muke tare?" Ki daina shakku Malam 'din kine har yanzu, har kuma gobe". Hawaye ya zubo mata ta ce "Na gode sosai! Sai da safe". Ya ce ai ba zan iya tafiya ban ga murmushinki ba". Ta kuwa murmusa sosai, ya sunkuya ya yi pecking dinta yasa hannu ya shafa cikinta. Ya ce Good night and stay blessed". Ya kashe mata fitila ya fita. Ta dinga shafa daidai inda ya shafa cikin, tana Jin kaunarsa na ratsata. Ta nisa tana hakaito kayan da Mk ya siya ya zuba mata ta tabbatar duk yadda Ma'aikatar shari'a take da albashi mai tsoka, sai ta shafe shekaru uku zuwa hudu kafin iya tara kudin siyan irinsu, ta tabbatar Farida kuwa iyayenta suka yi mata. Ta share hawayenta tana Jin tabbacin ko a birnin Abuja ba za'a raina mata nata kayan ba. Satin da ya zagayo aka yiwa su Jawad hutu. A hanyar su ta dawowa ya ce "Malam". Mk ya amsa da cewa"Jawad". "Dama wannan hutun ma ka ce mini ina nake son yin hutuna?" Dariya ta kama Mk ya ce "Dama ka bari muje gida tukun". Suka wuce Gadon 'kaya Jawad ya ce "Malam zamu biya wani waje ne? Na ga mun wuce hanyar gida". Ya ce "Na manta wani file a office ne, shine zamu je na dauko". "Ok" Jawad ya fa'da a gajarce. Suka iso mai-gadi ya bude musu. Jawad ya kasa hakuri, ya ce Malam ko kun yi parking zuwa wannan gidan ne?" "Mun dawo last two weeks" Mk ya amsa masa. Farida tana wurin aiki. Kai tsaye bangaren Sa'adah ya nufa da shi, bata falo, Jawad ya fa'da kan kujera ko sandal dinsa bai cire ba. Ya ce "Wow falon nan so mashallah! Ya 'dago a zabure ya ce Malam amma ka san me nake ji?" Kafin Mk ya yi magana ya zarce da cewa! "Ina jin irin 'kamshin gidan Maman Gombe (Sumayya) sannan ina jiyo 'kamshin Mamina! Aunty ta canja turare ne ko kuwa kewar Mami da nake yi ne?". Mk ya zuba masa ido yana gasgata kaifin kwakwalwar yaron. Kafin ya bashi amsa Sa'a ta fito cikin tattausar yadin material doguwar riga bubu, ta yi kyau sosai. Jawad ya daskare a zaune, ya murtsuka idanuwansa yana son ya tabbatar ba Farida ce take yi masa gizo ba. Ya budesu sosai ya tabbatar itace mussaman da kamshinta ya sake cika gurin. Ya kuwa fasa ihu ya kwasa a guje zai wawurota. Mk ya yi hanzarin ru'ko shi ya ce "Wallahi ba zaka ka kayar da ita ba, tana fama da kanta. Da Jawad ya rasa yadda zai yi, sai kawai ya yi tsalle ya 'dane Babansa. Yana fa'din thank you world best Father! Ka cika promise, na dawo na tarar da Mami a gidanmu, thank u very much Malam". Ya sauko ya nufi uwarsa cikin nutsuwa ya rungumeta, haka kawai sai ya tsinci kansa da fashewa da kuka. Itama ta dinga hawaye. Mk ya kallesu da tarin 'kauna ya ce "To kukan kuma na menene, ban da dai kin 'bata shi da kukan shagwaba, maimakon ki hana shi sai ki taya shi kuma?" Bata kula shi ba, ta ja hannun Jawad ta zauna akan kujera shi kuma ta dora shi a cinyarta tamkar 'dan shekaru biyar. Da azama Mk ya mayar da shi kan kujera ya ce "Ban son haka! sai ya buge ki? Ai kinsan ba lafiya ne da ke ba, da zaki sun'kuma wannan 'katon yaron a cinya, garama a samo masa 'kanne da yawa, ko ke da shi kwa yarda ya girma". Tissue ta dauko tana goge fuskarsa tana fa'din "is ok, ya Isa haka". Sun dade kafin su samu kansa ya daina kuka. Sai da ya yi wanka a dakinsa da aka shirya masa da kayan katako irin na 'kasar Turkey Ya fito falon yana cewa "Dakin nan nawa ya birge ni, ya mini kyau". Mk ya tuna kayan da Farida ta siya ta zuba masa a dakinsa na gidan gadon Kaya, masu tsananin tsada, amma bai ta'ba nuna sha'awarsa ba, bare ya yaba. Ya sake hakaito a yanzu haka dakinsa na bangaren Farida ya ninka wannan 'kawatuwa, amma ya san halin Jawad sai ya fi son wannan saboda shine na side din uwarsa. Yamma liss Farida ta dawo, a ranar Sa'adah ta karbi girki. Da ke Jawad a Farin ciki yake da sauri ya je ya yi mata barka da zuwa. Sai da dare ya yi Mk ya rufe ido ya ce Jawad ya tafi dakinsa na bangaren Farida ya kwana a can. Akan dole ya tafi, Sa'a ta bishi da Ido. Washagari tun sanyin safiya ya dawo side din uwarsa haka kullum yake yi. Rannan Mk ya balbale Sa'a da fa'dan itace bata nuna masa ya dinga zama a wurin Farida. Murya na rawa ta ce "Kullum ina yi masa fa'da, ji ne ba ya yi". Yana fita ta kalli Jawad da yake rakube a gefe ta ce "Ka ji da'di, da ka janyo mini bacin rai". "Ni wallahi Mami na gaji! A U.k. ba ayin haka, kowanne yaro ana barinsa ya rayu a inda yake so, bare ni da nake so na zauna tare da uwata". Ya fa'da da bacin rai. Mk da ba nisa ya yi ba, ya juyo daukan wayarsa. Ya ji Sa'adah tana cewa "Ai shikenan tunda ba zaka dinga jin maganar da nake fa'da maka ba, idan wani hutun ka dawo kaga ba nan din na koma gidan Baffah, ai ka zauna dole a inda ya ce maka". A sanyaye ya jiyo Jawad ya ce "sorry Mami na daina, zan dinga zama, har sai na yi wanka na karya. Ya hango ta mika masa yatsa tana cewa "promise". Wato ya miko nasa yatsar su K'ulla al'kawari. Sai suka tuno masa da rayuwarsu ta baya. Wannan hutun ba inda Jawad ya je ya kwana, ko gidan Hajiyar Bichi yanzu ya'ki kwana ta dinga yi masa gorin tunda yana ganin uwarsa, shiyasa yanzu baya nemanta tamkar ba shine yake kuka idan ance ba zai kwana a wurinta ba. Haka hutunsa na sati uku ya qare, Farida da Mk suka mayar da shi. Sa'adah har ta shirya Mk ya murje idonsa ya ce ta zauna a gida ba zata je ba da Farida zasu tafi. Har sun shiga mota ya kasa tafiya ya kalli Farida ya ce a minutes please. Ya nufi side din Sa'a ya tarar da ita zaune a falo ko mayafin bata cire ba. Ya ru'ko hannuta ya ce "Na kasa tafiya sabaoda baki mana addu'a ba". Ba tare da ta kalle shi ba ta ce "Ku dawo lafiya". Ya kirata a tausashe, ta dago suka zubawa juna ido. "Fishi ki ka yi ko?" Ta kasa cewa komai. "Ki yi hakuri! Na sani kina son zuwa, amma tunda da ita muka saba kai shi da zuwa visiting bai kamata yanzu na canja ba, zata dinga jin damuwar rashin haihuwarta, sannan kema wahala zaki yi, tausayin ki nake ji". Ba walwala a fuskarta ta ce "Na fahimta, sai kun dawo". Ya yi sukuri ya numfasa ya ce "Then smile". Ta tura masa baki gaba tabbacin ba maganar murmushi. Ya dara ka'dan ya ce "Akan 'dan fari kike wannan fishin, ke ko alkunya baki iya ba?" Ai kuwa nan da nan tasa hannunta ta rufe fuskarta tana fa'din"Bana so Malam " a shagwabe. Yasa hannu ya bude fusakr sai ta runtse idanuwanta tana murmushi murmurshi, kunya, kunya. Da haka ya lallaba ya tafi suka rabu k'alau. Zuwa yanzu hankalin iyaye, da dangin ma'auratan ya kwanta. Haka Mk yana iyakacin kokarinsa na kamatan adalci na gaskiya a gidansa. Amma idan ya kebe da Sa'a baya iya mallakar kansa. Ta bangaren matan nasa sun gamsu Mijjinsu ba munafikin namiji bane, sai dai kowacce tana ganin yana fifita yar'uwarta. Farida har zuciyarta ta gamsu yana yi mata adalci, amma ta san yafi son Sa'adah, Dan haka take zargin yafi walwala da kuzari ranar girkin Sa'a. Sa'adah kuwa gani take yi, Mk tsoron Farida yake yi, mussaman yadda yake tirsasa Jawad sai ya zauna a wurinta, sannan yafi fita unguwa da Farida akanta. Kawai hakuri take ta yi, dan kar ace itace babba sannan itace mai yawan korafi. A haka rannan sun je gaida Hajiyar Bichi da bata jin da'di, da kyar Mk ya shawo kan Iyah ta yarda su tafi tare, dan kuwa da tace ya tafi da Faridan ita zata je daga baya. Zuwa wannan lokacin cikinta wata bakwai, ta yi wani irin girma, fuskarta ta fara aunewa, haka baki da hanci tabbacin yadda cikin Jawad ya mayar da ita haka ma wannan zai yi mata. Farida ta yi matu'kar mamakin yadda ta ga Sa'adah da tsohon ciki, tunda ba kasafai suke haduwa ba. Wani irin kishi ya shaketa, amma sai ta yi ta addu'a tana namen tsari da yin jayayya a hukuncin Ubangiji. Kai tsaye Sa'a bayan mota ta shiga, matu'kar zasu fita tare dukkansu, ta sallamawa Farida gaban mota, wanda hakan na matu'kar yiwa Mk da'di. Duk yadda take boyen cikin sai da Hajiya ta gane Sa'a ta kusa sauka tabbacin da ciki ta tare, tunda basu cika wata hudu da tariyar ba. Sun dawo gida, maimakon Farida tabi Mk zuwa side dinta, sai kawai ta bi Sa'adah akan ta baata dambun da ta yi, tunda ta ga ta kaiwa Hajiya. Suka shiga, kamshin wurin yana matu'kar birge Farida amma ba zata iya tambayar wanne irin spices ne mai bada wannan kamshin mai kamawa ba, ga turaren wuta sai kamshin ya hadu ya ba da wani irin kamshi mai kwantar da zuciya. Duk da cewa side din Farida shima kamshi na mussaman yake yi, amma kamshin wurin Sa'a yafi kwanta mata a rai ko dan kishi ne oho. Sa'adah ta zauna tana haki, ta ce shiga ki dauko muku ya nan a cikin warmer. Ta shiga kicin din tana kallon komai, kayan tsilla tsilla amma kuma unique. Ta fito ta ce "Na gode sosai Gogel". Takaici ya kama Sa'adah wato Farida ba zata daina yi mata izgili cikin dabara ba. Ta tuna sunan garin su Farida Torondi, Amma bata ta'ba kiranta da hakan ba, ta tuna yadda yan set dinsu suke ce mata Taller saboda tsayinta, amma ita bata fa'da mata hakan ba. Ta sake tuna yadda ko Farida bata fa'da a gaban Jawad sai dai Anti! Amma shine ita zata dinga ce mata Gogel, ta tuno har a asibiti ta yi mata kashedi, amma saboda tsokana sai ta sake fa'da. Ta yi tsaki tana tunanin abin da zata yi mata idan ta sake. Ai kuwa washagari zata fita wurin aiki ta leko ta kawo mata dish dinta. Suka gaisa lafiya Lau ta kai kicin ta ajiye mata. Zata fita ta kalli yadda Sa'a ta zama gari guda. Ta ce "Gogel indai ba twins bane a cikinki, gaskiya kin kusa sauka, sai dai kuma na ga sai yanzu ne muke shirin four months a gidan nan". Kafin ta rufe baki Sa'a ta yun'kura ta ce "Idan zaki iya tuna kwanakin da kika yi ba kya ganinsa da rana, ba ya cin abincin ki da rana, to sune kwanakin da aka samu cikin, shi ya yi abinsa bayan an shafa fatiha ba wai shege bane". Nan da nan Farida ta muzanta ta ce "me ya kawo wannan maganar kuma Gogel?" Ai kuwa Sa'a ta ce "Tsugudidinki da tsokanarki, ta nunata da yatsa ta ce "Taller ki fita a idona tun muna shaida juna". Ga mamakin Farida sai ta ji Sunan da Sa'adah ta kirata da shi na Taller ya yi mata zafi ba ka'dan ba. Idonta ya ciko da 'kwallah ta ce "Sa'adah daga wasa?" Daidai lokacin Mk ya shigo! Sa'adah ta ce "ke Kika san wannan, to bana son wasan indai irin wannan ne". Ai kuwa Farida ta hau hawaye. Sa'a tana kallonta bata yi mamakin hawayen data fara dan ta ga mijinta ba, da'din abin dai bata isa tasa ya daketa ba. Ai kuwa Mk ya nemi jin ba'asin kukanta, ta ce Ba komai". Ta juya ta fita, shima ya bi bayanta, bai yarda ta fita da damuwa ba, sai da yaga ta saki ranta, da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga ta zauna, ya rankwafa ta windo yana cewa "drive with care please". Yayin da zuciyar Sa'a tamkar ta fashe saboda duk tana hangensu ta windo. Sai da Farida ta tafi sannan ya koma wurin Sa'a ya sameta, ya dinga yi mata sababi akan ta zo wurinta ne zata wulakantata har ta sakata kuka, har yana fa'din ke baki san halin Farida da son raha ba, ki dinga jin tausayinta mana". Ba'kin cikinsa yana neman kassarata. Ta hadiye kukan ta ce "Ai yanzu na gama ganeka, ita bata laifi, komai ta yi daidai ne, kome take so haka zaka yi mata, saboda ita din Babanta zai siya mata kowanne irin miji". Ai kuwa ya hassalo yana fa'din "wulakanci ki ya tashi ba? Ni kika fa'dawa wannan maganar?" Ta kasa magana saboda a yanzu shakkarsa take ji sosai, ba kamar da ba, hawaye ya balle mata. "Ta ce ta zo har 'dakina ta tsokane ni, bayan ka san har fa'da maka na yi akan ka yi mata togaciya, amma ba bincike ba komai, ka bi bayanta, ka rarrasheta, ni kuma ka zo kana mini jidali". "Jikinsa ya yi sanyi, fishinsa ya sauka, ya isa gareta da nufin rungumeta, ta goce ta ce "Tun bamu je ko ina ba kana son sai na gaza". Ya sassauta murya ya ce "Tausayinta nake ji, bata da lafiya sosai, bata samu haihuwa ba, sannan na fi son wata akanta, fa'da mini dan Allah bata cancanci a ririta farin-cikinta ba?" Ta zuba masa ido ta ce "Ban son wannan tausayin da ka tsananta akanta, ina jin fargabar abin da nake gani a idanuwanka akan lamarinta". "Ni meyasa baka jin tausayi na irin haka?" Ba ja in ja ya ce "Ina tsananin sonki Ubangiji ne shaida, kina da cikakkiyar lafiya, Ubangiji ya hore miki, kina haihuwa Ubangiji ya arzurtaki, Ubangiji ya arzurtaki da mahaifin da ba kowanne 'da ne yake samun irinsa ba. Fa'da mini ta inda baki kereta ba". Ya ru'ko ta, tana cigaba da kuka tana cewa "Allah ka bawa Farida haihuwa ko wannan tausayin da yake neman zame mini barazana ya yi sau'ki". Haka ya lallabata. Haka da Farida ta dawo, ya ja kunnanta da cewa "da bakin ki, kin ta'ba cemin kina fakar idon mutane kina tsokanarta, to ki bari tunda bata so, Nima bana so, ki kiyaye bana son muna samun sabani". Ta tsiri fishi! Ya tattara ya watsa da ita, ya shareta, dake bame yawan fishin bace da kanta kuma ta dawo hanya. Haka rayuwar take gudana yau fari gobe tsumma kowa ha'kuri yake yi da abin da rayuwa ta zaba masa. A haka Allah ya sauki Sa'adah lafiya! Ta haifi danta lafiyayye mai kama da Jawad sak, kenan Mk shima ya biyo. Kwananta'daya a asibiti aka sallamota bayan an tabbatar da lafiyarta da ta jariri. Tana zaune a dakinta ta tsurawa jaririn ido tana ayyana abubuwa masu yawa, bai zo da wuri ba a lokacin da Mk ya matsu ta haihu, haka bai yarda ya fito a jikin Farida ba, bai kuma fito a jikin wani namijin ba, tabbas kudurar Ubangiji yawa ne da ita, duk tsawon shekarun nan sai da ya jira ya fito ta tsatsonsu a lokacin da ba a yi zato ba, Wannan ka'dai ya isa aya ga mai hankali. Dai dai lokacin Mk da Farida suka shigo. Dukkansu suka isa gareta cike da kulawa suna yi mata sannu. Farida ta rungume yaron da tun jiya da ta 'dora ido akansa ta ji son yaron ya shigeta tamkar ta sace shi ta gudu. Sosai ta rungume shi, karon farko das tausayinta ya kama Sa'adah! Mk ya dinga tambayarta ko abin da take so ko bu'kata? Ta ce "Ba komai so dai nake yi na je gida ko kwana goma ne! Ka ga Umman Fanshekara bata jin da'di ba iya zama mini zata yi ba". Ya girgiza kai da sauri ya ce "ba zai yiwu ba, abar maganar". Ta yi shiru tana cewa "An barta". Mamamki ya kama Farida ada kallon mijin ta ce take yi masa indai akan Sa'adah ne, ashe ba ita ka'dai yake hana yin wasu abubuwa ba har da tauraruwar tasa. Tsawon lokaci sannan Farida ta mike da nufin basu guri ta ce "Tamkar na tafi da shi, tamkar na dawma ina kallonsa". "Tafi da shi mana Farida ai d'anki ne". Sa'a ta fàdi hakan a tausashe sannan ta mike da kyar tana janyo akawatin kayan yaron, Mk ya ce karfa ki fa'di". Ta dire a gaban Farida ta ce "Ki tafi da shi, ki dauwama kina kallonsa,ya dauma a 'danki, ina miki al'kawari ni dai a bakina wani mai rai ba zai ji ni na haife shi ba, ke din masaniyar magaganganuwa ce, kin san wadda zaki sha ya taimaka ruwan nono ya zo miki, na shayar miki da shi na kwana 'daya da yini, ubangiji ya taya ki tarbiya da juriyar raino, ina kuma yi miki fatan ki samar masa 'kanne ta tsastonko masu yawa". Mk ya mike da sauri ya rungume Sa'a yana jin sonta yana sake tumbatsa. Da rawar murya ya ce"Tunda kika yi sa'a Baffah na ya haife ki, na sani zaki yi abin da yafi haka na karamci! Na gode miki sosai Ina tabbatar miki har yau din nan ke ta dabance a cikin duniyata. Allah ya miki albarka! Idan har aljannarki tana 'damfare da yardata ne, wallahi daga yau na yarje miki, daga yau din nan Ubangiji ka shaida komai Sa'adatu zata mini na kuskure, har zuwa karshen zaman mu na yafe mata, na yarda da ita, Ubangiji ka yarda da ita". Farida tana tsaye tana kallonsu tana Jin inama itace Sa'adah! Ta matsa kusa da ita ta kalleta cikin ido ta ce "Wallahi Sa'adah kin fini kirki, kin fini hakuri, na tabbatar a yanzu da nake jin 'kaunar yaron nan ba zaan iya yin kyauta da 'da ba, koda na haifi guda goma. Ba abin da zance miki, sai fatan alheri, Ubangiji ya fini yabawa". Ta saba 'danta ta fice da shi, sai lokacin Sa'a ta fashe da kuka, tana jin girman 'karfin halin da ta yi. Ya dinga rarrashinta. Ta ce "shikenan Farida ta haihu, ta sami 'da Kamar Jawad! Sai ka daina takura shi sai ya je wajenta ya kwana, sai ka daina wannan tausayinta da yake neman zame mini barazana". Ya sake rungumeta tsantsan yana gasgata dinbin sonsa take yi, ya sani ba macen da take sonsa a doron 'kasa irin Sa'adah, idan aka cire Hajiya. Ya sani saboda tausayin Farida da yake yawan yi ne, ya sanya ta bada abin da yasan ba kowacce mace ce zata iya yin hakan ba. A fili ya dinga "cewa Madallah da ke Sa'adatu, a yau na sake ganewa ke din jarumace, mai kuma 'kaunata ce, zan sake maimata miki abin da na ce ba zan sake fa'da ba. Wallahi ban taba son wani abu a duniyata kamar ke da 'Yay'anki ba, Wallahi kune farin-cikina, kune duniyata, har na daina numfashi kece jagorar zuciyata. Ya rasa mai zai yi mata, sai ya ce ki shirya Gobe na kai ki gida, ki yi sati uku Inna ta sake gyara mini ke, kafin ba'di ina fatan ki haifo na ki wadda zaki ri'ke a hannun ki, a dakinki". *Wattanni shida a gaba* Zuwa lokacin Sa'a na dauke da wani cikin na wata biyar, yayin da yaron Farida mai sunan Mahaifinta Nasir(Amir) ta yi masa alkunya, yake wattanni shida. Yaron ya yi wani irin girma gashi fari kwal saboda farin Mk ya yi, sannan yana shan nonon farar mace, sai ya sake zama tamkar dan larabawa, irin ku'din da Farida take narkawa akan yaron abin tamkar a littafi, albashinta akan yaron yake karewa, haka Mahaifanta duk fitar da zasu yi sai anyi masa akwati guda, hatta Sa'a dalleliyar mota mahaifin Farida ya aiko mata a matsayin tukuicin sanya farin-ciki a zuciyar diyarsa. Shayarwa ba karamin karabar Farida ya yi ba, idan Sa'a tana ganin status din Farida da 'danta wani lokacin har kusan shidewa take yi tsabar kishin yadda suke daukar ido, domin komai designer take masa amfani da shi, yaron ya zama one in town. Haka fita goma shiga goma zata ganshi a kafadar Mk. Idan ya shigo da shi ta mika masa hannu sai ya ki, 'kiwa yake yi mata ba Yar kadan ba, tunda ko wurin aiki da shi Farida take tafiya da mai rainonsa. A wannan lokacin Mk ya kalallame Sa'a ta ajiye aikinta, ta zama lauya mai zaman kanta, a lokacin kuma tafiya zuwa kasar Amurka ta taso masa inda zai yi kwas na wattanni shida. Ya tisa Sa'adah ya tafi da ita. A can ta haihu still dai boy, ta saka rai girl zata samu sai dai Ubangiji ba hakan ya so ba. Sun more sosai a a zamansu na wattanni shida a U.S. Ta dawo da d'anta mai kama da ita wadda Baffah(Bashir) aka yiwa takwara Jawad ya ce *Jadid* za'a dinga ce masa. *Shekaru biyu a gaba*. Hankali kowa ya kwanta arziki da cigaba sai sauka yake yi a gidan Mk! Mussaman da ba'a yi masa tashin hankali, duk da kuma basa shiri. Dan hatta Amir har yau bai wani sake da Sa'a ba, idan Mk ya zo da shi baya yarda ya ajiye shi, ya dinga kuka yana cewa "Malam dauke ni" Ba zai yi shiru ba sai ya dauke shi, ko ya mayar da shi wurin uwarsa. A lokacin Sa'a ta yaye Jadid ta haifi mai sunan Mahmoud, da suke 'Kira da Junior, ta Kuma je asibiti ta sanya loop da amincewar Mk, tana addu'ar ta yi auta kenan, duk da tana tsananin son Baby girl, mussaman da ta lura Mk ma ya matsu ta haifi yar budurwa, amma itakam ta gaji ta fahimci ita da Sumayya basu da rabon haihuwar girls har gara ma Sumayya ta samu Khairat itama kuma sai a karshe domin itace ta biyar kuma autarta. A lokacin Ubangiji ya sua'kar da ayarsa Farida ta samu juna biyu, murnar da mk ya yi ba yar kadan bace, sosai yake tattalin ta har Ubangiji ya sa ta haihu lafiya duk da dai c.s aka yi mata, yarinyarta mace mai kama da su Jawad kwabo da kwabo mai tsananin gashi irin nata. Bidirin da akayi ba kadan bane, tun akan Amir farida ta gane jama'a na sonta na tausayinta, haka a wannan ma aka sake nuna mata kauna. Sosai Mk yake ji da yarinyar nan. Aka sanya mata sunan Hajiya Babba! Wato Aisha, Farida ta sanya mata Amira. Mafi yawa Mk ya fi yawo da Amir da Amira tun Sa'a na jin wani iri har ta hakura ta gane ba dan komai bane illah ya samu Amir ne bayan ya dauki lokaci babu haihuwa, ita kuma Amira only girl ce. Jawad ya kammala karatunsa na sakandire, ya wuce kasar Canada yana digiri dinsa akan engineering. Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin nasarori da kuma kalubale kala-kala. A yanzu haka Mk ya samu appointment ya zama minister ilimi na kasa, yayin da ya nada Mahmoud mai magana da yawunsa. Yana Abuja tare da Farida a dalilin itama ta samu transfer a wurin aikinta zuwa Abuja. Sa'adah kuma tana kano tana cigaba da zurfafa iliminta, a yanzu haka digiri na uku take duk a fannin shari'a. Duk week end din duniya sai ya biyo jirgi ya zo, sai dai idan baya ' kasar. Ta da'de da tarewa a gidan Jawad, haka nan Mk yana kan yi musu gini da ya zarta wadda take ciki. Ta dauko Hajiyar Bichi suna zaune tare cikin girmamawa. A yanzu da shekarun hankali da girma ya zo mata sai ta gane ba abu mai Dadi a rayuwar mace irin samun miji na gari mai adalci, ita da kanta idan ta tuno ta'barar da ta yi a baya sai ta ji kunya ta kamata, ta kuma godewa Mk domin ba abin da bai mata ba, ta kuma gasgata shi da ya ce shi din tamkar Sumayya ne a wajenta ba wai miji kawai ba, ba abin da bai yi mata, yana kuma tsaye akan dukkan bu'katunta, sannan yana hakuri idan borinta ya tashi. Haka nan ta gasgata shi da ya ce Baffanta Babansa ne ba nata ba, domin ba abin da bai yi musu ba, ya rushe gidansu ya zamanantar da shi, ya kai iyayenta sun sauke farali. Itama ta je, ta koma Umrah, duk da bata aiki kuwa. Ranar juma'ah ta yi ferfesun naman rago ta kaiwa Hajiyar Bichi dakinta, sannan ta ce "Hajiya zan je na gaida su Baffah". Da murmushi Hajiya ta ce "Ki gaishe su Sa'a, Ubangiji ya yiwa kokarinki albarka, yasa kema naki 'Ya'yan suji 'kanki. Ta isa gidansu ta tarar da iyayen nata zaune a falo sun yi shar da su tamkar tsufa bai cimma musu ba, ta zauna tana cewa "wayyo Baffahna". Da wata irin 'Kauna ya ce"sarkin hakuri, giwar mata, mowar 'ya'ya". Ta murmusa ta ajiye masa kwanon naman a gabansa. Inna ta ce "Danma dai uwa mafi uba ko da uban sarki ne". Cikin tsokana ta ce"Ai ni Baffah kam ya wuce ki Inna, sai dai ki yi 'hakuri kawai". Ta mike ta shiga kicin din da yanzu yana cikin falon ta debe bowls ta zuba musu, suna ci, suna saka mata albarka. Ta hada kan kayansu kananu ta wanke su tas. Ta yiwa Innah ganeral sanitation duk kuwa da ta daukar mata Yar aikin da take zuwa ta yi mata shara da wanke wanke. Amma duk da hakan duk karshen wata sai ta zo ta yi mata gyara na mussaman. Baffah ya tsura mata ido yana godiya ga Ubangiji, da ya arzuta shi da samun 'Yaya mata, ya tarbiyaantar da su har ya aurar da su, yanzu gashi sun zame masa gata, sun janyo masa mazajensu suna ta hidima da shi, ya yi Imani ko yana da 'yaya maza ba lallai su yi masa abin da Mukhtar d Idris din Sumayya suke yi masa ba. Gashi kuma ya'yan nasa sun haifa masa 'Ya'ya takwas maza, domin nassin al'kura'ani ya nuna jikanka danka ne. Madallah da iyayen da basa zaben jinsin da suke son su Haifa, suke godiya ubangiji ta hanyar tarbiyaantar da ya'yansu mata cikin adalci da tausayi. Sa'a ta koma gidanta, iyayenta suna saka mata albarka da nemawa zuri'arta tsari daga rudin *HALIN YAU* Mk ya cigaba da kula da iyalinsa cikin adalci da tausayi. 'Ya'yansa biyar Sa'a na da uku Jawad, Jadid da Junior. Yayin da Farida take da biyu Amir da Amira. Wani week end ya zo Kano, suna zaune a falo ya kalleta ya ce "sai nake tuna shekarun baya da kike ce mini kin yi mafarki, kin zama big Madam, na zama Alaji, na 'kera mana mansion". Itama ta ce "Na tuna amsar da ka ke bani cewar banga ka 'kara Aure ba?" Ya fashe da dariya tare da janyota Yana cewa 'dukkan mafarkin ki Allah ya tabbatar miki su, kin zama big Madam, abin alfaharin kowanne miji, tashi muje mu yi nafila mu sake godewa Ubangiji da ya cika mana ni'imominsa. Wani watan Ina son dukkan ku mini rakiya na gano 'Dan-iyah a Canada har da kannesa zamu tafi". Ta ce "Jawad bai zama 'dan Malam ba Sai D'an Iyah?" Da murmushi ya ce "shi ya ce mini sunan da zai sanyawa jirginsa kenan 'Dan-iyah Airlines. Yana kuma fatan ya samu sarautar 'Dan-iyan Bichi. Zan fadawa Baban Khairat zamu tafi da ita, ta gano mutumin nata, wata'kila dai zumuncin Jawad da Khairat nan gaba ya bada mamaki". A zuciyar Sa'a sai fata take Allah ya tabbatar da wannan hadin. ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH. *NA GODEWA ALLAH DA YA NUNA MINI WANNAN RANAR TA 27-7. DA NA KAMMALA RUBUTA WANNAN 'DAN LITTAFIN NAWA MAI SUNA A SAMA*. *INA MIKA GODIYATA GA DUKKAN WANDA YA KARANTA LABARIN*. *INA SAKE GODEWA MASU KIRANA, DA MASU YIN MAGANA TA WHATSAPP DAN SU YABA MINI, NA GODE MUKU SAOSAI, UBANGIJI YA FINI YABAWA* *INA ADDU'AR ALLAH YA KAWO MANA ZAMAN LAFIYA A KASARMU TA NIGERIA, YA KUMA BAMU DAMINA MAI ALBARKA*. *AUNTY RABI SANI GODIYA MAI YAWA, TABBAS KARFAFA GUIWAR DA KIKE YI MINI YA TAKA MUHIMMIYAR RAWA WURIN INGANTUWAR LABARIN NA GODE UBANGIJI YA FINI YABAWA*. *INA ADDU'AR ALLAH YA JIQAN MAHAIFANA DA DUKKAN WADDA SUKA RIGAYE MU*. *UBANGIJI YA SAKE HADA MU CIKIN WANI LABARIN, DA NAKE FATAN KU KAR'BE SHI TAMKAR HALIN YAU.* *INA RO'KONKU KAR A HA'DA MINI DOCUMENT, BANA SO, DAN ALLAH A KIYAYE.* *ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU*🤝 *SURAYYA DAHIRU GWARAM* ✍️✍️