Showing 27001 words to 30000 words out of 250533 words
Chapter 10 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
Kitchen hannunta ruƙe da tray an jera kayan breakfast ɗinsu, hankalinta kwance take tafiya jikinta na sanye da Skirt pensil baƙi yabi shape din Jikinta, Daga sama ta sanya Riga launin green, Ƙura mata ido yai yana kallonta, Idon su mami akanshi ganin yadda yake binta da ido.
Tsawa Ummi ta daka mashi a firgice ya waiwayo yana kallonta, fuskarta a ɗaure tace”Uban me kake kallo”? Yamutsa fuska yai”Kayan abincin dake a hannunta nake kallo ba wani abu ba,” yai maganar tare da wuce ya nufi dining table ɗin, da Ana take jera masu kayan breakfast, Kujera yaja ya zauna Yana faɗin”Ya ki ke”? Murmushi ta sakar mashi”lafiyalou, na gan ka ɗazu da safe zaku fita da baby junaid” 6ata fuska yai”shine baki min magana ba mun gaisa”?
Hankalinsu mami gaba ɗaya akanshi, Ummi tace”Oh Ni ƴar ubansu, Yaro ya zama mayen mata, In banda haɗama irinta Mahboob ina zai kai Ana”? Mami tace”tashen balaga ne kawai, nan da wani lokaci zai dawo hayyacin shi,” dariya suka saki, Kafin suka miƙe zuwa Dining ɗin domin suyi breakfast..
Lokacin da Zahra ta shigo ɗakin Aneelerh ɗauke da baby junaid, A zaune ta same ta gefen gado hannunta ruƙe da hoton su, wanda su ka yi aranar birthday ɗin Angel, tun da ta fito daga wanka, ta shirya kanta Cikin riga da skirt, kanta na ɗaure da mayafi, jin motsin shigowar Zahra yasa tayi saurin ɗaura hoton hannunta saman drawer, idanuwanta acike suke tab da ƙwalla.
“Aunty Aneelerh Ga Baby Junaid ɗinmu Ya dawo” cikin sanyin murya zahra tayi maganar don ta fahimci yanayin da Aneelerh take aciki, taƙi ɗagowa su haɗa ido, saboda ba ta san zahra taga hawayenta.
Sauke Junaid ta yi ƙasa, da gudu ya nufi Aneelerh ya haye saman Jikinta hannun shi ruƙe da ledar tsarabarta”Mommy ba ki yi missing ɗina ba”? a hankali ta ɗago ta kalle shi, wani irin farin ciki ya ratsa zuciyarta, duk halin da zata shiga idan tayi tozali da fuskarshi sai ta ji sanyi aranta, Ɗaukarshi tayi tare da ɗaura shi saman laps ɗinta sosai ta rungume abunta”Momy ga tsaraba ki ci” Zahra na atsaye tana kallon fuskar Aneelerh, tsananin tausayinta ta ke ji.
“Thank U my baby Boy, Nayi kewarka kamar zan zauce, Ya school ɗin? Surutu ya soma yi mata yana zayyana mata kyawun makarantarsu, yana magana ya buɗe ledar tsabar ya curo guntun donut daya ajiye mata abaki Ya tura mata, taunar shi ta soma yi tana murmushi, daga gefen su Zahra ta zauna still idonta akan fuskar Aneelerh, Sai kakkauce mata take yi duk don kada su haɗa ido
“Mommy uniform ɗina suna acikin motar bro, hada sandals ɗina, kuma ya ce in faɗa maki ba zai ƙara kaini school ba saboda fetur tsada yake yi, wai sai dai ke kina kai ni” dariya Aneelerh tasaki jin abunda yace”kwantar da hankalin ka, nima ai ina da mota, kuma zan fara zuwa aiki, Kamar yadda nake ɗawainiyar kai Angel makaranta lokacin da tana araye, inje in ɗauko ta kaima haka zan dinga yi maka....” zahra ce ta katse ta da cewa”nima ina da mota, kuma ashirye nake da in dinga ɗawainiyar kaishi,” sai da tayi wannan maganar Aneelerh ta ɗago tare da kallonta, Hawayen da take 6oye mata ne suke soma gangarowa saman kuncinta.
“Haba Aunty Aneeleeh i know it’s hard to let go of the past, but worrying about it won’t change anything wlh bamu jin daɗi idan muna ganinki cikin damuwa” zahra na rufe baki Baby junaid yace”sai da na mata faɗa ta daina kuka, ta ƙi jin maganana, mommy bata jin magana zanje na faɗa wa mami kina kuka” yai maganar yana ƙoƙarin sauka daga saman jikinta da sauri ta ƙanƙame shi”na daina babyna, tun da baka so, ba sai ka faɗa ma mami ba kaji ko” amsa mata yai da toh amma idan ki ka ƙara saina faɗa mata” murmushi Aneelerh ta saki idonta akan zahra dake kallonta.
“Idan ina kallon hotunansu ina tuna irin rayuwar farin cikin da mu ka yi, Shiyasa ni ke zubda hawaye na, Allah na gani bazan Iya mantawa dasu acikin rayuwata ba, waɗannan mutanan uku masu mahimmanci sun kafa tarihi acikin zuciyata, nayi imanin har in koma ga mahaliccina bazan ta6a samun wanda zai maye min gurbinsu ba, Nafi damuwa da Angel wlh ina son yarinyar nan naji takaicin rashinta naso ace sun rayu tare da ɗan uwanta junaid, Angel abun tausayice ta rayu ba tare da mahaifiyarta ba, Na rasa wata irin zuciya ce a ƙirjin benazir......” sosai Aneelerh ta fashe da kuka, Jikin zahra duk yai sanyi, zagayo da hannunta tayi saman bayan Aneelerh ta kwanto da kanta saman kafaɗarta”I feel ur pain Aunty Aneelerh, da inada halin da zan iya yaye maki damuwarki da nayi sai dai babu, abu ɗayane nayi maki alƙawari zan tayaki addu’a, ni a tunanina bai kamata ace anyi shiru da maganar nan ba, idan har ba a yaɗa labarinsu taya za’asan in suna araye? Yakamata atada zancen labarin 6acewarsu a social media, inaso labarin ya zama sabo tamkar a yau ya faru in dai har mu ka yi hakan in sha Allah indai suna araye zasu bayyana ne.......” tunda zahra ta soma magana Aneelerh ta natsu tana sauraronta, ga dukkan alamu ta gamsu da zancenta
Da sauri ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar zahra muryarta adisashe tace”Zahra kina ganin idan muka yi hakan za’a dace” fuskar zahra ɗauke da murmushi tace ƙwarai kuwa in sha Allah zamuyi nasara, Kibar komai a hannuna Idan Daddy ya dawo zamu yi magana dashi, tunda kinga shi mutunne na jama’a zai tsara mana yadda za’a watsa labarin 6acewarsu, so nake duniya ta ɗauka,” lumshe ido Aneelerh tayi har cikin ranta take jin ƙwarin gwiwa.
“Samu Ƴar uwa kamarki zaiyi wuya Zahra, shiyasa nakeson ki ina matuƙar ƙaunarki, ke ta dabance kina da kaifin basira, Ni ban ta6a tunanin tada zancen 6acewarsu tajuddeen ba sai da ki ka bani shawara, Allah ya Biya maki buƙatunki na alkhairi”
“Ameen auntyna, ko dan saboda farin Cikin ki zanyi ƙoƙari inga an watsa labaransu tare da hotunansu, “farin ciki ya cika Aneelerh, sosai ta rungume zahra, Baby Junaid yayi lamo saman ƙirjinta, sai faman lumshe ido ya ke yi bacci ne ke shirin ɗaukarshi
“Excuse ma’am” muryar Ana ce ta katse su, atare suka ɗago suna kallonta, tana daga tsaye bakin ƙofar ɗakin, a mutunce suka gaisa kafin ta sanar dasu cewa Breakfast yana jiransu a dining’ amsa mata su ka yi da toh, kusan atare suka miƙe, Aneeleh na ɗauke da babyn junaid”
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E6🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
*JUSTICE DEMOCRATIC PARTY*
(JDP HQ)
Manyan mutanene dattawa da matasa zazzaune a babban ɗakin taro na jam’iyyar Justice democratic party ɗaya daga cikin jam’iyun da su ka shara a ƙasar Nigeria, zungureran table ne wanda ke kewaye da kujeru, daga saman teburin akwai microphones na kowani member da zai yi magana, An tanadi kayan sha jere saman table, ɗakin taron yai tsit babu mai magana a cikin su, fitinannan ƙamshin turaren jikinsu ya gauraya da sanyin A.c na comference room ɗin da su ke a ciki.
Tsabar 6acin rai ne da fusata akan fuskokin su ga dukkan alamu suna fuskantar tashin hankali a jam’iyarsu, musamman party leader ɗin su Alhaji bukar mai guduma fuskarshi a murtuke ta ke babu annuri, baƙin shi ya nunku har shining ya ke yi, Ya dunƙule tafin hannayensa da ya ɗaura su saman table din, Kowannan su ya ɗauki wankar tsadaddiya shadda daga gani naira ta zauna masu, kuma gogaggun ƴan siyasa ne waɗanda su ka jima a harkar suna gwagwarmaya, tsawon mintuna goma shabiyar, kafin shugaban jam’iyar mai guduma ya sassauta fusatar fuskarshi idanuwanshi jawur ya ɗago yana kallon mambobin su, tun daga jerin waɗanda ke a 6angaren damansa, Alhaji ubaid wadata Alhaji musa wadata former president, Alhaji badamasi da sauran ƴa’ƴan jam’iya, A hankali ya ɗauke idanuwan shi daga ta 6angaren dama ya mayar dasu kan mambobin dake zaune 6angaren hagunsa, Jinjina kansa ya ɗanyi yayin da ya ke fitar da huci ya soma magana tamkar mayunwacin zaki”Me ke shirin faruwane da jam’iyar mu? Zamu zauna ne mu zuba ido kamar mazurai muna kallon su? Mun ɗaura shugaban ƙasa dudu 4 yrs ya faɗi aza6e, mun kuma tsayar da sabon ɗan takararmu ubaid wadata an kayar dashi aza6e, Ga dukkan alamu durƙushewar jam’iyarmu ce tazo, tayaya jam’iyar da bata fi shekara biyar da kafuwa ba zata nemi ruguza tarihin tamu party din? A zafafe ya kai ƙarshen maganar yana kallon kowan nan su, babu wanda yai yunƙurin tanka mashi saboda sunsan halin shi idan ranshi ya 6aci, wani irin bauɗaɗɗan mutunne,
Jinjina kan shi yai yayin da ya ke fitar da huci duk irin sanyin A.c da ke shawagi a ɗakin hakan bai hanashi fitar da gumi ba.
“Babu irin tarihin da jam’iyar mu bata kafa fa, Ina ce shi kanshi dattijon arziƙin rainon jamiyar jdp ce, daga baya ne ya sauya ra’ayin shi akan wata manufa tashi ta daban wadda ba mu da masaniya akanta ya kafa tashi jam’iyar mai taken Progressive action party (PAP) Yan zu ga shi cikin ƙanƙanin lokaci sun ƙwace ƙarfin ikon da mu ke da shi a ƙasar nan, tsabar haɗama gaba ɗaya ƴa’ƴan shi ke juya ƙasar nan idan har bamu ta6uka wani abu ba zamu tashi a tutar babu ne”! Ya ƙarasa maganar tare da kai hannu Ya daki table din gaban shi, kowa yasha jinin jikin shi, damuwace ƙarara akan fuskokin su.
Gyaran murya Alhaji Ubaid wadata yai kafin atsanake ya soma magana cikin dattako
“Allah ya huci zuciyar mai girma jagoran mu, Ni anawa ganin yakamata mu fito da dabarun da za mu bi don ganin mun dawo da ƙarfin ikon da mu ke da shi ada, idan ma ta kama mu bi tsarin da su ka ɗauko wanda yasa jama’a suke rububin tasu jam’iyar, Idan har muna so mu farfaɗo da tamu jam’iyar” bayan Alhaji ubaid yai magana sauran Ƴan jam’iyar kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, Idan ka cire mutun ɗaya wanda tun da ya zauna meeting ɗin idanuwanshi su ke a lumshe daga gani yana da jiji da kai da izza, ɗakin taron ya rikice da zafafan zantuttukan su kowa yana faɗin ta cikinsa, rai amatuƙar amace Ya sanya hannu ya daki table ɗin gabanshi wanda silar hakan ya janyo hankulansu ga dubanshi, Ƙaraminsu babbansu slowly ya buɗe idanuwanshi akan faces ɗin su, sun kasa kunne suna jiran jin me zaice hatta shugaban jam’iyar tasu ya natsu yana jiran jin bayani daga gare shi.
Cikin harshen turanshi Ya soma magana da kakkausar murya”Let’s take a step back and focus on what we need to do right now. We need to come up with a strategy for the next election, We need to come up with a plan to fight back. We need to show the people that we are the party that can make a difference in their lives. We need to show them that we are the party that cares about their needs. We need to show them that we are the party that will fight for them, And We need to let them know that we are the party that is on their side.” tun da Alhaji musa wadata ya soma magana ƴa’ƴan jam’iyar su ke jinjina kansu ga dukkan alamu ya ɗauko magana mai ma’ana a ƙarshe ya daki table din gabanshi ya furta”Sharafudden obinna ba zai haura 4 years a mulki ba! Alƙawarine na ɗaukar wa kaina, duk yadda za’ae sai mun kayar dashi a za6e na gaba, dole jam’iyar mu ce asama babu wani mahaluƙi da ya isa ya durƙusar da jam’iyar mu, abokan hammaya ba za su ta6a cin galaba akan mu ba,” yana kai ƙarshen maganar azafafe ya yunƙura ya miƙe yana gyara malunmalun ɗin jikin shi, Ko sallama baiyi masu ba, Ya haura ƙafa yabar cikin ɗakin taron, yayin da su ke bin bayanshi da ido, har saida ya 6ace ma ganinsu tukunna suka dawo da dubansu kan maiguduma. tattaunarwar tasu ta ɗauki tsawon awa ɗaya kafin suka rufe taron da addu’a da kuma fatan nasara ga jam’iyarsu, Ɗaya bayan ɗaya suke fitowa harabar headquater inda jerin danƙara danƙaran motocinsu suke a killace. Bayan sun ƙara gaisawa da juna kowa Ya nufi motarshi, Musa wadata Yana kishingiɗe a back seat na danƙareriyar motarshi tsadaddar gaske, Ya lumshe idanuwanshi sanyin A.c ta ko’ina, gefen shi P.A dinsa ne, security ɗin da ke jigilar tuƙa su yana zaune a driver seat yana jiran jin umarninsa.
Ƙwanƙwasa glass ɗin motar da akayi ne yasa shi ware manyan idanuwanshi, muryar Alhaji ubaid ce ta ratsa kunnuwanshi”Ina son magana da kai” Iya abunda ya furta mashi kenan, Muryarshi da izza ya amsa mashi da toh, daga haka yaba drivern nashi iznin ya tada motar su nufi gida” A jere motocin su su ka nufi gate ɗin fita daga cikin headquater ɗin su...
*JOS CITY*
Zaune ya ke saman darduma cikin shigar larabawa farare ƙal, kyakkyawan balarabe daga ganin fuskarshi ba ƙaramin mutun bane ya ɗan fara manyanta, Arab turban ɗin da ke nannaɗe akanshi, ya ƙara mashi kyau ga wani kwantaccen saje baƙi wulik mai matuƙar jan hankali, lallausar sumar kanshi ta sauko har saman wuyanshi dark black.
Daddaɗan ƙamshin turararen jikin shi mai matuƙar sanyaya zuciyar mai shaƙar shi, idanuwan shi suna a lumshe yayin da ya ke yin qira’ar Alqur’ani mai girma, Yatsun hannunshi na dama na a asargafe da cazbaha, Qur’anin da ya ke karantawa yana agabanshi saman wooden qur’anic stand dogayen eye lashes ɗinsa a jiƙe su ke sharkaf da hawaye ga dukkan alamu ayar da ya ke karantawa ce ta sanya shi tsuma.
Sam bai ji takun tafiyar mutun acikin ɗakin shi ba, tafi ƙarfin mintuna talatin da shigowa, idanuwanta akanshi ganin bai da niyar tsagaita karatun ƙur’anin nashi ne yasa ta ambaci sunan shi
*”DR SHUREIM*”Nasan kana jin takun tafiyata don haka idan ka kai ƙarshen Aya ina son magana da kai”! tamkar ta yi magana da bango ko kallo bata ishe shi ba, sai ma ƙara sautin muryashi da ya yi” dogon tsoki taja tare da zuwa gaban dardumar ta shi ta kai hannu ta rufe qur’anin da ya ke karantawa, a tsiyace ta ƙwace cazbagar dake nannaɗe a hannun shi ta ɗaura ta saman qur’anin, don ta fahinci da gayya ya ke yin karatun duk don kada ya saurari maganarta.
Tana huci ta ɗago tana kallon shi still bai buɗe idanuwanshi ba, kuma bai dakata da yin karatun ƙur’anin ba domin kuwa haddace akanshi
“Ka da ka bari raina ya 6aci wlh zan yi maka abunda baka tsammani, na rasa uban me na yi ma ka daka ɗaura mun karan tsana sai ka ce ba uwarka ba! Ko kana da wadda tafi ni ne a duniyar nan”? Ta jefa mashi tambayar, Shiru bai ce uffan ba, gyaɗa kai tayi”ilmin addinin na ka ya tashi abanza tunda ba ka san ka girmama iyayen ka ba, tsawon shekara da shekaru kana nuna wariya tsakanina da mahaifinka laifin me namaka Shureim”? Cikin jin ƙunar rai ta yi maganar, A hankali ya buɗe idanuwanshi farare ƙyal da su ya ɗaura su akan fuskar Mahaifiyar tashi, ba kowa ba ce fa ce Layla mahaifiyar Benazir, Doctor shureim shine babban ɗansu, Ya ya ne awurin Benazir mahaifiyar Angel.
Daddaɗar muryar shi ce ta ratsa kunnuwanta”ba ki min laifin komai ba, har yanzu kina nan a matsayinki na mahaifiyata, kawai bana buƙatar kusancin ki da ni” Zagayawa ta yi zuwa gefen gadon shi ta zauna suna fuskantar Juna”Nasan dalilin dayasa ka ke yin fushi dani, haba shureim tsawon shekaru nawa why za ka ruƙe abu aranka yai ta damun ka? Yakamata mu manta da abunda ya wuce, kuskure ne an riga da an ta6ka, kuma in sha Allahu hakan bazata ƙara faru wa ba” fuskarshi a ɗaure ta ke babu walwala” tayi tsammanin zai tanka mata sai ji ta yi ya yi shiru bai ƙara magana ba.
Ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, zuciyarta na ƙuna tace”na lura sam faɗuwar mahaifinka bata dame ka ba, An ya kuwa shureim kana ƙaunar mu a matsayin mu na iyayenka? Cos na fahimci baka son cigaban mu” murmushin takaici dr shureim ya saki, da ido tabi shi da kallo ganin yana dariya har fararen haƙoran sa su ka bayyana masu kyau da tsari.
“Mahaukaciya ka mai da ni? ina magana kana dariya” fuskarta a ɗaure tayi maganar, Yunƙurawa yai tare da mikewa Ya fuskance ta kafin ya soma magana”Saboda ku ba iyaye bane daya kamata a nuna damuwa akan ku! Daga ke har shi bakusan ciwon kan ku ba, Gaba ɗaya hankalin ku na akan son abun duniya damuwar ku akan cigaban ku ne ba akan mu ba! Ta ya ya zan damu don mahaifina ya faɗi a za6e? Aini abun farin cikine agare ni, don na fahimci siyasarshi tafi komai mahimmanci awurinku! Saboda rashin sanin ciwon ƴa’ƴa Yau tsawon shekara goma sha shidda Benazir bata a tare da ku, hankalin ku a kwance ba ku iya ta6u ka komai ba, duniya kawai kuka sa agaba, Wlh na jima ina danasanin kasancewar ku Iyayen mu! Na yi fatan ace mutun yana iya canza iyaye da tuni na yi hakan, Nifa ba ku da amfani acikin rayuwata! Kun riga da kun yi min abunda har abada zuciyata bazata ta6a mantawa da shi ba, kune silar duk wata masifa dana tsinci kaina aciki.......” daƙyar ya ƙarasa maganar cikin jin ƙunar rai, a bun ka ga farin mutun tuni fuskarshi ta canza launi zuwa ja, numfashi yaja muryarshi adisashe yace”kun manta cewa ƴa ƴa