A hankali yake bud’e idanuwansa..
Hasken da ya gani tarr!! A kansa ne ya sanyashi maida idanun nasa ya rufesu dan lokaci guda yaji kanshi yayi wani mugun sarawa.
Da sauri Mommy ta matso ta kama hannunshi tana murmushi tana goge hawaye tace
“Dad, kaga ya farka,
yanzunnan naga ya bud’e idanunsa.”
Da sauri Dad ya matso ya d’an shafa fuskarshi sannan ya juya da sauri yana cewa “bara in kira Likitan, Alhamdulillah.”
A hankali yad’an damk’i hannun Mommy da yake a cikin nashi, da sauri itama ta d’aura d’ayan hannunta a kai tace
“Aslam, sannu mai kake so? Ya jikin?.”
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya sannan yace
“Hasken yayi min yawa”
Da sauri ta mik’e ta rage hasken d’akin sosai sannan tace
“Na rage”
A hankali yake bud’e idanuwanshi da sukayi mishi nauyi sosai.
Fuskar Mommy ya gani tana kallon shi tana murmushi.
Murmushin shima ya sakar mata sannan ya fara k’ok’arin tashi.
Da sauri tasa hannu ta taimaka mishi, sannan ta saka mishi pillow a bayanshi ya d’an jingina.
Yana gama gyara zaman shi tayi huggin nashi sannan tace
“Congratulations Son”
Shiruuu, yayi chan kuma yasa hannu ya zarota daga jikinshi kafin yace
“Mommy dama ba mafarki na yi ba?”
Murmushi tayi ta kama kumatunshi ta d’an ja
sannan tace
“Ba mafarki bane!
Angon Huda.”
Dai dai nan Dad ya dawo da Likita yana binshi a baya.
Y’an gwaje gwaje Likitan yayi sannan ya tambayeshi “ina ke yi mishi ciwo?
Ya yake ji a jikinshi?”
A hankali yace
“Nothing much..
Kawai kainane yake d’an sarawa kad’an kad’an”