Showing 75001 words to 78000 words out of 250533 words

Chapter 26 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.

18 Feb 2025

116533

A waya ta kawo mana dinner mu ci atare ni da autana” tur6une fuska Hajiya saratu tayi”ba yunwa nake ji ba, Zuwa nayi mu yi magana, kafin barina ɗaki sai da nayi magana da masu aiki nasan sun kai min a ɗakina”
“Ai nasan ba yunwa kike ji ba, Ni nake ra’ayin cin abinci tare da ke, idan mun kammala sai mu yi magana” aruɗe take kallonshi, ƙiri ƙiri Ya hana tayi magana.
Ba tare da ya jira amsarta ba, Ya ɗauki waya dake saman bedside drawer, Ya kira landline na kitchen, bugu uku aka ɗaga kiran, muryar sophia ce ta ratsa kunnansa cikin girmamawa ta gaishe da shi.

“Ina buƙatar Dinner ɗina a shigo min da shi ɗaki yanzu” amsa mashi tayi da toh kafin yai rejecting call ɗin, idanuwanshi akan saratu da ta haɗe rai, kasa jurewa tayi don baƙaramin takura tayi ba hakan yasa ta soma magana ba tare da ta jiran umarninsa ba.

“Baba ni gaskiya ba a kyautamin agidan nan, akan me za’a dinga kushe min ƴa’ƴana ana yabon na wasu, abun yana ƙona min rai bana jin daɗi, haba dan Allah wannan ba adalci bane, kuma ba girman Yaya Lateef bane da yaya mubarak su zauna suna faɗan maganganun marasa daɗi akan ƴa’ƴana, ni kaɗai ke ba’ason ya’ya na a family din nan ko dan saboda ban auri jinsin mu bane” Rai a6ace take yin maganar, tun da ta fara magana bai dakatar da ita ba, ya natsu yana sauraronta idonshi akan fuskarta, dama tun kafin ta fara yin maganar yasan meya kawo ta, Yana mamakin Halin saratu, ko irin alkunyar nan babu, idonta ya rufe akan ƴa’ƴa da miji, abu ɗayane take jin nauyin yi wato idan tana zazzaga masifa bata bari su haɗa ido dashi, murmushine akan tausasan la66ansa
“Kin gama maganar ko akwai saura” bata ɗago ta kalle shi ba idonta na akan carpet ɗin da take a zaune dirshan
“Hateem Faɗa min menene sunan macan da take ɗaukar zigar miji”? ras taji gabanta yai mugun faɗuwa, A ruɗe ta ɗago da ido tana kallon fuskar obinna, ƙayataccen murmushine akan fuskarshi, Ji take tamkar ta yunƙura ta miƙe ta zuba da gudu don ta fahimci Video call yake yi da Yayanta hateem na ƙasar Canada, Hakan na nufin duk wata magana da ta ke faɗama babansu akan kunnanshi, Hankalinta ya tashi don ba ƙaramin jin shakkar shi ta ke Yi ba, duk acikin yayunta tafi fargabar sharafudden da hateem.

A hankali Obie Ya juya mata Lapton ɗin gabanshi don suyi magana da Yayanta, sunnar dakai ƙasa tayi sam ta kasa ɗagowa ta kalli screen ɗin laptop nasa
Daddaɗar muryar prime minister Hateem ce ta ratsa kunnuwanta
“Ji ra kike in gaishe ki”? Girgiza kai tayi tamkar tana agabanshi, cikin girmamawa ta soma gaishe da shi
“Ina wuni Yayana, Ya aiki Ya iyali”
“Ki ɗago da ido ki kalle ni Saratu”! Da kakkausar Murya ya furta hakan, Yawu ta haɗiya kafin A hankali kamar maijin tsoro ta saci kallon screen ɗin.

Tabarakallahu ahsanun khalikin!! Ni kaina da nake rubutawa sai da alƙalamina ya girgiza da ganin Kyakkyawar surar nan mai cikar kamala, gwarzon namiji jajirtacce, kallon ɗaya zaka Yiwa fuskarshi ka shaida Jinin Obinna ne, Yana ɗaya daga Cikin waɗanda su ke kama da babansu, basu baro komai nashi ba, Kyanshi, ɗabi’unsa da halayansa, Fatarshi kaɗai abun kallo ce, yadda kasan da ruwan madara ake mulketa saboda tsabar kyau, skin colour ɗinshi launin na mahafinshi ne, A zaune yake Cikin Katafaren Office ɗinsa dake a Presidential residence Na ƙasar Canada, tsayawa zayyana kyawun Office ɗin da dukiyar da aka kashe masa wurin zuba kayan cikinsa abune da hankali ba zai ɗauka ba, wata’ƙil zamu ƙare Takun tsakiyane wurin zayyana shi, wasu hadaddun tailored suit ne a jikinsa sunbi shape ɗin jikinsa, mutumin akwai ƙira.

“Bai kamata kiji kunyar haɗa ido dani ba Saratu, tunda har kika iya tako ƙafafuwanki kika zo ɗakin baba don kiyi mashi masifa, Ke ko kunya bakya ji? Ki zauna Miji Yana ziga ki Kan ƴan uwanki? Sara Ba haka nasanki ba, Ni ba haka ƙanwata take ba, jarumar macace mai hankali da tunani, why kike son bani Kunya”? Maganar Hateem tayi matuƙar sanyata jin kunya, duk sai ta ji haushin kanta ya kamata, tayi danasanin zuwa ɗakin obinna, saboda tana matuƙar jin nauyin Hateem, da ace tasan da shi suke yin video call da batayi gigin zuwa kawo ƙorafi ba.
“Kiyiwa kanki faɗa saratu, Ba girmanki bane, Ƴa’ƴanki ai namu ne, babu wani banbanci, nasan abunda Yaya mubarak da Yaya lafeef zasu faɗi bazai wuci akan Cigaban Ƴa’ƴanki bane, maisonka shike faɗa maka gaskiya duk min ɗacin ta, Maƙiyinka kuwa sai dai Ya 6oye maka yakamata Kiyi tunani ƙanwata” Cikin kwantar da murya yake yi mata nasiha, shi kanshi Obinna har lumshe ido yake yi saboda jin daɗin nasihar da Hateem Yake yiwa ƙanwarshi, kuma ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi sosai
Muryarta tamkar zata fashe da kuka ta soma magana”In sha Allah yaya zan kiyaye, bazan ƙara biye mashi ba, zuciya ce ta ɗibe ni, Ni kaina nasani kuna son ƴa’ƴana shiyasa kuke yi masu faɗa don su gyara, duk wanda ya rasa faɗi a duniya yai asara, ina jin daɗin ƙoƙarinku akaina da ƴa’ƴana, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku” idanuwanta har sun cicciko da ƙwalla
“Kada ki bari hawayen nan su zuba, Kinsan banaso ko”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh”Okey yi min murmushin nan naki in gani” Dariyace ta kubce mata, da sauri ta ɗaura kanta saman manyan laps ɗinta
“Ya aikin naki? Fatan komai na tafiya lafiya” amsa mashi tayi da”lafiyalou”

Jinjina kai Hateem yai”Allah ya taimaka” sallama sukayi da ita Obie Ya juya laptop ɗin, idon shi akan Hateem
“Shiyasa nake Ƙaunarku, Saboda ku ɗin na dabanne, ƴa’ƴana abun alfaharina, Allah Yabar munku, ubangiji Allah ya tsare mun ku Ya kare munku daga sharrin maƙiya da mahassada......”addu’o’i obinna yadinga jero mashi, Yana masa mashi da ameen ameen hada saratu wurin amsawa daga bisani Suka yi sallama dashi
Rufe laptop ɗin yai tare da miƙe ma saratu, Yunƙurawa tayi tare da matsawa gaban gadon ta kar6i laptop ɗin ta nufi saman desk ɗinta ta ɗaurata.

“Assalamu akaikum” muryar Hajjaty ce ta ratsa kunnuwan su, atare suka amsa mata da wa’alaikum salam shigo daga Ciki, Tura ƙofar tayi kamar kullum fararen Kayane a jikinta, Tasha uban ado kamar amarya, sam bata gaji da ca6a ado, Hannayenta sun sha ƙunshi na jan lalle.
Hajiya saratu dake a tsaye tana kallonta, Haushin Matar take ji, ta tsani taga ƴar aiki tana ɗaukar wanka kamar yar masu gida, zuciya da saƙe saƙe, sai ta dinga ganin kamar obinna bin jikinta yake yi da kallo, fargabanta kada wata rana dattijonsu ya ƙyasa, Ƙarasawa Hajjaty tayi cikin ɗakin Asaman Carpet ta ɗaura tray ɗin, sai faman sakar mashi murmushi take yi shima ɗin mayar mata da martanin murmushin yake yi, Hankalin Hajiya saratu yaƙi kwanciya Tana a tsaye ta ruke qugunta
“Yalla6ai fatan ka wuni lafiya, tun ɗazu nake jiran shigowarka gidan bansan kun dawo daga masallaci ba, ae da tuni na jima da kawo maka abinci” Yanayin yadda take magana muryarta tamkar ana busa sarewa, ƙamshin turarenta Ya addabi hancin hajiya saratu
Lumshe ido yai kafin ya amsa mata da”lafiyalou Alhamdulillah, nagode da kulawarki agareni, Kina ji da dattijon nan naki sosai nima na yaba da hakan”

Fuskar Hajiya saratu a ɗaure ta furta”ke! Tashi kibar ɗakin nan tunda kin kawo mashi abincin,ya gode sai anjima” miƙewa Hajjaty tayi tare da jiyawa ta kalleta”Ina wuni hajiya”
“Da ban wuni ba kin ganni, Ƴar rainin wayau sai yanzu kikasan dani aɗakin, dallah ni zo ki fuce waje” jikin Hajjaty yai sanyi duk sai ta ji ba daɗi

“Inaso zan zuba mashi abincin....” tunkan ta ƙarasa Hajiya saratu ta daka mata tsawa”Nace ki fita ko”? Matsawa tayi tare da fusgo hannun Hajjaty taja ta waje, Obinna dake a kishingiɗe saman gadon ƙayataccen murmushine akan fuskarshi, lamarin saratu sai addu’a ya fahimci kishin mahaifin nata takeyi.

Bayan fitarsu daga ɗakin, a bakin ƙofar suka tsaya da tafiya, Hajiya saratu na faman ciccije le6e ta furta”Ni ban yadda dake ba, akan me zaki dinga zuwa ɗakin Ubanmu, balallaga dake Ina laifin Ki turo matasan ƴan matan masu aikin su dinga yi mashi hidima”? Idanuwan hajjaty tuni sun cicciko tab da ƙwalla, ta tsani faɗan hajiya saratu, a shekaru kusan tsaran junane amma ta tasata gaba tanayi mata faɗa kamar wata ƙanwarta
“Ai shine ya za6eni bani nake kawo kaina ba, Yafi so ina yi mashi hidima, kuma ki tambaye shi zai fada maki hakan” Harara Hajiya saratu ta watsa mata”ae dole ya za6e ki, tun da kin riga kin asirce shi da wannan munafukin turaren naki, mace sai kace karuwa, Kin bi jiki duk kin feshe da turare Bakisan haramin bane mace ta fesa turare mai ƙarfi ba? Ina laifin wanda zaki ɗan matsa a hammata!” yawu hajjaty ta haɗiya batare da tace mata komai ba
“Idiot, daga yau karki kuskura In ƙara ganin Kin a ɗaki babanmu, tun fil azal ni baki kwanta min araina ba, Ina raga maki ne saboda mijina ba dan haka ba wlh da tuni na jima da korarki can ƙauyanku na can india, A tsawace takai ƙarshen maganar tare da ingiza hajjaty, tai taga taga zata faɗi daƙyar ta samu ta dafe bango, dogon tsoki Hajiya saratu ta buga kafin Ta juya ta koma ɗakin obinna.

Jiki asanyaye hajjaty ke tafiya yayin da hawaye ke bin fuskarta, Da mayafin hannunta take share ƙwallar dake sintiri saman kuncinta, Kalaman Hajiya saratu sun ƙona mata rai.

Tun fitar Hajiya saratu daga ɗakinta, Pravin Yana zaune gefen gadon shi, Shi da Tagwayensa zayn da zayn, suna zaune saman sofa, ransu ya 6aci matuƙa babu annuri akan fuskokinsu

“Yanzu me kuke so ayi”! ya jefa masu tambaya yana mai kallon fuskokinsu
“Ka sama mana hanyar da zamu bar ƙasar nan, saboda mun gaji da zaman gidan nan, a takure muke kowa baya son mu kusan kullum ne sai anyi mana Gori” murmushin gefen fuska Pravin ya ɗan saki Yana duban ya’yan nashi cikin so da ƙauna
“Kun bani Kunya wlh, Why maganar mutane zata dame ku? Har wani ya isa yasa kubar Danginku? Kenan wata rana zaku Iya kashe kanku saboda wani ya 6ata maku rai eye”! ɗaure mashi fuska suka yi don sun fahimci uban nasu babu zuciya a ƙirjinsa, shiyasa bai ganin illar abunda ake yi masu, yafi so su zama masu matattar zuciya irin shi
“Daddy pls, ka fahimce mu, bama jin daɗin zama gidan nan, america muke son komawa da zama” girgiza kai pravin yai”bazaiyiwu ba, ai baku keda kanku ba, Nima ina buƙatar ku atare dani, Ku faɗi wani abun na daban da kuke so zan iya yi maku shi” magiya suka dinga yi mashi akan ya amince masu su koma america,
“Daddy bafa da kuɗinka xaka ɗauki ɗawainiyarmu ba, munsan komai kakeso mommy zata yi maka taimakonmu kawai zakayi mu samu ta amince mana”
Ɗaure fuskarshi yai”saboda ni bani da arziƙin da zan Iya ɗaukar nauyinku”? Girgiza kai sukayi atare
Ta6e la66ansa yai”bansan me kuka ɗauke ni ba, Ita kanta mahaifiyar taku A yanzu bata kama ƙafata wurin arziƙi ba,” kallon Juna su ka yi da mamaki akan fuskokinsu
Miƙewa yai daga gefen gadon Ya nufi gaban drawer chest, Ya buɗe ya zaro atm card, dawowa yai ya zauna yana fuskantarsu
“Banyi maku Iyaka da kuɗin dake acikin acct bank ɗina ba, don nasan har abada bazaku Iya ƙarar da su ba, a duk lokacin da kukeso zaku Iya cirar kuɗi ku biya buƙatunku, sannan kuje ƙasar da kuke so, Farin Cikinku shine nawa”
Kallon da suke yi mashi kamar basu yarda da maganarshi ba, saboda sun raina arziƙinsa,
Still murmushine akan fuskarshi yace”baku yadda da mahaifinku ba ko”? Shiru basu tanka mashi ba, Aransu suna ayyana may be babu ko sisi a atm ɗin, idan ma akwai kudi to Na mommynsu ne tunda ita ke da kuɗi.

Miƙa hannu pravin yai tare da ruƙo wayarshi dake a gefenshi, kamar sakarkaru haka suka tsare shi da ido suna kallon shi, Daddana wayar yayi kafin Ya miƙa masu da sauri Zayn ya kar6i wayar Suka haɗa ido suna kallon screen ɗin wayar, Total balance ne na kudin dake a acct bank dinsa, tsabar firgita har saida suka ɗan zabura ganin millions of dollars, wanda a kuɗin nigeria Billions ne.
Aruɗe suka haɗa baki wurin furta”Daddy Numbobi ne waɗannan ko kuwa kuɗin ne dagaske” dariya ya sakar masu
“Abunda idanuwanku suka nuna maku, Just ku ɗauki atm ɗin zan tura maku pin ɗinsa ta text message,” lamarin yai mugun ɗaure masu kai,
Girgiza kai Zayn yai”a’a daddy kuɗin sunyi mana yawa, ni tsorona ma kada ace Na mommy ne” Miƙa mashi wayar yai
“Idan har kuka bari na kar6i atm ɗin nan kada ku ta6a tsammanin zan taimaka maku!” Kallon Juna sukayi zuciya na azalzalarsu akan su kar6i atm din suyi sharholiyarsu
“Zayn mu kar6a ko”? Girgiza kai zayn yai”A’a zaid kuɗin mommyne fa, idan muka ta6a zata gane ni dai ban goyi bayan hakan ba”
“Pls zayn tun da daddy ne ya bamu just mu kar6a kawai”
“No zaid, kuɗin sunyi yawa zasu sa mu shagala mu daina yin sallah ne” Pravin dake kallonsu ba ƙaramin dariya suka bashi ba.
“Har yanzu akwai ƙuruciya atattare daku, kuɗin kuke gudu? Ai nayi tunanin idan na baku jiki na rawa zaku kar6a, ban ta6a tunanin kuna da zuciyar Imani akan kuɗi ba, Sam baku da haɗama, Ga dama ta samu amma kuna ƙoƙarin yin watsi da ita”!
Muryar zayn na rawa ya furta”Daddy zamuyi shawara tsakaninmu, ka ajiye mana atm ɗin zamu kar6a” jiki na rawa ya ruƙo hannun Zaid suka fuce daga ɗakin.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa Ya maida atm ɗin inda ya ɗaukosa, komawa yai gefen gadon ya zauna yana cin abincin Da abla ta kawoma Hajiya saratu

*Dr.Jazz*

Tun zuwa shi gidan Mommynsa ta ke ta faman tarairayarsa tamkar ƙaramin yaro, Yana daga kishingiɗine saman doguwar sofa ya ɗaura kanshi saman laps ɗinsa, Sai zuba mata shagwa6a yake yi, yatsun Hannayenta na acikin sumar kanshi Tana yi mashi susa
Mahaifiyar Dr.Jazz Baturiyar ƙasar England ce, sunanta na asali Harriet, Silar zuwanta aikatau gidan ta musulunta suka canza mata suna zuwa khadija amma sunfi kiranta da Turai, Farace jawur tana da jiki bata da tsayi launin idonta green ne, sumar kanta launin blonde, A yanzu ba matsayin mai aiki take ba, Matace awurin Sir mubarak, Ya daɗe da auranta tun Bayan rasuwar matarshi Hajiya naja’at, Ƴa’ƴan shi biyu da uwar gidansa gaba ɗayansu ba mazauna Nigeria bane, Suna a ƙasar canada suna kula da Babban companynsu tare da sauran ƴan uwansu dake zaune agidan Hateem.
Turkish dress ne a jikinta, Riga da wando launin red colour, Ta ɗaura satin scarve asaman wuyanta, ta zubo da gashin kanta har gadon baya, Allah yayita da ruwan kyau.
“Jazz sai nake ganin kamar baka yi kewata ba, Meyasa bakasan zuwa ganina? kullum Sai in ni na shiga gida nake samun damar ganinka idan naci sa’a baka tafi aiki ba.
Fararen idanuwanshi ya daura akan fuskarta,
“Mommy ba haka bane, Ni just banason haɗuwa da daddyne, ya cika faɗa, kuma sharri yake yi min yana cewa wai ni mata maza ne, Fisabilillah”
“Ya faɗi hakanne donka Gyara rayuwarka, ni kaina ina mamakin shagwa6arka sai kace wani yaron goye, komai naka irin na mata”

Ɗaure mata fuska yai”mommy kina goyan bayansa kenan, yaci gaba da kira na mata maza”? Girgiza mashi kai tai”A’a, Ai nafi kowa jin haushin inji ya kiraka da hakan, Yana ta6a min zuciyana, donni nasan namiji na haifa ba maca ba” murmushi Jazz Ya saki”to kice mashi ya daina”
“Zan buga mashi warning, kada ka damuwa” maƙe mata kafadai yai”Allah mommy ni nasani wasa kikeyi, saboda ke kanki shakkarshi kike ji ba zaki Iya buɗe baki ki yi mashi magana akan ya daina ba”
Jan kumatunshi tayi da hannunta In jiwa ya faɗa maka! Ni bana jin tsoronshi awaja ne mutane ke jin shakkarshi, da zarar ya shigo nake juya shi son raina, Har girki yana yi min” Baki asake Jazz ke kallonta
“Uncle mubarak ɗin”! Jinjina masa kai ta yi”ƙwarai kuwa, ae dukkan Namiji bawan matane,
Har ya buɗe baki zai ƙara magana, Wayar Aljihun wandonshi ta soma ruri, miƙewa yai da sauri ya curo wayar, bayan ya duba sunan mai kiran nashi ya ɗago tare da kallon mommynsa, Wanene ya kira”?

Bai amsa mata ba sai dai ya sakar mata murmushi, da sauri Ya fito daga falon gidan, Kamar wani munafuki duk faɗin gidan bai isheshi ba sai da ya shiga garden tukunna ya dakata da yin tafiyar, Yai picking call ɗin jiki na rawa ya kara ta akan kunnansa, Kirari ya soma yiwa wanda ya kira shi wayar tamkar maroƙi,
“Yalla6ai Kajin nan suna nan cikin ƙoshin Lafiya, Suna samun kyakkyawar kulawa yadda ya dace,” dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, yana sauraron muryar mai magana,
“Ana basu hatsi yalla6ai mai rai da lafiya, Yanzu haka idan nagama magana da mama zan tafi gidan gona domin duba lafiyarsu,” sai faman sakin murmushi yake yi, aladabce yake yin maganar
‘kasan kajin turawa saida hatsi mai kyau, Gaskiya basu da matsala yalla6ai, biyu daga cikinsu ne kaɗai suke neman gazawa, shi zakaran ciwon nashi Ya lafa, sauran Kajin muna nan muna basu kyakkyawar kulawa, in sha Allah zasu samu lafiya harma asamu nayin farfesun sallah”

Tuntsirewa dr Jazz yai da dariya hada dafe ciki.
duk wannan surutun da ya ke yi acikin waya baisan Sir Mubarak na tsaye abayanshi ba, daga shi sai gajeran wando, Da singlet fara,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login