Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps

Chapter 32 of 83

gefe ɗaya ya jefar da shi, gaba ɗaya ya ɗauketa ya jefar saman gado, doguwar sumar kanta tuni ta tarwatse saman mattress, Ya sanya hannu ya zame Singlet ɗin jikin shi Ya haye saman gadon Yaja bargo Ya ƙudundune su, To jama’a nidai bansan me sukeyi a cikin bargon ba, na dai ji sautin gurnaninsu tamkar namun nawa na fafatawa. Bargon da suka lullu6a dashi sai yamutsewa yake yi yana motsi kamar ana dambe a cikinsa, ba yau bane karo na farko da ya fara biyan buƙatarshi da ita ba, sam basa gajiya da juna pravin da divya wato hajjaty, Babu wanda yasan suna harƙalla atsakaninsu.

(To fa, akwai gwarama yasin Ana wani abu agidan Obinna, Ko ina hajiya saratu taje? Ana nan za’a 6ata mata tarbiyar Miji🤣)

A hankali danƙareriyar Motar Hajiya saratu ta kunna kai Cikin Villa dinsu adai dai parking space security ɗin da ke driving nata yai parking na motar, Da sauri Ya fito daga driver seat Ya zagaya Ya buɗe mata ƙofa, ta zura ƙafarta dake sanye cikin High hills, dawowarta kenan daga meeting da suka yi a ministry of Health tare da manyan ministocin Kiwon lafiya da suka kawo masu ziyara daga Who (world health organization) don inganta Lafiya.

Tsadadden leshi ne fari a jikinta, riga da zani daga sama ta ɗaura lap coat, fararen idanuwanta na amanne da glass fari matar fa akwai Iya ɗaukar wanka, ta ko’ina Jikinta ƙamshi yake fitarwa.

Saukowa ta yi daga Cikin motar, da sauri ta nufi cikin gidan hannunta ruƙe da hand bag ɗinta, duk inda ta gifta masu aiki ne ke safa da marwa, cikin girmamawa su ke gaishe da ita, idan ta gama dama ta amsa idan bata ga dama ba sharesu take yi.

A katafaren Main palour na gidan ta shigo, Tafkeken gaske A ƙalla Yana ɗauke da Royal sofas two set saboda faɗinsa.

“Sannu da dawowa Hajiya” muryar Safa ce ta dakatar da ita daga Yin tafiyar, Fuskarta babu annuri a ɗaure take tamau kamar wadda aka 6ata ma rai”Pravin Ya dawo ne”? Tambayar da ta jefa mata kenan.


“Bani da masaniya, da ya ke mu na yin aiki a kitchen ne bansan ko ya dawo ba”

Gyaɗa kai Hajiya saratu ta yi”Okey, zan shiga ɗakin baba, kafin in dawo ki tabbatar kin kai min lunch ɗina a ɗaki, bana son 6ata lokaci” amsa mata tayi da toh hajiya.

Da sauri safa ta nufi kitchen don ta shirya mata abincin.

Kaitsaye hajiya saratu ta nufi sashen obinna.

Tana gab da zata shiga ɗakin Dr jazz ya fito Yana sanye da suit black colour. Ko da suka haɗa ido da ita gabansa ba ƙaramin faɗuwa yai ba.

Muryarshi asanyaye ya furta”ina wuni mommy” harara ta wurga mashi

“Kai bana ce kar na kuskura na ƙara ganinka acikin gidan nan ba? wannan wata irin mayuntaka ce? Meye haɗinka da babanmu”? Tafa Hannu ta yi haɗi da ruƙe ha6a.

Muryarshi adabarbarce ya furta”ai ba anan nake zaune ba tun lokacin da ki ka ce bakison ganina, na koma gidan daddy da zama...” daƙyar ya ida maganar ganin irin ƙasƙantaccen kallon da take wurga mashi.



“Uban waye daddyn naka? In banda yaudarar kai yaushe Yaya mubarak ya zama uban ka? Kai fa ba ɗan kowa bane a family ɗin nan, ka daina ɗaukar kanka wani shege, ai tun ranar da aka faɗamin cewa hada kai ake tsegumin ƴa’ƴana, naji na ƙara tsanar ka matsiyacin banza, in banda zaƙewa da shisshigi da kutsu da samun wuri irin na ɗan talaka ina kai ina haɗa kafaɗa da masu asali a dangi eyeh? A faɗace take yi mashi magana tamkar zata rufe shi da bugu, Bawan Allah dr jazz tuni hawaye sun cicciko idon shi.

Ta6e baki tayi”dallah jibarka, sai uban tsawo kamar fal waya ba ƙiba, duk irin arziƙin da ku ke ci a ƙarƙashin inuwar mu har yau baka ƙara komai ba, Sai Iya gulma da munafunci shashasha kawai, dallah ni bani wuri in wuce kar na ham6are ka” jiki na rawa ya matsa mata hanya, ta shiga ɗakin obinna.

Idanuwanshi sun kaɗa jawur, babu mai yi mashi gori irin hajiya saratu ƙiri ƙiri take nuna ta tsane shi, sam ya kasa motsawa saboda jirin da ke shirin ɗibarshi, a hanzarce ya dafe bango da hannu ɗaya, Ƴar ƙwallar da yake 6oyewa tuni ta gangaro saman kuncinsa, a hankali yake cizon pink lips ɗinsa haɗi da lumshe idanuwanshi.

“JAZZ”! Ras Ya ji gabanshi ya faɗi sam bai ji takun tafiyarsu ba, a fakaice Ya zaro hanky daga trouser pocket ɗinsa Ya share ƙwallarsa, Kafin ya ɗago yana kallonsu.

Turai ce mahaifiyarshi tare da Sir mubarak sun shigo gaida baba, jallabiya ce a jikinta ta yafa mayafi akanta, Sir mubarak yana sanye shima da jallabiya ta maza.

Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba ganin damuwa akan fuskarshi

“Jazz lafiya naga kamar idonka ya canza launi”?

Girgiza mata kai yai”bakomai mommy am ok, idona ne ke yi min ciwo, yanzu nike shirin zuwa gida.....” Sir mubarak ne ya katse mashi hanzarinshi.

“Jazz meke damunka ne? Sai kace wani ƙaramin yaro? Idan ba ka da lafiya baka san Hanyar zuwa asibiti bane? Ba za ka je aduba maka idon naka ba”?

Cikin sanyin murya yace”zanje in sha Allah, nagode da kulawar ka daddyna.

Hankalin turai bai kwanta da abunda ɗan nata ya faɗa mata ba, Matsawa tayi kusa dashi, ta ruƙo hannunshi acikin nata

“My Son, ka je gida ka kwanta ka huta, idan muka dawo zamuyi magana” cikin kulawa take yi mashi magana

Amsa mata yai da toh mommy, bayan yayi masu sallama ya kama hanyar fita daga gidan.

Hajiya saratu na zaune saman carpet, sir mubarak yai sallama hannun shi ruƙe dana matarshi, daƙyar ta amsa masu sallamar, A saman doguwar sofa ɗin ɗakin suka zauna, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, ganin ita ta zauna saman carpet su kuma sun Haye saman sofa.

“Yaya mubarak Ina wuni, Ya iyali”
“Lafiyalou saratu, Ya naki aikin ya kuma Iyali”Alhamdulillah” ta amsa mashi

Sir mubarak yace”baba baya nan”? Yai maganar yana bin ɗakin da kallo
Hajiya saratu tace”ya shiga toilet ne, shine yace min Injira shi” sir mubarak Ya furta Okey, ina mijin naki na shigo gidan ban gan shi ba, Ko ya tafi office ne” yai tambayar ne don yasan aikin nasu na Companynsu har Saturday suna zuwa banda sunday and Friday.

“Tun da safe muka rabu da shi, yana shirin tafiya office, bai dawo ba ne”

Ran turai ba ƙaramin 6aci rai ba, ganin hajiya saratu da tayi a ɗakin obinna ya tabbatar mata da cewa Itace silar halin da Jazz ya shiga, batun yau ba tasa ba yi mashi gori.

“Saratu Baki gaishe da Auntyn taki ba” kamar yayi magana da bango, Ta haɗe fuska ba annuri
Da ɗan tsawa Sir mubarak Yace”Saratu baki Ji ina magana bane” sai da ta mula tasha iska tukunna tace”yaya ai bani ya dace in fara gaishe da ita ba, saboda ni ce agaba da ita,” Ran Sir mubarak ya 6aci, zuciyarshi ta motsa, Tsawa ya daka mata har sai da turai ta zabura saboda firgitar da tayi.

“Kada ki kuskura ki bari in sake nanata maki! Nace ki gaishe da ita tunkafin na 6ata maki rai” sanin halinshi yasa ta wurga ma turai harara kafin tace”Ina wuni matar yaya”
Cikin sanyin murya ta amsa mata Lafiyalou.

Fitowa Dattijon arziƙi yai daga toilet, jikinsa sanye da jallabiya, dogon gemunsa kamar ana ƙara mashi tsawo fari fat, fuskarshi ɗauke da murmushi yake binsu da kallo

“Gayu mutanan Allah, wa nake gani kamar turai? Rufe fuska turai tayi da mayafin jikinta, Sir mubarak na murmushi yace”yau surukar taka tazo gaidaka, tun ɗazu da safe tasa naci akan saita shigo, nace tabari mu zo atare”

“Amma nayi farin ciki, ni nasan ɗiyata tana son zuwa duba babanta, kaine dai ka hanata zuwa mubarak, Allah ya kamaka, dama Ana kawo min tseguminka, akan ƙuntata mata da ka ke yi kana yi mata kulle agida”

Ƴar dariya Sir mubarak yai yana faɗin”gaskiya kowaye ya faɗa maka haka baba to ka bincike shi, Ni nasan ma baya wuce Jazz ne, Aiko inda shine yau a headquater zai kwana”

Dariya suka sanya banda hajiya saratu data ɗaure fuska, muryarta aƙula ta soma magana

“Baba dama na shigo ne don in gaishe ka, inaso zan wuce” Ganin tana yunƙurin miƙewa sir mubarak yai saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata magana”Koma ki zauna sarkin fushi, indai saboda mune kike ta 6ata fuska yanzu zamu koma gidanmu,” ya ƙarasa maganar tare da kallon Baban nasu, hankalin shi na akan fuskar saratu

“Zamu wuce baba”

“Ban gaji da ganinku ba, ku zauna muyi fira mana” acewar Obinna

“Auta Ya meeting ɗin naku?

Yamutsa fuska tayi”lafiyalou, baƙin har sun tafi, shiyasa na dawo gida”

“Masha Allah,” ya ambaci hakan tare da shafa gemunshi

“Ya shirye shiryen tarbar baƙinmu na gida da zasu zo? Ko kun manta da shagalin da zamuyi ne”?

Sai lokacin Saratu ta sassauta fushin fuskarta jin anzo inda tafi so”A’a baba taya zamu manta da rana mafi mahimmanci agaremu ranar da mahaifinmu abun al’faharinmu yazo duniya,” Kalaman saratu sun faranta mashi ranshi.

Sir mubarak yace”Ai nafi kowa zumuɗin ranar tazo baba, naso ace ni aka ba damar ɗaukar ɗawainiyar duk wani abu da za’ayi a ranar, sai dai kash Hateem yai min kutse, gaskiya ban ji daɗi ba, Haka last time Sharafuddeen ne ya ɗauki nauyin gudanar da shagalin”

Da murmushi akan fuskar obinna yace”ai ba wani abu, dakai da su din duk abu ɗayane awurina, ina matuƙar alfahari da ku, kuma Inajin daɗin yadda kuke nuna mini ƙauna”

Ya ƙare maganar tare da kallo Turai, da zolaya yace”Surukar wannan karon wani kalar wanka zaki ɗauka”? Duƙar da kai ƙasa tayi fuskarta ɗauke da murmushi.

Hajiya saratu tace”anko ne zamu fidda ae, zanyi magana da zahra ɗaya daga cikin matasan Yaran da suka yi mana decoration lokacin birthday din twins, ta ƙware wurin iya tsara anko in yaso ma sai su yi mana decoration ɗin”

Jinjina kai Obie yai’naji daɗin jin haka, nima na yaba da aikinsu, yarinyar da kike magana akanta ai na ganeta ƴar gidan ɗan Iya ce, suna da mutunci mutanan kuma mahaifinta yana yi mana hidima sosai, Yakamata ayi masu magana da wuri, tun da mun shiga watan”

“Insha Allah idan na koma ɗaki zan Kira zahran awaya in sanar da ita, amma baba kowa da kowa zai hallara ko? Dan banason inga babu wani adanginmu”
Sir mubarak yace”dolensu ma su zo ai, ƙwan su da kwarkwatarsu, babu wanda zamu yi ma uziri acikinsu, da na gida nigeria da na ƙasar wajen kowa zai zo, Inyaso mutun zai Iya komawa aranar da yazo don wlh bamu raga ma kowa, just rana ɗaya kacal zamu taya mahaifinmu birthday, banga dalilin da zai hana mutun zuwa ba” a tsanake obinna ke kallonshi, yana matuƙar jin daɗin girmama shi da su ke Yi.

“Ku kwantar da hankalinku, in sha Allah kowan nan su zai zo, munyi waya da lateef da abdul razak duk sun tabbatarmin da zuwansu, dama ni banida matsala dasu, Mutun ukun nanne suka fi shiga busy, sharafuddeen da Hateem inayi masu uziri sosai saboda yanayin aikinsu, to su dinma dai Alhamdulillah sun tabbatarmin da zasu samu damar halatta, hada sauran jikokina owais dai ne bani da tabbacin zai zo ko kuwa, har yau dai bansamu wayarshi ba,” muryarshi da rauni ya ƙarasa maganar.

ta6e la66a hajiya saratu ta yi aranta tace”sai kace wani ɗan gwal duk yabi ya dami kanshi akan owais, kamar shi kaɗai ne jikanshi”

Muryar sir mubarak ce ta fargar da ita daga yin zancen zucin”indai owais ne yana sane da wannan ranar mai muhimmanci, duk mun busy din da zai shiga bazai manta da ranar nan ba, saboda ƙaunar da yake yi maka, don haka ka kwantar da halinka baba, In sha Allah Jikanka zaizo.

Nauyayyar ajiyar zuciya obinna ya sauke, zallar farin ciki ne kwance akan fuskarshi har ya ƙosa ranar ta ƙaraso ko dan yaga Jikanshi daya daɗe yana mamarinsa.

“Baba Ni zan wuce ciki” hajiya saratu ce tayi maganar a yayin da take miƙewa tsaye tana gyara mayafinta.

“Har mun gama magana”? Ya jefa mata tambayar, murmushin yaƙe ta ɗan saki”inaso ne in shiga ciki, namanta na sanya mai aiki ta kaimin abinci, idan naci na huta zan Kira zahran awaya duk yadda muka tattauna da ita zanzo na sanar maka”

Gyaɗa kai obie yai”nima nafi so ki huta autana, ki ci abinci ki ƙoshi idan takama ki kwanta kiyi bacci” dariya ta dan saki tana kallon baban nasu, maganar shi ta tuna mata ƙuruciyarta, shi dai burinshi saratu taci abinci ta kwanta ta huta idan ta dawo daga makaranta, bayason tana aikin wahala.

“Nagode da kulawarka akaina baba, Allah yabar mana kai abun alfaharin mu”

Amasa mata yai da amin, Juyawa tayi ta kalli Sir mubarak da turai

“Ni zan wuce yayana, a huta lafiya” bata jira amsarsu ba, da sauri ta fuce daga ɗakin.

Bayan fitarta, tattaunawa suka cigaba da yi game da yadda za’a tsara komai na shagalin da za su yi.

Tun da ta shigo ɗakin, komai na ciki agyare ta same shi, Safa ta kawo mata lunch ɗinta yana asaman table ta ɗaura mata shi.

Cire lapcoat din jikinta tayi a saman Hanger ta sagala ta, shaf shaf ta canza kayan jikinta zuwa, rigar shan iska, daga bisani ta koma gefen gadon ta, ta zauna domin cin abinci, farawa da bismilla ta kai hannu ta damƙi haɗaɗɗan cup na cofee ta kur6e shi, bayan ta gama ta soma shan farfesun naman kaza da zafi zafinshi, cikin ƙanƙanin lokaci ta shanye shi ta kuma damƙar Chips ta cinye ta cakumi cheese burger ta tura abaki hankalinta kwance take cin abincinta.

Ringing ɗin wayarta ne ya janyo hankalinta ga duban hand bag dinta dake ajiye saman pillow.

Ba ta yi niyar ɗaga kiran ba, don ita a ƙa’ida bata picking call idan tana cin abinci saita kammala, hakanan dai tayi ra’ayin duba me kiranta, tissue ta yaga ta goge bakinta, kafin ta yunkura ta ruko handbag din, duba sunan me kiran nata tayi sunan ya fito 6aro 6aro asaman screen ɗin iphone ɗinta

*Princess Mujeedat* murmushi hajiya saratu ta saki da zumuɗi ta ɗaga kiran cikin harshen turanci ta soma yi mata kirari

“Uwargidan shugaban ƙasar Kanada, Gimbiya mai jiran gado ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa! Sarauniya ɗaya tilo da ke mulkin zuciyar Yaya Hateem, Wuu hu huu! ina gwanar wata ga tawa, Uwar gida sarautar mata daga ke babu ƙari mun kulle ƙofa” sautin ƙayataccen murmushin gimbiya mujeedat ne ya karaɗe kunnuwan saratu, da alama taji daɗin yabon da saratu ke yi mata.

bayan ta gama yi mata kirarin ta ɗaura da cewa”Habawa auntyna nayi fushi Allah, sai yau aka tuna dani, ai amana batace haka ba fisabilillah, daga ke har Yaya hateem ɗin baku tunawa da mutane sai wanda ya taka yaje inda ku ke” (idan kaga hajiya saratu na magana da mutun fuskarta asake to koma wanene ba ƙaramin mutun bane, babban gorone magogin ƙarfe dai dai da ita koma fiye da ita, zaranne yai dai dai da kalar yadin🤣)

Ni kaina da naji muryar mai magana saida naji shock, kai daga jin voice ɗinta zaka shaida jinin sarauta ce, gaba da baya, Jinin arziƙi waɗanda suka gaji abun, da izza da dattako ta ke yin magana tamkar bata son furtata.

“Ba abun da ki ke tunani bane ƙanwata, ban manta dake ba kina araina shiyasa ma na kira don mu gaisa” itama da turancin ta mayar mata da amsa don ba ta jin hausa.

“Duk da haka ban sauko daga fushin ba, gaskiya idan kinason mu shirya ki biyo yaya hateem kuzo Nigeria taya murnar birthday din baba, nasan halinki bakison taka ƙasarmu” fuskar hajiya saratu awashe take yi mata magana.

“Naji daɗin kirarin da ki ka yi mini, shiyasa a kullum nike ƙara godewa Allah daya bani surukai nagari irinku, wannan abun alfaharine, haƙika ban ta6a danasanin auran hateem da nayi ba, saboda tunda muka kasance a ƙarƙashin inuwa ɗaya har Allah ya azurtamu da samun zuri’a ban ta6a samun matsala da shi ko dangin shi ba, Kuna nuna min ƙauna sosai nima Ina sonku”

Hajiya saratu baki yaƙi rufuwa, sauran burger din dake abakinta tuni ta ƙarasa haɗiye ta, dadi take ji yau gimbiya mujeedat ta kirata awaya.

“Me kike ci ne? Naji bakinki acunkushe da wani abu, wato har yanzu ƙanwata baki daina ciye ciye ba ko”? Tuntsirewa hajiya saratu tayi da dariya annurin fuskarta sai ƙara nunkuwa yake yi. Mamaki takeyi yarda Gimbiya mujeedat keyi mata magana matar da saboda izzarta idan ka kirata awaya bata picking sai ka fara tura mata text message ka nemin iznin yin magana da ita, idan taga dama zata baka reply akan ka kirata a lokaci kaza, amma muddin mutun ya kira layin mujeedat batare da ya fara neman izni ba to bata ɗaga kiran nashi.

*A GIDAN ƊAN IYA*

Idan muka koma 6angaren su Aneeleeh tun ajiya Hajiya adama da Uncle abdallah suka sanar da su game da zancan komawarsu gida, Abie yace bazai yiwuwa ba su ɗan ƙara kwanaki mana, Anan uncle abdallah Yake sanar dasu cewa Ai sun samu gidan da zasu zauna a abuja ya 6oye ne bai sanar dasu, harma ya samu aiki a companyn sharufuddeen, ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba sun tayashi murna sosai, musamman da suka ji cewa bazasu raba Aneelerh da junaid ba ko da yakai shekarun da zasu Iya kar6ar shi ne, Zasu haƙura ne har Allah ya bayyanar masu da su Uzair, dama rashin ɗan nasu ne yaja har suke son kar6ar shi, Aneelerh hada kukan farin Ciki, Ta ƙara jin son surukan nata, ba ita kaɗai ba hatta su mami sun ji dadin ziyarar da suka kawo masu sun kuma jinjina ma ƙoƙarinsu na barma Aneelerh ɗanta, su kansu sun fahimci ba ƙarami so suke yima yaron ba tun da gashi ta dalilinsa sun dawo abuja da zama, ba su kai ga barin gidan ba, abie ne ya dakatar da su yace su ɗan jira

Download complete TXT · Novel page