Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps

Chapter 40 of 83

suka nufi motarsu.


Hajjaty na akwance cikin mawuyacin hali, idanuwanta sunyi luhu luhu sun rune zuwa Ja, sai faman shessheƙar kuka take yi, Har ya shigo ɗakin bata sani ba, Haye wa yai saman gadon ya zauna daga gefenta, Cikin sanyin murya Ya furta”My heart beat” har cikin kunnanta ta ji muryarshi, sai dai takasa ɗagowa ta kalle shi, hakan Ya tabbatar mashi da ranta Ya 6aci.

“kiyi hakuri, banji daɗin kalaman da saratu ta furta maki ba, ba yadda zanyi ne shiyasa ban dakatar da ita ba, nasan ranki ya 6aci but pls ki daure,”

Cikin shessheƙar Kuka tace”bazan iya jurewa ba, nagaji nagaji nagaji da irin wulaƙacin da suke Yi mini, sun tsaneni basu ƙaunar ganina, ita da zayn shima yaci mutuncina, zaid ne kaɗai ke ƙaunata”

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya, Kafin Yace”pls Ki ɗago muyi magana”
“Ai bana son kallonka, raina ƙara 6aci yake yi” lumshe idonshi yai haɗi da ware su saman Bayanta.

“Ban ji zafin kalamanki ba, saboda laifina ne, Ni ne silar komai, “ sai da yai wannan furucin ta ɗago da kanta, tana fuskantar ceilling, taƙi Yarda su haɗa ido.
Ba zato ba tsammani taji Ya kwanto da kanshi saitin fuskarta, ƙamshin turarensu ya addabi hancinansu.

“Ki faɗamin me kikeso nayi maki wanda zai kwantar maki da hankalinki”
Harara ta watsa mashi muryarta da shagwa6e ta furta”pls ka tashi ka tafi office, ka zauna kana 6ata lokaci akaina”
“Saboda kin cancanta ne, lokacina nakine, har aikin sai in fasa zuwa idan kinaso” Yai maganar Yana kashe mata ido.

Batasan ya akai ta tsinci kanta da sakar mashi murmushi.
“Inaso na faranta maki, don haka ki shirya dama kin faɗamin kinason haihuwa” zare mashi ido tayi’acikin gidan nan? Salon aganni da ciki a tuhumeni” da zolaya yace”sai kice na Obinna ne, kinga shikenan kin kashe bakin magana’ fashewa sukayi da dariya cike da nishadi.

“Idan hakan ta faru ko kowa zai ƙyaleni, Hajiya saratu saita kasheni” jan kumtunta yai da hannunshi”Ai ko dana kasheta nima,” lumshe ido tayi”pravin ka tashi ka tafi office aiki na jiranka.

‘Waya faɗa maki Ina yin aiki ni? Nifa salary kaɗai nake kwasa, bana yin Aikin komai ko naje office din, P.a dina ke taimaka min,” ya ƙare maganar tare da ɗaura tafin hannunsa ɗaya saman chest dinta, a hankali yaci gaba da yin squeezing dinsu, numfashintane ya soma canzawa ta soma cizon la66anta.

“Faɗamin Ina kika je”? Cikin yanayi najin shauƙi ta amsa mashi da cewa”Garden naje kaima Obinna da amininsa Kayan marmari” ganin ya ɗaure fuskarshi yasa tace”lafiya’
“Mutumin bai kwantamin araina ba! Bana son kina zuwa wurin obinna idan abokanansa suka zo, dattawan nan shegen son mata garesu, musamman irinki babu namijin da zai ganki ya kawar da idon shi”

Ta6e la66anta tayi yayin da suke kallon juna “Are you jealous of me?Meyasa shi obinna baka kishi da shi sai abokanan...” kasa ƙarasa maganar ta yi jin ya mannata da ƙirjinshi”saboda shi na yarda dashi, bazai ta6a nuna kwaɗayi akanki ba, dattijon yana da kamun kai, kuma baida burin ƙara aure tun da matanshi suka rasu, shi ko amininsa Jan kunne tsaf zai Iya cewa yana sonki”

“Idan hakan Ya faru mai za ka yi mashi” tayi maganar tana shafa Wuyanshi da yatsun hannunta.
Kashe mata ido ɗaya yai kafin Ya bata amsa da cewa
“Gemun shi zan tsige” dariya suka saki, da sauri Ya haɗe bakinshi da nata, Hannayenshi Biyu tallabe da kanta tamkar zasu cinye harsunan junasu.


*San Antonio Texas*

*Army headquarter*

Babbar headquater ce mallakin sojojin san antonio, Haɗaɗɗen gini mai girma da faɗi, launin fentin head quater din army green ne, Tun daga bakin entry way na shiga headquater din zaka fara cin karo da Giant soldiars Cikin ta da wajenta maƙil Yake da Gwarazan sojoji sadaukan Gaske masu ƙirar zakuna, kowan nan su Ya kimtsa cikin shiga ta Kakinsu, ƙafafuwansu sanye da army boots, sun ruƙe Jibga jibgan bindigu a hannuwansu, haka zaika ƙugunansu a soke suke da pistols, babu wasa akan fuskarsu cikin taku na majiya ƙarfi suke kewage ko’ina na Gate din shiga headquater din.

Danƙareriyar motace Haɗaɗɗiyar gaske mai numfashi ƴar ubansu ƙirar Mercedes-benz S-class launin black ta sharoro da matsakaicin gudu kaitsaye ta nufi Bakin Hq din, tunkafin ta ƙaraso sojojin suka ƙura ido suna jiran ganin wani isasshen ne wannan ɗan kasada mai shirin zuwa lahira yake yi masu tuƙin ganganci a saman titin su.

Sai da mai motar yakusa zuwa gabansu, Ya rage gudun motar, tamkar na cikin motar baisan da sojojin dake tsaron headquater dinba, Ya soma ƙoƙarin kutsawa zai ƙetare gate din, aiko kamar mayunwatan zakuna suka tunkari motar, Wasu fusatattu daga cikinsu tuni sun saita motar da bindigar hannusu, da kakkausar murya suke faɗin

“Hey! Stop the car! Otherwise we’ll attack you”!

Gaba ɗaya sun kewaye motar, Da ƙarfi wani baturen Soja Ya daki gaban motar da tafin hannunsa tamkar zai 6alle ta, A harzuƙe ya furta

“Ka sauke glass ɗin motar, Idan ba haka ba zaka fuskanci horo mai tsanani daga gare mu”

duk wannan suratan da sukeyi na cikin motar yaƙi fitowa babu alamun zai buɗe murfinta, Hakan ba ƙaramin hayaƙa su yayi ba”

“You’re running out of time. I want you to come out of the car now! If you don’t, I won’t hesitate to shoot! This isn’t a game, I’m serious. you have five seconds!” baturen sojan da ya dafe motar da tafin hannunsa ne Ya furta hakan, Sai da suka gama harzuƙa Zuciyarsu a maƙogaro, a lokacin da basuyi tsammani ba, mamallakin motar Ya tura murfin Ya buɗe, Rai 6ace suka ƙura ido suna jiran ganin wani isasshen ne wannan uban Ji da kan.


*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*


_~*BossLadiesWriters*~_


_~*BossLadiesWriters*~_


_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_


~Middle step~


_The Prisoners E22🔥💫_



*Daga alƙalamin Boss Bature*



_UMMIN AMERICA🔥🔥🔥_



A hankali ta zuro ƙafarta ɗaya daga cikin motar wow, high hills ne launin army green sanye a ƙafarta, sunyi bala’en yi mata kyau, Launin fatar ƙafarta ka ɗai abun kallo ce, kai kace hasken rana bai ta6a shafarta ba, tsabar kyan fatar da salƙinta.

Tun kafin ta ƙarasa fitowa sojojin suka sassauta fushin fuskarsu, Jikin kowan nan su yai la’asar ƙamshin shu’umin turaren jikinta ya daki hancinansu har cikin maƙoshin su fragrance din ya ratsa, Tabarakallahu ahsanul khaliƙin, gaba ɗaya ta tafi da imanin su, basu san sa’adda Bindugun hannunsu suka faɗi ƙasa ba, Ta yi matuƙar tafiya da hankalinsu, wani irin mayataccen kallo suke bin surar jikinta da shi kamar zasu kai mata hari.

Black american ce, A zubin halitta tana da tsayi da jiki, Launin fatarta Chocolate colour ne, Bodycon ce a jikinta, long sleeved gown dai dai gwiwa rigar ta tsaya mata launin Army green, daga ganin ta kaga ƴar duniya hayaƙin taba, baƙar a shana ƙona gari, Irin Ruƙaƙƙun karuwan nan ne Waɗanda suka amsa sunansu A harkar Bariki,Wannan da kuke gani bakowa bace face UMMIN AMERICA, hamshaƙiyar macace mai zaman kanta, Idanuwanta A tsaitsaye suke, Bata da mutunci, kuma bata da kunya ko misƙala zarratin,Tun daga kan shigarta zaka shaida fitsararta, Gaba ɗaya rigar ta bayyana tsiraicinta, boobs ɗinta sun cika faffaɗan kirjinta, tamkar zasu fasa rigar su fito waje don atakure suke an matsesu.

Flat tommy ɗinta tamkar ba’a saka abincin acikinsa tsabar ɗamewarsa, ga Uban qugu dake gareta tamkar ɗaura mata shi akayi saboda faɗinsa, ko kofi aka ɗaura a tudun mazaunanta tsaf zai zauna batare da ya faɗo ba.

Wani irin daddaɗan ƙamshine ke fita saƙo da lungu na Jikinta.


Round face gare ta,Tasha Uban make up, tamkar an zanata don kyau, Ga eye lashes da akayi mata fixing masu tsayi, dogon hancinta Na manne da Nose ring mai kyan gaske, Haka yatsun hannunta na dama na sanye da knuckle ring, long nails din yatsun hannunta fixing dinsu akayi.

Sumar kanta tasha gyara, sai dai daga gani hair wing ne ta daura ba asalin sumar kanta ba, amma zai wuya mutun Ya iya ganewa.

Hankalin maza fa ya tashi haiƙam, gaba daya sun rasa natsuwar su, sai faman haɗiyar yawu suke yi kamar zash lashe ta.

Muryarta tamkar ana busa sarewa ta furta”Zan Iya shiga Ciki”? Har suna haɗa baki wurin bata amsa da cewa”You’re welcome”

shu’umin murmushi ta sakar masu, har dimple din gefen fuskarta Ya lotsa, juyawar da za ta yi, mazaunanta suka girgiza gaba daya sojoji suka zabura tamkar zasu tallabe mata shi.

Komawa Cikin motar tayi, kafin ta rufe motar, wani daga cikin sojojin yai saurin datse mata murfin, A tsanake taci gaba da yin driving ta nufi cikin head quarter din.

Ta tafi tabar su da jarabar kallon surar jikinta da su ka yi, ba zasu iya jurewa ba ai ko da sauri suka nufi cikin head quarter din donsu samu damar ƙare mata kallo ko sun rage raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu.


Bayan tayi parking ɗin motar, ta fito hannunta ruƙe da i phone dinta, Hankulan sojojin dake Zarya a headquarter din gaba ɗaya ya dawo kanta, kamar sun samu talabijin, Matarce akwai Iya jan hankalin maza da surar jikinta, duk idan Tayi taku ɗaya jikinta sai ya girgiza hakan ba ƙaramin hayaƙa maza yake yi ba.


All eyes on her, Sojojin Tamkar zasu kai mata hari, sai dai ba damar Yin hakan,Wani irin ƙwarjini gareta, A fuska bata da wasa, Zazzafa ce, Me zaman Kanta.

Ta wutsiyar ido take kallon masu ɗago mata hannu da masu yi mata alamar suna son yin magana da ita.

Ko kallo basu ishe ta ba, jefi jefi takan ɗan wurga eye balls dinta akansu, da gangan take kashe masu ido ɗaya ko ta ciji lower lip dinta da harshe, ɗabi’arta ce Yin hakan, duk don ta ƙara hayaƙa su.

Kaitsaye ta nufi hanyar da zata sada ta da office din commender domin amsa kiran da yayi mata, tasan ko’ina na headquarter din, don ba baƙuwarta bace, Ba yau bane rana tafarko da ta fara shigarta.

Tun kafin ƙarasowar ta, tuni Anyi mata iso wurinshi, jiranta kawai Yake yi, yana daga zaune saman chair, acikin katafaren office dinsa, komai na cikinsa army green ne, hatta desk din gabanshi, dake dauke da computer dinsa, da wayar hannunsa tare da flag and map, daga jikin bangon office din akwai book shelf, da jerin hotunansa da awards dinsa, bashi kaɗai bane a office din hada Major.

Shigowarta office din, Tuni sanyin Iskar A.c ɗin cikinsa ta gauraya da ƙamshin shu’umin turarenta.

Har saida suka shaƙe shi sosai a hancinansu.

Da kwarkwarsa ta ƙarasa gaban desk dinsa, kamar yadda ta saba yi mashi duk in tazo office dinsa haka yau ma tayi mashi, Ta buga ƙafa tare da sara mashi, hakan ba ƙaramin ƙayatar da shi yai ba, har sai da suka saki murmushi, tun kafin Ya bata iznin zama, ta zauna saman chair din dake facing dinsa, ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, murmushi ta sakar mashi haɗi da ɗaga mashi gira ɗaya ta kashe mashi ido.

A wayance ta soma yin magana cikin harshen turanci”fatan na same ku lafiya” lumshe ido commender yai tare da kai hannu ya gyara zaman wuyan rigar kakinsa.

“Lafiyalou ummi, I’m glad to see u, Ina fata kiran da mukayi maki bai taƙura maki ba”?

Ɗaga mashi gira tayi alamar eh ba tare da ta furta ba, a mutunce suka gaisa da junansu. Bayan kowan nan su ya natsu, Major Ya miƙe ya bi ta ƙofa ya fuce waje jim kaɗan ya dawo hannayen shi ruƙe da mugs na coffee guda biyu ya ɗaura su saman desk, ya ɗago da ido Ya kalli Ummi”zaki Iya sha” ta furta okey, kafin takai hannu ta dauki mug din ta soma kur6an coffee din, da alama ya yi mata dadi kusan sau uku tasha kafin ta ajiye mug din, ta dawo da dubanta ga commender”am all eyes”

“Dalilin da yasa na kira ki ummi, Magana ce mai muhimmanci muke san yi da ke, Ina fata za ki bamu haɗin kai kamar yadda kika saba taimakon mu” cikin harshen turanci commender yayi maganar a tsanake.

Hankalin major na akan ƙirjinta har wani ƙara leƙensu yake yi kamar zai zura kanshi cikin rigarta.

Kallon da Commender ya watsa mashine yasa shi saurin kawar da idonshi ya kame mutuncin kansa

“Babu takura, ko da yaushe ina maraba da ku, zaka Iya faɗin komai ka ke so kai tsaye”

ta ƙare maganar tana shafa saman boobs dinta da yatsun hannunta.

Yawu commender Ya haɗiya Kutt throat dinsa Ya bada sauti, shi kanshi daurewa yake yi, surar ummin America na neman kwance mashi masarrafinsa.

“Ina so ki natsu ki fahimce ni kafin ki bani amsa” amsa mashi tayi da toh
Bayani ya soma yi mata dalla dalla tun daga farkon tsintarsu Angel da su ka yi a Daji, har izuwa kawosu asibiti, da kuma abun da su ke buƙata daga gare ta, tunda commender ya fara labarta mata, ta natsu tana sauraronshi.

“Muna so ki bamu haɗin kai wurin Kula da yaran ki ruƙe su tamkar ƴa’ƴanki, munsan zaki Iyane shiyasa muka za6e ki, tun da ba yau kika fara yi mana aiki ba, mun yarda dake ummi, burinmu ki tarairayesu ta yadda yaran zasu yarda dake har su Iya faɗamaki ainihin abun da ya faru arayuwarsu’ ya ƙarasa maganar idonshi akan fuskarta.
Lumshe ido ta ɗanyi kafin ta waresu akan fuskarshi

“ta ya ya zaku yi tunanin damƙa amanar yara har goma sha ɗaya a hannuna? Bayan kunsan wacece ni, Ban ta6a haihuwa ba, kuma ni banason Rainon ƴa’ƴa, ban ta6a sha’awar haihuwarsu ba, balle har in iya kula da yaran wasu, Ina mai baka haƙurin Cewa Ni bazan Iya wannan aikin ba! zaifi ku samu macen da tasan zafin haihuwa mai kamun kai ku bata rainon su” tana magana jikinta na jijjiga, major duk yabi ya susuce ya rasa natsuwarshi, ba dan commender na akusa ba da ba abun da zai hana ya damƙeta ko da zai sha mari ne.

“Ummi, Ki sassauta kalamanki, Kina yi min magana da tsiwa, Ko kin manta a ina kike ne? Ki duba da kyau ki gani, nan ba club ba ne, ba kuma gidan karuwai bane, sannan ba ga6ar taku bane, Head quarter din sojoji ce” Ya yi maganar tare da zaro bindiga daga cikin drawer chest na desk din gabanshi Ya daurata saman desk din.

Tuntsirewa Tayi da dariyar rainin wayau

“Kai ma ka sani, Ummin america bata tsoron bingida, ni da ni ke yin mu’amala da masu ruƙeta, yanzu haka da nake yi maka magana shigowa ta head quarter din nan gaba ɗaya na tada masu jarabarsu, suna can waje, wandunan su sunyi masu nauyi’ cike da shaƙiyanci tayi maganar, ta riga ta gama raina su bata jin tsoron su ko kaɗan.

Cikin kwantar da murya commender yace”is ok, kibar yi min wasa, Muyi magana ta hankali, ki taimaka ki kar6i buƙatarmu, kome kikeso zamuyi maki, sannan ɗawainiyar yaran da komai nasu mune zamu bada tallafin da za’a cigaba da kula da rayuwarsu, tun daga cinsu shansu, suturarsu, da karatunsu, Iya taimakon da muke so kiyi mana kija su a jiki ki zama tamkar mahafiyarsu” yamutsa fuska tayi tana faman wurwurga eye balls dinta tace”Kana nufin wai a gidana zasu zauna? Ka san gidana gidan mazane, a koda wani lokaci Ina busy wurin biya masu buƙatarsu, how ka ke tunanin zasu Iya samun kulawar data dace? Kuma naji kace yaran suna fama da depression hada me ciwon ciwo, gaskiga ba ƙaramar ɗawainiya bace kula da su, bazan Iya ba commender, kada ka tursasamin, kasan ina girmamaka saboda halaccinka agareni”

Kallon major commender yayi, hakan ya bashi damar Yi mata magana

“Ba zamu takura maki ba, amma kafin ki tafi Inaso zan nuna maki hotunan Yaran Ki gansu”

Miƙewa Major yai daga saman kujerar da yake a zaune Ya zagaya ta 6angaren Commender Ya juyo mata da laptop din saitin fuskarta.

Operating ɗinta Ya soma Yi, hotunansu Angel Ya buɗo, daga kan hotonta Ya fara Nuna ma Ummin america
“Sunanta Angel” Ya ambaci hakan yana kallonta, da alamun mamaki akan fuskarta ta furta “wow she’s beautiful sai dai daga ganin bakinta za ta yi tsiwa, ni kuma bana sha’awar Yara masu masifa” ta faɗa haɗi da yamutsa fuska, still murmushi ne akan fuskar major da commender.

Hoton Batul ya nuna mata, sai da ta ta6e la66anta kafin tace “tana da kyau, sai dai daga ganin fuskarta bata da masifa, wannan ko yatsa aka sanya mata abaki bazata Iya cizon shi ba” ta kare maganar tana hura hanci.

Hoto na gaba fuskar Hanna ce, Ummin america tace”har ƙwara Yarinyar daka wuce akan wannan, taci ka sanyi daga gani babu kuzari a jikinta” yadda take fayyace ɗabi’unsu kamar ta ta6a ganinsu.

Ko da akazo kan Hoton Parveen Ya cika screen din laptop din.

Da buɗar bakin Ummi sai cewa tayi”yarinyar nan daga ganin kumatuntu mayyar abinci ce, zai yi wuya idan ba asame ta da shegen ci ba, Ni bana so mutun mai ciye ciye” murmushin fuskar Major da commender sai ƙara faɗada yake yi, don ba ƙaramin nishaɗi take basu ba.

Hoton Jamimah Ya nuno mata, waro ido waje tayi hada sanya Hannu ta dafe saman ƙirjinta.

“Major, ruƙon wannan Yarinyar ai sai likitan mahauka, shi kaɗai ne zai Iya sarrafa ta, ba dai ni ba, Ni ina zan Iya kula da ita, daga ganin bakinta zatayi tsiwa” Major yayi dariya tare da nuno hoton Azeeza, shiru tayi tana ƙare mata kallo, kafin ta ɗago da ido ta kalli Major”sai naga kamar ƴan biyu ne ita da Yarinyar da ka nuna min kafin ita, sunyi kama” Major yace”haka muke tsammani, sai dai muna hasashen azeeza tafi Jemimah shekaru kamar yadda ɗan uwansu ya faɗa mana”

Yamutsa fuska Ummin america tayi”tana da kyau sai dai daga ganinta matsoraciya ce, wannan ko tsawa na daka mata zata Iya

Download complete TXT · Novel page