Showing 213001 words to 216000 words out of 250533 words
Chapter 72 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
da kike yi amma nagaza fahimtarki, har takai takawo ina zarginki, maimakon na kyautata maki zato, wallahi naji kunya, daren Jiya daƙyar na runtsa tsabar takaici, Ƴan kwanakin da muka samu sa6ani atsakaninmu aunty Aneelerh naji jiki ba kaɗanba, na ƙuntata, na gane mahimmancinki agareni, Ina da abubuwa dayawa da suka faru wadanda nakeso in samu abokin firar da zangayama wa ya tayani farin ciki sai dai kash babu, ke kaɗai ce nake jin dadin tattaunawa dake akan duk wani abu daya shafi rayuwata saboda nasan zaki ƙarfafa min gwiwa ki kuma bani shawarar da zata amfane ni....” zafafan hawayene suka wanke fuskar Zahra, tuni idanuwanta sun kaɗa jawur da su.
“Meyasa banyi dogon nazari ba akan shawarar da kika bani”?
Zuciyar aneelerh ba ƙaramar karaya tayi ba”zarah! Mahboob Ya fada maki ne”?
Jinjina kai tayi”ƙwarai kuwa ya fadamin komai, har gargaɗi na yayi akan kada na nuna na sani, saboda kince mashi kada ya gaya min, shi kuma a ganinshi bai kamata ki zubda mutuncinki a idanuwana ba, saboda ku rufa ma hajiya falmata asiri awurina, don in cigaba da ganin darajarta, hakan kuma bazai ta6a yiwuwa ba, saboda shi mutunci madarane idan ya zube baya kwasuwa, sai dai naji dadi da ke kika yi silar shiriyarta, ke din ta dabance Auntyna”
Rungume Aneelerh tayi, atare suka fashe da kukan farin ciki, yau sun shirya da juna, babu wanda baiji jiki ba acikinsu.
Bubbuga bayanta Aneelerh tayi da hannunta Cikin shessheƙar kuka take fadin”komai ya wuce zahra, abunda ya faru laifina ne dana baki shawarar banza duk da ko a lokacin bawai zan zuba maki ido bane don ina jarabaki ne nayi hakan, wallahi duk wani motsinki atafin hannuna, tun bayan dana baki shawarar, fargabana kada ki amince da shawarata ki kama hanya ki tafi kai mata kanki, shiyasa na sanya maki ido, akarshe na yanke shawarar zuwa gidanta don in gargadeta akan ta fita sabgarki, Cikin Ikon Allah sai gashi na 6uge da yi mata nasiha, ashe nice silar shiriyarta, naci ribar jarabawar da nayi maki zahra, Naji dadi kuma nayi farin cikin samun ƴar uwa mai tawakkali irinki, zan iya cewa duk namijin daya mallaki mace irinki yayi nasara sai dai fatan ya cika da imani”
Dariyar farin ciki zahra tasaki, tare da dago dakanta daga jikin Aneelerh
“Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya saboda babu su auntyna, Ina fatan nima Allah yabani abunda zan kyautata maki da shi, sannan mahboob Ya faɗamin cewa kin bashi kyautar kuɗi duk da yaƙi gayamin nawa ne kinsan halinshi May be Yana gudun kada Ince ya bani kasona, baisan cewa Nima na samu alheriba, abunda nake ta so in faɗa maki kenan”
Waro ido Aneelerh tayi da alamun farin ciki akan fuskarta tace”masha Allah, kice kun samu abun arziƙi” Jinjina kai Zahra tayi”zakisha mamaki auntyna, naga yanzu kika farka daga bacci, da anjima idan muka kammala yin breakfast zan fada maki komai”
Murmushi Aneelerh tasaki”Yau zansha kanun labarai, Yanzu bari na shiga toilet in yi wanka”
“Auntyna wai yaushe za’a dawo mana da baby junaid dinmu, nifa nayi missing dinshi, Allah na kusa zuwa in dauko shi, Jiya har mami na tambaya game da zancen dawowarshi”
Aneelerh tace”kada ki damu, Babyn mu yau zai dawo gida, Hajiya adama zata kawo shi, Nima yau da shi na tashi araina”
“Allah ya kawo su lafiya, shima na tanadar mashi kyautarshi ta musamman da zan bashi” Aneelerh taji dadin maganar zahra.
“Kada na cika ki da surutu, nayi kewarki ne auntyna, bari nabarki kiyi wankan in kin fito mun tattauna, amma kafin nan niko inaso in tambayeki wani abu in ba takura” dariya aneeleh tayi kafin tace”okey ina jinki fadamin menene”
Da ido tayi mata nuni da hoton dake amanne jikin bango.
“Wacece wancan black beauty din mai diri? Ita kadai ke bansani ba cikin ƙawayenki, nadai san Benazir mahaifiyar kyakkyawar yarinyar nan Angel”
Jim Aneelerh ta ɗanyi kafin ta furta”Aishatu bintu sheikh Iman Malik, shine sunanta, kamar yadda na fada maki aminnan juna ne mu”
Cike da son jin ƙarin bayani Zahra tace”to amma ta rasu ne ita? Naga ko waya ba ku yi, Ita dai benazir nasan abunda ya faru da ita” a kagare ta jefa mata tambayar.
Cikin sanyin murya Aneelerh tace”ƙaddarace ta afka mata wadda tayi silar tarwatsewar farin cikin rayuwarta, baiwar Allah, nan da kike ganinta mahaddaciyar alƙur’anice, tun tana ƴar shekara goma sha wani abu ta haddace shi, Tana da kaifin basira mace ce mai kamun kai, tana da aji, idan nace zan baki labarin rayuwar Aisha wallahi saikinyi sha’awar yin koyi da ita, saboda kyawawan ɗabi’unta da halayanta, Ni kaina ban ta6a tsammanin zamu rabu da itaba.....” tun da ta fara magana zahra ta kafe ta ido tana sauraronta, idanuwan Aneelerh sun kaɗa jawur, sam bata son tuna baya, hakan zai fama mata ciwon dake acikin zuciyarta.
“Aunty Aneelerh kinyi shiru? tun da kika ambaci kyawawan halayanta naji na kwaɗaitu da son jin tarihin rayuwarta”
Girgiza kai Aneelerh tayi”Am sorry zahra, bana son tunawa, “ bubbuga ƙafa zahra tayi tamkar zata fashe mata da kuka tace”please Aunty Aneelerh, wallahi tana burgeni duk da ban ta6a ganinta ba”
Murmushin yaƙe Aneelerh tasaki tana duban hoton yayin da hawaye ke bin fuskarta”Ni kaina bani da masaniyar tana araye kota mutu, tunkafin muyi aure tabar gidan iyayenta, Silar wani mummunan abu daya faru, wanda ni nayi imanin bata da laifi, tuggune da makirci aka shirya mata.....” dakatawa Aneelerh tayi dayin maganar tana kallon zahra, tsabar son jin gulma har ta jefar da cazbar hannunta batare da saninta ba.
“Aunty Aneelerh kinyi shiru! Meya faru da ita? Wanda yaja har tabar gidan iyayenta? Wani irin tuggune aka kitsa mata”?
Tuntsurewa Aneeleeh tayi da dariya, juyawa tayi da sauri ta nufi toilet door tana fadin”Zahra ƙwara ki fidda rai da son jin labarin Aishatu Bintu sheikh imam malik, dan zan baki shi ba yanzu ba sai kin ƙara hankali” ta kare maganar ta shige toilet taja kofa ta datse.
Ta tafi Tabar Zahra da cizon yatsa, idanuwanta akan hoton fuskar Aisha, aranta ta ayyana ai wallahi saina ji labarinki baiwar Allah, Ai ni dama tun da naga hotonki na shaida kinbar tarihi arayuwarki, Oh ni ƴar ubansu, gata kyakkyawa, mace har mace, ga diri kamar nicki minaj, ko tana ina ahalin yanzu”? Sambatu zahra tadingayi tana kallon hoton aisha, sai daga bisani ta duƙa kasa ta dauko cazbaharta, ta futo daga ɗakin ta nufi nata dakin don ta kimtsa kafin lokacin yin break fast.
*Daular Alhaji Musa🏙*
A zaune take kan darduma, bata jima da kammala sallar asubahi ba, hijab din data sanya launin milk, gaba ɗaya ta tattara natsuwarta akan addu’ar da take Yi, ta ɗaga hannayenta sama cikin harshen larabci take karanto addu’o’i, yayin da hawaye suka cika idanuwanta, bakomai take roƙo ba face Allah ya dawo mata da mijinta lafiya da ƴarta, bata da burin daya wuce tayi tozali da su, tayi matuƙar ƙagara da son ganinsu.
Ƙamshin turaren dr.shureim ne Ya dakatar da ita daga yin addu’ar da take yi, da sauri ta shafa saman fuskarta, A hankali ta fuskance shi, yana daga zaune gefen gadonta, bai jima da shigowa ɗakin ba, fuskarshi dauke da annurin farin ciki, Daren jiya da tunanin ƴar uwarshi ya kwana, ya damu da ita.
“Yayana nakaina, Ina kwana ka tashi lafiya”?
“Lafiyalou rabin raina, ina fata kin yi kwanan farin ciki agidan Uncle” shiru tadanyi tunawa da abunda ya faru duk da ta dauki hakan amatsayin mafarki, jinjina mashi kai tayi”Alhamdulillah, jiya naji dadin bacci, hada munshari, balle ni da nake atare da Zeenatu, yarinyar akwai shiga rai”
Murmushin gefen fuska dr shureim yasakar mata”hala tacika ki da surutu”?
Girgiza kai benazir tayi”a’a, ai yarinyar kunya gareta, tana jin nauyin yi min magana yadda kasan bafullatana”
Dariya dr. Shureim yai kafin ya tsagaita yace”hakane tana da kunya, amma fa ta iya zuba kamar aku, sai kun saba da ita zata saki jiki dake”
Dr shureim yasaki baki yana maganar zeenatu, baisan cewa tana la6e cikin toilet tana sauraronsu, hannunta ɗaya ruƙe da qugunta, kalmar akun daya furta ta ta6a zuciyarta.
Murmushi benazir tasaki, abunda baisani ba tun jiya tasan da surutun zeenatu, kafin su kwanta bacci, sunyi firar dare, ta saki jiki da ita tamkar abokiyarta.
“Yaya shureim, Ni yanzu damuwata Mijina da ƴata, mami ta fadamin cewa basa ƙasar, amma sun kusa dawowa, ni namanta ma ban tambayeta sunan ƙasar da suka tafi ba” ta fada tana dubanshi”yaya shureim ko kana da number wayar taj”? Ras yaji gabanshi ya fadi, saboda shi baisan komai dangane da mijin benazir ba.
Shiru yai mata batare da ya iya furta mata kalma ba, don baisan amsar da zai bata ba
“Au namanta, kaima bakasan mijina ba ko? Lokacin dana aure shi......” bata ƙarasa maganarba cak ta ɗago suna kallon juna.
Cikin sanyin murya yace”ai ba laifi kikayi ba, lokaci bana acikin hayyacina, ban kaiga farfaɗowa daga radadin abunda ya same ni ba, Benazir bansan mijinki ba, bana zumunci dashi, saboda ni kaina bana cikin natsuwata, kuma hada ƙarin ni ba azaune nake ba, idan baki manta ba, da abun duniya ya isheni, tattarawa nayi na koma egypt wurin ammim mu da zama” daƙyar yake furta maganar, launin idonshi harya fara canzawa
Numfasawa yai kafin ya ɗaura da cewa”nasan ban kyauta maki ba, amma kiyi hakuri, daga ni har ke ƙaddarar rayuwace ta afka mana,”Wallahi bazan Iya misalta maki ƙunci da radadin da naji ba, lokacin da labarin tafiyarki ya same ni, idan bazan manta ba, aunty zainab ce ta sanar dani komai dangane da guduwarki da jinjirar da kika bari, bayan haka bansan komai game da rayuwarsu ba nima ban jima da dawowa gida ba.......”
Bai ƙare maganar ba ta tari numfashinshi da cewa”kana nufin baka ta6a haduwa da ƴata Angel ba? Amma ni ayadda mommy ta fadamin taj yana kawota gidan mu, suna daukar dawainiyar kula da ita kuma suna nuna mata hotona harma tana tambayarsu Yaushe zan dawo”
Zaro ido dr.shureim yai alamar mamaki da jin ƙaryar da mommynsu ta shirgawa benazir, duk da ba a ƙasar yake zaune ba, yasan komai dake faruwa a gidansu, ta hanyar aunty zainab dake fada mashi akai akai, shi dai a iya saninshi Hajiya layla bata zumunci da tajuddeen, hatta auran benazir da Alhaji ubaid ya bashi bada son rantaba, saboda ita ta tsani bare, balle shi da yakasance mai rufin asiri ba attajirin mai kuɗi ba, har fada saida sukayi da Alhaji ubaid saboda yabama ɗan jarida auran ƴarsu.
Ganin yanayin fuskarshi ya canzane yasa jikin benazir yin sanyi,
“Yayana kayi shiru baka ce min komai ba! Mommy ba gaskiya ta fadamin ba ko”? Adabarbarce ya girgiza mata kai yana kokarin tattara natsuwarshi yace”bahaka bane, ai ni bana a ƙasarne, bani da masaniya akan komai, lokacin dana dawo Nigeria shi taj din da yarinyar sun riga sun bar ƙasar, nima awurin Aunty zainab naji labarin”
Ajiyar zuciya benazir ta sauke, fatanshi Allah yasa kada ta kuma tambayarshi wani abun da zai kasa amsa mata.
“Mommy ta fadamin cewa yarinyar kamanninta sak dana tajuddeen amma hasken fatarta nawane ta dauko, yarinyar kyakkyawace idan zan iya tunawa, kafin na gudu nabarta dana haifeta saida na kalleta har naga launin idanuwanta ruwan tokane kalar na amminmu, kuma tana da curly hair kalar nawa, ni dai fatana Allah yasa bata dauko halina ba, banason ace bata jin magana.
Dariyace ta kubce ma dr shureim, sambatun benazir ba ƙaramin kayatar dashi suke Yi ba.
Zeenatu dake a la6e tana sauraronsu, takasa fitowa daga toilet din, zuciyarta ta kwaɗaitu da son jin wacece yarinyar auntynta benazir? Ya akai bata ta6a ganinta ba? Kamar dai ta ta6a jin labarin jinjirar da benazir ta bari awajen mommynta sarah.
Lokaci ɗaya dr shurem yadaina yin dariyar, hawayen dake taruwa cikin idanuwanshi suka soma gangarowa saman kuncinsa.
Da sauri ya kifa kanshi on his laps,
Hankalin benazir ba ƙaramin tashi yai ba, Jiki na rawa ta mike daga kan dardumar ta koma gefenshi ta zauna haɗi da daura hannunta ɗaya saman bayanshi”yaya shureim meke faruwa? Meyasa ka zubar hawaye? Yanzu fa kake yin dariya? Kona fadi wani abune daya 6ata maka rai? Shiru bai ɗago ba, duk tabi ta ruɗe, zeenatu dake yi masu la6e jikinta yai sanyi jin dr shureim dinta yana zubar da hawaye, muryar benazir taci gaba da jiyowa tana fadin”dan Allah kayi min magana yayana nakaina, kasan bana son ganinka acikin damuwa” bazata iya jurar halin da dr shureim dinta ya shigaba, Har ta miƙa hannu zata buɗe kofar toilet din, sai kuma tafasa ta dan buɗe kadan ta yadda zata iya leƙen su
Ɗagowa yai da kanshi, hawaye sun wanke fuskarshi, benazir dake kallon shi itama hawayen ke fita a idonta
Zura hannunshi yai cikin aljihun jallabiyar jikinshi ya zaro wayarshi, batare dayace komai ba, Ya miƙa mata wayar, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskarta Yarinyar dake akan wallpaper dinshi.
Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, da sauri ya sanya tafin hannunshi ɗaya ya toshe mata bakinta, haɗi da girgiza mata kai, alamar tayi shiru, daƙyar ta haɗiye kukanta, yayin da suke kallon juna, sai yanzu tagane dalilin zubar hawayenshi.
A hankali ya zame tafin hannunshi daga saman bakinta, hakan ya bata damar yin magana Cikin rauni na murya ta furta”munyi babban rashi yaya shureim, babu rabon suyi rayuwa tare da ƴata Angel, yarinyar tana kama damu, kamar ni na haifeta, mutuwa tayi mana yankan ƙauna, Allah ya jiƙanta” daƙyar ta ƙare maganar a hankali ta mayar da rinannun idanuwanta kan hoton jinjirar yarinyar dake a nannanɗe cikin towel fari ƙal, an sanya mata kayan sanyi, farace sol kamar ka ta6a jini ya ɗigo, dara daran idanuwanta sun buɗe sosai.
“Bani da abun kallo daya wuce hotonta, da ita nake kwana da ita nake tashi, na mutu akan ƙaunarta, bazan ta6a daina sonta ba, kuma bana tunanin koda ace nayi aure zan samu madadinta a duniyar nan........ ⁉️❗
“Nayi danasanin abunda na akaita mata, har yau idan na tuna cewa da hannuna nayi hakan sai inji gaba ɗaya na tsani kaina....” cikin jin ƙunar yai ya ƙare maganar.
Tsananin tausayinshi ne ya kama Benazir, idanuwansu sun kada jawur
Harta bude baki zatayi magana, Motsin buɗe kofar toilet Ya dakatar da ita, sam ta manta da zeenatu a toilet, da sauri ta goge hawayenta, dr shureim ma ya share hawayen shi muryarshi adisashe yace”wanene a toilet”?
Kafin ta bashi amsa, zeenatu ta fito, fuskarta da alamun lemar ruwa, tamkar batasan me suke tattaunawa ba, Har kuka tayi masu saboda sun bata tausayi duk da bata fahimci kan zancen nasu ba, ita a tunaninta Yaya shureim dinta ya ta6a son wata, sannan hoton daya ta6a nuna mata awayarshi amatsayin nata yake kallo yanzu ta gane ba ita bace, ya 6oye matane, har cikin ranta ba ta ji dadin hakan ba, jikinta yai sanyi tamkar wadda ka zarewa laka.
Sun ƙura mata ido suna kallonta, fatansu Allah yasa bata ji me suke tattaunawa ba”
“Zeeentu dama kina acikin toilet tsawon lokacin dana shigo ɗakin”?
Jinjina mashi kai tayi”eh yaya shureim bansan ka shigo dakin ba, Uziri ne Ya ruƙe ni a toilet”
Ajiyar zuciya ya sauke jin tace batasan ya shigo ba.
“Ina kwana, ka tashi lafiya” muryarshi araunace ya amsa mata”lafiyalou” duban benazir tayi wadda tayi shiru tana kallonta, daga ita har dr. shureim din fuskokinsu sunyi jawur saboda kukan da suka sha, a hake suke ƙoƙarin 6oye mata damuwarsu bayan ga alama nan ta gani.
“Aunty Benazir, bari naje daki in yi sallar acan, namanta jiya ban ɗauko hijabina ba” ta fadi hakanne don ta basu damar cigaba da tattaunawarsu
Benazir tace”A’a basai kinje daki ba, Ga hijab dina kiyi da ita” ta fada tare da cire hijabin ta miƙa mata, da sauri zeenatu tace”a’a, Kibarshi, nafison naje daki nayi acan, naga kamar kuna yin magana ne keda ya shureim”
Murmushin yaƙe Benazir tasakar mata”kada ki damu ƙanwata, bawani abu muke tattaunawaba, kema zamu Iya yin firar dake”
“Assalamu alaikum!” Mom layla ce ta doko sallama, gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta, doguwar rigace a jikinta milk colour, ta yafa mayafi akanta, fuskarta dauke da fara’a take dubansu
Har suna haɗa baki wurin gaishe da ita”ina kwana mommy? Kin tashi lafiya”?
Cikin kulawa ta amsa masu da cewa”lafiyalou Alhamdulillah, fatan na same ku lafiya, zeenatu ya akai naganki atsaye”?
Washe baki zeenatu tayi tana fadin”yanzu na fito daga toilet, nayi alwala ne zanyi sallah”
Mom layla tace”okey, yakamata kiyi kada ki makara” amsa mata tayi da toh, da sauri ta nufi kofar fita dakin ta fuce cike da fargaban kada Aunty Benazir ta dakatar da ita, bayan ta fita daga dakin ajiyar zuciya ta shiga saukewa, haƙiƙa taji takaicin halin da taga dr shureim dinta da aunty benazir, ta shiga damuwa tabbas tana ji aranta wani mummunan abunne ya ta6a faruwa da su, a ƙagare ta ke da son jin wacece Yarinyar benazir dinta? Sannan kuma wacece matar da taji yaya shureim dinta yana magana akai har yake fadin bazai samu madadinta ba koda ace yayi aure, burinta ayanzu shine taga hoton matar da ya shureim yake nunawa benazir a wayarsa.
Da wannan tunanin ta nufi dakinta dake acan upstairs.
Bayan fitar zeenatu, dr shureim da Benazir suka miƙe tsaye suna fuskantar mahaifiyarsu dake binsu da kallon mai tattare da alamar tambaya.
“Meke damunkune? Ya akai naga fuskokinsu sun yi ja kamar wadanda suka yi kuka”! Tambayar data fara jefa masu kenan
Benazir ce tayi kokarin cewa”Ni da ya shureim ne muke yin firar yaushe rabo, mun tuna da rayuwar mu ta bayane kafin mu rabu”
“Hmm, yakamata ku manta da abunda ya wuce, tuna bayan nan baida amfani, tun da ba abun arziƙi bane ya faru”
Dr shureim yace”hakane mommy, zamuyi kokarin yin hakan”
Shiru tadanyi na wani lokaci tana kallonsu.
Har dai Benazir ta fahimci kamar akwai wani abu dake akasan zuciyar mahaifiyar tasu
“Mommy, kina son yin magana damu ne”?
Girgiza kai tadanyi kafin tace”tausayin rayuwarku nake ji, ina jin fargaban