Showing 228001 words to 231000 words out of 250533 words
Chapter 77 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
suka taimaki rayuwarmu ina da tabbacin zasu taimaka mana don ganin an gano su wanene munafukan dake sadaukar damu ta hakanne zamu tabbatar da zarginmu”
Javed yace’nima ina goyan bayanka Sajeed! Mu tona masu asiri kawai, idan da rabon mu rayu zamu rayune duk runtsi duk wuya, kai koda ace zamu mutu ne bayan mun tona masu asiri wallahi munci galaba akansu, tunda har muka yi nasarar guduwa daga cikin kurkukun ƙaddara, wanda ko a tarihi ba’a ta6a samun prisoners da suka gudu suka tsira ba sai akanmu”!
A hankali unaisah take binsu da kallo, ta fahimci ransu yakai maƙura wurin 6aci, Jininsu akan akaifarsu yake, kowannansu atsorace yake da abunda ke faruwa da danish.
Fashewa da kuka jemimah tayi haɗi da ɗaura hannayenta biyu saman kanta tana fadin”Wayyo Allahn mu mun shiga uku, Yanzu shikenan danish din mu ya zama dodon kurkuku zai ɗauke mu ya maida mu can mu cigaba da cin ganye” fuskarta sharkaf da hawaye, ruko hannunta Unaisah tayi acikin nata”Ya isa haka, Ki daina kuka, kanki zai Iya yin ciwo,” girgiza kai ta dinga yi tana fadin”genie ba zaki gane ba, wallahi banason komawa kurkukun nan, haushinsu nake ji, Allah zuciyata zata Iya bugawa in mutu kowa ya huta”
Gaba ɗaya idanuwansu na akan fuskar jemimah, ta haƙiƙance tana yin magana shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu saman fatarta.
“Sun kashe mun majnoon dina, sun kashe mana Unaizah, Yanzu kuma mu suke son kashewa fa” ta ƙare maganar tana faman jan majina’
Kwanto da kanta Angel tayi saman cinyoyinta, ta ɗaura hannunta kan sumarta cikin sigar lallashi take yi mata magana”in sha Allah bazamu ta6a komawa gidan kurkukun ƙaddara ba, Har bada, munbarshi kenan bi’iznillahi mune zamu kawo karshen kurkukun da fasiƙan Shuwagabannin su, zamu tarwatsa baƙin tarihin da suka kafa, zamu shafe babinsu a doron duniyar nan, zasu ɗanɗanin kuɗarsu har sai sunji inama ace ba’a halitto su a duniyar nan ba, wannan Alƙawarine!” da ƙwarin gwiwa unaisah ta ƙare maganar.
Shiru jemimah tayi tuni ta haɗiye kukanta, Jikin kowannansu yai sanyi, maganganun da suke yi yai silar fama masu tabon dake acikin zuciyoyinsu.
Daƙyar Hanna ta Iya buɗe baki tace”ni yanzu damuwata a wani hali danish yake aciki”? Tayi tambayar idanuwanta cike tab da ƙwalla
Angel ce ta bata amsa da cewa”har yanzu bai dawo mutun ba, amma ɗazu boss man ya fada min cewa malamin da zai duba jikinshi ya ƙaraso Ina da tabbacin Yana acikin gidan nan, shiyasa Big guy Yace mu zauna a ɗaki bayason ganin gifcinmu, yakamata mu tayashi da addu’a, ita yake buƙata daga gare mu” tunkan ta rufe baki, sukayi saurin daga hannayensu sama, Itama ta ɗaga nata,
“Jemimah ki tashi muyi ma ɗan uwanmu addu’a” Unaisa ce tayi mata magana, daƙyar ta ɗago da kanta haɗi da ɗaga hannayenta sama kamar yadda sukayi
Addu’o’i unaisah ta soma karantowa suna amsa mata da ameen ameen, bayan ta kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, kafin su zame hannayensu, kunnuwansu suka soma jiyo masu motsin buɗe ƙofar dakinsu, A hanzarce suka ɗago suna kallonsu.
Big guy ne ya shigo hannun shi ruƙe da faffaɗan tray Na kayan breakfast dinsu, Daga Bayanshi Ummin america ce, Ta ɗauki wankan turkish gown launin brown anyi mata adon stones launin yellow, mayafin da tayi rolling kala ɗaya ne da stones din rigar, ta sanya high heels a ƙafarta, daga sama rigar ta matseta ta bayyana surar kirjinta, daga bayan rigar tudun mazaunanta ya fito sosai.
Tunda batool taji ƙamshin turaren ummin america hankalinta ya tashi, tasan dole ta hukuntata akan fitowar da tayi daga ɗaki batare da saninta ba.
A tsakiyarsu big guy ya ɗaura tray din kayan abincin kafin Ya soma yin magana.
“Ga auntynku nan Ummi, zata zauna atare daku don ta ɗebe maku kewa, idan kuna buƙatar wani abu, ita zaku faɗa mawa” amsa mashi sukayi da toh.
Big guy ya maida dubanshi ga ummi dake atsaye ta ruƙe qugu da hannu ɗaya, Hadaddiyar agogon hannunta sai ƙyalli take yi.
“Ummi, ki kula da su, bana so asamu matsala, malamin ne ya buƙaci a tattara sauran yaran wuri ɗaya sannan aja hankalinsu gudun kada suji sautin abunda zai rikitar da su”
Lumshe mashi ido tayi, alamar taji mai yace, shi kanshi daurewa yake yi, domin kuwa wankan da ummi ta ɗauka yaja hankalinshi, musamman shu’umin ƙamshin humran dake fita a jikinta.
Muryarta da kwarkwasa tace”okey, baka da damuwa”
Bayan fitar big guy daga ɗakin.
Ummi ta kalli su unaisah, atare suka haɗa baki wurin gaishe da ita.
“Ina kwana aunty ummi” yamutsa fuskarta tayi”lafiyalou, Ina batool”? Ta jefa masu tambayar tana kallonsu, kafin su bata amsa idanuwanta suka sauka akan yatsun hannun batul, ta 6oye kanta abayan haris, duk don kada ummi ta ganta.
Babu wanda ya fahimci wani abu, sai ita data san meya haɗasu.
“Kunyarki take ji Aunty ummi, shiyasa ta la6e” acewar Unaisah.
Ta6e baki ummi tayi kafin tace”Ina maganin muran da boss man Ya baki”? Ta fada tana nuna unaisah da hannu.
sai lokacin ta tuna da maganin batasan tun yaushe ta jefar dashi ba.
“Kin yada kenan”? Girgiza kai tayi a’a, Yana a hannuna tun ɗazu, namantane ban kaiga bata ba”
Juyawa baya ummi tayi tana kallon tsakar dakin, Karaf idanuwanta suka sauka akan Blister pack din dake ajiye ƙasa, cikin takun Isa Ta nufi floor din ta zuƙunna ta ɗauki maganin”ajiyar zuciya unaisah ta sauke ganin ta gano shi’
“Ku matsa min anan zan zauna muyi breakfast,” ta faɗa tana nuna tsakankanin Batool da Haris, da sauri Ya matsa mata, taje ta zauna idonta akan batool data ƙanƙame haris, ruƙo hannunta ummi tayi tare da rabata daga jikin haris, duk tabi ta ruɗe, taƙi yadda su haɗa ido.
Bottle water Unaisah ta ɗauka ta buɗe murfin, ta tsiyaya ruwa acikin cup, ta miƙa ma ummi, kar6a tayi tare da fadin”thanks” kafin ta curo maganin ƙwaya biyu ta miƙa ma batul, yatsun hannunta na kerma ta kar6a ta sanya abaki, ta kar6i cup din hannun ummi ta kur6i ruwan ta haɗiye maganin, Bayan ta gama ta ajiye cup.
“Bata da lafiya ne”? Sajeed ne ya tambaya, parveen tace”Mura take Yi,”
“Shiyasa naji muryarta ashaƙe, sis Allah ya baki lafiya” amsa mashi da tayi da ameen, sauran mazan sukayi mata sannu ta amsa masu.
Kafin ummi ta fara serving dinsu, A plates ta zuba ma kowannansu abinci banda batool, ɗaya bayan ɗaya ta miƙa masu, suka kar6a suna ci, kallon Batul tayi”atare zamu ci” ta faɗa tana sakar mata shu’umin murmushi afakaice batare da su Unaisah sun gani ba.
A plate ɗaya ta zuba masu farfesun naman kaza, Yaji kayan kamshi ga uban romo.
Daƙyar batool take iya shan farfesun, saboda Ummi ta hanata sakat, da zarar ta ɗago sai ta haɗa ido da ita, ta rasa gane dalilin dayasa ummi take son takura rayuwarta.
Hankalin Unaisah ba akansu yake ba, saboda damuwar data bijiro mata, ta ƙosa taji me ke wakana da Danish, Malamin Ya fara Yi mashi aiki ko kuwa.......?
Shin meya faru bayan zuwan Sheikh Imam malik!?
Bayan ƙarasowar motarsu akatafaren Gate din shiga gidan Owais Jami’in dake driving dinsu yayi parking a agaban entry hall, Ya fito a hanzarce Ya zagaya ya buɗe masu murfin motar, A hankali Prime minister hateem ya fito daga Ciki, Kafin Sheikh Imam Ya zuro ƙafarshi waje shima Ya fito Yana ƙarema ginin gidan kallo, ya yaba da haɗuwar daular Owais, har saida ya furta masha Allah.
Kafin su ƙarasa falon, Glass door dinsa ta buɗe, Chief Owais Ne Ya bayyana gefe da gefenshi, Boss man ne tare da Big guy, da kuma sauran jami’an isod da suka hallara domin tarbarsu.
Murmushi prime minister hateem yasakar mashi, tare da nufarshi tunkan ya isa gare shi, Chief owais Ya riga shi zuwa Ya haɗa hannayenshi biyu yai hugging din uncle din nasa”
Kafin Ya ɗago Ya nufi Sheikh Imam Ya rungume shi, fuskar kowannansu ɗauke da murmushi.
“Owais fatan na sameka lafiya, tsawon lokaci bamu haɗuba, aiki ya 6oye ka,” Sheikh imam ne yai mashi maganar
Calmly ya furta”Ina lafiya, nayi missing dinka, amma naji dadin ganin ka yau, Ina fata uncle dina bai takura maka ba? Nasan shine Ya matsa maka akan zuwa Nigeria” da zolaya ya fada,
Shekh Imam Yace”kai dai bari, kamar yadda baiyi bacci ba adaren jiya nima haka ya hanani Yin bacci, babu shiri yasa na fara shirye shiryen zuwa Nigeria hada ƙoƙarin turamin jirgin da zai ɗaukoni” Da zolaya yai maganar,
Hateem dake sauraronsu, baice komai ba sai dai murmushin dake akan fuskarsa bai washe ba.
Dubanshi chief yai”uncle, sannu da zuwa, Mu shiga daga ciki, nabarku atsaye”
Atare suka jera zuwa babban falon gidan, saman sofa mai mazaunin mutun uku, prime minister da Sheikh imam suka zauna, Chief Owais Yana daga zaune kan 2 seater, Yayin da Big guy da Boss suke atsaye sun goya hannayensu saman kirjinsu.
Kallonsu chief Yai kafin Ya soma magana”Taj wannan uncle dina ne Prime minister Hateem na ƙasar Canada, Kai kaɗaine bakasan shi ba, wannan kuma Sheikh imam kenan, Aminin kakanmu Obie...”
Cire face mask din fuskarshi Yai, Cikin girmamawa ya soma gaishe da hateem”ina yi maku barka da zuwa, najima ina jin labarin prime minister awurin Owais sai dai ban ta6a ganinsa ba, ashe da rabon zamu haɗu, kuma tunda naga fuskarshi raina ya bani cewar Uncle dinka ne saboda kamanceceniyar dake a tsakaninku”
Ƙayataccen murmushi prime minister yasaki a yayin da yake kallon fuskar taj yace”Nagode da karramawarka agare ni, kuma naji dadin haɗuwa dakai, Ina fata zamu cigaba da yin zumunci a tsakaninmu”
Tajo yace”in sha Allah” har cikin ranshi mutumin ya kwanta mashi, kuma Yayi mamakin haɗuwarshi donshi a hoto yasanshi, kuma yayi mamakin sakar mashi fuska da ya yi a matsayinshi na babban mutun mai ruƙe da babban muƙamin shugaban ƙasar Canada, koda yake yasha ji awurin mutane cewa baida girman kai ko kaɗan, mutunne najama’a kowa nashine mai kudi da talaka awurinshi duk ɗayane.
Chief Owais Ya ɗaura dacewa”Uncle sunan shi Taj, Mahaifin Yarinyar nan, dana ta6a baka labari, ina fata ka gane shi”
Jinjina kai Hateem yai da mamaki akan face dinsa yace”masha Allah, ina ita yarinyar take ne? An gano ta”?
Ɗaga mashi kai yai alamar eh.
“Na tayaka murna my son, Allah ya tabbatar da alkhairinsa, Ina fata Yaya sharafudden Yasan da maganar mahaifinta da kuma ita kanta yarinyar”!?
Chief owais Yace”Ya sani, na faɗa mashi, sai dai basu ta6a haɗuwa da daddynta ba, amma na yanke shawarar zan haɗasu kwanan nan idan muka shawo kan matsalar yaron nan”
Ga dukkan alamu Hateem yaji dadin ganin tajuddeen, duba da yadda yake kallon shi.
Gyaran murya sheikh Imam yai masu”Idan kun gama magana ina jiranku, Kun ajiyeni kamar buhun masara, Yakamata ku bari in kammala aikina inyaso kunyi firar taku” gaba ɗaya suka sanya dariya banda Chief daya ɗan murmusa.
Prime minister yace”ay mana afwa ya sheikh, nayi kewar yarona, Mun jima bamu haɗu ba” Murmushi sheikh imam yasaki, da zolaya yace”wani yaro kake nufi? Wanda yahanaka runtsawa daren jiya? ko kuwa wanda kuke Yin fira da shi a yanzu”?
Prime minister yace”dukansu biyun nake kewa”
Sheikh imam yace”yanzu naji magana, bismillah owais Muje ka nuna min ɗakin da yaron yake” amsa mashi yai da okey
Atare suka miƙe tsaye tare da nufar Up stairs, tunkafin su ƙarasa ɗakin, suka soma jiyo kururuwar macijin Yana gurnani.
Sheikh Imam yace”Da alama Yasan da zuwana” murmushi kowannansu ya saki, abakin ƙofar ɗakin suka tsaya kafin su shiga sheikh imam Ya dubi Chief owais”naji kace akwai yarinya agidan nan ɗiyar mutumin da naji ka kira da taj ko”? Kafin owais ya bashi amsa Boss man ya riga shi cewa”ba ita kaɗai bace, akwai sauran ƴan uwanta dake rayuwa agidan”
Sheikh imam yace”Toh, ina buƙatar a killace su wuri ɗaya, sannan aja hankalinsu ta yadda baza su iya jin abun da ke faruwa cikin gidan ba, Idan ba haka ba zasu iya firgita arasa gane kansu” boss man ya amsa mashi da toh.
Kafin Ya dubi big guy”please kaje wajensu, ka aiwatar da abunda malam yace” da sauri big guy ya nufi hanyar komawa down stairs, Ya rage saura su uku.
“Bismillah mu shiga daga ciki” dafe ƙofar boss Yai, ta zuge a hankali kafin suka shiga dakin.
Jin motsin shigowarsu dakin Yaja hankalin salsabeel dake atsaye kai idonshi ga dubansu.
Hankalinsu na akan narkeken macijin dake zarya tsakiyar gadon wata irin kururuwa yake fitarwa yana huci.
Gaisawa sukayi da salsabeel, daga bisani, Chief Yai mashi alama da hannu, salsabeel Ya fahimci ƙarin bayani yake nema game da halin da Giant snake din yake aciki”
“Ni kaina bansan meke damun shi ba, Yanzu ya farka daga bacci, Yana huci, zai Iya yiwuwa saboda rashin ganin ƴar uwarshi akusa dashi ne”
Hankalin prime minister hateem ba ƙaramin tashi yai ba, sai yanzu yaga girman macijin Ya wuce misali.
Sheikh Imam Yace”Saboda ni yake wannan hucin, ku dan bamu wuri zan fara aikina” babu musu suka fito daga dakin, anan second floor suka tsaya suna jiran tsammani
Bayan fitarsu ya rage saura sheikh imam da Macijin a ɗakin, Toilet Ya shiga jim kaɗan ya fito da alama alwala ya ɗauro, Bakin gadon Ya tsaya tare dakai hannu Ya damƙi bargon dake a nannaɗe kan mattress, manyan Addu’o’i ya soma karantowa Yana tottofe bargon, kafin ya fara yin karatun alƙur’ani, Yayin da idanuwanshi suke akan macijin dake ta ƙoƙarin saukowa daga saman gadon Hanyar guduwa yake nema sai dai ya kasa yin hakan saboda ɗaurewar da Sheikh imam Yayi mashi da karatun kur’anin da yake yi, Bayan Ya kammala yin ƙira’ar, Ya daddage Ya haye kan gadon, Ya kifa mashi bargon saman jikinshi, Ya daddanne shi da ƙafafuwanshi, da hannayenshi yabi ko’ina ya dafe, wata irin kururuwa macijin yake saki tamkar ana ƙona jikinshi da wuta, hatta waɗanda ke a wajen ɗaki saida suka jiyo sautin, Har saida prime minister ya dafe kunnanshi da tafin hannun shi.
Jami’an dake a kewaye da gidan da gudu suka shigo part din hannayensu ruƙe da bindigu, sunyi tunanin wani mugun abunne ke faruwa, daga saman bene Boss Man Yai masu magana akan su koma bakin aikinsu hakan yasa suka juya da sauri suka bar part din.
Sheikh Imam Ya hada uban gumi, zufa ta wanke fuskarshi duk da sanyin A.c na ɗakin, Yaƙi Sakin bargon daya daddanne Macijin, sai ƙoƙari yakeyi donya kubcema ɗaurin da yayi mashi.
Maƙoshin shekh imam tamkar zai 6allo tsabar yadda yake cigaba da karanta mashi ayoyin ƙur’ani tare da addu’o’in karya sihiri, Yaci gaba da tottofe bargon da yake kudundune.
Ba zato ba tsammani, suka soma jiyo wasu irin muryoyi na baƙaƙen shaiɗanun aljanu suna fadin”kashe ka zamuyi sheikh imam! Dole ka mutu tunda ka shiga sabgarmu, zaka mutu”
Da karfin hali sheikh imam yace”Idan kunga na mutu lokacin mutuwatane yayi don ubanku, Ni da Allah na dogara bada ku ba, Raina a hannunsa yake, Ku bakusa ku cutar dani ba, face da izninsa, Kunsan bana jin tsoronku tun fil azal......” bai ƙare maganarba, sautin dariyarsu Ya karaɗe ɗakin, tamkar ana buga ganga, Hankalinsu boss man ya tashi matuƙa, damuwarsu kada wani abu ya samu sheikh imam.
Cigaba da magana sukayi da kakkausar murya suke fadin”mutuwa zakayi sheikh Imam, ajalinka ne Yazo, kai ka sani ba’a shiga huruminmu a zauna lafiya, mun kashe ire irenka da dama waɗanda suka yi ƙoƙarin yi mana shisshigi, Sheikh Imam kadaina janyo mana ayoyin alkurni bazasu ta6a yin tasiri akanmu ba, Mu ba kalar shaiɗanun da ka saba ƙonawa bane”
Runtse ido sheikh imam yayi, jin numfashinshi na ƙoƙarin ɗaukewa tamkar an shaƙe mashi wuyanshi, idanuwanshi suka kaɗa jawur tamkar garwashin wuta, sautin muryarshi daƙyar yake fita ahaka yake kokarin cigaba da yi mashi karatun kur’anin..........”
“Hankalina bai kwantaba, Inajin fargabar wani abu ya sami malamin nan, Mutanan nan fa ba ƙananun shaidanu bane” salsabeel ne yai maganar.
Boss man yace”ni kaina fargaba nake ji, gaskiya akwai matsala, kada mu jefa rayuwarshi cikin hatsari,”
Duk maganganun da sukeyi akan kunnan Chief owais da prime minister Hateem, jikinsu yai sanyi babu mai magana acikin su.
Lokaci ɗaya bugun zuciyar Prime minister ya ƙaru, arude ya furta”ku buɗe kofar nan” ya fada yana nuna ƙofar dakin danish” da sauri Bossman Ya nufi ƙofar ya sanya hannu ya dafe glass din wani iko na Allah ƙofar taƙi buɗewa, gashi sunji shiru babu motsin sheikh imam da kuma kururuwar macijin.
“Babu lafiya, salsaleel zoka taimaka min mu buɗe ƙofar” matsawa salsabeel yayi gaban kofar, suka haɗa ƙarfi shida boss suka dinga bugun ƙofar taƙi buɗewa.
Da ƙarfi suke ambaton sunan sheikh imam shiru bai amsa masu ba, babu alamun motsinshi.
Hankali atashe Chief Owais Ya ɗago da ido suka kalli juna shida prime minister.
“Bana so wani abu ya sami malamin nan, Ni ne silar kiranshi daga sudan, Idan wani abu ya same shi bazanji dadi ba, zanyi danasani Owais, Yakamata kuyi wani abu akai” damuwace ƙarara akan fuskar Hateem.
“In sha Allah Uncle babu abunda zai faru da shi, ka kwantar da hankalin ka” chief na ƙarasa fadar hakan, Ya nufi ƙofar ɗakin, da sauri salsabeel Ya matsa mashi hanya, Boss man Yaja gefe ɗaya, bismilla ya furta da kyakkyawar niya, kafin ya daki ƙofar da kafaɗarshi, nan take ƙofar ta zuge da gudun gaske, ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, salsabeel yayi mamakin ƙarfin owais.
An rasa wazai fara shiga dakin, kowa fargaban ganin abunda zai taras yake yi, hatta shi kanshi chief din....... 😳😳😳
*Something Unexpected*
*WAIWAYE🌹*
*A Obie International Hospital*
Emergency room
Abun da ya faru daren Jiya da Sir mubarak Ya dauki Dr jazz zuwa asibiti, tunkafin su ƙarasa Ya kira Dr fawan awaya ya sanar dashi game da zuwansu, tuni nurses sun fito