Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps

Chapter 83 of 83

kan table, Kafin ta juya tana fuskantar hajiya saratu data ruƙe qugu da hannu ɗaya, har saida taji gabanta ya faɗi ganin 6acin ran dake kwance akan fuskarta, cike da jin shakkarta ta furta”ko akwai wani abu da kike buƙata”? Atsiwace hajiya saratu tace”ke nake buƙatar ki fuce min daga ɗaki, kin wani tsareni da ido kina kallona kamar yau kika fara gani na” Jiki na 6ari Abla ta nufi ƙofar fita daga ɗakin bayan ta fuce hajiya saratu ta nufi gefen gadon ta zauna, ta soma cin breakfast dinta, farawa da bismillah kakkauran tea ta ɗauka ta kur6eshi dukanshi, kafin ta rarumi roasted chicken takai baki tana cizgarta atsiyace, daɗina da hajiya saratu damuwa bata hanata cin abincin, adai dai lokacin da ta ɗauki burger da hannu biyu ta gutsireta da baki, Muryar pravin ta dakatar da ita daka taunar burger din da takeyi, lokaci guda yanayin fuskarta ya canza ta haɗe rai kamar baƙin haɗari.

shigowa ɗakin yayi fuskarshi ɗauke da murmushi, yasan tsiyar daya tsula mata shiyasa yake jin shakkar tunkararta
Daga nesa da ita ya tsaya haɗi da goya hannayenshi on his chest cikin muryar lallashi ya furta”My wife, ina neman afwarki, dan Allah ki yafe min nasan ban kyauta maki ba, duk da ba laifina bane, laifin ki ne saboda kece kikaja nayi maki hakan, kin nuna bani da mahimmanci awurinki...” kau da idonta tayi daga kallon fuskarshi, taci gaba da cin burger dinta ta share shi kamar batasan da zaman shi ba.

“Dan Allah kiyi min magana sanyin idaniyata, kamar yadda na 6ata maki rai nima haka raina ya 6aci, saboda tunanin awani hali kika kwana jiya ko runtsawa banyi ba, nayi kewar rashinki atare dani, da pillow na kwana rungume a kirjina ina jin tamkar kece na rungume”

fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yayi mata maganar, duk don ya samu ta yafe mashi, burinshi ta aminta dashi su sasanta tsakanin su, duk don ya tunzurata akan maganar macijin daya tsoratar da ita jiya, yasan muddin saratu ta ƙyamaci zaman yaron a estate dinsu dole kowa ya amince saboda ƙaunar da yayyanta su ke yi mata.

“Bugun zuciyata, please ki kula ni mana, bana son sharenin da kike yi, wallahi ashirye nake dana kar6i duk wani horo da zaki bani ni kawai so nake mu sasanta tsakaninmu bana so kina fushi dashi” ƙara ɗaure mashi fuska tayi batare data juya ta dube shi ba.
Zuƙunna pravin yayi, tare da kama kunnansa Ya soma yin tsallan kwaɗi Yana nufar gaban table dinta Yana fadin”Am sorry my wife, nagane kuskurena bazan ƙara ba”
Tunkafin Ya ƙaraso gabanta, ta tsiyaya ruwan lemu acikin cup mai sanyi, ta ruƙe a hannunta, Yana zuwa dab da table din ta daddage ta watsa mashi ruwan lemun saman fuskarshi, da sauri ya runtse idanuwanshi jin raɗaɗin da ya shigar mashi, burger ta ɗauka ta yunƙura ta kifa mashi ita a fuskarshi, tunda tayi mashi hakan sai taji sauƙi acikin ranta, komawa tayi ta zauna tana dubanshi tace”Ina fata ka tashi lafiya” shiru pravin bai furta komai ba, ƙoƙarin buɗe idanuwanshi yake yi sai dai ya kasa, shu’umin murmushi hajiya saratu tasakar mashi tare da cewa”malam, ka tashi ka shiga toilet ka wanke fuskarka,” babu musu pravin ya miƙe kamar makaho Yana laluban hanya daƙyar ya gano ƙofar toilet......”


*✊💋ALHAMDULILLAH, END OF MIDDLE STEP, FATA NA SHINE ALLAH YA BANI IKON KAMMALA TAKUN ƘARSHE LAFIYA KAMAR YADDA NA KAMMALA TAKUN FARKO DA TAKUN TSAKITA💋✊*

(Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i layukan mu (08103884440 0r 08169856268)


Download complete TXT · Novel page