Karfe A Wuta

Chapter 110 of 167

ba, amma ta yi wa Habib ta tas.

****

Nabila tana tafe tana kallon hotunan hannunta, ta kira Viper ya ɗaga ta ce "V ina wuni?"

"Lafiya ƙalau, ya ake ciki?"

"Ina hanya zuwa zan yi"

"To, Allah ya kawo ki lafiya"

****
Ramma ta tsurawa Abdul ido, ya ce kunun gyaɗa yake so, yana sha yana waya, ya ajiye kofin kunun ya ce "Daddy ni dai dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya fito maka da rahama ba"

Ashariya Indabo ya din ga zabga masa, ya ce "Wallahi zan saka jami'an tsaro su kama ka, su ci ubanka, uwar yarinyar nan ta bayyana a kotu, an ambaci sunanka, duk da ba a faɗi cikakke waye kai ba, ga maganar kuɗi na yi maka, duk ka yi kunnen uwar shegu da ni, Abdul kana son ka gama da duniya lafiya kuwa? Dole sai ka tozarta ni?"

"Daddy ba tozartaka zan yi ba, makomar rahama nake dubawa ita ma....

Wata ashar ɗin indabo ya lailayo, kamar ba babba ba, ya gama masifar,  Abdul ya ajiye wayar ya dafe kai.

"Kai ma da naci kamar me, ka fitar da ni mana, ko ma me za ayi mini ayi mini, sai ɓoye ni ka ke yi kamar ciwo, ni kaina tun ina masifa har na gaji, haba dan Allah" tsaki ya ja, ya tashi ya bar mata dining ɗin.

***
"Abba ya yi tafiya, yau nake saka ran dawowarsa, zan nuna masa hoton nan, na ji mai zai ce, tun da kai kaƙi gaya mini wacece?"

"Yaya shari'ar ta kasance?"

"Alhamdilillah, babar ramma ta je kotu ta bayar da shaida, ina jin alamar nasara in sha Allah"

"Mhmm, a ina aka ganta?"

"Ta gudu ne wani wuri ta ɓuya, daga baya da taimakon barrister Habib, muka ganota"

Viper ya jinjina kai ya ce "ya nawa, ni ya ake ciki?"

"Shiyasa na zo ai"

"Ok"

"Kamar yadda na fara gaya maka jiya, dole ina buƙatar su oga walid, da wannan bugaggen a kotu su bayar da shaida"

"Wane bugaggen?"

"Oho ni na san sunansa ma? Amm sannan sai ka yi haƙuri, duk wasu rashin ji da ka yi, sai mun yi exposing ɗin su a kotu"

"Rashin ji kamar yaya?"

Ta kalleshi ta ce "Kamar yadda ka yi mana, sara suka, ƙulla wiwi black market duk da ka yi"

Haɗe rai yayi ya ce "Amma ba prison zan koma ba ko?"

"Idan ta kama ai dole ka koma"

Ya ce "What? Gaskiya ki yi yadda zaki yi, ba zan koma prison ba, wanda nayi 5yrs fa?"

Ta zumɓura baki ta ce "Ni na ɗaureka, sai abun da ya kama kawai, bari na je gidan, na ji wadda zamu yi da su, sai anjima"

*****

Nabila ta tafi ɗakin Abba, domin amsa kiran da yayi mata, ta tafi bakinta ɗauke da addu'a, ta shiga ɗakin da sallama, suka amsa ban da Abba da yayi shiru ransa a ɓace.

Ta je ta durƙusa ta ce "Abba gani"

"Nabila ban isa na gaya miki magana ki ji ba ko?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

"Dole sai kin nuna wa duniya cewa ban haife ki ba ko Nabila? Kin nuna mini iyakata, ban isa na nemi alfarmarki ba kenan ko Nabila?
Sai kin tozarta ahalin nan gaba ɗaya ko Nabila?"

Ta girgiza kai ta ce "Abba bani da wannan burin, kuma wallahi ba zan taɓa aikata wani abu da zan janyo maka zagi ba. Amma dan Allah Abba a yanzu, ka yi mini wani taimako, saboda zatin Allah kar abun da zan nema ya ɓata maka rai"

Ta miƙa wa Abba hotunan, da Viper ya bata, ta ce "Dan Allah Abba wacece wannan? Ni dai na san ba ni ba ce ba, dan Allah Abba ko kana da masaniya a kan ta jikin hoton nan.

Abba ya saka hannu, ya karɓi hotunan yana dubawa.

Ya gama ƙarewa hotunan kallo, ya ce "A ina ki ka samu hotunan nan?"


Ayshercool
08081012143

75
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa



https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*


Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*


Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "A office ɗina na gansu"

A take Abba ya fara yayyaga hotunan, cikin kuka ta ce "A'a Abba, dan girman Allah ka gaya mini idan ka san ta jikin hoton, Abba ba ka ga yadda kamaninmu suka ɓaci ba, dan Allah Abba ko sau ɗaya ka nuna mini wani a dangin mahaifina dan Allah Abba" ƙarasa yayyaga hotunan yayi, ya watsa mata cikin matsanancin ɓacin rai ya ce "Ki koma in da aka baki hotunan, su gaya miki koma wacece, ubanki kuma ga hanya nan, ki bar mini gida ki tafi yawon nemansa, yayi miki abun da ban yi miki ba, tashi ki bar gabana kan na tattaka ki, da uban naki ya damu da ke, da zuwa yanzu shi ya nemi in da ki ke".

Anty ta ce "Haba major, dan Allah ka yi haƙuri kar ka yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kan ta, kayi haƙuri dan Allah " gaba ɗaya jikin Nasir yayi sanyi, ganin yadda take ta uban kuka.

Cikin tsawa Abba ya ce "Ki tashi daga gabana, ki tafi ki bar mini gida, ki je ki nemi ubanki, amma ki bar mini gida kar na sake ganinki a gidana"

Wata irin ajiyar zuciya ta din ga yi, ta yinƙura ta tashi da kyar, ta bar ɗakin, ta koma ɗakinta ta kifa a kan gadonta, ta fara sabon kuka, shi kuwa Abba wace irin zuciya ce da shi haka? Ko menene a tsakanin sa da mahaifinta, yakamata ace ya wuce, ta san ya gama yi mata komai a rayuwa, yayi playing role ɗin uwa, yayi na uba a rayuwarta, amma duk da haka gurbin ido ba ido bane ba.

Baba magajiya ce tayi sallama, ta ƙarasa kan gadon, ta dafa kafaɗarta ta ce "Haba Arfa, ke a rayuwarki ba zaki iya haƙuri da tawakalli ba, tun da ya nuna miki baya son zancen nan ba sai ki haƙura ba, shekara nawa ana abu ɗaya kin ƙi ki gane ki haƙura".

Nabila ta tashi zaune, idanunta sun yi jawur ta ce "Baba magajiya"

"Na'am arfa"

"Kema laifina ki ke gani?"

Baba magajiya ta yi shiru tana kallonta.

"Ki bani amsa mana, laifi nayi dan na nemi sanin in da mahaifina yake na ganshi ko sau ɗaya? Baba magajiya mahaifi fa, a duniya na san Abba ko baki yayi mini, sai ya kamani, bana nufin yi masa butulci ko tozarta shi, amma ina son sanin babana, baba magajiya dan Allah ina da wata yar uwa ne? Ke kin san komai, hoto aka bani da wata a jiki irina ɗaya da ita sak, ko yar uwata ce, dan Allah ki gaya mini. Ni idan kin san in da zan ga babana ki gaya mini, ko sau ɗaya na je na ganshi na dawo dan Allah"

Baba magajiya ta girgiza kai ta ce "Ni ban san komai ba, lokacin da na zo gidan nan, an gama dambarwar da za ayi, na zo, ni bani da wani labari a kan mahaifinki"

Nabila tayi murmushi mai ciwo, hawaye na bin fuskarta ta ce "Haryanzu kallon yarinyar da ki ka raina ki ke yi mini ko, shiyasa ki ke tunanin bani da wayo ko? Shekaru ashirin da biyar a doron duniya, ai na girmi ki yi mini wayo baba magajiya, amma shikenan, ai Abban ya ce na je ne nemi babana, zan neme shi kuwa in sha Allah "

Baba magajiya ta waro ido ta ce "Baki san gatse ba Arfa?"

Nabila ta jinjina mata kai alamar eh, ta mayar da kai ta kwanta.

Baba magajiya ta ce "Arfa na san har da damuwar matsi da takura da ake yi miki a gidan nan, ya sanya ki ke damuwa da son ganin mahaifinki, ni dai roƙona da ke, ki yi haƙuri idan da rabo zaki haɗu da mahaifinki ko danginsa, amma dan Allah dan Annabi, kar ki bari ku samu saɓani da  maitama"

Nabila ta yi mata shiru, dan gani take yi babu wanda zai fuskanci halin da take ciki.

Tamkar zuciyarta Abba ya yaga, haka take jin zuciyarta, idan ta tuna yadda ya yayyaga hotunan nan, sai dai har a lokacin tana ganin hotunan yarinyar mai kama da ita a cikin idanunta.

****
Duk da Nabila bata jin daɗin komai na duniyar, jin ta kawai take yi gata nan dai, haka ta cigaba da up and down a kan muhimman abubuwan da ta saka a gaba.

Ta sake shigar da koke gaban hukumar'yan sanda, ta nemi su kama madaki da wasu daga cikin yaransa, bisa zargin kisan matar Viper, shekaru shida da suka gabata.

Yau tana da program a gidan radio, kuma yanayinta ya nuna wa Sumayya tana cikin matsananciyar damuwa, sai dai ta shigo a ƙurarren lokaci, zasu fara gabatar da shirin, dan haka ba ta samu damar yi mata tambayar meyake damunta ba.

Nabila tayi iya ƙoƙarin ta, wurin ajiye damuwa a gefe, suka fara gabatar da program.

Sumayya ta kalli takardar hannunta sannan ta ce "Jita-jita ta cika gari, cewa kin shigar da koke gaban kotu, a kan lallai kotu ta hana hukumar'yan sanda kamar shahararren ɗan ta'addan, da addabi wani yanki na garin nan, kuma akw zargi da kisan matarsa, duk da yadda hukumar ta 'yan sanda, take nemansa ruwa a jallo?"

Nabila ta kalli sumayya da rinannun idanunta, tayi mamakin yadda sumayya tayi mata wannan tambayar, a tsakiyar program ɗin su haka, saboda ba magana ce da ta fita ba, balle ta ce an yi Jita-jita a kai. Sumayya ma ta tsare ta da ido, alamar tana jiran amsa.

Tayi wani irin murmushi ta ce "Ba ɗan ta'adda bane ba, mutum ne kamar kowa, kuma ɗan ƙasa da ya dace ya samu duk wani 'yanci da kowane ɗan ƙasa ya dace ya samu. 'yan ta'adda na yawonsu a gari, an san in da suke, an san in da za a same su, hakkinsa muke nema a kotu, ba shi ya kashe matarsa ba. Na san mutane za su yi mamakin yaya aka yi mai dokar bacci ya ɓuge da gyangyaɗi, amma a bibiye ni a cikin shari'ar da zamu gudanar".

"Amma ba kya ganin hakan kamar taka doka ne, zaki yi amfani da damarki ta lauya ki taka doka, ki kare mai laifi?"

"Sam, dokar da aka wulaƙanta, da ita nake son yin amfani wurin gyara kuskuren da aka yi. Tayaya mutum zai shafe shekaru babu Shari'a, daga baya alƙali da saka hannunsa da umarninsa da komai, a sake shi bisa doron doka da ƙa'ida, kuma daga baya a zo ana nemansa. Shin wanke shi aka yi daga laifin? Ko kuma akwai wani ɗaurin ɓoye da yakamata a warware? " Tayi maganar tana ƙure sumayya da ido.

Sumayya ta kalli agogo, lokaci ya cika, ta na tsaka da sallama da masu saurare, Nabila ta tashi ta fice, tana kammalawa, ta tashi ta bi Nabila, amma tuni ta ja motarta ta bar wurin.

Ta koma tana sauke numfashi, kiran kankarofi ta gani, ta ɗaga wayar suka gaisa, ya ce "T ladan, meyasa ki ka yi wa Nabila wannan tambayar a tsakiyar program?"

"Sir nayi ne, dan tun yanzu ta kare kanta a wurin mutane, kafin abu ya bayyana su yi mata kallon, maciya amana mai fuska biyu "

"Sumayya waye ya gaya miki ana iya wa ɗan adam ne? Ba a taɓa iya wa mutum, dan haka ki kiyaye gaba, yayi wuri ki fallasa abun haka gaba ɗaya, amma babu laifi, baki yi kaifi ba, hakan zai ƙara mata ƙaimi"

Sumayya ta ce "Ok sir, na gode" ta ajiye wayar ta yi shiru, ita a zahiri tayi hakan ne, ko Allah zai sanya Nabila ta ji nauyin dubban al'ummar da suke goyon bayanta, ta sassauta koma ta haƙura da batun Vipern nan, amma ba ta ga alamar hakan a tattare da ita ba.

Abbu kuwa a zabure ya miƙe tsaye, jin program ɗin da yayi, shi ba wani ma'abocin jin radio bane ba, yau kawai ya kunna yana saurare, ya ji shirin ya ƙayatar da shi, haka zalika muryar barrister, kamar sananniya ce a gare shi.
Sai dai jin sun yi maganar Viper, ya sanya ya tashi a kiɗime, tare da ɗaukar radion ya fito tsakar gida.

Rahila ta ce "Ya dai na ganka a firgice haka?"

"Wani shiri na gama saurara, wata lauya ta shigar da koken kotu ta hana kama Aminu, ko gidan radiyon zan je, wataƙila su sun san in da yake"

Ta kwaɓe baki ta ce "Ina rabaka da sabgar yaron nan, idan sun san in da yake me zaka yi masa? Salon ka sanya kanka a masifa, wanda ake nema ruwa a jallo da laifin kisan kai? Ka ganshi ka yi masa me? Guduwa fa yayi daga gidan yari"

Ya ƙura mata ido, kawai ya girgiza kai, ya kashe radion ya fice.

****

Nabila tana driving, wani abu ya tsaye mata a maƙogwaronta, kukan ma gaba ɗaya ta kasa saboda baƙin ciki da ɓacin rai.

Katafaren gate ɗin aka buɗe mata, ta shiga da motarta, tayi parking, ta sauka ta nufi cikin gidan.

A falo ta tarar da mahaifiyar ramma, tana ganin Nabila, ta tashi da fara'arta, tana yi mata sannu da zuwa.

Nabila ta zauna cikin yaƙe, suka gaisa, kamar kullum yau ma mahaifiyar ramma, kallon Nabila take yi, kamar ta haɗiyeta, ita dai ban da an yi mata gargaɗi, da tuni ta faɗi abun da yake ranta, dan ta tantance abun da take tunani, sai dai an gargaɗeta a kan aikata hakan, dan haka ta ja bakinta ta tsuke.

"Mama ina fatan dai babu wata matsala ko? Ki cigaba da haƙuri, in sha Allah an kusa dawo miki da ramma, kuma hujjoji nake son kammala tattarawa, na gano ainihin mai laifin, za a gabatar da shi a gaban kotu, idan da wani abu ki gaya mini"

Ta girgiza kai ta ce "Ba wani abu, ina ta godiya Ubangiji Allah ya baki nasara, na gode sosai da sosai da ke da Alhajin da ya taimake ni, ina godiya Allah ya biya ku, ya ƙara miki zaman lafiya da mijinki"

Nabila ta ce "Ai ba mijina bane mama"

"A'a ba Alhajin ba, Aminu"

Cikin mamaki Nabila ta ce "Aminu kuma? Nifa ban taɓa aure ba, ba ni da aure" tayi maganar tana murmushi.

Babar ramma ta ɓoye mamakinta, kar kwaɓarta tayi ruwa ta ce "Au, ai na zata kina da aure ne, Allah ya kawo miki nagari, ya baki mai sonki da gaskiya, Allah ya tsaya miki, kamar yadda ki ke ta ƙoƙari a kanmu"

Nabila ta ce "Amin mama, dan Allah a cigaba da yi mana addu'a, addu'aeku, ita ce ke tasiri a rayuwarmu"

Maman ramma ta ce "In sha Allah, addu'a yanzu aka fara"

Nabila ta ce "Na gode sosai" ta tashi ta nufi hanyar fita, babar ramma ta bi ta da ido, dan ranar farko da ta fara ganin Nabila, ban da an gaya mata kafin ta zo, an yi mata bayani, da babu abun da zai hanata kurma ihu, ta ce taga gawa.

Tana driving sannu a hankali, ta tsaya ta sai abun da zata ci a gida, dan ba sabgar su take shiga ba.

A harabar gidan, ta wuce Nasir, ya zuba mata ido, duk ta bi ta rame, saboda ta saka jaraba a ranta, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce. Duk sai ya damu da ramar da ya ga tayi, amma yana nan a kan bakansa sai ya kama Viper, ko zata mutu dan haushi.

"Ga agolancin ga yawon ta zubar, ga ta'addanci, gashi an gandame an riƙa a gida babu aure, abun bai yi miki yawa ba kuwa Nabila" Sauda tayi maganar tana dariya.

Ta sake cewa "
An baki damar ki gusa ki bamu wuri, saboda baƙin naci, kin liƙe mana a gida, tun da ba zaki tafi ba, ki iya kanki, muna son ubanmu, ba zaki kashe mana da baƙin cikin ki a banza ba"

Nabila ta tsaya cak, tare da murnar Sauda ta takale ta, ko banza ta rage zafi idan ta yaɓa mata magana.

"Ke da ki ke son uban naki, sai gashi kin gagara zaman aure, kin ƙi karatu balle hankalinsa ya kwanta. Ai sauda zaki yi mini gorin aure ne, a lokacin da ke ki ka iya zama a gidan naki mijin. Kuma karki manta da ni agola ce mai 'yanci, a dalilina igiya biyu aka sauke wa babarki ta aure, idan ku ka cigaba da matsa mini, ragowar ɗayan ma sai na tsinketa, sai ku ji daɗin zawarci tare ga uwa ga 'ya. Yawon ta zubar kuma, ina da abun bayar wa yayi mini rana, kema idan ki na so ki bayar nonsense"

Sauda ta tashi a ƙufule, Nabila ta ce "Kin san dai ba dakuwa zan yi ba, dama koma wa ki ka yi ki ka zauna"

Sauran wanda suke wurin, suka tuntsure da dariya, dan yadda Sauda ke zuba mulki da rashin mutunci a gidan nan, Nabila ce kawai maganinta.

****
Cikin mamaki Abdul ya ɗago ya kalli indabo, saboda marin da ya kwaɗa masa.

"Ina na kai mini kuɗi Abdul?"

Abdul ya yi shiru yaƙi magana.

"Ka gaya mini in da ka kai mini kuɗi, kafin na tattaka ka a wurin nan? Yarinya da ka fito da ita, da kar ka fito da ita, matsalarka ce, ba zaka kashe ni da ɓacin rai ba, sai na samo wani wanda ba zai watsa mini ƙasa a ido ba, ina ka kai mini kuɗi?"

Mahaifiyar Abdul ta ce "Abdul wai ba magana ake yi maka ba? Ina kuɗin da ya zuba a account ɗin ka, da sunan campaign kuma ya muka yi da kai a kan yarinyar nan?"

Abdul ya numfasa ya ce "Na yi wa 'yan garin su rahama gyaran makarantu da hanyoyi, na yi musu boreholes, sai kuma registration da nayi mata na karatu bar zuwa jami'a"

Download complete TXT · Novel page