Karfe A Wuta

Chapter 124 of 167

Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra

Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa

Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka

*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻

07069711327  Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍

Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327  sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊






Major yayi wata irin nannauyar ajiyar zuciya, ba tare da ya ce komai ba.

Nasir ya ce "Abba"

"Nasir, ko ma ta ina ne ka bi, fatana kawai na cimmusu, shi kansa yaron na ji dalilin sa na shiga sha'anin iyalina ba tare da izinina ba".

Nasir ya ce "Ina ga hakan baya rasa nasaba, da ta jikin hoton da na kawo maka" Abba yayi shiru bai sake cewa komai ba.

Viper kuwa muryar Abbu ce ta cigaba da amsa kuwwa a cikin kunnuwansa, ya din ga jin muryarsa har cikin ƙirjinsa. Gefensa Nabila ta na ta kuka, ba yadda ya iya, ya ji zuciyarsa babu daɗi sam.

Ya matsa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ki daina yi mini wannan kukan, na gaya miki ba na so ko?" Shiru tayi masa ta cigaba.

"Babu buƙatar mu je in da zamu je, kina kuka a haka, idan kuma mu koma ne shikenan"

Cikin kukan ta ce "Ni ku tsaya ku sauke ni, koma ina ne ba zan je ba"

Ya ce "Saboda me?"

"Yanzu ku ka gama ci mini mutunci da kai da abokanka, bani da kamun kai, ina yawo a cikin maza, kai kuma dan na haɗaka da mahaifinka, ya zama tashin hankali, har ka manta har da fushin iyaye ya jefa ka a musibar da ka ke ciki, daga ƙoƙarin sasanta ku, wataƙila komai ya zo mana ma da sauƙi a dalilin hakan, amma kalli yadda ku ke cin fuskata, wallahi ƙaddara ce ta kawo ni in da ku ke, har gaban iyayena na bari nayi karatu, ban lalace ba, kuma ban saki jiki da maza ba, duk aikin ƙaddara ne, da ƙoƙarin ceto rai, amma bakomai na gode"

Sai kuma jikin liti yayi sanyi, Walid kansa bai ji daɗin abin da suka yi wa Nabilan ba.

Walid ya ce "Yi haƙuri Nabila, dan Allah ki ke yi ba dan halin su ba, kuma Allahn yana gani, shi ne zai biya ki, idan ki ka gama shari'ar nan, duk ki watsar da su ki yi ta kanki, kar wanda ki ka sake nema. Wallahi ni ina gani, kuma ina yabawa abin da ki ka yi"

Liti ya ce "Walid ba a haka, wannan ai ziga ce, ke yi haƙuri haushi ki ka bani ne"

Zazzage jakarta ta fara yi, saboda numfashinta baya sauka cikin ƙirjinta sosai, saboda kukan da ta yi.

Viper ya taimaka mata, ya ɗaukko mata inhaler ya saka a bakinta, sau biyu ya fesa mata, ta saka hannu ta karɓa ta mayar ta saka a cikin jakarta, tana share hawaye.

Message ya rubuta mata a wayarsa, ya tura ta ta, ya miƙa mata ta karanta, ɗagowa ta yi ta kalle shi, suka haɗa ido, ta galla masa harara ta gyara zamanta, tana kallon taga.

***
Asibiti kuwa sai da aka je da 'yan sanda, sannan suka karɓi rahila, shi kuma Abba aka je aka kamo shi.
Tuni labari ya karaɗe gari, yaro ya yi wa uwassa duka, a kan tayi masa faɗan daina ta'amalli da kayan maye.

Hannunta na hagu ta samu karaya, har guda biyu, ga gefen wuyanta da ya kumbura yayi suntum saboda duka.

Abbu ya ce "Daga hannun yan sanda sai dai su san yadda za su yi da shi, dan ba zai sake zamar masa a gida ba, ya koma hannun ubansa.

Abun takaici sai dangin rahila suka fara ƙananan maganganu wai da ɗansa ne, ba zai ce zai kore shi ba, tun da abin ƙaddara ne, bai wuce kan ɗan kowa ba.

Abbu ya ce "Ai ba ɗan nawa bane, nawa ɗan ma da ya ƙi ji bai ƙi gani ba, dan haka ba zai yi mini kisan kai a gida ba, tun da ya iya dukan uwarsa wataran ai ni zai daka"

"Yo Allah na tuba kisan kan, ai kai ba ka yi wa wani gorinsa ba, tun da dai kai ma naka ɗan yayi, kuma in sha Allah, Allah ba zai nuna mana wani yayi kisan kai a zuriyar mu ba"

Abbu ya ji zafin maganar da ƙanwar uwar rahila ta gaya masa, amma ya haɗiye yayi shiru, bai ce uffan ba ya fice ya bar su.

***
Ramma abin duniya ya isheta, wata irin kewar Abdul take yi kamar babu gobe, Abdul ɗan gayu ne kuma ɗan hutu, tun da ta ji an ce an kama shi, sai ta ji gabanta na tsananta faɗuwa, da zata yi masa adalci roƙonta da ya din ga yi, ta yafe masa yakamata ta yafe masa, da fari ta zata idan aka kama shi, aka hukunta shi zata huce, amma sai ta ji ba haka ba, tausayin sa ma take ji.
Gashi mahaifiyarta, ta saka ta a gaba, ko saurararta ma ba ta yi yanzu, ta kuma dage a kan lallai idan tana son su zauna lafiya, to sai an zubar da cikin nan, da ba zata taɓa yarda ta haɗa zuriya da marasa mutuncin mutane irin su Abdul ba. Gaba ɗaya dauɗa ce take bin zuriyarsa babu na Allah cikin su, mussaman zaluncin da aka yi wa ɗan ta Nura, wanda hakan yake ƙara tunzurata ta ji tamkar ta yi wa ramma shegen duk ko zata huce.

***

A nesa kaɗan da ƙofar gidan suka yi parking, Viper ya ce "Bari na je tukuna na dawo, ku jira ni ina zuwa"

Walid ya ce "To shikenan, babu matsala"

"'yar sugar am talking fa" yayi maganar yana kallon ta.

Haɗe rai ta yi ta share shi, tana ta tura baki, tana son tayi masa tsiwa, amma ta kasa sai harararsa da take ta gefen ido.

A zuciyarsa ya ce "Allah ya bamu ikon cin wannan jarrabawa" ya sauka daga motar, ya nufi gate ɗin gidan, yana yaba cigaban da suka samu, dan wannan gidan na su ya fi na cikin gari kyau da suka baro, nesa ba kusa ba.

Ya tsaya a bakin gate ya fara bubbugawa.

Wani yaro ne ya buɗe, yana cewa waye, Viper ya ce "Ka je ka ce ana sallama" yaron ya ce "To" ya koma cikin gidan, mintuna kaɗan Tijjani ya fito, kawai suka yi arba da Viper, ya kalle shi, shi ma ya kalle shi.

"Me ka zo yi mana gida kuma?"

"Wurin Baba na zo"

"Zai fi kyau ka kira shi da sunansa kawai, ba sai ka yi masa kara ba, bayan ka kashe masa 'ya"

Kai tsaye maganar ta soki, tsokar da ke tsakanin ƙirjin Viper wato zuciya, amma ya dake ya ce "Ina son ganin Baba, ka yi mini iso wurinsa"

"Ba zan yi ba, baka da abin da zaka gaya masa....

"Shhh Viper ya faɗa, a lokacin da ya ɗaga wa Tijjani, rigarsa.

Ya hangi ƙyallin iraƙi a ƙugun Viper "Haryanzu ina nan a yadda ka sanni, in saka maka ƙarfe, in tsallake ka, na shige gidan nan, ba zai zama sabon abu ba, a abin da na saba aikatawa ba, ka shiga ka yi mini iso da mai gidan" gummm tijjani ya rufe bakinsa.

Baba kuwa ya san da zai yi baƙo, sai dai bai san wanene ba, dan an kira an tambaye shi ne kawai yaushe za a same shi a gida, ya bayar da wannan lokacin.

Yana zaune a falonsa, yana karanta jarida, Tijjani ya shigo yana zazzare ido.

Mama ta ce "Lafiya kai da waye a wajen ne?"

Wata irin zazzafar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce "Mijin jauhar ne a waje, wai yake son ganin Baba" gaba suka yi sak suna bin sa da kallo, a gigice Abba ya tashi ya ce "Wace jauhar ɗin? Waliyiyya dai? Kana nufin Al'amin?" Ya jero masa dukkanin tambayoyin lokaci guda.

Zakiyya ta ce "Ya zo yayi mana me, ko kuma ya ce me? Shi har yana da kunyar sake tunkaro mana gida, alhalin ya kashe mana 'ya? Kenan da gasken dai sakinsa aka yi, yake yawonsa a gari yadda yake so?"

Hanyar fita Baba ya tunkara, Tijjani ya riƙe shi, ya ce "Dan girman Allah baba kar ka fita, yanzun ma da makami a jikinsa, kar yayi maka illa, ba fa mun san meya kawo shi ba.

Can waje kuwa, Saifu ne ya dawo, ya ajiye motarsa ya fito ya nufo shiga gida, kawai ya ga Al'amin a tsaye.

Kamar mai mafarki, haka ya ƙarasa gaban gidan, yana kallon Al'amin.

Ya ce "Kamar mai zamani mijin jauhar?" Viper ya kalle shi, bai ce komai ba.

"Me ka zo yi mana gida, saboda rashin kunya da rashin ta ido, sai yanzu bayan shekaru shida, ka zo ka kalli fuskokinmu, kaga wani hali ka sanya mu a ciki, bayan sakayyar da ka yi mana, aka ɗauki 'ya mafi haƙuri da tarbiyya a gidanmu a ka baka, duk tausayinta da soyayyarta gare ka bai hana kashe ta ba, ka zo ka yi mana gadarar iyayen gidanka sun sanya an sake ka ne kamar yadda ka saba?" Yayi maganar idanunsa na cika da hawaye.

"Har duniya ta naɗe, ka bar mana mummunan tabo a zukatanmu, tabon da ba zamu taɓa yafe maka ba, babu yadda ban yi da ita a kashe auren nan ba, amma taƙi ta dage, ita na rabu da ita tana son aurenta, ta san zaka shiryi, zaka daina duk abin da ka ke yi, amma kalli irin ƙarshen da tayi duk a dalilin rashin imaninka, wallahi ba zamu yafe ba" Viper ya ƙurasa masa ido, ya rasa abin da zai ce masa, duk da a baya ba wani shiri suke yi ba, amma yana ɗagawa saifu ƙafa, saboda yadda jauhar take yin sa, take yawan zancensa da shi da hafsa, mussaman ma shi. Tabbas ya cancanci ya shanye duk wani abu da za a gaya masa yau, komai ya samu shamuwa watan bakwai ne ya janyo mata.

Cike da ƙosawa Nabila ta ce "Ni fa gaskiya na gaji, wai me yake faruwa ne?"
Walid ya ce "Ki ɗan ƙara haƙuri kaɗan, za ki ga koma menene"

Babu yadda Tijjani bai yi ba, amma fafur baba yaƙi tsayawa, yayi waje a sukwane.

Viper yana ido huɗu da mahaifin jauhar, kawai sai ya karaya, gabansa yayi mummunan faɗuwa, bugun zuciyarsa ya ƙaru, jikinsa yayi sanyi ƙalau, ji yake yi kamar ƙafafuwansa na neman gazawa da ɗaukarsa, bai san ma da wane idon zai kalli baba ba, bai san me zai ce masa ba, rabonsa da shi tun kan mutuwar jauhar, da ya kawo musu ziyara da daddare, har Viper ya kusa abun kunya, bai san baba yana gidan ba, ya shigo yana mitar "To uwar son kuɗi, yau ba oyoyon babu ɗan karairayar, Allah ya sa ba neman kuɗin ki ka ƙule a ɗaki ki na yi ba" tana gaban baba, amma kamar ta nutse, sai da ya shiga falon ya ga baba, kamar ya juya ya koma saboda nauyinsa da ya ji.

Baba yayi murmushi ya ce "Ka sanya a ranka ban ji komai ba, ni babu abin da na ji"

Da kyar ya iya shiga suka gaisa, sun jima suna hira, har baban ya ba wa jauhar ruwan tofi da ya karɓo mata, wai saboda haihuwa. Ya na ta murna da ɗokin, zai ɗauki jika ta wurin jauhar.

Da Baba zai tafi, Viper ya raka shi, ya cigaba da yi masa nasihar ya nutsu, ya zama mutumin kirki, saboda yana daf da zama uba, yayi ƙoƙarin zama uba nagari ga abin da za a haifa masa.

Viper yayi masa alƙawarin hakan, tare da tabattar masa, duk wani abu da zai gusar masa da hankali, ko yayi ɓarna, yana ta iya ƙoƙarin sa a kan dainawa, kuma cikin ikon Allah ya rage kaso mafi yawa. Baba ya nuna masa jin daɗin sa a kan haka, tare da yi masa addu'a.
Ba ayi sati da zuwa gidan ba, tsautsayin nan ya faru, kuma ko a kotu, bai ga Baba ya je ba.

Viper cikin mamaki, ya ga Baba ya rungume shi, ya ce "Sannu Al'amin, sannu da zuwa" ya riƙo hannunsa, ya buɗe gate ɗin gidan, yana jan hannun Al'amin.

Saroro tijjani da saifu suka bi baba da kallo, duk tsawon lokacin da ya shafe, yana gaya musu bai yadda Al'amin zai kashe jauhar ba, ba su yadda da gaske yake ba, dan ya ce musu babu wata gamshashshiyar hujja a kan hakan.

Suka ankarar da shi cewa, yana ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, dan haka ba abin mamakin bane ba, amma ya ce shi dai har zuciyarsa bai amince da hakan ba.

Har tsakiyar falonsa ya shiga da shi, cikin murna da farincikin ganin sa, ya ce "Zakiyya, ku kawo masa ruwa, sannu Aminullahi amintaccen Allah, dama zan sake ganin ka bayan na rasa Waliyiyya? Sannu Aminu" kawai Viper ya durƙusa a kan gwiwoyinsa, ya riƙe hannayen Baba, ya ɗaga ido ya kalle shi, ya ce "Wallahi baba ban kashe jauhar ba, ban kashe waliyiyya ba, me tayi mini me zai sanya na kasheta? Idan da wanda zai tafka asarar mutuwarta to ni ne, ni ne nan baba, zan yadda idan aka ce nine sila, amma da hannuna ban kasheta ba baba, ba ni na kashe maka jauhar ba, na san duniya ba kowa zai yadda da hakan ba, amma na san ko yaya, kai zaka yarda da ni Baba, wallahi ban kasheta ba, nayi burin kashe kaina nima, ko dan kaucewa sake haɗuwa da kai, ban san me zan ce maka ba, ban san da wasu kalmomi zan yi amfani ba, kawai dai ban kasheta ba"

Cikin rauni, da dattaku, Baba ya rungume Viper a kan kafaɗarsa, yana dukan bayansa cikin sigar rarrashi, ya ce "Ko kowa bai yadda ba, wallahi ni shaida ne Aminu, ni na san me na gani, na san me na ji daga bakinta a kanka, kar ka damu, na san me ka ke ji, na taɓa tsintar kaina a yanayi mai kama da naka, ina fatan Allah ya yi wa jauhar rahama, Allah ya sa halinta na gari ya bi ta"

"Nayi asarar mace Baba, ta bar ni da raunin da ba zai taɓa gogewa a zuciyata ba, ba zan fasa zargin kaina da ni ne silar mutuwar jauhar ba, taurin kai da jinkirta barin aikata laifi, shi ya janyo mini haka, ina kewar matata" tamkar ƙaramin yaro, haka ya kwantar da kansa a kafaɗar Baba yana kuka, kukan da ya daɗe yana fatan Abbunsa ne ya fuskance shi ya bashi wannan damar.

Baba ma kukan yake yi, ya ce "Haka Allah ya tsara, ka yi haƙuri, mu duka na haka ne, zaman jiranta muke yi. Bayan an kama ka, mijin yayarta hafsa da ya so ya aureta, shi ya zo ya same ni, ya ce mini in ci gaba da addu'a, Allah ya bayyana gaskiya, amma ba kai ka kashe jauhar ba, abin ne akwai sarƙaƙiya, duk da ni dama tun farko ban yadda zaka kashe mini 'ya ba. To kuma daga baya ita ma hafsan zaman yaƙi daɗi, suka rabu".

Viper ya ɗago ya kalli Baba cikin mamaki, ya ce "Shi ne ya zo ya ce maka bani na kashe jauhar ba?"

Baba ya jinjina masa kai, ya ce "Eh, shi ya gaya mini haka"

Viper ya sauke numfashi ya share gumin da ya haɗa da hawaye, da handkerchief ɗin sa.

Gaba ɗaya cirko-cirko mutanen gidan suka yi, suna mamakin baba, yadda ya sake da Al'amin, wataƙila ma ƙarya kawai yake ta zuba masa, dan kawai a tausaya masa.

Viper ya ce "Na zo da wata tambaya da nake buƙatar amsarta baba"

Baba ya ce "wace tambayar ce?"

"Baba jauhar mutum nawa ce?"

Cikin mamaki baba ya ce "Kamar yaya?"

"Tana da wata 'yar uwa ne, da suke ciki ɗaya?"

"A'a itakaɗai ce"

Ya jinjina kai ya ce "Akwai lauyata, da muka zo tare, zaku tattauna da ita, wadda ita ce tambayata da nake son ka amsa mini" ya tashi tsaye, ya nufi hanyar fita.

***

"Kankarofi, zuwa yanzu ina fatan hankalinka ya kwanta baka da wata damuwa ko?"

Ya kalli indabo ya ce "Ba ni da ita Indabo, kawo ƙarshenka, babbar nasara ce, da rage mugun iri a ƙasa ko ma na ce duniya baki ɗaya"

"A'a, bari murna karenka ya kama zaki, da saura tukuna baka kawo ƙarshena ba, kuma kawo ƙarshena tamkar kashe maciji ne, baka sare kansa ba"

Kankarofi ya ce "Ko ban sare kansa ba, ya tashi, na rage masa karsashi da ƙarfin mugunta da zalunci. Kuma in sha Allah wannan kujerar da ka cimmata, ta hanyar zubar da jinin mutane bisa zalunci, da amfani da rayuwar talaka ka cimmata, ka wofantar da su ka tagayyara rayuwar su, sai ka barota, sai ka kuma fuskanci hukunci.
Yanzu haka ana shirin tsayar da kadarorinka, a kai gaban shari'a bisa laifin sata wato cin amanar ƙasa, bayan babban tattalin arzikinka da aka kama, na miyagun ƙwayoyi a Italiya. Ka san Waye yayi maka aikin kama ɗanka da kama maka dukiya? Viper! Abin ya baka mamaki ko? Wani banbarakwai, da yake ce maka ya saka an kama ɗan sa ka daɗe kana mamaki, da ganin ƙarya yake yi. Dodo babban sarki ya fi ka lissafi, da shu'umanci indabo, sirrinka da ya sani, ya san zaka kashe shi, ba za ku bar shi da rai ba, da shi da tawagarsa, shiyasa ya ƙara jan Viper, ya

Download complete TXT · Novel page