Karfe A Wuta

Chapter 128 of 167

ci gaba da daddanawa, bai fargaba kawai ya ga ta tashi tsaye, ta fizge ƙarin ruwan, jini yana zubowa daga hannunta.

Da azama ya tashi, ganin idanunta a rufe ko gani ba ta yi, ta nufi hanyar fita daga ɗakin.

Shan gabanta ya yi ya ce "Ina zaki je?" Da kyar ta buɗe rinannun idanunta ta kalle shi, ta je uban tsaki, ta raɓa shi za ta wuce, amma ya riƙe ta, ya danne hannunta da yake zubar da jini.

Ya ce "Abla, menene? Meyake damunki?" Ta tsaya ƙyam sai rangaji take yi kamar wadda ta sha ta bugu, tana lumshe idanunta ta na buɗe su.

"Abla" ya sake kiranta a hankali.

Kamar wadda ta farka daga bacci ta kalle shi, ta ce "Mafarki ne ko, ai ba gaske ba ne ko?" Kan ya kai ga ba ta amsa, ta kalli kayan jikinsa, ta kalli na ta, ta shafa fuskarta, ai sai ta saka kuka, ta fara kiran Abba da ƙarfi, tana ƙoƙarin ture Viper tayi waje.

"Shikenan, ya isa ki nutusu, bari ayi masa magana ya shigo ki ganshi, amma mu je ki zauna tukuna" kamar mahaukaciya sabon kamu, haka Nabila ta din ga misbehaving.

Viper ya yi waya, ya ce a ba su damar su shigo su ganta.

Sai ga su duk sun shigo, ga hafsa saifu da Tijjani, major da Bashir na rige-rigen shigowa, sai kuma su liti da walid da Nasir.

Bin su ta din ga yi da kallo, Hafsa ta ƙarasa gaban gadon Nabila ta ce "Waliyiyya, sannu kin tashi? Ina ɗan jaririnki yake? Shikenan yau sai ki koma gidan Master, ku ci gaba da shan soyayya" ƙuri Nabila ta yi mata da ido, dan ba ta santa ba sai a ɗazu ta taɓa ganinta.

Major ya ce "Arfa, ya jikin naki?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

"Arfa Abba ne fa, ba ki gane ni ba ne?"

Bashir ya zagaya ta gefenta, yana ƙare mata kallo, cikin matsananciyar soyayya da ƙauna.

"Yarinyata, ki kalle ni, ni ne mahaifinki" yayi maganar cikin matsanancin rauni.

Nabila ta ɗaga kai, ta kalle shi sau ɗaya, ta kawar da kanta, tabbas ta ɗokanta da son ganin mahaifinta, ba irin alwashin da ba ta yi ba, na idan Allah ya sa yana raye, su ka haɗu, babu ruwanta da Al'ada sai ta rungume shi, ko a yaya yake, sai dai kash! Ba ta ji daɗin a yadda mahaifin na ta ya kasance ba, duk da ba ta san mahaifiyarta ba, amma uwa uwa ce, ba ta ji daɗin abin da ta ji game da tarihin zaman su ba.

Nasir ya ce "Nabila, ki yi magana mana"

Major ya sake cewa "Arfa, ki kalle ni mana? Meyake damunki?"
"Ni ku daina nuna ku na so na, ba kwa so na ba kwa ƙaunata, meyasa za ku yi mini haka? Ni menene laifina a tsakanin ku? Ace ina da 'yar uwa ban ganta ba, ba ta ganni ba har ta koma ga Allah, kun san me nake ji kuwa? Ban san uwata ba, 'yar uwata kuma ta mutu ban taɓa ganinta ba, duk ba kwa so na, kun fifita tsamin alaƙar ku a kai na, ta mutu fa ba zan ganta ba kenan. Abba tsananin son da ka ke yi wa 'yar uwakka ya sanya ka yanke wannan hukunci, ni yanzu ba ka yi tunanin a wane halin nake ciki ba, da na rayu kamar wata mujiya, ba wani ɗan uwa da zan ɗaga in kalla ya na so na tsakani da Allah" tayi maganar tana wani irin kuka mai matuƙar sauti.

"Shikenan da ban haɗu da Viper ba, ba zan san ina da 'yar uwa ba, Abba ka ɓoye mini, kai kuma babana, duk burin da na ci na in ganka, gwiwata ta yi sanyi, meyasa ka yi wa mahaifiyarmu haka, da ba ka yi haka ba, da babu lallai a raba ni da 'yar uwata, ban fa taɓa ganinta ba, shikenan ta tafi har abada"
Ta miƙe tsaye a kan gadon, tana neman hanyar sauka.

Viper ya ce "Meye haka ne ki ke yi? Ina kuma zaki je?"

"Ka kira mini sumayya dan Allah" tayi maganar cikin sigar magiya.

"Sumayya kuma? Me za ta yi miki?"

"Ni dai ka kirawo mini ita"

"Magariba ta yi, ba za a kirata ba sai da safe"

Likita ne ya dawo, ya ce duk a fita a ƙyaleta, a stage ɗin nan da take, za ta iya samun matsalar ƙwaƙwalwa, a ƙyaleta ta huta.

Matsananciyar nadama da jin kunya, suka mamaye Bashir yanzu shikenan Nabila ba ta farincikin ganinsa.

Shi ma major, damuwa ce ta mamaye ilahirin fuskarsa, wani irin dana sani yake yi, na raba Nabila da jauhar da ya yi, wato duk wayon bawa ƙaddara ta riga fata.

***
Gidan su jauhar, tun bayan da Zakiyya ta yaudari maman saifu, ta aurawa Alhaji mu'azzam Hafsa, dama haɗin kan na su ya lalace, kullum cikin faɗa da tashin hankali suke, sai ka ce ƙanan yara, gaba ɗaya tarbiyyar yaran sai a hankali, ba wanda yake ganin uwar wani da gashi sai tasa.

Bayan tafiyar su Major, Zakiyya ta ce "Ke kin ga wani ikon Allah, wallahi saura kaɗan na haukace, na ɗauka gamo na yi, yanzu duk tsawon wannan lokacin dama jauhar 'yan biyu ne?"

"Wallahi kuwa, abin da mamaki ba kaɗan ba, kuma wani ikon Allah, ba ya zancen uwar su, tun wancan lokacin"

Zakiyya ta ce "Eh, amma ai yana kallon hotonta wasu lokutan, wai dan Allah maman saifu, wurin wani malamin ki ka kai Bashir, da aikin nan ya ci shi, ya manta da chubaɗo gaba ɗaya daga rayuwarsa, ashe a tagayyare haka ta haife su?"

A ƙule ta ce "Ban gane wurin wani malami na kai shi ba, muka kai shi dai, ke da yarinyar nan ta rayu a gidan nan, ai da wallahi kashinmu ya bushe, yadda ya din ga rawar kan nan, ya nemi ya mayar da mu borori a kan bafulatanar daji, kawai a daina wani tone-tone"

Zakiyya ta ce "Uhumm ai shikenan, zan ga yadda dramar nan za ta ƙare, shi ya ɗauki zafi shi ma wan uwarta ya ɗauka, amma abin da ya bani mamaki na kasa ganewa shi ne, yaya aka yi mijin jauhar ya samo ta, a ina ya ganota ya kawota nan ɗin?"

"Oho sanin gaibu sai Allah"

Su ka ci gaba da hira, su na mamakin yadda al'amuran suke cike da sarƙaƙiya da ban mamaki.

***
Nabila kamar tana tura magani, haka take shan youghurt ɗin gabanta, ta na yamutsa fuska, fuskar tayi jawur, Viper ya zuba mata idanunsa ko ƙiftawa ba ya yi.

"Kin ce ke youghurt, ku ma kin ƙi sha"

Hawaye ya gangaro kan fuskarta ta ce "Ka takura mini ne, babu yadda zan yi, dan Allah ka nuna mini hoton 'yar uwata na sake ganinta, idan an tuna ba zan taɓa ganinta ba, wallahi sai na ji zuciyata ta buga da ƙarfi ban santa ba, amma wallahi ina son ta, meyasa tuntuni ban sanka ba ka haɗani da ita ba?"

Ya shafi fuskarsa cikin dakiya ya ce "Allah ne bai ƙaddara ba"

"Kenan kai nake mafarkin tana nuna mini a cikin sarƙa?

Yayi ƙuri da ido yana kallon ta.

"Wallahi Vi da gaske nake son ta, ashe haka ka ji, kai da ka santa ya ka ji da ka rasata, gara ma kai ni fa ban santa ba ma, tsakani da Allah iyayen nan nawa sun kyauta mini?" Tayi maganar tana rushe masa da matsanancin kuka.

Allurar gefen gadonta, ya ɗauka ya buɗe ya zuƙe ta, ya ce "Kwanta ki bani hannunki na yi miki, sun shigo za su yi miki ki na salla" ta kalleshi tana sheshsheƙar kuka.

"Kar ki damu, ɗan ƙwaya ne ni, kuma ɗan daba na saba riƙe sirinji da allura.

Ya buɗe cannulan ya fara yi mata allurar, a hankali jikinta ya fara sanyi, ya kwantar da ita.

"Tun daga lokacin da na fuskanci bijirewa ƙaddara na nufin halaka ta dindin ko samar da damejin da ba shi da hanyar gyaruwa, ya sanya na yi saranda, na bawa ƙaddarar damar ci gaba da jujjuya akalar rayuwarmu, domin na fuskanci ƙaddarorinmu na da alaƙa da juna. Tamkar na kashe kaina, haka na ji bayan rasa matata, ni har hauka na yi ai, na kuma yi ƙoƙarin sake sabauta rayuwata. Kar ki tafka irin kuskuren da na yi, nake ta fama da dana sanin da ba shi da wani amfani a gare ni,  ina guje miki aikata haka. Ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara, ki karɓi mahaifinki kuma ki karɓi mariƙinki, ki sasanta tsakaninsu" cikin muryar jin bacci ta ce "Maza wasu ba su yi ba, Allah sarki babarmu 'yar fulanin riga, abin tausayi"

"Idan kuma abin da ya same ta ya na da alaƙa da jinsinta fa, su suka aikata komai, mu daina zargin jinsinmu da cutar da ɗaya, kawai mu mu zama adalai a kowane lokaci, da mahaifinki da major duk ba na yarwa. Zan iya rantse miki ban san mahaifinku da wani mugun hali ba, mutumin kirki ne, duk da ba ni hali na kirki, amma auren 'yar sa da na yi, ɗa ya ɗauke ni ba siriki ba"

Ta buɗe idanunta da kyar, cikin raɗa ta ce "Spy, wai nasiha ka ke yi mini? To ka fara yi wa kanka, zan iya rantse maka, Abbu mutumin kirki ne, bamu haɗu a zahiri ba, a waya muka yi magana amma dattijon arziki ne" ta yi maganar daidai lokacin da bacci yayi awon gaba da ita.

Dare ya fara yi, Viper ya fito daga sashin in da ɗakin Nabila yake, daga major har Baba duk suna nanz har a lokacin ba su tafi ba.

Viper ya ce "Ina ganin zaku iya tafiya gida, zuwa in Allah ya kaimu da safe, tun da an ce ƙwaƙwalwarta na buƙatar hutu, kar ta rikice gaba ɗaya. Amma dai yakamata ku sasanta kanku kafin Allah ya sanya ta sake farfaɗowa".

Major ya kalli Viper rai a ɓace ya ce "Ai kai ne kanwa uwar gamin komai, dan me zaka ɗauke ta, ka kai ta wurin wannan mutumin mara tsoron Allah, ita ma ya bari rayuwarta ta wulaƙanta kamar yadda ya wulakanta ta uwatta, kuma saboda rashin tsoron Allah ya aura maka yarinyar da ba ta ji ba, ba ta gani ba ka kasheta, kuma saboda zalunci ka dawo ka sanya ta tssya maka, take baka kariya, alhalin ka kashe yar uwatta, wane irin abu ne wannan?. Duk a dalilinka zumuncin da yake tsakanin yaran nan, ka watsa shi, ba ta jin maganar kowa sai ta ka, idan abin gaskiya ne, meyasa ni ba ka je ka same ni a gida, ka yi mini bayani ba kawai ka ɗauke ta ka kai wa wannan mutumin"

Maganganun Major sun yi wa Viper zafi sosai, yayi ƙuri da ido yana kallon major, amma bai yi magana ba.

Baba cikin mamaki ya kalli major ya ce "Ka ga wani iko na Ubangiji da yadda yake jujjuya al'amura yadda ya so, duk guje-gujen naka, da Allah ya ƙaddara, Nabila ce za ta tsaya wa mijin 'yar uwatta, ka yi ƙoƙarin tsayawa a kan iliminta da tarbiyyarta, amma Al'amin ba mutumin banza ba ne ba, haryanzu ban yadda zai iya kashe mini 'ya ba, kar ka ƙara danganta shi da kisan kan jauhar"

Saifu ya ce "Baba ka daina wannan maganar fa, ba ka da tabbas ya aikata ko be aikata ba"

Liti ya ce "Ji wani ɗan wahala kuma, to ai sai ka jira kotu ta tabattar da shi ya aikata, tun da shari'a za a fara kwanan nan. Mu mu ka yi rayuwa a gidan Viper a tsakanin sa da Jauhar. Mun san yanayin zamantakewar su, tsabar ƙauna ko sunanta ba ya iya faɗa sai 'yar madara, sai ka jira kotu tukuna, kafin ka yi wannan maganar"

Shiru saifu yayi, dan ya san halin liti farin sani, 'yan a mutun mai zamani ne.

Da kyar da siɗin goshi, aka samu suka tafi gida, shi ma sai da su ka tabbatar da Nabila tana cikin tsaron da babu wanda zai gudu da ita, dan kowa zargin kowa yake yi.

Viper a makwancinsa, yana ta jujjuya al'amarin ya san akwai sauran ƙura a gaba, major ya ɗauki zafi sosai da sosai, kuma haɗin kansu ne zai ba wa Nabila nutsuwar ci gaba da gudanar da shari'ar da take yi a cikin nutsuwa.

***
Sumayya duk wani abu da ya shafi Indabo, haka take yaɗa shi a kafafen watsa labarai ba tare da tsoro ko fargaba ba, ba shi kaɗai ba, mussaman Alhaji mu'azzam yake sanyawa ake nemo mata manyan rahotanni na bankaɗa tare da cikakkiyar hujja a kan miyagun harƙallolin da ake yi a ƙasar nan. Sai dai kash, ko an bankaɗo babu wani abu da talaka zai iya yi a kai face Allah ya isa. Dan ƴan siyasar sun din ga ƙoƙarin kare kansu kenan, lokutan zaɓe su sake lallaɓowa tare da fara ayyukan babu gaira babu dalili, da raba tallafin abin da bai kai kaso goma a cikin abin da suke wawaso na al'aumma ba. Sai dai a wannan karon al'ummar sun yi rawar gani wurin yin abin da ya dace, karo na farko a Nigeria da ake ƙoƙarin yi wa sanata kiranye. Duk da irin barazana da matasan da suke jagorantar abin suke yi, amma suka dage babu gudu babu ja da baya, dan tuni sun miƙa wasiƙa ga hukumar zaɓe ta ƙasa a kan son yi wa Indabo kiranye. Hakan ya ba wa wasu matasan daga sassa daban-daban na ƙasar nan ƙwarin gwiwa da ganin cewa ashe za su iya kawo canji ga waɗanda suke wakiltar su su ma.

Alhaji mu'azzam mutum ne na mutane, dan haka mutanensa su ka din ga kiransa a kan ya fito takara.
Dama harin kujerar inda
Bayan kammala program ɗin ta, ta ga kiran waya.

Lambar Nabila ta gani, ta ɗaga ta ce "Ke ya ne, program na kammala ko numfashi ban shaƙa ba, kin doko mini kira"

"Ta na asibitin barrack, ta na buƙatar ganinki da gaggawa" ƙuuu cikin sumayya ya yi ƙara, muryar Viper ce, a duniya Allah ya yi masa kwarjini, muryarsa da ta ji kawai gabanta ya faɗi. Kashe wayar ya yi, bayan kammala gaya mata saƙon.

A gurguje Sumayya take ƙoƙarin kammala ayyukanta, dan ya je ya ji me ya sami Nabila.

A jiya da major ya koma gida, kasa gane kansa matansa suka yi, dan babu wadda ya kula, kuma ya ce baya buƙatar kowa ta zo masa turaka.

Sai Nasir suka tutsiye, su na tambayar sa, ina su ka je jiya wuni guda ba sa nan.

Nasir ya labarta musu komai, gaba ɗaya suka yi shock. Anty ta ce "Dama mahaifin Nabila yana raye?"

"Eh, mun ganshi jiya ma, ɗan daban nan Viper da ake nema, 'yar biyun Nabila ya aura ya kashe, kuma saboda shirme take kare shi, shi ya ɗauke ta ya kaita wurin mahaifinta" al'amarin yana buƙatar nutsuwa kan a warware shi, dan ba kowa ne zai iya fahimtar bayanin ba sama-sama.

Ko da sumayya ta je, ba wanda ya hanata shiga, da ta tambayi in da Nabila take, Nabila na ganinta ta miƙe tsaye, fuskarta ta kumbura suntum saboda kuka.

Ta rungume sumayya ta ci gaba da kuka, Sumayya ta ce "Subhanallah, Nabila waye ya mutu? Kin ga yadda ki ka rame fuskarki ta kumbura kuwa?"

Cikin kuka ta ce "Sumayya na ga babana jiya" waro ido sumayyan tayi ta ce "A ina?"

"Viper ne ya kai ni, Sumayya ashe yar biyuna ya aura aka kashe, duk wannan haƙilon da nake yi, 'yar uwata aka kashe"

Sumayya ta ƙurawa Nabila ido, ta ce "Anya kanki ɗaya?"

"Kai na ɗaya Sumayya, amma ai kin san lokacin da nake ce miki ina mafarki da mai kama da ni, ki ke yi mini dariya, wallahi sumayya ina da 'yar uwa da ban taɓa ganinta ba, a kanta nake shari'ar Viper"

"Nabila, gaba ɗaya kin rikita ni, ban gane in da ki ka dosa ba wallahi, gaba ɗaya na rikice" Viper ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo.

Jiki na rawa sumayya ta gaishe shi ya amsa, ta kalli Viper ta ce "Vi ka yi wa sumayya bayani, ta ƙi yadda ta kuma kasa gane bayanin da na yi mata"

"Wa zai fuskanci wannan bayanin naki at once dama, ki ƙwarara jikinki, ki yi haƙuri ki daina wannan kukan, yana daga dalilin da ya sanya tun farko ban gaya miki ba"

Sumayya za ta yi magana, Abba ya turo ƙofa ya shigo da sallama, suka amsa masa. Sumayya ta gaida Abba ya amsa mata, suka gaisa da Nasir ma.

Viper ya yi masa barka da zuwa, amma ya yi masa shiru.

"Arfa, kin ji sauƙi ina son a sallame ki, mu koma gida ne" kawar da kanta gefe ta yi, ba ta kalle shi ba.

Sumayya ta ce "Nabila Abba ne fa"

Ta ɗaga kai ta kalli Sumayya ta ce "Abba disappointed me, meyasa ya ɓoye mini ina da 'yar uwa, gashi ta mutu ban taɓa ganinta ba...

"Wai mahaifiyarki ma ba rasuwa ta yi baki taɓa ganinta ba?" Viper ya yi maganar a kausashe.

"Amma jauhar ta yi tsawon rai ai, meyasa aka hukunta mu da laifin babanmu"

Nasir ya ce "Nabila Abban ki ke gaya wa haka?"

Major ya yi shiru, kawai ya tashi ya fita.

Sumayya ta ce "Nabila meyasa ki ka yi haka? Baki kyauta ba, duk ɗawainiyar da ya yi da mu, hakan da ki ka yi ba dai-dai ba ne ba. Idan aka sallame ki, dole mu je ki ba shi haƙuri.

Kiran gaggawa aka yi wa sumayya, ta tashi ta tafi, cike da mamaki da tunani daban-daban a cikin zuciyarta.

Bayan tafiyar major, sai ga Bashir, har da kayan abinci niƙi-niƙi sun zo duba Nabila.

Tana zaune, a kan gado, Viper yana gefe yana waya, yana ganinsu ya kashe wayar, ya risuna suka gaisa da Baba.

Ƙarasawa yayi gaban gadon Nabila ya zauna ya ce "Sannu ya jikin naki?"

Ƙura masa ido ta yi, amma ta kasa masa uffan.

Ya zauna ya dafa hannunta, amma ta

Download complete TXT · Novel page