Karfe A Wuta

Chapter 130 of 167

ba da yar uwakki ce ba zata yi haka ba, jauhar ta daban ce, mai tausayi da jin ƙai ce. Na san da ke aka yi wa abin da aka yi mata a kaina bijirewa zaki yi. Da haƙuri da siyasa ake cin ribar zaman duniya ba fushi da shirme ba. Kin nuna rashin jin dadin ki abin da aka yi miki da farko daga baya kuma sai ki saukko ki haƙura ai"

Sumayya da tana wurin, ita kanta sai da ta tsorata da faɗan da Viper yake yi.

Nabila kuwa kuka take yi wiwi, wasu lokutan gara faɗan Abba da na Viper, gaba ɗaya sai ya razanata ya saka ta rasa abin da yake yi mata daɗi.

"Ki tashi ki shirya, zamu je ki nemi afuwarsa, sannan mu je mu ga ɗan mama, da su Rahama"

Haka Nabila ta shirya, sumayya tana ta mamakin samun abin da zai iya tsorata Nabila ya sakata kuka, bayan Abba.

Yau ma a ƙofar gidan su jauhar, aka yi parking, tare da sumayya suka zo, da sallama suka shiga.

Baba yana gareji, yana ba wa saifu sallahun wanke masa mota, Nabila suka shiga.

Cak ya tsaya yana kallon su, da sumayya da Nabila.

Kallo ɗaya Sumayya ta yi wa Baba ta gane baban Nabila ne.

Rikicewa yayi ya nufota duk da jikinsa a sanyaye ya nufeta, idanunsa cike da hawaye.

Yana ƙarasowa ta faɗa jikinsa tana sakin wani irin kuka mai karya zuciya.

A hankali ta ce "Baba" tana kuka yana kuka, kamar wani zai ƙwace masa ita, haka ya ƙanƙame Nabila, yana kuka har da majina.

Sumayya da take tsaye ita ma fashewa ta yi da kukan, cikin matsanancin tausayin su, ta san irin artabu da ƙalubalen da Nabila ta din ga fuskanta a kan rashin uba, a gidan major yadda suke kiranta da tsintacciyar mage wai babu wanda ya san babanta, Nabila ba ta da wata magana da ta wuce fatan ganin mahaifinta, ta ji ina ma ita ma tana da rabon sake ganin mahaifinta a rayuwa.

Viper yana hango su daga waje, ya sunkuyar da kansa hawaye na cika masa ido, cike da fatan ina ma shi ne ya sake ganin Jauhar ta bayyana a rayuwarsa ba tare da ya yi tsammanin hakan ba.

Nabila ta ce "Sumayya ga babana, kin ga babana"

"Na gan shi Nabilata, Ina tayamu murnar ganin Baba, burin da muka daɗe muna fatan Allah ya cika mana"

"Ki yafe mini 'ya ta, abin da ya faru ba da son raina ba ne ba, wani abu ne da ba zan ce ga a yadda ya faru ba, na san mai laifi ne a gareku da mahaifiyarku, ke kaɗai ki ka rage mini a cikin su, dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini" yayi maganar cikin matsanancin kuka.

Ya rungumi Nabila zuwa cikin gidan, sumayya na biye da su, yaran gidan duk su ka kewaye su, wasu na taya su kuka wasu na kallon su.

Ya ce aje a ce wa Al'amin ya shiga.

Nabila ta kwantar da kanta a kan cinyar baba, tana cigaba da kuka.
Bayan Viper ya shigo su ka gaisa da Baba, ya kalli sumayya ya kalli Viper ya ce "Anya Aminullahi wannan ma ba tawa ba ce?"

Viper ya yi murmushi ya ce "Duk naka ne Baba, an baka"

"Na san fuskarta ne, ta na kama da wani wanda na sani, amma ba zan iya tuna waye ba? Ya sunan mahaifinki?"

Sumayya ta share hawayenta ta ce ba ni da wayon sanin mahaifina, amma dai sunansa Tahir ladan.

A take ya yi sak, ya ce "Wane Tahir ladan ɗin? Coustom ne?"

Sumayya ta jinjina masa kai ta ce "Ka san shi?"

Yayi shiru ya ce "Tare mu ka je ɗaurin aurena a jalingo, abokin aikina ne, lokacin da aka yi mini transfer daga in da na bar mairamu shi ne ya koma, ya je yayi reporting a wurin aiki, ya koma yayi hatsarin mota ya rasu.

Viper ya ce "Kenan dai duk 'ya'yan naka na kawo maka"

Kamar ƙaramin yaro ya kalli Sumayya ya ce "Ni babanki ne, ke ma 'ya ta ce ai, na gode Aminullahi, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"

Viper ya ce "Baba da ka yi haƙuri da kukan nan haka, saboda su ma su samu ƙwarin gwiwar yin haƙuri, mu gode wa Allah kawai"

Ya jinjina kai yana maimaita Alhamdilillah.

Baba ya din ga shafa kan Nabila, amma hawayensa suka kasa tsayawa.

Zakiyya tare da maman hafsa su ka shigo ɗakin da sallama, su na kallon yadda ya saka su Nabila a gaba yana kuka.

Viper ya na ganin Zakiyya ya haɗe rai, tamkar ya ga abin ƙyama.

Su ka zauna su ka din ga surutai marasa ma'ana, marasa tushe balle makama. Tare da taya su kukan cike da makirci.

"Baba ina hafsa?" Nabila ta tambaya da kyar.

"Ta je gidan kakaninta da su ka haifi mahaifiyarta".

"Baba shikenan ban san jauhar ba, ba kuma zan ganta ba, ban san mama ba, ita ma kuma ban santa ba, mun rayu a wurare daban-daban, ba mu san juna ba" tayi maganar tana sake fashewa da kuka.

Cikin sigar rarrashi ya ce "Hakan hukuncin Allah ne, ki yi haƙuri, mu masu tarin laifi ne a wurinki, mussaman ni, na san ni ne baban mai laifi, duk da major ma mai laifi ne, bai kamata ƙiyayyar da yake yi mini ya sanya, ya nesanta ni da ke ba, ya kawo mini yarinya amma bai kuma waiwaiyarta ba, amma Alhamdilillah na ji dadin yadda ya kula mini da ke"

Viper ya numfasa ya ce "Baba yakamata mu koma haka, da su"

Baba ya ce "Aminullahi, dan girman Allah ka bar mini ita"

"Ka yi haƙuri, ai aikin gama ya riga ya gama, tun da har komai ya riga ya bayyana, sai da na saka hannu na ɗauki excuse sannan na fito da ita, shi ma bisa uzurin aiki za ta yi, kuma ka ga a hannun Abba aka yi yarjejeniya a ka ɗauketa, da niyyar ba ta kariya, har a kammala shari'ata, addu'ar ka muke fata".

"Yanzu ka na nufin mijin 'yar uwatta take karewa, Allah al-hakimu, Allah ya bayar da nasara, yayi muku jagora dukkaninku"

Su ka amsa da Amin gaba ɗaya.

Baba ya ce ya bari su ci abinci, Viper ya ce "Lokacinsu a ƙididdige yake, idan su ka saɓa akwai matsala"

Har gaban mota ya rako su, yana rungume da Nabila kamar zai mayar da ita cikin sa.

Su ka je bakin motar, ya riƙe hannun sumayya, ya riƙe na Nabila, ya kasa tsayar da hawayensa, ya kalle su ya sake fashewa da kuka ya ce "Ku yafe mini dan Allah, ku ci gaba da haɗa kanku, Allah ya yi muku albarka, Allah ya jiƙan mahaifinki ke kuma Allah ya jiƙan mahaifiyarki da jauhar"

Su na kuka su ka shiga motar, su ka ja, su na tafe a hanya, Viper bai rarrashe su ba, dan ba wani ƙwarewa ya yi a hakan ba, ya yi musu shiru, su ka yi ta kukan, ya ce a fara kai sumayya gida, sannan su koma barrack washegari sai su je wurin su ramma.

***

Major ya sha mamakin yadda Nabila ta nuna fushi take yi da shi, taƙi saurarsa.

Mama kuwa sai ziga shi take yi, ta ce "Dama ga ubanta yaushe za ta saurare ka, ai kai ka gama yi mata amfani kuma, shiyasa tuntuni da yaranka ka kama, da ya fiye maka" shi dai bai furta komai ba, amma abin ya din ga cin zuciyarsa.

Rahila ma aka sallameta daga asibiti, bayan an yi mata ɗorin karayar hannunta, sai da Abbu ya dage ya ce sai Abba ya bar masa gidansa, aka kaɗa aka raya ya ce ba zai ci gaba da riƙe shi ba, idan kuma ta dage sai ya zauna, to sai dai ta bi shi su bar gidan.

Shahida ma ta dage a kan raba aurenta, da fari Abbu bai sani ba, amma bayan ya takurata, da ta gaya masa bai tausayawa halin da rahila take ciki ba, yayi mata tas, ya ce sai an raba auren, ba za a saka masa 'ya a halaka ba.

***
Sumayya ta labartawa ummanta abin da yake faruwa, sumayya na ce mata jalingo, ummanta ta ce ta san mahaifin Nabila, amma ba wani sani ba, ta dai san abokin aikinsa ne.

Madam halima ta gaya wa Nabila Viper ya zo, yana jiranta su fita.

Kallo ɗaya ya yi mata, ya san ba ta samu isasshen bacci ba, fuskar nan babu walwala.

"Ina kwana" tayi maganar a hankali.

Ya tsura mata ido, ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Akwai sauran damuwa ne? Kin haɗu da mahaifinki ba shi ne fatanki ba?" Yayi maganar yana kallon ta.

Ta girgiza masa kai.

Ya ce "To me ya yi saura kuma?"

"Kewar yar uwata, da tunanin yadda zan daidaita Baba da Abba, kowanne ya na da muhimmanci a gare ni, amma Abba ba zai saurare ni ba, saboda Nasir ba zai daina ziga shi ba, saboda haushin tsaya maka da na yi, zai ta ziga shi a kan lallai ya yadda kai ka kashe jauhar, ba ni da gaskiya ina tsaya maka"

"Ƙalubale ne ma hakan, amma yakamata tun ba yanzu ba ki san kuka ba magani bane ba, na san duk ni ne silar komai, shigowa ta rayuwarki, ki yi haƙuri"

"Ba kai ka shigo rayuwata ba, ni na shiga taka, ko in ce ƙaddara ce, amma in sha Allah zan yi iya yi na, sai an hukunta wanda su ka kashe 'yar uwata, ku ma na tabattar da an kwance sarƙar da aka sanya wa mijinta alƙawari ne na yi wa kaina" ta yi maganar tana share hawayenta.

Ya jinjina kai ya ce "Allah ya ba da sa'a"

"Amin" har ya yi gaba zai fita, ta ce "Viper" ya tsaya ya waiwayo.

Ta ƙarasa gabansa ta ce "Ina son ka ji abin da na ji a lokacin da na rungumi mahaifina, ina son ka yi amfani da nasihar da ka yi mini, a kan kanka. Mahaifinka yana da muhimmanci a rayuwarka"
"Wannan ni ya shafa, ba ke ba, dan haka babu ruwanki a ciki"

Ta ɗan yi murmushi ta ce "Ina roƙonka ne a matsayina na ƙanwarka, ba lauyar ka ba, ina fatan ka kasance cikin rahamar Allah kamar yadda nima ka ankarar da ni nawa kuskuren" Ajiyar zuciya ya yi, ya fice ta bi bayansa.

Haka kurum su na tafe a mota, yake tunanin da gaske yanzu Nabila a matsayin yaya ta ɗauke shi kawai?.

Harabar wurin 'yan sandan cike da motoci.

A can su ka tarar da sumayya, mahaifiyar ramma ma ta je wurin ita da ramma, Alhaji mu'azzam ya saka an kai su.

Nabila tana matuƙar jinjinawa gudunmuwar da Alhaji mu'zzam ya ba su, ya cancanci yabo da godiya, amma goga Viper hakan ko a jikinsa, balle ya nuna masa yabawar sa da jin daɗin sa.

Suka gaggaisa, ramma da ƙyar ta iya gaida Viper, saboda matsanancin tsoronsa da take ji.

Su liti tuni sun je wurin, dan sun kai wa ɗan mama abinci.

Sumayya ta zauna su ka sake tattauna wa da ramma, kasancewar su na jiran ƙarasowar su Abdul da lauyoyin sa a ɗauki statement ɗin su duka.

Sumayya ta naɗi wani sashi mai muhimmanci, na tattaunawar su da ramman, wanda zai yi wa Sumayya amfani haka Nabila, mussman ta ɓangaren Naja'atu Bunkure.

Viper kuwa cikin isa yake yawonsa a headquarter yan sandan, ya je ganin ɗan mama da kansa.

Sumayya ta dubi Nabila ta ce "Nabila, haryanzu ina mamakin yadda aka yi ki ka haɗu da Viper, ikon Allah ashe duk wannan haƙilon a kan sister ɗinki ki ke yin sa, amma Nabila idan ba shi ne ya kashe Jauhar ba, wanene?"

Nabila ta gyaɗa kai ta ce "Mu haɗu a kotu kawai sumayya, abubuwan su na da girma da faɗi sosai"

"Meye wani sai mun haɗu a kotu, ki ƙarasa mini, kin bar ni a cikin duhu da zullumi Abla, kamar yadda na ji ana kiran ki, Nabila gayen nan kuwa ba son ki yake yi ba?"

Nabila ta numfasa ta ce "Sumayya, ba ki yi ƙarya ba, ni ina son Viper, na kamu da sonsa ba tare da na shirya hakan ba, dan da farko dan na taimaki rayuwarsa ya dawo hayyacinsa ya sanya na ce ina son sa, sai dai ban yi aune ba, na faɗa son shi da gaske. Saboda Viper mutum ne na musamman ya kai a so shi, kin san meya ƙara jefani cikin ƙaunar sa da gaske?"

Sumayya ta ce "Sai kin faɗa"

"Zamantakewar sa da ya yi da jauhar" Nan Nabila ta fara ba wa sumayya labarin abin da ba ta sani ba, matakan da ta bi wurin haɗuwa da shi, zuwa labarin sa da Walid ya bata.

Ramma ta yi shiru ta na sauraron su, kawai ta din ga jin, idan jauhar tayi haƙuri da Viper mutum mai ban tsoro ta zauna da shi, ta yi wannan gwagwarmayar lallai idan aka yi haƙuri Abdul ma zai iya shiryuwa.

Wani ɗan sanda ne ya leƙo, ya ce su shiga, sun ƙaraso. Gaban ramma ya faɗi, maman ramma na can ta na shan hantsi, Nabila ta yi mata magana ta ce ta taso.

Gaban ramma ya tsananta faɗuwa, aka yi musu jagora zuwa ofishin da za a ɗauki statement ɗin.

A ciki su ka tarar da Viper a zaune, har da manyan mutane abokan Indabo da su ka zo, ga mahaifiyar Abdul yasar a wurin ita ma.

Ai su na shiga office ɗin, Abdul ya miƙe, kallonsa ramma ta yi, ya rame sosai da sosai, ba wai rama ta damuwa ba, rama ta ciwo.

"Rahama" ya kira sunanta a raunane.

Mugun kallon da Viper ya yi mata ne,ya sanya ba shiri ta nemi wuri ta zauna.

Tashi ya yi ya nufi in da take, wani ɗan sanda ya daka masa tsawa, amma bai saurare shi, ba ya nufi ramma. Ƙafa Viper ya saka masa, abin ka da mara lafiya, ya tafi luu zai faɗi, Viper ya riƙe rigarsa ya hana shi kai wa ƙasa.

Aka saka ɗan sanda ya janyo shi, ya zaunar da shi, tuni ramma ta fara kuka.

Kawai ya zuba mata ido ko ƙiftawa ba ya yi.

"Abdul da ma wannan ce yarinyar da ka ke ta wannan haukan a kanta, duk matan garin nan? Wallahi ka bani kunya" mahaifiyarsa tayi maganar a ƙule.

Aka tambayi ramma sunanta ta faɗa, aka nuna mata Abdul aka ce "Kin san wannan?"

Ta jinjina kai alamar eh.

"Waye shi?"

"Mijina ne" ta faɗa kai tsaye.

Gaba ɗaya su ka Kalle ta, cikin takaici mamanta ta ce "A gidan uban wa ya zama mijin naki?"

Nabila ta tashi ta je gaban ramma, cikin raɗa ta ce "Dan Allah ki nutsu rahama, ki yi bayanin komai, saboda a ƙwatar miki hakkinki"

Aka sake tambayar ramma "Meye alaƙarki da shi, me ya yi miki?"

Tayi shiru ta na kuka taƙi magana.

Abokin Indabo ya ce "Ni fa ina ga wannan abun duk da masalaha aka yi, aka sasanta abun nan, dan gudun ɓacin sunan yarinyar nan, tun da akwai aure kuma abin nan ya wu....

"Shut up, ba rikicin jam'iyya ba ne ba ko na siyasa, a ƙwatarwa yarinya hakkinta mu ke buƙata" Viper ya yi maganar cikin tsawa.

"Aminu Viper, mai bunu a ƙugu ba ya kai gudunmuwar gobara, ka bari ka fara kashe wutar gabanka, kafin ka zage ka na ɗaga jijiyoyin wuya, haryanzu ɗa na ya na da gatan da za a iya shafe ko ma me ya aikata, mu ka zaɓi ayi masalaha".

"Gobarar da nake ƙoƙarin kai gudunmuwar kasheta, ai ku ne gobarar, dan kun fi ni shiga matsala da hatsari, a ɗauki statement a gabatar da ƙararmu a gaban kotu "

"Ya isa haka, nan fa gaban hukuma ne, ba teburin caca ba. Ke ki yi magana mu na jiranki" Ɗan sandan yayi maganar yana kallon ramma.

Da ta ɗaga kai ta kalli Abdul, sai ta ji ta karaya.

"Talk" Viper ya daka mata tsawa, ta zabura ta rirriƙe Nabila ta na kuka.

A hankali Abdul ya ce "Ku daina yi mata tsawa, yes i rape her, na amsa laifina"

"Ba ka da hankali, lauyoyin ka ba su gargaɗeka a kan kar kayi magana ba?"

Nabila cikin rarrashi, ta ce "Rahama ki yi magana, dan Allah kar ki bari tausayi ya yi tasiri a zuciyarki, ki yi magana"

Cikin kuka ramma ta ce "Ai ya nemi yafiyata, kuma da gani ba shi da lafiya, dan Allah a sassauta masa, ko a bari wataran idan ya warke sai na yi magana".

Ayshercool
08081012143




Abu na farko da zamu buk’ata daga wajenka shine mahaifar matarka, Ma’ana ba zaku haihu da matarka ba.” Imaam ya ‘dago yana kallonsa Ya ji kansa ya wani sarà masa, amma sam ya kasa masa musu… Alwan yana murmushi ya ce “Ka kirata ku yi shawara…” Ya fice ya bar masa wajen. Da sauri Imaam Ya kira Safna. Tana d’agawa ta ce “Yaya? Imaam Allah yasa dai baka musu taurin kai ba?” Ya saki huci ka’dan ya furta “Ba zan iya abinda suke so ba….” “Zaka iya Imaam, ka yi koma me suke so? Yanzu fa ba abinda baa yi saboda ku’di, ana ya Kai Kai, mutum yana kwanciyar da y’ar cikinsa, da Uwar data haifeshi ma saboda ku’di, ana luwa’di da ma’digo saboda ku’di, ana bada Uwa ko y’a Yaya ko k’anwa, K’ani ko wa? Duk saboda ku’di, don haka ka yi ko me suke so Moddi Saboda ku’di… bana son musu…” ta fa’da tana zame kanta a duk sunayen da ta ambata, bata k’i ya yi komai ba in dai zai samar musu da ku’di, bata damu ta ji shara’din da suka bashi ba. Imaam Ya saki ajiyar zuciya, sai ya ji ya samu k’warin gwiwar bayar da mahaifarta tunda ita ta jawowa kanta ta ce ya yi komai saboda ku’di. A zuciyarsa Ya dinga jin baya so, amma harshensa ya kasa amince masa ya furta baya so d’in. Ya kalli Alwan da Ya shigo d’akin idanunsa a

Download complete TXT · Novel page