Karfe A Wuta

Chapter 134 of 167

yi sanadin shiriyar mutum ɗaya, ya fi a baka jajayen raƙuma guda ɗari. Ba mu san me Allah ya ɓoye a lamarin nan ba, ga juna biyu a tare da ita, ku na nan ta yi masa alƙawarin ya je ya gama prison ya dawo ta na jiransa. Duk wannan abun fa zai iya yiwuwa wata jarrabawar ce daga Allah muma yake yi mana, Abdul fa bawansa ne shi ma, kuma ya na kishin abin sa, ci gaba da jansa dan Allah ya ara mana dama ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Amma ina mai neman afuwar ku, ba ina nufin shari'ar Abdul ta sha ruwa ba ne, sam sonake ayi tunanin mafita.
Yallaɓai Al'amin, Allah ya baka haƙuri ni babu wanda ya bani wani cin hanci, ba kuma ƙoƙarin cin amanarka nake yi ba. Zan yi iya yi na Abdul zai je prison in sha Allah, muddin hakan zai samar muku da nutsuwa" ta ƙarasa maganar a nutse, ta ja da baya ta fice.

Ramma ta na tsaye ta na ji, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, ta fashe da kuka, ganin yadda ta ja aka ɓatawa Nabila rai.

Sojan da yake ba wa Nabila kariya, ya bi ta ya na yi mata magana, amma ta share shi, a ranta ta ce "Tsohon munafiki kawai"

Napep ta tara, ta nufi gidan Abba.

Maman ramma na shirin yin magana, Viper ya rigata, ya ce bari ya tafi.

A ɗaki ta iske ramma, ta yi mata ta tas, ta ce "Ramma ba kya tausayina, ɗa na ya rasa ransa a banza, a gabanki yaron nan saboda rashin tarbiyya, ni kaina so yayi da ya haike mini, amma yanzu kin fifita shi a kaina, na gode rahama"

Tabbas da zuciya za ta yi mata adalci, to da ba ta fara ƙaunar Abdul ba, amma ita haryanzu ta fi yarda tausayin sa take ji, ya ake so ta yi da rayuwarta ne.

Viper na fita, sojan ya fara gaya masa tafiya ta yi, ya ce ya rabu da ita, su tafi kawai.

Da daddare Viper ya din ga kiran wayar Nabila, amma ta ƙi ɗagawa, hakan ya tabattar masa da ta yi fushi ne.

Gidan major babu wanda ya kulata, babu wanda ta kula sai baba uwani, ta shirya ta tafi gidansu sumayya, sun daɗe su na tattaunawa, ta na yi mata nasiha da ba ta ƙwarin gwiwa.

****
Monday morning 9:30a.m

Tsaye take a gefen wani gini, tana ƙarewa harabar kotun kallo. Yadda aka cika harabar da manya da ƙananan motoci ne, ya sake tabattar mata da manyan shari'oi za a gudanar a yau.

Ta din ga kallon agogon hannunta, tana kallon gate ɗin shigowa harabar kotun.

Motar gidan yari ce ta shigo, aka yi parking ɗin ta, sai dai tsayuwar motar babu daɗewa wata danƙareriyar motar, ta shigo harabar kotun.

A ƙalla an kai mintuna goma da parking ɗin motar, sannan aka buɗe bayan motar, wata mata ta fito, sanye cikin coat.

Mutanen da ke harabar wurin, suka nufeta, wasu suka karɓi jakarta, ana ta yi mata fadanci, cikin girmamawa.

"Ya Allah kai ne Allah, kai ne buwayi gagara misali, Ubangiji da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Allah na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko ina, amma kai ne abun dogarona, na san ba za ka bani kunya ba. Allah sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu. Allah ka yi mini kunfayakununka a kan shari'ar nan, hasken gaskiya ya shafe duhun ƙarya, duk da ina da masu goya mini baya, amma Allah goyon bayanka nake buƙata" ta jima a tsaye tana karanto addu'a, tare da yi wa Allah kirari.

A hankali ta furta "What a hectic trial, Ubangiji ka iya mini" cikin nutsuwa, ta fara taka takalminta mai tudu, ta nufi shiga cikin kotun, da takunta mai kama da na ƙasaita, shigarta ta lawyoyi tayi matuƙar yi mata kyau, tana tunkarar ƙofar shiga, zuciyarta na tsananta bugawa,tana fatan Allah ya shiga lamarin ta.


Ayshercool
08081012143

91
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Sannu a hankali ta ke ƙoƙarin shiga cikin kotun, "Nabila" ta jiyo muryar sumayya a bayanta.

Ta waiwaya, sumayya ta ƙaraso ta ce "Ya aka yi ki ka riga ni zuwa?"

"Oho miki dai"

Sumayya ta yi murmushi ta ce "Best of luck my dear, Allah ya ba da sa'a"

Nabila ta ce "Amin sumayya, amma a tsorace nake, wannan shi ne trial mafi haɗari da nake tunanin zan fuskanta a rayuwata"

Sumayya ta ce "Haba mutuniyar, tsoro ba naki ba ne ba, ke jaruma ce i trust you dear, mu je kawai"

Su ka ƙarasa su ka shiga cikin kotun.

Su na nan zaune, Alhaji mu'azzam ya shigo, barrister Habib ma ya ƙaraso, sai ga murtala, su liti da Walid, cikin mamaki sai ga Nasir ma duk a cikin kotun daga baya sai ga mai gayya mai aikin shi ma ya iso kotun.

Ƙirjin Nabila na ta bugawa, amma ta tsananta maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, la haula wala ƙuwwata illa billah"

Ana ta gabatar da shari'oi, aka kira ƙarar su Nabila.

Tashi ta yi cikin nutsuwa, ta fita gaban shari'a.

Ta tsaya ta gabatar da kanta a da cikakken sunanta, da kuma wanda take karewa.

Lauyan da yake kare lakwari, ya fito ya gabatar da kansa, da wanda yake karewa.

Nabila ta nemi a karantowa masu laifi, laifin da ake tuhumar su da shi, a nan ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ya karantowa lakwari laifin da ake tuhumar sa da shi, da Madaki, duk da madaki ya na gadon asibiti ya na jinya.

Aka karanto tuhumar da turanci, cewar ana zarginsu da shiga cikin gidan Aminu Viper, su ka kashe mata da ɗan da kuma ɗan yake cikinta.

Kotu ta waiwayi lakwari domin jin ta bakinsa, bayan an fassara masa ƙusnhin tuhumar da ake yi masa, cikin harshen hausa.

A nan take lakwari ya musanta zargin, kamar yadda ya musanta a wurin 'yan sanda, da kuma yadda lauyansa ya jaddada masa kafin zuwan su kotu, domin kuwa ba ƙaramin kuɗi aka ba wa lauyoyi ba, a kan su yi duk mai yiwuwa ayi ta jan Shari'ar har ta lalace.

Daga haka kotu ta ɗaga cigaba da shari'ar, zuwa sati biyu domin bayyanar shaidun kowanne bangare.

Viper daga in da yake zaune, lakwari kawai yake kallo, ko ƙiftawa ba ya yi, zuciyarsa na raya masa kawai ya kashe shi ya huta, yanzu da haka za ayi ta jan ƙafa a shari'ar nan a ɗauki dogon lokaci ba a kammalata ba? Zuciyar sa azalzalarsa kawai take yi, ya na jin tamkar ba zai iya jira ba.

Ya na kallon lakwari, taswirar abin da ya faru a daren da jauhar ta mutu, na ƙara dawo masa a cikin ƙwaƙwalwarsa, yadda ya kasa kataɓus, ya na ji ya na kallonta ta na miƙo masa hannu.

Knasa ne ya yi wata irin sarawa, ya tashi cikin hanzari ya fita daga cikin kotun, gaba ɗaya fuskarsa ta sauya, tsantsar baƙin ciki da ɓacin rai, haɗi da tashin hankali ya mamaye ilahirin fuskarsa, tuni idanunsa su ka kaɗa su ka yi jawurrr.

Nabila ta na daga in da take ta bishi da kallo, ta san a rina, wani irin tausayin sa ya kamata, kamar ta tashi ta bishi, sai kuma ta tuna fushi take yi da shi, dan haka kawai ta basar.

Walid ne ya tashi ya rufa masa baya, liti ma biyo su yayi.

Walid ya cimma sa cikin hanzari, ya na kiran sunansa.

Bai tsaya ba, Walid ya riƙe rigarsa ta baya, ya juyo ya ture shi, amma ya sake riƙe shi.

"Mai laya" ya furta muryarsa na rawa.

Walid ya ce "Mai zamani"

"Idan zuwana wurin Shari'ar nan zai din ga fama mini gyambon da yake cin zuciyata ina ga zan haƙura kawai"

Walid ya ce "Ba zamu haƙura ba, bakin rai bakin fama, sai in da ƙarfinmu ya ƙare da yardar Allah"

Wata baranda Viper ya samu, ya zauna, ya miƙe ƙafafuwan sa, ya na jin yadda kansa yake ci ga ba da sarawa bugun zuciyar sa na ƙaruwa.

Liti ya zauna a kusa da shi, ya dafa kafaɗarsa ya ce "Haba maza, zuwa yanzu yakamata ace fa ka saba da jurewa, ka yi haƙuri"

Viper ya kalli liti ya ce "A ganinka ragwancina ya yi yawa ko? Ba ka san me nake ji ba, yau da jauhar mutuwa kawai tayi Allah ya karɓi rayuwarta, zan yi mata addu'a na haƙura na dangana, sai dai zan rayu da begenta a raina. Abdullahi a kan idona fa aka kasheta, ban iya aikata komai ba, a kan cikinta na watanni tara ta faɗi, ta na kiran sunana, ba ta ji ba ba ta gani ba fa" Viper ya yi maganar cikin ƙunar rai, ya na sauke numfashi.

"Mun sani mai zamani, amma ka ƙarfafi gwkwarka, ko ita ma ta samu ta yi abin da ya dace".

Ya sauke numfashi ya ce "Wannan karon, muddin aka kuma yi mini abin da aka yi mini a baya, zan ɗauki matakin da nake ganin ya dace"

Nabila su ka fito tare da Sumayya, Sumayya cikin damuwa ta ce "To a haka za ayi shari'ar, yau ai ba a yi komai ba"

"Ba a yi wa shari'a gaggawa, mace ce mai ciki ba a san me za ta haifa ba, a sannu a ke bi, ba aikin jarida ba ne ba, jakadun yaɗa gulama kwando kwando"

Duka wasa sumayya ta kai mata, a lokacin da barrister Habib ya fito, tare da Alhaji mu'zzam su na magana.

Viper ya na cikin mota, ya na jiran Nabila su tafi, kawai ta shiga motar barrister Habib, tare da Sumayya.

Bai ce uffan ba, ya yi umarnin a ja motar su tafi.

Gidan da su ramma su ke, su ka je, Nabila ta ɗauki ramma ta ce za ta fara zuwa awo, maman ramma na matuƙar jin nauyin Nabila, dan haka ta ƙyaleta da ita.

Hatta likitan da zai yi mata awon, Abdul ne ya gaya musu wanda zai yi mata, dan kar a cutar da ita. Asibitin abokinsa ne, su na ta hira da sumaya, ramma ko uffan ba ta iya cewa, hankalinta kacokan ya na kan ya jikin Abdul, dan baban fatanta bai wuce yau ma Nabila ta kaita wurinsa ba.

Su na shiga wurin likitan, ta ga ya zuba mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi.

Nabila haushi ya kamata, ta ce "Lafiya kuwa?"

Ya ce "Ahh lafiya ƙalau, wani cikin ki ka samu kenan?"

"Ban gane ba, matar abokin ka mu ka kawo, Abdul yasar da ya ce kai za ka yi mata awo"

Ya ce "Ok Allah sarki, Abdul yasar, ai ya haɗu da larura shi ma, gashi wai ba a zuwa dubiyarsa, ai mun yi mamaki yadda aka yi ya yi aure babu labari" yayi maganar cikin kame-kame ya na kallon Nabila.

Ganin ta haɗe rai, ya sanya ya ce "Wacece matar ta sa a cikin ku?" Yayi maganar yana kallon ta ita da sumayya.

Nabila ta nuna masa ramma, ya waro ido, Ganin ƙaramar yarinya, bai matsa da tambaya ba, ya ɗauki details ɗin ramma, ya tura su gwaje-gwaje.

Bayan sun dawo ya dudduba ya ce "Ya aka yi matar likita take fama da ƙarancin jini har haka, kuma ga shi ta ce ba ta iya bacci, menene yake damunta haka?"

Ya tattara hankali a kanta ya ce "Menene yake damunki ba kya iya bacci? Ko dan doctor ba shi da lafiya ne? Ki yi haƙuri zai warware, in sha Allah. Amma dan Allah ki din ga cin abinci yadda yakamata, ki sha magungunan ki, dan kanki ya daina ciwo, kuma ki din ga isashshen bacci, idan ba haka ba, jininki zai hau ki yi jijjiga ƙwaƙwalwarki ta taɓu"

Ramma ta jinjina masa kai, yayi counseling ɗin ta sosai, Su ka yi masa godiya, har sun miƙe, ya ce "Baiwar Allah dan Allah yi haƙuri, wai ba Zahra ba ce ba matar Al'amin, da yake ce miki 'yar madara? An ce ya kashe ki, ranar da ku ka zo nan, na ce washegari za ayi inducing ɗinki, kuma yanzu na ganki a raye"

Nabila ta yi masa wani marayan murmushi ta ce "Ba ni ba ce ba"

"Yaya za ki ce mini ba ke ba ce ba? Ki na ce master fa, ya na ce miki 'yar madara. Idan za ku zo awo, har da abokansa, wani Walid da wanenen na manta sunan su, ranar har ki ke cewa ya goya ki ba zaki iya tafiya ba kin gaji. Na yi miki scanic ya ce na gaya masa da wa ɗan yake kama ke ko shi? Baki gane ni ba, doctor muktar ne fa. A tsohon asibitina fa na gadon ƙaya da ku ke zuwa".

Nabila ta yi murmushi, hawayen idanunta ya gangaro. Ta ce "Ka taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo? Twin sister na ce, ba ni ba ce ba" sai kuma ya yi shiru ya na kallonta, ya ce "Ikon Allah, Amma ban taɓa ganin identical twins da kamaninsu ya ɓaci fiye da kima ba kamar ku, amma ban taɓa sanin ta na da twin sister ba, mu na hira da su sosai. Duk da mijinta ba shi da fara'a, amma muddin yaga na ba ta kulawa ta musamman sai ya saki jiki da ni ya yi ta mutunta mini.
Haryanzu ina mamakin yadda aka yi ya kashe ta duk da irin soyyayar nan da yake yi mata, kamar ya haɗiyeta.
Ga ta da sanyin hali, komai ta ce master yarinya mai haƙuri da girmama mutane"

Nabila ta katse shi, ta hanyar cewa "Bari mu je doctor, mun gode sosai da sosai".

Sai dai su na fita, ta saka musu kuka, Sumayya ta ce "Haba Nabila menene haka? Ya da kuka kuma"

"Wallahi sumayya duk lokacin da na tuna ban taɓa ganin jauhar ba, wallahi sabon baƙin ciki nake shiga, sai dai ina jin daɗin duk wanda na haɗu da shi, halinta na kirki yake gaya mini"

Ramma ta ce "Ki yi haƙuri ki daina kuka, mu yi mata addu'a, mama na yawan gaya mini, lokacin yaya Nura ya na da rai, kullum ya je sai ya bata labarinta, har ta na ce masa ya samo mata, za ta saka Yaya Aminu ya yi masa aure. Ana faɗar kyawawan halayenta, kamar dai yadda ki ke kema"

Duk da kuka Nabila take yi ta ce "Haba, dan Allah nima ina da kirki rahama? Za a iya faɗar alkhairina idan bana raye nima, ba za a din ga cewa masifaffiya ce ni ba?"

Ramma ta jinjina kai ta ce "Ki na da kirki sosai Anty Nabila, daga ke har Anty sumayya"

"Viper fa?" Shiru ramma ta yi ta na kallonta.

A tare Nabila da sumayya suka hau dariya, Ramma ma ta ɗan biye musu ta murmusa.

Nabila ta ce "Kar ki ƙullace shi, shi ma mutumin kirki ne, zuma ne kawai sai da wuta, ki yi ta banka masa addu'a, zamu shawo kansa in sha Allah.

***
Viper ya na kwance ya na ta juyi a kan katifa, ba kalar rarrashi da ban bakin da su Walid ba su yi masa ba, amma yayi shiru bai kula su ba. Ga wani malulun takaici da ya ƙule shi, Tun bayan da ya shiga iftila'in rashin Jauhar, babu wanda yake jin rarrashin sa ya na ratsa shi, kamar Nabila, gashi saboda wulaƙanci, ta na kallonsa, ya na kallonta, amma tayi banza da shi, ta hau motar da ake fita da ita saboda tsaron lafiyarta amma ta yi burus, duk da ta na kallonsa a ciki, kuma ta san ita suke jira.

Jin takaici ya cika masa zuciya, ya sanya ya tashi ya kunna sigari, ya koma gefe ya na ta busa hayaƙi a nutse, sai dai sam ya kasa samun sassauci a ransa.

Ya lumshe idanunsa, ya na hango jauhar.

Ta kalle shi, yadda ya zuba mata ido, ta na yi wa wani mayafi aikin bead.

"Mazajena ya aka yi ne?"

Guntun tsaki ya ja ya na daga kan doguwar kujera ya ce "Gaskiya na gaji, haba ke baki san me nake ji ba ne ba, wallahi kara uku na sigari ɗaya safe ɗaya rana da dare kamar wani magani, gaskiya yayi mini kaɗan, gaba ɗaya kin takura mini rayuwa kin hanani sukuni haka ake yi, ba sai ki bari na je na sha a waje ba, idan ma ba kya so na sha a gabanki ne ba" yayi maganar yana jin haushin kansa, yadda ta kirshe shi a gida, kamar wani ɗan ta wai ba zai fita ba, hadda ƙayyade masa iya adadin abin da zai sha"

Murmushi ta sakar masa, duk da faɗa yake yi, gashi dai ba ɗaure shi ta yi ba, amma ya na zaune ya na masifa, saboda ya san ya na fita ranar ba tausa ba hira, ba zata saurare shi ba sai ta wana shi.

Ta ƙarasa gaban kujerar ta na masa murmushi, ta na kallon yadda ya wani maze ya na kumbura, ba kuma iya rashin shan sigarin ne ya sanya yake ta faɗa babu gaira babu dalili ba, period take yi shi ne abin da ya ƙara sanya shi faɗan, yake cika ya na batsewa.

Ta shafi sumarsa ta na murmushi ta ce "Manya gatan wasa, tuba nake yi, kaina bisa wuyana, ban yi hakan dan takura walwalarka da nishaɗinka ba, lafiyarka nake yi wa. Ayi mini afuwa a daure a lallaɓa da kara ukun nan, zan soya maka wainar fulawa mai ɗan karen daɗi, fanka kuwa sai ka kasheta dan kanka, panel ɗin ya samu isasshen hasken rana, ba zaka kwana cikin zafi ba, za ka samu wadatacciyar iska, a maimakon sigarinka da na hanaka, ai ka na so ko?" Tunstirewa ya yi dariya ba tare da ya shirya ba, ya janyota jikinsa ya ce "Wai ke mai wayo ko?"

Ita ma dariyar ta yi ta ce "Ai na san ba faɗan sigarin kawai ka ke yi ba, tari idan ka

Download complete TXT · Novel page