Karfe A Wuta
Chapter 138 of 167
wai haɗa shi aka yi da sauran fursunoni ba, amma gaba ɗaya ya fita daga hayyacinsa.
Ya ƙara ramewa, gashi mutum ne mai kufan gashi, saboda haka tuni gashi ya cika masa fuska. Duk da ana kula da shan maganinsa ya na samun abinci, amma ba irin wanda yake so ba.
***
Da la'asar Nabila ta tashi, ta yi wanka, ta ɗauki abin da za ta ɗauka za ta fita.
Baba Magajiya ta tare ta ta ce "Arfa, duk yadda major yake kaffa-kaffa da ku, mussaman ke yake saka miki ido da kula da ke, amma ya zuba miki ido, ki na shige da ficenki, mutanen gidan nan har da maƙwabta su na ta surutu a kan hakan, yakamata fa ki kula ki yi wa kanki faɗa".
"Baba magajiya, Abba ya san ko nan da bangon duniya zan fita, Abba ya na da yaƙinin ba zan lalace ba, ba zan yi abin da zan cutar da kaina, ko na janyo masa abin kunya ba. Kar ki manta har ƙasar ƙetare na fita na yi karatu ban lalace ba, in sha Allah ba zan baku kunya ba"
"Abin kunya na nawa kuma, banda wanda ki ke aikatawa yanzu? Kwana a in da ki ka ga dama, yawo da ƙaratan 'yan daba me ya rage kuma?"
Nabila ta kalli mama cikin nutsuwa ta ce "Hajiya mama yaushe ki ka fara damuwa da ba na kwana a gida ne? Tun yaushe ki ke yi mini fatan abin kunya? Ni ban aikata abin kunya ba, ba kuma na fatan na aikata, Nasir shi ne mai abin kunya a ƙugunsa, da ya canza mota ya gama gini, yake wadaƙa da kuɗi wanda ya wuce samunsa ba ki tuhume shi ba, Abba ya yi yinƙurin tuhumarsa ki ka hana ki ka kare shi.
Ki daina shiga harkata tun kafin na nuna wa duniya waye ɗan naki"
Baba magajiya na takaicin yadda mama ta daɗe da zubar da mutuncinta da tun Nabila na jin nauyinta ta na girmamata, har an kai ƙadamin da ta daina ɗaga mata ƙafa.
Bayan ta fita wayar Viper ta kira, liti ya ɗaga.
Ta ce "Ina mai wayar?"
"Bacci yake" ya amsa mata kai tsaye.
Ta ce "Bacci da yammacin nan, shikenan"
Rabon Nabila da gidan har ta manta, liti ta tarar da ɗan mama a tsakar gidan su na hira, amma rabin hirar ɗan mama zagi kawai yake sha a wurin liti.
Amsa sallamar su ka yi, Nabila ta ce "Ɗan mama ka yi free kenan?"
"Eh belina aka bayar ai, dama za mu tattauna da ke, nima zan iya bayar da shaida"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ina Oga?"
Ya na cikin ɗaki, ya na ta aikin danna waya.
Nabila ta yi murmushi ta shiga ta tarar da shi, ya tashi daga baccin, ya na zaune ya na ta danna tab. Gefensa duk abin sauran sigari da ya sha.
Ta zuba masa ido, ya cigaba da abin da yake yi, sai da ya kammala sannan ya kalle ta ya ce "Daga ina ki ke?"
Ta kwaɓe baki ta ce "Gida"
"Wai meyasa ba kya ji ne? Ke duk wani abu da za ki aikata, ace ba ki kyauta ba, kin san shi kuma za ki aikata. Kin sani sarai you are not safe, an kai ki in da zaki zauna, an baki wanda za su din ga fita da ke, saboda tsaronki, amma sai yawonki ki ke yi yadda ki ka ga dama, tarar aradu da ka fa ki ke yi?" Tayi shiru kamar gaske ta na saurarsa.
"Meya haɗa ki da Naja'atu Bunkure, har ku ka yi faɗa ɗazu a court, kar ki je da gayya take yi miki abin da za ki yi reacting, ta samu kafar cutar da ke"
Nabila ta ja numfashi ta ce "Ni matar nan za ta kalli tsabar idona, ta ce mini wai jinin 'yar uwata ya tafi a banza? Ban san ya aka yi ta samu labarin cewa jauhar sisterna ce ba. Da fari na fara karaya, jin yadda take zaƙulo tambayoyi a kotu, duk da na yi tsammanin hakan, amma abin da ta gaya mini, tamkar ta yi mini allura ne, jinin jauhar sai ya zame musu bala'i ya zame musu guba mai mummunan hatsari"
Ya ajiye tab ɗin ya ce "Haka ta ce Jinin matata ya zuba a banza?" Ta jinjina masa kai.
Ya numfasa ya ce "Haryanzu su na wasa da ni, daga ita har ubangidanta, daga nesa suke hangena a cikin wutar, zatonsu hannayensu za su iya jure zafin da na ɗauka su ɗaukko ni, na san abin yi"
Nabila ta gyaɗa kai ta ce "Ko ni sai na ba wa matar nan mamaki, shashasha kawai"
Yayi shiru yana juya maganar, da jin zafin abin da Nabila ta ce Bunkure ta faɗa, kamar ita aka gaya wa.
Kamar wadda aka mintsina ta ce "Yauwwa kai kuma" ya juyo ya kalleta tamkar uwar da take shirin yi wa ɗanta faɗa.
"Viper ka bani haushi, zan iya cewa abin da ka yi ya kusa fin abin da Bunkure ta yi mini" tsuke fuska ya yi ya na kallonta.
"Ai ko za ka cinye ni ɗanya sai na faɗi abin da ya kawo ni. Abbu da kansa ya je Office ya same ni, ba aike ba a kanka, ni na ce ma ya zo kotu ya din ga ganin yadda shari'ar take gudana, ya damu ya damu saboda kai, amma a gaban mutane, a gaban kowa da kowa ka yi tafiyarka ka bar shi, me ka aikata kenan? Nuna wa duniya cewar mahaifinka bai isa da kai ba ko kuwa? Kai ka ce har da bijire masan da ka yi Allah yake jarabtarka, so ka ke wani bala'in ya same mu ne a sanadin wulaƙanta iyaye?.
A cikin Alƙur'ani mai tsarki sau nawa Allah ya maimaita yi wa iyaye biyayya? Ka daina kallon ya yi maka laifi, kai sai Allah ya hukuntaka da ƙaurace masa da ka ke yi. Nan fa ni ka zaunar da ni ka na yi mini nasiha, kai meyasa ba za ka yi aiki da nasihar ba"
"Ke shut up! Kullukum ra'in, wa kullukum mas'ulun an ra'iyatihi, sau nawa Abbu yayi wannan tunanin a game da ni? Ya wofantar da mu ni da ɗan uwana, an kashe shi ya ce ni ne sila, a duniya ina cikin 'ya'ya masu tsananin ƙawazucin iyayensu.
Kin san sau nawa daga gidana kan sallar asuba nake tafiya unguwarmu, dan ayi sallar asuba a idar ya wuce na ganshi na ji ƙamshin turaren sa, saboda ƙamshin ya na tuna mini lokutan da su ka gabata mu ka rayu cikin farin ciki da son juna.
Babu nasiha tsakanina da shi, babu rarrashi sai zagi hantara da kuma kora, alhalin ina kallon ya na ta haƙilon alkinta rayuwar yaran matarsa? Ni kuma ina yawo babu sana'ar kirki da zan kula ma da matar da ya aura mini, ki na tunanin ko na fi kowane ɗa lalacewa a duniya, idan mahaifiyata na da rai watsar da ni za ta yi?. Kin san sau adadin zuwan da nake yi in da yake ya na korata, kamar wani kare, kin san cin mutuncin da ya yi mini a lokacin da na baro prsion na je in da yake, ya kore ni ya ci mutuncina wai ba ya ƙaunar ganina na kashe jauhar, me ya rage nake nema a wurin Abbu ne tun da ya furta ba ya ƙaunar ganina? Har cikin zuciyata ina son mahaifina amma ba zan ɓoye miki ba, gaba ɗaya ya sire mini, uwata da ta mutu ma Allah ya raya ni, ɗan uwana mai tausayina da aka kashe shi, shi ma Allah ya raya ni. Dan haka zan iya rayuwata ko babu Abbu. Da ya tallafi rayuwata da wataƙila duk wannan azabar ban sha ta ba a rayuwa. Ki gaya masa ya rayu da waɗanda yake so, halarta wurin shari'ata ma na yafe ya zauna ya huta, Allah zai wanke ni"
Nabila ta yi masa ƙuri da ido, har ya yi gama, idanunsa su ka yi jawur kamar an zuba masa gauta, dama ga sigari ya sha.
Ta ja ajiyar zuciya ta ce "Ni da kai ta wata fuskar tamkar jirgi ɗaya ne ya kwaso mu, amma sai dai akwai in da ƙaddarorinmu su ka sha bamban.
Vi" ta kira shi a sanyaye.
Ya kawar da kansa gefe, ya na ta sauke ajiyar zuciya.
"Ka kalle ni mana magana za mu yi"ya ƙi waiwayo wa.
Ta zagaya saitin in da ya kawar da kansa, hawaye ya cika masa ido.
"Vi dan Allah kar ka yi kuka, ka yi haƙuri, amma kasancewar ka abu mafi soyuwa a wurin 'yar uwata ina fatan har a lahira ka kasance da rahamar Allah, ban yi maka wannan maganar dan na ɓata maka rai ba, lokuta da dama sai Allah ya jarrabi bawansa kafin ya yi masa wani tagomashi na alkhairi. Dan Allah ka yi haƙuri, amma ba zan haƙura da rarrashin ka ba, a kan ka daidaita da Abbu. Iyayenmu duk da sun dace da mataye na gari, da ba su aikata wani abun ba"
Ya haɗiye wani abu mai ɗaci ya ce "Tashi mu je na mayar da ke barrack, na san kan ki koma duhu yayi, kuma idan na sake ganin kin zo nan sai na ɓallaki na gaya miki"
"Ba zan sake zuwa ba, but smile mana dan Allah, kar mu tafi ka na huci, na ga ka ɗauki zafi da yawa"
Viper ya sake tsuke fuska ya ce "Tashi mu tafi" kamar yarinyar goye, ta maƙale kafaɗa ta marairaice ta ce "Dan ka yi murmushi Vi, ba na son wannan mood ɗin naka" tashi ya yi tsaye, ya ɗaukko face mask ɗin sa ya saka su ka fita.
Su na tafe a hanya, ta na ta yi masa hira, tun ya na basarwa har kuma ya saki jikinsa, har da yin murmushin.
Nabila ta sha faɗa wurin madam Halima, saboda rashin jin ta da taurin kai, na yadda take wasa da rayuwarta.
Madam Halima babu hausa sosai, gashi wai a dole sai ta yi wa Nabila faɗa, sai da Viper ya yi murmushi, dan Nabila ba ta san faɗa, ta haɗe rai.
***
Abdul ya cika sati uku a gidan kaso, amma duk ya firgice kamar ya kwashi shekaru a tsare, duk da halin da yake ciki, bai hana shi ganin ramar da matarsa ta yi ba, ga cikinta ya fara tasawa babban fatansa shi ne Allah ya sa tun da an ce za ayi masa sassauci ramma kar ta haihu ya na tsare.
Ba tare da sake yin wani dogon jawabi ba, kasancewar ya riga ya amsa laifinsa, lauyoyin sa su ka nemi a ƙara sassauta masa, tun da ya amsa laifinsa ba tare da ya wahalar da shari'a ba.
Alƙali ya yanke hukuncin a yi wa Abdul bulala ashirin, a kai shi gidan yari tsawon watanni biyar, da aiki mai wahala, sai kuma tara ta zunzurutun kuɗi naira miliyan biyar.
Kasancewar a chamber alƙali ake shari'ar, ba a cikin kotu ba, mahaifiyar Abdul ta marairaice a kan ya ƙara sassauta masa.
Alƙalin ya dubeta ya ce "Madam, mutanen nan fa sun yi muku adalci, da ba kotun shari'a su ka kawo ƙarar nan ba, ke kin san laifukansa sun fi ƙarfin hukuncin da aka yi masa, dan haka babu wani sassauci ko ɗaga ƙafa da za a kuma yi masa. Ku je ku yi ta haifar yara babu tarbiyya ku na sakin su a cikin al'umma su na fasadi a bayan ƙasa, ba tare da kun damu ba, iya yarinyar da ya ketawa haddi ba 'ya ba ce? Tarar ma idan ba zaku biya ba, sai ya je yayi zaman shekara bakwai a gidan yari, hakan ya zama izina da kuma darasi ga saura"
Ana gama zaman, Nabila ta janye ramma daga kotun, aikuwa su na tafe ta na kuka, mussaman jin za a dake shi, ga kuma aiki mai wahala an ce yayi a gidan yarin.
A waya Nabila ta kira Viper ta ce masa ta tafi da ramma barrack, washegari ta mayar da ita wurin mama, saboda ta ɗan samu nutsuwa.
Mama kuwa duk da ba haka ta so ba, amma ta samu sassauci daga baƙin ciki da kuma raɗaɗin da zuciyar ta take yi mata.
Ganin gigicewa da tashin hankalin da majaifiyar Abdul ta shiga, maman ramma ta ce "Kamar haka, haka na shiga tashin hankali, lokacin da ya ketwa 'ya ta haddi, kuma na rasa mai taimakona, Alhamdilillah ko iya haka na samu raguwar wata azabar da nake ji".
***
Rahama ta kasa bacci, ta kasa cin abinci, nan Nabila ta ƙara tabattar da soyayya bala'i ce wani lokacin. Duk wannan bala'in da ake yi a kanta, ita hankalinta ya na kan mijinta.
Haka Nabila ta yi ta aikin rarrashinta. Washegari ta kashe wayoyinta, ta ɗauki ramma aka kai su prison.
Sai dai aka sanar musu, Abdul ba zai iya fitowa ba, Albarkacin ID card na aiki, da yadda Nabila ta fara tashe, aka ba su damar shiga cikin prison har ɗakin da Abdul yake.
"Subhanallah" ramma ta furta, ganinsa a kwance ruf da ciki, bayansa a farfashe saboda bulalar alƙali da ya sha.
Ta ƙarasa in da yake da sauri, ya ɗago da kyar, jikinsa ya na karkarwa saboda zazzaɓi, Abdul zai iya cewa da wayonsa babu wanda ya taɓa dukansa, amma yanzu ga shi ya sha duka, hakan ya haifar masa da zazzafan zazzaɓi.
"Abdul" ta faɗa a raunane ta na kuka.
"Rahama zafi, bayana kamar ana ƙona ni"
"Ka yi haƙuri Abdul, dan Allah ka yi haƙuri, ban ma san me zan ce ba" tayi maganar cikin kuka.
"Ai an sassauta mini, ta wani fannin na ji daɗi da wuri zan fito in sha Allah, ni zan karɓi haihuwar ki da kaina" yayi maganar yana kwanciya a jikinta.
Ta haɗiye yawu mai zafi, ta ce "Abdul da sun bi ta tawa, da na daɗe da furta musu na yafe maka, babu yadda mu ka iya, ƙaddaramu ce ta zo a haka. Amma ka yi haƙuri na yi maka alƙawarin duk rintsi idan ka fito in sha Allah mu na tare"
Ya ɗago da kyar ya kalle ta ya ce "Are you sure, kar ki saka mini rai fa"
"Na tabattar in sha Allah"
"Wallahi ina sonki sosai rahama"
Nabila ta na tsaye ta na kallon ikon Allah.
****
Viper ya na ta shiri zai je wani aiki na musamman cikin sirri, wayarsa ta fara ringing, bai damu da duba waye ba kawai ya ɗaga.
"Aminu Viper"
"Ma'aruf Indabo" ya amsa masa kai tsaye.
Indabo ya ce "Ban yi mamakin saurin ɗaukar muryata da ka yi ba, kai a nan ka dage ka haɗa kai da kankarofi a kan lallai sai kun ga bayana, yanzu ka kafe kai da fata, saboda yar matsiyata ƙanwar Nura guduma, an kai mini ɗa gidan yari, to bari murna karenka ya kama Zaki mai zamani. Za a sake ni daga ɗaurin talalar da aka yi mini, sannan ka shirya abubuwan da ka iya biyo baya da ba ka yi tsammani ba. Za a ci gaba da zaman kotu a kan shari'ar matarka, amma ka sani reshe ka iya juyewa da mujiya, ka tsammaci abin da ba ka taɓa zatonsa ba a kotu".
"Gargaɗi ka ke yi mini? Ko alhinin kar asirinku ya tonu a kotu, idan gargaɗi ka ke yi mini kar na kama sunanka, ka kwantar hankalinka, ai an san da wuyan biri ake ɗaure shi a ƙugu, kai tsaye waɗanda su ka kashe matata kawai za a hukunta, sannan ka din ga sassauta lafazinka idan ka na magana da ni, saboda ni ke da makami mai linzamin ƙarasa tarwatsa rayuwar iyalinka, idan ka ƙi ji ba ka ƙi gani ba. Na san babu abin da za ayi maka ko da kuwa an ambaci da saka hannunka a ta'addancin da aka yi mini. Zan yi dragging ɗin ka zuwa kogon da ramina yake ne, na yi ta azabtar da kai da dafina, zuwa abin da hali zai yi. Amma ina P.A ɗinka yake ne? Kwana biyu ba a ganin gilmawarsa yakamata ka yi tunani a kan wannan" ƙit ya kashe wayar.
Ayshercool
08081012143
94
Viper ya ɗan ja lokaci ya na kallon wayarsa, ya na tunanin mai indabo yake shiryawa, da har ya samu ƙwarin gwiwar kiransa ya na yi masa surutan iska. Kodayake bai kamata ya ce surutan iska ba, domin kuwa a rashin imani irin na indabo babu abin da ba zai iya aikatawa ba.
Lambar Nabila ya yi ta kira, amma a kashe ba ta shiga, dan haka ya haƙura ya ci gaba da shirin fita.
Ramma ta yinƙura ta ce "Bari mu tafi, na san ba dan albarkacin Anty Nabila ba, babu yadda za ayi a bari na shigo har na ganka, Allah ya baka lafiya ya baka ikon cin jarrabawar nan. Ba an hukuntaka da an tsaneka bane ba, ina fatan tuban da ka yi ya zama taubatan nasuha, kuma wahalar nan Allah ya sa ta zame mana kaffara baki ɗaya mijina" ya ɗago ya kalleta ya ce "Kai, rahama baki taɓa kirana da sunan da na ji yayi tasiri har cikin zuciyata kamar yau ba, da har nake jin eh lallai kin yafe mini ba. Yanzu kin yadda ni mijinki ne?"
Ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Ai zamantowarka mijina tuntuni na yarda da wannan, da ban yadda wannan cikin ya samu ba" murmushi ne ya suɓuce masa, ta tashi ita ma ta na murmushin, ta fita daga ɗakin har ta fice ya na daga ruf da ciki ya na kallonta, duk wannan wahalar da yake sha, ko sau ɗaya bai ji wani abu daga son da yake yi mata ya ragu daga zuciyar sa ba.
***
Nabila ta biya ta ajiye ramma a gida, sai dai ramma ta fuskanci mama ta sassauta fushin da take yi da ita, saboda ta ɗan samu sassauci saboda hukunta Abdul da ta ga an yi.
Barrack Nabila ta koma, dan ita kanta ta ɗan tsorata da musayar yawu da su ka yi