Karfe A Wuta

Chapter 14 of 167

gane ba, interview zaku yi, ko kuma tattaunawa a kan cigaban da ya kaiwa mazaɓarsa?".

Sumayya ta ce "Bari kawai nabila, dama murtala ne yake program ɗin, kuma baya nan aka ce na yi, ina ta murna amma gwiwata tayi sanyi, kuɗi ya biya sosai za ayi program ɗin, amma a ɓoye campaign kawai zai yi, kin san zaɓe ya fara ƙaratowa"

Nabila ta ce "Taɓ abun tsiya, toshi da ƙosan rogo, wannan kawai tambaya da amsa zaku yi, haka yaya Nasir yazo yana gaya mini wai ƴan daban da ya kama, an kira shi daga sama wai ya sake su, abun babu daɗin ji, naga alamar sai mun zama jan wuya mun zage a kan ayyukanmu, yanzu dai ki ƙarasa, zamu yi waya zan shiga wata unguwa, muna da client zan duba wata shaida ne"

Sumayya ta ce "To shikenan, mu yi waya ko kuma ni sai in zo gida"

"Ok bye" ta tsayar da mai adaidaita sahun ya tsaya ta sauka.

Wata adaidaita sahun ta tsayar ta hau, ta tafi unguwar ƙofar na'isa.

Shagon nan da ta taɓa tsayawa ta sai lemo, nan ta tafi.

Cikin mutuntawa, mai shagon ya karɓeta suka gaisa, da yake ya gane ta  ya ce "Hajjaju kin dawo unguwar ta mu kenan?"

Ta ce "Eh malam, da wata alfarma na zo nema ne"

Ya tattara hankalinsa a kanta ya ce "Ok, ina jin ki"

Ta ce "Last da na zo, wannan mutumin da na tarar a nan, na ce masa ya taimaka mini ina son na haɗu da aminu Viper, amma ya kwatanta mini wani wuri, wai lungun iraƙi, suka kusa kasheni"

Mai shagon ya zare ido ya ce "Viper kuma? Ke menene haɗinki da shi?"

"Ɗan uwana ne, tun da ya fito daga prison, ban sake ganinsa ba"

Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Allah ya rufa miki asiri da ba su kashe ki ba, kin san yadda suke nemansa ruwa a jallo kuwa? Idan suka riga jami'an tsaro kama shi, kashe shi za su yi.
Kuma a iya sanina, babu wata mace da Viper yake da alaƙa da ita, dan haka ki rufawa kanki asiri, ko sunansa kar ki fiye ambata a cikin unguwar nan"

Nabila ta waiwaya bayanta, babu kowa a wurin, ta ɗebo kuɗi ta ajiye masa ta ce "Waye shi, ko a taƙaice ne ka gaya mini wanene shi, a ina zan same shi"

"Ki ka ce ɗan uwanki ne?"

"Ka manta kawai, ni dai ka taimaka mini"

Yayi ajiyar zuciya sannan ya ce "Hajiya, na tabatta kina da alaƙa da hukuma, gaskiya ina jin tsoro, ina da iyaye da ƙanne, da nake taimakawa, ko basu saka an kashe ni ba, sai an yi mini illa, muddin na gaya miki wani abu, daga baya su gano ni na faɗa"

Nabila ta ce "Manta da batun hukuma, ba ni da alaƙa da ita, kuma babu yadda za ayi na bar wata ƙofa da zata nuna ka gaya mini wani abu, taimakona zaka yi, idan kuɗin sun yi kaɗan zan ƙara maka wallahi".

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Aminu sun taɓa zama a unguwar nan, bayan ya zama ɗan daba na iraƙi ake ce masa ko kuma mai dogon zamani, ƴan sanda ne suka saka masa Viper, saboda rashin tsoronsa, da azabar kwarjinin da yake da shi, gagararre ne sosai, kuma dealer ne na miyagun ƙwayoyi. Kuma matasan yaran nan marasa ji, suna jin maganarsa fiye da ta iyayensu, ba zan iya gaya miki sama da haka ba, amma zan kwatanta miki, in da zaki samu wani yaronsa, amma dan girman Allah, kar ki bari sunana ya fito, ki taimaka"

Nabila ta ce "Na yi maka alƙawarin babu wanda zai ji".

Ya ce "Idan magariba ta yi, ki je tal'udu, hannunki na hagu, akwai wanda yake zuwa a kan babur ya zauna yana sayar da katin waya, ya saka facemask.
Ba katin yake sayarwa ba, balance yake karɓa na yaran da suke rarrabawa tabar wiwi, ƙananan dealolin su, da suke yi sayar musu da katan maye, yaron Viper ne makusantansa ne sosai, amma dan Allah ki riƙe alƙawari".

Nabila tayi ajiyar zuciya ta ce "Zan riƙe in sha Allah, na gode sosai". Ta sake ƙara masa kuɗi.

Fita daga shagon, tana jin kamar ta riski fiye da rabin matsalarta, idan Allah ya sa ta yi wa DSP hanyar kama aminu, atleast ta taimaka masa.

Babu tsoro ko tunanin komai, ta ƙallafawa ranta ko ta halin ƙaƙa za ta yi nasara.

Honorable Ma'aruf indabo, yana kashingiɗe a katafaren falon sa, hannunsa riƙe da waya ya kara ta a kunnensa, yana jiran a ɗaga.

Muryar madaki ce ya amsa da "Sai mai gida"

Indabo ya numfasa ya ce "An sakar maka yaran?"

"An sake su mai gida"

"Yayi kyau, ka fara ƙoƙarin yi mini aikina, zan shiga Abuja wannan satin, ka tabattar aikin nan ya kammala kan na dawo"

"Baka da matsala oga"

"Yauwwa, ya batun Aminu?"

Madaki ya ce "Wallahi duk wata kafa da za a bi wurin samunsu, ya tsosheta, jiya wani ɗan sanda yake tambayata wai idan na san in da yake"

Da sauri indabo ya tashi zaune ya ce "Waye shi? Meyasa yake tambayarka?"

"Wallahi ban sani ba, amma dai shi ne ya kama mini yara, Nasir mai tama na gani a jikin kakinsa"

Indabo ya jinjina kai ya ce "Shikenan zan bincika"

Wata mata ce ta buɗe ƙofar ɗakin, ta shigo, hannunta riƙe da ƙaramin plate ɗauke da tuffa, ta ƙaraso kusa da shi ta zauna.

"Ya dai na ganka kamar a tsorace?"

Indabo ya ce "Madaki ne ya ce mini wai wani ɗan sanda yana tambayarsa Aminu jiya, dole na saka a bincika waye".

Cikin takaici ta kalleshi ta ce "Au da kanka ka ke waya da ɗan daba, abun da ya faru tsakaninka da Aminu bai zame maka izina da darasi ba, kana ganin yadda ya zame mana barazana, ɗan tahaliki ɗaya ya hanaka sukuni".

Ya ce "Na san abun da nake yi bilikisu, komai a lissafe nake yin sa, ai na yi kuskure na farko, ba zan yi na biyu ba. Aminu kuma ina da tabbacin akwai wani abu a ƙasa, kuma zan kawar da shi, kafin ya buɗe bakinsa".

Ta ajiye trayn hannunta ta ce "Yanzu ya ake ciki da maganar Abdul, haryanzu Naja'atu ba ta ce komai ba?"

"Nima ita nake saurare, na fiki damuwa ma da wannan lamarin, amma dole ki ja masa kunne, na fara gajiya da rashin mutuncin sa, ba zai ɓata mini siyasata a banza ba, ina ta fafatuka a kai, ya je ya yi abun da ƴan adawa zasu samu abun faɗa a kai ba".

Ɓata fuska ta yi ta ce "Kai ma ɗanka ne ai, ka ɗauki matakin da ya dace da shi" ta ƙarasa maganar ta tashi ta bar masa ɗakin.

Yayi guntun tsaki, ya ɗauki wayarsa yana kiran wata lamba.

"Honorable, Allah ya taimake ka"

"P.A ya turo muku list ɗin tambayoyin da zaku yi mini ko?"

"Eh ya turo, mun kuma bawa mai gabatarwar da ka buƙata ta dudduba"

Ya jinjina kai ya ce "Ina fatan yarinyar da na ce maka ce?"

"Eh ita ce Yallaɓai"

Ya ce "Yayi khau, ku turota gidana, ta zo ta yi recording ɗin a nan, ba zan samu zuwa nan ayi program ɗin ba"

Cikin damuwa manager ya ce "Ina fatan ba wani laifin ta sake yi ba ranka ya daɗe?"

Indabo ya ce "Da zan hukuntata, tun laifin da ta yi mini na farko, da tuni na hukunta ta, wani abu mai muhimmancin gaske na gani a tare da ita, da nake son tabattarwa"

"Subhanallah, dan Allah yallaɓai ka yi haƙuri, idan laifi ta yi, ina nema mata afuwa ".

"Jamilu, ka turo yarinyar nan gidana, tayi recoding ɗin program, kar ka sake yi mini musu". Ya kashe wayar ya ajiye.


Yanayin yadda zuciyarta ke tsananta bugawa ne, ya sanya ta din ga karanto duk addu'ar da ta zo bakinta.
Sai dai ba ta ji za ta iya janye aikata abun da tayi niyya ba.
Nesa kaɗan da in ya kwatanta mata ta je ta tsaya, sai dai tun kafin duhun magariba ya gama rufawa, mutumin da aka kwatanta mata ya zo ya kafa teburinsa na sayar da katin waya, ya nemi wuri ya zauna.

Ta ɗan jima a tsaye, tana kallon sa, sannu a hankali ta fara tunkarar in da yake zaunen, tana addu'a a zuciyarta har ta ƙarasa in da yake.

Kafin ta yi magana, wani matashi ya rigata ƙarasawa, suka gaisa ya miƙa kuɗi, aka bashi wata baƙar leda.

Ta tattaro jarumtarta ta yi sallama ta ce "Sannu malam" ya ɗaga kai ya kalleta, sai dai kamar ya razana da ganinta.

Ta sake cewa "Sannu malam"

"Yauwwa" ya amsa da kakkausar muryar sa, yana cigaba da ƙare mata kallo.

"Dan Allah kaya nake so" ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, ya ce "Wane irin kaya?"

"Irin wanda ka ke sayarwa, amma ni direct nake son na din ga karɓa"

"Jami'ar tsaro ce ke?" Yayi maganar yana cigaba da kallonta

Nabila ta ce "Jami'an tsaron ai sun san da zamanka a nan, ina so ka haɗa ni da Aminu viper ne"

Waro ido yayi ya kalleta ya ce "Ke! Yayi maganar yana zazzaro mata ido"

Tayi ƙasa da murya ta ce "Kar ka ɗaga murya, ka taimaka mini, ɗan uwana ne, tun da ya fito daga prison ban sake ganinsa ba"

"Ƙarya ki ke yi wallahi! Ban da ke mace ce, da namiji ce ke, wallahi sai na ciro hanjinki waje na zubar a titi, bar wurin nan, kafin na karya ki"

Nabila ta marairaice ta ce "Ba ka da tabbacin ƙary.....

"Ki bar nan, kafin na tsarga ki biyu da makami" ta ja da baya a hankali, tana kallon sa.

"Ki bar nan na ce" ta juya da ɗan sauri, cikin tsoron yadda ya hayayyaƙo mata.

Wayarsa ya ɗaukko ya kira Walid yana huci, cikin sa'a ya ɗaga.

Walid ya ce "Maza ya ne?"

"Wata yarinya ta zo neman boss, wai ƴar uwassa ce, anya ba a fara bibiyar sa ba? Idan ba haka ba, yaya aka yi ta san na sanshi".

Cikin mamaki walid ya ce "Kar dai yarinyar da gagare ya ce mini ta je dabar madaki neman sa?"

"Ban sani ba, amma zan so ka ganta, ka ga wani abun mamaki, mai ɗaure kai, dan na kusa guduwa wallahi"

Walid ya ce "Kamar yaya?"

"Ka ga, ina hangota haryanzu, zan bita na yi mata magana, zan ce ta dawo gobe da safe, zaka ga abun da na gani"

Walid ya ce "Kai liti, ka tabatta ba matsala?"

"Babu, kawai sonake ka ganta"

"Shikenan, idan ka tashi yau, ka shiga area wurin dila, ya baka balance, idan na zo zan karɓa"

"Sai da kai, an gama"

Nabila na shirin hawa ɗan sahu, ta ji an yi fito a bayanta, ta waiwaya ta ga liti a tsaye.

"Zo mana" yayi maganar yana kallonta.

Kawai zuciyarta ta raya mata, ko wuƙa zai soka mata.

"Ki zo mana" yayi maganar cikin tsawa.

Cikin rauni ta ce "Dan Allah ba wuƙa zaka soka mini ba?"

Ya ce "Ke da kashe ki zan yi, kin isa na bari ki bar wurin nan, shawara na canza, ban san alaƙar ki da shi ba, dan haka zan haɗa ku"

Da sauri ta ɗan ƙarasa gabansa ta ce "Dan Allah, amma na ji daɗi na gode sosai da sosai".

"Mu haɗu a nan, gobe ƙarfe biyar na yamma, zan haɗaki da wanda ya san in da yake, amma wallahi ki ka yi wani abu na rashin gaskiya, kin san sauran"

Nabila ta ce "Babu wani abu na rashin gaskiya da zan yi, na gode yayana Allah ya saka da alkhairi"

Ya ce "Ke ki nemawa kanki tsari, da na zama yayanki, ware ki bar nan"

Hamadala ta yi, tare da jin kamar wata gagarumar nasara tana tunkarota.

Ƙwas-ƙwas takalminta yake bayar da sauti a kan tiles ɗin wurin, sai sauri-sauri take yi ta ƙarasa ofishin manager.

Da sallama ta shiga, ya ɗago ya amsa mata, ta ɗan risuna ta ce "Afuwan sir, na tsaya ƙarasa editing ɗin news ne, shiyasa ban zo kiranka da wuri ba".

"Bakomai sumayya, sannu da ƙoƙari, ina yabawa ƙoƙarin ki da himmarki".

Tayi murmushi ta ce "Na gode sir"

"Ina sisternki, young barrister ne? Nabila ko, kwana biyu ba ta kawo mana ziyara ba"

Sumayya ta yi murmushi ta ce "Ayyuka ne suka yi mata yawa, amma ko ɗazu muna tare"

Ya ce "To Allah ya taimaka, yauwwa dama batun program ɗin nan ne, honorable ya ce ba zai samu zuwa ba, sai dai aje can gidansa ayi recording program ɗin, dan haka driver zai kai ki, a can badawa gidansa yake, za a kai ki ranar Friday, sunday zai yi tafiya ki yi recording program ɗin"

Cikin mamaki da sanyin jiki, ta ce "Gidansa kuma sir? Amma ai yau murtala za su dawo, tun da su maza ne sai su je....

Ya ɗaga mata hannu ya ce "Look sumayya, ya zama dole ki je, murtala ba zai dawo yau ba, honorable ba wani abun zai yi miki ba, gidan da yake zaune da iyalansa ne, recording ɗin program kawai zaku yi. Idan kuma ba zaki yi ba, you know the consequences"

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi, ta ce "Allah ya kaimu" ta juya a hankali ta fice.




₦500 ne, via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Special wanda ba sa son group 1k.
Wanda za su jira document, idan an kammala 1k ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
wannan layin
Sai a tura mini shaidar biya ta
08081012143 ko 07063065680


Ayshercool
08081012143
[7/25, 1:18 PM] null: *ƘARFE A WUTA*



AREWABOOKS: ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
What's app: 08081012143



https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g




11


Bayanta manager ya bi da kallo, ta bashi tausayi sosai da sosai, sai dai yana addu'a Allah ya sa kar honorable ya cutar da ita.

Kamar ɓarawo, haka walid ya diro a tsakar gidan, maimakon ya biyo ta ƙofa, ɗan mama yana zaune yana shan sigari a ɗan tsakar gidan.
Bai kula shi ba, ya wuce ɗakin da viper yake, sai dai ya duba baya ciki.

Walid ya dawo, ya kalli ɗan mama ya ce "Ina Viper?"

Ɗan mama yayi dariya ya ce "Har ka gama fushin, ka dawo?"

Walid ya ce "Kai ka san ba zan iya ba, ƙular da ni yayi ne, ina yi masa uzuri ne kawai na san kansa ya taɓu, yana ina?"

"Baya nan" ɗan mama ya bashi amsa kai tsaye.

"Kamar yaya? Ina yaje?"

Ɗan mama ya zuƙi sigarinsa sannan ya ce "Ni na isa na hana shi fita ne? Ko kuma na ce sai ya gaya mini in da za shi? Da dai kai ne zai iya ɗaga maka ƙafa"

A fusace walid ya ce "Dan me zaka bari ya fita?"

"Au so ka ke na hana shi, ya karya ni, ko ya illata ni, kaɗaici ne ya dame shi, gidan babu kayan caji, sai na hayaƙi, shi ne ya fice. Yauwwa dama ina son gaya maka, ka daina kwashe kayan cajin nan gaba ɗaya, idan wani yayi rawa an bashi kuɗi, kai idan ka yi, na jaki zaka ci a hannunsa wallahi"

Cikin takaici Walid ya ce "Wai so ka ke sai ya kashe kansa ne? Kana kallon allurar nan ba ta ɗaukar sa, farar ƙwaya ma fa ba ta yi masa komai, sai rikita masa ƙwaƙwalwa, idan ya haukace fa?" Walid gani yayi ɗan mama yayi tsuru-tsuru, yana rarraba ido, dan haka ya waiwaya bayansa, Al'amin ya gani a tsaye a bayansa.

Bai kula su ba, ya zo ya raɓa walid ya wuce.

"Master"ya kira shi.

Al'amin ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, idanunsa sun yi ja, jijiyoyin kansa suka miƙe ya ce "Me na ce maka a kan kirana da haka?"

Walid ya ƙarasa kusa da shi, dai-dai kunnensa, ya yi masa raɗa.

Viper ya kalli Walid ya ce "Kasheni ka ke so ka yi sannan hankalinka ya kwanta ko Walid?"

Walid ya ɗage kafaɗa ya ce "Duk yadda ka gani"

Viper ya hankaɗe shi gefe, ya wuce ɗakinsa, ya rufe ƙofa.

Walid ya bishi ya leƙa ta taga ya ce "Me zaka yi ka rufe ƙofa?"

Leda ya ciro daga aljihunsa, ya haɗa allura a sirinji, zai yi wa kansa.

Walid ya ce "Al'amin, ba zaka daina yi wa kanka allurar nan ba ko? Ba za ta yi maka ba, ka haƙura mana"

Al'amin ya tashi, ya je ya ja tagar ya rufe, ya bar walid a waje yana surutu.

Sumayya kuwa tun da ta koma gida, mama ta lura da yanayinta, sai dai ta yi zaton ko gajiyar aiki ce, amma har dare ba ta walwala.

Dan haka ta magantu, ta ce "Ƴar mama, wai ko babu lafiya ne?"

Sumayya ta ce "A'a lafiyata ƙalau?".

"To faɗa ku ka yi da mutuniyar ne?"

"A'a bamu yi faɗa ba mama"

Ba ta gaza ba ta sake cewa "To ko wurin aikin ne suka yi miki wani abun?"

Sumayya ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Hajiya mama, bamu yi faɗa da ƴar ki ba, lafiyata kuma ƙalau, kawai kin san yanayin aikin namu ne, kayi ta ganin abubuwa na ban tausayi daban-daban".

Mama ta ce "Ai baku ba sumayya, mu ma masu saurare, kusan kullum cikin zullumin kunna radiyon muke, sai dai ku ƴan jarida ku ne idonmu, ta bakinku kawai muke jin wasu labaran da jin halin da duniya ke ciki. Allah dai ya saka muku da alkhairi ya tsare mana ku baki ɗaya, daga ke har Nabilan aikin tainakon al'umma ku ke yi, Ubangiji Allah ya tsare ku ya kawo mazajen aure na gari"

Sumayya kamar ta gaya wa mama, abun da aka umarceta a wurin aiki, amma ta san hankalinta tashi zai yi, zata iya hanata aikin ma, kuma Allah ne gatansu aikin nan ne gatansu, dan haka ta ja bakinta tayi shiru.

***

Sannu a hankali barrister Naja'atu take bin titin ƙauyen, sai tsaki take yi saboda yadda garin yake babu kyakkyawar hanyar shiga. Sai uwar ƙura da kwazazzabai a hanyar.
A hankali

Download complete TXT · Novel page