Karfe A Wuta
Chapter 141 of 167
ya ce "Ni ku matsa mini, na yi sujudar godiya ga Allah, gabasa ake kallo ko daga nan Arewa ma zan iya yin ta? Daɗina da kai wasu lokutan kana da wani ɓoyayyen rauni, da ya kan kusa cutar da kai Viper. Matar da ta rufe muku ƙofa, aka hallaka ɗan uwanka, shekarun da suka gabata, sharrin da ta aika ne, ya dawo mata kanta a kan ɗanta ita ma, cin amanar da ta yi, ita ma Allah ya ɗanɗana mata, Allah Allah ne, dan haka babu ruwanka".
"Liti kai mahaukaci ne? Ko kaza aka kashe wa mutum bisa zalunci, abin tashin hankali ne, mai rai a sassara shi, a saka a buhu, a kai a yar fa"
Walid ya ce "Yanzu idan ka je gidan me zaka yi musu? Salon ta ce kai ne ma ka saka aka kashe shi, ka san halinta ai, babu in da zaka je, taje Allah ne ya kamata".
Fafur suka hana Viper fita, ya koma cikin ɗaki, ya ɗaukki wayarsa ya kira Nabila.
Ta ɗaga tayi sallama ta ce "Vi ya ne?"
"Amm ki tambayi ƙawar nan taki Sumayya, ko labarin kisan da aka yi wa wani yaro Abba a unguwarmu, ya je mata dan Allah ina son a ɗan bikcika".
Ta ce "Subhanallah, ban sani ba, bari na kirata na ji"
"Yauwwa yi sauri, dan Allah idan gaske ne, Joseph ya kai ku station ɗin da case ɗin yake hannunsu, ku jiyo mini ya ake ciki?"
Ta ce "An gama ranka ya daɗe, amma ya sunan wanda aka kashe ɗin?"
"Ɗan matar Abbu ne, sunansa Abba idan ya kama ku je gidanmu, ku ƙara tabattar mini".
Mamki ya cika Nabila, amma ta ɓoye mamakin nata ta ce "In sha Allah zamu je" ya katse wayar cikin matsanancin jimami.
Walid ya ce "To wai meye amfanin hakan da ka yi? Meye naka a ciki Viper?"
Al'amin ya girgiza kai ya ce "Yaya ku ke abu kamar ba tsoffin 'yan hannu ba? Yanzu faɗan ɗaukar fansa zai ɓarke a tsakanin unguwannin, kuma ina gudun abin da ya faru da ni, ya sake faruwa a kan wani, ina son na bibiyi abin a kama waɗanda suka kashe shi, na tabattar da an hukunta su, domin ya zama izina. Kuma ko ba komai, musulmi ne, kuma mahaifina ne ya riƙe shi, an yi masa kisa mai muni, abin da taɓa zuciya"
Sai kuma suka yi shiru, liti ya ce "Haka ne, maganarka dutse, amma gaskiya ba zaka je ba, ba ruwanka daga nan kayi masa addu'a, idan komai ya lafa sai a san abin yi"
Viper ya ja tsaki, tare da girgiza kai.
Walid ya ce "Menene kuma?"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Walid, babu wani alfanu ko jin daɗi a rayuwar daba da shaye-shaye, duk kalle mu dai, babu wanda wannan rayuwar ta amfana da komai, face tabon baƙin ciki da tsantsar nadama. Akwai tarin ƙalubale, muddin za a ci gaba da tafiya a haka"
Walid ya ce "Haka ne, sai fatan Ubangiji Allah ya yafe mana ya shiryar da mu baki ɗaya".
Kamar yadda Viper ya buƙata, Nabila tare da Sumayya, suka tafi binciken da ya ce, jami'an tsaro suka tabbatar da faruwar Al'amarin.
Sumayya ta je har gidan su Viper, kamar sai dai ba su tafi tare da Nabila ba.
A rumfar zaman makoki, ta hangi Abbu, ta ƙarasa tayi musu gaisuwa, Abbu ya taso, suka sake gaisawa, ya ce "Sumayya ya aka yi ne?"
"Nabila ce ta kirani, Viper ya ce lallai mu zo a tabattar da abin da ya faru, ban san dai dalilinsa na yin hakan ba"
Ya ɗan yi shiru ya ce "Shi da kansa?"
Ta ce "Eh" nan ya sake yi mata bayanin abin da ya faru, maganar da yake yi mata ma, mahaifiyarsa na Asibiti allurar bacci kawai ake yi mata, tamkar zata haukace, saboda yadda aka kawo gawar Baba, jikinsa ya fara zagwanyewa, jikinsa ko ina sara, hannunsa ma daban aka kawo shi.
Sumayya ta tattara rahoton abin da ta samu, ta sanarwa Nabila, kuma ta samu na sanarwa a gidan rediyo.
Sosai batun ya ɗauki hankalin jama'a, Duk ita kanta Nabila, sai da ta ce Alhakin Viper ne, amma ta kaɗu matuƙa jin irin kisan tozarcin da aka yi wa Abban duk a silar ƙwaya. Kamar yadda ta wallafa a shafinta, suna nan suna zuba ido, su ga matakin da jami'an tsaro za su ɗauka, wurin cafke waɗanda suka aikata laifin.
****
Rahila dai abin da ya samu Abba ya zame mata masifa, ta daina magana ta daina cin abinci, ba ta gane kowa sai kuka, idan aka jima kuma ta yi ta kurma ihu, tana kururwa tana kiran ɗana Abba, Abba bai mutu ba, sai dai a daddaneta ayi ta yi mata allurar bacci.
Haka Shahida zata rungumeta, tayi ta kuka, ga Amira ta shilla ta yi nata wuri, tun da Abbu ya ce ba zai karɓeta a gidansa ba.
*****
Yau da yamma Viper ya je barrack wurin Nabila, sai dai tun kafin yayi magana, ta fuskanci matsananciyar damuwa a tattare da shi.
Ta ce "Vi meyafaru ne?"
"Abin da ya faru da yaron nan Abba ne ya yi bala'in tsaya mini Abla"
"To yaya za ayi, sai addu'a, amma in ganin kamar har da hakkinka abin da ya same su"
Viper ya girgiza kai ya ce "Ba na tunanin haka, haka kurum abin ya tsaye mini. Shikenan dai makomar ɗan shaye-shaye ko ɗan daba. Ko ka kashe ko a kasheka, ko a kashe maka wani makusancinka, da zai bar maka mummunan tabo a zuciya, babu riba sam a wannan harkar".
Ta gyaɗa kai ta ce "wannan haka yake, amma ka godewa Allah da ya sanya ka farga da wuri, har ka ke ta ƙoƙarin tuba ga Allah, ina fatan Allah ya karɓi tubanka"
Ya amsa da "Amin ya Allah, kuma kema ina yi miki godiya sosai Abla, kema kin bayar da gudummawa sosai da sosai a cikin rayuwata, kamar yadda sisternki jauhar ta yi mini, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi"
Tayi murmushi ta amsa da Amin, duk wannan basar da abubuwan da yake yi, ashe yane sane da duk alkhairin da ake yi masa.
"Amm ya maganarmu ta zuwa asibiti, me ka yanke a kai?"
Ya jinjina kai ya ce "Zani in sha Allah"
Faɗaɗa murmushinta ta yi, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, amma na yi murna na ji daɗi sosai da sosai, Allah ya tabattar da alkhairi"
"Amin"
"To menene next, idan an kammala shari'a, sannan ya zamu yi da batun indabo? Shi Shikenan ya ci bulus kenan, idan aka hukunta su madaki shikenan?"
Al'amin ya haɗiyi yawu, ya ce "Shi wannan iya jarrabawar da yake ciki ta ishe shi, ko iya yanzu ya san tasa ta ƙare, akwai jarrabawa a rashin mulki, tarwatsewar iyali kamar yadda na fuskanta. Bore daga magoya baya ga karayar arziki an kama kayansa a ƙasar waje da yaransa, ga tuhuma da yake fuskanta a cikin gida da sauransu, bana buƙatar wani ya hukunta indabo ni ne zan hukunta shi"
Ta waro ido ta ce "Dan girman Allah mun kusa zuwa gaɓar ƙarshe, kar ka mayar da mu baya ka ɓallo mana wani babban aikin dan Allah".
"Haba akwai bambanci tsakanin Al'amin ɗan daba da kuma jami'in tsaro, na san abin da nake yi, ki kwantar da hankalinki"
Nabila ta ce "Anya kwanciyar hankalin nan kuwa?"
"Trust me mana" yayi maganar yana murmushi.
Ranar Litinin, Nabila da Viper da rakiyar Sumayya, suka kai Viper Asibitin ƙwaƙwalwa, domin ya ga likita.
Ba su wani sha wahala ba, ya samu dukkanin kulawar da yake buƙata, hatta history na yadda ya fara shaye-shaye, sai da suka yi wa likitan bayani, aka tura shi yin wasu gwaje-gwaje.
****
Kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, wasu daɗi wasu akasin haka, ana tsaka da alhinin mummunan kisan gillar da aka yi wa Abba, Rahila ba ta gama dawowa dai-dai ba, aka sake sanar da ita, an kama Nazifi a Lagos, tare da manyan 'yan fashi, hakan ya ƙara tunzura nutsuwar ƙwaƙwalwarta.
Kwanci tashi asarar mai rai, aka sake shafe watanni guda curr, Ramma kullum cikin lissafi take, yaushe Abdul zai fito daga tsaren da yake.
Yau kotu ta fi ko yaushe cika, ana jiran hukuncin da kotun zata yanke.
Ƙarar su Viper ce ta uku da aka kira, bayan dogon rubuce-rubuce da Alƙali ya yi, da bayanai ya shiga karanto hukuncin da za a yanke wa su Lakwari.
Shekarun ɗaurin rai da rai, kowannensu, sannan kotu ta yi umarnin a cigaba da binciken in da sauran waɗanda su ka tafka ta'asar tare suke.
Wata irin ajiyar zuciya Nabila ta sauke, hawaye suka din ga zuba daga idanunta, ba zata taɓa manta wannan rana ba, domin kuwa wannan ita ce mafi ƙololuwar nasara da ta samu.
Viper ma sunkuyar da kansa ya yi a wurin, hawaye ya kasa barin idanunsa, duk da Madaki yana can gadon Asibiti, bai san ma waye a kansa ba.
Ana gama yanke hukuncin ta yi waje, da Sumayya ta fara arba, suka rungume juna, Nabilan sai kukan farinciki take yi.
'yan jarida ne suka baibaiye ta, suna yi mata tambayoyi, amma Sumayya ta ce su ƙyaleta ba ta cikin nutsuwarta.
Walid ne ya fito tare da Viper, yana ta rufe fuska da handkerchief, babu abin da yake iya sanya shi hawaye a take, sai tuna jauhar, 'yan jarida shi ma suka yo kansa, amma ya rufe fuskarsa, Liti ya ce "Ko me zaku tambaya ku tambayeni, ba zai iya magana ba"
"A'a da shi muke son yin magana"
"To ba zai yi ba, munafukai kamar baku ku ka din ga zuzuta lamarin baz da faɗar ƙarya da gaskiya, wallahi idan ba ku bi a hankali ba, sai aikin nan ya kai ku wuta, saboda yaɗa fasadi da sharrin da k...
"Kai liti wai waye ya tambayeka ne?" Walid ya dakatar da shi.
Baba yana tsaka da rarrashin Nabila, ta daina kukan da take yi, ya ga Viper ya fito, ya nufe shi, yana zuwa ya rungume shi ya na "Ina tayaka murna Aminullahi, Ubangiji Allah ya wankeka yau, ni dama na faɗa ba zaka iya kashe mini jauhar ba, Allah ya yi maka albarka".
Abbu yayi tsuru daga gefe, yana son yin magana, amma ya kasa wata irin kunya ta mamaye shi.
Alhaji mu'azzam ma gefe ya koma yana murmushi, amma bai tunkari in da Viper yake ba.
Viper ne da kansa ya tunkari in da yake tsaye, ya je gabansa ya miƙa masa hannun sa.
Sai da Alhaji mu'zzam ya waiwaya, ko ba shi yake miƙowa hannun ba.
Ya ga dai shi yake bawa hannu, ya miƙa masa hannu suka yi musabaha.
Viper ya rungume shi, ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na gode, ina sane da dukkanin gwagwarmaya da ka yi a kaina, duk dan saboda soyyayar da ka ke yi wa jauhar, da kuma ƙoƙarin ɗaukar fansa ta hanyata. Ka yi amfani da ni, ka cimma burinka, ba butulu ba ne ni, da na rintse idanuna daga kallon abin da ka ke yi mini, ina matuƙar kishin matata ne.
A karo na babu adadi, ina mai sake baka haƙuri, ka yi haƙuri da Nabila kamar yadda jauhar ba ta kasance taka ba, Nabila ma haka, mussaman da ake barin halak dan kunya, a wannan karon ma ita ma ɗin tawa ce. Na gode sosai da gudunmuwar ka".
Alhaji mu'azzam kawai ya yi murmushi ya ɗan daddaki bayan Viper ya ce "Ina tayaka murna, maganar Nabila kuma, ba a sanin ma ci tuwo, sai miya ta ƙare".
Nabila kuwa hankalinta ne ya kai kan Naja'atu Bunkure da take yi wa 'yan jarida bayanin cewa, za su ɗaukaka ƙara.
Ta gama bayanin ta nufi motarta, Nabila ta nufi in fa take, Sumayya ta riƙe ta, amma ta fizge ta nufi Bunkure.
Ayshercool
08081012143
96
Tsayawa Bunkure ta yi cak, tana jiran Nabila ta ƙaraso, Nabila ta ƙarasa gabanta tana wani irin huci, kamar fusatacciyar damusa. 'yan jarida na ganin haka, abin nema ya samu, yuuuu suka ɗiba suka nufe su, da abin magana da camerori.
"Ina fatan yanzu kin tabattar da jinin 'yar uwata ba zai taɓa tafiya a banza ba? Kuma matsayin da ki ke taƙama da shi, ki ka ce ba zan taɓa taka shi ba, ashe ba matsayin ba na arziki bane ba, na gode Allah da ki ka haska mini ko ke wacece, ban ci gaba da yi miki makauniyar soyyaya ba. Abin alfahari shi ne kayi amfani da damar da Allah ya baka, wurin kyautata wa mutane, yadda ko bayan ranka zaka yi alfahari da hakan, ba yin mugunyar shuka ba, da sharrinta zai ta bibiyarka har bayan ranka ba.
Na ji ki na iƙirarin ɗaukaka ƙara, to baki da wannan lokacin, ga copyn ƙorafin da zan shigar a kanki nan, ga hukumar shari'a, kuma ina fatan ta soke lasisinki da na ƙungiyar ki, ta ƙwatowa al'umma hakkinsu da ki ke dannewa, ta hanyar rufe kura da fatar akuya, ki na kare yaran masu kuɗi, kina tozarta masu ƙaramin ƙarfi. Bakk da lokacin ɗaukaka ƙara, zai fi kyau ki mayar da hankali a kan yadda zaki karenki" Nabila ta dangwara mata wani file, tare da yi mata kallon banza.
Tabbas tarihi ya maimaita kansa, domin kuwa sowa aka ɗauka da tafawa Nabila, yayin da ta bar Bunkure baki buɗe ta rasa abin cewa, ƙanƙanwar bayanta, da da auren wuri tayi, da ta kusa haifar Nabila, duk yadda ake girmamata kamar wata abar bauta, ita yau Nabila ta dizga kuma ta kayar a shari'a, wani malolon takaici ya ƙuleta, ta watsar da File ɗin, za ta shige cikin mota. Wani abokin aikinta ya ce "Kul, kar ki yar ki tafi da shi ki je ki duba, ki ga ta ina zaki ɓullowa lamarin".
Nabila kuwa wurin Barrister Habib ta waiwaya, da ya kammala wata Shari'a ya fito, yana ta yashe mata baki, "Congratulations our legit barrister"
Cikin murmushi mai haɗe da farinciki, ta ce "Na gode barrister, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Har duniya ta naɗe ba zan manta da kai ba, a lokacin da yan uwa abokan aiki suke yi mini kallon mara hankali, na ɗaukko dala babu gammo, ka tsaya tare da ni, tare da bani ƙwarin gwiwa da gudunmawa ta kowacce fuska"
Yayi murmushi ya ce "Honorable Mu'azzam Wada kankarofi shi ya dace ki yi wa wannan yabon, duk ƙoƙarin sa ne ya kawo haka"
Ta dubi Alhaji mu'azzam ta ce "Honorable, ban san me zan ce maka ba, sai dai ina fatan idan kujerar sanata alkhairi ce a gareka, Allah ya baka, ina kyautata maka zato, halacci da taimakon da ka yi mana, Ubangiji Allah ya shaida ya kuma biyaka, bamu da baki, ko wani kalami da zamu yi amfani da shi, da zamu yi gamshashshiyar godiyar da za ta wadaci hidimar da ka yi mana, mun gode sosai da sosai"
"Babu komai Nabila, yi wa kai ne, kun cancanci hakan ne, daga ke har Al'amin"
Walid ya ce "Shikenan Alhamdilillah, zaman rami ya ƙare, mun yi 'yanci, kumurcin cikin rami zai yi yawonsa freely a gari, Allah ya sa kuma kar ya addabi al'umma da sara" murmushi Viper ya yi.
"Yaya" suka ji an faɗa daga nesa, suna juyawa Shahida ce ta taho da gudu, ta ruƙunƙume Viper tana kuka.
"Yaya dama zan sake ganinka? Yaushe rabon da na ganka a rayuwata, ashe zan sake haɗuwa da kai?"
Wani irin sanyi ne ya ratsa Viper, duk da ba wani good time yake yi da Shahida ba, amma atleast yar uwassa ce ta jini, kuma duk da irin cin kashin da aka din ga yi masa a gidan su, sosai take nuna masa tausayi da jin ƙai"
Rungumeta ya yi, sai dai ya rasa mai ze ce mata.
Ta ɗago tana kuma ƙare masa kallo, ta ce "Na je prison ban san adadi ba, ba a bari na ganka, ina yawan yin kuka, idan na tuna halin da ka ke ciki, ɗazu na ga text ɗin Abbu, wai na taho kotu an wankeka daga zargin da ake yi maka, ni ban san yana ganinka kuna haɗuwa ba, na yi kewarka sosai yayana"
Ya riƙe hannayenta ya ce "Kin yi saurin girma Shahida, ƙarama ce ke fa, lokacin da aka tsare ni"
Zata yi magana ta haɗiyeta ta ƙarfin tsiya, sakamakon arba da ta yi da Nabila, cakumar rigar Viper ta yi, tana nuna masa Nabila.
Ya ce "Menene?"
"Ba ta mutu ba?"
Ya ce "Eh, amma ta dawo ne ta halarci taron kotu, ta ga yadda za a hukunta waɗanda suka kasheta, yanzu zata koma"
Nabila ta ce "Kaiiii"
Kiɗimewa Shahida tayi cikin matsanancin tsoro, Walid ya ce "Viper kai fa ka iya wasan banza wasu lokutan, ba fa ta san ainihin abin da ya faru ba, sai ka saka ta suma ai"
Baba ya ce "Na ga alama ai, Shahida wannan ba Jauhar ba ce ba, twins sister ɗin ta ce Nabila" tayi ƙuri da ido, tana kallon Nabila.
Liti ya ce "Ke kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo ne?"
Ganin Nabila ta samu nutsuwa, 'yan jarida suka cigaba da addabarta a kan tayi magana, tambayar da ta fi ɗaukar hankalinta, har ta ji zata iya amsata ita ce "Wane irin farinciki ki ke ciki a yau, ganin kin yi nasara a wannan shari'ar?"
Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah, nayi farinciki sosai da sosai, dan wannan ce nasara mafi girma da na samu, tun bayan zamana cikakkiyar lauya mai zaman kanta, kuma in sha Allah yanzu aka fara.
Sai dai na sadaukar da wannan nasara tawa kacokan, ga babana maganin kukana, abin alafharina baya goya marayu ginshikin da na jingina da shi, ya zame mini tsananin da na taka na cimma wannan nasara. Mutumin da ya saita ni a kan wani buri da ban taɓa tunanin ina da shi ba, kuma zan ci karo da shi ba, yau gashi wannan burin ya cika wato Major Yusuf maitama mai ritaya, ina alfahari da kai dattijon arziki matuƙa gaya. Ina fatan al'umma za su ci gaba da bamu goyon baya ɗari bisa ɗari wurin