Karfe A Wuta

Chapter 153 of 167

shiga falon Mummy, suna tare da Indabo, yana cin abincin dare.

Ko zama bai yi ba, ta hau shi da faɗa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, tana kiransa mara zuciya da bai san ciwon kansa ba.

Cikin takaici da mutuwar jiki, ya ce "Mummy ɗa na fa na rasa, haihuwa aka yi mini ɗan ya koma, kuma ɗa na halal ɗan sunna. Mummy idan iyayen rahama sun saka an rufe ni, meye na ɗa na a ciki? Yadda ki ke jin so da ƙaunarmu, haka nake ji a raina, ɗa na ne ya zo babu rai, amma baki tausaya mini ba, baki jajanta mini ba sai faɗa ki ke yi mini ya zan yi ne?"

Indabo ya ce "Abdul" Abdul ya kalle shi ya ce "Zo nan" Abdul ya ƙarasa gaban digning ɗin ya ce "Gani"

"Zauna mu yi magana" Abdul ya ja kujera ya zauna yana sauraren indabo.

"Yanzu Abdul duk abin da ka haddasa, duk bai dameka ba ko? Ka wulaƙantar mini da kuɗi, a kan shashashar 'yar ƙauye, ka yi asarar takarar da nake ta fafutukar na tsayar da kai, dan na san ina tsayar da kai, za ayi caa a tona asirinka, a sake ɓata mana suna, yanzu ni na riga na san na yi asarar takarata duk saboda wawancinka, kuma still baka yi regreting ba, kana faɗar maganganu kana cikin hayyacinka kuwa Abdul? Tun wuri tun da ta haihu, shikenan ina son lallai ka rabu da yarinyar nan, ka fita harkarta, ka zo ayi settling maganarka da yar party chairman haryanzu muna da sauran chances, a next tenure za a iya baka minista, ni kuma in san abin yi. Dan haka lallai ka saketa tun da dama ba wanda ya san ka aureta"

Ya kalli mahaufinsa cikin matsanancin takaici ya ce "Daddy, yadda Jafar yake Mexico a tsare, ranka yake maka zafi saboda an tsare maka 'ya, haka maman rahama take ji, koma fiye a duk lokacin da ta tuna na keta wa 'yar ta haddi.
Ba dan na zaɓi rahama a kan ku iyayena ba, amma sai da rahama ta shigo rayuwata, na fuskanci gaba ɗaya rayuwata jarrabawa ce, kasancewarku iyayena, babu wanda ya tsawatar mini da shaye-shaye, ko sauran laifuffukan da nake aikatawa ba, kuna kallon hakan a abu ne da zan daina a gaba, rayuwar cikin turawa ya sanya na zama haka. Ban ƙara tabattar da zamanku iyayena jarrabawa ce ba, dai da na nuna maka videon mummunan aikin da ka aikata, amma hakan bai wani dame ka ba, kuma bai girgiza Mummy ba, saboda duniyar ce kawai a gabanku, ni kuwa tuni rahama ta ankarar da ni fifikon Lahirata a kan duniya saboda ita ce dahir.
Na miƙa lamurana ga Allah, la'akari da Annabin Allah ma, Annabi Ibrahim alaihi salam, Allah ya jarrabe shi a kan mahaifinsa, haka an jarabci Annabi nuhu da ɗansa, kowane bawa da irin ƙaddararsa, wallahi ku ka ci gaba da matsa mini, zan bar gidan nan, zan je na ci gaba da rayuwata kawai"

Indabo ya kwantar da murya ya ce "Haba Abdul, duk wannan abubuwan da kaga ina aikatawa, duk dan mu yi surviving ne, na inganta rayuwarku, kuma abin da ka gani abu ne da ya riga ya wuce, na daina aikatawa, kowane ɗan Adam akwai irin laifin da yake yi wa Allah, kuma Allah mai rahama ne da jin ƙai"

"Amma Allah ba abokin wasanmu bane, da dan muna taƙama da mai rahama ne da jin ƙai, zamu din ha aikata zunubai yadda muka ga dama, mu ce gafurun rahimu ne ba. Kuma ace ɗan Adam baya kunyar saɓawa Ubangiji, Daddy har kisan kai fa ka ke saka wa a yi"

Indabo ya ce "Wa na ce a kashe?"

"Matar Aminu Viper, dan ɗan uwan rahama ne matata, aka kashe matarsa da ɗansa, ita laifin me ta aikata?"

"Shi ne yake hure maka kunne kenan? Shiga gonata yayi, na ce aje a koya mass hankali, tsautsayi ya faɗa kan matarsa"

Hawaye na bin fuskar Abdul ya ce "Kun samu ssɓani saboda yayi barazanar tona maka asiri na abun da na yi wa yayan rahama, ka tura a kashe shi, aka kashe matarsa, kuma sai aka ɗora masa laifin.
Daddy su iyaye ba a canza su, kuma ba a wulaƙanta su, ko da kuwa mushirikai ne, shiyasa tun a wancan lokacin na yi shiru na ci gaba da yi muku biyayya, kamar yadda Annabi Ibrahim alaihi salam yayi. Amma muddin ku ka ci gaba da takura mini, a kan rabuwa da rahama, zan bar gidan nan gaba ɗaya. Allah ne ya tashi kama ni, ya sanya na keta mata haddi ya jarrabe ni da son ta. Allah ne ha so ni da rahama, na haɗu da rahama, kuma shigowarta rayuwata ta zo mini da tarin alkhairi, ni duk abin da suka yi mini, ban ji haushi ba, domin kuwa ma sassauta mini suka yi, dan Allah ku bar ni na ji da zafin da zuciyata take yi mini dan Allah" yayi maganar yana haɗa hannayensa alamar magiya.

Har Mummy za ta yi magana, Indabo ya ɗaga mata hannu, Abdul ya wuce yana share hawaye, yana jin zuciyarsa na wani irin zafi saboda tuna wasu abubuwan.



*****
Viper ya tafi tare da Abbu ya duba ramma a asibiti. Abbu sun yi hira sosai, dan sai da hirar ta tuna masa da marigayiyya matarsa babbar su Viper zahra'u.

Abdul yana ta zarya a kan rahama, baya damuwa da shan ƙamshin da mama take yi masa, hatta medications ɗin ta, shi yake serving.
Duk abin da ake buƙata haka yake yi mata, baya nuna gazawa, dama yana zuwa mama ke bar musu ɗakin.

Ranar da Abbu ya zo duba ramma, Nabila ma tana nan, yana ankare da su daga ita har Viper, babu wanda yake kula wani, yayi musu shiru bai ce musu komai ba.

Sai da Ramma ta kwana biyar a asibiti, sannan Abdul ya yadda a sallameta, babu wani abu da yake damunta, ta samu sauƙi sosai da sosai.


Nabila na zaune a ɗakinta, a kan gado, ta baje takardu tana duddubawa tana nazarin shari'oin da take da su.
Abba yayi sallama a ɗakinta, ta amsa masa ta miƙe tana faɗin "Abba Allah ya sa ba laifi nayi ba?"

"Saboda kin saba da aikata laifuffuka ba" ta ɗan yi murmushi.

Ya zauna a gefen gadonsa ya ce "Maganganu ne da ni nake son mu yi" yayi maganar yana kallon jikin wardrobe ɗin ta, duk ta liƙe shi da hoton maciji da stickers na Viper.

Ta ce "To Abba ina jinka"

"Yanayin alaƙarki da ɗan uwanki Nasir, dan Allah ina son komai ya wuce, ba na son gabar da ku ke yi sam"

"Abba ba gaba nake da shi ba, kawai ika mamakin yadda ya din ga kware mini baya ne, yana haɗa ni da kai"

Major ya ce "Na sani Arfa, amma Nasir ba ƙashin yarwa bane, kin san kowane ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, kuma abin da ya aikata shi ake kira da rauni, irin na ɗan Adam"

Nabila ta jinjina kai ta ce "Haka ne"

"Yauwwa dan Allah ya wuce ki yi haƙuri"

"To Abba, in sha Allah ya wuce, Allah ya yafe mana baki ɗaya, yanzu ka yarda gaskiyar da ka tarbiyyantar da ni a kai a kanta nake dagewa, shiyasa wasu lokutan ake ganina kamar mara ji, ko mara ɗa'a ko"

Yayi dariya ya ce "Na yarda, Allah ya ci gaba da dafa miki"

Ta amsa da "Amin"

"Abu na gaba, babanki ya ce na gaya miki, An tsayar da ranar auren sisternki, ƙarshe watan nan, za a sake ɗaura aure, ta koma gidan tsohon mijinta, Alhaji mu'azzam"

Nabila cikin farinciki ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na ji daɗi sosai da sosai nayi farinciki, Allah ya sanya musu albarka ya daidaita su" ya amsa da "Amin, to ke ya naki batun ne? Kin ce ba kya son yaron nan, babansa sai magiya yake yi yana roƙo, ga Sumayya mamanta ta yi mini magana, wani ya fito ya ce shi kuɗin aure zai kawo, ke kuma kin ja bakinki kin yi shiru, baban yaron nan ya damu lallai a ba wa ɗan sa ke"

Jiki a sanyaye Nabila ta ce "Haryanzu Abbu bai haƙura ba? Wallahi ina jin nauyinsa sosai da sosai, amma ba zan iya auren Vi ba"

"Meye kuma vi?"

"Au Al'amin"

"Haryanzu yana shaye-shayen ne da harkar daba?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a, ai yanzu soja ne, kuma yana zuwa asibitin ƙwaƙwalwa, duk ya rage yin wasu abubuwan, kawai dai ba na son sa ne"

"Ita kuma wallpaper ɗinki, da wannan liƙe-liƙen na ɗakinki, duk cikin tsanar ta sa ne?"

Cikin jin kunya ta ce "A'a Abba, kawai dai ina sakawa ne, a lokacin ina da hope na ganin na saka kotu ta wanke shi daga zargi"

Abba ya tashi ya ce "Gaskiya ne, to ni dai duk hukuncin da babanki ya yanke ba ni da ta cewa, tun da na ga shi ma yana yin yaron, ni na fita sai na dawo"

"A dawo lafiya"

"Allah ya sa"

*****
Rahila ta ɗaga hankalinta sosai, ganin da gaske Walid da ba shi da komai zai aura wa Shahida, babu irin zagin da ba ta yi wa shahida ba, amma tayi bore ta ce ba ta so, amma Shahida ta ce ita ta ji ta gani.

Abbu ya ce "Ke dama ban isa sa ke ba, Shahida kuwa 'ya ta ce, dan haka ina da ikon zartar da duk wani hukunci a kan ta, idan bai yi miki ba, zaki iya tattara kayanki ki ƙara gaba, dan albarkacin ta kawai ki ke ci ki ke zaune a gidan nan" haka suka yi faɗa kaca-kaca, ƙarshe Shahida sai komawa tayi cikin ɗaki tana kuka.

Da daddare da Viper ya je gidan, ya ga Shahida kamar ba ta walwala, yake tambayarta ko lafiya.

Cikin damuwa ta ce "Dan Allah yaya, ka roƙa mini Abbu, na ji ya ce saboda ni mama take zaune a cikin gidan nan, dan Allah ka ba shi haƙuri, na san tun ba yau ba, yana matuƙar haƙuri da ita, amma dan Allah yayi haƙuri, ba ta da cikakkiyar lafiya kuma idan ya rabu da ita, babu in da za ta je, dan Allah yayi haƙuri"

Viper ya ce "Kar ki damu, barazana yake yi mata, kin san shi da tausayi, da kuma fushi wasu lokutan, amma in sha Allah ba zai rabu da ita, duk a kan maganar aurenki ne ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Ba zigaki nake ki bijire mata ba, amma ki samu miji irin Walid, sai kin daɗe kina tonawa, tun da ki ka ga Abbu ya amince shi ma, ba mutumin banza bane ba"

Shahida ta ce "Haka ne Yaya, ni dan Allah ma ka yi masa magana, wai ba zai yadda a bashi aurena, kuma a bashi wurin zama ba, wai haya zai kama, kuma ya dage sai ya yi mini kayan lefe ko babu yawa. Naga ba ƙarfi ne da shi ba, kuma ni ina duk abin buƙata. Budurwa ce ni ba bazawara ba, amma yaƙi yadda"

"Muhsin bai yarda da gazawa ba, wannan wata aƙida ce da muke da ita, ko zamu yi a raina, mun fi son mu ƙoƙarta, amma ki kwantar da hankalinki, zan yi magana da shi in sha Allah, kuma da mun kammala shiri, ba jira zamu tsaya ba da an kawo kuɗin aure lokaci za a tsayar, duk abin da ki ke buƙata ki gaya mini"

Shahida ta amsa da "To yaya in sha Allah "

Wasa-wasa girma ya hau kan Viper, ɓangaren ramma shi ne, haka gidansu, ga liti ga Walid, kowa Viper.


Al'amin sai da ya fara tausayawa Abdul, Abdul bai furta a bashi ramma ba, amma yadda yake sintiri kullum a tafe, ya ƙara tabattar da gaisuwa yake gami da roƙon iri, a kan a bashi matarsa.

Ita kanta mama ta ɗan fara saukkowa, ta zuba musu ido. Dan kuwa duk da jaririn ya mutu, sai da ya yanka san da ya saya ya ce idan ta haihu za ayi mata amfani da shi.

Duk da kayan da take da su, sai da yayi mata sayayya fal, na kayan sakawa.

Ranar da ya kawo, ta din ga yi masa godiya, ya tambayeta, me take so ta karanta zai yi processing komawarta makaranta.

"Nurse nake son zama"

Yayi murmushi ya ce "Shikenan, sai mu ƙarfafi asibitocinmu, mu kula da su sosai da sosai, amma rahama zaki dawo gidana sai ki yi karatun?"

Ramma ta ce "Ai ka san wannan ba maganata ba ce ba, maganar mama ce da yaya Aminu, amma kuma idan na dawo gidanka ai ba zan samu yin karatun ba, an ce ba a ɗaukar masu ciki"

Abdul ya ce "No, sai mu yi planing zuwa lokacin da zaki kammala"

Ta ce "Anya kuwa, yadda ka ke son yara, kar in je ka canza shawara"

"Haba rahama, kin fi kowa sanin halina, ni ɗan Adam ne, amma ban fiye yi wa mutum ƙarya ba dan ya yarda da ni, duk son yarana dolena na jure, kema na ga na inganta rayuwarki na kafa ki"

"To ka bari yaya Aminu ya dawo, ya koma wurin aiki ne, amma ka fara yi wa Daddy magana tukuna"

"Waye daddyn?"

"Alhaji mu'azzam mana, ko da nayi aiki a gidansa, ai haka ake ce masa"

"To shikenan, zan yi masa magana in sha Allah, kin san za a mayar da aurensa da yayar Nabila Hafsa".

"Ai ban santa ba, ni lokacin anty Jidda na fara aiki a gidan"

Abdul ya ce "Ok haka ne, ta koma gida ma, wai sai ya saketa duk a kan case ɗin mu, ni kowa ya ƙarata, a bar mini matata kawai"

Tayi murmushi suka cigaba da hira.


Nabila sai da tayi ta rarrashin Hafsa, a kan tayi haƙuri ta koma gidan Alhaji mu'azzam, dan fafur cewa tayi ba ta sonsa.
Kasancewar duk ƙarshen wata, sai tayi sayayya taje ta gaida Baba, hakan ya saka sun shaƙu sosai da hafsa, sai dai sauran mutanen gidan babu ruwanta da su, idan aka cire saifu, shi ma suna gaisawa.

Tare suka ta shirye-shirye, Hafsa tana cewa ita babu wani gyara da zata yi, lokacin da aka yi na farin ma, bai yi mata amfani ba balle yanzu.
Amma Nabila da taimakon sumayya suka ce, sai ta yi gyara da da yanzu ba ɗaya bane ba, zamani ya riga ya canza.

A lokacin Shahida ma Walid ya kai kuɗin aure, kuma Hafsa ƙawar Shahida ce, kasancewar iyayensu aminai ne. Watanni biyar aka saka, saboda babu yadda Viper bai yi da Walid ba, ya dage ya ce shi sai yayi mata lefe ko yaya yake, kuma sai ya kama gida. Shi ba ruwansa da bazawara ce, ba zai so ace shi aurensa na fari, ace ya naɗe hannu komai sai dai ayi masa ba.
Viper ya ce masa ya gyara nasa gidan, su zauna sai ya din ga biyansa kuɗin hayar.
Walid ya ce "Ai sakankancewa zan yi, na san naka ne, idan ma ban biya hayar ba, ba zaka damu ba, kuma zan ta damuwa gidan zai din ga tuna mini ƙanwata Jauhar, kuma kai a ina zaka zauna, idan ka yi naka auren?"

Viper ya ce "Ina da wurin zama ai ni, ko ka ƙi, ina wani gidan, na ji ba zan saka maka hannu ba, ka gyara shi da kanka, kayi lefen, amma ba zaka kama haya ba gaskiya ba"

Da kyar Walid ya amince da hakan, sai dai Liti ya zage kamar kayan lefensa zai tara, kuma Nabila suke turawa kuɗi take haɗa kayan, ita kanta Shahidan ba ta san da haka ba"

Sai dai daga Hafsa har Shahida sun dawo daga rakiyar iyayensu, na shirmen bin bokaye, domin sun tabattar da ba hanya ce mai ɓullewa ba.

Kasancewar Sumayya na ta'amalli da mutane daban-daban, a dalilin harkar aikinta, ya sanya ta nemi lambar maman dr., Domin haɗawa Alhaji mu'azzam da kuma ango Walid amayarsa. Tun da ita mace duk in da take sai da gyara. Kuma masu iya magana suka ce, idan kana da kyau ka ƙara wanka.
A cikin wata gudan nan, ba ƙaramin kyau Hafsat tayi ba, sai sheƙi tayi gwanin sha'awa, duk da ba ta da jiki, amma maman dr. Ta tsatsota, ta cika tayi fam, tayi ƙiba dai-dai misali, amma duk lokacin da Alhaji mu'zzam ya zo sai sun yi faɗa. Gashi can gidansa uwargidansa ta sako shi a gaba a kan ya ce zai dawo da hafsa, rashin mutunci na yau daban na gobe daban, gaba ɗaya ta ƙaurace masa, yadda Jidda ma ta fita, so take ta rayu itakaɗai a gidanta, shi kuma ya ce bata isa ba, yana da wadata da lafiyar da zai auri mace fiye da ɗaya.
Ya din ga ganin tamkar ranaku ba sa sauri, duk lokacin da ya je wurinta, da kyar yake saita nutsuwarsa, saboda kyan da tayi, da wani irin sihirtaccen ƙamshi da take yi. (Domin gyara da kankaro naku mutuncin kuma a naku gidajen auren, ku garzaya ku tuntuɓi maman dr. Likktar mata domin kar ayi babu ku 07069711327)


Viper yana zaune yana duba status ɗin sa na waya, yana son ya halarci ɗaurin auren hafsa, dan haka yana saka ran ana idar da sallar asuba zai nufo Kano, duk da ɗaurin auren na azahar ne sai an saukko daga masallaci.

Status ɗin Nabila da ya yi muting ya shiga, na farko Addu'a ce, kamar yadda ya zame mata ɗabi'a, yawan sanya addu'oi da shot videos na malamai.
Na gaba kuma, videonta ne, an yi mata lalle ja da baƙi, sumayya tana cewa our dear barrister marasa galihu, jin ki yafi ganinki, our anti serious beb" ta kwaɓe fuska tana harar Sumayya.

Ɗaya Videon kuma, Ita da sumayya ne da amarya hafsa, da wasu daga cikin yayyen su mata.

Haushi ne ya kama shi, ya san wataƙila duk mazan da suke cikin wayarta sun ga status ɗin, doguwar riga ce a jikinta, ta ɗora mayafinta a kanta, shigarta decent amma shi abin

Download complete TXT · Novel page