Karfe A Wuta

Chapter 166 of 167

da aikata duk wani mugun aiki.

A zahiri kuma ta ci gaba da rarrashinsa, tana kwantar masa da hankali.

*****
Rahila Allah ya taimaketa, aka sallamota daga asibitin masu rangwamen hankali, sai dai duk tayi wani iri, tsufanta ya fito sosai da sosai.

Shahida ta zauna ta yi ta mata nasiha a kan tayi haƙuri, ta kwantar da hankalinta, kar ta ɗorawa kanta kishi, idan ba haka ba ta bari Abbu ya saketa ba ta da wurin zuwa ta zauna.

Shi kuwa Abbu, hankalinsa ya kwanta, Al'amin ɗin sa ya zama mutum, ya nutsu ya shiryu, ga maman ramma sam ba ta da damuwa da hayaniya, su na zamansu lafiya.

Abdul ya takura a asibiti shi a sallame shi, da aka sallame shi su ka koma gida, ko fita baya iya yi, abinci ma sai ramma tayi da gaske yake iya ci.

Ta kira mama ta gaya mata, mama ba ta taɓa zuwa gidan ramma ba sai lokacin, suka je tare da Abbu.

Duk da da sauran pain ɗin abun da Abdul ya yi musu a zuciyarta, amma sai da ya bata tausayi.
Ta din ga jinjina girman ikon Allah, ganin katafaren gidan da rammar ke ciki, komai na jin daɗin rayuwa dai-dai gwargwado akwai shi.

Su ka jajanta musu, Abbu ya yi ta yi masa nasiha, tare da nusar da shi muhimmancin addu'a da kuma juriya.

****
Nabila kuwa na ta rainon cikinta, da aka raba kayan jauhar, kayan jariran da suka saya, ya faɗo a rabon Nabila, ya tambayeta ta na so ko a sayar a bata kuɗin, ta ce kayan take so.

Major buni-buni, sai ya zo gidan Nabila ya dubata, cikin nan yayi girma sosai da sosai.
Gaba ɗaya ta zauna a gida ta daina fita, saboda duk wanda ya ga cikin sai ya yi magana.

Liti ya saka babansa a gaba, tun da ya ga ya san Major, yake ta yi masa nacin, yaje ya tambayar masa auren Walida, amma babansa yaƙi ya ce sai ya ga kamun ludayinsa sai ya ƙara hankali.

Abbu ya samu mahaifin liti ya ce masa shi ne yake tare da su a kasuwa, liti ya yi hankali sosai da sosai, kuma shekarunsa ja suke yi.

Da kyar ya amince ya yi wa Major maganar, amma ya yi masa bayanin komai.

Major ya ce "Ai ɗanka nawa ne prof, kuma tun da shi ma ya shiryu haka muke so, in dai yarinyar ta na son sa, Ubangiji Allah ya tabattar mana da alkhairi, dama tuntuni  yayarta Nabila ta fara yi mini zancen, idan kun shirya ku zo ayi magana kawai"

Liti har gida ya je ya gaya wa Nabila Major ya amince ya bashi auren Walida, tare da ƙara yi mata godiya, bisa ƙoƙarin da ta yi masa.

Cikin Nabila na ganin gata, domin kuwa tuni a wannan karon ma Viper ya fara sayayyar kayan jariri, idan ya tambaye ta zaɓi, sai ta ce ita duk abin da ya saya shikenan, ita dai damuwarta ta rabu da cikin nan lafiya.

Shahida ce ta fara haihuwa, matar Walid, daga kai ta asibiti cikin dare tana ciwon baya, aka ce ai ta kusa haihuwa, abin har mamaki ya bashi.

Viper ba ya gari, Nabila kuma ta yi nauyin da ba za ta iya fita ba, Walid baki yaƙi rufuwa, wai shi ne ya zama uba, Allah ya bashi ɗa namiji.

Liti har ya fishi murna, kamar ɗansa, ya din ga bin sa yana cewa "Saura ka saka masa sunan Viper, alhalin gani, sunana zaka saka masa"

"Kai a wa?"

"Ni a baban yaron mana, dan Allah Walidi ka saka masa sunana Abdallah, na san rashin m ɗinka, tsaf zaka saka masa sunan Viper, dan muraran ka ke nuna fifikon ka fi son sa a kaina"

Kafin suna Viper ya zo gari, Nabila ta so ta bishi ta je ta ga yaron, amma ya ce ba zata fita a din ga tanka ta ba.

Viper kamar ya tafi da yaron, ya din ga addu'a Allah ya nuna masa na sa haka shi ma.
Yayi masa addu'a sosai da sosai yaron.

Walid ya sanya sunan mahaifinsa Umar.

Dubu ɗari Viper ya bawa Walid, ya ce masa yayi haƙuri, abubuwa ne sun yi masa yawa.

Yanayin jikin Nabila, ya sanya Major ya tura Baba magajiya ta zauna da ita.

Sai dai idan Viper yana nan 'yar kallo take zama, sai dai ta yi ɗan aikace-aikacen gida. Hatta wanka sakata yake a toilet ɗin ƙurya ya wanketa, undeas ɗin ta, idan ta cire duk shi yake wanke mata.

Shi kansa ba ƙaramin tausayi take bashi ba, idan ta zauna shi ma cikin nasa zaman yake yi.
Zama sai da dabara, tashi sai da dabara, haka bacci ma, gashi tun da ya ƙara tsufa, take fama da matsalar numfashi, dan ma ba ta da yawan complain, sai dai shi ya fuskanci akwai matsala.

Sanin alaƙar da take tsakanin Sumayya da Nabila, ya sanya mijinta ba ya damuwa, da yawan zuwa gidan Nabila da take yi, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata.

Duk shagwaɓa da rigimar Nabila idan ba ta da lafiya, yanzu babu, sai dai idan an yi mata sannu ta yi murmushi kawai, gaba haka kurum take jin ta sare, kamar mutuwa za ta yi idan ta zo haihuwa.

Duk da ita ce abin tausayi, amma tana tausya wa Viper sosai da sosai, bawan Allah sai ya zauna ya zuba mata ido, duk motsinta tausayinta yake ji, da ta motsa zai tambayeta me take buƙata, me take so.
Har nauyinsa take ji, ta ce tana buƙatar wani abu.

Ana haka mama uwargidan baban su Nabila, Allah ya karɓi rayuwarta, duk unguwa ba in da zancen jinyar wulaƙancin da 'ya'yanta su ka yi mata bai je ba.
Nabila tana ji tana gani, babu roƙo da magiyar da ba ta yi ba, Viper ya ce sai dai ta yi addu'a daga gida, ba zata je ko ina ba.

Mutuwarta ta ƙara razana Zakiyya, ta din ga ganin saura ita.

Watan jaririn Walid biyu, Nabila ta fara naƙuda, tun cikin dare suka tafi Asibiti, amma har garin Allah ya waye ba ta haihu ba.

Tun da aka gaya wa Major da sassafe sai gashi a asibitin, ya zo ya tarar da su da Viper da baba magajiya, an fito da Nabila tana zagaya wa, ta samu wuri ta zauna a jikin Viper saboda ta gaji da zagayen.

Viper na gaida shi, amma bai ji ba, hankalinsa na kan Nabila, ya riƙe hannunta ya ce "Sannu Arfa na, ya jikin?"

"Da sauƙi Abba"

"Allah ya rabaki da cikin nan lafiya, ki ci gaba da addu'a kin ji, muna taya ki"

Ta jinjina masa kai, mai haɗe da yaƙe.

Duk wanda ya wuce ya ga Nabila, sai ya sake waiwaiwayawa ya kalli cikin nan.

Shahida ta kira wayar Nabila, dan tun yammacin jiya ta kirata take tambayarta, wai ya mutum yake gane naƙuda yake yi.

Viper ne ya ɗaga ya sanar mata su na Asibiti.

Shahida ta gaya wa Walid, lokacin bai fita kasuwa ba, ya cewa liti ya wuce kasuwa, zai fara biyawa ya duba Nabila, liti ya ce "Saboda ka rigani ganin ɗan mai zamani ko? To baka isa ba"

A asibitin suka haɗu, Walid jikinsa yayi sanyi, dan bai manta yadda Shahida ta din ga fama ba.

Liti ya zata abin wasa ne, ganinsu a zaune a harabar wurin a kan kujera, har tana shan shayi.

Wata Nurse ta fito ta ce mata ta daure, ta tashi a mayar da ita labor ward a sake dubata.

Da Nabila ta miƙe sai da gaban liti ya faɗi, tare da mamakin yadda aka yi tayi rayuwa da wannan cikin, duk da da hijjabi a jikinta.

Su na tafe idan ciwon ya motsa sai ta rirriƙe Viper, tana yarfa hannu tana ambaton Allah.

Liti ya ce "Walid gaskiya tafiya zan yi, idan ta haihu ka kira ni a waya,na ci gaba da zama a nan kuka zan yi, wallahi na zata haihuwar ba wahala"

Walid zai yi magana ya ga da gaske hawaye ne a idon liti, wanda liti da bakinsa yake cewa shi fa sai a shekara ko ƙwalla bai yi ba.

Wasa-wasa har Baba sai da ya zo asibitin, Nabila ba ta haihu ba, Viper ji yake kamar ya tayata ciwon, tun da cikin nan ya samu a wahala take.

Idan ta gaji, sai ta fashe da kuka, sai dai Viper ya yi ta rarrashinta, yana ba ta haƙuri.

Har sai da ya cewa Abdul, ko ayi mata tiyata kawai.

Abdul ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri, lokaci ne zata haihu da kanta in sha Allah, haka kowace mace take ji. Babu tangarɗa a laborn dan haka a ƙara haƙuri.

Sai da ta kusa daf, sannan aka ce Viper ya fita waje, ya din ga sintiri a bakin ƙofa, yana addu'a, sai dai ya din ga tuna Jauhar, yana fargabar Allah ya sa kar wani abu ya samu Nabila da yaran.

Doctor Abdul Yasar, ma'aruf Indabo, shi ya karɓi haihuwar Nabila, ta sha wahala sosai da sosai. Dan bayan da jaririn ya faɗo, sai da ta kuma wani ciwon sannan ta biyun ta faɗo.
Hamdala ta din ga yi, tana yi wa ma'aikatan godiya, saboda gudunmawar da su ka bata.

Abdul ya ɗora mata jariran a kan ƙirjinta, ta rungume su, kawai ta fashe da kukan murna.

"Ya haiyyu ya ƙaiyyum ya zuljalalu wal ikram, ya Ubangijin Al'arshi ya Allah duk mai neman haihuwa in dai alkhairi ce , Ubangiji Allah ka bashi yara masu albarka, Allah ka bashi yara masu jin ƙai ababen alfahari ga addinin musulunci, Allah duk mai nema ka bashi, kamar yadda ka azurta Annabi Zakariyya Alaihissalam a lokacin da ya roƙeka. Allah na gode maka da wannan ni'ima, Allah ka raya mini yarana, ka shirya mini su"

Su ka din ga amsawa Nabila da Amin.

Viper ne kaɗai a wurin da labor room yake, su Major su na can waje.

Nabila ta sha ɗinki ciki da waje, ta ji yadda gaba ɗaya ɗakin ya cika da ƙarnin ƙazantar haihuwa, amma daga Abdul har Nurses ɗin, babu wanda ya nuna ƙyamar sa a gareta.

Aka shirya yaran tsaf, ita ma aka shiryata, ya basu wuri, nurses ɗin suka ƙarasa taimaka mata, ta shirya, aka yi mata allurai aka fito da ita.

Aka wuce da ita postnatal room, ana miƙo wa Viper yaran, amma bai bi ta kansu ba, ya nufi in da aka shiga da Nabila.

"Abla" ya kira sunanta.

Ta ɗago idanunta da suka yi jawur saboda wahala, ga bacci tana ji.

Rungumeta ya yi yana shafa kanta ya ce "Sannu my love, Ubangiji Allah ya yi miki albarka, ya dauwwamar da farinciki a rayuwar aurenmu"

Cikin shagwaɓa ta ce "Vi na sha wahala"

"Na sani sweetheart, na gani, sannu Abla. Alhamdilillah ala kulli halin. Na gode, na gode my world" yayi maganar yana sumbatar goshinta.
Hannunsa ta riƙe ita ma ta ce "Ni na gode da kasancewa tare da ni, ba tare da ƙosawa thank you very much" ya riƙe hannun nata sosai ya ce "Lokacin Jauhar na raye, ta din ga ce mini tsoro take ji, tana son na kasance da ita lokacin haihuwa. Allah bai amince ba, ban kasance da ita ba, amma na cika alƙawarin da na yi mata a kanki"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Na yi mata addu'a sosai da sosai, Allah ya jiƙan 'yar madararmu"

"Amin my love"

Abdul ne ya shigo da jariran a hannunsa ya ce "Wai ba kwa san yaran ne? Ana ta rawar ƙafa a baka su, amma ka ƙi kallonsu, ga su nan an yi musu rigakafi, BCG da HB kafin mutane su fara zuwa ɗaukar su"

Viper ya yi murmushi ya ce "Sun wahalar mini da mata, shiyasa na ɗan yi fushi, amma tun da tana nan ƙalau, barakallahu fihum" yayi maganar yana karɓar su, cikin wani irin maɗaukakin farinciki mara misaltuwa.

Abdul ya ce  "Wannan boss ɗin da kai yake kama, fuskarka ce wannan" Viper ya yi dariya.

Su Major ne su ka shigo, shi ma sai da ya fara nufar gadon Nabila, ya tabattar tana lafiya.

Kan ka ce kwabo, Asibiti ya ɗinke da mutane, 'yan barkar Nabila.

Da liti ya zo duk jikinsa a sanyaye, ya din ga jerawa Nabila sannu, halin da ya ganta a ciki ɗazu, ya ƙara sanya masa tausayin mata.

Ya ja gefe aka miƙo masa jarirai.

Bai san lokacin da ya ce "Kan uba, kumbo, Viper wannan fuskar ai taka ce, ka ga jariri yadda ya haɗe fuska kamar zai kai duka. Allah ya baki juriyar tarbiyya, wannan zai yi taurin kai kamar babansa"

Ba wanda bai yi dariya ba, macen ce take ta tsotsar hannunta, tana buɗe idanunta tana lumshe su a hankali.

"Allah ya raya mana ke 'yar madara, Allah ya sa ki ɗaukko halin mai sunanki"

Viper ya ce "Har ka saka mata suna?"

"Eh gaskiya, na saka mata suna fatima zahra, 'yar madara"

Viper ya yi murmushi ya ce "Babanki ya saka miki suna, Allah ya raya ki bisa tafarkin addinin musulunci"

Bayan awanni shida aka sallami Nabila, gida ma da suka tafi, ana ta zuwa barka.

Washegari hafsa su ka zo Kano da Hafsa, Hafsa kamar a bar mata jariran nan.

Alhaji mu'azzam ya ce "Wannan dai na san 'yar madara ce, shi kuma ogan fa ya sunansa".

"Takwara na yi muku kai da Abbu, Ibrahim ace masa mu'azzam ko Khalil"

Ita kanta Nabila ba ta zaci haka zai yi ba, ta ɗauka sunan Nura yayan ramma zai saka"

Alhaji mu'azzam bai taɓa zaton Viper zai yi masa kara haka ba.

"Masha Allah, amma na gode sosai da sosai, idan ina da rabo nima Allah ya bani ɗa namiji, Allah ya raya khalil"

Viper ya ce "Mu ke da godiya, har duniya ta naɗe, ba zamu taɓa manta abin da ka yi mana, Allah ya saka da alkhairi"

Kankarofi ya ce "Kar ka damu Viper, yi wa kai ne"

An sha shagalin bikin suna sosai, Alhaji mu'azzam ne ya yi wa jariran Viper hakika, sun samu tarin kyaututtuka, ta in da suka zata da in da ma ba su zata ba.
Sai dai Nabila ta fara fama da ɗawaniyar raino, Khalil ba shi da afuwa wurin tsotsotso, 'yar madara ba ruwanta idan an ba ta ta sha, idan ba a bata ba, sai tayi ta tsotsar hannunta.

Viper ya ce "Ba fa zai yiwu ka hana mini 'ya kumari ba"

Haka zai tsigo shi daga jikin Nabila yana tsala kuka, ya bata 'yar madara ta shayar.

Baba magajiya ce take yi wa Nabila wankan jego.

Watan Nabila ɗaya da haihuwa, aka yankewa Indabo hukuncin kisa a ƙasar saudiyya.

Ko a iya haka Viper ya ɗan ji sanyi a ransa, duk da ba za a taɓa wanke masa zuciya ba, haka ma maman ramma.

Bunkure kuwa ana ta jan shari'ar ta, saboda tuhume-tuhumen da ake yi mata da yawa.

Abdul ya sha tashin hankali, saboda yadda maganar kashe Indabo ta karaɗe ko ina a ciki da wajen ƙasar nan.

Nabila ta fara mayar da hankali a kan ƙoƙarin ta, na fito da hanyoyin taƙaita shaye-shaye, a tsakanin al'umma.

Ta fara da rubutun ƙanan litattafai, masu ɗauke da zane-zane, da suke ankarar da illar shaye-shaye da 'yan makaranta tun daga primary zuwa secondary za su iya amfani da shi.

Aka gudanar da babban zaɓe na ƙasa, gwamnati ta canza bara gurbi daga cikin muƙarabbanta, yayin da Alhaji mu'zzam ya ɗare kujerar sanata.

Jidda babu yadda ba ta yi ba ta koma gidansa, amma yaƙi.

Zakiyya kuwa sai abin ya zame mata ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa, ga kuɗi iya kuɗi hafsa na cikin daula, amma bata nutsuwar ƙwaƙwalwar da za ta ci, kullum a zabure take cikin tashin hankali.

Ba a rufa watanni uku ba, shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu, a kan sauya shugabannin da za su jagoranci rundunonin tsaro na Nigeria.

Viper mamaki ne ya cika shi, ganin matsayin da aka ɗauka aka ba shi.

Sumayya gwamantin kano, ta buƙaci su yi aiki da ita, ayi mata S.A daga ita har Nabila, amma suka ƙi hakan, saboda ƙungiyar da suke son kafawa, ba sa son siyasa ta shiga ciki, su na so tayi hannun riga da irin ta bunkure.

Nabila ta fito daga wanka ta na shirya, ta tsaya tana kallon kanta a mudubi, Viper yana ta rarrashin Khalil yayi bacci, ya ga ta tsaya ta yi shiru tana ƙarewa jikinta kallo a mudubi.

"Madam ya dai?"

"Vi, kalli duk na yi wani iri, kalli tumbina yadda yaƙi komawa gaba ɗaya, kalli stretch marks duk ya ɓata mini jiki, kalli yadda cikin yayi, kalli breast ɗi na ma, duk stretch marks, ni Allah ya sa kar su yi sagging ma idan na yaye su" tayi maganar cikin damuwa.

Ya tashi ya ƙarsa in da take, ya tsaya a bayanta, yana kallonta ta jikin mudubi.

Ya zagaya hannunsa a cikinta, yana shafa cikin a hankali ya ce "This is motherhood abla, yara biyu ne fa suka kwanta wata tara a cikinki, ta yaya ki ke expecting ki zauna a yadda ki ke?"

"Vi zan daina yi maka kyau, kalli tumbina fa, ji nankarwa, kalli breast ɗina, duk yadda ya cika maybe da na yaye su ma zubewa za su yi"

Ya kwantar da kansa a kafaɗarta ya ce "Idan na ce zaki daina yi mini kyau, ban yi wa kaina adalci ba ko kaɗan abla.
Ba zaki taɓa komawa yadda ki ke a da ba, kar ki damu kanki, ki ce sai kin yi abin da zai cutar da ke, sai nankarwa ta tafi, sai breast ya koma yadda yake a da, ban ƙi ba ki yi gyara, amma ban da cutar da kanki, ki yi alfahari da wannan nankarwa tambarin zama uwa kenan, ni kyau take yi mini ma, ba na cikin mazan da zan damu da sauyin da jikin matata ya samu, alhalin na san ba a haka na aureta ba, dan duk wanda yake a haka, zai zama mai yawan zalama da hange kuma ba zai taɓa samun yadda yake so ba.

Download complete TXT · Novel page