Karfe A Wuta
Chapter 34 of 167
kwashe kwanukan.
Yanayin garin da sanyi saboda ruwan da aka yi, amma ya takure yana bacci.
Ta fitar da kwanukan, ta ɗaukko bargo daga ɗakinta, ta zo zata rufe shi, ɗan ƙura masa ido ta yi. Al'amin ba shi da wata makusa, da yake baccin nan ma he looks very innocent and calm.
Kasa rufe shi ta yi, ta tafi tunanin ya aka yi ya fara shaye-shaye, ya aka yi su mama suka samo shi ma, suka aura mata? A ina yake ina ne gidansu? Duk take tambayar kanta.
Tashi ya yi zaune kamar aljani ya ce "Meye ne kin zo kin sakani a gaba kina kallona"
Zabura ta yi ta ce "Yi haƙuri, na zata bacci ka ke yi, ba kallonka nake yi ba, na ga kamar kana jin sanyi ne, bargo na kawo maka" tayi maganar tana tsuma.
Ya miƙa mata hannu, ta bashi bargon, ya ware shi ya lulluɓa, ta fita tana mamakin al'amin idan yayi wani abun mamaki yake bata, har da ajiyar zuciya ta ji yana yi alamun baccinsa yayi nisa, amma kawai ta ganshi a zaune.
***
"Allah ya taimaki maigida"
"An gaisheka, ya ake ciki?"
"Komai normal, ba wani abu"
"Yaya za ayi? An kama Ja'afar da kaya, hukumar nan sun ƙi sakinsa, ba zan matsa ba, amma ina buƙatar a musanya shi da wani"
"Oga ba zan iya sakinsa kai tsaye ba, amma dole za'a samu wani a kama shi da kayan, sai a saki jafar a kama shi, ka san wannan karon shugaban namu, yana da sanya ido sosai"
"Shikenan, ayi abun da yakamata kawai"
"Ok sir".
Cikin ikon Allah, matar nan tela, tana biyan jauhar, duk da ba wani kuɗin kirki take bata ba, amma tana jin daɗi sosai da sosai, ta sayi katin tara kuɗi, ɗan abun da tayi cefane, sauran sai ta saka a kati, kuma Allah ya saka mata albarka a ciki.
Yaran maƙwabta idan sun shigo, tayi musu tsifa da kitso, babu ko sisin iyayensu.
Ta duƙufa tana aikinta, ba ta ji motsinsa ba, sai jefo mata bargo yayi a ka.
A razane ta tashi, bargon kuma ya cukuikuyeta.
Ya ce "Zaki taka kwaɗo" Ihu ta saka ta samu ta cire bargon da ƙyar, tana dube-dube, yana tsaye yana kallonta, kamar ba shi yayi maganar ba.
Ta ce "Ina kwaɗon?" Ya yi shiru bai ce komai ba.
Ta kalli yadda stone ɗin ya zube kamar ta yi kuka ta ce "Kalli yadda ka saka na zubar da kayan sana'ata." Ta durƙusa za ta kwashe, sai kuma ta yi sauri ta hau kan kujera, ta maƙale ƙafafuwanta ta ce "Ina kwaɗon ya shiga ne?"
Haryanzu shi dai bai daina mamakin yadda kwaɗo ya zama abun tsoro ba.
Hanyar fita ya nufa, ta gane tsokanarta yake yi, nan ta ƙara jinjinawa ƙi faɗinsa, har ya iya ya tsokaneta, amma ya sha kunu ba fara'a.
"Master" ta kira shi. Ya tsaya bai waiwayo ba.
"Dan Allah idan Allah ya yassare, ka taho da omo, zan yi mana wanki".
Yanzu ma bai yi magana ba ya fita, ta naɗe bargonta, ta cigaba da aikinta.
Zakiyya kuwa, kamar zata zare, Rahila na ta janta wuraren malamai kala-kala, yadda za su samu, Hafsa ta auri Alhaji mu'azzam da zarar ya dawo.
Har sha ɗaya na dare, jauhar na aikin jera stone ɗin ta a kan gadonta, dan tun tana jin tsoron zaman gidan, har ta saba, sai da ta ji bacci yana kama idonta sosai, sannan ta tashi ta ajiye kayan, tayi wanka ta fito tana shirin kwanciya.
Ji ta yi ana buɗe ƙofa, dan haka ba ta damu ba, ta san mai gidan ne, sai dai bayan wasu mintuna ta ji kamar yayi jifa da wani abu a falo, yana ta haki mai kama da kakari, gabanta ya faɗi ta fito da sauri, ta tarar da shi ya riƙe hannunsa yana ta nishi, hannunsa an yanke shi, da ƙafarsa ta hagu, kasancewar da wuta, ya sanya ta ga yadda yake zubar da jini, a gigice ta ƙaraso cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Master faɗa ku ka yi da wani? Ya aka yi ka ji ciwo haka?" Yayi shiru yana fesar da iska daga bakinsa.
Da gudu ta shiga ɗakinta, ta ɗaukko zani ta danne masa na hannunsa da ya fi zubar da jini, ta rikice ta rasa me za ta yi, kawai ta nufi hanyar fita.
Ya ce "Ina zaki?"
Cikin tashin hankali ta ce "Maƙota zan je, a samo abun hawa a kai ka asibiti kar jininka ya ƙare".
"A haka kuma zaki fita?"
Sai a lokacin ta ga, ko hijjabi babu a jikinta, ta koma ɗaki, ta ɗaukko hijjabinta sai kuka take yi, tana dawowa falon ya ce "Kar ki fita"
"Meyasa? Jini fa ka ke zubarwa"
Ya ce "Ki ƙyale ni, zai daina zuba ne"
Cikin kuka ta ce "Ni dai dan Allah ƙyale ni, sai wani abun ya same ka, idan jininka ya ƙare fa mutuwa zaka yi" ba ta ma jira me zai ce ba, ta kasa da gudu, tayi waje. Ta din ga buga gidan maman halimatu, malam lawan ya buɗe, ya tsaya yana tambayarta menene?".
"Dan Allah baban su halimatu, ka taimaka mini, na ga kana da babur, mijina ne aka sare shi dan Allah a kai shi asibiti, sai zubar da jini yake yi"
Ya waro ido ya ce "A daren nan, haka kurum garin taimakonku, wani abun ya same ni, shi ma idan ya samu wani haka zai yi masa, sai da safe" ya rufe ƙofarsa.
Haka ta din ga buga gidajen layin nan, na ƙarshe ne mai gidan ya biyota, sai dai ba shi da abun hawa, suka zo ya tsaya a ƙofar gidan, ta shiga ciki.
Yana zaune, ya kashingiɗa ya lumshe idonsa, yana jin yadda raɗaɗi yake ratsa wurin saran.
"Master, taso mu je"
Bai buɗe idonsa ba ya ce "Ina?".
"Wai meyasa ka ke haka, asibiti mana" tayi maganar hawaye na ta ambaliya a fuskarta.
Ya miƙe yayi waje, ya tarar da maƙwabcin na su a tsaye, suka gaisa Al'amin ya ce "Malam ka rabu da ita dan Allah, ka je ka kwanta, ba wani abu in sha Allah"
Ya ce "A'a ga jini kana ta zubarwa, ni bani da abun hawa, na kira wani ƙanina, a nan titi chemist ɗin sa yake, ko taimakon gaggawa sai a baka"
Tayi farat ta ce "Yauwwa mun gode Allah ya saka da alkhairi"
Haka suka tafi, ya kira ƙanin nasa, ya buɗe chemist ɗin babban wuri ne sosai.
Ya fara yi masa ɗinki, saboda raunin na hannunsa yayi zurfi sosai da sosai.
Sai dai shi da ake ɗinkewa kamar ƙwarya ko a jikinsa, ita kuwa sai uban kuka take yi, tana yi masa sannu.
Kawai bin ta yake yi da ido, har mamaki yake yi, yadda take nuna matuƙar damuwarta a kansa.
Mai Chemist ɗin ya ce "Dan Allah ki daina kukan nan, ba wani abu, ba ki ga shi jarumi bane?"
"To jininsa ba zai ƙare ba, ya zubar da jini sosai tun a gida"
Ya ce "Ba zai ƙare ba in sha Allah, idan ma ya ƙare sai mu saka masa naki".
"Ki daina yi mini surutu a ka kin cika mini kunne" yayi maganar a ƙule. Haushi ne ya cika masa rai, kamar ya kife mai chemist ɗin da mari.
Ta ce "To na daina sannu" tayi maganar cikin kulawa.
A ka gama ɗinki, ya ce zai ɗan saka masa ruwa, saboda ya taimaka masa ya zubar da jini sosai, amma fafur ya ce ba ya so.
Ya haɗa masa magunguna, ya ce ya din ga zuwa ana wanke ciwon, jauhar ta ce "Sai dai ka bani kayan dressing ɗin, ba zai din ga zuwa ba".
Mai chemist ɗin yayi dariya, ya haɗa ya bata, ta ce "Nawa ne kuɗin maganin? Da abun da aka yi masa?".
Maƙwabcin ya ce "A'a kar ki damu, Allah ya bashi lafiya, ni zan biya".
Jauhar sai da ta risuna, ta din ga yi masa godiya, sannan ta ce "Tashi mu tafi" ya miƙe tsam ta bi bayansa.
Suka baro maƙwabcin na su a can, suka nufi gida.
"Sannu, ka na jin jiri ne? Idan kana jin jiri mu tsaya ka huta, ko ka dafa ni" kallonta ya yi ya ga me zai dafa. Ya dai yi shiru bai yi magana ba.
Suka isa gida, ya shiga ɗaki ya zauna, ta fito ta hau aikin wurin da ya ɓata da jini, dan a buɗe su ka bar gidan ma.
Ya zauna ya ci abincin da ya tarar a ɗakinsa, ta ga ledar omo ce da sabulu da ta ce ya sayo, su yayi wurgi da su.
Ta dawo ɗakinsa, ta tarar ya jingina ya lumshe ido, "Sannu master, yana yi maka zafi ne? Ga magungunan nan ka sha kan ka yi baccin".
Ya girgiza mata kai alamar ta ƙyale shi, gumi ya fara tsatstsafo masa, saboda allurar ta sake shi, zafi ya fara ratsa shi.
Saboda kar ta takura masa da surutu, ya kwanta ya hau baccin ƙarya.
Ta fita ta ɗaukko mafici ta dawo, ta zauna a gefensa, ta hau yi masa firfita.
Sai dai lokacin kusan ƙarfe biyu ne na dare, ta din ga zabga hamma, yana kallonta, har bacci ya ci ƙarfinta, ta saki maficin.
Ya buɗe idonsa fes a kanta, har mamaki take bashi, yadda take nuna matuƙar damuwarta a kansa, kuma komai zai yi mata ba ta jin haushi.
Hakazalika bai daina mamakin yadda aka yi, iyayenta suka yarda suka aura masa ita ba.
Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya kira walid, uku sauran nan, ya ɗaga.
"Walid"
"Maza, ya aka yi ne?".
"Ka san akuyancin da yaran nan suka yi mini?"
Walid ya ce "Wane yaran, suwaye?".
"Na baro chamber, na shigo cikin unguwa, kawai na ji sara a hannuna, sun kai su bakwai, suka hau ni da sara, kasheni suka so yi"
Walid ya zabga ashar ya ce "Suwaye?".
"Bari na yi wa ɗaya shaida, haryanzu ba su san waye ni ba, na karya biyu, sauran sun gudu, sun yi mini rauni a hannuna da ƙafata".
"Yanzu kana ina?"
"Ina gida, ni wallahi yarinyar nan ta fara takura mini, komai kuka, duk ta tashi hankalinta, iyayenta ba su yi mata adalci ba, ni fa ba zata hana ni rayuwata yadda nake so ba".
Walid ya ƙyalƙyale da dariya ya ce "Mai dogon zamani, da uban waye ya damu da ka ji koma menene mana, tana da tausayi ne kawai da alama, ka dai daina yi mata muzurai da zare ido kawai"
Yayi tsaki ya ce "Ka saka liti ya nemo mini suwaye yaran nan"
"Shikenan, zamu faso gobe in ga jikin naka, sai da safe". Ya ajiye wayar ya kalli fuskarta, tana ta bacci a zaune.
Hannunsa ɗaya ya saka, ya janyota ta kwanta a kan katifar, shi kuma ya jingina da bango ya cigaba da bacci.
Kasancewar ba salla za ta yi ba period take yi ya sanya, tana ji ana kiran sallar asuba, ta cigaba da baccinta, sam ta manta a ina take.
Ƙaurin da ya isheta ne, ya sanya ta fara tari, tayi juyi ta buɗe ido, da fuskarsa ta fara tozali, yana busa sigari. Ta tashi tana kallon ɗakin, sai yanzu ta tuna ta shigo tana yi masa fifita.
Ta hau soshe-soshen cizon sauro.
Ƙura masa ido ta yi, ya kawar da kansa gefe.
A raunane ta ce "Master"
Idonsa ya ɗago ya kalleta.
"Dan Allah ka daina, ba na so zuciyata ba ta yi mini daɗi, kuma zaka cutar da kanka, kalli yadda ka je aka yi maka rauni, ka zubar da jini, haba master manya ba sa haka" tsuke bakinsa yayi yana sakin hayaƙin, a ƙoƙarin sa na hana maganganun ta yin tasiri a zuciyarsa.
Ta girgiza kai ta ce "Shikenan, ya jikin?".
Yayi mata banza, ya cigaba da busa sigari.
"Dan Allah ko ba zaka daina ba, ka rage mana, lafiyar ka fa".
"Ke, ki koma in da ki ka fito mana, ko na ɗaure ki na ce ki zauna ne? Tashi ki bar mini ɗaki".
Ta gyaɗa kai ta ce "Abun har da gori, Allah ya baka haƙuri" ta miƙe idonta fal hawaye.
Tana kitchen tana aikin karin kumallo, aka buga ƙofa, ta saka hijjabi ta buɗe ƙofar, ta ga walid d wasu matsa su biyu, suka gaisa suka ce mata, wurin mak dogon zamani suk zo.
Ta haɗe rai ta ce "Sunan shi Al'amin, bari na yi masa magana".
Tana shiga ta tarar da shi a falo ya fito.
Ta ce "Ka zauna sai su shigo su ganka, amma ka ga da rauni a jikinka" tayi maganar tana sunkuyar da kai, tana jiran ya gaya mata baƙar magana.
Idonta ya ɗan yi ja, saboda kukan da ta yi.
Ya nemi wuri ya zauna, ba tayi tunanin zai yadda da hakan ba.
Ta je ta leƙa ta ce musu su shigo.
A falo suka tarar da shi, gida sai ƙamshi yake yi, gashi dai ba wani haɗaɗen gida ba, amma ta gyare gidan tsaf.
Suka zauna a falo, Walid ya ce "Maza wallahi ka more, mu ma Allah ya tsamo mu, dan Allah ji wani ƙamshi kamar a gidan masu kuɗi".
"Duba ni ka zo yi, ko munafunci ka zo yi?"
Walid ya ce "Duka, amma dai ya jikin? Kut ka sha ɗinki kamar ƙwarya, za su ci ubansu yaran nan, kan yamma an gano su in sha Allah".
Suna ta zuba, tana jiyo shi yana saka baki sama-sama, da ita ce dai ba zai yi hira ba, amma yana magana.
Tayi sallama suka amsa, ta zo ta ajiye musu kofuna, da cokula da flask ɗin shayi, ta koma ta kawo jallof ɗin taliya a faranti, sai ƙamshi take yi.
Liti ya ce "Allahu Akbar, sannu amarya, wannan hidima haka? Ai da mun sani tuntuni mun zo" Al'amin kallonta yake yi, da jinjinawa ƙarfin halinta, har ta ƙar sanwa, ta yi girki da su.
Suka kewaye, suka din ga cin taliyar nan, liti ya ce "Kalarta kalar girkinta, abincinta mai daɗi, ita kuma 'yar beauty, wallahi maza ka more, ga gida mai ƙamshi"
Ji yayi ya kasa haɗiye abincin, maimakon ya ji daɗin yabon suka yi mata, sai ya tsuke fuska ya tsame hannunsa daga kwanon abincin.
Har suka gama santin, bai sake cewa komai ba, Walid kuma yana ankare da shi, dan haka da gayya, ya cigaba da kunna shi, suka gama abun da za su yi, suka fita tsakar gida suka din ga yi mata godiya.
Walid ya ce "Wai ba zaka fito ka raka mu ba?"
Tayi farat ta ce "A'a ba shi da lafiya ai"
Walid ya ce "Au, to Allah ya baku haƙuri, Allah ya ƙara afuwa ya bar ƙauna".
Bayan fitarsu ta kwashe kwanukan, ta wanke, tana ta aikinta, yana kan doguwar kujera a kwance, sai dai ba ta kula shi ba.
Kusan kwanaki uku, jikin master yayi kyau, ba shi da ƙan jiki, ba zai sha magani ba sai ya ga dama, dressing kuwa cewa yayi ba ya so.
A kwanakin nan jauhar na jin ciwon kai, da ciwon jiki, sai dai ba ta wani damu ba.
Duk yadda ta so hana master fita, da 'yan dabaru sai da ya saka ƙafa ya fice, ya tafi nasa garari.
Cin abinci ne yake dawo shi, ko sau ɗaya bai tambayi yadda take samun yin cefane ba, sai da ya zo ya ci.
Tun da ya dawo gidan ya ji shiru bai ji motsinta ba, kuma bai ga abinci ba, sama da awa guda, saɓanin da, da ya shigo za ta fito.
Kasa kwanciya hankalinsa yayi, ya nufi ɗakinta.
A kwance take a kan gadonta, amma bai tabattar da idonta biyu ko bacci take yi ba.
Ya ƙarasa gaban gadon, sai dai ya manta sunanta, Fatima zahra kuma yayi masa nauyin da ba zai iya faɗa a bakinsa ba.
Ayshercool
08081012143
25
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Dukan gefen katifar da take kai yayi, amma ba ta motsa ba, ya zura kai ya leƙa fuskarta, ya ga bacci take yi. Duk da bai saba zuwa ya tarar da ita tana bacci ba.
Ficewa ya yi, ya bar ɗakin, shi babban takaicin sa, rashin samun abun da zai ci.
Jauhar kuwa, tun dare ta kwana ta na fama da matsanancin ciwon mara, ga ulcer ta tayar mata, sai gudawa take fama da tashin zuciya, ta samu ya lafa mata, ta kwanta ta hau bacci ga gidan yau babu abun da za ta dafa, ɗan kuɗin hannunta sam ba su da yawa.
Ƙarshe dai buredi ya fita ya samo, ya dawo ya zauna a falo yana ci.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga kiran indabo ne, kallon wayar ya cigaba da yi, yana cin buredinsa, sai da ta kusa katsewa ya ɗaga ya saka a kunnensa, yayi shiru.
"Aminu"
"Mmm"
"Na dawo, kai nake jira, haryanzu ba ka zo ba"
"Zan zo"
"Yaushe kenan? Haba kai kuwa dan Allah, ba ka san kiran me nake yi maka ba fa"
Al'amin ya ce "Na ce zan zo ai"
"To shikenan, Allah ya kawo ka"
Ya ajiye wayar, gaba ɗaya haushin buredin da yake ci ma yake ji, sam ba ya yi masa daɗi, har aka yi kiran la'asar, ba ta fito ba.
Ya tashi yayi salla, ya fito falo ya sake zama, sai ga ta ta fito tana ɗan yamutsa fuska. Fuskar duk ta ɗan ɗaga tayi jawur.
Ta zo ta nemi wuri ta kwanta, ba tare da ta ce masa komai ba.
"Wai yau ba abinci ne?" Yayi maganar yana wani basarwa.
Maimakon ta ce masa babu abun da za ta dafa ne, sai ta ce masa "Ba na jin daɗi ne"
Ya taɓe baki, ya tashi ya saka takalmansa ya fice daga gidan, fitarsa ba kaɗan, ta ji horn da tsayuwar mota a ƙofar gidan, mintuna kaɗan ta ji ana bugun gate, ta saka hijjabi ta je ta buɗe.
Baba ta gani a tsaye, cikin matsananciyar murna ta ce "Baba" yayi