Karfe A Wuta

Chapter 81 of 167

"Ai ba aro ba ɗani, balle kyauta" dama a karambani, Nabila ta iya mota, a kan ta Nasir, ya karɓi mukullin, walida ta ce bari ta zo a ɗana su, amma Nasir ya ce mata a'a, su biyu kawai za su fita.

Suna tafe yana driving, bakinta yaƙi rufuwa.

"Wow na zama big girl, idan zan je trial, sai dai a ganni a motata, a din ga cewa hajiya, shikenan na huta da hawa ɗan sahu, da masu warin hammata da zarnin fitsari" ya ƙare mata kallo, sai nishaɗi take yi tana murmushi.

"Arfa"

"Yes sir"

"Ina son mu yi magana ne"

Ta kalleshi ta ce "To yaya"

"Shari'ar da ki ke yi, da kuma adawa da Naja'atu Bunkure"

"Ok ina jinka"

"You have to withdraw the trial"

"What?"

Nasir ya ce "For your own good and safety, mace ce mai hatsarin gaske, kar wani abu ya same ki, Abba ba zai iya jurewa ba, nima kuma haka ki rabu da matar nan"

Nabila ta ce "Yaya, ni fa dama masu ƙaunata ba su da yawa a duniya, dan haka ka ƙyaleni, why would that innocent old man suffer just to cover someone's evil did, ita kuma ta din ga zaluntar mutane, kuma ayi mata shiri, i can't nima Allah ya tsaya mini".

"Shut up, ina magana kina mayar mini, babu wanda ya shiga cikin maganar sai ke, tun da ki ga kowa baya tsoma baki a lamarinta, dan me ke zaki yi? Ki janye shri'ar nan tun ban saɓa miki ba, tun da baki san ciwon kanki ba. Ya zama dole ki janye, idan ba ƙafar wando ɗaya ki ke so mu saka da ke ba" ya haƙiƙance yana yi mata masifa. Tayi masa shiru, gaba ɗaya ta nemi farincikin da take ciki ta rasa, saboda maganar da Nasir yayi, ya gama zagayawa suka koma gida.

Matan Abba kuwa mussaman mama, ta din ga mita a kan saya wa Nabila mota, itakaɗai a gidan, amma ya ce gidansa ne, abun da ya tsara shi za ayi, ba wanda aka tsara masa ba. Lokaci ne yayi da zasu girbi abun da suka shuka masa a kanta.

Gaba ɗaya sai ta rasa karsashi, ta na ta zumuɗin kiran sumayya, amma yanzu ta kasa, saboda haushi da mamakin abun da Nasir yayi mata yanzu.

Kawai sai ta kira Viper, ya ɗaga ya saka a kunnensa.

"Ina wuni, ya jikinka kuwa?"

"Alhamdilillah" sai da ta tashi tsaye jin ya amsa ta ce "Kai, yau ka amsa mini, masha Allah, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ya kare mana kai. Dama na kira ne in ji ya jikinka, kuma" sai tayi shiru, shima shirun yayi bai yi magana ba.

"To ka tambayeni menene mana? Shikenan ma na san ba kulani zaka yi ba, sai anjima" ta kashe wayar ta ajiye, ta kwanta tayi shiru, zuciyarta a cunkushe babu daɗi, ga abun farinciki, amma Nasir ya ɓata mata. Kawai ta fashe da kuka, ta yi ta gama, ta kwanta ta hau bacci.

***
Yau a kotu, hujjojin da Nabila ta bayar masu kyau ne sosai da sosai, sai dai lauyan gwamantin da yake kare ɓangaren ramma, sun fita gogewa suka din ga dankwafar da ita, kuma alƙalin ya din ga ɗaukar side, tare da soke wasu daga cikin hujjojin Nabila. Ya sake ɗaga shari'ar zuwa wata guda. Ta kalli dattijon, gaba ɗaya sai ta ji ta fara karaya.

Jiki a sanyaye ta fito, tana fitowa murtala yana tsaye a harabar kotun yana jiranta.

Kamar ta fashe da kuka ta ce "Yaya murtala kaga yadda shari'ar nan ke tafiya ko?"

Murtala ya ce "Kar ki damu, ai idan sun san wata, ba su san wata ba, kamar yadda muka tsara zan tattauna da ke a kan shari'ar yanzu, ki faɗi hints mai muhimmanci, zamu saka a live program yau da ni da Sumayya, sai dai duk mai faruwa ta faru.

Cikin damuwa ta ce "Kar fa ku samu matsala a wurin aiki"

"Manta da su, duk da su ake haɗa baki ai, dattijon ne ma abun tausayi"

Nabila ta ce "Wallahi ko kallonsa nayi, sai tausayinsa ya kama ni, bana son na kasa sakawa a wanke shi"

Murtala ya ciro recorder ɗin sa, ya tattauna da Nabila, na mintuna biyar, a kan shari'ar sannan ya tafi.

***
Indabo tamkar zai kwaɗawa Abdul mari, saboda takaici "Abdul wai me kake nufi da ni ne? Sai ka yi mini asarar wahalata, uwar me ka dawo kanon ka yi? Uban wa ka ajiye da ka taho, mutane sun zauna suna jiranka, kawai a nemeka a rasa, wane irin rashin mutunci ne, da iskanci har haka? Wato tona mini asiri zaka yi, ka nuna wa duniya ban isa da kai ba ko?"

"Daddy, uzurin gaggawa ne ya taso mini, wata tiyat.....

"Ubanka da kai da tiyatar, ko tunanin ɗan uwanka da yake mexixo a tsare baka yi, dole sai ka nuna mini ban isa da kai ba, ka cigaba kar ka fasa ka kuma kyauta"

Wayar Abdul ta fara ringing, ya cirota ya ga lambar ramma, ya ɗaga a saka a kunnensa, yayi ƙasa da murya ya ce "Beb"

"Abdul kana ina?"

"Ina gida meyafaru?"

"Tun jiya fa zazzaɓi nake yi, cikina sai ciwo yake ina amai"

A rikice ya ce "Subhanallah, kina ji na, ki duba side bed drower, akwai pcm, ki ɗauka ki sha, daga shi kar ki sha komai, gani nan zuwa kin ji, ki samu ki kwanta" sai da ya kashe wayar, ya tashi tsaye, ya ankare da katoɓarar da yayi, gaba ɗaya ya manta a gaban wa yake.

"Abdul karuwa ka ajiye gidanka, har take rashin lafiya, saboda iskanci a gabana kuma kake waya da ita?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a ba karuwa ba ce Daddy..ammm....

"Abdul, yanzu ba zaka daina sakarcin nan ba, sai abokan adawa sun farga, sun fitowa da duniya waye kai? Uban wa zai yadda ya zaɓeka, idan mutane suka san you are womanizer? Kuma har ka ajiye mace a gida, bama ka yi shahshashancin ta tafi ba. Na haramta maka kwana a waje, duk in da kake ka dawo gida ka kwana, kuma a cikin watan nan za ayi bikinka, ko ka yarda ko baka yadda ba".

Abdul ya kalli Indabo ya ce "Dan Allah Daddy ka bari na kawo wadda nake so na aura, ni wallahi bana son waccan yarinyar, ni ka bari zan yi maka bayani"

"Babu wani bayani da zan saurara daga gareka, dan nawa bayanin ne gaba da naka, kuma kaje ko sallami koma wace karuwar ce daga gidanka, tun kan na biyoka na ci maka mutunci" cikin sauri ya fice, yana sake kiran rahama, a ransa yake jin sai dai ayi wadda za ayi, ko da kuwa hakan yana nufin bayyanawa duniya ramma ne.

***
Yana tsaye a jikin bishiya, ya juya wa hanyar da take tahowa baya, yayi crossing ƙafarsa, hannunsa ɗaya riƙe da taba, ɗaya kuma yana danna wayarsa. Daga bayansa kawai, sai mutum ya so ya juyo ya ga fuskar sa, suffarsa ta ƙaƙƙarfan namiji duk a bayyane, saboda yadda damtsensa yake a murɗe, ya cika hannun shirt ɗin sa, hannunsa ɗaya kuma ya sha ɗinki. Rigar ja sai dogon wandonsa baƙi.

"You are under arrest, officer ku kama shi" ko motsi bai yi ba, balle ya waiwayo, ta zagaya ta gefen bishiyar, tana leƙa fuskarsa, ya ɗaga kai ya kalleta ta ce "Kai baka jin tsoro ne?, ba ka ji tsoro ba da na ce you are under arrest" ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Tsoro?"

Ta ce "Eh mana"

"Hmm" kawai ya ce, ya zuƙi sigarinsa, ya kawar da kansa gefe, ya din ga sakin hayaƙin, in a passionate way"

Ta zuba masa ido, komai nasa na daban ne, kuma na musamman.

"Wurinka na zo"

Ya ɗaga mata idonsa da girarsa ɗaya alamar yana jinta, hakan ya sanya ta ɗan diririce.

Ya samu wuri ya zauna, ita ma ta zauna, ta kalleshi ta ce "Sannu ya hannunka? Na ga da sauƙi ma baka da ƙan jiki" ya kalli ciwon, ya basar, ya sake zuƙar sigarinsa.

Yana sakin hayaƙin, ta fara tari, ya kashe sigarin a jikin bishiyar, ya ce "Ina jinki".

Tayi gyaran murya ta ce "Raina ma fa babu daɗi, shari'ar nan da nake yi, so suke su yi mink fin ƙarfi, na fara sarewa kuma hope ɗin iyalin mutumin duk a kaina yake, ni da na gansu ma sai in ji zan yi kuka" tayi maganar tana goge hawayenta.

"Ohh, a haka za a tsaya mini? Idan bamu yi nasara ba, sai mu zauna mu yi kuka?" Ta girgiza kai ta ce "A'a zamu yi nasara in sha Allah, shaidar fa da na gabatar babbar shaida ce, wani ya turo mini voice na maman Yarinyar, tana kuka ta ce a taimaka mata, amma wanda ya turo ɗin yayi blocking ɗina, sai kuma aka ajiye mini wannan a office ɗin" tayi maganar tana ciro file ɗin tarihin Naja bunkure ta miƙa masa daga cikin jakarta ta goyo.

Ya karɓi file ɗin ya fara dubawa, ya miƙa mata hannunsa, ya ce "Bani wayarki" ta ce "Wayata?" Yayi shiru yana kallont, dan ba zai maimaita ba.

Ta ciro ta cire password ta miƙa masa, ya karɓa yana dannawa.

Ta zura kai tana leƙa wayar, ta ce "Me kake nema a wayar?" Ya janye wayar ya cigaba da dannawa.

Kiran Nasir ne ya shigo, ya miƙe mata dan ta ɗaga, ta girgiza masa kai ta ce "Rabu da shi"

"Ki ɗaga ki gaya masa muna tare, ba nemana yake yi ba?"

Ta kalleshi ta ce "Ga wayar nan a hannunka, ka ɗaga ka gaya masa" kafin ta rufe bakinta, ya yi accepting call ɗin, ya kai wayar kunnensa.


Ayshercool
08081012143

56
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Wata irin zabura Nabila tayi, ta kai hannunta zata karɓe wayar, amma ya riƙe hannunta yana kallonta, girgiza masa kai tayi da sigar magiya tana kallonsa.

"Hello. Hello, Arfa" muryar Nasir ta fito rangaɗau a wayar.

Viper ya ɗaga idonsa yana kallon ƙwayar idonta, ga mugun riƙon da ya yi wa hannunta da take jin tamkar zai ɓalle.

"Arfa kina ina ne? Hello kina ji na?"

Kallon da Viper yake yi mata, gaba ɗaya sai ta rikice, ga kusancin da suke da shi, ta ƙara rikicewa. Kasa daurewa tayi ta ce "Wayyo hannuna"

"Nabila, menene? Kina ina ne?"

Al'amin ya sakar mata hannunta, ya katse kiran, ta ja da baya tana murza hannunta tana ƙifta ido.

"Amm meye ma sunan naki?"

Ta kalleshi tana turɓuna fuska ta ce " 'yar madara"

Cikin sauri ya kalleta ya ce "Iyee?"

"To idan ban kai 'yar madara ba, ka din ga ce mini 'yar suga, ko mazarƙwaila" tayi maganar tana cigaba da murza hannunta.

"Baki shiryawa wannan ranar ba, ki ka yi gammon ɗaukar abun da baki san a ina zaki sauke ba?"

Ta gyara zamanta ta ce "Nayi mana, ai shi ramin ƙarya ƙurarre ne. Amma yau  da ka gaya wa DSP muna tare, da ka gama kashe ni da raina, ban gama da aikin gabana ba, ka sake ɓallo mini ruwa.
Zaman kotun nan na yau ya bani haushi, Alƙalin alamu sun nuna side zai ɗauka, gashi dattijon nan ya musa ya ce ba shi bane ba, sun kafa hujja da shi ne, wai lokacin da abun ya faru daga shi sai ita, kuma ita da shi da wata mai aiki ne, amma har gidan ɗayar  naje ban same ta ba.
Su kawo ita rammar kotu, ba su kawota ba, ba su da wata tabbatacciyar shaida, recording ɗin da na gabatar, an soke an ce sai dai uwar taje da kanta, ni na rasa me ma zan yi wallahi" tayi maganar cikin matsananciyar damuwa.

Ya nuna mata file ɗin hannunsa ya ce "Waye ya baki wannan?"

"Ban san waye ba, a kan teburina kawai na ganshi da safe" ya cigaba da daddana wayarta, ba tare da ya kalleta ba ya ce "Kin ɗauki hotona, dan ki nuna wa yayanki ya kama ni?"

Ta kalli wayar hannunsa, ta ce "Ai nayi hiding ɗin hoton, ya aka yi ka buɗe?"

Ya sake kallonta ya ce "Me kike da hotona?"

Nabila ta ce "Saboda in din ga kallonka, ina jin daɗi, askin nan da aka yi maka kayi mini kyau sosai da sosai ne" tayi maganar tana murmushi.

"Amm, amma dan Allah ina ka tafi, naji su Oga walid sun ce, ɓata kayi, wai ranar da muka rabu ina ka tafi? Can ka koma ko? A can aka ji maka ciwon nan. Na tsorata da naga an yanki cinyar wani, da sun ganni nima kasheni za su yi ko?"

Gyaɗa kai yayi, ya ce "Kina da system?"

"Eh tana gida amma" ya cigaba da danna wayarta.

"Wai dama kana magana haka? Baka taɓa yi mini doguwar magana ba sai yau. Hmmm da tabon wuƙarka da ka yi mini zan koma ga Allah, ka kusa fa kashe ni ranar farko da muka haɗu, ban san laifin da nayi maka ba ka kusa kashe ni. Amma dai yau ba ka sha komai ba ko? Naga yau ka yi mini kirki" jefa mata wayarta yayi ya tashi tsaye, ya ce "Ki kula da kanki, ana bibiyar ki, ana bibiyar wayar da ki ke yi da wata sumayya, akwai alamar tana bin diddigin abubuwan da ki ke yi, ko kuma ana bibiya bata sani ba". Ta tashi tana zare ido ta ce "Sumayyan?"

"Wanda yake bibiyarki, shi ya turo miki wannan voice ɗin, ya baki tarihin bunkure, duk da bai baki complete ba. Yana bibiyar ki ko dan ya taimake ki, ko kuma yana da manufar da yake son cimma, dan haka ki kula"

Ta dafe ƙirji ta ce "Amma meyasa za a din ga bibiyata da sumayya? To wa ka ke tunanin yana bibiyata? Ka yi mini bayani sosai da sosai to me ma nayi za a bibiye ni?. Ya cigaba da tafiya bai bata amsa ba, tabi bayansa tana cigaba da magana.

Ya tsaya cak, ya waiwayo ya kalleta, tsayawa tayi ita ma, tana kallonsa tana jiran taji mai zai ce?.

"Kin haɗu da Indabo?"

Shiru ta yi, sai kuma ta waro ido ta ja da baya, ta ce "Wai indabo ɗan siyasar nan, shi ne dai na cikin labarinka? Na ganshi a wurin aikin su sumayya, subhanallah shiyasa tun a ganin farko da nayi masa naji na tsane shi".

"Ya ganki?" "Eh, sai dai ban kula shi ba. Ai ni bai sanni ba, nima kuma ranar na fara ganinsa, sunansa kawai nake ji, amma menene?"

Ya girgiza kai ya ce "Shikenan" ya cigaba da tafiya.

Ta sake bin sa tana ɗan haɗawa da gudu, saboda saurinsa ya fi nata sosai, "To ka yi mini bayani, ni menene haɗina da shi to?"

"Babu, ki je ki mayar da hankali a kan wannan case ɗin, idan kin yi wining sai ki dawo, kar na sake ganinki a wurin nan"

Cikin rashin fahimta ta ce "To amma"

"Take your way, ki tafi na ce" yayi maganar yana nuna mata hanya, ƙyam ta tsaya tana kallonsa, mamaki ne ya cika shi, tsawar da yayi mata ko a jikinta, ta tsare shi da idanunta masu matuƙar haske, yanayin yadda take abubuwan ta, ya sake tabattar masa da akwai sangarta a tare da Nabila.

Ya juya ya tafi, ita kuma ta tsaya cak, tabi bayansa da kallo, tafiyarsa kawai gwanin burgewa, tafiya yake yi cike da ƙasaita, da bayyanar da ƙarfin da yake da shi, sai dai shi bai san yana hakan ba, har ya ƙulewa ganinta, sannan ta juya ta fara tafiya.

Sai yanzu take wasu lissafe-lissafe, tabbas sumayya ta canza, sun rage yin waya sosai yanzu, kuma ba ta kiranta da layinta sosai yanzu, kenan da gaske haɗa baki aka yi Sumayya a bibiyeta? To waye yake bibiyar ta ta? Farar motar nan ce ya faɗo mata a rai.

"To idan kuma an san ina zuwa nan fa, aka tona mini asiri, ina zuwa wurin mai laifi da ake nema ruwa a jallo. Wace amsar zan bayar na kare kaina?.

"Wai me ma ya aike ni tun farko? Ina zaman zamana" tana tafe a hanya, wani irin ciwon kai ya saukar mata, da kyar ta ƙarasa gida.

***
A kwance Abdul ya tarar da ramma, cikin damuwa ya ce "Rahama ya aka yi baki da lafiya, har na fita baki gaya mini ba?"

Ta yamutsa fuska ta ce "Na zata zan warke ne, ba sai na sha magani ba"

"Wannan ai ganganci ne, ko dai ciki ne?"

Da sauri ta ce "A'uzibillah, Allah ya yi mini tsari, ai kai ma ka san ba shi bane ba"

"Duk da haka, sai na gwada" first aid drower ɗin sa ya buɗe, yayi mata gwaje-gwaje, babu ciki sai malaria.

"Rahama, wurin nan babu sauro a ina ki ka samo malaria kuma?"

Ta kalleshi ta ce "A jikinka"

Yayi murmushi, ya haɗa allurai, zai saka mata cannula, ta hau kuka wai ba ta so.

"Rahama kina wahalar da ni, yanzu alluran baki zan yi ki shanye ko kuwa?"

"Ni hannunka da zafi gaskiya, ka samo wani yayi mini" ya harareta ya ce "Wani wa? Babu wani mahaluki da zai ganar mini jikinki a doron duniyar nan, ina kallon shi"

"Eh amma ai kai ka iya kallon na wasu"

"Duk cikin aiki ne, kuma ki yi mini shiru nayi aikina, ko na caccaka miki allurar har a baki"

Ya saka mata cannula, yayi mata allurai, ya saka mata ruwa, da duk ya ajiye su a gidan, saboda ramma.

Ya rungumeta a jikinsa, yana shafa saman cannulan, ɗaya hannun kuma yana matsa jikinta a hankali.

Ya zubawa hannunta ido, daga lokacin da ya ɗaukkota zuwa yanzu, ta canza sosai da sosai, fatarta tayi kyau, tayi haske. Ramma ba wani shahararren kyau ne da ita ba, amma yana jinta a kusa da zuciyar sa, duk da ba wani shiri suke yi ba, duk in da ya tafi tana ransa.

Bai taɓa raping

Download complete TXT · Novel page