Karfe A Wuta

Chapter 84 of 167

yi magana ka amsa laifinka, ka sauƙaƙa mana kai ma ka sauƙaƙawa kanka, idan ba haka ba mu zamu bi hanyoyin da zasu sama mana sauƙi"

Al'amin ya ɗago da kyar, saboda a cikin mayen da yake, suka yi dukan tsiya, tamkar sun samu jaki, jikinsa ya ƙara mutuwa, kowace gaɓa ta jikinsa ban da ciwo, babu abun da take yi.

"Ka amsa, ka ce ka sha kayan maye ka kashe matarka"

Gefen bakinsa duk jini, sun tuɓe shi, daga shi sai vest da gajeren wando, ya sake ɗaga idonsa, karo na farko yayi magana ya ce "Ina jauhar?"

"Ban sani ba, ni kake tambaya ina juahar? Bayan ka kasheta?" Tsaki yayi, ya taƙarƙare ya yinƙura ya tashi tsaye, suka saka kokara suka daki ƙafafuwansa, ya hantsila ya faɗi a wurin.

Duk abun nan da ake yi, da jibgar da yake ci, shi kawai mafarki yake yi, jira yake yi ya farka, dan ba ya son baccinsa ya cigaba da nisa, zai kai Jauhar asibiti da wuri.

A haka aka shafe kwanaki bakwai, amma Al'amin, yaƙi sakawa ransa cewa gaske ne ba mafarki ba.

Kwanaki bakwan nan, babu wanda ya zo in da yake, ba wai dan ba a samu masu zuwan ba, an hana kowa ganinsa.

Liti da walid, da sauran jama'arsa babu irin sintirin da ba su yi ba, amma aka hana su ganin sa.

Mutuwar jauhar, ta karaɗe kowane gidan jarida, unguwanni zuwa gidaje.

Abbu yayi kuka tamkar zai yi hauka, yayi dana sanin kasancewar sa mahaifin Al'amin.

Gidansu jauhar kuwa, ba su san sun yi rashi ba, sai da aka tabbatar da mutuwar jauhar, kowa kuka da zubar da hawaye.

Abbu yana kuka, ya sanya gwiwoyinsa a ƙasa, yana roƙon Baba ya yafe masa, da ya san Al'amin zai kashe masa 'ya, ba zai yarda a aura masa ita ba.

Baba ya girgiza kai ya ce "Alhaji Ibrahim, ni wallahi haryanzu ban ji na yadda Al'amin zai kashe mini 'ya. Akwai abun da ya faru ni ban yadda shi ya kashe mini jauhar ba"

Abbu ya ce "Wace hujja kake nema ko shaida bayan wannan? Ni na haifi Al'amin, kuma kowa ya san yana ta'amalli da miyagun ƙwayoyi"

Cikin kuka mama ta ce "Yaron nan ya cuce mu, bai yi mana adalci ba, haihuwar ɗa irin jauhar a gidan nan, daga kanta an gama, ba ayi ba, kuma ba za ayi ba"

Hafsa ta girgiza kai ta ce "Baba nima ina bayan maganarka, ƴan kwanakin nan, ina zuwa gidanta sosai da sosai, ina haɗuwa da shi, ita take bani labarin galabar da ta ci a kansa, da bani misalai daban-daban da aurenta. Son da yake nuna mata a gabana ba ya jin kunyata ko nauyina, suna matuƙar ƙaunar junansu. Har take gaya mini na tayata da addu'a, yanzu sigari ce kawai damuwarta da shi, har sai da na ji raina ya biya, da irin kalar soyayyar da suke yi wa junansu, dan haka gaskiya ban yadda mai zamani zai kashe jauhar ba, mutumin da idan zata fita baya nan, yake sawa ana bibiyarta dan kar wani ya kawo mata farmaki, mugwayen karnuka ya ajiye a layinsu, suna gadinta lokacin da yayi tafiya, duk dan kar a taɓa ta, gaskiya ban yadda ba".

Anty ma tana kuka ta ce "Babu abun da mai shaye-shaye ba zai iya aikatawa ba, dan haka ba abun mamaki bane dan an ce ya kasheta, Allah sarki jauhar wannan wane irin mummunan ƙarshe ki ka yi?"

A fusace Saifu yana kuka ya ce "Kar ki sake aibata mana gawar jauhar, wallahi ba ta yi mummunan ƙarshe ba, ta bi Allah, ta yi wa iyaye biyayya, ta yi biyayyar aure, idan ana nuna ɗan aljanna a duniya to jauhar ce, koma wane irin mutum ne shi, ai ku kuka yi bita da ƙullin da ta aure shi, kuma wallahi Allah ba zai bar kowane azzalumi ba, ita ta mutu ta huta". Haka aka din ga musayar yawu, har sai da Baba ya tsawatar tukuna.

Da taimakon Naja'atu Bunkure, suka haɗa kai da lawyoyin gwamnati, Indabo ya cika su da kuɗi, har da alƙalin kansa. Domin tsayawa tsayin daka wurin tattara shaidu da hujjoji.

Haka zalika ta fito ta bayyanawa duniya cewa, zata tsaya tsayin daka, har sai ta ga abun da ya ture wa buzu naɗi, sai an bi wa jauhar hakkinta, na kisan gilla da viper ya yi wa jauhar, mussaman dama ya riga yayi suna a harkar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma harkar daba.

Ranar fara shari'a, haka aka zo da mai zamani a cikin sarƙa, yana ɗingisa ƙafa, saboda azabar da ya sha a hannun 'yan sanda, a kan ya amsa cewa shi ya kashe jauhar.

Aka fara gabatar da shari'a, wani lawyer ya gabatar da kansa a matsayin wanda zai kare Al'amin, bai taɓa ganinsa ba, sai ranar a cikin kotun.

Aka gabatar da charges ɗin da ake yi wa Al'amin.

Ɓangaren tawagar lauyoyin gwamanti, da su Naja bunkure, suka din ga gabatar da shaidun bogi, suka kawo ƙwayoyin da suka samu a gidan Al'amin, tare da kawo bayanan likita, na cewa dukanta aka yi har ta kai ga rasa ranta, da abun da yake cikinta.

Abun bai tsaya a nan ba, sai da aka kawo malam lawan, bayan shaƙa masa wasu muhimman kuɗaɗe, ya zo ya bayar da shaidar Al'amin ya saba dukan jauhar, idan ya je ya sha ya bugu, haka za su yi ta jiyo ihunta yana dukanta, a ranar ma sun ji kukanta, sai dai ba su yi zaton zai kasheta ba.

Muryar Liti ce ta dawo da Al'amin hayyacinsa, dan duk surutan da ake yi, bai san me ake cewa ba.

"Ƙarya kake yi dan ubanka, Viper ba ya dukan yar madara, ba ita ba kowace mace ma baya duka, a matsayin ku na maƙota idan yana dukanta, meyasa baku kai wa yan sanda ba, ƙarya kake maƙiyin Allah la'ananne, Viper ba zai taɓa cutar da matarsa ba, ba shi ya kasheta ba" jami'an tsaro suka yi waje da liti.

Sai dai wani irin ihu da Viper yayi, sai da wasu suka fara gudu, ya daki katakon gabansa da ƙafarsa ya ce "Ƙarya ne, jauhar tana nan a raye, gobe zata haihu, matata  bata mutu ba"

Da ƙyar aka danne shi, Alƙali ya aika shi gidan prison, tare da ɗage shari'ar.

Haka ya cigaba da buge-buge, tamkar zai jefar da motar gidan yarin, sai da suka sumar da shi, sannan suka samu nutsuwa.

Tun daga wannan ihun, bai sake magana ba, ba cin abinci, sai dai zai yi salla kawai.

Har aka yi zama na biyu a kotu, bai ce uffan ba, duk wasu hujjoji Bunkure ce ta samar da su, lawyern gwamanti gabatarwa kawai yake yi.

Sai dai juyin duniya, ya yi magana, yaƙi yi.

Bunkure ta je gaban Al'amin ta tsaya ta ce "Amsa ɗaya kawai kotu take buƙata daga bakinka, kai ka kashe matarka jauhar?"

Ya ƙura mata rinannun idanunsa, ta din ga yi masa wani irin kallo, mai cike da rainin wayo.

Ya jinjina mata kai alamar eh.

A nan suka buƙaci a ƙarƙare shari'ar, ba tare da wata huɓɓasa ba, lawyern Al'amin, ya ce ya yarda da duk abubuwan da masu gabatar da ƙara suka gabatar. Daga haka aka sake ɗaga shari'ar zuwa wata guda.

Wata gudan da sai da ya shafe shekaru biyar a prison, ba a cigaba da shari'ar ba, ba kuma a sallame shi ba.

Kullum burinsa shi ne ya farka daga mafarkin nan da yake yi, shi dai ya san matarsa na raye, ba ya cin abinci baya iya bacci, ya koma tamkar mahaukaci.

Sai dai lokaci zuwa lokaci yana yi musu ihu, da kiran matarsa, ya kan kira sunan madaki da Indabo.

Lokaci lokaci, ya kan ga aiken abinci, hakan ya sanya ya ƙara sakankancewa jauhar ce ke yi masa aike, bai sake ganin wani yazo wurinsa ba, tsawon shekaru biyar ɗin nan.

Rana tsaka aka ce masa ya fita ya tafi gida an sallame shi.

A ƙofar prison ɗin ya tsaya, yana tuna lokacin da ta zo tafiya da shi, lokacin da aka rufe shi, aka ce an kama shi da cocaine.

Bai tsaya ko ina ba, sai unguwarsu, da ƙafa ya taka ya tafi, amma ya tarar da gate ɗin a rufe.

Sai yayi tunanin ta koma gida ne, dan haka sai ya fara tafiya gidansu, dan tabattar wa.

Gidansu ya fara zuwa, rahila da yaranta, gaba ɗaya suka dare, suka gudu ɗaki tana ihu ta ce "Ka fita ka kore shi, gashi can an sako shi, Allah wadaran yan siyasa, sun sako masifa da annoba, wanda bai san halacci ba".

Abbu ya fito ya kalli Al'amin, ya koma kamar wani mahaukaci, a gigice ya nufo Abbu ya ce "Abbu, ina jauhar? Ta haihu ne? Ina abun da ta haifa?"

Abbu ya ja da baya ya ce "Kar ka matso kusa da ni, Jauhar tana gidan uwarka da ubanka, dama ka gaya mini zaka kasheta, kuma ka cika alƙawarin ka Al'amin, na gode da muguwar sakayyar da ka yi mini, da ɓata mana sunan zuriya. Ka fita babu ni babu kai, ka nemi wani uban bani ba, na sallamawa duniya kai, ba zan cigaba da rasa makusantana, mutanen da nake ƙauna ba saboda kai, ka je na yafeka a duniya"

"Na ji na yadda, amma ina jauhar? Sun ce idan na ba su abun da suke so, zasu kai ni in da take"

"Sai dai ka bita kabari ka ɗauki ɗan naka, mara mutunci, ka fita ka bar mini gida, bana ƙaunarka bana ƙaunar ganinka"

"Ba zai yiwu ba, wallahi sai kun fito mini da matata" ya juya ya fita da gudu, ya tafi dabar su, incomplete building ɗin da suke zaman shaye-shaye.

Su Walid suna ganinsa, suka rirriƙe shi suna kuka, ya watsar da su ƙasa, ya ce "Walid, ina jauhar? Na san ta haihu ko?"

Walid ya tashi tsaye ya ce "Viper ka nutsu mana, ya aka sako ka ne? Ba yadda bamu yi ba, a ƙarasa shari'arka mu ɗaukaka ƙara aka ƙi"

"Dalla ina tambayar ku, ina jauhar, ko ta koma gidansu, ku bani kaya na canza na je wurinta, na san hanata ganina aka yi"

Hawaye na zuba a idon liti ya ce "Viper, Ƴar madara fa ba ta raye, ta rasu"

Al'amin yana zuwa nan a maganar, yayi shiru, yayi fatali da kayan gabansa, ya fara wani irin haki, yana nema ya kurma ihu.

Nabila tana kuka, ta toshe masa baki tana girgiza masa kai.

Ya saka hannu, ya cire hannunta daga bakinsa ya ce "Ban cancanci na haukace ba? Ban cancanci na nemi fansa ko ta wane hali ba kenan?"

Nabila ta girgiza masa kai, kuka ya hanata magana.

"Na kashe matata, ni na kashe jauhar ɗina, halittar da ta nuna mini tsantsar so da ƙauna"

"Ba kai ka kasheta ba"

Cikin tsawa ya ce "Ni ne, ni na kasheta. Meyasa da Abbu ya ce mini zai yi mini aure, na ce zan kasheta, ya ce mini Allah ya taimaka? Meyasa na kasa tuba na daina bangar siyasa da daba, a lokacin da zabra take ta ankarar da ni illarta, mai yasa sakamakon laifina ya faɗa kan matata?"

"Astagfirullah, Viper kar ka yi saɓo"

"Meyasa ban karɓi ƙaddarata ba tun da farko, na furta idan aka yi mini aure zan kasheta? Meyasa na jinkirta barin aikata laifi, sai da na rasa mutane masu muhimmanci a sanadin daba da shaye-shaye. Daba da bangar siyasa ta yi mini mummunan tabo, na kasa zubar da hawaye ko sau ɗaya tsawon shekarun nan, meyasa ba zan haukace na huta ba.
Ina son matata, laifina ya shafe ta, ba ta ji ba bata gani ba, na kasa yadda ta mutu, haryanzu ina ganinta ina ganin ɗana a jikinta. Ko ban ɗauki fansa ba, ina fatan na haukace, ko na bita na huta. Ina ma jauhar ba ta sanni ba, da yanzu tana nan tana rayuwa cikin farin ciki, bani da sa'a ko kaɗan a rayuwata, duk wanda na saka sonsa a raina, sai Daba da bangar siyasa tayi masa illa"

Huci yake yi, idanunsa suka rine zuwa ja mai ban tsoro.

Ta sake mayar da hannunta bakinsa, ta rufe masa, tana kuka ta fara furta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Astagfirullah wa atubuilaihi"

A hankali ya fara maimaitawa shi ma, jikinsa na kyarma, kamar wanda ake kaɗawa gangi.

Nabila ta ce "Ka yi i ajiyar zuciyan da kake dannewa" ya kama ɗaya hannun nata, ya ɗora saitin zuciyarsa, yana wani irin haki, wani irin bugu zuciyarsa take yi mai ban tsoro.

A take ya saki wata irin nannauyar ajiyar zuciya, tare da hawayen da suka maƙale a tsakiyar zuciyarsa tsawon shekaru shida!

Ayshercool
08081012143

58
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Cikin matsanancin tashin hankali, Nabila tana kuka ta ce "Viper zuciyarka fa, dan Allah ka nutsu zata daina aiki, idan ta cigaba da bugawa a haka, ka cigaba da istigfari da maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un" tayi maganar cikin damuwa, ƙara danna hannunta yayi a kan ƙirjinsa, yana wata irin shaƙuwa mai haɗe da haki, numfashin sa na fita sama-sama.

A jejjere zuciyarsa take bugawa da ƙarfin gaske.

Cikin tausayawa take kallon sa, Al'amin yana buƙatar kafaɗar da zai kwanta yayi kuka, babu wanda ya fuskanci ainihin matsalar sa, kowa ɗora masa laifi kawai yake yi, iftila'in da ya faɗa masa, kowa ya dare ya bar shi, sai abokansa duk da suna iya ƙoƙarin su a kansa, amma ba abun da yake buƙata suke yi masa ba.

Ji tayi ina ma tana da damar, da zata rungume shi, ta bashi dama yayi kuka yadda yake so, ko zai samu afuwa a zuciyarsa, tsawon shekaru shida, yana dakon baƙin ciki da damuwa, kuma ya kasa zubar da hawaye sai a wannan lokacin.

Haka yayi shiru ya sunkuyar da kai, sai dai bai saki hannunta ba, hawaye ne kawai yake zuba daga idonsa, taya shi take yi, sai dai ta rasa me ma zata kuma ce masa, a tsorace take da kar zuciyarsa ta buga.

A hankali ya saki hannunta, ya goge hawayen sa, ya tashi zumbur, ya tattare kayan  ya mayar ɗakin, hatta kayan jauhar suna nan, lokaci lokaci, su Walid ne ke zuwa su karkaɗe gidan su share, dan idan ya bushi iska yana zuwa cikin dare, yayi ta tuna irin rayuwar da suka yi.

Yanzun ma yana shiga ɗakin, ƙwaƙwalwarsa ta nuna masa ita zaune a kan gado, tana shirin dutse, gefe ga boti a kusa da ita a kwance, ya mimmiƙe yana ta goge jikinsa.

Ta ɗago ta kalleshi tana murmushi ta ce "Manya gatan wasa, me ake so ne ake ta kallona? Ko fankar ce?" Tayi maganar tana kashe masa ido.

Gadon ya nufa da hanzari ya kai hannu ya riƙe ta, amma ya ga pillow ne kawai a wurin.

Ya dafe hannunsa a wurin, daga baya ya fito jiki a sanyaye ya ce "Mu tafi" Nabila ta saki niƙabinta tana ta kuka, suka nufi hanyar fita, ya gyara facemask ɗin sa suka fita.

Yana fita yaga wasu daga magidantan layin, a ɗan tsaitsaye, suka yi ido huɗu da malam lawan, ya zura da gudu ya shige gidansa, ya rufe ƙofa.

Ya danƙi hannun Nabila ya din ga sauri da ita, maimakon su bi titi, lunguna suka din ga bi, suna tafe yana haki, yana dafe ƙirjinsa.

A dai-dai wata kan kwana, ya saki hannunta, ya danƙo wani mutum da yake zaune yana jin radiyo, yana cin karas, zuwa wani lungu.

Nabila ta ce "Me yayi maka shi kuma?"

Ya zaro iraƙi a ƙugunsa, ya saita masa a maƙoshinsa, ya ce "Bani wayarka"

Jiki na rawa, ya ciro wayar, ya miƙa wa Viper.

"Ka janye mini mutanenka, zan yi walƙiyya, idan ba haka ba, zan yi maka rami a maƙoshinka"

Mutumin ya diririce, ya ce "Ban gane me ka ke nufi ba"

Ya ɗaga mutumin ya haɗa shi da bango da ƙarfi, ya ce "Ka janye mini mutanenku zan tafi, idan na kuma magana, hanjinka zan naɗo da wuƙar nan"

Mutumin ya ce "Ya aka yi ka gane ni, ka san identity ɗina?"

"Saboda tsohon mai laifi ne ni, ba yau na fara aikata laifi ba" yana ƙoƙarin zira hannu a aljihu Viper ya riga shi, ya ciro bindigar da take aljihun mutumin ya ce "Ka yi abun da na ce, ko na harbe ka"

A razane Nabila ta ce "Viper bindiga ce fa, dan Allah kar ka yi wani laifin mu shiga uku" bai kulata ba, ya sake saita mutumin da bindiga.

Ya saka wayar a kunnensa ya ce "Zaku iya tafiya, we missed the target" ya katse wayar ya ce "Sai ka bani bindigata na tafi"

Viper ya ce "Ɗaga hannunka, ka wuce mu je" ya tasa mutumin a gaba, tamkar ya kamo mai laifi, yana gana suna bin sa a baya, da ya motsa sai ya ji Viper ya ce "Idan ka waiwayo zan fasa kanka da bindigar nan" haka suka yi doguwar tafiya a haka, sai kuma ya ji shiru.

Ya waiwaya, ya neme su ya rasa, a rikice ya bi hanya, saboda bindigar sa da take hannun Viper.

Yana shan wata kwana, ya ga abokin aikins a tsaye da bindigar a hannunsa.

"Gata, tun da ya ritsaka nake biye da ku, a hanya ya yar da ita, suka yi wani wurin, nayi ƙoƙarin bin su, amma ban cim musu ba".

"Ohh shit, meyasa ba ka yi making wani move ba, wannan ai shirme ne kayi"

"No, kar ka gargaɗe mu a kan haka, ka ce sai abun da ka ce, kai ka ke son ka kama shi da kanka"

Ya fesar da iska ya ce "Kuma haka ne, amma gayen nan ya bani mamaki, na rasa ya aka yi ya gane ni a cikin fararen kaya.
Kaga fuskarsa?"

"A'a sir, fuskarsa a rufe take ai, ban ganshi ba, ni bayansa ma kawai na gani".

"Na so naga kammaninsa,

Download complete TXT · Novel page