Abban Sojoji Book 3 (Takun Karshe)

Chapter 67 of 104

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*






Saman Sofa ya zauna,Sehrish ta ƙaraso ta ajiye mashi plate ɗin saman table ɗin gabanshi,hannu tasa ta cire murfin da ta rufe gurasar dashi,ɗan ɗagowa tayi tare da satar kallonshi samun shi tayi ya jingina bayanshi a jikin kujerar,idanuwanshi a lumshe suke,gyaran Murya ta ɗan yi mashi"Ya rafayet,"slowly ya buɗe idanuwanshi akanta,nuna mashi gurasar tayi alamar yaci,

Muryarshi a kasalance yace"who asked u to pick the call?" gabanta ne ya fadi calmly tace"dama naga baka dade da yin bacci ba,don kar kiran ya tashe ka yasa na dauka don in fadi ma mai kiran bacci kake,to kuma sai naji banjin abunda ake cewa shine nai rejecting kiran,amman kayi hkr"ta karasa kanta a kasa,still yayi yana cigaba da kallonta can taji yace"Ni zanci da kaina?" dagowa tayi suka hada ido, saurin kawar da idanuwanta tayi saboda kunyarshi da take ji,musamman inta tuna abunda tayi mashi asaman shimfiɗarshi,

Daƙyar ta iya buɗe baki tace"zan iya baka idan kana so,"

Nuna mata gefenshi yayi ta zagayo ta zauna,ƙamshin turarenshi har cikin kanta,A yangance tasa hannu ta nannaɗo gurasar,tana ƙoƙarin kaiwa bakinshi idanuwansu suka haɗu wuri guda,kasa janye idanuwanshi yayi daga kallonta,wasu abubuwa sun ɗan fara ɗaure mashi kanshi,Ta canza mashi sosai ba kamar daba time ɗin da ko haɗa ido bata iyayi dashi amma yanzu takan ɗan kalleshi harma su haɗa ido,kuma jikinta ya daina wannan rawar da yake yi duk in tazo part ɗinshi,hakan na nufin ta rage jin tsoronshi?ko meyasa?ko dan saboda romancing ɗin da yake yi mata ne?

Ganin ta kasa tura mashi gurasar abaki yasa ya ruƙo hannunta tare da matso dashi saitin bakinshi ya tura gurasar ya ɗan 6alla yana Ci,yayin da idanuwanshi ke kallon fuskarta,ita kuwa tuni ta kawar da idanuwanta daga kallonshi da take yi,sai dai satar kallon mouth ɗinsa da take yi,yadda yake chewing ɗin gurasar,soft lips ɗinsa na motsi ba ƙaramin fisgarta yake yi ba,sun 6ata mintuna a wurin nan,har sai da ya kammala ci sannan Sehrish ta miƙe ta nufi fridge,Coke ta ɗauko mashi mai sanyi ya kora da shi,bayan ya kammala sha Ya nufi bedroom ɗinshi,bin bayanshi tayi don ta gyara mashi ɗakin,A tsaye ta same shi ya kara waya a kunnanshi yana magana,
  Shiga ciki tayi da sallama abakinta,kaitsaye ta fara gyara mashi bed ɗinshi,tana jin moving ɗinshi lokacin daya kammala yin wayar ya faɗa toilet,jim kaɗan ya fito yana gyara wrist watch ɗin hannunshi"Am leaving"Shi ne abunda taji yace,juyowa ta ɗan yi tare da kallonshi"when are u coming back"?daƙyar ta samu ta iya tambayarshi,tana ƙoƙarin yin practice ɗin abunda Azeema ta koya mata,
  Shi kanshi ya jinjina tambayar da tayi mashi,hakanan kawai dai yace"Zan kai 12 na dare,"
  Gyaɗa kai tayi tare da mayar da hankalinta kan Gadon da take gyarawa,tun kafin ma ya fita harta fara Missing ɗinshi,ga wani abu da ke yi mata yawo a kanta,Tana so ta sanar dashi about Junaid's ring da ta gani a cikin drawer ɗin Azmee amma ta kasa faɗa mashi,saboda bata ƙarasa investigation ɗinta ba,Amma taci alwashin muddin ta gano dasa hannun Azmee dumu dumu saita gaya mashi ne,'

tana cikin wannan zancen zucin unexpected taji yayi hugging ɗinta ta baya,gaba ɗaya ya saukar mata da kasala,hannayenshi ya zagayo ta saman stomach ɗinta,A hankali yake rubbing tsinin Hancinshi asaman fatar wuyanta,lumshe idanuwanshi yayi tamkar maijin bacci,bakomai yake yi mashi yawo acikin kanshi ba,fa ce zancen Marshal Na little Junaid,Still yana deciding din lokacin da ya dace ya aiwatar da hakan duk da yanzu baya cikin kwanciyar hankalinshi,wata irin kasala ce ta kama kowannansu ya jima ahaka kafin ya saketa,da sauri ya fuce daga Bedroom ɗin yana jiyo voice ɗinta tana yi mashi adawo Lafiya,

Fitarshi ke da wuya,Sehrish ta zauna gefen gadonshi tana tunanin ta yadda zata iya taimaka masu,remain 4 days Yanzu acikin waɗannan kwanakin Yakamata Su gano Abu biyu waɗanda suka kashe Junaid,ko kuma shi junaid ɗin if he'a still alive,Kamar yarda Aunty azeema take hasashe,abubuwa da yawa sun shige mata kanta,akwai buƙatar zuwanta ɗakin azmee domin ƙara yin bincike,Sai dai tana tsoran Azmee ta kamata,

Miƙewa tayi taci gaba da gyaran ɗakin,bedroom ta fara gyarawa,kafin ta shiga toilet ɗinshi nan ma ta gyara,dawowa palourn tayi tana Aiki tana sambatu kamar wata zautacciya,

Wuraren ƙarfe 4 na yamma,Amrish na kwance tana bacci saman katafaren gadonta,daga ita sai gajeran wando black colour,sai half vest wadda bata rufe cibinta ba,juyi ta soma yi alamun zata farka daga baccin,lokaci guda ta ware manyan idanuwanta tana kallon ceiling,ranta yayi matuƙar 6aci lokacin da ta tuna dalilin yin baccin nata,sam batasan ya ɗauketa ba,kuma tana zargin cewa maganin bacci aka bata,dama kwanakin nan duk in Mommynta zatayi baki saita ɗura mata ƙwayar da zata sata bacci,Yawanci acikin abunsha take sanya mata,miƙewa tayi daƙyar saboda kasalar da take ji,Saukowa tayi daga saman gadon tana miƙa tare da yin Hamma,toilet ta nufa zata shiga sai kuma ta fasa,Fitowa tayi daga cikin ɗakinsu ta nufi bedroom ɗin Mommynta,hannu tasa zata ruƙo handle ɗin ƙopar ɗakin don ta buɗe,Surutun da tajiyo daga cikin ɗakin yasa ta dakata,tare da kasa kunnanta tana sauraranta,
  "Wlh bazan ta6a ƙyalesu ba,Zasu yi galaba akanmu ne,ai kawai ku kashe shi,ku kashe shi kawai,ko ku cire mashi idanuwanshi,Uban kowa ya rasa,idan har ba zaku iya ɗaukar mataki ba,to ni zan ɗauka dakai na,"da alama waya take yi,yadda kasan yar daba,
  Hankali amatuƙar tashe,ta toshe bakinta da hannunta,gudun kada ta saki ihu,jikinta sai kerma yake yi,lalla6awa Amrish tayi cikin sanɗa ta koma bedroom ɗinta,agefen gado ta zauna,Yayin da zuciyarta ke ta bugawa,Dama ta jima tana zargin Momynta,
  "Amma mommy bata da Imani,sai cewa takeyi akashe akashe,kamar wata zararra,wlh nima bazan ƙyaleki ba mommy ki yi kisan kai ina gani,Zan cigaba da samaki ido ne batare da kinsani ba,kuma Allah muddin nagano cewa kashe ƴa'ƴan mutane kikeyi da kaina zan kaiki ƙara wurin hukuma su garƙameki,"tana magana tana cizon le6enta,

Turo ƙopar ɗakin nata akayi,da sauri ta baje saman gadon tana baccin ƙarya hada minshari,mommy ce ta shigo hannunta ruƙe da wayarta,

Zuba ma Amrish ido tayi tana kallonta,kafin ta Kanga wayar a kunnanta
  "Har yanzu Bata farka daga baccin ba,Ni na bata maganin bacci,Wlh ta cika sa ido,ga bin ƙwaƙƙwafin tsiya,Har sa'insa take yi dani shiyasa nake bata maganin bacci"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar tana sauraron wanda suke yin wayar dashi,

"Ae ni na kwace wayar hannunta,Shiyasa ko ka kira bazaka same ta ba,idan ba haka ba zata iya zame mun matsala,"
  Kasa kunne Amrish tayi tana sauraronta,Aranta tace"Asirinki ya tonu mommy,yau naji da kunne na,wato ke kike bani maganin bacci ina sha,ko wa take faɗama cewa ina bacci hmmmm,ta ƙarasa zancen zucin tare da jan dogon numfashi irin na wanda yayi nisa a baccin nan,
  "Okey,Bazan barta da yunwa ba,Yanzu zan tashe ta taci abinci,Ae bazan ƙara wasa da lafiyarta ba,duk da bata da hankali,"
  Sallama sukayi da mutumin da take yin wayar dashi,zama tayi daga gefen gadon,a tsanake ta soma kiran sunanta
  "Amrish!Amrish!"kusan sau biyar tana ambaton sunanta,hada bubbuga ƙafarta,A hankali Amrish ta ɗan buɗe idanuwanta,muryarta a kasalance ta furta"Mommy,lafiya kike ƙwala mun kira"?
  "Tun ɗazu kike bacci,Ko sallah bakiyi ba halan?Ga la'asar ma na ƙoƙarin yi,ki tashi ga Abincinki can a dining kije ki ci,"
miƙewa tayi daga zaune,tana yin hamma kafin ta wuce cikin toilet,koda zata rufo ƙopar saida ta ƙara leƙen Mommynta,kafin ta datse ƙopar,

*AMANI*

Zaune suke acikin falon gidan,Hayaam Da Abra na zaune saman 3 seater,Yayin da Amani ke zaune saman 2 seater,hayaam ce ta soma magana"Aunty Amani,mun yanke shawarar zamu koma gida gobe,bai kamata mu cigaba da zama anan ba muna ɗaura maku nauyinmu,kinyi mana abunda bazamu ta6a mantawa ba,"ta ƙarasa maganar yayin da idanuwanta ke acike tab da kwalla,
Ajiyar zuciya amani ta sauke tare da cewa"Shikenan,gaskiya yakamata ku koma kam kodan Saboda Mammy da Abra ta baro kwance tana jinya,Bamusan a wani hali take ciki ba ayanzu,'
  "Aunty laila fa'?Abra ce tayi tambayar,
  Hayaam tace"Ina ruwanmu da ita?tana raye kota mutu matsalarta ce,bata da amfani acikin rayuwarmu,"
  "Kada ki ce haka hayaam,itafa ƴar uwarkuce,duk da bata kyauta maku ba amma bai kamata kuyi watsi da ita ba,Yanzu dae bamu san awani hali take ciki ba,Amma mujira mu gani,indai Laila ce nasan zata dawo ne,sannan ina ƙara gargaɗinku akan irin rayuwar da kuka ɗaurawa kanku,musamman ke Abra,kinga dai irin abunda ya faru da hayaam kema kuma in baki kiyaye ba,zaki jefa rayuwarki cikin hatsari ne,mazan da kuke mu'amala dasu ɗaya daga cikinsu bazai iya aurenku ba,Idan ma ya aureku to bazai darajaku ba,sannan kullum zaku kasance cikin zargin juna,so wannan rayuwar ba mai 6ullewa bace,kuma ku mika dukkan al'amuranku wurin Allah,duk abunda yake rabonka ne kana zaune zai same ka,in ku ka ga baku samu abunda kuke so ba,to Allah bai kaddaro rabon ku bane...."sosai Amani tashiga yi masu nasiha jikinsu duk yayi sanyi,hada kuka,

Suna cikin tattaunawar nan,Amal ta faɗo cikin falon,hannunta ruƙe da wayar Amani,ƙarasowa tayi wurin da amanin take a zaune ta miƙa mata wayar"Yaya Abbas ne ya kira,"
Harararta Amani tayi"Dama wayata tana a hannunki,"?sunnar dakai ƙasa tayi tana dariya,
  "tare da Amal zamu tafi gobe'?acewar abra,tayi maganar tana kallon Amal ɗin
   Wani irin kallo Amal tayi mata,hada cizon la66a,dariya Amani tayi tare da cewa"Ba zaki bisu ba,kinga yanzu komai ya dai daita,ki amince kawai ki koma cikin ƴan uwanki da zama,
  A shagwa6e Amal ta bubbuga ƙafarta tare da ruqe qugunta"Nifa wlh bazan bisu ba,idan kin gaji da zamana ne a gidanki,nan bada jimawa ba,Yaya Jahan zai ɗauke ni,"
Gaba daya suka zuba mata ido suna kallonta cike da mamaki a fuskokinsu,banda Amani dama ita tasan tsakaninta da Jahan,
  Murmushi Amani ta saki tare da cewa"Nima wasa nake maki,Ae Amal ta gama zaman maiduguri in ba dai zuwa kai ziyara ba,daga Abuja sai ƙasar waje ko ba haka ba?'cike da zolaya tayi mata maganar,
Murmushi Amal tasaki,tare da juyawa da gudu tabar falon tana dariya
Tashin sense,jikinsu Abra ba ƙaramim sanyi yayi ba,duk irin burin da suke dashi na zama surukan Alexandra ya tashi abanza,Sai gashi Yarinyar da suka raina,Suke wulaƙantawa ita ke da rabon auran jinin Alexandra,Abun ba ƙaramin ta6a masu zuciya yayi ba,sunyi danasanin rayuwarsu,zuba masu ido Amani tayi tana kallonsu ganin yadda kowa tasha jinin jikinta,

*General Ishaq*

Fitowarshi kenan daga cikin toilet,Jikinshi sanye da jallabiya,tun yana acikin toilet yaji ringing ɗin wayarshi,ƙarasawa yayi tare da kai hannu ya ɗauki wayar,New number ce aka kirashi da ita,Bin kiran yayi kiran na shiga aka ɗaga wayar"Assalama Aleekum"muryar wani inyamurin mutunce,
  "Wa'alaikum salam,ko zan iya sanin dawa nake magana"?
On the other hand mutumin yace"Yalla6ai dama wani bawan Allah ne keson magana dakai,Shine yace in taimaka in kira mashi layinka,"
  "To bashi wayar,"tsayawa yayi yana jiran jin muryar mutumin da akace yana son magana dashi,
  Abun mamaki sai yaji kukan Laila Acikin wayar,ya cika kunnanshi,cikin shessheƙar kuka ta wanda ya galabaita ya jigata sosai ta soma magana"Abban hafsat ni ce laila,dan Allah akawo mun ɗauki,ina cikin mawuyacin hali,"
  Murmush Ishaq ya ɗanyi tare da cewa"Bangane wake magana ba?kodai wrong number ne aka kira"?
  Jin haka yasa ta ƙara sautin kukan nata"Ishaq kada kayi mun haka,Wlh ina cikin masifa,gani nan a Enugu yashe gefen bishiya,sai an bani sadaqa sannan nake samun abunda nake sawa acikina,Wlh Ishaq na tuba nabi Allah,Akawo mun agaji ƙafata ta lalace ta ru6e...."tana magana tana kuka,
  Handsfree ya sanya don yaji daɗin sauraronta,Sai da takai ƙarshen maganarta sannan yace"the number you're trying to call is switch off,pls try again Later"yana kai ƙarshen maganar,yayi rejecting kiran yana dariya,ko kaɗan baiji tausayin kukanta ba,Don tafita aranshi kwata kwata,Yayi mamakin jin wai tana a Enugu ko ubanme yakaita enugu?ta6e le6enshi yayi tare da faɗin"I don't care Allah ya raka taki gona,nasamu na rabu da jangwamgwam,"
  Ƙarar shigowar message yaji,da sauri ya duba screen din wayar ya soma karanta saƙon
  _Ishaq ka taimaka ka ceci rayuwata,wlh ina cikin masifa,naga tashin hankalin da banta6a gani ba Ishaq,wayar ma aronta nayi a hannun wani inyamuri,kayi taimakon musulunci ishaq karka duba halina,dan Allah zakayi,ataimaka a dauko ni daga Enugu ko maiduguri ne a mayar dani in mutu acan_
  Guntun tsoki ishaq yaja,tare da yin deleting ɗin saƙon,a karshe ma blacklist ya tura number,yadda ko an kira baza a same shi,"
  Murmushi ya saki lokacin daya tuna da hajjaju,macen da yake burin aure,duk da taƙi amince mashi amma kullum saita kirashi ta tambayi lafiyarshi,Wannan ya tabbatar mashi da cewar tana sonshi,tunda ta damu dashi,sannu a hankali Zai samu yayi Wuff da ita ya kawota Cikin gidan shi,

*Boss Bature*

Yinin Ranar Sehrish da Ciwon kai Tayi shi saboda tsabar tunane tunanen da take yi,ta kasa tsaye ta kasa zaune,Har magani tasha amma kan yaƙi lafawa kamar ana kunna wuta acikin ƙoƙan kan nata,abun ya ɗaure mata kai yadda Azmee ta share zancen bata Labarinta,Har lokaci suka samu amma bata tada zancen ba,kuma ko tayi yunƙurin zata tuna mata sai tayi saurin Canza zancen,hakan ne yasa Sehrish ta fara accusing ɗinta,Ta sanya mata ido sosai duk wani motsinta akan idanuwan sehrish take yinsu,

Wuraren ƙarfe 9;30 na dare,gidan yayi tsit da alama wasu daga cikinsu sunyi bacci,Oummansu kaɗai ta rage a ɗakinsu,Zaune saman sallaya tana tasbihi,Yayin da su sehrish ke kwance saman gadon,hosana da jahad sunyi Bacci banda Sehrish wadda idonta biyu,ta kasa runtsawa,jira take yi Oummansu ta kammala Sallar ta dawo saman gadon ita kuma ta koma ɗakin Azmee,

Tana cikin Jan cazbahar nan wani abu ya faɗo mata aranta,abunda ta jima tana ƙoƙarin tunanawa,a hanzarce ta miƙe jiki na rawa ta tunkari gefen da sehrish take kwance saman gadon,Hannu tasa tana ɗan bubbuga kafaɗarta"Rishi!rishi!ko kinyi bacci ne,"yatsina fuskarta ta ɗan yi daƙyar ta iya huɗe idanuwanta,
  "Tambayar da kika yi mun game da wannan Auntyn taku Azmee,Na tuna inda nasanta.."tunkan takai ƙarshen Maganar,jiki na rawa Sehrish ta tashi daga zaune tana kallonta"Oumma a ina kika Santa?
  "Zan faɗa maki Sehrish amma fa karki kuskura ki sanar da ita cewa nasanta,tunda bansan da wata manufa take zaune acikin gidan nan ba,"
  "Bazam faɗamata ba Oumma"
Jinjina kai abu ta ɗanyi"Wannan matar da kike gani,Lokacin da na haifeku babu wanda yazo yi mun wankan jego,Sai daga baya Ya sayyadi yazo da ita amatsayin ƴar uwarshi da zata yi mun wankan jego...."
  Jin wannan maganar yasa hankalin Sehrish yayi mugun tashi,Saboda tsabar kiɗima gaba ɗaya idanuwanta suka firfito waje,Hannu tasa ta daki ƙirjinta"Ƴar uwar Ya sayyadi!"ta ambaci hakan a tsorace
  Abu ta lura da Yanayin da Sehrish ta shiga,bata dakata da yin maganar ba taci gaba da cewa"Wlh Sehrish matarcan da kike gani,Ba ƙaramar shu'uma bace!abun tsoroce ita,Dalilin dayasa nace maki haka,Lokacin da sayyadi yazo mun da ita don tayi mun wankan jego,Kamar kurma haka ta koma,duk in naso na bugi cikinta don ta sanar dani wani abu game da danginsu,Sae taƙi tanka mun,Nasan dai ta bani kyakkyawar kulawa a lokacin amma gaskiya ba abun yarda bace,saboda nayi mamaki dana ganta acikin gidan nan,Kuma sai surutu take yi kamar ba ita ba,Sa6anin a yadda nasanta lokacin da tazo gidanmu ko uffan bata cewa,daga um sai um um shine abunda ke fitowa daga bakinta,"
Hannu sehrish tasa tare da dafe kanta dake jujjuya mata,a hankali tashiga furta"Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un!Amma Azmee ta gama damu!indai abunda nake zargi ya tabbata to tabbas Azmee Itace Ƴar leƙen asirinsu dake fitar da surrukan gidan nan......"
Cike da mamaki abu ke sauraron kalamanta sae da takai ƙarshen maganarta Sannan tace"Meyasa kika ce haka?Dama kina zarginta ne?Amma naga kamar kuna zaman lafiya da ita,'
Hawaye na kwaranyowa akan furkarta ta shiga faɗin"Oumma,muna cikin tashin hankali in har ya kasance AZMEE itace take shirya maƙarƙashiya acikin gidan nan...."dafa kafadarta abu tayi"ki sanar dani abunda yasa kike zarginta inaso inji,ko Zan iya taimaka maku"
  Duk da tana cikin mawuyacin hali na firgici,haka ta zauna ta kwashe dukkan abunda ke wakana acikin gidan ta sanarwa Oummansu,abun mamaki tana kai ƙarshen maganar sai taga Abu na murmushi gami da girgiza kanta,
  "Oumma ko kin gano wani abu akanta ne?naga kina murmushi,"
  "Akwai wani abu da nakeso na sanar dake sehrish!Shi ɗan adam ba abun yadda bane,Bakomai zaisa kiyi kokwanto akan azmee ba fa ce Yardar da kukayi da ita,Ta ko'ina azmee ta gama daku,Ta siye zuciyoyinku ta hanyar kyautatawar da take yi maku,Shi mutun maison ɗaukar fansa,Zai iya yin 6adda kama ya shiga jikin maƙiyansa har na tsawon shekaru Yana yi masu bauta batare da gajiyawa ba,yayin da yake shirya masu maƙarkashiya batare da sun ankare ba,Har sai ranar da ya tarwatsa su gaba daya tukunna zai bayyana kanshi,Yanzu kinga gaba ɗaya ta gama sanin surrukanku......"dakatawa abu tayi da yin maganar,Ta jinjinawa azmee sosai,ta iya shirya tuggu
  "Gaskiya sehrish dole kiyi taka tsantsan,don wlh in har ya kasance zargin da muke yi ya zama gaskiya,To fa Azmee ba ƙaramar shu'uma bace,Kuma zata iya kashe duk wanda yayi gigin tona mata asiri,a yadda ta faro shirinta tsawon lokaci yanzu bazata bari wani Ya fallasa ta ba,"
  "Amma Oumma,nibansan ya zanyi ba,abubuwa sunyi mun yawa akaina,"tayi maganar damuwa ƙarara a kan fuskarta,
  Dafa kafaɗarta abu tayi"Ni dai shawarar da zan baki shi ne,Ki samu wani babba ki sanar dashi komai dangane da ita....."
  A ruɗe sehrish tace"Wazai yarda dani Oumma!idan har na faɗi cewa Azmee ƴar uwar sayyadi ce,kuma ina zarginta da mutuwar Junaid"
  "Tabbas kuwa babu wanda zai yarda dake a halin yanzu,a ƙarshe ma reshe zai iya juyewa da mujiya,Zata iya ɗaura maki laifin kinsan fa shi mugun mutun hatsari ne shi,balle su da suke da tsafi,duk da dai mu mun dogara da Allah ne,babu ja da baya Allah shi zai bamu kariya,"
  "Yanzu ya zanyi!inaso naci gaba da bincike akanta,Saboda inaso na tambayeta dangane da zoben Junaid dake a wurinta me yakai shi cikin kayanta,"
  "Nace maki karki kuskura ki ce zaki nuna cewa kinsan wani abu game da ita,in ba haka ba zatayi maki mummunar illane,Nidai shawarar da zan baki A yanzu ki damƙa binciken nan a hannun ɗaya daga cikin mutanen gidan nan,Zaifi ma ki sanar da Daddynku,Zan ma yi mashi magana,nasan zai yarda dani sosai'
Shikenan Oumma,Yanzu zan iya zuwa ɗakinta in kwanta"?
  "Me zai hana amma dai ina ƙara jan kunnanki akanta,karki kuskura ki tsananta bincike akanta,Don zata ganoki ne,"gyaɗa kai Sehrish tayi tare da saukowa daga saman

Download complete TXT · Novel page