Abban Sojoji Book 3 (Takun Karshe)

Chapter 76 of 104

zugudum cike da jimami suna jiran Tsammani,Sgr da Omar Sunfi kowa shiga matsananciyar damuwa,Saboda suna ganin sune silar Halin da Abbansu Yake ciki,

Tunda suka fito daga Office ɗin Doctor Emran,a tsaye suke sun jingina bayansu da wall,Sgr Ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,zuciyarshi sai tafarfasa take yi,wani irin bugun zuciya yake ji,Omar kuwa idanuwanshi na kallon Ceiling,tsantsar damuwa ce akan fuskarshi,

Mommy tuni ta jima da kifa kanta saman cinyoyinta,tayi kukan harta gaji tayi shiru,Abu na zaune a gefenta,Yayin da Jahad ta kwantar da kanta saman kafadar Oummansu,idanuwanta a lumshe,Hosana na kwance saman cinyoyin Jahad,ta ɗan aza kanta saboda baccin da take ji,

Su fawan kuwa,Duk sun rufe idanuwansu yayin da kwalla ke zuba,Abusufyan dae Ya gaza samun natsuwa Sae faman safa da marya yake Yi a tsakanin Corridor ɗin dakin da Abban yake,

Dirar Motarsu Sehrish keda Wuya,Motar Sergeant ɗin daya ɗaukota daga gida ta faɗo asibitin dama Yana biye dasu,A bayan motarsu yai Parking ɗin tashi,Fitowa Sergeant ɗin Yayi,Sae ga Baba maigadi ya fito daga back seat na motar,Ashe lokacin da suka barshi acan asibitin,Masallaci Yaje don Yayi sallar azhar da bai samu yayi ba yana fitowa motarsu na fita shine sergeant ya taho da shi,

Wayar aljihunsa sai ringing take yi,sam hankalinshi baya a wurin,har sai da Abusufyan ya ambaci sunanshi"Rafayet ka ɗaga kiran mana,"
A kasalance Ya sanya hannu ya curo wayar,Abbas ne ke kiranshi,picking call din yayi tare da kara wayar a kunnanshi,akan rashin lafiyar Abbansu suke tattauna,

Kamar daga sama Sehrish ta faɗo wurin da suke bakinta ɗauke da sallama,jin muryarta yasa Jahad ta ɗago da kanta tana kallonta,kanal Yousouf ma ya ɗaura idonshi akanta,Haka Abusufyan da abu ma duk ita suke kallo,Sauran kuwa duk hankalinsu baya a wurinta,abun ya ɗaure masu kai ganin tana ta faman sakin Murmushi kamar wata zautacciya,
"Anya Sehrish tana da lafiya kuwa?sai kace batasan halin da muke ciki ba,Sai murmushi take ta saki kamar wata zararra,kodai Hosana batayi wannan haukan ba,"Jahad ce tayi maganar acikin zuciyarta,
  "Sehrish!waya kawo ki?dama bada ke muka zo ba"?Oummansu ce tayi mata tambayar,don ita bata lura ma babu ita ba,
"Daughter,"Abusufyan ya kira sunanta yayin da yake tunkaro wurinda take a tsaye,duk wannan abun dake faruwa Sgr bai ankara da ita ba,Saboda Ya juya bayanshi Yana waya da Abbas,
  A hankali ta soma magana"Bani kaɗai nazo ba"tana kai ƙarshen maganarta ta matsa gefe,Sae ga nurses guda biyu sun shigo da Junaid asaman gadon daukar marasa lafiya suna gunguroshi a wani irin Slow,

Ya mu'allim na a bayansu tare da Amrish da kuma Baba mai gadi,
Zuba ido Abusufyan yayi yana kallon fuskar mara lafiyan da suka ɗauko,Lokaci guda Ya ambaci sunanshi"JUNAID!!!"da tsantsan mamaki akan fuskarshi,Jin sunan Daya Ambata ne Yasa Su fawan suka ɗago da idanuwansu,Ai ko da sukayi Arba da Junaid kwance saman gadon,A wani irin firgice Suka mike suna ambaton Sunanshi Junaid! Junaid!!,Tuni Jahad ta ƙame a tsaye,gaba ɗaya ta rikice Sai faman zazzare idanuwanta take yi akan fuskarshi gani take Yi tamkar Mafarki ne ba gaske ba,Tsabar razanar da tayi ne Yasa ta Yanke jiki ta zube anan wurin,Gaba ɗaya sun miƙe tsaye cirko cirko agaban gadon,Surutun da suke yi ne Ya jawo hankalin Omar kansu,koda Yayi arba da Junaid nan take kirjinshi Yayi wani irin mugun bugu,Waro ido waje yayi yana ƙare mashi kallo a ruɗe ya ambaci sunanshi"JUNAID"!
Adai dai Lokacin Sgr Ya ɗan juyo a sukwane don Yaga meke wakana Yaji sunata ambaton Sunan junaid,baiyi tsammanin wani abu ba,Juyowarshi keda Wuya idanuwanshi Suka sauka direct kan gadon Da junid yake kwance,Saboda tsabar firgitar da yayi baisan Lokacin daya Saki wayar dake hannunshi ba,ta faɗo ƙasa,
Hannu yasa saman idanuwanshi Ya murzasu dakyau don Yaga in dagaske ne,A sukwane Ya kalli Marshal a lokacin shima Omar ya juya a hargitse suka haɗa ido,Just speechless sun gaza magana sai dai nuni da hannu,Sun zama kurmayen Ƙarfi da Yaji,Girgiza kai Sgr ya shiga yi,Alamar bai Yarda ba,
  "I can't believe it,Wannan bazai ta6a yiwuwa ba,Junaid Daya mutu Ya dawo,how can that be possible?Yaron daya ƙone a mota,dama ana mutuwa adawo ne....its just a dream...."acikin ranshi yake wannan Sambatun,Sae faman motsa la66ansa Yake yi amma ya kasa buɗe baki Yayi magana,sunyi matuƙar razana,Sun gigice da ganinshi,Duk da basu Yarda cewa shi bane,Ido kawai suke binshi dashi,

Su kuwa Sauran Matasan Sae murna Suke Yi baby Junaid ɗinsu Ya dawo,Duk da matsananciyar damuwar da suka Shiga na ganin halin da Junaid ɗin yake ciki,Tuni Fawan ya fashe da matsanancin kuka,haka su Irfan sun tasa shi gaba sai kuka sukeyi sun hana nurses ɗin su wuce dashi ciki,
Koke koken da suke Yi ne ya farkar da Alex,Dagowa tayi fuskarta sharkaf da hawaye,Ganinsu tsaitsaye cirko cirko Yasa ta miƙe tare da nufarsu tana Tambayar Lafiya,Matsa mata su kayi don ta ganshi dakyau,A sukwane Alex ta zube saman guiwowinta agabanshi Tana kallon fuskarshi,Yatsun hannunta Na kerma ta azasu asaman ramammar fuskarshi,
  Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka tana ambaton Sunan shi"Romeo ɗina ne ya koma haka"?rufe bakinta tayi da tafin hannunta tana cigaba da yin kuka,
  Ganin Suna 6ata Lokaci Yasa nurses ɗin suka nemi alfarmar su basu hanya su wuce dashi ciki,Gungurashi sukayi da sauri Abusufyan tare dasu Kanal Yousouf suka bi bayansu,Ɗakin da aka kwantar Da Abbansu nan suka nuna suna son a shigar dashi,Ko Allah zaisa adace Abba Ya dawo hayyacinshi,shiga ciki Su kayi dashi,anan gefe aka kwantar da Junaid,dandazo likitoci su Kayi acikin ɗakin domin duba Lafiyarshi,gwaje gwaje suka fara yi mashi,Yafi buƙatar blood ajikinshi fiye da Komai,tsabar so da ƙauna har kokawa su Fawan suke yi don a ɗebi jininsu,Kowa so Yake a sanya ma Junaid nashi,One by One aka dinga gwada Jininsu,A ƙarshe aka ɗibi jinin Fawan dana Ayaaan,kusan Leda huɗu za'a ƙara mashi,

Abun sai ya baka mamaki,Gaba ɗaya sun kasa samun natsuwa sae faman sintiri Suke Yi,da taimakon Oummansu Jahad ta farfaɗo da matsanancin Ciwon kai,Still bata Yarda da abunda idanuwanta suka nuna mata ba,Asaman laps ɗin abu ta kwanta,wani irin zazza6i ne ya rufe ta,duk a tunaninta Fatalwarsa ce aka kawo masu,Mommyn Junaid kuwa tana bakin ƙopar ɗakin tsaye ita da Abusufyan,jikinta sae tsuma Yake Yi,ji take kamar ta faɗa ɗakin,

Ya Mu'allim yana a tsaye tare dasu Amrish,ba ƙaramin tausayi suka bashi ba,sam babu kwanciyar hankali atattare dasu,Tunda Allah yasa su kayi arba da Junaid,hankalinsu gabadaya ya koma akanshi,shiyasa basu nemi ƙarin bayani a wurinsu ba,Wuri Sehrish ta nuna masu suka zazzauna,kafin ta wuce izuwa wurinsu Marshal Omar dake a tsaye,Suna bin kowa da ido,Su da suka san Cewa Junaid Ya mutu,Abun ya matukar jijjigasu,

"Ya Omar,"firgit ya wurga idanuwanshi akan fuskarta,A lokacin Shima Sgr Ya mayar da hankalinshi akanta,
  Da hannu Yake tambayarta taya akai hakan ta faru"?
  Murmushi ta ɗan saki,kafin ta soma magana a tsanake,
  "Nasan zaiyi wuya ku yarda,Amma tabbas Junaid ne,bai mutu ba,Lokacin da hatsarin motar nan ya faru,Junaid baya acikin motar,"a iya nan ta dakata,dan tasan brain ɗinsu a yanzu bazata Iya ɗaukar dogon bayani ba,
  "Idan muka samu natsuwa zamu fahimtar daku komai,Atare da malamin makarantarmu,Da kuma ƙawata Amrish muka kawo shi,"tayi maganar tana nuna masu Ya mu'allim dake a zaune,
Sai Lokacin Sgr yaja dogon numfashi hadi da sauke nauyayyar Ajiyar Zuciya,runtse idanuwanshi Ya ɗanyi yana tariyo abunda Ya wakana a lokacin da suka je wurin da hatsarin motar ya faru,Tabbas sunyi kuskure da basu kwantar da hankali sun tsananta bincike ba,Shi kanshi Yajima yana ji aranshi cewa Kamar Junaid Yana araye,Koba don haka ba,Yayi mamakin Yadda akai ba'asamu ƙashi ko ɗaya ba na jikinshi,wata irin zufa ce ta wanke mashi fuskarshi,Ganin Yadda ta tsastsafo mashi akan fuskarshi ne Yasa Sehrish ta zame mayafinta,goge mashi zufar fuskarshi tayi,kafin ta mayar da mayafin akanta,
"Alhamdulillah,Junaid bai mutu ba,dama yana raye,Ya salaam!"Omar ne ya ambaci hakan fuskarshi ɗauke da wani irin murmushin farin ciki,
Doctor emran ne ya fito daga Medical room ɗin da aka kwantar dasu,Fuskarshi ɗauke da murmushi,kaitsaye wurinsu Sgr ya nufa yana dariya,Kallo Ya koma Sama,
  "Wonders shall neva end"!Ya ambaci hakan lokacin daya ƙarasa wurinsu,
  "Yau naga abun al'ajabin da banta6a gani ba,Dan Allah ku wayarmun da kaina!wanda ya mutu ne ya dawo ko kuwa ghost dinsa ce"?Yayi tambayar yana kallonsu,a lokacin Sgr ya ɗan buɗe idanuwanshi,Sun canza launi sosai,
  "Nikaina Abun Yayi mugun ɗaure mun kai wlh,Still ina doubting,Am confused Allah,ni dai idan ma mafarki nake yi kada ku tashe ni,Ku barni inta yin shi,"cike da tsantsar farin ciki Omar yayi maganar,hannunshi na dafe da saitin Zuciyarshi,No more tension
  Dafa kafaɗar Sgr Dr emran Yayi da hannunshi yana kallon fuskarshi,
  "Sgr fa kamar suman tsaye yayi,Ku tayani dubawa,"Dariya Sehrish tayi,Da alama farin cikine Ya hanashi yin magana,Ko ƙyafta idanuwanshi baiyi,Ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi ya shiga zurfin tunani sosai,hankalinshi Ya tafi wani wurin daban,

Wayarshi daya jefar ƙasa sai dai Sehrish ta ɗauketa,komawa Sehrish Tayi wurin Oummansu,wuri ta samu ta zauna tana kallon Jahad da ta kifa kanta saman laps ɗin Oummansu,
  Cikin sanyin murya ta Ambaci sunanta"Jahad"
"Na'am"ta amsa mata,batare da ta ɗago da kanta ba,'
  "Inason magana dake,"jin haka yasa ta ɗago da kanta,fuskarta duk a yamutse,idanuwanta sunyi jawur,
  "Sehrish amma dai ba gaskiya bane ko!nasan hakan bazai ta6a zama gaskiya ba,Junaid Ya mutu akan idona,Ni naji kukan shi acikin mota Lokacin da yake ƙonewa,Yau kuma sai gashi ya dawo da ranshi"?tayi tambayar a ruɗe,
  "Just believe it!Junaid bai mutu ba,Yana araye,ba lalle ne ki fahimce ni ba a yanzu,Amma tabbas Junaid muka shigo dashi,"_
  "Bazan ta6a yarda ba Sehrish,Sa dai ko me kama dashi ne kuka ɗauko,Amma Junaid dana sani baya acikin duniyar nan"tana kai ƙarshen maganar ta fashe da kuka tare da mayar da kanta saman laps ɗin Oummansu ta kwanta,Tsananin tausayinta ne Ya kamasu,
  "A yanzu ba lalle ne ta fahimce ki ba,Kada ki wahalar da kanki wurin yi mata bayani,"A cewar abu,da ta raba tsakaninsu,
  Gyaɗa kai Sehrish tayi tare da jingina bayanta jikin seat ɗin da suke,

Har time ɗin sallar Magrib ya shige basu ankara ba,Sae da Abusufyan ya tunasar dasu,daƙyar Ya tattarasu gaba ɗaya suka tafi masallaci,

Ya rage daga Alex dake tsaye a bakin ƙopar ɗakin,Sae Su Sehrish da Oummansu dake zaune saman waiting seat,Hosana dae tuni ta jima da yin nisa a baccinta,Duk wannan budurin da ake ita bata sani ba,anan Cikin asibitin ke akwai masallaci,Na mata dana maza,lokacin da suka tashi Yin sallar suna neman inda zasuyi wata Nurse ce ta yi masu jagora zuwa masallacin mata,Kowa sai da Yayi sallah banda Mommy da Hosana,Basu jima da yin magrib ba aka fara kiraye kirayen Sallar Isha'e,basu Baro masallacin ba sae da suka kammala Sallar Isha'en Sannan suka dawo,Ba ƙaramin natsuwa suka samu ba,

Dawowar su Sehrish da ƴan mintuna,ɗaya daga cikin likitocin dake dubasu Ya fito tare da basu izinin Shiga ciki,Alex ce ta fara Shiga,Oumma tare da su sehrish suka bi bayanta,gefen gadon ta zauna yayin da idanuwanta ke akan Junaid,sun canza mashi kayan jikinshi,Riga suka sanya mashi kamar uniform blue colour iya guiwarshi ta tsaya,hannunshi na sanye da kanula ana yi mashi ƙarin jini,Hancinshi na sanye da robar Oxygen,Sai jan numfashi Yake Yi da ƙarfi da ƙarfi,siraran hawaye ne suka sauko akan fuskarta,ruƙo yatsun hannunshi tayi acikin nata,

Jahad dai ta toge a bakin ƙopar ɗakin tana lekenshi,A tsorace take dashi gani take kamar fatalwarsa ce aka kawo masu,taƙi yarda cewa Shi ne Ya dawo,
  Matsawa Abu tayi zuwa gaban gadon ta samu wuri saman kujerar dake fuskantar gadon ta zauna,Addu'o'i ta soma karantowa tana tottofa mashi akan fuskarshi,hakan baƙaramin daɗi yayi ma Alexandra ba,
  Amrish dae na tsaye ta lullu6e kanta da kallabin lace dinta,hannunta na ruke dana Sehrish,gabanta sae faɗuwa yake yi,tana cikin mawuyacin hali,Duk ta tsani kanta,Gani take yi kamar in suka ji cewa Mahaifiyarta ce tayi ma Junaid haka zasu koreta ne,ko su fara ɗaukar fansa akanta,
  "Ki kwantar da hankalinki,ba abunda zai faru,nasan kina jin tsoro ne shiyasa kika tashi hankalinki,"Sehrish ce tayi maganar cikin sigar lallashi,don ta lura da yanayin da Amrish ɗin ke ciki,
  Ƙasa ƙasa suke magana,a tsakaninsu,
"Ji nake kamar in gudu,kafin kowa yaji labarin ainihin abunda Ya faru da Junaid,ni nasan cewa tawa ta ƙare,Ga kuma Mommy tana can tana nemana ta kashe ni"ta shiga damuwa sosai,batasan yanzu ina zata dosa ba,
'Kina tunanin cewa zamu barki ki tafi ne?duk irin ƙoƙarin da kikayi mana,indai kina fargaba ne akan Family ɗinmu,to ki kwantar da hankalinki,Suna da kyakkyawar Zuciya zasu fahimceki su kuma kar6eki hannu bubbiyu,In ma basu amshe ki ba,ni bazan bari Ki tafi ke kaɗai ba zan bi ki ne,"on a serious note,Sehrish tayi maganar,
Har cikin zuciyarta taji daɗin kalaman Sehrish kuma hankalinta ya kwanta,duk da akwai sauran fargaba,

"Assalamu Alaikum"Abusufyan Ne ya shigo fuskarshi ɗauke da Murmushi Hannunshi ruƙe dana Sgr,Omar na abayansu tare da Ya mu'allim,yayin dasu Fawan ke biye dasu,Kowa ka kalla tsantsan farin cikine bayyane akan fuskarshi,tsayawa su kayi agaban gadon cirko cirko suna kallon Junaid,Har lokacin Abbansu na kwance gefen Junaid,tunda akayi mashi allurar bacci bai farka ba,

Sai faman sauke ajiyar zuciya Omar da Sgr suke yi,sun jinjinawa lamarin,ƙaryar da suka shirya ta zama gaskiya,Ga ƙannensu sae murna Suke yi Junaid ya dawo,kidnappers sun sake shi,basu san dawan garin ba,
Da zarar Sgr ya haɗa ido da Omar saisu sakarwa juna murmushi,abun ba'a magana,shigowa ciki doctor Emran Yayi fuskar nan ɗauke da ƙayataccen murmushi,jerawa yayi tare dasu,yadda kasan sun Samu talabijin haka suka ƙurawa Junaid ido suna kallonshi,
Dr emran ne ya soma magana a tsanake,
  "In sha Allah,Zasu samu sauƙi,dama damuwarshi rashin Junaid ne,Yanzu gashi Allah ya dawo mana dashi"yana kai ƙarshen maganar,
  Ya mu'allim ya ɗaura da cewa"Yakamata mu nuna godiyarmu ga Allah subhanahu wata'ala,daya bayyanar mana shi,sannan muyi masu addu'a"
Atare suka ɗaga hannayensu sama,Ya mu'allim ya shiga yi masu addu'a suna amsa mashi da Ameen,sun ɗauki tsawon Lokaci kafin suka shafa Addu'ar,
  Suna zame hannayensu daga saman fuskokinsu,yatsun hannun Junaid suka fara motsi,Da ƙarfi Mommy ta ambaci sunan"Junaid"fuskarta ɗauke da murmushi,hankalin sauran ya dawo kanshi,
  Mutsu mutsu yaci gaba da yi,Jahad sai leƙenshi take yi daga tsayen da take abakin ƙopar,ita dai har yanzu bata yarda ba,
  Mutsu mutsun yaci gaba da yi,duk sun zuba ido suna kallonshi,la66ansa sae kerma suke yi,Slowly ya soma sambatu tun yanayi ƙasa ƙasa harya fara yi da ƙarfi Sunan Abbansu yake ambato,"Abba!Abba!"cikin fitar hayyaci ya soma kokarin ɗaga hannunshi zai cire Oxygen ɗin da aka sanya mashi,Da sauri Dr emran da Omar suka ƙarasa ta gefenshi tare da rurruƙe hannayenshi,hankalinsu gaba ɗaya ya tashi ganin yadda Junaid ke ta firgita,
  "Abba!Abba"daƙyar sautin ke fitowa daga bakinshi,tunda Ya Mu'allim yaji hakan,Sae ya basu shawarar Su matso da Junaid kusa da Abbansu,tunda akwai interval a tsakaninsu,da alama yana ji aranshi cewa mahaifinshi na a kusa dashi,Shiyasa yake ambaton sunanshi,
  Dubara su kayi a hankali suka janye Junaid zuwa gefen Abbanshi,Abun mamaki suna gyara mashi kwanciyarshi sae gashi yana kokarin lalubar jikin Abbansu,Abun yayi mugun ɗaure masu kai,Sam fa baya acikin hayyacinshi amma yaji aranshi Abbanshi na kusa dashi,daƙyar ya iya ɗaga hannunshi ya ɗaurashi akan fuskar Abbansu yana shafata,kuma wani abun mamaki idanuwanshi arufe suke gam,jikin ne kawai ke motsi,

Har saman wuyanshi Junaid yakai hannunshi zuwa saman ƙirjinshi,har lokacin bai daina ambaton sunanshi ba,ga la66anshi sae kerma  su ke yi,
  Murmushi kawai suke saki suna kallonshi,
"Gaskiya tunda nake banta6a ganin ƙauna tsakanin mahaifi da ɗansa ba,irinta mahaifinku da wannan ƙanin naku,"Dr emran ne yayi maganar,da mamaki akan fuskarshi,
  Sai lokacin Alex ta samu damar yin magana
  "Nikaina da nake mahaifiyarshi bana tunanin yanayi mun irin son da yake yiwa mahaifinshi,Koda yake dole yaso mahaifinshi akaina,shaƙuwarsu ta wuce tunaninmu,"
  Suna cikin yin maganar,Abbansu ya fara ƙoƙarin buɗe idanuwanshi,Wani irin nauyin bacci ne ya hanashi tun ɗazu ya farka,amma yana jin muryar Junaid acikin kanshi,sake ambaton sunanshi Junaid yayi da wata irin kasalalliyar murya,
  "Abba,"tunkafin Ya buɗe idanuwanshi ya soma kiran sunanshi"Junaid"gaba ɗaya suka matso kewaye da gadon suna murmushi,Yayin da idanuwansu ke akan Abbansu,
  Ruƙo hannun Junaid yayi acikin nashi,sosai har cikin ranshi Yaji dagaske Shi ɗinne,kokawa ya shiga yi da baccin dake ƙoƙarin hanashi buɗe idanuwanshi,
  Daƙyar ya ɗaure ya ware idanuwanshi,a wani slow ya wurga eye balls ɗinshi kan Junaid dake kwance agefenshi,Tunda ya ɗaura eyes ɗinshi akan fuskar Junaid ko ƙyaftawa baiyi kamar an dasa mashi aya,wani irin farin ciki ne ya lullu6eshi lokaci guda hawaye suka shiga wanke mashi fuskarshi,Muryarshi na kerma Ya ambaci sunanshi"Junaid!dagaske kaine a kusa dani,Junaid ɗina ne atare dani"?
  "Yaya hossein dagaske ne abunda kake gani,ga Junaid ɗinka nan,an dawo maka dashi"Abusufyan ne yayi maganar,
  Lumshe idanuwanshi yayi tare da sake buɗesu a hankali yana cigaba da kallon fuskarshi,Lokacin daya ankara da Jini da ake ƙara mashi aruɗe yace"Me ya same shi?Sun cutar mun dashi ko?duk sun canza mun Junaid ɗina kamar bashi ba,"
  "Abba,ka kwantar da hankalinka,Junaid yana samun sauƙi,"Omar ne yayi maganar cikin sigar lallashi,
   "Alhamdulillah Ya Allah daka dawo da farin cikana"ya ƙarasa maganar tare da dago da hannunshi zuwa cikin sumar kanshi,
  "Allah Ya baka lafiya Junaid ɗina,ka yafe mun duk laifina ne halin daka shiga,Bazan ƙara yin kuskuren da zan rasaka a kusa dani ba"yana magana hawaye naci gaba da sauka akan fuskarshi,

Jikinsu duk yayi sanyi,tsananin tausayinsu ne ya kamasu,

Wuraren ƙarfe 10 na dare,Abusufyan ya kwashe su Sehrish zuwa gida,Su biyar ya ɗauko hada Amrish da Oummansu,Ba don sun so ba ya ɗaukosu,lokacin da ya ƙaraso cikin gidan bayan yayi parking ɗin motar,Buɗe motar Oummansu sehrish tayi tare da fitowa waje,Bayan Abusufyan Ya fito ya zagaya ya buɗema su Sehrish,saukowa tayi daga cikin motar,Amrish ma ta sauko bayan ita sai Jahad,duk suka fito banda Hosana,ruƙo hannunta Yayi tare da ambaton sunanta,Daƙyar ta iya buɗe idanuwanta,
  "Ki fito ku wuce gida,Sae ki kwanta ki ƙarasa baccin naki,"A yamutse ta fito daga cikin motar,ruƙe hannunta Sehrish tayi ganin tana tangal tangal zata faɗi ƙasa,
  Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da kallonsu yace"Ku wuce ciki mana,Ni zan koma ne,zuwa gobe zamu dawo gida sai acigaba da jinyar tasu a gida,"
  Gyaɗa kai abu tayi tare da cewa"shikenan,Allah ya basu Allah,Amma Mommy fa?zata dawo itama"?
  "Sai zuwa gobe zamu dawo tare da ita,"ya ƙarasa maganar tare da kallon Jahad,
  "Banga kina farin ciki ba,ko bakiyi murna da ganin Masoyin

Download complete TXT · Novel page