Abban Sojoji Book 3 (Takun Karshe)

Chapter 89 of 104

naji ajikina Daughter,danasan hakan zata faru da ban tursasa mashi akan ya sakeki ba,da duk hakan bata faru ba,"Sai lokacin Sehrish ta gane dalilin dayasa Sgr yayi mata hakan,
Janyeta yayi daga jikinshi,tare da sanya hannunshi asaman fuskarta yana share mata hawayenta yace"Ina babban yayan naku?nayi tunanin atare dashi zaku dawo,'
Girgiza kai ta ɗan yi"A'a,Sai zuwa anjima zai dawo,Ya Omar ne ya kawo ni,Na matsa mashi ne akan inaso na dawo gida," sunyi pretending ne don kada Oummansu ta gano gaskiyar abunda Ya faru da ita,
"Allah ya baki Lafiya Daughter,"
"Ameen daddy,"
Turo kopar ɗakin akayi,Mommy ce ta shigo hannunta ruke da plate mai ɗauke da farfesun nama,da zafi zafinshi sai ƙamshi yake yi,

Ƙarasowa ciki tayi fuskarta a ɗan sake tace"Ya jikin naki,"
Batare da sehrish ta kalleta ba ta amsata"da sauki Mommy,"
Miƙa ma Abu plate ɗin tayi"Ga wannan nasan zata buƙace shi,Akwai tea dana haɗa mata,bari naje na ɗauko mata shi,"
Hannu bibbiyu Oumma tasa ta kar6i plate ɗin"Mun gode sosai,"
"Kada ki damu,duk yiwa kaine"takai ƙarshen maganar,tare da juyawa a hanzarce tabar bedroom ɗin,Abusufyan ya lura da sehrish,tunda Mommy ta shigo bata kalli fuskarta ba,tayi hakanne saboda ta tsani ganin fuskar Sgr,Ita kuma Mommy dashi take kama shiyasa taƙi kallonta,
Shafa fuskarta yayi"Daughter,"murmushi ta ɗan saki batare data ɗago da idanuwanta ba,Sun cika tab da kwalla,
Juyawa yayi tare da kallon Abu dake tsaye hannunta ruƙe da plate,.
Kar6ar plate ɗin yayi daga hannunta,
Ruƙo hannun Oumma Mommy azeema tayi"mu koma kitchen munbar Aiki acan,In sha Allah zata samu sauƙi,"atare suka fuce daga ɗakin,
Ya rage daga Abusufyan Sai Hosana da Jahad dake kewaye da ita,
jim kaɗan Mommy ta dawo hannunta ɗauke da Cup wanda ta haɗa mata Kakkauran tea acikinsa,
Asaman side drawer ta ajiye mata Cup ɗin,
Kafin ta juya tabar dakin,
"Rishi wai ina kika shiga ne?Kin tafi kin barmu da tunani,"Hosana ce tayi maganar fuskarta a yamutse,
Jahad tace"Dan Allah kibarta ta huta,Ba kiga bata da lafiya ba,Sannu Sehrish Allah ya baki Lafiya,muryarta ƙasa ƙasa ta amsa mata da Ameen,
Abusufyan da kanshi Ya zauna yana bata farfesun abakinta,Cike da kulawa,ba ƙaramin daɗinshi taji ba,sosai tasha,kusan duka ta shanye duk da hosana ta tsoma masu hannu,Ta dinga ɗaukar naman tana turawa abakinta wai ae itama bata ci ba,

Bayan ta kammala Ya ajiye plate ɗin Ya dauki cup of tea ɗin da mommy ta ajiye mata,A baki ya kafa mata shi,Sosai ta shiga kur6arshi abakinta,
"Amma nima ka bani tea ɗin abaki"?
Hosana ce tayi maganar,tana tura mashi bakinta,Hakan ba ƙaramin dariya yaso ya basu ba,murmushi sehrish ta ɗan saki tana kallonta,
"Daddy ka bata tasha,"
Cike da zolaya Abusufyan yace"Na mara lafiya ne,Hosana kiyi hakuri wannan na sehrish ne,bata baki tausayi ba Kalli fa ki gani duk ta rame,"
A shagwa6e Hosana ta langwa6ar da kanta,tasa hannu tana nuna mashi ƙashin wuyanta,
"Daddy ae nima banda Lafiya,Kalli ka gani,"
Kallon wuyanta yayi acike yake babu wani ƙashin daya leƙo,
Harara Jahad ta ɗan watsa mata"Saboda kofin tea zaki jama kanki ciwo,Tirr da wannan halin naki,Shegen Ci kamar gara"
Guntun tsoki Hosana taja"eh ɗin ina ruwanki,Ƴar shigar shugula,ba'a kasa dake ba,kin tsomo mana baki,".
Dariya sosai Abusufyan yayi yana kallonsu,ita kanta Sehrish murmushi ne kwance akan fuskarta,Hankalinta Ya kwanta sosai,gata ga iyayenta ga kuma ƴan uwanta,

Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,Abusufyan yace"Wanene"?
"Nice Amrish,"
"Okey shigo daga ciki,"turo ƙopar ɗakin tayi,jikinta sanye da hijabi dai dai guiwa,Waro ido waje tayi ganin Sehrish
Da ƙarfi ta ambaci sunanta"SEHRISH"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6ete,har ta manta da abusufyan dake zaune,Da gudu ta ƙarasa gefen gadon,Ta haura sama ta rungumota ajikinta,
"Sehrish ina kika shiga ne?ina ta nemanki?Oumma tace mun kunyi tafiya keda Babban yayanku,"
Fuskar Sehrish ɗauke da murmushi tace"Am sorry Amrish,Nayi laifi ban sanar dake ba,Tafiyarce ban shirya mata ba,ni kaina bansan da ita ba,"
ɗagowa amrish tayi daga jikinta ta sanya tafin hannayenta ta tallabo fuskar Sehrish"Duk kin rame,Baki lafiya ne "
"Zazza6i nake yi,"
Gyaran murya Abusufyan yayi mata,Da sauri Amrish ta sauko daga saman gadon ta zuƙunna tana gaishe shi"Ina kwana daddy,An tashi lafiya,Ya mai jiki,"
Murmushi Abusufyan ya sakar mata tare da cewa"Lafiya Lou,yaushe rabon dana sanyaki acikin idanuwana,bakyason zuwa kina gaishe ni ko"?
Sunnar dakai ƙasa tayi cike da jin kunyarshi tace"A'a,inason zuwa,"
"Baki ɗaukeni a matsayin mahaifinki bane"?
Da sauri tace"Na ɗauke ka,"
"To meyasa bakya sakin jiki dani ne"?
Shiru tayi batace Komai ba,
"Daga yanzu inaso ki saki jikinki dani,Dake dasu Sehrish duk ɗaya kuke a wurina,duk wani abu da kike buƙata na rayuwa,ki sanar dani ni kuma zanyi maki shi,"
"Nagode sosai Daddy,"ta ambaci hakan tare da miƙewa,
"Sehrish wayarki na ɗaki,bari na ɗauko maki ita,"
Da sauri ta juya ta fuce daga ɗakin,Kallonta Abusufyan yayi,
"U need a rest,ki kwanta ki huta,Zuwa anjima zan sake zuwa dubaki,Yanzu hankalina ya kwanta,ashe da rabon yau inyi bacci hada minshari don tunda kuka tafi wlh ban runtsawa sai dae bacci 6arawo ya dan dauke ni Daughter,"
Murmushi ta ɗan saki,mikewa yayi tare da kallonsu Jahad yace"Ku kulamun da ita pls,"
Atare suka amsa mashi da toh,kafin ya bude kopar ɗakin ya fuce,

Baijima da fita ba,Amrish ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da wayar Sehrish,zama gefen gadon tayi tare da miƙa mata wayar,hannu tasa ta kar6i wayar,
"Ya jikin naki"?
"Am feeling better now,nayi missing dinku sosai,"
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Nima nayi missing ɗinki sosai,Kullum saina tambayi Oumma yaushe zaki dawo,"
"Allah sarki,nagode sosai da nuna damuwarku akaina,"

Bayan fitar Abusufyan kaitsaye ya nufi ɗakin Ammi,A lokacin khadija da nafeesat suna acikin ɗakinta,Suna tattaunawa game da bikin da za'ayi,

Da sallama ya shiga ɗakin,atare suka amsa mashi,da sauri suka soma gaisar dashi,fuskarshi asake ya amsa masu,Suna zaune ƙasa sun lankwashe kafafunsu,Ammi kuma na zaune gefen gadonta,
Agabanta ya zuƙunna"Ina kwana Ammi,kun tashi lafiya,"
"Lafiya lou,Autana,Ina fata kaima haka,"
"Alhamdulillah"ya amsa mata,
"Da alama yau akwai labari me daɗi akan fuskarka,murmushi ya saki tare dacewa"Ammi Sehrish ta dawo,Yanzu haka daga ɗakinsu nake,"
"Masha Allah,Kai amma naji daɗi sosai wlh,Amma waye ya kawota?
"Omar ne ya ɗaukota,"
"Amma ya lafiyar jikin nata"
"Da sauki ammi,"
Miƙewa tayi hannunta ruƙe da sandarta,kallonsu Nafisat tayi"yanzu zan dawo,Zanje na duba jikin jikata ne,"
Mikewa sukayi atare"Muma zamu je ammi,"
Murmushi tasaki"shikenan bismilla,"Abusufyan Ya shiga gaba suka bi bayanshi,har zuwa ɗakin Su Sehrish,
Ba ƙaramin farin ciki ammi tayi ba,Ganin yadda sehrish take ta faman sakin murmushi,tashi Amrish tayi daga gefen gadon,Ammi ta sauna suna fuskantar juna ita da sehrish,
Atare suka haɗa baki suna gaishe da ita,Bayan ta amsa masu tace"Ya jikin naki"?
"Naji sauki,"
Jinjina kai ammi tayi"Alhamdulillah mun godewa Allah,Haka mukeso,"Takai ƙarshen maganar tare da kallonsu Khadija dake atsaye,Ga ƴar uwarku nan,ɗaya daga cikin ƴan ukun Abusufyan ne,Bata da lafiya ne,"

Har suna hada baki wurin yi mata Ya jiki,fuskarta asake ta amsa masu,kafin ta soma gabatar masu dasu,
"Jikokin modibbo ne,Ƴa'ƴan ƙanwar Mahaifiyarsu Omar,sannan kuma nan bada jimawa ba,Zasu zama surukan Abba,ta 6angaren Adam Da Osman"

Farin ciki ne ya lullu6esu,Ammi taci gaba da cewa"su kuma waɗannan zasu bi sahunku suma,Wato zasu Zama surukan Abba,Ga Sehrish nan Amaryar Babban Yayansu,ɗan wurin Fatima," tunda ammi ta ambaci hakan ran Sehrish ya 6aci sosai,tuni ta ɗaure fuskarta,Sam babu wanda ya lura da ita,
"Bayan ita kuma Sai Jahad,Amaryar shalelen Abba wato Junaid,"da sauri jahad Ta kife kanta saman katifar saboda kunya,
"Ita kuma wannan,Mai hankalin cikinsu,Amaryar Omar ce in sha Allah,"
Fashewa Hosana tayi da dariya,kowa najin kunya banda ita,
"Inason nayi magana da ita, ku ɗan bamu wuri,"

Amsa mata suka yi da toh,Gaba ɗaya suka fuce daga dakin,A waje suka tsaya suna fira atsakaninsu,Amrish dai tayi shiru saboda ita batasan matsayarta ba,Amma taso ace hada ita za'a ɗaurama aure,Itama ta zama ɗaya daga cikin amaren gidan,

Bayan fitarsu Ammi ta zauna tayi mata nasiha sosai,ta kuma nuna mata 6acin ranta akan abunda Sgr yayi mata,A ƙarshe ta ruƙe hannayenta"Bazanso abunda zai cutar dake ba,Dama jiran dawowarki nake yi,Saboda inaso inji ra'ayinki game dashi,Kina son Cigaba da rayuwa dashi,Ko kuwa A'a,"
kamar jira takeyi da sauri tace"Banaso ammi,dan Allah ku rabani dashi,wlh bazan iya rayuwa dashi ba,Ni dai kawai asanyashi Ya sake ni,"hada hawayenta,
Shiru ammi ta ɗan yi tana kallonta,Kafin tace"Amma fa yana sonki sosai,Wanda silar hakan ne yajawo har ya aikata maki hakan,Saboda anyi ƙoƙarin rabashi dake,"
Cikin shessheƙar tace"Nidai bana sonshi ammi,wlh yafita araina,"
Ajiyar zuciya ammi ta sauke,
"Shikenan,In sha Allah zan shiga tsakaninki dashi"

WANNAN KENAN!

*masu yi mun ya jiki nagode sosai da irin kulawarku,kuma in sha Allah kamar yadda nace very soon zan kammala maku littafi in Allah ya yarda,koda ba lafiya indai yatsun hannuna na motsi zan daure inyi ne,Don in gama akan lokaci,kafin watan ramadan,*Ga mai buƙatar karanta Littafin Abban Sojoji from Book one to 3,Yayi mun magana ta whatsapp 08103884440*
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*


*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*




Story And written By

*Hafsat Bature*




Not edited



Ammi ta jima zaune a wurinta,kafin daga bisani tayi mata sallama ta fita,A hankali ta gyara kwanciyarta samam gadon,lumshe idanuwanta tayi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abunda ya faru lokacin Da Sgr Ya farmaketa,wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta,a irin kallon da take yi mashi yanzu Mara tausayi mara Imani,sanna kuma ba sonta yake yi ba, Jikinta yake so,shiyasa yake yi mata komai da mugunta don yaga yaƙarar da ita,kafin Ya koma U.s,tunda yasan rabasu Za'ayi,

Yinin ranar tana kwance samn gadon,Anan Abba ya same ta,Yayi mata ya jiki,da kuma ban haƙurin abunda Sgr yayi mata,taji daɗin yadda Abba Ya nuna 6acin ranshi,kuma yace duk abunda takeso Yanzu shi za'ayi,bayan fitar Abba,Su jahad da Amrish suka dawo cikin ɗakin,Yanzu kowa Ya Zuba Ido Yana jira dawowar SGR,

Wuraren Ƙarfe shida na mare ce,Omar Ya fito daga cikin toilet,Jikin shi sanye da Jallabiya,Yana ƙoƙarin Zama gefen Gadon,Wayar shi dake ajiye gaban mirror ta soma ringing,miƙewa Yayi izuwa gaban madubin ya tsaya,Hannu yasa ya ɗauki wayar,Ya duba me kiran nash,A hankali Ya furta Sunanshi"Rafayet,"kafin ya ɗaga kiran tare da manna wayar a kunnashi,
Tunkafin yayi magana,Sgr ya ambaci sunanshi"Omar,"cikin sanyin murya,tamkar bata shi ba,
  Ajiyar zuciya Omar ya sauke"Rafayet,Meyasa ka tafi ka barni?Nasan ban kyauta maka ba,dana barka a wannan yanayin,Amma banji daɗin tafiyar da kayi ba,"
  "Bani da za6ine Omar,bansan ya zanyi ba,banyi tunanin zaka ɗaga kira na ba,Saboda kowa fushi yake yi dani,"
  "Dole suyi fushi dakai,abunda kayi sam bai dace ba rafayet,duk in na tuna cewa ɗan uwanane ya aikata hakan sai inji ɗaci araina,why Rafayet?
  "Omar,I ave regretted,i hate my self,ban kyautawa kowa ba,Zan ba kowa hakuri,In yi nesa da kowa,"
  Waɗannan kalaman na Sgr ba ƙaramin ta6a mashi zuciya su kayi ba,tuni Ya karaya,
  "Am Sorry Nayi maka laifi na ɗauko Sehrish batare da saninka ba,"
  "Don't worry about that,Nima nayi niyar na dawo da ita gida,just ina fargabar abunda zai biyo bayane,"
  "Rafayet,ka dawo gida kawai,Ka nemi afwar Abba da uncle,nasan zasu sauko ne,".  .
  "Its Okey,Zan dawo,amma sai zuwa sha biyu na dare".  .
  "Shikenan,i will be waiting for u,Ko bacci bazan bari ya ɗaukeni ba,har sai naga ɗan uwana,Nayi hugging ɗinsa ajikina,"
  Sun jima suna waya da juna,Kafin daga bisani su kayi sallama,yana ajiye wayar gaban mirror,Hosana ta bango ƙopar ɗakin nashi,cak ya tsaya yana kallonta ta cikin madubi,doguwar rigace ajikinta mai baza daga ƙasa,babu mayafi akanta,da alama gayu akayi mashi,ta sauko da Curly hair ɗinta,An shafa jan baki ja,

A tsiyace ta toge tare da ruƙe qugunta"Ya Omar,"
  A sukwane Ya juyo yana kallonta,from head to toe,Ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,cikin sanyin Murya ya ambaci sunanta"Hosana,"
  Murguɗa mashi baki tayi,Yace"To fa!Halan wani laifin nayi,"
  Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
  Ashagwa6e tace"Ya Omar wai dagaske idan aka ɗaura mana aure bada ni zaka tafi U.s ba,Wai a gida zaka barni,"?
  "Wurin wa kika ji hakan"?
Bubbuga ƙafarta tayi"Nidai ka amsa mun tambayata,"
Jinjina kanshi yayi tare dacewa"Eh,Anan zan barki,amma zan dinga zuwa duk ƙarshen.....  ..'
Bai ƙarasa maganar ba saboda wani kallo da yaga tana jifarshi dashi,kallon baka isa ba,
  "Ya omar ae wlh baka isa ba,Ko kana so ko ba kaso,Dole ne duk in da zaka tafi mu tafi tare,Ƙafata ƙafarka,Nida kai mutu karaba takalmin kaza,"ta ƙarasa maganar tana jefarshi da harara,
"Oh,a haka zan tafi dake can?Kina murguɗa mun baki,Sai kace wani tsaranki,Nifa in kika takuramin Allah,Zan fasa auren ne,"
Turo baki tayi"Yo he me?Ka fasa,Kai kasani wlh ya omar,Maza rubibina suke yi saboda kyau na,Don ma dai kawai ina sonka yasa nake kulaka,"
  Ƙumshe dariya yayi acikin bakinsa,don baisan tayi tunanin ko wasa yake yi mata,juya mata baya yayi batare daya ƙara tanka mata ba,

Yayi tunanin zata fita daga ɗakinne Amma sai yaga ta tattare bazar rigarta,ta haye saman gadonshi can tsakiyarshi ta baje tana kallon ceilling,
  Girgiza kai yayi"Oh ni Omar na ɗebo ruwan dafa kaina,"Yayi maganar acikin zuciyarshi,

"Ya Omar"ta ambaci sunanshi yayin da idanuwanta ke kallon ceilling kamar me nazarin wani abu,
  "Na'am,"ya amsa mata,

"Ya Omar,idan aka ɗaura auren kai kana America,Ni ina a nigeria,To wai taya za'ae in samu Ciki,"
  Rass Yaji gabanshi Ya faɗi,A firgice ya juyo yana kallonta,Hankalinta kwance tayi mashi tambayar,Abun ya ɗaure mashi kai,mamaki ne ya kamashi,
  "Ke!Waya faɗa maki cewa dole sai muna atare zaki samu ciki,"?
  "Yo oho,Nidai nasani ae,Ko kaza sai da zakara take samun cici,Kaga kenan,Nima sai kana tare dani zan....."bata ƙarasa maganar ba,da gudun gaske ta turo daga saman gadon ta nufi hanyar fita,A hanzarce ya damƙo hannunta,Ya juyo da ita,a jikin bangon yayi mata rumfa,sai faman zazzare mashi manyan idanuwanta takeyi,
  "Saboda rashin gaskiya,daga ganin na nufoki,kika watsa da gudu ko"?
   Runtse idanuwanta tayi"Ya omar,wai menene haka,kalli yadda ka takure,"
  "So nake ki faɗamun,Wayake koya maki waɗannan maganganun da kike gaya min,ko kunyata bakya ji"
Turo baki tayi"Babu kowa,"
  Sam bai yarda da ita ba,A matsayinta name ta6in hankali baya tunanin zata Iya sanin wannan,Sai dai ko gaya mata akeyi ko kuma tana kallon a wayarta,
  "Kiji tsoron Allah,ki faɗamun gaskiya,taya akai kikasan cewa dole sai muna atare da juna zaki samu ciki"
  A ƙule tace"Nifa babu kowa,"
Jinjina kanshi yayi"where's ur phone"?
  "Tana a ɗakinmu,"
"Ok,je ki ɗaukomin ita"

"Toh,"ta amsa mashi tare da juyawa da gudu taje ɗakinsu ta dauko wayar ta dawo bedroom ɗinshi Ta miƙa mashi"Gata,"
  "Cire pass word din"
Ashagwa6e tace"Sunanka ne,"
Ta6e baki ya ɗanyi,Acikin Zuciyarshi kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba,
  Yana rubuta sunanshi Omar,Nan take pass word ɗin Ya cire,
   Bincike yashiga yi mata acikin wayar,Gallery ya fara shiga kaf ya duba videos ɗin dake a wurin,baiga abunda yake zargi ba,ita kuwa sai faman sakin murmushi takeyi,
  ɗagowa yayi suka haɗa ido da ita"Kin gogesu ko"?
 "`Wai me kake magana akai Ya omar,"
Moving yayi kusa da ita,lalla6ata ya shiga yi"Pls My hosana,Ki fadamun gaskiya,Bazan maki komai ba,A ina kike sanin abubuwan da kike faɗamun,"?
    Kafin ta bashi amsa,aka kwankwaso ƙopar ɗakin,
  "Omar,zoka buɗe mun ƙopa,"muryar abbansu ce,da sauri ya saki hosana,ya ƙarasa bakin ƙopar ya bude mashi,
  "Abba,"omar ya kira sunanshi,
"Kunyi waya da rafayet"?fuskarshi da alamun damuwa yayi maganar,
Omar yace"eh,munyi magana dashi,"
  "Dan Allah omar,kasan yadda za'ae ya dawo gida,"
  Murmushi Omar ya ɗan saki kafin yace"Abba,kana missing dinshi ne ko,"
"Omar bazaka gane ba,inaso ya dawo ne,"tun da ya shigo bai lura da hosana ba,don tuni ta la6e bayan labule,kamar wata mara gaskiya,
  "In sha Allah zai dawo abba,Yace mun around 12 na dare zai shigo gidan,"
Ajiyar zuciya abba ya sauke tare da cewa"Allah ya kawoshi lafiya,Naga an fara kiran Magrib,Ka hanzarta shiryawa mu tafi masallaci,"
  Amsa mashi yayi da toh,Bayan fitar abba,Shaf shaf Ya shiga toilet Ya ɗauro alwala,Kafin Ya fito tuni hosana ta bar ɗakin,Dama haushinshi take ji ya tsareta da tambayoyi kamar wata ƙaramar yarinya,acewarta

Wuraren ƙarfe 10 na dare,Wayar jahad ta soma ringing,a lokacin har Bacci Ya fara ɗaukarta,Tana kwance gefen Sehrish,Hosana dake bayanta tuni bacci yayi awon gaba da ita,Oummansu kuwa na zaune saman darduma tana karatun qur'ani,

A saman mattress ɗin ta ajiye wayar,Bayan ta ɗauketa ta duba mai kiranta Sunan Fawan ne ya bayyana akan screen ɗin wayar tayi matuƙar yin mamakin ganin kiranshi,

Picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta,
  "Assalamu Alaikum"
On the other hand,Fawan ya amsa mata"Wa'alaikum Salam,Ya kike"?
  "Lafiyalou,"
"Sorry fa,bansani ba ko na tashe ki daga bacci,naji muryarki kamar kin fara ko"?
Murmushi ta ɗanyi kamar tana agabanshi"Hakane na fara amma banyi nisa ba,"
  "Dama junaid ne,ke son magana dake,ya bi ya ishe ni ya hanani sakat,Kinsan yanzu babu waya a hannunshi,Ina fa bacci sai gashi har bedroom ɗina,wai in kira mashi juliet dinshi,Sai kace baisan hanyar zuciya ɗakinku ba"
Wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Jahad,a hanzarce ta miƙe daga zaune,
   "Gashi ku gaisa"jim kaɗan taji muryar junaid,
  "My juliet,"batasan lokacin da ta saki murmushi ba,
  "Na'am My romeo,Dama kana tunawa dani,"?
   "Yeah,ae bakison zuwa duba jikina,shiyasa nake fushi dake,"
  "Kaine ka juyamun baya,tun rana ta farko da nazo wurinka,Ka nuna tamkar baka sanni ba,abun ya tsayamun araina,rana ta biyu dana zo,kaƙi kallona,rana ta uku dana zo,Kana yin tozali ka rufe idanuwanka,kamar kaga wani mugun abu,"
   Sai da takai ƙarshen maganarta,Sannan yace"Am sorry,just forget about it,I really missed u,In ba damuwa inason ganinki yanzu,"
  Da sauri ta kalli agogon bangon dakin
  "Ƙarfe goma fa?Kuma oumma na kallona bansan ko zata barni in fito ba,"
  "Idan ta tambayeki,Ki sanar da ita cewa,Mijinki ne ke kira,Ae an biya sadaki,"
Jin wannan maganar yasa jahad ta fashe da dariya,Har oummansu dake karatun qur'ani saman darduma sai da ta ɗago ta kalleta,
  "still baka canza ba,kana nan a romeo ɗin dana sanka,"
  "Of course,I will be waiting for u pls,"yana kai ƙarshen maganarshi yayi rejecting ɗin kiran,
  Ajiye wayar tayi,A hankali ta sauko da ƙafafunta ƙasa,Jikinta na sanye cikin night gown pink colour,ta ɗaure gashin kanta da ribbom,
  Sai da ta miƙe tsaye sannan ta soma tunanin abunda zata ce ma Oumma,
  Gaban wadrobe taje ta bude ta lalubo hijab Ash colour ta zura ajikinta,saɗaf saɗaf Ta nufi hanyar fita,jin Oummansu Ta janyo doguwar aya,tasan bazata katse taba,balle

Download complete TXT · Novel page