So Da Buri Book 1
Chapter 11 of 43
“U too”
Sannan ta mik’e tace
“Please sir zan tafi muna da test.”
Mik’ewa shima yayi yana murmushi kafin yace “sai yaushe? Ba kiyi mini kwatancen gidanku ba balle in kawo miki ziyara idan an yi hutu, ko bakya so in zo???“
Da sauri ta d’aga mishi kai
alamar ‘eh’.
With surprise yace
“Y”
“Nothing”
Kawai ta iya ce mishi sannan ta sunkuyar da kanta k’asa, tana adduar Allah yasa ya bata izinin tafiya, dan bata san daliliba in dai suna waje d’aya ji take tamkar zuciyarta za ta
faso k’irjinta ne ta fito waje, tsabar bugawa.
Abba fahimtar da yayi kamar yana yin komai cikin sauri..kar kuma yaje ta k’i shi idan taga zalamarshi…hakan ya sanya ba dan ya gamsu da shawarar da zuciyarshi ta bashi ba kawai ya bata izinin tafiya.
Ai kuwa da sauri ta juya ta fita a office d’in.
Zama yayi a kan kujerar sa, sannan ya bud’a hannunshi kafin ya kaisu duka biyu bayan k’eyarsa kamar zai yi filo da su…
Lumshe idanuwanshi yayi sannan ya fara tunanin duk wani possible hanya da zai b yayi getting close to her, dan ya lura he needs her attention first.
A bakin Admin block d’in taci karo da Zainab tana ta faman kai kawo, tana hango ta kuwa ta iso tana tambayarta inda office d’in nashi yake..kwatance Maryam d’in tayi mata daga haka tayi gaba, bata san ya sukayi ba....
A b’angaren Abba kuwa, a da
k’arfe 2 yake tashi ya tafi gidanshi, amman yanzu voluntarily yayi exceeding time d’inshi har 10 pm (Time d’in tashi daga night prep) ko tsoron hanya baya yi, hakanan
yacewa mai principal kawai zai dinga supervising evening and night prep, Friday kuma zai samu aji ya dinga k’ari a sms. Da murna kuwa principal d’in ta yarda, dan yace ba sai an bashi ko sisi ba.
Kasancewar Maryam shadow ce ya sanya ba a ajin su take night prep ba, a jss2 take zama tana supervising d’insu.
Tana zaune kawai ta ji kamar an shigo tana kallon k’ofa kuwa suka yi ido biyu….kujerar teacher ya janyo ya kawo dai dai gefen sit d’inta ya ajjiye sannan ya zauna kafin yace mata “Good evening ma.”
Da sauri ta kalleshi sai kuma ta yi k’asa da kanta tace “evening sir.”
Murmushi yayi kafin yace “na takura ki ko?”
Girgiza kanta kawai tayi ta ci gaba da karatunta…
Jifa jifa yake mata hira har aka tashi.
Tun daga ranar kuwa haka kullum zai shigo ajin da sunan supervising zai yi
amman su daya kamata ace sun hana Yara surutu har a tashi bakin Abba baya yin shiru na minti goma.
A haka har aka yi sati…
Yau friday Maryam tanata murna ba zasu had’u ba atleast zuciyarta sa ta huta da bugawa da take yi.
Sai dai kuma tana zuwa sms d’in ta ganshi a bakin gate na main mosque yana tarar y’an makara, ai kuwa ganin tazo a makare ba k’aramin dad’i yayi masa ba, sai da ya bawa kowa punishment sannan ya juyo ya fara tanbayarta “mai yasa ta makara bayan tana matsayin shadow?”
Uzurinta ta fad’a mishi…maimakon ya barta ta tafi ko yayi punishing nata, instead, sai kawai ya hau tambayarta ajin da take. Yaso ace itama d’aliba ce amman sai ya ji tace “ajin y’an Izu 60 take koyarwa, thou he was amazed.”
Ganin zata makara sosai ya sanya ya barta ta shiga taje wajen d’alibanta….
Sai da ya samu ajin da tabarmar su take facing tata tukunna yace su zai koyar......
Idan ana maganar ‘Nacii!!’ tou shi Abba yake yiwa Maryam, tun bata sakewa da shi har ta fara, dan ya iya labarin ban dariya, sannan yana burgeta , thou har yanzu bata gama sanin ma’anar bugawar da zuciyarta keyi idan suna tare ba.
Ahaka aka shafe 3 weeks.
Kamar kullum yau ma suna zaune a night prep yana bata labarin Mahaifin sa….tanata mamaki saboda ita dai ita da Mahaifinta they are like best friends sab’anin shi dan a yadda yake bada labarin Mahaifin nasa kamar wani boss na horror movie, he is not even close to him kwata kwata kuma wai a haka duk cikin y’aya’ansa yafi sonshi, saboda ya ci sunan mahaifinsa ne…
Hayaniyar wasu Yara ne ya juyo da hankalinsu suna waigawa kuwa suka ga ana dambe! Da sauri ta tashi ta isa wajen, shima ganin hakan yasa ya biyota….garin k’ok’arin raba damben d’ayar Yarinyar jin an rik’e hannunta ta d’auka y’an class d’insu ne nan ta buge hannun Maryam d’in da k’arfi!! wanda bai sauk’a a koina ba sai a kan louvers na window kuma daman a fashe yake, nan da nan kuwa ta yanke jini ya fara tsiyaya…
Abba bai san lokacin da ya finciko Yarinyar ya wanka mata marin da har sai da ta fad’i kasa itama gefen bakinta ya fashe, sannan yayi sauri ya kamo hannun Maryam, ganin jini ta koina yana zuba duk ya ma rud’e bai san lokacin daya kama k’asan rigar shaddar jikinsa ba ya yaga ya kamo hannun ya d’aure da kyallen sannan ya fara janta yana cewa “ta zo su tafi clinic, a dubata.” Duk ya rikice, dan har kwalla Maryam ta hango ya taru a idanunsa.
Suna fita suka had’u da prep mistress d’in hakan yasa suka d’unguma har ita aka je akayi mata dressing, a tafin hannuta ta yanke amman Allah ya taimaka ba’ai mata d’inki ba. Har sukaje suka dawo yana jera mata sannu ko motsi tayi sai ya tambayi “mai takeso?” Har bakin unity gate ya rakata tukunna ya juya dan a lokacin an tashi daga prep.
Kusan bai samu yayi ishashhsen bacci ba, juyi kawai ya dinga yi yana Allah Allah gari ya waye.
Allah ya taimaka ma washegari za ta kasance Tuesday ne, so yanada su har double period.
Kamar kullum yau ma Zainab tayi kwalliyarta suna zaune suna jiran shigowarshi, yau kamar da rashin mutunci ta tashi dan sai hararar Maryam take yi, tana fama yada mata magana har da cewa “ idan ma za ta ware gara ta ware tun wuri dan ba abinda za ta tayata da shi.”
Ita dai maryam ta yi shiru tana fama da zugin da hannunta ke yi mata, ga idanunta da suka yi jaa, dan jiya bata samu isheshshen bacci ba.
Shigowarsa ce ta sanya ajin yin shiru kowa ta maida hankalin ta gareshi, shi kam yau k’arara kowa sai da ya lura da kalar kallon da yake yiwa Maryam dan tunda ya shigo daga bak’in k’ofa ya kafeta da idanu har ya isa inda bench d’inshi yake, garin kallon ta ma har da d’an yin tuntub’e.
Ganin tak’i d’agowa ta kalleshi yasa kawai ya amsa gaisuwar y’an aji sannan ya fara lesson..dictation ya fara kamar kullum dan baya musu note a board amma yaga Maryam d’in ta kasa yi, k’ok’ari takeyi ta rubuta da hannun hagu amma ta gagara, ganin tana neman fama ciwonta ga ciwon kan da ya addabeta yasa kawai ta tura littafin gefe ta kifa kanta a benchi.
Abba kam zuwa yanzu ji yake kamar ya kori gaba daya y’an ajin ya lallasheta, ganin gaba d’aya hankalinshi baya ajin kar yaje ya fara musu dictating shirme yasa yayi rounding up, sannan yace “akwai mai question?”
Mutane uku ne suka yi question ciki harda Zainab tanata faman karairaya, shi bai ma san tana yi ba, ya bata amsa daga haka yace “Let’s call it a day”.
Sai a lokacin Maryam ta d’ago ta juya ta tambayi wata classmate d’insu ta ara mata note d’inta, bayan ta mik’o mata ta had’a da nata ta ajjiye a kan bench, duk a kan idonsa.. Har ya yi hanyar fita sai kuma
kawai ya dawo ya d’auki littafin nata da na wadda ta karb’a za ta kwafa d’in, ya juya ya fita da sauri.
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
11
Yana fita y’an ajin suka fara tofa albarkacin bakin su, har da masu cewa ‘ai tayi sneaking ta shigo da waya dan da gani free call suka kwana suna yi jiya shiyasa daga ita har shi idanuwansu suka nuna alamun rashin barci. Wata Ramlat wadda hostel d’insu d’aya kuma k’awar Zainab ce k’ut da k’ut tace
“Tab! Yanzu girman kai zai k’aru, su o’o ba’a da had’add’en saurayi ma ana kallon mutane a kan hanci, ballantana yanzu anyi..”
D’agowa Zainab tayi ta kalleta a take tayi shiru bata k’ara cewa uffanba. Abinda ya bawa Maryam mamaki shine har suka koma hostel, aka yi lesson na evening, suka sake fitowa night prep kwata kwata Zainab bata ce mata uffan akan maganar ba. Sai dai kawai ta ga tanata yawan kallonta.
Straight jss2 ta nufa tana shiga ta gansa a zaune a gefen sit d’inta kamar ko yaushe.
Yana jin shigowa ya d’ago kai ya kafeta da ido har ta k’araso ta zauna ta gaidashi. A hankali ya amsa sannan yace “Ya hannun??”
Itama a hankali tace “ da sauk’i.” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e jakarta domin da d’auko littafi ta samu ta fara karatu.
Littattafan d’azu ya mik’o mata yace “gashi, gobe sai ki bata nata ko?!”
D’agowa ta yi ta kalleshi sannan ta d’auka littafin ta bud’a da niyyar ta d’an k’ok’arta ta kwafa, saboda Yarinyar har ta fara mata maganar littafinta wai ‘tanaso za tai karatu’, amma kawai sai ta ga wani had’add’en rubutu ya baiyyana daga dai dai inda suka tsaya, dubawa tayi tai comparing da na k’awar tata taga Note d’in nata ya zama complete, kallonshi tayi taga shima Itan yake kallo da murmushi a kan fuskarshi kafin yace “Ko ban iya rubutu ba?”.
Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba saboda yadda yayi maganar yana wani langab’ar da kansa, kuma harga Allah tayi mugun jin dad’in taya ta d’in da yayi dan bata san ya za tayi ba, bata da wanda zata rok’a ya tayata dan kusan kaff y’an class da room d’insu daga safe zuwa yanzu kamar haushin ta duk suke ji wanda ita bata san dalilin su na Jin haushin nata ba.
Ganin tana murmushi kawai ya tsaya yana ta kallon ta dan ji yake kamar kar ta daina.
A hankali ganin ya kafe ta da ido tace “Ni ka daina kallo na.”
D’auke idanunsa yayi daga fuskanta yana murmushi….idanunsa suka kai
kan hannun rigarta, dayake da d’an jini jini a jiki tun na jiya, har zai tambayeta dalilin da ya sanya bata wankeba sai ya tuna da hannunta, kuma a yadda take da shiru shiru d’innan ya san ba zata iya saka Junior wanki ba.
Dan haka kawai sai yace mata
“Ki dinga kawo kayan wankin ki zan na kai miki wajen wanki har zuwa lokacin da zaki warke .”
Murmushi kawai tayi tace mishi “to”
Sannna yace duk note d’in da bata yi ba ta kawo, da kyar ta bashi na physics, ragowar kuma tace “za ta k’ok’arta da hannun hagu.”
Har aka tashi suna hira yau kam ta sake dashi, hakan kuwa yayi mishi dad’i sosai.
Washegari kam da bata zo da wankin nata ba taga b’acin ransa matuk’a, dan kicin kicin yayi, kuma ko da aka tashi da kyar ya yarda ta tafi bayan ya sanya ta ta rantse akan washegari za ta kawo.”
Hakan kuwa akayi, washegari ta saka a leda ta sako a skul bag d’inta ta kawo mishi.
Ko da yaje gida akwai washing machine, ga dry cleaning a arean da wajen wanki dai kala kala, amman haka Abba ya zage ya tik’i wankin nan nata da hannunshi, abinda bai tab’a yiba kenan tun tasowarshi, cook d’insa kam da mai yi masa gyaran gida tsayawa suka yi suna kallon ikon Allah, dan babu yadda basu yi da shi ba akan ya kawo su wanke ba amma sam ya k’i.
A wajen ya zauna ya jira ya bushe, ya kwashe ya tafi d’aki ya goge mata, yana yi yana murmushi……
Hakanan ya mayar da abun aikin sa….note da wanki shi zai yi mata ko jinkiri ta d’an yi wajen kawowa ya dinga mita kenan yana fushi, hannun nata ya warke amman kwata kwata ya hanata wanki k’arfi da yaji.
Zuwa yanzu shak’uwa sosai ta shiga tsakaninsu, bak’in jini kuwa a wajen y’an class da hostel d’inta ta kwasheshi ba ‘a magana, dan zuwa yanzu kowa ya sani saboda indai ya shigo aji har ya fita hankalinshi gaba d’aya yana a kanta suna had’a ido kuwa zai sakar mata murmushi ba ruwanshi da inda suke.
Ganin da yayi shak’uwa da sabo ya shiga tsakaninsu ya yanke shawarar fad’a mata shifa sonta yake yi, dukda ya San zuwa yanzu ta fahimci hakan, amman dai gara ya fad’a mata baki da baki.
Dan haka ya yanke shawarar sai ranar da za a tafi hutu tukunnan zai gaya mata daganan ya karb’i land line d’insu (idan suna da shi) ta yadda za su dinga communicating.
Ranar hutun kuwa!
Sunyi ita da shi a kan za su had’u 11, amma sai aka yi rashin sa’a ana bud’e gate motar gidansu ce ta fara shigowa, abunda bai tab’a faruwa ba….suna hostel ma lokacin suna shirya wasu kayyayakin su metron ta zo ta kira su, a gurguje suka k’arasa shiryawa suka yiwa ragowan mates d’insu sallama…
Kamar kullum Madu da ya Usman ne suka zo d’aukar su kasancewar shi Ya Jamilu ba mazauni bane ba, kafin yayi wayo yake nacin zama soja shiyasa tun yana k’arami su Madu suka mik’a sa nda....
Tana isowa bakin Admin ta hango Ya Usman wanda tun fitowarta shi alredy ya riga ya ganta ya kafeta da ido yana tsaye da Madu a gefensa, tana k’arasawa ta fad’a jikin Madu ta rungume sa, sannan ta juyo ta gaida Ya Usman, itama Zainab hugging Madun nasu tayi sannan ta yi huggin Ya Usman shima wanda yake ce
musu “suyi sauri su shiga su kama hanya…..”
Sai da suka shiga motar tukunna suke ji, ashe ‘Madu da Shuwa da Ya Usman ne za su tafi Hajji, jirginsu 7 na dare zai tashi yau shiyasa aka zo d’aukar su da wuri dan a samu a kintsa komai a kan lokaci’…ai kuwa nan suka hau murna.
Usman shi yake driving amman har kusan zubar da su yayi a hanya tsabar yadda gaba d’aya hanakalinsa ya tafi kan Maryam wadda ta fara gajiya da kallo da murmushin da yake da zuba mata ta glass d’in saman motar tun tasowarsu.
A haka suka iso gida, ita Maryam gaba d’aya zuciyarta a cunkushe take saboda rashin yin sallama da Abba, shi kuma Usman mamakin girma da kyan da Maryam d’in ta k’ara yake yi…..dan haka yana shiga gida bayan an d’an yi oyoyo
ya samu Baaba Talatu da maganar
“shifa gaskiya ya kamata a fara maganar auren su shi da Maryam”
Har sai da Baaba Talatu ta fara yi masa tsiya tana cewa “shi, ko irin y’ar kunyar nan baya ji??”, tukunnan ta samu ya kyaleta ya tashi ya fita yana murmushi.
K’arfe 5:30 kuwa, da Baba Bashir da Ya Jamilu da Maryam da Zainab da Bilkisu wadda take kuka sai ta bi Shuwa, suka rankaya suka yi musu ranki ya zuwa Airport. Sai da suka zo rabuwa tukunna itama Maryam taji kwalla na shirin zubo mata, dan haka ta yi saurin barin wajen.
Suna komawa gida, Baaba Talatu ta saka Maryam ta k’arasa had’a kayanta da na Bilkisu, daman Shuwa ta kusa gama had’awa, kafin su tafi.
Suna gamawa kuwa aka rufe gidan suka dawo gidan Baba Bashir.
Sai yanzu Maryam ta gano tabbas son Abba take yi…ta yi mugun dana sanin rashin yi mishi kwatancen gidansu da tayi, babu yadda bai yi da itaba amman ta k’i.
Duk da cewa bai tab’a gaya mata ba ta san shima yana sonta…a haka da kyar a daddafe take gurgura hutun Allah Allah kawai take yi a koma….
A b’angaren Abba kuwa kusan d’an k’aramin hauka ya yi….ya je gandun albasa sau babu adadi, yana tambayar gidansu Maryam Muhammad amman bai samu ba (kasancewar Maryam d’in a file dinta ne kawai take amfani da Madu).
A haka aka kusan gama hutun yanata faman zirga zirga…daga k’arshe kawai rashin lafiya ta rufesa, sai da yayi doguwar jinya tukunna ya samu kanshi, yana ta Allah Allah a koma makaranta, dan duk tsawon rayuwarshi bai tab’a ganin hutun da aka yi yayi masa masifar tsaho kamar wannan ba.
Haka akayi Sallah lafiya, a tsakanin Zainab da Maryam in dai sun yi magana tou a gaban mutane ne, sanin yadda Maryam take son Bilkisu ne ya sanya haka kurum idan Zainab ta lura ba kowa a wajen sai ita da Maryam kawai sai ta hau dukan Bilkisu, haka kurum ba abinda ta yi mata duk dan kawai ta bak’antawa Maryam rai, itakam Maryam sai dai taje ta janye Bilkisu uffan ba zata ce da itaba, domin itakam yanzu sha’anin Zainba ba ya d’ad’ata da k’asa.
Yau tun safe a gidan Baba Bashir aketa shirye shirye, dan sun yi waya da su Shuwa yau za su taso tun asuba amman har wajen d’ayan dare shiru.
Washegari ma shiru, wata washegarin ma haka!
A haka har aka shafe sati d’aya da kwana biyar...
Zuwa wannan lokacin y’an unguwa kowa hankalinshi ya tashi Baba Bashir kam shi da Jamilu shiryawa suka yi suka nufi Abuja.
Baaba Talatu kuwa sau uku ana mata k’arin ruwa, idan ka ga Maryam Zainab da Bilkisu sai baka tausayi, basu da aiki sai kuka, yau kam har da Baaba Talatu aka zauna ana shan kuka…Baaba Laraba wadda ta shigo ita da Sadiya ba da jimawa ba ne suke ta basu baki, duka kuwa itama Sadiyar kukan take yi.
Abun yayi musu yawa gashi Babba Bashir da Ya Jamilu ma da suka je Abuja yau kwanan su hud’u suma basu dawo ba, ko ta landline ba su kira ba.
Suna cikin kuka kawai suka ji ana bud’e gate, da sauri da sauri suka hau rige rigen fitowa tsakar gidan, suna isowa suka ga motar Baba Bashir.
K’arasawa suka yi bakin motar da sauri, ta cikin glass d’in suka hango su Shuwa, ai kuwa da kyar suka iya barin su suka samu suka fito dan duk sun rufe motar anata kukan