So da Buri 3
Chapter 13 of 36
hango su ya taso,
duk da halinda yake ciki hakan bai hanashi k’arasawa yayi welcoming Arshaad warmly ba.
Aslam ne ya katse su ta hanyar cewa
“Mai ya faru ne?
You sound worried!
Yanzun ma kuma you look worried”
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Tana Ina please?
Bani da energy…..”
Gaba kawai Aslam d’in yayi
shi kuma ya bishi a baya.
Suna zuwa k’ofar d’akin nasu ya murza ya shiga Auwal d’in kuma ya tsaya a waje.
A zaune ya sameta, ta rafka uban tagumi…sanye cikin doguwar rigar da ta fitar d’azun zata saka.
A rayuwarshi blue is one of his favorite colours, gashi blue d’in mai d’an duhu wanda ya taimaka wajen fito da ainahin kyawun farar fatarta..Yanayin dim light d’in dake kunne a d’akin ne ya taimakawa stones d’in jikin rigar tata wajen yin kyalkyali na musamman mai d’aukar ido da hankali…
Normal d’aurin d’ankwali tayi irin na ture ka ga tsiya
wanda ya fitar da uban tulin gashinta da ta tufke ta nannad’eshi a k’eyarta.
Ba komai a fuskarta ko mai bata shafa ba amman kalar kyan da tayi masa yau dole ya bada tukuici!.
A hankali k’asa k’asa yadda ta tabbatar ba zai ji ba tace
“Ni fa bana son kallo”
Tana mai d’auke kanta daga gareshi had’i da d’an turo baki.
Murmushi kawai yayi sannan ya tako gabanta ya tsaya yace
“Saboda me yasa bakya son kallon?”
Runtse idanuwanta tayi, a ranta tace
“Wannan ko maciji albarka”
Batai auni ba taji yasa hannunshi a nata ya mik’ar da ita tsaye yana kallon rigar jikinta kafin ya maida idanunsa a kan d’ankwalin, murmushi yayi yace
“D’aurin masifaffu dama yafi yiwa masu tsiwa kyau.”
Haka kawai sai ta tsinci kanta da kasa d’agowa da kuma kasa cewa komai, still bata san daliliba amman maganar tasa ba k’aramin dad’i tayi mata ba!
A take taji haushin shi da fushin da take yi da shi suna d’an raguwa…
Ya jima yana kallonta kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace
“Ki je Auwal yana parlour yana jiranki, muryarsa har rawa take yi, da alama emergency ne.”
Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya dan ta san me ya kawo shi.
Sai da ya sake cewa
“Ki je”
Tukunna ta iya jan k’afafuwanta ta d’anyi baya kad’an ta yadda ta tabbatar ba zata gogeshi in ta zo wucewa ba sannan ta wuce.
Har ta kusan k’ofa taji yace “ungo”
Tana juyowa ta ganshi a kusa da ita yana bata hijab d’inta.
Tsayawa tayi bata matso ba balle yayi tunanin zata saka…
A hankali ya matsa inda take yana kallonta itan ma shi take kallokafin ta yi k’asa da kanta kamar d’azu.
Yanayin yadda ta yi d’aurin tabbas in ya saka mata a haka zai iya shak’eta shiyasa yasa hannu ya zare d’ankwalin ya rik’e a hannunsa
So yake ya saka mata hijabin amman kyau da shek’in da gashin yayi da kuma yanayin parking d’in da tayi ne ya yi mugun tafiya da imaninshi dan haka ya tsaya ya shagalta da kallo….
A hankali yaji tace
“Bara in je, ka ce ce emergency ne”
Ba tare da ta d’ago kanta ba.
Wata nannauyar ajiyar zuciya taji ya sauk’e kafin a hankali ya ware hijabin kamar baya so..sai da ya nemo fuskar hijab d’in tukunna ya ajjiye d’an kwalin nata a gefe ya sa hannuwanshi duka biyu ya bud’a ya kawo dede setin fuskarta yace
“Raise your face”
Tana d’agowa suka had’a ido yana kallonta itan ma shi take kallo ta cikin hijabin.
A hankali ya matsar da hijabin yasa mata a fuska sannan ya d’an jashi ya zauna dede kafin ya ida warewa ya sakar mata shi ya rufe ilahirin jikinta.
Tana shirin wucewa taji yayi cupping fuskarta yad’an matso kusa da ita.
A zabure ta d’ago tana kallonshi shima ita d’in yake kallo kafin ya lumshe idanunsa a hankali ya kai lips d’insa dede goshinta ya sakar mata light peck d’in da ya sanya ilahirin jikinta d’aukar rawa!
A hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya matsar da bakinsa a dede setin kunnenta yace
“You look beautiful tonight”
Yana gama fad’in haka ya cikata ya wuce toilet
dan yana buk’atar yad’an watsa ruwa kafin lokacin dinner, garin yau akwai zafi
sannan shi kanshi kwana biyun nan yana saurin jin zafin yanayin dauriyace kawai yake yi.
Da kyar ta samu k’irjinta ya d’an ragu da bugawa
sannan ta d’an dedeta kanta ta fita wajen Auwal.
Tare ta tadda su a parlourn shi da Arshaad.
Gaba d’aya sai ta tsinci kanta da diriricewa kamar mara gaskiya, ta tsaya.
Tun sanda ta fito
Arshaad ya ganta, ganin duk ta rikice ta kasa k’arasowa ne yasa yace
“ko In baku guri ne?”
Ya fad’i hakan da d’an k’arfi ta yadda ya san za ta jiyo sa.
Da sauri ta d’ago ta kalli inda suke, suna had’a ido ya sakar mata lallausan murmushi sannan ya sake maimaita tambayar tasa.
A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta fara takawa ta isa inda suke ba tare da ta sake yarda sun had’a ido da Arshaad d’in ba.
Murmushi kawai yayi ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga daddanawa….,
Tana zama Auwal ya juyo gaba d’ayanshi gareta ko gaisawa bai iya tsayawa sun yi ba yace
“Dan Allah da gaske gobe za a kawo kud’in auren Sakina?”
Ba k’aramin tausayi ya bata ba dan har wata kwalla taga ta taru a idanuwanshi..
A hankali tace
“Ya Auwal duk abunda kaga Allah bai yi ba muddin ka yi addu’a to ba alkhairi bane, ka kwantar da hankalinka zaka samu wadda ta fita in sha Allah.”
Cikin katseta yace
“Da gaske ne kenan”
A hankali muryarshi na d’an rawa.
D’agowa tayi da niyyar sake bashi hak’urin ya rungumi k’addara
kawai
taga hawaye bibbiyu suna zubo masa!
Da sauri ta runtse idonta tace
“Ya Auwal dan Allah ka daina mana, ka rungumi k’addara kayi adduar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi”
Bud’e baki yayi da niyyar yin magana sai kuma ya kasa,
da sauri ya tashi ya fita a side d’in gaba d’aya ba
tare da ya sake waiwayon su ba.
Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali tana jin tsananin tausayin Auwal a ranta.
Kamar ance ta d’ago, tana d’agowa suka had’a ido da Arshaad, murmushi
ya sake sakar mata
kafin yace
“Abun tausayi, ko?”
Sunkuyar da kanta tayi
a hankali ta d’aga kan alamar
“Eh”
Yana shirin yin magana Ummi ta sauk’o! Har ga Allah haka kurum sai ta tsinci kanta da rashin jin dad’in ganinsu a zaune su biyu.
Tana zuwa ta nemi guri ta zauna kusada Huda ta kamo hannunta k’asa k’asa tace
“Huda tunda ba ku kad’ai bane a gidan, ku dinga saka key a k’ofar ku mana.
Wallahi ban san ta ina zan fara kallon Aslam ba”
Da sauri Huda ta sunkuyar da kanta k’asa sosai
wanda hakan har sai da ya sanya Ummi ta d’anyi murmushi.
Sarai Arshaad ya ji abunda suka ce amman bai nuna musu ba! Hasalima chatting d’insa kawai yake yi yana murmushi.
Ganin hirar tata ba zata yiu da Hudan ba yasa ta juyo ga Arshaad tace
“Ka je wajen Mammy?”
Sai da yad’an k’ura mata ido, kamar ma bai ji abinda tace ba
tukunna yad’an gyara zaman shi ya maida wayar aljihu kafin yace
“A’a,
direct daga airport nan nayo”
A hankali tace
“Bata da lafiya”
Bata ida rufe bakinta ba yace
“I know!”
Ta lura da yadda yanayinsa ya chanja amman hakan ba zai hanata yi masa nuni da gaskiya ba dan
haka tace
“Arshaad no matter what, ko me tayi maka
Mahaifiyarta ce!
She’s sick!
Very sick!
She needs you!
Aiima bata nan ita kad’aice.
Ajiyar zuciya ya sauk’e yana kallon Ummin ido cikin ido yace
“Abba baya nan ne?”
“Eh, yayi tafiya
shi da Daddy
business trip
sannan za su bud’e
branch d’in construction company d’insu shi da Aslam a UK sun ma bud’e
It was successful sannan trip din nasu was also successful
shiyasa jibi za mu yi double celebration in sha Allah.”
Ummin ta zayyano mishi
dan so take su yi magana kar
ya samu question d’in da zai sake jifanta da shi as an excuse.
“Ma sha Allah
Allah ya k’ara d’aukaka”
Yace, daga nan ya mik’e.
Itan ma mik’ewa tayi
tace “We are not done”
Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e kafin ya kalleta yace
“Ummi ko In koma inda na fito ne?
Although i came for Shuraim and Sudais but it’s like bakya murna da ganina!”
Da sauri tace
“Arshaad ba haka ba...”
Cikin katseta da d’an b’acin rai yace
“To na rok’eki da girman Allah ki daina yi min maganar Mammy
Ummi kina so inje In zauna Ina ganin suna fad’a kullum ita da Dad ko yaya?”
Tausayin sa ne ya fara rufeta dan haka ta k’arasa inda yake ta kamo hannunshi ta rik’e a nata tace
“Ba haka bane son, ka
fahimceni”
Kamar zai yi kuka yace
“Me kike so inyi yanzu?”
Har ta bud’e baki za tayi magana sai kuma tace
“Ba komai,
nothing”
A hankali ya zame hannunsa a cikin nata ya juya ya shige dakinsa.
Ta d’an jima a tsaye
kafin ta sauk’e ajiyar zuciya ta juya ta nufi kitchen ta fara setting dining table.
A hankali itama Huda ta mik’e ta k’arasa ta shiga tayata.
Sai da suka gama tukunna Huda ta wuce d’aki, ita kuma
Ummi ta zauna anan kan dining d’in ta rafka tagumi.
A gaban dressing mirrow ta sameshi yana taje gashinsa..
Sanye cikin pyjams dark ash da suka yi mishi kyau matuk’a!.
A hankali ta k’arasa bakin gado ta zauna ta d’auki wayarta da ta mak’ala a charge ta danna kiran Sakina
Bayan ta zare wayar a charging.
Tana d’auka tace
“Yanzu Ya Auwal ya tafi”
“Um”
Kawai Sakinar tace, a hankali.
Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace
“Yayi matuk’ar bani tausayi, har da kuka fa yayi.
Da kin sani baki gaya mishi yanzu ba”
Shiruu, ta ji Sakinar tayi
kafin chan tace
“Ya dameni da kira da massages!
At least yanzu zan huta
sannan i don’t want him to have any false hope.”
Cikin son kawo k’arshen maganar Auwal d’in tace
“Za ki zo goben?”
Sai da ta kalli Aslam wanda yanzun yake zaune akan sofa yana k’ok’arin kunna computer tukunna tace
“Ya hanani”
Da d’an k’arfi ta yadda ta san zai ji.
“Ki lallab’ashi”
Shine kawai abunda Sakinar tace.
Har zata kashe wayar sai kuma tace
“Jiya su Shuraim ma sun biyo nan daga school, sun
kawo mana invitation d’in birthday d’insu
Su Mama dai ba zasu zo ba
amman ni da Sumayya za mu zo goben
In sha Allah.”
Cike da murna Huda tace “Allah ya kaimu da rai da lafiya.
Ku zo da sassafe dan Allah ayi shirye shiryen komai da ku”
Murmushi kawai Sakina tayi tace
“Ai inaga 3 hours ma kawai za mu yi, za mu zo 2 mu tafi 5 haka, ba lalle ma mu samu event d’inba kawai dai za mu zo ne
dan
naga sai wajen 10 ma tukunna za a fara, so kawai za mu d’an lek’o.”
Da sauri Huda tace
“To ku kwana mana”
Dariya Sakina tayi tace
“Bara in yi sallah. Sai anjima”
Dan so take ta kashe wayar sakamokon kanta da yake mata tsananin ciwo da kuma rud’anin da zuciyarta take ciki!
Dauriya ce kawai take yi
da har aka samu take iya yin magana.
“Okay, ki gaida Ummu da Sumayya”
Hudan tace
daga nan suka katse kiran.
Ita bata ma san Aslam ya fita ba sai da ta d’ago tukun taga ba ya nan
“Hmm, mutum sai basirar iya san’da kamar munafuki”
Ta fad’a a ranta.
Tana mik’ewa tayi haramar kimtsawa domin ta gabatar da tata sallar dan taji an shiga masallaci.
Tana idarwa ta fita da sauri ta d’ebo abinci a plate ta d’auko ruwa ta shigo har da d’an gudu dan taji kamar mutum zai fito a kitchen.
Da wuri tayi ta cinye ta sha ruwa ta yi brush, ko plate d’in bata d’auke ba ta kwanta ta k’udundune a cikin bargo!
Ala dole Ita tayi barci kenan saboda gudun kar ma wani ya shigo yace ‘taje tayi dinner’
Saboda ita har ga Allah kunyar had’uwa da Arshaad take yi
after what he saw daga zuwanshi gidan
bata jin zata iya sakewar had’a ido dashi balle zama waje d’aya.
Kusan kamar 40 minutes wayarta ta fara k’ara!
Dan haka ta tashi ta d’auka, tana ganin sunan Abba ta d’auka da wuri cike da zumud’i
tace “Abba,
Ina wuni,
kun taho ko?”
Murmushi yayi yace
“A’a tukunna, yanzu dai muke shirin isa airport.
Gobe around 7:00am in sha Allah za mu k’araso saboda muna da transit”
“Okay, Allah ya kawoku lafiya”
Murmushi yayi yace “Ameen princess, Ina Aslam?”
Sai da ta d’anyi shiruu, tukunna tace
“Yana waje, suna dinner”
Da sauri yace “ke fa?”
A hankali tace “yanzu na gama a d’aki”
Zai yi magana ya ji tace
“Ya Arshaad ma ya dawo.”
Shiruuuu, taji Abban yayi
kafin yace
“Okay,
sai mun k’araso goben in sha Allah”
A hankali tace
“Safe fligh Abba”
Murmushi yayi yace
“Thank you princess”
Daga nan suka katse wayar,
tana shirin ajjiyewa
Aslam ya shigo!
Hannunsa rik’e da plate a
da ruwa. Ta ji shigowar tasa amman bata d’ago ba, har ya tako ya zo inda take ya zauna a gefen gadon kusa da ita.
Sai a sannan ta d’ago tana kallonsa da plate dinsa..
a ranta tace “shima a nan zai ci abincin yau ko me?”
A hankali taji yace
“Kin ci abinci kena?”
D’agowa tayi tana kallonshi
taga yana kallon plate d’in gefenta wanda ta ajjiye akan side drawer.
A hankali ta d’aga masa kai alamar ‘eh’.
Shiruuu, suka yi chan taji yace
“Ya za muyi da wannan??”
D’agowa tayi taga shima itan yake kallo!
Da sauri ta sunkuyar da kai dan yau wani kalar kallo taga yana yi mata wanda ya sanya kwata kwata bata son had’a ido da shi.
Shirun ne ya sake biyowa baya
kafin ta ji ya bud’e plate d’in da ya rufa a kan na abincin ya fara tab’a spoon d’in….
Bata gama tunanin me yake yi ba taji yace
“Haa”
Tana juyowa taga ya d’ebo fride rice d’in wadda taji hanta
ya kawo kusa da fuskarta.
Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta kawar da kai tace
“Na k’oshi”
Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya d’an matse a cikin nasa a hankali ya sake cewa
“Haa”
Yana sake matso da cokalin.
“Ya subahanallah!
Wannan wanne irin mutum ne?”
Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta.
Ji tayi ya murza tafin hannunta da nashi hannun still a hankali taji ya sake cewa
“Haa”
Da sauri ta juyo ta bud’e bakin ta lumshe idanunta numfashinta na fita da sauri sauri.
Murmushi yayi ya saka mata cokalin a baki ita kuma ta karb’a ya juye mata
tukunna ya zare.
A hankali ta shiga taunawa,
har yanzu idanuwanta a lumshe suke.
Kamar wanda ya samu tv haka ya nutsa ya maida hankalinsa wajen k’arewa kyakkyawar fuskarta kallo.
Sai da ya ga ta had’iye tukunna ya mayar da cokalin ya fara k’ok’arin d’ebo wani,
da sauri ta d’aura hannunta a kan nasa ba tare
da tayi laakari ba, tace
“Nafa ci abinci
Mai yawa.
Please Ya Aslam kar in yi amai”
Sannan ta fara k’ok’arin bud’e kyawawan idanuwanta da suka taru da kwallah.
Tana gama bud’ewa taga ya ajjiye spoon d’in ya na k’ok’arin bud’e robar ruwa…
Ba yadda ta iya haka ta yarda ya bata a baki ta sha tukunna
ya mik’e ya d’auke plate d’in da ta ajjiye a kan side drawer ya had’a da wanda ya shigo da su ya fitar.
A yadda ya fita ya barta a haka ya dawo ya sameta, bai kalletaba bai ce mata komai ba ya nemi waje ya zauna ya ci gaba da aikin da yake yi d’azun kafin ya fita sallah.
Ya d’an jima yana aikin, kafin yaga ta taso ta k’araso ta zo inda yake. A hankali ta zauna a gefensa tace
“Ya Aslam”
“Um, Anty Huda”
Ya ce ba tare da ya kalleta ba, yana mai ci gaba da typing d’in da yake yi.
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “zan je dan Allah,
goben.”
“No”
Yace, still bai kalleta.
Turo baki tayi kafin tace
“Na dawo fa d’akin”
This time around dariya yayi
kafin ya rufe computer gaba d’aya sannan ya juyo gareta yace
“Ki yi hak’uri, baza ki je ba.”
Kamar da wasa kawai sai yaga ta fashe ta kuka!
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya matso ya kama hannunta yace
“Mama ce tace kar a barki ki sake fita sai nan da wata d’aya. Idan kina son fita ki kira Hajiya Shuwa idan ta barki sai ki je.”
Da mamamki take kallonsa tana rage sauti da yawan kukan nata. Jinjina mata kai yayi alamar tabbatarwa.
A hankali ta shiga share hawayenta tana sauk’e ajiyar zuciya a hankali.
“Yanzu zaki kuma yin wani yajin kenan?
Tunda dai kinga ba damar fita gobe
Ba ni zan barki ba Hajiya da Mama ne”
A hankali ta girgiza kanta tace
“Ka yi hak’uri, a kan
abinda nayi”
Murmushi yayi yace
“Ai kuwa na hak’ura!
Tunda har kwalliya da turaren wuta aka saka duk dan saboda ni. Ko ba dan ni akayi ba??”
Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kanta k’asa.
A hankali yana kallonta kafin yace
“Je ki kwanta.
Gobe tashin asuba ne, ko?”
Ba tare da ta d’ago ba tace
“Kaje ka kwanta kai,
ni a nan zan kwana.
Da bananan ai a gadon kake kwana.”
Sai da yad’an k’ura mata ido tukunna yace
“A nan d’in nake kwana..
Har gyara miki gadon nake yi kullum thinking you will come back
A haka bacci yake d’ibana kullum.”
Shiruuu suka yi duk su biyun kafin yaji tace
“Ka fini tsayi,
ina gani kullum kujerar bata isar ka, ka je ka kwanta don’t be stubborn”
Dariya taji yayi
kafin yace
“In da acting stubborn nake miki yanzu ai da na san tuni kin fita a d’akin nan da gudu”
Bata fahimci kan zancen nashi