So da Buri 3

Chapter 33 of 36

take jinsu a cikin ranta haka nan suma suke jinta
suke kuma tsananin girmamata...

Tsakaninta ita da Abba kam tabbas Mama zata iya cewa tana cikin mata first class a sa’ar miji a duniya, ko kuma ma ta ce ita kam ta fi kowa sa’ar Miji a duniya…...Tsantsar zallar k’auna da kulawa had’e da tattali yake bata
baya duba shekarunsu
sam dan shi
idan ya tashi gwada mata soyayya kamar wasu teenagers haka yake ganinsu shi da ita........


A b’angaren Mommy itama bata bawa Aaima reason d’in da zatayi missing Mammy ba,
kulawa da shak’uwa ce a tsakaninsu ta musamman
dan ita Mommy ce mata ta yi ta d’auketa a matsayin best friend d’inta.........
........
Kamar kullum yadda suka saba yau ma Sakina ta kirata suka shiga hirarsu gwanin ban sha’awa duk da kuwa Sakinar ba wani dad’i take ji ba saboda murar da take ta faman mata on and off!
Ta rasa sukuni gaba d’aya sanyin garin ya isheta.

Jin yanayinta da muryarta
da kuma rashin lafiyar da take ta yi kwana biyu
ya sanya Hudan ta ce
“Maman baby je ki kwanta ki huta
Allah ya sauwake.”
Ta k’arashe maganar da d’an dariya k’asa k’asa sannan tana addu’ar Allah yasa harsashenta akan Sakinar ya zamo gaskiya ne.

“Ok na gode
sai da safe” Sakinan ta ce..Ba ta kashe wayar ba
ta d’an yi shiruu kamar mai tunani sai kuma ta kwashe da dariya kafin ta ce
“Ai ni sai yanzu ma na fahimceki!
Tab! Inaaa ba wannan tukunna
wallahi iyaka mura ce kawai take damu na.”

Cikin rashin fahimta Huda ta ce “Ba kince an sallameku ba?”

Dariya Sakina ta yi ta ce “to
kuma daga an sallamemu sai me?”
Bata jira amsar ta ba tana dariya ta ce
“Eh, an sallamemu
dan jikin nashi ya yi kyau
amman muna lek’awa, kullum,
check up”.

Shiruuu, Huda ta yi kafin ta ce
“Anya kuwa Sakina?”

Sai da Sakina ta yi dariya sosai tukunna ta ce mata
“Allah da gaske,
babu komai ma fa tsakaninmu har yanzu
sai dai hira kawai da tsantsar kulawa da soyayyyar da yake gwada min.

Da sauri Hudan ta ce
“Kai!”

Cikin murmushi Sakina ta ce
“Kin san Allah nima kaina ina mamakin shi, ba daban ina fahimtar yanayin sa ba
tou da sai in iya cewa ma bashi da lafiya…Ban san dalilinsa ba kinga ni kuwa ai bazan ce gani ba!
Besides ni nama fi son haka.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin ta ce
“Kuma bai chanja miki ba? As in ba ya wani fushi da ke”

“Ko d’aya, wallahi
kulawar ma da yake bani ni kaina banyi tunanin ta ba
kawai dai maybe shi tsarinshine haka ko kuma dai wani abun
besides ai bamu fa wani dad’e ba so it’s not an issue.”

“Shikenan tou, ki gaidashi”
Shine abunda Huda ta ce. Daga nan suka yi sallama suka kashe wayar.

Murmushi kawai ta yi tana duba wayar, a hankali ta sauk’e ajiyar zuciya
ta shiga tunani
....Kullum tare suke kwana, a jikinsa take yin bacci, tana jin yanayin bugun zuciyarshi da yadda yanayinsa yake alamun lafiyarsa k’alau kuma a k’age yake amman in banda hug ba abunda ya tab’a shiga tsakaninsu……

Sam bata san ya shigo d’akin ba dan yaje siyo musu milkshake a chan k’asan hotel d’in da akeyi wani mai dad’i!
Sai da ta ji ya kwanta a bayanta tukunna ta yunk’ura da sauri tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa
“Sakina I love you fisabilillah
Ba wai wani abu daban ba!
Shiyasa kika ga ban yi yunk’urin komai ba saboda
Ina so ne har sai kin fahimci hakan, kin yarda dani, kin saki jiki dani tukunna.
Na san zan takura amman yadda nake jin ki a raina
tsaf zan iya rayuwa dake a haka muddin baki gama fahimtar kalar k’aunar da nake yi miki ba……..”

A hankali ta juyo sosai tana kallonshi suka yi facing juna a kwancen!
Kasa cewa komai ta yi kawai sai ta sunkuyar da kanta k’asa kafin chaan! Ta ce
“Ya Auwal na yarda da kai na yarda da chanjin da na gani a tattare da kai.
Tunda har kaga na aureka tou yarda da k’auna ce ta kawo hakan.
Sannan zan rayu da kai a ko wanne hali.…..”
Yadda ta ga yana kallonta ne ya sanya ta yi saurin b’oye fuskarta a k’irjin shi
dan tashi d’aya sai ta ji duk kunya ta lullub’eta.

Murmushi ya yi yad’an shafa kanta, a hankali ya yi kissing kan nata yana mai shak’ar k’amshin da yake fitarwa kafin ya shiga binta da wani mayen kallo k’irjinsa yana bugawa da masifar gudu….
Sannu a hankali yanayinsa yana k’arasa sauyawa ya sa hannu ya janyota ya saka ta a jikinsa sosai!.

Sai da numfashinta ya kusan d’aukewa sakamokon wasu sak’onnin da ya shiga aika mata waenda suka girmi hankali da wayonta.
Da sauri cike da tsoro da fargaba muryarta na rawa ta ce “Dan Allah!!!
Ni fa da nace haka bawai ina nufin yanzu ba.”

Ko sauraronta Auwal bashi da niyyar yi, dan tun kafin a je ko’ina notikan kansa suka kwance hankali ya fara barin gangar jikinsa…
Tabbas ya yarda kuma ya sake tabbatarwa ‘kamilalliyar mace daban ta ke! Sannan matar sunna sinadarinta na musamman ne’ Gashi kuma abun sai ya taru ya had’e masa da giyar zazzafan feelings da soyayyar da yake yi mata, shi yasa ya manta kowa ya manta komai hatta shi da karankansa ya manta kansa.

A ranar Huda ta sha Allah ya isa dan ita ce ta kirata a waya har ta janyo mata wannan jalalar.

Sam bata tab’a tunnanin zatayi rai ba
dan Mr Auwal sai da ya yi mata dalla dalla……..

Tun daga ranar kuwa ta rasa nutsuwa da sukuni. Daga nan ma Las Vegas suka wuce Honeey moon…
Auwal shi kad’ai yake k’ibarsa yana enjoyment d’inshi
Ita kam in banda rama ba abunda take yi
dan
kwata kwata ba enjoying garin take yi ba
dan ita gani take ma kamar su suke tunzurashi yin wasu abubuwan.........


Da kyar Aaiima ta iya samun Abba ta yi masa maganar Junaidu dan zuwa wannan lokacin kam soyayya mai k’arfin gaske ta k’ullu a tsakaninsu.

Abba ne ya samu su Dad ya yi musu bayani su kuma suka ce a tambayi su Mama indai har ba shi da wani mugun hali sai a shirya komai
dan
kasancewarsa d’a ga Usman hakan ba shi zai sanya su shiga tsakanin Aaima da farin cikin ta ba dan k’iri k’iri ta nuna shi take matuk’ar so!.
Sannan su a ganinsu yanzu Aaiman abar tausayi ce
duk da kuwa sun san idan suka ce rashin Mammy yana a cikin matsallolin Aaima ba su yiwa Mommy adalci ba
duba da yadda take iyakar k’arshen k’ok’arinta wajen ganin Aaiman bata rasa komaiba
amman kuma uwa dole daban take.
Dan haka za su yi k’ok’ari wajen ganin sun taimaka farin ciki ya wanzu a rayuwarta na dindindin......


Tabbas Mama ta ji dad’in wannan had’in
dan haka tashi d’aya
ta faiyyacewa Abba halayen Junaidu wanda tun tasowarta dashi bata tab’a ganin shi da wani mummunan hali ba
sai dai mai kyau
sannan yanada zuciyar nema da amana
ga sanin ya kamata…..

Abba ma ya ji dad’in jin haka
dan haka ya ce “bara ya je kawai ya samu su Dad ayi komai a gama. Kafin Aaiima ta tafi rubuta finals d’inta a saka rana, tana dawowa a d’aura aure in shaa Allah.”

A hankali Mama ta ce
“Amman fa Abba akwai wani abu guda d’aya!
Kasan case d’in Junaidu na zaman jail
wanda tunda ya je ya dawo ya kud’ance! Kud’i na ban mamaki….
Last week ma sai da aka sake gano Gidaje da kadarorinsa
dan shi b’oyewa yake yi..a iyaka Kano fa Gidajensa masu matuk’ar kyau da tsada sun fi ashirin
ga kadarori ga filaye
wanda bamu san source of income d’inshi ba!
Inda hali gaskiya a d’an yi mishi tambayoyi akan wannan lamari a bincika.
Naji dai kwanaki su Abba Madu sun ce sun yi mishi tambaya
amman banji sun ce ga amsar da ya bayar ba.”

Jinjina kai Abba ya yi daga nan ya ce ‘zai nemi zama da Junaidun ko zuwa gobene in shaa Allah, su tattauna.”



.....Har gida kuwa Junaidun ya zo ya sameshi bayan ya ce masa ‘ya zo yana son ganinsa’
Shi da Daddy ya tarar
dan haka ya gaidasu cikin girmamawa
suka amsa masa da kulawa.

Ba tare da b’oye b’oye ba Abba ya ce “sun san bashi da wani mummunan hali amman kuma suna buk’atar sanin kwakkwaran source of income d’inshi”

A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara basu labari....
“A lokacin da aka sallame ni daga prision…………
Mun fito mun kama hanya,
bamu kai ga zuwa inda za mu je ba cikina ya b’aci!
Dan haka na nemi alfarmar su tsaya in d’an yi uzuri.
Suna tsayawa na fita…
Ina kutsa kai cikin d’ajin kamar an ce in juyo nan na ga wasu maza da mask su uku sun nufi motar.
Duk sai da suka fito da y’an motar suka dubasu amman sam babu abunda suke nema wanda sai daga baya na gane waenda Arshaad ya tura ne
kuma ni suke nema.

Kamar na sani a lokacin sai na b’oye kaina. Bayan na b’oye kaina su kuma suka gama dube duben su suka tafi.

Su kuma Abokanan tafiyar tawa inaga tsorata suka yi dan ina shirin fitowa naga duk sun shige motar suna shirin tafiya.

Da sauri na yunk’ura zan tafi na ji an rik’e min k’afa!
Sai da gabana ya fad’i da na juya dan ni sam ban lura akwai tsoho ma a wajen ba a durkushe sai da ya rik’o nin.
Cikin kuka tsohon ya ce “bawan Allah ko baiwar Allah dan Allah taimakon musulunci zan mutu yunwa nake ji.”

Da sauri na ce “Baba dan Allah Abokanan tafiya ta za su tafi ka cikani In wuce.”

Cikin kuka tsohon ya ce “yunwa nake ji ka taimakeni dan Allah”

Haka nan inaji ina na gani na kama hannunshi ya mik’e su kuma Abokanayen tafiyar tawa suka wuce dan maybe sunga na dad’e su kuwa a tsorace suke.
Na ji takaici sosai
amman yadda tsohon nan yake karkawa da kuka yasa kawai na yanke shawarar In taimakeshi.

Sai da muka fara tafiya na fahimci ashe makaho ne!
Haka muka yi ta kutsawa dan hanyar ba jama’a sosai
har muka iske wata mai k’osai da kunu na siya da d’an kud’in da aka bani in yi na mota na bashi ya ci ya sha.
A hankali muna zaune a wajen ya ce “in bashi labarina”
Haka kurum ban sanshi ba amman na tsinci kaina da fad’a mishi komai na rayuwata
har kawo yanzu.

A hankali ya ce “kuma kana ganin ba kai ake nema ba kuwa!?.
Ka zo mu je Gidana ka d’an b’uya kafin kwana biyu sai ka wuce gudun kar ka je suna nan har yanzu ka fita a kamaka.”

Tsoro ya sanya ni na amincewa wannan tsohon, dan a yadda naga mutanen nan babu kalar imani a tattare da su.

Gidan nasa y’ar bukka ce
sai band’aki wanda aka yishi da langa langa a gefe
sai wani murhu da rijiya. Sam babu wani katanga ko wani abun da yake nuni da wajen keb’antacce ne.

Y’ar bukkartashi muka shiga muka zauna anan yake ce mini “Matarsa ta rasu watan da ya mutu,
Allah bai bashi d’a ba!
Danginsa kuma duk sun guje shi saboda basa son d’awainiya.”

Atake na ji tausayin bawan Allahn nan ya rufe ni, kuma a take muka saba shak’uwa ta shiga tsakaninmu…..
Kwana na biyu a wajensa,
na siya mishi abinci da d’an abun da ba a rasa ba duk a cikin kud’in da aka bani
a lissafina idan na tashi ni sai In d’auki drop har gidan Abokina ya biya.
Ban b’oyewa tsohon nan ba na ce masa “muma ba wasu masu arzik’i baneba, ba daban haka ba da na tafi da shi” dan na lura yana cikin kad’aici da buk’atar taimako “kuma akwai abubuwa da dama a kaina amman dai bara mugani in shaa Allah idan na koma gida na yi settling zan dawo in duba shi.
Dan nima a yanzu Ina matuk’ar buk’atar kud’i.”


Daga nan na nemo wata mata a gefe na rok’eta akan “dan Allah ta d’an dinga lek’ashi”
Ita kam Matar mamakima ta dinga yi dan a cewarta “duk zaman ta a k’auyen ita bata san da shi ba”.
Bayan Matar wuce ne muka yi sallama muna ji kamar kar mu rabu…
A bakin bukkar tashi Ina fitowa na ci karo da wani mutum cikin suite! Da akwati a hannunshi,
kamar yana cikin sauri, ya nuna min hotonshi da wannan tsohon kamar lokacin tun suna samari ya ce min “an ce yana nan! Da kyar da wuya ya samu location d’insa, dan Allah na san shi?”

Ba tare da b’ata lokaci ba na ce masa “eh”

Dan haka mutumin ya ce mini
“sun tab’a yin businesses da tsohon ne, tsohon ya aminta da shi amman shi sai
ya gudar masa da kud’insa
so tun daga lokacin abubuwa basu yi mishi kyau ba!
Shiyasa ya yanke shawarar dawo mishi da dukiyarsa.”
Ya d’aura da cewa
“Dan Allah in bashi in ce masa
ya ce sunanshi Kabir,
Alhaji Kabir.
Ya taimaka ya yafe masa”

Yana min maganar ne
shi duk a tunaninsa ma ni d’an tsohon ne.
Jin muryar tsohon ya fito yasa ya yi sauri ya yi min sallama a cewarsa ‘ba zai iya facing d’insa ba dan
kunyarshi yake ji.’

Duk da nace ya d’an tsaya ko ruwa ne ya sha
saboda naga inba magana ya yi ba tsohon ba zai gane shi ba dan ba gani yake yi ba, amma sam yak’i yarda, ya damk’a min akwatin yana d’an waiwayowa yana kallon tsohon har ya shige motarshi driver ya ja suka tafi.

Akwatin na ja na kai d’aki na fito na kama hannun tsohon muka shiga ciki na zauna.
Na zuge akwatin ba tare da na ce komai ba.

Sai da gabana ya yanke ya fad’i dan gabaki d’aya akwatin cike yake da mak’udan kud’ad’e dollars!

A hankali na ji tsohon ya ce
“Kai da waye d’azu a waje?”

Cikin In inaa na ce
“wani mutum ne ya zo neman ka! Ya ce kun tab’a yin buisiness kai da shi ya gudar maka da kud’i.”

Shirruuu tsohon nan ya yi kafin chaan! Ya yi murmushi ya ce
“na kasa tunawa”
Kafin ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya ce
“Akwai abunda ban gaya maka ba…
Inada sabara a kwakwalwata
shiyasa ma kaga wasu lokutan Ina zama ina yin kuka ni kad’ai.
Wani makwafcina anan ya d’auke ni satin baya ya kaini asibiti aka tabbatar da cewa ‘ba zan k’ara sati uku a duniya ba!’.”

A take wani tsananin tausayinshi ya lullub’e ni!
Ga dai kud’ad’e nan ya samu
bayan
ya sha wahalar rayuwa amman a lokacin da kud’ad’en suka riskeshi
sai ya zamana ba za su yi mishi amfanin komai ba.
Ban san lokacin da kuka ya kufce mini ba!.

Jin ina kuka yasa tshon ya hau tambayata “menene? Mai ya faru?
Me ye a cikin jakar? Ko wani abun tsoron na gani?”

Shiru na d’anyi kafin ince mishi
“Kud’i ne a ciki,
Dollars.”

Shiruuu na ji ya yi…
Ya jima tukunna ya ce
“Ka taimakeni ko masallatai ne in gina dan Allah.
Saboda kaga ni ba ido da lafiya gare ni ba.
Bana bukatar ka gina min gida ko wani abu daga kud’in tunda kaga ba lallae inga k’arshen aikin bama
kawai dai ka rik’e Allah ka tayani gyara lahirata ta hanyar gina masallatai da islamiyoyi a k’auyukan nan.”

A lokacin tabbas ina son komawa gida
amman kuma
wannan tsohon yana buk’atar taimakona a yanzu
sannan inaso a ida auren Huda da Arshaad kafin In koma dan tabbas na kasa cire ta a cikin zuciyata
kuma na riga na d’auki alk’awarin ba zan aureta ba!
Tunda na lura sam bana cikin zuciyarta tun ranar da ta ce min Arshaad zata aura
k’ok’ari kawai nake yi inga na fitar da ita a raina
saboda no matter how much I love her ba zan tab’a iya zama da ita idan bata ra’ayi na ba!
Amman kuma
bana buk’atar a aurar da ita a gaban Idona
sannan still ina jin fargabar fitowata
duba da sharrin da aka yi min
da kuma waenda nake tunanin ni suke nema..A ganina gara In d’an fahimci abubuwa daga b’oye kafin a kaini lahira
tun da ban san waye yake farautata ba!
Sannan aikin da zan yiwa wannan tsoho tabbas lada zan samu…
Shiyasa a take na yanke shawarar jifan tsuntsu biyu da dutse daya....

...Haka nan na tsaya tsayin daka wajen taimaka masa kamar yadda ya buk’ata aka shiga gina masallatai a duk k’auyukan da makarantun islamiyya
gini mai kyau da had’uwa, na ban mamaki.

Tabbas Ina da buk’atar kud’i
amman ban tab’a yunk’urin d’aukar ko naira biyar ba!
Apart from kud’in motar da yace In dinga d’auka a ciki dana abinci da shelter.

Akwai kud’i sannan na samu maaikata masu yawa sosai
dan ko wanne k’auye masu ginin daban suke
shiyasa kafin wata uku aka fara shirin kammalawa.

Ba abunda yafi sakani farin ciki irin yadda Allah ya arawa wannan tsohon tsawon rai har na tsawon lokacin da aka zo kammalawa duk da dai jikin nashi sai a hankali.

Ranar da na kammala aikin da
washegari ya tashi da tsananin ciwo wanda kana gani ka san sai a hankali kawai.
A wannan bukkar tashi muke har kawo wannan lokacin
amman fa muna cin mai kyau mu sha mai kyau.

Ina ganin yana yin jikin nashi na ce “bara inje In nemo mai abun hawa a kaishi asibiti cikin gaggawa”
Amman sai ya rik’eni ya rok’eni akan in tsaya akwai maganar da yake so ya yi da ni.

Abu na farko da ya fara tambayata shine sunana!
Duk tsawon lokutan nan Yaro yake kirana da shi ni kuma in kirashi da Baba.
Sai da mutanen last k’auyen da aka yiwa masallaci suka tambayeni ‘suna son
rubuta sunanshi’
Tukunna da

Download complete TXT · Novel page