Showing 162001 words to 165000 words out of 452169 words
Chapter 55 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
"Ki bude baki kiyi min magana don Allah, sakin ki Mamudan yayi wai??" Ganin Maheer ya shigo Parlon Hajja ta nufesa da sauri jiki na rawa tana nuna masa takardan tace "Maheer takardan meye wannan din?" Maheer yayi shiru yana kallonta da farko, can yace "Mayraah ce ta rubuta" Hajja tace "Mayraah kuma? Na meye to?" Maheer yace "Ta tafi" Hajja ta zaro ido tana kallonsa tace "Ta tafi? Ta tafi ina?" Maheer bai bata amsa ba ya juya ya fita daga parlon ya koma balcony ya tsaya, Hajja ta dawo da sauri tace "Ina wai Mayraahn ta tafi Ammi?" Cikin kuka Ammi tace "Allah ya gani ko 'ya yan cikina ban gwada masu son da nake ma Mayraah ba, ban taɓa mata kallon ba ni na haifeta ba tunda Allah ya bani ita, kallon jinina nake mata, soyayyar uwa da ɗan ta nayi mata....." Ta kasa ci gaba saboda kukan da ya ci karfin ta, Hajja ta zauna kan kujera ta rasa abun cewa, can ita ma ta fashe da kukan ta daga hannu sama tace "Allah mun gode maka, wannan wani irin fitina ne ke ta billo mana ni Sadeeyah daga wannan sai wannan? Wa ta sani a duniyar da har zata ce ta tafi? Ta tafi ina? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya tsine ma wannan mata ta Maheer duk ita ta jagwalgwala al-amarin nan, muna zaman mu lafiya ya auro annoba ta tarwatsa mana farin cikin mu, yanzu ita kanta Badiyyar bamu san inda ta tafi ba bamu san wani hali take ciki ba, ga Mayraah ma wai ta tafi, ta wa ta sani da zata ce ta tafi?" A ranan Abba ya maida Hajiya Amina sabon gidansa da ya gama ginawa har yayi furnishing not long ago a Miller road, he wanted to take Ammi by surprise, don ko su Maheer basu san da gidan ba balle ita, kawai rana daya yayi niyyar ce masu su shirya za su fita kawai sai ya kai su gidan daga nan kuma sai tarewa ba lallai ma su koma tsohon gidan ba, don shi ma a yanzu yana son barin anguwan da ya taso ya koma area with full security ya zauna, tsohon gidan nasa kuma ya saka cousin dinsa da matansa uku don kar gidan ya kasance babu kowa, Chalet kuma dama wani makocinsu dake biyan kudin haya da kyar don yawanci shi ke biya masa kudin hayan ma duk shekara, to shi yayi niyyar ba ma chalet din da matarsa da yaransa su zauna, to a yanzu kam ya ji zaman gidan ya fita ransa, tafiyar Mayraah ba karamin daga masa hankali yayi ba da distablizing dinsa, he wish zata canza tunani ta dawo gida don bata da wani gata a duk inda ma zata je yanzu, ya kuma san he tried his best, yayi bakin kokarinsa na ganin she wasn't traumatized or felt dejected with all what was happening, yayi iya kokarinsa all through the Saga but all his effort prove abortive, yasan da Ammi bata mata abinda tayi mata ba koma me zai ci gaba da faruwa bazata bar gida ba, baya jin zai iya yafe ma Ammi da ahalinta gaba dayansu, ba don yaranta ba babu abinda zai hanasa tura mata text kar ta dawo masa gida don har cikin ransa yaji baya ma son ganinta, amma bazai yi hakan ba ko don albarkacin su Maheer, don haka gwara kawai ya bar mata gidan kawai, daga ita har yaran nata. Karfe bakwai da rabi bayan gari yayi duhu Maheer ya kai Hajja gidanta, Throughout hours din da suka yi gidan Maheer kuka kawai Ammi take regretting so many things, kana ganinta kasan ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, she never expect things to go this way, ba kowa ya ja mata duk wannan abun ba sai Hajja da take kokarin ganin ta rabu lafiya da, pressure din Hajja duk shi ya ja mata wannan abu, she was only trying to please her mother in so many ways kar su samu matsala, Hajja kam ba bakin magana amma ta tsine ma Haseenah ya fi a kirga, ta rantse ta kuma rantse Maheer bazai ci gaba da zama da annoba, Abincin da ya fita ya siyo masu ma duk basu ci ba saboda babu kwanciyar hankalin ci, Maheer na maida Hajja gida ganin Ammi zata sauko daga motar Hajja ta kalleta tace "Ina kuma zaki kike kokarin saukowa?" Cike da karfin hali Ammi tace "Me zan koma gidan in yi Hajja? Babu amfanin komawata kawai" Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Hajja tace "Ni kuma me zaki shigo min nan kiyi, ni fa ina ji a jikina babu inda Mayraah ta tafi in ma zaki kwantar da hankalinki, ki kwantar da hankalinki ki dukufa da addu'a ba ji ba gani wallahi zata dawo, babu abinda kukan nan zai kara ki da shi sai ma ki ja ma kanki wata cutar dama ke ba lafiyayya ba yanzu, kwanaki ma ba haka ta dinga yi ba da aka fasa auren kuma daga baya sai ta dawo, duk bacin rai ne da rashin madafa ba wai wani abu bane yasa tace ta tafi, tunda ita kanta tasan bata da inda za ta, bata da kowa da ya wuce mu, ai yarinya ce me hankali Mayraah, ina da tabbacin kilan gidan kawayenta ta tafi ta samu nutsuwa na ɗan lokaci, amma in sha Allahu zata dawo komin dare, ke kin taɓa ganin inda ɗa ya guji iyayensa komin laifin da suka masa? To ki sa ma ranki salama ki koma dakinki ki samu kuyi shawaran yanda za a fara cigiyarta a gun yan makarantarsu ke da mai gidan ki, wannan kawar tata da kika kira daxu ai ba ita kadai bace kawarta, kilan wajen wata daban taje, kar ki biye abinda Mamuda ya maki ki samesa a san na yi tun dare bai tsala ba, in sha Allahu Mayraah tana nan gun kawayenta, nima yanzu ina shiga zan buga lamban yan bichi in ji ko Badiyyah ta je can ko hankali zai kwanta, amma Mayraah kam nutsuwarta da sanin ya kamata ma bazai sa ta tafi wani waje ba, tana nan kusa da mu in sha Allah" Hajja na kai wa nan ta bude gidanta dake bude har sannan ta shiga ciki a hankali tana cewa "Wai ni yau da mutuncina da girmana aka kai Caji opis" Sai kuma ta fashe da kuka ta kulle gidan. Maheer ya bar anguwan bayan sun ajiye Hajja, tun dazu ko magana bai yarda ya hadasa da Ammi ba balle ya bata hakurin kukan da take, to me ma zai ce mata.
Wajen karfe tara Mayraah ta farka daga baccin da take, it was still raining but not heavily, zuwa sannan zazzabi ne sosai jikinta, ta daure ta sauka daga kan gadon ta lallaba ta bude jakarta ta ciro wani hijab ta saka sannan ta dau Atm card dinta, tana tafiya a hankali ta bude kofar dakin ta cire makullin sannan ta fita ta kulle kofar ta sauko kasa, reception din hotel din ta nufa cike da karfin hali tana kallon receptionist din tace "Plss where can i locate...." Kasa ci gaba tayi ta dafe kanta, receptionist din ta zagayo inda take da sauri ta riketa ganin tayi baya zata fadi tace "Are you okay Madam?" colleague din receptionist din shi ma ya taho da sauri suna mata sannu, Mayraah dai gyada masu kai kawai, receptionist din ta karasa da ita inda kujera yake ta xaunar da ita kan kujera tana kallonta, sauran ma'aikatan wajen ma duk suka taho suka tsaya kan su, Receptionist din tace "Amma baki da lafiya ko?" Mayraah ta kasa bata amsa sbda sarkewa da breathing dinta ya soma yi, nan duk suka rikice aka fara mata fifita duk da sanyin gari, wata worker din wajen na cewa ko dai a tafi da ita asibiti don babu wani tanadi incase of such emergency a hotel din, Wani mutumi ne ya shigo Reception from upstairs zai fita waje, ya tsaya ganin yanda ma'aikatan hotel din suka taru waje daya sai fifita suke ma Mayraah, ya karasa inda suke yace "Hope all is well?" Wani ma'aikaci yace "Bata da lafiya ne muna jiran za a dauko makullin mota a tafi da ita asibiti" Yace "Subhanallah, why not mu tafi asibitin since i am with my car key, i am going out now" Yana fadin haka ya tsaya gaban Mayraah yana kallonta yace "Sannu, are you Asthmatic?" Mayraah bata ma san yana yi ba don zuwa sannan double take ganinsu gaba daya, da sauri ya kalli receptionist din yace "Ku fito da ita kawai, mu tafi asibitin" Yana fadin haka ya fita in a haste don tada motarsa dake parking space, receptionist din suka tafi da Mayraah motar tasa, ya bude masu back seat, ma'aikaciyar hotel din daya ce ta shiga motar tare da Mayraah za su tafi asibitin bayan ta amshi Atm din Mayraah dake hannunta kar ta yar, makullin dakin kuma ta ba colleagues dinta su mayar cikin hotel din, tuni ya ja motar suka bar haraban hotel din bayan an bude masu gate. Mutumin na driving din ya kira wani abokinsa yana dagawa yace "Hello Dr kana hospital ne?" Sai kuma yace "Ohk, to dama emergency ne, wata baiwar Allah ce bata da lafiya muna hanyan asibitin yanzu" Daga haka ya katse wayar. A hankali Mayraah ta bude idonta after an hour a asibitin, ido hudu tayi da receptionist din dake zaune ward din ana jiran tashin Mayraah don ta kira yan uwanta kafin ma'aikaciyar ta koma hotel bakin aikinta as instructed by the hotel manager, matar ta sakar ma Mayraah murmushi ta mike tace "Sannu fa" Mayraah ta mike zaune da kyar tana bin ward din da kallo, it's so big and clean, daga gani kasan ba karamin asibiti bane ko daga gadon da take kwance zaka gane hakan, Receptionist din tace "Bari in masu magana ince kin tashi...." Daga haka ta fita daga babban ward din, Mayraah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kalli Cctv camera dake ward din, maida dubanta tayi kan drip da aka makala mata a hannu, dai dai nan aka bude kofar ward din ta daga kai da sauri, wani mutumi ne ya shigo tare da wani dake biye da shi a baya with white lab coat da stethoscope a wuyansa, ita dai duk kallonsu take har suka iso bakin gadon da take, mutumin da ya fara shigowa dakin ya ɗan duka ya dafa gadon yana kallonta yace "Baiwar Allah ya jikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah naji sauki" Likitan ya karaso ya kara gudun drip din kafin shi ma ya kalleta yace "Hope you are feeling much better now?" Tace "Sure" Yace "To Maa sha Allah" Receptionist din tace "Manager yace ta kira yan uwanta sai ni in koma bakin aikina" Sosai gaban Mayraah ya fadi, likitan yace "Eh gaskiya ne, ai kun ma yi kokari for such hospitality" Sai kuma ya kalli Mayraah yace "Ki kira yan gidanku yanzu ki sanar masu kina asibiti" Da sauri tace "Ai wayar na dakin hotel din" Mutumin da ya kawota hospital ya ciro wayarsa ya mika mata yace "Za ki iya amfani da nawa" Sosai gabanta ya fadi, ta amshi wayar tana tunanin yanda zata yi, nan da nan dubara ya fado mata tayi dialing din layinta dake kashe ta sa handsfree, duk suka dinga kallonta jin switch off, a hankali tace "Number Abbanmu ne, bari in kira yayana" Daga haka ta sake dialing other line dinta nan ma aka ce switch off, Mayraah ta kalli receptionist din tace "Za ki iya tafiya, Nagode sosai, nasan zuwa anjima zan samesu a waya" Receptionist din tace "Toh Allah ya kara lafiya, ga Atm card dinki" Mayraah har ta mance da Atm card din, ta amsa tana juyawa tace "Nagode" Receptionist din tayi mata Allah ya kara lafiya, zata fita mutumin da ya kawo su yace "Ko za ki jira mu koma tare in 30mins time" Tace "Ayya, kar ka damu zan samu Cab idan na fita, kaga instruction din manager dinmu kenan, yace tana farkawa in dawo bakin aiki" Yace "To ba laifi" Daga haka ta fita daga ward din. Mayraah na gyara Hijab din jikinta a hankali tace "Naji sauki fa, kawai za a iya sallamata in biya bill din" Dr Khalil ya kalli abokinsa Ahmad kamar yanda Ahmad din ma ya kallesa, can Dr Khalil yace "Ae ba a gama baki proper medications ba, kuma kinga ko rabi drip din hannunki bai kusa ba" Mayraah tace "Ni fa i am okay, kawai jinina ne yayi kasa, but i am better now" Ahmad yace "Ohk then, ka sallameta Dr, sae kawai a rubuta mata drugs" Dr Khalil yayi kasa da murya yace "To ae kasan ka'idar hospital din nan...." Ahmad yace "To tace zata canza hospital, It's not ur fault" Dr Khalil yace "Ohk then"
Mayraah is 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
47
Musharraf na dakinsa bayan la'asar Maminsa tayi knocking, yasan ita ce but saboda damuwar da ya cika zuciyarsa ya ki tashi ya bude kofar, may be idan taji shiru zata yi tunanin bacci yake ta wuce kawai, continuously yaji take knocking din kofar, hakan ya sa ya ajiye wayar hannunsa da yake ta dialing number Mayraah amma switch off, ya mike ya nufi kofar ya bude yana kallonta bai dai ce komai ba, daga sama har kasa take kallonsa tace "Me kake yi a ciki nake knocking baka responding Musharraf?" Ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yace "Kawai na kwanta ne Mami, i want to get some rest" Mami ya dinga kallonsa, ganin damuwar dake fuskarta yace "Is anything wrong Mami?" Ta karasa cikin dakin ya bi bayanta yace "Mami wani abu ya faru ne" Mami ta juya tana kallonsa cike da damuwa tace "I should be asking u that Musharraf, tell me what are you hiding from me? menene ke faruwa?" Musharraf ya shafa kansa yace "Me ke faruwa kamar me fa Mami, kin ga anyi wani abu ne?" Mami tace "You are not saying the truth, tell me kai da waye ku ke da matsala? Menene kake boye min?" Ya dan buda ido yace "Matsala kuma? I don't have issue with anyone" Mami tayi shiru still looking at him kafin tace "Then me yasa police officers suka zo gidan nan nemanka yanzu?" Kallonta ya dinga yi cike da mamaki yace "Police officers kuma? I don't understand" Mami tayi kasa da murya sounding so disturbed tace "Kar ka boye min komai don Allah son, me yake faruwa?" Musharraf yace "Wallahi Mami ban sani ba.." Bai sake cewa komai ba ya fice daga dakin Mami ta bi bayansa tana kiransa bai tsaya ba har ya sauka downstairs, ya nufi 48......
RA
kofar parlor ya bude, was mutane uku ya gani tsaye dai dai bakin kofar parlon, daya daga cikinsu yace
"Musharraf Abdallah??" Musharraf yace "Yes, how may i help you?" ID card dinsa ya ciro don dukkansu ba uniform bane a jikinsu, Dan sanda na nuna ma Musharraf ID card din yace "You are under arrest" Juyawa Musharraf yayi ya kalli Mami dake tsaye bayansa, trying all possible best to calm her down yace "U need not to worry pis Mami, it's not something serious, zan bi su mu je" Mami da hankalinta yayi mugun tashi bata ko kallesa ba balle ta sauraresa tana kallon officers din tace "Pls wani division din ne?" Wani officer ya gaya mata, ta juya ta koma sama da sauri don dauko makullin motarta da gyale, Musharraf ya bi yan sandan har kofar gida zuwa gun motarsu, babu wanda zai ce yan sanda ne don motar ma me yau ce suka zo da shi, nan suka kama hanyar station tare da Musharraf. Maheer na zaune asibitin da aka kwantar da Haseenah wajen karfe biyar na yammacin ranan, she is responding to treatment don har ta fara iya cin abinci a hankali, amma fa tana jin jiki don fuskarta ya kumbura suntum saboda azaban bugun da kanta ya sha, tun da abun ya faru shi dai bai ga mahaifiyarta ta zo asibitin duba ta ba, danginta ne kullum ke sintirin asibitin su kawo mata wannan su kawo mata wancan, kuma ko sun zo basa ce ma Maheer komai, ko Aunties dinta idan ya gaishes basa amsawa fuska a murtuke suke wucesa shi kam ko a jikinsa don duk ya kagu a sallameta a asibitin shi ma ya sallameta zuwa gidansu don har ransa yasan bazai iya zama inuwa daya da Haseenah ba kuma, shi mamakin ma yanda aka yi har ya auri Haseenah yake kamar wanda aka yi ma rufa ido, ko da yake baka sanin halin mutum ai sai ka zauna da shi dama, he regret knowing her har suka kai ga aure, yana zaune haraban hospital din yayi nisa tunanin da yake don shi har a sannan gani yake Mayraah na gun Musharraf, infact bai ma yarda bata wajensa ba, few minutes ago Abba ya kirasa ya sanar masa anyi arresting Musharraf, so kawai yana jiran Abba ya sake kiransa yace masa Musharraf yayi admitting Mayraah na wajensa, yana wannan tunanin kiran Abba ya shigo wayarsa, da sauri ya daga, Abba yace "Akwai wanda ke tare da matar taka a asibitin ne ka taho Miller road ka sameni yanzu?" Maheer yace "Miller road, Ina kenan a nan Abba?" Abba yace "I will send you the full address" Maheer yace "To" Shi fa duk tunaninsa Abba baya kano da bai gansa a gida ba, though ya dai lura kamar Hajiya Amina ma bata can gida amma he was thinking tare Abba ya tafi da ita, mikewa yayi don Aunties din Haseenah na ciki tare da Haseenar ya shiga motarsa ya bar hospital din, address da Abba ya tura masa ya bi har dai daga karshe ya ga kansa a wani hadadden layi na manyan masu kudi, don duk gidajen wajen hadaddu ne na karshe, yayi parking a number gidan da Abba yace yayi parking yana kallon gidan wondering whose house Abba yace ya zo, bude gate din