Mayrah

Chapter 84 of 152

bude back seat ganin bai da alamar bude booth din motarsa ta ajiye ledojin siyayyan da tayi, bayan ta ajiye ta dawo gaban motar ta zauna keeping a straight face just as she saw him keep, driving kawai yake lokaci lokaci yana kallon agogon wrist dinsa.... Gaban wani apartment taga yayi parking daga karshe, ta juya tana kallonsa da mamaki, duk gidajen wajen iri daya kuma ko wanne da parking space dinsa a gaba sai garden ta baya, sauka yayi daga motar ita dai bata bude motar ba, yana kallonta da kyau yace "Ko ni zan sauko da ke?" Ta sake kallon gidan da ma anguwan gaba daya tace "Where is this?" Yace "Ni kike tambaya? Ki bari in kin shiga ciki sai ki tambayi warce tace a kawo ki, ai tana ciki she will explain" Mayraah dai kallonsa take ta kasa cewa komai, ya wani hade rai yace "Malama kina bata min lokaci" Bude motar tayi a hankali ta sauka tana kallonsa, ganin ya kulle motarsa da lock ya fara tafiya ta wani hade rai tace "To ban ciro ledan kayan da zan nuna mata ba ai" Banza yayi mata ya nufi entrance din gidan, ta wani hararesa sannan ta bi bayansa, yana bude kofar ya shiga, leaving the door open for her, ganin ta tsaya bakin kofa ya hade rai yace "Are you okay?" Ta sauke idonta sannan ta shiga parlon tana bin ko ina da kallo, kulle kofar yayi ta juya tana kallonsa, ya karasa cikin parlon ya zauna without looking at her, babu yabo babu fallasa ya nuna kofar wani daki yace "Go in there and meet her" Mayraah couldn't stop looking at him, ya mike yana mata wani kallo yace "Baki ji na ne? Ko bata gaya maki airport za mu tafi daga nan ba?" Ta sauke idonta ta nufi kofar dakin da ya nuna mata tana tafiya a hankali lokaci daya kuma tana waigosa, shi ko ya ciro wayarsa yana dannawa, a hankali tayi knocking kofar ya daga kai ya kalleta, yace "Bude Ki shiga" Bata san sanda ta girgiza kai ba gabanta na faduwa tace "Wallahi ba kowa a gidan nan ka kawo ni" Mikewa yayi ya saka wayar aljihunsa yace "Ashe kin san babu kowa, to yau sai kin min bayanin dalilin da ya sa kika raina ni kika zama kece Boss din ni kuma kika maida ni staff...." Ta marairaice masa tace "Don girman Allah kayi hakuri wallahi bazan sake ba kaji har na rantse" Tana ganin ya nufota ta bude kofar dakin da gudu ta shige zata kulle sai ta ga babu makulli jikin kofar, kasa kakkwaran motsi tayi gabanta na bugawa, ganin ya shigo dakin ta durkusa tana kallonsa ta kara marairaice masa tace "Sir plss i am sorry ka yafe min wallahi sharrin shaidan ne, i promise i will be obedient from henceforth" Ya kulle kofar dakin yace "Ohk shaidan ne yasa kika raina ni kike zagina ko?" hankalinta yayi mugun tashi amma taki nuna hakan a fuskarta ta mike ta koma can jikin bango tana kallonsa tace "Wallahi ban taɓa zagin ka ba, me yasa zan zage ka bayan ka girmeni kuma kai boss dina ne" har wani zufa ke keto mata a goshi duk da sanyin da ake, tana ganin ya nufota ta wani hade rai tace "Wallahi zan maka ihu fa" Ya wara ido yace "Oh Haba? To yi ihun mana ki ga ko yana da amfani" Ta wani turo baki ta rungume hannu tace "To oya yi hakuri, wallahi na daina abinda nake har abada...." Tana fadin haka ta tafi gefen gado ta zauna ta nuna masa dan nesa da ita tace "Ka zauna let settle this amicably now...." Kallonta kawai yake, bata jira me zai ce ba, using her fingers to count tace "Kaga na farko daga yau zan dinga gaisheka duk inda na ganka, kai ma kuma dole ka amsa baza kayi ignoring ba, sannan zaka dinga treating dina yanda kake treating sauran staffs don naga su baka masu masifa ni kadai kake ma, sannan baza ka sake ce in maka gyara a office dinka ba tunda ba aikina bane na cleaners ne, and u should apologize for calling my first class a botany first class, and i will also apologize for calling a whole qualified Medical Doctor a Quack...." Confidently take maganarta looking at him straight in the eyes, sai kuma ta tallabi chin dinta da hannayenta biyu tana juya idonta tace "I am waiting for ur feedback now" Kasa ci gaba da kallonta yayi ya dauke kai.... Ta mike tace "If you've finish deciding ina parlor ina jiran feedback" Daga haka ta nufi kofa gabanta na mugun faduwa don kawai karfin hali tayi take maganar nan da take, ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin, zaunawa yayi gefen gadon yana shafa kansa, sai kuma ya mike da sauri ya ciro wayarsa dake ring yaga ceo ce, zaro ido yayi ya fita daga dakin da sauri, ga mamakinsa bai ganta parlon ba, yana fita waje ya ganta can jikin mota a tsaye, dauke kai tayi bata sake kallon direction din ba, ita dai ba ta samu ta fito daga gidan lafiya ba, rufe gidan yayi ya karaso parking space din yana kallonta yace "Kin zata kina da wayo ko? Zaki gane" Ta marairaice tace "But i was waiting for ur feedback" Bude motar yayi ya shiga, ita ma ta bude front seat, sai da ya tada motar sannan yayi dialing number Ceo yace mata suna hanya, cikin yan mintuna suka isa gidan, Ceo ta dinga kallon ledan hannun Mayraah tace "Shopping nace kiyi what's this little thing u bought?" Mayraah tayi murmushi tace "Wannan ya isheni Ma" Ta kalli MD tace "Meye wannan din ta siya?" Yace "Na mata magana tace she doesn't need anything just chocolate" Mayraah ta kallesa da sauri, Ceo tace "Ohk then, je ki shirya a daki" Mayraah ta wuce dakin rike da ledojin. Karfe bakwai da rabi na dare suka bar gidan Ceo zuwa airport, ita da kanta tayi driving dinsu zuwa airport, Bayan Mayraah ta sauka, MD ya fiddo akwatinta a booth, Ceo ta mata side hug tace "Take care of ur self dear, my regards to ur parent" Jikin Mayraah yayi sanyi ta daga kai tana kallonta a hankali tace "Ma yaushe zaki zo Nigeria?" Ceo ta mata murmushi tace "Sai bayan wata biyu in sha Allah" MD dai na tsaye sai kallonsu yake, Mayraah tace "To Allah ya kai mu, thank you so much Ma, i appreciate" Ceo tace "You are welcome" Daga haka ta daga ma MD hannu, ta shiga motarta ta bar airport din, Mayraah ta bi motarta da ido babu ko kiftawa, lokaci daya ta juya taga MD har yayi shigewarsa cikin airport din ya bar ta wajen a tsaye, Business class Ceo ta sa MD yayi masu booking, but because he wants to rest kasancewar he wasn't too fine a conference ranan kawai sai ya biya masu ticket din first class. Sune farkon boarding plane din, Mayraah bata taɓa shiga first class ba iyakarta business class, wajen karfe takwas da rabi jirginsu ya tashi, ya kira flight attendants telling them he is taking nothing don bai ma son a zo a tambayesa, bayan Flight attendants din ta bar wajen, after few minutes Mayraah ta juya ta kallesa taga ya kwanta ya lullebe da duvet, two hours into the flight Mayraah tayi bacci. Bayan awa daya ta farka, ta mike zaune tana kallonsa, har sannan a kwance yake idonsa a lumshe sae karamin towel dake forehead dinsa, ta mike tana tafiya a hankali ta nufi inda yake, bude ido yayi da sauri jin motsi kusa da shi, ta ɗan koma baya kamar munafuka tace "Are you okay?" Flight attendant ce ta iso wajen with pain reliever, Mayraah ta bi ta da ido har ta basa maganin sannan ta zuba masa ruwa a daya daga cikin glass cups da aka ajiye masa da goran ruwa uku, bai amshi glass cup din ba ya dau bottle water instead ya kurbi ruwan ya sha maganin, bayan Flight attendants din ta ajiye glass cup din hannunta ta kalli Mayraah don tana son sake masa labulen wajen for his privacy, kafin tace komai Mayraah tace "We are together" Flight attendants din ta mata murmushi tace "Okay Ma" juyawa tayi ta bar wajen, Mayraah ta kai hannu kan karamin towel din forehead dinsa taji a jike yake da ruwa, cire towel din tayi don har a sannan he is running temperature, ta tafi toilet ta kara jika towel din sannan ta dawo, ta duka kusa da shi zata daura a goshinsa ya fixge towel din yace "Don't worry, je ki ci gaba da baccin ki" Ta wani hade rai tace "But i am a nurse" Daga sama har kasa ya kalleta yace "Nurse with no license and working experience, pls go back to ur seat Madam and sleep" Kwace towel din tayi tace "I don't mind what ever u will say, but i am sticking to the ethical obligations of a Nurse to a patient" Daga haka ta fara goge masa forehead dinsa that is hot with the towel din, kallonta kawai yake, sai kuma ta cire duvet din jikinsa tace "You are running temperature so there is no point in covering ur body with a Duvet" Ko minti goma ba ayi ba ya sake komawa bacci. Kafin su isa Nigeria he felt much better saboda painkillers da ya sha a jirgin, karfe biyu da rabi na dare suka sauka airport din Abuja. Bayan ta dauko akwatinta ta kalli inda yake zaune ya jingina da kujera idonsa a lumshe, shi dama bai taho da komai ba, ta karasa wajen da yake zaune tace "Zan kira yayana ya daukeni, u can leave me here" Ya bude ido da sauri yana kallonta yace "Karya kike ba yayanki bane" Tace "To naji ba yayana bane" Ya mata wani shegen kallo ya mike ya fara tafiya, he is just acting he is fine whereas he is sick, ta bi bayansa suka fito haraban Airport din, taxi suka shiga.... Bayan sun fita daga airport din yace "Ni zan gaya masa address din gidanku da kika yi shiru?" Tace "To ai naga kasan gidan tunda ka taɓa bin Dr Khalil" Juyawa yayi ya kalleta da sauri, ta maida hankalinta kan driver tana gaya masa address din gidan da zai kai ta, MD yace "Shi Khalil din ne yace maki ni na bi sa?" Without looking at him tace "Ai ba sai ya gaya min ba i saw it with my eyes" Bai sake tanka ta ba cause ba shi da strength din hakan, 10 mintues into the journey ya fara bacci, ta ɗan juya ta kallesa, da zata matsa ta koma edge din kujeran kuma dai kawai ta basa access to her shoulder, har suka isa gida yana bacci, Mayraah ta juya ta kallesa, after few seconds calmly tace "I am home" A hankali ya bude ido, sai kuma ya gyara zamansa da sauri, ta ɗan kyabe baki ta bude motar tace "Sai da safe" Daga haka ta sauka ya bi ta da kallo, drivern taxi din ya sauka ya dauko mata akwatinta a booth, bayan ta amsa ta kalli MD dake kallonta, sauke ido tayi ta daga masa hannu sannan ta juya da sauri ta nufi gate din gidan ya bi ta da kallo, Kwankwasa gate din tayi taji security na tambayarta waye, bayan ta basa amsa ya bude gate din ta shiga cikin gidan ya kulle gate din, sai a sannan MD ya sa taxi driver din ya ja motar suka bar unguwan. Mayraah ta zauna saman kujeran dake compound ta ciro wayarta tayi dialing number Maheer, sai da ya kusa katsewa ya daga a hankali yace "Mimi" Ta wara ido tace "Sorry i woke u up" Yace "Ya aka yi? Hope ba ciwon cikin bane?" Tana murmushi tace "Aa ba shi bane, ai tun ranan da aka min allura bai kara ciwo ba, yaya na dawo" Maheer ya mike zaune yace "Da gaske?" Tace "Eh" Yace "Yaushe?" Tace "Just now" Yace "In taho airport inyi picking dinki ne?" Tayi dariya tace "Eh ka taho" Yace "Right away" Daga haka ya katse wayar, mayar da wayar tayi cikin handbag dinta, ta daura handbag din kan akwatin sannan ta karasa chalet da sauri ta tsaya bakin stairs yanda bazai ganta ba har sai ya sauka kasa, bayan kusan minti bakwai sai gashi ya fito sanye da jallabiya, yana sauka stairs din tayi er kara saitin fuskarsa, ya juya da sauri yana kallonta da mamaki, ta kyalkyale da dariya tace "Wallahi nasan ka ji tsoro Yaya" Tun da Haseenah taji ya bude kofar dakinsa dama ta farka daga baccin da take a nata dakin, sai ta fito parlor, bai bi ta kanta ba as usual, tana ganin ya fita compound ta taho window tana leka waje, kawai kuma sai taji muryar Mayraah, Maheer dake kallon Mayraah daga sama har kasa yace "Wa yayi dropping din ki?" Mayraah na murmushi tace "MD dinmu, taxi muka shiga a airport din" Yace "Har kin kara haske daga zuwa Uk, are you sure we are not relocating there?" Tayi dariya tace "Wani haske? Bayan sanyi ake a can sosai, har fa mura sai da nayi, ni dai bana son kasar saboda sanyi" Yana murmushi yace "To ina akwatin?" Ta nuna masa inda ta bar akwatin tace "Yaya i bring you so many chocolates irin wanda kake so" Yace "Really" Tace "Wallahi" Gun akwatin ya nufa ta bi bayansa, Haseenah dake jikin window tana jin duk abinda suke cewa ta bi su da ido.

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda

Ur evidence via 07087865788

76
Mayraah na biye da Maheer dake dauke da akwatin ta suka shiga main building din gidan, ya kunna wutan parlon cause everywhere was dark, ya juya yana kallonta yace "Nasan dai kinyi bacci a jirgi" Tana cire jacket din jikinta tace "Eh nayi bacci amma ai ba da yawa ba, though i am not sleepy now" Ya kalli agogo dake nuna karfe uku da kusan rabi yace "Yunwa fa?" Ta wara ido tace "First class fa muka shiga yayana, kasan me da me na ci?" Da mamaki yace "First class?
Ke da wa? Hospital din ne ya biya maku first class?"
Tayi murmushi ta zauna tace "Wa enda muka je conference din mana, tare muka dawo da su ai" Ya zauna yana facing dinta yace "So how was the conference like?" Ta langwabar da kai tace "Duk fa ban je ba Yaya" Yace "Baki je conference din ba?" Ta gyada masa kai tace "Kawai a gidanta na tsaya duk 2 days din nan" Shiru Maheer yayi bai ce komai ba amma deep down him yana mamakin amfanin zuwa da ita kasar da aka yi, can yace "Ku nawa ku ka je?" Tace "I think 4, yaya Abba yana nan?" Maheer ya girgiza kai yace "Yana kano" tace "Ohk.... yaya har bana son in tuna cold din kasar" Yayi murmushi yana kallonta, Hira ta dinga yi masa a parlon yana biye ta duk da baccin da yake ji don dama wajen karfe biyu ya kwanta, ya fara bacci ba dadewa ta kirasa, har kusan lokacin da za a tada sallan asuba suna zaune parlon, suka ji ana saukowa downstairs, Maheer ya kalli agogo yaga nan da minti goma za a tada sallah a masallaci, tuni Mayraah taji kamshin turarensa ta gane shi ne, yana saukowa parlor tun da ta kallesa 77
sau daya ta dauke kai tana ci gaba da yi ma Maheer maganar da take masa, kallo daya shi ma ya mata ya nufi kofa ta bi sa da kallon gefen ido har taga ya bude kofa, tayi kasa da murya tana kallon Maheer tace
"Yaya yaushe ya dawo?" Maheer yace "Jiya da rana"
Ganin ya ja kofar parlon bayan ya fita ta wani tabe baki tace "Yaya kasan abinda yayi min ne a UK?"
Maheer yace "Me ya ma ki?" Tace "Ai babu ruwana da shi daga yanxu, kawai fa daga...." Mikewa tayi da sauri ganin Usman ya dawo Parlon ashe yana jikin kofar bai tafi ba, tana ganin ya nufota ta ruga sama da gudu tayi bangaren Ammi, ya juya ya fice daga parlon, Maheer dai ya bi sa da kallo, Mayraah na shiga parlon Ammi ta kulle kofar tana turo baki, Ammi da ta fito daga bandaki ta taho parlon jin alamar an shigo, buda baki tayi tana kallonta tace "Mayraah" Dariya Mayraah tayi ta tafi da sauri ta rungumeta tace "Ammi na dawo" Ammi tace "Ikon Allah, yaushe kika dawo?" Mayraah tace "Dazun nan wajen karfe uku" Da mamaki Ammi tace "To wa ya dawo dake gida?" Mayraah tace "MD din mu" Ammi tace "Maa sha Allah, welcome daughter" Mayraab bata yarda ta bar bangaren Ammi ba don tsoron tafiya dakinta take ta hadu da Usman, wajen karfe shidda Ammi ta sauka downstairs don hado mata shayi ta kawo mata da bread, Ammi na ajiye shayin ta tadda ta ta jinginar da kanta da kujera ta fara bacci, Ammi ta dafata tace
"Tashi ki sha shayin sai kiyi wanka ki kwanta"
Mayraah ta buda ido a hankali tace "Ammi akwatina na downstairs" Ammi tace "Aa babu akwati downstairs, ko Maheer din ya kai maki daki" Mayraah tace "Zanyi brush in fara wanka kafin in sha shayin" Ammi tace "To je kiyi, in kin gama sai ki hado wani shayin bari in sha wannan" Mikewa Mayraah tayi ta fita daga bangaren Ammi da sauri ta tafi dakinta, tana shiga ta kulle da makulli. Wajen karfe takwas tana parlon Ammi ta gama breakfast kenan Usman ya shigo parlon, tun da ta kallesa sau daya taki dago kai Ammi ta amsa gaisuwar da yake mata, yace "Zan je kaduna Ammi" Ammi tace "Kayi breakfast din?" Yace
"Nayi" tace "Toh Allah ya tsare hanya, Allah ya kiyaye, yau din zaka dawo?" Yace "Aa sai Monday in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu lafiya, ya

Download complete TXT · Novel page