AJIYA A DUHU BOOK 1

Chapter 41 of 76

Ammie!”. Yarinyar ta faɗa cikin hanzari itama tana fisgar hijjab. Dai-dai nan Ammie ta dawo da kallonta kan yarinyar data sake wani ƙwallara uban ƙara tana tittirza ƙafafu da faɗin, “Ni dai kar a hanashi. Sai ya ramomini....”
    Tsawa Ammie ta daka mata. Tare da nunata da yatsa. “Idan baki min shiru ba na rantse da ALLAH zan tsantsama miki jiki da magribar nan. Ai dama tunda naga kun jima baku dawo ba nasan kina can ɗaukar maganar da kika saba. Shima Ajwaad ɗin sakarai dake biye miki, kin tashi kin cire uniform ɗin ko sai na ci ƙaniyarki....”
          Kuka ta sake fashewa da shi amma bamai sauti ba yanzu dan tana tsoron Ammie. Sai kuma ta nuna ƙafar tana faɗin, “Ammie nafa karye ne a ƙafar...”
    “Karyewa?”.
Ɗayar yarinyar da zata kaiwa sa'an saurayin yaron, idan ma ta girmesa kaɗan ne dake tsaye tana kallonta ta faɗa kafin ma mahaifiyar tasu ta amsa.
           “Eh wlhy Didi. Ba Najib ɗin gidan Maman Ayna bane ya bugeni da keke mun fito islamiyya. Kuma shine yaƙi tsayawa harda cema Besty wai in ya isa yazo ya rama min”.
     Shigowar Amaal da wata ƙyaƙyƙyawar mata mai kama da yaron sosai yasa babu wanda ya tanka mata. Matar ta nufeta tana faɗin, “Subahanallahi Baby na miya faru?”.
          Fuska ta taɓe tana satar kallon Ammie, sai kuma ta ɓarke da kuka tana nuna ƙafarta da shigewa jikin matar da takai kusa da ita zaune. “Oum ba Najib bane ya karyani a ƙafata. Kuma na kasa tafiya sai da Besty ya goyoni ma”.
      Sosai Oum ta shiga faɗa tana dudduba ƙafar da faɗin in fa har taji ciwon da gaske bazasu yarda ba. Ammie da taga abin nasu bana ƙare bane ta katseta da faɗin, “Aunty ALLAH ki daina biyema iskancin Manaal. Ni yanzu ma sonake nasan baki dai bar Ajwaad ya fita ba ko?”.
         Kafin Oum ta bata amsa Amaal ta ce, “Wlhy Ammie ya tafi, inata kiransa ko kallona baiyiba ma ya kwashi keke da gudu”.
    “Innalillahi banga ta zama ba”. Ammie ta faɗa tana shiga ɗaki. Babu jimawa sai gata ta fito da hijjabi a hannu. Sai lokacin Oum ta dubeta tana dariya. “Wai ina zaki je?”.
         “A binsa zan mana. Sai na bari a cutar min da yaro tunda ke naga kinama ɗaukar abun bada muhimmanci ba, in dai kika biye ta wannan yarinyar wataran sai ta saka har ke an kai station ɗin ƴan sanda” Bata jira amsar Oum ba ta fice abinta.

     Fitowar Ammie a gidan dai-dai da isowar Ajwaad a kekensa rigarsa ta islamiyya a yage. Fuskar nan ciɗin-ciɗin ga goshinsa ya ɗan kumburo kaɗan, sai gefen lips ɗin da jini kaɗan shima. Da sauri ta nufesa tana riƙe keken da faɗin, “Innalillahi Ajwaad, yanzu faɗan kaje kayo saboda ALLAH. Anya wataran Manaal bazata saka a maka dukan da zaka kasa tashi ba a anguwar nan?”.
           Cikin ɓacin ran da muryarsa dake fita can ƙasa-ƙasa ta kasa ɓoyewa ya ce, “Ammie ciwo fa yaji mata a ƙafa, sai na ƙyalesa yaci bulus? Ko yanzu ban ƙyalesa ba sai na jera sati ina masa duka”.
    Ƙasa magana ma Ammie tayi ta zuba masa ido kawai. Har ya shige shi da keken gidan bata iya ta motsa ba. Wannan abota na bata mamaki tsakanin Manaal da Ajwaad. Wata irin abotace mai ban mamaki da tsayawa a zuciya. Basu kasance sa'anni ba dan ya girmeta sosai kusan shekara bakwai ne tsakaninsu ma, sannan basu kasance jinsi ɗaya ba. Amma akwai wata irin shaƙuwa a tsakaninsu da sam babu ita a tsakaninsu da ƴan uwansu na jini ma. Ita abun har tsoratata yake yi.........✍️

     

_Tofa wasa farin girki, 🥱🥱yanzu zamu koma tushe fa._








✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖5️⃣5️⃣


______________

.......Su ɗin ƴan asalin jihar Kebbi ne, a garin Giro dake ƙarƙashin Suru LG. Aiki ne ya kawo mijinta nan cikin Kano kasancewarsa jami'in ɗan sanda. Ba Kanon suka fara zama ba. Sun zauna jihohi kusan uku a tsahon shekarun aikinsa. Sai dai shekara biyu data wuce aka maidosu nan cikin Kano suke zaune a anguwar sharaɗa. Yaransu uku ne duk mata. Shahidah itace ta farko, sai Amaal. Sai Manaal. Lokacin da sukazo Kano shekarar Manaal huɗu kacal, amma sai baƙar fitina a cikinta da shegen surutu. Manaal irin yaran nan ne masu shegen wayon tsiya da ɗan karan surutu kamar an musu ƙauri da kan akku. Ga ɓarnar masifa da jan faɗan tsiya. Sam bata ragama ƴaƴan jama'a dan ko anfi ƙarfinta saita ƙwaci kanta da cizo da bula ƙasa ko jifa. Gata suke mata matuƙa kasancewar itace kamar auta a gidan yanzu. Kowa ya kwaso abunsa zai ce Maanal. Musamman ma mahaifinsu da suke kira Baabu.
      Dawowarsu cikin Kano sun samu abubuwan cigaba da dama, ciki harda ƙarin girma da Baabu ya samu, ita kuma ta fara kasuwancin turarruka da gyaran jiki irin na mata. Inda suke sabon wajene da aketa gine-gine, dan ko gidan dake a jikin nasu ma ana kan gina shi ne ba'a kammala ba. Sai dai an kusa kammala aikin. Hakan yasa kusan kullum zakaga mai gidan yazo da yaransa maza uku musamman ma weekend. Jefi-jefi sukan ɗan gaisa da Baabu idan anyi sa'a yana gida ko ya dawo wajen aiki. A haka ranar wata asabar yana gida suka tashi da shirin yin alala da yace yana buƙatar ci. Ammie ta kammala gyara wake ita da Shahidah da zata kai markaɗe. Sai kawai Maanal ta sanya rigima itama zataje. Cikin haushi Shahidah ta ce, “Dama kin bar damun kanki dan babu inda zanje dake. Haka kawai muje kita jibgar yaran mutane a gidan markaɗen kamar ranar da kika fasama ƴar mai markaɗen kai”.
    Ihu Maanal ta sake ƙwallarawa tare da zubewa ƙasa tana burgima akan ita wlhy sai taje fa. Dai-dai nan Ammie ta fito da bulala da nufin tsula mata amma sai Baabu ya hana ta hanyar amshe bulalar ya ɗaga Maanal daga ƙasan. Daga haka ya fita da ita a gidan yana lallashinta. A dai-dai lokacin motar makwafcin nan nasa ta iso anguwar. Baabu bai wani maida hankalinsa ba dan baima san shi bane kasancewar bawai ya wani riƙe motar tasa bane. Sai da yay parking a gaban gidan nasa ya fito tare da matasan samarin ƴaƴansa uku sannan Baabu ya maida hankalinsa kansa. Sun gaisa cikin mutunta juna, yayinda suma yaran suka gaida Baabu da girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana mai shafa kansu, yayinda shima babansu yakema Maanal wasa.
       “Ƴan samari yaya sunanku?”.
Cewar Baabu yana shafa kan ƙaramin su. Babban ne ya bashi amsa da. “Ni Fadeel. Wannan Fawzan. Sai Auta Ajwaad.”
      “Masha ALLAH, ALLAH ya albarkaci rayuwarku manyan gobe.”.
   A tare suka amsa da Amin. Yayinda mahaifinsu keta faman murmushi saboda surutun da Maanal ke zuba masa. Sai kuma can ta kalla Ajwaad dake ta faman cin chocolate ɗinsa, cikin ɗan tura baki ta ce, “Kai yaron nan bazaka tsammin alawanka bane. Inata haɗiyan yawu amma sai sha kakeyi rowa haramun dai”.
       Ba ƙaramin dariya ta basu ba. Banda Ajwaad ɗan kimanin shekaru goma sha ɗaya daya wani yamutsa fuska ya harareta ya ɗauke kansa. Sai Baabu da ya ɗan harareta shima. Amma ita ko'a jikinta ta maida kallonta ga Babansu ta na sake faɗin, “Abbansu kace masa ya tsammin raina ya biya”.
          “Kinga manta da shi Babyna. Muje na baki ina da ita da yawa. Daga yau kuma kema ni Abbanki ne ba nasu su kaɗai ba.”
    Cike da murna tace, “Eh”.
Gaba yay da ita zuwa motarsa. Ya fiddo chocolate uku ya bata biyu a hannu, tare da ɓare ɗaya ya sake miƙa mata. Cike da jin daɗi ta amsa. Tare da juyawa ta murguɗama Ajwaad baki da faɗin, “Mai rowa ɗan wuta. Nima kuma ga nawa”.
        Harararta nan ma yayi. Yayinda su Fawzan sukayi dariya. Shiko Baabu duk kunya ta ishesa. Ƙarfin halin Maanal da banne a rayuwa. Shegen surutunta da wayonta da suka girmi shekarunta na tada masa da hankali. Duk inda ake neman fitinannen mutum aka samu Maanal an rufe littafi kawai. Sai dai yana mata fatan idan ta ƙara girma ta canja daga hakan.. ƙiri-ƙiri da zai shiga gida yace tazo suje taƙi. Dole babu yanda ya iya ya barta wajen Alhaji kamar yanda ya roƙa.
      Yini guda Maanal na tare da Alhaji Aliyu Darma, Tare da yaransa uku da tuni ta saki jiki da su. Musamman Ajwaad da tunda ya fito da kayan wasansa ta naniƙe masa. Lokacin da rana tayi sai ga Shahidah da kula cike da alala an kawo musu. Sosai Alhaji Aliyu ya nuna jin daɗinsa tamkar ya ari baki dan godiya. Anan ma Shahidah tayi-tayi Maanal ta bita suje gida amma taƙi. Dole ta barta itama ta tafi. Sai da akai la'asar sazu tafi sanan su Fawzan suka rakata har gida da ledan kayan ciye-ciye da kulan da aka kawo musu alala sukai godiya. Yayinda ita kuma ta shiga kuka saita bisu, sai da Baabu ya mata tsawa sannan ta nutsu. Dan a duniya Maanal na tsoron hargagi musamman na Baabu..
      Wannan rana itace sanadin tarayyar waɗan nan ahali guda biyu. Dan kuwa washe gari sai ga itama mahaifiyar su yaran ta biyosu domin yin godiya. Anan ne kuma ta tarar da Ammie nama wata amarya gyaran jiki, itama tace ai sai ai mata kuwa.. tunda tazo Maanal na manne da ita. Kasancewar yaranta ita duk maza ne tana masifar son ƴar budurwar yarinya, shiyyasa tana ganin Maanal da jiya tasha labarinta a wajen ƴaƴanta yarinyar ta shiga ranta. Ga wayonta da surutunta na sakata nishaɗi. Yau ɗin ma dai da ƙyar aka raba Maanal da su, musamman Ajwaad da wasansu na yau yafi na jiya armashi. Dan yau ya saki  jikinsa ba kamar jiyan ba. Haka yake bashi da saurin sabo sam, akanyi baƙi a gidansu kwana da kwanaki babu ruwansa da su, dan shi yarone mai irin shegen tsantsenin nan, ga zuciyar tsiya da ƙulafucin iyaye. Ammafa idan ya soka to yaso ka kenan. Idan kuwa baka masa ba to babu abinda zakai masa ka birgesa ko kaja ra'ayinsa da shi. Shiyyasa a yau ɗin ma mamakinsa ya kasa barin Oum ganin yanda ya saki jiki a gidan tamkar a gidansu. Dan duk inda kaga Ajwaad yaje yaci maka abinci kansa tsaye to lallai yanayi da masu gidan....

★★★
         Kafin Alhaji Aliyu ya kwaso iyalansa su tare a sabon gidan nasu daya haɗu matuƙa gaya shaƙuwa da zuminci mai ƙarfi ya shiga tsakaninsa da iyalan Baabu ta yanda har suna kallon kansu tamar wasu ƴan uwa na jini. Oum ba itace kawai matarsa ba, ashe tana da amarya ma, sai da suka tare su Ammie suka sani. Bayan tarewar tasu kuma sai al'amarin ya ƙara ƙarfi fiye da tunanin mai hasashe. Ba shaƙuwar ahalin biyu ne kawai abin mamaki ba. Wadda ke a tsakanin Ajwaad da Maanal tafi zama abin kallo ga kowa. Dan takai a yanzu ako ina ɗaya yake ɗaya na wajen, shiyyasa idan baka sani ba baka taɓa gane ainahin gidan kowannensu. Dan takai yanzu ma Maanal taƙi zama a makarantar da take yi da yan uwanta. Da safe anta dagama kenan tace ita Ajwaad zata bi tasu makarantar. Anyi lallashin, an daka, anyi kurarin duk a banza. Hakan yasa Alhaji Aliyu roƙar Baabu damar maida Maanal makarantar su Ajwaad ɗin, kasancewar itama tana tare da Nursery, primary harda da secondary ne a tare. Daƙyar Baabu ya yarda dan bashi da yanda ya iya, haka aka maida Maanal makarantar su Ajwaad amma a ɓangaren Nursery. Shiko yana a primary 3 ne. To ashe rigima bata ƙare ba, dan kuwa Maanal sam bata zama ajinsu saina su Ajwaad. Anyi-anyi amma taƙi, da malaman sukaga tanada ƙwalwar karatu matuƙa, dan duk abinda akayi kafin kace me ta ɗaukesa a kanta harma tafi wasu ƴan ajin sai kawai aka ƙyaleta. Dan koma an kaita can ɗin ba zama take yi ba, sai dai taita jibgar ƴaƴan jama'a tana kukan ita dai wajen AA zataje. (Dan itace ta saka masa AA daga ji Oum ta faɗa ta kama ta haye tana kiransa AA).
       Hajiya Maanalu mai abin mamaki kenan. Dan daga Nursery 2 dai tuni tayi jumping zuwa primary 3 abinta. Hakama a islamiyya tuni ta koma ajin su Ajwaad. Dambe da rigima kuwa sai abinda ya ƙaru. Duk da tana a cikin waɗanda suka girmeta kullum cikin takalar tsiya take. Taimaka rashin kunya kace zaka daketa ka gamu da Ajwaad. Dan duk abinda zai taɓa Maanal a duniyar nan Ajwaad baya ƙaunarsa. Hatta Ammie idan ta daki Maanal sai taga fushi a fuskarsa. Idan ko su Shahidah ne duk da sun girmesa koda yake kusan sa'an Amaal ne yana girmeta kaɗan sai fa yarama mata. Idan kuwa yana gidan tai laifi Ammie tace zata daketa sai yaje yace shi a dakesa a maimakonta, idan kuma ta riga ta ritsata tana duka zaije ya kareta shi a dake san. Idan abu aka bama ɗaya ɗaya bazai taɓa cinsa ba sai ɗaya na nan. Hatta da kaya ya koma yanzu iri ɗaya ake musu, idan kuma ya banbanta na mace da namiji kamar atamfa, lass, yadi to dole a ɗakko kala guda. Ajwaad shine tsifar kan Maanal, shine rakata kitso, shine wankin ƙananun kayanta irinsu pant, hula, vest da sauransu. Haka shima nashi idan zai yi tare zasuyi tana jagwalgwalo. Tun ana ɗaukar abun nasu wasa har kowa ya fahimci ba wasan bane aka kawo ido aka zuba musu. Sai dai iyayen na matuƙar kulawa da duk wani motsinsu saboda tsoron bin wata hanya mara ma'ana da a yanzu har yaran akan samu a ciki....

     Alhamdullah a yanzu dai haka Maanal nada shekara tara cif a duniya, yayinda Ajwaad keda goma sha biyar. Suna a ajin ƙarshe na primary. Kasancewar Ajwaad nada tsayi kamar ƴan uwansa tuni ya tserema Maanal a girman jiki fintinkau duk da dama can ya fitan. Itako tana tsaka tsaki a tsayi saboda bata gama girma ba, gata muguwar siririya kamar ka hureta ta zube a ƙasa. Zuwa yanzu shaƙuwarsu ta sake wuce inda ake tunanani, baka isa kaji kansu ba. Hatta abinci tare suke cin abinsu. A hakan ma dan ana tsaye a kansu wasu abubuwan da yawa ana ƙoƙarin hanasu da tunatar da su halacci da haramcin dake a tsakanin iyakar da alaƙarsu zata yiwu. Kuma Alhamdullah suna fahimta da kiyaye abubuwa da dama duk da bawai sun balaga bane ba. Garama shi Ajwaad alamomin hakan sun fara kusantoshi yanzu...

__________________★

          Yanda take tura baki gaba ya sashi tsayawa yana kallonta. Sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga agogon falon. Ganinfa idan ya biye mata makara zasuyi ya sashi duƙawa. Dariya ta saki da siririyar muryarta kafin ta ɗane bayan nasa. Lunch box ɗinta da school bag ɗin dake ajiye ya tattara ya ɗiba sannan ya miƙe. Dariyarta tasa Ammie dake kitchen leƙowa. Takaici ya sata tsayawa kawai tana kallonsu, sai da ya kai ƙofa yana ƙoƙarin fita ta dakatar da shi.
     “Yanzu Ajwaad bazaka hutama ranka ba dai?. Ka sauketa ta taka da ƙafarta, dan ubanta ba tun jiya ta taka ƙafar ba”.
         Cikin yanayinsa na sanyin murya ya ce, “Ayya Ammie ALLAH ƙafan bai sakin mataba har yanzu. Bari muje su yaya Fadeel na jiranmu a mota”. Kafin ma ta sake cewa wani abu harya fice. Kai kawai Ammie ta girgiza tana komawarta, dan babu abinda suke buƙata yaran nan sai addu'a. Idan ta tuna mutuwa zata iya ɗaukar wani a ciki tabar wani har tausayi suke bata. Idan kaga Ajwaad na farin ciki ko surutu to tare yake da Maanal. Dan duk rashin son maganarsa sai da ta sakashi ringa yi, idan ma baiyi ba addabarsa take har sai ya tanka zata barsa. Kokuma taje ta takalo masa faɗan da dole ya tafi ramo mata......✍️.

     😀😂🤣Eh lalle su Maanal an tsula tsiya a nahiyar arewacin Najeriya 😆🏃









✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖5️⃣6️⃣


______________


........Tuni su Fawzan har sun shiga mota. Da sauri driver ya amshi kayan hannunsa, shi kuma ya ƙarasa gaba ya buɗe ya sakata dan nan ne wajen zamanta dama. Sai da ya gyara mata skirt ɗin ta sannan ya rufe ya zagaya kusa da ƴan uwansa ya zauna. Cikin tsokana da dariya Fawzan ya ce, “Oh oh Lilly bestyn Auta (Dan haka suke kiranta). Auta bestyn Lilly. Idan yaran nan kuka girma munada kallo a anguwar nan wlhy. ALLAH yasa dai kar ku haɗiye juna ko ku ƙone mu saboda eh......” ya ƙare maganar cikin shaƙiyanci. Banza Ajwaad ya masa, sai ma ƙoƙarin fiddo books ɗin Maanal yake yana dubawa. Yayinda Fadeel da suke kira (Babban yaya)  yay ƴar dariya, hakama driver. Tsagal Maanal ta ce, “Yaya F minene eh...? Kuma sai mu cinye kammu kamar mayu”.
     Dariya Fawzan ɗin ya sake kwashewa da shi. Tare da faɗin, “Lilly ba yanzu zaki san eh.. ba. Sai nan gaba. Ke dai ALLAH yabar tare”.
       

Download complete TXT · Novel page