AJIYA A DUHU BOOK 1

Chapter 51 of 76

cikin da tsirfar tsiya, yana son wancan baya son wannan. Tun yana watanni biyar yay wani irin girma na tsiya kai kace tagwaye ko ƴan uku ta ɗauka, dan Oum da Abah har tsokanarta suke akan wannan karan kodai ƴan uku ne ko twins. Murmushi kawai take yi akan batun, amma a can cikin ranta tana ma kanta fatan hakan itama. A lokacin da cikin ya shiga watanni bakwai sai wahalar ta ninku matuƙa. Har takai bata iyama kanta komai sai da taimakon Oum da Aba. A haka aka shiga watan haihuwa da ƙyar, har ALLAH ya kawo ranar haihuwar. Ansha gumurzu, gumurzu na haƙiƙa dan kwananta biyu akan gwiwa kafin a na uku ALLAH ya sauketa lafiya. Wannan karan ma dai namiji ne sargaɗeɗe mai kamanni da ƴan uwansa, sai dai shi ya ɗan ɗakko duhun fatar Mamy saɓanin Fadeel da Fawzan dake farare tarr dasu tamkar mahaifinsu da Oum. Jaririn nan ƙato ne na gaske, dan bayan fiddosa hatta ma'aikatan asibitin zuwa kallonsa suke da mamaki. Haka dai aka sallamesu suka koma gida, a wannan karon ma dangi tako ina sun cika gida anata huɗar arziƙi.
     Ƙalubale na farko akan wannan haihuwar shine tunda Mamy ta ɗaura idonta akan jinjiri wata kalar ƙaunarsa mai zafi data bambanta data ƴan uwansa ta shigeta. Ƙalubale na biyu tun a asibiti yaƙi kama nn. Ƙalubale na uku Abah da kansa suna dawowa gida gaban ƴan uwanta da nasa ya sake tisama kowa alƙawarin Mamy na ranar haihuwar Fawzan akan mallakama Oum wannan ɗan ma a karo na uku, dan haka ya sake tabbatar musu wannan alƙawari na nan daram bai canja ba. Sai dai suyima Mamy addu'a kuma da fatan alkairin ALLAH ya kawo ƴaƴa na gaba da suma zasu kasance matsayin nata mallakin. Ƙalubale na huɗu shawarar da Umma ta bada akan tunda jinjiri yaƙi kama maman Kamila bazai yiwu a barshi a haka ba fa sai a koma asibiti, koda aka koma asibitin sai likitoci suka fahimci fa akwai matsala ne, matsalar canjawar kalar nn Mamy daga fari zuwa yellow, dole suka shiga binciken ainahin matsalar, suka kuma bada shawarar sai dai a shayar da yaron madara gudun kada a shiga hakkinsa, dama gashi yanata kukan yunwa. Ita kuma aka ɗorata akan magani da tabbatar musu in sha ALLAHU komai zai wuce ta samu lafiya kamar ba'ai ba. Jin haka sai Umma tace baza'a bashi wata madara ba Oum ce zata sha magani ta shayar da shi. Baba Sardauna ya yarda da wannan shawara ta matarsa, hakama Abah da sauran dangi. Dan haka mahaifin Oum wato Dr Kasheem Kura da kansa ya aikoma Mamy ingatattun magunguna tun daga Paris da zai bata ruwan nn. Dan su basu zo ba a lokacin babu jimawa da sake haihuwar matarsa (Maryam kenan mahaifiyar Oum ina fatan kuna fahimta). Itama ta samu ɗa namiji cikin na huɗu da yaci sunan Rafeeq. Oum bataje ba saboda yanayin da Mamy ke ciki a lokacin.
      Cikin amincin UBANGIJI Oum nashan magani kuwa sai ga ruwan nn mai ƙyau. Aiko ta hau shayar da jinjirinta da yaci suna Ajwaad. Yayinda aka bar Mamy da jiyyar zuciya da kukan ɓoye. Gashi kuma babu yanda ta iya, dan ita dai tai alƙawarin nan babu wanda ya tirsasata, a zahiri kuma taƙi nuna ma kowa damuwarta saboda neman soyayyar Abah da take ganin saita wannan hanyar kawai zata iya samunta. Ita dai Oum ranta fes, ƴaƴanta uku cif sun kammala, tsakaninta da UBANGIJI sai godiya. Sai kuma aminiyarta Kamila da har abada take jin a ranta bata da kamarta a wannan duniyar idan ka cire iyayenta da iyayen riƙonta da mijinta. Ƙaunar yaran nan uku take da zuciya ɗaya, da iya gaskiyarta. Bata taɓa jin ƙaiƙayin cewar ba itace ta haifesu ba. Kai ita mantawama take da ba itan ce ta haifesun ba. Dan a zahirance dai Mamy kawaici take yi. Bata taɓa jingina kanta da yaran koda wasa. Sai ta faki ido ta dinga aibanta Oum a zuciya, gefe ga tsananin kishinta da take ji da hassadar finta komai na rayuwa da tayi. Wanda ada can iyakar kishin soyayyar mijinta Aliyu kawai take ji. Amma bayan auren data sake fahimtar wacece Oum a wajen Aliyu da nasarorin rayuwa dana iyayenta ke da shi sai hassadar hakan ta shigeta.
        (Wannan hassadar al'adace kamar a zukatan matanmu akan kishiya. Ya rabba ALLAH ka yaye mana hassada dan mugun dafi ce mai kassara rayuwa da cigaban cikinta)........✍️



✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖6️⃣9️⃣


______________


.........To rayuwa fa ta fara shuɗawa. Abubuwa da yawa nata faruwa. Ciki harda yaye Ajwaad da Oum tayi bayan cikarsa shekara biyu cif yana sha daga jikinta. Tuni ta sanyama Ajwaad Auta, tunda dai Mamy da kanta ta tabbatar da iya gejin abinda zata bata kenan haihuwa ta gaba tata ce. Autancin ko yabi Ajwaad tun da ƙarancin shekaru. Dan ALLAH yayisa irin yaran nan masu tsananin ƙulafucin iyaye. Sam baya ƙaunar koda wasan wasa Oum tayi nesa da shi. Wani lokacin ko toilet ta shiga yana ƙofar bayi yana jiranta har saita kammala abinda take ta fito. Idan zataje wajen Abah kuwa a ranar girkinta sai fa da wayo da dabara idan ta tabbatar barcinsa yayi zurfi can cikin dare. Wani lokacin kuma dashi dole take tafiya ta kwantar da shi a falo ko in barcin nasa yay nisa ta maidosa cikin ƴan uwansa. Akowane motsinsa shi dai Oum ce. Gashi da shegen ƙiwa tun yana watanni biyar zuwa shida baya yarda da kowa sai Oum sai Fadeel idan yaso. Amma ko Abah da Mamy basu isa taɓashi ba ya hau ihu yana bin Oum da kallo yana kuka. Sanda ya cika shakara ɗaya da wasu watanni kuwa idan ka takura sai ka ɗaukesa cizo zakasha ta yanda dole ka saukesa ya koma wajen uwarsa. In ma anguwa suka fita bai yarda wani yako taɓasa daga jikin Oum. Baba Sardauna ne ma ke ɗan samun wannan alfarmar shima ana ɗan yarda da shi saboda yana bashi irin chocolates ɗin da yake so. A haka ya cika shekara huɗu aka saka shi a makaranta kamar sauran ƴan uwansa. Duk da su an sakasu tun suna da shekara uku-uku, shiko ƙulafucin uwa ya hanashi. A yanzun ma dai badaƙala ake sha dan baya ƙaunar zaman makarantar, yata kuka kenan da kiran Oum! Oum! Shi akaisa wajen Oum ɗin sa. Shi gida zaije wajen Oumyn sa. Karatu yaƙiyi ya hana sauran yara yi. Duk wanda ya nuna kulawarsa da son rarrashinsa ya danƙarama yaro cizo sai an rabasu da ƙyar. Ganin haka yasa makarantar suka bada shawarar a ƙara masa lokaci ya ƙara wayo, dan inma ba hakaba bafa karatun zai yi ba. Dole su Oum suka yarda da hakan, amma tana ƙoƙarin masa a gida ita da Fadeel musamman na ɓangaren addini. Gashi kuma da ƙwaƙwalwa Masha ALLAH.
        Sai da Ajwaad ya cika shekara bakwai a duniya sannan Mamy ta sake samun ciki, a lokacin yana zaman makaranta da ƙyar dan yana a nursery 2 ma. A islamiyya kuwa Alhamdullah ya tashi da ƙwazon karatu kamar sauran ƴan uwansa biyu. A wannan karon abinda ya fara tadama Mamy hankali kamar Abah bai damu da cikinta ba kamar ukun can na farko, sai Oum ce ma ke dama-dama da ita da bata kulawa. Idan tai magana yace to mikuma ya rage shida keda uku rigis, ai sai fatan alkairi da addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya. Wannan furuci nashi na cimata zuciya, amma haka take dannewa ta maida abin wasa. A haka ta shiga watan haihuwa, a kuma lokacin Abah ya fara musu gini dan yace wannan gidan ya musu kaɗan ga zuri'a suna tarawa. A wata juma'a Mamy ta sauka lafiya ƴan biyu duk maza. Musalta muku irin farin cikin da wannan ahali suka shiga a wannan karon ma ɓata lokaci ne. Anyi shagalin suna kamar yanda akai na baya, duk da Mamy taso ace na wannan karon yafi na bayan armashi kodan biyu data santalo. Haka dai suna ya tashi lafiya yara sukaci sunan Hassan da Hussain. Dan tace bata son a canja mata suna a barsu da nasu. Duk da a wannan karon Mamy batace ta mallakama Oum su ƴan biyu ba bata fasa yin hidima a gareta da jinjirayen ba kamar yanda ta saba. Dan har takai Ajwaad na nuna kishinsa a fili, sai dai suyita masa dariya kawai. Bayan yaye su ƴan biyu da wata uku Hussain ya fara laulayin haƙora, ya dinga gudawa irin na haƙora mai wahalarwa. Abin ALLAH kwana biyu kacal a wannan halin UBANGIJI ya ɗauke abinsa. Duk da rasuwar yaro ce ta girgiza wannan ahali, dan daga Oum har Mamy kuka rurus sai Abah ne ke lallashinsu, da ƙyar suka haƙura suka sabarma kansu da rashinsa. Sai kuma tunda Hussain ya rasu shima Hassan lafiya ta masa ƙaranci. UBANGIJI mai rahama da jin ƙai shima bai cika kwana arba'in ba yabi ɗan uwansa. Ai neman zautuwa Mamy tayi, da ƙyar ake tausarta. Sai dai kuma babu yanda ta iya da hukuncin ALLAH.
       Tun bayan rasa ƴan biyu ko ɓatan wata Mamy bata sake yi ba. Har suka tare asabon gidansu da a yanzu suke ciki wanda ke maƙwaftaka da nasu Maanal. Zuwa yanzu tsanar Oum Mamy keji mai zafi a ranta, amma a zahiri bazaka taɓa fahimtar hakan ba, gefe ga uwarta da ƴan uwanta dake zugata. Ba Oum kawai ba, hatta duk wanda Oum ke huɗɗa da shi Mamy ta tsanesa. Dan haka bata taɓa son Ammie da su Maanal ba. Amma koda wasan wasa bata taɓa nunawa a koda fuskarta ba. Sai ma nunawa take kamar tanama Oum kawaici musamman akan tarayyar Maanal da Ajwaad dake a bayyane ga kowa. Ita ko Oum soyayya takema Mamy ta gaskiya da kuma zuciya ɗaya, jin girmanta take da kimarta ta yanda zuciyarta koda hasashe bata taɓa kallon munininta ba. Kai a yanzu koda Abah yazo yace da Oum ga munin Mamy to tabbas bazata amince ba. Ta bata matuƙar yarda da gaskiya ta yanda bata ko jin wani ɓurɓushin kishita a ranta. Kai sam bama ta mata kallon kishiya sai ƴar uwa. Hatta da sirrinta bata taɓa canjawa daga yanda take sanar mata ba a sanda suna amintaka da ƙawance. Komai buɗema Mamy take da zuciya ɗaya ta nema shawara. Kuma a cikin ƴan uwanta kaf babu wanda ya taɓa kallon illar hakan dan suma yarda ɗaya suka bama Mamy saboda ɗunbin hallaci da yakana da dattakon data nuna ga Oum ɗin. Lallai Mamy ta samu fada da soyayya tako ina daga zuri'ar Baffa Ishaq Darma. Yarda suke mata ta gaskiya, basa taɓa banbantata a matsayin bare a cikinsu, basa taɓa banbantata tsakaninta da Oum dake matsayin tasu. Kai sai suyi mata abu basu yima Oum ba musamman ma mahaifinta Dr Kasheem Kura. Dan shi yakance Mamy itace ƴarsa. Oum kuwa ta Baba Sardauna ce.
        Itama a zahiri ta riƙe dukkanin abinda zasu kalleta da wannan mutuncin, duk da zuciyarta cike take da shirin maido da ƴaƴanta gareta komai tsahon lokaci da rayuwa zata bata. Hakama duk damar data samu daga Abah da yarda bata gamsar da ita ba, kullum cikin sake harin ninkin baninkin ɗinta take yi. Duk da kuwa ta wawashi kaso mafi girma daga soyayyar tasa. Dan tun fara girman su Fadeel Oum ta sake sallama mata Abah ɗin kaso saba'in cikin ɗari, ita kuma yake riƙe da talatin cike da kawaici da dattakonta. A yanzu ko tafiya Abah zai yi da ita ne. Idan wani abu ya taso kai tsaye Oum zatace yaje suyi da Mamy ita bazata iya yin nesa da yaranta ba. Tun abin na bama Abah haushi har ya haƙura ya sallama dan ya fahimci mai raba Fateema da ƴaƴan nan nata sai dai ALLAH. Musamman Autan ta uban ƴan ƙalata da ƙulafucin uwa.
       Duk da Oum bata taɓa fitowa ta sanar ma yaran ainahin mahaifiyarsu ba tana nuna musu girma da darajan Mamy a garesu. Kullum cikin cusa masu soyayyarta take a zukatan yaran cike da hikima. Tana ƙawata musu girma da kimar Mamy a zukatansu. Tun abin baya tasiri a ransu harya fara. A hankali Fadeel da Fawzan suka ɗan fahimci wani abu kaɗan bamai yawa ba. Sai dai hakan bai taɓa canja musu Oum ɗinsu a matsayin da suke kallonta ba. Ita dai suka sani, ita kuma suke kallo da matsayi irin na uwa da mahaifiya. Amma suna girmama Mamy da bata hakkinta da mata soyayya kamar yanda Oum ta koyar da su take ma kan koyar da su ɗin. Shi dai oga Ajwaad Auta Oum ɗinsa kawai ya sani. Shi uban kowama ya mutu har liman in dai za'a bar masa Oum ɗinsa. Farin cikinsa ce ita, sannan duniyarsace. Bai haɗa soyayyarta data kowa ba a duniya...
      Wannan halin na Ajwaad na cima Mamy rai matuƙa, dan ALLAH ya jarabceta da soyayyar Ajwaad fiye da duk sauran yaranta. Ƙaunar yaron take har ƙarƙashin zuciyarta. Ga shi kuma hankalinsa san baya a kanta yana akan maƙiyarta ne. Shiyyasa take sake jin ninkuwar zafin Oum ɗin matuƙa. Gashi ta fahimci itama Oum ɗin tanama Ajwaad wata irin soyayya mai girman gaske. Hakan na nufin bayan Aliyu sun sake yin tarayya akan abu guda kenan. Wato soyayyar AJWAAD ALIYU ABUBAKAR DARMA...

     _MUN SAKE DAWOWA DAI CIKIN LABARIN RAYUWAR AJWAAD DA MAANAL DATA GABATA🙏😀_

   
*GIRO:-* A Giro dai an ɗaura auren Babu da amaryarsa Safarah. Safarah yarinya ƙyaƙyƙyawa mai busashen ido. Dan cikakkiyar ƴar tallace a tashoshin motoci na yankin ƙauyen Giro da cikin Suru. Musamman a ranakun kasuwanni. Kai har cikin Kebbi idan ta kama suna zuwa kawo kayan sayarwa ita da ƙawayenta. Gwaggo ta zaɓama Babu ita ne dan a cewarta itace dai-dai da Asiya. Anko sha biki, dan su Ammie sun sha kallo. Bajinta sosai Gwaggo tayi a bikin dan dabbobinta har goma ta saka a kasuwa. Bayan tarewar amarya a nan dai gidan ɗakin dake a tsakanin Gwaggo da Ammie ango yasha bidiri. Dan Babu dai kura ne ba'a bashi ajiyar nama. Duk da ma dai abin bai masa armashi ba saboda samun Safarah ba'a cikakkiyar budurwa ba ita dai. Amma tsabar iya bariki na yarinyar nan da dudu shekarunta goma sha tara ne a duniya sai ta dinga zumbuɗa masa ihu da kururuwa ita a dole tana shan wahala. Wannan ihu ya tadama Ammie hankali, bawai akan kishi ba, duk da bazatace bata kishin mijin nata ba. A'a saboda su Shahidah ne. Dan takai yaran nan sai da suka farka a barci suma. Yayinda itama kanta Gwaggo data fito tsakar gida a wannan tsohon dare take faman kiran sunan Babu da gargaɗinsa akan wai yabi Safarah a hankali, ya dai san yarinyar ƙarama ga mutuncinta ta kawo. Wannan abu shine ya taru ya saka Ammie kuka dan su Amaal nata jera mata tambaya akan ko mi ya samu amaryar haka. Sai dai bata kula yaran ba, daga ƙarshe ma ta musu tsawa suka kwanta. A ranta dai tana sake godema ALLAH da su Abah suka wuce da Maanal. Dan tabbas kaɗan daga aikinta tama fita itama koda safe ta tsare Babu ɗin da tambayoyi.
      Wannan kuka da amarya tasha da ihun iskanci yasa kowa ya yarda ta kawo mutuncinta. Shi ko Babu tai masa ɗaurin goro dan bashi da damar  musawa. Ga wata irin kunya da nauyin Ammie da ALLAH ya jarabceshi da ita. Dan ƙiri-ƙiri ya kasa yarda ya haɗa ido da ita a wannan yinin baki ɗaya. Ko hanya suka haɗa duk sai ya daburce. Itako Ammie ta dake abunta ko'a fuska bata nuna masa ba. Amma a dare na biyu saita tura Amaal da Shahidah kwana ɗakin Zainabu ɗaya daga cikin matan gidan, kasancewar tasan mijinta baya gari. Dan gara ta nesanta yaranta da shiyyar gaba ɗaya kafin su fahimci abinda ke faruwa.
         Aiko Ammie tayi dabara, dan daren yau ɗin ma bata canja zani ba. Sai da Safara tayi duk iya yinta ta hillaci Babu ya kasance da ita. Gashi dama ta ɗirki magunguna shima an ɗirka masa ta hanyar abinci. Ai sai ihun ya zama nasu su biyu yau ita da shi. Kai jama'a wannan iskanci dami yay kama haka. Cewar Gwaggo cikin mitar son yin barcin da suka hanata. Amma da safe ko'a fuska bata nuna ba saima kulawa take bama amarya ta musamman dan Ammie taji haushi. Sai kuma Ammien ta tabbatar mata ita ɗin ƴar halak ce dan bata nuna damuwarta ba koda a fuska.  Kasancewar daren jiya ta kwana salla da karatun Alqur'ani sai ta tashi sakayau zuciyarta cike mamaye da farin ciki. Musamman daya kasance da safe ta kira Oum a waya sun sha hirarsu harda Maanal dake ta faman bata labaran daɗin da Oum da Bestyn ke ciyar da ita. Shi kansa Babu ɗin sai yanayin na Ammie ya sake jefa shi a ƙaulani da ɗunbin kunyarta da shakkarta ma..........✍️



✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖7️⃣0️⃣


Download complete TXT · Novel page