AJIYA A DUHU BOOK 1

Chapter 54 of 76

burin akan Ajwaad da Maanal. Sai kuma bayan kwana biyu dayin walimar yazo har gidan abinda bai cika yi ba. Zaunar da Oum da Abah da Mamy yayi, bai ɓoye musu komai ba akan batun da yazo da shi na son haɗa auren Ajwaad ɗin da Maanal tare da ƴan uwansu. Ya kuma kawo musu hujja mai ƙarfi akan abinda ya hango game da shaƙuwar yaran. Dan gara ya kasance akwai igiyar aure a tsakaninsu gudu sharrin shaiɗan saboda kusancinsu yayi yawa. Gashi kuma suna a wata gaɓa ce mai ban tsoro akan duk wani yaro dake a wannan shekarun musamman ma shi Ajwaad da Babban Yaya ya sameshi ya warware masa komai akan halin da Autan yake ciki tun kafin ya koma, shiyyasa ya saka ido shima ya fahimci komai ya ya kuma tabbatar. Su duka ukun babu wanda ya musa ko jayayya akan abinda Baba Sardauna yazo da shi. Sun kuma gamsu da cewarsa akan ai shiru da batun kada a sanarma Ajwaad ɗin da Maanal. Su kuma barsa da Baabu shi zai yi magana da shi.
     Haka kuwa akayi, Baba Sardauna ya kira Babu har gidansa sukai magana ta fahimta. Ya kuma gamsu shima ya bada goyon baya. Bayan haka Baba Sardauna yay kiran Baba Haruna shima a waya suka tattauna. Shima kuma ɗari bisa ɗari ya gamsu. Daga haka aka fara shirin bikin ƴan gata su shidda. A ɓangaren Babu babu wani ƙwaƙwƙwaran shiri, dan gwaggo da Amaryarsa sun gama zugesa tsaf ta bayan fage. To dama dai Abah yayi niyyar shiryama yaransa biyu gida da kansa. Shi ko Ajwaad dama sai sun kammala secondary za'ayi biki. Oum kuwa duk wani abu da uwa ya kamata tayi ta ɗauki ɗammarar yin komai, duk da haka Ammie ta sameta da abinda ke a hannunta, ta kuma nema shawararta akan tunkarrar Babu da gadonta da iyayenta suka bari. Oum ta bata goyon baya badan zata amshi kuɗin a hidar yaran ba, sai ɗan abinda take shiryama zuciyarta. Tana shiri akan in har aka kammala bikin yaran to lallai koma miza'ayi dole Babu ya saki Ammie. Dan ta gaji da ganinta cikin wannan zaman zaluncin da ƙuncin. Ita ba kwanciya da miji ba, ita ba ƴancin aure ba, duk ta lalace ta rame ta fita hayyacinta. Kamar ba Ammie ƴar gayu ƴar ƙwalisa ba. Sarkin tsafta da gyara jiki. Tofa dole ne su taya mata ta amshi hakkinta a wajen Babu tun yanzun.
     Babu wasa kuwa Ammie ta tunkari Babu da batun kadarorinta da komai ma da iyayenta suka bar mata akan son yin hidimar biki, abinda ya tadama Babu hankali kenan, dan kuwa ya salwantar da kaso biyu bisa ukun wannan dukiya, suma kuma dangi sun ci. Shi kansa kaso ɗayan daya rage ma yana a ƙila wakala ne kawai. Ƙin cema Ammie komai yay a lokacin, face kalmar “Yaji”. Yay gaba abinsa. Bata damu ba, ba kuma ta kawo komai a ranta ba tunda rayuwar daya ɗauka ma kansa kenan a yanzu..........✍️



✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖7️⃣3️⃣


______________


........Matakin farko na shirin biki shine shirya zuwa Dubai da Oum tayi tare da Umma (Matar baba Sardauna) da Gwaggo Khadijah. Sai dai zasu fara zuwa suyi umrah ita da Ajwaad da Fawzan da Maanal. Amaal da Shahidah kuma za'a fara musu gyaran jiki dan ita Maanal bazata tare ba sai sun kammala secondary. Sunyi wannan tafiya Maanal na'a cikin ɗunbin farin ciki, dan wannan shine karonta na farko hawa jirgin sama. Fawzan ya tasata da tsokana da dariya. Itako ko'a jikinta. Sai mutum nata data dama da surutu wato Ajwaad, yana ɗan biye mata sama-sama batare da tasan dalilin komawarsa hakan a gare ta ba yanzu. Sunyi Umrah Alhmdllh, inda suka samu kwanaki goma sha biyu kafin su nufi Dubai, can suka haɗu da Umma da Gwaggo Khadijah da suka taho daga Nigeria su kuma. Duk kannin abinda ya kamata an shirya shi, suka tura kaya Nigeria, a kuma wannan lokaci ne Ajwaad ya bada aka yi agogon nan da Manaal ta zana ta hanyar babban aminin Baba Sardauna dake da company anan Dubai. Kusan komai a gaban Ajwaad aka yisa, wannan kuma shine ya zama dalilin farko na fara jin sha'awarsa akan hakan. Duk da yana da nashi burin.
      Sun dawo Nigeria suka iske Saheeba a gidan, wai tazo hutu. Babu wanda yay magana balle kawo wani abu a cikin ransa game da haka. Tunda dama tana ɗan zuwa jefi-jefi (Saheeba ɗiya ce ga ƙanwar Mamy). Bayan dawowarsu da kwana biyu babban yaya ya iso shima. Shirin biki fa ya fara kankama, dan ta ko'ina babu wasa. Sai dai Ammie da Baabu suna tsaka da tafka rigima saboda wasa da hankali da yaketa mata akan batun hakkinta, wato dukiyarta da iyayenta suka bar mata. Oum ce ta tausheta akan ta bar batun har ALLAH yasa su Baba Haruna suzo wajen biki, koma mi za'ayi sai ayi kawai. Da wannan ta tausheta akan al'amarin....

       A ranar akai kamu, normal kamu ne dai irin namu na mutan da, ɗan turare kawai aka fesama Amaal da Shahidah, sai ƙawayensu daketa ƙunshi. A ranar gayyar mutanen Giro suka iso. Hakama can gidan su Oum mutanen Yola sun iso. Sai wanda ke anan cikin Kano ta ɓangaren su Oum data ɓangaren Mamy. Dama ƴan paris kwanansu uku kenan. Koda yake Mammah ce kawai tazo saboda yara na karatu, hatta Auta Rafeeq ba'azo da shi ba.
      Washe gari aka shirya walima anan cikin gidan su Oum ta iya mata, Umma ce ta ɗauki nauyin malaman da zasuzo mata suyi lectures da abincin da za'aci. Wannan Rana itace tushen komai na wargajewar alaƙar waɗan nan ahali guda biyu. Ranar da zukata suka rarrabe cike da ƙuna da girgizuwa. Ranar da komai ya lalace, zaren ƙaddarar daya ƙullesu a waje guda shekara aru-aru jarabawar ƙaddara ta datse shi da almakashi mai matuƙar kaifi. Datsa irin ta kwaf ɗaya da har yanzu an rasa mai sake kamawa ya ƙulla shi.
      Masu shirya waje sun kammala wajen ƙarfe biyu na rana, a dai-dai lokacin Maanal na daga can ƙarshen garden ɗin zaune saman lilo ita kaɗai. Tunda ta tashi bata jin daɗi yau, haka kawai kuma sai take son kaɗaici. Kwana kusan huɗu kenan tana acan gidansu, yanzu ma hayaniyar ƙawayen su Amaal suka isheta dan tana ɗakinsu kwance yasa ta fito ta dawo nan gidan su Ajwaad. Koda ta shigo ciki nan ma hayaniyar tayi yawa, sai kawai ta nufi ɗakin su Ajwaad. Cike ta sameshi da abokan su Fawzan, sai dai babu Bestyn nata. Gaishesu kawai tayi ta ɗakko wayar Ajwaad dake caji a gefen gadonsa ta fito. A hanyar fita falon suka kusa cin karo da wata ƴar budurwar yarinya kanta ɗauke da boket cike da gorinan zoɓo da kunun aya. Sosai Maanal na son zoɓo a rayuwarta, dan haka ta tsaidata tana tambayarta. Yarinya ta bata amsa da cewar mamansu ce tace ta kawoma Oum a ƙara a baiwa baƙi. Sai kuma ta nuna mata na hannunta, ta ce, “Wannan kuma zan bama yayana”. Maanal tasan yayan nata abokin Fawzan ne sosai, dan baima da wani aboki sai shi, suma dai maƙwaftansu ne. Sai kawai ta amshi na ledan ta ɗauki ɗaya. Daga haka ta fice ita kuma yarinyar tai ciki tana tura bakin haushin ɗaukar ma yayanta da Maanal tayi, babu kuma damar magana tasan zata iya dukanta, dan yaran anguwar nan kusan duk tsoron Maanal suke saboda fitinarta. Manyan ma in dai kace zaka shiga sabgarta kasha rashin kunya kuwa. Can garden ta nufa, sai da ta gama kalle gyaran da akai sannan ta wuce can ƙarshe ta zauna a saman lilo ta buɗe zoɓon ta fara sha tana game a wayar Ajwaad ɗin. Tafi mintuna biyar da zama sai gashi, sai da ya kai zaune a kusa da ita sannan ta ɗago duk da taji ƙamshin turaren da suke amfani da shi tunda ya shigo wajen. Harrarsa tayi, shima ya rama dan faɗa sukai kwana biyu kenan shiyyasa ma ta koma gidansu. Koda ya rama hararar sai ta tura baki gaba. Baki ya taɓe da ƙarɓar zoɓon hannun nata shima ya hau sha. Haka suka dinga shan wannan zoɓo babu mai ma ɗan uwansa magana har suka kammala. A lokacin ne ya fiddo wani ƙyaƙyawan box ya miƙa mata. Kallon box ɗin tayi, sai kuma ta kallesa, ta kai hannu zata amsa ya janye da faɗin, “Oh nama manta haushina kike ji fa”.
       “To bana huce ba”. Ta faɗa kamar zatai kuka.
    “Kin tabbata kin huce?”.
Da sauri ta ɗaga masa kai alamar eh. Sai ya sakar mata murmushi ya miƙa mata box ɗin. Wayarsa ta ɗaura masa a saman jikinsa, ta hau kiciniyar buɗewa. Da wani irin zaro idanu ta ce, “Wooow!!! Besty!. Amma agogon nan ya haɗu wlhy”.
    Murmushi ya saki mai sanyi, ƙyawawan fararen idanunsa na kallonta da wani irin yanayi mai zafi. Cikin ƙanƙanuwar muryarsa data ƙara ƙanƙancewa a yanzu ya ce, “Besty, ai duk ƙyawunsa kin fisa ƙyau. Sannan kefa kika zana shi da hannunki shekaru shida kenan”.
       Itama cikin sanyi ta ce, “Ni kuma Besty!”.
    “Yes! Kefa”.
Ya bata amsa yana zaro wani note book a aljihunsa ya miƙa mata. Amsa tai tana kallon zanen agogon da tabbas ta tuna itace ta zana shi. Sai kawai taji hawaye sun cika mata ido. Dan zanen agogon bashi da maraba da agogon daya batan. Cikin rawar murya ta ce, “Besty!”.
      “Uhmyim Bestyn Besty!”.
   Ya faɗa da wani irin shauƙin da shima kansa bai san mi yake yi ba. Ga idanunsa na wani irin mata kallo mai zafi, sun kuma ƙanƙance sun kaɗe kamar ba shi ba. Itama kanta kallon nasa take tsakkiyar ido da wani irin yanayi dake cizon zuciyarta. Fin mintuna biyu suna kallon junansu kafin kiran waya ya katse su. Wayar ta kalla cike da kasala, ganin Babban Yaya ya sakashi ɗagawa murya a sarƙe. Bata san mi babban yayan ya gaya masa ba. Ya dai miƙe a raunane yana kallonta da miƙa mata wayar. “Ina zuwa ki jirani anan”.
    Kanta kawai ta iya jinjina masa. Sai da bayan ya wuce ta iya sauke numfashi. Sai kuma cikinta yay wani irin murɗawa. Fuska ta yamutse da sakin ƴar ƙara tana dafesa da hannu biyu. Sai kuma jikinta ya kama rawa. Tama rasa yanda zata fassara ciwon cikin nata. Ta jima tana matse-matse kafin ya saki mata. Sauka tai akan lilon ta wuce cikin gidan neman Oum danta faɗa mata cikinta na ciwo. Sai dai koda ta shiga ɗakinta cike yake da baƙi, ita kuma bata a ciki. Fitowa tai domin nemanta cikin nata ya sake murɗewa. Da ƙyar ta iya kai kanta ɗakin su Ajwaad dan gara ta nemosa shi sai ya nemo mata Oum ɗin. Cikin ɗakin yanzu kam babu kowa saɓanin ɗazun, ga cikinta yay matuƙar ƙullewar da tafi ta farko, dole ta durƙushe gaban gadon Ajwaad ta dafe cikin nata hawaye masu zafi na rige-rigen sakko mata daga idanunta zuwa kumatun ta. Tun tana fahimtar halin da take ciki har komai ya fara mata nisa. Sama-sama taji ƙarar buɗe ƙofa, tare da ƙamshin turaren Ajwaad. Kamar muryarsa taji yana kiran sunanta a rikice, sai kuma taji ya ɗagata gaba ɗayanta ya maida saman gadon, tana ƙoƙarin yimasa magana taji ya kwanto mata a jiki ya rungumeta, duk da a yanayin da take sai da taji hankalinta ya tashi, dan abune da kullum ake musu nasiha a kansa. Oum tayi, Ammie tayi, Abah da su babban yaya da su Didi suyi. Jikinta ne ya kama rawa jin yana ƙoƙarin cire mata kaya, ga lips ɗinsa na ƙoƙarin sauka akan nata. Ƙoƙarin turashi take amma bata da wani ƙarfi, sai ma kama hannunta da yay duk biyu ya murɗe da ƙarfin da har sai da taji zafin har a cikin ƙwalwar kanta da tsakkiyar zuciyarta. Ya kuma danne mata baki ta yanda ta kasa ihun datai niyyar yi. Daga haka bata sake fahimtar komai ba sai wata irin rikitacciyar hayaniya da ihun mutane mai hawa saman kai......
         A hankali ta shiga buɗe idanunta da sukai mata nauyi, hakama jikinta kamar ba nata ba, ga wani irin zafi da take ji acan ƙasanta. Akan Oum dake a rungume da ita tana kuka ta saukesu, sai kuma ta fara bin mutane da kallo. A tsakar gidansu ne, saɓanin gidan su Oum data san ta shiga. Ba kowa ke hayaniyar nan ba mai ban tashin hankali sai dangin su na Giro, gwaggo har riƙeta ake saboda yanda ta birkice tana zage-zage daga ita sai bujen cikin zani da riga. Amma zani da ɗan kwali duk ta wancakalar. Gefe su Shahidah ne ke kuka suna rungume da Ammie dake kwance kashirɓan. Sam Maanal ta kasa fahimtar komai, face cigaba da kallon kowa da sauraren ihunsu da sam bata fahimtar komai a ciki. A haka Abah da baba Sardauna da likitan data san family doctor ɗin su Oum ɗin ne suka shigo. Abah da shima yake a matuƙar damuwa ne ya bama Oum umarnin ɗaga Maanal zuwa ciki. Amma sai Gwaggo tace Oum bazata shiga musu ba, kuka Oum ɗin ta sake fashewa da shi mai ban tausayi. Hakan bai sa Gwaggo taji tausayinta ba, ta saka ƴaƴanta biyu kama Maanaal zuwa ciki, a haka doctor ya bisu bisa umarnin baba Sardauna.
      Fin mintuna ashirin sannan doctor ya fito, zuwa sannan gidan ya ɗan lafa bisa tsawatarwar baba Haruna da basu jima da isowa ba. Doctor ya buƙaci ganin iya su Abah, amma gwaggo tace sam ba'a isa ba, ya faɗi duk ma abinda zai faɗa anan gaban kowa. Dan ita bata son munafunci. Ganin yanda take nema tada sabuwar tarzoma Baba Sardauna yace ya faɗa ɗin. Cikin damuwa doctor ya tabbatar musu amma Maanal fyaɗe. Kuma dole ai gaggawar zuwa da ita asibiti saboda jinin dake zuba a jikinta yana ƙara yawa. Wata irin kururuwar tashin hankali gwaggo ta fasa ita da sauran ƴan Giro, yayinda Oum ta yanke jiki ta faɗi. Dole aka kwashi Oum zuwa gida, Maanal da Ammie kuma asibiti.
     Anan gidan su Oum ɗin ma dai a harmutsen yake. Ga Ajwaad ya kulle kansa a ɗaki anyi-anyi ya buɗe yaƙi. Sai da aka ɓalle ƙofar. Samunsa sukai kwance wanwar a ƙasa babu numfashi, ga jikinsa duk ya ɓaci da jini, shima dole aka kwashe shi zuwa asibitin....

     _____________★

       Komai ya dagule, dagulewa mai ban tashin hankali ga waɗan nan ahali guda biyu. Ɗaurin aure dai bai yiwuba washe gari. Dan anyi zama a tsakanin manyan ana tuhumar Ajwaad da tun a daren jiya ya farfaɗo akan wannan ruɗaɗɗen al'amari. Ya jima bai tankama kowa ba, kafin ya buɗe baki da ƙyar yace musu eh ya aikata.
       Wannan amsawa tashi ta matuƙar birkita kowa. Ajwaad ɗan shekara ashirin da ɗaya a duniya, da yarinyar da suka rayu tun ƙuruciya. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Ran baba Sardauna a ɓace ya ce, “Shike nan tunda ya amsa ya aikata ɗin sai a ɗaura musu auren yau suma su tare kawai kamar sauran ƴan uwansa. Amma mi, a mamakin kowa sai Ajwaad ɗin ya shiga girgiza musu kai da faɗin, “Aure? Baba kuyi haƙuri ban taɓa kallon Maanal da sigar zama matar aure a gareni ba. Ita ɗin ƙanwata ce ai..”
     Cikin ɓacin rai Baba Sardauna ya katsesa da faɗin, “Amma ka keta mata haddi?!!”.
      “Kuskure aka samu”.
  Ajwaad ya bada amsa babu ko ɗigon damuwa balle nadama a tattare da shi. Wani irin mari Abah ya fara sauke masa. Da ƙyar aka iya riƙesa dan hadda hauri ya fara kai ma Ajwaad ɗin. Da ƙyar aka samu ya zauna yanata zaginsa ga hawaye ba zuba masa. Tabbatarma Ajwaad yake dolene ya auri Maanal. Dan haka babu fashi za'a ɗaura auren yau ɗin na na su duka ukun. Zaram gwaggo tace sam bazasu haɗa zuri'a da su ba. Idan kuma har Babu ya amince babu ita babu shi har abada sai ta tsine masa wlhy..........✍️

_Tofa wannan fa shine rikici._




✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖7️⃣4️⃣


______________


........Hankalin kowa ya tashi a falon. Aka shiga ƙoƙarin fahimtar da ita amma tace bafa zai yiwu ba, tana kan bakanta. Babu ya rasa yanda zai yi, jikinsa sai rawa kawai ma yake yi. Wannan ɓacin rai yasa Baba Haruna yanke jiki ya faɗi a falon, ga shi yanzu baida iko a kanta tunda babu aure tsakaninsu. Dama yana da hawan jini. Babu shiri aka kwashesa zuwa asibiti, sai dai kafin ma akai rai yayi halinsa ALLAH yay masa rasuwa.
     Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wannan rasuwa ta sake harmutse kowa. Duk yanda su Abah suka kai da son a sake zaman sassantawa bai yiwu ba. Dan baba Haruna kafin ya rasu yabar wasiyyar a maidashi tushensa a biznesa dan ALLAH. Wannan yasa tun a ranar kaf mutanen Giro har su Ammie da su Maanal dake a cikin wani birkitacen yanayi kama hanyar Kebbi. Kwana sukai a hanya, sai washe

Download complete TXT · Novel page