AJIYA A DUHU BOOK 1
Chapter 56 of 76
akan ku yarana. Ina roƙon ku kuyi haƙuri da koma minene zukatanku suke tunawa da suka faru a baya. Ba'a fushi da iyaye, ba kuma a ƙin su sai idan akan abinda zai zama saɓon ALLAH ne. Koma minene ya faru ya rigada ya farun ya wuce. To a barsa a ya wuce ɗin a tari gaba. Yau ga mahaifinku sunzo garemu da muhimmiyar magana kamar yanda suka faɗa, sai dai dama bamu kai ga tattaunata ba ALLAH ya kawo ku. Dama a nawa shirin shine na buƙaci ganinku a gobe idan ALLAH ya kaimu, sai kuma komai ya sauƙaƙa.” Sake maida hankalinsa yay ga su Babu, fuskarsa da murmushi ya cigaba da faɗin, “Inaga tunda ALLAH ya sauƙaƙa gasu sunzo kafin ma mu nemesu ya kamata mu tattauna ko”.
“Hakane”. Cewar Kawu Aƙilu yana gyara zama. Sai kuma cikin dakiyar murya ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda ka faɗa abinda ya faru ya riga ya wuce hakane Alhaji, dan haka maganar tuna baya da anyi kaza ko anyi kaza babu zancen maimaita shi ko tada shi. Dama munzo nan ne akan batun ita Maanal, wanda yake neman aurenta yaje garemu a satin daya gabata kuma mun bashi. Saboda dalilan ganin shi ɗin mutumin kirki ne da muke da tabbacin zai riƙeta da mutunci kamar yanda muka samu sauran ƴan uwanta a mutuncinsu.......”
Cikin mamaki da ruɗani Ammie da Nene da su Maanal duk suka kallesa. Yayinda Daddy ya kasa jurewa shima dan shi zatonsa haƙuri suka zo basu da neman yafiyar su Ammien akan abinda suka aikata musu a baya, ashe wata fitinar ce suka zo da ita kuma. “Me neman aurenta kuma? Wanene shi haka da mu anan bamu sanshi ba?”. Cewar Daddy da mamaki.
Wani irin ɗaure fuska gwaggo tayi, Babu zai yi magana ta hararesa. Cike da isa ta ce, “Sunansa Alhaji Bukar. Sanata ne babba a ƙasar nan, kuma mun bashi, munzo nan ne ma saboda mu tabbatar muku mun bashin sannan mu wuce da ita can Giro dan nan da sati biyu za'ayi biki kamar yanda ya buƙata”.
Tuni zufa ta gama wanke Daddy, ya dai daure da ƙyar ya maida dubansa ga Maanal da take ma su gwaggo wani irin shegen kallo, sai dai uffan batace ba. “Manaal” Daddy ya kirayi sunanta a hankali. Juyawa tai tana amsa masa.
“Waye kuma Alhaji Bukar?”.
“Daddy ban sanshi ba nikam, bana kuma buƙatar saninsa. Sai dai ina roƙonka cike da girmamawa ka faɗama waɗan nan mutanen su bar mana gida su koma inda suka fito. Idan ba hakaba wlhy wlhy wlhy sai na kawo musu human right.” sai kuma ta miƙe a hankali tana duban gwaggo da wani irin ƙasƙantaccen kallo. “Ke kuma idan kina buƙatar mutuncin furfurar kanki kiyi gaggawa tarkata komatsanki ku kama gabanku. Ashe kina da baki ko ido da kwallin kwaso waɗan nan ƙazaman ƙafafun naki zuwa garemu? Kin manta mu ba jininki bane? Kin manta a yawon tazubar uwarmu ta samo mu? Kin manta bazaku haɗa zuri'arku da lallatacciya mai ɗauke da cikin shege ba? Kin manta... Kin manta.... Da yawa. To karki yarda ki bari na tuna miki, dan tunawar na nufin shiga ukun ki, tun kina iya banbance su waye a gabanki ki koma inda kuka fito. Inba haka ba kuwa.....” ta saki wani murmushin da jinjina kanta tai wicewarta da karkaɗa ma gwaggo yatsa na tabbatarwa.
Harga ALLAH gwaggo ta matuƙar tsorata da yanayin Maanal. Eh tasan dama yarinyar tun tana ƙaramarta fitsararriya ce, amma bata san rashin kunyar tata har ya kai haka ba. Da ƙyar ta iya ƙarfafa zuciyarta ta maida dubanta akan Ammie. “Asiya ni ƴarki kema wannan ɗibar albarkar a gabanki kina jinta”.
Murmushi sosai Ammie tayi, kafin a karo na farko ta sanya idanunta a cikin na gwaggo. “Mi kuke son nace da ita Talle....”
“Talle?! Asiya ni kike kira da Talle?”. Gwaggo ta faɗa a zabure tana katse Ammie. Murmushin Ammien ta sake sakin mata, sai kuma ta ɗan laɓe baki, “Shi nasan sunanki, tunda shi na tashi nasan ana faɗa miki. Tabbas kamar yanda Maanal ta faɗa kuyi gaggawar barin gidan nan tunda mutuncinku, dan wlhy bazan hanata ɗaukar dukkan matakin datai niyya ba ita da ƴan uwanta. Tun farko ma da nasan abinda ya kawoku gidan nan kenan da bazaku ko zauna ba balle shigowa nan. Amma kunci arziƙin mahaifina ya fito ne daga ku, hakama mijin aurena daya ce na saurarenku, dan shi tuwo dai tuwo ne ba'a canja masa suna. Amma waɗan nan yaran baku da wani hurumi akansu, dan da bakinki kin tabbatar ma da duniya ba jinin ɗanki bane ba. Shima kuma ya tabbatar da hakan, idan duk kun manta maza kuje ku sake sabon tunani dan tuna hakan zai matuƙar taimaka muku. Idan kuma na sake ganin ƙafar ɗayanku a cikin gidan mijina na rantse da ALLAH sai kunyi dana sani da nadamar sani na. Yarinyata kuma nada mijin aure, kai koda bata da shi gara na jerata naita kallo matsayin kayan adon ɗaki da ace kune kuka zaɓa mata mijin aure........”
“Asia!”.
Daddy ya kirayi sunanta a hankali yana mai riƙo hannunta, ƙoƙarin fisgewa Ammie tayi idanunta na cikowa da hawaye, dan gaba ɗaya neman birkice musu take yi kamar ba Ammie Sarkin haƙuri ba, dole ya miƙe tare da jawota jikinsa kawai ya rungume. Murmushi Nene da ko a bata furta ba ta saki, hakama Shahidah da Amaal sai suka miƙe suna wata ƴar dariyar shaƙiyanci. Dan su kam ai ba sai sun ce komai ba, Auta ta gama komai ita da Ammie. Babu kam rawa jikinsa ya fara yi, da sauri ya duƙar da kansa ƙasa hawaye na cika masa ido. Yayinda gwaggo ta gama macewa a zaune ita da Kawu Aƙilu. Oho ko'a jikin Daddy, dama yayi hakan ne da gayya duk da sai da ya yaƙi kansa matuƙa saboda kunyar Nene. Kusan minti ɗaya tana a jikinsa kafin ya cirota a hankali ya zaunar da ita shima ya zauna a kusa da ita. Kallon su gwaggo yay babu ko kunyarsu ta sisi.
“Ina fatan basai mun cigaba da wata jayayya ba. Amma ni zan baku haƙuri, in sha ALLAHU kuma zamu zo gareku domin auren ita Maanal, dan kamar yanda mahaifiyarta ta sanar muku tana da mijin aurenta a hannu.”
Wani irin miƙewa Kawu Aƙilu yay a fusace yana kallon Daddy, “Alhaji munzo nan ne domin mutuntaka. Dan haka kada ka zubar da wannan darajar, kar kuma ka biyema sheɗaniyar can Asiya dan zamu iya yin komai a wannan karon kan yaran nan”.
Murmushi kawai Ammie tayi, hakama Daddy. Sai Nene ce a wannan karon ta furta, “To kudai yi a hankali”.
Harararta Kawu Aƙilu yayi, hakama gwaggo. Babu kam da har yanzu kansa ke'a ƙasa sai ya share hawaye. Cikin sanyin murya ya ce, “Gwaggo dama na ce muku abinda ake shirin yi kuskure ne, sannan mutumin nan wlhy bai dace da Maanal ba. Kada kuɗi su rufe muku idanu ku.....”
“Rufe min baki shashasha kawai sallamamme, anƙi a bari ɗin, mu da su kuma mu zuba ɗan halak ka fasa. Dalla tashi mu wuce”.
Komai Babu bai sake cewa ba ya miƙe. Haka suka fice yana waiwayen Ammie data ɗauke kanta gefe......
_______★
“Amma mutanen suna da ƙarfin hali gaskiya. Tab ɗi jan”.
Murmushi Daddy yayi da kallon Nene da tai maganar, sai kuma ya kauda cike da girmamawa ya ce, “Bayin kansu bane Nene kuɗi ne ke angiza su, amma in sha ALLAHU zan bincika wanene shi wannan Alhaji Bukar ɗin da suke faɗa. Karku wani damu da su in sha ALLAHU babu abinda zai faru. Ina ganin kuma kawai a haɗe auren nan na Maanal itama shine kawai masalaha. In ba hakaba zasu iya zagayewa su ɗaura mata aure da mutum nan fa”.
“Eh kaima kazo da magana mai muhimmanci, amma suma sun san basu isa yin hakan ba....”
“Idan har aka ɗaurama Maanal aure dan saboda su ma ai munji tsoron su kenan. Ka barsu suyi duk abinda suke tunanin zasu iya. Danni ma so nake suyi ɗin domin allura ta tono garma. Dan haka ina roƙonka Daddyn Hameed komai ayisa kamar yanda aka tsara tun farko. Yanda aka shirya bikin nan da farin ciki bana son a ɓata ma Yazeed shi dan ALLAH”.
Ɗan jimmm Daddy yay yana kallonta. Sai kuma can ya saki ajiyar zuciya da jinjina kansa. “Shike nan na fahimceki. ALLAH yasa haka shine mafi alkairi”.
A tare suka amsa da amine...
Bayan fitar Daddy Nene ta kalla Ammie. “Asiya miyyasa kikace masa haka. Kamar bazai ji daɗi ba, zai kuma ga da gaske baƙya son wannan haɗin ne”.
“Nene sam ba so bane bana yi, bana son a ɓatama Yazeed farin cikinsa. Hakama Mahaifiyarsa ina son a bata damar masa auren gata kamar yanda ta shirya. Wlhy ban taɓa baƙin ciki ko fatan kasancewar Maanal matar Yazeed ba. Shi ɗin mutumin kirki ne. Amma ina fargabar ta tsinta kanta a irin rayuwar dana tsinta kaina a shekarun baya. Wadda gashi nan har yanzu tana bibiyata. Yanzu ashe Nene har mutanen nan nada ido da kwallin zuwa su nuna suna da alaƙa da yaran nan?....” hawaye suka shiga zarya a fuskarta.....
______________★
“Sir! An tabbatar min yau bata shigo aiki ba kwata-kwata”.
AS ne da furucin cike da girmamawa. Fin minti ɗaya kafin AA ya ɗago idanunsa daga rubutun da yake yi, akan AS ya zubasu. Hakan yasa AS saurin rissinar da nashi ƙasa. Shima janyewar yayi ya maida ga rubutun da yake yi. Kafin da ƙyar ya furta, “Tayi wani reporting ne akan rashin zuwan nata?”.
“Gaskiya bana jin hakan, amma zan sake bincikawa.”
Komai baice ba. Hakan ya saka AS fita sum-suma ransa fal mamakin boss ɗin nasa yau. Anya kuwa babu wata alaƙa tsakaninsa da yarinyar nan? Koda yake ɗan uwansa ne ya kawota companyn ai, maybe ƴar uwarsu ce. Da wannan tunanin ya kai a kujerarsa. Sannan ya jawo phone ya shiga neman shugaban department ɗin su Maanal.
A ɓangaren AA kam tunda AS ɗinsa ya fita sai ya samu kansa da kasa cigaba da fa aikin nasa, zuciyarsa ce ke ta faman kai-kawo. Karfa yarinyar nan da gaske take tabar aiki? Kai ina bata isa ba. (To wane ƙarfi gareka akan hakan?) Wani sashe na zuciyarsa ya ayyana. Fuska ya yamutse, sai kuma ya saki siririn tsaki yana kai hannunsa saman goshinsa ya murza. Fin mintuna biyu sannan ya miƙe. Jikin ƙaton window ɗin office ɗin nasa ya nufa, ya zubama waje ido na fin mintuna biyar. Sai kuma ya kalla agogon hannunsa mai shegen ƙyau. Wajen zamansa ya koma, ya ɗauka wayarsa dake fes-fes kamar ba'a amfani da ita yau da kullum ya shiga sarrafawa. Koda yay kiran number ɗin da yake buƙata sai ya ajiyeta ya ɗauka Bluetooth ɗinsa ya manna a kunnen...
“Assalamu alaikum Son”.
Daga can RK yay sallama. Cikin taɓe baki AA ya amsa masa, sai kuma ciki-ciki ya ce, “Ka nema ɗanka tun dare bai maka ba”.
Dariya RK ya sanya da faɗin, “Sai dai ƙari dan na riga na samu gaka nan. Lafiya kake mun kiran tsakar rana?”.
Ɗan jimm AA yay, sai kuma ya sake tsuke fuska kamar yana gaban RK ɗinne kafin ya furta, “Miya hana yarinyar nan zuwa aiki yau?”.
“Yarinya kuma? Wace kenan?”.
Kamar AA bazai amsa ba, sai kuma dai a daƙile ya ce, “Wadda ka kawo”.
“Oh Maanal wai? Am sorry laifina ne wlhy, naso shigowa na nema mata alfarma sai aikin gaggawa ya sameni, taje Kaduna ne Mamanta babu lafiya. Amma yanzu nan munyi waya ta tabbatar min jikin da sauƙi ma. Gobe ma zasu dawo”..
Ɓoyayyar ajiyar zuciya AA ya saki, a fili kam sai ya hau faɗa. Wai dan mi ita bazata zo da kanta ta sanar ba. Ai ita suka ɗauka aiki ba shi ba. Miye-miye ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Ko tanka masa RK bai sake yi ba ya yanke wayarsa........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣6️⃣
______________
........Wannan yanke waya ya sake ƙona ran AA matuƙa. Dama RK ɗin bai san yanda yake jin zafinsa bane. Aiko sai ya sake cika yay fam. Ƙarshe ya kira Oum da ƙorafi, sai masifa yake yi ita har ma ta kasa fahimtar faɗan. Sai da yay mai isarsa cike da kulawa ta ce, “Auta ɗauka ruwa kasha. Ka kuma ja numfashinka sau uku. Idan a zaune kake ka kwanta kai shiru na kamar mintuna biyar kaji ɗan albarka”.
Karan farko ya saki ajiyar zuciya. Sai kuma ya kashe wayar ya ɗauka ruwan yasha kamar yanda tace. Ya kuma ja numfashin da fesarwa sannan ya koma rukunin kujerun office ɗin ya kwanta a 3 sitter ya lumshe idanunsa. Fin mintina ashirin yana a wajen sai da akai kiran sallar zuhur sannan ya miƙe.....
★A ɓangaren Oum kam, wayar RK ta kira. Bayan sun gaisa ta tambayesa mike faruwa shi da Autan ta. Kansa kawai ya girgiza bai ɓoye mata komai ba ya sanar mata. Sannan ya ɗora da faɗin, “Karki wani damu da shi, kin san masifa bata masa wahala yanzu. Saboda aikin kamfaninsa sai taƙi zuwa taga mahaifiyarta.”
Murmushi kawai Oum tai da faɗin, “ALLAH ya ƙyauta. Barni da shi idan ya dawo zamuyi magana. Kaima kuma ALLAH ka daina fusata min yaro”.
Ƴar dariya yay daga can shima. “Ya daina dai fusata kanshi Aunty Babba. Ko kuma ki masa aure koya rage wannan zafin ran mara amfani. Ni bara naje inada theater ne yanzu”.
Koda ya ajiye wayar sai ya saki murmushi. A fili ya furta, “Ajwaad kenan, ai kayi sakaci, in dai nine babu gudu babu ja da baya akan Maanal. Komai rintsi sai na mallaketa dan ina sonta. Sanin ainahin alaƙarku a yanzu bazai sa na janye ba tunda da bakinka ka furta ba sonta kake ba ba wani ya matseka ba. In sha ALLAHU a ƙarhen watan nan za'aje nema min aurenta sai dai koma mizai faru ya faru”. Ya ƙare zancen da murmushi....
Eh lallai Uncle RK namu ka shirya kenan😂👍. Ina bayanka walle🏃🏃🏃
_______________★
“Ammie mufa munce miki muna nan har biki”.
“Ban yarda ba, kowacce ta koma ɗakin mijinta ranar juma'a sai ku dawo. Ko kun manta duk kuna aiki? Kuma kun san zamanku a gidan nan bazai haifar da ɗa mai ido ba. Musamman Maanal. Idan kuma so kuke ku ɗaga min hankali itama a birkitata to”.
Da sauri Shahidah ta ce, “A'a kiyi haƙuri Ammie, zamu tafin anjima in sha ALLAHU”.
Badan su Shahidah sun so ba suka shiryo a ranar suka dawo Abuja. Dan sam Ammie taƙi yarda su sake tattauna batun su gwaggo. Da sun ɗakko maganar sai ta zame. Gashi ma daga ƙarshe ta korosu. Kuma har so sukai suyi mata maganar su Oum. Amma yaya zasuyi, farin cikinta shine nasu.
Washe gari dole su duka sukai shirin komawa kan ayyukansu. Duk da dai da farko Maanal ta turza akan rashin komawa wajen nata aikin. Sai da Shahidah ta buɗe mata wuta da tabbatar mata zata haɗata da Ammie sannan ta shirya rai a ɓace. Shahidahn ce ta sauketa sannan ta nufi nata wajen aikin. Shigowar Maanal ɗin dai-dai da fitowar AA daga mota hannunsa akan kunne ya manna waya alamar magana yake. A kanta ya fara sauke idanunsa dake cikin gilashi, cak ya samu kansa da tsayawa, yayinda ita kuma datai kamar bata ganshi ba tai wucewarta. Idanu ya lumshe a hankali tare da buɗewa a lokaci guda. Sai kawai ya miƙama AS wayarsa dan sam ba fahimtar mi'ake cewama daga can ɗin yake ba....
A reseption suka sameta tsaye ita da Yaqub suna signing. Nan ɗin ma tamkar bata gansa ba ta wani irin ɗauke ido tana sakarma Yaqub wani shegen murmushi daya sanya zuciyar AA ɗin neman kamawa da wuta. Dan Yaqub ɗin na gaishesa ma ko kulashi baiyi ba ya wuce fuu. Hakama sauran mutane da wasu a ma'aikatan dake wajen domin yin signing ɗin bai kula gaisuwar kowa ba. AS na biye da shi da drivern sa dake ɗauke da basket alamar abinci ne a ciki. Ƙus-ƙus ma'aikatan suka fara na shigowar boss a fusace yau. Maanal dai batace uffan ba, batama nuna tasan mike faruwa ba. Koda suka bar wajen Yaqub ya maimaita maganar shima bata kulashi ba. Sai dai me suna zama sai ga waya wai ana nemanta a office ɗin CEO. Jitai kamar tace bazataje ba, amma dai ta dake ta miƙe tana sanarma Yaqub da zasuyi wani aiki tare cewar tana zuwa. Da kallo su Zaharadeen suka bita bakunansu cike da gulma. Dama tun shigowarsu ita da Yaqub ɗin suke binsu da kallon gulma. Ita kuma bata basu fuska ba bayan gaisuwa tai zamanta bata ko kula tambayar da suke mata na rashin zuwa aiki jiya ba da sukai...
Bayan AS ya mata iso yace ta shiga. Batako kallesa ba ta tura kai cikin Office ɗin fuskarta a matuƙar ɗaure. A zaune gogan nata yake saman 1 setter dake a rukunin kujerun hutawar office ɗin. A saman Centre table ɗin abinci ne da alama shi yay zaman ci a wajen. Dan sanda ta shigo ma yana ƙoƙarin zuba kunun gyaɗa ne dake a wani kyakkyawan ƙaramin flaks. Yanda ta turo ƙofar babu neman izini da tsaiwar da tai daga jikin ƙofar baisa ya motsa ba ko kallon inda take. Hidimar zuba abincinsa ya cigaba da yi hankali kwance. Sai da ya kai dankali har kusan sau uku bakinsa tare da shan kununsa a nutse sannan ta tako cike