Bakar Taada

Chapter 26 of 65

ishe ka ba. Har umarnin ta yi maka girki a kicin d'ina ka bata?"
Na fada cikin kuka sosai.
Dada ta dauki salati tana ce wa "A cikin gidan auren ki, ya yi irin wannan ba'kin zunubin? Eh lallai ba laifin ki ba ne, nasa ne. Wato ni a lokacin da nake kamar ki yaushe za'a mini hakan na bar al'amarin salin alin ba tare da na fitarwa da ja'irar jini ba. Na goge hawaye na ce "Ban yi komai ba na kai k'ara wajen Ubangiji. Sannan kuma har abada bazan sake ba shi abincina ba. Ba kuma zan huce ba, daga nan har na tsufa".
Dada ta yi maza ta ce "Eh to ba dan ina jin tsoron kada kwanaki arba'in din ta cika auren ya samu karaya ba. Dana goyi bayan wannan tutsun na ki. Amma yanzu ki yi ha'kuri, ki yafe, ki huce! Ubangiji yana son masu afuwa da sassauci. Idan ya kuma ni da kaina ne zan sanar da iyayenku. Ai bazan yarda ki yi irin wannan zaman na kuttu ba".
Na girgiza kai na ce "Ai Dada babu maganar huce wa. Babu ni babu sake shiga shirginsa tunda juninsa wula'kanci da nema mini raini ne".
Kafin Dada ta yi magana ya yi fit ya ce "Ban san zaki ji haushi ba Asiya. Na rantse ban yi da gayya ba. Amma tunda ban kyauta ba. Allah ya baki hakuri. Ba zan sake ba."
Na dauke kai ina harara tamkar idona zasu fa'do k'asa.
Ya ce "Dada ki ce ta yi hakuri mana."
Ta nisa ta ce "ki yi ha'kuri kin ji. Ta shi ki ba shi abincin ba dan halinsa ba. Dubi Allah, ki duba Manzonsa."
Ban sake ce wa komai ba. Na mik'e din.
Ban san ya aka yi ba, da na isa kicin din na samu kaina da d'auko plastic plates masu fadi guda biyu.
Na zuba masa na rufe na dora cokali a kai. Na dauka na nufi falon. Ina jin Dada na fa'din "kada ka sake kuskuren saka wata ta yi maka girki. Ban da sakarci ma ina kai ina doguwar magana da ita, bare har kasa a yi maka girki akan idon matar ka. Ai gwara da ta murd'e maka. Kasan halin fa'dan ta ai, bare kuma an tsokano ta".
Murya ba amo ya ce "ki bar maganar nan, sai na zo dakin ki. Yanzu dai lallaba mini ita Dada kawai".
Na shiga na ajiye a gabansa. Ya saki murmushi ya ce "
"Madallah da Asiya". Na cuna baki na dauko ruwa na ajiye masa a gabansa na koma gefe na zauna.
Ya dauki abincin ya dinga ci tamkar bai ta'ba cin abinci irin hakan ba. Cikin kankanin lokaci ya tashi da uban abincin da na danne farantin da shi.
Fanka na kad'awa amma zufa sai yanko masa take yi.
Ya ta'ba ruwan ya ji sanyi sosai.
A hankali cikin kwantar da murya ya ce "Asiya idan kina da ruwan Lipton taimake ni da shi mana please" .
Na dauke kai, kamar bazan amsa ba, sai kuma na tashi na fita ba tare da na ce komai ba.
Dada ta bini da ido tana fa'din "Kasaitacciyar mace. K'aramar halitta mai babban al'amari".
Sai da na isa kicin na yarda na yi dariya.
Na dauko kofi da cokali. Sannan na dauki filas din ruwan zafin.
Na sake ajiye wa a gabansa ba tare da na ce komai ba.
Na zauna na dauki waya ta ina danne danne.
Dada ta ce "Ba ki kawo masa sigari ba."
Kafin na yi magana ya ce "Idan zata dafa take zubawa, dan rage masa tasiri."
Ta murmusa ta ce "Yabi mutanan turai".
Shi ma ya taya ta murmushin. Ni kuwa ban ce komai ba.
Ya kammala, ya yi gyatsa tare da hamdala.
Ya ce "Har na ji ni a duniya. Na gode sosai Asiya. Allah ya yi miki albarka."
Ban amsa ba. Dada ta amsa da sauri tare da fa'din "Barka da arziki Yabi! Kin rabauta tunda kika samu farar addu'a daga mijin ki".
Na yi shiru ban tanka ba. Yayin da shi kuma ya mik'e yana cewa "Bari na canja riga na zo na mayar da ke."
Yana fita Dada ta ce "Yabi maganar nan ta wuce. Ku zauna lafiya. Ko makaho ya zo gidan nan sai ya gane mijin ki na son ki".
Cikin fishi na ce "Baya sona Dada. "
Ta murmusa ta ce "Yana son ki. Ke ma da gangan kike inkarin hakan. Yanzu bazan fa'dawa kowa ce wa ba k'alau kuke zaune ba.
Amma fa idan na dawo gidan nan, na fahimci baku shirya kanku ba. Ku tabbatar sai na ha'da muku iyayenku da Malamai. Dan bazan yarda da zaman kafirci ba."
Na dinga k'unk'unin babu ruwanta da shiga al'amarin da bai shafe ta ba.
Ta gyada kai ta ce "komai zaki ce Yabi ki fa'da. Amma ki sani, ni bazan ha'inci shari'ar musulunci ba. Tilas ne ku bi ka'idojin shari'a a kan aurenku."
Ya lek'o daga bakin k'ofa ya ce "kin gama Dada, ko na je na dawo bayan maghariba sai na kai ki?"
Ta yun'kura tana fa'din "Na gama, yinin ya isa, ba sai na kai almuru a waje ba."
Nima na bi bayan ta muka fito. Na kalle shi ya sanya jallabiya. Ko mai bai shafa ba, bare tuarare. Àllah ya sani ina son na dinga jin k'amshin na tashi a jikin mutum.
Na shiga daki, na d'auko ledar kayan da ya siyo. Na dauki dubu guda a cikin ku'din da na tara na lalle. Na saka mata a ciki. Na k'ulle. Na sake k'ara wata ledar.
Na tarar har sun kusa fita.
Na bu'de baki na ce "Dada mun yi sallama ne?"
Suka dakata na isa garesu. Na mika mata tare da ce wa "Ga shi Dadarmu na gode da ziyarar ki. Amma Wallahi bakin ki k'anin kafar ki akan sha'aninmu Dada. Idan kuwa kika fa'di wani abu, sai dai a neme ni a rasa."
Ta sassauta ta ce "Ayyah Asiya me na ga ni ma ban da alheri? Ai ko da na ce zan fa'di baku zauna lafiya ba. Dan ban fahimta ba ne. Yanzu da na fahimci shine da laifi, ai na fa'di gaskiya. Kawai da ke da shi ku yi kokarin d'abbaka sunna, kada auren naku ya b'aci ba'a ankara ba.
Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na rasa yadda zan yi, sai kawai na juya da sauri na yi ciki na barsu.
Shi kuma ganin hakan ya sanya ya ce "Allah yasa dai ba sai yanzu kika yi mata wannan bitar ba Dada?
Domin a zaune zaki yi mata ba a kurarerren lokaci irin haka ba. Idan kuma zaki fasa tafiyar sai bayan Isha da na fi haka gode wa Dada".
Ta nuna shi da yatsa ta ce "Tabataccen marar ta ido. Oh ni Binta ina kallon shak'iyanci. Ai gara ma da Asiyan ce matar ka, ita ce maganin ka. Haba kana da fitina Wallahi".
Ya yi gum. Ta d'aga murya ta ce "Na tafi Yabi, na gode Allah ya yi albarka.
A ci gaba da hakuri."
Ina zaune ina kallonsu ta windo har suka fice.
Suna tafe a hankali yake jan mashin d'in gudun kada ta subuto tunda ba iya hawa ta yi ba.
A hankali take fa'din "Ashe haka zaka yi mana? Akan me zaka kawo wata har gidan auren ka?"
Ya ce ba ni na kawo ta ba. Wajenta take zuwa fa.
Kuma kunshi take yi, wai ni rage mata aiki nasa aka yi"
Ta hassala ta ce kaniyarka da rage mata aikin. To bata so. Kada ka kuma wannan d'anyen aikin."
Ya ce "To bazan sake ba, da gaske."
Suna isa ana kiran magariba. Dan haka da ya kafe mashin din a zaure bai shiga gidan ba, ya nufi masallaci.
Da nutsuwa ya isa kofar Baban Marina ya gaisa da su Gwaggo cikin kunya da girmama wa.
Kansa a k'asa ya ce "Gwaggo idan uniform din Asiya na nan wai a bata zata fara koyon dinki"
Da sauri ta shiga daki tana ce wa "Sabon yana nan. Tsohon dai Ikilima tana amfani da shi."
Jimawa ka'dan ta kawo masa a bak'ar leda.
Hannu biyu ya sanya yayin karba.
Ya yi godiya, ya yi musu sallama ya tafi.
A gurguje ya yiwa Dada sallama ya wuce gidansa. Yana Jin zumudi da d'okin zama kusa da Yabi.
Yana son yi mata ba zata. Yana son ya shawo kanta, ya d'ora mata girma ko zata rage tsiwa da zafin kai.

*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*

✍️.

*BAKAR TA'ADA*

*45&46*


*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.

*Tallah Tallah Tallah*

Shaharriryar marubuciyar nan wacce tanishaɗantar ku a littafin ta mai sunan
SAMHA```!

```Ta sake sabon shirin ta, wajan ƙara faranta maku rai' tazo maku da sabon book ɗin ta Wato KECE SANADIN [rayuwa]```

```Masoyana kufito ku nunamin ƙaunar da kuke cewa, kuna min```
```farashin KECE SANADIN ₦500 0nly```
```wacce bata shirya ba kada tamin magana```
```masu san fara pyarment da wuri gashi, 810353370 kimin screen shot ki turo ta wannan no 08138012334```
```masu kati kuturo ta wannan layin 08108353370```

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.

45&46.
Ya shiga da kuzari. A falo ya tarar da ita tana kallon tashar Bollywood.
Yana wahalar gaske ya ga tana kallon tashoshinmu. Har gara tana kai wa Sunna TV sa'i zuwa sa'i.
Ya manta da uniform a cikin but din mashin din.
Ya zauna kusa da ita.
Ya sassauta ya ce "Asiya Toro babu magana, babu yi mini barka da zuwa?"
Na galla masa harara na ce "To ni ina ruwana da kai da zan yi maka magana? Ba gaba mu ke yi ba?"
Ya ce "mun shirya ai. Na baki hakuri, kakarmu ta baki, mene ne kuma ya yi saura?"
Na ja tsaki mai tsananin gaske na ce "Da wa din ka shirya? Ai ni duk mutumin da zai tozarta ni, ya kuma ta'ba lafiyata da sunan duka to babu ni, babu shi har gaban abada".
Na fa'da cikin matsanancin fishi.
Jikinsa ya fara mutuwa. Ya numfasa ya ce "Ashe duk maganganun Dada basu shige ki ba? Daga tafiyar ta Asiya zaki fara d'aga mini hankali, mene ne nak'asuna ne da kika washe ni har hakan?"
Yana rufe baki na ce"nak'asunka ai birjik ne. Mafi muni baka da kamun kai.".
Ya zuba mini ido ya ce "sai me kuma Asiya?"
Kai tsaye na ce "Baka burge ni ko kadan. Domin bana jin k'amshi a tare da kai. Baka iya kwalliya ba. Kullum kayan ka babu guga. Kalli faratan hannun ka.
Kullum na kalle ka ba'kin ciki ne yake kama ni maimakon farin-ciki."
Jikinsa ya yi sanyi kwarai da gaske. Idanuwansa suka canja launi sosai.
Murya a dashe ya ce "Sai me kuma?"
Na ce "Idan na tuna, na fa'da maka".
Ya numfasa ya ce "Duk zan gyara indai sune cikas dina a wajen ki. Idan na sauya din shi ke nan zaki daina tsananta mini?"
Na sake shan kunu ban tanka ba.
Ya ce "To nima ina da damar da zan fa'di abubuwan da kike yi mini da bana sonsu?".
Kamar bazan kula ba.
Sai kuma na ce "Baka da damar domin ni ba so nake sai na burge ka ba. Ba kuma so nake ka zauna da ni akan dole ba.
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shike nan! Amma ina ro'kon ki kada ki sake shiga mini da mata dakina".
Na tunzura! Na tashi zaune sosai na galla masa harara na ce "Sannu mai d'aki. Komai dakinka, dakinka. To sai na shiga d'in.
Shima ya hassala ainun ya nuna ni da yatsa ya ce "Kada ki fasa Asiya. Ai tunda na gane ba kya son sulhu da sassauci, to mu zuba tsiyatakun mu ga wa zai janye wa wani".
Na ja tsaki na ce "Ai ka k'oshi shi yasa ka samu kuzarin yin musayar yawu da ni".
Ya juyo a tunzure, ni kuma na zabura na yi shirin kai masa naushi.
Dariya ta kama shi ya ce "Wai dambe zaki yi da ni? Ko da yake ai mai hali baya fasa wa."
Na ce "oho dai."
Ya fita ban sake jin sa ba, sai da asuba ya tashe ni.
Da safe ba yadda bai yi ba akan na tafasa masa wani abu, duk da ya shigo da burodi a safiyar, kawai bai dame shi ba ne. Na yi tsallen bad'ake na ce bansan zancen girki ba, gara mu cigaba da zaman doya da manja kawai.
Ya shiga ya tafasa farar taliya ya zuba yajin *Annur food* da manja. Ya ci ya fice bai bi ta kaina ba.
Sai da na gama komai sannan na d'ora shayi.
Na karya na yi wanka. Ina zaune babu wuta, kuma babu kowa.
Sai da azahar sai ga y'anmata uku sun zo k'unshi.
Muka shiga d'akin da ake ta mini kashedin kada na shiga na fara yi musu.
Na gama wa mutum d'aya sai ga Hajiya babbar mace sosai. Dan zata haife ni. Mun saba tuntuni, wani lokacin har gidanta ina zuwa na yi mata, sanadin haka suka saba da Gwaggona.
Na marabce ta da murna.
Na kammala saka musu. Na kammala yiwa Hajiya a hannu.
Sai ga shi ya dawo. Ban san me yasa ba, na ji faduwar gaba ainun. Wata'kila ko dan ya yi ta jaddada mini kada na shigar masa d'akin da nufin yin kunshi ne?
Ya lek'o ya tabbatar ban ji maganar sa ba.
Ya juya ko gaisuwarsu bai amsa ba.
Ya dauko bokiti ya janyo ruwa.
Hajiyar ta ce "tashi ki je ki masa sannu".
Na ce To" ba dan ina so ba, na yun'kura na fita. Na gan shi ya gama cika bokitin, ya dauko na tsaya ban ce masa kanzil ba.
Zuciyata ta tsinke a dalilin yanayinsa ya koma na Bulkachuwa na asali, ba na yanzu da ya koyi sassauci ba. Ya shige ni bai ko kalli inda nake ba. Ya kai ruwansa band'aki. Nima na koma na cigaba da lallena.
Mintina biyar sai ga shi ya shigo d'akin babu sallamah. Y'anmatan suka fara gyare gyaren jikinsu yayin da Hajiyar ta rasa yadda zata yi a dalilin duk na yiwa hannuwanta k'unshin.
Ba zato ya cire rigarsa ya mak'ale. Zuciyata ta tsinke. Wani irin abu ya tokare ni. Kafin na wartsake sai kawai ya zame dogon wandonsa, ya yi saura daga shi sai singileti da gajeran wando. Hankalina ya kai k'ololuwar tashi lokacin da ya cire singletin.
Ya dauki tawul din da yake rataye ya daura a kugunsa. Ban san me ya hana shi zame gajeran wando ba. Yasa kai ya fice zuwa band'aki.
Na yi kasa da kaina hawaye ya b'alle mini.

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

Gaba'daya y'anmatan suka bi shi da kallo. Wani irin mak'aki ya tokare ni. Na sani zai burgesu tunda Ubangiji ya masa kyakkawar sifa kwarai da gaske. Motsa jikinsa da yake yi, ya sanya jikinsa ya ginu sosai.
Wanne irin wula'kanci Tijjani ya yi mini yau? Na fa'da a zuciyata.
Matar ta ce "Cire mini lallen nan. Ai bansan maigidan baya so ba. Na tabbatar ba da izininsa kike wannan sana'ar ba. Shiyasa ya dauki wannan k'azamin matakin.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yau na ga lukutar tsiya ni Hadiza."
Ta fa'da cikin kad'uwa.
Na fara kuka sosai, ina yi, ina cire mata. Ai kuwa ina gamawa ta ja ni jikinta ta mak'ure ta rufe ni da duka tana cewa "wanne irin shak'iyanci kike yi masa da ya janyo miki wannan d'anyen hukuncin. Shin baki da makusanta da suke fa'da miki gaskiya ne? Kowa ya kalle shi yasan yana tsananin son ki. Me kike yi masa?"
Dama so nake na yi kukan sosai, ko na samu sau'kin zugin da kirjina yake yi mini.
Dan hakan na bu'de baki na dinga canyara ihu. Ita kuwa sai dukana take tamkar ita din Gwaggo ce.
Sai kuma ya fito a bazame. Dan ya ga me ya sani irin wannan kukan. Ganina a hannun Hajiyar ta matse ni tana ta mintsini na ya sanya shi ce wa "Na ha'da ki da Allah ki bar ta haka nan Hajiya, k'yale ta"
Ai kuwa ta k'yale ni. Ya tsaya daga ba'kin k'ofar ya mika hannu ya d'auko jallabiyarsa da take rataye. Ya yi baya, ya sanya.
Ya dawo ba'kin kofar ya ce "Darajar wannan baiwar Allah

Download complete TXT · Novel page