Bakar Taada

Chapter 28 of 65

kuskure na yi, da na dauke kai.
Tunda kin san kishi kin kuma iya har a kaina da ba sona kike yi ba shike nan, magana ta k'are zan d'ora miki girman da zai sanya ki dinga jin nauyin fa'da mini duk abin da ya zo bakin ki."
Na yi muk'us ban da b'ari ba abin da jikina yake yi.
Ya sake ni, ya fita. Ai ina ganin ya fita, na zabura na rufe k'ofar da sakata.
Na yi shiru ina ta zare ido domin har lokacin zuciya ta bugawa take yi da tsananin gaske.
Can na ji yana kwankwasa k'ofar. Na yi bakam a zuwan barci nake yi.
Bai tsananta ba, ya juya ya tafi.
Da asuba ban yarda na fita ba duk yadda fitsari ya matse ni, sai da na ji fitarsa masallaci sannan na yarda na bu'de k'ofar.
Har ya je gidan burodi ya dawo barci bai dauke ni ba.
Kamar daga sama na ji muryar Baban Marina a tsakar gidan.
Zuciyata ta tsinke sosai. Gumi ya dinga yanko mini. Gaba'daya na tsorata na tabbatar Tijjani ne ya kai k'arata.
A sanyaye na bu'de k'ofar, na taya Tijjani marabtarsa.
A falo muka sauke shi. Ya amsa gaisuwa ta da walwala na d'an samu kuzari. Domin na lura babu bacin rai a tare da shi.
Ganin hakan ya k'arfafa mini guiwa na mike na bu'de firij na d'auko ragowan k'wai uku da ya ragu.
Na soya masa a gurguje tunda nasan da burodi.
Kafin na gama shirya kofina a tray har shayin ya kusa juyawa.
Na dauka na kai gaban Baban.
Ina dawowa kuwa shayin har ya tafaso na juye a flask na kai masa.
Cikin soyayyar da na kwana biyu ban ga ni ba a dalilin fishin da ya yi da ni akan auren Tijjani.
Ya ce "Sannu Yabi. Allah ya yi miki albarka. Na ji da'din yadda na tarar da ku, kuna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Allah ya dauwamar da aurenku, ya baibayeku da albarka ta inda kuka zata da ta inda baku zata ba. Wanzuwar aurenku na cikin burina a wannan duniyar. Ki zauna lafiya, ki yi ha'kuri da kawaici irin na uwarki."
Kaina na k'asa amma hawaye nake yi. Tabbas idan da Tijjani zai bu'de baki ya yi masa bayanin yadda muke zaune da bai yi wannan farin-cikin ba. Da bai sanya mini albarka irin hakan ba.
Tijjani ya ha'da masa shayi ya ce "Bismillah Baba ka ci abincin Asiya".
Da murmushi ya ce "Na riga da na karya, amma tunda Ubangiji ya nufe ni da zuwa gidanku zan ci abin da kuka ba ni. Ina fatan Ubangiji ya buda maka k'ofofin ciyar da iyali cikin sau'ki Tijjani".
Nan da nan ya masa da "Ameen Baba".
Yana kurb'an shayin Tijjani na yankar biredin yana cusa masa k'wai a ciki, yana mik'a masa.
Ba wani sosai ya ci ba. Amma ya shanye shayin. Ya yi hamdala ya ci gaba da sanya albarka cikin marari.
Ya ce "Tijjani ina fatan dai lafiya kuke zaune babu damuwa?"
Jikina ya d'auki rawa.
Amma ga mamakina sai ya ce "Lafiya k'alau muke zaune Baba. Ai Asiya har bayan idonka tana kiyaye tare da girmama umarninka".
Da'di ya k'ara kama shi. Ya ce "Alhamdulillah! Allah ka so Asiya, ka sanya soyayyarta da tausayinta a zuciyar mijinta. Shi kuma ka bashi lafiya da jarumta da arziki mai gudana. Àllah ka zaunar da su lafiya, ka basu zuri'a dayyiba."
Daga haka ya mik'e ya gyara rigarsa ya ce "Nurun ala nurun a dukkan rayuwar da zaku yi".
Tijjani ya bishi suka fita, yayin da na bisu Ina fa'din "A gaida mutanan gidan, Allah ya k'ara lafiya mun gode".
K'aran mashin din Tijjani ya tabbatar mini ya tafi mayar da shi ne.
Bai dawo ba sai wajen k'arfe d'aya da rabi na tabbatar kuma sai da ya yi sallah.
Kai tsaye wanka ya yi, ya sanya jallabiya ya shigo falon, k'amshin turaren da ya tsiri sawa ya bugi hancina.
Ya zauna. Na yi kokarin kyautata fuskata na ce "Sannu da dawo wa."
Ya kalle ni ya ga na yi kwalliya cikin wani fitinan material.
*Wanda Umm Nihla mazauniyar Malaysia take odarsu.*
Tuntube ta akan wannan lambar ta *manhajar Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa.*07020695644*

Ya ce "Wow Asiya kin yi kyau tamkar yar tsana. Na murmusa na ce "Na gode".
Ya numfasa ya ce "Wannan sannun ta ki nasan kin yi saboda rufin asirin da na yi miki ne".
Na cuna baki na ce "Yo kai ma ai na rufa maka naka asirin ai".
Ya matso kusa da ni ya ce "Fa'da mini rufin asirin da kika yi mini, ni da kin fallasa da ba hakan ba".
Na dauke kai ina hura hanci irin na ta'bara da shagwaba.
Ya sake susucewa ya ce "Saboda Allah me zaki ce masa ina yi miki na musguna wa?"
Cikin yanayin tab'ara na ce "Abubuwa masu yawa, yo ni abubuwan da ka yi mini ban da dai ni din mai hankali ce, da tuni ba'a yi b'atacciya ba".

*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*

Ya maze ya ce "Ni nasan hankalin ki yawa ne da shi ai".
Na sake ce wa "Ban da dai ina tsoron fishin Baba ai da tun ranar da ka sanya aka shigar mini kicin da tun ranar zan bar maka gidan, ita sai ta zauna kawai a madadina".
Da sauri ya bar kan kujerar ya gurfana a gabana, ya ru'ko dukkan hannuwana ya sassauta murya ya ce "Asiya" cikin wani irin yanayi.
Na kasa amsa wa, karon farko da ya ri'ke ni ban fizge ba. Domin gaba'daya maganganun Baba ya dagargaza ni, ya fahimtar da ni zama da Tijjani tilas ne.
Zamana lafiya a gidan aurena yana nufin farin-cikin mahaifina na tabbatar Gwaggo ma ba zata so ta gan ni a gabanta da sunan mutuwar aure ba.
Na zum'bura baki na ce "Uum".
Ya yi kasa da murya ya ce "kalle ni".
Na sake juyar da fuskata ba tare da na kalle shi ba.
Da wata irin murya ya ce "Pls mana Asiya Toro".
Na zakuda da sauri, na fara kokarin cire hannuna a nasa. Ina ce wa "Ai dai kasan bana son gatsa mini sunana da kake yi."
Da azama ya ce "Indai zaki daina yi mini rashin kunya ai daga yanzu na daina fa'da miki. Kwanaki kin ce mini bana goge kaya, bana saka turare. Yanzu na fara yi dan kisan ba abin da bazan yi dan na samu aminci da nutsuwar ki ba. Amma ko ki nuna kin gane na canja, balle ki yaba mini na ji dadi".
Na bata rai na ce "Akan me zan yaba? Bayan ba dan ni ka yi ba. Ina ce jiyan da ka fita sai da dare ya raba kana zan ce, idan ta yaba maka ai shike nan"
Ya kame baki ya ce "Tabdi jam!
Ya bar maganar ya canja da ce wa "Yanzu zan sake ba ki hakuri, ki manta maganar shiga kicin din ki. Na yarda na yi kuskure, dan Allah ki shafe ta a zuciyar ki. Nima na yafe miki zargina da kika yi jiya. Kin ga dai murna da addu'ar da Baban Marina ya yi. Kamata ya yi mu ha'da kanmu mu zauna lafiya".
Na bata rai na ce "To ai kai abin haushin ka yawa ne da shi Tijjani. Bana son na ga namiji ya cika kule kulen mata, kai kuma kana tafiya a mashin ma kana iya tsayawa ka yiwa mata magana ko baka sansu ba".
Ya sake ru'ko hannuna sosai ya ce "Billahillazi a da ne Asiya. Tunda muka yi aure bana yi, na rantse miki da Allah. Mussaman da kika ce mini mai kamun kai kike so, sai na sake kame wa sosai".
Na yi shiru ya ce "shike nan komai ya wuce zamu zauna lafiya, zaki yarda na zama mijin gaske ba na wai ba?"
Na ce "Sai ka yarda wanccan dakin ya zama zan yi yadda nake so a cikinsa".
Ya ce "Kin san ban iya yaudara ba. Idan kin yarda na zama mijinki na sosai, ai gaba'daya ma ya zama naki, to me zan yi da shi?"
Na ce "Ban gane ba?"
Ya jima yana kallona har sai da jikina ya amsa sannan murya a dashe tabbacin ya shiga cikin shauki sosai.
Ya ce "Idan dakinki ya zama shine nawa, kayana sun koma ciki, kin adanasu tamkar yadda kika adana na ki, sannan a ciki zan dinga kwana, a ciki zan yi komai. Shike nan dakin ya zama na lallen ki da duk bak'on kwana da zamu yi".
Gabana ya yanke ya fa'di tamkar yanzu na fara jin ya kamata ya dawo dakina".
Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai.
Ya marairaice fuska ya ce "Ki ce to Asiya, na matsu ki zama matar aure ta sosai, na k'osa ki zama babba."
Kunya ta kama ni, na rasa yadda zan yi, sai kawai na fara kananun kukan shagwaba tare da ce wa "Ai yanzun ban girma ba kake nufi?"
Da sauri ya ce "kin girma mana, shi yasa nake son na sake mayar da ke babba sosai".
Na sunkuyar da kai na k'asa domin kunya ce ta sosai ta yi mini k'awanya.
Ya dinga murza mini tafin hannuna wanda hakan ba k'aramin abu ya haifar mini a gangar jikina ba.
Haka shima gaba'daya ya yi sanyi ido ya canja.
Kunya ta sake kama ni. Kan dole sai da ya sake wanka kafin ya tafi sallar la'asar.
Nima dai abin da na gani na kasa gane wanka zan yi ko tsarki. Dan haka sai na yi wankan gudun kokwanto.
Na dinga mamakin lokacin da muka cinye bamu nemi ko abinci ba.
Na shiga kicin na dauko plask din abincin wanda jallof din shinkafa ne.
Na koma na dauko plates da cokula.
Ya dawo ya tarar da abinci. Ya ce "Kamata ya yi muci a plate daya Asiya".
Ga mamakinsa sai ya ji na ce "To."
Na zuba mana, muna ci yana yi mini hira kala kala.
Muna gamawa ya kalli agogo ya ce kwaso kayan ki na wanke miki".
Na girgiza kai na ce "Bar shi zan wanke da kaina".
Ya mike ya na ce wa "Bari na debo da kaina.
Kan dole na bar masa wankin nan ya yi, ina baranda yana ta faman zuba mini hira. Ni kuma na kasa tanka masa, sai dai eh ko a a.
Da daddare yana tafiya sallar isha na rufe k'ofata. Da ya dawo ya ga na rufe. A hankali ya dinga buga mini tare da kiran sunana, amma na kasa bu'de masa. Wata irin fargaba ta dinga ratsa ni. Kan dole ya hakura ya bar ni.
Da safe da na fito ya amsa sallamar da na yi masa, kansa na kan doguwar rigata da yake goge wa.
Tausayinsa ya tsirga mini, duk yadda na rufe masa k'ofa, kuma ban yarda na bu'de masa ba, bai sanya ya fasa goge mini kayana ba.
Gasu nan birjik a gabansa da alamu ya jima yana yi. Tunda rigar da yake kan yi ne ta k'arshe. Sai da na yo brush na ce masa "Ina kwana?".
Ya amsa babu yabo babu fallasa"
Da ya gama zai fita na ce "Zaka dawo ne da rana?"
Ya girgiza kai tare da ce wa "To me zan dawo na yi?"
Na yi shiru sai na ce "To idan an zo k'unshi zamu shiga d'akin, kada ka zo ka dizga ni."
Ya girgiza kai alamun bai yarda ba.
Ya bu'de baki ya ce "Ban yarda ba. Kada ki fara, idan kuma kin ki ji, to ki tabbatar zaki ga abin da baza ki so ba".
Na Kwakkabe fuska tare da fa'din "Amma dai kai ne ka ce zai koma nawa".
"Na fa'da tabbas. Amma ai na fa'di sharadina. Baki yi abin da na ce ba, dan haka kada ki sake ki kai mini mutane d'aki".
Daga hakan ya fita. Ina gama abun da zan yi. Na fara tunanin yau laraba, zan samu masu kunshi sosai har zuwa gobe. Ina matu'kar son sana'a ta, ina samun nisha'di da walwala a cikinta. Sannan ina son na dinga aika wa iyayena wani abu. Idan bana sana'a kuma bazan samu wannan alherin ba.
Na tabbatar kuwa matu'kar da kayan Tijjani a dakin da nake son ya zama na zaman sana'ata, to kuwa da sannu zai kore mini jama'a.
Na zabura na shiga dakin na dauko jakar kayansa. Na kai ta d'akina. Na sake dauko kwalin makorinin da ya zuba takalmansa a ciki.
Na fito da shi tsakar gida na bu'de. Kafa hudu ne da alamu biyu a lokacin aurenmu ya siyesu tunda sabbi ne.
Na goge su na kai su daki.
Jallabiya da tawul din da suke rataye, na fito da su na shanya tunda da danshin ruwan wanka a tare da su.
Bargo da filon kawai na ninke na barsu gefe daya.
Na dauko kaskon turaren wuta da yake ci a dakina na saka na sakayo k'ofar.
Cikin sauri na d'ora shinkafa da wake.
Na kammala na ji almajiri yana bara.
Na kira shi na bashi naira dari ya siyo mini salak da kokomba, domin kayan ganye sau'ki ne da su a Toro tunda muna kusa da Jos.
Nan da nan ya siyo mini, na bashi guntun burodin jiya.
Ina tsaye na yanka na wanke na rufe shi.
Na ha'da kwanukan da na bata na wanke.
Na shiga wanka. Na shirya cikin doguwar riga cotton mai gajeran hannu.
Na saka hular da ta dace da rigar.
Na kalli agogo na ga shad'aya ne da rabi.
Ai kuwa sai ga wata ta zo kunshi da kitso.
Na bude dakin muka shiga, na fara yi mata lallen, cikin kankanin lokaci na gama saka mata. Na dauko kujera a kicin muka fara kitson.
Mun yi rabi sai ga tawagar yan mata wajen su bakwai har da amarya.
Murna ta kama ni, domin ku'di zan samu ba ka'dan ba.
Sannan bana cikin zullumin wula'kancin Tijjani.
Ina gama kitson na fara yiwa amaryar tunda nata yafi wahala na salatif ne.
Na gama yi mata, na fara yiwa daya cikin kawayen na ji k'arar mashin dinsa.
Ya shigo da sallama. A zabure na mike na fita y'an dakin suka bini da kallo.
A bakin kofar na tare shi da ce wa
"Sannu da dawowa".
Bai amsa ba ya sha kunu ya fara kokarin shiga d'akin duk da na tare k'ofar.
Baki na rawa na sake ce wa "Sannu da dawo wa, muje ka sha ruwa, ka ga ni".
Bai musa ba. Ya yarda ya bini zuwa d'akina. Na nuna masa jakar kayansa da take gefe akan kwalin takalmansa.
Na ce "Babu kayan ka a dakin Wallahi. Ka ga tawul dinka ma?" Na d'aga labule ya gan shi akan k'ofa.
Ya daure fuska ya ce "Indai a hakan zaki bar mini su, to kawai ki mayar mini abina can."
Idona ya ciko da hawayen takaici. Murya na rawa na ce "Kawai dai sana'a ce baka son na yi Tijjani. Ban da haka, ga yadda ka ce na yi, zaka bar mini d'akin, na yi kuma ka ce ba haka ba".
Ba wasa ya ce "Ai ba ki adana mini su kamar yadda kika adana na ki ba. Kin ajiye su tamkar suna wancan d'akin dan haka mayar mini su can din kawai."
Da sauri na bu'de masa durowar na ce "Ka ga inda na bar maka fa, bana son na bu'de maka kaya ne baka nan. Da sai dai ka dawo ka tarar na jere maka".
Ya saki fuskar ya ce "To shike nan. Amma kin yi sallah kuwa?"
Na ce "dama d'aya zan k'arisa wa sai na yi kafin na fara yiwa wata".
Ya kalli agogo ya ce kusan uku saura, kina neman duniya baki yi abin da aka halicce ki yi ba? Yau ne rana ta k'arshe da za ki ji ana kiran sallah baki bar k'unshi kin yi ba".
Na ce "To".
Ya ce "Je ki yi alwallah ki zo ki yi sallar a nan".
Na fita ban ce komai ba.
Yayin da Tijjani ya cigaba da ambaton *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Cikin farin cikin ganin tasirin addu'ar akan lamarin Yabi. Domin tunda ya ga al'amarin ta babu ragayya, babu soyayyar sa ko kad'an sai ya nace wajen yin wannan adduiakan al'amarin. Ya kuma fara ganin sassauco mai yawa. Mata ku rik'e wannan addu'ar sirrikanta yawa ne da shi.
Na idar, na mike na kai masa abincin falo. Na dawo na gan shi kwance shame shame akan gadona. Gabana ya yanke ya fa'di. Saboda ya tube riga daga shi sai gajeran wando. Wani irin tsoronsa ya kama ni a dalilin duk jikinsa gashi ne. Kirjinsa kuwa yafi ko ina gashi.
Ranar da ya tub'e a gaban su Hajiya da yake a kidime nake ban ga gashin irin haka ba. Na dauka iya kirjin ne kawai.
Murya na rawa na ce "Abinci yana falo".
Muryarsa a dashe tabbacin yana jin barci ko wani al'amari daban.
Ya ce "Sannu da aiki".
Na amsa da ce wa "Na tafi".
"Tom, idan na ci zan fita, nasan ba son na lekoku zaki yi ba".
"Na ce "Eh. To sai ka dawo din".
Na saki labulen na je na cigaba da yi musu.
Bai fita ba sai da la'asar ta yi.
Sai wajen biyar na gama yi musu tunda na yiwa mutum biyu kitso a cikinsu.
Ina gamawa na karkade jikina na wanke hannuna da sabulu.
Na shiga kicin, na ga akwai donot sai kawai na dafa shayi na cika filas tunda akwai ragowar abincin rana da na yi
Ana kiran magariba suka tafi bayan sun bani kudina.
Na kirga na ga alherin da na samu ba ka'dan ba ne. Na

Download complete TXT · Novel page