KANWAR MAZA 1&2

Chapter 31 of 78

a kan wuta take, ba ta son zaman gidan nan.


Aka yi abin karin kumallo, kunun tsamiya da wainar gero, ga kunun na daka ne, sai ƙamshi yake, sai dai tun da Aliyu ya ga an kawo kunu, kuma kunun babu suga yake kallon ruma ya ga, wani action za ta yi, za ta sha ne ta yi kara ko halin za ta nuna.


Ta kalli kofin kunun, ta kalli Aliyu, amma ya kawar da kansa, ya na shan nasa.


Lawalli da yake yayan lawisa ya ce "Rumaisa ki sha kunun mana"


"Bana shan kunu" ta faɗa a raunace.


Ya ce "Au mutan birni ba cimarku ba ce ba, Gwaggo dafa mata shayi, bari na sayo madara a shago, a sayo miki burodi"
Dariya ruma ta yi ta ce "Meye kuma burodi, buredi ake cewa ai" karo na farko da tun da ta zo ta yi dariya, gaba ɗaya hausar ta su wani iri take jin ta.


Shima ya yi dariyar ya ce "To shikenan buredi bakanuwa".


Ta ce "Banda buredi, shayin kawai zan ci wainar geron"


Aliyu ya galla mata harara, ta basar kamar ba ya ganshi ba.


Haka kuwa aka yi, sai da aka samo shayi sannan ruma ta karya.


Gwaggo ta ce lawisa ta zagaya da ruma sashen matan yayyenta su gaisa, su ga ruma.


Jiki na rawa lawisa ta amsa, ta jagoranci ruma zuwa ɓangarorin gidan.
Ruma ta sha mamakin waɗanda ta din ga gani a matsayin ma'aurata, duk yara da su.


Sai dai Mutanen gidan akwai su da kirki, hannu bibbiyu suka din ga karɓar ruma, suna yi mata barka da zuwa.


A hanyar komawarsu sashen gwaggo ruma ta ce wa lawisa "Wai duk wannan sirikan gwaggo ne?"


Cikin jin daɗin ruma ta kulata lawisa ta ce "Eh" ruma ta jinjina kai.


Bayan sun koma sashin gwaggo, lawisa ta ɗau niƙa za ta kai, ruma ta ce za ta bita. Suna tafe a hankali ruma ta fara sakin jiki da lawisa, ta din ga kallon garin, yayi kyau sosai, 'yan garin ma'abota noma ne.
Duk wanda ya ga Lawisa da ruma sai ya tambaye ta wacece ruma, ta ce musu 'yar uwatta ce. Abin yayi ta bawa ruma mamaki, ita a gida unguwarsu wa ma ya damu da wani, da za a din ga tambayarka waye wannan.


Ko da suka dawo gida ma, ruma a hankali take sakin jiki da lawisa, suka fara aiki tare suna ɗan taɓa hira.


Wajen sha ɗaya na safe, lawalli ya ɗauki Aliyu a babur ɗin sa suka tafi can wani ƙauye, in da a nan wasu daga cikin gonakin nasu suke, wurin gidan wani kawunsu da suke kira da baba Habu.


Ruma ta zazzage kayan da ta zo da su tana sake ninkewa, bayan ta gama ta ɗauko wayar nan ta ta, ta fara kallon hotunan ta.
Lawisa ta zauna a kusa da ita tana leƙawa. Gwaggo ce ta kira lawisa, ta tashi ita kuma ruma ta cigaba da kallon wayar.


Hotuna ne da videos da ta din ga yi ciki har da wani sashe na wannan jakar ta bullet da ɗaya daga cikin mutanen nan ya rataya, sannan a hotunan akwai in da gefen fuskar ɗaya daga cikinsu ta fito.
Ruma ya ajiye wayar tana tunin wasu abubuwa da suka dabai baye mata kai ta kasa gane kansu.
Bindiga dai jami'an tsaro ne suke ta'amalli da ita, amma ta yaya za ayi ace da saninsu ana shiga da fita da su ba tare da sun tsawatar ba?' ajiye wayar ta yi, tana son ƙara nutsawa cikin tunani, amma kwanyarta ta gaza bata komai.


"Ruma zaki je rafi, muje ki ga ruwa da duwatsu".


Gwaggo ta ce "Ke kar ki kaita ki wahalar da ita mana"


Ruma ta ce "A'a gwaggo zan je" tayi maganar tana miƙewa tsaye, ta saka hijjabi suka sake fita.


Wani ɗan madaidaicin rafi suka je, 'yan mata wasu na wanki a gefe, wasu kuma suna ɗiban ruwa. Ruma ta samu na yi, ta din ga ɗaukar hoto, ta din ga tsalle-tsalle a wurin, yanayin ya burgeta.


Kan wani ɗan dutse ta hau, can nesa ta hango wani wuri baƙiƙirin kamar an yi gobara. Ta kalli lawisa ta ce "Lawisa, can gobara suka yi ne?"


Lawisa ta ce "Wallahi wasu fulani ne suka kafa sansani a wurin, cikin dare aka kawo hari, aka ƙona musu shanunsu, suka ce manoma ne suka yi musu ake ta rigima, da ƙyar abin ya lafa"


"Kaii aka ƙona musu shanunsu, kuma da gaske manoman ne suka yi musu?"


Lawisa ta kai bakinta kunnen Ruma ta ce "Ke 'yan ta'adda ne fa suka yi musu, amma aka ce faɗan fulani da manoma ne, amma kar ki ɗaga hankalinki fa, mu nan haka lafiya lau muke zaune, an fi tashin hankalin a wuraren su Baba habu".


Ruma ta yi ajiyar zuciya ta ce "To kuma ba a gayawa 'yan sanda ba?"


Lawisa ta ƙwalo ido ta ce "'yan sanda, a ina zamu ga 'yan sandan ko sun zo me zasu yi, wataran dai sojoji na zuwa ayi ta harbe-harbe abin tsoro"


"Zo mu je wurin, in ga wurin sosai da sosai "


"Ke, Aikuwa tsaf fulanin nan zasu illata mu, yadda suke a ƙule zo mu tafi gida, na cewa Gwaggo ba zamu daɗe ba"


"Ke ki tafi, ni ba yanzu zan taho ba".


"To ai baki san hanya ba"


Ruma ta ce "Idan na ɓata na tambayi hanyar, ni wurin can nake son zuwa " tsoro ne ya kuma kama Lawisa ta cewa ruma "Ki zo yanzu mu koma gida, akwai hanya mai sauƙi da zan bi da ke muje wurin ".


Ruma ta ɗan rausayar da kai ta ce "Ina fatan ba ƙarya ki ke yi mini ba, ina son in ɗauki hotunan wurin in ɗau komai, yadda zan ji daɗin bayar da labari, kuma idan na bayar a yadda tunda ina da hoto".


Lawisa ta yi murmushi ta ce"Haka ne, karki damu" ta lallaɓa ruma suka koma gida.


Sai dai a washegari ruma ta faki idon mutanen gidan ta fice, kai tsaye wurin da aka yi wa fulanin nan ƙone-ƙone ta je. Sai dai tafiyar da nisa sosai, wurin shiru ba kowa sai ragowar abubuwan da aka ƙona, da tsirarun bukkoki a can gaba kaɗan, wurin kamar an yi wata annoba.


"Ke wace wannan me ki ke yi a wurin nan?" A hankali ta waiwaya taga wani dattijo a tsaye s bayanta, hannunsa riƙe jallon ruwa.


"Sannu baba" ya amsa da yauwwa.


Yana cigaba da ƙarewa ruma kallo.


"Baba gidan 'yan uwanmu mu ka zo, na hau wani dutse na hango nan shine na ce bari na zo na gani, Allah ya mayar da alkhairi amma kun gayawa 'yan sanda abin da ya faru?"


Kallon ruma yake, yadda take magana fiye da shekarunta.


Yayi ajiyar zuciya ya ce "Gidan wa ki ka zo a garin nan?"


"Gidan dagaci ne, ɗan uwan babanmu ne" ya jinjina mata kai ya ce "To mun gode da jajen da ki ka yi mana, amma maza ki tafi kar sauran mutanen rigar nan su ganki".


"To in sun ganni mai zai faru me na yi musu?"


"Kasheki za su yi, dan haka muje na raka ki hanya" babu musu ya saka ruma a gaba har zuwa cikin gari, suna tafe suna hira ruma tana addaba masa da tambayoyinta da ba sa ƙarewa"


A hanya suka yi sallama, ya koma ita kuma ta ƙarasa gida.


Gwaggo duk ta tashi hankalinta rashin ganin ruma, ita kuwa ko a jikinta ta ce kallon gari ta fita yi.


Sai dai a tattaunawar ta da dattijon nan ya gaya mata wasu abubuwa da suka sake ɗaure tunaninta.


****
Hajiya Lubabatu ce ta tsaya a tsakiyar ɗakinta, tana kallon hoton Galadima mai ci a yanzu, wands ya kasance mijinta da yake can ƙasar Germany yana jinya, ta ɗan lanƙwasa yatsan hannunta ɗaya sannan ta furta "Ka yi haƙuri ranka ya daɗe, bani da isasshen lokacin da zan cigaba da ɓatawa a kan ka, goben ɗana ita ce a gabana yanzu " ta yi maganar tamkar na cikin hoton yana jinta.




Khalifa ne zaune a kan kujerar da take kallon wadda mahaifinsa yake, mahaifinsa sai murmushi yake sannan ya nisa ya ce "Ina jinka Khalifa".


"Yauwwa daddy, kamar yadda nayi maka bayani, na tsara komai kuma ina da yaƙinin komai zai tafi dai-dai da yardar Allah".


"Haka ne, banƙi ta taka ba, na kuma yabawa ƙoƙarin da kake yi, amma gani nake komai zamu yi wa yaron nan ba zamu huce ba, yanzu haka bayanai sun zo mini yana garin Abuja, sai dai ban san wurin wa yaje ba, idan har ya cigaba da abin nan EFCC zata bincike ni, kuma daga haka ya ɓata siyasata, ya ci mutuncina kuma ya ɓata gobenka".


Khalifa ya gyara zama ya ce "Daddy, ai shiyasa nake ta ƙoƙarin aikin nan ya tabatta, ta yadda zan kau da hankalinsa a kan komai, ya tattarashi a wuri ɗaya, ka harda dani, abin nan zai yiwu daddy, kuma akwai nasara a ciki".


Senator wakili ya yi murmushi ya ce "To shikenan, ina saurarenka, sannan duk abin da kake buƙata, i will make sure that I provide it".


"To Shikenan Daddy, godiya nake "


Yayi murmushi tare da jinjina masa.


***
Kwanakin su ruma uku, ta saki jikinta, duk da kullum sai sun yi waya da mama, yawo kuwa kamar ta ci ƙafar kare, har gona suke zuwa ita da Lawisa, har ta saba da sirikan gwaggo da yaran maƙwabta.
Sai dai gona ɗaya aka samu aka sayar, a gonakin baban nasu, kuma shima dubu ɗari bakwai kawai aka samu, saboda yanayin in da gonar take babu tsaro sosai.
Ana i gobe zasu dawo kano, Gwaggo ta shirya ruma, ta haɗata da lawisa lawalli ya kai su can wani ƙauye, gidan wani ƙanin mahaifinsu, wai su gaishe su.
Aliyu sai mita yake yana tambarat gwaggo yaushe su ruma za su dawo, saboda da sassafe yake son su kama hanya, gwaggo ta ce kar ya damu, gobe da safe zasu dawo.


Har washegari da safe su ruma ba su dawo ba, Aliyu ya ce "Gwaggo, wai haryanzu su ruma ba zasu dawo ba, tafiya fa zamu yi, bana son rana tayi mana".


Gwaggo ta ce "Gadanga, sai dai kayi tafiyarka kai kaɗai, ina sane na tura ruma can, sai za a koma makaranta zan dawo da ita da kaina, yanayi ya nuna mini babu isasshen tsari a jikinta, kuma akwai buƙatar ta zaga ta san dangin mahaifinta suma su santa"


Aliyu ya ce "Amma gwaggo ba mu yi haka da mama ba, dan Allah kar ki yi mini haka".


Gwaggo ta ce "Mhmm, sai kuma ka yi, na gama magana"


Saroro Aliyu ya yi ya ma rasa mai zaice, ya ciro wayarsa ya kira mama a waya.


Yana kira mama ta ɗaga ta yi sallama.


"Mama, gwaggo fa ta tura ruma wani ƙauye, wai ba zamu taho tare ba sai an koma makaranta zata da wo da ita".


Gwaggo ta ɗan ɗaga murya ta ce"Eh, ni na ce ba zata dawo yanzu ba, sai na gama nema mata tsarin jiki, sannan kuma ta san dangin mahaifinta, tunda ba zuwa take ba"


Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Aliyu ka taho kawai, idan ka tsaya zai zama abin magana, ƙyaleta taho"


"Amma mama...


"Kar ka ce komai, in dai ruma ce, da kansu za su tattaro su dawo da ita, ka taho ka barsu".






Ayshercool.




*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*












Abin da gwaggo ta yi ba ƙaramin ɓatawa Aliyu rai yayi ba, da ya san haka ne da ba zai taɓa bari ta saka a kai ruma ko ina ba, daga zuwa ziyara kawai ta riƙe 'ya wai sai wani lokaci.


Ya sake duban gwaggo ya ce "Gwaggo, ruma fa ba zata yarda ta zauna a garin nan ba, rigima za ta yi miki idan ta dawo ta tarar na tafi na barta".


Gwaggo ta ce "Babu komai, na san yadda zan shawo kan kayata, amma a yanzu dai ba in da zata".


Takaici ya ishi Aliyu, ya bi gwaggo da kallo.


"Gadanga ko dukana zaka yi ne? Na gama yanke hukunci, idan kuma kaima zaka zauna ne ni haka nake so, sai mu zauna idan lokacin yayi sai ku tafi duka".


Tabbas ba dan gobe yana da test mai muhimmanci a makaranta ba zama zai yi, ya saka lawalli a gaba sai ya kai shi ya ɗauko ruma, amma ba yadda iya ya ɗauki jakarsa ya fice.


****
Har Adam yayi kwanakinsa uku a birnin tarayya, bai iya aikata komai ba, saboda da ya fita da niyyar zuwa wani wuri, sai jiki ya hau rawa kai ya hau ciwo, ga ruma da ta addabawa rayuwarsa ya kasa mantawa da ita, komai yake yi sai ya din ga ganinta.
Bayan ya cika kwanaki huɗu, ya kira Ammi yayi mata ƙaryar bai gama abin da yake yi bane, sai dai tattaunawar haka aka yi ta babu shi, duk da halartarsa tattaunawar na da matuƙar muhimmanci.
A kwana na biyar ya kira direbansa a waya, ya ce ya zo da mota ya same shi a hotel ɗin da yake.
Ƙarfe biyu direban ya sameshi, sai dai a wannan karon cikin ikon Allah tun da ya fito sau ɗaya kan ya sara, jiri ya ɗan ɗebe shi, amma ya tattara nutsuwartsa, yana addu'a, ya nufi motar.
Suka gaisa da direban nasa, yayi masa ya hanya, daga nan ya ce ya gaya masa in da zai kai shi.
Mintuna ashirin ce ta kaisu, a harabar wata plaza suka yi parking, Adam ya buɗe motar ya fita.


Wani matashi ne zaune wanda zai yi sa'an Adam, yana danna computer, yana ganin Adam ya miƙe cikin girmamawa yana murmushi ya ce "Barka da zuwa"


Adam ya ƙarasa yana murmushi, ya miƙa masa hannu suka gaisa, sannan ya zauna.


Matashin ya kalli Adam ya ce "Adam, ya aka yi an shirya zama da kai, amma ba ka yi attending ba?, na din ga kiran wayarka ba ka ɗagawa, har wayar ma ta daina shiga gaba ɗaya?"


Adam ya ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa ya ce "Am sorry Habib, wata matsala aka samu, amma komai normal yanzu in sha Allah".


Cikin kulawa Habib ya ce "Are you safe?"


Adam ya jinjina kai sannan ya ce "Me aka tattauna, wace matsaya aka cimma?"


Habib ya ɗan rausayar da kai ya ce "To, mun tattauna yadda yakamata, amma dai kamar yadda na yi maka bayani da farko, ko da ka fito ƙarara ka bayyana lamarin nan, ko an je kotu za a sake su, saboda haryanzu baka da wata cikakkiyar hujja ta zahiri da zaka kafa, yanzu ko kun yi wani abu a kai, ya riga ya gama shiri, da tattaunawa da lawyoyinsa, ya shirya tsaf da ka yi attacking zai yi depending, yanzu abin da yafi shine ka sake mayar da hankali sosai da kai da abokan aikinka, ku samo hujja ta gaske, ta zahiri da za ayi amfani da ita, nima zan shirya tsaf domin cimma nasara ni da tawagarmu"


Adam yayi ajiyar zuciya tare da dafe goshinsa, ya sake ɗagowa ya kalli Habib ya ce "Duk wata hanya da zan bi domin neman hujjar kama mutumin nan an tosheta, kuma kullum kallon mutunci ake masa, ana sake bashi girma tare da shigar da shi cikin al'amuran ƙasar nan, bayan su ne babbar matsalar mu"


"Adam, tun da ka ga haka, ba shi kaɗai bane, ko dai an san me yake yi ake rufa masa asiri, ko kuma akwai wasu manyan da suke aikin tare "


"Haka ne, abin da nake tunani kenan nima, amma babu komai in sha Allah zamu yi nasara, zan cigaba da ƙoƙari, ina son magana da saifu ma, zan zauna a garin nan sai Allah ya kaimu monday zan koma kano".


Habib ya ce "To shikenan, Allah ya yi jagora, gashi ko shayi ban baka ba"


Adam ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu"


Daga haka Adam ya tashi ya fita, ya saka direbansa ya mayar da shi masauki. Sam ya ƙi yadda yaje gidan sa, saboda wani Dalili nasa.


***


Ƙauye ne sosai in da aka kai ruma, sai dai mutane masu matuƙar karamci da girmama ɗan Adam, tamkar za su goya ruma, dan wasunsu duk basu santa ba, sai dai sun san mahaifinta sosai tunda ɗa ne a wurinsu.
Garin sun yi noma sosai, sai dai an girbe an tare shi a cikin gonaki, ba a kwashe an kai gida ba, ga yanayin garin kamar yanayin garin da aka yi wata annoba.
Wani wurin a ƙone, wani wurin dai gashi nan.
Tun da safe ruma ta fara cewa ita azo a mayar da ita gidan gwaggo, yau zasu koma gida ita da yaya Aliyu, amma dattijon da ya kasance ƙanin kakanta ne ya ce "Ai jikata ba ke ba tafiya, sai hutun makarantar bokonku ya ƙare, kina nan tare da mu"


A ɗan razane ruma ta ce "Saboda me?"


"Haka gwaggonki ta ce"


"Ni gaskiya ba zan iya zama a garin nan ba, gida nake so na koma na ga mama, na gaji, ni ku mayar da ni gida" ta yi maganar tana kuka.


Matarsa da ake kira da iya ta ce "Haba rumaisa, muma fa duk iyayenki ne, muna ƙaunarki sosai, ki kwantar da hankalinki kin ji, za a mayar da ke, idan ki ka matsa zasu iya ƙwaceki gaba ɗaya, 'yan kwanaki zaki yi a mayar da ke"


"Ni mama nake son na gani".


"Ki yi haƙuri, za a mayar da ke in dai wurin mama ne" An kai ruwa rana sosai da ruma, kan ta daina koke-koke, sai dai ita ma ta haɗa musu aiki, ba komai take ci ba, tsirfar yau daban ta gobe daban.


In da ta ɗan ƙara samun sassauci, shine tana tare da lawisa, kuma a gidan akwai wata sa'ar tata zaliha, dan haka sukan ɗebe mata kewa.


***
Ba ƙaramin ɓacin rai 'yan mazan

Download complete TXT · Novel page