KANWAR MAZA 1&2

Chapter 71 of 78

na yanke da zartar da shi dole sai da izininka, kuma kai zaka yi mini jagora zuwa ga tabattauwar abun cikin hukuncin Allah"


Ya jinjina mata kai cikin nutsuwa alamar yana sauraren ta.


Ta ɗora da cewa "To bisa ga al'ada ta masauratar nan, duk cikakken ɗa a gidan nan, a kan yi masa zaɓi na matar da zai aura, ko ya kawo wadda yake so ƴar mutunci idan ta yi a aura masa. wani abu ne ya taso a kan yarinyar nan rumaisa, ƴan unguwar su suna ta yaɗa jita-jitar wai ciki ta yi aka kaita aka ɓoye ta haihu, sunanta dai ya ɓaci a unguwar su, na ga babu wata hanya da zamu bi domin wanketa face Adam ya aureta, duba da irin matsanancin son da take yi wa yaron nan da ta zo da shi, har ina ganin kamar rabata da yaron na shiga hakkinta, saboda na san ciwon abun, ga wannan abu da ya kunno kai game da rayuwarta, na ga abu ɗaya zan iya yi shi ne in sanya adam ya aureta, amma ya ka gani ranka ya daɗe?".


Turaki ya ce "Ikon Allah, kin ga nan Jamil ya zo mini da zancen, akwai buƙatar Samha ta maye gurbin Fulani, duba da yadda ta daɗe tana son adam, dan har na yi na'am na so na tuntuɓeki, to sai gashi kuma kin zo da wani zance da yakamata a tsaya a duba. Tabbas! Idan har da yadda zamu yi yarinyar nan bai kamata mu bari ta wulaƙanta ba, dan haka a wannan karon ma samha sai dai ta yi haƙuri, ko kuma idan yana da ra'ayi ya haɗasu biyu, amma rumaisa ita tafi cancanta ya aura, duk da ƙanƙantarta".


Ammi ta ɗan ji rasss, ba za ta yi fatan adam ya haɗa rumaisa da samha ba, duk da rumaisa yarinya ce amma ba za ta yi fatan ta zama bora ba, tun da dai haryanzu ba ta isa rayuwar aure ba, tana son ya aureta ne dan ya inganta rayuwarta, a haka idan ta ce za su cigaba da ɗawainiya da rumaisa, ƴan uwanta ba zasu harda ba, dan ta lura suna da gudun abun hannun wani.


Turaki ne ya katse mata tunanin ta hanyar cewa "Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kin san akwai ƙalubale, a ƙa'idar masarauta, ƴaƴan sarakuna ƴaƴanmu suke aure, ko ƴaƴan wasu manya, akwai gwagwarmaya idan aka kai maganar nan gaban su wambai"


"Allah ya taimakeka shi ya sanya na zo wurinka, na san kai kaɗai ne zaka iya shiga lamarin nan ka tsayawa adam, jikina yana bani akwai alkhairi a game da lamarin nan, rumais alkhairi ce ga adam"


Ya ɗan yi shiru ya ce "To babu laifi, in Allah ya yarda idan na dawo, zamu yi magana da su, na sanya zancen cikin addu'a idan alkhairi ne Allah ya tabattar ya kawo komai da sauƙi"


"Amin ya rabb, idan komai ya daidaita bana son abun ya wuce watanni uku, kar wani abun ya kutso"


Turaki ya ce "Babu damuwa, babu abun da zai gagara da ikon Allah"


Ammi ta risuna, ta sake yi wa turaki godiya, sannan ta tashi ta fita.


Samha ce ta raka ammi har mota, tana yi mata ta gaida gida.


Ammi na tafiya samha ta koma ɗakin ta, ta ɗau wayarta ta kira jamil.


Yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Yaya jamil, yau ma ammi ta zo wurin mai girma turaki, dan Allah idan ka zo yau ka tuntuɓe shi da maganar, ka ji ko ita suka yi?"


Jamila yayi tsaki ya ce "Ke kin fiye abun haushi wallahi"


"Dan Allah yaya ka taimaka".


Ya ce "Gaskiya bana nan, bana gari sai dai ki jirana dawo, idan na dawo kuma yana umara, na san duk abun da ake ciki dai, in dai a kan maganar ne zasu tattauna da mama"


Samha ta ɗan yi shiru sannan ta ce "To shikenan, na gode " ta kashe wayar cike da fatan Allah ya sa tattaunawa suke a kan ta maye gurbin Fulani.


***
Ana idar da sallar magariba, Huzaifa ya saka rumaisa a gaba yana ta mata faɗa, ta ƙi cin abinci sai mita take a kan abun da aka yi mata a unguwa.
Aikowa aka yi wai ana sallama, ganin ba a faɗi da wa ake sallamar ba, ya sanya Usman tashi ya fita ya ga waye yake yin sallamar.
Aikuwa yana fita ya tarar da mijin maƙwabciyarsu, ya kawo ƙarar rumaisa a kan abun da ta yi musu, na jifa a cikin gida ta yi musu ɓarna, ga uwa uba fashewa matarsa baki ada marmara da rumaisa ta yi.


Usman ya ce "Malam shamsu ai ɓarnar da matarka ta yi mana ta fi wadda ruma ta yi mata, shiru kawai muka yi, duk yadda ruma take girmamata bai hanata yi mata ƙazafi a cikin unguwa ba, ba dan mama ta hana ba, ga kuma albarkacin aure, sai na yi mata wankin babban bargo a cikin unguwar nan, amma tun da abun ya zo da haka, kawai duk sai mu haɗu mu yi haƙuri".


Cikin takaici malam shamsu ya ce "Au haka ma zaka ce? Ta rotse mana ƙwan lantarki na tsakar gida, ta fashe mana glass ga zubarwa da matata jini, amma ka gaya mini wannan maganar?".


"To me zance maka, yanzu dai idan baka haƙura ba, kai ma ka tsinto duwatsu ka yi mana jifa a cikin gidan, ko in kirawo maka rumaisa ka daketa ko? Sai ka huce" aikuwa malam shamsu ya harzuƙa ya fara zage-zage, Usman kuwa ya zage shima yana ramawa, suka nemi bawa hammta iska.


Mama har ta manta da Usman ya fita, ta jiyo zage-zagen usman, yana idan baa rufe masa baki ba, sai ya falla masa mari, kuma ya ɗaga shi ya buga da ƙasa.


Cikin tsananin faɗuwar gaba mama ta taso, hankali a tashe za ta fita, Huzaifa ya ce "Mama ba zaki fita ba, yaya usman bai fiye faɗan rashin gaskiya ba, kuma yaya Abubakar yana kusa, na san zai raba"


Mama ta ce "Kai dan ubanka bani hanya, kar ya janyo mini magana, na ji da malam shamsu suke yi, ba zai wuce a kan abun da rumaisa ta yi bane, usman in dai a kan rumaisa ne, ko ba ta da gaskiya goya mata baya yake yi, shi ba ya bin komai a sannu, wani fannin halinsu ɗaya da ita, zuciyarsu babu afuwa" mama na cikin maganar yaya Abubakar ya shigo hannunsa riƙe da na usman yana yi masa faɗa.


Usman ya ce "Haba yaya, mu bamu suka fi yi wa illa ba, sun yi mana baƙin fenti a unguwa, bamu yi magana ba sai shi, wai shi tattabara wanda ya yankewa ƙauna cibiya, shi ga mai mata, banzar matar da fuska kamar baƙar jaka, wallahi da namiji ce sai na yi mata shegen duka".


Rumaisa ta ce "Ƙazama da ita ba, mai bleaching"


Mama ta dungurewa rumaisa kai, Abubakar kuma ya cigaba da yi wa usman faɗa.


Usman ya ce "Da ne nake adawa da aurar da rumaisa, amma wallahi yanzu na zubar da makaman yaƙi na bi, wallahi party zamu shirya na tashin hankali a unguwar nan, mu hayo dokuna ayi ta kilisa, zamu kaita gidan manyan mutane, mu ga ƙarshen munafurci, mu rufe bakin munafukai" ya kalli rumaisa ya ce "Ke, dan ubanki na daina adawa da auren nan, ki yarda kawai, kuma daga yau daga ita har mijinta kar ki sake gaishe su, ta kuma yi miki maganar banza, zan samo miki duwatsu, daga nan har bamfai ba mai shari'a da ke yarinya ce, na tsaya miki ayi da ni".


Mama ta ce "A'a babu ruwana, kai maimakon ka saita yarinyar nan, ku bi komai a sannu amma kana yi mata huɗubar tsiya, Nuraini har da kai fa kake zigata take rashin ji, babu ruwanka da mutumin nan ku fita sabgarsu, ni ba zan iya tashin hankali da mutane ba".


Usman ya miƙe ya ce "Mama irin masu haƙurinki ake cuta, komai ki ce ayi haƙuri a barwa Allah, da haƙurinki muka ɗauko, muna zaune za a fille mana wuya ki ce mu yi haƙuri"


Dariya rumaisa ta yi, mama kuwa ta rarumi takalmi, ta jefawa usman, ya goce tare da shigewa ɗakinsu.


Ruma ta ce "Allah ya biya yaya usy nawa, Allah ya bar mini kai".


"Ki cigaba rumaisa, yayi ta ɗoraki a keken ɓera ya kai ki ya baro, tun da ke dai ba namiji bace ba".




***
Ko da ammi ta koma gida, Nusaiba da Iman suka tareta suna tambayarta yaya suka yi da turaki?
Nan ta kwashe komai ta gaya musu, iman ta ce "Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya mai girma turaki ya shawo kansu komai ya tafi cikin sauƙi, ni dai ina sonta wallahi"


Nusaiba ta ce "Mhmm, ni kam kawai yadda za ayi zaman nan nake hangowa, ba fa sa shiri ammi, kin ga ita tana da tsiwa, shi kuma akwai faɗa"


Ammi ta ce "Ke rabu da shi, rayuwar aure ta fi ƙarfin wasa, idan suka zauna za su nutsu, sannan a rayuwarsa da ita akwai wani darasi da nake fatan ya koya, kuma kan ayi auren ai dolensa ya dinga zuwa wurinta su saba"


Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai rikici kenan?"


Ammi ta ce "Ta bani tausayi ɗazu da muka yi waya, wai an ce ta yi cikin shege, ana yi mata kallon ƴar iska, saboda ta zo da sabir, idan ban saka takawa ya aureta ba, shikenan an yi mata mummunan tambari, mutane ɗa idan ba na su bane ba, sun din ga janyo masa jafa'i kenan"


Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya shirya, ya tabbatar da alkhairi" suka amsa da amin.


Baba uwani da take laɓe ta ji hirar ta su sama-sama, sannan bakomai ta ji ba, amma a abun da ta jin, ta ƙudurce za ta je ta sanar da Mummy.




Rumaisa mita a cikinta, kamar an yi mata gori, yau wuni ta yi tana cigaba da mitar abubuwan da ake yi mata a unguwar nan, mama tun tana yi mata nasiha tana cewa ta bar wa Allah, har ta yi mata banza ta ƙyaleta, Abdallah ya sakata a gaba yana cigaba da kunnata, tana mita. Bayan fitar Abdallah rumaisa ta shiga ɗakinsu, ta duba wurin da yake ajiye fensiransa na zane kasancewar sa architect.


Ta zauna ta nutsu sosai, ta hau zane-zane.


Mama ta ce "Uban me ki ke yi musu a ɗaki, ki ka shiga ki ka yi shiru?"


Rumaisa ta ce "Bakomai"


"To fito musu daga ɗaki, tun basu dawo sun tarar da ke ba"


"Mama zan fito ina zuwa"


Sai da ta gama abun da Allah ya nufeta da yi, sannan ta fito ta fice ba tare da sanin mama ba.


Maƙwabciyarsu ta zana, kuma zanen ya fita sosai, ta yi headline da munafukar unguwa, a ƙasa ta rubuta by Rumaisa Mahmud ƙanwar maza. Ta je ta liƙe a ƙofar gidan matar, ta nausa ta tafi gidansu Habiba, ba tare da mama ta san ta fita ba ma.




Ayshercool.


paid book ne, ₦500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143




*KANWAR MAZA*


*39*






*PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*








Jin shirun yayi yawa ya kuma sanyawa mama ta ƙwalawa rumaisa kira, amma har ta kira kusan sau uku shiru, ba ta amsa ba, mama ta kaste abun da take yi, ta fita domin duba me rumaisa take aikatawa ta ji shiru. Sai dai da ta fito tsakar gida babu rumaisa ba alamarta.
Mama ta leƙa ɗakin ƴan maza, amma babu rumaisa ƙarshe ma sai shiga Maman ta yi ta kwaso kwanukan ta, da suka kai ɗakin suka bar su, ta fito ta duba banɗaki da kitchen duk babu rumaisa, tsayawa ta yi tana tunanin ina rumaisan ta tafi ba ta gaya mata ba?.


Tana cikin jimamin in da rumaisa ta tafi babu izininta, shamsiyya maƙwabciyarsu ta yi sallama, ita da wata mata.
Mama ta amsa musu cikin sakin fuska, ba tare da nuna mata ta san ta yi wa ƴarta ƙage ba.


"Maman rumaisa ni ba zama zan yi ba, ki shiga tsakanina da yarinyar nan, kalli abun da ta yi mini jiya a fuskata, da ɓarnar da ta yi mini a cikin gida, maigidana ya kawo ƙararta, ƙarshe ba wani mataki da kuka ɗauka, sai ma cin mutumci da ya biyo baya, yau kuma ta je ta yi zane ta liƙe mini a ƙofar gidana ya ƙi fita, wai munafukar unguwa, me na yi muku haka ne?"


Cikin dattaku mama ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, yaran zamani ne sai godiyar Allah, wallahi da kaina na yi niyyar shigowa na baki haƙuri, wallahi ban san ta yi ba, kin san dai ni ba zan goyi bayan ta yi wannan rashin kyautawar ba, ban san ta yi miki ba, dan Allah dan annabi ki yi haƙuri, bari ta shigo gidan, zan hukunta ta kuma zan sanya ta je ta cire, dan Allah ki yi haƙuri"


"Wallahi banda ina jin nauyinki, Allah da sai na kama rumaisa na yi mata shegen duka".


Mama ta ce "Ashsha, ba za ayi haka ba, ai ke ma ƴarki ce, yanzu kina taɓata komai zai ɓaci, yayyenta ba sa ganin laifinta, amma dai ina baki haƙuri, da kaina zan hukunta ta, kuma zan aikota ta baki haƙuri".


Haka Jamila ta yi ta farfaɗar maganganu, mama tana bata haƙuri, da alwashin hukunta rumaisa, bayan tafiyarta mama ta dafe kai, haryanzu rumaisa babu alamar hankali a tare da ita, tuno damben da suka sha da ƴar ajinsu ta yi, abu har wurin ƴan sanda saboda wannan shegen zane-zanen da take yi, shi kansa Abdallah dan ba yadda za ta yi da shi ne, abun da yake karanta kenan, ga rumaisa na neman gadarsa, in dai zane-zanen banza da na wofi ne, a litattafan makarantar ta ma yi take.


Mama ta rasa mai ma yakamata ta yi, ba ta san ta ina zata fara neman rumaisa ba.


Rumaisa kuwa gidansu habiba ta tafi, suka shantake suna ta hira, ta bawa habiba labarin abun da ta yi wa maƙwabciyarsu.
Habiba ta ce "Kin mini daidai, da nice ba zan iya ba, tsoro nake ji, kin ji yadda matar nan ta din ga yayata maganar nan a cikin unguwar nan, ummanmu ce ta fara taka mata burki ta ce ƙarya take yi, daga nan ta je ta gayawa mamanku"


Rumaisa ta ce "Hmm, ai sai ta gane ba ta da wayo kan ma bar unguwar nan, da ina mutunta ita da mijinta, amma tun da ta taɓo ni, za ta gane bata da wayo"


Cikin rashin fahimta habiba ta ce "Ki bar unguwar nan ki koma ina?"


Rumaisa ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "Ke share kawai, na san zuwa yanzu wataƙila ta je ta kai ƙarata gidanmu"


"Me ki ka yi mata?"


Cikin ƙwarin gwiwa rumaisa ta ce "Zanata na yi, na rubuta munafukar unguwa, na liƙe mata a ƙofar gida, na san yau za a azabtar da ni a gida, amma ba zan koma yanzu ba"


Habiba ta ce "Wai ruma ba kya jin tsoro ke? Mama ba ta san kin zo nan ba?"


"Ba ta sani ba, idan aka kai ƙarata ina gidan, a gabanta mama zata bani rashin gaskiya, duk da abun da ta yi mini, zuwa yanzu kuwa na san ta tafi, in koma gida a haɗani da mai sunan baba, ya bani gwale-gwale"


Dariya habiba ta yi ta ce "Wato ke har ma kin san me za ayi miki, ina yaya Aliyu?"


Rumaisa ta yi mata kallon ƙasan ido ta ce "Yana makaranta, in ce kina nemansa ne?"


Habiba ta waro ido ta ce "Ke a'a, kawai dai tambayarsa na yi"


"Meyasa duk cikin yayyena shi ki ka sani?"


Habiba ta ce "Bakomai, ya na da kirki ne"


Rumaisa kawai ta yi dariya, tana lissafa yadda zata wanye da mama idan ta je gida.


Mama kuwa sai kallon agogo take yi, tana lissafa, ina rumaisa ta tafi haka? Ta ƙi dawowa, zuciyarta ta bata saboda abun da ta aikata ne ya sanya ta fece.


Kasancewar azahar ta yi, kuma juma'a ce ya sanya ƴan samarin mama dawowa gida, domin shirin masallaci, kuma aka yi sa'a ana public holiday, rumaisa ba makaranta ta je ba.


Faɗan Abdallah mama ta jiyo, yana faɗin "Uban waye ya taɓa mini kayan zanena, bana son rashin mutunci, Huzaifa ban hanaku taɓa mini kaya ba?"
Huzaifa ya ce "Ni na iya amfani da wannan abubuwan naka ne? Sai dai ko Yasir"


Yasir ya tari numfashin Huzaifa ta hanyar cewa "Saboda ni ka raina ba, yaushe na zauna a gidan balle na taɓa masa kaya".


Mama ta fita tsakar gida ta ce "Ba aikin kowa bane, rumaisa ce ta taɓa maka, ita ta shiga ɗakin ta yi shiru, ita ce ba wani ba".


"Tana ina, sai ta ci ubanta yau sai na zaneta, har da gum ɗina ta buɗe ta bar mini a buɗe"


"Hmm, wannan yarinyar ai sai fatan shiriya, ina fatan Allah ya sanya auren nan ne mafi alkhairi, ko yau aka ce za ayi zance a ɗaura su tafi da ita"


Abdallah ya ce "Tana ina?"


Mama ta ce "Ina na sani, ta yi wata aika-aikar ta gudu, ban ma san ta fita ba".


Yasir ya ce "Kai wannan yarinya, Allah ya yi mata maganin abun da yake damunta yake sanyata rashin ji".


Rumaisa ba ta tashi tafiya gida ba, sai da unguwa ta yi tsit, duk an tafi masallaci, sannan ta nufo gida, cikin shirin karɓar kowane irin hukunci za a yanke mata.


Da sallama ta shiga gidan, ta yi sa'a mama tana salla, ta lallaɓa ta shiga ɗakin ta zauna, tana jiran mama ta idar, ta shirga mata ƙaryar da zata kare kanta.


Mama tana jin motsin rumaisa, amma ta shareta, ko da ta idar da sallar ma ta yi lazumi, ba ta tankawa rumaisa ba.


Cikin tsoro rumaisa ta ce "Mama" banza tayi da ita ta shige uwar ɗaki ta bar rumaisa.


Tun rumaisa

Download complete TXT · Novel page