Kanwar Maza 3&4

Chapter 17 of 69

zaku yi mata adalci ta maye gurbin aisha ba, taƙi auren kowa ta dage sai shi, amma ka yi burus, ku ke je waje nema masa auren wata?"


Turaki ya ce "Ban fifita kowa a kan ƴaƴana ba, sai dai son da nake yi wa ƴaƴana, ba zai sanya na zaɓi son zuciya ba. Ba zai yiwu sun kawo wadda suke so ya aura na wuce masa gaba a matsayina na ubansa, na yi amfani da ƙarfin ikona, na ce sai ya auri ƴa ta ba, ki sani zan iya tursasa shi ya auri ƴa ta, amma ba zan iya tursasa shi ya so ta ya kyautata mata ba, na yi mata nasiha tun ba yau ba, a kan ta haƙura da shi, ta yi addu'a ta nemi wani ta aura, har haɗata da na yi da ɗan gidan madaki, Muhammad Sani, ya ce ya na sonta ta watsa mini ƙasa a ido, sai yanzu kuma ku ce ga abun da ku ke so sai na yi, ba zai yiwu ba, kuma ku yi haƙuri, da Samha da takawa duk ƴaƴana ne, ba wanda zan yi wa dole a kan wani abu da yake son zuciya"
Ba ƙaramin ƙuluwa ta yi ba, da jin maganganun turaki, ba ta sake cewa komai ba, ta tashi ta bar ɗakin.


Zainab ce ta shiga falon mama, in da Samha ke zaune tana kallon tv, hannunta riƙe da wayarta, ta zauna tana faɗin "Ohh God, ita wannan yarinyar ita kenan kullum cikin ciwo?"


Samha ta kalleta ta ce "Wacece?"


"A status ɗin Nusaiba na gani, wai iman babu lafiya, ba ta san waye a kanta ba ma, shikenan ita giwa kullum tana hanyar asibiti saboda ƴar tsintuwa, dama ta mutu ko sa huta gaba ɗaya"


Samha ta yi ajiyar zuciya, tare da ji a Jikinta, aikin ta ya fara aiki kenan.


Fuuu mama ta shigo falon,. Kamar mai tafiya a kan iska.
Duk suka bita da kallo, suna tambayar ko lafiya?.


"Hmm, ni da turaki mana, ya gaggaya mini magana a kan kawai na ce, meyasa bai saka adam ya auri Samha ba, wai nema masa aure suka je yi ranar juma'a.


Ƙuuuu Cikin Samha ya bayar, wani irin fargaba da faɗuwar gaba ya kamata, neman aure aka je yi wa Adam?.


"To kin ji, a wannan karon dai kya haƙura ko?" Zee ta yi maganar tana kallon Samha.


"Mama, neman aure kuma? Ba iman za su bashi ba?".


"Bana tunanin ita ce, wata ce daban gaskiya, tun da ya ce sun je nema masa ne, da ita ce ai ba sai sun yi haka ba"


Wani irin gumi ne ya shiga ratsowa daga cinyar Samha, gaba ɗaya kanta ya toshe, saboda jin abun a bazata an shammaceta da yawa.


"Amma mama wacece haka?"


"Oho ina na sani, bai gaya mini ba, ni takaici ma bai barni na san wacece ɗin ba".


Cikin hanzari, ta tashi tafi ɗakinta zuciyarta na yi mata zafi, tsabar wulaƙanci a waje ma ake je aka nema masa wata bayan ita gata a zaune an san tana san shi


Zama ta yi daɓas a gefen gado, zuciyarta na ƙuna, wannan shine baba na ɗaka gemu na waje, amma mayar da ita wata sako tumaki ɓallo jakai.


"Tun da naga aikin malamin nan yana aiki, Adam da ni ka ke zancen, wallahi kana ji kana gani sai an mayar da kai mace, ba zaka amfani kowacce mace a rayuwar aure ba, sai dai ta kalleka ka kalleta, amma kai da sake kwamciya da wata matar, har abada sai dai idan ni ka aura, zaka gane baka da wayo".


***
Mai sunan baba yana tsaye a kitchen, yana kwashe abinci, kasancewar mama bata nan, babu kowa a gidan, mama tana kasuwa, sai shi da ya dawo gidan yanzu, yayi saurin ɗora girki, dan ya san tsaf rumaisa zata dawo a kowane lokaci idan ba a gama abinci ba, idan ta din ga kwanciya tana kuka, sai ta saka ya daketa. Ga lokaci ya riga ya ja.


Mama ce ta kira shi a waya, ya ɗaga yayi sallama.


Ta amsa sannan ta ce "Babana kana ina ne?".


"Na dawo gida, na ɗora girki ne".


"Yauwwa, dan Allah idan rumaisa ta dawo, ka saka ta yi wanka ta yi salla, ka tafi da ita asibitin da ta kwanta, an kwantar da iman ku wakilceni ku dubata, yanzu muka yi waya da hajiyar, wai an kaita asibiti ba ta san waye a kanta ba, ni kuma bana tunanin zan dawo da wuri".


"Tom" ya faɗa a taƙaice ya ajiye wayar, ya cigaba da aikinsa.


"Assalamu alaikum" rumaisa ta yi sallama, sai dai kan ya amsa ta fara cewa "Wani gardin ne yake yi mana abinci yau, Allah ya sa yayi daɗi, na ji ƙamshin miyar har tsakiyar kaina, Allah yasa ko shinkafa an gama, in fara rage hanya, dan yunwar da nake ji ba a cewa komai" ta ji shiru ba a amsa ba, ta nufi kitchen ɗin tana cewa "Baƙon aljani muka yi ko kurma, da nake magana aka shareni".


Tozali da tayi da shi ne, ya sa ta ci wani wawan burki, rabon da yayi girki har ta manta, dan haka ba ta kawo shi ne ba.


"Yi haƙuri, ban san kai ne ba, dan Allah ka yi haƙuri"


Kifi yake sakawa a miyar, ba tare da ya kalleta ba, sum-sum ta bar wurin ta koma ɗaki ta kwanta.


Mai sunan baba bai tashi gaya mata saƙon mama ba, sai da ta fara shirin islamiyya, ya ce "Na gaya wa shugaban makarantarku ba zaki shiga ba yau, zamu je dubiya"


"Ina?" Ta tambayeshi tana kallonsa, sai dai ta manta shi mai sunan baba, idan ya ce ayi kawai ayi, ba tare da tambayoyi ba.


Har suka tafi dubiyar, mamaki take yi, waye babu lafiya, ta lissafa wannan ta hango wancan, amma ta kasa gano waye babu lafiya.
Sai dai ba ta ƙara sarewa da al'amarin ba, sai da ta gansu a asibitin da aka kwnatar da ita.


Lambar mama ya kira, ya tambayeta wani ɗakin ne, ta sanar masa, yayi gaba rumaisa ta bishi a baya.
Sai da suka je ƙofar ɗakin sannan ya tsaya, ya kalleta ya ce "Ƙwanƙwasa ki fara shiga"


Ta matsa gaban ƙofar, ta ƙwanƙwasa sannan ta buɗe ta shiga da sallama babu kowa a ɗakin, sai iman da ke kwance, hannunta ɗauke da cannula, an rataye robar ruwan da aka gama saka mata a drip stand.


Shiga ya yi shima, sai dai babu kowa a ɗakin sai ita kaɗai.


Da sauri rumaisa ta ƙarasa gaban gadon tan faɗin "Subhanallah, Anty Iman, baki da lafiya ne?" Sai dai ta tarar bacci take yi.


Ta kalli mai sunan baba ta ce "Amma ya naga babu kowa a wurinta" shirun da yayi mata ya sanya, ta tuna ta yi tambaya ba a gurbinta ba.


Da sauri ta ce "Bari na duba waje, ko zan ga wanda yake zaune tare da ita". Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya a tsaye, ya sake kallonta tana kwance cikin doguwar rigar material, dogon gashin nan ya sha ribbon, duk da ya ɗan hargitse, ga farar fatarta gwanin sha'awa, babban abun burgewa da jikinta, bai wuce wuyanta ba, duk da ba ta da ƙiba, amma tana da irin wuyan nan, mai guru-guru.


Da sauri ya sunkuyar da kansa yana a'uzubil'ahi.


Zagayawa rumaisa ta shiga yi a cikin asibitin, tana mamakin waye yake zaune da iman a asibiti, ya bar ta ita kaɗai babu kowa?


A hankali Iman take furta "Ammi, Ammi ruwa, ƙishirwa nake ji" yana jin ta, yayi shiru, kamar babu kowa a ɗakin.


Tun bayan farfaɗowarta, kasancewar ciwon kan baya sauka, ya sanya likitocin, suka yi ta yi mata allurar barci, da sai yanzu ta saketa ta tashi.


Duk da tana cikin ciwo, sai da ta razana da ta ganshi, a tsaye yana danna wayarsa.


Tunani take yi ko a mafarki take, ta miƙa hannu jikinta yana rawa, tana ƙoƙarin ɗaukko robar ruwan da ke kan side bed.


Sai a lokacin ya motsa, ya ƙarsa, ya ɗau kofi, ya zuba ruwan ba tare da ya kalleta ba ya ce "Tashi ki sha"


Cikin tsananin tsoro ta ce "Bani in sha a kwance, ba zan iya tashi ba"


Miƙa mata ruwan yayi, ya ga iya gudun ruwan ta, ta fara ƙoƙarin sha a kwance, ya karɓa kofin ya ce "Tashi!"


Kamar zata fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri kaina ciwo yake yi"


Haushi ne ya kama shi, gani yake kawai tsabar langwai ne, da iskanci. Ya saka hannu ya ɗagota gaba ɗaya, hakan yayi dai-dai da shigowar nusaiba.


Wani irin ihu ta saki, ta riƙe hannunsa, hawaye na bin fuskarta, sabodaa ji ta yi, kamar kanta ya rabe biyu.


Da gudu Nusaiba ta ƙaraso tana faɗin, "Wanene wannan, bawan Allah lafiya?" Tayi maganar tana yi masa kallon sani, amma ta manta a ina ta san shi.


Wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Wane irin shirme ne zaki tafi ki bar mara lafiya ita kaɗai, wace irin jinya ce haka?"


Gaba ɗaya ruɗewa nusaiba ta yi, ba ta san waye ba, amma kwarjinin sa ya razanata, ta ce "Likita ne ya ce a bani jininta na kai gwaji yana buƙatar result yanzu, ammi kuma ta riga ta tafi gida ta je ta huta, shine na je lap ɗin asibiti, suka ce ba sa yi, shi ne na fita waje, da takawa nake jira ya zo ya kai, likita ya ce lallai yanzu yake so"


Tsaki yayi, ya kalli iman ya ce "Ke kuma cikani" wata irin kunya ce ta kamata, dan ba ta san ta riƙe shi haka ba.
Ta sakar masa riga, ta karɓi ruwan ta fara sha.


"Ita kuma wannan ma shiririciyar ko ina ta tafi oho mata".


Rumaisa kuwa lungu da saƙo na asibitin take ta bi, har ta gaji ta kama hanyar komawa ɗakin, kawai ta hango motar takawa, yayi parking ya fito daga motar, hannunsa riƙe da leda.


Aikuwa ta nufe shi, babu tsammani ya ganta a gabansa.


"Dama kai ne a wurin Anty Iman? Haka ake jinyar mutum dama, ka yi tafiyarka ka barta? Kai idan aka yi maka haka zaka ji daɗi ne?"


Sororo yake bin ta da kallo, yadda take yi masa haƙilon masifa kamar babarsa.


"Ya ina magana kana kallona, sai wani abun ya sameta? Kawai ka ɗau mota ka tafi yawonka, ka bar mara lafiya ita kaɗai? To wallahi sai na gaya wa ammi" banza yayi mata, ya nufi cikin asibitin, rumaisa kuma ta bishi tana cigaba da mita.


Cike da shiga taitayi, Nusaiba ta bawa mai sunan baba haƙuri, ita dai ba ta san waye ba, amma ta tsinci kanta da shakkarsa.


Ta kalli iman ta ce "Iman, me zan baki ki ci to, tun jiya baki ci komai ba, an ce lallai ki samu ki ci wani abun, ga abinci ga fruit wanne zaki ci?"


Iman ta girgiza kai ta ce "Na ƙoshi, bana son cin komai" mai sunan baba a ransa yake jinjina halin mata, su a rayuwarsu ta duniya komai sai an lallaɓasu? Abincin ne ba zata ci ba, sai an yi ta rarrashinta, alhalin ta san kanta zata cuta idan ba ta ci ba.


Takawa ne yayi sallama, ya shigo hankalinsa a kan iman, ya ƙarasa gaban gadon ta.


Nusaiba ta ce "Maman sabir, yaushe ki ka zo?"


"Tun ɗazu muka zo ni da mai sunan baba, ashe wannan ne yake jinyarta, ya tafi ya barta ita kaɗai" tayi maganar tana nuna Adam.


Nusaiba ta ce "Eyya, ni ce tare da ita, jininta na tafi kai wa a gwada, ba yadda zan yi ne shiyasa na tafi na bar ta".


Rumaisa ta ce "Au na zata shi ne ai".


Ta ƙarasa ta leƙa fuskar iman ta ce "Anty Iman ya jiki?".


Cikin ƙarfin hali ta ce "Da sauƙi Alhamdilillah ".


Adam ma lallaɓata yake yi, ko za ta ci wani abun, amma ta ce ita ba ta cin komai, ya din ga rarrashin ta, ta ce tuffa take so, takawa ya tashi ya ce bari ya je ya duba, ya sayo mata.
Daga mai sunan baba har Adam babu wanda ya kula wani, takawa na tafiya, iman ta fara ƙoƙarin kwanciya, mai sunan baba ya kalli Nusaiba ya ce "Ke, zuba mata abincin nan" gaba ɗaya suka tsaya suna kallonsa.


Rumaisa ta jinjinawa Nusaiba kai, dan ba ruwansa da baƙunta yanzu sai ya balebalesu da masifa.


Romon kifi ne da dankalin turawa, sai ƙamshi yake yi, idon iman ya cika da hawaye, dan ko ƙamshin abinci ba ta so, ya karɓa ya je gaban iman ya ajiye shi, ya tsaya mata ƙiƙam a ka, ba tare da ya furta komai ba, ta kama cokali, ta fara cin abincin nan, jikinta yana rawa, saboda tsoro da fargaba, ga wata irin Muguwar kunya, dan ba ta saba cin abinci a gaban maza ba, ko a taron mata ba iya ci take ba.


Sai da ta ci sosai sannan cikin faɗa ya ce "Kuna sane kuke wahalar da iyayenku, dan kun ga suna ta taku. Ke kuma tashi mu tafi" yayi maganar yana kallon rumaisa.


Ta tashi, kamar ta tuntsire da dariya, daga Nusaiban har iman ɗin kamar ka ce kyet su zura da gudu, saboda tsoro.


Ruma ta ce "Anty iman, Allah ya ƙara afuwa".


Cikin sanyin jiki ta ce "Amin maman sabir na gode".


Bayan tafiyarsu Nusaiba ta ce "Ke iman, wannan jarabbaben mutumin fa?"


"Yayan rumaisa ne" ta bata amsa.


"Kam bala'i, yau na ga wanda ya taka takawa iya tsare gida, daga zuwa ya hau ni da masifa"


Iman ta sunkuyar da kai ta ce "Mhmm, baki ga komai ba"


Babu daɗewa takawa ya dawo da tuffa, Nusaiba ta bashi labarin abun da ya faru, bai ce komai ba yayi shiru, dan shi kansa jin kan mai sunan baba yana bashi mamaki.


***
Iman jikinta yayi sauƙi, mama ma ta je asibitin ta dubata, ta warware, sai dai lokaci lokaci, kan ya kan matsa mata da ciwo, aka sallameta daga asibiti. Sai dai tun da ta koma gida, washegari ta sake tashi da ciwon kan, sai dai ta yi ƙoƙari ta jure, saboda ba ta san sanya ammi a damuwa.
A ranar da aka sallameta daga asibiti ranar Jabir ya dira Nigeria, daga wurin duba mahaifinsa.
Hajiya Lubabatu ta yi mamakin ganinsa ya dawo, dan sun yi da shi zai yi sati uku a can kan ya dawo.


"Wai kai Jabir, menene ya dawo da kai tun a yanzu?"


"Bakomai, ji na yi an ce iman babu lafiya, shiyasa na dawo ita ma na dubata".


Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Iman ɗin, kai a wa? Meye haɗinka da ita?"


"Bakomai zumunci kawai".


"Ban gane zumunci ba? Jabir kar na zo na ji wata magana saɓanin wadda nake son ji, ka san halina dai ban da kyau"


"Babu wata magana da zaki ji, kawai dai ina yi ne saboda Adam" tsaki tayi, ta shiga wata sabgar daban ta ƙyaleshi.


***
Yau tun da safe ammi ta kira mama, ta sanar mata da Adam zai zo wurin rumaisa, domin idan da wani abu da take buƙata ta gaya masa na game da shirin biki.
Amma mama ta ce "A'a hajiya, a ƙyaleta kawai, duk abun da aka yi Allah ya amfana"
Ammi ta ce "Ai da ni da ke, babu ruwanmu, namu ido abu ne na ma'aurata, dan haka yakamata su din ga tattaunawa domin su fahimci junansu!.




Ayshercool.
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*


*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*


*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*


*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*


*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*


*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*


*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*


*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*


*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*


*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*


*15. Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso

Download complete TXT · Novel page