Kamar yadda Arshaad ya fad’a, mintuna ashirin d’in bama su cika ba! Ya gama abunda zai yi…
Ya sa komai a sai ti
sannan ya kira Granpa
da landline d’in wajen ya sanar dashi ya gama, komai yayi normal.
Daga nan ya nufi hanyar office d’inshi cikin d’an sauri saboda very important magana suke yi shi da Aslam kafin Granpa ya kirashi ya sakashi aikin.
Tun kafin ya k’arasa ya hango k’ofar office d’in nashi kamar a bud’e!
Yana suwa kuwa ya gasgata hakan sakamokon ganinta da yayi a wangale sosai..
Da mamaki ya kutsa kai ya shige ciki…
Tun bai gama shiga ba
ya fahimci
babu Aslam babu alamar shi a cikin office d’in.
A hankali ya sanya hannu ya rufe k’ofar office d’in yana mamakin abubuwa guda biyu
‘Tafiyar da Aslam yayi bayan ya san maganar da suke yi mai mahimmanci ce!’
Da kuma ‘yadda yazo ya samu k’ofar office d’in nashi a wangale’
Could it be Aslam d’in ne ya fita a rikice?
Ko kuma dai bayan ya fitan ne wani ya shigo mishi office
May be Auwal?
No it can’t be!!…..
Duk shi kad’ai yake ta sak’e sak’en shi a cikin ranshi.
Ganin babu inda waennan tunane tunanen zasu kaishi ne ya sanya kawai ya yanke shawarar ‘gara ya kira Aslam d’in! Ya ji ko lafiya’.
Shafa aljihun shi yayi da niyyar d’aukar wayarshi yaji wayam
Yasan daman da guda d’aya ya fito d’ayar kuma tana gida bai ma fito da ita ba!
To ko dai ya jefar ne a inda ya baro…
Har zai juya ya fita dan yaje ya dubo wayar sai ya hangota a kan table d’inshi a ajjiye.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya k’arasa yasa hannu ya d’auka da niyyar kiran Aslam..
Sai dai