TSUTSAR NAMA BOOK 2

Chapter 28 of 38

ina na Ummu-Hidaya ne. Hatta da idanunta irin na maguna da gashin kai mai yalwa bai bar komai ba. Sai da ta haihu da kusan awa uku zuwa huɗu sannan tace mu sanar da mutanen gida, dan Abbie baya nan yayi tafiya. Da alama kuma ta sanar da shi, dan zuwa dare sai gashi ya dawo gida. Hakama Mu'azz baya nan a lokacin, shima washe gari ya dawo. Faɗa miki yanda ahalin biyu dama duk mai alaƙa dasu ke farin ciki ba'a magana. Dan hatta fitinanniyar surukarta a wannan rana cikin farin ciki da walwala take. Kafin wani dogon lokaci labarin wannan haihuwa ya zagaye jama'arsu na nesa dana kusa. Dan danan fa shagali ya tashi, abinka da akwai kuɗi, tako ina facaka ake da su tamkar ba'a san ciwonsu ba. Ranar suna yaro yaci suna *_Muhammad Awwab”_*. Yanda akai wasa da kuɗi a wannan shagalin suna al'amarin har ba'a magana. Sai dai abinda zai baki mamaki duk wani motsi Ummu-Hidaya na kaffa-kaffa da ɗanta ne. Daga ni sai Mamana ta yarda mu ɗauke sa. Sai ko Abbienta da Mu'azz. Sai surukanta Adams da mahaifiyar Mu'azz. Bayan bikin suna ya tashi kulawa da Awwab ya dawo kaina. Sai kuma ita Ummu-Hidaya ɗin idan tana gida. Dan tana gyagijewa ta koma harkar kasuwancinta. Kafin Awwab ya cika shekara biyu sun sake buɗe sabon kamfani na yin lass da atamfa da yadika. Sun kuma saka resunansu a jihohi ukku na kudancin ƙasar bayan Lagos.
Muhammad Awwab yaro mai masifar wayon tsiya. Ga ƙyau da shiga ran mutane Masha ALLAH. Sai dai miskilancin tsiya. Baya yarda da kowa sai ni sai Ummien sa sai ko kakansa Abbie da Abdul-wahab. Hatta da mahaifinsa ƙiwa yake masa. Yaro ne mai zafin naman tsiya, dan haka ɓarna sam bata masa wahala. Yayi kuma ya cisgune fuska tamkar bai aikata ba. Yana da shekara huɗu aka sakashi a makaranta, a lokacin ne kuma aka sake kawo mana wata mai aikin, dan acewarta ni ba mai aiki bace ƙanwarta ce. Har kuka nayi kuwa da jin wannan furuci nata, dan haka na ƙara ƙaimi wajen kula da Awwab fiye da komai a gidan. Shekarar sabuwar mai aikin nan ɗaya a gidan itama ta aurar da ita ga drivernta. Shima mutumin kirki ne dan baida hayaniya, ƙani ne ga kai bayin bulawoyi a gidan shima. Shekararsu guda suma ALLAH ya azurtasu da samun haihuwa yaro. Lokacin Awwab nada shekara biyar cur a duniya. Yaronsu yaci suna Hayatu. Tunda aka haifi Hayatu Awwab ya ɗauki son duniya ya ɗora masa. Koda yaushe yana nanne da jinjirin nan. Makaranta ma da ƙyar ake samu ya tafi, yata fitina kenan sai da Hayatu. Tun abin na bamu mamaki har ya koma bamu dariya da birgemu. Shaƙuwar Awwab da Hayatu yasa shima rainonsa ya dawo hannuna dan har lokacin ni ko ɓatan wata ban taɓa yi ba. Hakama Ummu-Hidaya bata sake samun ciki ba. Tama maida hankalinta akan kasuwancinta sai mijinta da shima dai harkokin kasuwancin da suke yi taren yasa ba wani zama yake ba sosai. Dan haka har lokacin Ummu-Hidaya dai na a gidansu ne tare da mahaifinta da bai taɓa ko kwatanta sake yin aure ba. Zuwa yanzu ma shi ya ajiye komai na harkoki ya damƙa a hannun ɗiyar tasa. Yini yake damu a gida da Awwab da Hayatu. Sai idan Adams da ayanzu ake kira Baba prof.. a gidan yazo sunsha hirarsu ko sun fita wata sabgar. Awwab nada shekara bakwai cikin ta takwas Ummu-Hidaya ta sake samun ciki, abin mamaki nima sai ga ciki a jikina. Musalta miki irin farin cikin da muka tsinta kammu a ciki ma ɓata lokaci ne. Mun cigaba da rainon ciki a tare har zuwa watan haihuwa. Itace ta fara haifo ɗanta namiji mai kama da Mu'azz da a yanzu Awwab ke kira Paah matuƙa. Dan tamkar yayi kaki ya ajiye shi kuma. Idanun Ummu-Hidaya kawai jaririn nan ya ɗakko shi kuma. Ranar suna anyi shagali sosai, yaro yaci suna Fahad. Washe garin sunan Fahad nima na haihu mace. Sosai Ummu-Hidaya ta nuna farin cikinta dana duk wanda yake gidan. Ranar suna yarinya taci Ummu-Hidaya. Wannan abu yama Ummu-Hidaya daɗi, dan haka ta ɗauki son duniya ta ɗorama yarinya. Saboda sunata aka sakaya ake kiranta da Falak. Bayan sunan Falak suka tilasta Abdul-wahab ajiye aikinsa. Acewarsu shi yanzu uba ne. Alkairi suka masa mai yawan gaske da zai iya kafa kasuwanci mai ƙarfi, amma duk da haka ya roƙa Abbie akan shi dai zai cigaba da tuƙashi koda zai koma wani kasuwancin ne. Hakan kuwa akayi, duk da ma yanzu shi Abbie ba wani fita yake ba sai idan ta kama dole. Kusan rainon Falak da Fahad ya tashi ne a hannun Ummie da su Awwab, sai da ya shiga primary 5 sannan ya sakarma su Hayatu. A shekarar da Awwab ya shiga jss 2 a secondary ranar wata alhamis Abbie da Abdul-wahab sukai accident a hanyarsu ta zuwa Katsina daga Kaduna duba sabon companyn da Abbie ɗin ke ginawa na sarrafa karfe. Jirgi zasu bi sai aka tashi da hazo, dan daga nan Lagos ta jirgi suka je Kadunar. Mun shiga matsanancin tashin hankali a wannan rana da bazai taɓa musaltuwa ba. A daren ranar ALLAH ya amshi rayuwar Abdul-wahab yayinda Abbie ke cikin mawuyacin hali. Anso yima Abdul-wahab sutura anan Lagos sai dai bai yiwuba, dan yan uwansa tun daga kano sukaje can Kadunar suka ɗaukesa, shi kuma Abbie aka wuto da shi nan Lagos. Ina son tafiya Kano hakan ya gagara, dan ban san irin tarbar da ƴan uwansa zasu min ba saboda basa son auren tun fil azal. Shiyyasama bai taɓa kaini garinsu ba. Ina dai jin sunan a bakinsa. Sai matarsa da mukan ma juna aike idan zai je ko zai dawo. Sai bayan sati ɗaya da rasuwar bisa tirsasawar mahaifiyata muka shirya muka je. Da ƙyar muka iya gano garin Gwarzo. Hakan yasa muka isa a wahalce. Sai dai me duk da azabar tafiya da mukaci bamu sami tarba daga ahalin Abdul-wahab ba. Sai ma kaca-kaca da sukai mana, tare da tabbatar min su basu san Abdul-wahab nada wata mata ba bayan matarsa da suke tare anan gida da ƴaƴansa uku. Dan haka naje can na nemawa ɗiyata ubanta su bazasu karɓa ba tunda tun farko sun tabbatar min basa buƙatata a cikinsu amma na nace sai da na auri musu yaronsu.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_




........Raina yayi matuƙar ɓaci, hakama na mahaifiyata. Dan haka a daren muka baro gwarzon rai ɓace, har ƙaddara ta samu mahaifiyata aka faɗi da ita a mashin. Ciwon da taji ne ya zama sanadin ajalinta. Dan mun dawo Lagos da kusan kwana tara ALLAH yay mata rasuwa ashe ciwo ya shigeta ba'a sani ba. Wannan al'amari ya sani yin alƙawarin tattara dangin Abdul-wahab na watsar, na cigaba da takaba ta. Ga tashin hankalin Ummie akan ciwon Abbie. Duk da nawa tashin hankalin nima sai na danne na shiga bata kulawa da shawarwari. Watan Abbie kusan uku a asibiti yana jiyya jikinsa yaƙi daɗi, a wani daren lahadi yay ganawar sirri da ƴarsa ɗaya tilo da lauyiyinsa da Baba prof.. sai Awwab dake da shekaru goma sha uku a duniya. Wannan zama da su kaɗai suka san mi suka tattauna sai ALLAH kuma shine zama na ƙarshe. A washe gari Abbie shima yace ga garinku nan. Tashin hankali da ba'a saka masa rana kenan. Dan baki labarin yanda Ummu-Hidaya da Baba prof... Suka kasance a wannan rana ba'a magana. Awwab kam kulle kansa yay a ɗaki tsahon kwana uku. Duk da yarone ƙarami dan shekaru sha uku fa amma a kallo ɗaya zaka san mutuwar nan ta bugesa. Saboda akwai shaƙuwar mai ƙarfi tsakaninsa da Kakan nasa, sannan yarone da ALLAH ya bama wayo sosai da nutsuwa..
Rasuwar Abbie ya fara canja al'amurra Ummie. Office ma ta daina fita kusan wata guda. Sai dai tayi zaune shiru tana kallon yaranta kawai Awwab da Fahad. Sam idanunta basa ƙafewa da zubar hawaye. Cikin ƙanƙanin lokaci ta rame sosai tai duhu. Tun kowa na ɗaukar al'amarinta a matsayin damuwar rashin mahaifi saboda shaƙuwarsu har muka fara fahimtar akwai matsala. Ƙawarta data zama likita a yanzu Hajiya Lawusa (Hajiya ƙarama) naje na sanar mawa. Dan bazan iya tunkarar Abban su Awwab ba ko Baba prof.. itace ta fara tabbatar mana da Ummie na cikin halin depression ne. Kowa ya tausaya mata matuƙa, yayinda Baba prof.. da Mijinta (Paah) suka maido hankalinsu kan bata kulawa sosai. Muma ba'a barmu a baya ba, kowa tattalinta da tattalin lafiyarta yake. Sai dai me al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta koma babba. Dan daga depression sai muka tsinci baiwar ALLAH a halin hauka tuburan. Gaba ɗaya komai ya ƙwace mata. Tun ana ɓoyema yaranta musamman Awwab har ya fahimci halin da take a ciki. Tuni ya tattara karatunsa ya ajiye, ya maida hankalinsa gaba ɗaya gareta duk da ƙarancin shekarunsa shike mata komai hatta da bata abinci da tsaftar muhalinta. Sai ya zama bata aminta da kowa ma sai shi kawai. Babu kalar likitocin da basu ganta ba amma da an fara ɗorata akan magani sauƙi ya fara samuwa sai kuma abu ya rikice. Sunsha bin yawon ƙasashe daban-daban akan matsalarta. Amma kamar dai baya. Da lafiya ta samu sai kuma jiki ya sake rikicewa.
Wani bawan ALLAH ne ya bada shawarar gwada mata maganin Islamic da namu na gargajiya, dan acewarsa babu wani ciwon damuwa manyan aljanu ne ke damunta, basuyi jayayya ba kuwa suka sa aka fara kawo musu masana akan hakan. Kamar dai yanda kika sani, magani dace ne, kowa nata gwada tashi sa'ar, sai dai tsahon lokaci ba'a dace ba. Amma dai ana ganin ɗan sauƙi a wasu lokutan. Gaba ɗaya ragamar kula da Ummie a hannun Awwab take, dan tun bai iya wasu abubuwan ba har ya iya. Hatta da kitso zama yake yay mata kiga tamkar mace tayi mata shi. Sai dai me yana da shekara goma sha bakwai komai ya fara sassautawa. A hankali ya fara ja baya da al'amuran mahaifiyar tasa. Takai ma idan yaje gareta sai ta hausa da duka da jifa har saita jimasa ciwo. Idan ya matsama kansa da damuwa sai shi kuma ya hau ciwon kai koya yanke jiki ya faɗi babu rai. Tun kowa na ɗaukar abin wasa dai har ta tabbatar zamansu waje ɗaya bazai yuwuba. Sosai hankalinmu ya tashi da wannan al'amari nasu, musamman ma ni da sukafi shaƙuwa da ni.
Canjawar al'amuran ya saka mijina na yanzu bama Awwab shawarar komawa makaranta ya cigaba da karatunsa. Amma sai ya nuna mana shi babu inda zaije. Ya haƙura da komai na rayuwa zai cigaba da kula da Ummiensa. Munta lallashinsa harda Yayar Mahaifinsa Hajiya Nafisa. (Hajiya Mammah). Kunyarmu da yake ji da addu'ar da muka duƙufa a kansa ta sanya ya amince zai koma. Dan haka da kansa ma yayma Baba prof.. da mahaifinsa maganar komawa makarantar. Sun nuna farin cikinsu suma, a take kuma suka shiga suka fita ya zana ssce ɗinsa. Cikin amincin UBANGIJI aka dace ya samu result mai ƙyau. Awwab ya shiga jami'a, kuma har lokacin yana nacin taimakon mahaifiyarsa amma dai babu daɗi dan wahala kawai yake sha. Yayinda Fahad ƙaninsa da shima a lokacin ya ke gab da kammala secondary. Hakama Hayatu suke ƙarƙashin kulawarsa. A farkon fara karatun Awwab ya ɗan fara kula da Companys ɗin mahaifiyarsa da ke neman durƙushewa duk da mahaifinsa tsaye yake akan komai, sai dai aikin ya masa yawa matuƙa dole sai da Awwab ɗin ya fara taimaka masa abubuwan suka fara dai-daita da dawowa fiye ma da yanda ya kamata. Dan shima UBANGIJI ya saka nasibi a hannunsa komai ya taɓa sai ya zama kuɗi. Yanda al'amuran nasa ke haɓaka sai ma ya fara danne na mahaifiyarsa. A haka ya kammala jami'a, yayinda ƙaninsa da Hayatu suke can ƙasar turai suna nasu karatun. Anan ɓangaren kuma Falak na nata a gida Nigeria, dan yanda Paah ya tsaya akan karatunsu itama bai banbanta da ita ba. A hankali ragamar kasuwancin ya koma hannun Awwab, yayinda yake kuma cigaba da karatunsa. Cikin amincin UBANGIJI a wannan lokaci kuma sai aka dace ta hanyar wani bawan ALLAH daga ƙasar Togo Ummie ta fara samun lafiya. Hakama al'amarin Awwab ya fara dai'daita..


Alhamdullah komai ya dawo dai-dai, farin cikinmu da duk zuri'ar Baba prof.. ma haka. Dan samun lafiyar Ummie ba ƙaramin kwanciyar hankali ya kawoma kowa ba. A lokacinne Hayatu ya kammala karatunsa ya dawo gida Nigeria. Saura Fahad da zai ƙara shekara ɗaya. Sai dai yana zuwa hutu musamman ma yanzu da Ummie ta samu sauƙi. Wannan gidan da kike gani itace da kanta ta fara ginashi a lokacin data samu lafiya. Acewarta tana fatan haɗa kan iyalinta waje guda idan su Awwab sunyi aure duk nan zasu zauna da matansu. Muma ta ware mana sashenmu tana mai tabbatar mana mune zuri'arta na ɓangaren mahaifa. Jin daɗin samun lafiyarta yasa Awwab sake maida hankakinsa akan harkar kasuwancin sosai. Yayinda itama take ƙara masa ƙarfin gwiwa. Sai dai me, ana murna ɓarawo ya tafi ashe yana laɓe a bakin ƙofa. Dan kuwa a wani dare labari ya koma baya. Jikin Ummie ya sake hargitsewar da yafi na baya muni da tashin hankali. A wannan lokacin ma dai Awwab sake tattara komai da komai yayi ya dawo da gaba ɗaya hankalinsa da ƙarfinsa akan mahaifiyarsa. Anyi-anyi ya koma kan harkokinsa yayi biris da kowa da komai. Bashi da aiki sai addu'oi da karatun Alqur'ani ga mahaifiyarsa. Da farko lafiya lau yake mata komai, sai dai zuwa wani lokaci matsalar baya ta sake dawowa ta rashin jituwa a tsakaninsu. Ya matuƙar tada hankalinsa akan hakan amma an rasa mafita. Manyan likitocin babu irin waɗanda ba'a gani, hakama masu maganin gargajiya dana Islamic duk inda aka jisu sai an kawasu. Shima na ƙasar Togon anje nemansa aka samu babu shi, wai dama zuwaune a wajen ba'a san takamaimai ɗan wane yanki bane ba. Shekara guda ana cikin wannan zaune tsaye aka bama Paah shawarar yin aure. Amma yaƙi firr sai da aka tsaya a kansa sannan da ƙyar ya amince. Sai dai kuma babu wacce zai aura kamar yanda ya faɗa. Yawan kulawa da Hajiya Lawusa (Hajiya Ƙarama) ke bama Ummie yasa Baba prof.. bada shawarar aurenta. Dan itama a lokacin mijinta ya rasu tanada ƴa ƙarama wadda ita kaɗai ta haifa.
Sosai akasha fama kafin Hajiya ƙarama ta amince. Sai dai duk abinda ake Awwab bai sani ba sai daga baya. Sosai ya nuna ɓacin ransa da kishin mahaifiyarsa. Hakanne dalilin tada wannan ginin gidan ya cigaba da yinsa. Abinka da maganar kuɗi, cikin abinda baifi watanni uku ba komai an kammala. Shine ya dawo da mahaifiyarsa nan acewarsa ya bama Paah spiece da matar tasa su ƙarata, duk kuwa da can ɗin ma gidan mallakin Ummie ne. Dan gidan da mahaifinta ya gina da guminsa ya kuma rayu a cikinsa. Hakan yayima Paah zafi, dan Awwab ya tattara kowansu ya watsar, baya shiga sabgar Hajiya ƙarama duk da kuwa a baya kowa yasan aminiyar mahaifiyarsa ce, harma da mahaifin nasa ya tattarashi ya ajiyesa gefe.
A ƙalla mun kusa shekara guda a gidan nan da dawowa muketa ɗawainiya da Ummie, dan Awwab dai ya ajiye zancen kasuwanci gaba ɗaya sai kula da mahaifiyarsa. Kullum cikin jimasa ciwo take amma hakan baya hanashi zuwa gareta. Baba prof.. ne akoda yaushe baya gajiya da kawo masu magani, zuwan wani da ga Niger ya bada shawarar Awwab ya rage zaman gidan, dan in har suna a muhalli guda da mahaifiyarsa to lallai lafiyarta zatayi wahalar samuwa. Dan an riga an saka rashin jituwa a tsakaninsu. A samar da masu kula da ita har ALLAH ya bata lafiya. Sam Awwab yaƙi aminta da wannan shawara. Kowa ya buga sai yace babu inda zaije. Hatta da mahaifinsa da basa jituwa a yanzu sai da yazo yana bashi haƙuri da lallashinsa amma ina firr yaƙi amincewa. Mu kammu duk yanda yake girmamamu da jin kunyarmu yaƙi sauraren mu. Hakama Baba prof da kakarsa ta wajen uba matar Baba prof... Ɗin. Ana cikin haka ɗan uwansa Fahad ya dawo ya kammala karatun, ana murnar dawowarsa sai kuma murna ta koma ciki. Dan kuwa sam babu jituwa tsakaninsa da Awwab. Sosai suke nunama juna tsana. Zama inuwa ɗaya ya gagaresu. Akwai randa babu wanda yasan abinda ya haɗosu kawai Awwab ya kama zanesa. Da ƙyar aka amshi yaron a hannunsa sai da ya kwanta asibiti kuwa saboda jigata. Yana samun sauƙi ko hanyar gidan nan bai dawo ba ya tattara inasa inasa ya koma inda ya fito. Daga ranar bai sake leƙo ƙasar nan ba har yanzu. Shima kuma Awwab ɗin bana jin ya sake waiwayar inda yake. Sai su Baba prof.. da Paah.......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_


....Abinda ya

Download complete TXT · Novel page