Showing 48001 words to 51000 words out of 250533 words

Chapter 17 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.

18 Feb 2025

116504

barguna Ya lullu6e su, sannan ya shiga daji Ya samo itace ya haɗa masu wuta saboda sanyin Dajin, Tun da suka fara tafiyar nan Danish bai runtsa ba, Su kaɗai suke Yin baccinsu, Baya gajiya dayi masu hidima, basu da matsalar komai Abinci har sai sun ture, Nama iri iri suke Ci na dabbobin da yake yi masu farautarsu, Ga kayan marmari availabe cikin Dajin, wasa wasa kusan Watansu ɗaya suna tafiya babu alamun zasu taddo cikin gari, Lamarin Ya ɗaga hankulansu, A haka ma Danish yana taimakon su ba tare da sun sani ba, Duk idan dare ya nutsa bacci ya ɗauke su ɗaya bayan ɗaya ya ke ɗaukar su Ya nutsa dasu Cikin dajin ya yi tazarar tafiyar awanni dasu, basu ta6a lura da hakan ba, duk don ya sauƙaƙa masu wahalar tafiyar, shiyasa ya ke yi masu hakan, don kuma su yi gaggawar barin Dajin, Don ya fara Jin alamun wani baƙon Yanayin a jikin shi, fargabarshi kada Giant’s heart ɗinshi ta motsa batare daya Nisantu daga dajin ba.

*PRISONERS💔*


Dare Ya nutsa sosai suna akwakkwance suna bacci, Hasken Wutar Dake Ci Ya haskaka zagayen wurin da suke, yana a Zaune gaban wutar idanuwanshi akan shimfiɗarsu, Sai faman lumshe idanuwanshi Yake yi, ga dukkan alamu baccine yake ƙoƙarin fuskarshi.

Angel da ke a kudundune cikin bargo taƙi runtsawa duk don saboda shi, ta kasa samun natsuwa, Yaye bargon tayi tare da fitowa daga Ciki Ta miƙe tana miƙa ta nufi inda yake zaune, Tunkan ta ƙarasa taga yana gyangyaɗi Ƙiris Ya rage ya kifa kanshi Cikin wutar dake agabanshi da gudun gaske Ta ƙarasa tare da zubewa gefen shi saman gwiwowinta, da hannyenta biyu ta tallabo fuskarshi tana bin shi da kallo, Sam ya gaza buɗe idanuwanshi sunyi mashi nauyi, rungume kanshi tayi saman kirjinta, idanuwanta suka ciko tab da ƙwalla, tsananin tausayinshi take ji.
“Danish muje mu kwanta,” muryarshi ƙasa ƙasa ya furta mata”bazan iya bacci ba Angel idan har ba barin Dajin nan mukayi ba, Ina jin fargabar wani abu ya same ku ta silar rauni na” ƙara ƙanƙame shi tayi a jikinta”In sha Allah ba abunda zai same mu Danish, Allah Yana atare damu, Kuma Inayi mana addu’a, Kada kaji komai kazo mu kwanta, rashin yin baccin zai Iya ja maka wata matsalar da bana fata” A hankali ya zagayo da hannayenshi saman waist ɗinta, kafin ya lumshe idanuwanshi. Jin shiru bai ƙara motsi ba yasa tayi tunanin ko baccin ya ɗauke shi ne, Kiran sunanshi tayi”Danish” amsa mata yai”Na’am” cikin kulawa tace dashi”nayi tsammanin ka fara baccin ne, pls kayi bacci Danish, inaso ka huta, bana so kana wahala” daɗin murya yake ji acikin kunnuwanshi, har baison intana magana tadaina, Yafi son taita yi mashi surutu.
“Danish naji ka yi shiru baka ce komai ba”? Har saida ta fidda rai da zaiyi mata magana tukunna taji yace”Angel ni wannan ba damuwata bace, i ave told u duk wahalar da zanyi indai akan ku ne bana gajiya, ke ce ƙwarin gwiwar da nike da shi Angel “ murmushi tasaki idanuwanta akan Kitson zanan dake akanshi,
“Faɗamin me ka ke ji akaina? sannan Meyasa kake ƙaunata? Ta yi maganar tare da Ɗaura yatsun hannunta saman kanshi, tuntuni ta ke son ta kwance mashi kitson da akayi mashi a prison don bata son ganin shi da kitso kamar mace tafi son ta ganshi a Namijin shi.


“Nikaina bansani ba” amsar daya bata kenan,
Ɗagowa yai da kanshi tsinin hancinsu Ya haɗe jikin na juna, Hasken wutar dake cine ya haskaka fuskokinsu
Hakanan Taji gabanta na faɗuwa, ganin launin idonshi na canza mata, duk tabi tasha jinin jikinta, ƙwarjini yayi mata da sauri ta kawar da idonta gefe ɗaya
“Abu ɗaya nake fargaba a duniyar nan! Shi ne ace za’a raba ni da ke!” Dawo da dubanta tayi akan fuskarshi, jaddada mata maganar shi yai”Zan iya komai a wannan lokacin,”
“Maganar raba ni da kai ma bata taso ba Danish, dani da kai tamkar anta da jini ne, mutuwace kaɗai zata Iya raba ƙaunar dake a tsakanina dakai, Amma agidan duniya bani da madadinka” kalamanta sun ɗan sanyaya zuciyarshi,
“Ina tsoron ranar da zaki Canza min, duk da bana kawo hakan araina, Angel wani zai Iya ƙwace min ke, kinga ni bani da komai da zan iya faranta maki da ya wuce kaina” Muryarshi araunace yai maganar.

Ɗaure mashi fuska ta yi “Danish zaka Iya bari wani ya ƙwace maka ni”? Girgiza mata kai yai alamar a’a, ya ƙara da cewa”Sai inda ƙarfi na Ya ƙare, “

Lumshe ido ta ɗan yi calmly ta furta “Yadda muka sha wahala atare Danish, Haka nake so Mu ji daɗi atare, Bani da abokin rayuwar daya wuce kai a faɗin duniyar nan, Kaine mallakina, masoyi na har abada, ta ya ya kake tunanin zan iya canza ma ka? Ai kaine nake tsoron Ka canza min idan mun shiga Cikin gari, saboda nasan mutane da yawa zasu dinga rububinka saboda kyawun Da Allah yayi maka, Sannan bansan su wanene Iyayenka ba, amma inaji araina ba ƙananun mutane bane yadda kake da kyan nan da izza ɗabi’unka sak Irin na ƴa’ƴan Hamshaƙan masu kuɗi ne, Ni ko ka ga ba ƴar kowa bace, Mahaifina ɗan Jarida ne kuma ya rasu ma, “ Idanuwanta acike tab da ƙwalla tayi maganar, ƙwallar na gangarowa saman kuncinta yai saurin sanya tongue dinshi Ya lasheta, nan ta ke ta ji yanayin jikinta ya fara canzawa.


“Ni bani da iyaye Angel, Ki daina yi min maganarsu bana son ji, ke ce uwata kuma kece ubana, Kece gatan da nake dashi, Idan ina dake bani buƙatar kowa,” muryarshi a kausashe yake yi mata magana, Ta fahimci bayason zancen Iyayen shi da take yi mashi.

“Meyasa bakason Inayi maka maganar iyayenka? Danish Salsabeel ya faɗamin tun kana jariri aka sadaukar dakai, Naji raɗaɗi jin hakan acikin zuciyata, sai dai Ni bazan Iya yankewa iyayenka hukunci ba, Kada ka manta sadaukarwar kurkukun ƙaddara ba dole sai iyayenka ba, zai iya yiwuwa ba sune suka sadaukar dakai ba, wata’ƙil ma basu da masaniyar kana araye....” bai bari ta taƙarasa maganar ba yai saurin toshe mata bakinta da tafin hannun shi”Is ok, Kije ki kwanta dare Yana ƙara yi,” maƙe mashi kafaɗa tayi”Idan Kaga na kwanta toh muna atare da juna ne,”kafiya ta sanya mashi ya rasa ya zaiyi da ita, A ƙarshe dole Ya haƙura Ya ƙyaleta, kwantar dakanshi yai saman ƙirjinta, Taci gaba da kwance mashi kitson kanshi, Kafin bacci Ya ɗauke su saida ta warware kitson duka, A manne da juna suke ta sharar baccin su, Karo na farko da ya fara runtsawa Acikin Dajin❗❗❗


*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*KURKUKUN ƘADDARA*_



_The Prisoners E10🔥💫_


*Daga alƙalamin Boss Bature*


~Middle step~



_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._





A Kwance ya ke saman shimfiɗeɗan gadonsa, Kamar kullum cikin shigar larabawa, hannun shi a ruƙe da wayarshi, Ya ƙurawa Hoton wallpaper ɗin shi ido, ko ƙyaftawa bai yi sam baya gajiya da kallon hotonta, Yanayin fuskarshi Ya nuna tsantsar damuwa, a hankali ya ɗaura yatsun shi saman hoton kan wayar yana shafa fuskarta, lumshe idanuwanshi Ya ɗanyi kafin a hankali ya ware su kan hoton, waƙar larabci ya soma rairawa da daddaɗar muryarsa duk akan hoton wadda ya ke kallo, ya dage yana yi mata waƙa mai nuni da ƙaunarta da yake yi, Tunawa da bata a raye yasa shi dakatawa da raira waƙar, Ya jefar da wayarshi gefe ɗaya saman mattress ɗin, haɗi da kifa kanshi saman pillow, kamar ƙaramin yaro ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, abun ne yana damunshi ya hana rayuwarshi sakat.


“Shureim, Ka yi haƙuri Ka daina sanya damuwa aranka, I know it hurts you, but worrying won’t make anything better, it’ll only make things worse kuma ka tuna Allah yanasan bayinsa masu tuba, Kana fa da ilmin ka ba sai na tunasar da kai ba,”

bai tsammaci jin muryarta ba, A hankali Ya ɗago da idanuwanshi Waɗanda su ka kaɗa jawur da su, ya ɗaura su kan fuskar Zainab.

Tana a tsaye cikin shiga ta riga da skirt, kanta sanye da hula, ga dukkan alamu daga kitchen ta fito.

“Babu wanda yasan nashigo shureim, Satar hanya nayi don nasan idan hajiya layla ta sani ba za ta bar ni in zo wurin ka ba.......” numfasawa ta ɗanyi kafin ta ɗaura da cewa”Tuntuni na so mu samu lokaci muyi magana sai dai ban samu damar yin hakan ba saboda baka nan, till today” har cikin zuciyarshi ba ƙaramin sanyi yaji ba, yunƙurawa yai tare da miƙewa ya zauna ya jingina bayansa jikin headboard din gadon Yana kallonta, Still hawaye basu daina wanke fuskarshi ba, Zainab ta damu dashi sosai, har mamaki ta ke yi yadda wasu iyayen Allah ya basu damar haihuwar ƴa’ƴa nagartattu amma suke watsi da su, basu damu da damuwar su ba, yayin da wasu neman ƴa’ƴan su ke yi ruwa Ajallo, tana matuƙar jin takaicin haka.

“Aunt Zainab, Kin tabbata ba wanda yasan kin shigo? Ina mommy da daddy ne”
“Layla tana a palour, mahaifin ka kuma Yana a garden shi da kawunka Musa” Jin hakan Yasa shi saukowa daga saman gadon shi Ya nufe ta, tsayawa yai suna fuskantar Juna.

“Ka faɗa min wani taimako ka ke so In yi maka? in sha Allahu babu abunda zai gagara, a shirye nake da in share maka hawayen ka”

Hannayen ta biyu ya ruƙo a cikin nashi gabanta sai faɗuwa ya ke yi, tsoronta kada wani daga cikin Iyayenshi ya faɗo ɗakin, muddin hakan ya faru zata ɗanɗani kuɗarta ne.

“Aunt Zainab I feel in my heart that she’s still alive! Tun bayan da abun ya faru I’ve never dreamed of her as dead, I’ve always seen her alive in my dreams.” tun kafin ya ƙarasa maganar ta katse shi “How could that be possible, Shureim? Mutumin da ya mutu ai baya dawowa and the dreams you’re having aren’t real Don’t believe what you see in your dreams.”

Fuskarshi a yamutse ya ke dubanta

“Amma ni inaji araina bata mutu ba!” kafe mata yai akan zancen shi
Ta fahimci ya fara zaucewa, Zaifi ta lalla6a shi don ta kwantar mashi da hankalin shi”shureim, idan ma tana araye da buƙatar mu shirya plan don mu tabbatar da abunda muke zargi,”

Jinjina mata kai yai alamar yana fahimtarta.

“Dole Ka bi duk a bun da zan faɗa maka,” amsa mata yai da in sha Allah, mu zauna sai muyi magana” girgiza mashi kai tayi”a’a ina tsoron Mahaifiyarka ta faɗo dakin nan, Just A tsaitsaye zan faɗa maka matakin da zaka ɗauka domin mu ci nasara akan binciken da zamu yi” zame hannunta tayi daga cikin nashi da sauri ta nufi ƙofar ɗakin ta leƙa tana duban ko’ina don kada wani ya faɗo masu, ganin bakowa yasa ta gyara labulan ɗakin nashi, ta juyo da sauri ta nufe shi Yayin da take cigaba da yin maganarta”mataki na farko shine Dole ka tanƙwashi zuciyarka, ka danne raɗaɗin da ka ke ji ka daina sanya damuwa aranka”

“Mataki na Biyu Ka daina gudun Iyayen ka, Ina nufin Ka koma masu tamkar yadda ku ke da su Ada, Biyayya sau da ƙafa, ka nemi yafiyarsu akan 6ata masu rai da ka ke Yi.....” tun kan ta kai ƙarshen maganar ta lura da canzawar da yai, a marairaice yace da ita”Aunty zainab taya zan iya yin hakan? Ni bana jin zan Iya sakar masu fuska mu koma kamar yadda muke ada” murmushi ta ɗan saki kafin tace”Shureim kenan, Nafi so ina magana kana fahimtata, ta wannan hanyarce kaɗai zamu Iya gano meke wakana a tsakanin Iyayenka” jinjina mata kai yai alamar ya fahimta.

Har ya buɗe baki zai yi Magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa

“Me ka ke buƙata in kawo maka? nasan kana jin Yunwa”

A ruɗe ya ke kallonta da mamaki Akan fuskarshi, Me ya kawo zancen yunwa acikin maganar su.

“Ko dai kana buƙatar chips in haɗo maka da shi”? Ta wutsiyar idon shi Ya hango Layla A tsaye bakin ƙofar, Ta kifa ɗaurin ɗan kwalin atampa akanta, Riga da skirt ne sun bi shape ɗin jikinta, duk da alamun manyantaka atattare da ita, hakan bai 6oye kyawun surarta ba.

Wahalallan Yawu ya haɗiya haɗi da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, aranshi ya ayyana ko yaushe tazo bakin ƙofar! Sai yanzu ya fahinci dalilin canza maganar zainab, ita tun kafin layla ta shigo tajiyo takun takalmanta saboda bata sanya takalmi idan ba mai tsini ba, Ba don Allah yasa taji motsinta ba da ko ta yabawa aya zaƙin ta


“Aunty zainab wai meyasa ki ke son takurani akan dole sai naci abinci, nace maki bana jin yunwa ki tafi kawai, Ni bana buƙatar ganin kowa akusa da ni, ana dole ne” Ranshi a matuƙar 6ace yai maganar, tare da Juya mata baya, Ya ruƙe qugu da hannu ɗaya, Zainab dake kallon bayanshi tace”Shureim zama da yunwa zai Iya haifa maka wata matsalar, abunda bama fata, Ni bari naje na faɗawa mahaifiyar taka kaƙi cin abinci wataƙil idan ita tayi maka magana ka ci” Har zata Juyawa shureim Ya juyo a sukwane Ya daka mata tsawa”Karki Kuskura ki ce zaki haɗani da ita, Ko kin faɗa mata abanza, matar da bata damu da ci na ko sha na ba.....” Sai da yai wannan maganar, Layla ta kai hannu ta ɗan kwankwashi Jikin Ƙofar ɗakin nashi Don hankalinsu ya dawo kanta, tamkar basu san da zamanta ba suka ɗago suna kallonta, Fuskarta tasha uban make up, gashinta baki wulik har mid back ɗinta, Cikin takun izza da nuna isa Ta nufo su tana magana”Zainab Nagode da kulawarki akan ɗana, ki ƙyale shi, shureim ya daina jin maganar kowa a yanzu bansan laifin me mu ka yi mashi ba da yake gudun mu,’ tun da ta fara magana Zainab take sauke ajiyar zuciya, jin bata gano me suke tattaunawa ba, shureim ko sai ƙara ɗaure fuskarshi ya ke yi kamar zata fashe saboda tsabar nuna fusatarshi.

Idanuwan mahaifiyarshi akan fuskarshi, Cikin girmamawa zainab tace”Shureim har yanzu yaro ne, tun da yana a ƙarƙashin kulawarku, sai ana haƙuri dashi ana kuma lallashin shi da jan shi a jiki ta hakanne zamu iya sanin meke damun shi” jikinta na ɗan kerma tayi maganar, gyaɗa kai Layla tayi”is Okey, ba sai kin koyamin yadda zan Kula da ɗana ba, Ni da na haife shi ni nasan kayana, Zaki Iya tafiya ki bamu wuri” ta yi maganar tare da nuna mata ƙofa da hannu.

layla kenan Ita ba’a mata gwaninta, Jiki asanyaye zainab ta kama hanyar fita ɗakin tana tafiya tana waiwayon shureim da ido take Yi mashi alamar Ya sake mata, kada ya manta da shirinsu, Lumshe mata idon da yai ne yasa ta fahimci ya gane me take nufi, Bayan fitar zainab, Layla ta tsare shi da idanuwanta

“me zan yi maka wanda zaisa Ka daina guduna? Haba Shureim saboda na kore ka cikin fushi shine ka kama Hanya ka tafi egypt wurin Ammi, Kasa ta kirani awaya tana ta zazzaga min masifa, ‘ ranta a6ace take yin maganar, har ya harzuƙa zai mayar mata da martani kalaman zainab suka faɗo mashi arai da sauri ya danne fushinsa, abunda ta tsana dashi tana magana Yana shareta, Wuyan farar jallabiyar jikinshi ta damƙa da hannayenta waɗanda ke a sanye da awarwaro da zabba na zallar zinari, Jijjiga shi tai”Shureim so kake baƙin cikin ka ya kashe ni? Na rasa benazir kaima kuma kana neman ɗaura min hawan jini, so ka ke zuciyata ta buga in mutu shureim”? hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba, ganin hawaye sun ciko idonta.

Duk da yasan ta yi hakanne don ta samu kanshi, sassauta muryarta tayi tare da sakin Kwalar rigarshi”Kai kaɗai nake gani naji daɗi, Meyasa ba za ka manta da abunda yawuce ba, ina magana kana share ni, kasan bana son hakan, Yana ƙona min rai” baisan sa’adda hawaye suka cigaba da wanke fuskarshi ba, muryarshi na ɗan rawa ya furta”?mommy saboda ni za ki zubar da hawayen ki”? Muryarta a kausashe tace”Shureim, how many times have I cried for you? I understand that you’re trying to drive me crazy,” Shureim ka daina ƙaunata” Tai maganar tana watsa hannayenta’ shiru Ya ɗanyi yana kallon fuskarta, tabbas ya ga 6acin rai acikinta.

“Astagfurillah” jin ya ambaci haka Yasa ta zaro idonta akan fuskarshi
“Mommy, I didn’t know you cared about me that much, I thought you’d stopped loving me, amma yanzu mommy akaina kike zubar da hawayenki”?

Mamakin kalaman shi ne yasa ta kafe shi da ido ba ƙyaftawa, Hadisi Ya soma janyo mata da ayoyin al’kur’ani mai girma waɗanda ke magana akan wanda Ya ƙuntatawa iyayen shi.

“Shureim ka sani kuma kake take sani? Shine Ka rufe ido Kana ƙuntata min? Meyasa”? Marairaice mata fuska yai”ya zanyi! Sharrin zuciyane da kuma sharrin shaiɗan, sune suke azalzalar zuciyata akan abunda Ya faru, sunƙi bari na manta komai,” Dafa kafaɗar shi tai da hannunta ɗaya”Ka yafe min shureim, nayi maka alƙawarin zan tarairaye ka na baka kulawa kamar yadda muke ada, Sannan inaso kamanta da abunda ya wuce, Ba laifin mu bane, mu ne sila, amma kaine ka aikata komai ba tare da ka yi shawara damu ba, kai kasan ba yadda za’ai da hankalin mu da tunanin mu mu goyi bayanka akan aikata hakan, a lokacin da ace ka yi shawara damu wlh shureim ba zamu goyi bayan abunda ka aikata ba” har cikin zuciyarta ta ke magana, Shi kanshi Yaji jikinshi yai sanyi, zuciyar shi ta karaya, tabbas maganar da ta faɗi gaskiya ne.

“ Mommy, ni ne ya kamata na nemi yafiyarki, akan gudun ku da nake Yi ke da Daddy, Dan Allah ku yafe min, na gane kuskurena”

yai maganar yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login